Recent Updates

Wacece Ni Book 1

 


Hakkin Mallaka(M): Hafsat C. Sodangi

Shekarar Bugu a: 20

GODIYA

Godiya ta har kullum ga Ubangijinmu Allahu
take, masanin abin da yake boye da wanda yake
bayyane. Mai kowa, mai koma1 masanin yau da
gobe, gwani mai hikima cikin dukkan aiyukan shi,
wanda ya yi wa dan adam baiwar da ya bambanta
shi da sauran dabbobi ta hanyar yin furuci ya
kuma sanar da shi abin da bai sani ba.
Tsira da amincin Allah ya tabbata ga
Annabin karshe Manzon da ya kawowa duniya
shiriya. Annabin Raharna Muhammad (S.A.W.)
da Aiayycnsa da Sahabbansa da wadanda suka bi
ma tafarkinsa na gaskiya har zuwa ranar karshe,
wato ranar Alkiyama.

Godiya mai dinbin yawa ga makaranta
littattafaina a ko'ira suke na gode da irin kulawar
ku, Allah ya bar zumunci, amin.
Na gode.
Ta ku:
Hafsat Cindo Sodangi
2

DAGA LITTAFIN SODANGI

Uwar Miji
Naga Ta Kaina
Waiyo Duniya
Tabbataccin Al'amari
Yi wa Wani
Rabon Kwado
Cikar Alkawari
Abu Na ku
Mata Masu Duniya
Nufin Allah
Kifi Na Ganin ka..
Da Kamar Wuya
Shamaki
Daga Kin Gaskiya
Hattara
Duk Daya
Mata da Kicin Din su.
Littafin Sodangi ba sa nufin yi da wani ko
habaici ga kowa, an yi su ne kawai don
nishadaintarwa, da fadakarwa. Ana neman afuwa
ga duk wanda ya ga wani sashi na su ya yi daida
danabin da ya shafe shi, ba da shi ake yi a, an dai
yi dacen hakan ne kawai.
Na gode:
Ta ku: Hajiya Hafsat C. Sodangi.

3
GAISUWAR SADA ZUMUNCI GARE KU:
Shamsiya Ibrahim Funtua Katsina State
Hauwa'u Bashir Ikara
Fatima Sulaiman A Zaria
Habiba Ibrahim Alabura
Sulamatu Isa Kasim
Amina Muhammad Maiduguri
Ummce "Yar Mtan Azare
Sakina Baba Diddi Jalingo Mrs Abdullah
Modibbo
Yagana Kacallah Kaltuma a Ali Yaskari
Primary School Alairo Auwalu Azarc
Sa'adatu Sa'ee Katsina
Hadiza U. Audi
Hindatu Usaini Gombe
Dukkan ku ina yi muku fatan alheri na gode
da.kulawar ku a rubutuna.

SADAUKARWA
Sadaukarwar littafin ta mahaifina ne Alhaji
Chindo Sodangi da Hajiya Fatima C. Sodangi
Ubangijinmu ya saka da mafificin
sakamako bisa renon da kuka yi mini.

4

TUKUICI
Tukuici na ka ne Baban su Yunus mijina,
Alhaji Yunusa Abdullahi Dabai. Baban su
Maryma, Aisha Yunusa da Abdulmajeed. Na gode
da kulawarka a gareni.

JINJINA
Jinjinar ta ki.ce amarya ba kya laifi.
Hajiya Khadija C. Sodangi Mrs. Alhaji Nasir
Idris Kiru.
Ubangiji ya ba ku zaman lafiya da fahimtar
juna. Amin Summa Amin.
5
WACE CE NI?
Cikin kwalliya na ke sosai, idan na ce
kwalliya kuwa to ina nufin irin ta 'yan
matan zamani, gwanayen yin
kwalliyar ta burgewa, masu kuma abin yin
kwalliyar.
Tun ina yar karamata kwarai mutanen da
suka sanni suka san ni din gwanace kwarai wajen
tsara kwalliya ta yi kyau, to balle kuma yanzu da
na zama cikakkiyar budurwa.
Taku daidai nake yi cikin nutsuwar da ke
kara bayyanar da gwanintar iya tafiyata. Lokacin
da na shigo cikin fence house' din mu, wurin da
Baba ya killace don kiwon dawakan shi.
Kayataccen wuri ne sosai da aka katange shi
da farin katako. Harabar shi kuma aka mamaye
shi da koriyar ciyawar lawn ta yi kore shar babu
komai a wurin illa skable din daure dawakai, sai
ko ginin katako da Baba ya yi ya kawata shi da
kayan alatu, don hutawa a cikin shi.
Ina shiga wurin na hango Yaya Almu can
nesa sanye ikin fararen icaya, yana rike da
sprinkler a hannunshi. yana fesawa 'yan shukokin
da ke wurin ruwa, saboda kasancewar mu cikin
lokacin raai.
Can wurin shi na nufa ina tafiyata a hankali

6

don haka lokaci mai tsawo na dauka kafin in isa
wurin shi, saboda kasancewarwurin mai girma ne
sosai.
"Sannu da aiki."
Yaya Almu ya juya a hankali ya kalleni cikin
nutsuwa kafin ya maida kanshi ga kallon agogon
da ke daure a hannunshi. Ya sake dago ido ya
dube ni.
"Ke kam kin yi sa'a komai na ki a makare
kike yin shi dubi lokaci sai yanzu kika fito?"
Na dan ja baya kadan saboda irin kallon da
yake yi mini. A hankali cikin sanyin murya na ce
mishi.
"Yanzun ma fa fitowa kawai na yi, amma ko
karyawa ban yi ba."
Da sauri ya ce, "Eh ai yana da kyau. Haka
din yana da kyau, sanyin jikin ki ya rinka ja miki
dalilin rashin karyawa a gida, tun da ke ba ki san
ki tashi da wuri ki yi abin da ya daçe ki yi ba,
akan komai sai kin makara je ki sai kin dawo."
Na yi maza na kauce daga wurin feshin da
yake shirin jika ni, na ce mishi, "Ai zuwa na yi da
in ce ko za ka sauke nine?"
Ya ci gaba da aikin shi yana tambayata, "Ina
su Junaidu?"
Na ce, "Ai.babu. kowa a gidan duk sun tafi."

7
Bai bata lokaci ba ya kashe sprinkler din ya
Diyo bayana ya wuce ni ban iya yin komai akan
lokaci ba, in mutum yana da abin yi ai ba zai yiwu
ya iya hakurin jirana ba, in dai shi ma ba zama
mai latti irina zai yi ba. Kan in fito waje tuni ya
tayar da motar da na wuce a gindin bishiyar da ke
bakin get din shiga fence house din Toyota
Camry 2008 model, fara sol hakan nan
kayayyakin da ke cikinta.
Ina zama a cikin motar ya hau kan hanya har
lokaci bai daina mitar da yake yi ba. Jaddada mini
muhimmancin yin abu akan iokaci yake yi.
"Kin san ma ma anar iokaci kuwa?"
Ya dan waiwayo ya kalleni. Ban kalle shi ba,
balle in tanka mishi.
"Yana da kyau a ce mutum yana kiyaye
muhimmancin okacin shi, ya rinka amfani da shi
yanada ya dac ya rimka barin shi yana tafiya a
aka kawai ba, ba tare da ya yi wani abin da ya
amfanu a cikin shi ba. Ki yi kokari kina amfani da
lokacin ki a yarda ya dace, sannan kar ki yarda ki
saba da yin latti a kan komai ko kuma yawan sab6a
alkawura."
Na yi kokari na bude bakina na ce mishi,
To Yaya afuwan na gode."
Gaskiya ne Yaya Almu yana daya daga cikin

8
mutanen da suke kiyaye lokutansu, suke amfani
da su a yanda ya dace. Kullum ka shiga dakin shi
matukar ya gama komai na wunin ranar yana
shirin kwanciya, to za ka same shi ne yana rubuta
abubuwan da zai yi a wuni mai biye daga karfe
kaza zuwa kaza, zan yi abu kaza da kaza, ko kuma
za ni wuri kaza da kaza. Zai yi kuma wuya kwarai
a ce bai yi hakan ba. Ma'abocin yawan istigifari
da yawan salatin Annabin Rahama (S.A.W.). a
kowanne lokaci ko da kuwa wani aiki yake yi in
dai ba magana da wani yake yi ba. In ma maganar
yake yi yana gama ta za ka ji ya koma kan abin da
ya saba yi. Wani irin mutum da hira ba ta dame
shi ba, ya kan yi magana nc kawai a lokacin da
hakan ya zama mishi dole, don ko ni ce na saki
baki ina ta surutu ya rinka kallon kenan. Sau da
yawa kuma idan na gaya mishi wata magana zuba
mini ido yake yi cikin nazari sai in na ce mishi
Yaya Almu ba ka yarda da ni ba ne? Sai ya dan
motsa kafada tare da tabe baki ya ce, ba zan iya
fadin hakan ba, tun da ban saba kama ki da laifin
yin karya ba, sai dai kina da alamomin hakan, don
kuwa surutu ya yi miki yawa. Shi mutum kuwa in
ba ki sani ba an hore shi ne da fadin alkhairi ko
kuma ya kama bakin shi ya yi shiru, amma ba ya
yi ta sakin magana ratata-ratata ba.
9

Har muka iso hukumar zabe inda aka toro ni
zaman sanin makamar aiki, saboda kasancewata
daliba mai karatun diploma a Federal Poly garin
mu. Yaya Almu bai daina yi mini nasiha akan
mubimmancin lokaci ba, ta hanyar kawo mini
ayoyi da hadisi da suka jaddada muhimmancin
lokacin, ni kam kullum cikin mamakin Yaya
Almu nake, musamman in ji shi yana karatun
alkur'ani mai girma ko yana kawo hadisi da
maganganun manyan malaman addini. Sai in ce
oh oh! Ko yaushe ya samu damar yin karatun
addini haka? Oho. Tun da ni dai na san Yaya
Almu ne bayan na yi wayo shekarun kuruciyar shi
gaba daya a London ya yi su. can Baba ya kai shi
karatu tun sa'ad da ya gama primary school
dinshi, bai kuma dawo gida ba sai da ya kammala
karatun shi.
Yaya Almu wanane da muke uba daya.
Mutane da yawa suna yabon shi, saboda tsayuwar
shi da kuma kulawar shi kan al'amari na. Ni kuwa
nake kallon abin da yake mini din a matsayin
takura, ko kuma ma in ce yan ubanci irin na dan
uba, don kuwa kafin dawowar shi gida cin karena
nake yi babu babbaka, in ci duniya, kuma da
tsincke. Shi ne ya dawo ya takura mini ya hanani
rawar gaban hantsi, ya tasani a gaba da yawan

10

fadi da yawan tsawa da yawan zare ido, da yawan
fadin ke nutsu. Ga barazanar duka a kowanne
lokaci, saboda ni wai ya je ya sayi wata
sharbebiyar dorina, irin ta Baba maigadin gidan
mu da yake fito da ita kowanne lokaci ya
sharbaneta da mai ya shanyata ta sha rana kafin ya
daukcta ya je ya rataye ta a dakin shi wai don
ranar da ya bugeni da ita, in ji jiki.
Yaya Almu ne ya dawo ya same ni ina
tsakiyar zuba shagwabata ya katse mini hakan
cikin kasa da makonni biyu.kacal da dawowar shi.
Kasancewar shi mutum daya tal da Ummana
ba ta daga ido ta kalli abin da ya yi mini, balle
tambaye shi dalilin yin hakan ya bashi cikakkiyar
dama ta shiga ahrkokin rayuwata ya takura su,
kafin dawowar na shi ni din shagwababbiyar
yarinya ce takin kárawa, gashi dai ni kadai ce yar
da Ummana ta haife, ni kadai ce kuma ya maçe a
wurin baba. Gani kuma da sunan mahaifiyar shi,
kowa a gidan mu gudun bacin raina yake yi, don
kuwa ya san bacin ran nawa yana nufin bacin ran
Umma, don kuwa a fili take fada ba ta boye ba da
6atawa Adawiyya rai gara ita a zo inda take a bata
mata. Wannan dalili ya sa kowa yake kaffa-kaffa
da ni, saboda an san abin da bacin ran Umma
yake nufi a gidan nan. Yau na zama zagin baba,

11
ba komai ba ne a wurina hakan nan in na ga dama
ina iya warware yanyatsuna in wanke fuskar na
gaba da ni da mari, yin hakan ba wani abu ba ne
in an kai kara a wurin Umma hakuri take bayarwa
ta ce kuruciya ce. Wata rana ko da kudi aka ce ta
yin hakan ba za ta yi ba, don ta yi hankali.
Hakan nan da wayona na san Umma tana
goyani ta kuma ba ni abinci a baki. Ina cikin
wannan sha'anin ne ya dawo ya same ni bai kuma
yi kwana goma sha hudu a gidan ba sai da ya
dauke ni daga gidan ya kai. ni makarantar
secondary yan mata ta kwana dama kuma ya zo
ya same ni ne ina J.S.S 1, ya kuma yi hakan ne ba
tare da ya shawarci kowa ba, bai kuma sanar da
makarantar da ya kai nin ba, balle a samu damar
kai mini ziyara. Yana kai ni mamakarantar nan
nan tsinci kaina cikin wata irin matsananciyar
rayuwar da ban taba mafarkin ana yin irin ta ba.
Ni da na saba tashi daga barcina Baba Talatu, ko
Umma wata cikin su ne za ta yi mini brush ta yi
mini wanka, ta dauro mini alwala, sannan in fita
in zo in yi sallah, a shafa mini mai a taya ni n
sanya uniform dina, a kawo mini abin karyawana
in karya, direban da yake kai yaran gidan nmu
makaranta ya y1 ta zirga-zirgar neman in fito in
ban ga dama ba in ce ni ban gama ba, umma ta ce

12
mishi kai je ka in ta gama za a kawo ta wata ra
a kai ni, wata ran kuwa in ce ba za ni ba, in hau
gado in yi kwanciyata da uniform din a jikina ina
kallon finafinan yara. Shi ne wai Yaya Almu ya
dauko ni ya zo ya jefar da ni a wannan
fankaceciyar makarantar da kowa ta kan shi take
yi.
Wuni nake yi ina kukan bakin ciki da rashin
sanin abin yi, tun ina bai wa yara tausayi su taru
suna ba ni hakuri sai suka koma cewa ai sai ki y1
ta yi har sarkin kuka ya zo ya same ki, da yake kin
ga wata wacce ba daga gida ta fito ta zo nan ba da
za ki tasa mu a gaba da kuka kowanne lokaci in ba
ki sani ba mu gaya miki muma duk iyaye ne da
mu suna son mu kuma suka kawo mu, bake kadai
ce mai iyaye ba. Da. abu ya kai matuka ma suna
ganin bawaye sun soma zubowa daga idanuna za
su watse su ba ni wuri, Suna fadin maiya in ba ki
daina kukan nan ba sai mamanki da babanki sun
mutu kya yi kukan mai dalili. Wannan kalma ta su
ita ce ta yi matukar razanani ta yi dalilin da na
daina kuka, na koma zaman bakin ciki da damuwa
da kunci da yunwa.
Ina cikin wannan halin ne har ranar ziyara ta
zo Yaya Almu ya kawo mini ziyara yana sanye da
faraen kaya kaftani da wandonsu, sun yi matukar

13
kar6ar shi. Rike hannuna ya yi ya jani ya kai ni
cikin motar da ya zo a cikinta wacce take ta kan
shi saboda ta dace da samun ma'abocin tsabta.
Tasa ni a gaba ya yi yana yi mini kalamai, saboda
irin kukan da na rinka yi mishi.
"Hakuri kawai za ki yi R abi, ya zame
mini dole ne kawai in yi miki hakan, saboda ba
zai yiwu in barki ki girma cikin yanayin da na
same ki ba, in na yi miki hakan ban yi wa kainaa
adalci ba, ke ma kuma ban yi miki ba. Hakan nan
ban yi wa Baba ba, ke din kina bukatar zama
jaruma ne, saboda al'amuran da ke gabanki ki
zama wacce wadansu za su dogara da ke, don
tsayuwar su ba wacce ba za ta iya dogaro da kanta
ba, komai sai an yi mata. Ki zama wacce ta san
darajar dan adam da girman shi, ba wacce take
taka shi a.duk lokacin da ta ga dama ba. Wannan
dalili ne kawai ya sa na rabaki da gida, don haka
ki yi hakuri ki saki ranki, ki kwantar da
hankalinki, ki koyi mu'amallah da mutanen da
kika samu kan ki a cikin su, don ki ji dadin
rayuwa tare da su."
Har ya yi maganganun shi ya gama ban tanka
mishi ba, ban kuma dainan kukan da nake yin ba.
"Ina kawayenki?"
Ya tambaye ni yana kallona cikin nutsuwa

14
  duk da bai furta ba, tsananin ramar da ya gani a
tare da ni ya ba shi tsoro da tausayi.
"Ki yi kawaye 'yan guda biyu ko uku za su
taimake ki ki fita daga cikin damuwa mai yawa
kin ji?"
Ban amsa mishi ba, ya ci gaba da magana.
"Ki maida hankalin ki akan karatunki, ki
shiga duk harkokin da ake yi a makaranta za ki ji
dadi yanzu mu je in kai miki kayayyakin amfanin
da na zo miki da su."
Ban tankaba, ban kuma musa mishi ba.
Shake bayan but din shi ya yi da kayayyakin
amfani gaba daya aka jide su aka shirya mini su a
lokata da lokar yarinyar nan da ke kusa da ni
Asabe Aliyu, duk yaran da muke daki daya kuma
sai da ya ba su sabulai da omo da kayan tea,
sannan ya kama hanya ya tafi ya bar ni ina ta
faman kukan takaici wanda in ban da tsananin
tsoron shi da nake ji da rike shi na yi na ce mishi
ya kai ni kawai wurin Ummana.
A haka na yi zaman makaranta, tun ban iya
hidimominta ba har na koya kullum ba ni da wani
aiki in na kwanta sai na lissafin ranar hutu. Ranar
da Yaya Almu ya gaya mini kenan zai kawo ni
gida in sadu da Ummana ranar da zuciyata ta
rinka shakkun isowarta, saboda tsaikonta da nake

15
gani.
Duk ranar ziyara dai Yaya Almu bai fashin
zuwa, in zai zo kuwa hatta ruwan sha kawo mini
yake yi, amma duk da haka a banza ban ganin
alherin shi. Kawayena dai ba su da wata hira in
banda hirar kai Yayan Rabi'atu yana sonta, ji
rannan ma da ya zo ya yi mata abu kaza da kaza,
muma ya ba mu abu kaza da kaza. Ni kam zuba
musu ido kawai na yi ina kallon su.
Ana gobe za a ba mu hutu kuwa ni kam
kwana na yi idona biyu ko gyangyadi ban 1ya yi
ba, saboda zumudi, gar na wayewa na gama
shirina ko wanka ban yi ba na tasa jakata a gabana
ina zaman jiran zuwan Yaya Amu da na rinka
ganin kamar ba zai iso ba. Sai wajen karfe goma
sha biyu ya. iso kan nan kuwa na riga na gaji da
jira wai da ya kalleni sai ya ce mini;
"Na dan sarara ne ki samu ki gama kintsa
kayanki: "
Ban tanka mishi ba, kawai yaran ajin mu
suka biyo ni da jakata suka kawo mini ita cikin
motar, Yaya Almu shi kuma ya kawo kudi ya ba
su.
A gida rannan Ummana da Baba Talatu kuka
suka yi ta yi suna fyace majina ana ba su hakuri
da suka ganni.

16
"Mu je in yi miki wanka in dirje miki
wannan dattin da ya zauna miki a jiki, saboda
rashin wanka mai kyau." In ji Baba Talatu. Na ce
mata, 'A'a zan yi wankan da kaina."
Da daddare muna kwance a kan gadon
Umma tana kankame da ni, tanfar so take ta
maida ni cikinta ta ce; "Bari hutun nan ya zo
Rarshe zan ga yanda za a yi Lamido ya ce zai
maida ke wannan makarantar ja'irin yaro káwai ya
je ya kai ki wata munafukar makarantar da ya ki.
fadar inda take balle in rinka zuwa duba ki inda
na san inda kike ai ko ban rinka zuwa ganinki
kullum-kullum ba zan je kowanne sati."
Ni kam tun da Umma ta ce ba za ta bari Yaya
Almu ya maida ni ba, na samu kwanciyar
hankalinan da nan na dan yi kyau na yi kumari
kibata ta soma dawowa.
Kullum ina tare da Ummana ita da kanta dai
ta yarda cewar wai zaman makarantar ya canzani
na zama nutsatstsiya mai son aiki na daina zagin
mutane ba na ma shiga harkar su in ba sune suka
tsoma ni a ciki ba, to amma kuma ta kafe kan
cewar wahalar ta ta yi yawa, don haka zan dawo
gida a canza mini wata wacce za a ninka ba ni
cikakkiyar kulawar da ta dace da ni.
Shi kam Yaya Almu harkokin shi kawai yake

17
yi, tsakanina da shi dai ina kwana ne ina gajiya?
in na yi kamar ban gan shi ba, kuma shima ya yi
kamar bai san da ni ba, ni kuwa ko motsin
tahowar shi na ji sai in yi maza na shige dakin
Ummana, don ban son ganin shi. Rannan da safe
ranar wata litinin ya shigo falon Unma da safe
cikin shirin fita, shigar shi ce dai a tare da shi ta
fareren kaya kamar kullum, kuma ya yi kyau yana
sosa kunnenshi da dan makullin motar da ke
hannun shi.
"Ina Rabi take Umma?
Ba tare da ta yi wani tunani ba ta ce misba,
Tana ciki." Ya bude bakin shi ya kirani, "Rabi zo
mu je nan ki yi mini rakiya."
Kullum kalmar da yake amfani da ita kenan
in zai ce in yi mishi rakrya, bakan nan ya sha fita
da ni don haka abim ba1 zamo mana wani sabon
al'amari ba.
Mun fito mun hau kan hanya muna taifya ya
dan juyo kadan ya kalleni kafin ya tambayeni,
Yaushe ne butun makarantar ku zai kare?" Sai da
na ji kirjina ya yi dam kafin na shiga kici-kicin
kokarin tunanowa cikin fargaba da tsoro sai dai
ban iya tunowa ba, saboda tun da ka ba mu
hutun ban taba damuwa da son in san yaushe
hutun zai kare ba, ni dai bukatata kawai ita ce in

18
ganni a gida.
Tsawon lokaci ina nazari ban iya bashi amsa
ba, sai shi da kan shi ne ya gaji ya ce mini, "Hutun
ya kare tun shekaran jiya, don haka yanzu
daukoki na yi zan maida ke makarantar kár kuma
ki ce za ki yi mini kuka, don wancan karon
wahalar da kika ba ni ba karama ba ce, in kika ce
za ki sake yi mini haka a yanzu ba zan rinka zuwa
duba ki ba."
Kankame bakina na yi na rike don kar ya ji
Rarar kukan da nake yi na yi ta zubar da hawaye
kawai, har muka isa makaranta kuwa maganganu
yake yi mini kan muhimmancin ilimi da kuma iya
mu'amalla da jama'a. Muka isa makaranta ya bude
bayan motar shi ya yi ta ciro jakankunan da ya
riga ya yi mini.sayayya yara suka dibar mini
jakankunan ni kuma na bi bayan su ina kuka.
Ina shiga dakin mu yaran da na tarar a ciki
suka hayayyako mini.
"Kai Rabi'atu hutun ma ke da kuka ki ke
dawowa? To Maman ki ta bar ki a gida mana
kawai ta rinka dora miki tallan kamu."
Gaba daya suka kwashe da dariya, suna
fadin, 'Ai kuwa wannan za ta yi kyau da daukan
tiren kamu da sassafe."
To a kwana a tashi haka dai har na hakura na

