Recent Updates

Yarima Suhail Complete Hausa Novel


 

  *  👑YARIMA SUHAIL.👑*

  _STORY,WRITTEN &EDITED BY._
         *SIS NERJA'AT.*

        _COMPILATION BY._


  *HAWWA M.U (®EAL $MASHER).*
?👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_


_Jinjina agareki my hafnan ina tayaki murnar fara new novel d'inki *HIBBATULLAH* akowane lokaci kina a ❤👈🏻 d'ina_


_~Sak'on gaisuwata agareki my blood sis *Aufana* sonki a cikin jinin jikina yake😘😘~_

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Wannan page d'in nakine Sainah Ummun Meenal uwa tagari Allah yabar mana ke😍_

page 1⃣

garin gazban garine mai albarka da yawan mutane yana d'aya daga cikin garuruwan da ake alfahari da su.

sun kasance suna da babbar Masarautar da babu kamarta wajen girma da kyau  sarkin garin ya kasance sarki mai adalci duk kud'in mutum bai isa yazalunci nak'asa da shi ba indai har yazalunta labari yazo ma sarki toh sai yad'auki mataki,

sarki umar yana son talakawansa sosai suma suna sonsa abun mamaki wannan sarki ya manyanta domin zai kai shekaru 76 ammah indai ba ka saniba sai kad'auka d'an shekara 50 ne,  domin babu alamun tsufa a tare da shi idan dukiyarce ya tara,  idan sarautarce yana d'aya daga cikin manyan sarakuna kai intabbatar muku wannan babbar Masarautar ko da me kazo anfika.

Sarki faruk matarsa d'aya dattijuwa dada,  saidai abun mamakin duk mulkin nasa ammah 'ya'yansa biyu dukansu maza ne Ahmad shine babba sai k'anensa Abbas sun taso atare sun kasance suna son junansu.

saidai a tsarin mulkin garin indai sarki yahaura shekaru arba'in (40) saman karagar mulki toh d'ansa ba zai ta6a gadon mulkinba saidai babban jikan gidan, saidai idan babu jika namiji shine d'an sarkin yake hawa mulkin

lokacin da 'ya'yansa suka tasa yaza6a musu mata inda Ahmad ya auri d'iyar sarkin agadaz wato sultana Bilkisu,  shi kuma Abbas sarki ya aura masa  d'iyar d'an uwansa da yamutu yabari wato Sultana Sadiya.

A cikin babbar Masarautar kowa aka fitar masa da 6angarensa.

Suna zaune lafiya da matansu,  inda sultana Bilkisu takasance macece mai hak'uri da tawakkali ga ta macece mai kyauta ta kasance mai son jama'a,

inda Sultana Sadiya takasance akasin haka domin bata son talakkawa suna ra6arta dan ma mijinta a tsaye yake sun d'auko hali irin na mahaifinsu, ammah duk da haka taci alwashin ita take da burin tafara haihuwar d'a namiji.

saidai kash sultana Bilkisu ita tafara samun ciki, hankalin sultana Sadiya ya tashi sosai ganin ita ko 6atan wata bata ta6a yiba,

Bayan wata goma sultana bilkisu tahaifi d'iyarta mace murna wajen iyayen ba'a magana hatta ita kanta sultana Sadiya tayi murna ganin ba namiji bane ta haifa.

ranar suna anyi shagali sosai kud'i sunyi kuka tsakanin masarautar gazban da masarautar agadaz anzuba naira sosai a inda yarinya taci sunan dada wato Asma'u ammah ana kiranta da husna.

Bayan shekara ukku Sultana bilkisu tak'ara haihuwa inda tasamu d'anta namiji kyakkyawa domin ita yabiyo kamar antsaga kara murna wajen su sarki ba'a magana hatta su kansu jama'a sun shaida wannan haihuwar domin sarki sadaka yadinga yi da dukiya sosai, 

akasin sultana Sadiya da takasa 6oye bak'in cikinta turakar mijinta taje tasameshi a zaune yana ta kiran waya yana fad'a ma mutane,  zama tayi gefensa tana kallonsa cike da takaici har yagama wayar sannan yakalleta fuskarsa d'auke da murmushi yace sultana akwai abinda kike buk'ata ne?

sultana sadiya d'auke fuskarta tayi daga kallonsa tace ranka yadad'e meyasa kake murna dan matar d'an uwanka ta haifi namiji kar fa kamance shine zai hau karagar mulki bayan ran sarki, 

da mamaki sultan abbas yake kallonta yace sultana ba dai bak'in ciki kike ma d'an uwana ba dai ko?

d'aure fuska sultana tayi tace bak'in cikin me zanyi masa,  naga kana ta murna ne mukuma kaduba kaga ko 6atan wata ban ta6a yiba bamu da d'a ko d'aya kuma kyau ace d'an kane zai gaji masarautanan.

sultan Abbas sakin baki yayi yana kallonta har takai aya sannan yace sultana inaso kisan wani abu wlh da zuciya d'aya nake son d'an uwana ban damu da sarautar da d'ansa zai hau ba domin nima d'ana ne sannan da kike magana akan rashin haihuwa inaso kisani Allah shi yake badawa ga Wanda yaso kuma yahana Wanda yaso ban cire rai ba idan da rabo nima zanga tsatsona, dan haka kar ink'ara jin kinyi wannan maganar,  kibinneta daga nan da kika yi ta.

Mik'ewa sultana tayi cikin fushi tace daman nasan ba zaka ta6a fahimtaba ammah nan gaba dakanka zaka fahimci abinda nake nufi. wucewa tayi fuuu tafita tabar d'akin.

Sultan Abbas binta yayi da kallo har tafita sannan yagirgiza kai cike da takaicin abinda matarsa tayi yace Allah yashiryeki sadiya.



Ranar suna yaro yaci suna Umar sunan maimartaba ammah suna kiransa da suhail,

suhail yataso cikin gata domin yana samun kulawa sosai a wajen iyayensa da kakanninsa hatta shi kansa sultan Abbas yana ji da d'an nasu,

akasin sultana sadiya da ta tsanesa bata d'aukarsa sai idan gaban su Dada ne nan take nuna tana sonsa sosai, ammah a cikin zuciyarts ji take ina ma ace yamutu.

ahaka yataso cikin gata tun yana shekara ukku maimartaba yakesawa ad'aukosa akawo sa fada yazaunar da shi kusa da shi saisa suhail yataso ya shak'u da kakansa sosai.

Bayan shekara biyu sultana sadiya tasami ciki murna wajensu da wajebnsu sultan Ahmad ba a magana,

kulawa sultana sadiya take samu sosai daga wajensu maimartaba da mijinta hatta ita kanta sultana bilkisu tana bata kulawa sosai.
inda sultana sadiya take addu'a akan Allah yasa tahaifi d'a namiji.

inda itama sultana Bilkisu take d'auke da d'an k'aramin cikinta.

bayan wata tara sultana sadiya tahaifi d'iyarta mace ta yi bak'in ciki sosai ammah daga baya tahak'ura,  murna wajen su maimartaba ba'a magana kowa ya nuna farin cikinsa, 

ranar suna yarinya taci suna sumayya, anyi shagali sosai anci ansha.
inda sultana sadiya taci alwashin ta kowane hali sai d'iyarta ta auri sarki mai jiran gado .

bayan wata ukku sultana bilkisu tahaifi d'iyarta mace inda taci sunan mahaifiyarta wato Rahama,

tun daga lokacin babu wadda tak'ara ko da 6atan watane,  sumayya da Rahma sun taso a tare komai nasu d'aya bacci kawai yake rabasu.

Yarima Suhail duk halin maimartaba yad'auko yatashi mutum ne mai tausayi kuma mai girmama na sama da shi saidai ya kasance bai da son hayaniya miskiline na sosai baya shiga abinda bai shafesaba baya da yawan fara'a sosai saidai ga wanda bai sansaba zai masa kallon mutum mai girman kai.

In ko kagansa a fada toh maimartabane yasa yaje ammah shi kwata-kwata baida burin yin sarauta,  ko da dakagansa komai nasa irin na sarauta yakeyi. 

tun da yataso abokinsa d'aya d'an waziri wato shahid tare suka taso tun suna yara sunyi makarantar arabi da boko a garinsu.

bayan sun gama secondary yarima suhail yanuna yanaso yafita waje yayo karatunsa, anyi daga sosai da maimartaba afin ya amince domin cewa yayi shi da zai gaji sarauta mezaisa yafita waje karatu, daga baya dai dakyar aka samu maimartaba ya amince inda yarima  yaje india yayi karatunsa na likitanci inda yakaranci surgeon.

bayan shekara biyu akasha bikkin Gimbiya husna inda ta auri d'an chairman d'in garin anyi shagali sosai anyi bikkin da ba a ta6a irinsaba a garin, inda husna tatare a gidan mijinta
yarima suhail yaso yazo ayi bikkin da shi ammah iyayensa suka hana sukace yazauna yayi karatunsa.

Gimbiya Sumayya da Gimbiya Rahama sun shak'u da juna sosai saidai suna da banbancin halayya sumayya tana da wulak'anci sosai kuma ta tsani talaka yara6eta bata abota da kowa sai wanda yakasance jinin sarauta ko d'an wani attajiri.

akasin Gimbiya Rahama da takasance mai son jama'a kuma bata da wulak'anci kowa natane abinda yake had'ata fad'a da sumayya kenan ko a school.





Bayan shekara hud'u yarima suhail yakammala karatunsa yadawo k'asarsa ta haihu ya k'ara girma da kyau miskilancinsa ya k'aru da kagansa ka ga jinin sarauta,
murna wajen maimartaba da iyayensa ba a magana hatta kansu jama'ar gari sunyi murnar dawowarsa.
ba kamar abokinsa shahid da yayi missing d'insa sosai.

gidan sarautar hidima akayi sosai inda dukkan ma'aikatan gidan suka had'u adafa wancan asafke ad'aura wancan,

walima akayi ta azo agani hatta kansu talakawa sun ci sun sha,

Sumayya tun da tad'aura idonta akansa tace ai tayi miji ba zata auri kowaba sai shi ko da taje ma mahaifiyarta da maganar itama tayi murna sosai domin itama burin da take da shi kenan a rayuwarta inda tabata shawara akan taje tasanarwa dada.

sumayya ta d'auki shawarar da mahaifiyarta tabata dan haka tawuce tanufi 6angaren su maimartaba lokacin da tashiga d'akin dada zaune take saman kujera gefenta dama da haggu duk kuyangine suna ta mata hidima,

sumayya bisa kujerar da kaka take zaune taje tazauna tace ranki yadad'e 'yar tsohuwarmu Allah yak'ara miki tsawon kwana,

dariya dada tayi tace Ameen gimbiya ganinki da nayi haka nasan bakinki yana d'auke da magana,
sumayya murmushi tayi tace tabbas hakane ranki yadad'e akwai abinda yake tafe da ni.

kaka sallamar kuyanginta tayi duk suka fita sannan tatattara kallonta ga jikartata cike da kulawa tace ya ke sumayya inaso kifad'a min abinda yake tafe da ke nikuma indai baifi k'arfina zan taimaka miki.

sumayya duk'ar da kanta tayi cike da kunya tace dada daman akan yaya suhail ne,
murmushi kaka tayi jin an ambaci nagaban goshinta tace ina jinki me suhail d'in yayi?

sumayya tace babu abinda yayi saidai nice wlh dada tun tuni nakeson yaya suhail kuma ina tsoron intaresa da maganar dan nasan zai iya min wulak'anci saisa nace bari infara samunki da maganar wlh dada ina sonsa har cikin raina.

dada tunda sumayya tafara maganar kasa rufe baki tayi saboda jin dad'i,  saida sumayya takai aya sannan dada tace masha Allah gaskiya naji dad'in labarin nan da kikazo dashi domin daman nima ina da burin hakan a raina ammah tunda har kikafurta da kanki toh ai shikenan.

sumayya kallon dada take cike da jin dad'i tace toh dada shikuma yaya suhail fa idan yace baya sona?

dada tace kikwantar da hankalinki zai ma soki domin babu yadda za'ayi nagida bai k'oshiba aba na waje ke dolene mane yasoki dan haka kikwantar da hankalinki shalele kamar kin zama matarsane kibari zamuyi maganar da shi da maimartaba.

sumayya cike da jin dad'i taduk'a takwashi gaisuwa tare da yin godia sannan tayi ma dada sallama tafito tanufi 6angarensu duk inda ta gifta tun kan ta ida isowa inda bayi da ma'aikata suke ake zubewa kwasar gaisuwa kowa tsoronsa kar tace yayi badaidaiba domin sunsan halin gimbiya sumayya da mahaifiyarta yi musu laifi abune maisauk'i,  kowa yau yana mamakin yadda fuskarta take a sake sa6anin da dakullum take a d'aure.

dada ko da tasamu maimartaba da labarin shima yayi murna sosai inda yace zai gana da su gobe.



yarima suhail ne kwance saman makeken gadonsa inda shahid yake gefensa yana ta zuba masa surutu shi dai yarima daga uhm sai uhm-uhm bai cewa komai sai ma dannar wayarsa da yakeyi.

shahid ya k'ule sosai tsaki yaja yace kai fa matsalata da kai kenan sai ana yi maka magana kadinga share mutum kamar ba dakai akeba.

shuru yarima yayi yacigaba da dannar wayarsa takaici yakama shahid dan haka yafizge wayar, ganin haka yasa yarima yamaida idanunsa yalumshe.

shahid baiyi mamaki ba domin yasan halin abokin nasa tun suna yara.

knocking d'in k'ofar da akayine yasa shahid yabada izini da ashigo,  wani dogarine yashigo tare da zubewa k'asa yana k'wasar gaisuwa shahid ne kawai ya amsa masa,

dogarin kansa yana k'asa yace Allah yaja da ran yarima mai jiran gado daman Maimartaba ne yake kiranka ya ce kasamesa a turaka,

yarima batare da yabud'e idonsaba yad'aga ma dogarin hannu alamun yatafi.

tashi dogarin yayi yace nabarku lafiya sannan yaficce daga d'akin.

shahid kallonsa yayi yana murmushi yace yau sarautar ta motsa kenan.....



_Comment_
     *nd*
_Share_



_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Sak'on gaisuwata agareku intelligent writer's   Allah yabar k'auna😘_

_My k'anwa janaf Allah yabar min ke😘_


_*Wannan page d'in nakine Asma'u Yusuf Beji kiyi yadda kikeso da shi ina godia da kulawarki agareni😍*_

page 2⃣

Yarima suhail saida yayi kusan minti biyar yana a kwance sannan yabud'e idonsa ahankali yamik'e yasafka daga kan gadon,  alkyabbarsa yajawo yasa batare da ya kalli shahid ba saida yataka yakusan zuwa k'ofa sannan yace kajirani bari indawo,  shahid cike da tsokana yace toh ranka yadad'e

yarima baice komai ba yafita yana tafiyarsa ta k'asaita, dogarawan da suke zaune k'ofar d'akinsane suka zube suna kwasar gaisuwa sannan suka tashi domin sutake masa baya,  yarima batare da ya kallesuba yad'aga musu hannu.

ganin haka yasa duk suka tsaya, yawuce yacigaba da tafiyarsa shi kad'ai duk inda yagifta kwasar gaisuwa akeyi, d'aga ma mutane hannu kawai yake idan da sabo sun saba da halin yarima ahaka har yashiga turakar mai martaba da mamakinsa yaga har da iyayensu a zaune,

waje yasamu gefen maimartaba yazauna a k'asa tare da kwasar gaisuwa wajensa da wajen iyayensu nan duk suka amsa masa, 

maimartaba gyaran murya yayi yace toh Alhmdllh nasan duk zakuyi mamaki akan dalilin taraku nan da nayi ammah ba abun mamakibane alkhairine muke tafe da shi, ba akan kowaba sai akan yarima suhail,

maimartaba cigaba yayi da cewa domin na riga na yanke hukunci saboda nasan zai kar6i abinda nake tafe dashi na alkhairi,  bakomai bane sai akan dubawa da cancantar da naga yayi dan haka naza6a maka matar aure bakowa bace face 'yar uwarka sumayya.

yarima gabansane yaji ya fad'i dasauri yad'ago kai yakalli maimartaba har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa dan haka yasunkuyar da kansa k'asa tare da runtse idonsa cike da takaicin za6in da maimartaba yayi masa, nan iyayensu sukaita murna suna tofa albarkacin bakinsu akan maganar.

shidai yarima saurarensu kawai yake,

muryar maimartaba ce yatsinkayo yana cewa toh kai uban gayyar bakace komai ba,

yarima suhail kamar ba zaiyi magana ba sai chan yace ranka yadad'e na amshi za6in da kayi min hannu bibbiyu Allah yak'ara tsawon rai.

cike da Jin dad'i maimartaba yace masha Allah, naji dad'i sosai tabbas nasan daman bazan samu matsala daga garekaba wlh ka faranta min nima Allah yakawo lokacin da zan faranta maka,

gaba d'ayansu sukace Ameen, yarima suhail nan yak'ara kwasar gaisuwa sannan yamik'e yafita

umman sumayya kamar tazuba ruwa k'asa tasha saboda murna domin ko bakomai tasan burinta ya kusan ciki ko da taje ma d'iyarta da labarin sumayya har da rawa tataka saboda murna dagudu tafita taje 6angarensu rahama tashaida mata, nan rahama tatayata murna.


yarima suhail yana komawa d'akinsa saman gadonsa yafad'a tare da lumshe idonsa cike da bak'in ciki domin an 6ata masa plan saboda shi baida burin yin aure a yanzu ko ma da zaiyi sumayya bata daga cikin irin tsarin matan da yake da burin aure saidai kawai zai amince ne saboda maimartaba domin baya iya jayayya da shi,

shahid ganin yarima acikin wannan mood d'in yasa bai tambayesa abinda yake damunsaba domin yasan ko da ma ya tambaya toh ba zai samu amsaba saidai idan shi yaso yafad'a masa toh dakansa zai basa labari dan haka yasharesa yacigaba da kallon ball d'insa.

yarima ya dad'e a kwance sannan daga baya yatashi yashige toilet.


bayan sallar isha'i yarima turakar iyayensa yaje inda yatadda mahaifiyarsa kishingid'e wata baiwarta tana mata tausa inda wasu biyu suke gefenta suna mata hira.

suhail yana shiga yatsaya bakin k'ofa ganinsa yasa duk suka zube suna kwasar gaisuwa sannan daga baya suka tashi suka fita suka basa wuri domin yagana da mahaifiyartasa,

sultana bilkisu tashi tayi daga kishingid'en da take nan suhail yataka yaje inda take yazauna sannan yagaishe da mahaifiyartasa cike da fara'a ta amsa masa.

suhail duk'ar da kansa yayi k'asa baice komai ba, ganin haka yasa mahaifiyarsa tace yarima me yake faruwane? kafad'a min damuwarka domin bakada wata uwar da tafini,

suhail d'ago fuskarsa yayi cike da damuwa yace ummi yanzu Sumayya ita zan aura?

murmurshi ummi tayi tace toh menene dan ka aureta ina ce 'yar uwarkace kuma ta cancanta da hakan,
dan haka kakwantar da hankalinka kakoya ma zuciyarka sonta insha Allahu zakuji dad'in zaman aurenku.

cike da damuwa suhail yace ammah ummi kinsan halin Sumayya ko kad'an halinmu bai zo d'ayaba,

ummi tace injiwa yace maka haka?  duk abinda kaga tanayi harda yarinta,  nidai burina kakwantar da hankalinka tunda ita kaga bata tada hankalintaba kakoya ma zuciyanka sonta insha Allahu zakuji dad'in zaman aurenku.

yarima suhail yace toh ummi nagode, nabarki lafiya.

ummi tace toh my son dan Allah kar katashi hankalinka tunda kaga an amince da aikinka yanzu haka mahaifinka ya sa afara maka ginin hospital d'inka.

murmurshi yarima yayi yace nagode ummi sannan yafita daga turakar yakoma tasa.

Bayan kwana biyu aka tsaida maganar aurensa da sumayya nan da wata biyu masu zuwa,  yarima yaso asa lokacin dayawa ammah maimartaba yace a'a, ,sumayya farin ciki tayi sosai agaban kowa take nuna murnarta, 

yarima ganin dagaske ake yasa yad'an saki jikinsa har suna d'an ta6a hira da sumayya shima d'in kafin yayi magana d'aya tayi biyar, in ko kaga sunyi waya toh itace takirasa shima daga gaisuwa yake kashe wayarsa.

Bayan wata biyu akasha bikkunsu anyi shagali sosai ak'allah saida akayi events kusan guda biyar ammah dakyar aka samu yarima suhail yaje d'aya daga ciki shima saida ummi tasa baki, ammah sauran duk k'in zuwa yayi k'arshe idan yaga za'a takurasa sai yakashe wayoyinsa yace kar abari kowa yashigo sashensa,

ranar asabar aka d'aura aure, auren da dubban mutane daga nahiya dadama suka hallara,

amarya ta sha kyau har ta gaji,  inda amarya tatare a part d'in yarima da aka fitar da shi a cikin gidan sarauta, k'arshen gata an nuna mata babu abinda ba a zuba masu na amfani ba.

kowa yazo sai ya yaba tsarin gidan domin babu wanda zai ce acikin gidan sarautane saboda part d'in yarima antsarasa kamar a turai inda aka fidda ma sumayya 6angarenta sai na yarima sai wani part d'in da aka fara ginawa aka aje sai kuma part na ma'aikata da bayinsu maza da mata.


da daddare saida shahid yayi dagaske  sannan yasamu  yarima suhail yayi wanka yashirya suka fito suka rakasa gidansa.

suna ta tsokanarsa shidai yayi shuru yakyalesu saboda wani irin haushi da yakeji,  hatta su kansu haushinsu yakeji tunda su suka matsa masa sai yaje.
saida suka rakasa har part d'in amaryarsa sannan sukayi masa sallama suka tafi.

yarima suhail 6angarensa yabud'e da mamakinsa yaga dogarawansa zaune a k'asa suna ganinsa suka zube suna kwasar gaisuwa, yarima suhail batare da ya amsaba yace kun iya tafiya ,

k'ara kwasar gaisuwa sukayi sukace toh ranka yadad'e sannan sukace atashi lafiya sai suka tashi suka fita

bedroom d'insa yashiga komai na ciki very  need da mamaki yakalli yadda aka shimfid'a masa farin bedsheet mai kyau a saman gadonsa d'auke kansa yayi yawuce yashiga toilet yawatsa ruwa , bayan ya fito yayi shirin kwanciyarsa yahaye gadonsa.

A 6angaren gimbiya sumayya bayan ta gama shirinta su jakkadiya suka take mata baya zuwa turakar yarima,  da sallamarsu suka shiga ganin baya parlour yasa suka kwank'wasa masa bedroom,

yarima da yake kwance yabada izinin ashigo,  da mamaki yake kallonsu sumayya da suka shigo, nan su jakkadiya suka zube k'asa suna kwasan gaisuwa,  ita dai sumayya zuba masa ido tayi tana kallonsa cike da son mijinta,

haydar bai damu da kallon da take masaba yace lafiya kukazo man d'aki?

jakadiya da take durk'ushe tace ranka yadad'e yarima mai jiran gado daman dada ce tace mukawo maka amarya,

yarima suhail shuru yayi baice komaina yamaida idonsa yalumshe. 
ganin haka yasa su jakadiya sukace mun barku lafiya gimbiya da yarima Allah yaja da ranku atashi lfy.

Gimbiya sumayya tace idan kun fita sai kurufe mana k'ofan, 

yarima suhail yana jinta mamakine yakamasa domin bai ta6a ganin amarya hakaba.

suna fita sumayya tatako ta iso bakin gadon tazauna gefen da yarima yake kwance,   suhail batare da ya bud'e idonsaba yace kije kid'auro alwallah,

sumayya turo baki tayi sannan tatashi tashiga toilet d'insa tad'auro alwallah,

lokacin da tafito yarima yana shimfid'a darduma nan yajasu sallah raka'a biyu sukayi sannan yakama kanta yayi mata addu'a.

bayan ya gama yayi mata tambayoyi akan addininta baiyi mamaki ba da yaga bakomai take iya basa amsaba,  wata amsarma ba daidai take basaba nan ya Ida tsurewa da lamarin sumayya ammah kuma sai yashare, mik'ewa yayi yanufi saman gadonsa yabarta nan saida yakwanta sannan yace ga nama nan idan zaki ci.

haushine yakama sumayya ganin yadda takejin labari wajen friends d'inta yadda mazajensu suka nuna musu tattalin so a daren aurensu ammah ita ba hakaba,  cikin ranta tace lallai yarima halinsa sai shi.

tashi tayi itama taje saman gadon takwanta bayansa saida sukayi kusan minti goma ahaka ammah sumayya taga yarima bai da alaman nemanta dan haka tarungumesa ta baya,

yarima shareta yayi, ganin haka yasa sumayya tajuyosa tare da kwanciya saman jikinsa,  yarima bud'e idanuwansa yayi da suke lumshe yawurga mata harara yace ke bakida kunya?

sumayya turo baki tayi tace yarima yau fa daren amarcinmune ammah shine kake shirin yin bacci kabarni hannu takai tana shafa jikinsa.

yarima da mamaki ya gama cikasa kasa komai yayi,  jin hannunta yayi yana yawo cikin jikinsa, dasauri yarik'e hannun yace ke bakida kunya?

sumayya tace ammah ai naga ba abun kunya bane tunda munyi aure,
bakinta takai cikin nasa tana kissing d'insa cikin wani irin salo nan da nan yarima yafita hayyacinsa ya'aje sarautarsa gefe yabiye mata suka sha amarcinsu.

yayi mamaki sosai ganin yadda sumayya take zak'ewa babu alamun tsoro atare da ita, 
a yadda yasameta bai kawo ma ransa komai ba gudun kar zargi yashiga tsakaninsu dan haka dayasamu nutsuwa janye jikinsa yayi yaje yayi wanka sannan yadawo yayaye bedsheet d'in yayi  yakwanta tare da juya mata baya,

sumayya ma tashi tayi taje tayi wanka sannan tadawo bayansa yakwanta tare da rungumarsa ta baya, 

da asuba yarima har yadawo masallaci ammah sumayya bata tashi tayi sallah ba,  saida yayi dagaske sannan yasamu sumayya tatashi tayi sallah tana ta k'unk'uninta, komawa yayi yakwanta yana kallonta sallarma shaf-shaf tayita ko addu'a bata tsaya yiba tahaye gadon.

dasafe jakkadiya ce tatashesu nan tashigo takwashi gaisuwa sannan tad'auki bedsheet d'in tafita.

turakar dada taje, tun da dada tahangota take fara'a jakkadiya duk'ewa tayi takwashi gaisuwa sannan tace ranki yadad'e ga zanen gadon,

dada tace masha Allah bud'e mugani ko da jakkadiya tabud'e babu komai a jikinsa nan hankalin dada yatashi tace nashiga ukka ya akayi haka kar dai ace yarinyarnan ba budurwa bace.

jakkadiya duk'ar da kanta tayi tace ranki yadad'e ai ita mace budurwa ba dole sai anga jiniba ake gane budurwace wasu basu jinin budulci,

dogon numfashi dada taja tace hakane shikenan yanzu aje awankesa amaidasa ma'ajinsa ammah naso ace kowa ya shaida.


kowa na gidan kasa kunne yayi yaji ana gud'a ammah shuru kuma kowa tsoron tambaya yakeyi,  kasancewar al'adarsuce duk amaryar da aka kowa idan budurwace da anga jinin ake ganewa nan za'a d'auki zanen gadon ayi ta yawo ana gwadawa daganan sarki zai bada shanuwa da rago ayanka ma amarya.

yarima suhail har yagama shirinsa ammah gimbiya sumayya tana kwance tana kwasar baccinta haushi ne yakamasa yaja tsaki yace mutum kamar kasa sai bacci,  da mugunta yakai mata bugu,  firgit tayi tafarka daga baccin

haushi ne yakamata ganin yarima tsaye,  d'aure fuska tayi tace haba yarima ya za'ai katasheni bayan jiya kaine kahana ni bacci,  gaskiya kadaina domin idan ina bacci ba'a tashina.
yarima da mamaki yake kallonta jin tace shi yahanata bacci bayan itace takawo kanta,

tashi tayi tad'auko alkyabbarta tasaka sannan taficce tabarmasa d'aki,
tsaki yarima yaja sannan yacigaba da abinda yake,

bayan ya gama yafito parlour yatarar da anshirya masa breakfast dogarawansa suna ganinsa suka zube suka kwashi gaisuwa sannan d'aya daga cikinsu yayi serving d'insa,

kad'an yaci sannan yatashi nan suka rufa masa baya sunacewa takawarka lafiya yarima.
tsayawa yayi batare da ya juyoba kamar ba zaiyi maganaba sai kuma yace kuje kawai zan nemeki,
su dukansa sukace angaisheka yarima umurninka muke cikawa Allah yatsare mana kai mun barka lafiya.

daganan yawuce yacigaba da tafiyarsa shi kad'ai duk inda yagifta kwasar gaisuwa ake ahaka har yazo 6angaren gimbiya ko da yashigo parlour saida ma'aikatanta sukayita kwasar gaisuwa ko inda suke bai kallaba yawuce direct bedroom d'inta,

lokacin gimbiya sumayya tana zaune bayinta suna shiryata,  bud'e k'ofar da akayine yasa duk suka maida hankalinsu domin suga mai shigowa ganin yarimane yasa suka zube gaba d'ayansu suka kwashi gaisuwa sannan suka mik'e zasu fita 

gimbiya sumayya ce tace ina zakuje batare da kun gama shiryaniba,
yarima kallonta yake cike da mamaki sannan yanuna musu k'ofa dasauri dukansu suka fita har suna tuntu6e.

takowa yayi cikin takunsa na k'asaita ya iso bakin gadon, gimbiya sumayya tace haba yarima ya zaka korar minsu alhali basu gama shiryaniba,

zama yarima yayi kusa da ita batare da ya kalletaba yace ke ba zaki iya shiryawaba har sai sun shiryaki?
sumayya ta6e baki tayi tace ammah ai tun ina gaban iyayena su suke min kwalliya,  banza yarima yayi yakyaleta dan haka taci gaba da shirinta.
banza yarima yayi yakyaleta.

bayan ta gama kiran jakkadiya tayi tace akawo mata breakfast d'inta a nan,  cikin minti biyar ancika mata gabanta da abinci da kayan marmari iri-iri

nan tazauna zata ci kallon yarima tayi tace kaifa ba zakaciba,

yarima batare da ya kalletaba yace no kici kiyi sauri kigama muje mugaishe da su maimartaba,

gimbiya sumayya tace tun yanzu?
yarima bai tanka mataba,
ganin haka yasa tacigaba da breakfast d'inta domin tasan halin mutumin nata magana tsada take masa......



_Comments_
      *nd*
_Share_





_Sis Nerja'art✍🏻_
?👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_*Sak'on gaisuwata agareku My Haleema H.A.S nd mummy Zill😍👌*_

_Wannan page d'in nakune nabaku shi a kyauta my fan's😘_

page 3⃣

bayan ta gama d'auko alkyabbarta tayi tasaka sannan suka jera ita da yarima suka fito, a k'asa suke tafiya a jere, kuyangin gimbiya suka take musu baya ahaka har suka isa fada nan mutane suka dinga kwasar gaisuwa,  d'aga musu hannu kawai yarima yakeyi har suka isa gaban maimartaba dasauri dogarawa sukazo suka kare su yarima daga ganin mutane suna cewa Allah yataimaki yarima da gimbiya  azauna lafiya, har saida suka tabbatar da yarima da gimbiya sun zauna sannan suka matsa nan su yarima suka kwashi gaisuwa wajen sarki nan fadawa suka d'auka,  sarki ya amsa muku yarima da gimbiya, sarki yana godia yarima mai jiran gado ku ma angaisheku.


sannan yarima yatashi yaje kujerar da take kusa da sarki yazauna,  ita dai gimbiya tana tsugunne a k'asa sai yatsina take tana kallon mutane a wulak'ance.

maimartaba ne yad'auko wata alkyabba maikyau da tsada yamik'a ma gimbiya sumayya hannu biyu gimbiya tasa takar6a tare da yin godia sannan tamik'a ma jakkadiya,  jakkadiya tazube gaban sarki tace ranka yadad'e gimbiya tana k'ara godia Allah yaja da ran sarki mai adalci sarkin sarakai,

gyad'a kai sarki yayi nan fadawa gaba d'ayansu suka d'auka angaisheki gimbiya sarki ya ji godiar ki.

nan sarki yayi musu nasiha tare da yi musu addu'an zaman lafiya, sannan suka k'ara kwasar gaisuwa suka tashi suka fito,  cikin gida suka shiga turakar dada,

nan suka gaisheta itama tayi ma gimbiya kyauta sannan suka wuce 6angaren ummi suka gaisheta itama kyauta tayi ma gimbiya sannan daganan sukaje 6angaren umman sumayya suka gaisa daga nan suka koma 6angarensu

suna shiga yarima yanufi hanyar zuwa 6angarensa ganin gimbiya tana niyar binsa yasa yadakata da tafiyar batare da ya kalletaba yace zaki iya tafiya 6angarenki domin yanzu inason inhuta bai jira jin abinda zata ce ba yawuce part d'insa.

Gimbiya sumayya tsaye tayi takaici duk ya cikata ganin yadda yarima yadizgata gaban bayinta,  tsawa tadaka musu tace suwuce subata waje dasauri duk suka bar wajen,

nan gimbiya tanufi part d'inta cike da jin haushi.



haka sukayi sati d'aya suna shan amarcinsu tun yarima bai kulata daga baya sumayya saida tasan yadda tayi yarima suhail yad'an sake mata, ammah idan yana jin 'yan miskilancin ko sarautar takad'a masa toh ko kallon inda take bata yi.





bayan sati guda gimbiya sumayya ce kishingid'e a parlourn ta inda bayinta suke zagaye da ita wasu suna mata tausa wasu fifita,  d'aya tana karanta mata labari, wayartace tashiga ruri baiwar da take rik'e da wayoyintane tamik'a mata, cike da Jin dad'i sumayya tayi picking d'in wayar ko sallama batayiba tace haba zinat ai ni fushi nake da ke wai har ayi aurene bakya garin,

daga chan 6angaren Zinat tace toh sarkin k'orafi yanzu dai gani a k'ofar gidanki dogarawa sun hanani shiga kituro a shigo da ni,

cike da jin dad'i sumayya tace yanzu ko zan aiko,  kallon d'aya daga cikin bayinta tayi ta yamitse fuska tace ke jeki waje kishigo min da bak'uwata,

dasauri tamik'e tace angama ranki yadad'e

batafi minti biyar da fitaba sai gasu sun shigo da zinat,  sumayya tashi tayi daga kishingid'en da take tace oyoyoo k'awata takaina,  nan bayi suka zube suka kwashi gaisuwa wajen wadda aka kira da zinat sai yamutsa fuska take tana taunar chewing gum tazauna saman kujera, nan gimbiya sumayya takori duka bayin daga d'akin,

gimbiya sumayya kusa da ita takoma tazauna kafin kace mi ancika gaban zinat da kayan ciye-ciye da na shaye-shaye, sumayya cike da farin ciki tace k'awata kenan ai ban d'auka zan ganki a yanzu ba,

zinat kur6an ruwan inibi tayi sannan ta aje cup d'in tace wlh jiya nadawo garin shine nace ba zan fad'a mikiba surprise kawai zan baki yau.
.
murmushi Sumayya tayi tace kin ko kyauta wlh, na ma d'auka sai kin gama hutawa zaki dawo domin na sanki da son tafiya kihuta,  zinat tace ai saboda ke nadawo amarya kinsha k'amshi kinga ko yadda kika koma?

murmushin jin dad'i gimbiya sumayya tayi tace ya nakoma dear?

zinat tace ai kin fito a gimbiyarki ta ainahi ke ni bani insha kifad'a min yadda kuke zaune da wannan miskilin mijin naki.

sumayya gyara zamanta tayi tace ai lafiya lou miskilanci kau saidai abinda yayi gaba, zinat tace ke ya batun first night d'inku,

dariya gimbiya sumayya tayi tace ai babu abinda yagane game da hakan kinsan nayi amfani da magungunan da kikasa aka had'a min wlh har tausayi yabani ganin bai gane komai ba.

ta6e baki zinat tayi tace ke inbanda abinki wa yace miki ana tausayin maza indai kina lalla6a miji ai sai yarainaki, shawarace zan baki daga inda miji yafara d'aga miki murya ke kinuna masa kinfi sa hauka,

sannan ba kowane lokaci zaki dinga ba mijinki kankiba saboda idan kika saba masa da haka toh sai kin gunduresa yaji ya gaji da ke daga k'arshema sai kiga kishiya

zaro ido sumayya tayi tace kishiya kuma?  zinat gyad'a kai tayi tace eh man ai wlh namiji ba a basa amana ke nifa saboda tsoron halin maza yasa nakasa aure nake cin karena babu babbaka dukiya ce natara bakin gwargwado a lokacin da kuma naji ina buk'atar namiji ga mazanan birjit sai na za6a, inma macen nake buk'ata kema kin sanni.

dariya sumayya tayi tace hakane k'awata wlh kin kawo shawara mai kyau, ke nima fa sonake inga natara dukiya dan ban had'a kud'i da komai ba tunda ga mulki ga miji kinga dukiya yarage dan haka business zan fara. saidai anya zamu kwashe lafiya da yarima?

harararta zinat tayi tace kefa matsalata da ke wani lokacin baki da ganewa ammah asannu zan ganar da ke yadda zaki fahimta,  ammah nagargad'eki da lallashin miji bare ma wannan mijin naki  idan yashareki kema kifita harkarsa ke da nice da nasan yadda zan juyasa yakoma a tafin hannuna,

gimbiya sumayya tace hmm ba dai yarima ba anya akwai macen da zata iya juyasa?
zinat tace kefa matsalata da ke kenan bakida ganewa,  kedai kigwada kigani dakanki zaki bani labari, yanzu dai taso mushiga daga ciki.

mik'ewa sumayya tayi tana dariya zinat tana binta a baya suka shige bedroom,
a ranar haka zinat tawuni gidan gimbiya sumayya tana k'imsa mata makirci iri-iri har saida taga gimbiya sumayya ta hau ta zauna sannan tabarta.



Tun daga ranar gimbiya sumayya tadaina shiga sabgar yarima shima shareta yayi yacigaba da hidimar gabansa,

yarima tun  bai damuwa  har abun yazo yafara damunsa yanzu tsawon wata d'aya da aurensu tun satin farko rabonsa da gimbiya domin ko d'akinsa bata zuwa.


yau da dare kasa daurewa yayi dan haka yatashi yasaka alkyabbarsa yafito yanufi 6angaren gimbiya sumayya, da key d'insa yabud'e direct bedroom d'inta yashiga chan tsakiyar gado yahangota ta baje sai baccinta take ahankali yataka yaje yahau saman gadon.

gimbiya sumayya da take bacci jin ana shafata yasa tafarka,  da mamaki take kallon yarima,  chan kuma sai tad'aure fuska tace lafiya?

yarima cigaba yayi da abinda yake kamar ba zaiyi magana ba sai kuma chan yace sumayya yanzu saboda Allah hakan da kike min kina ganin kin kyauta?  hak'k'ina nazo kar6a,

gimbiya sumayya janye idonta tayi daga kallonsa cikin ranta tana jin dad'in shawarar da k'awarta tabata ganin yau dakansa ya aje girman kan yazo d'akinta,

ganin yarima suhail yana shirin rikitata yasa tajanye jikinta gefe tace haba dan Allah yarima wai menene haka nifa a gajiye nake.

da mamaki yarima yake kallonta yace haba sumayya saikace wadda tayi wani aiki nidai yanzu kibari inyi inyaso daga baya sai kiyita baccinki.

gimbiya sumayya komawa tayi takwanta tare da juya masa baya tace ni ba zan iyaba gaskiya,  yarima binta yayi yana lallashi dakyar ta amince masa shima saida taita masa k'orafin ta gaji kan dole a k'arshe yahak'ura yabarta batare da ya ida samun nutsuwaba,

toilet d'inta yashiga yayi wanka sannan yadawo yakwanta tare da juya mata baya cike da mamakin yadda sumayya tasauya hali .

gimbiya sumayya ko murna takeyi ganin ta d'an ci nasara har Yarima suhail ya zo d'akinta yau, kuma ya aje girman kai da sarautar ya lallasheta.




Tun daga lokacin  yarima shi yake biyota d'akinta ko da ace ya yi mata wulak'anci a wani wajen ita kuma sai ya nemeta take ramawa sai ya-yi dagaske yake samun hak'insa a wajenta ahaka suka haura wata shidda ammah ko 6atan wata bata ta6a yi ba,

dada ta fi kowa damuwa domin tisata gaba take a d'aki tana tambayarta ko akwai abinda take sha ita dai gimbiya a'a take cewa, dada tace a'a gimbiya indai akwai abinda kikeyi,  gimbiya saidai tayi dariya tace dada inda ina yin wani abu ai da kun gane, dada saidai tace toh Allah yakawo.

ko da yarima yazo yagaishe da dada bayan sun gaisa dada tace yarima wai har yau ba wani labari?

yarima shuru yayi saida yayi kusan minti biyu sannan yace dada labarin me kuma?

dada tace hmm ciki mana.

murmurshi kawai yayi yace dada ai haihuwa lokacine, idan da darabo zamuyi.

dada tace toh Allah yakawo mai albarka yarima yace Ameen.

sannan yarima yatashi yafita dogarawansa da suke tsaye bakin k'ofa suna ganin ya fito nan suka fara masa kirari yana gaba suna biye da shi tun kan ya isa wajen jerin motocinsa da yasa aka tanadar masa dan yafita dasauri aka bud'e masa dank'areriyar motarsa da take tsakiya nan yashiga baya yahakimce sannan dogarawa suka shiga sauran motocin akasa tashi a tsaka nan aka kama hanya.

asibitoci yaje yakai ziyara yaduba marassa lfy yayi musu kyauta sannan yawuce gidan marayuwa yabada kayan abinci kowa yaji dad'in ziyarar da yakawo domin daman halinsane kyauta,

daga nan suka kama hanyar gida, ko da suka isa bai shigaba saida yatsaya yasa aka tara ma'aikatansa yaraba masu kud'i nan suka zube suna ta godia daganan yawuce part d'insa yana shiga yacire kayan jikansa yafad'a toilet yayi wanka,  bayan ya shirya saman gado yafad'a yana hutawa bud'e k'ofar da akayine yasa yabud'e idonsa dayake a lumshe,

ganin gimbiya sumayya ce yasa da mamaki yakalleta domin yasan bata shigowa d'akinsa sai idan tana buk'atar wani abu,  maida idanunsa yayi yalumshe,

takowa tayi tahau saman gadon tazauna gefensa ganin baida niyar bud'e ido yasa tace ashe har kadawo tun d'azun nake aikowa adubomin idan kana nan, 

yarima batare da ya bud'e idanunsaba yace ya akayi kika shigo min d'aki ba'a fad'a miki nace kar wanda yashigo ba? gimbiya sumayya murmushi tayi tace yanzu dan zan shigo d'akinka har sai anbani izini a matsayina na matarka?

banza yarima yayi yakyaleta,  ganin baida niyar tanka mata yasa takwanta a jikinsa ta d'auka zai gwalisheta ammah taji ya yi shuru baice komai ba,  dan haka takai hannu tana shafa fuskarsa daga nan tafara kissing d'insa daman abu ga mai nema nan yarima yabiye mata,

ya yi mamaki yadda yau bata hanasa kantaba domin yasan hali da ya fara zata fara cewa ta gaji,  ammah yau saida yagaji dan kansa sannan yabarta.

rungume take a jikinsa cikin shagwa6a tace my sweetheart dan Allah inaso kabani 2 million,

yarima baiyi mamakin jin hakan daga garetaba, domin daman yasan za'a rina ba zata ta6a bashi kantaba sai da dalili,

bud'e idonsa yayi yasafkesu akan fuskarta kamar ba zaiyi magana ba sai kuma chan yace mezakiyi da kud'i?

Sumayya batare da damuwaba tace business nakeso inyi kaga zaman hakanan ai baya yuwuwa zamu had'a jari da k'awata zinat zata dinga zuwa tana saro mana kaya, zamu bud'e babban boutique a chan Abuja.

yarima tunda tafara bayanin yatsareta da ido har takai aya sannan yace yanzu ke bakiji kunya ba kice zakiyi kasuwanci akwai abinda narageki da shi ne?

gimbiya Sumayya d'aure fuska tayi tace kai fa matsalata da kai kenan to shi business dole sai marar wadata yakeyinsa?

yarima janye jikinsa yayi yace idan ke bakida hankali toh ni ina da shi kuma ba zakiyi ba,  yana gama fad'in haka yawuce yashige toilet domin yayi wanka.

gimbiya Sumayya binsa tayi da kallo cike da takaici tace tsiyata da kai bakasan arzik'iba saida nagama baka kaina sannan kanemi kawulak'antani toh wlh baka isa kahananiba  dan haka muzuba mugani,

tana gama fad'in haka tajanyo kayanta tasaka tatashi fuuuuu  tafita tabar d'akin.



_Comments_
      *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_*~Sak'on gaisuwata agareki Mummyn khalil fatana Allah yabaki lafiya, Allah yasa zakkar jikine~*_


_kuna ina Kuzo yau ranar takuce wlh ina ji daku har cikin zuciyana *My k'anwa Safiyya Aliyu, Mrs Abubakar,  Ma zeenart, Hafsat Kanty, Cool Angel, Chubby, Asma'u Yusuf Beji,  Husnah,  Mugirat Musa, Maman Sadiq, My k'anwa Khairyy, Maman Haidar, Hadiza Abubakar,  Maman Amira, Kubcy Auwal, Dr Xeey Xeey,  Aisha Baba Audu, ummu walid nd Abdul, Maman khaleesat,  Sadiya Abubakar, Billy....* da ma sauran wad'anda ban lissafoba,  wannan page d'in nabakushi Allah yabar k'auna😘_

page 4⃣

tana fita daga d'akin yarima part d'inta tawuce ko ta kan su jakkadiya batabiba da suke tsugunne suna ta kwasar gaisuwa wucewa tayi tashige bedroom d'inta, wayarta tad'auka takira zinat, zagaye d'akin tashiga yi tak'agara zinat tad'aga wayar ammah har tatsinke bata d'agaba,  tsaki gimbiya taja tace itafa matsalata da ita ayi ta kiranta sai taga gama take d'auka,

k'ara Kiranta tayi bugu biyu tad'aga
ko gaisawa basuyiba tace zinat kinajin wancan d'an rainin hankalin wai bazai barni inyi business d'inba

zinat cikin tsawa tace what!  shi har ya isa yahanaki kuma kihanu? gambiya tace hmm yoh ke kina tunanin ma zan hanu?

zinat dariya tayi daga chan 6angaren tace wlh innice yanemi yaraina min hankali tuni zan nuna masa iyakarsa ke ak'arshema zan iya kashe auren tunda dama dashi yake tak'ama,

gimbiya zaro ido tayi kamar tana gaban zinat tace kirufa min asiri ai wlh ba zan iya rabuwa da shi ba saidai nasan ta inda zan 6ullo masa kibarni da shi.

zinat tace toh shikenan nidai ina jira cikin week d'innan inga alert saboda so nake inje ingama komai dawuri indawo,

gimbiya sumayya tace toh shikenan kar kidamu,  nan sukayi bankwana.

suna gama wayar gimbiya ummanta takira saida takusan tsinkewa sannan sultana sadiya tad'aga da sallamarta,  sumayya ko gaisheta batayiba tace ummana wlh yarima baida mutunci

sultana sadiya a rikice tace nashiga ukku shalele miyake faruwa ne?  wlh indai wani cin mutuncin yayi miki zan rufe ido inci masa mutunci shima daga shi har mahaifiyartasa a tafin hannuna suke,  kifad'a min abinda yake faruwa.

Sumayya cike da jin dad'in ganin yadda mahaifiyarta take kula da ita, sannan tabata labarin business d'in da takeso tayi da yadda suka kwashe da yarima.

sultana sadiya tace ai bai isaba Indai ina raye ba zaki ta6a yin kukaba ammah kafin ind'au mataki da hannuna kije kifara samun dada kuyi maganar domin nasan ita zata fahimceki sosai inko ta yarda nasan yarima ma zai amince ko da ace baya so.

cike da jin dad'i sumayya tace hakafa za'ayi ummana wlh saisa nake k'ara sonki saboda duk abinda nake so kema kina sonsa.

'yar dariya sultana tayi tace idan ban so abinda kikeso ba toh nawa zan so? kekad'ai fa ce namallaka,  ke nifa ba ma wannan ba wai har yanzu ba wani bayani?

sumayya ta fahimci inda mahaifiyarta tadosa ammah sai tanuna bata fahimtaba tace ummah wane bayani kuma?

ummanta tace ke gidanku ni zakiyi ma kwana-kwana?  ke ni ban yarda da keba anya bakiyin family planning?

dariya sumayya tayi tace ni babu abinda nakeyi kuma nima insha Allahu sai na shekara biyar sannan zan haihu.

sultana sadiya tace nashiga ukku ke gidanku wa yace miki ana gudun haihuwa a gidan sarauta?

gimbiya cikin shagwa6a tace ummah kema fa saida kika dad'e sannan kika haihu.

ummah tace toh ai nima ba dan ban soba Allah ne bai baniba a lokacin, inma kinsan kina yin wani planning toh wlh kidaina,

gimbiya tace nidai yanzu dai shikenan ummah tunda nace miki babu abinda nake ai sai kibar maganar,  ni nafi buk'atar business d'innan bari dai inje muyi magana da dada, ummah ba dai dan ta yardaba tace toh shikenan sai najiki,

gimbiya tana gama wayar wanka tashiga tayi bayan ta fito shiryawa tayi cikin shigarta gwanin sha'awa sannan tafito nan kuyangi da bayinta suka take mata baya har suka shiga turakar sarki,

lokacin da tashiga parlour dada tana kishingid'e ana mata tausa,  nan duk ma'aikatan dada suka gaisheta tare da yi mata kirari, tana yatsina ta amsa musu,  nan bayinta suma suka zube suka  kwashi gaisuwa a wajen dada,  gimbiya zama tayi gefen dada tagaisheta,

dada cike da fara'a ta amsamata tace 'yar albarka meyake tafe da ke Allah yasa ba wannan sarkin 'yan iyayin bane yayimiki wani abu.

gimbiya k'ara 6ata fuska tayi tace dada kamar kau kin sani wlh k'ararsa nakawo,

dada tace oh ni Asma'u yanzu yaron nan nake ganinsa miskili ashe shima ya iya mugunta.

yanayin yadda dada tayi maganar yaso yabata dariya, gimbiya kallon bayin tayi da suke tsugenne tace dallah kutashi kuba mutane waje kunzo kun saki kunnawa kuna saurarenmu.

dasauri suka rausaya gaba d'ayansu sukace Allah yahuci zuciyar gimbiya mun barku lafiya,  sannan suka tashi suka fita.

dada kallonta take cike da mamaki tace sumayya ashe har yanzu kina nan da halinki na wulak'anci?

gimbiya murmushi tayi tace toh ai sune basusan suba mutane waje suyi maganaba sai suwani yi zaune kuma idan nasakar musu fuska sai surainani.

dada sakin baki tayi tana kallonta har saida takai aya sannan dada tace sumayya na haneki da wannan halin ya kamata kizauna da kowa lafiya domin wata rana mijinki shi zai kasance sarkin garin nan.

murmushi sumayya tayi tace toh ranki yadad'e tuba nake, murmushi dada tayi irin nasu na manya sannan tace ina saurarenki me mijin naki yayi miki?

gimbiya gyara zamanta tayi sannan tace dada daman kasuwanci nakeso inyi shine natambayi yarima yabani jari sai yahanani kuma wai ba zanyiba.

murmushi dada tayi tace in banda abinki sumayya me kika nema kika rasa a gidan nan?  kuma na tabbata babu abinda zaki nema wajen yarima kirasa domin nasansa da kyauta.

sumayya 6ata fuska tayi kamar zatayi kuka tace dada nima inaso indinga cin gashin kaina kuma fa k'awatace zata dinga kular mana da kayan ba sosai zan dinga zuwaba ita zata dinga yi mana komai.


dada ganin sumayya ta 6ata fuska yasa taji babu dad'i domin tana son jikartata sosai jininsu ya zo d'aya dan haka tace kikwantar da hankalinki yanzu kiramin shi awaya.



yarima bayan ya fito wanka yashirya cikin shigarsa ta alfarma ya yi kyau sosai wayansa yad'auko yakira shahid inda yashaida masa yazo suje yarakasa gidan gona akwai abinda yakeso yayi a chan.

shahid yace to shikenan ranka yadad'e daman yanzu haka zan fito daga fada sai kafito muhad'e,

yarima yace ohk sai nafito.

cike da k'asaita yake tafiya duk inda yagifta kallonsa ake cike da sha'awa,  ana kwasar gaisuwa yarima yau 'yan jin kan suna a kansa ko hannunma basu samu matsayin da yad'aga musuba

lokacin da yafito dogawara duk suka taso d'aga musu hannu yayi alamun a'a har ya kusan kaiwa wajen motar sai yaji wayarsa tana ringing tsayawa yayi daga tafiyar da yake yad'auko wayar ganin mai kiransa kamar ba zai d'agaba har saida takusan tsinkewa sannan yad'aga batare da ya ce komai ba yakanga a kunnensa.

gimbiya sumayya jin baiyi maganaba yasa tamik'a ma dada tace gashi kuyi magana,

dada tana kangawa a kunnenta tace toh sarkin miskilanci bakaji ma zaka iya magana,

yarima jin muryar dada da yayi yasa yad'anyi murmushi yace toh me zan ce?

dada tace eh babu fa abinda zakace yanzu dai kazo ina son ganinka.

yarima yana jin haka yasan da wata a k'asa musamman ma da yaga da wayar gimbiya aka kirasa,

dada tace toh ko nima wahalar yimin maganar ake ji?  murmushi yarima yayi yace dada yanzu fita zanyi kibari sai nadawo sai muyi maganar.

dada tace sannu babana toh idan ni kana ganin ka rainani toh sai inkira ubanka shi da ya isa da kai sai yasa kazo.

yarima yace shikenan kakus gani nan zuwa ai abun bai kai ga hakaba,

dada tace ina saurarenka,  yarima batare da yabata amsaba yakashe wayarsa kallon shahid yayi da yake tsaye yana kallonsa yace shahid bari inje wajen waccen tsohuwar tana nemana tun kan tajamin sharri wajen daddy.

dariya shahid yayi yace toh ranka yadad'e sai ka fito.


yarima ko da yashiga baiyi mamakin ganin gimbiya sumayya ba dan haka zama yayi bisa kujerar da take opposite d'in wadda su dada suke a bisa,  nan yagaishe da dada cike da girmamawa itama ta amsa masa.

daga nan shuru yabiyo baya chan sai dada tace suhail kaban mamaki wlh,

yarima kallonta yake da mamaki ammah baice komai ba.

dada batayi mamakin shurun da yayi ba saboda tasan halinsa dan haka tacigaba da cewa saboda Allah dan matarka tanason tayi kasuwanci sai kahanata?

yarima harara yawurga ma sumayya sannan yamaida kallonsa ga kaka .

kaka tace kai tambayarka nake shine kayi min shuru?

yarima cikin rashin damuwa yace dada ai nad'auka ta baki amsar abinda nace mata.

dada rik'e baki tayi tace wai kai wane irin mutum ne amsar ma bakaji zaka iya bani?

yarima shuru yayi kamar ba zaiyi magana ba chan kuma sai yace toh ai nace mata ban aminceba saboda babu abinda narageta da shi kuma indai kud'ine zan iya bata ammah ban yarda tayi kasuwanci ba ai sai taja mutuncina yazube a idanun mutane,  daka ma gimbiya tsawa yayi yace ke ba haka nace mikiba? ??

Gimbiya ta tsorata da tsawar da yayi mata ammah sai tadake tad'auke kanta daga kallonsa.

dada ta6a hannu tashiga yi tace nashiga ukku yanzu a gabana kake mata tsawa ai da had'emu kayi ni da ita kadokemu sai inga kamar zai fi maka sauk'i.

yarima yace Allah yabaki hak'uri ammah dai yakamata kiduba kiga maganar nan bai daceba ace tadinga yawo tana chakud'a cikin maza,

kaka kallon sumayya tayi da taci face sannan tamaida kallonta ga yarima tace ai tace ba sosai zata dinga zuwaba abokiyar kasuwancin ce zata dinga kula da komai dan haka inaso kabata kud'in inkuma baka iya bata sai inkira 'ya'yana su subayar tunda su na isa da su.

Yarima baice komai ba yad'auko cheque yacike mata yamik'a mata yace gashinan kuma duk abinda yafaru kiyi kuka da kanki.

dada tace insha Allahu babu abinda zai faru sai alkhairi,  kuma dan bak'in ciki baka ji zaka iya bata cash, yarima suhail mik'ewa yayi yace dada so kike kijasa min ciwon kai,  bari intafi ana jirana.

dada tace ka dai ji dashi marar mutunci kawai,

yarima murmushi yayi yace na barki lafiya 'yar tsohuwa, sannan yaficce yabar turakar.

Gimbiya sumayya tana ganin yafita tatashi tahau tsalle da murna daga k'arshe da rungume dada tace nagode sosai ranki yadad'e Allah yak'ara tsawon rai wlh kin gama min komai.

dariya dada tayi tace ni sakarni ja'irar yarinya kawai ammah a gaban yarima bi kikayi kika marairaice kamar da gaske.

itama gimbiya dariya tayi tace ai wlh dan ina neman abu a wajensa saisa nabarsa yaci min mutunci son ransa ban tankaba.

dada rik'e ha6a tayi tace toh daman ashe bashi kad'ai yake rashin mutuncin ba harda ke, toh wlh kigyara domin aure ba abun wasa bane kuma kidaina ganin nasashi yabarki kiyi toh wlh kikama kanki kirik'e mijinki kar kififita kasuwanci akan aure kuma dan kince k'awarki zata dinga kula da komai saisa nagoyi bayanki.

gimbiya sumayya tace naji dada zan kula,  nagode sosai.

mik'ewa sumayya tayi tana gyara alkyabbarta sannan takwala ma jakadiya kira,  dagudu jakadiya tashigo tare da zubewa k'asa tace na amsa kiranki ya shugabata,

kallonta gimbiya tayi tace kuzo kucigaba da aikinku na kula da dada , jakadiya tace toh ranki yadad'e.
sannan gimbiya tayi gaba tana cewa kakus na wuce, dada tace toh sumayya

gimbiya sumayya tana fitowa nan bayinta suka mik'e suka take mata baya takoma 6angarensu.


Yarima suhail yana fitowa fuskarsa a d'aure yakar6i key d'in mota hannun driver dasauri d'aya daga cikin dogarawansa yabud'e masa motar yashiga.

shahid ganin yarima bai ko kallesaba kamar baisan da shiba ya shige mota dan haka shima yaje yabud'e yashiga yana cewa yau dakanka zaka ja mu?

yarima baice komaiba yaja motar yabar gidan, gudu yakeyi sosai da motar shahid yanata yi masa magiya akan yarage gudu ammah yarima kamar ba dashi ake ba.

cikin k'ank'anin lokaci ya isa gidan gona horn yashiga yi dasauri maigadi yazo yahangame masa gate yashiga da motar yana yin parking fitowa yayi yashige ciki bai ma kula da gaisuwar da ma'aikatan gidan sukeyi masaba.

shahid numfashi yake maidawa cike da jin dad'in sunzo lafiya domin bai kawo ma ransa zasu iso lafiya ba,  daga k'arshe dai yabud'e motar yafito nan yatsaya saida suka gama gaisawa da ma'aikatan sannan yawuce cikin gidan.

A parlour yatarar da yarima kwance saman kujera idanuwansa a lumshe ya yi matashin kai da hannuwansa, 

shahid tsayawa yayi gefensa yace wai yarima meyake faruwa ne naga tun da kadawo daga kiran da dada tayi maka fara'arka tagushe?
kuma dan mugunta kadinga gudu da mu toh idan kai bakason ranka toh ni inason nawa.

yarima idanuwansa a lumshe bai tanka masaba.

shahid tsaki yaja tare da zama yace kai nifa matsalata da kai kenan sai anayi maka magana kashare mutane kamar ba da kai akeba.

shidai yarima suhail baice komai ba saida yayi kusan minti biyar sannan yabud'e baki dakyar yace shahid wlh sumayya batada mutunci yanzu saboda Allah duk mutuncina ammah tana nema tazubar min dashi.

shuru yayi nad'an lokaci sannan yacigaba da cewa ni duk abinda takemin ban ta6a kai k'ararta ga kowaba ammah ita da mun d'an samu sa6ani toh sai kowa ya sani,  ya za'ayi matar aure kuma matar yarima kamarni ace wai nabarta tana business har dada tagoya mata baya ai sai aja mutane suzageni.

Shahid cikin ransa yace ai indai wannan marar mutuncin ce zata aika domin bazan ta6a mance rashin mutuncin da tayi minba ranar da nazo wajenka.

chan kuma sai shahid yace kayi hak'uri kasan mata sai da hak'uri kacigaba da hak'urin da nasanka da shi.

yarima bud'e idonsa yayi da suke a lumshe yayi murmushin da yafi kuka ciwo sannan yace shahid kallon da akemin nine macuci cutar sumayya nakeyi babu Wanda yata6a tambayata yadda zaman aurenmu yake ammah wai ni zan saki matata tadinga yawon kasuwanci garuruwa.

shahid cike da tausayi yake kallon abokin nasa domin yasan ba'a ta6a jin matsalarsa saboda zurfin cikinsa ammah yau shine yake fad'a masa abinda yake damunsa tabbas yasan ba k'aramin 6ata masa rai akayiba, shahid yace dan Allah yarima kacigaba da hak'uri kadinga yi mata fatan alkhairi kar kad'auki mataki insha Allahu dakanta zata daina abubuwan da take.

Yarima shahid maida idanuwansa yayi yalumshe yana jin wani iri a ransa,

ganin haka yasa shahid yatashi yafita yana zagaya gidan gonar....




_Comments_
        *nd*
_Share_







_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Sak'on gaisuwata agareki aduk inda kika kasance my Aysha hak'ik'a ina yinki irin sosai d'in nan, ina tayaki murnar sabon novel d'inki da zaki fara mai suna *K'AUNACE SILA* Allah yasa afara lafiya agama lafiya my dear, Happy Birthday in advance🎊🎉🎈_

_*Ba zan gaji da sadaukar muku da page ba Masoya ina jin dad'in comments d'in da nake samu daga gareku a group's da masuyimin ta pc wlh ina yinku over,  wannan page d'inma kuje da shi nabakushi a kyauta👌 sis Nerja'art tana sonku irin sosai d'in nan😍*_

page 5⃣

yarima duka wayoyinsa yakashe dan kar adamesa da kira dan yasan confirm ne sai maimartaba ya nemesa,
bayan sallar isha'i suka bar gidan gonar,  shahid ne yakar6i key d'in motar yayi driving d'insu domin cewa yayi ba zai yarda yarima yatuk'asuba gudun kar yak'ara irin driving d'in da yayi d'azun shidai yarima baice komai ba yamik'a masa key d'in.

ko da suka isa yarima cema shahid yayi yazo sufara shiga fada sugaishe da sarki,  shahid bai musaba yabi bayansa a jere suka shiga fad'a nan duk mutane suka zube suna kwasar gaisuwa ahaka har suka iso gaban sarki,

dasauri wani dogari yad'auko wani had'ad'en carpet yashimfid'a musu nan sauran dogarawa suka zo suka baza manyan rigunansu suka kare su yarima daga ganin mutane suna cewa azauna lafiya yarima, saida suka tabbatar da sun zauna sannan suka matsa nan su yarima suka gaishe da sarki, sarki fuskarsa d'auke da fara'a ya amsa nan fadawa suka d'auka angaisheku yarima mai jiran gado sarki ya amsa gaisuwarku Allah yaja da ranka.

sannan yarima suka gaishe da su daddy da abban sumayya, nan ma fadawa suka d'auka da angaisheku kuma,

maimartaba kallon yarima yayi da yake durk'ushe k'asa yace yarima tun d'azun nake aikawa akira min kai ammah sai adawo acemin tunda kafita baka dawoba.

yarima suhail murmushi kawai yayi.

ganin bashida niyar yin magana yasa shahid cewa ranka yadad'e munje gidan gona ne tun d'azun muna chan.

maimartaba murmushi yayi irin nasu na sarakai sannan yace Alhmdllh gaskiya ina jin dad'in hakan kuma duk ayyukan alkhairi da kukeyi a gari  yana dawo min a kunnena tabbas nasan ko bayan raina nabar magajin da zai gadeni Wanda zai so kuma yatausaya ma jama'arsa tabbas kaine yafi cancanta da kakasance *Sarkin sarakai*

yarima dasauri yad'ago kai yakalli mai martaba har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa,

gaba d'aya fadawa suka d'auka angaishe da yarima mai jiran gado,  angaishe da kwarzon namiji, angaishe da namijin zaki sarki ya gaisheka.

yarima da shahid k'ara gaishe da sarki sukayi sannan suka mik'e dasauri sauran jama'a da fadawa suma suka mik'e nan suka shiga yi ma yarima kirari har saida yafita daga fadar sannan suka zauna.

shahid saida yaraka yarima har wajen turakarsa sannan yayi masa sallama yatafi gida.

yarima yana shigowa dasauri dogarawa suka zube suna kwasar gaisuwa sannan suka mik'e suka take masa baya suna masa kira,  takawarka lafiya yarima, Takawarka lafiya babban dodo mai rikita 'yan maza,  takawarka lafiya sarkin sarakai, nan bayi da ma'aikata sukaita fitowa suna gaishesa tun yana amsawa har yagaji yakoma d'aga musu hannu ahaka har ya isa part d'insa dasauri wani dogari yabud'e masa d'akin,nan suka d'auka ashiga lafiya yarima,  batare da yarima ya juyoba yad'aga musu hannu nan duk suka duk'a sukace munbarka lafiya yarima akwana lafiya, nan suka tashi duk suka watse, sai guards d'insa kawai suka rage yarima yana shiga bedroom d'insa kawai yawuce.

wanka yayi sannan yakwanta.




tun daga ranar suka rage had'uwa da gimbiya sumayya saidai idan tana son wani abu wajensa sannan take zuwa d'akinsa, yarima bai damuwa da rashin zuwanta hidimar gabansa kawai yake sai inyaji yana buk'atarta sannan yake zuwa d'akinta idan ma yaje sai yayi da gaske yake samu tana amince masa cikin 6acin rai suke rabuwa.

A sibitinsa da aka gina masa yana bada gudunmawa sosai baya bari ana wulak'anta masa patients kamar yarda baya bari awulak'anta masa staffs, hatta talakka idan yazo asibitin ana kar6arsa sannan kud'in magani rabi ake kar6a ana yafe musu rabi nan da nan asibitin yayi suna a garin da wajen garin.


Gimbiya sumayya business d'insu suke kud'i suna shigo mata sosai ammah har lokacin bataje tagano boutique d'in nasuba da yake a garin Abuja inda zinat tazuba ma'aikatan da suke kular musu da kayan kullum tsegumi take ma gimbiya akan rashin zuwanta tagano boutique d'in,




yau ma dai kiran gimbiya tayi a waya,  gimbiya sumayya da take kishingid'e bayinta zagaye da ita tuface ake bata a baki tana ci ahankali inda gefenta baiwace take karanta mata labarai anutse, wayarta da tahau rurine yasa kowa yanutsu wadda take rik'e da wayar tatsugunna tace ranki yadad'e gashi ana kira,

gimbiya sumayya yamutsa fuska tayi tace wake kirana?
jikin haule yana kyarma tace bestie naga ansa,  harararta gimbiya tayi tace ashe ke kin d'anyi karatu ba laifi ai na d'auka jahilace irinsu indo,  indo da take tsaye tana ma gimbiya fiffita murmushi kawai tayi batace komai ba,

gimbiya sumayya d'aukar wayar tayi tare da cewa my zinat dafatan kina lfy?
daga chan 6angaren zinat ta amsa da lfy lou kema dafatan haka sarauniya mai jiran gado
'yar dariya sumayya tayi tare da cewa ke ni har na hangoni ko nazama sarauniyar, Allah dai yakaimu lokacin
zinat tace am wai yaushe zakizo yau fa kusan 5 months ammah shuru bakizo kikaga yadda komai yake tafiya ba? saidai kawai kiji alert d'in kud'i.
gimbiya k'ara gyara kishingid'ar tayi tare da cewa zinat wlh nima inso inzo kawai ina tsoron wulak'ancin yarima.
tsaki zinat taja tace ke wlh kina bani mamaki sai kace ba big gurl ba? yanzu saboda Allah duk class d'inki ammah kizauna wai sai yadda miji yayi dake,  ke ya dai kamata kizo munfayi customers sosai kuma akwai kayan da nakeso ink'ara d'auko mana saboda haka kifitar da rana kizo,

gimbiya sumayya dogon numfashi taja sannan tace toh shikenan baby kar kidamu zanzo nima ai daman nayi missing d'inki,

dariya zinat tayi tace koma dai mekenan saidai kinzo, kinga sai kimin ko 2 weeks ne,

gimbiya sumayya tace ina ma dai laifi kice 1 week, shima sai munyi daga da yarima sannan zan samu yayarda,  koma dai mekenan zamuyi waya.

nan sukayi bankwana, gimbiya sumayya tunani tashiga yi yarda zata samu tatunkari yarima da maganar batare da yak'i amincewaba.

chan kuma sai taja tsaki cikin ranta tace dolema ya amince dan babu yadda za'ayi yak'unsheni cikin gida shi yana yawon gararanbarsa a gari. bari ma yadawo.


gimbiya sumayya kallon haule tayi tace yau inaso kisamin ido ga yarima idan ya shigo kiyi min magana?

haule cike da ladabi tace tau ranki yadad'e umurninki shine abun cikawata.


wajen k'arfe tara gimbiya tagama shirinta cikin kayan baccinta sannan tad'aura alkyabba daga sama tafeshe jikinta da turare mai k'amshi sannan tafito dasauri ma'aikata da bayi suka hau gaisheta tare da yi mata kirari,

gimbiya sumayya sai yatsina take tana ji suna k'ara mata girman kai,  baiwarta haule kawai tace tazo tarakata nan haule cikin sauri tataso tatake mata baya har sukaje 6angaren yarima nan ma dogarawa suka shiga gaisheta sannan suka bud'e mata k'ofa, kallon haule tayi fuskarta ba yabo tace zaki iya tafiya.

haule durk'usawa tayi k'asa tace toh ranki yadad'e atashi lafiya,

sumayya tana shiga ganin yarima baya parlour yasa dan haka tashiga bedroom tana bud'ewa yarima da yake tsaye yana sanya kaya da alama daga wanka yafito yakallota, kallo d'aya yayi mata yad'auke kai gimbiya sumayya cire alkyabtarta tayi ta aje gefe tare da takawa inda yarima yake tsaye tace my sweetheart ko intaimaka maka?

yarima bud'ar bakinsa sai cewa yayi a yau kuma?  kedai kawai kifad'amin me kikeso?

gimbiya tace haba yarima daga nace zan taimaka maka shine harda tambayar me nakeso?
kenan banda ikon yi maka komai sai idan ina buk'atar wani abu.

yarima a wulak'ance yace ai hakan halinki yake, kema kuma kinsan hakan kike,  yana gama fad'in haka yazagayeta yawuce yaje yahaye gadonsa yakwanta.

gimbiya sumayya tsaye tayi tana mamakin halin yarima cikin ranta tace nasan ta yadda zan 6ullo maka,  itama takawa tayi tanufi gadon tahau
takwanta tare da rungume yarima tace sweetheart ni bana buk'atar komai sai kai mijina.

yarima murmushi yayi yace ashe anyi miki karatun ta nutsu gaskiya natayaki murna idan har dagaske kin gyaru.

cike da k'ulewa gimbiya tace haba yarima wai meyasa kakeson kaga ka cimun fuska wani fa lokacin har a gaban bayina da kuyangina kake yada min magana.

yarima shuru yayi baice mata komai ba,  ganin haka yasa tad'ago kanta takallesa sai ganin idanuwansa a lumshe,  shafa sajen fuskarsa tayi tare da yin murmushi tace my dear ba dai bacci zakayi ba,

yarima batare da ya bud'e idonsaba yace ya dai?
gimbiya sumayya bakinta takai cikin nasa nan da nan yarima yacafke suka shiga faranta ma junansu.

saida yarima yadirjeta son ransa sannan yabarka atare sukayi wanka sannan suka kwanta tana rungume a jikinsa, yarima yana mamakin sauyawar da sumayya tayi ahaka bacci yayi awon gaba da su.


da asuba ko da sukayi sallah komawa sukayi bacci sai wajen k'arfe tara sannan suka farka a tare sukayi wanka sukayi breakfast bayan sun gama gimbiya jerawa sukayi da yarima suna tafiya inda dogarawa da kuyangi suka take musu baya har saida yarima yazo wajen motar da zai je wajen aiki da ita sannan sukayi sallama dasauri wani bawa yabud'e masa motar  yashiga, saida sukaga tafiyarsa sannan gimbiya tajuya suka koma gida, cikin ranta tana ayyana yadda zata biyo ma yarima ya amince batare da tashin hankali ba.


ko da yarima yadawo wajen k'arfe biyu ita taje tataresa cikin shigarta ta alfarma tafito a sarauniyarta ta asali sannan tarakasa har d'akinsa shidai yarima kansa yad'aure sosai ganin wata irin kulawa da yake samu a wajen gimbiya wadda tun satin aurensu rabon da yasameta,
ita tataimaka masa yayi wanka yashirya duk k'uiyarta ajeta tayi gefe tatattali mijinta




bayan kwana biyu yarima ne kwance da gimbiya manne da juna suna ta wasanninsu, gimbiya ganin yarima yana shirin nemanta yasa tadakatar dashi, yarima kallonta yake da mamaki idanuwansa duk sun canza kala, yarima dakyar yabud'e baki yace  ya dai?

Gimbiya turo baki tayi cikin shagwa6a tace sweetheart Please wani taimako nakeso kayi min,  yarima zuba mata ido yayi baice komai.

ganin haka yasa gimbiya sumayya yin murmushi tana wasa da gashin da yake kwance a k'irjinsa tace dan Allah so nake kabarni inje Abuja.

yarima da mamaki yake kallonta yace me zakiyi kuma a abuja?  Sumayya d'ago kai tayi tana kallonsa tace so nake inje inga boutique d'in da muka bud'e kaga tunda aka bud'e banjeba kuma badad'i ace har tsawon wannan lokacin ban lek'aba,

yarima d'auke kai yayi tare da cewa ba zakije ba,  gimbiya a firgice takallesa tace yarima meyasa? dan Allah kar kahana ni.

yarima suhail wani mugun kallo yawurga mata tare da cewa idan ke bakida hankali to ni ba mahaukaci bane,  babu yadda za'ayi insaki matata tayi irin wannan tafiyar mai nisa kuma ya kike tunani mutane zasu d'aukeni?  kawai akan kasuwanci?

gimbiya sumayya tashi tayi daga jikinsa cikin fushi tace wlh ban ta6a sanin kai butulu bane sai yau duk hallacin da nayi maka kwana biyu ammah baka ganiba?  toh bari kaji akan *KUSUWANCI NA* zan iya yin komai dan haka muzuba mugani kuma tafiya tana nan daram ko da baka. ....

wani gigitaccen mari da yarima yad'auketa dashine yasa takasa k'arasa maganar,  kallonsa take da mamaki saida 'yan cikinta sukaso sukad'a ganin yadda yake huci,

yarima dakyar ya iya bud'e baki yace ke har kin isa kidinga min shouting haka?  ko dan kinga ina lalka6aki? toh bari kiji albarkacin iyayena kawai kikeci kuma babu inda zakije  sannan daga yanzu kidinga ladafta maganarki idan kina a gaban *yarima suhail*, yana gama fad'in haka yad'auko rigarsa yasaka yaficce daga d'akin fuskarsa babu alamun annuri a tattare da shi ahaka yawuce yatafi part d'insa.

gimbiya tana ganin ya fita tafad'a saman gadon tacigaba da rizgar kuka takaicinta marin da yarima yayi mata tun da take iyayenta basu ta6a sa hannu suka daketaba sai yau wani yadaketa kuma wai miji.

tashi tayi tajanyo alkyabtarta tasaka tafito fuuuu dasauri kuyanginta suka mik'e zasu take mata baya cikin fushi gimbiya tadaka musu tsawa tace duk wacce takuskura tabiyoni abakin aikinta.

dasauri duk suka koma suka zauna domin sunsan abinda gimbiya tafad'a zata iya zartar da shi.

cikin sauri take tafiya kamar ta6a66a har ta isa 6angaren ummanta duk mutanen da suke gaisheta bata luraba saboda hankalinta baya a tare da ita tana cikin matsanancin bak'in ciki,


ummah da take zaune bayinta suna ta mata hidima saidai ganin gimbiya tayi kamar an jefota, a firgice ummah tatashi daga kishingid'en da take tace sumayya lafiya?

sumayya dasauri tazo tafad'a jikin ummah tare da fashewa da wani sabon kukan nan hankalin ummah ya ida tashi, cewa take sumayya kifad'a min abinda yake damunki mana,

ummah cikin 6acin rai takori ma'aitanta duk suka fita suka bar d'akin,  sannan tad'ago kan sumayya cike da damuwa tace shalele wa yata6a min ke?

gimbiya share hawayen fuskarta tayi nan takwashe dukkan abinda yafaru tsakaninta da yarima tafad'a ma sultana sadiya

sultana sadiya ranta ya 6aci sosai musamman ma da taji wai ya mari sumayya,  cikin 6acin rai taharzuk'a tamik'e dasauri sumayya tarik"ota tace ummah ina zakije?  ummah tace sakarni inje inci mutuncinsa sai yafad'amin dalilin da yasa yamareki ko mu da muka haifeki hannunmu bai ta6a kaiwa ga fuskarkiba da sunan mari sai wani banza zai mareki.

sumayya tace ummana kibarsa kawai ai sai na rama marin da yayi min dan ba zai ta6a ta6aniba azauna lfy,  nidai yanzu kisamo min mafita saboda ina da burin tafiyar nan cikin satin nan.

ummah komawa tayi tazauna tare da cewa ai dole ma ne kitafi dan haka taso muje wajen dada nasan yadda zan 6ullo ma lamarin

cike da jin dad'i sumayya tace nagode ummana wlh saisa nake k'ara sonki, murmushi sultana sadiya tayi tace ai dole inso duk abinda kikeso shalelena. nan suka tashi suka d'unguma turakar su dada. .........




_Comments_
       *nd*
_Share_





_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔


page 6⃣

suna shiga a parlourn dada batanan saidai ma'aikatanta nan suka zube suka kwashi gaisuwa wajen gimbiya sumayya da sultana sadiya ammah ko kallon arzik'i basu samuba, gimbiya ce a wulak'ance tace dada bata nan ne?

jakadiya tace ranki yadad'e ta d'an shiga ciki ammah yanzu zata fito,

gimbiya kallon sultana sadiya tayi tace ummah muzauna kafin tafito.
sultana sadiya bata musaba nan suka zauna suna jiranta.

bayan kamar minti biyar sai ga dada tafito dasauri duk suka mik'e tsaye hatta ummah da gimbiya saida suka mik'e nan kuyangi suka d'auka angaisheki sultana takawarki lafiya, daganan sukayi shuru domin sun san dada batason ana mata kirari.

nan tazo tazauna saman kujera, sultana sadiya da gimbiya nan suka duk'a suka gaisheta,  fuskar dada d'auke da fara'a ta amsa sannan suka zauna saman kujera, dada ganinsu da tayi haka yasa tasan muhimmin abune yake tafe da su dan haka tasallami kuyanginta gaba d'ayansu.

maida kallonta tayi ga sultana sadiya tace daga ganinku akwai abinda yake tafe daku ina saurarenku,

sultana sadiya murmushi tayi takalli gimbiya da tazuba mata ido tana jiran taji abinda zatace,  d'auke idonta tayi daga kallonta tamaida kan dada tace ranki yadad'e daman sumayya ce tazo tasameni da maganar da ban ji dad'intaba shine nace ai ke yafi dacewa muzo mufad'a mawa saboda daga sarki sai ke ne shuwagabanninmu.

dada dai zuba ido tayi tana kallonta chan sai tagyad'a kai tace ina saurarenku.

sultana sadiya tace daman sumayya ce tasamen akan ta yi ma yarima magana domin yataimaka yabarta taje tagano yanayin yadda business d'insu yake tafiya saboda tunda suka fara wata biyar kenan ammah bata samu talek'a ba abokiyar kasuwancintata ta matsa
akan ko da sau d'ayane taje taga yanayin wajen kuma akwai wani signing da akeso tayi shine takeso ko kwana biyune tayi toh tunda tafad'a ma yarima haka nan yahauta da fad'a da  cin mutunci a k'arshe ma har da marinta yayi,
haka tazomin a firgice shine nace muzo wajenki saboda ke yafi cancanta kishiga lamarin nan.

dada kallon sumayya tayi da idanuwanta suka kumbura saboda kuka,  haushine yakamata ganin irin cin mutuncin da yarima yayi ma jikarta, cikin fushi tace wannan bazai ta6a yuwuwaba domin bana son azalunci wani bare ma ace nawane yazalunci d'an uwansa tafiyace kuma da bazan aminceba saboda baidaceba amatsayinta namatar yarima guda ace tana yawo kuma tunda kika taso a nan gidan sarauta bakiga iyayenki suna haka ba kuma kinsan memartaba bazai ta6a amincewa da hakanba,

gambiya sumayya marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace dada dan Allah kitaimaka min,

dada tace toh shikenan ai tunda har yaci mutuncinki toh sai kintafi dan haka kiramin shi a waya.

gimbiya sumayya da ummanta sunji dad'i sosai da jin zancen dada,  dan haka sumayya takar6i wayar dada domin takira yarima.


yarima tunda yaje d'akinsa saman gadonsa yafad'a cike da jin haushin sumayya ammah baiyi mamakin hakanba domin daman chan yaba ma ransa da biyu take nuna masa kulawa sai idan tana neman wani abu daga garesa, a gefe guda kuma na zuciyarsa ya ji haushin marin da yayi mata domin shi a rayuwarsa ya tsani hakan.

wayarsace da tafara ringing kamar ba zai d'aukaba saida takusan tsinkewa sannan yad'auko ganin sunan dadane yasa yatashi zaune tare da yin picking d'in wayar yasa a kunnensa yayi sallama,

dada ko amsa masa sallamar batayiba cikin fad'a tace toh marar mutunci kazo kasameni ina jiranka yanzun nan kar kuma kakuskura ka6ata min lokaci domin idan bakazo cikin lokaciba ba kaiba hatta mahaifinka sai ransa ya 6aci, tana gama fad'in haka takashe wayar.


yarima haushine yakamasa jin rashin mutuncin da dada tayi masa kuma wai harda mahaifinsa tsaki yaja yace tabbas wannan nasan had'in sumayya ne lallai yarinyar nan batada mutunci, tashi yayi yashiga toilet yayi wanka cikin sauri yafito yashirya sannan yakama hanyar 6angarensu dada, hana dogarawa yayi surakasa shi kad'ai yatafi yana tafiyarsa ta k'asaita babu alamun fara'a tare da shi tsakaninsa da mutane saidai yad'aga musu hannu ko da daman halinsane hakan.

baidamu da gaisuwar da kuyangi sukeyi masaba yashiga d'akin da sallamarsa ko kallon inda su gimbiya suke baiyi ba yazauna cike da izza.

dada sakin baki tayi tana kallonsa,  gaisheta yayi, bata amsa masaba tace me yahad'aka da matarka?

murmushi mai aji yarima yayi yace dada ko gaisuwar ma baza'a amsa min ba?
dada tace bana buk'atarta karik'e abunka,  nace me yahad'aka da sumayya,

yarima sai a lokaci yakalli sumayya da sultana Sadiya yayi murmushi yace ashe ummah ce barka da rana.

sultana sadiya kamar tad'aura hannu saman kai tafasa ihu saboda takaicin yadda yarima yayi mata,  ganinta a matsayinta na uwar matarsa ammah baya ji zai iya gaisheta cikin girmamawa.

ganin yadda dada tatsaresa da ido yasa yace dada wani abu tace miki ya faru a tsakaninmu?

dada tace kai banason shashanci ashe bakada mutunci, dan rashin imani har ka iya d'aga hannu kamari matarka, toh bari kaji wannan yazama nafarko kuma na k'arshe sannan maganar tafiyar da tace zatayi inaso kasani dole kabarta tatafi dan bak'in ciki d'an abinda take samune yake tsone maka ido.

murmushi yarima yayi yana kallon kaka sannan daga baya yamaida kallonsa ga gimbiya da tatsaresa da ido yace toh  kinji dai abinda dada tace sannan yamik'e tare da kallon dada yace toh dada nabarku lafiya.

dada nace nashiga ukku ni Asma'u yanzun suhail saboda Allah baka d'aukeni da daraja ba?  ina maka magana zaka tashi?

yarima komawa yayi yazauna tare da cewa sorry dada ba haka bane kawai naga kin yanke hukunci saisa.

da mamaki dada take kallonsa tace kana nufin kai baka aminceba?

yarima suhail shuru yayi kamar ba zaiyi maganaba saboda maganar da yakeyi ta gunduresa ga wani irin haushin sumayya da yakeji da kullum batada buri sai na had'asa da su dada, sai chan yace ammah dada kin yanke hukunci batare da kinji nawa uzurinba.

dada tace karik'e abunka domin babu abinda zaka fad'amin tunda ka gama zaluntar 'yar uwarka ni yanzu amincewarka nakeso

yarima cike da jin haushi yace na amince saboda ke dada, wani murmushin mugunta yayi yace ammah dai duk abinda yafaru ina gargad'inki da kiyi kuka da kanki sumayya.

sultana sadiya a fusace tace insha Allah ba abinda zai faru sai alkhairi bakinka da bak'in nufinka sukoma maka, sumayya tace wlh kau ummah .

yarima murmushi kawai yayi baice komaiba dada tace toh ka kyauta ammah yanzu sai kabata hak'urin marin da kayi mata kuyafe ma juna domin farin cikinku da zaman lafiya mukeso,

yarima wani irin kallo yayi ma dada domin yasan bayan mahaifiyarsa sai dada kawai yasan matan da zai iya ba hak'uri, duba time yayi sannan yace yanzu dai bari intafi saboda kaina ya fara ciwo.

ganin dada batace komaiba yasa yarima yamik'e tare da cewa na barki lafiya ranki yadad'e sannan yawuce cikin takunsa yabar d'akin.

gaba d'aya binsa sukayi da kallo cike da mamakin halin yarima, sultana sadiya ko k'arshen k'ulewa ta k'ule ta cika fam.

dada kallonta tamaido agaresu tace saidai hak'uri kunsan halin yarima suhail wani lokacin hatta ni kaina nuna min yake kamar ban isa da shi ba ammah dai Alhmdllh tunda ya amince kitafi ni nasan yadda zanyi da maimartaba sai kije kifara shiri kifitar da rana koma dai mi kenan zan fad'a miki ammah dan girman Allah kar kidad'e domin kinsan halin mijin nan naki.

Gimbiya sumayya cike da jin dad'i tace insha Allahu dada ba zan dad'eba baifi inyi 1wk ba,  dada tace toh shikenan Allah yataimaka sukace Ameen, sannan sultana sadiya da Gimbiya suka k'ara duk'awa suka kwashi gaisuwa sannan sukayi mata sallama suka bar d'akin cike da jin dad'in nasarar da suka samu.



Yarima suhail ransa ya 6aci sosai kawai daman yana 6oyewane dan kar sugane halin da yake ciki yana fitowa direct 6angaren iyayensa yanufa a parlour yatarar da ummi kishingid'e ana mata tausa,


bayi da kuyangi suna ta yi mata hidima, suna ganinsa ko yazube yakwashi gaisuwa,  yarima batare da ya tankaba yad'aga musu hannu cikin sauri kowa yatashi suka fita daga d'akin takawa yayi ya isa Saman kujerar  da ummi take zaune zuba masa ido ummi tayi tana kallonsa,  yarima zama yayi shima yana kallonta da idanuwansa da suka kad'a daga launin fari zuwa na ja saboda 6acin rai sannan yajanye fuskarsa daga kallonta,
ummi tace suhail miyake faruwa ne?  kafad'a min damuwarka.

yarima suhail saida yad'auki kusan minti biyu kamar ba zaiyi magana ba sai kuma chan yace ummi yanzu saboda Allah ina auren sumayya ammah ta d'aukeni kamar ba mijintaba ban isa in hanata abu ba sai ta had'ani da dada, kullum cikin kai k'arata take.

shuru yad'anyi nalokaci sannan yakalli mahaifiyar tasa da tazuba masa ido yace wai abun haushin har da mahaifiyarta take goyan mata baya toh ni cewa nayi bata min laifi?  duk hak'urin da nake da ita bata gani duk abinda takemin wa nata6a samu nafad'a ma wa? kawai ina kyaletane albarkacin iyayenmu da zumuncin mu.

girgiza kai yayi cike da takaici yace ummi hak'uri ya k'are zan d'au k'wak'waran mataki akai.

Sultana Bilkisu cike da tausayin d'an nata take kallonsa domin tasan halin d'an nata ko da za'a cutar da shi ba ya ta6a damuwa saidai idan an kaisa k'arshe shine zakaga 6acin ransa.

tashi ummi tayi daga kishingid'en da take tarik'o hannun d'an nata tace suhail kacigaba da hak'urin da nasanka da shi insha Allahu komai zai zo k'arshe, wani lokacin dakanta zata daina.

yarima suhail murmushi yayi wanda iyakarsa baki sannan yace ummi har wane lokacin kuma?  kiduba kiga tsawon dad'ewarmu ammah kullum halinta k'ara canzasa take ni wlh da ace ina da wadda nakeso da aure zan k'ara domin sumayya da ita da babu, banbancinsu kad'an ne.

ummi zaro ido tayi tace karufa mana asiri yarima wane irin aure?  dukafa yanzu aurenku baifi shekara d'aya ba.

murmushin takaici yarima yayi yace ummi ba zaku ta6a fahimtataba.

ummi tace indai baso kake a zargemuba.

yarima suhail jingine kansa yayi a kan kujera tare da lumshe idonsa yana jin wani iri a ransa.

sultana bilkisu kallon d'an nata take cike da tausayi ganin tunda yayi auren nan yabi ya rame tabbas tasan akwai abinda yake damunsa dandai miskilancinsa ya zame masa yana da zurfin ciki sosai.
itama jan bakinta tayi tayi shuru domin tasan d'an nata baya da son hayaniya.

A ranar yarima bai fitaba d'akin ummi yawuni ak'arshema bedroom d'in ummi yakoma yasha baccinsa,  ummi hana kowa tayi yashiga.


Gimbiya sumayya suna komawa turakar sultana sadiya kallon ummantata tayi cike da farin ciki tace wlh ummi kin gama min komai, tabbas nayi sa'ar uwa mai son farin cikina.

Sultana murmushi tayi tace ai wlh akanki ba na jin zan iya ragama kowa, wannan mijin naki na tsanesa dandai babu yarda zanyi ne, gimbiya zaro ido tayi tace ummah mijin nawa kika tsana?

sultana Sadiya tace eh man saboda ni naci burin in haifi Wanda zai gaji memartaba ammah ban haifaba saisa tunda aka haifesa naji bana sonsa.

dariya gimbiya tayi tace toh ai yanzu sai kikwantar da hankalinki tunda ni yake aure kuma duk wanda zai gaji masarautarnan ni zan haifa masa.

Sultana tace hakane ammah ai har yanzu naga bawani bayani wlh hankalina tashi yake ganin kunyi shekara da'ya har da d'oriya baki haihuba.

gimbiya tace haba ummah wa yake ta haihuwa yanzu sai mun gama cin zamaninmu sannan zan haihu

sultana sadiya sakin baki tayi tana kallonta da mamaki tace sumayya ban ta6a sanin ke sakara bace sai a yanzu keda kike auren yarima ai kyau ace kinyi saurin haihuwa ko da ace biyune kibari kiyi in yaso daga baya sai ki tsayar da haihuwar sai lokacin da kikeso.

Gimbiya sumayya cikin fushi tace gaskiya ummah ni nagama tsara yadda nakeso rayuwata tatafi kuma na tabbata yarima bazai ta6a k'ara aure ba domin su dada ba zasu ta6a amincewa da hakan ba.

sultana sadiya tace kima daina wannan maganar wlh ko ni ba zan ta6a bari yayi miki kishiba,  nidai burina kijanye wannan plan d'in naki kihaifar mana baby,

gimbiya mik'ewa tayi tsaye tana gyara alkyabtarta tace ummah bari inje dai infara shirin tafiyarnan da zanyi saboda jibi nakeso inyita nabarki lafiya.

Sultana Sadiya bin d'iyartata tayi da kallo domin tasan dandai ajanye maganar haihuwarne shiyasa tace zata tafi,  murmushi tayi tare da girgiza kai tace sumayya kenan Allah yasa kifahimci abinda nake nufi. .....





_Comments_
       *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
?👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_sak'on gaisuwata agareku *Zaynav mtz fan's, Yarima suhail fan's 1&2, Ummun meenal fan's, hibbatullah fan's, janaf fan's, zauren sainah fan's, mummyn khalil fan's  Aufana true fan's* da sauran groups d'in da ban samu nalissafoba😍👌 ina jin dad'in comments d'inku Allah yabar k'auna_


_*Wannan page d'in nakune my hafnan, Janaf, Aysha nd ummun meenal ina ji daku cikin zuciyana😍😘*_

page 7⃣

yarima sai dare sannan yabaro turakar su ummi yakoma part d'insu,  saida yayi wanka yashirya sannan yafito dining yad'anci abinci bayan ya gama kallo yakunna yana yi, bud'e k'ofar akayi aka shigo bai ko d'ago kai ba domin ya san gimbiya ce.

gimbiya sumayya ganin bai kalletaba yasa tatako tazauna gefensa cike da isa tace daman nazo infad'a maka jibine fa zan tafi kuma kasan ba zan iya tafiya mai tsayi a motaba dan haka sai kabada kud'i ayomin Visa,

wani mugun kallo da yarima yawurga mata saida hantar cikinta takad'a, batare da ya janye idonsa a garetaba yace ni na'aikeki?

Gimbiya sumayya itama kallonsa take tace toh naga kai yafi dacewa da kasa ayankar min ticket tunda k'ark'ashinka nake.

yarima shuru yayi kamar ba zaice wani abuba sai chan kuma yace ke ban ta6a sanin bakida hankaliba sai yanzu  baizama dole inyi miki hakanba kuma bana tunanin akwai Wanda ya isa yasani dole,  dan haka tashi kifitar min daga d'aki tun kan in6ata miki rai.

gimbiya sumayya mik'ewa tayi saida takai bakin k'ofa sannan tajuyo takalli yarima suhail tace koma dai me kenan katabbatar zuwa gobe ka yimin abinda nakeso inkuma bahakaba zan fad'ama dada, tana gama fad'in haka taficce daga d"akin.

yarima suhail takaicine da bak'in ciki suka taru sukayi masa yawa tsaki yaja kawai ak'arshe ma yakashe kallon yatashi yashige bedroom d'insa cike da 6acin rai yakwanta,  yanajin wani iri a zuciya ji yake an cucesa da aka za6a masa gimbiya sumayya a matsayin matarsa domin kwatakwata halinta baiyi masaba.
ak'arshe wayarsa yajawo yakira d'aya daga cikin yaransa yace zuwa gobe a tabbatar anyi ma sumayya Visa.



Wanshe kare wajen k'arfe sha biyu da yarima yagama shirinsa fitowa yayi yanufi d'akin gimbiya sumayya inda yataddata a lokacin tafito daga wanka,  a wulak'ance yakalleta sannan yawurga mata ticket yace ba dan halinki nasa akayi mikiba dan ganin damanane.

harararsa gimbiya tayi tace eh ahaka d'in dai saida nayi magana,  yarima suhail murmushin mugunta yayi sannan yataka inda sumayya take,  dak'arfi yajawota tafad'o jikinsa har saida tad'anyi 'yar k'ara sannan yace sumayya inaso kisani darajar iyayena kawai kikeci da badan hakaba wlh da sai kin gane kuskurenki.

gimbiya sumayya tace suhail kadad'e baka nuna min kuskurenaba kuma yadda kake tak'ama da sarautarnan nima ai jinintane, bamuda banbanci ni da kai,  kuma idan ka cika d'an halak kata6ani kagani, kuma bari kaji jikina kagama samunsa tunda har kata6amin fuskata jiya yanzu daidai nake da kai.

yarima suhail d'auke ta yayi da mari yak'ara mata wani tare da wurgata saman gado yace banyi niyar kwanciya da ke ba ammah yau zan nuna miki na ciki d'an halakne ni, saman gadon yabita tare da fizge towel d'in da yake jikinta nan suka shiga kokawa ak'arshe yarima suhail yasakarmata nauyinsa.

mugunta yasa mata yadirjeta son ransa, gimbiya sumayya kuka kawai take, yarima saida yagaji dan kansa sannan yabarta,

kayansa yad'auka yasanya bai ko k'ara kallon inda sumayya take kwanceba tana ta ja masa Allah ya isa,  fita yayi daga d'akin yakoma part d'insa yayi wanka yashirya sannan yaje fada yagaishe da sarki daga nan yafita yabar gidan.


Tun daga lokacin basu k'ara had'a hanya da gimbiya sumayya ba baima san lokacin da tatafiba sai wajen dada yakeji, 

hatta umman sumayya yanzu ko ya gaisheta bata amsawa dan haka shima yadaina gaisheta,  ko da ace tana tare da abban sumayya toh abbah kawai yake gaishewa tsakaninsa da ita saidai tahararesa shikuma yanuna ko inkula.

__________________

awata anguwa mai suna yamza wata yarinyace take tafita a nutse kanta a k'asa yarinyar ba zata gasa shekara ashirinba wani gidane tashiga gidan da kagansa kasan bamasu hali bane saidai rufin asiri,  da sallamarta tashiga,  wata matace da nahango zaune tana wanke-wanke ciki-ciki ta amsa mata sallamar

cike da ladabi zarah tak'arasa inda matar take tare da tsugunnawa tace mama sannu da gida.

harara matar tawurgamata tace ke shine bakiyi min wanke-wankeba kika kama hanya kika fita daga gidan ko?

zarah cike da nutsuwa tace mama dan Allah kiyi hak'uri wlh ganinayi na makara islamiyya shiyasa.

rik'e baki mama tayi tace eh islamiyya fad'amin nida banyi islamiyarba, ke ga ustaziya ko?  to wlh inbaki canza haliba haka zakizo kik'are cikin gida,  kiduba kiga 'yan uwanki kullum sai sun fita sun samo mana 'yan kud'in da zamuyi hidima ammah ke kina nan jibge a cikin gida saidai aciyar dake ashayar da ke iyakarki kashi,  toh wlh indai bakiyi dagaskeba sai kin rasa mashinshini domin wannan girman kan naki babu inda zai kaiki.

zarah shuru tayi batace komai ba domin idan da sabo ta saba da halin iyayen nata,

tsawa mama tadakamata tace watau ga mahaukaciya ina magana shine kikayi shuru kika kyaleni watakau ga mahaukaciya tana magana.

zarah cikin nutsuwa tace Allah yabaki hak'uri mama kawo wanke-wanken in k'arasa miki.

ummah d'auraye hannunta tayi tamik'e tace ai ko bakiceba daman ke zaki idashi tunda baki aikin komai sai karatu saikace alhuda-huda.

mama tana tashi zarah tacire hijab d'inta tarataye saman igiya sannan tazauna tacigaba da wanke-wanken.

tana cikin yi saiga yayarta tashigo babu ko sallama kallonta zarah tayi cike da takaicin ganin irin shigar da take jikinta kayan sun matseta gyalen da tayafa ko dashi k'ara babu,  d'auke kanta tayi daga kallonta tacigaba da wanke-wanke tana addu'a cikin zuciyarta Allah yashirya su sugane gaskiya.

muryar yaya rauda ce tajiyo tana cewa zarah ina mamanmu take?  batare da takalletaba tace tana cikin d'aki.

Rauda kira tashiga kwala ma mama daga inda take tsaye,  mama datake d'aka dasauri tafito kallabinta a hannu tana washe baki tace a'ah 'yar albarka har kin dawo?

Rauda yamutsa fuska tayi tace eh ga wannan ledar da take hannunta tamik'a mata,  ummah cike da farin ciki ta amsa tana cewa me muka samu yau?

malam yusuf ne yashigo gidan yana cewa a'a 'yar baba ai naga lokacin da aka safkeki kinga har da 'yan canji mutumin yabani gaskiya yana da kirki.

Rauda yamutse fuskarta tayi tace ammah ai abba nace kadaina tambayarsu kud'i inkana tambayarsu ai sai kaja surainani ,

abba yace 'yar baba bafa tambayarsu nakeba sune suke bani kuma kinga babu kyau maida hannun kyauta baya ko ba haka bane Zainabu?
mama tace hakane malam,  yanzu dai mik'o wani abu nan dan musamu daren nan muci mai d'an dad'i-dad'i.

abba yace toh naji yanzu dai menene cikin ledarnan?

mama duba ledar tayi tare da washe baki tace ashe kazace yau shagali zamuyi kenan.

Abba ma washe baki yayi yace gaskiya naji dad'i daman wannan bakin nawa yakwana biyu bai ci namaba,  ammah dai 'yar baba Allah yaimiki albarka,

mama tace toh yanzu dai kakawo asiyo kayan miya muyi d'an pepper chicken,
abbah dubu d'aya yamik'a mata yace gashi sai akasiyo har da buredi wanda zamu d'an dangwala romon ai haka zaifi ko?

mama tace eh malam,  ai saima autarka tadawo muga ita mi zata kawo mana,  ai ni yau naga amfanin haihuwar 'ya'ya mata daman malam ai nafad'a maka 'ya'ya mata dad'i garesu,
malam yace hakane sannan yakai dubansa ga zarah da take tsugunne tana ta wanke-wanke, yamutsa fuska yayi yace Asma'u wlh d'iyar chan duk cikin 'ya'yana ita kad'aice batada k'ashin arzik'i wani ma lokacin ji nake anya jininace?

ummah tayi karaf tace a'ah malam  wannan cin mutuncin da me yayi kama idan ba d'iyarka bace toh wanene ubanta?  ko akwai wani mijin da na aura bayanka? ko kuma kana nufin ina bin mazan banza.

malam yace a"a zainabu nidai ina nufin kwata-kwata bata d'auko halinaba,  kiduba kiga ko farin jinin samarin nan ita batadashi,

ummah tace ah toh yanzu naji bayani,  ai malam kakalli wannan munafukar kawai bak'in ciki kawai take yi mana dan kar muci moriyarta kasan yanzu sai kahaifi d'a baka haifi halinsaba, wlh akwai samarin wulak'antasu kawai take tana korarsu sai wannan matsiyacin malamin nata da ta lik'e mawa me na k'asa yaci bare yaba nasama.

malam yace oh ni wlh daman nayi zaton haka ni wlh wannan sakaryar d'iyar bansan yaushe zata waye kamar 'yan uwantaba,  Allah dai yashiryata.

mama tace Ameen dai

malam yace yanzu dai dafa mana kazar a d'ansa kayan yaji nasan zatafi dad'i haka bari ind'an fita.

ummah tace toh malam adawo lafiya.

zarah dai zaune take tana wanke-wankenta duk firar da iyayenta sukeyi akan kunnenta hawayene yacika mata ido tana jin wani abu ya tokare mata mak'oshi saboda takaicin halin iyayenta,  cikin ranta addu'a take Allah yashirya mata iyayenta da 'yan uwanta sugane gaskiya.

bayan ta gama alwallah tad'aura sannan tad'auki hijab d'inta tashige d'akinsu,  lokacin yaya rauda tana shafa da alamu daga wanka tafito.

zarah shimfid'a darduma tayi tad'auko alk'ur'aninta tana karantawa har aka tada sallar magrib sannan tatashi tayi sallah

ido tazuba ma rauda tana kallon yadda take sallah cikin sauri babu alamun nutsuwa atare da sallartata

ko da rauda tagama sallar zarah kallonta tayi cike da nutsuwa tace yaya rauda ya kamata idan kina sallah kidinga nutsuwa domin duk abinda zakije nema yana a hannun wanda kike gabansa a yanzu.

harararta Rauda tayi tace toh malama yimin wa'azi tunda kinfini sani,  kinsan Allah zarah idan baki fita daga hancinaba sai na 6a66allaki a cikin gidan nan
kuma da kike maganar sallah ai Allah da zuciyar mutum yake amfani, kuma idan ke kike raba ladar toh dan girman Allah kihanani 'yar bak'in ciki kawai.
tana gama fad'in haka tatashi fuuuu taficce tabar d'akin tana ta mita.......





_Comments_
     *nd*
_Share_






_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔


page 8⃣

tashi tayi fuuu tawuce tabar d'akin tana mita ita dai zarah bin rauda tayi da kallo cike da bak'in cikin halin 'yan gidansu a kullum addu'anta Allah yasa sugane gaskiya.

addu'a tayi sannan tatashi tacire hijab d'inta tafito takar6i kayan miyan da suke hannun mama tajajjaga mata sannan tatambayeta idan akwai abinda za'a,  mama tace a'a,
sannan tawuce takoma d'aki koda tayi sallar isha'i zama tayi tana ta bitar karatunta sai wajen k'arfe takwas sannan k'anwarta Aysha tadawo gida hannunta d'auke da leda tun daga zaure tafara kwalah ma mama kira

mama da take tsugunne tana hura huta jikinta yana 6ari tamik'e tana washe baki tace a'ah autata har kin dawo.

Aysha tana yatsine fuska tace eh wlh ,
mama kar6ar ledar hannun Aysha tayi tace me kuma muka samu?

Aysha kar6e ledarta tayi tace kai mamanmu ba fa wani abu bane d'inkinane nabiya na amso,

fara'ar da take d'auke a fuskar mama ce taragu tace kina nufin babu abinda kika kawo mana?  kiduba kiga 'yar uwarki kaza takawo mana gata chan saman wuta ina mana ferfesu,

Aysha tace oh mama kedai kullum burinki abaki kud'i, jakkarta tabud'e tad'auko 2k tace gashinan kid'auki d'aya kiba abbah d'aya.

mama kar6a tayi tana washe baki tace kai 'yar albarka gaskiya naji dad'i ammah ba zan ba mahaifinkuba dan shima d'azun ya samu kud'i kar ma kikuskura kifad'a masa kin bamu kud'i,  Aysha wucewa tayi tanufi d'akinsu tana cewa nidai mamanmu wannan tsakaninku da abbane,

zarah tana zaune saman darduma tana sauraren dukkan abinda suke tattaunawa,

Aysha ce tashigo d'akin tana cewa wash wlh na gaji, jafe jakkarta tayi bisa katifa takalli zarah tace yaya zarah kina nan kina ta bitar karatun?

zarah batare da takalletaba tace Aysha daga ina kike?  meyasa kikeso kiga kinyi dare a waje a matsayinki na mace?

Aysha turo baki tayi tace ammah ai mama tasan da tafiyata,  zarah aje littafin da yake hannunta tayi tare da tattara dukkan hankalinta ga k'anwarta tace Aysha wannan rayuwar da kika d'aukar ma kanki ba mai 6ullewa bace k'ara tun wuri kigyara tun kan lokaci yak'uremiki gudun kar kiyi nadamar da batada amfani.

mama ce da tazo wucewa tajiyota tana magana lek'owatayi d'akin takalli zarah taharareta tace toh sarkin 6akin ciki mekike ce mata? badai hure mata kunne kikeyi ba dai ko? 

zarah kallon mama tayi tace a'a mama kawai ina bata shawarace d's zata fisheta.

salati mama tahau yi tace nashiga ukku ni Zainabu yau Allah yabani d'iya mai bak'in ciki da ni, yanzu 'yan kud'in da take kawo mana ne kike ma bak'in ciki?  toh idan suka zauna gidan ubanwa zai dinga ciyar da mu? kinsan dai mahaifinku bai bada abinda zamu ci muk'oshi .

zarah cikin lallashi tace mama kiyi hak'uri ni ba haka nake nufiba, idan na 6ata miki rai kiyi hak'uri.

mama tace daman ai haka zakice munafuka kawai wlh da ace ba ni nahaifekiba da na ce ke ba jinina bace.

zarah dai shuru tayi tana sauraren maganganun mama har mama tagama fad'anta tafita tabar d'akin.

karatunma zarah kasa cigaba tayi saboda haushi nan ta tattare littafan tamaida su ajakkarta,  sannan tahaye saman katifarsu takwanta.

Aysha wanka tayo tashirya akan idon zarah wani yakirata a waya tafita tabar gidan, 'yar nokianta ce da taji tana ruri yasa takai idanunta a wajen ganin wanda yake kiranta saka tayi murmushi har dimples d'inta suka lotsa cike da farin ciki tayi picking domin tasan ko bakomai Malam Bello zai d'ebe mata kewa sallamata tayi masa,  shima cike da farin ciki ya amsa mata,  bayan sun gaisa malam Bello yace gimbiya zarah ya gida? 

murmushi zarah tayi tace wai gimbiya dan Allah kama daina kar kaja akamani 

dariya malam Bello yayi yace ai gimbiyarce.

zarah tace hmm dan Allah kadaina.

malam Bello yace toh malama zarah ta gida da mutanen gida?

zarah tace Lafiya lou Alhmdllh.
malam musa gyaran murya yayi yace zarah wlh ina sonki so nagaskiya dan Allah kitaimaka kirik'e min amanar kanki domin har ga Allah aurenki nake son yi,  dama zaki bani dama da naturo an aje maganata inyaso daga baya idan nak'are karatuna sai muyi aure.

zarah murmushi tayi tace kar kadamu malam ba ma sai ka turoba insha Allahu banda miji sai kai domin ka cancanchi kakasance mijina inko kaga ban aurekaba toh wannan daga Allah ne,

malam Bello dogon numfashi yaja yace Allah yasa haka my zarah, wlh gani nake idan narasaki toh na rasa farin cikina domin kece kawai kika dace da rayuwata.

zarah cike da tausayinsa tace kar kadamu malam insha Allahu ma ba zaka ta6a rasaniba.

Bello cike da jin dad'i yace nagode sosai zarah,  yanzu inzo mugaisa ko?

zarah kallon agogo tayi tace a'a malam yanzu dare yayi kadai bari sai gobe.

malam Bello yace toh malama zarah duk yadda kikeso ai haka za'ayi Allah yakaimu,  murmushi zarah tayi tace toh malam ahuta lafiya sai Allah yakaimu.

malam bello  yace au korata ma akeyi?
zarah tace wane ni inkoreka kawai dai zanyi bacci ne,
bello yace toh gimbiya atashi lafiya
zarah tace Allah yasa, nan sukayi sallama sannan suka kashe wayoyin.
zarah bin wayar tayi da kallo tana murmushi domin har cikin ranta tana jin malam bello ko da tasan mayuwacine iyayenta su amince da shi tunda baida kud'i ammah ta ci alwashin shikad'ai ne mutumin da zata iya aure saidai wani hukuncin daga ubangiji.....kiran da mama takeyi matane yakatseta daga tunanin da takeyi,  dasauri tatashi tafita a tsakar gida tasamu mama da abba Zaune saman tabarma suna cin nama suna dangwala romon da bread,
kusa da mama tatsugunna tace mama gani,  mama fuskarta a d'aure tace ga naki nan su kuma tunda su suka kawo saisa nafitar masu da nasu yafi yawa,

kar6a zarah tayi tace nagode sannan tatashi takoma d'akinta ,

abbah binta yayi da kallo cike da takaici yace ni inma rasa abinda yarinyarnan take k'unshewa a d'aki kullum tana d'aki ko fitowa batayi tasha iska.
ummah tana yagar nama tace ita dai tasani matsalarta.

zarah tana shiga d'akinsu zama tayi taci naman bayan ta gama tafiddo kwanon sannan tayi ma iyayen sallama takoma d'aki saida tayi wanka sannan takwanta.

duk yadda taso tayi bacci ammah takasa tunanin wulak'ancin da takesha wajen mutanene da halin iyayenta da gwagwarmayar da tasha ne yasa tafara hawaye kullum batada buri da yawuce taga iyayenta da 'yan uwanta sun canza hali musamman ma idan tatuna da lokacin da suna yara haka suka taso a sake iyayensu basa kwa6arsu




Malam musa da Zainab sune iyayensu su ukkune suka haifa,  Rauda itace babba sai zarah da take bi mata sai 'yar autarsu Aysha ko da ba wani tserataiya bane irin sosai d'innan a tsakaninsu k'ara ma Rauda itace taba zarah shekara biyar,  inda zarah kuma taba Aysha shekara biyu.

Suna da kyau sosai kasancewar iyayensu fulanine na usuli,  saidai zarah itace zaka kallah kaga sak mama, inda su Rauda da Aysha suke kama da abbansu saisa zarah tayi musu fintinkau wajen kyau dan ma Suna halin rashi.

sunyi karatu bakin gwalgwado dan dukansu daga secondary school suka tsaya da karatunsu babu wacce tacigaba duk suna gida Zaune, zarah ma ce tashiga makarantar koyan sana'a tayi Catrine (6angaren girki) sannan itace mai zuwa islamiyya ammah su rauda babu wacce take da lokacin zuwa islamiyya sharholiyarsu kawai sukeyi.

abun mamakinma a gaban iyayen nasu ake zuwa ad'aukesu ammah iyayensu ko da sau d'aya basu ta6a nuna 6acin ransuba domin basuda burin da yawuce akawo musu kud'i,

hatta abincin da zasu ci wani lokacin rauda da Aysha ne suke ciyar da su kasancewar Abbah baida tak'amaiman aikinyi daman ginine da kanikanci shima sai idan ya samu yakeyi.

ahakanma iyayensu sun tsani suga talakawa suna ra6ar 'ya'yansu, su ma kansu su rauda basa son talakawa 'yan uwansu saisa duk samarinsu masu kud'ine.

duk wanda zai nuna yana son zarah toh wulak'ancine sai yasha wajenta,
mama tun tana fad'a har tagaji takyaleta,
hantarace da wulak'anci babu wanda bata sha wajensu, ko kud'in wata na islamiyya sai tayi dagaske take samu wajen iyayenta inma basu bataba toh wajen k'anwarta ko yaya rauda take samu su ma sai tasha wulak'anci da gori suke bata.

kayan shafa ma sai sunga dama idan zasu siyo nasu suke had'awa da ita suna d'an siyo mata mai da powder da turare shima a wulak'ance ake bata.


duk aikin gida ita aka sakarmawa inba ka saniba ba zaka ta6a cewa zarah d'iyar gidan bace sai kad'auka *'YAR RIK'O* ce,

wa'azi nasiha babu wanda batayi ma 'yan gidan nasuba ammah sunbi son zuciyansu da na iyayensu.

zarah tun abin yana damunta ammah yanzu ya rage damunta



Malam bello malamin islamiyyarsu zarah ne yana da kirki sosai  jininsu ya had'u da zarah saisa suke mutunci, daga baya yanuna yana sonta dakyar yasamu zarah ta amince masa suna soyayya,  duk wasu littafan karatun zarah shi yake siya mata.

zarah tun tana nuna bata so ammah daga baya tahak'ura tana kar6a dan tasan iyayenta ba zasu ta6a siya mataba kuma babu inda zata samu kud'i tasiya, shima dan taga yana da hankali da nutsuwa kuma a yadda yake nunawa shi dan Allah yakeyi mata kuma yana so yasamu lada idan ta karanta.

Malam Bello karatu yake a university sannan yana tsare ma wani mutum shago da kud'in islamiyya da ake biyansa a nan yake samun d'an abinda zai rik'e kasancewar iyayensa suma ba masu hali bane sosai.

mama lokacin da tagano zarah tana soyayya da shi har kusan dukanta tayi tace me zatayi da wannan talakkan me nak'asa yaci bare yaba nasama ita dai zarah shuru tayi domin tasan abinda mama take nufi,  ammah a ranta itadai bata da burin auren kowa sai malam bello dan shine kad'ai yake taimakonta.





bud'a k'ofar da akayine yadawo da ita daga kogon tunanin da ta lula, Aysha ce tashigo da leda a hannunta tana waya, zarah duba agogo tayi taga kusan k'arfe goma da rabi dan haka tajuya domin tayi bacci cike da takaicin maganganun da Aysha takeyi a waya batare a taji kunya ko nauyin Zarah ba.

ahaka Aysha tagama wayan itama takwanta har sukayi bacci yaya Rauda bata dawoba.



da asuba zarah har tayi sallah ammah Aysha bata tatashi ko da zarah tak'ara tadata cewa tayi dan Allah kikyaleni idan natashi zanyi nace miki.

zarah tace haba Aysha yanzu har sai gari yayi haske sannan zaki tashi kiyi sallah?

Aysha tace ko ma dai yaushe nayi babu ruwanki malama dan haka kikyaleni.

zarah tsaki taja tace Allah yakyauta sannan tacigaba da laziminta har gari yafara haske sannan tamik'e taje tayi wanke-wanke tagyara gida bayan tagama tadawo tayi kwanciyarta sai alokacin Aysha tatashi tayi sallah.




wajen k'arfe goma zarah tafarka lokacin babu kowa d'akin batayi mamakin hakanba domin tasan Aysha ta tafi gantalinta daman ita yaya Raiuda ba gidan takwana ba.

zarah gyara d'akin tafara yi sannan tafito tayi brush tawuce d'akin mama lokacin Abbah yana shirin fita nan taduk'a bakin k'ofa tace Abbah ina kwananku.

Abbah ciki-ciki ya amsa mata, mama kau daman harararta tayi tace yanzu saboda Allah zarah sai yanzu kika tashi baccin?

zarah tace mama ai saida nagama komai sannan nakwanta,

mama cikin fad'a tace haka dai zaki k'are daga bacci sai zaman gida ko 'yan kud'in kashewar baki yarda kifita kisamo saboda bak'in cikin kar muma muci daga wajenki.

zarah shuru tayi mama tace toh yau dai ba ayi karin kumalloba muma nan ruwan Lipton da sauran biredin jiyane muka ci, 
Kinga da ace kina da kud'inki ai da kin d'an siyo ko indomie ce kinci irin yadda 'yan uwanki sukeyi, yanzu dai bari inbaki kije kiyo mani cefane

zarah tace toh mama

mama kallon abbah tayi tace malam kabada kud'in cefanen.

abbah laluba aljihun rigarsa yayi yad'auko d'ari biyu yamik'a mata, mama tsayawa tayi tana kallonsa

yace ki amsa mana,
mama tace haba malam me d'ari biyu zatayi mana bamu da fa abinda zamu dafa muci,

abbah yace toh nidai su gareni koma minene kujalabta kuyi abincin.

mama tace gaskiya wannan babu abinda zatayi mana.
abbah yace kihad'a da canjin jiya ai nasan dai anrage wani abu cikin d'ari biyar d'in.
mama tace naira sittin fa ce.
yace toh inbakuso sai inmaida abuna aljihu.
Jin haka yasa mama takar6i kud'in domin tasan zai iya.

bayan ya fita mama kallon zarah tayi tace ni tashi kimik'o min jakkata ko d'ari biyu ce ink'ara dan ma Allah yaso akwai kud'in da Aysha tabani jiya da ban san yau ya zamuyi ba.

zarah tashi tayi taje tad'auko ma mama jakkar tamik'a mata.

mama d'ari biyar tabata tace kisiyo garin d'an wake rabi sai mai rabin gwangwani da tashi da Maggi ko shine musamu abinda zamu saka ma bakunanmu kafin yarana sudawo

kar6a zarah tayi tace toh mama.

zarah tashi tayi taje tasako hijab d'inta sannan tafita taje tayo siyayyar,  bayan ta dawo tad'aura girkin.

tana cikin yi mama tafito ta shirya sanye da gyale tace toh idan kin gama kijuye a cikin plastic d'innan zan je gidan mariya barka kuma kar kisaki kici kibari sai nadawo nad'ibar miki.

zarah cike da ladabi tace toh mama Allah yakiyaye hanya.

zarah bayan ta gama gyara gidan tak'ara yi sannan taje tayi wanka tashirya tayi sallah.

bayan ta gama saman katifarsu takwanta tana jiran mama tadawo saboda wata irin yunwa da takeji.

mama sai wajen k'arfe ukku tadawo lokacin bacci har ya d'auke zarah.

maganar mama ce tajiyo sama-sama dan haka firgit tayi tafarka.

mama tsaye take bakin k'ofa tace yanzu dan gidanku zarah bacci kikeyi kinbar mana gida bud'e?

Zarah mik'ewa tayi tace wlh mama ban san lokacin da bacci yad'aukeniba kiyi hak'uri.

tsaki mama tayi tace kullum bakida aiki saidai ayi hak'uri ke da ace bamu hak'uri da ke ai da tuni na 6allaki, ni kizo kikwaso mun kwanika inraba abincin.

zarah tace to mama sannan tabi bayan mama takwaso kwanuka.

Zarah bayan ta gama cin abincinta alk'ur'ani tad'auko tana bitar hardar da zata bada islamiyya har aka kira sallah la'asar tayi sannan tashirya taje d'akin mama tace mama zan tafi islamiyya.

mama harararta tayi tace ke ni banma yarda dakeba anya ma islamiyya kike zuwa?  ko dai wajen wannan malamin naku kike zuwa.

zarah raurau tayi da ido tace wlh mama babu inda nake zuwa sai islamiyya.

mama tace eh ai dan kihad'u da shi islamiyyar saisa kike zuwa,
zarah tace a'a wlh mama.

mama tace munafuka kawai kedai kika sani ahaka dai zaki k'arata ni tashi kiban waje.

zarah tashi tayi tafita.

ko da taje islamiyya lokacin ajinsu har anfara taruwa kowa zaune yake yana bitar hardarsa kafin malam yashigo.

sit d'in gaba tazauna kusa da k'awarta khairy kasancewar nan ne wajen zamansu tare da mik'a ma khairy hannu suka gaisa.

khairy kallon zarah tayi tana murmushi tace yau dai na rigaki Zuwa.

itama zarah murmushi tayi tace nima dai nayi mamakin ganinki dawuri

khairy tace ai infad'amiki tun d'azun ina nan ina koyon harda kafin malam bello yashigo kedai nasan kinsha taki hardar.

murmushi zarah tayi tace kedai kicigaba da haddarki.

suna cikin bita malam bello yashigo idanuwansa akan zarah,
suna had'a ido dasauri zarah tajanye idonta, khairy murmushi tayi ahankali tace malam bello yau sabon yadi yasa nasan kuma saboda ke ne.

harararta zarah tayi tace wlh zan fad'a masa..... muryar malam bello suka tsinkayo ya ce khairy surutu kukeyi ko?
khairy tace a'a malam muna wani nazarine.
yace toh ya isa haka, kallonsa yamaida ga 'yan aji yace duk Wanda yasan baiyi hadda ba toh yafita waje dan kar ku6ata min lokaci.

nan aji yayi shuru kowa yafara raba ido, chan wasu mata hud'u suka tashi suka fita.

malam bello kallon zarah yayi yace kufara yau sit by sit zan bi saboda k'urewar lokaci.

nan layinsu zarah suka fara malam bello yana kallon bakin kowa har suka gama gyara biyu yayi musu sannan yacigaba da kar6ar na sauran har aka gama sannan yayi musu k'ari lokacin tashi yayi akayi addu'a.

zarah jerowa sukayi da khairy suna tafiya d'ago kan da zatayi taga malam bello ya tsareta da ido murmushi tasakar masa sannan suka cigaba da tafiya.

khairy da take kallonsu tana murmushi tace wlh k'awata soyayyarku da malam bello tana burgeni.

zarah murmushi kawai tayi sannan suka cigaba da tafiya har sukazo inda suke rabuwa sukayi sallama sannan zarah tacigaba da tafiya.

Zarah lokacin da tazo k'ofar gida mota tagani tsaye batare da takalli nacikin motarba tawuce zata shige gida.

muryar yaya rauda ce tajiyo tana kiranta nan tatako tanufi wajen motar daga nesa kad'an tatsaya takalli yaya rauda da take zaune gaba tace yaya Rauda gani.

ledace tamik'a mata tace shigar min da wannan gida, kar6a zarah tayi har zata tatafi taji mutumin yace sannu ko 'yan mata,

zarah bata tankasaba tawuce zata tafi yaya zarah tace ke dan ubanki bakiji ana miki magana?

zarah kallon mutumin tayi da yatsareta da ita yana murmushi,  fuskarta a d'aure tace ina wuni? bata jira ya amsaba tawuce tashige gida tana jiyo yaya rauda tana ta fad'a..






_Comment_
     *nd*
_Share_





_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Sak'on gaisuwata agareku a duk inda kuka kasance *My hafnan, Mamansadiq nd Mrs Dawud* I heart you all😘_


_*My blood sis Aufana yau ranar takice dan haka na mallaka miki wannan page d'in, ina so kisani sonki a cikin jinin jikina yake Allah yabarmu tare😘*_

page 9⃣

Saurayin yaya raudane yashiga lallashinta yace haba baby menene kuma nafad'a a ciki? ni wlh k'anwar ma taki ta burgeni.

Yaya Rauda tace hmm baby kenan bakasan wannan yarinyar ba ai kwata-kwata ita ba wayaiya bace.

murmushi yayi yace har ina shirin ince ina ciki.

wani irin kallo Rauda tayi masa tace k'anwar tawa?
murmushi yayi yace eh man toh menene?

Rauda ta6e baki tayi tace ai wlh ba zai yuwu kajefi tsuntsu biyu da dutsi d'ayaba dan haka abar ma maganar nan baby,  yanzu idan katafi sai yaushe zaka dawo?

cije le6e yayi tare da jingine kansa a sit d'in da yake zaune sannan yace 1 week kawai zanyi cike da tsokana yace kinsan matata kwana biyu nayi missing d'inta.

Rauda d'aure fuska tayi tace haba Alhaji Munnir wai meyasa kake min irin haka.

murmushi yayi yace sorry dear kinsan akwai aikin da zanje inyi, yanzu dai fatana kikular min da kanki har indawo.

Rauda tace kar kadamu dear insha Allahu zaka dawo kasameni yadda kabarni,

murmushin jin dad'i yayi yace yauwa baby nagode, 10k yad'auko yamik'a mata yace ga wannan kirik'e kafin indawo,

Rauda kar6a tayi tace nagode baby Allah yamaido min kai lafiya
yace Ameen dear,  nan sukayi sallama.

Rauda ba ko sallama tashiga gida kallon zarah tayi da take hura wuta tace ke ina ledar da nace kishigo min da ita?
zarah batare da ta kalli Rauda ba tace tana d'akinmu, Mama da take cikin d'aki jin muryar Rauda yasa tafito tana washe baki tace a'a 'yar albarka ashe kece kika dawo, tun jiya muna ta zuba ido ammah shuru.
Rauda yamitsa fuska tayi tace ammah mamanmu kinsan dai duk ma inda naje toh zan dawo.
Mama tace hakane saidai duk abinda kuke nafison inganku kun dawo gida komai dare kun kwana.

Yaya Rauda batare da tace komai ba tawuce tashige d'akinsu.

wannan 'yar maganar da mama tayi zarah taji dad'inta sosai domin duk abin mama toh tanaso taga yaran nata sun kwana a gidansu, saidai duk maganar da zatayi musu Yaya Rauda idan tasa kanta waje take kwana,  idan ma iyayen sunyi magana sai tabasu kud'i tarufe bakin.

Mama kallon zarah tayi tace tashi kije kikar6o min 500 wajen Rauda kizo kisiyo taliya a Zuba naga ruwan ya kusan tafasa,
zarah tace toh mama.

tana shiga d'akin kallon Rauda tayi da take shirin shiga wanka tace Yaya Rauda mama tace kibada d'ari biyar asiyo taliya.
Rauda tace mik'o min jakkata, zarah zuwa tayi tad'auko jakkar tabata nan Rauda tamik'o mata kud'in sannan tashige wanka.

Zarah wajen mama tadawo tace mama guda nawa za'a siyo.
Mama tace siyo biyu sai kikawo min canjin,  zarah tace toh sannan tatafi.


_*After 2 weeks later*_

Zarah ce zaune tana tsifar kanta, wayartace tashiga ringing nan tad'auko ganin sunan malam Bello da yabayya a screen yasa tayi picking tare da yin sallama,
daga chan 6angaren ya amsa mata, nan suka gaisa,  sannan malam Bello yace dear gani a k'ofar gidanku kifito inganki please.
zarah jim tayi nad'an lokaci sannan taduba agogo taga k'arfe biyar d'in marece. muryasa taji yana cewa zarah ya kikayi shuru ko bakiso nazoba?
zarah tace bahaka bane malam gani nan zuwa batare da tajira jin abinda zai ce ba takashe wayarta,

nan ta tufke kanta da ribbon sannan tajanyo hijab tasaka saida talek'a ganin ba kowa tsakar gida yasa tayi hamdala sannan talalla6a taficce.

A k'ofar gida tasamesa tsaye ya zuba ido domin yaga ta ina zata fito, suna had'a ido dasauri zarah taduk'ar da kanta k'asa tare da yi masa sallama.

fuskar malam Bello d'auke da murmushi ya amsa mata yace zarah na tadoki ko batare da nasanar da ke zuwana ba.

zarah ahankali tace bakomai malam nan tagaishesa ya amsa,

kallon da yakeyi mata duk sai ya gundureta tad'ago kai tad'an kallesa,
murmushi yasakar mata yace kiyi hak'uri wlh ji nayi yau idan ban gankiba ba zan samu sukuniba tunda ko a islamiyya 6oyemin kanki kike bakya ko bari mugaisa,  kinsan dai yadda nake sonki.

Zarah murmushi tayi batare da ta ce komai ba.
malam Bello yace shurun da kikeyi fa yana cutar da ni dan Allah kimin magana.
zarah d'ago kai tayi takallesa har ta bud'e baki zatayi magana sai ganin Abbah sukayi tsaye.

A tsorace zarah takallesa bakinta yana rawa tace Abbah sannu da zuwa,  wani irin kallo Abbah yawurga mata.
malam Bello dasauri yaduk'a tare da cewa Abbah barka da rana ina wuni?
Abbah yace da ace ban wuniba da ka ganni?
Me yakawoka wajen 'ya ta?  duk hure mata kunne da kakeyi a islamiyya bai ishekaba sai ka biyota gida?
malam Bello kansa a k'asa yace kayi hak'uri Abbah wlh ba haka bane,
Abbah yace toh yaya ne?
Malam Bello yace wlh ni tsakani ga Allah son zarah nake kuma ina da burin aurenta.
Abbah yace a haka? Minene aikinka?
Malam Bello yace eh toh  gaskiya ni karatu nake ammah ina tsare shago ana biyana.

Abbah yace kana karatu ammah dan rigima kace kana son 'ya ta toh bari kaji d'iyata ba irinka zata auraba domin kwata-kwata baku daceba,  bakada abinda zaka iya aurenta dan haka tashi kabar min k"ofar gida.
malam Bello yace kayi hak'uri Abbah insha Allah zan iya rik'on zarah.
Zarah tace dan Allah Abbah kayi.... tsawa Abbah yadaka mata yace wuce kishiga gida ko ranki ya6aci,  dasauri zarah tawuce tashige gida tana hawaye.

Abbah kallon malam Bello yayi yace tashi kabar nan kuma kar ka kuskura kak'ara takomin k'ofar gida, Abbah na gama fad'in haka yawuce yashige gida. .

malam Bello yamik'e tsaye daga tsugunnen da yake yatafi yana jin ba dad'i cikin ransa.

Zarah saman katifarsu tafad'a tafara rusar kuka,  Abbah ne yashigo gidan yana ta fad'a.

mama ce tafito daga d'aki tace malam lafiya?
Abbah yace ina fa lafiya wlh yarinyar chan idan batayi wasaba sai na sa6a mata a cikin gidan nan,  mama tace wa kenan?
Abbah yace zarah mana wai ace tarasa Wanda zata tsaya da shi sai talakka d'an uwanta da baida komai inba wahalaba babu abinda zata tsinta a wajensa.

mama tace hmm malam kenan ai wlh indai zarah ce toh kad'an kagani ita kwata-kwata batada tunani ai ni wlh ban ma San lokacin da tafitaba da bazan bartaba,

mama wucewa tayi tanufi d'akinsu zarah a bakin k'ofa tatsaya tare da d'age labulen d'akin, kallon zarah take da taketa faman kuka cikin fad'a tace ke dan kin raina ni watau da narabaki da wancan yaron baku rabuba ko? shine yanzu dan anyi miki magana shine kike kuka, toh bari kiji ko da ace zakiyi kukan jini bazaki auresaba kuma dole kurabu inma bakiyi hankaliba islamiyyar ma sai inhanaki zuwa, butulun banza inba ma asaraba me zakiyi da d'an uwanki talakka duk kyaun naki baida amfani wlh,  hatta k'anwarki tafiki sanin daidai.

zarah dai tana jin  mama tana ta fad'anta har tagama tatafi itadai kuka take.

kiran Sallar magrib da akayine yasa tatashi taje tayo alwallah har lokacin fuskarta babu walwala.

bayan sallar isha'i kwance take saman katifa gefenta Aysha ce kunnenta d'auke da earpiece da waya a hannu da alama kallo takeyi.

zarah wayarta tad'auko talalubo number d'in malam Bello takirasa, tana fara ringing yakashe yakira,
zarah tana d'aga wayan yayi mata sallama.
jin muryarsa yasa taruntse ido tana jin wani iri acikin zuciyarta sai a lokacin taji kunyar abinda Abbah yayi masa.
muryarsa ta tsinkayo yana cewa hello zarah bakya ji na?
zarah cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace malam dan Allah kayi hak'uri akan abinda yafaru
murmushi malam Bello yayi yace kar kidamu zarah wlh bakomai kawai dai ina tunanin anya zan iya rabuwa da ke? domin ni kaina nasan ina miki wani irin mahaukacin so.

zarah ajiyar zuciya tayi tace malam Bello wlh nima ina sonka kuma ina ji a raina akwai lokacin da iyayena zasu amince mana muyi aure.

malam Bello yace hakane ammah ni fatana kitaimaka kirik'e min amanar kanki har ingama karatuna muyi aure.

zarah tace kar kadamu nariga na amince maka kuma insha Allahu idan da rabo zamuyi aure.

cike da jin dad'i malam Bello yace nagode sosai zarah Allah yamallakamin wannan tauraruwar yarinyar.
dariya zarah tayi daga nan suka shiga yin hira, sai da sukayi kusan awa d'aya sannan sukayi sallama suka kashe wayoyinsu kowa yana jin dad'i a ransa,  nan zarah tanemi damuwarta tarasa.

________________

Gimbiya Sumayya lokacin da jirginsu ya safka zinat ce tazo tatarbeta cike da farin ciki suka rungume juna daga nan suka nufi inda motar zinat take suka shiga suna ta hira, zinat tace baby yanzu gida zamu wuce ko boutique din zan kaiki kifara ganowa?  Sumayya jingine kanta tayi a sit din da take zaune tace dear muje gidanki kawai yanzu agajiye nake, murmushi zinat tayi tace toh ranki yadad'e angama.
dariya sukasa gaba d'ayansu Sumayya tace abun ma har da tsokana kenan,  daidai lokacin tayi horn maigadi yazo yabud'e mata gate tacinna motarta a ciki a parking space tayi parking sannan suka fito suka d'unguma cikin gida.

bedroom suka wuce Sumayya tafad'a saman gado tare da cewa wash.

dariya zinat tayi tace baby keda kikazo ta flight ammah shine har kin gaji?  kokuma namance ku jinin sarauta bakwa motsawa dayawa saidai ayi muku komai.

harararta Sumayya tayi tace ke dai kika sani da tsokana, ni yanzu dai taimaka kisa ahad'a min ruwan wanka infarayi tukun,

zinat mik'ewa tayi tanufi k'ofa tafara kwalah ma 'yar aikinta kira,  dasauri tazo tare da russunawa k'asa ranki yadad'e gani,  zinat yamitsa fuska tayi tace shiga toilet kihad'a ruwan wanka, dasauri tatashi tashiga tahad'a ruwan sannan taficce tabar d'akin.

Zinat kallon sumayya tayi tace baby kitashi kije kiyi wankan ko intaimaka miki,

sumayya mik'ewa tayi tad'auki towel tacire kayan jikinta tawuce tashiga bathroom.

bayan ta fito kwalliya tayi tashirya cikin English wears riga da skirt tafeshe jikinta da turare, kallon Zinat tayi da tatsareta da ido tace dear wannan kallon fa? 

Zinat tace Mrs yarima kinyi kyau sosai.

gimbiya sumayya ta6e baki tayi tace har kin tunomin da wannan d'an jin kan,  nidai muje inyi lunch domin yunwa nakeji yanzu.

Zinat mik'ewa tayi suka fito suka nufi dining nan Zinat tayi serving d'insu suna ci suna hira.

bayan sun gama saman 3 seater suka dawo suka yada zango,  sumayya wayarta tad'auko tace bari inkira su ummah inshaida musu na iso lfy tun kan surigani kira,

Zinat tace hakan fa zaifi.

nan sumayya takira sultana sadiya da dada tafad'a musu ta sauka lafiya.

bayan sumayya ta gama wayar zinat tace toh baki kira miskilin mijin nakiba.

ta6e baki tayi tace kibarsa kawai wannan d'an rainin wayaun ai wlh indai bashi yakiraniba toh ba zan kirasaba _(lallai sumayya kin mance wanene yarima suhail)_

Zinat tace ai wlh kina ma hak'uri da shi ai ni kwata-kwata ban tunanin zan iya zama da irin su mijinkiba.

sumayya tace hmm nima dai dan ina sonsa ai da ban iya zama da halinsa, ke kafin fa intafo jiya saida mukayi drama, yanzu dai tashi muje inga boutique d'in dan na k'agara ingansa.

zinat murmushi tayi tace baby ai nad'auka sai ansallameni sannan zamuje kinsan fa nayi missing d'inki dayawa.

sumayya 'yar dariya tayi tace kidai bari mudawo tukun dan ni yanzu hankalina ya fi karkatuwa da zuwa.

zinat tace ke Alhaji Jamilu fa yana nan Abuja ai kinsan na fad'a miki.

sumayya yamitse fuska tayi tace wanene kuma jamilu,

harararta zinat tayi tace ammah fa ke 'yar iskace baby yanzu Alhaji jamilu kika mance?

yamitsa fuska sumayya tayi tace hmm zinat kenan ai ban mance da shi ba dan mugunta kikaja nabasa kaina shine namijin da yafara sanina,

dariya zinat tayi tace ammah ai lokacin mun samu abinda mukeso,  ke ni yanzu haka in kinason ganinsa nasan gidansa sai muje inrakaki.

sumayya harararta tayi tace Allah yakyauta ke nifa yanzu namiji Indai ba mijinaba bana jin zan k'ara amince ma wani,

zinat da mamaki take kallonta tace saboda me?  sumayya cikin rashin damuwa tace haka kawai mazan basu gabana.

zinat tace toh wlh ko da sau d'ayane ki amince muje gidan Alhaji jamilu domin yana ta tambayata ke,  kinga mun k'ara jari.

sumayya mik'ewa tayi tsaye tace nidai kitashi muje ko mun dawo domin inaso inhuta.

zinat tace toh nima dai kenan yau ba tani akeba,  sumayya rik'o hannunta tayi tace haba baby ai ke ta dabance nima fa nayi missing d'inki, muje dai mudawo ai muna tare daga yau har next week.

A motar Zinat suka fita ko da sukaje boutique d'in sumayya ta yaba sosai da kayan da zinat tazuba ciki, nan zinat ta gabatar da sumayya ga ma'aikatan wajen cike da girmamawa suke gaisheta sumayya a wulak'ance take amsawa nan tad'an d'auki kaya set biyu tace tana sonsu.

daga nan suka zagaye gari sai dare sannan suka koma gida, gaba d'ayansu saman gado suka fad'a suna hutawa,  zinat kallon sumayya tayi tace baby muje muyi wanka,

sumayya tafara mik'ewa sannan zinat atare sukaje sukayi wankan bayan sun fito su dukansu d'aure suke da towel suna rungume da juna nan suka nufi saman gado suka kwanta........




_Comments_
     *nd*
_Share_





_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_~Sak'on gaisuwa agareku masoya a duk inda kuka kasance inaso kusani Sis Nerja'art tana yinku over😍😘~_



_*My hafnan nd My leemah H.A.S yau Ranar takuce, page d'innan nakune kuyi yadda kukeso dashi sai wanda kukaso zai karanta, wlh ina ji da ku sosai a cikin zuciyana,  Allah yabarmu tare😘*_

page 1⃣0⃣

_*After 3 days later*_
sumayya ce kwance tayi matashin kai da cinyar zinat tana waya da ummanta bayan sun gama sumayya d'aga kai tayi takalli zinat da take ta dannar waya da alama chart takeyi, tace baby mutuminki fa har yau bamuyi wayaba.

murmushi zinat tayi tace toh sai me minene abun damuwa tunda dai bai nemekiba toh kema kisharesa, ke ni jiya da nafita na ga Alhaji jamilu kuma nafad'a masa muna tare wlh bakiga yadda ya rikice min ba wai sai ya biyoni ya zo wajenki.

murmushi sumayya tayi tace ke dai kina son jona ni da Alhaji jamilu,

zinat tace toh ai nasan zamu samu cash masu tsoka a wajensa,  ke nifa inda ke da kud'i a nan nafi wayau.

dariya sumayya tayi tace nima haka dear, wlh dan dai ina tsoron kar yarima yagane da nabi maganarki naje munyi sharholiyarmu da shi inyagi abinda nayaga.

Zinat tace haba baby kefa matsalata da ke kenan taya kike tunanin mijinki zaya gane tun farko ma bai ganeba sai a yanzu?

Sumayya jinjina kai tayi alamun gamsuwa sannan tace toh yanzu dai ta ina zamu fara?

zinat murmushi tayi tace ai ya bani number d'insa bari kawai inkirasa sai kuyi magana ko kuma inbaki number d'insa.

dasauri sumayya tagirgiza kai tace a'a kirawo min shi dai da wayanki kinga yanzu nayi aure kar wataran yakirani gaban mijina.

zinat tace hakane nan tafara dialing d'in number d'insa tanaji yad'aga dasauri tasa ma sumayya a kunne,  jin muryarsa yasa sumayya yin murmushi tare da kallon zinat.

zinat alama tayi mata na tayi magana.
sumayya kwantar da muryar tayi tace Alhajina dafatan kana lafiya.

Alhaji jamilu da yake kwance jin muryar sumayya da yayi yasa yamik'e zaune tare da cewa sumayya daman kina nan?

sumayya murmushi tayi tace aikam dai ina nan Alhaji ya gida ya kake?

Alhaji jamilu cike da jin dad'i yace lafiya lou baby gaskiya naji dad'in jinki da nayi wlh daman nadad'e ina cigiyarki wajen zinat.

sumayya tace ayya kar kadamu yanzu ai gani.

yace baby toh inaso muhad'u  ya za'ayi?

sumayya kallon zinat tayi sukayi murmushi sannan tace toh katuron address d'inka sai inzo

cike d's jin dad'i Alhaji jameel yace yanzu ko zan turo miki ammah please kizo yau,
sumayya tace kar kadamu zan shigo da anjima,  yanzu dai ina jira sai ka turo.
nan sukayi sallama suka kashe wayan.

sumayya kallon zarah tayi da tatsareta da ido tace baby nidai ko da na je gaskiya bana iya bari yayi sex da ni.

zinat zaro ido tayi tace haba baby saboda mi? toh kud'in fa?

murmushi sumayya tayi tace kar kidamu dolene ma sai na samo mana kasonmu kin d'auka a banza chan baya yamoreni?

dariya zinat tayi tace toh ai lokacin ma mun yagi kasonmu,
sumayya tace a yanzu ma dole yabamu, bari ma kiga inje inyi wanka,  tana gama fad'in haka tamik'e tafara cire kaya.

bayan ta fito wanka shiryawa tayi cikin riga da skirt na atamfa sannan tayafa d'an k'aramin veil,  kallon zinat tayi da tatsareta da ido tayi murmushi tare da jujjuyawa tace baby ya kika ganni?

zinat ma murmushi tayi tare da mik'ewa tace kinyi kyau sosai anya kau Alhaji mukhtar zai barki?

dariya sumayya tayi tace muje dai kiyi dropping d'ina.

wani dank'areren gida aka hangame musu gate suka shiga gefe guda zinat tayi parking sannan takalli sumayya da take bin gidan da kallo tace haba baby kema fa gidanki ya tsaru naga sai kallon wannan kikeyi

murmushi sumayya tayi tace balaifi yayi min kyau.

zinat tace toh kifita kishiga ni bari inje koma dai me kenan sai kindawo.

sumayya tace toh tare da bud'e motar tafita nan zinat taja motarta tabar gidan.

ahankali sumayya take takawa tanufi k'ofar da zata sadata a cikin gidan cikin karambani take bin hanya saidai ganinta tayi a parlour lokacin Alhaji jamilu yana kwance saman 3 seater yana kallo, jin anbud'e k'ofane yasa yad'ago ganin sumayya yasa yamik'e dasauri yanufi inda take tsaye,  rungumeta yayi yace oyoyoo babyna.

sumayya janye jikinta tayi daga nasa tana murmushi tace baby kwana dayawa.

rik'o hannunta yayi suka zo saman 3 seater suka zauna har a lokacin idonsa cikin nata yace baby ban d'auka zan k'ara ganinki a yanzu ba saboda nisan da kikayi min kin 6oye.

sumayya murmushi tayi tace no ni ina gefe kune dai siyasa ta6oye.

Alhaji jamilu hannunsa na sark'e da nata yace mu muna gefe baby inkinson ganinmu zaki ganmu dan ba irinku muke 6oye mawaba, yanzu dai taso mushiga daga ciki.

sumayya mik'ewa tayi tabi Alhaji jamilu bedroom d'insa suka yada zango saman gadonsa, rungume yayi yakai bakinsa cikin nata suka fara kissing d'in junansu inda hannuwansa suke yawo cikin rigarta.

sumayya dai kawai tana biye masane har yarabata da kayan jikinta romance d'in sunansu suke son ransu daga k'arshe sumayya da taga yana shirin shigarta tadakatar da shi.

da mamaki Alhaji jamilu yake kallonta yace baby saboda me zaki hanani?  Please kibarni inyi kinsan fa nakwana biyu banji d'umin jikinkiba.

murmushi sumayya tayi tace dear kayi hak'uri just dai muyi romance d'in juna ammah bana buk'atar sex, ganin yana shirin yin magana yasa tarufesa masa bakinsa da nata cike da kwarewa itama tadinga sarrafasa saida taga ya gamsu batare da sex ba sannan tabarsa.

Alhaji jamil kallonta yayi da take shirin tashi yace baby ina zakije?

murmushi sumayya tayi tace gida zan koma yace haba dan Allah kiyi min ko da kwana d'ayane

sumayya tace a'a Alhaji tafiya dai zanyi inyaso wani lokacin sai indawo.

Alhaji jamil ba dan yasoba yace toh atare sukaje sukayo wanka, duk yadda taso tatafi dawuri hanata yayi saida tayi dagaske sannan yad'auko yamaidata gidan zinat.

A mota ma bai bartaba rungumeta yayi inda hannuwansa suke yawo a cikin rigarta saida yagaji dan kansa sannan yabarta, cheque d'in 1.5 million yarubuta mata yamik'a mata.

cike jin dad'i sumayya takar6a tare da yin godia sannan sukayi sallama tafito daga motar tana d'aga masa hannu har yatafi sannan tashiga gida.

A parlour tatarar da zinat zaune da d'an k'aramin veil a gefenta da alama itama bata dad'e da dawowaba.

daga gefen zinat tazauna tare da cewa wash wlh na gaji.

dariya zinat tayi tace ya dai baby?  ai nasan Alhaji jamil ba zai ta6a barinki hakanan ba.

ta6e baki sumayya tayi tace ke ni kawai dai na amince masane ammah banbari yayi sex da ni ba,  wlh yarimana yafisa iya sarrafa mace saisa nace miki bana tunanin akwai namijin da zan iya jin dad'insa kamar yarima.

ta6e baki zinat tayi tace haka dai kike gani ammah wlh inkina so zan iya had'aki da guys d'ina zakiga banbanci sosai

sumayya tace bama naso.
zinat tace yanzu dai babu abinda yabamu kenan?
sumayya bud'e jakkarta tayi tafiddo cheque d'in tamik'a mata.

zaro ido zinat tayi tace baby yanzu Alhaji jamilu yabaki kud'in nan batare da yayi miki komai ba?

murmushi sumayya tayi tace kawai dai munsha minti ammah babu abinda yashiga tsakaninmu,  ke ni sai bayan natafi nake tunani ai da nayi ma yarima magana da zai bani saboda duk abinsa ammah baya da rowa 

zinat yamutsa fuska tayi tace ai k'arama da bakiyi masa magna ba dan banason mutumin nan saboda wulak'ancinsa.

sumayya tace zinat ammah wlh yarima baida rowa.
zinat ta6e baki tayi tace matsalarsa, nidai ynz tashi muje mukwanta inyaso gobe sai muje muciro kud'in mud'ibi kasonmu sai muyi order d'in wasu kayan da sauran kud'in, nima kinga ga 1 million nan d'azun nakar6esu wajen wani guy d'ina.

dariya sumayya tayi tace ai daman tunda nadawo naga veil d'inki a gefe nasan kin fita.

zinat tace ai ina dropping d'inki ban dawo gidanba nawuce chan, yanzu dai nidai agajiye nake muje daga ciki.





Tun daga ranar sumayya idan Alhaji jamilu yakirata take zuwa gidansa ammah bata bari yayi sex da ita tun yana k'orafin har yagaji, ahaka tacika 1 week a garin.

zinat rok'onta tayi kar takoma gida dakyar tasamu sumayya tazauna domin tak'ara ko da kwana biyu ne ammah saida takashe wayarta gudun kar su dada sukirata. 

____________

Yarima suhail tunda sumayya tatafi bai damuba harkar gabansa kawai yakeyi domin a ganinsa da ita da babu basuda banbanci, ko da sau d'aya bai d'aga wayaba da zumar yakirata.

ahaka har tayi 1 week ammah bata dawoba,

Dada jin sumayya shuru bata dawoba yasa takirata a waya ammah wayanta a kashe dan haka ta aika aka kira mata yarima.

yarima yana kwance a 3 seater kujerar da take opposite d'insa Shaheed ne zaune duk yadda shaheed yaso suyi hira da yarima suhail ammah yarima ya k'i,

ganin haka yasa shaheed yaja bakinsa yayi shuru dan yasan halin mutumin nasa har korarsa ma zai iyayi, gajiya yayi da shurun daga k'arshe yakalli yarima da yazuba ma ceiling ido da alama tunani yake,  yasheed yace yarima meyake damunkane?

shuru yarima yayi yakyalesa.

murmushi shaheed yayi yace ranka yadad'e ko kana tunanin gimbiyarkane.

yarima juyowa yayi yawurga ma shaheed harara sannan yamaida kansa ga kallon ceiling.

dariya ce takama shaheed ammah yadanneta yace Allah yahuci zuciyarka.

