Recent Updates

Sekatariya Ta Complete Hausa Novel

 


*SAKATARIYA TA*
......(My Secretary).......

*©Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Barka da sallah 'yan uwa. Fatan ansha ruwa lafiya. Allah ya amshi ibadunmu ya kuma kawo ma na ƙarshen wannan annoba ta covid 19. Amin*

*Free page*

0️⃣0️⃣1️⃣

Idon sa ya rintse, lokaci guda kuma ya daka tsawa "get the hell out of here!" Gigicewa yarinyar ta yi, jikin ta na rawa.
Sai da ya sake ma ta magana cikin tsawa " out of my office!"  Sannan ta fita daga office ɗin a bircike, yai tsaki tareda jawo wayar landline ya danna kira, cikin muryar shi mai ɗauke da amo ya ce " Anas, i need another secretary"
Bai saurari mai zai ce ba ya ajiye phone ɗin. Ya ja tsaki sannan ya fara  latsa laptop da ke gaban shi...

"Ene what happened?"  Matashin saurayin ya  tambayi yarinyar da ke harhaɗa files ta na yi ta na share ƙwalla.
Ta ɗago jajayen idanun ta ta kalleshi ba tareda ta ce komai ba sannan  ta cigaba da abinda ta ke yi.

A hankali ya ce " please stop crying, i'll talk to him" ya wuce cikin katafaren ofishin da ya fi kowanne girma acikin kamfanin.

Har yanzu aiki ya ke yi, shi ya sa ko da ya ji alamar buɗe ƙofa bai ma ɗago ya ga waye ba. Ya san sarai mutum ɗaya ne zai iya shiga ma sa office karangatsau haka.

" what exactly is your problem, wai kai for once ba za ka iya haƙuri da juriya da zama da mutane ba. Yanzu mi ta ma ka dan Allah?"

Ya fi minti biyu bai ce komai ba kuma bai ɗago ba.

"Najeeb magana fa na ke yi"

Sai a lokacin ya ɗago kykykyawar fiskar shi ya ce " Oh na ɗauka ƙara ka kawo ai"

Ya ja kujera ya zauna sannan ya kalli Najeeb ya ce " wannan kuma mi ye matsalarta?"

Kamar abin da Najeeb ɗin ke jira kenan ya fara kwarwa " the girl is so dumb, imagine jiya na ba ta report ba ta yi ba, wai ta manta. Yau kuma na ba ta wani, ta je ta yi min shirme....."

" ya isa haka ba sai ka kai ƙarshe ba, na san ƙarshen labarin. Yanzu ya ka ke so ayi?"

"Change her, May be wannan karon ka kawo namiji"

" kamar da gaske, Secretary biyu kafin wannan ba maza ba ne, su ma ba korar su ka yi ba"

Najeeb ya ɗan haɗa rai yace " look dude, ka san yanda na ke son aiki na, you either work perfectly or you leave.  Ba na son shirme"

"Na ji za a nemo wani, but gaskiya Najeeb this time around ka yi haƙuri da koma wanene"

"Yallaɓai Anas na ji na amince. Sai me kuma?"

Anas yai dariya ya ce " duk yadda ka ce Engineer"


...............................................

Waya ce ɗare a kunnen ta lokacin da ta tsaida mai keken. Sai da ta zauna sannan ta ce Muda-Lawal ta ci gaba da waya wanda duk rabi masifa ta ke yi.
Ta na ajiye wayar ta kalli ƙeyar mai keken ta ce " nawa ne?"

"Ɗari da hamsin" ya faɗi hankalin sa na tuƙin da ya ke.

" hala ka fara fashi da makami ko?"

Mai keke ya tunzura  ya ce" ban gane maganar ki ba"

"Idan na baka tamanin ka sa makami ka ƙwaci sauran kuɗin"

" gaskiya 'yan mata idan ba za ki ba da ɗari da ishirin ba ki sauka" ya na magana ya na rage gudun keken.

" sai ka zo ka fitar da ni ai"

Mai keke ya ja keken sa ya tsaya "sauka dan ba zanje a naira tamanin ba"

" duniya da 'ya'yan ta. Idan na sauka a keken nan na zama turmi" ta daka ma sa tsawa "za ka ja keken ka mu tafi ko dai!"

Mutumin da ke gefen ta ya ce " mai keke mu je zan biya kuɗin"

Sai a lokacin ta kalli mutumin. Saurayi ne dan a ƙalla ba zai wuce shekara ishirin da tara zuwa talatin ba. Ta ce "yawwa shishshigi. An gaya ma ka ban da ɗari da hamsin ɗin biyan sa ne?"

"Allah ya ba ki haƙuri"  ya faɗi ya na kauda kai gefe saboda yadda ta tsare shi da manyan idanun ta.
"Ba zan gaya ma ka sunana ba  hakanan ba zan ba ka numbata ba dan na san dalilin shishshigin kenan"

Murmushi yai ba tareda ya kalleta ba. Mai keke ya cigaba da tafiya, a hankali mutumin ke satan kallon ta sai dai ita hankalin ta ya karkata ne kan wayan ta. Chan ta lura ya zuba ma ta ido. Ta ɗago idon ta da sauri ta ce "Malam kallon yai yawa, idan idon ka bai faɗo ba zan ƙwaƙwaleshi da kai na"
Mai keke ya fashe da dariya a zuciyar shi ya na mamakin masifar budurwan nan.
Har aka iso  inda za ta sauka ba wanda ya tanka ma ta. Ta na sauka ta fito da naira ɗari biyu ta miƙawa mai keke ta ce ban ɗari da Ishirin. Mai keke ya ce "Oga ya biya mi ki duka kuɗin"
" chan ta matse mu ku " ta faɗi tareda maida kuɗin ta cikin purse.

Ta ƙarasa wajen park ɗin ta na tafiya ta na waya. Yayinda hayaniyar masu mota ke tashi  a tashar.

"Dan Allah baiwar Allah ki saurare ni" ta ji an faɗi a bayan ta, ta juyo a tsanake.

"Sai aka yi ya?"

Yadda ta yi maganar da faɗa-faɗa ya sa ta ƙara burgeshi. Yai Murmushi ya ce "suna na Rayyan, kar ki min fassara amma idan ba za ki damu ba ko zan iya sanin sunan ki? Please" yai maganar yana haɗa hannun sa alamar roƙo.
"Ai da ma na san dalilin biya min kuɗin kenan. To ba zan faɗi sunan....."
Chak ta tsaya lokacin da aka ƙwala sunan ta
*'Aisha mai gwanjo'*

ta juya ba ta ga mai kiran ba, ta yi tsaki.
Wani saurayi ne ya ƙaraso akan machine ɗin sa ya na murmushi
" Allah ya ja zamanin ki 'yar kasuwa"
Sai a lokacin ta gane shi.
"Sabi'u Inuwa Manzo" ta faɗi ta na maida hankalin ta gareshi.
"Aka ce kina Yola, ya na ganki a Bauchi"

"Wallahi na je gida biki ne yanzu ma na ke son komawa Yolan. Kai fa ina aka turaka?"

"Sun turani Ilorin amma na relocating na dawo Bauchi, kin san mutum mai iyali sai a hankali"

'Yola...Yola..Yola mutum ɗaya' ake kira ta yi saurin sallama da Sabi'u Inuwa Manzo ta wuce wajen motar.
Har Sabi'u zai wuce Rayyan ya tambayeshi sunan Aisha da numbarta. Sai da Sabi'u ya sha dariya kafin ya bashi numbar bayan da Rayyan ɗin yai ma sa bayanin masifar da ya sha shi da mai keke. Sabi'u ya ce ai indai Aisha Farida Salihu ne to kaɗan ka gani.

................................

Tana shiga makarantar aka ce principal na neman ta ta sani saboda tafiyar da tayi ne dan haka hankali kwance ta wuce office ɗin sa. Da mamakin ta sai taga ashe neman saboda wasu 'yan mata 'yan aji shida da ta daka ne kafin ta tafi.

Ba ta bashi haƙuri ba balle ta nuna ta yi nadamar abinda ta yi sai da ta bari ya gama masifar shi ta ce " Mr principal dududu saura sati uku na bar makarantar nan. Yara kuma na dake su ne saboda raini da izgilanci da su ke min, ko gobe su ka sake zan dake su dan ni ba sa'ar su ba ce"

"Idan ba dan Yasir ba ai da tuni mun rabu da ke. Aisha tunda ki ka fara bautar ƙasa a makarantar nan koyaushe ana complain ɗin ki"

"Zan iya tafiya?"

Principal ya girgiza kai "kai kai kai, wannan mijin ki ya shiga uku wallahi"

Lokacin da aka tashi break ta haɗu da Yasir a staff room.

"Tawan ya ki ke, gida ya ƙarɓe ki fa sai wani ƙyalli ki ke"

"To miya fi raina"

Kujera ya ja zuwa kusa da ita kamar kullum ya na ƙoƙarin shawo kan ta. Sai dai kamar kullum ɗin zancen ta ɗaya ne.

"Mun kusa gama bautar ƙasan nan fa Farida ki taimakeni ki amince da ni" ya faɗa haɗe da haɗa hannunwan sa biyu alamar magiya.

"Yasir kenan, soyayyar talaka da maikuɗi a Nigeria its a nonono option for me. Wahala kawai zan sha ni kuma ban shirya ba. Balle kai da ka ke ɗan bare-barin nan ina zaman zama na iyayenka su turomin Yasin mai walƙiya na bi duniya"

Yasir ya sa dariya sai da ya yi mai isar sa ya ce "wallahi shiyasa na ke ƙara son ki, ba kya rabuwa da abin dariya. Yanzu miye kuma Yasin mai walƙiya"

"ka fini sani sarai"
Yasir ya cigaba da dariya.

......................

*Wacece Aisha Farida Salihu?*

Malam Salihu ɗan ƙaramar hukumar Wase ne da ke jahar Plateau. Sai dai tun yana ɗan shekara sha takwas da ya ƙare sakandare ya dawo cikin Jos da zama. Sana'ar sai da kayan gwari ya fara kuma Alhamdulillah yana samu. Su biyar ne a wajen mahaifin su wanda ya jima da rasuwa tun yana shekara bakwai a duniya, shi ne na huɗu a gidan kuma su biyu ne maza. Babban yayansu Musa shi yana Kano inda yake kasuwancin sa acan  sai yayun sa mata Halimah, Asma'u da ƙanwar sa Fatima, wanda a lokacin duka sun yi aure  Shekarar sa biyar a Jos yai aure.

Aminah 'yar Jos ce domin iyayen ta anan su ke da zama tun shekara da shekaru sai dai asalin su Fulanin Dukku ne da ke Jihar Gombe.
Shekarar Aminah shabiyar aka yi auren wanda a lokacin JSCE kawai ta kammala. Suna zaune da Salihu lafiya cikin so da ƙauna har wata takwas kafin mummunan ala'amari ya faru. Tana zaune ta shirya abincin rana ta tsara kwalliya tana jiran sa, saboda ko yaushe Salihu a gida ya ke cin abincin rana, taji sallamar mutane  daga waje. Ta sa mayafi ta fita inda taga Alhaji Nuhu ne wanda su ke haya a gidan sa da kuma Yusufu wanda rumfar sa ke kusa da na Salihu a kasuwa. Yanayin su kaɗai ya tabbatar ma ta akwai matsala. A hankali Alhaji Nuhu ya sanar ma ta Salihu ke asibiti ya yi hatsari. Cike da tashin hankali ta bisu asibitin inda Salihu ke kwance rai a hannun Allah.  Da asuba Salihu ya cika wanda sanadiyyar haka ya sa Aminah suma. Da ta farfaɗo ma dai rikicewa ta yi wanda da ƙyar Nanna wato mahaifiyar Aminan ta shawo kan ta. Sai da aka yi bakwai ɗin Salihu Nanna ta fahimci Amina ciki gareta wanda ko Aminan ba ta san da shi ba.  A hankali Aminah ta dinga renon cikin ta wanda Inna mahaifiyar Salihu ta ke matuƙar farin ciki da cikin. Tsakar daren ranan Alhamis Amina ta tashi da naƙuda,aka kira wata nurse da ta ke ƙasan layin su, zuwa asuba ta haihu, ta samu ɗiya mace.  Aisha Farida aka sa ma ta saboda sunan da Salihu ke cewa zai sawa 'yar sa ta fari kenan saboda sunan innar sa Aisha ya ce zai haɗa da inkiyar Faridah.

Amina ta cigaba da renon Aisha Farida a gidan su. Tana son ɗiyar ta sosai, ko kaɗan ba ta ma ta karan 'ya'yan fari irin na fulani. Shekarar Aisha Farida biyu da rabi Baba ya fara yiwa Amina maganar aure saboda a lokacin akwai manema dayawa da suke son ta. Duk ciki ba ta da zaɓi dan ita tun Salihu ba ta kuma sa soyayyar wani namiji a ranta ba. Cikin maneman ta Baba ya zaɓa ma ta Malam Haruna wanda shima mutumin Dukku ne yana ɗin ki a Terminos. Matar sa ɗaya da yara shida. Lokacin da Amina za ta tare Inna ta so a bar ma ta takwarar ta sai dai Amina ta nuna batason hakan dan a ganinta Farida ta yi ƙaranci a raba ta da uwarta. Ba laifi Haruna na ƙoƙarin nuna adalci tsakanin matansa sai dai Laraba sam ba ta da haƙuri kullum cikin tsangwaman Amina da 'yarta ta ke yi. Amina za ta lamunci komai amma idan akan Farida ce to ba za ta bari ba. Watarana Amina ta dawo daga unguwa lokacin watan ta takwas a gidan ta samu Laraba na dukan Farida tsabar wahala sai da yarinyar ta suma amma haka Laraba ta cigaba da jibgar ta. Da gudu Amina ta yi kan 'yar ta tana ihu. Daga asibiti dai Amina gidan su ta wuce ta yi yaji. A ranan Haruna ya zo biko sai dai ta nuna ma sa matuƙar za ta zauna da shi to dole ne ya raba mu su gida. Yai-yai da ita ta ƙi chanja ra'ayinta, daga baya ya yarda da hakan. Har ya kama ma ta haya ɗaki ɗaya a wani gidan haya a tudun Fera. Ana saura kwana ɗaya tak ta tare saboda har an je an jera ma ta kayanta sai ga Haruna ya zo neman ta da yamma, ta fita ta sameshi a ƙofar gida. Bai amsa gaisuwarta ba ya damƙa ma ta takardar saki ɗaya. Ba dalili ba komai. Ƙarshe dai yadda aka je aka jera kayanta haka aka dawo da su gida. Ta ƙare iddar ta ta cigaba da zaman gida. Da tanada hali ma makaranta za ta koma sai dai iyayenta ma su ƙaramin ƙarfi ne. Kuɗin makarantar Farida. Baffanta Musa ke aikowa tareda kuɗin buƙatunta duk wata, ya so ya ɗauketa sai dai Amina ta ƙi musamman da ya maida Inna zuwa gidan sa a Kano.
Ganin zaman gidan shiru ya sa ta fara yin su kunun zaƙi da zoɓo tana siyarwa. Shekararta ɗaya tana zawarci Ibrahim ya fito neman ta shima dai yanada mata, ba ta bashi dama ba sai dai ganin Haruna ya dawo yana son maida auren su ya sa ta yi saurin amincewa da Ibrahim. Haruna yai nadamar sakin ta acewar sa bai san ya akayi ya saketa ba.

A Saminaka Ibrahim ya ke da zama da shi da matarsa da yaran su uku. Watannin farko an tafi lafiya-lafiya sai daga baya Matar sa Kubura ta fara nuna halin muguntar ta, ƙarshe sai raba mu su gida Ibrahim yai Lokacin Amina na laulayin ciki.  Sai da su ka raba zama Amina ta samu sakewa ita da 'yar ta. Da cikin ya cika wata tara Amina ta haifi ɗa namiji. Hakan ya farantawa Ibrahim rai saboda yaran Kubura duka mata ne. Wannan haihuwar ya jawo Kubura ta sake jin tsanar Amina. Da daɗi dai ba daɗi su na zaune har Faruƙ ya shekara biyu. Kasancewa abubuwa sun fara ja baya wa Ibrahim ya sa su ka bar gidan haya su ka koma gidan sa. Zama tareda Kubura dai sai ma abin da ya ƙaru.

Watarana Farida da Safiya 'yar Kubura su ka yi faɗa. Kubura na kitchen ta ji kukan Safiya aikuwa ta fito da gudu, ba tareda bin bahasi ba ta kama jibgar Farida daga ƙarshe ta kaita kitchen ta sa wuƙa a cikin wuta sai da ta yi jaa sannan ta cire ta manna a bayan Farida. Farida ta calla ihu wanda Amina da akewa kitso a makwabta sai da ta ji kukan 'yarta. Da gudu ta sa hijab ta taho gida inda ta samu har lokacin Kubura ba ta cire wuƙan da ya ke kwance a bayan Farida ba har wajen yai rami, tsabar wuya tuni Faridan ta suma.  Amina ta yi kan Kubura ta kama ta da faɗa wanda a sanadiyyar kokawa da sukayi Amina ta rasa cikin ta. Wannan ya sa Amina ta nemi saki a wajen Ibrahim. Duk wani magiya da roƙo ya yi amma ta ƙi yarda ƙarshe cewa ta yi idan bai saketa ba da shi da matar sa za ta shigar da su ƙara a kotu na zubewar cikin ta da kuma ƙunar da Kubura ta yiwa Farida. Dole haka Ibrahim ya saketa ba tareda ya so ba. Ba ta bar ma sa Umar Faruƙ ba ta ce idan ya cika shekara uku za ta bawa ƙanwar sa Sadiya da ba ta jima da aure ba. Hakan kuwa aka yi dan Amina da kanta ta kai Faruƙ wajen Sadiya da ke aure a Kaduna.  Ta ce ma ta madamar Ibrahim yana tareda Kubura bata yarda ta mayar da Faruƙ Saminaka ba.

Aikin cleaner Amina ta fara a wata private school da ke anguwar su. Inda anan ta saka Farida. Dalilin Farida ta haɗa Amina da Alhaji Kabir mai makarantar. Wata rana ta yiwa wata 'yar ajin su duka iyayen yarinyar su ka kawo complain makaranta. Da komai ya lafa Alhaji KB ya kira Amina ya fara ma ta faɗa akan rashin ƙwaɓar Farida da ta ke wanda hakan ya jawo Farida ta zama ba ta jin magana. Amina ta sa kuka tareda cewa tunda kallon da ake yiwa 'yarta kenan za ta cire Farida a makarantar. Alhaji KB da ya ke da tausayi ya fara bata haƙuri. Daga ranan su ka fara mutunci, watarana da ya ji tarihin rayuwarta ya ce ma ta mi zai hana ta koma makaranta. Ta ce za ta so hakan amma yanzu kam ba hali sai dai gaba. Alhaji KB ya ce ma ta idan ta samu mai taimaka ma ta zata koma? Amsar da ta bashi ya sa zuwa sati biyu ya samo ma ta form ɗin SS1 a wani makarantar gomnati.  Da farko ta ƙi sai dai daga baya data yi shawara ta amince. Ta dena aikin cleaning ta koma makaranta. Bayan shekara biyu lokacin tana SS2 Alhaji KB ya bayyana manufar sa. Da farko ta ƙi shi daga baya ta amince amma da sharaɗin ba za ta zauna da matarsa ba. Sai a lokacin ya tabbatar ma ta shekara huɗu da rasuwar matar sa kuma basu taɓa haihuwa da Ita ba har ta rasu.

Auren Alhaji KB Amina ta samu kwanciyar hankalin aure wanda rabonta da shi tun aurenta da Salihu. Bayan da result na Waec ɗin ta ya fito Alhaji KB ya nema ma ta admission a UJ ba ta samu ba dan haka kawai ya nema ma ta ADR CLIS (AD Rufa'i College for Legal and Islamic studies) da ke Misau inda ta fara karantar Law. Da ta gama diploma lokacin ɗan su ɗaya Hamza, ta fara koyarwa a makarantar sa kafin ta cigaba da karatu. Sai dai samun wani cikin ya sa ta ajiye batun karatu a gefe tukunna. Ta cigaba da renon cikin ta.
Zaman Amina da Alhaji KB zamane na amana yana son Farida tamkar shi ya haifeta har lokacin da ta haifi Hamza bai taɓa nuna wa Farida banbanci ba. Alhaji KB ɗan asalin Jahar zamfara ne yanada 'yan uba amma a wajen mahaifiyar sa su biyu ne shi da ƙanwar sa Hannatu. Mahaifiyarsa ta rasu tun yana shekara shida. Uƙuba na matan uba ya sa ya koma wajen ƙanwar Mamansa da ke aure a Jos lokacin yana shekara sha ɗaya. Anan yai karatu ya zauna har ya kai matsayin da ya ke yanzu. Hannatu ta jima da rasuwa. Ta rasu jim kaɗan da barinsa Zamfara. Raliya ɗiyar Hajiya Aina'u mariƙiyar sa ya aura. Sai dai har Allah ya ma ta rasuwa ba su taɓa haihuwa ba. Haka nan bai ƙara aureba sai akan Amina. Sau biyu tak ya kai Amina Zamfara inda anan ta gane 'yan uwan Alhaji KB ba sa ƙaunar ta, shi ɗin ma abin hannunsa ya sa su ke ɗan girmamashi.

Abdul na da shekara biyu Alhaji KB ya rasu. Mutuwar da ta gigita Amina da Hajiya Aina'u. Lafiya-lafiya ya tafi Zamfara kawai sai yayan sa Ubaidu ya kira wai Kabiru ya rasu zazzaɓi ya sashi a gaba da dare kafin safiya ya cika.
Amina ba ta shiga tashin hankali ba sai da kwana ishirin kacal da rasuwan Alhaji KB 'yan uwan sa su ka zo su ka koreta a gidan sa. Ƙarshe a gidan su ta ƙare takaba. Kafin wata uku da rasuwar sa su ka saida makarantar sa da gidan sa da mafi yawancin kadarorin sa. Hajiya Aina'u da Amina sun yi ƙoƙarin shigar da ƙara Kotu sai dai tun farko da su ka yi yunkurin hakan aka rufe bakin su. Haka nan Amina wadda 'ya'yanta ke kira da Ummi ta koma gidan jiya sai dai wannan karan tana da ilimi daidai gwargwado da kuma wayewa. Wata makarantar ta nema aiki kuma ta samu da wannan ta ke yin hidimar yaranta da shi. Tsohon mijinta Ibrahim ya nemi ta yi kome saboda yanzu ya rabu da Kubura kuma Alhamdullillah matar sa Hafsatu tanada kirki. Ummi ta ƙi tace ita da aure har abada. Ba yadda Babanta bai yi ba amma ta ƙi ta ce aure huɗu da tayi a baya sun isheta. Yaranta uku na gabanta Farida, Hamza da AbdulMalik. Shi ma Faruƙ ya kan zo hutu wajen Ummin sa lokaci zuwa lokaci har lokacin a Kaduna ya ke. Hajiya Aina'u na ƙoƙarin taimakawa Amina da ɗawainiyar yara daidai gwargwado sai dai fa har yau 'yan uwan KB ba su waiwayeta ba balle su nemi taimakawa yaran marigayi. Gado da ya bari kuma babu batunsa dan tuni sunyi wasan kura da dukiyar sa.

Aisha Farida Salihu yarinya da ta taso da ƙiriniya ga surutu. Ba dai ka faɗa ta yi shiru ba. Kwata-kwata ba ta da tsoro, tana son umminta sosai gashi ba ƙaramin shaƙuwa su ka yi ba, idan ka ga suna hira tamkar wa su ƙawaye. Sau tari ma akan ɗauka ya da ƙanwa ne su. Tunda su ka koma gidan su Ummi, Farida ta dena zaman banza ganin dai yanzu ba da bane. Ta koyi kitso da lalle tana yi, ga saida kayan ƙwalama da ta ke yi a school. A haka har ta ƙare secondary school ɗin ta. Jamb ɗin ta na farko ba ta ci ba dan haka ta fara zuwa koyon computer a shagon ƙanin Umminta Ahmad. Ta koyi abubuwa da dama dan Alhamdulillah Allah ya bata ƙwaƙwalwa. Da ta sake Jamb ta tafi Federal polytechnic da ke Bauchi saboda UJ da ba ta samu ba. Business Administration ta karanta a ND da ta zo  HND ta koma Marketing. Aisha Farida 'yar kasuwa ce tuƙuru. Dan tana makaranta ba ta zauna haka ba ita ce saida turare, takalma da jakukkuna. Ga shi duk hutu idan ta je Jos za ta saro gwanjuna ma su kyau ta zo tana sayarwa students. Wannan ya sa 'yan ajin su ke kiranta Aisha mai gwanjo.
Yanzu shekarar ta ashirin da uku, tana service a Yola. Tun a camp su ka haɗu da Yasir Sa'ad ɗa ga senator Sa'ad Babagana. A UK Yasir yai karatu. Da farko su na fita daga camp zai relocating zuwa Abuja Inda iyayen sa su ke sai dai soyayyar Farida da ya shigeshi farat ɗaya ya sa ya fasa. Hakan ya sa a Inda aka turata primary assignment ɗin ta shi ma ya je. Duk iya watannin da su ka yi tare Farida ba ta bashi dama ba. Tausayin sa ta ke ji ta girme shi da shekara ɗaya ita kuma tana ganin tsayawa soyayya da shi ɓata lokaci ne. Ga uwa uba kiran da Hajiyar sa ta mata akan ko da wasa kar ta amince da soyayyar Yasir saboda karatu zai yi hakanan akwai alƙawarin aure tsakanin sa da wata. Ita dai Farida ba dan tsoro ta ke baya-baya da shi ba ko kuma ta ƙi son sa ba sai dai bazata bawa kanta ciwon kai a kan Yasir ba. "Yaushe ma ka girma?" Abinda ta ke yawan gaya ma sa kenan.