19
saba da zaman makáranta, har na kwaci kaina
wurin yaran da sakarcina ya sa suka rainani a
farkon shiga ta makarantar a haka na kasance har
na zo aji uku muka yi jarabawa na dawo gida ina
Jiran fitowar sakamakona, har a wannan zaman
ma Yaya Almu bai bar ni na sarara ba, samin ido
ya yi ya kafa mini dokar tashi in je masallacin
gidan mu da Asuba in yi sallah, bai yarda a ce
mishi na yi a daki ba, in na zo másallacin ma wai
sai na bari ya ganni tukunna kafin in bar
masallacin in dawo daki. Ni kam cewa Umma na
yi sai dai ya san yanda zai yi da ni ba dorina ba ya
sa takobi ya fillce mini kai, in ga karshen kiyayya
kenan da tsana. A ce tun daga nan sai na tafi har
masallaci kafin in yi sallah? Umma ta zuba mini
ido tanan kallona ta ce.
Ba dai Babangida kike wa wadannan
naganganun ba ko?"
Na kara daure fuska na ce mata, Shi mana
Umma ai kina kallon abubuwan da yake yi mini
na 'yan ubanci, amma ba ki taba yi mishi magana
ba."
Ta kama baki ta Tike nuna alamar mamaki ta
ce, "Babangidan ne mai nuna miki yan ubanci?"
Na ce, "Eh mana."
Ta gyada kai tare da cewar, "Lalle ba ki da

20
wayo."
Sau biyu na san Yaya Almu ya kiranı ya
jaddada mini dokar da ya kafa mini ta zuwa sallar
Asuba a masallaci, bai kuma yarda in zo in tafi ba
tare da na jira mun hada ido da shi ba, ni kuwa na
yi ko in kula. Rannan da Umma ta zo tana tashina
da Asuba ma kurma mata ihu na yi na ce, "Ni
Umma ki bar ni ki daina tashina a wannan muku
mukun sanyin."
Ina jin Yaya Almu okacin da ya zo gaishe ta
yana gaya mata har yanzu Rabi.ba ta soma zuwa
sallar Asuba a masallacei ba, kamar yadda sauran
yaran gidan suke zuwa?
Umma ta bashi labarin sakarcin da na yi
mata sanda ta zo tashina tana dariya da ta gama
sai ta ce mishi ai ina ganin hakuri za ki. yi da
wannan dokar sai badi war aka kan nan ta kara
kwari. Bai ce mata komai ba ya sauko musu wata
hirar.
Washe gari kuwa da Asuba ina cikin
kwanciyata ina lullu6e cikin bargona mai laushi
sai kawai na ji an fige bargon na shiga rarume-
rarumen-abin rufawa, ina fadin, "Umma me ye
haka? Umma me ye haka? Umma ba na son irin
wanna.
Kan in karasa fadin abin da zan fada din sai

21
kawai na ji saukar bulala a jikina tsal! Tsal!!
Saboda gigicewa sai na saki fitsari akan gadon,
kafin na iya kurma ihu da gudu Baba Talatu ta
shigo tana fadin, "Me Uwar dakina ta yi wa
Lamido? Ka yi hakuri, ka yi hakuri, ka huce ka
hadiye wannan fushi da ka yi."
Da sauri ya juya ya fita ya bar dakin, ni kuwa
na samu damar kurma ihu ina birgima a cikin
fitsarin da na yi, ifa kuwa sai rarrashina take yi
tana kakkana ni da kyar ta shawo kaina na yarda
na je na yi wanka na yi alwala na zo na yi sallah.
Tun daga ranar tashi daya Umma take yi
mini ta ce mini tashi ki yi alwala ki tafi masallaci
an kira sallah, in kuma kin ki kin san sarai
Babangida zai shigo bar nan ya zo ya same ki. Ina
ii ta fadi hakan zan tashi in je in yi alwala in nufi
masallaci, tun ina tashin ina tsaki har na saba ya
zame mii dabi'a.
A wannan zaman da na yi ne Yaya Almu ya
tiasta mini cin abinci, tare da yaran gidan mu. A
farko ya hada ni da wadanda na girma da na ce
mishi ba su iya tauna ba, kuma in muna cin abinci
suna ci mini gabana. Sai ya ce to ya raba ni da su
ya hada ni da wadanda suka girme ni, ya kuma
gaya mmusu cewar tun da ni ce karamna to ni-ce zan
rinka zuwa ina dauko abincin 1n an gama kuma in

22
fita da kwanukan su kuma abin nema ya samu don
su dukkansu da wuya in akwai wacce ba ta jin
haushina saboda rashin kunyar da na rinka yi
musu a baya, don haka gaba dayansu tasa ni a
gaba suka yi in na yi magana su kai karata wurin
shi, suka hada suka takura mini babu halin in ce
na koshi sai su daka mini tsawa su ce kamon wa
za ki barwa sudi? Na gaji da matsin su na ce mishi
ya maida ni cikin yaran kawai ya ce a'a anan yake
son ganina.
A haka na zauna a gida har lokacin komawa
makaranta ya yi a wannan karon ni da kaima na
gayawa Yaya Aimu wasu daga cikin sayayyar da
ya yi mini sai dai hakan ba vwai yana nufin na
Soma son karatun ba ne, a'a sani dai kawai na yi
ya zama dole zan koma don baka a yanzu Allah-
Allah nake yi in gama makarantar in dawo gida in
ga kuma inda za a sake turani da sunan karatu.
A makaranta a yanzu na wastsake na fita
daga cikin mafi yawancin wahalhaluna da na yi
gamuwa da su a karatuna na junior a yau na zama
cikin yan mata masu fada a da yawan yara
tsorona suke yi, wasu don tsiwata wasu-kuwa don
Kullum cikin ba su abin masarufi nake.
A haka har muka zo ajin karshe wato S.S. 3
muka yi jarrabwa muka dawo gida sakamako ya
23
fito na samu C guda biyu da B daya, ba zan iya
kwatanta bacin ran Yaya Almu ba, ranar da ya
duba sakamakon nawa ya zo ya tasani a gaba ya
ce, "Credit a Hausa da Islamic Studies Rabi?"Na
bata rai na ce, 'Allah bai wa masu F9 hakuri." Ya
kalleni cikin takaici ya ce, "To amin."
Alhaji Bello Mustapha sannanan mutum ne
da sunan shi. ya riga ya shahara saboda dalilai
masu yawa. Farko dai kasancewar shi babban dan
kasuwa, yana rike da sarautar gargajiya a garin
mu, ban da haka mai taimakon jama'a ne.
Gidan mu babban gida ne kwarai, ba zai
yiwu in tsaya ina kwatanta girman shi ba, abin da
zan iya fadi kawai shine da katangar gidanmu
data pen House din mu sune sukamamaye sashin
bangaren da mukegaba daya girman gidanmu ya
wucea tsaya ana kwatantashi akwai sashin baba
dana wurin saukar bakin shi da wurin ajiye
motoci da dakunan taro da sashan matanshi guda
uku wadanda aka yi musu ne ba da juna akwai
sashan yara maza wanda shima kashi biyu yake
bangaren samari dana yara kanana haka nan
sashin yan mata shima yake ga bangaren masu
aiki da wurin yin girki haka nan can karshen
bangon gidanmu ta baya wani babban fili ne da
aka yi shuke-shuken bisbiyoyi a wurinne kuma

24
baba yake kiwon raguna amma basa iya shigowa
cikin gida saboda akillace suke.
lyali ne masu yawan gaske a gidanmu a
lokacin dana ta so ina kara mata mu kusan arba'in
ne yara a gidan maza da mta manya da kuma
kanana amma daga cikinmu duka mu biyu ne
kadai muke amfani da sunan baba dagani sai yaya
Almu duk sauran 'ya'yan dangine dana tsofafftin
abokan da aka taso tare don ko akan idona ma an
kawo yara da yawa daga kauyenmu wadanda suka
isa sawa a makaranta don ma dawowa yaya Almu
ya ajiye ka'ida na kawo yaro daya ko biyu daga
gida guda in za'a kawo biyun kuma to sharadi ne
akawo mace da namiji ba maza kawai ba, shine
abin ya danyi sauki amma in da donta babane shi
babu ruanshi. kO guda nawa za'a kawo ba zai ce
komai ba.
Baba mutume mai daukan nauyi da
dawainiyar jama'a bai taba gajiya da hidimar
mutane ba rikon ya'yna yan uwa da yakeyi ya
dauki hidimar komai na al'amarin rayuwarsu bai
hanawa kuma iyayensu su taho neman wasu
bukatun nasa a wurinshi tun ma ba lokacin
damuna ba kullum zaka sameshi yana aiken kudin
takin zamani wai wanda zasu yi amfani da shi a
gonakinsu wata ran ina tare dashi yana ta fadin

25
abinda za'a baiwa kowanne nace mishi haba baba
kudin takin ma kaine maibasu in sunyi nomanfa
basa kawo mana komai gidan nan sai ya kalleni
yayi murmushi ya ce ai sun taimakeni uwata da
suke yarda in sun karbi kudin takin su tsaya su
noma gonakin nasu su samu abinda za su ci basu
rinka jiran sai ni na kawo musu ba, shi dan
uwanka makusanci da ki ke ganishi. yana da
hakkin mai girma cikin abinda ka mallaka shi
yasa ma baya cikin lissafin mutanen da aka ce ka
baiwa zakka kin gane?
Na ce mishi eh baba.
Baba mutumne mai saukin hali ga sanyin rai
ga hakuri ga kanrama mutanen da basu sanshi ba
sukan yi mamakin ganinshi in ance musu wannan
shine Bello Mustapha' da kuke jin sunanshi
saboda sau kin al'amarinshi kullum zaka same shi
ne cikin yadi dan shara shura da aka yiwa dinkin
kwado da linzami.
Dawowar yaya Almu ne ya tsara zaman
gidan ya zamo samarin gidan suna da karfi sosai
akan al'amuran gida sune ma suke tafiyar da mafi
yawancin al'amuran gidan maimakon da da matan
gida ne suke sa ido akan komai tunda baba ba
mazauni bane.
Tsarin da yaya Almu ya yi ne yasa gaba daya

26
yaran gidan suna karkashin kulawar yaya Zubairu
ne in an kawo sabbin yara shine zai basu wurin
zama da sutura shi zai yi maganar sanya su a
makaranta wurishin ake kawo kara babu wani mai
hukunta yara a gidanin ba shi ba sabanin da da
kowa aka yiwa laifi sai yayi duka to an hana yin
hakan babu mai yanci hukunta kowa sai dai a
kawo kara wurin yaya Zubairu hakan sai ya
tabbatar da bin doka da oda arami ya girmama na
gaba da shi shi kuma babba ya yi wa na kasa ashi
adalci.
Yaya Junaidu kuwa shine yake kula da sito
din gida shike fitar da duk wani abin bukata tun
daga kayan abinci har zuwa na masarufi duk wani
abin amfani a wurinshi akr karba hakan ya
taimaka kwarai wajen rage yawan ta'adin da ake
yiwa baba a gida haka nan in baba zai zo gida
shike zuwa dauko shia airport.
Sai yaya Kabiru shine yake. kula da cefanen
gidan a hannunshi komai na cefane yake saboda
dama matan baba basa cikin wadanda ake yin
girkin da su.
Shi kuwa yaya Almu shike kula da tsabtar
gidan dabbobin gidan da ma'aikata da kuma
lafiyar mutanen gidan gaba daya duk wani wanda
bai da lafiya wurinshi yake zuwa.

27
Wannan tsari da yaya Almu ya yi ya kawo
canji mai yawa da kwanciyar hankali urin
mutanen da ke gidan sabanin da da ake gwada
karfin tsakanin matan baba in wannan ta bayar da
umani sai wannan ta ce a'a ba abinda, za'ayi ba
kenan.
Kamar yanda ake da manyan samari haka
Dan akr da manyan yan mata a wannan lokacin ni
bana cikin manyám yan matan gidan don akwai
biyar a gabana wadanda a lokacin da nake final
year dina a secondary su sun fara karatunsu na
HIND' sune su Aina'u, Basira, Rahma, Kubra da
Rashida su din su yaya Almu ya baiwa kula da
abinda ya shafi yara mata, ganin yanda suke
tafiyar da al'amuran shugabancin da aka basu ya
sani 2akuwa da ganin anyi musu aure don in zamo
ni ce babba a gida tunda sauran 'yan matan da
zasu biyo bayana duk na girme su kullum inna
kadaice tunanin na baya wuce in aka kawar da su
ni yanda zan tafiyar da nawa shugabancin gashi
kuma zanyi hakan ne a lokacin da shima yaya
Almu ya bar gidan shine kuma dama mai takura
min a duk lokacin da nayi wannan tunani to bana
sanin lokacin da anke kyalkyalewa da dariya don
dadi.
Baba yana da wata dabi'a ko al'ada da yake

28
burge mutanen da suka sanshi da ita take kuma
kara baiyanar da darajar shi wurin yaran da yake
rikewa ita ce ta hada aure a tsakaninsu.
A duk lokcin daya reni samari da 'yan mata
suka kawo munzalin yin aure mazan suna gama
samun aiki zai tarasu ya gaya musu cewar ga 'yan
matan da zai basu wane zan hada shi da wance
wane ma da wance tun da yake yin hakan kuma
bai taba samun tangarda ba.
Umma na ita ce matar baba ta farko auren
saurayi da budurwa ita ce kuma marikiyar yaya
Almu don shi yaya Almu amaryar gidan Umma
amarya ita ce ta haifeshi Umma karama itace
matar baba ta biyu ita ce kuma ya auro daga cikin
dangishi haka nan ita da Ummana sune suke
fafata matsanancin kishi a cikin gidan don kuwa
har a shekárun nan nasu na girma babu sassauci a
cikin lamari don ma dawowan yaya Almu ya
dauki matakan kawo gyara a tsakaninsu an kuma
samu dan sassauci saboda kasancewar shi wanda
Ummana take sauraro yaya Almu ne ya kawo
Rarshen zaman wariyar da Ummana da Umma
amarya suke yi wa Umma karama. Zuwan shi ne
ya ki yarda da wareta da suke yi a cikin dukkan
al'amura ya ce lalle ne a rinka sanya ta a ciki tun
da dai ita ma matar Baba ce.

29
Ummana tana barin abubuwa da yawa,
saboda Yaya Almu misalı, kowa ya san ita da
Umma Karama ba sa jituwa, ni da kaina na san
ranar da suka yi 'yar tankiya tsakaninsu a falon
Baba, don sun hadu dukkansu a can, saboda shi
din yana gari Yaya Almu ne ya biyo bayanta har
falo ran shi a bace ya zo ya durkusa a gabanta ya
ce, 'Umma ashe har yanzu ana yin wannan abin aa
gidan nan? Har yanzu ba a kai lokacin da za ki
daina sauraron irin wadannan abubuwan ba ki
kawar da kan ki akan komai?"
Cikin yanayin jin kunya ta ce mishi, Yi
hakuri Babangida ni ban san kana wurin ba da ban
tanka mata ba."
Ya ce mata, "Bana nan a wurin Junaidu ne ya
yi waya ya kirani, amma ina so in roke ki daga
yau kar ki sake daga ido ki kalleta balle ki gane
wani abin da ta yi, don ranki ya baci in kin yi
hakan ba tsoronta kike ji ba ni da Rabi kika
rufuwa asiri."
Ta yi maza ta ce mish1, "Ba za a sake ba na
yau din nan shi ne zai zamo na karshe." Ya yi
mata godiya ya tashi ya tafi. Ni da kaina ba
karamin tsayuwa Yaya Almu ya yi ba katin na
rinka zuwa gaida Umma Karama kullunm safiya,
saboda a bayyane yake ba ta sona komai

30
kankantar abin da na y1 sai ta ce mini wai ai 1n
ban yi haka ba sai a yi mamaki, ko a yi shakkun
asalina, in kuma rabon abu take yi sai ta gama
rabarwa ni ba ta ba ni ba sai da wata rana ya je ya
same ta ya ce mnata don Allah in abin da take da
shi bai isa ta bai wa kowa ya samu ba to ta rinka
ajiyewa kawai ko kuma ta aika da shi can a waje a
bayar sadaka, amma ba a cikin gida a bai wa wasu
a hana wasu ba. Ta ce mishi to.
Akwai kyakkyawar alaka ta soyayya da
biyayya tare da ganin darajar juna tsakanin Yaya
Almu da Umma, duk wani abin da ya shafi Umma
yana da girma a vwurin shi, ko bakinta ya gani a
gidarn karbar da yake yi musu daban ne, ita ce
abokiyar shawarar shi kan lkomai in kuwa ya
ganta cikin wan: yanayi na daban ya rinka gaya
mata maganganu masu dadin j1 kenan da kwantar
da hankali, har sai ya ga ta samu nutsuwa. Da
yawan mutane dauka suke yi Ummana ita ce
mahaifiyar shi, saboda yanda suke ganin
mu'amalarsu, ba sau daya ba, ba sau biyu ba ya
sha zuba kudin shi ya gyarawa Umma wurinta,
saboda kasancewar mafiyawancin bakin da ke
Zuwa gidan wurinta suke sauka sai ya zamo a duk
lokacin da Baba ya yi musu gyara na ta wurin kan
riga na saura bukatar a sake duba shi, a duk

31
lokacin da Yaya Almu ya lura da hakan sai kawai
ya sa a fitar da kayan wurinta ya zuba mata
sababbi.
Shi Yaya Almu da daya ne tamkar da goma
kasancewar shi da namiji guda daya da Baba ya
haifa bai sa shi ya maida kan shi daban da sauran
mutanen da ke gidan ba, yana matukar girmama
Yaya Junaidu da Yaya Zubairu, saboda dan
girman da suka yi mishi, wanda bai wuce shekara
ko shekara da yan watanni ba, komai a ka zo
nema a wurin shi sai ya ce a jira sai sun dawo ya
yi shawara da su, in kuwa bakin Baba ne suka zo
suka same. shi to ya kan saurare su ne kawai idan
ya san ba sa nan a gidan, in kuwa suna nan to
cewa zai yi bari ya kira musu Yayan shi, ga shi da
kokarin gami da tausayin iyaye, tun dawowar shi
daga karatu daya nutsu ya soma tafiyar da
al'amuran shi a matsayin shi na Lauya, ya shiga
taimakon baba da hidimomin gidan ba komai sai
an nemi Baba ya yi aiken kudi ba.
A lokacin da na ke karama ta babu abin da
na ki irin in ga baki sun cika wurin Umma su yi ta
furzar mata da goro a ko'ina su ajiye kunshe-
kunshen bahunansu masu boye da daddawa da
kukar da suke kawo tsaraba. A duk lokacin da na
gan su daure fuska nake yi, wani lokacin ma

32
shigewa daki nake yi in yi kwanciyata ko gaishe
Su ban fitowa in yi sai in Umma ta kwala mini
kira,
"Ke Adawiyyah ba ki ji zuwan baki ba ne?"
Sannan ne nake fitowa in gaishe su ina gama
gaisawar kuma zan fara jidar kayan su ina kaiwa
dakin baki, in na gama in ce musu ga kayan ku na
kai muku can su ce mini to su bi bayan kayan na
Su, babu yanda Umma ba ta yi da ni ba in daina
yin hakan na ki kowanne lokaci ta yi mini magana
sai na ce mata to tun da yan 'uwansu Baba ne su
rinka zuwa gun Baba Karama mana, ita ma ba 'yar
uwarsu ba ce sai su zo nan su rinka gurbata miki
yanayin wuri da warin daddawa? Kowanne lokaci
na fadi hakan ita Umma cewa take yi Allah dai ya
shirye ki Adawiyya.
Rannan sai muka yi haka da Umma a gaban
Yaya Almu bai ce mana komai ba sai da ya tashi
zai fita sai ya ce mini, To zo. mu je mana Rabi."
Na ce mishi to. Na yi maza na bi bayan shi zuwa
dakin shi. Muna shiga ya juyo ya cafke mini
kunnena ya rike da karfin shi, sannan ya soma
tambayata.
"Sau nawa na ji Umma tana yi miki kashedi
akan bakinta?"
Ihu nake kurmawa, saboda tsananin zafi shi

33
kuwa sai kara matse kunnen yake yi yana fadin,
"Sai kin gaya mini abin da ya sa kika maida
Umma abokiyar wasan ki, saboda kin ga ba ta iya
yi miki komai sai rokon miki shiriya?"
Yaya Jnaidu ya turo kofar ya shigo dama
kuma su biyu ne da dakin.
"Sakar mata kunne Mustapha ko ba ka rike
shi ba za ta ji abin da kake son gaya mata." Yaya
Almu ya kallé shi cikin nutsuwa da kwanciyar
hankali ya ce mishi, "So nake in cire mata wannan
guda dayan in barta da daya."
Yaya Junaidu ya yi murmushi ya ce, "Kai da
Baba kenan in ka cirewa Adawiyyar shi kunne.
Ya sa hannu ya rike hannun na shi da ke rike da
kunnen nawa ya ce, 'Sake ta." Ya saki kunnen ba
tare da ya sake ce mishi komai ba sai dai ya kallen
ya ce mini ina so in sake ganin an yi baki kina
kwashe musu kayan su ba tare da kin jira an baki
umarnin yin hakan ba.
Washe gari da safe ya shigo ya same ni a
falon Umma ina ganin shi na mike tsaye na fara
tafiya ina gaishe shi, bai amsa ba ya ce mini, "Zo
mana." Na dawo na ce mishi gani. Ya nuna mini
kujera ya ce mini, 'Zauna mu yi hira." Na koma na
zauna don tsoro da bin umarni ya zuba mini ido
cikin nutsuwa ya ce, "Labari nake so ki ba ni

34
yanzu misali a ce ke din kin je gidan mijinki kin
zama uwar gida a wurin mij1 mai yawan jama'a
wane irin shugabanci za ki yi?"
Na daga ido ina kokarin in kalle shi na kasa
saboda yanda ya tsura mini na shi idanun yana
kallona. Ya ce, "Gaya mini mana za ki sa hannu
biyu ne ki rike shi tare da jama'ar shi ko kuwa za
ki watsa mishi su ne?"
Na kawar da kaina don kaucewa idanun na
shi, sai da na yamutsa fuskata sannan na ce mishi,
"To ni zan zama uwar gida ne?" Na tauna bakina
kafin na ce mishi ba na so ni in mutum ya ce zai
karo wata bayan ni tafiyata zan yi in ba shi wu.
Na sake hada rai na ce kai ni in mutum zai auren
ma sai na yi mishi kashedi, don ya san da sanin
shi yin auren shi bayan nawa auren yana nufin ne
kowa ya kama gaban shi tsakanin ni da shi.
Zuba mini ido Yaya Almu. ya yi cikin
al'ajabin jin kalamaina. Can dai ya daure ya bude
baki ya ce mini, "To ita Umma anan gidan baba
ya yi sa'a halinta ba irin na ki ba ne, ita ta amince
ita din uwargida ce tana kuma iyakacin kokarinta
akan hakan....."
Tun kan ya karasa na kasa-kasa da muryata
na ce mishi, "Madallah.
Ya yunkura yana tambayanta, "Me kika ce?