K'ofar d'akin aka shiga knocking,  Shaheed ganin yarima baida niyar yin magana yasa yabada izinin ashigo.

wata baiwace tashigo dasauri tazube k'asa a bakin k'ofa tace ranku yadad'e Allah yaja da ran yarima mai jiran gado, daman sultana dada ce tace tana nemanka.

shaheed kallon yarima yayi yaga baida niyar yin magana kuma yana jin ta, shima bakinsa yaja yayi shuru.

saida aka d'au kusan minti ukku tana tsugunne sai chan yarima yad'aga mata hannu batare da ya kalletaba alamun tatafi.

dasauri tak'ara duk'ar da kanta tace ranka yadad'e  afito lafiya sannan tatashi tafita tabar d'akin.

shaheed kallon yarima yayi yaga baida Niyar tashi, cikin ransa yace yau abun ya motsa kenan, nan yacigaba da kallon ball d'insa.

saida akayi kusan minti goma sannan yarima yamik'e tare da d'auko alkyabbarsa yasaka, batare da yayi ma shaheed maganaba yafita yabar d'akin,

nan mutane sukayita zubewa suna kwasar gaisuwa yau ko d'aga musu hannunma bayayi ahaka har ya isa turakar dada.

ko da yashiga dada tana kishingid'e anayi mata tausa, ganinsa yasa duk suka zube suna kwasar gaisuwa, tsaye yarima yayi har saida suka tashi suka ficce sannan yatako yazo yazauna bisa kujerar da take opposite d'in dada.

dakyar kamar bayason yin maganar yagaishe da dada.
dada cikin fara'a da sakin fuska ta amsa masa, gyara zamanta tayi sannan tace yarima daman akan maganar matarkane yaushene zata dawo?

Yarima kallon dada yayi sannan yamaida kallonsa akan wayarsa da yake dannawa cike da jin haushin maganar da dada tayi,

dada zuba masa ido tayi tana kallonsa baida niyar bata amsa,
sai chan yace ranki yadad'e ai nad'auka kunyi magana kinsan lokacin da zata dawo tunda nidai bata fad'amin kwanakin da zatayiba.

dada baki tasaki tana kallonsa har yagama maganar sannan tace suhail kana dai so kacemin bakuyi waya da itaba tunda tatafi.

yarima shuru yayi bai tankaba,
dada tace ammah wlh da kacika marar kirki har yanzu kana nufin baka huceba kenan.

yarima kallon dada yayi tare da yin murmushi yace dada kenan ni ba fushi nakeba, kawai dai nad'auka kinsan lokacin da zata dawone ammah kiyi hak'uri idan maganata ta6ata miki rai,

dada tace toh yanzu nafahimta ammah dan Allah kakirata kaji yaushe zata dawo saboda sati guda tace zatayi ammah yau kusan kwananta takwas.

  mik'ewa yayi yace toh dada, bari inwuce ana jira.

dada tace toh shikenan nidai dan Allah kakirata.

yarima baice komai ba yawuce yafita cikin ransa yana cewa saidai kar tadawo indai sai na kirata zata dawo.


Bayan kwana biyu gimbiya sumayya tayi shirin komawa gida lokacin Kwananta goma,  Alhaji jamil da zinat su suka kaita airport a chan ma Alhaji jamil yana manne da ita kud'i masu tsoka yabata, har saida sukaga tafiyarta sannan suka bar wajen.

Gimbiya sumayya ko da tadawo  da su dada suka tambayeta akan rashin dawowarta k'arya tayi musu akan wai wata matsala ce tatashi akan business d'insu saida tajira komai yakoma normal sannan tadawo.

ko da tadawo sai da takwana biyu batasa yarima a idontaba dan tayi tunani zaizo d'akinta ammah sai gashi tsawon kwana biyu bai zoba.

dan haka da daddare shiryawa tayi taje 6angaren yarima domin ta san Indai ba ita tajeba toh ba zai ta6a zuwa wajentaba saidai idan yana buk'atarta.

lokacin da tashiga yarima suhail yana shirin bacci ko inda take bai kallaba,  takawa tayi taje inda yake still dai bai kalletaba sai ma wucewa da yayi yahaye gadonsa yakwanta.

Sumayya cikin ranta tace toh yau kuma naga yadda zamu kwashe da wannan d'an jin kan,  binsa tayi saman gadon takwanta gefensa tace my sweetheart ko welcoming d'in ma bazan samuba, tsawon kwana biyu da dawowata ammah ko kanuna ka damu.

yarima suhail batare da ya kalletaba yace ashe kini dawo?

da mamaki sumayya take kallonsa tace au da ba zan dawoba?

yarima bai tanka mataba yajuya mata baya.

sumayya ganin haka yasa tarungumosa ta ba tace haba yarima wai meyasa kake son wulak'antani ko dai bakaji dad'in dawowataba?

yarima banza yayi yakyaleta cike da k'ulewa.

gimbiya sumayya tace haba yarima wlh banason sharewar nan da kakemin.

yarima suhail yace sumayya ai da baki dawoba dan dabakinan hankalina ya fi kwanciya wlh,  ni da kin taimaka kin tashi kinkoma d'akinki dan yanzu banason a dameni hutu nake buk'ata.

sumayya cike da k'ulewa tace kai wlh tsiyata da kai bakasan arzik'iba duk yadda mutum zai nemi yakyautata maka sai ka kushesa nifa kawai tausayinka nakeji ganin lokacin da nad'auka bana nan nasan kayi missing d'ina.

Yarima tashi yayi yazauna yana kallonta a wulak'ance yace sumayya me kika d'aukeni?  na fa san abinda nakeyi ni a yanzu bana buk'atarki dan haka kitashi kifitarmin daga d'aki,

da mamaki gimbiya sumayya take kallonsa tace yarima ni kake kora?  me nayi maka daga dawowata sai kahauni da fad'a?

wani mugun kallo yarima suhail yayi mata tare da nuna mata k'ofa.

tashi sumayya tayi tare da d'aukar alkyabbarta tasaka sannan tace naji zan fitar maka daga d'aki sauk'inma nima ina da nawa d'akin daman taimaka maka zanyi ammah tunda......

tsawa yarima yadaka mata cikin 6acin rai yace I said get out!!!

sumayya ta tsorata sosai da ganin yanayinsa dan haka dasauri taficce tabar d'akin cike da jin haushin wulak'ancin da yarima yayi mata daga dawowarta......





_Comments_
       *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_*Sak'on gaisuwata gareka M.B.A a duk inda ka kasance nagode sosai👍*_

_~Masha Allah Sis leemah nd my k'anwa Janaf ina tayaku murnar kammala novels d'inku masu suna *BABBAN KUSKUREN DA NATAFKA nd NATAFKA KUSKURE* hak'ik'a kunyi namijin k'ok'ari wajen baje basirarku da hikimarku kun wa'azantar, kun nishad'antar sannan kuma kun fad'akar gaskiya na yaba muku sosai Allah yak'ara basira da zak'in hannu, I heart u all~_

_*Ummun Meenal Mummyn fadyl nd my chubby kuna ina kumatso kusa yau filin nakune, wannan page d'in mallakinkune ku kad'ai kuyi yadda kukeso da shi*_

page 1⃣1⃣

Yarima suhail bayan gimbiya sumayya ta fita dafe kansa yayi cike da jin haushin sumayya da take nema taraina masa wayau,  watau ta ma san ya yi missing d'inta? to kenan ita  batayi missing d'insaba tana nufin taimakonsa ma zatayi. tabbas yasan ya yi *BABBAN KUSKURE* da ya amince ya aureta domin ko kad'an batasan minene aureba
tsaki yaja yace Allah yashirya sannan yakoma yakwanta yana mamakin halin sumayya.

Sumayya a fusace takoma d'akinta cike da bak'in cikin wulak'ancin da Yarima yayi mata, ace kamarta daga ta je tataimaka masa shine yakoreta
tana shiga bedroom tamurza key nan tafad'a saman gado tafara kuka.

tun daga ranar aka koma 'yar gidan jiya ba mai kula d'an uwansa kowa harkar gabansa yakeyi

_______________

A 6angaren su zarah har yanzu babu abinda yasauya daga halaiyar 'yan gidansu, malam bello yanzu islamiyya kawai suke samu suna had'uwa

yauma bayan ta taso daga islamiyya tafiya take a nutse kanta sadde a k'asa daga bayanta taji ana mata sallama kamar ba zata amsaba sai kuma chan ta amsa batare da ta tsayaba mutumin cigaba yayi da binta yace dan Allah 'yan mata kitsaya kisaurareni mana,

Zarah ahankali tad'ago kai takalli mutumin da bazai gaza shekaru ashirin da biyarba, k'ara d'aure fuskarta tayi tace lafiya malam kaketa bina?

Murmushi mutumin yayi yace ni dai sunana hamza ina zama chan waccan rumfar mai kayan miyar kullum ina ganin giftawarki idan kin dawo islamiyya kuma gaskiya ina sonki saisa natunkareki nafad'a miki domin insamu matsugunni a zuciyanki wlh ina sonki, ina k'aunarki ina begenki, wlh indai baki amshi tayin soyayya taba zan iya mutuwa.

zarah baki tasaki tana kallonsa maganganunsa har sukaso subata dariya tadake tace ka gama?

hamza yace eh nagama ina dai son inji daga gareki domin kema nasan nayi miki 

Zarah d'an murmushi tayi tace nagode sosai da tayinka ammah saidai kayi hak'uri domin ina da wanda nake......

katseta hamza yayi yace dakata malama ai daman abinda naji ma tsoro kenan saisa tun tuni nak'i tunkararki da maganar ammah wlh bakiyimin adalciba danma kin samu ance ana sonki wanene anguwarnan bai san halin gidankuba waye baisan ku 'yan iska bane,  dan ma kin samu antaimaka ance ana sonki.

zarah murmushin takaici tayi sannan tace toh nagode kuma so ne bazan ta6a sonkaba, tana gama fad'in haka tawuce tabarsa tana jinsa yana ta yada mata bak'ak'en maganganu ammah tasharesa cikin ranta ko wani irin abune yatokare mata mak'oshi tabbas tasan abinda bawan Allahn nan yafad'a gaskiyane a game da gidansu,  ahaka ta isa gida da tunani iri-iri cikin ranta.




*BAYAN SATI 'DAYA*

Rauda yau kasancewar ta tashi da matsanancin ciwon kai da zazza6i kwance tawuni bata iya komai, da kaganta kasan tana jin jiki tuni ta fita hayyacinta saboda Amai da take yawan yi

su mama sun tusata a gaba kowa tausayinta yakeji ganin irin wahalar da take sha kallonsu kawai zakayi kasan suna cikin matsanancin tashin hankali.

zarah ko kuka kawai takeyi tana rik'e da hannun yayartata ko kad'an bata yarda tamatsa daga kusa da itaba domin ita tana da k'wallafar 'yan uwanta.

mama ce tahad'o mata ruwan bunu tare da indomie matsa mata sukayi sai taci, ba dan tasoba tadaure tamik'e dakyar tayi loma ukku shima dan taga hankalin dangin nata a tashe, kafin kace mi dagudu tamik'e tanufi toilet tadinga kwarara amai dasauri zarah tabita tarik'eta tana mata sannu har saida tagama, Aysha ce tad'ebo musu ruwa a buta nan zarah tataimaka mata tawanke jikinta sannan suka fito takoma takwanta.

zarah kallon su mama tayi da sukayi jugum tace mama dan Allah kice ma yaya Rauda tatashi muje asibiti domin bai dace tazauna da ciwo ba.

mama dogon numfashi taja tare da cewa hakane zarah nima abinda nake tunani kenan domin cikin d'an lokacin nan duk ta fita hayyacinta.

Rauda dakyar tabud'e baki tace a'a ba zanje asibitiba kubarni a nan kawai in muturwace inyita a gida.

zarah da Aysha fashewa sukayi da kuka ganin yarda 'yar uwar tasu take jin jiki, mama tace A'a Rauda dole fa kitashi muje asibiti.

Zarah tace mama ni zan rakata kice tatashi mutafi.

mama tace ke mezaki iya idan kinje? Ni dai zan tafi da ita.

Zarah tace dan Allah mama kibarni muje tare,  mama ganin yadda zarah duk hankalinta yake a tashe dan ko abincin kirki bata samu taciba dan haka tace toh shikenan kushirya kutafi.

Mama tataimaka ma Rauda tacanza kaya,  Rauda cema Zarah tayi tad'auko handbag d'inta akwai kud'i a ciki dan kar a buk'aci wani abu.

Aysha ce tafita tasamo musu adaidaita nan suka tafi General Hospital d'in garinsu.

basusha wahala ba wajen ganin likita, ko da Rauda tashiga zarah zaune tayi tana jiran fitowarta, 

Rauda take zaune opposite d'in kujerar Doctor Xeey Xeey cike da kulawa doctor Xeey Xeey take mata tambayoyi ita kuma tana bata amsa nan Dr Xeey Xeey tarubuta mata taste tace taje tayi kuma tatabbatar yau ta kawo mata.

Rauda Kar6a tayi tafito dasauri zarah tamik'e daga inda take zaune tana jiran fitowar 'yar uwartata.
tace Yaya Rauda sannu.
Rauda dakyar tace Zarah taste ne tabani muje lab.

zarah tace toh yaya Rauda.

ko da sukaje lab aka d'ibi jininta sannan aka bata 'yar roba tayi fitsari a ciki nan akace sujira nan da 30 minutes result zai fito.
zama sukayi suna jira har minti talatin yacika aka basu nan Rauda taje takaima Dr xeey xeey sakamako.

Dr xeey xeey tana dubawa murmushi tayi sannan tayi 'yan rubuce-rubucenta bayan ta gama tad'ago kai takalli Rauda tace toh Alhmdllh ina tayaki murna domin kina d'auke da ciki tsawon wata biyu nasoma ace tare kukazo da mijinki.

Rauda da tunda Dr ta ambaci ciki tarikece cikin d'aga murya tace doctor ciki?
Dr xeey xeey tagyad'a mata kai tace of course dan haka za'a maida miki folder d'inki a ANC kidinga zuwa awo tunda har yakai kusan 2 months batare da anduba lafiyarsaba zaki dinga zuwa awo.

Rauda zufa ce tafarayi dasauri taduk'e k'asa tare da fashewa da kuka.
da mamaki Dr xeey xeey take kallonta tace menene abin kuka?  kyautar da Allah yabakice bakyaso ko mi?

Rauda cikin sheshek'ar kuka tace Dr dan girman Allah kitaimaka kiciremin cikin nan wlh bana sonsa.

Dr xeey xeey fara'ar da take fuskarta tagushe cikin fad'a tace akan wane dalili zaki cire ciki idan ke bakyaso toh mijinkifa? ni gaskiya bana zubar da ciki.

Rauda cike da tashin hankali tace Doctor yadda Allah yataimakeki nima kitaimaka min wlh bana son cikin nan idan nakoma da shi gida bansan da wane ido zan kalli iyayena ba.

Doctor da tunda Rauda tafara maganar tazuba mata ido tana kallonta cike da 6acin rai tace idan na fahimceki kina nufin cikin nan na shegene baida uba ko?
Rauda shuru tayi batace komai ba.

ganin haka yasa Doctor tacigaba da cewa toh bari kiji ni bazan ta6a zubar miki da cikiba k'ara ma kiyi hak'uri kihaife abinki ammah kuma kin cuci abinda yake a cikinki domin kin samesa ba tahanyar da tadace ba, k'arama kiyi hak'uri kihaifesa domin kar zunubin yak'aru dan haka tashi kije nidai nabaki shawara haihuwar shi zai fiye miki.

Rauda dakyar tamik'e jiki ba kwari tafito daga office d'in doctor.
tana fita kallon zarah tayi nan hankalinta yak'ara tashi sai alokacin taji wata irin kunya tsaye tayi takasa k'arasawa wajen da zarah take tsaye.

ganin haka yasa zarah tamik'e cikin sauri ta isa inda Rauda take cike da tashin hankali tace yaya Rauda lafiya naganki a haka me yake faruwane?

Rauda hawaye suna zuba daga idonta dakyar tabud'e baki tace zarah ciki gareni.

Zarah a firgice taja da baya cike da tashin hankali tace yaya Rauda ciki kuma?

Rauda gyad'a mata kai tayi tare da mik'a mata takardar da doctor tabata,  jikin zarah yana kyarma ta amsa taduba, aiko nan tafashe da kuka tace yaya Rauda meyasa kuka za6a ma kanku irin wannan rayuwar? meyasa kuka za6i son abun duniya kuka 6ata rayuwarku, kingani ko yanzu gashinan kiyi cikin shege cikin da ke kanki bakisan ubansaba kun d'auki alhakinsa idan kika haifesa me zaki ce masa?

Rauda da take kuka dasauri tarik'o hannun zarah tace zarah wlh nima bansan ya zanyiba yau ne karo nafarko da nafara nadamar abinda nake aikatawa dan Allah kizo muje murok'i wata doctor d'in tacire min shi.

zarah fizge hannunta tayi daga rik'on da Rauda tayi mata tana ja da baya tare da girgiza kai, cikin kuka tace yaya Rauda badani za"a had'a bakiba ayi kisan kai meyasa kikeso kikashe ran da baida alhakin kowa saima shi da yake da naku?
kiji tsoron had'uwarki da ubangiji ga laifin zina ga na kisan kai, kituna tsayuwar ki gaban Allah ranar gobe k'igama,  baki tsoron garin zubar da cikin kije kirasa ranki?

Yaya Rauda wani irin nadamane taji ya zo mata nan tak'ara fashewa da wani sabon kukan tare da rik'o hannun zarah da itama take kuka tace zarah nafasa zubarwa wlh nayi nadamar abinda na aikata a yanzu kuma ba zan zubar da cikinba.

zarah cike da jin dad'i tace nagode sosai Yaya Rauda da kika fahimceni.

Yaya Rauda d'an tsagaitawa tayi da kukan da take tace saidai kuma inaso kiyimin taimako guda.

zarah dasauri tace Yaya Rauda kifad'i abinda kikeso zanyi miki.

Rauda tace inaso kafin muje gida kifara rakani wani waje

zarah da mamaki take kallonta tace yaya Rauda ina zamuje?
Rauda rik'o hannunta tayi tace muje kawai zarah.

zarah batayi musuba tabi bayanta.

mai adaidaita tatsaida musu tafad'i anguwar da za'a kaisu zarah dai shuru tayi tana mamakin inda zasuje.

Rauda ce tadinga gwada ma mai napep hanya bayan sunzo anguwar, bakin gate d'in wani gida aka safkesu nan Rauda tabiyasa kud'insa sannan tayi Knockin d'in k'ofar maigadi ganin Rauda ce yasa yabud'e saboda daman ya saba ganinta nan suka shiga ciki,  ita dai zarah binta kawai take

cikin wani parlour suka shiga da sallamarsu ammah bakowa ciki Rauda kallon zarah tayi tace Zarah shigo muzauna,

zarah girgiza kai tayi tace a'a yaya Rauda nan gidan wanene.
Rauda ganin zarah duk ta rikice yasa tace kar kidamu bawani abu inaji suna ciki kizo kizauna.

Zarah a tsorace tabi Rauda suka zauna nan Rauda tad'auko wayarta tayi kira itadai zarah kawai ji tayi ta ce gani cikin gidan ka sannan takashe wayar.

zarah a tsorace tace yaya Rauda wai nan gidan wanene me zamuyi?

Rauda har ta bud'e baki zatayi magana sai ga wani mutum ya fito daga cikin gidan,  da kallo duk suka bisa fuskarsa d'auke da murmushi yazo yazauna d'aya daga cikin kujerun d'akin tare da washe baki yace baby daman kina tafe baki fad'amin ba?  kallon zarah yayi da itama take kallonsa yace sannu 'yanmata halan ke sister d'intace naga kuna kama?

duk tambayoyin da yayi musu babu wanda yatanka mushi sai ma ido da suka zuba masa.

Rauda fuskarta a d'aure tace Alh umar nazone infad'a maka ina d'auke da cikin wata biyu.

nan fara'ar da take fuskarsa tagushe yace ciki kuma rauda?

Rauda hawayene suka fara zuba daga idonta tace eh ciki.

dariya yayi irin ta rainin wayau yace lallai Rauda toh garin yaya kika bari har ciki yashigeki? toh wai ma wanene yayi miki cikin?

Rauda da mamaki take kallonsa tace Alh Umar in bakaiba wanene nake huld'a da shi? ai kaine uban d'an saisa nazo nafad'a maka.

d'aure fuska Alhaji umar yayi tare da daka mata tsawa yace ke banason sakarci kingama zuwa kinbi 'yan iska sannan kizo kice d'a nane,

Rauda cikin kuka tace wlh d'ankane

Alh umar a harzuk'e yamik'e tsaye yace toh bari kiji duk wanda yatsaya miki a garin nan bai isa yasa in amshi cikin kiba a matsayin d'ana kije dai kigano uban cikinki dan haka kutashi kufitar min daga gida.

Zarah ranta ya 6aci sosai jin kalaman da Alh umar yake jifan yayarta dasu ga Yaya Rauda kuka kawai takeyi,  cikin 6acin rai tamik'e tsaye tare da nunasa da yatsa tace kai malam kar karaina ma mutane wayau kana nufin k'arya akeyi maka ba cikin naka bane? ai ni wlh naga wautar yaya Rauda da ta iya ba jakki irinka kanta, ni ai ko a k'afa aka d'aura min kai sai na kwance.

Alh umar ransa ya 6aci sosai cikin fushi yake ke karkinemi kigaya min magana wlh yanzu insa ad'aureki ni nace tabani kanta ba kwad'ayi yaja mataba?

zarah cikin d'aga murya tace kai kar kasaki kak'ara d'agamin murya kuma idan bakasa and'aureniba toh ba'a haifekaba.

Alh Umar a zuciye yad'aga hannu zai mari zarah cikin zafin nama zarah tagoce.
yaya Rauda da take zaune tana mamakin yadda zarah take balbala fad'a tabbas tasan ankai zarah k'arshe domin zarah tana da hak'uri sosai, da sauri Rauda tamik'e tare da rik'o zarah tace zarah ki kyalesa tunda dai har ya k'aryata alhali kuma ya san gaskine toh yaje shi da Allah.

Zarah fizge hannunta tayi tace yaya Rauda kikyaleni ya za'ayi mutum yana akan gaskiyarsa a tauye masa hak'i wlh dole yakar6i cikin nan.

Alh umar dariya yayi yace ke yanzu har kina tunanin zan kar6a ko?  toh muzuba agani wanene zai ci nasara.

Rauda cikin kuka tace umar *LAIFI NANE* da na amince na mallaka maka kaina ammah inaso kasani ba zan d'auki matakiba saidai kaje kai da Allah domin shine kad'ai zai kwatarmin hak'k'ina kuma kai shedane kaine karabani da budulcina kayaudare kace zaka aureni,  wlh a yanzu na tsaneka kaje kawai

rik'o zarah tayi tace zarah wuce mutafi zarah har ta bud'e baki zatayi magana Rauda tadaka mata tsawa tace kiwuce nace miki!

Zarah ba dan tasoba tabi bayan Rauda suka fita suka bar Alh umar a tsaye cike da takaicin bak'ak'en maganganun da suka yada masa.

Ko da suka fita zarah kallon Rauda tayi cikin 6acin rai tace haba yaya Rauda ya za'ayi kina da gaskiyarki sannan kibari atauye miki hak'i.

Rauda cikin kuka tace zarah ina kokwantone domin bansan ainahin cikin na waneneba.
Zarah cikin tashin hankali tace ban fahimcekiba yaya Rauda.

Rauda share hawayen fuskarta tayi sannan tace   zarah ba zan 6oye mikiba wlh mutum biyune kawai nasan ina mallaka ma kaina.

zarah tace yaya Rauda wannan wace irin rayuwace toh wanene gudan?

Alh munir ne wlh bayan su bana huld'a da kowa.

Zarah tace toh yaya Rauda me zai hana shima muje wajensa?

Rauda jinjina kai kawai tayi nan suka samu mai adaidaita Rauda tafad'a masa anguwar da zai kaisu........



_Comments_
        *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....✔*


_Jinjina agareku sis Mugirat marubuciyar *KISHI KO HAUKA*  da sis Ummie Adnan marubuciyar *HAUWA JIDDAT* gaskiya inajin dad'in novels d'inku basirarku da k'wazonku suna burgeni kunyi namijin k'ok'ari a wajen rubutunku Allah yak'ara basira da zak'in hannu acigaba da sambad'o mana,  *KISHI KO HAUKA DA HAUWA JIDDAT* duk Wanda bai karantaba anbarsa a baya dan haka kugarzaya kukaranta,  muje zuwa😍👍_

_~Gareka *DR ZAIN* 👍 ina jin dad'in novels d'inka Allah yak'ara basira da zak'in hannu,  nagode sosai da kyautan pages d'in da nasamu, *'YAN GUDUN HIJIRAH* labari maicike da darussa duk wanda bai karantaba anbarsa a baya~_

_*Yau page d'in nakune Mummyn Afrah nd Meena Abbah Wlh ina ji daku irin sosai d'innan, jinjina agareku marubutan *NI DA MIJIN YAYATAH gaskiya kunyi namijin k'ok'ari a cikinsa Allah yak'a basira da zakin hannu I heart u all😘*_

page 1⃣2⃣

Ko da suka isa nan ma maigadi bai hanasu shigaba saboda ya san Rauda sosai.

hango Alh munir sukayi a parking space yana shirin shiga motarsa ganin Rauda tare da zarah yasa yatsaya yana kallonsu fuskarsa d'auke da murmushi har suka iso wajen da yake su dukansu fuskarsu a d'aure take,

Washe baki Alh munir yayi yace Rauda kece tafe tare da sister d'inmu?  ya dai ko itama tana cikine?  ai daman na fad'a miki kud'ine abokan rayuwa nasan daman itama zata amince,  yanzu dai mushiga daga ciki muyi magana ko tafiya zakiyi kibarni da ita?

Rauda cikin fushi tace ni ba wannan yakawomuba nazone in shaida maka ina d'auke da cikinka tsawon wata biyu.

Alh munir saida yafirgita jin ta ambaci ciki ammah yadake yayi 'yar dariya ta rainin wayau yace ciki kuma? Haba kina big gurl ya za'ayi kibari kiyi cikin shege kuma dan kin rainani shine sai kice cikinane?

zarah cike da k'ulewar dariyar da yayi musu tace idan ba cikin ka bane toh na uban wanene?

Alh munir tsagaitawa yayi daga dariyar da yakeyi yace ke kardai kisaki kizageni naga kamar kunya bata ishekiba,

Zarah dariya tayi tace girma dai ya riga da ya fad'i akwai marar kunya bayanka? kabaro iyalanka kazo kana 6ata rayuwar 'ya'yan wasu kuma ciki dole kakar6esa dan baida uba bayan kai.

Alh munir cikin 6acin rai yace baku isa kulik'a min d'an shegeba ita ai tasan wad'anda take bi saitaje tagano wanda yayi mata ciki ammah ni wlh babu wanda ya isa yace cikinane kuma barakiji rauda daga yanzu kar ma kik'ara nuna kin sanni ko da ahanyane, motarsa yabud'e yad'auko kud'i yamik'a masu yace ga wannan kinje kisamu kicire cikin tunda daman kwad'ayi yaja miki sannan kufitarmin daga gida tun kan ranku ya6aci.

Zarah kallon Rauda tayi da taketa aikin kuka ran Zarah ya 6aci sosai, sannan tamaida kallonta ga Alh munir takar6i kud'in tawatsa masa a fuska  tace karik'e kud'inka bama so, eh dole kace haka tunda ka ci moriyar ganga, saidai inaso kasan wani abu kaima kana da 'ya'ya kuma kana da mata dan haka kasaurari naka, kar kamance Allah ba azzalumin bayinsabane kuma fad'an ubanginine abinda kayi sai anyi maka,  murmushin takaici Zarah tayi kwallah duk ta cika mata ido tace alhaki kwikwiyone muje zuwa, rik'o hannun Rauda tayi har sun fara tafiya sannan tatsaya batare da ta juyoba tace kuma ciki ba zamu ta6a zubar da shiba sai ta haifesa anan zamu gane wanene ubansa kuma ko jinin wanene dole mukai ma matarsa tareni cikin shege.

Tana gama fad'in haka taja Rauda suka fita sukabar gidan.

Hankalin Alh munir ya tashi sosai domin tunda yaga zarah yasan zata iya yin komai ma, chan kuma sai yayi murmushi yace naga ta yadda za'ayi inkar6i dan shege, yana gama fad'in haka yakoma cikin gida fitarma yafasa

Suna fitowa Rauda duk'ewa tayi k'asa tacigaba da kuka,  zarah share k'wallar idonta tayi tace yaya Rauda kinga abinda nake guje muku kingani ko yanzu gashinan dukansu babu wanda takar6i cikin kowa ya ce banasa bane.

Rauda tsagaitawa tayi daga kukan da takeyi tace tabbas zarah nagani kuma nasan *NATAFKA BABBAN KUSKURE* da na'amince nabi son zuciyana yanzu gashinan najawo ma kaina babar matsalarma bansan ya zanyi intunkari su mama da cikiba bansan ya zasu d'auki lamarinaba, zarah kawai kitafi gida.


Zarah cike da tausayi tad'ago yayartata daga tsugunnin da tayi tace haba yaya rauda meyasa zakice haka duk abinda yafaru kid'aukesa a matsayin *K'ADDARA CE* kar kidamu nayi miki alk'awali ni zan tsaya miki ga su mama har sai sun fahimceni *KIYARDA DANI* yaya Rauda.

Rauda kallon k'anwartata takeyi cike da gamsuwa ta jinjina kai domin tasan zarah tana da hankali zata iya shawo kan iyayen nasu, share hawayenta tayi tace shikenan Zarah na yarda da ke ammah naga illar abinda na aikata.

Zarah murmushi tayi tace kikwantar da hankalin yaya Rauda nidai fatana kidaina wannan rayuwar da kikeyi kikoma mutuniyar kirki

Rauda tace zarah insha Allahu nadaina domin nakoyi darasi tun a nan yanzu dai muje gida fatana su Abbah su fahimceni.

Mai adaidaita suka samu suka fad'a masa inda zai kaisu har k'ofar gidansu yasafkesu suka sallamesa.

Rauda tsaye tayi takasa shiga gidan ganin haka yasa zarah tarik'o hannunta suka shiga lokacin Abbah da mama Suna zaune tsakar gida Suna cin abinci,  jin sallamarsu yasa Aysha tafito daga d'aki rataye da d'an k'aramin veil da alama fita ma zatayi.

Mama ce tace Rauda har kun dawo?  yanzu daman muke maganarku da malam muna cewa shuru har yanzu baku dawoba.

Zarah da Rauda tsaye sukayi suna kallon juna kowa hankalinsa a tashe,  mama da abbah zuba musu ido sukayi suna kallonsu domin daga ganin yanayinsu babu alamun gaskiya a tattare da su,  jikin Mama ya yi sanyi tace Rauda lafiya naganku haka?

Rauda kuka tafarayi tare da zaunawa k'asa tace mama kuyafemin wlh na cutar da rayuwata tabbas ban d'aukoma kaina hanyar da zata 6ulleba a yau nayi nadamar dukkan mugun halin da nayi a baya na cuci kaina ina tsoron had'uwata da ubangijina.

Mama cikin tashin hankali tace Rauda meyake faruwa? Zarah kuyi min bayani menene yafaru?

Zarah murmishin takaici tayi tana hawaye tace mama tarbiyar da kukabamuce kar kuzargemu duk abinda yafaru tunda kwad'ayi da son abun duniya gareku.

abbah tsawa yadaka musu yace kuyi mana bayani mana me yake faruwa?  sai wani kwana-kwana kukeyi mana

Rauda ce tad'ago kai takallesu tace Abbah mama kuyi hak'uri ina d'auke da ciki tsawon wata biyu.

Mama dafe k'irji tayi dak'warai tace Rauda ciki?  Abbah ma yace ciki? ??
Aysha cikin tashin hankali tace yaya Rauda ciki kuma?

Zarah kallon iyayen nasu tayi tace eh ciki gareta.

Mama k'asa tasulale tazauna tace nashiga ukku Rauda gidan ubanwa kikayi ciki

Yaya Rauda ta kasa cewa komai face kuka da takeyi.

Abbah hularsa yacire yafara fifita yace idan baki fad'amin inda kika samo cikiba sai na karyaki a cikin gidan nan.

Rauda cikin kuka tace Abbah kar kuga laifina duk abinda yafaru ku ma kuna da naku laifin a ciki domin baku bamu tarbiya tagari ba, ko da nafara wannan rayuwar ko da sau d'aya bamu ta6a ganin kun nuna rashin jin dad'in hakan ba saboda kwad'ayinku da son abin duniya

tabbas ayanzu nayi takaicin kasancewarku iyayenmu nayi Allah wadai da hali irin naku, wlh nayi nadamar abinda na aikata natuba insha Allahu daga yanzu na sauya rayuwata,  kallon Zarah tayi da take tsaye ta jingine da bango idonta a lumshe hawaye kawai suke fita, Rauda tace kukalli baiwar Allahn nan itace kawai tafita zakkah a cikinmu kawai kasancewarta mutuniyar kirki yasa muka tsaneta muka hantareta ammah baiwar Allahn nan hakan baisa tak'imuba a kullum k'ara jawomu take a jikinta tana mana wa'azi a k'arshe ma sai munemi muci mutuncinta ammah hakan baisa tabarmu ba, muna mata kallon bagidajiya ashe itace wayaiyar tamu tabbas Zarah rayuwarki ta burgeni natayaki murna da son zuciya bai rud'ekiba har kika fad'a wannan mummunar rayuwar da iyayenmu sukaja muka fad'a, tabbas yanzu nagane *DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA* shi ruwa kan doka.

Rauda nisa tayi sannan tamaida kallonta ga Aysha tace Aysha kitaimaki kanki kema kigyara rayuwarki tun kan rayuwa tajuya miki baya domin a yau nagane mecece rayuwa kowane saurayi naje ma maganar ciki saidai yawulak'antani yacimin mutunci a k'arshe zarah ce taso takwatar min 'yancina.

Aysha dasauri tacire veil d'inta tare da duk'ewa kasa tafashe da kuka tace wlh yaya rauda nad'auki darasi a wajenki nima nadaina abinda nake, maida kallonta tayi ga su Abbah da sukayi jugum tace tsakaninmu da ku Allah ne kad'ai zai mana *SAKAYYA* domin bamu dace da iyaye nagariba dakanku kuke turamu muna aikata 6arna wlh da ace ana canza iyaye da babu abinda zai hanani canza nawa

Zarah dasauri tabud'e idonta tana kuka tace kun gani ko mama?  Abbah kunga halin da kuka jefamu a ciki kuma wlh ranar lahira sai Allah ya tambayeku game da kiyon da yabaku, yanzu gashinan duniya ta juya muku baya, idan yaya Rauda tahaihu kundinga kallon abinda tabari kutuno kuskuren da kuka tafka, girgiza kai tayi cike da takaici tace da ace akwai inda zamuje da muntafi munbar muku gidanku muje muyi rayuwa mai tsafta.

Mama fashewa tayi da kuka tace wlh son zuciyane da sharrin shaid'an suka ja mana kuma insha Allahu muma mundaina kuyafe mana, 

Aysha mik'ewa tayi tazo inda Zarah take tace yaya zarah tabbas kin ciri tuta a cikinmu duk abinda muke aikatawa baisa kin k'yamacemuba sai ma soyayyar da kike nuna mana, Dan Allah kiyafe min abinda nayi miki.

zarah murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo tace bakomai Aysha Allah yayafe mana gaba d'aya.

Rauda mik'ewa tayi tsaye tace dan Allah kuzo muje mubar musu gidan nasan ba zamu rasa wajen zama ba Allah yana tare damu. Aysha tace hakane yaya Rauda mun amince mutafi.

mama k'ara fashewa tayi da kuka tace nashiga ukku dan girman Allah kar kutafi kubarmu wlh muma mun tuba,  mama kallon Abbah tayi da yayi jugum sai zufa yakeyi tace haba malam dan Allah kace wani abu mana kar sutafi.

Abbah dakyar yabud'e baki yace Zarah, Rauda, Aysha kudawo kuzauna muyi magana,

tsaye sukayi sukak'i motsawa zarah ce tayi k'arfin halin cewa yaya Rauda kuzo muje muzauna.

A tare sukazo suka zauna har a lokacin mama kuka takeyi,  Abbah ne yayi gyaran murya sannan yace.......




_Comments_
        *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Masha Allah *Mummyn Afrah nd Meena Abbah* ina tayaku murnar kammala novel d'inku mai suna *NI DA MIJIN YAYATAH*  hak'ika kun wa'azantar, kun fad'akar sannan kun Nishad'antar damu,  gaskiya tsarin rubutunku da fasahar da kuka zuba ta sun burgeni, Allah yabada ladan abinda aka fad'a daidai, kurakuren da suke ciki Allah yayafe muku, inaso kusani ina muka son so, Allah yabar k'auna my Aunties😘_

page 1⃣3⃣


Abbah gyaran murya yayi sannan yace maganar barin gida duk bata tasoba a yanzu muma mungane kuskurenmu tabbas duk abinda mutum yashuka shi zai gir6a wlh banga laifinkuba tabbas bamu dace da mukasance iyayenkuba, Abbah girgiza kai yayi yace kaicona da nabari son abun duniya yarud'eni har nawatsar da tarbiyar yarana alhali ni iyayena bahaka sukayi min ba,  son zuciya da kwad'ayine suka ja mana dan Allah kuyi hak'uri da mummunar d'abi'ar da muka d'auraku akanta,  wannan ya zama darasi a garemu ayi hak'uri a yafi juna.

mama cikin kuka tace dan Allah kuyafe mana insha Allahu yanzu zamu gyara tsarin gidanmu da komai zakuyi alfahari da mu.

Zarah ce tace bakomai wlh mun yafe muku duniya da lahira muma kuyafe mana.
kallonta tamaida ga su Rauda da basu da niyar yin magana tace yaya Rauda dan Allah kuyafe ma su mama tunda sun gane kuskurensu.

Rauda da Aysha cikin kuka sukace shikenan mun yafe musu Allah yayafe mana gaba d'ayanmu.

gaba d'aya suka amsa da Ameen.

sannan Abbah yace toh Alhmdllh da Allah yataimakemu muka farka tun kafin lokaci yak'ure mana naji dad'in hakan, insha Allahu zanyi k'ok'ari duk wani hak'inku da yarataya kaina inga na safke muku shi, saidai matsala d'aya yanzu cikin da yake jikin Rauda bansan ya zamuyi da Shiba.

Mama ma tayi nisa sannan tace mezai hana azubar da shi?

Zarah da sauri tagirgiza kai tace a'a mama bai dace azubar da shi ba karfa mumanta shi fa d'an baida alhakin kowa sai ma su da yakeda alhaki akansu da suka samesa ba ta hanyar halak ba,  ga laifin zina ga na kisan kai ai k'ara tahak'ura tafauwala ma Allah lamurranta saboda Allah yana sane da halin da take ciki kuma komai rubutaccene ya riga ya tsara ma kowa yadda rayuwarsa zata kasance,  shin baku tsoron wajen zubar da cikin tarasa rayuwarta?  idan taje me zatace ma ubangijinta ranar gobe k'iyama?  Shin kunsan yadda rayuwa zata kasance a nan gaba ko kuna tunanin nan gaba zata k'ara haihuwa? yakamata mumik'a lamurranmu ga Allah ubangijinmu mucigaba da rok'onsa tare da neman gafararsa Allahu gafurur rahim ne.

Dukkansu jinjina kai sukayi alamun gamsuwa da bayanin Zarah, Abbah yace tabbas Zarah nagamsu da bayaninki Allah yayafe mana kuskurenmu wlh ke d'iyar kirkice, kekuma Rauda Allah yasafkeki lafiya.

Gaba d'ayansu sukace Ameen, mama tace Allah yayi muku albarka Allah yaraya mana ku.
cike da jin dad'i sukace Ameen mamanmu,
muma muna alfahari da ku Allah yabar mana ku.

daga nan suka shiga tsara yadda zasu tafiyar da rayuwarsu, Aysha da Rauda 'yan kud'in da suke hannunsune suka tattara suka ba iyayen nasu sukace asiyo kayan abinci,

tun daga ranar suka rabu da samarinsu  gidan yagyaru, inda Aysha takoma islamiyya suna zuwa tare da Zarah, Rauda kuma tacigaba da rainon cikinta, a gida Zarah takeyi masu k'arin karatunsu Rauda da Mama.

cikin ikon Allah Abbah yasamu d'an aikin da ake biyansa duk wata da taimakon Allah yake samu yana rik'e gidansa gwalgwadon k'arfinsa,

su kansu a yanzu suna jin dad'in sauyawar da suka samu ta rayuwa.

_______________

Yarima Suhail yau tunda yatashi jinsa yake wani iri ga tsananin buk'atar sumayya da yakeyi daurewa kawai yake tsawon wata biyu kenan rabonsa da ita.

yau bayan yadawo wajen aiki yayi wanka ya shirya cikin shigarsa ta alfarma fitowa yayi yanufi part d'in sumayya domin yau ji yake hak'urinsa ya k'are baya iya cigaba da daurewa


Yarima d'akinn sumayya yashiga lokacin sumayya tana zaune a parlour tsakiyar kuyanginta suna ta mata hidima.

ganinsa yasa dukansu suka zube suna kwasar gaisuwa yarima baibi ta kansuba yashige bedroom d'in sumayya, da harara sumayya tabisa sannan tamik'e tabi bayansa.

tana shiga ta tarar da shi zaune saman gado batare da ta tanka masaba taje tazauna itama kusa da shi nan wajen yad'au shuru.

ganin baida niyar yin magana yasa sumayya tace lafiya?

Harara yarima yawurga mata tare da cewa lafiyar kenan, hak'ina nazo kibani.

'yar dariya gimbiya sumayya tayi sannan tace sai a yau za'a waiwayeni? ai nad'auka anrufe shafina, ko ka mance lokacin da nazo d'akinka kakoreni?  ai nad'auka nagama amfani a wajenka ashe ina da sauran amfani.

yarima suhail wata muguwar harara yawurga mata cikin 6acin rai yace sumayya da ace akwai yadda zanyi inguje ma kusantarki da nayi domin nima ba dan nasoba nake nemanki domin kwatakwata ke ba ajina bace dandai *K'ADDARA CE* kawai tasa na amince ma aurenki, wlh kikiyayi ranar da zaki kaini k'arshe domin zan d'auki mummunan mataki akanki.

Sumayya ta6e baki tayi cikin rashin damuwa tace kai fa matsalata da kai bakasan arzik'iba sai kanaso ataimaka maka maimakon kalalla6ani shine kakemin fad'a da gori. wlh nima ashirye nake nakad'auki kowane irin mataki nasan dai duk abinka ba zaka ta6a k'ara aureba dan su dada ma nazasu amince ba.

yarima har ya bud'e baki zaiyi magana nan wayansa tafara ringing ganin ummi ce yasa yasaita nutsuwarsa sannan yayi picking tare da yin sallama.

chan 6angaren sultana sadiya ta amsa masa tare da cewa yarima kazo kasameni inason ganinka.

yarima suhail cike da ladabi yace ummi lafiya dai ko?

Ummi tace lafiya lou kawai  inaso mutattauna ne akan kayan da kace aware akai gidan marayu da gajiyayyu.

yarima shuru yayi nad'an lokaci sannan yace toh ummi ganinan zuwa,  nan yakashe wayar tare da mik'ewa ko inda sumayya take bai k'ara kalloba yaficce yabar d'akin.

sumayya haushi yakamata saboda ba haka tasoba taso ace sai tagama ja masa rai sannan zata amince masa domin itama buk'ace take da shi kawai dai tana daurewane domin tanuna masa kuskurensa na wulak'antata da yayi,  tsaki taja tare da mik'ewa tsaye tace nasan dai dole zai dawo gareni.



yarima ko da yafita direct turakar iyayensa yaje a parlour yatarar da k'anwarsa Gimbiya Rahma a tsakiyar kuyangi sun zagayeta suna mata fifita da tausa inda ita kuma take waya.

ganinsa yasa gaba d'ayansu suka zube k'asa suna kwasar gaisuwa,  Rahma ma dasauri tamik'e tsaye tare da d'an rissinawa cike da girmamawa tace barka da shigowa.

Yarima batare da ya tanka musuba yayi musu nuni da k'ofa alamun sufita.

gaba d'ayansu suka mik'e suka fita daga d'akin,  Rahma ma har zata fita yace ke dawo.

Rahma dawowa tayi tazauna kujerar da take opposite d'in wadda yake zaune, kallon yayan nata take taga baida niyar yin magana gashi duk ya canza, ahankali tace yaya suhail bakada lafiya ne?

Yarima suhail ahankali yamaido kallonsa gareta kamar ba zaiyi magana ba sai kuma can yace tashi kije kihad'o min ruwan lipton da lemun tsami kar kizuba komai ciki.

Rahma mik'ewa tayi tare da d'an rissinawa sannan taffice daga d'akin.

Yarima jingine kansa yayi akan kujerar da yake zaune tare da lumshe idonsa shi kad'ai yasan abinda yake ji.

ummi tana fitowa daga d'akinta ganin yarima a haka yasa tayi tsaye tana kallon d'an nata ahankali tace suhail daman ka shigo shine baka fad'a min ba? 

Yarima suhail ahankali yabud'e idanuwansa da suka rikid'a suka koma launin ja yasafkesu akan fuskar ummi tare da yin d'an guntun murmushi yace sorry ummi ban dad'e da shigowaba.

ummi tsaye tayi tana kallon d'an nata yanayinsa yasa saida gabanta yafad'i a rud'e tace suhail me yake damunkane bakada lafiya?

Yarima murmushi yayi yace lafiya ta lau ummi.

ummi kasa cewa komai tayi saidai binsa take da kallo tana nan tsaye Rahma tashigo da wani plate d'auke da ruwan lipton da lemon a gefe,  gaban ummi ne yashiga fad'uwa ganin Rahma ta aje gaban yarima tare da duk'awa tana matsa lemon d'in cikin cup d'in,

tausayin d'antane yakamata domin tabbas tasan abinda take tunani shi yakasance,  ahankali taga yarima suhail yad'auki cup d'in yana sha yana yamitsa fuska duk Wanda yagani yasan ba dan dad'i yake sha ba kawai dai dan ba yadda ya iya.

ganin haka yasa ummi tawuce tana jin wani iri a cikin ranta bata zarce ko'inaba sai turakar mijinta bata damu da gaisuwar da akeyi mataba domin kwatakwata ma hankalinta ba anan yakeba.

ko da tashiga lokacin yana zaune saman gado hannunsa rik'e da newspaper yana dubawa, jin anbud'e d'akin yasa yamaida kallonsa ga k'ofa,  yanayin yadda yaga matar tasa ta shigo yasa ya aje newspaper d'in da take hannunsa yazuba mata ido.

Sultana bilkisu itama tsaye tayi tana kallonsa ta bud'e baki zatayi magana kenan sai hawaye suka fara zuba daga idonta, Sultan Ahmad cike da rud'ewa yamik'e yanufo inda matar tasa take yace bilkisu lafiya me yake faruwane?

Sultana Bilkisu fashewa tayi da kuka tace ranka yadad'e kagafarceni akan abinda zan fad'a domin hak'urina ya k'are ace d'ana tunda yayi aure baida kwanciyar hankali kaduba kaga duk mulki, sarauta, kyau, dukiya babu wanda *YARIMA SUHAIL* yarasa saidai abu d'aya shine kwanciyar hankali.

Sultan Ahmad zuba ma matar tasa ido yayi yana kallonta domin yasanta akwai hak'uri duk abinda za'ayi mata batanuna 6acin ranta saidai idan ankaita bangone,  Sultana bilkisu cigaba tayi da cewa tun lokacin da d'ana yayi aure baida kwanciyar hankali domin kwatakwata bai samun nutsuwa, kula da tattali a wajen matarsa Sumayya, ba wai shi yafad'a minba kawai dai nafahimci haka kaduba kaga yadda yarame koda yarima baya fad'in matsalarsa saboda zurfin cikinsa ammah yanayinsa kawai zaka kallah kagane yana cikin matsala,  girgiza kai tayi tace ya za'ayi ace da matarsa ammah yana shan ruwan lipton da lemon, ranka yadad'e ina tsoron ranar da d'ana zai kasa jurewa har yafara neman mata, bawai fata nakeyi masaba kawai dai ina tsoron hakan domin shima mutum ne kamar kowa, 
rik'o hannun sultan  Ahmad tayi tare da durk'usawa k'asa tace ranka yadad'e idan maganganuna sun 6ata maka rai kayi hak'uri ammah ina tausayin halin da d'ana yake ciki,  Sultana Bilkisu tana kaiwa nan tasake fashewa da wani sabon kukan.

Sultan Ahmad cike da tausayi yarik'o hannun matar tasa yamik'ar da ita tsaye yarungumeta yace Bilkisu nima ina lura da lamurran Suhail narasa ya zanyi ne domin ko bakomai d'iyar d'an uwana yake aure narasa ya zanyi in magance matsalarnan domin ina tsoron abinda zai samo min matsala ni da d'an uwana.

Gimbiya Bilkisu d'ago kanta tayi tana kallon mijin nata tace ammah shi d'anka fa kaduba kaga matsalar da take shirin 6ullomasa dan Allah kataimaka kaduba lamarin yarima Suhail domin yana buk'atar taimakonmu.

Sultan Ahmad rik'o hannun matarsa yayi sukaje bakin gado suka zauna yace Bilkisu nima inajin Suhail sosai a cikin raina kikwantar da hankalinki zanyi shawara muga yadda zamu 6ulloma lamarin cikin ruwan sanyi kema inaso kije kiyi tunani a kai kidaina sanya damuwa a ranki kinji.

Sultana Bilkisu cike da gamsuwa da maganar mijin nata ta jinjina kai tare da yin murmushin jin dad'i, shima Sultan Ahmad murmushin yayi sannan yashiga goge mata hawayen da suke fuskarta.

godia tayi masa tare da mik'ewa tsaye,  kallonta yayi yace Bilkisu ina kuma zakije? ai nad'auka zuwa kikayi kitayani hira?

murmushi tayi tace kayi hak'uri d'ana yana parlour yana jirana bari inje insallamesa sai indawo.

Sultan Ahmad shima murmushi yayi yace toh shikenan sai kin dawo.

Sultana Bilkisu d'an rissinawa tayi cike da girmamawa tace nabarka lafiya sannan tajuya tafita tabar d'akin,

Yarima Suhail ko da yagama shan lipton d'in komawa yayi yajingine kansa da kujerar da yake zaune yana jiran mahaifiyartasa tafito anan bacci yafara d'aukesa.

Sultana Bilkisu ko da tashigo ganin d'an nata yana bacci yasa tazauna gefensa tare da d'aura kansa saman cinyarta.

ahankali suhail yabud'e idonsa sanin mahaifiyarsa yasa yasakarmata murmushi tare da maida idanuwansa yalumshe,

itama sultana Bilkisu murmushin tayi nan tashiga shafa gashin kan d'an nata cike da so da k'aunarsa,  a gefe guda na zuciyarta tausayinsace ta baibayeta.

****     ****    *****

mama ce da su zarah zaune tsakar gida suna k'ulla zo6o da kunun aya suna fira cike da nishad'i,  Aysha ce takalli zarah tace wai yaya zarah yaushene ma zakuyi walimar saukarku ta alk'ur'ani?

Murmushi zarah tayi tace kedai Aysha kin cika zumud'i sai fa nan da sati biyu kinga ai da d'an sauran lokaci.

Mama tace kud'in ma da kikace kina buk'ata suna nan ajiye tun jiya Abbanku yabani inbaki idan kin tashi tafiya islamiyya sai kituna min inbaki kikai dan kar ma inta6asu.

Zarah cike da jin dad'i tace nagode sosai Allah yak'ara girma da rufin asiri.

gaba d'ayansu sukace Ameen,  Rauda tace toh anko d'in da zakuyi fa?

Zarah murmushi tayi tace bazanyi wannan ba yaya Rauda domin bazan matsa ma kaina ba abinda nakeda hali shi zanyi saidai in naje suhanani shiga taron.

Mama tace a'a zarah baridai muga abinda hali zaiyi idan da hali ai sai ayi miki.

zarah tace a'a mama kar kud'aura ma kanku d'awainiya abarsa kawai.

Mama tace zarah kibari dai muga abinda hali zaiyi idan da rabo ai za'ayi.

Aysha tayi karaf tace aikam dai dole ayi anko d'innan dan walima zamuyi sosai, nima zan bada gudumuwata.

Dariya Rauda tayi tace jarin sana'arki zaki bamu ko?

Aysha tace sosai ma ai har nafara tari ribar nake zubawa asusu.

dariya suka sanya mata zarah tace gaskiya nagode sosai 'yar uwata da k'aunar da kike nunamin.

Aysha murmushi tayi tace wannan kuma halinkine domin ke kike nuna mana k'auna ta gaskiya.


A islamiyya zarah ce da k'awarta zaune suna d'an ta6a hira kafin malam bello yashigo, khairy kallonta tayi tace wai k'awata me kike shirya mana na walimar nan?

murmushi zarah tayi tace abinda hali yabani domin ba zan matsa ma kainaba abinda nake da halinsa shi zanyi dan ni ko ankoma bana tunanin yinsa.

Khairy zaro ido tayi tace kai zarah dan Allah kiyi anko d'in kinga kowa fa zaiyi ya za'ayi ace kekad'aice ba zakiyiba.

zarah murmushi tayi tace ba zan damuba domin kowa da bazarsa yake taka rawa, abinda Allah yahoremin shi zanyi.

Khairy jinjina kai tayi cike da gamsuwa da maganar k'awartata sannan tace toh Allah yashige mana gaba.

zarah tace Ameen ya rabb, shigowar malam bello ne yasa ajin aka nutsu daga nan aka fara darasi.

bayan angama anyi addu'a antashi zarah tace muje khairy inkai ma malam kud'in walimana,

a office suka samu malam hambali bayan sun gaishesa ya amsa musu, zarah tace malam ga kud'in walimata,

malam hambali yace zarah banda kud'in da kika biya ko k'arine muka samu?

zarah da mamaki take kallonsa tace ni kuma nabiya kud'i?  da yaushe?

murmushi malam hambali yayi yace Malam bello yazo yakawo kud'inki.

Zarah da khairy kallon Juna sukayi sannan sukayi ma malam hambali sallama suka fita daga office d'in.

A wajen islamiyya suka hango malam bello tsaye ya zuba ma k'ofa ido da alamu zarah yake jira yaga fitowarta, 

zarah saida suka d'anyi gaba sannan tad'auko wayarta takira malam bello tace gamu muna jiranka.

suna gama wayar malam bello yazo yasamesu fuskarsa d'auke da murmushi yayi musu sallama nan suka amsa masa tare da k'ara gaishesa.

zarah tace malam naje biyan kud'in walima shine aka shaida min ka biya nagode sosai ammah gaskiya bazanso kadinga matsama kankaba tunda kaga kaima karatu kake dan haka ga kud'inka na maido maka.

malam Bello yace a'a zarah ni dan Allah nayi miki dan haka bazan kar6aba, kuma kidaina maganar karatu nake koma me nakeyi ai dan ina da halin yi miki da ace banda su ai da bazan mikiba.

zarah tace hakane saidai ina tsoro kar asamu matsala aurenmu yak'i yuwuwa, malam Bello murmushi yayi yace kar kidamu ko da ace ban aurekiba wannan nasan *K'ADDARA CE* kuma wani baya auren matar wani dan haka kikwantar da hankalinki.

murmushi zarah tayi tace nagode sosai malam da taimakon da kakeyi min Allah yataimakake kamar yadda kake taimakona.

malam Bello yace kar kidamu ai yi ma kaine, yanzu muje inrakaki gida naga magrib ta gabato kuma k'awarki ta tafi ta barki, 

zarah murmushi kawai tayi nan suka jera da malam Bello suna tafiya suna hira har saida yarakata har k'ofar gida sannan sukayi sallama yatafi itakuma tashiga gida.





_Comments_
       *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

page 1⃣4⃣

Zarah ko da tashiga gida d'akin mama tashiga ta tarar da mama tana linkin kaya ganin zarah yasa tasakarmata murmushi tare da cewa 'yan makaranta andawo?

zarah ma murmushi tayi tace eh mama dafatan mun sameki lafiya?

mama tace lafiya lau, nan zarah takama mata suka cigaba da linke kayan,  cike da nutsuwa zarah tad'auko kud'in tamik'a ma mama tace mama ga kud'in da kuka bani.

mama da mamaki take kallonta tace zarah ya haka?  ya naga kin maido kud'in?

murmushi zarah tayi tace  mama daman da naje inbiya shine akace malam bello ya biyamin kuma na kai masa kud'in yace bazai kar6aba shi dan Allah yayi min nayi-nayi yakar6a ammah ya k'i.

mama tace Allah sarki gaskiya yana d'awainiya dayawa mungode sosai Allah dai yabiyasa,  yanzu kud'in ki aje wajenki kinga sai kiyi anko d'in da su,

zarah tace toh mama nagode sosai Allah yak'ara girma da rufin asiri.

mama cike da jin dad'i tace Ameen 'yar albarka nidai fatana a kullum Allah yakawo muku mazaje nagari kuyi aure.

zarah dagudu taficce tabar d'akin cike da jin kunya,  mama dariya tayi sannan tacigaba da linkin da takeyi.


tun ana saura kwana hud'u ayi walimar aka bugo Invitation card aka gayyaci mutane da dama daga cikin wanda aka kaima katin gayyata har da maimartaba.


A gidansu zarah suma shirye-shirye suke daidai k'arfinsu,  Abbah bakin gwalgwado yasiyo mata abinda zata raba ma abokanta da 'yan uwa.

malam Bello ma ba'a barsa a bayaba domin carton din lemu  yasiyamata yakai mata dakyar yasamu zarah takar6a.

ana gobe za'ayi walimar gidansu zarah tun dare aka fara shirye-shiryen abinda za'a raba ma mutanen da suka gayyata kasancewar da k'arfe goma za'ayi walimar.
_______________

yarima tun daga lokacin yafita harkar sumayya ganin tana neman rainasa akan hak'insa yasa yajefar da ita gefe yacigaba da hidimarsa,  sumayya tun tana daurewa itama taji bata iya daurewa.

yau ma kwance take tana ta juyi saman makeken gadonta tsaki kawai takeja tana neman mafita,  chan tayi nisa tace daman ace zinat zatazo da nad'an samu sauk'in abinda nakeji,  ammah bari inkirata ko ta flight ce tabiyo tazo yau, wayarta tajawo takira zinat ammah kashe wayartake, 

tsaki sumayya taja tare da wullar da wayar tace matsalata da ita kenan ayita nemanta ba'a samu.


Sultana Bilkisu ce zaune a turakarta tana kallon wata drama a faskekiyar TV d'in da take manne a bangon d'akin, gefenta kuyangine zaune k'asa suna jiran jin umurni daga wajen mai d'akintasu.

Sultan Ahmad ne yashigo da sallamarsa dasauri duk suka zube suna kwasar gaisuwa,  cike da fara'a ya amsa musu,  nan suka tashi suka ficce daga d'akin ahankali yataka yaje inda matarsa take zaune tazuba masa ido fuskarta d'auke da murmushi,

shima murmushin yayi tare da zama kusa da ita, rik'o hannunsa sultana bilkisu tayi cike da kulawa tace daddynsu suhail barka da dawowa muje daga ciki.

sultan Ahmad tallabo fuskarta yayi yace sultana ai banje ko'inaba yau ina fada daga chan naje wajen dada munata shan hira.

Sultana Bilkisu tace Allah sarki, ya wajen memartaba duk kwanan nan bamu gaisa da shiba duk lokacin da zanje gaishesa toh yana chan fada.

sultan Ahmad yace lafiya lou,  daman nima sawa yayi aka kirani yayi min magana akan wata walima da aka gayyacesa shine yace ni inwakilcesa inje tunda gobene zaya fita, kuma babu dad'i ace babu Wanda yaje daga wajensa.

Sultana Bilkisu tace tabbas hakane k'ara ko kaine kaje, murmushi sultan yayi yace ai tare da ke zamuje goben, yarima ma zan kirasa domin yashirya muje tare. 

Sultana Bilkisu cike da farin ciki tace Allah yakaimu da rai da lafiya.

Sultan Ahmad yace Ameen, taso mushiga daga ciki akwai maganar da nakeson muyi,

dariya Sultana Bilkisu tayi tace kai Abban suhail kawai dai kace mushiga ciki ammah nasan babu wata magana da zamuyi.



wanshekare chan makarantarsu zarah cike take mak'il da mutane, daga wajen islamiyyar aka kafa rumfuna inda daga tsakiya aka tanadi wajen da za'a gudanar da walimar.

Rumfa d'aya aka fitarma da Yarima Suhail, Sultan Ahmed da Sultana bilkisu dukkansu sanye cikin kayan alfarma sai dogarawansu da kuyangi da suka zagayesu,  nan aka cika musu gabansu da kayan ciye-ciye da shaye-shaye,

shi dai yarima suhail tun da yazauna dannar wayarsa kawai yake ko da sau d'aya bai d'ago kai ba,  domin tun da yazo yaga anzuba masa ido mata da maza suna kallonsa saisa yajawo wayarsa yashiga dannawa.


inda daga bisani mai gabatar da shiri yafita yafara bayan ankira shugaban makaranta ya bud'e taron da addu'a nan aka fara gabatar da kowa, bayan angama aka fara kiran d'aliban da zasuyi walimar da d'ai-d'ayansu suna fitowa sugabatar da karatu.

Daga chan gefe nahango zarah da k'awarta khairy zaune cikin anko d'insu sunsha dogayen hijab d'insu.

zarah kallon khairy tayi da take ta kalle-kalle tazungurota tace ke wai mekike kallo tun d'azun kin zuba ma waje guda ido?

Murmushi khairy tayi tace wlh wancan yarima din nake kallo ya burgeni sosai kiduba kiga yadda ya hakimce, harararta zarah tayi tace kekuma rashin aikinyi miye abun kallo,  ke nifa tunani nake anya zan iya fita inyi karatun nan?  wlh jikina yayi sanyi sosai kuma nasan ganin mutanen da nayine.

Dariya khairy tayi tace nifa tsiyata da ke tsoron mutane gareki, kidaure kisa ma ranki babu kowa wajen insha Allahu zakiyi karatunki batare da fargaban komai ba.

zarah murmushi tayi tace nagode sosai khairy Allah dai yasa zan iya.

khairy tace Ameen.
kiran khairy da akayine yasa tamik'e tanufi filin tazauna bisa kujerar da aka tanadar masu nan aka mik'a mata lasifika tafara karatu.

tunda aka kira khairy zarah hankalinta ya tashi sosai nan gabanta yashiga fad'uwa, addu'a tashiga yi cikin zuciyanta ahankali taji nutsuwa tazo mata.

bayan khairy ta gama kiran sunan zarah aka yi,  k'in tashi zarah tayi saida aka maimata kiranta sannan tamik'e ahankali tana tafiyarta a nutse,  duk wanda yake wajen kallonta yakeyi yanayin yadda take takunta a nutse ta sadda kanta a k'asa ahaka ta isa filin taron tazauna, nan aka mik'o mata lasifika.

amsa tayi nan tad'anyi shuru na d'an minti biyu saida tasaita nutsuwarta sannan tafara karatun cikin muryarta mai dad'in saurare inda take karanta suratul bak'ara daga izif na ukku _Sayak'ulus-sufaha'u minan-nasi ma wallahum ank'iblata humullazi kanu alaiha_...... cike da nutsuwa take karatun, wajen yad'auki tsit kowa saurarenta yakeyi, yarima suhail tunda aka fara bai d'ago yakalli kowaba ammah lokacin da zarah tafara ji yayi yanason ganin wadda ta mallaki muryar,  ahankali yad'ago kansa yasafke idonsa akan zarah da take karatu a nitse, kallo d'aya yayi mata yajanye kansa bai k'ara kallontaba har tagama sannan tamik'a lasifikar tare da mik'ewa tabar wajen.

gaba d'aya aka d'auki kabbara daga nan aka cigaba da kiran saura suna fitowa sunayi har aka gama.

bayan angama aka kira wasu daga cikin d'alibai sukayi drama ta larabci,  da suka gama aka kira zarah tayi tafsirul alk'ur'ani kowa na wajen ya jinjina mata,  da tagama nan aka d'auki kabbara, yarima suhail magana yayi ma iyayensa sannan yasa aka kira masa shugaban makarantar yadamk'a masa kud'i daganan yawuce yashiga motarsa yabar wajen.

daga bisani aka fara raba kyautukan da aka tanadar ma wad'anda sukayi walimar.

ko da akazo kan zarah, Sultana Bilkisu ce akakira tazo tabata itama ta azamata kyauta ta musamman sannan akayi musu pic's.

zarah har da k'wallarta ganin kyautukan da tasamu dan ko na makaranta kusan guda ukku tasamu sannan wanda mutane sukayi mata.

bayan angama raba kyautuka nan akayi d'an bayani sannan aka rufe taro da addu'a aka fara watsewa,

sultana bilkisu kallon d'aya daga cikin kuyanginta tayi tace taje tatafo mata da zarah,

ko da taje tafad'ama zarah zarah bata musaba tabiyota.

tun da suka tafo sultana bilkisu tazuba mata ido ganin yadda take tafiya a nutse har suka iso nan zarah taduk'a ta gaishesu, cike da fara'a Sultan Ahmad da Sultana Bilkisu suka amsa mata, sultana tace 'yanmata ya sunanki?
ahankali tace zarah,
sultana tace nice name,  nan sultan Ahmad yad'auko 50k yabata.

cike da ladabi zarah ta amsa tare da yi masu godia sannan tawuce tabar wajen itadai Sultana Bilkisu binta kawai take daga kallo daga bisani suka tashi suka koma gida.

Zarah tattara mutanenta tayi tatafi dasu gisansu tabasu abinci na musamman sannan taraba musu kayan da tatanada,  ita kanta ta jinjina ma 'yan gidansu ganin namijin k'ok'arin da sukayi dan sufitar da ita kunya,  bayan anci ansha nan aka watse kowa yana murna.

nan zarah tad'auko kyautukan da tasamu taba iyayenta nan aka bud'e ana gani ana murna,  kud'in da tasamu tadamk'a ma iyayenta rabi,  sauran taraba taba 'yan uwanta rabi tad'auki sauran rabin,  nan sukayi ta mata godia,

___________

Sultana Bilkisu ce zaune gefen Sultan Ahmad suna hira chan ta nisa tace Daddyn suhail wlh walimar da mukaje ta burgeni da alama makarantar akwai karatu sosai.

murmushi sultan Ahmad yayi yace nima ta burgeni sosai

sultana bilkisu tace ka san wani abu wlh yarinyarnan ta yi min sosai,

sultan murmushi yayi yace ai naga alama saisa kika aika aka kiramiki ita,

sultana bilkisu d'an guntun murmushi tayi tace inama yarima ya amince ya aureta, wlh da naji dad'i domin daga ganinta kasan ta fito daga gidan mutunci wlh inason yarinyar takasance surukata,  kallon sultan Ahmad tayi taga yana ta dannar remote yana canza channel, hannu takai taruk'o remote d'in nan yajuyo yakalleta kwallah duk ta cika mata ido.

sultana bilkisu murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo tace daddyn suhail nasan sumayya d'iyar d'an uwankace ammah kataimaka ka amince da yarima ya auri zarah domin inaji ita alkhairi ce, ina ji ajikina aurenta zaisa yarima yasamu nutsuwa da kwanciyar hankali.

sultan Ahmad rik'e hannun sultana yayi yace Bilkisu ba wai na k'i bin maganarkibane kawai dai ina tsoron abinda zaije yadawo,  kina tunanin suhail zai amince yasota?  kina tunanin su memartaba zasu aminta da hakan?

murmushi sultana bilkisu tayi tace insha Allahu zasu amince yarima bamuda matsala da shi domin mu muka haifesa,  indai su memartaba sun amince toh komai ya yi daidai, kabani izini inje gidansu yarinyar mugana da iyayenta inyaso daga baya sai muyi tunanin yadda zamu 6ullo ma lamarin.

dogon numfashi sultan Ahmad yaja yace toh tayaya kike tunanin zasu amince batare da ansha wuyaba?

murmushi sultana tayi tace kafara bani izini inje gidansu yarinyar ingana da iyayenta, muji idan zasu amince mana subamu aurenta.

shima sultan murmushi yayi yace nabaki izini Allah dai yashige mana gaba.

cike da jin dad'i sultana tace Ameen.


_*BAYAN SATI 'DAYA*_

Sultana Bilkisu ce naga tayi shiga ta alfarma ta yi kyau sosai bayanta kuyangi biyar ne suka take mata baya,  wajen wata dank'areriyar mota daga cikin jerin motocin ukku da take tsakiya naga ta nufa tunkan ta isa aka bud'e mata baya, dan haka tana shiga aka maida aka rufe.

kuyanginta d'ayar motar suka shiga nan aka tada motar, dasauri maigadi yahangame musu k'aton gate d'in suka fita daga Amir palace.

bayan 'yan mintina suka isa islamiyyarsu zarah, 

a mota sultana bilkisu tazauna tatura dogari yaje yayi mata magana da shugaban makarantar.

bayan kamar minti ukku sai ga dogarin ya fito bayansa shugaban makarantane yana ta zuba sauri.

duk'awa yayi yana gaishe da sultana bilkisu cike da fara'a ta amsa, nan kuyangi da dogarawa suka d'auka sultana ta amsa gaisuwarka kaima angaisheka,
sannan sultana tace inason k'arin bayani akan d'alibarku mai suna zarah musa.

dasauri d'aya daga cikin dogarawan yace sultana tanason sanin wacece ita, ina ne gidansu.

shugaban makaranta washe baki yayi yace toh toh zarah musa ai gidansu yana chan gaba da nan kad'an.

sultana bilkisu signal tayi ma driver da ido.

driver yace yimin kwatancen gidan yadda zan gane,  nan shugaba yayi masa kwatance saida yafahimta sannan yaduk'a yace angama ranki yadad'e

sultana bilkisu kallon kuyanga tayi tace tamik'o mata jakkarta, dasauri kuyanga tamik'o mata nan sultana tad'auko bandir d'in 'yan 1k tamik'a masa tace ga wannan kun k'ara wajen hidima.

jikin shugaba yana kyarma ya amsa tare da duk'awa yana godia nan suma dogarawa suka hau yi ma sultana godia.

sultana izini tabada aka tayar da motar suka kama hanyar gidansu zarah.

ko da suka isa driver tsayawa yayi yatambayi wasu matasa da suke zaune a majalisa, basusha wahalar gane wadda yake nufiba kasancewar kusan kullum zarah ta gabansu take wucewa taje islamiyya kuma tadawo, sukace yak'ara gaba kad'an yashiga hannunsa na dama gida na ukku, nan yayi musu godia sannan sukacigaba da tafiya.

A k'ofar gidansu zarah yayi parking, daidai lokacin malam musa ya dawo gida,  ganin dank'areriyar mota k'ofar gidansa yasa mamaki yacikasa dasauri ya ida isowa, daidai lokacin driver yafito daga motar, malam musa sallama yayi mashi yace wani gida kuke nemane?

driver yace eh gidan su wata zarah musa.

malam musa yace toh toh ai nan ne nine mahaifinta.

driver zuwa yayi daga bayan mota yayi knocking d'in glass d'in, jin knocking yasa sultana bilkisu tawane glass d'in.

driver duk'awa yayi yace ranki yadad'e nan ne ga ma mahaifinta nan.

sultana bilkisu kallon mahaifin zarah tayi dasauri shima yaduk'a yagaisheta domin yanayinta kawai da yagani da dogarawan da suke tare da ita yasa yagane daga babban gida take.

sultana bilkisu cike da fara'a ta amsa.

malam musa yace ranki yadad'e ko dai wata zarah d'in ce kuke nema?

murmushi sultana tayi tace zarah dai taka, munaso kayi mana izini mushiga ciki sai mutattauna abinda yake tafe da ni.

malam musa jikinsa yana 6ari yace bismillah kushigo,
dasauri dogarawa sukazo suka bud'e mata murfin motar tafito nan kuyangi suka take mata baya, akabar dogarawa tsaye wajen motocinsu,

malam musa yana gaba har cikin gida, suna shiga yafara k'walama mama kira yana zainabu!  zainabu!!

dasauri mama tafito daga d'aki tana malam lafiya? ganinsa tare da wasu mata yasa tayi tsaye tana malam bak'i mukayi?

malam musa yace kinyi wani tsaye kiyi sauri kid'auko musu tabarma mana, ina yarannan suke? .

mama tace basunan sunje gidan kitso sannan  takoma d'aki tad'auko sabuwar tabarma tazo ta shimfid'a tace bismillanku.

sultana zuwa tayi zata zauna dasauri kuyanginta suka k'ara kakkafe tabarmar suna cewa ranki yadad'e azauna lafiya sarauniya, bayan ta zauna nan kuyanginta sukayi tsaye gefenta.

ganin haka yasa su mama suka ida fahimtar koma daga ina wannan tafito toh motar wani babbace, Dan haka mama tazo taduk'a tagaisheta.

fuskar sultana d'auke da murmushi ta amsa,  nan kuyangi suka d'auka 'sultana ta amsa gaisuwarki kema angaisheki'

malam musa jikinsa yana 6ari yace bari inje insamo musu ruwa susha.

sultana murmushi tayi tace kabarsa nagode kazauna kawai muyi magana akan abinda yakawoni.

dasauri mama taje tad'auko wata tabarmar tashimfid'a ita da malam musa suka zauna.

sultana kallon kuyanginta tayi tace mero kubamu waje zamuyi magana.

dasauri duk suka zube sukace angaisheki sultana atashi lafiya sannan suka tashi suka bar wajen.

sultana kallonta tamaida ga su malam musa tace kune iyayen zarah ko?

malam musa da mama sukace eh ranki yadad'e .

sultana bilkisu tace toh Alhmdllh ni matace ga d'an sarkin garin nan, agaskiya ba zan 6oye mukuba tun lokacin da mukaga d'iyarku wajen walimarsu da sukayi a islamiyya nan muka ganta kuma mun yaba da halinta da tarbiyarta dan haka muke neman ma d'anmu *yarima suhail* aurenta.

ba mamaba hatta shi kansa malam musa ya firgita a tsorace suka d'ago kai suka kalli juna jin an anbaci yarima suhail Wanda suke jin sunansa a bakin mutane, dasauri suka maida kallonsu ga sultana bilkisu,
atare suka had'a baki sukace zarah ta auri yarima suhail?

sultana gyad'a kai tayi tace indai kun amince zaku bamu aurenta.

shuru sukayi na d'an lokaci sannan malam musa yace ranki yadad'e kiyi hak'uri gaskiya ba zamu iya amincema  buk'atarkiba.......

_*Comments d'inku shine k'warin gwiwana Indai babu more comments toh hakan zai tabbatar min da baku tare da ni dan haka nima zan dakata da rubutawa daga wannan page d'in, dan haka muje zuwa*_



_Comments_
      *nd*
_Share_





_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_*Jinjina agareki My Dala inaso kisani akoda yaushe ina ji dake😘*_

_Sak'on gaisuwa agareka *Mu'az* a duk inda ka kasance wannan *page* d'in mallakinkane kayi yadda kakeso da shi nagode sosai da kulawa_

page 1⃣5⃣

Malam musa yace gaskiya ba zamu iya amincewa da buk'atarkiba domin kunfi k'arfinmu ku masu kud'ine mu kuma talakkawane, kinga ba zaiyuwuba ace masu sarauta kamarku sun had'a zuri'a da muba.

sultana bilkisu tace kar kudamu ai anzama d'aya kar kumance da talakka da maikud'i duk Allah ne ya haliccesu kuma shi yakeba Wanda yaso yahana wanda yaso, jahiline kawai zai iya gudun talakka, ammah duk wanda yasan abinda yakeyi toh ba zai gujesaba domin yasan wake azurtawa da hanawa,  a lokaci guda Allah zai iya maida talakka mawadaci sannan yamaida mawadaci talakka, toh tayaya kuke tunanin zamu gujeku? saidai idan kuna tunanin d'iyarkune kar mucutar da itane, insha Allahu ba zamu nuna banbanciba zamu kula da ita kamar yadda zamu kula da 'ya'yanmu da muka haifa a cikinmu, burina kutaimaka ku amince kubamu auren zarah.
mu musulmaine munsan girman alk'awali dan haka nayi muku alk'awali zamu kula da ita bakin gwalgwado.

gaba d'ayansu shuru sukayi suna saurarenta,  yanayin yadda sultana tayi maganar yasa suka yadda da ita, kuma sunsan adalci da kirki irin na sarkin garin indai shi zuri'arsa suka biyo mutunci toh ba zasu samu matsalaba.

chan Abbah yakalli mama yace tataso suje suyi shawara dan haka mama tatashi suka shiga d'aki suka bar sultana zaune wajen tana dannar waya, 

a chan d'akin abbah yakalli mama yace zainabu abun nan yad'aure min kai kina ganin zai yuwu mubasu d'iyarmu? nifa ina tsoron su wulak'anta mana ita domin su masu arzikine mukuma talakkawa.

mama jinjina kai tayi tace nima abinda nake tunani kenan gaskiya kar mubasu domin bamusan yadda gaba zata kasanceba, ace duk matan garin nan surasa wadda zasuce sai zarah, so suke sujamana zagi da surutun mutanen gari.

malam musa jinjina kai yayi yace ni bama dai wannan ba kiduba kiga bayanin da tayi mana tabbas daga gani tasan daraja da mutuncin mutane daga jin kalamanta, ta ni bandamu da surutan mutaneba saidai inajin tsoron su  wulak'antamin zarah domin yarima suhail ya wuce ajin zarah wajen komai, ammah kuma ina jin nauyinta bana iya hanasu zarah.

ummah tace hakane malam ko dan matsayin da darajar da ke garesu kaduba kaga bata nuna mana k'yamaba nima wlh ta wajena babu matsala domin halayyarta ta yi min kuma nasan indai d'antane takeson hadawa da zarah toh bamuda matsala saboda da alama zai kasance mai irin kyawawan halinsu saidai ba a nan takeba matsalar tana wajen zarah.

malam musa jinjina kai yayi yace tabbas zarah itace matsalar ina tsoron taki amincewa saidai nasan zarah akwai biyayya zata iya bin ra'ayinmu ko da ace bataso, dan haka idan kinga hakan ba matsala toh muje mu amsa mata,

mama tace toh nan tabi bayan malam musa suka fito, yadda sukabar sultana haka suka dawo suka taddata, suka koma mazauninsu suka zauna.

kallonsu sultana tayi tace dafatan kun yanke hukuncin da kuke ganin ya dace wlh Indai baku aminceba zamu iya hak'ura domin ta yuwu zarah ba matarsa bace.

malam musa yace ranki yadad'e mun ma amince domin darajarki da martabanku yasa bama iya ji zamu iya hanaku zarah fatanmu dai zaku rik'eta kukular mana da ita tsakani ga Allah.

sultana bilkisu tunda taji ya ambaci sun amince wani irin farinciki yakamata kasa 6oye murnarta tayi tace gaskiya naji dad'i kuma nagode sosai insha Allahu zamu kular muku da ita, sannan zanje muyi magana da iyayensa koma dai mekenan zamuyi waya, takalli mama tace bani number d'in wayanki nan mama takaranto mata sannan sultana bilkisu takira kuyanginta suka dawo, fuskarta d'auke da fara'a tace naso ace naga d'iyartawa ammah tunda batanan zamu had'u wani lokacin.

mama tace a'a ranki yadad'e ai sai inje inkirata tana chan bayan layin nan sunje kitso,  sultana tace a'a kibarta kawai zamu gaisa wani lokacin, kar6ar jakkarta tayi a wajen d'aya daga cikin kuyanginta tazaro 100k ta aje musu sannan tamik'e tace bari inwuce.

Abbah yace a'a kibar kud'inki mu dan Allah mukayi.

sultana murmushi tayi tace karkadamu nima dan Allah nayi domin babu kud'in da zasu iya sayan zarah, kuyi hak'uri kyautace.

Abbah da mama sukayi godia, har wajen mota suka rakata saida sukaga tafiyarta sannan suka dawo cike da farin ciki.

Mama kallon Abbah tayi tace malam toh yanzu ya kake ganin za'ayi idan zarah tadawo?  kana tunanin zata amince?

Abbah murmushi yayi yace kar kidamu kibar komai a hannuna.

mama tace toh Allah yashige mana gaba.
Abbah yace Ameen.

daidai lokacin su zarah suka shigo gidan suna dariya, mama da Abbah kallon juna sukayi sannan suka maida kallonsu ga 'ya'yan nasu suna murmushi,  su zarah isowa sukayi tare da duk'awa sukayi ma iyayennasu barka da rana,  mama tace 'yan albarka har kunyo kitson?

sukace eh mama, gaba d'ayansu suka mik'e zasubar wajen, abbah yace kudawo kuzauna munason magana da ku.

A tare suka zauna suna jiran Jin abinda iyayennasu zasu ce, Abbah ne yayi gyaran murya yace duk inda kuka tsinci kanku kukasance masu dogaro ga Allah, kurik'e gaskiya sannan duk mijin da Allah yaza6a muku kukar6esa hannu biyu domin ita rayuwa ta yuwu abinda mukeso ba alkhairi bane wanda bamuso zai iya kasancewa shine mafi alkhairi, gaba d'ayansu shuru sukayi suna sauraren mahaifin nasu da suka kasa gane dalilinsa nayi musu wannan nasihar,

mamace tacigaba da cewa ku 'ya'ya matane ba zaku dauwama a k'ark'ashinmu ba wata rana dole kubarmu kukoma k'ark'ashin mijinku a kullum addu'anmu Allah yahad'aku da mazaje nagari kuyi aure.

Abbah yace tabbas zancenki hakane zainabu sannan yamaida kallonsa ga zarah yace saidai kuyi hak'uri domin munyi wani karambani a matsayinmu na iyayenku munyi abinda muke gani kamar daidaine saidai a wajenku bansan yadda zaku d'aukesaba musammanma ke zarah!

gaba d'ayansu mamakine yacikasu sun ma rasa gane inda zancen abbah yanufa,  zarah ce ta nisa tace Abbah bana tunanin akwai abinda zakuyimin yazama laifi wlh duk hukuncin da kuka d'auka kaina daidaine domin kun cancanci hakan.

Abbah dogon numfashi yaja yace hakane zarah ammah kiyi hak'uri da maganar da zata fito daga bakina, zarah munyi miki miji.

zarah a razane tad'ago kai takalli abbah muryanta yana kyarma tace abbah miji kuma?  Aysha da Rauda sukace miji!!!

Abbah gyad'a kai yayi cikin rashin damuwa yace tabbas miji kuma nasan zaki sosa kema bakowa bane face d'an sarkin garinnan *Yarima Suhail*

zarah a tsorace tamik'e tsaye tare da ja baya tace abbah aura min wani zakayi ba malam bello ba?

Abbah yace zarah kidawo kuzauna inyi muku bayanin komai,

zarah hawaye tafara tare da dawowa tazauna,  nan abbah da mama suka kwashe labarin zuwan sultana bilkisu da yadda sukayi da ita babu abinda suka 6oye masu hatta kud'in da tabasu.

Zarah fashewa tayi da kuka tace Abbah kuyi hak'uri wlh bana sonsa shima nasan ba zai soniba dan Allah kubarni in auri wanda nakeso wlh malam bello shine za6ina.

Aysha da Rauda murmushi sukayi suna jin wani irin dad'i a ransu.

mama ce tace haba zarah ya kamata kid'auki k'addara muma ba a son ranmu hakan takasanceba dan dai babu yadda zamuyine kinga ba zamuk'i amincemataba tunda har tazo gida tanemi alfarmarmu.

Zarah mik'ewa tayi tsaye tana kallon iyayen nata tana girgiza kai,  cikin kuka tace kawai dai kuce kun siyar da ni, yanzu kud'i zasusa kubayar da ni?  bakwa tsoron suwulak'antani? wlh bana sonsa kuma ba zan ta6a sonsaba inma dan kud'insu yasa kukayi min haka toh wlh saidai kumaida musu kud'insu domin ban aminceba, ni malam bello zan aura.

Yaya Rauda tace zarah wai minene haka kikeyi?

zarah cikin d'aga murya tace kubarni yaya rauda ba zan ta6a amincewa ba.

Aysha tace yaya zarah su abbah fa kike d'aga ma murya.

Zarah dasauri tatoshe bakinta da hannuwanta tana girgiza kai tace kugafarce ba zan iyaba,  tana gama fad'in haka tashek'a da gudu tashige d'aki tafad'a saman katifarsu tana wani irin kuka saikace wadda aka aikoma da sak'on mutuwa.

gaba d'ayansu jikinsu yayi sanyi musammanma su Abbah da mama da basu d'auka abun zaiyi zafi hakaba.

Rauda ce takalli iyayennasu tace Abbah kuyi hak'uri 6acin rai ne yasa zarah tayi haka ammah ai tana da sanyi natabbata zata sauko daga fushin da take.

mama tace kar kudamu nasan halin d'iyata ni zan shawo kanta da kaina.

Abbah dai girgiza kai yayi takaici duk ya cikasa

Aysha ce tace Abbah kayi hak'uri zata safko yanzu tad'auki zafine saisa,  ammah fa naji dad'i da zata auri yarima wlh ya had'u sai ma da nagansa a wajen safkarsu.

Rauda tace wlh kau ni har nahango sunyi match sosai,  cike da murya Aysha tace yayata zata zama *Gimbiya Zarah* matar *Yarima Suhail* dak'uwa mama tayi mata tace gidanku munaso murarrasheta tasafko sai kinja ta jiyoki.

Aysha cike da farin ciki tarik'e bakinta da hannu tace afwan na daina.

mama kallon Abbah tayi tace malam kar kadamu insha Allahu Zarah zata safko ni zanma je na lallasheta har tafahimcemu.

malam murmushi yayi yace toh Allah yasa tafahimta inma dai bata aminceba zan fasa basu domin ba zanyi mata doleba, duk yadda kukayi da ita sai kufad'amin yanzu dai bari intashi infita koma mekenan sai nadawo

gaba d'ayansu sukace adawo lafiya.

bayan Abbah ya fita Rauda kallon mama tayi tayamutsa fuska tace mama yau naman kaza nakeson ci,  murmushi mama tayi tace Rauda kin cika kwad'ayi tashi ga 1,500k kuje wajen dauda mai kaji yayanka yafige sai kuzo kuyi mana pepper kowa yaci.

Rauda cike da jin dad'i tace toh mama yanzu ko zamuje muna godia.

Aysha ma cikin murna tace Allah yabarmana ke maman gimbiya.

Mama duka takaima Aysha tagoce suna dariya ita da rauda,  mama tace sai naci gidanku inbakuyi wasaba.

mik'ewa mama tayi tace kuyi sauri kuje kudawo ni bari inshiga wajen d'iyata in rarrasheta.

mama ko da tashiga lokacin zarah ta ci kukanta, kwance take kanta yana kallon ceiling d'in d'akin hawaye kawai suke zuba ta gefen idonta, mama gefen inda zarah take kwance tazauna tana mai k'arema zarah kallo da duk idanuwanta sun kumbura.

A hankali mama tace zarah kuka kikeyi ko?  shuru zarah tayi batace komaiba, mama cigaba tayi da cewa kiyi hak'uri zarah wlh muma ba'a son ranmu hakan takasanceba dan dai babu yadda zamuyi mubijire ma buk'atarta domin yadda tazo ta aje girma da matsayinta tana rok'onmu mu amince mata muba d'ansu aurenki,  hmm zarah munsan zakiyi tunanin ko k'wad'ayine yasa mukayi miki haka ammah wlh ba haka bane *k'addara ce* kawai, domin kowane iyaye suna burin ganin farin cikin 'ya'yansu koya suke suna son ganin farin cikin yaransu ko da ace zai tauye nasu farin cikin,  canzawar yanayinki yasa abbanki ya ji ba dad'i domin har ya fara tunanin yaje da kansa yafad'a musu ya fasa badake, domin kowane iyaye suna burin ganin 'ya'yansu sun auri mijin da yacancanta mutumin da zai kular masu da 'ya, wanda yake sonta kuma danginsa suma suna sonta.

zarah lumshe idanuwanta tayi hawaye suna zuba tana jin wani iri a ranta, mama cigaba tayi da cewa saidai mu kuskuren da mukayi a baya har yanzu akwai sauran tabonsa bai warkeba a zuciyan zarah,  zarah har yanzu kallonmu take a matsayin kwad'ayayyun iyaye,  idan barinki ki auri wanda kikeso zaisa kigane cewa ba dukiyarsu muke k'wad'ayiba toh mun amince kije ki auri bello domin shima mutumin kirkine saboda farin cikinki shine namu fatanmu kigane cewa tuni iyayenki sunbar wacchan rayuwar da sukayi a baya,  ko da ace za'a kallemu a matsayin k'ananun mutane masu magana biyu toh bazamu damuba saboda munfi buk'atar naku farin cikin.

zarah dasauri tatashi tarungume mama tare da fashewa da sabon kuka tace mama kuyafemin wlh ba haka nake nufiba, na amince da za6inku bana fatan ayi ma iyayena kallon marassa cika alk'awali koda ace zan mutu toh nagwammace inmutu ta dalilin faranta ma iyayena rai, tabbas nasan bazaku ta6a yimin za6in da zai cutar da ni ba wlh na hak'ura da malam bello wanda kuka za6amin shine zan aura,  tana kaiwa nan tasake fashewa da kuka tace mama kuyafemin.

mama ma hawaye takeyi cike da tausayin d'iyartasu tace zarah bakiyi mana komai ba saima mu da mukayi miki.

zarah girgiza kai tayi tace mama kidaina cewa haka duk abinda kuka yanke akaina daidaine kuma cancanta da matsayine sukaja hakan.

mama rungume d'iyarta tayi tana hawaye tausayin zarah duk ya kamata, lallashin zarah tashiga yi har saida taga tayi shuru.

zarah mik'ewa tayi tace bari inje inba baba hak'uri nasan fushi yake da ni,  mama tace ai baya nan ya fita.

zarah komawa tayi tazauna tace toh idan ya dawo zan je.

Mama murmushi tayi tace Allah yayi miki albarka zarah wlh kin cika d'iyar kirki,  Allah yayi muku albarka gaba d'ayanku.

Zarah murmushi tayi tace Ameen mama.

Mama mik'ewa tayi tace bari inje  nasan yanzu su Rauda zasu dawo

zarah batace komai ba, tana ganin mama ta fita yasa tatashi tashige toilet tare maida k'ofa tarufe anan tafashe da sabon kuka mai tsuma zuciya duk tausayin kanta da na malam bello yakamata domin tasan so d'ayane yakeyi mata batasan yadda zai fahimci maganarba idan taje masa da ita, saida taci kuka mai isarta sannan tawanke fuskarta tare da tad'auro alwallar magrib  tashinfid'a darduma tad'auko alk'ur'ani tana karantawa domin samun sauk'in abinda takeji a ranta.




Bayan sallar isha'i zarah zaune tayi a d'akinsu har lokacin fuskarta babu walwala duk yadda su Rauda sukaso tasaki jiki ammah ta k'i, abincima dakyar tad'anci kad'an.

wajen k'arfe takwas tanajin dawowar Abbah saida tadaidaici daidai lokacin da yagama cin abinci sannan tataso tanufi d'akinsa jikinta a sanyaye tayi sallama.

Abbah da yake zaune hannunsa rik'e da redio yana sauraren labarai amsa mata sallamar yayi tare da rage k'arar redion.

Zarah shigowa tayi taduk'a k'asa muryarta tana rawa tace Abbah dan Allah kayafe min abinda nayi maka wlh na amince zan auri za6inku domin nasan ba zaku ta6a cutar da rayuwataba duk hukuncin da zaku zartas akanmu daidai ne burinku a koda yaushe kuga farin cikinmu, wlh akoda yaushe ashirye nake da incika umurninku domin 6acin ranku daidai yake da rugujewar farin cikina.

Abbah murmushi yayi cike da jin dad'in maganar zarah yace wlh zarah bakiyimin komai ba, indai baki sonsa kifad'a min wlh bazanyi miki doleba zan aura miki wanda kikeso domin farin cikinki nafi buk'ata.

zarah girgiza kai tayi tace Abbah wlh wanda kaza6amin shi nakeso ashirye nake a koda yaushe in amshi za6inka.

Abbah kasa 6oye farin cikinsa yayi yace nagode sosai zarah Allah yayi miki albarka kema Allah yabaki wad'anda zasuso farin cikinki,  insha Allahu wannan auren zakiji dad'insa, Allah yayi muku Albarka gaba d'ayanku, zarah cike da jin dad'in addu'an da abbah yayi musu tace Ameen Abbana nagode sosai.





Zarah tunda takwanta kasa bacci tayi juyi kawai take abin duniya duk ya isheta tana tunanin yadda za'ayi ta auri wanda bata so,  tunowa tayi da yarima suhail lokacin da yazo walimarsu yadda yake shan k'amshi, ba ya ma kallon kowa, tsaki taja tace wannan d'an jin kan zan aura,  hawaye ne suka zubo mata tunawa da tayi da malam bello ta yaya zata fuskancesa da maganar zata auri wani ba shiba batasan yadda zai fahimci maganarba,  tana ta sak'e-sak'e a ranta a haka bacci yayi awon gaba da ita batare da tashirya yinsaba........




_Comments_
       *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
?👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Yau page d'in nakune k'annena nakaina *JANAF nd SAFIYYA ALIYU* inaso kusani ina sonku irin totally d'innan Allah yabarmu tare😘_

Page 1⃣6⃣

Sultana Bilkisu ko da takoma gida cike da farin ciki tasamu Sultan Ahmad take bayyana masa yadda sukayi da iyayen zarah, shima farin cikinsa yanuna a fili yace gaskiya naji dad'i ammah kuma ba'a nan takeba,

murmushi sultana tayi tace nasan kana tunanin matsalar da zamu fuskantane wajensu memartaba da yarima?

Sultan Ahmad shima murmushi yayi yace tabbas hakane ammah Insha Alkahu komai zaizo da sauk'i kibani lokaci nima inyi tunanin yadda zamu 6ulloma lamarin domin maganar nan tana buk'atar tunani mai zurfi a cikinta.

Sultana Bilkisu Cike da damuwa tajinjina kai tace hakane nima zanje inyi tunani domin musamo mafita.

Sultan Ahmad tausayin matarsa yakamasa domin yasan yadda take son d'an nata, yace kidaina damuwa indai Allah ya k'addara akwai aure tsakaninsu toh za'ayi inkuma babu toh hak'uri zamuyi domin wani baya auren matar wani fatanmu dai Allah yashige mana gaba.

Sultana Bilkisu cike da gamsuwa da maganar mijin nata tace Ameen.



Gimbiya sumayya duk yadda taso tadaure kar tabada kanta ga yarima ammah kasawa tayi a daddafe tayi kwana biyu.

bayan sallar la'asar shiryawa tayi sosai tafito tanufi 6angaren yarima tana shirin shiga sai gashi ya fito da alamu fita zaiyi, kallo d'aya yayi mata yad'auke kai yana shirin ra6awa ta gefenta yawuce dasauri Gimbiya Sumayya tasha gabansa tace haba yarima wajenka fa nazo.

fuskar yarima babu alamun fara'a yace me zanyi miki?

Gimbiya kallonta takai ga dogarawansa da guards d'insa da duk kansu yake sunkuye suna jiran ogan nasu, ga kuyanginta da suke bayanta tsaye, kallonta tamaida ga yarima tace am daman, nan tafara kame-kame tace ko dai zamu shiga...... Yarima hannu yad'aga mata yace whatever ma dai  you should meet me later, bai jira jin abinda zataceba yawuce dogarawan da guards d'insa suka take masa baya.

Gimbiya sumayya takaici duk yacikata ganin yadda yarima yadisgata gaban guards d'insa hararar kuyanginta tayi da kansu yake sadde a k'asa tacemunafukai kun zuba min na mujiya duk sai nad'au mataki a kanku.

dasauri duk suka zube k'asa suna cewa Allah yahuci zuciyar gimbiya, Allah yaja da ran gimbiya.

wucewa tayi fuu dasauri suka tashi suka take mata baya sunayi mata kirari.

ko da takoma part d'inta saman gadonta tafad'a tare da dafe kanta tsaki taja tace wannan mutumin bansan irinsaba anya yarima bai fara bin mataba? ya za'ayi yad'auki tsawon wannan lokacin batare da maceba? gabantane yashiga fad'uwa cikin d'aga murya tace No! i dont think yarimana akwai macen da zai iya kulawa wlh ba halinsa bane, chan takaima katifa bugu da hannunta tace inma akwai zan bincika domin nasan yarima baya iya kai tsawon wannan lokacin without ya yi making sex da niba ko da ace bana so, inma har naga akwai wadda yake tare da ita toh wlh ba zan bartaba sai na kasheta!!! 

wayarta tajawo takira zinat bugu biyu tad'auka, muryar sumayya tana rawa tace wai ke zinat yaushe zaki dawo k'asarnan?

dariya zinat tayi tace kinyi missing d'ina ko? 
tsaki sumayya tayi tace ke ni tambayarki nake.

zinat murmushi tayi tace Allah yahuci ran gimbiyar yarima very soon zan dawo nima ai nayi missing d'in k'asata.

Sumayya tace hmm Allah yasa dagaske kike, nidai in kindawo kifara biyowa ta wajena.

'yar dariya zinat tayi tace sai kin ganni, sumayya dai badan ta yadda da maganar zinat ba takashe wayanta tare da komawa takwanta tana sak'e-sak'e cikin ranta.


Da daddare ganin ta kasa bacci yasa tamik'e tajawo alk'yabbarta tad'aura saman kayan baccinta tafito batare da ta nemi rakiyar kowaba tanufi 6angaren yarima addu'a take Allah yasa kar yadisgata domin ita tasan yau duk wulak'ancin da zaiyi mata ba zata damuba Indai zai biya mata buk'atarta inyaso daga baya sai tarama.

lokacin da tashiga ganin yarima baya parlour yasa direct tanufi bedroom d'insa,  tsakiyan gadon tahangosa kwance idanuwansa a lumshe,  cikin ranta tace lallai ma  bacci yake

ahankali tataka tanufi gadon tahau takwanta a saman jikin yarima, muryarsa taji yace me kike buk'ata?

dasauri tad'ago kai takalli fuskarsa har a lokacin idanuwansa a lumshe suke ita tayi azan bacci yake,  komawa tayi takwanta tace zuwa nayi intayaka bacci.

yarima dakyar yabud'e idonsa yasafkesu akan fuskarta yace sumayya kitafi kawai daman ai bake ketayani baccin ba saidai idan akwai abinda kike buk'ata.

Sumayya tallabo fuskar yarima tayi tace dear ni bacci kawai nazo muyi.

yarima janyeta yayi daga jikinsa yace ohk muyi baccin.

takaici yakama sumayya ganin yadda yake faujewa kamar bai fahimci abinda take nufiba,  komawa tayi jikinsa tace wai yarima meyasa kakemin haka?

yarima kallonta yayi yace me nayi miki?

Shagwa6e fuska tayi tace naga yanzu kamar ka daina buk'atata, ka ma fita harkata, baka kula da ni bakasan yadda nake kwana nake tashiba baka tsoron hak'in aure?

yarima wata muguwar harara yawurga mata yace sumayya ashe kinsan hak'in aure?  murmushin takaici yayi yace ammah ni kike tauyemin hak'ina.

sumayya haushine yakamata ganin yadda yarima yake neman wulak'antata cikin ranta tace kayi kagama ba zan damuba tunda ni nakawo kaina.

shafa sajensa tayi tace sweetheart yanzu dai shikenan na amshi laifina, yanzu kafad'i abinda kakeso zanyi maka.

yarima shuru yayi yakyaleta, marairaicewa sumayya tayi tace kayi magana mana.

Yarima murmushi yayi yace da zaki taimaka kibarni inyi bacci da nafi buk'atar hakan.

haushine yakama sumayya domin bata d'auka haka zaice mataba, ganin yadda tayi kicinkicin da fuska abun yaso yabashi dariya ammah yadake yace ya dai?

Sumayya d'auke kai tayi daga kallonsa tace suhail yanzu naga kamar ka daina buk'atata ko kasamu watane?

murmushi yarima yayi domin ya gano inda gimbiya tanufa yace Sumayya akanme zanta bibiyarki aini yanzu jikinki bai dameniba please kikyaleni ina buk'atar hutawa yanzu kinsan bana son yawan magana.

Sumayya fashewa tayi da kuka tace Suhail kaji tsoron Allah hak'ina fa? idan kai baka buk'atata nifa?

yarima d'aure fuska yayi yace ai banga alamun kina buk'ataba ni hak'ina nawa kika tauye?

gimbiya cikin kuka tace toh wlh ba zan yaddaba nidai nace kayi hak'uri.

Yarima cike da rashin damuwa yace shikenan naji zan taimaka miki,  idan kin shirya toh bismillah.

Sumayya dai haka tabiyema yarima wulak'anci iri-iri yayi mata ammah lalla6asa tayi itadai burinta ya yabiya mata buk'atarta.

bayan komai ya lafa yarima tashi yayi yaje yayi wanka yazo yakwanta Sumayya mirginawa tayi jikinsa zata kwanta dasauri yarima yatureta yace kar kisaki kira6eni batare da kin tsarkake jikinkiba.

takaici yakama sumayya takoma gefe takwanta domin ita batayi shirin wanka yanzuba sai da asuba, cikin ranta tace yanzu ko zan fara rama wulak'ancin da kayi min.

da asuba saida yayo alwallah sannan yatadata dakyar tatashi saida yaga ta mik'e sannan yawuce masallaci.

tun daga ranar da sumayya taga tasamu biyan buk'atarta sai tadaina zuwa wajen yarima shi abunma  dariya yake basa ganin sai tana buk'atar wani abu take zuwa wajensa, yarima bai wani damuba yace shi hakan ya fiyemasa da tazo tadameshi da surutu da haukanta.


*BAYAN KWANA BIYU*

yarima suhail ne a gidan gona tare da shaheed cikin wani k'ayataccen lambu, suna zaune bisa wani lallausan carpet da aka shimfid'a musu suna shan iska, daga chan nesa da su kad'an k'osassun guards d'insane tsaye, hannun yarima suhail rik'e yake da cup mai d'auke da ruwan inibi ammah ba sha yakeba, shaheed da yake zaune yana cin tufa kallonsa yakai ga wata 'yar tsuntsuwa da tad'auke hankalin yarima.

murmushi shaheed yayi cike da zaulaya yace ranka yadad'e tsuntsuwannan ta burgekane asa guards d'inka sukamo maka ita?

yarima suhail shima murmushi yayi tare da kai cup d'in bakinsa yad'an sha ruwan inibin batare da ya kalli shaheed ba yace kawai ina kallonta ne ammah...

shaheed jira yayi yaji abinda yarima zai ce ammah yayi shuru, ganin haka yasa yace ammah ta burgeka ko?

yarima suhail aje cup d'in hannunsa yayi tare da juyowa yad'an kalli shaheed sannan yamaida kallonsa ga tsuntsuwar yace eh kusan haka.

shaheed ma kallonsa yamaida ga tsuntsuwar yana shirin yin magana nan wayan yarima suhail tafara ringing dasauri d'aya daga cikin guards d'insa yazo yad'auko tare da russunawa yamik'a masa.

Suhail kar6a yayi ganin Daddynsane yasa cikin sauri yayi picking tare da yin sallama.

daga chan 6angaren daddy amsa masa yayi tare da tambayarsa yana ina?

yarima cike da ladabi yace daddy ina gidan gona.

daddy yace toh kazo gida kasameni domin akwai maganar da nakeso muyi me muhimmanci.

Suhail baikawo komai a ransaba yace toh daddy ganinan zuwa.

bayan ya gama waya da daddy kallon shaheed yayi yace muje gida daddy nason ganina.



ko da yadawo direct turakar iyayensa yaje a parlour yasamu daddy da ummi zaune da alama jiransa suke, dasallama yashigo tare da samun waje k'asa gefen daddy yazauna nan yak'ara gaishe da iyayen nasa suka amsa masa.

daddy ne yayi gyaran murya yace suhail wani taimako ne mukeso kayi mana ammah bamu san ko zaka iyaba.

yarima suhail d'ago kansa yayi yakalli daddy yace daddy kunfi kar6in haka a wajena ni mai cika umurninku ne.

daddy jinjina kai  yayi yace nasan haka,  sannan yace suhail aure mukeson muk'ara maka.

A firgice yarima suhail yad'ago kai yakalli iyayen nasa yace aure kuma daddy? Ina fa da aure.

ummi tace munsan haka wannan ma za6inmu ce mukeso ka aura, halinta da tarbiyarta sunyi mana, sumayya 'yar uwarkace kasan muna sonta, kawai alkhairine muka hango a tattare da k'arin aurenka,  wannan alfarma ce muka nema a wajenka.

yarima suhail cike da tashin hankali yace kugafarce ni ummi ba wai nak'i bane kuduba kuga sumayya had'ani akayi da ita ba za6ina bace za6in memartaba ce, kuma a yanzu kuna neman kuhad'ani da wata, indai auren kukeso inyi toh na amince zanyi ammah kubari insamo za6in zuciyata. 

Sultan Ahmad da ummi kallon juna sukayi sai chan sultan yace yarima ba wai munk'i ta takaba wannan auren za6inmu ne kaima kana da ikon auren za6inka a nan gaba ammah mudai muna buk'atar ka amince ma za6inmu insha Allahu akwai alkhairi a cikinsa.

Yarima shuru yayi na d'an lokaci yana tunani cikin ransa ko haushi yakamasa ammah baya ji zai iyayi ma iyayensa musu sai da yayi kusan minti biyu a haka sannan yad'ago kai yakalli iyayen nasa da suka zuba masa ido suna sauraren jin amsar da zai basu  ahankali yabud'e baki yace daddy na amince zan aureta.

ummi da daddy farin ciki yakamasu kasa 6oye murnarsu sukayi sukace gaskiya munji dad'i sosai suhail yadda kafaranta mana kaima Allah yafaranta maka insha Allahu ba zakayi da nasaniba a cikin auren da zakayi.

yarima suhail murmushi kawai yayi batare da yace komai ba domin shi kad'ai yasan abinda yakeji a ransa na bakin ciki.

Daddy ne yanisa yace saidai wani hanzari ba guduba wannan auren bamusan kowa yasan mu muka had'asa munaso kanuna kaine kakeson yin auren, matsalar ma yanzu bamusan yadda yakamata a tunkari su memartaba da maganar ba.


gyad'a kai yarima yayi yace shikenan daddy ni zanje insamesa nasan abinda zance masa.

ummi tace a'a suhail kabari dai musamo mafita domin amincewarsu a lokaci guda kamar zatayi wahala.

d'an guntun murmushi yayi yace kar kidamu ummi kubarmin komai a hannuna.

ummi tace to yaushe zakaje kagano matar taka?  na tabbata kaima zaka sota

haushi yak'ara kama yarima jin wai ummi ta ce zaiso wata, girgiza kai yayi yace no ummi ba sai najeba.
nan yayi musu sallama yataso yafito ransa duk a 6ace duk gaisuwar da mutane suke duk'ewa suna k'wasa bai amsama ko mutum d'ayaba  yawuce yakoma part d'insu yana shiga 6angarensa guards d'insa yayi ma warning kar subari kowa yashigo ko da kuwa gimbiya sumayya ce.


koda yashiga saman gadonsa yazauna tare da dafe kansa yana jin wani iri a ransa ganin duk an watse masa budget domin kwata-kwata bai shirya k'ara aure yanzuba yafiso sai yasamu macen da yakeso sai ya aureta, tsaki yaja tare da kaima katifa naushi cikin d'aga murya yace wacece wannan wadda iyayena sukeson had'ani da ita me ke gareta da har tarud'esu taja duk wani plan d'ina ya watse tashi yayi yashige toilet tare da sakarma kansa shower.


_Comments_
      *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Wannan page d'in nakune my *Blood Sis Aufana nd Mummy Sainah Ummun Meenal* hak'ik'a kunfi k'arfin page a wajena, fatana Allah yabarmu tare 'yan uwa nagari😘_

*PAGE* 1⃣7⃣

Bayan ya fito shiryawa yayi sannan yahau saman bed d'insa yakwanta tare da jawo wayoyinsa yakashesu gudun kar adamesa da kira, nan yayi ta tunanin yadda zai 6ulloma lamarin, domin kwata-kwata bayaso yasa dada cikin maganar gudun kar tatarwatsa komai.

kiran sallar magrib ne yafarkar da shi daga tunanin da yakeyi, jiki babu k'wari yaje yad'auro alwallah yaficce masallaci.

Bayan sallar isha'i yarima fada yaje domin yagana da memartaba, lokacin memartaba da wazirine kawai cikinta suna tattaunawa akan wasu kud'i da za'a ware akai gidan marayu da gajiyayyu,  yarima gaishesu yayi, nan suka amsa masa cike da sakin fuska da fara'a,  sannan yasamu gefe d'aya yazauna yajanyo wayansa yana dannawa yana jiran sugama.

ganin yarima a wannan lokacin ya tabbatar ma da memartaba fa akwai magana dan haka cikin sauri ya sallami waziri.

Bayan waziri ya fita memartaba kallonsa yamaida ga yarima yace suhail na tabbatar akwai magana me muhimmanci da take tafe da kai domin kwata-kwata ban saba ganinka a wannan lokacinba.

yarima murmushi yayi yace ranka yadad'e tabbas hakane akwai maganar da take tafe da ni.

memartaba murmushi yayi yace ina saurarenka ka sanar da ni.

yarima kunyace takamasa yafara kame-kame yace am dama ranka yadad'e..... sai kuma yayi shuru.

memartaba murmushi yayi a karo na biyu yace suhail kayi min bayani mana.

ahankali suhail yad'ago kai yakalli memartaba cike da nutsuwa yace ranka yadad'e kagafarceni daman aure nakeson k'arawa ammah idan ka amince.

memartaba cike da mamaki yace aure kuma suhail?  yarima gyad'a kai yayi yace ammah amincewarka nafi buk'ata ranka yadad'e domin ba zan iya zartas da hukunci batare da amincewarkaba.

memartaba shuru yayi nad'an lokaci yana nazari sai kuma chan yace suhail ba zan hanaka raya sunnar ma'aikiba, idan nace zan hanaka aure to natauye maka hak'inka kuma bazanyi jayayya da maganar ubangijiba domin shine yayi umurni da muyi aure, saidai bansan ko kuna samun matsalaba da matarka domin baku ta6a kawo k'arar junaba, inma akwai wata matsakar ba zance dole sai nasantaba domin wannan sirrinkune, ko da aure nufine na ubangiji,  yanzu dai katashi katafi gida zanyi shawara in Allah yakaimu gobe zan nemeka.

yarima rissinawa yayi yace Allah yak'ara maka tsawon rai nagode sosai atashi lafiya,

memartaba gyad'a kai kawai yayi, ahankali yarima yamik'e yabar wajen yana sak'e-sak'e cikin ransa yadda za'a kwashe da su dada domin shi k'wata-k'wata baya jin ta gimbiya sumayya dan ashirye yake da yafad'a mata.

ko d's yakoma shirin bacci yayi yakwanta duk yadda yaso yayi baccin ammah ya kasa juyi kawai yake saman gado takaici duk ya cikasa ganin kamarsa ammah ace sai anza6a masa matan da zai aura, takaicinsa ma ba'a ma basa za6in  kansa saidai aza6a masa saikace wani k'aramin yaro, tsaki yaja. haka yayita tunane tunane da sak'e-sak'e cikin ransa a zaciyansa sai yaji yana burin ace memartaba bai aminceba, wani irin dad'i yaji nan yasaki murmushi mai sauti ahankali yace Allah ma yasa memartaba yace a'a, ahaka bacci yayi awon gaba da shi.




*WANSHE KARE*

Yarima suhail cikin sauri yagama shirinsa kasancewar yayi late a gurguje yad'anyi breakfast sannan yaficce  yanufi wajen aikinsa.


Bayan sallar la'asar zaune yake a parlour d'insa yana kallon wrestling cike da nishad'i kasancewarsa yanason kallon irin boxing da wrestling, wayarsa ce fara neman agaji, tsayar da kallon yayi tare da d'auko wayansa ganin memartaba ne yasa yayi picking dasauri tare da yin sallama.

amsa masa memartaba yayi sannan yace kazo turakata kasameni, cike da ladabi Yarima yace toh ranka yadad'e.

mik'ewa Yarima suhail yayi yaje yad'auko alk'yabbarsa yasaka sannan yafito nan guards d'insa suka take masa baya har turakar memartaba da sallamarsa yashiga.

mamakine yakamasa ganin iyayensa da na sumayya sai dada, cikin ransa yana mamakin dalilin da yasa aka tarasu.  a k'asa yazauna tare da gaishesu.

memartaba ne yayi gyaran murya yace toh Alhmdllh nasan zakuyi mamakin tarakun da nayi, toh ba wata babbar magana bace dan kufad'i ra'ayinku domin wannan taron duk akan suhail akayisa saboda yazomin da wani babban zance.

shuru memartaba yayi nad'an lokaci sannan yace suhail yana da burin k'ara yin aure .

gaba d'ayansu suka rikice a firgice dada tace aure kuma? wane irin aure? duka-duka yaushe akayi aurensa da sumayya?

Sultana Sadiya tanaso tayi magana ammah bata iyawa saboda memartaba yana wajen, 
wani k'ululun bak'in cikine yatsaya mata harara tashiga wurga ma yarima suhail.

Memartaba murmushi yayi yace dan baidad'e da yin aureba wannan ba matsala bane domin yana da ikon auren sama da mata d'aya kuma baidace atauye masa hak'insaba inda matsalar take shine yasafke ma kowace mace hak'inta da yarataya a wuyansa, 
kallonsa yamaida ga sultan Ahmad da Abban sumayya yace toh ku iyayensa kuyi magana ya kuke ganin ya dace.

Abban sumayyane yayi karaf yace ranka ya dad'e abarsa yayi aurensa tunda yana da iko kar a tauye masa hak'insa.

Daddyn suhail yace ammah...... dasauri Abban Sumayya yakatsesa yace yaya dan Allah kar kace wani abu abarsa kawai yayi aurensa Bayan wannan ma yana da ikon k'aro wasu matan biyu.

Sultana bilkisu da Sultana Sadiya sudai basuce komai ba saidai binsu da suke da ido, sultana sadiya haushin mijinta taji ganin za'ayi ma d'iyarsa kishiya ammah bai damuba sai ma turawa da yakeyi.

dada ce cikin 6acin rai tace suhail inbanda abunka miye na gaugawa shi fa aure lokacine, kaduba kaga mutuncin matarka 'yar uwarka.

memartaba murmushi yayi yace dada kubarsa yayi aurensa tunda yana da burin yi.

dada tace ranka ya dad'e gaskiya ni ban aminceba ban yarda yawulak'anta min jikaba daman nasan yanayin zamansu kuma kaduba kaga.....  memartaba d'aga mata hannu yayi yace ya isa haka k'ara auren da zaiyi ba shine yake nufin zai wulak'anta sumayya ba kuma na yarda da suhail nasan ko fiye da mata biyu aka basa zai iya kula dasu domin yana da hankali.

dada shuru tayi batace komai ba.

memartaba yace ko akwai me magana acikinku?

gaba d'ayansu sukace a'a ranka ya dad'e.

memartaba kallonsa yamaida ga Yarima suhail da yake zaune k'asa kansa sadde a k'asa yana sauraransu domin shima kansa baiso amincewarnan da akayiba dan dai ba yarda zaiyi ne kuma yanason cika umurnin iyayensa,  muryar memartaba ce yaji yace suhail ka fad'ama iyayen yarinyar zamu tura a neman maka aurenta, dafatan dai ka fad'a ma matarka zaka k'ara aure?

Yarima Suhail girgiza kai yayi yace a'a ranka yadad'e bata saniba,  memartaba yace toh shikenan kaje kasanar da ita nasan sumayya batada matsala zata amince.

Yarima Suhail yace toh ranka yadad'e.

memartaba yace zaku iya tafiya idan ba mai magana.

gaba d'ayansu duk'awa sukayi suka kwashi gaisuwa sannan suka tashi suka ficce.

Yarima bai koma 6angarensuba motarsa yashiga yaficce yatafi asibiti saboda akwai theater d'in da zai yi ma wasu.


Sultana Sadiya cike da tashin hankali takoma 6angarensu a parlour tayada zango tare da korar duk ma'aikatan da suke ciki nan tafara saffa da marwa  tana jiran Sultan Abbas da yatsaya suna magana da Daddyn yarima.

Bayan kamar minti biyar sai gashi ya shigo, da mamaki yatsaya yana kallonta yace lafiya Sadiya naganki haka?

Cike da 6acin rai tace haba Abban sumayya wannan wane irin cin mutuncine yaron nan yakeson yi mana, kaduba kaga duka yaushe akayi bikkinsu dukaba shekara d'aya da rabi kenan ammah wai aure zai k'ara.

Murmushi Sultan Abbas yayi yace toh menene dan zai k'ara aure?

Sultana Sadiya tace kai wai naga kamar baka damuba d'iyarka fa ce za'ayi ma kishiya saikace bakasan ciwontaba?

Murmushin takaici Sultan Abbas yayi yace sadiya nine bansan ciwon Sumayya ba?  nine mahaifinta kuma ita da suhail basuda banbanci dukansu 'ya'yanane kuma bari kiji dakaina ma zan iya zuwa inneman masa aurenta dan haka idan zaki sa d'iyarki tanutsu tabi mijinta toh inkuma taje garin haukanta takashe aurenta toh baruwana dan haka shawara tarage taku, yana kaiwa nan yaficce yabarta nan tsaye.

da harara sultana sadiya tarakasa tace ai zamu gani, wayarta tad'auko takira sumayya.

Lokacin Sumayya tana kishingid'e tsakiyar kuyanginta nan aka mik'o mata wayar tayi picking tace ummah ya dai?

ummah cikin fad'a tace ke jakkar inace mijinki yana nan yana shirin k'ara aure.

'yar dariya sumayya tayi tare da mik'ewa tanufi bedroom d'inta tana cewa haba dai yariman nawa? taya zaiyi aure?

Sultana Sadiya ta k'ule sosai cikin tsawa tace ke wace irin bahuwace?  ina fad'a miki ammah baki ma damuba.

Sumayya zama tayi saman bed d'inta tace ummah ai nad'auka tsokanata kike.

Sultana Sadiya tace wace irin tsokana yanzu muka zauna da iyayenku akayi maganar har da memartaba kece kawai baki saniba.

Sultana Sumayya a firgice tamik'e tsaye tace ummah yariman nawa zaiyi aure batare da na saniba?

Ummah tace k'warai kuwa sumayya abun bak'in cikinma har da mahaifinki cikin masu goya masa baya.

sumayya k'asa tazauna tare da fashewa da kuka tace ummah yanzu yarima ne zai yaudareni yak'ara aure? 

ummah tace ai saisa naso kihaihu ammah kika k'i d'aukar shawarata daman abinda nake guje miki kenan domin nasan halin yaudarar maza saboda basuda tabbas.

Sumayya cikin kuka tace wlh bazan yaddaba babu macen da zata auri yarima duk ma wadda tayi gigin shigowa wlh sai na kasheta domin bazan zauna da kishiyaba.

ummah tace kisa kuma sumayya?  kibari mubi komai a hankali nima kinsan ba zan ta6a amincewa ayi miki kishiyaba domin farin cikinki shine nawa.

Sumayya cikin kuka tace kuma dada tasan da maganar?  Ummah tace babu fa Wanda bai saniba.

K'ara fashewa tayi da sabon kuka cikin d'aga murya tace wlh k'aryane babu macen da ta isa ta auri mijina wlh ko ma wacece sai na kasheta,  tana fad'in haka tayi wurgi da wayarta tare da duk'ewa tana wani irin kuka me tsuma zuciyan mesaurare dasauri tatashi tafito tanufi 6angaren yarima ammah tana shiga taga baya nan.

dan haka tafito tadawo d'akinta tana wani sabon kukan nan tafara watsi da kayan d'akinta dan dressing mirror d'inta batabar komai ba duk ta watsesu k'asa masu fashewa sunayi masu zubewa sunayi sumbatu tafarayi wlh sai nakashe ko wacece ba zan ta6a yadda a auremin mijiba saman gado tafad'a tana me cigaba da risgar kuka,

ma'aikatanta tsaye sukayi daga wajen d'akin sukayi cirko-cirko suna jinta ammah ba mai iya shiga d'akin gudun kar suma 6acin ran yashefesu.....



_Comments_
    *nd*
_Share_





_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔


_*Wannan page d'in na sadaukar da shi agareku Mamansadiq, Mummyn khadija nd Mrs Dawud  ina alfahari da ku a kodayaushe, godia ta agareku bazata ta6a gushewaba wlh ko da page ko ba page nariga na ajeku waje guda acikin zuciyata😘*_

*PAGE* 1⃣8⃣

Jin abun gimbiya ya k'i k'arewa yasa haule tafita dagudu tanufi turakar yarima tana zuwa nan guards suke shaidamata baya nan, juyowar da tayi zata koma taji tsayuwar motar yarima dagudu tafita tanufi inda yake.

yarima yana fitowa daga mota daidai lokacin haule ta iso dasauri tazube gaban yarima yarima kallonta yake cike da mamaki,  tace ranka yadad'e kagafarceni daman gimbiyace tana cikin d'aki.

yarima shuru yayi kamar ba zaiyi magana ba sai kuma chan yace me yasameta?

Haule duk'ar da kanta tak'ara yi tace ranka yadad'e gaskiya bamu saniba mun dai jiyota a d'aki kamar tana kuka.

yarima baice komai ba domin yagane dalilin da yasa sumayya yin hakan, wucewa yayi yabar wajen, da har zai shige part d'insa domin baiyi niyar zuwa wajentaba,  chan kuma sai yafasa yanufi 6angarenta har a lokacin kuyanginta suna tsaye cirko-cirko anrasa mai iya ta6uka wani abu.

ganin yarima yasa suka zube suna k'wasar gaisuwa sannan suka tashi sumi-sumi suka fita sukabar d'akin.

ahankali yabud'e bedroom d'in yashiga mamakine yakamasa ganin yadda tawatse komai na d'akin, sannan yasafke kallonsa kan  sumayya da take raku6e k'asa saikace wadda tayi rashin iyayenta tana ruzgar kuka,  jin anshigo yasa tad'ago kai ganin yarima yasa tamik'e dasauri tanufi wajensa tare da rungumesa tana shashek'ar kuka tace yarima kafad'a min cewar abinda naji ana fad'a akanka k'aryane.

yarima da yake tsaye yace sumayya me kikaji akaina?

sumayya d'ago kai tayi takallesa tace aure wai zaka k'ara.

janye idonsa yayi daga kallonta yace hakane aure zanyi.

gimbiya turesa tayi a firgice tare da matsawa tace suhail aure? ni zakayi ma kishiya?

Yarima Suhail murmushin mugunta yayi yace tabbas aure zanyi sumayya domin ke tuni kikayi wasa da damarki.

cikin d'aga murya sumayya tace enough suhail!  enough!!! nan tafashe da sabon kuka tace dan Allah kafasa auren nan wlh zan kula da kai.

ta6e baki yarima yayi yace kin rin rasa damarki dan haka k'ara kawai kiyi hak'uri koma wacece tashigo kikar6eta hannu biyu kuyi zaman lafiya.

sumayya cikin k'araji tace ank'i d'in, wlh babu wadda ta isa ta auremin miji domin gidan nan ba za'a ta6a samun zaman lafiya ba.

yarima suhail fuskarsa babu alamun wasa yace kidinga tace maganar da kike a gaban yarima suhail domin kinsan wanene ni bana son raini, sannan indai kinason zaman gidana dole kiso abinda nakeso kuma kuyi zaman lafiya.

gimbiya sumayya a fusace tace Idan ank'i fa?
murmushin mugunta yarima yayi yace igiyar aurenki zata fara rawa, yana kaiwa nan yajuya yaficce yabar sumayya tsaye sake da baki tana binsa da kallon mamaki,  yana fita tasake rushewa da kuka tace nashiga ukku yanzu ni suhail zai yaudara?
kamata ace zaiyi ma kishiya har yana ik'irarin sakina.

saida taci kuka me isarta sannan tajawo wayarta da tawullar taga har screen d'in yatsage dan haka tad'auko d'ayar takira zinat har tatsinke ammah zinat bata d'agaba.

A fusace gimbiya tamik'e tad'auko alk'yabbarta tasaka tafito nan duk kuyanginta  suka take mata baya duk wanda zai ganta a lokacin yasan tana cikin 6acin rai, tana fitowa bata zarce ko'inaba sai sai turakar iyayenta, a parlour ana ta kwasar gaisuwa bata kalli kowaba ganin ummanta bata parlour yasa tashige bedroom.

lokacin sultana sadiya tana zaune saman bed d'inta tana waya, ganin yadda sumayya tashigo yasa arikice tamik'e tsaye tace sumayya lafiya?

dagudu sumayya tazo tafad'a jikinta tare da fashewa da sabon kuka tace ummah nashiga ukku yanzu ni suhail zaiyi ma kishiya.

Sultana Sadiya rarrashinta tashiga yi tace haba sumayya kiyi hak'uri man kinsan dai tunda memartaba ya amince toh babu wanda ya isa yace a'a dan haka kibarsa kawai yayi auren munga ta yadda amaryar zata zauna lafiya, sai tasan tashiga rayuwarki dakanta zata fita tabar miki gidan.

sumayya kallon sultana sadiya take cikin rashin gamsuwa, ta bud'e baki zatayi magana kenan nan wayarta tafara ringing ganin zinat ce yasa takalli sultana sadiya tace ummah ina zuwa.

mik'ewa tayi tafito tashiga d'ayan bedroom d'in sannan tayi picking d'in wayar ko sallama batayiba tafashe da kuka tace zinat nashiga ukku.

zinat a firgice tace sumayya me yake faruwane?

sumayya kasa magana tayi sai ma kuka da takeyi,  zinat cewa take sumayya kiyi min magana mana please nima inbaso kike inyi kukanba.

sumayya tsagaitawa tayi daga kukan da take tace zinat yarimana kasheni yakeson yi wai aure zai k'ara.

'yar dariya zinat tayi tace yoh d'an wannan zaisa hankalinki yatashi?

sumayya daina kukan tayi tace zinat kin ko ji abinda nace?

zinat tace na ji man ba aureba?  yaje yayi kema ai wani sauk'in ne zaki samu domin yanzu zaki samu right d'in zuwa inda kikeso kinga business d'inmu zaya ha66aka,  koma wacece kibarta tashigo wlh dakanta zata bar miki gidan.

sumayya tace haba zinat kamar ya inbari yayi aure ya za'ayi kamata ace anmini kishiya 

zinat tace haba sumayya matsalata da ke kiyita abu kamar baki wayeba, kinsan ni kaina ba zan amince ayi miki kishiyaba dakanmu zamu fitar da ita gidan.

Sumayya jinjina kai tayi tace yanzu nafahimceki baby,  zinat tace yauwa dear ai nasan zaki fahimceni nan zinat taita k'unsa mata makirci saida taga sumayya tad'auka sannan sukayi sallama takashe wayarta.

sumayya dawowa tayi wajen sultana sadiya tace ummah shikenan nad'auki shawararki ammah wlh bazan ta6a bari amaryar tasamu zaman lafiya a gidanaba.

cike da jin dad'i sultana sadiya tace gaskiya naji dad'i da kika fahimceni ai inma kin bari tazauna lafiya toh baki haihuba kibarshi kawai daga shi har amaryar tasa sai sun san sun ta6o tsuliyar dodo.

dariyar jin dad'i sumayya tayi tace za'a fara babban wasa dominba mai ta6a gimbiya sumayya azauna lafiya, muje zuwa.

__________________

Zarah duk yadda taso tacire damuwa a ranta ammah ta kasa kawai dai tana 6oyewane dan kar iyayenta sukaranto halin da take ciki, ga malam bello da kusan kullum sai ya kirata ammah takasa fad'a masa matsalar da ake ciki.

shi kansa ya sha tambayarta abinda yake faruwa domin jin yadda duk tacanza masa saidai tace bakomai.

Yau Zarah ita kad'aice gidan kasancewar  mama taje asibiti raka yaya Rauda awo, Aysha kuma taje bikkin k'awarta da akeyi.

ji tayi bata iya barin malam bello batare da yasan halin da ake cikiba dan haka wayarta tad'auko tanaso takirasa ammah ta kasa sai juya wayar take a hannunta ta rasa yadda zatayi daga k'arshe dai tadaure takirasa.

malam bello baiyi picking ba har saida tatsinke tana shirin tak'ara kiransa sai gashi ya kira,  zuba ma wayar ido tayi ta rasa yadda zatayi tad"auka domin batasan abinda zatace ba, saida taga takusan tsinkewa sannan tayi picking tare da yin sallama.

malam bello ya amsa mata nan suka gaisa sannan Zarah tace malam idan kana kusa dan Allah kazo akwai maganar da nakeso muyi.

Cike da jin dad'i malam bello yace ganinan ko zuwa kinsan dama nakwana biyu bansaki a idonaba fatana dai ba laifi nayiba.

Zarah duk yadda taso tamaida kukanta kasawa tayi muryarta tana rawa tace babu komai sai kazo, dasauri takashe wayar batare da taji abinda zai ceba takife kanta saman katifarsu tashiga rera kuka cike da tausayin malam bello da kanta domin batasan yadda shima zai fahimci maganarba

bayan kamar minti biyar wayarta tashiga ruri ganin malam bellone yasa dasauri tamik'e taje toilet tawanke fuskarta sannan tafito tasaka hijab d'inta tafita jikinta duk a sanyaye.


A k'ofar gidansu tasamesa tsaye yana jiranta kanta yana sadde k'asa gudun kar yagano yanayin da take nan tayi masa sallama

malam bello fuskarsa a sake ya amsa mata tare da tambayarta mutanen gida tace duk suna lafiya,  daganan shuru yabiyo baya sai chan malam bello ya nisa yace Zarah Allah yasa ba laifi nayiba dan fitama zanyi nafasa nace bari infara amsa kiran gimbiyata sannan sai inwuce

Zarah  runtse idonta tayi tana jin wani iri a ranta jin kanta yafara sarawa yasa tajingina da bango.

malam bello rikicewa yayi yace Zarah lafiya? meyake faruwane?  wani abu yasamu su abbah?  Please kifad'amin matsalarki.

Zarah batare da ta bud'e idontaba tashiga girgiza masa kai hawaye suna zuba cikin muryar kuka tace ko d'aya malam bello babu abinda yafaru,  inaso ne kayafe min wlh ba a son raina hakan takasanceba saidai dan ba yarda zanyi kuma banaso ink'i bin umirnin iyayena kayi hak'uri da..... sai kuma tayi shuru tare da fashewa da kuka.

malam bello jikinsa ya yi sanyi sosai yace Zarah da me zan hak'ura?  kiyi min bayani, su Abbah basu amince da ni inkasance surukinsuba ko?

Zarah dakyar tabud'e idanuwanta da suka kumbura saboda kuka tace su abbah sunyi min miji muhak'ura da juna haka Allah yak'addara kai ba mijina bane.

Malam bello murmushi yayi Wanda yafi kuka ciwo yana kallon Zarah da taketa kuka yace Zarah daman kan wannan 'yar maganar kike ta faman kuka?

Zarah tsagaitawa tayi da kukan da take tace bakaji abinda nace bane?  miji fa akayi min?

Malam bello daurewa yayi cikin rashin damuwa yace  najiki mana, toh menene Zarah? dole kiyi hak'uri kibi za6in iyayenki domin ba zan ta6a yadda inbaki shawara akan kibijire ma iyayenkiba, Allah daman ya k'addara ba matata bace ke, ita rayuwa duk yadda tazo maka kayi hak'uri kakar6eta domin shi aure nufine na ubangiji babu mai auren matar wani kar kimance mune muke haukanmu ammah Allah yariga da yatsara ma kowa yadda rayuwarsa zata kasance wlh nabaki goyon baya kiyi ma iyayenki biyayya insha Allahu zakici ribar biyayyar da zakiyi musu kema kuma Allah zai baki wad'anda zasuyi miki biyayya domin su iyaye sun wuce abin wasa yakamata muguji fushin iyaye, ni yanzu shawarar da zan baki itace kiyi ma iyayenki biyayya insha Allahu zakici moriyar hakan.

Zarah da tunda yafara maganar tazuba masa ido hawaye kawai suke zuba daga idonta dakyar tabud'e baki tace yanzu kana nufin ka rabu da ni?

malam bello murmushi yayi wanda iyakansa baki sannan yace tabbas Zarah narabu da ke domin ko nine bazan iya bujirema umirnin iyayenaba saidai inaso kisani sonkine da nake yajawo hakan kuma har abada bazan daina sonkiba saidai inyi addu'an Allah yarage min sonki a cikin zuciyana, fatana Allah yasa wanda zaki aura yasoki fiye da yadda nake sonki,  kema inaso kiyi min alk'awali d'aya shine zai tabbatar min da kina sona.

Zarah cikin kuka tace wane irin alk'awali kakeso inyi maka wlh indai shi zaisa kagane ina sonka toh na amince koma minene kafad'a.

malam bello d'an guntun murmushi yayi sannan yace inaso kiso mijinki fiye da yadda kike sona sannan kinuna masa kulawa kar kisa6a masa kiyi masa biyayya indai ba hanyar Allah yanemi yakauceba.

Zarah girgiza kai tashiga yi tace bana tunanin zan iya son wani fiye da yadda nake sonka bazan iya d'aukar alk'awalin da nasan bazan iya cikawaba.

malam bello juyawa yayi cikin dabara yagoge hawayen da suke shirin zubo masa sannan yace wannan zai shaida min da cewar bakya sona.

Zarah girgiza kai tashiga yi tace malam kar kace haka wlh ina sonka shikenan na amince zanyi duk abinda kace.

malam bello juyowa yayi yace dagaske kin d'aukar min alk'awali?

gyad'a masa kai tayi tace eh saidai kayi hak'uri ba zan iya tursasa zuciyana taso wani fiye da yadda take sonkaba.

murmushi malam bello yayi yace natabbata zaki ma soshi indai ya amsa sunansa namiji wanda yadace mace taso, dan haka ina miki fatan alkhairi zarah idan nasa6a miki kiyafemin domin inaso wannan takasance had'uwarmu tak'arshe.

zarah fashewa tayi da wani sabon kukan tare da durk'ushewa k'asa cikin kuka tace nagode sosai malam bello hak'ik'a kai masoyinane nagaskiya tabbas duk macen da ta aureka tayi dacen miji fatana Allah yabaka wadda zata soka fiye da ni, bazan ta6a daina yi maka addu'a ba domin kabani gudunmawa sosai a rayuwana wlh *K'ADDARA CE* kawai tarabani da kai ammah ka cancanci kasancewarka mijina.

malam bello murmushi yayi yace kar kidamu zarah daman kyaun kowane musulmi ya yarda da k'addara me kyau da marar kyau,  ina miki fatan alkhairi nabarki lafiya .

juyawa malam bello yayi yatafi yana jin wani k'unci acikin ransa ji yake inama yayi kuka ko yasamu sauk'in abinda yake ji, yana jin kukan zarah tana ta kiransa ammah yak'i juyowa gudun kar shima yaga yanayin da take yayi kuka.

zarah da take tsugunne tana kuka tare da k'walah masa kira saida taga yayi mata nisa sannan tatashi takoma gida tafad'a saman katifarsu tacigaba da kukanta.

Tun daga ranar zarah da malam bello suka daina waya saidai text shima na gaisuwane kawai sukeyi, daurewa kawai take tacigaba da addu'a akan Allah yaza6a mata wanda zaifi zama alkhairi, su yaya Rauda su suke k'ara kwantar mata da hankali da tayi hak'uri tacigaba da addu'a.


****      *****      *****   ****

memartaba kamar yadda yafad'a hakan kuwa akayi domin kiran yarima suhail yayi yace yafad'a ma iyayen yarinyar zuwa gobe zasu aiko da komai na neman aure domin basuson aja lokaci dayawa.

yarima suhail a firgice yad'ago yakalli memartaba yace ranka yadad'e duk dawuri za'ayi haka?  nad'auka za a bi Komai ahankali.

murmushi memartaba yayi yace suhail kenan toh me zamu jira?  k'ara dai muyi komai dawuri domin banaso ana d'aukar lokaci dayawa ammah indai iyayen yarinyar suka nemi aja lokaci toh lafiya lau saidai bazanso hakaba

yarima yace toh ranka yadad'e.

memartaba yace koma mi kenan kaje kuyi magana da waziri domin shine zaije yanemo maka auren sai ku yanke shawarar yadda zaku tafiyar da komai.

duk'awa suhail yayi yakwashi gaisuwa sannan yayi ma memartaba sallama yatashi yafita yanufi 6angaren iyayensa.

yana shiga daidai lokacin daddynsa yana shirin fita ummi tana bayansa cike da girmamawa yagaishesu sannan suka koma suka zauna, nan yake fad'a musu yadda sukayi da memartaba gabad'ayansu sun nuna farin cikinsu.

ummi tace toh zan kira iyayen yarinyar infad'a musu halin da ake ciki,  sannan driver d'in da yakaini shine zai kai su waziri.

suhail ahankali yace toh ummi.

daddy murmushi yayi yace son kaima ai yakamata kaje kagano matar taka domin baidaceba ace baka san wadda zaka auraba.

yarima suhail sosa kansa yayi yace ranka yadad'e ba ma sai najeba hakan ma lafiya lou zan zauna da ita, ko da ace ban santaba a yanzu, zan santa bayan aurenmu.

ummi tace haba suhail ammah..... hannu da daddy yad'aga matane yasa tayi shuru, daddy yace shikenan zaka iya tafiya.

yarima godia yayi ma iyayensa sannan yatashi yafita cike da jin haushin auren had'in da ake shirin k'ara masa a karo na biyu.

daddy kallon ummi yayi bayan yarima ya fita yace kibarsa kawai tunda ya amince zai aureta kar mumatsa masa akan dole sai yaje yaganta.

ummi jinjina kai tayi tace hakane ranka yadad'e fatana dai suhail yasota domin zarah ta cancanci kowane namiji yasota.

murmushi sultan Ahmad yayi yace zai ma sota insha Allah yanzu dai bari inje muyi magana da waziri yadda za'a tafiyar da komai.

cike da jin dad'i Sultana Bilkisu tace adawo lafiya ranka yadad'e.




_Comments_
      *nd*
_Share_



_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔


_Yau Ranar takuce *'yar mutan zariya mummyn uswan nd Mummyn Fadyl* wlh ina ji daku irin sosai d'innan😘_

*PAGE* 1⃣9⃣

ummi kiran mama tayi a waya lokacin mama tana zaune tsakar gida ita da abbah suna cin abinci, mama jin wayarta tana ringing yasa tad'auko ganin sunan sultana bilkisu da yabayya yasa tazaro ido tare da cewa malam sultana ce take kirana.

Abbah yace toh toh d'aga muji abinda zatace, mama saida ta saita nutsuwarta sannan tayi picking d'in call d'in tare da yin sallama.

daga chan 6angaren sultana bilkisu ta amsa mata cike da fara'a, nan suka gaisa cike da girmama juna, ummi tace ya su zarah dafatan duk suna lafiya?
mama tace lafiya lou, nan ummi take shaida mata akan maganar neman auren zarah da za'a zo gobe.

mama kallon abbah tayi da yake sauraren firar tasu,  alama yayi mata da tace toh.
mama tace toh ranki yadad'e Allah yakaimu.
cike da jin dad'i ummi tace Ameen mungode sosai, ammah idan mahaifinsu yana kusa kiban shi inaso muyi magana inkuma baya kusa idan yadawo zan kira,

mama tace ranki yadad'e yana ma kusa gashi, nan tamik'a ma abbah waya.

Abbah kar6a yayi tare da yin sallama nan suka gaisa cikin mutunta juna,  sultana bilkisu tace yauwa daman akan tsaida rana ne agaskiya mu a Royal family d'inmu ba'a yin baiko ad'auki lokaci shine nakeson in rok'eka alfarma dan Allah kar asa lokaci dayawa,

Abbah Jim yayi yakasa cewa komai.
sultana bilkisu tace kayi mamakin jin haka ko? kuyi hak'uri wlh tsarin masarautarmu ne haka.
Abbah cike da damuwa yace ranki yadad'e gaskiya hakan bazai yuwuba domin mu ba halinmu d'ayaba idan mukace ayi bikkin cikin gaugawa toh gaskiya zamu cutu tunda bamu fara tara komaiba da dai ataimaka asa ranar da d'an nisa domin musamu muyi mata abinda Allah yahore mana.

daga chan 6angaren ummi murmushi tayi tace kar kadamu ni zan d'aukema zarah duk wani abu da iyaye yakamata suyi ma 'ya'yansu wlh ko da ba d'ana zata auraba zan iya yi mata haka.

Abbah yace a'a ranki yadad'e kar hidimar tayi yawa kibari dai zamuyi.

ummi tace kar kadamu tunda nace zanyi kubarsa kawai wannan yazama sirri tsakanina da ku domin bana fatan wani yasan da hakan saboda gori da wulak'anci

maganarta tayi ma abbah dad'i sosai ganin yadda take Royal Family ammah bata d'auki kanta komai ba tasan abinda yadace da wanda bai daceba, muryar sultana bilkisu yaji tana cewa bawai ina nufin naraina k'arfinkuba wlh ko d'aya ko da ace ba zarah bace zan iya yi ma wata barema zarah da zata auri jinina dan Allah ka amince ma buk'atata a karo na biyu, malam yace toh ranki yadad'e mungode sosai Allah yabiyaki da gidan Aljannah,
ummi tace Ameen nice da godia da kuka amince min sai kunjimu, agaishe da su zarah.
malam yace haba bakomai ranki yadad'e, su zarah zasuji.

bayan sun gama wayar Mams kallon Abbah tayi tace malam toh yanzu ya za'ayi? wannan neman aure ba ko  shiri.

Abbah yayi murmushi yace gaskiya mutanen nan suna da kirki sosai bamuda abinda zamu biyasu da shi saidai muyi musu addu"a.

mama tace hakane da ace haka masu kud'i suke da ansamu sauk'in wani abun ammah yanzu sai kaga maikud'i sai d'iyan masu kud'i, Hajiya da Alhaji, d'an malam Audi me goro sai 'yar Malam idi mai icce, bakowane iyaye suke amincewa 'ya'yansu su auri 'ya'yan talakawa ba,
Abbah yace hakane abun ne yanzu sai addu'a domin masu son talakawa suna ra6arsu basuda yawa wani lokacin ni abun har mamaki yake bani ince toh wai su mancewa suke da Allahn da yabasu zai iya amshewa a duk lokacin da yaso? ko suna mancewa Allahn da ya azurtasu shine yayi talakka kuma ba dan baya son saba, ko suna mance fad'arsace cewa shi yake azurta wanda yaso yakuma hana wanda yaso, Allah dai yasa mudace.

mama tace Ameen y rabb.
Abbah yace toh yanzu sai kurubuta duk abinda kuke buk'ata na tarar bak'in sai insiyo muku, ko kuma kuta6a kud'in nan kud'ibi yadda zasu isa kuje kasuwa yanzu kusiyo abinda kuke ganin ya dace dan ni yanzu fita nakeson yi zan ma biya gidan yaya manu inshaida masa dan yasan da zuwansu gobe yashigo da wuri,

mama tace toh malam Allah dai yashige mana gaba,  bari inje insanar da yaran chan.

Bayan Abbah ya fita mama tashi tayi tanufi d'akinsu zarah lokacin zarah tana kwance saman katifarsu gefenta Rauda da Aysha ne zaune suna hira itadai bata sanya musu baki ammah tana saurarensu.

shigowar mama ne yasa suka tsagaita daga hirar da sukeyi mama kallonsu tayi tana murmushi tace 'yan albarka kuna nan kuna hira?

murmushi Aysha da Rauda sukayi sannan Rauda tace eh mama akwai abinda kike buk'ata da za'ayi ne?

mama tace a"a bakomai sannan tamaida kallonta ga zarah da take kwance tace gobe in Allah yakaimu za'a zo neman auren zarah,  wani irin fad'uwan gaba yaziyarci zarah ahankali tamaida idanuwanta talumshe tana jin wani iri a ranta.

Rauda da Aysha murna suka shiga yi suna kai wlh munji dad'i mama ashe zamusha bikki, bikkinma na princess zarah inji Aysha tare da kallon zarah taga idanuwanta a lumshe suke.

mama tace toh yanzu dai Aysha kitashi kishirya zamuje kasuwa musiyo abinda yadace dan haka Rauda ke zaki rubuta abinda kike ganin yadace asiyo.

Rauda tace toh mama nan tamik'e tad'auko paper da biro tashiga rubutawa.

Bayan su mama sun tafi Rauda kallon zarah tayi tace sister nasan abinda kikeji game da auren nan musamman ma da yakasance ba wanda kikeso bane zaki aura, kiyi hak'uri kikar6i k'addararki insha Allahu zakici ribar hak'urin da kikayi.  zarah bud'e idanuwanta tayi da suka cika da k'wallah ahankali tabud'e baki tace yaya Rauda bawai nak'i ta taku bane wlh na amince saidai ina tsoron abinda zaije yadawo domin bana tunanin shima yana sona nasan dai had'in iyayensane inma bahakaba tun daga yanayinsa kinsan yafi k'arfin kasancewa mijin zarah,  zarah duk yadda taso ta6oye kukanta kasawa tayi fashewa tayi da kuka tare da kallon Rauda da tazuba mata ido tace Yaya Rauda kiduba kiga ko da sau d'aya baizo da sunan mugaisaba kingako wannan aure namu kawai za'ayisane ammah yarima suhail ya wuce ajin zarah duk kyawawan 'yan matan da suke garin nan arasa wadda za'a basa sai zarah?

yaya Rauda cike da tausayin k'anwartata tarik'o hannun zarah tace inji wa yace zarah ba maikyau bace? kema kinsan kanki kuma natabbata shima zaya soki domin kina da halayyar da yadace kowane namiji yaso mace saboda su, wlh zarah kin cancanci asoki,  murmushi Rauda tayi tace nayarda da k'anwata zata iya sace zuciyar kowane namiji.

Zarah jikin Rauda tafad'a tare da k'ara sautin kukanta tace a'a yaya rauda kar kice haka wlh wannan yana da jin kai tun daga ma yanayinsa da nagani a wajen saukarmu kuma kema nasan kinga haka saidai idan zaki 6oye gaskiyane kuma fa su Abbah sunce mana yana da mata.

Murmushi yaya rauda tayi tare da shafa kan k'anwartata tace zarah nayarda dake nasan zaki iya k'watar ma kanki 'yanci.

zarah mik'ewa tayi tashige toilet tamaida tarufe tacigaba da kukanta kamar wadda aka aikoma da sak'on  mutuwa saida tayi me isarta sannan tawanke fuskarta tafito bata damu da kallon da rauda takeyi mataba tayi kwanciyarta tare da maida idanuwanta tarufe ganin haka yasa rauda takyaleta.




Tun da asuba da sukayi sallah shirye-shirye suke natarar bak'i inda aka rabama kowa aikin da zaiyi, girki sukayi masu rai da lafiya kala biyu,  aka soya kaji kafin kace mi gida ya gaure da k'amshi sannan suka had'a drinks iri-iri .

wajen k'arfe sha d'aya suka gama komai kowa yaje yashirya ammah banda uwar gayya saida yaya rauda tace zata je ta sanar da su mama sannan tatashi taje tayi wanka suka d'auko mata atamfarta cikin kayan da ta d'inka da kud'in da tasamu na walimar safkarsu tasaka.

wajen k'arfe 12 lokacin su Abbah da d'an uwansa malam manu suna zaune waje suna jiran isowar bak'i,  motocine guda ukku suka tafo a jere a k'ofar gidansa sukayi parking dogarawane suke fitowa daga ciki dasauri duk suka nufi wajen motar tsakiyar suka kare tare da baza manyar rigunansu suka bud'e wa su sultan Abbas(Abban sumayya) da waziri suka fito nan dogarawa suka take masu baya suna ranku yadad'e takawarku lafiya.

ganinsu yasa su Abbah suka mik"e suka nufi wajensu domin sun gane waziri, ganin sun nufosu yasa d'aya daga cikin dogarawan yace ranku yadad'e ga maigidan nan, suna isowa waziri da sultan Ahmad suka mik'a musu hannu cikin sakin fuska suka gaggaisa, Abbah yace bismillah kushigo daga ciki.

basuyi musuba sukabi bayansu a zaure suka zauna saman k'atuwar tabarmar da aka shimfid'a dogarawa a k'ofar gidan suka tsaya.

Nan suka k'ara gaisawa sannan su Abbah suka shiga gida suka kwaso kulolin abincin da aka shirya.

A gabansu su sultan Abbas suka jerasu, sultan Abbas yagabatar da kansu a matsayinsa na k'anen mahaifin yarima sultan sannan yagabatar da wazirin sarki,

nan shima malam muda yagabatar da kansa a matsayin yayan mahaifin zarah sannan yagabatar da malam musa a matsayin mahaifin zarah,

Nan suka shiga tattaunawa akan maganar neman auren dakyar suka samu abbah ya amince akan ayi bikkin nan da sati shidda masu zuwa dan shi cewa yayi sai nan da wata ukku,

dubu d'ari ukku sultan Abbas yabada yace kud'in nagani inaso da na neman aure,

abbah yaso arage kud'in saboda shi aganinsa sunyi yawa ammah sukak'i, 
dubu d'ari suka bayar sukace ga kuma sadakin zarah, nan waziri yaba dogarawa izini da su kwaso kayan da suke cikin boot d'in mota,

nan aka fara shigowa da kwalayen biscuits, chewing gum sai sweets, sai alkyabba kala ukku da atamfa biyar akace na amarya ne, sai shadda yadi goma-goma kala ukku akace na uban amarya ne, sannan sai  atamfofi kala biyar su kuma na uwar amarya.

Abbah rasa bakin godia yayi nan sukayi ta jero musu addu'o'i, dakyar suka samu su sultan abbas suka amince suka d'an ci abincin sauran akaba dogarawa suma sukaci,

bayan sun gama Abbah shiga yayi gida yace su zarah suje sugaisa,  gaba d'ayansu suka fito zarah rufe fuskarta tayi da gyale saikace sabuwar amarya,  nesa dasu kad'an suka tsaya suka tsugunnah cike da girmamawa suka gaishesu, cikin sakin fuska suka amsa musu tare da tambayarsu ya gida? sukace lafiya lou.

Waziri ne yace ina amaryar tamu cikinku?  Aysha ce tayi saurin nuna zarah da take k'ara sunkuyar da kai tace gatanan.

Sultan Abbas da Waziri sukace masha Allah amaryartamu dai ta cika kunya dayawa toh Allah yasa alkhairi Allah yakaimu lokacin saidai kinyi hak'uri domin kinsan cikin danginsa zaki zauna kinsan dai yanayin gidan namu na sarauta.