*ga mai son cigaban labarin zai biya #200 kacal ta wannan account ɗin 3099546325 Azizat Hamza, firstbank. Idan kuma credit card ne to MTN card na 200 za a turo wa wannan numbar 08137311900. Sannan za a turo shaidar biya (screenshot) na kuɗin zuwa numbar nan still 08137311900. Ko kuma ka biya #300 ka samu labarai biyu**SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Barka da sallah 'yan uwa. Fatan ansha ruwa lafiya. Allah ya amshi ibadunmu ya kuma kawo ma na ƙarshen wannan annoba ta covid 19. Amin*

*Free page*

0️⃣0️⃣2️⃣

Da dare baƙuwar number ya kirata, da ta ɗauka sai ga muryan Rayyan.
"Ɗankwassi! a ina ka samu number ta?"
"My Farida kenan, abinda ka ke so ai duk wuya duk rintsi sai ka samu"
"Chan ta matse ma ka" ta faɗi tareda kashe wayar.
Ya sake kira ba ta ɗauka ba. A hankali a hankali Rayyan ya cigaba da kiran Farida, tun tana ƙin ɗauka har ta koma idan ta ɗauka za ta surfa ma sa masifa, shi kam da gaske ya ke dan haka bai damuba duk abinda za ta ce ma sa shanyewa ya ke. Cikin sati uku sai da ya san yadda ya ja hankalin Farida har tana ɗan kulashi ta dena ma sa faɗa idan ya kira.
Ranan da su ka yi passing out ɗin su sai ga shi a Yola. Ta ji mamaki hakanan kuma ya ɗan samu matsayi a zuciyarta. Saboda Yasir ya  haƙura da ita ya sa ta introducing Rayyan a matsayin saurayin ta. Yasir kamar ya haɗiyi ran sa saboda baƙin ciki haka su ka rabu da shi baran- baran. Ko sallama babu.

Rayyan Abdullahi ɗan Kano ne kuma ma'aikaci a Zenith bank. Ya je Bauchi ta'aziyar 'yar yayarsa da ta rasu su ka haɗu da Farida. Sosai ya ke jin Farida a ransa, tsiwarta da masifarta yana burgeshi matuƙa. Ya ɗau ɗamaran koyawa Farida son sa musamman da ya gane ba ta da wani tsayayyen saurayi. To ina za ta yi saurayi bayan masifarta kaɗai ya isa ya sa samarin su dinga gudun ta.

..................................

Isowar sa kenan cikin gidan a gajiye. Kai tsaye ɗakin sa ya wuce dan ya san Daddy ba ya nan balle ya je ya gaida shi. Ya na shiga ya danna SHS zuwa Main kitchen "lemon tea in 10minutes" ya faɗi tareda zama ya fara cire socks na shi daga nan ya cire gaba ɗaya kayan jikin sa sannan ya shiga toilet.

Adama ta zo haurawa ɗauke da tea ɗin Najeeb ta haɗu da Afrah da ke shirin haurawa saman. Ta duƙar da kai ta gaisheta, Afrah ta amsa a gatsine.
"A Ya Najeeb za ki kai wa?"
Adama ta amsa da "eh"
"Kawo zan kai masa" ta ƙarɓi tray ɗin daga hannun Adaman.
Ta cigaba da hawa stairs ɗin tana tafiya ƙarar takalminta na ba da sautin ƙas- ƙas- ƙas...

Tana jin ƙaran ruwa a banɗaki lokacin da ta ajiye ma sa tea ɗin a ɗakin, kamar za ta fita sai kuma ta samu kujera ta zauna tana jiran sa. Kusan minti biyar sai ga shi ya fito ɗaure da towel. Ya na faman goge gashin sa da ɗan ƙaramin towel ya ganta ta ƙura ma sa ido.
"What the fuck! Mi ki ke yi a ɗaki na" Ya daka ma ta tsawa

Daburcewa ta yi ta fara kame-kame.
"Get out" ya daka ma ta tsawa ba shiri ta fita da gudu dan ta san halin sa sarai.

Sai da ya shirya cikin farar riga da wando baƙi three quater sannan ya buɗe laptop ɗin sa ya na duba wani aiki da Joseph sabon sakatarin sa ya turo ma sa. Yana dubawa yana sipping tea ɗin sa a hankali. Ba laifi Joseph yai ƙoƙari, da alama ya san aikin sa dan tunda ya fara ma sa aiki bai samu kuskure ɗaya cikin ayyukan da ya ke sa shi ba, sai dai da saura tunda dududu sati biyu da Joseph ɗin ya fara ma sa aiki kenan.

..........................

A hankali soyayyar Rayyan da Aisha Farida ta fara nisa, domin har ya je Jos ya gaida Ummi...

"Farida ba magana na ke mi ki ba"

"Ummi dan Allah ki haƙura da wannan zancen, zan dai dinga zuwa mu su akai-akai yanzu tunda na gama bautar ƙasa"

"Kin sani sarai har yau Alhaji Musa ni yake ɗaurawa laifi akan na raba ki da dangin Baban ki. Sun fi ni iko da ke Farida"

"Ni kan Ummi ki yi haƙuri, ba zan je ba, albarkacin Inna na ke zuwa mu su dama, kuma ta rasu shikenan"

"Ki yi yadda ki ke so Farida" Ummi ta faɗi tareda barin ɗakin.

Ita ta rasa dalilin da zai sa sai yanzu Baffa Musa zai takura wai ta koma wajen sa da zama. Ita yaushe ma za ta juri zafin Kano balle uwa uba rashin kunyar yaran sa. Dama dalilin Inna ke kaita Kano kuma tunda ba ta nan kowa ya riƙe kan sa. Da wannan tunani ta janyo purse ɗin ta tana irga kuɗin da ke ciki a karo na biyar kenan tun safiyar yau.

Sosai Ummi ta nuna ɓacin ranta akan ƙin zuwa Kano da ta yi, ko gaisuwarta yau da safe ba ta amsa ba.

"Nanna dan Allah ki cewa Ummi ta bar ni na yi zamana anan. Wallahi ba jin daɗin zaman Kano na ke yi ba"

Nanna da ke shan kunu da ƙosai ta ce " kin dai san da daɗewa Ummin ki tai alƙawarin za ki koma Kano da zaran kin gama makarantar ki. Alhaji Musa da kan shi ya kirata jiya ya ke cewa ya ji shiru. Ke idan ba ke bama ba saurayin ki ɗan Kano bane, idan ki ka je chan sai ku saita kan ku, kinga ba sai an sha wahala ba daga nan sai dai mu je bikin ki chan Kanon"

Ta turo baki tana faɗin "Allah dama kun gaji dani. Ni dai ba zan je Kano ba"

"Ah to, sai ki kira Baffan na ki ki gaya ma sa ai"

Farida ta zumbura ba ki ta fice a ɗakin....

Cikin kwana biyar ta gama shirin ta tsaf, ba wai tana son zuwa Kano bane, sai dai tunda abinda Ummi ke so kenan dole ta yi shi. Ranan asabat ta wuce Kanon tsabar haushi ko kiran Baffa Musan ba ta yi ba balle ta sanar ma sa da zuwan ta.
A ƙofar gida ta haɗu da su Kamal yaran Baffan su na wasa, da gudu su ka zo su ka tareta sannan su ka tayata ɗaukan kayan ta.

Da sallama ta shigo tana ƙarewa cikin gidan kallo wanda ya sha sabon fenti da alama dai saboda bikin Hajara da Salima da za a yi ne.
Baaba Sabuwa ta fara gani wanda ihun yara ya sa ta fito daga kitchen. Duk cikin matan Baffa Musa ita Farida ke ɗan gani da mutunci saboda itace uwargida kuma ba laifi tana da kirki.

"Oyoyo mutanen Jos. Sannu da zuwa"

Gyalenta ta saƙala ajikin igiyar shanya tana faɗin "fatan mun sameku lafiya"
"Lafiya lau, ya su Ummin na ku?"
Daga kitchen ta ke amsa ma ta da lafiya. Sai faman buɗe tukwane ta ke yi tana neman abin da za ta sa a baka.

"Baaba Sabuwa ni kam har yanzu  ba ku bar baƙar al'adar ku ba, ace abincin rana sai ƙarfe uku"

"Lah yanzu na ke son ɗaurawa ai"

Farida ta dubi wayar ta tana faɗin " a ƙarfe ɗayan!"...

Sai da dare Baffa ya sa aka kirata. A falon shi ta sameshi yana cin abincin dare. Bayan ya ma ta ya hanya sannan ya fara bayani " Aminah ta ce ba ki fara aiki ba dan haka zan sa Yakubu ya nema mi ki aiki a kamfanin da ya ke aiki ko za a dace kema ki samu. Kafin nan kuma ki cewa yaron da ke neman ki ya turo saboda mu san da gaske ya ke yi. Kin dai ga yanzu shirin auren ƙannen ki a ke yi, zuwa ƙarshen shekara ke ma ayi na ki"

"Ni dama na san dalilin cewa in dawo Kano kenan, ni  Baffa ban san mi na tare ma ka ba. Kanata wani ƙannena-ƙannena, na ga su suka ƙi karatu su ka ce aure za su yi. Ni dana zaɓi karatu na yi kuma na gama ai sai a bar ni na ɗan sha iska kafin a fara maganar aure na"

Ya ma ta daƙuwa ya ce "Uban ki Farida, na ce kin ci ƙaniyar ki. Wato har yanzu ba ki bar rashin kunyar ki ba ko" .

"To Baffa ina zaman zamana a Jos, ka takura Ummi wai ta turoni Kano. Duk abinda na yi ai kai ka ji za ka iya..."

Marfin kwanon silver ya wurga ma ta ta kauce ba shiri. " ki kiyaye ni Farida wallahi zan mummunan saɓa mi ki. Tashi ki bani ware! Ja'ira kawai"

Sum-sum ta tashi ta fice a falon dan ta san ƙarshe zai iya marin ta ko ma ya daketa. Dan Baffa Musa akwai saurin hannu.

..........................

Ba ƙaramin kyau yai ba cikin shirin sa na riga da wando baƙi sai kuma blazer kalar navy blue. Ɗauke da briefcase ɗin sa ya sauko daga stairs ɗin cikin takunsa na girma da ƙasaita.
Ƙai tsaye wajen dining ya je inda iyalen gidan ke cin abinci. Ya sunkuya yaiwa wata budurwa peck a kumatu yana faɗin " good morning baby"

"Morning Big B" ta amsa tana ma sa murmushi

Itama Afrah da ke gefe ta ce " Good morning Yaya"
"Morning" ya faɗa a taƙaice.

Tea ɗin da ke gaban Baby ya ɗan ƙurɓa ya ce " sai na dawo ko"

Wata haɗaɗɗiyar mata da ke zaune opposite da Baby wanda tun saukowar shi idon ta ke kan sa ta ce "have breakfast with us, please"
A dararance ya kalleta ya ce "na gode Justice Nabilah"
Har ya bar falon ba ta dena kallon sa ba, zuciyar ta na ƙuna. Sai yaushe ne ɗan ta zai kira ta da sunan uwa? Sai yaushe alaƙar su zai dawo dai-dai kamar kowace uwa da ɗan ta? Shekaru sun ja amma har yau babu wata chanji tsakanin su.

Baby ta ce"Sorry Mom"
Justice Nabilah ta girgiza kai ta ce " kar ki damu Najdah" ta ƙaƙaro murmushin dole dan jaddada maganar da ta yi.
Ita dai Najdah jikin ta ne yai sanyi, har yau ta kasa gano dalilin ƙiyayyar Yaya Najeeb da Mom, wanda tun tasowar ta haka ta same su.
Tambayar duniyar nan ta yiwa Big B da Mom amma duka babu wanda ya bata gamsashshiyar amsa. Harta Daddy bai san dalilin wannan gabar ba. Tun yana faɗa akan wannan ƙiyayyar  ta su har ya haƙura ya zuba mu su ido...

Tunda ya fita daga gidan kai tsaye wajen motar sa ya wuce. Wanda tuni aka fito ma sa da ita daga parking lot. Sau ɗari zai ɗau driver sau ɗari zai koresu. Shi ya sa yanzu kusan wata uku kenan rabon da ya sake ɗaukan driver. Shi ya ke tuƙa kan sa, ran da yake son yin aiki a cikin mota kafin ya ƙarasa office to zai sa drivern Daddy ya kai shi office.

*Najeeb Adam Jibo*

matashin da ya ke ji da kyau,kuɗi,ilimi da kuma gata. Ɗa namiji guda ga tsohon Ambassador kuma Professor Adam Jibo da Justice Nabilah Al-Jabir.

Adam Usman Jibo ɗan asalin ƙaramar hukumar Kumo ne da ke jahar Gombe, sai dai kasancewar tun rasuwan mahaifinshi ya dawo wajen ƙanin Baban sa da ke Kano da zama ya saka zamansa ya koma Kano. Alhaji Mustafah Jibo babban ɗan kasuwa ne da ya ke da arziƙo tun a wancan  lokacin.

lokacin da Adam ke da shekara bakwai a duniya mahaifin sa ya rasu, dan haka zaman sa da shi da ƙannen sa mata biyu su ka dawo hannun Alhaji Mustafah , lokacin Mustafah da matar sa shekarar su takwas da aure amma basu taɓa haihuwa ba. Sun riƙe Adam da ƙannen sa Ruƙayya da Fatima tamkar 'ya'yan da su ka haifa. Sai da su ka shekara goma sha biyar da aure ba haihuwa sannan Hajiya Mama wanda haka su Adam ke kiranta ta dage akan lallai Alhaji Mustafah ya ƙara aure ko za a dace.

Wata ƙanwar maƙocinsa kuma amininsa ya aura. Budurwace dan a lokacin da aka yi auren su shekararta shashida. Cikin ikon Allah watan Halima goma ta haifi ɗan ta namiji ya ci suna Sulaiman. Murna wajen Alhaji Mustafah ba a magana. Bayan Sulaiman ta haifi Abubakar  sai da ta shekara huɗu kafin ta haifi Aisha wanda lokacin haihuwanta ta wahala sosai, tun lokacin haihuwar kuma ta ke jinya bayan sati uku ta rasu. Mutuwar da ta girgiza iyalen Alhaji Mustafah gaba ɗaya.

Hajiya Mama ba ta haifa ba amma ta ɗauki duka yaran tamkar ita ta haifesu, wanda ko kaɗan ba za  ka taɓa ganin abu ɗaya da zai nuna ma ka ba ita ɗin ta haife su ba. Ba ma kamar Aisha wanda ita ta shayar da ita. Haka yaran su ka taso ba su da wata uwa da ta wuce Hajiya Mama. Kuma har lokacin da Alhaji da Hajiya Maman ba wanda ya banbanta tsakanin yaran  marigayi Usman Jibo da kuma ainihin yaran Alhajin. Sai dai a hankali su ka fahimci Aisha ba ta magana, kurmiya ce. Anyita magani amma shiru, tana ji amma ba ta iya magana. Wannan lalura ta sa da Alhaji da Hajiya Mama su ka maida hankalin su wajen kula da Aisha sosai.

Da Adam ya gama primary school na shi Alhaji Mustafah ya kaishi Lagos karatu. Bayan kammala secondary school na shi a kings college da ke Lagos ya wuce Harvard yai degree ɗin sa a fannin International relation,daga nan ya wuce London Business school yai wani degree ɗin a fannin Business sannan yai masters na shi da Phd a Yale University. Ya fara koyarwa a Yale kafin Nigeria ta tura shi Canada a matsayin Ambassador daga nan aka maida shi USA daga USA sai Belgium daga nan sai South korea wanda daga south korea  ɗin ne yai retire ya dawo Nigeria inda yai zaman shekara ɗaya yana hutawa, gomnati ta mi shi chaaa akan ya shigo siyasa a dama da shi sai dai shi ya fi son koyarwa saboda ya amfanar da mutane  ilimin da ya tara. An awarding na shi professor kuma yana visitin lecturer a jami'o'i da dama a ƙasar, musamman ABU, BUK, UJ, UI da sauran su.

Adam Jibo ya haɗu da Nabilah Aljabir ne a Yale University lokacin yana masters na shi. 'Ya ce ga wani hamshaƙin mai kuɗi Aljabir Al Mukhtarr ɗan asalin ƙasar Bahrain. Soyayya ce mai ƙarfi ta shiga tsakanin su tun haɗuwar su a library. Ba ƙaramin sa'insa aka samu ba kafin aka amince da auren su musamman da ya ke tana balarabiya shi yana bafulatanin Nigeria. Sai dai Nabilah ita kaɗai ce 'ya mace a wajen mahaifinta kuma mahaifinta na son ta sosai. 

Bayan auren su da shekara ɗaya ta haifi Najma wanda sunyi niyyar sawa yaransu sunayen da su ka fara da harafin N da A da J. Harafin N saboda Nabilah, harafin A da J kuma na Adam Jibo.  Bayan shekara uku ta haifi Najeeb wanda daga shi sai da shekaru su ka ja kafin Najdah ta zo duniya, kusan shekara sha uku Najeeb ya bata. Dawowar su Nigeria Nabilah ta yi Pre Law school na wata shida  kasancewar a ƙasar waje ta yi karatu kafin ta yi regular Law school. Ta yi aiki a kotuna da dama kafin daga bisani ta kai matsayin Justice.
Najma ɓangaren likitanci ta karanta tana aiki a National hospital Abuja a matsayin gyneacologist. Tana auren wani hamshaƙin mai kuɗi ɗan kasuwa kuma likita Dr Mujahid, yanzu haka yaran su uku.

Tun kafin Adam Jibo ya dawo Nigeria dama ya riga ya gina wani ƙaton gida a Kano. Anan iyalen sa ke sauka idan sun zo hutu Nigeria. Ƙannen sa sun yi aure suma da nasu iyalin Fatima na aure a Kano yayinda Ruƙayya ke aure a Katsina. Suma ƙannen sa 'ya'yan Alhaji Mustafah sun yi aure da iyalen su. Sulaiman yana Kano yayinda Abubakar ke Abuja. Duk wata su kan haɗu ayi meeting a gidan tsohuwa wato Hajiya Mama. Alhaji Mustafah ya jima da rasuwa tun kafin rasuwan Aisha. Hajiya Mama tana nan a gidan Alhajin sai fama da jikoki. A gefen gidan Alhajin duka Sulaiman da Abubakar su ka yi gininsu. Shi Adam ne gidan sa yai nisa da su. Sai dai shima indai yana gari to kullum sai ya je ya gaida Hajiya Mama wannan ya zamo ma sa al'ada.  Hajiya Mama ita ya sani a matsayin uwa. Goggon su ta jima da rasuwa bayan rasuwar Mahaifin su ta sake wani auren a Ashaka inda wajen haihuwa ta rasu.  Haƙiƙa Hajiya Mama uwa ce ta gari. Ba ta haifi nata ba amma ta riƙe yaran mijinta tsakani da Allah wanda har yau suna darajata. Inda ace ta ha'ince su da tuni sun watsar da kashinta musamman bayan da Alhaji Mustafah ya rasu.

Duka karatun Najeeb a ƙasar waje ya yi su. To dama a ƙasar wajen aka haife shi. Yai degree na shi na farko a MIT (Messacheusettes Institute of Technology ) inda ya karanchi Engineering and Technology daga nan ya sake wani degree ɗin a ɓangaren Architecture. A London yai Masters na shi kafin ya tafi Korea yai Phd na shi.
Ya fara aiki a Korea da wani construction company kafin ya ajiye aikin ya je yai wani course a India, lokacin Mahaifinsa Professor Adam Jibo ya dawo Nigeria da zama. Bayan ya ƙare course ɗin ne ya dawo Nigeria ya buɗe Kamfanin sa mai suna *Najeeb constructions* shekaru bakwai da su ka wuce kenan.

Ya taso cikin kuɗi kuma ya nemi kuɗi ya samu. A shekarun sa talatin da huɗu, ba abinda ke gaban sa da ya wuce kamfanin sa. Zai iyayin komai saboda samun ɗaukakar kamfanin sa.

Anas shi ne babban aminin sa, jinin su ya haɗu sosai duk da kuwa Najeeb ya girmeshi da shekara uku, amintar su ta sa lokacin da ya buɗe kafanin sa ya jawo shi gefen sa  su ka haɗu su ka ɗaukaka kamfanin saboda shima Architect ne. Bayan Daddy da Najdah wanda ya ke kira Baby to Anas shi ne mutum mafi kusa gareshi idan ka ɗauke Hajiya Mama. Sun jima da baran-baran da yayarsa Najma a kan ƙin Mahaifiyar su daya ke yi wanda har yau babu wanda ya san dalili abu kusan shekaru ishirin kenan.*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Free page*

0️⃣0️⃣3️⃣

Kamar kowani lokaci idan ta zo Kano ɗakin Inna ta ke kwana, wannan karan ma hakan ce ta faru, sai dai yanzu Maijiddah da Zainab ke kwana a ɗakin bayan rasuwar Inna. Daga zuwan Farida ta kori Zainab a ɗakin tace ba za su kwana su uku ba. Zainab ta fice daga ɗakin tana ƙuƙuni.

Maijiddah 'yar Baaba Sabuwa ce, kuma duk cikin yaran gidan tafi su hankali, kasancewa anyi auren ƙannenta biyu gashi za'ayi wasu biyun ya sa ake goranta mata rashin miji, kullum a takure take, dududu shekarar ta ishirin amma yadda ake mata gori a gidan ka ɗauka ta shekara talatin ne ba tayi aureba. Wai har 'yar Zainab da ke shekara shahuɗu tanada samari ita ba ta da kowa. Duk masu zuwa wajenta ba sa jimawa su ke guduwa. Islamiyya kaɗai ta ke zuwa yanzu, sai kuma takan taɓa ɗinki a keken Baabarta sannan tana sana'ar kitso. Dan wani lokaci har gida ake zuwa a kirata ta je ta yi kitso, domin gaskiya Allah ya bata baiwar iya kitso.

Shekarar ta uku da gama secondary, dokar Baffa Musa ce, sai dai mace ta yi karatun gaba da secondary a gidan mijinta amma ba a gidan shi ba, shi ya sa Maijiddah ba ta yi wani hoɓɓasa domin ta cigaba da karatu ba, saidai cikin ran ta tana ƙwaɗayin hakan. Ba wai muni gareta ba tana da kyau dai-dai gwargwado sai dai gaskiya guntuwa ce. Dan harta Zainab da bata gama tsayinta ba, ta fita tsayi.
Maijiddah tafi ganin gajartar da Allah ya mata a  dalilan da ya sa ta rasa manema...

Suna sallar Asuba Maijiddah ta gaida Farida sannan ta fara gyara ɗakin su har lokacin Farida na yin azkar. Da ta gama ta fita dan ta fara hidiman cikin gida. Lokacin da Farida ta fito daga ɗaki Maijiddah kaɗai ta samu a tsakar gida tana shara.  Cikin isa ta riƙe ƙugu tace " Jiddah ina batun dokokin dana sa a gidan nan wancan zuwana Kano?"

"Anty Farida kin san yau Lahdi ne ba a tashi da wuri"

Murya sama-sama ta fara magana. " Tab! wato dan bana gidan shine aka watsar da dokokina ko. To ku sani Wallahi duk wanda ya san yau ranan aikinsa ne bai fito ba ganinan zuwa har ɗakin uwarsa in dakeshi kuma ba abinda zai faru. Zan irga uku ɗaya....biyu...." sai ga yaran suna fitowa daga ɗakunan su da gudu. Da ke sun manta tsarin da ta musu, kowa sai ya fito dan kar ya zama ranar sa ce kuma bai fito ba ta bishi ɗaki ta zane. Ba yau Farida ta fara zane yaran gidan ba, yanzu haka yadda su ke tsoronta ko su Yaya Yakubu iya kaci.

Maijiddah ta ɗan yi murmushi lokacin da ta ga ƙannen nata na fitowa da gudu.

...............................

Ba tareda ya ɗago ya kalli Joseph ba ya ce " three days" Joseph ya haɗiyi yawu moƙot saboda ba shi da ta cewa, amma taya kwana uku zai ishesa ya je Enugu burial na Maman sa ya dawo a kwana uku, bayan Enugun ma chan cikin wani ƙauye mai nisa su ke. 

"Anything else?" Muryar Najeeb ta dawo da shi daga tunanin da ya ke. Joseph ya girgiza kai da sauri ya ce "no sir". Da hannu Najeeb ya ma sa nuni da yai waje. Joseph ya bar office ɗin da sauri...

Tare su ka fita da Anas, sunje sun duba wani site da kamfanin su ke ginawa. A hanyar su ta dawowa Anas ya nuna yunwa ya ke ji dan haka dole su ka tsaya a wani restaurant da ke kusa.

Fiskar san nan tamau ta ke kamar bai taɓa dariya ba a tarihin rayuwar sa. A haka su ka shiga wajen cin abincin, shi idan ba dan Anas ba ba abinda zai sa ya tsaya a irin wannan waje. The restaurant is not even classy.

Sai da su ka zauna waiter ya zo dan ya ƙarɓi order ɗin su. Da sanin Najeeb ya faɗi wani kalar girki wanda baya cikin menu ɗin su. Saurayin ya ɗan  tausasa murya ya ce "sorry sir, we dont have that in our menu"

Najeeb ya smirking ya ce " then, water will be fine"

Har zai tafi Anas ya tsayar da shi ya ce ya kawo wa Najeeb irin abinda ya ordering.

"Seriously!" Najeeb ya faɗi yana ɗan girgiza kai.

"Mutumina kai fa ba engine ba ne, tun safe fa ba abinda ka ci. Gara ni naci ɗumame na ƙoshi kafin na fito, amma kai na san bayan tea ba abinda ka sa a baki"

"Did i complain?"

"Idan kai ba za kula da kan ka ba, i'll help you do that"

Kafin a kawo abincin wayar Anas ta yi ringing ganin mai kiran ya sa ya ce da Najeeb yana zuwa. Fita yai daga wajen don ya samu daman magana sosai.

Wata budurwa da saurayi su ka shigo wajen cin abincin . Hankalin Najeeb na kan wayar sa dan haka bai lura da su ba, sai dai  table ɗin da ke kusa da na su su ka zauna,  da ke budurwar ce ta bashi baya dan haka bai ga fiskarta ba sai dai ya ga na saurayin lokacin da ya ɗago zai ɗau ruwan da waiter ya ajiye mishi.

