Recent Updates

Zaman Aure Complete Hausa Novel

 


[3/19, 10:27] ‪+234 814 620 5819‬: [8:10pm, 2 





*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦



  *💦T <W >F*💦






  *ZAMAN AURE*

    💦  🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦




*Bisimillahir rahamanir rahim*

*Allahumma la sahala illa ma jaaltahu sahala waanta tajjialil hazina iza shi itu sahala*👏🏻👏🏻👏🏻





💦

*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin mu*💦




*Godiya ta tabbata ga Allah subahanahu wataala da yabani ikon kawo muku sabon novel dina me suna ZAMAN AURE ina rokon allah yabani ikon rubuta dai dai ya kubutar da hannu na daga rubuta kuskure*




*shimfida*



*littafin ZAMAN AURE kirkirar labari ne wanda nai duba ga irin yadda wasu maauratan Kan tsinci kansu gidan aure*


*mawakin nan yayi gsky da yake cewa  zaman aure yana da dadi yana daci wani gidan zasuyi walwala wadan su ko nayin sakaci wadansu kuwa tona sirrikan su keyi haka wasu na cin amanar junan su ne gsky ne soyayya da dadi haka nan tana da daci ko de biyoni danjin labarin *ZAMAN AURE*🤦🏻‍♀







*sakon gaisuwa gareku TALENTED WRITTERS*



*Rafeeat yahaya*

*fayeex usman*

*Umyma danjani*

*jidda tijjani*

*Aeshab roshni*

*islah tasiu*

*sadeey smart*

*pherteenjay*

*Rukayya*

*Anib*

*Husnah*

*Husnah umar*

*Halieymarh ameen*

*Hawee*

*pretty*

*umma I uba*

*maryam lawan*

*Sadiya  ibrahim*

*indian fidy*

*zahra*

*Qamshin talented*

*suhylat*


*Hakika kunayi inajin dadi naseeba na biye da ku guys*💦








         *Dedicated 2 alhj ismail uba GAWO family*😍





           

             *1*





~~~Bakajin komai sai haushin karnukan da suka karade unguwar sai kuma karar injina daaka kunna a gida jan unguwar, ko wane ma gidanci ya dawo cikin gidansa ya kulle banda gidan kamal domin har wannan lokacin be dawo ba 


*sakna* ce zaune ta rafka uban tagumi lokaci zuwa lokaci tana duba agogon da yake manne a jikin bangon bedroom dinta ta takure acan karshan gado lokaci zuwa lokaci take goge hawaye, wani mahaukacin horn taji a zabure ta tashi tadaga labulan tagar isa tagani ya fito daga dakinsa da gudu yazo ya budewa kamal gate ya shigo da motar sa a guje sakin labulan tayi ta fito katon parlorn su mai adon blue da silver tasami guri ta zauna dan jiran shigowar kamal 



Sai da yadade a mota kafin yafito yana rangaji da kyar yake iya bude idonsa saboda nauyin da sukai masa da mugun karfi ya bugo kofar parlorn wanda haka yasa sakna razana ta mike Cikin sauri ta nufoshi ta fara yimasa sannu da zuwa 

tare da fadin innalillahi wainna ilehirrajuun


*kamal* sannu da zuwa"


Tureta yayi ta tafi kamar zata fadi Mass cikin murya irin ta yan meye yafara maana 


*sakna* kar ki kuma kirana da kamal *bobson* zakice me kike jira baki kwanta ba eye, kin tsaya gulma ko "



Yana gama fadar haka ya sheko mata amai ajikinta wani mugun wari taji ya bigi hancinta nan take tasaki kuka mai ban tausayi lokacin agogon parlorn yabuga 1:00 na dare. 





Labiba ce zaune a katafaren parlorn ta tacaba kwalliya sai taunar cingam take tana kas kas wani kyakyawan matashi ne ya murda wata kofa ya fito daga wani daki kusa da ita yazo ya zauna ya sakar mata kiss a wuyanta dauke kanta tayi cikin kidima yafara yimata maana 




"me kuma ya faru Labiba,ko dai abincin dana dafa miki ne bakya so kinsan fa fushin ki fitina ne a rayuwar *jameel*



Cikin shagwaba da yanga tafara magana 



*jameel*gaskiya bana son ka fita ka barni ina jin tsoro ne fa kuma baka bani abinci ba zaka fita "




" pls labiba kiyi hakuri kici da kanki kinga fa nayi late zuwa gurin aiki ga shi natara aiki a office "


" shikenan jameel katafi amma wlh bazanci amincin ba "



Kansa yadafe breafcase dinsa yaajiye ya tashi ya dakko kulolin abincin daga Kan dining yazo yaajiye su gaban labiba zubawa yayi ya shiga bata a baki sai da ta koshi sannan ya kwashe ya kai kitchen sai wajen 9:30am yafita zuwa office itakam kwanciya tayi abinta 



Abangaran abdul malik kuwa yana zaune gefansa kuma ruhaima ce take tafaman zuba masa shagwaba shagwaba dubanta yayi hade da kashe mata ido yace 



"Ruhaima kidena bata ranki akan kirana da yarinyar nan take a waya kisa a ranki malik nakine ke kadai "



" kullum abinda kake cewa kenan amma ka kasa tsawatar mata "



" karki damu kinji matar *B malik*"



Sallamar hajiyar abdul malik ce ta dakatar da furcin da ruhaima zatayi take gaban ta ya hau dukan uku uku ido tazubawa malik shi dinmma ita yake kallo 




Abangaran gidan hafeez kuwa tun safe yake ta shirin komawa garin kaduna kasancewar acan yake aiki mai da dubansa yayi ga matar sa *areefa* wacce take ta faman cika tana batsewa murmushi yayi kana ya karasa gabanta ya tallafo fuskar ta yace 



"haba areefa fushin na meye haka kinfi so in zauna a gida kar infita neman abincin da zan kawo miki "


Shiru tayi kamar bazata amsaba can tanisa tace 



" ni banhanka neman abinci ba amma kasan abinda kake min ba kya kyautawa ko, ko kamanta nima mutum ce mai bukatar abokin rayuwa kamar ko wacece matar da take da miji, gaskiya 


hafeez nafara gjy wlh kana fa jefa rayuwa ta cikin hatsari, yanzu ace inka shuda ka tafi sai na ganka wane irin *zaman aure* kenan mukeyi, ni de wlh katafi dani "



" Hmmm areefa kenan to yanzu innatafi da ke makarantar ki fa, kiyi hakuri wannan karan bazan dade ba kinji "


Nan ya lallaba ta ta hakura yai mata sallama yatafi bayan yaajiye mata rafar yan 200 guda 3, yana fita wayarsa tafara ringing dagawa yayi hade da sakin murmushi 



Nataho yanzu haka nakusa karasowa garin kaduna" 



Yanagama fada ya kashe wayar tare da sauke ajiyar zuciya. 









[9:54Pm,2018]






*®💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦




  *💦N I G*💦




*Junuary 2018*


 



   

  *_SANADIN ABOKI_*....!


           (🙆🏻)




*_NA_*



*_NASEEBA I UBA_*💐




      


*Rabbana atina fidduniya hasanatan wafil akhairati hasanatan wakinna azabar nar*👏🏻





              *_2_*





~~Gyaran murya Mardiya ,tayi cikin sauri matashin saurayin ya sauke idonsa daga kanta ,da salon muryar ta mai dadi tace,



"sannu da zuwa,dafatan kazo lafiya"



"yauwa sannu yanmata ,lafiya kalau, suna na Nuraddeen Kasim "



"Mashaallah,

bisimilla ga ruwa,momy tana kitchen yanzu zata fito"



"ok,badamuwa sai dai banji sunan kanwar tawa ba"...



"Mardiya"


kawai tace,

tana gama fada tai gaba,atake yaji yarinyar ta burgeshi,ahankali ya maimaita sunan nata,Nabil ne yakatse shi daga duniyar  tunanin da ya lula, da fadin,



"Bakonmmu barka  da zuwa ,sai  dai kazo Dady ya dan fita amma bazai jimaba zai dawo ni suna na,Nabil"



murmushi yayi kasancewar sa mutum mara son hayaniya ,ya dora da,



"yauwa Nabil nagode ,dafatan zaka daukeni yaya ,kuma aboki,tare da  zama lafiya"



"A why not,kar ka damu kaji Yayana"



fitowar momy ne yasa shi yin shiru ahankali yazamo daga kan jujerar ya shiga gaisheta,da sakin fuska taamsa,take taji yaron ya burgeta,ya kuma kwanta mata a rai,duban Nabil tayi tace,



"Nabil,karaka yayan naka,daki yayi wanka ya huta,sai kazo ka karbar masa abincinsa "



"angama Momy na, Bross,taso muje"



cikin nutsuwa Nuradden yatashi tare da yiwa Momy godiya yafita,kitchen takoma nan ta iske,Mardiya da Yasmeen na karasa mata aikin duban Yasmeen tayi tace,



"Yasmeen  amma bakiji zuwan bakon nan  ba ko?,shiyasa kika  kasa zuwa ku gaisa,har kinmanta maganar Dadyn ku ,yayi miki kyau,kiyi kina sane"



turo baki tayi tare da shagwabe fuska tace,



"Momy bansan fa yazo ba"



tsaki kawai Momy tayi takarbi aikinta takarasa, Mardiya ido kawai ta zubawa Yasmeen domin lamarin yarinyar yana daure mata kai,Alhj Habib bedawo gida ba,sai wajen 2:30 kai tsaye bangaransa yawuce,sai da ya canja kaya daga shadda zuwa farar jallabiya,sannan yafito,a parlor yasami iyalin nasa amma banda Nabil,wanda yatare gurin Nuradden ,guri yasamu ya zauna,nan suka shiga jera masa sannu da zuwa,da sakin fuska yaamsa,tare da duban matar tasa yace,



"Maijidda,d'ana yakaraso ko"?



"Eh yallabai yazo,yana dakin da aka gyara masa,ai mutumin ka ma tunda yazo ya daukar musu abinci besake dawo wa ba"



"Nabil ko ,ai zaifi kowa jin dadin zuwan Nura,ke Yasmeen maza ki kirawo min su"



"tohm Dady"


 

Tashi tayi tanufi dakin da Nabil da Nura suke,ahankali tafara kwankwasa kofar,daga ciki aka amsa,



"waye"?



"Yasmeen ce,Ya Nabil bude min mana sauri nake fa"



cikin nutsuwa Nuraddeen yataso ya bude mata,har zata fara masa rashin kunya sai kuma taga bashi bane,ahankali ta furta,



"sannu,ko kaine bakon da dady yace zaizo"



"eh nine,Nabil yashiga wanka,inyafito zanfada masa,wazance masa tazo kiran sa"



"Bani ke kiranku,ba Dady ne,suna na Yasmeen"



"ok"



tanagama fada ta juya takoma ciki,daki yakoma ,nan yaci karo da Nabil yafito,dubansa yayi yace,



"Nabil maza ka shirya Dady yadawo yana kira"



"Angama Bross"



murmushi kawai Nuradden yayi,yadan jira shi yakintsa ,sannan suka fito zuwa parlorn da Dady yake,Nabil ne agaba sai Nuradden na biye dashi ko wanne dauke da sallama abakinsa suka shiga,kusa da dady Nabil yakarasa ya zauna yayin da Nuraddeen ya zauna daga dan nesa dasu,cikin hanzari dady yadubeshi yace,



"Haba dana,matso kusa,kar ji  dar,nan ma ai gidanku ne"



ahankali yakarasa kusa da shi tare da sunkuyar da kai ya gaisheshi ,cikin girmamawa,hannu dady yabashi su gaisa ya noke,tare da fadin,



"Nuraddeen ya hanya,dafatan kazo lafiya,ya Abban naku,da kowa da kowa"?...



"lafiya kalau,dady,duk suna lafiya,suna gaosheku"



"To,madalla muna amsawa,abinda nake so dakai shine kasaki jikinka kaji,muma iyayanka ne,ga kannan ka nan nabaka wuka da nama duk wanda yayi ba dede ba ka hukunta shi abin nagaba ka maida hankali kan abinda yakawo ka kar biyewa masiriritan abokai kaji ko"...



" inshaallah Dady zankiyaye ,Nagode  Allah yakara girma"...



"Ameen ya Allah Dana"


cewar momy,

sundanjima A parlorn suna dan taba hira ,hankalinsa gaba daya yana kan mardiya wacce bata kuma kallon inda yake ba tun bayan data kuma yimasa sannu da zuwa,yasmeen ce ta dubeshi tace,



"Yaya N,karka dinga kula yaya Nabil,tsokana gareshi"



Dariya yayi kawai  yatashi yafita,Momy ce tadubeta tace,



"Allah yashiryeki Yasmeen daga zuwansa zakifara nuna masa kalar ki ko"?



cikin shagwaba tace,


"Momy nifa gaskiya kawai nafada masa"



"yaisa kutashi kuma kuje kuyi shirin salla laasar ta kusa,"



cewar Dady yafada yana kokarin fara cin abincinsa,



washegari takama Monday tun safe suka shirya domin zuwa makaranta ,dukkansu zaune suke kan dining suna shan tea,cikin nutsuwa,Nuradden yai sallama yashigo,tsugunawa yayi yagaida su Dady,suka amsa da sakin fuska,da hannu dady yaimasa nuni da gurin zama,ahankali yaja kujera ya zauna,cikin nutsuwa  Mardiya tadago da kanta ta kalleshi,cikin siririyar muryarta tace,



"ina kwana"...


"lafiya kalau,kanwata ,Yasmeen kintashi lafiya"



"Lafiya lau,yaya N,ya bakunta"



murmushin da yazame masa jiki yakuma yi,Momy ce tadubeshi tace,



"yi sauri ka karya karabu dasu kaji dana ke Mardiya zuba masa tea  kisa masa dankalin da kwan"



"Haba Momy tare fa zamu tafi,ko Bross"



cewar Nabil,cup da plate Mardiya ta dauka ta cika masa shi da ruwan tea kamar yace yai yawa sai kuma yai shiru zata sa masa madara kenan ya dakatar da ita da fadin,





 No,kar ki sa min madara nafison lipton,Nabil hanyar mu daya kenan "?



"eh wajen B U K school din su take,dan haka,in zaka fita da wuri sai ka dinga sauke su,ga karamar mota ta nan,ka dinga amfani da ita,wajen zirga zirga"



"Nagode Dady,Allah yakara girma,Momy atayani godiya"



"Haba Dana,ai ba godiya atsakanin mu"



cikin kankanin lokaci suka kammala break fast dinsu,suka fita, Nabil ne agaba,sai su Mardiya abaya,dada gyara mudubin motar Nuraddeen yayi dan yadinga hango fuskar Mrdiya,cikin kankanin lokaci suka isa makarantar su Nabil dake kan titin kabuga,godiya sukai masa suka wuce,yaja motar ya nufi B U K,


Mardiya mamakin kyawun Nuraddeen take,aranta take yaba irin haduwar sa,ahaka takarasa

 class dinsu sai dai takasa sakin jiki dashi kasancewar ta yarinya mara saurin sabo,shiyasa wasu suke mata kallon mai girman kai,



Abangaran Nuradden kuwa tun da ya sauke su Nabil yake tuna fuskar Mrdiya domin yarinyar ta burgeshi bata da hayaniya,a haka yakarasa cikin makarantar tunda yashiga wasu yanmata suka zuba masa ido,bema san suna yi ba,kai tsaye tiyata ya wuce,domin daukar lecture,anan yahadu da wasu abokai ,take yaji hankalinsa ya kwanta dasu,Muktar da Nazifi,nan sukai sabo kamar dama sunjima da sanin juna,duk macen datayi tozali da Nuraddeen sai ta kuma kallonsa,


*wai waye wannan Nuraddeen din*???








*_NASEEBA GAWO_*✍🏻





*NASEEBA GAWO*

                 ✍🏻

[3/19, 10:27] ‪+234 814 620 5819‬: [9:58Pm,2017] 



*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦



   *💦T <W >F*💦





  


   *ZAMAN AURE*

                  👩‍👩‍👧




*NA*


NASEEBA I UBA 💐






*Allahumma la sahala illa ma jaaltahu sahala waanta tajjialil hazina iza shi itu sahala*😰👏🏻




💦


*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin mu*💦







*Ina dada jaddada godiya ta gareku masoyana bisa kwarin gwirar da nake samu daga gareku gsky kunayi ina jin ONGA, ANA TARE*🤣🤝




💙

*Dedicated 2 my dear friend DAHARA NURA*💙






               *3*





~~~Kamal be tashi daga bacci ba sai misalin 8:30am lokacin har sakna ta tashi ta Kammala komai na gidan ta hada musu break tayi wanka hade da doro alwalar ta bakin gadon tazo tafara tashin kamal cikin magagin bacci ya fizgota tafada jikin sa ture shi tafara yi ya rike ta gam hade da kaiwa wuyan ta kiss cikin raunin murya tafara magana 




"honey bee, baki salla ba fa pls katashi kaje kayi alwala yanzu fa almost 9:00 oclock "



" my dear, kina da damuwa da yawa, ai zanyi ko amma bani da nutsuwar yin hakan mutukar ban samin nutsuwa daga gareki ba "



Yana gama fadar hakan ya shiga sarrarfata cikin kwarewa kuka tasa masa sam be kula da hakan ba sai da yasami nutsuwar kamar yadda yace tashi yayi yanufi toilet dan yin wanka da salla ita kam kwanciya tayi taci gaba da aikin kuka a haka yafito ya sameta dauke kansa yayi kamar be ganta yasa jallabiya ya tayar da salla tashi tayi ta shiga toilet ta kuma yin wani wankan ta fito yana gaban mirror yana taje kai aranta tace 


_ahaka kamar mutum amma ni kadai nasan matsalolin sa_



Jiyowa yayi ya zuba mata ido da manyan idanunsa masu mutukar kyau yace 



"my dear nacanja miki ne kike satar kallo na "


A hankali ta taka zuwa gaban sa ta lumshe idonta tace 



" kwarai kuwa honey bee kafini sanin ka canja ko baka canjaba, honey bee yana dakyau kaji tsoron Allah ka tuna zaka mutu, be kamata ace kana sakaci da salla, honey bee marabar musulmi da kafiri fa imani "



Wani kallo ya bita da shi take jikin ta ya hau bari da kyarma tafara Ja da baya 



*jameel*  kuwa tunda 2 tayi hankalin sa ya koma gida saboda yasan labiba nacan tana jiransa yana cikin tunanin karan wayar ta ya shigo da sauri ya dauka jikin sa har wani bari yake ya kara wayar a kunan sa ya dora da 



"sarauniyar mata uwar gida kuma amarya a gidan jameel ko ince *danmarayan zaki*



"Hmmm jameel kenan ai a gurin hajiyar ka kake danmarayan zaki a gurin labiba kuwa abin ba haka yake ba "



" kuma fa hakane everlasting "



Wata shuumar Dariya tasa sannan ta nisa tace 



" wlh jameel yunwa nake ji gashi inason zuwa salon gsky ka dawo gida haka "



" haba everlasting kinsan irin aikin da jameel ya tara a office kuwa pls kiyi hakuri atashi sai indawo ko gidan hajiya bazan biya ba 


Tana gama jin abinda yafada ta kashe wayar hankalin sa ne yatashi yai ta kiran layin wayar ta ta taki dagawa ba shiri ya tattara aikin da yake ya fita daga office din da abokin sa ya hadu shima ya fito daga nasa office din hannu yabashi suka gaisa nazeer ne ya dube shi yace 



"aa namijin duniya yana ga kafito ko zaka office din manaja ne "? 




Tasaki yaja sannan yadubi abokin nasa yace 



Kabari akwai mutumina wlh yunwa ce ta ke neman illatani tun dazu nasa labiba taimin girki shine zanje indawo" 




"aa intaho kenan muje mu kwashi girkin amarya "



Hantar cikin sa ce takada dan shi ba abinda yatsana kamar ace zaazo gidan sa murmushin karfin hali yayi sannan ya ce 



" A, badamuwa shiga ka fito ina mota"


"ok badamuwa yanzu zan fito "




Ai jameel yana shiga motar sa yai mata key yabar gurin nazeer na fitowa yaga ba motar abokin nasa dariya yayi ya shiga neman layin wayar sa lokacin har ya isa gida yana gaban labiba  wayar nazeer ta shigo  hannu ta mika masa ba musu yabata wayar sai wani harare harere take  daga wayar tayi tafara magana 







Gidan abdul malik kuwa tun bayan tafiyar inna ruhaima take kuka, har cikin ransa yake jin kukan matar tasa a hankali ya shiga dakin tana zaune akan carpet ta hada kai da gwiwa zaman dirshan yayi a gaban ta ya kira sunan ta 




"matar B malik dan Allah kukan ya isa haka kiyi hakuri ki taimaka min wajen yiwa inna biyayya kar fa kumanta ina sonki to mezai daga miki hankali kuma ni nasan haihuwa ta Allah ce dan Allah ki share hawayenki "




" B malik meyasa inna bata so na ina bakin kokarina dan ganin na kyauta ta mata amma she cant see why? 



"kiyi hakuri wataran zata gani ai yanzu tashi muje ki tai maka min inyi wanka inje inbata hakuri "




Tashi tayi takama hannun sa suka nufi toilet din tare sukai wanka suka fito shiryawa sukayi cikin wata hadaddiyar shadda light purple sunyi kyau dubanta yayi yace 




" kai matar B malik kinyi kyau daga nan sai ina? 




Dariya tayi hade da shafa sajen fuskar sa tace 




"Ummmm gidan ummata zaka kaini kaji "




Rusunawa yayi da kansa yace," angama madam


Dariya tayi Suka jera suka fito sai da yafara sauketa a gidan su sannan ya wuce gidan su sanda yaisa gidan inna tana zaune tana kulla gishiri a leda zama yayi ya gaisheta hade da ban hakuri tasaki taja taci gaba da aikin ta gjy tayi da nacin da yake mata tayi tace 




"kaga Abdul malik ba sai naje gidan naka ba zaka sami damar cimin mtunci shiyasa na biya ta gidan rabi tabani jari nasaro gishiri dan na dunga saidawa"




"subahanallah haba inna wani irin siyar da gishiri kuma dan allah kiyi hakuri "




" zan hakura amma 

da zaiyu sharadin abu daya "



Gaban sa ne ya yanke ya fadi aransa ya jinjina sharadin inna anyawa kuwa zai amsa 







Areefa kuwa take tabiyewa wannan bawan Allah suka shiga charts take soyayya ta kullu tsakanin su har da alkawarin haduwa 





Shima hafeez yana garin kaduna ya tare a gidan khady zama su keyi kamar mata da miji yanzu haka kwance yake ya dora kansa a cinyar khady yana ta danna waya video call din areefa ya shigo kallon khady yayi ita dinmma shi take kallo. 









*NASEEBA GAWO*

        ✍🏻

[3/19, 10:27] ‪+234 814 620 5819‬: [3:47Pm,2017] 



*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦


    *💦T <W >F*💦



  


   *ZAMAN AURE*

       💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦






*NA*


NASEEBA I UBA 💐






*Rabbi yasir wala taasir Allahumma yasir alaina*👏🏻👏🏻



💦

*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin*💦






*Dedicated 2 fiddausi sodangi MUGUN MAKOCI kinyi munji ONGA naseeba tace ana tare*🤝







                *4*





~~~cikin fushi da masifa ya dubi sakna yafara surfa mata ruwan masifa da balai 




"sakeena ni kike fadawa haka me kike so kice? kina son kice kamal ya kafurta ko jahili zaki mai dani to bari kiji, wlh daga rana irin ta yau kar ki sake yimin irin wannan stupid zancan naki, kinji dai na fada miki "




Yanagama fada ya figi rigar sa yasa ya shiriya tsaf tana tsaye tana kallonsa a hankali ta karasa gaban sa ta dau turare zata fesa masa kamar   yadda ta saba hannu ya daga mata alamar ta dakata karba yayi ya fesa ya mayar ya ajiye ya kafa hular sa yayi kyau  sosai duk inda ake son namiji yakai kamal yakai  mukulin motar sa ya dauka yai hanyar parlor cikin sauri sakna tasha gabansa tai nare nare tace 



"honey bee, pls kayi hakuri bazan kuma   ba kazo muje kayi break fast kar  ka fita baka ci komai ba kaji "



" meye damuwar ki da rashin yin break fast dina,malama matsa ki bani hanya in wuce "


Matsawa tayi ya wuce ko kallon ta be kuma yi ba guri tasami ta zauna take taji kanta ya sara hawaye ne ya shiga ambaliya a fuskar ta sai da tayi mai isar ta sannan ta tashi tayi alwala tayi sallar walaha ta dau alkuranin ta tafara karantawa take tasami nutsuwa taji zuciya  tayi wasai parlor ta  fito zuba ruwan tea tasha hugun daakewa kofar parlorn ne yasa ta tashi dan ganin me hugun tana budewa tasaki faraa dan ganin bakuwar tata 






labiba kuwa tana karbar wayar jameel ta kashe bata ma duba waye ba duban sa tayi tace 



"jameel yazaai ne yunwa nake ji wlh "



" to mezakici everlasting ko in karbo mana abinci gurin hajiya ta "



"  a wane lokacin kenan kawai ka shiga kitchen dan sauri nake nafada ma saloon nake son zuwa "



Kin tsefe Kan naki ne"? 




" kafiya jan magana wlh jameel taya zan iya tsefe kai na kai zaka tsafan to, kagama girkin sai muyi tsifar "



" yes, ma"


Yanagama fada ya nufi hanyar dakin sa sai gashi ya fito daga shi sai vest da gajeran wando tana kwance murmushi ya sakar mata ya shiga kitchen indomie ya dora cikin kankanin lokaci ya kammala ya zubo musu a plate ya kawo da kyar ta sakko ta fara ci sai shagwaba take wai tagaji kwantar da murya yafara yi yace 



"haba everlasting ki daure kici sai ayi tsifar sai muyi wanka in gasa miki jikinki da ruwan dumi "



" jameel, dawa zakai wankan kar kace dani cab Allah ya sawake to wa zai min wankin undies dina ko salon mu tsaya wanka na batawa kaina lokaci"


"Hmmm shikenan everlasting badamuwa sai in zauna kije ki dawo "


" better"


Tsefemata  Kan yayi tashiga toilet tayi wanka ta fito ta shirya mukulin motar yabata ta fita guri yasamu ya zauna ya dafe kansa  yashiga tunanin irin bakar rayuwar da ya tsinci kansa ciki 





Abangaran abdulmik kuwa gaba daya hankalin sa ya bawa inna dan jin wane irin sharadi zata furta duban sa tayi tace 



"Abdulmik so nake a dinga kawo min amincin gidan ka tun daga na safe har na dare "



" inna abincin gidana kuma? 


"baze samu bane, a hakura "



" aa inna, ina ganin de kamar dan aike ne zai zama matsala "



" oh! meye amfanin kudinka malik, ai tunda kana kana da kudi dan aike zaa samo, sai kasai masa babur kana biyan sa duk wata"




Shiru yayi yana jin jina kalaman innar tasa can ya nisa yace


"shikenan inna badamuwa inshaallah zaai yadda kika ce"





"yauwa saura kuma yar mulkin tayi son ranta dan bazata so hakan ba tafiso daga ita sai yanuwanta Hmmm naso ace kana da kanne, wlh da taga yadda *kannan miji*  zasuyi ko da yake ai ko basu akwai *uwar miji*  "



Shiru yayi mata   takaraci surutun ta kudi ya ajiye mata a gabanta karshe yaimata sallama yatafi tana ta sama sa albarka  wani shuumin murmushi inna tayi 



Kai tsaye abdulmik gidan su ruhaima ya wuce lokacin tana tare da ummanta da kannan ta dasuka zagaye ta sai wasa da dariya suke ummanta ce ta dube ta tace 



"ruhaima dafatan kuna nan lpy ko "? 



" lpy kalau umma sai dai matsalar innar sa kawai"



"bakomai ruhaima ke de kicigaba da yaimata biyayya kamar yadda zaki min ban yarda ki saba mata "



" shikenan umma inshaallah zan kula "




Sallamar abdulmik ce ta katse musu zancan da suke yi  da faraa umma ta tari abdulmik suka gaisa cikin mutun tawa  sukai mata sallama suka tafi tun a hanya  abdulmik yarasa yadda zaiyi ya fada mata bukatar inna ahaka har suka isa  gida sai da suka zo bacci sun kwanta yajata jikin sa sannan yafada mata Shiru ruhaima tayi can ta janye daga jikin ta daga nasa tace 




Abangaran hafeez kuwa sai da ya bari kiran areefa ya katse sannan ya tashi ya fita cikin motar sa ya shiga sannan ya kira ta bugu 2 ta dauka cikin shagwaba tafara magana 



"Hello yallabai, katafi kabarni da kewa ni de gsky kadawo "



" sarka mai rikicin gan gan, to indawo me zan miki, me kike so daga gurin hafeez, fadan inji "



Dariya tayi sannan tace," sai kace ka manta areefa ko, to bari in tuna maka areefa bazata iya rayuwa batare da hafeez ba ayanzu haka ina kwance sai juyi nake nakasa bacci wlh "



" ayya muyi daya sweet hert nima nakasa baccin, amma abinda zaai yanzu ki rufe idon ki zan ta fada miki kalamai masu dadin sauraro da kwantar da hankali har kiyi bacci "



Dariya tayi, tayi yadda yace nan ya shiga jero mata kalamai masu dadi akarshe ya juya zancan zuwa na tada hankali da shaawa areefa rasa yadda zatayi tayi saboda yadda taji kewar mijin nata ta dawo mata sabuwa karshe yai mata sallama ya kashe wayar Shiru tayi karshe ta yanke shawarar kiran saurayin data yi a school 








*NASEEBA GAWO*

              ✍🏻

[3/19, 10:27] ‪+234 814 620 5819‬: [5:54Am,2017] 



*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦



  *💦T <W >F*💦






   *ZAMAN AURE*

         💦 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦






*NA*


NASEEBA I UBA 💐






*Allahumma salli ala sayyadina muhammad wassalim*📿👏🏻




💦

*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin mu*💦





💦💦

*Wannan shafin nakine kawata fayeex usman hakika kin cancanci yabo bisa namijin kokarin da kikai wajen kawo mana novel dinki mai suna hanyar yaman mun waazantu kuma munnishadantu Allah ya kara basira kina yi munjin dadi sai munji ki a sabon novel dinki naseeba tace ana ana tare*🤝💦💦






     


              *5*







~~~ganin maman su kamal ne ita da lubna kanwar sa ne ya sa sakna sakin murmushi ta karasa gurin su hade da rungume lubna dubansu tayi tai musu sannu da zuwa mama ce ta amsa da 



"yauwa sakeena sannu kinji dafatan kuna nan lpy ko "



Tsuguna wa sakna tayi ta gaida mama  cikin girma ma wa ta amsa da kulawa duban lubna sakna tayi tace 



" gsky lubna nayi fushi sai yau ko kullum cikin zuba idon ganin ki nake  sai yau kika biyo mama "


Dariya lubna tayi sannan ta dubi mama tace 




" mama dan Allah ai kullum ina son zuwa ko wlh aunty sakna makaranta, amma kisha kuruminki kwana 2 zanmiki "



Cikin jin dadi sakna ta dubi lubna tace 


" kai amma naji dadi sosai kice yau ina da babbar bakuwa, mama yasu aunty da su suhaif "



" kowa lpy kalau sakeena ya kamal din dafatan dai kuna lpy ba wata matsala ko "




Cikin ran sakna matsala ce fal hade da damuwa amma bazata iya bayyana sirrin su ga wani ba dan *mijin ta sirrin tane*  afili ko sai tace wa mama 



" Aa, mama ba wata matsala muna zaune lpy "



" To Alhmdulillah ayi ta hakuri kinji ita rayuwar auri da kike ganin ta hakuri ake yi da juna, amma hakan bazai sa in daya ya cutar da daya akasa daukan mataki ba duk abinda kamal yai miki ba dai dai ba nabaki dama ki fadamin kinji yata "



" Hmmm to, mama nagode Allah yakara girma "



Tashi tayi ta je ta kawo musu danbun nama da ruwa da lemo da kyar mama ta dan ci kadan tai musu sallama ta tafi sabulai sakna ta dakko ta bawa inna nan suka zauna ita da lubna sukai ta hira 



Da yamma sukai girkin su tare har bayan magariba lubna bata ga kamal ya dawo ba duban sakna tayi tace 




"Aunty wai yaya fa, dama baya dawo wa da wuri ne? 



Shiru tayi saboda bata san amsar da zata bata ba can ta nisa tace 



"eh to, yadanganta da yanayin uzurin sa a ranar lubna "



" Au wlh nazaci baya dawo wa da wuri ne infadawa Mama "



Dariya kawai tayi nan suka ci abinci suka taba hirar su hamma lubna tafara yi duban ta sakna tayi tace 




" Bacci ko,? taso muje ki kwanta "



Tashi lubna tayi suka nufi bedroom ta kwanta duban ta sakna tayi tace 



" Haba, lubna yazaki kwanta ba tare da kinyi alwala ba "



" kai Aunty wlh bacci nake ji dan Allah ki barni "



Da kyar sakna ta lallaba ta ta yi alwala sannan ta zo ta kwanta parlor ta koma ta sa plate din Quraani tanaji wayar ta ta dauka ta shiga neman layin kamal tana ta ringing be dauka ba ahaka bacci baro yai gaba da ita 


Kamar kullum kamal be dawo ba sai wajen 12:30 na dare abige ya shigo yana ta surutai tozali yayi da sakna tana kwance a Kan kujera tana bacci kawai sai jin mutum tayi ya fado kanta wata kara tasaki wacce ta gigita lubna da ke kwance a daki hannu yasa ya toshe mata  baki sai kuma ya shiga kwarara amai ba kakkautawa ahaka lubna ta. 




Abangaran labiba kuwa tana fita kai tsaye gidan su ashanty ta nufa tana shiga tayi tozali da kawar tata suka rungume juna cikin so da kauna duban ta ashanty ta dubi labiba tace 



"kai kawata kingan ki kuwa gsky kina balai jameel ya tsaya miki wlh "



" cab jameel ya tsaya min ko na tsaya wa kaina sai kace kin manta halin jameel Hmmm yanzu dai kawata aikin malam yayi kyau ko ince yana kyau dan sai yadda nayi dashi dan yanzu haka yana gida nabar shi da wanki da girki "



" kai kawata baki da kyau wlh mijin ki ne fa "



" ashanty kenan sai kace baki san halin

maza ba, ko mai mace tai musu su suka janyo saboda in suka sami dama sai su maida mace tamkartamkar baiwar da suka sa kudi suka siyo, to wlh ni labiba ban yarda wani da namiji ya dan dana min bacin rai ba "



" Da kyau kawata, to yanzu ki shiryo akwai wani sabon malami daaka bani labari zan raka ki wajen sa "



" Allah, Ashanty to zamuje gobe gobe nan "



Nan dai sukai ta kulla mugun nufin su akan bawan Allah karshe sukai sallama labiba ta tafi kai tsaye gurin salon ta wuce 





Jameel kuwa tun bayan fitar labiba ya hada under wears dinsu ya wanke tas ya wanke toilet din bayan yagama tsaf ya nufi kitchen girki ya dora musu yana yi yana share gumi ahaka ya kammala ya zuba a kuloli, wanka yayi ya dora alwala har zai fita masallaci labiba ta shigo da mota tsayawa yayi ta shigo ya mai da gate din ya rufe ahannu yasa ya bude mata murfin motar ta fito jakar ta ta mika masa yadanyi jum kafe shi tayi da ido take jikin sa yafara rawa a hankali ya ce. 





Abangaran gidan Abdul malik kuwa jan ruhaima yayi jikin sa yashafi fuskar ta yace 



"my dear dan allah kiyi hakuri da abinda zance "



" ina jinka malik fadi abinda kake son fada ruhaima me biyayya ce agareka"




"to godiya nake dear, ammm, dan Allah zaa dinga kai wa inna abinci tun daga na safe  har na dare dafatan zaki bani goyon baya wajen kyauta ta mata "



Shiru tayi kamar bazata amsa ba can kuma ta nisa tace 




" Badamuwa malik inshaallah zaayi kamar yadda inna take so "


" yauwa my dear nagode sosai Allah ya bamu zuria ta gari, dan haka ki shirya a wannan daren mai tarin albarka  zan baki baby kinji "




"Allah yasa sweet malik" 



Tana gama fada ta shige jikin sa tare da sakarwa kirjinsa kiss bargo yaja ya rufe su 


Washegari tun da safe ruhaima ta tashi ta dora girki kunun gyada tayi da doya da kwai ta kammala ta zuba a kula tasa a kwando ta dau nasu ta kai dining area ta ajiye daki ta koma ta shiga tashin abdulmalik a hankali ya bude  idonsa janyo ta yayi jikin sa ya rungume ta cikin shagwaba ta dube shi tace 


"sweet malik dan Allah katashi angama amincin inna ka kaimata kaji "


Ido ya lumshe ya shafi fuskar ta sannan ya mike ya zura jallabiyar sa ya fito bin bayan sa tayi tasa masa kwandon amincin a bayan motar sa taskar masa murmushi mayar mata yayi yaja motar sa ya tafi 



Sanda ya isa gidan inna tana parlor ta rafka uban tagumi yayi sallama ya shiga ko kallon sa batayi ba sai da ya tsuguna a gabanta yace 



"inna sannu da gida dafatan kin tashi lpy 


"Bansaniba Abdulmalik sai yanzu kuka ga damar kawo min karin kumallo duba fa kaga agogo karfe nawa to ka dau abincin ku bana ci "



Tana gama fada tasa kuka ruhaima ta mallake mata da rasa ma me zaice mata yayi can yanisa yace. 






Abangaran areefa kuwa kiran hydar 

tayi awaya sukai ta hira cikin hirar tasu ne  take fada masa tana gyayatar sa gidan ta, Shiru yayi can kuma ya amsa da 



"shikenan baby badamuwa to amma iyan yanki fa in suka tambaye ki waye ni mezaki ce? 