Abbah yace haba bakomai ai shi aure babu inda baya kai mutum duk inda mace tatsinci kanta hak'uri zatayi tazauna.

gaba d'ayansu sukace hakane Allah yasa alkhairi.

su zarah tashi sukayi suka koma cikin gida, inda su Abbah sukayi musu rakiya har wajen motarsu gaba d'ayansu godia sukeyi ma juna irin karamcin da suka nuna ma juna,  saida su Abbah sukaga tafiyarsu sannan suka dawo gida.

shigowa sukayi da kayan nan sukaita gani suna mamakin ganin neman aure kawai aka kashema wannan mak'udan kud'in, nan abbah yake fad'a musu yadda suka tsaida shawara lokacin da za'ayi auren, itadai uwar gayya tana d'aki ta k'umshe kanta harda kukanta.

Abbah shadda kala d'aya da dubu ishirin yaware yaba yayannasa, sannan ya d'ibar masa kayan sa ranar bikkin dayawa, malam muda godia yayi cike da jin dad'in kyautan da k'anen nasa yayi masa.



A chan 6angarensu Sultan abbas da Waziri a cikin mota sukaita labarin kirkin iyayen zarah,

ko da suka isa a fada suka safka lokacin memartaba da suhail sai mahaifin suhail ne zaune a fadar suna lissafin wasu kud'i.

nan sultan Abbas da Waziri suka labarta musu irin kirki da karamcin da suka samu daga wajen iyayen zarah.

Yarima suhail yana saurarensu shidai baice komaiba.

memartaba murmushi yayi tare da kallon yarima suhail yajinjina kai yace natayaka murna za6enka yayi kyau sosai, tun daga nan nasan d'iyar mutuncice zaka aura, ko da mahaifinka daman yafad'amin ba d'iyar masu kud'i bace wlh naji dad'i sosai domin suma talakkawa suna da 'yancin shiga gidan sarauta kuma ta haka mutane zasu k'ara tabbatarwa bamu banbanta kowa dukansu namune.

yarima suhail murmushi kawai yayi, 

nan su sultan Abbas suka d'auka Allah yaja da ran sarki me adalci

Sultan abbas ko da yafito daga fada turakarsu dada yaje yagaishe da mahaifiyartasa lokacin sultana bilkisu da sultana sadiya sunje gaisheta, 

nan sultana bilkisu tagaishesa suka gaisa cike da mutunta juna, inda sultana sadiya taketa had'e fuska ita ala adole fushi take domin tun kafin yatafi saida sukayi 'yar rigima akan zuwan da zaiyi neman ma Yarima suhail aure cike da 6acin rai suka rabu.

Dada tace har kun dawo kenan?
Sultan Abbas murmushi yayi yace eh ranki yadad'e gaskiya mutanen suna da mutunci sosai dan sun karramamu yadda yakamata, nan yake basu labarin irin tarbar da akayi musu yace ko da iyayenta masu k'aramin k'arfine ammah sunyi k'ok'ari sosai wajen ganin sun tarbemu a mutunce.

Sultana Sadiya ce tayi karaf tace  au wai duk jin kan na yarima ammah akan d'iyar talakkawa yak'are?

Sultan Abbas murmushi yayi yace inbanda abinki sadiya ai talakka da me kud'i duk d'ayane.

Dada tace ina akwai banbanci domin bakowane talakka ake amince mawaba, ga yaron nan kaifi d'ayane ba a isa abashi shawara yad'auka ba.

ita dai sultana bilkisu tana saurarensu batace komai ba.

Sultana Sadiya tace ma dada Ranki yadad'e ai harda laifin mahaifiyarsa da ace tana yi masa magana ai da gyara.

Dada tace a'a kar kice haka rabani da suhail ni nasan halinsa natabbata ko itama bai zama dole yaji kowace maganartaba ni nasan halinsa.

Sultana Bilkisu murmushi kawai tayi, Sultan abbas yace ranki yadad'e aikin gama ai yariga da yagama addu'an zaman lafiya kawai za'ayi musu.

Dada tace hakane duk wad'annan surutan basuyi fatanmu dai kamar yadda kace sun karramaku toh muga karamcin da mutuncin atare da ita.

sultan abbas yace hakane ranki yadad'e, Sultana sadiya bahaka tasoba taso ace dada tahau tazauna tace ba zata amince ayi aurenba.



_Comments_
     *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Yau page d'in mallakinkune ku kad'ai *Umm Abideen nd Queen Meenali* hak'ik'a ina muku so na hak'ik'a, chancantar kuce taja da haka😘_

*PAGE* 2⃣0⃣

A chan gidansu zarah duk inda yakamata araba kayan baikonta anraba  kowa yayi murna sosai tare da fatan alkhairi.

k'awarta khairy tsegumi tashiga yi mata akan tabar malam bello zata auri wani daban itadai zarah shuru tayi.

duk yadda khairy taso zarah tafad'a mata wanda zata aura zarah k'iyawa tayi, sai Aysha ce take fad'a mata.

khairy murna tayi sosai har da tsallenta tace da girman kujerarki gimbiya zarah ai ni wlh tun lokacin da nagansa naga kunyi matching, gaskiya guy d'in ya had'u ba k'arya gaskiya natayaki murnar samun miji irin yarima suhail ana ta shi waketa malam bello kud'i, kyau, nasaba, mulki, aji babu wanda yarima yarasa.

murmushin takaici zarah tayi tace khairy kenan bakisan micece soyayyaba wlh son da nake ma malam bello ya wuce yadda kike tunani, kuma wannan d'in da kike maganarsa bana tunanin zai soni, ko da sau d'ayane bai ta6a zuwa muka gaisaba, wannan aurenfa iyayensane suka nema masa ni, wlh nayi da nasanin walimarnan da nayi a islamiyya domin itace silar faruwan komai,  kukan da take dannewane yaci k'arfinta,

khairy rungumota tayi jikinta tana lallashinta tace a'a zarah kidaina cewa haka, domin haka Allah yak'addara yarima shine mijinki ba malam bello ba kiyi hak'uri kid'au k'addara kicire malam bello a ranki kisamarma yarima matsugunni a cikin zuciyanki.

dasauri zarah tad'ago kai takalleta tace khairy taya kike tunanin suhail zai samu matsugunni a cikin zuciyana?

murmushi khairy tayi tace na tabbata zai samu domin ta ko wane fanni ya dace kisosa dan daganin yanayinsa ma ya iya soyayya.

zarah ganin abin na khairy har da tsokana yasa tashareta.

A chan 6angaren yarima zaune yake yana dannar laptop d'insa da alama wani abu me muhimmanci yakeyi gimbiya sumayya ce tashigo ba ko sallama, ko da sau d'aya yarima bai d'ago takalletaba.

daga nesa da shi kad'an tatsaya tare da yamitsa fuska tace suhail kenan gaskiya kabani mamaki ace duk mulki, kyaun da Jan ajin ammah ace d'iyar talakawa zaka aura, gaskiya najiye maka haushi ammah fa dakunya ace talakka itace zata kasance kishiyata natabbata ko matsayin baiwata bata kaiba.

yarima d'ago kai yayi yawurga mata wata irin muguwar harara  wadda har saida sumayya tatsora, yace ke dad'ina da ke wani lokacin k'walwarki a toshe take in banda abinki me yahad'a kud'i da soyayya ina so kisancewa kud'i basa siyan soyayya kuma bari kiji ahaka nakesonta dan haka kifitar min daga d'aki ko in 6a66allaki ,

sumayya ganin babu alamun wasa a fuskarsa yasa tafita tana k'unk'uni,

tsaki yarima yaja sannan yacigaba da aikinsa a cikin zuciyansa ko yana mamakin halin sumayya da kwata-kwata ta kasa gyarawa.


shaheed a wajen mahaifinsa yakeji sunje neman aurensa baiyi mamakin rashin fad'a masa da baiyiba domin yasan halinsa,

ko da yaje yi masa Allah yasa alkhairi yarima suhail ko kallonsa baiyiba, shaheed ba haka yasoba yaso yarima yabiyemasa ko dan yaji yadda akayi yasamu mata shi da mata basa gabansa.


*BAYAN SATI BIYU*

a gurguje sultana bilkisu shiryawa tayi itada wata aminiyarta Hajiya sa'adatu sukaje gidansu zarah inda ta rok'i iyayen zarah alfarma akan subata zarah tanaso taje da ita ayi mata gyara sosai sannan akoya mata yadda zata dinga tafiya, magana, girki dadai sauransu a gidan sarauta saboda a matsayinta na matar yarima guda ana buk'atar ace ta san yadda ake komai na gidan sarauta.

dakyar tasamu su mama suka amince zarah ma harda kukanta kafin tabisu.

sultana bilkisu gidan hajiya sa'adatu sukaje da ita,  zarah tun da suka shiga gidan mamaki yacikata ganin irin daular da aka zuba a gidan babban gidane sosai mai d'auke da part ukku.

part  guda aka fitar mata da shi kasancewar darene akace taje tahuta gobe za'a kawo mata wad'anda zasu dinga yi mata hidima da koya mata komai, zarah dai jikinta rawa yake har saida ummi tagane halin da take ciki.

murmushi ummi tayi tare da rik'o hannunta sukaje bakin gado suka zauna, ummi kallonta tayi tace zarah kinutsu kicire tsoro a ranki ba zamu cutar da ke ba duk abinda kikaga zamuyi miki dan gudun magana ne kinsan gidan sarauta yadda yake, dan Allah kiyi hak'uri kibamu had'in kai.

zarah da kanta yake sunkuye k'asa wani irin nauyin ummi ne taji sa6anin da dasuka tafo da ita wani irin haushinsu da takeji, 

batare da ta d'ago kai takalletaba cike da kunya tace toh.

ummi cikin jin dad'i tace yauwa nagode insha Allahu gobe zaku fara gudanar da komai akwai wad'anda zasu dinga kula da ke duk abinda kikeso kiyi musu magana zasuyi miki, ummi jakkarta tabud'e tad'auka waya IPhone7 tamik'a ma zarah tace ga waya akowane lokaci kike buk'atar gaisawa da 'yan gidanku sai kugaisa nima zan dinga kiranki.

zarah batare da ta k'ar6aba tace ranki yadad'e ina da waya.

murmushi sultana bilkisu tayi tace da zaki taimaka kidaina cemin ranki yadad'e da naji dad'i.

ahankali zarah tad'ago kai takalleta, murmushi sultana bilkisu tayi tace kikirani da ummi, itama zarah murmushi tayi tace toh ummi insha Allahu hakan zan dinga Kiranki.

cike da jin dad'i sultana bilkisu tace yauwa daughter toh ina wayan taki?

zarah tashi tayi tabud'e akwatin kayanta tad'auko rugwagwar nokia d'inta tace gatanan.

kar6a ummi tayi tace wannan wayan yanzu ta gama amfani bari insaka miki number d'in wayan su mamanki a wannan,

zarah tace toh ummi.

nan ummi tasaka mata number d'in mama da abbah, sannan tad'ago takalli zarah tace daughter bari insaka miki harda number d'in yarima in case ko da ace zakuyi waya.

zarah da tunda ummi ta ambaci yarima gabanta saida yafad'i dakyar tace toh.

bayan ummi tasaka numbers d'in mik'a ma zarah wayar tayi tare da k'ara kwantar mata da hankali saida taga hankalinta ya d'an kwanta sannan tayi mata bankwana tafita taje tayi sallama da Hajiya sa'adatu tatafi.

Bayan ummi ta fita zarah mik'ewa tayi tana k'arema d'akin kallo tana mamakin dukiyar da aka zuba sannan daga bisani taje toilet domin tad'auro alwallah tayi sallar isha'i da karambani tasamu tayi alwallar tafito.

bayan ta gama sallah tana zaune saman darduma aka yi knocking d'in k'ofa nan tabada izini ashigo, hajiya sa'adatu ce tare da 'yar aikinta d'auke da kuloli, nan zarah tagaisheta,

cike da sakin fuska hajiya sa'adatu ta amsa tare da cewa yi hak'uri mun barki ke kad'ai ko?

murmushi zarah tayi tace lah bakomai mummy,  hajiya sa'adatu umurni taba mai aikinta ta aje ma zarah abinci sannan tace kiyi hak'uri da kad'aici, inma kina buk'atar kallo toh zaki iya kunnawa akwai komai a parlour, sannan kayan da zakiyi amfani da su duk suna cikin wardrobe

zarah tace toh mummy nagode, nan hajiya sa'adatu tayi mata sallama tafita tabar d'akin.

abincin zarah tazuba taci sannan tatashi tashiga toilet nan ma da karambani takunna shower tayi wanka,

bayan ta fito gaban dreesing mirror tazauna tashafa mai tana ta mamakin kayan kwalliyar da tagani jibgi guda a saman dressing mirror d'in,

koda tagama wardrobe taje tabud'e mamakine yakamata ganin jibgin kayan da ke akwai, doguwar rigar bacci tajawo bak'a tasaka sannan tadawo parlour tak'are masa kallo takunna kallo tana yi domin yarage mata kad'aici,

tana zaune tana kallo saida taji tafara jin bacci sannan takashe tare da mik'ewa tashige bedroom tafad'a saman makeken gadon da yake d'akin saida tayi addu'a sannan takwanta nan bacci yayi awon gaba da ita.


da safe knocking d'in da akeyine yatadata daga baccin da takeyi saboda tunda tayi sallar asuba takoma bacci, dakyar tabud'e idonta tare da safkowa tazo tabud'e k'ofar, cike da girmamawa 'yar aikin tagaisheta tare da cewa ga breakfast d'intanan saman dining sannan zata gyara mata d'aki,  zarah tace toh ammah kibar gyaran zanyi.

'yar aikin tace a'a ranki yadad'e aikinane kuma umurnine daga shugabata, zarah batace komai ba takoma ciki tabar 'yar aikin tana gyaran parlour.

wanka tashiga tayi lokacin da tafito tatarar har ta gyara mata bedroom d'in,

zama tayi gaban dreesing mirror tayi simple makeup sannan tatashi tabud'a wardrobe tad'auko less riga da skirt tasaka tayi mamaki sosai ganin yadda d'inki yakar6eta kamar an aunata.

bayan ta gama parlour tadawo tazauna a dining tahad'a breakfast tayi, sannan takoma bedroom tad'auko wayanta takira su mama domin sugaisa,
tana cikin wayan ne taji anbud'e k'ofar anshigo juyowar da zatayi taga hajiya sa'adatu ce dan haka tayi sallama da yaya rauda da suke waya tare da tsinke kiran,  cike da ladabi taduk'a tagaisheta.

fuskar hajiya sa'adatu d'auke da fara'a ta amsa mata tare da tambayar ta tatashi lafiya ya kuma bak'unta?.

murmushi kawai zarah tayi batace komai ba,  hajiya sa'adatu tace dafatan dai kinyi breakfast?

zarah tace eh mummy,

hajiya sa'adatu tace yauwa haka nakeso, nafison kisaki jikinki kidaina bak'unta domin nan ma gidane,
zarah tace toh mummy.


hajiya sa'adatu tace idan kin gama kisamemu a parlour muna jiranki.
zarah tace toh nama gama, 

bayan hajiya sa'adatu tabiyo suka fito parlour,  mamakine yakama zarah ganin wasu mata sanye da kaya iri d'aya su ukku sai wata mata zaune saman kujera.

tana fitowa matan suka duk'a suna gaisheta, zarah duk sai taji wani iri ganin irin gaisuwar ban girman da suke yi mata kasa amsawa tayi, nan itama zarah ta duk'a tagaishe da matar, nan ta amsa mata cikin sakin fuska tare da kallon hajiya sa'adatu tace ranki yadad'e wannan ce?

hajiya sa'adatu tace eh itace,

matar kallon zarah tayi tana murmushi sannan tamaida kallonta ga hajiya sa'adatu tace ranki yadad'e tunda dai ku customer's d'inane kawai kubiya 1.5 million, domin banason inyi jayayya da ku tunda ni nakema 'ya'yanku gyara, ko in antashi bikkinsu ninake zuwa ina musu duk abinda yadace kuma kunsan aikina, bana son intsaya ciniki da ku saisa nace abani hakan.

murmushi hajiya sa'adatu tayi tace shikenan za'a baki mudai fatanmu kifito mana da ita kinsan matar yarima ce.

dariya matar tayi tace ai hajiya tafad'a min komai dan haka bakuda matsala ai kunsan aikina cikin k'ank'anin lokaci nakeson incanzata domin daga ganin yanayinta ba zamusha wahala ba,

hajiya sa'adatu tace hakane Allah yataimaka ynz kibada account number d'in da Za'a turo miki kud'in ko kinfi son cash?

matar tace a'a kudai min transfer d'in fa wannan account number d'in da nata6a turo miki.

hajiya sa'adatu tace toh badamu sannan takalli zarah tace zarah ina fatan zaki bata had'in kai kuyi komai kugama lafiya.

zarah kanta yana sunkuye k'asa tace insha Allahu mummy.
hajiya sa'adatu tace yauwa d'iyata, sannan hajiya sa'adatu tanuna matan ukku da suke tsaye tace wad'annan kuyangin sultana bilkisune ita taturosu domin sudinga miki hidima dan haka duk abinda kikeso zasuyi miki Allah yataimaka.

gaba d'ayansu sukace Ameen.


bayan hajiya sa'adatu ta fita matar kallon zarah tayi tace sunana hajiya kubra nice wadda zan dinga koya miki kwalliya, girki,  yadda zaki dinga tafiya irin ta k'asaitattun mata sannan kula da miji, kissa  da duk wani abinda yakamata, sannan zan miki gyaran jiki sosai dan haka kid'aukeni a matsayin 'yar uwarki domin zaki kasance tare da ni natsawon wani lokaci, dan haka tun daga yau zamu fara.

zarah murmushi tayi tace toh Aunty kubra nagode.

hajiya kubrah tace kar kidamu aikinane dan haka yanzu zamu fitar da lokacin da zamu dinga gudanar da lecture d'in,

zarah cike da jin dad'i tace toh.




tun daga ranar hajiya kubrah tatsara yadda zasu dinga gudanar da komai,

tafara koya ma zarah yadda zata dinga tafiya mai aji,  ita kanta zarah yanayin tafiyar ta burgeta, batasha wuyaba wajen ganin ta koya.

idan zarah tayi wanka zama take hajiya kubra tana mata kwalliya tana gwadamata kayan makeup d'in da amfanin kowane d'aya,  idan tagama mata sai hajiya kubra tatambayeta amfanin kowane daga cikinsu, tans mamaki sosai ganin yadda kan zarah yakeja dan tana da saurin fahimta.

alkyabba ma sai da tadinga koya mata yadda zata sanyasu,  da yadda zatayi tafiya Idan tana sanye da alkyabba dan har sa kuyangi hajiya kubra take suna takema zarah baya tayi tafiya tagani.


duk bayan sallar la'asar suke zama tana koya mata yadda zatayi magana, da shagwa6a da yadda zata dinga tarbar miji da yi masa rakiya,  da yadda zata dinga narke masa kai hatta kwanciyar aure saida tadinga koyama Zarah, zarah tun tanajin kunya tana ma hajiya kubra kallon marar kunya har daga k'arshe tad'an sake mata.

girki kala-kala hajiya kubra take koya ma zarah dan a rana sai suyi girki kusan kala goma gobe kuma sai tasa zarah tamaimaita kuma tana maimaitawa lafiya lau.

A 6angaren gyaran jiki tana yi mata sosai zarah ta canza sosai dan ita kanta tana mamakin kyaun da tak'ara da haske fatarta Idan kata6a kamar jini yazubo saboda ja da tsantsi duk inda tagifta k'amshi take fitarwa medad'i .

turaren tsugunni ma ana had'amata tana yi, hajiya kubra bata wani d'irka mata magungunaba tace saboda ita budurwace da ni'imarta bata buk'atar k'ari saidai tana sata tana cin 'ya'yan itatuwa (fruits) sosai sai kuma dahuwar 'yan shila da takeyi mata akai akai


a gurguje *BAYAN SATI UKKU*

Nan da nan komai na  zarah yazanza idan kaganta sai kad'auka 'yar gidan wani mai muk'ami ce,  ita kanta hajiya sa'adatu ko da tazo taganta tayi mamaki sosai ganin canjin da tayi cikin k'ank'anin lokaci,

ita kanta zarah tana jin dad'i idan taduba taga yadda takoma saidai duk lokacin da tatuna saboda Wanda akeyi mata gyaran mutumin da baisan da zamantaba baisan wacece itaba,  duk sai taji haushi da takaici sun kamata tarik'a ji ina ma ace malam bello ne,  saidai ta6oye tasha kukanta ita kad'ai.

kusan kullum sai sunyi waya da su mama da 'yan uwanta. da sultana bilkisu dan sultana bilkisu ta WhatsApp taturo mata pics d'in kayan d'aki tace taza6i design d'in da takeso da colour d'in da takeso, lefe kuma cewa tayi zarah tayi hak'uri domin ba za'a je kai lefentaba za'a aje mata a gidanta saidai kayan da zatayi hidimar bikki za'a aika mata da su,

A cikin satin ne hajiya kubra tak'ara zage damtse wajen gyaran jikin zarah kasancewar a yanzu saura sati guda yarage ayi bikkinsu,


akwati guda aka kai gidansu zarah cike da kaya kala ashirin, kayane na azo agani da alkyabba da shoes nd bags akace wanda zarah zatayi hidimar bikkine saboda masarautarsu ba'a kai lefe saidai a ajema amarya kayanta a gidanta, kowa ya yaba sosai da kyaun kayan ana ta santinsu, ko da su yaya rauda suka kira zarah a waya nan suke fad'amata kayan da aka kawo mata, zarah dai bata damuba saboda ita aganinta basu take buk'ataba burinta abarta taje taga iyayenta. da 'yan uwanta.

ko da sultana bilkisu tayo mata waya nan take tambayarta idan akwai events din da takaeso tayi, zarah cewa tayi bazatayi komai ba ko ma I.V card bazata rababa domin batada abokai sosai, sultana bilkisu bata takuramata ba saboda ko da tatuntu6i yarima da maganar shima cewa yayi ba dai halarci party ko d'ayaba, sultana bilkisu kyalesa tayi tace tunda dai ka amince da auren ai babu matsala.



kud'i sosai yarima suhail yadunk'ula yaba sumayya domin tayi amfani da su, gimbiya sumayya runtse ido tayi tace bazasu ishetaba, dan haka saida yak'ara mata sannan tatafi tana cewa idan ban amsaba ai wata zakaje kaba.

sultana bilkisu ganin har bikki saura sati guda ammah yarima baidamu da yaje yaga matar da zai auraba ko da sau d'ayama baya maganarta ko ma ita tayi masa maganarta sharewa yake  dan haka wayarta tajawo takirasa tace yasameta tanason magana da shi.

sultana bilkisu ko da yazo matsa ma yarima suhail tayi akan dole sai yaje yaba zarah kud'i wad'anda zatayi hidimar bikki da su, yarima saida yaga ran ummi yana neman ya6aci sannan ya amince zai je gobe idan Allah ya kaimu.

yarima ko da yakoma 6angarensa zama yayi saman kujera takaici duk ya cikasa, tsaki yaja yace sai asa mutum yayi aure kuma amatsamasa dole sai yaje, wayarsa yajawo yakira shaheed bayan shaheed yayi picking yace ranka yadad'e ina mik'o gaisuwa.

tsaki yarima yaja yace kaiwai bakasan kayi ma mutane sallama ba.

dariya shaheed yayi tare da yin sallama,
nan yarima ya amsa masa, daga nan kuma bai k'ara cewa komaiba.

ganin yarima baida niyan yin magana yasa shaheed yace kaifa tsiyata da kai sai kakira mutum kuma kakasa yin magana.

tsaki yarima suhail yaja yace gobe idan Allah ya kaimu kashirya muje wajen wannan yarinyar ka san ummi ce ta matsamin sai naje dole.

cike da jin dad'i shaheed yace Allah yakaimu, _domin shima yana burin ganin matar da yarima zai aura_, chan sai yace kai yarima bakada dama yanzu matar da zaka aurace kake cema yarinya?

tsaki yarima yaja tare da kashe wayarsa domin shi yanzu haushin kowa ma yakeji.

murmushi shaheed yayi tare da bin wayar da kallo yace yarima kenan jin kanka ya yi yawa.




_Comments_  
      *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
?👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_I dedicated this page to my fan's, thank you for love nd concern, I really appreciate it😍😘_

*PAGE* 2⃣1⃣

Da daddare sultana bilkisu takira zarah bayan sun gaisa nan take fad'amata zuwan da yarima zaiyi gobe,

zarah saida gabanta yafad'i ammah tadake tace ummi Allah yakaimu.

A ranar kasa baccin kirki tayi, tunani da fargaba duk suka cikata.

wanshe kare shaheed shiryawa yayi yanufi gidan yarima, lokacin da yaje part d'in yarima nan guards d'insa suka gaishesa sannan d'aya yashiga yasanar da yarima zuwan shahid nan yarima yabada izini  abarsa yashigo.

ko da shahid yashiga parlourn tsaye yayi bakin k'ofa yana kallon yarima da yake kwance saman 3 seater cike da mamaki yace haba yarima kaifa kacemin after la'asar zamuje ammah jibeka baka shiryaba.

yarima batare da ya d'ago kai ya kallesaba cike da rashin damuwa yace ina kenan?

cike da jin haushi shshid yace au kana nufin ka mance inda zamuje?  yanzu saboda Allah amaryartaka ce kamance da ita ko me?

ta6e baki yarima yayi saboda shi shaf ya ma mance da maganar zuwan da zasuyi wajen zarah.

shahid jinjina kai yayi yace lallai yarima ka cika d'an wulak'anci.

harara yarima yawurga masa yace toh ina ruwanka ai sai kazauna kajirani inshirya,

dariya shahid yayi yace ba fa ruwana ranka yadad'e yanzu dai kaje kashirya kafito muje dan Allah kar kadad'e.

ko kallonsa yarima baiyiba yashige bedroom d'insa.

tashi shahid yayi yakunna kallo sannan yabud'e freezer yad'auko maltina yazauna yana sha yace kafin wannan d'an rainin hankalin yafito.

bayan minti ashirin yarima suhail ne yafito sanye cikin dakakkiyar shaddarsa blue wadda tasha aiki,  kansa sanye da hula kalar shaddar, kamshin turarensane ya ankarar da shahid daga kallon da yake dasauri yajuya yazuba masa ido yana kallonsa yace kai yarima wannan kyau haka saikace yau zaka angwance?  gaskiya kayi kyau sosai natabbata ita kanta amaryar bazata ganekaba kar fa karikita d'iyar mutane,

yarima suhail wayoyinsa yad'auka batare da yace ma shahid komai ba yawuce zai fita,

dasauri shahid yamik'e yabi bayansa, ko da suka fita nan guards d'insa suka take masu baya, wajen da aka tanadar musu motocin da zasu fita da su suka nufa tun kan su ida isa naga anbud'e musu bayan wata dank'areriyar mota bak'a da take tsakiyan sauran motocin, saida suka shiga aka maida aka rufe sannan cikin sauri guards d'in sukaje suka shiga sauran motocin.


A chan 6angaren zarah Aunty kubra sata tayi tashirya, sosai tayi kwalliya had'ewa tayi cikin material Black colour mai ratsin marron nan tamurza d"aurin kallabinta tare da yafa veil marron, takalmanta da jakkarta ma duk maroon colour ne.

ba ita kantaba hatta su Aunty kubra sun yaba ma kyaun da zarah tayi, 6arin turaruka akayi mata sosai a jikinta.


ko da su yarima suka iso mai gadi hangame musu gate yayi motocinsu a jere suka shigo; dasauri guards d'insa suka fito daga cikin motocin da suke sukazo suka bud'ema su yarima murfin mota, ahankali yasafko k'afarsa sannan daga baya ya ida fitowa daga cikin motar, cike da tafiyarsa ta k'asaita yake takonsa shaheed yana gefensa nan wasu daga cikin guards d'insa suka take masu baya har part d'in mummy sa'adatu, daga wajen parlour guards d'in suka tsaya inda yarima suhail da shaheed suka shiga ciki da sallamarsu lokacin mummy sa'adatu tana shirin tafito taje ta tarosu,

ganinsu yasa tayi murmushi tare da cewa marabanku da zuwa, yarima murmushi kawai yayi shaheed ne yace yauwa mummy sa'adatu shidai shaheed kansa a d'aure yake har suka zauna domin yayi tunanin d'iyar mummy sa'adatu ce yarima zai aura, shidai yarima daman ummi ta fad'amasa zarah tana nan gidan hajiya sa'adatu kuma ta ce yabiya gidansu zarah yagaishe da iyayenta saisa baikawo komai a ransaba.

bayan sun zauna nan suka gaisheta cike da girmamawa, ta amsa cike da kulawa tare da tambayarsu mutanen gida sukace kowa yana lafiya,  nan da nan aka cika musu gabansu da kayan tand'e-tand'e da shaye-shaye, mik'ewa hajiya sa'adatu tayi tare da cewa son kugama cin abinci sai inkira muku ita.

shaheed ne yatsiya musu ruwan inibi yamik'a ma yarima sannan yace mummy wlh a k'oshe muke abincin bazai shigaba.

murmushi mummy sa'adatu tayi tace ku daman ina rik'e da ku bakwacin abincin ginnan, kokuma ma ai bazuwa kukeba duka wannan zuwanku na ukkune shima duk ta dalilin umminku, bakwason zumunci ko?

yarima suhail murmushi yayi yace insha Allahu zamu gyara, tace kullum wak'ar kenan bari inje inkira muku ita toh tunda kunk'i cin abinci.

ko da hajiya sa'adatu tafita shaheed apple yad'auka yana ci tare da kallon yarima da yake rik'e da cup d'in ruwan inibi yace kasha mana,

yarima batare da yayi maganaba ya aje cup d'in tare da jawo wayarsa yana operated d'inta, shaheed murmushi yayi tare da ci gaba da cin Apple d'insa.

Hajiya sa'adatu lokacin da tashiga part d'in da su zarah suke tun daga bakin k'ofa tafara washe baki tana kai daughter wannan irin kyau haka?

zarah dai murmushi kawai tayi tare da sunkuyar da kanta domin gabanta fad'uwa kawai yake,

Hajiya sa'adatu tace yauwa toh yanzu kitashi kije parlour na suna chan suna jiranki.

kallon Hajiya kubra zarah tayi, Hajiya kubra tace kitashi mana.

idanuwanta nan suka ciko da k'wallah, Hajiya kubra tace a'a zarah dan Allah kar kiyi kuka ki6ata kwalliyarki.

zarah murmushi tayi tace Toh Aunty kubra, nan kuyangin da ummi ta aiko mata da su suka take mata baya tafiya take cikin takunta mai aji hango motocin su yarima da tayi da sauran guards d'insa saida gabanta yasake fad'uwa duk tsoro da fargaba suka cikata har ta isa parlour nan guards d'in da suke tsaye wajen k'ofar suka gaisheta ahankali tabud'e labulen dakin tashiga inda tabar kuyangin tsaye waje.

cikin 'yar siririyar muryatarta tayi sallama, shaheed ne ya amsa mata tare da d'ago kai yakalleta zaro ido yayi yace wow masha Allah matarmu bismillah mana.

ahankali zarah tatako tazauna saman kujerar da take opposite d'insu cike da nutsuwa tagaishesu, shahid ne kawai ya amsa mata domin yarima har lokacin bai d'ago ya kalli inda takeba barema asa ran zaiyi magana.

Shaheed kallonta yayi yace amaryarmu gaskiya kin had'u, dafatan mun sameki lfy? , murmushi zarah tayi tace lafiya lou ya gida?

shahid yace kowa yana lafiya,  sannan yamaida kallonsa ga yarima da yake zaune kamar baisan abinda akeyiba, murmushi shahid yayi yace ranka yadad'e kayi shuru bakace komai ba,

Zarah ahankali tad'ago kai takalli mutumin da tunda tashigo baiyi maganaba dannar wayarsa kawai yakeyi saida gabanta yafad'i, batare da yad'ago kai ya kalletaba yace akawai event d'in da zakiyi ne?

shuru zarah tayi tana kallonsa, ahankali yarima yad'ago kai yakalleta nan suka had'a ido, dasauri yajanye idonsa daga kallonta yace kamar nawa kike buk'ata inbaki?

zarah dakyar tabud'e baki tace bana buk'atar ko naira, ta6e baki yarima yayi, ganin haka yasa shahid yace a'a amarya kar kice haka kifad'i yadda kike buk'ata nagama kamar kunyata kukeji kowa yakasa magana bari inbaku waje kuyi magana.

Yarima yace no nima ai tafiya zanyi yanzu, harararsa shaheed yayi yace toh ai sai kugaisa dan naga ko gaisawa bakuyi ba kar ace ni nahana nabarku lafiya, yana gama fad'in haka yaficce yabar musu d'akin,

nan d'akin yad'auki shuru ba'ajin motsin komai zarah wasa kawai take da yatsun hannunta, jin baida niyar yin magana yasa tad'ago kai takalli yarima dayake ta dannar wayarsa kamar baisan da zaman mutum ba a wajen,  zarah wani k'ululune taji ya tsaya mata a mak'oshi, janye idonta tayi ga kallonsa mamakinsane yacikata cikin ranta tace mutumin nan ko dai kurma ne? chan wata xuciyantace toh kuma ai yanzu taji ya yi ma d'an uwan nasa magana, chan da tagaji da shurun ahankali tace ina wuni?

shuru yarima yayi bai amsaba jin shurun da yayi yasa tad'auka baijitaba nan tak'ara d'ago kai takallesa har lokacin dannar  wayarsa yake, sai a lokacin ya amsa mata cikin muryarsa mai dad'i, zarah mamakine yakamata domin bata d'auka miskilancin nasa yakai hakaba, ahankali tace lallai wannan mutumin d'an wulak'ancine, jiyo muryasa tayi yace magana kikayi?

cike da k'ulewa tace ni bance komaiba,

d'ago kai yarima yayi yakalleta kallo d'aya yayi mata yad'auke kai tare da mik'ewa tsaye, takawa yayi yaje inda take ya aje mata cheque a gefenta sannan yace gashinan idan basu ishekiba sai kiyi magana.

zarah ida k'ulewa tayi ganin baima jin zai iya bata saima ajemata yayi, cike da jin haushi tace kabarsu kawai ba abinda zanyi da su.

yarima kallonta yayi cikin rashin damuwa yace indai nafitar da kud'i bana maidasu idan basu ishekiba zaki iya yin magana, yana gama fad'in haka yawuce yafita yabar d'akin,

tsaki zarah taja tare da mik'ewa tabi bayansa domin suyi sallama da shaheed,  ganinta yasa shaheed yatafo wajenta yana murmushi yace amaryarmu yanzu nake shirin zuwa muyi sallama.

Murmushi itama tayi tace nima cewa nayi bari nazo muyi sallama,  yarima gaba yayi aka bud'e masa mota yashiga saida suka iso wajen motar sannan zarah tayi musu sallama takoma ciki tana mamakin halin yarima, cikin ranta tace ashe akwai babban aiki a gabana.

ko da su yarima suka kama hanya shahid kallon yarima yayi yana murmushi yace gaskiya yarima ka iya za6en mata kaga yadda kukahad'e kukai matching? yarima batare da ya kallesaba yace bawani dacewa ai wlh kai yakamata ma ace anma dole ka yi aure, dariya shahid yayi yace nima fa abin yana damuna ganin har kana shirin yin na biyu ammah ni ko d'aya banda ita, yamitsa fuska yarima yayi yace nima ba ason raina nayi aure yanzuba dan banma shirya yinsaba by my age,  kaduba kaga duka yanzu fa 28yrs ammah mata har biyu tsaki yarima yaja cike da takaici yace ina ma amfanin hakan.

dariya shaheed yayi yace ai abun jin dad'ine hakan kuma matsayinka ya kai hakam, nima insha Allahu kwanannan zan faso zan baku mamaki,

ta6e baki yarima yayi yace wajen surutunka kayo yarinya ko?

shahid gyara zamansa yayi tare da cewa haba dai kabari zakasan ko wacece nan gaba jira nake agama wannan hidimar auren naka nima in6ullo kai dan bama zanso asa sama da wata d'ayaba,

yarima suhail jingine kansa yayi da sit din da yake zaune tare da lumshe idonsa,

ganin haka yasa shahid yaja bakinsa yayi shuru dan yasan maganarce ta ishi yarima.

tunda suka kama hanya basu zarce ko inaba sai gidansu zarah saboda tun dare sultana bilkisu ta kira iyayen zarah ta shaida musu yarima yana nan zuwa zai gaishesu, dan haka tun da safe suka dinga hidindimu kaji shidda baba yasiyo akayi pepper da ukku aka soya ukku, had'add'ar wainar shinkafa su mama sukayi da miyar ganye sannan suka had'a kunun aya wanda yasha madara, bayan sun gama duk suka shirya suna jiran zuwan yarima dan su Aysha sun k'osa sosai suga mijin zarah.

A gaban gidansu zarah sukayi parking d'in motocin dasauri guards d'in sukafito daga motocin da suke ciki sukazo suka bud'ema su yarima k'ofa tare da cewa ranka yadad'e nan ne,

yarima batare da yafitoba yadinga k'arema gidan kallo cike da mamaki, shima shahid mamakine yacikasa ganin gidan da yarima yanemi aure.

malam musa da yake zaune cikin gida jin k'arar mota yasa yakalli su mama yace ina tunanin sun iso bari inje induba,
cike da jin dad'i Aysha tace yauwa Allah yasa sune.

malam musa ko da yafito yaga jerun motoci cike da fara'a yanufo wajen,  ganinsa yasa yarima yafito daga motar, nan guards d'insa suka shiga gaishe da malam musa.

malam musa hannu ya mik'a ma su yarima suka gaisa yace maimakon kushigo sai kukayi tsaye?  shaheed ne yace daman yaro muke nema mu aikasa yayi mana sallama da kai,
malam musa yace ayyah Allah sarki toh  bismillanku.

batare da sunyi musu ba sukabi malam musa suka shiga har cikin soron gidan,  saman tabarma suka zauna.

cike da girmamawa suka gaishe da malam musa ya amsa musu tare da tambayarsu mutanen gida, shaheed ne yace suna lafiya lou, sunce agaisheku

malam musa yace muna amsawa sannan yakalli yarima da tunda yagansa yagane shine mijin da zarah zata aura, malam musa yace ya su mahaifiyartaka?

murmushi yarima yayi kansa yana sadde a k'asa yace lafiya lau suke.

malam musa yace toh masha Allah, mik'ewa yayi yace ina zuwa nan yashiga gida.

bai dad'e da shigaba yafito tare da su Rauda da suke d'auke da kuloli da sallamarsu suka shigo, su yarima suka amsa musu gabansu suka aje kulolin,  tare da gaishesu cike da sakin fuska su yarima suka amsa, malam musane da yake tsaye yanuna rauda yace wannan itace yayar amarya,  kallonta yarima yayi yana murmushi yace sannu yayarmu.

itama rauda murmushin tayi tace yauwa k'anena.

Aysha ce tayi karaf tace nikuma nice k'anwar Aunty zarah kuma autarsu.

gaba d'ayansu dariya sukasa mata banda yarima da yayi murmushi kawai, shahid yace tun ba'a tambayekiba?

yarima suhail yace ina ruwanka ai ni tafad'a mawa ko k'anwata?

'yar dariya Aysha tayi tace eh yayana,  ammah ai kaine angon namu ba wannan ba (tanuna shaheed)

shaheed yace nine mana.

Aysha tace chab gaskiya wannan nafiso yakasance mijin yayata.

murmushi yarima yayi yace saboda me?

Aysha tace saboda kunfi dacewa da ita,
yaya rauda tace zanci gidanku Aysha banason rashin kunya.

shaheed yace a'a babbar yaya kibarta kawai tunda tace bamu daceba sai inhak'ura inbar masa.

Aysha tace A'a ni ba haka nake nufiba kaima ka dace da yayata sosai.

shaheed kallon yarima yayi  yana murmushi yace toh ka dai ji abinda tace kaje nabarmaka ita.

shima yarima murmushi yayi yace k'yalesa my sis ai nine angon ba Shiba tsokanarki kawai yakeyi.

cike da jin dad'i Aysha tace yeahhh wlh naji dad'i,  murmushi kawai suhail yayi batare da yace komai ba.

daidai lokacin abbah yafito daga cikin gida d'auke da swan water yace kutashi kubasu waje suci abinci mana.

atare suka mik'e suka shige gida, abbah ajiye ruwan yayi yace dan Allah kuci abinci.

shaheed ne yace Alhmdllh abbah wlh a k'oshe muke.

abbah yace gaskiya ba zanji dad'in hakan ba nasan kunfi k'arfin abincinmu ammah ko yayane kusanya albarka.

yarima ne yakalli abbah yana murmushi yace kar kadamu abbah zamu ci.

abbah yace yauwa gaskiya naji dad'i bari inshiga ciki kafin kugama.

Bayan abbah yashiga gida shaheed ne yabud'e kulolin cike da jin dad'i yace yarima ur best food ne fa,

yarima batare da yakalli abincinba yayi murmisho, shaheed ne yayi serving d'insu ya aje ma yarima nasa a gabansa.

yarima waina biyu yaci tayi masa dad'i sosai saida ya jinjina ma k'ok'arin da iyayen zarah sukayi wajen tarbarsu,   kunun ayan dai saida yashanye 1 cup kasancewar yana sonsa sosai, shidai shaheed loda ma cikinsa kawai yake yana santi har yaso yaba yarima haushi.

bayan sun gama abbah yadawo nan yazauna suna d'an ta6a hira kad'an-kad'an sannan yashirga da su cikin gida suka gaishe da mama cike da girmamawa, da zasu fito yarima dubu d'ari yamik'a ma Aysha yace sunyi hidimar bikki, da fari k'in kar6a tayi dan baba yahana saida yarima yace shifa ba dan wani abu yabataba kawai saboda tayi kwalliyar bikkin yayarta da za'ayi a matsayinta na auta, dariya sukayi sannan sukayi masu rakiya har wajen mota suna godia, cike da jin dad'i domin suna ganin zarah tayi sa'ar miji mutumin kirki.

A cikin mota shaheed kallon yarima yayi yace gaskiya mutanen nan suna da mutunci sosai daman daga ganin zarah kaga mutuniyar kirki ashe wajen iyayenta tagada.

yarima a tak'aice yace danginta suna da kirki sosai.

shahid Jin maganar da yarima yayi yasa yayi murmushi yace Allah yabarmin kai yarimana.

kud'in da yarima yaba zarah nan tabarsu inda ya aje mata saida hajiya sa'adatu tashiga tagani sannan takaima zarah,

zarah ganin cheque din 300,000 saida ta tsorata tace nashiga ukku ina zan kai wad'annan mak'udan kud'in, daga k'arshe yanke shawara tayi tace kawai iyayenta zataba idan takoma gida.

Agurguje ana sauran kwana ukku bikki sultana bilkisu ta aika da mota aka d'auki zarah aka maidata gida, kasancewar tun ana saura kwana hud'u hajiya kubra takoma gidanta.

mummy sa'adatu taso abarmata zarah har sai ranar bikki ammah sultana bilkisu tace a'a abarta takoma wajen iyayenta tunda suma suna buk'atarta a kusa.

ko da aka maida zarah gida 'yan gidansu basu ganetaba mama ce kawai taganeta itama dariyar zarah tagane.

murna sukayi sosai da ganinta mamaki yacikasu ganin yadda takoma kamar ba itaba dan komai nata ya canza dan Aysha ma cewa tayi an canza mata yaya anbata 'yar gayu.


zarah kud'in da yarima yabatane taba abbah tace ayi gyaran gida, da fari k'in kar6a abbah yayi yace taje tayi hidimar bikki sauran kud'in neman aurantama suna nan zai d'auko mata,  zarah tace a'a ta bar musu

abbah yace ai hak'intane, zarah saida tasa ma su abbah kuka sannan suka kar6i 300,000 d'in yace sauran kuma natane,

Aysha da ta zauna labarin yarima kawai takeba zarah irin kirkinsa da rashin girman kansa,  ita dai zarah saidai tayi murmushi cikin ranta tace ku dai kukaga haka ammah inba ji da kai ba me ya aje...



_Comments_
     *nd*
_Share_



_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔


*PAGE* 2⃣2⃣

Abbah gyara gidansa yayi sosai akayi masa fenti yacanza ma mama kujerun d'akinta,  d'inkuna kala ukku-ukku yayi ma su mama.

khairy ko da tazo taga zarah rikicewa tayi cike da murna tace sis anya kuwa kece ba canza mana wata akayiba mai kama da ke?

murmushi zarah tayi tace toh indai ana canza mutum toh nima an canzani,

khairy tace wlh kuwa dan ma bakiga yadda kika koma wata 'yar gayuba,  ke ni ya maganar rabon invitation card gashi saura kwana biyu bikki ammah ba Wanda muka gayyata.

ta6e baki zarah tayi tace ba wanda zan gayyata domin ba abinda zanyi ayi bikkin kawai a haka.

khairy rik'e baki tayi tace kai zarah ammah dai bakida mutunci yanzu saboda Allah bazaki gayyaci kowaba?  gaskiya bai daceba ace kamarki zaki auri yarima guda ammah ba ayi wani shagaliba,

zarah cikin rashin damuwa tace ba fa zanyiba kema kinsan auren nan zanyisane kawai ba dan ina soba.

zaro ido khairy tayi tace zarah kar dai kice min har yanzu baki daina son malam bello ba? yarima fa yafisa komai.

murmushin takaici zarah tayi tace har yau har gobe ina son malam bello,  saidai idan nayi aurene zan daure inga na nisantar da zuciyata daga tunaninsa gudun kar injefa kaina ga halaka.

dariya khairy tayi tace kin dai karanta a islamiyya kuma kinsan babu kyau ehe.
ke wlh yaci ace kin cire son malam bello a ranki kifad'a sabuwar soyayya.

murmushin takaici zarah tayi tace kar fa kimance da tsohuwar zuma ake magani.

dariya khairy tayi tace injiwa?  ai itama sabuwar zuman tana magani wani lokacin ma tafi wata tsohuwar, zamu dai zuba ido mugani.


su Hajiya sa'adatu sune ummi tasa sukaje sukayi jeran zarah, part d'aya aka fitar mata dashi daga cikin gidan yarima suhail,
d'akine mai d'aukeda parlour nd 2 bedrooms sai kitchen, kaya aka zuba mata na gani na fad'a a duka bedrooms d'inta sannan aka tsara mata parlourn ta yayi gwanin kyau,  kitchen d'inta cika mata shi akayi da kaya, antsara ma zarah part d'inta sosai kamar na wata d'iyar wani attajirin mutum.

Abban sumayya ma canza ma d'iyar tasa kayan d'aki yayi masu kyau da tsada,  sumayya taji dad'i sosai sai a lokacin ta safko daga fushin da take da mahaifinta akan auren da yaje yanemo ma yarima.



ana gobe bikki sultana bilkisu ta aiko da mota akazo aka d'auki zarah aka kaita wani hadad'en shagon gyaran jiki wanda sai amaren da suka amsa sunansu suke zuwa.

saloon akayi mata sannan aka zizira mata k'unshinta tayi kyau sosai.

gidan sarautar hidima ake ta gani ta fad'a ko da kowa 6oye murnarsa yake a ciki,  ammah sumayya da mahaifiyarta  a fili suke nuna basason auren.

gimbiya rahma ita take zuwa tana kwantar ma da sumayya hankali tun da bikkin ya matso kasancewar itama ba'a son ranta yayan nata zai k'ara aureba saboda tana ji da sumayya sosai tun k'uriciyarsu suke abota,  taso ace ummi ta hanasa yak'ara auren ammah ummi tace babu ruwanta ita taje ta samesa tayi masa magana,  jin haka yasa taja bakinta tayi shuru dan tasan bama zata iya tunkarar yarima da maganar ba.

________________

zarah bayan angama mata gyara around 3:30pm aka maidota gida, mamakine yacikata ganin mutane da suke shiga gidansu, kanta bai ida d'aurewaba saida tashiga cikin gida taga kowa ya shirya, Yaya rauda ce tafara hango zarah tace yauwa ga ma tanan ta dawo.

dasauri khairy da Aysha suka zo wajenta sukace tun d'azun muna ta jiranki please kizo kishirya lokaci yana k'urewa, zarah cike da mamaki tace ban fahimcekuba me zanyi?

jawota sukayi suka nufi d'aki da ita suna cewa koma dai minene kizo dai kishirya.

zarah fizge hannunta tayi tace wai mi za'ayi? ya naga kowa ya shirya?

dariya aysha tayi tace kai yaya zarah wa'azi fa za'ayi?

zarah da kanta ya ida d'aurewa tace wa'azi kuma?  wa yashiryasa?  muryar yaya rauda sukaji tace mune nan muka shiryasa mun gayyaci mutane, munga idan muka biye ta naki toh babu abinda zakiyi dan haka kiyi sauri ki shirya.

zarah turo baki tayi tace kai dan Allah yaya rauda meyasa zakuyi min haka?

yaya rauda d'aure fuska tayi tace isarmu ce tasa mukayi miki haka dan haka kiyi sauri kije kiyi wanka ko inje inhad'aki da mama.

zarah jin za'a had'ata da mama yasa cikin sauri tawuce taje ta shiga wanka tana fushi.

bayan ta fito kwalliya akayi mata sosai sannan aka d'auko mata material ash nd black colour tasaka sai aka d'aura mata alkyabba black colour mai ratsin ash daga saman kayan, tayi kyau sosai ya yaba da kyaun da tayi.

su yaya rauda ne suka fito da ita, a tsakar gidansu ya cika da jama'a a nan aka zauna akayi wa'azi, manyan malamai mata guda biyu sukayi wa'azin,  wa'azin aure mai ratsa jiki inda aka jawo musu ayoyi da hadissai,  ba zarah ba hatta sauran mutanen da suke wajen saida suka koka.

bayan angama su yaya rauda suka raba kayayyakin da  suka tanada zasuba mutane,  zarah dai mamakine yacikata cikin ranta tace nasan zaku aika tunda dai khairy tamatsa sai anyi wa'azi, chan kuma sai tayi murmushi cikin ranta ta ji dad'in hakan.

nan mutane suka watse kowa yana fad'in albarkacin bakinsa.


_*RANA BATA K'ARYA SAIDAI UWAR 'DIYA TAJI KUNYA*_

A yau juma'a masallacin juma'a da yake anguwarsu zarah cike yake da jama'a dan saida aka rasa masaka tsinke saboda yawan mutane anguwar cika tayi sosai dan har memartaba saida yahallara wajen.

Bayan anfito masallacine aka d'aura auren *Yarima Suhail Ahmad Umar* da *amaryarsa Fatima Zarah Musa* akan sadaki naira dubu d'ari,

a chan tsakiyar taron nahango ango da shaheed, ango yasha kyau har ya gaji sanye yake cikin shaddarsa fara wadda tasha aiki da bak'in zare,  hularsa da takalmansa duka jajayene nan mutane sukaita zuwa suna gaisawa tare da yi masa Allah yasa alkhairi shidai yarima yana murmushi ne kawai dan saboda memartaba kawai ya amince yazo d'aurin auren.

takeaway aka shiga rabama mutane kowa yaci yasha aka watse cike da farin cikin auren nan masu tsegumi sunayi masu murna nayi.

gidan su zarah cike yake da 'yan uwa da abokan arzik'i abbah yayi k'ok'ari sosai wajen ganin anyi abinci na azo gani wanda kowa zaici yasan yaci hatta naman kaji sunyi kuka sosai a ranar.

A chan tsakiyar gadon mama nahango zarah zaune ta ci kwalliya ta had'e cikin less d'inta pink colour mai ratsin blue head ne blue a saman kanta tayi kyau sosai sai sharar k'wallah take gefenta su yaya rauda ne da Khairy suna lallashinta dan ita gani take duk wasane auren saida tajiyo hayaniyar mutane suna gud'a ana and'aura aure sannan ta tabbatar dagaskene.

mama ce tashigo d'akin taganta cikin wannan halin tace haba zarah miye abun kuka hak'uri zakayi domin shi aure haka yake.

zarah cigaba tayi da sharar k'wallarta ganin haka yasa mama taficce tana fad'a,

zarah da take kuka jin sallamar mutane da tayi yasa tashare fuskarta cike da mamaki take kallon jama'a buya guda da sukazo, nima kaina natsorata saida najawo My Hafnan muka koma gefe nace kin gane mutanen nan da sukazo?

hafnan harararsu tashiga yi tace hmm nagane wasu man wacchan tawagar masu pink d'in atamfa 'yan group d'in *yarima suhail fan's* ne,  sai tamurga baki tare dagwada masu anko d'in blue tace wannan kuma na *Hibbatullah* fan's ne, sannan sai masu red d'in anko *Intelligent writer's fan's* ne, sai kuma tanuna wasu tace masu green *Nazir* fan's ne,  masu coffee kuma *Aufana true fan's* da *sainah true fan's*, Masu navy blue kuma *Zaynav mtz fan's*  sannan *Mummyn khalil fan's*, *Surbajo fan's*, *Sadnaf true fan's* ke da dai sauransu.

rik'e baki nayi nace chab nashiga ukku my hafnan yanzu saboda Allah duk wa yagayyaci wad'annan uwayen mutanen?  murya muka jiyo daga bayanmu ance yoh wa fa yagayyacesu k'wak'wace takawosu kawai,  juyawar da zanyi sai ganin My blood sis aufana da mummy sainah ummun meenal nayi, dafe kai nayi nace nashiga ukku kukuma wace k'wak'war takawoku?  My blood hararata tayi tace yoh mu da tun d'azun muna nan damu akaci aka sha,  su Mummyn afrah, meenah abbah, k'anwarki janaf, haleemah H.A.S, sis Aysha ke dama sauran intelligent writer's duk suna nan yanzu haka sunje kar6o mana nama kinsan mummy zill da 'yar mutan zariya basa barin nama, 

had'e fuska nayi nace toh wlh wannan abun kunyar ba da sis nerja'art ba dole kowa yazo yakama gabansa babu wanda zai zauna,  nan nakorasu nace muje inda muka fito nima nafasa zaman,  kallon zarah sukayi sukace toh gimbiyarmu sai mun dawo wani taron,

murmushi kawai zarah tayi bayan sun fita takalli yaya rauda tace wad'annan masoyanmune fa nasan basu ganekuba saisa, yaya rauda dariya tayi tace haba saisa naga rawar kansu yayi yawa saikace Maman sadiq da mrs dawud😜 ke wani abun ma sai ummie adnan da mugirat ammah basukai mummyn khadija ba, aini naji dad'i da aka korasu.


Bayan sallar magrib wanka akasa zarah tayo bayan ta fito hafnan nd Aufana makeover ne suka zauna suna shirya amarya,  kwalliya sukayi mata sosai wadda ita kanta zarah da takalli madubi saida tayaba kanta, atamfa tasa riga da skirt sun mata cif sannan aka murza mata d'aurin kallabi inda kyaun nata yak'ara bayyana.


bayan sallar isha'i aka aika da motoci biyu d'aya wadda amarya zata shiga,  d'aya kuma na kuyangin da sukaje sutafo da itane saboda cewa akayi babu wanda za'aje da shi kai amarya, amarya kawai za'a tafi da ita.

wajen su mama aka kai zarah sukayi mata nasiha sosai  mai ratsa jiki duk dauriyar mama kasa daurewa tayi saida tayi kwallah, zarah tana kuka aka rik'ota aka fito da ita.


'yan unguwa sunji haushi sosai domin kowa yaci burin yaje yagane ma idonsa, wasu kuma burinsu suje suga sarki, wasu kuma suje suga yarima,  wasu kuma burinsu suje sugano kwakwaf,  Aysha kuka tayi sosai dan taso tabiyo 'yar auwartata, dole suka hak'ura suna gani aka fito da amarya an nad'eta da lifaya, jakadiya ce rik'e da zarah sai kuyangi biyu da suka take musu baya ahaka aka shigar da ita mota tana kuka.

nan 'yan unguwa wasu sukaita tsogumi ai iyayen zarah saboda son abun duniya suka siyar da d'iyarsu babu wanda yasan inda za'a kaita

haka akaita tafiya ita dai zarah ji take kamar ba a mota takeba saboda wani irin k'amshi mai dad'i da yake ratsata da d'in motar,  bata d'ago kantaba har alokacin hawaye take tana tausayin kanta da takaicin iyayenta da suka amince suka aura mata wanda bata so.


ko da aka isa da zarah gidan sarautar tana ji bushe-bushe suna ta tashi batasan lokacin da aka tsayaba saidai gani tayi anbud'e mata k'ofa

nan jakkadiya tace ranki yadad'e kifito anzo,  zarah ahankali tasafko k'afarta daga motar har a lokacin fuskarta na a rufe dasauri bayi da kuyangi suka zube k'asa suna k'awar gaisuwa angaishe da gimbiya angaishe da tauraruwar mata takawarki lafiya gimbiya, zarah duk jin abun tayi wani iri saboda bata saba jin hakaba sai a film tunda ita ba zuwa gidan sarauta takeyi ba ammah yau itace ake gaishewa ta bangirma.

muryar jakadiya tajiyo tana cewa ranki yadad'e muje mana,  jakkadiya da wata kuyanga suka rik'eta inda sauran kuyangi da bayi suka zagayesu aka sa su tsaka ahaka ake tafiyar har aka isa turakar dada,  duk mutanen da ke wajen taga sun duk'a suna kwasar gaisuwa a wajen dada,  zarah har zata duk'a dada tace a'a akawota nan tazauna.

jakkadiya takamota takaita har kusa da kujerar da dada take zaune, zarah dasauri tazauna k'asa har a lokacin fuskarta a kulle take kyarma kawai take domin gani take kamar a mafarki.

nan duk sauran kuyangi da bayi suka bar d'akin, d'akin yad'auki shuru daga dada sai zarah,  dada ce tayi gyaran murya tace barkanki da zuwa wannan gida namu mai albarka fatanmu kizauna da kowa lafiya, domin kinsan gidan sarauta sai anji ank'i ji, agani ak'i gani, kizauna da kishiyarki lafiya indai kikabi sumayya sau da k'afa toh zaku zauna lafiya domin ita batada matsala ko da kema da alama daga ganinki ba zakiyi matsalaba.

itadai zarah sauraren dada take batace ufanba har a lokacin kanta na sunkuye a k'asa ahaka har dada tagama nasiharta sannan takira jakadiya domin tazo tatafi da zarah 6angarenta,  zarah duk'awatayi cikin muryarta da tadashe tace nagode sosai insha Allahu ba zan kawo muku matsalaba zan zauna da kowa lafiya,

dada taji dad'in lafazin zarah a karo na farko da taji ta d'an burgeta domin taga da alamu zatayi hankali.

dada tace zaku iya tafiya, jakadiya tace to ranki yadad'e muje,

zarah mik'ewa tayi suka fito nan duk sauran kuyangi suka take musu baya suka nufi part d'inta, 

bedroom d'inta aka wuce da ita aka zaunar da ita bakin gado sannan jakkadiya tace ma kuyangi sutafi nan kuyangi suka zube suka kwashi gaisuwa wajen zarah itadai zarah tana jinsu batace komaiba daganan suka mik'e tare da cewa afito lafiya gimbiya, daganan suka fita daga d'akin.

nan  jakkadiya tashiga toilet tahad'a mata ruwan wanka wanda yasha turaruka sannan jakkadiya tafito tad'auko towel  tarussuna ta aje sannan tace ranki yadad'e ruwan wankanki sun had'u zaki iya shiga,

zarah tace a'a ba ma sai nayi wankaba,

jakadiya tace kigafarceni ya shugabata umurnin sultana ne nake cikawa kuma wannan tsarin gidan nan ne,

zarah tana jin haka tamik'e tare da janye lullu6inta,  gabantane yashiga fad'uwa tana bin d'akin da kallo cike da mamakin tsaruwarsa cikin ranta tafara kokwanto anya wannan nawane?

muryar jakkadiya taji tanacewa ranki yadad'e akwai abinda zan iya taimaka miki da shi?

zarah d'aukar towel d'in tayi tare da cewa bana buk'atar komai daga nan jakkadiya tanufi 6angaren wardrobe d'in zarah,

nan zarah tacire kayanta taje tashiga toilet ko da tashiga tsayawa tayi tana k'arema tsarin toilet d'in kallo cikin ranta tace lallai idan kana duniya zakayi kallo,  tsoron Allah ne taji ya k'ara ratsamata zuciya nan tashiga cikin ruwan da yayi mata dad'i dan saida tadad'e tana wanka sannan tafito.

ko da tafito jakkadiyace da wata kuyanga tsugunne a k'asa ganinta yasa suka mike cikin sauri tare da cewa takawarki lafiya gimbiya.

zarah wajen dressing mirror tanufa nan suka bi bayanta suka mik'a mata mai hadad'e mai k'amshi tashafa waccan kuyangar ce tayi mata 'yar simple makeup    sannan kayan baccine masu kyau da tsada jakadiya tafito mata dasu,

doguwar rigace silk har k'asa mai hannun vest nan zarah tasaka, su jakkadiya suka dinga yi mata 6arin turaruka a jiki masu sanyin k'amshi, suka tufke mata gashinta da rubon Sannan aka sakamata had'ad'ar alkyabbar da aka tanada.

ko ni kaina da naga zarah saida nace wow masha Allah kamar ba zaran da nasani bace saboda kyaun da tayi

su kansu su jakkadiya saida sukayita santinta suna yaba kyaun da tayi itadai murmushi kawai take nan ma suka k'ara fesheta da turaruka,  sannan sukace ranki yadad'e idan ba wani abu da za'ayi zamu iya tafiya.

zarah fuskarta d'auke da mamaki tace ina zamuje?

jakkadiya kanta a sunkuye yake cike da girmamawa tace d'akin yarima zamu rakaki.

zarah saida gabanta yafad'i jin an ambaci yarima dakewa tayi tace da munyi zamanmu a nan.

jakkadiya tace a'a ranki yadad'e ai tsarin sarautar gidan nan ne yau d'akin mijinki zaki kwana.

zarah batace komaiba tawuce gaba suna biye da ita a cikin ranta mamaki kawai take ganin komai na gidan sarauta a tsare yake,  ko da suka zo parlournta nan sauran ma'aikata suka zube suka kwashi gaisuwa sannan suka take mata baya, jakadiya tana gaba ta rik'e zarah inda sauran suka bi bayansu,

zarah gabanta fad'uwa kawai yake domin batasan irin wulak'ancin da zata fuskantaba wajen mutumin da yake a matsayin mijinta.


yarima bai dawo gidanba sai wajen k'arfe takwas da rabi na dare fuskarsa babu annuri atattare da ita duk wanda yaduk'a yakwashi gaisuwa saidai yatashi hakanan domin yau ko d'awar hannun da yake musu basuda arzik'in samu.

ko da yashiga part d'insa komai yadda aka gyara masa ya burgesa direct bedroom yawuce nan ma Komai very need,  mamakine yakamasa ganin farin bedsheet mai kyau da aka shimfid'a masa saman gado,

cikin ransa yace toh ba za a daina wannan al'adar ba yanzu aure nabiyu ammah shima ba za'a barni inhutaba,  tsaki yaja cike da jin haushi yawuce yashiga bathroom,

bayan ya fito saida yatsane jikinsa yashafa mai sannan yad'auko kayan baccinsa yasaka yazauna bakin gadonsa yajawo laptop d'insa yacigaba da wani aiki nasa akan drugs d'in da yake buk'ata ayo masa order d'insu.

knocking d'in k'ofar da akayine duk atunaninsa gimbiya sumayya ce dan haka yace yes.

jakadiya ce tana rik'e da zarah suka shigo da sallamar jakadiya, yarima kallo d'aya yayi musu yad'auke kai jakadiya takowa tayi tazo gaban yarima sannan tasaki zarah ita taduk'a cikin girmamawa tace ranka yadad'e daman sultana ce tace akawo maka amaryarka, yarima cigaba yayi da aikinsa bai tankaba bare yace wani abu, zarah ma k'asa tazauna jikinta sai 6ari yake,

jakadiya ganin yarima baida niyar yin magana yasa tace Allah yaja da ranka akwai abinda ake buk'ata,  yarima batare da ya kalletaba yayi mata nuni da k'ofa  jakadiya cike da girmamawa tace ranka yadad'e nabarku lafiya,  Sannan takalli zarah tace ranki yadad'e atashi lafiya sannan jakadiya tatashi tafita tare da jawo musu k'ofa

daga nan d'akin yad'auki shuru tsoro da fargaba duk suka d'arsu a zuciyan zarah,  yarima ko kamar wanda aka ajema kayan wanki ko inda zarah take bai kallaba,

zarah dai har lokacin tana zaune a k'asa fuskarta a rufe cikin ranta tana cewa wannan wane irin mutum ne ko dai bebe ne aka auramin,  ahaka tayita sak'e-sak'e a zuciyanta har tsawon awa d'aya tana zaune daga k'arshe bacci yafara d'ibanta,

nan k'asan ta ida kwanciya bata dad'eba bacci yayi awon gaba da ita,  yarima sai wajen k'arfe sha biyu sannan yagama abinda yake kallo d'aya yayi ma zarah da take takure waje guda tana bacci, sannan yahaye saman gadonsa yakwanta cike da takaici wai ace kamarsa yakeda mata biyu duk friends d'insa daga mai d'aya sai wad'anda ma basuyi auren ba,  gloves yakashe kad'an-kad'an ya yi tsaki ahaka bacci yad'aukesa........





_Comments_
       *nd*
_Share_






_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_*Alhmdllh nasamu sauk'i, nagode, nagode da addu'o'inku agareni my fan's hak'ik'a kun nunamin so da k'auna zallah dan ni kaina saida nayi mamakin yawan callings da messages d'in da nasamu daga gareku, bansan irin godiyar da zanyi mukuba, bazan iya lissafokuba saboda yawanku, wad'anda ban samu naduba messages d'insuba kuyi min hak'uri ammah inaso kusani ana mugun tare, Sis Nerja'art tana sonku over Allah yabar k'auna😍*_

_~Wannan page d'in mallakinkune my fan's kuyi yadda kukeso da shi akodayaushe ana tare~_

*PAGE* 2⃣3⃣

Sumayya a ranar kasa bacci tayi kuka kawai takeyi musamman ma idan tatuno da yarima yana chan kwance da wata ba itaba,  nan takeji tsanar zarah ta k'aru a ranta duk yadda taso tayi bacci kasawa tayi motsi kad'an sai ta duba lokaci daga k'arshe zinat takira a waya

zinat da take bacci dakyar tajawo wayarta tana tsaki ganin sumayya ce yasa tad'aga cikin muryar bacci tace ya dai baby?

sumayya cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace dear ke bacci kike hankalinki kwance nikau nan nakasa

zinat cikin ranta tace kujimin mace sai ink'i bacci saikace ni akayi ma kishiya... chan kuma sai tace toh dear kema ke kika sa kanki rashin baccin miye na damuwa tunda dai kinsan dole yakasance da matarsa yau k'ilama ya mance da batunki.

sumayya cikin sheshek'ar kuka tace dolene indamu zinat kiduba fa kiga irin son da nakema yarima ammah yau ace shine tare da wata ba niba wlh natsani ko ma wacece,

zinat tace kikwantar da hankalinki ai wlh ba zamu kyaletaba nima ai dan bana k'asar ammah bari indawo sai munsan yadda mukayi muka fitar da ita daga gidan kinsani ai

sumayya cike da jin dad'i tace saisa nake sonki k'awata yanzu dai yaushe zakizo domin nima kaina ina kewarki

zinat 'yar dariya tayi tace kar kidamu dear very soon zan zo miki domin nima kaina ina kewarki sosai yanzu dai kikwanta kisamu kiyi bacci

sumayya tace hmm dear bana tunanin zan iya bacci a daren nan ni kid'an turomin d'an abinda zai sani nishad'i

zinat tace toh dear muhad'e a online.

sumayya tace ohk,  sannan suka kashe wayar a tare,

sumayya ta dad'e batayi bacciba tana kallon abinda zinat taturo mata har daga k'arshe dai bacci yayi awon gaba da ita.


Kiran sallar asubane yatashi yarima daga baccin da yakeyi kallon zarah yayi da take takure k'asa ta6e baki yayi yawuce yashige toilet, jin motsinsane yasa zarah tafarka daga baccin da takeyi dasauri tamik'e tare da gyara alkyabbarta tafito daga d'akin, da karambani tamaida kanta part d'inta lokacin masu tsaron part d'intane kawai a wajen,  cike da girmamawa suka gaisheta ta amsa sannan suka bud'e mata tashiga.

zarah alwallah tad'auro tazo tagabatar da sallar asuba bayan ta gama hayewa tayi saman gadonta saboda wani irin bacci da takeji nan da nan bacci yayi awon gaba da ita.

yarima ko da yafito daga toilet baiwani damuba ganin zarah bata d'akin yaficce yafita masallaci.

bayan ya dawo bai koma bacciba yad'auko laptop d'insa a parlour yazauna yacigaba da aikinsa.

wajen k'arfe 8 guard d'insa yashigo duk'awa yayi yagaishe da yarima, yarima batare da ya kallesaba ya amsa, cike da girmamawa guard d'in yace ranka yadad'e daman jakkadiyace tazo shine nace bari infara dubawa inga in kana parlour,

yarima yace me zanyi mata?

guard yace ranka yadad'e bari inje intambayeta.

yarima kallonsa yayi nad'an lokaci sannan yace kubarta tashigo.

Duk'awa guard yayi yak'ara kwasar gaisuwa sannan yamik'e yafita yabar d'akin.

bayan kamar minti biyu sai ga jakkadiya ta shigo da sallamarta, ciki-ciki ya amsa batare da ya kalletaba.

zubewa jakkadiya tayi tace ranka yadad'e Allah yaja da ran yarima mai jiran gado, Allah yabaka tsawon rai, Allah yad'aukaka mana kai, Allah ya kunyata mak'iyanka  dafatan katashi lafiya.

me ke tafe da ke?  cewar yarima.

jakkadiya kyarma tafara tace am daman.

yarima batare da ya kalletaba yace ina jinki.

k'ara duk'ar da kanta tayi tace ranka yadad'e kagafarceni daman dada ce ta aikoni tace inzo induba lafiyarku sannan ind'auko bedsheet awanke.

ta6e baki yarima yayi yacigaba da abinda yakeyi saida yayi kusan minti goma sannan yace zaki iya shiga kid'auka.

shiga jakkadiya tayi tad'auko tafito nan tak'ara duk'awa tace atashi lafiya yarima sannan taficce daga d'akin.

wajen k'arfe goma zarah tafarka daga baccin da take daidai lokacin d'aya daga cikin kuyanginta tashigo dasauri taduk'a tagaishe da zarah cike da girmamawa, zarah amsawa tayi cikin sakin fuska, sannan kuyangar tatashi tashiga toilet d'in zarah tawankesa fes sannan tahad'a mata ruwan wanka, sannan tad'auko mata towel.

bayan ta fito duk'awa tayi gaban zarah tace ranki yadad'e ruwan wankanki ya had'u.

zarah murmushi tayi tare da kar6ar towel d'in tace nagode zaki iya tafiya.

kuyangar k'ara duk'ar da kanta tayi tace ranki yadad'e nice wadda zan dinga gyara miki d'aki mu biyune d'ayan tana parlour tana jiran fitowarki,

murmushi zarah tayi tace kubarsa kawai ni zan dinga gyarawa.

A tsorace kuyangar tace a'a ranki yadad'e kigafarceni aikinmune idan har akaga mun bari kinyi da kanki za'a iya korarmu.

zarah girgiza kai tayi tace baza'a koreku ba,  mik'ewa tayi tare da wucewa tanufi toilet.

lokacin da zarah tafito angama gyara mata ko'ina k'amshi kawai yake tashi, ita kanta zarah yanayin gyaran da akayi ya burgeta,

gaban dressing mirror tazauna ta tsantsara kwalliyarta sannan taje tabud'e wardrobe saida ta tsorata ganin lodin kayan da suke ciki, Holland atamfa tasaka Red nd white colour, d'ankunnenta ma red colour tasaka, murza d'aurin kallabi tayi nan kyaunta yak'ara bayyana, k'ara kallon kanta tayi a mirror sannan tafeshe jikinta da turaruka masu sanyin k'amshi, plat shoes tasaka tatako ahankali tafito parlour,  ganinta yasa duk kuyangi da bayin dasuke parlourn suka zube k'asa suna ranki yadad'e gimbiya, Allah yaja da ranki takawarki lafiya dafatan kin tashi lafiya?

zarah tana murmushi tataka cikin takunta taje saman cushin tazauna, saida sukaga ta zauna sannan suka d'ago kansu,

zarah har a lokacin fuskarta tana d'auke da murmushi tace wacece shugabarku?

d'aya daga cikinsu ce tace ranki yadad'e ganinan nice shugaba, sannan kowa anraba masa aikin da zaiyi.

jinjina kai zarah tayi tace dat's gud, dafatan dai zaku bani had'in kai muzauna lafiya,  indai kukayi haka toh zakuji dad'in zama da ni sosai.

gaba d'ayansu sukace Allah yaja da ran gimbiya insha Allahu zaki samemu masu amana.

murmushin jin dad'i zarah tayi tace nagode zaku iya tafiya, nan suka k'ara duk'awa sukace atashi lafiya,

gyad'a musu kai zarah tayi nan suka mik'e,  biyu daga cikinsu ne sukatsaya sukace ranki yadad'e mune masu kula da abincinki ga breakfast d'inki chan a dining idan kin bamu izini sai muje muhad'a miki.

zarah mik'ewa tayi tanufi dining nan suka take mata baya, dasauri suka jawo mata kujera nan tazauna, ganin zasuyi serving d'inta yasa tadakatar da su dakanta tazuba tad'anci kad'an sannan tamik'e,

nan suka gyara wajen, zarah saman kushin takoma tazauna tare da d'aukar wayanta takira mama suka gaisa,

tana cikin waya yarima suhail yashigo cikin takunsa nak'asaita sanye da alk'yabba yasha kyau, zarah  kashe wayar tayi dasauri tamik'e tsaye tare da d'an russunawa tace barka da safiya.

yarima kallo d'aya yayi mata yad'auke kai yace kije kishirya kizo muje mugaishe da su memartaba.

zarah ahankali tace toh sannan tawuce tashige bedroom.

gyalenta tad'auko white tayafa tafito lokacin yarima yana zaune saman cushin, kallonta yayi yace babu alkyabbane cikin kayanki?

zarah tace akwai.

shuru yarima yayi baik'ara cewa komai ba,  ganin haka yasa zarah takoma bedroom, red d'in alkyabba tad'auko tasaka sannan tafito tasamu yarima a zaune,

kallonta yarima yayi har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa,  mik'ewa yayi yace muje.

zarah bayansa tabi suka fito a jere nan guards d'insa da kuyanginta suka take musu baya yanayin yadda suke tafiyar kawai zaka kallah sai sun burgeka ko da ad'ankwai 'yar tazara a tsakaninsu anutse suke tafiya har suka isa fada itadai zarah duk fargaba da tsoro duk sun cikata kanta sadde yake k'asa har suka shiga fada da take cike mak'il da jama'a nan mutane suka fara gaishesu, yarima ne kawai yake amsawa ahaka suka isa gaban memartaba,

lallausan carpet ne aka shimfid'a musu nan dogarawa sukayi musu zobe har saida suka zauna bisa sannan suka janye manyan rigunansu gaba d'ayansu suka duk'a suka gaishe da su yarima, yarima gyad'amusu kai yayi nan suka mik'e sannan yamaida kallonsa ga memartaba da yake kallonsu yana murmushi.

Zarah ce tafara gaishesa sannan yarima suhail, gyad'a musu kai sarki yayi alamun amsawa, nan fadawa suka d'auka sarki ya amsa gaisuwarku yarima da gimbiya ku ma angaisheku, Allah yaja da ranku,

memartaba kallon zarah yayi yace Alhmdllh ina tayaki murnar shigowa wannan masarauta tamu muna fatan Allah yasa alkhairi a cikin aurennan naku.

nan fada tad'auka da Ameen.

wata 'yar jakka sarki yasa aka mik'o masa yaba zarah yace ga kyautata gareki.

zarah hannu biyu tasa takar6a tare da duk'ar da kai tace nagode ranka yadad'e Allah yak'ara girma da d'aukaka, nan kuyanga takar6a

nan fadawa suka d'auka sarki ya amsa godiarki gimbiya angaisheku.

memartaba kallon yarima yayi yace Allah yatayaka safke wannan nauyin da yahau kanka fatana Allah yasa ka kwatanta adalci atsakaninsu.

yarima kansa na sadde k'asa yace Ameen ranka yadad'e.

memartaba murmushi yayi yace zaku iya tafiya.

godia sukayi, dasauri dogarawa sukazo suka baje rigunansu suna ranka yadad'e atashi lafiya, takawarka lafiya jarumin jarumai saida suka tabbatar da sun mik'e sannan su kuma suka duk'e k'asa nan zarah da yarima suka fito sukabar fadar,  kan zarah ya d'aure sosai ahaka suka shiga cikin gida turakar dada.

duk inda suka gifta duk'awa ake ana gaishesu, yarima d'aga musu hannu kawai yake itakuma zarah saidai tabisu da ido,

masu tsaron k'ofar dada ganinsu yasa sukayi saurin bud'e k'ofa tare da duk'awa sukace ranku yadad'e Allah yaja da ran yarima me jiran gado.

yarima bai tankasuba yana gaba zarah na biye da shi ahaka suka shiga nan kuyangin dada suka zube suka Kwashi gaisuwa sannan cikin sauri suka tashi sukabar d'akin.

yarima takawa yayi yaje saman cushin yazauna, zarah ko k'asa tazauna cike da ladabi tagaishe da dada.

dada nan ta amsa mata,  fuskar yarima d'auke da murmushi yace 'yar tsohuwa ina kwana?

dada tace au yau kuma da tsokana kazo?  toh bazan amsaba, yarima yace ayya yi hak'uri, murmushi dada tayi tace dafatan kun tashi lafiya?

yarima yace lafiya lou,  dada kallon zarah tayi da har lokacin bata d'ago kai ba tace amarya ya bak'unta?  zarah murmushi tayi tace Alhmdllh.

dada kallonta tamaida ga yarima tace akwai matsala fa
yarima yace tame fa?

dada gyara zamanta tayi tace babu wata sheda da kuka nuna mana, mutane suna nan sun kasa kunne suna saurare ammah shuru wai meyake faruwa ne naga bedsheet d'in babu komai a jikinsa, ta k'arashe maganarta tare da kallon zarah.

murmushi yarima yayi yace ranki yadad'e saboda Allah komai ace sai mutane sun shaida, wannan ai tonon asirine.

dada tace a'a yarima wannan kasan shine zai d'aga darajar mace a idon kowa dake masarautarnan sannan kuma gada mukayi tun kaka da kakanni,  rashin ganin jini zai iya sa ad'auka mace tazubar da mutuncinta a waje.

zarah da take saurarensu saida gabanta yafad'i dan ta fahimci akan abinda dada take magana.

yarima cike da rashin damuwa yace haba dada inbanda abinki yanzu ai anbar wannan.

dada tace injiwa?  abinda muka gada tun kaka da kakanni?  kai ni banyarda da kaiba anya kakwanta da yarinyarnan? inkuma ka kwanta da ita toh ya akayi babu wani alama da yanuna budurwace?

murmushi yarima yayi tare da kallon zarah da duk tabi tatsure cikin ranta mamakin maganganun dada take tace gidan sarauta akwai tonon asiri,
ahankali yarima yace dada period takene saisa hakan takasance, zarah dasauri tad'ago kai takalli yarima da yake dannar wayarsa saikace bashine yayi maganar ba,  yarima ya fad'i hakane gudun kar su ummi suji labari dan yasan sai dada ta fad'a musu kuma sai sun fahimci wani abu.

dada ce tace ayyah Allah sarki 'yar nan ai bamu saniba, kinsan haka abun yake, kinsan daren farko munaso muga alamar da zata nuna mana mace cikakkar budurwace dan hakan ne yake d'aga daraja da k'imarta.

zarah cike da kunya tak'ara sadda kanta k'asa,  dada tace kikwantar da hankalinki zanyi ma kowa bayani yadda zasu fahimta.

yarima ne yace haba dada wannan ai tonon asirine.
.
dada tace gidanku, kaima ai kasan dokokinmu na wannan masarautar,  yanzu dai yaushe ne zakiyi tsarki?

zarah kallon yarima tayi da shima yazuba mata ido,  muryar dada taji tace ina saurarenki.

zarah batasan lokacin da tayi su6ul da baka tace jibi ba.

murmushi dada tayi tace Allah yakaimu,  nan dada tamik'o mata alkyabba maikyau da turare tace ga tukuici na,

kar6a zarah tayi tare da godia ammah har lokacin jikinta rawa yakeyi.

nan yarima yayi ma dada sallama suka mik'e suka fito, daganan suka nufi part d'in sultana sadiya,

lokacin da suka shiga tana tsakiyan kuyanginta,  da sallama suka shiga nan kuyanginta suka gaishesu sannan sukabar d'akin,  ganinsu yasa gimbiya sadiya tad'aure fuska tare da wurgamasu harara,  yarima baidamu da yanayin kallon da take musuba yaje saman kujera yazauna, inda zarah kuma tazauna k'asa tare da gaisheta, .

sultana sadiya shuru tayi bata amsaba, yarima suhail ne yace ranki yadad'e ana gaisheki fa,  yamutsa fuska sultana tayi tace oh banjiba amarya kin tashi lafiya?

zarah k'ara duk'ar da kanta tayi tace lafiya lou, yarima suhail yace ranki yadad'e barka da safiya dafatan kin tashi lafiya.

lafiya, cewar sultana.

murmushi yarima yayi tare da kallon zarah yace wannan itace ummah sadiya mahaifiyar matata sumayya,

gyad'a kai kawai zarah tayi,  ummah tace hmm mu ai muna nan muna jira muji anyi gud'a ammah har yanzu shuru babu abinda mukaji hakan yana nufin ba budurwa bace kenan kayayo mana cikin masarauta.

murmushi yarima yayi yace ranki yadad'e ai gud'a bashine ba kar kimance sumayya ma ba'ayi gud'aba lokacin da na aureta,

cike da 6acin rai sultana sadiya tace kar fa kayi min rashin kunya,
yarima cikin kwantar da murya yace haba ummah ni na isa inyi miki rashin kunya? kawai dai tuna miki nayi saboda laifi tudune katake naka kahango na wani.

zarah abun ya d'aure mata kai ganin yadda yarima yakeyi ma surukarsa,

sultana sadiya har ta bud'e baki zatayi magana sai ga sultan Abbas ya fito daga d'aki fuskarsa d'auke da fara'a yace a'a wai amarene?

murmushi kawai suhail yayi tare da d'an zamowa daga kujerar da yake yace abbah ina kwana?

sultan Abbas zama yayi yace lafiya lou yarima dafatan kuna lafiya?

murmushi suhail yayi yace lafiya lou Abbah,  zarah k'ara sadda kanta tayi cike da ladabi tagaishesa.

cikin sakin fuska sultan abbas ya amsa mata tare da cewa amaryarmu ya kike ya bak'unta?
zarah tace Alhmdllh Abbah.

sultan Abbas yace masha Allah,  dafatan zakiyi hak'urin zama da mu kinsan yanayin gidan sarauta sai andinga hak'urin zama da juna fatanmu kizauna da kowa lafiya, ko da yanayin ya nuna bazakiyi fitinaba. 

Zarah cike da ladabi tace insha Allahu Abbah, mik'ewa sultan Abbas yayi yashiga bedroom bai dad'eba sai gashi yafito da wata leda nan yamik'a ma zarah yace ga kyautata,

zarah hannu biyu tasa takar6a tare da yin godia.

yarima suhail ne yamik'e yace abbah bari muwuce,  sultan abbas yace to yarima mungode sosai a dai cigaba da hak'uri da juna.
yarima yace insha Allahu abbah mungode, nan zarah tak'ara yin godia sannan tataso suka fito.

ko da suka shiga turakar ummi duk inda suka gifta nan ma zubewa ake ana gaishesu,  a parlour suka sameta kishingid'e ita kad'ai,  ganinsu yasa tatashi zaune fuskarta d'auke da fara'a hannu tamik'a ma zarah tace zo nan kusa da ni d'iyata.

zarah cike da jin kunya tataka taje kusa da ummi tazauna, inda yarima yazauna saman cushin.

zarah cike da girmamawa tace ummi ina kwana?  ummi tace lafiya lou daughter ya bak'unta?
zarah murmushi tayi tace Alhmdllh.
yarima ma cikin girmama yagaishe da ummi, itama ta amsa masa fuska a sake tace ya sumayya?

murmushi suhail yayi yace tana lafiya ummi, daddy fa yafita?
ummi mik'ewa tayi tace yana ciki bari inkirasa kugaisa nan tawuce tashiga bedroom d'insa bata dad'eba saigata sun fito tare da daddy,

bayan dady ya zauna nan suka gaishesa, daddy ya amsa musu daganan yad'anyi musu nasiha sannan yad'auko cheque yamik'a mata yace ga kyautata gareki.

zarah hannu biyu tasa takar6a tare da yin godia,  daddy yace bakomai adaiyi  hak'uri da zaman aure,  sannan yatashi yafita.

ummi kallon yarima tayi tace inason magana da kai, saida tamik'e sannan tamaida kallonta ga zarah tace daughter yi hak'uri bari inzo,
zarah murmushi tayi tace toh ummi bakomai.

yarima tashi yayi yabi bayan ummi, bayan sun shiga bedroom ummi kallonsa tayi tace suhail menene haka kayi ban fahimcekaba daman nasan bakason auren nan yanzu saboda Allah kakyauta gashinan anata surutu akan baiwar Allahn nan?

yarima shuru yayi saida sultana bilkisu takai aya sannan yace ummi please kifad'amin menayi?

harararsa ummi tayi tace au kana nufin bakasan abinda kayiba kenan,  yanzu saboda Allah an aura maka yarinya ammah babu abinda yashiga tsakaninku.

yarima sosa k'eyarsa yayi cikin jin kunya yace ummi am ba daman,

ummi tace daman me?
murmushi suhail yayi yace daman tana period ne.

dogon numfashi ummi taja tace toh ai shikenan na d'auka wulak'ancin nakane yamotsa nidai fatana karik'e min ita tsakani ga Allah kar kabani kunya.

murmushi suhail yayi yace ummi kenan saikace baki yarda da niba,  kina tsoron inzalunceta ko?

murmushi itama ummi tayi tace ai nayarda da d'ana 100% Allah yayi maka albarka, murmushi yayi yace ameen ummina, 

atare suka fito inda suka tarar da zarah inda suka barta, ummi murmushi tayi tace daughter munbarki kekad'ai ko?

itama zarah murmushin tayi tace bakomai ummi,  wata leda ummi tamik'a mata tace ga wannan, sannan ummi tace rahama batanan da kun gaisa ammah insha Allahu idan tadawo zan turota kugaisa.

zarah tace toh ummi tare da yi mata godia, nan sukayi mata bankwana suka fito suka koma 6angarensu.

ahanyarsu ta komawa yarima suhail yakira sumayya

lokacin sumayya tana breakfast fuskarta babu walwala jin haushinta taje part d'in yarima ammah bata samesaba,  dasauri wata baiwarta tamik'o mata wayar tace ranki yadad'e ana kiranki, kar6a gimbiya tayi a wulak'ance ganin mai kiranta yasa taja tsaki kamar bazata d'aukaba saida takusan tsinkewa sannan tad'auka babu ko sallama tace haba yarima yanzu saboda Allah ka.... yarima baijira tak'arashe maganarba yakatseya yace kisameni a part d'ina yanzu, bai jira jin abinda zataceba yakashe wayarsa.


_Comments_
        *nd*
_Share_



_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔


*PAGE* 2⃣4⃣

Yarima ganin zarah tana shirin wucewa part d'inta yasa yace suje part d'insa yanason ganinta,  zarah bata musaba tabi bayansa dan bata iya musama yarima saboda girmansa da take gani.

ko da suka shiga saman cushin yarima yazauna, zarah har zata zauna k'asa yace tazauna saman cushin tunda suka zauna d'akin yad'au shuru.

yarima kiran sumayya yayi tana d'auka cike da jin haushi yace kinsan dai bana jira kuma baki isa inzauna ina jirankiba.

tsaki sumayya taja tace ai ganinan a hanya.

bayan minti biyu saiga sumayya tashigo fuskarta babu alamun fara'a ganin zarah yasa taja bakin k'ofa tatsaya,  dasauri zarah tamik'e tad'an russuna tace Aunty barka,

wata uwar harara gimbiya sumayya tawurga mata tare da jan tsoki, tace Auntyn munafunci? kece kika auran min miji ko?  lallai natayaki murna tak'arashe maganar tare da yin k'wafa

jikin zarah duk sai yayi sanyi.

yarima da yake dannar waya yana saurarensu batare da yakallesuba yace ma gimbiya sumayya ai saikizo kizauna kin wani yi ma mutane tsaye,

sumayya tana hararar zarah tatako cike da isa tazauna saman kujerar da yarima yake zaune,  zarah ma jiki ba k'wari tazauna inda take tare da saddar da kanta k'asa.

yarima shuru yayi yana dannar wayarsa baice komaiba saida akayi kusan minti ukku,

sumayya ta k'ule kallonsa tayi tace haba yarima ya zakayi shuru kabarni a zaune.

banza yarima yayi da ita saida yagama abinda yake sannan yad'ago kai yakallesu d'aya bayan d'aya tare da gyaran murya kamar bayason yin magana yace toh Alhmdllh ba akan komai natarakuba sai dan infad'a muku dokokina domin duk wadda takeson zama da ni dole tabisu, kallon sumayya yayi da taci face yace ke sumayya kece babba dan haka kija girmanki banason fitina ko tashin hankali,  sumayya cike da masifa tabud'e baki zatayi magana, yarima hannu yad'aga mata yace kar kikuskura, kin san wanene ni idan ina magana ba'a tsinkemin.

sannan yamaida kallonsa ga zarah da take wasa da yatsun hannunta yace ke kuma kece k'arama dan haka dole kibata girmanta sannan kizauna da ita lafiya kar kikuskura inji kinyi mata rashin kunya,  zarah shuru tayi batace komai ba.

yarima yacigaba da cewa kar wanda yasaki yakawomin tashin hankali a gidana,  sannan maganar kwana bayan sati guda zaku koma kowace kwana bibbiyu, jinjina kai yayi yace na fad'amuku kar inji kar ingani banason tashin hankali wlh duk wadda tanemi takawo min raini zan d'au k'wak'waran mataki a kanta, yana kaiwa nan yayi shuru na d'an lokaci sai chan yace idan akwai mai magana zata iya yi.

ba sumayya hatta ita kanta zarah taji haushin maganganunsa, sumayya ce tace yanzu dai wad'annan maganganun naka ban ganeba kafito fili kace da ni kake wannan shine adoki mutum sannan ahanasa kuka, ka gama yimin kishiya sannan ka...... hararar da yarima yawurga matane yasa tayi shuru,  d'an guntun murmushi yayi yace ban miki alk'awalin bazan k'ara aureba kai koda ace a nan gaba naga wadda tayimin nakeso toh sai na aureta saidai duk wadda taji bata iya zama toh k'ofa a bud'e take dan haka kutashi kuban waje.

zarah ce tafara tashi dasauri tafita sannan sumayya.

zarah tana cikin tafiya taji muryar sumayya tace ke!
zarah batare da ta juyoba tatsaya nan sumayya tatako cike da isa tazo inda zarah take, kallonta sumayya tayi daga sama har k'asa sannan tace gimbiya zarah ko?  l
dariya sumayya tayi tace gaskiya natayaki murna gaki d'iyar talakkawa ammah zaki had'a miji da gimbiya kamata, chan kuma sai gimbiya sumayya tad'aure fuska tace wlh baki isa inyi kishi da keba dan haka yazama dole kirabu da mijina, inkuma ba hakaba bakeba hatta talakkawan iyayenki sai sunsan kwad'ayi yakaisu ya baro, dan suma sai sun gane kurensu dan haka shawara ta rage ga mai shiga rijiya.

tana gama fad'in haka tazagaye zarah tawuce tabarta nan tsaye.

zarah dai binta take da kallo cike da mamaki kasa cewa komai tayi tawuce tanufi part d'inta zuciyanta cike da k'unci

zarah ko da takoma part d'inta sama-sama tatsaya suka gaisa da kuyanginta sannan tashige bedroom d'inta, saman gado takwanta tana tunanin maganganun da sumayya ta yada mata, sai tatuno da yarima suhail,  tsaki taja tace wlh darajar alk'awalin da nad'aukar ma malam bello da kuma darajar aure wlh da bazan yadda a wulak'antaniba.

hawayene suka fara zarra daga idanunta chan tafashe da kuka cike da tausayin kanta.


wajen azuhur kuyangarta tashigo tahad'a mata ruwan wanka.

bayan zarah ta fito wanka tad'and'ara kwalliyarta gown d'in atamfa tasaka, bayan tayi Sallah tafito parlour, ganinta yasa kuyanginta suka zube suna kwasar gaisuwa,  zarah bata ce komai ba saida taje saman cushin tazauna sannan tace banason irin wannan gaisuwar da kukeyimin kudaina duk'amin.

zabba'u shugaban kuyangince cike da girmamawa tace ranki yadad'e kigafarceni matsayinkine da k'imarki da cancantarki sukaja haka, murmushi zarah tayi tace nagode ammah kudaina,  yanzu dai inason asani nishad'i wazai ban labari mai dad'i?

nan zabba'u takalli d'aya daga cikinsu tace daso aikinkine,  wadda aka kira da daso nan tafara ba zarah labari suna dariya, cike da nishad'i suke hirarrakinsu.

chan wajen k'arfe ukku zarah tace yanzu lokacin cin abincinane,  nan suka duk'a sukace toh ranki yadad'e atashi lafiya sannan suka mik'e suka fita.

masu kula da abincinta har sun tsaya nan zarah tace sutafi kawai.

zarah dakanta taje tayi serving d'in kanta taci abinci,  bayan ta gama nan takira tace suzo sukwashe abincin suje suci.

bayan sallar la'asar zarah kallo takunna tana yi duk kad'aicin 'yan gidansu ya dameta, saida aka kira magrib sannan taje tayi sallah dakanta tashiga kitchen tadafa 'yar indomie,  duk yadda kuyanginta sukaso tabari suyimata ammah tak"i tace musu zaman ne ya isheta saisa takeso tad'an motsa jikinta,  kan dole suka hak'ura suka barta.

bayan sallar isha'i zarah 'yan gidansu takira sukasha hira tare da tambayarsu yaushe zasuzo, Aysha tace saidai kin ganmu kawai abbah ne yahanani dan naso inzo yau yace a'a sai kinkwana biyu.

zarah cikin rashin jin dad'i tace toh Allah yasa ya amince kuzo kuyi min kwanah ni wlh kad'aici yana damuna.

dariya Aysha tayi tace haba yaya zarah wane kad'aici bayan gidan akwai mutane kuma ga kallo, ni wlh ji nake daman nice.

tsaki zarah taja tare da kashe wayanta tace Aysha kenan, shirin bacci tayi ta sallami kuyanginta tayi kwanciyarta.

*wanshe kare* bayan zarah ta yi sallar asuba bacci takoma sai wajen k'arfe goma tafarka,  nan aka had'a mata ruwan wanka tayi tashirya cikin material coffee colour kayan sun kar6eta sosai, nan tafito suka gaisa da kuyanginta tayi breakfast,  bayan ta gama breakfast kallo takunna tanayi kasancewarta mai son kallo, kuyanginta suna zaune k'asa, sallamar da taji anyine yasa tad'ago kai, Rahma ce tashigo cikin shigarta ta alfarma sanye da alkyabba,  ganinta yasa kuyangi suka duk'e k'asa suna kwasar gaisuwa, zarah tunda taganta tasan jinin yarima ce saboda taga kamansu dasauri tamik'e tare da d'an rissinawa cike da girmamawa tace sannu da zuwa, kuyangi bayan ta amsa musu tashi sukayi suka fita daga d'akin, nan Rahma tatako taje tazauna saman d'aya daga cikin kujerun d'akin saida tazauna sannan zarah ma tazauna tare da gaisheta.

Rahma da take k'arema d'akin kallo amsawa tayi ciki-ciki,  zarah fuskarta d'auke da fara'a tamik'e tace bari inkawo miki ruwa,

sumayya yamutsa fuska tayi tace no kibarsa kawai am ohk, daman nazone mugaisa ina fatan kinji labarina wajen mijin naki, nice k'anwarsa.

murmushi zarah tayi tace eh ummi ta fad'amin jiya tace bakyanan ne saisa bamu had'uba, Rahma mik'ewa tayi tsaye tace zan wuce Allah yabada zaman lafiya,  zarah ma mik'ewa tayi tare da rissinawa tace mungode Allah yakiyaye, Gimbiya Rahma batace komai ba tawuce tafita.

zarah komawa tayi tazauna tare da dafe kanta cikin ranta tace wannan indai halin yarima ne takwaso daga gani zatayi wulak'anci _(Ni kuma nace haba zarah gani d'aya kawai ammah har kin fassarata)_


bayan sallar azuhur wanka tashiga tayi.

zarah bayan ta fito daga wanka kwalliya tazauna tayi sosai sannan tashirya cikin boyel less d'inta blue nd orange colour d'inkin riga da skirt ne kayan sun kar6eta sosai sannan tad'aura alkyabba orange colour daga saman kayan tayi kyau sosai saida tafeshe jikinta da performs sannan tafito parlour lokacin kuyanginta na zaune k'asa suna jiran fitowarta ganinta yasa gaba d'ayansu suka rissina sukace barka da fitowa sarauniya tsarki ya tabbata ga ubangiji da yahalicci wannan kyakkyawar kuma mata ga sarki mai jiran gado angaisheki gimbiya.

gimbiya zarah takowa tayi tana murmushi kamar ba zatayi maganaba ammah ganin basuda niyar d'agowa yasa tace nafad'a muku banason hakan da kukemin ammah kunk'i dainawa ko?

kuyanga d'aya batare da ta d'ago kaiba tace ranki yadad'e kigafarcemu ke shugabace agaremu kuma mai mutunci dan haka girmamawa yazama dole muyi maki,
murmushi zarah tayi a karo nabiyu sannan tace wasu sutaso surakani 6angaren gimbiya sadiya.

kuyangi hud'u suka mik'e nan zarah tashiga gaba suna biye da ita a baya, tako take irin na masu ji da kansu,

duk inda tazo wucewa sai anduk'a angaisheta itakuma tana tsayawa tana amsa musu fuska a sake sannan tacigaba da tafiyarta ahaka har tazo 6angaren gimbiya sumayya.

bayin gimbiya sumayya biyu da suke tsaye k'ofar d'akinta ganin gimbiya zarah yasa suka duk'a suka gaisheta nan ta amsa musu fuska a sake dasauri suka tashi suka bud'e mata d'aki tashiga.

gimbiya sumayya da take zaune saman kujera inda bayinta da kuyangi suke zagaye da ita tana ta dannar wayarta.

gimbiya zarah ce tashigo da sallamarta fuskarta d'auke da fara'a kuyanginta suna biye da ita, ganinta yasa gimbiya sumayya tahad'e fuska,

nan ma'aikatan sumayya suka zube suna kwasar gaisuwa,  tsawa sumayya tabuga musu dasauri duk suka mik'e tsaye,  gimbiya zarah bata damuba tad'an rissina tace barka da rana.

wata irin harara gimbiya sumayya tawurga mata cikin tsawa tace meyakawoki d'akina?

zarah murmushi tayi tace nazo ingaishekine

gimbiya sumayya tace ashema kinzo kigaisheni to kirik'e gaisuwarki bana so ke ga kicifaffa watakau kinzo kimin iyayi
toh bari kiji kibar ganin kin auri yarima yadda kika shigomin gida dole kifita kibarsa sannan daga yanzu kar kik'ara shugo min d'aki duk ranar da kika k'ara gigin shigowa sai nanuna miki matsayinki a gidannan ke bakomai bace face talaka makwad'aita.

damamaki zarah takebin gimbiya sumayya da kallon yadda tadage tana ta zuba mata ruwan rashin mutunci.

sumayyw k'walama bayinta da suke tsaye bakin k'ofan d'akinta kira tayi dasauri suka gurfana gabanta kamar zasuyi mata sujjada dan tsoro sukace gamu mun amsa kiranki ya shugabarmu,

sultana sumayya a wulak'ance tace meyasa kuka bari wannan d'iyar talakawan tashigo min d'aki?

shuru sukayi suka fara 'yan kame kame

gimbiya sumayya kishingid'awa tayi a saman kujerar tare da cewa kufitarmin da ita na baku kinti biyu idanko ba hakaba a bakin aikinku.

zarah murmushin takaici tayi tare da cewa bama sai kinsa an fitar da ni ba,  ni zan fita da kaina saidai inaso kisan wani abu d'aya, talauci da dukiya duk na Allah ne dan haka na barki lafiya.

tana gama fad'in hakan tajuya tafito cike da 6acin rai duk Wanda yake wajen baiji dad'in abinda gimbiya tayima zarah ba saidai kowa yabar abun a ransa domin gudun 6acin ran gimbiya

suna fita daga d'akin kuyanginta suka zube k'asa sukace Allah yahuci zuciyar gimbiyanmu,

murmurshi zarah tayi sannan tawuce gaba suka tashi sukabi bayanta ahaka har suka shiga part d'inta bata kula kowaba tawuce tashige bedroom tare da maida k'ofar tarufe tacire alkyabtarta cike da takaici tafad'a saman gado tace wannan wace kalar rayuwace duk inda nayi babu sauk'i,  takaicinta maganganun da Gimbiya sumayya tafad'a a kanta,  hawayene suka cika mata ido tace Allah gani gareka.

wanshe kare zarah tara kuyanginta tayi taraba musu kud'i tace kowa yaje yasiya abinda yake buk'ata, sunji dad'i sosai nan suka duk'a sukayi mata godia sannan suka fita kowa yana murna

haule ce da zabba'u zaune bayan part d'in zarah suna cin abinci, haule takalli zabba'u tace gaskiya natayaku murna dan kunyi dacen uwargijiya ba kamar tamuba.

murmushi zabba'u tayi tace mukam ai saidai muce Alhmdllh dan wlh tana da kirki sosai batada girman kai.

haule tace hmm muko kinga tamu girman kai da wulak'anci gareta ke ni har tsoro nakeji inga na6ata mata rai dan sai kagane kurenka, duk abinda zakayi mata toh bazaka ta6a burgetaba, daman nima amaidoni wajen gimbiya zarah ko bakomai zan samu sauk'in wani abun, zabba'u har ta bud'e baki zatayi magana ganin rabi tanufo inda suke yasa tafasa.



bayan sallar magrib dada wani farin bedsheet d'in taba jakkadiya tace aje a shimfid'a part d'in yarima,  jakkadiya kar6a tayi tare da rissinawa sannan tafito.

ko da taje part d'in yarima baya nan guards har sun hanata shiga saida tace dada ce ta aikota tagyara masa d'aki sannan suka barta.

ko da tashiga saida tak'ara gyara d'akin fess sannan tafito tanufi part d'in zarah, lokacin tana kishingid'e tana chart,

jakkadiya duk'awa tayi tagaishe da zarah cike da girmamawa,  cikin sakin fuska zarah ta amsa mata, nan jakkadiya tak'ara saddar da kanta k'asa tace ranki yadad'e daman dada ce tace inzo intayaki kishirya sai inrakaki d'akin yarima.

zarah saida gabanta yafad'i jin an ambaci mutumin da kusan kwana biyu rabon da tasakasa a idanunta.

kuma ta fahimci abinda ake nufi, cikin ranta tace nashiga ukku.

muryar jakkadiya taji tace kigafarceni ranki yadad'e, idan kin ban izini sai inje inhad'a miki ruwan wanka.

zarah gyad'a mata kai kawai tayi nan jakkadiya tamik'e taje tahad'a ma zarah ruwan wanka.

zarah dakyar taje tayi wankan gabanta fad'uwa kawai yake duk tsoro da fargaba sun cikata,

bayan ta fito lotion mai k'amshi aka bata tashafa, sai humra da kulacca, powder kawai tashafa ma fuskarta sai lipstick, had'ad'ar night gown ce fara har k'asa aka bata tasaka, zarah ganin rigar shara-shara yasa tazaro ido tare da cewa a'a jakkadiya ba zan sa wannan ba canzamin wata.

murmushi jakkadiya tayi tace ranki yadad'e kar kidamu ai alk'yabba zaki d'aura a sama.
Zarah dai badan tasoba tahak'ura tabar rigar,

saida aka k'ara fesheta da performs sannan aka d'aura mata alk'yabba daga saman kayan nan tayi gwanin kyau.

duk'ar da kai jakkadiya tayi tace ranki yadad'e kinyi kyau, d'an guntun murmushi zarah tayi.
jakkadiya tace ranki yadad'e idan kin bamu izini zamu iya tafiya,

zarah gaba tawuce suna biye da ita a baya fuskarta kawai zaka kallah kagane tana cikin tashin hankali marar misaltuwa.


_Comments_
     *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
?👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_*Ina kuke team d'in zarah da kuma team d'in yarima suhail kuzo yau ranar takuce, lallai kunyi k'ok'ari sosai, saidai kash ni bana tare da ku, duk wanda yake tare da ni a team d'in Gimbiya sumayya toh yafito😍*_

*PAGE* 2⃣5⃣

ko da suka shiga part d'in yarima lokacin bai dad'e da dawowa aikiba kasancewar busy yake idan yafita baya samun dawowa sai dare,  tsaki yaja ganin bedsheet an shimfid'a masa yace kai dada ba zata ta6a kyaleni inhutaba.

bayan ya fito wanka ya shirya zaune yake bakin gadonsa yana waya jin ana knocking d'in k'ofa yasa yabada izinin ashigo.

zarah ce gaba sai jakkadiya a baya ido hud'u sukayi da yarima sai da gabanta yafad'i tsaye tayi takasa k'arasawa, jakkadiya ce tazube tana kwasar gaisuwa, d'aga mata hannu yarima yayi nan tafara kame-kame am daman... yarima katseta yayi yace zaki iya tafiya.

jakadiya  k'ara duk'ar da kanta tayi tace atashi lafiya ranka yadad'e, sannan takalli zarah tace saidasafe gimbiya,  zarah gyad'a mata kai kawai tayi.

bayan jakadiya ta fita yarima bai waiwayi inda zarah takeba, zarah tsayuwa tayi na kusan minti biyar ga tsoro da yabaibayeta ga gajiyar tsayuwa har tafara tunanin tazauna k'asa chan sai taji muryar yarima yace zaki iya zuwa kid'auro alwallah.

zarah muryarta tana rawa tace ina da alwallah,  d'ago kai yarima yayi yakalleta sannan yatashi yashiga toilet yad'auro alwallah.

bayan ya fito wajen da aka tanada dan sallah yanufa babban dardumane a shimfid'e sai 'yar k'aramar drawer mai d'auke da alqur'anai da sauran littafan addini.

yarima batare da ya kalletaba yace kizo muyi sallah.

zarah ahankali tace nayi sallah, ganin yarima yajuyo ya kalleta yasa dasauri tazo bayansa ta tsaya, sannan tace banzo da hijab ba.

yarima batare da ya kalletaba yawuce yaje yabud'e wardrobe sai gashi da hijab nan yamik'a ma zarah takar6a tasaka.

yarima yana gaba zarah tana bayansa yaja musu sallah, raka'a biyu yayi musu bayan sun sallame addu'a sosai yayi musu sannan yajuyo yakama kan zarah yayi mata addu'a.

zarah ko da tana a tsorace saida ta jinjina ma ilimin yarima dan bata d'auka yana da addini hakaba.

yarima kallonta yayi nan yayi mata tambayoyi akan addininta zarah a nutse take basa amsa, shi kansa yarima saida taburgesa ammah bainuna mataba, wayarsace da tafara ringing yad'auka yana ta wayarsa akan wata kwangila da zai bada saida yayi kusan minti talatin yana waya har ya mance da zarah da take zaune bayansa a nan tafara gyangyad'i.

mik'ewar da yarima yayi ne yalura da ita, janye wayar yayi daga kunnensa yace kije kikwanta in bacci zakiyi.

zarah batace komai ba tana kallonsa yasa k'afa yafita daga d'akin.

parlour yakoma yasha ruwa sannan yazauna saman cushin yacigaba da wayar.

zarah jin shuru bai dawoba cikin ranta tace ko dai yabar min nan inkwanta shi parlour zai kwana, murmushi zarah tayi nan hankalinta yad'an kwanta tatashi taje saman bed d'insa saida tacire alkyabba da hijab d'in sannan takwanta tare da jawo blanket tarufe jikinta takashe gloves nan da nan bacci yayi awon gaba da ita.

yarima ko da yagama wayar d'aga kai yayi yakalli agogon bango ganin 11:55pm yasa yamik'e yanufi bedroom dan yakwanta, kunna gloves yayi nan haske yagauraye d'akin hango zarah yayi tayi daid'aya saman gado sai baccinta takeyi,  shi shaf ma ya mance da akwai mutumin a d'akin.

tsaki yaja har ya juya zai fita sai yayi wani tunanin, ahankali yataka yaje saman gadon yahau, kwanciya yayi gefen zarah tare da juya mata baya yana sak'e-sak'e cikin ransa.

saida yayi kusan minti goma sannan yajuyo yana mai k'arema zarah kallo ya dad'e yana kallonta sannan daga baya yakai hannu yajanyota jikinsa tare da rungumeta saida gabansa yafad'i, nan yakai hannu yafara shafar jikinta, wani irin yarr yaji saida yadad'e yana shafarta sannan yafara k'ok'arin rabata da rigar da take jikinta

zarah har k'ara gyara kwanciyarta take a jikinsa alamun taji dad'in kwanciyar jin ta6awar da akeyi mata tayi yawa yasa cikin bacci  tayi firgit tafarka ganinta jikin yarima yasa wani tsoro yad'arsu a zuciyanta cike da tashin hankali tashiga turesa tace nashiga ukku menene haka please kakyaleni.

yarima k'ara matseta yayi a jikinsa muryarsa tana rawa yace kinsan dai dole ko bama so sai mun amince ma juna saboda ansa mana ido yin hakan kawai zaisa kar a zargemu.

zarah cigaba tayi da turesa tace nidai kakyaleni wlh bana so,  bata ankaraba sai jitayi yarima ya rabata da rigar da take jikinta, fashewa tayi da kuka tare da turesa da dukkan k'arfin.

yarima ganin zata 6ata masa lokaci yasa yakwantar da ita tare da danneta, zarah cikin kuka tace dan Allah kayi hak'uri kar kayimin komai, yarima bakinsa yakai cikin nata yafara kissing d'inta, inda hannuwansa suka kasa tsayawa waje d'aya a jikinta,  ba yarima ba hatta ita kanta zarah saida salon yarima yarikitata batasan lokacin da tafara mayar masa da martaniba, sun dad'e a haka sannan daga bisani yarima yanemi hanya..........

kuka, yakushi, cizo babu wanda batayi masaba ammah bai kyaletaba dan yarima tuni ya fita hayyacinsa baisan inda kansa yakeba saida yasamu nutsuwa sannan yamirgina gefe yakwanta yana maida numfashi.

wani irin nishad'i ne da sanyi yaji yana ratsasa ji yake kamar bai ta6a sanin wata maceba sai akan zarah, ahankali yabud'e idonsa yasafkesu kan zarah da hawaye suke zuba idonta, blanket yajanyo yalullu6e mata jikinta sannan yamik'e yashiga toilet dan yatsarke jikinsa.

bayan ya fito d'aure yake da towel saida yashirya sannan yazo inda zarah take har lokacin kwance take tana cize le6e idanuwanta a rufe,  hannu yakai yafara yaye blanket d'in da take rufe da shi, dasauri zarah tabud'e idanuwanta da sukayi jawur tare da rik'o blanket d'in.

yarima kallonta yayi cike da tausayi yace ba abinda zanyi miki, taimaka miki kawai zanyi kiyi wanka.

zarah cikin muryarta da tadishe saboda kuka tace ni kakyaleni dakaina zanyi.

yarima yace ai baki iya takawa.
zarah cikin muryar kuka tace zan iya, tashi tayi zaune dakyar tare da k'ara gyara rufin blanket d'in.

ganin haka yasa yarima yatashi yad'auko mata towel yabata, nan zarah tafara kicin-kicin d'aura towel tana kare jikinta,  yanayin yadda takeyi taso taba yarima dariya, ganin haka yasa yajuya har saida tad'aura sannan yajuyo,  hannu yakai zai ruk'ota nan tafizge tace kabarni zan iya tafiya.

tana cize Le6e tasamu tamik'e, dakyar tasamu tayi taku d'aya nan tatsaya tare da lumshe ido, tana k'ara taku na biyu wani irin k'ara tasaki.

ganin haka yasa yarima yace ai daman nasan bazaki iyaba,  d'aukarta yayi bai zameta a ko'inaba sai cikin ruwan d'umin da yahad'a mata, wata irin k'ara zarah tasaki tare da ruk'unk'umesa,  yarima maidata cikin ruwan yayi tare da fizge towel d'in da yake jikinta, zarah dasauri takai hannu tarufe k'irjinta cikin kuka tace katafi zanyi da kaina,

jin haka yasa yarima yafito yabarta a toilet d'in,  saida tadad'e cikin ruwan sannan tacanza wasu.

saida tagasa jikinta sosai sannan tayi wankan tsarki tajawo towel tad'aura,  ahankali take takawa tana cize le6e har tafito,  lokacin yarima har yacanza bedsheet

ganinta yasa yanufi wajenta, zarah muryarta tana rawa tace kabarni zan iya.

jin haka yasa yarima yatsaya yana binta da kallo har taje wajen gadonsa tazauna.

Zuwa yayi cikin lallashi yace kikwanta mana,  girgiza masa kai tayi cike da tsoro tace a'a nan ma yayi,

yarima haushi yaji ganin yadda yake lalla6ata ammah sai botsarewa take dan haka yawuce yaje yayi kwanciyarsa tare da juya mata baya.

zarah ganin haka yasa tajingine kanta da gadon a nan bacci yafara fizgarta, daga k'arshe da taga ba dama ta ida hayewa saman gadon ta kwanta chan k'arshen gado tare da takure jikinta har a lokacin tsoron yarima takeyi.

bayan kamar minti goma yarima yajuyo yanayin yadda take baccin yasa yayi murmushi nan yamik'e ahankali yagyara mata kwanciyarta tare da rufeta da blanket.

gefenta yakwanta tare da zuba ma kyakkyawar fuskarta ido yana kallon yadda take baccin cikin nutsuwa,  daga k'arshe yajuya tare da maida idanuwansa yarufe, tunanin darensu na farko da sumayya yafad'o masa a rai, dasauri yajanye tunanin daga zuciyansa gudun kar zargi yashiga,
ya dad'e kwance sannan daga baya bacci yayi awon gaba da shi

saida aka fara sallar asuba sannann yafarka, kallon zarah yayi da taketa baccinta sannan yamik'e yaje yad'auro alwallah bayan yafito,  tadata yashiga ammah tak'i tashi,

ganin haka yasa yarima yafara k'ok'arin zareh mata blanket d'in da take rufe da shi,  dasauri zarah tabud'e idanuwanta cikin muryar bacci tace na farka.

yarima yucewa yayi yakabbara sallarsa, har yagama sallah zarah tana nan zaune saman gado, saida taga ya juyo ya kalleta sannan tamik'e dakyar tana bin bango tare da cize le6e ahankali take takawa har tashiga toilet.

bayan tayo alwallah rigarta tad'auko tamaida sannan tasaka hijab, nan tasamu tayi sallah.

bayan ta gama a nan k'asa tayi kwanciyarta tare da k'udindine jikinta nan da nan bacci yad'auketa.

yarima bayan ya gama addu'o'insa ganin zarah tayi bacci yasa yawuce yahaye gadonsa yayi kwanciyarsa.

zarah juyi takeyi baccin duk batajin dad'insa saboda k'asan da take kwance, juyawa tayi tare da farkawa jin wuyanta zaiyi ciwo yasa tamik'e dakyar tataka taje takwanta chan k'arshen gado nan tacigaba da baccinta.

wajen k'arfe tara yarima yafarka, mamakine yakamasa ganin zarah saman gadon baisan lokacin da tadawoba.

tashi yayi yaje yashiga wanka bayan ya fito shiryawa yayi cikin boyel d'insa fari yayi gwanin kyau,  jin ana knocking d'in k'ofa yasa yakalli zarah da taketa bacci ahankali yabud'e k'ofar yafita gudun kar tafarka,  a tsakiyar parlour yatarar da jakadiya tsugunne k'asa ganinsa yasa duk ta dabarbarce tare da duk'ewa k'asa tace ranka yadad'e kagafarceni daman dadace ta aikoni.

haushine yakama yarima cikin ransa yace wannan tsohuwar ba zata ta6a barina inhutaba,  fuskarsa ba alamun fara'a yace me tace?
jakadiya tace Allah yaja da ranka daman bedsheet ne tace ind'auko a wanke.

yarima zama yayi saman cushin sannan yace zaki iya shiga kid'auka.

jakadiya tun kan ya ida rufe baki ta mik'e ta nufi bedroom d'insa bayan ta d'auko duk'awatayi tace ranka tadad'e... hannu yarima yad'aga mata tare da nuna mata k'ofa.

dasauri jakadiya tamik'e tafita.

yarima tashi yayi yashiga bedroom,  kallon zarah yayi da har lokacin take bacci sannan yaje saman bedside yad'auko yawarya,  yana d'auka zarah tabud'e idonta nan sukayi ido hud'u da yarima,  ahankali yajanye idonsa daga kallonta, saida yafara tafiya zai fita batare da ya juyoba yace zan sa akawo miki kayanki nan sai kiyi wanka ga magani nan saman bedside idan kinci abinci sai kisha, wayarsace da tafara ringing yayi picking tare da fita daga d'akin.

zarah binsa tayi da kallo har yaffice yamaida mata k'ofar yarufe, runtse idanunta tayi hawayen da take dannewane suka shiga kwaranya daga idanunta tana jin wani k'unci a ranta.

yarima bayan ya fita part d'in zarah yaje bayan kuyanginta sun gaishesa nan yake basu umurni sukaima zarah kaya a part d'insa sannan yatafi.

A chan 6angarensu dada jakadiya da gud'arta tashiga part d'in dada,  dada jin jakadiya tayi gud'a yasa tafahimci dalilin haka.

jakadiya gaban dada taduk'a cike da girmamawa tace ranki yadad'e,  gimbiya ta kawo mana mutuncinta a masarauta, nan jakadiya tabud'e ma dada bedsheet tagani.

murmushi dada tayi tace Alhmdllh daman daga ganin yarinyarnan nasan zatayi hankali, gaskiya naji dad'i yanzu aje ayi sanarwa kowa yasani sannan kuje kugwada ma su memartaba da iyayen yarima.

duk'awa jakadiya tayi tace an gama ya shugabata sannan tamik'e tafita tana gud'a.

A fada memartaba shanuwa guda yaba zarah, sannan yabada babban sa guda yace ayanka kowa yaci,  abban yarima rago biyu yabayar,  sultan abbas ma rago yabayar,  ko da akaje wajen sultana sadiya bak'in cikine yacikata haka tadaure taje tad'auko turmin Holland tabada, sultana bilkisu kuma sark'ar zinari tabayar,

nan gida yakauraye da murna, sumayya ko da taji dalilin murnar shigewa tayi bedroom d'inta tafad'a saman gado tacigaba da risgar kuka kamar wadda aka aikoma da sak'on mutuwa tsanar zarah taji ta k'aru a cikin ranta, dakyar tajawo wayarta takira sultana sadiya, sultana tunda taga Kiran tasan dalilin kiran da sumayya tayi mata.

tanayin picking tajiyo kukan sumayya cike da tashin hankali tace sumayya menene abin kuka?  meyasa kikeson 6ata hawayenki akan wata banza 'yar talakkawa kiduba darajata da ta mahaifinki a gidannan kema kinsan kin zarce kowace mace.

sumayya cikin sheshek'ar kuka tace ummah wlh na tsani yarinyarnan zan iya kasheta saidai nima akasheni.

sultana sadiya cike da tashin hankali tace kisa kuma?  haba sumayya nace kidaina ik'irarin kisa kibari mubi komai ahankali,

sumayya cikin kuka tace haba ummah kiduba kigani yanzu anyimin adalci saboda Allah?  ni lokacin da na auri yarima duk bansamu wad'annan abubuwan na al'adaba ammah wata bare daga zuwanta ta samu.

sultana sadiya cike da lallashi tace haba sumayya kiyi hak'uri man, nima hakan yayi min ciwo kibarmin komai a hannuna wannan yarinyar dole tabarmiki kidinki kiwala ke kad'ai, ina gargad'inki kar kikuskura kija ta rigima, dan kinsan abun fad'a baya wahala a masarautarnan, kibarta daga ita har wannan miskilin mijin naku duk zanyi maganinsu.

sumayya share hawayen fuskarta tayi cike da jin dad'i tace yauwa ummana saisa nake k'ara sonki.

sultana sadiya saida taga ta kwantar ma d'iyartata da hankali sannan sukayi sallama takashe wayan.

A chan 6angaren zarah bayan yarima yafita dakyar tasamu tasafko daga saman gadon saida tagyarasa sannan tashiga toilet, tak'ara gasa jikinta tayi sannan tayi wanka.

mai tashafa, fuskarta powder da lipstick kawai tasamu,  knocking d'in k'ofar da akeyine yasa tamik'e tajanyo hijab tasaka sannan tabada izini ashigo.

d'aya daga cikin kuyangarta ce tashigo cike da girmamawa taduk'a tagaishe da zarah, fuskar zarah d'auke da murmushi ta amsa, kuyangarta tace ranki yadad'e daman maigirma yarima ne yace akawo miki kaya.

zarah kar6ar kayan tayi nan kuyangar tamik'e tabar d'akin,  zarah gown d'in atamfarta tasaka, tana gaban dressing mirror tana d'aurin kallabi taji ana Knockin dakyar tafito parlour sannan tabada izini ashigo jakadiya ce fuskarta d'auke da fara'a tashigo, duk'awatayi k'asa tace Allah yataimaki gimbiya da fatan kin tashi lafiya?

zarah tace lafiya lou.

zarah ganin bakin jakadiya yana motsi yasa tace jakadiya ya dai?

jakadiya washe baki tayi tace ranki yadad'e ai mu abun murna ya samemu shiyasa nazo inmiki albishir kyauta kika samu mai tsoka a gidannan.

zarah cike da mamaki tace kyauta kuma? ta me?

jakadiya gyara zamanta tayi tace mrmartaba yabaki sa, mahaifin yarima da mahaifin gimbiya sumayya sun baki raguna, mahaifiyar sumayya ta baki atamfa, mahaifiyar yarima tabaki zinari duk suna wajen dada sai yarima yadawo za'a damk'a masa yabaki.

zarah da mamaki ya ida kasheta tace jakadiya duk na minene?

murmushi jakadiya tayi cike da jin dad'in labarin da take badawa tace ranki yadad'e ai nakawo butulcinki da kikayine gidan miji.

zarah saida gabanta yafad'i cikin ranta tace nashiga ukku yanzu saida kowa yasan abinda nayi?

jin tayi shuru yasa jakadiya tace kinsan gidan sarauta mutuncin mace shine taje a cikakkiyar budurwarta.

zarah kwallah tacika mata ido ahankali tace yanzu saboda Allah saida kowa yasan wannan abun?

jakadiya gyad'a kai tayi tace eh ranki yadad'e ai dole kowa yasani dan abun murna da farin cikine, nan jakadiya tak'ara duk'awa tace nabarki lafiya ranki yadad'e.

zarah kasa cewa komai tayi har jakadiya tafita daga d'akin, ahankali tace wannan wane irin tonon asirine, yanzu saboda Allah sai kowa yasan abinda nayi?
kife kanta tayi tadinga rusa kuka saida tayi mai isarta sannan tatashi taje dining tad'anci abinci kad'an sannan tajanyo alkyabbarta tasaka tafito takoma part d'inta.

sama-sama ta amsa ma kuyanginta gaisuwarsu tashige bedroom d'inta,  kwanciya tayi kanta yana kallon ceiling ahankali tunanin abinda yarima yayi mata daren jiya yadinga dawo mata a rai, hawayene suka dinga zuba daga gefen idonta, cikin ranta tace nasan ba'a son ransa yakusanceniba tsaki taja tace ina amfanin wannan masarautar da ake tursasa mutum dole, tunowa tayi da malam bello wani abu yatsaya mata a mak'ogwaro tace Allah sarki malam bello ina ma ace kaine kakasance mijina ba wannan ba, dasauri tajanye tunanin a ranta tare da cewa Astagfirrullah, sannan tajawo wayarta takira su mama dan sugaisa.


A chan 6angaren sumayya kuka taci sosai a ranar kasa cin abincin kirki tayi, kad'an-kad'an ummah ta kirata tabata hak'uri.

yarima ko da yadawo daga wajen aiki ko 6angarensa ba'a barsa yashigaba wani dogari yazo ya isar da kiran da dada takeyi masa,

ko da yaje turakarsu dada bayan yagaisheta dada fara'ar fuskarta takasa 6oyuwa kallonsa tayi tace d'an albarka hak'ik'a naji dad'in za6en da kayi dan ko bakomai takawo mana mutuncinta a gida kuma munasa ran bazata bamu matsalaba fatanmu nan da watanni tahaifo mana magaji.

shidai yarima tun da yazauna dannar wayarsa kawai yakeyi baice ufan ba, dada tana kallonsa tace yarima ina maka magana kayi shuru ka kyaleni, murmushi yarima yayi batare da yad'ago kansaba cike da k'osawa da maganar dada yace ina jinki dada.

dada tace au wulak'ancin nakane yamotsa?  shuru yarima yayi baice komai ba,  ganin haka yasa dada tace toh nidai nasihar da zan maka itace kazauna da matanka tsakani ga Allah, banda nuna banbanci, kahad'a kan matanka suzauna lafiya.

yarima yace toh dada,

mik'ewa dada tayi taje tad'auko masa kyautukan da zarah tasamu tabashi tace ga kyautukan da matarka tasamu sannan sanuwarta da raguna suna garke.

cike da mamaki yarima yace dada duk naminene?  dada tace na mutuncinta ne da takawo mana a masarauta,

yarima murmushi yayi yace kai dada har yanzu dai kuna nan da wannan abun.

dada tace kuma bazamu ta6a dainawaba,

yarima mik'ewa yayi tsaye cike da tsokana yace ranki yadad'e indai kuna raye ba

dada ganin tsokanarta yake yasa tayi shuru takyalesa har yafita daga d'akin.



_Comments_
        *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_~Alhmdllh laifin dad'i k'arewa, my blood zaynav ina tayaki murnar kammala novel d'inki mai suna *BASSAM* Allah yabaki ladar abinda kika fad'a daidai,  kurakuren da suke ciki Allah yayafe miki, muje zuwa sai munjiki a sabon novel~_

_*Yau page d'in nakine Sis Harirah nagode sosai da kulawa da soyayyar dakike nunamin Allah yabar k'auna😍*_

*PAGE* 2⃣6⃣

yarima ko da yafito daga turakarsu dada tasu yakoma direct part d'in zarah yawuce, lokacin zarah tana kwance saman bed d'inta kanta yana kallon ceiling,

a parlour kuyangintane zaune ganinsa yasa suka zube suna kwasar gaisuwa yarima baice musu komai ba yawuce yashiga bedroom d'in zarah,

zarah da take kwance jin anbud'e k'ofa yasa tad'ago kai ganin yarimane yasa cikin sauri tamik'e tare da d'an rissinawa cikin girmamawa tace sannu da zuwa,

yarima takawa yayi yaje yazauna bakin bed d'in nata tare da yi mata nuni itama tazauna jikinta sai 6ari yakeyi, ahankali cikin tsadaddar muryarsa yace ya jikin naki?

zarah murya tana rawa tace nawarke, yarima kallonta yayi nad'an lokaci sannan yakai hannu yata6a wuyanta, yace kinsha drugs d'in da na'aje miki? zarah gyad'a masa kai tayi.

yarima har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa, saida yad'auki kusan 2 minutes sannan yamik'a mata ledar da take hannunsa tare da mik'ewa.

zarah ganin yana shirin fita batare da yayi mata bayaniba yasa tace aje maka zanyi?

yarima tsayawa yayi da tafiyar da yake batare da ya juyoba yace kyautar da su dada suka bakine sannan a garke akwai shanuwa daga memartaba sai raguna daga abbah da daddy,  yana gama fad'in haka yafita yabar d'akin.

zarah binsa tayi da kallo har yafita sannan tabud'e ledar tana kallo dan daman jakadiya tayi mata bayanin komai, 'yar k'aramar sak'ar da tad'auke mata hankaline tad'auko tana dubawa tare da yin murmushi dan ko ba'a fad'aba tasan babbace, bayan ta gama duba kayan tashi tayi taje tasaka cikin wardrobe d'inta sannan tad'ibi kud'i taba wata kuyangarta tace takaima jakadiya.

tun daga ranar zarah bata k'ara taka d'akin yarima ba, shima kansa bai waiwayetaba ahaka har suka cinye sati d'aya.

A ranar da zata cika saki d'aya zaune take parlourn ta tana cin apple ammah hankalinta yana wajen kallo, bata ankaraba sai ganin gimbiya sumayya tayi ta shigo ba ko sallama,

fuskar zarah d'auke da murmushi tamik'e tsaye tare da d'an rissinawa tace sannu da zuwa,

gimbiya sumayya tsaki taja tana bin d'akin da kallo chan sai ta ta6e baki tace eh balaifi talakkawan iyayen naki sunyi d'an k'ok'ari wajen ganin sun fitar da ke kunya Allah dai yasa ba bashi sukaciba dan indai ma suna tunanin zaki samu kibasune toh bazaki ta6a samuba.

zarah da tunda tafara maganar tazuba mata ido cike da takaici tace sumayya duk wulak'ancin da zakiyi kitsaya a kaina kidaina saka iyayena a ciki.

dariyar rainin wayau sumayya tayi tace aikam dole ne iyayenki sushiga tunda kwad'ayi yasa suka bada aurenki, sannan inaso kisani yarima na gimbiya sumayya ne ita kad'ai babu macen da ta isa tara6i mijina tazauna lafiya, kinci sa'a da har kika iya had'a shimfid'a da mijina batare da nad'au matakiba, wama yasani ko kwad'ayayyun iyayenki suka cinna masa ke dan bana tunanin yarima zai iya son d'iyar talakkawa kamar ki.

zarah cikin 6acin rai tace haka dai kikace ammah ai shi yariman ba jahili bane yasan... katseta sumayya tayi cikin tsawa tace kar kisaki kid'aga min murya yakamata kisan da wadda kike magana
girgiza kai sumayya tayi tace hmm idan bakiyi gaggawar fita harkar mijinaba toh wlh zan iya yin komai, dan haka shawara tarage naki
tana kaiwa nan tajuya tafita tabar d'akin

zarah haushi ya ida cikata komawa tayi tazauna tare da dafe kanta tace wannan wace irin rayuwata? dole in samar ma kaina mafita dan wannan matar nalura bazata ta6a barina inhuta ba, chan sai zarah tayi murmushin da ita kad'ai tasan ma'anarsa.

_*After 1 week later*_

gimbiya sumayya ce nagani cikin shirin bacci ta fito sai karairaya take tanufi part d'in yarima,

ko da tashiga yarima kansa saida yayi mamakin ganinta shareta yayi yacigaba da kallonsa, sumayya ganin bai kulataba yasa ta isa wajen da yake zaune tazauna gefensa tare da kwantar da murya tace haba my sweetheart daga shigowata sai kad'auke min kai? yarima shareta yayi yacigaba da kallonsa,

sumayya kwantar da kanta tayi jikinsa tace kana fa jina, sai alokacin yace toh sumayya me kikeso ince miki? ko kina buk'atar wani abune wajena?

sumayya haushi yacikata cikin ranta tace wannan mutumin fa baida mutunci, chan sai tayi murmushi tace bana buk'atar kowa sai mijina rabin rayuwata.

yarima kallonta yayi alamun rashin yadda sannan yamaida kallonsa ga T.V

Sumayya kallon agogo tayi sannan tace sweetheart bacci nakeji please muje mukwanta.

yarima batare da ya kalletaba yace zaki iya tafiya kikwanta ni ba yanzuba,

gimbiya sumayya gyara kwanciyarta tayi a jikinsa cikin shagwa6a tace toh ni nan zan kwanta sai katashi kwanciya.

yarima baice mata komai ba yacigaba da kallonsa sai wajen 11pm sannan yatasheta suka shige master bedroom.

ahaka sumayya tayi kwananta biyu a d'akin yarima ko da sau d'aya bata yadda ta6ata masa rai ba.



zarah dai a kullum tana k'unshe a d'akinta bata yadda talek'o ko da wajen part d'inta ne.

yau dakanta tashiga kitchen tahad'a breakfast kasancewar ta tashi da wuri kuma tana da burin yarima yafara cin abincinta, dan tana ganin kamar hak'intane ita yafi cancanta tagirka masa ba masu aikiba. 

had'add'en yam ball tayi sannan tahad'a kunun gyad'a wanda yaji madara peak.

bayan tagama, wanka taje tayi tare da shiryawa cikin gown white nd black colour har  k'asa rigar take tana ja da k'asa sannan tayi rolling d'in kanta da bakin veil tare da feshe jikinta da turaruka,

kitchen takoma tajera kular da flask d'in saman tray sannan taba kuyangarta d'aya tad'aukar mata nan tafito tanufi part d'in yarima, duk inda ta gifta gaisheta akeyi tana amsawa cikin sakin fuska,  tun kan ta ida isa guards suka hangame mata k'ofa tare da rissinawa suka gaisheta, cikin sakin fuska ta amsa sannan tashiga,

a saman dining taba kuyanga umurni tad'aura tray d'in sannan tasa tasafke breakfast d'in da taga anje masa, bayan ta gama zarah tace zata iya tafiya.

bayan ta fita fargaba da tsoro duk suka kama zarah dan tana tunanin wulak'ancin da zata fuskanta a wajen yarima, ta dad'e tsaye sannan daga baya tabud'e bedroom d'insa tashiga.

tsaye zarah tayi bakin k'ofa tana kallon baiwa da take sharema yarima d'aki.

ganin zarah yasa baiwar taduk'a tagaisheta cike da girmamawa,  zarah hankalinta ya tashi sosai tace mekikeyi nan?

baiwar kanta a k'asa tace ranki yadad'e daman nice wadda gimbiya sumayya ta wakilta ina gyarama yarima d'aki.

daidai lokacin yarima yafito wanka, baiwar saida ta tsorata domin bata d'auka yarima yana nan ba tad'auka ya fita.

zarah batare da ta kallesaba tace mata daga yau kar kikuma shigowa d'akin nan nadakatar da ke daga gyaransa.

duk'awa kuyangar tayi tace  ranki yadad'e Allah yahuci zuciyanki yadda kikeso haka za"ayi.

zarah hanya tanuna mata, dasauri kuyangar tafita, zarah ma a tsorace tafito tadawo parlour, nan tahau gyarawa mamakin gimbiya sumayya yacikata cikin ranta tace duk ajin nata ammah bata ji zata iya gyaran d'akin mijinta.

bud'e k'ofar da akayine yasa tad'ago takalli gimbiya sumayya da tashigo ranta a 6ace.

zarah d'an rissinawa tayi tace barka da safiya, wata uwar harara sumayya tawurga mata tare da cewa ke har kin isa insa ayimin abu kihana?

zarah kallonta tayi tare da kallon kuyangar da take tsugunne k'asa sannan tayi murmushi tace ban fa isaba saidai nima ina da right inyi abinda nagadama tunda d'akin mijinane,

sumayya a harzuk'e tace ke kar kisaki kiyi min rashin kunya,
bawani maganar rashin kunya idan ke kikaso kigyara to zaki iyayi ammah wlh ban amince 'yar aiki tadinga shigomin d'akin mijiba yadda kike da iko da shi nima haka ina da iko, dan haka indai ke bazakiyiba toh ni zaniyi.

sumayya tayi mamakin zarah domin bata kawo ma ranta zata iya magana hakaba, 'yar dariya sumayya tayi tace lallai talakka bai iya samun wajeba idan yasamu sai yanuna yafi masu gida zak'ewa.

murmushi zarah tayi ko da taji ciwon maganar da sumayya tayada mata ammah bata nunaba, tace Indai shi maigidan ya kasa gyarawa ai ba laifi bane dan an zak'e, tana gama fad'in haka tawuce tacigaba da gyaran d'akin tabar sumayya tsaye tana ta balbala bala'i saida tagaji dan kanta sannan tawuce a zuciye tashiga bedroom d'in yarima suhail.

duk abinda suke akan kunnuwansa dan yana saurarensu,  ko da sumayya tashigo ko kallonta baiyiba yacigaba da abinda yakeyi, sumayya a k'ule tace yarima yanzu saboda Allah.... d'aga mata hannu yarima yayi tare da nuna mata k'ofa,  tsaye tayi tak'i tafiya,

d'ago kai yarima yayi yaimata wani irin kallon da yaja ba shiri tafita tabar d'akin.

zarah ko da tagama gyara masa parlour ganin har lokacin bai fitoba yasa taje tayi knocking tare da bud'e k'ofan tashiga.

yarima da yake zaune ahankali yad'ago kai yakalleta.
zarah d'an rissinawa tayi tace ga breakfast d'inka chan a dining.
yarima shuru yayi baice komai ba, sai chan yamik'e yafito.

dining yaje yazauna zarah dakanta tayi serving d'insa sannan taje bedroom d'insa tagyara masa tass, bayan tagama tafito takoma part d'inta.

yarima ya d'anci ba laifi dan rayuwarsa yana son abincin gargajiya shi da memartaba halinsu ya zo d'aya.

bayan ya gama bedroom d'insa yakoma yad'auki wayoyinsa yafito yanufi wajen aiki.

zarah saida tatabbatar da ya fita sannan tafito tanufi part d'insa ko da taduba abincin taga yaci balaifi, har cikin ranta taji dad'in hakan, kuyangarta tasa takwashi kulolin tace suje suci, ko da tadawo part d'inta tunani tashiga yi me zata girka masa a k'arshe dai tayanke hukuncin tayi masa tuwon shinkafa miyar ganye dan daman ummi ta fad'a mata yarima yanason abincin gargajiya sosai,

kitchen tashiga bata yadda kuyanginta suyi mataba cewa tayi subarsa saidai gyaran kayan miya da blending kawai sukayi mata.

haka tazage tad'and'ara girkinta tasaka masa acikin had'add'un culars d'inta, nan kuyangi suka gyara mata kitchen tas.

Gimbiya Zarah  saida ta tabbatar da dawowar yarima sannan tasa aka jera abincin asaman tray kuyanginta suka d'auka tana gaba suna biye da ita a baya har sukaje 6angaren yarima nan guards d'insa suka gaisheta cike da girmamawa sannan suka bud'e mata k'ofa tashiga, kuyangi a saman dining suka jera abincin sannan suka zube tare da cewa mun cika umurninki ya shugabanmu,  gimbiya zarah gyad'a musu kai tayi sannan tace zaku iya tafiya.

suna fita cikin takunta  tanufi bedroom d'in yarima suhail tayi knocking yarima da yake tsaye gaban mirror yana shiryawa jin ana knocking yasa yace yes saboda a tunaninsa gimbiya sumayya ce.

gimbiya zarah bud'e k'ofar tayi a hankali tashigo daga d'an nesa da shi kad'an tatsaya tad'an rissina kad'an tare da cewa ur lunch ix ready.

yarima suhail d'auke kansa yayi daga kallonta yacigaba da abinda yakeyi kamar ba zaiyi magana ba sai da suka share kusan minti biyu a haka sannan yace ohk am coming.

gimbiya zarah d'an rissinawa tayi sannan tafito tadawo parlour tazauna saman d'aya daga cikin kujerun d'akin, saida tayi kusan Minti goma a zaune sai ga yarima ya fito sanye da kayansa na alfarma yana takun nan nasa na k'asaita,  zarah tana ganin ya fito tamik'e tsaye yana gaba tana biye da shi har sukaje dining ganin ya yi tsaye yasa tagane abinda yake nufi dan haka tajanyo masa kujera yazauna,
sannan tayi serving d'insa itama tajawo kujera tazauna tana dannar wayarta, ta gefen idonta tana kallon yarima suhail yana cin abincinsa ahankali yana yatsina fuska kamar Wanda akayi ma dole, yana cikin ci aka kira wayarsa, baici wani abun kirkiba yamik'e. 

itama mik"ewa tayi tabi bayansa suka nufo k'ofa zasu fita,  zarah tayi knocking dasauri guards suka bud'e k'ofar nan suka duk'a suna kwasar gaisuwa wajen yarima da gimbiya zarah,

yarima hannu kawai yad'aga musu sannan yawuce gimbiya gefensa tatsaya nan guards suka take musu baya.

gimbiya sumayya da tadawo daga 6angaren iyayenta kuyangi suna take mata baya tsayawa tayi cak tana kallon yarima da yake jere da zarah suna tafiya,  dasauri tanufi inda suke tana zuwa tasha gabansu tatsaya,  yarima suhail kallonta yayi batare da yace komaiba,  gimbiya zarah d'an rissina ma sumayya tayi tace barka.

gimbiya sumayya harara tawurga mata sannan tamaida kallonta ga yarima tace yarima inason ganinka.

yarima suhail cikin rashin damuwa yace toh ai gani kin ganni,  gimbiya ta6e baki tayi tace ai ba irin wannan ganinba magana nakeso muyi.

yarima suhail shuru yayi kamar ba zaiyi magana ba sai kuma chan yace ina saurarenki,

gimbiya cikin fushi tace haba yarima dan zanyi magana da kai ba zaka zo muke6eba kaduba kaga wannan 'yar talakkar tana nan kuma ga bayi da kuyangi gabansu kakeso inyi?

zarah murmushin talaici tayi tare da d'an rissinawa tace ranki yadad'e nabarku lafiya, har tajuya zata tafi da mamakinta kawai sai taji yarima ya rik'o hannunta dasauri tajuyo takallesa fuskarta d'auke da mamaki ammah shi kuma yarima ba ita yake kalloba fuskarsa tana akan ta gimbiya sumayya.

gimbiya sumayya cike da mamaki take kallonsa ganin baida niyar yin magana yasa tace yarima ya haka magana fa nakeso muyi miye nawani rik'o wannan gajar?

yarima suhail fuskarsa babu alamun wasa yace itama matatace kamarki kuma indai kinsan ba zaki iya maganar a gabantaba toh kibari kinzo room d'ina kisameni yana gama fad'in haka yaja hannun gimbiya zarah suka bar wajen nan guards suka take musu baya.

gimbiya sumayya takaici ya cikata ga kunyar dizgin da yarima yayi mata gaban ma'aikatansu jinjina kai tayi tace lallai yarima ni kawulak'anta kafifita bare akaina toh wlh ba zan yardaba, juyowa tayi takalli kuyanginta da suka sunne kansu k'asa domin sunsan yadda ran gimbiyarsu ya6aci toh suma sai ta6anasu,  tsawa tadakamusu tace uban mi kuka tsaya kuyi min a nan watau saurare kukeko?  jikinsu yana kyarma sukace a'a ranki yadad'e kigafarcemu,  hanya tanuna musu cikin fushi tace kubar nan,  dasauri har suna rige-rige sukabar wajen.

gimbiya sumayya cike da takaici tashiga zagaye wajen tana jin tsanar zarah tana dad'a k'aruwa a ranta.

zarah har wajen motarsa tarakasa saida taga ya shiga sannan tasunya jikin window tace adawo lafiya,

yarima hannu kawai yad'aga batare da yayi maganaba yabada izini akaja motar.

zarah ko da takoma part d'inta saman gadonta tafad'a murna shar takeyi dan tana ganin ko bakomai yarima yanuna itama tana da d'an matsayinta a wajensa ko da ace ba haka bane a cikin zuciyansa.

murmushi tayi tace yanzu zan nuna miki talakka ma daidai yake da kowa.



_Comments_
      *nd*
_Share_



_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

*PAGE* 2⃣7⃣

da dare zarah tunani take abinda zata girka ma yarima dan tana tsoron kar tagirka wani abu yak'i ci dan dama ummi ta fad'a mata ba kasafai yacika cin dinner ba, wayarta tajawo tanaso takirasa ammah ta rasa yadda zatayi takirasa, chan dai tadaure tayi dialing d'in numbers a karo na farko, wayar ringing take har tatsinke ammah baiyi picking ba, tsaki taja tace wannan mutumin ya cika wulak'anci wlh, a karo na biyu tak'ara dialing d'in number d'insa saida takusan tsinkewa sannan yayi picking,  zarah gabantane yashiga fad'uwa kasa yin magana tayi,  a chan 6angaren yarima ma shuru yayi yana jiran ayi magana dan Number d'insa da aka kirasa da ita wadda yake waya da family d'insa ne,

zarah jin baida niyar yin magana yasa tayi sallama, yarima da kamar ba zai amsaba sai chan daga baya ya amsa, zarah gabantane yashiga dukan ukku ukku muryarta tana kyarma tace am za zarah ce, yarima agadarance yace ohk, ya dai?

zarah shuru tayi tarasa abinda zatace sai chan tace daman tambayarka zanyi ko akwai abinda kakeso agirka maka,

yarima cikin rashin damuwa yace no bana cin abinci da dare, bai bari zarah tayi magana ba yakashe wayarsa.

zarah komawa tayi takwanta tare da jan dogon numfashi tace lallai mutumin nan halinsa sai shi.

around 9pm dot zarah  wanka taje tayi tashirya cikin kayan baccinta,  sannan tad'aura alkyabba daga saman kayan k'amshi kawai yake fita a jikinta, fitowa tayi tanufi part d'in yarima gabanta yana ta fad'uwa gudun kar ya wulak'antata sama-sama ta amsa ma guards d'insa gaisuwar da sukeyi mata,  ko da tashiga parlour ganin baya nan yasa taji sanyi a ranta, kallon k'ofan bedroom d'insa tayi tarasa yadda zatayi taje tabud'e tashiga cikin ranta tace toh in na shiga mi zan ce masa?  kawai ji tayi Zuciyarta ta karaya har ta juya zata bar d'akin sai kuma tayi wani tunanin, juyowa tayi takoma ahankali tabud'e bedroom d'in ahankali take bud'e k'ofar tashiga, yarima da yake zaune bakin gadonsa yana dannar wayarsa d'ago kai yayi yakalleta cike da mamaki ganinta tazo a lokacin,

zarah murmushi tayi tare da d'an rissinawa tace barka da dare, yarima da yake kallonta gyad'a mata kai kawai yayi, zarah takawa tayi cikin takunta mai jan hankali tanufi wajen bed d'insa,  cire alkyabbar tayi ta aje gefe sannan tazauna gefen yarima da yazuba mata ido.

itama kallonsa tayi tana murmushi tace ranka yadad'e ko dai inhad'o maka coffee ko shine kasha nasan bakaci komai ba,  yarima suhail d'auke kansa yayi daga kallonta yacigaba da dannar wayarsa.

zarah cikin ranta tace anya mutumin nan zai bada kai? murmushi zarah tayi tare da mik'ewa tanufi wajen freezer tabud'e nan tatsiyayo hollandia cikin cup sannan tadawo tazauna inda take,  mik'a masa cup d'in tayi tace ranka yadad'e gashi, 

yarima cike da mamaki yad'ago kai yakalleta dan bai ta6a tunanin haka takeba yad'auka wayewarta batakai hakaba,  zarah cikin siririyar muryarta tace kakar6a ranka yadad'e.

yarima kamar bazai amsaba sai kuma yatuno wulak'anci baida dad'i dan haka yamik'a hannu yakar6a ahankali yakai cup d'in bakinsa yayi kur6a d'aya sannan ya aje saman bedside,  zarah mik'ewa tayi tace  akwai abinda kake buk'ata ne?.

yarima suhail cike da rashin damuwa yace no zaki iya tafiya.

zarah murmushi tayi tace ranka yadad'e abun kuma har da korata ake? komawa tayi tazauna tace toh bayanzu zan tafiba.

yarima batare da yakalletaba yace duk yadda kikayi daidai ne,  ida kwanciya yayi saman bed d'insa tare da yin pillow da hannuwansa yamaida idanuwansa yarufe chan sai yace idan kin tashi fita kiyi switching d'in light d'in,

zarah jinjina lamarinsa tayi cikin ranta tace lallai mutumin nan yakai inda ban tunani baisan nima daurewa kawai nayi na aje kunya da tsoron da yake cikin rainaba, batace komai ba tayi switching d'in light d'in sannan takwanta gefensa cike da tsoro da fargaba babu wanda yak'ara yin magana ahaka bacci yayi awon gaba da su.

da asuba yarima ne yafara farkawa ta hasken da yake d'akin yakalli zarah da take ta baccinta yanayin yadda take baccin kawai zaka kallah kagane ta takure kanta, janye idanunsa yayi daga kallonta tare da mik'ewa yanufi toilet.

bayan yayi alwallah tsaye yayi bakin gadon yarasa yadda zaiyi yatasheta, dabara ce tafad'o masa nan yakunna gloves haske yagauraye d'akin.

ganin zarah ta motsa yasa yace kitashi kiyi sallah,
ahankali tabud'e idonta tasafkesu akan yarima da yake shirin fita,
saida yafita sannan tamik'e  tashiga toilet.

bayan ta gama sallah alk'ur'ani tad'auko tana karantawa har yarima yadawo daga masallaci yakoma ya kwanta, kallonta yake a karo nafarko da yaji ta d'an burgesa dan arayuwarsa yanason mace mai rik'on addininta, tunani yashiga yi yanaso yatuno tun da ya auri sumayya idan ya ta6a ganinta da alk'ur'ani tana karantawa..... muryar zarah ce takatse masa tunani tace ranka yadad'e ina kwana?

yarima batare da ya kalletaba yace lafiya.

zarah kwanciya tayi gefensa nan suka koma bacci.

wajen 8am zarah tafarka daga baccin da take, kallon yarima tayi da yake baccinsa hankali kwance  yanayin yadda yake baccin ma saida tajinjina kai cikin ranta tace baccinma cikin izza akeyinsa, doguwar fuskarsa take kallo cikin ranta tace wannan da ummi yake kama dan kyauntane yad'auko, gaskiya ya... gabantane taji ya shiga fad'uwa dasauri tajanye idonta daga kallonsa, ahankali tasafko daga saman bed d'in tad'auki alkyabbarta tasaka sannan tafita daga d'akin.

ko da takoma part d'inta kuyanginta suka dinga zubewa suna kwasar gaisuwa, ko da tashiga kitchen ruwan zafi tadafa wanda yasha kayan k'amshi sannan tasoya chips,

bayan ta gama bedroom d'inta tashiga taga angyarasa tass dan haka tawuce toilet tayi wanka, bayan ta fito gaban dressing mirror tazauna tad'and'ara kwalliyarta sannan tabud'e wardrobe d'inta tad'auko material blue mai ratsin lemon green tasaka sannan tad'aura alkyabbarta lemon daga sama, ta dad'e tana kallon kanta a mirror sannan tafito tatarar da kuyangarta kande ta shirya breakfast d'in a tray tana jiran fitowarta.

zarah tana gaba hinde tana bayanta sukaje part d'in yarima, hinde a saman dining ta jera sannan tafita.

zarah tura k'ofar bedroom d'in tayi ahankali, ido suka had'a da yarima da yafito wanka, murmushi tasakar masa tace barka da safiya, yarima janye idonsa yayi daga kallonta yana taje kansa yace barka.

zarah ahankali tataka zuwa wajen bed d'insa tagyara sannan tafita takoma parlour tagyara masa tare da kunna turaren wuta, nan da nan d'akin yagauraye da k'amshi.

zama tayi takunna TV tana kallo bud'e k'ofar da akayine yasa tamaida kallonta ga yarima da yafito ya yi gwanin kyau yana ta zuba k'amshi,  ko inda take yarima bai kallaba yawuce yanufi dining, zarah mik'ewa tayi tabi bayansa, ita tajanyo masa kujera yazauna sannan tayi serving d'insa, itama tajawo kujera gefensa tazauna tana wasa da yatsun hannunta

yarima batare da ya kalletaba yace ke bakya breakfast d'in.

kallonsa zarah tayi fuskarta d'auke da murmushi tace nafison kai kafarayi ni zanyi daga baya.

yarima ta6e baki yayi baice komai ba yacigaba da breakfast d'insa, bayan ya gama mik'ewa yayi yanufi bedroom d'insa.

zarah binsa tayi da kallo har yashiga, bai wani dad'eba yafito zarah ganin zai fita yasa tace Allah yakiyaye adawo lafiya, yarima batare da ya kalletaba yace Ameen sannan yaficce.

zarah had'a breakfast d'inta tayi, bayan ta gama bedroom d'insa tashiga tagyara sannan takira kuyangarta tazo tad'auki sauran breakfast d'in tafita.



da rana ma haka tashirya masa lunch mai rai da lafiya takai masa part d'insa.


around 9pm coffee tahad'a ma yarima bayan ta gama shiryawa tayi cikin shirin bacci taje part d'in yarima, a bedroom tasamesa yana shirin kwanciya fuskarta d'auke da murmushi tace ranka yadad'e barka da dare.

yarima batare da ya kalletaba yace barka.

bakin gadonsa zarah tazauna ta aje cup d'in coffeen a saman bedside,  bayan yarima ya gama zarah tace masa ga coffee nahad'o maka, yarima kallonta yayi yaga itama kallonsa take fuskarta d'auke da murmushi zuwa yayi yazauna gefenta tamik'o masa cup d'in, yarima k'ar6a yayi yana d'an sha a hankali saida yasha kusan rabin cup d'in sannan ya aje tare da mik'ewa yanufi toilet.

bayan ya fito saman bed d'in yahau yakwanta ganin haka yasa zarah takashe gloves masu haske tabar marassa haske sosai, sannan itama takwanta gefensa, bayan kamar minti biyar ahankali tamaida kanta a saman k'irjinsa, ba yarima ba hatta ita kanta zarah saida taji wani iri,

muryar yarima taji yace ya dai?
zarah cikin wata irin muryar da ita kanta batasan tana da itaba tace bakomai ji nayi kwanciyar batayi min dad'iba saisa,
yarima kallonta yayi sannan yamaida idanuwansa yalumshe.

zarah murmushi tayi tace wannan mutumin jin kansa yayi masa yawa, tunowa tayi da lecture d'in da Hajiya kubra tayi mata, ahankali tad'ago kanta tana k'are ma kyakkyawar fuskarsa kallo tana tunanin ta yadda zata 6ullo masa, yarima bud'e idonsa yayi yana kallonta yace wannan kallon fa?

zarah har ta bud'e baki zatayi magana bata ankara ba saidai jin bakinsa tayi cikin nata, zarah biye masa tayi tashiga nuna masa nata salon, ammah nan da nan yarima yarikitata tafita hankalinta batasan lokacin da yarabata da rigar jikintaba, ko da tadawo hankalinta kyarma tashiga yi tana neman turesa ammah ta kasa. nan tafara k'wallah muryarta tana rawa tace dan Allah kadaina bana so.

yarima yanayin yadda tayi maganar ta so tabasa dariya, murmushi yayi yace ai naga abinda kikeso kenan,
zarah fashewa tayi da kuka tace wlh bashi nakeso ba dan Allah kakyaleni bana so,  yarima shareta yayi yana jinta tana ta magiyarta ammah bai saurara mataba,

ko da ahankali yabi da ita ammah saida zarah tayi kuka, bayan ya samu nutsuwa janye jikinsa yayi yatashi yabar zarah tana kuka yaje yayi wanka.

bayan ya fito komawa yayi yakwanta, zarah harara tashiga wurga masa karaf suka had'a ido dasauri tajawo towel tad'aura tamik'e taje tashiga toilet, saida tagasa jikinta sannan tayi wankan tsarki.

bayan ta fito rigarta tamaida sannan takwanta chan k'arshen gado tare da juya masa baya, yarima murmushi yayi yajuyo da ita batare da yace komai ba yajuya chan gefen,  zarah da mamaki take kallonsa cikin ranta tace shi kuma wannan me yake nufi da hakan?  d'an guntun tsaki zarah taja sannan tagyara kwanciyarta.

da asuba bayan sunyi sallah bacci suka koma zarah ba ita ta farkaba sai wajen 11 da mamaki tabi d'akin da kallo, jin ba alamun yarima a d'akin yasa tamik'e har parlour tazo taduba ammah babu alamunsa zama tayi saman kujera tare da dafe kai tace badai fita yayi baiyi breakfast ba?

mik'ewa tayi tagyara ko'ina sannan tafita tabar d'akin, ko da takoma part d'inta ji take ba dad'i tausayinsa yakamata ganin baici komai ba yafita, wayarta tajawo takirasa har saida takusan tsinkewa sannan yayi picking.

zarah jin yayi shuru yasa tace dafatan ka tashi lafiya?  yarima shuru yayi nad'an lokaci sannan yace lafiya.
zarah marairaicewa tayi tace shine kafita bakayi breakfast ba?
ai naga bacci kike, cewar yarima.
zarah kamar zatayi kuka tace ai da ka tasheni na had'a maka,
yarima shuru yayi baice komai ba, 
zarah tace ko inhad'a yanzu inbada akawo maka?
yarima yace no kar kidamu kibarsa kawai, yanzu ina aiki ne bye,
bayan ya kashe wayar zarah murmushi tayi tare da bin wayar da kallo, dialing din number d'in number d'in abbah tayi suka gaisa sannan yaba mama itama suka gaisa a wajensune takejin labarin yarima jiya yaje suka gaisa mama ce take shaida mata har kayan abinci ya aiko musu, zarah murmushi tayi har cikin ranta taji dad'in yadda yake mutunta iyayenta har da 'yar k'wallarta, bayan sun gama wayar tashi tayi tashiga kitchen had'add'ar fried rice tagirka wadda taji kayan lambu sannan tayi pep chicken,  bayan ta gama kunun aya mai dad'i tahad'a.

sawa tayi aka d'auka aka  kai masa part d'insa.


da dare tun da takwanta part d'inta juyi kawai takeyi tana jin duk badad'i musamman ma idan ta tuno yanzu haka yana chan tare da gimbiya sumayya sai taja tsaki, a k'arshe tajanyo wayarta tahau chart ba ita ta safkaba sai wajen 1am sannan tasamu tayi bacci.