Surutun da budurwar ke yi ya sa ya ƙara tsanar wajen saboda hayaniya da ta cika shi. Tukunnama, ta ya mace za ta dinga surutu haka in a public place kamar wannan. Tun da su ka shigo siririn muryanta ya gauraye wajen. Kafin saurayin da su ka shigo tare  yai magana ɗaya budurwar ta yi ɗari. A haka Anas ya shigo ya same shi, su na fara cin abincin Najeeb yai tsaki ya aje fork da sokali sannan ya ɗau tissue ya goge bakin sa.

"Abincin bai ma ka ba ko?" Anas ya tambaya yana kallon sa. Najeeb ya ɗau ruwa ya kora batareda ya bawa Anas amsa ba. Tsakani da Allah ba wai  abincinne bai ma sa ba, ba kuma yunwanne ba ya ji ba. Sai dai surutun wannan budurwane ya cika ma sa kunne. A rayuwarsa ya tsani hayaniya balle kuma yawar magana.
Kamar Anas ya gane damuwarsa ya ce a hankali "wannan yarinya ba dai surutu ba. Kamar radio"

Najeeb ya cigaba da danna wayarsa ba tareda ya ce komai ba...

..........

"Ka san Allah,  idan na yi wata ɗaya a garinkun nan toyewa zan yi. Irin wannan zafi haka!. Da wayona Ray ban taɓa fin sati uku a Kano ba, ina ma zan iya"

Farida ta faɗi tana kora ruwa amaƙoshinta saboda tunda su ka zauna ta ke ta zuba surutu.

Rayyan ya ce "gashi ɗan Kano za ki aura ba"

"Ai ka ji inda matsalar ta ke, ina ga fa sai dai kai ka dinga zuwa Jos, dan ba zan tare a Kano ba. Tukunna Ray, wai a garin nan ka taso cikin wannan zafin?"

Rayyan ya langwaɓe kai dan wannan tambayar kusan karo na uku kenan da za ta yi shi a ɗan zaman su a wajen nan.

" My Farida mu ci abincin nan, zai yi sanyi fa"

A hankali ta fara tauna jollof rice ɗin wanda ko loma uku ba ta kai ba ta ajiye cokali. Ta yiwa wani waiter hannu akan ya zo.

Rayyan ya ma ta kallon mi ke faruwa amma ta kauda kan ta ta yi kamar ba ta gani ba.

"Waye ya girka abincin nan?" Tambayar da ta yiwa waiter kenan.

"Any problem ma'am?" Ya tambaya with politeness.

Farida ta kalli abincin ta kalle shi sannan ta ce "abincin ku shine problem ɗin ai. Na san wadda ta girka abincin nan ko tantama babu Bayarabiya ce. Idan ba haka ba taya za'a yi jollof rice a restaurant kuma a cika ma sa yaji. An gaya mu ku kowa ne ke son yaji? ko kuma dai so ku ke mutum ya ci ya koma gida yana gudawa. Da a garin da ba zafi ne sai ace ya yi dai-dai amma wannan Kanon na ku da shegen zafi kuma ku dafa abinci mai yaji kuna ba wa mutane. Mi ku ke nufi?"

Waiter ɗin bai gama fahimtar maganar Farida ba, saboda ba wani hausan kirki ya iya ba. Shekaran sa na uku kenan a Kano. Ya dai gane kalmar 'Yaji' dan haka ya ce " ma'am with due respect, i dont think the food is pepperish"

Farida ta hangame baki " Yo  ƙarya na ke yi kenan?"

"Sorry ma'am"

Rayyan ya girgiza kai ransa a ɗan ɓace ya ce " Farida dan Allah ki barshi haka, bari a kawo mi ki fried rice"

"A'a Ray, sai ya taɓa abincin nan ya ji dan ya tabbatar da magana ta"

Wani matashi wanda tun shigowar su Farida ya ke ankare da yadda ta cika wajen da surutu ya taso ganin dramar da ake yi.

"Haba Madam. Tun ɗazu ki ke damun mutane da surutu fa, kar ki manta nan public place ne"

Kallon sama da ƙasa ta ma sa sannan ta ce " Malam sa'ido,gulma da munafurci. Kunnen ka bai jiyo surutun da ke fitowa daga TV ba sai nawa. Tsabar ha'inci ka bar matarka da cin garau-garau , ka zo ka tisa tumbinka a gaba kana cin fried rice da chicken, Allah wadai"

Kunyar da Rayyan ya ji ko wanda aka yiwa maganar bai ji ta ba. A ƙalla mutumin nan zai kai shekara Arba'in, amma Farida ba ta ga girman sa ba ta ke yaɓa ma sa magana.

Mutumin ya zuba ido yana kallon ta kawai tsabar mamaki.

"Kalleni da kyau Malam na fi ƙarfin ka, inma kana ƙungiyar mafiya ne to jinina fau-fau ya fi ƙarfin ka"

Mutumin ya kalli Rayyan ya ce "ɗan uwa gaskiya kana ƙoƙari. This girl is fire" sannan ya koma table ɗin sa.

Ta ce "Ba fire ba Volcano. Mtsww"

Ta kalli waiter ta ce "taste this food before i loose my temper"

Da sauri ya ɗau sokali ya ɗeba abincin ya taɓa. Irin masifan da ta yiwa mutumin nan wai ta ce ba ta loosing temper ba to idan ta yi ya za ta zama kenan.

Tabbas abincin ya ɗan fito da taste ɗin yaji amma bai kai har yadda Farida ta kururuta ba.

"Sorry ma'am, i apologise on behalf of our kitchen...."

Lokaci guda Najeeb ya miƙe tsaye hakan ya bashi damar ganin fiskar budurwar wanda alokacin ke yiwa waiter bayanin abinda zai kawo ma ta a madadin jollof rice mai yaji da su ka kawo. A yadda ta ke masifa ya ɗauka zai ganta gabjejiya sai ya ganta 'yar mitsila bai fi mutum ya mangajeta ba amma sai shegen baki. Kallo ɗaya ya ma ta ya ɗauke idon sa ya fice daga restaurant ɗin.
A mota ya jira Anas wanda shi kam sai da ya ci yai naƙ sannan ya fito.

"Mutumina ka san yarinyar nan ta bi waiter har kitchen ɗin su. Na ji tausayin saurayinta wallahi,  haka yai wani lafau da shi abin tausayi"

Najeeb ya ce " its his fault ai,  ta ya zai dating lousy girl kamar wannan"

"Yarinyar tana da kyau ba laifi, sai dai surutu kam Tabarakallah ko gidan radio iya ka ci" ...

Rayyan da Farida kuwa ba su suka bar restaurant ɗin ba sai da Farida ta sauke masifar ta ta huce. Shi Rayyan abincin ma kasa ci yai, ita kuwa aka kawo ma ta fried rice ta naɗa harda take away ta yi.

....................

"Gaskiya Yaks idan na ce ma ka akwai vacancy a ƙasa na yi ƙarya, sai dai ka bani lokaci nan zuwa next week zan bincika, idan ma ba ta samu anan ba zan iya nema ma ta a wani wajen. Ai ƙanwar mu ba za ta rasa aiki ba Insha Allah"

Yakubu yai ma sa godiya sannan ya fice daga office ɗin.
Anas kenan, yana da sauƙin kai ba kaman Oga kwata-kwata ba, wanda mulki da girman kai ya hanashi sakewa da mutane. A shekarun sa na uku da fara aiki a Najeeb constructions sun saba da Anas sosai, tamkar  yayansa haka ya ɗauke shi...

Anas na tattara wa su files kiran Najeeb ya shigo wayar sa, dama files ɗin wajen Najeeb zai kai su dan haka ya amsa wayan da sauri dan ya san abokin na sa da gajen haƙuri.

"Mr Man yanzu na ke shirin kawo ma ka files ɗin"

Cikin huci Najeeb ya ce " Anas ka san that stupid boy bai zo ba, and numbar sa ba ta shiga. Find a replacement, ba zan iya da shi ba"

"Calm down Yallaɓai, barin zo office ɗin sai mu yi maganar...

Duk yadda Anas ya so Najeeb ya ƙarawa Joseph lokaci hakan bai yiwu ba, ƙarshe dai cewa yai ya nemo ma sa wani ko wata.

"Gaskiya you need to change abokina, this guy is good, and kai ma tsakani da Allah ka san kwana ukun da ka bashi ya yi ma sa kaɗan"

"I dont bloody care. Zaman shi a chan ba zai dawo da wanda ya mutu ba neither will it profit him in anyway. So why will he risk his job for that"

"It's his mother's burial, kuma kasan al'adun su da namu ba ɗaya bane"

"And so freeking what?. Just ka nemo wani kawai"

Anas ya kalli abokin na sa cike da takaici ya ce " ba kowa ke da mummunan ra'ayi irin taka ba Najeeb, just because ba ka ɗauki mahaifiyar ka a bakin komai ba doesnt mean kowa ma haka ya ke. Joseph yana son mahaifiyar sa, shiya sa ya tsaya yaiwa mahaifiyar sa proper burial kaman yadda al'adar su ta tanada. I hope you understand that"

"Oh please Anas! Not this talk again"

"Ka na so, ba ka so, gaskiya ce dole na faɗa ma ka duk min ɗacin ta kuwa"

"Find another secretary for me Arch Anas Ali Almustafah"

Kallon-kallo su ka yiwa junan su kafin Anas ya fice daga office ɗin.*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Free page*

0️⃣0️⃣4️⃣


Ranan Tuesday sai ga Joseph ya zo office, ya sani sarai Najeeb zai yi fushi da shi amma bai ɗauka abin zai kai ga kora ba. Infact, irin koran walaƙancin da Najeeb ya ma sa sai da yai dana sanin fara aiki da Najeeb. Tun farkon zuwan sa kamfanin ya samu labarin halin maigidan na sa a wajen sauran ma'aikata, sai dai bai ɗauka  abin na sa ya kai yadda ake faɗi ba sai da ya gani muraratan.

Anas dai ba yadda ya iya ne amma ran sa ya sosu da abinda Najeeb yai wa Joseph.

"Sir, he gave me 3 days, only 3days. I left Kano on tuesday morning, i reached my village on wednesday. My mother was buried on saturday and i make sure i squeezed myself and came back to Kano on Monday night. But he wont listen"

Joseph ya faɗi yana goge hawaye. Shi takaicin sa ma bai wuci yadda Najeeb ya nuna halin ko in kula da mutuwar mahaifiyar sa ba.

Anas ya kalle shi ya ce "please dont take it personal, Najeeb doesnt even respect his own mother. I'm sorry about your loss Joseph, i lost my mother when i was only 7yrs so i know how you feel"

Kalaman Anas su suka kwantarwa Joseph hankali har ya ƙarɓi check ɗin da Anas ya bashi sannan ya tafi...

.....................

Ido Yakubu ya zaro lokacin da Anas ya gaya ma sa akwai vacancy na ɓangaren secretary ɗin Najeeb.

Indai kana aiki da Najeeb Constructions to dole ne ka san halin Najeeb balle kuma jiya-jiya Najeeb ya gama koran Joseph wanda harda kira ma sa security su fita da shi, ba dan Anas ya sa baki ba Allah kaɗai ya san halin da  Joseph zai shiga.

"Kana tsoron kar a walaƙanta ƙanwarka ko?" Anas ya jefa ma sa tambaya

"Na ma ka alkawari zan yi ƙoƙari na ga ƙanwarka ba ta walaƙanta ba, za tai aiki da Najeeb na lokaci kaɗan ne ana samun wani vacancy ɗin zan chanja ma ta aiki"

Yakubu ya sauke ajiyar zuciya ya ce " Aikin Farida da Sir Najeeb ba mai yiwuwa bane, idan Farida ba ta ƙona shi ba to shi zai murɗe ma ta wuya ya kasheta. Ka san Farida kuwa? Ai Najeeb da Farida su ka haɗu anan kamfanin inaga ƙonewa kawai zai yi dan wuta da wuta ne"

Dariya Anas yai ya ce " har akwai yarinyar da za ta iya karawa da Najeeb? Gaskiya zan so ganin wannan Faridan"

"Hmm, na san halin Sir Najeeb na kuma  san 'yar uwata Farida, amma wallahi duk inda Sir Najeeb ya kai da jin kai da miskilanci to Farida ta taka shi. Maganar ta zama Sakatariyar sa ma bai taso ba. Farida Farida Hmm..."

"Wallahi ni kuma da ka yi bayanin nan sai na ga sun dace gara a samu wacce za ta iya taka ma sa birki ko zamu huta da halin san nan"

"Allah akwai matsala idan Farida ta yi aiki da Sir Najeeb, yaƙi za'ayi fa a kamfanin nan"

"Kar ka damu mutumina, ka turo ta kawai na ma ta interview"

...........................

Ɓangaren turaruka ya nufa a Mall ɗin saboda favourite perfume na shi ya kusa ƙarewa. Kamar daga sama ya fara jin muryan ta, kamar ranan da ya fara ji yau ma masifa ta ke yi. Zuciyar sa ce ta raya ma sa ba ita bace amma kunnensa ya ƙaryata hakan, domin kuwa muryar sak da wadda ya ji ranan a restaurant. Yana so ya maida hankalinsa kan abinda ya ke dubawa amma kuma idanuwan sa na ƙwaɗayin gaskata abinda ya ke ji, shin yarinyar ranan ce? ko kuwa wata ce mai irin muryarta.
Kasa daurewa yai sai daya juya ya maida dubansa ga inda ya ke jiyo muryan. Ita ɗince dai, 'yar mitsilar yarinya mai shegen surutun nan. Ya kai duban sa ga wanda ta ke wa masifan ya ga ba saurayin ranan bane wani ne daban, haka kawai ya ji tsanar yarinyar dama ma su irin halinta kam ina za su iya kama kai.

He couldn't believe it, garin kallonta sai ga shi har turaren da ya ɗauka yana shirin faɗuwa daga  hannunsa. Yai saurin taro turaren tareda sake murmushi saboda wautar da yai, garin gulma. Abin haushin ma ba wai ya san yarinyar bane amma kuma gashi halayyarta ya dameshi. Ya saurin kauda kan sa lokacin da su ka zo za su wuce shi, tana tafiya tana surutu, kafaɗarta ya ɗan gogi bayansa kaɗan, yai saurin juyowa ya bi bayanta da kallo amma she's too busy talking to even notice what happened.

"Lousy girl" ya faɗi a fili sannan ya ɗau turaren ya bar wajen...

"Ni wallahi da na san ɗan abinda za mu saya kenan da ban biyoka ba Yaya Faruƙ. Duk abinda mu ka ɗauka ka ce yai tsada. Dama ai abu mai kyau shi ake siya da tsada"

"Wallahi mijin ki ya shiga uku Farida, ke fa ki ka ce mu zo nan ba ni ba. In ba dan ke ba mi zai sa na zo siyayya a nan"

"Amma Yaya ai ba ka cemin ba ka da kuɗi ba ko!"

"Allah ya shiryeki dai"

Har su ka bar Mall ɗin ba ta dena complain ba, dama wasu kaya ne Yaya Faruƙ zai siya na bikin ƙannen sa.  Ƙarshe dai daga Mall ɗin kasuwa su ka wuce...

......................

Ana zaune ana duba kayan da su Faridan su ka siyo Maijiddah ta shigo tsakar gidan da sallama, dawowarta kenan daga yiwa Hajiya Yelwa kitso. Kai tsaye ɗaki ta nufa bayan ta gaishe su.
"Ke Jiddah zo nan" Farida ta kirata.
Ba mu su ta dawo ta tsugunna gefen Faridan ta ce "gani Anty"

"Kina gani kowa yana duba kaya yana sa albarka ke za ki tsallake ki shige ciki"

"Lah Anty zan cire hijabi ne na wanke hannuna sai na fito"

Zainab ta ce " ba wani, baƙin ciki ta ke ba nata kayan bane"

Farida ta wurga mata wani awarwaro wanda ya doki hancinta maimakon bakinta da Faridan ta yi niyya.

"Zan ci Ubanki agidan nan, sa'arki ce da zaki dinga yaɓa ma ta magana son ran ki. Na ce sa'arki ce!" Ta daka ma ta tsawa.

Anty Hanne wanda ita ce ta biyu a matan Baffa Musa kuma Umman Zainab ta ce " Yo ba gaskiya ta faɗa ba. Anyi auren ƙannenta biyu yanzu za a sake wasu biyun. Ai abin kunya ne ace ko mashinshini ba ta da shi"

"Da kyau, dama Zainab ai daga nono ta sha. To barin gaya mu ku, tafi ƙarfin tayi baƙin ciki da bikin ƙannenta saboda duk cikin su ba wanda yake auren mijinta. Na ta mijin na nan zuwa, za ku ganshi handsome gentleman da shi"

Hajara ta ce " waya ga handsome mijin shortie"  gaba ɗaya sai aka sa dariya banda 'yan ɗakin su Maijiddan wanda su ke tausayinta. Maijiddah ta fashe da kuka ta tashi za ta bar wajen Farida ta riƙe hannunta ta ce " ba inda za ki je. Ki tsaya ki kalli kowacce ido cikin ido ki maida mata martani daidai da ita"

"Anty Farida gaskiya su ka faɗa, na yi kwantai"

"Ji mim shirme, inba dan ke da su ɗin duk 'yan ƙauye bane dan kina 20yrs ba ki yi aure ba shine kin yi kwantai. Tukunnama ke za ki aurar da kan ki ne? Ko mijin ya zo kin ce bakya so"

Ta kalli Hajara da ke dariya ta ce " ke kuma fantsararriya, za ai aurenki at 16yrs ba abinda ki ke hangowa sai kwanciyar aure saboda abinda ki ka sani kenan. Gaya min me ki ka iya? Wacce sana'ar ki ka iya? Jakar banza kawai, yanzu haka wankar tsarki mai kyau ba ki iyaba, tun tasowar ki ke daƙiƙiya ce,  shiyasa ko jarrabawar WAEC ma ki ka ce ba za ki rubuta ba. Har mijin da za ki aura abin alfahari ne, ina shi ma wani tunkuzan ne kamar ki, ba ilimin Arabi bare boko"

"A hakan dai auren za ta yi, ta fi wasu da maneman ma ba ta da su" Anty Hanne ta faɗi tana hararan Farida

"Wallahi Jiddah ta fi ƙarfin ta auri miji kaman Haladu, mi za tai da irin su Haladu ai shi kam sai jaka irin Hajara. Mijin Jiddah ɗan gayu kuma mai ilimi ne Insha Allah"

Tuni wajen ya kaure da hayaniya, Baaba Sabuwa dama tuni ta shige ɗaki saboda takaici, ita ɗin kanta ba daɗin ganin Maijiddah ta ke agidan ba. Anyi auren ƙanwarta Murja duk da kuwa tsakaninta da Murjan shekara ɗaya ne to yanzu ga Salima ma za ayi na ta amma ita shiru. Tana jin hayaniyar su amma ko leƙowa ba ta yi ba.
Farida kam duk ta inda aka ɓullo kare Maijiddah ta ke ta hanata tafiya kuma ta hanata kuka. Ƙarshe dai sai gajiya su ka yi su ka barta dan indai wajen ɗasa magana ne to Farida ta kere su...

Da dare da za su kwanta Farida ta sa Maijiddah a gaba da masifa.

"Ke sai ana magana ki fara kuka, ba dole su raina ki ba. Ai su na magana ki na magana, wanda ya gaji ya bari. Tukunna ma ke idan za ki fita sai ki dinga saka dogin hijabai kamar matan Malam, a haka kam ai ko mutum zai tsaida ke a hanya ma zai ɗauka ke matar aure ce ya fasa"

" Lah na saba ne ai"

"A wannan zafin, to kul,  kisa ɗan dai-dai amma banda dogin nan, idan ba haka ba zan sa almakashi na rage mi ki tsayin su"

"Kai Anty"

"I'm serious"
Maijiddah ta sa dariya...

Washe gari da sassafe Farida ta shirya za ta bi Yakubu wajen aiki saboda interview da ya ce za a ma ta yau. Sai da za ta fito daga ɗaki taga Maijiddah na shiryawa itama da alama fitan za tai,

" 'Yan mata ina zuwa da sassafe haka"

" Hajiya Yelwa ce ta kirani wai dan Allah na zo na yiwa jikokinta kitso yau za su tafi"

"Ba za dai ki gyara ba ko"

"Mi na yi Anty?"

"Jiya mi na gaya mi ki?"

"Kayya Anty"

Farida ta je ta binciko ma ta wani hijabi cikin kayanta wanda bai da tsayi ta miƙa ma ta. "Sa ka wannan"

"Anty da kin barshi, skirt ɗin da na sa fa ya ɗan kama ni"

"Saka!"

Ba mu su ta amsa hijabin ta saka, da ke ita ɗin guntuwa ce ya kusa kai ma ta gwiwa.

Haka su ka jero su ka fito, ɗakin Baaba Sabuwa kawai    su ka shiga su ka gaisheta sannan su ka fita...


..............................

A office ɗin su Yakubu ta zauna wanda shi da colleage ɗin sa Engr Mathew su ke sharing. Tun a office ɗin ta dinga sa Mathew dariya da surutunta. Ƙarfe tara da rabi Yakubu ya dawo office ɗin ya ce Farida ta biyoshi. Kai tsaye office ɗin Anas su ka je. Da sallama su ka shiga office ɗin lokacin Anas na duba wasu takardu. Ɗagowar da zai yi ya ga yarinyar ranan, ta ke murmushi ya suɓuce ma sa cikin ransa yana ayyana abubuwa dayawa.

"Bismillah zauna" ya faɗi yana nuna ma ta kujera.

Yakubu ya ce " sir ni zan wuce office"

" Ok Yaks"
Sai da Yakubu ya fita sannan ya kalli Farida ya ce " Aisha Farida Salihu right?"

"No" ta faɗi tana kallon cikin idon sa.

"No kuma, ba sunan ki kenan ba" ya faɗi da mamaki

"To yallaɓai ka ga takarduna ka ga sunan da ke jiki kuma sai ka sake tambaya"

"Hmmm. Well na ga takardun ki kuma ba laifi i'm impressed. Sai dai aikin da za ki yi babban aiki ne kuma aiki ne da sai kin yi haƙuri sosai"

"Rayuwar duniya kanta sai da hakuri, balle aiki a ƙarƙashin wani" ta amsa tana kallon laptop ɗin da ke gaban Anas

"Da alama dai Yaks bai yi ƙarya ba gameda yarinyar nan, tabbas za a sha kallo tsakaninta da Najeeb" abinda Anas ya faɗi a zuciyarsa kenan. A fili kuma ya ce

"Malama Aisha, kasancewa muna buƙatan Secretary da sauri so gobe za ki fara aiki. Kafin nan zamuje ki ga office ɗin ki sannan zan nuna mi ki yadda za ki dinga gudanar da ayyukan ki"

"Abin da sauri-sauri haka?" Ta tambaya

"Ko ba za ki iya ba ne?"

"Kana ganin Ogan ka zai iya korana ne? Dan ance mini abu ƙiris mutum zai yi ya koreshi"

" I see, ashe kinada labarin  wanda za ki yi aiki a ƙarƙashinsa. Kin san ba ya ɗaukan raini, Malama Aisha"

Farida ta ɗan yi murmushi ta ce "ni kuma banda mutunci ba, ga rashin haƙuri kamar zawo"

Anas yai murmushi sannan ya miƙe ya ce " welcome to Najeeb constructions miss Aisha Farida"

"Thank you" ta faɗi tareda miƙewa itama...

Ta yi mamakin ganin girman wajen da aka nuna ma ta a matsayin office ɗinta, cikin ranta tana ayyana irin shagalin da za ta yi a wannan waje, ga ƙaramar fridge ga AC, kai  aiki cikin jin daɗi haka.

"Ehmm, Ogan ki bai ƙaraso ba tukunna so zuwa gobe idan kin fito za ki ganshi. Ba sai an nuna mi ki shi ba kina ganin sa za ki ganeshi" maganar Anas ya dawo da ita daga tunanin da takeyi.

"Ba matsala Sir Anas"

Anas ya ce " Kira ni da Anas ɗin kawai ai ke ƙanwar mu ce"

"Rufa min asiri, rashin kunyata ba ta kai nan ba. Kai fa sa'an Yaya Faruƙ ɗin mu ne"

"To kirani da Yaya kawai kinga dama ba ni da ƙanwa mace"

"Na gode Ya Anas"...

Ba su shiga office ɗin Najeeb ba haka su ka fito. Ya ƙara ma ta wasu bayanai gameda aikin, sannan ya ba ta takardar shaidar ɗaukanta aiki. Sai da ta biya office ɗin Yakubu sannan ta wuce gida.

Anas kuwa Farida na fita daga office ɗin sa ya ɗau waya ya kira Najeeb. A take ya sanar ma sa an samu sakatariya kuma gobe za ta fara aiki.

"she better be good" abinda Najeeb ya faɗa kenan.

Anas ya ce " ai mutumina sai ka ganta kawai. Wannan karan kai da chanja Secretary sai dai in ita ce ta ajiye aikin"...

Sai da Najeeb ya tsaya har Hajiya Mama ta gama ganin likita sannan ya maida ta gida. Da zai tafi kamar kullum sai da ta tsokale shi 

"A dawo lafiya tuzuru"

"Ke fa tsohuwar nan kinada matsala" ya faɗi yana ɗan hararanta

"Matsala ta ɗaya ce, kai aure ka ajiye iyali kamar kowa. Ko sai ka gama tsohewa kafin kai auren"

"Ke zan aura ai, zan ɗau ragowar Alhaji Mustafah"

"Allah ya jiƙan rai, ai shi bai fi rabin shekarunka ba ya ajiyeni a gidan sa"

"Tsohuwa na tafi, kar ki riƙeni da surutu"

"Allah ya bada sa'a tuzuru"

Girgiza kai kawai yai sannan ya fice daga falon. Idan da sabo ya saba da tsokalar kakar ta sa, wanda da ita ya ke sakewa yai walwala kamar mahaifiyar sa. Kulawar da bai nunawa mahaifiyar sa ba a Hajiya Mama ya ke ba wa...*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Free page*

0️⃣0️⃣5️⃣

Daga Najeeb constructions kai tsaye gida Farida ta wuce, ba ta samu Maijiddah a gida ba dan haka kaya ta chanja su ka wuce kasuwa da ƙanwar Maijiddan, amarya Salima. Da ke ita ɗin tafi Hajara mutunci shiyasa ta su ta ɗan zo ɗaya da Farida, duk da ba ta kai Maijiddah kirki ba inji Faridan.