"ka kwantar ma da hankalin ka basa kasar nan sunyi tafiya "



" ok badamuwa Baby sai goban  zan shigo "




Nan sukayi sallama ta kashe wayar ta kwanta 


Hafeez kam suna gama waya da areefa ya koma ciki a parlor yasami khady daga ita sai vest da gajeran wando ta bazo da gashin ta sai taunar cingam take har zai wuce sai kuma ya dawo ya zuba dara daran idanunsa tasowa tayi tana rangaji kamar bishiyar da iska ke kadawa 











*NASEEBA GAWO*. 


          ✍🏻

[3/19, 10:28] ‪+234 814 620 5819‬: [5:44Am,2017] 



*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦



  *💦T <W >F*💦






   *ZAMAN AURE*

   💦  🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦






*NA*



NASEEBA I UBA 💐







*Rabbi yasir wala taasir Allahumma yasir alaina*👏🏻






💦

*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin mu*💦








*Sakon gaisuwa gareki Hafsat Hamza hakika naji dadin shawarar warinki gareni hakan shi ya tabbatar min da cewar ana tare to, naseeba ma tace ana mugun tare Nagode kawata*🤝









            *6*






~~~Dada tsorata lubna tayi taja bargo tarufe kanta tana ta zare ido ga uban gumi da yake ta keto mata da kyar tasamu bacci ya dauke ta 


   Sakna kuwa kuka tasaki mai ban tausayi yana gama aman yai bacci kamar wani karamin yaro ga dakin ya dumame da wari hade da tasamin giya da kyar ta zame jikinta tashiga toilet ta dauro towel parlorn ta dawo ta gyara gurin tas to goge sannan ta fesa air freeshner hade da kunna turaran wuta take dakin ya kauraye da Qamshi wanka tayi hade da dauro alwala tazo ta tayar da sallar nafila da rokawa mijin nata shiriya gurin sarki Allah 



Be farka ba sai misalin hudu saura kansa ne ya sara take yafara kwallawa sakna kira cikin bacci taji kamar muryar kamal da sauri ta fito ganin sa ta yi dafe da kai da sauri ta karaso gurin sa idonsa arufe yace 



"Hada min ruwan dumi zanyi wanka "



Batare da taamsa ba ta tashi ta nufi bedroom dinsa ta hada masa ruwan dawo wa tayi tafada masa cikin layi ya dubeta yace 



Oya, kama ni intashi" 


"Honey bee, bazan iya daga ka ba "




Wata razanan niyar tsawa yadaka mata ba shiri ta kama shi ya mike suka nufi daki tai maka masa tayi ya tube kayan sa ya shiga toilet din zama tayi bakin gado tana share hawaye kwalla mata kira yayi ta tashi da sauri ta nufi toilet din 




Gidan jameel kuwa labiba ce ta dubi jameel tace 




"ya de, ka tsaya kana kallo na lpy "


" wai labiba meyasa kike min haka ne kin manta matsayina a gurin ki ko "



" NA manta Jameel sai ka tuna min "



Tana gama fada tai gaba cikin fushi jikin sa yai sanyi ya bi bayan ta a daki ya sameta tana cire kayan jikin ta da sauri ya karasa gurin ta da niyar tai maka mata hannu ta daga masa a hankali ta ce 



" kar ka tabani Jameel bana so kabarni kawai "



Janye hanunsa yayi ya ja gefe ya tsaya ya ma manta salla zaiyi dauke kanta tayi ta nufi toilet dan watsa ruwa sai lokacin ya tuna da salla, sallaya ya shimfida ya tayar da salla har ya idar bata fito ba addua yayi ya shafa ya tashi ya bude wardrobe ya dakko wa labiba wata riga mara nauyi yaajiye mata akan gado hade da rafar kudi ta 500 ya fita parlor ya rafka uban tagumi tana fitowa taga kudi akan gado murmushi tasaki wata rigar ta dauka tasa tadanyi kwalliya ta fito zuwa parlorn yana zaune yasa abinci agaba yana jiranta guri tasamu nesa da shi ta zauna cikin rawar jiki yataso ya zauna kusa da ita a hankali ya kira sunan ta 



"Everlasting, dan Allah kiyi hakuri da abinda na fada miki inshaallah i will never do it again "



" Jameel inka gaji da ni ai basai ka wahalar da kanka ba just tell me "



Toshe mata baki yayi da nasa ya shiga tsotsa cikin rawar jiki kamar zakin da yasami abinci sai da ta bari yayi nisa gaba daya yagama fita hayyacinsa sannan ta zame jikinta ta yunkura zata tashi riko hannun ta yayi ya mare rece fuska a hankali yace 



" pls Everlasting ki taimaka min yau daya insami nutsuwa wlh nakai karshe zan iya mutuwa fa "



" Hmmm I am sorry 2 say *kasa ta rikice*  dazu da safe "



Shiru yayi yana juya kalamanta, me take nufi da *kasa ta rikice*  bashi da wannan amsar dole sai ita zata war ware masa wannan kullin. 




Abangaran Abdulmalik da inna kuwa yarasa da wacce kalma zai rarrasheta can ya tashi ya nufi kitchen ya dakko plate da cup yazo ya zuba mata doya da kwai sai kunun gyada ya tura mata gabanta yace 



"innar Malik dan Allah kiyi hakuri kici inshaallah bazaa kuma makara ba "



Fakar idonsa tayi taga abinda aka kawo mata hadiyar yawu tayi can tanisa tace 



" Naji amma wlh aka yimin irin haka bani ba abincin gidan ka, haba yaro ya hadu da karfan kafa ni wlh raina bayason matarka ko kadan saboda wayo take maka "



" ki de yi hakuri Inna ki dena fadar haka, yanzu me zaa dafa miki da rana "? 



" duk abinda kuka dafa ina ci kai da zaabawa meye na ka nazaba "



Shiru yayi karshe yaimata sallama yatafi gishirin ta ta dakko taci gaba da kullawa tanayi tana mita 



Sanda Abdulmalik ya karasa gida Ruhaima ta kammala komai tayi wanka jiran sa kawai tana jin shigowar sa ta fita zuwa parking space ta tareshi da faraa rungume ta yayi tare da sakar mata kiss ciki suka nufa duban sa tayi tace 




"Sweet Malik sannu da zuwa, ka dade zo muje kaci abinci "



" kai my dear ba lokaci na makara a wajen aiki sai dai ki zuba min intafi dashi, bari nayi wanka "



Shiru tayi saboda yadda take ta jiransa yazo suyi break fast, tashi tayi taje ta zuba masa a kula ta koma daki ta taimaka masa ya shirya cikin sauri ya fita ta koma parlor tayi nata break fast din kwanciya tayi tana hutawa take bacci ya dauke ta cikin bacci taji sallama kamar ta inna gabanta ne yafadi. 







Bangaran Areefa kuwa tun safe take ta shirye shiryen tarbar Hydar karfe uku dai dai ya iso cikin farin ciki ta tare shi nan suka zauna a lafiyayyun kujerun parlorn sai karairaya take masa ta caba ado duban ta yayi yace 



". My love kinyi kyau Allah yasa nazama mijin mai kyau "



Dariya tayi ta dau juice ta shiga zuba masa sai da ya hada hannun sa da nata sannan ya karba ajiyar zuciya ta saki kallon ta yayi cikin wani irin kallo yace 



" My love, wannan ajiyar zuciyar fa ta mecece "




" cikin sanyi da kashe ido, tace 


"Hydar ne sila"



Dariya yayi sosai Kan ya bata amsa suka ji ana buga gate din gidan da karfi cikin mamaki Areefa ta kalli Hydar shi dinmma ita yake kallo. 



Hafeez kuwa cikin kwarewa ya shiga sarrafa khady janta yayi zuwa daki nan suka zube a gado suka shiga aikata barnar su ahaka

Suka raba dare suna abu daya, rungume ta yayi tsam a jikin sa ahaka bacci ya daukesu be farka ba sai 7 nasafe yana tashi wayar sa tafara ringing da sauri ya duba ganin mai kiran ne yasa gabansa faduwa da sauri ya kara wayar a kunansa bayan ya mai da duban sa ga khady wacce take ta baccin ta 








*NASEEBA GAWO*

           ✍🏻

[3/19, 10:28] ‪+234 814 620 5819‬: [6:32Am,2017] 



*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦



  *💦T <W >F*💦





*ZAMAN AURE*

   💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦




*NA*


NASEEBA I UBA 💐





*Wallahu galabun ala amrihi wala kinna akasarin nasi la yaalamun*👏🏻



💦

*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin mu*💦







*Assalamu alaikum masoyan littafin Naseeba Gawo hakika naji dadin yadda littafin kannan mijina ya nishadantar daku har kuke tabbatar min da yafi zaman aure dadi to dan Allah kuyi hakuri yadanyi nisa mugani hakika littafin zaman aure yazo da wani salo wanda yatara akalla taurari 6 domin in muka duba da irin rayuwar da muka tsinci kanmmu a wannan zamani abu akwai ban tsoro da tausayi a ciki, amma fa Naseeba bata ce baazaman lpy a gidan aure ba, aa kawai dai ina yawan jin damuwar da ke cikin wasu gida janne, kar ku manta ban san gidan ki ba labarina kirkirara nayi Allah yabamu zaman lpy a gidan auran mmu AMEEN Godiya ta musamman gareki Garkuwar Fulani bisa kwarin gwiwar da nasamu daga gareki bisa wannan littafin na zaman aure gaskiya na yarda ana mugun tare*🤝🤝








             *7*




~~~Sanda sakna ta shiga toilet din kamal yana cikin barb yana ta danna jikinsa duban sakna yayi da lumsassun idonsa yace 



"oya sakeena tai maka min ki tayani wanka bazan iya ba "



" Hone beey, dan Allah ka dena abinda kake wlh ba kyau Allah ya hana "



Shiru yayi mata hannu tasa tafara cuda shi janta ya zuwa jikin sa a hankali ya fara kissing dinta tun tana tureshi har ta hakura ahaka Suka gama wankan suka fito akan gado suka zube ya zuba mata ido can yanisa yace 




" my dear dan Allah kiyi hakuri da ni da halina inshaallah zan dena duk wani hali mara kyau ki cigaba da yimin addua kinji "



Hannun sa takama ta hada da nata tare da Lumshe ido tace 



" Honey be, naji dadin abinda kace ina nan kuma ina tayaka da addua "



Rungume ta yayi tsam a jikin sa tare da kissing din karamin bakinta zame jikinta tayi taje ta kawo masa abinci ta zuba masa tare da tura masa gabansa dubanta yayi yace 




" Nakoshi gsky tunda da kaina zanci "


Yana gama fada ya kwanta dariya sakna tayi can ta nisa tace 


" I am so sorry Honey bee, taso inbaka kaji "



Tasowa yayi nan tashiga bashi yana ci ahaka har ya koshi dubanta yayi yace 


" my dear yau munyi baki ne? 



"Eh mama tazo yanzu haka ma lubna tana daki anan zata kwana "


Ido yazaro waje cikin yar kidima yadubi sakna yace. 





abangaran jameel kuwa tashi yayi yabi bayan labiba tana kwance a gado tana ganin sa ta dada tsuke fuska bayan ta yaje ya kwanta ya rungume ta can ya nisa yace 



" Everlasting kinsa jameel a duhu meye maanar kasa ta rikice "? 


Shiru tayi kamar bazata amsa ba can kuma ta dubeshi tace 


" eh, ina nufin alada nake ko zaka karbi hakkin ka ahaka ne "



" Aa haba dai amma dai gaskiya yaimin shigar wuri wlh Everlasting ina cikin damuwa komai kiga inayi karfin hali ne kawai "


" Allah sarki sai kai hakuri ai yanzu de yunwa nake ji wlh "



" ok bari inkawo miki abinci "



Tashi yayi yaje ya dakko kayan abincin yazo ya zuba mata taci sai da ta koshi sannan Shima yaci 


Wayar sa tafara ringing yana dubawa yaga sunan Hajiya ta a jikin screen din wayar da sauri ya dauka tare da kara wayar a kunansa yace 



" Assalamu alaikum, Hajiya barka da dare "



" waalaikasalam, barka ka de *Dan marayan zaki*  kwana 2 dafatan de lpy, ina labiba "



" lpy kalau Hajiya tana nan kalau tana gaisheki"



Wata harara labiba ta zabga wa jameel dauke kansa yayi kamar be ganta ba, 



"To alhmdulillah, yanzu kazo ina son ganin ka duk abinda kake kabari kazo "



" To shikenan Hajiya gani nan zuwa "


Sukai sallama ya kashe wayar mai da duban sa yayi ga labiba wata uwar harara ta zabga masa tace 


" ina kuma zaka je Jameel "? 



" zanje gurin Hajiya ta ne ko da wani abun "



" Kwarai kuwa Dan wlh ba inda zaka "


Shiru yayi yarasa ma me zaice mata can ya nisa yace. 






Abangaran Ruhaima kuwa a gigice ta tashi ta fito a tsakar gida ta tarar da inna da mamaki tashiga yaimata sannu da zuwa cikin isa ta dubeta tace 



" sannun ka de, ai ta kwada sallama kina jin mutane ko saboda raini yayi kyau "



" wlh inna bacci nake yi shiyasa kika ji Shiru kiyi hakuri "



" Dole ki bacci ai Ruhaima kinci kin ta da kai, abun haushin ma ke ba haihuwa kike ba, kazo gida me makon kaji ana gida ana hayaniya irin ta yara amma ina "



" Hajiya dan Allah kiyi hakuri shigo ciki "



" Aa barni anan bazan shiga ciki ba "


Shiru Ruhaima tayi ta nufi kitchen ta kawo mata nama da lemo duban ta inna tayi tace 



" ki dauke kayan ki banaci "


Tana gama fada ta dan kashin gida take bacci ya dauke ta ahaka Abdulmalik yazo yaga inna  da sauri ya karaso inda take ya shiga tashin ta tana ganin sa ta fara kuka cikin daga murya ya shiga kiran Ruhaima. 





Abangaran Areefa kuwa cikin sauri ta nufi bakin gate dan jin waye tana isa bakin gate ta tambaya 




"Waye ne? 



"Ashiru ne Abdulmalik ne ya aiko ni gurin ki "



" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta bude ta karbi skon ta maida kofa ta rufe ciki ta koma suka ci gaba da hirar su da Hydar kamar ba matar aure ba 



Shi kuwa Abdulmalik yana ganin kiran manajan su ya kidime da sauri ya daga wayar 



"kazo kasameni yanzu ina jiran ka  "



Mai da duban sa yayi ga khady tashi yayi ya shirya ya ajiye mata kudi ya dau kayansa ya fita 






*NASEEBA GAWO*

         ✍🏻

[3/19, 10:28] ‪+234 814 620 5819‬: [5:55Am,2017] 






💙💙💙💙💙💙    💙💙💙💙💙💙

       💙💙💙💙

               💙


    *ZAMAN AURE*

💙💙💙🤦💙💙💙

💙💙💙💙💙💙

    💙💙💙💙

               💙






*NA*


NASEEBA I UBA 💐






*Alhmdulillahil Ala kulli Halin Allahumma salli ala sayyadina muhammad wassalim*👏🏻







             *8*







~~~Mamaki sakna tayi ganin cikin kankanin lokaci kamal ya kidime duban sa tayi tace 



"Honey bee me yafaru naga kamar ka razana da jin kalamai na lpy de ko 


Sumar kansa ya shafa tare da kwantar da kansa akan cinyar ta yace 



"my dear Allah ya sa lubna bata jiyo ni ba dan nasan wlh sai ta fadawa mama halin  da ake ciki "



Ido ta tsura masa cikin gano dalilin sa na fadar haka can ta nisa tace 



" Haba honey bee ta yaya zan bari lubna taji sirrina da kai ai kamar na dabawa kaina wuka ne kar fa ka manta *mijina sirrina* ne, nide abinda nake so da kai kawai ka gyara wlh ba kyau fa Allah ya haramta shan giya kai ka halatta "



Rufa idonsa yayi kamar mai bacci yana jinta sai can ya bude ya zuba wa kyakyawar fuskar ta ido a hankali yace 



" Najj bani guri inkwanta malama 



Matsa masa tayi ya kwanta ta koma gefansa itama tayi kwanciyar ta ahaka 

bacci ya daukesu 


Da safe da wuri lubna ta tashi kitchen ta shiga ta hada musu break fast ta kammala ta jere Kan dining daki ta koma tayi wanka sakna bata tashi ba sai wajen 8 :30 saboda zazzabin da yarufeta da kyar ta yunkura ta tashi kamal yana kwance yana ta bacci a hankali ta ke tashin sa 



"Honey bee pls wake up "


Sumar kansa ta shafa a hankali ya bude idonsa murmushi ya sakar mata ya shafi fuskar ta ji yayi jikin ta zafi rau, da sauri ya dubeta yace 



" my dear me yasameki haka naji jikin ki  zafi Allah ya sa ba ciki ne da ke ba "



Shiru tayi kamar bata ji shi ba ta mike da kyar zata shiga toilet luuu tayi kamar zata fadi da sauri ya karasa ya tare ta ta fada jikin sa toilet din ya nufa da ita nan yahada musu ruwan dumi yayi mata wanka shima yayi suka  fito   wardrobe ya bude ya dakko mata wata doguwar rigar material pink yasa mata shima ya dakko hadaddiyar shadda fara kal yasa turare ya fesa yazo zai fesa mata ta ture hannun sa hade da toshe hancinta murmushi yayi yace 



"me hakan yake nufi kenan my dear "



" Honey bee, wlh bana son kamshin turaran ka gaskiya "



" sakna wlh mutukar ciki ne dake to ina mai tabbatar miki a kwai matsala "



Banza tayi masa ta fita zuwa parlor biyo ta yayi yana ta masifa ganin lubna zaune tana kallon sa ne yasa shi yin. 






Jameel kuwa kallon labiba yayi yace 



" Haba everlasting Hajiya ce fa ke son gani na pls kiyi hakuri inje in dawo kinji "



Murmushi tayi ta dube shi tace 



" ok badamuwa jameel sai ka dawo "


Kiss yasakar mata ya tashi ya shiga toilet dan watsa ruwa labiba kuwa da sauri ta tashi ta rufe kofar parlorn ta zare mukulin ta boye ta sami guri ta zauna 


Jameel kuwa cikin sauri ya shiriya ya fito parlor dan fita duban ta yayi yace 



" Everlasting sai na dawo, me zan siyo miki "? 


" Bana son komai, ka gaida Hajiya da kyau "



Tana gama fada tayi daki ta mai da kofa ta rufe tana dariya, shikuwa jameel kai tsaye hanyar fita ya nufa da karfin sa yaja kofa abin mamaki a rufe take da mukulli dabawa yayi yaga ba key din ajiki kansa ya dafe ya nufi hanyar dakin labiba shima a rufe a hankali ya shiga buga kofar yana kiran sunanta banza tai masa ya kusa minti talatin a tsaye karshe ya gaji ya dawo Kan kujera ya kwanta sai juyi yake ta faman yi ahaka bacci ya dauke shi 


Da safe da wuri ya tashi yayi aiyukan da yasaba ya kammala ya nufi daki dan yin wanka sai lokacin labiba ta fito cikin kwalliya ido kawai ya zuba mata ya shigewar sa toilet ita kam parlor ta dawo ta zauna  ta ja kular gabanta ta zuba dankali da kwai tafara ci tana cikin ci ne taji ana buga kofa tashi tayi dan budewa tana budewa taga Hajiyar jameel ce




Abangaran gidan Abdulmalik kuwa Ruhaima tana kitchen tanai wa inna abinci taji Abdulmalik yana ta kwalla mata kira da sauri ta ajiye ludayin hannun ta tafito wata uwar harara inna ta watsa mata duban sa tayi tace 



"Sannu da zuwa malik "



" yauwa, ya kika bar inna a nan baki kaita daki ba kuma ina abincin ta "



" wlh malik sai da nayi nayi da inna ta shigo ciki taki ko abincin taki ci "



Salati inna tasaka ta hau matse ido sannan ta dora da 




" yan nan kiji tsoran Allah yaushe kika ce in shigo dakin ku kai amma yarinyar nan kin iya sharri "



Abdulmalik kam rasa ma me ze cewa inna yayi can ya dubeta yace 



" kiyi hakuri inna inshaallah zaa gyara yanzu taso ki dawo ciki "



"Allah ya sawake ba inda zanje wlh ai yanzu abinda zakai min ka burge ni shine kasaki wannan matar kawai shine ka cika dan halak" 




Cikin sauri da kidima Ruhaima da Abdulmalik suka dago suka kalli inna 





Areefa bata bar Hydar ya tafi ba sai  bayan magariba tunda ga wannan ranar kullum sai ta fita sun hadu da  Hydar ahaka ta  hadu da wani Alhajin birni nan suka shiga soyayya kamar ba matar aure ba 




Hafeez yana fita wajen aikin sa ya wuce  nan ya shiga office din ogan nasu takarda ya dakko yabashi yana dubawa yaga taransfer akai masa zuwa kano be bata lokaci ba ya shirya  ya nufi kano sanda ya isa gida Areefa bata nan mamaki ya shiga yi nan ya shiga neman layin ta akashe 






*NASEEBA GAWO*

             ✍🏻

[3/19, 10:28] ‪+234 814 620 5819‬: [9:28 Pm, 2017] 





*®💦💦💦NASEEBA GAWO 💦💦💦*




*💦N I G*💦







*ZAMAN AURE* 🤦

     💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦







*NA*


NASEEBA I UBA 💐






*Alhmdulillahil Ala kulli Halin Allahumma ya mukallabul kulubi sabbit kalbi ala dinika*👏🏻👏🏻






              *9*






~~~cikin dakewa da basarwa kamal ya dubi lubna yace 




"ke, yaushe kika zo kin wani zubawa mutane ido "



Sunkuyar da kanta tayi can kuma ta dago ta dube shi tace 



" jiya muka zo da mama, ina kwana yaya "



" lpy kin tashi lpy "



" lpy kalau, Aunty sakna antashi lpy "



" lpy kalau lubna sannu da aiki  na barki da aiki ko, kiyi hakuri wlh yau natashi da zazzabi ne ". 


" Ayya sannu aunty". 


Tabe baki kamal yayi yaja kujera ya zauna, sakna ma zama tayi ta dau cup ta fara zuba masa ruwan tea plate din soyayyan kawai ya bude take sakna tafara yunkurin amai tashi tayi ta nufi toilet da sauri yana zaune ko motsawa beyi ba kallon lubna yayi yace 



"oya lubna jeki taimaka mata "



Tashi tayi ta bi bayan ta  shi kuwa mai da hankali yayi   wajen cin abincin nan sa, a haka suka fito sai sannan ya mike ya rungume sakna a jikin sa ya shiga yi mata sannu dauke kanta tayi can ya dubi lubna yace 



" lubna kawo mata tea tasha "



A hankali sakna ta dago ta dube shi tace 



" Honey bee, bazan iya sha ba pls ka barni "



" Aa my dear kisha kadan sai muje asibiti ko "? 



hannu yasa ya karbi cup din da lubna ta zubo ruwan tea da kansa ya shiga bata tana sha, kadan tasha ta dauke kanta, duban lubna ya kuma yi yace 



" jeki dakko mata mayafinta "



" To yaya "



Kai tsaye daki ta nufa ta dakko mata mayafinta ta kawo da kansa ya karba ya yafa mata suka bar lubna a gida suka nufi asibiti suna isa suka shiga ganin likita cikin kankanin lokaci ya dubata take ya gano shigar ciki na sati shida da fararsa ya dubi kamal yace 



"congratulation abokina matarka na da ciki na tsawan sati shida "



A razane kamal ya dago ya dubi likitan hade da watsawa sakna wani irin kallo jikin ta ne yai sanyi ta tsura masa ido 






Labiba kuwa duban Hajiyar jameel tayi tai mata sannu da zuwa da sakin fuska taamsa ta sami guri ta zauna cikin kwantar da murya ta gaishe ta 



"Hajiya ina kwana ya hanya "



" lpy kalau yar albarka kuna nan lpy de ko "



" lpy kalau Hajiya, bari akawo miki abinci "



" Aa yi zaman ki ina Dan marayan zaki, yana nan de ko "



" ba ya nan  Hajiya ya fita tun dazu "



Hajiya najin haka ta mike dan tafiya tare da duban labiba yace 



" to shikenan badamuwa zan neme shi a waya, sai anjima "



Tafiya tayi ita kuwa labiba dariya tayi  ta dawo ta zauna jameel ne ya fito cikin shirin fita office duban labiba yayi

yace 


" Everlasting sai naji kamar muryar Hajiya ko "? 



A hankali ta dago ta dubeshi tace 





Su kuwa su Ruhaima hakuri suka shiga bawa inna tai musu banza Abdulmalik ne ya dubi innar yace 



" Dan Allah inna kiyi hakuri wlh ina son ta "



" Wani kallo ta yi masa hade da tabe baki tace 



"shikenan Abdulmalik na barka da matar ka amma wlh bazaka kuma gani na a gidan ka dan bana son matarka juya kawai wacce bata haihuwa saboda mugun ta "



Tana gama fada tayi gaba da sauri Abdulmalik yabi bayan ta afusace ta juyo tace 



" wlh mutukar baka dena bina ba zan tara maka jamaa "


Shiru yayi can kuma yanisa yace 





Abangaran Hafeez kuwa zaman jiran areefa yai tayi bata dawo ba sai laasar lokacin har ya gaji da jiran ta ransa yagama baci tana shigowa gidan tayi tozali da motar sa cikinn ta ne ya murda daakewa tayi ta shiga parlorn yana kwance daga shi sai vest da gajeran wando wani banzan kallo yai mata yace 



"Daga gidan uban wa kike kuma da izinin wa kika fita "


Banza tayi masa can ya hassala ya mike cikin fushi da bacin rai ya nufi kanta tsugunawa tayi ta shiga bashi hakuri dan tasan zuciyar Hafeez yanzu ya bige ta abanza da sauri ta ce 






*NASEEBA GAWO*

         ✍🏻

[3/19, 10:28] ‪+234 814 620 5819‬: [6:10Am,2017] 





*®💦💦NASEEBA GAWO💦💦💦*





      *💦N  I G*💦




 *ZAMAN AURE*

   💦   🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦






*NA*


NASEEBA I UBA 💐



*subahanallahi wabihamdihi subahanallahil azeem Rabbi yasir wala taasir Allahumma yasir alaina*👏🏻






         *10*







~~~Hannu kamal ya mikawa likitan suka gaisa sannan ya dubi sakna yace ta taso su tafi jiki a sabule ta bi bayan sa a mata ta same shi ransa a mutukar bace bata kula shi ba Shima be ce mata kala ba ahaka Suka isa gida kowa da abinda yake sakawa ya na ajiye ta a gida ta fita daga motar ya figeta a guje ya bar gidan kai tsaye gurin aiki ya wuce anan ya hadu da abokin sa *shaba*  yana ganin abokin nasa ya fiskanci yana da damuwa cikin barkwanci ya dube shi yace 



*"Bobson*  kamar kana tare da damuwa ko "



Tsaki yaja sannan ya dubi abokin nasa yace 



" shaba akwai matsala fa wai yarinyar nan ciki gareta, haba da Allah nawa nake da zanfara haihuwa yanzu ina tsaka da jin dadin rayuwa ta kai imposible "




Dariya shaba ya ringa yiwa kamal har sai da yagaji da kansa sannan ya dubi abokin nasa yace 



" abokina akwai shawara matso kaji "



Matsawa kamal yayi ya rada masa magana a kunne dariya yasaka suka tafa 



Sakna kuwa tunda ta koma gida take kwance dan ma lubna ta nan ita ta taimaka mata da aikin gida ana yin magariba kamal ya dawo gida da wasu ledoji a hannun sa a a parlor ya tarar da lubna tana kallo  nan tai masa sannu da zuwa ya amsa  leda daya ya mika mata mai dauke da kaji aciki ya dora da 



"ki juye a plate ki dau taki ki kawo wa sakna tata "



" To, yaya kamal, kaifa "? 



" wannan ta ishemu "



dakinsa ya nufa tana ciki a kwance ta takure a Kan gado, Kan gadon ya nufa ya yaye bargon da ta rufa dashi yajata jikin sa yace 




" My dear sannu da jiki ya kika wuni "? 



Idonta a rufe take magana," Honey bee sannu da shigowa, yau da wuri haka, jiki Alhmdulillahil"



"Eh dole ce tasa na dawo da wuri saboda jikin naki, gsky kinashan wahala dear kina jina ko nazo da wata shawara ne wacce zata amfane mu ina son kibani hadin kai"



Shiru tayi tana juya zancan nasa aranta can ya nisa yace 






Labiba kuwa duban jameel tayi tace 



"Oh, tambaya ta kake jameel to da baka ganta wai meyasa kake son jan zancan da bashi da amfani bare maana "



" Allah ya huci zuciyar ki, miko min flaks din tea din na diba "



" Babu na shanye sai dai in wani zaka dafa "



Murmushi kawai yayi ya dau berif case dinsa ya fita da sauri ta biyo shi tasha gaban sa tace 



" jameel kana jina ina magana kai min Shiru ko, saboda ka maidani yar iska ko "? 



" Everlasting kiyi hakuri indawo ko ma meye ayi wlh nayi late fa "



Yana gama fada ya fita ya barta tana ta masifa wayar ta ta dauka ta shiga neman layin ashanty 



Jameel yana fita gidan Hajiyar sa ya nufa tana zaune a parlor yai sallama ya shiga dagowa tayi ta zubawa dan nata ido kusa da ita yasamu ya zauna ya gaisheta kasa amsawa tayi can ta dubeshi tace 



*Danmarayan zaki* anya kuwa kalau kake, yanzu daga Ina kake "



Shiru yayi saboda yadda yake jin sa wani iri zuciyar sa a takure hotan labiba kawai yake gani dagowa yayi yace 



" Hajiya daga gida nake, dan Allah ki yi min addua narasa me yake damuna kwana 2 "



Mamaki ne yakamata da yace daga gida yake can ta nisa tace 






Abdulmalik kuwa duban inna yayi yace 


" inna kifadi duk abinda kike so zan miki amma kar ki rabani da mata ta dan Allah "



" Naji bazan rabaka da matar ka ba mai mata to amma ina son zan dawo gidan ka da zama, dan naga me ke faruwa ni fa ban yarda da matar ka ba asiri take maka baka sani ba "





" shikenan inna ki dawo amma sai 

angyara miki dakin da zaki sauka "




" yaushe kenan, dan bana son bata lokaci "



" yau dinnan zaa gyara inna "




" to shikenan yanzu daga nan gidan yayarka zanje nafada mata sai tazo ta hada min kayana "




" to shikenan inna bari nazo na kai ki "



" Aa basai ka kaini ba kabarshi kaje ka dakko masu gyara min dakin "




Tana gama fada tai gaba tana ta mita gida ya koma a daki ya tarar da Ruhaima tana hada kaya dubanta yayi ya kwace kayan hannun ta jikin sa ya jata ya shiga rararashinta duban ta yayi yace 





Bangaran Hafeez kuwa ido ya tsurawa areefa yana sauraran amsar da zata bashi cikin inina tace 




"Dan Allah sweet hert  kayi hakuri wlh cikina nane ke ciwo shine naje asibiti kuma nakira wayar ka switch off "




" Areefa kinsan halina ko bana son karya kar ki sake naka ma ki da laifin karya, wuce ki dora min abinci nadawo tun dazu ba kya nan "



Da sauri ta shige kitchen ta dora masa girki wayar sa ya dauka ya fara charts da yanmata cikin Kan kanin lokaci ta kammala ta zubo masa wayar ta taa jiye Kan kujera tashiga toilet dan yin wanka yana cikin cin abincin wayar tata tafara ringing hannu ya kai ya dauka 





*NASEEBA GAWO*

           ✍🏻

[3/19, 10:28] ‪+234 814 620 5819‬: Shiru yayi can ya nisa yace, "Au daga gurin abokina nake tun safe na fita" 



"To ai shikenan Allah ya kyauta kai de ka dage da addua nima kuma zan tayaka dan na kula akwai abinda ke damun ka "


" To shikenan Hajiyata inshaallah zan dage, kina da abinci "?



"abinci kuma ina na gidan ka"? 



Wlh banason komawa gida ne Hajiya office zan wuce" 


"ai shikenan bari in zubo maka "


Tashi tayi ta zubo masa fatan wake da wainar kawai sai ruwan tea nan ya zauna yaci ya koshi tashi yayi yaimata sallama bayan yaajiye mata kudin cefane kamar yadda yasaba kai tsaye office ya nufa sanda ya karasa ya makara da manajan su ya ci karo duban sa yayi cikin tuhuma yace 


"yayi kyau jameel kasame ni a office dina "



Hankalin sa ne yai masifar tashi dan yasan tasa tasami shi karshanta ma a koreshi 





Labiba kuwa tana kiran ashanty tace tazo tasameta a gida, so take tadada mallake kamal sai yadda tayi dashi, dariya ashanty tayi tace 



" kawata baki da dama, ki tausaya masa haka mana "



" eh intausaya masa nakuma yaci ubana ko, to badani ba, sai dai in kin gaji ne to sai ki fada min shifa *zaman aure*  ayanzu sai ka shirya yanzu sai ayi baki "



" hakane kuma kawata, to sai nazo "





***************



Abangaran Abdulmalik kuwa ido ya zubawa Ruhaima yace 



" Haba sweet hert, me kike shirin aikatawa kina son kice min zaki tafi ki barni ne ko kuwa kina son kice min bazaki iya hakuri da halin mahaifiya ta ba, kina tunanin zan iya *zaman aure* da wata ba keba, Dan Allah kiyi hakuri ki rufa min asiri kar ki tafi ki barni kinji




Kuka tasa masa tafada jikin sa dada rungume ta yayi tsam a jikin sa yana shafa gadon bayan ta cikin kukan tace 



"Sweet malik, inna bata so na yazanyi ta tsaneni, dan Allah ka barni in tafi bazan iya ba "



Toshe mata baki yayi da nasa yashiga tsotsar lebanta kamar mai tsotsar alawa dada lafewa tayi a jikin nasa can ya dago da idanunsa dasuka kada sukai Ja zur yace 



*matata ki yimin alkawari bazaki taba guduna ba duk runtsi kuma kiyimin alkawarin zaki jure da halin inna zaki kau da kai "



Shiru tayi kamar bazata amsa ba can kuma ta dago da kanta ta dube shi 




Inna kuwa bata zame ko ina ba sai gidan yayar Abdulmalik tana kitchen taji sallamar ta fitowa tayi taga inna da faraa ta tare ta tai mata sannu da zuwa parlor suka shiga suka gaisa can ta dubi inna tace 



"inna daga ina haka "? 



" Daga gidan Abdulmalik nake, yanzu ma zuwa nayi infada miki kizo muje ki hada min kayana zan koma can da zama ".



Shiru Rabiaa tayi tana sauraran inna saboda ita kanta tagaji da rigimar innar tasu can ta dubeta tace 



" Haba inna ta yaya zaki koma gidan Abdulmalik da zama gsky kar ki koma wlh kiyi zaman ki a gidan ki " 



Wani kallo inna tayi wa Rabiaa idon ta fal fada ta shiga surfa mata masifa 





************



hafeez yana daukar wayar areefa sai gata da sauri tasa hannu ta karba kallon ta yayi kawai yaci gaba da cin abincin sa be kawo komai ba ita kuwa da sauri ta koma daki dan amsa wayar 



"Zankira ka"



Kawai tace ta kashe wayar parlorn ta koma ta sami gefan sa ta zauna duban ta yayi yace 



"waya kiraki awaya "? 



" oh, Habibu ne wai yadawo daga bauchi zai zo "



Habibu kani ne ga areefa daga ita sai shi 



" oh yana bauchi ko "? 



" Eh mana yana can, karatu ya rike shi "




" yayi kyau ai, kwashe kayan abincin nan kikai kitchen "



" tohm amma yau de kwana zamuyi muna...... 



"muna me karasa mana "



Kaima kasan sauran ai" 



Shiru yayi mata karshe ya tashi ya shirya tsaf ya fita 


Murmushi tayi dataga ya fita nan

ta jawo 







*NASEEBA GAWO*


         ✍🏻

[3/19, 10:28] ‪+234 814 620 5819‬: [6:54Am, 2017] 




💦

*®💦💦NASEEBA GAWO💦💦💦*




   *💦💦N I G*💦💦







    *ZAMAN AURE*

       💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦





*NA*



NASEEBA I UBA 💐






*Alhmdulillahil lazi ahayana baada ma amatana wailehiln nushur*👏🏻👏🏻





*wannan shafin nakine kawata BILY LADAN ina tayaki murnar birthey dinki dafatan Allah ya karo shekaru musu dubun albarka naseeba tace ana ana tare*🤝






             *11*






~~~Sakna ido ta zubawa kamal tana sauraransa ci gaba yayi da magana Cikin rarrashi da kwantar da murya 



"my dear kinaji na ko me zai hana ki sha wannan kwayar da nazo da ita, musamu cikin jikin ki ya zube kinga fa haihuwa da wahala, ki duba fa kiga tun yanzu irin wahalar da kike sha kuma ni sai nake ganin kamar be kamata ace mun haihu yanzu ba a yadda muke yanzu ko "? 



Tunda kamal yafara magana sakna ta ke kallon bakin sa sai da yayi Shiru sannan ta dube shi cikin kidima tace 




" Honey bee, me kake shirin aikatawa kenan wacce hajja gareka da har zuciya zata debeka ka aikata kisan kai, Honey bee nice baka so ko? shi yasa baka son haihuwa dani, kar fa ka manta abinda kake son ai katawa babban laifi ne a gurin ubangiji kuma......... 