A chan 6angaren gimbiya sumayya tun daga ranar da suka had'u da zarah da yarima bata k'ara sa zarah a idoba dan a yanzu batada aiki da tazauna sai chart tana gudunar da online business d'inta da zinat ta jonata, harkokinta kawai take kud'i suna shiga a account d'inta.

da dare shiryawa tayi taje part d'in yarima saida sukayi 'yar rigima sannan suka kwanta.

zarah tun da tayi sallar asuba bacci takoma ba ita tafarka ba sai wajen 11am nan tayi wanka tashirya, sannan tafito tanufi part d'in yarima dan a lokacin tasan ya fita,  tana zuwa daidai lokacin kuku d'insa yake shirin fitowa daga part d'in yarima d'auke da kayan abinci ganinta yasa yaduk'a Cikin girmamawa yagaisheta.

zarah cikin ranta tace toh wannan dama shi yake girka ma yarima abinci? zarah cikin sakin fuska ta amsa har yatashi zai fita nan zarah tace am me kake da suna?

washe baki yayi yace ranki yadad'e nine kuku halladu babu irin girkin da ban iyaba nine nake girka ma yarima abinci.

zarah tace ayyah Allah sarki halladu toh kayi hak'uri zan d'an dakatar da kai daga yi ma yarima girki dan nafiso yaci na matansa.

kuku cike da tashin hankali yaduk'a yace ranki yadad'e kiyi hak'uri kibarni incigaba wlh ta nan nake samu ana biyana.

murmushi zarah tayi tace kar kadamu hakan bazai shafi albashinka ba za'a cigaba da biyanka, kuma naji ance tunda shugaban masu kula da girkin gidannan yarasu ba'a nad'a waniba toh kaje kazama madadinsa.

cike da jin dad'i yaduk'a yak'ara yi mata godia,  murmushi zarah tayi tace bakomai kaje ai ka cancanci fiye da haka tunda ka san aikinka.

bayan ya fita zarah gyara d'akin tayi fess sannan takoma part d'inta tashiga kitchen, burabiscon shinkafa da miya tayi masa sannan tahad'a had'ad'en zo6o tasaka a freezer.

bayan ta gama wanka tashiga tayi tashirya cikin gown d'inta ash colour har k'asa tana sharar k'asa sannan tayi rolling da veil d'in rigar tayi kyau sosai.

parlour takoma tazauna tana jiran dawowar yarima,  saida ta daidaici lokacin da yadawo sannan tasa aka d'aukar mata abincin suka nufi part d'insa suna shiga daidai lokacin yarima da gimbiya sumayya suka fito daga bedroom d'insa,  cike da mamaki gimbiya sumayya take kallonta cikin ranta tace wannan yarinyar bazata daina shiga hurumina ba?
zarah ganinsu saida gabanta yafad'i murmushi tayi tare da d'an rissinawa tace ranku yadad'e barkanku da fitowa, yarima ne kawai yad'aga mata kai.

gimbiya sumayya kamar daman jira take cikin 6acin rai tace ke!  banason shishigi wa yabaki izini kigirka ma mijina abinci?  abin naki yana nema yayi yawa watau har ranar girkina sai kin zak'e ma mijina?

zarah murmushi tayi tace ranki yadad'e ba haka bane kawai gani nayi mu yafi dacewa mugirka masa ba kuku ba.

sumayya a fusace tace toh sarkin iyayi toh bari kiji ba za'a girkaba ke in girkawar kikeson yi toh kibari sai ranar girkinki ba nawaba, murmushi zarah tayi batace komai ba tamaida kallonta ga yarima tace ranka yadad'e lunch fa yana jiranka,

yarima wucewa yayi yanufi dining nan zarah tabisa suka bar sumayya tsaye takaici duk ya cikata, a gaban idonta zarah tayi serving d'in yarima sannan tawuce tafita tabar d'akin, sumayya ji take kamar tashak'eta dan bak"in ciki, tsanar zarah nan tak'aru a ranta,  ta dad'e a tsaye sannan daga baya a fusace tawuce tafita takoma part d'inta, saman gadonta tafad'a tare da k'walah ma shugabar kuyanginta kira mairo,  cikin sauri mairo tazo, sumayya cike da 6acin rai tace bani wayata,  dasauri mairo taje tad"auko mata wayar tamik'a mata rikicewa tayi ganin uwargijiyar tasu tana k'wallah,  cike da tashin hankali tace ranki yadad'e me yake faruwa?  sumayya batace komai ba takar6i wayar takira ummanta,  ummah tana d'auka cikin 6acin rai tace badai akan wannan gajar yarinyar bace kike kuka,

sumayya cikin shashek'ar kuka tace ummah kece kike hanani d'aukar mataki akan yarinyar chan toh wlh nagaji da abinda takemin,

a chan 6angaren sultana sadiya da take zaune mik'ewa tayi tafara zagaye dakin cikin 6acin rai tace wlh nabaki dama kid'auki duk matakin da kikaga ya dace, kikwaci mijinki tun kan wannan maýyar tak'wace miki shi, kema ai har da naki laifin, sumayya tsinke wayar tayi batare da sun gama magana ba,  dan a rayuwarta ta tsani taji ummah tace tana da laifi.

kallonta tamaida ga jakadiyarta da take tsugunne tace zaki iya tafiya,  jakadiyar d'ago kai tayi takalli gimbiya sumayya tace ranki yadad'e yanzu akan wannan yarinyar kike 6ata ranki? aini daman tunda naganta banga alamun mutunci a tare da itaba ranki yadad'e a duk lokacin da kike 6ukatar taimakona ashirye nake zan taimaka miki wajen ganin kin kwaci mijinki daga hannunta, tana kaiwa nan tak'ara dukar da kanta tace Allah yahuci ran gimbiya nabarki lafiya, mik'ewa tayi har zata fita daga d'akin sumayya ahankali tace dawo muyi magana.........



_Comments_
       *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_~Masha Allah *Dr Zain* ina tayaka murnar kammala novel d'inka mai suna *YAN GUDUN HIJIRA* hakika ka fad'akar, ka ilmantar sannan ka nishad'antar gaskiya na jinjina ma namijin k'ok'arin da kayi a cikinsa Allah yabada ladar abinda kafad'a daidai,  kura-kuren da suke ciki Allah yayafe maka sai munjiki a new novel 😍~_

_*My classic Feedoh marubiciyar SUHANA yau page d'in nakine kiyi yadda kikeso da shi my friendy ina ji da ke har cikin zuciyana Allah yabarmu tare*_

*PAGE* 2⃣8⃣

ko da jakadiya tadawo tatsugunna, gimbiya tattare nutsuwarta tayi tamaida gareta tace bakomai yasa nakirakiba sai dan naga alamun zaki iya taimaka min, inaso kirik'e min sirrina Indai kikayi haka toh zaki ji dad'ina ammah duk ranar da kika nemi kitona min asiri. murmushin mugunta gimbiya sumayya tayi sannan tace kinsan wacece ni

jakadiya duk'ar da kanta tayi tace ranki yadad'e kar kidamu a kodayaushe ina tare da ke zanyi duk abinda kikeso.

jinjina kai gimbiya sumayya tayi tace shikenan zaki iya tafiya

zarah ko da takoma part d'inta zama tayi saman cushin cikin ranta duk sai taji bataji dad'in abinda tayi ma sumayya ba dan tasan hakan da tayi bai daceba, ko da daman tayine dan tanuna mata talakka ma daidai yake da kowa, kuma duk saboda haka take daurewa tana nuna ma yarima kulawa dan har a lokacin batajin sonsa a cikin ranta,  jikinta taji duk yayi sanyi cikin ranta tace insha Allahu bazan k'ara shiga hurumin da banawa ba dole inje inbata hak'uri dan bansan yanayin da zata shiga ba.

sawa tayi aka fara kira mata kuku nan tayi masa bayani tace yakoma bakin aikinsa ammah banda ranar girkinta, dan bata buk'atar mijinta yaci girkin wani ranar girkinta,  nan yayi mata godia sannan yatashi yafita cike da jin dad'i.

zarah tashi tayi tanufi part d'in gimbiya sumayya daidai lokacin sumayya tafito daga bedroom d'inta, cikin 6acin rai sumayya tace me kikazo yi min nan munafuka?  ko munafuncin da maitan akazo yimin nan?

toh bari kiji Indai kin shanye yarima toh ni kurwata fes take duk wani maita da asiri bazasuyi tasiri akainaba.

zarah k'wallah ce tacika mata ido ahankali tace dan Allah kiyi hak'uri da abinda yafaru wlh...... A fusace sumayya tace wlh me munafuka? toh bari kiji wlh dole kirabu da mijina duk wani zak'ewarki daman ku 'ya'yan talakkawa haka kuke baku iya samun wajeba ina gargad'inki da kifita harkar mijina inko ba hakaba zan fiddo miki halina a fili zakisan wacece gimbiya sumayya,

zarah k'wallar da take cikin idonta tanemi tazubo dasauri tagogeta tace dan Allah kiyi..... ke! ni fice kiban waje tun kan in karyaki a nan wajen, matsiyaciya kawai.

zarah da mamaki take kallonta ahankali tajuya tafita tabar d'akin kwata-kwata bataji dad'in yadda gimbiya sumayya takasa fahimtarta ba.

tun daga lokacin zarah tadaina shiga sabgar yarima indai ba ranar girkinta bace.

_*Bayan Sati 'Daya*_

zarah tana zaune saman cushin hannunta rik'e da wayarta tana operated d'inta, kiran da yashigo wayartane yasa tabi wayar da kallo cike da mamaki ganin mai kiranta, ahankali tayi picking tare da yin sallama, daga chan 6angaren ciki-ciki yarima ya amsa mata sannan yace kizo inason ganinki, yana fad'in haka yakashe wayarsa.

zarah cike da mamaki tabi wayar da kallo cikin ranta tace ko me zanyi masa, mik'ewa tayi taje tad'auko veil d'inta tayafa sannan tafito tanufi part d'insa.

sumayya da bata dad'e da shiga ba zaune take gefensa tace sweetheart kiran me kakemin a wannan lokacin ko akwai abinda kake buk'ata?  banza yarima yayi yakyaleta, har ta bud'e baki zatayi magana shigowar zarah yasa tafasa a wulak'ance tad'aga kai takalleta cikin tsawa tace me kikazo yi mana nan kuma uwar shishigi?  zarah d'an rissinawa tayi tace barkanku da hutawa, sumayya tace kifita kibamu waje tun kan ranki ya6aci.

zarah kallon yarima tayi da yake kallon TV ammah hankalinsa yana wajensu, ganin baida niyar yin magana yasa tajuya zata fita,
muryar yarima tajiyo yace umurninta zakibi ko nawa?

ahankali zarah tajuyo takallesa har a lokacin kallonsa yana ga tv, ahankali yajuyo yakalleta tare da nuna mata kujera tazauna,

key d'in mota yad'auko yamik'a ma sumayya yace ga wannan key d'in motarki ne da nasiya miki,

sumayya kar6a tayi tana juya key d'in tace dagaske tawa ce yarima?  cike da Jin dad'i tarungumesa tace nagode sosai gaskiya naji dad'i,  Allah yabarmu tare d'an bak'in ciki kuma saidai yamutu.

murmushi zarah tayi tace Allah yasa alkhairi Aunty gaskiya natayaki murna, sumayya harararta tayi tace inma bak'in ciki kike toh saidai kimutu.

yanayin yadda tayi maganar taso taba yarima dariya, d'ayan key d'in da yake hannunsa yamik'a ma zarah yace kekuma ga naki, zarah da mamaki take kallonsa ji take kamar a mafarki ahankali tace ni kuma?

yarima yace kikar6a mana, zarah tasowa tayi tad'an rissina takar6a tace nagode Allah yasaka da alkhairi Allah yak'ara girma da d'aukaka,

sumayya da tunda taji yace ga ta zarah yasa tacanza fuska, cikin 6acin rai tace ban fahimcekaba? ya naga kaba wannan d'iyar talakkawan kana nufin matsayinmu d'aya da ita ko me?

yarima shuru yayi yakyaleta, sumayya a fusace tace gaskiya yarima baka kyautamin akan me zaka dinga had'ani da wannan 'yar ma..... kallon da yayi matane yasa takasa k'arashe maganarta, maida kallonsa yayi ga zarah da kanta yake sadde k'asa sannan yace motocinku suna parking space zaku iya zuwa kugansu, ke za'a fara koya miki taki ko da ace ba fita zaku dinga yi ku kad'ai ba na mallaka mukune abisa ra'ayin kaina.

zarah ce kawai tace  toh mungode Allah yasaka da alkhairi Allah yak'ara bud'i, mik'ewa tayi tace nabarku lafiya sannan tafita tabar d'akin takoma part d'inta.

sumayya kallon yarima tayi tace haba yarima gaskiya banajin dad'in abinda kakeyi min.

yarima da mamaki yake kallonta yace sumayya me nayi miki? 

shuru sumayya tayi batace komai ba,
kifad'a min abinda nakeyi miki Wanda ba daidai ba,  cewar yarima.

Jin batada niyar yin magana yasa yamik'e yashige bedroom d'insa yabarta nan parlour, cike da 6acin rai sumayya tatashi takoma part d'inta.

tun daga ranar yarima yasa aka fara koya ma zarah mota kasancewar sumayya da dama chan ta iya.

*Bayan kwana biyu*

gimbiya sumayya ce tafito daga part d'inta zataje turakar mahaifiyarta, tsaye tayi tana kallon zarah da tanufi part d'in yarima bayanta kuyangarta ce d'auke da tray.

gimbiya sumayya kallon kuyangarta mairo tayi tace ya kike ganin ya dace inyi inaso kar yarima yaci abincin,

murmushi mairo tayi tare da d'an rissinowa ahankali tayi ma sumayya rad'a nima kaina bansan abinda take cewa ba saidai gani nayi gimbiya sumayya tayi murmushi tare da jinjina kai tace hakan kuwa za'ayi yanzu nasan yarima bai dawoba,  mukoma ciki nafasa fita.

Bayan sun koma gimbiya sumayya sawa tayi aka duba mata fitowar zarah daga part d'in yarima, Bayan anzo anfad'a mata mik'ewa tayi tanufi part d'in yarima fuskarta d'auke da murmushi.

yarima ba shi yadawoba sai around 3 o'clock, zarah saida ta daidaici daidai lokacin da tasan yadawo sannan tatashi tanufi part d'insa kasancewar itace take da girki ranar.

tana shiga part d'insa daidai lokacin yafito daga bedroom d'insa hannunsa rik'e da waya yanayi, kallon zarah yayi da take murmushi sannan yawuce yanufi dining ko da yazauna zarah serving d'insa tayi sannan tazauna kusa da kujerar da yake zaune tana jira yagama waya.

gimbiya sumayya tana ganin wucewarta murmushi tayi tace munafuka yau zanso inga yadda zaki kwashe da yarima bari ma inbi inga yadda za'ayi wannan dramar.

lokacin da gimbiya sumayya tashiga part d'insa daidai lokacin yarima yagama wayar da yake,  ganinta yasa zarah tamik'e tsaye fuskarta d'auke da murmushi tace ranki yadad'e sannu da zuwa,

murmushi gimbiya sumayya tayi tace yauwa gimbiyar yarima,

da mamaki zarah takalleta dan wannan ne karo nafarko da taga murmushi a fuskarta gimbiya sumayya, 

yarima d'aukar spoon d'in yayi yad'ebo abincin zai kai bakinsa, kallon sumayya yayi da tazuba masa ido yace inzakici kizo kizauna kici.

gimbiya sumayya jayo d'aya daga cikin kujerun tayi tazauna nan zarah tayi serving d'inta, yarima ahankali yakai lomar farko a bakinsa, yana fara taunawa dasauri yazubar da abincin yana yamitsa fuska, zarah da mamaki take kallonsa tace yarima lafiya?

mik'ewa yayi dasauri yashige bedroom yanufi toilet, zarah kallon sumayya tayi itama sumayya kallonta tayi tace me yake faruwa?

zarah tace nima ban saniba ammah bari inje ingani dasauri tatashi tabisa a toilet tajiyosa yana ta kakarin amai, dagudu tabisa tarik'osa a rikice tace me yake faruwa please kafad'a min?

kuskure bakinsa yayi yafito yabud'e freezer yatsiyayi hollandia yasha, kallon zarah yayi da take tsaye yawurga mata harara yace wannan wane irin iskancine?

daidai lokacin gimbiya sumayya tashigo tace wai sweetheart me yake faruwa?

zarah tace me nayi maka?

harararta yayi yace au kina nufin bakisan abinda kikayi ba?

zarah tace wlh ban saniba.

yarima fizgota yayi yanufi dining da ita, kallonta yayi yace d'ibi abincin kici,

zarah d'iba tayi takai baki wani irin gishiri da yaji taji dasauri tazubar, cikin tashin hankali tace nashiga ukku ya akayi hakan takasance?

harararta yarima yayi yace kitambayi kanki, kwashi kwanukanki kifitar min daga d'aki,

zarah kwallah ce tacika mata ido tace wlh bansan yadda akayi hakan yakasanceba nidai lafiya lau nayi girki na dan Allah kayi hak'uri bari toh inje indafa ma mai d'an sauk'i.

hanya yarima yanuna mata yace kwashi kayanki kifita,

gimbiya sumayya tana tsaye duk dad'i ya cikata, ahankali tatako inda yake tace sorry sweetheart bari inje insa akawo maka abinci, kallon zarah tayi da take kwashe kwanoni tace ammah dai baki kyautaba wlh ya dai kamata kigyara halinki.

murmushi zarah tayi tad'auki tray zata fita, yarima kallon gimbiya sumayya yayi yace kema bita.

gimbiya sumayya tace haba yarima ni kuma me nayi?

hararar da yawurga matane yasa tawuce dasauri tafita cikin ranta tace tunda dai naci nasara ai bazan damu da kowane wulak'anci zakayi min ba....






_Comments_
    *nd*
_Share_


_Sis Nerja'art✍🏻_👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_*Wannan Page d'in nakune my Facebook fan's ina ganin sak'onninku nagode sosai inaso kusani nima inaji da ku irin sosai d'innan*_

*PAGE* 3⃣7⃣

bayan ta gama shirin fitowa tayi kuyanginta biyu suka take mata baya zuwa turakar dada, da sallamarta tashiga parlourn lokacin sultana sadiya da wasu mata ukkune sai dada kawai a cikin parlourn.

daga dada sai matan kawai suka amsa mata ammah sultana sadiya inba hararaba babu abinda take wurga mata har zarah tazauna k'asa cike da girmamawa tagaishesu nan suka amsa mata,

d'aya daga cikin matanne tace sannu 'yanmata kema kinzo kiga abun arzik'in ko?

sultana sadiya ce tayi karaf tace ko kuma tazo gulma ba, dada ce takalli sultana sadiya tace haba 'yarnan ko baki ganetabane? matar yarima fa ce,
murmushi sultana sadiya tayi tace ammah dada bakiga cikinmu tazo tazaunaba ko nan akwai sa'anta?
dada rik'e baki tayi tace oh ni.

d'aya daga cikin matan ne tacema zarah matso kusa kiduba ashe surukace, murmushi zarah tayi sannan tamatso sama-sama taduba kayan tana jinjina kai dan k'arshen kud'i an kashesu a wajen anzuba kaya nagani nafad'a, kasa sakin jiki tayi ganin kallon da sultana sadiya takeyi mata dan haka tayi murmushi tace masha Allah, Allah yasa alkhairi,
gabad'ayansu suka amsa da Ameen sannan tayi musu sallama tamik'e tabar d'akin.

daga nan tawuce part d'in iyayen yarima, lokacin da tashiga parlourn ummi ce da rahma sai Aunty husna (yayar yarima) zaune suna tattaunawa, gaba d'ayansu suka amsa mata sallamar da tayi,
ummice cikin sakin fuska tace oyoyo daughter,
murmushi zarah tayi tare da zama k'asa cikin girmamawa tagaishe da ummi,nan ummi ta amsa mata, sannan tagaishe da matar da taga tana kallonta, Aunty husna amsa mata tayi fuska sake, rahma ce tamik'e tace ummi bari inshiga daga ciki induba d'unkunan da aka kawo min, zarah ahankali tace rahma ina wuni?
lafiya kawai tace sannan tawuce tashiga bedroom d'inta.
Aunty husna kallon ummi tayi tace ummi wannan fa ammah ban santaba ko?
murmushi ummi tayi tace zarah ce matar yarima itace wadda akayi bikkin baku k'asar,
sannan ummi tace zarah wannan itace yayar yarima itace husna.
d'ago kai zarah tayi tad'an kalleta sannan taduk'ar da kanta.
dariya Aunty husna tayi tace ji wani kicifi miye nawani satar kallona? toh ai kin ganni nadai fi mijinki kyau.
dariya ummi tayi tace kindai fi sa ammah yarimana yafiki.
zarah k'ara duk'ar da kanta tayi cike da jin kunya.
Aunty husna tace haba ummi bama za'a ta6a had'amuba wannan d'an naki da jin kansa yayi yawa ko aurennan fa sai a wajenku nakeji kuma ko da nayi masa magana jiya da muka dawo yace min dai zai kawota,
ummi murmushi tayi tace ai my son abun nasa sai shi.
husna da take kallon zarah tace zarah halan ku ma yana yi muku miskilancin?
girgiza kai kawai zarah tayi alamun a'a
dariya husna tayi sannan tace kina dai karesane, yanzu dai nice babbar yaya dan haka kisashi yakawoki gidana kimin wuni.
ahankali zarah tace toh Aunty husna.
mik'ewa husna tayi tace ummi bari inshiga wajen dada,
ummi tace toh shikenan sai kin fito,
kallon zarah tayi tace zarah kigaishe da kishiyar taki tunda ita batazo muka gaisaba ko da kema d'in da sunan wajen ummi kikazo.
murmushi zarah tayi tace Allah Aunty husna bansan kinzoba da tun d'azun nazo, wucewa husna tayi zata fita tace bawani nan.

bayan ta fita ummi kallon zarah tayi tace zarah kinshiga wajen su dada?
zarah cike da jin kunya tace eh ummi naje naga lefe Allah yasa alkhairi,

Ameen, sannan tamik'e tace ina zuwa,
bayan kamar minti ukku sai ga ummi tadawo da wata leda saida tazauna sannan tamik'a ma zarah tace ga anko d'inki daman d'azun nake cema rahma zan aiketa takaimiki, zara kar6a tayi tace toh ummi nagode, nan zarah tabud'e hand bag d'inta tad'auko cheque d'in da yarima yabata tace ummi ga wannan ya bamu muyi hidimar bikki.

murmushin jin dad'i ummi tayi tace aikam dai kin gode ki aje wajenki.

ummi daman na ashoben ne,
ummi murmushi tayi tace no ki aje, ni nasaimiki ashoben yanzu sai kishirya kije kikai d'inki ko kuma inturo miki madam zainab tazo ta aunaki dan ta iya d'inki sosai,  sannan idan kina buk'atar wani abu sai kisa akaiki kisiyo.

zarah tace toh ummi nagode sosai Allah yak'ara girma da d'aukaka, Allah yak'ara rufa asiri.

ummi ta ji dad'in addu'an sosai tace Ameen zarah,
nan zarah tayi mata sallama tatashi takoma turakarsu,
daidai da zata shiga sai ga yarima da shaheed zasu fita, kallonta yarima yayi da mamakinta taji yace har kin dawo?
itama kallonsa tayi tace eh  tare da gaishe da shaheed, murmushi shaheed yayi yace lafiya lou amaryarmu, kinga najanyo miki ango zamuje rabon IV,
murmushi zarah tayi tare da kallon yarima da yatsareta da ido, sannan tamaida kallonta ga shaheed tace ai kai ne angon yanzu, Allah yasa alkhairi ,Allah yasa ayi damu.
cikin jin dad'i shaheed yace Ameen amarya, gaskiya naji dad'in addu'an nan saidai ince Allah yabarki da angon naki,
zarah kallon yarima tayi nan sukayi ma juna murmushi, sannan yarima yace toh sarkin surutu yanzu dai kazo mutafi ko infasa zuwa, dasauri shaheed yayi gaba tare da cewa amarya sai mundawo,

toh zarah tace sannan takalli yarima da yake tafiya tace sai kun dawo dear,
cak yarima yatsaya daga tafiyar da yake batare da yajuyoba saida yad'anyi murmushi sannan yace Allah yasa,

itama zarah murmushin tayi sannan tawuce tashige gida.

da ta isa part d'inta zama tayi saman cushin nan tabud'e ledar tana kallon anko d'in, less ne brown colour, sai material d'in dinner maroon sai head d'in da za'a had'a silver ne,  bayan tagama dubawa mik'ewa tayi takai ta adana sannan takwanta saman 3 seater tana kallo.

bayan sallar magrib madam zainab tazo har gida ta auna zarah nan zarah tabada kaya kala biyar ad'inka mata nan madam zainab tayi mata alk'awalin nan da kwana ukku zata kawo mata d'inkinta.


A chan 6angaren su yarima bayan sun gama kai I.V d'in ahanyarsu takomawa gida shaheed ne yake driving d'insu juyowa yayi yakalli yarima da yake jingine da sit d'in da yake, murmushi shaheed yayi yace ranka yadad'e duk gajiyarce hakan?
kallonsa yarima yayi yai murmushi cikin tsokana yace kawai ina tunanin auren shaheed ne kamar a mafarki.

dariya shaheed yayi yace to ya aka iya tunda kaima ka aje har biyu.

uhm shaheed kenan kaima kasan indai ason rainane da yanzu ban aje mace ko d'ayaba dan aure baya cikin plan d'ina a wannan lokacin kaduba fa kagani duka shekaruna nawa?

dariya shaheed yayi yace ai memartaba ya kyauta da yasa kayi aure  tunda a k'arshe ji kayi mace d'aya bata isarka saida kak'ara da wata, ai kai gaba takaika.

tsaki yarima yaja yace kai dai kasani,

eh d'in ni nasani kuma harda kai cikin sanin nawa.

uhm da rabon inhana wani auren k'anwata.

wani irin burki shaheed yaja jikake k'iiitt ya tsaya, dasauri yajuyo yakalli yarima da shima yake kallonsa rik'o hannun yarima yayi yace dan Allah yayanmu kar kaimin haka wlh inason rahma kamar raina.

yarima fisge hannunsa yayi daga rik'on da shaheed yayi masa sannan yace indai kaimin biyayya toh, inkuma kacigaba da rainani sai insa afasa.

Allah yahuci zuciyar yaya yarima duk yadda kakeso haka za'ayi.

oya ja motar mutafi.

cikin sauri shaheed yaja motar yace angama ranka shidad'e,
dariya sukasa gaba d'ayansu sannan yarima  yakoma yajingine kansa kamar bashine yagama yin dariya ba.

*WANSHE KARE*

yarima sawa yayi aka tara dukkan ma'aikatan gidan yabada kud'i da atamfofi aka raba ma mata, maza kuma yabada yadi da kud'i suma aka raba musu, nan sukaita murna suna shi masa albarka tare da yi masa addu'a.

lokacin da yarima yafito daga part d'insa zai fita gaba d'ayansu suka taru suka duk'a suna masa godia, murmushi kawai yarima yayi tare da d'aga musu hannu sannan yawuce.


Zarah tun da tatashi wani irin nishad'i takeji wanda ita kanta tarasa murnar me take.

kuyanginta da ma'aikatanta sukazo cikin murna suka nuna mata kyautan da yarima yayi musu tare da ce mata tak'ara yi musu godia wajen yarima, murmushin jin dad'i tayi dan har cikin ranta taji dad'in abinda yarima yayi.

yarima sawa yayi aka kawo ma rahma pics d'in design d'in gado da kujeru nan taza6a yace aje ayi mata room nd bedroom shine gudunmawarsa, ba rahma ba hatta su ummi sunji dad'i nan sukaita shimasa albarka.


6angaren shaheed ma yarima d'aukarsa yayi a mota yakaisa shagon d'inkinsa aka aunasa nan akace ma yarima zuwa jibi za'a kawo masa kayan, shidai shaheed mamakin yarima kawai yake dan baisan lokacin da yabada ayi masa d'inkuna ba, ko da yatambayi yarima shuru yayi bai tankasaba ganin haka yasa shaheed shima yaja bakinsa yayi shuru.

da dare zarah bayan tayi wanka saida tashafe jikinta da mayuka masu k'amshi da humra sannan tad'auki 'yar night gown d'inta wadda iyakarta gwiwa tasaka mai hannun vest, sannan tafeshe jikinta da turaruka kallon agogo tayi taga goma saura dan haka tad'auki hijab d'inta har k'asa tasaka sannan tafito tanufi part d'in yarima,

tana shiga a parlour tacire hijab d'in talinke ta aje sannan tabaza gashinta yasafka a kafad'unta, bud'e bedroom d'in tayi tashiga,

yarima da yake zaune saman gadonsa yana dannar wayarsa jin anbud'e k'ofa yasa yamaida kallonsa ga k'ofar, tunda yakafeta da ido bai d'aukeba.

zarah cikin takunta mai jan aji tatako tanufo gadon fuskarta d'auke da murmushi tahau, har a lokacin idanuwan yarima suna a kanta,
hura masa ido zarah tayi nan yak'yafta cikin sauri yajanye fuskarsa daga kallonta.

tallabo fuskarsa zarah tayi suka kalli juna nan tasakar masa murmushi, yarima zuba mata ido yayi sai chan yace ba dai haka kika tafoba,

shagwa6e fuska zarah tayi tace ya za'ayi intafo haka bayan nasan da mutane a gidan, gaban mijina kawai nazo haka.

yarima bakinta yake kallo tunda tafara maganar yanayinin yadda takeyi ne yaburgesa, fari zarah tayi masa da ido tare da cewa kallon fa?

janye idonsa yayi daga kallonta tare da ta6e baki sannan yacigaba da dannar wayarsa, zarah fisge wayar tayi daga hannunsa,

kallonta yayi yace ya haka? kibani akwai abinda nakeson yi.

bayanta tamaida hannuwanta tare da mak'e kafad'a tace nak'i,

murmushi yayi tare da kwanciya yalumshe idonsa, zarah zuba masa ido tayi tana murmushi sai chan takwanta itama saman k'irjinsa nan gashin kanta yarufe masa fuska.

fuskarsa d'auke da murmushi batare da ya bud'e idonsaba yajanye gashin, zarah d'agowa tayi tana k'are ma fuskarsa kallo nan k'irjinta yafara bugawa ahankali takai bakinta cikin nasa.

yarima kamar daman jira yake nan yacafke batare da ya bud'e idonsaba sukacigaba da kissing d'in junansu, kowa nuna k'arshen k'warewarsa yake nan duk suka fita hayyacinsu daga nan kid'i yacanza, dan yarima baibar zarah ba saida yabata wahala sosai shi kansa yasan ya wahalar da ita jurewa kawai tayi.

bayan komai ya lafa zarah jawo blanket tayi tarufe jikinta cikin d'an hasken da yake d'akin takai dubanta ga yarima da yake kwance idanuwansa a lumshe ammah fuskarsa d'auke da murmushi, saman jikinsa takoma takwanta tare da gyara musu rufin blanket,
ahankali taji yarima ya rungumeta tare da jan ajiyar zuciya,
k'ara gyara kwanciyarta tayi tanajin wani irin sanyi a ranta ahaka bacci yayi awon gaba dasu kowa da abinda yake sak'awa cikin ransa.

kiran sallar farkone yatashi yarima daga baccin da yake ahankali yajanye zarah daga jikinsa yazuba mata ido yana ganin yadda take baccinta a nutse ya dad'e yana kallonta sai kuma chan yajanye idonsa tare da mik'ewa yanufi toilet.

bayan ya fito saida yashirya sannan yaje yashiga tashinta, dakyar zarah tabud'e idanuwanta sannan tamaida talumshe, ahankali yarima yace kitashi lokacin sallah yayi.
juyar da fuskarta tayi gefe d'aya cike da jin kunya sannan tace umhum natashi.
jin haka yasa yarima yawuce yafita yatafi masallaci.

saida zarah taji fitarsa sannan tamik'e dak'yar tanufi toilet saida tagasa jikinta sannan tayi wankan tsarki tare da d'aura alwallah, bayan tafito rigarta da hijab tasaka nan tagabatar da sallar asuba.

bayan tagama a nan saman darduma tanad'e nan bacci yayi awon gaba da ita.

yarima ma koda yadawo daga masallaci bai shiga bedroom d'inba a parlour saman 3 seater yayi kwanciyarsa.

sai wajen k'arfe takwas yafarka nan yatashi yanufi bedroom, koda yashiga a saman darduma yaga zarah kwance tana bacci nan yawuce yashige toilet.

bayan ya fito a gurguje yashirya sannan yad'auki wayarsa da key d'in mota yafita saboda akwai patient d'in da zai ma operation nan da 'yan mintuna.

zarah ko da tafarka kallon agogo tayi ganin har 10:30am yasa cikin sauri tamik'e ganin ba yarima saman gadon yasa tafito parlour nan ma wayam cikin ranta tace Allah yasa wanka yakw ba fita yayiba.

har tagyara bedroom d'in ammah bataji k'arar ruwaba dan haka taje taduba toilet bakowa nan tagane yarima baya nan bataji dad'iba dan tasan dak'yar idan yayi breakfast.

saida tagyara masa ko'ina fes sannan tafita tabar d'akin takoma part d'inta

yarima sai wajen 4pm yadawo gida
bayan yayi wanka kwanciya yayi saman gadonsa dan yahuta saboda a gajiye yake yau.

gimbiya sumayya ce tashigo fuskarta d'auke da murmushi tace ashe kadawo? yarima baice mata komaiba nan taje tahau gadon takwanta gefe tare da tsaresa da surutu shi dai yarima idanuwansa a lumshe suke bai tanka mataba domin surutun da take duk ya ishesa,  ganin haka yasa gimbiya sumayya tad'anyi murmushi tace sweetheart na isheka da surutune?  yarima batare da ya bud'e idonsaba yace wani abu kike buk'ata?

haushi yakama gimbiya sumayya ganin kusan tambayar da yarima yake mata kenan idan yaga tana shige masa ko da kusan hakane ammah bakowane lokaci bane sai tana buk'atar wani abuba.
ahankali tace haba yarima meyasa kake min haka yanzu banda ikon zuwa wajenka sai idan ina buk'atar wani abu?

yarima banza yayi mata baice komai ba,  bud'e k'ofar da akayine yasa duk suka maida hankalinsu ga k'ofar,

zarah tsaye tayi tana kallonsu cike da mamaki kishine k'arara yabayyana a fuskarta ganin sumayya wajen yarima alhali kuma duty d'intane,  yarima cikin rashin damuwa yamaida idanuwansa yalumshe,

inda sumayya itakuma take ta wurga ma zarah harara kamar idanuwan zasu fito. chan sai tace malama lafiya zakizo kiyi ma mutane tsaye kina kallonsu?

Zarah abun ya bata haushi ganin sumayya tana nema taraina mata wayau wannan shine adoki mutum sannan ahanasa kuka,  d'aure fuska zarah tayi tace malama ba wajenki nazoba wajen mijina nazo dan haka babu ruwanki,  zarah takawa tayi ta isa wajen gadon tahau d'ayan gefen yarima takwanta tare da d'aura fuskarta saman k'irjinsa tace dear ashe kadawo, bacci zakayi?

yarima shuru yayi bai tanka taba ganin haka yasa takai hannu tafara shafar fuskarsa cikin wani irin siga.

haushine yakama sumayya ganin yarinya k'arama tana neman taraina mata hankali dan haka itama komawa tayi takwanta tana shafar gashin da yake kwance saman k'irjinsa, nan ita da zarah suka dinga wurga ma junansu harara,

cike da jin haushi zarah takai bakinta ga na yarima tafara kissing d'insa,  sumayya cikin 6acin rai tace kam ke ni zaki nuna ma tashanci?

ahankali zarah tazare bakinta daga cikin na yarima tayi murmushi tace Auntyna kin mance yau duty na ne?

yarima duk yana jinsu yayi shuru yakyalesu.

harara sumayya tawurga mata tare da cewa uban dutynki ke har kin isa daga kin samu antaimaka an aureki shine zaki zo kinuna min kema daidai kike da ni.

yarima bud'e idonsa yayi tare da tashi zaune fuskarsa a d'aure yace bakuda hankali zakuzo min d'aki ku duka biyun kukwanta min?

sumayya cike da nuna ita ta isa tace ai itace tashigo dan neman rigima

zarah tace ammah ai yau duty nane tayi min shishigi

yarima fuskarsa babu walwala yace kutashi kufitar min daga d'aki.

sumayya cike da isa tace ammah ai.....wani mugun kallo da yawurga mata yasa tayi shuru.

ganin haka yasa zarah tasafka daga saman gadon tana kumbure-kumbure nan itama sumayya tasafka.

yarima hanya yanuna musu da hannunsa fuskarsa ba alamun wasa ganin haka yasa gaba d'ayansu suka fita daga d'akin kowa yana hararar d'an uwansa.

gimbiya sumayya tace ke wlh idan kina min shishigi sai na miki dukan da bazaki iya tashiba saboda tare da yarima kikazo kika sameni.
inma banda abun talaka da yasamu waje sai yanuna yafi mai gida zak'ewa.

murmushi zarah tayi tace kar kidamu miji dai kike tak'ama da shi toh nima ina tak'ama da hakan sannan kuma arzik'i na Allah ne shi yakeba wanda yaso yahana wanda yaso dan haka yakamata kisan haka,  nabarki lafiya gimbiya sumayya tana gama fad'in hakan taficce tabar sumayya tsaye domin ta kashe mata baki bata d'auka zarah zata iya magana hakaba.

sannan daga baya itama taficce tana sak'e-sak'e cikin ranta.

yarima suna fita yakoma yakwanta tare da dafe kansa yana mamakin irin halin wad'annan mata nasa da kwata-kwata basu jituwa indai za'a had'u sau goma toh sai anyi fad'a sau goma koda ya san laifin duk na sumayya ne.

Zarah tana komawa d'akinta batabi takan kuyangintaba tashige bedroom tafad'a saman gado nan tafara wani irin kuka haushin sumayyane yacikata da tsananin kishin *yarima suhail* tabbas ayanzu tasan tana ma yarima wani irin so da baya misultuwa, tabbas ta yarda da maganar malam bello da yace zata so mijinta saidai idan bai amsa sunan namijiba.

A ranar haka tasha kukanta batada walwala ko kad'an kuyangi da bayinta duk sunyi mamakin ganinta acikin wannan yanayi.

sumayya ma ko da tashiga d'akinta korar kowa tayi tafad'a saman gadonta tajanyo wayarta takira ummanta
ummah bugu biyu tad'auka tun kan tayi magana sumayya cikin fushi tace ummah nagaji nagaji wlh natsani inbud'e idona inga yarinyar chan cikin gidan nan.

ummah cike da damuwa tace me yake faruwane?

sumayya tace ummah wlh so take tashiga tsakanina da mijina sai wani shishige ma yarima takeyi yau ma muna tare tazo tatak'uleni rigima ak'arshe yarima yakoramu gaba d'ayanmu wlh ummah zan iya kashe yarinyar nan akan yarima.

ummah itama cikin 6acin rai tace wlh ba'ayi yarinyar da zatazo tahanaki sak'ewa a gidan mijinkiba dole ma ne ind'auki mataki ammah kidaina maganar kisa kibari abi komai a sannu.

sumayya tace ummah wlh yarinyar nan batada kunya
sultana sadiya tace koma dai menene kema harda laifinki sumayya kawai dai ina goyon bayankine.

sumayya d'if takashe wayarta cike da jin haushin ummah tunda itama tace tana da laifi.

wayar zinat takira har saida takusan tsinkewa sannan zinat tad'aga tun kan tayi magana sumayya tace ke wai sai kinga dama zaki d'aga waya

zinat daga chan 6angaren tace kiyi hak'uri dear yanzu dai meke faruwa naji muryarki kamar kina cikin fushi.

sumayya tace hmm zinat bansan ya zanyiba wlh yarinyar chan ce tatisoni gaba.

zinat tace ban fahimtaba meyake faruwa?

sumayya kwashe abunda yafaru tsakaninsu tayi tas Tafad'a ma zinat.

zinat dariya tashiga yi har sumayya tafara k'ulewa...



_Comments_
     *nd*
_Share_



_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Wannan page d'in mallakinkune *Zahra nd pinky novel* nabakushi a kyauta, sak'on gaisuwa gareka *S Dan muri* nagode sosai da soyayyarku agareni_

*PAGE* 3⃣8⃣

zinat dariya tashiga yi har sumayya tafara k'ulewa tace dallah malama idan kinsan dariya zakiyimin ai sai inkashe wayana daga na fad'a miki damuwata sai kitsareni da dariya.

zinat tsagaida dariyar tayi tace sorry my dear toh ai kece da laifi

sumayya tace ban fahimtaba me kike nufi?

zinat tace kefa ina fad'a miki kiyi baya-baya da mijinki domin su maza da sunga ana shige musu sai kiga sun 6ullo da sabon wulak'anci musamman ma wannan mijin naki, ammah da sunga anyi baya da su toh nan ne zakiga yadda zasu tattaleki.

hmm dear kenan kin mance har da hakan tajamin yarima yak'ara aure?

zinat tace ba dai hakan ba ko kin mance lokacin da kikayi baya da shi yadda yake zuwa yana tattalinki?
Dogon numfashi sumayya taja tace hakane yanzu nafahimta,  shikenan dear koma dai mikenan sai munyi waya.

Ohk baby ammah please kikular min da kanki,
Dariya sumayya tayi tace ai kullum ina kular miki da kaina.
Aha dear fiye fa da yadda zaki kularma yarima.
Sumayya tace kema kinsan hakan, dariya sukayi sannan daga baya sukayi sallama.

Bayan sun gama wayar sumayya zagaye d'akin tashiga yi tana tunanin mafita dan ita sam shawarar da zinat tabata bata gansu da ita ba; sai chan daga baya tayi dariya tace yarinya da ni kike ja ayanzu zaki gane ainahin kalata.

Har wajen k'arfe goma Zarah shuru bataje part d'in yarima ba,  kad'an kad'an ya duba lokaci duk ji yake ba dad'i rashin zuwanta har lokacin,  tsintar kansa yayi da cewa kodai fushi take yi?  ahankali yaja d'an guntun tsaki.

A chan 6angaren zarah ko da tagama shirinta kwanciyarta tayi part d'inta dan har a lokacin batada walwala duk yadda taso tayi bacci kasawa tayi juyi kawai take a saman gadon tana jin wani irin k'unci a ranta,  ahaka har bacci yad'auketa.

Yarima ma haka yai ta juyi yana mamakin yadda duk yakasa cire damuwa akan rashin zuwan zarah cikin ransa yace ko dai fushi take da ni? Dasauri yabud'e idanuwansa tare da mik'ewa zaune yadafe kansa ahankali yace me hakan yake nufi da ni?  Meyasa nadamu da wannan yarinyar?  Chan 6angaren zuciyansa yace masa toh ko sonta kake?

Dasauri yarima yace No! It can't be possible wlh!  Mtsw wani irin haushin kansa ne yakamasa chan sai yaja dogon numfashi yace zan iya yarda dai nadamu da itane, to saboda me? Yatambayi kansa,
saboda tana nunamin kulawa,;,yaba kansa amsa,, chan kuma sai yayi murmushi tare da komawa yakwanta yamaida idanuwansa yalumshe yanajin wani iri a ransa,  saida yakai kusan 1am sannan yasamu bacci yad'aukesa.

Dasafe ma haka yafita ammah zarah bata lek'osaba,  ko da yaje hospital daurewa kawai yayi yaduba patients d'insa ammah duk motsi kad'an sai zarah ta fad'o masa a rai saidai kad'an-kad'an yayi ta jan tsaki.

Zarah ko breakfast bata samu tayiba dan jinta take wani iri sai wajen k'arfe ukku dataga yunwa tacita sosai ta fara gani bibiyu sannan tasa aka dafa mata indomie tad'anci kad'an,

Tun daga ranar bata k'ara shiga sabgar yarima ba haka take tursasa ma zuciyarta dan ganin ta danne sonsa da rashin ganinsa.

Ahaka kwana yadawo hannun sumayya sukasha kwanansu biyu ammah yarima har lokacin shi kansa ya rasa gane abinda yake damunsa, gashi yanason ko da sau d'ayane yasa Zarah a idonsa ammah girman kansa ya hana yaje inda take duk yadda tunaninta yafad'o masa a rai cikin sauri yake janyesa, dan ma yanzu sauk'in ba cika zama yayiba suna ta shirye-shiryen bikki.


Dangin ummi na masarautar agadaz sunzo da dama 6angare d'aya aka fitar musu daga cikin masarautar, ita kanta zarah da tagansu saida ta jinjina kai cikin ranta tace dole yarima da su rahma suyi kyau.

d'iyar yayar ummi ce safiya talik'e ma zarah saboda kusan kansu d'aya kullum tana 6angaren zarah ita take d'ebe ma zarah kewa kasancewar safiya akwai surutu, ahaka ranar girkin zarah yawuce ammah bata lek'a part d'in yarima ba.
Ita kanta sumayya tun lokacin da sukayi kaca-kaca da zarah rabon da zarah tasaka ta a idonta.


Ranar laraba aka gudanar da walimar bikkin rahma a cikin masarautar aka yanki fili akayi inda aka gayyato manyan malamai suka gabatar da wa'azi mai ratsa zuciya a chan tsakiyar fili naga an ajema amarya kujerar alfarma ta zauna alkyabba ce take sanye da ita tayi kyau sosai, daga 6angare guda kuma dangin amarya ne, sai d'ayan gefen dangin ango,
chan gefe nahango zarah da safiya zaune kusa da Aunty husna sunyi zugum suna sauraren wa'azi, nidai har nagama zagayena banga sumayya ba, bayan ank'are mutane sunci sunsha sannan aka watse.

ranar alhamis safiya part d'in zarah takwana tun da safe da suka tashi zarah tahad'a musu breakfast sukayi,  nan suka zauna sukaita fira,

Bayan sallar la'asar suka shirya cikin anko d'insu na lace sunyi kyau sosai, musamman zarah d'inkin nata ya kar6eta,  tana zaune gaban dressing mirror safiya tashigo,  tsaye tayi tana kallon zarah,  juyowa zarah tayi takalleta tasakar mata murmushi tace ya dai safiya?

Murmushi safiya tayi tace gaskiya kinyi kyau sosai Mrs prince (kasancewar sunan da take kiran zarah da shi kenan)
Kai safiya banason tsokana.

Wlh ba tsokana bane kema kinsan kina da kyau sosai,

Hmm safiya kenan ammah ai kinfini.

Safiya zaro ido tayi tace waceni? Wlh ban kamo ko k'afarkiba.

Harararta zarah tayi tace kedai kika sani da tsokanarki.

Hmm gimbiya kenan kema ai kinsan gaskiyane,  yanzu dai kigama shirin gashi chan anfara d'aukar mutane ana tafiya da su wajen kamun,  ko cikin motarki zamuje?

Zarah shuru tayi nad'an lokaci sannan tace anya zan yi driving d'innan? Kodai insa akaimu?

Haba kawai kijamu muje, ni nafiso muje a motarki.

Toh ai bansan wajen da za'ayiba.

Kar kidamu ni nasani sai muje.

Harararta zarah tayi tace keda ba garin kikeba ina kikasan wajen.

Dariya safiya tayi tace Allah dagaske, jiya munje mungano wajen, yanzu dai kiyi sauri kigama nasan anfara yanzu.

Zarah saka sark'a take tace ke banfa tambayi yarima ba.

Chab har ma sai kin tambayesa?  Kizo kawai muje ai yasan hidima ake.

Mik'ewa zarah tayi tad'auki veil d'inta tayafa sannan tace bari inzo, bata jira Jin abinda safiya zatace ba tafita.

Ko da ta'isa part d'in yarima itama saida taji wani iri dan rabonta da d'akinsa kusan 5 day's kenan,  ganin baya parlour yasa tawuce bedroom nan ma baya nan.

Fitowa tayi takoma part d'inta wayarta tad'auka takirasa har tatsinke bai d'agaba,  mamakine yakama zarah nan tak'ara dialing d'in number d'insa sai da takusan tsinkewa sannan yarima yad'aga lokacin yana gidansu shaheed.

Zarah naji ya d'auka bata bari yayi maganaba tace ina wuni?
Daga chan 6angaren yarima saida yalumshe idonsa jin muryar zarah, sai da yayi kusan 3 minutes sannan yace ina jinki.

Zarah ma wani sanyi taji aranta saida tazauna saman gado sannan tace am dan Allah inaso zanje wajen kamu,

Sai kindawo, yarima yafad'a tare da kashe wayarsa.

Zarah murmushi tayi tare da mik'ewa tsaye, had'a ido sukayi da safiya da take tsaye itama tana murmushi, dariya zarah tayi tace kekuma fa?

Itama safiya dariya tayi tace ina kallon yadda ake waya da habiby, harararta zarah tayi tace nidai wuce muje sarkin 'yan sa ido,
Dariya safiya tayi tace gaskiya zanso inga soyayyarki da prince,  na sansa da jin kai ku ma matansa yana yi muku? fad'amin sirrin.

Zarah d'aukar hand bag d'inta tayi da key d'in mota tawuce gaba,  bayanta safiya tabi tana mata dariya har suka fita sukaje wajen motar zarah,

Zarah bud'e k'ofar tayi tashiga tazauna saida tayi addu'a sannan tatada motar abun yabata mamaki ganin yadda tatada motar batare da tsoron komai ba saboda wannan ne karo nafarko da tafita da mota dan tun lokacin da aka koya mata rabon da tashigeta,  ahankali tajasu suna tafiya suna hira ammah duk hankalinta yana ga driving d'in da take ahaka har suka isa babban hall d'in da aka tanada.

Motocine duk inda kaduba gefe guda tasamu tayi parking sannan suka fito suka shiga daga chan gefe suka samu waje suka zauna daidai lokacin amarya da ango suka iso sunyi gwanin kyau, nan abokan amarya sukaje suka tarbosu aka kaisu har wajen da aka tanadar ma ango da amarya,

Daga gefen amarya sumayya ce zaune tayi kyau sosai itama sai yatsina take tana nuna isa, dan ma bawanda yadamu kowa hidimar gabansa yake,

Shaheed ne yaketa baza ido ammah baiga yarima ba ahankali yaduk'o yace ma rahma kinga yarima baizo ba ko? Bayan munyi da shi shiryawa zaije gida yayi.

Murmushi rahma tayi tace indai Bro ne zai aika wlh,
hmm barni da shi, wayarsa yad'auko yashiga kiran wayar yarima,
Yarima da yake shirin fitowa daga part d'insa ganin kiran Shaheed yasa yayi murmushi sannan yawuce yafita,

Lokacin da ya isa hall d'in abokan amaryane a fili suna ta kwasar rawansu shigowar yarima da abokinsa Dr khalil ne yasa gaba d'ayansu suka zuba masa ido, sanye yake cikin boyel milk colour wanda yasha d'inkin zamani ya yi masa kyau sosai kansa babu hula gashin kansa yasha gyara, nan MC yafara masa kirari
Daga chan gaba suka samu table d'in da ba mutane suka zauna, nan maza sukaita zuwa wajensa fuskar yarima a sake suke gaisawa.

Shaheed ne yayi ma MC magana nan mc yazo inda yarima yake cike da girmamawa yagaishesa sannan yace ranka yadad'e ga wajen da aka tanadar maka chan.

Yarima kallon saman high table yayi sannan yace no nan ma ya yi min, MC har yabud'e baki zaiyi magana nan yarima yad'aga masa hannu cikin sauri yawuce yabar wajen.

A chan nahango sumayya tunda yarima yashigo tafara washe baki dan duk a tunaninta wajenta yarima zaizo yazauna sai taga akasin haka ga 'yan mata sai wucewa suke tagaban su yarima ko Allah yasa sutaya, sumayya da take kallon matan murmushin mugunta tayi tace yau duk wacce tanemi tataya mijina za'ayi bura'uba wajen nan.

A chan 6angaren zarah ma safiya hira take yi mata ammah hankalinta gaba d'aya yana wajen yarima tun lokacin da yashigo, ganin matan da suke bi tagabansa  yasa tacika fam ji take kamar taje tashak'esu.

Shidai yarima tunda yazauna bayan sun gama gaisawa da mutane dannar wayarsa yake baisan wainar da ake toyawaba.

nan aka fara kiran babban abokin ango yashiga fili ammah yarima ko motsawa baiyiba ganin haka yasa shaheed yace ma MC akira muhammad abokinsa dan yasan babu wanda ya isa yasa yarima yin abunda baisa kansaba, a k'arshe dai saidai muhammad yakoma madadin yarima.

Bayan yashiga yayi rawa sannan aka ce kowa yafita yanzu filin yakoma na amarya da ango.

Shaheed rik'o hannun rahma yayi suka tashi suka safko daga high table suka shiga tsakiyar fili yana rik'e da ita suke d'an takawa ahankali, sumayya ce tamik'e taje tafara watsa musu kud'i nan abokansu ma suka take mata baya aka dinga watsi da kud'i.

Dr khalil yana murmushi yace ranka yadad'e kataso muje muyi ma aboki da k'anwa lik'i.
Ta6e baki yarima yayi yace ba zan iya shiga wajen chan ba saidai kai idan zakayi.

Haba yarima ammah dai da baka kyautaba, yarima bandir biyu na 'yan 1000 yafiddo ya aje gaban dr khalil yace idan kai zakaje sai kawakilceni.

Zaro ido Dr khalil yayi yace ni kuma? A'a kai dai yafi dacewa kaje da kanta.

Banza yarima yayi masa yacigaba da dannar wayarsa,
Ganin haka yasa Dr khalil yamik'e yatafi dan yasan tunda dai har yarima yafurta a'a toh bawanda zaisashi yace eh, nan yashiga yi musu lik'i yace ma shaheed, yarima ne yawakiltashi yayi masu lik'e madadinsa.

Rahma da shaheed kallon juna sukayi sukai murmushi shaheed yace lallai yarima halinsa sai shi.

Safiya kallon zarah tayi tace Mrs prince muje muyi ma adda rahma lik'i,

A'a Safiya kije nidai ina nan,
Rik'o hannunta tayi tace haba Mrs prince dan Allah kitaso muje kinga ba dad'i.
Zarah ba dan tasoba tatashi suna rik'e da hannunsu suka nufi filin.

Kud'i suka ciro daga cikin jakunansu suka fara yi ma amarya da ango lik'e, zarah ji tayi ta bayanta ana zubo mata kud'i itama, dasauri tawaiwaya wani guy ne tagani fuskarsa d'auke da murmushi,

Harararsa zarah tayi tace dallah malam menene haka?
Fuskarsa d'auke da murmushi yace duk cikin sonkine baby kiban izini ingabatar miki da kaina,

Zarah Zaro ido tayi dasauri takai kallonta ga yarima da shima idanuwansa suna wajensu, ai yarima tunda yaga mutumin yana ma zarah lik'i wani irin abune yaji ya tokare masa zuciya wata irin harara yashiga wurga ma zarah,

Zarah saida 'yan cikinta suka kad'a ganin hararar da yarima yayi mata, cikin sauri tafito daga wajen, mutumin ma binta yayi yana ta mata magana ita kanta batama san me yake cemata ba har takoma mazauninta tazauna.

Shima zama yayi gefenta yace haba baby wai menene haka wulak'ancifa baida dad'i daga na ce ina sonki sai ki6ata rai?

Zarah cike da tashin hankali tace dan girman Allah kakyaleni ni fa matar aurece,
Murmushi saurayin yayi yace nima mijin aurene.

Zarah kallon yarima tayi da yake kallonsu idanuwansa sun kad'a sunyi jawur, shima mutumin kallon inda take kallo yayi dan yaga duk ta ida daburcemasa ganin yarima yasa yayi murmushi yace baby kinsan prince ne?

Zarah mik'ewa tayi cikin d'aga murya tace malam na ce kafita harkata ni matar aurece!
Tana fad'in haka tawuce tanufi inda yarima yake zaune ya cika fam.

Kujerar da take kusa da shi taja tazauna rau-rau tayi da ido kamar zatayi kuka tace wlh bani nace yabi niba kuma nafad'a masa ni matar aurece.

Yarima ta6e baki yayi sannan yace wani abu kikaji na ce?
Girgiza kai zarah tayi.

Cikin nuna rashin damuwa yarima yacigaba da dannar wayarsa yana d'an murmushi, nan ko zuciyansa cike take da bak'in ciki,

Daidai lokacin Dr khalil yadawo yaja kujera yazauna, fuskarsa d'auke da murmushi yace amaryarmu watau kinzo kin tsare mijinki dan kar wata tayi miki k'wace ko?

Murmushi zarah tayi sannan tace ina wuni?

Lafiya lou amarya ai da nahangoki nad'auka irin 'yan matan nan ne suka samu kar6uwa wajen yarima ashe amarya ce tazo takasa tatsare abinta, hakan da kikayi yayi kyau nabaki goyon baya dan na lura da 'yan matan amarya sai rawar kai suke akansa sunaso suyi masa magana ammah ya yi mu k'warjini.

Murmushi kawai zarah tayi.

Yarima kallon Dr khalil yayi fuskarsa d'auke da murmushi yace Dr gaskiya ni nagaji kazo kawai muwuce.

Haba Dr tun yanzu zamu tafi?
Hmm bakaga time d'in sallah ya kusaba? Yarima na fad'in haka yamik'e tare da cewa idan ba zaka tafiba toh ni na tafi dan ko 1 minute ba zan k'araba anan, kallon zarah yayi yace kitashi mutafi.

Zarah ma kallonsa tayi tace da mota nazo, yarima mik'ama Dr khalil key d'in motarsa yayi yace gashi katafo da ita,

Kar6a Dr khalil yayi tare da mik'ewa yace nima ai bazan zaunaba.
Yarima kallon zarah yayi yace muje.

Zarah mik'ewa tayi tabi bayansa, wajen motarta suka nufa nan tamik'a masa key d'in.

Tunda suka fara tafiya kowa shuru yayi, yarima gudu kawai yake da motar, ahankali zarah tajuyo takallesa gani tayi ya wani had'e rai babu alamun fara'a a fuskarsa, janye idonta tayi daga kallonsa cikin ranta tace kai dai kasani.

Suna isa gida yana yin parking key d'in motar ya aje mata sannan yabud'e yafita batare da yayi mata magana ba, itama zarah bud'ewa tayi tafita tabi bayansa tana shiga direct part d'inta tawuce.

Saman cushin tazauna tare da jan numfashi tace Allah ya taimakeni da mutumin chan ya ja min bala'i wajen yarima, chan kuma cikin zuciyanta tace  bayan basonki yakeba bai damu da ke ba to akan me zaiyi kishinki? Jinjina kai tayi k'wallah duk ta cika mata ido tace hakane kuma, wayarta tad'auka takira safiya nan tashaida mata da ta tafi gida.

Yarima ma zama yayi saman cushin d'in parlournsa yadafe kai hango zarah da wannan mutumin abokin shaheed yayi sai murmushi yake ma zarah, da k'arfi zuciyansa tabuga jingine kansa yayi tare da lumshe idonsa dan shima ya san yayi namijin k'ok'ari da bai d'au matakiba akansa kuma bayason zarah tad'auka ko ya fara damuwa da ita ne, bugu da k'ari a gaban idonsa aka aiwatar da komai babu ta yarda za'ayi yazargeta.
Ahankali yaja tsaki cikin ransa yace toh wai ma akan me zan damu? Gefe guda na zuciyansa yace dole kadamu tunda akwai aurenka abisa kanta.
Kiran sallar magrib ne yasa yamik'e yanufi toilet dan yad'auro alwallah.

wajen k'arfe tara zarah na shirin kwanciya safiya tashigo, kallonta zarah tayi tace kar dai kicemin yanzu kika dawo?
No tun d'azun muka dawo ina cikin gida wajensu mamina, kinsan wani abu?
Girgiza kai zarah tayi.
Wani guy ne yatambayeni wai dagaske kina da aure, inkuma baki da aure toh please inbasa number d'inki, bansan lokacin da nazaro idoba nace karufa min asiri kar kaja prince yasa arufeni, ai matarsa ce.

Shima guy d'in bakiga yadda yarikiceba wai wlh bai d'auka matar aure bace kuma matar prince ya ce dan Allah inbaki hak'uri wlh da ya sani da bazai miki maganaba, kuma ya ce zai samu prince yabasa hak'uri nace ai da kuwa hakan ya fi.

Murmushi zarah tayi tare da kwanciya tamaida idanuwanta tarufe cike da kewar yarima ammah ko bakomai ta d'anji sanyi a ranta da tasakashi a idonta, nan itama rahma takwanta.

Gimbiya sumayya kallon yarima tayi da yake kwance ita kuma tana gefensa tace yarima Allah ya taimaki 'yan matan wajen nan da basuzo wajenkaba dan na lura da kallon da suka dinga yi maka wlh da sunzo da sai munyi bala'i.
Shine katafi ban saniba saidai nawaiga naga bakanan, kuma fa ko lik'i baka shigo kayi masuba.

Murmushi kawai yarima yayi tare da rungumota jikinsa, dasauri sumayya takallesa tace a gajiye fa nake yau, yarima kallonta yayi sannan yamaida idanuwansa yalumshe  ganin haka yasa sumayya tagyara kwanciyarta ahaka bacci yayi awon gaba da su.

Ranar juma'a safiya jan zarah tayi sukaje part d'in ummi ammah zarah kasa sakin jiki tayi cikin dangin yarima daga uhm sai uhm-uhm daga k'arshema tattarawa tayi tadawo turakarsu.

Da dare duk inda zaka nufa a cikin masarautar shirin tafiya dinner akeyi, mutane duk sun saka material sunyi kyau.

sumayya tare da rahma sukaje shago akayi musu shiri suka fito gwanin kyau musamman ma amarya rahma.

Wajen 8:30pm zarah tagama shirinta cikin anko d'inta tufke gashin kanta tayi sannan tasaka head d'inta tayi gwanin kyau kallabin tayafa a kafad'arta sannan tazura takalminta tad'auki hand bag d'inta tana fitowa sukayi kici6is da safiya da wata 'yar uwarta tsaye sukayi suna kallonta itama kallonsu tayi fuskarta d'auke da murmushi tace masha Allah 'yan mata kunyi kyau sosai.
Haba Mrs yarima wlh bakiga yadda Kikayi kyau ba kamar kece amaryar.
Uhm zaki dai fara tsokanata ne da kika saba.
Safiya kallon 'yar uwartata tayi tace dan Allah iman ya kika ga matar prince?
Murmushi iman tayi tace wlh tayi kyau sosai ji nake daman ma nice ita.

Ku dai kukasani da tsokanarku, tana fad'in haka tawuce tanufi part d'in yarima tabarsu nan suna ta binta da kallo.

Zarah tana shiga lokacin yarima yana zaune saman 3 seater yana kallo, ahankali tayi sallama, juyowa yarima yayi yakalleta saida gabansa yafad'i ganin wani irin kyau da tayi, Zarah ma tsura masa ido tayi sanye yake cikin dakakkiyar shaddarsa coffee colour ya yi mata wani irin kyau, sun dad'e suna kallon juna sannan yarima yajanye idonsa yamaida ga TV, zarah ajiyar zuciya tasafke sannan tace barka da hutawa.
yauwa yarima yace batare da ya kalletaba.
Ahankali tace dan Allah zan tafi wajen dinner d'in.
Juyowa yarima yayi yakalleta sannan yace bazaki jeba.
Marairaicewa zarah tayi tace dan Allah kabarni
Wani irin kallo yarima yayi mata sannan yace kije kihad'o min coffee.
Zarah aje jakkarta tayi tafita tana turo baki ko da takoma part d'inta kallon su safiya tayi da suke jiranta tace bari tayi sauri tahad'a ma yarima coffee.
Sukace toh, nan tayi sauri tashiga kitchen tad'aura.

Bayan tagama d'auka tayi tanufi part d'insa tana shiga mik'a masa tayi, sannan tace dan Allah toh intafi?
Yarima kallonta yayi tana ta turo baki sannan yace na fad'a miki bazakijeba, juyawa zarah tayi zatabar d'akin cike da jin haushi.
batare da ya kalletaba yace kisamu waje kizauna.
Kujerar da take opposite d'insa tazauna ta cika fam,
A hankali yakai cup d'in bakinsa yana sha.
Wayartace tafara ringing saida takalli yarima da yake kallonta sannan tayi picking tace safiya kutafi kawai bazan samu damar zuwaba, tana fad'in haka takashe wayarta,
Sun dad'e a zaune zarah duk ta k'ule ji take daman yabarta tatafi part d'inta ko baccine tayi.

Har wajen goma saura suna Zaune a haka, Kiran wayan shaheed ne yashigo a wayarsa murmushi yayi sannan yayi picking yace ya dai ango?

A chan 6angaren shaheed cike da k'ulewa yace dallah malam katafo kawani bar mutane suna ta jiranka.
Ta6e baki yarima yayi yace ai bance ajiraniba.
Kar dai kacemin bazaka zo ba? Cewar shaheed
Yarima yace ni ban fad'aba malam.
Toh mujiraka kenan?.
Uhm zan gani, yana  fad'in haka yakashe wayarsa gaba d'aya gudun kar ak'ara kiransa.
Zarah da tunda yafara wayar kafesa tayi da ido har yagama ahankali tace toh saidai muzauna gidan tare.

Kallonta yarima yayi yace me kikace?
Dasauri tagirgiza kai tace ba magana nayiba.
Murmushi yarima yayi sannan yacigaba da shan coffee d'insa.

Zarah duba time tayi ganin har 11 ta kusa sannan tamaida kallonta ga yarima tace bacci nake ji inje inkwanta?
Yarima batare da ya kalletaba yace zaki iya shiga kikwanta.
Zarah turo baki tayi tace a nan?
Yarima komawa yayi yakwanta a saman kujerar tare da d'aukar remote yacanza channel.




_Comments_
      *nd*
_Share_





_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Wannan page d'in mallakinkine *Ummu Rahma* marubuciyar *'DAN GARGAJIYA* nagode sosai da kulawarki agareni Allah yabarmu tare_

*PAGE* 3⃣9⃣

Zarah zamanta tayi nan tafara gyangyad'i saida taji baccin yana cinta sosai sannan tamik'e tana turo baki tashiga bedroom d'in yarima,

Har ta kwanta saman gadonsa sai kuma taji bata iya yin bacci haka dan haka tatashi saida tacire kayan sannan tashiga toilet d'insa cikin sauri tayi wanka tafito d'aure da towel, saida tatsane jikinta sannan tafara tunanin abinda zata sanya, raba ido tafarayi daga k'arshe da taga ba yadda zatayi yasa taja tsaki tace nasan halinsa ina iya zuwa zan fita yayi min wulak'anci
saman gadon tahau  takwanta tare da k'udindine jikinta da blanket bata kawo komai a rantaba takashe gloves ahaka bacci yad'auketa.

Wajen 12 yarima yakashe kallon yatashi yashiga bedroom kunna gloves d'in yayi tare da kai kallonsa a bed d'insa zarah k'udindine take tana baccinta hankali kwance murmushi yayi sannan yacire kayansa yawuce yashiga bathroom

Bayan ya fito shiryawa yayi sannan yakashe gloves d'in yakunna marar haske sosai yaje yakwanta gefen zarah,

Zuba mata ido yayi yanayin yadda take bacci tana burgesa, ya dad'e yana kallonta sannan daga baya yajanyo blanket d'in zai rufa shima, zaro ido yayi ganin yadda jikinta yabayyana dan gaba d'aya towel d'in ya rabu da jikinta, k'irjinta yazuba ma ido yana kallo sannan daga baya yaruntse idonsa yana jin wani iri a jikinsa, duk yadda yaso yadaure kasawa yayi ahankali yabud'e idonsa tare da yaye dukkan blanket d'in.

Rungumota yayi jikinsa zarah baccinta kawai take hankalinta kwance ahankali yafara zagaye hannuwansa a jikinta daga k'arshe yamaida yakwantar da ita sannan yacigaba da wasa da kowane sashe na jikinta,

Zarah cikin bacci taji kamar wani abu yana bin jikinta dan ji tayi kamar ana mata tafiyar tsutsa, dak'yar tabud'e idonta tare da safkesu akan yarima da yake a k'irjinta,

Zaro ido tayi tare da d'aura hannunta a kansa tana nema taturesa muryarta tana rawa tace pppplease yarima kadaina,

Yarima duk yafita hayyacinsa ahankali yad'ago kai yakalleta da narkakkun idanuwansa batare da yayi mata magana ba yahad'a bakinsu yafara kissing d'inta, inda hannuwansa suke yawo a kowane sassa na jikinta nan da nan Zarah tamik'a wuya dan dama ita kanta tasan tayi missing d'insa.

Sun dad'e suna abu d'aya har Zarah tagaji ammah yarima bai k'yaletaba saida yagaji dan kansa sannan yabarta.

Zarah tana turo baki takalli yarima da yake kwance idanuwansa a lumshe yana maida numfashi tace shine katasheni daga baccina?  Chan k'arshen gado takoma takwanta tare da janyo blanket tarufe jikinta ita kanta wani irin sanyi takeji a ranta fuskarta d'auke da murmushi a haka bacci yayi awon gaba da ita.

Yarima ma yadad'e a haka shi kansa yasan yana cikin farin ciki dan ji yake kamar yau yafara sanin Zarah, ahankali yabud'e idonsa yakalleta chan k'arshen gado ta k'udundune jikinta, jawo wayarsa yayi yaduba time lokacin 1:50am.

Dak'yar yasamu yamik'e jikinsa ba k'wari yashiga bathroom dan yatsarkake jikinta.

Bayan ya fito komawa yayi yakwanta tare da juya mata baya fuskarsa d'auke da murmushi ahaka bacci yayi awon gaba da shi.

Zarah ko da yarima yatayar da ita tayi sallah tana ganin ya tafi masallaci tasaka kayanta tafito takoma part d'inta, tama yi tunani safiya nan takwana ammah sai taga bakowa, saida tatsarkake jikinta sannan tad'auro alwallah tazo tayi sallah.

Bayan tagama saman gadonta tahau tayi kwanciyarta ahaka bacci yayi awon gaba da ita.

Wajen 10 safiya tatashe dak'yar Zarah tatashi dan ji take baccin bai ishetaba, kallon safiya tayi tace kekuma yaushe kika shigo?

Dariya safiya tayi tace tun d'azun nashigo ina parlour jin shuru baki fitoba yasa nashigo, Zarah maida idanuwanta tayi talumshe tace please safiya kibarni inyi baccina.

Janye blanket d'in da Zarah take rufe da shi safiya tayi tace ank'i d'in tunda kinje kunsha love da prince shine har yanzu baki tashiba,

Zarah tunowa tayi da darensu na jiya nan tabud'e idonta tana murmushi tace toh ina wuranki?

Hararta safiya tayi cikin wasa tace aikam dai daruwana tunda kika hana babban abokin ango zuwa dinner, mutane suna ta nemansa.
Da munsa rai tare zakuzo sai mukaji shuru ashe kina nan kin rikitamana prince dan tunda naga gayun da kikayi nasan dak'yar idan prince zai iya barinki kitafi batare da wani abuba

Ta6e baki Zarah tayi tare da tashi zaune tace kinsan dai halin yarima indai yasa kansa toh babu wanda zai iya hanasa dan haka nidai bani nahanasa zuwaba daman chan baiyi niyaba.

Safkowa tayi taje tashiga toilet tayi wanka bayan ta fito zama tayi tatsantsara kwalliyarta sannan tad'auko super English blue colour tasaka nan tamurza d'aurin kallabinta, sark'arta ta gold tasaka nan kyaunta yak'ara fitowa.

da k'arfe biyu daidai aka d'aura auren rahma da shaheed, auren da mutane dayawa suka hallara.

Saida su zarah sukayi sallar azuhur sannan suka shiga cikin gida da yake cike da jama'a.
Safiya jan Zarah tayi suka shiga part d'in sultana sadiya dayake a chan rahma tazauna,

A parlour suka tarar da sultana da sumayya sai wasu abokan sultana sadiya a zaune suna hira.
Cike da girmamawa su zarah suka gaishesu, nan abokan sultana sadiya suka amsa ammah banda ummah da sumayya da suka had'e rai.

Safiya ce takalli sumayya tace Aunty sumayya ina adda rahma?
Ta6e baki sumayya tayi tare da cewa kin bani ajiyartane?
Safiya murmushi tayi tace yi hak'uri dan naga tare kukene saisa natambayeki.
'Daya daga cikin k'awayen ummah ne tace kai sumayya miye nabak'ar magana? Kikasani ko k'awayen amaryane?

yamutsa fuska sumayya tayi tace nasan baku gane wacchan ba? tanuna zarah
Eh gaskiya bamu santaba wacece ita?

Ummah ce tace toh wacece banda munafukar kishiyarta.
'Daya daga cikin matan ne tace tace wlh sumayya banga laifinkiba toh waima ubanmi tazo yi mana a nan?
Sumayya tsaki taja tace gulmar da tasaba ko?

Safiya da zarah tsaye suke suna kallon ikon Allah , k'arama zarah da bata wani damuba dan tasaba da wulak'ancinsu Ummah.

Safiya ce tace haba bayin Allah daga tambaya sai cin mutunci? Sumayya cikin 6acin rai tace ke safiya kikiyayeni ko ranki ya6aci.
Ta6te baki safiya tayi tace Allah yabaku hak'uri sannan takama hannun zarah suka wuce wani room da taga wata abokiyar rahma ta shiga.

A chan saman gado suka hango amarya zaune taci k'walliya tasha kyau har ta k'oshi, gefenta k'awayentane suka zagayeta sunata hira.

Safiya jan zarah tayi sukaje suka zauna bakin gadon.
Zarah fuskarta d'auke da murmushi tace sannunku? ina wuninku?
Gabad'ayansu suka amsa sannan tacema rahma amarya kinsha kyau Allah yabada zaman lafiya.
Murmushi rahma tayi sannan tace Ameen nagode sosai,

'Daya daga cikin 'yan matan amaryace tace gimbiya wannan ma friend d'inki ce?
Girgiza kai rahma tayi tace matar Bro ce.
Kallonta sukayi sukace ba dai yarima ba?
Shi man amaryarsace 2 months kenan yanzu da aurensu, cewar rahma.

Gabad'ayansu suka juyo suka kalli zarah d'aya daga cikinsu tace ashe matansa biyu, masha Allah gaskiya tana da kyau sosai kamar prince.
Wata tace saisa baya kallon mata ashe yasan ya aje mata kyawawa a gidansa.
Sai tayita haifo mana kyawawan yara, cewar safiya.
Zarah da kanta yake sunkuye d'ago kai tayi tagallah ma safiya harara.

Dariya safiya tayi tace daga fad'in gaskiya sai harara?
shuru zarah tayi tak'yaleta, tanajib wasu daga cikin 'yan matan suna ta maganar yarima har taso taji haushi, sai daga baya suka canza hira.

Saida sukayi sallar la'asar sannan suka fito sukaje part d'in dada basu wani dad'eba suka koma na ummin yarima nan suka zauna suna hirarsu.

Saida akayi sallar magrib sannan aka d'auki amarya aka kaita gidanta da yake kusa da masarautar, zarah cikin motarta sukaje gidan amarya, kowa saida yayaba tsari da kyaun gidan anzuba mata gaya na'azo agani dan room nd bedroom 3 akayi mata, nan akaita santi daga k'arshe kowa yayi Allah yabada zaman lafiya sannan aka watse aka bar amarya da wasu abokanta.

Shaheed kallon yarima yayi da yake shirin barin gidansu yace haba yarima yanzu kana nufin bazaka rakani wajen amaryataba?
Harararsa yarima yayi yace akace maka dole sai naje? Idan su muhammad sukaje ai ya wadatas,
Cike da jin haushi Shaheed yace shikenan duk yadda kayi daidaine daman jiya k'in zuwa dinner kayi.
Wai kai baka ganin rahma k'anwace agareni akanme zan dinga shige muku.
Ta6e baki Shaheed yayi yace nikuma abokine wanda bakada kamarsa, toh laifine dan kaje?
Rik'o hannun yarima yayi yace please yarima kataimaka karakani d'akin amaryata.

Murmushi yarima yayi yace toh shikenan naji jeka ka ida shiryawa kazo muje dan ni yau dawuri nakeson komawa gida saboda agajiye nake.
Shaheed yace angama ranka yadad'e.

Wajen k'arfe tara suka raka Shaheed gidansa, Tunda suka shiga d'akin da amarya take yarima bai d'aga kai yakalli kowaba dannar wayarsa kawai yake, nan abokansu da na amarya sukaita tsokanar ango da amarya, duk yadda wasu sukaso yarima yayi magana ko sunsamu shiga ammah baiyiba dan nunawa yayi kamar baisan da zamansu, nan aka k'ara yi musu nasiha sannan suka tashi sukabar gidan,
yarima yana shirin shiga motarsa saiga wasu mata biyu sun iso cikin kwantar da murya sukaimasa sallama.
Rik'e yake da murfin motar ya amsa musu ciki-ciki.
Ahankali d'aya tace dan Allah in bazaka damuba munaso kayi dropping d'inmu.
Ta6e baki yarima yayi sannan yace ba hanyarmu d'ayaba kudaije wajen wad'anchan su k'ila hanyarku sukayi.
Matan kallon juna sukayi sannan d'aya tace toh please zamu iya samun phone number d'inka?
Wani irin kallo yarima yayi musu sannan yashiga motarsa yaja yabarsu nan tsaye.
A k'arshe saidai suka koma wajen sauran abokan ango suka shiga motocinsu Cike da takaicin abinda yarima yayi musu.

Yarima ko da yakoma gida wanka yayi sannan yabi lafiyar gado yakwanta.

Zarah ko daman koda tadawo dak'yar tasamu tayi wanka takwanta batayi tunanin daman zuwa part d'in yarima ba dan agajiye take.

_Toh mudai saidai muce amarya rahma da ango shaheed Allah yabada zaman lafiya_

*BAYAN SATI 'DAYA* 'yan bikki duk suka watse zarah tayi missing d'in safiya dan 'yan kwanakin nan da sukayi sun saba sosai, yanzu saidai zaman kad'aici kuyangintane suke d'ebe mata kewa tahanyar bata labarai masu dad'i.

Yau kasancewar girkin zarah ne kwance take saman bed d'inta kanta yana kallon ceiling da alamu tunani take, ringing d'in wayantane yakatseta ganin mai kiranne yasa tasaki murmushi dan rabonta da yarima tun lokacin bikki, saida takusan tsinkewa sannan tayi picking, yarima baijira tayi maganaba yace kihad'o min coffee yana fad'in haka yakashe wayarsa, fuskar zarah d'auke da murmushi tamik'e tanufi kitchen dan ko bakomai tasan yau zata sakasa a idanunta.

Bayan tagama had'a masa hijab d'inta tasaka kasancewar daman har tayi shirin kwanciya,

Ahankali tabud'e bedroom d'insa tashiga yarima dasauri yad'ago kai yakalleta sannan yamaida kansa yacigaba da dannar laptop d'insa, zarah k'arasawa tayi kusa tashi tare da zama gefensa sannan tace ga coffeen.
Yarima batare da ya kalletaba yace ina zuwa,
Haka yabar zarah rik'e da cup har kusan 5 minutes sannan yakar6a,
Mik'ewa zarah tayi zata tafi, batare da ya kalletaba yace ina zakije?
Murmushi zarah tayi tace zanje inkwanta ne.
Ban baki iziniba, cewar yarima da yake dannar laptop.
Marairaicewa tayi tace wlh bacci nakeji.
Ko inda take yarima bai kallaba.
Zarah turo baki tayi sannan takoma tazauna,
Yarima tagefen ido yana kallon yadda take ta fushi.

Zarah ita kanta har tagaji da zaman cikin ranta tace lallai mutumin nan ya raina min wayau miyake nufi da ni ne? Chan kuma sai tayi murmushi tare da cire hijab d'inta nan gashinta yabazu kallon yarima tayi da ya aje cup d'in yana cigaba da dannar laptop, amsar laptop d'in tayi ta aje gefe, yarima binta yayi da kallo cike da mamaki Ahankali tafad'a jikinsa tare da rungumesa cikin shagwa6a tace please kazo muyi bacci kaga har 11 fa tayi.
Wani iri yaji a ransa ammah yadake yace kikwanta mana ni sai nagama abinda nake.
Zarah d'ago kai tayi tana kallon cikin idonsa ahankali takai bakinta cikin nasa yarima daman kamar jira yake nan yacafke nan suka fara rikita junansu sun dad'e a haka sannan zarah tazare jikinta takwanta tare da jawo yarima jikinta dak'yar yasamu yakashe gloves.

yau makara sukayi sallar asuba har saida gari yafara haske sannan zarah tafarka duba time tayi taga 6:15am zaro ido tayi sannan takalli yarima da yake kwance yana bacci har takai hannu zata tadasa sai kuma tafasa, rigarta tajanyo tasaka sannan tafara k'ok'arin janye blanket d'in da yake rufe ciki,
Jin ana jan blanket yasa yafarka, zarah saida tasafka daga saman gadon sannan tace katashi yau munyi late.
Tana fad'in haka tazura hijab inta tafita tabar d'akin.

Yarima janye blanket d'in yayi cikin sauri yamik'e yashiga toilet yana mamakin yadda yamakara yau baisamu jam'i ba, chan kuma yaja tsaki da yatuno basuyi bacci da wuriba.

Zarah ma ko da takoma part d'inta saida tatsarkake jikinta sannan tayi sallah, bayan tagama kitchen taje tashiga nan tafara tunanin me zata had'ama yarima na breakfast, chan kuma sai tayi tunanin tahad'a mai kunun gyad'a dan tasan yana sonsa sosai.

Nan tad'aura ruwan kunun sannan tafere doya tadafa, bayan ta dafu tadaka tayi yamball.
Bayan ta gama wanka tashiga tayi da tafito tashirya cikin swiss less d'inta, veil tayafa sannan taje tad'auki basket d'in taba wata kuyangarta tarik'e suka nufi part d'in yarima

A gaban dressing mirror tagansa tsaye yana fesa turare, d'an rissinawa tayi tagaishesa, tacikin mirror yarima yake kallonta saida yagama fesa turaren sannan ya amsa.
Fuskarta d'auke da murmushi tace breakfast d'inka na dining,
Shuru yarima yayi har ta juya zata fita ahankali yarima yace kije kishirya in ajeki gida.
Dasauri zarah tajuyo cike da jin dad'i tace yanzu?
Eh, ammah idan baki shirya zuwaba shikenan.
Zarah cikin sauri tace na shirya kagani?
Yarima kallonta yayi sannan yazo yawuce yafito yanufi dining,

Zarah bayansa tabi har yaje yazauna nan tayi serving d'insa sannan itama tazauna tayi serving d'inkanta,
nan sukacigaba da breakfast d'insu ba wanda yai magana, zarah saboda zumud'i bataci abun kirkiba tatashi, yarima kallonta yayi yace shi kuma sauran wa zai ida cinye miki?
Itama kallonsa tayi tace nak'oshi ne,
Wani kallo da yayi matane yasa takoma tazauna tacigaba da turawa ba dan tana jin dad'insaba yarima yarigata tashi yabar wajen, nan zarah tabisa da kallo har yashige bedroom d'insa, sannan takalli plate d'insa ahankali tace shi bai cinyeba ammah ni shine zai ce incinye,
Mik'ewa tayi tatattara kayan tasaka cikin basket tad'auka tafita tabar d'akin.

Ko da takoma part d'inta cike da farinciki tashiga bedroom d'inta tad'auko handbag d'inta sannan tacanza veil saida tak'ara gyara fuskarta sannan tafito.

Daidai zata shiga part d'in yarima sai gashi ya fito, kallonta yayi sannan yace muje, a tare suka jero suka fito, guards d'insa har sun taso nan yarima yad'aga musu hannu, d'aya daga cikin motocinsa suka shiga dakansa yayi driving d'insu tunda suka fara tafiya ba wanda yayi magana zarah ko k'agare take su isa gida taga iyayenta wani irin nushad'i takeji dan fuskarta takasa 6oye farin cikinta,
Yarima ta mirror yakalleta yaga tana ta murmushi ta6e baki yayi sannan yamaida kallonsa ga titi, gudu yake sosai cikin k'ank'anin lokaci suka isa gidansu zarah,
zarah cikin sauri tabud'e k'ofar tafita sannan takalli yarima da shima yake kallonta tace zaka shigo kugaisa?
Yarima duban agogon hannunsa yayi sannan yace saidai in nadawo,
Toh sai kadawo Allah yakiyaye,
Ameen yace sannan tarufe motar har saida taga ya tafi sannan tashiga gida da gudu ba ko sallama tana k'walama mama kira,

Mama dasauri tafito d'aki tana cewa muryarwa nakeji kamar ta d'iyata, zarah rungume mama tayi tace oyoyoo mamanmu,
mama dariya tayi tace kai zarah har yanzu dai dasauran k'uriciya atare da ke, dariya zarah tayi tace mamanmu nayi missing d'inki fa, daidai lokacin yaya rauda da rahma suka fito daga d'akinsu sukace wa mukeji kamar zarah?
Zarah kallonsu tayi tana dariya tace nice dai, Aysha ce tazo tarungumeta tana murna mama tace sakarmin ita kar kikayar da ita.
Aysha sakinta tayi tana turo baki tace kai mamanmu ya za'ayi inkayar da ita.
mama jan hannun zarah tayi sukaje suka zauna saman tabarma.
Aysha da yaya rauda kallon juna sukayi sukai murmushi sannan suma sukaje suka zauna.

Cike da girmama zarah tagaishe da mama, nan mama ta amsa mata tare da tambayarta ya mutanen gida?.
Duk suna lafiya lou suna gaisheku.
Mama tace muna amsawa,
Sannan zarah takalli yaya rauda tagaisheta.
fuskar yaya rauda d'auke da murmushi ta amsa, zarah tace ya k'arfin jikinki?
Yaya rauda tace ai jiki ya warke,
Nan Aysha tagaisheta, zarah tace 'yar k'anwata ya gidan?
Dariya tayi tace Alhmdllh, ya yayana?
Zarah murmushi tayi tace yana gaisheku,
Aysha tace nad'auka ma tare zakuzo.
Eh shi yasafkeni yana saurine zaije hospital saisa bai shigoba ammah da anjima zai shigo.
Toh Allah yakawosa lafiya, sukace Ameen.

Daidai lokacin Abbah yashigo d'auke da leda yace a'ah yau mune da manyan bak'i?
Zarah cike da jin dad'i tace abbah sannu da dawowa, ina wuni?
Lafiya lou ya gidan da mijin naki?
Lafiya lou abbah kowa yana lafiya,
toh masha Allah.
kallon mama yayi da takar6i ledar hannunsa yace bari inje insamo abinda za'a dafa ma d'iyata mai d'an dad'i-dad'i.
Zarah murmushi tayi tace a'a abbah kabarsa agirka abinda ke akwai.
harararta rauda tayi tace toh baki isa kiyi mana buk'uluba sannan tace abbah ahad'o da kaji,
Dariya abbah yayi yace toh d'iyata yanzu kau dan yau dole aci dad'i.
gaba d'ayansu dariya sukayi sannan abbah yace sai nadawo, sukace adawo lafiya.
Nan suka zauna suna hira.

Mama shinkafa tabada aka 6arzo mata tad'aura burabusco, bayan abbah yadawo su rauda suka gyara kayan miya nan suka d'aura miyar dage-dage wadda tasha naman kaji, hadad'en kunun zak'i suka had'a.

Bayan sunyi sallar azuhur gabad'ayansu suka had'u saman babbar tabarma suka had'u suna ci cike da nishad'i.

Bayan sun gama atare sukayi wanke-wanke sannan suka zauna hira,

Abbah ne yace zarah rauda tafad'a mana yadda kukayi da wannan saurayin nata saidai banji dad'iba da kika amsar masa kud'insa, murmushi zarah tayi tace abbah kadaina cewa haka hak'intane fa na amsar mata kaduba kaga irin wahalar da tasha ai dan taci kud'in bawani abu bane,
jinjina kai abbah yayi yace hakane to yanzu ya kuke gani ya dace ayi da kud'in?
Mama ce tace nidai atawa shawarar ina ganin yafi dacewa shine kasiyar da wannan gidan kasamu gida wanda yad'anfi wannan girma ko mai d'akuna ukkune  kasiya mana tunda akwai sauran kud'i a wajenka,
Gabad'ansu sukace hakan ko za'ayi,
Abbah yace bank'i ta takuba toh yanzu idan maganar auren Aysha tatashi ya za'ayi?
Zarah ce tayi karaf tace aure kuma abbah?
Murmushi sukayi gabad'ayansu sannan abbah yace kiyi hak'uri bamu fad'a mikiba malam bello ne yazo yasameni yace yanaso abashi aurenta,
Zarah a firgice tace malam bello?
Mama ce tace Malam bello dai naki,
Zarah kallon Aysha tayi tace daman soyayya kukeyi?
Aysha dasauri tagirgiza kai tace wlh bahaka bane Aunty zarah shine yace yana sona da nak'i amince masa sai yasamu abbah yafad'a masa kuma nanashi labarin rayuwata yace ba matsala daman yasan komai tunda yanzu nadaina toh yana sona yanaso inmaye gurbinki, yanzu haka har danginsa sunzo sati guda da yawuce sun nemi aurena,
Zarah farincikine fal yabayyana a fuskarta cike da jin dad'i tace gaskiya nayi murna sosai kar kidamu 'yar uwata ni tuni nacire malam bello daga cikin zuciyata gaskiya nayi murna Allah yakaimu musha bikki.
Sukace Ameen,
bud'e jakkarta tayi tad'auko cheque d'in 500,000 tamik'a ma abbah tace abbana nima ga tawa gudunmawar ataimaka acanza mana gida insha Allahu ko da bikkin Aysha ya zo Allah zai rufa mana asiri.

Abbah yace a'a zarah baza'ayi hakaba ki aje kud'inki rannan ma fa kin aiko mana da kud'i kema kisamu abu mai amfani kisiya.

Zarah tace abbah bana tunani zan iya tara kud'i alhalin ku kuna nan kune yafi cancanta kutara baniba, ban ta6a tunanin samun naira d'ayaba batare da kun fad'omin arai ba, k'wallah ce tacika mata ido tace abbah dan Allah kataimaka kakar6a kusanya min albarka.
Dukansu tabasu tausayi yanayin yadda tayi maganar nan abbah yakar6a shi da mama sukaita sa mata albarka suna jinjina halin 'yar tasu tabbas sunsan sunyi sa'ar d'iya kamar zarah.
Abbah yace toh shikenan kuban lokaci zanyi tunani akan maganar canza gidan ammah fa kuyi hak'uri dan bawani babba za'a siyaba.
Sukace eh bakomai mun amince.
Abbah yace toh masha Allah, Allah yayimuku albarka gabad'ayanku.
Cikin jin dad'i sukace Ameen y rabb.
Nan abbah yamik'e yace bari inje wajen Yaya muda mugaisa.
Sukace Adawo lafiya.
Bayan ya fita nan suka cigaba da hirarsu.



_Comments_
       *nd*
_Share_


_Sis Nerja'art✍🏻_👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Sak'on gaisuwa da jinjina agareki yayata takaina *SADNAF* kinfi k'arfin page a wajena kema kin sani ina ji dake irin sosai d'innan, nagode sosai da soyayyarki agareni saidai ince Allah yabarmu tare, I hrt u dear😘_

*PAGE* 4⃣0⃣

Zarah sawa tayi Aysha taje gidansu khairy takira mata ita nan suka zauna suna ta hirarsu cike da jin dad'i da nishad'i.

Bayan sallar isha'i yarima ne ya iso k'ofar gidansu Zarah wayarsa yad'auka yakirata, zarah ganin maikiranta yasa tayi murmushi sannan tayi picking tare da yin sallama,

Daga chan 6angaren yarima amsa mata yayi sannan yace gani a waje,.zarah ahankali tace toh zaka shigo kugaisa da su abbah ko?

Jim yarima yayi sai chan yace kizo kishigo da ni, yana fad'in haka yakashe wayarsa.
Zarah mik'ewa tayi tayafa gyalenta sannan tace ma su abbah ga yarima nan zai shigo sugaisa, abbah yace toh badamuwa.

Fitowa tayi waje tagansa zaune cikin motarsa ya jingine kansa a sit d'in da yake zaune sai yafiddo k'afa d'aya a waje inda d'ayar take cikin motar.
Takawa tayi ta isa inda yake tarik'e k'ofar motar tare da yin sallama.
Yarima bud'e idanuwansa yayi da suke lumshe yakalleta, ahankali ya amsa mata.
Murmushi zarah tayi tace sannu da hanya ya aiki?
Yarima saida yajanye idonsa daga kallonta sannan yace Alhmdllh.
Bismillah kashigo kugaisa, cewar zarah.
Ahankali yarima yafito daga motar yamaida yarufe chan kuma sai yabud'e yad'auko hularsa yasaka, kallon zarah yayi da tatsaresa da ido yace kallon fa?
Fuskar zarah d'auke da murmushi tace kayi kyau
'Dan guntun murmushi yarima yayi sannan yace kema haka.
Dariya zarah tayi tace ni kyaun mi zanyi ai kafini.
Yarima ma kallonta yake yace shikenan mushiga dare yakeyi,
Zarah tsayawa tayi tace wuce gaba sai inbiyoka.
Harararta yarima yayi yace gidankune ko namu?
Murmushi zarah tayi sannan tawuce nan yabi bayanta har cikin gida, da sallamarsa yashiga, nan suka amsa masa.

Saman tabarmar da aka shimfid'a masa yazauna, cike da girmamawa yagaishe da abbah da mama suka amsa tare da tambayarsa mutanen gida.
Kansa sunne k'asa yace duk suna lafiya suna gaisheku.
Abbah yace masha Allah muna amsawa.
Sannan rauda da Aysha suka gaishesa, cikin sakin fuska ya amsa masu tare da tambayar rauda ya k'arfin jiki tace Alhmdllh yanzu ta warke.

Mama kallon zarah tayi tace kikawo masa abinci man,.zarah mik'ewa tayi tace toh mama.
Murmushi yarima yayi yace Alhmdllh abarsa kawai a k'oshe nake.

Kusan a tare su abbah suka mik'e sannan yace a'a yarima nan ma ai gidane bari mubaka waje kaci, nan suka wuce suka shiga d'aki, daidai lokacin zarah tadawo d'auke da kulolin abinci ta aje gabansa sannan tazauna gefensa, tana bud'ewa wani irin k'amshi yadaki hancin yarima nan tafara serving d'insa, bayan tagama kallonsa tayi fuskarta d'auke da murmushi tace bismillah,
Yarima d'aukar spoon d'in yayi yafara cin burabuscon sannan yakalli zarah da take wasa da gefen gyalenta yace ke bazaki ciba?
Kallonsa tayi tana murmushi tace ni naci d'azun,
Daganan Yarima yacigaba da ci, bai wani ci dayawaba yature plate d'in saidai kunun zak'in da yasha sosai,
Zarah kallon plate d'in tayi tace ba dai ka k'oshiba? Bakafa ci dayawaba.
Yarima kur6ar kunun zak'in yayi sannan yace kinsan banason cin abu mai nauyi da dare.
Zarah shuru tayi sannan takwashe kwanukan, bayan ta dawo Yarima kallonta yayi yace kije kiyi ma su abbah magana muyi sallama dare yakeyi.

Zarah 6ata fuska tayi tace tun yanzu?
Banza Yarima yayi mata,
Ganin haka yasa tamik'e taje tasanar da su abbah, kusan a tare suka fito, sama-sama suka d'anyi hira sannan sukayi musu sallama, har wajen mota yaya rauda da Aysha suka rakasu, Yarima bandir d'in 'yan 1000 yad'auko yamik'a ma Aysha yace tasiya kayan kwalliya, godia Aysha tayi masa sannan suka tafi.

Tunda suka kama hanya ba wanda yayi magana har suka isa gida, yana yin parking d'in motar daidai lokacin sumayya tafito daga 6angaren iyayenta, tsaye tayi fuskarta d'auke da murmushi tana jiran Yarima yafito, zarah ce tafara fitowa sannan Yarima, ganin zarah yasa fara'ar da yake fuskar sumayya tagushe ahankali tace ina Yarima yaje da wannan matsiyaciyar? Watau dakansa ma yake kaita anguwa? tsanar zarah ce taji tak'aru a cikin zuciyarta, batasan lokacin da suka iso inda takeba saidai ji tayi yarima ya ce kekuma daga ina kike?

Sumayya ta6e baki tayi tace daga wajen ummah na amso wani sak'one, zarah d'an rissinawa tayi tace Aunty sumayya ina wuni?
Wata uwar harara sumayya tawurga mata tare da jan tsaki sannan tawuce tabi bayan yarima da yayi gaba,
Zarah ko kad'an batayi mamakin hakan ba nan tabi bayansu tawuce part d'inta.

Cire kayan jikinta tayi tashiga wanka, bayan tafito tayi shirin bacci nan tabi lafiyar gado takwanta.

Sumayya har part d'in yarima tabisa lokacin yana shirin cire kaya yashiga wanka tsaye tayi tana kallonsa, kallonta yayi yace ya dai?
Sumayya ta6e baki tayi tace gaskiya yarima baka kyauta min.
Da mamaki yarima yakalleta kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace da akayi miki mi?
Matsowa tayi kusa da shi tace akan me zaka d'auketa kakaita anguwa alhali tana da motarta kuma zaka iya sawa akaita.

Murmushi yarima yayi yace ko da ace iyayenki ba a tare muke da suba zan iya d'aukarki in kaiki sumayya ammah banda gidan abokai dan baya cikin tsarina, yana fad'in haka yawuce yaje yashigewarsa bathroom,

Sumayya fitowa tayi cikin fushi tawuce part d'inta.

Yarima bayan ya fito shima shirin bacci yayi yakwanta.

Sumayya ma koda takwanta sak'e-sak'e kawai take a ranta ta yadda zata kawar da zarah, dan gani take itace kawai matsalarta a rayuwa.

*BAYAN KWANA BIYU*

Sumayya ce zaune a bedroom d'inta nan ta aika aka kira mata zabba'u bayan tazo tsugunnawa tayi tagaisheta cike da girmamawa, fuskar sumayya ba yabo ta amsa sannan tace kinsan dai ba akan komai zan kirakiba sai akan waccen matsiyaciyar yarinyar, kud'i sumayya tamik'a mata jikin zabba'u yana rawa takar6a tace ranki yadad'e me kikeso wlh zan iya komai kifad'i yadda kikeso ayi yanzu.

Murmushin mugunta sumayya tayi sannan tace matso kiji abinda nakeso kiyi min dan yau banso taje wajen yarima,
Dasauri zabba'u tamatso sumayya bata damu da tsamin da jikin zabba'u yakeba nan tayi mata rad'a a kunne, washe baki zabba'u tayi tace angama indai dan wannan d'an aikin ne ranki yadad'e kikwantar da hankalinki

Murmushin Jin dad'i sumayya tayi sannan tace haka nakeso zaki iya tafiya, bayan zabba'u ta fita sumayya zagaye d'akin tashiga yi cike da jin dad'i cikin d'aga murya tace yes yau burina zai cika.

Wajen k'arfe tara yarima kiran zarah yayi yace tahad'a mai coffee.
Bayan tagama saida tak'ara gyara jikinta sannan tazumbula hijab tafito, kuyanginta tasallama sannan tad'auki cup d'in coffeen tanufi part d'in yarima, tafiya take wani tsantsi taji ya ja ta wata irin k'ara tasaki kafin takai k'asa nan duka coffeen yazube a jikinta, duk yadda taso tamik'e kasawa tayi nan tafara hawaye saboda wani irin zafi da zugi dak'afar takeyi mata, waige tashiga yi ko Allah ya sa taga wani saida tayi kusan min biyar ahaka sai ga wata baiwarta tazo wuce, ganin zarah yasa tarud'e cikin sauri ta iso inda take tace ranki yadad'e meyake faruwa da ke?
Zarah tana cije baki cike da dauriya tace taimakamin intashi nan baiwar tataimaka mata tatayar da ita duk yadda zarah taso tataka k'afar kasawa tayi daga k'arshe saidai baiwar tarik'eta tana k'engasawa suka koma part d'in zarah, nan saman gado tazaunar da ita tare da taimaka mata tacire hijab d'inta,

Zarah jingine kanta tayi da jikin gadon tare da runtse ido, baiwar cike da rikicewa tace ranki yadad'e bari inje infad'a ma yarima, har ta mik'e cikin sauri zarah tarik'ota  dak'yar tabud'e baki tace kar kifad'a masa please je kikira min sahura (kuyanga) dasauri baiwar tafita daga d'akin,

bayan minti biyu sai gasu sundawo, a firgice Sahura tanufi wajen gadon tace ranki yadad'e me yake faruwa da ke?

Murmushin k'arfin hali tayi tace kar kidamu bawani abu 'yar fad'uwace nayi, yanzu so nake kitaimaka kihad'omin coffee kikai ma yarima.

Sahuru matsar k'wallah tafarayi tace ranki yadad'e ya akayi hakan takasance?
Murmushi zarah tayi tace kidaina kuka inaji miyar ku6ewa ce aka d'an zubar da ita ammah nidai yanzu kitaimaka kije kihad'a min coffeen, mik'ewa sahura tayi tace toh ranki yadad'e Allah yabaki lafiya,
Gyad'a kai kawai zarah tayi, bayan sun fita ta6a k'afar tad'anyi kad'an dasauri taruntse ido tare da furta wash saboda wani irin zafi da taji, ahankali takwanta tare da runtse idonta tanajin wani irin zogi.

A chan 6angaren yarima zaune yake a parlour yana kallo ammah gabad'aya hankalinsa baya ga kallon kad'an-kad'an ya duba time ammah shuru zarah batashigo ba, nan yak'ule tsaki kawai yake ja.

'Daya daga cikin guards d'insane yashigo yace ranka yadad'e wata kuyangace tazo ta ce gimbiya ta aikota
Yarima izini yabada yace abarta tashigo.

Sahura ce tashigo d'auke da cup tsugunnawa tayi cike da girmamawa tace ranka yadad'e gimbiya ce ta umurceni inkawo maka coffee,
Yarima da tunda tafara maganar bai kalletaba sai alokacin yajuyo yawatsa mata wani mugun kallo yace ke nasa kihad'o min ko ita? Kikoma kimaida mata abunta kice ita tafi k'arfin tazo takawo min?

Duk'ar da kanta kuyangar tayi tace ranka yadad'e kagafarceni wlh gimbiya bata jin dad'ine,
Yarima a firgice yace bata jin dad'i? Me yasameta?
Kuyangar k'ara duk'ar da kanta tayi tace ranka yadad'e lokacin da tafito zata kawo maka sai tazame yanzu tana chan k'afarta ke ciwo.

Yarima a firgice yace what! Garin ya hakan yafaru.
K'ara duk'ar dakanta tayi tace kagafarceni miyar ku6ewace aka zubar a waje itace ta zameta.

Yarima lumshe idonsa yayi tare da jin gine kansa jikin kujerar da yake zaune, d'aga ma kuyangar hannu yayi alamun tatafi, saida tak'ara duk'ar da kanta tagaishesa sannan tatashi tafita tabar d'akin.

Yarima wani iri yakeji a ransa ya dad'e zaune sannan yamik'e yafito yanufi part d'in zarah, bai samu kowaba a parlournta yana shiga bedroom yatarar da ita zaune saman gado kuyanginta biyu tsugunne k'asa suna yi mata sannu,
Yarima bai kula da gaisuwar da kuyangin sukeyi masaba yanufi wajen zarah, cikin sauri kuyangin sukabar d'akin.

Yana zuwa rikicewa yayi ganin yadda take cize le6e, k'afar yarik'o a rud'e yace sannu ko muje asibiti? Nan kawai yake miki ciwo?
Zarah zuba masa ido tayi tana kallonsa cike da mamakin ganin yadda yarikice mata,
Ganin haka yasa yarima yasaki k'afar tare da zama yadafe kansa dogon numfashi yaja sannan yad'ago kansa yakalleta yace garin ya hakan tafaru?
Zarah murmushi tayi tace inaji wani yazubar da miyar ku6ewace bai luraba nima bansan da itaba nataka shine nafad'i ammah dasauk'i.

Yarima rik'o k'afartata yayi yana dubawa ahankali yafara murza mata, wata irin k'ara zarah tasaki tare da ruk'unk'umesa nan k'wallah tafara fita daga idonta cikin muryar kuka tace please kadaina akwai zafi,

Yarima shi kansa saida yalumshe idonsa ahankali yajanyeta daga rik'on da tayi masa tare da tallabo mata kai yana kallon cikin idonta yace kidaure ind'an murza miki kar tayi tsami inyaso gobe sai muje hospital bazanyi miki da zafiba,

Zarah share k'wallar idonta tayi tace please kayi min ahankali wlh da zafi.
Yarima murmushi yayi yace kar kidamu ahankali zanyi miki.
Sakinsa Zarah tayi sannan takoma takwanta nan Yarima yajanyo k'afartata yad'aura saman jikinsa, ahankali yashiga murzawa yana kallon Zarah da take cize le6e, haka yayi ta murza mata ahankali chan daga baya sai yakoma murzawa da k'arfi nan Zarah tasaki k'ara tare da rik'o hannunsa, Yarima cigaba yayi da murzawa inda yakejin kukan nata har cikin ransa haka yadaure yacigaba da murza har saida yaga kumburin ya d'an sa6e sannan yabarta, Zarah jikinsa tafad'a tacigaba da rusa kuka, rungumeta yayi tare da lumshe idonsa ahankali kamar mai rad'a yace kukan ya isa haka please,
Zarah cigaba tayi da kukan nan yarima yashiga d'an bubbuga mata bayanta ahaka tad'an rage sautin kukan nata, sun dad'e a haka daga k'arshe bacci yad'auketa
ahankali yarima yakwantar da ita tare da gyara mata kwanciyar sai alokacin yakula da hannunta da tak'one ya yi ja abunka da farar mace dan ma Allah ya taimaketa k'unar bata tashiba, shafa hannun yayi cike da tausayi nan zarah tamotsa, tausayintane yak'ara kamasa, har ya mik'e zai tafi sai kuma yaji baya iya tafiya yabarta dan haka yadawo yakwanta gefenta tare da zuba mata ido cike da tausayinta ahaka shima bacci yad'aukesa.

kiran sallar asubane yatashesa kallon zarah yayi da take baccinta sannan yaduba k'afar yaga kumburin ya safka ahankali yasafko daga saman gadon yashiga toilet d'inta yad'auro alwallah bayan ya fito a d'akin yashimfid'a darduma yayi sallah,

yana zaune saman dardumar yana addu'a zarah tafarka, ido tazuba masa cike da mamaki, cikin ranta tace kar dai ace nan d'akin yakwana?
Kallon agogo tayi ganin 6am yasa tatashi zaune dak'yar tare da safko k'afarta k'asa tamik'e tana fara taku d'aya tasaki wata irin k'ara tare da komawa tazauna.

Yarima cikin sauri yashafa addu'an yataso yazo inda take yace kin farka? Ya k'afar taki?
Zarah cize le6e tayi sannan tace dasauk'i, rik'ota yarima yayi yace muje kiyi alwallah,
Zarah k'engesawa take ahankali yarima yana rik'e da ita har suka shiga toilet, tsaye yayi yana kallonta ganin haka yasa Zarah tamarairaice fuska kamar zatayi kuka tace please kafita.
ta6e baki yarima yayi sannan yafita tare da janyo mata k'ofar.

Bayan ta gama knocking d'in k'ofar tayi nan yarima yabud'e yana rik'e da ita yazo da ita wajen darduma, saida yazaunar da ita saman darduma sannan yaje yad'auko mata hijab tasaka sannan yakoma saman gadon yazauna yana kallonta, daga zaune tayi sallar,

Bayan ta gama ganin tanaso tatashi yasa yarima yaje yad'auketa cak yamaidata saman gado yakwantar da ita sannan shima yakwanta gefenta, Zarah shigewa tayi jikinsa nan yarima yarungumeta ahaka suka koma baccinsu.

Wajen k'arfe goma yafarka ahankali yazareta daga jikinsa sannan yamik'e yafita yabar d'akin yakoma part d'insa.
Nan yarubuta drugs yaba guard d'insa yace yasiyo masa sannan yashiga bathroom yayi wanka.

Bayan ya fito shiryawa yayi bai ko tsaya breakfast ba yafito saida yakar6i drugs d'in sannan yawuce part d'in zarah.

ko da yashiga bedroom d'in zaune take saman gadonta tana ta fama zata zage zip d'in rigarta amman ta kasa, shigowar yarima yasa tabisa da kallo, suna had'a ido nan tajanye idonta  garesa tare da gaishesa,
Yarima saida yazauna gefenta sannan ya amsa mata tare da tambayarta ya jiki, zarah tace Alhmdllh sannan tacigaba da kai hannu zata zage zip d'in rigar,
Ganin takasa yasa yarima yakai hannunsa zai zage mata, zarah kallonsa take shima yazuba mata ido suna kallon juna bata san lokacin da yazage zip d'inba saidai ji tayi ya salu6e mata hannuwan rigar ta safka k'asa, zaro ido tayi cikin sauri tafad'a jikinsa tarungumesa tareda kare k'irjinta,
sun dad'e a haka sannan yarima yajanyeta daga jikinsa tare da d'auko towel d'in da yaga an aje gefe yamik'a mata, cikin sauri zarah takar6a tad'aura tare da duk'ar da kanta k'asa cike da jin kunya,

Cike da rashin damuwa yarima yamik'e sannan yace muje inrakaki toilet d'in, zarah bata musaba tamik'a mai hannunta yatasheta tsaye yana rik'e da ita har suka shiga toilet sannan yafito tare da jawo mata k'ofar yakoma saman gado  yazauna yana jira tafito.

Bayan kamar minti goma sai gata tabud'e k'ofar, cikin sauri yarima yaje yarik'ota yazo yazaunar da ita bakin gado sannan yad'auko mata lotion tashafa, Bayan ta shafa magani yad'auka yashafa mata a k'afar yana d'an murzawa zarah saboda zafi har da 'yar k'wallarta, dakansa yaje yabud'e wardrobe yad'auko mata kaya yamik'a mata sannan yaduba agogon hannunsa yace bari insa akawo miki breakfast kiyi sannan ga tabs nan kisha guda biyu ni nawuce hospital,

Zarah binsa tayi da kallo har ya juya ya fara tafiya tace am bakajiba,
tsayawa yayi cak batare da ya juyoba,  ahankali tace nagode sosai da taimakon da kayi min.
Yarima murmushi yayi sannan yabud'e k'ofar yafita.
Zarah ma murmushin tayi nan tafara saka kayanta.

Bayan tagama nan aka kawo mata breakfast tayi sannan tasha magani takoma takwanta, tunda takwanta tunanin yarima kawai take musamman ma idan tatuna hidimar da yayi mata daga jiya zuwa yau dan batayi tunanin samun hakan daga garesaba ta dalilin haka har yakwana part d'inta, murmushine yasu6uce mata, wani irin sonsane taji yana fizgarta.

A chan 6angaren gimbiya sumayya koda kuyangarta tazo mata da labarin abinda yafaru da zarah tayi murna sosai har d'aga hannuwanta tayi tai ddu'a Allah yasa ta sanadiyar haka zarah tagurgunce a ranar baccinta tayi cikin jin dad'i da kwanciyar hankali.

Wajen k'arfe 12pm zarah ce a parlour zaune saman cushion ta mik'e k'afafuwanta, gefenta plate ne mai d'auke da tufa tana ci, sumayya ce tashigo da sallamarta fuskarta d'auke da murmushi.

Ba zarah ba hatta kuyanginta sunyi mamakin ganinta cikin wannan yanayin, gaba d'ayan kuyangin zarah suka duk'a suka gaisheta
Sumayya nuni tayi musu alamun subar d'akin.
Cikin sauri suka tashi suka fita,
saman d'aya daga cikin cushin d'in tazauna har a lokacin fuskarta d'auke da murmushi takalli zarah da tazuba mata ido tace gimbiya zarah ashe tsautsayi yafad'a miki, gaskiya banji miki dad'iba toh waima garin ya hakan takasance da ke? Ke bama hakaba Ina fatan dai baki gurgunceba.

Zarah tunda sumayya tafara maganar tazuba mata ido cike da mamaki, chan sai tayi murmushi tace kar kidamu tsautsayi ne da k'addara, kuma da kike maganar gurgwancewa ko da ace na gurgunce ai ba abun damuwa bane tunda Allah ne daman yabani k'afar dan ya kar6a alokacin da yakeso shine zan damu bayan naci moriyarta? Inaso kisani ni nayarda da k'addara nasan duk abinda zai sameni daga ubangijine.

Ta6e baki sumayya tayi tace hakan ya yi kyau saidai fa natayaki murna da baki nakasaba dan kinsan babu yadda za'ayi yarima yazauna da gurguwa.

'Daga mata hannu zarah tayi tace please ya isa haka idan kin gama abinda yakawoki zaki iya fita dan a yanzu banda lokacinki.

Dariyar mugunta sumayya tayi sannan tamik'e tsaye tace dakyau zarah am naga kamar kina jin jikin buguwar da kikayi bari dai inbarki kid'an samu kihuta saidai ince sai mun had'e a karo nagaba.

Murmushi zarah tayi tace kar kidamu nagode sosai, saduwar alkhairi.

nan sumayya tawuce tafita daga d'akin zarah binta tayi da kallo sannan daga baya tajinge kanta a jikin cushin d'in da take tare da maida numfashi




_Comments_
      *nd*
_Share_



_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_*Sak'on gaisuwa mai tarin yawa agareka Dr S Fulani😍👍*_

_Yau page d'in nakine *Sadiya Sidi Sa'id*, ko da ace sau goma zan mallaka miki page toh bazan ta6a gajiya ba saboda cancatarkice tasa haka, nagode sosai da soyayyar da kike nunamin_

*PAGE* 4⃣1⃣

Wajen k'arfe biyu da taimakon wata kuyangarta zarah tasamu tayi wanka tai sallah ko da tayi lunch maganin tak'ara shafa ma k'afar sannan takwanta saman 3 seater nan bacci yayi awon gaba da ita.

Wajen k'arfe ukku yarima yadawo daga wajen aikinsa, bayan yayi wanka ya shirya yai lunch sannan yafito yanufi part d'in zarah dan yak'ara dubata, ko da yashiga ganinta yayi tana bacci ahankali yataka yaje wajen kujerar da take kwance a kanta, daga gefen k'afarta yatsaya nan yakai hannu yad'an tatta6a k'afar gani yayi kumburin ya sa6e kad'an yarage nan yad'auki maganin yak'ara shafa mata sannan yafita yabar d'akin.

Zarah ko da tafarka k'amshin turaren yarima ne da taji yashaida mata yazo d'akin murmushi tayi sannan tatashi tana bin bango tasamu har taje toilet tad'auro alwallar sallar la'asar, bayan ta fito shimfid'a darduma tayi daga zaune tayi sallah bayan ta gama ahankali tamik'e tana d'an k'engesawa har taje parlour tazauna.


Wajen 8 yarima yashiga part d'inta lokacin tana zaune saman gadonta cikin shirin baccinta tana tufke gashin kanta, ido tazuba mai har yazo gefenta yazauna, kallonta yayi sannan yad'auke kai ahankali yace ya k'afar ina fata dai tayi sauk'i?
Zarah marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace da dai sauk'i, yarima ido yazuba mata sai chan yad'auko k'afar yad'aura jikinsa yana dubawa batare da ya kalletaba yace ammah ai kumburin ya sa6e kuma zaki iya d'an takawa, jin shuru batayi maganaba yasa yad'ago kai yaga ta tsaresa da manyan idanuwanta, janye k'afar yayi daga jikinsa sannan yace kinsha magani?
Gyad'a mai kai tayi alamun eh,
Yarima mik'ewa yayi yace akwai abinda kike buk'ata ne?
Zarah k'wallah ce tacika mata ido tayi shuru,
Yarima har zai shareta yatafi sai kuma yaji baya iyawa, komawa yayi yazauna tare da rik'o hannunta yace ya akayi ne?
Zarah jikinsa tafad'a tare da rungumesa tana jin wani irin sonsa a cikin zuciyanta.
Lumshe idonsa yayi tare da kai hannu yana shafa gashin kanta, nan ta ida lafewa a jikinsa,
ahankali yajanyeta idanuwanta suna a rufe yakwantar da ita ya d'an jima yana kallon fuskarta  chan kuma ko me yatuno cikin sauri yamik'e har ya juya zai tafi kawai sai ji yayi ta ruk'o masa hannu.

Cikin sauri yajuyo yakalleta wani irin tattausan murmushi zarah tasakar mai wanda yakusan zautasa sannan tasaki hannunsa tace sai dasafe.
Yarima kasa magana yayi dak'yar yaja k'afafunsa yafita yabar d'akin cike da kasala,

ahaka yakoma part d'insa yakwanta cike da kewarta dan duk jikinsa ya mutu jiyake kamar yakoma d'akinta yakwanta ko bakomai zai rungumeta yad'anji sauk'in abinda yakeji tare da ita ammah yasan jin kansa bazai barsa yayi hakanba, chan kuma sai yatashi zaune tare da dafe kansa yace me yake faruwa da nine? kar dai ace... dasauri yamik'e tsaye yafara zagaye d'akin yace hakan bazai ta6a kasancewa ba, ni dai nasan tausayinta nakeji, inba hakaba ya za'ayi inso yarinyar chan, me takeda shi da kamata *yarima suhail* zaiso? Nasan dai abu d'aya yasa nake zaune da ita saboda za6in iyayena ce ammah babu soyayyarta a tare da ni.
Nan sarautar tamotsa masa cikin rashin damuwa yakoma yakwantar tare da kashe gloves d'in d'akin, zarah ce kawai yake gani a duk juyin da zai yi saidai yaja tsaki ahaka yasamu bacci yad'aukesa.

A chan 6angaren zarah ma bayan yarima ya fita daga d'akin jawo pillow tayi tarungume a jikinta tare da lumshe idonta tana jinta cikin wani irin yanayi, chan kuma sai ga k'wallah tana fita daga idonta ahankali tafurta Allah kasa ma wannan bawan sona koda da k'wayar zarrane tausayin kantane yakamata dan ita kanta tasan yadda takeson yarima suhail batayi ma malam bello rabin sonba, tana acikin yanayin baccin yad'auketa.

Da asuba taji sauk'in k'afan sosai dan dakanta taje tayo alwallah batare da antaimaka mataba dan jitayi ta daina yi matazafi,
Bayan tayi sallah komawa tayi takwanta dan jiya ta dad'e bacci bai d'auketaba.

Wajen k'arfe goma yarima yagama shirinsa saida yayi breakfast sannan yafito yanufi part d'in zarah, yana shiga lokacin zarah ta fito daga wanka tana zaune tana shafa kallo d'aya yayi mata yajanye kai,

Zarah saida gabanta yafad'i dan ya yi mata wani irin kyau, ahankali tagaishesa,
Amsa mata yayi batare da ya kalletaba sannan yace ya k'afar dafatan yanzu tayi sauk'i?
Zarah shuru tayi,
Ahankali yarima yatako yazo saman gadon yazauna,
Zarah kamar jira take nan tad'auko k'afar  tad'aura a jikinsa,
Kallonta yayi nan tad'aga mai gira tare da yin fari da ido tace duba kagani,

Yarima zuba mata ido yayi yana kallonta dan gaba d'aya ta rikitasa,
Zarah turo baki tayi tace kaduba min, yarima baisan ma tana yiba dan gaba d'aya hankalinsa ya tafi wani wajen daban, ganin haka yasa zarah tata6osa,
Firgit yayi,
murmushi tayi tace ya dai tunanin me kake?
Yarima janye idonsa yayi, cikin borin kunya tare da duba agogon hannunsa yace ina tunanin wani theater ne da zanyi a hospital yanzu, janye k'afar zarah yayi daga jikinsa tare da mik'ewa,
Zarah binsa tayi da kallo sannan tace am baka dubamin k'afarba,
Juyowa yayi yakalleta yace naga ai alamun tayi sauk'i, yana fad'in haka yajuya yayi tafiyarsa.

Zarah murmushi tayi sannan tatashi tad'auko kayanta tasaka sannan takoma parlour tayi breakfast.

Bayan tagama kallo takunna tana yi cike da jin dad'in da ita kanta tarasa namenene.



Yarima baibaro hospital ba sai dare saboda ranar suna clinic ga kuma meeting sunyi,
Bayan ya dawo yayi shirin bacci yakwanta sai kuma yaji yanaso yaje yaga zarah dan rabonsa da ita tun safe,
Shigowar sumayya ne yasa yad'ago kai cikin sauri yakalleta ganin itace yasa yajanye idonsa daga kallonta,

Gefensa tazo takwanta tare da shafa sajen da yake a fuskarsa tace yarimana ya kake?
Batare da ya bud'e idonsaba yace klau, kefa?
Rungumesa tayi sannan tace nima haka dear,
Murmushi kawai yayi.

Sumayya d'ago kai tayi takallesa cike da so tace ina sonka sosai masoyina,
Murmushi Yarima yayi tare da bud'e ido yakalleta har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa.
Sumayya zuba masa ido tayi ahankali tace toh kaima kace kana sona dan tunda mukayi aure baka ta6a furtamin hakaba a k'arshema sai kayi min rashin adalci.

Fuskar Yarima cike da mamaki yace sumayya rashin adalcin me nayi miki?
Maida kanta tayi takwantar a k'irjinsa sannan tace na auren da kak'ara man.
Murmushi yayi yace k'arin aure shine rashin adalci sumayya?
Ta6e baki tayi sannan tace ammah ai baidace kayi min kishiyaba kuma karasa wadda zaka aura sai 'yar talakkawa,
Cikin d'aga murya Yarima yace ya isa haka sumayya!!
Sumayya cike da mamaki tad'ago kai takallesa har ta bud'e baki zatayi magana wata uwar harara da yawurga mata yasa takoma takwanta cike da tsanar zarah dan tasan duk saboda itane yacanza mata har yake yi mata tsawa, cikin zuciyanta tace dasannu zan kawo k'arshen wannan matsalar, ahaka tayita sak'e-sak'e cikin ranta har Yarima yayi bacci yabarta sai daga baya itama baccin yad'auketa.

A 6angaren zarah tun tanasa ran Yarima zaizo dubata ammah har dare baizoba nan takaici yacikata tace daman nasan bai damu daniba nan k'wallah tashuga zuba a idonta cike da tausayin kanta.





_Comments_
     *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_~Masha Allah my dear *Sadiya Sidi Sa'id* ina tayaki murnar kammala novel d'inki mai suna *MAHAIFIYA* hak'ik'a kin baje mana basirarki a cikinsa mun ilmantu, mun nishad'antu sannan kuma mun wa'azantu, gaskiya na jinjina miki sosai da namijin k'ok'arin da kikayi, Abinda kika fad'a daidai Allah yabaki ladan kurakuren da suke ciki Allah yayafe miki, nagode sosai da soyayyarki agareni inaso kisani ina ji da ke har cikin zuciyana saidai ince Allah yabarmu tare~_

_*I dedicated this page to you Admin of Admins*_

_On your birthday, today I wish u a year with loads of fun, excitement nd beautiful memories. Happy Birthday Admin of Admins *Hayatu Baba Zubairu (Yaya Hayat)*_

*PAGE* 4⃣3⃣

Da asuba saida yayi sallah sannan yatada zarah saida yataimaka mata tayo alwalla sannan tazo tayi sallah.

tana gamawa k'wallah ce cike da idonta takalli yarima da yake zaune ahankali tagaishesa.

Gyad'amata kai kawai yayi alamar ya amsa, janye idonta tayi daga kallonsa sannan tace nasan bazaka ta6a yadda cewa bani nazuba poison d'inba ko? Wlh ko da sau d'aya ban ta6a kawo ma raina incutar da kai ba, juyowa tayi takallesa da shima ita yake kallo sannan tace nasan bazaka ta6a yadda daniba a yanzu ka tsaneni ko?

Har a lokacin kallonta yake baice komai ba, zarah mik'ewa tayi dak'yar taje inda yake  zaune tatsugunna tace koda ace zaka yanke min hukunci inaso kataimaka kayi min wanda iyayena bazasuji labariba, ammah dan Allah kataimaka kayi bincike kafin kazartas min da hukuncin,

Sai a lokacin yarima yajanye idonsa agareta sannan yace zarah kinji na ce miki wani abu?

Girgiza kanta tayi cikin sauri har a lokacin k'wallah tana fita daga idonta.

Toh indai banceba kikyaleni kije kikwanta kihuta.

Zarah girgiza kai tayi cikin kuka tace taya kake tunani zan iya kwanciya alhali ina cikin wannan matsalar?
Tausayi tabashi yanayin yadda tayi maganar, d'aura hannunsa yayi a kumatunta sannan yace kar kidamu, yana fad'in haka yatashi yafita daga d'akin,
Zarah kife kanta tayi da gadon tana mai ci gaba da kukan.

Koda yaje magana sukayi da doctor sannan yashigo yace ma zarah tataso sutafi har a lokacin kuka take jikinta ba k'wari dakyar take takawa, har bakin mota doctor yarakasu sannan sukayi sallama.



lokacin da sumayya tatafi d'akinta takaicine yacikata ganin burinta bai cikaba domin taso ace poison d'in yafara aiki agabansu dada saboda tasan da anga haka k'arshen rabuwar yarima da zarah tazo.

tsaki taitayi daga k'arshe dabara tafad'o mata nan takira kuyangarta zabba'u tace taje tasa mata ido akan duk wani motion d'in zarah 

nan zabba'u takwashi gaisuwa sannan tafito tasamu inda ba za'a gantaba tala6e,  tun daga fitowar zarah har tafiyar da sukayi da yarima asibiti duk akan idontane,

nan tazo taba sumayya labari dariyar mugunta sumayya tayi tare jinjina kai ahankali tace lallai zarah kinyi jarumta.

tunda asuba tazuba ido domin taga dawowarsu,

lokacin da yarima yayi horn suka shigo gate da mamaki yake kallon dada da umman sumayya da ita kanta sumayya da suke tsaye cikin ransa yace tabbas wannan aikin sumayya ne.

zarah kau rikicewa tayi takalli yarima tace shikenan yarima sun gano ni nashiga ukku.

yarima batare da ya kalletaba yace kar kisaki kinuna akwai wani abu indai kika nuna suka gane babu ruwana sai kisan yadda zaki Kare kanki,

daidai lokacin yagama parking d'in motar yabud'a yafita batare da ya kalletaba.

zarah tana ganin haka itama tabud'e tafito cikin zuciyanta tana ta addu'a


bayan yarima tabi a tsorace shidai tafiyarsa yake hankali kwance gab da zai isa wajen da su dada suke nan wayarsa tafara ruri tsayawa yayi yad'auko wayar yana dubawa murmushin nasara yayi sannan yayi picking d'in wayan batare da yayi magana ba,

daga chan 6angaren akace ranka yadad'e Dr, Ahmad ne yake magana daman wannan patient d'inne da kayi ma theater toh ya farka.

yarima shuru yayi nad'an lokaci sannan yace idan kun tabbatar da babu abinda yake damunsa toh sai kuyi masa wannan injection d'in da na aje inyaso da anjima idan nashigo sai in rubuta masa drugs.

daga chan 6angaren akace toh ranka yadad'e sai ka shigo,  yarima baice komai ba yakashe wayarsa, sannan yamaida kallonsa ga dada da tatsaresa da ido ammah ko inda su umman sumayya suke bai kallaba.

murmushi yasakar ma dada yace ranki yadad'e ya akayi naganki nan a tsaye a wannan lokacin?

fuskar dada a d'aure tace daga ina kuke? 

shuru yarima yayi yana murmushi,

dada tace ashe yarinyar nan dagaske guba tazuba maka tunda da taci abincin saida kukaje asibiti,  kai wlh bansan samna bane sai yanzu matar da tayi shirin kasheka itace kataimaka mawa toh wlh dole memartaba yaji maganar nan.

har a lokacin yarima murmushi yake sai chan yace dada bai dace kice hakaba tunda baki gani da idonki ba, kirana fa akayi daga hospital akan wani emergency case cikin dare shine zarah tace zata bini mukaje tare kuma ma yanzu ai gabanki aka kirani waya.

sumayya tayi karaf tace wlh bahaka bane poison d'in da tacine a cikin abinci kiduba kiga yadda duk tazure,
ummanta tace ai wannan dama daga ganinta poison taci.

yarima murmushi yayi sannan yace sumayya gabanki tazuba min poison d'in?  gabanki tayi girkin? Lokaci guda yajero mata wad'annan tambayoyin.

sumayya tace toh ai lokacin da takeyi naga ta zuba wani abu.

yarima wani mugun kallo yawurga mata yace toh kina dai nufin la6e kikayi mata.

sumayya hararar zarah tayi da take raku6e bayan yarima tace wannan gajar zan yi ma la6e?  tak'aryata mana idan batayiba, kuma naga lokacin da katafi kakaita asibiti.

murmushin mugunta yarima yayi yace toh in ko ta zuba min poison toh tare da ke aka zuba kokuma ke d'in kika Zuba.

zaro ido sumayya tayi tace ni ya za'ayi inzuba maka poison?

yarima kallon dada yayi yace ranki yadad'e kiduba kiga inda ace yarinyar nan ta zuba poison kina tunanin zata amince taci abincin alhali tasan zata iya mutuwa? 

dada jinjina kai tayi batare da tace komai ba.

yarima suhail rik'o hannun zarah yayi yace bari mushiga daga ciki.

kallon ummah yayi da tacika tayi fam yayi murmushi yace ummah gaskiya ya kamata kija ma d'iyarki kunne tadaina la6e,  na barku lafiya.
jan zarah yayi suka shige sukabar su dada a tsaye, sultana sadiya da harara tabi yarima ji take kamar tashak'esa yamutu kowa yahuta,

dada kallon sumayya tayi tace sumayya yakamata ki iya bakinki yanzu gashinan kinja naji kunya,  tana gama fad'in haka tawuce tanufi turakarta.

sultana sadiya kallon sumayya tayi da duk tasusuce tace ai ga irinta nan gashinan kinja yaro k'arami yana nema yarainani,

sumayya turo baki tayi tace ammah ai ummah bak'arya nayiba.

ummah tace ko da ace ba gaskiya bane ai bakida k'wak'warar hujja,  wlh matsalata da ke bakida isashen wayau, duk yadda zakiyi abu bakisan yadda zaki fitar da kankiba.

sumayya cikin fushi tace haba ummah dame zan ji?  da rashin cin nasara ko da surutun da kikeyi min?

sultana sadiya ganin d'iyartata tayi fushi yasa tafara lallashinta har saida taga ta hak'ura sannan tace tafi kiyi baccinki kicire komai a ranki ina tare da ke kinji ko d'iyata.

Toh ummana kema kije kihuta, murmushi sultana sadiya tayi sannan tatafi cike da tausayin 'yartata.

Yarima ko da suka shiga cikin gidan yana rik'e da zarah har part d'insa umurni yaba guards d'insa yace kar subar kowa yashigo koda ace sumayya ce, gaba d'ayansu sukace to ranka yadad'e angama.

Suna shiga zarah cikin sauri taduk'e k'asa saboda wani irin juwa (jiri) da yake kwasarta.
Tsaye yarima yayi yana kallonta sai chan yace kitashi mushiga ciki sai kikwanta.
Zarah kasa magana tayi dak'yar tamik'a mai hannun.
Ganin haka yasa yarima yatayar da it's tsaye ganin bata iya tafiya yasa yad'auketa yanufi bedroom da ita.

Maida idanuwanta tayi tarufe ahaka yakwantar da ita Saman gadon daga gefenta yazauna tare da shafa fuskarta cike da tausayinta yace bari insa ahad'a miki breakfast kiyi.

Girgiza kai zarah tayi alamun a'a tare d's rik'o hannunsa.
Yarima ido yazuba mata ahaka har tayi bacci,

Ahankali yazare hannunsa daga cikin nata sannan yakoma gefenta yakwanta dan rama baccin da ake binsa.

Wajen 11am yafarka har lokacin zarah bacci take, wanka yashiga yayi lokacin da yafito ganin zarah yayi ta farka,
Ganinsa d'aure da towel yasa tamaida idanunsa tarufe, yarima kallonta yayi yace kin tashi?
Batare da ta bud'e idontaba tace uhm.

Cigaba yayi da shirinsa saida yagama sannan yashiga bathroom yahad'a mata ruwan wanka, bayan ya had'a dawowa yayi kusa da ita yazauna sannan yace taso muje kiyi wanka ko kin samu k'arfin jikinki,

Zarah bud'e idonta tayi ahankali sannan tace toh,
Yunk'urin mik'ewa tashiga yi amma takasa, ganin haka yasa yarima yataimaka mata tatashi zaune sannan yamik'a mata towel, juyawa tayi alamun yazage mata zip d'in rigar,

Hannu yakai yazage mata, ganin tana ta kare-karen jikinta yasa yarima yata6e baki sannan yajuya mata baya.
Ganin haka yasa zarah tacire rigar sannan tafara yunk'urin mik'ewa, juyowa yarima yayi yarik'ota tasafko daga saman gadon tana fara takawa nan tayi baya zata fad'i cikin sauri yarima yatarota, cak yad'auketa yanufi toilet da ita, zare towel d'in yayi daga jikinta sannan yasakata cikin ruwan,
Zarah dasauri takai hannu takare k'irjinta ahankali tace kafita zanyi.

Kallonta yarima yayi yace kina ganin zaki iya? Gyad'amasa kai zarah tayi, baice komai ba yajuya yafita yabar toilet d'in.

Zarah kwance tayi cikin ruwan tana jin dad'in ruwan, kasa yin wankan tayi nan tamaida idanuwanta talumshe.

Yarima tura guard d'insa yayi part d'in zarah wajen kiyanginta aka kar6o mata kayan da zatasa,
Ya dad'e Zaune ammah zarah bata fitoba, ganin haka yasa yarima yamik'e yanufi toilet d'in.

Tsaye yayi bakin k'ofar toilet d'in yana kallonta, zarah idanuwanta a lumshe batamasan da shigowarsaba, wucewa yarima yayi ya ida isa wajen k'irjinta yazuba ma ido sai daga baya yad'ibi ruwan ya watsa mata a jiki, firgit tayi tabud'e idonta, sponge yad'auka yafara wanke mata jikinta zarah kasa hanasa tayi dan tasan indai tace zata hanasa toh ita bazata iya yiba, ganin yadda yazuba ma k'irjinta narkakkun idanuwansa yasa ta maida idanuwanta tarufe cike da jin kunya ahaka yarima yawanketa tas, bayan ya gama nad'ota yayi a towel yana rik'e da ita suka fito.

Bakin bed d'insa yazaunar da ita sannan yad'auko mai yashafa mata, shi yataimaka mata tasaka kaya sannan rik'ota suka koma parlour yazaunar da ita,  dining yaje yakwaso musu breakfast, a saman lallausar carpet d'in da yake shimfid'e a tsakiyar parlourn, kallon zarah yayi yace kisafko muyi breakfast d'in.

Zarah kallonsa tayi tace na k'oshi, kallon da yayi matane yasa tasafko tazauna, dakansa yahad'a musu breakfast yatura mata nata gabanta, da k'in shan tea tayi sai juya spoon d'in take ganin yarima ya kalleta yasa tad'aga cup d'in tafara sha kad'an-kad'an batasha wani na kirkiba ta aje sannan tad'an ci chips d'in.

Yarima ma bawani nakirki yaciba yamik'e, nan yabada umurni akazo aka kwashe komai, bedroom yashiga yad'auko mata drugs yazo yabata dak'yar takar6a tasha kasancewarta batason shan drug's,
Nan yahad'a injection yayi mata.
Zarah har da 'yar k'wallarta takoma saman 3 seater takwanta.

Yarima bedroom d'insa yashiga, bayan 'yan mintuna yafito da key d'in mota, kallonta yayi da itama tazuba mai ido, saida yajanye idonsa daga gareta sannan yace akwai abinda kike buk'ata?
Ahankali tace a'a.
Ohk, ni na wuce hospital, cewar yarima.
Ahankali Zarah tace adawo lafiya.
Chan k'asan mak'oshinsa ya amsa yace Allah yasa.

Ko da yafita k'ara gargad'in guards d'insa yayi kar subar sumayya tashigar mai part, sannan yawuce yatafi.

Zarah taso tatashi takoma part d'inta ammah takasa, a dudduk'e tatashi tagyara mai bedroom d'insa tasa aka gyara parlour sannan takunna kallo tana yi.

Wajen k'arfe biyu wanka tayi tashirya sannan tayi sallar azuhur, Ko da aka kawo lunch k'inyi tayi dan ji take gabad'aya abinci ya fita ranta yanzu dan haka tayi zamanta.

Around 3 o'clock yarima yadawo, har lokacin Zarah tana zaune tana kallo, kallonsa tayi tace sannu da zuwa.
Yauwa, cewar yarima da yazuba mata ido, sai Chan yace ya k'arfin jikin?
Saida tad'an ciji le6enta sannan tace Alhmdllh yai sauk'i.
Wucewa yayi yashiga bedroom d'insa dan yakimtsa.

Bayan ya gama yafito kallon zarah yayi yace kinyi lunch?
Uhm kawai zarah tace.
Kallonta yarima yayi alamun rashin yadda sannan yace muje kik'ara.

Zarah turo baki tayi tamik'e tana tafiya dak'yar har suka isa dining, ko da suka zauna yarima ne yayi serving d'inta sannan shima yazuba nasa, ahankali yakeci idonsa yana kan zarah da take turo baki har lokacin batayi ko loma d'ayaba.

'Dago kai tayi takalli yarima ganin yana kallonta yasa tad'ibi abincin takai bakinta, dak'yar take taunawa saida tayi kusan minti biyar tana tauna sannan tahad'e, ganin haka yasa yarima yajanyo plate d'in gabansa yad'ebo batare da ya yi magana ba yakai wajen bakinta, kallonsa zarah tayi cike da mamaki, ganin fuskarsa ba alamun wasa yasa tabud'e bakin yasaka mata, zarah tana yatsine fuska take taunawa, yanayin yadda take taunar ya burge yarima dan haka yaita bin bakinta da kallo, ahankali yacigaba da feeding d'inta idanuwanta sukayi rau-rau kamar zatayi kuka, d'ura mata yacigaba da yi har saida yaga alamun ta k'oshi sannan yabata drugs yamik'e yabar wajen.

Zarah goge k'wallar da tazubo mata tayi sannan takalli plate d'insa da ko rabin abincin bai ciba, ahankali tace to shi kuma wa yabarma nashi yacinye?.

Mik'ewa tayi tadawo parlour nan tatarar da yarima kwance saman 3 seater yana kallon wrestling, chan saman 2 seater taje tazauna ganin wrestling yake kallo yasa haushi yakamata ahankali tace mutum yana kallonsa an canza mai channel, batasan maganar ta fitoba saidai jin yarima tayi ya ce d'akinki ko d'akina?
Kallonsa zarah tayi taga hankalinsa yana ga T.V kamar ba shi yayi maganan ba, mamaki yakamata shuru tayi batace komai ba.

Kiran wayan yarima da akayine yasa yamik'e yafita batare da ya ce mata komai ba.
Mik'ewa tayi taje tad'auko remote tacanza channel tacigaba da kallonta.

Har akayi sallar isha'i yarima bai dawoba wanka tashiga tayi tashirya, dinner kad'an tayi tasha drugs d'inta sannan tabi lafiyar gadon yarima tayi kwanciyarta.

Wajen 9pm yarima yadawo ganin tana bacci yasa shima yayi shirin kwanciya yakwanta, zuba ma fuskarta ido yayi yana kallo cike da tausayinta daga k'arshe yarungumota jikinsa tare da jan dogon numfashi, yanayin yadda yamatseta har saida tamotsa sannan yad'an safsafta mata rik'on, zage mata zip d'in rigarta yayi sannan yatura hannuwansa cikin rigar tare da lumshe ido yana jin wani sanyi a ransa, ahaka bacci yad'aukesa.

Cikin dare juyin da zarah zatayi jinta matse yasa tafarka, mamakine yakamata ganinta jikin yarima, jin hannunsa tayi a k'irjinta murmushi tayi tare da zuba ma fuskarsa ido tana kallo cike da sonsa k'wallah ce tacika mata ido cike da tausayin kanta tace ina ma ace kana sona muka kasance haka, jin k'irjinta ya fara bugawa yasa takoma takwanta tare da gyara kwanciyarta.

Da asuba ko da yafarka ahankali yajanyeta daga jikinsa sannan yatashi yashiga toilet saida yayi wanka sannan yad'auro alwallah, yana fitowa zarah tafarka zage zip d'in rigarta tayi sannan tamik'e tashiga toilet.

Lokacin da tafito har ya fita masallaci dan haka tayi sallarta ko da tagama saman gadon takoma takwanta, ba ita tafarka ba sai wajen 11 lokacin yarima har ya fita.

Gyara masa part d'insa tayi sannan takwashi kayanta takoma part d'inta, bayan sun gaisa da kuyanginta bedroom d'inta tashige wanka tayi tashirya sannan tafito tayi breakfast.

Bayan ta gama saman 3 seater takwanta wayarta tad'auko tahau chart daga k'arshe da tagaji tabud'o novel  *(K'ADDARA CE)* cikin wayar tana karantawa gaba d'aya tamaida hankalinta ga karatun, sallah ce kawai takesawa tana ajewa ahaka har tagama.

Da dare kwanciyarta tayi part d'inta duk sai taji babu dad'i, tana kwance wayarta tafara ringing janyowa tayi tana ganin yarima ne batasan lokacin da murmushi yakubce mataba, zuba ma wayar ido tayi har saida taga ta kusan tsinkewa sannan tayi picking tare da yin sallama cikin 'yar siririyar muryarta, daga chan 6angaren yarima amsa mata yayi daganan shuru yabiyo baya sai chan yarima yace ya jikin naki?
Zarah kwantar da murya tayi sannan tace Alhmdllh ya yi sauk'i.
Ohk, kinsha drugs d'in?
Cikin shagwa6a tace uhm,
Daga chan 6angaren yarima saida yalumshe idonsa sannan yace kin tabbata.
Zarah kamar zatayi kuka tace dagaske fa na sha.
Daga nan duk sukayi shuru saida sukayi kusan minti ukku sannan yarima yace sai dasafe.
ahankali tace Allah yakaimu ko inzo intayaka bacci?
Yarima baisan lokacin da murmushi yaku6uce masaba sannan yace no kiyi kwanciyarki, yana fad'in haka yakashe wayarsa.

Zarah ma murmushi tayi sannan ta aje wayar saman bedside tare da kashe gloves.

Sumayya tsaye take bakin k'ofar yarima ta cika tai fam dan duk wayar da yayi da zarah a gaban idontane, cikin fushi tatako ta iso bakin gadon tace haba yarima wannan wane irin zaluncine?
Yarima kallonta yayi cike da mamaki yace zalunci kuma?
Cikin d'aga murya tace eh zalunci, akan me zaka kira waccan jakkar yarin....
'Daga mata hannu yayi fuskarsa ba alamun wasa yace kar kikuskura kik'ara min shouting koda ran girkin kine sai akace banda ikon yin waya da matata? Toh bari kiji wlh kikiyayeni ko in sassa6a miki.

Sumayya ta6e baki tayi tace eh d'in adai dunga jin tsoron Allah.

Wani irin kallo da yayi matane yasa tasha jinin jikinta, cikin 6acin rai yace indai kinsan abinda yakawoki kenan toh kifita kiban waje kar kimin hauka yana fad'in haka yajuya mata baya.

Sumayya ta ji haushin abinda yayi mata cikin ranta tace babu inda zanje, infita waccan gajar tashigo, ahankali tahau gadon takwanta tare da rungumo yarima ta baya tace toh kayi hak'uri na daina.

Yarima lumshe idonsa yayi sannan ahankali yace shikenan sumayya.