Ɓangaren Maijiddah kuwa da ta je ta samu jikokin Hajiya Yelwa suna karyawa dan haka sai da ta jira su ka gama sannan ta mu su kitson, da ke ba wannan ne karan  farko da ta ke mu su kitso ba, su na yi su na hira. Yawanci in sun zo hutu wajen Hajiya Yelwa to ita ke mu su kitso.

Ta tsantsara mu su kitso mai kyau harda adon beads. Dama ga yaran 'yan gayu da su. A Lagos su ke da zama ko hausan kirki ba sa ji. Maryam da su ke kira da Baby saboda sunan Hajiya Yelwa da ta ci 'yar shekara bakwai ce, sai ƙaramar Alizah 'yar shekara huɗu.

Maijiddah ta na zaune a ɗakin Hajiya Yelwa tana jiran ta, ta riga ta gama yiwa yaran kitso tun ɗazu amma Hajiyar ba ta nan, ta ce kuma ta jira ta har ta dawo.
Tana zaune kan carpet tana danna ƙaramar wayarta ƙirar Tecno wanda ya ji jiki ya tsufa. Tun wanda Yaya Faruƙ ya siya ma ta ne lokacin da ta yi sauka shekara huɗu da su ka wuce.
Ba ta ankara ba ta ji shigowar Alizah ɗakin da gudu. Ɗago idon da za ta yi ta ga ƙatuwar kyanwa ta yo kanta, ƙwalla ƙara ta yi ta hau gadon Hajiya Yelwa da sauri, ai kuwa kyanwar ma kawai sai ta hau gadon da alama kyanwar gudun Alizah ta ke. Maijiddah ba shiri ta dira a gadon ta nufi ƙofa da gudu. Ɗaga labulen da zai yi yai karo da ita, da ke guntuwa ce kanta ya tsaya ma sa iya ƙirjinsa. Ƙoƙarin  tureshi ta ke ta wuce dai dai nan kyanwar ta shuri ƙafarta ta fice daga ɗakin. Laushin jikin kyanwar da ya taɓa ƙafarta  ya sa Maijiddah ta yi suman tsaye a wajen.
Alizah ta fara cewa " Daddy, please catch the cat for me"

Bai saurari yarinyar ba, ya ɗauki Maijiddah cak yai kan gadon Hajiya Yelwa da ita.  Miƙar da ita yai sosai sannan ya cire ma ta hijabi dan ta samu iska ya shigeta sosai, Ƙaramin fridge da ke ɗakin ya buɗe ya ɗau goran ruwa mai sanyi.  Ya zuba ruwan a hannunsa ya shafa ma ta a goshinta da wuyanta amma still ba ta farfaɗoba. Ya sake yin haka a karo na biyu wanda yana shafa wuyanta da ruwan sanyin ta jaa dogon numfashi ta buɗe ido, ta fara ƙoƙarin tashi dan ta zauna, ya sa hannu ya  tallafa ma ta tareda faɗin "relax"
Sai alokacin ta fara wuri-wuri da ido saboda ganin ba hijabi ajikinta ɗankwalin kanta ma ya zame.
"Duk a dalilin kyanwa ki ke son hallaka kan ki. Miye abin gudu a jikin kyanwa?"

Ba ta bashi amsa ba sai ma ta sunne kanta cikin  cinyoyinta. Ƙananun ƙitson kalaba (braids) da ta yi su ka zubo.

Ganin yadda gashin ke da tsantsi ya sa shi taɓawa dan ya tabbatar gashin kanta ne ba na aro ba (wig). Yana son mace mai gashi, haka nan ya tsani mace ta ƙara gashi abinda har yau matarsa Aneesah ba ta dena sawa ba kenan tun yana faɗan har ya gaji.
Tabbas gashin ta ne ya faɗi a ransa. Ga shi baƙi ga tsawo ga tsantsi.

Shigowar Hajiya Yelwa ya sa yai saurin cire hannunsa.

"Alhamdulillah!, ka ga yadda na tsorata da Alizah ta ce wai Hauwa'u ta mutu"

Yai saurin miƙewa ya ce " ai Hajiya ba dan ina wajen ba ƙila mutuwar za ta yi. Kin ga yadda ta firgita kuwa, sumewa fa ta yi"

"Ai Hauwa'u kam sai dai Allah shi albarka kawai. Tukunna ma waya fito da kuliyar ne?"

Alizah ta ɓuya bayan Daddynta dan ta san ita ce ta tafka aika-aikar nan. Tun kafin Maijiddah ta zo Hajiya Yelwa ta sa aka rufe kuliyar kuma ta mu su kashedin kar su yadda su buɗe ta.

Hajiya ta kama hannun Maijiddah ta ce " dan Allah ki yi haƙuri kin san sha'anin yara. Fatan ba ki ji ciwo ba?"

Maijiddah ta girgiza kai sannan ta lalumo hijabinta ta saka.

Yana tsaye ƙikam yana jira ta ɗago yaga fiskarta da kyau, ɗazu cikin ruɗu ya ke bai tsaya ya kalleta sosai ba. Sai da ya ƙare ma ta kallo sannan ya ce "Hajiya an gama haɗa kayan ne?"

"Angama Yaya, na ce da Faty ma ta kai su cikin mota"

"Barinje in gani kar su yi mantuwa"

Har ya kai bakin ƙofa sannan ya sake juyowa ya kalleta, har a lokacin bata gama nitsuwa ba jikinta na ɗan kakkarwa, yai murmushi sannan ya fita...

Hajiya Yelwa sai da ta tabbatar Maijiddah ta nitsu sannan ta sa autarta Faty ta raka ta har bakin gate duk da kuwa Fatyn ta tabbatar da an sake kulle kuliyar.

Hannunta riƙe da ledar da Hajiya Yelwa ta bata su ka fito da Faty.

Yana gindin mota ya ga fitowar su dan haka yai saurin ɗaga wa Faty hannu alamar ta zo.

"Kinga barinje Yaya na kira na" Faty ta gayawa Maijiddah.

" Lah ba komai, sai anjima" Maijiddah ta faɗi ta yi hanyar gate ɗinsu. Ba ta yi wasu taku mai yawa ba Faty ta ƙwala ma ta kira.
Da ta juyo ta ma ta hannu alamar ta zo. Tsayawa ta yi ta rasa mi za ta yi. Ga Daddyn su Alizah ya ƙura ma ta ido.

"Ki zo inji Yaya" Faty ta faɗi da ɗan ƙarfi. Ba yadda za ta yi haka ta fara taku a hankali har ta kai wajen motar, gefen Faty ta tsaya tana kallon ƙasa a hankali ta furta " ina kwana"
"Ki shiga ya kai ki a mota" Faty ta faɗi tana ɗan murmushi ƙasa-ƙasa.

A hankali ta ce " Lah Faty sai ka ce ba ki san gidan mu ba, ƙasan layi ne ba nisa"

"Wato dai ladar ne ba kya so na samu" Ya katse ta

"A'a Yaya, Allah ba nisa. Na gode"

" ki shiga mota ko na sa akawo kyanwar ɗazu"

Ai cikin firgici ta kama handle ɗin ƙofa tana kokawa da shi. Faty ta fara ma ta dariya.
Shi ma murmushin yai sannan ya danne key ɗin hannunsa ƙofar ta buɗu...

Sai da su ka fita daga cikin gidan ya ɗan kalleta ya ga ta takure gefe ya ce " ki na tsoron kar na sayar da ke ne?"

Ta girgiza kai

"Ko nima ina da kamannin  kyanwa ne"

"A'a"

"To ya kika takure, kin ƙi ki sake jiki haka nan ba ɗan hira"

Shiru ta yi dan ba ta san mi za ta ce ba. " ashe ke ce me yiwa Hajiyata kitso. Kin san yadda ta ke yabonki kuwa.  Ga ki 'yar ƙarama da ke, anya kin kai shashida kuwa?" Yai tambayar ne dan samun damar gabatar da ƙudirinsa, yanayin tsayinta da ƙaramin fiskarta ya ke ganin kamar ba za ta kai 18yrs ba shi kuma a gaskiya ba zai iya auren under 18 ba.

"Na wuce mana" ta faɗa a hankali

"Faɗamin gaskiya, shekarun ki nawa?. Idan ki ka min ƙarya  ma zan gane"

"20"

"Ishirin! Kai yarinya ba ki kai ba"

"Yaya kawai ƙaramin jiki ne dani fah, amma anyi auren ƙannena har biyu yanzu ma an kusa wasu biyun" sai da ta yi maganar sai kuma taji haushin maganar da ta yi.

Cikin zuciyar sa ya ke jimami sai dai bai bayyana ba ya ce " ke mi ya hanaki auren? Karatu ki ke?"

Shiru ta yi ta juyar da kanta wajen glashi tana kallon waje.

Bai sake tambayarta ba yana dai sake karantar yanayinta. Sai da su ka iso ƙofar gidan su sannan ya  miƙa ma ta wayarsa ya ce " sa min numbar ki anan"

Kwarjininsa da girmansa shi ya hana ta mishi musu. Ta ƙarɓa wayar ta saka nambobin ta.

Miƙa ma ta kuɗi yai ta ƙi ƙarɓa.

"Kuɗin ƙitson da ki ka yiwa su Baby ne"

"Hajiya ta bani ai"

"Hajiya daban ni daban. Ki ƙarɓa ko na sa a kawo kyanwar gidanmu na ɗaure  mi ki ita a ƙafa"

Ta ƙarɓi kuɗin ta ce " na gode Allah ya saka da alkhairi" ya amsa da amin. Sai da za ta fita ya ce " a samu a addu'a, Insha Allah anjima zamu hau hanya"

"Allah ya kaiku lafiya ya tsare mu ku hanya"

"Amin"

...........................

Su Faridah ba su dawo ba sai yamma lis, da su ka dawonma hidimar gida ya sa ba su zanta da mutuniyarta ba. Sai da ƙarfe goma ta gota na dare bayan ta gama goge doguwar rigar da za ta saka gobe sannan Maijiddah ta fara ma ta bayani.

"Anty Farida barin nuna mi ki wani abu"  

Ta miƙa ma ta  wayarta. Farida ta amsa wayar tana faɗin " wannan tsohuwar wayar ta ki ma ya kamata ki chanja ta"

*Alhamdulillah! ni da yara na mun sauka lafiya. Na gode da addu'arki gare ni*
*AbdulWahab Bello Hassan*

"Weeeeeehuhu. Waye wannan dan Allah? ki ce addu'ar mu ta kusa karɓuwa"

"Kayya Anty, ɗan Hajiya Yelwa ne fa"

"Sai aka yi me. Abeg gist me, ya akayi ya samu numbar ki?"

Maijiddah ta labarta ma ta duk abinda ya faru.

"Ai Insha Allah mun sameshi 'yar uwa ki dai cigaba da tashin dare da kikeyi. Allah ya kusa amsar addu'ar mu. Tukunna ke da me ki ka ma sa reply?"

"Ban ma sa ba"

" amma anyi 'yar ƙauye anan"

"To Anty mi zan rubuta?"

"Mtsssw, give me the phone jooor"...

.........................

Doguwar riga ta atamfa ta saka kalar atamfar ja ce da ratsin fari dan haka ta saka ƙaramin gyale fari. 'Yar powder ta murza sannan ta goga jan janbaki kaɗan wanda ya ke ƙara haska fiskanta.

A karo na biyu Yakubu ya aiko ta fito shi zai tafi.

"Jiddah wannan yayan na kun ko"

Maijiddah dai sai dariya ta ke ma ta...

Su na tafiya Yakubu na ta yiwa Farida faɗa akan indai haka za ta dinga makarar da su to zai dena tafiya da ita kowa yai hanyar sa. "Haba Ɗan Musa, sai kace wanda mu ke aikin asibiti. Ban isa na fito ban karya ba, Allah na gani"

"Lallai kuwa, Sir Najeeb zai samu dalilin koran ki cikin sauƙi kenan"

"Ba Sir Najeeb ba Allah ya sa Sir Salihu ne"...

Office ɗin Anas ta fara zuwa dan ta gaishe shi ta samu cleaner tana shara.
Ta juya za ta fita sai ga Anas ɗin ma ya shigo.

"A'a  ƙanwar mu ce da wurwuri haka, ashe da dai ba za kuyi faɗan latti da Ogan ki ba"

"Ina kwana Ya Anas"

"Lafiya Aisha Farida"

Bayan sun gaisa sannan ta wuce na ta office ɗin.
Nan ma ɗin ana kan gogewa ne hakan ya tabbatar ma ta Ogan na ta bai ƙaraso ba, ta zauna tana danna wayarta...

Cikin takunsa na ƙasaita wanda ke ƙara ma sa kyau da kwarjini ya shigo kamfanin na sa. Duk inda ya wuce gaishe shi ake yi sai dai fuskarsar nan mur ta ke balle ma asa ran zai amsa gaisuwar. Dama idan da sabo to sun saba. Sir Najeeb ba ya amsa gaisuwa.

Yana shiga lifter ya danna 3rd floor wanda nan ne za ta sada shi da office ɗin sa.

Ya ma manta batun yau sabuwar sakatariyar sa za ta fara aiki dan haka kai tsaye ya shiga office ɗin, sai dai tundaga bakin ƙofa muryarta ya fara dokan kunnensa.

"No it cant be her" ya faɗi lokacin da ya tako cikin office ɗin. Sai dai itan ɗin ce dai ya gani, ba ta san ya shigo ba saboda hankalinta na kan wayar da ta ke yi.
Ƙanshin turarensa da ya cikata ne ya sa ta ɗago da idon ta.

"And who are you?" Ya faɗi yana ƙare ma ta kallo.

" The new secretary" ta amsa ma sa

" This is bullshit" abinda ya iya faɗi kenan ya nufi hanyar office ɗin sa.

Tunaninta baƙon Oga ne dan haka ta yi saurin tsaida shi. Cikin bayanin da Anas ya ma ta. Bai kamata wani ya shiga office ɗin Oga ba tareda izininta ba.

" Mr Arab you cant enter the office, my boss is not around"  ta faɗi da ƙarfi.

Tsayawa yai da buɗe ƙofar Office ɗin ya juyo ya kalleta, lokacin ta baro wajen kujeran ta ta nufo shi.

" you can seat and wait for him there" ta nuna ma sa kujeran da baƙi za su zauna Idan sun zo.

Ƙura ma ta ido yai, itama idon ta na cikin na sa. Hazel eyes na shi ta ke kallo wanda ya sa ta ji wani kasala nan da nan ta yi saurin ɗauke na ta idon. Ta yi gyaran murya sannan ta ce
" please go and wait for him"

Girgiza kai yai ya sa hannu zai buɗe ƙofar Farida ta yi saurin buge hannun sa ta shiga gaban sa ta stretching hannayenta tana tare ƙofar da su. "Dan Uban ka, dan kana balarabe sai ka ce ba za ka bi doka ba, to ba ka isa ba"
Idonsa ne su ka firfito lokacin da ya ji abinda ta faɗi.

Ta kalleshi ta ce " you will not enter this office. Anta La adkul.....a'a ba haka bane, Anta La Tadkulul Bab.... mtsww, yau ga ranan zuwa Islamiyya nan, ni Aisha ɗan Larabcin ma ta gagareni"

Hannu ya sa a aljihu ya zaro waya ya kira wata number, ana ɗaga kiran ya ce  da kakkausar murya "Come to my office now"  

Mamaki ne ya mamaye fiskan Farida lokacin da taji  abinda ya ce sai dai ta dake a wajen ba ta matsa ba.

Suna tsaye a haka Anas ya shigo. Ganin yadda Farida ta yi kane-kane a bakin ƙofar office ɗin Najeeb ya sa shi fashewa da dariya.

"Tell this crazy girl to get out of my way" Najeeb ya faɗi cikin tsawa.

Anas ya dubi Farida wanda jin abinda Najeeb ya ce ya sa jikinta yai sanyi, ta sauke hannayenta amma ba ta matsa a bakin ƙofar ba.
Ya ce " Aisha ya ki ka hana Ogan na ki shiga office? ko salon na ki aikin kenan?"

"Ya Anas ni ban san shi bane ai. Akace sunan Oga na Najeeb Jibo, kuma na ga wannan balarabe ne. Suna *Jibo* kan ba na fulani ba ne?"

Anas ya fashe da dariya ya ce " kuma da gaskiyan ki fa. Sai dai wannan bafulatanin ruwa biyu gareshi, ruwan fulani kuma ruwan larabawa"

"Ya Anas ina dai ba ya jin Hausa?"

"Hausa kai, hausa kamar Jakar Kano ma"

"Shikenan ni Aishatu, daga fara aiki har na tafka katoɓara"

"Fatan dai ba ki zage shi ba?"

A sanyaye ta ce " sai dai gobe kar a ƙara"...

"Barin ji mi Ogan zai ce" Anas ya faɗi tareda shigewa office ɗin Najeeb. Dama tuni Najeeb ya shige ya barsu su.

Yana zaune kan kujerar sa ya na kallon ƙofa lokacin da   Anas ya shigo.

" lokacin da na ce ka nemo min secretary, ban ce ka nemo mahaukaciya ba. She's fired, find another one" abinda ya faɗi kenan lokacin da Anas ya ƙaraso wajen sa

Maimakon Anas ya bashi  amsa sai ya sa dariya har da riƙe ciki.

"This not funny, da na yi aiki da wannan gara na dawo da Joseph"

Har lokacin Anas bai bar dariya ba, sai da yai mai isar sa sannan ya zauna ya kalli Najeeb da ya cika yai fam.

"First of all Aisha ba mahaukaciya ba ce, secondly, a iya sanina da Najeeb na san girman kan sa ba zai taɓa bari ya dawo da Joseph ba. Thirdly idan ka kori Aisha, kai za ka ɗau nauyin neman wata ko wani da kan ka. Aisha ƙanwar Architect Yakubu Musa Wase ne, and as far as i know Yakubu is like a brother to me dan haka ƙanwarsa ƙanwata ce"

"Wow! Ban san ka fara kalen dangi ba ai"

"Ni ma kuma ban san ka fara tsoron mata ba"

"What do you mean?" Najeeb ya faɗa a fusace

"Na san ka gane Aisha ita ce yarinyar da ta tada hayaniya a restaurant ranan. Shi ya sa ka ke tsoron aiki da ita"

"Tsoro?" Ya furzar da iska daga bakin shi sannan ya ce " i'll give her a chance, idan ba ta iya aiki ba zan koreta. And i dont care who's sister she is"

"Ko kai fa mutumina" Anas ya faɗi tareda tashi tsaye. Har ya fara tafiya ya juyo ya ce " Dan Allah, ya ka ji da ta hanaka shiga office ɗin ka?"
Najeeb ya jefe shi da biro, Anas ya goce yana dariya...

Yana fita ya samu Farida tana zaune hankalinta kwance kamar ba laifin da ta yi.

" ƙanwata na roƙa miki shi, dan haka ba wata matsala amma ki bishi a hankali"

"Na gode Ya Anas"...
Ta so jin maganarsu, amma bangon office ɗin sa soundproof ne ba abinda ta ji shiyasa ta haƙura da laɓen da ta yi ta je ta zauna...
Fitan Anas ke da wuya telephone ɗin office ɗinta ya fara ƙara. Ta san shine, dan ta nan Anas ya ce za ta fi comminicating da Ogan ta.
Ba tareda wani tsoro ko fargaba ba ta amsa kiran.

"In my office now"  abinda ta ji ya faɗa kenan da kakkausan murya..........



*still on the free pages**💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Free page*

0️⃣0️⃣6️⃣

Ta fi Minti biyar a tsaye bai ce ma ta komai ba, aiki ya ke yi ma a system na shi.

"Sir kai ka kirani kuma ka shanya ni kamar kayan wanki, idan ba abinda zan yi zan koma dan bana iya juran tsayuwa"

Ɗago ido yai yana kallonta. Lallai ma yarinyar nan, shi a tunaninsa da ta shigo office ɗin sa za ta bashi haƙuri sai ta yi ƙum da bakinta ko gaishe shi ba tayiba.

"Let me make this clear to you..."

"Sir Najeeb ka yi Hausa kawai zan fi ganewa, turancinkan nan ban faye ganeta ba. Lanƙwashe harshe ka ke kamar bature"

Bai ji mamakin maganarta ba duba da yadda ya san halinta.

" i will say this only once Miss Salihu. I do not tolerate laziness. This is an office, you should learn to behave yourself according to this company's rules. Is that clear?"

Kallon sa kawai ta ke yi ba ko kiftawa

"Miss Salihu is that clear!" Ya daka ma ta tsawa.

"Yes...yes Sir"

"Good, now get out of my office"...

Tafi minti goma ta rasa yadda za ta arranging files ɗin da ya bata, kamar da gayya aka hargitsa files su ka zama haka. Tana cikin yi kira ya shigo,  ta yi tsaki kafin ta ɗauka.

"In my office now"

Doguwar tsaki ta ja sannan ta tashi ta wuce office ɗin sa.

Ce ma ta yai yana da meeting ƙarfe shabiyu. Baƙin ciki ya zo ma ta har wuya. Maimakon ya gaya ma ta da ya kira sai da ya bari ta sha wahala ta zo har office ɗin sa.

"Why are you still standing, get out?"

"Sir, na san kai Oga na ne kuma zan ba ka girman ka amma kuma wallahi ba zan ɗau walaƙanci ba. Sir daga zuwa na na yi jelen tsakanin office ɗinka ya fi sau goma. Haba dan Allah, indai saƙon magana ne idan ka kirani sai ka gaya min ba wai sai na zo har nan ba. Wannan ai salon mutum ya samu ciwon baya ne"

Ganin ya miƙe ya sa tai shiru. Har gabanta ya tako ya tsaya. " Miss Salihu, i know you are a lousy crazy girl but that should stop outside this company. Here, you are just a secretary, so work like one" yana gama faɗin haka ya fice daga office ɗin ya bar Farida baki buɗe.

"Allah ya isa na, mugu kawai. Daga ranan farko a addabi mutum da aiki kaman Jaki" ta yi tsaki sannan ta fice daga office ɗin...

...........................

Ƙarfe sha biyu saura minti biyu ya fito daga office biye da shi kuma sakatariyar sa Farida, tana ɗauke da wasu files a hannunta. Lifter su ka shiga saboda a second floor za a yi meeting ɗin.  Ƙanshinsa ne duk ya bi ya cikata, ta rasa wannan ƙanshin na shi, its so inviting, so cool.

Kiiiinnnnn. lifter ta tsaya su ka fito yana gaba tana bin bayan sa har su ka shiga hall ɗin.
Kowa ya hallara a wajen dama shi ake jira. Dokar Najeeb ne lateness is a punishable offence.

Ta samu kujera kusa da mace ɗaya da ke wajen ta zauna bayan ta ajiye files a gaban Najeeb.

Duk yawancin bayanan su ba ganewa ta ke yi ba, ko dan maganar ta fi karkata zuwa ga ayyukan gine-gine da kamfanin ke yi ne...
Ƙarfe ɗaya saura minti biyar aka rufe meeting,su ka fito.

Yanzu ma bayanshi ta bi su ka haura. Sai dai ta yi laushi sosai tana ajiye files akan table ta kwantar da kanta.

Rufe ƙofar da yai ya sa ta ɗago idon ta. Ya cire suit ɗin sa, farar shirt ɗin ne kawai ajikinsa yana warware hannun rigar da alama dai alwala yai. Su na haɗa ido ya ƙara haɗa rai...

Sai da ya tafi ta fara ƙoƙarin neman banɗaki dan ta yi tsarki ta yi alwala. Office ɗin ta dai babu, ƙoƙarin fita ta ke matar ɗazu ta shigo office ɗinta.

"Assalamu Alaikum sister"

"Wa'alaikissalam, 'yar uwa sannu da zuwa"

"Suna na Munibat AbdulHamid, i'm an Engineer. Office ɗina na second floor"

"Masha Allahu. Suna na Aisha Farida, sabuwar sakatariyar Sir Najeeb"

"Na ce dama ko zamu sauka mu je sallah. Akwai masallaci a ƙasa"

"Wallahi na gode, kamar kin san abinda ke raina kenan , dama banɗaki na ke nema"...

Fita su ka yi Sister Munibat ta nuna ma ta inda banɗakin mata ya ke, sannan su ka sauko su ka wuce masallaci. Anan Farida ta ga wa su ma'aikata matan duk wanda tacewa ita sakatariyar Sir Najeeb ce sai su ce "Hmmm, Allah ya sa ki iya dan Sir Najeeb Sai a hankali"

Ita kam ba ta ce komai ba dan tun kafin su faɗi haka ta ji a wajen Yakubu da Anas.
Daga masallaci canteen ɗin kamfanin su ka wuce, su na shiga Farida ta hango Yakubu da wasu su na cin abinci dan haka ta yi saurin ƙarasawa wajen table ɗin su.

"Yaya Yakubu ka siya min abinci yunwa na ke ji"
Yakubu ya harareta ya ce " idan ba ki da kuɗin siya ki je ki karɓi ruwa, ruwa is free for all the workers here"

"Haba dan Allah, na ce ma Yayan ma ba za siya mun ba"

"Yayan ai ba na Allah Annabi bane. Na cin hanci ne"

Engr Mathew da ke gefe ya ce " sister ki zauna za'a siya miki abinci. You are our beautiful sister ai"

Farida ta je ta jawo kujera ta zauna. Yakubu ya ce "Matt, wannan yarinyar ci ta ke kamar gara ga ta da shegen son bati. Idan za ka bi shawarata ka barta ta siya da kanta idan ba haka ba kullum kai za ta maƙalewa"

"No problem, this beauty deserve to be serve like a Queen"

Farida ta yiwa Yakubu gwalo...