Cikin tsawa ya dakatar da ita ya shiga surfa mata ruwan masifa 



"Dalla malama dakata ke har kin isa ki yimin waazi ke awa, daga fadar raayina sai kifara fadawa mutane maganar banza, to bari kiji ni kamal nace ban shirya haihuwa yanzu ba dan haka wallahi tallahi sai anzubar da shi ke har abada bazaki taba waye waba"




Shigowar lubna ne yasa shi yin Shiru duban sakna tayi tace 


"Aunty sannu ya jikin naki "



Kai kawai ta gyada mata saboda datayi magana kuka ne zai kubce mata plate din kazar taajiye zata fita kamal ya dakatar da ita 



" ke lubna dawo ki fita da kazar ki kai mata parlor ga ta nan fitowa "



Dawo wa tayi ta dauke ta fita tana mamakin halin yayan nata, mai da duban sa yayi ga sakna yace 




" Tashi ki fitar min a daki, kuma wlh kishirya karbar duk abinda ya biyo baya, dan zan baki mamaki "



Yunkurawa tayi ta tashi da kyar ta fita inbanda jiri ba abinda ke dibar ta tana fita ya dakko wasu zungura zunguran kwalabe ya bude daya ya kafa kai ya fara sha take hankalin sa ya gushe 


Sakna kuwa tana fita dakin ta ta wuce ta kwanta tasaki kuka mai ban tausayi aranta take tambayar kanta wane irin *zaman aure* ne sukeyi da kamal kullum burinta taga ya nutsu yadena abinda yake amma dada lalacewa yake, lubna ce ta turo kofar dakin ta shigo ganin aunty tata tana kuka yasa hankalin ta tashi da sauri ta karasa gareta ta shiga tambayar ta 




************




Hajiyar jameel kuwa duban tuhuma takewa dan nata tace 



"Anya kuwa Dan marayan zaki ba wata matsala tsakanin ka da matar ka kuwa, naje gidan naka tace min bakya nan kuma kace daga gida kake

[3/19, 10:28] ‪+234 814 620 5819‬: [8:36pm, 2017] 



*®💦💦NASEEBA GAWO💦💦💦*




      *💦N I G*💦






💦                           

      *ZAMAN AURE* 

         💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂   💦






*NA*


NASEEBA I UBA 💐






*subahanal wahidul ahadi subahanal faradul samadi subahanal lazi lam yalid walam yulad walam yankun lahu kufuwan ahad subahal lazi lam yattakiz sahahibatan wala waladan ajib daawatana ya Allah*👏🏻👏🏻



💦

*TALENTED WRITTERS naseeba tace ana tare*🤝




*wannan shafin nakine sister ummu aymana ina tayaki murnar fara novel dinki mai suna RABO AJALI Allah ya sa kinfara a saa*😍








              *12*


~~~Da sauri sakna ta share hawayen fuskar ta ta dago da idonta ta kalli lubna da sauri lubna ta tari numfashin ta tace 



"Aunty me yaya kamal yai maiki, shine ko, nafiskanci kamar akwai matsala a *zaman aurenku*  dan Allah kifada min abinda yake maki"




Shiru sakna tayi can ta nisa tace 



"kar ki damu kanwata ba komai kawai de batajin dadi ne shiyasa, amma bawata matsala tsakani na da kamal, bani kazar inci "



murmushi kawai lubna ta yi ta mika mata plate din kazar karba tayi tafara ci take taji zuciyar ta na tashi ture plate din tayi ta shiga toilet da sauri ta sheka amai, tagama tayi wanka ta fito daure da towel  lokacin lubna har ta yi bacci mawakin baccin lubna ta yi, ko rigar bacci bata sa ba ta koma parlo ta kwanta, kuka ne ya kwace mata da ta tuno da rikicin da kamal yazo da shi a haka bacci ya dauke ta 



Kamal kuwa sai da yasha giyar sa yayi tatul yai ta surutai

kafin bacci ya dauke shi, be farka ba sai wajen 3 da rabi na dare, wanka yayi ya dauro alwala yai sallar ishai yunwa ce ta isheshi ya murda kofar bedroom din ya fito parlorn tozali yayi da sakna kwance da towel a jikin ta fuskar ta tayi kyau ga santala santalar cinyo yinta wani iri yaji a jikin sa a hankali ya karasa gabanta ya tsuguna cikin ta ya shafa, a bacci taji ana shafa mata jiki, da sauri ta bude idonta ta dora su akan kamal shi dinmma ita yake kallo tashi tayi da sauri zata bar gurin towel din ya rike take ya janyota jikin sa, kuka tasa masa dago da idonsa yayi 





Abangaran *JAMEEL KUWA*


Cikin tashin hankali  ya bi bayan MD dinsu a office yasame shi zaune Kan kujerar sa sai juyawa take da shi kujerar gaban tebirin sa ya samu ya zauna dago da kansa yayi ya zubawa jameel ido kana yanisa yace 



"Wato jameel lamarin ka yana bani mamaki ko de kagaji ne da aikin? 



Cikin rawar baki jameel ya dago ya ce 



"aa, yallabai wlh mata ta ce bata da lpy, shiyasa, amma inshaallah zan gyara "


" To ai ina ganin sai ka zaba ko aiki ko matarka, saboda kafin auran ka ba haka kakeyi ba, kafi kowa kwazo, amma gaba daya ka canja, why? 



"yallabai Ayi hakuri inshaallah zan gyara "


" Gsky wannan shine magana ta da kai, takarshe wlh in nakuma kama ka da sakaci akan aiki to, fa bazakaji dadin hukuncin da company zai yanke ba, tashi kaje ".



" Nagode yallabai, atashi lpy "



Ko kallon sa beyiba haka ya tashi ya fita    ya nufi office din sa zama yayi Kan kujerar sa ya dafe kansa yashiga tunanin irin bakar rayuwar da ya tsinci kansa ciki hawaye ne ya shiga ambaliya a fuskar sa aransa ya ke fadin *_wane irin zaman aure_*  ne sukeyi  bashi da wannan amsar a haka yasamu ya kammala aiyukan sa na ranar karfe 5 suka tashi kai tsaye gidan sa ya nufa sanda ya isa gidan labiba na kwance ta caba ado kamar mai shirin zuwa gasar kyau da sallama ya shiga parlorn ko kallon inda yake batayi ba kusa da ita yasamu ya zauna a hankali ya kira sunan ta 


"Everlasting sannu da gida, dafatan baki da wata damuwa "? 



Afusace ta dago ta dubeshi tace 




" jameel kana tambaya ta ne, saboda ma ka maidani yar iska, ko me? ka duba fa kagani karfe nawa yanzu, tun safe da ka fita bansa komai a bakina ba "




" subahanallah, i am so sorry wlh yau na tara aiki ne a office shiyasa kikaji ni Shiru, yanzu me zaki ci in je in siyo miki "? 




" kut, jameel labiba ce zata ci abincin siyarwa, Allah ya sawake wlh kai zaka dafa min "




Angama ranki ya dade ina zuwa, bani minti 2". 



Banza tai masa ya nufi bedroom din sa sai gashi ya fito daga shi sai vest da gajeran wando kai tsaye kitchen ya nufa ya dora jollofe din taliya da dafatan kwai cikin kankanin lokaci ya kammala ya zubo musu a plate ya kawo tana kwance tana kallo dubanta yayi yace 




"Everlasting bisimillah sakko kici abincin kinji ". 




" ok"



Kawai tace nan suka fara cin abincin da kansa ya ke bata can ya dubeta yace 




"Amma, Everlasting pls yau atausaya min in sami nutsuwa da tattausan jikin ki, mai dadin kamshi, yau de mu raya wannan dare mai albarka, kamar ko wane maaurata, ko kuwa? 




"Cab lallai ma jameel to anawa hakan zai faru "? 



Rasa ma me ze ce mata yayi kawai yaxuba mata ido 






A bangaran *Abdulmalik kuwa*




Ruhaima ta daga masa hankali da kukan data ke faman yi ido yazura mata yana sauraran maganar datake yi game da matsalar ta da inna 



" Malik dan Allah kayi hakuri karabu dani wallahi inna bataso na ka zauna da ita lpy "



Rarshinta yashiga yi tare da fada mata kalamai masu dadi da kwantar da hankali nan ya shiga nuna mata soyayya mai rikita mutum a haka ya mantar da ita damuwar da take ciki sai da komai ya lafa sannan ya jata suka nufi toilet da kansa yai mata wanka Shima yayi suka fito shiryawa sukayi cikin kananun kaya blue din shirt an rubuta *for ever*  da bakin rubutu sai bakaken wanduna sunyi kyau harabar gidan suka fito nan suka shiga wasan tsere abun su gwanin shaawa Abdulmalik ne ya rungume Ruhaima a jikin sa sunaiwa juna dariya yace 


"Baby gsky mugodewa Allah munyi dace 

*zaman aure*"





Dago da idonta tayi ta zubawa dan karamin bakin sa mai zagaye da gashi ido tasakar masa 





Inna kuwa cikin masifa ta dubi Rabia tace 





"Rabi bakin ciki kike yi dan nace zankoma gidan Abdulmalik, to sai kiyi bakin cikin ki ya kashe ki ba shegen da yaisa ya hana ni komawa gidan dana ehe "




" Haba inna wani irin bakin ciki kuma daga fadar gaskiya, Allah ya huci zuciyar ki "





" Ameen, yarinya sai shegen son zuciyar tsiya "




Tana gama fada tai gaba tana mita kai tsaye gidan ta ta wuce nan ta shiga hada kayanta nan da nan ta kammala mota tasamo ta kwashe mata komai sai gidan Abdulmalik 





Abangaran 

*Hafeez kuwa*



Yana Fita gidan su ya wuce suka gaisa da iyayansa nan mahaifinsa yai tai masa nasiha yabada hankalin sa kamar ya dauka yai musu sallama tare da yi musu alheri ya tafi yana cikin tafiya ya hadu da wata kyakyawar yarinya da sauri yai parking agabanta yafito nan yashiga tsarata murmushi tayi tashiga motar yaja suka tafi 





Areefa kuwa Alhj Namadi takira a waya nan sukai ta hirar su data gama shi ta kunna data sukai ta charts da Hydar suka gama gajiya tayi da jiran Hafeez ahaka bacci ya dauke ta be dawo ba. 







*NASEEBA GAWO*

                          ✍🏻

[3/19, 10:29] ‪+234 814 620 5819‬: [5:48Am, 2017] 




*®💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦




      *💦N I G*💦






   *ZAMAN AURE*

      💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦





*NA*


NASEEBA I UBA 💐






*Rabitu billahi rabban wabil islami dinan wabi muhammadan S A  W nabina*👏🏻👏🏻






 *Dedicated 2 ummy Aisha we are stil waiting 4 u, 4 the new novel sis*👌🏻







               *13*







~~~Sakna kasa kwace kanta tayi daga jikin kamal shi kuwa dada Kankameta yayi daukar ta yayi cak yai bedroom da ita akan makeken gadonsu ya ajiye ta nan yashiga sarrafata cikin kwarewa kmr bashi ne wanda yai mankas da giya ba a hankali ya kira sunan ta 



".my dear, dan Allah ki fahimceni, nifa bawai bana son muhaihu bane kin gane kawai de nafi son sai nan gaba, kinga yanzu baki da kwarin da zaki haihu, 



Fuskar ta ya shafa, sannan ya dora da, 


"kuma wlh sakeena tausayin ki nake ji, duk abinda zai saki a matsala wlh bana son sa "



Da sauri ta dago da idanunta da suka kada sukai ja saboda kuka ta dora su a kyakyawar fuskar sa tace 




" Honey bee, naji kace baka son abinda zai sani a matsala, to ai ni sakna na dade cikin matsala, saboda haka bana tsoron shiga wata, kullum fada maka nake illar datake cikin shaye shaye, wlh bazan kaffara ba wannan shaye shayen naka ne ya janyo har kake kokarin aikata kisan kai, to nide ban yarda ba, kuma kaji tsoran Allah "



Tureta yayi can gefe har sai da ta bige da jikin gado cikin masifar fada yafara magana 


" sakeena ni kike fadawa haka saboda kin raina ne, to ki bude kunan ki da kyau kiji mezan fada miki, ni kamal, 








Abangaran 

*jameel kuwa*




Kallon labiba kawai yake saboda cikin kankanin lokaci rayuwar *zaman aurensu*  ta sauya a hankali ya ce 



"Everlasting yanzu ni da hakkina amma sai na biya sannan zaki bani banda sadakin dana biya abaya "



" Hmmm, jameel kenan ai ban maka dole ba, dan haka sai ka hakura ai "



Shiru yayi can yanisa yace," shikenan yanzu nawa zan biyaki"




"Dubu ashirine baya wa, amma fa sai kafara mana wanki tukunna "


Dagowa yayi yazuba mata ido ita dinmma shi take kallo can ya nisa yace 



" Everlasting anya kuwa kinajin tsoron Allah nifa mijin ki ne "




Wata ashar tasaki wacce tayi dai dai da zuwan Hajiyar jameel gidan. 





Abangaran 

*Abdulmalik kuwa*



Suna ta zuba soyayyar su shi da matar sa sai jin tsayuwar mota sukayi Ruhaima ce ta dube shi da dara daran idonta a hankali tace 



" malik inna ta dawo ko, nashiga uku na "



" Haba sweet hert, ya daga jin tsayuwar mota zakice inna ce bayan ni zanje intaho da ita "



Be rufe bikin sa ba suka ji ana buga gate din gidan da sauri Abdulmalik ya tashi ya tafi budewa Ruhaima kuwa tsayawa tayi a jikin taga tana kallon me shigowa yana budewa yayi tozali da inna dafe kansa yayi ya boye damuwar sa duban sa tayi tace 



" sannu bawan mace to, ai sai kashigo min da kayana, gwanda indawo duk abinda zaai ayi agabana, yauwa ina munafukar matar taka take 


Cikin Ruhaima ne ya bada kululu saboda tasan tunda inna ta dawo shikenan tarasa farin ciki acikin *zaman aurent*




A bang a ran 

*Hafeez kuwa*



Tun ahanya yake ta nunawa budurwar da ya dakko soyayya duban ta yayi yace 




"kyakkyawa ya sunan ki, dan da dukkan alamu Hafeez yasami matar aure "



Fari tayi da ido sannan ta dube shi tace 



" kash sai gashi fauziya ba aurene a gabanta ba, ya kenan zaayi Hafeez "




Dariya yayi hade da kashe mata ido yace 


" To ai badamuwa mai sunan larabawa zan iya jiranki haka nan kuma zan tai maka miki wajen cikar burin ki, kinji beauty"




"Nagode Hafeezi, sai dai fa ni bana son muamala da mai aure bansaniba ko gwarzon nawa yana da aure "? 



Murmushi yayi hade da shafa sajen da yake waye fuskar sa yace 



" Bani da aure, bantaba aure ba ma ke ko shaawar yinsa banayi sai yanzu dana hadu da ke beauty, yanzu dai ina muka dosa kenan abin nufi ina zankai ki "



Shiru tayi kamar me nazari can tanisa tace....... 



Areefa kuwa tun da ta kwanta bata farka ba sai wajen  11 na dare har lokacin Hafeez be dawo ba tashi tayi tayi wanka ta saka kayan bacci wayar ta ta dauka tashiga neman layin sa tana ta ringing be daga ba ajiye wayar tayi ranta a mutukar bace yau ta kudiri niyar yin rigima da Hafeez. 







*NASEEBA GAWO*

              ✍🏻

[3/19, 10:29] ‪+234 814 620 5819‬: [6:20Am, 2017] 



*®💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦


    *💦N I G*💦



  *ZAMAN AURE*

      💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦




*NA*


NASEEBA I UBA 💐




*Allahumma salli ala sayyadina muhammad wassalim*📿

   *JUMAATU BABBAR RANA kar mu manta da yiwa annabi salati*👏🏻






*Wannan shafin nakune ango da amarya wato Rukayya B uba da Anas B uba GAWO naseeba na tayaku murnar auranku ina rokon Allah yasa ayi lpy agama lpy Allah yasa kushiga a saa AMEEN dole yau GAWO family su kwaso shooki*💃🏻💃🏻







             *14*





~~~inbanda aikin kuka ba abinda sakna keyi kamal kuwa cikin masifar fada yake magana Shiru tayi tana sauraran kalaman sa masu mutukar daci da zafi 



"Kinki yarda azubar da cikin nan ko, to bari kiji bani ba cikin jikin ki ba ruwana da shi duk wani abu da zai taso miki game da shi to kisan yadda zaki yi, kinaji na ku, shasha sha kawai wacece bata san ciwon kanta ba "



Cikin tsananin tashin hankali ta dago ta dube shi can taja doguwar ajiyar zuciya tace 



" Nagode kamal hakika yau nadada sanin waye mijina, amma badamuwa inshaallah ni sakeena naji nagani na kuma karbi cikin jikina a matsayin kyautar ubangiji, kuma ina mai tabbatar maka bani ba kai kanka sai kayi alfahari da abinda zan haifa, kuma ina dada jaddada maka cewar kaji tsoran sarki Allah, kasani zaka mutu...... 



Kan ta karasa ya katseta ta hanyar daka mata tsawa



"Ya isa haka malama, ni kike kalla kice inji tsoron Allah zan wani mutu, oh mutuwar a hannun ki take ko, yayi kyau dan Allah yau base gobe ba ki kashe kamal, stupid, oya tashi ki fitar min a daki, kuma wlh zan baki mamaki "



Tashi tayi ta gyara daurin towel din ta, ta fita kai tsaye dakin ta, tanufa lubna nata bacci toilet tashiga ta dauro alwala tazo ta tayar da salla tare da rokon Allah samin sauki cikin rayuwar *zaman aurenta*   ta dade a zaune kafin ta koma ta kwanta bacci mai dadi ya dubeta 


Washegari da wuri lubna ta farka ta hada musu break fast lokacin sakna ta koma bacci bayan tayi sallar asuba, kamal ne ya murda kofar dakin sa ya fito ransa a mutukar bace tozali yayi da lubna duban ta yayi. 





*Jameel*



Cikin mamaki Hajiya ta dubi labiba tace 


"subahanallah haba, labiba, ya da irin wannan ashar haka, ke da waye,? 



Jameel ne yai caraf ya karbi zancan, "Hajiya waya takeyi ne, ita da kawar ta ne" 



"Allah ya kyauta amma de kidena be kamata ace kina matsayin uwa kina irin wannan ba "



" kiyi hakuri Hajiya inshaallah bazaa kuma ba "




" yauwa ai gwanda, kuna lpy de ko "? 


" lpy kalau Hajiyata, me makon ki zaman ki inzo kika fito a yamman nan "



" Hmmm, Dan marayan zaki, kenan hankali na yana gunku ai shiyasa nakasa hakuri kazo"



Wani banzan kallo Labiba take watsawa jameel be ma san tana yi ba, miiewa Hajiyar tayi dan tafiya, suka tashi dan mata rakiya dubanta jameel yayi yace 



"Hajiya bari inzo inkaiki "



" Aa Dan marayan zaki yi zaman ka tare nake da yusif "


Fita yayi suka gaisa da yusif din, suka ja motar suka tafi ciki ya koma kafin ya karaso labiba ta mai da kofar dakin ta, ta rufe guri yasamu ya zauna ya dafe kansa jin ta murda kofar dakin ne yasa shi saurin dago da kansa. 




*Abdulmalik*



 Daki ya shigo yasami Ruhaima a Kan gado da sauri ya karasa gurin ta jikin sa yajata yashiga rararashinta tare da kwantar mata da hankali cikin daga murya inna ta kira shi da sauri suka fito agabanta Ruhaima ta tsuguna dubanta tayi tace 



"sannu hakima kinajina kikai kana naye shi a daki ko, to ai sai kitashi kije ki gyara min daki gani nadawo gidan da zama "


" to, inna kiyi hakuri dan Allah "



Haka rayuwa ta dinga tafiya a gidan Abdulmalik da Ruhaima inna kullum cikin fada da korafi yanzu haka zaune take a parlorn su tadora kafa daya Kan daya tana kallo kwadawa Ruhaima kira tayi ta fito da sauri ta zo duban ta tayi 






*Hafeez*



Duban fauza yake da shaawa saboda yadda ita dinmma take kallon sa a hankali ta furta   


"zoo road, zaka kaini 


"dan rausayar da kansa yayi yace 


"Angama mai kyau, ai tunda Allah ya hada ni dake dole in baki lokacina "



Suna tafe suna hira ahaka yakawo ta kafar gidan su sun dade a mota suna hira kafin suyi sallama ya tafi tare da musayan number 

Sanda ya koma gida Areefa tana zaune a parlor ya shigo hade rai tayi ta taso ta sha gabansa duban ta yayi da mamaki saboda bata taba yimasa haka ba cikin tsiwa tafara magana 






*NASEEBA GAWO*

               ✍🏻

[3/19, 10:29] ‪+234 814 620 5819‬: [5:09pm,2017




*@💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦




    *💦N I G*💦




 


   *ZAMAN AURE*

       💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦





*NA*



NASEEBA I UBA💐







*Alhmdulillah hakika Allah kaine abin godiya bisa niimar da kaiwa bayinka,inabawa makaranta littafin ZAMAN AURE hakuri bisa jina shiru  daakayi hakan yafaru ne sakamakon  batan da  wayata  tayi,wasu sunyimin magana shiru  ba reply ina maitabbatar muku cewa Naseeba ta canja layi amma da yardar Allah ana tare🤝saboda haka muje zuwa*




*ina taya kawata ALIYA SANI MAIHULA murnar haihuwar baby girl ubangiji Allah yaraya yaimata albarka AMEEN*








             *15*





~~~cikin daure fuska kamal yakarasa gurin da lubna take zaune dubansa tayi da mamaki shinfide a  fuskar ta ,ta gaida shi 



"yaya kamal barka da asuba,dama inason magana da kai ne "




"kintashi lpy,wace magana kenan lubna"?




"amm,dama game da  aunty sakna ne ,naga kamar akwai matsala tsakaninku ,shine....




kan takarasa yadakatar da ita ta hanyar dagamata hannu hade da wurga mata uwar harara yace




"ke,antaba ball dake,ko ni saanki ne  da har zaki tsaya yimin banzar magana ,to meye naki ,wlh tallahi kinji narantse ko inkika shiga abinda ba ruwanki sai nayi ball da ke ,stupid girl,tashi dalla kibani waje"



da sauri ta tashi ta nufi kitchen tana turo baki saboda ta tsani fada ,shikam kai tsaye dakin sakna ya nufa tana kwance tana bacci ,sai ji tayi a yaye bargon data rufa da shi da sauri ta farka tozali tayi da kamal sai huci yake,kamar wani zaki take gabanta ya yanke ya fadi.






*Jameel*




cikin shigar kananun kaya labiba ta fito daga daki tazo ta wuce ta gaban jameel sai taunar cingum take ,da sauri ya tashi yasha gabanta hade da marairaice fuska dauke kanta tayi cikin sassanyar muryarsa yafara magana




"Everlasting pls kiyi hakuri ki tausayawa jameel wlh fushinki kamar garwashin wuta  yake agurina ,pls help me"



harara ta wurga masa cikin izza da kasaita  ta dube shi tace 


"mekake so inmaka jameel nifa nagaji da magiyar ka wlh ,haba wai kai baka da zuciya ne ,kamata yayi ace kayi zuciya ka dena neman abinda bazaka samu ba haba"



shiru yayi ,can cikin kwarin gwaiwar da yasamu daga zuciyar sa yajata jikinsa ya hada bakinsa danata ya shiga tsotsa tureshi ta shiga  yi dada danne ta yayi cikin karfi yasamu ya biya bukatar sa tureshi tayi ta shiga rera kuka ta tashi ta nufi bedroom thade da rufo kofar kwanciya yayi yana maida numfashi  yanajiyo sautin kukanta hankalinsa ne yatashi dan yasan sai labiba tai masa abinda bazai taba yimasa dadiba

tashi yayi ya nufi dakinsa yai wanka ya kwanta tunaninta fal ransa ahaka ya kwana da sassafe ya nufi dakinta har lokacin a rufe yake a hankali ya shiga kiran sunanta tanajinsa taimasa bsnza kitchen ya nufa ya dora break fast 






*Abdulmalik*



Duban Ruhaima inna tayi cikin isa tace



"mekike aciki da kika shige ,uban waye zaimiki girkin ko kuma bakin cikin abinda zanci kikeyi "



"inna kiyi hakuri dama gyaran wardrobe nakeyi ne shiyasa,yanzu zan dora amma"



"Dallacan rufemin baki ,garin banzan surutunki kinsa anwuce inda nakeson kalla ,haba ni wlh narasa wacce irin mata Abdulmalik ya aura ,yarinya sai bakin hali ,zaki wuce ne ko kuwa"




Dasauri Ruhaima ta tashi ta nufi kitchen ta dora abinci cous cous ta dafa da farfesun kifi sai hadin salad ta gama ta kawowa inna nata dubanta tayi tace,



"Ai sai ki bude inga abinda kika dafa ko"



ba musu Ruhaima ta bude ,tana ganin cous cous ta ya tsine fuska ta dora da 


"meye wannan ,dazaki kawo min bakisan bana cin wannan abun ba da zaki wani dafo ki kawo min ,to bana ci sai kisan yadda zakiyi da shi"



shiru Ruhaima tayi can tanisa tace ,



"Amma inna baki fadamin bakyacin sa ba ,wlh da bazan dafa ba kuma ga shi gas din ya kare wlh da sai indafa miki wani abun"



"matsalar ki ce,wacce bata gaji arziki ba ,ni wlh banga me yaron nan yagani a jikinki ba"



gajiya Ruhaima tayi da fadan inna ta tashi ta nufi daki tasaki kuka ,Abdulmalik bedawo ba sai dab da magariba kai tsaye bangaran inna ya nufa tana ganinsa tafara share hawaye  hankalinsa ne yatashi ya shiga tambayar ta dada fashewa tayi da kuka nan tashiga shirya karya da gaskiya ransa ne ya baci cikin fushi ya nufi dakin Ruhaima da karfi yashiga kwada mata kira,







*Hafeez*




tsayawa kawai Hafeez yayi yana kallon Areefa yadda ta dage tana zuba masa rashin kunya 



"Hafeez wlh nagaji da wulakancin da kakemin ,nifa nafara zargin.....


kan takarasa ya katseta cikin karaji idonsa yakada yai ja borin kunya duk ya kamashi ya ce




"Areefa!,dakata kar kiyi gigin cewa kina zargina dan mutukar kika furta hakan ,wlh sai na dau mummunan mataki akanki ,kinfara daukar zugar kawaye ko ,to kiyi bazan hanaki ba amma kisani bazatai miki kyau ba"




"Hmm,Hafeez kenan ai banason dama taimin kyau kawai de kana borin kunya ne ,kuma wlh bazan yarda ba"



dagowa yayi ya zuba mata daradaran idanunsa masu mutukar kyau kan yayi magana wayarsa tashiga ruri hannu yasa a aljihunsa ya zaro wayar kan yadaga ta fizge wayar ta nufi daki da sari.





*NASEEBAGAWO*

         ✍🏻

[3/19, 10:29] ‪+234 814 620 5819‬: [6:19Am,2017]





*@💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦





   *ZAMAN AURE*

         💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦





*NA*


NASEEBA I UBA💐






*Subahhhanallahi wabihamdihi subahanallahi azim,tawakallatu ala hayyu lazi la yamutu,Alhmdulillah ,ala kul halin*






*sakon gaisuwa gareki ummy aisha dafatan kina lpy,Naseeba nata cigiyarki,ina gaidaki kyauta bada ko sisi ba*😃









            *16*






~~~cikin dakewa sakna ta dago da idonta ta dubi kamal,shiru tayi batare data ce masa kalaba,cikin daurewar fuska ya dubeta yace,



"wace magana kika fadawa lubna,da har zata tareni wai tanason magana dani"?



yafada yana zare mata idanu kamar wani ubanta,ahankali tadago da kanta ta zubawa fuskar sa ido tace,



"Banfahimceka ba kamal,kana tunanin zan zaunar da lubna infada mata sirrin *zaman auren mmu* ne,to bahaka nakeba,saboda haka kadena zargina akan abinda bani da masaniya akai,duk me yayi zafi,kawai dan naki biye maka wajen sabawa ubangijinmmu,bisa ga  kyautar da ba kowa yakewa ba,sai ga wanda yaso,asanda yaso,shine kullum burinka ka daga min hankali,wlh kamal ka ji tsoran Allah"



tana kaiwa nan taja bakinta tayi shiru shikuwa dada harzuka yayi yacigaba da surfa mata masifa ,cikin daga murya yadakatar daita tare da daga mata hannu ya dora da


 "malama yaisa haka ki adana kalaman bakinki dan karshenta zasu amfaneki nan gaba,amma bayanzuba,dan kunnuwa na basa,kaunar jinsu"



kuka ne ya kwacemata cikin fushi ta dubeshi tace



"wlh kamal kaji tsoran Allah ,kasani Allah yana iya jarabar ka ta inda yaso asanda yaso wace irin rayuwa ce wannan kakeyi inajiye maka  fadawa tarkon abokai domin *sandin aboki* babu halin da bazaka fada ba,wlh nasan su suke zuga ka"



wata razananniyar tsawa yadaka mata ya zubawa fuskar ta ido kana ya dora da 


"sannu,yar masana ko ince alhuda huda,sarkin sani ,meyashafeki dacsbokaina dahar zaki sako su cikin lafazin bakinki,to kibude kunanki da kyau kiji abinda zanfada miki,





*Jameel*



cikin kankanin lokaci jameel ya kammala hada break fast,juyewa yayi a kula yanufi dakin labiba yai saa ta bude tana tsaye jikin mudubi daga ita sai towel juyowa tayi ta kalleshi ta dauke ido,ajiye kayan hannunsa yayi, yakaraso kusa da ita ya tsaya ta bayanta ahankali ya kira sunan ta da kasalalliyar murya 



"Everlasting,pls kiyi hakuri da abinda naimiki jiya wlh nakasa control din kaina ne,nakai makura,baason raina hakan tafaru ba,but innshaallahu ,i will never do it again"




banza tayi masa tacigaba da shafa mai a fatar jikinta,tare da yaye towel din jikinta ,take tsigar jikin jameel ta tashi saboda yanayin da yaga labiba ,dama tarko ta dana masa ya kuma kamashi ,shiru yayi yacigaba da kallonta ,ahaka ta shirya tsaf,hannuta yakama ya nufi inda yaajiye kayan abinci yazuba mata ,tare da bata abaki ,cikin kissa da shagwaba,tadubeshi,tace



"jameel,wlh mutukar kanason= zaman lpy,a gidannan sai ka biyani wahalar da kabani jiya kuma

 bakai ba fita ko nan da can sai bayan kwana uku,haba ka dinga abu ba tausayi ba imani aciki"

ido ya tsuramata saboda yadda 

kalamanta suke mutukar sosa masa rai,amma ba shi da yadda zaiyi haka ya hakura ya  biye mata ,yarasa dalilin da yasa baya iya yiwa labiba musu,ahaka rayuwa tai tafiyarwa da jameel shi yake komai na aikin gida ,yau tun safe,yatashi da wankin kayan labiba ,dan taki,yarda adinga kaiwa gurin wanki,tana kwance  a parlor tanacin apple kawai sai ji tayi ,





*Abdulmalik*




sanda Abdulmalik ya shiga parlon Ruhaima tana toilet da sauri tafito tasameshi tsaye kallonsa tayi tace




"Malik,lafiyarka meyafaru haka,wlh ka daga min hankali "



cikin kankancewar ido ya dubeta ya dora da ,



"yazaki ki bawa inna abinci,kan wane dalili,hakan tafaru,Ruhaima inna fa uwa tace,bazanyarda ki wulakanta min ita ba,gsky "



shiru Ruhaima tayi tarasa ma mezatacewa Abulmalik ,inna kuwa tana labe tanajinsu ,kuka ne ya kwace mata cikin shasheka tace



"Haba Malik,tayaya zanhana inna abinci  ,wlh nadafa mata couse couse,tace bataci ,kuma gas ne yakare da sai nadafa mata wani abun,gaskiya nagaji wlh ya kakeso nayi "




jikinsa ne yai sanyi ganin ta tana kuka rarrashinta yashiga yi tare da kwantar mata da hankali ,hakan da inna tajine yadada bata mata rai aranta take tunanin Ruhaima ta asircemata da ,kwafa tayi tajuya zuwa dakinta ,haka rayuwa tai ta tafiya yau da dadi gobe ba dadi kamar kullum Abdulmalik ne zaune a parlorn inna misalin 9. 30 na dare  ta tsare shi da hira tun yana fahimtar ta har yagaza ganewa ,Ruhaima kuwa tana daki tana jiransa shuru be shigoba,sai wajen 11 sannan tabarshi ya koma parlornsu kai tsaye daki ya nufa yai wanka yashirya cikin kayan baccinsa masu kyau da taushi ya haye gadon jikinsa yajata ya shiga yana shakar kamshin turaranta ,dada shigewa tayi jikinsa ,tare da aikawa junansu sakonnni kamar daga sama sukaji muryar inna tana buga musu kofa shiru sukayi can yataso yana tambayar ta lpy,cikin rawar baki tace,





*Hafeez*





cikin zafin nama Hafeez ya riko Areefa tare da murde hannunta ya kwace wayarsa,nan tashiga surfa masa rashin kunya ,banza yaimata yai shigewar sa,dakinsa hade da sawa kofar key,gajiya tayi ta nufi dakinta wanka tayi ta haye gadonta tashiga neman layin Alhj Namidi kamar jira,yake ta,kirashi bygu biyu ya daga nan suka shiga hirar su kamar ba matar aure ba,


washegari Hafeez be fitoba ,sai wajen 8,lokacin tana zaune kan dining tana break fast,ko kallonsa batayiba ,zama yayi yaja cup yashiga hada tea yanayi yana danna wayar sa can tanisa tace


"zanje gida anjima,dan haka ina bukatar kudi ,saboda zanbiya saloon"


shiru yaimata kamar bejita ba ,sajen da yakewaye fuskar sa yashafa yace.


"ya da saurin sakkowa haka,kenan kin tabbatar min nike da iko da ke ,da kuma gidana ko,kwana biyu kina da damuwa Areefa,ko meye dalilin hakan?"



shiru taimasa ta hau karkada kafa tare da lumshe idanunta ,murmushi yayi sannan ya dora da 



"mutukar naisa dake ,to bainda zakije dan banbarki ba"



yana gama fadar haka ya kwshi wayoyinsa tare da ajiyemata kudin cefane ya fita,harara tabi bayansa da ita ,sai kuma ta mike tanufi daki.





_Lallai wannan shine zaman aure ko wanne da irin nasa_🤦🏻‍♀





*NASEEBA GAWO*✍🏻

[3/19, 10:29] ‪+234 814 620 5819‬: [6:19Am,2017]




*@💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦💦

  

      *💦N I G*💦






 *ZAMAN AURE*

      💦🤦🏻‍♀🙆🏻💦




*NA*


NASEEBA I UBA💐






*Alhumma anta amartana biduaika,wa wa,addana biijabattika,fakadi daaunaka kama amartana yazul jalalu walikiram,wahasbunallahu,waniimal wakil*👏🏻😰






*Hakika wannan shafiin nakine kawata ta kaina BILLY LADAN,marubuciyar prince sadeeq,Naseeba na mika sakon gaisuwa gareki,bazan boye miki ana mugun tare* 🤝🤣







              *17*






~~~shiru sakna tayi tana sauraron kalaman kamal masu kama da zubar garwashi,shikuwa cikin isa,da irin salon masifar sa yake fadin,



" sakeena,nafiskanci yadda wuyanki  yai kwari ko tunda har kinkai matsayin da  ina fada kina mayar min yayi kyau, lubna kike gani shiyasa kike dada narkewa bakya hassala komai a gidannan saboda kina ikirarin wai kina da ciki ko ,to yau ba sai gobe ba zata koma gida sai naga yadda zakiyi ,kuma ban dauke miki komai ba game da kula dani ,haka kazalika ni kamaludeen na dau alkkawarin raba ki da cikin jikinki dan banga dalilin haihuwarki yanzu ba ,dafatan kalaman bakina sun shiga kunnuwan ki ,masu kama da kashi"



da sauri ta dago da kanta ta zuba masa idanunta masu ambaliya da ruwan hawaye murya adashe tace



"kamal kayi min duk abinda kaga dama ,kuma ina nan akan bakata wlh tallahi baka isa karabani da kyautar da Allah yaimin ba ,dangane da tafiyar lubna kuwa ,ai ba wani abun bane Allah zai taimake ni wajen kula da aiyukana ni kullum mai nema maka shiriya ce gurin Allah ,kuma ina rokon Allah ya darsa maka tsoransa "



tsawa yadaka mata hade da nuna ta da dan yatsa ,yana huci yabar dakin cikin daga murya ya shiga kiran lubna,da sauri ta fito,daga kitchen din


"yaya kamal gani"



"oya,kije ki hado kayanki kizo na saukeki a gida ,zamuyi tafiya ne"


dagowa tayi ta kalleshi ,dauke kansa yayi batare da ya kuma kallon ta ba ,tashi tayi ta nufi  dakin sakna a kwance ta tarar da ita ,gaban gadon ta karasa,ta zauna ahankali ta kira sunanta,



"Aunty sakna,yaya yace zakuyi tafiya yau ,saboda haka inshirya ya kaini gida amma aunty,sai nake ganin kamar yaya,akwai abinda yake nufi"



murmushin karfin hali sakna tayi ta dubi lubna kan tayi magana sai ganin  ,shigowar sa   sukayi  shiru sukayi dada hade rai yayi 





*jameel*



~~~cikinta ne ya murde hade da tashin zuciya ,jameel na toilet sai jin zubar amai yayi ,da sauri yabar aikin da yake ya nufo dakin tozali yayi da labiba tana ta amai ,hankalinsa ne yatashi nan ya rungumeta ,har sai da ta gama tsaf sannan ya taimaka mata tayi wanka parlorn yadawo ya gyara wajen tsaf ,dakin ya koma  ya tarar da ita tafito tana kwance a gado,daga ita sai towel ,kan gadon ya karasa hade da janta jikinsa  yace



"sannu Everlasting,meke damunki?me kikaci yasa ki amai"



shiru tayi tadada lafewa a jikinsa jiyayi shaawar ta na fisgar shi amma bazai sami biyan  bukata ba dole ya hadiye shaawarsa can ta nisa tace



"jameel,kadafa min danwake kaji ,shinakeson ci "


da sauri ya dubeta ,"Everlasting dan wake kuma ? ai  bansan yadda akeyi ba ,yanxu yazaai keenan ?



"haba jameel,tambayata ma kake  yazaai,kafini  sanin yadda zaai ai ,nide abinda nasani kawai shine, danwake  zanci"


"ok yi hakuri mrs jameel bari asamo miki danwake aduk inda yake"



cikin rawar jiki ya janyeta daga jikinsa ya dora da , 


"karki damu,bari inje ,sai dai bankarasa wankin ba"


banza taimasa hade da gyara kwanciyar ta ta kwanta,shiryawa yayi tsaf,yakarasa gabanta yahada fuskar ta da tasa ya sakar mata kiss ,sannan ya fita,kai tsaye gidansu ya wuce ,gurin hajiyarsa tana ganinsa tasaki faraa nan ya zube ya gaidata taamsa da walwala,dubansa tayi tsaf take tagano dan nata kamar bashi da nutsuwa a hankali ta kira sunan sa ,da sanyin murya yaamsa nan ta dora da ,





*Abdulmalik*




~~~cikin hanzari Abdulmalik yabude kofar dakinsu inna kuwa sai raba idanu take da sauri ya tambayeta ,



"inna lafiya meyafaru a tsohon daren nan"?