_Comments_
      *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_*Wannan page d'in tukuicine agareki mummyna chubad'o muhammad, hak'ik'a kin wuce duk yadda kike tunani a zuciyana saidai ince Allah yabarmu tare mummy😘*_

*PAGE* 4⃣5⃣

Ahankali yake warwarewa har yagama sannan yabud'e yafara karantawa gabansane yafad'i ganin sunansa aka rubuta da larabci, sai wasu rubutu da shi kansa baisan menene aka rubutaba saboda mitsi-mitsine daga chan k'asa kuma sunan zarah yaga anrubuta sannan daga gefe akasa  d'aya ansa _ni zarah zan mallaki yarima_ gabansane yacigaba da fad'uwa cike da mamaki yace zarah ce tasamin laya dan tamallakeni? Me take nufi da hakan? cikin sauri yaje yad'auko na toilet d'in yawarware sunansa da na zarah kawai ne jikin takardar, tsaye yayi cike da mamaki yana k'ara bin takardun da kallo,

Zarah kwance take d'akinta duk kasala ta rufeta tanaso taje part d'in yarima ammah ta kasa saboda batajin dad'in jikinta, daga k'arshe dai daurewa tayi tamik'e tad'auko alkyabbarta tasaka sannan tafito tanufi part d'insa.

Ahankali tabud'e bedroom d'insa tashiga tsaye tagansa rik'e da layar, juyowa yayi yaimata wani irin kallo, cak zarah taja tatsaya cikin ranta tace shikuma wannan mutumin me yake nufi da hakan?
Muryarsa taji ya ce abinda kikayi shirin yi toh bai yuwuba dan haka sai kicanza sabon shiri ammah ni nafi k'arfin duk wani sihiri.

Zarah zuba masa ido tayi tana kallonsa cikin rashin fahimtar abinda yake magana a kai, ahankali tace ban fahimci akan abinda kake nufiba.

Yarima wurga mata harara yayi yace kar kimaidani wanda baisan abinda yakeba ko kin d'auka banga layun da kika ajeminba cikin toilet da k'arshin pillow na ba, zarah zaro ido tayi tace ni kuma?

Mik'amata yarima yayi yace toh ai sai kiduba kigani idan k'arya akayi miki, cikin sauri takar6a tashiga dubawa, tsoro da fargaba duk suka cikata, cikin sauri tad'ago kai takalli yarima da shima yake kallonta, muryarta tana rawa tace wlh ban aikataba bansan wanene yake neman jamin sharri ba, innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, dasauri taje wajen yarima tarik'o hannunsa k'wallah duk ta cika mata ido tace kayarda dani wlh bani bace nakawo maka laya,
Fizge hannunsa yayi cikin d'aga murya yace idan bake bace toh wanene? Kuma sunan wanene a jiki?
Zarah kallonsa take cike da mamaki tace yanzu ka yarda zan iya yi maka asiri? Cike da rashin damuwa yace toh idan ban yardaba me kikeso inyi?
Murmushi Zarah tayi wanda yafi kuka ciwo sannan tace da ace ni mushrikace da ba akanka zan faraba kuma ba zan ta6a amincewa in aurekaba da tun farko zan san yadda zanyi inga ban aurekaba saboda nima inada wanda nake so, kuma da ace ina asiri da tun farko zanyi maka ba sai munkai wannan lokacinba, wlh nagaji da wannan sharrin da ake ja min komawane yaje dan kansa, tak'arashe maganar cikin kuka,

Yarima kallonta yake har takai aya sannan yace idan kin gama zaki iya tafiya dan magangununki bazasu ta6a tasiriba agareni, Zarah d'ago kai tayi takallesa tace bakomai insha Allahu gaskiya zatayi halinta komawanene asirinsa zai tonu, tana fad'in haka tawuce tafita tabar d'akin.

Tafiya take zata koma part d'inta hawaye suna zuba daga idanunta ita kanta batasan inda take jefa k'afartaba, hawaye d'aya na bin d'aya, ahankali take furta ya ubangiji kakawo min mafita a cikin wannan al'amari, ya ubangiji katona asirin duk wani mai nufin sharri agareni, me nayi musu? Meyasa sukeson ganin sun 6atamin rayuwa, wanene yake nufina da sharri haka?
Tuntu6e ne tayi batasaniba nan tatafi zata fad'i, cikin sauri taji an rik'ota tafad'a jikin mutum, d'ago kai tayi cike da mamaki dan ganin kowanene? Ido tazuba ma jakadiya da itama take kallonta, ahankali jakadiya tace ranki yadad'e meyake faruwa dake ne haka?
Zarah runtse idanunta tayi nan wasu sabbin hawayen suka shiga gangarowa, jakadiya cikin sauri tawaiga gaba da bayanta ganin bakowa yasa tarik'e Zarah suka ida isa part d'in Zarah.

Jakadiya kallon kuyangin Zarah tayi tace kubamu waje, cikin sauri duk suka ficce sukabar d'akin.

Zaunar da Zarah tayi saman d'aya daga cikin cushin sannan tazauna k'asa gaban Zarah, kallon Zarah tayi da tajingine kanta a jikin cushin d'in hawaye suna zarra daga idanunta, tace ranki yadad'e meyake faruwa da ke ne?
Zarah ahankali tabud'e idonta takalli jakadiya, nan tayi murmushi wanda yayi kuka ciwo sannan tadafe kanta.

Jakadiya gyara zamanta tayi tace gimbiya kifad'a min matsalarki ni nayi alk'awali zan taimaka miki kid'aukeni a matsayin uwa,
Zarah d'ago kai tayi takalli jakadiya har a lokacin hawaye suna zuba daga idonta cikin muryar kuka tace ya akeso inyi da rayuwata? Narasa wanene yake k'ullamin sharri da angama wanchan sai afad'a ma wannan shin ya akeso inyi? Ni zan iya hak'ura da auran inkoma gidanmu,
Cikin sauri jakadiya tagirgiza kai tace a'a ranki yadad'e kar kice haka dan Allah kifad'amin abinda yake faruwa nayi alk'awali zan taimaka miki.

Zarah kallonta tayi cike da gamsuwa da maganar jakadiya sannan takwashe duk makircin da akeyi mata tafad'a ma jakadiya,

Jakadiya jinjina kai tayi tace wannan ba aikin kowa bane sai na gimbiya sumayya,
Zarah cike da mamaki tace yanzu kina ganin itace zata yi min haka?
Jinjina kai jakadiya tayi tace tabbas itace dan nasan wacece gimbiya sumayya da mahaifiyarta fiye ma da haka zasu iya yi.

Zarah share hawayen fuskarta tayi tace toh wlh zan iya hak'ura da auren inkoma gidanmu.

A'a gimbiya kar kice haka bai dace kikaraya ba, mu munsan halinsu, kuma sumayya da kikaga yarima ya aura toh auren had'ine ba auren soyayya bane sukayi.

hatta shi kansa yarima da kike gani akwai abinda mahaifiyar sumayya take k'ullawa akansa wanda ita kanta sumayya bata saniba.

Zarah ido tazuba mata cike da mamaki.

Jakadiya tacigaba da cewa akwai wani lokaci da dada ta aikeni wajen sultana sadiya, lokacin da nashiga parlour bakowa har na juyo zan baro d'akin najuyo magana k'asa-k'asa a bedroom d'in sultana sadiya tsaye nayi lokacin da najuyo tana cewa so take gimbiya sumayya tahaihu idan yaron yafara wayau tanaso tabi kowace hanya dan ganin ta kawar da yarima inyaso mijinta abashi rik'on k'warya kafin jikan nata yagirma daga baya yazama shine sarkin gari, ta san idan yahau toh sai yadda taso mulkin gidan zai tafi, dan ta tsani mahaifiyar yarima taso ace itace tahaifi d'a namiji Wanda zai gaji garin ba mahaifiyar yarima ba, ina jin haka cikin sauri nafito nabaro part d'in gudun kar taganni dan nasan idan taganni toh bazata ta6a barinaba.

Zarah cike da rud'ewa tace daman haka matarnan take? Toh shi yarima baisan halintaba ya amince ya auri d'iyarta.

Murmushi Jakadiya tayi tace tabbas yarima yasan kad'an daga cikin halayyarta dan tun yana k'arami idan yaje part d'inta wahalar dashi take dan akwai lokacin da tata6a watsa mai ruwan zafi, tagargad'e ni da idan nafad'a ma wani sai tayi sanadiyar barina aiki, kasancewar nikad'aice lokacin da abun yafaru.

Toh ba'a gane taba? Cewar zarah.
Eh toh, yarima yana da wani irin hali wanda ba komai bane yake iya bud'e cikinsa yafad'aba wannan halinsane tun yana k'arami, kuma na tabbata shi kansa yana sane da abubuwan da tayi masa kawai dai ya sharene,
indai wajen makircine toh kala-kala matarnan ta iya dan ina tunanin dasa hannunta sumayya takeyi miki wad'annan abubuwan.

Zarah jingine kanta tayi cike da jin tausayin mijin nata, Jakadiya tace ranki yadad'e kigode ma Allah da basubi ta wata hanyarba dan ganin sun kawar da ke, koda basubin boka ammah sun san makirci kala-kala.

Jinjina kai zarah tayi cike da mamakin halin su sumayya, ahankali tace duk makircinsu basu isa suyi abinda Allah bai nufa ba, kuma ina neman kariya daga ubangijina, saidai bansan yadda zanyi inshawo kan yarima yafahimceniba.

Jakadiya tace kar kice haka ranki yadad'e kuma baidace kiga laifin yarima ba tunda duk baya makircinsu da suke miki baiyi tasiriba a garesa ammah a yanzu kiduba kiga har da sunansa da naki aka had'a kinga ai bakowa bane zai iya k'in yarda, yanzu dai abu d'aya zakiyi shine nake tunani kamar zai taimaka wajen ganin kin ku6utar da kanki, zarah kallon Jakadiya tayi tace wane abune please kifad'a min.

nan Jakadiya tace kice yatambayi guards d'insa sufad'i Wanda yashiga da baya nan tunda ke kince baki shigaba,
Zarah tace anya kina tunanin zai amince?
Eh insha Allahu ai ya aminta da su yasan bazasu ta6a yi masa k'aryaba,

Zarah jinjina kai tayi tace nagode sosai jakadiya, hak'ik'a kin taimakeni a lokacin da nake buk'atar taimako nakekai kukana ga ubangijina,

Jakadiya tace kar kidamu gimbiya har cikin raina nake jinki dan kece kikafi dacewa da yarima ba sumayya ba kuma ina fatan yakasance kece zaki fara aje mana magajin yarima.

Zarah saida gabanta yafad'i dasauri tagirgiza kai tace kar kice haka, sumayya ita tafi dacewa tahaihuwa da yarima.

'Yar dariya jakadiya tayi tace tuni tayi watsi da damanta koda haka mahaifiyarta taci buri itama ammah a yanzu k'addara ta riga fata,

Zarah cike da mamaki take kallonta tace ban fahimci abinda kike nufiba?
Murmushi jakadiya tayi tace kar kidamu dasannu zaki fahimta nan ba da dad'ewaba, jakadiya tana fad'in haka tamik'e tare da d'an rissinawa tace nabarki lafiya ranki yadad'e.

Zarah d'aga kai tayi tace nagode sosai jakadiya saidai ince Allah yabaki ladar abinda kikayi min.

Jakadiya murmushi tayi tace kar kidamu ai yi ma kaine, nidai fatana kirik'e sirrin maganar da nafad'a miki.

Zarah murmushi itama tayi tace insha Allahu babu wanda zai san maganar nan bayan mahaliccinmu sai ni da ke.

Jakadiya tace nagode, nan sukayi sallama tafita, zarah tsaye tayi tana tunani cike da jinjina ma sumayya da mahaifiyarta sannan daga baya tawuce tashige bedroom d'inta takwanta, nan hawaye suka cigaba da fita daga idonta tana tunanin hukuncin da yarima zai yanke mata akan laifin da ba ita ta aikata shiba, fashewa tayi da kuka tace ya ubangiji kakawo min d'auki, kuka tayi sosai saida taji kanta ya fara ciwo sannan tadaina haka taita juyi saman gadon daga k'arshe bacci yayi awon gaba da ita.

Yarima bayan zarah ta fita zama yayi saman gadonsa tare da dafe kansa cike da takaici, mamakin zarah ne yakamasa dan baita6a tunanin haka daga garetaba tun daga yanayin tarbiyarta, ya dad'e zaune yana jinjina lamarin dan abun ya d'aure masa kai sosai dan idan ya ce ba ita bace toh wanene zaiyi hakan?, tsaki yaja cike da takaici sannan yakwanta abu guda yatsaya masa a rai kalmar da tafurta ta nima ina da wanda nakeso, haka kalmar yaita jinta a kunnensa tana masa yawo har daga k'arshe bacci yad'aukesa..

A chan 6angaren sumayya kiran sultana sadiya tayi tana yin picking bata bari tayi ko sallama ba cikin jin dad'i tace ummah na aiwatar da komai kuma ina tunanin nasara a cikin aikin namu, daga chan 6angaren sultana sadiya dariya tayi tace gaskiya naji dad'i daughter ai ina fad'a miki ta ruwan sanyi zatabar gidannan dan makirci kala-kala babu Wanda ban iyaba idan akayi wani baiyiba sai acanza wata hanyar, cikin jin dad'i sumayya tace saisa nake k'ara sonki ummana dan duk abinda nakeso kema kinasonsa na rabbata yanzu yarima zai zama nawa ni kad'ai.
Murmushi sultana sadiya tayi sannan tace kar kidamu d'iyata farin cikinki shine nawa, saisa nake burin kihaifo min jika wanda zai gaji masarautar nan ammah kinkasa fahimtar inda nadosa, Indai kinsan kina yin planning toh kitaimaki kanki kidaina tun kan waccan munafukar tafara haihuwa,
Gaban sumayya saida yafad'i dan bata ta6a yin tunanin hakaba, ahankali tace hakane kuma ummah insha Allahu bama zata haihuba zata bar gidan.
Sultana sadiya tace na dai fad'a miki kirufa ma kanki asiri kidaina.
Cikin shagwa6a sumayya tace toh ummah na ji.
Uhm Allah yasa dagaske, cewar sultana sadiya.
Ameen ummana.
Yauwa toh yanzu kikwanta kiyi bacci dare keyi.
Toh ummah ko mi kenan sai kinjini, nan sukayi sallama suka kashe wayoyin.
Sumayya fad'awa tayi saman gadonta cikin murna tace yes nasan zuwa gobe waccan munafukar zata koma kongon gidansu, ahaka tayi bacci cike da farin ciki.


Cikin dare zazza6i da ciwon kai suka tashi zarah daga baccin da take nan taita juyi saman gadon daga k'arshe k'asa tasafka takwanta, ciwon cinta yake  babu wanda zata iya kira dan ko hannunta kasa d'agawa tayi daga k'arshe, tana nan tana juyi ahaka aka kira sallar asuba.

Har aka gama sallah akan kunnenta ammah takasa tashi dakyar tasamu tamik'e tana dafa bango har tashiga toilet, saida tahad'a ruwan d'umi tayi wanka sannan tad'auro alwallah daga zaune tasamu tayi sallah sannan talalubo paracetamol tasha, nan saman darduman tayi kwanciyarta har saida gari yafara yin haske sannan tamik'e tajanyo alkyabbarta tasaka, cikin rashin k'warin jiki tafito duk wanda yaganta ya san batada lafiya, ko da kuyanginta suka gaisheta hannu kawai tad'aga musu taku take dak'yar tana dafa bango tana tsayawa tahuta ahaka ta isa part d'in yarima.

Tana murd'a k'ofar bedroom d'in yarima tsaye tayi tare da jingine kanta jikin k'ofar tana maida numfashi,

Yarima da daidai lokacin yasafka daga saman gadonsa tsaye yayi yana k'are mata kallo ko da cikin fushi yake da ita ammah hakan bai hana yaji wani iriba da yaganta cikin yanayin.

Zarah ahankali tatako tamatso kusa da shi, yarima d'aure fuska yayi yace meyakawoki wajena? Ko wani abun kikazo kik'ara shirya min?

murmushin k'arfin hali tayi sannan ahankali tace nasan kana jin haushina akan abinda yafaru, shuru tayi nad'an lokaci sannan tace ammah dan Allah ina neman alfarma guda,
saida takalli cikin idonsa sannan tacize le6e cike da dauriya tace kataimaka kayi bincike kafin kazartas da hukunci, katambayi guards d'inka sufad'a maka wanda yashigo part d'inka da bakanan dan ni wlh duk jiya ban shigoba sai dare, k'wallah ce tacika mata ido tace bawai na ce kar kad'auka ba ni bace sannan kuma ban hanaka d'aukar matakiba idan kagane niceba kawai ina tunatar da kai ne kar kayanke hukunci batare da kayi bincikeba, a kullum addu'a ta Allah yabayyanar da gaskiya bazan ta6ayin bak'in cikiba idan hakan yazama k'arshen tarayyarka da ni, saboda ni nasan gaskiya bata k'arewa saidai k'arya tak'are,

Yarima cike da mamaki yake kallonta koda ya san har cikin ransa ya san maganganun da tafad'a gaskiya ne ammah hakan baisa yanuna a fili ya aminceba, zarah dafe kanta tayi ahankali tace na barka lafiya juyawa tayi tana fara tafiya nan jiri yakwasheta tayi baya zata fad'i.

cikin sauri yarima yatarota tafad'o jikinsa,  ahankali yafurta ya salam, saboda wani irin zafi da yaji jikinta saikace zafin garwashi, rikicewa yayi yama mance da abinda yafaru cike da damuwa yace zarah daman bakida lafiya? Me yake damunki? Lokaci guda yajero mata tambayoyin duk ya rud'e.

Zarah dak'yar tabud'e idonta tare da dafe kanta da yake sara mata, cikin muryar kuka tace kabarni inma mutuwa nayi babu abinda yadameka, wlh abinda akeyi min ya fi wannan ciwo kabarni kawai inmutu kowa yahuta, k'ila idan namutu zaka yarda da magana ta,
Yarima cike da rud'ewa yace kidaina cewa haka zarah, kifad'amin abinda yake damunki,

Zarah turesa tashiga yi cikin kuka tace ni kabarni wajen mamana zanje nasan su zasu fahimceni tunda sunsan abinda zan iya aikatawa da wanda ba zan iyaba.

Yarima rungumeta yayi a jikinsa yace kidaina cewa haka zarah, baisan lokacin da yayi su6ul da baka yace nima na yarda da ke.
Zarah idanuwanta suna lumshe batare da ta bud'eba tace dagaske ka yarda da ni?
Shuru yarima yayi yana mai nazarin maganar sai kuma chan yace eh.
'Dan guntun murmushi tayi sannan ahankali tace nagode.
Chak yarima yad'auketa yad'aurata saman gadon yakwantar da ita, wayarsa yad'auko yakira Dr feedoh (babbar likitace ta 6angare mata da take aiki a hospital d'insa) bayan sun gaisa yace kizo gida kisameni, cikin sauri tace toh ranka yadad'e, kashe wayar yayi tare da kallon zarah da taketa cize le6e tana girgiza kai daga ganin yanayinta kasan tana jin jiki, sannan yace ina zuwa, yana fad'in haka yafita
wajen guards d'insa yaje suna ganinsa duk suka duk'a suka kwashi gaisuwa,
yarima hannu kawai yad'aga musu sannan yakallesu d'aya bayan d'aya..........





_Comment_
     *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_*Wannan page d'in tukuicine agareki mummyna chubad'o muhammad, hak'ik'a kin wuce duk yadda kike tunani a zuciyana saidai ince Allah yabarmu tare mummy😘*_

*PAGE* 4⃣5⃣

Ahankali yake warwarewa har yagama sannan yabud'e yafara karantawa gabansane yafad'i ganin sunansa aka rubuta da larabci, sai wasu rubutu da shi kansa baisan menene aka rubutaba saboda mitsi-mitsine daga chan k'asa kuma sunan zarah yaga anrubuta sannan daga gefe akasa  d'aya ansa _ni zarah zan mallaki yarima_ gabansane yacigaba da fad'uwa cike da mamaki yace zarah ce tasamin laya dan tamallakeni? Me take nufi da hakan? cikin sauri yaje yad'auko na toilet d'in yawarware sunansa da na zarah kawai ne jikin takardar, tsaye yayi cike da mamaki yana k'ara bin takardun da kallo,

Zarah kwance take d'akinta duk kasala ta rufeta tanaso taje part d'in yarima ammah ta kasa saboda batajin dad'in jikinta, daga k'arshe dai daurewa tayi tamik'e tad'auko alkyabbarta tasaka sannan tafito tanufi part d'insa.

Ahankali tabud'e bedroom d'insa tashiga tsaye tagansa rik'e da layar, juyowa yayi yaimata wani irin kallo, cak zarah taja tatsaya cikin ranta tace shikuma wannan mutumin me yake nufi da hakan?
Muryarsa taji ya ce abinda kikayi shirin yi toh bai yuwuba dan haka sai kicanza sabon shiri ammah ni nafi k'arfin duk wani sihiri.

Zarah zuba masa ido tayi tana kallonsa cikin rashin fahimtar abinda yake magana a kai, ahankali tace ban fahimci akan abinda kake nufiba.

Yarima wurga mata harara yayi yace kar kimaidani wanda baisan abinda yakeba ko kin d'auka banga layun da kika ajeminba cikin toilet da k'arshin pillow na ba, zarah zaro ido tayi tace ni kuma?

Mik'amata yarima yayi yace toh ai sai kiduba kigani idan k'arya akayi miki, cikin sauri takar6a tashiga dubawa, tsoro da fargaba duk suka cikata, cikin sauri tad'ago kai takalli yarima da shima yake kallonta, muryarta tana rawa tace wlh ban aikataba bansan wanene yake neman jamin sharri ba, innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, dasauri taje wajen yarima tarik'o hannunsa k'wallah duk ta cika mata ido tace kayarda dani wlh bani bace nakawo maka laya,
Fizge hannunsa yayi cikin d'aga murya yace idan bake bace toh wanene? Kuma sunan wanene a jiki?
Zarah kallonsa take cike da mamaki tace yanzu ka yarda zan iya yi maka asiri? Cike da rashin damuwa yace toh idan ban yardaba me kikeso inyi?
Murmushi Zarah tayi wanda yafi kuka ciwo sannan tace da ace ni mushrikace da ba akanka zan faraba kuma ba zan ta6a amincewa in aurekaba da tun farko zan san yadda zanyi inga ban aurekaba saboda nima inada wanda nake so, kuma da ace ina asiri da tun farko zanyi maka ba sai munkai wannan lokacinba, wlh nagaji da wannan sharrin da ake ja min komawane yaje dan kansa, tak'arashe maganar cikin kuka,

Yarima kallonta yake har takai aya sannan yace idan kin gama zaki iya tafiya dan magangununki bazasu ta6a tasiriba agareni, Zarah d'ago kai tayi takallesa tace bakomai insha Allahu gaskiya zatayi halinta komawanene asirinsa zai tonu, tana fad'in haka tawuce tafita tabar d'akin.

Tafiya take zata koma part d'inta hawaye suna zuba daga idanunta ita kanta batasan inda take jefa k'afartaba, hawaye d'aya na bin d'aya, ahankali take furta ya ubangiji kakawo min mafita a cikin wannan al'amari, ya ubangiji katona asirin duk wani mai nufin sharri agareni, me nayi musu? Meyasa sukeson ganin sun 6atamin rayuwa, wanene yake nufina da sharri haka?
Tuntu6e ne tayi batasaniba nan tatafi zata fad'i, cikin sauri taji an rik'ota tafad'a jikin mutum, d'ago kai tayi cike da mamaki dan ganin kowanene? Ido tazuba ma jakadiya da itama take kallonta, ahankali jakadiya tace ranki yadad'e meyake faruwa dake ne haka?
Zarah runtse idanunta tayi nan wasu sabbin hawayen suka shiga gangarowa, jakadiya cikin sauri tawaiga gaba da bayanta ganin bakowa yasa tarik'e Zarah suka ida isa part d'in Zarah.

Jakadiya kallon kuyangin Zarah tayi tace kubamu waje, cikin sauri duk suka ficce sukabar d'akin.

Zaunar da Zarah tayi saman d'aya daga cikin cushin sannan tazauna k'asa gaban Zarah, kallon Zarah tayi da tajingine kanta a jikin cushin d'in hawaye suna zarra daga idanunta, tace ranki yadad'e meyake faruwa da ke ne?
Zarah ahankali tabud'e idonta takalli jakadiya, nan tayi murmushi wanda yayi kuka ciwo sannan tadafe kanta.

Jakadiya gyara zamanta tayi tace gimbiya kifad'a min matsalarki ni nayi alk'awali zan taimaka miki kid'aukeni a matsayin uwa,
Zarah d'ago kai tayi takalli jakadiya har a lokacin hawaye suna zuba daga idonta cikin muryar kuka tace ya akeso inyi da rayuwata? Narasa wanene yake k'ullamin sharri da angama wanchan sai afad'a ma wannan shin ya akeso inyi? Ni zan iya hak'ura da auran inkoma gidanmu,
Cikin sauri jakadiya tagirgiza kai tace a'a ranki yadad'e kar kice haka dan Allah kifad'amin abinda yake faruwa nayi alk'awali zan taimaka miki.

Zarah kallonta tayi cike da gamsuwa da maganar jakadiya sannan takwashe duk makircin da akeyi mata tafad'a ma jakadiya,

Jakadiya jinjina kai tayi tace wannan ba aikin kowa bane sai na gimbiya sumayya,
Zarah cike da mamaki tace yanzu kina ganin itace zata yi min haka?
Jinjina kai jakadiya tayi tace tabbas itace dan nasan wacece gimbiya sumayya da mahaifiyarta fiye ma da haka zasu iya yi.

Zarah share hawayen fuskarta tayi tace toh wlh zan iya hak'ura da auren inkoma gidanmu.

A'a gimbiya kar kice haka bai dace kikaraya ba, mu munsan halinsu, kuma sumayya da kikaga yarima ya aura toh auren had'ine ba auren soyayya bane sukayi.

hatta shi kansa yarima da kike gani akwai abinda mahaifiyar sumayya take k'ullawa akansa wanda ita kanta sumayya bata saniba.

Zarah ido tazuba mata cike da mamaki.

Jakadiya tacigaba da cewa akwai wani lokaci da dada ta aikeni wajen sultana sadiya, lokacin da nashiga parlour bakowa har na juyo zan baro d'akin najuyo magana k'asa-k'asa a bedroom d'in sultana sadiya tsaye nayi lokacin da najuyo tana cewa so take gimbiya sumayya tahaihu idan yaron yafara wayau tanaso tabi kowace hanya dan ganin ta kawar da yarima inyaso mijinta abashi rik'on k'warya kafin jikan nata yagirma daga baya yazama shine sarkin gari, ta san idan yahau toh sai yadda taso mulkin gidan zai tafi, dan ta tsani mahaifiyar yarima taso ace itace tahaifi d'a namiji Wanda zai gaji garin ba mahaifiyar yarima ba, ina jin haka cikin sauri nafito nabaro part d'in gudun kar taganni dan nasan idan taganni toh bazata ta6a barinaba.

Zarah cike da rud'ewa tace daman haka matarnan take? Toh shi yarima baisan halintaba ya amince ya auri d'iyarta.

Murmushi Jakadiya tayi tace tabbas yarima yasan kad'an daga cikin halayyarta dan tun yana k'arami idan yaje part d'inta wahalar dashi take dan akwai lokacin da tata6a watsa mai ruwan zafi, tagargad'e ni da idan nafad'a ma wani sai tayi sanadiyar barina aiki, kasancewar nikad'aice lokacin da abun yafaru.

Toh ba'a gane taba? Cewar zarah.
Eh toh, yarima yana da wani irin hali wanda ba komai bane yake iya bud'e cikinsa yafad'aba wannan halinsane tun yana k'arami, kuma na tabbata shi kansa yana sane da abubuwan da tayi masa kawai dai ya sharene,
indai wajen makircine toh kala-kala matarnan ta iya dan ina tunanin dasa hannunta sumayya takeyi miki wad'annan abubuwan.

Zarah jingine kanta tayi cike da jin tausayin mijin nata, Jakadiya tace ranki yadad'e kigode ma Allah da basubi ta wata hanyarba dan ganin sun kawar da ke, koda basubin boka ammah sun san makirci kala-kala.

Jinjina kai zarah tayi cike da mamakin halin su sumayya, ahankali tace duk makircinsu basu isa suyi abinda Allah bai nufa ba, kuma ina neman kariya daga ubangijina, saidai bansan yadda zanyi inshawo kan yarima yafahimceniba.

Jakadiya tace kar kice haka ranki yadad'e kuma baidace kiga laifin yarima ba tunda duk baya makircinsu da suke miki baiyi tasiriba a garesa ammah a yanzu kiduba kiga har da sunansa da naki aka had'a kinga ai bakowa bane zai iya k'in yarda, yanzu dai abu d'aya zakiyi shine nake tunani kamar zai taimaka wajen ganin kin ku6utar da kanki, zarah kallon Jakadiya tayi tace wane abune please kifad'a min.

nan Jakadiya tace kice yatambayi guards d'insa sufad'i Wanda yashiga da baya nan tunda ke kince baki shigaba,
Zarah tace anya kina tunanin zai amince?
Eh insha Allahu ai ya aminta da su yasan bazasu ta6a yi masa k'aryaba,

Zarah jinjina kai tayi tace nagode sosai jakadiya, hak'ik'a kin taimakeni a lokacin da nake buk'atar taimako nakekai kukana ga ubangijina,

Jakadiya tace kar kidamu gimbiya har cikin raina nake jinki dan kece kikafi dacewa da yarima ba sumayya ba kuma ina fatan yakasance kece zaki fara aje mana magajin yarima.

Zarah saida gabanta yafad'i dasauri tagirgiza kai tace kar kice haka, sumayya ita tafi dacewa tahaihuwa da yarima.

'Yar dariya jakadiya tayi tace tuni tayi watsi da damanta koda haka mahaifiyarta taci buri itama ammah a yanzu k'addara ta riga fata,

Zarah cike da mamaki take kallonta tace ban fahimci abinda kike nufiba?
Murmushi jakadiya tayi tace kar kidamu dasannu zaki fahimta nan ba da dad'ewaba, jakadiya tana fad'in haka tamik'e tare da d'an rissinawa tace nabarki lafiya ranki yadad'e.

Zarah d'aga kai tayi tace nagode sosai jakadiya saidai ince Allah yabaki ladar abinda kikayi min.

Jakadiya murmushi tayi tace kar kidamu ai yi ma kaine, nidai fatana kirik'e sirrin maganar da nafad'a miki.

Zarah murmushi itama tayi tace insha Allahu babu wanda zai san maganar nan bayan mahaliccinmu sai ni da ke.

Jakadiya tace nagode, nan sukayi sallama tafita, zarah tsaye tayi tana tunani cike da jinjina ma sumayya da mahaifiyarta sannan daga baya tawuce tashige bedroom d'inta takwanta, nan hawaye suka cigaba da fita daga idonta tana tunanin hukuncin da yarima zai yanke mata akan laifin da ba ita ta aikata shiba, fashewa tayi da kuka tace ya ubangiji kakawo min d'auki, kuka tayi sosai saida taji kanta ya fara ciwo sannan tadaina haka taita juyi saman gadon daga k'arshe bacci yayi awon gaba da ita.

Yarima bayan zarah ta fita zama yayi saman gadonsa tare da dafe kansa cike da takaici, mamakin zarah ne yakamasa dan baita6a tunanin haka daga garetaba tun daga yanayin tarbiyarta, ya dad'e zaune yana jinjina lamarin dan abun ya d'aure masa kai sosai dan idan ya ce ba ita bace toh wanene zaiyi hakan?, tsaki yaja cike da takaici sannan yakwanta abu guda yatsaya masa a rai kalmar da tafurta ta nima ina da wanda nakeso, haka kalmar yaita jinta a kunnensa tana masa yawo har daga k'arshe bacci yad'aukesa..

A chan 6angaren sumayya kiran sultana sadiya tayi tana yin picking bata bari tayi ko sallama ba cikin jin dad'i tace ummah na aiwatar da komai kuma ina tunanin nasara a cikin aikin namu, daga chan 6angaren sultana sadiya dariya tayi tace gaskiya naji dad'i daughter ai ina fad'a miki ta ruwan sanyi zatabar gidannan dan makirci kala-kala babu Wanda ban iyaba idan akayi wani baiyiba sai acanza wata hanyar, cikin jin dad'i sumayya tace saisa nake k'ara sonki ummana dan duk abinda nakeso kema kinasonsa na rabbata yanzu yarima zai zama nawa ni kad'ai.
Murmushi sultana sadiya tayi sannan tace kar kidamu d'iyata farin cikinki shine nawa, saisa nake burin kihaifo min jika wanda zai gaji masarautar nan ammah kinkasa fahimtar inda nadosa, Indai kinsan kina yin planning toh kitaimaki kanki kidaina tun kan waccan munafukar tafara haihuwa,
Gaban sumayya saida yafad'i dan bata ta6a yin tunanin hakaba, ahankali tace hakane kuma ummah insha Allahu bama zata haihuba zata bar gidan.
Sultana sadiya tace na dai fad'a miki kirufa ma kanki asiri kidaina.
Cikin shagwa6a sumayya tace toh ummah na ji.
Uhm Allah yasa dagaske, cewar sultana sadiya.
Ameen ummana.
Yauwa toh yanzu kikwanta kiyi bacci dare keyi.
Toh ummah ko mi kenan sai kinjini, nan sukayi sallama suka kashe wayoyin.
Sumayya fad'awa tayi saman gadonta cikin murna tace yes nasan zuwa gobe waccan munafukar zata koma kongon gidansu, ahaka tayi bacci cike da farin ciki.


Cikin dare zazza6i da ciwon kai suka tashi zarah daga baccin da take nan taita juyi saman gadon daga k'arshe k'asa tasafka takwanta, ciwon cinta yake  babu wanda zata iya kira dan ko hannunta kasa d'agawa tayi daga k'arshe, tana nan tana juyi ahaka aka kira sallar asuba.

Har aka gama sallah akan kunnenta ammah takasa tashi dakyar tasamu tamik'e tana dafa bango har tashiga toilet, saida tahad'a ruwan d'umi tayi wanka sannan tad'auro alwallah daga zaune tasamu tayi sallah sannan talalubo paracetamol tasha, nan saman darduman tayi kwanciyarta har saida gari yafara yin haske sannan tamik'e tajanyo alkyabbarta tasaka, cikin rashin k'warin jiki tafito duk wanda yaganta ya san batada lafiya, ko da kuyanginta suka gaisheta hannu kawai tad'aga musu taku take dak'yar tana dafa bango tana tsayawa tahuta ahaka ta isa part d'in yarima.

Tana murd'a k'ofar bedroom d'in yarima tsaye tayi tare da jingine kanta jikin k'ofar tana maida numfashi,

Yarima da daidai lokacin yasafka daga saman gadonsa tsaye yayi yana k'are mata kallo ko da cikin fushi yake da ita ammah hakan bai hana yaji wani iriba da yaganta cikin yanayin.

Zarah ahankali tatako tamatso kusa da shi, yarima d'aure fuska yayi yace meyakawoki wajena? Ko wani abun kikazo kik'ara shirya min?

murmushin k'arfin hali tayi sannan ahankali tace nasan kana jin haushina akan abinda yafaru, shuru tayi nad'an lokaci sannan tace ammah dan Allah ina neman alfarma guda,
saida takalli cikin idonsa sannan tacize le6e cike da dauriya tace kataimaka kayi bincike kafin kazartas da hukunci, katambayi guards d'inka sufad'a maka wanda yashigo part d'inka da bakanan dan ni wlh duk jiya ban shigoba sai dare, k'wallah ce tacika mata ido tace bawai na ce kar kad'auka ba ni bace sannan kuma ban hanaka d'aukar matakiba idan kagane niceba kawai ina tunatar da kai ne kar kayanke hukunci batare da kayi bincikeba, a kullum addu'a ta Allah yabayyanar da gaskiya bazan ta6ayin bak'in cikiba idan hakan yazama k'arshen tarayyarka da ni, saboda ni nasan gaskiya bata k'arewa saidai k'arya tak'are,

Yarima cike da mamaki yake kallonta koda ya san har cikin ransa ya san maganganun da tafad'a gaskiya ne ammah hakan baisa yanuna a fili ya aminceba, zarah dafe kanta tayi ahankali tace na barka lafiya juyawa tayi tana fara tafiya nan jiri yakwasheta tayi baya zata fad'i.

cikin sauri yarima yatarota tafad'o jikinsa,  ahankali yafurta ya salam, saboda wani irin zafi da yaji jikinta saikace zafin garwashi, rikicewa yayi yama mance da abinda yafaru cike da damuwa yace zarah daman bakida lafiya? Me yake damunki? Lokaci guda yajero mata tambayoyin duk ya rud'e.

Zarah dak'yar tabud'e idonta tare da dafe kanta da yake sara mata, cikin muryar kuka tace kabarni inma mutuwa nayi babu abinda yadameka, wlh abinda akeyi min ya fi wannan ciwo kabarni kawai inmutu kowa yahuta, k'ila idan namutu zaka yarda da magana ta,
Yarima cike da rud'ewa yace kidaina cewa haka zarah, kifad'amin abinda yake damunki,

Zarah turesa tashiga yi cikin kuka tace ni kabarni wajen mamana zanje nasan su zasu fahimceni tunda sunsan abinda zan iya aikatawa da wanda ba zan iyaba.

Yarima rungumeta yayi a jikinsa yace kidaina cewa haka zarah, baisan lokacin da yayi su6ul da baka yace nima na yarda da ke.
Zarah idanuwanta suna lumshe batare da ta bud'eba tace dagaske ka yarda da ni?
Shuru yarima yayi yana mai nazarin maganar sai kuma chan yace eh.
'Dan guntun murmushi tayi sannan ahankali tace nagode.
Chak yarima yad'auketa yad'aurata saman gadon yakwantar da ita, wayarsa yad'auko yakira Dr feedoh (babbar likitace ta 6angare mata da take aiki a hospital d'insa) bayan sun gaisa yace kizo gida kisameni, cikin sauri tace toh ranka yadad'e, kashe wayar yayi tare da kallon zarah da taketa cize le6e tana girgiza kai daga ganin yanayinta kasan tana jin jiki, sannan yace ina zuwa, yana fad'in haka yafita
wajen guards d'insa yaje suna ganinsa duk suka duk'a suka kwashi gaisuwa,
yarima hannu kawai yad'aga musu sannan yakallesu d'aya bayan d'aya..........





_Comment_
     *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Wannan page d'in mallakin kine maman fodio hakik'a ke masoyiyace ta gaskiya saidai ince Allah yabar k'auna_

*PAGE* 4⃣6⃣

Kallonsu yayi d'aya bayan d'aya sannan yace jiya bayan na fita zarah ta shigo part d'ina?

Gaba d'aya shuru sukayi suna tunani sai chan d'aya daga cikinsu yace gaskiya bata shigoba,

Yarima ido yazuba mai sannan chan yace toh ko akwai wanda yashigo?
Nan ma shuru sukayi, Yarima yace kuyi tunani dai.

Chan sai suka kalli juna sai suka eh toh ranka yadad'e gimbiya sumayya ta shigo bayan magrib, gaskiya inba itaba babu wanda yashigo.

Yarima jinjina kai yayi yace kun tabbata? Gabad'ayansu sukace eh ranka yadad'e.
Yarima baice komai ba yawuce yashige,
Koda yashiga parlour saman kujera yazauna tare da dafe kansa mamakin sumayya duk yacikasa ahankali yace idan na fahimta toh duk wani abu da yake faruwa toh dasa hannun sumayya a ciki, toh meyasa sumayya take yin haka? Meyasa takeso taga ta yi silar mutuwar auren zarah? Anya ba da sa hannunta aka zuba poison a abincinba? Wani huci yafitar mai zafi sannan yace koma me kenan da sannu gaskiya zatayi halinta ba zan zargetaba, yana nan zaune a wajen wayarsa tafara ringing ganin mai kiransa yasa yai picking tare da cewa Doctor kin iso?
Daga chan 6angaren tace eh ranka yadad'e gani a waje dogarawa sun hanani shigowa.
Yarima yace ohk, ba d'aya daga cikinsu wayar.
Toh ranka yadad'e, cewar doctor feedoh, nan tamik'a ma dogari d'aya waya, yana d'auka Yarima yace kubarta tashigo.
Jin muryar Yarima yasa yarissina kamar yana gabansa sannan cikin girmamawa yace toh ranka yadad'e angama.
Yarima kashe wayarsa yayi tare da mik'ewa yashiga bedroom d'in tsaye yayi bakin gadon yana k'are ma zarah kallo da gabad'aya ta galabaita, ahankali yazauna gefenta tare da dafa kanta yace ya jikin?
Gyad'amai kai kawai tayi,

Mik'ewa yayi yafito waje yasa d'aya daga cikin guards d'insa yaje yazo mai da doctor feedoh, cikin sauri yatafi.

Nan Yarima yadawo parlour yazauna yana jiransu, bayan minti biyar sai ga guard d'in tare da doctor feedoh sun shigo, duk'awa guards d'in yayi yace gata ranka yadad'e,
'Daga masa hannu yarima yayi,
Fuskarsa d'auke da murmushi yace u ar wlcm Dr.
Dr feedoh saida tazauna sannan tace thanks Dr, ya mai jikin.
Alhmdllh yace tare da mik'ewa yace bismillah mushiga daga ciki kidubata,
Ohk sir, cewar dr feedoh nan yarima yawuce gaba tana biye da shi har cikin bedroom d'insa, daga gefen da zarah take kwance yazauna, kallonta yayi da tazuba ma Dr feedoh ido, ahankali yace ga doctor nan zata dubaki.
Fuskar Dr feedoh d'auke da murmushi tace sannu gimbiya, ya k'arfin jikin naki?
Zarah ma d'an guntun murmushi tayi cikin k'arfin hali tace Alhmdllh.
Dr matsowa tayi tana fiddo kayan aikinta daga cikin jakka tace ranki yadad'e ko zaki iya fad'amin abinda yake damunki?
Zarah kallon yarima tayi da shima yatsareta da ido, shafa kanta yayi sannan yace kidaure kiyi mata bayani kinji? d'aga mai kai tayi alamun toh, yana fad'in haka yamik'e yace doctor bari inbaku waje.
Doctor feedoh murmushi tayi cikin girmamawa tace a'a ranka yadad'e kayi zamanka ka ga inda na6ace sai kataimaka min.
Murmushi yayi yace kar kidamu ai nasan aikinki, bakida matsala, yana fad'in haka yafita yakoma parlour

Yana fita doctor feedoh gefen gadon tazauna, fuskarta d'auke da murmushi tace ranki yadad'e kamar da me dame kike ji?
Ahankali zarah tabud'e baki tace zazza6i da ciwon kai.
Dr rubutawa tayi tace bayansu babu abinda kuma kikeji?
Zarah shuru tayi kamar tana tunani sai chan tace sai kuma yawan kasala da bacci, jinjina kai Dr tayi tace bayansu bakya tashin zuciya?
Girgiza kai zarah tayi.
Nan Dr tarubuta sannan tace toh kina cin abinci?
Ba sosai ba, cewar zarah.
Dr idon zarah d'aya taduba sannan tad'auko wata roba tamik'a mata tace ko zaki taimaka kiyo fitsari nan ciki, saboda akwai awon da nakeso inje yanzu inyo.

Zarah kar6a tayi tamik'e dak'yar, ahankali take tafiya har taje toilet d'in yarima, nan tayo fitsarin tafito tamik'a ma doctor, kar6a Dr tayi ta aje sannan tace ranki yadad'e kiyi hak'uri munason mud'an d'ibi jininki kad'an.

Zarah bata musaba tamik'a hannunta tare da runtse idonta nan Dr feedoh tad'ibi jinin sannan tamik'e tace bari inje inhad'o miki result d'in.
Gyad'a kai kawai zarah tayi.
Dr ko da tafito a parlour tasamu yarima kallonsa tayi fuskarta d'auke da murmushi tace ranka yadad'e munyi duk abinda yadace yanzu zanje inyi mata test zuwa anjima kad'an insha Allahu zan dawo da result,

Jinjina kai yarima yayi sannan yace toh bakomai Dr Allah yamaidoki lafiya.
Ameen tace sannan tawuce tafita.

Bayan ta fita yarima mik'ewa yayi yashiga bedroom d'in, kallon zarah yayi da take lumshe ido alamun bacci zatayi hannunta yaduba sannan yace baby bari ind'an sa miki drip,
Zarah batace komai ba, kalman babyn da yakirata da shi takemata yawo a cikin kunnenta dan wannan ne karo nafarko da yakirata da hakan,
Shima kansa yarima saida yaji wani iri ammah yashare nan yahad'a drip d'in yasa mata, sannan yawuce yashiga bathroom dan yayi wanka.

Lokacin da yafito zarah har tayi bacci dan haka yashirya sannan yakomo gefenta yazauna yana ganin yanayin yadda ruwan yake shiga jikinta.

Bayan awa d'aya sai ga Dr feedoh tadawo, nan yarima yabada izini abarta tashigo bayan ta shigo fuskarta d'auke da murmushi tace ranka yadad'e albishir nazo maka da shi kuma ina fatan samun goro daga wajenka.
Kallonta yarima yayi cikin rashin fahimta sannan yace albishir kuma?
Har a Lokacin fuskarta d'auke da fara'a tace eh ranka yadad'e.
Yarima yace ohk, ina jinki.
Dr feedoh kallon zarah tayi da tad'an bud'e idonta alamun ta farka tasakar mata murmushi sannan tace madam tana d'auke da juna biyu.
Yarima kalmarce yaji tana yawo acikin kunnensakamar a mafarki, Kallonta yake yace me kikace?
Murmushi Dr tayi sannan tace tana d'auke da ciki na tsawon wata ukku da rabi (14wks) kenan, nan tamik'a masa result d'in tare da takardar magani.
Yarima kar6a yayi ya duba sannan ya jingine kansa a jikin gadon tare da lumshe idonsa yana jin wani irin nishad'i a cikin ransa ahankali yace Alhmdllh, Allah nagode ma, nan yabud'e idonsa yasafkesu akan zarah da take kallonsa ammah bata gane abinda ake nufiba.

Kallon Dr yayi fuskarsa d'auke da murmushi yace nagode doctor tabbas kinmin babban albishir kuma dole inbada tuk'uici, ammah abun mamaki ya akayi har yakai tsawon wannan lokacin ammah ban ganeba?

Murmushi Dr tayi sannan tace kuma doctor kana saurin fahimtar na wasu matan ammah kai naka sai gashi cikin ikon Allah, Allah ya 6oye abunsa har tsawon sati goma sha hud'u (14 wks) sannan yabayyana kuma har da k'arin ba wani laulayi takeyi ba.

Jinjina kai yarima yayi tare da kallon zarah da idanuwanta suke rufe yace hakane, Allah shi yake ajiyarsa kuma sai ya so yake bayyanata, yana fad'in haka yamik'e yaje yabud'e wardrobe d'insa yad'auko cheque yacike sannan yazo yaba Dr feedoh yace ga goron albishir d'inki.
Dr feedoh d'an rissinawa tayi takar6a cikin jin dad'i tace nagode sosai Dr, Allah yasafketa lafiya, nan tacigaba da yin addu'a.

Fuskar yarima d'auke da murmushi yace Ameen mungode.
Dr feedoh jakkarta tad'auka sannan takalli zarah tace toh ranki yadad'e Allah yasafke mana ke lafiya, sai anjima.

Yarima ne kawai yace Ameen tare da mik'ewa yarakata har bakin k'ofa nan tak'ara yi masa godia sannan tatafi.

Yarima dawowa yayi bedroom d'in inda yatarar da zarah har a lokacin idanuwanta a lumshe suke, tunda taji an ambaci ciki gabanta yashiga dukan ukku-ukku dan ita ta ma rasa shin murna take ko bak'in ciki, a chan 6angare guda kuma murna take, bata ankaraba sai jin Yarima tayi ya d'age mata riga yana shafar cikinta, sharesa tayi tak'i bud'e idon nata, ya dad'e ahaka sannan yamik'e yace kitashi kiyi breakfast,
Zarah shuru tayi ta k'yalesa da mamakinsa sai ganin hawaye yayi sun gangaro daga idonta, da mamaki yake kallonta cikin ransa yace kar dai ace cikin ne bata so? Haushi ne yakamashi dan haka yashareta yawuce yafita daga d'akin.

Zarah tana jin fitarsa tabud'e idonta tare da bin k'ofar da kallo cike da tausayin kanta tace taya zan haihu da mutumin da baya sona, chan kuma gefe d'aya na zuciyanta tace ammah kuma yanason abinda yake cikin cikinki, hannu takai tashafi cikin cike da mamaki tace taya ciki yazauna min tsawon wannan watannin ban saniba? Toh wai ma duka yaushe akayi aurenmu?
Tunani tashiga yi sai kuma chan tace idan ban mantaba wata ukku da sati ukku kenan ya kama sati (15) kenan, gabantane yafad'i tace na shiga ukku yanzu cikin satina na biyu ciki yashigeni? K'wallah ce tacigaba da fita daga idonta, batasan lokacin da Yarima yashigoba sai ji tayi ya ce kitashi kiyi breakfast.

Zarah kallon yadda yahad'e rai tayi sannan tamik'e dak'yar, Yarima yataimaka mata yasa mata pillow a bayanta ta jingine sannan yahad'a mata tea mai kauri yamik'a mata, kar6a zarah tayi tafara kur6a jikinta yana rawa saboda wata irin yunwa da takeji.

saida tasha kusan rabin cup d'in sannan tamik'a ma Yarima ya amsa ya aje sannan yazubo mata chips, cikin sauri zarah tajanye kanta ahankali tace na k'oshi.

Yarima ido yazuba mata sannan yace ammah yanzu ba ke kad'ai bace kuma bakiga yadda duk kika rameba ya kamata kidinga daurewa kina d'an cin abinci.

Zarah rik'o hannunsa tayi tare da marairaicewa tace dan Allah kar kafad'a ma kowa ina da ciki.

kallonta yayi cike da mamaki yace saboda mi?
Rau-rau tayi da ido sannan tace kawai hakanan.
Yarima har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa nan yakwashi kayan breakfast d'in yafita da su parlour, zarah da kallo tarakasa har yaficce sannan takoma takwanta tare da maida idonta talumshe tana tunanin wai itace da ciki, hannunta tad'aura saman cikin, tana nan kwance haka sai ga Yarima ya shigo hannunsa d'auke da ledar drugs da injection da yabayar asiyo.

Ajewa yayi saman bedside tare da d'auko ruwa sannan yace kitashi kisha maganin,
Marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace idan nasha amai zanyi.

Yarima zama yayi gefenta tare rik'o hannunta yace kar kidamu bazakiyi amai ba,
Toh kawai tace, nan yataimaka mata tatashi zaune sannan yabata maganin saida ta runtse idonta sannan takar6a takai baki cikin sauri takora da ruwa, sannan tabud'e ido,
Nan yafara k'ok'arin had'a injection, kallonsa take a tsorace ahankali tace kuma harda ita za'ayi min?
Shuru Yarima yayi saida yagama had'awa sannan yakalleta har da d'an guntun k'wallarta taso tabashi dariya ammah yadake yace kigyara sai inyi miki.

Zarah komawa tayi takwanta  tana kuka ciki-ciki, kallonta yayi yace kar kimotsa fa.
Batace komai ba jin zai shigar da allurar yasa tarik'esa gam, tare da runtse idonta.

Murmushi Yarima yayi sannan yatsira mata ahankali, bata ma san lokacin da yazare inj d'inba dan kwata-kwata bataji zafintaba, sai ji tayi yana cewa toh shikenan angama, zarah k'in sakinsa tayi saidai ji yayi tana fitar da sautin kuka k'asa-k'asa.
Ahankali yajanye daga rik'on da tayi mai tare da zuba mata ido sai chan yace kukan fa?
Turo baki tayi cikin shagwa6a tace ba kaine ba kayimin injection ba.
Murmushi yayi tare da jan d'an k'aramin bakinta sannan yace toh ai banyi miki da zafiba ko ak'ara wata?
Cikin sauri tagirgiza kai tare da cewa a'a.
Ido yazuba mata itama shi take kallo, ahankali tace kaida ma kake fushi da ni,
Murmushi yayi yace ni ba fushi nake da keba, kidaina maganar ta wuce kinji ko?
Murmushi zarah tayi tare da d'aga mai kai, hannunsa tarik'o tad'aura saman cikinta tace kana son babynmu?
Yarima ido yazuba mata sai chan yace ke kina sonsa?
Cikin sauri tace eh,
Mik'ewa yayi yace bari inje inhad'a miki ruwa kid'an gasa jikinki.
Murmushi kawai zarah tayi tare da komawa takwanta.

Toilet d'insa yashiga yahad'a mata ruwan wanka, bayan ya had'a fitowa yayi d'auke da towel yamik'a mata, kar6a tayi tare da mik'ewa dak'yar tacire rigar jikinta sannan tad'aura, yarima kamata yayi yarakata har toilet sannan yajanyo mata k'ofar.

Kwance tayi cikin ruwan tana jin wani irin nishad'i a cikin ranta, tunowa tayi da sumayya saida gabanta yafad'i, tsintar kanta tayi cikin zuciyanta tana addu'an neman kariya daga sharrinta.

Nan tafara wanka duk jikinta ya yi sanyi ahaka tagama sannan tafito, lokacin yarima baya d'akin, gaban dressing mirror tazauna tashafa mai sannan tamik'e taje tagyara gadon, bayan ta gama parlour tafito tasami yarima da yake zaune yana jin wani irin dad'i a cikin ransa,  kallonsa tayi da shima yakalleta, turo baki tayi sannan tace ni banda kayan da zansa.

Janye idonsa yarima yayi sannan yamik'e yafita yaje ya aiki d'aya daga cikin guards d'insa part d'in zarah dan yakar6o mata kaya.

Lokacin da yadawo zarah tana bedroom nan yarima yakar6a yaje yakaimata sannan yadawo parlour yayi Kwanciyarsa saman 3 seater.

Bayan ta gama kwanciyarta tayi saman gadonsa nan bacci yayi awon gaba da ita,

Saida aka kira azuhur sannan yarima yamik'e yashiga  bedroom, kallon zarah yayi da take baccinta hankali kwance, takowa yayi yazo yazauna gefenta tare da yaye blanket d'in da tayi rufa da shi gani yayi tana zufa alamun zazza6in ya safka, hannu yakai yad'age mata riga tare da shafa cikin nata, ido yatsura ma fuskarta duk tayi fayau da ita, murmushi yayi sannan yamik'e yaje yacire kayansa yashiga bathroom,

Bayan ya fito wanka shiryawa yayi sannan yaficce yatafi masallaci, rufe k'ofan da yayine yasa zarah tafarka, ji tayi zazza6in ya safka, ahankali tasafka daga saman gadon saida tagyara mai sannan tafito takoma part d'inta.

Koda tashiga saida tak'ara wanka sannan tad'auro alwallah.

Bayan ta yi sallah sawa tayi akayi mata faten tsaki taci saboda shi taji tana buk'ata.
tana cikin ci saiga yarima ya shigo, ido yazuba mata tare da yamitsa fuska,
Ganin haka yasa zarah tayi murmushi tace bismillah.

menene wannan? Cewar yarima.
Faten tsakine kazo kad'and'ana kaji akwai dad'i.
no, aci lafiya, ya jikin naki?
Dasauki, cewar zarah.
Ohk, Allah yak'ara sauk'i, idan kin gama kisha drugs d'inki.
Ahankali tace toh,
Juyawa yayi yafita yabar d'akin nan zarah tacigaba da cin faten.

A chan 6angaren gimbiya sumayya tun tana sa ido dan taga yarima ya kori  zarah ammah shuru a k'arshema a gaban idonta yaje d'akin zarah sannan agaban idonta yafito.
Ahankali tafurta da alama aiki ya 6aci, takaici ne yacikata batasan lokacin da tace anya waccan munafukar bata asirce yarima ba? Tsaki taja cikin jin haushi tace akwai alamar tambaya a cikin  lamarin nan, dan babu yadda za'ayi ace kullum itace da nasara, wlh duk sihirinta sai nayi silar barinta gidan nan


A haka zarah tacigaba da kula da cikinta, yanzu ta samu sauk'in zazza6in da takeyi saidai yawan amai idan taji k'amshin abinda bata so, abinci ko sai ta za6i irin wanda takejin zata iya ci, ta d'an rame ammah ta k'ara haske da kyau fatar jikinta ta k'ara laushi.

A 6angaren yarima yana zuwa yaduba lafiyarta, sannan yana kiranta a waya koda ace bai jeba, itama tana k'ok'arin ganin ta je part d'insa koda sau d'ayane a cikin kwana biyun, har lokacin ba wanda tabari yagane tana da ciki.

*BAYAN SATI BIYU*

A ranar da cikinta yacika wata hud'u, bayan sallar la'asar ji tayi kwanciyar ta isheta, mik'ewa tayi tanufi part d'in yarima lokacin da tashiga a parlour tasamesa yana sa agogo a hannunsa da alama fita zaiyi. kallonta yayi ganin ta zuba mai ido yace ya dai?
Murmushi zarah tayi tare da marairaicewa tace dan Allah inaso inje ingaishe da su dada.
Keda bakida lafiya kuma zaki fita? Cewar yarima.
Zarah shuru tayi sai chan tace na fa samu sauk'i kuma ni zaman ne ya isheni saisa nakeson ind'an mik'e k'afar.
'Daukan hularsa yayi yasaka sannan yace ohk, muje nima yanzu fada zanje.
Cikin jin dad'i zarah tafad'a jikinsa tare da cewa nagode,
yarima janyeta yayi daga jikinta tare da kallon cikinta yace kar kiji ma baby ciwo.

Murmushi zarah tayi tare da jawo hannunsa tad'aura saman cikinta tace kar kadamu babynka yana lafiya,
Janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace muje memartaba yana jirana, zarah wucewa tayi gaba yarima yabi bayanta suna fitowa a jere suke tafiya, saida suka zo wajen turakar dada sannan  zarah tashiga yarima yawuce fada.

koda tashiga a parlour ta tarar da dada da kuyanginta ana mata tausa a k'afarta, nan kuyangin dada suka dinga duk'awa suna gaisheta, zarah tadinga amsa musu cikin sakin fuska sannan tasamu waje a k'asa saman carpet tazauna gefen dada da take saman cushin, fuskar dada d'auke da murmushi tace a'ah yau amarya ce dakanta?

Murmushi zarah tayi tare da duk'ar da kai cikin girmamawa tagaishe da dada.
dada amsa mata tayi cikin sakin fuska tare da tambayarta ya suke.

Alhmdllh duk muna lafiya, cewar zarah cike day kunya.
Ina wannan miskilin mijin naki? Kwana biyu ban gansaba, ko kuma kun min k'wace yanzu ku kad'ai yasani, dada tafad'i maganar cikin tsokana.

Murmushi zarah tayi sannan tace taya zai mance da ke uwar gida? Ai mu bamu isa mushiga tsakaninku ba, aikine kawai ya6oyesa.
Gidanku ja'irar yarinya kawai, ammah shi aikin bai 6oye muku shi ba sai ni dan rashin adalci.

Dariya zarah tayi sannan tace ranki yadad'e taya zai mance da mu sabon jini?.

Knocking d'in k'ofan da akayine yasa dada tabada izini a shigo, d'aya daga cikin kuyangartace d'auke da wani tray, nan tazube takwashi gaisuwa wajensu sannan tacema dada ranki yadad'e gashi angama.
Murmushi dada tayi tace toh mik'omin shi nan itama kishiyata taci, cikin sauri kuyangar takai gaban dada ta aje.
dada kallon zarah tayi da take wasa da yatsun hannunta tace ga fa dambun kifi kici dada tafad'i haka tare da bud'e murfin da aka rufe shi da shi.
zarah k'amshin yadaki hancinta daurewa taso tayi nan zuciyanta yafara tashi, wani irin tuk'a taji yana taso mata cikin sauri tamik'e dagudu tanufi k'ofa, dada cike da mamaki tace lafiya me yake faruwa?
Batama san dada tanayi ba kafin tafita daga k'ofan sai aman yakubce mata nan tafara kwararashi..




_Comment_
      *nd*
_Share_



_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Jinjinar bangirma agareki mummyna chubad'o muhammad, nagode sosai da dedicated d'in book da nasamu saidai ince Allah yabarmu tare 4ever😘_

*PAGE* 4⃣7⃣

Dada da take zaune ido tazuba mata tana kallon ikon Allah ganin tana ta aman kamar zata amayen 'yancikinta yasa tafara yi mata sannu nan tasa kuyangarta d'aya tad'auke dambun kifin daga wajen.

Bayan zarah ta gama aman a galabaice alkyabbarta kawai tacire saboda ita kad'ai ta6aci.
dada kuyangi tasa sugyara wajen nan tacigaba da jera ma zarah sannu sannan tace tashiga ciki tagyara jikinta,

A kunyace tace toh sannan tawuce toilet da yake cikin bedroom d'in dada batare da ta kalli dada ba,

Dada ido tazuba mata tana kallonta har tashige sannan tayi murmushin jin dad'i tace Alhmdllh da alama mun samu rabo.

Zarah jiki ba k'wari tahad'a ruwan d'umi tayi wanka bayan ta fito kayan jikinta tamaida tunda su basu 6aciba, zaune tayi takasa fitowa saboda wata irin kunyar dada da takeji na amai da tayi mata a parlour.

Ta dad'e a zaune sannan daga baya tamik'e lokacin da tafito parlour da mamakinta taga angyara wajen tes d'akin sai k'amshin turaren wuta yake, kallonta dada tayi har tazauna sannan tace sannu 'yar nan ai da kin fad'i bakison k'arnin kifin da ban bud'eba, kuma bakida lafiya baku fad'amin ba ai da nazo na dubaki, kokuma wannan miskilin mijin naki taya zai fad'a, abinda ma yashafesa bai fad'aba barema ayi tunanin fad'an na wani.

K'ara duk'ar da kanta tayi k'asa cike da jin kunya.

Ganin haka yasa dada tace yanzu me kikeson ci? Naga kin amaye duk abinda kikaci.

Cikin jin kunya tace na k'oshi.

A'a wane irin kin k'oshi keda ba komai cikin cikinki, k'walah ma kuyangarta kira dada tayi tace aje akawo ma zarah tuwo, cikin sauri kunyarta tace angama ranki yadad'e sannan tafita tabar d'akin.

Dada tace ai nasan shi tuwo zaki so shi, murmushi kawai zarah tayi.

Bayan 'yan mintuna sai ga kuyangar nan ta shigo d'auke da kular tuwo, wata kuma tana rik'e da na miya da plate nan suka aje gaban zarah.

Dada tace suzuba mata taci, nan suka zuba sannan suka bud'e miya kala biyu ce sukace ranki yadad'e wace za'a zuba miki?

Zarah kallon miyan tayi ganin miyan ku6ewa d'anya da ta ganye ce yasa tace azuba mata ta ku6ewa nan suka zuba mata sukace ranki yadad'e man shanu fa?
Cikin sauri tagirgiza kai tace kar kuzuba min.
Cikin sauri sukace angama ranki yadad'e sannan suka tashi suka fita daga d'akin.

Dada kallon zarah tayi fuskarta d'auke da murmushi tace kici man.

Murmushi zarah tayi sannan tafara d'iba taci, ta ji dad'in miyan sosai ga tuwon mai laushi irin mai wucewa silif wanda take so nan tacigaba da ci ahankali cike da jin nauyin Dada.

Ganin haka yasa Dada ta tattara hankalinta ga news d'in datake kallo dan zarah tasamu taci sosai.

Haka zarah tad'anci sannan tature plate d'in, kallonta dada tayi tace ba dai har kin k'oshiba?

Zarah ahankali tace eh dada na k'oshi.
Kidaure kid'an k'ara ko kad'anne, cewar dada.
Zarah cikin jin kunya tace na k'oshi.

Dada tace toh shikenan, nan tamaida hankalinta ga TV.

Zarah samu tayi tamik'e dan tawanko hannu.

Da kallo dada tabita cike da farin ciki dan ko ba'a fad'a mataba yanayin zarah da tagani yasa ta gane cikine gareta, ahankali tace Allah sarki  sumayya naso inga jininki ammah da rabon na zarah zan fara gani....tana chan tana tunani batasan lokacin da zarah tadawo ba sai da tafara tattara kwanukan sannan hankalin dada yakai wajen, zaro ido dada tayi da cewa miye haka zakiyi?
Zarah batare da ta kalli dadaba tace ranki yadad'e zan d'an rage kayanne.

Dada tace a'a aje bari ma'aikatan suzo sukwashe keda bakya jin dad'in jikinki, kawai kizauna kihuta.

Dada ai zan iya, cewar zarah.

A'a kibari suzo sukwashe.

Zarah ajewa tayi sannan takoma tazauna,
Dada tace da kin shiga ciki kin d'an kwanta kihuta.

Murmushi Zarah tayi sannan tace dada ai yanzu ma nakeso inwuce gida.

Jinjina kai dada tayi tace kar kikwanta nan musaceki ko?
Yanayin yadda dada tayi maganar saida yaba Zarah dariya tace a'a dada kawai dai akwai abinda zanje inyine.

Cikin gamsuwa da maganar dada tace toh ai shikenan hakan ma mungode Allah yabada ladan zumunci, Allah yayi muku Albarka.

Ameen ranki yadad'e, nan Zarah tayi ma dada sallama tafita.

Dada binta tayi da kallo cike da sha'awa tace Allah sarki sumayya kema Allah yasa ina da rabon ganin naki d'an,
Ita kanta dada tana mamakin yadda cikin jikokinta ta fi son sumayya, hakan ya samo asaline ta dalilin duk cikinsu ita sumayya tun tana k'arama daman itace ta wajen dada inbata wajen ummanta to tana wajen dada, dan a k'arshema dada ce tayi yayenta.


Zarah tana cikin tafiya har zata shiga 6angarensu sai ga sumayya ta fito, saida gaban Zarah yafad'i dan rabon da taga sumayya Ita kanta ta mance dan zata iya cewa tayi kusan 2 weeks.

Tsaya sumayya tayi tana kallon zarah cike da mamaki ganin yadda tacanza tak'ara fresh da kyau, chan sai taja tsaki sannan cikin fad'a tace ke dabbar ina ce kina ganin mutane zasu wuce ammah kikasa basu hanya suwuce.

Zarah murmushi tayi cikin rashin damuwa tare da dakewa tace kar kidamu ke ai naga ko cikin dangin namu na dabbobi kamar makauniyace tunda duk fad'in hanyarnan kirasa ta inda zakibi sai ta wajena.

Cike da mamaki sumayya takalli Zarah dan bata d'auka zata iya yada mata magana irin hakaba, ran sumayya in yayi dubu toh ya 6aci cikin d'aga murya tace eh dole kice haka dan a yanzu kinsha jan miya kin waye kina gani kamar daidai kike da ni, toh wlh bari kiji ni nan da kike gani bani ta6uwa kuma duk ubanda yace zai ta6ani toh aikam zai ta6o ma kansa masifa da bala'i ke sai kinyi kuskuren abinda kika aikata agareni.

Zarah dafe kanta tayi cikin kwantar da murya tace please malama kiban waje inwuce idan ke kinsaba hargagi toh ni ban sababa dan har kin fara haddasa min ciwon kai.

Sumayya a harzuk'e tace ke ko ubanki bai isa yafad'amin maganaba bare ke jakkah,

Zarah murmushin takaici tayi sannan tace Allah sarki kar kidamu nasan jahilcine yayi miki yawa ammah dan Allah ya kamata kikoma islamiyya gimbiya, tana fad'in haka tacanza hanya tawuce tabar sumayya tsaye tana ta balbalin bala'i.

Sumayya cikin 6acin rai tawuce tanufi turakar iyayenta, a parlour ta tarar da sultan Abbas da mahaifiyarta, ganin Abbanta yasa tad'an saki fuska gefensa tazauna cikin sakin fuska tagaishesa.
Murmushi sultan Abbas yayi sannan ya amsa mata tare da tambayarta mijinta.
Sumayya cikin shagwa6a tace Abbah yana lafiya.
Toh ya 'yar uwartaki dafatan kuna zaman lafiya?
Sumayya ji tayi kamar ya da6a mata wuk'a a mak'ogwaro jin ya kira wadda tafi tsana a rayuwarta a matsayin 'yar uwarta, murmushin yak'e tayi sannan tace abbah tana nan lafiya.

Toh masha Allah adaicigaba da hak'uri sumayya kizauna da ita lafiya banason fad'a ko tashin hankali.

Toh Abbah daman muna zaman lafiya.
Cikin jin dad'i sultan abbas yace yauwa 'yar abbah Allah yaimiki abarka.
Ameen abbana, cewar sumayya sannan takalli sultana sadiya da tazuba musu ido tana murmushi, itama sumayya murmushin tayi sannan tace ummana ina wuni?
Lafiya lou daughter ya gidan?
Alhmdllh ummah,
Toh masha Allah ina fatan mijinki da 'yar uwartaki suna lafiya.
Sumayya cike da mamaki take kallon ummah ganin yadda ummanta take Magana a gaban abbah.

sumayya murmushi tayi mai fassara sannan tace duk lafiya lou ummah.

Sultan Abbas mik'ewa yayi yace bari inje fada nasan yayana yana chan yana jirana dan akwai wata jana'iza da zamuje ta abokinsa.

Sultana da sumayya nan sukayi mai adawo lafiya dan sultana sadiya har bakin k'ofa tarakasa sannan tadawo.

Da mamaki take kallon sumayya da lokaci guda tacanza fuska, sultana sadiya cike da damuwa tace sumayya lafiyarki?

Sumayya k'wallah ce tafara fita daga idonta cikin muryar kuka tace ummah na tsani yarinyar chan natsani inbud'e idona inganta cikin gidannan.

Sultana sadiya cike da damuwa tazauna gefen sumayya tare da rungumota jikinta cikin rarrashi tace sumayya kema kin sani nima hankalina ba zai ta6a kwanciyaba in ina ganinki cikin damuwa, kicigaba da hak'uri insha Allahu zarah ta kusan fita tabar miki gidanki.

Sumayya cikin sauri tad'ago kai takalleta tace ummana taya hakan zata kasance, wlh yarinyar chan yadda kikasan ta asirce yarima, kiduba kiga duk makircin da ake k'ullah mata ammah bai ta6a d'aga kai yakalletaba, ni wlh har na fara gajiya ina tunani akwai abinda tak'ullah.

Murmushi sultana sadiya tayi sannan tace kidaina damuwa daughter kibarni da ita in ta san wata toh batasan wataba ni nasan yadda zanyi da ita dan suhail na sumayya ne ita kad'ai.

Cike da jin dad'i sumayya tak'ara ruk'unk'ume ummanta tace nagode sosai ummana Allah yabar min ke.

Sultana sumayya cike da son d'iyartata tace Ameen daughterna.


A chan 6angaren zarah lokacin da tashiga part d'inta a parlour ta yada zango saman 3 seater tare da jingine kanta da kujerar tana maida numfashi ahankali, chan taji wani irin tuk'a ta taso mata, cikin sauri tamik'e tanufi toilet,
Saida ta amaye dukkan tuwon da taci duk ta galabaita, dak'yar tasamu tawanke fuskarta tafito tahau saman gadonta tayi kwanciyarta,
Tana mamakin yadda yau daga safe zuwa yanzu ta yi amai ya kai biyar.

Juyi kawai take saman gadon har aka kira sallar magrib tayi sallah tana zaune saman darduma tana lazumi aka kira isha'i.

Bayan ta gama sallah wanka tashiga tayi sannan tayi shirin bacci, yunwa taji tana ji ammah gudun kar tayi amai yasa tayi kwanciyarta haka.

Wajen 8:30pm kwance take saman gadonta ga yunwa duk ta addabeta, kawai ji tayi tanason shan ice cream,

Sharewa tayi tai kwanciyarta tana ta juyi daga k'arshe ji tayi bata iya daurewa indai batasha ice cream d'inba toh akwai matsala, dan haka tamik'e cikin sauri tad'auko hijab tazumbula tafito tanufi part d'in yarima har tana tuntu6e.

Tana shiga tasamesa zaune a parlournsa yana kallon ball gabad'aya ya tattara hankalinsa a TV d'in kasancewar yana son wasan, bai ankaraba sai jinta yayi ta fad'o jikinsa,

Kallonta yayi cike da mamaki yace ke lafiya? Zarah k'irjinsa tashige tare da fashewa da kuka.

Yarima gigicewa yayi yace lafiya zarah? Meyake faruwa?
Cikin sheshek'an kuka tace ni ice cream nakeson sha, bana iya cin abinci da naci amai nake, d'azun ma saida nayi wajen dada.

Yarima ajiyar zuciya yasafke sannan yace yanzu saboda ice cream kike kuka?

Turo baki tayi cikin shagwa6a tace uhm.

Wayarsa kawai yajanyo batare da yayi magana ba yakira wani guard d'insa yace yaje yasamo masa ice cream yanzu, daga chan 6angaren guard d'in cike da girmamawa yace toh ranka yadad'e angama.

Kashe wayar yarima yayi tare da kallon zarah da tatsaresa da ido har a lokacin k'wallah tana fita daga idonta, sannan yace bari akawo miki.

Gyad'a kai kwai tayi sannan tacire hijab d'inta takoma ta lafe a k'irjinsa wani irin numfashi taja dan har cikin ranta taji dad'in hakan,

Yarima maida idanuwansa yayi yalumshe yanajin yanayin d'umin jikinta.

Haka suka kasance babu wanda yak'ara magana sai chan wayarsa tafara ringing, d'aukota yayi ganin mai kiransa yasa yayi picking batare da yayi magana ba,
Daga chan 6angaren akace ranka yadad'e ansamo,

Kallon zarah yayi da tazuba mai ido sannan yace ohk ina zuwa.

Jin haka yasa zarah tasafka daga jikinsa nan yamik'e yanufi k'ofa yakar6o yadawo saida yazauna sannan yamik'a ma zarah k'atuwar ledar.

Cikin sauri tak'ar6a fuskarta d'auke da murmushi tace nagode sannan tabud'e robabin ice cream ne manya kusan guda biyar nan tafito da guda, kallon yarima tayi da yake kallonta tace zakasha?
Girgiza mata kai kawai yayi.
Mik'a mai d'ayan tayi cikin shagwa6a tace karik'e min insaka sauran cikin freezer kar yanarke.

Yarima zuba mata ido yayi batare da ya yi magana ba kamar ba zai kar6aba sai kuma chan yakar6a.

Mik'ewa tayi tanufi freezer d'insa tasaka sannan tadawo tazauna saman cinyarsa tare da kar6a tabud'e robar, jikinta har rawa yake  nan tafara sha.

yarima ido yazuba mata yana kallon yadda take sha saikace wadda akace za'a k'wacemawa, hannu baka hannu k'warya takeyi.

Har saida takusan shanyewa sannan ta aje takalli yarima tayi murmushi ahankali tace nagode nan takwanta k'irjinsa tayi lamo,

Ahankali taji yarima yana neman tura hannuwansa cikin rigarta, maida idanuwanta tayi talumshe fuskarta d'auke da murmushi.

Cikinta yashiga shafawa, yanayin yadda yake shafarsa wani irin shock takeji a jikinsa, nan tak'ara lafewa,

Ahankali yamaida hannuwansa a k'irjinta yana shafa cikin wani irin salo, zarah nema tayi tarikice mashi nan taruk'unk'umesa.

Cigaba yayi da abinda yake saida yayi kusan 5 minutes sannan yafitar da hannunsa daga cikin rigarta, ahankali yabud'e idanuwansa da suke lumshe tare da lek'a fuskar zarah da tatura cikin k'irjinsa kamar zata shige ciki sai maida numfashi take kad'an kad'an, murmushi yad'anyi kad'an sannan yad'auketa cak yanufi bedroom d'insa bai zameta a ko'inaba sai saman bed d'insa.

Zarah na ji ya safketa cikin sauri tajuya mai baya, murmushi yayi sannan yawuce yakoma parlour yakashe kayan kallon sannan yadawo bedroom d'in, kashe gloves yayi nan yahau gadon yakwanta daga bayan zarah.

Hannunsa taji yad'auro saman cikinta, murmushi tayi sannan ahankali itama tad'aura hannunta saman nashi tana shafawa juyowa tayi takallesa cikin d'an hasken da yake d'akin har a lokacin hannunta yana cikin nasa ganin shima idanuwansa suna a kanta yasa tamaida kanta a k'irjinsa takwanta.

Lumshe idonsa yayi yana shak'ar k'amshin gashin kanta, sai chan yace meyasa bakison cin abinci?
Zarah d'ago kai tayi takallesa ganin idanuwansa a rufe yasa kamar zatayi kuka tace amai yake sanyani.

Bud'e idonsa yayi yakalleta, sannan yace kidinga ci kokad'anne.

Umhum kawai zarah tace.

Hannu yakai yajanye mata gashinta da yabazu har gefen idonta, ido suka zuba ma juna suna ma junansu wani irin kallon da su kansu basusan ma'anarsaba, yarima ne cikin sauri yafara janye idonsa daga cikin nata.

Zarah ma cikin jin kunya tamaida kanta takwantar a k'irjinsa,
Ahankali taji ya kai hannunsa yana neman rabata da 'yar rigarta.

Yana cirewa tazame jikinta daga nasa.
Da mamakinta sai ganin yarima tayi ya dawo bisa ita, zaro ido tayi kafin tayi magana sai jin bakinsa tayi cikin nata, sun dad'e a haka sannan yagangaro wuyanta zuwa k'irjinta.

Zarah bada kai tayi dan ita kanta tasan abuk'ace take da mijin nata.

Bayan komai ya lafa Zarah kukan shagwa6a tasaka mai, yarima rungumota yayi jikinsa yana d'an bubbuga bayanta ahankali alamun lallashi.

Zarah cigaba tayi da kukan, ahankali yabud'e idanuwansa da suke lumshe cikin muryarsa da tadashe yace kukan fa?

Turo baki Zarah tayi cikin kuka tace toh bakaibane kaban wahala, kuma wanka nakeso kayi min.

Ido yazuba mata sai chan yace na ji.
Janyeta yayi daga jikinsa yamik'e yanufi toilet, saida yatsarkake jikinsa sannan yahad'a mata ruwan d'umi.

Bayan ya fito kallonta yayi yace muje.

Hannu Zarah tamik'a mai alamun yad'auketa.
Yarima babu yadda ya iya haka yaduk'a yad'auketa yanufi toilet da ita, cikin komin yasakata.

Har ya juya zaya tafi Zarah cikin sauri tarik'o hannunsa tare da fashewa da kuka tace kayi min wankan.

Yarima haka yatsaya yana mata wanka ita kuma tana zuba mai shagwa6a, har yagama sannan yahad'a mata wasu ruwan yace tayi wankan tsarki.
Ganin ya juya zai tafi yasa zarah tace bana fa iyayi please kataimaka kayi min.

tsaye yarima yayi cikin ransa yace yarinyar nan ta raina min wayau, kamar yace bazaiyiba sai kuma chan yafara yi mata.

Zarah kallonsa tayi ganin yadda yahad'e rai yaso yabata dariya, nan tafara yin dariya ciki-ciki, tanak'unshe dariyar karaf suka had'a ido da yarima.

Wata uwar harara yawurga mata sannan yasaketa yafita yabar toilet d'in.

Zarah dariyarta tacigaba dayi ahankali sai daga baya da tatuna a inda take yasa tatsagaita yin dariyar sannan tayi wankanta.

Bayan ta gama fitowa tayi tatarar yarima lokacin har ya kwanta, dan haka itama rigarta tamaida sannan taje bayansa takwanta.

_*BAYAN KWANA UKKU*_

Sultana bilkisu ce zaune parlourn dada bayan sun gaisa nan suka shiga yin hira suna cikin hirar ne dada tace ummin suhail ashe da rabon zanga jinin yarima.

Ummi cikin rashin fahimta tace dada ban ganeba.

dada har ta bud'e baki zatayi magana sai ga sultana sadiya ta shigo da sallamarta.

Gabad'ayansu suka amsa mata nan tazauna saman d'aya daga cikin cushin d'in, cike da girmamawa tagaishe da dada.
nan dada ta amsa mata tare da tambayarta gida.
Alhmdllh cewar sultana sadiya fuskarta d'auke da murmushi tace ina fatan kina cikin k'oshin lafiya?
Dada tace Alhmdllh saidai abinda ba'a rasaba kinsan yanayin tsufa.

Gabad'ayansu sukace Allah yak'ara lafiya.
dada tace Ameen.

Sultana bilkisu fuskarta d'auke da murmushi tace sultana anwuni lafiya?
Kallonta sultana sadiya tayi tare da yin d'an guntun murmushi sannan tace lafiya lou sultana dafatan kina lfy?
Alhmdllh, cewar ummi.

Sultana sadiya tace wai ni ina yarima ne naga kwana biyu bansashi idonaba ko baya garin?

Mamakine yakama sultana bilkisu ganin yadda tayi tambayar, bayan jiya-jiyannan yarima da yaje gaisheta yace mata daga turakar umman sumayya yake ya je sun gaisa.
Sultana bilkisu d'an murmushi tayi sannan tace yana nan man, ashe baya zuwa yagaisheki, gaskiya yarima halinsa sai shi ya kamata kuyi mashi fad'a yagyara.

Rik'e baki sultana sadiya tayi tace taya zanyi mai fad'a? Rufamin asiri wa zai iya da halin wannan miskilin yaron.

Dada murmushi tayi tace ina ruwan yarima, ni har mamakin halinsa nake wani lokacin ma cewa nake anya shi kad'ai ne?

Ta6e baki sultana sadiya tayi tace ranki yadad'e shi kad'aine kawai dai iskancine yayi masa yawa dan ko mahaifiyartasa kamar bata isa da shi ba.

Sultana bilkisu murmushi tayi tace haba sultana kema shedace tsaye nake kan suhail, kuma ina masa fad'a akan wannan hali nasa ammah ya k'i canzawa.

Ta6e baki sultana sadiya tayi tace duk dai lokacin da yafara aje 'ya'ya ai dole ya aje wannan iskancin nasa.

Dada murmushi tayi sannan cikin jin dad'i tace ai insha Allahu nan ba da dad'ewaba zamu sha suna.

Gabad'ayansu kallon Dada sukayi cike da mamaki sukace suna kuma?

Murmushi dada tayi tace ashe ku ma baku saniba, ai matarsa cikine da ita.

Murmushi sultana sadiya itama tayi sannan tace ranki yadad'e batada komai ai sumayya har yanzu Allah bai kawoba.

Dada kallonta tayi tace kekuma kinji ki da wata magana ai amaryarsa ce keda ciki.

Sultana sadiya jin maganar tayi kamar an jefota cikin kunnenta, nan gabanta yayi wani irin mugun fad'uwa, cikin k'ani'anin lokaci fara'ar fuskarta tagushe,

akasin sultana bilkisu da taji abun kamar a mafarki farin ciki nan yadabaibaye zuciyanta cikin ranta Alhmdllh kawai take cewa, dan batada buri a duniya da yawuce taga jinin yarimanta.........




_Comment_
      *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_*Yau page d'in nakune my fan's mutanen saudiya, sak'onku yana zuwa a gareni nagode sosai da soyayyar da kuke nunamin saidai ince Allah yabarmu tare, jinjinar bangirma agareku Sis Aisha*_

*PAGE* 4⃣8⃣

Sultana sadiya dak'yar tasamu tad'an tsaida nutsuwarta sannan tad'an yi d'an murmushi mai kama da yak'e tace ranki yadad'e ya akayi kikasan cikine da ita kuma an tabbata shi d'inne?

Murmushi dada tayi sannan tace tabbas cikine da ita dan rannan k'arnin kifi kawai taji ammah saida tayi amai ke ko yanayinta zaki kallah sai kin gane hakan kuma ko jiya da yarima yazo gaisheni saida namatsa mai da tambaya sannan yafad'amin ashe cikin har ya kai tsawon wata hud'u, kinsan halin yarima ba komai yake fad'aba.

Sultana sadiya saida gabanta yayi wani irin fad'uwa, cikin zuciyanta tace wata hud'u??? batasan lokacin da tace hmm ai yarima ya iya munafunci.
Ganin yadda sultana bilkisu da dada suka zuba mata ido yasa tayi murmushi tace ya za'ayi ni a matsayina na mahaifiyarsa yak'i fad'amin, ai ya kamata tasamu kulawa sosai a wajenmu tunda mune matsayin dangi yanzu a wajenta saboda da mu take zaune.

Dada murmushi tayi tace tabbas maganarki gaskiya ce koda munso ace sumayya ce tafara haihuwa ammah bakomai tunda haka Allah yak'addara kuma dukkansu d'ayane tunda duk matansane,

Sultana sadiya cikin rashin nuna damuwa tace ai d'a nakowane da zarah da sumayya duk d'ayane a wajena.

Murmushi sultana bilkisu tayi tace nima haka ina sa rai nan ba da dad'ewaba  my dota nima tahaifo mana baby.

Dariya sultana sadiya tayi sannan tace saidai daga baya dan mu nan ba da dad'ewaba zamu amshi jika.

Eh munji babu komai muma namu insha Allahu yana nan zuwa.

Dada ido tazuba musu cikin jin dad'i sannan tace Allah yakawo masu albarka.

Gabad'ayansu suka amsa da Ameen.

Mik'ewa sultana sadiya tayi tana murmushi tace ranki yadad'e zan wuce akwai bak'uwa da zanyi yanzu hakama ina sa ran ta iso, insha Allahu zan je induba jikin my daughter.

Cikin jin dad'i dada tace toh bakomai.
Sultana bilkisu tace sai anjima sultana.

'Dan rissinawa sultana sadiya tayi sannan tace na barku lafiya, tana fad'in haka tajuya tafita.

Nan sultana bilkisu da dada suka cigaba da hirarsu, saida maraice yayi sannan sultana bilkisu tayi ma dada sallama takoma part d'insu cike da farin ciki akan cikin zarah.

A 6angaren sultana sadiya ko da tafita bak'in cikine yatokare mata mak'ogwaro, takaici duk yacikata ita kanta ta yi mamakin yadda akayi ta iya danne bak'in cikinta a gaban su dada.

Ko da ta isa part d'inta a parlour tayada zango nan tashiga kaiwa da kawowa ahankali take furta na shiga ukku ya akayi wata daga zuwanta tariga d'iyata samun ciki, kai da sake dole ne inbi ta kowace hanya wajen ganin na zubar da shi, taya wata d'iyar talakka zata fara aje jika a masarautar nan? Ba dai hakan yana nufin plan d'in da nashirya ya rugujeba? Inaaaa hakan ba zai ta6a yuwuwaba wlh, Tsanar zarah sa yarima ne taji ya k'aru a cikin zuciyanta.

Cike da 6acin rai tajanyo wayarta takira sumayya, sumayya na yin picking sultana sadiya cikin d'aga murya tace ke kina ina?
Daga chan 6angaren gimbiya sumayya tace ummah lafiya naji ki haka? Ina gida.
dan ubanki kizo yanzu kisameni ina jiranki.
Sumayya cike da mamakin mahaifiyartata tace toh ummah,
Sultana sadiya bata k'ara magana ba ta kashe wayar tare da wulli da ita saman cushin.

Daga chan 6angaren sumayya da mamaki tabi wayar da kallo ahankali ta furta lafiya? Kiran me ummah take min haka cikin gaugawa? Ba abinda yafi d'aure mata kai sai jin yadda ummah tayi mata magana cikin tsawa.
Ahankali tafurta Allah dai yasa lafiya, tana fad'in haka tamik'e tasaka alkyabbarta sannan tafito tanufi part d'in mahaifiyartata.

Ko da ta isa a tsaye tatarar da sultana sadiya tana zagaye d'akin tana cize le6e, cike da rud'ewa sumayya ta isa wajenta tace ummana lafiya me yake faruwa?
Ajiyar zuciya sultana sadiya tayi tace sumayya komai ma ya faru.
Cike da mamaki sumayya tace ummana ban fahimcekiba.
Taya zaki fahimceni sumayya bayan kinyi wasa da damarki? Toh gashinan abinda nake guje miki ya faru..."sultana sadiya tafad'i hakan cikin d'aga murya"
Sumayya tsaye tayi tana kallon ummanta cikin rashin fahimtar inda tadosa.
Sultana sadiya ajiyar zuciya tayi tace sumayya kishiyarki tana d'auke da cikin yarima na tsawon wata hud'u.

Wani irin fad'uwan gaba yaziyarci sumayya tsaye tayi cak tana jin abun kamar a mafarki, chan sai ta k'yalk'yale da dariya tace ummah ciki kuma tsawon wata hud'u? Kina nufin zata haihu da yarimana? Chan kuma sai ta fasa k'ara tare da furta wlh k'aryane hakan ba zai ta6a faruwaba.
Kallon ummah tayi tafashe da kuka tace ummana wlh ban yardaba babu yadda za'ayi inbar wacchan matsiyaciyar tahaihu da yarimana ummah wlh sai na kasheta saidai nima a kasheni.

Sultana sadiya jin d'iyartata tana surutai cikin d'aga murya gudun kar ajisu yasa tajanyo sumayya suka shige bedroom d'inta.

Suna shiga sumayya tafad'a jikinta tare da fashewa da kuka tace na shiga ukku ummana ya zanyi da rayuwata ummah na tsani yarinyar chan, ba zan ta6a yadda cin mutuncin da yarima yayi minba ace 'yar talakkawa yayi ma ciki wlh ya munafunceni Allah ummah Sai na kasheta saidai shima yakasheni.

Sultana sadiya rungume d'iyartata tayi cike da tausayinta tace kidaina cewa haka sumayya kinga abinda daman nake guje miki yanzu gashinan kinyi wasa da damarki.

Sumayya cikin kuka tace ummana wlh ba zan ta6a yarda a zalunceniba inma haihuwarce ai ni yafi dacewa inyita.

Sultana sadiya rik'ota tayi sukaje bakin gado suka zauna cike da tausayi tace sumayya kiyi shuru hakanan muyi magana.

Sumayya share hawayen fuskarta tayi nan tazuba ma umman ido.

Sultana sadiya tace yauwa ko kefa, yanzu dai da farko inaso kikwantar da hankalinki kinutsu kar kice zaki kawo tashin hankali a gidan aurenki dan kinsan wannan mijinnaki ba zai d'auki hakan ba, sannan indai kinsan kina planning toh kidaina kisamu kema cikin nan kiyi sa, inyaso ita zarah kibarni da ita nasan yadda zan 6ollo ma lamarin.

Sumayya tace ummah toh cikin nata fa?

Tsiyata da ke Sumayya wani lokacin baki ganewa, tunda dai nace kibarni da ita ai nasan abinda zanyi, na dai fad'a miki kar kikuskura kice zakiyi mata wani abu da kanki.

Sumayya tace toh ummah.
Yauwa kokefa.
Murmushi kawai Sumayya tayi batare da tace komai ba.

A 6angaren sultana bilkisu kuwa koda takoma 6angaren su a bedroom d'in sultan Ahmad tayada zango lokacin yana zaune yana duba wata newspaper,

Bud'e k'ofan da tayi tashigo yasa yad'aga kai yakalleta ganin yadda taketa fara'a yasa ya aje newspaper d'in tare da yin murmushi yace da alamu yau matartawa tana cikin farin ciki.

Sultana bilkisu Ida k'arasowa tayi wajensa tazauna fuskarta d'auke da fara'a tace tabbas ranka yadad'e ka yi gaskiya domin yau ina cikin wani irin farin ciki.

Rik'o hannunta yayi yace toh nima afad'amin farin cikin da ake nima intaya.

Sultana bilkisu murmushi tasakar masa sannan tace ranka yadad'e mun kusan samun jika.

Jika fa kikace?

Eh ranka yadad'e, tabbas auren zarah da yarima akwai alkhairi a cikinsa, my son ya kusan zama daddy.

Sultan Abbas kasa 6oye farin cikinsa yayi yace Alhmdllh Allah abun godia, gaskiya naji dad'i kuma nayi farin ciki dan arayuwata inason ganin jinin yarima,

Dariyar jin dad'i sultana bilkisu tayi tace was yaga yarima da d'a.

Shima sultan Dariyar yayi yace Allah dai yasafke lfy, Allah yakawo masu albarka.

Ummi cikin jin dad'i tace Ameen farin cikina.
Gabad'ayansu suka sakarma juna murmushi, jin kiran sallar magrib ne da aka fara yasa suka mik'e, sultan Ahmad yayi alwallah yawuce masallaci.


Sumayya ko da takoma 6angarensu bedroom d'inta tashige tafad'a saman gado nan wani sabon kukan yakubce mata yi take babu k'ak'autawa tausayin kanta yakamata, saida tayi mai isarta sannan tajanyo waya takira zinat.

Zinat nayin picking babu ko sallama sumayya tace baby na shiga ukku.

Daga chan 6angaren zinat tace haba baby akan wane dalili zakice kin shiga ukku, me yake faruwa ne?

Sumayya fashewa tayi da kuka tace zinat dole ince haka domin ina cikin matsala bansan ya zanyi da rayuwataba.

Baby kinutsu kimin bayanin abinda yake faruwa kidaina kuka.

Sumayya tsagaitawa tayi da kukan da take tace zinat wannan bagidajiyar yarinyar daga zuwanta wai har ta samu ciki, wlh ba zan ta6a yarda ba.

Zinat cikin d'aga murya tace kina nufin wannan kishiyar taki?

Toh in ba itaba wa kike tunani ni wlh kasheta zanyi kowa yahuta inyaso nima daga baya akasheni.

Zinat ajiyar zuciya tayi tace kar kice haka baby kiyi hak'uri kijira zan shigo,
Har sai yaushe zaki shigo kina nufin inbari har sai ta haihu? Cewar sumayya
A'a baby ai very soon zan shigo, kijirani zuwa next month zan shigo wlh sai munyi silar zubar da cikin.

Sumayya tace toh zan gwada inga idan zan iya hak'uri har sai kin shigo.

Zaki ma iya baby, yanzu dai nidai burina kikwantar da hankalinki kar kije ki aikata abinda zai je yadawo.

Hmm baby kenan kidaina maganar kwanciyar hankali dan ayanzu hankali ya gama kwanciya kawai dai sai anjima yanzu zan d'an huta.

tana fad'in haka bata jira jin komai daga wajen zinat ba takashe wayarta.

Mik'ewa tayi taje tawatsa ruwa tayi shirin bacci tahaye gadonta dan yau cewa tayi babu abinda zai kaita wajen yarima saidai yayi baccinsa shi kad'ai dan shi kansa haushinsa takeji,
duk yadda taso tayi baccin kasawa tayi kalmar cikin zarah yatsaya mata a rai duk yadda taso tayi bacci kasawa tayi daga k'arshe saida tasha maganin bacci sannan tasamu bacci yayi awon gaba da ita.

_*Washe gari*_

Wajen 12 zarah zaune take saman cushin hannunta rik'e da waya tana chart sallamar da taji anyine yasa ta amsa tare da d'ago kai takalli mai sallamar, da mamaki take kallon sultana sadiya da take sakar mata murmushi, cikin sauri zarah tamik'e tsaye fuskarta itama d'auke da murmushi tace sannu da zuwa ummah.

Yauwa d'iyata, a'ah kice jiki ya warware, cewar sultana sadiya.

Zarah cikin Jin kunya tace bismillah ummah kizauna.
Zama sultana sadiya tayi har a lokacin fuskarta tana kan zarah, cike da jin kunya zarah tazauna k'asa tace ummah ina wuni?
Lafiya lou dafatan kina Lafiya, ya k'arfin jikin naki.
Cikin jin kunya zarah tace ummah ai na warke,
toh masha Allah, Allah yak'ara sauk'i, ai ba a fad'amin bakida lafiya ba sai jiya naji wajen dada.

Zarah shuru tayi tana wasa da yatsun hannunta tana murmushi, ahankali tamik'e tace ummah bari inkawo miki ruwa.
Murmushi sultana sadiya tayi tace kibarsa kawai saikace wata bak'uwa.

Wucewa zarah tayi tace ummah bari dai inkawo miki, sultana sadiya binta tayi da wani irin kallo har tashige kitchen, ahankali tafurta tabbas yarinyar nan cikine da ita.

Zarah ko da tashiga kitchen dafe k'irjinta tayi tare da safke ajiyar zuciya dan ta tsorata sosai da fari da taga ta shigo sai daga baya da taga ba da wata manufar tazoba sannan taji dad'i, ahankali tafurta Allah yasa umman sumayya ta shiryu.

Nan tacigaba da had'a mata kayan marmari da drinks kala-kala a saman tray ta d'aura tad'auko tafito.
A gaban sultana sadiya ta aje tace ummah kifara da wannan kafin ingirka miki abinci.

Murmushi sultana sadiya tayi tace a'a zarah keda bakida lafiya kibarsa kawai dan ni nan a k'oshe nake,
Zarah ruwan inibi tatsiyaya a cup tamik'a mata tace ummah toh ko yayane kisa albarka.

Kar6a sultana sadiya tayi tana murmushi tace nagode zarah, kur6a d'aya tayi ta aje sannan tace zarah kiyi hak'uri akan abinda nayi miki wlh sai daga baya nagane hakan ba daidai bane,

Murmushi zarah tayi tare da d'ago kai takalleta tace ummah bakimin komai ba wlh dan ke matsayin uwa kike a wajena.

Nagode sosai zarah, Allah yaimiki Albarka, Allah yasafkeki lafiya.

Zarah kasa amsa mata tayi saboda wata irin kunya da tarufeta.

Mik'ewa sultana sadiya tayi tace toh ni zan wuce.

Ummah tun yanzu?

Haba zarah me zan zauna inyi ni da nake matsayin suruka, yanzu dai indai kinsan kina buk'atar wani abu kidinga aikawa ana fad'amin insha Allahu ni kuma zan samo miki koma menene, yanzu haka ga zogale chan nasa ana dafawa na baro sun kusan gamawa, Indai angama zan aiko miki da ita nasan zakiso cinta..

Murmushi zarah tayi cikin jin dad'i tace toh ummah nagode.

Haba minene abun godia ai keda sumayya duk d'aya nad'aukeku, zansa a ma k'wad'a miki da k'uli-kul'i dan akwai wata baiwata data iya irin wad'annan k'wad'on masu dad'i ita zansa tayi miki.

Zarah duk'ar dakanta tayi tace nagode sosai ummah, Allah yak'ara girma da d'aukaka.

Sultana sadiya tace Ameen sai na aikon, tana fad'in haka tawuce nan zarah tarakata har wajen part d'inta tare da k'ara yi mata godia.

Sultana sadiya tace bakomai, nan tawuce cike da farin ciki dan ta san tarkonta ya kama kurciya...






_Comments_
        *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Masha Allah my dota *hafnan* Ina tayaki murnar kammala novel d'inki maisuna *FATALWAR MIJINA* hak'ik'a kin zuba basira sannan kin koyar da darasi a cikinsa gaskiya salon novel d'in ya burgeni, Allah yabaki ladar abinda kika fad'a daidai kurakuren da suke ciki Allah yayafe miki, ur mommo love you more😘_

_~Masoya sak'onku yana isowa agareni ina godia sosai Allah yabar k'auna, mutanen katsina ku ma sak'onku ya iso agareni nagode sosai nima ina gaisheku~_

*PAGE* 4⃣9⃣

Haka sultana sadiya ta isa 6angarensu farin ciki fal a zuciyanta, cikin sa'a ko da ta isa tatarar angama dafa zogalen, nan tasa wata baiwarta tak'wad'a mata, sannan tawuce cikin bedroom d'inta inda tad'auko k'ullin maganin da tasa aka samo mata.

Bayan an gama kwad'on a parlour aka kawo mata cike da jin dad'i tabud'e taduba saida tad'ibi nata sannan tazuba ma sauran maganin tamotse yadda ba za'a ganeba sannan tajuye a cikin wata kula mai kyau, murmushin mugunta tayi tace zarah kinyi babban kuskure da kikayi saurin yarda da ni dan bakisan wacece ni ba,

Sallamar da akayine daga wajen d'akin yasa ta amsa saida tagama abinda take sannan tabada izinin ashigo, jakadiya ce tashigo cikin sauri taduk'a tagaishe da sultana sadiya cike da girmamawa.

Sultana sadiya kallonta tayi a wulak'ance saida tayamutsa fuska sannan ta amsa.

Jakadiya k'ara duk'ar da kanta tayi k'asa tace ranki yadad'e daman dada ce ta aikoni wajenki.

Shuru sultana sadiya tayi na d'an lokaci sannan tace ina saurarenki.

Jakadiya ledar da take hannunta ta mik'a mata tace gashi tace akawo miki.

Kar6a sultana tayi tabud'e batasan lokacin da Murmushi yakubce mataba ganin wata had'ad'ar sark'a da dada ta aiko mata da shi, cikin sakin fuska sultana sadiya tace kice mata nagode.

K'ara duk'awa jakadiya tayi tace Allah yaja da ranki nabarki lafiya,

Gyad'a mata kai kawai sultana sadiya tayi,
Har jakadiya ta wuce zata fita sultana sadiya takirata.

Cikin sauri jakadiya tadawo taduk'a tace ranki yadad'e na amsa kiranki.

Sultana mik'a mata kular tayi tace gashi kikai ma gimbiya zarah.
Cikin sauri jakadiya takar6a cike da mamaki tace ranki yadad'e gimbiya zarah ko gimbiya sumayya?

Harara sultana tawurga mata cikin fad'a tace zarah nace miki ko sumayya?

Jikin jakadiya yana rawa tace kigafarce ranki yadad'e gimbiya zarah zan kaimawa Allah yahuci zuciyanki.

K'ofa sultana sadiya tanuna mata, cikin sauri jakadiya tad'auki kulan tafito.


A chan 6angaren zarah bayan sultana sadiya ta tafi komawa tayi saman cushin tazauna tare da dafe kanta mamakin sultana sadiya duk ya kamata dan yau ne karo nafarko da tafara ganin fara'arta, tunowa tayi da duk wulak'ancin da take yi mata a baya, murmushi zarah tayi wanda ita kad'ai tasan ma'anarsa.

Jakadiya tafiya take ammah mamakine yacikata ahankali take furta miye had'in sultana sadiya da gimbiya zarah? Miyasa batace inkai ma gimbiya sumayya ba sai zarah? Anya ba wata k'ullalliya da matarnan take shiryawa?
Bari dai inje sai inji daga bakin gimbiya.

Lokacin da ta isa a parlour tasamu zarah zaune tana shan fruit salad, cike da girmamawa taduk'a tagaishe da zarah, cikin sakin fuska zarah ma tagaisheta tare da tambayarta su dada.

Murmushi Jakadiya tayi tace suna lafiya sannan tamik'a mata kular tace ranki yadad'e gashi daga sultana sadiya tace inkawo miki.

Murmushi zarah tayi batare da ta kar6a ba tace bud'e mugani.

Cikin sauri Jakadiya tabud'e, zarah lek'awa tayi tace ba laifi kwad'on ya min kyau saidai ba zan iya ciba.

Murmushi Jakadiya tayi tace ranki yadad'e wai miye tsakaninku dan nayi mamakin ganin ta bada kwad'o akawo miki.

Itama zarah murmushi tayi sannan takwashe komai tafad'a ma Jakadiya.

Jinjina kai Jakadiya tayi tace duk tak'are cikinki ne da taji ance kina da shi takeso taga bayansa.

Ta6e baki zarah tayi tace koma mekenen ta Allah ba tataba dan ni nafi k'arfinsu, ban yarda da kwad'on ba aje kawai azubar da shi a 6oye inda wani ba zai ganiba bare yaci.

Jakadiya tace angama ranki yadad'e, Allah yatsare mana ke.

Zarah jingine kanta tayi da kujera nan jakadiya tamik'e tafita tabar d'akin.

Bayan fitarta Zarah mik'ewa tayi tashiga bedroom d'inta, saman gadonta takwanta tana mamakin halin sumayya da mahaifiyarta, ji take da ace sumayya zata amince suyi zaman lafiya da zatayi farin ciki da hakan dan ita da zuciya d'aya take zaune da ita.

Tunowa tayi da gogon nata nan tayi murmushi dan ita kanta ta san tayi missing d'insa rabonta da shi kusan 3 day's kenan, wayanta tad'auko talalubo number d'insa, lokacin yarima yana cikin duba patients d'insa ganin me kiransa yasa yamaida wayan silent yacigaba da aikinsa dan lokacin gab yake da yatashi yakoma gida.

Zarah ganin ta tsinke baiyi picking ba yasa ta aje wayar tare da maida idanuwanta tarufe dan tasamu tad'anyi bacci, ammah gefe guda ji take tana buk'atar son cin zogale da balango dan tunda taga wadda sultana sadiya ta aiko mata taji tana kwad'anta.

Mik'ewa tayi tafito parlour dan tasa asamo mata, daidai lokacin sumayya tashigo d'akin babu ko sallama.

Zarah tsaye tayi tana kallonta cike da mamaki dan sumayya had'e rai tayi sosai ba alamun fara'a a tare da ita daga gani kasan ba mutunci yakawotaba.

Ta6e baki zarah tayi tace haba baiwar Allah ya za'ayi kishigo min d'aki babu ko sallama saikace kin shigo d'akin arna.

Wata uwar harara sumayya tawurga mata cike da 6acin rai tace tunda gidan ubankine ai dole inyi sallama, ke ni nan bai min kama da d'akiba sai dai kongo dan haka ank'i ayi sallamar banza matsiyaciya, kuma cikin da kike tak'ama da shi indai ina numfashi bazaki ta6a haifesaba ke gidannan ma dole kibarsa dan yarima ba ajin aurenki bane, ni banga abinda yagani a jikinkiba har ya amince ya aureki, banza 'yar matsiyata.

Murmushi zarah tayi cikin rashin damuwa tace sumayya ni yanzu banada lokacinki abinda yake kaina ya isheni, kuma ciki da kike magana Allah ne yabani baki isa kiyi min abinda Allah baiyi min ba.

Cikin k'araji sumayya tace kar kikuskura kiyi min gori dan wlh zansa kiyi nadamar da bakita6a yiba a rayuwarki, kinci sa'a ina rangwanta miki ammah wlh da tuni kinbar gidannan kuma cikine kirufa ki aje sai nayi silar zubar da shi.

Zarah shafa cikinta tayi tace malama kinfa dameni da haukanki, kifita kiban waje ko yanzu insa afitar min da ke.

Ta6e baki sumayya tayi tace duk yadda kikayi daidaine ammah inaso kisani ni sumayya na tsaneki, tsanarki bazata ta6a fita daga zuciyana har sai ranar da naga na cika burina, tana fad'in haka tajuya tafita daga d'akin a harzuk'e.

Zarah tsaye tayi tabita da kallo har ta fita, ahankali tafurta Allah yashiryeki sumayya.

Ringing d'in wayanta da tajiyo yasa cikin sauri takoma bedroom d'in tad'auko, ganin mai kiranta yasa tasaki murmushi tare da zama gefen gado saida tasaita nutsuwarta sannan tayi picking.

Gabad'ayansu shuru sukayi sai chan Zarah tayi sallama,
Daga chan 6angaren yarima amsa mata yayi.
Zarah murmushi tayi tace barka da hutawa, ya aiki?
Yarima saida yalumshe idonsa sannan ahankali yace Alhmdllh, y kk?
Cikin shagwa6a tace ina lafiya, saidai babynka da yake wahalar da ni.
Uhm sry, kawai yarima yace,
Zarah kamar zatayi kuka tace ni balango nakeson ci please katafo min da shi.
Yarima shuru yayi nad'an lokaci sannan yace yanzu duk nan gidan ace kin rasa naman da zakici, kuma baki iya sawa ayi miki?

Zarah kukan shagwa6a tasanya sai tace ni wlh nasiye nakeson ci na nan banason k'amshinsa.

Yarima jin kukan nata yake har cikin ransa dan duk ta kashe masa jiki, ahankali kamar mai jin bacci yace toh shikenan zan tafo miki da shi, kukan ya isa.

Zarah tsagaitawa tayi daga kukan da take tace toh nagode please kahad'o min da shawarma, sai kadawo.

Yarima tsinke wayar yayi tare da dafe kansa yana tunanin ta yadda zai fara tsayawa wajen me nama siyan nama, tsaki yaja nan yajanyo wayarsa yakira d'aya daga cikin yaransa yace yaje yasiyo mai balango mai dad'i da shawarma.

Yana gama wayan yamik'e yad'auki key d'in motansa yafito yanufi gida.

Zarah bayan sungama wayar dariya tayi sannan tatashi tashiga wanka.

Bayan ta fito simple makeup tayi nan tashirya cikin gown d'inta maikyau. Saida tayi sallah sannan tajanyo wayarta takira su mama dan sugaisa, hira sukayi sosai nan mama take shaida mata jibi za'ayi baikon Aysha da malam bello, Zarah murna tayi sosai dan har cikin ranta taji dad'in hakan dan tasan malam bello zai kular mata da k'anwarta, nan tace insha Allahu zata shigo ranar, bayan sun gama waya da mama takira Aysha sukasha waya tana tsokanarta daga nan kuma tasa taba yaya rauda wayar nan ma sukaita hirarsu sun dad'e suna hira sannan sukayi sallama.

Mik'ewa Zarah tayi tad'auko veil d'in gown d'in, a gaban dreesing mirrow tatsaya tatufke kanta tayi kamar gambo sannan tayi rolling d'in k'aramin veil d'in nata nan tayi gwanin kyau, tafito tanufi part d'in yarima dan tasan indai ba ita tajeba toh mawuyacine yakawo mata dakansa.

A parlour tasamesa zaune yana waya, gefensa sumayya ce sai wannan cika take tana batsewa, ganin zarah yasa tawurga mata harara tace malama lafiya zaki shigo ma mutane?
Murmushi zarah tayi tace malama ba fa wajenki nazoba.

Yarima da yake waya juyowa yayi yazuba mata ido, itama Zarah kallonsa tayi tasakar mai murmushi, muryar sumayya taji ta ce kedai wlh ban san wace irin natatta bace ke kullum kina manne da mutum, ta6e baki zarah tayi tace kanki akeji.

Yarima kashe wayar yayi batare da ya kallesuba  yace kudai bakuda aiki sai fad'a.

Sumayya kwantar da kanta tayi a kafad'ansa tace dear itace tawani shigo ma mutane dan neman fad'a...tak'arashe maganar tare da wurga ma zarah harara.

Zarah murmushin mugunta tayi mata sannan ta ida isa gefen Yarima tazauna 6ata fuska tayi kamar zatayi kuka tace baby nifa zuwa kawai nayi inkar6i abinda nace kasiyo min wlh yunwa nakeji babynku yana wahalar da ni yau, janyo hannunsa tayi tad'aura saman cikinta tace baby kaji motsi yakemin....tak'arashe maganar tare da kashe mai ido d'aya.

Yarima janye idonsa yayi daga kallonta tare da safke ajiyar zuciya ahankali yace bari inkirasa.

Sumayya cikin 6acin rai tace babbar bura'uba ke wa zakiyi nuna ma duniyanci? Wlh baki isaba kanki farau cikine?

Zarah murmushi tayi tace sorry Auntyna wlh ba kaina farauba kawai dai ina buk'atar ci ne,

Yarima mik'ewa yayi tare da yin dialing d'in number d'in yaron nasa yana shirin kira, knocking d'in k'ofa da akayine yasa yabada izini ashigo.

'Daya daga cikin guards d'insane yashigo d'auke da leda d'an rissinawa yayi yace ranka yadad'e sak'one aka kawo maka.

Kar6a Yarima yayi batare da yayi magana ba, nan guard d'in yajuya yafita.

Yarima juyowa yayi ya kallesu duk sunci face, yanayin yadda sukayi ya so yabashi dariya, tsaye yayi da ledar sai chan yabud'e yaduba ganin kashi biyu ne yasa yad'auki kashi d'aya yamik'a ma sumayya yace ga naki.

Yamitsa fuska sumayya tayi tace duk naman da yake gidannan sai ansiyo na waje, ni gaskiya bazan iya ciba.
Ta d'auka yarima zai lallasheta kawai sai gani tayi ya mik'a ma zarah duka ledar yace gashinan.

Kar6a zarah tayi tare da yin murmushi tace nagode sosai baby, nan tamik'e tare da kallon sumayya da tacika tayi fam tace Aunty sumy kiyi hak'uri idan na 6ata miki sai anjima, tana fad'in haka tajuya tafita tabar d'akin.

Yarima komawa yayi yazauna tare da d'auko remote yana canza channel, sumayya kallonsa tayi tace yarima kana ganin abinda yarinyarnan take min ammah baka iya yi mata magana.

Wani irin kallo yawurga mata kamar ba zaiyi maganaba sai kuma chan yace sumayya akan me zanyi magana bayan a da tana baki girmanki kece dai kikak'i kirik'e girman naki kinga kenan laifin nakine dan haka in zaki gyara toh kigyara.

Sumayya haushine yakamata gani take kamar ya goyi bayan zarah, yamutsa fuska tayi tace ya dai kamata kadinga adalci a tsakaninmu dan mu dukanmu matankane kuma ita d'in da kake ma rawan kai ai.......wata irin harara da yawurga matane yasa tayi shuru batare da ta k'arashe maganartaba,

Cigaba yayi da kallonsa inda Sumayya tamik'e cike da jin haushi taficce tabar d'akin.

Cikin rashin damuwa yarima yayi kwanciyarsa saman kujerar, dan shi yanzu halayyar Sumayya har ta daina bashi mamaki.


A chan 6angaren sultana sadiya koda jakadiya tadawo mata da kular tambayarta tayi zarah ta ci kwad'on? Jakadiya saida taduk'ar da kanta k'asa cike da girmamawa sannan tace eh ranki yadad'e dan dukansa tacinye ta ce tana godia sosai.

Murmushin jin dad'i sultana tayi sannan tace kai haba toh menene abun godia a ciki? Ai taimakon kai ne, yanzu zaki iya tafiya.

K'ara duk'awa jakadiya tayi tace toh ranki yadad'e atashi lafiya, tana fad'in haka ta tashi cikin sauri tabar d'akin.

Bayan ta fita sultana k'yalk'yalewa tayi da wata irin dariya tace yarinya bakisan wacece ni ba wayace miki koda da second d'aya zan iya sonki? Kallon agogon da take manne ga bangon d'akin tayi sannan tace nan da minti talatin cikinki zai tashi aiki, tana fad'in haka tayi murmushin mugunta sannan tajanyo wayarta takira sumayya nan tafad'a mata komai.

Sumayya murna tayi sosai har da 'yar taka rawarta nan tanemi 6acin ranta tarasa.

Yau ko da taje d'akin yarima da dare shi kansa saida yayi mamakin ganinta cikin farin ciki bai dai tambayetaba yashareta yai kwanciyarsa haka tazo bayansa takwanta yanajinta tarungumesa nan yamaida idanuwansa yalumshe ahaka bacci yai awon gaba da su.

Da safe sumayya sa wata kuyangarta tayi takular mata da duk wani motsin zarah dan ta yi tunanin za'a fito da ita aje asibiti ammah da mamakinta har wajen 10am ammah shuru dan haka tashirya da kanta tanufi part d'in zarah dan tagane ma idonta abinda yake faruwa, cikin ranta tace ina ma insameta kwance tana fama da ciwo, murmushine yakubce mata tace Allah yasa haka, daidai lokacin tad'aga labulen d'akin zarah tashiga, curus taja bakin k'ofa tatsaya ganin zarah da tayi zaune saman lallausan carpet d'in da yake shimfid'e a tsakiyan parlourn hannunta rik'e da waya tana dannawa da ka ganta kasan tana cikin k'oshin lafiya.

'Dago kai zarah tayi takalleta tare da sakar mata murmushi sannan tace sannu da zuwa Aunty sumy, kishigo man.

Ta6e baki sumayya tayi cike da mamaki tace bashi yakawoni ba.

Zarah ma kallonta takeyi tace toh me yakawoki?

Cikin nuna isa sumayya tace wannan ba matsalarki bace malama saidai inaso ink'ara tunatar miki akan mijina babu abinda ban iyayi, dan haka a kowane lokaci kisaurareni, tana fad'in haka tajuya tafita tabar d'akin.

Zarah binta tayi da kallo har tafita sannan tayi murmushi tace Allah yashiryaki sumayya, A kullum ba zan ta6a yin k'asa da gwiwaba wajen addu'a Allah yakareni daga dukkan sharrinku.

Sumayya tana fita bata zarce ko'inaba sai part d'inta a parlour tayada zango tashiga zagaye d'akin cike da tashin hankali nan takira wayan ummanta.

Ummah tana d'aga wayan sumayya tace ummah na shiga ukku wlh waccan matsiyaciyar tana nan lafiya lau babu abinda yasameta anya kuwa ummah kin zuba mata?

A firgice sultana sadiya tace sumayya me kikace? Tana nan lafiya lau fa kikace kai ba zan ta6a yaddaba.

Gimbiya sumayya kamar tafashe da kuka tace wlh ummah tana nan babu abinda yasameta ummah gaskiya cutarki akayi ba maganin zubar da ciki bane aka baki.

Cike da jin haushi ummah tace ke gidanku sumayya da me zanji da rashin zubewar cikin ko da banzar maganarki marar amfani, ni babu wanda yacuceni wannan maganin na sanshi kuma nasan nazubar da cikine dan da anyi amfani da shi ba'ayin rabin awa sai ciki ya fita , toh inhakane ya akayi cikin nata bai zubeba?
Shuru ummah tayi tana nazari sai chan tace kenan hakan yana nufin zarah bataci k'wad'onba? Tabbas bataciba.

Sumayya cike da mamaki tace ummah kina nufin bata ciba? Toh ko tasan k'ullalliyar da kikayi matane?

Ummah girgiza kai tayi kamar tana a gaban sumayya, tace batasan komai ba akan haka saidai idan wani dalili yahanata ci.

Toh fa ummah yanzu ya za'ayi wlh banason cikinnan nata kokad'an...sumayya tak'arashe maganarta cikin kuka.

Ajiyar zuciya sultana sadiya tayi tace kidaina kuka sumayya kikwantar da hankalinki yau zansa ashirya mata wani kwad'on ni zanje da kaina inkai mata taci.

Sumayya fashewa tayi da dariya kamar ba ita bace take kuka cike da jin dad'i tace ummah hakan kawai za'ayi gaskiya da kin gama min komai dan ni yanzu wlh cikinta ya fi aurenta da yarima d'agamin hankali.

Hmm duka dai da matsala sumayya ammah dasannu zamu magance komai.

Sumayya cikin jin dad'i tace Allah yabar min ke ummana.

Dariya sultana sadiya tayi tace Ameen shalelena yanzu dai bari inje inyi abinda yadace.

Toh ummana sai najiki, nan sukayi sallama kowa yakashe wayarsa.

Sultana sadiya k'wala ma d'aya daga cikin kuyanginta kira tayi, cikin sauri tashigo jikinta yana rawa taduk'a cikin girmamawa tace ranki yadad'e na amsa kiranki.

Yamitsa fuska sultana sadiya tayi sannan tace  kije kisami baiwata sabura kice nace yanzu tahad'amin kwad'on zogale yaji kayan had'i sai takawo min nan ina jiranta.

Kuyangar tace toh ranki yadad'e angama, cikin sauri tamik'e tafita tabar d'akin.

Sultana sadiya maida kanta tayi ta jingine ga kujerar da take tana murmushin mugunta.



_Comment_
      *nd*
_Share_


_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Masha Allah my friendy *Sadiya Sidi S* Ina tayaki murnar fara sabon novel d'inki mai taken *RAYUWAR MATA* yadda kika fara lafiya Allah yasa kigama lafiya, Allah yabamu ikon d'aukan darasin da yake cikinsa, kurakuren da suke ciki Allah yayafe miki, I hrt u over dear😘_

*PAGE* 5⃣0⃣

Sultana sadiya tana nan zaune tana sak'e-sak'e a ranta a k'allah ta ci kusan minti goma sha biyar a haka, zuwan da baiwarta tayine yasa tabata izini tashigo.

Baiwar shigowa tayi d'auke da wata kula a hannunta cikin sauri tazube k'asa tana kwasar gaisuwa wajen sultana sadiya.

Sultana yatsine fuska tayi sannan ta amsa ciki-ciki, baiwar k'ara duk'ar da kanta tayi sannan tace ranki yadad'e na cika umurninki.

Sultana kallon kular tayi sannan tace bud'e mugani,
Cikin sauri tabud'e mata, tana addu'a cikin ranta Allah yasa kar sultana tace baiyiba dan tana tsoron wulak'ancinta.

Ta6e baki sultana tayi tace tashi kitafi.

Cike da jin dad'i baiwar tace toh ranki yadad'e nabarki lafiya, tana fad'in haka tamik'e cikin sauri tafita tabar d'akin.

Mik'ewa sultana sadiya tayi taje tad'auko maganin tazuba tamotse sannan tayi murmushi tace yau dai dole kicisa zarah, k'ulle maganin tayi tamaida ma'ajinsa sannan tadawo tasaka alkyabbarta tasa wata kuyangarta tad'aukar mata kular suka fito suka nufi 6angaren su zarah.

Zarah lokacin kwance take saman 3 seater tana ta juyi saboda wata irin yunwa da takeji gashi ta kasa cin komai, wayarta tad'auko takira yarima har tatsinke baiyi picking ba.

Haushine yakamata ta aje awar tana ta jan tsaki kad'an kad'an, bayan minti biyu sai ga kiransa ya shigo.

Zuba ma wayar ido tayi har tatsinke batare da tayi picking ba.

Daga chan 6angaren yarima da yafito wanka mamakine yakamasa ganin batayi picking ba kuma tsakanin kiran da tayi mai zuwa lokacin baifi 2 minutes ba, har zai k'ara kiranta a karo nabiyu sai chan 6angare d'aya na zuciyansa yace ba ajinka bane kak'ara kiranta, tsaki yaja ya aje wayan yacigaba da shirinsa ammah kuma duk da haka a cikin ransa yana jin ba dad'i dannewa kawai yakeyi dan shi abun har mamaki yake bashi ganin yadda yake ma zarah ko sumayya bata samun haka.

Lokacin da sultana sadiya ta iso part d'in zarah har a lokacin zarah tana kwance, ganin sultana sadiya yasa gabatanta yayi wani irin mummunan fad'uwa cikin ranta tsarin ubangiji take nema, koda sultana sadiya yau ma kamar jiya fuskarta a sake take.

Zarah cikin sauri tamik'e tsaye, murmushi tayi tare da d'an rissinawa tace ummah sannu da zuwa.

Sultana sadiya ma maida mata martanin murmushin tayi saida tazauna sannan tace yauwa zarah.

A k'asa zarah tazauna cikin girmamawa tagaisheta.

Amsa mata sultana sadiya tayi tace ya k'arfin jikin naki?

Zarah duk'ar da kanta tayi tace Alhmdllh ummah.

Kuyangar da sukazo tare da sultana sadiya duk'awa tayi tagaishe da zarah.

Cikin sakin fuska zarah ta amsa mata, nan sultana ta amshi kular tace tafita tajirata a waje, ahankali tace anganma ranki yadad'e sannan tamik'e cikin sauri tafita tabar d'akin.

Sultana sadiya kallonta tamaida ga zarah da take wasa da yatsun hannunta tace yau ma dai ga kwad'on na kawo miki dan nasan masu ciki akwaisu da kwad'ayi bare ma irin wad'annan kwad'on ganyukan...tak'arashe maganar tana 'yar dariya.

Murmushi zarah tayi tace toh ummah nagode sosai.

Sultana sadiya tace haba zarah ai bakomai ke da sumayya duk d'aya nad'aukeku.

Zarah ahankali tace hakane ummah Allah yasaka da alkhairi.

Ameen, kibud'e kigani man,,,cewar sultana sadiya.

Zarah bata musaba tajanyo kular tabud'e saida tahad'iyi yawu saboda kwad'on ya burgeta kamar taitaci dan ganinsa yasa yunwar da takeji ta tashi, maidawa tayi tarufe takalli sultana sadiya da tatsareta da ido tace ummah ya yi min sosai kuma nagode Allah yasaka da alkhairi.

Murmushi sultana sadiya tayi tace kar kidamu zarah, kici kawai naga kamar yunwa kikeji.

Gaban zarah saida yafad'i jin sultana ta ce taci cikin ranta tace Allah yaimin tsari da abinda kuke shiryawa akaina, itama murmushin tayi tace ummah zanci sai zuwa anjima yanzu bana jin cin komai.

Fara'ar da take fuskar sultana sadiya raguwa tayi tace haba zarah yau fa dakaina nayi kwad'on kuma nayo tattaki nakawo miki ai bai dace kik'i ciba.

Zarah marairaicewa tayi tace ummah zan ci ai inason kwad'on kawai dai nafiso sai zuwa anjima.

Sultana sadiya cikin ranta tace wannan d'iyan akwai d'an banzan wayau anya batagane abinda nayimataba? murmushi sultana sadiya tayi tace hakane ammah ko kad'anne kid'anci kiji.

Zarah kallon sultana sadiya tayi, gyad'a mata kai sultana tayi alamun taci.

Zarah ido tazuba ma kwad'on tarasa yadda zatayi tana tsoron taci asamu matsala, d'ago kai tayi takalli sultana.

Sultana sadiya tasakar mata murmushi tace kici man.

Zarah har ta kai hannu zata d'iba sai ga yarima ya shigo da sallamarsa da mamaki yake kallon sultana sadiya itama ido tazuba masa tana kallonsu dan kwata-kwata bataji dad'in zuwansaba.

Zarah hamdala tayi tare da janye hannunta daga cikin kular.

Sultana sadiya murmushi tasakar mai tace ranka yadad'e ashe kana nan ai ban saniba da na aiko ankiraka mun gaisa.

Yarima batare da ya ce mata komai ba yasamu waje yazauna, kallon Zarah yayi da take zaune gaban kula sannan yamaida kallonsa ga sultana sadiya, ahankali kamar wanda baya son magana yace ummah barka da rana?

Sultana sadiya washe baki tayi tace yauwa yarima dafatan na sameku lafiya? Ai na ji labarine wajen dada ashe amaryarmu batada lafiya shine nazo ind'an dubata.

Jinjina kai kawai yarima yayi batare da yayi maganaba,

Haushine yakama sultana sadiya cikin ranta tace ka ji dai da abunka munafuki, chan sai tace ya jikin nata?

Murmushi yarima yayi yace Alhmdllh

Kallon zarah yayi da tatsaresa da ido har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa janye idonsa yayi yamaida ga kallon dramar da ake a TV d'inta.

Wajen shuru yayi ba wanda yak'ara magana, ammah gabad'aya yarima hankalinsa yana ga zarah dan ransa ya bashi dakyar inba wani abu sultana sadiya take son shiryawaba.

Sultana sadiya ko ta cika ta yi fam takaicinta shigowar da yarima yayi batare da tasamu zarah ta ci kokad'an bane, ji take kamar tarufe yarima da duka, ganin baida niyar basu waje yasa takalli zarah tasakar mata murmushi tace dota bari intashi intafi Allah yak'ara lafiya.

Itama zarah murmushin tayi sannan tace nagode ummah, sultana sadiya kallon yarima tayi tawurga ma k'eyarsa harara sannan tace ni na wuce.

Yarima batare da ya juyo ya kalletaba yace toh ummah mungode.

Wucewa sultana sadiya tayi zata fita cikin sauri zarah tamik'e tabi bayanta koda suka fito sultana sadiya kallon zarah tayi fuskarta d'auke da murmushi tace zarah kikoma kar kibar mijinki shi kad'ai.

Zarah duk'ar da kanta tayi cike da jin kunya tace toh ummah mungode sosai Allah yabada lada,

Sultana sadiya tace Ameen.

har zarah ta juya zata tafi sai jin sultana sadiya tayi ta kira sunanta, tsayawa zarah tayi tare da juyowa.
Murmushi sultana tasakar mata sannan tace dan Allah kitabbata kinci kwad'on nan ko kin d'an samu k'arfin jikinki dan daga ganin yanayinki yunwa kikeji, na san zai taimaka miki sosai idan kikaci kinga badad'i ace kina zama da yunwa.

Zarah murmushi itama tayi sannan tace toh ummah insha Allahu zan ci.

Cike da nuna kulawa sultana tace kin tabbata?

Zarah d'agamata kai tayi alamun eh.

Murmushin jin dad'i sultana sadiya tayi tace yauwa Allah yaimuku albarka.

Zarah tace Ameen ummah, nan suka k'ara bankwana sannan zarah tajuyo tadawo part d'inta, yarima har a lokacin yana zaune inda tabarsa, ahankali tace sannu da zuwa?

Yarima batare da ya kalletaba ya amsa

Wucewa tayi tad'auki kwad'on sai a lokacin yarima yajuyo yakalleta yace ina kika sami wannan abun?

Zarah kallon kular kwad'on tayi sannan tace ummah ce takawomin.

Ta6e baki yarima yayi sannan yace kinci?
Girgiza mai kai kawai tayi alamun a'a.

Janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace ban amince kiciba.

Zarah fuskarta d'auke da mamaki tace saboda mi?

Yarima juyowa yayi yawurga mata harara sannan yace saboda hakan nayi ra'ayi.

Shuru zarah tayi batace komai ba, cikin zuciyanta tace daman ai ba ci zanyiba, chan kuma tace anya yarima baisan wani abuba game da matarnan?

Muryar yarima taji ya ce meyasa da nakira wayanki bakiyi picking ba?

Zarah cikin zucinta tace kujini da mutum saikace ba ni nakirasa bai d'aukaba, kallonsa tayi taga idonsa yana a kan tv, ahankali tace bana kusa da wayanne.

mik'ewa yarima yayi yana kallonta yace akwai abinda kike buk'atane?

Zarah kallonsa tayi tace inason cin faten tsaki.

Toh ai zaki iya sa ma'aikatanki suyi miki ko?

Zarah gyad'amai kai tayi alamun eh.

Wucewa yarima yayi zaifita cak yaja yatsaya batare da ya juyoba yace wannan abun kije kizubar a shara sannan ko nan gaba ban amince a aiko miki wani abu kiciba, duk abinda kike buk'ata kisa ma'aikatanki suyi miki indai bakya iya yi dakanki.

Zarah cike da mamakin maganarsa tace Toh.

Wucewa yarima yayi yai tafiyarsa yabar zarah nan tsaye rik'e da kula.

Bayan ya fita Wucewa tayi tashek'a ma zogalen ruwa saida tawankesa tass sannan tak'ulle a leda takira wata kuyangarta tace taje tazubar a bola ammah kar tabari kowa yaganta.

Kuyangar duk'awa tayi tace Toh ranki yadad'e sannan tamik'e tafita.

Zarah komawa tayi tazauna tare da dafe kanta tana mamakin yarima tace anya baisan wani abuba game da halin su sultana? Chan kuma tatuna da maganar jakadiya da tafad'a mata cewa yarima ko iyayensa bai cika bari suna sanin ta cikinsaba saboda yana da zurfin ciki sosai, jinjina kai tayi sannan tamik'e taje tahad'o coffee dan ji tayi fatenma duk ya fita ranta.

Ahankali tasamu tasha coffeeen ba laifi sannan tajanyo remote tacanza channel tacigaba da kallonta, ahaka har aka kira magri tamik'e taje tad'auro alwallah.

Bayan sallar isha'i saida tayi karatun alk'ur'ani sannan tamik'e taje tashiga wanka,
bayan ta fito shafe jikinta tayi da lotions masu k'amshi, powder da lipstick kawai tashafa sannan tad'auko night gown d'inta iya cinya tasaka, gyara gashin kanta tayi tafeshe jikinta da perfumes alkyabbarta tad'auko tad'aura saman kayan jikinta saida takashe gloves d'd'in d'akin sannan tafita tasallami kuyanginta tawuce tanufi part d'in yarima.

Ko da tashiga parlournsa bakowa dan haka tawuce tanufi bedroom d'insa ahankali tabud'e k'ofar kwance tahangosa tsakan makeken gadonsa ya yi pillow da hannuwansa kansa yana kallon ceiling kamar mai tunani.

Maida k'ofan tayi tarufe saida tacire alkyabbarta sannan tataka tanufi wajen bed d'insa, tsaye tayi tana kallonsa har a lokacin bai juyo yakalletaba da alama ya yi nisa cikin tunanin da yake, ahankali tahau gadon takwantasaman jikinsa tare da d'aura kanta saman faffad'an k'irjinsa, yarima sai a lokacin yakallota.

Zarah murmushi tasakar mai tare da shafa d'an siririn sajen da yake a fuskarsa, da mamakinta sai gani tayi shima ya sakar mata tsadadden murmushinsa ahankali ya d'aura hannunsa a bayanta ya rungumeta zarah ido tazuba mai inda yarima shikuma yazuba ma k'irjinta ido, sai daga baya yamaido kallonsa a fuskarta yana kallon cikin idonta sai kuma chan yamaida idanuwansa yalumshe,

Zarah murmushi tayi sannan tazame jikinta daga nashi tamik'e dan takashe masu gloves, da mamakinta sai ji tayi yarima ya rik'o mata hannu, cikin sauri tajuyo takallesa shima d'in ita yake kallo daga sama har k'asa, sun dad'e a haka sai daga baya  yajanyota tafad'o jikinsa yarungume ahankali kamar mai rad'a yace kinci abinci yau?

Zarah turo baki tayi kamar zatayi kuka tace na sha dai coffee,
hannunsa yakai yajenye mata riga yana shafar cikinta yace coffee ai ba abinci bane,

Zarah d'ago kai tayi takallesa cikin shagwa6a tace toh ai kaima shi kakesha da dare.

Yarima ido yazuba mata har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa.

Zarah maida kanta tayi takwantar a kafad'ansa sannan cikin wata irin siga tace please dear inason zuwa gida gobe?

Yarima shuru yayi nad'an lokaci sannan yace me akeyi gidan?

Zarah murmushi tayi sannan tace gobe za'ayi baikon Aysha.

Da mamakinta sai gani tayi ya yi murmushi sannan yace toh Allah yakaimu kishirya sai insa akaiki,

Cike da jin dad'i zarah tad'ago takai mai wani hot kiss a baki cikin wani irin salo wanda yakusan rikita yarima, sannan cikin wata narkakkiyar muryarta tace nagode dear, yarima wani iri yaji danma ya dake bai nuna mataba, kashe mai ido d'aya tayi tace ka gama min komai dear,

Yarima hannu yakai yashafi wuyanta ahankali yace bakomai, daga nan yagangaro da hannunsa yazame mata d'an siririn hannun rigarta wanda yasa fiye da rabin k'irjinta yafito waje, zarah ido tazuba mai ganin yadda yakafeta da manyan idanunsa, hura mai ido tayi ahankali, lumshe idonsa yayi sannan yakai bakinsa a wuyanta yafara kissing d'inta cikin wani irin salo da yarikita zarah daga nan yagangaro zuwa k'irjinta gaba d'aya yasalu6e mata rigar da take jikinta,  inda hannuwansa suka kasa tsayawa waje d'aya a jikinta, zarah ma ba'a barta a bayaba biye mashi tayi suka cigaba da faranta ma juna.


Bayan sun samu nutsu zarah a k'irjin yarima tashige tana mai kukan shagwa6a, yarima jin kukan nata yake har   ransa duk yadda yaso yashare kasawa yayi ahankali yace zarah wai me kike ma kuka haka?

Zarah k'ara tura kanta tayi cikin k'irjinsa sannan tace ni bacci nakeji

Yarima batare da yayi maganaba yashiga d'an bubbuga mata baya kad'an-kad'an, cikin sanyayyar muryarsa yace sorry my princess.

Zarah d'ago kai tayi kallesa tace princess?

Yarima shuru yayi dan shi kansa baisan kalmar ta fito daga bakinsaba, ganin ta tsaresa da ido yasa yace Zarah kikwanta kiyi bacci,

Komawa Zarah tayi takwanta tana murmushi dan har cikin ranta ta ji dad'in sunan da yakirata da shi, ahankali tace ina ma yasoni, maida idanuwanta tayi talumshe tana ji yana shafa mata baya ahaka bacci yad'auketa

Da asuba saida yai wanka yad'auro alwallah sannan yatasheta yawuce masallaci,
kayanta tamaida sannan tafito takoma part d'inta a chan tayi wanka tai sallah sannan tabi lafiyar gado takwanta.



wajen 9am zarah tafarka tayi wanka tashirya cikin tsadadden lace d'inta black colour mai ratsin red, ya yi mata kyau sosai, bayan tagama shirinta cikin jin dad'i tafito tanufi part d'in yarima, a dining tasamesa zaune cikin shirinsa yana breakfast, wajensa tanufa tajawo kujerar da take opposite d'in tasa tazauna, kallonsa tayi taga ya tsareta da idanunsa, murmushi tasakar mai tare da kashe mai ido d'aya sannan tace ina kwana?

Yarima janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace lafiya, ya jikinki?

Langwa6e kai zarah tayi tare da 6ata fuska kamar zatayi kuka tace da d'an sauk'i ammah jiya ka ban wahala sosai.

Harara Yarima yawurga mata yacigaba da breakfast d'insa,
Zarah k'unshe dariyarta tayi tare da d'an duk'ewa tace wash cikina,
Bata ankaraba sai ganin Yarima tayi ya mik'e cikin sauri ya nufo inda take, rik'ota yayi yace lafiya? Meyasami cikin?

'Dago kai zarah tayi takallesa tasakar mai murmushi tace kar kadamu dear kawai d'an motsamin yayi.

Ajiyar zuciya yarima yasafke sannan yajuya zai bar wajen, zarah ruk'o hannunsa tayi, yarima tsaye yayi batare da ya juyoba.

marairaicewa tayi tace kanason babynmu ammah bakason Zarah ko?

Yarima runtse idonsa yayi yana jin tambayartata taimai nauyi sosai a kai shi kansa baisan amsar tambayartataba, ahankali yazare hannunsa daga cikin nata sannan yace idan kin gama shirin kije zan sa akaiki gidan.

Zarah shuru tayi batace komai ba saima binsa tayi da kallo har yafita yabar d'akin,,,Zarah safke ajiyar zuciya tayi cike da tausayin kanta sannan tamik'e tashiga tagyara mai bedroom bayan ta gama tagyara mai parlour sannan tafita takoma part d'inta.

Veil d'inta red tad'auko tayafa tarik'o handbag d'inta kuyanginta biyu suka take mata baya sannan tafito, a gaban gidan taga motocin Yarima ukku jere da guards d'insa hud'u suna jiranta,

ganinta yasa sukayi sauri suka bud'e mata dank'areriyar motar da take tsakiya, Zarah tana shiga aka maida aka rufe, motar baya kuyanginta suka shiga inda guards d'in Yarima suka shiga suma nan akaja motocin ajere suka fita daga masarautar.

Koda suka isa unguwarsu Zarah wani irin nishad'i Zarah takeji dan rabonta da gida ta kwana biyu, a k'ofan gidansu akayi parking d'in motocin cikin sauri guards sukazo suka bud'e mata k'ofan tafito.




_Comment_
     *nd*
_Share_



_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Sak'on gaisuwa da jinjina agareki mrs oga, *Hauwa A Usman* nagode sosai da kulawan da nake samu daga gareki mummyn zarah, inaso kisani ko da page ko babu ke tadabance a wajena saidai ince Allah yabarmu tare Allah yasa zumuncinmu yad'aure har jikokinmu I hrt u more dear❤_

*PAGE* 5⃣1⃣

Zarah tana fitowa nan kuyanginta suka take mata baya har cikin gidansu, Zarah dagudu ta isa wajensu mama da suke zaune suna 'yan soye-soye, jikinmama tafad'a tace cikin murna tace oyoyoo mamana.

Mama ma rungumeta tayi cikin jin dad'i tace oyoyoo Zarah na.

Yaya rauda kallon Zarah tayi tace ikon Allah kedai har yanzu baki girmaba.

Zarah turo baki tayi cikin shagwa6a tace yaya rauda na fa kwana biyu banga mamanaba, mama janye Zarah tayi daga jikinta tace rabu da ita zarahna,

Daidai lokacin kuyangin zarah suka iso  suka duk'a cikin  girmamawa suka gaishe da su mama
Cikin sakin fuska su mama suka amsa musu tare da tambayarsu gida sukace Alhmdllh, kallonsu zarah tayi tace zaku iya tafiya amaidaku gida, duk'awa sukayi sukace to ranki yadad'e angama, mama leda tasamu tak'ulla musu su donut tabasu, nan sukayi sallama da su mama sannan suka mike suka tafi.

Zarah kallon mama tayi da tazuba mata ido, murmushi Zarah tayi tare da duk'awa tagaishe da ita.

Mama amsa mata tayi cikin sakin fuska tare da tambayarta mijinta da mutanen gida
Zarah cikin jin kunya tace duk suna lafiya mama.

Juyowa tayi tana dariya tace yaya rauda ina kwana? Harararta yaya rauda tayi tace yanzu k'arfe sha biyu zaki kira mana kwana.

Afuwan yaya rauda ina wuni?
Murmushi yaya rauda tayi tace lfy lou ya gidan?
Zarah tace Alhmdllh komai daidai.

Sai a lokacin zarah taji k'amshin soyen ya daki hancinta, yamitsa fuska tayi jin zuciyanta yana shirin tashi tace wai banga amaryaba,

Mama tace tana nan d'aki tana k'ullah kunun aya, cikin jin dad'i zarah tace wow bari inje insha har na ji ina son sha, cikin sauri tawuce tanufi d'akin.

Mama da yaya rauda binta sukayi da kallo cike da sha'awa dan ko ba'a fad'a musuba sunsan zarah cikine da ita.

Tana shiga d'akin taja tatsaya, Aysha da take zaune tana k'ullin kunun aya ganinta yasa tataso dagudu tarungumeta tana oyoyoo Aunty zarah, zarah ma dariya tayi tace ke zaki karyani ni sakanni,

Aysha janye jikinta tayi tana dariya tare da zuba ma zarah ido tace Auntyna kinga yadda kika koma kamar ba keba

Murmushi zarah tayi tace ke banson tsokana, amaryarmu ya shirye-shiryen bikki? Allah yasa kar asa mana bikkin nesa.

Dariya Aysha tayi tace wlh Aunty zarah nima addu'an da nake kenan.

Da mamaki zarah takalleta tace lallai Aysha ashe bakida kunya toh Allah yakyauta,,,,tana fad'in haka tawuce tanufi wajen kunun ayan tabar Aysha tana ta dariya.

Zarah zubawa tayi sosai tasha har saida taji ta k'oshi sannan tabarshi.

Duk yadda taso tataya su mama girki kasawa tayi saboda k'amshin tayarmata da zuciya yake, dole tahak'ura tayi zamanta.

Abbah ma koda yadawo ya yi murna sosai da ganin 'yar tasa.

Wajen k'arfe ukku 'yan neman aure sukazo anmusu tarbar mutunci, inda aka tsaida maganar akan nan da watanni hud'u masu zuwa.

Sun kawo su biscuits su alewa bakin gwalgwado sun bada sai kud'in nagani inaso da na neman aure.


ko da abbah yazo musu da labarin su mama sunyi murna sosai nan sukaita fatan alkhairi.

Nan aka zauna aka k'ullah kayan aka d'ibi na dangi sannan aka aika mak'ota nasu.

Mama duk yadda taso zarah taci abinci k'iyawa tayi daga k'arshe saidai tabada aka siyo mata awara nan tazauna taci.


Bayan sallar isha'i suna zaune suna hira zarah handbag d'inta tabud'e tad'auko dubu d'ari biyu tamik'a ma abbah tace gashinan Abbah ko kayan kitchen anfara siya mata.

Abbah girgiza kai yayi yace a'a zarah akwai kud'i hannuna dan na ware wanda zan cika incanza mana gida, kud'in da suka rage ne nasamu nabud'e shago ina kasuwanci dasu nakeso inmata siyayyarta.

Zarah cikin jin dad'i tace hakane Abbah ammah dan Allah kataimaka ka amsa kuk'ara sai asamin albarka.

Kar6a yayi nan sukaita sa mata albarka.

Aysha da take cikin d'aki tana waya fitowa tayi takalli zarah tana murmushi tace Aunty zarah kizo kugaisa da malam bello yana nan k'ofan gida.

Zarah girgiza kai tayi tace a'a Aysha kinga ban tambayaba, marairaicewa Aysha tayi tace iyakarki fa zaure nan zaku gaisa,,,tafad'i haka tare da mik'ama zarah gyalenta.

Zarah kar6a tayi tayafa ba dan tasoba tamik'e tabi bayan Aysha.

Daga waje suka hangosa tsaye zarah wajen k'ofar gidansu tatsaya, malam bello kallo d'aya yaimata yad'auke kai fuskarsa d'auke da murmushi yak'araso wajen da suke yana mai cewa a'ah ashe yayarmuce.

Murmushi zarah tayi tace malam ina wuni?
Lfy lou zarah ya gida da mai gidan.

Cikin jin kunya tace kowa yana lafiya, kallon Aysha tayi da taketa murmushi tace malam ga dai amanar k'anwatanan akularmin da ita.

Dariya malam bello yayi yace kar kidamu yayarmu insha Allahu zanyi  iya bakin k'ok'arina.

Zarah cikin jin dad'i tace Allah yasa malam mungode sosai, Allah yakaimu lokacin.

Gabad'ayansu sukace Ameen.


Daidai lokacin motar yarima ta iso wajen da suke, yana yin parking saida gabansa yafad'i ganin zarah tsaye da wani, baima lura da Aysha ba datake gefe, suna had'a ido da zarah wata irin harara yawurga mata, zarah saida gabanta yafad'i cikin ranta tace nashiga ukku, dakewa tayi tataka ta isa inda yake fuskarta d'auke da murmushi tabud'e mai k'ofan tace sannu da zuwa.

yarima wani irin kallo yaimata yace wanene wancan kuke tare da shi?

Koda ta tsorata da hararar da yai mata ammah tadake tayi murmushi sannan tace mijin da Aysha zata aurane...shine dan bakida hankali kike tsaye da shi ke kad'ai kina ta yimai dariya?

Zarah da mamaki takallesa tace bafa ni kad'ai bace baga Aysha chan ba.

Sai a lokacin idonsa yakai ga su Aysha dasuke tafowa inda suke, ajiyar zuciya yasafke sannan yafito daga motar daidai lokacin su Aysha suka iso wajen da suke,

malam bello cikin girmamawa yarussina zai gaishe da yarima.

Cikin sauri yarima yarik'o hannunsa sukayi nusabaha fuskarsa a sake yace Allah yasa alkhairi ango,
Malam bello duk'ar da kansa yayi cikin girmamawa yace Ameen ranka yadad'e nagode,
Aysha ce tace yayana ina wuni?

Kallonta yayi fuskarsa a sake yace k'anwata kin wuni lafiya? Sai mukaji labari, Allah yasa alkhairi,

Aysha cikin jin kunya tarufe fuskarta, malam bello ne kawai ya amsa da Ameen.

Dariya zarah tayi tace magulmaciya kawai.
Yarima kallon zarah yayi yace menene kuma abun gulma? Daga tana jin kunyan yayanta.

zarah fari taimashi da ido.
Yarima janye idonsa yayi daga kallonta yace k'anwata bari mushiga ciki ingaishe da su abbah.

Aysha murmushi tayi tace toh yayana afito lafiya.

Zarah jerawa sukayi da Yarima suka shiga gida inda sukabar malam bello da Aysha suna ta hirarsu.

Koda sukazo shiga yarima ja yayi yatsaya, zarah kallonsa tayi tana shirin yin magana yace muje mana.

Zarah murmushi tayi sannan tawuce gaba yarima yabi bayanta har suka shiga cikin gida, har a lokacin su mama suna zaune tsakar gida, zarah tabarma tad'auko tashimfid'a mashi yazauna cike da girmamawa yagaishe da su abbah,

Fara'a bayyane a fuskarsu suka amsa mashi tare da tambayarsa mutanen gida, yarima saddar da kansa yayi k'asa yace Alhmdllh, Ya hidima?

Alhmdllh,,cewar su abbah.
Masha Allah, Allah yasa alkhairi, Allah yakaimu lokacin.

Cikin jin dad'i suka amsa da Ameen y rabb.

Yaya rauda kallonsa tayi tace ranka yadad'e barka da dare.

Murmushi yarima yayi yace yayarmu anwuni lfy?

Yaya rauda tace lafiya lou Alhmdllh, y hak'uri da mu?

Murmushi kawai yarima yayi.

Zarah mik'ewa tayi taje tad'auko abinci takawo mai, ganin haka yasa su abbah suka tashi suka bashi wuri dan yasamu yaci.

Bayan su Abbah sun tashi zama tayi gefensa dan tazuba mai, kallonta yarima yayi yace kindai san bana cin abinci da dare.

Zarah ma 6ata fuska tayi takallesa kamar zatayi kuka tace abincin gidan namu ma bazakaciba?

Yarima kallon kunun ayan da takawo mai yayi yace zuba min wannan dai.

Toh tace sannan tatsiya mai a cup tamik'a mai, kar6a yayi yafara sha kad'an kad'an, wayarsa da ya aje gefe zarah tad'auka tana wasa da ita, yarima baice mata komai ba ahaka har yashanye, kallonsa tayi tace ko ak'ara ma?
Girgiza kai yarima yayi sannan yace kije kiyi ma su mama sallama kizo mutafi dare yakeyi.

Mik'ewa Zarah tayi, yarima kallonta yayi yace wai ke yau kin ma ci abinci?

Zarah yamitsa fuska tayi tace na dai ci awara.
Shuru yarima yayi baice komai ba,

wucewa tayi taje tasanar da su mama zasu tafi nan tafito tare da su mama,
Nan suka yi sallama suka fito daidai lokacin Aysha zata shigo gida, kallonsu tayi tace ba dai tafiya zakuyiba.

Yarima murmushi yayi yace ko mukwana?
Dariya Aysha tayi tace eh ranka yadad'e.

Zarah kallonta tayi tace ina angon har ya tafi?

Susa kai Aysha tayi cikin jin kunya tace uhm.

Dariya Zarah tayi nan Aysha tarakasu har wajen mota sukayi bankwana takoma gida.

Tunda suka fara tafiya tsit motar tayi, ahankali yarima yajuyo yakalli zarah da tajingine kanta a sit d'in da take zaune ta zuba ma waje d'aya ido kamar mai tunani, janye idonsa yayi daga killonta yacigaba da tuk'insa duk sai yaji babu dad'i yanayin da yaganta.

Ahankali yace akwai abinda kike buk'atane?

Zarah juyowa tayi takallesa taga ba ita yake kalloba idonsa yana a titi, shuru tayi tana kallonsa jin tayi shuru yasa yarima yad'an juyo yakalleta karaf suka had'a ido, zarah duk'ar da kanta tayi sannan tace ice cream nakeson sha.

Yarima janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace meyasa kikeson shan kayan sanyi, ya kamata kidaina tunda yanzu ba ke kad'ai bace.

Zarah 6ata fuska tayi kamar zatayi kuka tace toh.

Yarima saida yabiya yasiyo mata sannan suka wuce gida, yana yin parking Zarah tabud'e tafita, kallonta yarima yayi yace wannan fa wa zai kawo miki?

Murmushi Zarah tayi tace sorry mancewa nayi nan tad'auka sannan tawuce cikin gida.

Yarima ma fitowa yayi yawuce fada dan sugaisa da memartaba.

___________

A 6angaren sultana sadiya ranta a 6ace takoma part d'inta a parlour tatarar da sumayya zaune tana jiranta dan sumayya tunda taga shigar sultana part d'in zarah yasa tafito tazo turakar iyayenta dan tasamu labari wajen ummanta idan tadawo,, ganinta yasa sumayya tamik'e cikin murna tace ummana angama komai ko?

Kallonta sultana sadiya tayi tare da jan tsoki tace sumayya wanchan banzan mijin naki ya 6ata min duk wani plan nawa.

Sumayya a tsorace tadafe k'irji tace ummah kar dai kicemin asirinmu ya tonu?