Su na cin abinci Najeeb da Anas su ka shigo, nan wajen yai tsit. Kai tsaye wani gefe su ka je su ka zauna inda wajene da aka tanada ɗan gefe da sauran mutane. Kujerun wajen da table ɗin ya fi sauran ƙayatuwa. Wajen cin abincin Sir Najeeb kenan, da ke Anas shi ne na hannun daman sa sai ya zamana tare su ke zama su ci a wajen.

Jin wajen yai shiru ba kamar yadda ta fara shigowa ba ya sa Farida cewa " ni kam mutuwa ce ta wuce ne? Na ga kowa yai shiru sai ƙaran sokala da fork kawai"

Yakubu ya taƙaleta ya mata nuni da ido. Sir Najeeb da Anas ta hango su na cin abinci.
Ta gane saboda Sir Najeeb ne kowa ya nitsu a wajen. Sakamakon da da ake cin abincin ana hira yanzu kam kowa abincin ya ke ci baki gum.

"Ya Anas...Ya Anas" muryarta ya karaɗe wajen.

Anas da ya ke kurɓan juice ya ajiye glass ɗin ya juyo da sauri. "A'a 'yar uwa ke ce, ya aiki"

"Lafiya yayana. Yaya wai ni an saka dokan hana magana ne anan? na ga anyi shiru"

Anas ya ce " ni ma ban sani ba amma ki tambayi Ogan ki"

Farida ta maida kallonta wajen Najeeb da ya cika ya kumbura kamar zai fashe. Ta ce " Sir Najeeb ka hana magana a nan ne??"  Tambayar ta fi kama da gatse ko shaƙiyanci kuma da gangan ta yi hakan. Tashi Najeeb yai ya bar wajen. Yana fita daga canteen ɗin aka sa ihu. Wasu sai a lokacin su ka san miye aikin Farida, ta burge kowa, sai dai dayawa sun ji tausayinta dan a tunaninsu ƙarshen aikinta ya zo kenan. Harta Anas sai da yai dariya, shi kam sai da ya cinye abincinsa kafin ya tafi.

Suna fitowa a canteen ɗin Yakubu ya ce " tunda aikin ne bakyaso shikenan. Idan ya koreki za ki san zafin neman aiki ai"

"Haba Yakubu, mutumin nan fa mutum ne amma yadda ku ke zuzuta shi ku ke tsoronsa sai ka ce wani ifritun Aljani"

"Ni dai na gaya mi ki"

Wai da su ka taho da Sister Munibat ma harda ba ta addua'ar da za ta yi idan ta shiga office, ita kan dariya kawai ta yi ta wuce.

..........................

Tana zama a kujerar ta aka kira, as usual dai cewa yai ta zo.

"Sir gani"

Kallon walaƙanci ya ma ta sannan ya jefa ma ta takardar da ke hannunsa.
"Read it"
Tsugunnawa ta yi ta ɗauko takardar ta fara karantawa a zuciyarta.

"Read it loud" ya daka ma ta tsawa

Haka ta fara karanta ma sa daga farko har ƙarshe. Sai da ta tsaya sannan ya ce " i'm sure lokacin da aka baki takardar ɗaukan aiki an haɗa mi ki da wannan takardar, but you are so dumb to not have read it. Now, daga gobe ki fara shiga irin yadda aka tsara a dress code ɗin nan. This is a construction company not a fashion show"

"Sir, ni banda kuɗin siyan kaya irin wannan, kuma dai yau na fara aiki balle ace zan samu albashi dan haka sai ka yi hakuri har na karɓa albashi tukunna"

"Miss Salihu you are stepping beyond your limits, dont you dare talk back to me again" ya nuna ta da yatsa

"I gave you a week to find cooperate clothes. A week Miss Salihu"

"Ok Sir"

Hannu ya ɗaga ma ta ta juya ta tafi.
Ta ɗauka zai ma ta maganar abinda ya faru a wajen canteen sai ga shi bai yi ba. Ita kan bonus ɗin ta dama ta riga ta tanadi amsar da za ta bashi idan ya ma ta magana...

Aiki dai ta aikatu dan da gayya ma ya ke sata wasu ayyukan.  Sai dai tunda ranar farko ce haka ta haƙura ta dinga binshi a hankali kar ya ce ma ta lazy.

A haka su ka ƙare aikin ranan, ƙarfe huɗu za su dinga tashi dan haka ƙarfe huɗu saura kwata ta fara haɗa kayanta. Kiririnkiririn sai ga telephone na ƙara.
"Mtsww sarkin naci" ta ɗauka fiska ɗaure kamar tana gaban Sir Najeeb ɗin.

Ajiye wayar ta yi ta shiga office ɗin sa. A ranta tana ayyana abin da za ta ce idan wani aikin zai ba ta.
Tana shigowa ya nuna ma ta wata laptop ya ce ta ɗauka ta tafi da shi gida wanda za ta dinga ƙarasa aiki da shi a gida kenan.

"O'o ni Aisha, wato agidan ma ba hutu za kai ba"

"What do you say?"

"Babu, na ce Thank you Sir"

Sai da ta juya za ta fita ya ce "Miss Salihu"
Haɗiye miyau ta yi tareda dunkule hannunta ɗaya ta juyo.

"Fix a meeting with the Sudanese tomorrow"

Wa su Sudanese kuma? Ta faɗi a zuciyarta a fili kuma ta ce "Ok sir"

Ta san ko ta tambaye shi ma ba gaya ma ta zai yi ba dan haka ta bari akan za ta samu Anas ya ma ta bayani...

......................

Gaba ɗaya a gajiye ta isa gida, Yakubu sai dariya ya ke ma ta wai indai a haka za ta ci gaba ba za ta jima da Sir Najeeb ba dan shi kam aiki ya ke so a mishi tuƙuru.

Bayan Maghrib ta kira numbar da Anas ya bata na wasu Sudanese da ke son haɗa hannun jari da Najeeb. Ta faɗa mu su meeting ɗin su da Najeeb gobe ƙarfe goma.

Su na cin abincin dare Baffa Musa ya aiko a kirata. A falonsa ta sameshi yana aikin lissafi a takarda. Ɗan nesa da shi ta zauna a ƙasa ta gaishe shi.

"Ya aikin dai"

"Alhamdulillah Baffa"

"Allah ya taimaka, iyayen yaron nan sun sameni kuma mun tattauna da su. Na ce su bani lokaci na yi bincike saboda kar a samu matsala irin na baya"
Farida ta rintse ido tana tuno abinda ya faru a baya. Ta ya za ta manta wannan babban al'amari daya faru a rayuwarta.
Maganar Baffa ya dawo da ita.

"Sun ce Asalin su 'yan Wudil ne amma kuma tunda Kakansa ya dawo cikin Kano da zama ya zamana 'yan uwan su sunfi yawa anan. Ina so idan komai ya daidaita da yardar Allah da ke da Maijiddah ƙarshen shekara ayi bikin ku tare. Tunda Allah ya sa Saminu ya amince. Na huta da yawan maganganu da ake akanta"

"Baffa wani Saminu kuma?"

"Yaron shagona"

"Baffa auren sadaka za ka yiwa Maijiddah, haba dan Allah sai ka ce wanda ta ke da wani aibu"

"Bance tanada aibu ba. Amma tunda har yanzu shiru ba wanda ya zo neman aurenta kinsan dai ba zan zuba ido ina ganinta haka har a gama auren ƙannenta ba"

"Wallahi Baffa kai bagidaje ne. Wai za ka aurar da ita wa yaron shagonka, irin ta yi kwantai ɗin nan,cab ɗi"

"Tashi ki bani waje. Ba shawararki na nema ba"

"Baffa dan Allah ka saurareni, Wallahi indai ka aurar da ita wa Saminu Jiddah ba za ta taɓa samun kwanciyar hankali ba. Walaƙantata zai yi dan ya san sadaka aka bashi ita"

"Ban nemi shawaranki ba. Tashi ki tafi "

"Baffa akwai wanda ya ke sonta fa"

"Waye?"

"AbdulWahab sunan shi, ɗan gidan Hajiya Yelwa wanda Jiddah ke wa kitso"

"Hajiya Yelwa?"

"Cikakken sunan sa AbdulWahab Bello Hassan"

Baffa ya ajiye biro ya kalli Farida da kyau ya ce " na san ki da yawar magana amma ban sanki da sharri ba. Yaushe ɗan gidan Alhaji Bello Kachako ya ce yana son Maijiddah"

"Allah Baffa da gaske na ke, ka tambayi Jiddah"

"Shi kenan, kiramun ita"

Ko da ta shiga ɗaki Maijiddan ta samu tana waya. "Ki je inji Baffa"...

Farida na shirin kwanciya ta jiyo muryan Baffa yana faɗa. Da sauri ta zari hijabi ta fita saboda ƙaramar riga ce a jikinta.

" kin san ko waye shi kuwa?, babban ma'aikacin custom ne fa. Ba na son sharri Maijiddah ki riƙe matsayin ki"
Duka matan sun hallara a falon dan suma faɗan Baffa ya tado su daga matsugunninsu. Maijiddah kam ta kifa kai tana kuka dan ta tsorata da masifar Baban na ta.

"Ikon Allah! Yanzu dan ba ki da mashanshani sai ki yiwa bawan Allah sharri. Ba ki tsaya ma kusa ba sai chan nesa da ke ki ke hangowa. Ni dama na san yawan zuwa gidan Hajiya Yelwan nan kwaɗayi zai sa miki" Anty Hanne ta faɗi tana tafa hannu.

"Munafukai anzo gulma. To ta Allah ba taku ba" ta kalli Baffa ta ce "Baffa ina ni na ce ma ka AbdulWahab na son ta, to ka manta da na yi maganar. Idan gaskiya ce ai ba za ta ɓuya ba idan ma ƙarya ne za a gani. Jiddah ta shi mu tafi"

Jiddah kam tana tsugunne a wajen ko motsawa ta kasa yi. Haka Farida ta zo ta ja ta su ka bar falon...

"Dan Allah ki bar kukan nan, tukunna kukan mi ki ke yi? Saboda Baffa bai yarda da ke ba? Shareshi idan AbdulWahab ya turo ai za su ga zahiri"

Cikin kuka ta ce "Anty Farida wai Baba cewa yai idan ma asiri na ke son yi akan shi gara na bari. Allah ya bani miji Saminu, ta ya mahaifina zai min wannan zargin. Har rashin miji zai sa na koma asiri"

" Jiddah ki godewa Allah, domin addu'arki ta ƙarbu Insha Allah. Ba ga ni ba, ko kin manta abinda ya faru da ni shekaru uku da su ka wuce, i was exactly your age lokacin. Wani surutu ne ba ayi ba, an zage ni an zagi Ummi, hatta Abbana da ke kabari sai da ya samu kason shi. Dan haka ki cigaba da addu'a kuma ki yi ƙum da bakin ki. Duk lokacin da AbdulWahab ya turo su za su ji kunya ai"

"Na gode Anty"

Ta gode Allah da Anty Farida ta yadda da ita lokacin da ta ji record ɗin hiran da su ka yi a waya. Ta rintse ido tana tuno abinda ya faru tsakaninsu duk da kuwa alokacin ba ta cikin hayyacinta saboda firgicewa da ta yi da ganin kyanwa.

Hiran su ta tuno wanda ya sa duk wani baƙin ciki ya kau daga zuciyarta.

*" Hauwerh za ki iya auran tsoho?"*

*"Mi zai hana?"*

*"wannan tsohon fa shekarunsa ɗai-ɗai har arba'in da ɗaya, ga yaran sa har biyu"*

*"ai ba tsoho ba kenan"*

*" haka ki dai ki ka ce gimbiya Hauwerh"*

*"zan samu amsata anjima ko?"*

*"sai bayan kwana uku"*

*"wai-wai har 3days. To, Allah ya kaimu"*

*amin*

Gaskiyarsa ya fi komai birgeta. *" ina son matata sosai Hauwerh, sai dai umurnin Hajiyata ne akan lallai in ƙara aure kafin shekara ta ƙare. Kuma kallo ɗaya na mi ki na ji kin birgeni"*

Ta sha ji ana hiran sa idan ta je yiwa Hajiya Yelwa kitso. A yadda ta fahimta matarsa na aiki a Abuja shi kuma da yara su na Lagos, sai ƙarshen wata ta ke zuwa mu su. Wannan ne dalilin da ya sa Hajiya Yelwa ta sa shi ƙara aure.

Kamar yadda Anty Farida ta ce za ta yi shiru har sai ya aiko gidan su. A da tunanin da ta yi shine gobe da safe ta playing record ɗin hiran su wa Baabar ta ta ji saboda ta yadda da maganarta ta kuma yiwa Baba bayani...

........................

Washe gari ma shigar atamfa ta yi duk da kuwa a dresscode ranar Jumua'a ne kawai aka amince asa kaya native.
Yana shigowa ta bi bayan sa da sauri.

"Sir kana da meeting da Sudanese ƙarfe goma. Sannan akwai wani Mr Habib Olalekan da ya kira ya ce yana buƙatar ganinka na ce ya zo ƙarfe tara"

"What about the files that i asked you to arrange?"

" na gama Sir"

"Bring them here"...

.........

Sati ɗaya kenan da fara zuwa aiki. Duk wani kafa da Sir Najeeb ya ɓullo da shi dan ya muzguna ma ta tana shanyewa, acewarta dole ta jure kar ya ɗauka ta gaza aikinta ne. Tsawa da masifa kam tana shan shi kullum.

A ɓangaren Maijiddah kam tunda sauran 'yan gidan su su ka ji labarin abinda ya faru sai su ka koma tsokanarta da habaici da Matar custom. Abin yana sosa ma ta rai sai dai ba yadda za ta yi tunda dama sun saba tsokanarta. Bisa umurnin Farida ta amince da AbdulWahab. A yadda ya tsara immediately zai tura iyayensa ayi maganar sai dai ta ce ya bari a gama bikin ƙannenta tukunna.

Da sati ta zagayo ta je yiwa Hajiya Yelwa kitso, kunya duk ya cikata lokacin da Hajiyar ta kira ta da 'surkuwa ta' da kyar ta iya ƙarasa kitson saboda yadda ƙannen AbdulWahab su ka sa ta agaba da tsokana.

Shirye-shiryen biki ake ba kama hannun yaro. Dan asabat za a ɗaura aure...

Kallon rainin hankali ya ma ta sannan ya ce "repeat what you just said"

"Sir Najeeb ina son ɗaukan leave na kwana uku. Ba zan zo aiki ba ranan Laraba Alhamis da kuma Jumma'a"

"You are crazy right? Yaushe ki ka fara aiki da za ki ɗau 3days leave?"

Ta yi shiru

"Answer me!" Ya daka ma ta tsawa.

"Sir, bikin ƙannena za ayi kuma..."

"And so?"

"Sir...."

"Get out of my office"....

Washe gari laraba ya ɗauka ba za ta zo ba sai ya ganta. A zuciyarsa ya ce ashe ta san mi ta ke yi. Sai dai ƙarfe ɗaya na yi da aka fita sallah ta yi tafiyarta.

Da ya dawo daga masallaci ya shiga office ya ga takarda akan desk ɗin sa.

*Sir na tafi, sai Monday zan dawo. Ka yi haƙuri wannan hidimar ta gida ce dole ayi komai da ni*

Duƙunƙuna takardar yai sannan ya cillar " crazy bitch"
Ya ɗau waya ya kira Anas.

"Hello mutumina ya aka yi?"

"Find another secretary"...*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Free page*

0️⃣0️⃣7️⃣

Hankali kwance Farida ta ke hidiman biki. Anas dai ya kira ya ma ta faɗa akan tafiyarta, acewarsa kwana uku yai yawa sannan ya sanar da ita Najeeb ya koreta sai dai kar ta damu ta zo ranan Monday ɗin kafin nan zai roƙe shi. Ita kam ko ajikinta dan ta san abinda ta shirya wa Najeeb.

Ranan Jumma'a su Ummi su ka zo daga Jos, murna wajen Farida ba'a magana. Ranan Asabat aka ɗaura auren *Hajara Musa Wase da Haladu Iliyasu* sai *Salima Musa Wase da Jabir Muhammad*

'Yan uwa daga Wase da Giyaɗe duk sun zo, da ke Baffa Musa da Baaba Sabuwa duka 'yan Wase ne. Ita Anty Hanne kuma 'yar Giyaɗe ce.
Haka aka sha hidima lafiya, duk da an ɗan samu rikici ranan yini saboda magulmata wanda su ka tisa Baaba Sabuwa a gaba kan rashin auren 'yarta Maijiddah. Maijiddah ta yi kuka har ta ƙoshi duk da ta san akwai alamun kukan na ta ya kusa ƙarewa amma kuma madamar ba auren ta yi ba, ita ko Baabarta ba wanda zai samu sukuni...

.......................

Shigar Abaya ta yi mai adon  duwatsu kalar gold. Gyalensa ta yi rolling da shi sannan ta ɗau jakarta ta fito, gidan dai an watse sai 'yan tsiraru. Ummi ma ta tafi jiya saboda aiki da za ta koma.

"Allah dai ya sa Sir Najeeb ya haƙura idan ba haka ba kuma kin gama aiki kenan a Najeeb constructions"

"Ya ma isa ya koreni. Lallai! ai Yakubu ka zuba ido kawai ka sha kallo amma yau ko ana ha maza ana ha mata bazan ajiye aiki ba"

Yakubu girgiza kai kawai ya yi ya tada machine ɗinsa su ka tafi...


Sandy mai goge office ɗin Najeeb ne ta cewa Farida Najeeb ya zo lokacin da su ka haɗu, za ta shiga lifter ita kuma Faridan ta fito.

Ta na ajiye jaka ta wuce office ɗin sa. Yana duba wa su takardu ta shigo.
"Good morning Sir"
Ya ji shigowarta amma ya share ko ɗagowa bai yi ba.

"Sir akwai aikin da zan yi ne?"

Sai a lokacin ya ɗago ya kalleta.
"What part of my message did you not understand?"

"Sir na ga saƙo ta email ranan Laraba wai an koreni daga aiki"

Ya ɗaga ido ya ce "and?"

"Ban koru ba mana. Ba laifin da na yi sannan ko na yi laifi ma, tsarin da ka shirya min ya hana ka koreni"

"Listen Miss Salihu. Na san Saboda Anas ki ka dawo, but ki sani. This is my company, just like you Anas is my employee. So, na koreki ba abinda Anas zai iyayi akai. Now get out of this place bitch"

Fita ta yi daga office ɗin ba tareda ta ce ƙala ba. Minti biyu sai ga ta ta zo da takardu a hannunta

"Ga shi nan, wannan takardar shedar amincewarka ce da tafiyata. Wannan kuma kai ka amince zan yi aiki da kai na wata shida ba tareda ka koreni ba, idan har ka koreni to za ka dinga biyana salary har wata shida ta cika kuma......"

"Wait whats this? When did i sign this? I never signed this"

"Ka kalla dai da kyau Sir Najeeb Jibo. Ka san tabbas signature da ke jiki kai ka yi, you stamped and signed it"

"This is bullshit" ya faɗi tareda yaga takardun

Farida ta yi dariya ta ce " na nawa kuma wannan ma ba original ɗin bane. Original ɗin na nan, so ba inda zan je"

Ta fita daga office ɗin...

Anas ne ya shigo office ɗin ta da sauri "'yar uwa mi ya faru? Najeeb ya kira ni yanata kwarwa"

"Ce ma sa na yi bai isa ya koreni ba"

"Barin shiga na ji mi zai ce"  ya shige office ɗin Najeeb da sauri...

 
Yadda Anas ya ɗau alamarin fa ba da sauƙi bane. Domin Najeeb faɗa ya ke ma sa kamar tsohon zaki, cewa yai ya kawo ma sa mahaukaciya, yarinyar ba ta ganin girma ko darajar sa.

"Amma Najeeb we've talked about this ai, na roƙeƙa ka bata wani chance ɗin"

"To hell with her. I dont want to work with her, can you imagine wannan yarinya ta creating documents ta sa na signing ba tareda na san miye a ciki ba. The girl is a crook, she's just...."

"Haba yallaɓai. Duk wannan tashin hankalin akan mace, ban sanka da haka ba"

Najeeb ya kalli Anas ido cikin ido ya ce " get her out of this office or i will use force, and you know i will do it"

Ganin yadda Najeeb ya bircike ya sa ya fita ya samu Farida ya ce dan Allah ta koma gida zuwa gobe idan Najeeb ya huce zai kirata sai ta dawo. Farida ta tafa hannu ta riƙe ƙugu ta ce "Ya Anas ba inda zan je. Ai yau idan bai haƙura ba zai ga haukata muraratan. Ba ri ma kaga"

Ta wuce office ɗin Najeeb.

"Ka ga Sir Najeeb kar ka bari na nuna ma ka haukata anan, kai shikenan ba dama mutum ya ɗan yi ƙaramin laifi sai ka ce kora, to yau ka gamu da gamonka. Ba inda zan je idan ka takura kuma na shigar da kai ƙara tunda da izininka na tafi hutu"  ta san hakan zai iya faruwa shiyasa ranan laraba da ta zo ta typing documents ɗin ta haɗa cikin wasu da zai signing shi kuwa ko dubawa bai yi ba ya dinga signing ɗin su.

"Well lets see how tough you are" ya faɗi tareda ɗaukar waya ya kira security.
Anas da ya shigo office ɗin ya fara bashi haƙuri. "please dont do this. Ba girmanka bane wallahi. Za ta bar maka aiki amma banda koran walaƙanci dan Allah"

Farida ta ce " Ya Anas ka barshi, security ɗin su zo ina nan ba inda zan je"

"Farida ki yi shiru ki fita, i'll handle this"

"Yadda ya ke ji da taurinkai ni nawa ya ninka na shi. Mun fafata da arnan Jos ma balle shi"

Ana haka sai ga wasu murɗaɗɗun security sun shigo, dukkan su biyu da ka gansu ka san basu da mutunci da alama ma ba musulmai ba ne.

Najeeb ya tashi ya zo gaban Farida ya ce " for the last time, LEAVE"

"Allankatafir ba inda zan je"

Shi kam Anas baza ido kawai yai yana kallon wannan dramar.

Najeeb ya dubi securities ɗin ya ce " throw her out of my company, i dont want to see her here again"

Ɗaya daga cikin securities ɗin ya nufo ta yana ƙoƙarin   riƙe ta, aikuwa ta yi tsalle ta faɗa jikin Najeeb ta cukwuikuyeshi tana ihu tana faɗin wallahi ba zan fita ba ko za a kashe ni.
Najeeb ya rintse ido lokaci guda kuma hankalinsa ya tashi. Cikin zuciyarsa ya ke mamakin abinda ya faru, ba wai rungumeshin da ta yi ba, sai dai effect ɗin da rungumar ya jawo ma sa. He cant believe he got erection because of this crazy girl.

Security ɗin ya kai hannu zai janyo Farida daga jikin Najeeb, Anas ya daka ma sa tsawa ya ce su fita daga office ɗin.

Najeeb har lokacin idonsa a rufe, ya rasa ya zai yi, he's afraid of pushing her away saboda Anas da securities za su ga yadda engine ɗinsa ta miƙe. He cant embarrass himself infront of this crazy girl dan haka cikin hikima ya sa hannu ya turata da ƙarfi before you knew it ya juya da sauri yai hanyar banɗaki.

Anas da ke recording abinda ke faruwa yai kan Farida da ta faɗi ƙasa warwas. " sorry 'yar uwa, tashi" da ƙyar ta miƙe da taimakon Anas saboda ƙugunta da ya bugu sosai...

Ya ƙara zuba ruwa a fiskarsa a karo na ba adadi. Ya kalli kan sa a madubi sai lokacin ya ga yadda jacket na shi ya ɓace da janbakinta.

"This girl is a witch. How could this possibly happen?"Rabon shi da shiga yanayi irin wannan ma ya manta....

"Oga ka fito ayi magana, ka haƙuran ne ko dai" muryan Anas ya katse shi.

Ajiyar zuciya yai sannan ya fito riƙe da jacket a hannunsa yadda ya riƙe ka ce kashi ne ajikin jacket ɗin. Yana fitowa Anas ya sa dariya.

"Get out Anas, i dont want to see anyone"

"Ka huta mutumina irin wannan al'amari sai da hutu ai"
Najeeb ya wurga ma sa jacket ɗin. Anas ya chafe ya ce " wannan jacket ɗin ta tarihi ce"
Sai da ya kai bakin ƙofa ya ce " kar ka manta za ka saurari presentation daga Team D ƙarfe goma. Zan sa sakatariyarka ta tuna ma ka idan lokaci ya yi"

Najeeb ya ce " Anas  i'll kill you"....

Anas na fita ya samu Farida ya ce " gaskiyar Yaks da ya ce ke da Najeeb fire and fire ne sai dai gaskiya ta ki wutar ta fi tasa zafi. Kar ki bari kowa ya shiga office ɗin sa sai nan da 1hr kafin nan ya huce"

Farida ta amsa da " ok"

Ko ajikinta dan ta san haƙarta ya cimma ruwa...

Yana zaune ya sa hannu a ƙirjinsa yana shafawa ashe yarinyar nan har cizonsa ta yi, da ya duba wajen a madubi yai wani jaa abinka da farin mutum.

"She'll pay for this, i'm not sending her away. Not until she suffer, i'll make sure she cry and cry and cry"

Yana zaune ya kunna laptop ɗin sa " lets see what the witch is doing"

Tana zaune tana danna waya ga biscuit agefe tana ci. Har zai kashe sai ya tsaya saboda shigowar Khalidah da ya gani. " another bitch" ya faɗi a ran sa...

Kai tsaye hanyar office ɗin Najeeb ta yi Farida ta ce " Malama tsaya"

A gadarance Khalidah ta juyo "and who are you?"