35
Na yi maza na soma yi mishi kuka ina cewa;
To ni me na ce?"
Ya mike ya kama hanyar fita tare da fadin,
Kwanan nan zan yi maganin ki tun da har nima
kunkuni za ki fara yi mini."
Sati biyu bayan wannan lokacin Yaya Almu
ya dawo daga wurin aikin shi ya aiko a kira ni na
yi maza na bi dan aiken zuwa wurin shi, don a
kwanakin nan duk ni da shi dasawa mukÄ— sai da
na bi ta wajen Baba maigyada mai dafa abincin
gidan mu nan karbi na Yaya Almu sannan na
wuce na je na kai mishih tare da yi mishi sannu da
zuwa, sannan na nemi wuri na zauna. Yaya
Junaidu ya fito daga bar dakin da ke dakin ya
kalli Yaya Almu da ke tashe da kwanon abinci ya
ce ni fa gaskiya na gundura da.cin abincin Baba
Mai gyadan nan. Yaya Almu ya yi dariya ya ce,
"Ka ce dai kawai ka kosa baba ya yi sallama a
koma cin na iyali."
Yaya Junaidu ya yi murmushi ya ce, "Ba ka
ji Zubairu ba rannan yana fadin wai har yanzu
Baba bai gane mun girma ba ne."
Ya wuce ya fita ya nufi masallaci ya bar
Yaya Almu yana dariya, sannan ya kuma soma
cin abincin shi Ko loma biyu bai gama hadiyewa
bai sai ya kalleni ya ce mini gaskiya Rabi irin

36
tunanin maida girkin gidan ya koma hannun yan
matan gidan baba maigyadan nan ta gaji, ni kuma
ba zan sake dauko wata mai girkin ba, alhalin ga
kartin 'yan mata a gidan. Na yi maza na ce masa,
"Eh Yaya Almu ka sa su girkin kawai don in ba
haka ba zuwa za su yi suna kwaba muku shirme a
gida don ba su iya komai ba in ban da su wanke
goma su tsoma biyar in kana so. ka ga kokarin su
to wurin iya kwalliya ne kawai, na kuma ji Umma
ma rannan da Baba ya yi mata waya tana gaya
mishi cewar ya fa tsare ku da yawa gara ya
sallame ku haka ya ba ku matanku kowa ya koma
inda zai zauna da iyalin shi, tun da duk kun dade
kuna aikin ku kai da Yaya Almu ina jin anti
Aina'u za a ba ka, don duk cikin su ta fi su iya
hadin kwalliya."
Dago idon da na yi na kalle shi ne na gane
tuni ya dade da hada fuska, nima sai na yi maza
na kawar da murmushin ta hanyar tsukewa. Tsaki
mai karfi ya ja kafin ya ce mini, "Ki daina na gane
ki kunya ta anini ba ki da ita, ni kike yi wa
maganar aure? Me kike cewa a yi a sallame mu? "
Na yi tsuru-tsuru da ido saboda irin wannan
maganar ba ta taba hada ni da shi ba.
Washe gari kuwa da safe sai na ji shigowar
Yaya Almu wurin Umma. Bayan sun gaisa sai ya

37
ce mata,
"Umma da za ki amince da sai yan matan
gidan nan su karbi aikin abincin daga hannun
Baba Maigyada ita ta zama tana sa musu ido nne
kawai, amma ba ta rinka yi ba."
Umma ta dan jinjina lamarin kafin ta ce
mishi, "Abincin baya dadi ne?"
Ya ce, 'A'a Umma mun dai gaji da cin natan
Tie kawai ita ma ta dan huta ai ta girma tun muna
yara fa muke cin abincinta."
Umma ta yi murmushi ta ce, "Za ku gaji da
komai ma yanzu ai Alhajin ya rike ku da yawaa a
gidan nan bai taba rike samari haka ba ko Kabiru
da ya gama karatu baya bayan ku yafi shekara da
kama aikin shi rannan ma sai da na ce mishi ni me
yake jira da ku ne haka?"
Ganin da ta yi Yaya Almu bai amsa maganar
tata ba ya sa ta gane kunya yake ji, ta ce mishi, "In
kun ga bakan zai gamsar da ku sai ka yi."
Ya yi mata godiya kafin ya ce mata,"To
Umma tun da su Kubura dukkansu suna zuwa
karatu ita Rabi ce har yanzu ba a samar mata wata
makarantar ba, saboda matsalar jarrabwarta, ina
ganin sai su rinka yi daga Monday zuwa Juma'a
na dare kawai ban da na rana, ita sai ta rinka yin
na Asabar da Lahadi na rana da na dare."

38
Ina zaunc ina sauraron jin abin da Umma za
ta fadi akan wannan mummunan hukunci na Yaya
Almu. Sai kawai na ji ta ta ce mishi, "To." Haba
ai ban san lokacin da na kurma musu ihu ba, na
shiga birgima ina cewa,
Gaskiya na gaji na gaji da 'yan ubancin da
Yaya Almu yake nuna mini, na gaji da takurar da
yake yi mini. Na.gaji da tsanata da ya yi ta sani a
gaba ya hana ni sakat, ni da gidan ubana ni ina
cikin 'yan matan gidan nan ne da zai yi kason
girki har da ni? Gaskiya ni Umma ni ki karban
mini.
Ban karasa maganar ba na ga ta zabura ta
sunkuto wani murfin tangaran da ke gefenta wai
shi za ta rotsa mini. Yaya Almu ya yi maza ya tare
ta yana fadin;
"Ki yi hakuri Umma in na bar ki kika rotsa
mata wannan a gabana ai sai yan ubancin na mu
ya kara bayyana."
Bayan fitar Yaya Almu Umma ko kallona ba
ta sake yi ba sai dai na ji ta tana ta rokon min
shiriya alamar dai ranta ya kai matuka wajen baci
kenan da abin da na yi. Ni kuwa ko a jikina,
saboda na samu na dan gayawa Yaya Almu abin
da ya dade yana cina a rai, shi ne yan ubanci ke
sawa yana takurawa rayuwa ta, yana bakin cikin

39
ganina cikin walwala.
Fuskarta a daure ta kalleni ta nuna mini
bokitin da ta shake da damammiyar fura ta ce
mini, "Dauki ki kai wa su Babangida." Hada
fuskar da ta yi ne ya sani daukan bokitin, amma in
ban da haka da na ce mata gaskiya Umma aiki
wani ya kai musu. Daga nesa na hange shi a kan
bayan motar shi yana zaune a gindin bishiya baba
maigadi ne á gefen shi a tsaye suna yin hira, na
matsa wurin na ce mishi;
"Ga damammniyar fura mai sanyi Umma ta
ce in kawo muku."
Ya kalleni cikin nutsuwa ya ce, "Kai wa su
Zubairu suna dakin su sai ki zo."
Na je na kai musu na dawo na samu ya sauka
daga kan motar yana cikinta har ya tayar da ita shi
ma baba maigadi ya tafi ina ce mishi gani ya ce
mini shigo mu je in kai ki wani wuri ladan rashin
kunyer da kika yi mini. Ban yi musu ba don kuwa
ni in har akwai abin da ba ni musun shi to fita
yawo nea zaga gari.
"Me kike so yau a sai miki?"
Na yi maza na ce mishi, "Oho." Ya ce, "Uh
kin san ni yanzu lallabaki zan rinka yi tun da kin
gane 'yan ubanci ne ya sa na ke yi miki abin da na
ke yi miki na takura, na tsane ki na takura miki,

40
na tasaki a gaba abin da kika fada kenan ni kuma
a wurina ban taba tsanar ki ba, ban taba takura
miki ba, balle in kai ga saki a gaba ni in kika bar
nima a wautata sai in ce miki ko Umma ba ta fini
sonki ba, sai dai nina bambanta son da nake yi
miki da irin wanda ita take yi miki, ita taná yi
miki so ne irin wanda babu kwaba a cikin shi, ba
ta iya bude ido ta kalle laifin ki, balle ta ga
kuskurenki, ta yi miki gyara ita komai kika yi a
wurinta daidai ne, saboda ba ta son bacin ranki ba
ta so ki wahala, farin cikin ki kawai take son gani,
saboda tana so ta jiyar da ke dadi ko da kuwa me
hakan yake nufi in ba kya son abu to komai
alherin shi sai ta taya ki kin shi."
Ya dan waiwayo ya dan kalleni a hankali
cikin sakin fuska ya ce, "Soyayyar sangartarwa
kenan Rabi, idan na taya Umma muka yi miki irin
wannan son dukkan mu to ni da ke ne za mu cutu,
don ke kan ki ba za ki ji dadin kan ki ba, ni kuma
sai a bar ni da wahalar ki. Wannan dalili ne ya sa
na bambanta nawa son da nata mafi girmanyan
ubancin da na yi miki dai na san bai wucde raba
ki da ita da na yi na kai ki makaranta ba, inda za
ki je ki yi wa kan ki komai, ki zauna da mutanen
da ba 'yan'uwanki ba ne, balle su saurara miki. Ki
yi mu'amalla da mutanen da suko son ki da

41
wadanda ba sa son ki, maimakon zaman ki na
gida da kowa gudun bacin ranki yake yi, abin da
kika ga dama kuma shi za a yi wannan dai na san
shi ne babban 'yan ubancin nawa ko akwai wani
da ya fi shi?"
Ban tanka mishi ba sai ya ce, "To in ba ki
sani ba ni bukatata ta biya kan abin da na yi na kai
kis makarantar ne don ki je ki yi mu'amalla da
jama'a kin yi don ki koyi ki wa kan ki hidima,
kinkoya, da kin tsaya kin yi karatu to da kin jefi
tsuntsu biyu ne da dutse daya, ina nufin kin yi
mini nawa kin kuma yi wa kan ki karatu da ba ki
yi ba kuma wannan ko a jikina don ni fitowar ki
da credit biyu bai shafen ba, na dai ji miki takaici
ne kawai a a ce kin shekara shida kina karatu kin
fito da credit biyu."
Raina ya kara baci da yanda Yaya Almu
yake cire mini B3 din da na samu sai credit biyun
kawai yake ambata.
Wani babban shagon kayan kwalliya ya kai
ni ya ce, "Shiga ki zabo abin da kike so dan ni
yanzu zan kara ka fa-kaffa da ke ne, don kar ki
sake cewa ina yi miki 'yan ubanci, duk abin da
kika ce yan ubanci ne ya sa na yi, to ba żan sake,
shi ba."
Wadannan kalaman na Yaya Aimu ba su sa

42
ya cire ni cikin masu girkin gidan mu ba, kamar
yanda na yi zato tun da ya ce ya daina duk wan
abin da zan ce 'yan ubanci ne.
Ranar da girkin ya iso kaina har dakin
Umma ya biyo ni da bulalarshi ta dorina a hannun
shi ya ce mini;
"Rufin asirin ki kawai shi ne ki fito ki yi
girkin nan in kuwa ba haka ba to sai na tara yara
kanana, sannan in yi miki dukan tsiya a gaban
su.
Ya juya ya tafi, sanin halin shi da na yi ya sa
ban 6ata lokaci ba na fito cikin zuciyata dai sai
fadi nake yi, "Ba ka dai yi sa'a ba, tun da ba kai
kadai baba ya haifa ba."
Na kama aikin girki duk ranar da ya zo kaina
sai kawai in kwaba shi yanda na ga dama, ni kaina
ba na iya cin abin da nake girkawan, balle kuma
sauran jama'ar da ake yi wa. Yara sun rinka zirga-
zirga da kofunan gari kenan ko kuma in sun
hango Yaya Junaidu su ruga wurin shi suna
tambayar ko akwai indome a store a ba su. Wani
lokaci yaba su indome, wani lokaci ya raba musu
biredi ya ce su je su sha tea, wani lokacin garin
rogo.
Rannan ina zaunc a dakin Umma da safe ina
shan kunun gyada da Umma amarya ta aiko mini

43
da shi, sai ga Yaya Almu ya shigo. Sa hannu ya yi
ya karbe kofin da ke hannuna ya dangwarar ya ce
mini,
"Wuce mo je."
Na tashi sum-sum na bishi. Wurin wankc
wanke ya kai ni. Duron guda aka shake da abincin
da na yi jiya na rana da na dare aka kasa ci ya
kama bakin duron din da hannunshi ya rike yana
kallona cikin wani irin yanayi da ke kama da na
tausayin kai, ya kalleni cikin nutsuwa ya ce mini.
"Wannan abincin da Baba ya nemo ne ya
kawo mana don mu ci kika yi dalilin da aka juyec
shi anan ana neman inda za a kai shi, don a zubar
da shi. Abin abin tausayI ne wai ke daya kamata
ya yi kifi kowa jin tausayin shi, ke ce kike
jagorancin yi mishi ta'adi, a shekarun shi na girma
shckarun da ya kamata ya yi su cikin hutu tare da
iyalin shi bai zauna ba, saboda kokarin ganin
asirin mu ya rufu, amma bai cancanci tausayawa
ba a wurin ki, ko in kina yin hakan ne don in gaji
da ganin abin da kike yi in fidda ke cikin masu
yin girkin ba zan fidda ki ba, kin fi kowa
cancantar ki ciyar da mutanen gidan nan, ban ga
dalilin da zai sa ba za ki yi hakan ba, sai ki zauna
ke ana yi ana ba ki ranar da babu shi da su Umma
kina nufin za mu bar mishi iyalin shi ne yunwa ta

44
watsa mishi su?"
Ya yi tambayar cikin wani yanayi da ya sa
jikina ya dauki rawa, ya zuba mini ido tsananin
bacin ran shi ya kara bayyana. Ya ce, "Kina so ne
ki nuna mini ba za ki taya ni rike wa Baba iyalin
shi ba? Kina so ne ki nuna mini cewar ba ki san
kowa ba, sai kan ki? Yaran gida su rinka kwana
da yunwa hankalinki a kwance, saboda ke ba za ki
kwana da yuwar ba?"
Yana ganin na fara kuka ya wuce ya bar ni a
tsaye. Na jima a tsaye a wurin ina kuka, saboda
kalaman da ya yi mini da kuma ganewar da na yi
ban cutar da kowa ba, sai baba. Na biyo bayan shi
don in ba shi hakuri ban gan shi ba, sai Yaya
Junaidu na gani yana tsaye ana sauke katon-katon
din taliya, yana kallo ana shiryawa a store shi ma
cikin bacin ran.yake saboda irin kallon da na ga
ya yi mini, kafin ya ce mini;
"Mustapha zai zabi daya cikin biyu..."
Ban bar shi ya gaya mini dayan biyun da
Yaya Almu zai zaba ba, don na san bai wuce kan
maganar zaman da yara ke yi da yunwa ranar da
na yi girki ba, na durkusa na ce mishi, "Ka yi
hakuri Yaya Junaidu." Bai amsa ba na mike ina
dawowa kacibis muka yi da Anti Aina'u da Anti
Basira.

45
"Ke." Sunan da suka kirani da shi kenan. Na
matsa kusa da su na ce musu, "Gani." Anti Aina'u
ce ta fara bude baki ta ce mini;
"Daga yau kika sake kwaba kwaba66en
abincin ki kika turo a kawo mana a ce wai ke kar
mu jira ki kin koshi, za ki ga abin da zan yi miki."
Ita ma anti Basira ta dalla mini harara ta ce,
"Sakaryar yarinya kawai, sokuwa." Na wuce na
bar su cikin raina ina cewa na dai kusa hutawa in
a ka tattaraku aka kai ku gidajen mazan ku.
Gaba daya samarin gidan tsuke mini fuska
suka yi ko gaishe su na yi ba sa yi mini amsawar
da ta wuce guda daya shi kam yaya Zubairu da
yake hakuri bai ishe shi ba, kwakkwara mini zagi
ya yi, tare da tambayata so nake in nakasa yara da
yunwa? Na ce mishi a'a, ya ce to ke kina cin
abincin da kike yin? Na yi shiru ina kallon shi. Ni
da Umma gaba daya muka shiga cikin damuwa,
don ba'ta son ganina a takure.
"In ban da Babrngida ba zai yarda ba ai da
sai in sa Talatu ta rinka tayaki wannan aikin a
yafi karfinki,  ina ke ina girkin abincin mutanen
gidan nan?"
Ranar Asabar da safe ina gama gaida su
Umma wurin yin girkin na nufa ko bari in karya
ban yi ba na gayawa Baba Maigyada in masu
46
gyaran wurin sun gama ta sa a kira ni. Na je na
duba abin da ake da shi a cikin frezeer na fito na
nufi wurin Yaya Kabiru na gaya mishi abin da
babu a gida, wanda zan yi amfani da shi ya kalleni
ya ce, "Ki je ki yi haka ba zan sayo komai ba, yau
don mai bayar da kudin ba a kasa yake debo su
ba."
Yaya Junaidu da Yaya Almu sun riga sun fita
don haka wurin Ummana na koma na gaya mata
abin da ake ciki ta yi murmushi ta ce, "Ai shi
Alhaji sa'a ne da shi tun da yake bai taba rike dan
da bai so shi ba, lissafa abin da kike son sai in sa
akai Talatu kasuwa ta sayo miki."
Na ce mata to. Na zauna nan lissafo mata
kasancewar miyar Afang na yi niyyar yi. Ga
lissafin da na bukata.
Nama.                 Barkono
Ganda.                Maggi, gishiri
Busasshen kifi.    Albasa
Cray fish.           Sai kayan kamshi
Ganyen Afang Manja

Umma ta kalli lissafin nawa tayi murmushi
ta ce, 'A ce dai ki iya tsarawa ya yi kyau, to je ki
ki duba abin da babu a ciki sai ki zo ki gaya
mini." Na ce mata to.
Kafin tara rannan na shiga kicin sai da na

47
tafasa ganda ta yi laushi, sannan na hada shi da
naman na sake dafa su a tukunya guda daya na
kuma zuba musu maggi da gishiri na dauko asalin
tukunyar da zan yi miyar a ciki wacce take
katuwa sosai na dorata kan wnai kunannen karfe
din na zuba wadatacciyan manja da isashsshiyar
albasa, ban bari ta gama soyuwa ba na dauko
tukunyar da naman nan da ganda suke ciki na juye
duk da ruwan ciki na kawo gyararren busashshen
kifin na jufa, na kawo garin barkono da kayan
kamshi gami da maggi da gishiri na zuba na sa
murfi na rufe na bar shi yana ta dahuwa. Jimawa
can na kawo ganyen water leafda Baba Maigyada
ta yanka mini, na bar shi ya yi kamar minti biyar
sannan na juye ganyen Afang din na rufe. Nan da
nan kamshi ya gauraye ko'ina. Baba Mai gyada
sai salati take yi tana cewa,
Yanzu nan ke dama yarinyar nan ashe kin
iya girki haka, amma kika rinka tabka irin wannan
tsiya? Ai kuwa inda na sani da na gayawa su
Lamido cewar dukan tsiya ya kamata su yi miki."
Ni kam ban ce mata komai ba, kokari kawai
nake yi in ga na gama tare kuma da addu'ar komai
ya tafi daidai. Tuwon shinkafa na yi wa mutanen
gidan duka, su Baba Maigyada da su Baba Talatu
suka tuka shi suka tayani, suka yi mini rabon. Su

48
Yaya Almu kuwa na dafa doya na sa aka daka
musu sakwara kafin karfe biyu har na baiwa kowa
abincin shi na gama na koma kusa da Umma na
kwanta ina kallonta tana cin tuwon da na
mata, tare da shan miyar da cokali, dadi ya
kamata sai faman sanya mini albarka take yi.
Ina idar da sallah sai ga Baba Talatu ta shigo
tana tambayata.
"Uwar dakina ko dabara za mu yi ne mu yi
miki girkin daren?" Na ce mata, 'A'a gani nan
fitowa zan zo in dora." Ta ce mini, "To." Ta tafi
bayan ta ne na sha kunun zaki da Umma ta ba ni,
na dan ji sanyi a raina. Na je na samu har su Baba
Maigyada sun shirya mini kurfo-kurfo din sun
kunna gawayi don haka ina zuwa na dora
sanyawar miya. Baba Maigyada ta ce, "Ke yan
nan yi musu dafaduka ki huta. "
Na ce mata, "Bari kawai Baba Yaya Junaidu
baya son cin shinkafa da daddare.".
Ta ce, "Uhu! Haka ne
Tuwon alkama miyar kuka na yi, suma sun yi
matukar jin dadi. Na gama salamar kowa na
dawo daki na shiga cikin baf na kwanta cikin
ruwan zafi tsawon lokaci ina tunanin wahalar da
na yi a yau wajen aikin abincin gidan nan. Wai a
gobe ma haka ake so in sake yi. Na dade a

49
kwance ina tunanin kafin na yi wanka na fito na
zo na yi sallah na gyara jikina na zo na zauna
gaban Umma tana shafa mini gashin kaina, kafin
ta taje mini shi ta tubke mini wuri daya.
"Yau kam kin wahala bari zan gayawa
Babangida ya rage miki girkin nan."
Na yi maza na ce mata, "Bar shi kawai
Umma, ya ce mini nina fi kowa cancantar in ciyar
da mutanen gidan nan, tun da baba ne ya tara su,
to zan yi hakan komai wahalar shi."
Umma ta zuba mini ido tana kallon cikin
tunani, na san tausayina ne ya kama ta, don haka
sai na ce mata, "Kar ki damu Umma nima na riga
na gane ya zama dole in zama jaruma ba zai yiwu
a ce ni da gidan ubana in zauna sai wasu ne za su
rinka yin abincin gidan ba."
Ta yi maza ta ce, "Haka ne, haka ne
Adawiyyah, Allah dai ya yi miki albarka."
Tun tara ba ta yi ba barci ya dauke ni a nan
wurin saboda gajiya.
Washe gari kuwa Fried Rice na yi. Ga
abubuwan da na yi amfani da su:
Shinkafa.            Tumatur
Nama      Maggi, gishiri
Kwai.                  Albasa
Butter Curry

50
Tumaturin gwangwani.
Ga yanda na yi hadin sai da shimkafar ta yi
ta tafasa na tsawon minti goma sha biyar sannan
na sa aka juyeta a kwanduna ta tsantsame aka ba
za ta ta sha iska. Na sa aka yi wa albasa yankan
kwabo-kwabo aka yanyanka naman suka zamno
yan madaidaita, sannan aka soya su cikin butter
na sake. hada shinkafar nan tare da butter da
yanlkakken kayan lambun nan su karas, kabeji,
koren wake, curry da maggi na gauraya su gaba
daya, sannan na nrufe na sake maidawa kan
wutar. Bayan na rage mata karfi na soya kwan,
sannan a zauna na yi mishi yanka na ban sha'awa.
Sannan na sauke shimkafar na shiga yin rabo su
Baba Talatu, da Baba Maigyada sai murna suke
yi, suna fadin wannan yarinya da iya shege kike
yanzu a kwanakin bayan nan wa zai ce kin 1ya
girki haka? Da daddare kuma saboda Yaya
Junaidu sai na sake. yin tuwon semobita da miyar
kubewa bushasshiya suma sun yi dadi ba kadan
ba.
Tun daga rannan ban sake samun matsala da
girkina ba, kullum zan yi abinci zan tabbatar na yi
shi mai ban sha'awa a ido, mai dandano a baki.
Tuni na maida yin girki daga cikin abubuwan da
suke san ya ni nishadi, sai na zamo ba ni da

51

matsalar yawan abincin gidan mu, musamman da
na gane yaran gidan ma zumudin zuwan girkin
nawa suke yi, don kuwa yan matan gidan da ke
biye da ni cika wurin girkin suke yi mu yi ta yi
tare da su, suna tambayata anti Adawiyya daga
ansa wannan sai wanne kuma? In ce musu sai
kaza, shi kuma in an zuba shi minti kaza zai yi
kafin a sake zuba wancan. A haka sai in yi girkin
in gáma ban galabaitaba, suma su Baba Maigyada
wurin girkin sa1 ya zamo musu wurin hira ko ban
nemi taimakon su ba za su zo su zauna a yi ta hira
ana raha suna taya mu dariya, suna fadin kai
yaran nan sai a bar ku.
Suma masu gidan su Yaya Almu da su Yaya
Basira dadi sosai muke yi da su, tun ma ba Yaya
Junaidu ba, wanda ko yaushe zai shigo dakin
Umma ya same ni yana zolayata.
"Ni Adawiyya ki daure ki karbi girkin gidan
nan mana gaba daya."
In yi murmushi in ce mishi, "To Yaya
Junaidu in ka ce a yi hakan ai sai a yi."
Ya zauna mu yi ta hirar mu sai ya ga na fara
gyangyadi sannan yake tashi ya fita.
Tun da yan matan gidan suka kyalla ido
suka ga gaba daya jama'ar gidan kara sona suke
yi, saboda gwanintar iya girkina, sai aka shiga