"kai dannan aljanune adakina kaji yadda suke hira ,kai akwai lauje cikin nadi ,nafiskanci de kawai baason na zauna a gidan dana ne kawai"



shiru yayi can ya numfasa yace ,



"haba,inna wane irin aljanu kuma,gsky gidannan ba komai,muje inrakaki dakin mugani "


da sauri tace,"Aa,basai munje ba tunda zuwan bashi da amfani bari intafi inkwanta da safe mayi maganar"


kan yaankare ta tafi ,Ruhaima tana bakin kofa tana jinsu ,mamaki lamarin inna yabata ciki ta koma tai kwanciyar ta ,bashi da zabi ,shima binta yayi suka kwanta ,


Dasafe sunje gaida ta ta dubi Ruhaima tace 



"to,uwar kinibibi daga yau nasa doka agidannan kai Abdulmalik inzaka bada kudin cefane ,to ni zaka dinga kawowa inyaso tazo ta karba a guna "



da sauri suka dago da kansu suka kalleta Abdulmalik ne yai karfin halin cewa,







*Hafeez*






~~~cikin kankanin lokaci Areefa tashirya tsaf,ta fito gidan ta rufe tai tafiyarta kai tsaye gidansu kawar ta tanufa ,nan sukai ta hira ,wayar tace ta hau ruri tana dubawa taga sunan Alhj namadi dariya tasaki suka tafa da kawartata dada gyara fuskar ta tayi suka fita a cikin mota suka sameshi  



hafeez kuwa yana fita kai tsaye gidansu fauza ya wuce ,yana isa,yakirata awaya tafito,daukar ta yayi a mota suka fita,kai tsaye,wani babban hotel suka nufa ,isar su keda wuya ,suka ci karo da ,






*NASEEBA GAWO*✍🏻

[3/19, 10:29] ‪+234 814 620 5819‬: [5:57Am,2017]





*@💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦


      💦N I G💦





   *ZAMAN AURE*

        💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦




*NA*



NASEEBA I UBA💐






*Alhmdulillahi lazi ahayana baada ma amatana wailehir nushur,Rabbi yasir wala taasir allahumma yasir alaina*👏🏻






*Wannan shafin🍆 nakine kawata JIDDATULLAH TIJJANI ,mai littafin ALMAJIRA,ina godiya bisa kwarin gwaiwar da nasamu daga gareki nagode sosai,hakan shi ya tabbatarwa da Naseeba ana tare ,dan haka kiyi komai da wanga page ba komai domin kuwa nakine ke kadai*🍆🤣🤣






💦

 *Tsokaci game da littafin ZAMAN AURE, anya kuwa abinda naseeba ke rubutawa yana faruwa a gidajan auranmmu ko de shaci fadi ne  kawai irin namu na  marubuta ?fadi raayinki game da hakan*🙅🏻








                *18*





~~~cikin daurewar fuska kamal ya ke dubansu sunkuyar da kai lubna tayi sakna kuwa kallon mamaki take masa cikin ranta take fadin



_"wai dama haka rayuwar aure take ,miji yacanja kamar bashine wanda ada kafin auran ku baya son duk wani abinda zai bata miki rai ,kullum burinsa ya faranta miki rai ba,amma gashi yau anwayi gari yazama kamar bakin kumurci ,wane irin ZAMAN AURE ,kenan sukeyi_


*Nasseeba kuwa cewa tayi da sakna,haka rayuwar auran take ,gaba dayanta hakuri ce domin kuwa ankirata da ibada,kenan ibada sai anyi hakuri*





maganarsa da yakewa lubna ne yadawo daita daga zancan zucin datake ,cikin dakewa yake fadin



"malama,tashi kishirya,minti 10,kawai nabaki zaki zo ki wani zauna,uban me kike cewa ,wlh lubna ki shiga ki maida hankalinki,kinji de  nafada miki"



yana gama fada ya koma parlor ya zauna ,lubna kam baki ta turo tana kunkuni ahaka ta shiga toilet ta yi wanka,cikin kankanin  lokaci tagama shirinta tsaf ,sakna na kwance tana kallonta kusa da ita tadawo ta zauna ahankali takira sunanta



"Aunty sakeena zantafi,nasan bainda zakuje ,kuma nafiskanci akwai matsala a *zaman auranku* saboda haka wlh sai nafadawa Hajiya da na koma kiyi hakuri"



saurin katse ta sakna tayi ta cikin raunin murya tace



"Haba lubna ,meakayi da har zakije kifadawa hajiya,to gaskiya banyardaba,kuma maganar tafiya da zamuyi tunda yafadi hakan,may be tafiyar zamuyi ,dan haka ni ban aikeki ba kuma kar ki soma "



dariya kawai lubna tayi,ta dau jakar kayanta ta mike dan tafiya,yunkurawa sakna tayi ta tashi tahadomata wasu materials sababbi da kayan kwalliya hade da kudi tabata ,godiya taimata ta nufi parlor ,yana zaune ya dora kafa daya kan daya ,yana ganin ta fito yaja dogon tsaki ya mike ,yafita binsa tayi a cikin mota tasameshi ,baya ta bude ta zauna, afusace ya juyo ya kalleta yace



"ke waye driver direbanki dazaki wani kame abaya ,dalla dawo gaba "



dariya ce taso kubcemata tayi kokari ta gumtseta  gaban tadawo tazauna da sauri ya figi motar wani gigitaccan horn yashiga yi da gudu mai gadin yazo ya bude masa gate din ya fita,cikin kankanin lokaci suka isa gidan nasu ,begama yin parking ba lubna tafito daga motar kai tsaye dakin Hajiyar su tanufa tana zaune akan sallaya sai ganin lubna tayi ta zube ajikinta nan ta shiga tambayarta




"Auta wane irin sammako ne wannan kamar wata korarriya,ina sakeena ,da kamal din"?




baki ta turo gaba hade da narkewa ajikinta nan ta kwashe komai ta fada mata game da *zaman auran* kamal da sakna ranta ne yai masifar baci ,ana haka sai gashi ya shigo da kayan lubna da bata tsaya ta dauka ba wani kallo Hajiyar ta watsa masa take jikinsa yai sanyi jikinsa ne yabashi lubna tafadawa Hajiya tabbas yasan bazasu kwashe ta dadi ba,







*jameel*




~~"Dan marayan zaki anyawa kuwa babu abinda ke damun zuciyar ka nifa tunda ka auri yarinyar nan gaba daya kasanja ,meke faruwa da *zaman auranku*"?



murmushin karfin halin yayi ,dan bazai iya furta,mata komai ba yasha zuwa takanas dan yafada mata amma dayazo gabanta sai yakasa hoton labiba ne kawai a zuciyarsa ahankali ya dago da kansa yace




"Hajiyata,kar ki damu danki bashi da wata damuwa ,yanzumma dai labiba ce bata da lpy shine tace danwake zataci ,zuwa nayi kiyi mata kinji Hajiyata"



murmushi tayi dan ta fuskanci inda zancan nasa ya dosa tashi tayi ta shiga kitchen cikin kankanin lokaci sai gata da danwake a kula mai kyau,ta kawo masa yana kwance idonsa alumshe kamar me bacci ahankali takira sunan sa,



"Danmaraya,tashi ka kaimata kar tai ta jira,har yafitar mata a rai"



"to,Hajiyata sannu angode ,Allah yaja mun da ranki"



dariya tayi taamsa da "Ameen"



yatashi ya tafi,sanda ya karasa gidan tana parlor a zaune ,cikin rawar jiki yakarasa gabanta yaajiye mata kular agabanta kallonsa tayi awani yatsine tace



"jameel,sai yanzu ,to kadauke abinka banaci ,tun yaushe kafita"



cikin sauri yadago ya dubeta yarasa ma mezaice mata kawai sai ya ,




*Abdulmalik*



~~shiru inna tayi tana sauraran abinda Abdulmaliki zaice 



"inna dan Allah kiyi hakuri,da abinda zance ,ni sai nake ganin kamar Ruhaima ita yakamata ana bawa kudin cefane ,amatsayinta na,mai girki......




batabari ya gama fada ba ta daka masa wata uwar tsawa tadaka masa tadora da 



"yayi kyau,Abdulmalik,

yau ka tabbatar min da cewa matar ka gaba take da mahaifiyarka to nagode da irin wannan sakayyar to amma kasani ,kan takarasa tasaki kuka


hankalinsu ne yatashi Ruhaima ce ta dubi Abdulmalik tace 



"Malik,ayi yadda inna keso ai ba wani abu duk daya ne ,dan Allah inna kiyi hakuri "



"Dallacan rufemin baki munafuka ,juya kawai baki da aiki sai lashewa dana kudi ki haihu ,kinki ki haihu saboda tsabar mugunta "



shiru sukayi karshe suka bata hakuri hade da bata kudin cefanan yafita daki Ruhaima ta koma tasaki kuka mai tsuma rai ,



da yamma tana kitchen ta kusa kammala girki kawai sai ga inna taja ta tsaya a kofar kitchen din ,cikin daga murya ta kira sunanta 



"ke Ruhaima uban me kike dafawa ,ko san ranki kike dafawa "



"inna sannu da fitowa,amm dama tuwan shinkafa nake miki "




"to,sauke bashi zanci ba,alkubus nakeso"



shiru Ruhaima tayi tarasa ma mezatace can ta sauke girkin ta koma daki ,binta innar tayi har dakin ,




*Hafeez*




~~cikin kissa Areefa ta kalli Alhj namadi shi dinmma ita yake bi da asirtaccan kallonsa irin na yan duniya hade da kiran sunanta 




"my love,daga nan sai ina muka nufa,?




dariya tayi hade da kashe masa ido sanan tace,


"Duk inda ranka yaimaka zabi,domin kuwa zabinka shine nawa"


jinjina kai yayi hade da lakacemata hanci yaja motar suka tafi kai tsaye guest house dinsa suka wuce,nan suka hole abinsu ,dazata tafi yadakko kudi masu tarin yawa yabata ta bude kofar gidanta ta shige




Abdulmalik kuwa karo sukai da tsohuwar budurwar sa mai suna  Anisa,murmushi yasakar mata ya karasa gurinta nan suka gaisa tambayarta yashiga yi 



"Anisa ,kwana da yawa kinya dani "



kallonsa tayi ta lumshe ido,take yagane nufinta


Fauza kam tana tsaye tana kallonsa ,yagama da Anisa,ya karasa inda take wani banzan kallo tasakar masa tai tafiyarta .








*NASEEBA GAWO*✍🏻

[3/19, 10:30] ‪+234 814 620 5819‬: [6:00Am,2017]





*@💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦💦




    💦N I G💦






  *ZAMAN AURE*

     💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦




*NA*



NASEEBA I UBA💐





*Hasbunnallahu waniimal wakil laila hailla anta subahanaka inni kunti minal zalimin*😰👏🏻






*Innalillahi wainna ilehir rajuun allahumma ajirni fi musibati waakilfini khairan minha ,ina taya daukacin dangin ALHJ UBA GAWO alhini bisa rashi da mukayi na SHAMSUDDEN Y UBA, muna rokon Allah yajikansa da rahama yasa ya huta ,hakika misalta  halin da muka shiga abin zaizama kamar bata yawun baki da wannan damar nake rokon Allah da ya bawa iyalan Alhj ISMAIL UBA GAWO hakurin ibtilain da yaafka mana na rashin yaron nan ,haka kazalika ina rokon Allah da yaji kan SHAMSUDEEN B  UBA Allah yaimasa rahama yasa ya huta Allah karaya SHAMSUDEEN U UBA kabashi halin yaya shamsun da muka rasa AMEEN*😭👏🏻









              *19*






~~~Ahankali kamal ya karaso yasami gefan mahaifiyarsa ya zauna lubna ce ta dago da kanta ta kalleshi harara ya auna mata da sauri ta dauke idonta cikin ladabi ya gaida mahaifiyar tasu taamsa ba yabo ba fallasa can tadubeshi da kulawa tace



"kamaludeen ,meke faruwa a gidan naka,gashi kuma naga kakawo auta da sassafe lpy de ko?



kansa yadada dukarwa kasa ya zubawa kafet ido,kamar maison samo amsa a nan,can yadago suka hada ido da mahaifiyar tasa ahankali yace



"Hajiya,dama sakna ce bata da lpy ga shi inason zuwa kwatano,shine nakeson na maidata gida,saboda yanayin jikin nata,amma bawata matsala da muke da ita"



ido tazubawa fuskar dannata dan son gano gskyr zancan nasa lubna kwa takafe shi da ido cikin saa ya dago ya kalleta da ido ya gargadeta hajiya ce takatse shi ta hanyar kiran sunansa


"kamaludeen,ni kullum bazan gaji da fada maka cewar kaji tsoran Allah ba kasani akwai mutuwa akwai hisabi,mutukar ka zalinci yar mutane tofa ,Allah baze barka ba,to ma me zaihana ka kawo min ita nan har kadawo"



shiru yayi dan yasan dole hajiya zata iya  cewa haka cikin kwantar da murya yace



"Hajiya ai nariga nafadawa mamanta zankawo ta ,da sai nakawo miki ita "



"To shikenan badamuwa ai duk daya ne ,Allah yabata lpy "



"Ameen Hajiyarmu ,Abba fa yanan ne ?



"eh yana nan dazu de yafita taaziya amma yadawo,kashiga ka gaida Mama "



"To,ke lubna zo nan"



fita yayi tabi bayansa,sai da suka bar dakin Hajiyar sannan ya tsaya ya juyo ya zuba mata ido,hade da daure fuska yace



"ke ,wlh mutukar kikafadawa Hajiya  zancan gidana wlh sai jikinki yafada miki ,kinji de nafada miki "



turo baki tayi gaba tana kunkuni kasa kasa,ganin yayo kanta ne yasa ta amsawa da 


"Thom,naji"



tafiyarsa yayi ya nufi saman Abbansu,suka gaisa bejima ba ya sakko,dakin mama ya nufa ,nan yasameta zaune a parlonta sai suhaif dake kwance da waya a hannunsa yai sallama ya shiga guri yasamu ya  gaisheta taamsa da sakin fuska ,suhaif ne yatasu ya gaida yayan nasa 




"Yaya kamal barka da asuba,ya auntyna"



"yauwasuhaif ,lpy kalau,yana ganka a kwance ba shirin school,lpy de ko?



 dan karamin tsaki yayi ,sannan yashafi sumar kansa kana ya dora da 


"wlh yaya yau sai ahankali, wani banzan abokina ne yabani ciwon kai da safen nan,shiyasa nakasa fita"



dariya suka sa kasancewar suhaif mutum mai barkwanci ,sallama yaimusu yatafi kai tsaye office ya nufa ,


sakna kuwa tun bayan futarsu ta koma ta kwanta kuka tasaki mai tsuma rai tare da shafa cikinta tana kwance sai ji tayi,






*jameel*




~~kai jameel ya dafe,saboda yadda labiba take yawan bashi ciwon kai,ahankali ya jata jikinsa yace



"Everlasting,to mekikeson ci yanzu,wai ma meke damunki"?




shiru tayi tare da lumshe ido,ahamkali takira sunan sa 



"jameel,tashi ka kaini asibiti kawai ni kam bansan meke damuna ba"




cikin sauri yadaga ta daki yanufa ya dakko mata mayafi ya yafa mata hannuta ya rike suka karasa gurin motar dakansa ya bude mata ta shiga ya mayar ya rufe,da sauri ya ja motar suka nufi Amir hospital basu wani jimaba suka shiga ganin likitan yana zaune akujera sanye yake da farin glass a fuskar sa,sai rubuce rubucansa yake can yadago yabawa jameel hannu suka gaisa,take yafara duba labiba,tare da yimata tambayoyi ,gwajin farko yagano tana dauke da ciki,na wata biyu,murna gurin jameel baamagana labiba kuwa duf tayi ranta yaimasifar baci ,tashi tayi ta fita binta jameel yayi da ido,take gabansa ya fadi,dan yasan yanacikin wata masifar,sallama yayiwa likitan ya fita tana cikin mota ,nan ya shiga,yasameta,shiru yayimata can yadago ya dubeta suka hada ido,harara tasakar masa take ya dauke idonsa ahaka yaja motar suka bar harabar asibitin cikin bacin rai tace




"ka kaini gidanmmu kawai"



"Angama madam,amma ....



"Dan Allah kaimin shiru jameel,kabarni inji da damuwar da kabani "


shiru yayi,har suka karasa gidan su ,ya sauketa , shiru yayi can ta dago ta dubeshi tace



"kawuce gida ,sai zuwa dare kazo ka daukeni"



"To,madam,amma ina neman alfarma daya"



"kaadana ta inmun koma gida naji,baka da abinda zaka ce dani yanzu 



fita tayi ta nufi ciki,yadade yana kallon kofar gidan nasu sannan yaja motar kai tsaye office ya nufa yana zuwa sukai kacibus da manajan wani kallo yabishi dashi ya gyada kansa dakatar da shi yayi anan gurin batare da yabarshi ya nufi office din nasa ba,







*Abdulmalik*




~~Inna na tsaye a kofar dakin Ruhaima Abdulmalik yai sallama ya shigo da ledoji a hannunsa yozali yayi da inna a kofar dakin su,da sauri ya nufota,yace





"inna sannu,da gida dafatan de lpy?



cikin kwabe fuska tace 


"To,lafiyar kenan,ni da matar ka ne,yanzu ni banisa infada mata gsky ba,sai ta tsiri yimin rashin kunya,ko ba uwar mijin ta ba ce ni ,ai a haife na haifeta,ko ma ince na haifi uwarta ko,amma ba komai nagode "




shiru yayi sai kuma yace



"inna,dan Allah kiyi hakuri inshaallahu zanmata magana,banga matar da zan aura ba ta wulakanta min uwa ba"



leda daya ya mika mata da sauri tasa hannu ta karba ,ta nufi dakinta ,ciki ya nufa  tana zaune,tahada kai da gwiwa tanata aikin kuka wayar ta a hannunta da dukkan alamu kira take,da sauri ya karasa gabanta wayar hannunta yafara karba yanadubawa yaga sunan ummata dubanta yayi ransa a mutukar bace yace





"Haba my dear ,yanzu akan abinda betaka kara ya karya ba zaki kira umma kifadamata ,dan Allah kiyi hakuri inshaallahu komai zaizama normal"




"malik,nagaji,inna batasona nagaji kabarni intafi ka auro wacce inna zata so,ko kaima ka zauna lpy"



katseta yayi tahanyar dora danyatsansa a lebanta zaiyi magana kenan sai jin muryar inna yayi tana kwalla masa kira shiru sukayi sai can kuma ya ,






*Hafeez*




Areefa tana shiga gidan ta mayar da jakar ta da takalmanta daki kamar bata fita ba kudinta tafito dasu tana kirgawa 50k murmushi tasaki komawa tayi tai kwanciyar ta a kujera take bacci barawo yai gaba da ita,



Hafeez kuwa da sauri yabi bayan fauza yana kwallamata kira banza taimasa ahaka yasha gabanta yafara bata hakuri dakatar da shi tayi tace 




"Hmmm,haba,

Hafeez,yaushe akai daran bare gari ya waye?




"ban fahimci inda kalamanki suka sa gaba ba ,my queen"



"eh zakaiya cewa haka tunda badaga jinsin hausawa ka fito ba"



tanagama fadar haka taitafiyarta wani mai mota ta tsayar kawai tashiga ,bashi da wani zabi banda yashiga tasa motar ya nufi gidansa ,cikin kankanin lokaci yakarasa gidan yanashiga yai tozali da Areefa,tana kwance a kujera kan table kuwa kudi yagani tsayawa yayi yazuba musu ido can kuma yadada karasawa yasa hannu ya,








*NASEEBA GAWO*✍🏻

[3/19, 10:30] ‪+234 814 620 5819‬: [5:59Am,2017]




*@💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦💦



       *💦N I G*💦



 *ZAMAN AURE*

      💦🤦🏻‍♂🤦🏻‍♀💦




*NA*


NASEEBA I UBA💐





*ya hayyu ya kayyumu birahamatika astagisu aslihili shaani kullahu la ila hailla anta*👏🏻




💦

*Nasadaukar ga wannan shafin ga SHAMSUDEEN YUSIF UBA GAWO ya Allah kajikan sa kai masa rahama kabamu hakurin rashinsa dan Allah duk wanda yai tozali da wannan page din ya taimaka mana da addua*😭👏🏻








                  *20*






~~~Bugun kofar da ake yi ne yadakatar da sakna daga kukan da take ,tashi tayi da kyar ta nufi toilet ta wanke fuskar ta ,ta fito parlor tadanyi shiru nan aka cigaba da bugun da ake,da muryar ta mai sannyi ta tambayi waye ,shiru akai hannu tasa ta bude kofar tana budewa ta yi tozalli da kanwar ta Fiddausi murmushi ta sakar mata tare da rungume juna ,nan suka sami guri sukka zauna,cikin kulawa fiddausi ta dubi yayar tata tace



"Yaya sakna,meke damunki ,kinganki kuwa?"


murmushi tayi tare da shafar cikinta kana ta dora fuskar ta akan ta yar uwar tata tace,




"Ai de kya bari mugaisa ko?da farko ya su umma da malam ina usman?



"Duk suna lpy,to meyasameki dan Allah?



"Fiddausi kenan,bani da lpy ba ina kwance ,amma nasami sauki"



"Ayya sannu,kuma ko kiyi waya kifada ,kekam zurfin cikin ki ya isa"



Nan de suka yini ita taimata komai dangane da aikin gida ko dawasa sakna bata fadawa fiddausi abinda ke faruwa da ita ba dangane da *zaman auransu* da kamal,da yamma ta shirya ta tafi,tun bayan tafiyar ta ta dau kuraani tashiga karantawa nan tadada samun nutsuwa,


kamal bedawo ba sai misalin12,na dare kamar kullum abige ya shigo tana parlor bacci ya dan debeta sai jin gigitacan,




*jameel*




jameel na tsaye a gurin ,manajan ya fito,dawata farar takarda a hannunsa,mika masa yayi ,hannunsa na rawa ya karba yana dubawa yaga,takardar sallama ce daga aiki hankalinsa ne yai masifar tashi,hakuri yashiga bashi ko sauraran sa beyiba,yai tafiyarsa,bashi da zabi,haka ya fita jikinsa asabule ya shiga mota ya nufi gurin hajiyarsa



labiba,kam tana shiga gida tasami mahaifiyar ta a parlor ,jikinta ta fada tasaki kuka nan hankalin uwar ya tashi,tashiga tambayarta ,



"ke labiba,lafiyar ki ,meyadameki ,da har zai saki kuka haka,kinsanni sarai banyarda yata tayi kuka a gidan miji ba,meyayi miki jameel din"?



dagowa tayi ta kalli mahaifiyar tata tace



"momy daga asibiti muke,wai ciki ne dani,ni wlh banaso ,zubarwa zanyi"


ido momy tazaro waje cikin kwantar da murya ta ce 



"Bazaa zubar ba,labiba,ai wata damacce tasamu ,kinsan dalili?


kai ta girgiza alamar aa,






*Abdulmalik*



Tashi yayi ya fita,a bakin kofa ya hadu da inna dariya tayi ,sannan tadora da 



"yauwa yaron kirki taho muje kaci abinci kaji"


shiru yayi shi yarasa yazaiyi da inna ,ba yadda zaiyi binta yayi zuwa dakin nata ta zuba masa abincin yafara ci amma hankalinsa yana gurin matar sa,hira tashiga yimasa tun yana fahimta har ya gaza fahimtar ta ,kiran sallar ishaai ne yabashi damar fita ,kai tsaye dakin Ruhaima ya nufa tana zaune akan sallaya agabanta ya tsuguna tare da cire hijjab din jikinta  ,ahankali ya jata jikinsa tare da zuge zip din rigarta hannunta tasa tarike nasa hannun ta zubawa fuskar sa ido,cikin kasalalliyar murya yace,



"my dear ya zaki dakatar da hannaye na daga taba abinda yake mallakin ki,why?



shiru tayi ,sai hawaye kamar anbude fanfo,ahankali ta dago da idanunta ta dube shi tace,



"Malik,kayi hakuri,da furucin da bakina zaiyi baason raina zanyi ba,sai dan bani da wani zabi ,agaskiya ina mai bakin cikin sanar da kunnuwanka ,


sai kuma tayi shiru tada sakin kuka mai tsuma rai,shikuwa hankalinsa ne yadada tashi,cikin shashshekar kuka ta cigaba da fadin,





*Hafeez*




Areefa,tana ta bacci Hafeez ya dauke kudin da ta samo a gurin Alhj Namadi,daki yanufa dasu ya bude side bed yazuba wanka yadhiga yayi ,ya dawo parlorn yasami guri ya zauna ya zaro wayarsa ya fara chart da yanmatansa can,Areefa ta bude idonta tozali tayi da shi yana karkada fkafa,mai da dubanta tayi ga,kudin ta ,sai gani tayi babu su,da sauri ta dubeshi ta gefan ido yake kallonta,tasowa tayi ta tsaya a gabansa tace



"Hafeez,kamar da kudi a kan center table dinnan ko?



"kina tambaya ta ne,ko me? to,intambaya kike,ni bangansuba"



wani banzan kallo ta watsa masa,kana tadora da ,


"Hmm,baka gansuba,to ai bangansu ba,wata kalma ce da makafi suke amfani da ita,ke kuwa,iya sani na da kai baka jerin makafi "


cikin daga murya da tsawa ya dakatar da ita ,



"Areefa ni kike kalla kike fadawa haka,saboda kin raina ni ,ko me"


wayarta ce ta hau ruri atare suka nufi inda wayar take tare da rigen dauka,








*NASEEBA  GAWO*✍🏻

[3/19, 10:30] ‪+234 814 620 5819‬: [8:45PM,2017]




*@💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦



  *💦N I G*💦





 *ZAMAN AURE*

     💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦 





*NA*


NASEEBA I UBA💐






*Astagafirilla waatubu ilehe,Allahumma afini fi badani Allahymma afini fi sami,Allahumma afini fi basari,Allahumna afini fi sam,i*👏🏻




*Dedicated 2 my friend, Rukayya Ashir imam thanx 4 ur support Naseeba said we are 2gether*🤝🤝






           

               *21*







~~Cikin tsananin firgici sakna ta mike saboda bugun daakewa kofar parlorn nasu,da sauri ta karasa bakin kofar ta shiga tambayar waye?



murya a dakile kamal ya ce,


"Yaazancin ,waye,wace irin tambaya kenan?,malama bude min kofa"



da sauri tasa hannu ta murda key din kofar jin muryar kamal,tana budewa ya shigo,ransa a mutukar bace,sai dai baa bige yakeba amma fa inbanda tsamin giya baabinda yake,rabewa tayi tabashi hanya ya shige ,yasami guri ya zauna ,tare da zuba mata lumsassun idanunsa,da sauri takarasa kusa da shi da zummar zama ,sauri tayi tatashi saboda yadda zuciyar ta take barazanar faso kirjinta ta fito,dubanta ya kuma yi ,akaro na biyu,ahankali ya furta ,



"ki hada min ruwan wanka"


"To"


kawai taiya cewa ta nufi toilet ruwa ta hada masa kamar yadda ya bukata ,tadawo ta sameshi idonsa rufe kamar me bacci tace



"Honey bee,nahada maka ruwan"



"oya ,muje ki taimakamin dan bazan iya yi da kaina ba"



shiru tayi kamar bazata amsa ba,ba yadda taiya,haka tabi bayansa,ta taimaka masa ya kwabe kayansa,toilet din suka nufa,suna shiga yajata jikinsa nan yashiga kissing dinta ido ta runtse,ahankali yashiga zuge zip,din rigarta wata yar kara yasaki ganin yadda kirjinta yadada cika take ya gigice,yashiga sarrafasu cikin kwaraiwa ,takasa tabuka komai sai da yagaji dan kasa ,sannan ya kyaleta sukai wanka suka fito,jallabiya ta dakko masa fara kal itama tadakko wata yaloluwar farar riga da adon pink tasa,taimata,kyau ga cikinta da yadan daga gwanin shaawa ,duk inda tayi sai ya kalleta,cikin salon iya maganarsa yakira sunanta,



"my dear"


da sauri ta juyo ta kalleshi da mamaki kunshe a fuskar ta ,dan ta manta rabon da yakirata da wannan sunan,



murmushi yasakarmata tare da kashemata ido,abinci tazuba masa tare da tura 

masa gabansa,dauke kansa yayi tare da hade rai take gabanta ya yanke yafadi.





*Jameel*



~~cikin sauraran mahaifiyar tata labiba ta zuba mata ido,ahankali momy take magana kamar me rada tace,



"labiba haihuwarki da jameel ita zata baki damar mallakar abinda ya ke dashi,ke dashi ma kansa ,dan haka kar ki damu dan kinsami ciki kinji diyar momy"



dariya labiba tayi ,tare da rungume mahaifiyar tata, nan sukacigaba da tattaunawa akan jameel bawan Allah



jameel yana isa gun hajiyar sa,ya zube tare da zubar da hawaye,hankalinta ne yatashi tashiga tambayarsa 



"subahanallah Dan marayan zaki lpy,meke faruwa ina labiba?



shiru yayi karshe yasamata kuka sai da yayi mai isarsa sannan ya dago ya dubeta yace,



"Hajiya nashiga uku,ankoreni daga aiki,yazanyi"



salati tasaki tare da tafa hannaye cikin kidima tace,



"jameelu,mekayi musu haka?"



"Baabinda nayi hajiya ,banmusu komaiba,yazanyi da labiba"?



shiru tayi can tanisa tare da sauke ajiyar zuciya tace



"Bkomai Danmarayan zaki akwai Allah,yanzu meyakamata kayi ?



shiru yayi yatafi nazari can yadago yadubi mahaifiyar tasa yazuba mata ido da yakada yai jazur yace,


"Hajiya kasuwa zankoma kawai ,ki tayani da addua akwai abinda ke damuna ,narasa gane kaina"



"kamar me kenan fadamin inji"


shiru yayi can yadago yadubeta,






*Abdulmalik*



~~malik,ayau basai gobe ba inason nakoma gidanmmu ina nufin gaban mahaifana ,nagaji ,wlh nagaji"



kuka ne ya kwacemata ,jikinsa yajata shima kukan yasamata,ganinsa yana kukanne yadada sata cikin tashin hankali,

dada rungumeshi tayi ahankali tace



"kayi hakuri malik,nafasa ina tare da kai inshaallh "


cikin sauri yadagota suka hada ido,murmushi yasakar mata nan yasa hannu yashiga share mata hawayen fuskar ta,tashi sukai dan doro alwala,kamar saukar aradu sai jin muryar inna sukayi tana kwalla Ruhaima kira,ja sukayi suka tsaya,bata fasa ba takuma kwalla mata da sauri ta zare hannunta daga na Abdulmalik,tayi waje


tana fita ta dubeta a wulakance tace



"sannu,uwar san mijin tsiya ,kede da jaraba kike,wlh ku kule adaki ko uban me kikemasa oho,ki wuce muje ki.....



kan takarasa Ruhaima ta katseta da fadin,


"inna salla zanyi"



wani mugun kallo ta watsa mata tare da fadin,



"a,lalle kinisa kinci kin ta da kai,sannu hanshakiya kidubi tsabar idona ki katseni ina magana ko ,to yayi kyau,to amma kibude kunanki da kyau kiji abinda zanfada miki,






*Hafeez*



~~cikin saa Areefa ta riga Hafeez daukar wayar ta takashe,tsayawa yayi yana kallonta cikin masifa yace,



"wlh Areefa kishiga hankalinki dani ,dan naga take taken ki,akwai rigar da kika dauka kika sa wacce bata dace da keba"



dariya tasaki hade da fari da ido,tace



"Hmm,Hafeez kenan ,to ai kan Areefa tasa riga kai ka fara sawa nagani nima naara nasa,kaga ashe bawani abu bane sabo ko,kai de kaji da burin kunyar ka kawai"



harzuka yayi ,yanufota kamar wani zaki,bashiri ta kwasa aguje tayi bedroom,parlorn yadawo ya zauna ransa a mutukar bace,wayarsa ya dauka yakira layin fauza tana ta ringing bata daga ba,can yazari mukullin motar sa yafita,yana fita yaci karo da wata hadaddiyar budurwa cikin sauri yaja ya tsaya tare da fitowa daga cikin motar ya nufota ,










*NASEEBA GAWO*✍🏻

[3/19, 10:31] ‪+234 814 620 5819‬: [6:32AM,2017]





*@💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦💦


         *💦N I U*💦





   *ZAMAN AURE*

         💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦




*NA*


NASEEBA I UBA💐





*Alhmdulillahi ala kulli halin,allahumma la takilni ila nafsi darfati ainin*🤗👏🏻






*wannan shafin sadaukarwa ne ga yan group din SADNAF ,NASEEBA tace ana  tare, kai atakaice ma de ina yinku yasin ana mugun tare*🤝🤝








              *22*






~~cikin dakewa sakna tabude baki taiwa kamal magana,da  sanyin muryarta mai zaki da amo mai ratsa dodon kunne tace,




"Honey bee me yafaru nabata ma rai ko?pls kayi hakuri"



murmushi kawai yayi ,tare da shafar gefan fuskar ta ya dora da ,



"my dear,bakimin komai ba,amma yau shagwaba nakeji saboda haka kibani abincin nan da kanki"



ahankali ta sauke ajiyar zuciya,tare da sakin murmushi mai sauti,nan tashiga bashi abincin abaki ,suna dantaba hira ,cikin hikima ta dago tazuba masa ido tace,



"Honey bee,dan Allah inason muyi wata magana in ba damuwa kaji"



shiru yayi kamar mai nazari can kuma yanisa yace,



"inafatan baakan cikin jikinki bane,dan ni wlh sakeena banason ,haihuwa yanzu ,kuma banfidda ran raba ki da shi ba ,amma anay way,inajinki"



shiru tayi saboda yadda kalaman bakinsa suka razanata ,yake tayi ta dora da ,



"Honey bee,ni kullum bazangaji da tunasar da kai hakkin Allah ba,abinda fa kake yi ,shi yake baka damar aikata sabon dakakewa mahallicinmmu,kuma kake ganin kamar bawani abu bane,shaye shayen da kakeyi fa zai iya jefaka cikin mummunar halaka karfa ka manta Allah fa yanacewa ......



Dakatar da ita yayi tahanyar daga mata hannu,hade da daure fuska kamar betaba dariya ba ,hantar cikinta ce takada saboda yadda ta tsorata da yanayinsa cikin masifar fada ya ce,



"malama tashi kibani guri,dan wlh zaniya yimiki illa,banda raini ni zaki kalla,kidinga yiwa wani waazi ilimin naki cikin cokali,to,kirike abinki banason ji ,ke da har abada baza ai zaman jin dadi dake ba,sai ki tsiri,yiwa mutane waazi"


tunda yafara fadansa ta mike ,tana mikewa tasaki wata razananniyar kara,akidime ya taso meze gani salati kawai yakeyi,






*Jameel*





~~karar wayarsa ne yakatse shi ,hannu yasa a aljihunsa yazaro wayar tasa,yana dubawa yaga Everlasting da sauri yaddana tare da kara wayar akunnansa cikin isa da takama tafara magana,




" jameel,kana ina yakamata kazo muwuce gida ko"



cikin rawar baki yace,



"Everlasting,gani nan inshaallah ,naje gurin Hajaya ne"



"to ,kenan sai ka gama zakazo ka daukeni,ko me kake nufi"



"Haba de,wane ni gani nan ,tahowa kiyi hakuri"



ido kawai Hajiya tazubawa dan nata,yana gama wayar,ya dubi Hajiyar tasa wacce tausayin dan nata yacikata yace,

?