"Idon ki dai bai makance ba ina?. Kin san dai aikin wanda ke zama a kujeran nan ko"

"Ya kamata ki sani, matsayin ki bai kai ya hanani shiga office ɗin Najeeb ba"

Farida ta taso " Sir Najeeb ya ce bai son ganin kowa sai nan da awa ɗaya dan haka. Ko ke wacece sai dai ki dawo anjima"

"Ki hanani shiga idan kin isa?" Khalidah ta faɗi tana ƙoƙarin shiga. Farida ta sa hannu ta jawota da ƙarfi.

"Ki riƙe matsayinki Malama, ko kuma wallahi ni da ke sai mun kwashi 'yan kallo"

"Ki matsa na shiga. Ke kin ma san ni wacece a kamfanin nan?"

"Najeeb constructions na gani ba Najeeba constructions ba dan haka duk matsayinki a ƙarƙashin mai kamfanin nan ki ke"

"Hmmm za ki sha mamaki yarinya, ko kwana ɗaya ba za ki ƙara anan ba Najeeb zai koreki, wanda su ka fi ki nitsuwa ma ba sa daɗewa balle ke shashasha"

"Eh na ji dai. A bi doka a zauna lafiya"

Khalidah ta yi tsaki ta fita. Sai da ta tafi Farida ta ja numfashi ta ce " wai! na sha da ƙyar. Wannan matar fa ta riƙe ni ba ƙaramin jin jiki zan yi ba. Allah ya yi halitta anan"

Najeeb da ke kallon komai ya ce "scary bitch"...

..............

Ƙarfe goma saura minti biyar ya fito daga office ɗin sa.
"Sir na biyo ka ne?"
Bai kulata ba ya fita bayan ya harareta.

Da ya tafi ta ce " ka ji dashi, ni kam kujeran nan tawa ce ina nan daram da kai"

Lokacin da zai dawo tare su ka dawo da Khalidah. Su na shiga office ta cigaba da bayanin abinda Farida ta ma ta sai dai hankalin sa ma baya gareta yanaga takardun da ya shigo da su.

"Najeeb ba ka ce komai ba"

"She's doing her job" ya faɗi ba tareda ya kalleta ba

"Najeeb yarinyar nan 'yar iska ce, ƙila ma 'yar ƙwaya ce kaga ɗazu wai za ta yi kokawa da ni idan na ce zan shiga office ɗinka"

"So?"

"Najeeb ka koreta, ina wancan Joseph ɗin nan  da ya ke aiki da kai kafin na yi tafiya"

"Look Khalidah, i fire who i want to. For now that girl stays"

"Najeeb i demand you to sack that girl"

Da ƙarfi ya buga desk ɗin gaban shi.

"Look Khalidah, dan mahaifinki yanada 8% share a kamfanin nan doesnt mean you can make rules here. I owned 75%, i make the rules here. Understand that or ask your father, he'll explain to you. Now get the hell out of my office"

Khalidah ta fice fuuu cikin fishi.

.............

Cikin sati uku da Farida ta fara aiki a Najeeb constructions ba wanda bai santa ba. Wanda su ke tunanin ba za ta jima ba sai gashi har sati uku, shi kan sa Anas yai mamakin yadda Najeeb ya haƙura da Farida. A zuciyarsa kuma yana ganin kamar akwai lauje cikin naɗi.

Babban matsalar Farida a office ita ce Khalidah, a second floor ta ke amma kusan koyaushe tana third floor. Magulmatan kamfani su ka sanar da Farida cewa Khalidah son Najeeb ta ke, lokacin da ta zo ta yi service ɗin ta a Kamfanin ta haɗu da Najeeb tun daga lokacin kuma ta ƙi tafiya, da ke dama mahaifinta na da share a kamfanin sai ta samu ɗaurin gindi. Shekararta uku a Najeeb constructions amma ba alamar nasara sai dai ta ƙi haƙura...

Ta gaji da cin abincin canteen kullum sai kashe kuɗi ga abincin a zuba ma ka kamar kana roƙo duk da ma mafi yawancin lokuta Engr Mathew ko Arch Hamza wani cikin abokan Yakubu ke siya ma ta. Ba ma wannan ba abincin ma bai ma ta yadda ta ke so ba.

Ta zuba faten doya da ya ji ganyen alayyaho da kifi a plate. Gaba ɗaya ƙanshi ya baɗe office ɗin, ta na ci tana korawa da zoɓonta mai sanyi a haka Najeeb ya shigo. Bai ma ta magana ba ya shige office ɗin sa, yana shiga ta ji kira. Tsaki ta yi ta ce " yana gani fa abinci na ke ci" haka ta ajiye ta shiga office ɗin sa.

"Miss Salihu. The next time you eat in the office, 10% zan cire a albashin ki. Is that clear?"

"Ok Sir " ta faɗi ta fita tana ƙunƙuni...

.....................

Farida ta zaunar da Baaba Sabuwa ta yi ma ta bayanin abinda ke faruwa tsakanin AbdulWahab da Maijiddah. Da kuma ƙudurin AbdulWahab ɗin na son turo iyayen sa.
Baaba Sabuwa ta ce idan dai da gaske ne za ta sanar da Baffa Musa sai ya basu lokaci.
Farida ta ce " yanzu Baaba Sabuwa ba ki yarda ba kenan?"

"Farida na fi kowa damuwa da rashin auren Maijiddah, sai dai maganar AbdulWahab ɗin ne ta zo kamar almara"

"Addu'arta ne ya ƙarbu. Kin san tunda na zo gidan nan kullum dare Maijiddah sai ta fi awa ɗaya tana sallah tana roƙon Allah ya bata miji. Ko ba ta sallah sai ta tashi ta roƙeshi. To Ubangiji  mai jin ƙan bayinsa sai ya kawo ma ta wanda ba ta taɓa tsammani ba. Baaba Sabuwa ki godewa Allah kawai ki cigaba da yi ma ta addu'a"

Cikin satin Alhaji Bello Hassan Kachako da wa su wakilan AbdulWahab su ka zo. Bakin Baffa Musa kasa rufuwa yai, shi ba dan ya gani zahiri ba ko lokacin da Baaba Sabuwa ta gaya ma sa bai gama yarda ba.  Su zuwan da su ka yi idan an basu Maijiddah su na so bikin kar ya ɗau lokaci.

Baffa Musa kam zani ne ta tadda muje. Dan haka ya amince da sauri.
Sati na zagayowa aka kawo sadakin Maijiddah, dubu ɗari da hamsin. Wata uku aka sa biki su ka nemi a dawo da shi wata biyu Baffa Musa ya amince. Duk da kuwa bashida kuɗi a ƙasa dan ya gama kashe kuɗi wajen bikin su Salima. Sai dai ba zai bari damar da ya ke nema tun da jimawa ya kuɓuce ma sa ba. Allah na gani ya so a haɗa bikin Maijiddah da Farida sai dai hakan bai yiwu ba. 'Yan uwan Rayyan sun ce Rayyan yana so ya haɗa ginin sa kafin ayi biki...

Wannan babban al'amari ya sa kishiyoyin Baaba Sabuwa kowa yai tsit dan abin ya ba su mamaki, duk cikin yaran da aka aurar ba mai sa'an Maijiddah. A gaba ɗaya yaran ma Yayar Maijiddah wadda ita Maijiddan ta biyo wato Bilkisu ita kaɗai ta auri wanda yai boko sosai kuma ya ke da hali yana aiki a kamfanin insurance, sai gara-gara mijin Kulthum wanda shima ma'aikacin Kamfanin Airtel ne.

Abu kamar mafarki fa yadda su ke tsokanarta da Matar Custom sai ga shi har sadakinta an bayar saura a ɗaura aure kawai.

......................

Tana kwance wayarta ya fara ringing tana ɗagawa ta ga Sir Najeeb. Mi zai sa ya kira a wannan lokaci? Ta dai ɗauki kiran.

"Miss Salihu, i asked you to send me a copy of the proposal before you leave. What happen?"

"Ya Allah! Na manta zan turo ma ka yanzu"...

Yana zaune yana sipping tea ɗin sa ta turo ma sa saƙon. Sai da ya duba ya ga aikin bai yi kyau ba akwai gyararraki. Nan ya sake kiran ta.
Tana amsa waya ya fara faɗa "Miss Salihu what is this? Mi ki ka turomin? Haka na ce ki yi?" Jin ƙorafin yai yawa ya sa ta ce

"Domin kai ƙorafi danna ɗaya, domin neman ƙarin bayani gameda aikin da aka maka danna biyu, domin magana da Aisha Farida kai tsaye danna uku...."

Ba ta gama ba ya kashe wayar.
Farida ta yi tsaki, " shi agidan ma ba za ka huta ba aiki, ya san da ya na yi wannan ɗin. Wallahi ba za ka kasheni da aiki ba"

Najeeb ya cillar da wayar yana cize leɓen sa na ƙasa. He's waiting for the perfect time ya aiwatar da ƙudurinsa, just a perfect time. Yarinyar nan sai ta raina kanta...*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Free page*

0️⃣0️⃣8️⃣

Washegari a office Najeeb bai ma ta maganar shaƙiyancin da ta ma sa ba, iya kaci tana nuna ma sa proposal ɗin ya ce ta je ta gyara.

Tana aiki sai ga Sister Munibat ta shigo.

"Sister Farida ya aiki"

"Alhamdulillah"

"Sir Najeeb yana ciki?"

"Eh ki shiga"

Minti biyar sai ga ta ta fito har za ta wuce ta ce " Sister Farida ɗan bani ruwa mai sanyi ma na, fridge ɗin office ɗina ya ɓaci"

Farida ta miƙa ma ta satchet water mai sanyi.

"Na gode sister" har za ta tafi Farida ta ce " yawwa idan kina son zoɓo ko kunun aya, gobe zan fara zuwa da shi"

Sister Munibat ta ɗan yi dariya ta ce " a cafeteria za ki dinga ajiyewa?"

"A'a anan office ɗina, mai so sai ya zo ya siya"

"Toooo, ke da Sir Najeeb kunfi kusa, amma bana tunanin zai amince da haka"

"Sister Munibat ke dai ki sanar da 'yan wajen kun nan kawai"

Sister Munibat tace "Allah ya kawo kasuwa" Farida ta amsa da Amin...

Washe gari Farida ta haɗa zoɓo gora shabiyar da kunun aya gora goma. Tun kan ta shigo ta ɗan bibbiya wajen mutanenta ta sanar da su, wasu a lokacin su ka ƙarɓa dan wa ya ke da garajen zuwa har Office ɗin Sir Najeeb siyan zoɓo...

Tana aiki a computer Najeeb da Anas su ka fito.

" 'yar uwa sannu da aiki ko"

"Na gode Yayana"

Har zai shige ta ce " Ya Anas ga zoɓo fa, harda kunun aya"

" ƙanwata kenan, kina sha'aninki"

"Yaya ai mai neman kuɗi kam kowani ƙofar samu ya gani shiga ya ke"

"Well Hakane, Allah ya kawo kasuwa"

"Na kawo ma ka zoɓo ko kunun?"

"Ki bari anjima yanzu zamu fita wani waje nida mutumunki ne"

Kafin ya gama surutun sa Najeeb kam ya yi gaba...

.....................

Tana tsugunne gaban fridge tana duba sauran zoɓonta wanda na  Anas ne da na Sir Najeeb da ta ajiye mu su, yanzu Yakubu ya zo ya ƙarɓi na sa.

"Miss Salihu"

A firgice ta juyo dan ba ƙaramin tsorata ta yi ba.
"Ya Allahu! Sir Najeeb ai sai ka sa hawan jinin mutum ya tashi. You scared the hell out of me"

"To my office, Now"

Yana shigewa ta fara mimicking na sa " Miss Salihu, to my office now nnnnnnaa. Mtsww"

Ta ɗau zoɓo ɗaya wanda yai sanyi sosai ta shiga da shi.
Tana zuwa ta ajiye ma sa akan table ta ce "Sir na san kafi son shan tea ko coffee amma wannan zoɓon one in town ne. Albarkacin haƙƙin maƙotaka za ka dinga samun kyautar goran zoɓo ɗaya"

Tunda ta fara magana ya zuba ma ta ido har sai da ta kai aya. Duk yadda ya ke jin tsanar yarinyar nan wannan quality na ta na rashin tsoro yana impressing na shi. Idan ka cire Anas duk girman Kamfanin nan babu wanda ke iya tsayawa gaban sa ya faɗi magana son ransa sai ita. People fear him, but this skinny girl idonta ƙyam ya ke duk lokacin da ta ke gabansa babu tsoro ko fargaba a tattare da ita.

"Sir ka taɓa zoɓon ka ji, Allah sai ka yi santi"

"Miss Salihu, duk wani rules and regulations na wannan Kamfani yana da muhimmanci. But na ga alama ba ki ɗauke su da daraja ba. You dont wear cooperate clothes, you eat in the office you... you... you  and only you Miss Salihu"

"Haba Sir, tun ranan da kace na dena cin abinci a Office fa na dena"

"Oh really, and that yellow thing you ate in the morning yersterday?"

"Kai Sir ya akayi ka gani? Ban karya ba na fito shine na karya a office"

"I see. And this"  ya nuna goran zoɓo da ta ajiye"

"Alakoro na kawo ma ka fa. Tunda dai Allah ya haɗamu maƙotaka"

"Look Miss Salihu, get this in to your dumb skull. Office ba wajen ciye-ciye ko kasuwanci bane, you keep on doing it i keep on cutting your salary. Now out of my office"

Ji take kaman ta make shi amma ba hali. Ta juya a hankali tana tafiya.
"Miss Salihu" dama a kufule ta ke ta juyo da sauri ta ce " Sir yanzu kuma mi na yi"

"Take this stupid thing out of my sight"

Ta kalli zoɓon ta kalle shi tace "idan ka ga dama ka wanke bahayarka da shi"

"Wait what?"  Ai da sauri ta fice daga office ɗin...

Sana'ar zoɓo da kunun aya kam Farida ba ta fasa ba sai dai ta chanja salo. Duk mai so zai yi booking ne tana zuwa tun kafin ta shiga office za ta bi ta rarraba ta ƙarɓi kuɗinta wani lokaci kuma sai an kusa tashi ta biya ta karɓi kuɗi. Anas na ɗaya daga cikin ma su son zoɓonta kullum sai ya sha gora biyu. Najeeb bai sake ma ta maganar sana'ar da ta ke ba duk da ya san bata dena ba.

Yau wani ƙaton kula ta fito da shi daga keke saboda sana'ar zoɓo da ya ƙarɓe ta. Dan ko gora hamsin ta yi sai ya ƙare.
Tana faman ɗauka sauke da kular Najeeb ya zo wucewa, a lokacin ta sauke ta na ƙoƙarin murza hannunta saboda zafi, ya tsaya yana kallonta. Haka kawai ya ji ta bashi tausayi. Yarinyar nan da garaje ta ke ina ita ina wannan ƙaton abu. Ya wuceta ba tareda ta ganshi ba, yana zuwa bakin ƙofa ya ce da security da ke wajen ya je ya ɗauka ma ta kayan...

Yau ɗan wake ta zo da shi dan haka da su ka je Cafeteria ita da Sister Munibat ta wuce wajen su Anas.

"Yayana ban san ko kanacin ɗanwake ba?"

Anas ya ce " ci kai. Ai duk lokacin da mu ka je gidan Hajiya Mama sai ta sa an yi min"

"To barin zubo ma ka" 
Ta je ta zubo ma sa a plate harda dafaffiyar ƙwai akai da ɗan ganyen lettuce da albasa sai ƙamshi ya ke yi.

"Gaskiya na gode sweet sister. Allah ya miki albarka"

Ta yi murmushi ta tafi. Ko kallon inda Najeeb ya ke ba ta yi ba.
Anas ya fara haɗa ɗanwake da shinkafa yana ci yana santi.

"Are you flirting with her?"

Anas ya ɗago da mamaki ya kalli Najeeb.

"Wannan shine dalilin da ya sa yarinyar nan ta ke abinda ta ga dama a office. Because of you"

"Dude are you....are you jealous?"

" im serious Anas  stop flirting with her"

Tashi yai ya bar wajen ya bar Anas da baki buɗe.

Idan dai idon sa ya ga dai-dai to tabbas kishi ya gani a idon Najeeb. But why?.... ko dai.....
Ya juya ya kalli Farida da ke ta zuba uwa surutu cikin zuciyar sa ya ce " indai abinda na ke tunani ne to, Farida kin ciri tuta. I wish ke za ki maye gurbin Sabreen a zuciyarsa"...

.....................

Tana ɗaki tana cin abinci taji alert na kuɗi ya shigo ma ta daga wajen aiki. Sai dai tashi ta yi cikin sauri saboda abinda ta gani.  Ba abinda aka ce za'a biyata ba kenan, kusan kaso sittin kawai aka biyata cikin albashinta.
Cikin tashin hankali ta fara kiran numbar Najeeb sai dai bai ɗauka ba.

Ta kira numbar Anas shima bai ɗauka ba.
"Lallai ma! Kan Uba. Wallahi ba zai yiwuba na yi uwa ayyukan nan ba dare ba rana ace wannan kuɗin za'a turomin. Ta tashi ta fara shiryawa.

Maijiddah da ta shigo ɗaki ta ce "  Anty ina zuwa haka"

"Wajen aiki zan je. Yau Sir Najeeb ya taɓo ni"

"Anty ba yanzu ki ka dawo ba"

"Ke dai bari zamu yi maganar idan na dawo"

A hanya Anas ya kirata akan ta yi haƙuri ɗazu suna meeting ne shiyasa bai ɗau kiran ba.

"Yayana kuna tareda Sir Najeeb ne?"

"Eh tare mu ka yi meeting ɗin amma ni na fito na barshi a office yana ƙarasa wasu ayyuka. Lafiya dai ko?"

"Ba lafiya ba Ya Anas 60% na albashina kawai na gani"

"60% kuma?"

"Eh. Na san Sir Najeeb ne yamin haka, dan haka yau ni da shi, sai ya bani cikaton kuɗina ko yaga bala'i" ta kashe wayar tana huci.

Kamfanin yai tsit saboda an riga an tashi. ID card ta nuna aka bari ta shiga duk da kuwa ma su gadin sun santa. Ba ta wuce ko'ina ba sai office ɗin Sir Najeeb. Ba ya main office ɗin sa dan haka ta je wani ɗaki da ya ke yin ayyukan sa na zane acikin office ɗin. Ta ƙwanƙwasa ƙofar.
Yana tsaka da zane ya ji ana ƙwanƙwasa ƙofa. Who could it be? Dan ya san Anas ya tafi tuntuni.

Na'urar computer da ke gabansa ya danna nan da nan Farida ta bayyana. Yadda ya ganta ya san maganar albashi ne ya kawota.  Wajen da ya ke waje ne da bayan shi sai Anas babu wanda ya ke da access na shiga, work place na shi kenan. Anan ya ke duk wani zane-zanen sa. Wajen zagaye ya ke da glass. Glass ɗin daga ciki za ka ga mutum amma daga waje mutum ba zai ga na ciki ba. Kana shigowa ɗakin idan ba ka da katin buɗe ƙofar glass ɗin to ba tayadda zai buɗu...

Tana tsaye ya buɗe ƙofar ya fito.
"Sir Najeeb ban gane manufarka ba. Me na yi aka cire 40% na albashina?"

Yadda ta ke maganar kamar  za ta doke shi.

Bai kulata ba ya je ya zauna a kujerar sa.

"Sir Najeeb i demand an explanation"

"Ofcourse Miss Salihu. Ni na cire 40% na albashinki as a compensation for all your irrational behaviours in this company"

"Sir Najeeb idan ma yaren China ka ke gara ka dena dan ni banjin wannan yare. Ka tura min cikaton kuɗina kawai, abinda na sani kenan"

Murmushin yaƙe yai sannan ya ce " next month ma ki dinga take dokokin kamfani and i'll keep on cutting your salary"

"Cabɗi! Wallahi ba ka isa ba"

Tasowa yai ya nufi kanta ta fara ja da baya.
"Mi za ki yi idan na cire? Yau ma hugging ɗina za ki yi? Go ahead and i'll make sure you get what you are looking for"

Ganin ta kai jikin bango ya sa ta haɗiyi miyau.

"Come on hug me. Na san abinda ki ke so kenan, well yau ba Anas ba yayanki, nobody is here just me and you"

"Idan ma giyan wake ka sha. Wallahi na fika hauka. Kkkka matsa min"

Kallonta ya ke yi yadda take fitar da numfashi da sauri-sauri har yanajin bugun kirjinta.

"Scary bitch..."

Buɗe ƙofar da akayi ya sa yai saurin juyawa to his dismay sai ga Joseph biye dashi kuma wasu zaratan maza guda uku.

"What the hell are you doing here Joseph?"

Bindiga su ka fito da shi Farida ta ƙwalla ƙara ta ɓoye a bayan Najeeb jikinta na rawa tana salati.

"If you comply, nobody gets hurt" a cewar Joseph

Najeeb ya ce "Let the girl go"

"Shut up"  ɗaya daga cikin guys ɗin ya daka ma sa tsawa

"Tie them both"

Farida na jin haka ta ƙwalla ƙara ta ƙara ƙanƙame Najeeb....

..........................

A yadda ya tsara sai ƙarshen wata idan Aneesa ta zo Lagos zai ma ta bayanin komai sai dai ko a ina Aneesar ta ji labari?.

Yana zaune a office su na waya da gimbiyarsa, Aneesa ta shigo fuuuu.

"You liar, sai yaushe ka ke son sanar da ni? Bayan an ɗaura aure?. You evil son of a bitch"

"Anny minene haka kuma"

"Munafuki, asirinka ya tonu ai. Wato har sadaki ka kai. To barin gaya maka Abdul wannan auren ba zai taɓa yiwuwaba"

"Aneesa kenan. Dama abinda ya taso da ke daga Abujan kenan. To ki sani aure babu fasawa tunda dama na gaya miki ai"

"Abdul Wallahi ba zai yiwuba. Idan ma wasa ka ke gara ka janye, i will never share you with anyone"

"Ina son ki Aneesa amma duk abinda ya faru ke ki ka jawo. Ba ni da ra'ayin mata biyu sai da ki ka zaɓi aikin ki fiye da ni"

"Wallahi sai dai ka zaɓa ko ni ko ita dan ba zan zauna da kishiya ba"

"Its too late Aneesa. Wata biyar da su ka wuce da na gaya miki saƙon Hajiyata what did you say?"

"Haka za ka ce ko. To mu zuba mu gani and i'm taking my kids with me"

"Tunda daga gidan ku ki ka zo da su ba"

Ficewa ta yi daga office ɗin kamar wata zararriya...

............................

Har ƙarfe tara na dare ba Farida ba dalilinta ga numbarta ba ya shiga. Maijiddah ta je ɗakin su Yakubu lokacin shima ya dawo daga hira kenan zai ci abinci.

"Amarya Amarya, ya akayi?"

"Yaya Yakubu Anty Farida ta kira ka ne?"

" Farida kuma. Ai ni tun da mu ka dawo daga wajen aiki rabona da ita"

"Yaya numbarta ba ya shiga kuma ta ce za ta je Kamfani wajen Oganta"

"Sir Najeeb"

"Eh"

"To barin kira Anas na ji"
Sai da ya sake gwada numbar Farida still baya shiga kafin ya kira Anas.
Anas ya sanar ma sa yadda su ka yi da Farida sannan ya ƙara da cewa shima ya yi ta gwada numbar Najeeb amma ba ta shiga.

Yakubu ya ajiye waya ya kalli Maijiddah ya ce " barin je Kamfani in dubata. Ko tana chan dan numbar Sir Najeeb ma ba ta shiga"...

Anas ne ya riga shi isa Kamfanin, lokacin da  Yakubu ya iso a wajen motar Najeeb ya tarar da Anas da wasu securities su na magana.

"An ganta kuwa?" Yakubu ya faɗa a kiɗime

Anas ya girgiza kai ya ce " Yaks i think they have been kidnapped"

"What!"....



*Free pages sun kusa zuwa ƙarshe*

*ga mai son cigaban labarin zai biya #200 kacal ta wannan account ɗin 3099546325 Azizat Hamza, firstbank. Idan kuma credit card ne to MTN card na 200 za a turo wa wannan numbar 08137311900. Sannan za a turo shaidar biya (screenshot) na kuɗin zuwa numbar nan still 08137311900. Ko kuma ka biya #300 ka samu labarai biyu sakatariya ta da kuma tsohuwar soyayya**💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Free page*

0️⃣0️⃣9️⃣

"Wayyo Allah Ummi na. Wayyo Ummi naaaaa" abinda ta farka da shi kenan lokacin da ɗaya daga cikin mutanen da su ka sato su ya watsa musu ruwa.

"Shut up" ya daka ma ta tsawa. Nan kuma ta fashe da kuka tana cewa " dan Allah kar ku kashe ni, ni ɗaya ce a wajen Mahaifina kuma ko jika ban haifa ma sa ba"

Tare aka ɗauresu da Najeeb bayansu na gogan na juna sai dai tun da ya farfaɗo baice ƙala ba.

"Sir Najeeb ka ce su bar ni na tafi. Iyayena talakawa ne, ba su da kuɗin da za su basu, yanzu ma Baffa na cikin bashi yake saboda hidimar biki da yai..."  saukar mari taji a fiskarta wanda ba shiri ta fashe da wani matsananci kuka.

"Chachachacha, you talk too much abeg"

Buɗe ƙofar ɗakin aka yi Joseph da sauran su ka shigo.

"Well well well. The Almighty Sir Najeeb, the perfect man. Mr get out of my office"  ya sa hannu ya murɗe kunnen Najeeb da ƙarfi.

"I will make sure you suffer before this is over"

"Untie him" ya faɗi yana yiwa Najeeb kallon tsana.

Kunce shi su ka yi ya ce su ma sa tsirara ai Farida na jin haka ta fara bada haƙuri.