52
gasar girke-girke kowacce wai so take a ce ai ita
ce gwana, amma ina? Na riga na yi musu
fintinkau. Umma kuwa sai cewa take yi, ai shi
girki da kike ganin shi har da baiwa a ciki, ni kam
dariya na ke yi in na ji ta fadi haka a zuciyata
kuma in ce girkin zamani dai har da koyo a ciki.
Tun da na riga na saba da girki ko ba ni ce da
shi ba sai in ga ina sha'awar yin shi, don haka sai
na shiga shiryawa Ummana abin karyawa da safe
in ni ce da girkin kuwa sai Baba Talatu ta yi
mana.
Rannan ina cikin kicin din Umma ina
kokarin shirya mata abin karyawa yayin da ita
kuma ta shiga wanka, sai ga Yaya Almu ya shigo
cikin kicin din.
"Me kike yi ne Rabi na ke jin kamshi haka?"
Na yi murmushi na ce mishi, 'Abin karyawa
nake yi wa Umma."
Ya kara matsowa kusa yana kallon yanda
nake gauraya tankadadden garin fulawa da citta a
cikin narkakken butter, sugar, zuma, da lemon
tsami da ke kan wuta. Ya kasa hakuri da abin da
yake ganin ya gaji ya ce mini;
"Ni Rabi a ina kika koyi girkine haka?"
Na yi murmushi na ce, "Yaya Almu kenan ka
mance credit biyun da kake cewa na ci a

53
Jarrabawa akwai wata B3 da baka ambatonta
wacce na samu a Home Management"
Yaya Almu ya rike baki ya ce, "Haka kuwa
aka yi, wato har da girki kika koya a zaman
makarantar nan da kika yi?"
Na ce mishi, "Eh."
Ya ce, "To ya tabbata dai na kin ne kawai ba
ki tsaya kin yi ba, amma nawan duka sun samu
tun da ko ba komai gashi nan yanzu kowwa
zumudin zuwan girkin ki yake yi, yara da manya.
To me ya fiye miki haka dadi?
Na ce mishi, "Babu."
Ban san Umma tana jin mu ba, sai da na ji
tana cewa, 'Ai wannan 'yan ubanci da ka yi wa
Adawiyya ya yi matukar zama mata alheri tun da
ya rufa mata asiri."
Yaya Almu ya yi dariya ya zauna muka
karya tare da shi.
Tun da su Yaya Almu suka gane ina yi wa
Umma abin karyawa da safe sai suka maida
sashinta wurin karyawar su kullum kuma da irin
abin da nake shiryawa. Rannan da rana sai ga
Yaya Junaidu ya dawo cikin sauri ina ganin shi na
ce lafiya? Ya ce, 'Lafiya Adawiyya na dawo ne
zan yi shirin tafiya garin Edo gobe da safe." Na
rike baki na ce, "Za ka dade ne?" Ya ce, 'A'a na

54
  
sati guda zan dai yi missing din ki ne na wannan
satin, kin san yanda nake son cin abincin ki
kuwa?"
Ya zuba mini ido yana kallona, cikin
nutsuwa na dan yi murmushi na ce mishi, "Na
sani Yaya Junaidu to, bari in je in shirya maka
abin da za ka rike ka rinka karyawa da shi."
Ya yi maza ya.ce mini, "Ai kuwa da kin
taimake ni, don ni lokacin karyawa da abincin
dare sunan cikin lokutan da nake so a kula mini daa
abin da zan ci sosai."
Na ce mishi, "Haka ne."
Na juya na tafi na je na soma yin shirye-
shiryen yi mishi White Bread da Raisin Bread. A
White bread din ga abin da na yi amfani da su:
Sugar
Ruwan dumi
Yeast.
Margarine
Flour
Gishiri
Shi kuma Raisin Bread sai na yi amfani da
wadannan kayayyakin:
Seedless raisin cup
Flour.                      Sugar
Baking powder.      Kwai

55
Soda.                  Madara
Gishiri.                Lemon Tsami
Oat.                    Butter
Ina gama wadannan na sake yi mishi Meat
Ball shi ma ga kayan hadin shi:
Nama                Madara
Albasa.              Flour
Garin bredi         Kwai
Butter.               Chese
Maggi.                Mangyada
Gyada mai laushi da gishiri.
Ba zan iya kwatanta farin cikin Yaya Junaidu
ba, a lokacin da na kai mishi kasa ce mini komai
ya yi ya zuba mini ido ya ce, 'Adawiyya mijinki
zai more." Na yi maza na rage fara'ata na ce
mishi, "Sai ka dawo na." Na juya na koma sashin
Ummana.
Ni kaina ban san mun shaku da Yaya
Junaidu sosai ba, sai a wannan tafiyar tashi duk da
gidan mu cike yake da jama'a ina kuma da
al'amuran yi masu yawa kewar shi sosai na yi don
kuwa mutam ne ma'abocin hakuri da juriya ga na
kasa da shi, mu'amalla da shi kuwa mai dadi ne
sosai, saboda komai na shi akwai 'yanci mai yawa
a cikin shi, saboda ya san yancin dan adam. Yaya
Junaidu yana cikin mutanen da na sha jin Ummna

56
tana cewa ba za ta mance dawainiyar da suka yi
mata da ni ba, ita da kanta tana mutunta shi, haka
nan kasancewar shi dan'wan Baba ya sanya shi ya
zamo mai karfi sosai a wurin Baban, kuma
yardajjen shi mafi yawancm al'amuran da yakan
wakilta a yi mishi in dai akan dukiya ne to shi
yake dorawa a kai.
Mu'amallar shi da Baba mai karfi ce kwarai
ban da zamowar shi shi ne mai zuwa ya dauko shi
in zai zo gida, babu kan yarda wani ya tuka shi ne
kawai in dai yana gari a lokacin da yaya Junaidu
baya nan ko yana wurin aiki shi din mutum ne
mai cikar halitta yana matukar kama da Yaya
Almu, ma'abocin yi ado ne, yana kuma kyau da
adon. Mutum ne shi da bai cika son hayaniya ba,
8ai dai yakan yi magana cikin nutsuwa, ga shi da
ilimi don ba na mantawa a ranar da baba ya dawo
gida na kai mishi sakamakona na gama Secondary
ya karba ya gani .ya yi ta yabon kokarina, wanda
ba haka Yaya Almu ya so ba, da ya miko mini
takardar cewa ya yi;
"Maza je ki ki Boye abincki kin yi kokari kar
ki yarda ki bari Junaidu ya gane miki ita, don kar
ya yi miki ba daidai ba, kin san shi a lokacin da va
gama karatun shi na Secondary Excellent bakwai
da Credit biyu ya fito da su."

57
Ya juya wurin Junaidu cikin fara'a ya ce
mishi, "Baka ga takardar ta ba ko?" Ya ce mishi,
"Na gani Baba sai dai ban lura da abin da yake
cikinta ba." Yana dariya ya ce, "Yauwa to ka
kyauta da ka yi hakan, ka kuma yi dabara kwarai."
Ni kaina na san Yaya Junaidu yana cikin
yayyena da na ke so,  nake girmamawa,  nake
kuma yawan mu'amalla da su zan iya cewa ma
mu'amalla da shi kan yi mini dadi akan da Yaya
Almu, saboda shi Yaya Almu akwai tsoro mai
yawa a tsakanina da shi, sai kuwa Yaya Junaidu
komai na shi mai sauki ne babu fada, babu zare
ido balle ga yin barazana ko duka.
Sati guda Yaya Junaidu ya yi kafin ya dawo,
tun safe ya yi waya ya taso amma. bai iso ba sai
gab da za a yi sallar Magriba. Yana isowa sashin
Umma ya fara ziwa dama kuma dukkan su al'sdar
Su, kenan duk inda suka je suka dawo. to wurin
Umma za su fara zuwa, su gaishe ta kafin su je su
gaida sauran matan gidan. Ina ganin shi na yi
tsalle na karbi jakar da ke hannun shi. Ina ta tsalle
kamar wata 'yar karamar yarinya,
Umma ta ce, "Kai ke kam Adawiyya Allah
ya shirye ki har yanzu ba ki daina yi wa Junaidu
irin wannan oyoyon ba?" Yaya Junaidu ya yi
murmushi ya zauna a kasa a gabanta suna gaisawa

58
  
tana tambayar shi labarin hanya yana gaya mata al
wurin da nisa. Umma suka dan yi hira da ya tashi
za1 fita sai ya ce mini ina fata kin tanadar mini
abin da zan ci don tun sauran bread din ki da na ci
da safe ban sake cin komai ba.
Na ce,"Na yi maka girki, amma ina ganin ba
za su hanaka cin abincin gida ba. Anti Basira ce ta
yi girkin na kuma ji Umma ta ce ya yi dadi, don ta
kawo mata."
"Ke ba ki ci ba kenan?"
Na ce, "Eh, saboda ban sha ruwa ba tukunna
na yi azumi."
Ya ce,"To bari in je in gaida su Umma kafin
a yi kiran sallah ni in yi sallah in yi wanka, ke
kuma kin sha ruwa sa1 ki kawo mini dakin mu."
Na ce mishi to.
Sai da na gama shan ruwa, sannan na dauki
abin da na shirya mishi na je na kai mishi shi da
Yaya Almu na samu a.cikin dakin na su suna hirar
tafiyar tashi. Na je na duruksa na gaida Yaya
Almu kafin na sake yi mishi sannu da zuwa na
ajiye mishi kwanukan da na zo mi shi da su a
gaban shi na kuma bude mishi ya zuba ido yana
kallo cikin murnmushi;
"Ke Adawiyya ba zan ci girkin nan na ki ba,
sai kin gaya mini sunan shi da yanda kika yi kika

59
yi shi"
Na kalle shi na yi murmushi na ce, "Ai kuwa
don na matsu da ka ci ne kawai zai sani yin hakan
ka ga wannan salad ne, amma kaza wato cikin
salad, wannan kuwa."
Na kara karkata mishi kwanon don ya gani
da kyau na ce mishi, "Salmon pie sunan shi, bari
in lissafa maka abubuwan da na yi amfani da suu
kafin in gaya maka yanda na' yi."
Shi kam Yaya Aimu bai jira bayanin da zan
yin ba ya mika hannu ya dauki Salmon pie din
guda daya sai da na gyara zama sosai na fara
lissafawa Yaya Junaidu kayayyakin amfanin na
ce, Bari mu fara da Salmon pie, na yi amfani da
kwababbiyar fulawa da na cakudata da butter,
gishiri, pakin powder, sai shinkafa, albasa, cream,
kafin gwangwani, dafaffen kwai, butter da na dafa
shinkafa na tsameta na tsantsame sai na yanyanka
albasa na soya shi cikin butter, sannan na zuba
shinkafar da kifin tare da cream na gauraya su da
kyau na rinka yanko kwababbiyar fulawar nan ina
amfani da board wajen murzata tana yin fadi. Sai
na rinka debo hadin shinkafa da kifin nan ina
zubawa a tsakiya ina rufewa da rabin 6arin
fulawar bayan na zuba yankakken kwai a kan
shinkafar in ya ruhu da kyau sai in sa wuka in

60
 
yanke sama da kasa, don ya zamo a bude kamar
haka."
Na daukoo guda daya ina nuna mishi, don ya
gane sosai.
"Don ya rinka fitar da tururi daga nan sai na
salka a oven ya gasu na kusan mintoci ashirin, shi
kuwa chiken salad ga abubuwan da aka yi amfani
da su:
Dafaffiyar kaza,       kwai dafaffe
Mai, cokali biyu.       Atile
Mayonniase.             Tafarnuwa
Dakakken 6awon lemon tsami, yaji.
Ina shirin fara gayawa Yaya Junaidu yanda
na yi na shirya mishi chicken salad din sai kawai
wayata ta yi kara in dauka sai na ji muryar Julde
yana tambayata.
"Ina kika shiga ne? Gani nan a falon Umma
ina jiranki." ne?
Na kashe wayar na kalli Yaya Junaidu cikin
murmushi na ce mishi, "Kawai Yaya Junaidu tun
da ka ce sai na yi maka bayanin yanda na yi na yi
za ka ci, to ka ci salmon pie din kawai, tun da shi
na yi maka bayanin komai barwa Yaya Almu
kawai ya cinye chicken salad din. Ni na yi bako
Julde ya zo wurina zan je mu sha hira." Ina fadin
haka na fice dakin da gudu na nufi sashin Umma,

61
  don ganin Julde
Julde dan aminin Baba ne da suka taso tare
suka kuma matukar son juna, har suka zama
kamar yan'uwa saboda dadewar abotar su baba
Wulle.
Ina shiga falon Umma na same shi a zaune
ya sha kwalliyar Rananan kaya dama kuma
ma'aboCin sanya su ne sai kamshi yake yi, yana
ganina ya saki wani lallausan murmushi ya ce,
Ban gajiya na zo miki."
Na yi maza na yi wura-wura da ido don
ganin ko Umma tana kusa ta ji abin da ya fada, da
na ga an yi dace ba ta nan sai na fada mishi a
hankali.
"Kai Umma fa ba ta san na je ba."
Gaba daya ya bude baki da idanuwa nuna
alamar mamaki.
To ya ya aka yi haka?"
Na dan yi murmushi na ce mishi, "Kai dai ka
shown kawai."
Ya yi murmushi ya ce, "To na yi."
Na je na kawo mishi abin sha na kuma zauna
muna hira, har sai wajen goman dare, sannan ya
tafi saboda ya san 1yakacin hirar da bako ke yi a
gidan mu kenan in dai ba kwana zai yi ba, don
goma tana yi ake rufe get din gidan mu, in an rufe

62
kuma ba a budewa. Wannan umarmin Baba ne.
Sati guda da faruwar haka mun fita unguwa
ni da Yaya Almu cikin sabuwar motar shi
Kwalliya sosai na yi na kuma yi matukar yin
kyau, sai ma da Umma ta yi ta rokona sannan na
yarda na yane kaina da dan siririn gyale, don
kuwa kwalliyar kananan kaya na yi muna tafiya
cikin motar ina sauraron wakar da Yaya Almu ya
sanya a cikin motar mai matukar dadi ta Whitney
Auston ce mai taken 'lam sabing all my love for
you.
Yaya Almu ya dan waiwayo ya kallen ya ja
tsaki mai karfi tare da galla mini harara ya ce, "In
wani ya ga yanda kike kada wannan sai ya yi
zaton wani rawar arziki kika iya, nan kuwa ba ki
iya komai ba."
Cikin sauri tanfar na mance da wanda nake
magana na ce mishi, "Allah ya sauwaka ai ni
cuwa na rantse ba daga nan ba, lalle ma baka
sani ba Yaya Almu ai ni duk wanda ya sanni ya
san ni gwansce wajen iya rawa in ba ka sani ba
ma ni lokacin da nake S.S.3 har Queen kawayena
suke kirana. "
Na seke kallon shi na ce, "Tafdijan ashe dai
ba ia sanni ba, ai lko kwana biyar da suka wuce na
faki idon Umma tana barci na fita na je gidansu

63
Asabe Aliyu tana partin cika shekarunta a can
muka gamu da Julde har muka yi rawa tare da shi,
shi ne ma ya biyo ni'wai ya yi mamakina har yana
yi mini rantsuwar ai duk 'yan matan da ke wurin
babu wacce ta kai ni iya rawa."
Shirun da na ji Yaya Almu ya yi ne mai
tsawo ya barni ina ta zuba yasa na juyo don in ga
abin da ya ke yi. Yanayin da na gani a tare da shi
kuma sai ya kara fahimtar da ni cewar ba karamin
sabutar baki na yi ba naa bashi wannan labarin.
Tsoro ya yi matukar kama ni, har na rinka tunanin
lalle ni kam ina jin ungozman da ta yi bikina ba ta
gasa mini baki ba da kyau.
Jimawa kadan sai na ji ya ce, 'Ai ni ma na
yarda ban sanki ba Rabi, amma yanzu zan soma
neman sanin naki, wato har party kike zuwa da
daddare, Umma ba ta sani ba? Shi Baba maigadi
fa yana ina?"
Jikina ya dauki rawa na ce mishi, 'Ai sau
daya ne kafin nan ban taba zuwa ba."
Ya ce, 'Wannan shi ne karya." Ya juya kan
motar ya fasa inda ya ce za mu je ya juyo damu
gida kai tsaye dakin shi ya wuce da ni.
"Ta ina kika fita kika bar gidan nan ko kuwa
Baba Maigadi ne ya bude miki?"
Na yi maza na ce mishi, 'A'a." Cikin rawar

64
Jiki da rawar murya na ce mishi, Ta can baya ne
wurin raguna akwai wata wayar da ta balle tanan
na bi"
Yaya Almu ya kara zuba mini ido fuskar shi
dauke da alamar mamaki ya sake cewa, "Na kara
yarda dai ban sanki ba, to da kika dawo sai kika
cewa Umma me?.
Jikina ya dauki rawa sosai na shiga yi mishi
kuka ina ba shi hakuri, ya ce, "Ai sai kin gaya
mini in kuma kika yi mini karya zan yi bincike in
na gano za ki gane kuskurenki."
Muryata tana rawa na ce mishi, "Cewa
Umma na yi dakai muka tafi don in ba haka ba za
ta yi wa duk wanda nan kira mata sunan shi
magana."
Ya yi shiru ya buga uban tagumi ya zuba
mini ido yana kallona, ban da kukan da nake yi
kirjina sai dakan uku-uku yake, saboda tsananin
tsorata da na yi da irin kallon da yake yi mini gani
nake tanfar in ya mike kaina zai nufo.
"Ka yi bhakuri Yaya Almu. Ka yi hakuri ka
rufa mini asiri kar ka gayawa Baba da Umma za
su yi fushi da ni gara ka yi mini koma me za ka yi
mini na roke ka kar ka bari su ji su yi fushi da ni,
tun da ka ce mini fushin iyaye bala'i ne akan da."
Ajiyar zuciya mai tsananin karfi ya yi, kafin

65
ya sauke tagumin shi ya ce, 'Ai ke ba kya tsoro, ba
kya gudun bacin rai wa zai taba tsammanin za ki
1ya yin wannan abin da kika yi? "
A hankali ya bude baki ya ce, "Ko a mafarki an
taba zaton za ki iya yin hakan ba, amma je ki zan
yi tunanin abin da ya dace in yi a kan ki."
Har kusan kwana bakwa ina sauraron
hukuncin da Yaya Almu zai yi mini. A duk
lokacin da na gan shi da Umma sun kebe kuwa
gabana ya rinka faduwa kenan, sai in rinka ganin
kamar abin da ya zo ya gaya mata kenan. Gaba
daya hankalina baya tare da ni, kowanne lokaci
cikin zullumi da tunani nake na me zai yi mini?
Ko me zai faru?
Rannan dai da safe sai aka wayi gari ana kara
tsawon katangar gidan mu, ashe dama tun washe
garin wannan maganar ya sa aka soma aikin ginne
can bayan dáma kuma shi ne bangaren da aka yi
amfani da waya wajen tsare shi aka kara gini,
sannan aka zagaye saman katangar da
murdaddiyar wayar nan ta tsaro mai dauke da
wutar lantarki.
Ban samu dan kwanciyar hankali a jikina ba
har sai da na ga Baba ya zo gida ya yi kwana biyu
ya tafi ban ji an ce mini komai ba, haka nan
Umma sai na gane dai Yaya Almu ya ji rokon da

56

  na yi mishi na kar ya hada ni da su. Julde kuwa
tun daga wannan lokacin ban san dalili ba, ko
waya na yi mishi baya dauka in kuwa a wani wuri
muka hadu to yana ganina zai yi maza ya bar
wurin.
Ana cikin haka ne yaya Almu ya samar mini
Federal Poly garin mu na soma zuwa har ga shi na
shekara guda har da wasu 'yan watanni a cikin ta
tun da ga shi an turo ni nan hukumar zabe ina
zaman koyon sanin makamar aiki.
Tun da na fara zuwa dai Yaya Almu ne mai
dawainiyar kai ni da dauko ni, saboda ku san
kullum a makare nake zuwa su Yaya Junaidu ba
sa iya jirana, saboda su dukkansu ma'aikatan
gwamnati ne, shi kuwa Yaya Almu Lawyer ne
mai zaman kan shi, in ba yana da zama a kotu ba
uzurin gaban shi kawai yake yi, tun da harkokin
kasuwancin shi ma yake yi, tsakanin Nijeriya, da
kasar China.
Ina zaune kan kujerata da ke Daura da ta
yallabai a offishin hukumar zabe 'yan takardun da
aka nuna mini yanda zan rinka cikewa nake ta
faman kokarin yin hakan cikin tsaiko don na san
yallaba1 yana ganin na gama cike su zai sake
miko mini wadansu.
Ran Hajiya Rabi'atu ya dade gabana ya

67
yanke ya fadi jin iin kiran da yallabai ya yi min1,
don dai na san kwanan zancen a duk lokacin da ya
yi mini irin wannan kiran na dan zuba mishi ido
cikin suararo da nuna girmamawa ya dan sha mur
kadan a dalilin ya fara gajiya da murmushin da
yake yi mini, a duk lokacin da zai mini irin
wannan maganar.
"Ina fata dai yau ba za ki sake kawo mini
wani uzuri akan 'yar rakiyar da nake cewa ki yi
mini ba?"
Na zuba mishi ido cikin nutsuwa na ce mishi,
To bari tun da ka matsa a kan hakan in Yayana
ya zo sai in nemi izini wurin shi."
Da sauri yallabai ya fara cewa, Kai ashha!
Ashsha!!" Sannan na ja wani irin mummunan
tsaki kafin ya fara cewa, 'Ke kam ina jin ke ce 'yar
farin gidan ku? Gaba daya saboda wautarki ta yi
gaban kwatance."
Na ce.mishi, 'A'a ba ni ce 'yar farin Babanmu
ba."
Ya ce, "Eh ai na yarda da abin da kika gaya
mini na cewar shi wannan miskilin mutumin mai
muzuran tsiya wanki don sai da na je na yi bincike
kan hakan aka tabbatar mini, saboda ko kadan
dabi'unshi ba na watarin na kusa ba ne, yafi kama
da saurayi mai matukar kishi akan budurwarshi,

68
shi ne za ki je kna gaya mishi wannan maganar ta
shirri da za ta kasance tsakanin ni da ke kawai ko
kin san tun da yake zuwa wurin nan bai taba amsa
gaisuwar da nake yi mishi ba? Ni kuwa ina yi
mishi gaisuwar ne kawar darajar an tabbatar mini
ubaku daya, amma inda don ta bayanin da kika yi
mini ne ba yarda zan yi ba, sai in dauka kawai irin
wayon ku na yan mata za ki yi mini."
Turo kofar kawai ya yi ya shigo ba tare da ya
nemi izinin yin hakan ba, abin da na yi ta rokon
ya daina yin hakan, saboda yanda kullum sai
yallabai ya gaya mini cewar shi bai taba ganin
mai yi mishi irin wannan cin kashin ba a ofis din
shi, sai shi. Kullum na yi mishi maganar sai ya ce
mini wai shi bai san hakan yake yi ba, amma bari
gobe in ya zo zai kula ya gyara, amma kuma
hakan ba zai hana shi goben in zo zai kula ya
gyara, amma kuma hakan ba zaj hana shi goben in
ya zo ya sake ba. Na daga ido na kalle shi fuskar
shi kadaran-kadahan yana tsaye cikin shigar suit
farare sol, ya zuba hannayen shi duka biyu cikin
aljihun wandon shi, ko kallon inda yallabai yake
bai yi ba, balle ya sa ran zai gaishe shi.
Ya ya kin gåma ne ko da saura?"
Cikin nutsuwa na-ce mishi, "Da dan saura
kadan."