Sultana sadiya zama tayi saman kujera cikin 6acin rai takwashe komai tafad'a ma sumayya duk abinda yafaru.

Sumayya ajiyar zuciya tayi sannan tace ummah wlh banji dad'in faruwar hakanba, yanzu saboda Allah ido zansa mata har tahaihu? Yanzu ita zata aje ma yarima magaji?,,,sumayya tafad'i haka tare da fashewa da kuka, cikin kuka takalli sultana sadiya da abun duniya yadameta tace ummah ko kid'au mataki ko kar kid'auka wlh ba zan ta6a barin zarah ba sai naga bayanta.

Sultana sadiya jawota tayi tazaunar da ita gefenta tace sumayya banaso kije kiyi abinda zai jawo abinda za'ayi da ansani,

Sumayya shigewa tayi jikin ummanta tana kuka tace ummah a kullum ina fad'a miki bandamu da abinda zai faruba indai burina ya cika.

Sultana sadiya d'ago kan sumayya tayi tana share mata hawaye tace kidaina cewa haka sumayya  kibari abi komai a sannu, sumayya mik'ewa tayi tana ja da baya tace a yaushe duk za'ayi hakan bayan ta haihu? Girgiza kai tayi tace ummah kibarni kawai, tana fad'in haka tajuya tafita daga d'akin.

Sultana sadiya k'walah mata kira tashiga yi ammah ina sumayya tafiyarta tayi.

Dafe kanta sultana tayi tace wannan wace irin rayuwa ce?

Sumayya koda takoma part d'inta batabi ta kuyanginta da suke gaishetaba dagudu tashige bedroom d'inta tamaida tarufe, jingine kanta tayi da k'ofar tashiga rusa kuka, tana jin wayanta tana ringing tashare tacigaba da kukanta, daga k'arshe takoma saman gadonta takwanta nan tak'ara sautin kukanta saida taji kanta ya fara ciwo sannan tatsagaita kukan nata.

Wasa-Wasa ciwon kai da zazza6i suka rufeta haka tajanyo blanket tarufa ahaka tayi ta juyi har cikin dare sai daga baya bacci yayi awon gaba da ita.

Da safe ko da kuyangarta zabba'u tazo tayita knocking jin shuru yasa tatura k'ofan tashiga cikin sauri ta isa inda Sumayya take k'udundune da bargo tana rawan sanyi,

Kallonta zabba'u tayi a firgice tace ranki yadad'e mi yasameki?

Sumayya dakyar tabud'e baki muryarta na fita ahankali tace je kikira min yarima.

Cikin sauri zabba'u tamik'e tace toh ranki yadad'e.

Yarima zaune yake yana breakfast inda zarah take gefensa tana shan ruwan lipton wanda yasha kayan yaji, knocking d'in k'ofa akayi zarah kallon Yarima tayi da yature cup d'in tea d'insa gefe yamik'e saida yabaro dining area sannan yace yes,

Guards d'insane yabud'e yashigo saida yad'an russuna sannan yace ranka yadad'e gimbiya sumayya ce tayo aike,

Yarima saida yazauna saman cushin sannan yabashi izini yabarta tashigo.

Kuyanga zabba'u koda tashigo zubewa tayi k'asa takwashi gaisuwa wajen yarima, hannu kawai yarima yad'aga mata, zabba'u k'ara duk'an da kanta tayi tace ranka yadad'e daman gimbiya sumayya ce batada lafiya tana chan kwance yanzu haka ita ta aikoni inzo insanar da kai.

Zarah jin an ambaci sumayya batada lafiya yasa tamik'e tabaro dining area,
yarima nuni yayi mata alamun tatafi, zabba'u k'ara duk'awa tayi takwashi gaisuwa sannan tamik'e cikin sauri tabar d'akin.

Zarah kallon yarima tayi da yamik'e cike da jin tausayi tace meyake samunta?

Shima yarima kallonta yayi yace bari inje indubata, Zarah bayansa tabi tace muje tare.

Yarima baice komai ba nan suka fito suka nufi part d'in sumayya duk inda suka ratsa bayi da Kuyangi duk'awa suke suna kwasar gaisuwa,

ko da suka shiga parlournta nan ma kuyanginta suka zube suka gaishesu, hannu yarima yad'aga musu cikin sauri suka fita sukabar d'akin.

Bedroom d'inta suka nufa, nan Zarah tayi knocking d'in k'ofan, zabba'u da take tsugunne k'asa tana jera ma sumayya sannu, mik'ewa tayi taje tabud'e k'ofan ganin su yarima ne yasa cikin sauri taja gefe tare da d'an rissinawa tace ranka yadad'e sannunku da zuwa,

Yarima baibi takantaba yawuce yanufi wajen bed d'in sumayya, cikin sauri zabba'u tafita tabar d'akin.

Zarah ma bayansa tabi suka isa, sumayya d'ago kai tayi takalli yarima sai hawaye, daga gefen gadon yarima yazauna yace sumayya bakida lafiya? Meyake samunki.

Sumayya d'agowa tayi tarungume yarima tare da fashewa da kuka,
jikinta yaji da zafi ahankali yace zazza6i kike? Gyad'a mai kai tayi, sorry yace nan yashiga shafa bayanta.

Zarah da take tsaye kamar zatayi kuka saboda tausayi, cikin muryar tausai tace sannu Aunty sumayya ya jikin naki?

Sumayya cikin sauri tad'ago takalli Zarah dan kwata-kwata bata lura da itaba, duk ciwon da takeji ammah hakan baihata wurga ma Zarah hararaba sannan takoma jikin yarima talafe.

Tsaye Zarah tayi duk jikinta ya yi sanyi,

Yarima janyeta yayi daga jikinsa tare da maidata yakwantar yace bari inje ind'auko drugs kinji?.

Gyad'a mai kai sumayya tayi, mik'ewa yayi yakalli Zarah yace kisa ahad'a mata breakfast bari indawo.

Toh Zarah tace sannan takalli sumayya da taketa rawar zazza6i tace Aunty sumayya Allah yasauke.

Banza sumayya tayi takyaleta, Zarah bata damuba tawuce nan tasa kuyangin sumayya suka had'o mata breakfast takar6a tadawo bedroom d'in, a saman bedside ta aje sannan takalli sumayya tace intaimaka miki kitashi kiyi breakfast d'in?

Kallonta sumayya tayi cikin tsana tace ba ruwanki da ni malama.

Daidai lokacin yarima yadawo kallon Zarah yayi yace batayi breakfast d'inba?

d'aga kai kawai Zarah tayi batare da ta yi magana ba.

Yarima wucewa yayi yazauna gefen gadon yace sumayya kitashi kiyi breakfast sai kisha drugs.

Yamutsa fuska sumayya tayi tace na k'oshi, taimaka mata yarima yayi tatashi zaune yace kidaure kici ko kad'an ne.

Sumayya jikinsa tafad'a tace ni bana iya ci,
Kallon Zarah yayi da take tsaye yace zuba mata breakfast d'in.

Zarah toh tace sannan tazo tazuba chips cikin plate sannan tahad'a tea mai kauri tamik'a mai cup d'in.

kar6a yarima yayi sannan yace ma sumayya kidaure kisha ko kad'anne, sumayya ganin yadda yarima yake lalla6ata yasa ta amince zatasha dan tasan halinsa idan yaga tana haka zai iya shareta yayi tafiyarsa, haka tabud'e baki yashiga bata tanasha ahankali tana k'ara langwa6ewa saida yaga ta d'an sha nakirki sannan yabarta,

Kallon zarah yayi da take rik'e da plate d'in chips tana yamitsa fuska dan k'amshin ya fara isarta, ganin haka yasa yarima yakar6i plate d'in yad'aura saman bedside nan yad'auki fork yad'ibo yafara bata, kad'an taci nan yabata drugs d'in tasha.

Zarah cike da tausayi tace sannu Aunty sumayya, banza sumayya tayi tak'yaleta.
ganin haka yasa yarima yace sumayya tana miki magana fa.
Wani irin kallo tayi ma zarah sannan ciki-ciki tace yauwa.

Yarima ganin tana shirin komawa takwanta yace sumayya kitashi kid'an watsa ruwa ko kinji dad'in jikinki.

sumayya langwa6e kai tayi tace toh kataimaka min ban iya yi.

yarima kallon zarah yayi da take kallonsu, murmushi tasakar mai tace bari inje inhad'a mata ruwan wankan, bata jira jin abinda yarima zaiceba tamik'e tanufi toilet d'in sumayya.

yarima binta yayi da kallo har tashige sannan yamaida kallonsa ga sumayya da tatsaresa da ido ganin yadda yake bin zarah da kallo Wani irin takaici yacikata.

Ahankali yace akwai abinda kike buk'ata?
Girgiza kai kawai sumayya tayi, daidai lokacin zarah tafito daga toilet d'in kallon yarima tayi tace ga ruwan chan na had'a,
Yarima kallon sumayya yayi yace muje kiyi wankan.

Marairaice fuska tayi kamar zatayi kuka tace bana iya tashi jiri nakeji please kad'aukeni,,,tafad'i hakan tare da kallon zarah.

zarah d'auke kanta tayi kamar bataji abinda taceba.
Yarima shuru yayi kamar ba zaiyiba, zarah juyowa tayi takallesa nan suka had'a ido, cikin rashin damuwa tasakar mai murmushi ,  janye idonsa yayi daga kallonta babu yadda ya iya haka yad'auki sumayya yanufi toilet da ita.

zarah tana ganin sun shige bata kawo komai a rantaba nan tagyara mata bedroom d'inta tas sannan tafita takoma part d'inta.



_Comments_
      *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

*PAGE* 5⃣2⃣

Koda suka fito daga toilet d'in da mamaki yarima yaga zarah bata d'akin ammah ko'ina angyarsa fes room d'in sai k'amshi yake, murmushi yayi dan ya san ko ba'a fad'aba toh aikin zarah ne.

Ita kanta sumayya saida tayi mamaki dan bata ta6a tunanin haka daga zarah ba.
Ta6e baki tayi cikin ranta tace gulmammiyar kawai duk dai abinda zakiyi bazanta6a fasa k'udirinaba akanki, muryar yarima taji ya ce muje kizauna.

Haka yarik'ota sukaje bakin gado yazaunar da ita, marairaicewa tayi tace please kashiryani.

Wani irin kallo yayi mata yace shiryawarma bazakiyi da kankiba?

K'wallah ce tacika mata ido tace kaga fa banda lafiya, Banza yarima yaimata nan yamik'e yaje yabud'e wardrobe d'inta yad'auko mata kaya, saida yashafa mata lotion sannan yataimaka mata tasaka kayan.

Komawa tayi takwanta yarima kallonta yayi yace bari intafi hospital

Sumayya cikin muryar tausayi tace yau bazaka hak'uraba?, kaga fa banda lafiya.

Wani irin kallo yarima yaimata sannan yace zan turo miki kuyanginki in akwai abinda kikeso sai sutaimaka miki,, yana fad'in haka yajuya yafita yabar d'akin.

Sumayya ba haka tasoba cikin ranta tace ammah da wacchan gajarce ai da ka zauna,,nan tak'ara jin wata irin tsanar zarah, knocking d'in k'ofa da akayine yasa tabada izinin ashigo.

Kuyanginta ne suka shigo nan suka zube suna kwasan gaisuwa wajen shugabartasu tare da yi mata ya jiki.

Sumayya fuskarta ba yabo ba fallasa ta amsa musu sannan tace sufita subata waje tana son hutawa, cikin sauri har suna rige-rige suka fita sukabar d'akin.

Nan Sumayya tagyara kwanciyarta dan Wani irin bacci takeji, ahaka bacci yai awon gaba da ita.



Bayan sallar la'asar zarah fitowa tayi tanufi part d'in Sumayya dan tadubata da jiki.

Lokacin Sumayya tana Kwance suna waya da zinat dan tunda tafarka baccin taji zazza6in ya safka dan har wanka tasamu tayi taci abinci sannan tasha drugs d'in da yarima ya aje mata.

knocking zarah tayi ahankali, Sumayya jin ana knocking yasa tabada izinin shigowa dan tayi tunanin ko kuyangintane.

Ahankali zarah taturo k'ofar tashigo tare da yin sallama,,, ganinta yasa fara'ar da take fuskar Sumayya tagushe ahankali tace baby ina zuwa bata jira jin abinda zinat zataceba takashe wayan tana kallon zarah a wulak'ance, cikin d'aga murya tace me yakawoki part d'ina?.

Zarah murmushi tayi tace Aunty Sumayya ya jikin naki?

Harara tawurga mata tace wannan ba damuwarki bane kar kik'ara shiga sabgata ke ni ko ganinki banason yi saboda bana sonki na tsaneki,

Zarah da mamaki take kallonta ahankali tace Sumayya har ga Allah ni da zuciya d'aya nake zaune da ke kuma inaso kisani ni ban iya irin wannan zamanba dan ita rayuwa duka nawa take.

Tsawa Sumayya tayi mata tace ke kifita idona duk wani dad'in bakinki bazaiyi tasiriba akaina kuma wannan cikin da kike tak'ama da shi ke kina jin dad'i zaki haifarma yarima magaji toh indai ina numfashi bazaki ta6a haihuwarsaba.

zarah bataji haushin kalaman da Sumayya tafad'aba dan idan da sabo toh tasaba jin irinsu, Ta6e baki tayi tace Sumayya kenan ciki Allah ne yabani kuma shikad'ai zai iya ikonsa akan abunsa ni na yarda da k'addara duk abinda yasameni nasan *DAGA ALLAH NE* bazan ta6a jayayya da ikon Allah ba dan shi musulmi anaso yadinga yarda da k'addara mai kyau ko marar kyau, dan haka *K'ADDARA CE* kawai zatasa cikin nan yabar jikina.

Sumayya har ta bud'e baki zatayi magana sai ga yarima ya bud'e k'ofa, cikin sauri tafashe da kukan k'arya tace yanzu saboda Allah zarah ni zakiyi ma gorin haihuwa?

Zarah mamakine yacikata cikin sauri takalli yarima da yake gefe wata irin harara yawurga mata.

Sumayya dasauri tataso tazo tafad'a jikinsa tana kuka, cikin sheshek'ar kuka tace yarima kana jinta tana min gorin ciki ni dan Allah bai baniba.

Yarima tausayinta yaji nan yarungumeta jikinsa,, zarah  mutuwar tsaye tayi dan bata ta6a tunanin makircin Sumayya ya kai hakaba,,, k'wallah ce tacika mata ido muryarta tana rawa tace please yarima kafahimceni wlh ba haka bane.

Wani kallo da yarima yaimata zarah saida takusan sakin futsari cikin 6acin rai yace kin kyauta gorin ciki kikayi mata, shin ke wayonki ko dubararki suka baki?,

Zarah matsowa tayi tace yarima kar kayarda da maganarta wlh duk abinda tafad'a ba haka bane.

Hanya yarima yanuna mata yace kifita tun kan ranki ya6aci.

Zarah kallon Sumayya tayi da take manne a k'irjin yarima tana mata gwalo, juyawa tayi tafita tabar d'akin cikin 6acin rai tare da nadamar zuwanta.

Sumayya tana ganin zarah ta fita nan tasake fashewa da wani sabon kukan, cikin kuka tace yarima kana jin abinda tacemin ko, daman mutum yana ba kansa haihuwa?

'Dagota yayi daga jikinsa cike da tausayinta yace Sumayya kidaina cewa haka kiyi hak'uri ita haihuwa ubangiji shi yake bayar da ita ga wanda yaso sannan kuma shi yake hana wanda yaso, a tsawon dad'ewarmu kin ta6a gani na nuna damuwata dan baki haihuba?

Girgiza kai Sumayya tayi,
yace gud, dan haka kar kik'ara damuwa kema Allah bai mance da keba in da rabo zaki haihu.

Sumayya rungumesa tayi cikin jin dad'in maganarsa tace na gode sosai ranka yadad'e....A chan k'asan zuciyanta kuma cewa tayi koma me zakace bazan ta6a amincewa waccan jakkar tarigani haihuba  dole ind'au mataki akan cikinnan nata.

Yarima janyeta yayi daga jikinsa tare da tallabo fuskarta suka k'ura ma juna ido, murmushi sumayya tasakar mai.

Yarima har ya bud'e baki zaiyi magana nan wayansa tafara ruri, ganin daddynsane yasa yasaki sumayya tare da d'an matsawa kad'an sannan yayi picking d'in wayan tare da yin sallama.

Daga chan 6angaren sultan Ahmad amsa masa yayi.

Yarima cikin girmamawa yagaishe da mahaifin nasa, nan sultan Ahmad ya amsa masa sannan yace yarima kana ina yanzu?
Ina gida daddy,,,cewar yarima.
Kazo yanzu kasameni.
Toh daddy.
Juyowa yayi yakalli sumayya da tatsaresa da ido yace ni na wuce.

Sumayya cikin rashin jin dad'i tace Toh.
Nan yarima yafita yabarta.

Sumayya tana ganin fitarsa nan tabushe da dariya cikin jin dad'i tace lallai yarima da ni kakeja ai wlh ba abinda zai hanani d'aukar k'wak'waran mataki akan wannan bagidajiyar matar taka, yanzu ko tana ina? Nasan dai ana chan ana ta kuka,,,nan ma Sumayya tayi dariyar jin dad'i sannan tawuce taje tabud'e bedside d'inta tad'auko wani pills tasha sannan tahau saman gadonta tajanyo wayarta takira zinat nan sukacigaba da wayansu.


Zarah bayan ta bar part d'in gimbiya Sumayya nata takoma tana shiga bedroom d'inta tamaida tarufe, saman gadonta taje tazauna tadafe kanta mamakin makircin da Sumayya tayi matane yadameta, maganganun da yarima yafad'a matane suka cigaba da yawo cikin kunnuwanta.

Ita ba komai tafi ji ba sai yadda yarima yayarda da maganar da yaji Sumayya ta fad'a , ba abinda yafi 6ata mata rai irin taga yarima yana fushi da ita.

Duk yadda taso tadanne kukan da yake cinta kasawa tayi nan tarushe da kuka,,,,haka tasha kukanta tak'oshi sannan tamik'e taje tawanke fuskarta tare da d'auro alwallah nan tazo tashimfid'a darduma tad'auko alk'ur'aninta tacigaba da karantawa dan samun sauk'in k'uncin da takeji a zuciyanta.

Tana nan zaune har aka kira sallar magrib tayi sallah.



Bayan sallar isha'i wanka taje tayi tai shirin baccinta tahaye saman gadonta takwanta.

Yarima kasancewar fita sukayi da su daddy basu dawo gida ba sai around 9pm, koda suka dawo part d'in sumayya yawuce dan yadubata, lokacin da yashiga kwance yatarar da ita tana waya, ganinsa yasa tayi saurin janye wayar a kunnenta tare da sakar mai murmushin rashin gaskiya.

Kallonta Yarima yayi yace dawa kike waya?
Gabantane yafad'i chan dabara tafad'o mata tace am daman ummah ce muke waya da ita ta kirani ne tayi min ya jiki.

Ta6e baki yarima yayi sannan yace ohk, ya jikin naki ina fatan dai yanzu yai sauk'i dan naga tun d'azun zazza6in yasafka?

Sumayya langwa6e kai tayi Sannan tace dasauk'i.

Yarima duba agogon da take manne a hannunsa yayi sannan yace ohk, Allah yak'ara sauk'i, kikwanta kiyi bacci.

Murmushi sumayya tasakar mashi sannan tace toh dear Allah yakaimu.

Ciki-ciki yarima yace Ameen sannan yafita yabar d'akin.

Sumayya na ganin ya fita tajanyo wayarta takanga a kunne tare da cewa baby kina jinmu da mutumin?

Zinat da ta saurari duk hirarsu dariya tayi tace ina jinki baby da wannan munafukin mijin naki ai bari inzo garin wannan cikin da yake tak'ama za'a haifa mai sai munga bayansa.

Dariya sumayya tayi tace baby ina fa jin haushi idan kina ce ma mijina munafuki.

Daga chan 6angaren ta6e baki Zinat tayi tace yoh wanene inba munafukinba ai tunda har ya amince yayi miki kishi toh na gama ganinsa da mutunci.

Murmushi sumayya tayi tace kina sa ina jin haushi in kina tunomin da waccan bagidajiyar.

Dariya zinat tayi tace ai wlh bari inshigo garin zata gane kurenta, dear yanzu dai kikwanta kiyi bacci dare keyi.

Sumayya kallon agogon da take manne a bangon d'akin tayi tace nasan dai yanzu akwai abinda zakiyi saisa kike korata.

Dariya zinat tayi tace yoh mefa zanyi.

Hmm kedai kika sani wlh nasan bakida gaskiya, yanzu dai kije kar intsaidake....sumayya na fad'in haka tayi switching off d'in wayanta tana dariya ta aje saman bedside sannan tagyara kwanciyarta tare da kashe gloves.

A 6angaren yarima koda yakoma part d'insa bayan ya yi shirin bacci kwanciyarsa yayi, zarah ce tafad'o masa a rai, wani irin haushi yaji lokacin da yatuna gorin haihuwan da tayi ma sumayya, tsaki yaja sannan yajuya yayi kwanciyarsa.


Tun daga ranar zarah take 6oye kanta a room d'inta dan bata yadda kwatakwata suhad'u da yarima koda abun yana damunta kawai dai daurewa take.

yarima ma shi kansa daurewa kawai yakeyi duk yadda zaiji yanason ganinta danne zuciyansa kawai yake koda daman shi a tunaninsa ba ita yakeson ganiba saboda babynsa da yake manne a cikintane kawai yasa yake jin kewarta.


Sumayya ko gaba takaita dan tunda tafahimci yarima da zarah basu jituwa nan wani irin farin ciki yadabaibayeta dan hakane ma tatsiri k'ara shige ma yarima dan ma baya bata had'in kai sosai.


*BAYAN SATI 'DAYA*

Yarima ne zaune d'akinsa yana cike wasu files, wayansa yad'auko yakira abban sumayya bayan sun gaisa yake tambayarsa sauran files d'in, daga chan 6angaren abbah cewa yayi ai d'azun da sumayya tashigo nabata tabaka halan bata bakaga?

Murmushi yarima yayi cikin girmamawa yace abbah ina tunanin mantawa tayi bari inmata magana.

Sultan Abbas yace toh lafiya lau kome kenan sai kakirani.

Yarima yace toh abbah nagode sosai.

Bayan sun gama wayan yarima lalubo number d'in sumayya yayi yakirata ammah har tak'arashi ringing batayi picking ba, tsaki yayi yace ko ina taje ta aje wayar....mik'ewa yayi yafito yanufi part d'in sumayya a parlournta kuyanginta ne kawai cikin girmamawa suka zube suna kwasar gaisuwa yarima baibi ta gaisuwar da sukeyi masaba yace sumayya fa?

'Daya daga cikinsu ce tace ranka yadad'e tana cikin d'akinta, wucewa yarima yayi yashiga bedroom d'inta da mamakinsa yaga babu kowa motsin ruwan da yaji a toilet ne yasa yagane wanka take, waje yasamu a gefen gadonta yazauna, abinda yahangone saman bedside d'inta yasa yamik'e yanufi wajen da mamakinsa, tsaye yayi kamar wanda ruwa yaci sai chan yakai hannu yad'auko saida yarazana da yaga drugs jibgi guda, d'aya bayan d'aya yad'auka yana dubawa inda zuciyansa tashiga bugawa da k'arfi, daidai lokacin sumayya tafito daga wanka dan saurin da take kenan tazo takwashe gudun kar yarima yashigo yagani, tsaye tayi kamar wadda ruwa yaci tsoro da fargaba duk suka cikata.

Yarima juyowa yayi yalalleta da idanuwansa da suka rine suka koma launin ja saboda 6acin rai..




_Comments_
     *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
   👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

*PAGE* 5⃣3⃣

Sumayya hawaye ne suka fara zuba daga idonta cikin muryar kuka tace please yarima kafahimceni wlh ba abinda kake tunani bane, sharrin shaid'anne kawai.

Wata uwar harara yabanka mata yace na tambayeki?......wlh Sumayya kin ban mamaki daman pills kikesha dan kar kisamu ciki? Inaso kisani duk abinda kika aikata kanki kikayi mawa kuma kanki kika zalunta, na gode ma Allah da bake kad'ai gareniba, kuma idan ke bakyason had'a zuri'a da ni toh wata tanaso, cikin ikon Allah sai gashi Allah yaba zarah ciki har kina ik'irarin cewa tana miki gorin ciki, ashe nan kekad'ai kikasan abinda kike shukawa tsawon dad'ewar da mukayi.
Ammah fa zarah ta burgeni.

Sumayya cikin sauri tad'ago kai takallesa hawaye sha6e-sha6e a fuskarta.

murmushin tskaici yayi sannan yace eh Sumayya,,,sannan inaso kisani kanki kika cuta ba ni ba kuma bazakiga illan hakanba sai nan gaba, a duk lokacin da kika 6ata mahaifarki kar kiyi kuka da kowa sai kanki.

Sumayya rusgar kukanta take kamar wanda aka aiko ma da sak'on mutuwa,girgiza kai tashiga yi dak'yar ta iya bud'e baki tace dan Allah yarima kayi hak'uri wlh sharrin shaid'anne.

Murmushi yarima yayi cikin rashin damuwa yace Sumayya kidaina cewa Sharrin shaid'anne, duk abinda kikayi daidai dake ne bazan yi komai akaiba dan da hankalinki  saidai ina gargad'inki da kiguji lokacin da zaki kaini k'arshe dan wlh had'uwarmu bazatayi miki kyau ba....fuskarsa a d'aure kamar wanda bai ta6a dariyaba yace ina kika ajemin files d'ina?

Hannunta yana rawa tayi mai nuni da chan saman wani d'an k'aramim table.

Yarima zuwa yayi yad'auka batare da ya k'ara kallon inda takeba yawuce zai fita daga d'akin, cikin sauri Sumayya tabiyosa tace please yarima kasau.....hannu yad'aga mata sannan yaficce yabar d'akin.

Sumayya na ganin fitarsa nan taduk'e k'asa tashiga rusa sabon kuka cike da bak'in ciki da danasi, ita ba pills d'in da yarima yakamata da su bane yafi tayar mata da hankali, kawai tana tsoron labarin yaje ma su dada dan idan labari yakai musu ta san kashinta ya bushe, cikin sauri tamik'e tajanyo wayanta talalubo number d'in mahaifiyarta takira, sultana sadiya tana yin picking taji kukan sumayya ya cika wayan, a rud'e tace lafiya sumayya? Me yake faruwa?

Sumayya duk yadda taso tayi magana kasawa tayi kuka kawai take,,,sultana sadiya ta yi tambayar ammah ba amsa sai kuka, k'ulewa tayi tadakama sumayya tsawa tace ke ni kinutsu kiyi min bayani!

Sumayya tsagaitawa tayi daga kukan da take tace ummah yau nashiga ukku asirina ya tonu wajen yarima kuma nasan sai su memartaba sunji.

a chan 6angaren sultana sadiya da take tsaye zama tayi tace sumayya me kika aikata?

Sumayya k'ara fashewa tayi da kuka tace ummah ya shigo ya kamani da pills.

Zaro ido sultana tayi cikin fad'a tace sumayya anya kina da hankali? Ban gargad'ekiba akan yin family planning? Ke wace irin kidahumace, wlh kije na gama shiga subgarki tunda ke bakida wayau, toh yanzu ga kishiyarki chan da ciki k'ila idan tahaihu zaki dawo cikin hayacinki.

Sumayya k'ara rushewa tayi da kuka tace ummah dan Allah kitaimaka min wlh na daina daga yau,

Sultana tsaki taja cikin 6acin rai tace kar ma Allah yasa kidaina inma wani yake zugaki kina wannan iskancin toh ba abu bane mai kyau, kin barni ina ta fama wajen ganin na taimakeki anzubar da cikin wata ashe ke kina nan kina d'irkan maganin hana haihuwa, kije kawai kiyi yadda kikeso ni na zare hannuna ga lamurranki....sultana sadiya tana fad'in haka takashe wayanta.

Sumayya tana jin sultana sadiya ta kashe wayan, dafe kanta tayi tacigaba da rusa wani irin kuka, tunowa tayi da zinat cikin sauri tanemo number d'inta tayi dialing.

Har tatsinke zinat batayi picking ba, tana shirin k'ara kira saiga kiran zinat ya shigo, cikin sauri sumayya tayi picking.

Zinat cikin muryar bacci tace ya dai baby,

Sumayya fashewa tayi da kuka tace zinat na shiga ukku.

Zinat cikin tashin hankali tace sumayya me yake faruwa? Wanine yarasu?

Sumayya cikin kuka tace zinat asirina ya tonu wajen yarima ya gano ina amfani da pills.

Tsaki zinat tayi tace toh sai me dan ya gane?

Sumayya tsagaitawa tayi daga kukan da take tace sumayya kinsan abinda kike cewane? Ko bakiji abinda nace mikiba.

Zinat murmushi tayi tace haba sumayya ni wlh kunya kike bani yanzu saboda Allah saboda d'an wannan abun kike 6arnan hawayenki?

Sumayya shuru tayi tana saurarenta fuskarta d'auke da mamaki.

Zinat jin batayi maganaba yasa tace baby kikwantar da hankalinki kimori rayuwa kar ki saki kiyarda kifara haihuwa yanzu dan wlh zakiyi saurin tsufa kuma daga inda kika fara haihuwa yara duk sai sun rikitaki bakida lokacin kanki, kuma mijinki zaiyi baya da ke.

Sai a lokacin sumayya tayi magana tace zinat kifahimceni wlh yarima yana son haihuwa.

Tsaki zinat tayi tace kefa matsalata dake kenan baki ganewa, kinsan daga inda kika fara aje 'ya'ya komai zaibi ya jagule miki mijinkima zai fara tunanin k'ara aure dan gaba d'aya zaki gunduresa, kibari kawai sai shekara mai zuwa lokacin kin tara abinda kika tara na dukiya a lokacin mijinki yana muradin 'ya'yan sosai toh zakiga rawan kai wajensa  dan bazai k'ara yarda yayi nisa da ke da babynkiba, indai kuma kina tunanin cikin wannan bagidajiyar yarinyar ne toh kidaina tunani kikwantar da hankalinki dan da nazo zai tashi aiki.

Sumayya cike da gamsuwa da maganar zinat tace hakane saidai yanzu ummah ta yi fushi da ni bansan ya zanyiba.

Dariya zinat tayi tace kar kidamu zan fad'a miki yadda zaki shawo kan yarima da ummah.

Sumayya murmushin jin dad'i tayi tace nagode sosai zinat saisa nake k'ara sonki.

Dariya zinat tayi tace bakomai baby nima kinsan ina sonki sosai insha Allahu nan da upper week zan shigo  garin, Sumayya wani irin farin ciki taji ta dabaibayeta tace kai baby ammah wlh naji dad'i kuma nayi murna, ji nake kamar injawo lokacin yayi.

Dariya zinat tayi tace kai baby gaskiya naga alama kinyi missing d'ina sosai, yanzu dai bari inje bank zan yi miki depositing d'in wasu kud'i idan nagama komai zan kiraki muyi magana.

Sumayya ciki jin dad'i tace ohk dear sai najiki.


Yarima koda yakoma part d'insa tisa files d'in yayi gaba yana kallo ya kasa cigaba da aiwatar da komai, tausayin zarah ne da nadamar abinda yayi mata suka kamasa, dan tabbas ya san zarah ta cika mace ta gari tunda tana d'auke masa buk'atunsa kuma har ta amince tayi renon cikinsa abinda 'yar uwarsa ta jini takasa, tunowa yayi da wulak'ancin da yakeyi mata tsaki yaja tare da dafe kansa yace ya akayi hakan ya kasance?  Tabbas nasan zarah fushi take da ni, ji yayi duk ba dad'i dan haka yamik'e yafito yanufi part d'inta.


Yarima ahankali yatura k'ofa yashiga ganin babu kowa parlour yasa direct yanufi bedroom d'inta.

Zaune yahangota saman gadonta ta buga tagumi, zarah juyowa tayi takallesa wani irin dad'i taji a ranta sannan tajanye idonta daga kallonsa,

Yarima tsaye yayi yana k'are mata kallo ta d'an rame, duk sai yaji ba dad'i,,,ahankali yataka yanufi inda take daga gefen gadon yazauna,

Kallon zarah yayi da tad'auke kanta tak'i kallonsa tabbas ba k'aramin fushi take da  shiba, hannu yakai yarik'o nata gabad'ayansu wani irin shock sukaji a jikinsu yarima runtse idonsa yayi ahankali yafurta zarah....shuru yayi maganar ta lak'afe a mak'ogoronsa dan baisan ta inda zai faraba.

Har a lokacin fuskar zarah a d'aure take kuma bata juyo takallesaba tana dai saurare taji abinda zai ce mata,

Chan k'asan mak'oshinsa kamar wanda akayi ma dole yace please kiyi hak'uri.

Ba zarah ba hatta shi kansa yarima da yayi maganar saida yaji wani iri dan a karo na biyu da zarah taciri tuta yaimata abinda bai ta6a yi ma waniba bayan iyayensa shine kalman hak'uri,

Zarah fizge hannunta tayi tamik'e cikin sauri tanufi toilet, yarima kiran sunanta yashigayi ammah ina tuni ta shige nan tamaida tarufe,

Cike da takaici yarima yadafe kansa da hannuwansa biyu shi kansa ya san tabbas ba k'aramin 6atama zarah rai yayiba a karo na farko da yaji haushin kansa ya kamasa dan gaba d'aya zuciyansa zafi take masa.

Ya dad'e zaune saida yayi kusan 30minutes ganin batada niyan fitowa yasa yamik'e jiki babu k'wari yafita yabar d'akin.

Zarah tunda tashiga toilet d'in kuka tashiga rerawa ita kanta batasan tak'amaiman dalilin da yasa take kukanba, saida taji fitar yarima sannan tawanke fuskarta tabud'e k'ofan tafito tahaye saman gadonta takwanta tana sheshek'ar kuka.

Shi kansa yarima duk ji yayi ba dad'i dan gaba d'aya ji yake komai ya kwancemasa duk wanda yakallesa sai yasan yana cikin damuwa, koda yakoma part d'insa key d'in motansa yad'auka yafita yabar gidan yaje gidan gona.

A saman 3 seater d'in da take parlourn yakwanta gabad'aya shi kansa ya rasa gane tak'amaiman abinda yasa duk yacanza  dan wani iri yakejinsa daga k'arshe kallo yakunna nan yazauna yana kallon wrestling.

A nan yayi sallar isha'i sannan yakama hanyan gida.

Koda yakoma gida, part d'in zarah yakallah  har zai wuce nasa sai kuma yaji baya iya wucewa dan haka yafasa yanufi part d'inta, a parlour yasamu kuyanginta zaune baibi ta gaisuwar da sukeyi masaba yawuce yanufi bedroom d'inta.

Lokacin zarah tana kwance saman darduma tana tasbihi, k'amshin turarensane da taji yasa tagane ya shigo d'akin, cikin sauri tamaida idanunta tarufe kamar mai bacci,

Yarima tsaye yayi yana kallonta dan duk atunaninsa baccin takeyi, ahankali yatako ya iso inda take duk'awa yayi yad'auketa yanufi gado da ita.

Koda yakwantar da ita zama yayi gefenta ahankali yazare mata hijab d'in da take jikinta sannan yazuba ma fuskarta ido ganin yadda tayi fayau da ita.

Zarah ahankali take safke numfashi kamar irin na masu bacci, tana jinsa yakai hannu yad'age mata rigar da take jikinta nan yashiga shafa cikinta, duk'ar da kansa yayi yai kissing d'in cikin sannan yagyara mata rigarta yajanyo blanket yalullu6eta.

Mik'ewa yayi yanufi k'ofa koda yabud'e saida yajuyo yakalleta sannan yafita tare da rufe mata k'ofan.

Zarah tana jin fitansa tabud'e idonta, yaye blanket d'in tayi tamik'e taje tamurza ma k'ofanta key sannan taje tayi wanka tayi shirin baccinta takwanta.

Yarima ma koda yakoma part d'insa wanka yayi yashirya sannan yahau saman gadonsa yakwanta, ina nan bacci yace baisan batunba, haka yaita juyi, nan zarah tacigaba da fad'o mai a rai ko ya runtse idonsa ita kad'ai yake gani duk yadda yaso yajanye tunaninta a ransa kasawa yayi, yarima ya ja tsoki ya fi sau goma a lokacin, sai daga baya yasamu bacci yad'aukesa.

____________

Dasafe bayan yarima ya gama shirinsa yana shirin fita sai ga sumayya ta shigo d'akin, kallo d'aya yayi mata yad'auke idonsa nan gabad'aya fara'ar da take a fuskansa tagushe.

Sumayya bata damu da yanayin da tagansaba zuwa tayi tazauna gefensa cikin kwantar da murya tace please yarima kayi hak'uri kayafemin abinda na aikata insha Allahu bazan k'araba na daina.

Ko inda take bai kallaba yashareta,
Sumayya marairaicewa tayi tace dan Allah kayafemin na yi maka alk'awali wlh bazan k'araba.

Wani irin kallo yarima yawurgamata sannan yace sumayya duk abinda kika za6a ma kanki daidai da ke ne, bana bak'in cikin hakan,

Shuru yad'anyi na lokaci kad'an sannan yace a tunaninki mata nawa suke bibiyata, mata nawa duk'awa suna rok'ona sukeso in auresu? Ke kin samu dama saisa kike yadda kikeso, hanya yanuna mata yace tun kan mutuncinki ya ida zubewa a idona tashi kifita kiban waje.

Sumayya kallonsa tayi taga babu alamun wasa a fuskansa dan haka tayi sauri tamik'e, tsayawa tayi gabansa tace please yarima ka.....wani irin kallo yawatsa mata cikin sauri tajuya tafita tabar d'akin.

Binta yayi da kallo cike sa takaici dan gani yake duk ita taja zarah take fushi da shi, tsaki yaja sannan yamik'e yad'auki wayansa da key d'in mota yafito.

Part d'in zarah yawuce dan yadubata saboda baya jin dad'in fushin da take da shi.
yana shiga zaune yatarar da ita a parlour saman cushin ta ci kwalliyanta tana sanye cikin english wears riga da skirt ta tufke gashin kanta, gabanta cup d'in coffee ne aka d'aura saman table.

Yarima tsaye yayi yana kallonta dan gabad'aya taso tarikitasa da yaganta, zarah d'ago kai tayi suka had'a ido saida gabanta yafad'i cikin sauri tajanye idonta daga kallonsa dan ita kanta saida tasamu tasaita nutsuwanta.

Takowa yayi yazo inda take zaune daga gefenta yazauna gab da ita nan yazuba mata ido, sharesa zarah tayi tad'auke kanta gefe kamar batasan da zamansaba.

Yarima ma janye idonsa yayi daga kallonta nan sukayi shuru gabad'ayansu, ganin batada niyar yin magana yasa yarima yace ke baki iya gaisuwaba?

Zarah d'aure fuska tayi kamar ba zatayi maganaba sai kuma chan tace ina kwana?

Shuru yarima yayi kamar bai jitaba saida yayi kusan minti d'aya sannan yace ya kike?

Ta6e baki zarah tayi sannan tace lafiya,,,,,tana fad'in haka tamik'e zatabar wajen.
Cikin sauri yarima yajanyota tafad'o jikinsa, ido suka zuba ma junansu zarah cikin sauri taruntse idanunta, yarima cigaba yayi da kallonta sai chan yakai hannunsa yashafi k'ashin wuyanta, ahankali kamar mai rad'a yace baby bakison cin abinci duk kin rame.

Zarah shuru tayi tak'yalesa tana ji yatura hannunsa cikin rigarta yana shafa cikinta tare da kwantar da kansa saman k'irjinta, su dukansu cikin wani irin yanayi suka shiga

Zarah ce tafara dawowa cikin hayyacinta dan haka tabud'e idanunta tanemi taturesa ganin ta kasa yasa tafashe mashi da kuka,

Cikin sauri yarima yad'ago yakalleta yace lafiya?..

Cikin kuka tace ni kakyaleni.

Yarima batare da ya yi maganaba yasaketa nan cikin sauri tamik'e tashige bedroom d'inta.

Yarima binta yayi da kallo har tashige nan yamaida kansa yajingine da kujera haushi da takaicin kansane yakamasa, daga k'arshe mik'ewa yayi jiki ba k'wari yawuce yabar part d'inta.



_Comments_
      *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

*PAGE* 5⃣4⃣

Ahaka yarima yaje wajen aiki ammah kwata-kwata baida kuzari, Dr khalil shi kansa saida yalura da yanayin yarima,,,,,ko da yatambayesa abinda yake damunsa yarima banza yayi dashi yak'yale, kan dole Dr khalil yaja bakinsa yayi shuru dan ya san kome zaiyi toh bazai samu amsar tambayarsaba.

Zarah koda tashige bedbroom d'inta saman bed d'inta tafad'a tashiga tacigaba da kukanta wani irin son yarima ne yake fizgarta daga gefe guda kuma haushinsa takeji,,, ahaka tasha kukanta saida taji yunwa tana niyar yi mata illah sannan tamik'e taje wanko fuskarta tafita tad'auki coffeenta tasha.

Sumayya koda yarima yakoreta daga part d'insa bata wani damuba sosai cikin ranta cewa tayi na zan hanyar da zan 6ullo maka,,,,daga nan wucewa tayi tatafi turakar iyayenta.

Tana shiga a parlour ta tarar da sultana sadiya kishingid'e tsakiyan kuyanginta suna ta yi mata hidima, ganin sumayya yasa suka zube gabad'ayansu suna kwasar gaisu sumayya ko kallon inda suke batayiba ganin haka yasa cikin sauri suka ficce daga parlourn gudun kar suyi laifi.

Sultana sadiya tana ganin sumayya ta shigo nan tahad'e fuska babu alamun fara'a ko kad'an a tare da ita.

Sumayya jiki ba k'wari tazo tazauna gefenta ahankali tace ummana.

Sultana sadiya batare da ta kalletaba tace me yakawoki wajena.

Sumayya fashewa tayi da kuka tare da fad'awa jikin sultana sadiya, shuru sultana tayi tak'yaleta.

Cikin kuka sumayya tace ummah dan Allah kiyi hak'uri wlh na daina.

Sultana sadiya sai a lokacin ta kalleta tace sumayya kikyaleni kawai tunda bakyajjn magana kije kawai na sallamaki wajen wad'anda kike jin maganarsu.

Sumayya Cikin kuka tashiga girgiza kai ahankali tace ummah wlh ina jin maganarki akasine kawai aka samu kuma insha Allahu na daina bazan k'araba, dan Allah kiyafe min wlh duk na zubar da pills d'in.

Sultana sadiya cike da tausayin d'iyartata tashiga d'an bubbuga mata bayanta kad'an cikin sigar lallashi tace toh shikenan sumayya na hak'ura ammah dan Allah kidaina irin haka kinsan idan labari yajema su dada bazakiji da kyauba ke kinsan ko mahaifinki yaji sai kashinki ya bushe.

Sumayya share hawayen fuskarta tayi cikin jin dad'i tace insha Allahu ummah  ba zan sakeba.

Murmushi sultana sadiya tayi tace yauwa d'iyata, yanzu sai kije kisamu kilallashi wanchan miskilin mijin naki ko shima ya safko, Allah yaimiki albarka.

Ameen ummana, insha Allahu zan k'ara bashi hak'uri....nan tazauna sukasha hira da ummah cike da jin dad'i sannan daga baya tayi mata sallama tafito tanufi turakarsu dada dan tagaisheta.

koda tashiga fuskarta d'auke da murmushi taduk'a tagaishe da dada,

Cikin jin dad'i dada ta amsa mata nan sumayya tazauna gefen dada tana murmushi tace 'yar tsohuwa me kika ajemin?

Ido dada tazuba mata tace me fa zan aje miki bayan gakinan kinyi 6ul-6ul da ke kin koma d'imemiya wai mi wanchan miskilin yake d'irka miki?

Dariya sumayya tayi tace wlh dada hutune kawai,,,dada cikin rashin yarda tace kodai mun samu k'aruwane?

Girgiza kai sumayya tayi tace wlh dada banda komai.

Rik'e ha6a dada tayi tace sumayya kodai zakije asibiti aduba lafiyanki, tunda shi wanchan miskilin bai damu da hakanba.

Dada na je ance lafiya ta lau fa kawai dai lokacine baiyiba.

Ajiyar zuciya dada tasafke sannan tace toh Allah yanuna mana lokacin, Allah yasa ina da rabon ganin d'an cikinki.

Dariya sumayya tayi tace Ameen dada.

Ho 'yar nema ko kunyata bakyaji....cewar dada.

Dariya sumayya tashiga yi tace kunya ai ya wa-ne yanzu.

Dak'uwa dada tayi mata tace gidanku sumayya, ja ira kawai.

Sumayya tsagaitawa tayi da Dariya da take tace afuwan ranki yadad'e na daina.

Murmushi dada tayi tace toh ya wajen 'yar uwartaki ina fata tana lafiya.

Ta6e baki sumayya tayi tace inaji lafiya lou take.

Sakin baki dada tayi tana kallonta tace sumayya ban fahimcekiba? Kar dai kicemin baku zaman lafiya.

Sumayya k'wallah ce tacika mata ido tace toh dada ya zanyi yarinyar da bata k'aunata kullum batada aiki sai had'ani da mijina, ni me natsare mata da zata dinga min haka.

Dada da mamaki take kallon sumayya tace sumayya yanzu yarinyar nan da nake gani kamar babu ruwanta itace takeyi miki haka?

Hmm dada kenan kawai dai abar maganar dan in kikaji wasu abubuwanma da takeyi sai kinyi mamaki, ni yanzu babbar matsalata fushin da yarima yakeyi da ni kusan kullum sai ta had'amu.

Dada salallami tashiga yi tace na shiga ukku ni Asma'u, yanzu saboda Allah yarinya tazo tararar da ke gidan mijinki sannan tace zatayi miki  irin haka?

Toh kibarni da yariman yadawo zan gansa idan shi bazai iya d'aukan matakiba a kai toh ni zan d'auka ko inhad'asa da memartaba tunda shi yana jin maganarsa.

Cikin jin dad'i sumayya tace yauwa Dadata ammah dan Allah kar kifad'ama yarima ni nafad'a miki dan wlh zai iya kakkaryani.

Cike da tausayin jikartata dada tace kar kidamu sumayya insha Allahu bazan ceba, kuma ko na ce ai bai isa yata6akiba dan ko dole inrama miki.

Cikin jin dad'i sumayya tace kibarsa kawai Dada ni zaman biyayya da hak'uri kawai nake da shi, duk abinda yayi min dan kansa, dan na ma fi ganin laifin wacchan munafukar matar tasa mai mugun hali.

Tsaki Dada taja tace kibarni da su kawai,

haka sumayya tazauna tayi ta 6ata zarah a wajen dada nan Dada tahau tazauna tana ta jimamin halin zarah.




Yarima koda yadawo wanka yayi yashirya sannan yad'anci lunch kad'an, yana gamawa fita yayi yanufi part d'in zarah dan kwata-kwata yanzu wani iri yakeji game da ita rashin zuwanta part d'insa ba k'aramin d'aga mai hankali yakeba.

Yana shiga bedroom d'inta daidai lokacin tafito wanka d'aure take da towel tana tsaye gaban dreesing mirror tana yin shafa.

'Dago kai tayi takallesa nan suna had'a ido tajanye fuskarta daga kallonsa, yarima tsaye yayi yana kallonta batare da yayi maganaba.

Tana gamawa tawuce tanufi wajen wardrobe d'inta tabud'e tad'auko kayanta, juyowar da zatayi sai ganin mutum tayi bayanta tsaye, k'ara d'aure fuska tayi ta ra6a ta gefensa zata wuce yarima jawota yayi tafad'o jikinsa yarungumeta,

K'ok'arin turesa tashiga yi nan yak'ara matseta a jikinsa ahankali yace wai ke meyasa kike min haka?

Harararsa zarah tayi tace wani abu kaga na yi maka?

Zuba mata ido yayi yana kallonta da mamaki sannan yace dan kinga ina lalla6aki saisa kike min yadda kikaga dama
Ta6e baki zarah tayi tace kar ma kalalla6ani indai nice na gama shiga sabgarku tunda daman sai kunga na shiga sannan zaku sami daman wulak'antani,,,,fashewa tayi da kuka tace ni duk abinda sumayya takemin me nata6a cewa shine ni kamar jira ake ko banyi mata wani abuba sai ace na yi toh ya kukeso inyi!!! tak'arashe maganar cikin d'aga murya.

Yarima shuru yayi yakasa magana sai chan yarungumeta a k'irjinsa tare da runtse idonsa yana jin wani iri a ransa,,,ahankali kamar me rad'a yace ix owk zarah, insha Allahu hakan ba zai k'ara faruwaba,

Zarah janye jikinta tayi daga nasa tawuce zatabar wajen, kallonta yarima yayi yace wai ke dan kin samu ina lalla6aki shine kike min haka?

Zarah juyowa tayi takallesa sannan tace toh ni me kaji na ce maka?

Yarima har ya bud'e baki zaiyi magana nan wayarsa tafara ringing,,,d'aukowa yayi yaduba ganin me kiransa yasa yayi picking tare da yin sallama.

Daga chan 6angaren dada amsa mashi tayi sannan tace toh dodo kazo yanzu ina son ganinka.

Yarima kallon agogon hannunsa yayi sannan yace yanzu kuma?

Cikin fad'a dada tace eh, inkuma bazakazoba saboda ka rainani toh sai infad'ama ubanka shi sai yasa kazo.

Yarima shuru yayi baice komaiba.

Jin ya yi shuru yasa dada tace ko bakaji abinda naceba?

Cikin k'osawa da maganar yace ganinan,,,,yana fad'in haka yakashe wayar ko inda zarah take bai kallaba yawuce yafita yabar d'akin

Zarah da ido tabisa har yatafi sannan tad'auki kayanta tasaka, cikin ranta ji take daman batayi ma yarima hakaba.

Yarima koda ya isa turakar su dada a parlour yasameta zaune tana jiransa, ko da yayi sallama ciki-ciki ta amsa masa, saman d'aya daga cikin kujerun yazauna cikin girmamawa yagaisheta.

Amsa masa dada tayi daganan d'akin yad'au shuru ba wanda yak'ara magana, ganin baida niyar yin magana yasa dada tace toh d'an nema watau shine kayi zaune baka ma jin zaka iya tambayata dalilin kiran da nakeyi maka.

Murmushi kawai yarima yayi batare da ya yi maganaba.

Dada gyara zamanta tayi ta fuskanci yarima sosai sannan tace suhail na ji abinda kakeyi ma 'yar uwarka kuma na gode ba ita kayimawa ba ni kayimawa.

Da mamaki yarima yake kallonta har saida takai aya sannan yace ranki yadad'e wani abu tace na yi mata?

Harararsa dada tayi tace kai kar kamaidani k'aramar yarinya ko ka d'auka duk abinda kukeyi mata kai da matarka bai dawowa a kunnena?

Yarima har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa nan yacigaba da dannar wayarsa da take hannunsa.

Nan dada tacigaba da cewa Toh bari kaji ko kaso ko kak'i sumayya 'yar uwarkace kuma za6inmu ce sannan wannan aure naku mutuwa kawai zai raba, ita wacchan matar dan kaga za6inka ce saisa kake ma 'yar uwarka wulak'anci son ranka kuma inaso kasani ciki Allah yake bayarwa kuma itama sumayya in da rabo zata haihu.

Yarima banza yayi mata kamar ba da shi take maganaba,,,dada k'ulewa tayi ganin baida niyar yin magana tace watau ga sakarya tana magana bakaji ma zaka iya tankamin.

Saida yarima yayi Kusan minti biyu sannan yad'ago yakalli dada da tatsaresa da ita, murmushi yayi sannan yace toh ranki yadad'e na ji.

ta6a hannu dada tashigayi tace na shiga ukku yanzu saboda Allah suhail ni kake ma haka? Ko mahaifinka bai isa yayimin hakaba sai kai?

Shuru yarima yayi yakyaleta nan dada tayita masifarta daga k'arshe jingine kansa yayi da kujerar da yake zaune yamaida idanunsa yalumshe.

Dada tsura masa ido tayi takasa cigaba da fad'an dan gabad'aya yarima ya gama kashe mata baki, cike da takaici tanuna k'ofa tace tashi kafita kabani waje.

Yarima bud'e idonsa yayi tare da d'aukan wayansa yace na barki lafiya.

Dada binsa tayi da kallo har yaficce takaici yacikata saisa batason wani abu yahad'ata da yarima dan takaici kawai take kwasa, cikin ranta kuma tana jinijna ma halinsa, ahankali tace wannan mutumin halinsa sai shi, ina amfanin miskilanci irin haka, lallai matansa da suke zaune da shi suna k'ok'ari.

Yarima koda yafita daga nan 6angaren iyayensa yawuce, ko da yashiga parlour ummi batanan, bakowa ciki, dan haka yasamu waje yazauna tare da dafe kansa dan shi gabad'aya anhad'a masa zafi dayawa tsaki yaja yace ta ko'ina ba sauk'i.

Sultana bilkisu da tafito daga bedroom tsaye tayi tana kallon d'an nata da gabad'aya hankalinsa baya a jikinsa, cike da tausayinsa tataka ta isa inda yake daga gefensa tazauna, Sai a lokacin yarima yad'ago yakalleta nan yasakarmata murmushi.

Sultana bilkisu ma maida masa martani tayi sannan tace my son lafiya naganka nan zaune?

Yarima duk'ar da kansa yayi yace ummina barka da rana.

Ido tazuba mai tace dafatan kuna lafiya?
Lafiya lou ummi.
Toh ya wajensu sumayya da zarah.
saida yajingine kansa da kujera sannan yace duk suna lafiya.

Toh ya d'iyartawa da jiki?
Yarima d'an sosa kai yayi alamun jin kunya sannan yace ummi dasauki.
Toh masha Allah, Allah yaraba lafiya.
Shuru Yarima yayi baice komai ba.

Sultana bilkisu rik'o hannunsa tayi tace my son me yake damunka?

Yarima kallonta yayi yana murmushi yace bakomai ranki yadad'e.

Sultana bilkisu batayi mamakin jin hakan daga garesaba dan ta san halin d'an nata, murmushi tayi tace shikenan ammah dan Allah kadinga hak'uri ka san ganinka cikin irin wannan yanayi ba k'aramin d'agamin hankali yakeba.

Yarima kwantar da kansa yayi saman cinyar ummi yace kar kidamu ummina babu abinda yake damuna kawai dai ji nayi inaso inzo inganki.

Cikin jin dad'i sultana bilkisu tashiga shafa gashin kansa tace Allah yaimaka albarka my son.

Ameen ummina....nan Yarima yamaida idanunsa yalumshe, sultana bilkisu tazuba mai ido tana kallon d'an nata cike da so da k'auna.

Tun daga lokacin Yarima yadaina shiga harkar kowa dan yanzu tun safe idan yafita baya dawowa sai wajen 9pm saboda meeting da suke zama, kuma idan yadawo sai ya  gargad'i guards d'insa akan kar subar kowa yashigo masa hutawa yakeson yi.
ba zarah ba hatta ita kanta sumayya saida tad'an shiga damuwa.



_*After one week later*_

Yau yarima kasancewar bai fitaba zaune yake d'akinsa a parlour yana kallo zarah ce tashigo da sallamarta.

Yarima batare da ya juyo ya kalletaba ya amsa, zarah wani irin sanyi taji a ranta da tagansa, takawa tayi ta isa inda yake zaune da mamakinsa sai gani yayi ta zauna saman cinyarsa,

Sai a lokacin yarima yakalleta shi kansa wani irin sanyi yaji a ransa, zarah k'irjinsa tashige tare da fashewa da kuka.

Runtse idonsa yarima yayi yana jin kukan nata har cikin ransa, rungumeta yayi muryarsa tana rawa yace zarah me yake samunki?

Zarah tsagaitawa tayi daga kukan da take sannan tace akwai abinda yake samuna bayan wanda kayi min?

Ido yarima yazuba mata batare da ya ce komai ba,

cikin sheshek'ar kuka tace shine kagujemin kadaina shiga sabgata gabad'ayama kadaina zaman gidan.

Yarima tallabo fuskarta yayi yace toh ya kukeso inyi muku naga kamar kinfison hakan, kefa kikace kin daina shiga sabgata saisa nabarki kihuta.

Zarah rungumesa tayi tace hakan da kayi ba k'aramin d'agamin hankali yayiba dan Allah kayi hak'uri na daina.

Yarima kallon cikin idonta yayi sannan yace meyasa bakison cin abinci?

Zarah turo baki tayi tace taya zanci abinci bayan babynka yana matsamin ina tunanin missing d'in daddynsa yayi......tak'arashe maganar tare da kashe mashi ido d'aya,

Yarima hannunsa yakai cikin rigarta yana shafar cikinta, zarah maida idanuwanta tayi talumshe tana jin dad'in hakan da yakeyi mata.

Gabad'ayansu shuru sukayi ba wanda yak'ara magana, ahankali taji hannunsa suna yawo cikin rigarta,

Chan kuma sai ya janye hannunsa daga cikin rigarta yace tashi muje kici abinci,

Zarah d'ago kai tayi takallesa tare da turo baki tace nifa na k'oshi.

Yarima zuba mata ido yayi sannan yace ammah ai ga shedanan yau bakici abinciba.

Zarah kamar zatayi kuka tace ni ice cream nakeson sha,

Jan hancin yarima yayi sannan yace toh kije kici abinci zan bayar asiyo miki,

Zarah mik'ewa tayi tana gyara rigarta sannan tace toh ammah fa kad'an zan ci.

'Daga kai kawai yarima yayi batare da ya yi maganaba.

Juyawa Zarah tayi tafita tabar d'akin, nan yarima yakoma saman 3 seater yakwanta yana ci gaba da kallonsa yana jin wani irin nishad'i a ransa.

Daga k'arshe yamik'e yazari key d'in motarsa yaficce yabar gidan.


Zarah koda takoma part d'inta kad'an taci abincin nan tazauna zaman jiran yarima yakawo mata ice cream d'in ammah shuru, zuwanta biyu part d'insa ammah baya nan.

Ahaka har akayi sallar isha'i taje tayi wanka tai shirin baccinta,,,,tana cikin saka night gown d'inta sai ga kiran yarima ya shigo wayanta cikin jin dad'i tayi picking kamar zatayi kuka tace shine kabarni ina ta jiranka.

Daga Chan 6angaren yarima cemata yayi tazo ta amsa gashinan.

Cikin jin dad'i Zarah tace toh.

Cikin sauri ta ida shirinta tafito tanufi part d'in yarima.
Tana shiga ganin baya parlour yasa tawuce bedroom d'insa ahankali tatura k'ofan tashiga, saman gadonsa tahangosa zaune yana ta waya hannunsa rik'e da paper da biro yana rubutu.

Takowa tayi ta iso bakin gadon, d'ago kai yarima yayi yakalleta sannan yai mata nuni da ledar da take aje k'asa.

Cikin jin dad'i zarah taje tad'auki ledar, a nan k'asa tazauna tabud'e tad'auko d'aya sannan tatashi tasaka sauran cikin freezer d'insa.

Dawowa tayi tad'auki wanda ta aje taje gefensa tazauna tabud'e tana sha.

Har a lokacin yarima yana ta 'yan rubuce-rubucensa, zarah ahaka tashanye sannan taje toilet d'insa tawanke bakinta.

k'arshen gadon taje takwanta tana kallonsa yana ta wayansa, daga k'arshe da taga wayar batada niyar k'arewa dan haka tamik'e takoma gefensa tazauna, marairaicewa tayi ahankali tace wai wayar ba a gamata hakanan dare fa ya yi.

Kallonta yarima yayi nan zarah tad'aga mai gira,
idanuwansa yamaida ga agogon da take manne ga bangon d'akin ganin har 11pm ta yi yasa yayi sallama yakashe wayar.

Kallon zarah yayi da tatsaresa da ido sannan yace bazaki kwantaba?

Zarah batare da tayi magana ba tamik'e taje takwanta, yarima kashe gloves d'in d'akin yayi sannan shima yahau gadon daga gefen zarah yakwanta.

Zarah tana ganin ya kwanta nan tamaida kanta saman k'irjinsa, yarima kamar daman jira yake nan yarungumota jikinsa tare da k'ok'arin rabata da rigar jikinta, yana cirewa Zarah tazame jikinta takoma gefe,

numfashi yarima yaja, cikin kasalalliyar muryarsa yace ya dai?

Zarah cikin tsokana  tace ni bacci nakeji.

Yarima matsawa yayi gab da ita sannan yace tun d'azu me yahanaki baccin?.

Zarah turo baki tayi har ta bud'e baki zatayi magana sai ji tayi yarima ya had'e bakinsu waje guda yafara kissing d'inta cikin k'warewa,

Zarah gabad'aya tafita hayyacinta inda kowane 6angare na jikinta yake kar6an sak'onsa, k'ara rungumesa tayi jikinta ita kanta ta san ta yi missing d'insa.

nan yashiga sarrafata son ransa, har tagaji ammah yak'i barinta daga k'arshe kuka tasa mashi ammah Yarima baima san tana yiba dan gabad'aya hankalinsa baya tare da shi.

Saida yagaji dan kansa sannan yabarta zarah chan gefe takoma takwanta tana sheshek'an kuka.

Yarima duk sai yaji ba dad'i dan haka yajanyota jikinsa batare da ya yi maganaba yashiga d'an bubbugamata baya alamun lallashi.

nan zarah tarage sautin kukan nata daga k'arshe bacci yayi awon gaba da ita.

Yarima na jin ta yi bacci yajanyeta daga jikinsa yalullu6eta da blanket sannan yatashi yanufi toilet dan yayi wanka.

Bayan ya fito shiryawa yayi sannan yahau gadon yakwanta tare da jawo zarah jikinsa yarungume yana shafar cikinta d'an wata biyar, a haka bacci yad'aukesa


Da asuba saida yayo alwallah sannan yatayar da zarah yawuce masallaci.

jikinta duk ciwo yake haka tajanyo kayanta tasaka tafita takoma part d'inta, a chan tayi wanka tad'auro alwallah tai sallah bayan ta gama tahaye saman gadonta takoma bacci.




_Comment_
       *nd*
_Share_






_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

*PAGE* 5⃣5⃣

Bayan sallar la'asar yarima zaune yake saman cushin daga gabansa table ne ya d'aura laptop d'insa yana dannawa yanayin yadda yamaida hankalinsa gabad'aya akan laptop d'in zai tabbatar maka da abu mai muhimmancine yakeyi.

Sumayya kamar anjefota tashigo d'akin ba ko sallama.

Yarima d'ago kai yayi yakalleta sannan yacigaba da abinda yakeyi,
Takowa tayi ta iso inda yake, tsaye tayi gefensa fuskarta a d'aure tace haba yarima gaskiya bakayimin min adalci.

Yarima d'ago kai yayi yakalleta fuskarsa ba alamun wasa yace ke baki iya sallama ba?

Ta6e baki Sumayya tayi sannan tace a inda yadace ake sallama, nidai na fad'a maka kaji tsoron Allah, kuma inma laifi nayi maka ai na baka hak'uri.

Ture laptop d'in yayi gefe tare da d'ago kai yakalleta cikin 6acin rai yace ke matsalata da ke bakida isassar tarbiya yanzu haka ake magana da miji?

Sumayya kallonsa tayi cikin 6acin rai tace nice banda tarbiya? lallai yarima nagode, ammah inaso kasani ba babbar marar tarbiya sai wacchan d'iyar matsiyatar da ka auro wadda talauci yai mata..... yarima a fusace yamik'e tsaye, marin da ya wanka matane yasa takasa k'arasa maganar.

Da mamaki Sumayya take kallonsa tace yarima ni kamara?

Nunata yayi da yatsa yace anmareki ko zaki ramane? Wlh Sumayya kikiyayeni na fara gajiya da wannan haukan naki, kuma wadda kike kira matsiyaciya Wlh ta fiki daraja a idona dan kwatakwata yanayin tarbiyanku ba d'aya bane,

Sumayya fashewa tayi da kuka tace wlh ba zan yardaba sai na rama abinda kayimin kuma sai na fad'ama dada saboda wacchan matsiyaciyar ka.... yarima k'ara wanketa yayi da mari yace indai kika k'ara kiranta da matsiyaciya wlh sai na takaki cikin d'akin nan kuma inda sabo toh kin saba had'ani da su dada saidai inaso kisani babu wanda ya isa yasani inyi abinda banyi niyaba,  harara yawurga mata sannan yace fita kiban waje ko yanzu in6ata miki rai, shashashar banza.

Sumayya tana dafe da kuncinta tajuya saida takai bakin k'ofa sannan tajuyo tace kasaurareni zaka san ka ta6a Sumayya,,,,tana fad'in haka tajuya tafita tabar d'akin.

Yarima komawa yayi yazauna tare da dafe kansa zuciyansa tana masa wani irin zafi, takaicin Sumayya ne yacikasa cikin ransa yace ina amfanin auren irin wad'annan mata,,, daga k'arshe mik'ewa yayi yaje yashige bedroom d'insa.

Sumayya koda takoma part d'inta kuka take sosai takaicinta duk akan zarah yarima yayi mata mari biyu,,,nan tsanar zarah tak'ara kamata ji take kamar taje takashe zarah kowa yahuta,

Haka tawuni tana kuka, kiran zinat ne da yashigo wayanta yasa tatsagaita da kukan da take har saida takusan tsinkewa sannan tayi picking.

Daga chan 6angaren zinat cewa tayi baby tun d'azun nake kiranki ammah bakiyi picking ba why?

Sumayya shuru tayi, zinat tace hello baby kina jina?
Sai a lokacin Sumayya cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace sorry bana kusa.

Daga chan 6angaren zinat dafe kanta tayi tace oh my god baby ke kullum bakida aiki sai kuka? Yanzu kuma wa yata6aki.

Sumayya cigaba tayi da kukan, cikin kuka tace dole kice haka zinat bakisan cikin halin da nakeba yau akan wacchan jakkar yarima yai min mari biyu.

Cikin d'aga murya zinat tace mari?

Sumayya cikin sheshek'ar kuka tace eh, wlh ba zan k'yaletaba sai na rama abinda yayimin akanta, inma saboda cikinta yaimin haka toh wlh sai na zubar da shi.

Ajiyar zuciya zinat tayi sannan tace baby kiyi hak'uri gobe zan shigo garin  sai musan yadda zamu 6ullo ma lamarin dan wlh bazamu hak'uraba.

Koda Sumayya kuka take ammah kuma bai hanata murnaba, cikin jin dad'i tace dagaske kike baby gobe zakizo?

Dariya zinat tayi tace ai daman kiran da nake miki kenan kishirya gobe kina da babbar bak'uwa.

Hmm kinjiki da tsokana wai bak'uwa, ammah fa naji dad'i sosai baby ai dole inyi babban shiri, Allah yakaimu goben da rai da lafiya, wlh har kinja bak'in cikin da nake fama da shi ya ragu.

Dariya zinat tayi tace kai baby, yanzu dai bari inje inyi visa dan ta flight nakeson zuwa, me kikeso intafo miki da shi.

Shuru sumayya tayi kamar mai tunani sai kuma chan tace kiza6o min abu mai dad'i wanda zaisani farin ciki.

Ohk baby angama koma mekenan zan kiraki.

Sumayya kashe murya tayi tace baby kiyo shiri sosai dan gobe ba d'agi, kema kinsan nayi missing d'inki ga wanchan banzan kwana biyu rigima kawai muke bare ma ind'an samu sauk'i.

Dariya zinat tayi tace shikenan baby ai dole gobe mukasance da juna dan nima ba k'aramin missing d'inki nayiba,  zan kiraki da anjima muyi magana.

Ohk baby sai najiki, nan sukayi sallama suka kashe wayan.

Sumayya hawayen fuskarta tagoge tace lallai gobe koma me za'ayi saidai ayi ammah sai nayi silar zubewar cikin chan nata, shi kansa sai ya gane kuskurensa na marina da yayi,,,murmushin mugunta Sumayya tayi sannan tamik'e tanufi toilet dan tawatsa ruwa saboda gabad'aya jikinta ciwo yakeyi mata.


A chan 6angaren zarah tana chan d'akinta kwance dan wata irin kasala takeji daga wanka sai sallah kawai suke tashinta, daga k'arshe da kwanciyar ta isheta tashi tayi tad'auko littafatanta na islamiyya takoma parlour tazauna tana nazari.

Bayan ta gama kiran ummi tayi a waya suka gaisa nan ummi take tambayarta idan akwai abinda take buk'ata.

Zarah tace bakomai ummi.

Toh indai kinji kina buk'atar wani abu kiyo waya kisanar da ni Zarah banason nok'e-nok'e ni uwace kinji?

Cikin Jin dad'i Zarah tace toh ummi insha Allahu, nagode sosai Allah yak'ara girma da d'aukaka.

Ummi ta ji dad'in addu'an sosai tace Ameen daughter adai cigaba da hak'uri,,,,nan sukayi sallama suka kashe wayan.

Murmushi Zarah tayi cikin jin dad'i dan har cikin ranta tanason matar.

Daganan takira su mama a waya suka gaisa.



Bayan sallar isha'i koda tagama shirinta kwanciyarta tayi part d'inta dan cewa tayi ba zata koma wajen yarima ba yak'ara wahalar da ita irin na jiya dan ita kad'ai tasan wuyar da tasha.

Yarima ma koda yagama shirinsa kwanciyarsa yayi dan shi kansa ya san inba sa'a ba dawuya yau Zarah tadawo, murmushi yayi wanda baisan ya su6uce masaba, shi kansa ya yi mamakin yadda yacanza haka cikin k'ank'anin lokaci, cikin ransa yace toh me hakan yake nufi?,, 6ari guda na zuciyansa yace kodai ka fara sonta?

Zumbur yayi yatashi zaune cikin d'aga murya yace hakan ba zai ta6a yuwuwaba, toh me hakan yake nufi?

Ahankali yace kawai dai na damu da itane saboda babyna da yake tare da ita ammah ban yarda cewa akwai macen da nakesoba dan har yanzu ban samu *ZA'BINA* ba, ajiyar zuciya yayi cikin gamsuwa da tunanin da yayi sannan yakoma yakwanta.

______________

sumayya tunda tatashi shirye-shiryen tarban zinat take daga tasa a girka wanchan sai a sauke a girka wanchan, part d'inta wani irin gyara yasha a ranar duk ma'aikatanta saida sukasan tana cikin farin ciki,

Kad'an kad'an ta kira zinat taji idan sun tafo, zinat dariya kawai takeyi mata tace har yanzu muna airport.



Yarima ne zaune part d'insa rik'e da laptop yana duba wasu drugs da yakeso ayo masa order d'insu, nan wayarsa tafara ringing, baibi ta kan wayarba saida yagama abinda yake sannan yad'auko yaduba ganin Aunty husna ce yasa yayi murmushi tare da yin dialing, tana yin picking yace ranki yadad'e big sis.

Daga chan 6angaren Aunty husna dariya tayi tace da girman kujerarka Yarima mai jiran gado, daman cewa nayi bari inkiraka inji inkananan kazo mugaisa gani a part d'in ummi tunda mu ka fi k'arfinmu baka iya zuwa inda muke yanzu.

Yarima k'ayataccen murmushinsa yayi mai k'ara bayyanar da kyaun fuskarsa sannan yace sorry sweet sis wlh ina ta so inshigo hidima ce tahana ammah yanzu bari inshigo sai muyi magana.

Murmushi husna tayi cike da k'aunar d'an uwan nata sannan tace ohk ina jiranka sai ka shigo.

Murmushi yarima yayi sannan yakashe wayan tare da mik'ewa yashiga bedroom d'insa saida yawatsa ruwa sannan yashirya cikin wata maroon d'in gizna nan kyaunsa yak'ara bayyan feshe jikinsa yayi da perfumes batare da ya sa hulaba yafito yad'auki wayoyinsa a parlour yawuce yafita.

A chan harabar gidan yatarar da shaheed tsaye rik'e da waya da alama neman number d'insa yake, murmushi yayi sannan yawuce yanufi wajensa, sai a lokacin shaheed yad'aga kai yakallesa yana murmushi cikin sauri ya isa inda Yarima yake yace ranka yadad'e yanzu daman nake neman number d'inka sai ma gaka.

Hannu Yarima yamik'a mai sukayi musabaha sannan yace toh gani me aka kawomin?

Dariya shaheed yayi sannan yace nazo ingaishekane kawai, rahma ce taji zuwan Aunty husna shine nakawota sugaisa.

Murmushi Yarima yayi yace kace ka had'a zumunci, toh ya kake ya kwana biyu?

Ajiyar zuciya shaheed yayi sannan yace Alhmdllh ai mun kwana biyu bamu had'uba dan ko a fada ban ganinka.

Wlh kau busy nakene aikine yatisoni gaba banda lokacin zama.

Cikin tsokana shaheed yace aikin iyaliba,

Wata uwar harara yarima yawurga masa sannan yace kana tunanin mace zata hanani fita?

Dariya shaheed yayi sannan yace idan so yai so ai ba abinda bai iya faruwa, na lura da kai yarima kamar har yanzu bakasan menene so ba.

Yarima sharesa yayi tare da duba agogon hannunsa yace mushiga mugaisa da big sis.

Girgiza kai shaheed yayi yace a'a ni ai na shiga mun gaisa kawai kaje in ka fito kasameni a fada, murmushi yarima yayi yace mutum sai gulma kai a dole sirikine kunyar ummi kakeji.

Uhm dole inji kunyarta tunda ta ban auren d'iya.

Ta6e baki yarima yayi yace kaji da gulmanka, ni bari inshiga.

Toh shikenan sai mun had'e, nan sukayi sallama suka rabu.


around 3 o'clock, flight d'in su zinat yasafka, tun kan ta iso takira sumayya nan sumayya tatura driver yaje yad'aukota.

Lokacin da suka iso tun a parlour tafara k'wala ma sumayya kira.

Da gudu sumayya tafito daga bedroom d'inta tazo tarungumeta, tana murna dariya zinat tayi tace toh sakarni haka kar kikayar da ni dan agajiye nake.

Sumayya janye jikinta tayi daga na zinat fuskarta d'auke da murmushi tace sannu da zuwa babyna.

Dariya zinat tayi tace yauwa baby kinga yadda kika koma kuwa? Ni da naganki a video chart na d'auka camera ce tamaidake haka ashe kinma fi haka a fili, baby kodai kin k'unsa?

Ta6e baki sumayya tayi tare da shafa cikinta tace wlh baby bakomai nan.

Murmushi zinat tayi tace inma akwai ai zan gane...tak'arashe maganar tare da kashe mata ido d'aya.

Dariya sumayya tayi tace bare ma bakomai yanzu dai muje kici abinci kihuta.

Ohk dear, suna rik'e da hannun juna suka wuce suka nufi bedroom d'in sumayya, saman gado zinat tafad'a tare da furta wash.

Daga gefenta sumayya tazauna tace sannu baby kinsha hanya, bari in had'a miki ruwa kiyi wanka.

Kallonta zinat tayi tace saidai in ke zakiyi min.

Murmushi sumayya tayi tace bakida matsala koma me kikeso zaki samu dan ni yau ina cikin farin ciki,,,,,tak'arashe maganar tare da mik'ewa tanufi toilet.

Bayan ta had'a mata ruwan wankan fitowa tayi taga har a lokacin kwance take, dariya sumayya tayi tace kedai baby ragguwace wlh.

Harararta zinat tayi cikin wasa sannan tace eh d'in na ji, yanzu dai zo kitaimaka min incire kayan.

Kusan a tare suka shiga wankan, bayan sun fito shiryawa sukayi sannan suka fito parlour cikin plate d'aya suka zuba abinci suka ci,

Bayan sun gama a saman 3 seater kusa yada zango inda sumayya tayi matashin kai da cinyar zinat suna hirarsu suna dariya.

Zinat kallon sumayya tayi tace baby mushiga ciki kiban hak'ina kinsan d'azun da muna wanka daurewa kawai nakeyi.

Dariya sumayya tayi tace kai baby bama zaki bari mugama hirarba, yauwa yanzu taso mufara zuwa wajen wacchan 'yar matsiyatan dan inbanga mun aiwatar da k'udirinmu ba akanta toh hankali bazai ta6a kwanciyaba dan a yanzu nasan yarima baya gidan maybe ma sai dare zai dawo saisa nakeso muyi komai mugama.

Zinat dariya tayi tace hakan fa za'a baby tashi muje,,,kusan a tare suka mik'e suka fito suka nufi part d'in zarah.

Lokacin zarah tana zaune ita kad'ai tana kallo, dan gabad'aya kuyanginta basa nan, turo k'ofan da akayine aka shigo yasa tad'ago kai takalli su sumayya, tsaye sukayi su dukansu fuskarsu babu alamun fara'a.

Saida gabanta yafad'i ammah tadake tace sannunku da zuwa, bismillah mana kuzauna.

Harararta sumayya tayi tace ba zamane yakawomuba dan haka kar kidamemu.

Zinat ce tayi karaf tace sannu amarya ya ciki? Gaskiya cikin nan ba k'aramin kyau yak'ara mikiba saidai kiyi hak'uri dan sai mun cika k'udirinmu akansa.

Da mamaki zarah take kallonsu tace ban fahimci abinda kuke nufiba.

Zinat da sumayya kallon juna sukayi sukai dariya sannan sumayya tace kar kidamu yanzu zaki gane.

Zarah ganin suna nufo inda take Zaune yasa tayi sauri tamik'e tsaye tace wai me zakuyi min?

Suna isowa sumayya tad'aga hannu takwasheta da mari, cikin sauri zarah tadafe kuncinta tace sumayya me nayi miki da zaki mareni?

Bata rufe bakiba nan zinat itama tamareta,

Zarah hawaye suka fara fita daga idonta cikin zafin nama tad'aga hannu itama ta sharara ma sumayya mari,

Sumayya dafe kuncinta tayi tace kam bura'uba lallai yarinyarnan kin isa tunda har zaki iya marina,

Zarah cikin 6acin rai tace kamar yadda kika isa toh nima haka na isa, yadda bana shiga harkarki toh nima kidaina shiga tawa, juyowa tayi tanuna zinat tace kekuma inke babbar marar kunyace toh kik'ara ta6ani.
wlh duk wadda tak'ara ta6ani sai tagane batada wayau, ni kubani hanya inwuce.

Turata sumayya tayi tafad'a saman kujera sannan tace wlh yau nice silar zubewar cikinki,,,tana fad'in haka nan suka rufe zarah da duka, ta ko'ina bugunta suke.

Zarah duk'ewa tayi gudun kar subugar mata ciki, kuka kawai take, daga k'arshe sumayya tajawota daga saman kujerar tafad'o k'asa, nan suka cigaba da bugunta suna takata zarah kuka take tana neman agaji,

Wata baiwartace tajiyo ihunta cikin sauri tanufo d'akin tana zuwa taga su sumayya akan zarah janta suke suna nema subugi cikinta ammah ta duk'e, k'ara baiwar tasaki cikin sauri tanufo wajen tare da rungume zarah jikinta tana kuka tace dan Allah kuk'yaleta,

Sumayya cikin 6acin rai takaima baiwar mari tace ke har kin isa ina waje kitako kizo har ma kinemi kishiga harkar da ba takiba tashi kiban waje ko yanzu in kasheki.

Baiwar ture sumayya tayi tace wlh saidai kukasheni ammah bazan bari kucigaba da dukantaba.

Kan baiwar suka koma suka fara dukanta dak'yar ta k'waci kanta tatashi taruga dagudu tabar d'akin.

Zarah amai tafarayi tana maida numfashi sama-sama, ganin haka yasa suka kwashe da dariya sannan sumayya tace a haka kawai idan muka barki mungama da ke matsiyaciyar banza.

Zinat kallonta tayi tace anya sumayya cikin nan ya zube?

Sumayya k'afa takai zata harbi cikin zarah cikin rashin sa'a sai k'afar tatsaya a k'irjinta
sannan sumayya tace ai dolema yazube muje kawai baby, nan tajawo Zinat suka fita daga d'akin suna dariya.

Zarah kwance tayi wajen tana maida numfashi sama-sama dan ko hannunta bata iya d'agawa.


Ko da baiwar tafita dagudu tayi part d'in yarima cikin rashin sa'a guards d'insa sukace bayanan dan haka tanufi hanyar waje.

Yarima koda yashiga part d'in ummi bayan sun gaisa zama yayi suka d'an ta6a hira da su Aunty husna saida aka kira sallar la'asar sannan yatashi yatafi masallaci.

Bayan ya gama sallah a hanyarsa ta dawowa tsayawa yayi suka gaisa da jama'a sai wajen biyar sannan yasamu yanufo gida, part d'in su ummi yai shirin komawa sai ga wannan baiwar da gudu tana zuwa gabansa tazube k'asa tana haki.

da mamaki yarima yake kallonta yace ke lafiya?
Cikin rawar murya tace kagafarceni ranka yadad'e ga su gimbiya sumayya chan d'akin gimbiya zarah suna dukanta wai zasu zubar mata da ciki.

A firgice yarima yace duka kuma!, kuna aikin mi kukuma?

Girgiza kai tashiga yi tace kagafarceni wlh na shiga intaimaka mata shine suka had'a da ni har suka fashemin baki dak'yar nasamu nagudo.

Yarima bai ida saurarentaba yayi gaba cikin sauri yanufi 6angarensu, bai damu da gaisuwar da akeyi masaba dan baima san anayiba cike da tashin hankali yawuce  part d'in Zarah, yana shiga yaganta kwance k'asa tana maida numfashi, cikin sauri yanufi inda take tare da janyota jikinsa a rud'e yace Zarah sannu garin ya haka yafaru, hannu yakai saman cikinta yana shafa.

Zarah fashewa tayi da sabon kuka muryarta tana fita ahankali cikin wahala tace me natsare ma sumayya takeson ganin bayana? Me yasa tatsaneni haka? Wannan wane irin tsanace tayimin har take ik'irarin kasheni.

Yarima runtse idanunsa yayi dak'arfi yana jin wani irin tsanar sumayya a ransa,,,ahankali yabud'e idanunsa yasafke akan fuskar zarah sahun hannuwansu sumayya ne kwance a fuskarta, bakinta kuma jini ne yake fita, handchief d'insa yajanyo yagoge mata jinin, ahankali yakai bakinsa cikin nata yayi kissing d'inta, sannan yad'auketa chak yanufi toilet da ita,

Ruwan d'umi yahad'a yasakata ciki dakansa yaimata wanka sannan yad'aukota yafito da ita, zaunar da ita yayi bakin gado, cikin sauri zarah taruk'osa, kallonta yayi cike da tausayinta yace bari ind'auko miki kaya.

Zarah sakinsa tayi nan yawuce yanufi wardrobe d'inta yabud'e yad'auko kaya yataimaka mata tasaka sannan yad'auko magani yabata tasha saboda jikinta da yaji alamun zazza6i, zama yayi gefenta nan zarah tafad'a jikinsa tare da fashewa da sabon kuka.

Yarima shafa kanta yayi yace please kukan ya isa haka, zarah rage sautin kukan tayi sannan tace please kamaida ni gidanmu inba hakaba sumayya sai ta ida nufinta a kaina,

Yarima k'ara rungumeta yayi jikinsa sannan yace kar kidamu babu abinda zata iya yi miki wannan ma a bisa kuskure ta aikatasa ammah....sai kuma yayi shuru batare da ya ida fad'in maganar da take bakinsaba.

Janye zarah yayi daga jikinsa yamik'e, cikin sauri zarah taruk'o hannunsa, kallon fuskarsa tayi da gaba d'aya ta canza saboda 6acin rai,,,muryarta tana rawa tace ina zakaje? Please kar kayi mata komai.

wani irin kallo da yayi matane yasa cikin sauri tasakesa dan gaba d'aya ya gama tsoratata.
Batare da yayi maganaba yajuya yafita.

a 6angaren su sumayya koda suka koma part d'inta dariya suka cigaba da yi, sumayya cikin jin dad'i tace yanzu nasan burina ya cika, zinat tsagaitawa tayi da dariyarta tace baby toh yanzu idan mijinki ya dawofa ya zakiyi.

Ta6e baki sumayya tayi tace bazan damu da abinda zai min ba tunda nasan duk abinsa bai isa yasakeniba, dariya zinat tayi tace angaisheki gimbiyar yarima aikinki yana yin kyau, yanzu dai muje kiji da ni tunda hankali ya kwanta.

Kallonta sumayya tayi tace ina zuwa, nan sumayya tafito tasamu kuyanginta da suke tsaye waje tana yamutsa fuska tace kar kubari kowa yashigo min nan duk wanda kuka saki kukabari yashigo toh a bakin aikiku.
gabad'ayansu suka duk'a sukace angama ranki yadad'e.
juyawa sumayya tayi takoma ciki.
Suna rik'e da junansu suka wuce suka shiga bedroom tun a hanya suka fara cire ma junansu kaya, jikin  sumayya har rawa yake tajanyo zinat suka fad'a saman gado.

Cike da 6acin rai yarima yake tafiya yanufi part d'in sumayya, duk bawan da yatunkaresa zai masa magana da yaga yanayinsa zaiyi sauri yaja baya.

Kuyangin sumayya da suke gadin k'ofa ganin yarima yasa sukayi saurin ja baya tare da duk'awa suna kwasar gaisuwa, yarima baibi ta kansuba yawuce,

koda yashiga a parlour yatarar babu kowa dan haka cikin sauri yawuce yanufi bedroom d'inta.




_Toh fa koya za'a k'are idan yarima yashiga yaga sumayya tare da zeenat?_

_ko wane irin mataki zai d'auka akanta?_

_*duk amsar tana cikin next page dan haka Muje zuwa*_




_Comment_
      *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Masha Allah, sak'on gaisuwa agareku masoya a duk inda kuka kasance, gaskiya ina jin dad'in yadda kuke comments a groups akan novel d'in *YARIMA SUHAIL* da yadda nake samun sak'on gaisuwa daga gareku nagode sosai saidai ince Allah yabar k'auna, Sis Nerja'art tana yinku over_

*PAGE* 5⃣6⃣

Cikin zafin nama yarima yatura k'ofan, abinda yaganine yafirgitasa a kid'ime yafara furta innalillahi wa'inna ilaihiraji'un.

Sumayya da zinat da suke manne da juna basu ma san shigowarsaba dan gabad'aya basu cikin hayyacinsu saida sukaji yana salati sannan sukayi saurin rabuwa da Juna, cikin sauri zinat tajanyo bedsheet tarufe jikinta.

Sumayya wata irin razanannar k'ara tasaki tare da furta na shiga ukku na bani na lalace dan Allah yarima kayi hak'uri ba laifina bane sharrin shaid'anne.

Yarima da yake tsaye jikin k'ofa ya runtse idonsa innalillahi kawai yake nanatawa dan samun sauk'in abinda yakeji a ransa inba hakaba ya san zai iya abinda za'azo ana da na sani.

Cikin sauri zinat tajanyo zanenta tad'aura tana zare ido saboda a tsorace take, Sumayya ko bedsheet d'in tayaye tarufe jikinta da shi har a lokacin kuka take tana jin abun kamar a mafarki.

Ahankali yarima yabud'e idanuwansa da suka koma launin ja saboda tsananin 6acin rai, murmushin takaici yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace Sumayya ban ta6a sanin ke dabba bace sai a yau, ke ko dabba ma ta fiki k'wak'walwa mai kyau, ace a matsayinki na mace kina aiwatar da wannan mummunan halayyar, wlh a yau na tsaneki Sumayya bana fatan k'ara sakaki a idona, na yi da nasanin amincewa da nayi na aureki.

kallon zinat yayi yace kekuma har da tako min gida kika daki matata sannan kuka aikata masha'a a cikin gidana!

Sumayya cikin kuka tace dan Allah yarima kayi hak'uri wlh nabi ka nai maka alk'awali bazan k'araba dan Allah kar katona min asiri.

Zinay had'e hannuwanta tayi waje guda tana kuka tace dan Allah ranka yadad'e kayi hak'uri wlh tsautsayine yakawoni.

Yarima maida d'akin yayi yarufe sannan yace da fari zan fara rama ma matata dukan da kukayi mata,,,wucewa yayi yajanyo adaptor irin mai kaurin nan yatsige kan yad'auki wire d'in, wajen da suke yanufa daga bakin gadon yatsaya yafara shaud'a musu, ihu suke suna kuka nan tacigaba da had'awa da mari daga k'arshe k'asa yajanyosu yacigaba da duka da harbi da k'afa, ihu suke suna kuka ammah yarima bai k'yalesuba saida yaga ya had'a musu jini da majina basu iya kotsin kirki sannan yabarsu,

Jikinsu duk sahun bulala ya kwanta duk saida sukayi da sun sani akan ta6a zarah da sukayi.

Yarima kallon Sumayya yayi da take kuka yace wannan ramama matata nayi, sannan kuma ada nazo da niyar inyi miki saki d'aya ammah ganin abinda kike aikatawa ya sa zan miki....cikin sauri Sumayya tace dan Allah yarima kar kasakeni please kacigaba da dukana kar kafurta kalmar.

Wani irin kallo yarima yai mata mai tattare da tsana sannan yace kije na sakeki saki ukku dan bana buk'atarki a cikin rayuwata.

Wata razanannar k'ara Sumayya tasaki tare da rarrafowa ta iso inda yarima yake cikin kuka tace dan Allah kabarmin saki d'ayan wlh shi kad'ai ma ya isheni please ka janye biyun tafad'i haka tare da ruk'o rigarsa.

Yarima fizge rigarsa yayi yace kar kik'ara ta6ani da wannan hannun naki mai najasa, wucewa yayi yabud'e bedside d'inta yad'auko paper da biro nan yarubuta mata saki ukku ya cilla mata sannan yace na baki nan da awa d'aya kitattara komatsenki kifita kibarmin gida inko ba hakaba zan sa6a miki.

Sumayya dafe kanta tayi tare da k'ara sautin kukanta tace na bani na lalace yau ni ya zanyi da rayuwata,,,,kallon zinat tayi da take raku6e waje guda fuskarta duk ta kumbura tace shikenan zinat kinja min yau nima aurena ya mutu yau ni nashiga ukku ina zansa rayuwata.

Yarima a fusace yace na dai fad'a miki kar kibari indawo in tarar da ke,,, yana fad'in haka yajuya yabud'e d'akin yafita.

Sumayya tana ta k'wala mai kira yai mata banza, nan tacigaba da kukanta.

Zinat na ganin ya fita ta rarrafa tajanyo rigarta da veil d'inta tasaka, dakyar tamik'e tsaye, sumayya ganin zata fita yasa cikin kuka tace zinat ina kuma zaki tafi kibarni kina ganin matsalar da kika jefani.

Zinat jakkarta tad'auka batare da ta kalli sumayya ba tace tafiya zanyi tun kan yarima yadawo ya6allani koma me kenan nidai sai munyi waya dan haka kinga ma tafiyata kisan yadda zakiyi kikare kanki,,,zinat na gama fad'in haka tabud'e k'ofan taficce cikin sauri, gudu-gudu haka tasamu tafita daga masarautar bata tsaya jiran abun hawaba tacigaba da sauri sai da tayi nisa sannan tasamu tahau abuabun hawa.

Sumayya na ganin zinat ta fita nan ma k'ara fashewa da sabon kuka tayi tace na bani ni yanzu ya zanyi da kaina wai nice yarima yasaka wlh ba zan yardaba sai anmaida aurenmu,,,,rarrafawa tayi tajanyo wayarta tana kuka tai dialing d'in number d'in ummanta.

Ummah tana yin picking taji kukan sumayya yana tashi, ahankali tace ya salam sumayya me kuma kike ma kuka kedai inba kukaba ba abinda kika iya.

Cikin kuka sumayya tace ummah ya sakeni.

Ummah da take kishingid'e zumbur tamik'e tsaye tace me kikace sumayya saki?

Eh ummah.
Innalillahi wa'innah ilaihiraji'un garin ya haka yakasance sumayya? Nashiga ukku ni halima, dan ubanki kifad'amin me kikayi yasakeki.

Sumayya cikin sheshek'ar kuka tace ummah daga na daki matarsa shine yasakeni.
Dan Allah asashi yamaida ni

Sultana sadiya ajiyar zuciya tayi tace sumayya kin tabbata abinda kika fad'amin gaskiya ne?
Eh ummah.
Toh shikenan yanzu yi maza kije wajen su dada kisanar da su, nima ganinan zuwa ai dole kikoma d'akinki.
Sumayya cikin kuka tace Toh ummah,,,nan takashe wayar tare da mik'ewa tajanyo kayanta tasaka.

A firgice tafito cikin sauri tanufi turakar su memartaba, tana shiga parlour dada ce kawai nan sumayya taduk'e k'asa tare da fashewa da sabon kuka.

Dada rud'ewa tayi tace lafiya sumayya me yake faruwane? Bakida lafiya ne?

Sumayya girgiza mata kai tayi tace kod'aya dada, yarima ne yasakeki.

Dada dafe k'irji tayi tace Innalillahi wa'innah ilaihiraji'un, saki fa kikace?

Memartaba da yake ciki yana shirin fita jin hayaniya yasa yafito yana cewa hayaniyar me nakeji haka?

Sumayya duk'awa tayi tagaishesa cikin girmamawa,
Saida memartaba yazauna sannan ya amsa mata tare da cewa lafiya sumayya kike kuka?

Dada girgiza kai tashiga yi tace ranka yadad'e wlh yarima baya da mutunci yanzu saboda Allah ace ya saki 'yar uwarsa?

Memartaba cikin d'aga murya yace saki kuma? Anya kuwa sakinta yayi dan bana tunanin yarima zai zartas da wannan hukuncin batare da na saniba.

Dada tallabe ha6a tayi tace wlh indai yarima ne zai aika.

Memartaba kallon sumayya yayi yace ke kallanni nan fad'amin me kikayi masa yasakeki?

Sumayya rage sautin kukanta tayi sannan tace banyi masa komai ba daga matarsa ta ja ni fad'a har da cemin juya marar haihuwa, shine nikuma nabiye mata nan mukayi fad'a shine yakamani yai min duka,tafad'i hakan tare da d'age hijab d'inta su memartaba salati suka shiga yi da suka ga kwanciyar bulala a jikinta.
Cikin sheshek'ar kuka tace bayan ya gama dukana shine yasakeni.

haushine yacika memartaba yace banyi tunanin hakan daga wajen yarima ba banta6a tunanin zai iya min cin mutunci irin hakaba ammah bari inkira iyayenku suzo asan yadda za'a 6ullo ma lamarin.

Memartaba wayarsa yad'auka yakira mahaifin yarima da na sumayya yace duk suzo da iyalansu susamesa.

Bayan kamar minti goma sai gasu su duka sunzo harda Aunty husna da rahma da suke gidan basu koma gidajensuba,

Lokacin su memartaba suna zaune suna tattauna al'amarin gabad'ayansu suka duk'a suka gaishesu, kowa da mamaki yake kallon sumayya.

Bayan su memartaba sun amsa gaisuwa, gyaran murya yayi yace wani ya aika akira min yarima dan na kira wayansa a kashe.

Abban sumayya ne yace toh ranka yadad'e nan yamik'e yaje ya aiki wani dogari yace yaje yakirasa.

Yarima bayan ya baro part d'in sumayya nan yakoma 6angaren zarah yanayinsa kawai zaka kallah kasan ba k'aramin tashin hankali yake cikinsaba, kallon zarah yayi da take kwance ta zuba ma waje d'aya ido tana kallo, daga gefen gadon yazauna tare da dafe kansa yana tunanin lamarin sumayya dan gabad'aya ta gama ficce masa a rai, wayoyinsa yakashe gabad'aya dan ya san dole sai memartaba ya nemesa dan dama gudun kar amaido masa aurenta yasa yaimata saki ukkun.

Zarah ruk'o hannunsa tayi cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace tunanin me kakeyi?

Kallonta yarima yayi cike da tausayi yace in kaiki asibiti adubaki ko?

Girgiza kai zarah tayi tace babynka lafiyarsa lau dan basu samu sun ta6asa ba nikuma ciwon jikine kuma nasan zan warke insha Allahu.

Yarima d'aura hannunsa yayi saman fuskarta sannan yace ammah kina buk'atar asa miki drip kuma jikinki akwai zazza6i.

Zarah maida idonta tayi talumshe, yarima zuba mata ido yayi yana kallonta.

Knocking d'in k'ofan da akayine yasa yamik'e yaje yabud'e kuyangar zarah ce cikin sauri taduk'a tagaishesa, yarima batare da ya amsa mataba yace ya dai.

Jikinta yana rawa tace ranka yadad'e daman dogari ne aka aiko daga turakar sarki yace yana son ganinka.

Yarima baiyi mamakin hakaba, dawowa yayi yakalli zarah da take kwance ta ji duk maganarsu, janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace bari indawo sai muje hospital.

'Daga mai kai kawai zarah tayi, nan yarima yajuya yafita yanufi turakar memartaba.

Lokacin da ya isa baiyi mamakin ganin family d'insa da suka hallaraba, bayan ya yi sallama, waje yasamu k'asa chan gefen Aunty husna yazauna, cikin rashin damuwa yagaishe da su memartaba.

Ciki-ciki memartaba ya amsa masa nan d'akin yad'au shuru kowa saurare yake yaji memartaba ya fara magana.

Gyaran murya memartaba yayi sannan yakalli yarima da kansa yake sunkuye k'asa yace wannan taron ba dan kowa nayisaba sai dan kai yarima.
suhail ka bani kunya ban ta6a tunanin hakan daga garekaba koma menene ai ana son sasacin a cikin aure, wace irin zuciyace ta d'ibeka har kasaki matarka.

Gabad'aya 'yan d'akin sukace saki!! Nan aka fara kallon kallo.

Memartaba nuna sumayya yayi da take kuka har Lokacin Sannan yace toh gatanan dai ya saketa, ke kifad'a musu dalilin sakin suma suji.

Sumayya saida takalli yarima da kansa yake sunkuye sannan tamaimaita abinda tafad'a ma su memartaba.

Da mamaki yarima yad'ago yakalleta jin k'aryar da tadage tana shararawa, wata uwar harara yawurga mata nan Sumayya tafara dabarbarcewa.

Yana hararanta karaf a idon dada cikin fushi tace kikwantar da hankalinki kiyi bayaninki dan babu abinda ya isa yayi miki tunda kina a gabanku,
Nan Sumayya tacigaba da bayani.

Bayan ta gama d'akin yad'au shuru kowa yana jimami a cikin ransa, dadyn yarima ko kunyace takamasa ganin abinda d'ansa ya aikata ma d'iyar d'an uwansa, ummi ma jin abun take wani iri dan bata ta6a tunanin hakan daga garesaba.

Gyaran murya memartaba yayi yace kunji jawabinta, kunga abin kunyar da yarima ya aikata kan bare yarabu da 'yar uwarsa, toh yanzu ba sai anja maganar da nisaba na umurceka kamayar da ita d'akinta.

Sai a Lokacin yarima yad'ago yakalli memartaba cike da girmamawa yace ranka yadad'e kagafarceni, bata fad'a muku saki nawa nayi mataba? Ko daman idan anyi saki ukku ana komawa.

Nan d'akin yarikice da salati memartaba yace da hankalinka zakayi ma matarka saki ukku yarima? Sakin da ubangiji bayaso ana yi, ina iliminka da tuninka suke.

Yarima har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa.

Memartaba yace inji a lokaci guda kayi sakin?

Sumayya tayi karaf tace eh ranka yadad'e gabad'aya yayimin.

Toh Alhmdllh tunda gabad'ayane kuma cikin fushine zamu iya d'aukansa a matsayin saki d'aya kaga sai kamaidata d'akinta yanzu....cewar memartaba

Yarima k'ara duk'ar da kansa yayi sannan yace kagafarceni ranka yadad'e na riga da na haramta ma kaina k'ara auren Sumayya,

A firgice kowa na d'akin yakalli yarima, nan Sumayya tafashe da kuka tace na shiga ukku dan Allah kutaimaka min yamaidani d'akina.

Memartaba kallon yarima yayi yana jinjina kai dan ya ma rasa abinda zai ce masa,

Dada ce tashare kwallar da tazubo mata saboda tausayin Sumayya sannan tace ranka yadad'e ka gani ko? Lokacin da nake fad'a maka wulak'ancin da yarima yake ma Sumayya ba ka yarda, duk wulak'anci da cin mutuncin da matarsa takeyi mata bai ta6a tankawaba sai ita da suka d'an samu sa6ani shine yadank'ara mata har saki ukku.

Ummi kallon yarima tayi kallon mamaki, yarima cike da jin kunyar ummi yaduk'ar da kansa k'asa.

abban Sumayya ne yai k'arfin halin cewa kuyi hak'uri yanzu haka wani haukan ne Sumayya tayi masa kuma ba a ji daga garesaba.

Memartaba murmushin takaici yayi sannan yace bana buk'atar jin komai daga garesa, nagode sosai suhail ni kawulak'anta tunda ni na aura maka Sumayya yanzu ka maido min abuna ka ce ban isa inyi maka abinda bakasoba,
Saboda ganin kamar ban kyauta makaba yasa nabarka kaje ka auro za6inka bayan shekara d'aya da aurenku da Sumayya, duk labarin da ake bani akan abinda kake ma Sumayya ban ta6a yardaba sai gashi yau na gane ma idona abinda zai d'aga min hankali abinda d'ana nacikina bai aikataba sai gashi jikana namiji tilo d'aya ya aikata ma 'yar uwarsa.

Yarima d'ago kai yayi yakalli memartaba yace kagafarceni ranka yadad'e nima ba a son raina na aikata hakanba, wlh Sumayya ba gaskiya tafad'a mukuba.

Memartaba d'aga masa hannu yayi yace dakata bana buk'atar jin komai daga wajenka abinda idona yagane min ya isheni.

Daddyn yarima kallon yarima yayi cike da takaici yace suhail ka ban kunya kana gani yadda nake zaune da d'an uwana lafiya ammah karintse ido kakarta min rashin mutunci har haka, yanzu da wane ido kakeso ink'ara kallonsa.

Girgiza kai yarima yashiga yayi yace kayi hak'uri daddy wlh nima ba a son raina hakan takasanceba.

Memartaba a hankali yafurta innalillahi wa'innah ilaihiraji'un, kallon kowa yayi d'aya bayan d'aya sannan yamaida kallonsa ga dada yace kin gani ko? Ni yanzu banma san wane hukunci zan yanke masaba ko zan samu d'an sauk'i a raina.

Dada kallon yarima tayi sannan tace ma memartaba ranka yadad'e kaga ita tagaban goshin tasa tana chan tana hutawa babu abinda yadameta bata ma san wainar da ake toyawaba ita ga 'yar gaban goshi me ciki.

Jinjina kai memartaba yayi sannan yace nasan abinda zanyi, kallon Rahma yayi da take kuka yace ke jeki kisamo min takarda da biro, mik'ewa Rahma tayi tafita.

Nan kowa yayi jugum yana jira yaji hukuncin da memartaba zai yanke.

Bayan kamar minti biyar sai ga Rahma ta dawo rik'e da takarda da biro, tsugunnawa tayi gaban memartaba tamik'a mai,

Kar6a memartaba yayi yace yauwa, sannan yakalli yarima da yake zaune har Lokacin bai d'ago kansa mik'a masa memartaba yayi yace kar6a.

'Dago kai yarima yayi yakalli takardar sannan yamaida kallonsa ga me martaba, a karo na biyu memartaba yace kar6a mana.

Hannu yarima yamik'a yakar6a tare da tsare memartaba da ido yana jira yaji abinda zai ce.

Shima memartaba kallonsa yake sannan yace inaso karubuta ma wacchan matar taka itama saki ukku.

Gabad'aya d'akin d'agowa akayi aka kalli memartaba cike da mamakin kalmar sakin da ya ambata.

yarima ko gabansane yayi wani irin fad'uwa saida biron takubce daga hannunsa, tashin hankaline k'arara yabayya a fuskarsa.

har a lokacin memartaba kallonsa yake fuskarsa ba alamun wasa yace indai kana son cigaba da zama a gidannan toh dole kasaketa saboda hakan shi zaifi dacewa karabu da kowace d'aya daga cikinsu.

Dada gyad'a kai tayi tace tabbas ranka yadad'e ka kawo shawara mai kyau inma cikin da yake jikintane yake ma rawar kai toh taje gidansu da abinda tacigaba da raino zamu dinga aika mata da duk abinda take buk'ata har sai ta haihu, intaso tashayar da abunta inkuma batasoba tabamu abunmu a haka zamu sami wacce zata kular mana da shi.

Ummi ita kanta saida gabanta yafad'i dan ita jin abun take kamar a mafarki tabbas ta san d'anta akwai dalilin da yasa ya saki sumayya saidai miskilanci da zurfin jikinsa bazasu ta6a barinsa yafad'aba.

Abban sumauya ne yaduk'ar da kansa yace ranka yadad'e ataimaka a sassauta ma yarima wannan hukuncin yai masa tsauri.

Sultana sadiya da take gefe takaici duk ya cikata tana ji kamar tashak'e yarima yamace kowa yahuta, jin maganar da mijinta yayi yasa tawurga masa harara, sai a lokacin tace ranka yadad'e tabbas wannan hukuncin da kayanke shine daidai dan yarima ya tozarta min d'iya,,,, d'aga mata hannu sultan abbas yayi yace ke banason hauka na san duk abinda yaima sumayya toh tana da laifi a ciki dan na san sumayya bata ji.

Sultan Ahmad ne  yai k'arfin hali yace ma sultan Abbas kadaina cewa haka domin yarima bai kyautaba.

Memartaba gyaran murya yayi nan kowa yanutsu, sannan yace duk naji k'orafinku saidai inaso kusani babu wanda ya isa yasa incanza maganata dan ku kanku kunsani ni kaifi d'ayane bana magana biyu.

Duk'ar da kansu sukayi sukace Allah yaja da ran sarki me adalci.

Memartaba kallon yarima yayi da duk sanyin A-C d'in da take d'akin ammah bai hana yayi zufaba, murmushi Memartaba yayi sannan yace suhail ina saurarenka dan kaji abinda nafad'a.

Aunty husna ce tad'auki biro d'in da tafad'i tamik'a mashi.

Cikin sanyin jiki yarima yak'arfi biro d'in yad'aura saman paper, nan kowa yazuba mai ido ana jira yarubuta.

Ido yazuba ma paper tare da d'aura biro d'in kamar zaiyi rubutu nan gabansa yashiga dukan ukku-ukku jinsa yake wani iri gabad'aya komai ya kwance masa, yarasa cikin biyu wane zaiyi shin sakin zarah zaiyi ko kuma ya amince yarabu da family d'insa, runtse idanunsa yayi yana jin wani irin k'unci a ransa........



_Shin yarima zai amince yasaki zarah?_

_Ko zai amince yarabu da family d'insa kamar yarda memartaba yafurta?_

_*Muje Zuwa dan jin yadda  zai kasance*_



_Comment_
     *nd*
_Share_





_Sis Nerja'art✍🏻_👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_*Nagode Sosai da kulawarku agareni masoya, gaskiya naji dad'i dan naga k'auna zallah daga gareku, banda abinda zanyi inbiyaku saidai ince Allah yabar k'auna da dank'on zumunci😘*_

*PAGE* 5⃣7⃣

Ahankali yabud'e idanunsa da gaba d'aya suka canza launi, ji yake kamar yarubuta ma zarah saki sai kuma yaji bazai iya aikata hakanba dan shi kansa ya san idan yasaketa bai mata adalciba.

'Dago kai yayi yakallesu d'aya bayan d'aya har a lokacin idanunsu suna a kansa,,,Yarima kallonsa yasafke ga memartaba cikin sanyin jiki muryarsa tana rawa yace kagafarceni ranka yadad'e bazan iya rabuwa da matataba.

Gabad'ayansu a firgice suke kallonsa hatta shi kansa memartaba yayi mamakin furucin da yafito daga bakin yarima.

Murmushi memartaba yayi sannan yace suhail idan na fahimceka toh kana nufin ka za6i matarka akanmu ko?

Cike da damuwa yarima yagirgiza kai yace ranka yadad'e ba haka nake nufiba kawai dai... katseshi memartaba yayi yace kawai dai me!!! Toh bara kaji indai har bazaka iya rabuwa da itaba toh mu yazamar mana dole murabu da kai, dan haka kaje kawai na cireka daga cikin masarautata yanzu ka fita daga cikin iyalaina dan haka na baka awa d'aya kaje duk wani abu da kasan mallakinane kaje kakawo min sannan kafita kabarmin masarauta, inkuma ba hakaba zansa a fitar da kai a wulak'ance.

Gabad'aya d'akin shuru sukayi kamar ruwa ya cisu dan sunsan tunda har memartaba yafurta toh tabbas ba wanda ya isa yacanza.

Yarima runtse idonsa yayi yana jin yadda maganar memartaba take dukan dodon kunnansa wani irin d'acine yakeji a ransa

Ummi ko rufe fuskarta tayi da alkyabbarta tana goge hawayen da suka taru a idonta, gabad'aya lamarin ya rikitata.

Daddy ma shikad'ai yasan abinda yakeji a ransa game da maganar da mahaifinsa yafurta, kawai dai ya dakene bai nuna ba.

Dada ce takalli memartaba tace ammah ranka yadad'e ba... d'aga mata hannu memartaba yayi yace banason jin maganar kowa daga cikinku dan ni nariga da nagama magana yanzu lokacin da nabaka zai fara aiki.

Yarima har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa, ahankali yamik'e jiki ba k'wari kamar wanda kwai yafashe mawa a ciki haka yake tafiya har yafita daga d'akin.

Rahma da Aunty husna ko kuka sukeyi ahankali, inda sumayya take kuka akan mutuwar aurenta.

Yarima ahaka ya isa part d'insu, bakin gadonsa yazauna yadafe kansa shi kad'ai yasan abinda yakeji gashi an hanasa yai magana, tunani yashiga yi shin in ya bar gidansu ina zaije? Tunowa yayi da maganar memartaba da yace ya fara cin lokacin da yabasa, dan haka yajanyo wayarsa yakira wata number bata dad'e tana ringing ba akayi picking,

Yarima k'ok'arin saita nutsuwarsa yayi suka d'an gaisa sama-sama sannan yace Dr Mu'az kana gari?
Daga chan 6angaren wanda aka kira da Dr mu'az yace eh ranka yadad'e.
Ohk, please kaje kasamar min hotel maikyau yanzu zan shigo Abuja.
Cikin jin dad'i Dr mu'az yace angama ranka yadad'e Allah yakawoka lafiya.

Ameen yarima yace sannan yakashe wayar,
Sannan yakira yasa ayankar masa ticket na mutum biyu yace yanzu yakesonta, kasancewar sanannene nan suka amsa masa, bayan sungama wayar yai musu transfer d'in kud'insu, bayan ya gama Dr khalil yalalubo bai wani 6ata lokaciba yai picking

Yarima ko gaisawa bai bari sunyi ba yace Dr khalil kana ina yanzu?

Daga chan 6angaren Dr khalil yace ranka yadad'e ganinan wajejan anguwarku gidan Auntyna.

Ohk, please kazo yanzu akwai inda nakeso kakaini.

To ranka yadad'e ammah ya naji muryarka haka? Lafiya dai ko?

Yarima kashe wayarsa yayi batare da ya bashi amsaba,,,,mik'ewa yayi yaje yafara had'a duk wani abu da yasan ba mallakinsa bane yaware ma daddy da memartaba nasu sannan yad'auki nashi, wajen wardrobe d'insa yaje yabud'e nan yafara fitar da kayansa yana sawa a trolly, cikin trolly guda yazuba duk wani abu da yake buk'ata sannan yajawo,

Tsaye yayi yana k'are ma room d'insa kallo yana jin k'unci a ransa, janyo trollyn yayi yafito cikin sauri guards d'insa suka zo suka kar6a nan yace suwuce masa da shi waje.
Cike da ladabi suka amsa masa.

Daga nan part d'in zarah yawuce kallonta yayi har lokacin tana kwance, ita kanta zarah yanayinsa kawai tagani tasan yana cikin tashin hankali,

Yarima batare da ya janye idonsa akantaba yace tashi kihad'a kayanki,

Zarah saida gabanta yafad'i tace na'am.

Shareta Yarima yayi yawuce wajen wardrobe d'inta yabud'e nan yafara zuba mata a trolly duk abinda yasan zata buk'ata saida yazuba mata a ciki, bayan ya gama juyowa yayi yakalli zarah da tatsaresa da ido yace tashi muje.

Zarah k'wallah ce tacika mata ido tace ina zamuje?

Tsawar da Yarima yadaka matane yasa tamik'e ba shiri tajanyo veil d'inta tayafa nan Yarima yawuce gaba tana biye da shi, wata kuyangarta ce cikin sauri takar6i trollyn da yake hannun Yarima

Zarah tana biye da yarima gabad'aya kanta ya d'aure gashi yarima bai bata fuskar da ma zata iya tambayarsaba ahaka har suka fito harabar gidan, da mamakinta sai gani tayi sun nufi turakar su memartaba.

mamaki bai ida kamataba saida suka shiga d'akin taga gabad'aya family d'in yarima suna a ciki, bata lura da yanayin da suke cikiba, dasauri tatsugunna tagaishesu, gabad'ayansu babu wanda ya amsa mata,

Ta d'auka basujiba nan tak'ara gaishesu, dady da abbah ne kawai sukayi k'arfin halin amsa mata,

'Dagowa tayi takalli ummi da talullu6e kanta da alkyabba, sai kuma takalli su Aunty husna da rahma da suketa kuka, nan jikinta yak'ara yin sanyi, daganan tamaida kallonta ga sumayya da take gefen dada tana ta rusa kuka, inda dada tabuga uban tagumi,  sultana sadiya ko ta cika tayi fam.

gani tayi yarima ya wuce wajen memartaba nan yarussuna yamik'a masa wasu files, a wulak'ance memartaba yakar6a sannan yace ina fata komai ne nan kakawo min.

Ahankali yarima yace eh ranka yadad'e,

Jinjina kai memartaba yayi sannan yace yarima ka bani mamaki yanzu saboda mace ka amince karabu da kowa naka, inaso kasani dangi basu canzuwa ammah ita mata a kowane lokaci zaka iya canzata, tunda ka za6i mace akan danginka toh sai katashi kutafi.

Zarah cikin sauri tad'ago kai takalli memartaba da yake maganar dan kwata-kwata bata fahimci inda maganarsa tadosaba,

Dada ce cikin damuwa tace ammah har a yanzu suhail idan ka amince zaka rabu da ita toh bismillah dan kasan memartaba yana nan akan bakansa,,,tak'arashe maganar tare da mik'a masa takardar.

girgiza kai yarima yayi yace kugafarceni har yanzu ina akan bakana nima yana fad'in haka yamik'e

Sumayya ce tasake fashewa da kuka tace yanzu saboda waccan jakkar kasakeni saki ukku yarima, wlh bazan yardaba sai ka maidani d'akina, duk inda kaje zaka dawo kataddani.

Zarah sai a lokacin ta fahimci abinda ake tattaunawa gabantane yashiga dukan ukku-ukku a firgice takebin kowa na cikin d'akin da kallo,

Rahma ce tayi saurin mik'ewa dagudu taje tafad'a jikin yarima, cikin kuka tace dan Allah bro kar katafi kabarmu dan Allah ka amince karabu da matarka kazauna cikin danginka.

Yarima idanuwansa ne suka kad'a sukayi jawur kallon daddy yayi da ya janye fuskarsa gefe, a 6angaren abbah ma gefe d'aya yake kallo,

Yarima har ya bud'e baki zaiyi musu magana sai kuma yafasa, janye rahama yayi daga jikinsa, kallon umminsa yayi da taketa k'unshe kukanta, wani iri yaji a ransa gudun kar yaimata magana yaja tayi kuka saisa baice mata komai ba yawuce yanufi inda zarah take tsugunne tana hawaye.

Kallonta yarima yayi yace tashi muje.

Girgiza kai zarah tashiga yi dak'yar tabud'e baki muryarta tana rawa tace please yarima kar karabu da danginka ni yafi dacewa karabu da ni dan danginka sune komai naka, mik'ewa tayi tare da fashewa da kuka had'e hannuwanta tayi waje guda tace dan Allah yarima na rok'eka kacika umurnin memartaba kasakeni kawai, cikin sauri taje takar6o takardar hannun dada tadawo inda yake tsaye tamik'a mashi tace please karubuta min sakina, kar katafi kabar su ummi, neman tura mashi tankarda tayi a hannunsa ganin ya k'i kar6a yasa tawuce inda ummi take zaune tatsugunna cikin kuka tace please ummi kisa baki yarima yarubuta min sakina bana son yasamu matsala da kowa dan ku kune farin cikinsa.

Ummi kasa 6oye kukanta tayi nan tafara sheshek'ar kuka, zarah ganin ummi batada niyar cewa komai yasa tamik'e takoma wajen yarima tace kaduba kaga ummi da 'yan uwanka kuka suke yanzu ka amince katafi kabarsu cikin....wani gigitacce mari yarima yakwad'a mata wanda gabad'aya 'yan cikin parlourn saida suka kallosu, yarima cikin 6acin rai yace zarah kidawo hayyacinki.

Nan zarah tashiga hankalinta tare da kife kanta a k'irjin yarima tarushe da wani sabon kukan, yarima jin kukan nata yake har cikin ransa, janyeta yayi daga jikinsa nan yarik'e mata hannu suka fara tafiya, memartaba janye idonsa yayi daga kallonsa inda su daddy daman basu d'ago ba dama.

Aunty husna ce cikin sheshek'ar kuka tace yarima na rok'eka kar ka aikata hakan dan Allah kadawo,

Jan hannun zarah yayi suka ficce daga parlourn Aunty husna har ta mik'e zata bi bayansa nan taji muryar memartaba  ya ce kar wanda yasaki yabi bayansa.

kan dole takoma tazauna.

Yarima yana fita nan yatarar da Dr khalil tsaye yana jiransa, wajen motar dr khalil yanufa.

Cikin sauri Dr khalil ya iso inda yake yace yarima ya naganku haka?

Yarima kallon guards d'in yayi yace susaka masa kayansa a boot, cikin sauri suka cika umurninsa.

Nan suka bud'e masa motar yashiga, zarah da take tsaye fuskarta rufe da mayafi itama aka bud'e mata baya tashiga.

Dr khalil da yake tsaye zuwa yayi yashiga motar tare da kallon yarima yace ranka yadad'e ina muka nufa?

Yarima batare da ya kallesaba yace airport.

Cikin sauri Dr khalil yatayar da motar, lokacin da zai fita daga masarautar yarima runtse idanunsa yayi yana jin wani iri a cikin ransa,

Tafiya suke ammah gabad'aya babu wanda yayi magana,

Dr khalil juyowa yayi yakalli yarima da yazuba ma titi ido cike da damuwa yace ranka yadad'e wace irin tafiya ce ta gaugawa takamaka haka? Ina zakaje?

Yarima batare da ya juyo ya kallesaba yace Doctor ga amanar hospital d'ina nan na damk'a a hannunka domin nasan zaka kularmin da shi kamar yadda zan kula da shi ammah ban saniba ko nan gaba za'a kawo wanda zai maye gurbina, koma mekenan nidai na aminta da kai.

Kiiittt yaja burki yatsaya tare da juyowa yakalli yarima, cike da damuwa yace please yarima kaimin bayani yadda zan fahimta dan gabad'aya ka d'aure min kai, wace irin tafiya ce zakayi haka? Ina zakaje please kafad'a min.


Yarima duba agogon hannunsa yayi sannan yace please kayi sauri flight d'in da zamu bi ya kusan safka.

Tada motar Dr khalil yayi dagudu yafigi motar.

Yarima ta mirror yakalli zarah da tabuga uban tagumi, jingine kansa yayi a kujeyar da yake zaune tare da k'ura mata ido ta mirror d'in, zarah ko bata ma san yanayiba dan gabad'aya ta yi zurfi cikin tunani.

Suna isa flight d'in yana safka, Dr khalil cikin sanyin jiki yakalli yarima yace Dr toh yanzu sai yaushe zaka dawo?

Murmushin k'arfin hali yarima yayi sannan yace kar kadamu ba wani dad'ewa zanyiba.

Jinjina kai Dr khalil yayi sannan yace ammah zanyi kewarka dayawa,

Yarima kallon abokin nasa yayi yace nidai fatana karik'e min amanata kacigaba da tafiyar da komai daidai kamar ina nan.

Murmushi Dr khalil yayi yace karkadamu insha Allahu zanyi kamar yarda kace,
Nagode sosai abokina,,, yarima yafad'i hakan cikin jin dad'i, sannan yabud'e k'ofar yafita,

Nan shima Dr khalil yafita, yarima dakansa yabud'e ma zarah k'ofan, dak'yar tasafko k'afanta tafito, nan yarima yana rik'e da ita yai waya akazo aka kawo masa komai nasa, kayansu aka fitar aka saka a cikin flight d'in.

Dr khalil har wajen jirgin yarakasu nan suka k'ara sallama da yarima cikin rashin jin dad'in nisan da zasuyi da juna.

Zarah ko saboda tashin hankalin da take ciki baisa tayi murnaba koda wannan shine karo na farko da tafara shiga jirgi.

Daga gefen yarima take zaune har jirgin yatashi, wani irin kunci da bak'in ciki yaziyarci zuciyan yarima a lokacin da suka fara tafiya, bak'in space d'insa yajanyo yadad'e idonsa, zarah cikin rashin k'arfin jiki takwantar da kanta a saman k'irjin yarima.

Rungumeta yayi cike da tausayinta, ahaka zarah tayi bacci.

Cikin k'ank'anin lokaci suka isa garin abuja.

Jirginsu na dira yarima yakira Dr mu'az yace gamu mun safka.

Dr mu'az cewa yayi ranka yadad'e ai gani nan tun d'azu nake jiran safkarku.

Tada zarah yayi da take bacci nan suka fito.

Wani mutum ne wanda bazai wuce tsaran yarima ba koda ma zai girmi yarima toh dakad'an ne, nan ya iso inda suke fuskarsa d'auke da fara'a.

Yarima koda yana cikin damuwa ammah hakan baihana sa nuna jin dad'in ganin abokin nasaba,

Dr mu'az cike da jin dad'i yace sannu da zuwa prince suhail.

jinjina kai kawai yarima yayi sannan yamik'a masa hannu sukayi musabaha.

kallon zarah yayi yace sannu madam.
Zarah batare da ta kallesaba tagaishesa, daga nan yace prince zamu iya tafiya.

Murmushi kawai yarima yayi nan yaruk'o hannun zarah, inda Dr mu'az yasa aka d'aukar musu kayan aka saka bayan boot.

Koda suka kama hanya Dr mu'az kallon yarima yayi yana murmushi yace prince ka kwana biyu bakazo garin nan ba yau ma ji nake kamar a mafarki naganka.

Murmushi yarima yayi yace kaima kasan yanayin aikinmu ne yake 6oyemu tunda kaima kakwana biyu baka lek'aniba.

Dariya Dr mu'az yayi yace wlh abokina nima naso inzo abubuwan ne sukaimin yawa kowane lokaci busy nake ammah da badan hakaba ai da ba abinda zai hanani zuwa dan kaima ka san banda aboki sama da kai dan kaimin *HALARCI* a rayuwata wanda bazan ta6a mantawaba.

Murmushi yarima yayi yace kadaina magana akan abinda yariga da yawuce.

Hmm ai duk zuciya mai adalci bazata ta6a mance alkhairin da akayi mataba,,,daidai lokacin Dr mu'az yashawo kwanar gidansa.

Kallonsa yarima yayi cike da mamaki yace ni da zaka kai hotel ya naga ka kawomu gidanka?

Murmushi Dr mu'az yayi yace taya kake tunani zan iya barinka kazauna a hotel alhali ina cikin garin nan, ai kaima kasan hakan bai daceba.

Yarima janye idonsa yayi daga kallonsa sannan yace kar kadamu ni nasan fiye da hakan ma zaka iya yimin ammah ni nafi buk'atan son zama a hotel d'in.

Doctor Mu'az tsayar da motar yayi yajuyo yakalli yarima cike da damuwa yace ranka yadad'e kayi hak'uri da inbarka kazauna a hotel na k'wammace ni inbar maka gidana kazauna inje inkama haya,
Yarima shuru yayi baice komai ba.
cike da damuwa Dr mu'az yace dan Allah ka amince muje gidana.

Zarah da take zaune baya tana saurarensu ita kanta cikin ranta bata son suje hotel.

Murmushi yarima yayi yace shikenan na amince Dr.

Cike da jin dad'i Dr mu'az yace nagode sosai doctor.

Nan yatada motar, a bakin gate d'in gidansa yayi horn, cikin sauri megadi yazo yabud'e masa gate nan yacinna motarsa cikin makeken gidan.




_Comment_
      *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Ummu Zainab tsakanina da ke saidai addu'a dan banda abinda zan biyaki da shi, Allah yak'ara lafiya, Allah yasa ciwon zakkar jikine, Allah yatashi kafad'unki, Nagode, Nagode, Nagode sosai Allah yabiyaki abinda kikayi min_

*PAGE* 5⃣8⃣

Koda yayi parking kallon yarima yayi yace ranka yadad'e mun fa iso.

'Daga kai kawai yarima yayi, nan Dr khalil yakalli zarah ta mirror yace gimbiya bismillah mun iso, murmushi zarah tayi cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace toh.

Gabad'ayansu suka bud'e motar suka fito, yarima kallon zarah yayi da take taku dak'yar yace ko intaimaka miki?

Zarah batare da ta kallesaba tagirgiza kai, nan Dr mu'az da yarima sukayi gaba tana bayansu har suka shiga a main parlour suka tarar da matar gidan zaune ganinsu yasa tamik'e fuskarta d'auke da fara'a tace oyoyo ga manyan bak'i,
Dr mu'az ne yayi murmushi yace dear yau fa ga prince a gidan namu,
Murnushin jin dad'i tayi tace yau muntaki sa'a gaskiya,

Saman kujerun da suke d'akin suka zauna nan matar dr mu'az tad'an russuna cikin girmamawa tagaishe da yarima.

Murmushi yarima yayi sannan ya amsa mata,
Wajen zarah tanufa tana murmushi tace gimbiya sannu da zuwa ina wuni?

Murmushi itama zarah tayi sannan tace ina wuni.

Bayan sun gama gaisawa, Dr mu'az yace ranka yadad'e ga d'an akurkin gidan namu ina fata zaku iya rayuwa a cikinsa.

Harararsa yarima yayi yace kai fa tsiyata da kai ka iya tsokana.

Dariya Dr mu'az yayi yace ai gaskiya ce nafad'a,
Kallon matarsa yayi yace jamila gashinan prince yau wani irin farin ciki nakeji da naganni tare da shi, abokina ne tun daga primary har secondary  tun lokacin banda komai muke tare da shi, shine silar yin karatuna dan a lokacin iyayena basuda komai mu talakkawane sosai da taimakonsa nayi karatu har nakai wannan matsayin da nake da shi kinga ko taya zan iya mance prince?

Jinjina kai matarsa tayi tace tabbas hakane bazaka ta6a mancewa da halacci da yayi makaba, saisa a kullum yana cikin addu'anmu.

Kallonta yarima yayi yace madam kema kin biye ma wannan mijin naki sarkin tsokana.

Murmushi Dr mu'az yayi yace prince kenan kaima kasan gaskiya nafad'a saidai idan kanason 6oyetane.

Shuru yarima yayi baice komai ba.

Zarah dai tana zaune tana saurarensu ita dai burinta takwanta tahuta.

Matar mu'az mik'ewa tayi tace bari akawo muku ruwa kusha kafin agama abinci.

Bayan ta fita Dr mu'az kallon yarima yayi yace ranka yadad'e muje kuza6i part d'in da yayi muku a cikin gidan nan.

Girgiza kai yarima yayi yace no ba sai mun za6aba duk wanda aka bamu munaso yanzu magrib ta gabato muna buk'atar kimtsawa ga madam babu lafiya ina so asamo min drip zansa mata,,,yak'arashe maganar tare da kallon zarah.

Dr mu'az yace ayya Allah yasauk'e bari inje insa asamo daga nan ashigo muku da kayanku, yana fad'in haka yamik'e yafita yabar d'akin.

Yarima kallon zarah yayi da ta jingine kanta a kujerar da take yana shirin yin magana sai ga Matar mu'az ta shigo dan haka yafasa.

A gabansu ta aje k'aton tray d'in da yake d'auke da kayan marmari nan tatsiyaya musu drinks a cups ta aje ma kowa gabansa sannan tace kuyi hak'uri abincin ya kusan zama ready.

Murmushin k'arfin hali zarah tayi tace bakomai Aunty hakan ma mun gode, nan tad'auki cup d'in tafara shan drink d'in.

Nan Dr mu'az yashigo bayansa megadine janye da trollies d'in su yarima d'aya daga cikin rooms d'inne Dr mu'az yasa aka shigar da kayan sannan yakalli yarima yace ranka yadad'e kuduba kuga idan part d'in baiyi mukuba sai a canza.

Murmushi yarima yayi yace kar kadamu yayi mana, kallon zarah yayi yace muje kisamu kihuta.

Jamila cike da tausayi takalli zarah tace sannu gimbiya, Allah yabaki lfy.

Cikin Jin kunya zarah tace Ameen Aunty nagode, nan tamik'e tabi bayan yarima.

Wani makeken d'akine mai d'auke da room nd bedroom ya tsaru sosai komai na cikinsa mai kyau da tsada ne, angyara ko'ina fes, suna shiga bedroom zarah saman gadon tafad'a takwanta agajiye, kallonta yarima yayi sannan yawuce yashige bathroom dan yawatsa ruwa.

Bayan ya fito kallon zarah yayi da take kwance yace kitashi kije kiwatsa ruwan ko kinji k'arfin jikinki.

Zarah kallonsa tayi ganinsa d'aure da towel yasa tad'auke kanta, batare da ta k'ara kallonsaba tamik'e tanufi wajen kayansu wardrobe d'in tabud'e saida tagogeta sannan tabud'e trollies d'insu duk tajere musu kayansu, Bayan ta gama ta gefen yarima taratsa taje tashige bathroom, cikin sauri yarima yad'auko kayansa yasaka sannan yatayar da sallar magrib a gida, dan a lokacin ana gab da sallame sallah a masallaci.

Yana saman darduma zarah tafito d'aure da towel tawuce wajen wardrobe d'in tad'auko gown tasaka sannan tayi sallah.

Koda yarima yagama saman gado yakoma yazauna nan yajanyo wayoyinsa yacire dukkan sim d'insa yakashe wayar ya aje.

Dafe kansa yayi yana jin wani iri a ransa dan baisan halin da umminsa zata shigaba dan gabad'aya itace damuwarsa, abubuwan da suka faru nan suka fara dawo masa a rai.

Zarah da take tsaye tana kallonsa wani irin tausayin mijin nata takeji, ita kanta zuciyanta zafi take musamman ma da tasan ta dalilinta yarima yafad'a wannan matsalar, hawayene suka fara fita daga idanunta, ahankali tataka ta isa inda yake daga gefensa tazauna,
'Dago kai yarima yayi yakalleta ganin tana hawaye yasa yace zarah meyake samunki ko jikin ne?
Girgiza kai tayi tace banso karabu da kowa nakaba saboda ni, da ace ni karabu da ni inyaso koda bayan na haihu ne sai ka amshi babynka.

wani irin abu yaji ya tokare masa zuciya akan maganar da tayi, janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace zarah ba zan miki doleba indai kinsan bazaki iya zama da ni ba toh kifad'amin insha Allahu zan baki takardarki dan zan iya rayuwa ni kad'ai koda ace banda kowa,

Jikinsa tafad'a tare da fashewa da kuka tace kayi hak'uri ni ba haka nake nufiba wlh zan iya zama da kai a kowane hali.

Wani irin sanyi yaji a ransa,
Knocking d'in da akayine yasa yajanyeta daga jikinsa tare da mik'ewa yawuce yaje yabud'e.

Dr mu'az ne yana murmushi yace  ranka yadad'e ga fa dinner chan a dining yana jiranku inkuma nan za'a kawo muku toh.

Yarima murmushi yayi yace ohk, gamunan zuwa nan yamik'a mai ledar hannunsa yace ga sak'on ansamo.

Kar6a yarima yayi yace nagode.

Koda yajuyo kallon zarah yayi da take kuka, itama d'ago kai tayi takalleshi, ahankali yace kukan fa?

Zarah turo baki tayi tace bakai bane kake fushi da ni.

Yarima wucewa yayi ya aje ledar saman bedside batare da ya kalletaba yace tashi muje kiyi dinner inyaso sai insanya miki drip d'in daga baya.

girgiza kai zarah tayi tace ni na k'oshi.

Kallonta Yarima yayi yace me kikaci da kika k'oshi?
Shuru tayi batace komai ba dan haka yarima yace oya tashi muje.

Mik'ewa zarah tayi taje tad'auko hijab d'inta tasaka sannan tabi bayan yarima suka fito.

A main parlour suka tarar da su zaune suna jiransu ganinsu yasa suka mik'e suka nufi dining.

Jamila ita tayi serving d'in kowa, zarah tunda tarik'e spoon d'in kallon plate d'in kawai take.

Yarima ahankali yad'ebo yaci idanunsa suna kan zarah, d'ago kan da zatayi ne suka had'a ido cikin sauri tad'ebo taci,

bawani dayawa yaciba nan yatsare zarah da ido har saida yaga ta d'an ci na kirki sannan yamik'e yakalli Dr mu'az da shima yake kallonsa yace Dr ba dai har ka k'oshiba.

Murmushi yarima yayi yace am ohk.

Jamila ce tace ranka yadad'e ko dai girkin ne baiyi makaba acanza maka wani?

No madam girkin ya yi min dad'i sosai kawai k'oshine nayi.

Zarah ma ganin zai bar wajen yasa tamik'e, kallonta jamila tayi tace gimbiya kodai kema abincin baiyi mikiba.

Girgiza kai tayi tace wlh Aunty jamila yai min dad'i sosai sai ma nazo kin koyamin.

Dariya jamila tayi tare da kallon mijinta tace sweet kana jin gimbiya tana tsokanata.

Dr mu'az murmushi yayi yace kibarsu na lura kamar abincin baiyi musu ba.

No kawai dai a gajiye muke muna buk'atar hutune....cewar yarima.

Ohk doctor ahuta lafiya, nan sukayi musu sallama suka koma masaukinsu, zarah wajen wardrobe tanufa dan tacire kayan jikinta dubawa tayi ammah ba sleeping dress ko kala d'aya, juyowa tayi takalli yarima kamar zatayi kuka tace baka sakomin kayan bacciba.

Kallonta yarima yayi batare da yayi magana ba, ganin haka yasa zarah tace ni kuma ban iya bacci da na jikina.

Toh ya kikeso inyi ina zan je yanzu insamo miki sleeping dress a yanzu, kibari zuwa gobe insha Allahu zan samo miki, yanzu kizo insa miki drip d'in.

Zarah turo baki tayi taje tahau gadon takwanta nan yarima yahad'a drip d'in yasa mata, bayan ya gama daga gefenta yayi zaune yazuba ma waje d'aya ido,

Zarah kallonsa take cike da tausayinsa dan ko ba a fad'aba yanayin yarima kawai zaka kallah kasan yana cikin damuwa kawai dai daurewa yakeyi baya nunawa.

maida idanuwanta tayi talumshe tana ji kamar tarungumo mijinta talallashesa ko ya rage damuwar da take tare da shi.

Wajen k'arfe tara yarima yatashi yaje yashiga wanka, lokacin da yafito daidai lokacin ruwan yak'are nan yacire mata sannan yawuce wajen wardrobe yafiddo kaya.

Zarah mik'ewa tayi itama tashiga toilet dan tawatsa ruwa.

Lokacin da tafito tsaye take d'aure da towel tana kallon yarima da yake zaune bakin gado ya dafe kansa, ahankali tataka ta isa inda yake, janye hannuwansa tayi da yadafe kan, nan yarima yad'ago yakalleta damuwa k'arara a fuskarsa.

Cike da rashin damuwa zarah tazauna saman cinyarsa nan idanunta suka cika da k'wallah ahankali tace meyasa kake shiga damuwa? Bakasan ganinka cikin irin wannan yanayin yana d'agamin hankali ba? Taya ni hankalina zai kwanta alhali kai gabad'aya naka hankalin a tashe yake, dan Allah kadaina shiga damuwa wlh ni ina tare da kai a kowane lokaci,,,,tak'arashe maganar tare da fashewa da kuka.

Yarima runtse idanunsa yayi yana jin wani iri akan kukan da takeyi rungumeta yayi a k'irjinsa nan zarah ta narke mashi tacigaba da wani irin kuka
Cikin wata irin murya yace please zarah kukan ya isa haka.
Cigaba tayi da kukanta, nan yarima yacigaba da lallashinta ammah tak'i daina kukan, tallabo fuskarta yayi yana kallonta yace wai zarah ya kikeso inyi ne? Nima kinaso inyi kukan ne?

Cikin sauri zarah tagirgiza kai tare da rage sautin kukanta.
Da mamakinta sai gani tayi yarima ya sa harshenta yana lashe hawayen fuskarta, ai nan sai kukan yatsaya tacigaba da binsa da kallo, daga karshe yatura bakinsa cikin nata yana mata tsotsar lolli pop, kamar daman zarah jira take nan tabiye masa suka cigaba da kissing d'in juna, tana ji lokacin da yazare mata towel d'in da yake a jikinta nan yacigaba da yawo da hannuwansa a jikinta, zarah ma hannuwanta tad'aura tana shafar lallausan gashin da yake kwance a k'irjinsa cikin wani irin siga.

Sun dad'e a haka sannan daga k'arshe yarima yad'auketa suka haye gado nan zarah ta dage sosai wajen ganin mijinta ya samu nutsuwa duk yadda takejin batada lafiya ammah haka tadaure taba yarima kanta, shi kansa ahankali yadinga bi da ita saboda ya san batada lafiya kawai dan ba yarda zaiyi da sai yahak'ura yabarta.

Bayan komai ya lafa yarima rungumeta yayi a k'irjinsa yana shafar gashin kanta, zarah ko cikin jikinsa talafe idanuwanta a lumshe tana numfashi ahankali.

kallon agogo yayi ganin lokaci ya ja yasa nan yajanyeta daga jikinsa yamik'e.

Zarah batare da ta bud'e idanunta ba tayi saurin rik'o hannunsa, yarima juyowa yayi yakalleta yace ya dai?

Cikin shagwa6a zarah tace nima ina son wankan.

Batare da ya yi magana ba nan yaduk'a yad'auketa yanufi toilet da ita saida yatara ruwa sannan yasafketa ciki, zarah sai a lokacin tabud'e idanunta ganin baida niyar shigowa yasa tace please kashigo muyi wankan.

Shuru yarima yayi.
Ganin baida niyar yin magana yasa tajingine kanta tare da runtse idanunta, da mamakinta sai ji tayi ya shigo cikin ruwan bud'e idanunta tayi tare da komawa jikinsa.

Ganin batada niyar yin wankan yasa yarima yayi mata sannan shima yayi  nasa, wankan tsarkine kawai tayi da kanta bayan sun gama shagwa6a tasa mashi kan dole yad'auketa suka baro toilet d'in.

A saman gadon yadireta nan shima yakwanta tare da jawo blanket yalullu6esu, zarah jikinsa takoma takwanta nan yarungumeta ahaka har tayi bacci ammah yarima bai samu yarintsaba sai wajen k'arfe ukkun dare.

Da asuba sun so sumakara sallah, dan saida gari yad'an fara haske sannan suka tashi.

Bayan sunyi sallah baccinsu suka koma, basu suka farka ba sai wajen 11am.

Yarima yafara shiga yai wanka lokacin da yafito zarah ta gyara ko'ina k'amshi kawai yake tashi.

Bayan ya fito itama taje tashiga lokacin da tafito yarima har ya gama shirinsa cikin dakakkiyar shaddarsa ya yi gwanin kyau, gaban dreesing mirror zarah tatsaya nan tafara shafa lotion, tana ganin yarima ta cikin mirror d'in yadda yatsareta da ido, karaf suka had'a ido.
'Daga masa gira zarah tayi alamun ya dai?
Janye idanunsa yayi daga kallonta.
zarah tana cikin shafa takallesa kamar zatayi kuka tace wayana fa tana chan na baro ban zo da itaba.

Shuru yarima yai mata, ganin haka yasa tacigaba da shirinta nan tawuce tabud'e wardrobe tad'auko atamfa d'inkin riga da skirt nan tasaka sannan taje gaban mirror tamurza d'aurin kallabinta tare da feshe jikinta da turaruka, juyowar da zatayi nan suka had'a ido da yarima murmushi tasakar mashi tace nayi kyau?

Janye idanunsa yayi daga kallonta sannan yace ba laifi.

Matsowa zarah tayi kusa da shi kamar zatayi kuka tace kana nufin dai banyi kyau ba toh bari inje incanza kayan,,,juyawa tayi kamar da gaske.

Ruk'o hannunta yarima yayi baisan lokacin da yace kinyi kyau ba.

Juyowa zarah tayi tana murmushi tace kaima kayi kyau sosai k'albina.

Kallonta yarima yayi yanaso yagaskaka kalmar da tafito daga bakinta.

Kashe masa ido tayi tare da janyo hannunsa tad'aura saman cikinta tace babynka fa yunwa yakeji.

Janye hannunsa yayi daga cikinta yace muje kiyi breakfast.

Zarah tana rik'e da hannunsa suka tafo har zasu fita nan yarima yatsaya, kallonsa zarah tayi tace ya dai naga ka tsaya?

Shima kallonta yayi sannan yace haka zaki fita ba mayafi.

Oh sorry dear wlh mancewa nayi, nan tawuce taje tabud'e wardrobe tad'auko veil d'inta tayafa sannan tazo suka fita a jere.

Zaune suka tarar da mu'az da matarsa a main parlour suna hira, ganin su yarima yasa suka fad'ad'a fara'arsu mu'az ne yace sannunku da fitowa, hannu yarima yamik'a mashi sukayi masabaha sannan suka samu waje suka zauna

Jamila ce cikin girmamawa tagaishe da yarima nan ya amsa mata.

Zarah ma saida ta gaishe da mu'az sannan tagaishe da jamila.

yarimane yace ashe baka fita aikiba?

Taya zan fita bayan ina da manyan bak'i, ai yau ina tare da kai kwana zamuyi muna hira jiya ma dan naga agajiye kuke saisa nabarku,

Murmushi kawai yarima yayi batare da ya yi magana ba.

Jamila ce tamik'e tace muje kuyi breakfast gashichan tun d'azun yake jiranku.

Gabad'ayansu suka mik'e suka nufi dining nan jamila tayi serving d'in mijinta.
inda zarah itama tayi serving d'in yarima, ruwan lipton kawai zarah tazuba ma kanta tafara sha.

Kallonta jamila tayi tace gimbiya menene wannan zakisha?

Zarah kallon yarima tayi da shima yatsareta da ido sannan tamaida kallonta ga jamila saida tasakar mata murmushi sannan tace Aunty jamila banaso da madara nafi jin dad'insa a haka.

Ayyah Allah sarki ammah ai hakan baya maganin yunwa.

Murmushi Zarah tayi tace kar kidamu lafiya lou nake jina idan nasha.

Haka suka cigaba da breakfast d'in duk d'agowar da zatayi sai sun had'a ido da yarima,
Ganin batada niyar cin chips d'in yasa yarima yace ya za'ayi ruwan lipton kad'ai yarik'eki kici chips d'in mana.

Zarah yamutsa fuska tayi tace na k'oshi.

Mu'az ne yace toh in batasonsa dear ko kije kigirka mata wani abun taci.

murmushi Zarah tayi tace a'a abarsa kawai nafi jin dad'in hakan kawai.

Nan kowa yacigaba da breakfast d'insa, bayan sun gama Zarah taimaka ma jamila tayi suka kwashe kwanukan suka kai kitchen sannan suka dawo nan suka tarar da su yarima a parlour suna ta hira koda rabin hiran duk mu'az ne yakeyinta dan yarima daga uhm sai uhm-uhm sai in tabada amsace shine zaiyi magana, ganin haka yasa jamila taja Zarah sukaje parlournta suka zauna suna hira.

Zarah kallon wani pic d'in wata yarinya tayi da yake manne a bangon d'akin tace Aunty jamila wannan fa babynki ce?

Jamila kallon pic d'in da Zarah take kallo tayi sannan tace eh itace d'iyan da nahaifa tana da 2yrs tarasu tun daga kanta har yau ban k'ara ko 6atan wataba.

Cike da tausayi Zarah take kallonta tace Allah sarki, Allah yakawo masu albarka.

Cikin jin dad'i jamila tace Ameen gimbiya nagode sosai.

nan sukayi shuru nad'an lokaci sannan jamila takalli Zarah cike da sha'awa tace  Allah yasafke mana ke lafiya musha suna.

Cikin jin kunya zarah tace lah Aunty jamila banda fa komai

Dariya jamila tayi tace gimbiya kenan ai saidai kifad'a ma wani ba dai ni ba dan daga ganin yanayinki ya nuna cikine da ke gaskiya kinyi sa'a da kika samu yarima a matsayin mijinki dan ina jin labarinsa sosai wajen mijina yarima mutumin kirkine.

Murmushi Zarah tayi sannan tace Aunty jamila kema ai kuna da kirki sosai.

jamila tana shirin yin magana sai ga Dr mu'az ya shigo kallonsu yayi yace a'ah kuna nan kuna ta hira.

Kallon juna sukayi sukai murmushi sai jamila tace eh mun baku wajene kud'an labarta, muma sai mukazo nan muyi namu dan kar mu matsa muku.

Dariya mu'az yayi yace eh kun kyauta gaskiya, yanzu ma fita zamuyi saisa nalek'o, kallon zarah yayi yace gimbiya kije prince yana son ganinko.

Ahankali tace toh sannan tamik'e tafita takoma masaukinsu, a bedroom tasami yarima zaune yana jiranta.

Daga gefensa taje tazauna, kallonta yarima yayi yace bakyajin magana ko? Na yi miki magana akan zama da yunwa ammah kink'i dainawa.

Zarah saman kafad'ansa tad'aura kanta cikin siririyar muryarta tace kayi hak'uri wlh idan naci amai zanyi.
Cike da tausayinta yace ammah ai sai kija su mama sud'auka bana kula da ke.
d'ago kanta tayi takalleshi sannan tace babu wanda zai ce baka kula da ni saidai wanda baisan wanene yarima ba,,,tak'arashe maganar tare da kashe mai ido d'aya.
Yarima jan hancinta yayi yace bakijin magana ko?
K'irjinshi takwantar da kanta cikin shagwa6a tace ina ji man, inshirya muje tare?
Rungumeta yayi sannan yace ina zamuje tare?
Turo baki tayi tace inda zakaje man.
No kar kidamu kiyi zamanki ba wani dad'ewa zanyi ba, kifad'i abinda kikeso insiyo miki.
Murmushi zarah tayi tace duk abinda kasiyo min inaso.
kallonta yarima yayi yace kidai fad'a kar insiyo abinda baiyi mikiba.
Wani irin fari tayi mashi da ido sannan tace za6in mijina shine nawa indai ya yi maka toh nima zaiyi min kar kadamu my prince.

Ajiyar zuciya yarima yasafke sannan yace shikenan, mik'ewa yayi nan zarah itama tamik'e tabi bayansa har suka fito main parlour lokacin mu'az yana zaune yana jiransa ganin yarima yasa yamik'e.

Jamila da zarah har wajen k'ofa suka rakasu sukai musu Allah yakiyaye hanya sannan suka dawo suka zauna suna hira.







_Comment_
      *Nd*
_Share_





_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Wishing an amazing day and many great things to come to a wonder person. *Happy Birthday my dear umm abideen🎈*_

*PAGE* 5⃣9⃣

Wajen k'arfe biyu su yarima suka dawo lokacin zarah tana a room d'insu tsaye gaban dreesing mirror tana kwalliya yarima yaturo k'ofan yashigo,

Dagudu zarah taje tafad'a jikinsa cikin wata irin siririyar murya tace sannu da zuwa my prince.

Rungumeta yayi sannan cikin kasalalliyar murya yace yauwa ya gidan?

'Dago kai zarah tayi suka had'a ido tace gida ba dad'i saboda baka nan ammah yanzu da kadawo yayi dad'i.

Yarima baisan lokacin da murmushi yasu6uce masaba yace tsokana ko?

Marairaicewa tayi tace dagaske fa.

Rik'o hannunta yayi yace muje parlour kiga abinda nasiyo miki,
Zarah bata musaba tabisa suka fito parlour.

Babban trolly ne tagani aje koda yarima yabud'e cike yake taf da kaya, saman kujera yazauna yace duba kiga.

Zarah bin kayan tayi da kallo sannan tafara d'agawa d'aya bayan d'aya daga gowns ne sai English wears jibgi d'aya da sleeping dress, rigunan tafara d'agawa daga mai budad'en k'irji sai 'yar firit wadda bama zata rufe cibi ba, wasu ma sharashara ne, sai mini skirt da wando atak'aice dai dukkan kayan ba wanda zaka iya zama da su cikin gida bane, saidai in daga kai sai mijinkane.

'Dago kai tayi takalli yarima murmushi yasakar mata yace ya sunyi?

Itama zarah murmushi tayi tace sunmin kyau sosai.

Cikin jin dad'i yarima yace toh kije kigwada, zarah kallonsa tayi tace toh ammah ai kayan bazasu sanyuba cikin gidannan tunda bamu kad'ai bane.

Yarima jingine kansa yayi da kujera sannan yace zasu sanyu man in zaki fita ba sai kidinga d'aura zaneba.

Shuru zarah tayi nan taja trollyn tashiga bedroom da shi, d'auko kayan tayi tafara dubawa tana gwadawa a jikinta daga 'yar riga iya cinya, sai wacce bata rufe cibiba sai marar hannu, gunguni tafara tace inbanda abin Yarima ya za'ayi yasiyo min wad'annan kayan sai kace wata arniya,,,daidai ta d'auko wata zata saka sai gashi ya shigo.

Juyowa tayi takallesa yana tsaye bakin k'ofa ya hard'e hannuwa, murmushi suka sakar ma juna sannan tajuya tasaka rigar,

Kallon kanta tayi ta mirror rigar shara-shara komai na jikinta a waje yake ga iyakar tsawonta iya cinya.

Tana shirin cirewa sai jin yarima tayi ya rungumeta ta baya, lumshe idanuwanta tayi tana murmushi, yarima ta cikin mirror d'in yake k'are mata kallo, ahankali cikin kunnenta yace kinyi kyau baby.

Zarah bud'e idanunta tayi ta mirror suka had'a ido nan tasakar mai murmushi sannan tace nagode,

Gyad'amata kai kawai yayi sannan yajanye jikinsa daga nata, Zarah tana shirin cire rigar yace please kibarta.

Juyowa tayi takallesa sannan tace lunch fa zamuje kayi,

Duba agogon hannunsa yayi sannan yace no zan fara wanka before inyi lunch.

Ohk, bara inje inhad'a maka ruwan,

Yarima baice komai ba yawuce yad'auko towel,
zarah toilet tawuce tahad'a mai ruwan wanka lokacin da tafito ganin yana cire kaya yasa tafito takoma parlour.

Zarah tana zaune yafito sanye cikin k'ananun kaya sunyi mai gwanin kyau.
Tsaresa tayi da ido tana kallonsa.
Ganin batada niyar daina kallonsa yasa yarima yace ya dai?