"Hajiya ,zantafi labiba najira na amma inshaallah zandawo gobe ,dan Allah ki tayani da addua cikin *zaman aurena* "



"Haba jameelu *zaman auranka* kawai,ai komai naka yana bukatar adddua dan haka zandage,dama kuma kullum acikinta ake,kaji kaima ka dage,amma nafara tsorata da matar ka amma de bakomai ,tashi ka tafi Allah ya tsare"




"Ameen "



kawai yace,ya mike yafita,kai tsaye gidan su labiba ya wuce,waya yaimata kin dauka tayi ,fitowa yayi daga motar yanufi cikin gidannasu da  sallama abakin sa ya shiga 



bakowa a tsakar gidan sai masu aiki ,suka gaisa,yace  suyi masa magana da labiba,ba musu suka shiga parlorn suka fadamata ,momy ce tace," ace masa yashigo"



sallama yayi ya shiga,yasami guri yazauna ya gaida momy da girmamawa ,labiba kam ko kallonsa batayiba,nan momy tashiga yimasa bayani kan ya kula da labiba,yadda yakamata ,yaamsa da to,suka tashi zasu tafi,jakar ta ta mikamasa ,cikin sauri yasa hannu yakarba,yai waje sai da momy tadada bawa labiba wasu magunguna sannan sukai sallama tafito tasameshe a mota ya hada  kai da siitiyarin motar, dagowa yayi ya kalleta,da sauri ya budemata tashiga yaja motar suka nufi gida,suna isa tadubeshi tace




"jameel,yaakamata,kashiga kitcheen ka dora mana abinci mana,yunwa fa nakeji,yakamata ace kasan abinda yadace"



kansa yadafe saboda yadda damuwa ta taru taimasa yawa take yafara ganin duhu duhu a idonsa kawai sai gani tayi ya,







*Abdulmalik*




~~shiru Ruhaima tayi tana sauraron mugayan kalaman inna,masu zafi da radadi,




"Ni nagaji da bakin halinki,dan haka ki sani inshaallah kwanan nan dana,zai sake aure,tazo ta haifa min jikoki,sai kije ki karata da bakin halinki muguwa kawai"



Abdulmalik,ne ya katse inna da fadin ,



"Dan Allah inna kidena fadin haka wai meyasa kike haka ne ba kyaufa,kuma haihuwa ai ta Allah ce"



"yimin shiru,sakarai kawai dama ai bazaka fahimci inda nadosa ba,munafuka tacinye maka dukiya ,amma saboda sakarci ka kasa ganewa,kai nifa nagaji da muna nan halayen yarinyar nan "



Daki Ruhaima ta koma tana kuka cikin ranta take fadin wane irin *zaman aure* ne haka ,kai tsaye wardrobe tanufa tafara fito,da kayanta tana zubawa a akwati,tagama tsaf,tadau mayafinta ta yafa ta fito,kacibus sukayi da inna  nan ta tsurawa akwatin kayan nata ido tace,



"au ke daga fadar wannan maganar sai ki jido kaya kice zaki tafi ,to yayi kyau ki tafin ,haka dama nakeson mutum mai zuciya,to amma wannan akwatin ai bataki bace dan haka sai ki san inda zaki zuba kayan naki kibawa dana akwatinsa"



shiru Ruhaima tayi can tanisa tace,






*Hafeez*





~~cikin sauri  yakarasa gaban yarinyar yace




"kyakkyawa barka da dare,ya kike,inbadamuwa ko zansan sunan ki"




banza taimasa tare da dauke kanta tadan kara taku zuwa gaba ,binta ya kuma yi ,nan yashiga tsarata da kalamai masu dadin sauraro take ta sakar masa murmushi tace





"Ni sunana Rumaisa,ina zaune a garin katsina karatu ne yakawo ni nan garin"



"wow nice name,gaskiya sunanki yadace da ke ,to inbadamuwa ko zaki shiga mota nakaiki inda zaki"



"why not,baka damuwa muje"



murmushi yayi saboda yadda tarkoonsa yakama kurciya suka nufi mota yajasu yai gaba,





Areefa kam daki ta nufatashiga binciken inda Hafeez yaajiye mata kudin ta ,tana janyo side bed taci karo da ,wasu hotuna cikin tsananin tashin hankali tasa hannu ta dakko su,hawayene yashiga ambaliya afuskar ta,









*NASEEBA GAWO*✍🏻

[3/19, 10:31] ‪+234 814 620 5819‬: [6:11Am,2017]





*@💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦




   *💦N I G*💦






  *ZAMAN AURE*

      💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦





*NA*


NASEEBA I UBA💐






*Rabbana atina fidduniya hasanatan wafil akirati hasan wakinna azabar nar*👏🏻👏🏻





💦

*Wannan shafin nakune ZAMAN AURE group kyauta fa nabaku shi  kuyi komai ba komai NASEEBA💐 ta yarje muku yasin🤣 akarshe kuma nace ana mugun tare*🤝









            *23*







~~cikin kidima kamal ya rungume sakna ,saboda yadda jini yake bin kafafunta ,ita kam inbanda murkususu baabinda take daukarta yayi cikin sauri ya nufi mota da ita ,sannan yadawo ya daukar mata mayafi tare da rufe kofofin gidan,da gudu yafigi motar yanufi asibiti da ita,cikin kankanin lokaci suka isa,Amir hospital, suna isa likitoci suka rufa akanta,da kyar suka shawo kan matsalar,kamal kam yana zaune yarafka uban tagumi ,babban likitanne yafara fitowa dan yaro dashi mai tsananin kyau ,da haduwa ,duban kamal yayi kunshe da murmushi afuskar sa yace,



"Abokina bisimilla biyoni office"


cikin rawar jiki kamal ya mike yabi bayan likitan nan,yana shiga ya tarar da shi atsaye ajikin famfo yana wanke hannunsa,sai da ya kammala sannan ya dau karamin towel ya goge hannunsa cikin nutsuwa ya juyo ya kalle shi hade da zama kan kujerar sa,biro ya dauka yadanyi rubuce rubuce sannan ya gyara zaman glass dinsa afuskar sa ya fiskanci kamal yace



"Abokina,agaskiya matarka tana cikin matsala koma ince babyn ku ya tsallake rijiya da baya,saboda yadda mahaifar uwar take da rauni wajen daukar baby,sannan kuma ita kanta tana da damuwa domin kuwa jininta ya hau,amma de ,munshawo kan matsalar cikin yardar sarki Allah,saboda haka  zaka barta ta huta na kwana biyu saboda daurin mahaifar daakaimata,ga  magunguna nan kaje kasiya mata ,Allah yasawake"


tunda Dr yafara magana kamal yakeson yaji yace cikin ya zube,sai kuma yaji sabanin haka,jiki asabule ya mika masa hannu ya dora da,


"inshaallah Dr jibiril zaakiyaye"


dariya yayi har sai da fararan hakoransa suka bayyana yace


"Not,Dr jibiril,i am Dr yahaya Gali"



murmushin karfin hali kamal yayi tare da dafe goshinsa yace


"ok Dr yahaya thankyou"



yana gama fada yafita ,dakin daaka kwantar da sakna ya nufa tana kwance tanata bacci numfashi take sannu a hankali,wayar sa yazaro ya shiga neman layin Hajiyarsa,tana dauka yafara yimata bayani yana kammalawa ,batace masa komai ba takashe wayar jiki asabule yacire wayar daga kunnansa yazubawa wayar ido kamar maison gano dalilin da yasa Hajiya yin shiru,





*Jameel*



~~cikin fusata, jameel ya yo kanta kamar kumurci yana huci yace



"labiba,ya isheki haka wai mekike son maidani ne,kina son nayi hauka ne ko da me kikeson naji ,haka ake  *zaman aure* a gidsnku,to ki shiga hankalinki inbahaka wlh zanbaki mamaki "


yana gama fadar haka ya wuceta yanufi daki,baki kawai labiba ta bude tana kallon jameel da mamaki wani gumi ne yashiga keto mata guri tasamu ta zauna cike da firgici ,can kuma tazaro wayar ta ,takira momy ,bugu uku ta dauka,



"momy na shiga uku na,jameel ya birkicemin yazanyi"



murmushi momy tayi,tadora da 


"labiba kenan ta yaro kyau ta ke bata karko,ina maganin dana baki dazu"?



"momy gashi ajakata"



"yauwa maza kitashi kiyimasa girki da wannan garin magani ki tabbatar yaci,shikuma wannan mai ruwan kishafa afuskarki "



"tohm shikenan momy na ,yanzu ma kuwa zanyi"



cikin kankanin lokaci ta tashi ta nufi kitchen tadora jollofe rice ta zuba wannan garin maganin aciki ,cikin kankanin lokaci ta kammala ta zubo a kula tanufi bedroom yana kwance a kan gado daga shi sai vest da gajeran wando yayi rub da ciki,akasa kan kafet taajiye masa ahankali ta nufi kan gadon tadora kanta a bayansa tashiga shafashi  tare da kissing din sa cikin daurewar fuska yadago yazuba mata ido take ya,







*Abdulmalik*





~~inna ta kafe Ruhaima da manyan idanunta tana sauraronta cikin sanyin murya tacigaba da fadin,



"inna kiyi hakuri a iya zaman da mukayi da ke inshaallahu yau zanbar miki danki,kuma kaya dakika karbe ,bakomai ai dan dankine yaimin shiyasa amma karki manta inna shi Allah baya barci haka kuma baya zalinci,kowa yai nagari kansa"



"to tabbatacciya mara mutunci ,lalle kinuna min kin isa ,to jeki Allah yaraka taki gona"


kan inna tagama masifar ta Ruhaima tai tafiyarta ,tana fita ta tari na pep tahau sai gida tun a waje ta hadu da mahaifinta tana ganinsa tasaki kuka tanufi ciki,



Abdulmalik bedawo ba sai yamma yana shiga ,ya tarar da kofar parlorln ta a rufe kai tsaye dakin inna yanufa ,tana ganinsa tafara share kwalla guri yasamu ya zauna tare da fuskantar ta yace,


"inna meke faruwa a gidan ,lafiya kuwa?"


shuru tayi can tanisa tace



"Abdulmalik bakai saar mata ba ,yarinyar nan dazu bakaga cin mutuncin da taimin ba karshe tasa kai tafita "


shiru yayi kansa yagama kullewa ma gaba daya yarasa mezeyi hankalinsa yakasu gida biyu can yadago da idanunsa dayakada yai jazur yace,







*Hafeez*






~~mamaki ne yakama Areefa aranta take tambayar kanta ,



_yaakayi Hafeez yacanja meyasa yajefa rayuwar_ *zaman auransu* _cikin yaudara da cin amana_



bata da wannan amsar hawayenta ta share tare da tattare hotunan ta maidasu cikin dakinta taadana ,murmushi tasaki tare da daukar wayar ta ,tashiga neman layin Alhaji namadi,




Hafeez kuwa bezame ko ina ba sai wani katafaran hotel nan suka tsaya a respetion ya karbi mukulli suka nufi dakin tare da wannan budurwar ,mantuwa yayi a mota ya sakko zai karba kamar ance yadaga kansa kawai sai ganin wata yayi kamar  Areefa,dada bude idonsa yayi ko de gizo,kawai sai gani yayi ta .










*NASEEBA GAWO*✍🏻

[3/19, 10:31] ‪+234 814 620 5819‬: [4:53AM,2017]




*@💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦💦



      *💦N I G*💦







  *ZAMAN AURE*

       💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦





*NA*


NASEEBA I UBA💐








*Allahumma la sahala illa majaaltahu sahala waanta tajalu haznah iza shiitu sahala,Rabbi yasir wala taasir allahumma yasir alaina*👏🏻👏🏻










*Dedicated 2 my lovely daughters suhyla mustafa khalid   (suly)andFadila Bilal abdullah*

*(fadilaty binty)* 😍💕💙💜💘😘









                *24*









~~Ran Hajiyar kamal ne yai masifar baci dan tasan akwai dalilin da yasa sakna rashin lafiya ,mai da dubanta tayi ga lubna wacce take ta  aikin  gyaran wardrobe tace



"lubna , kibar aikin nan mutafi muduba jikin sakeena wai tana asibiti"



cikin firgici lubna ta dubi Hajiya tace,



"wlh Hajiya yaya kamal yana da matsala ,Allah sai kinyi da gaske yana bawa Aunty sakna damuwa fa "



"kibarni dashi lubna zamu hadu ne,kuma zanfada wa yayanku duk irin tsiyar da ya keyi ai "



"yauwa gwanda hakan ai "


tafada tana kokarin maida kayan datake gyarawa ,nan suka shirya tsaf suka fito  tare dayiwa maman su suhaif sallama taimusu fatan dawo wa lafiya tare da yiwa sakeena sannu, awaje suka hadu   da,yayan nasu sharif ,dauke da  faraa kunshe a fuskar sa ya dubi Hajiyar tasu yace,



"Hajiya ina zaku haka da daren nan ?


cikin bacin rai tadubi dan nata tace,



"wlh yanzu kamalu yaimin waya wai matar sa tana asibiti ba lpy ,shine zamuje"



"Ayya to mutafi mana tare"


nan suka rankaya suka nufi mota lubna ce ta mai da dubanta ga yayan nata tace,




"yaya sharif barka da dare,yasu ikiram?



"yauwa auta,duk suna lpy,ya school ana ta hutu ko?



"Eh"


tabashi amsa,tare da sa hannu ta dau wata jarida ,kallonta kawai yayi batare da yace komai ba kasancewar sa mutum mai saukin hali,



ahaka suka  karasa asibitin suna isa ,suka ci karo da kamal yadawo daga siyan magani wani banzan kallo Hajiya ta watsa masa take hantar cikinsa ta kada, jagora yaimusu zuwa dakin daaka kwantar da ita ,suna shiga tana farkawa,da sauri Hajiya ta karasa gaban gadon tare da kamo Hannunta tahada dana ta,tace




"sannu sakeena kinji ya jikin naki"?


kai kawai ta gyada mata ,lubna da sharif ma suka shiga yimata sannu, kamal kam yana gefe sai raba ido yake ,Hajiya da kanta ta bata ruwan tea tasha tabata magani ,basu bar gurinta ba sai da sukaiwa gidansu waya sannan maman ta tazo da kanwarta fiddausi ,



kamar yadda Dr yabada umarni sai da tai kwana 2 a asibiti sannan aka sallameta,tun a asibiti Hajiya ta yanke hukuncin tafiya da ita gurinta bashi da zabi,haka ya hakura yabarta badan ransa yaso ba,daki guda aka waremata nan Hajiya tashiga bata kulawa, yanzu haka zaune take adaki tajiyo muryar kamal shi da Hajiya cikin kwantar da murya yake fadin,



"Dan girman Allah Hajiyata kibarni inganta in duba jikin nata ,wlh bazan kuma sata adamuwa inshaallah"



shiru taimasa kamar bataji shi ba can tanisa tace, 






*Jameel*




~~Tunda jameel yahada ido da labiba take yamanta  da wata damuwa nan yashiga ririta ta,tare da makaleta a jikinsa yana dada tusa kansa cikin rigarta,wata ajiyar zuciya labiba tasaki,saboda yadda take, tarkonta yakama kurciya nan yashiga kissing dinta ta ko ina cikin rawar jiki yasa hannu ya zuge zip din rigarta,take yadada kidimewa ,tayashi tashiga yi ahaka suka samarwa kansu nutsuwa sai da komai ya lafa sanan suka nufi toilet sukai wanka ,suka fito daure da towel ,kai tsaye gurin kulolin abincin suka nufa ,labiba ta zuba masa yaci dayawa dubanta yayi da lumsassun idanunsa yace,



"Everlasting,

kici abincin mana ,karki zauna da yunwa fa ,ko dan baby na"



yafada yana shafa cikinta ,yatsine fuska tayi tare da dubansa tace,



"wlh,jameel ko, banason cin komai ,Babyn ka bayason barina cin abinci,nide kawai ka dafa min tea kaji"



cikin kashe ido yadubeta yace,



"angama madam,da girman kujerar ki ,umarnin ki kawai nake jira,a aiwatar"


murmushi mugunta tasaki,hade da narke fuska,



tashi yayi yanufi kitchen ya dora mata tea bejima ba yadawo da cup  a hanunsa ,da kansa yashiga bata ,har sai da ta koshi 


haka rayuwar jameel tai ta tafiya a juye ,ba ya zuwa ko ina kullum yana tare da matar sa yanaimata bauta cikin ta ya girma ,kamar kullum suna zaune suna kallo kwance take a jikinsa suka ji ana buga kofa ,kin daga shi tayi yaje yaga waye,wayar sa ce ta hau ruri ,hannu yasa zai dauka itama takai hannu, dole yajanye nasa hannun yabarta ta dauka,duba scereen din wayar tayi ,taja tsaki,







*Abdulmalik*





~~ido inna tazubawa Abdulmalk,wanda yarasa da kalaman da zaiyi amfani wajen furtawa inna cikin sanyi jiki da na murya yace,




"inna dan Allah karki rabani da Ruhaima wlh ina sonta ,bazan iya rayuwa batare da ita ba"


  

wata uwar harara ta watsa masa ta dora da,



"sannu,Abdulmalik, lallai ka nuna min kai dan zamani  ne, yayi kyau,wato bazaka iya rayuwa ba ita ba ko,lallai ashe kuwa karshen rayuwar ka ne yazo,to bari kaji ,wlh kagama *zaman aure*  da juya ,kaji ko,inbanda sha shanci yaushe zaka zauna da mai bakin hali,to bari ma kaji na nema maka auran yar gidan kawata zahra,ita nakeso "



shiru yayi ,kalaman inna suna zame masa kamar saukar garwashi ,sai da tagama tsaf sannan yatashi ,kai tsaye gidan su Ruhaima ya nufa,


tsayawa yayi akofar gidan yana jiran dan aike ,ita kam tana shiga,

tafada jikin mahaifiyar ta,hankali tashe uwar tashiga yimata magana,



"Subahanallah ,Ruhaima lpy meke faruwa,ina Abdulmalik din"?



shiru tayi ana haka sai ga mahaifinta ya shigo,guri yasamu ya zauna tare da gyaran murya yace,



"ke,Ruhaima tashi ki zauna bana son shashanci,yazaki zo kisamu agaba kina kuka,meye haka?



tashi tayi,tare da share hawayen fuskar ta tace,



"Abba,innar malik,batasona,tarabani da shi,ta korone,wai dole sai ya sakeni"


Ransu ne yaimasifar baci ,ana haka sai ga Abdumalik yayi sallama yashigo,


a tare  suka daga kansu suka dubeshi ko wanne fuska ba walwala cikin fushi abba yadubeshi yace,








*Hafeez*




~~wata kyakyawar yarinya Hafeez yagani amma abin haushi kan yadago ya dago har ta bacewa ganinsa murmushi yasaki tare da shafa sumar kansa,wata jaka karama ya dauka ya koma dakin da suka kama yana shiga idonsa yagane masa,



Areefa kam tana kwance da wayar ta a hannunta ,bugu biyu Alhaji Namadi ya daga kiranta ,wata dariya yasaki tare da fadin,



"zumata,sanyin idaniyata masoyi yata,abar alfaharina yaakanyi ne?



murmushi tasaki mai sauti tare da kashe murya tace,




"sweet heart,kewar ka tahana ni sukuni ,nakasa runtsawa wlh ,yazaayine?


"ya kike so ayi mai zakin"?



"kana ina yanzu?


"Ni ina guest house,dina amma zaniya zuwa inda kike cikin kankanin lokaci ya kikeso ayi ?


shiru tayi tana nazari can tanisa tace masa,







*NASEEBA GAWO*✍🏻

[3/19, 10:31] ‪+234 814 620 5819‬: [6:41Am,2017]




*@💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦💦


     *💦N I G*💦





    


  *ZAMAN AURE*

      💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦







*NA*



NASEEBA I UBA💐






*Allahumma salli ala muhammad wasallim,ya hayyu ya kayyumu birahamatika astagisu*👏🏻




💦

*wannan shafin sadaukarwa ne ga tsohon  principal din sheik maihula secondary school Allah kaji kansa da rahama ,halinsa nagari yabishi ,ina mika sakon taaziya gareku daliban wannan makaranta musamman yan shekarar 2009  wato kiyaya*🎓






             *25*





~~Dada rusunawa kamal yayi,yana sauraron Hajiyar tasa,



"kamalu kanajina ko,bazaka samu damar ganin sakeena ba,saboda bansan mezakace mata ,bana bukatar dada sata a damuwa kai kuma baka da burin da ya wuce,kabata ciwon kai,saboda haka shige ka tafi naka guri,ka karaci sakarcinka kai kadai"



"Dan Allah ,Hajiya 

kiyi hakuri ,wlh bazan sata a damuwa ba,inshaallahu zankiyaye"



dariya tayi har sai da hakorin ta na maka ya bayyana tadora da,



"Kamalu kenan ,ai sai kayi amma nikam nagama magana,saboda haka tashi ka tafi gidanka ka kwanta"



shiru yayi kamar zeyi kuka,can ya mike kamar wanda aka tsirawa allura,abakin kofa yaci karo da saif,dubansa yayi da kulawa yace




"Yaya kamal,lafiya kuwa,meyasameka haka?"



dada hade rai yayi tare da dan yin gaba yaja dogon tsaki, sai kuma yaja yatsaya yace



"Abba fa "?



"Abba yana sama ,bedade da dawowa ba,dan yau ya dade a waje"




tsawa  yadaka masa tare da sakar  masa harara yace,



"kai de banza ne wlh kawai tambaya daya naima amma sai da kabani amsa goma,malam wuce da Allah"



murmushi kawai saif yayi,ya shige dakin Hajiya gurin sakna ,kamal kuwa kai tsaye part din abban su ya wuce dauke da sallama a bakinsa ,mama ce taamsa cikin nutsuwa ya kutsa kai ya shiga tare da samun gefan abban nasu ya zauna ,cikin kwantar da murya yace,



"Abba,barka da dare"



"yauwa kamalu,kana lpy,ya jikin matar taka"?



shiru yayi  tare da shafa sumar kansa dan dama abinda yakawo shi kenan,can yanisa yace



"Abba bansan yadda jikin nata yake ba,Abba Hajiya tahana ni ganinta wai ciwon kai nake bata,dan girman Allah Abba kasa baki tabarni inga jikin nata"



shiru Abba yayi tare da zubawa dan nasa ido,can yanisa yace,





*Jameel*



~~ido,jameel ya zubawa labiba,tare da sauraron mezata ce,game da mai kiransa shiru tayi can ta nisa can tanisa tace,



"jameel,number ce,may be ma kiran bashi da amfani kawai bari akashe wayar ko?



"bani da wani zabi face zabin ki Everlasting,a kullum jameel mai bi ne a gareki"



wani shuumin murmushi tasaki tare da kashe ido,


abangaran Hajiyar jameel kuwa gajiya tayi da bugu,ga shi wayar sa ma ankashe,hakura tayi ta tafi,kai tsaye gidan yayar ta nufa,tana zuwa tasameta zaune a madai daicin parlornta,da sakin fuska ta tareta ,suka gaisa ,shiru Hajiyar jameel tayi ,dubanta Hajiya Dije,tayi tace,



"Bilkisu,fuskar ki ta nuna damuwar da take cikin zuciyar ki,ko meke damunki"



nannauyar ajiya zuciya tare da duban yayar ta tace,



"yaya,ina cike da damuwa matar Dan marayan zaki bata da kirki nadade da fuskanta akwai matsala a *zaman auransu*  to gudun zargi naki gasgata hasashena amma yanzu nagama tabbatarwa ,yaya jameelu,fa yarasa aikinsa asanadin matarsa ,nide banyi saar sirika ba "



dubanta Hajiya Dije tayi,da tausayawa kana ta numfasa tace,



"subahanallah,abu be dadiba bilkisu,meyasa baki taba fadaminba,to amma ba komai mudage da addua ai baabinda yafi karfin Allah ,mukaiwa Allah kukanmmu inshaallahu zai mana magani"



nan de sukai ta tattaunawa karshe taimata sallama ta tafi tare da daura dammara kubutar da tilon dan nata,


kamar kullum jameel ne a kitchen yana soyawa labiba doya da kwai kawai sai ganin ,






*Abdulmalik*



~~Gaban Abdulmalik ne ya yanke ya fadi saboda,yadda abbban Ruhaima yake duban sa dada russunawa yayi yana sauraransa,

cikin masifar fada yake fadin,




"Abdulmalik,ina ganin in *zaman auran nan* zai kawo matsala tsakanin ka da mahaifiyarka to gwanda a hakura "



cikin sauri yadago da kansa ya dubi abbban Ruhaima,yace,



"dan Allah aimin afuwa,wlh inason Ruhaima kar arabani da ita dan Allah"



"Abdul malik kenan kanason Ruhaima ,to ai mahaifiyar ka bata sonta kaga kuwa akwai matsala ,ni ina ganin kaje kawai ka aikomin da takardar sakin Ruhaima hakan kamar shi zaizama masalaha"




a razane Abdulmalik ya dago ya dubi abbba,zaiyi magana ya dakatarda shi tahanyar daga masa hannu yadora da,



"tashi kaje ,kawai zan nemeka"



ido Abdulmalik yazubawa Ruhaima itama shi take kallo,atare wasu hawaye suka zubo daga idanunsa,sauri yayi yamike ya fita kai tsaye mota ya nufa yasaki kuka mai tsuma rai,


inna kuwa waya taiwa yayar Abdulmalik da tazo tana kiranta,bata jima ba ta zo tana shiga tasaki kuka ,cikin tsananin tashin hankali Rabia ta dubi inna tace,



"yasalam,innarmu,meyasameki,me akaimiki,ina matar gidan?



sai da inna ta share majina da gefan zaninta sannan ta dubi Rabiaa tace,






*Hafeez*




~~Yarinyar da yadakko ya nema yarasa ta kwashe masa wayoyinsa guda biyu masu masifar tsada,nan yashiga duba amma baita ba alamar ta fitowa yayi reception din ya shiga tambaya ko anganta duk maaikatan sai suce basu gantaba,gajiya yayi ya koma dakin ya dibi ragowar shirgin sa ya nufi gida ransa a mutukar bace,yana shiga gidan 

 yatarar da Areefa, bata nan,take ransa ya kuma baci kan  doguwar kujera yasamu ya kwanta aljuhunsa yafara dubawa dan daukar wayarsa dan jin inda matar tasa ta fita batare da sanin sa ba, ji yayi wayam,hannu yasa yadafe kansa,tare da sakin dan siririn tsaki,ya maida kansa ya kwanta idonsa ya kada yai jazur saboda bacin rai,



Areefa,kam suna cikin waya da Alhj Namadi ta tabbatar masa da gatanan zuwa inda yake bata bata lokaci ba,ta shirya tsaf ta nufi guest house dinsa dan sheke ayarsu,sun dan jima atare sannan ya dakko ta yadawo daita gida ,kamar amafarki Hafeez yaji tsayuwar mota a kofar gidan nasa tashi yayi ya leka dan ganin waye a motar ,cikin bugun zuciya idonsa yagane masa abinda betaba tunani ba,take,yaji shi yanajiri yatafi luuu ya,





_ZAMAN AURE_🤔





*NASEEBA GAWO*✍🏻

[3/19, 10:31] ‪+234 814 620 5819‬: [6:45AM,2017]




*®💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦


    

   *💦 N I G*💦






  


   *ZAMAN AURE*

         💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦





*NA*


NASEEBA I UBA💐








*wallahu galibun ala amrihi wala kinna aksarin nasi la yaalamun,subahanallahi wabihamdihi subahanallahil azim*👏🏻






💘💕💘

*wonderful day 2 a  wonderful girl ,2  day, is a special day the day that borne a queen Happy birthety Fadila Bilal Abdullah whish u many yrs a head ,my dear  daughter  HIP HIP HURRY FADILATY BINTY*🎊🎂🍭

*Assadiq said Happy birthday fadilaty ukuty*😘👌🏻









              *26* 






~~shiru kamal yayi yana sauraran abinda abban nasa zaice,cikin nutsuwa abban yake fadin,



"kamalu,to ai hakuri zakai bisa  hukuncin da mahaifiyar ka ta yanke,kabari matar taka tadada samun sauki tukunna kaji"



cikin shagwaba yadago yadubi abban nasa yace,



"Abba ,baka fahimceni ba,nifa bacewa nayi adawo da ita ba ,kawai abarni inga yanayin jikin nata ,dan Allah mama kisa baki"




murmushi mama tayi tare da duban mai gidan nata tace,




"Alhj dan Allah kasa baki kamal yasamu yaga matar sa ayi hakuri"



"Dakata du Allah ,Hajiya mama,ke kamalu tashi kaje gida,gobe kadawo"



Abba.....


kan yakarasa ya dakatar dashi ,ba yadda yaiya haka yatashi jiki ba kwari ya fito,kai tsaye gurin motar sa yanufa ya dade aciki kafin yaja ta ,mashaya yanufa,yana zuwa aka kawo masa ruwan da yasaba sha,ido yazubawa kwalabar kamar mai son gano wani abun aciki,a hankali ya furta 



"No,imposible"



tashi yayi ,yafita kai tsaye gidansa ya nufa ,yanashiga yai parking din motar sa ,yanufi parlornsu a kan doguwar kujera ya kwanta tare da jan dogon tsaki,wayarsa ya dauka yashiga neman layin sakeena ,tana kwance tunanin kamal dinta fal ranta sai jin karar wayar ta tayi da sanyin jiki tasa hannu ta dauka tana dubawa taga *honey bee* a screen din wayar da sauri ta danna tare da kara wayar akunan ta ,







*Jameel*




~~cikin azabar jin zafi jameel yafasa kara,sakamakon mai da ya sheko masa akafa,da sauri labiba,tayunkuro ta nufo kitcheen din ganin jameel na yarfa hannu ne yasa ta tambayar sa,




"Jameel lafiyar ka,sai kace ba namiji ba kafasa uwar kara ,wlh kabamu tsoro"



cikin radadi da azaba jameel yadago ya dubi labiba yace,



"Haba Everlasting meyasa baki da tausayi konewa fa nayi da mai ,amma me makon ki tausayamin sai kina yimin mitar nabaki tsoro"



"oh! ashe konewa kayi ai bansaniba sai da bakinka ya furta hakan ,Allah ya kiyaye gaba,ni bani wacce kasoya ,wlh yunwa nakeji"



ido jameel yazubawa labiba ,saboda yadda take gwada masa rashin tausayi,hannu tasa ta dauki wacce yasoya,tafito,gas din yakashe yafito kai tsaye bedroom ya nufa ya kwanta,yai lamo yana tunanin hali irin na matar tasa,


abangaran Hajiyar sa kuwa tun da taisa gida ta dukufa da addua da sadaka dan samun kan dannata ahankali yafara samun nutsuwa a ransa ,yauma kamar kullum yana zaune a parlor labiba tafito cikin kwalliya ga cikin ta da ya tsufa da kyar take takawa dagowa jameel yayi ya kalleta tare da fadin 


"ina zaki kenan da wannan katon cikin,kina son ki haihu a hanya ne"



shiru tayi saboda yadda kalaman sa suka bata mamaki cikin fitsara da gadara ta dubeshi tace



"jameel ,wacce irin magana naji bakinka na furtawa yaushe kafara daga min murya haka,cabdijan,au dama inzanfita sai na tambayeka ko kuma wani sabon salone haka"



cikin fushi da zafin rai jameel ya taso yayo kanta tare da ,







*Abdulmalik*




~~Bakunya ba tsoran Allah inna ta dubi Rabia tace



"Rabi ,matar Abdumalik zagina tayi tare da yimin rashin kunya dama fa tunda nazo gidannan sai taga dama take bani abinci,shine yau ta tattare dukiyar yaron nan tabar gidan ,wlh Abdulmalik be saar mata ba kai cona "




"Haba inna tayaya Ruhaima zata zageki gsky kamar bazata iya zaginki ba kai abin da kamar wuya "



wani kallo inna ta watsawa Rabia tare da matse hawayan idonta tadora da,




"Rabi,me kike nufi kenan karya nake ko ,yayi miki kyau nagode da irin sakayyar da zakimin 



"Aa yi hakuri inna bahaka nake nufi ba,shikenan kiyi hakuri ,yanzu mekikeso ayi "




kan tai magana Abdulmalik ya shigo guri yasamu ya zauna tare da sunkuyar da kansa kasa hawaye ne yafara bin fuskarsa cikin tausayawa Rabiaa tadubeshi tace,




"Abdulmalik kayi hakuri dan Allah kadena kuka ,sai kace ba namiji ba ,yanzu yaake ciki"?



shiru yayi can yadago yadubi innar tasu yace,



"inna gani durkushe agabanki ki yanke duk hukuncin da yadace game da *zaman aurena* da Ruhaima"



wani murmushi inna tasaki har sai da hakoranta suka bayyana wadanda suka rine da goro,tadubi yayan nata tadora da ,



"Dafarko inason kasaki matarka yau ba sai gobe ba,


atare suka dago suka dubi innar tasu wani irin jiri ne yadibi Abdulmalik yana daga zaune,






*Hafeez*





~~Areefa tadade kafin suyi sallama da Alhj Namadi ,sannan tashigo gida tana shiga taci karo da motar Abdulmalik gabanta ne ya yanke yafadi ,amma sai ta dake ta kutsa kai zuwa parlorn azaton ta yana parlorn abin mamaki baya nan dakinta ta wuce tare da adana kudin da Alhj Namadi yabata,tacire kayanta ta dakko wato yar figigiya tasa tadawo parlorlorn kamar ance tadubi wajen taga sai ganin Hafeez tayi kwance yana ta jan numfashi da gudu takarasa gurin da yake tashiga kiran sunan sa,




"Hafeez! Hafeez! ,meyasameka nashiga ukuna"




ahankali yajanye jikinsa daga nata ya maida kansa jikin bango ,dada matsowa tayi cikin azama ya dakatar da ita murya a raunane yace,




"Areefa,kincuceni,

kinyaudareni kincutar da *zaman auernmmu*


wacce irinn rayuwa kika jefa kanki ciki haka"?



dubansa take da rashin fahimta ,duba irin na mai tabin hankali,can tai karfin hali wajen tattaro kalmomin da zatai amfani da su,


"Hafeez mekakeson fada ne,nifa nagaza gane inda kalaman bakinka suka dosa,kaimin bayani da yaran da nafi ganewa"



kallonta yake duba na tsana da kishi can kuma ya,








*NASEEBA GAWO*✍🏻

[3/19, 10:31] ‪+234 814 620 5819‬: [6:18Am,2017]





💦                     💦

*®💦NASEEBA💦 💦GAWO* 💦 







    *ZAMAN AURE*

         💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦





*NA*


NASEEBA I UBA💐






*Rabbana atina fidduniya hassanat wakinna azabar nar,Rabbana takabbal minna innaka antal wahab*👏🏻👏🏻





💦

*ina taya daukacin al ummar musulmai  murnar zagayowar wata mai girma da daraja,wato watan daaka haifi shugaban mmu annabi MUHAMMAD( S W A) dafatan Allah yabamu albarkacinsa AMEN*💦








    


               *27*






~~cikin siririyar muryar ta mai zaki da dadi ga maabocin sauraro ta fara magana,




"Hello,Honey bee"



ahankali ya sauke ajiyar zuciya tare da sakin murmushi wanda ya bayyana kyawun hakoransa yace,




"matar kamal,yanzu abinda akaimin kina ganin anyimin adalci kuwa,yaake so nayi,Hajiya tahana ni ganinki kwata kwata"



cikin kwantar da murya tare da kwantar masa da hankali tace,



"Honey bee,dan Allah kayi hakuri muyiwa Hajiya biyayya ,kaga fa tayi haka ne dan inganta lafiyar jikan ta ne,tunda kai da bakinka kace baka son kyautar da Allah yaimana,kuma ga .......



da sauri ya katseta ba tare da barinta ta karasa ba   runtse idanunsa yayi,ya dora da ,




"ya isa haka sakeena ki adana kalaman bakinki masu barazanar fasa min kirji da dodon kunnuwa ,haba dame zanji,yakuma akeso nayi ne wai?



shiru tayi tana sauraran sa can ta numfasa tace,



"Allah yabaka hakuri Honey bee,banfadi haka dan na bata maka rai ba,kawai de nafadi abinda ka dade kana furtawa ne ,na  kin kyautar da Allah yabamu"



"A,kwarai kuwa ada nafadi haka,amma a yanzu baabinda nafi kauna kamar cikin jikinki, sakeena, ki cigaba da kular min da abina kinji ko,,inason ganin gudan jini na"



dariya yabata sosai ,saboda yadda yake furucin ba kunyar abinda ya dinga yimata  abaya a hankali ta furta,



"Baka da damuwa dani ,mijina zankula inshaallah"



"yauwa",yafada adake sai kuma yacigaba da fadin,



"yanzu ya zaayi ne ina mutukar bukatar ki a kusa dani,inason jin dumin jikinki,sakna wlh bazaniya kwana ni kadai ba,dan haka gani nan tahowa ,Hajiya fa tayi bacci?