69
Ya dago ido ya kalli agogon da ke ofice din
alamar lokaci yake son sani a bankali ya bude
baki ya ce mini, "Bari in jira ki."
Ya juya ya fita. Yana barin office din
yalla6ai ya dube ni cikin takaici ya ce, 'Shi kuma
don fitinar tsiya ba ma zai rinka bari sai an tashi
ba, ya rinka zuwa daukar na ki? To duk tsiyar shi
ma dai ai dolen shi ya bai wa wai auren ki ko
kuma a bayar yana kallo tun da bai taba ganin
inda wa ya auri kanwarshi a, balle ya ce shi haka
zai yi."
Ya rufe zancen na shi da jan wani mummunan tsaki.
"Tashi di bishi ku tafi ke ashe ma ba wani
niss ya yi ba, gashi nan na hapgo shi koma ya ji
maganata ne ya sa ya yi motsin? Oho,"
Na yi maza na karasa cike takardun na mika
mishi na dauki jakata na fito. Na samu ya dan fara
tafiya na biyo bayan shi.
A hanya muna tafiya na shiga rokon Yaya
Almu akan ya rinka gaida yallabai. Ya ce mini,
"Ke kar fa ki kawo mini sakarci nine zan rinka bin
samarin ki ina gaishe su? Ina ce a ka'ida ni ya
kamata su rinka gayarwa tun da nine in ta dauro
zan ba su." Na yi maza na ce, "Yallabai yana
gaishe ka Yaya Almu ko yau din nan na ji shi ya

70
gaishe ka sau biyu, sannan ma shi ba saurayina ba
ne. "
Ya ce, "To ban ji gaisuwar ba, gobe in na zo
daukan ki zan kasa kunne in ji, don in amsa."
A gida da daddare ina hira a dakin su Yaya
Almu shi da Junaidu ne a ciki suna cin danbun
shinkafar da na yi wa Umma na debo musu suna
ci muna hira sai kawai na ji bakina ya sako wani
zancen na daban. Na ce, "Kai ana teba a duniyar
nan. Tebar yallabai din office din mu fa ta kai
girman wancan filon sau biyu."
Yaya Almu kam ko motsawa daga inda yake
bai yi ba, bai bar cin abincin shi ba, hakan nan bai
daga ido ya kalli fillon da nake magana akai din
ba, balle ya nuna wata alama ta ya ji maganar da
na yi. Sai Yaya Junaidu ne ya ce mini, To ai
burgewa kenan ita teba da kike ganinta ai ado ne
wurin namiji da.yawan mata kuma ita suka fi so
da sha'awa a jikin mutums, kuma ga dukkan
alamu ke ma kinan cikin su, don na lura son
yallabai din kike yi, saboda kullum sai kin yi
mana hirar shi, ai in kin ji mace tana yawan
maganar namiji ko da kushe shi take yi, to son shi
take yi, ita irin nata salon soyayyar kenan."
Na ce, "Kai Yaya Junaidu."
Ya yi maza ya ce,   "Eh mana ai in kin ga kare

71
yana sunsunar kashi to daukan shi zai yi." Na juya
ta wurin Yaya Almu don in ji shi kuma abin da
zai fada. Yanayin da na gani a tare da shi ya sa na
yi maza na mike na yiwo waje da gudu bayan na
ce musu sai da safe.
A daki kuwa ina kwance ina tunanin ya
kamata a ce ni da kaina na dauki matakin gasawa
kaina baki.
Ranar Asabar din karshen wata ya zo ranar
da yake zamowa ranar tsabtar muhalli ne a kasa
gaba daya, ban da haka kuma mu a gida mu ranar
zuwan Baba ne, don haka ana fitowa daga
imasallaci muke kama aikace-aikacen tsabtar gida,
wanda su Yaya Almu suke jagoranta, daga gidan
mu bar zuwa fence house babu inda ba a gyarawa
tsab. A irin. wannan ranar suma su Umma ba a
zaune suke ba, rana ce ta haduwar matan gidan a
babban kicin din taraiya na kusa da sashin baba,
don shirye-shiryen abincin da za a tanada don
Baba da bakin da za su cika gidan don zuwan shi.
Kasancewar Umma Karama ce a can ita ce
za ta dawo yau tare da shi, sai Umma amarya ta
tafi ita da Umma Amaryar ne a gida sune za su
jagoranci aikin da za a yin komai na su a tsare
yake, tuni sun riga sun shirya duk wani abin da za
su yi saboda akwai hadin kai da fahimtar juna

72
cilkin lamarin su. A duk lokacin da Umma za ta yi
wani abu tare da Umma Amarya abin kan zo mata
da sauki kwarai, saboda irin biyayyar da Umma
Amarya ke yi mata, ita kuma tana matukar
kokarinta wajen kame ginmanta ba ta yarda ta yi
amfani da ra'ayinta kawai wajen zartar da hukunci
sai ta saurari na Umma Amarya ko da kuwa ba ta
gida to za ta yi waya ta tambayeta hakan nan duk
wani abin da za ta saiwa kanta, to takan tabbatar
ta sai biyu ne.
Wajen karfe goma. sha biyu na shiga kicin
din don in kira baba Maigyada ta tayani nawa
aikin, saboda nima yau ban shiga aikin tsabtar
gida ba, a dalilin ni ce mai yin abincin gida, kuma
mafi yawancin yaran yan matan da kan tayani
aikin su na wasu aikace-aikacen da aka sanya su
tun a lokacin na samu har an gama sinasir, masa,
funkaso, da miyoyin su, masu dandano daban-
daban an kuma shiga yin wani abin daban.
Shia biyu da rabi na yi na bar wa su Baba
Maigyada sauran aikin na je na yi wanka, na yi
sallah, na yi kwaliya mai ban sha'awa cikin wata
atamfar Holland fara sol, zani da riga da
dankwalinta. Na sanya sarka da yankunne,
awarwaro da zobuna sannan nan yi amfani da jaka
da takalmi tare da gyalen da suka dace da kayan.

73
Wani kamshi mai nutsar da zuciya nake yi lokacin
da na iso inda Yaya Almu yake zaman jirana a
Cikin motar shi ya kuma yi jiran ne don ya san
tuni tun ba yau ba tun ina 'yar kankanuwata baba
ya sanya dokar tafiya da ni wurin taro shi bai
yarda a bar ni a gida in jira isowar shi ba. Ina
shiga na zauna na ce mishi;
Kar dai har su Yaya Junaidu sun tafi?"
Daidai yana kan titi ya ce mini, "Ai sun isa
Aiport yanzu muma dai ina ganin daga kafa za
mu yi, don kar ya iso ba ma nan."
Ba mu fi minti goma da isa airport din ba
jiriginsu Baba ya sauka.Yan mutanen da suka
fito kadan ne sai ga Unmma Karama ta bayyana
Baba yana biye da ita. Cikin zuciyata na ce kai
Baba ya more kyawawan mata, to wace ce ba
wacce ba a cikin su?
Umma Karama doguwar macece ta samanta
ba ta da girma sosai, kamar ta kuturinta, sannan
fara ce sol tafi duk sauran matan farar fata. Ita
kuwa Umma Amarya madaidaicin tsawo ne da ita,
wankan tarwada ce, tana da cikakkiyar fuska mai
dauke da manyan idanuwa. Sai Ummana wacce
take doguwa a tsaye ingarmar mace mai surar jiki
mai kyau da bayyanar da yawan shekarunta, kalar
jikinta yana tsakanin na Umma Karama ne da

74
Umma Amarya tati wanan ba ta kai wancan ba.
Gata da gashin kai mai yawan gaske, har a yanzu
da furfura ta soma ratsa shi, tsawon shi da cikar
shi yana nan a hakan kuma na san jin Yaya Almu
yana gaya mini ke kam in da kin yi sa'a kin dauko
gaba daya gashin Umma da ban san abin da kika
yi ba. Ni da kaina na san ni din kama da Ummana
ake yi a komai in ban da wuri biyu na darata
manyan idanuwa sai kuma hasken fata da ban
karasata ba, ta dan wadannan abubuwan guda
biyu tanan ne nake ganin na dauko Baba, don shi
mam Yaya Almu da Yaya Junaidu duk kalarmu
kusan daya ne, dan hasken da na fishi bai wuce na
ni din, don ina mace ba ne.
Motar da, aka dauko Baba na shiga dama
kuma haka yake yi in shigo gaba ni da Yaya
Junaidu shi da matar da ya dawo da ita kuma suna
baya.
"Ya ya dai uwata?" Ya yi mini tambayar
bayan na gama gaishe su shi da Umma Karama.
"Tsakanin Junaidu da Zubairu da Kabiu da
Lamido wanene mai takura miki? "
Na yi murmushi nace,  "Baba ai su Yaya
Kabiru su ba sa fada su sai dai kawai a yi ta
mutunci da su, babu ruwan su
Baba ya yi dariva ya ce. "Sun dai fi Junaidu

75
da Lamido kirki kenan?"
Na yi murmushi na ce, 'A'a Baba ba haka
nake nufi ba, ba su dai kawai mu'amallar mai dadi
ce ba ruwansu da ka ga sun sawa mutum ido in
dai ba gani suka yi za a fita can waje ba, shi ne za
su ce ina zuwa?"
Baba ya yi murmushi ya ce, 'A'a lalle lamarin
su.mai dadin ne, to bari tun da ba kya son sa ido
zan yi magana da su Junaidun su kawar da
idanuwansu daga gare ki kar wanda ya takurawa
uwata,"
Na yi murmushi kawai don na san raha
kawai Baba ke mini a dalilin na sha kai karar
Yaya Almu wurin shi kan takurawar da yake yi
mini sai kawai ya ce mini in je wurn mu ta yi
wannan shari'ar amma shi ba zai shiga tsakanin
mu ba. don mun fi kusa, Umma kuwa ko akan
idonta Yaya Aimu ya yi mini ba ta magana don
haka babu amfanin in kai mata karar shi.
Muna isa gida sashin Ummana baba ya zarce
duk da ya samu mutane da yawa da suka san da
zuwan shi, sun zo Suna jiran sh1 al'adar baba ne a
duk lokacin da ya iso gida sashin matan shi yake
Wucewa sai ya gama gaisuwa da sù, sannan ya
taho wurin jama'ar da ya samu mati yawancin
lokaci ya kan ci abincin shine tare da su, sannan

76
ya gana da wadanda zai gana da daddare kuma ya
kan yi zama tarc da su Yaya Junaidu gaba daya
manyan samarin gidan su bata lokaci suna
tattauna al'amura hakan nan bai tafiya sai ya samu
lokaci ya zaga dakunan kwanan yara ya kuma gan
su gaba daya, mun cika falon Baba mu yaran
gidan bayan fitowa daga sallar Asuba kananan
yara amsa gaisuwar su ya yi suka tafi. Ni da su
Anti Rashida da su Yaya Almu kuwa dukkan mu
muna ciki har da Umma na ma don ita ce ta
kasance tare da shi a zuwan nashi saboda in ya
tashi tafiyar zai tafi ne da Umma amarya.
Anti Aina'u ta sake gaisheshi ya amsa sannan
ta soma zata yi mishi magana akan bukatarsu kan
karatun su bai bari ta karasa ba ya katseta ta
hanyar ce mata bana zaton hakan zai yiwu kuna
nan gidan Aina'u in kun lura sa ku ga ban taba
tsare samari da yan mata sun kai matsayin
dadewarku ba akwai wani kwadayi da buri da
nake dashi ne yasa nayi haka na jira lokaci to
yanzu kuwa ina ganin lokacin yayi don haka nan
bada dadewa ba zan sallameku ku je dakunan
mazajenku ku huta maganar karatunku zai zammo
tsakaninku da su ne duk da dukanku abin iko na
ne hakan ba zai sa in shiga cikin hakkin aurenku
ba saboda haka in kunje gidajenku sai ku yi

77
kokarin sasantawa da su.
Ina jin haka na saki wani lallanlausan
murmushi da ya kara baiyanar da tsananın farın
ciki na na dan mike na duckusa kan kafafuwa na
don ya ganni da kyau na ce.
"Uhum, Baba." Ya juyo da natsuwarshi zuwa
gare ni ya ce.
"Menene Uwata?"
Na sake sakin wani murmushin kafin nace
mishi "Zan zama kenan nice babba a cikin gidan
nan idan su anti Kubra suka tafi gidajensu da su
yaya Almu dukansu."
Baba yayi murmushi ya ce "Ai yan zuma ke
ce babba a cikin gidan nan uwata ko da wani
wanda ki ke ganin ya girmeki ne? Kece fa uwata
ina wani girma daya wuce miki wannan? in kuwva
Su Lamido da Junaidu nc suke saki ki ke shakkar
hakan bari iny miki maganinsu ina Lamido?"
Ya ya Almu ya ce mishi "Gani baba."
Baba ya kalleshi ya ce "Kai kafi kowa ta
kurawa uwata na hana ku daga yau shekara daya
da rabi daya wuce ta kawo min kararka kan kasata
girkin da bazata iya ba to daga yau na sauke mata
wannan giurkin da ka dora mata karta sake shiga
kicin sai don ra'ayinta hakan nan sauran yan
matan dukansu a nemt sabbin masu aiki in kuna

78
ganin wadan nan sun girma."
Yaya Almu ya amsa ckin ladabi ya ce "To
Baba."
Baba ya sake kallona ya ce "Yaya da akwai
wata mas'alar uwata?"
Na yi murmushi na ce "Babu."
Ya ce "To dena tunanin wani girma da ya
wucc naki na yanzu kece uwar mutanen gidan nan
gaba daya don haka kina da girma mai yawa kin ji
ko?"
Na ce mishi "To baba." Na koma na zauna
cikin zuciyata kuwa ina tunanin baba bai gane irin
girman da nake nufi ba.
Gaba dayanmu baba ya sallemmu bayan ya
yi mana addu'a ya sanya mana albarka kowa ya
tashi ya fita ni kuwa nayi nufin ci gaba da zamana
a wunin sai da yaya Almu ya sake lekowa ya kira
ni na tashi naje inda yake tsaye sai kawai ya
kalleni ya ce "Mun ke kam zan ga ranar da zakiyi
hankali baki ji kalmar da yayi amfani da ita bane
wajen sallamar mu? yace mu dan bashi wun ya
ga matarshi kafin jama'a su zo."
Na bata rai na ce "A'a, to ba Ummana banc a
ciki kuma ma ai wasa yake. yi daya fadi hakan ba
shima dariya ya yi ba?"
Ya ce "Wasa? To daga yau na sake ganin shi

79
da Umma suna ciki kin shigar musu ba tare da kin
Jira sun kra ki ba, sai na 6ata miki."
Da karfi na ce mishi "Ha'a ba ance muku ku
sakar min mara ba?"
Ya ce "Ai yanzu ki kace duk maganar da
akyi ana dariya ko murmushi wasa ake yi." Ya
dan saki fuska ya ce" Wuce muje can falon
Umma ki shirya mana abin karyawa kafin ta fito."
Na ce "A'a yau baba kadai zan yiwa abin
karyawa."
Ya ce"To muje ki yi mishin in taya ki."
Na waiwaya na kalleshi nayi murmushi na ce
"Ka taya ni fa ka ce?"
Ya ce"To menene don na taya ki kinyi wa
Umma da baba abinda za su ci? Muna cikin din
Umma ina aiki na shi kuma yana zaune kan kujera
mai tsayi yana gaya min ya kamata ki rinka ganc
kingirma rabi ki rinka barin Umma tana morcwa
rayuwarta amma ba kowane lokaci kina manne da
ita ba tana daki kina daki manne da ita ba tana
daki kina daki tana waje kina waje wai babuma
inya zo sai kin je kin zauna musu ba zaki barta ita
kadai tare da shi ba kamar yanda kowacce a
cikinsu take yi.
Na 6ata fuska na ce "To meye? "
Ya ce "Ba komai bane tunda ta kyaleki kina

80
yi mata shima Baba ya sa muku ido amma ni da
wanda ya sa ya shiga tsakani na da mata ta ne?
Ranar farko."
Da naji yaya Almu ya yi min maganar da ta
sahfi matarshi nayi murmushi na ce mishi "Ka ce
in na zo gidanku kai da anti Aina'u in bi a
hankali."
Ya kalleni yayi murmushi ya .ce Wai me
yasa ki ke zaban min Aina'u ne a cikin duka 'yan
matan?"
Na ce mishi "Nafi ganin kyau kwalliyartya in
ka lura kwalliyarta daban take da ta sauran ba
kowacce irin sutura take sanyawa ba bata kumna
dauri ta wani karka toshi, amma kuma kana
kallonta ka san yar gaye ce." Na ce "Kuma ta kasa
6oye son da take yi maka."
Yayi maza ya tsuke fuska ya ce "Kar ki yi
mata sharri to gaya min wacece mai hankalin
cikinsu?"
Da sauri na ce mishi "Anti Rahma ai ta fisu
natsuwa ma ko sallah akan lokaci ta fisu ni nama
fison ta saboda mun fi shiri da ita, ita ba ruwanta
ma da tadin samari."
Ya ce"To me yasa baki yi tunanin ki za
6anmin ita ba tunda gashi ma kuna shiri ko da
yake ban tabbatar ba don kuwa kakan yi shin ne

81
da mutumin halaiyar ta dan zo zaya ke kuwa baki
da irin halayen nan nata da ki ka lissafa natsuwa,
hankali da sallah akan lokaci."
Na ce "Uhm, aikina shi kuwa hran yake so
mu yi don haka sai ya sake shigo da wani zancen
amma ai ina ganin rabi in aka kwashe 'yan matan
gidan nan aka yi aurensu aka barki daga ke sai
yan yara aiki zai miki yawa.
Da sauri na kalleshi na kyalkyale da dariya
na ce "Ai ni a dadina babu wani aikin da zai
dameni wa za rinka sani? dama kai da yaya
Juanidu ne wadannan samarin da za'a barni da su
kuwa kwanta-kwata shekara biyu zuwa uku suka
bani ba wani takura min da zasu yi don bazan
yarda ba shi ya sama tun bara na dena sake musu
fuska ko gaishesu zany sai na bata rai don karsu
ga alamar wasa suce zasu kawo min raini."
Sai da na kawo nan naji gaba na ya fadi nayi maza
na waiwaya na kalli fuskarshi don in gani ko yau
ma nay subutar bakin nawa dana saba banga
alamar hakan ba don haka naci pgaba da yi msih
baya ni "Kuna bari gidan nan ko kwana bakwai
bazaku yi ba zan fara hawa mota."
Ya ce "A'a haba Hajiya zumuzi ai kya bari ki
koya."
Na yi maza na ce "Ni na dade da iya tuki
82

wurin jul... Nayi maza nayi gum ban karasa
ambaton sunan ba, shima sai ya nuna bai gane
wanda nayi -niyyar ambaton ba.
"Abin karyawan na mutum nawa zaki yi ne?"
Na ce "Da Baba da Umma da Umma amarya
dani."
Ya ce "To ki hada da Umma karama ko
kuma ki kai mata na.wajenki ki zo mu karya ana
gida." Ya tashi ya fita ya barni ina fadin hu'un.
Kwanaki biyun baba sun cka ya kuma dauki
amaryarshi sun tafi sun barmu da kewa shi kam
yaya Almu ko a jikinshi har mamakinshi nake yi
bai taba nuna ya damu da Umma amarya ba balle
ka ga alamar wata shakuwa a tsakanin su.
Ranar monday na isa wurin 1.T.  na a makare
saboda a safiyar na muka yi sallama da Baba
shima yaya Almu sauke. ni ya yi ckin sauri ya
wuce don yana da case a kot yau, cikin ladabi na
gaida yallaba ya amsa tare da bina da kallo in ce
ko yau daga wurin party ku ke ne ke da yayan
naki?
Nayi maza na dago ido na kalleshi ya ce "Eh,
ai wannan yayan naki yayan zamani ne babu
abinda da bazai ya ba ai na ganku shekaran jiya
can ranar juma'a da yamma ke da shi saboda haka
ban sake karbar wani uzuri ni da shi duk so muke

83
yi don haka babu wani mai haramtawa wani"
Nayi shiru ina sauraronshi sai da naji ya yi
shiru sai na ce mishi "To ba shi bane shekaran jiya
ba muje ko'ina ba ni da shi da yaya Junaidu muka
fita."
Ya ce "Afto ke ki ce mun duk gidan naku
samarin kine to koma dai menene banga laifinsu
ba kina da kyau don haka na guji .da zamun
zurawa juna ido da muke yi in baki sani ba ni a
takure nake yau wa muyi mu'amallar hadin kai
kawai ki amfane ni ni ma in amfancki in bak sani
ba ita mu'amulla mai dadi in anyi ta babu wanda
bata amfani in bazan miki karyar kudi da gold ba
tunda ki na dasu ai kuma takardunki zasu biyo ta
hannuna knga kenan ina da wani abin yi akanki."
Shiru kawai nayi ina sauraronshi dana ji yayi
shiru sai kawai na sunkuyar kàn ai kina sha biyu
tuna ciki ya mike ya ce "To lokacin break ne
yanzu tashi muje mu dawo da sauri. kan ya zo
daukan naki, na daga ido na kallesh jikina sai
daman rawa yake yi saboda ganin da nayi mishi a
tsaye a kaina, ai sai kin tashi min tafi yau na gaji
da cintar da ki ke yi min ya miko hannu zai taba
min jikina nayi maza na shige karkashin teburin
na mukure ina ta faman bashi hakuri.
"Ai sai kin fito abin da bai wuce in ture

84
teburin ba."
Sai kawai ga yaya Almu a office din ya yi rin
shigowar shi da ya saba ta rashin ne izini.
Yallabai yana ganinshi ya saki hannuna da
ya riga ya kamo yana kokarin jawoni in fito daga
karkashin teburin yana fadin fito kawai ba komai
a hankali ma za'a gani na fito daga karkashin
teburin jiki na sai faman bari ya ke yi kam in
gama fitowa tuni yaya Almu ya yi waje na mike
ina kuka na biyo bayanshi zan fita shi kuma
yallabai yana tambayata wai kukan na menene ko
so nake in kulla mai irin janhurun da yan masa
suka saba kullawa mutane shi da nan da nake
ganinshi babu abin da zai firgita shi don babu
Irin mutumin da bai gani ba ban tanka mishi
ba, na share hawaye nakwai na fita na taho wurin
yaya Almu ina tunania irin tuhumar da zai minkan
abin da tarar yana faruwa tsakanina da yallabai.
Ina zama a cikin motar ya tasheta cikin sauri
ya fada kan hanya bai ce min komai ba ni ma
bance mishi ba har muka iso shatatalen unguwar
mu yana gama shi yayaya tsaya bai kallen ba, ya
ce min sauka ki shiga gida sauri nake yti na
dankalleni cikin damuwa na ce mishi dagan da
zuwa cikin gida da.. kan in karasa ya daka min
tsawa sauka ki bani wuri nace da sauri na fita na

85
bar mishi motarshi na kama hanya ina tafiyaa
hankali cikin zuciyata ina tunanin to ni da ba tashi
muka yi ba me ya dawo dani gida wannan tafiyar
da nake yi ma ai kafin in gama ta an koma break
din.
Ina shiga falin Umma nayi sa'a na sameta a
ciki ita da baba talatu kwanciya nayi a jikinta ina
kuka ina gaya mat "Umma bana son 1.T ya isheni
a takure nake zama a wurin ki taimake ni ki yiwa
yaya Almu magana ni a barin haka bana son
karatun bokon wahla yake bani yanzu ma
kafafuwana ciwo suke yi min."
Baba Talatu tayi maza ta shiga matsaminsu
tana fadin "Sannu da kokari uwar dakina."
Ina na wurin akwance jikin Umma har yaya
Almu ya shigo "Tashi mu je in mai da ke." Na
daure fuska na ce.
"Ni abarni kawai in huta a gida."
Ya ce "Yi hakuri rabin Umma."
Umma ta yi dariya ta ce "Haba babangida
Adawiyya ai takace tashi ku je tashi tashi maza
kina ji yayank yana baki hakuri kina wani
minmike."
Na mike na tashi naje na samu motar a
sashin Umma don haka ban yi tafiya mai yawa ba
na bude ta na shiga sai dai zuciyata cike take da