Janye idonta tayi cike da jin kunya tare da mik'ewa tace bari incanza kaya muje kayi lunch, ta gefensa tatafo zata ratsa tawuce, jawota yarima yayi tafad'o jikinsa, wani irin kallo yake aika mata da manyan idanunsa kallon da yake kashe mata jiki sannan yace ba sai kin canza kayaba  kisaka hijab da zane kawai sai muje.

Cikin kasalalliyar murya tace toh,  ba yadda ta iya haka tawuce bedroom tad'auko zane, cikin ranta tana cewa ina ma ace guy d'innan sona yake da naji dad'i.

Hijab d'inta har k'asa tad'auko tazura sannan tafito tasamesa a parlour yana jiranta, tsaye tayi tana kallonsa ganin yadda ya jingine kansa da kujerar da yake zaune samanta, cike da tausayi tabisa da kallo dan ko ba'a fad'aba tasan tunani yakeyi.

Gyaran murya zarah tayi nan yarima yad'ago kai yakalleta yace kin fito?

d'aga masa kai zarah tayi batare da tayi magana ba, nan yamik'e yana gaba tana biye da shi suka fito main parlour basu tarar da kowaba cikinsa nan suka wuce dining, zarah kujera tajawo masa yazauna sannan tazauna gefensa nan tayi serving d'insa, ganin bata da niyar zuba nata yasa yarima yace ke ina naki?

Yamitsa fuska zarah tayi sannan tace ni na k'oshi.

Kallonta yarima yayi yace  me kikaci da zaki k'oshi? Turo baki zarah tayi tace ban iya ci.

Yarima batare da yayi magana ba yad'ebo yace bud'e bakin.

Zarah ganin fuskarsa ba alamun wasa yasa tabud'e bakinta yasaka mata, tana yatsine fuska tana tauna ahaka yakeci yana feeding d'inta itama, har saida yatabbatar da ta k'oshi sannan yabarta nan suka tashi suka koma part d'insu.

Suna shiga zarah tacire hijab d'in tashiga bedroom takai cikin wardrobe ta aje sannan tafito tasami yarima a parlour zaune ya tsura ma waje guda ido, wajen da yake tanufa bai ankaraba sai jinta yayi a jikinsa, kallonta yayi nan tasakar mashi k'yataccen murmushinta, shima maida mata yayi tare da d'aura hannunsa saman cikinta yana shafa yace kinga babyna shima ya samu wadataccen abinci ammah da sai kizauna da yunwa kina k'wararman shi.

Zarah kamar zatayi kuka tace toh ai shine yake wahalar da ni, kuma baka ganin laifinsa sai nawa shi dayake ana sonsa ammah ni ba a sona.

Yarima kallonta yayi yace zarah wanene baya sonki?

K'wallah ce tacika mata ido tace kai man, kawai dai kana zaune da ni ne ba dan kana sonaba,,,tak'arashe maganar tare da fashewa da kuka.

Cike da mamaki yarima yake kallonta ganin batada niyar daina kukan yasa yace, kukan ya isa haka zarah toh ke tsakaninki ga Allah kina sona?

Tsagaitawa tayi daga kukan da take sannan tace akwai macen da zata ganka tace bata sonka?
Tsareta yayi da ido yace tambayarki nayi kiban amsa
Kwantar da murya tayi tace  ina sonka sosai,,,cikin sauri tafad'a k'irjinsa tare da rufe idonta alamun kunya.

Murmushi me sauti yarima yayi sannan yace yau kika fara sona ko?

Girgiza kai zarah tayi cikin sauri sannan tace ni tun tuni nake sonka.

Shafa bayanta yarima yayi yace toh nagode.

'Dago kai tayi takallesa tayi kalar tausayi sannan tace toh kai baka sona ni ba ajin aurenka bace ko?

Yanayin yadda tayi maganar yaso yaba yarima dariya, murmushi yayi sannan yace ni ban ce ba.

Langwa6e kai tayi  tai kalar tausayi tace toh kana sona?

Jan hancinta yayi yace ko ban furtaba jikina ai ya isa yanuna miki amsar tambayarki.

Girgiza kai tayi tace babu abinda zan iya ganewa ta haka nafiso kafurta min da bakinka, in ma bakasona toh ya zanyi dole in hak'ura k'ila wani lokacin zaka soni nidai fatana kar inhaihu babyna yataso yaga daddynsa baya son mahaifiyarsa.

Tausayinta yakama yarima goge mata hawayen fuskarta yayi sannan yace kikwantar da hankalinki zarah domin duk kin mallaki abinda  kowane namiji zaiso mace dan shi, kuma da ace bana sonki kina tunani zan amince inrabu da kowa nawa inza6eki?

Girgiza kai zarah tayi tare da maida kanta takwantar a k'irjinsa tana jin wani irin dad'i a ranta son mijinta yana fizgarta ga tausayinsa da yadabaibaye mata zuciya, hawaye yana zuba daga idonta tace nagode sosai my soulmate insha Allahu bazan ta6a yin abinda zai 6ata maka raiba, nayi ma alk'awali zan kasance da kai a kowane hali, fashewa tayi da kuka tace ina sonka sosai zan iya rasa komai saboda kai, ina fata kaima zaka kasance da ni duk rintsi duk wuya.

Wani irin sonta yaji yana zagaye duk illahirin jikinsa shI kansa mamakine yakamasa ganin a lokaci guda ya ji kamar an dasa masa sonta a k'irjinsa, matseta yayi jikinsa tare da runtse idanunsa yace baby nima ina sonki insha Allahu nima babu abinda zaisa inrabu da ke indai zaki cigaba da sona toh nima zan cigaba da nuna miki *K'AUNA* har k'arshen rayuwata.

Zarah dasauri tad'ago kai takallesa dan jin maganar tayi kamar a mafarki yarima ya furta mata kalmar so.
'Daga mata kai yayi, alamun eh.
cikin jin dad'i tarungumesa tace nagode sosai insha Allahu nikuma zan cigaba da nuna maka k'auna zallah.

Ringing d'in da wayar yarima tafara yasa yajanye Zarah daga jikinsa yamik'e yaje yad'auko dan yasan mu'az ne kawai yake da new number d'in da yacanza.

Picking yayi tare da yin sallama
Daga chan 6angaren mu'az amsa masa yayi tare da cewa sorry prince kun fito lokacin mun shiga ciki da madam.

Murmushi yarima yayi yace kar kadamu ai nayi muku uzuri.

Dr mu'az dariya yayi Sannan yace godia muke ranka yadad'e, ina fata princess zata aramin kai  mud'an fita.

Yarima kallon Zarah yayi da tatsaresa da ido sannan yace toh zan dai tambayeta inji idan zata amince.

toh kodai inzo da kaina intambaya?,,cewar mu'az.

Murmushi yarima yayi yace kar kadamu ganinan zuwa.

Bayan sun gama wayar kallon Zarah yayi yace princess bari inje indawo.

6ata fuska Zarah tayi tace yanzu saboda Allah ba zaya barka kazauna da matarkaba duka yaushe kuka dawo?

Matsowa yarima yayi yazauna gefenta tare da shafar fuskarta yace kar kidamu baby bazamu dad'eba.

Zarah turo baki tayi tace nidai uhm-umh.
Tallabo fuskarta yayi yakai bakinsa cikin nata yafara aika mata da wani mayen kiss, gabad'aya yarikita zarah jikinta yamutu, ahankali yazare bakinsa daga nata yace baby sai nadawo.

Kasa magana zarah tayi saidai kai kawai tad'aga mashi dan gabad'aya jikinta yai sanyi.
murmushi yayi sannan yamik'e yafita.
Da kallo tabisa har yaficce sannan tajingine kanta da kujerar da take zaune sama, nan tashiga maida numfashi, ita kanta tana jinjina ma yarima dan duk hanyar da zaibi yarikita mace ya santa, hannu takai tashafa le6enta tana murmushi.

Tana zaune taji ana knocking d'in k'ofa cikin sauri tamik'e tashiga bedroom tad'auko hijab tasaka sannan tadawo tabada izinin ashigo.

Jamila ce taturo k'ofan tashigo had'e da yin sallama.

Zarah kallonta tayi tana murmushi tace oyoyoo Aunty jamila.

Zama jamila tayi kusa da Zarah sannan tace najiki shuru tun d'azun baki fitoba,
Murmushi zarah tayi tace wlh kau Aunty jamila nima inata so infito sai gashi kin rigani.

Hmm kedai ko prince ne yarik'e ki dan da alama prince d'an love ne.

Dariya zarah tayi tace kai Aunty kin bani dariya wlh, ku ma fa damukaje yin lunch kuna chan.

Dariya tayi tace au kin rama kenan.

Nan suka cigaba da hira sai gab da magrib sannan jamila takoma part d'inta.

Bayan sallar isha'i zarah wanka tayi tashirya cikin d'aya daga cikin sleeping dress d'in da yarima yasiyo mata, riga da wando iya cinya, tufke gashin kanta tayi tadawo parlour tazauna tana jiran yarima, kad'an kad'an ta kalli agogon bango dan a k'agare take yadawo.

Sai wajen k'arfe tara sannan yaturo k'ofan yashigo, juyowa tayi dasauri takallesa,
tsaye yayi yahard'e hannuwansa shima yana kallonta , mik'ewa tayi dagudu tanufi inda yake tafad'a jikinsa,

Rungumeta yarima yayi, zarah cikin shagwa6a tace shine kaje kayi zamanka kabarni ko?

Yarima shafa kanta yayi yace sorry baby yanzu gani ai nadawo inkuma ba'a murna da dawowar tawa sai inkoma.

'Dago kai tayi takallesa idanuwanta sukayi rau-rau da hawaye tace kuma zaka iya komawa?

Murmushi yarima yayi tare da janyeta daga jikinsa yace toh sarkin kuka yanzu dai muje kitaimaka min inyi wanka dan agajiye nake.

Rik'o hannunsa zarah tayi suka shiga bedroom towel tad'auko tamik'a mashi sannan tawuce bathroom tahad'a mashi ruwan wanka,
koda tafito yana tsaye inda tabarsa, kallonsa tayi tace na ma d'auka ka cire kayan?

Wani irin kalloh yayi mata wanda yake sakar mata da kasala sannan yace baby ke fa nake jira kizo kitayani cirewa.

Zaro ido zarah tayi tace karufan asiri wlh ba zan iyaba.

Murmushi yarima yayi tare da tunkaro inda take yace zaki iya man, ai lada zaki samu.
kallonsa tayi nan yad'aga mata gira.

cikin sauri tajuya zata bar wajen, janyota yarima yayi yace dole fa sai kinyi min abinda nakeso kinsan ban ta6a neman komai narasaba a rayuwata kuma umurni nabaki indai kinaso mushirya dole kiyi abinda nakeso.

Zarah kallonsa tayi ganin dagaske yake yasa tafara cire masa button d'in rigarsa, ahankali tacire rigar nan tasafke idanunta akan lallausan gashin da yake kwance saman k'irjinsa, d'ago kai tayi takallesa nan yad'aga mata gira.

Marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace please kataimaka kacire wandon da kanka,,,tafad'i hakan tare da mik'a mashi towel.

Ganin yadda tamarairaice yasa yarima yayi Murmushi sannan yakar6i towel d'in.
Dasauri tajuya masa baya dan yacire.

Yarima koda yacire, saidai ji zarah tayi ya sungumeta ya nufi toilet d'in da ita bai zarce ko'ina ba sai cikin ruwan da tahad'a mashi nan shima yashiga,

Zarah kunyace takamata cikin sauri tarufe fuskarta da hannunta tare da sa kukan shagwa6a.

Yarima bai damuba nan yazage zip d'in rigarta yacire rigar sannan yarabata da wandonta,

Daga gefe yakoma yana wankansa ammah idanuwansa suna a kan zarah.

Jin ya kyaleta yasa tajanye hannuwanta daga fuskarta, karaf suka had'a ido da yarima da yake wankansa, cikin sauri tamaida idanunta tarufe tana jinsa yagama wankan yafita yabarta cikin ruwan.

Saida taji fitarsa sannan tabud'e idanunta nan tayi wankan sannan tad'auro towel d'inta tafito.

Tsakiyan gado tahangosa kwance ya yi matashin kai da hannuwansa, ganinsa a wannan yanayin yasa taji ba dad'i a ranta takowa tayi tazo tahau gadon tare da kwanciya saman k'irjinsa, cikin 'yar siririyar muryata tace meyake damunka?
Batare da ya kalletaba yace ba matsalarki bace kikyaleni.
Zarah kamar zatayi kuka tace wlh matsalarka tawace indai kana cikin yanayinnan toh nima damuwa nake shiga.

Wani irin kallo yarima yayi mata sannan yace wai har zan nemi abu wajenki kik'i yimin, hakan ya nuna min son da kike ik'irarin kina min toh ba gaskiya bane.

Zarah jikintane yayi sanyi tace kayi hak'uri wlh kunyarka ne nakeji ammah bazan k'ara sa6ama umurninkaba.

Shuru yarima yayi yakyaleta.
Tallabo fuskarsa tayi tace please my soulmate *KAYARDA DA NI*

sai a lokacin yarima yakalleta yace shikenan na yarda da ke baby, atare suka sakar ma juna murmushi nan yarima yakai hannu yacire towel d'in da take d'aure da shi.
kafin tayi magana har ya birkiceta takoma saman katifar nan yadawo kanta.
Zarah ga jikinta bata jin dad'insa ammah haka tadaure taba yarima kanta yayi yadda yakeso,
Saida yagaji dan kansa sannan yabarta.
Shi kansa yana jinjina ma dauriyarta dan ya san ya bata wahala sosai.

daga k'arshe d'aukanta yayi yanufi toilet da ita dakansa yayi mata wankan tsarki, shima yatsarkake jikinsa sannan yad'aukota suka fito.

Saman bed d'in yahau da ita nan suka kwanta tana manne a jikinsa yana shafa gashin kanta, cikin kunnenta yake rad'a mata cewa nagode sosai zarah, hak'ik'a kina sani cikin farin ciki Allah yaimiki albarka yadda kike faranta min kema Allah yabaki masu faranta miki.

Zarah k'ara shigewa tayi jikinsa cike da jin kunya,,ahaka bacci medad'i yayi awon gaba da su.

________________

A chan masarautarsu yarima ko bayan yarima yabar gidan, memartaba kallon family d'in nasa yayi da gabad'aya kowa yake cikin yanayi, saida yak'are musu kallo d'aya bayan d'aya sannan yace toh kunga dai abinda yafaru, yarima ya ci amanata ya nuna min ban isa da shi ba dan haka tunda ya za6i matarsa a kanmu shikenan yaje na sallama mata shi yaje yaga idan za'a iya rayuwa ba dangi ko dashi ko babu shi gidana ba zai k'i cigaba da tafiya daidai ba,

sannan yakalli sumayya da take ta kuka yace kekuma sai kiyi hak'uri da k'addararki dan dama chan Allah ya k'addara yarima ba mijinki bane na da'iman, dan haka daga yanzu zakije kifara iddah kafin muga yarda Allah zai tafiyar da al'amarinsa, saidai muce Allah yamusanya miki wani mijin da zaifi zama alkhairi agareki.

Yanzu kai Ahmad kaine yakamata kakasance magajin garina a yanzu.

Sultan Ahmad k'ara duk'ar da kansa yayi cike da biyayya yace ranka yadad'e ka gafarceni ba nak'iba ammah da d'an uwana aka nad'a magajin garin.

Girgiza kai memartaba yayi yace na riga na gama magana, dan haka idan da mai magana zai iyayi.

Kowa shuru yayi, ganin ba mai niyar yin magana yasa memartaba yasallamesu nan duk suka duk'a suka kwashi gaisuwa sannan suka tashi kowa yawatse cike da damuwa a ransu.


Ummi koda takoma part d'inta a parlour saman kujera tazauna tarushe da kuka, rahma da husna da suke bayanta tsaye sukayi suna kallon mahaifiyar tasu cike da tausayinta suma hawayen yana fita daga idanunsu.

Wajen da take suka nufa cikin sauri suka fad'a jikinta suna kuka, rahma ce tayi k'arfin halin cewa ummi kikira bro a waya please kice yarabu da matarsa yadawo gida wlh muna sonsa bamu iya zama babu shi, meyasa yaza6eta akan mu, dan Allah kice yadawo

Ummi cigaba tayi da kukanta cike da tausayin d'an nata, ahankali tace rahama na yarda da yarima nasan abinda zai iyayi da wanda bai iyawa kuma na tabbata akwai abinda sumayya tayi masa wanda yaja har yasaketa dan ban yarda da maganar da tayiba a gaban memartaba.

Rahama tsagaitawa tayi daga kukan da take sannan tace ummi bakya tunanin ko wacchan matar tasace tashiga tsakaninsu har hakan yakasance?

Girgiza kai sultana bilkisu tayi tace bana tunanin haka daga wajen zarah dan zarah mutuniyar kirkice.

Kidaina cewa haka ummi kinsan fa ita za6insa ce sumayya kuma za6in iyayenmu ne kinga daman bason sumayya yakeba,,,,cewar Aunty husna.

Murmushi ummi tayi wanda yafi kuka ciwo sannan tace zarah ba za6in suhail bace kamar yarda yake zaune da sumayya toh itama biyayyace kawai tasa ya aureta.



_Comment_
      *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Sak'on gaisuwa da jinjina agareki my besty *Sadiya Sidi Sa'id* ina tayaki murnar kammala novel d'inki mai suna *RAYUWAR MATA* hak'ik'a kin zuba darasi da fad'akarwa acikinsa gaskiya dole inyaba miki, Allah yak'ara basira da zak'in hannu, Allah yabarmu tare_

*PAGE* 6⃣0⃣

Ummi cigaba tayi da cewa Zarah za6ina ce ni da mahaifinku mu mukasa yarima ya aureta saboda tunda sukayi aure da sumayya baida kwanciyar hankali, bai ta6a zuwa yakawo min k'orafiba koda sau d'aya, gudun kar d'anmu yashiga cikin wani yanayi yasa ni da mahaifinku muka had'asa aure da zarah batare da kowa ya san mune silar aurenba sai yanzu da ku kukasani.

Su rahma ido suka zuba ma mahaifiyar tasu suna kallonta cike da mamaki,
Nan ummi tacigaba da cewa kuma zarah tana zaune da yarima tsakani ga Allah na yarda da tarbiyarta kuma da kuke maganar ko magani tayi masa, ko d'aya ba haka bane.
mace zata iya mallakar namiji ta hanyar kulawa da yi masa duk abinda kikasan yana so dan haka nima nafi tunani ta haka zarah tasamu fada sosai a wajen suhail.
Hawayene yacigaba da fita daga idanun ummi girgiza kai ummi tayi tace burina duk inda d'ana yake sukasance suna cikin k'oshin lafiya shi da matarsa.

Su Husna jikin ummi suka fad'a suna kuka cike da tausayin d'an uwan nasu.


Sultan Ahmad koda suka fito daga fada kallon d'an uwan nasa yayi cike da jin kunyan abinda yarima ya aikata ma d'iyarsa, cike da damuwa yabud'e baki zaiyi magana nan sultan abbas yatari numfashinsa yace kar kace komai yaya indai akan mutuwar auren sumayya ne nasan wani abu tayi ma d'ana saisa ya yanke mata wannan hukuncin kuma dan memartaba yana cikin 6acin rai bai tsaya yasaurari ta bakinsaba saisa abun yakasance haka yanzu dai addu'a zamu cigaba da yi masa duk inda yakasance Allah yatsare mana shi, kar kasa komai a ranka yayana zumuncin mu mai d'aurewane har k'arshen rayuwarmu tun bamu mallaki 'ya'ya da mataba muke tare taya zasuzo a yanzu kayi tunanin zasu shiga tsakaninmu?

Sultan Ahmad jinjina kai yayi cike da jin dad'in kalaman d'an uwan nasa yace nagode sosai abbas samun d'an uwa irinka sai antona a fad'in duniyarnan
Murmushi sultan Abbas yayi yace kar kadamu ai duk a wajenka nakoyi wannan halayyar.

Haka suka rabu kowa yanufi part d'insa cike da k'aunar d'an uwansa.

Sultan Ahmad koda yashiga yatarar da su sultana bilkisu zaune suna kuka, tsayawa yayi daga bakin k'ofa yana kallonsu yana jin wani irin k'unci a ransa, ganinsa yasa ummi tataso cikin kuka tafad'a jikinsa tace dadyn suhail yanzu shikenan na rasa d'ana bana k'ara ganinsa?

Sultan Ahmad janyeta yayi daga jikinsa yaje yazaunar da ita sannan shima yazauna a gefenta, cike da k'warin gwiwa yace bilkisu ke kanki kinsan abinda suhail ya aikata bai kyautaba kiduba kiga d'iyar d'an uwana jininsa yayi ma saki d'aid'aya har ukku, har yana ik'irarin cewa ta haramta ma kansa sumayya, na d'auka yarima yana da tunani koma me sumayya ta aikata masa ai baidace yaimata saki ukku ba, toh taya kike tunanin abinda ya aikata bazai 6ata mana rai ba?

Sultana bilkisu tsagaitawa tayi daga kukan da take tace nasan haka ranka yadad'e ammah hukuncin da aka yanke ma suhail ya yi masa tsauri dayawa yanzu bamusan yanayin da zai shigaba ga matarsa da ciki ina zasuje wa suka sani?

Rik'o hannunta sultan Ahmad yayi yace bilkisu kikwantar da hankalinki suhail fa ba yaro bane insha Allahu duk inda zasu kasance suna cikin k'oshin lafiya addu'a kawai zamucigaba da yi har Allah yataimakemu memartaba yasafko daga fushin da yake insha Allahu suhail zai dawo yayi rayuwa cikin danginsa.

Murmushin jin dad'i ummi tayi tace hakane ranka yadad'e Allah yakawo mana ranar da hakan zai kasance da nafi kowa farin ciki,

Su rahma da suke gefe suna sauraren iyayen nasu cike da jin dad'in maganar da mahaifinsu yayi sukace Allah dai yatsare mana su.

Ameen sultan Ahmad yace tare da mik'ewa yawuce part d'insa.

A 6angaren su sumayya koda suka isa 6angaren iyayenta tusa sultana sadiya tayi a gaba tana kuka har da mirgina lallashinta sultana sadiya take ammah kamar k'ara tunzurata take, sumayya kuka take sosai tana cewa dole sai ta koma d'akinta wlh bazata ta6a yadda ba zarah asiri tayi tarabasu da yarima.

Daga k'arshe jugum sultana sadiya tayi tana sauraren d'iyartata, suna cikin haka sai ga sultan abbas ya shigo ganin sumayya kwance k'asa tana mirgina yasa yadaka mata tsawa yace ke menene haka kikeyi?

Sumayya tashi tayi a zaune tana cigaba da kukanta.
Sultana sadiya ce tayi k'arfin halin cewa yauwa gama kanan dan Allah kazo kataimaka asan yadda za'ayi sumayya takoma d'akinta wlh tana son mijinta sosai.

Murmushi sultan abbas yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace sadiya kenan ai ban d'auka zaki mance da saki nawa bane suhail yayi mata,

Ke kuma,,yanuna sumayya da yatsa yace garin haukanki kinje kin kashe aurenki na tabbata suhail ba zai ta6a yimiki saki ukku ba batare da wani k'wak'waran daliliba, toh yanzu wa gari yawaya? Sai kizo kujera da mahaifiyartaki kiyi ta zaman gida, babban bak'in cikina ma da kikayi silar raba yarima da family d'insa.

Cikin 6acin rai sultana sadiya tace haba Alhaji wannan wane irin cin mutuncine tun a gaban memartaba kake ta kware ma d'iyarka baya toh inaso kasani hannunka baya ru6ewa kacire kayar kuma ni nasan sumayya ba abinda zatayi ma yarima wanda zaisa yaimata wannan saki haka saidai idan wacchan munafukar matsiyaciyar yarinyarce tashiga tsakaninsu.

Dakata ke banson shashanci nalura kamar ke kike goya ma yarinyar nan baya tana yadda takeso dan haka kukiyayeni ko gabad'ayanku insa6a muku, wlh kikiyayi lokacin da zakiji kunya dan naga kina d'orema k'arya gindi, ni a wajena da yarima da sumayya duk d'ayane dan dukansu 'ya'yanane bana goyon bayan kowa sai gaskiya dan haka gatanan tayi ta zaman gidan zata gane ai idan iyaye da miji d'ayane, duk dai inda mace takasance komai gatanta toh gidan miji shine kwanciyar hankalinta,
Sannan ke sumayya ina k'ara tunatar da ke saki ukku ne yarima yaimiki bakida ko sauran igiya d'aya dan haka dole yanzu kicire tunanin komawa gidansa dan yariga da yayi miki nisa,,,,sultan abbas yana kaiwa nan a zancensa yawuce yashige part d'insa cike da 6acin rai.

Sultana sadiya da kallo tabisa dan gabad'aya ya kashe mata baki ga takaici da yacikata, cikin kuka sumayya tace ummah yanzu shikenan na rasa yarima ya zanyi da rayuwata.

Cikin 6acin rai sultana sadiya tace ai ga irintanan ke kibar ganin ina goyon bayanki kema ai kina da naki laifin a ciki yanzu gashinan kinja mijina nima yad'au fushi da ni yadda kika kaso aurenki toh nima bazakiyi silar mutuwar nawaba dan haka dole kihak'ura kicire suhail a ranki tunda bashikad'ai bane namiji a duniyar mutumin ma da baya k'aunarki baisan darajarkiba toh miye amfanin zama da shi hak'urin dai zakiyi Allah yamusanya miki da mafi alkhairi.

Sumayya ganin mahaifiyarta kamar itama tana nema takware mata baya dan haka tamik'e tawuce tashige room d'inta tana kuka.

________________

Yarima koda yafarka baccin da suka koma bayan sallar asuba kallon agogo yayi ganin har 11 ta yi yasa yajanye zarah daga jikinsa, zaune yayi yana k'arema fuskarta kallo cike da sonta dan yanzu ya tabbatar ma kansa yana son zarah, janye gashin da yasafko wajen idonta yayi nan yaduk'a yakai mata peck a goshi, ahankali zarah take bud'e idanunta nan tasafkesu akan fuskar yarima, murmushi tasakar masa tare da rik'o hannunsa d'aya.

Shima murmushin yamaida mata yace baby kin tashi?
Mik'a zarah tayi tace jikina ciwo yakemin, jan d'an k'aramin bakinta yarima yayi yace toh muje inmiki wanka.

Turo baki zarah tayi tace saidai kad'aukeni dan ban iya tashi.

Hmm shikenan yadda kikeso haka za'ayi ai nasan nine nagajiyar da ke d'in,,yafad'i hakan tare da d'aura hannunsa saman cikinta yana shafa.

Ido zarah tazuba ma kyakkyawar fuskarsa bata ko kyaftawa, hura mata ido yarima yayi nan talumshe idanunta cike da jin kunya.

Murmushi yayi tare da d'aura kansa saman k'irjinta yace baby kallon fa?

Zarah batare da ta bud'e idanuntaba tace ni ba kai nake kallo ba,

Bakinsa yakai yad'an ciji le6enta har saida tad'anyi k'ara sannan yace toh wa kike kallo.

Rik'e le6enta tayi kamar zatayi kuka Sannan tace ni mijina na kallah ko laifine dan na kallesa?

Batare da ya bata amsaba yad'auketa yanufi toilet da ita atare sukayi wanka sannan suka fito suna rungume da juna, tana tsaye gaban dreesing mirror tana kwalliya nan yarima yai mata tsaye yana kallon kwalliyarta kashe mashi ido tayi tace nayi kyau?
Ta6e baki yarima yayi yace ko d'aya bakiyi kyauba,
Haushine yakama zarah nan ta6ata fuska tace Allah a'a
K'unshe dariyarsa yayi yace ammah ai kinsan nafiki kyau ko?
Harararsa tayi cikin wasa sannan tace saidai muzo d'aya ammah bakafiniba.

Murmushi yarima yayi tare da rungumota jikinsa yace ban yardaba nan yajanyo wayarsa yai musu selfie.

Zarah zame jikinta tayi tanufi wajen wardrobe nan tad'auko wata gown cikin kayan da yarima yasiyo mata tasaka nan tanad'e gashinta kamar gammo sannan tayi rolling d'in d'an k'aramin veil d'in kayan nan tayi gwanin kyau, juyowa tayi takalli yarima da yatsareta da ido tace toh yanzu ya kaganni?

Murmushi yayi yace har yanzu dai ina akan bakana, dariya tayi nan tamatso yacigaba da yi musu pic's saida sukayi kusan kala ashirin ganin baida niyar dainawa yasa tajasa suka fito main parlour nan suka tarar da mu'az da matarsa nan suka zauna suka gaisa daganan suka wuce dining gabad'ayansu suna breakfast.
Zarah da yarima saidai kallon love suke aika ma junansu mu'az da jamila suna lura da su saidai suyi murmushi ahaka har suka gama breakfast d'in nan suka hau yin hira, yarima kallon mu'az yayi yace abokina inaso insamu gida insiya dan gaskiya ba zan iya cigaba da zama a nan ba saboda da takura muzauna muku nan zamu d'aura muku nauyi nikuma banason hakan indai kana ganin ba matsala toh kasanya min cigiyar gida.

Cike da damuwa Dr mu'az yace ranka yadad'e banta6a tunanin jin haka daga garekaba da kai da kaya ai duk mallakar wuyane, idan har kai ka mance abinda kayimin toh ni ban manceba kuma bana iya mancewa, wlh yarima zan iya sadaukar da duk abinda namallaka a gareka dan ka fiye min komai dan Allah kataimaka kucigaba da zama da mu Indai akwai abinda mukeyi muku wanda bakuso kusanar da mu insha Allahu zamu daina, gyad'a kai jamila tayi tace eh wlh zamu daina dan muna jin dad'in zamanku a tare da mu.

Yarima murmushi yayi yace kar kudamu ba wai saboda wani abu nakeson barin gidanba kawai dai dan kar mushiga hak'inku ne.

Girgiza kai mu'az yayi yace kar Allah yakawo ranar da zanji wani abu game da zamanmu tare nidai ka amince mucigaba da zama wlh munajin dad'in zama tare da ku.

Yarima kallon zarah yayi nan tasakar mashi murmushi, kallonsa yamaida ga mu'az yace shikenan na amince ammah ban d'aukar maka alk'awaliba.
Murmushin jin dad'i mu'az da matarsa sukayi nan sukaima yarima godia daganan suka cigaba da hira koda rabin hirar mu'az da matarsa sai zarah ne sukeyi dan shi yarima da ido yake binsu saidai yayi murmushinsa mai tsada.

Sun dad'e suna hirar sannan Dr mu'az da yarima suka tashi suka fita inda zarah da jamila suka shiga kitchen dan suhad'a musu lunch, a tare sukayi komai duk yadda jamila taso zarah tabarta tayi ita kad'ai ammah zarah k'iyawa tayi saida aka gama komai tare da ita sannan suka kai saman dining suka jera daga nan kowa yawuce part d'insa dan yashirya jikinsa.

Koda yarima yadawo Zarah taimaka masa tayi yai wanka yashirya bayan sungama cin abinci part d'insu suka dawo nan tayi d'aid'aya saman cinyarsa tana zuba masa shagwa6a yana biye mata a ranar haka suka kasance takasa tatsare  indai ba masallaci yarima zaijeba toh suna manne har dare yayi, taje tahad'o musu coffee a one cup a tare sukasha sannan sukaje sukayi wanka suka kwanta saida sukayi 'yan wasanni batare da sunyi making sex ba sannan sukayi bacci kowa yana jin d'an uwansa sosai a cikin ransa.

*BAYAN SATI 'DAYA*

Dr mu'az ne da yarima zaune a parlour suna hira, kallon yarima yayi yace yauwa prince ina zuwa,
d'aga masa kai kawai yarima yayi batare da yayi magana ba nan Dr mu'az yamik'e yanufi part d'insu,

Bayan minti biyu yafito rik'e da wasu files, kujerar da yarima yake zaune yaje yazauna, kallon yarima yayi suka fuskanci juna sannan yace prince dan Allah wani taimako ne nakeso kayi min.

Kallonsa yarima yayi yace ina jinka Indai baifi k'arfinaba toh insha Allahu zanyi maka.

Murmushi Dr mu'az yayi yace tabbas baifi k'arfinkaba, nan yafiddo files d'in yamik'a ma yarima yace gashi ammah kayi hak'uri da karambanin da nayi maka muna buk'atarkane a hospital d'inmu.

Yarima dubawa yayi yaga upper ce ta aiki aka basa har da babban matsayi an nad'asa head of department d'in surgeon.

Girgiza kai yarima yayi yace gaskiya kayi hak'uri ba zan iyaba kaima sanin kankane ina da hospital d'ina.

Marairaicewa Dr mu'az yayi yace nasan da haka ammah dan Allah kataimaka ka amince ko yayane kasa albarka a cikin aikin nan kar kak'i amincewa dan muna buk'atar babban surgeon kamarka.

yarima shuru yayi kamar yana nazari sannan yace shikenan zanyi tunani akai.

Cikin jin dad'i Dr mu'az yace Allah yasa inji alkhairi.

Bayan yarima yadawo part d'insu kwance yake saman 3 seater ya yi matashin kai da hannuwansa kansa yana kallon ceiling,

Fitowar zarah kenan daga bedroom rik'e da apple tana ci, tsaye tayi tana kallon yarima da kwata-kwata batama san lokacin da yashigoba dan duk atunaninta bai dawoba.

Takowa tayi ta iso inda yake janye kansa tayi tazauna sannan tamaida kan nasa saman cinyarta, yarima lumshe idanunsa yayi.

shafa sumar kansa tayi tace ashe ka dawo ban saniba.

Murmushi yarima yayi yace uhm ban dad'e da dawowaba,
duk'o da kanta tayi takaimashi peck a saman idonsa da yake lumshe, ahankali yabud'e idanunsa nan suka sakar ma juna murmushi, d'age rigarta yayi yayi kissing d'in cikinta sannan yace ina fatana kuna lafiya keda babyna.

Cike da tsokana zarah tace lafiya lou muke prince saidai missing d'inka da mukeyi.

Shafa cikinta yashiga yi yace nima nayi missing d'inku sosai yanzu muje ciki inga in dagaske kunyi missing d'ina.

Dariya zarah tayi tace nak'i wayon naka babu inda zanje.

Mik'ewa yarima yayi yad'auketa yanufi bedroom da ita tana wuntsila k'afa bai direta a ko'inaba sai saman gado, zarah shirin safka take nan yarima yarik'ota yace toh sarkin tsoro ni ba abinda zanyi miki magana ce nakeso muyi.

gyara zamanta tayi tafuskacesa tana jira taji abinda zaice mata.

Yarima janye idanunsa yayi daga kallonta yayi shuru har na kusan minti ukku sannan yakwashe yadda sukayi da Dr mu'az yafad'a mata.

Zarah kasa 6oye farin cikinta tayi nan tashiga washe baki, kallonta yarima yayi yace toh ya kike gani?

Cikin jin dad'i tace wlh nima na goyi bayan hakan kaga kaima zaka ji dad'i kuma taimakone Allah zai baka lada dan irin wannan aikin naku duk abinda za'a ba mutum baza'a ta6a biyansaba ladarku tana wajen Allah.

Murmushi yarima yayi yace hakane shikenan tunda kin amince toh nima na amince.

cikin jin dad'i  tarungumesa tace nagode sosai my soulmate Allah yabarmin kai ni kad'ai.

Dariya yarima yayi yace toh Allah yasa,

'Dago kai zarah tayi takallesa tace ashe ka iya dariya haka gaskiya tana yi maka kyau saidai kai bakacika yin dariyaba murmushinma kafin kayi sai ansha wuya.

Jan hancinta yarima yayi yace yau kuma tsokanata akeji?

Murmushi zarah tayi tace ba tsokana bace gaskiya ce nafad'a dan ranar da nafara ganinka lokacin da kukazo islamiyarmu ranar da muke walima saida nakusan rikicewa dan ka burgeni sosai saidai a lokacin fuskarka a d'aure take.

Murmushi yarima yayi yace kedai kin cika tsokana nidai yanzu tashi muje muyi wanka mukwanta dan ni yau agajiye nake ga bacci da nakeji.

Mik'ewa zarah tayi tace angama ranka yadad'e, nan suka cire kayansu sukaje sukayi wanka bayan sun fito shiryawa sukayi cikin kayan baccinsu sannan sukabi lafiyar gado suka kwanta.

Wanshe kare koda yarima yaje ma mu'az da batun amincewarsa sosai mu'az yai murna,

bayan kwana biyu yarima motarsa yasiya maikyau da tsada sannan yafara zuwa wajen aikin.

Sosai ma'aikatan asibitin suke girmamasa musamman ma da sukasan matsayinsa da kuma matakin karatunsa, kamar dai yadda yake  baya shiga harkar kowa toh nan ma haka hidimar gabansa kawai yakeyi.

Sosai sukejin dad'in aiki da shi musamman ma da sukaga k'wararrene sosai a 6angaren theatre.

Bayan kwana biyu
Zarah kwance take saman gadonsu tunanin 'yan gidansu kawai take dan tasan dole sai sun nemi wayarta, tana cikin tunanin batasan lokacin da yarima yashigoba saidai jin mutum tayi gefenta, murmushi tasakar masa tare da cewa sannu da zuwa ashe ka dawo.

Shima murmushin yayi sannan yace ai daman bazakiji dawowataba tunda kin tsunduma kogon tunani wai ma tunanin me kikeyi haka?

Ajiyar zuciya Zarah tasafke sannan tace tunanin su mama nake nasan zasuyita neman layina bazasu samuba,,,tak'arashe maganar kamar zatayi kuka,

Yarima kallonta yayi yace kar kidamu ai sunsan dai kina cikin k'oshin lafiya zan kira miki su wani lokacin kugaisa.

'Daga kai Zarah tayi cike da gamsuwa da maganar yarima, jikinta yarima yakwanta tare da tura hannuwansa cikin rigarta yana cakud'ata
Ganin yana shirin nemanta yasa tazame jikinta takoma parlour dan yanzu gabad'aya ji take batason yarima yana kusantarta saboda sai takwana jikinta yana ciwo ga yawan amai da tashin zuciya musamman yanzu da cikinta yafara yi mata nauyi, ammah indai wassani zaiyi da ita bata damuwa saidai tasan halin gogan nata dawuya ya iya tsayawa iya romancing.
Ganin ta gudu yasa yarima yashareta yai kwanciyarsa dan ya lura kwana biyu haka take masa Indai zai nemeta toh sai tasan hanyar da tabi takubce masa.



_Comment_
       *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_[5/3, 9:51 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Aunty Aliyah Sharif bazan iya mancewa da ke ba akodayaushe kina raina dan haka kimatso kusa yau page nakine big Aunty, sai wanda kikaso zai karanta, jinjinar bangirma agareki 😍_

6⃣1⃣

Sumayya tunda takwana biyu ganin dagaske aurenta ya mutu gashi bata ganin yarima yasa tahak'ura tasaki ranta, ahaka akaje aka kwashe kayanta a part d'inta sannan aka rufe gabad'aya 6angaren yarima aka kaima memartaba key d'in.

Sumayya kwance take saman gadonta sai a ranar tajanyo wayarta takunna dan rabonta da ita tun ranar da aurenta yamutu, number d'in yarima tayi dialing da mamakinta taji bata shiga, dan haka talalubo ta zinat nan tafara ringing har ta tsinke ammah batayi picking ba, nan ma sumayya tak'ara kira saida tayi mata 3 missed call ammah bata d'aukaba dan haka tatura mata message dan daman tasan mawuyacine zinat tayi picking d'in wayar.

Bayan kamar minti biyar sai sumayya tak'ara kira da mamakinta saiga zinat tayi picking, cike da jin dad'i sumayya tagyara kwanciyarta tare da cewa Hi baby.

Daga chan 6angaren zinat a tsorace tace sumayya ya dai?

Murmushi sumayya tayi tace ke fa tsiyata da ke kin cika tsoro toh kisaki jikinki komai ya wuce.

Uhm sumayya kenan taya zan saki jikina bayan d'an banzan dukan da wannan mugun yayimin ke yanzu dai ya maganar aurenki?

Murmushi sumayya tayi tace hmm kibarsa kawai ai yanzu aurena da yarima ya k'are wlh ban ta6a tunanin zaimin wannan cin mutuncinba haka koda nasan inason yarima ammah babu yadda zanyi dole inciresa a raina tunda ko giyar wake nasha aurenmu bazai ta6a komawaba.

Zinat cikin ranta murna fal ji take kamar tazuba ruwa k'asa tasha saboda murnar auren sumayya ya mutu, a fili 6oye murnarta tayi tace Allah sarki baby ba haka nasoba toh yanzu ya su memartaba sukayi da sukaji labarin rabuwarku Allah dai yasa basuji abinda mukayi ba.

Dariya sumayya tayi tace kefa tsiyata da ke kin iya tsoro, daman fa nasan miskilancin yarima bazai ta6a barinsa yafad'aba kuma koma ba hakaba nasan yarima bazai iya tonamin asiriba saboda bayason tashin hankali, nikuma gudun kar ma yatona min yasa nayi sauri narigashi kai k'ara......nan takwashe duk abinda yawakana talabarta ma zinat.

Ajiyar zuciya zinat tayi tace gaskiya kinyi namijin k'ok'ari toh yanzu yarima shikenan ya bar gida bazai dawoba?

Hmm ba zai ta6a dawowaba, ni wlh kin ban mamaki da kika iya tafiya kikabarni ban ta6a tunanin hakaba daga gareki zinat.

Kwantar da murya zinat tayi tace kiyi hak'uri baby wlh gabad'aya rikicewa nayi ammah insha Allahu wani lokacin zan shigo.

Cikin jin dad'i sumayya tace gaskiya da naji dad'i dan gabad'aya kad'aici ya isheni Allah yakawo min ke lafiya.

Ameen baby zankiraki anjima.
Ohk, sai kin kira,,nan sukayi sallama.


Tun daga ranar sumayya da zinat suka koma suka d'inke kullum suna manne da juna ta waya inba wayaba toh ta chart da video call, yanzu sumayya kusan kullum tana d'akinta suna waya da zinat.

Sultana sadiya ganin yanzu hankalin d'iyarta ya kwanta yasa itama tad'an kwantar da hankalinta ammah magana bata had'asu da ummin yarima dan da taga ummi zata fara d'aure fuska koda ummi tayi mata magana indai sukad'aine shareta takeyi inkuma gaban su dadane toh shine take amsa mata ciki-ciki.
Ummi tun abin yana bata mamaki ganin ba ita tayimataba ammah da ita take gaba, daga k'arshe abun yadaina damunta.

Dada da memartaba ma danne damuwarsu kawai suke akan tafiyar yarima ammah su ma suna jin abun yana damunsu cikin rai, daga inda suka tuna da abinda yayi ma 'yar jikarsu sai kuma suji ba dad'i, dan haka ne suke nuna ma sumayya kulawa sosai ga tausayinta da sukeji saboda akanta akafara sakin aure a masarautarsu.

_________________

Zarah ganin yarima kwana biyu bai nemetaba dan yanzu har romance ya dainayi mata saidai kawai yarungumeta suyi bacci, nan abun yad'an fara damunta.

Yau ma tana fitowa daga wanka ganinsa tayi a kwance yana duba wata newspaper dan haka taje tafad'a jikinsa, kallonta yarima yayi yace Zarah sai kin ji ma babyna ciwo?

Turo baki tayi cikin shagwa6a tace au ba ma ni zanji ciwon ba babynka zanji mawa ko? babyn da yanzu andaina kulamu.

Aje newspaper d'in da take hannunsa yayi yace wajen me nadaina kulaki?

Kwantar da kanta tayi a k'irjinsa tace toh ba kai bane kadaina min komai?

Yarima ya fahimci inda tadosa ammah yanuna bai fahimtaba yace magana nadaina yi miki ko kulawa?

Girgiza kai Zarah tayi cikin jin kunya tace ka daina making sex da ni.

Murmushi yarima yayi yace toh ai naga kamar bakiso saisa nabarki kihuta.

Zaro ido Zarah tayi tace karufa min asiri taya zan k'i son lada, kawai dai babynka ne yake wahalar da ni, dan dadyn nasa jarumi ne,,,tak'arashe maganar tare da kashe masa ido d'aya.

Murmushi yarima yayi yace kar kidamu nima banason babyna yana wahalar min da ke kihuta warki kawai nayi miki uzuri.

Da mamakinsa sai yaga Zarah ta fashe masa da kuka.
Cike da mamaki yace lafiya zarah? Me kikeyi ma kuka?
Cikin kuka tace toh bakai bane.

Murmushi yayi yace toh kinaso inyi?

Cikin sauri tad'aga kai.

Toh shikenan kidaina kuka, nan yakwantar da ita yashiga lashe mata hawayen fuskarta daga nan yalalubo bakinta yacigaba da tsotsa kamar wanda yasamu lolli pop, gabad'ayansu jikinsu rawa yake dan sunyi missing d'in juna sosai, daga nan yarima yazare towel d'in da yake jikinta yagangaro da kansa a k'irjinta, ahankali yacigaba da lalla6ata har saida yaga sun samu nutsuwa sannan yabarta.

Duk da lalla6ata da yayi ammah saida jikin zarah yai ciwo dan daurewa kawai take, ko shi kansa yana lura da yadda take cize le6e.

Cike da tausayinta yashiga yi mata sannu daga k'arshe yad'auketa sukaje yaimata wanka shima yayi nasa sannan suka fito hatta kaya shi yasaka mata, jin jikinta ya d'au zafi yasa yad'auko drugs yabata sannan yad'auketa suka dawo parlour nan yakwantar da ita saman cinyarsa yana wasa da gashin kanta ahaka bacci yai awon gaba da ita.

Ganin tayi bacci yasa yarima yajingine kansa a jikin kujerar da yake zaune cike da tausayin zarah, nan family d'insa suka fad'o masa a rai, tunani barkatai yashiga yi daga k'arshe janye zarah yayi yagyara mata kwanciyarta nan yasafko k'asa yadafe kansa da hannuwa biyu, tunowa yayi da yadda yarabu da danginsa kowa yana d'aura masa laifin da bashida laifi a cikinsa, kukan da ummi takeyi ne ahankali yashiga dawo masa a kunne da lokacin da tad'ago idanuwanta da sukayi ja tasafkesu akansa,
Girgiza kai yashiga yi yace taya zan samu kwanciyar hankali ummina kin zubar da hawayenki saboda ni, ya zanyi da rayuwata.

Zarah da tafarka tun lokacin da yajanye mata kai, ido tazuba mashi tana sauraren duk abinda yake cewa tausayinsa ne yakamata dan sau tari daman yarima yana k'ok'arin ganin ya 6oye damuwarsane saboda ita saidai inaaa tuni ta gama karantar hakan, safkowa tayi daga saman kujerar tadawo k'asa kusa dashi tazauna tare da dafasa,

'Dago kai yarima yayi yakalleta murmushi yasakar mata tare da 6oye damuwarsa sannan yace kin farka?

Zarah k'wallah ce tacika mata ido tace taya kake tunani ni zan samu kwanciyar hankali alhali kai bakada shi?

Ido yazuba mata cike da mamaki sannan yace wa yace miki bana cikin kwanciyar hankali?

Hawayen da take dannewane suka zubo tace suhail me kamayar da ni, ko duk  farkawar da kake cikin dare katashi kayita tunani ka d'auka ban san komai ba?

Mamaki k'arara yabayyana a fuskar yarima yace Zarah wa yafad'a miki haka?

Fad'awa tayi jikinsa tana kuka tace yarima babu abinda ban saniba sau tari kana k'ok'arin 6oye damuwarka idan kana a gabana saidai in bamu tare shine kake zama kayita tunane tunanenka, meyasa kake haka, kai doctor ne kasan illar yin haka tunda kuna fad'a ma wasu sudaina yawan damuwa ammah sai gashi kai kanayi.

Yarima rintse idanunsa yayi da k'arfi yana jin wani iri a ransa dan tunda yabaro iyayensa bai ta6a samun kwanciyar hankali ko na second d'ayaba saidai yana k'ok"arin 6oyewane saboda Zarah ga kuma ciki da take d'auke da shi bayaso ta silarsa wani abu yasamesu,
janyeta yayi daga jikinsa tare da bud'e idanunsa da suka kad'a sukayi ja, cikin sanyin jiki yace Zarah kukan ya isa haka, kidaina sa damuwa a ranki idan kin ganni haka, kinga bake kad'ai bace kar wani abu yasameku ke da babynmu.

Girgiza kai Zarah tayi tace taya hankalinmu zai kwanta bayan wanda muke a k'ark'ashinsa yana cikin damuwa? Taya zan yafe ma kaina bayan ta dalilina karabu da kowa naka?
K'ara fashewa tayi da sabon kuka sannan tace banso karabu da sumayya ba dan 'yar uwarka ce ko bakomai itace matarka ka tafarko, indai har saboda ni kasaki sumayya toh wlh na yafe mata abinda tayi min duniya da lahira, please ka amince mukoma gida kamaida matarka kazauna cikin danginka, ko da ace hakan zaiyi silar mutuwar nawa auren.

Wani irin abu yarima yaji ya soki mak'ogwaronsa jin ta ambaci rabuwa da shi, tureta yayi daga jikinsa cikin 6acin rai yace Zarah na sha fad'a miki ko babu ke zan iya rayuwata, ammah kar kik'ara min zancen sumayya dan na riga nayi mata saki ukku kuma kidaina tunanin ta dalilinki nasaketa wlh ko d'aya, na saketane saboda wani dalili nawa kuma idan kin gaji da zama da ni zaki iya fad'amin,,,yana fad'in haka yamik'e yad'auki key d'in motarsa yaficce yabarta nan zaune dan gabad'aya ya kashe mata baki ta ma rasa abinda zatace masa.
Cigaba tayi da kukanta kamar wadda aka aiko ma da sak'on mutuwa, ita takaicinta rabuwar yarima da danginsa gashi kwata-kwata ya kasa fahimtar inda tadosa, dan ita tasan tanason yarima sosai, k'ara sautin kukanta tayi cike da tausayin kanta da mijinta saida tayi mai isarta sannan takwanta nan k'asa.

Har akayi sallar isha'i yarima bai dawoba dan haka Zarah tana nan zaune inda take, sallah kawai take tayar da ita, koda yadawo taddata yayi inda yabarta tahad'e kanta da gwiwa cikin ransa duk sai yaji ba dad'i haka yawuce yashige bedroom nan yai wanka yashirya har ya hau gado ya kwanta sai kuma yaji bai iya barinta a wannan halin dan haka yamik'e yafito parlour.

Zarah da tana jin shigowarsa ammah tashare jin bai kulataba ya wuce bedroom yasa siraran hawayen bak'in ciki suka zubo daga idonta, tunani tashiga yi anya yarima da yace yanasonta da gaske yake? Anya ba kawai ya fad'a bane dan yakwantar mata da hankali?, tana cikin haka sai jinsa tayi ya dafata, ahankali tad'ago kanta takallesa,
Cike da damuwa yarima yace Zarah meyasa kikeson d'aga min hankali? Menene abin kuka, ke kuka baimiki wahala na lura, yanzu dai taso muje kiyi wanka ga ice cream chan nasiyo miki kisha kinji?

Zarah shuru tayi nan yarima yataimaka mata tamik'e suka shiga bedroom saida yad'auko mata towel sannan yaje yahad'a mata ruwan wanka, lokacin da yafito har tacire kayanta ta ma d'auka zai taimaka mata tayi wankan ammah sai taga ya je yai zamansa dan haka tawuce taje tayi tana mamakin yarima yadda kwata-kwata shi bai iya lallashin maceba saidai shi a lallashesa.

Bayan ta fito wankan lotion kawai tashafa sai humra sannan tawuce taje tabud'e wardrobe tad'auko sleeping dress d'inta tasaka, zuwa tayi tahau gadon takwanta, yarima kallonta yayi yace bazakisha ice cream d'inba yau?

Kamar tace masa eh ammah ganin tanason sha yasa tamik'e batare da tayi magana ba taje tad'auko tazauna tasha, saida tashanye roba d'aya sannan tamik'e taje tasaka sauran cikin freezer taje tawanko bakinta tadawo takwanta, lokacin yarima har ya kwanta, daga gefensa itama takwanta dan yau haka sukayi kwanciyarsu batare da sunji d'umin junaba, tana jin yarima yana ta juyi batasan ya yak'areba har bacci yai awon gaba da ita.

Da asuba bayan sunyi sallah baccinta takoma inda tabar yarima zaune yana dannar system d'insa.

Wajen k'arfe goma da tafarka da mamakinta baya nan, kallon agogo tayi taga har k'arfe goma ta yi, mik'ewa tayi tafito parlour nan ma bainan dan haka tasan ya je wajen aiki, gyara d'akin tayi sannan tashiga tayi wanka tashirya.

Bayan ta gama fitowa tayi main parlour nan tatarar da jamila zaune tana kallo,
Cikin sakin fuska zarah tagaisheta.
Murmushi jamila tayi tace maman baby kin farka, ya gidan.
Lpy lou Aunty jamila, halan har sun ficce.
Dariya jamila tayi tace lokacin kina bacci suka fita dan prince cewa yayi akwai theater d'in da zai shiga k'arfe tara saisa tun 8:30am suka fita.

Numfashi zarah taja tace gaskiya Aunty jamila kina k'ok'ari tun da safe kike tashi kina had'a breakfast.

Toh zarah ya muka iya, indai kace bazaka girka da wuriba ai sai miji yafita batare da yayi breakfast ba daganan kuma sai afara cin abincin masu siyarwa nikuma natsani inga mijina yana cin abincin waje ke ni ko na 'yar aiki banaso inga yana ci.

Jinjina kai zarah tayi tace wlh nima Aunty jamila banaso inga mijina yana cin girkin 'yar aiki ammah ba yarda na iya.
Murmushi jamila tayi tace toh ya kuka iya ai gidan sarauta ya gaji haka, kedai shawarar da zan baki kikula da mijinki sosai dan kinsan 'yan matan yanzu bare ma irinsu yarima na tabbata bakowace mace bace zata gansa batare da taji ya burgetaba, dan rannan mijina ya fad'amin a hospital har 'yan mata sun fara shige masa dan ma baibasu fuska saisa suke yin baya da shi.

Ajiyar zuciya zarah tasafke tace toh ya zanyi Aunty jamila jin dad'inama da baya kulasu ammah ni kaina indai zai fita hankali baya kwanciya sai yadawo kuma dai gashi badaman ayi masa kulle.

Dariya jamila tayi tace kinjiki da wata magana wai kulle, kedai kicigaba da addu'a Allah yakare miki mijinki.
Ameen y rabb,,nan zarah taje tahad'o breakfast tadawo tazauna tana yi suna hira.

Bayan sun gama a tare suka shiga kitchen suka had'a lunch sannan zarah tawuce part d'insu tayi wanka tashirya.

Wajen k'arfe ukku gabad'ayansu parlour suka dawo suka zauna suna kallo suna hira jefi-jefi har akayi sallar la'asar ammah su yarima basu dawoba, jamila kallon zarah tayi tace mutanen shuru basu dawoba.
Uhm wlh kau Aunty jamila nima tunanin da nake kenan Allah dai yasa lafiya.
Ameen y rabb,,,cewar jamila, suna cikin haka sai ga su yarima sun shigo da sallamarsu.

Juyowa sukayi suka kallesu tare da amsa musu sallamar sannan sukace sannunku da zuwa.

Amsawa sukayi,
jamila ce tace tun d'azun muna ta jiranku ammah shuru.
Dr mu'az kallon yarima yayi sukayi murmushi sannan yace munje neman auren prince ne dan cewa yayi yanaso ya auri 'yar garin nan,,,yak'arashe maganar tare da kallon zarah da tacika tayi fam.
Jamila ma kallonta tayi tace laahhh my har da kai ake had'a baki dan ak'aro ma gimbiya abokiyar zama? Gaskiya ni ban goyi bayankuba.
Zarah saboda bak'in ciki kamar tad'aura hannu saman ka tafasa ihu,
Yarima murmushi yayi yace toh ya aka iya tunda ina so, yanzu dai bari inshiga ciki ind'an watsa ruwa, batare da ya kalli zarah ba yawuce yashige yana dariya ciki-ciki.

Murmushi mu'az yayi yace sorry gimbiya kar kiga laifina prince ne yaimin dole saisa nabisa mukaje,
Jamila k'unshe dariyarta tayi tace ku dai kukasani nidai ina bayan gimbiya.

Zarah shuru tayi kamar ruwa ya cita ta ma rasa abinda zatace,
Nan dr mu'az yashige yana dariya ciki-ciki.
kallonta jamila tayi tace ranki yadad'e kitashi prince fa na chan yana jiranki.
cike da k'ulewa tace Aunty jamila toh me zanyi masa.
Rik'e baki jamila tayi tace haba Zarah banyi tunanin jin haka daga garekiba ai na d'auka ko da ma kishiyarce bazata firgitakiba tunda kinsan kinriga kin zarce mata, kinga tashi kije kitaimaka ma mijinki nima kinga tafiyata.

Zarah ba dan tasoba tamik'e tanufi part d'insu lokacin da tashiga bedroom tsaye taga yarima gaban dressing mirror yana shafa da alama daga wanka yafito.

Tsaye Zarah tayi tana kallonsa, shareta yayi yai kamar baimasan tana wajenba, bayan ya gama ta gefenta yazo zai gifta yawuce sai a lokacin ya kalleta ta cika tayi fam, danne dariyarsa yayi Sannan yace kekuma fa?

Ai zarah kamar daman jira take yayi magana nan tafashe da kuka,,,,da mamaki yake kallonta yace Allah yabaki hak'uri daga tambaya sai kuka? Toh indai tambayarce toh nadaina nan yawuce yai tafiyarsa yabud'e wardrobe.

Dagudu zarah taje tarungumesa tabaya tacigaba da kukanta.
shuru yarima yayi yana jin kukan nata yana ta6a har cikin ransa,
ganin baida niyar yin magana yasa zarah cikin kuka tace menakeyi maka da kakeso kayi aure? Dan Allah indai wani abu nakeyi maka kafad'amin wlh zan daina,
juyowa yarima yayi yakalleta yaga haik'an take ta kukanta, murmushi yayi yace zarah ni na ce kinmin wani abu?
Girgiza kai tayi tana mai cigaba da kukanta.
tallabo fuskarta yayi yace kuma ni kikaji nace aure zanyi?
Nan ma Girgiza kai tayi.
murmushi yayi sannan yace tsokanarki fa daman mu'az yake dan yaga yadda zakiyi sai kuma gashi ya gani.
Zarah fad'awa tayi jikinsa tana cigaba da kukanta, dariya yarima yayi yace lallai ashe matar tawa tana tsoron kishiya ai na d'auka da jaruma nake zaune.
Duka zarah takaimasa a k'irji cikin kuka tace kai ko? Wlh ban yarda sai na rama,
dariya yarima yayi yace toh nidai bani nayi maganar ba.
'Dago kai zarah tayi takallesa tare da tsagaitawa da kukan da take tace ina sonka sosai akanka ba abinda bazan iyaba idan mace tara6eka ji nake wani iri sumayya ma dan ba yadda na iya nasan idan nace zanyi kishinta toh banyi ma kaina adalciba.

Murmushi yarima yayi yace aiko sai kinyi hak'uri dan yarima mijin mace hud'une.

Turo baki zarah tayi tace insha Allahu a haka zaka tsaya ba k'ari.
Dariya yayi yace lallai yarinya sai kinji ana gud'a ankawo min amaryata sabuwa gal.

Harararsa tayi cike da k'ulewa tace ai nima d'in gal aka kawo maka ni,
K'unshe dariyarsa yayi sannan yace toh ni mekikaji na ce?

Marairaicewa zarah tayi tace dan Allah kayi hak'uri akan abinda nayi maka jiya insha Allahu ba zan k'araba, wlh bana jin dad'i inga kana fushi da ni duk sai inji wani iri.

Goge mata hawayen fuskarta yayi yace kar kidamu ni ban rik'ekiba daman ai ke bakya laifi.

Murmushi zarah tayi tace ka dai fad'a dai kawai nidai yanzu kashirya muje kayi lunch dan nasan ka kwaso yunwa.
Toh ranki yadad'e yadda kikeso haka za'ayi.
dariya zarah tayi tace au abun harda tsokana?
uhm ni na isa intsokaneki,

nan zarah tataimaka mashi yashirya sannan suka fito inda suka tadda su mu'az suna zaune suna jiransu.

Ganinsu yasa mu'az yakyalkyale da dariya yace prince har ka gama lallashin?
Harararsa yarima yayi yace tunda ka had'aba.
Zarah duk'ar da kanta tayi cikin jin kunya.
jamila tace ammah dai nasan saida akasha da-ga kafin kashawo kanta.
Murmushi yarima yayi yace baby toh gaki gasu kisan zaman da kike dasu dan so suke suga ank'ara miki kishiya.
Turo baki Zarah tayi tace kabarni da su ai insha Allahu dagani ba k'ari ni kad'ai na isheka ko?
Dariya sukasa mata dan yanayin yadda tayi maganar ya basu dariya, yarima murmushi yayi yace kekad'ai fa kin isheni baby.

nan suka wuce dining suna dariya, zarah ganin tsokananta suke yasa tasharesu nan sukayi lunch, bayan sun gama nan taja yarima suka koma part d'insu sukaita shan love d'insu




_Comment_
       *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
[5/3, 9:52 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

*PAGE* 6⃣2⃣

*BAYAN WATA DAYA*

Zarah cikinta ya girma sosai dan a lokacin watansa takwas da ta zauna k'afafuwanta har kumbura suke, lalla6ata kawai yarima yake dan indai yana gida baya bari tana komai saidai shi yayi mata.

Yau ma kwance take saman cinyarsa suna kallon wani series film, d'ago kai tayi takallesa tace my dan Allah kataimaka kakira min su mama mugaisa kaga har yanzu bamuyi waya da su ba.

Kallonta yarima yayi batare da yayi magana ba, ganin haka yasa zarah tace ammah Indai kaga da matsala toh kabarsa kawai.

janyo wayarsa yayi yace ai dolema inkirasu dan nasan hali yanzu kin fara min kuka.

Murmushi zarah tayi tace karufa min asiri kai ai d'an alalla6ane ranka yadad'e inba hakaba yanzu mutum ya amsa query.

Hmm haka dai kikace, yanzu dai bari inkirata mugaisa, nan yarima yakira mama cikin girmamawa yagaisheta, bayan sun gaisa nan yamik'a ma zarah.

Cike da jin dad'i zarah tace hello mamana,
Daga chan 6angaren mama tace zarahta.
Murmushi zarah tayi tace ina wuni mama?
Lfy lou zarah, ya gidan,,cewar mama.
Lafiya lou mama nayi missing d'inku kwana biyu.
Daga chan 6angaren mama tace aikam dai zarah kun 6oye, ai muna neman wayanki bata shiga.
Zarah d'ago kai tayi takalli yarima da hankalinsa yana wajen T.V sannan tace eh wayarce tasamu matsala saisa, ina fata duk kuna lafiya ina abbanmu da su yaya rauda?
Mama tace babanku baya nan saidai su rauda, ai muna ta kiranki mufad'a miki munkoma sabon gida.

Wata irin k'ara zarah tayi cike da murna tace Alhmdllh gaskiya naji dad'i Allah yasa alkhairi, Allah yatsare sai munzo ganin gida.

Dariya mama tayi tace Ameen y rabb, toh Allah yakawoku lafiya.

Ameen mama, aba su yaya rauda mugaisa.

Nan mama tabasu sukasha hira har suna cewa zasuzo dan sun fitar da anko d'in bikkin Aysha, nan zarah tace a'a kar suzo dan sun d'anyi tafiya ammah idan sun dawo zata nemesu, sun dad'e suna hira sannan sukayi bankwana suka kashe wayar cikin jin dad'i.

Mik'ama yarima wayarsa tayi tace ka gama min komai nagode sosai my soulmate,
Murmushi yarima yayi yace toh yanzu hankali ya kwanta ko?

Girgiza kai zarah tayi tace har yanzu da saura, hankalina bai ida kwanciyaba.

Kallonta yarima yayi yace toh menene yayi saura?

Marairaicewa tayi tace dan Allah kakira ummi mugaisa da ita ko tasamu sauk'i a ranta dan nasan duk inda ummi take yanzu bata cikin kwanciyar hankali.

Nan da nan fara'ar da take fuskar yarima tagushe gabad'aya damuwa tabayyana, shuru yayi baice ma zarah komai ba.

Ganin haka yasa zarah tace dan Allah kataimaka koda minti biyune mugaisa da ummi.

Da mamakinta sai gani tayi ya janye mata kai daga saman jikinsa nan yamik'e yashige bedroom.

Da kallo zarah tabisa cike da tausayinsa, nan tamik'e tabi bayansa, saman gado ta tarar da shi kwance yayi pillow da hannuwansa, takawa zarah tayi taje tahau gadon takwanta daga gefensa tare da rungumesa cikin kwantar da murya tace kayi hak'uri mijina idan na 6ata maka rai, nima ba ason raina hakan yakasanceba kawai dai gani nayi yakamata ace koda sau d'ayane ka kira ummi dan nasan a yanzu duk inda ummi takasance toh hankalinta a tashe yake, ammah da taji kana cikin k'oshin lafiya na tabbata hankalinta zai kwanta,
Yarima maida idanunsa yayi yalumshe yana jin wani iri a ransa.

Zarah cigaba tayi da cewa kafini sanin yadda ummi takeji a game da kai, kana tunani ko da sau d'aya hankalinta zai kwanta alhali batajin ko muryarka?

shuru yarima yai yakyaleta kamar yaba banza ajiyarta.

Ganin haka yasa zarah tafashe da kuka tace shikenan kayi yadda kakeso tunda haka kaza6a idan namutu ba shikenan ba.

Yarima jin maganartata yayi har cikin ransa, rungumeta yayi tare da bud'e idanunsa yace zarah kidaina cewa haka insha Allahu bazaki mutu kibarni ba, indai ummi ce bari inkirata yanzu.

Zarah cikin jin dad'i tarungumesa tace nagode sosai mijina Allah yasaka da alkhairi.

Murmushin k'arfin hali yarima yayi yace Ameen dear, wayarsa yajanyo yalalubo number d'in ummi.


Ummi tun bayan tafiyar yarima bata samun kwanciyar hankali dan ko abincin kirki bataci, sultan Ahmad shi yake tsareta yake samu tana ci, kullum aikin d'ayane daga lallashi sai wa'azi ahaka tad'an safko tafara sakewa.

Yauma zaune take saman darduma tana lazimi, wayartace datake kusa da ita tafara ringing, ido tazuba ma wayar ganin sabuwar number ce kamar ba zata d'aukaba har saida takusan tsinkewa sannan tayi picking tare da yin sallama.

Yarima jin muryar umminsa yasa yalumshe ido yana jin wani irin nishad'i a ransa, nan Ummi taita magana ammah shuru.

Zarah ce tata6osa ahankali tace kayi magana.

sai a lokacin yabud'e idanunsa sannan yace hello Ummina.

Jin muryar yarima yasa sultana bilkisu tarikice tarasa mezatayi murna ko kuka, ai sai ji yayi ta fashe da kuka tace my son kaine? Shine katafi kabarni baka ko nemana? Ni miye nawa laifin da kagujeni, baka tunanin halin da zan shiga?

Yarima runtse idanunsa yayi yanajin wani irin d'aci a ransa, cike da tashin hankali yace ummina kiyafemin wlh ba ason raina hakan yakasanceba, kema kinsani ba zan iya zaman second d'ayaba batare da kina a rainaba.

Cikin kuka Ummi tace nasan haka my son dan Allah kadawo gareni ko nasamu sauk'in abinda nakeji a raina, kataimaka kazo inganka ko hankalina ya kwanta.

Yarima hawayene yaji suna zuba daga idanunsa, ahankali cikin muryar lallashi yace Ummi kikwantar da hankalinki muna cikin k'oshin lafiya, indai har kina kuka toh nima zaki sani inyi.

Jin haka yasa ummi tayi saurin tsaida kukanta tace nadaina my son, yaushe zakazo?

Karkidamu ummina very soon zanzo gareki kicigaba da yi min addu'an da kikasaba.

Murmushin jin dad'i sultana bilkisu tayi tace Allah yaimaka albarka kaida zuri'arka my son, a yanzu hankalina ya kwanta da naji kuna cikin k'oshin lafiya, kuma insha Allahu akowane lokaci zakucigaba da kasancewa cikin addu'ana, yanzu kuna ina?

Shuru yarima yayi nad'an lokaci sannan yace ummi muna nan cikin k'oshin lafiya.

Ajiyar zuciya tayi tace masha Allah gaskiya naji dad'i toh ina d'iyar tawa?

Yarima waigawa yayi yakalli Zarah da tahad'e kai da gwiwa tana kuka k'asa k'asa, dafata yayi nan tad'ago kai yamik'a mata wayar kallonsa tayi, nan yai mata nuni alamun takar6a.

Bayan ta amsa muryarta tana rawa tayi ma ummi sallama, amsa mata ummi tayi nan Zarah ta gaisheta cike da girmamawa.

Ummi bayan sun gaisa, cikin sanyin jiki tace Zarah kiyi hak'uri da abinda yafaru mune muka ja miki.

Girgiza kai Zarah tashiga yi cikin sheshek'ar kuka tace ummi kidaina cewa haka *K'ADDARA CE* kawai taja hakan kuma har ga Allah ban ta6a tunanin kun cutar da ni ba koda sau d'aya, saidai abu d'aya nake tunanin kunyi min shine kun sama ma rayuwata farin ciki, baku k'yamaceniba a matsayina na talakka kun had'ani aure da d'anku, taya zan yi wani tunani nadaban akanku? Wlh ummi ku masoyanane nagaskiya ku iyayene agareni dan dani da 'ya'yanku duk d'aya kukad'aukeni,
K'ara fashewa da kuka Zarah tayi tace ummi wlh kun gama min komai a rayuwata tsakanina da ku saidai addu'a dan banda abinda zan biyaku.

Ummi Murmushin jin dad'i tayi tare da goge hawayen fuskarta sannan tace Allah yaimuku albarka Zarah, Allah yasafkeki lafiya mucigaba da addu'a insha Allahu memartaba zai safko daga fushin da yake kudawo gida.

Murmushi zarah tayi tace Allah yasa ummi,
Yarima zare wayar yayi daga kunnenta tare da switching off d'inta gabad'aya.

Zarah da mamaki take kallonsa da ya aje wayar tare da komawa yakwanta yamaida idanunsa yalumshe, saman k'irjinsa takwanta ahankali cikin muryar lallashi tace kayi hak'uri insha Allahu komai zaizo k'arshe.

'Dan guntun murmushi yarima yayi sannan yace niko zama na nan ya fi min dad'i koda sau d'aya bana tunanin komawa gidanmu, nidai burina iyayena susami kwanciyar hankali.

Da ido take binsa har yakai aya sannan tace kadaina cewa haka yarima koma me akayi maka yakamata ace ka hak'ura domin 'yan uwa dabansuke ba a iya canzasu, cikin dangine zakashiga kai rayuwarka kaji dad'i.

Murmushi yarima yayi yace naji yanzu dai aji da ni sarkin surutu.

Zaro ido zarah tayi tace anya zan iya? Kaga fa yanzu nayi nauyi.

Kar kidamu baby zaki iya nima ai ahankali zan miki dan banason wannan rakin naki.

shagwa6e fuska tayi kamar zatayi kuka tace au nice ma sarkin raki?

Dariya yayi sannan yace toh ai haka kike,

Uhm naji ai kaine baka tausayina.

Yarima yace au haka kikace? Toh shikenan bari kigani.

Zaro ido zarah tayi tace dan Allah kayi hak'uri da wasa fa nake.

Shareta yarima yayi nan yakwantar da ita, ganin tayi rau-rau da ido yasa yai murmushi tare da komawa gefenta yakwanta, kansa yana kallon ceiling.

Kallonsa zarah tayi ganin baida niyar yi mata komai yasa tace toh ka fasa?

Juyowa yayi yakalleta yana murmushi yace sarkin tsoro ni ba abinda zan miki daman.

Dukan wasa zarah takaimasa tace kai ko?
Dariya yayi yace ya na iya tunda Allah ya had'ani da matsoraciyar mata.

Uhm kaima kasan ni jaruma ce.

Nidai bansan komai ba ammah bari inyi  just na 5 hours tanan zan d'an gane jarumtarki.

Zaro ido zarah tayi tace karufamin asiri ai sai inmutu.

Kumatunta yaja yace ba zaki mutuba dear, maida kanta tayi saman k'irjinsa tace Allah yasa ina da rabon rayuwar,
Yanzu in namutu shikenan aurenka zaka sake kamance da ni,,,tak'arashe maganar kamar zatayi kuka.

Rungumeta yayi yana ji kamar ta soka masa mashi a mak'oshi da ta ambaci mutuwar, ahankali yace zarah kidaina cewa haka dan ni bana tunanin zan iya son wata bayan ki, ban ta6a son wataba sai ke.

'Dago kai tayi takallesa tace har sumayya?

Yarima ji yayi wani irin takaici da tsanar sumayya sun dabaibayesa musamman ma da yatuna halin da yasameta ita da k'awarta,,,cike da takaici yagirgiza kai yace sumayya auren had'ine akayi mana,
Zuba mai ido zarah tayi tace toh kai bakada za6in kanka mu dukanmu baka akayi?

Cike da k'osawa da tambayoyinta yajanyeta daga jikinsa yamik'e yace baby kin cika tambaya har kinsa kaina ya fara ciwo yanzu dai bari inje ind'anyi wani research a system,,yana fad'in haka yaje yad'auki system d'insa yakoma parlour.

Zarah da kallo tabisa cike da so da k'auna har yaficce, sannan tayi murmushi tare da janyo pillow tarungume a k'irjinta.

______________
Ummi bayan yarima ya kashe wayar ajiyar zuciya tayi dan har cikin ranta taji dad'i da taji d'anta yana cikin k'oshin lafiya kuma ta ji hankalinta ya kwanta, a ranar saida kowa yasan tana cikin farin ciki dan rabon da aganta a yanayin tun ran da yarima yabar gidan.

A 6angaren sumayya ko hidimarta kawai take koda tanajin ba dad'i akan mutuwar aurenta ammah zinat tuni ta fara mantar da ita damuwarta dan basuyin ko 2 hours batare da sunyi wayaba nan wata shak'uwa tak'ara shiga tsakaninsu, da ace za"a duba wayarta a lokacin blue films da pic's ne kawai cikinta da ta zauna part d'inta batada aiki sai kallo sai waya, wulak'anci ko k'aruwa yayi dan ma'aikatansu har ji suke daman bata dawoba dan gabad'aya indai zata fito toh sai ta hanasu kwanciyar hankali.

Sultana sadiya ganin hankalin sumayya ya kwanta yasa itama taji dad'i a ranta, hatta shi kansa sultan abbas koda ya nuna fushi yake da ita saida taje tasamu tabasa hak'uri sannan tasamu sauk'in mahaifin nata.

Yau ma kamar kullum kwance take tayi d'aid'ai a saman gadonta tana waya da zinat, inkaganta sai karantse da namiji take waya dan shagwa6a kawai take zuba mata akan tazo taimata ko sati guda ne.

Zinat tace anya baby kina ganin ba matsala ni fa ina tsoron abinda yafaru da farko yak'ara faruwa dan kinga wanchan mijin naki har tabbai yabarmin a jiki.

Ta6e baki sumayya tayi tace ke kema tunawa da shi ai wlh tunda yasakeni toh sai nayi silar rabasa da wannan tsinannar matar tasa.

Dariya zinat tayi tace baby har yanzu dai kina akan bakanki, yanzu dai kisaurareni end of this week zaki ganni.

Wani irin k'ara sumayya tayi tace dagaske kike ko wasa?

Dariya zinat tacigaba da yi, sai chan tad'an tsagaita dariyar tace kai baby zaki ciremin kunne, zan shigo man ammah anya ba a hotel zan safkaba, saboda ni a yanzu gidanku yafi k'arfina.

Cike da Jin dad'i sumayya tace bawani fin k'arfi, dan Allah kizo kawai wlh babu matsala kinsan ba za'a barni indinga fitaba a yanzu.

Ajiyar zuciya tasafke tace toh shikenan baby sai na shigon.

Jibi kenan ko? Cewar sumayya.

Kai kedai kin cika hanzari zan dai gani idan jibin.
Chab wlh baki isaba tunda dai kika furta toh dole kizo ranar dan ba kad'an nayi missing d'inkiba.

Toh shikenan dear yadda kikeso haka za'ayi.
Nan sukacigaba da hirarsu sunfi 1 hour sannan daga baya sukayi sallama kowa yakashe wayarsa,


Memartaba tun bayan tafiyar yarima shi kansa ji yake duk ba dad'i, indai yana zaune fada kad'an kad'an ya kalli kujerar da yarima yake zama saidai yaga sultan Ahmad ne madadinsa, daurewa kawai yake yana danne zuciyansa dan shi kansa yasan yana kewar yarima ammah daga sa'ilin da yatuno abinda yarima ya aikata masa sai yaji wani irin haushinsa ya cikashi.

Dada ita kanta tana jin ba dad'i akan tafiyar yarima dan abu biyu yahad'e mata ga mutuwar auren sumayya ga tafiyar jikanta,
Tausayin sumayya yasa kusan kodayaushe sai ta aika ankira mata ita taji abinda takeso, nan sumayya take ida komawa kalar tausayi tafad'i abinda takeso ko menene nan da nan Dada take sanyawa ayi mata, ciki kuwa harda canza mata mota tasa akayi mata, tana jin tausayinta sosai saboda akanta aka fara jawarci a masarautar tasu.

Shaheed ma ba k'aramin girgiza yayiba da yaji labarin tafiyar yarima, duk inda yake tunani yarima ya sani toh ya je babushi babu alamunsa.

_*Bayan Kwana Biyu*_
Sumayya ce zaune a parlour suna hira da ummanta cike da jin dad'i sunyi nisa da hirarsu sultana sadiya takalli d'iyartata cike da k'auna tace sumayya idan kika gama iddah kinga sai kisamu wanda kike gani yana da dama-dama ki aura.

6ata fuska sumayya tayi tace haba ummah wane irin aure yanzu ai ni nayi sallama da aure.

Zaro ido sultana sadiya tayi tace kirufa min asiri kinsan dai su memartaba da abbanki bazasu ta6a amincewaba, indai manemanki sukazo kawai kisamu kishige kicire wanchan matsiyacin a ranki.

Yamutsa fuska sumayya tayi tace ummah har kina tunanin zan iya zama da wani bayan yarima? Ni koda ma an matsamin sai nayi aure toh wlh saidai inyi auren kisan wuta inyaso daga baya infito inkoma wajen mijina dan ni Indai ba yarima ba babu wanda zan iya aure.

Jinjina kai sultana sadiya tayi cike da mamakin furucin d'iyartata tace sumayya anya yarima bai asirce min ke ba? Taya ana ga gabas kekuma kina ga yamma, ubanme suhail yakeda shi da zaki nace masa?

Dariya sumayya tayi tace kai ummah ni wlh kina ban dariya,,,,yauwa na ma mance infad'a miki gobe k'awata zinat zatazo.

Washe baki sultana sadiya tayi tace ayya na gane, wai ya business d'in naku yana dai tafiya daidai ko?

Yatsina fuska sumayya tayi tace eh toh dan tana turo min kud'i sosai, gobe ma zatazo min da wata sark'an gold da nasa tasiyo min cikin kud'in.

Cikin jin dad'i sultana sadiya tace angaisheki d'iyar albarka, kina jan kud'i, kai gaskiya naji dad'i Allah yakaimu goben, Allah yakawota lafiya.

Ameen ummana, nan sumayya tacigaba da bata labari akan business d'insu.

Wanshe kare sumayya shirye-shirye tayi sosai na tarbar zinat, girki ko anyi yakai kala goma, ummah dai binta take da kallo dan ko ba'a fad'a mataba tasan zinat tana da muhimmanci sosai a wajen sumayya, tun daga kan yanayin hirararta da take yawan yi mata sannan kuma batada k'awar da takema rawar kai kamar zinat dan haka take kallon shak'uwace sukayi sosai tunda tun a school suke tare.

Sumayya taso abarta taje da kanta tatarbo zinat ammah ummah tace ba ruwanta taje tasami abbanta tatambayesa, kan dole tahak'ura dan tasan bazai ta6a barintaba dan haka tatura driver d'insu yaje yad'aukota.

Koda ta iso sumayya tayi mamaki sosai ganin shigar da zinat tayi dan shigace ta mutunci ba kamar wadda takeyiba in zatazo, haka takaita wajen sultana sadiya cikin mutunci suka gaisa idan kaga yadda zinat tagaishe da sultana sadiya sai karantse ga Allah cewa d'iyar mutunci ce.

Bayan sungama gaisawa sumayya janta tayi zuwa part d'inta, suna shiga dariya sumayya tashiga yi tace kai baby wannan shiga da kikayi sai mutum yarantse cewa musulmace kamila, yau kece da babban veil.

Hmm kedai bari baby nima jina nake wata iri ke dakyar na iya tako gidannan dan gani nake kamar zamu had'u da wannan mugun.

Ta6e baki sumayya tayi tace wannan ai tuni yai nisan kiwo dan soyayya tarufe masa ido ya za6i matarsa yabar iyayensa, inma asiri waccan makirar tayi masa to sudai sukasani.

Ke ni naji dad'in tafiyarsa dan yanzu zamu wala zamuci karenmu babu babbaka.

Haka dai kikace baby ammah nifa banso aurena yamutuba dan inason mijina.

Ta6e baki zinat tayi tace ni da bakyaso ko?

Kirufan asiri kema ai shedace kinsan ina sonki sosai baby da ace ban sonki da bazan kulakiba,,,cewar sumayya.

Ammah ai kinfi sonsa,,,
Dariya sumayya tayi tace zinat kenan ba bayaba wajen kishi, ni banfi sonsaba kowa da matsayinsa a wajena yanzu dai muje kiyi wanka kici abinci.

Ohk ma.
nan suka sakarma juna murmushi sannan sukawuce sumayya tataimaka mata tayi wanka sannan suka je tayi lunch bayan tagama suka zauna hira daga nan suka haye saman network.

Haka zinat tacigaba da zama gidansu sumayya kullum suna manne da juna, sultana sadiya har mamaki take yadda yanzu sumayya ko firar da take fitowa suyi ta daina kullum suna k'unshe cikin bedroom,,,nan tai mata uzuri ta d'auka duk saboda jin dad'in zuwan k'awarne dan ankwana biyu ba a had'uba kuma ko bakomai yanzu taga d'iyarta tana cikin farin ciki dan rabonta da taganta cikin yanayin tun tana tare da mijinta.




_Comment_
     *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
[5/3, 9:52 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

*PAGE* 6⃣3⃣

Yarima tsaye yake gaban dressing mirror yana shiryawa inda zarah take zaune chan saman gado rungume da pillow ta zuba masa ido tana kallonsa.

Yana gama shirinsa juyowa yayi yakalleta tare da sakar mata murmushi yace ya dai baby?

Murmushin itama tayi tace ina kallon yadda handsome man yayi kyau nidai fatana kar aimin kwacensa.

Har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa.

Ganin haka yasa itama taja bakinta tayi shuru, nan yazo yad'auki key d'in motarsa da waya.

Rik'o hannunsa zarah tayi tare da marairaicewa tace please kakulanmin da kanka.

Zuba mata ido yarima yayi chan sai yajanye kallonsa daga fuskarta zuwa kan cikinta d'an kuntun murmushi yayi sannan yace nima kikular min da babyna.

Zarah sakin hannunsa tayi tare da d'aga masa kai, kallon fuskarta yayi yace sai nadawo.

Ahankali tace adawo lafiya.
Nan yajuya yafita yabarta nan zaune, shafa cikinta tayi sannan takoma takwanta tana mamakin halin yarima yadda cikin lokaci guda idan miskilancinsa yamotsa ko ita kanta bai saurara mata.


koda yaje hospital bayan ya gama round ya duba patients d'insa da suke ward, office d'insa yakoma nan yajanyo system d'insa yacigaba da research kasancewar kusan abinda yake kenan indai yazauna shikad'ai dan yasamu sauk'in yawan tunane-tunanen da yake.

Knocking d'in da akayine yasa yabada izini ashigo, ahankali taturo k'ofan tashigo tare da yin sallama.

Jin muryar mace yasa yarima yad'ago kai yasafkesu akan wata kyakkyawar yarinya wadda bazata gaza 25yrs ba sanye take cikin lace ta d'aura labcut daga sama sannan tayi rolling da veil kalan kayan, janye idanunsa yayi daga kallonta yamaida kan system d'in tare da d'aure fuska.

Bata damu da yadda yad'aureba tatako ahankali tazauna kujerar da take opposite d'insa, cikin kwantar da murya tace sannu da hutawa doctor.

Yarima batare da ya kalletaba yace meyakawoki office d'ina?

Batayi mamakin yadda yayi mataba dan daman tasan halinsane saidai ba yadda ta iya dole tafurta masa sirrin da yake cikin zuciyanta.

Murmushi tayi tace sorry doctor yanzu zan fad'amaka dalilin zuwana dafarko dai am Dr leemah ni staff ce a hospital d'innan dan nasan baka sanniba.

A gaskiya kana burgeni sosai yanayin yadda kake tafiyar da rayuwarka kuma naga kamar baka shiga harkar kowa komai naka da kakeyi me ajine saisa kake burgeni dan Allah idan ka amince inaso muk'ulla friendship.

'Dago kai yarima yayi yawurga mata wata irin harara har saida Dr leemah tatsorata ammah tadake dan a yadda takejinsa a ranta bata damu da duk abinda zaiyi mataba.

Ganin baida niyar yin magana yasa Dr leemah tacigaba da cewa kar kadamu indai zaka amincemin duk abinda kakeso zanyi maka koma menene,,,

Janye system d'in gabansa yayi tare da kallonta kamar ba zaiyi maganaba sai da yayi kusan 3 minutes sannan yace kin gama?.

Fari tayi masa da ido sannan tace eh my dear.

K'ara d'aure fuskarsa yayi tamau sannan yace ni anfad'a miki irin wad'annan banzayen mazan ne?

Ammah ai taimaka ma juna zamuyi ni kawai burina inga ka amince muna friendship koda ace bakasoniba nasan wata rana zaka soni.

Hanya yarima yagwada mata cikin tsawa yace get out of my office! kokuma yanzu in 6ata miki rai.

Ganin ba alamun wasa a tare da shi ga wani irin k'warjini da yayi mata, cikin sauri tamik'e tafita tabar office d'in tana mamakin halin yarima.

Bayan ta fita dafe kansa yayi saboda 'yar hayaniyar da yayi har yaji kansa ya fara ciwo, mamaki yake yadda daga fara aikinsa zuwa yanzu matan da sukazo daga different departments suka kawo masa kansu sunkai goma, tsaki yaja cike da jin haushi daga k'arshe tashi yayi yatattare komai yad'auki key d'insa yaficce, saida yafara zuwa masallaci yayi sallar azuhur sannan yawuce gida.

Lokacin da ya isa zarah tana zaune a parlournsu tana kallon wani indian series film, gabad'aya tamaida hankalinta a kallon dan tunda tayi wanka tayi sallah tazauna kallon hannunta apple ne take ci.

Sallamar da yarima yayine yasa tajuyo takallesa cike da mamakin ganin ya dawo ukku batayiba murmushi tasakar masa tare da cewa sannu da zuwa.

Yauwa kawai yace batare da ya bi ta kantaba yawuce yashige bedroom.

Mamakine ya ida kamata ganin yadda daga jiya zuwa yau duk ya canza mata, mik'ewa tayi dakyar tanufi bedroom d'in tana shiga lokacin yarima yana cire kayansa.

Takawa tayi ta isa inda yake, murmushi yarima yasakar mata yace ya dai?

Ajiyar zuciya zarah tasafke tace na d'auka laifi nayi maka.

Kallonta yarima yayi yace mekika gani?
Langwa6e kai zarah tayi tace toh ai naga duk ka canzamin.

Murmushi yayi tare da shafa fuskarta yace kar kidamu baby babu abinda kikayi min ai ke bakya laifi, yanzu dai bari inje inyi wanka kije kijirani kinji?

'Daga kai zarah tayi tare da sakar masa murmushi.

Yauwa baby, yarima yace sannan yawuce yashiga toilet.

Zarah zuwa tayi tafiddo masa kayan da zaisa sannan tazauna tana jiransa yafito.

Koda yafito ita tataimaka masa yashirya sannan suka fito, ita taje tad'ebo musu abinci takawo musu nan yarima yana ci yana lalla6ata itama tana ci,
Bayan sun gama zarah tagumi tazuba tana kallon yarima cike da son mijin nata.

Janye mata tagumin yayi yace kallon fa?

Duk'ar da kanta tayi cike da jin kunya.

janyota yayi jikinsa yakwantar da ita saman cinyarsa tare da zame mata kallabinta yana shafar gashin kanta.

'Dago kai tayi takallesa tana murmushi tace my heartbeat akodayaushe naganmu a tare wani irin farin ciki nakeji a raina, ina k'ara godema Allah da ya mallakamin kai a matsayin miji abun sona.

Murmushi yayi sannan yace zarah banta6a tunanin zan iya son wataba a yanzu dan ko kusa bansa ma raina yin soyayya ba ammah a lokaci guda kinchanza min ra'ayina sai gashi Allah ya dasamin sonki a raina, a yanzu na gama yadda da cewa kece macen da nafara so a rayuwata ina fata Allah yabarmu tare  dan kincika macen kirki tabbas su ummi gata sukayi min da suka za6amin ke a matsayin mata.

Tashi zarah tayi zaune tafuskancesa tana murmushi  tace nafi kowa farin ciki dan gani nake kamar nafi kowace mace sa'ar miji dan komai na mijina daban yake.

jan hancinta yayi yace kedai kin iya tsokana na lura da ke.

shagwa6e fuska tayi kamar zatayi kuka tace ni fa gaskiya nafad'a dan mijin nawa komai nasa maitsada ne sauk'inma da yanzu nad'an samu sauk'in miskilancinsa,,,tak'arashe maganar tare da kashe masa ido d'aya.

Matsota yayi a jikinsa tare da tura hannuwansa cikin rigarta yace zarah nagama amincewa da ke a rayuwata sannan kuma d'an zaman da mukayi da ke a yanzu nima ina mamakin yadda gabad'aya nafara canzawa, girgiza kai yayi sannan yace bansaniba ko dan na baro gidanmu, murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace nima kaina ina mamakin hakan.

Zarah fad'awa tayi jikinsa cike da tausayinsa da k'aunarsa tace my heartbeat kakwantar da hankalinka insha Allahu zaka koma cikin family d'inka dan nima ina buk'atar inganka cikinsu.

Yarima batare da ya bata amsaba yalalubo bakinta yakaimata zazzafan kiss sannan yakwantar da kansa saman cinyarta tare da maida idanunsa yalumshe.

Zarah ajiyar zuciya tasafke nan tacigaba da wasa da gashin kansa batare da ta k'ara maganaba dan hakan kawai da yarima yayi ya sa tagane bayason maganar.

______________

Yau ma kamar kullum sumayya da zinat manne suke da juna suna hirarsu dan a 'yan kwanakin da zinat tayi saida tasan yadda tayi tasa sumayya tafara cire yarima a ranta, suna cikin hirar zinat kallon sumayya tayi tace baby inaso kirakani kasuwa daga chan muje gidan wannan friend d'in tawa khausar saboda jibi nakeso inwuce yola.

Shuru sumayya tayi kamar ba zatayi maganaba sai kuma chan tace baby kina ganin za'a barni infita? Kinsan halin abbana ba zai aminceba.

Ta6e baki zinat tayi tace ni fa tsiyata da ke kin cika tsoro fitar da zamu d'anyi kawai mudawo, kuma ai ko a 6oyene sai kifita batare da ya saniba kifad'ama ummah kawai dan gaskiya dole muyi tafiyarnan a tare inkuma ba hakaba ban k'ara zuwa gidannan idan natafi.

Zaro ido sumayya tayi tace baby meyayi zafi haka, indai hakane toh na amince muje ammah gaskiya sai zuwa gobe saboda su abbah yanzu suna nan fada, zansan yadda zanyi inlalla6i ummah ta amince, ammah kikace zaki daina zuwa wajena ai bansan yadda zanyi da rayuwataba da mi zanji da mutuwar aurena ko da rabuwarki da ni?

Rungumota zinat tayi tace kiyi hak'uri baby kema kinsan bana iya rabuwa da ke,
Murmushin jin dad'i sumayya tayi tace nagode sosai baby Allah yabarmin ke.

Ameen babyna, cewar zinat.


Wanshe kare shiryawa sukayi cikin atamfarsu sukayi anko d'inkin riga da skirt kayan sun kamasu sosai, nan sukayi gwanin kyau, sumayya ce tafito tanufi part d'in mahaifiyarta

Zaune tasamu sultana sadiya tana waya dan haka tasamu gefenta tazauna tana jiranta.
Bayan ta gama wayar juyowa tayi takalli d'iyartata cike da so tace sumayya wannan gayu haka sai kuma ina?

Murmushi tayi sannan tace ummana dan Allah taimako guda nakeso kiyimin.

Zubamata ido sultana tayi tace ina jinki.
Gyara zamanta tayi tamarairaice tace ummah kinga zinat gobe takeson tawuce gida shine takeso dan Allah inrakata kasuwa tanaso tayo siyayya.

Ajiyar zuciya tasafke tace sumayya bank'i ta takiba saidai mahaifinki nake ji ma tsoro kinsan halinsa idan har nabari kika fita toh ba keba hatta ni kaina sai raina ya 6aci.

Rik'o hannunta sumayya tayi kamar zatayi kuka tace dan Allah ummah kibarni inje, wlh indai banjeba bazataji dad'iba Indai abbah ne bazan bari muhad'uba kuma yanzu ai sun fita da daddy.

Shuru tayi kamar menazari sannan tace toh shikenan kije ammah dan Allah kar kidad'e sannan kutafi da guards da kuyangi.

Cikin jin dad'i sumayya tarungume ummanta tace nagode sosai ummana insha Allahu bazan dad'eba.

Dariya sultana sadiya tayi tace nidai na fad'a miki.

Mik'ewa tayi itama tana dariya tace karkidamu ummah bazan dad'eba.

Koda tadawo room d'inta zaune tatarar da zinat tana jiranta, ganinta yasa tamik'e tana Murmushi tace baby da alama naga munyi nasara.

Itama Murmushin tayi tace sosai ma, d'auko key d'in motarta tayi tare da d'an k'aramin veil d'inta tace yanzu dai zo mutafi tun kan abbah yadawo.

Cikin sauri suka fito sumayya bata tafi da kowaba kamar yadda sultana sadiya taso,
Motarta suka shiga tayi mata key, dagudu tafita daga masarautar.

Kasuwa suka fara zuwa sukayi shopping sosai duk inda suka ratsa kallonsu ake, sun dad'e a kasuwan sannan bayan sun gama suka wuce gidan k'awar zinat.

Kasancewa khausar tasan da zuwansu sosai ta tarbesu nan suka baje sukaita hirarrakinsu, sumayya jin irin labaran da suke fitowa daga bakin khausar saida ta jinjina kai ganin da aurenta ammah har zina take, abinda ita batayiba kenan saidai shan minti.

Sun dad'e suna hirar nan tamatsa ma zinat tatashi sutafi ammah zinat tak'i, tana kallo yadda khausar take shige ma zinat nan haushi yakamata,
Zinat ita kanta saboda sumayya ne yasa bata biye ma khausar ba dan duk yadda take huld'a da mata toh batayi gaban sumayya dan ta tsani ganin 6acin ranta sannan bataso taga kowa ya ra6eta.

Ganin yadda sumayya tacika tayi fam yasa zinat tace tatashi sutafi, haka khausar tacikasu da sha tara na arzik'i ammah kwata-kwata bata birge sumayya ba dan Indai mace zata ra6i zinat toh tsanarta takeyi.

Koda suka kama hanya gabad'ayansu shuru sukayi, murmushi zinat tayi tare da kallonta tace baby ya dai naga duk kin canza lokaci guda.

uhm dole kiga na canza baby wlh waccan friend d'in taki inbatayi wasaba sai na nakasata dan naga take-takenta nema take tashige miki.

Zaro ido zinat tayi tace kai sumayya yanzu khausar d'in?

Ta6e baki tayi tace koma wacece, nasan kina harkokinki abayan idona wannan bazan damuba tunda ba gabana kikayiba.

ajiyar zuciya zinat tasafke tace sumayya kema kinsan yadda nake jinki a raina bana tunanin akwai wadda nakeso sama da ke.

Kedai ayi sha'ani kawai baby nidai nasan ba kowace jakka zan iya ba kainaba,

Dariya zinat tayi dan tasan kishintane sumayya takeyi.

Daidai lokacin sumayya tayi horn, ganin motarsa yasa masu gadi cikin sauri suka bud'e mata gate dan sunsan halin gimbiyartasu yanzu zatace anyi mata laifi komai girmansu bazai hana tawulak'antasuba.

Koda tayi parking d'in motar nan ma'aikata sukayita zuwa gaiahesu a wulak'ance suke amsawa sannan tasa aka shigar musu da kayansu ciki.

Koda tashiga a parlour tasamu ummah tana ta saffa da marwa hannunta rik'e da waya,  ganinsu yasa tayi ajiyar zuciyata tace ku sai yanzu kukaga damar dawowa?

Kallon juna sukayi sukai Murmushi sannan sumayya tace ummah siyayyarce dayawa mukayi.

Uhm kudai kawai kuce kun biya yawonku, ni kun barni nan cikin tashin hankali yanzu inda ace abbanki ya tambayeni mezance masa? Yanzu kuduba kuga yanayin shigarku dukkanku veil k'arami kuka fita da shi, ke sumayya kinsan dai yanayin gidan nan ammah kike komai yadda ranki yakeso

Marairaicewa sumayya tayi tace kiyi hak'uri ummana insha Allahu bazan k'araba.

Toh shikenan kushiga ciki kuhuta bari insa akawo muku abinci.

Toh ummah,,sukace tare da mik'ewa suka shiga bedroom d'in sumayya.

Koda suka shiga zinat kallon sumayya tayi da take shirin cire kaya tace baby yakamata kihuce hakanan daga fushin kinga ni gobe zan bar garin.

Shareta sumayya tayi tad'aura towel tana shirin wucewa toilet nan zinat tasha gabanta tace yau kuma baza'ayi wankan da ni ba?

Cike da jin haushi sumayya tace kije wajen wad'anda sukafini sai kuyi.

Rik'o hannunta zinat tayi tace baby *KIYARDA DA NI* babu wadda tafiki a wajena kekanki shedace dan kinsan hakan.

Murmushi sumayya tayi tace toh shikenan baby yanzu kicire kayan muje muyi wanka.

Cikin jin dad'i zinat tace toh nan suka wuce suka shiga wanka.

Bayan sun fito zinat wucewa tayi tasama d'akin key tazare tanufo inda sumayya take tsaye ta tsareta da ido, murmushi tasakarmata tace baby gobe zamu rabu dan haka kizo kisallameni dan nasan kafin ink'ara zuwa garinnan sai ankwana biyu tunda ke bazuwa kikeyiba.

Murmushi sumayya tayi tace shine harda sa key?
Uhm ina tsoron abinda yafaru yak'ara faruwa dan gabad'aya yarima ya gama tsoratani.

Dariya sumayya tayi tace lokacin fa kinban dariya dan kinma fini rikicewa, gaskiya yarima ba bayaba.

itama dariyar tayi tace wlh yana min k'warjini saisa banaso inzo gidanki idan yana nan.

Ta6e baki sumayya tayi tace baby kidaina tunomin har kinja raina ya fara 6aci.

Janyota zinat tayi tace sorry baby muje infaranta miki ran naki.

Haka suka wuce saman bed suna dariya nan suka shiga faranta ma junansu rai.


Abban sumayya da sultan Ahmad da suke tsaye daga chan waje guda suna hira a gaban idanunsu su sumayya suka dawo.
Cike da jin takaici sultan Abbas yace ma d'an uwansa yaya kaduba kaga wai d'iyar cikinace take sanye da wad'anchan suturar har ma tafita batare da saninaba.

Shi kansa sultan ahmad baiji dad'in yanayin da yaga sumayya ba ammah dan yakwantar ma da d'an uwannasa hankali yace kayi hak'uri kasan fa sumayya yarinyace kuma ko ba ma hakaba yaran yanzu addu'a kawai yakamata mucigaba da yi musu Allah yatsare mana su, insha Allahu da ta samu miji aurar da ita zamuyi tunda shi wanchan shashashan ya yi ma kansa.

Murmushi kawai sultan abbas yayi ba dan ya amince da maganar d'an uwannasaba haka yadaure suka gama hira sannan sukayi sallama kowa yawuce turakarsa.

Sultana sadiya da take zaune a parlour ganin mijin nata tayi kamar anjefosa yanayinsa da tagani saida tagirgiza, cikin 6acin rai yace da izinin wa wacchan yarinyar tafita?

Gaban sultana sadiya saida yafad'i rasa abinda zatace masa tayi.

Tsawa yadaka mata yace ba tambayarki nakeba!!!
rikicewa tayi tace am daman.....katseta yayi yace wlh kikiyayeni inba hakaba zan sassa6a miki, ashe har kwashe-kwashe tayi min cikin gida batare da saninaba daga ganin wacchan yarinyar da suke tare babu alamun tarbiya a tare da ita dan haka bazan d'auki wannan dak'ik'ancinba.

Ahankali cikin rarrashi tace Allah yahuci zuciyanka dan Allah kayi hak'uri.
cikin 6acin rai yace yanzu ina sumayyar take?
Nuni tayi masa da room d'inta tace tana ciki.

Wucewa yayi yanufi part d'in sumayya tura k'ofar yayi ammah yajita a rufe gam da alama key akasanya mata, har zai yi knocking sai kuma yafasa dan haka yawuce yatafi part d'insa.

Sultana sadiya da take zaune taga wucewarsa ajiyar zuciya tasafke tace Allah ya taimakeni, suma k'ila sunganshi saisa suka rufe d'akin.

Tana cikin tunanin kawai sai ganinsa tayi ya fito rik'e da spire key a hannunsa,,,zaro ido tayi tace ranka yadad'e me zakayi haka?
Wata uwar harara da yawatsa mata yasa ba shiri taja da baya.



_Comment_
     *nd*
_Share_



_Sis Nerja'art✍🏻_
[5/3, 9:53 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_*Masoya nagode sosai da addu'o'inku agareni, gaskiya nayi farin ciki da irin kulawar da nasamu da kiran da kuka dinga yimin, ban ta6a tunanin ina da masoya irin hakaba saidai ince Allah yabar k'auna, sis nerja'art tana sonku over*_

        ❤❤❤

_~Masu tambayata yarima suhail daga farko ta pc,  please kuyi hak'uri insha Allahu mun kusa gamawa za'a baku document idan muka gama~_

*PAGE* 6⃣4⃣

K'ok'arin bud'e d'akin yashiga yi, yana bud'ewa mutuwar tsaye yayi lokacin da ya hangosu tsakiyar gado lullu6e cikin blanket, gabansa ne yayi wani irin mummunan fad'uwa ganin abun yake kamar a mafarki murza idanunsa yayi yabud'e yagadai a zahirine nan yafara rafka salati.

Sumayya jin muryar abbanta yasa tadawo hayyacinta nan tarikice tafito daga cikin bargon, cikin sauri yajanye idanunsa daga kallonsu hawaye suna malala daga idanunsa.

Ganin abbanta yasa tasaki wata irin razanannar k'ara tare da rufe duka jikinta da bargon tana kuka cike da tashin hankali.

Zinat ma lek'o kanta tayi daga cikin bargon cike da tsoro da firgita.

Sultan abbas girgiza kansa yacigaba da yi cike da takaici yana salati muryarsa tana rawa yace sumayya kin cuceni kin zalunceni ni a matsayina na mahaifinki ba irin wannan tarbiyar nabakiba Allah yasani, wlh baki isa kisani jin kunya a gaban ubangijinaba.

Cikin sauri sultana sadiya tanufo d'akin dan ta d'auka dukansu yakeyi da tajiyo k'arar sumayya cewa take haba Alhaji dan Allah kayi ha....maganarce talak'afe a bakinta lokacin da ta hango su sumayya a wannan yanayin wata irin k'ara tasaki tare da zama dirshan a k'asa tana wani irin kuka, nuna sumayya tayi da yatsa tace sumayya abinda kikeyi kenan? abinda kika za6ar ma rayuwarki kenan? nashiga ukku ni sa'adiya mekikeso duniya tad'aukeni? K'ara sautin kukanta tayi tace wlh daman tunda naga wannan munafukar k'awartaki hankalina bai kwanta da itaba, kaicona ni sadiya wannan wace irin *K'ADDARA CE* tafad'amin.

Sumayya ko inba kukaba ba abinda take tsanar zinat ce da mummunar rayuwar da tayi takamata a karo nafarko da taji ta yi nadama akan abinda take aikatawa, girgiza kai tashiga yi tace wlh ba laifina bane kuyafe min abba, ummah kiyafemin wlh bazansakeba nadaina daga yau.

Kallon zinat tayi da take k'udundune tana zare ido gabad'aya jikinta rawa yake, cike da tsanarta sumayya tace Allah ya isa zinat kin 6ata min rayuwata wlh na tsaneki na tsaneki.

Sultana sadiya dak'yar tasamu tamik'e cikin kuka tanufi inda sumayya take tace wlh kasheki zanyi sumayya inhuta da wannan bak'in cikin naki.

Sultan Abbas ne yajanyota cikin d'aga murya tace ni kasakeni ina amfanin haihuwar d'iya irin sumayya? Kaduba kaga mugun abinda take aikatawa.

Sultan Abbas share hawayen fuskarsa yayi tare da kallon sumayya yace kinyi farin ciki kin saka iyayenki kuka kin kyauta ni bazan miki komai ba tunda ke babbace ba yarinyaba kinsan daidai ammah ni ban haifi d'iya irinkiba dan haka kije na sallama ma duniya ke, sannan dole memartaba yasan da maganar nan,,,,yana fad'in haka yaja sultana sadiya suka fita daga d'akin.

Sumayya cigaba tayi da kukan tana k'wala ma iyayenta kira ammah ahaka suka fita suka barta, juyowa tayi takalli zinat tace kin cuceni kin 6atamin rayuwa kin kashemin aure munafukar banza 'yar iska wlh dole yau asirinki yatonu dan ba nawa bane kawai yatonu.

Zinat cikin kuka tace sumayya dame kikeso inji da abinda yasameni ko da wulak'ancinki? Ni yanzu bari intashi intafi

'Daga hannu sumayya tayi tasharara mata mari tace babu gidan ubanda zakije dole ne kema kizauna duk abinda za'ayimin kema ayi miki.
Cikin kuka zinat tace wlh baki isaba wannan tsakaninkine da iyayenki ni babu ruwana.

'Daga hannu sumayya tayi tak'ara d'auketa da mari cike da jin haushi zinat tace kam ni kika mara? Nan tad'aga hannu itama tarama sai dambe yakaure a tsakaninsu dukan juna suka shigayi.
Daga k'arshe safkowa akayi daga saman gadon aka cigaba da dambe, duk suka fashe ma juna baki, sumayya samu tayi tayada zinat k'asa tabi tadanne tacigaba da bugunta ta ko'ina, kuka kawai zinat take tanaso takwaci kanta.
Sumayya cikin kuka take cewa wlh baki isaba dole kizauna munafuka, yadda asirina yatonu toh dole kema naki yatonu..tana fad'in haka tatadata taje tajanyo doguwar rigarta tasaka.

Sultan Abbas koda yafito zama yayi saman kujera tare da dafe kansa takaici da bak'in ciki duk sun cikasa, sultana sadiya na a gefensa k'asa zaune tana ta rusa kuka itama cike da takaici da bak'in ciki, gabad'aya akarasa me lallashin wani

Wayarsa ce datafara ruri yajanyo ganin mahaifinsane yasa yayi picking muryarsa tana rawa yai sallama.

Jin yanayin muryarsa saida hankalin memartaba yatashi yace abbas ya najika haka ko bakada lafiya ne?

Ahankali yace a'a ranka yadad'e,
memartaba cewa yayi toh kazo yanzu akwai sak'on da nakeso inbaka zaka kaima governor,
Shuru Sultan Abbas yayi dan baima san abinda memartaba yake cewaba.

Daga chan 6angaren memartaba cewa yayi abbas ko bakada lafiya ne?

Girgiza kai yashigayi kamar yana a gaban memartaba sannan yace ranka yadad'e kagafarceni bansan ya zanyi da rayuwataba wannan wace irin masiface.

memartaba kwata-kwata bai fahimci inda yadosaba yace wai abbas me yake faruwa? sai a lokacin yajiyo sautin kukan sultana sadiya,,,cike da tashin hankali memartaba yace meyake samunku haka? Mutuwa akayi ko me?

Cikin karyayyar zuciya yace ranka yadad'e ko d'aya, kataimaka kazo kaga halin da muke ciki da idanunka.

Toh yanzu dai gamunan zuwa kasaurareni.
Toh kawai yace sannan yakashe wayar.

Sumayya fitowa tayi daga d'akin tana sand'a wuri tasamu daga chan nesa da iyayenta tazauna k'asa cikin kuka tace dan Allah kuyafemin abbah wlh na tuba bazan k'araba.

Wata uwar harara sultan abbas yawurga mata.
Sultana sadiya ko rarrafawa tayi ta isa inda sumayya take tarufeta da duka tace kin cuceni sumayya ban ta6a sanin wannan rayuwar kike aikatawaba wlh sai na kasheki kowa yahuta.

memartaba saida yakira sultan ahmad yace suhad'u gidan abbas sannan yamik'e yakalli dada da tuni ta shirya hankalinta a tashe tana jiransa sutafi, yace muje.

Koda suka fito kusan a tare suka shiga gidan da su sultan ahmad da ummi, suna shiga parlourn ganin sultan abbas sukayi ya dafe kai inda sultana sadiya take dukan sumayya tana kuka.

Dada da ummine sukayi saurin isa wajen suka rik'e sultana sadiya.
Dada tace sadiya menene haka kikeyi sai kin kasheta?
Cikin kuka sultana sadiya tace ranki yadad'e kubarni inkasheta kowa yahuta wlh sumayya batayiba ina ma ace ba jininabace.

Sultana bilkisu ce tayi saurin toshe mata baki tace haba sadiya menene haka kike cewa? Yakamata kidawo hayyacinki.

Gyad'a kai sultana sadiya tayi tace kune zakuga kamar banda hankali ammah ni nasan abinda nake kubarni kawai.

Memartaba da gabad'aya an d'aure masa kai waje yasamu yazauna sannan yace kowa yasamu waje yazauna ayi magana Cikin kwanciyar hankali.

Gabad'ayansu k'asa suka zauna, memartaba da dada ne kawai saman kujera,  sumayya ko tana daga chan nesa da su tana kuka.

Kallonsu Memartaba yayi d'aya bayan d'aya sannan yace kun d'aure mana kai dan gabad'ayanku kuka kukeyi ya kamata kufitar da mu bak'in duhunnan da kuka sakamu a ciki

Sultan abbas share hawayen fuskarsa yayi sannan yanuna sumayya yace ranka yadad'e kaduba kaga wai wannan d'iyar cikinace ammah kwata-kwata bata d'auko halinaba ina amfanin haihuwar d'iya irinta me bak'in hali.

Dada zuba masa ido tayi sannan tace kuyi mana bayani yadda zamu fahimceku mana.

Cike da takaici yashiga girgiza kai tare da runtse idanunsa sai chan yabud'e.

memartaba ne yace muna saurarenka.

Muryarsa tana rawa yace ranka yadad'e gatanan wai jininkace take neman mace 'yar uwarta.

Gabad'ayansu cikin rashin fahimta suke kallonsa

Sumayya da take raku6e gefe k'ara sautin kukanta tayi

Dada ce tace kayi mana bayani yadda zamu fahimta.

Nan yakwashe yadda yashiga yaganta da k'awarta yafad'a musu.

Gabad'aya labarin ya girgizasu nan aka fara salallami.

Dada batasan lokacin da tazamo k'asaba daga saman kujerar da take zaune, kallon sumayya tayi tace Allah wadai wlh bakiji dad'in rayuwarkiba ashe hakanan nake ganinki kamar mutuniyar kirki nan ko 'yar banzace,,,tak'arashe maganar tare da fashewa da kuka.

Memartaba idan ransa yayi dubu toh ya 6aci duk sanyin A-C d'in da take d'akin ammah zufa yake, yana kallon sumayya  cike da mamaki, sannan yace sumayya abinda kika za6arma kanki kenan abinda ubangiji yaharamta, laifin da Allah ya kife mutunen annabi lud'u saboda shi, kina zuwa islamiyya kin karanta kuma kinsani saidai bakiyi amfani da saninkiba shin mancewa kikayi da fad'ar ubangiji da yace ya halitta mana mata dan musamu nutsuwa daga garesu, haka kuma yahalitta maza dan kuma mata kusamu nutsuwa daga garesu, shin hakan da kikeyi ke kina ganin shine daidai agareki? Rayuwar da ko dabbobi basu irinta, wlh baki gani dabba tana neman jinsinta, Ko kinsan makomarki idan kika koma ma mahaliccinci?

Girgiza kai sumayya tashiga yi cikin kuka har muryarta ta fara dishewa tace kuyafemin wlh na daina zinat itace ta6ata min rayuwa da ace ban amince ma zinat ba a matsayin k'awata da hakan bata kasance da ni ba.

Murmushi memartaba yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace tashi kizo min da k'awartaki

Mik'ewa tayi jiki ba k'wari tanufi bedroom d'inta, tana shiga tatarar da zinat ta had'a komai nata, cike da tsanarta sumayya tace munafuka alguguma babu inda zakije kizo memartaba yana nemanki.

Cike da tsoro zinat tadafe k'irji tace eyeh na'am.
Harara sumayya tawurga mata tace dallah kizo mutafi ko yanzu asa afiddoki.

Ai zinat cikin sauri tawuce tabi bayan sumayya, suna fitowa parlour nan ta ida tsurewa tsaye tayi tana binsu da kallo cike da tsorata.

Sultan ahmad ne yadaka mata tsawa yace bazaki zaunaba?
Cikin sauri tazube k'asa jikinta yana kakkarwa.

Memartaba kallonsu yayi d'aya bayan d'aya yajinjina kai yace toh wanene mijin wacece matar?

Kuka kawai suke aka rasa me amsawa a cikinsu.
Dada ce cikin 6acin rai tace dan ubanku ba tambayarku akeba ko sai ansa dogarawa sun tambayeku?

Sumayya rage sautin kukanta tayi cike da nadama tace wlh duk abinda na aikata zinat ce silah, ita ce silar mutuwar aurena, ita tahanani inyi ma mijina biyayya.

Gabad'ayansu salati suka saka, dada tace kar dai kice min yarima baida laifi acikin sakin da yayi miki.

'Daga kai tayi tace eh baida laifi wlh duk abinda nafad'a muku k'aryane, yarima yana k'ok'arin kyautatamin wannan ce take hure min kunne.

Gabad'ayansu saida maganar Sumayya tarikitasu sultana sadiya cikin kuka tace wlh sumayya banda abinda zance miki saidai ince kije da halinki duniya zata koya miki darasi.

Dada ko mik'ewa tayi tanufi wajen sumayya tahauta da duka tana fad'in sumayya kin cuceni kin rabani da jikana kin had'ani da shi kinsa nad'aura masa karan tsana, bazan barkiba dole kema yau kibar gidannan.

Sultana bilkisuce tazo tajanye sumayya da takasa tashi, cikin muryar kuka tace narok'eki dada kiyi hak'uri kibarta, dada girgiza kai tashiga yi tace ya akeso inyi ina zanga jikana?

Rik'o hannunta sultana bilkisu tayi taje tazaunar da ita tace kiyi hak'uri dada duk inda yarima yakasance yana cikin k'oshin lafiya.

Memartaba da yake binsu da kallo sai a lokacin yayi magana yace kaicona ina ma ace naba yaronnan dama yafad'i ta bakinsa, tabbas 6acin rai baiyiba kamar yadda zartas da hukunci cikin fushi baiyiba.

Sumayya kin zubarmin da k'ima da daraja a cikin masarautata kin rugazamin duk wani farin cikina na rayuwa, kin rabani da jikana da nafi so a rayuwata.

Sumayya tsagaitawa tayi daga kukan da take tace kuyafemin wlh *nayi nadama*

Jinjina kai Memartaba yayi yace sumayya kenan dole ku amsa hukuncin abinda kuka aikata kamar yadda nake zartas ma da sauran al'ummah dan haka zansa ayi muku bulala tamanin tamanin

Murmushi sumayya tayi tace indai har haka zaisa insamu sauk'in abinda na aikata toh na amince.

Sultan Ahmad ne yace ranka yadad'e yakamata a sassauta musu.

Girgiza kai Memartaba yayi yace wannan shine adalci nan yajanyo wayarsa yakira wani amintaccen dogarinsa sahalu,
ko da yazo nan memartaba yace ashiga da su sumayya ciki ai masu bulala tamanin tamanin, kasa tashi dogarin yayi dan jin maganar yayi kamar ba daidai yajiyoba, saida memartaba yace umurni nabaka kuma amana dan haka banda ragi,
cike da girmamawa yace toh ranka yadad'e.

Nan aka shiga da su sumayya cikin d'akinta dan gudun kar wasu sugani, sumayya tafara kwanciya dan ita bata tsorata da bulalar da akace za'ayi mataba ita dai burinta ubangijinta da iyayenta suyafe mata, bulalar farko wata irin k'ara tasaki koda akan adalci yayi musu ba kamar wadda za'ayi ma namijiba su ya d'an safsafta musu saboda matane, bai kyaletaba saida yayi mata tamanin tun tana iya motsi har takasa daga k'arshe sumewa tayi ahaka aka gama tana a sume, sannan yadawo kan zinat itama tana ihu da hargagi ahaka aka gama aka barta kwance bata iya motsin kirki.

Memartaba gudun kar suji k'ara yasa aka kunna tv tare da cika volume ammah duk da haka sunaji sama-sama, ummi, dada, sultana sadiya kuka kawai suke ahankali cike da takaicin abinda sumayya ta aikata

Bayan dogarin ya fito nan yatabbatar ma da memartaba ya yi kamar yadda ya umurcesa nan memartaba yasallamesa yatafi.

Sawa yayi aka rage volume sannan yakallesu cike da damuwa yace yanzu ya duniya zata d'aukeni? Da wane suna za'a kirani? Innalillahi wa'innah ilaihiraji'un wannan wace irin *k'addara ce* yanzu duk mutuncina da darajata sun zube a idanun mutane

Sultan abbas cike da damuwa yace ranka yadad'e ni kaina narasa ya akayi ina zaune da sumayya ammah bansan abinda take aikatawa ba, kokuma ni k'arani kan waccan uwar banzar da akodayaushe take tare da ita ammah batason laifinta sannan ace batasan duk wani motion d'in d'iyartaba toh wannan wace irin soyayyace takeyimata, wannan ba so bane haukane tunda baki iya tarbiyar da d'iyar cikinki dan haka daga ke har ita kutafi kuban waje bana buk'atarku a cikin rayuwata.

Sultana sadiya k'ara fashewa tayi da sabon kuka tace nashiga ukku idan karabu da ni ina kakeso inje inji dad'i bayan banida kowa bayanku dan Allah kayi hak'uri kayafe min wlh bansan sumayya tana wannan mummunar halayyarba.

Cikin d'aga murya sultan ahmad yace kai miye haka kakeyi idan rai ya 6aci ai baidace zuciya ta6aciba yakamata kadawo hayyacinka ita kuma sadiya miye nata laifin aciki? Itada ba ita tayimakaba shine zaka had'a da ita?

Girgiza kai sultan abbas yashigayi yace kubarni nikad'ai nasan abinda nakeji su dukansu banason ganinsu.

Memartaba jinjina kai yayi yace babu inda zasuje, sannan yakalli sultana bilkisu yace jeki kigano min su sumayya.

Mik'ewa sultana bilkisu tayi cikin sauri tanufi part d'in sumayya tana shiga yanayin yadda taga sumayya saida tatsorata dan batada banbanci da matatta, zinat ko numfashi take fitarwa sama-sama tana jan jiki daga kwancen.

Cikin sauri ta isa inda sumayya take tashiga jijjigata ganin bata motsi yasa tamik'e taje tad'ebo ruwa tamakaka mata, wani dogon numfashi sumayya taja ahankali tashiga motsa hannunta nan hawaye suka shiga malala daga idanunta, ahankali tabud'esu tasafke akan ummi da itama take hawayen, muryar sumayya ciki-ciki tace ummi kice min mafarki nake ba gaske bane, wlh ummi nayi nadama nadaina kuyafemin.

Ummi rungumo sumayya tayi a jikinta tace shikenan sumayya yanzu dai bari ingasa miki jikinki kinga duk ciwone.

Murmushin k'arfin hali sumayya tayi tace ummi ciwon da nakeji a zuciyata yafi radad'in bulalarnan dan Allah kitayani ba su abbah hak'uri.

Ummi sharemata hawayen fuskarta tayi tace kar kidamu yanzu dai muje kifara gasa jikinki,,,,haka ummi taje tahad'a mata ruwan d'umi ita tataimaka mata tagasa jikinta tayi wanka sannan tashiryata takwantar da ita saman gadonta saboda jikinta yad'au zafi sosai.

Juyowar da ummi zatayi nan taga zinat tana d'aukar kayanta tana bin bango dakyar take tafiya har tafita daga d'akin.

Ai tana fitowa parlour tacikaro da su memartaba rikicewa tayi tasaki jakkarta tare da duk'awa tace dan Allah kuyafemin wlh natuba bazan k'araba.

Murmushin k'arfin hali memartaba yayi yace dole ki amsa hukunci tunda kece silar lalacewar sumayya, kuma kece silar rugujewar duk wani farin ciki na masarautar nan dan haka yanzu zansa akaiki gidan yari kid'an kwana biyu.

Zinat sake fashewa tayi da sabon kuka tace dan Allah kuyi hak'uri wlh ba zan sake dawowaba.

Memartaba wayarsa yad'auko yai kira, cikin mintuna kad'an saiga wani k'aton barde yashigo nan memartaba yace atafi da zinat gidan yari duk wani aiki me wahala asata kar a sassauta mata .

Cike da girmamawa yace angama ranka yadad'e, nan yatusa zinat gaba tana kuka tana rok'onsu ammah ahaka aka fita da ita babu wanda yasaurareta.

Sultana bilkisu fitowa tayi tashaida musu halin da sumayya take ciki ammah kowa shareta yayi yace baruwansa, dada ma cewa tayi tamutu mana ina ruwan wani, sultan ahmad ne kawai yatausaya mata nan yakira family doctor d'insu.

Memartaba da takaici ya isheshi mik'ewa yayi batare da yayi ma kowa maganaba yawuce yaficce nan dada tabi bayansa.

Ganin haka yasa sultan abbas ma cike da 6acin rai yatashi yawuce part d'insa, sultana sadiya ma tashi tayi tabi bayansa dan gabad'aya hankalinta atashe yake addu'a take cikin ranta akan Allah yasa kar aurenta yamutu.

Sultan ahmad da sultana bilkisu ne suka cigaba da zama har doctor yazo yaduba sumayya yabata drugs tasha, nan sultan ahmad yatafi yabar sultana bilkisu wajen sumayya tana cigaba da kula da ita tare da kwantar mata da hankali har dare sannan tafara shirin komawa turakarsu, sumayya ba dan tasoba haka tahak'ura tabar ummi tatafi.

bayan ummi ta tafi nan tadasa wani sabon kukan cike da nadamar abinda ta aikata, ji take ina ma tabud'e ido taga duk a cikin mafarkine komai yafaru saidai inaa *k'addara ta riga fata* haka tayita juyi tana kuka har wajen k'arfe d'ayan dare nan tatashi dakyar jiki ba k'wari taje tad'auro alwallah akaro na farko a rayuwarta da tafara tunanin yin nafila, nan taita sallah tana neman yafiyar ubangiji har wajen k'arfe ukkun dare, tana zaune a saman darduma tana lazumi ahaka bacci yai awon gaba da ita.

Sultana sadiya koda tabi sultan abbas part d'insa tana ganin ya zauna bakin gado nan tazo tatsugunna gabansa cike da nadama, cikin kukan tace Dan Allah kayafemin wlh zan canza rayuwata, duk abinda na aikata wlh akan kuskure da *SON ZUCIYA* na aikatasa, tabbas a yanzu nasan ba gata bane nanuna ma sumayya, dan Allah kataimaka kayafemin ba dan halinaba ko nasamu d'an sauk'i acikin raina.

Murmushi sultan abbas yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace sadiya kin aikata babban kuskure wanda tabonsa ba zai ta6a gogewaba a raina, na aureki ina gani kamar zaki taimaka min wajen ganin mungina rayuwarmu da ta 'ya'yanmu cikin tsafta, ashe bahaka bane ni kad'ai nake haukana ke kin riga kin tsara taki rayuwar, toh me yayi saura a yanzu? Me zakice min?

Cikin kuka tashiga girgiza kai tace kayi hak'uri wlh tsautsayine insha Allah yanzu zan gyara.

A wulak'ance yakalleta yace kar ma kigyara dan ba matsalata bane dan haka kitashi kifita kiban waje tun kan ranki ya6aci.

Cikin sauri sultana sadiya tamik'e tare da cewa Allah yahuci zuciyanka sannan taficce tabar d'akin tana waiwayensa.

Memartaba koda yakoma turakarsu cike da tashin hankali tare da nadamar abinda yayi ma yarima suhail maganganun da yayine akansa yadinga dawo masa a k'wak'walwa, jiyake ina ma ace ya tsaya yai bincike kafin yakori jikansa dayafi k'auna a rayuwarsa Memartaba harda 'yar k'wallarsa, dada ita kanta koda tana cikin tashin hankali ammah haka tadanne tashiga lallashin mijin nata dan soyayi yaje yafara neman yarima a lokacin, dakyar tasamu taja ra'ayinsa yafasa zuwa dan darene,

A 6angaren ummi ma koda takoma part d'insu kuka taci sosai har sultan ahmad yashigo yatarar da ita, cike da tausayinta yazauna gefenta d'ago kai tayi takallesa cikin kuka tace kagani ko suhail d'ina baida laifi dan Allah kasa baki memartaba ya amince sudawo gida.

Rungumota yayi jikinsa cikin lallashi yace sultana kikwantar da hankalinki suhail zai dawo agaremu tunda baida laifi a ciki, na tabbata memartaba zai sa anemo masa shi dan shi kansa yana cikin damuwar rashin suhail.
Kicigaba da addu'a kinji ko?
'Daga masa kai tayi alamun eh, nan yacigaba da kwantar mata da hankali daga k'arshe suka kwanta.

Gabad'aya family d'in babu wanda yasamu yayi baccin kirki dan kowa hankalinsa atashe yake.



_Comment_
      *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_[5/3, 9:53 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

*PAGE* 6⃣5⃣

Asubar fari sumayya tafarka koda daman ba wani baccin kirki bane tayi, alwallah taje tad'auro tazo tagabatar da raka'atanil fijir sannan tazauna tayi ta tasbihi da istigfari kafin atayar da sallah.

Bayan ta gama sallah alqur'ani tad'auko tashiga karanta abinda ta iya acikinsa har saida gari yai haske sannan tayi addu'a takoma takwanta ammah bacci yace d'aukarni inda kika barni, haka tayita juyi ga baccin tanaji ammah ba dama, saidai hawaye kawai da suke fita daga idanunta.

A ranar haka tawuni cikin d'akinta bata fitaba saboda kunyar iyayenta da takeji, ko breakfast batasamu tayiba koda tana jin yunwa dan rabonta da abinci tun jiya da rana.

A 6angaren memartaba ko tun dasafe yatura aje abinciko masa yarima duk inda ake tunani za'a gansa anje babushi har gidansa da yagina saida akaje ammah babu labarinsa har marece yayi ana nemansa  sannan daga baya akazo aka shaida ma memartaba.

Memartaba baiji dad'iba cikin daren har so yayi yafita dakansa yak'ara bincikawa ammah su sultan ahmad suka bashi baki dak'yar sukasamu yahak'ura.

Sumayya ko sallah ce kawai take tashinta daga saman gadonta cikin d'an k'ank'anin lokaci duk tatsure tarame kamar ba itaba, chan wajen marece ummi tashigo ganin sumayya a wannan yanayin saida tatausaya mata nan tasa aka kawo mata abinci dak'yar tasamu tad'anci kad'an sannan tak'ara yi mata nasiha da wa'azi, sumayya kuka tayi sosai sannan tace ummi dan Allah kuyafemin wlh bazan k'araba, sharrin shed'anne nadaina, k'ara sautin kukanta tayi tace ummi ina jin tsoron had'uwana da ubangijina.

Ummi cike da jin tausayinta tashare mata hawayen fuskarta tace yauwa sumayya indai har kinyi tuba wadda bazaki koma abisa abinda kike aikatawa toh ubangiji zai yafe miki zai kar6i tubanki domin ubangijinmu mai tausayin bayinsane idan yaso yana yafe abinda yake tsakaninsa da bawansa komai yawan zunuban mutum Indai katuba toh zai yafe maka inyaso, hak'ine kawai baya yafewa dan wannan tsakanin mutum da wanda aka zaluntane, dan haka kicigaba da istigfari da yawan tasbihi tare da addu'a, sannan yanzu kitashi kije kinemi gafarar iyayenki dan suma suna da hak'i a gunki.

Rik'o hannun ummi tayi cikin dashashar muryarta da tasha kuka tace ummi kitaimaka min kirakani k'ila idan dakene zasu iya yafemin ammah idan naje nikad'ai korata zasuyi.

Shafa kanta ummi tayi tace kar kidamu sumayya bazasu korekiba insha Allahu, tashi muje ammah bazan shigaba kekad'ai zaki shiga.

Mik'ewa sumayya tayi dakyar take tafiya jiki babu k'wari sultana sadiya tana rik'e da ita sukanufi part d'in iyayenta.

Daga bakin k'ofa sultana taja tatsaya, nan sumayya tatura d'akin ahankali tashiga, sultan abbas zaune yake a parlournsa yana kallo ammah idan mutum yalura zai gane ba kallon yakeba dan gabad'aya hankalinsa yayi wani wajen daban, daga nesa da shi kad'an sultana sadiya ce ta buga uban tagumi ta tsura ma waje guda ido.

Shugowar sumayya yasa gabad'ayansu suka juyo suka kalleta daga nesa dasu kad'an tatsugunna bata damu da mugun kallon da sultana sadiya take watsa mataba, duk'ar da kanta tayi nan hawaye suka cigaba da zuba.

Ummah ce cikin fushi tace ubanmi kikazo yi mana nan? Ko sai kinga kin kashemu sannan hankalinki zai kwanta?

Girgiza kai tashiga yi, muryarta tana rawa tace ummah Abbah dan Allah kuyafemin wlh nadaina.

Munafukar banza wlh ko kitashi kifita kiba mutane waje ko yanzu insa6a miki.

Shuru sumayya tayi kamar ba da ita takeba saida sultana sadiya ta kwatsa mata tsawa sannan tamik'e jiki babu k'wari kallon iyayen nata tayi d'aya bayan d'aya sannan tafita tana kuka.

Ummi da take tsaye ganin ta fito tana kuka yasa tace sumayya basu hak'uraba?

'Daga mata kai sumayya tayi tace ummi kitaimaka muje tare k'ila insuka ganki zasu hak'ura.

Rik'o hannunta sultana bilkisu tayi tace kar kidamu yanzu dan suna cikin fushine kibari ak'ara koda kwana biyune sai kik'ara komawa yanzu muje kikwanta kihuta.

Girgiza kai sumayya tayi cikin muryar tausayi tace ummi dan Allah zanbiki part d'inki inzauna tunda wajenkune kawai nake samun sauk'i.

Murmushi ummi tayi tace shikenan sumayya muje ai da nan da chan duk d'ayane, cikin jin dad'i sumayya tayi ma ummi godia sannan sukaje part d'inta tahad'a kayanta suka tafi.

Room d'in da rahama tazauna nab taza6a aka shigar mata da kayanta, bayan ta yi sallah gado tahau takwanta nan tashiga rama baccin da ake binta.

Ummi bata barinta tana zama ita kad'ai janyota take sufito parlour suzauna takunna musu kallo, daga k'arshe malami tasamo mata yake zuwa yana koyar da ita littafan addini duk bayan sallar magrib.

Nan da nan sumayya tacanza takoma so silent dan magana ma bata dametaba bare fita babu inda take zuwa indai bata room d'inta toh tana tare da ummi, idanuwanta sun wani k'ank'ance saboda yawan kuka dan kuka kawai takeyi tasamu sauk'in zuciyanta ganin da take itace silar rugujewar duk wani farin cikin family d'insu, ga su yarima da take ganin ta zalunta, kullum addu'arta d'ayace Allah yabayyanasu ko tasamu tarok'i gafararsu.
su kansu ma'aikatan gidan saida suka dinga mamakin sauyin da sumayya tayi.

Memartaba ko badan komai yakyale sumayya ba sai dan ya fiso sai yarima ya dawo yayanke mata hukunci da kansa dan aganinsa hakan shine daidai.
a yanzu tare dashi da 'ya'yansa ake fita neman yarima idan suka fita tun safe basu dawowa sai dare, wasa-wasa duk inda ake tunani za'a gansa anje ammah babushi babu dalilinsa saida akayi sati guda sannan yasa anayi masa safka tare da addu'a akan Allah yabayyanasa.

Gabad'aya memartaba ya fita hayyacinsa dan ko abincin kirki baida lokacin zama yaci, dada ita kanta batada buri sai nason ganin yarima.

Su ko iyayen gayya ba a magana dan danne zuciyarsu kawai suke ammah basuda buri da yawuce suga d'ansu, dan ita kanta ummi kusan kullum sai ta kira number d'in da yarima yakirata da ita but switch off take, tasha ta6oye a part d'inta taci kukanta, tana danne damuwartane saboda 'ya'yanta da sumayya.

Dan rahama saida ummi  tataka mata burki sannan tadaina zuwa gidan, shaheed kullum baida aiki sai lallashinta dan gabad'aya tarikice masa koda shima yana cikin damuwar rashin abokinsa.

ita ko husna daman ba gwanar zuwa bace koda ma tayo ma ummi waya tace zatazo toh hanata zuwa ummi take kan dole suke hak'ura.


Memartaba yau tunda yatashi da wani irin zazza6i yatashi hankalin kowa saida yatashi anso akira masa family doctor ammah yahana, chan zuwa anjima tun yana daurewa saigashi yakasa daga k'arshe saida zazza6in yakwantar da shi, wasa-wasa sai ciwon ciki, gabad'aya saida hankalin kowa yatashi dan ko abinci baya yadda yaci, dakyar aka samu ya amince akakira family doctor d'insu yadubasa.

Da family dr yazo yadubasa maganin zazza6i yabada sannan yace dole sai anje anyi masa scanning anga menene yake causing d'in ciwon cikin dan cikin har d'an kumburi yafara.

Koda akaso memartaba ya amince aje k'iyawa yayi yace shi ba inda zaije ai Allah yana sane da halin da yake ciki sucigaba da yi masa addu'a kawai in da rabon yatashi toh zai tashi, shidai burinsa suje sucigaba da bincika masa yarima.

Nan fa hankalin kowa ya ida tashi aka shiga lallashinsa akan ya amince aje, ita kanta sumayya hankalinta ya tashi sosai dan wajen ummi takejin komai taso taje taganosa ammah ummi tace a'a kar tatafi saboda gudun kar wata matsalar takunno kai, su rahama ma kusan kullum yanzu sai sunzo dubasa ummi da taga suna niyar zama sudad'e sai tahad'e fuska kan dole suke tashi sukoma gidajen mazajensu.

Ita kanta sultana sadiya gabad'aya tayi sanyi sosai dan kowa saida yai mamakin sanyin da tayi, dakyar tasamu mijinta yasafko daga fushin da yake da ita shima saida taje tana ma dada kuka tana rok'onta sannan dada ta amince takirasa tarok'esa akan yai hak'uri sannan yahak'ura ammah ya ce kar wanda yasa baki akan sumayya,

_______________

Yarima firgit yayi yafarka daga baccin da yake nan yatashi zaune tare da dafe kansa yana furta innalillahi wa'innah ilaihiraji'un, mafarkin da yasabayi ne kusan kullum dan a yanzu mafarkin ya zame masa jiki, saidai na yau yafi firgitasa.
memartaba ne yake gani cikin wani irin yanayi yana kiransa yana cewa yadawo garesa, yau kuma har da umminsa da sauran danginsa yagani a ciki,,,,dafasa da akayine yasa yajuyo yakalli zarah, cike da tashin hankali tace meyake faruwane ko mafarki kayi?

Murmushi yasamu yak'ak'aro yayi mata, ganin idanuwanta sun cika da k'wallah yasa yajanyota jikinsa yarungume sun dad'e a haka sannan yace zarah kidaina damuwa mafarkine kawai nayi ba wani abuba.

Ajiyar zuciya tasafke tace toh ai ina lura da kai kusan kullum sai ka tashi a razane.

Kidaina damuwa dear kinsan sharrin mafarki nima daga yanzu ban k'ara damuwa addu'a kawai zan cigaba da yi incanza hannu.

'Dago kai tayi takallesa cikin ido tace promise?
'Daga mata kai yayi yana murmushi sannan yakwantar da ita tare da rufeta da blanket, rik'o hannunsa tayi, ganin haka yasa yakwanta a gefenta nan suka sakar ma juna murmushi, hannu yakai yana shafar cikinta ahankali yace oya sleep now.

Maida idanuwanta tayi tarufe, nan yazuba ma zara-zaran eye lashes d'inta ido, yanaji har bacci yad'auketa sannan yazare hannunsa yamik'e jiki babu k'wari yanufi toilet.

Mafarkin da yayi yashiga dawo masa nan yad'ibi ruwa yawatsa ma kansa tare da safke ajiyar zuciya, alwallah yad'auro sannan yafito yacigaba da yin nafila bashi yadainaba har saida aka kira sallar asuba yayi raka'atanin fijr sannan yaje yatashi zarah.

Saida yaga ta mik'e sannan yawuce masallaci.

Lokacin da yadawo gari ya d'anyi haske dan a chan Dr mu'az yabarosa shi yadawo gida.
Daga bayan zarah yaje yakwanta tare da rungumota ta baya ahaka yasamu bacci yai awon gaba da shi.

Chan cikin bacci juyin da zaiyi yaji ba zarah yalaluba bai jitaba dan haka yabud'e idanunsa, bin d'akin yayi da kallo ko'ina fes sai k'amshi ke tashi ammah babu zarah a ciki, murmushi yayi sannan yakai kallonsa ga agogon da take manne a jikin bango.

Zumbur yayi yamik'e ganin har 12pm tayi, mamakine yakamasa ganin irin baccin da yasha kuma zarah bata tashesaba cikin sauri yawuce yashiga bathroom.

Bayan ya fito tsaye yake gaban dressing mirror yana shiryawa baisan lokacin da zarah tashigoba saidai ji yayi anrungumesa ta baya, murmushi yayi tare da kallonta ta cikin mirror, itama murmushin tasakar masa sannan tace ashe ka tashi dear? Dafatan antashi lafiya my heartbeat, jawota yarima yayi tadawo gabansa saida yaja kumatunta sannan yace shine kika tashi baki tasheniba?

Ash dazafi fa,,,tafad'a tare da turo d'an k'aramin bakinta da yasha jambaki, sannan tace toh ai gani nayi jiya bakayi baccin kirkiba tunda katashi baka komaba.

Cije le6enta yayi sannan yace injiwa yace ban koma bacciba?

Fari tayi masa da ido tace ina fa kallonta lokacin da kake sallah duk farkawar da zanyi sai naganka kana sallah.

Hancinta yaja yace toh naji sarkin sa ido yanzu dai jeki kid'auko min kaya insa intafi kinga nayi late.

Kwantar da kanta tayi a k'irjinsa tare da marairaicewa tace please kahak'ura da zuwa yau tunda baku clinic kaga sai kazauna gida kahuta.

K'ara rungumeta yayi a jikinsa tare da tura fuskarsa cikin gashin kanta da yazame mata d'ankwali, jin baiyi maganaba yasa zarah tace please kar kaje.

Janyeta yayi daga jikinsa yace toh in nazauna me zakiyi min, Inma ba ciwon kai ba da zaki sanyani.

Zarah turo baki tayi tace au nimace nakesanya ka ciwon kai? Toh shikenan kayi tafiyarka inda ba a sanyaka ciwon kai,,,tana fad'in haka tajuya taficce daga d'akin.

Murmushi yarima yayi yace ina ruwan zarah sarkin rigima, nan yawuce yabud'e wardrobe yad'auko kayansa yasaka sannan yafito parlour yatarar da zarah zaune ta had'a rai.

Murmushi yayi  yazo gefenta yazauna tare da rik'o hannunta yace baby fushi kuma?

Fizge hannunta tayi tace ni kakyaleni kaje kawai chan inda ba'a sanyaka ciwon kai, daman nasani ni ba ajin aurenka bace kawai dai nayi babban kuskure da na amince ma zuciyata tafara sonka.

Yarima ido yazuba mata cike da mamaki har saida takai aya sannan yace nifa zarah dawasa nakeyi miki babu inda zanje yau ina nan gida tare da mummyn baby.

Mik'ewa zarah tayi tana turo baki tawuce zata bar wajen nan yajanyota saman cinyarsa yace please fushin ya isa haka tunda na fad'amiki babu inda zanje.
Uhm ni da nake sanya maka ciwon kai.
Oh zarah ni fa wasa nake miki yakamata kiyarda dani.

Murmushi zarah tasakar masa tare da tallabo fuskarsa da hannu biyu sannan tace idan ban yarda da kai ba habibinah toh dawa zan yarda?

Shima maida mata martanin murmushin yayi yace nima tunanin da nake kenan baby, yanzu dai jeki ki kawo min breakfast inyi dan yunwa nakeji inyaso daga baya naji da rigimar taki.

Kissing d'in bakinsa tayi tace angama ranka yadad'e yadda kakeso haka za'ayi sannan tamik'e tana tafiya dakyar tafita taje parlour tad'ebo musu breakfast sannan tadawo nan suka zauna sukayi breakfast.

Bayan sun gama bajewa sukayi saman carpet yarima yad'aura kansa saman cinyarta, turo baki zarah tayi tace ni kad'agani inba so kuke kai da babynka kukaryaniba.

'Dago kai yayi yakalleta yace shikenan tunda haka kikace bari ma kawai intashi intafiyata.

Cikin sauri zarah tagirgiza kai tace a'a kayi kwanciyarka ni da wasa nakeyi.

Dariya yarima yayi yace dad'ina da matarnan tawa matsoraciya ce toh me kikeji ma tsoro a ciki?

Zarah d'aure fuska tayi tace ai dole inji tsoro saboda 'yan matan garin nan kamar mayu nasan kullum idanunsu suna a kan mijina saisa duk fitar da zakayi hankalina a tashe yake har sai ka dawo,,,tak'arashe maganar kamar zatayi kuka.

Da mamaki yazuba mata ido yana kallonta, ganin hawaye sun fara zuba daga idanunta yasa yatashi zaune tare da janyota jikinsa yace zarah yakamata kisan abinda mijinki zai iya da wanda ba zai iyaba, ni a yanzu 'yan mata basu a gabana dan babu ma wacce ta isheni kallo.

Uhm ammah ai su kana gabansu idan su basa gabanka.

Janyeta yarima yayi daga jikinsa tare da jingine kansa a jikin kujera yamaida idanunsa yalumshe.

Ido zarah tazuba masa sannan tarik'o hannunsa ahankali tace kayi hak'uri.

Bud'e idanunsa yayi yakalleta yace zarah mekikayi min da kike ban hak'uri?

Cikin shagwa6a tace toh ai naga kamar fushi kake da ni.

Ta6e baki yayi yace no ko d'aya ni ba fushi nake da keba kawai rigimarkice naga tanaso tafi k'arfina.

Rik'o hannunsa tayi tare da marairaicewa tace toh nadaina kayi hak'uri.

Murmushi yarima yayi tare da duba agogon da take mak'ale a hannunsa sannan yace bakomai baby yanzu dai tashi muje kirakani wata 'yar unguwa, cike da jin dad'i zarah tace dagaske dear.

Murmushi yayi tare da d'aga kai.
Fad'awa tayi jikinsa tarungumesa tace nagode sosai dear wlh daman ina ta so infita inga gari dan tunda mukazo babu inda naje.

Dariya yarima yayi tare da janyeta daga jikinsa yace baby kibi ahankali kar kiji ma babyna ciwo.

Itama dariyar tayi tace ni na isa inji masa ciwo ai da sai na amsa query wajen dadynsa tak'arashe maganar tare da mik'ewa taje bedroom tacanza kaya, Cikin atamfa tafito d'inki riga da skirt sannan tayafa veil tayi gwanin kyau.

Koda tafito ido yarima yazuba mata, matsowa tayi tahura masa ido kad'an, ajiyar zuciya yasafke sannan yace koma kisanyo hijab.

Turo baki tayi tace kaduba fa babban gyalene a jikina,
Mik'ewa yayi tare da d'aukan key d'in motarsa yace tunda baki shirya fitaba ni na wuce.

Cikin sauri tarik'o hannunsa ahankali tace dan Allah kayi hak'uri toh bari insanyo.

Kumatunta yaja yace muje hakan kar inja saboda turo bakin nan yata6o k'asa, duka zarah takai masa cikin wasa nan yagoce yana dariya yace kisameni a waje, yana fad'in haka yawuce yafita.

Zarah saida tabiya tashaida ma jamila zasu fita nan tayi mata adawo lafiya sannan tazo tatarar da yarima cikin motarsa zaune yana jiranta, tunda tafito yatsareta da ido har tabud'e motar tashigo sannan yajasu batare da yayi maganaba.

Gugu yakeyi sosai da motar zarah ko titi tazuba ma ido tana kallon tsarin garin cike da burgewa, gaban wani babban Boutique yayi parking daga sama zarah taga ansa symbol d'in baby's paradise, muryar yarima taji yace bismillah madam.

Murmushin jin dad'i zarah tayi sannan tabud'e tafito, tare suka jera suka shiga ciki yanayin tsarin wajen ya burgeta sosai bin ko'ina da kallo take duk kayane masu kyau da tsada ahaka har suka haura saman step nan kuma taga kayan jarirai da na k'ananun yara, kallon yarima tayi tana shirin tambayarsa nan yasakarmata murmushi yace kiza6ar ma babynmu kaya.

Zaro ido zarah tayi tace babyn da baizo duniyaba bamusan ko namiji bane ko mace.

Murmushi yayi a karo nabiyu sannan yace kar kidamu baby duk wanda Allah yabamu munaso kuma in munsiya zamu iya ajewa ko saboda gaba.

Murmushi tayi cike da gamsuwa da maganarsa tace hakane dear, nan tafara d'iban over roll saida tad'ibi kusan kala goma sannan tad'auki kayan baby gurl kala biyar na baby boy kala biyar.
kallon yarima tayi da yazuba mata ido tace nagama, janye idanunsa yayi batare da yayi maganaba nan yacigaba da d'iban kaya duk wanda yayi masa d'auka yake saida yahad'a kusan kala talatin, trolly guda yacika da kayan baby's, zarah ko baki tasaki tana kallonsa har yagama sannan suka dawo k'asa itama yasata tad'ibi nata kayan sannan sukaje wajen payment yabiya su kud'insu nan aka kaimasa har cikin motarsa sannan suka shiga yatada suka tafi.

Yawo yayi da ita sosai yanuna mata wajaje dadama sunje pack da malls iri-iri, sayayya yayi mata sosai tun daga kayan tand'e-tand'e zuwa na amfani dan ko turaruka masu tsada yasiya mata, sai gab da magrib sannan suka dawo gida agajiye.

Bayan sallar isha'i kwance suke saman gadonsu zarah tana rungume a jikinsa shikuma yana dannar wayarsa, ahankali zarah tad'ago takallesa, yanayin yadda take kallonsa yasa yagane magana takesonyi dan haka ya aje wayar gefe sannan yace ina saurarenki dan wannan bakin naki nasan akwai magana a cikinsa.

Murmushi tayi tare da gyara kwanciyarta sannan tace tabbas hakane my heartbeat taimako da alfarma nakeso kayimin.

zubamata ido yayi batare da yayi maganaba, zarah janye idanunta tayi daga kallonsa sannan tace dan Allah kataimaka kakira min su mama mugaisa kuma kaga k'ashen watannan za'ayi bikkin Aysha.

Murmushi yarima yayi yace ai muna waya da su suna ma cewa ingaisheki bana fad'amikine saboda gudun rigimarki sannan maganar bikki kuma saidai kiyi hak'uri bazan iya barinki kijeba kuma na fad'ama su mama mun d'anyi tafiya, suma sunsan yanzu kinyi nauyi, dan haka kibari idan Allah ya safkeki lafiya sai muje kigansu.

Mamakine da bak'in ciki suka cika zarah tamarasa abinda zatace masa daga k'arshe zame jikinta tayi takwanta saman gadon tare da juya masa baya.

Shareta yarima yayi dan yasan inyace zai lallasheta a wannan lokacin rigima zatayi masa sosai, daga k'arshe mik'ewa yayi yakoma parlour yai kwanciyarsa saman kujera a nan yagama abinda zaiyi yai baccinsa.

Zarah ma saida tasha kukanta sannan bacci yai awon gaba da ita, cikin dare ko da tafarka talaluba taji babu yarima nan tatashi taduba bata gansaba dan haka tadawo parlour, ganinsa tayi kwance saman kujera yana ta baccinsa.

Zuwa tayi tazauna k'asa gefen kujerar nan tad'aura kanta saman kujerar ahaka tacigaba da baccinta.

Juyin da yarima zaiyi nan yaji abu ya takuresa, yana bud'e idanunsa da mamaki yake kallon zarah da take bacci a takure, dafe kansa yayi tare da furta oh zarah, sannan yamik'e yad'auketa yanufi bedroom da ita, yana kwantar da ita saman gado  tana bud'e ido, daga gefenta yarima yakwanta yace kedai kinason wahalar da kanki menene nakwanciya a chan.
Kanta tad'aura saman k'irjinsa tace toh ai kaine kak'i kwanciya kusa da ni bayan ka sabamin ban iya bacci sai tare da kai, kuma fushi kake da ni,
Shafa kanta yayi yace ni ba fushi nake da keba zarah kawai na d'an baki wajene kihuta.
marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace toh kadaina guje min dan Allah kayi hak'uri na daina.
murmushi yarima yayi yace shikenan zarah nadaina yanzu dai kiyi bacci sai dasafe.
k'ara shigewa tayi jikinsa tare da cewa Allah yakaimu my heartbeat.
Tura kansa yayi cikin gashin kanta yana shak'ar k'amshinsa inda hannunsa yake shafar bayanta da shi ahaka bacci mai dad'i yai awon gaba da su.