"Honey bee pls kayi hakuri kar ka fito a daran nan ,kabari gobe kazo ,kaji nayi maka alkawarin faranta ranka inshaallahu,kuma fa Hajiya tana parlor ita dasu lubna"




"munafukar yarinyar nan batai bacci ba kenan,amma kinmanta dare ba matsalar kamal ba ne,amma de,shikenan na hakura, da sharadin zakiyi taimin hira mai dadi har nayi bacci"



"Honey bee kenan na yarda"



nan tai taimasa hira mai cike da so da kauna da wannan damar tayi amfani tai masa nasiha mai ratsa jikin mai sauraro shiru yayi yana sauraranta tare da godewa Allah da yabashi mace mai addini,tun tanayi yana amsawa har taji shi shiru,kiran sunan sa tayi yaamsa da kyar saboda baccin da yafara fisgar sa, ,ahankali tace



"Mijin sakeena,bacci ko?




kai ya gyada mata kamar tana ganinsa ya dora da ,



"sakna gwanda nayi baccin muryar ki dada tayar min da hankali take"



"kayi hakuri mijina,bari naimana addua sai mu kwanta ko"



addua tai musu suka shafe jikinsu kusan atare ,kiss yasakar mata ta cikin wayar ,dariya tayi ta kashe wayar tare da shafa cikinta ,kai tsaye toilet ta nufa ta dauro alwala tazo ta tayar da sallah tare da mika godiyar ta ga sarki Allah bisa ganar da mijinta gaskiya,




washe gari da sassafe kamal ya shirya tsaf yanufo gidan nasu ba kowa a wajen  kasancewar,safiya ce duk suna daki,kai tsaye part din Hajiyar tasu yanufa,yana shiga ya hangota zaune a parlor tana jan carbi,da sauri yaja da baya,






*Jameel*




~~cikin masifar fada jameel ya dubi labiba yace,



"labiba,karki sake ki fita,ko ina wai ke wace irin macece me kika maidani ,sha sha ko sakarai,to ki shiga hankalinki dani tunkan nabaki mamaki,kina tunanin duk abinda kikeyi bansani ba ko me?



mamaki ne ya kama labiba,saboda yadda jameel ya rufe ido yana zazzaga mata ruwan masifa,dubansa tayi tace,



"jameel,me kunnuwana suke jiye min ,ni kake fadawa haka ,dama  inzanfita sai ka yarda?, to wlh sai na fita,kayi duk abinda zakayi,kuma kayi min girki kan nadawo,haka ake *zaman aure* a garinku"?


cikin zafin nama ya kwasheta da mari,zai kara  mata kenan yai tozali da cikin jikinta  take ya sauke hannunsa  ,idonsa ya kada yai jazur,kuka tasa tana ihu tare  da fadin,




"wlh jameel baka mari banzaba  kuma sai nafita kayi duk abinda zakaimin mugu kawai,azzalimi,

butulu"



Ransa ne yadada baci ya dubeta yace,



"Tohm shikenan haka kikace ko ,to kibude kunanki da kyau dan kiji abinda zai fito daga bakina,



"wlh kika sake kika fita to abakin auranki,dan sai narabu dake rabuwa ta har abada ,kina tunanin jin dadin *zaman auranki* nakeyi,inmma tunaninki kenan to ki dena ,dan haka shawara tarage ga mai shiga rijiya"




yana gama fada yasa kai ya fita ,yabar mata gidan kai tsaye, gidan su yanufa,labiba kam haushi ne yakamata tare da daukar wayar ta takira layin momyn ta,tana dagawa tasaki kuka cikin tashin hankali tashiga tambayar ta 




"ke,labiba lafiyarki,meyafaru kike kuka?




nan ta kwashe komai tafadamata masifa tashiga sirfawa ta dora da,



"maza maza,ki taho gida wlh sai ya gane kuransa ,shi din banza kitaho  yanzu ba sai anjima ba"



katse wayar tayi tahada kayanta tsaf ta fita batare da ta tuna furucin nasa ba ,ta nufi  gidan su,


jameel kuwa yana zuwa gidansu yazube gaban hajiyar sa yasaki kuka kamar wani karamin yaro,cikin tashin hankali Hajiya tashiga tambayar dannata ,



"Dan marayan zaki lafiya da girmanka zaka zo kanaimin kuka"


shiru yayi can yanisa yace,




"Hajiya labiba ce,labiba tana sani a damuwa,labiba bata da wani buri da yawuce,tabani ciwon kai "



shiru kawai Hajiyar tayi tana sauraran dan nata,





*Abdulmalik*



~~dafe kai kawai Abdulmmalik yayi tare da runtse idonsa ,inna kuwa ko ajikinta tacigaba da fadin


"Abdulmalik inkasaki Ruhaima, mariya zan aura maka yar gidan aminiyata ,ni nasan zakai farin ciki da zabin da zanmaka"



gaba daya baya fahimtar kalaman innar tasa ,Rabia ce tadubi innar tasu tace,



"Haba inna wai meyasa kike haka ne ,yanzu inni akaiwa haka zakiji dadi kenan,gsky kar kiyi haka,wannan yarinyar da bata da tarbiya da ita zaki hada Abdul,danki nagar tacce......



dakatar daita inna tayi ta dora da ,



"Rabi ,karki sake sa mana baki ,wannan magana ce tsakanin d'a, da uwa dan haka kija bakinki ki tsuke,tunda bazaki fadi alkhairiba,ai kema kinhaihu ko?,to kije ki gwada naki ikon akan yayanki,amma banawa dan ba"



"Haba inna meyai zafi ,daga magana ta fatar baki ,Allah ya huci zuciyarki"



"Ameen"



sai yanzu Abdulmalik yadago yadubi inna yace,



"shikenan inna,na saki Ruhaima saki daya"



"yauwa yaron kirki,ga biro da takarda ka rubuta a rubuce,sai nabayar akai mata gidan su"




dauka yayi ya rubuta jikinsa da hannnunsa sai rawa suke,


yana gama rubutawa ya mika mata  ya mike ya koma dakinsu tare da maida kofa yarufe kan gado ya hau ya kwanta ya runtse idonsa tare da dafe kansa dayaimasa nauyi da sauri da sauri numfashinsa yake harbawa,




Rabia kuka tasawa inna saboda yadda kanin nata yabata tausayi,inna kuwa tashi tayi ta shirya tsaf ta nufi gidan su Ruhaima,










*Hafeez*





~~jikin Areefa ne yai sanyi saboda yadda taga Hafeez ya canja mata tai shiru tana sauraran kalamansa ,




"Areefa,waye ya kawo ki amota,kuma ina kikaje? da izinin wa kika fita?"



shiru tayi tana sauraran sa kamar wata kurma ,sai da yadakamata tsawa sannan ta dago ta dubeshi tace,



"Hafeez,wlh waya akaimin ummata ba tajin dadin shine.....



"malama yimin shiru ,karki sake kiyimin karya duk abinda zaki furta yazama gaskiya zaki fadamin saboda bazaki raina min hankali ba kinji ko,inajinki"



"umm,shine shine naita kiran wayarka akashe zanfada maka,amma dan Allah Hafeez kayi hakuri bazan kuma ba"



"waye shi din dayakawoki gida abinda nakeson ji kenan "



"dan yayar ummata ne ,a asibiti muka hadu ,shine ya ...



"dakata dalla malama Alhj Namadin ne dan uwanki ,to kicanja wata karyar wannan bataiba "



mikewa tayi tsaye tare da kafe shi da ido tashiga yimasa masifa tare da ,








*NASEEBA GAWO*✍🏻

[3/19, 10:31] ‪+234 814 620 5819‬: [6:43AM,Z2017]





💦               💦    💦

    

*®💦NASEEBA*

 *💦GAWO*💦



     *💦N I G*💦








    *ZAMAN AURE*

        💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦






*NA*


NASEEBA I UBA💐







*Allahumma inni asalika afuwa walafiyata fidduniya wal akhirati yaman huwal hayyu la yamutu*👏🏻





💦

*Wannan shafin nakune kainuwa writters associa🌈 Naseeba💐 nagodiya gareku bisa gayyatar da kukaimin cikinku kar ku damu ana tare🤝 Allah yakara daukaka AMEEN*👏🏻








               *28*







~~Kamal yadan jima atsaye yana lekawa yaga ko Hajiya ta tashi,cikin ikon Allah ta yunkura ta tashi dakin sakna tanufa ,dafe kai yayi,duk hakan na faruwane akan idonsa,bata wani jimaba ta fito kai tsaye bedroom din ta ta shiga ,ahankali ya sauke ajiyar zuciya ,cikin sassarfa,ya sa kai ,ya shiga tare da maida kofar ya rufe,sakna na kwance ta rufa da bargo sai jin mutum tayi abayanta,baki ta bude da niyar kurma ihu,da sauri kamal ya manna bakinsa anata,kamshin turaransa ne yadaki hancinta ahankali ta bude idonta ta dora su kan fuskar kamal hannu tasa tashafi sajen da ya kewaye fuskar tasa,tare da shagwabe fuska tace,




"Honey bee,shine kabani tsoro ko,ni gsky sai narama"



dariya yayi saboda yadda tayi maganar dada janta yayi zuwa jikinsa cikin kunnanta yafara magana,



"my dear i am so sorry,banason Hajiya taganni ne shiyasa,ya kwanan baby na"


yafada yana shafa cikinta,hannunta ta dora akan nasa tace,



"lpy lau ,amma Honey bee baka tsoran Hajiya ta dawo ta ganka a dakin nan,nide  gaskiya.....



katseta yayi ta hanyar dora yatsansa akan lips dinta ya dora da,



"Bawanan maganar my dear,yanzu de meye labari,me kamal zai samu?



shiru tayi tare da dada lafewa a kirjinsa tana wasa da gashin fuskar sa ahankali ta dago ta kalleshi ,hada ido sukayi,yadaga mata gira, yatashi  yasawa kofar key yadawo kan gadon tare da rage kayan jikinsa nan yashiga sarrafa ta cikin kwaraiwa,gabadaya kamal ya susuce,yazama kamar zakin da yaga abinci ,kasa jurewa sakna tayi saboda yadda yake gurzarta ahankali tafara fitar da numfashi da sauri da sauri,kamal kuwa bema san tanayi ba,har sai da yasami nutsuwa sannan ya daga ta ,yana sauke numfashi ,sai lokacin ya kula da yanayin da matar tasa ke ciki,cikin kasala ya mirgina kusa da ita tare da janta zuwa jikinsa yazubamata ido,take hankalinsa yadan tashi yashiga kiran sunanta



"sakeena! sakeena! 



shiru yaji tayi ,kan ya kuma yin wata magana yajiyo muryar Hajiya tana kiran sakeena,ido ya zaro waje ya shiga tunanin ya zeyi,hannu Hajiya tasa ta murda kofar mezata gani,




*Jameel*



~~Ajiyar zuciyar Hajiya ta sauke tare da sauke tagumin da tayi ta dubi dan nata a karo na biyu tace,




"Dan marayan zaki,maganar gaskiya nadade ina jiran wannan rana domin kullum cikin rokon Allah nake akan Allah yai maka zabin alkhairi game da *zaman auranka* da labiba,hakikanin gaskiya jameelu bakai saar mata ba ,to yanzu tana ina ?"



"nabarta a gida ,nace mata mutukar ta fita to abakin auranta"



"Allah ya kyauta ,yashiryeta"



kan yaamsa da kalmar ameen wayarsa ta shiga ruri hannu yasa yadauki wayar da yaajiye kan center table,yana dubawa yaga sunan momy kamar baze dagaba sai kuma ya daure yadaga tare da kara wayar a kunansa ,cikin masifa momy tafara magana



"Jameelu me labiba taimaka da zaka marar min ita ,dama acikin *zaman aure* akwai mari ,to bari kaji wlh baka mari banza ba dan sai.....



katseta yayi da fadin,


"momy bata fadamiki abinda taiminba ,kuma nafadamata wlh intasake ta fita abakin auranta "



"sannu mara mutunci ,to bari kaji labiba ta na gida,kenan hakan na nufin kasaketa ,ko me kake nufi"?



"kwarai kuwa momy, nasaki labiba,saki uku,tunda taketare sharadin dana gindaya mata"



yanagama fadar haka ya katse wayar

tare da mai da dubansa ga Hajiya,ya kwashe komai yafada mata,shiru tayi can tanisa tace,



"Saki ba dadi Danmarayan zaki,to amma wani lokacin masalaha ne ga maaurata, Allah yasa haka shine mafi alkhairi"


"Ameen Hajiyata"



yafada yana share kwallar da ta gangaro masa,


labiba kam ana fadamata ,ta kurma uban ihu,take tayanke , 







*Abdulmalik*





~~cikin kankanin lokaci inna ta isa gidan su Ruhaima tana shiga ta tarar da umman Ruhaima tana aiki ,sallama tayi da sauri ta juyo ta zuba mata ido can kuma tace,



"maraba sannu da zuwa,shigo mana"


"aa,basai na shigo ba,gashi nan abawa yarinyar nan ,dan Allah ku gaggauta zuwa kwashe kayanku dan Abdulmalik aure zaiyi"



"ikon Allah ,to shikenan mungode Allah yasa haka shi yafi Alkhairi"



"Ameen"


cewar inna tanagamafada tai tafiyarta ,Ruhaima kam tana tsaye tana kallon ikon Allah take ta rushe da kuka ,hankalin ummanta ne yadawo kanta take ta karasa kusa da yar tata,




inna tana fita kai tsaye gidan su mariya ta nufa akofar gida taci karo da ita ,da sakin fuska ta dubeta tace,



"Aa mariya  ina zuwa haka, babar  taki na ciki"?



"tana ciki"


"to,yar albarka ,bari inshiga,sai kindawo"



ciki inna tashiga tasami babar mariya zaune a rumfa tana gyaran zogali da faraa ta tareta nan tasami guri tazauna,kusa da aminiyar tata,


Abdulmalik kuwa tunda yashiga daki zazzabi mai zafi ya rufe shi ,da kyar yaiya daukar wayar sa ya kiran layin abokinsa mai suna mansur,yana dagawa yace



"mansur pls kazo gida kasameni yanzu"



"To"


kawai yace,ya katse kiran,nan yadada dukunkunewa baajima ba,mansur ya karaso,waya yaiwa Abdulmalik yakarasa,cikin tsananin jin sanyi yatashi ya fita a mota yasami abokin nasa cikin tsananin tashin hankali mansur ya dubi abokin nasa,






*Hafeez*



~~cikin rashin kunya da tsiwa Areefa ta dubi Hafeez tace,



"Hafeez,Alhj Namadi ne ya kawo ni kayi duk abinda zakayi,kai wayasan irin abinda kakeyi,ba sai Allah ba,to kaimin duk abinda zakai haba"



cikin tsananin mamaki Hafeez yake duban bakin Areefa,har ta gama,can yanisa yace,



"mekike nufi,Areefa,kina zargina nane"



"oho,nide banceba,amma de koma mene ne kafini sani"



ransa ne yabaci yatashi yabar mata parlorn daki ya koma yakwanta,




da daddare yana kwance a daki ,yakirata tanajinsa taimasa banza tai kwanciyar ta a parlor,


washegari da wuri Areefa,ta shirya tabar  gidan ,Hafeez yana fitowa ya tarar da Areefa bata nan zama yayi yarasa ma mezaiyi,wayar sa,yadauka ya shiga neman layin Ashanty,sai da ta kusa tsinkewa sannan ta daga,





*NASEEBA GAWO*✍🏻

[3/19, 10:31] ‪+234 814 620 5819‬: [6:33AM,2017]




*®💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦


     

    *💦N I G*💦







   *ZAMAN AURE*

      💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦





*NA*


NASEEBA I UBA💐







*Hasbunallahu wani imal wakil la haula wala kuwata illa billahi aliyul azeem*👏🏻






*HIP HIP HIP HURRY,HAPPY BIRTHEY  IN ADVANCE MY DEAR UMMI AISHA,I  WAS LATE IN WHISHES BUT LET ME DO IT NOW,I WHISH U A DAY SOFT AS SILK WHITE AS MILK SWEET AS HONEY AND FULL OF BLESSING AND HAPPINES I LOVE U MORE THAN DESERV SIS*🎂🎂🎂🎂🎂









             *29*






~~cikin tsananin mamaki Hajiya taga kofar dakin ansa mata key ,a hankali tafara kiran sunan sakeena ,ji tayi shiru ,kamal kuwa yana rungume da ita tana  ta sauke numfashi sannu a hankali, ana haka lubna ta fito daga nata dakin duban Hajiyar tasu tayi tace,



"Hajiya lafiya naganki a nan ,meyafaru da aunty sakeena"



"lafiya kalau Auta,inason dada duba jikin nata ne ,kuma ga shi ankammala karin kumallo da tafito ta karya,dazu kofar a bude take ,amma kinji yanzu ansa key"



"Hajiya kenan ,tunda kika jita shiru karshanta bacci take inta tashi zata fito,bari inje ingaida abba indawo"



"to shikenan Auta nima gani nan zuwa"


duk abinda ake a kunnan kamal  yana jinsu ,yana ta kokarin ganin numfashin sakna ya dai daita ,ga cikinta da ya dunkule waje daya,hakan ba karamin daga masa hankali yayi ba, ahankali tafara sauke ajiyar zuciya tare da daga ido ta zuba masa ,murmushin karfin hali  tasakar masa tare da lumshe idonta,cikin sauri kamal ya fara jera mata sannu ,kai kawai ta iya daga masa,tashi yayi ya nufi toilet ya hada musu ruwan zafi yadawo ya taimaka mata ta mike ,da kyar yar kara tasaki sakamakon dunkulewa da cikin jikinta yada  yi,da ssuri yasa hannunsa ya toshe mata baki tare da girgiza mata kai,ahankali ya tallafeta suka nufi toilet din,shi ya taimaka mata wajen wankan shima yayi ,gaba daya yadada susucewa da kyar ya iya hakura suka fito,gafen gado sakna tasamu ta zauna,kai tsaye akwatin kayan ta ya nufa ya daukko mata wata doguwar riga mara nauyi,tare da dakko mai yashafa mata,yasa mata rigar ,kiss ya sakarwar cikinta,shima ya shirya tsaf,dubansa tayi tace,



"kayi kyau mijin sakeena,amma kwalliyar tayi yawa gaskiya"



dariya yayi,tare da shafa kyakkyawar fuskar ta yace,



"Nagode matar kamal,to amma fa neman aure zani ,tunda ke kinzama raguwa bazaki iya jure bukatar mijinki ba"


yafada yana  kashe mata ido,da sauri ta dago ta zuba masa dara daran idanunta mikewa tayi ta nufi bakin kofa da niyar bar masa dakin cikin sauri yasha gabanta tare da janta jikinsa ya shiga rarrashinta fisge jikinta tayi ,ta kuma sa hannu ta murda key din ,tana budewa taci karo da lubna abakin kofar,






*Jameel*





~~cikin tsananin tashin hankali labiba tafara birgima akasa tana ihu tare da fadin,



"Nashiga uku,momy wlh inason sa ,bazan iya rayuwa ba tare da shi ba,na cutar da shi, ya hakura,betaba cemin komai ba,na mallake shi na mallaki dukiyar sa wayyo Allah na,asirin dana dade inai masa ne ya karye ko momy"?



hankalin momy ne yai masifar tashi dataga yar tata kamar ta zauce,dagata tayi suka nufi daki ,nan tashiga yimata saka da bakin zare,tare da nuna mata hanyar da bazata bulle da ita ba,ta dora da,


"Haba labiba,jameel din banza akan sa kike wannan kuka,to bari kiji infada miki,inbanda kaddararan cikin jikin ki,da da zarar kingama idda zaki sami wanda ya fishi" 



cikin kuka ta dubi momyn tace,



"wallahi momy bazan sami kamar jameel ba, nariga narasa shi kawai kuma wallahi ke kika jamin faruwar hakan "


shiru kawai momy taiwa yar tata karshe ta tashi tabar mata dakin,



jakarta  tajayo ta dakko wayar ta ,nan  ta shiga neman layin kawar ta ,sai da ta kusa tsinkewa sannan ta dauka,



jameel kuwa yadade tare da Hajiyar sa ,sannan yai mata sallama ya nufi gidansa,yana shiga dakinsa ya nufa,ya shiga bincike durowowin gadonsa takardunsa ya ke nema yadade yana dubawa sannan ya gansu ,parlor ya koma ya zubawa takardun nasa ido,wayar sa ce tafara ringing yana dubawa yaga sunan abokinsa usman,murmushi yayi sannan ya danna tare da kara wayar a kunnan sa ,



"Hello  muryar nakeji kamar ta abokina usman"


dariya usman yasa da yaji muryar jameel ,yadora da ,



"jameel  kenan ni ne mana lafiya kuwa najika so silent akwai matsala ko "?


ajiyar zuciya jameel ya sauke sanan yadora da ,


"usman kana gari kenan "


"nadawo jameel ,yanzu haka ma ina hanyar zuwa gidanka inafatan kana gida"?



shuru jameel yayi kamar  mai nazarin wani abu,a hankali ya bashi amsa tare da godewa Allah da dawowar usman ,zama yayi yacigaba da jirans karasowar sa,






*Abdulmalik*




~~cikin son jin damuwar abokin nasa mansir yake tambayar Abdulmalik shiru kawai yaimasa tare da cigaba da dafe kansa,ahankali yace,



"mansir asibiti zaka kaini,koma de meye mayi maganar daga baya"



"To amma abokina zanso.......



hannu yadaga masa alamar yai shiru ,yadora da,



"Dan Allah dan annabi mansir kabarni ka na neman dada bani ciwon kai ,nace zanfada maka koma mene ne ko"



sanin halin abokin nasa ne yasa mansir yin shiru ,yaja motar suka nufi asibiti basu jimaba suka karasa sundan dade  kafin susami ganin likitan suna shiga Abdulmalik ya yanke jiki yafadi,da sauri likitan yataso ya nufo kansa hankalin mansir ba karamin tashi yaiba,



inna,kuwa bayan sungaisa da babar mariya  ta dada gyara zama tace,



"wato Hajiya asabe, dama zuwa nayi nemawa Abdulmalk auran mariya,dan dada karfafa zumuncinmmu"


shiru Hajiya asabe tayi can tanisa ta dubi aminiyar tata tace,



"To,naji dadin batukinki Binta,to amma ina matar sa take,kinsan fa mariya bazata zauna da kishiya ba "


dariya momy tayi sannan ta dora da,



Ruhaima,kuwa innalillahi kawai take furtawa cikin tausayawa ummanta tafara yimata nasiha tare da kwantar mata da hankali murmushin karfin hali Ruhaima tayi ana haka sai ga mahaifinta ya shigo ganin yanayin da yar tasa take ciki ne yasa shi saurin zama tare da mai da dubansa ga umman ta,





*Hafeez*



~~Ashanty tana daga wayar Hafeez tai shiru ajiyar zuciya yasaki sannan ya dora da ,



"Hello my dear Ashanty,kina lpy"



"lpy ,yau ka tuna dani kenan,ai wlh Hafeezu,baka da mutunci"



"yi hakuri tawan ,kiyimin uzuri wlh abubuwa ne suka sha kaina amma de yanzu kina ina?



"Hmm,ina inda kasanni mana,har yanzu bancanja sheka ba tukunna"



"yauwa tawan kinajina yanzu ina gidana ko zaki zo kosameni"



dariya tayi sai datayi mai isarta sannan tace,



"Hafeez kenan bama kai kazo ba ni zanzo lallai kam"



"eh akwai dalilin dayasa nake son kizo ne pls"



shiru tayi can ta nisa  tare da tauna cigam yace kas ,tace,


"ok badamuwa kajirani nana minti 30"



"yauwa tawan "


sukai sallama suka kashe wayar tashi yayi yanufi kitchen dan nemawa cikinsa abinci,



Areefa kuwa tana fita kai tsaye gidan su Hafeez ta nufa tana shiga tasaki kuka ,cikin tashin hankali mahaifiyar sa tashiga tambayar ta 



"Areefa lafiya meyafaru,ina Hafeezun"




shiru tayi can tashare hawayenta ta dubi mahaifiyar tasa tace,






*NASEEBA GAWO*✍🏻

[3/19, 10:31] ‪+234 814 620 5819‬: [6:00AM,2017]



*®💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦


    *💦N I G*💦







   *ZAMAN AURE*

      💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦





*NA*


NASEEBA I UBA💐





  *Astagafirillah waatubu ilehi Astagafirillahi azim*👏🏻👏🏻








 *Dedicated  this page 2 my brother Nazeer yusif  muazu  ango 2 be may Allah bless ur marrige live in peace ,Happines love , and Honest  ya Allah!  i whish them 2 live 2gether Ameen*👏🏻💔




 


               *30*






~~cikin sauri kamal ya labe abayan kofa sakna kuwa murmushi tasakarwa lubna tare da jan hannunta suka nufi parlor ,dubanta sakeena tayi tace



"kanwata, har kintashi , Hajiya fa ?"


" tun dazu, Hajiya,suna parlorn Abba ita da mama,tun dazu take ta murda kofar ki arufe"



shiru sakna tayi can ta dago ta kalleta tace,



"Ayya nakoma bacci ne,yanzu de yunwa nakeji wlh me Hajiya taimana,?



"tea da dankali da kwai ,amma ke,me kike son ci ?"



" wlh,lubna dama zansami kunu da nasha ,shi nakeson sha banason shan tea"



"Ai kuwa naga Suhaif yana shan kunu,bari inje inkarbo miki"



"yauwa kanwata nagode sosai"



dariya lubna tayi ,ta tashi tafita ,cikin sauri sakna ta tashi ta leka dakinta ,dariya tasaki saboda yadda kamal ya labe abayan kofa,cikin tsokana tace,



"kazo Hajiya tana kiranka "



dariya kawai yaimata tare da janta zuwa jikinsa yashiga kissing dinta da sauri tazame jikinta ta fito daga dakin kan doguwar kujera ta samu ta kwanta tare da sauke, numfashi,da sauri kamal yabar dakin ,batare da kowa yaganshi ba,kai tsaye dakin abban su ya nufa ,sallama yayi ,aka amsa ,sannan yasa kai ya shiga,kusa da abban yakarasa yazauna,tare da gaisheshi,sannan ya juya gurin su Hajiya da mama suma ya gaida su,ana haka sai ga yayansa shareef shima ya shigo,nan suka hadu sukaita hira can kamal yadago da kansa tare da narkar da fuska yadubi mahaifin nasa,yace,



"Abba,  dan girman Allah yau zantafi da sakeena ,tunda tadan sami sauki"



Hajiya ce tai caraf tace,




"kamalu wani ne yafadamaka tasami sauki ko kuma shiga kayi kaganta"?



shiru yayi bece mata kala ba ,sai sosa kai da yakeyi,dubansa ta kuma yi akaro na biyu tace,



"To,bainda zaka tafi daita,ai baka san darajar ta ba,shiyasa kake cutar da ita a *zaman auranku* "



Abba ne ya dubi Hajiyar yace,



"Haba ,Hajiyar lubna,meyasa kike haka ne ,meye amfanin hanashi matarsa,akan wane dalili kikai haka,dama ido kawai na zuba miki,to tun da girma da arziki ki bashi matarsa su tafi"



shareef ne ya gyara zama  tare da  dubi abban nasu   yace,



"wlh Abba kamal yana da matsala gaba daya besan hakkin 

*zaman aure* ba,gwanda abar yarinyar nan ta huta ,inbaya ganinta kila yasan amfanin ta"



"Haba sharifi,yazaka fadi haka ,ai ita fitina kwantar daita ake ba dada tayar da ita ba,abashi matar sa kawai,kai kuma kamalu kaji tsoran Allah a *zaman auran* ku kaji"


cewar mama tafada tana kallon kamal abba ne ya katse zancan da duban kamal yace,



"kamalu tashi kaje ka dau matar ka kutafi gida,Allah yakara sauki ka kula da ita kaji ko"



"to ,Abba nagode Allah ya kara girma yaja kwana,mama atayani godiya,

Hajiya muntafi,yaya shareef sai ka fito"


banza Hajiya taimasa ta dauke kanta,

yana gama fadar haka ya fito kai tsaye dakin Hajiyar ya nufa ,sakna na zaune  ita da lubna suna kallo,ya shigo hade rai yayi ya dubi sakna ya ce ,



"oya,sakeena hado kayanki zamu wuce"


da sauri ta dago da kanta tadubeshi,lubna ce tai  caraf tace,



"yaya kamal Hajiya fa tace kar ka tafi daita kabari tadada samun sauki"


cikin fushi hade da murtike fuska ya nufi kan lubna,








*Jameel*




~~Jameel yadade zaune yana jiran karasowar usman can wayar sa ta hau ruri da sauri yasa hannu ya dauka yana dubawa yaga usman dinne dannawa yayi tare da kara wayar a kunnan sa ,


"usman ka karaso kenan"



"eh gani a kofar gida"



"ok"



kawai yace,yafita acikin mota ya tarar da shi ,jikin motar ya karasa tare da kwankwasa glass din ,cikin sauri usman yafito,murmushi suka sakarwa junansu,tare da rungume juna kai tsaye gidan suka nufa,a parlor suka yada zango jameel ya dubi usman yace,



"Abokina ka ganka kuwa,gaskiya ka kama kasa,meye labari ne"?



"jameel kenan wace kasa ,kawai de ina samin kulawa ne daga gurin madam,yanaji gidanka shiru ko madam bata nan ne"?



shiru jameel yayi can ya nisa yace,



"kai amma mutumina kayi saa gaskiya  ,ai ni lamarin  baacewa komai sai de addua kawai"



"banfahimci zancanka ba abokina meke faruwa"



shiru jameel yayi can yadubi usman ya kwashe komai game da yanayin *zaman auransu* yafada masa har aikin da yarasa a dalilin matar tasa ,usman ya tausaya masa sosai can yadago ya dubi abokin nasa yace,



"Amma banjin dadin zancan nan  ba jameel to ,yanzu wane aikin kakeyi"?



"Haba usman ina maganar aiki ,bana komai fa yanzu ai kai de lamarin baa cewa komai kawai"



dubansa usman yayi yace,



"tohm shikenan abokina yanzu abinda nake ganin zaayi shine,



"kakawo takardunka inkaiwa yayana dan ya bude sabon kamfani dama ana ta daukar maaikata "



cikin farin ciki jameel ya mikawa usman takardunsa 

yace,



"kasan kuwa neman aiki zantafi,kai amma naji dadi gaskiya abokina"



"bakomai jameel ai ana tare,yanzu abinda zaayi shine gaskiya ka nemi mata ka aura,dan zaman ka haka ba zeyuba"



arazane jameel ya dubi usman yace,



"dan Allah usman mubar wannan maganar ni wallahi tsoran mata nakeji"




"haba jameel ai ba duka suka raro suka zama daya ba dan haka mubar maganar na dan Allah"


bayadda usman ya iya,kyale shi yayi karshe yai masa sallama ya tafi ,




labiba kam kawarta mero tana daga wayar tace,


"Kawata,kina ina akwai matsala,jameel ya sakeni dan Allah kizo"



"subahanallah ,kai amma abu be dadiba yanzu kina ina kawata"?



"Aa,ina gida mana kizo kifadamin yadda zanyi kinde san irin son danakewa jameel ko"?



"gaskiya ne ,sai dai bana gari labiba,amma na kusa dawowa,innadawo zanzo"



dan haushi labiba ko amsa bata bawa mero ba ta kashe wayar komawa tayi ta kwanta cikinta ta shafa ta lumshe ido,





*Abdulmalik*




~~Da sauri likitan ya nufi inda Abdulmalik suke ,daukar sa sukayi suka daura shi kan gado nan likitan ya shiga duba shi tare da yimasa gwajin jini take ya gano yadda jininsa yai masifar hawa mai da dubansa yayi ga mansur yace,




"Gaskiya jininsa ya hau sosai,kuma hakan zai iya haddasa masa mutuwar barin jiki domin yana da damuwa ,sosai "



cikin tashin hankali  mansir yadubi likitan yace,



"Tabbas yana da damuwa sai dai bansan damuwar sa ba,dan befadaminba ,yanzu likita meye abunyi?




"eh to dole zamu bashi gado dan sai ankwantar dashi anabashi agajin gaggawa yanzu naimasa allurar bacci ,zaamaida shi dakin dayakamata ya kwanta"




"Tohm shikenan Dr nagode sosai"




haka kuwa akai aka bawa Abdulmalik gado ,yanata bacci mansir yana zaune yazuba masa ido can tafara motsi ahankali yana kiran Ruhaima ,



inna kuwa tana can bata san halin da danta yake cikiba,duban  babar mariya tayi tace,




"Haba kawata ai yanzu haka ma daga gidan su matar tasa nake nakai mata takardar saki ,ai sunrabu ,bata da hali fa yarinyar nan wlh cutar yaron nan takeyi gashi ba haihuwa take ba,saboda haka nan kusa nakeson ayi komai agama"




"Aa to ai shikenan bakomai nabashi auran mariya bari yayan ta yazo zanfada masa"




"yauwa to madalla nagode ,bari intafi sai kinjini agaidamin da yar tawa"



tana gama dada tai gaba kai tsaye gida ta nufa tana zuwa tasa mukulli tashiga dakin Abdulmalik a rufe ,hankalinta be tashi ba sai da taga dare yayi bedawo ba nan ta shiga nemansa Rabia taiwa waya tana kuka ta fada mata,




Ruhaima kuwa hawaye kawai take abban tane ya tambayi ummanta yace,



"wai mekuma yafaru naganku kunyi cirko cirko"



takardar kawai umma ta mika masa yasa hannu ya karba tare da war ware takarda ya duba shiru yayi can yanisa yace,



"Allah ya sa haka shi ya fi alkhairi kinji Ruhaima tashi ki koma ciki kar kisa damuwa aranki "



bata iya amsawa ba ta mike tanufi daki tana share hawaye,





*Hafeez*



~~indomie yadafa yafito kenan yaji bugun kofar ajiye plate din indomie din yayi yanufi kofar tamba yayi 


"waye ne?


"inka bude kagani"


dariya yayi mai sauti  da yaji muryar ashanty cikin sauri yabude tare da jan hannunta suka nufi ciki,dubansa tayi tace,



"Hafeezu kana cikin hankalinka kuwa matarka fa"



"karki damu daita mukarasa ciki"



 atare suka jera suka nufi parlorn tana shiga tadau plate din indomie din tashiga ci ,cokali ya dakko yazo yasa suka shiga ci tare,can tadago ta dube shi tace,


"meye dalilin nemana har gidanka?


janta yayi zuwa jikinsa can ya dubeta,



Areefa,kuwa,karya da gaskiya tashiga fadawa ma haifiyar Hafeez ,ranta ne yabaci tashiga fada kamar yana gabanta wayar ta tadakko ta shiga neman layin Hafeez tana ta ringing be daga ba dubanta tayi tace,



"yanzu yana gida"?



"Eh yana gida"



"madalla tashi mutafi gidan naku zancan banza da wofi kai"







*NASEEBA I UBA*✍🏻

[3/19, 10:31] ‪+234 814 620 5819‬: [6:13AM,2017]



*®💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦


    *💦N I G💦* 







   *ZAMAN AURE*

      💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦







*NA*


NASEEBA I UBA💐







*Allahumma la sahala illa majaaltahu sahala waanta tajaalul haznah iza shiitu sahala*👏🏻👏🏻







              *32*







~~Dada tsurawa Hajiyar ido kamal yayi,dan sauraran abinda zai fito daga bakinta cikin nutsuwa Hajiyar tace masa,



"sai katashi kutafi ai,kuma wallahi tallahi kaji de narantse inka kuma kuntatawa sakeena banyafe maka ba,matarka yarinyar kirki amma katsaya kana shashancin banza da wofi"



sumar kansa yashafa tare da narke fuska yace,



"Hajiya dan Allah kidena fadin haka ,nifa baabinda nake mata kitambayeta ma kiji"



"matsalar kace kuma ai kamal, baabinda zan tambayeta ni kam,sakeena tashi kidakko mayafinki kutafi kinji Allah yakara lafiya"



"Ameen Hajiya Nagode Allah yakara girma "



"Ameen bakomai kede nafadamiki duk abinda yaimiki karki shiru da bakinki kiyimin waya kifadamin kinji" 



murmushi kawai sakeena tayi ,ta nufi daki tadakko mayafinta,lubna ce tai sallama ta shigo dakin tana ganin sakeena da mayafi tace,



"Hajiya wai dagaske Aunty Sakeena tafiya zatai,nide gaskiya karta tafi yanzu"



wani mugun kallo Kamal ya watsa mata tare da fadin,


"To,uwarmu bazata tafi yanzu ba,sai sanda kika sa mana lokaci,wallahi lubna kishiga hankalinki dani ,inbahaka ba wallahi wataran sai na lakada miki dukan tsiya ,shegiya mai siffar munafukai"



cikin fushi Hajiya tadaka masa tsawa tare da fadin,


"kamalu wallahi kafita a idona inrufe,yar tawa ce,mai siffar munafukai,to ka kasheta inkatashi yimata  hukuncin kaji ko,tashi kabani guri,mai zafin ran tsiya"


tashi yayi yadau wayarsa da mukullin motar sa yafita ,sakeena taiwa Hajiya sallama tare da godiya ,lubna ce ta daukar mata akwatinta,tarakata dakin Maman su saif taimata sallama tare dayimata godiya itama,har bakin mota suka rakata ,kamal sai aunawa lubna harara yake ,yaja motarsa suka nufi gida,



tunda takoma ya gyara halayansa shiyake mata komai kan yafita,yanzu haka kwance take kan doguwar kujera ga cikinta da yakara girma sai juya kai take saboda yadda ta tashi jikinta badadi,shikam yana kitchen yana soya mata kwai sai jinta yayi tasaki kara da sauri yafito daga kitchen din daga shi sai vest da gajeran wando,yakaraso kusa da ita ya zauna,tare da janta jikinsa yashiga tambayar ta,



"matar kamal ,menene,meyasameki?


shagwabe fuska tayi tare da dada narkewa a jikinsa tace,



"Honey bee,wallahi kayiwa babyn ka magana tun danatashi yau sai naushi na yake,nide wallahi banso"



tanagama fadar hakan tasa masa kuka,shi sai yarasa ma mezaice mata saboda yadda tabashi dariya ,rigar ta ya yaye,tare da shafa cikin nata, yana kallon yadda babyn yake ta wutsil wutsil,wata karar tasaki,cikin dariya yace,



"Babyn kamal dan Allah kabari bakasan maman ka bataso ba,kukafa takeyi ,kazauna kawai kaji"


dariya yabata yadda ya dage yanaiwa dan cikinta magana can tadaga kansa daga cikin nata tadubeshi tace,



"Honeybee,may be  fa babyn nan yunwa yakeji ,shiyasa yake ta motsi ko?"



dariya yayi saboda yadda tai maganar kamar ba ita ke kuka ba,yace,



"bari inkawo miki wainar ki kici, ko babyn kamal yazauna lafiya"



"Honey beey nifa baby girl zan haifa,gaskiya"


Da sauri ya jiyo yazuba mata dararan idanunsa ,masu bata tsoro wani lokacin tare da  yadda ya hade rai,





*Jameel*



~~jameel yana kashe wayar sa yadada jan dogon tsaki ,kwanciya yayi kan doguwar kujera yashiga tunanin yadda zaisami macen arziki yaaura dan shikansa yasan zaman sa haka bashi da amfani yana mutukar bukatar mace,wayarsa ya dakko yashiga neman layin abokinsa usman bugu biyu ya dauka,



"Hello Abokina ,kana lafiya"



"lafiya kalau usman ya madam,da yarana na"


"Duk suna lafiya"


"kana ina ne yanzu,inason ganinka yanzu"


"ok badamuwa ina gida zaka iya zuwa"



"Tohm shikenan usman gani nan zuwa"


sallama sukayi ,mikewa jameel yayi ya nufi bedroom dinsa ya shirya tsaf yafito kai tsaye gidan usman ya nufa ,be dau dogon lokaci ba yakarasa gidan nasa ,kiransa ya kuma yi awaya ,tare da shaida masa gashi yakaraso,bejimaba yafito ,hannu suka bawa juna suka gaisa tare da karasawa ciki,a parlor suka zauna jameel ya gaisa da Huda matar usman tunda yashiga yai tozali da wata kyakyawar yarinya ido yazuba mata har sai da yarinyar ta tsargu daga kallon da yake mata dago da kanta tayi ,atare suka hada ido,murmushi yasakar mata,



labiba kam suna isa asibiti aka shiga daita labour room nan da nan likitoci suka rufu akanta take suka gano yadda jininta yai masifar hawa,nan suka shiga ceto rayuwar ta, data babyn ga azabar ciwo gabadaya tafita a hayyacinta sunan jameel kawai take iya kira ,cikin kankanin lokaci tafita hayyacinta kamar wasa tafara jijjiga,hankalin momy yai masifar tashi,da kyar akasamu ta dena jijigar cikin ikon Allah ta haihu amma babyn yarasu saboda wahalar da yasha,momy sai kuka takeyi wayar jameel tashiga kira tanata ringing yaki dagawa,labiba kam tanacan ankaita dakin duhu wato dakin daake kai masu jijjiga,kiran Abban jalila momy tayi bugu daya yadaga cikin kuka tashiga fadamasa gasu asibiti ,hankalinsa ne yaimasifar tashi  wata nurse ce tafito cikin tashin hankali ta nufi momy,dada gigicewa momy  tadada yi,tare da zubawa nurse din ido,danjin mekuma zatace mata,