86
tsoro saboda ban san me zai faru ba, tsakanin a da
yallabai ni zu manar ba don nasan halin yaya
Almu cewa zai yi sharri zan yi mishi nice nake
sonshi, haka dai na daure na koma office bayan ya
auke ni gabana yana faduwa na shiga office din
yallabai yana zaune kankujerarshi kirjina yana
bugawa na ce mishi "Barka da aiki yallabai." bai
daga ido ya kallen ba, ya masa kanshi a sunkuye.
"Yauwa, baiwar Allah." na wuce sum-sum
na je na zauna ina aikina ina kuma sauraron abin
da zai ce min har aka tashi bai kalli inda nake ba
balle.ya yi min wata magana nayi mishi sallama
yan labini sai gobe ba, tare da ya kallo ni ya ce
min yauwa mu kwana latiya na fito ina mamaki
tare da tunanin abin da ya hana yaya Amu zuwa
daukana sai da na fito kofar ma'aikatarmu na
ganshi a zaune a bayan motarmu yana kallon
masu wuce wa na shiga na zauna muka dawo gida
tun daga ran nan yaya Almu bai sake leka office
dinmu ba in ya zo a waje yake jira na in fito in
same shi da na tambaye shi dalili sai ya ce wai ya
lura ne bana son shigan nashi danhaka ya dena,
shima yallbai bai sake kallona ba balle a ci ga
anbaton suna ko har a samuyin wata magana na yi
1.T. na na gama cikin kwanciyar hankali muka yi
sallamar arziki sabanin yanda ya yi ta rantsuwar

87
zai rike min takardu na.
Kullum na dauko zancen daon in yiwa yaya
Almu hirar yallabai da mamakin canzawar shi, sai
ya tsuke fuska ya ce wai bawanini daikawai naga
na dawo gida bai biyo ni ba nikuma gashi ina
mutuwar son shi, a dole na dena kawo mishi hirar
yallabai.
Ina gama hutun gama I.T. da nayi na sati
guda na koma zuwa makaranta karatun da ba wani
dadin shi nake ji ba dama dai inyi za'a in maye
gurbin carry over da nake da shi a jarrabawa ta ta
second semester gashi na ce wa yaya Almu ya je
ya ga malamin tun kafin su kai makon ya fito
aboda ni ma nasan ban kulla wani abin kirki ba a
cikinshi ya ce wai abinda ba zai taba zuwa ya yi
ba kenan ya bada wani abu don aba ni cin
jarrabawa in bazan yi ba, to inje inyi ta cin carry
over ni ta saba shima yaya Junaidu da nayi mishi
maganar sai ya ce mun haba Adawiyyah kamar.
kikuma sai anje ana neman wani malami don ya
baki ci to me zaki yi da wannansakamakon tunda
kin san ba na guminki ba ne? Ai kije ki yi
jarrabawarki kawai tas zaki cinye sai dai in baki
tsaya kin duba note din ki ba.
Haka dole na hakura na yi jarrabawar tunda
babu halin in gaya musu cewar ba sosai nake

88
hallatar lectures ba.
Ana cikin wannan lokacin ne tafiyar Umma
ta zo, saboda dawowar Umma Amarya dan kiris
ya rage mini in roki Ummana ta bar tafiyar in ya
so ita Umma Karama ta je sai na tunan maganar
Yaya Almu ta cewar in daina shiga lamarin jin
dadin ta da mijinta, don haka na ja bakina na yi
shiru muka yi musu rakiya muka dawo na shiga
falon ta na zauna cikin kewa da tunanin kwanakin
da za ta yi kafin ta dawo.
Duk da hirar da su Yaya Zubairu suka zo
suka yi mini bai hana ni kewar Umma ba, da
sassafe na kama goge hotunta da ke ajiye a falonta
da ke ajiye a falonta, duk wanda na goge kuwa sai
na zuba mishi ido ina kallonta a jiki tanfar dai na
shekara rabona da ita. Sai da na gama wannan
aikin na tsabtace ko'ina, sannan na shiga kicin don
shirya abin karyawa. Yaya Almu ya shigo ya
same ni.
"Wa kike yi wa abin karyawa haka bayan
Ummana ba ta nan?"
Na kalle shi na dan yi murmushi, don na san
cewar da ya yi Umman shi ya yi amfani da yanda
nake kiranta ne na ce, 'Umma anmarya? Ni fa na ce
kai ma za ka iya samu, don na mutum hudi: zuwa
biyar na nke shiryawa." Ya ce, "To bari in je in

89
dawo."
Sai da na gama komai sannan na dauki abin
karyawar na je na kai mata, daga nan na zauna
mata muka dan yi hira kafin na dawo saboda na
san Yaya Almu zai zo nemana.
Na shigo kenan ina shan kunun gyadar da na
taho da shi daga wurinta sai ga shi shi ma ya
dawo na je na kawo mishi yana karyawa ina gaya
mishi.
"Umma amarya ta ce in rufe ko'ina in koma
can wurin ta."
Yaya Almu ya yi maza ya ce, 'A'a Rabi sai
dai in so kike duk ki takura mana yanzu nan muu
biyu ba za mu iya rike dakin uwar mu ba? Sai
kuma kawai don ba ta nan mu rufe wurinta gaba
daya mu koma wani wuri? Kenan har yanzu mu
din yara ne kanana? Ai kawai mu yi zaman mu
anan su Junaidu ne za su rinka zuwa mana hira,
kin ga kamar tana nan kenan ko kuwa?"
Na ce, "To bari in anjima in na je kai mata
abincin rana sai in gaya mata inta yarda shi
kenan." Ya cc, "To rokonta za ki yi sai ki gaya
mata cewar za ki iya zaman ba cewa za ki yi wan
zai taya ki ba."
Na ce mishi, "To."
Zaman da Yaya Almu ya sani na yi a sashin

90
Umma ya sa baki ba su yanke ba a wurin kowa ya
zo nan din dai yake sauka tanfar. dai tana nan.
Hakan sai ya sani a cikin kidima da ayuka masu
yawan gaske, don sai na zamo ni ce mai karbar
su, sai na sauke su anan sannan na ke kai su wajen
su wato masaukın su ni ke tsayawa in ga an kai
musu wadataccen abincin da zai ishe su, kumna
akan lokaci in kuwa gari ya waye ina idar da
sallah zan je in ga na ba su ruwan wankan su su
da 'ya'yan su, in je in kawo musu abin karyawa, in
sun gama in je in sakc kawo wani in ajiye musu,
saboda ya'yan su kar su ji yunwa kafin a gama
abincin rana.
Nan da nan na wastsake na shiga hidimar da
da ba na kulawa da ita, sai dai in ga Umma tana ta
faman zirga-zirga tana dawainiyar jama'a ban san
wahalar abin ba, sai da na samu kai na a cikin shi
lokacin ne na gane ashe ba karamar hidima
Umma take wuni a cikinta ba, gashi ko na je na
samu Umma Amarya na ce mata Umma ga bakin
nan sun ce za su tafi sai ta ce ai ba sai kin zo kin
gaya mini ba, kina ganin yanda Hajiya Babba take
yi ba in na ce ch sai ta ce to je ki ki yi hakan don
haka komai zan yi a kan su Yaya Almu nake kira
in gaya mishi kamar yanda na ga Umman tana yi.
Rannan na sallami wasu baki na yi musu

91
rakiya suka yi wa Umma Karama da Umma
Amarya sallama sai da suka tafi na dawo na sanu
Yaya Almu a falon shi kadai yana zaune na zo na
wuce da doguwar riga a jikina na shiga kicin na
dauko filas din kunun gyada na zo na zauna zan
sha ya kalleni ya ce, "Kar dai tuntuni ba ki sha
kunun nan ba?"
Na. ce, "Na jira ne in sallame su su tafi
takunna."
Ya dago idanuwan shi ya kalleni cikin
nutsuwa ya ce mini, "Amma ba ki ga kamar za ki
iya gadon Ummana a kan komai ba? Ai na ga
kamar za ki iya uwargidanci ki iya sa hannu biyu
ki rungumi mijinki, shi da jama'ar shi."
Na yi maza na tsuke fuska na ce, "Ni fa ba na
Son irin wannan maganar,. na ce ba na son
maganar uwargidancin, ni ba na so, ba na so na
kara." Na kara fuska ya ce, "To yi hakuri Rabi ba
maganar bacin rai ba ne, ni dai ina yi miki
sha'awar girman ne tun da kema na ga kina yi wa
kan ki."
Na yi maza na ce, 'A'a ni ba na yi wa kaina
wani sha'awa in dai irin wannan ne."
Sati biyu bayan nan na wayi gari cikin
murnar cikana shekaru goma sha tara, sai dai abin
takaicin shi ne Ummana ba ta nan duk da haka

92
Umma Amarya ta sa an yi ta tuyan masa da
funkaso tun cikin dare ana idar da sallar Asuba
tasa aka yi ta fita da shi a mota ana kaiwa
makarantun allo na cikin gari a gida ma an yi
saukar Alkur'ani mai girma abin da na sani kuma
shi ne ko Umma da baba suna nan iyakacin abin
da za su yi kenan.
Na fito daga sashin Umma amarya bayan na
yi kwalliyar kara wata shekarar, na je gaisheta.
Addu'o'i da nasihohi masu yawa ta yi mini, na
shiga falon zuciyata cike da jimamin al'amuran da
Umma ta yi mini nasiha a kan su. Ina shiga ko
gama zama ban yi sai ga yaya Junaidu ya shigo
yana rungume da wani kwali yana ganina ya saki
wani irin lallausan murmushi ya ce;
"Kai mun ji dadi yau Adawiyya ta kara wata
shekarar. Na tayaki murma bebina." Na taya shi
murmushin na ce mishi, "Na gode maka Yaya
Junaidu."
Ya durkusa a gabana ya ce, Dan lumshe
mini idanuwan na ki sai na kirya goma kafin ki
sake bude su."
Na sake yin wani murmushin, sannan na yi
mishi yanda ya ce din, na kuma shiga taya shi
kirgen cikin nutsuwa, sai na ji ya kai karshe ya ce
in bude idona. Na sake yin wani murmushin don

93
dadi wani kayataccen cake ne da aka kayata shi
da kalmomi na fatan alheri ya sa yar kankanuwar
wukar da ke soke jikin cake din ya yanke dan
kankanin loma ya ce, "Bude dan bakin na ki in
jefa miki shi a ciki."
Ban yi mishi musu ba don haka sai na
lumshe idona na bude mishi bakin nawa kamar
yanda ya nema sai da na ji gardin shi ya sauka kan
harshena sannan ne na maida bakin nawa na rufe
na kuma bude idanuwana ina tauna cikin
murmushi na ce, "Wace ce ta yi cake din gwana
ce kwarai."
Ya ce, Uhm Adawiyyah ba ta kai ki iyawa
ba, ke dai na sa ta ta yi ne kawai don ina son
burge ki."
Na sake yin wani murmushin cikin
lumshewar idanuwa, saboda tsananin. dadin da
nake ciki na ce mishi, "Na gode Yaya Junaidu."
Ya mike tsaye alamar fita zai yi ya ce mini,
"Bari in je in dawo Adawiyya zan zo in yi miki
hira." Na ce to sai ka dawo. Yana fita na kira
Hauwa na ba ta cake.din na ce ta je ta yanyanka ta
raba musu. Ta ce to, ta dauka ta tafi.
Wajen karfe biyu da rabi na barwa Baba
Talatu 1ura da sashin Umma na tafi ferce house
don amsa kiran da Yaya Almu ya yi mini. A bakin

94
get din shiga wurin na same shi yana sanye da
farar kufta ya yi matukar yin kyau yana harde da
hannayen shi akan kirjin shi, hanyar da zan fito
yake kallo yana ganina ya dan saki ranshi kadan
ya dan yi mini kallon sama da kasa, kafin ya ce
mini.
"Wasa-wasa dai kin iya wani abu."
Ya dan mintsina zuciyata na ce, "Ni ma fa ka
ce kenan da wacce ta fini?" Na yamutsa fuka na
ce, "To ai ko budurwar da za ka aura sai dai ta
koya a wurina." Ya zuba mini ido yana kallona a
hankali ya ce mini, "To hadiye fushin naki ki
maida wukar, in ma abin da na gaya mikin bai yi
miki dadi ba ki ranki na yi don in faranta miki rai
in taya ki murna Rabo ba don in 6ata miki ba,
yanzu ina kike so in kai ki?"
Na dan yi shiru kadan cikin tunanin dadin da
nake ji ba mai yawa ba ne, a dalilin rashin Umma
kusa da ni na ce mishi, "Mu shiga nan kawai."
Bai yi musu ba ya wuce gaba na bi bayan shi
yana fadin, "Duk yanda kika ce ai hakan za a yi."
Mun keta cikin fence house din dawakin
suna ganin Yaya Almu suka shiga haniniya, suna
zarya, wai su ma nan sun ga wanda suka sani. Na
ce, "Oh ka ji mini dawakin nan wai suma sun
gane ka." Ya dan kalle su ya ce, "Eh yau da gobe

95
ai ta ki karfin wasa, suma kuma suna irin tasu
fahimtar." Na ce haka ne.
Cikin gidan katakon yaya Almu ya bude
mana komai na ciki a tsare yake gwanin sha'awa
ga kamshi ga iskar da ke kadawa ta ko'ina, tana
kara nutsar da zukatan dan adam. Ina zama yaya
Almu ya miko mini kofin ruwan sanyi na ce,
"A'a." Ya ce dan karbi ki sha ko kadan ne ai ruwa
rayuwa ne. Ban yi mishi musu ba na karba na sha,
shi kuma ya nemi wuri ya zauna yana fadin,
"Shekaru goma sha tara ne yau tun da Rabi ta
shigo cikin duniyar nan mai cike da al'amura
masu ban mamaki da al'ajabi a wancan shekarar
kamar yau na gaya miki muhimmancin shekaru
goma shatakwas na kira miki su shekarun girmna
da hankali da nutsuwa, haka ne ko ba haka ba
ne?"
A hankali cikin nutsuwa sosai na ba shi amsa
da cewar, "Haka ne." Ya sake kallona ya ce, "TTo
tun da kin shekara kina da hankali ya kamata a ce
mafi yawancin abubuwa na rashin hankali kin
rage su, in ma ba ki daina gaba daya ba. Sai na ce
to bari yau in yi amfani da muhimmancin ranar
wajen baki shawara ina fata ba zan takura miki ba,
ko ki dauka ina yawan shiga cikin harkokin ki,
tun da baba ya ce bai yarda a yanzu a yi miki

96
hakan ba."
Na dan yi murmushi na ce, "A'a babu
takura" Ya ce, "To me zai hana ki canza yanayin
shigar da kike yi? Ina nufin ta yawan mu'amala da
kananan kaya, ba ina nufin ba sa karbarki ba ne,
amma ado ne da na ke ganin ya dace ki yi a gidan
mijin ki, yanzu ba da ba ne kin riga kin girma, in
kowa bai lura da hakan ba, ya kamata ke ki lura
da kan ki misali dubi siket din da ke jikin ki, ko
gwiwar ki bai rufe ba, sharabarki tana waje ji 'yar
rigar da ke jikin ki kin yi kyau har kyau tun da
kina da shi, amma bai dace kowa ya rinka ganinki
a haka ba. Rabi ai kina da daraja ya kamata a ce
kinan rowar kyan jikinki ga mutane da bai dace su
rinka gani ba."
Na kalleshi cikin sakin fuska na ce mishi,
"To. zan gyara.
"Kin yarda za ki gyara da gaske?"
Na ce. mishi,, "Eh ai in nka ba ni shawara ina
amfani da ita." Ya yi maza ya ce, "Haka ne aike
mai ganin girman na gaba da ke ne. Rabi to tun da
kin yarda za ki gyara bari mu fara gyaran daga
yau sai ya zama tun ranar da kika tun daga ranar
da kika cika shekaru goma sha tara ba ki sake
sanya suturar rashin hankali ba, ko ya ya kika
gani?

97
Na dan yi shiru cikin nazari da tunanin abin
da hakan ke nufi, kenan ba zan sake sanya
kananan kaya ba? Na tuna irin kyan da nake yi a
cikin su da nishadin da suke sanyani kan in ce
mishi komai sai ya dan matso kusa da ni ya rada
mini.
"Mafi darajar tuban da ake so bawa ya yi shi
ne na barin abu a lokacin da yin abin yake
matukar yi mishi dadi, sannan in ba ki sani ba
daina sanya su ba yana nufin daina yin kwalliyar
ba ne, a'a sai dai fita daga yin wacce ba ta dace ba,
zuwa komawa wacce dace da ke." Na gyada kai
nuna alamar yarda tare da cewar hakan ne.
Yana jin na fadi hakan ya yi maza ya mike
ya dakin hutawar baba ya fito rungume da wani
dan madaidaicin kwali da aka kawata shi ya sha
ado tanfar dai kar a kwance shi a bar shi haka in
ya so ma a yafe abin da ke cikin shi, Zuwa ya yi
ya ajiye shi a gabana yana kallon cikin sakin
fuska.
"Zan bude miki kwalin ne ko za ki yi da kan
ki?"
Na yi murt ushi na ce, "Bari in yi da kaina."
Na matso na durkusa a gaban kwalin ina ta
faman ailkin daye adon nan da aka kawata shi da
shi, har na kai ga jikin kwalin, wani kyakkyawan

98
kati na 1ara gani a jikin shi an yi rubutu kamar
haka:
Happy Birthday to my lovely sister. "
Sannan wasu kalmomi suka biyo baya. Na
bude kwalin sosai gaba daya cikin shi dogayen
rigunane, hijab, after dress da wani dan akwati a
can Kasan kwalin na sa hannu na dauko shi,
madaidaitan warwaraye ne masu matukar kyau na gold guda hudu na kalle shi cikin farin ciki kan in
yI mishi wata magana sai ya cc mini;
"Ban sai miki zobe ba saboda ga al'ada
saurayike bada kyautar zobe." Na yi murmushi na
ce, "Na gode Yaya Almu." Ya kallc ni cikin
nutsuwa ya ce, "To yanzu da ba ki da saurayi ya
ya kenan ko kuwa zan yi wa Umma magana ne ta
sai miki zobunan da za su dacc da su?"
Na cc mishi, "Aa ba ma sai an saya ba, na
gode."
Hira sosai muka yi da yaya Almu har muka
gangaro kan zancen aure na ce mishi, a1 in aka yi
bikin ku kuka tafi zan yi kcwar ku. Ya dan kalleni
cikin nutsuwa kafin ya ce anya kuwa Rabi? Ai
nafi zaton murna za ki yi maimakon kewa
musamman ni da na kc takura ki da yawa na ke
yawan shiga al'amuran ki wadanda suka dacc in
shiga da wadanda ba su dace ba duka.

99
Na dan yi murmushi na ce, 'Ai Umma ta ce
mini in daina dauka 'yan uwanci kake yi mini
kana yi mini hakan ne don ganin kai ne ka
cancanci ka rinka kwabata kan abubuwan da nake
aikatawa. Sai da ya dan gyara zama kadan kafin
ya ce mini gaskiya ne Rabi ban iya kawar da ido
kan kuskuren ki don so nake in ji ana cewa kin fi
kowa hankali, kin fi kowa nutsuwa da sanin ya
kamata shi ya sa kike ganin ina yi miki abin da
nake yi mikin, amma ba don ina kin ki ba.
Na ce, 'Ai na yarda."
Ya tashi ya je ya yi alwala ya dawo nima na
je na yi na dauki riga guda daya a cikin rigunan
nan na saka na yane kaina da gyalanta na yi sallah
ta. Sai da muka yi sallar Isha'i, sannan muka fito
daga wurin maimakon mu shiga gida motar shi ya
ce mu shiga na bi umarnin shi yana tashinta yana
gaya mini, "Bari mu je mu ci abinci tun da ba mu
je gida da wuri ba, balle ki yi mana girki." Na ce
mishi to. Muna tafiya cikin tafiyar ya danna mana
faifan da ke cikin rediyan motar tashin muryar
Maria kelly ce ta soma tashi cikin wakarta mai
taken Always be mine baby! Chines Restaurant
ya kai mu sai da muka ci muka sha, sannan muka
yi wa su Umma take away din abin da muka cin
muka kawo musu.

100
Tun daga rannan yaya Almu ya shiga sa
mini dogayen riguna masu matukar kyau, kan kaa
ce me ye wannan sai suka zamo sune suturar da
nake am fani da ita na maida kwalliyar hijab ita ce
kwalliya mafi daraja a wurina.
A haka muka kasance har ranar zuwan baba
ta zo na zamo cike da zumudi fiye da kullum a
dalilin ranar ce kuma za ta zamo ranar dawowar
Ummana. Tun dare nake ta faman shirye-shiryen
abincin saukar da nake shirya mata.
Gari na wayewa na gama kintsa komai na
tsabtace wurin ta tsab, ko'ina sai kamshi kake ji
yana tashi. Na yi wanka na zauna na tsala
kwalliya cikin wata doguwar riga mai ruwan kasa,
gaban rigar ya sha ado da wasu duwatsu masu
daraja na yane kaina da gyalanta, sannan na dauko
warawaran Yaya Almu na sanya a hannuna tare
da wasu zobuna guda biyu da Yaya Junaidu da ya
ba ni kyautar cika shekara na farin gold na yi
matukar yin kyau ga kwarjini na fito cikin wani
sansanyan kamshi na iso wurin yaya Almu na
samu wai lokaci ne zai yi wanka na ce mishi;
"To ni gaskiya zan bi Yaya Junaidu sai ka
zo."
Ya kalleni cikin murmushi ya ce, "Haba Rabi
dan jiran da za ki yi mini na mintina da ba su fi

101
talatin ba.
Na yi maza na ce mishi, 'A'a ni kam ba zan
iya ba." Ya ce, "To shi kenan sai na zo." Da gudu
na fito don gudun kar Yaya Junaidu ya tafi ya bar
ni, ina shiga motar na zauna wacce take ledusc
Jeep ce. Yaya Junaidu ya kallcni cikin murmushi
ya cc kar dai ki cc mini doki ba zai barki jiran
Mustapha ba?" Na ce uh gaskiya ba zan iya ba ya
yi dariya ya ce Adawiyya kenan, yau za ki ga
Umma ai dole ki yi zumudi.
A Airport mun isa babu dadewa sai ga jirgi
ya sauka ana bude kofar jirgin sai ga Ummana ta
bayyana cikin kwalliyar da ta saba yi in har za ta
tafi wani wuri, tarc da baba ko kuma za su dawo
tarc wato kwalliyar lafaya. Suna fitowa daga cikin
filin suka shigc motar nima na shigc gaba tare da
Yaya Junaidu.
Tun ba mu gama gaisawa ba baba ya kalleni
cikin fara'a da murmushin da ke bayyanar da farın
cikin shi ya cc, "Lalle na yarda har da zaman ki
kusa da Ummanki yakc kara maida ke yar
kankanuwar yarinya, 'uwata kin ga irin giriman da
kika yi kuwa a dan tsakanin nan kin kara girma
kin kara kyau kin kara hankali, domin gashi yau
na ganki cikin suturar da ta kara miki kwarjini. "
Na ji dadin kalaman baba cikin ladabi na ce

102
mishi, "Ai na kara shekara baka nan baba shi ya
sa ba ka sani ba." Ya ce na sani ban mance ba, ya
ya ma za a yi in mance da ranar haihuwar uwata?
Sannan ma ai ga Ummanki tare da ni kin kuma
sani ita ma ba za ta taba mancewa ba." Na yi
maza na ce haka ne Baba.
Na tanadar miki kyautar ki tana nan zan baki,
na kuma san anan ma ba za ki rasa mai baki ba,
tun da ga su Junaidu nan a gidan." Na yi
murmushi na ce kowa ya yi mini kyauta Baba.
Yaya Junaidu ya yankana mini cake din barthday
ya kuma ba ni kyautar wadannan zobunan." NNa
daga yan yatsuna na nuna mishi zobunan ya ce,
'A'a lalle Junaidu ya burge ki." Na ce eh Baba shi
kuwa Yaya Almu ya bani wadannan warawaran
tare da kyautar dogayen riga ya kuma roken in
maida su suturar da zan rinka yawaita amfani da
Su.
Da sauri baba ya ce,"Ya yi daidai uwata, don
kuwa nima ba akan son raina nake ganinki da
Kananan kayan nan ba, barin ki dai kawai na yi
don in gane yaushe ne za ki girma ki daina, don
kan ki? To ga shi girman ya zo."
Muna ta hirar mu da Baba ita kam Ummana
shirnu ta yi, don dama in tana cikin mota da
wuya kwarai ka ganta tana magana.