_Comment_
      *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
[5/3, 9:53 PM] Sis Naj Atu: . 👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....✔*

🎈🎈🎈
_~Happy Born day momcy sady wsh u many more years ahead nd Allah's noor🎊🎉~_
🎈🎈🎈

_*My friendy Beebah M Shehu nd my lil sis Aysha Eesho kumatso kusa yau page d'in nakune sai yadda kukeso zakuyi da shi😍👌*_

6⃣6⃣

A chan 6angaren memartaba koda yana a kwance ammah har a lokacin maganarsa d'ayace shidai yarima, ahaka yasa aka ware kud'i masu yawa yace agyara ma suhail d'insa part d'insa dan yana ji a jikinsa zai dawo garesa, kowa ya d'auka magagin ciwone har anshare maganar saida sukaga ran memartaba yana shirin 6aci sannan akasa akafara yi masa gyara.

Yanzu mulkin hannun waziri suka damk'asa dan bawani mai kwanciyar hankali a cikin 'ya'yansa, gabad'aya family d'in abubuwa goma da ishirin sun had'u sun cakud'e musu, kullum maganar d'ayace shine memartaba ya amince aje ayi scanning d'in ammah ya k'i saidai ruwan addu'o'i da malamai suke aiko masa da shi ake bashi yana sha, masallatai ko duk sallah sai sunyi ma sarkinsu addu'a dafatan Allah yatashi kafad'unsa.

Yau ma kamar kullum 'ya'yansa ne zagaye da shi daga gefensa dada ce, cike da damuwa sultan ahmad yaruk'o hannun mahaifin nasa yace ranka yadad'e kataimaka ka amince muje ayi scanning d'innan kaga gabad'aya hankalinmu atashe yake babu sauran mekwanciyar hankali dukkanmu nan a k'ark'ashinka muke burinmu d'aya shine muga kasamu sauk'i.

Murmushin k'arfin hali memartaba yayi sannan ahankali muryarsa tana fita dakyar yace Ahmad kucigaba da yi min addu'a in da rabon intashi toh zan tashi domin waraka ta ubangiji ce.

Dada fashewa tayi da kuka tace hakane ranka yadad'e ammah ai ubangiji bai safkar da cutaba saida yasafkar da maganinta dan Allah kataimaka aje asibitin kaga bamu kad'aiba hatta sauran mutane hankalinsu atashe yake.

Cikin dauriyar ciwo memartaba yace shikenan na amince muje ammah ubangiji ya gama tsara komai akan lamarinsa.

Cike da jin dad'i tare da neman gasgata kalmar da kunnuwansu suka jiye musu nan suka shiga kallon juna suna murmushi.

Sultan Abbas ne yace dagaske ya amince muje?
Shima sultan ahmad murmushi yayi yace nima kusan abinda kunnuwana suka juyo min kenan.

Dada share hawayen fuskarta tayi tace Alhmdllh yanzu kuje kusa ashirya motocin da zamu tafi da shi, asibitin suhail kawai zamuje.

Cikin jin dad'i sukaje sukasa aka shirya motoci nan aka fito da memartaba aka shigar da shi motar da aka tanada dominsa Dada kawai tashiga cikinta.

Su kuma cikin d'ayar motar suka shiga ahankali ake tuk'in duk inda aka wuce talakkawa d'aga masu hannu suke suna ma shugabansu fatan samun lafiya.

Koda suka isa Prince.S hospital, cikin gaugawa akazo aka tarbesu dan motocin kawai da suka gani yasa sukagane daga inda suke,

Dr khalil da sauran manyan likitocine tsaye akan memartaba a cikin wani k'ayataccen room suna ta bincike bayan anyi masa scanning d'in, inda shi kuma yake ta baccinsa.

Gabad'aya hankalinsu ya tashi saboda basusan yadda zasuyi sushawo kan matsalar ba nan sukayi 'yan maganganunsu.

Dr khalil ne yafito jiki ba k'wari yanufi inda su dada suke zaune, ganinsa yasa gabad'ayansu suka mik'e suna tambayarsa jikin memartaba.

Murmushin k'arfin hali yayi yace Alhmdllh dasauk'i sannan yasamu waje yazauna, ya umurcesu da suma suzauna bayan sun zauna, kallonsu Dr khalil yayi sannan yace Alhmdllh mun gano abinda yayi causing d'in ciwon cikin ba komai bane face 'yan hanjinsane da wasu suka nad'e,

Gabad'ayansu saida gabansu yafad'i sukace 'yan hanjinsa sun nad'e?

Ganin yadda hankalinsu yatashi yasa Dr khalil yad'anyi murmushi yace kar kudamu ba wata babbar matsala bace tunda daman ana samun masu shiga wannan condition d'in kuma suna rayuwa saidai ta hanya d'aya za'a bi.

Gabad'aya suka had'a baki wajen cewa ta wace hanya kenan?

Ajiyar zuciya yasafke sannan yace ta hanyar yin theatre.

Sultan abbas ne yace toh Dr indai ta hakan za'a samu sauk'i toh mu relatives d'insa mun amince ayi masa kawai.

Jinjina kai Dr khalil yayi yace abbah saidai wani hanzari ba guduba jinin memartaba ya hau sosai babu yadda zamuyi mu iya yin wannan aikin batare da jininsa ya d'an yi low ba.

Salati suka sanya cike da tashin hankali, dada kuka tasaka tace yanzu khalil babu yadda za'ayi a iya yin komai?

Cike da jin tausayinta yace ranki yadad'e kar kidamu zamu duba mugani.
Yauwa Dr dan Allah kubincika sosai.
Dr khalil yace kar kidamu ranki yadad'e zamuyi iya bakin k'ok'arinmu.
Yafuto sultan Ahmad yayi da ido sannan yamik'e yace ina zuwa.

Saida yafita sannan sultan Ahmad yamik'e yabi bayansa.

A office d'insa suka je, bayan sun zauna Dr khalil kallonsa yayi cike da damuwa yace daddy adai cigaba da yi masa addu'a dan jininsa ya hau over, kuma a wannan condition d'in da yake ciki baikamata ad'au lokaciba batare da anyi masa aikinba, ammah a yanzu zamu d'aurasa akan wasu drugs tsawon kwana ukku idan har jinin baiyi low ba toh saidai afitar da shi abroad.

Innalillahi wa'innah ilaihiraji'un daddy yashiga nanatawa cike da damuwa.

Dafe kai Dr khalil yayi kamar mai tunani sannan yace yauwa akwai wani mai irin wannan condition d'in da aka kawo mana bamuyi aikinba sai dagabaya akace mana ankaisa a wani gari wani likitane yayi masa aikin saidai ban tambayi wane gari bane ammah gaskiya ance yanzu haka mutumin yana nan lafiya lau ya warke.

Cike da damuwa sultan ahmad yace dan Allah khalil kataimaika kagano wane garine inyaso sai muje.

Murmushi Dr khalil yayi yace insha Allahu daddy zan bincika yanzu dai bari inje infara kawo drugs d'in da zai fara amfani da su mugani, Indai har akayi kwana ukkun bai safkaba sai kutafi chan.

Jinjina kai daddy yayi cike da gamsuwa da maganar Dr khalil yace Allah yashige mana gaba.

Ameen,,cewar Dr.
Sannan suka tashi suka fito tare inda sultan ahmad yakoma wajensu dada yai musu bayanin rik'esu da za'ayi tsawon kwana ukku ad'aurashi akan magani, ammah bai fad'a musu sauran bayaninba gudun kar hankalin tsohuwar tasu yatashi sosai.

Haka Dr khalil yaje yakawo drugs d'in, tun daga wajen d'akin dogarawane aka zuba suna gadinsa, sultan ahmad ne yace zai dinga kwana da mahaifin nasa ahaka su dada suka amince suka koma gida.

Kulawa sosai memartaba yake samu daga ma'aikatan asibitin ba a awa d'aya batare da anzo anduba lafiyarsaba, abinci dakyar ake samu yana d'an ci kad'an kafin yasha magani, su dada kullum suna hanyar asibitin sai dare suke komawa.

Mutanensa dadama sunzo dubasa dan ma ana hanasu shiga wajensa saboda ba aso ana damunsa dayawa.

*BAYAN KWANA UKKU*

Nan likitoci suka k'ara taruwa akan memartaba aka k'ara bincikawa ammah har a lokacin jinin nasa bai yi wani low ba saidai d'an ragewa da yayi kad'an.

Gabad'ayansu hankalinsu ya tashi, nan Dr khalil yakira sultan ahmad da sultan abbas cikin damuwa yasanar da su,

Su dukansu hankalinsu ya tashi, ganin haka yasa yace ammah Alhmdllh na binciko garin da kwararren doctor d'in yake ance min garin Abuja saidai sunce bazasu iya tuna sunansaba ammah yana aiki a babbar asibitin garin, insha Allahu inaji a jikina za'a dace idan akaje chan.

Cike da gamsuwa suka ce insha Allahu zuwa gobe zasusa ayi masu komai sukama hanya dan yanzu ma dare ne kuma sunaso suyi shirye-shirye saisa bazasujeba a lokacin.

Dr khalil yace Allah yasa adace.

Nan sukaje suka sanar ma dada akan batun zuwansu jihar abuja, saida ta jinjina ma lamarin sannan tace toh shikenan Allah yakaimu goben yanzu muzo mutafi gida muyi 'yan shirye-shiryenmu.

Koda suka koma gida kayansu suka shirya nan sultan abbas yaje yayankar musu ticket, su sultana bilkisu da sultana sadiya sunso subi aje dasu dada tace a'a subari sai daga baya sai suzo ammah yanzu in suma sunbi wa za'a barma gidan.

Haka suka hak'ura suka zauna tare da yin fatan Allah yasa adace.

Da dare koda waziri yashigo duba jikin memartaba, rik'o hannunsa memartaba yayi cikin muryarsa da bata fita sosai saboda zafin ciwo yace ga amanar gari da talakkawana nan na damk'a maka.

Rik'e hannunsa waziri yayi kwallah duk tacika masa ido yace na amsa ranka yadad'e Allah yabani ikon cikawa kaikuma Allah yabaka lafiya.

Cikin jin dad'i memartaba yayi murmushi tare da maida idanunsa yalumshe.

Wanshe kare tun dasafe motoci kusan guda goma sukayi layi suna jiran fitowar su memartaba, wajen k'arfe goma suka fito, inda su sultana bilkisu sukayi musu rakiya har airport, inda dandozon mutane suke tsaye ahaka suka shige jirgin mutane na d'ago musu hannu tare da addu'an Allah yaba shugaban nasu lafiya, saida sukaga tashinsu sannan kowa yakoma gida.

*GARIN ABUJA*
Suna isa garin nan sukatarar da motoci da shi kansa sarkin garin tsaye suna jiran isowarsu, kasancewar daman tun jiya sun sanar da shi akan zuwan da zasuyi.

Cikin karamci da jin  dad'i suka tarbesu daga nan suka d'unguma wani k'ayataccen gida da aka tanadar masu dan suzauna a ciki, sunso sufara wucewa asibitin ammah sarkin garin yace sufara zuwa su huta sannan.

Haka suka hak'ura saida sukaje suka kimtsa suka ci abinci sannan sukafito suka shiga motocin da sarkin ya aje musu aka jasu zuwa asibitin.

Koda suka isa yanayinsu kawai aka gani da motocin da suke ciki yasa aka gane daga inda suka fito, koda daman sarki kabir ya kirasu ya sanar da su akan zuwan sarkin gazban.

Tarbarsu akayi sosai inda aka wuce da memartaba a amenity, nan suka duba history taken d'in da ke cikin folder d'insa na chan garin, saida suka k'ara yi masa scanning d'in dan tabbatarwa nan kowa yai shuru.

Sultan Ahmad ne yasanar da su abinda Dr Khalil yafad'a musu akan wani mai irin condition d'in da aka ta6a yi ma theatre kuma BP d'insa yayi high.

Jinjina kai MD Dr Muhammad bashir yayi sannan yace shikenan zanje intuntu6i Dr S domin nasan shine kawai zai iya hakan.

Cikin jin dad'i sukayi masa godia nan yatashi yanufi office d'in Dr suhail da baisan wainar da ake toyawaba.

Lokacin da M-D yashiga zaune yatarar da shi yana research a cikin system d'insa.

Nan yamik'a masa hannu suka gaisa, bayan sun gaisa nan yake sanar da shi akan zuwan wasu da irin condition d'in da patient d'in yake ciki.

Shuru Dr suhail yayi na d'an Lokaci sannan yace zan iya ganin file d'in patient d'in?

Nan Dr muhammad bashir yayi waya, ba a wani dad'eba saiga wani Dr hannunsa rik'e da file nan yabud'o yamik'a ma Dr suhail, saida gaban Dr suhail yafad'i ammah yadake yana karanta history taken batare da ya duba sunan me file d'inba.

Saida yagama karantawa nan gabansa yai wani irin fad'uwa lokacin da yaga sign d'in Dr khalil, cikin sauri yajuya bayan folder d'in, baisan lokacin da saki folder d'inba lokacin da yaga sunan da yake jikinsa, nan gabansa yacigaba da dukan ukku-ukku tashin hankali yabayyana k'arara a fuskarsa.

Bai san MD yana masa magana ba saida Dr muhammad bashir yata6osa tare da cewa Dr S lafiya.

Ajiyar zuciya suhail yasafke cike da damuwa yace ba zan iyaba kusami wani yayi.

Kallonsa Dr muhammad bashir yayi cike da damuwa yace ammah ai an tabbatar min da cewa kaine kata6a yi ma wani mai irin condition d'in.

Dafe kansa yarima yayi yace ni ba zan iyaba kakyaleni.

Cikin d'aga murya Dr muhammad bashir yace haba Dr suhail baidace kace haka ba bayan aikinka ne kuma inaji a jikina zaka iya.

Mik'ewa suhail yayi tare da kife system d'insa yace bazan iyaba nafad'a maka!.

Cikin jin haushi shima yamik'e yace zaka iya man, dan haka umurni nabaka a matsayina na shugabanka dole kacika umurni na.

Wani irin kallo suhail yawurga masa yace shugaba kuma?

Murmushi Dr muhammad bashir yayi yace eh shugaba kaga indai kanaso kacigaba da aiki a k'ark'ashina dole sai ka bi umurni na.

Cikin d'aga murya suhail yace ank'i abi umurnin naka, kai bari kaji baka isa kasanyani abinda banyi niyaba, kuma dayake kaga su masu haline saisa kake rawar k'afa a kansu, ammah talakkawa wane irin wulak'ancine bakayi musu?

Cike da k'ulewa yace suhail ni kake fad'a ma magana haka?

An fad'a maka, shin ko ka mance lokacin da me irin case d'in yazo wulak'ancin da kayi ma relatives d'insa kafin ka amince? Ko ka mance da yadda ka wulak'antasu a lokacin da kud'insu bai cikaba? Ko ka mance da nayi musu aikin yadda kadinga nuna hakan bai burgekaba.
Matsowa suhail yayi kusa da shi yace idan ka mance toh ni ban mance ba kuma ni wajena da talakka da mekud'i duk d'ayane, dan haka a yanzu idan kai zaka iya yi saikaje kayi.

Dafe goshinsa Dr muhammad bashir yayi yace wai kai suhail maganar me kakeyi haka, kuma kasan ni ba cadre ta bane, ni doctor ne iyaka induba marassa lafiya kawai, kaiko har theater kanayi.

Key d'in motarsa yad'auka yace sai kasan yadda zakayi,,,yana fad'in haka yajuya zai fita.

Cikin d'aga murya Dr muhammad bashir yace suhail kar kasaki kafita daga hospital d'innan inkuma ba hakaba zaka fuskanci hukunci daga gareni.

Juyowa suhail yayi yakallesa a wulak'ance yace indai kana tak'ama da matsayin medical director da aka bakane toh daga yau kakoreni kaga idan zan daina numfashi kuma idan kana tunanin ina cin kud'ine a wannan aikin da nake toh nabaka satar amsa kaje katambaya kaji nawa nake kar6a, inaso kasani babu abinda zaku bani kawai dai ina wannan aikin ne saboda Allah,,,yana fad'in haka yajuya yaficce yabar Dr muhammad bashir tsaye.

Cike da mamaki Dr muhammad yakebin k'ofar da kallo sannan daga k'arshe yaficce yanufi office d'in Dr mu'az.

Yarima koda yafita motarsa yashiga yai mata key dagudu yafita yabar asibitin cikin k'ank'anin lokaci ya isa gida, lokacin da ya isa zarah tana bedroom dan haka yai kwanciyarsa saman 3 seater, jin kansa yake yana wani irin sara masa, ahaka yamaida idanunsa yalumshe zuciyarsa tana masa wani irin zafi.

Zarah da tafito daga bedroom tsaye tayi da mamaki tana kallonsa dan batasan dawowarsaba, takowa tayi ta iso inda yake daga gefen da yake kwance tad'an zauna tace ashe ka dawo.

Shuru yayi yakyaleta,
Am ko bacci zakayi? Cewar zarah.
Batare da ya bud'e idanunsa ba ahankali yace please kibarni banason damu.

Marairaicewa tayi tace toh bakada lafiya ne?

Bud'e idanunsa yayi da suka canza launin ja yai mata wani irin kallo da yasa zarah tamik'e ba shiri dan sak yarima suhail d'insa yakoma mata, maida idanunsa yayi yalumshe.

Juyawa zarah tayi takoma bedroom tana mamakin canjin da yarima yayi mata cikin k'ank'anin lokaci tunani tashigayi toh ita me tayi masa? Ko dai wani ya6ata masa a wajen aiki? daga k'arshe sharewa tayi tacigaba da hidimunta.


Dr muhammad Bashir ba ko sallama yashiga office d'in Dr mu'az kujerar da take opposite d'insa ce yaja yazauna fuskarsa ba alamun fara'a yace Dr wane irin marar kunyane kakawo mana muka d'auka aiki har yake ik'irarin fad'amin magana.

Cike da mamaki Dr mu'az yace ranka yadad'e wa kenan nakawo muku?

Cikin d'aga murya yace akwai wani bayan wanchan Dr suhail d'in.

Cike da mamaki yace suhail kuma anya shine zai maka rashin kunya?

Toh wa kake tunani bayansa duk matsayina a hospital d'innan ammah har zansa shi yayi  theater yak'i bayan kuma abinda yazoyi kenan aikin, toh wlh kafad'a masa idan baiyi wasaba zan sa akoresa, su daman 'ya'yan talakkawa basu iya samun wajeba daga ya samu ana biyansa albashi mai tsoka shine har yai bakin da zai fad'amin magana ko yana tunani daidai yake da ni? Daman tunda naga take-takensa nasan bazamu zauna lafiya da shi ba dan ya cika jin kai.

Dr mu'az baki yasaki yana kallonsa har yakai aya sannan yace Dr suhail d'in da kansa?

Tsaki yaja cike da k'ulewa yace kai wai ma shi d'an gidan uban wanene a garin nan? Wlh in dai har baizo yayi abinda nasa shiba toh zanyi sanadiyar barin aikinsa.

Mik'ewa Dr mu'az yayi yana murmushi tare da jinjina kai yace ranka yadad'e kayi hak'uri saidai ina tunanin bakasan waye prince suhail ba.

Da mamaki Dr muhammad Bashir yake kallonsa yace prince suhail kuma? Wanene kuma haka.

Murmushi Dr mu'az yayi a karo na biyu sannan yace prince suhail tun daga zubinsa da yanayinsa da komai nasa yaci ace ka gane babu talauci a tare da shi dan ko hanyar talauci bai saniba, d'an sarautane gaba da baya dan shine zai kasance magajin garinsu, saidai nasan kanka zai d'aure da kaga ya zo yana aiki a k'ark'ashinka.
shuru yayi nad'an lokaci sannan yace prince yana da babban hospital wanda yake mallakinsa ne, kuma kud'in da yake rik'ewa per month ko rabinsu ba a biyanka, ko salary d'in da ake biyansa a nan ba shi yake cinsuba yana raba ma talakkawa mabuk'ata, girgiza kai mu'az yayi yace idan prince yaso takarda kawai zai rubuta ba kai ba hatta ni zai iya yin silar barin aikinmu, dan de bai d'au kansa komai ba saisa bai bayyanar da kansaba ga sarkin garin nan.

Dr muhammad Bashir zare ido yake cike da tsoro dan gabad'aya maganganun Dr mu'az sun firgitasa, shi kansa ya yarda da maganar saboda yanayin yarima kawai zaka kallah kagane cewa kud'i sun zauna masa.
kuma nasan prince yana da dalilinsa da yasa yak'i yin aikin, ammah prince mutum ne mai tausayi.

Ajiyar zuciya Dr muhammad Bashir yayi tare da mik'ewa yashiga zagaye office d'in sai chan yace mu'az meyasa tun farko bakaimin bayani akansaba?

Murmushi Dr mu'az yayi yace ranka yadad'e ai shine bayaso ana bayyanasa yanzu ma nafad'a makane dan naga kana da buk'atar sani tun kan katafka babban kuskure.

Jinjina kai Dr muhammad yayi yace tabbas ka taimaka min kuma nagode, ammah akwai wani taimakon da yarage kayi dan Allah kataimaka kaje kalallashesa yazo yayi wannan aikin yaceci rai wlh wannan shima daga royal family yafito duk ga danginsa chan suna jirana kuma sarkin garin nan yakirani yafad'amin zuwansu.

ajiyar zuciya yasafke yace shikenan zan kwatanta yanzu bari inje office d'in nasamesa.

Ai baya office d'in ina tunani ya tafi.
ohk bari inje gida ina tunani yana chan.

Dr muhammad yace dan Allah kataimaka kashawo kansa.
kar kadamu Dr zanyi iya k'ok'arina.
jinjina kai yayi yace Allah yataimaka.
Ameen Dr mu'az yace,,,nan suka fita a tare.

Tunda yayi horn aka bud'e masa gate d'in gidan a chan parking space yahango motar yarima, murmushi yayi sannan yaje ya aje tashi koda yafito cikin sauri yashiga gida, bai ko je part d'insuba direct yawuce na su yarima.

Knocking yayi zarah da take cikin bedroom ita tafito da mamaki taga yarima yananan inda yake nan tawuce taje tabud'e, ganin Dr mu'az yasa tayi murmushi tare da gaishesa.

Amsa matayayi sannan yace prince fa?
Juyowa tayi takalli yarima da baida alamar motsawa sannan tace gashinan, bismillah kashigo.

Da sallamarsa yashigo nan zarah tashige bedroom tabasu waje.
Kujerar da take kusa da yarima yaje yazauna tare da fuskantarsa yace prince ba dai bacci kakeba ko?

Yarima batare da ya bud'e idanunsaba yace ya dai?

Murmushi Dr mu'az yayi yace ranka yadad'e da ka taimaka ka tashi sai muyi maganar

Banza yarima yayi yakyalesa
Ganin baida niyar tashi yasa yace prince dan Allah kayi hak'uri da abinda yafaru tsakaninku da MD kataima kayi ma patient d'innan theater d'in domin yana buk'atar taimakonka.

Ahankali yarima yabud'e idanunsa yasafkesu akan Dr mu'az murmushin k'arfin hali yace shikenan ka gama?

Girgiza kai Dr mu'az yayi yace kayi hak'uri ranka yadad'e ban gamaba kawai dai ina neman alfarma ne koda banga patient d'inba bansan irin condition d'in da yake cikiba shi kansa MD a yanzu ya yi nadama akan abinda yayi maka.

Ta6e baki yarima yayi yace wannan matsalarsa ce dan ni banda lokacinsa, kuma da kake maganar patient wannan ba matsalarku bace kuma ga surgeons nan mezai hana kunemi wani tunda bani kad'ai bane.

Haba prince bansanka da hakaba please kataimaka ka.....
'Daga masa hannu yarima yayi yace please mu'az kana cikani da surutu kabarni zanyi nazari akai.

Jinjina kai mu'az yayi yace angama ranka yadad'e Allah yasa muji alkhairi ahuta lafiya.

Yarima batare da yayi magana ba yamaida idanunsa yalumshe, ganin haka yasa Dr mu'az yamik'e yafita yabar d'akin.

koda yafita kiran Dr muhammad Bashir yayi yashaida masa yadda sukayi, ajiyar zuciya MD yayi yace toh Alhmdllh zamu sauraresa,,,,bayan sun gama wayar zuwa yayi yasamu su sultan ahmad da suke jiransa cike da girmamawa yace kuyi hak'uri na tsaidaku.

cikin zak'uwa sultan abbas yace ya kukayi da Dr d'in da zaiyi theatre d'in?
Ajiyar zuciya yasafke yace ranka yadad'e kuyi hak'uri yanzu haka shi muke jira muji daga garesa.
Dr ahmad ne cikin sanyin jiki yace toh ko zaka rakamu wajensa muje mu dakanmu murok'esa.

Kar kudamu kukwantar da hankalinku insha Allahu munasa ran zai zo yayi masa domin Dr d'in baida matsala.

jinjina kai sukayi cike da gamsuwa da maganarsa sannan sukace Allah yasa.

Bayan Dr mu'az ya fita yarima wayarsa yad'auko yakira wani doctor da yake k'ark'ashin yarima nan sukayi magana.




_Comment_
     *nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
[5/3, 9:53 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Sak'on gaisuwa agareku Mamar rumaissa nd khadija mekano ina ji da ku irin sosai d'innan😍_

        ❤❤❤

_*Mum chubad'o muhammad a kullum ina alfahari da ke har cikin zuciyata Allah yabarmu tare😘*_

*PAGE* 6⃣7⃣

Su sultan ahamad suna a tsaye nan wasu doctors guda ukku sukazo zasu shiga room d'in da memartaba yake a ciki,,Dr muhammad Bashir ne yace ku kuma ina zakuje?

'Daya daga cikinsune yace ranka yadad'e Dr S ne yabamu umurni akan muje muyi ma patient d'in injection sannan musanya masa drip, ya ce sai zuwa gobe by 10am zai shigo.

Gabad'ayansu murmushin jin dad'i sukayi tare da furta Alhmdllh.

Haka suka shiga sukayi abinda aka umurcesu sannan suka fito, su dada nan aka basu izini sushiga suzauna ammah kar sudinga yin hayaniya saboda patient d'in ba a so atashesa daga baccin da yake.

Haka suka dawo bayan drip d'in ya k'are suka cire sukace kar asaki abashi wani abu yaci, nan ma da dare suka dawo sukayi masa wata injection d'in tare da k'ara gargad'insu kar abashi komai.

Yarima ko a ranar kasa samun sukuni yayi dan tun baiga yanayin da memartaba yake cikiba ammah hankalinsa ya tashi sosai musamman ma da yaga case d'in da yake tare da shi, dafe kansa yayi yana jin k'unci a ransa nan hawaye yashiga kwarara cike da tausayin memartaba da baida kamarsa bayan iyayensa.

Zarah da take gefensa ganin halin da yake ciki yasa tafashe da kuka dan tun d'azu yarima bai kalli ko inda takeba bare tasa ran zaiyi mata magana.

Kukanta yasa yadawo cikin hayyacinsa ahankali yabud'e idanunsa tare da share hawayen fuskarsa sannan yakalleta yace Zarah meyake faruwa ne? Bakida lafiya ne?

Cigaba tayi da kukanta tare da juya masa baya, murmushin k'arfin hali yayi sannan yajanyota a jikinsa yarungume d'ago mata kanta yayi yakalli cikin idanunta yace kifad'amin abinda yake damunki.

Rage sautin kukanta tayi tace ba kai bane kake ta shareni inma wani abu nayi maka ai sai kafad'amin inbaka hak'uri, kuma tun d'azun kake cikin damuwa har fa kuka kayi yanzu.

Jan hancinta yayi yace injiwa yace miki kuka nayi? Kidaina damuwa kidinga yi min addu'a kinji ko baby?

Turo bakinta tayi tace toh, murmushi yayi yace fushin ya isa haka.
Murgud'a masa baki tayi tace ank'i d'in.
Kwantar da ita yayi a k'irjinsa yace baby please muyi bacci.
Nan Zarah talumshe idanunta saboda daman baccin takeji ganin yarima ne a wannan yanayin yahanata bacci,
Shafa bayanta yashiga yi ahankali ahaka bacci yai awon gaba da ita, nan yazameta daga jikinsa tare da tashi zaune yadafe kansa,,,,,ya dad'e a zaune sannan daga baya yakoma yakwanta yana ta juyi ahaka bacci yai awon gaba da shi.

Wajen 8am yagama shirinsa kallon zarah yayi da take baccinta hankali kwance, zuwa yayi yai mata peck a kumata tare da shafar cikinta sannan yaficce batare da yayi ko breakfast ba.

Koda ya isa direct office d'in MD yaje lokacin MD yana zaune yana cike wasu files, ganin yarima yasa saida gabansa yafad'i dan fuskarsa ba alamun fara'a kujera yarima yajanyo yazauna muryar MD tana rawa yace am Dr S sannu da shigowa.

Wani irin kallo yarima yawurga masa yace Dr muhammad kar kayi tunani na shigo hospital d'innan ko zanyi theater d'innan saboda kai ne, murmushi yarima yayi sannan lokaci guda yahad'e fuska  yace na amince zanyine saboda amfanina da na dangina, jiya ka fad'a min magana son ranka ammah na yi maka uzuri saboda bakasan wanene ni ba, ammah inaso kasani ya zama dole kakiyaye kalamanka  akaina inbahaka zansanyaka kayi nadamar da batada amfani.

K'ut dr muhammad yahad'e yawu sannan yace shikenan dr s nagode sosai da ka fahimtar da ni.

Ta6e baki yarima yayi tare da mik'ewa yace wannan ya rage ruwanka, har ya fara tafiya sai kuma yajuyo yace am ban yarda akar6i ko naira d'ayaba daga garesu domin duk abinda ake buk'ata na bada ansiyo min sannan kuma nasaka kud'i a account d'inku na hospital zaka iya zuwa wajen accountant for confirmation, ammah idan nasaki naji kun kar6i kud'insu, girgiza kai yayi tare da murmushin mugunta sannan yace a lokacin zani nuna muku kalata zakusan wanene ni,,,,yana fad'in haka yajuya yafita yabar office d'in.

Cike da takaici MD yabuga hannunsa a table d'in da yake gabansa yace suhail ka 6atamin duk wani budget nawa,, dan dama abu guda yasa yashige gaba a lamarin dan yasan ba k'aramar riba zai samuba cikin jin haushi yamik'e yashiga zagaye d'akin cikin ransa yashiga tunanin maganar yarima yace anya mutanen chan ba wajen Dr s suka zagaye sukaje ba suka bashi kud'i? toh inma ba hakaba taya zai iya biya musu mak'udan kud'i,, chan kuma yace kokuma ai yana da taimako,,,cikin d'aga murya yace inaaa hakan ba zai ta6a yuwuwaba akwai dai wata a k'asa, fuuu yawuce yafita daga office d'insa rai a 6ace.

Yarima koda yakoma office d'insa system d'insan yazuba ma ido yana wani nazari a cikinta, dr mu'az ne yaturo k'ofan yashigo tare da yin sallama bai jira aka amsa masaba yashigo tsaye yayi wajen kan yarima yace haba suhail ammah baka kyautaba ashe memartaba ne su daddy suka kawo bayada lafiya shine baka fad'aminba har kana ik'irarin cewa bazakayi masa operation ba, toh na je na gansu.

'Dago kai yarima yayi cikin sauri yace mu'az bakadai fad'a musu ina nan ba dai ko?

Cike da mamaki mu'az yake kallonsa yace toh menene dan sun sani? Kawai dai kaci sa'a basu ganeniba ammah da sai nai musu bayaninka.

Ajiyar zuciya yarima yasafke sannan yace ka taimaki kanka ammah please kar kasaki kafad'a musu cewa ina nan kuma kar kabari sugane cewa nine wanda zaiyi theater d'in.

Mamaki k'arara yabayyana a fuskar Dr mu'az yace saboda me Dr?

Saboda wani dalili nawa,,,yarima yafad'a a tak'aice.
Dr mu'az har ya bud'e baki zaiyi magana nan yarima yai sauri yatari numfashinsa yace saura 30minutes inshiga theatre room please kaje kakar6o min constant foam kawakilce ni kaje kuyi agreement da relatives d'insa inkuka gama sai kakawo min inyi sing.

Toh kai saboda me bazakaje da kankaba?

Yarima duba agogon hannunsa yayi sannan yace kana 6ata min lokaci kasan dai na yi maka duk wani bayani.

Murmushi Dr mu'az yayi sannan yajuya yafita yabar office d'in.

Zuwa yayi sukayi komai da su sultan ahmad sannan yazo yakawo ma yarima foam d'in yayi singing.

Bayan yarima ya gama singing d'in kallonsa yayi yace saura abu d'aya yanzu dai kaje kasasu subar wajen sannan kasa nurse sutura min shi a theater room ganinan zuwa.

Haushi ne yakama Dr mu'az yace wai kai prince ni zaka maida kamar wani yaronka.

Shuru yarima yayi yakyalesa, ganin haka yasa Dr mu'az yawuce yafita yana 'yan maganganu.

Sa nurses yayi suka tura memartaba zuwa theater room sannan yakalli su sultan abbas da sukayi jugudum yace ranku yadad'e zaku iya shiga daga cikin room kuzauna kujira yanzu doctor d'in zai shiga.

Dada ce tace a'a d'annan kabarmu Kawai a nan dan inmukaje wani wajen hankalinmu bazai ta6a kwanciyaba.

Murmushi Dr mu'az yayi yace ranki yadad'e hak'uri zakuyi kucigaba da yin addu'a akan Allah yasa adace, saidai doctor d'inne idan yafito yaganku a nan bazaiji dad'iba domin bayaso yaga ana tsayawa a nan ransa yake 6aci.

Cike da gamsuwa da maganarsa sultan abbas yace toh shikenan doctor bari mubar wajen fatanmu dai Allah yasa adace, Ameen sukace sannan suka wuce sukashige room.

Yana ganin sun shiga nan yajanyo wayarsa yakira Dr suhail yashaida masa, mik'ewa yarima yayi yacanza kayansa zuwa na theater sannan yafito yanufi room d'in, a bakin theater room d'in yatarar da doctors biyu da nurse d'aya suna jiransa, har ya wuce zai shiga doctor mu'az yakira sunansa.
tsayawa yayi batare da ya juyoba, cikin sanyin jiki Dr mu'az yace ina maka fatan sa'a.
'Daga masa hannu kawai yayi sannan yawuce yashige theater room d'in.

Tsaye yayi yana kallon memartaba da gabad'aya baisan inda hankalinsa yakeba saboda allurar da akayi masa, tausayinsane yakamasa,,,dafasa da akayine ta baya yasa yadawo cikin hayyacinsa nan yamatsa domin sufara aikin.

Su dada alwallah sukayi suka fara sallah tare da rok'on Allah sa'a acikin aikin nan da za'ayi wayoyinsu ko saidai suka kashesu saboda kiran da akeyi musu tun daga iyalansu zuwa mutanen garin gazban dan har gajiya sukayi da amsa wayoyi daga jiya zuwa yau.
dan su sultana bilkisu, sultana sadiya, rahama, sumayya, Aunty husna dukkansu suma sallah suka shigayi, hatta wasu daga cikin mutanen gari, fada ko liman yashige gaba aka dinga suburbud'a addu'o'i da karatun alk'ur'ani, gabad'aya garin wani irin shuru yayi mutane d'aid'ayane zaka gani suna raharsu sai kuma k'ananun yara da basusan abinda ake cikiba, hatta gidansu zarah.

Tun wajen k'arfe goma suka shiga theater room d'in ammah basu suka fitoba sai wajen 12 suka gama komai dan daga k'arshe baya sukaja sukayi cirko-cirko sukabar Dr suhail da aikin kasancewar shi yayi komai dama su kayan aikin ne kawai suke mik'a masa har yagama yamaida yad'inke, bayan ya gamane yajuyo yakallesu yai musu nuni da sunyi nasara ai nan sai suka shiga murna.

Zamewa yayi yaficce daga theater room d'in yakoma office d'insa yacire kayan yasaka nashi.

Nan nurses suka tura memartaba zuwa room d'in da aka admitting d'insa, su dada akayi ma albishir da anyi a sa'a nan suka hau godia ga ubangiji harda duk'awa yin sujjada, dasauri suka fito sukanufi room d'in zasu shiga nan nurses sukace a'a babu damar sushiga a yanzu saboda bacci yake, daganan suka bud'e wayoyinsu kamar jira ake suna kirawa kira na shigowa nan suka shiga yi ma mutane albishir da anyi a sa'a kowa yayi murna sosai.

Yarima kife kansa yayi a table d'in da yake gabansa shi kansa ya rasa shin murna yake ko me, dan ji yake hankalinsa ya d'an kwanta a yanzu ba kamar kafin ayi aikin ba, nan Dr mu'az yashigo yataya murna akan nasarar da aka samu.

Wajen k'arfe ukku badda kama yayi yaje yashiga room d'in yak'ara duba memartaba da har lokacin yake bacci nan daga gafe ya aje wata injection sannan yafito, bai d'ago yakalli su dada ba lokacin da zai wuce ta gabansu ammah saida gabansa yafad'i su kansu saida fad'uwar gaba ta ziyarcesu, haka yafito yawuce yashiga motarsa yanufi gida.

Koda aka kirasa akafad'a masa farkawar memartaba umurni yabada akayi masa injection d'in da ya aje sannan yace za'a iya barin iyalansa sushiga sugansa ammah kar a bari suyi hayaniya.

Zarah da take zaune gefensa ta kafesa da ido tana sauraren wayar da yake, bayan ya gama juyowa yayi yakalleta yace baby ya dai?
Murmushi tayi sannan tace ai tunda naga ka fita da wuri nasan theater ce zakayi.

Murmushi suhail yayi,,,kwantar da kanta tayi saman kafad'ansa nan ta marairaice kamar zatayi kuka tace please kadaina fita bakayi breakfast ba, indai ka san zaka fita da wuri toh tun dare kadinga fad'amin kaga sai intashi dawuri inhad'a maka breakfast.

Murmushi yayi yace toh ranki yadad'e angama.

'Dago kai tayi takallesa saida tad'aure fuska sannan tace duk ranar da kak'ara fita batare da kayi breakfast ba zamu had'e.

Dariya ce taci Yarima ammah yadanneta yace toh Aunty angama.

au nima ce Aunty?
Eh man tun kan inji safkar bulala,,,dariya sukasaka gabad'ayansu nan yad'age mata riga yana kallon cikinta da yake motsawa, d'ago kai yayi yakalleta, murmushi tasakar masa tare da lumshe idanunta,
shafa cikin yashiga yi yace kinga babyna shima ya k'agara yafito yaga daddynsa.

Uhm nima ai na k'agara yafito inhuta da wahalar nan, har ma rasa rigimar wa zanji da ita nake tsakanin babyn ko daddynsa.

Ido yazuba mata yace au nima rigimar nake?
Fari tayi masa da ido sannan tace wata ran ma k'ara na babyn dan taka rigimar har rasa yadda zanyi nake.

Haka kika ce?
Eh,
Tallabo fuskarta yayi tare da kallon cikin idanunta yayi ahankali kamar me rad'a yak'ara cewa haka kikace?
Gira tad'aga masa alamun eh, bata ankaraba sai jin bakinsa tayi cikin nata nan tabiye masa suka shiga nuna ma juna salon so, gabad'aya suka fita hayyacinsu a nan parlour suka baje, saida taga yana shirin wuce tunaninta sannan tasamu tazame jikinta tamik'e dak'yar tanufi bedroom dan gabad'aya ya kashe mata jiki.

Nan yarima yai pillow da hannunsa tare da maida idanuwansa yalumshe, ahankali yayi k'ayataccen murmushinsa cike da k'asaita.


Bayan kwana d'aya sultana bilkisu da sultana sadiya visarsu tafito nan suma suka kama hanyar garin Abuja sosai sukaji dad'i da sukaga memartaba dan a yanzu har 'yar magana yana d'anyi.

Yarima ko tun ranar da yayi masa aiki rabon da yak'ara sakasa a idonsa, saidai yatura wasu doctors domin sugano masa lafiyarsa ammah duk da haka duk wani abu da za'ayi masa shi yake bada umurni ahaka har memartaba yacika sati guda yawarke garas kamar bashiba dan har takawa yakeyi dakansa batare da anrik'esaba, dressing ko kusan kullum akeyi masa dan a yanzu d'inkin ma ya had'e har an warwaresa.

A ranar da yacika sati guda saida yarima yatabbatar da ba abinda yake damunsa sannan yasallami doctors d'in da suka taimaka masa wajen kula da memartaba dan burinsa ya cika nan shi kuma yafito yanufi gida.

A ranar bayan wani doctor yashigo yai masa injection nan dr muhammad bashir da Dr mu'az suka shigo, bayan sun gaisa da su memartaba, Dr muhammad Bashir kallon memartaba yayi yana murmushi yace ranka yadad'e ya kake jin jikin naka?

Shima memartaba murmushin yayi yace Alhmdllh discharge kawai nake jira dan najini daidai nake, ance min ma har yanzu baku fad'i kud'in da za'a biyaba ai yakamata ace zuwa yanzu kun fad'a anbiyaku.

Murmushi sukayi tare da kallon juna sannan Dr mu'az yace kar kudamu ai angama komai ranka yadad'e.

Memartaba kallon sultan ahmad yayi yace karubuta musu cheque kabasu tunda bazasu fad'i kud'inba hakama mungode da karamcin da akayi mana Allah yabiya.

Dada ce tace ai naso inga wannan d'an albarkan da yayi aikin inmasa godia ammah har yau doctor baku gwada mana shi ba.

Dr muhammad Bashir yaga samu yaga rashi haka aka basu cheque d'in ammah yak'i kar6a.

Sultan abbas ne yace kukar6a mana ai duk abinda zamuyi muku bamu biyakuba saidai addu'a,,,
girgiza kai Dr mu'az yayi yace ai doctor d'in da yayi theater d'in ya riga yabiya komai babu abinda baiyiba dan ya ma ce kar a kar6i komai naku.

Gabad'ayansu da mamaki suke binsa da kallo,,,sultan ahmad ne yayi k'arfin halin cewa ya biya komai fa kace? Saboda me zai biya?

Dr muhammad Bashir murmushi yayi yace wannan kad'anne daga cikin halin Dr S, mutum ne mai kyauta da karamci.

Girgiza kai sultan ahmad yayi yace duk da haka baidace yataimaki irin mu ba, taimakon da yayi mana na theater ma kawai ya isa mungode dan bamuda abinda zamu biyasa, yanzu kukar6i wannan kukaimasa.

Memartaba ne yace wai wanene wannan Dr S d'in? Miye full name d'insa? Dan Allah kuyi masa magana yazo mugaisa insaka masa da abinda yayi mani.

Shuru Dr mu'az yayi dan shi ya ma rasa abinda zaice musu,,,muryar Dr muhammad Bashir ce yajiyo yana cewa Dr suhail shine full name d'insa.

Gabad'ayansu saida gabansu yafad'i kusan a tare suka maimaita Dr suhail? Ummi da dada fashewa sukayi da kuka dan antuna musu da suhail d'insu.

Memartaba ne yace dan Allah wanene wannan Dr suhail d'in? daman d'an nan garin ne ko zuwa yayi? Kutaimaka kukaini ingansa ko jikanane.

Shuru sukayi sukarasa amsar da zasu bashi sai chan Dr muhammad yakalli Dr mu'az Girgiza masa kai Dr mu'az yayi alamun kar yafad'a.

Memartaba mik'ewa yayi ya isa inda suke yace dan Allah Kutaimaka min ingansa inaji a raina suhail d'ina ne da nake nema kusan wata ukku kenan yatafi yabarni.

Sultan abbas ne yazo yarik'osa yace ranka yadad'e anya suhail d'inmu ne? Kayi hak'uri kaga bakada lafiya, bana tunanin shine me zaizo yi a garin abuja alhali baida kowa a nan, kuma taya zai ganmu batare da yayi mana magana ba.

Girgiza kai memartaba yayi yace bazan ta6a gamsuwa da maganarkaba har sai nagane ma idona, nidai kukaini ingansa dan Allah.

Dr mu'az cike da jin tausayinsu yace tabbas suhail d'inku ne ranka yadad'e.

Arazane gabad'ayansu suke kallonsa ummi dasauri tamatso inda yake tsaye dada da sultana sadiya suka take mata baya, memartaba ko rik'o masa hannu yayi yace k'ara maimaita min abinda kace kamar kunnena bai jiye min daidaiba kasan inba sunan yarima ba babu abinda yake son ji.

Murmushi Dr mu'az yayi yace tabbas ranka yadad'e abinda kaji gaskiya ne, yarima ne yai maka komai shi yabuk'aci da kar abayyana muku kansa.

Alhmdllh, sultan abbas da sultan ahmad sukashiga furtawa.

Hawayene suka shiga zuba daga idanun memartaba yace dan Allah kataimaika kakaini inga suhail d'ina.

sultana bilkisu ma cikin kuka tace na rok'ek'a kataimaika kakaini inga d'ana.

Dada ma cikin kuka tace kakaini inga jikana ko nasamu sanyi a raina.

cike da tausayin family d'in Dr mu"az yace na amince zan kaiku kugansa a duk lokacin da kuka shirya.

Sultan abbas ne yayi karaf yace yanzu mukeso kataimaka kakaimu.

jinjina kai Dr mu'az yayi yace toh shikenan ranka yadad'e zamu iya tafiya.


Yarima yana komawa gida a bedroom yatarar da zarah tsaye tana shiryawa da alamu wanka tafito, kallonta yayi yace yisauri kishirya yanzu zamubar gidannan.

da mamaki zarah take kallonsa tace barin gida? Ina kuma zamuje daga nan?
Wata uwar harara yarima yawurga mata yace ba shawara nake nemaba umurni nabaki,,,,yana fad'in haka yawuce yaje yabud'e wardrobe yafara tsintar musu kayansu.

Zarah kasa ida sanya kayan tayi nan tai tsaye tana kallonsa cike da mamakin dalilin da zaisa subar gidan alhali mutanen suna da kirki, chan kuma sai tace ko dai gida zamu koma, har yagama shirya kayan tana tsaye ,,,juyowar da zaiyi ganinta tsaye yasa cikin fad'a yace bazakisa kayanba?

Nan cikin sauri Zarah tacigaba da saka kayan dan gabad'aya ya koma mata yarima suhail sak.




_Comment_
       *Nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_[5/1, 7:01 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

*PAGE* 6⃣8⃣

Tana gama sa kayan bayan yarima tabi suka fito, kallon part d'in jamila tayi taga a kulle yake kasancewar jamila taje anguwa, har cikin ranta bataji dad'iba dabasu samu sunyi sallama da jamila ba.

Suna janye da trolly d'insu sukafito zasu nufi wajen motar yarima, daidai lokacin aka hangame gate motoci hud'u a jere suka shigo, tsaye sukayi suka zuba ma motocin ido cike da mamaki dan basusan ko suwanene ba a ciki.

Tun kan a ida yin parking ummi tabud'e murfin mota tafito dagudu tanufi wajen yarima.

Mutuwar tsaye su yarima sukayi tana zuwa tafad'a jikinsa tarungumesa tare da fashewa da kuka tana cewa kaine my son, daman zan k'ara ganinka?

Tsaye yarima yayi yakasa ta6uka komai, d'ago kai tayi takallesa tare da shafa fuskarsa tace suhail d'ina kaine a gabana ko mafarkin da nasaba ne?

Muryar yarima tana rawa yace ummi na.
Rungumeta yayi sosai a jikinsa yace ba mafarki kikeba nine dai a zahiri ummina nayi missing d'inki.

K'ara shigewa tayi a jikinsa tace shine kuma katafi kabarni baka nemeniba? Meyasa? Meyasa kaimin haka suhail.

Ahankali yabud'e baki zaiyi magana hango su memartaba da yayi sun zuba masa ido yasa maganar ta lak'afe a bakinsa.

Takowa memartaba yayi yanufo inda suke,,,ganin haka yasa yarima yajanye ummi daga jikinsa tare da d'an ja baya kad'an.

Memartaba yana isowa wanka ma yarima mari yayi, gabad'aya wajen ido aka zuba masa cike da mamaki ganin yadda yake d'okin ganin suhail ammah daga had'uwa sai mari, zarah ko jikin sultana bilkisu tafad'a tana kuka,,

Duk'ar da kansa yarima yayi ammah ko kad'an bai gezaba,,,muryar memartaba tana rawa yace sake guduwa kake shirin yi a karo na biyu saboda kar muzo gareka?  ka kyauta suhail yanzu har kayi tsawon wata ukku batare da kazo ka nemeniba? Hakan da kayi daidai ne?

Cike da mamaki yarima yad'ago yakallesa,,,,memartaba yacigaba da cewa eh suhail koda ni nakoreka ammah ai cikin fushine kaduba kaga yadda nakoma duk akan rashinka, ni kaina nasan na aikata babban kuskure da na iya korarka daga cikin danginka, suhail taya kake tunani zan iya yafema kaina bayan daga baya nagane kaine akan gaskiya, wlh sumayya ta cuci rayuwata, ya zanyi a yanzu inwanke wannan laifin da na aikata kaicona ina ma ace duk cikin mafarkine.

Girgiza kai suhail yashiga yi cikin sauri yafad'a jikin memartaba yace ranka yadad'e kayi hak'uri bahaka bane, ni ban rik'ekaba ko kad'an kawai dai umurninka nacika, kayi hakuri da bijire ma maganarka da nayi wlh nima bahakanan na rabu da ku ba kawai dan gudun abinda za'a aikata daga baya azo ana da nasani ne domin zarah kwata-kwata batada laifi acikin maganar, ina tsoron in cuceta domin na tabbata sai Allah ya bi mata hak'inta, tunda tana k'ok'arin kyautata min taya zan saketa batare da tayi min komai ba, kayi hak'uri ranka yadad'e,

Shafa bayansa memartaba yayi yace hakan da kayi shine daidai suhail nidai burina kabiyoni mukoma gida.

Janye jikinsa yayi daga na memartaba tare da yin murmushi ahankali yace zarah,,,sai a lokacin memartaba yakalli zarah da take a jikin ummi, murmushi yayi yace d'iyata zo mugaisa mana,

Ummi janye zarah tayi daga jikinta, nan zarah taduk'a cikin sauri tagaishe da memartaba.

Amsa mata yayi cikin sakin fuska sannan yace kiyi hak'uri da abinda yafaru zarah.

Girgiza kai zarah tayi cikin kuka tace bakuyi mana komai ba ranka yadad'e duk abinda kukayi akanmu daidaine tunda kune sama da mu, mune yafi dacewa mubaku hak'uri tunda mu mukayi laifi.

Jinjina kai memartaba yayi cike da jin dad'in lafazin zarah, yace Allah yai muku albarka.

Sultan abbas isowa yayi yarungume yarima, yace yarimana naji dad'in ganinka dafatan zaka yafe mana abinda yafaru.

Murmushi yarima yayi yace abbana akodayaushe bakwa laifi nine dai nayi muku laifi.
Yarima ma baya laifi hakan da yayi shine daidai,,,cewar sultan abbas.

K'ara shigewa jikinsa yarima yayi yace nagode sosai abbana.

Yarima janye jikinsa yayi daga na abbah yaje yarungume dadynsa cikin jin dad'i yace daddyna kayi hak'uri kayafe min nasan nayi muku laifi.

Shafa kansa yayi yace kar kadamu my son tuni laifinka yagogu daga garemu bare ma suhail d'ina baya laifi, Allah yaimuku albarka

Dariya Yarima yayi yace nagode sosai daddyna, ina alfahari da ku,,,kallonsa yakai ga su dada dasuke gefe d'aya tsaye ita da  sultana sadiya, murmushi yayi sannan yawuce yanufi inda suke tsaye ganinsa yasa dada tahad'e hannunta biyu waje guda cikin kuka tace suhail,,,rungumeta yarima yayi cikin sanyin murya yace meyasa matata zatayi kuka bayan ga mijinta a tare da ita? Cikin kukan tayi dariya tare da rungume yarima tace suhail ina farin cikin ganinka, kayi hak'uri da abinda yafaru kayafemin wlh duk abinda nakeyi maka sumayya ce take kawomin zuga.

Murmushi yayi tare da d'ago kai yakalleta yace kakata duk abinda kikayi daidaine kuma kin cancanci kiyi fiye da haka saboda kin isa da jikanki.

Itama d'agowa tayi tace dagaske, d'aga mata gira yayi yace toh ya kikace.

Jan kumatunsa tayi tace suhail bakada dama ammah nagode da naganka.

Murmushi yayi yace nima haka matata,,, daganan yamatsa kusa da sultana sadiya da taduk'ar da kanta tana hawaye, gyaran murya yayi, kamar daman jira take cikin sauri tafad'a jikinsa tare da fashewa da kuka tace suhail kayafemin na cuceka na k'untata ma rayuwarka tun kana k'arami na d'aura maka karan tsana, dan Allah kayafemin akan abubuwan da nayi maka wlh nayi nadama insha Allahu yanzu zan gyara rayuwata.

Janyeta yayi daga jikinsa yace ummah kidaina tunawa da abinda yariga yawuce na yafe miki tun tuni.

Cikin kuka tace nagode sosai suhail Allah yabiyaka.

Ameen ummana.

Nan sultana sadiya da dada sukaje cikin jin kunya sukaba zarah hak'uri akan abinda sukayi mata.

Girgiza kai zarah tayi cikin kuka tace wlh bakuyi min komai ba inma kunyi toh na yafe.

Dr mu'az da yake tsaye chan baya yana kallonsu takowa yayi ya iso inda suke nan yaimusu jagora suka shiga cikin gida
Sultana bilkisu tana manne da yarima haka suka shiga kamar wani ya ce zai k'wace mata shi

A main parlour suka yada zango nan zarah taje tad'auko musu ruwa da lemu, memartaba yai gyaran murya yace Alhmdllh gaskiya naji dad'i sosai da naga yarima a yanzu ji nake duk wani ciwo da yake tare da ni ya warke, dan haka gida kawai zamu koma gabad'ayanmu gobe.

Girgiza kai yarima yayi yace kagafarceni ranka yadad'e a yanzu banaji zan iya komawa gida kubarni nan kawai inyaso zan dawo daga baya.

Gabad'ayansu ido suka zuba masa, memartaba ne yai k'arfin halin cewa saboda me suhail, me zaka zauna nan kayi? Kodai baka huceba?

Cike da girmamawa yace ba haka bane ranka yadad'e ina nufin zamu tafo daga baya.

Ina wlh bazaka k'ara kubce manaba k'afarka k'afarmu kayi hak'uri kawai mukoma gida,,,,cewar dada.

Sultana bilkisu ma rik'o hannunsa tayi tace suhail kar kace haka ka amince kawai mutafi 'yan uwanka suna chan suma suna burin ganinka.

Eh suhail ka amince kawai,,,,cewar sultan abbas.

Shuru yarima yayi nad'an lokaci sannan yakalli mu'az da yazuba masa ido, nan mu'az yad'aga masa kai alamun eh, murmushi yarima yayi sannan yace shikenan na amince zan biku.

Gabad'aya nan sukayi murna, haka sukayi ma mu'az godia sosai akan kulawar da yaba su yarima, murmushi mu'az yayi yace duk abinda nayima yarima ban biyasaba domin shi yamin fiye da haka addu'a ce kawai zanyi masa inbiyasa.

Nan memartaba yasa aka kira waya yace ayankar musu ticket.

Jamila ma koda tadawo nan tatarar da su memartaba cike da girmamawa tagaishesu nan mu'az yagabatar da ita.

Sai gab da magrib sannan memartaba yace sutashi sukoma masaukinsu dan su shirya, yaso su yarima subisu masaukinsu ammah yarima yace a'a sai dai goben zasu shigo, ummi rik'esa tayi dan gani take kamar zai k'ara kubce mata.

Murmushi yarima yayi yace kar kidamu ummina babu inda zanje ina tare da ke, kuje kawai gobe zan shigo dasafe.

Kwallah ce tacika mata ido tace kayi alk'awali?

Murmushi yayi a karo na biyu sannan yace eh ummi.

ajiyar zuciya tasafke nan sukayi musu rakiya har wajen motocinsu, saida sukaga tafiyarsu sannan suka dawo, mu'az zama yayi saman kujera tare da dafe kansa.

Ganin haka yasa yarima yazo gefensa yazauna tare da cewa abokina ya dai?

'Dago kansa yayi Cike da damuwa yace prince yanzu tafiya zakayi kabarni? Ya zamuyi idan kuka tafi wlh mun saba da ku bamuso kutafi.

murmushi yarima yayi yace mu'az wa yace maka zamu iya rabuwa? Ai ko muntafi zamu dinga kawo muku ziyara inma takama dakaina zan neman maka transfer kakoma hospital d'ina kacigaba da aiki tunda dama bakada kowa a garinnan aikine yakawoka.

Murmushin jin dad'i Dr mu'az yayi yace prince wlh da ka gama min komai, dan Allah idan kakoma kayi min wannan taimakon.
Murmushi yarima yayi yace kar kadamu kafi k'arfin haka wajena insha Allahu zanyi iya k'ok'arina.
Nagode sosai prince  Allah yasaka da alkhairi.

Koda su yarima suka koma part d'insu kallon zarah yayi da takasa kulle baki saboda murna yace kina murna zaki tafi gida ko?

Eh man sosai ma, kaima kana murna?.
Shuru yarima yayi yakyaleta,,,matsowa tayi kusa da shi tare da tallabo fuskarsa saida takalli cikin idanunsa sannan tace kaima nasan zakaso mukoma garinmu dan zamanmu cikin family d'inka shine kwanciyar hankalinmu.

jan hancinta yayi yace kedai tunda kina murna shikenan ammah ni nafison zamanmu a nan.

Marairaicewa tayi tace saboda me kace haka,

Murmushi yayi har saida beauty point d'insa suka lotsa sannan yace saboda a nan babu mai takura mana, a chan ko baza a barni inhuta da matataba.

Murmushi itama zarah tayi tace kar kadamu  hearty babu abinda zai hanamu kasancewa da juna dan a yanzu mun riga munzama d'aya.

Ajiyar zuciya yasafke yace hakane dear, ammah zanso kihaihu nan.

Langwa6e kai tayi tace kayi hak'uri mukoma chan garinmu tunda kaga haihuwar da sauran lokaci kuma zatafi dad'i muna cikin danginmu,,,kaga fa kungama magana da su memartaba cewa gobe tare zamu tafi

Shikenan dear tunda kinfi son mutafi toh nima na amince.

Rungumesa tayi a jikinsa tace Nagode sosai my heartbeat.


Su sultan abbas sunkira su waziri a waya sunce gobe zasu dawo nan cikin jin dad'i sukayi musu addu'a akan Allah yamaidosu lafiya.

Memartaba fadar sarkin garin yasa suka wuce suka gaisa tare da yi masa godia akan karamcin da yayi musu a nan suke shaida masa gobe sukeso suwuce garinsu.

baiji dad'iba da yaji sun ambaci tafiya nan yashiga rok'onsu akan suk'ara kwaana biyu.
ammah memartaba yace a'a nan suka shaida masa har ticket sun sa a yankar musu.

ba yadda ya iya kan dole yahak'ura a nan sukayi sallar magrib sannan suka wuce masaukinsu, tare da yi musu alk'awali gobe dashi za a je rakiyarsu.

Koda suka koma had'a kayansu suka shigayi cike da farin ciki biyu ga lafiyar da memartaba yasamu ga ta bayyanar yarima.

Daga chan 6angaren su yarima ma haka zarah tak'ara shirya musu kayansu, duk yadda yarima yaso tazo sukwanta k'iyawa tayi saida tagama shirya duk abinda tasan suna so sannan taje takwanta.

Washe gari tun k'arfe goma wayar da ummi tayo masane ta tashesu daga baccin da suke, bayan sun gaisa nan take shaida ma yarima flight d'in k'arfe biyu zasubi dan haka sugama komai dawuri kafin biyu.

Wajen k'arfe sha biyu suka gama shirinsu gwanin kyau, a parlour suka tarar da su Dr mu'az suna jiransu nan suka gaisa sannan suka wuce sukayi breakfast daga nan sukahau yin hira saboda gabad'ayansu basuson rabuwa da juna,

yarima key d'in motarsa yad'auko yadamk'a ma Dr mu'az yace gatanan ka k'ara, zaro ido Dr mu'az yayi yace ranka yadad'e kodai a ajiye maka ko inje dakaina inkai maka har gida?
Girgiza kai yarima yayi yace kod'aya na mallaka maka ita halak malak yanzu tazama taka.

Dr mu'az da matarsa godia sukayi ma yarima sosai cikin jin dad'i har da duk'awa k'asa saida sukaga ran yarima ya fara 6aci sannan suka daina godiar

Memartaba ne yadamesa da kira dan haka suka tashi gabad'aya suka nufi chan masaukinsu har da su Dr mu'az, 

Rungume yarima Memartaba yayi cikin jin dad'i, sultana sadiya ko jan zarah tayi kusa da ita, duk yadda zarah take nok'ewa ammah duk motsi kad'an da zatayi sai sultana sadiya tayi mata sannu.

Bayan sunyi sallah sarkin garin dakansa yasa aka shirya motoci nan yazo dakansa masaukinsu, lunch ma daga masarautarsa yasa aka kawo musu, bayan sungaisa nan Memartaba yagabatar mashi da yarima da matarsa.

Sosai sarkin garin yanuna farin cikinsa akan ganin yarima da akayi.

Bayan sungama kimtsawa gabad'ayansu suka nufi airport nan suka zauna har saida flight d'in ya iso sannan sukayi bankwana da juna cikin rashin jin dad'in rabuwa da za'ayi.

Dr mu'az, matarsa da zarah har da 'yar kwallarsu yarima ma ne maik'arfin halin basu baki.

Basu sukabar wajenba har saida flight d'in yatashi sannan.

A cikin flight d'inma Memartaba yana tare da jikansa, inda zarah take gefen dada kad'an kad'an da tad'aga ido sai taga yarima idanunsa suna a kanta gabad'aya sai taji kunya saboda su Memartaba da su daddy dan hakama sai tadaina kallonsa.

A chan airport d'in garin gazban tun kan su iso ya cika da jama'a kowa yana farin cikin son ganin memartaba dan basusan tare suke da yarima ba.

Lokacin da flight d'insu yasafka gabad'aya wajen yarikice da murna musamman ma da Memartaba yazo fitowa tsaye yayi yana d'aga musu hannu cike da jin dad'in ganin jama'arsa yadda sukazo tarbarsa.

Ai suna ganin yarima sai wajen ya ida rikicewa nan aka cigaba da murna dan ma dogarawa sun hana kowa yamatso inda suke nan aka bud'e musu motocin da aka tanadar masu suka shiga dakyar suka samu hanya sai emir palace,

A chan d'inma mutanene dank'are suke jiran isowarsu, nan ma anyi murna sosai da ganin yarima, shaheed ko rugowa yayi yarungume abokin nasa cikin jin dad'i shima yarima yarungumesa.
Shaheed yace abokina ina katafi kabarni? shine katafi kabarmu muna ta nemanka.
murmushi yarima yayi yace kayi hak'uri shaheed yanzu gani nadawo ba inda zan k'ara tafiya inbarka.
cikin jin dad'i yace dagaske?
'Daga masa kai yarima yayi alamun eh.
nan shaheed yayi murmushi yace nagode sosai abokina ammah fa nayi kewarka.
Memartaba baishiga gidaba saida yatsaya suka gaisa da mutane tare da yi masu godia sannan suka rantaya a turakar su Memartaba, rahama da husna dasauri suka nufo dan tarbar iyayen nasu ganin yarima yasa suka rikice suka nufi wajensa har da kukansu, rungume 'yan uwannasa yayi cikin jin dad'i, rahama cikin kuka tace Bro meyasa katafi kabarmu? Baka tunanin halin da zamu shiga, kaduba kaga tun bayan tafiyarka gabad'ayanmu bamu cikin kwanciyar hankali.
shafa kanta yayi yace kiyi hak'uri Lil sis yanzu gani nadawo yayanki zai kasance da ke akowane lokaci,
murmushin jin dad'i tayi tace nagode sosai yayana, nan takoma wajen zarah tarungumeta cikin jin dad'i.

Kallon husna yayi da take ta kuka yace akan me babbar yaya zata dinga kuka bayan ga k'anenta a kusa da ita? 'Dago kai tayi takallesa nan yad'aga mata kai, cikin sauri tafad'a jikinsa tare da fashewa da sabon kuka.
rungumeta yarima yayi yace please sis kukan ya isa haka indai baso kike nima kisanyaniba.

Cikin sheshek'ar kuka tace meyasa katafi kabarni, kai kanacan hankalinka kwance bakasan halin da muka shigaba saboda rashinka.
Murmushin k'arfin hali yarima yayi yace big sis duk inda suhail yakasance toh shima tunaninsa yana a wajenku, daidai da kwana d'aya ban ta6ayiba batare da kuna a raina ba.
toh dan Allah kar kak'ara tafiya kabarmu.
Jan kumatunta yayi yace angama big sis, cikin jin dad'i takai mai peck a goshi sannan suka rantaya zuwa turakar su memartaba.

Gabad'ayansu a saman carpet d'in da yake shimfid'e tsakiyan d'akin suka zauna inda memartaba da dada suka zauna saman cushin.

gyaran murya memartaba yayi sannan yace Alhmdllh godiya ta tabbata ga Allah da yasa cikin ikonsa nasamu lafiya akan ciwon da ni kaina banyi tunanin zan tashiba saidai cikin ikon Allah ayanzu gani garas saidai d'an abinda ba a rasaba.
gabad'ayansu sukace Alhmdllh Allah yak'ara lafiya da nisan kwana.
Shuru yayi nad'an lokaci  yacigaba da cewa yarima suhail munatayaka murnar dawowa cikin family d'inka tare da baka hak'uri akan abinda yafaru.
Murmushi yarima yayi yace bakomai ranka yadad'e.
masha Allah sannan magana tagaba itace......shuru memartaba yayi alokacin da yaga sumayya ta shigo d'akin, gabad'ayansu ido suka zuba mata.

daga nesa dasu kad'an tatsugunna tana kuka,,,abban sumayya ne yai k'arfin halin cewa ubanmi kikazo kiyi mana nan? Ko kitashi ko insa6a miki.

Cikin kuka sumayya tace dan Allah kuyi hak'uri kuyafemin abinda nayi maku wlh nayi nadama nadaina bazan sakeba.

Memartaba jinjina kai yayi yace zancen banza koda kikaga na k'yaleki bansa aka had'a da ke aka sa prison ba toh nabarkine yarima yadawo yayanke miki hukunci dakansa saboda shi yafi dacewa yayanke miki ba niba tunda kuma yanzu gashi ya dawo toh alhmdllh wuk'a da nama suna hannunsa dan haka suhail ga sumayya nan kayanke mata hukuncin da yadace da ita.

dada tace tabbas hakane suhail duk abinda kazartas daidaine.

Mik'ewa sumayya tayi tamatso kusa da yarima tatsugunna cikin kuka tace yarima ban damu da hukuncin da zaka zartas ba akaina nidai burina d'aya kataimaka kayafemin abubuwan da nayi maka wlh duk abinda nayi ba yin kaina bane zinat ce silar komai, tasha fad'amin cewa bazan iya rabuwa da itaba saboda akwai abinda tashirya min tun farkon had'uwarmu, indai zinat zatayi magana toh tatanake d'auka inbar ta kowa koda ace ta iyayenace, sannan nasha k'ullah makirci dan inga nashiga tsakaninku da zarah dan ina gani nice nadace da kai ba zarah ba ammah a yanzu nagane cewa zarah ita tafi dacewa da suhail,
Kallon zarah tayi tace zarah nai miki abubuwa dadama ammah baki ta6a d'aga ido kin kalleniba dan tsakani ga Allah kike zaune da ni.

Zarah da tunda sumayya tafara maganar kuka take dan ta bata tausayi sosai musamman ma da taga duk ta fita hayyacinta.

Yarima Kallon memartaba yayi yace ranka yadad'e dalilin da yasa ban fad'a mukuba tun farko saboda nafiso ku ma kugani da idanunku gudun kar kuk'i yarda musamman ma dada da  ummah gabad'aya basuson laifin sumayya a lokacin.

Uhm kaidai bari d'annan ai yanzu dai mungane komai,,,cewar dada.

Jinjina kai yarima yayi sannan yace ashe saida k'awartata tak'ara dawowa gidannan,
Memartaba yace yanzu ma haka tana a prison bari insa atafo da ita, nan memartaba yayi waya.

bayan mintuna kad'an saiga wani barde yazo da zinat duk ta yi bak'i ta k'ok'e inba ka kalletaba sosai bazaka ta6a cewa ita bace hatta ita kanta sumayya da taganta saida tafirgita.

Daga nesa dasu kad'an taraku6e tana hawaye, kallonta sumayya tayi cikin kuka tace zinat dan Allah kiwanke ni wajensu susan banda laifi a ciki.

Zinat ma cikin kuka tace idan bakida laifi toh wa yake da laifi? wlh sumayya kin cuceni.

Duk mutanen da suke zaune wajen shuru sukayi sukarasa megaskiya tsakaninsu,,,yarima ne yace bari akira dogarawa suzo atambayesu.

Zinat a tsorace dan ta tsorata sosai da bulala tamanin d'in da akayi mata cikin kuka tace dan Allah kar kakira ni zan fad'i komai ammah kar kasa ak'ara dukana.

Indai har kika fad'amin gaskiya batare da kinmin k'aryaba toh babu wanda zai dakeki sannan zani sallameki kiyi tafiyarki.

Share hawayen fuskarta tayi sannan tace tabbas sumayya batada laifi a ciki nice silar fad'awarta wannan harkar dan tun muna school sumayya tana da wulak'anci bata yadda tayi abota da kowa sai 'ya'yan masu kud'i nikuma tun lokacin da nafara ganinta naji ta burgeni ganin nima d'iyar masu kud'i ce yasa nayi amfani da dadamata muka k'ullah abota nan mukacigaba da wulak'anci saida naga sumayya ta saba dani batada abokiya kamarni sannan nabijuro mata da buk'atata akanta ammah tak'i yadda ban nuna mata 6acin rainaba daga k'arshe naje wajen wani malami yaimin aiki akanta yazamana duk abinda nakeso shi takeyi bata iya tsallake maganata, a lokacin wani saurayina yanuna yana buk'atarta yabani kud'i masu yawa nikuma naimasa silar samun sumayya shima saida taga raina yana neman 6act sannan ta amince har yayi zina da ita.
gabad'aya d'akin suka saka salati cike da al'ajibin abun kowa yana Allah wadai.

memartabane yatsaidasu, nan zinat tacigaba da cewa tun daga lokacin nima nafara neman sumayya har nasaba mata da harkar itama tabi layi.
a lokacin da take fad'amin zatayi aure na nuna bak'in cikina sosai saboda inason sumayya banaso inga abinda zai rabani da ita, daga k'arshe koda tayi aure ni nadinga hure mata kunne akan kar tayi ma mijinta biyayya duk wani abu da sumayya takeyi da sa hannuna a ciki saboda bata iya tsallake maganata, hatta pills ni nasakata tana sha duk dan kar tahaihu saisa kukaga bata ta6a ko 6atan wataba,
ahaka nacigaba da bibiyarta gidan aurenta mukacigaba da harkarmu batare da tsoron komai ba sai gashi lokaci guda dubunmu tacika ankama mu muna aikatawa.
Dan Allah tunda na fad'a maka gaskiya kabarni intafi wlh bazaku k'ara ganin ko k'eyataba nima  nadaina.

Gabad'aya matan da suke d'akin kuka suke, sultana sadiya cikin kuka tace Allah ya isa ashe kece kika 6atamin d'iya.
sumayya girgiza kai tayi tace zinat babu abinda zance miki saidai kawai kije munhad'e gobe k'iyama gaban ubangijinmu ammah hakanma nagode da kika wankeni a wajen dangina.

Sultan abbas murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace kema sumayya harda laifinki a ciki nasha kwatanta miki akan kibi rayuwa a sannu ammah rawan kanki ya hana daman ita rayuwa *DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA* shi ruwa kan doka dan haka kije gashinan duniya ta nuna miki hankali daman ita duniya ta ishi kowa riga da wando.

Sultan ahmad da memartaba shuru sukayi kamar ruwa ya cisu

Yarima kud'i yad'auko yamik'a ma zinat batare da ya k'irgasuba yace nabaki minti ukku kifita kibar gidannan ko k'eyarki kar kibari ink'ara ganinki.

cikin sauri zinat takar6i kud'in gudu-gudu sauri-sauri haka tafita.

Sai a lokacin yarima yakalli sumayya yace kije kawai sumayya duk abinda kikayi min dan kanki daman tuni nagano haka kawai dai gudun kar zargi yashiga tsakaninmu shiyasa ban ta6a magana ba ammah yanzu Alhmdllh da gaskiya tabayyana

Rik'o hannunsa tayi cikin kuka tace dan Allah suhail kataimaka kayafemin ba dan halinaba ko na sami sauk'in abinda nakeji.

Fizge hannunsa yayi, ganin haka yasa zarah cikin kuka tace dan Allah kataimaka kayafe mata tunda ta gane laifinta kuma kunji batada laifi a ciki.
murmushi yarima yayi yace shikenan dear ta ci albarkacinki nayafe mata.

Cikin jin dad'i tace nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, koda taje wajen zarah tunkan tayi magana zarah tace kar kice komai sumayya ni tuni na yafemiki daman ban rik'ekiba.

haka sumayya tazagaya wajen kowa tanemi gafararsa kowa yace ya yafe mata cikin jin dad'i tayi musu godia.

memartaba sai a lokacin yayi magana yace toh Alhmdllh tunda anyafe ma juna, dan haka yanzu wannan ya kamata yazama darasi ga kowa, kekuma sumayya yanzu tunda kin nuna kin tuba kicigaba da neman gafarar ubangiji akan abinda kika aikata sannan kicigaba da zama har Allah yakawo miki miji kiyi aure.

Cikin jin dad'i sumayya tace toh nagode sosai ranka yadad'e.

Memartaba kallon yarima yayi yace suhail ga part d'inku chan nasa angyara maku zaku koma kucigaba da zamanku guards d'inka da ma'aikatanku duk suna nan.

Sosa k'eyarsa suhail yayi yace ranka yadad'e da gidana da nagina naso inkoma da zama idan ka amince.

Girgiza kai memartaba yayi yace a'a suhail kar kayi haka kayi hak'uri kucigaba da zama nan kusa da ni dan hankalina ya fi kwanciya da haka.

murmushi yarima yayi yace toh ranka yadad'e yadda kakeso haka za'ayi.

Toh masha Allah, Allah yasafke matarka lafiya, idan da me magana sai yayi.
gabad'aya shuru sukayi alamun babu memagana dan haka memartaba yasa sultan ahmad   yarufe taron da addu'a aka sallami kowa yawatse cike da farin ciki da jin dad'i.




_Comment_
     *Nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_
[5/2, 5:19 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

*PAGE* 6⃣9⃣

Yarima koda sukaje 6angarensa da mamakinsa yabi ko'ina da kallo yaga angyara sosai duk anzuba masu sabbin ma'aikata da bayi, koda yaje part d'insa tsaye yatarar da guards d'insa nan suka zube suka kwashi gaisuwa, amsa musu yayi cikin sakin fuska sannan yawuce yashiga ciki komai a gyare yake fes, murmushin jin dad'i yayi dan shi kansa yasan memartaba yana sonsa sosai.

Zarah ma koda tashiga part d'inta nan kuyanginta suka kaure da murna da jin dad'in ganinta harda d'an kukansu.

Zama Zarah tayi suka gaisa cikin mutunta juna sannan tatashi tashiga bedroom d'inta ko'ina a gyare yake fes nan aka shigo mata da kayanta, saida tayi wanka tai sallah sannan tashirya nkayanta cikin watdrobe daganan tabi lafiyar gado takwanta nan bacci yai awon gaba da ita.

Sumayya ma wajen sultana bilkisu tacigaba da zama inda sultana bilkisu tacigaba da kula da ita cike da tausayinta.

Yarima bayan yagama shirinsa cikin shigarsa ta alfarma yafito a yarimansa sak fitowa yayi inda yatarar da shaheed yana jiransa saida suka k'ara gaisawa cike da jin dad'in ganin Juna sannan suka d'unguma zuwa fada.

Suna shiga nan duk mutanen da suke ciki suka zube Suna kwasar gaisuwa haka yacigaba da amsa musu cikin sakin fuska daga k'arshe da yagaji sai yakoma d'aga musu hannu ahaka suka isa har chan wajensu memartaba da waziri sai iyayensa da suke zaune, cikin girmamawa yaduk'a yagaishesu suka amsa masa sannan yaje yazauna kujerarsa da aka tanadar mashi sai kujera ta kusa da tashi shaheed yazauna.

Bayan jama'a sun nutsu memartaba lasifika yakar6a ahankali yai sallama sannan yafara yi musu godia akan addu'o'in da sukayi masa daga k'arshe yak'ara bayyanar masu da Yarima da yadawo sannan yak'ara shaida musu akan shine magajinsa ko bayan ransa.

Nan fada tarud'e da murna da kabbara cikin jin dad'i, bayan ya gama bayani yatambayi Yarima ko yana da magana nan Yarima yagirgiza kai.

Waziri ne yakar6i lasifikar yak'ara yi ma jama'a godia sannan yanuna farin cikinsa akan samun lafiyar memartaba yakuma yi murna akan bayyanar Yarima daganan yaba wasu fadawa umurni akan suje susa akawo abincin da yasa ashirya a gidansa saboda gaggarumar walima yahad'a yanaso kowa yaci yanuna farin cikinsa.

Haka akaje akazo da abincin me rai da lafiya aka zuba ma kowa na cikin fadar hatta su memartaba saida akasa masu nasu, bayan angama nan akaba kowa umurni yaci nan jama'a aka shiga ci ana jinjina ma karamcin wannan masarauta hatta su memartaba da shi kansa waziri sunci.

Shaheed ne ganin suhail baya ci yasa yata6osa yace kaci man.

Murmushi Yarima yayi yace na k'oshi, harararsa shaheed yayi yace ammah kasan bazasuji dad'iba idan sukaga bakaciba.

Jin haka yasa Yarima yad'ebo abincin cikin izza yaci, cokali biyar yayi yature abincin yajanyo wayarsa yashiga dannawa.

Bayan kowa ya gama nan sarki ya amshi lasifika yanuna godiarsa ga waziri sannan yad'auko wata alkyabba da rawani masu kyau yadamk'a ma Yarima.

Kar6a Yarima yayi cikin jindad'i sannan yanuna godiarsa, daga k'arshe yayi ma su memartaba sallama yaja shaheed suka fita, motarsa suka shiga suka nufi hospital d'insa.

Lokacin da ya isa sosai staffs d'insa suka nuna farin cikin dawowarsa, dr khalil ko rungumesa yayi cikin jin dad'i.
Yarima farin ciki yayi sosai alokacin da yaga komai yana tafiya daidai nan yanuna jin dad'insa tare da  godia ga manyan staffs d'insa.

Bayan sallar isha'i bayan ya gama shirinsa na bacci saman gadonsa yahau yakwanta kad'an kad'an ya duba lokaci yayi tsaki ganin har wajen k'arfe tara ammah zarah batazo part d'insaba, daga k'arshe mik'ewa yayi yasaka alkyabbarsa sanan yafito yanufi part d'inta.

Koda yashiga babu kowa a parlour dan haka yawuce bedroom d'inta, kunna gloves yayi nan yahangota tsakiyan gado ta baje sai baccinta takeyi, murmushi yayi sannan yai light off yawuce yanufi saman gadon yahau yakwanta a gefenta.
Janyota yayi jikinsa yarungume ahankali tabud'e idanunta cikin muryar bacci tace bakayi bacci ba daman?

Uhm taya zanyi bacci bayan baki lek'aniba tunda muka dawo nifa ban yadda adinga nisa da niba dan ina buk'atar kulawa,

K'ara shigewa jikinsa tayi tace kayi hak'uri d'azun saida naje lokacin ka fita insha Allahu bazan dinga nisa da kaiba yanzu ma dan a gajiye nake saisa nakwanta.

Kina gudu kar inyi miki wani abu ko saisa bakijeba?
Marairaice murya tayi tace bahaka nake nufiba kawai dai baccine da gajiyar tafiya ammah nima naso inzo.
na k'i wayon naki yanzu dai kiyi baccinki babu abinda zanyi miki
K'ara tura kanta tayi cikin k'irjinsa tana murmushi.

Washe gari zarah part d'in yarima taje tagyara fes ko a gyare yake sannan tahad'a masu breakfast, bayan sun gama breakfast a part d'in yarima fitowa tayi tabarosa yana waya takoma part d'inta,

wardrobe d'inta tabud'e tad'auko wayanta takunna cikin jin dad'i tahau saman gadonta takwanta sannan tayi dialing d'in number d'in abbah ammah har ta k'arashi ringing baiyi picking ba dan haka talalubo ta mama, tana fara ringing mama tayi picking cikin Jin dad'i zarah tagaisheta nan mama ta amsa tace d'iyata ba dai kun dawoba.
Eh mama mundawo dafatan kuna lafiya? Ya su yaya rauda? Na kira wayan abbah ammah baiyi picking ba
Murmushi mama tayi tace duk muna lafiya nima sa'a kikayi wayartana hannuna kinsan yau ake d'aura auren Aisha.

zumbur zarah tayi tatashi zaune tace yau kuma mama? Shine baku fad'amana ba.

Haba zarah ke ai mun d'auke miki zuwa tunda kinyi nauyi yanzu, kuma shi suhail ai yana sane da maganar bikkin tunda kusan kullum muna gaisawa, kima tayamu godia a wajensa dan ya turo mana gudunmawa dasu mukayi ma Aisha siyayyar kayan d'aki kedai kinyi sa'ar miji mekirki saidai muce Allah yabiyasa.

Zarah kwallah ce tacika mata ido koda taji dad'in abinda yarima yaima iyayenta saidai abun yaimata ciwo da ba'asanar da ita yau ake bikkin Aisha ba, cikin fushi tace gaskiya mama ba'a kyauta minba ace ana bikkin 'yar uwata ammah ba wanda zai iya fad'amin.

Haba zarah kuda bakunan kiyi zamanki kawai kihuta, yanzu dai bari inje inji da bak'i munyi waya anjima,,,,mama batajira jin abinda zarah zataceba takashe wayarta.

Nan zarah takira yaya rauda waya, yaya rauda tana yin picking zarah cikin fushi tace haba yaya rauda yanzu saboda Allah kun kyauta min ace yau ake bikkin Aisha ammah banda masaniya.

dariya yaya rauda tayi tace toh sarkin tsogumi kuda baku gari taya zamu fad'a miki bayan babu waya a wajenki kuma mijinki ai ya sani tunda har gudunmawa yaturo, abbah ne yace kar yafad'a miki dan ya san halinki matsamasa zakiyi sai kunzo.

Hawaye suka fara fita daga idanun zarah cikin muryar kuka tace toh ai yanzu mundawo kuma sai nazo ko bakuso.

Dariya rauda tayi tace wannan tsakaninki da mijinki ne mudai babu ruwanmu.

Cikin jin haushi zarah takashe wayarta nan takife kanta tafara rera kuka.

Wajen k'arfe d'aya yarima yagama shirinsa yafito yanufi part d'in zarah a bedroom yasameta ta kife kanta, kallonta yayi yace baby bacci kike?

'Dagowa tayi takallesa sanye yake cikin galilarsa maroon colour ya yi gwanin kyau, fuskarta a d'aure tace ina zakaje?

Da mamaki yake kallonta yace ikon Allah yau kuma tambayata ake inda zanje saikace mace?

Shuru zarah tayi tare da janye idanunta daga kallonsa cikin muryar kuka tace gaskiya baku kyauta minba wai ana bikkin Aisha ammah banda masaniya alhali kai kana sane, koda ace ba barina zakiyi injeba indai kafad'amin ko addu'a nayi musu ai yayi,,,tak'arashe maganar cikin kuka.

Takowa yarima yayi yazo kusa da ita yazauna cikin sauri zarah tajuya mashi baya.
murmushi yayi cikin rashin damuwa yace zarah kinsan dai babu yadda za'ayi mudawo jiya sannan aganki yau kinfita kuma ga ciki.

Toh ai fitar kamawa take kuma ko yayane nad'an lek'a ai yafi banjeba.

Kibari bayan bikki sai inkaiki kiyi mata wuni.

mak'e kafad'a tayi tare da k'ara sautin kukanta.

Dafe kansa yayi da hannu biyu dan babu abinda yatsana sama da jin kukanta ahankali yace toh shikenan yanzu tashi muje kilek'a da an d'aura aure zan d'aukoki mu dawo.

Juyowa tayi tana share hawayen fuskarta tace dagaske kake?

Murmushi yayi yace toh ya zanyi.

Rungumesa tayi cikin jin dad'i tace nagode sosai hearty ka gama min komai.

Janyeta yayi daga jikinsa yace yanzu dai yisauri kishirya kinsan k'arfe biyu za'a d'aura auren mik'ewa zarah tayi tahau cire kaya tace please bari ind'an watsa ruwa ba zan dad'eba.

Yanzu har sai kinyi wanka ina nan?
Turo baki tayi tace duka fa minti ukku zanyi.

Hmm toh shikenan ammah indai kika dad'e saidai kifito kitarar baninan.

Bama zan dad'eba insha Allah,,,,cikin sauri taje tashiga wanka, bata wani dad'eba tafito d'aure da towel dan tasan halin kayanta zai iya tafiya yabarta,,,d'ago kai yayi yakalleta sannan yamaida idanunsa akan wayarsa da take hannunsa yana dannawa.

Gaban dressing mirror tazauna tayi simple makeup sannan tamik'e tanufi wajen wardrobe d'inta kallon kayan da suke jikin yarima tayi tai murmushi sannan tad'auko shadda marron gown wadda tasha aiki da pink d'in zare tasaka, gaban dressing mirror tazo tamurza d'aurin kallabi sannan tad'auko veil da hand bag da takalmi duk pink colour tasaka, k'ara feshe jikinta tayi da turare sannan tayi masa gyaran murya.

juyowa yayi yakalleta nan tasakar masa murmushi, zuba mata ido yayi yana kallonta bai ko k'yaftawa, kashe masa ido d'aya tayi tare da d'aga gira tace nayi kyau ko?

Janye idanunsa yayi daga kallonta tare da mik'ewa tsaye yace muje, rik'o hannunsa zarah tayi tare da langwa6e kai tace bakace nayi kyauba.
Cize le6e yayi sannan yace ba laifi ammah da hijab kika ssnya da zakifi yin kyau.
Jin haka yasa zarah tawuce gaba gudun kar yace sai tasa hijab, murmushi yarima yayi sannan yabiyo bayanta.

Cikin motarsa suka fita, suna cikin tafiya zarah kallonsa tayi tace sunfa tashi daga wanchan gidan na mance ban tambayesu inda suka komaba.

Batare da ya kalletaba yace ba sai kin tambayesuba na san gidan abbah yaimin kwatance.

Gaban wani madaidaicin gida yai parking ganin mutanen da suke shige da fice yasa yagane nan ne gidan.

K'ik'irin bud'e k'ofa zarah take cikin zumud'i, rik'ota yarima yayi yace zan fa dawo ind'aukeki da and'aura aure.

Langwa6e kai tayi tai kalan tausayi cikin kwantar da murya tace please kabari sai dare.

Ta6e baki yarima yayi yace na dai fad'a miki.
Toh naji,,cewar zarah tare da bud'e k'ofar tafita nan kallo yadawo wajenta daman jira ake aga wanda zai fito daga motar, ratsa mutane tayi tashiga cikin gidan nan suka gaisa da mutane, yanayin tsarin gidan ya burgeta koda flat house ne med'auke da d'akuna ukku, dakyar tagano mama nan tarungumeta tana murna itama mama murna tayi sosai nan tatambayeta jikinta da mutanen gida.

Alhmdllh duk suna lafiya cewar zarah, nan tagaishe da abokan mama daganan tawuce d'ayan room d'in da taga abokan amarya suna shiga rumgumeta su yaya rauda da Aysha sukayi cike da jin dad'in ganin 'yar uwartasu itama zarah rungumesu tayi cikin jin dad'i, nan suka baje suna hira, Aisha kamar ba ita bace amaryar dan sakin jikinta tayi sukai hira sosai da zarah saida taji ana gud'a ana shelar and'aura aure sannan tadawo hayyacinta harda d'an kukanta.

Bayan sallar la'asar akasa amarya tashirya nan zarah tazage taimata kwalliya tashiryata sosai tayi kyau sannan aka tafi da ita wajen su mama dan suyi mata nasiha, zarah komawa tayi takwanta saman gado sukacigaba da hira da yaya rauda.

wajen k'arfe biyar akace amarya tafito atafi da ita dan dama abbah ya ce dakansa zai kai d'iyarsa saisa ba wanda yasa ran tafiya.

zarah fita tayi suka gaisa da abbah nan tatarar da yarima wajensa, bayan sun gama gaisawa yarima yace tafito sutafi, ba dan ta so ba haka tashiga tayi sallama da su mama taja yaya rauda gefe tad'auko cheque d'in 1 million tabata tace taba su abbah gudunmawarta ne.

Koda suka kama hanyar gida fushi kawai take a mota dan taso yarima yabarta takai dare.

Dariya yarima yake ciki-ciki har suka isa, yana yin parking batajirasaba tashige gida.

Bayan sallar isha'i yarima kiranta yayi a waya, zarah tana kallon wayar kamar bazata d'aukaba saida takusan tsinkewa sannan tayi picking  batare da tayi maganaba.

Baby please kikawo min coffee insha yunwa nakeji.
umhum kawai tace takashe wayarta.

Nan tatashi tashiga kitchen saida tasoya mashi kwai sannan tahad'a mai coffee tad'aura saman tray, komawa tayi bedroom d'inta tak'ara gyara jikinta sannan tad'aura alkyabba saman sleeping dress d'inta.

Kuyangarta d'aya  taba tray d'in tad'auka nan suka nufi part d'in yarima.

Guards d'insa tun kan ta iso suka bud'e mata k'ofa nan suka russuna cikin girmamawa suka gaisheta, amsa musu zarah tayi takar6i tray d'in da yake hannun kuyangarta tashiga.

Ganin baya a parlour yasa tanufi bedroom d'insa tare da yin sallama ciki-ciki, yarima da yake zaune yana waya ganin yadda tahad'e fuska yasa yad'anyi murmushi sannan yacigaba da wayarsa.

Wucewa zarah tayi chan gefensa tad'aura saman bedside sannan tajuya zatabar d'akin.

Janyota yarima yayi tafad'o jikinsa nan yai sallama yakashe wayar tare da kallonta yace baby haka ake ba miji abu?
Fuskarta a d'aure tace toh me kakeso inyi maka bagashinan na aje makaba ni kabarni intafi.

Hmm ammah ai kinsan agajiye nake kuma ga yunwa ina ji indai kinaso insha saidai kibani dakanki,,,yak'arashe maganar tare da kashe mata ido d'aya.

Kallonsa zarah take cikin k'ulewa tace chab ashe ba yunwar kakejiba.

Shima yarima idanunsa a kan fuskarta yace indai ba zaki baniba kid'auki kayanki kiyi tafiyarki na k'oshi.

Jin haka yasa zarah tad'auko cup d'in takai masa a baki, yarima kallonta yake yadda take cika tana turo baki, hannunsa yad'aura saman cikinta yana shafa.

sharesa tayi tacigaba da bashi nan tad'ebo wainar kwai takaimasa a baki, ahankali yake ci, ta k'ule sosai ganin yadda yake ci kamar ba ya so kuma ahaka wai yunwa yakeji.

Bai wani yi cin kirkiba yajanye kansa alamun ya k'oshi.

harararsa tayi tace daman ba wata yunwa da kakeji dukafa rabin cup d'in kasha.

Toh baby naga kamar ba'aso insha saisa nahak'ura yanzu dai tashi muje toilet kiwanke hannunki.

Tashi zarah tayi sukaje toilet saida yai brush ita kuma tawanke hannunta sannan suka fito.

Suna fitowa yarima janyo zarah yayi jikinsa yace baby kayannan sunyi miki yawa bari inrage miki ko alkyabbarce.

Harararsa tayi tace ni kakyaleni tafiya zanyi.
Tallabo fuskarta yayi yace baby please yakamata fushin yak'are hakanan Indai gidane kibari insha Allahu idan kin haihu zan kaiki kinga fushin nan da kikeyi yana ta6amin zuciya nasan shima babynmu bayajin dad'in yadda mummynsa take ma dadynsa yakamata kitausayamin,,,yak'arashe maganar tare da cire mata alkyabba sannan yarik'o hannunta yace muje kiji wata magana.

Turo baki tayi tace ni nasan ba wata magana da zaka fad'amin wayau kakeson yi min, kwanciya yayi tsakiyan gadon sannan yamik'a mata hannu alamun tazo.

Rik'o hannun nasa tayi nan tahau yajanyota a jikinsa yakwantar da ita nan yashiga shafa mata baya, a kunnenta cikin wata irin murya merikitar da ita yace baby please fushin yak'are hakanan kinji?
'Daga masa kai tayi alamun toh, nan yacigaba da shafa mata baya yana lasar kunnenta cikin wata irin siga da yasa zarah tafara sakin layi, ahankali yasalu6e mata riga.

Sanin halinta yasa yadinga binta ahankali ammah duk da haka saida tayi masa raki.

washe gari koda suka tashi yarima tarairayata yayi sosai har saida yaga gabad'aya ta safka daga fushin da take.

Bayan sungama breakfast zarah d'aid'aya tayi bisa yarima tana ta zuba masa shagwa6a akan kar yafita, kan dole yahak'ura yazauna nan sukaita soyewarsu, sai wajen azuhur sannan memartaba yakirasa yafito fada nan zarah tasamu talalla6asa ya amince akan zataje tagaishe da su ummi, nan kuyanginta suka take matabaya zuwa   wajensu ummi.
Saida tafara zuwa turakarsu dada sosai dada tanuna mata kulawa, daganan tawuce wajen sultana sadiya nan ma sultana sadiya tarasa inda zata sanyata saboda farin ciki, duk nok'e-nok'en zarah saida sultana sadiya tasamu tad'an saki jiki suka yi hira, kwad'on zogale sultana sadiya tasa akayi mata nan Zarah tazauna taci sosai, tarairaya tasamu sosai ita kanta zarah tajidad'in yadda tayi mata ta dad'e a nan sannan tayi mata sallama taje wajen ummi a chan parlour tagamu da sumayya tayi matashin kai da cinyar ummi suna hira dan gabad'aya sumayya tadawo wajen ummi ammah duk da haka tana lek'awa wajen iyayenta da dada koda a yanzu ba kamar da ba sun sake mata.

Ganinta yasa sumayya tatashi zaune cikin jin kunyarta.
Zarah cike da girmamawa tagaishe da sultana bilkisu, cike da so sultana ta amsa mata tare da tambayarta jikinta da gida.
cikin jin kunya tace Alhmdllh sannan tajuyo tace Aunty sumayya ina wuni?
Amsa mata sumayya tayi batare da ta d'ago ta kalletaba saboda kunyarta da takeji.
ummi ce tace Zarah kizauna saman kujera man kin zauna k'asa.
Ummi nan ma ya yi nafi jin dad'in k'asan...tafad'i hakan cikin jin nauyinta.
Murmushi sultana bilkisu tayi tace toh lafiya lau, ya gida da hidima? Ashe bikkin k'anwarki akayi wlh bamusaniba ai da mun lek'a.
Eh ummi daman saida mama tayi min magana tace lokacin taji ance memartaba baida lafiya saisa bata aiko maku da invitation card ba.
ayyyah Allah sarki toh Allah yabada zaman lafiya.
ameen ummi.

nan ummi tak'walama wata kuyangarta kira tace akawo ma Zarah kayan motsa baki.
Duk'ar da kanta zarah tayi tace ummi subarsa kawai ak'oshe nake.
a'a zarah baridai sukawo miki.
kafin kace mi nan aka cika gaban zarah da kayan marmari da abinci, mik'ewa sultana bilkisu tayi tace ina zuwa nan tawuce tashige bedroom d'inta.

sumayya kallon zarah tayi a karo na biyu ahankali tace zarah zan k'ara rok'onki akan abubuwan da nayi miki dan Allah kiyi hak'uri.
kallonta zarah tayi cike da tausanta tace wlh Aunty sumayya ko kad'an ban rik'ekiba kuma ai komai ya wuce please kidaina tunawa.
k'wallah ce tacika ma sumayya ido tace hmm zarah taya kike tunani zan iya mance cin mutuncin da nayi muku, wane irin makircine banyiba akanki ammah daga k'arshe kinga yadda rayuwa takoma min nayi wasa da damana ni kaina ina jin haushin wannan halin da najefa kaina.

girgiza kai zarah tayi tace Aunty sumayya kidaina cewa haka kema fa wasu abubuwan kowa yasan ba laifinki bane, kuma ko ba hakaba ni wlh tuni na yafe miki.

Share k'wallar idanunta tayi tace nagode sosai zarah Allah yasaka da alkhairi, Allah yasafkeki lafiya.
Nan suka d'an ta6a hira kad'an-kad'an ganin marece ya yi yasa taje tayi ma ummi sallama tafito sukai sallama da sumayya tawuce part d'inta.

cike da sha'awa sumayya tabita da kallo tanaji ina ma ace itace da cikin hawayene suka shiga gangaro mata alokacin da tatuno zuwa hospital d'in da sukayi da ummi aka tabbatar mata bazata ta6a haihuwaba saboda pills d'in da tasha da injections d'in da take na tsawon lokaci sun6ata mata mahaifa, kukane yaso yakubce mata cikin sauri tatashi tashige room d'inta tafad'a saman gado saida tasha kukanta me isarta sannan taje tawanke fuskarta tare da d'auro alwallah, nan tashimfid'a darduma tad'auko alk'ur'aninta takaranta.

Zarah koda takoma part d'inta a parlour tayada zango nan kuyanginta suka zagayeta suna mata hira, haka tabiye musu har aka kira sallah sannan tamik'e taje tayi alwallah tai sallah.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya yarima yana tafiyar da aikinsa, a gefe guda kuma ga mulki dan memartaba yanzu bai cika bari yai nisa da shi ba dan a kullum cewa yake nan ba da dad'ewaba ko rai yayi halinsa kokuma insafka daga kan karagar kahau dan gabad'aya yanzu shekaru sunja sosai,,,a duk lokacin da yake maganar yarima yanaji babu dad'i a ransa, shi kansa waziri idan yaji memartaba yai furucin cewa yake a duk lokacin da mulkinka yak'are toh nima nawa ya k'are dan haka dole waziri mejiran gado shima yadinga yawan zaman fada, haka ake matsama yarima da shaheed suna zaman fada sosai.

Zarah sosai take samun kulawa daga wajen dangin yarima, dan sultana sadiya da sultana bilkisu kullum sai sun kirata a waya sun tambayi lafiyarta dan wani lokacinma sultana sadiya da kanta take zuwa tadubata takawo mata abubuwan da tasan meciki tana buk'atar ci dan Zarah kulawa take samu sosai a wajenta kamar yadda zata kula da sumayya.

A 6angaren Dada ma tana aikowa aduba mata lafiyar Zarah kuma tanayi mata aike da kwad'on ganye iri-iri.

su kansu su rahama yanzu wani irin kulawa sukeba zarah dan nan da nan zarah tasaba da rahama.

Yanzu sumayya danginta sun sake suna nuna mata kulawa sosai shima saida sultan ahmad yak'ara tunatar da su akan batada laifi fa sosai tunda da sa hannun zinat take wasu abubuwan, nan suka fara janta a jiki ammah duk da haka sumayya tayi sanyi sosai dan yanzu batada yawan magana.

*BAYAN WATA 'DAYA*

Sumayya ce tafito daga room d'inta dasafe da mamakinta taga su ummi suna ta zirga-zirga da shirye-shirye cike da girmamawa tagaishe da ummi, fuskar ummi a sake ta amsa mata.
murmushi sumayya tayi tace ummi bak'i zamuyine naga kuna ta shirye-shirye?
Kedai bari sumayya wlh wani d'an yayanane zaizo daga agadaz zaikawo min ziyara dan rabonsa da garin nan tun yana k'arami lokacin da nahaifi husna akazo da shi.

Murmushi sumayya tayi tace Allah sarki Allah yakawosa lafiya.
ameen daughter yanzu dai je kiyi breakfast muma ai mungama komai dan ina sa ran nan da awa biyu zai safka.

Bayan ta gama breakfast d'inta zaune take ita kad'ai a parlour hannunta rik'e da hisnul muslim tana dubawa, sallamar da akayine yasa tad'ago kai takallesa tare da amsa masa sallamar.
Wani matashi ne wanda ak'allah bazai gaza shekaru talatin da shidda ba sanye yake cikin manyan kaya yanayin kamaninsa yasa tagane shine wanda ummi tace mata zaizo, ido yazuba mata yana kallonta, ganin kallon ba mai k'arewa bane yasa tagaisheshi.
tattare nutsuwarsa yayi sannan ya amsa tare da tambayarta ya gida?
Lafiya lou sumayya tace sannan tamik'e zata wuce room d'inta.

Gyaran murya yayi yace am ummi fa tana nan?
Batare da ta juyoba tace eh bismillah kazauna bari inmata magana, tana fad'in haka tawuce tanufi part d'in ummi tasanar da ita zuwan bak'on sannan tafito tawuce room d'inta.

ummi koda tafito cikin jin dad'i tace oyoyo yau ga salim mutanen agadaz dakansa ya kawo mana ziyara.

Murmumushi wanda takira da salim yayi tare da d'an zamowa daga kujerar da yake zaune yace ummi ina wuni.

Lafiya lou salim ya gida da mutanen gidan dafatan kowa yana lafiya.
lafiya lou ummi.
masha Allah toh ya k'arin hak'uri? Ayi dai hak'uri ban samu nadawo ba bayan sadakar ukku, ni ina ji tun ma lokacin rabona da agadaz.
Alhmdllh ummi ai bakomai.
masha Allah toh Allah yajik'anta, Allah sarki khadija mutuniyar kirki Allah dai yasa ta huta, ina yaran naku ina fatan suna lafiya?
Duk suna lafiya.
toh masha Allah, Allah yaraya mana su,

Ummi kira tashiga k'walah ma sumayya, fitowa tayi sanye da hijabi a jikinta tace ummi gani.
murmushi ummi tayi tace sumayya wannan shine bak'on nawa matsayin yaya yake a wajen su yarima kije kisa su kuyanga zinnira sushurya masa abinci.
Kallon bak'on tayi da a yanzu ma yatsareta da ido ahankali tace sannu da zuwa ina wuni?
Murmushi yayi yace lafiya lou ya gida?
Batare da ta bashi amsaba tawuce taje tabada umurni akawo masa abinci daganan tawuce wajen dada.

Cika masa gabansa akayi da abinci iri-iri ci yake ammah gabad'aya hankalinsa yana ga k'ofa.

Bayan ya gama kallon ummi yayi yace ummi wai ina prince? Kinsan bana k'asar akayi bikkinsu shi  da rahama.

Murmushi ummi tayi tace duk suna nan lafiya lou yanzu ma zaka ganshi dan na fad'a masa zakazo, ina fata dai ka dawo k'asarka ta haihuwa kenan bazaka koma india ba, haba salim mutuwa ai bata wuce kowaba yakamata ace zuwa yanzu ka cire khadija aranka tunda wanda yabaka ya kar6i kayansa shekara biyu da wani abu fa kenan yanzu, kadaure kayi aure karik'e 'ya'yanka ukku wajenka suma sutaso hannun iyayensu, dan su yaya munir hankalinsu ba a kwance yakeba basuda buri dayawuce suga ka saki ranka ka canza aure, d'azun koda yakirani a waya cewa yayi ink'ara kwatanta maka, kaifa salim ba yaro bane kai yakamata kakwatanta ma wasu.

Ajiyar zuciya salim yasafke yace insha Allahu ummi zanyi aure dan a lokaci guda wata ta fara canza min tunani.

Cikin jin dad'i ummi tace masha Allah wace me sa'a ce haka?

Dariya salim yayi yace ummi kuma a wannan garin naku daga zuwana yau d'innan.
Gyara zama ummi tayi tace salim fad'amin inda take insha Allahu zanje dakaina insami iyayenta.

Dariya salim yayi yace ummi kima kwantar da hankalinki ba wata bare bace nidai fatana Allah yasa ba matar aure bace.
Toh Alhmdllh tunda 'yar gida ce wacece ita?

Duk'ar da kansa yayi alamun jin kunya sannan yace ummi ba wata bace face wadda nagani nan wlh ummi tunda nashigo taburgeni Allah dai yasa batada aure.

Murmushin jin dad'i ummi tayi tace in na fahimceka sumayya kenan kake nufi?
Eh ummi ita indai zaku bani ita toh wlh na amince zanyi aure.

Cikin jin dad'i ummi tace toh sumayya dai ta ta6a aure ammah a yanzu basu tare sa mijin nata Indai har kana sonta tsakani ga Allah toh nikuma insha Allahu zan sameta muyi magana.

Shima Cikin jin dad'i yace wlh ummi ina sonta kuma zan kular muku da ita, da gobe naso inkoma ammah a yanzu na canza ra'ayi har sai ta amince sannan zan bar garin nan.

Jinjina kai ummi tayi alamun gamsuwa sannan tace toh Allah yashige mana gaba.
Salim yace Ameen.

Koda yarima yashigo zama yayi sukasha fira cikin jin dad'in ganin d'an uwannasa kuma babban yaya dan dama tun yana karatu a india ummi tahad'ashi da shi.
Yarima fita sukayi tare suka zagaya gari yanuna masa wurare sai dare suka dawo gida.

Bayan sallar isha'i sumayya zaune take ta gama shirin bacci tana  duba wasu addu'o'i.
Ummice taturo k'ofan tashigo tare da yin sallama.

Murmushi sumayya tayi ta amsa mata tare da fad'in sannu da zuwa ummi.

Yauwa daughter nan tazauna bakin gadon tare da kallon sumayya tace daughter daman bakiyi bacci ba?
Eh ummi ammah yanzu nake shirin yi.
Ohk ya yi kyau ammah inaso kitaimaka kiban aron hankalinki zamu d'anyi magana, gyara zamanta sumayya tayi tace toh ummi.

Ummi ma fuskantarta tayi tace sumayya aganina yakamata ace wannan lokacin kinyi aure indai kina da wanda kikeso yake sonki saidai idan babune shine sai kizauna har sai Allah ya kawo.
Murmushi sumayya tayi cikin jin kunya sannan tace ummi ai har yanzu babu wanda mukeson juna.
Murmushi itama ummi tayi sannan tace toh sumayya Allah yakawo, sai kuma  tayi shuru kamar metunani sai chan tace am yauwa sumayya d'azun salim ya tuntu6eni akan maganarki ya nuna min yana sonki sosai indai zaki bashi dama sai yagabatar miki da kansa.

Gaban sumayya saida yafad'i cikin damuwa tace ummi ya za'ayi in amince masa daga ganinsa ba irina bane ko kin mance abubuwan da na aikata kuma fa doctor ya ce ba zan ta6a haihuwa ba taya kike tunani zai iya aurena,,,,tak'arashe maganar hawaye suna zuba daga idanunta.

Ummi cike da tausayinta tarungumota jikinta tace sumayya kidaina cewa haka tunda kin tuba ai Allahu gafururrahim ne, sannan da kike maganar haihuwa kikwantar da hankalinki nasan salim Indai yana sonki toh zai iya aurenki ahaka dan shima yana da yara ukku marayu da mahaifiyarsu ta mutu tabari shekara biyu da wani abu kenan kizauna kiyi tunani ko ma ince zuwa gobe kibashi dama kuhad'u kuyi magana dan jibi yakeson barin garin, ammah Indai baiyi mikiba kar kiji komai kisanar da ni kinji ko?

'Daga kai sumayya tayi nan ummi tamik'e tace kikwanta kiyi bacci kar kisa damuwa a ranki kinji ko?
Ahankali tace toh ummi.
Murmushi ummi tayi tace sai dasafe dota.

Bayan ummi ta fita sumayya zama tayi taita tunani akan maganar ummi ta dad'e ahaka sannan dagabaya takwanta tai bacci.

Wanshe kare wajen 11am bayan ta gama breakfast fitowa tayi parlour dan tayi kallo, zaune ta tadda mutum shi kad'ai yana kallo, ganinta yasa salim yazuba mata ido, sumayya bataji dad'in had'uwarsuba ahankali tace ina kwana? Amsa mata yayi fuskarsa d'auke da fara'a.
Juyawa tayi zata koma room d'inta nan taji muryarsa ya ce please sumayya in ba damuwa kiban dama yanzu muyi magana.

Tsaye tayi tai shuru batare da ta juyoba, ahankali yak'ara cewa please.

Juyowa tayi batare da tayi magana ba tadawo tazauna bisa d'aya daga cikin kujerun da suke parlourn.
Salim tashi yayi yakoma bisa kujerar da take saitinta yazauna, kallonta yayi da take wasa da yatsun hannunta yai murmushi sannan yace hajiya sumayya ina fata dai ummi ta yi miki bayani akan komai.

Shuru sumayya tayi, ganin haka yasa yace toh ammah duk da haka bari ink'ara miki bayani da kaina agaskiya sumayya tunda naganki jiya naji k'aunarki ta shiga raina, ina sonki tsakani ga Allah idan kin amince sai kiban dama in nuna miki irin son da nake miki dan ni har ga Allah aurenki nakeson yi.
Batare da ta d'ago kantaba tace ummi bata fad'a maka na ta6a aureba?
Kar kidamu indai wannan ne toh ba matsala dan nima na ta6a aure shekara tara kenan  rasuwa matata khadija tayi muna da yara ukku, Al-ameen shine babba shekararsa takwas sai Amina shekara shidda sai autansu Sadiq shekara ukku, indai har kin amince zaki zauna da marayu kikasance uwa agaresu toh insha Allahu bazaki ta6a samun matsala daga garemuba zamu zauna da ke tsakani ga Allah, dan ni tun mutuwar matata ban ta6a tunanin zan k'ara son wata maceba ammah sai gashi cikin k'anganin lokaci na fad'a tarkon sonki.

Cikin tausayi sumayya tace Allah sarki Allah yajik'anta su kuma Allah yaraya su,
Ameen nagode saura inji daga gareki.
Sai a lokacin tad'ago kai takallesa tace ammah fa ni bana haihuwa zaka iya zama da ni ahaka.
Murmushi yayi a karo na biyu sannan yace kar kidamu sumayya ni naji na amince ina sonki kuma muna da su Sadiq gasunan zan mallaka miki su sugama 'ya'yanki halak malak.

Sumayya har cikin ranta taji dad'in maganar da yayi ko bakomai itama yanzu zata fara sabuwar rayuwa....murmushi tayi masa a karo na farko sannan tace kabani lokaci zanyi tunani.

Marairaicewa yayi yace please kitaimaka kizartas da hukunci yau dan gobe nakeson barin garin saboda wani aiki da nabaro kinsan 'yan kasuwa.

Shuru tayi nad'an lokaci sannan tace shikenan zuwa anjima zaka ji ni.
Murmushin Jin dad'i yayi yace toh Allah yasa inji alkhairi.
Ameen tace tare da mik'ewa zata wuce d'akinta har ta fara tafiya yakira sunanta, a nutse tajuyo takallesa,
Marairaicewa yayi yace please ataimaka atausaya min kar ayanke min hukuncin da ba zan iya d'aukaba.
Yanayin yadda yai maganar ya bata dariya nan tajuya tashige d'akinta.

A ranar taje tasamu ummanta tafad'a mata maganar da sukayi da salim, sosai sultana sadiya tanuna farin cikinta tace na tabbata sultana bilkisu bazata ta6a za6a miki abinda zai cutar da keba koda salim d'an uwantane kuma jiya sun shigo tare da yarima mungaisa na yaba da hankalinsa, Indai ya yi miki toh ki amince ki auresa.
Cike da gamsuwa da maganar mahaifiyartata tace toh ummah nagode sosai Allah yaza6a abinda zaifi zama Alkhairi
Ameen sultana sadiya tace nan suka d'an ta6a hira da d'iyartata sai bayan azuhur sannan sumayya takoma part d'in ummi.

Bayan sallar la'asar sumayya ta shaida ma salim ta amince sosai yanuna farin cikinsa tare da yi mata godia, nan suka zauna sukasha hira sama-sama dan rabin hirar duk shi yakeyinta, musanyar number waya sukayi.

Koda akayi sallar isha'i haka yakirata sukasha hira saida yasan yadda yayi tad'an saki jikinta da shi har wajen k'arfe goma na dare suna tare.
Ummi taji dad'i sosai da taga sun amince ma juna.

Hatta memartaba, dada, sultan abbas, sultan ahmad aranar sukasan da maganar salim nan sukayi musu fatan alkhairi.

Washe gari saida suka k'ara gaisawa sosai da sumayya sannan yai musu sallama yakoma tare da yi mata alk'awali zai dawo ba da dad'ewaba, a mota koda yarima zai kaisa airport labarin sumayya kawai salim yake bashi shidai yarima saidai yayi murmushi nan yai musu fatan alkhairi shima.

Tun daga ranar soyayya mai k'arfi ta k'ullu tsakanin sumayya da salim dan ko da yakoma saida yasanar da danginsa nan suma sukayi murna tare da yi masa fatan alkhairi.
Kusan kullum sai ya bata yaransa a waya sunsha hira sosai da sumayya, ita kanta har mamakin kanta take dan bata ta6a tunani zata iya son waniba bayan yarima ammah sai gashi lokaci guda salim ya canzata.

_________________

A lokacin da cikin zarah yacika wata tara cif kulawa sosai take samu a kowane 6angare yarima ko bayaso yana nisa da ita ko da ace yana wajen aiki toh suna manne da juna a waya, bayan 30 minutes batare da ya kirata ya tambayi lafiyartaba.
Kuyanginta ma basu yin nisa da ita indai yarima baya nan dan idan yadawo yaganta ita kad'ai fad'a yake musu sosai, saidai idan bacci zatayi shine take sallamarsu takwanta.

_*BAYAN SATI BIYU*_

Zarah zaune take gefen yarima inda gabanta plate d'in apple ne aje ammah ba ci takeba kad'an-kad'an ta cije le6e, kallon yarima tayi da yake cike wasu files, rik'o file's d'in tayi nan yad'ago kai yakalleta, murmushi tasakar masa tace hearty ka aje hakanan kahuta man tun d'azun fa kaketa abu d'aya kaga dare ya yi kazo muje mukwanta zuwa gobe sai ka ida..

Shima murmushin yamaida mata sannan yace sorry baby ai na kusan gamawa gobe nakeso inje inyi submitting d'insu kiban minti goma kinji?
Kwantar da kanta tayi a kafad'ansa tace toh shikenan hearty ammah minti goma kawai nabaka,
Ohk angama ranki yadad'e.

Bayan ya gama kallonta yayi yace baby muje mukwanta.
Mak'e kafad'a tayi tace ni saidai kad'aukeni mutafi.

Hancinta yaja yace shikenan baby as you wish.

Koda sukaje bedroom Kwantar da ita yayi sannan shima yakwanta, juyawa tayi chan gefen tana murmushi bata ankaraba sai ji tayi ya rungumota ta baya, cikin kunnenta ahankali yarad'a mata baby yau guduna akeyi?
Juyowa tayi takallesa tare da marairaicewa tace bahaka bane hearty wlh ji na nake yau duk wata iri,
Kwantar da kansa yayi a k'irjinta yace baby daman tun d'azun da naga yanayinki nace bakida lafiya ammah kikace lafiyarki lau.
Shafa sumar kansa tayi tace ni lafiya ta lau hearty.
Toh bari ingani idan kina da lafiyar ganin ya d'age mata riga yasa tayi saurin cewa dan Allah kabarni kar kayimin komai.
Murmushi yayi yace toh sarkin tsoro ni ba abinda zanyi miki lafiyar babyna kawai zan duba.
Nan yashiga shafa cikinta tamaida idanunta talumshe tana jin sauk'in ciwon da takeji daman tana daurewane dan kar ta tayar mashi da hankali, ahaka bacci medad'i yai awon gaba da ita.

Yarima ma gefenta yadawo yakwanta tare da rungumota jikinsa.

Cikin baccin ne taji kamar wani abu yana tsikararta firgit tayi tafarka tana jin wani irin ciwo tun daga cikinta zuwa mararta, ahankali tazame jikinta tasafko k'asa tazauna tana murk'ususu nan da nan tafita hayacinta sai hawaye, jin ciwon ba mek'arewa bane yasa tafara kiran sunan Yarima da yake baccinsa.

Cikin bacci yaji ana kiransa ahankali yabud'e idanunsa ganin zarah yayi a k'asa tana ta murk'ususu cikin sauri yasafko daga saman gadon yazo inda take tare da rik'ota cike da tashin hankali yace zarah lafiya?

Hawaye suna fita daga idanunta tajawo hannunsa tad'aura saman mararta, dak'yar tabud'e baki tace ciwo.
Cikin tashin hankali yace bari inzo muje hospital ina tunani haihuwar ce,,,tashi yayi yacanza kaya sannan yad'auko mata zane da hijab yasaka mata, jakkar da suka tanada ta haihuwa yad'auko cikin sauri yax'auko key d'in motarsa sannan yad'auki zarah yafito.

Guards d'insa k'arfan jakkar da take hannunsa sukayi nan suka take masa baya har wajen mota, a back sit yasakata sannan yabud'e mazaunin driver yashiga, kallon guards d"insa yayi yace kar su biyosa, wuta yaba motar tun kan ya isa gate yafara horn cikin sauri megadi yazo yabud'e masa yafita daga masarautar.

Gudu yake sosai cike da tashin hankali ga zarah da take kwance baya tana ta kuka da salati, cikin k'ank'anin lokaci ya isa hospital d'insa, tun kan ya isa yakirasu yasanar da su zuwansa dan haka suna isa yatarar da su suna jiransa nan aka fito da zarah cikin sauri aka turata zuwa labour room.

Dr leemah ce tatsaya kanta, yarima ko gefenta  yatsaya yana taimaka mata cike da tausayin matar tasa, zarah ta sha wahala dan gabad'aya gidansu babu sunan wanda bata kiraba, yarima waje biyu yaraba hankalinsa da wajen lallashin zarah sai wajen ceto babynsa, cikin ikon Allah batafi minti sha biyar tana nak'uda ba tahaifo shantalelen d'anta, Dr leemah ce tayi saurin d'aukesa tamik'a ma wata nurse dan tagyarasa, inda yarima yakoma wajen zarah yana mata sannu batare da ya ga abinda aka haifar masaba.

Hawaye suna fita daga idanunta tana maida numfashi sama-sama ahaka dr leemah tagyarata.

Koda nurse d'in tagyara yaron Dr leemah tafara kar6ansa tana yaba kyaunsa tana cewa wannan prince ne sak yabiyo.

Sai a lokacin yarima yamik'a hannu yakar6esa murmushin jin dad'i yayi tare da furta Alhmdllh, nan yai masa addu'a da kiran sallah, zuba ma yaron ido yayi cike da so, zarah ahankali talek'o yaron da yake hannun yarima saida gabanta yafad'i batasan lokacin da ta furta masha Allah ba dan yaron kyakkyawane kamar daddynsa, kallonta yarima yayi yana murmushi yace kinga kyautan da ubangiji yabamu ko?

Itama murmushin tayi tace masha Allah yanzu nan ni na haifesa?

Yanayin yadda tayi maganar ta ba yarima dariya, murmushi yayi yace eh man kece, ammah ai da ni yake kama.

Itama murmushin tayi cikin jin dad'i tace saidai kai d'in dai.

Nan su Dr leemah suka taimaka mata tatashi tayi wanka, a cikin daren yarima yakira sultana bilkisu yashaida mata, da har ta ce gasunan zuwa asibitin nan yashaida mata ai ta haihu cikin k'oshin lafiya yanzu dan dare yayi ammah tun da asuba zasu dawo.

Sosai ummi tanuna farin cikinta tare da addu'an Allah yaraya.

A nan hospital d'in su yarima suka kwana, tun asubar fari sultana bilkisu takira sultana sadiya tashaida mata sosai sultana sadiya tanuna farin cikinta inda tasa ma'aikatanta su d'aura ruwan wanka kafin su zarah su iso.

Dada ma koda taji labari murna tayi sosai har da hawayenta zataga jinin suhail d'inta shi kansa memartaba ya nuna farin cikinsa sosai,
Kan kacemi gabad'aya masarautar ta san da maganar haihuwar zarah.
gabad'aya su dada suka taru bayan sunyi sallar asuba suna jiran dawowarsu yarima cike da tsaguwa da son ganin babyn.


_Comments_
    *Nd*
_Share_



_Sis Nerja'art✍🏻_
[5/3, 7:55 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑

   _*YARIMA SUHAIL*_
        
             👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE  PEN OF LOVE  😘 HEART  TORCHING  ❤  TEARS  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Sak'on gaisuwa da jinjinar bangirma agareku masoyana, nagode sosai da soyayyarku agareni, hak'ik'a kun nuna min kulawa sosai banda abinda zance maku saidai addu'a Allah yasaka da alkhairi Allah yabar k'auna.😍😘_

        💝💝💝

_*Yayata ko ma ince Auntyna jiddah mumyn zarah bazan ta6a mancewa da keba a rayuwata ke d'in tadabance saidai ince Allah yabar wannan zumuncin namu💞*_

       💓💓💓

_~M.B.A nd Mu'az banda abinda zance maku saida addu'an fatan alkhairi🤩~_

        🧡🧡🧡

```My dala dole ingaisheki kuma in jinjina miki da namijin k'ok'arin da kike Allah yabar k'auna😍```

          💕💕💕

_Intelligent Writer's ni kaina bansan abinda zan ce ba akan k'warin guiwar da kuke bani saidai ince Allah yak'ara d'aukaka mana k'ungiyarmu ya albarkaceta, Allah yak'ara had"a kanmu gabad'ayanku na gaisheku, Aunty maryam Allah yaraya mana newborn baby muhammad🥰_

          💘💘💘

_*S.A.N 4EVER na jinjina maku tagwaye ukku ku d'in na daban ne acikin zuciyata😍👍*_

🔚🔚🔚🔚🔚🔚

*PAGE* 7⃣0⃣

Yarima saida yai sallar asuba sannan yad'auko zarah suka dawo gida, staffs d'insa wad'anda sukayi night duty zuwa suka dinga yi suna tayasa murna,, a mota zarah da take rungume da babyn ido tazuba masa tana kallo cike da sha'awa, yarima da yake tuk'i juyowa yayi yakalleta yai murmushi har zaiyi magana sai kuma yafasa.

Lokacin da suka isa gida suna fitowa daga mota su dada da suke tsaye suka iso inda suke, sultana sadiya ce tafara kar6an babyn cikin jin dad'i tadubasa tai masa addu'a sannan tamik'a ma dada nan dada har da hawayenta tace suhail ashe da rabon zanga d'an cikinka, cikin jin kunya yarima yasosa kansa, zarah ko rufe fuskarta tayi da hijab d'inta saboda kunya, nan su memartaba ma suka amshesa cikin farin ciki sukayi ma yaron addu'a, sultana bilkisu ko d'an kallonsa tayi ta gefen ido saboda  kunya, nan sultana sadiya takar6esa taja zarah suka wuce 6angarenta, room guda tasa aka bud'e ma zarah, jakkadiya tazo takar6i jaririn dan tayi masa wanka.

Dada aikawa tayi da mota aka d'auko mata wata hajiya tsohuwa da tayi ma husnah wankan jego lokacin da tayi haihuwar farko, koda tsohuwar tazo nan tayi ma zarah wankan jego.

Bayan sun fito tea mekauri aka had'a mata tasha kafin agama tuwo, sultana sadiya tayi-tayi zarah tashayar da babyn ammah tak'i wai ita kunya saida taga tana niyar kiran dada sannan takar6esa tana nok'e-nok'e cikin jin kunya tabashi yasha, daurewa tayi duk zafin da takeji cije le6e takeyi, nan sultana sadiya tatsareta saida taga ya k'oshi sannan takar6esa tace zarah takwanta tahuta, nan zarah tayi kwanciyarta dan rama baccinta.

Sultan bilkisu sosai taji dad'i da sultana sadiya tawuce da zarah part d'inta dan ta san halin d'an nata.

Yarima koda yakoma part d'insu nan kuyangi da bayi suka dinga tayasa murna akan k'aruwar da aka samu, saida yakira su mama yafad'a musu haihuwar sannan yaje yai wanka yakwanta ammah yakasa bacci saboda farin ciki, daga k'arshe mik'ewa yayi yajanyo alkyabbarsa yasaka yafito yanufi part d'in sultana sadiya, cikin sa'a yatarar da bakowa parlour Dan haka yawuce room d'in da zarah take yana tura k'ofan yaji ta bud'e cikin jin dad'i yashiga, hangota yayi saman gado ta baje tana ta kwasar baccinta, ahankali yamaida k'ofan yarufe sannan yawuce yaje yahau gadon yakwanta daga gefen zarah kallonta yake cike da tausayinta baccinta take a nutse, hannu yakai yana shafa fuskarta cikin so da k'aunarta ganin ta motsa yasa yajanye hannunsa nan yarungumota jikinsa ahaka shima yasamu bacci yad'aukesa.

Wajen k'arfe goma knocking d'in k'ofar da akene yatashesu daga baccin da suke, zarah cike da mamaki takalli yarima tace nashiga ukku yaushe kashigo nan? Murmushi yayi yace kina tunani zan iya yin nesa da ke?

6ata fuska tayi kamar zatayi kuka tace haihuwa fa nayi kuma nan ai ba 6angarenmu bane yanzu ya kakeso inyi idan aka shigo aka ganmu a tare?

Kedai baby tsiyata da ke kin faye tsoro toh menene dan anganmu.

Har ta bud'e baki zatayi magana nan aka k'ara knocking d'in k'ofar, nuni yarima yai mata alamun taje tabud'e.

Mik'ewa tayi tanufi k'ofan ahankali tabud'e tad'an lek'a kanta ganin sultana sadiya ce rik'e da baby daga bayanta wata kuyangata d'auke da tray nan wata irin kunya takamata dakyar ta iya matsawa tabata hanya.

Ganin yarima zaune saman gado yasa sultana sadiya tace suhail ba dai zuwa kayi ka hanata bacci ba?

Murmushi yayi yace a'a ummah ni ban hanata bacci ba yanzu ma tafarka,
Toh hakan ya yi, nan taba kuyangar dama ta aje tray d'in tafita.

Yarima kar6an babyn yayi daga hannunta.

Sultana sadiya kallon zarah tayi tace ga tuwo nan kizauna kici dada ta aiko miki da shi ta ce kicinyesa sannan ga pepper nan shima kar kirage komai har romon.

Ahankali zarah tace toh ummah ammah ai ban iya cinye duka.

Kedai yanzu safko kifara ci, mik'ewa zarah tayi taje tawanke bakinta sannan tadawo tazauna tabud'e tuwon ahankali takeci.

Kallon yarima tayi da yake wasa da babynsa tace kasafko muci.

Sai a lokacin yakalli tuwon yamitsa fuska yayi kamar Wanda yaga wani kashi yace menene wannan kuma?

Harararsa zarah tayi tace ba kasan tuwo bane.
Ta6e baki yayi yace ni irin wannan tuwon ya fi k'arfina aci lafiya.

Dariya sultana sadiya tayi tace daman wannan na masu jegone, yanzu dai yi sauri kici kiba yaron nan yasha dan yunwa yakeji.

Haka sultana sadiya tatsareta saida taci tuwon sosai taci pep d'in da aka kawo romon dukansa tashanye.

Bayan ta gama zuwa tayi tawanke hannunta tafito, nan sultana sadiya takalli yarima tace suhail gatanan katsareta taba yaron nan yasha dan yunwa yakeji.

Kallon zarah yayi da take turo baki sannan yace toh ummah.

Bayan sultana sadiya ta fita ahankali yace  sweetmee kizo kizauna man.

Daga nesa dashi kad'an tazauna nan yamatso yad'aura mata babyn saman cinyarta.

babu yadda ta iya haka tadaure tashayar da shi, suhail saida yaga ya k'oshi sannan yad'aukesa yace baby kikwanta kihuta bari inkai ma ummah shi inkama gabana tun kan jama'a sufara zuwa.

Komawa tayi takwanta nan yabata peck a goshi sannan yafita a parlor yatarar da ummah nan yamik'a mata yaron sannan yaficce.

Kafin azuhur mutane dayawa sun taru gidan,  sultana sadiya dakanta taje tahad'o ma zarah kayanta da na baby a chan part d'insu.

Su Rahama da sumayya sosai suka nuna farin cikinsu da suka ga babyn nan sukaita santinsa.

Yarima kud'i yaba Aunty Husna sosai taje tahad'a ma baby da mejego kaya na azo agani masu kyau da tsada.

Yarima yaso amaida masa matarsa part d'insu ammah sultana bilkisu tace kar yakuskura yatunkari sultana sadiya da maganar yabari tazauna chan har tagama wanka ba dan ya so ba kan  dole ya hak'ura yabarta saidai kusan kullum yana manne da ita da babynsu, tun sultana sadiya tana fad'a har tagaji tadaina.
Ita kanta dada koda talura da yadda yake shige ma zarah fad'a tayi masa sosai ammah yashareta baifasa abinda yakeba.

Sosai su dada suke nuna ma zarah kulawa inda hajiya tsohuwa tazage tana gyara mejego sosai.

Su yaya rauda ko kusan kullum sai sunzo gidan hatta ita kanta amarya Aisha.

Tun ana saura kwana ukku suna 'yan agadaz sukazo 6angare guda aka bud'e masu sosai masarautar tacika da bak'i.

Ranar suna yaro yaci suna Faruk Umar Faruk (Ameer Faruk) memartaba sosai yanuna farin cikinsa da karar da akayi masa shanuwa biyu da rago biyu yabada ayi hidimar suna, inda yaware shanu hud'u da garken tumaki sannan yakawo alkyabba yabada yace na takwaransa ne.

Su daddy da abbah ma ba'a barsu a bayaba dan filaye sukaba Ameer faruk sai cheque na mejego

Sultana sadiya da sultana bilkisu suma gudunmawa suka bada ta azo agani.
Dada kanta ba'a barta a bayaba kaya masu kyau da tsada tasa aka had'o ma mejegmejego da baby.

Shagali akayi sosai inda jama'a sukaci sukasha, zarah tasami kyautuka sosai a wajen 'yan uwa da abokan arzik'i hatta abokan suhail da matansu ba'a barsu a bayaba suma sun bada tasu kyautar.

Jamila da Dr mu'az ma tun ana saura kwana biyu suna suka dura garin dasu akayi komai.

Yarima raguna hud'u da shanu ukku yayanka ranar sunan aka had'a da Wanda memartaba yabayar, a ranar anyi shagalin da ba"a ta6a kamarsaba a garin anci ansha har aka bari.

Da dare sultana sadiya ce sai su sumayya suke duba kayan da zarah tasamu dan turame da kayan baby kamar za"a bud'e shago, ga mak'udan kud'i, bayan sungama dubawa nan sukai mata sallama suka fita.

Ido tazuba ma kayan tana kallo turo k'ofan da akayine yasa tad'ago kai takallesa murmushin jin dad'i tayi dan rabonta da mijin nata tun d'azu da safe.

Takowa yayi ya iso inda take daga gefenta yazauna nan yakai hannu yad'auki Ameer da yake bacci sannan yace baby ya gidan da hidima?

Kwantar da kanta tayi a kafad'ansa cikin shagwa6a tace shine ko kalek'o kadubamu kabarmu da kewarka.

Murmushi yayi yace  sweetmee taya zan shigo bayan gidan cike yake da mutane, kuma ga su dada sun sanya min ido, ke ni nagaji zuwa zakiyi mukoma part d'inmu kawai dan zanfi samun kwanciyar hankali in kina kusa da ni.

Mik'ewa zarah tayi tace ina zuwa nan taje tad'auko hand bag d'inta tafiddo kud'ad'en da tasamu tamik'a masa batare da ya kar6aba yace na menene?

Murmushi tayi tace wanda nasamu ne na suna kad'auka na mallaka maka, sannan ga kayan da muka samu nan ni da Ameer.

Murmushi shima yayi yace my sweet wannan hak'in kine ki aje wajenki kawai nagode, idan ban k'ara mikiba ai bazan kar6aba.

Turo baki tayi tace nidai a'a toh me zanyi dasu ni?
Janyota yayi jikinsa yace bakisan abinda zakiyi da su ba?

'Daga masa kai tayi alamun eh.
Murmushi yayi yace toh kid'ibi wani abu kiba su baba sauran kuma sai kizuba a account d'inki inyaso daga baya sai kiyi tunanin abinda kikeso ayi miki.

Cike da gamsuwa da maganarsa ta jinjina kai.

Hannunsa yatura cikin rigarta tare da k'ara matsota jikinsa.

Zaro ido zarah tayi taturesa tace ban fa gama wanka ba.
Hmm toh wani abu nace zanyi miki? Na ma lura kamar dad'i kikeji da kikayi nesa da ni, ke nifa so nake kidawo hakanan.

Rungumesa tayi tare da marairaicewa tace wlh a'a kawai dai kunya nakeji kabari ingama wanka sai indawo nima ai nayi missing d'inka.

Janyeta yayi daga jikinsa yace nak'i wayon, in dagaskene kibini mukoma.

Dariya tayi tace wlh baza'ayi wannan abun kunyar da ni ba

Shuru yayi nan yasa hannunsa cikin aljihunsa yafiddo wani d'an k'aramin zoben azurfa mekyau da tsada yasa ma sultan a k'aramin hannunsa.

Zarah ma kallon hannun tayi tana murmushi tace yai kyau.

'Dago kai yayi yakalleta yace dagaske?

Fari tai masa da ido, Kwantar da sultan yayi sannan shima yakwanta tare da safke ajiyar zuciya.

Kallonsa zarah take cikin tsoro tace please katashi kaje kakwanta dare yayi fa.

Janyota yayi jikinsa yarungume tare da yin light off, k'ara shigewa tayi jikinsa ahaka sukayi bacci.

Washe gari tun da asuba yatashi yakoma 6angarensu.

Zarah turamen tad'auka tad'ibar ma su dada, babu wadda bataba ba k'in kar6a sukayi, sukace a'a kije kid'inka kayanki hak'in kine.

Hajiya tsohuwa tad'ibar mawa, koda taba su sumayya suma k'in kar6a sukayi saida tanuna bataji dad'iba sannan suka kar6a sukayi mata godia.

Koda yaya rauda tazo nan tad'ibar mata nasu da na mama sannan tabata kud'i dayawa tace na su baba ne, nan taware wasu tace natane ita da aisha.
Sosai sukanuna farin cikinsu sukai mata godia.

Hata tacigaba da zama wajen sultana sadiya tana samun kulawa sosai daga kowane 6angare ga gyara da takesha wajen hajiya tsohuwa, Ameer yaro me farin jini da shiga rai  kulawa yake samu sosai dan baima cika wuni wajen Zarah ba indai ka gansa ankawo mata toh yunwa ce takeji.

Shi kansa suhail saida ummi taimasa dagaske sannan yarage shige ma Zarah.


Ranar da tayi arba'in kitso da k'unshi tasha, sannan bayan sallar magrib aka maidata part d'inta, mamakine yakamata ganin ancanza mata kayan d'akinta komai sabo.

Bayan tayi sallar isha'i wanka tayi tashirya cikin wasu sleeping dress masu kyau, feshe jikinta tayi da turaruka masu k'amshi sosai.

Lokacin da tafito har an shirya ma Ameer dan haka tasa wata kuyangarta tad'aukesa suka nufi part d'in yarima.

Gani tayi shima komai ancanza masa sabo room d'insa ya burgeta sosai.
Kar6an Ameer tayi daga wajen kuyangar tasallameta, ahankali tatura k'ofan bedroom d'in tashiga kwance tahangosa saman gado yai pillow da hannuwansa.

Ganinta yasa yatashi zaune tare da mik'a mata hannu cikin sauri ta iso inda yake, mik'a masa Ameer tayi sannan tazauna gefensa, murmushi suka sakar ma juna yace baby dafatan kin dawo lafiya? Tun d'azun nake ta jiranki ammah shuru, hmm Nasan dai ba wani missing d'ina kikayi ba, ni kad'ai nayi missing d'inki.

Rungumesa tayi  tace hearty wlh nima nayi missing d'inka tsayawa nayi ind'an kimtsa sannan inzo wajen rabin raina.

Wani irin kallo yai mata mai d'auke da sak'onni wanda yasa saida taji wani yar a jikinta, cikin sauri tasadda kanta k'asa.

Kallon Ameer yayi da yake baccinsa sannan yamik'e yaje yakwantar da shi yadawo nan yakwanta saman gadon.

Biyosa zarah tayi takwanta k'irjinsa tace hearty kayi hak'uri nima kasan kunyarsu ummah ne da nakeji ammah ai da tuni na gudo wajen mijina abun alfaharina dan nayi missing d'insa sosai.

Rungumeta yayi yana shafar bayanta yace baby aike bakya laifi duk abinda princess tayi daidaine dan ta cancanta tunda har tasace zuciyar suhail ai ba abinda yai saura, dole yahak'ura yabita yadda duk takeso.

K'ara shigewa tayi jikinsa tace hearty kaima ka sani da ace ana bud'e zuciya aga sirrin da yake cikinta da tuni na bud'e maka kaga abinda yake cikinta.

Janyo hannunsa tayi tad'aura saman k'irjinta tace duk wani bugu da zuciyata zatayi tare da sonka takeyinsa.

Tsura mata juna ido sukayi suna karance duk wani sirri da yake cikin ransu, zarah ce cikin sauri tazame jikinta tazauna saman gadon tana jin wani iri.
Inda yarima yamaida idanunsa yalumshe yana jin sonta yana fizgarsa, cikin sauri hannunsa har k'yarma yake nan yajanyota yarungume tare da had'e bakinsu waje guda yafara kissing d'inta, cikin dabara yarabata  da duk kayan da suke jikinta  nan yacigaba da sarrafata son ransa gabad'aya yafita hayyacinsa nan yaita mata sumbatu.

Zarah tausayin mijinta yakamata ganin yadda gabad'aya yarikice mata ita kanta ta san ya yi missing d'inta sosai.

Ta wahala sosai a hannunsa ya sa mata albarka ya fi ak'irga.

Bayan komai ya lafa yarima d'aukanta yayi sukaje sukayi wanka bayan sun gama d'aukota yayi yamaidota saman gado yakwantar da ita sannan shima yakwanta yarungumeta a jikinsa cike da shauk'in sonta, wata irin runguma  yayi mata kamar zai maidata cikin ciki har saida zarah tayi 'yar k'ara sannan yasafsafta rik'on,

Cikin dare koda Ameer yafarka saidai yarima ne yaje yad'aukosa daga cikin gadonsa dakyar yasamu zarah tatashi shima saida yataimaka mata sannan tabashi yasha.

Bayan ya k'oshi shi yaita riritashi inda zarah takoma baccinta har saida sultan yai bacci sannan yarima yakwanta.

Washe gari bayan sunyi breakfast zaune suke suna hira cikin nishad'i, mik'ewa yarima yayi tare da rik'o hannun zarah yace sweetmee taso muje kiga wani abu.

Mik'ewa tayi tabi bayansa koda suka shiga gaban dressing mirror yatsaya da ita sannan yatsaya a bayanta yace tarufe idanunta.

Koda tarufe sarka ce yasaka mata da zobe sannan yadamk'a mata keys a hannunta yace tabud'e.

Wuyanta tabi da kallo tana shafa sark'an da yasaka mata cikin jin dad'i sannan takalli keys d'in da suke hannunta juyowa tayi tafuskancesa tace hearty wannan sark'an kamar ta gold ce yanzu tawa ce?

Murmushi yayi tare da d'aga mata kai yace tabbas ta gold ce ga d'ankunnen nan, wannan keys d'in kuma d'aya na motar da nacanza miki ne d'ayan kuma na gidane na mallaka maki halak malak.

Zarah rasa me zatayi tai shin farin ciki ko me? Fashewa tayi da kuka tare da rungumesa tace nagode, nagode, nagode sosai hearty Allah yak'ara girma da d'aukaka Allah yarabaka da iyayenka lafiya, bansan me zanyi inbiyakaba dan Allah kafad'amin abinda zanyi wanda zaisa ko kad'anne kaji dad'i a ranka.

Rungumeta yayi yace kidaina yi min godia dear dan kin riga kin gama min komai dan akowane lokaci kina faranta min rai, saidai ince Allah yabaki masu yi miki kema, yanzu dai muje inbaki labari medad'i.

Haka yajata suka dawo parlour suka zauna nan sukacigaba da hira.

_______________

Kamar yadda yai ma Dr mu'az alk'awali hakan ko akayi dakansa yarubuta takardar neman masa transfer ya aika da ita, batare da 6ata lokaciba akayi requesting.

Gidan da zasu zauna ma shi yasiya masu nan mu'az yadawo hospital d'in yarima yacigaba da aiki.

Zumunci ake sosai tsakanin jamila da zarah.

A ranar da tayi arba'in ranar yad'auketa yakaita gidansu tayi wuni daga nan yawuce da ita gidan Aisha, saida yajera kwana ukku yana kaita gidajen 'yan uwa day abokai.



_*A gurguje please*_

Sumayya da salim sosai kawai ake zubawa daga k'arshe dangin salim sukazo suka neman masa auren Sumayya ba a wani sa bikkin dayawaba, ahaka har akayi  bikkin aka kaita agadas, sukaita zuba soyayyarsu me tsafta ga yaransu atare da su, sosai sumayya takejin yaran a ranta dan jinsu take kamar ita tahaifesu.


Yaya rauda ma Alh munir zuwa yayi yanemi gafara a bisa abinda ya aikata mata, dakyar yasamu yashawo kanta ta yafe mashi nan yanemi yafiyar iyayenta, daga baya yanuna yanaso ya aureta da ta nuna ba zata aminceba saida yanuna shi dagaske tsakani ga Allah yake sonta sannan ta amince sukayi aure.

_*BAYAN SHEKARA UKKU*_

Yarima kud'i sun zauna ya k'ara kyau da cika, sarauta  ta k'aru.

Wani d'an yarone kyakkyawa wanda bazai gaza shekaru ukku ba naga ya shigo dagudu cikin maganarsa da bata ida k'warewaba yana kiran daddy daddy daddy dagudu yafad'a jikin suhail da yake kwance saman cinyar zarah
d'aukansa suhail yayi yad'aura saman jikinsa yace little prince wa yata6a min kai?

Cikin gwarancinsa yace daddy wajen meenal zaka kaini.

Shafa kansa yayi yace yanzu ko zan kaika.

Zarah da take saurarensu 6ata fuska tayi tace haba hearty kasa akaisa kawai ko yaje wajen hinde takaishi magana fa nakeson muyi ganin kana waya yasa najira kagama.

'Dago kai yayi yakalleta yace sorry sweetmee me kikeso kice ina saurarenki, chocolate yamik'a ma Ameer nan yafara sha.
murmushi tayi sannan tace yauwa d'azun naji kana waya ka ce asa sunan su mama cikin wad'anda zasuje aikin hajji ka mance wanchan shekarar duk tare kabiya mana mukaje?

Murmushin shima yayi yace eh ina sane so nake sukoma, kema naso mukoma ammah hakan bazai yuwuba saidai muje umara tunda mefaruwa ta riga da ta faru.

Ido tazuba masa cikin rashin fahimtar maganarsa.

'Daukan sultan yayi yamik'e yace bari inje inshirya inzo inkaisa gidan shaheed wajen meenal daga chan zan wuce fada tunda gabad'aya yanzu memartaba ya daina shiga sha'anin mulkin ya sakar min komai....yana fad'in haka yawuce yashige bedroom d'insa.

Zarah da kallo tabisa cike da son mijin nata sai kuma chan tamik'e tabisa bedroom d'in ganin sultan tayi zaune saman gadon yarima yana shan chocolate yana game da wayar yarima, inda yarima yake cire kayansa zai shiga wanka, takawa tayi ta isa inda yariman yake nan tashiga tayasa fuskarta d'auke da murmushi, rungumeta yayi jikinsa yace sweetmee wannan murmushin fa?

Kwantar da kanta tayi saman k'irjinshi tace hearty baka bari muka ida magana ba zaka fita.

Shima k'ara rungumeta yayi yace kijirani da nadawo zamuyi magana kinsan a yanzu haka nasan waziri yana chan yana jirana dan shima so yake ya aje mulkin yadamk'a ma shaheed.

Cikin wata irin murya tace toh shikenan hearty muje intayaka yin wankan.

Nan suka shige toilet sukabar Ameer zaune yana shan chocolate yana game.

A tare suka fito kowa d'aure da towel suna dariya nan suka shirya, ido tazuba ma suhail lokacin da yake sa alkyabba, juyowar da zaiyi nan suka had'a ido murmushi yasakar mata yace sweetmee wannan kallo haka ai sai kija infasa fita.

Fari tayi mashi da ido sannan tace duk cikin sonkane hearty, rungumota yayi tare da had'a goshinsu waje guda suna aika ma junansu wani sihirtaccen kallo,
muryar Ameer sukaji ya ce daddy kazo kakaini wajen meenal,

Janye zarah yayi daga jikinsa yarik'e hannun Ameer sannan yace baby bari muje sai mundawo.

Duk'awa tayi tace Ameer so kake daddy yatafi yabar mummynka ko?
Girgiza kai yayi cikin maganarsa yace a'a mum kibari inmuka yi wasa da meenal zanzo inkaiki wajen granny sultana.

Shafa kansa tayi tare da bashi peck a goshi tace toh shikenan my boy ina jiranka.
Shima peck d'in yabata a kumatu sannan tad'ago takalli yarima tace please hearty kar ka dad'e.

Kar kidamu baby zan dawo dawuri, hannu tasa tarufe ma Ameer ido sannan tayi ma yarima kiss a baki.

Murmushi suka sakar ma juna tace adawo lafiya my heartbeat.
Allah yasa baby nan tad'aga masu hannu har suka fita.

Take masa baya guards d'insa sukayi nan yasa Ameer a mota yace akaishi gidan shaheed sannan yawuce yagaishe da su memartaba da yake fama da ciwon k'afa bayan sungaisa yaje yagaishe da su ummi da sultana sadiya daga chan yawuce fada.


Wajen k'arfe takwas koda yadawo yatarar da zarah har tayi bacci nan yai shirin baccinsa sannan yahau gadon kallon zarah yayi da tabaje tana ta kwasar bacci ahankali yad'age rigarta yakai hannu yana shafa cikinta daga k'arshe yad'aura kansa saman cikin.

Jin abu samanta yasa tafarka daga baccin da bata dad'e da fara yinsaba, kallon yarima tayi tashafa kansa sannan tace hearty me kakeyi nan?

Murmushi yayi batare da ya d'ago kansaba yace ina gaisawa da baby na ne.

Zaro ido tayi tace wane irin baby?
Sai a lokacin yad'ago yakalleta yace Wanda yake manne a cikinki.
Karufan asiri ni banda komai.

Murmushi yayi yace taya kike tunani zan k'ara bari kisamu ciki batare da nagane ba, wanchan karen ma dande ban maida kaiba ammah ai naga alamomi kawai jin kai ne yahana intabbatar da hakan.

Ajiyar zuciya tasafke tace toh taya akayi kagane ina da ciki bayan ni kaina bansan da shi ba.

Rungumota yayi jikinsa yace baby ko kin mance ni doctor ne? Insha Allahu nan da wata shidda zaki haifo min wani babyn.

Zaro ido tayi tace nashiga ukku yanzu har ina da ciki wata ukku batare da na saniba?

Jan hancinta yayi yace toh kidai shirya ni d'in kinsan ba ma wasa bane.

Marairaicewa tayi tace toh ammah duka fa Ameer shekararsa ukku.

Toh ai ya ma kwana biyu ai na gama wasa duk bayan shekara biyu zaki dinga haihuwa Insha Allahu k'ara ma kishirya dan mijin nan naki yana da son yara, wlh zarah indai  kece bazan damuba dan inaso inga  kin haifar min yara kodan susamu irin tarbiyanki, dan halayyarki ce ta kirki tacanza min rayuwa, tabbas na yarda kud'i basu bane rayuwa, rayuwa medad'i itace aginata akan ilimi na addinin musulunci, duk kud'in mutum indai baida ilimi toh bai cika mutum ba yana da tauwaya a rayuwarsa, a kodayaushe ina k'ara gode ma Allah da yamallaka min ke a matsin matata tagari wlh wani lokacin har ji nake kamar ba zan iya rayuwaba in babu ke, zarah kece komai nawa, ina fata zaki cigaba da haifamin yara masu irin tarbiya da hak'urinki wad'anda duniya zatayi alfahari da su.

Rungumesa tayi kamar zata maidasa cikin ciki hawaye suna fita daga idanunta tace nagode sosai mijina Allah yabarmu tare, duk abinda kakeso toh nima shi nakeso dan ka riga ka zama ni nima nazama kai fatana Allah yabarmu tare har k'arshen rayuwarmu, ka gama min komai a rayuwata kaine silar dawowar duk wani farin ciki nawa, a kodayaushe bakina cikin yi maka addu'a nake dan addu'a ce kawai zanyi maka inbiyaka abubuwan da kakemin, kaduba kaga gidan da su mama suke zaune yanzu babba ne sosai kuma kai kamallaka masu, sannan duk wata sai ansafke masu kayan abinci, hatta su yaya rauda baka barsuba kullum cikin kyautata masu kake sannan.......cikin sauri yarima yasa hannu yarufe mata baki yace baby ya isa haka duk abinda nayi ma su abba cancantace tasa haka ko da ace bana aurenki zan iya yi masu fiye da haka, kukan ya isa haka dear indai ba so kike nima inyiba, cikin sauri tagirgiza kai tace a'a kar kayi,,,harshensa yasa yashiga lashe mata hawayen fuskarta bayan ya gama nan yashiga yi mata rad'a a kunne chan sai suka saka dariya gabad'ayansu, turesa zarah tashiga yi tace nak'i wayon naka ni kak'yaleni.

Rik'o hannunta yayi yace please dear kitaimaka min.
Tallabo kansa tayi tatura bakinta cikin nasa nan suka shiga kissing d'in juna kowa yana nuna ma d'an uwansa k'warewarsa cikin salon so daga k'arshe yarima suhail yajanyo blanket yarufesu.

_Laifin dad'i k'arewa_

_*Alhamdulillah* anan muka kawo k'arshen wannan novel mesuna *YARIMA SUHAIL* abinda muka fad'a daidai Allah yabamu ladar kurakuren da suke ciki Allah yayafe mana_

_Fatan alkhairi agareku dukkan masoyana naji dad'i kuma nagode ma Allah akan yadda wannan novel d'in yasamu kar6uwa sosai a wajenku_

_Duk wani wanda nata6a 6atamawa ina fata zai yafemin domin duk d'an Adam ajizine tsakanin harshe da hak'ori ma ana sa6awa balle tsakanin mutane, Allah yayafe mana gabad'ayanmu al'ummar musulmai_

_Daga k'arshe ina taya dukkan d'aukacin al'ummar musulmi murna akan wannan wata mai albarka da zamu shiga, ina fata Allah yabamu ikon shiga watan ramadan lafiya sannan yabamu ikon azumtarsa, ya ubangiji kasa muna daga cikin bayinka wad'anda zaka 'yantar a cikin wannan watan me albarka_

_Sis Nerja'art takuce a duk inda kuka kasance masoya,😍👍_


_Comment_
    *Nd*
_Share_




_Sis Nerja'art✍🏻_

No comments