*Abdulmalik*




~~cikin kankanin lokaci Rabia takaraso asibitin bata sha wahala ba wajen samun dakin da Abdulmalik yake,shigarta keda wuya tayi tozali da kanin nata kwance,mansir yanata fama dashi yaci abinci yaki ,


"Dan Allah mansir kabarni Ruhaima nake jira tazo tabani abincin"


shiru mansir yayi ganin Rabia tashigo da sauri takarasa gaban gadon da yake,tashiga yimasa sannu tare da kwantar masa da hankali,cikin muryar rarrashi tace,


"Abdul kaci abinci tukunna sai inkira  maka Ruhaima "



shiru yayi tare da zuba mata jajayan idanunsa ,can ya miko hannu  yakarbi ruwan tea yafara kurba,mansir ne yadubi Rabia yace,



"Aunty wai meye musabbabin ciwon Abdulmalik ne?



shiru tayi tare da kallon Abdulmalik din tace,



"Au befada maka ba?


da sauri Abdul malik yatare ta da fadin,


"Dan Allah kubar maganar nan haka innayi bacci kya fada masa"


yanagama fadar haka yashiga share hawaye,



yana gama shan tea din Yaya Rabia takira masa Ruhaima tana daga wa ta mika masa wayar dasauri yafara magana,


"Hello Ruhaima ! Ruhaima!"



shiru taimasa sai faman kuka takeyi cikin rawar murya yace,


"pls stop crying,say something to me"



cikin tsananin tashin hankali tashiga rera kuka tare da fadin 



"Abdul malik dan Allah kabarni kadena kirana kana fama min raunikan da suke cikin zuciyata na shiga uku"



kuka tasa masa gaba daya kasa magana yayi saboda tsananin tashin hankali dif yaji takashe wayar kansa ya kife akan filo yasaki kuka kamar mace,take kansa yadada sarawa yasaki wata kara ya sulale,cikin tsananin tashin hankali Rabia da Mansir suka fita dan kiran likita,



inna kuwa tanacan tarabka uban tagumi tana tajiran Rabia ta kirata tafada mata inda Abdulmalik yake,tun tana sa ran jin wayar ta har ta hakura karshe ta yanke shawarar daukar mayafi tanufi gidanta ,






*Hafeez*




~~Hafeez yanacan sun lula duniyar shedanci shi da Ashanty ,acikin gidan auransa agadonsu na sunna waiyazu billahi *Naseeba tace* *wannan wane irin zaman aure kenan Allah katsare mu*



wayarsa tana parlor tanata faman ringing  besaniba ,sai da suka gama shedancin su sannan tafito parlor hannu yasa yadauki wayar yana dubawa yai tozali da missed calls din maman sa dana yayar sa da sauri yabi kiran tanashiga maman tasu tadaga tare da fadin,



"sannu Hafeezu ,sai yanzu kaga damar daukar wayar yayi kyau to gamu akofar gidanka inkaga dama kazo ka bude mana"



hantar cikinsa ce tabada kulu lulu ya maida dubansa ga Ashanty wacce tafito daga ita sai towel,takarasa ta kwantar da kanta agadon bayansa zagayo daita yayi tare da zuba mata ido,



Areefa kam gabadaya hankalinta ne taji yai masifar tashi gabanta sai faman daduwa yake haka kawai tarasa dalilin faruwar hakan,






*NASEEBA GAWO*✍🏻

[3/19, 10:31] ‪+234 814 620 5819‬: [7:24AM,2017]




*®💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦




    *💦N I G*💦







   *ZAMAN AURE*




*NA*


NASEEBA I UBA💐






 *lahaula wala kuwata illa billahil aliyul azim tawakaltu alal lah wala haula wala kuwata*

*subahanalla wabihamdihi subahanal azim*👏🏻👏🏻







              *31*







~~Da gudu lubna ta nufi daki tare da banko kofa,tsaki kamal yaja tare da fadin ,



"mara kunyar karya meyasa kika gudu ai da sai ki tsaya,wlh da sai na karya miki kafa shegiya"


sakeena  de tana zaune tana kallonsa mai da duban sa yayi ga matar tasa yakarasa kusa da ita ya zauna tare da kama hannuta yahada danasa yace,



"matar kamal muwuce gida ko?"


shiru tayi tare da narai narai da ido ,dorawa yayi da fadin ,



"karki damu sakeena ina nufin karkiji komai inshaallah zamu shinfida rayuwar aure mai cike da so da kauna, zan canja tsarin *zaman aurenmmu* kinji,haka kuma nadena duk wasu muna nan dabiu danakeyi tunda kince ba kyau ko"?



ahankali ta dago ta dubeshe zatai magana kenan sukajiyo muryar Hajiya da sauri kamal ya matsa daga kusa da sakeena ,karasowa Hajiya tayi ,tare da samun guri ta zauna ,ahankali kamal yadago da kansa ya kalleta dada hade rai tayi ,tace


"kamalu burinka yacika kafadawa Alhaji zakatafi da matarka ko,to yayi kyau katashi kaje gurin aikinka in kadawo kabiyu ka dauketa dan bazaka kaita gida ba, katafi kabarta ita kadai bazai yu ba"



da sauri yatari Hajiyar tasa da fadin,


"Hajiya ai bazanje aiki ba a gida zan zauna inkula da ita"



"Hmmm,kamalu kenan ,to ai bazaiyuba,akan me zaka ki zuwa aiki,kaga tashi kawai kabani guri,haba yaro sai son zuciyar tsiya kai duk abinda kake so shi zakayi to wlh sai da yamma zata tafi,kuma inta koma ka cigaba da bata ciwon kai kar ka fasa"



shiru yayi tare da daukar mukulun motar sa  yafita ransa a mutukar bace, sakeena kam dariya yabata ,Hajiya ce ta dubeta tace,



"sakeena inkinkoma duk abinda kamalu yaimiki ki fada min kinji kuma kidinga samun isash shan hutu,banda yawan aiki dayawa "



"To Hajiya inshaallahu zan kula"


lubna ce tafito sai waige waige takeyi kamar mara gaskiya Hajiya ce ta dubeta tace,



"Auta lafiyarki kike  ta waige waige keda waye"



kusa da Hajiyar tasamu tazauna tare da sauke ajiyar zuciya  tace,



"Hajiya yaya kamal ne ,yabiyoni daga fadar gaskiya wai sai ya dakeni,wallahi Hajiya kimasa magana, ba ruwansa dani shi yafiya masifar tsiya"



"Rabu dashi Auta nima  akwai tawa dashi lamarin kamalu sai addua shi kam narasa irinsa "



karfe hudu kamal yadawo lokacin sakeena tana daki tana bacci guri yasamu ya zauna sai raba ido yake Hajiya na zaune tana kallonsa can yashafi sumar kansa yace,



"Hajiya ,sakeena fa?,gwanda mutafi da wuri ko"?



"gaskiya kam tunda birnin sin zakutafi ba,to bacci takeyi kuma ba wanda zaitashe ta sai ta tashi dankanta"



ido kawai   yazubawa Hajiya kamar mai nazarin wani abun ,muryar sakeena ce ta katse masa duniyar tunanin da ya lula, da sauri yadago da kansa ya zuba mata ido sanye take da duguwar rigar shadda ja tai mata kyau sosai ga cikinta da yadada fitowa a hankali tasami guri ta zauna Hajiya ce ta dubeta tace,



"sannu sakeena kinji kintashi"



"eh Hjiya natashi tun dazu ma"



kamal de yana zaune jira kawai yaji Hajiyar tabasu izinin tafiya ,can tadubeshi tace,







*Jameel*



~~kamar yadda usman yaiwa jameel alkawarin sama masa aiki ,yasamu ,cikin kankanin lokaci yafara aikinsa  tare  da kwanciyar hankali , yasami nutsuwa,bashi da wata damuwa raba dare yake yana salla tare da rokon Allah kariya  daga sharrin mai sharri,kamar kullum in yatashi daga aiki gurin Hajiyar sa yake wucewa yanzu haka zaune yake gaban Hajiyar  tasa yanacin tuwon shikafa da miyar taushe, cikin so da kauna da tausayi Hajiya ta dubeshi tace,



"Dan marayan zaki yakamata kasamo mata kayi aure zaman haka bashi da amfani kaji"



ahankali ya cire hannunsa daga abincin tare da ture kwanikan gabansa yazubawa Hajiyar tasa ido ,can yanisa yace,



"Hajiya ni wallahi tsoron auran nan nakeji saboda mata basu da tausayi ,nifa hankalina yafi kwanciya yanzu dan Allah  Hajiya kiyi hakuri kibar maganar auran nan"



"Haba jameelu ,kenan baka yarda da kaddara ba ko me? ,ai baduka ne suka taru suka zama daya ba,mata fa da kake gani suna suka tara kaide kacigaba da addua kaji nima ina nan inayi"



"shikenan Hajiya Allah yazaba abinda yafi alkhairi"



"Ameen Dan marayan zaki"



nan suka ci gaba da hirar su karshe yaimata sallama yatafi,



labiba kam tunda tadawo gida bata da sukuni hankalinta yana kan jameel ,sai yanzu ta  tabbatar tana son jameel kamar wacce aka tsikara ta mike zumbur ta dakko wayarta nan tashiga neman layinsa sai da ta kusa tsinkewa san nan jameel ya dauka



kuka tasa masa sai da kyar tasami damar yimasa magana,



"Yaya,jameel dan Allah kayi hakuri ,kadawo dani dakina wallahi bazan iya rayuwa batare da kai ba"



tsaki yaja ya kashe wayar ,dada rushwa tayi da kuka take taji bayanta ya rike da marar ta kara tasaki,da sauri momy ta nufo dakin nata ganin labiba a durkushe ne yaasata sakin salati tare da karasawa gurinta cikin tsananin tashin hankali,tashiga tambayar ta ,



"ke ,labiba meyasameki ,na shiga uku,ko haihuwar ce"



labiba kam ba baki sai faman nishi takeyi,da sauri momy taiwa direbansu magana yafito da mota ,da kyar labiba ta mike tare da dafa momyn suka nufi asibiti,






*Abdulmalik*






~~Da sauri mansur ya nufi kan Abddulmalik yakama hannunsa bude ido yayi yazubawa fuskar mansur ido can yabude baki yace,



"Mansur Ruhaima fa? tazo ko ,tana ina kira min ita kaji"



shiru mansir yayi yarasa me zaice masa cikin kwantar masa da hankali yace,



"Abokina kayi hakuri ,gata nan zuwa yanzu tafita gurin likita "




shiru yayi kamar mai son tuno wani abu can ya runtse idonsa a hankali yace,



"Mansir inna,inna tarabani da Ruhaima tasa nasaketa ,zo karakani inbata hakuri  bani da laifi"



gabadaya mansir kansa ya kulle nan yashiga rarrashin abokin nasa karshe ya fita ya kira likita yadada dubashi tare da yimasa allurar bacci,




Dariya ce taso subucewa Rabiaa dataji inna tana kuka,dakewa tayi tace,



"Haba inna Abdul fa ba yaro bane duk inda yake zai dawo,amma bari inkira wayar sa inji"




"yauwa Rabi kira min kiji,inda yake kinji naje na nemo masa auran mariya ina tason infada masa"



shiru Rabia taimata saboda haushi takashe wayar tashiga neman layin Abdulmalik sai da ta kusa tsinkewa sannan Mansir yadaga nan ya shaida mata rashin lafiyar  Abdulmalik hankalinta ne yatashi ba shiri ta nufo asibitin ko ta kan inna bata bi ba,




Ruhaima kam tana shiga daki tafada kan gadon umman ta tasaki kuka wayar ta tajawo ta zubawa number Abdulmalik ido kamar ta danna kiransa wani sashin na zuciyar ta na gargadinta kamar aamafarki taga kiransa ya shigo,





*Hafdeez*




~~dada shigewa jikinsa Ashanty tayi tazuba masa ido tare da shafa sajen fuskar nan yadora da ,



"wato Ashanty ina mutukar son kasancewa da ke,me zaihana muyi aure"



dariya tayi irin tasu ta yan duniya tace,



"Aure ko? matarka fa ita ?


"EH aure Ashanty Areefa,batai ba ,bata da kirki ko na minti daya shiyasa nakeson Auranki amma ya kika gani"




su Areefa,kuwa sun shirya kenan ita da maman Hafeez ,yayar sa tashigo dubansu tayi tace,




"Mama inazakuje haka,naganku cirko cirko "



nan tabata labarin abinda ke faruwa dubansu tayi tace,



"aa mama bahaka zaai ba mezai hana ai masa waya yazo "



"To,waya kuma tanawa Hafsatu "



"Bari inkira shi de muji"


kiransa tashiga yi a waya be daga ba can tadubi maman tasu tace,








*NASEEBA GAWO*✍🏻

[3/19, 10:32] ‪+234 814 620 5819‬: [6:38AM,2017]




*®💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦



   *💦N I G*💦







  *ZAMAN AURE*

      💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦





*NA*


NASEEBA I UBA💐







  *Allahumma salli ala sayyadina muhammadin wasallim,Bisimillahil lazi la yaburru maa ismihi filarbi wala fismawati wahuwal samiul azim*👏🏻👏🏻




               *33*








~~cikin fargaba sakeena tadubi kamal tace,



"Honeybee,nabata maka rai ko?,dan Allah kayi hakuri kaji"



murmushi yasakar mata tare da girgiza kansa yadora da,



"ko daya ,matar kamal baki bata min rai ba,kawai ina tunanin yadda zanzama baba ne"



ajiyar zuciya ta sauke tare da lumshe idanunta,shikuwa yana gama fadar haka yanufi kitchen sai gashi da wainar da yasoya mata ,da maltina ,kusa da ita yasamu yazauna,yashiga bata da kansa,tanaci ,cikin shagwaba ta dubeshi tace,



"Honey bee,nakoshi gaskiya,kaima kaci"


hannu tasa ta gutsiro wainar takai bakinsa hadawa yayi da hannun nata ya ci,tare da dan cizar yatsanta ,kara tasaki,tare da shagwabe fuska,



"wayyo Allah na,Honey bee,shine ka cije ne gaskiya sai narama"



Dariya tabashi yai sauri ya mike yakoma can nesa da ita,yanai mata dariya tare da kashe mata ido,yunkurawa tayi da kyar zata tashi takasa,dubanta yayi yace,



"inkinisa kitashi cikin second daya ,nikuma natsaya kizo kirama cizanki"


hararar sa tayi,tare da dafa kujera ta mike da kyar tabiyo shi,yanaganin ta nufo inda yake ya mike ,nan suka shiga zagaye parlorn,suna dariya sai da sakeena tagaji dankanta sannan takyaleshi,hade rai tayi ,tare da komawa daki ,ta kwanta biyota yayi tana ganinsa ta dauke kanta,murmushi yayi tare da kama kunnuwansa yace,



"yi hakuri matata,kamal ya wahalar da ke ko,nadena bazan kuma ba"


ahankali tadago da idonta tadubeshi kamar bazatai magana ba,can kuma tadubi hannun dayacijeta tace,


"Honey bee,nide gaskiya sai narama"


murmushi yayi tare da janta jikinsa yazubawa fuskar ta ido,yace,



"Dagaske,ramawa kikeson yi"



kai, kawai tadaga masa,cikinta yashafa tare da kara kansa acikin yace,



"Baby kaji momynka ko,zata ciji dady,nakyaleta ko kar inbarta"



dariya yabata sosai yadda yadage yana magana da babyn cikinta,shammatar sa tayi tarama cizon dayaimata yar kara yasaki tare da dubanta yace,



"shikenan ko,anyi 50 50"



banza taimasa tare da gyara kwanciyar ta,ahankali ya lallabo yazo bayanta ya kwanta nan yashiga lalibar bakinta tureshi tayi ,zip din rigar ta yazuge,tozali yayi da lafiyayyun halittunta ahankali yashiga sarrafasu tun tana tureshi har tagaji ta kyaleshi sai da yagama  narkar mata da jiki ,sannan yaimata rumfa ,kara tasaki ,saboda yadda yadanne mata ciki,ahankali yashiga sarrafata gabadaya yafita a hayyacinsa ,sai da komai yalafa,sannan yadagata tare da mirginawa can gefe yana sauke numfashi,ahankali sakeena tadube shi tace,



"Honey bee,nagaji ,wallahi kana bamu wahala"



dada mirginowa yayi kusa daita yajata jikinsa acikin kunnanta yarada mata magana,dariya tayi tare da cusa kanta akirjinsa,tashi yayi  yahada musu ruwa ,yafito,taimaka mata yayi ta mike da kyar suka nufi toilet,dakansa yaimata wanka shima yayi ,sannan suka fito tare da sa kayan bacci masu kyau ,suka  koma,suka kwanta,fuskar sa sakeena tashafa tare da kiran sunan sa,



"Honey bee"


"Naam matata,yaakayi ko akara ne"


da sauri ta girgiza kanta tare da fadin,



"Aa,da wuya fa,kawai de inason mugodewa Allah bisa sauyin da mukasamu na *zaman aurenmmu* "



"gaskiya ne,matar kamal Allah mungode maka,ai shi *zaman aure* hakuri da juriya yake bukata ko ba haka bane,shiyasa nakewa Allah godiya dayabani mata mai addini da hakuri"



jintayi shiru ne yasashi dada duba fuskar ta ganin tayi  bacci ne yasashi yin murmushi tare da dada gyaramata kwanciyar ta a faffadan kirjinsa yaja bargo yarufe su,



Ahaka rayuwa tai ta tafiya cikin farinciki da kwanciyar hankali,yau tunsafe kamal yafita aiki,bejima da fitaba sakeena na kwance tana bacci ,sai jitayi kamar antsira mata allura a gigice tafarka,nan tashiga sintiri tun tana iya tafiya har ta durkushe gashi ta gigice tarasa inda wayar ta take,







*Jameel*



~~sunkuyar da  kai yarinyar tayi ,tare da komawa daki tana tashi yadubi usman yace,



"Abokina wacece wannan gaskiya ta hargitsamin lissafi"


dariya usman yayi tare da duban jameel yace,



"kanwar Huda ce,munira ,kana ciki kenan"



"sosai ma kuwa ,gaskiya abokina kayimin iso gareta,dan gaskiya naga matar aure"



"angama abokina ,ina zuwa"


tashi usman yayi yanufi dakin Huda aciki yasami munira dubanta yayi yace,



"kanwata inbadamuwa abokina yanason ganinki"


Huda ce ta dago tadubi mijin nata tace,



"yallabai kafasan halin  munira bason kula maza take ba"


"aa Huda,kibarta mana tazo su gaisa,


shiru tayi tare da kallon munira tace,



"jeki kiji"


 

tashi tayi tafita jameel na zaune  yana kallon Tv tashigo murmushi yadada sakar mata tasami guri tazauna suka gaisa yagabatar mata kansa take suka kulla soyayya karshe yaimusu sallama yatafi,


kaitsaye gurin Hajiyar sa yanufa ,yanazuwa yai shaidamata yasami matar aure murna tayi sosai wayarsa ce tashiga ringing dubawa yayi yaga sunan momyn labiba,kamar baze dagaba can kuma yadaure yadaga,



"jameelu labiba ce ba lafiya tahaihu muna asibiti"



"ok gani nan"


mai da dubansa yayi ga Hajiya yace,



"Hajiya wai labiba ce ba lafiya tana asibiti"


"subahanallah to ai sai mutashi muje"



tashi sukayi suka nufi asibitin suna zuwa suka ci karo da momy tanata faman kuka,karasawa sukayi suka shiga tambayar ta ,



"ya mai jikin,ta haihu ne "?



"Tahaihu sai dai danbarai"


kai tsaye jameel  office din likitan ya nufa dan jin abinda yasami labiba  yana shiga yabashi hannu suka gaisa tare da yimasa bayanin abinda yasameta ,fitowa yayi yasami Hajiya yafadamata gawar babyn akabasu ,jameel dayaga babyn sai da yai kuka ,kai tsaye gida suka wuce akaimasa suttura aka kaishi gidansa na gaskiya,labiba kam bata san abinda kefaruwa ba kwanan ta biyar a asibitin sannan tafara dawowa hayyacinta,zaune take tana kurbar ruwan tea jameel da abokinsa usman sukai sallama suka shigo,ido tazuba masa,






*Abdulmalik*




~~cikin sauri likitan yashigo dan duba jikin Abdulmalik allurar bacci akaimasa cikin kankanin lokaci bacci yadaukeshi,


Rabia naganin yasami bacci taiwa mansir sallama tanufi gida dan sanarwa da inna ,kai tsaye gidanta tanufa abakin kofa suka cikaro da inna cikin tashin hankali ta dubeta  



"Rabi,ina Abdulmalik din "


"inna yana asibiti akwance bashi da lafiya,amma yaji sauki"



"subahanallah,rakani gurinsa Rabi,nashige su"


bayadda Rabiia taiya haka suka kuma juyawa asibitin taraka inna tana zuwa taganshi kwance yanata bacci da sauri takarasa gaban gadon nasa ta kamo hannusa tafara sharbar kuka,





*Hafeez*





~~cikin sauri yadubui Ashanty yace,



"Ashanty ga mama ta nan,da yayata ,yanzu ya zamuyi kenan"



"oho kai kasani ,nikam bani da damuwa da hakan sai kasan yadda zakayi"



shiru yayi can wayar sa takuma daukar kara jiki asabule yadaga cikin bacin rai maman tasa tace,



"Hafeez wai mekake  har yanzu baka karaso bane,meyasa kake haka ne "


"mama yanzu zanzo inbude muku"




"uban me zaka bude mana"?



"kofar"



"kai banason hauka bacewa nayi kazo gida kasa meni ba,ko de kafara shaye shaye ne,Hafeezu"



ajiyar zuciya yasauke tare da fadin ,"aa mama afuwan gani nan inshaallah"


duban Ashanty yayi yace,



"tawan ,tashi muje kishirya in saukeki a gida da yamma kijirani"



banza taimasa tanufi daki tasaka kayanta shima ya shirya suka fito atare kai tsaye gida yakaita sannan yanufi gidansu tunda yakarasa yake zabgawa Areefa harara itama hararar sa takeyi zama yayi yashiga gaida mahaifiyar tasa wani banzan kallo tawatsa masa take jikinsa yai sanyi,yashiga rarraba idanu,







*NASEEBA GAWO*✍🏻

[3/19, 10:32] ‪+234 814 620 5819‬: [6:35MA,2017]




*®💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦



     *💦N I G*💦





  *ZAMAN AURE*

      💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦



*NA*


NASEEBA I UBA💐






*Hasbunallahu waniimal wakil*👏🏻








             *34*






~~Tunda kamal yafita hankalinsa yakasa kwanciya gabadaya tunanin sakeena ne yahana zuciyar sa sukuni,duk motsin da yayi sai ta fado masa arai,wayar sa ya dauka yashiga neman layinta ,tana ta ringing bata dauka ba,dada shiga damuwa yayi,mai da dubansa yayi ga abokinsa Adam ,yace



"Adams,bari inje gida wallahi gabadaya hankalina yana kan sakna,Allah yasa de lafiyar ta kalau,abinka da mai tsohon ciki"


dariya Adams yayi tare da duban abokin nasa yace,



"yasalam,gaskiya kam abokina gwanda kaje kadubata kagani,irin wannan gigicewa da kayi haka,ashe yanzu kana son cikin nata,yaakayi haka kuma mutumina"?



dariya kawai kamal yayi ya mike tare da daukar mukullin motar sa ,yafita,cikin sauri ya figi motar tasa ,bewani jimaba ya karasa gida,mukulli yasa ya bude kofar gabansa inbanda faduwa baabinda yake,kai tsaye parlorn ya nufa ya shiga kwala mata kira ,shiru bata amsa ba,daga cikin daki yafara jiyo nishin ta,da sauri yakarasa dakin halin da yaganta aciki ne yai masifar daga masa hankali,da sauri yakarasa gabanta,yana kiran sunan ta,



"Sakeena,lafiya ,ko haihuwar ce"



shiru tayi tare da runtse idonta,takama hannusa ta kankame  ,kasa zare hannunsa yayi saboda rikon datayi masa,cikin sauri ya dauketa yasata a mota,tare da dawowa ya daukar mata mayafi da kayan babyn da suka hada,cikin matsanan cin gudu yafigi mota,kai tsaye asibitin Annury ya wuce da ita,cikin kankanin lokaci aka shigar da ita,dakin haihuwa,kamal dada gigicewa yayi dayaga anrufo kofar andakatar da shi abakin kofa,wayar sa yazaro yakira Hajiyar sa yafada mata,cikin kidima Hajiyar take masa magana,



"Kamalu,yanzu kuna ina"?



"Hajiya muna asibitin Annury,dan Allah Hajiya   kitaho ,sakeena zata mutu"



"Haba kamalu kana haukane ,wace irin mutuwa, daga haihuwa sai mutuwa kanutsu kaji ko,kafadawa ummanta ne?"



"Aa Hajiya banfada musu ba"



"yauwa kar ka fada musu,kar adaga musu hankali, badadi fadar nakuda,gani nan zuwa"



kashe wayar yayi tare da lekawa dakin da sakeena take inbanda salati baabinda takeyi ,baajimaba Hajiya ta karaso kamal yana ganinta yakarasa gabanta tare da share kwallar da ta zubo masa,dubansa tayi tace,



"Haba kamal meye abin kuka addua zakai mata ,tana ina?


" tana wancan dakin ,wallahi Hajiya tana shan wahala "


kan tayi magana sunjiyo ,

wata razananniyar kara  da sakeena   tasaki wacce tajanyo hankalin kamal da Hajiya ,da sauri yakarasa bakin kofar dakin yana kokarin shiga wata nurse ce ta dakatar da shi ,sai da Hajiya taimasa magana sannan yadawo tare da samun guri yazauna,can sai ga nurse din data hanashi shiga dakin takuma fitowa da sauri suka nofota ,dubansu tayi da sakin fuska tace,


"congratulation,

tasauka lafiya,ansami baby boy"



farinciki ne yakama kamal tare da daga hannu yagodewa Allah ,dada dubansu nurse din tayi tace,



sai dai wani hanzari ba guduba,


zuba mata ido kamal yayi dan jin me nurse din zata fada,







*Jameel*




~~Dkewa jameel yayi yakarasa gaban gadon da labiba,take yana daga tsaye suka gaisa da momyn ta, fita tayi tabasu guri,mai da dubansa yayi ga Labiba



"sannu yajikin naki"?


kasa amsawa labiba tayi,tazuba masa ido kawai tana kallonsa,usman ne yakatse mata tunanin datakeyi



"Labiba yajikin naki sannu Allah yakara lafiya"



ahankali taamsa da 


"Ameen nagode"



wayar jameel ce tashiga ringing da sauri yasa hannu yazaro yana dubawa sunan *munira* ne yabayyana a screen din wayar dagawa yayi tare da sakin murmushi



"Hello sweethert ,ya kike,yajin dadi"



labiba dake zaune tana kallonsa suman zaune tayi tare da dada zuba masa ido,sai da yagama wayarsa tsaf ,sannan yadubeta yace,



"labiba mu zamuwuce,ga wannan kirike ko zaanemi wanin abu Allah yakara sauki"


usman ma yabata kudi tare dayimata fatan samun lafiya ,yafita kantaankare jameel har yakai bakin kofa da sauri takira sunansa,



"Jameel!


ahankali yaja yatsaya batare da ya juyo ya kalleta ba,sai da takuma kiran sunan sa,sannan ya juyo suka hada ido,cikin sanyin murya tafara magana,



"jameel dan Allah kayafemin abinda naimaka abaya ,wallahi nayi nadama,bazan kuma ba,kataimaka min kamaidani dakina,jameel kaine rayuwata kaine farinciki na pls"


malalacin murmushi jameel yasaki tare da dubanta yace,




"karki damu labiba,nayafe miki,amma batun komawar ki gidana,kinmakara dan ni ahalin yanzu ma nakusa aure,kema inai miki fatan samun mujin da yafini,batun kuma nine rayuwarki ai bata taso ba dan haka ki manta dani sai anjima,Allah yakareki da lafiya inadada mika godiyata gareki bisa rainon cikina dakikai min dafatan Allah yajikan babyn mmu ameen"



yanagama fadar haka yafita,wani kuka ne ya kwacemata,momy datafita dan bawa su jameel guri ne tashigo akidime dan ganin halin da diyar tata take ciki,cikin kidima tashiga tambayar ta,




"labiba,meyai miki ,maramutuncin yaron nan "



"momy jameel mai mutunci ne ,kidena kiransa mara mutunci ,wallahi momy kincutar da rayuwata,kinrabani da mijina"


momy rasa ma mezatacewa labiba tayi kawai sai tashiga  hada kayanta zata tafi,kuka labiba tasa mata,



jameel ne zaune gaban mahaifiyar sa yana bata labarin matar da yasamu zai aura murna tayi sosai tare da fadin



"yanzu abinda zaayi shine,zanje da kaina insami kawun ka ,infada masa dan bazaai wasa ba"



"Hajiya da wuri haka,mezai hana abi abin sannu ahankali"



"Danmarayan zaki kenan,to kode baauren zakayiba"


dariya yayi tare da shafa sumar kansa ,






*Abdulmalik*




~~kwannan Abdulmalik uku,a asibiti aka sallameshi yadawo gida ,sai da yayi sati guda sannan ya warware yakoma aiki,inna kam ta tura kanin baban Abdulmalik neman auren mariya cikin kankanin lokaci akasa rana duk wannan bidirin daakeyi Abdulmalik betaba zuwa zance gurin mariya ba,amma bata damuba,dan itama bawani sonsa takeba,yanzu haka zaune suke shi da inna suna dan taba hira ,can tanisa tace




"Abdulmalik yakamata kaje kugaisa da mariya kaga biki yanata karatowa ko"



shiru yayi can yanisa yace,




"zanje inna inshaallahu"



yanagama fadar haka yatashi,dan bayason jin zancan wata inba na Ruhaima ba"



da yamma yashirya yaje gidansu Mariya tajima kan tafito,can sai gata ,ido kawai yazuba mata yana karewa halittar ta kallo ja tayi ta tsaya tare da gaidashi a yangace,hade rai yayi sannan yaamsa ,basu wani jimaba yaimata sallama yatafi bin bayan motar sa tayi da kallo,tace,



"zaku shigo hannuna ne,daga kai har innar taka"



haka lokaci yai ta tafiya ranaku suna juyawa suzama sati haka sati yana juyewa yazama wata yayin da wata yake zama shekara,bikin Abdulmalik da mariya yarage saura sati daya inna tanata ta hidima, anfara biki cikin farinciki da jin dadi abangaran ango Abdulmalik kuwa abun bahaka yakeba domin jiyake kamar yakashe kansa ya huta saboda bakin ciki,yau takama daurin aure da kyar yaje daurin auran nasa da tarin abokansa ,anyi komai angama da daddare aka kawo amarya dakinta,







*Hafeez*



~~maman Hafeez ce tadubeshi ranta a mutukar bace tafara magana,




"Hafeezu,meyahada ka da matarka"?



sumar kansa yashafa tare da lumshe ido,dan shi besan mezai cewa maman tasa ba,maganar yayar sa ce takatse masa shirun da yayi



"Hafeez kaifa muke sauraro"




"yaya nibansan abinda naimata ba amma ita tafada da bakinta mana"



maida dubansu  sukayi ga Areefa mama tace,



"Areefa fadi duk abinda kikasan yanayimiki"




nan ta karkace tashiga fadar karya da gaskiya ,sai datagama sannan yadago ya dubeta yace,




"Areefa  kiji tsoron Allah karfa kimanta zaki mutu"




"Rufemin baki Hafeezu baka da gaskiya dan haka kaima kaji tsoran Allah karike yar mutane da amana meyasa baka son zaman lafiya ne wai ,haba,Areefa kiyi hakuri kinji kuzauna lafiya kuyi hakuri da juna"



"inshaallahu mama nagode sosai Allah yakara girma nagode"



"bakomai tashi ka dau matarka kutafi"



tashi yayi suka fita,tunda suka shiga mota yake aunamata zagi tare da harara dubanta ya kuma yi akaro na biyu yace,




"wallahi Areefa kinji narantse bakici bulus ba kubude banzayan kunnuwanki masu kama da kashi kijini


nan da kankanin lokaci zankara aure,dan nikam bazan zauna da fasika ba,mazinaciya kawai"



Arazane Areefa ta juyo takalli Hafeez,cikin zafin nama tasa hannu ta,








*NASEEBA GAWO*✍🏻

[3/19, 10:32] ‪+234 814 620 5819‬: [9:18PM,2018]




   *_®💦💦NASEEBA GAWO_*💦💦💦




        *_💦N I G_*💦





   *_ZAMAN AURE_*

        💦 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦







*_NA_*


*_NASEEBA I UBA_*💐







    *_Rabbi yasir wala taasir Allahumma yasir alaina_*👏🏻




 *_Inabawa masoyan wanga littafi hakuri bisa tsaikon daaka samu na rashin ganin posting dina kwana biyu  hakan yafaru ne bisa wasu dalile da suka haddsa faruwar hakan bisa wanga daliline yasa nafara rubuta sabon novel dina mai suna SANADIN ABOKI,  sakamakon yawan tambayar da ake min ci gaban labari ,zankokarta wajen ganin nakarasa muku labarin  inshaallah, duk zaku dinga ganin  posting din  wanga novels   din guda biyu kullum,bawanda zanajiye da yardar mai kowa mai komai,nasan masoyana zasuce,Naseeba tazama surbajo ne,🤔mai rubuta novel biyu   at one time,to zande jarraba ingani ko zaniya,   faruwar hakan shi yatabbatar min da  ana  mugun tare,karfa ku manta farin cikinku shine naseeba  ismail Gawo_*👌🏻😘







              _*35*_






~~cikin zakuwa kamal ya shiga sauraran abinda Nurse din zatace,dada gyara dan karamin hijjabin ta tayi tace,



"yauwa,agaskiya matarka tana bukatar jini dan tazubar da jini da yawa"



cikin rawar baki kamal yadubi Nurse din yace,


"Haba,Hajiya wani irin jini ,meye amfanin nawa muje adibi nawa asamata,banason narasa matata"



Hajiya ce tadafa kafadarsa tace,



"Dan girman Allah ksmalu kanutsu,wai meyasa haka ne,yata injininsa zaiyi adiba asamata "



"tohm Hajiya badamuwa,kuje agwada agani inyayi dai dai sai   adiba ,amma gaskiya kuyi da hanzari"



"tohm shikenan bari muje"



cikin kankanin lokaci akai komai aka gama,cikin saa jinin su yayai  daidai dakin hutu aka maida sakeena aka jona mata karin jinin ,tunda kamal yai  tozali da Babyn nasu yaji wani farinciki yarufe rungume shi yayi ajikinsa,sai da Hajiya tadubeshi tace,



"Oh ni yasu,yanzu kamalu bakajin kunya kakama da ka kankame da kanason dan kadinga watangaliya da da mahaifiyarsa lokacin datake da cikinsa,banishi nan"


kunya ce takama shi ,yamika mata dan,dada zubawa sakeena ido yayi tana ta bacci tarame sai uban haske datayi,tausayinta ne yakamashi,kankace kwabo,yanuwa da abokan arziki suncika asibitin kowa na yaba kyawun jaririn ,lubna batasami zuwaba,sai yamma ,saboda rigestiration din datakeyi har lokacin Sakeena bacci take,bata tashiba sai wajen 6:30,ahankali tafara bude idonta jitayi cikinta fayau,hannu tasa tashafa,tozali tayi da ummanta zaune da Baby ahannu,ahankali tafara kiran sunanta


"wash,umma cikina ciwo yakemin"


da sauri ta mike ta yo kanta,tare da jera mata sannu,likita aka kira yazo yadada dubata,tare da cire mata robar jinin daakasa mata,nan aka kimtsa mata jikinta aka hada mata tea tadansha,sai yanzu aka mika mata Babyn kunya ce takamata,dakyar takarbeshi ta zuba masa ido kamar su daya da Kamal,ana cikinhaka,sai ga Kamal din yadawo,farinciki ne yakamashi dayaga Sakna ta tashi har ta zauna ,cikin farin ciki yashiga gaisar da ummanta , kasancewarHajiya ta tafi gida  tadawo,fita tayi tabasu guri,cikin farinciki Kamal yakarasa gaban gadon yazubawa Sakeena ido,tare da rungumesu ita da babyn yashiga jera mata sannu,ahankali tadago tadubeshi tace,



"Honey bee,bazan kuma ba,wlh"


dariya ce tasubuce masa,yashiga tambayar ta,


"Sakna bazaki kuma me ba,baki san ribar *zaman aure* shine samun zuria ba,ko kinmanta to bari kiji inbaki labari wasa farin girki ,just the beging inji bature"



shuru tayi tana murmushi,kukan da jaririn  yakeyi ne yaadawo dasu nutsuwarsu dubanta Kamal yayi yace,



 "Maman Baby akulawa Kamal dansa mana,kidanbashi yasha "


shagwabe fuska tayi tace,



"Nide gaskiya baniya ba,kuma fa dazafi wallahi dazu baka ji zafin danaji ba"


hade rai yayi tare da dubanta  yace,



"ni naiya ai ,bari kigani"



Babyn yakarba yakara mata shi ajikinta , cikin sauri kuwa jaririn yakama yaitasha ,sai da yakoshi sannan ya kwantar dashi,



dariya abin yaso bawa Sakeena ,Kamal sai rawar jiki yake dasu,lallai ta yarda *zaman aure* dan hakuri ne,


kwanan ta biyu aka sallamosu,kai tsaye gidansu aka wuce,daita.