103
Muna isa gida Yaya Almu ya sa hannu ya
budewa Umma kofar motar ta fito Cikin
girmamawa ya ce mata, Sannu da zuwa Umma.
Ta kalle shi cikin nutsuwa a hankali ta bude baki
ta tambaye shi,
"Lafiya na ganka a gida?" Ya sake shiga
wata nutsuwar kafin ya ce mata,
"Rabi ce ta ki jirana sai na ji kasalar yin
tafiyar babu ita don haka na ce bari in jira isowar
ku kawai a gida."
A falon Umma tana zaunc ana ta yi mata
sannu da zuwa, ni kuwa ina kwance a jikinta ita
ma sai shafani take yi, cikin fara'a tana fadin,
"Adawiyyata ta girma a bayana."
Rannan kusan kwana aka yi ana hira a falon
Umma wajen karfe goma ta dawo daga falon baba
ta zo ta same mu ni da su yaya Almu da sauran
yan matan gidan muna zaman jiranta ta zo a yi
hira.
Tana shigowa anti Basira ta sake ce mata,
'Sannu da zuwa Umma, gaskiya daga yanzu in za
ki yi tafiya sosai-sosai za ki rinka sallamar mu
don in bakya nan bushewa yake yi gaba daya aka
dauka eh Umma.
Umma ta yi murmushi ta ce, To ni ban da ku
Basira kwana nawa ma za ku kara ai ina ganin ko

104
zan sake yın wata tafiyar kuma zai zamo sai bayan
bikin ku, don abin da babanku ya gaya mini kenan
zan tsaya in kula mishi da hidimar shirye-shiryen
bakin ku." "Yan mata suna jin haka kunya ta kama
su suka rinka mikewa suna sallama da Umma
suna tafiya dakin su ni kuwa ina ganin sun gama
fita na kara mimmikewa a jikin Umma cikin
murna da farin ciki na ce mata,
"Umma ba karamin farin ciki zan yi ba in
aka sallami kartin yan matan nan suka kama
hanya suka tafi gidan mazajen su."
Umma ta yi dariya ta ce, "Ke kuwa
Adawiyya me suka tsare miki haka?"
Na yi murmushi kawai na ce, "Uhum Umma
kenan ke dai tun da sun riga sun kusa tafiya to mu
bar zancen kawai ba zan kawo miki karar su. ba,
don kar su je suna cewa na hada ki da su, amma in
ban da haka ai ba dadin su nakeji ba."
Yaya Almu ya ja tsaki mai karfi, nuna jin
takaicin a fili, ya kalleni ya ce mini, "In an sallami
kowa ya tafi an bar ki a gidan nan Rabi na roke ki
arziki kar ki ci duniya da tsinke, ki rinka cinta da
bakin allura."
Yaya Junaidu da Umma suka kyalkyale da
dariya, Umma ta ce mishi, "Ba dai fushi ka yi ba
Babangida?"

105
Ya ce, "A'a Umma wai dai ta ji dadi ne sosai
shi ne nake kara ba ta shawara."
Ina kwancc jikin Umma suna ta hirar su har
dai barci ya daukeni na farka cikin dare sosai na
samu duk kowa ya watse daga Yaya Almu sai
Umma su biyun suke ta hirar su, alamar za su
tashi na gyara kwanciya na juya ta daya gefen
Umma ta kara mikewa sosai wai don in kara jin
dadin barcina. Sai wajen karfe hudun Asuba na ji
tana yi mini gyara kwanciyar ki da kyau
Adawiyya, ko ki tashi ki shiga daki ki kwanta, ni
zani in yi alwala. Na ji muryar Yaya Almu yana
ccwa,
"Ta gyara kwanciya Umma? Ai gwara ta
tashi ta yi wa Junaidu girkin da ya ce sammako fa
zai yi."
Ina in haka na yi maza na watstsake don na
riga na san da maganar tafiyar tashi na kuma riga
na sabar mishi da yi mishi guzurin abin da zai
rinka karyawa da shi a duk lokacin da zai yi
tafiya.
Baba yana gama kwanakın shi guda biyu ya
dauki Umma Karama suka yi tafiyar su, gida ya
saura daga Ummana sai Umma Amarya. Sati guda
da tafiyar Baba Ummana ta bayar da umarnin yan
mata su yi shiri za a kai su su je su yi gaisuwar

106
sallama a cikin dangıi, alama dai kenan lalle biki
ya matso. Suna gama shiryawa suka zo suka yi
sallama ta kawo kudi masu auki ta ba su ta ce su
zuba a jakunkunan su, suka yi mata godiya suka
tafi, ni kuwa sai na tashi na na nufi sashin 'yan
mata. Ina kara duba fasalin sashin namu da irin
gyare-gyaren da zan yi a cikin shi kafin in dawo
zaman cikin shi na sosai da sosai, don ina son
wurin suna fita nan zan dawo ko yanzu abin da ya
sa ba na zama wurin sosai takura mini ne da su ke
yi da yawan aiki ko aika komai za a yi in dai ina
wurin to Adawiyya za su ce. Adawiyya ban kawo
abu kaza, Adawiyya ban abu kaza, Adawiyya
dauko mini wannan, Adawiyya sharc nan, goge
can, waya ce miki ki yi haka? Aikin su kenan shi
ya sa nake gudu in bar musu wurin,, don haka
suna fita zan shiga, don babu mai mini wannan
takurar kuma na gama nazarın wurin na dawo na
zauna ina rubuce-rubuce na tsare-tsaren abubuwan
da zan gudanar,Yaya Almu ya shigo ya same ni.
"Aiken me yau kike yi haka Rabi? Kin kuwa
san ban taba ganin ki kina rike da biro kina aikin
makaranta ba?"
Na ce, "Ai ba aikin makaranta ba nc ina
tsare-tsaren yanda zan gudanar da al'amurana ne
in kun tafi."

107
Ya,nemi wuri ya zauna cikin nutsuwa ya
mika hannu a hankali ya karbi takardar ya zuba
mata ido yana kallonta cikin nutsuwa tsawon
lokaci kafin ya dago ido ya kalleni ya ce mini,
"Wato ke dai Rabi ina jin kin yin karatu kawa
kika yi yanzu ki duba ki ga abin da kika zaunan
kika tsara da yake wannan yin kan ki ne da a
makaranta ne aka ce ku yi wani abu makamancin
wannan dä kin ce ba ki gane ba."
Ya miko mini takardar tare da cewar tsarin
ya yi kyau.
"Saura kawai lokacin aiwatarwar, kuma jiya
mun shiga makarantar ta ku ni da Zubairu sun
manna sakamakon ku carryover ki biyu."
Na yi maza na daure fuska na ce, 'Ai na sani
kawayena sun yi waya sun gaya mini."
Ya ce, "Okey ai ban sani ba."
Umma ta shigo ta zauna tana yi mishi
magana alamar ta san da shigowar na shi da suka
gama wannan magnar sai ya ce mata, "Ni zan iya
yin tafiya ne yanzu Umma ko dole sai na jira yan
matan sun dawo?"
Ya yi murmushi ta ce mishi, "Me ye gamin
tafiyar ká da ta su?"
Ya ce, "Babu."
Ta co, "To ai sai ka yi ta ka kawai suma suna

108
  yin ta sun ko da yake Dan san in da kake son zuwa
ba."
Ya ce mata, "Katagun."
Ina jin haka na yi maza na ce mishi, "Nima
za ni." Dan na san wurin dangin Umma za shi. Ya
ce, "Me za ki je ki yi wo ki bari sai za a yi miki na
ki auren kya je nima yanzu za ni yi musu sallama
ne su yi mini ganin karshe ina saurayi daga yanzu
kuma za su sake ganina ina matsayin mai iyali."
Umma ta yi kamar ba ta jin abin da yake fadi
ta hanyar kawar da kanta can gefe ni kuwa sai na
shiga marairaice mishi ina cewa;
"Haba yaya Almu in na yi maka rakiya ai ba
laifi ba ne, tun da dama ka saba zuwa da ni ba sai
nima in yi maka rakiyar karshe kana saurayin ba.
Daga yanzu kuma ai zan rinka rakaka ne kana
matsayin mai iyali."
Ya yi maza ya ce, 'A'a yanzu dai shirya yau
mu je ki raka nin, amma ana ba ni iyali ai kuma
na yi sallama da rakiyar ki kenan, iyakaci na ce za
ta rinka raka ni nan da nan." Na ji wani abu ya
dan mintsinen a zuciyata, har sai da ya bayyana a
fuskata, na kasa boye bacin raina. Shi kuwa yaya
Almu tanfar bai gane hakan ba, sai cewa ya yi,
"Ai ni in na yi aure Rabi matata zan ba ta matsayi
mai karfi a rayuwata, komai zan yi da ita zan

109
rinka yi"
Na cc, "Uh hakan yana da kyau." Na tashi na
shige daki na yi kwanciyata.
Wajen arfc goma sha biyu ya shigo cikin
shiri. kwalliyar doguwar rigar tazarce ya yi na
yadin farin koil ya yi matukar yin kyau. Ya-7auna
ya yi sallama da Umma, sannan ya tambaycta ina
Rabin take? Ta mishi ga ta can a cikin dakinta. Ya
dan daga murya ya ce, "To fito mu tafi mana
Rabi"
Na ce mishi. 'Ai na riga na fasa zuwa sai ka
dawo ka gaishe su."
Da sauri Umma ta ce, "Kar ki fara wannan
maganar fito ku tafi sai da kika sashi ya 6ata
lokaci yana jiranki shi ne za ki ce kin fasa? in da
don tashi kadai nc ai da da wuri ya tafi ya dawwo
yau ba, saboda kin cc za kin ba ne ya sa ya ce to
bari ku je ku kwana don ki gaisa da mutane
sosai."
Na cc, "Uh, uh! Ya je kawai."
Umma da Yaya Almu suka yi rarrashi har
suka gaji na cc babu inda za ni har Umma ta
tunzura ta shiga balbaleni da fadi abin da ba ta
taba yi ba. Ni kuwa sai na fashe mata da kuka ina
cewa, "Ni Umma ni ban san abin da nake yi miki
ba, kin fi son Yaya Almu a kaina, komai ya yi shi

110
daidai ne a wurinki da7u kina Jin shi yana ccwa
daga ya yi auren shi shi kenan ya daina yin
mu'amalla da ni, amma ba ki ce mishi komai ba,
ba ki kwabc shi kan maganganun da yakc ta fada
ba, sai ni kawai don na ce na daina bin shi daga
yau ba sai ya yi aure ya daina ba, shi ne za ki
lullubeni da fadi?"
Yaya Almu ya ce,  "To yi hakuri Rabi ai ban
san zancen ba zai yi miki dadi ba, da ban gaya
miki ba, sai in bar abin kawai a cikin zuciyata."
Na yi maza na ce, "Kin ji shi ko Umma kin ji
shi yana nan akan bakan shi na cewar in ya yi aure
ya samu mata to ya daina mu'amalla da 'yar uwar
shi, kuma kin yi shiru ba za ki kwabe shi ba, ai in
ya rabu da ni saboda ita kema zai rabu da kc don
haka ba zani ba ya je ta fara yi mishi rakiyar daga,
yau."
Ya ce, "A'a yau kam ai ba a nuna mini ita b
tukunna."
Umma ta daure fuska ta ce, "Kai Babangida
daina wadannan maganganu naka marasa dadin
ji." Ya ce to Umma a yi hakuri.
Duk da hakurin da ya yi ta bani bayan fitar
Umma daga falon ba mu bar gida ha sai wajen
karfe ukun yamma a dalilin tuburcwar da na yi na
ce babu inda za ni.

111
Muna tafiya a motar Yaya Almu hirar auren
shi da matar shi yake yi mini ni da da kike kallona
zan so matata Rabi, zan so mu'ammala mai dadi
tare da ita, zan so a ce muna da cikakkiyar
fahimtar juna ni da ita, ba zan yarda wasu can su
shiga cikin mu'amallar mu ba. Zuciya ta raya mini
wato ni ce wasu can, ya ci gaba da cewar;
'Shi aure da kike ganin shi karfin shi yafi
Karfin komai, kusancin shi kuma yafi karfin
kowanne irin kusnaci mu'amallar da ke tsakaninka
da matarka mu'amalla ce ta kut-da-kut ta rufin
asiri ta taimakekeniya da kuma nunawa juna
kauna, don haka ai ina ganin bai kamata ka bar
wasu su shiga cokin lamarin ka har su zosuna
kawo muku matsala ba."
Na ce, "Uh haka ne." Na tsuke fuska ta don
dani in samu ya yi shiru cikin raina kuwa sai
tunani nake yi. ashe dai shi ma yaya Almu irin
sullutayen mazan nan zai zama wadanda daga an
yi aure sai kuma su mance da iyaye da 'yanuwa
sai a koma gindin mata a tare sai kuma yanda ta
yi.
Ina cikin tunanin nawa ya katse mini shi ta
hanyar cewa, "Ni fa na dade ina tunanin
hikimomin da kc cikin aure Rabi, ni fa ina ganin
duk abin da ka yi wa matarka ba ka fadi ba, to

112
wake maka irin abin da take maka? Wurinta fa
kake sauke dukkan lalurornka, to balle kuma a ce
ka yi sa'a ta haifar maka da, caf ai ni kam sai in
bar komai in zauna in yi ta tarairayarta ina tayata
son abin da take so, in tayata kin wanda ba ta so,
in ta kalle farin abu ta ce mishi baki ne in yi maza
in ce mata kirin kuwa, don dai kar ranta ya baci."
Na kalli Yaya Almu na ce mishi, to amma
haka aka ce ayi zaman aure ya yi máza ya ce Yaya
aka ce a yi? Kin sanni ban sani ba, tun da ban taba
yi ba.
Ba tare dana gance abin da yake nufi da fadin
hakan ba sai na ce mishi ina ce cewa aka yi, ku
kare kan ku da iyalanku daga shiga wata irin wuta
wacce makamashinta yake mutane ne da
duwarwatsu. Ya yi maza ya ce haka ne Rabi na ce
to amma a yanda kake cewa za ka yin nan za ká
ya yin wannan aikin? A maida fari baki, ka ce
mishi bakikkirin? Kenan in aka maida gaskiya
karya za ka yarda? Gaskiya ni ba haka na ga
1yayen mu suna auren su ba."
Ina fadin haka na soma kuka ina fadin,
"Kenan zan rasa ka zan rasaka Yaya Almu, na
gane matarka za ta kwace mini kai, dama kuma ba
ni da kowa sai kai. Kai ne dan'uwana da uban mu
ya haife mu tare muka kuma taso a daki daya. Kai

113
ne nafi shakuwa da kai, kai na fi so kai ne nake
damuwa da duk wani al'amarinka tun inan ganin
abubuwan da kake yi mini 'yan ubanci ne da
takura a dalilin ba ka son ganina a cikin gida har
sai na fahimci cewar kana yi mini abubuwan da
kake yin ne don kana nufin gyara a kaina, to
amma yanzu wadannan kalaman naka me suke
nufi?"
Ya yi maza ya kauce hanya ya nemi wuri yaa
yi parking a cikin jeji ya fita ya je ya bude but
idin motar ya dauko jakaar ruwa ya zo ya bude
wurin zamana ya miko mini jarkar.
"Bar kuka Rabi ki wanke fuskar ki kar mu
isa su ga hawaye a idon ki, ai tun da na gane kin
damu da ni haka ba zan bari ta raba mu gaba daya
ba, zan rinka yi miki waya a kai a kai duk sati
biyu zan yi kokarin in kiraki." Na sa hannu na
karbi jarkar ina wanke fuskata cikin zuciyata
kuwa fadi nake yi, lalle wannan ya gama tafiya ba
zan sake kuka a kan shi ko.damuwa da shi ba, in
kuma ya kira n1 a waya bayan sati biyu da kiran
farko to ba zan taba dauka ba, gara mu yanke
kawai gaba daya.
A Katagun a gidansu Umma karba sosai aka
yi mana dama yaya Almu ba bako ba ne a gidan
yama fini sanin 'yan'uwan Umma da mu'amalla da

114
su, don haka ban sake komawa ta kan shi ba,
kowa harkar gaban shi yake yi, ko wani wuri za ni
ba na neman shi sai kawai in kira yaran gidan su
rakani, shi ne ma in zai je wani wuri yake aikowa
in zo mu tafi tare, sai in ce mishi ya je kawai ni na
riga na je.
Wani abin takaicin dai kawai da ya kara
kular da ni a tafiyar shi ne yanda duk inda na je
sai a rinka nuna ni a matsayin wai ni ma a
amaryar ce, har suna tambayata to in ban da
sakarci irin na ki me ya hanan ki biyo sauran
yanmatan ku yi tahowarku tare gwanin sha'awa
sai ki wani coge sai Lamido ya kawo ki don ba ki
da kuny? Na yi ta kokarin yi musu bayani ni fa
rako Yaya Almu na yi ya zo ne ya yi muku
sallama armma ni ai ba yanzu zai a yi mini aure ba
Umma ta ce bikina ni kadai za a yi ba za a hadani
da wadannan kartin ba, wajen shekara hurhud fa
suka ba ni sai a ce mini ke tafi can ko shekara
nawa-nawa suka baki ai kin kamo su har ma kin
dara su tun da duk cikin su waccce ba ki kercta a
tsayi ba? Na ce to shi kenan ku tambayi Yaya
Almu kan wannan dalilin nema har na nemi Yaya
Almu don ya bayar da shida kan cewar babu ni
cikin wadanda za a aurar din ya ce musu ch a1 ita
yanzu ita ce za a bar wa rikon gidan, in an hada

115
har da ita ai zai zama babu wata mai kula da
sashin 'yan matan kuma ba ta karasa karatun ta ba,
ga shi tun da tana faduwa jarrabawa to ba bana
nema za ta fita ba, sai badi za ta gama diploma,
sannan ta yi H.N.D. kamar na su Aina'u kenan
don haka ina ganin auren Rabi kam da saura
tukunna.
Gaba daya suka shagala kan cewar kai amma
kuwa da abin bai yi dadi a irin wannan girma da ta
yia ce kuma sai an kara wasu shekaru nan gaba? Ya
yi murmushi ya ce yarinya ce fa kwanakin baya ne
ai ta cika shekara goma sha tara, suka ce au to in
ban da nan wurin ku ina ake yin haka ka bar 'ya tana
ta yi maka wanki a gida? Ai mu nan shekaru sha
biyu, sha uku in ta yi tsauri sha hudu sai a gabatar
da yarinya.
Kwana biyu muka yi muka kamo hanyar
dawowa a wannan lokacin ba wani dasawa muke yi
da Yaya Almu ba, don sau uku yana subutar baki
yana kirana da sunan Aina'u sai ya kiranin sai ya ce
mini wai sorry please na riga na sanya ta ne a raina
a dalilin ke ma ita kika zaban mini sai na ke ganin
to watakila dai ita din za a ba ni bari in koyi sonta
tun kafin a ba ni itan, doon komai ya tafi mana
daidai, ko kuwa? Kin san ni ba zan taba yin musu
da baba bkan wacce zai ba ni ba, to balle kuma in yi
sa'a a ce ita din na samu ga ta mai kyau, ga ta

116
gwanar iya kwalliya, ga 1ya taku. Na yi maza na ce
a'a nan kuma daya. Ya ce au to ashe kwalliya kawai
ta iya ban da takun tafiya? Uh to amma ai na samu
mace gwanar kwalliya ai dadi ne da ita za ta fidda
ka kunya duk inda kuka shiga ni ko ba ta iya girki
ba babu komai zan nemo mai yi mata girkin, ta yi
kwalliya kawai ta yi zamanta in na dawo gida ta yi
ta tarairayata tana ina taka saka da ni, tana mini
tausa tana mini abin nan. Ai ni kuma shi kenan ta
tafi da komai nawa ta. gama da ni ta tafi da ruhin
rayuwata. Na tsuke fuska cikin jin takaici na ce,
"Kai Yaya Almu dai wani abu ya same shi tir!" Na
ja tsaki.
Ya dan waiwayo ya kallen ya ce, "Ba dai ni
kike wa tsaki ba ko?" Na yi shiru ban ce mishi
komai ba.
'Rashin kunyar taki har ta kai ga yi mini
tsaki?"
Shiru na yi ban kula shi ba, da na ji zai yi
magana sai na katse.shi na ce mishi, to wai ni yaya
Almu me ya sa duk inda muka tsugunna muna
magana sai ka gaya musu faduwa jarrabawa nake
yi? Ya ce ban san ba kya so a sani ba ba zan sake
gayawa kowa ba, tun da ma ai kin san in na yi aure
zan dauki matata in yi tafiya ta da ita, ba zama ki
rinka ganina a kai a kai ba, balle in je ina fadin abin
da ba kya so a sani.