Ɗaya daga cikin su wanda ya ke kamar shine Oga ya zuƙa wiwi da ya ke sha ya ce ma sa ɗan uwa ba haka akeyi ba, idan kana so su biya kuɗi to dole 'yan uwan sa su tabbatar yana cikin ƙoshin lafiya.
"Emeka why now?" Joseph ya faɗi cike da takaici

"Bros let me handle it" wanda aka kira da Emeka ya faɗi. Zuwa yai ya cirewa Najeeb takalmansa da agogo  yace  " so na designer you wear" naushin cikin Najeeb yai wanda sai da Najeeb ya wantsila.
Shi kuwa Joseph zuwa yai ya taka kafar Najeeb. Ba ƙaramin zafi ya ji ba amma haka ya shanye bai nuna ba.
Lokacin da za su tafi Joseph ya tofa wa Najeeb miyau a fiska.  Har su ka fita daga ɗakin bai buɗe ido ba saboda tsananin ƙyanƙyamin abinda Joseph ya ma sa.
Ɗankwalin atamfar ta ta ɗan yaga ta zo ta goge ma sa miyau ɗin.
"Wai mi ka yiwa wannan guntun ne? Joseph ko me su ke kiran sa"

Bai buɗe ido ba kuma bai yi magana ba.

"Dalla buɗe idon. Ba na riga na goge miyau ɗin ba"

A hankali ya buɗe rinannun idanunsa ya ɗaura akan na ta. Itama ɗin shi ta ke kallo for some weird reasons sai ta ji ya ba ta tausayi. Wannan fa ɗan gata ne gaba da baya, CEO na babban kamfani amma Joseph ya ma sa wannan walaƙanci.

"Wannan bayan kuɗi da su ke so akwai bita da ƙulli tsakanin ku. Allah ya sa dai kar su kashe mu"

Ta kalli ƙafar da Joseph ya taka yatsun wajen sun yi jaa sun kumbura. Ta kai hannu za ta taɓa ya janye ƙafarsa da sauri.
" kaa! Dan ma zan taimaka ɗin, to ka ci kan ka"
Ta koma chan gefe ta zauna. Yanzu da aka kuncesu ta ɗan ji saƙayau.

"Ni wallahi yunwa na ke ji, ba dan kai ba da yanzu ina gida ina cin abinci. Ni daga mun kai gida lafiya ma ajiye ma ka aiki zan yi. Irin wannan aiki da kasada ba dani ba"

Tana cikin surutu aka buɗe ƙofa, abinci aka kawo mu su, take away guda biyu na shinkafa da satchet water guda biyu. Ko kallon inda abincin ya ke Najeeb bai yi ba. Farida kam jawo abincin ta yi ta fara ci dan Allah na gani ba ta iya juran yunwa. Abincin ba wani yawane da shi ba hakanan nan taste ɗin dai ba laifi da alama daga restaurant su ka ƙarɓo.

"Sir Najeeb ka ci abinci fa, da zafin sa kar yai sanyi"

Tashi yai ya ɗau ruwa ya shiga wani ƙofa da ke cikin ɗakin wanda ya ke tunanin banɗaki ne. Banɗakin ne sai dai gaba ɗaya a ƙazance ya ke da ƙyar ya kama ruwa yai alwala ya fito dan ba ruwa a wajen, famfom baya aiki.

Sai da ta ga ya je gefe ya tada sallah itama ta ankara ba ta yi sallar maghrib da Isha ba, gashi ta shanye ruwanta.
Dole sai taimama ta yi bayan ta leƙa banɗakin ta ga ba ruwa.

Tana zaune ta jingina  da bango ta fara gyangyaɗi ƙarshe baccin wahala ya saceta....

..........................

Kafin ƙarfe goma na dare iyalen Alhaji Adam Jibo sun samu mummunan labarin rashin Najeeb da Sakatariyar sa. Abinda ya ɗaure mu su kai har lokacin ba a kira su gameda ransom ba. Bacci kam ƙauracewa iyalen yai bama kamar baby da ta dinga kuka wiwi da ƙyar Mom ta shawo kan ta ta yi shiru.

Gidan Baffa Musa ma dai hankulansu a tashe ya ke. Ba ma kamar Baffa Musa wanda ya ke gani kamar sakacin sa ne ya sa Farida ta faɗa wannan hali. Yadda Baffa ya hana a sanar da Ummi amma hakan bai yiwuba dan kafin yai maganar ma tuni Anty Hanne ta kirata ta sanar ma ta an sace Farida. Hankalin mutanen Jos ya tashi a wannan dare, a daren Ummi ta so ta zo amma Baba da Nanna su ka hanata, su ka ce ba abinda za ta yiwa Farida sai addu'a ta bari idan gari ya washe sai ta je.

Haka aka wayi gari gidajen biyu ba kwanciyar hankali. Ƙarfe tara na safe aka kira Alhaji Adam Jibo bayan an tura ma sa hoton Najeeb da Farida ɗaure. Miliyan hamsin su ke buƙata cikin awa ashirin da huɗu  ko kuma su rasa su gaba ɗaya.

Anas ya sanar da Yakubu cewa kidnappers ɗin sun nemi ransom na 50million. Ya kuma kwantar ma su da hankali akan za a kuɓutar da su.

Baffa Musa da Yakubu su ka nufi gidan su Najeeb. Sun samu su Alhaji Adam su na meeting da wasu special police kan al'amarin  sai da su ka gama sannan Dad ya saurare su.

"Alhaji dama maganan kuɗin nan ne. Ni dai a wajena idan na shiga na fita za a samu miliyan uku sai dai kaga ko rabin abinda su ke buƙata ba a kai ba"

"Alhaji Musa ka kwantar da hankalinka Insha Allahu komai zai zo da sauƙi. Maganar kuɗi kuma Alhamdulillah an fara arranging na su. Kar ka damu"

.......................

Da safe Emeka ya shigo ɗakin ya fara faɗa harda marin Najeeb wai 'yan uwansa ba sa son shi suna buƙatar 48hrs su haɗa 50million.

"I thought your parents are super rich. They better not play games with me"...

Emeka cousin ɗin Joseph ne, ya jima yana fashi da makami kafin daga baya ya koma harkan kidnapping. A Kaduna ya ke operation ɗinsa sai dai wata ɗaya da ya wuce Joseph ya kira shi akan yanaso ya kidnapping Najeeb saboda ya ɗau fansar abinda ya ma sa. Wannan ya sa ya zo Kano su ka fara tsare-tsaren yadda komai zai tafi. Da ke Joseph yai aiki a Najeeb constructions hakan ya bashi daman sanin hanyoyin da za su aiwatar da ƙudirin su.

Da safe ba a basu abinci ba haka da rana, gaba ɗaya Farida ta galabaita. Tana chan ta cure gefe guda ta yi kukan ta yi surutun har ta gaji. Najeeb kam ko ehem bai ce ma ta ba.

Buɗe ƙofar ɗakin aka yi, ɗaya daga cikin ma su tsaresu ya shigo ɗauke da bindiga. Zuwa yai ya jawo Farida da ƙarfi, Najeeb ya tashi zai yi kan sa. Ya nuna ma sa bindiga tareda cewa "sit"

Farida ganin anyi hanyar waje da ita ta fara cewa Najeeb ya taimaketa.

"Dont hurt her" Najeeb ya faɗi da kakkausar murya

Wani ɗakin ya shiga da Farida bayan ya kulle Najeeb a ɗakin da su ke da farko.

Ganin ya yo kanta ya sa ta ƙwalla ƙara tana kiran Sir Najeeb da Umminta.
Guje-guje su ka fara yi a ɗakin wanda ya ke cike da tarkacen kayan maye. Cak ta tsaya lokacin da ƙafarta ya taka wata fashashshiyar kwalba. Hakan ya bawa mutumin damar kamata ya kwantar da ita da ƙarfi, sai ihu ta ke ta na ƙoƙarin tureshi amma ta kasa. Ya kama hannayenta da hannunsa ɗaya, ɗaya hannun kuma yana ƙoƙarin zuge zip ɗin wandonsa.
Wani razannannen ƙara ta ƙwala wanda gaba ɗaya gidan sai da ya ɗauka.

Emeka da wasu biyu su ka yo ɗakin da su ka ji ƙaran da gudu. Ganin Larry na shirin afkawa Farida ya sa Emeka ya ture Larry tareda kwaɗa ma sa mari.

"Are you crazy?"

Larry ya ce" the girl too hot Oga. I feel...."

"Will you shut up. You want to ruin my business abi"

Ce wa ɗayan yai ya maida Farida ɗakin da Najeeb ya ke.
Da ɗingishi ta shigo ɗakin saboda har lokacin kwalbar da ta caketa na ƙafar.

Tunda aka fita da Farida hankalinsa ya tashi yasan ba kasheta za'ayiba amma ba makawa sai sun yi raping ɗinta. Lokacin da ya ji ƙaran da ta yi sandarewa yai a wajen jikinsa ya fara ƙyarma yana ayyana abinda zai yiwa Joseph da crew ɗin sa idan sun fita anan. Ganin yadda aka shigo da ita ya sa yai kan ta da sauri. For the first time tun jiya da aka kawo su ya ma ta magana.
"Miss Salihu are you Ok. Mi su ka miki?"

Shiga jikinsa ta yi tana kuka jikinta na rawa. Ta gama tsorata dan ta sadakar Larry shigarta zai yi. Tausayinta ya mamayeshi dan ya san saboda shi ta shiga wannan haɗarin dan Joseph da shi yake gaba. Cuddling ɗin ta yai so tight yana ba ta haƙuri. " I'm sorry, i'm very sorry Miss Salihu"
Sun jima a haka shi kan sa ya rasa dalilin da ya sa ya ji wani nitsuwa ya shigeshi farat ɗaya, like kada ya saketa su cigaba da tsayuwa a haka.

Zafin da ta ji a ƙafarta ya sa ta tuno da kwalbar da ta taka. Cikin sheshsheƙar kuka ta ce "Sir Najeeb ƙafa na" sai alokacin ya saketa ya fara duba ƙafan wanda ke ta zubar da jini.

Zaunar da ita yai sannan ya ɗaura ƙafar a cinyarsa ya ce " zan cire mi ki kwalbar, sorry it will hurt"
Girgiza kai ta yi tareda rufe idonta, ta cize leɓe. A hankali ya cire kwalbar tareda ɗaure ƙafarta da farin hankerchief sannan ya sake jawo ɗankwalinta wanda ya faɗi lokacin da Larry ya fita da ita. Ya yaga ya sake ɗaure ƙafar sosai.

"Are you Ok?" Ya tambaya yana kallonta.

Girgiza kai ta yi ta ce nagode.

Bayan minti shabiyar aka kawo mu su abinci, ko kallon wajen Farida ba ta yi ba duk da kuwa yunwar na cinta.

"Ki tashi ki ci abinci" ya faɗi lokacin da ya ga ta share abincin.

"Ba zan ci ba. Wataƙila ma sun sa magani"

Zuwa yai ya ɗau take away ɗaya da ruwa ya kawo gabanta. " ba abinda za su sa aciki, because they need us alive. Besides na san yunwa ki ke ji"

Ta kalleshi ta kalli abincin ta ce " to kai ma ka ci, tunjiya ba abinda ka ci"

"Na saba da rashin cin abinci"

"Ana sabo da yunwa ne?" Bai amsa ma ta ba sai sokalin abinci da ya kawo dai-dai bakinta ya ɗaga ma ta kai alamar ta ci. Ba tai musu ba ta fara ci. Haka ya dinga bata abincin a baki har ta cinye.

"Kin ƙoshi?"

Ta gyaɗa ma sa kai...

Da dare zazzaɓi ya rufeta, tsoratar da tayi da kuma ciwon da taji su suka haɗu su ka sa mata ciwon kai da zazzaɓi.  Tana kwance ta fara rawan sanyi harda kakkarwa. Daga inda ya jingina ya jiwo nishinta.

"Miss Salihu are you OK?"

Jin shiru ya sa ya taso ya je wajenta. Jikinta yai zafi sosai ga ba ruwa balle ya dinga shafa ma ta.
A hankali ya ɓalle buttons ɗin shirt ɗin sa ya mannata da ƙirjin sa. Thats the only option he can think of...

Ta jima a haka kafin zazzaɓin ya saketa amma bai janyeta daga jikinsa ba har bacci ya tafi da ita. Shi kam ya manta yaushe rabon da yai bacci without his pills.

Farkawan da za ta yi ta jita ajikinsa. For the first time tun haɗuwarsu sai ta ji kunyar sa. Da ƙyar ta iya tashi, nan ma sai da ya tallafa ma ta saboda ƙafarta da ya kumbura yana ma ta zogi.

Suna buƙatar ruwa dan haka ya je ya fara bubbuga ƙofa.

"What do you want?" Aka faɗa da kakkausar murya.

"Water"

"Una no go get any water for here ooo"

" please, give Us some water" Najeeb ya rintse ido saboda tuno matsayinsa ada da kuma matsayinsa a yanzu wai shi ke roƙon ruwa.

Da ƙyar wanda ke gadin ƙofar ya kawo mu su ruwa biyu, nan ma sai da ya cire belt ɗin Najeeb wai itama designer ce idan ya sayar zai samu kuɗi...

Ƙarfe shabiyu na rana Emeka da Joseph su ka zo mu su da albishirin yau za a sake su idan har an biya cikakken kuɗin da aka buƙata.

A fili Farida ta ce " miliyan hamsin ɗin. Kai amma karayar arziƙi ta sameka Sir Najeeb"

Dariya ta bashi saboda bata san networth na shi a shekara ba. Ko za a cire miliyan hamsin sau goma ba zai girgiza ba. Balle ya san idan har da gaske za a biya waɗannan kuɗaɗe to Dad ɗin sa ne zai biya, ba sai ya nemi taɓa masa kuɗi ba.

"Kenan  za ka kori ma'aikata dayawa idan ka koma. Dan Allah kar ka kori ɗan uwana. Yakubu shi kaɗai yai degree a gidan Baffa Musa, kaga yayansa Faruƙu mai ƙaton hancin nan, ko sakandari bai gama ba, kasuwanci ya jona kaman na ubansa. Dan Allah ka min alƙawari ba za ka koreshi ba"

Murmushi kawai  Najeeb ya yi.

"Sir Najeeb ka ga yadda ka yi kyau kuwa da ka yi murmushin nan. Dan Allah idan an koma office ka dena haɗa ran nan, ba ka kyau"

Juyar da kai yai yana kallon gefe duk da kuwa hankalinsa na ga surutun da Farida ke yi...

........................

Har za a tashi Dad ya ce ayi addu'a.
Aka ɗaga hannu aka yi addu'a sannan aka shafa.

Anas ya ce Dad " Insha Allah ko mi zai tafi according to plan"

"Allah ya sa Anas"

Anas ya kalli sauran officers ɗin ya ce "gentlemen, let's go"...

Emeka yana zaune da Joseph su na jiran Larry da ya tafi ɗauko kuɗi. Tun ɗazu aka ce an ajiye kuɗi a inda su ka buƙata.
Sun gargaɗi Larry akan ya tabbatar ba wanda ke binsa lokacin da ya ɗau kuɗin, shi ya sa ma su ka ce yana tabbatar da kuɗin na cikin jakar to ya sa jakar a ƙatuwar jakar Ghana-must-go da su ka bashi.

Minti biyu sai ga kiran Larry. Emeka ya sa ihu lokacin da Larry ya ce ya ɗauka kuɗin. Ya kalli Joseph ya ce "Bros we are rich"

Plan ɗin da su ka shirya shine, dama suna da mota, a daren za su bar Kano shi kuma Joseph saboda Najeeb ya ganeshi suna barin Kano daga Kaduna zai wuce ƙasar Ghana. Anan zai zauna har komai ya lafa kafin ya dawo.
Suna cikin tattauna plan ɗin su Larry ya shigo da jakar kuɗi.

Da sauri Emeka ya buɗe jakar ya ce su duba kuɗi sannan su duba ko akwai tracker aciki dan a matsayinsa na wanda ya kwana biyu yana aikin yasan ana iya samun wannan idan aka aiko da kuɗin ransom. Ganin babu tracker ya sa su ka fara jera kuɗin a wata jakar daban.

Abinda ba su sani ba shine sai da aka buɗe jakar aka sa ƙaramar tracker chip aciki sannan aka ɗinke kamar ba a sa komai ba.

Su Emeka na duba kuɗi sauran na shan giya suna ihu su ka ji kamar ana buɗe ɗaya daga cikin ƙofofin gidan.

Emeka ya ce su je su duba ko su Najeeb ne ke son guduwa.

"Larry, you sure say nobody follow you"

Larry ya gyaɗa ma sa kai.

Fitar sauran ke da wuya su ka ji ƙaran bindiga...


"Shi kenan, Sir Najeeb kashe mu za su yi. Ga shi sun fara harbin junan su"  Farida ta faɗi kamar za ta yi kuka ta kuma matsowa kusa da Najeeb ɗin.
Shi Najeeb ya gane abinda ke faruwa dan ƙaran bindigan ba iri ɗaya bane.

Jin ana shirin buɗe ƙofa. Najeeb ya kalli Farida ya sa yatsunsa biyu a baki alaman ta yi shiru...

Joseph ne ya buɗe ƙofar ɗauke da bindiga,yana shigowa bai gansu ba zai juya kenan aka kwaɗe kan sa daga baya, sai bindigar ta faɗi, yai taga-taga zai faɗi shima Najeeb ya kuma jawoshi ya gwara shi da gini. Ƙiɓar Joseph ya ke kamar wanda aka aiko shi.
Wani police ne da Anas su ka shigo ɗakin lokacin da Farida ta ga Anas ta ce "Alhamdulillah ashe ku ne"

Najeeb kam yana kan Joseph yana ƙiɓar sa sai da Anas da police su ka zo su ka ɗaga shi, dan tuni Joseph ya suma jini na fita ta hanci da baki...

Da ɗingishi ta ke takawa lokacin da su ka fito, komai ya lafa, Anas ya ce mu su an kashe ɗaya daga ciki sauran kuma duk an kamasu. Emeka da yake ogansu ma an halbeshi a cinya.

"Miss Salihu" muryarsa ya doki kunnenta, ta tsaya da tafiya sannan ta juyo a hankali. Kafin ta yi magana ya sa hannu ya ɗauketa cak.
Mamaki ƙarara ya bayyana a fiskarta. Anas da ke gefe ma mamakin ne ya kamashi.

Kai tsaye motar Anas ya nufa da ita sai da ya kwantar da ita a backseat sannan ya dawo gaba ya shiga, Anas ya ja su su ka bar wajen.

Suna cikin tafiya Anas ya ce "asibiti za mu je ko gida"

"Asibiti" Najeeb ya faɗi a hankali....

Ƙarfe goma da rabi su ka baro asibitin bayan an duba ƙafar Farida. Ganin an yi wata hanya da ba ta gidan su ba ya sa ta ce " Ya Anas ka kaini gida ina so na ga Ummi na. Na san tana chan hankalinta ya tashi"

Anas ya ce " ai su Baffan na ki su na gidan su Najeeb"

Ba ta sake cewa komai ba har su ka isa gidan su Najeeb.
Ana jin tsayuwar mota gaba ɗaya aka fito dan dama duk iyalen gidan a matse su ke. Baffa Musa, Yakubu da Ya Faruƙ su ma suna nan suna jiran dawowarsu. Dama tunda abin ya faru su ke sintiri tsakanin gidan su Najeeb. Ummi ta so ta biyosu Baffa Musa ne ya hana...

Najeeb ne ya fara fitowa da sauri ya buɗewa Farida ƙofa ya taimaka ma ta ta fito duk da kuwa yanzu ƙafar ta rage zogi.

Baby ce ta fara zuwa da gudu ta rungume Najeeb kafin sauran su ka ƙaraso.

Baffa Musa abinda bai saba ba yau ya yi. Shima zuwa yai ya rungume Farida yana hamdala. Ita kaɗai ce ɗiyar ɗan uwansa, ita ya ke gani ya tuna da ɗan uwansa.

Daga compound ɗin gidan Baffa Musa ya ce za su wuce gida. Dad ya ce su bari sai da safe tunda dare ya yi. Baffa ya ce " Alhaji ai idan ban kai 'yar nan wa uwarta ba, uwarta za ta iya haɗiyar zuciya. Bari mu tafi kawai"
Musabaha su ka yi da Dad sannan su ka wuce wajen na su Motar. Yakubu ne ya tallafa ma ta har su ka isa wajen motar Baffan...

Idan ka cire yara ƙanana duk sauran kowa idon sa biyu saboda jiran dawowar Farida. Su Baffa ba su iso gida ba sai sha biyu saura na dare.

Su ma ɗin daga bakin gate aka taresu. Farida ta rungume Ummi tana kuka Ummin ma na yi. Da kyar aka raba su.

Wanka da ruwa mai zafi ta yi, ta gasa jikinta sosai, ta jima a banɗakin dan kwana biyu kenan ba wanka. Tana fitowa Ummi ta sa ta a gaba da abinci. Allah na gani bacci ne yanzu a idonta ba abinci ba amma da Ummi ta takura dole ta zauna za ta ci.
Ummi ta ƙarɓa cokali ta fara ba ta abincin a baki. Hakan ya sa Farida ta tuno lokacin da Sir Najeeb ke ba ta abinci, haka kawai sai ta tsinci kan ta da murmushi.*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Free page*

0️⃣1️⃣0️⃣

Tana tsaye jikin balcony na gidan tana kallon mai yankan flower  wanda ke faman gyara flowers ɗin gidan, ya saƙalo hannunsa ta ƙugunta sannan ya manna ma ta kiss a wuya ya ce "do you like it?"

"Gidan yai kyau sosai. Its perfect" ta amsa ma sa

Juyo da ita yai ya ce"This is our home Aysherh"

Murmushi ta yi ta manna ma sa light kiss sannan ta ce "our home is beautiful my love"....

A hankali ya buɗe idonsa wanda su ka ma sa nauyi saboda gajiya, ya rufesu saboda hasken da ya karaɗe ɗakin yaiwa idonsa ƙarfi. Ɗan wasu daƙiƙai ya ɗauka kafin ya sake buɗe idon a karo na biyu.
Lokaci guda kuma mafarkin da yai ya dawo ma sa. Da sauri ya tashi zaune saboda tunowa da yai da abinda ya gani a mafarkin. Agogo ya duba ya ga ƙarfe shaɗaya na safe, kenan ya jima yana barci. Idan ya tuna da kyau to ba maganin bacci ya sha ba jiya. Ya shigo ɗaki, ya taking hot shower ya sanya jallabiya ya gabatar da sallar maghrib da Isha, kaman yana azkar bacci ya tafi da shi. To wa ya maidashi kan gado? Ya janye tunanin ta hanyar tashi ya shiga banɗaki...

Fitowar da zai yi bayan ya shirya cikin ƙananun kaya baƙar shirt da guntun wando baƙi na jeans ya haɗu da Mom tana haurawa sama.

"Son ya jiki?" Ta faɗa a hankali

" lafiya Justice" ya faɗa ba tareda ya kalleta ba.

Mom ta bishi da ido tana haɗiye wani abu mai ɗaci da ya taso ma ta tun daga wuya.

Adama ya samu tana goge-goge a falo.

"Hey ina baby?"

"Sir ta tafi makaranta"

"Dad fa"

"Yana waje"

Fita yai daga falon dan ya san inda zai samu Dad ɗin.

A wajen gazebo da ke garden ya samu Dad, yana zaune yana karatun littafi.

"Come here son" Dad ya faɗi lokacin da Najeeb ke ƙoƙarin zama a ɗaya kujeran.
Zuwa yai ya tsugunna a gaban Dad, Dad ya manna ma sa peck a goshi ya ce "Allah ya ma ka albarka"
Najeeb ya amsa da Amin

"Ya jikin na ka?"

"I'm fine Dad"

"Allah ya ƙara sauƙi"
Dad ya ajiye littafin ya fara bayani

"Ka ga irin abinda na ke gaya ma ka ko. Joseph ya ce korarsa da ka yi shi ya sa shi ɗaukan wannan mummunan mataki a kan ka. Ɗa na, ka dinga danne zuciyarka kana haƙuri da mutane, Allah ya baka ɗaukaka da daraja ne domin ya jarrabaka. Su wanda su ke ƙasa da kai akwai haƙƙin su akan ka kuma Allah zai tambayeka ranar gobe"
Ƙaran wayan Dad ne ya katse hirar ta su. Yana ɗauka ya ce " to muna shigowa"

"Najeeb, Hajiya ce ta zo. Mu shiga ciki"

Ba mu su ya tashi su ka jera da Dad ɗin.

Hajiya Mama da kan ta ta yiwa Najeeb girki ta kawo, wai dole sai ya cinye dan ta san bai ci abinci ba a chan. Haka ta tisa shi a gaba yana cin abinci tana tambayarsa gameda kwana biyun da yai a hannun su Joseph. Mom na gefe tana kallon su, kwaɗayin wannan dama da ta rasa ta ke yi, hira tsakanin uwa da ɗa.
Ko sai yaushe Najeeb zai ba ta dama ta gyara kura-kurenta na baya?...

........................

Da yamma Yakubu ya kawowa Farida wayarta wanda aka samu a gidan da aka tsaresu duk da kuwa an yarda sim ɗin ciki.

"Anas ya ce zai zo ya gaishe ki bayan sallar isha"

"Allah ya kawoshi lafiya" ta faɗi tana cin farfesun kayan cikin da Ummi ta haɗa ma ta...

Tana sallar Isha aka kira wayar Maijiddah. Maijiddah ta duba numbar ta ja tsaki ta ajiye wayar gefe.
Kwana biyu kenan Aneesa matar AbdulWahab tana damunta da kira da texts, ranan da ta fara kira ba irin ɗibar albarkar da ba ta ma ta ba. Gashi ita ba mai iya maida magana bane, haka ta gama zagin ta kashe wayar. Lokacin jimamin rashin Farida ya sa ba ta wani damu da abinda Aneesar ke ma ta ba.

"Matar AbdulWahab ce ta kira ki ko?"

Maijiddah ta gyaɗa kai.

"Ban wayar na bata amsar maganganunta"

Maijiddah ta langwaɓe kai ta ce " Anty dan Allah ki barta. Idan ta gaji za ta bari"

"Hmmm a tarihin rayuwata ba na gani in ƙyale dan haka bani wayar kawai"

Maijiddah ta miƙo wayar dan ba yadda ta iya.
Bugun farko ba a ɗauka ba sai a na biyu.