*_Jameel_*




~~Kuka sosai Labiba take yi ,Momy kuwa bata fasa hada kayantaba,zuwan mahaifinta ne yasa ta dakata  ta hakura da tafiyar da zatayi nan yashiga yimata fada,



"Haba, Hajiya Zainab akan me zaki biye mata,baki tausaya mata halin datake ciki,meyasa kike haka ne ,ku wallahi mata wani lokacin baku da nisan tsinkaye wallahi,to yanzu inkika tafi  kika barta wa zai kula da ita , tambayar ki nake"?



shiru tayi tana sauraran fadan  da mai gidan nata yake yi can tanisa tace,


"Haba Alhj,sai kace kamanta halin labiba,wallahi yarinyar nan daka ke gani tana da damuwa fa ,halinta sai ita,bakaji magan ganun datadinga fada min ba dazu"



"Naji ai hakuri ake shi dama mara lafiya ai sai kabishi asannu, kide zauna ki kula daita da me zataji ne wai haba"


Labiba de inbanda sharar kwalla baabinda take,dan sai yanzu tada tabbatarwa da kanta irin  son datakewa Jameel,kwananta 14 aka sallamota,suka dawo gida,



kullum cikin kunci zuciyar ta take,aranta take dadin,


_lallai duk matar data zalinci mijinta a_

*zamantakewar aure* kanta ta cutar yau gashi tarasa farincikin rayuwa,



kamar yadda Hajiyar Jameel tafada ,anaika gidan su Mnira nemawa Jameel auranta ,iyayanta sun amince,ankai kudi hade da sa rana ,murna gurin Jameel baamagana ,bayan yadawo daga aiki ne,kai tsaye gurin Hajiyar sa ya wuce,tana zaune, tana lazimi yashigo tare da samin guri yazauna,sai da tagama sannan tadubeshi da faraa kwance kan fuskar ta tace,



"Dan marayan Zaki andawo,yaaiki"



" yauwa Hajiyata Nadawo aiki angode Allah sannu da gida"



"yauwa ga abinci inzaka ci"


kan yabata amsa

wayarsa  tashiga ruri ,hannu yasa a aljihu yazaro ta,kan yadaga ta katse,dubawa yayi yaga mai kiran nasa Murmushi  yasaki mai dan sauti wanda yajanyo  hankalin Hajiya  ,dubansa  tayi tace,



"kai dawaye kake murmushi saikace wani sabon ango"



"Haba Hajiya ai sabon angon ne,Munira  ce"



"Hmmm,Allah sarki ,yauwa yakamata kafara gyaran gidanka,kuma afara hado lefe,kaga bawani lokaci aka sa mai yawa ba"



"To,shikenan Hajiya inshaallahu zaayi"


Nan suka cigaba da hirarsu irin ta d'a da uwa,Jameel jinsa yake kamar wani sabon mutum tunda yarabu da Labiba,komai nasa yadawo daidai.






*_Abdulmalik_*




~~Kai tsaye dakin Inna aka fara kai Mariya,inna kamar tahadiye ta dan murna,nan tai mata nasiha ,suka fito da ita,aka kaita nata dakin wanda yasha kayan daki dai dai gwargwado,yan kai amarya suka watse,aka bar amarya ita kadai,sai faman raba ido  take,ango yana can kwance,a gurin abokinsa,yanata fama  dashi yataso yarakashi,yaki ,dubansa abokin yayi yace,



"Abdul tunda kaki ,tashi inrakaka ko, ,to dan bani guri inason inkwanta dan bacci nakeji wallahi"



"oh! korata ma kake yi nagode, Allah yasa nima  inada makwanci "


"kwarai kuwa,wanda ma yafi nawa,mutumin dayake da sabuwar amarya ina zaahada shi da gauro"


cewar abokin nasa yafada ,yana dariya kasa kasa,


cikin fushi Abdulmalik ya dau babbar rigar sa da wayoyinsa ya fita,dariya ma yabawa abokinnasa ,


sanda yakarasa gidan, da inna yacikaro tafito daga dakin Mariya  wata uwar harara ta watsa masa tace,


"Sannu Abdulmalik sai yanzu kaga damar dawo wa,ko? sai kace ba mai sabuwar amarya ba yayi maka kyau"



"inna kiyi hakuri kaza ce bansamuba,ahaka ma sai hakura nayi bansiyo ba"


"eh ai baka so kasamuba inbanda kafara raina ni ko ince dama bason zabin danai maka kakeyi ba,tun yamma baka sai kazar ba sai yanzu"



shide shigeta yayi yanufi dakin nasu, yabarta tanata mita,adaki yasami amaryar tasa zaune abakin gado luldibe kamar ko wacce amarya,tsayawa yayi ajikin mudubi yace,



"kibude fuskar ki kiji abinda zanfada miki


mamaki ne yacika Mariya domin kawayanta sunyi aure sunbata labarin yadda ango yake zumudi kan amaryar sa  sai ga nata angon yazo da wani sabon salo,shiru tayi 

kamar bataji shi ba.





Ruhaima kuwa tunda  tagama idda manyan masu kudi sukai mata caa,amma taki yarda takula kowa,ummin tace tasa ta gaba tai taimata fada  da nasiha,da haka ta hakura tacire Abdulmalik  aranta tafara kulasu ,duk cikinsu hankalinta yafi kwanciya da Alhj Faisal ,Matar sa ce tarasu wajen haihuwa,matashin dan kasuwa ne,cikin kankanin lokaci aka kawo kudi tare da sa rana.




*_Hafeez_*






~~sitiyarin motar Areefa ta kama da hanyanta tasaki ihu tare da fadin



"Wallahi Hafeez kayi kadan kaimin kishiya ,kai din banza da wofi,sai dai inkashemu kowa ya huta,mugu azzalimi"


cikin zafin nama yadauketa da wani wawan mari tare da ture hannunta gefe,



"Areefa kina hauka ne,ko kuma kinfara shan kayan maye ne,to wallahi ki kiyayeni ki maida hankalinki kina jina ko"



"Eh, Hafeez hauka nafara amma irin wanda kakeyi kuma maganar shaye shaye  dakake fada inhar inayi ai kafi kowa sani,mugu kawai wanda besan hakkin *_zaman aure_* ba"



"eh ai naga ke kinsan hakkin

*_zaman auran_* ko? shashar kawai"



ahaka de suka karasa gida,cikin masifa da fada kamar ba mata da miji ba, yanayin parking yafito yabarta yanufi cikin gidan kai tsaye dakinsa ya wuce,ya sawa kofarsa key yabarta a parlor tana ta zage zage,wanka yayi, yai shirin baccinsa tsaf ,nanan yadau wayarsa yashiga waya da Ashanty sunjima suna hira kafin suyi sallama yakashe wayar yai baccinsa,


Areefa kam bacci gagarar idanunta yayi sabida ya dda takejin zuciyar ta kamar tafaso kirjinta tafito,ahaka ta kwana tana sake saken matakin dazata dauka akan Hafeez.









*_NASEEBA GAWO_*✍🏻

[3/19, 10:32] ‪+234 814 620 5819‬: [8:41Am,2018]




*_®💦💦NASEEBA GAWO_*💦💦💦



     *_💦N I G_*💦




  


  *_ZAMAN AURE_*

        💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦





*_NA_*


*_NASEEBA I UBA_*💐







*_Allahumma afini fi badani allahumma afini fi basari allahumma afini fi sam'iallahumma ihfaz min baina yadayya wamin kalfi waan yimani,waan shimali_*👏🏻







             *_36_*




~~Kulawa sosai Sakeena take samu daga gurin ummanta haka a bangaran Kamal kullum yana gidansu,gurin jaririn nasa,tare da musu hidima kamar baya jin kudi,ranar suna yaro,aka rada wa jaririn suna, khalid,anyi taro lafiya anci ansha ,Hajiyar su Kamal tayi hidima,nan aka cigaba da kula da mai jego da danta, kamar ko wacce yamma, ankaiwa Alhj Bashir jaririn yaganshi  tare da sa masa albarka,   mai da dubansa yayi ga Kamal yace,


"

Kamalu Allah yaraya abokina ya albarkaci rayuwarsa,kaga de kazama Baba du Allah,ka maida hankalinka kaji ko"



sunkuyar da kansa yayi kasa tare da shafa keyar sa yace,



"inshaallah Abba  zankula"



 Murmushi Mama tayi tadora da,



"Alhj kaga aboki ka kankameshi,to bani nima inganshi"



dariya suka sa gaba dayansu,Babyn bejima ba aka maida shi,



  ,Kamal ne zaune adakin da aka warewa Sakna, hannunsa rike da Khalid,yanai masa wasa kamar  wani me wayo,can yadago ya kalli Sakna yace,



"matar Kamal,yakamata fa kudawo gida kuma haka,dan gaskiya antakura ni da yawa anmaidani gwauran karfi da yaji"



shagwabe fuska tayi tare da turo baki gaba tace,



"Haba dan Allah Honey bee bafa nayi arbain ba"



cikin tsananin mamaki yadago suka hada ido,sauke kanta tayi kasa,cikin wata kasalalliyar

 murya yace,



"oh! ke yanzu jira ma kike yi, kiyi wani arba'in,cab wasa ma kenan to ai kafin sannan nagama mutuwa"



dariya yabata,dajin furucin nasa,dada zuba mata ido yayi take yaji wani alamari na ziyartar gan gan jikinsa,cikin sauri yafara jan numfashi,ahankali ya kwantar da khalid a cikin dan gadonsa,gefanta yadawo yajata zuwa jikinsa,cikin zakuwa yafara shafa gadon bayanta,hannun sa yakai kan zip din rigarta zai zuge da sauri takama hannusa tarike gam ,dagowa yayi ya zuba mata idanunsa da suka rine suka zama jajaye cikin wata iriyar murya yace,



" me kuma haka? yanzu sakna bakijin tausayin mijinki ko? yaushe rabon da inji dumin jikinki, ko kina son inje innemi matan waje ne?"



yafada yana tsareta da ido,ahankali ta girgiza masa kai alamar aa,muryar ta na rawa tace,



"Honey bee,wlh tsoro nakeji kar inkuma samun ciki,kuma...



kan takarasa maganar yatoshe mata baki danasa nan yashiga tsotsa kamar wanda yasami alawa yayi nisa ,ya kuma shgala kawai saijin muryar umman Sakeena sukayi.






*_Jameel_*





~~Haka rayuwar labiba tai ta tafiya cikin kunci da bacin rai tare da tunanin tsohon mijinta Jameel,yau tun safe take shiri zata fita,Momy na kallanta tazuba mata ido,tagama shirinta tsaf tacaba   kwalliya kamar mai shirin zuwa gasar kyau,dad'a dubanta Momy tayi tace,



"ke kuma,ina zaki haka"?


"Momy zanje gidan Khadija ne fa"



baki ta tabe,tare da kawar da kai gefe tace,



"sai kindawo,kar kuma ki dade"



shiru Labiba tayi kamar batajita ba tasa kai tafita,


tana fita ta tsare adai daita sahu,ta

 hau,tun fitowar ta wani Alhajin birni ya ganta bayan adai daitan yabi dan ganin yacimmata, kaitsaye gidan jameel ta nufa dauke da addua abakinta ,




cikin kankanin lokaci hidimar bikin jameel ta kankama, ankai lefe, nagani na fada,kamar mai shirin yin auran fari,biki yarage  saura sati biyu,



tun yamma Jameel yake zumudin zuwa wajen Munira,yana tashi daga aiki yakoma gida yai wanka tare da caba ado,sanye yake da shadda multi colour,tai masa mutukar kyau,sai kamshi yake zubawa,wayarsa ce tahau ruri da sautin kida mai dadi,hannu yakai kan mudubi,wanda ke daure da agogo silver da zoban azurfa,ahankali yakara wayar a kunansa,yace,



"Hello bride 2be"


dariya tayi har sai da yajiyo sautin dariyar tata

ta  muryar ta mai dadi tace,


"Hello Groom 2be "


"Au ramawa kikayi to  shikenan nagode yaakayi"?



cikin shagwaba tare da karyar da murya tace,


" nifa ba ramawa nayi ba,kafasa zuwa ko"?


kwaikwayar muryar ta ta yayi yace,



"Banfasa ba,mekika tanadar wa angon naki"


"shine kake kwai kwayata ko,shikenan nafasa fada maka abinda zanfada"



dariya yayi tare da bata hakur,karshe sukai sallama yakashe wayar,mukullin motar sa ya dauka yanufi hanyar waje dan  tafiya gurin sahibar tasa,


fitowarsa tayi dai dai da zuwan Labiba,da sauri ta sallami mai adaita ta,takaraso inda Jameel yake,haka Alhajin nan yana cikin mota yana kallonsu,





*_Abdumalik_*



~~cikin dakakkiyar murya Abdulmalik yacigaba da fadin,



"Dafarko inai miki barka da zuwa gidana ,sannan inai miki murnar samun nasarar auran gangar jikin Abdulmalik,nasan kinsan komai game da aurena da ke ko?bakya bukatar karin bayani saboda haka sai kisan yadda zaki tsara *_zaman auranki_*"



ita de tana zaune tayi shiru saboda d'unbun mamaki ,ahankali tasa hannunta dayasha zanan  kunshi ,ta yaye mayafinta tare da dagowa ahankali ta kalleshi dan murmushi tayi tace,




"Hmm,Allah sarki ango,to ai Mariya ma bawani sonka take ba,kawai mun taimakawa tsohuwa ne,dan haka kar kadaga hankalinka akaina shi *_zaman aure_* ai kamar karatu ne,wanda yaiya allonsa ya wanke"



mamaki yashiga yi sosai dajin furucin nata,basarwa yayi ya nufi dakinsa yabarta,itama shirin kwanciya tayi ta kwanta,da safe inna ce tayo musu break fast,taajiye shi a dakinta,Abdulmalik kuwa,da sassafe yafito da shirin sa tsaf na fita,dakin inna ya nufa tana zaune da kayan abinci agaba,guri yasamu ya zauna suka gaisa,dubansa tayi tace,



"Aa Abulmalik yanaganka kai kade ina Mariyar "?



kamar bazai amsaba dan besan mezaicemata ba can yagyara zaman hularsa yace,



"Tana daki"



"kamar yaya tana daki,ba tare kuka kwana ba ne"?



jin tambayar tata yayi kamar saukar aradu,dan sunkuyar da kansa kasa yayi ,dan bashi da amsar da zai bata,anahaka sai ga Mariya ta fito,sanye take da riga da zani na atamfa ta tsiro daurin dankwali,inna tana ganinta ta hau washe baki,daure fuska Mariya tayi tasami gefan innar ta zauna ,kamar bazata gaisheta ba,can kuma tanisa tace,


"inna antashi lafiya"



jikin inna na rawa tare da washe hakoran da suka dafe da goro tace,



"lafiya lau yata,ya bakunta,dafatan de bawata matsala"



"lafiya lau,wace irin matsala kuma inna?,dagayin auran,Allah yaimana katangar karfe da matsala"



Ameen diyar albarka ai dama baafatan ta"


Abdulmalik de yana zaune mamaki yagama kashe shi,inna ce takatse masa tunanin dafadin,


"Mariya ga abun karyawa bisimillah "



"ya tsine fuska Mariya tayi,tare da duban inna tace,



" Inna gaskiya bazan iya ciba,saboda ni ba abincin kowa nake iya ciba"


shiru inna tayi ta zubawa Mariya ido  amma sam bataga laifintaba,haushi ne yakama Abdul malik yatashi yafita batare da  yayiwa innar tasa sallama ba,aransa yake fadin _kindakko ruwan dafa kanki_





*_Hafeez_*






~~da safe Hafeez yagama shirin sa tsaf,ahankali yabude kofar dakinsa,da Areefa yai tozali kwance kan kujera tanata sharar bacci wani murmushi ne yasubuce masa,ya shigeta yai tafiyar  sa,kai tsaye gidan wan mahaifinsa ya wuce,yai saa kuwa yasameshi bayan sungaisa ne yadada gyara zama yace,



"Baffa dama wata muhimmiyar magana ce takawo ni gurinka"




"inajinka Hafeez,Allah de yasa lafiya"




"lafiya kalau,Baffa,ina son zankara aure ne,shine nakeso anema min auran yarinyar"




"To,ai babu matsala,Hafeez,

Maman taku tasan da maganar auran naka"?



"Eh Baffa tasani"




"mashaallah babu damuwa zanje ,sai kaimin kwatancan gidan su Matar"




"To,shikenan Baffa nagode Allah yakara girma"


nan yaimasa sallama yatafi tare dayimasa alheri,kai tsaye gidansu Ashanty ya wuce,



nan suka sha hirarsu,tare da fadamata zai aiko neman auranta,wata shu,umar dariya tayi irin tasu ta yan duniya,



Areefa kuwa sanda ta farka da sauri ta tashi ta nufi dakin Hafeez,abude taji dakin da sauri ta kunna kai ciki,abun mamaki baya ciki,da sauri ta nufo harabar gidan,gani tayi babu motar sa,wani mahaukacin ihu tasa,tare da zabarar mayafi tafita,










*_NASEEBA GAWO_*✍🏻

[3/19, 10:32] ‪+234 814 620 5819‬: [7:55PM,2018]



*_®💦💦💦NASEEBA GAWO_*💦💦💦



     *_💦N I G_*💦






*_ZAMAN AURE_*

       💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦




*_NA_*


*_NAEEBA I UBA_*💐






*_Allahumma salli ala sayyadina muhammadin wasallim_*👏🏻






             *_37_*




~Cikin sauri Kamal yacika Sakna tare da gyara mata zip din rigarta,cikin inda inda taamsa kiran da Umman  ke mata,


"Naam Umma"



"zo kidaukarwa Kamaluddeen ,abinci Hajir har yanzu shiru bata dawo ba"


to,Umma gani nan"


kafe ta da ido kamal yayi,tare sakar mata murmushi,dauke kanta tayi ,tafita tana dariya,motsin da Khalid yayi ne yasa Kamal tashi daga inda yake yakarasa gaban gadon Babyn, yasa hannu ya dakko shi,tare da komawa bakin katifar yazauna kuka yafara yi tare da neman Nono,ahankali yasa masa lebansa  a baki cikin sauri yakama yashiga tsotsa,ahaka sakna tashigo tasameshi, tare da ajiye tray din hannunta zama tayi a gefansa ,tazuba musu ido,can tanisa tace,



"Honey bee,baka tsoron yayima tunbud'i"



mikamata Babyn yayi ,tare da sa tissue yagoge bakinsa yace,


"Badamuwa ai ana tare ko Born boy, da Allah yi kibashi yasha banason jan rai"



ashagwabe takalleshi tace,



"Honey bee,wallahi yaron nan naka tsotsone dashi,ka duba fa kaga yadda nabi na rame nide..."



ido yazubawa bakinta harta kai aya,zata kuma dorawa kenan ya katseta ,



"Haba Sakeena yanzu dan kina shayar min da d'a shine zaki sani gaba kina mita,ok badamuwa,abinda nake ganin zai zamar mana masalaha shine,kifadi nawa zanbiyaki kishayar min dashi cikin kwanciyar hankali"



da sauri tadago da kanta ta kalleshi ,shima kallonta yacigaba dayi ,danjin amsar da zata bashi,



cikin kwanatar da murya tadubeshi tace,




"Afuwan Honey bee,wallahi bahaka nake nufi,amma innabata ma rai Allah ya huci zuciyarka"



"Ameen,zuba min abincin inci,sauri nake zanwuce gida,kuma kizama cikin shiri nan da ranar assabar zaki koma"


shiru tayi masa dan tafahimci yabirkice yanzu data kulashi zasu yi kaca kaca aranta tace,



_Zaman aure kenan sai hakuri_


abincin tazuba masa tare da tura masa gabansa,dauke kansa yayi cikin dakewa yace,



"Au abincin ma bazaki sami damar baniba,da kaina kikeso naci ko me?



hannu tasa tadauki cokalin tashiga bashi abaki ,ahaka har ya koshi,kudi yaajiye mata ,yamike zai tafi,ahankali takira sunan sa,



"Abu khalid"


dadine yakamashi  yace,


"Sakeena,yaakayi"?



"pls kayi hakuri kaji,inshaallah bazan kuma ba"



"karki damu yawuce,ki kularmin da Born boy"


yanagama fadar haka yasa kai yafita,shiru Sakna tayi tana mamakin hali irin na kamal.




*_Jameel_*





~~Dauke kai Jameel yayi yasa hannu yabude motar sa,dasauri  tasa hannu ta dakatar dashi, tare da kiran sunansa,



"Yaya Jameel"



haushi da mamaki ne suka kama Jameel cikin daure fuska yace,



"Yaakayi"?



shiru tayi saboda yadda yaimata kwarjini can tanisa tace,



"Dan girman Allah da mamzansa kayi hakuri kayafemin wallahi nayi nadama  kadawo dani dakina inshaallah zaka sameni mai mutukar yima biyayya"



murmushi yayi mai cike da takaici ko na kinma rainawa kanki hankali yace,



"Labiba ai kinbar kari tun ran tubani,atakaice de ina mai tabbatar miki da kin makara dan ayanzu haka saura sati daya bikina da matar danake fatan yimin biyayya tare da *zaman aure* bisa gaskiya da amana,saboda haka kukara hakuri ga wannan kibawa Abba ko zai sami halatta ,sai anjima ko?



shigewarsa yayi cikin mota yai tafiyarsa yabarta tsaye da katin daurin auransa a hannu,kasa dubawa tayi saboda fargaba,sai da kyar tasauke idanunta kan iv din kamar amarfaki taga sunan jameel da wata ba ita ba,wata razananniyar kara tasaki take ta sulale kasa,cikin matsanancin sauri Alhjn nan yanufo gunta,tozali yayi daita numfashinta nasama da kasa wasu mata ya kira akidime suka taimaka masa aka sata a mota,har yazagaya zaishige motar ya hango jakarta komawa yayi yadauka kai tsayecasibiti yanufa daita,


Jameel kuwa bezame ko ina ba sai wajen su Munira nan suka zauna a sittroom din gidansu ,suka sha hirar su mai cike da so da kauna katin bikinsu ya mika mata,hannu tasa tare fuskar ta dariya tabashi saboda yadda take jin kunyarsa kallonta yayi yace,



cab,naga ta yadda zaai wannan  *zaman auran*matar  najin kunyar mijin"



dariya kawai takuma yi tare da karbar katikan da yakawo mata,sallama sukayi yatafi cike da begenta kai tsaye gurin Hajiyarsa yawuce nan yabata labarin zuwan Labiba murmushi tayi tace,



"Ai Danmarayan zaki  arayuwa karka sake ka dau hakkin mutum,gashinan alhakinka yahana rayuwar ta sukuni,Allah de ya kyauta"



"Ameen Hajiyata"

nan suka cigaba da hirarsu gwanin shaawa .






*Abdulmalik*






~~yadda inna tadafa  abincinta haka Mariya da Abdul maleek suka barmata,kitchen Mariya tashiga tadafa abincinta mai rai da lafiya,takammala tsaf parlor tadawo tazauna taci ta koshi,ta maida kwanikan kitchen kenan sukai karo da inna tafito daga kitchen din ,wani kallon banza ta watsawa inna sannan tace,



"inna nazaci nan kitchen dina ne"?



dasauri inna tabata amsa da,



"Kwarai kuwa yata nakine,dama nazo tayaki aikine"



"nagode dakika san nawa ne,to,gaskiya inna bana bukatar kina shigomin kitcen ,gaskiya banso in wani abun kike bukata kimin magana zan dakko miki in har da halin yin haka"



batajira cewar ta ba tarufo kitchen dinta takoma daki tai kwanciyar ta,inna kuwa suman tsaye tayi ,karshe taja jikinta takoma daki tana juya kalaman mariya aranta,




sanda Abdul  malik yadawo Mariya taimasa girki mai rai da lafiya ta jere masa adakinsa,yana  shigowa yai tozali da kayan abincin dauke kansa yayi yawuce bedroom nan yacire kayan jikinsa yashiga toilet ya watsa ruwa,bejima ba yafito,a nan yai tozali da Mariya dubanta yayi rai abace yace,



"lafiya de ko? yaakayi?




rau rau tayi da ido ,zatai kuka tayi kalar tausayi dubanta yayi take yaji tausayinta yakamashi cikin shashshekar kuka tace,




"Sweet Abdul dan Allah kadaure kaci abincin dana dafa maka kaji ko kadanne"



shiru yayi yana sauraran ta,tsane sumar kansa yayi da  dan karamin towel yace,




"naji zanci ,bani guru insa kaya tukunna"



fita tayi tabashi guri nan yashirya tsaf cikin milk din jallabiya a parlor yasameta zaune tana murza dan tsanta ,zama yayi

 a kan carpet ,cikin sanyin jiki ta sakko ta zuba masa abincin ,ta tura masa gabansa,ahankali yace,



"sannu nagode"



bata amsaba,ita adole yaji tausayinta cikin nutsuwa yai bisimilla yafara cin abincin yayi dadi ba  laifi dagowa yayi yakalleta yace,



"kinzubawa inna abincin"



da sauri ta dubeshi tace,



"Nazuba mata ,itace ma farko"


"yayi kyau ke kinci ne"?



"Aa,nakoshi"



"me kikaci? dazakice kinkoshi matso muci"



ahankali tamatsa suka fara ci,tanayi tana kallon sa ahaka har suka gama ta kwashe kwanikan takoma daki tai wanka tsaf tafito tasa kayan bacci,ta kwanta,amma tsoro yahanata runtsawa abangaran Abdul malik kuwa gaba daya yakasa bacci domin yau yakai makura yana bukatar mace akusa dashi duk yadda yaso ya daure kasawa yayi,ahankaki yamike tare da fitowa daga dakinsa kai tsaye dakin Mariya yanufa ahankali ya tura kofar dakin yashiga dakin duhu,bedroom din yakarasa ahankali yakarasa bakin gadon yatsuguna agabanta yazubawa fuskar ta ido,tunda yashigo taji wani matsanan cin tsoro yakamata ,ta runtse ido,ahakali yakai hannu yashafa fuskar ta,wata razananniyar kara tasaki dasauri yasa hannunsa yarufe mata baki,



inna kuwa tana zaune tazuba uban tagumi saboda azababbiyar yunwa,






*Hafeez*




~~Areefa tana fita kai tsaye gidansu tawuce,tana zuwa ta tarar da yayar ta tazo,suna ta hira da mahaifiyar su,cikin matsanan cin tashin hankali tasaki kuka ,hankalinsu ne yatashi nan suka shiga tambayar ta ,da kyar ta saurara da kukan tai musu bayanin auran da Hafeez zaiyi,cikin bacin rai mahaifiyar tasu tadubeta tace,




"shine me? dan Hafeez zaiyi aure,au ke da kina tunanin zai zauna dake ne ke kadai,to kin yaudari kanki,kuma wallahi kika yadda kika kashe auranki to bede gidannan ba ,sai dai kinemi wani gidan sha sha kawai"




"umma,dan Allah kiyi mata a hankali,ke Areefa kiyi hakuri kinji shifa *zaman aure* dan hakurine"



nan de sukai mata nasiha karshe taimusu sallama ta koma gida tun daga wannan ranar tashiga hankalinta sai dai kash tamakara Hafeez yayi nisa wajen neman auran karuwar sa,



kwanace suke tayi lamo a jikinsa ,yana ta danna waya,can wayar tahau ruri sunan my love ne yafito a jikin screen din da sauri ya kalli Areefa ,wacce takafe shi da ido,basarwa yayi yadaga kiran,



"zankiraki zuwa anjima"



kawai yace yakashe wayar sauraron haukan dazataimasa yakeyi sai yajita shuru yana dada kallon ta yaga tayi bacci dada janta yayi jikinsa ya rufeta da bargo ,wayar yakuma dauka yakira budurwar tasa suka sha hira sai wajen 1:30 sukai sallama ya gyara kwanciyar sa ya kwanta mamakin Areefa yakeyi yadda tayi sanyi .












*NASEEBA GAWO*✍🏻

[3/19, 10:32] ‪+234 814 620 5819‬: [4:32PM,2018]




*_®💦💦💦NASEEBA GAWO_*💦💦💦


      *_💦N I G_*💦





   *_ZAMAN AURE_*

        💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦





*_NA_*


*_NASEEBA I UBA_*💐





*_Hasbunallahu wani imal wakeel,lahaula wala kuwata illa billah,subahanallah walhamdulillah_*👏🏻







             *_38_*






~~Kamar yadda Kamal yafada Sakeena zata koma  ranar Assabar,tofa rana bata karya,yau tacika kwana arbain cif,tun dare tafara shirin komawa dakinta ,anmata kitso kananu kafar ta da hannunta sunsha kunshi,zaune take gaban mahaifinta gefansa umman tace,yana dada yimata nasiha tare da kara hakuri kan *_Zaman aure_* shiru tayi tana sauraron sa,har ya kammala tare da sa mata albarka,mahaifiyarta, ma tadorata tata,hawayen datake dannewa ne suka rinjayi idanunta suka shiga ambaliya a fuskar ta,karshe ta tashi takoma dakinsu,nan tacigaba da hada kayanta,karfe 7pm Kamal yakaraso kofar gidan nasu,gabanta ne ya yanke yafadi da kaninta yafada mata zuwansa,bejimaba sai gashi yayi sallama yashigo gidan a tsakar gida yatsaya suka gaisa da ummanta tare da yimata godiya,alheri yaimata sosai, nan kannan nata suka fitar mata da kayanta zuwa mota,Khalid yakarba a hannun Hajir ya fita zuwa mota,Sakeena kuwa tadade kan tafito sai da umma taimata dagaske sannan tafita ,ransa yadan baci amma da yatuna yau ango yake ,sai ya basar,dakansa yabude mata murfin motar tashiga yajasu suka kama hanya,tun a hanya yashiga tsokanar ta,




"My dear,yaufa kishirya dan Kamal ango yake,sai anbiya bashin kwana arbain,danhaka ma bari intsaya insai kazar siyan baki ko"?




yakarashe maganar yana kashe mata ido,kau da kanta tayi gefe,batare aatace masa uffanba,cikin kankanin lokaci suka karasa gida,

a parlor Sakeena tarakube kamar ba gidanta ba,ya kula daita tsab,shi dariya ma take bashi,kazar da yasiya musu ya bude ,yafara yaga,yakai mata bakinta,kau da kai tayi gefe,dariya yayi sosai sannan yace,




"cab yarinya gwanda kibude bakinki ma kici dan baabinda zanfasa"




Ashagwabe tadubeshi tare da nuna masa Khalid dake kwance kan cinyarta tace,



"Honey bee,Born boy fa yanajinka dan Allah kabari kaji,ni wallahi tsoro nakeji "



takarashe maganar kamar zatayi kuka dada matsawa yayi kusa daita ,har sunajiyo numfashin junansu,kamar mai rada,yace,



"My dear kiyimin afuwa mana ,kibani hadin kai wajen karbar hakkina ko kinaso inrasa raina"?




girgiza masa kai tayi alamar aa,dariya yayi tare da shafa sajen fuskarsa yace,


"that is good,dan haka yanzu tashi muje inrakaki daki kiyi wanka kishirya"



jaririn yadauka yanufi dakin baccin su dashi,yakwantar dashi acikin gadonsa,da kansa yashiga toilet yahada mata ruwa wanka yafito rike da towel a hannunsa,mika mata yayi yace,



"oya,kicire kayanki kishiga kiyi wanka"



karba tayi taajiye gefan gadon,tafara kokarin cire kayan ta yana tsaye yana kallonta tacire tsaf wani yawo yahadiye ,tare da karasawa kusa daita,yasa hannu yafara kokarin balle mata bra dafe hannun nasa tayi ,akunne yarada mata magana dariya tayi,ta daura towel din tanufi toilet ,kasa jurewa yayi ,yabita cikin toilet din,tare sukai wanka sunjima kan su fito, towel daya suka shiga dashi sauri tayi ta daura wanda tashiga dashi tafito tabarshi ciki tana dariya,nan yashiga kiranta,



"Sakeena miko min towel"


"Babu,kafito haka"



tafada tana dariya,dada kiranta yayi,sai data tasa rigar bacci sannan ta mika masa najikinta,hadawa yayi da ita yarungume sannan ya daura ,suka fito,kai tsaye kan gadon suka zube,nan yashiga shafa koina najinkinta,tare da saka bakinsa cikin nata yashiga tsotsa,ahankali yafara fidda numfashi da sauri da sauri kidimata yayi nan tashiga mayar masa,sungama shagala a farantawa junan su rai,gabadaya Kamal yagama kidimewa ,kamar yadda yafada yau ango yake,to tabbas yakwashi gara a jikin matarsa,be barta ta runtsaba sai wajen 1:00 sannan bacci barawo yadebesu yana rungume ajikinta kamar wani karamin yaro.









*_Jameel_*





~~Tunda wannan Alhajin yadauki Labiba bata motsa ba,ahaka har suka karasa asibitin mai tsananin kyau da tsada,cikin kankanin lokaci aka shigar da ita wani hadaddan daki,akashiga dubata allurai akaimata tasamin bacci yadda zata sami hutu sosai, yana zaune yazuba mata manyan idanunsa,sai sake sake yake aransa,tunawa yayi da jakarta a mota,ya mike a hanzarce,yafita zuwa mota yadakko jakar tata yadawo,wayar ta yadakko yashiga laliban numbobin mutane,cikin ikon Allah yaga sunan Momy,dannawa yayi cikin ikon Allah tafara ringing ,sai da takusa tsinkewa sannan tadauka ,



"Hello Labiba,ina kika tsaya ne"?



"Momy barka da warhaka,amm dama tadansami matsala ne,yanzu haka ma muna asibiti,sunana Alhj  Sagir"



"subahanallah ,bawan Allah wane asibutin kenan"?



kwatanta mata yayi,sukai sallama yakashe wayar ,cigaba yayi da kallonta cikin kankanin lokaci saiga Momy ta iso nan yagaidata tare da yimata karin bayani shiru tayi can tanisa tace,



"Nagode sosai Alhaji Allah yasaka da alkhairi o ni yasu"



ahankali labiba tafara bude idonta dukkansu kanta sukayi ,suna kallonta hannunta Momy takama tafara yimata sannu



"Sannu Labiba yanzu meyake damunki"?


  ,Muryar sa ce tasa Labiba juyowa ta kalleshi kawar da kanta tayi dan yanzu ta tsani ganin fuskar ko wane da namiji inba Jameel, 


shiru tayi masa kamar bataji shi  ba,fita yayi sai gashi da kaya fal katan katan din ruwa da lemo tufa kaji ,Momy baki tasaki tana kallonsa tare da yimasa godiya tundaga wannan rana yashiga hidima da Labiba,kwanan ta biyu aka sallameta kullum cikin kuka take haka befasa zuwa gidan suba ,tun bata kulashi har tafara saurararsa,



yau aka fara bikin Jameel da Munira ,hidima akai sosai anyi diner  ango da amarya sunyi kyau gwanin shaawa,washegari aka tashi da daurin aure,ana daurawa Jameelyakira layin Munnira sai data takusa tsinkewa sannan ta dauka,



"Hello Amaryar Jameel,yau Allah yacika mana burinmmu ko"?



"uhmmm"


kawai tace saboda kunya shi kadai yai ta hirarsa  karshe yaimata sallama yakashe wayar karfe 7,Pm aka  tafi kai Munira gidanta sai da aka fara kaita gidan Hajiya tukunna nan tai mata nasiha sosai kan *_zaman aure_* sannan  aka wuce daita gidanta dakinta yahadu iya haduwa sai wajen 9 yankai amarya suka watse,angwaye suka shigo basu jimaba sukaimusu sallama suka tafi bayan sunyi adduoi yarage daga amarya sai ango a daki .






*_Abdulmalik_*




~~Cikin murya kasa kasa Abdulmalik yafara magana,



"pls Mariya kiyi shiru mana nine fa Abdul"



dada kankameshi tayi,ahakali yajanyeta daga jikinsa tare da gyaran murya yace,



"Amm kinajina ko,kitashi miyo alwala muzo muyi sallar da kowane amarya da ango keyi"



shiru taimasa kamar batajiba,sai da yakuma maimaita mata sannan ta mike sanye take dawata yar figigiyar rigar bacci iya gwaiwa toilet ta shiga danyin alwala binta yayi da kallo,har tafito idonsa yana kan kofar toilet din,tashi yayi ajigace ya shiga yayo alwalar shima yafito,tana zaune gefan gado wardrobe din yabude ya dakkomata doguwar riga da hijjab tasa yajasu salla suka idar yaimusu addua ,ido tafara lumshewa kallonta yayi yace,



"Bacci ko"?


kai ta gyada masa ahankali ya mike ya jata zuwa kan gadon  tare da rikohannunta yahada da nasa yace,



"Mariya pls kiyi hakuri akan abinda nafada miki rannan inaso muyi *zaman aure* bisa gaskiya da amana,ki kula min da ita dan Allah"


ahankali ta gyada masa kai, janta ya kumayi jikinsa nan yashiga aikamata da sakonni tun tana nokewa har tabada kai bori yahau,



tundaga wannan rana Mariya da Abdulmalik suka hada kai suke zaune lafiya sai dai abayan idonsa gallazawa 

Inna take  ko abinci tadafa sai taga dama take bata yanzu haka cous cous tadafa da miya tadan dibar mata a kula takaimata ,karba tayi tabude tana ganin cous cous ta mayar da murfin tarufe kallonta tayi tace,



"Mariya yazaki kawo min abinda kikasan banaci ,meyasa"?



To,ai inna inbakyaci sai kisan yadda zakiyi dashi dan kuwa shi mijina yakeso ,kinga kuwa dole indafa masa"



tana kaiwa nan takada kanta tabar inna cike da mamaki abincin taajiye gefe tanajiran Abdul malik yadawo,





*Hafeez*




~~cikin kankanin lokaci  maganar auran Hafeez ta kankama kamar wasa sai gashi anyi angama amarya ta tare ,nan fa akafara *zaman aure* nan Areefa tafara raina kanta domin Ashanty ta kere mata wajen rashin mutunci,gata yar duniya ,sau tari sai taga Hafeez na gida sai ta tsiri iskanci dan kawai Areefa taji haushi,yau tun safe tashirya tafita lokacin Hafeez ko tashi beyiba kasancewar Areefa ke da girki,sai da yatashi yanufi bangaranta nan yatarar dashi a kulle ransa yabaci hankalinsa  yatashi bangaran Areefa yakoma yana banbami ko kallonsa batayiba,can tanisa tace,



"Haba Hafeez kai da amaryar taka kuma,ko ka manta amarya bata laifi"



wani kallo watsa mata kafin yadora da,



"Areefa kinsan halin yarinyar nan kuwa"?



"meye alakata da ita da zansan halinta,ai sanin halinta sai kai "



tanagama fada masa ta tafiyar sa tabarshi yana tunani yakara aure dan ya huta ashe sai dai ya huce.









*_NASEEBA GAWO_*✍🏻

No comments