117
Tun da na gane duk wata magana da za a y1 da
shi sai ya ciko ta da maganar auren shi ko da
farkonta ba ta auren na shi ba ne, sai kawai na kame
bakina na daina yin maganar da shi har muka isa
gida ni da shi ba mai magana da wani.
Tun daga rannan kuma na daina shiga harkar
shi, ko abinci na yi ba na zuba mishi. Yana zaune a
falon Umma hira suke yi tare na shigo na same su
na ce mishi sannu yaya Almu, ya ce yauwa Aina'u.
Umma ta kwashe da dariya ta ce, 'Adawiyya ce yau
ta zamc maka Aina'u Babangida?" Ya ce au yi
hakuri Rabi. Ya ci gaba da zancen shi a zuciyata na
ce ba laifinka ba ne laifina ne da na gaisheka.
Ban sake tsinkewa da lamarin Yaya Almu ba
na kara tsoraa da shi sa a ranar da Umma ta aike ni
wurin shi wai in kai mishi sinasir da miya, wanda ni
na yi mata ta dibar mishi. Samun shi na yi a kwance
a dakin shi ya yi rigingine kan katifar shi yana
kallon dama wasu baitoci yake rerowa cikin labarci
masu dadin ji, duk da ban san abin da suke nufi ba,
don in ka debe gaisuwa ban san komai ba cikin
wannan harshen mai daraja cikin kowane karshen
baiti daya kai sai in ji shi yana fadin Ainau. A
zatona haka amshin wakar yake. Ina tsugunne ina
sauraron shi ina jiran ya gama in gaya mishi abin da
ta ce in gaya mishi, sal da ya gaman sai ya kalleni
ya yi murmushi ya ce, "Wannan wakar wani

118
mawaki ne na lokacin jahiliya' da ya ta6a yin nasara
aka rubuta wakar shi da ruwan zinare a kasuwar
mawaka, shi ne ya zauna ya yi wa masoyiyar shi
wakar nan da kika ji ina yi ya siffaintata da kyau, ya
bayyana ta a matsayin mai cikakkiyar sura, da
darararan idanuw..Ya dan kalle ni ya ce, 'Ashe
ke kanwata ce bai kamata in tsaya ina gaya miki
siffofinta ba, ke dai kawai."
Ya sake yi mini wani murmushin, sannan ya
ce, "Ta yi mini kama ne da antin ki Aina'u shi ya sa
na cire sunan budurwar ta shi na sa na tawa
budurwar don tafi tashin cancantar wadancan
baitocin, ko ya ya kika gani?"
Na yi kamar in ce mishi ai da kirkiro baitocin
ka yi da taka hikimar sai na kasa saboda har yanzu
na kasa daina ganin girman shi, illa dai kawai
tausayinsa da kan kamani in ce oho mutum har
mutum kamar yaya Almu dai wai tun ba a fara zama
ba ya zama ta ce, to n an fara zaman ya ya zai
zama? Oho. Ina cikin wannan tunanin ne ban kai
karshe ba ya katse i ta hanyar cewa ina son aure
Rabi, ina so in ga mace a kusa da ni mai kyau a ce
ita din kuma ta wace. Ya dan shinfida hannu kan
faffadan kirjin shi yana shafawa tare da yin ajiyar
zuciya, sannan ya ce "Kin ji dadi in na sanmu
hakan? Kin sanni ina son mace."
Ya dan lumshe ido a hankali ya sake bude su

119
cikin nutsuwa ya sake kallona ya ce, "Ke 'yaruwata
ce ba zan iya boye miki ba Rabi ina son aba ni mata
zaman nawa haka ya ishe ni, wani lokaci na kan
kasa barci in bukatar hakan ya taso mini, sai dai
babu yanda zan yi dole in yi hakuri shi ya sa nake
gaya miki tun da ke kina hira da Umma ko za ki
rokar mini ita ne ta yi wa Baba magana ya taimake
ni bana kar ya bar ni in wuce damunar nan mai
zuwa ina tuzuru, ya yi mini aure, zaman nawa haka
ya isa'yan watanni kadan masu zuwa ne fa zan cika
shekaru talatin a duniya, to ko ban fada ba ai ya
kamata a ce ita Umma ta san na girma. Za ki
taimaka ki yi mata magana?"
Na 6ata fuÅŸka na ce, 'Ai ka fini kusa da ita."
Ya ce to ai kunya nake ji ko ke din ma in za ki yi
mata maganar ai za ki yi ne a matsayin ki na
kanwata kina tausayin zamana haka, tun da kin san
zaman nawa a haka ya ishe ni ba cewa za ki yi ni na
aiko ki ba, kin ga nima da na gane kin isa aure kin
fara bukatar wami mutum kusa da ke sai in yi maza
in ce a gabatar da ke."
Yaya Junaidu ya lcko dakin ya gan mu, "Ya ya
na ga Adawiyya tana durkushe kamar mai neman
gafara?
Ya dago ido ya kalle shi cikin nutsuwa ya ce,
Wai sinasir ta kawo mini, ni kuma ina da abin da
nake bukata fiye da wannan shi ne nake rokonta ta

120
taimaka ta sa a yi mini aure."
Yaya Junaidu ya galla mishi harara tare da jan
tsaki ya ce mini, Ke Adawiyyah tashi ki yi
tafiyarki in ya matsu shi zai san yanda zai yi tun da
ai ba fin shi bakin magana kika yi ba." Ina jin haka
na yi maza na mike dama zaman nawa a wurin ya
ishe ni, don ba jin dadin hirar nake ji ba.
Ina shiga falon Umma na kalleta na ce mata,
"Daga yau Umma kar ki sake aike na wurin Yaya
Almu."
A hankali ta daga ido ta kallen ta ce, "Me ya yi
zafi haka ke da dan'uwanki?" Na ce kai ina ganin
kamar zan yafe shi kin san wai zuwa na yi na same
shi yana yi wa Anti Aina'u wakar larabci? Wai har
yana kwacewa Baralabe baitocin shi yana cewa wai
da ita suka da ce?"
Maimakon Umma ta taya ni jin takaici sai
kawai na ga ta kyalkyale da dariya mai karfi har
tana tambayarta wai me kika y1 wa Baangida ne
yake miki irin wannan sakarcin? Na ce me na mishi
Umma in ban da kawai idona shi da ya rufe? Kin
ma san wai dame, yake kwatanta ta? Ta ce, 'A'a."
Na taba baki na ce to wai da cikkakiyar sura da
daradaran idanuwa. Tana da su Umma?" Na zuba
mata ido ina kallonta ta sake sakin wani lallausan
murmushin kafin ta ce, To tana da su din kenan tun
da ya gani?" Na ce, "Haba Umma ni da ke muke

121
magana kuma dukkan mu mun san gaskiya Aina'u
fa ba wata mai cikakkiyar sura ba ce. Sannan kuma
ko Anti Basira ai sun fita manyan 1danuwan.""
Na lura maganar da nake yin dariya take sanya
Umma sai na mike zan shiga cikin kicin in debo
kunun aya in sha na ce gaya mini Umma sun fini
kyau ne ya kidime har a kanta? Ta yi maza ta ce,
"Wane su." Ina jin ta fadi haka na yi maza na dawo
kusa da ita na zauna. Ta ce, 'Ai ko baiwar tsayin da
aka yi miki ya ishe ki Adawiyya. A ce dai ba ki da
komai sai tsayin nan na ki ya isa ki gamsu. ki yi
godiya kan ni'imar da aka yi miki, balle ga ki mai
daradaran idanuwa farare tas, gaki da dogon gashi
mai matukar kyau, gaki da cikkakkiyar sura. Ai ni
inda Lamido zai yi karfin halin yin wannan rashin
kunyar a gabana to da kuwa na yi karfin karyata shi
in ce mishi kul daina irin wadannan kalaman naka
na karya da kake yi kai ma ka san ba Aina'u ce mai
wannan siffar ba."
Kalaman Umma suka sanya ni jin sanyi cikin
raina na ce, 'Umma. Ta dago ido tana kallona na ce
da sannu zan kawo miki suruki wanda zai so ni fiye
da son da Yay.. Almu yake yi wa Aina'u, don in ba
hakan aka yi ba zan rinka tunanin ta kware ni, don
ta riga ta kwace mini yaya Almu ta raba ni da
dan'uwana, bai tunanin kowa a yanzu sai ita."
Hawaye suka zubo mini sharr! Nan take kuma

122
na kasa shanye kukan, saboda nauyin da zuciyata ta
yi, a dalilin tsananin kuncin da ta samu kanta a ciki.
Kuka na yi ta yi, Umma tana ba ni hakuri, ina
jaddada mata cewar babu dama wata a ce ta shiga
tsakanina da dan'uwana hakan ba zai yiwu ba. Ba
mu tashi daga wurin ba sai ga shi ya shigo.
"Aina'u da sauran sinasir din nan ne?"
Umma ta yi baza ta bata fuska ta ce kai
Babangida shiga hankalinka kar in sake jin ka kira
mini Adawiyyata da sunan da ba nan ta ba, ranka
zai baci."
Ya nemi wuri ya zauna Cikin nutsuwa ya ce, *A
yi hakuri Umma subutar ba ki na yi." Ta sake cewa,
"Kar ka sake don ba zan lamunci ganin Adawiyya
cikin bacin rai ba, sannan bacin ran ma a ce. daga
gareka ne."
Ya ce, 'A ba ta hakuri kuma in ta yarda ta
shirya mu je in kai ta ta shah iska, don bacin ran da
na sanyata."
Na ce, "Bab inda za ni." Umma ta ce tun da ta
ce ba za ta ba, to ba za ta ba.
Bayan fitar shi nena kalle ta na ce mata share
shi zan yi ta gyada kai nuna alamar yarda.
Tuni na yi watsi da yaya Almu da duk wata
harka tashi, ita ma anti A ina'un na daina kulata don
sai na rinka ganin tanfar wani gani-gani take yi
mini. Komai zan yi sai in je wurin Yaya Junaidu in

123
ma unguwa za ni can wurin shi na ke zuwa ya kai ni
a kowannc lokaci kuma in muna hira in dai na kawo
mishi zancen auren su ya kan gaya mini shi zai aure
ne kawai don yin shi din ibada ne, shi ya sa yake
addu'ar idan baba ya tashi ya zabar mishi mace to
ya zabar mishi mai hankali da nutsuwa, wacce za su
yi zaman fahimta shi da ita, saboda shi a fahimtar
da ya yi wa auren da kuma lura da al'amuran iyayen
mu ya gane babu komai a cikin shi, illa hakuri da
juriya, shi ana shi fahimtar in ma har da akwai wani
Jin dadi to bai wuce na kare mutunci ba, don haka
shi kyan mace da iya kwalliyarta yana dashe shi, to
amma ba shi ne abin da yafi bukata a wurinta ba.
zai fi son ta zama mai hakuri da juriya,, saboda ta
ya rungumar al'amuran shi da na yan uwan shi in
ya so sai kyau da kwalliyar su biyo baya.
Cikin Zuciyata na ce waiyo ni Ina ma dai yaya
Junaidu ne yake da matsayin yaya Almu a wurina,
da ban samu matsala ko shiga bara/anar rasa
dan'uwana ba, amma shi tun ba a yi aurcn ba har ya
fara yi mini kashedin babu mai shiga tsakanin shi da
matar shi, karewa ma har ya fara mancewa da
sunana.
Na kalle shi Cikin nutsuwa na ce mishi
"Amma kuna hira da yaya Almu. Yaya Junaidu
kana gaya mishi irin wadannan abubuwan?"
Ya dan yi ajiyar zuciya a hankali, sannan ya ce

124
mini, "Ba na iya yin hirar auren da Mustapha a yan
kwanakin nan saboda zukata sun yi nauyi
Adawiyyah, duk lokacin da na yi tunanin dauko
hirar sai in ga to me za mu tattauna? Farin cikin
rabuwa da 1yayenmu KO kuwWa tausayin zaman mu
da su ya zo karshe? Zaman da muka yi da su mai
dadi? Zaman da muka yi da su suna dawainiya da
mu suna kokarin ganin mun zama mutanen kirki?
Kullum burin su bai wucc son ganin sun kyautata
mana ba, ni kam tausayi kan kama ni in na dubi
shekarun baba na ga wai har yanzu bai daina
dawainiya da mu ba, ba ni kuma da wani abin da
zan yi mishi wanda shi bai taba yi mini ba, komai
za ka yi tunanin yi mishi to shi din ya yi maka,
wanda yafi shi kafin ka yi, don haka ni ko kadan ba
na zumudin auren ba na kuma kin yin shi, ni dai
gani nan ne kawai ina dai addu'ar samun dacewa ne
kawai."
A wannan dan tsakanin sai na kara son yaya
Junaidu na kara girmama shi, na kara ganin darajar
shi saboda na gane shi din babu abin da yake so da
kauna irin iyayen shi, musamman ma kuma Baba.
Kullum na kan samu Yaya Junaidu a waje ko a
falon Ummana mu yi hira sai dai ban zuwa dakin su
na daina ya yi, ya yi in gaya mishi dalilin hakan na
ki, saboda na riga na kudurawa zuciyata ba zan taba
yi wa wani hirar kalaman da yaya Almu ya gaya

125
mini ba, akan auren shi da matar shi ko da kuwa
Umma ce, wadanda ya yi a gabanta sun isa su zama
shaida in ma wani abu ya taso a tsakanina da shi a
can gaba.
Ita kuwa Umma hidimarta kawai take yi na
shirin auren 'ya'yanta maza da mata, dama kuma
haka ne a duk lokacin da za a yi hidima irin
wannan, ita mai tsayuwa kan komai don haka tuni ta
yi nisa da shirye-shiryenta a yanzu jiran isowar baba
kawai take yi, ta ji lokacin da zai sanya ranar auren.
Ina zaune muna hira da ita yaya Junaidu ya
shigo ya samc ta cikin nutsuwa ya ce mata,
Wurinki na zo Umma."
Bayan sun gama gaisawa ta ce mishi, "To
Junaidu ke Adawiyya tashi ki ba mu wuri." Ya ce,
'A'a Umma ta yi zamanta kawai." Sabanin yaya
Almu da ya fito. mini dá wani sabon wulakanci na in
ya zo wurin Umma zai mata magana sai ya ce mata
wai sirTi za mu yi Umma, Rabi ta ba mu wuri, ita
kuma sai ta ce wai in fita takaic1 ya kama ni in ce.in
dai haka 'yan'uwan suke zama in za su yi aure to ba
za a rinka zumud n auren na su ba. Umma ta ce to
ina jin ka Junaidu ya gyara zama cikin nutsuwa ya
ce, "In har baba ba zai yi fushi ba to ki rokar mana
shi ya ba mu izinin yi wa matan mu kayan aure,
maimakon yanda ya saba yi in zai yi irin wannan
hidimar ya yi wa mata kayan daki, ya kuma yi wa

126
maza kayan aure, matan su ba wai mun girma ba ne,
Umma amma mun duba ne muka ga mu din dukkan
mu ma'aikata ne wannan ra'ayin na mu ne dukkan
mu don Kabiru ne ya fara kawo shawarar don haka
da yawun su dukkan su na zo ki rokar mana shi ki
kuma ba shi hakuri don kar ya dauka hakan da wani
tunani.
Umma ta ce to ban san abin da zai ce ba, tun
da auren nan ba duk zai bayar a cikin gidan nan ba,
ya ce haka ne mun sani, amma duk da haka nan na
Cikin gidan muna rokon a yi mana wannan alfarmar
ta ce to bari ya zo mu ji, yau ai bai fi kwana goma
ba watan zai kare. Ya ce haka ne. Ya dan zauna ya
yi hira kafin ya tashi ya fita. Na kalli Umma na ce
mata,
"Shi kam yana son baba."
Ta ce mini, 'Dukkan su ai shi Alhaji yana da
wata baiwa bai taba rike' mutumin da bai son shi
ba."
Na ce, 'Ai baba dole a so shi." Umma ta yi
murmushi, "Wannan fadi ki kara Adawiyyah Alhaji
mutum ne."
Ban fara sanin auren zumudin shi sosai ake yi
ba, sai da na ga irin shirye-shiryen 'yan matan da
kuma yanda kullum sai an kwashe su an kai su
wurin gyaran jiki kuma wai wurin Ummana ake
zuwa karbar kudin gyaran, sannan ko nawa aka zo

127
aka ce mata sai kawai in ga ta zaro kudi ta bayar na
kalleta na ce, "Umma mene nc haka, ya ya kamar a
Kasa kike debo kudi? Komai suka ce sai ki ce musu
ga shi"
Ta yi murmushi ta ce, 'Aure fa za su yi kin
kuwa san menc ne auren? Ai dole amarya ta gyara
jiki ta yi kyau ta burge angonta." Na ce to ni fa
Umma? Ta ce ai ke ba yanzu za a yi auren ki ba, in
na ki auren ya zo ni da kaina zan gyara ki ba sai na
tura ki kin je wani wuri ba, sanin da na yi Umma
gwanar gyaran jiki ce, don wani lokaci ta kan yi
ini 1na kuma ganinta tana yawan yi wa kanta,
musamman a ce ga baba nan zuwa ya sa na yarda da
maganar ta.
Washe gari Juma'a babu zato babu tsammani
don ba ranar zuwan Baba ba ne, ko dama karshen
wata ne, balle ma watan sauran kwana takwas ya
kare. Ana cikin aikace-aikacen gida ni kam ma a
kwance nake yayin da Umma take jan carbinta a
inda ta idar da sallar Walaha, sai kawai muka ji gida
ya kaure da hayanıyar oyoyo mai karfi ga kuma
dirar motoci, suna ta shigowa gida. Da sauri na fito
falo ina tambayar Umma mene ne? Sai ta yi maza ta
shafa fatiha ta ce mini.
"Alhaji ya iso."
Da gudu na fita tuni har jama'a sun fara cika
gidan mu. Yaya Junaidu kuwa yana ta kokarin

128
bubbude mishi wuraren da yake amfani da su a
zuciyata na ce an yi saa dama kullum wurin a
tsabtace yake.
Akan dole na dawO sashin Ummana ba tare da
gaishe shi ba, saboda mutane ina shigowa na samu
yaya Almu yana tambayar Umma abin da za a fitar
musu tana gaya mishi na sake fita, don na daina
zama inda yaya Almu yake, na je na gaida Umma
Karama da suka iso tare, sannan na shiga kicin na
samu Umma Karama da ta riga Umma shiga kicin,
don fara shirye-shiryen aikin da za su yi na
kwatsam da ya same su, su baba Talatu ma duk sun
hallaro akn kama aiki gadan-gadan ita ma Umma ta
iso suna shawara ita da Umma Amarya kan abin da
za su yi. Ina ganin abincin rana za mu shirya don
Babangida ya fita da abin da za su karya da shi ya
kuma ce zai isa don haka ba ma bukatar saurin mai
yawa. Umma Amarya ta ce, To haka ne bari in
koma daki don ban yi sallar Wahala ba." Umma ta
ce mata to.
Umma da su Baba Maigyada suna shirin abin
da za su girka ni kuwa na ja gefe na shiga shiryawa
baba miyoyi kala daban-daban tare da abin sha.
Miyar koda na soma shirya mishi. Ga
abubuwan da na yi amfani da su
Koda
Albasa

129
Butter
Flour kadan
Maggc 2
Ganyen Pcrsley
Kayan kamshi
Na yanka kodar kananan yanka na soyata tare
da albasa cikin butter na zuba flour tare da maggi na
dan gauraya kafin na zuba mishi ruwan tafashe na
rufe ya yi ta tafasa sai da ya yi laushi sannan na
zuba ganyen persley da kayan kamshi na rufe ya yi
ta tafasa yana nuna har sai da na gamsu da nunar shi
nan sauke na kuma dafa farar shinkafar da zai ci da
shi, daga nan kuma sai na yi mishi miyar hanta da
tumatir ita kuma na yi amfani da:
Hanta.               Kayan kamshi
Flour.                 Nikakken bawon lemon tsami
Maggi.               Tumatur manya
Albasa.              Mangyada
Butter
Na yi wa, hantar yankan shankwabo guda goma
sha biyu suka zamo da kadan suka dara fadin
gongonin madara. Na hada kayan kamshi da maggi
da 6awon lemon tsami da flour na gauraya sannan
na barbade hantar nan da shi gaba daya, na yanka
albasa ita ma shan kwabo na yi guda shida na
soyata cikin butter ta dan fara laushi na yanka
tumatir sni ma shan kwabo na dan soya kadan duka

130
na tsame su na ajiye, sannan na dauko hantar nan da
na rige na bade da hadadden garin fulawa na soya
shi ya soyu da kyau sai in sa round tumatir kafin in
dora faifin hanta sannan in shinfida faifan albasa sai
in dora wani faifan hanta a kai sai in kawo na
tumatir. A haka har na gama shirya su suka yi
matukar yin kyau sai da na gama shirya wannan
duka na kammala su uwuri daya, sannan na yi maza
na shirya mishi juice cikin sauri in da na yi amfani
da lemon zaki, manya sosai guda hudu na tsami
guda daya, abarba rabi, matse ruwan lemon na yi
duka da na abarbar na hada su wuri daya ban wani
tsaya kara suga ba, saboda an yi dace da lemon da
abarbar dukkan su masu zaki ne sosai, sannan shi
baba ma ba ma'abocin shan suga ba ne.
Da kaina na je na kai mishi na yi sa'a sun
hallara wurin cin abincin tare da mutane da yawa,
amma ba su fara ci ba, na je na ajiye kusa da shi, na
kuma bude mishi ya gani ya zuba ido yana kallo
cikin sha'awa na dan kara matsawa kusa da shi na yi
mishi rada a kunne na ce mishi,
"Baba wannan ni na girka maka da kaina."
Ya yi murmushi ya ce, To zauna ki zuba mini
Hwata." Yana fadin haka na fara zuba mishi
shinkafa da miyar Kazar na ajiye mishi, shi kuwa
sai ya kalli jama'ar da ke wurin ya ce musu, A fara
Cin abinci jama'a ni yau girkin uwa ta zan ci." Suna

131
jin haka suka fara murmushi suna cafko naman
kajin da aka kawo, shi kuwa baba ya sunkuya ya ci
shinkafar nan yana ci yana gaya mini dadinta, yana
kuma daga ido yana hango hantar nan yana gaya
mini.
"To ai na kosa ki ba ni wannan Mamana.
Na yi maza na jawo na fara yanyanka mishi
ina murmushin jin dadi.
"Amma kin iya girki haka uwata me ya sa
tuntuni ba ki rinka yi mini ba?
Na ce mishi, 'Ka yi hakuri baba daga yanzu
kullum ka zo zan rinka yi maka girki."
Ya gama shan fuwan lemon ya ce maza a sake
yi min1 wani saboda wannan zakin shi ya yi mini
daidai. Na ce mishi to. Na shigo dakin Umma ina ta
tsalle na murna, ina gaya inata abincina baba ya c1
sai da na gama tsallen nawa De na juya na ga yaya
Almu a zaune, don haka na yi nmaza na tsuke fuskata
na wuce zan shiga daki ta ce ina sauran da kika
rage? Saboda na san in na kawo mata tare Za su ci,
na ce mata na kai wa Umma Amarya. Ina fadin
hakan kuma na je na nkwashe na kaiwa Umma
Amarya. Na zauna na-yanyanka mata tana ci muna
yin hira, tana yi mini nasiha akan muhimmancin
hakuri da mutanen da zama ya hada ku tare da su.
ita mace da kike gan1 ita ce jagora ta duk wani
al'amari, a gidan mijinta in ta zama ta kirki sai gaba

132
daya gidan ya zama haka, in kuwa ta lalace to gidan
ne yake lalacewa, domin namiji shi kadai bai iya
wadatarwa. Na ce mata to Umma.
Da yamma na sake komawa kicin na shiryawa
baba miyar kuka da naman kaza, sai da ta yi ta nuna
ta farfashe sannan na tsame kasusuwan na burga
miyar. Tuwon dawa na yi mishi, saboda na san
tuwon da Umma ke yi mishi kenan idan tana son
burge shi. Da daddaren ma nina kai mishi tuwon ya
sake kallon ya ce mini.
To wai ni uwata kin iya abinci haka me ya sa
ba ki rinka yi mini ba Ni Junaidu ya taba ba ni
labarin 1ya girkinki, anmma ban taba dauka ya kai
haka ba."
Na cc. 'Ai yanzu na co kullum zan rinka yi
maka Baba." Ya kallen1 a hankali cikin nutsuwa ya
ce mini, To na kwana nawa za ki yi mini?"
Da daddarc ne bayan sallar Isha'i aka kira mu
gaba daya muka hallara a dakin Baba tuni kuwa su
Umma sun shiga sun hallara, ganin su Baba Malle
da na yi da Baba Maishanu ya kara tabbatar mini da
cewar lalle akwai wani muhimmin abin da ya kawo
baba gida.
Gaba daya an tanu an zauna a kasa har su
Umma a kasan suke zaune. Can gefe sai yayyan
baba guda biyu tare da baba da abokan shi ne akan
kujera. Nima na raba na tafi sai da na je kusa da

133
Ummana na makure wurin ya yi tsif tanfar ba
mutane a ciki kowa ka gani a nutse yake kai a
sunkuyc cikin nutsuwa.
"Bude mana zaman da addu'a."
Maganar da Baba ya yi kenan yana kallon
Baba Mai shanu.
Nan da nan kuma Baba Mai shanu ya fara
karanto addu'o'i masu matukar karti yana gamawa
Baba ya soma yn magana cikin nutsuwa.
Tun shekaru kusan uku ko hudu da suka wuce
ne ya kamata a ce na tara mutane an yi wannan
zaman saboda tun a wancan lokacin ku din nan da
kuke zaune anan wurin a gabana duk kun aure in
ban da mutum daya. Sha'awa ia tason in hada ku
gaba daya ban bar kowa a baya ba shi ne dalilin da
ya sa na yi ta jan wannan lokacin bar aka kawo
yanzu ina fata wannan rikewa da na yi muku ba ku
dauketa a matsayin takura ko rashin adalci ba?"
Gaba daya su yaya Junaidu suka kara
sunkuyar da kawunan su kasa, donmafi karfin
maganar tashi Su yake fuskanta. Sai ya ci gaba da
cewa;
'A yau, na gaiyato yan uwana ne da aminaina
kamar yanda na sabab yi kullum a irin wannan
lokacin kan al'amari irin wannan, don su taya ni
shaidawa da abin da na yi niyya kan ya'yana,
saboda halin rayuwa, ko ban kai lokacin da na

134
anbatan ba su tsaya wajen ganin sun cika mini burin
da na yi. Mun yi irin wadannan bure-buren a baya
mun kuma yi dace da samun ikon cika su, to a yau
ma za mu sake sanya wani lokacin don cika wani
burin muna fata mu sake samun damar cikawar in
kuma hakan bai samu ba to ina fata wani cikin
'yan'uwana ko abokaina ya tsaya wajen ganin an
cika mini shi."
Baba Malle ya yi addu'ar baba ya samu damar
cika burin na shi, gaba daya aka amsa da amin,
amin.
Da Baba ya sake gyara zama sai ya nisa ya ce,
"Zuwa na yi a yau don in shaida muku cewar na
sanya ranar bikinku ta zamo ranar 7 ga sabon wata
mai kamawa shi ya sa ban iya jira sai karshen wata
in zo ba, don bai dace in dibawa bikin wa'adin


   

No comments