"Assalamu Alaikum Uwargida ran gida, da fatan kina ta shirye-shiryen zuwan amarya?"

Daga ɓangaren Aneesa ta ce " who's this?" Dan muryan bai yi kama da na Maijiddah ba wacce ranan farko da ta kirata haƙuri ta dinga ba ta.

"Aisha Farida ce, yayar Amarya Hauwa Maijiddah. Na kira ne in gaya mi ki kar ki kuskura ki sake kiran ƙanwata saboda naga alama ƙwaƙwalwar kifi ce a kwanyar ki"

"Ke! ƙaramar karuwa ki kiyayi bakin ki. Ki kuma ja wa ƙanwar ki kunne karta yadda ta shigo gidana"

"Ashe ke Jaka ce, daƙiƙiya, Tinkiya mai kamar Aladu. Har kin isa ki hana Jidda zuwa gidan ki. Idan ba kwartonci ba, mijinki na Lagos kin maƙale a Abuja wai ke sarkin aiki. To tunda ke bakisan yadda ake riƙe miji a tarairayeshi ba, shi ya samu wacce za ta zauna kusa da shi ta kula da shi. Kuma wallahi wallahi ki ja girman ki ki dena kiran ƙanwata ko kuma mazaunanki su yi tsami"

Yadda Farida ke magana da faɗa-faɗa ya ƙara tunzura Aneesa.

"Ke matsa chan jahila mai kama da...."

Farida ba ta bari ta ƙarisa ba ta amsa da cewa " ke ce jahilar ai. Kwartuwa mai bin gindin maza, Allah ya wadai da halin ki. Tir da ke Aneesa mai ƙaton baki. Hooooo ashewo....Hoooo ashewo" (ashewo- karuwa)

Aneesa ta yi saurin kashe wayar saboda zuciyarta da ke bugawa da ƙarfi-ƙarfi.
Wannan wace irin yarinya ce haka, lallai kuwa Maijiddah za ta ci ubanta idan ta shigo ma ta gida. Sai da ta gama banbamin bala'i sannan ta dubi screen ɗin wayarta ta sa hannu ta shafa lips ɗin ta.
"Ko wa yace ma ta ina da babban baki? Ba dai AbdulWahab ba"...

Farida na jin an kashe wayar ta sa dariya ta ce " ƙaramar 'yar iska, da ki tsaya ma na"
Ta kalli Maijiddah da ta yi zuru-zuru da ido
"Ke kuma ki cigaba da yin shiru-shiru har wannan matar ta sa mi ki ciwon zuciya. Gara ki ɗaure ɗamara dan wannan matar da alama 'yar tasha ce"

"Sannu Malama Farida, expert a ɓangaren rashin mutunci"

"Kai Yakubu ba na son iskanci fa"

"Ki fito Anas na jiran ki a waje"

Gyale kawai ta yafa ta fita bayan ta gayawa Ummi. Gaishe shi ta yi lokacin da ta shiga motar na shi.

" 'yar uwa ya jiki"

"Da sauƙi yaya na"

" ashe ba ƙaramin jin jiki ku ka yi ba. 'Yar uwa ya abin ya faru ne? Najeeb ya ƙi ya bani labari"

Dama abinda ta ke jira kenan ta fara karanto ma sa yadda abin ya faru. Labarin da tun safe ta ke faɗawa 'yan gidan su da maƙota da ke zuwa gaisuwa.
Abu ɗaya ta ƙi faɗa wanda ita kanta duk yawar maganarta ta rasa dalilin ƙin faɗar da ta yi. Ta ƙi faɗin cewa Joseph ya tofa wa Najeeb miyau.

Sai da ta gama ba da labarin Anas ya ba ta wani envelope ya ce "wannan daga Najeeb constructions ne. Kuɗin magani"
ya miƙa ma ta wani envelop ɗin ya ce " wannan kuma Dad ne ya baki, kuma ya ce na gaishe ki da jiki"

"Kai na gode sosai, ka miƙa godiyata wajen Daddy dan Allah. Najeeb constructions kuma sai mun zo mu ku sallama"

"A'a, 'yar uwa sallama kuma. Ba dai aikin za ki bari ba"

"Eh yayana, zan ajiye aiki da ku"

"Gaskiya ban yarda ba. Ai hutu kawai za ki yi na sati zuwa kwana goma ki dawo bakin aikin ki"

"Ya Anas Ummi na ba ta so, ta ce na ajiye aikin"

"No Farida, Najeeb needs you. Ki ba wa Ummi haƙuri ta barki ki dawo dan Allah"

" to bari mu ga ni dai. Na gode Yaya"

Sai da za ta fita daga motar ta ce " Ya Anas ya jikin Sir Najeeb?"
" da sauƙi ƙanwata" ya faɗi yana murmushi...

Ita ɗin ma da ta shiga gida sai ta ji kamar ba za ta iya haƙura da aikin ba. Musamman idan ta tuna bikinta da Rayyan zai iya kaiwa wata shida ma su zuwa...

Washe gari su ka wuce Jos ita da Ummi bayan ta yi welcome back ɗin layinta.

.....................

Yana zaune a kujerar sa yana duba wasu files amma  hankalin sa na kan wayar sa, jira ya ke ya ga ko an turo ma sa saƙo. Sai yanzu yai da na sanin ƙin bin Anas da yai ranan. Ko ba komai da ya ganta ya tabbatar lafiyar ta ƙalau.

Duk da ya san ba ta da numbar da ya tura saƙon. Ya ja dogon tsaki ganin har awa ɗaya kenan da tura saƙon na shi amma ba amsa, saboda ka da ta gano shi ma ya sa ya ke rubuta saƙonnin da Hausa. Da ya gama duba files da takardun da ke gaban sa ya tashi ya fita a office ɗin. Ganin kujerarta wayam ba kowa ya sa shi jin wani abu a zuciyar sa, ba dai da gaske barin aiki za ta yi ba. Kai tsaye office ɗin Anas ya wuce wanda ba nisa da na shi office ɗin.

Waya ya samu Anas na yi lokacin da ya shigo, ya samu waje ya zauna yana kallon sa.

"Miss Salihu ta bar aiki ne?" Ya faɗa da harshen ko in kula lokacin da Anas ya gama wayar.

"Ka fara kewar ta ne?" Anas ya amsa ma sa

"Oh please, ka amsa min tambayata ba na son shirme"

Dariya Anas yai sannan ya ce " well, ta ce za ta dawo amma sai Monday"

"Monday is too far"

"Mutumina da alama ka ƙagu ka ganta ko?"

Tashi Najeeb yai ya ce " idan ba ta dawo Monday ɗin ba, ka nemo min wata sakatariyar"

Anas ya ɗan yi dariya ya ce " kamar da gaske"......

...........

Ghana-must-go manya guda biyu ne a gabanta tana faman jera kayan gwanjo da ta saro da za ta kai Kano.

Adiyya wata jikar Nanna ta miƙo ma ta waya wai ana ta kiranta tun ɗazu.
Amsa wayar ta yi ta ranƙwashi kan yarinyar wadda ba za ta wuce shekara takwas zuwa tara ba. "Na hana ki ɗaukan wayata ba kya ji ko. Yanzu jiba yadda kuka cinye min chaji"

"Allah Anty ba ni kaɗai bane har da Mubashshir, shi ne ya ke game, ni kallon hotuna kawai na ke yi" yarinyar ta faɗa tana shafa wajen da Farida ta ranƙwasa.

Duba wayar ta yi ta ga missed call ɗin Maijiddah ne da na sister Munibat sai saƙo guda ɗaya wanda wani number ya turo. Numbar na yawan damunta da saƙo tun lokacin da ta yi welcome back ɗin layinta. Ta buɗe saƙon ta karanta kamar haka.

* Fatan ki na lafiya Aysherh? Ina so ki yadda da ƙaddarar da ta same ki, ki ɗauke shi a matsayin jarrabawar Ubangiji. Zai fi  ki koma al'amuran rayuwar ki kamar da, ba tareda wani tsoro ba. N J*

Tsaki ta yi ta ce " shi wannan N J ɗin sai shegen naci, ka kira ba za ka kira ba, sai gatan tura saƙo kamar kamfanin Airtel."

Ta tura masa reply kamar haka *" Malam NJ ko Mr NJ, koma wa ka ke dai, ina ma ka gargaɗi da ka dena turomin saƙo, saboda ni matar aure ce. Idan ka cigaba kuwa duk inda ka ke, mijina zai nemoka kuma ba za ku wanye lafiya ba"*

Sai da ta tura saƙon ta ke ƙara alhinin wannan NJ ɗin wanda take tunanin ƙila cikin abokan Yakubu ne da su ke aiki tare a Najeeb constructions. Idan ba haka ba ta ya NJ zai san an kidnapping ɗin ta har ma ya san ta ji ciwo a ƙafa. Ƙafarta ya fara tambaya ranan da ya fara turo saƙonsa wanda kuma ta san idan ba Yakubu da Anas ba ba wanda ya san ta ji ciwo a wajen aikin su. Ta kawar da tunanin ta hanyar kiran Maijiddah dan ta ji mi ye labari...

Yana zaune ya ji ƙarar shigowar saƙo. Ya ɗauki waya ya duba, sai da ya karanta sannan yai murmushi dan ya san yanzu kam ta samu lafiya tunda har ta iya ma sa reply.

.........................

Yau sammako yai a office dan ko mai shara ba ta yi aikinta ba lokacin da ya shigo. Fakewa yai da cewa wasu ayyuka zai ƙarasa a office ɗin lokacin da Najdah ta tambayi dalilin fitarsa da wurwuri haka. Duk da kuwa dama shi ɗin mai fitar wuri ne amma na yau daban ne...

Har ƙarfe takwas da rabi ba ita ba alamarta. Haka dai ya ke aikin na shi ba tareda samun kwanciyar hankali ba...

Tun takwas saura ta zo, ta fara biyawa tana tallen gwanjon da ta saro a office-office da ke hawa na farko da na biyu. Sannan ga uwa uba labarin kidnapping ɗin su da ta ke bayarwa ga duk wanda ya ma ta jaje.  Ba ta ankara ba tana office ɗin sister Munibat ta ga ƙarfe tara har da kwata.

"Kai ashe haka lokacin ya tafi barin je na kama aiki kafin Sir Najeeb yai ƙuli-ƙulin Kubra da ni"...

"Najeeb na samo ma ka wani secretary, he's a good guy idan ka amince zai fara aiki gobe"

Ya kalli Khalidah kallon ki na da hankali kuwa.

"Ban sa ki wannan aikin ba.  Idan ina buƙatar secretary na san inda zan nema"

"Najeeb, sati ɗaya kenan wancar shashashar ba ta zuwa. Na san abinda ya faru ne ya sa ta ƙi dawowa, ni wallahi da da su...."

"Out"

"Najeeb.."

" i said get out"

Khalidah ta kai maƙura wajen ɓacin rai amma ba yadda ta iya dole ta kwantar da kai idan tana son samun Najeeb.

"Shi kenan zan fita amma ka yi tunani"

Tsaki ya ja sannan ya cigaba da aikin da ya ke akan system ɗin sa.

Shigowar Farida kenan Khalidah ta fito daga office ɗin Najeeb.

"Ina kwana Anty" Farida ta faɗa dan abinda ta ke kiran Khalidar da shi kenan idan tana son tunzurata. Khalidah irin matan nan ne da Allah yai wa baiwar jiki da tsayi.

" da kin rufawa kan ki asiri kin bar aikin nan da zai fi mi ki, dan ni Khalidah sai na sa Najeeb ya kore ki daga aiki"

"haba Anty! daga zuwa na. Ba ga ruwa balle ya hanya?" Farida ta faɗi tana farfari da ido.

Khalidah tai tsaki ta tafi...

"Sir Najeeb Ina kwana" ta faɗi lokacin da ta shigo office ɗin sa. Bai ce komai ba bai kuma ɗago ba.

"Miss Salihu you are late"

" na san ba ka son latti Sir, a min afuwa na yau ne kawai"

Sai a lokacin ya ɗago idon sa ya kalleta.
Shigar riga kalar maroon ta yi sai wando kalar ash da jacket shima kalar ash, ta yi ɗaurin turban da ɗankwali kalar maroon.

"Sir Najeeb ka gama kallon da kyau. Duk haɗuwar da na yin nan gwanjo ne ajikina, grade one ma kuwa. Kuma akwai irin su-irin su da na saro ko da za ka ɗaukawa ƙanwar ka ko..."

"Miss Salihu, go back to your office" ya faɗi yana sauke idon sa

"Haba Sir, ba sannu, ba ya jiki, ba..."

Wani file ya miƙa ma ta ya ce " ina son aikin nan cikin minti goma"

Ƙarɓan file ɗin ta yi a hannunsa tana kumbure-kumbure har ta fice daga office ɗin...


*NB: free page zai ƙare @pg 15 Insha Allah,  ga mai so zai iya biyan kuɗin karatu kafin lokacin.*

*ga mai son cigaban labarin zai biya #200 kacal ta wannan account ɗin 3099546325 Azizat Hamza, firstbank. Idan kuma credit card ne to MTN card na 200 za a turo wa wannan numbar 08137311900. Sannan za a turo shaidar biya (screenshot) na kuɗin zuwa numbar nan still 08137311900. Ko kuma ka biya #300 ka samu labarai biyu sakatariya ta da kuma tsohuwar soyayya**💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Free page*

0️⃣1️⃣1️⃣

*Na fara typing shafin nan na tuno cewa akwai wata 'yar uwa da ta yi ƙorafi lokacin ina typing labarin Duk kyan namiji, akan cewa na rage saka turanci cikin rubutu na saboda kasancewarta 'yar Niger ba ta iya turanci ba. Kamar yadda mu ka sani ƙasar Niger ta samu 'yanci daga ƙasar Faransa ne, shiyasa su ke amfani da yaren French saɓanin mu 'yan Nigeria da mu ke amfani da turanci. To Insha Allah zan gyara, idan ma na saka dogon turanci, to zan fassara Insha Allah. Da fatan makarantan mu na Niger za su dinga haƙuri da mu ( kuma fa da su ma za su yi rubutu su dinga sako french sai dai mu baza idanu kawai😁 ko kuma mu koma browsing abinda aka rubuta) Niger readers muna yin ku sosai*



A kishingiɗe ta ke a kan kujerarta bacci ya sace ta. Tun ƙarfe goma da ta gama aiki ba abin da ta ke yi, chatting ta ke yi a waya baccin ya sace ta.

"Miss Salihu...Miss Salihu" ta yi firgigit ta farka. Kallon  sa ta farayi tana murza ido.

"Biyo ni"

Kafin ta wartsake ta tattara office ɗin tuni ya fita.
A hawa na farko ta sameshi yana yiwa wasu bayani. Anas ne ya ce ma ta yana ƙasa, dan da ba ta san inda yai ba.

Tana tsaye tana ƙoƙarin saita kan ta saboda har lokacin ba ta gama wartsakewa ba ta ga yai hanyar parking lot na kamfanin. Da sauri ta bi bayan shi tana jiran ƙarin bayani amma bai ce komai ba. Sai da su ka iso wajen motar sa ta ce "Sir fita za mu yi ne?"

"Shiga mota" abinda ya iya cewa kenan. Sai da ta zauna da kyau sannan ta kalleshi ta ce "Sir  da ka gayamin fita za mu yi ai da na ɗan gyara fiskata ko. Yanzu ko ɗan hodan nan ban ƙara tisawa fiskata ba, fiskata ta yi wani bauu"

" Miss Salihu ina so ki sa a ran ki cewa wannan kamfani ba fashion industry ba ne inda ake gudanar da fashion shows. This is a constructions comp...."

"Daɗina da kai Sir Najeeb akwai wasge mutum. Kuma dan ina aiki a kamfani irin wannan sai ba zan yi ado ba. Yanzu idan a yamutse na ke fitowa kai kan ka ba za ka ji daɗin aiki da ni ba, balle ma su zuwa wajenka kullum"

"Miss Salihu..." ya faɗa da ɗan ƙarfi

"Sir Najeeb ina neman alfarma dan Allah"

Ɗan juyowa yai ya kalleta na ɗan daƙiƙai sannan ya maida hankalin sa ga tuƙin da ya ke yi.

"Sir dan Allah ka dena kirana da Miss Salihun nan. Shi fa Salihun nan yana chan kwance cikin kabari amma ka dinga kirana da sunan sa. Ga Aisha ga Farida duk bai maka ba, sai ka kirani da Salihu" ta ɗan yi ƙasa-ƙasa da murya ta ce "Salihun ma fa a hoto kawai na ganshi ban ganshi a zahiri ba, amma abi a dameni da Miss Salihu Miss Salihu"

Wannan karan muryarsa a kausashe ya ce " our relationship is strickly formal Miss Salihu. So ba abinda zai sa na kira ki da first name na ki"

"Abin ai son kai ne. Ita sister Munibat ai Miss Munibat ka ke kiranta ba Miss AbdulHamid ba. Ga wancan ƙatuwar nan Khalidah, itama sunan ta ka ke kira. Sai ni ne za a raina a dinga wani yaɓa mani Miss Salihu kamar wata marar suna. Gaskiya Sir ka dinga kirana da suna na nima"

"Or what?" Ya faɗi yana kallon ta

"Sir ni dai ka gyara dan Allah"

Bai sake cewa komai ba har sai da su ka iso inda za su je. Ya ce ta fito kuma ta kimtsa kan ta baya son yawan surutu. Wani ɗakin taro ya shiga ya barta a reception wai ta jira shi.

Kusan awa ɗaya yai a wajen sannan ya fito.  Tunda su ka bar wajen su ke tafiya tun tana shiru-shiru har dai ta kasa jurewa ta ce "Sir Najeeb wai garin za mu bari ne kam?" Bai kulata ba sai ma ƙara volume ɗin kiɗan da ke tashi a motar da yai.
Haka ta haƙura ta yi shiru har su ka isa wajen. Tana fitowa a mota ta fara miƙa tana cewa " kai! yau na zaunu gaskiya. Irin wannan nisan waje haka"

Wani site ne da kamfanin su ke ginawa ya zo dubawa. Bayan zaunuwa to Farida ta taku domin kaf wajen sai da su ka zaga duk girman shi. Su kan tsaya da wasu ma'akata yai mu su tambayoyi da 'yan bayanai. Anan ta ke ɗan rubuta wa su abubuwa kamar yadda ya buƙata.

Ƙarfe uku sai ga kiran Anas ya shigo wayar sa. Lokacin su na hanyar dawowa. Yana ajiye wayar ya kalli Farida da ta yi lanƙwas a motar ya fara faɗa.

"Miss Salihu are you nuts?"
(Miss Salihu kin yi hauka ne?"

"Kin fixing meeting da Mr Abraham ƙarfe uku ba tareda kin gayamin ba a wani dalilin?"

"Sir, ba ka ce min za ka fita ba ai. Kuma mantawa na yi"

"To hell with mantuwar ki. Miss Salihu, akwai dubban mutane da su ke neman aikin nan, idan ba za ki yi aiki da kyau ba zan kore ki"

Shi kan sa sai abin ya zamo ma sa banbaraƙwai wai 'zan kore ki' ba ma 'na kore ki ba' kamar yadda ya saba faɗi.

"Sir Najeeb dan Allah ka dena ɗaga min hankali, dududu yaushe na dawo aiki bayan wannan iftila'in da ya sa me mu. Irin wannan rashin godiyar ne ya sa wallahi aikin nan ke fita min a ka. Ga shi mutum duk ya fiffige saboda aiki amma ba ka gani. Ni mutum ce kuma ba abun aibi ba ne ace na yi mantuwa tunda yana kan kowa"

Yana son maida ma ta martani amma ya rasa me zai ce. Yawan maganarta shi ne abu na farko da ya ja hankalinsa ranan da ya fara ganinta a restaurant, haka nan har yau bakin nan na nan. A kowani lokaci tana da abin faɗi choichoichoi. Tunowa da yai da kama su da aka yi da irin surutun da ya sha, ya sa ya san wannan Aisha Faridan a ko ina sai ta yi magana ba ta iya yin shiru......

............................

Tana zaune tana typing memo Anas ya shigo office ɗin ta.
Sir Najeeb ya jima da fita kuma a yadda ya ce ya tashi kenan saboda  zai daɗe. So ta ke ta ƙarasa abinda ta ke yi ta tafi itama duk da kuwa ƙarfe biyu ne saura. Ciwon cikin period ke damunta tun safe shiyasa ta ke nan laƙwas ba kuzari sosai duk da kuwa ta sha magani ya lafa ma ta kaɗan.

" 'yar uwa yau ba zoɓo ne? Kin san i'm addicted to your zoɓo"

" Ya Anas ban yi ba yau. Ni zoɓon ma zan dena gaba ɗaya tunda Sir Najeeb ya nuna indai na cigaba da sana'a a office to cikin albashina"

"Ya Najeeb zai ma na haka kuma?"

"Hmm kaman ba ka san shi ba, watan da ya wuce da ya zare 40% ai har yau shiru ka ke ji. Wai jiya Halima tana duba gwanjo anan da ya shigo ya gani haka ya dinga faɗa har da cewa wai ya ƙara ganin na buɗe hajata a office zai cire 10% a cikin albashina. Kuma fa ya Anas lokacin break ne ba wai a lokacin aiki ba"

Anas yai murmushi ya ce " kin fara gajiya da shi ne Farida? Ko za ki bar aikin?"

"Yaya kenan. Ni fa idan ka ga na ajiye aikin nan to aure na yi, na gano take-takensa ai, dama so ya ke na yi wani abu ya koreni. Mutum sai shegen taurin rai"

"Well, ni na ga alamun tun fara aikin ki da shi ya  chanja, he's becoming more tolerant now. Allah! Farida da Najeeb ɗin da ne da tuni kin bar aiki a nan"

"Hmm shi ya sani, wai ace mutum yai ta haɗe rai shi kaɗe ya ƙi shiga jama'a. Ai jama'a Rahama ne"

"Kowa da irin rayuwarsa 'yar uwa"

Har zai fita ya ce " ki ji har na manta. Akwai baƙin da za su zo gobe wajen Najeeb, ki scheduling lokacin meeting da su sannan ki sanarwa Najeeb on time kar ayi irin ta ranan"

"Ai ranan na sha kwarwa. Allah, Ya Anas na ɗauka mari na zai yi yadda ya dinga banbamin nan"

"Sai ki kiyaye"...

Yana fita ta cigaba da aiki, tana so ta ƙare ta tafi gida da wuri dan kar ta yi staining dan ba ta zo da pad ba, ta ajiye a bakin gado za ta sa a jaka ta manta shi a wajen.

Minti ishirin ta haɗa komai sannan ta turawa Najeeb lokacin meeting ɗin sa ta email. Tana kan tattare kayanta Halima ta shigo.

Halima Baballe tana aiki a hawa na ɗaya ne a HR department. Halima irin matan nan ne ma su gutsuri tsomi, 'yan haɗa waje. Bazawara ce aurenta biyu tana fitowa. Tun farkon zuwan Farida ta ke ƙoƙarin manne ma ta sai dai Faridan ba ta bata dama ba. Yawanci su ka haɗu a masallaci haka za ka ga tana liƙewa Farida tana kawo gulma da zunɗen mutane duk dan ta samu fada a wajen Farida tunda Farida sakatariyar Sir Najeeb ce, kuma kusan kowa a kamfanin yana son samun kusanci da Sir Najeeb.

"Anty nah Anty nah, ba dai kin tashi ba" ta faɗi tana washe baki

"Zan tafi gida, Sir Najeeb ba zai dawo ba kuma na gama aiki na"

"Sai na ga kin min wani lakwas, lafiya kuwa?"

"Halima yau ba na jin magana. Mi ya kawo ki?"

" Anty na kenan, baƙon wata ya zo kenan"

Farida ta yi tsaki ta saƙale jakarta a kafaɗa ta ce " mi ya kawo ki?"

"Anty na, za a yi bikin 'yar yata nan da sati biyu kuma wallahi adashen da na ke jefawa akwai mutum uku a gabana kafin na amsa shine na zo ko za ki ara min kuɗi?"

Kallon sama da ƙasa Farida ta ma ta sannan ta ce " kar ki kawo min rainin hankali nan wajen. Yaushe mu ka haɗa hanya da ke da har zan ba ki aron kuɗi na?"

Halima ta yi dariya tareda ɗan dafa kafaɗar Farida ta ce "ƙawata kenan..."

"Cire hannun ki a jikina tukunna" Farida ta katse ta

" duk yadda na ɗauke ki da zuciya ɗaya amma ke har yau ba ki ɗauke ni haka ba. Ita Sister Munibat ɗin da ki ke maƙalewa an gaya mi ki son ki ta ke? Kwanaki fa har cewa ta yi ke 'yar ƙwaya ce"

"Dalla gafara daga nan. Ba na son munafurci, halin ki na haɗa guri ya sa ba na son mu'amala da ke, idan da ba ki sani ba ki sani"

Halima ta ɗan haɗa rai ta ce " na rantse da Allah Munibat ta ce wai ke 'yar ƙwaya ce"

Farida ba ta ce komai ba ta ce biyo ni.
Tiryan-Tiryan su ka wuce office ɗin Sister Munibat inda ta ke ta faman aikin zane.

"A'a Sister Aisha ke ce tafe, ban ganki a masallaci ba ko lafiya?"

Farida ta kalli Sister Munibat sannan ta kalli Halima ta ce " maimaita abin da ki ka faɗa a office ɗina"

Halima ta ji ras dan ba ta ɗauka abinda Farida za ta ce ba kenan. Ta ɗauka su na zuwa za ta fara yiwa Sister Munibat masifa.
Sai dai kamar yadda ta ke pro a wannan ɓangare sai ta dake, ta kalli Sister Munibat ta ce " cewa na yi Sister Munibat ta ce ke 'yar ƙwaya ce"

"Astagfurullah" Sister Munibat ta faɗi da sauri tana yin wiki-wiki da ido tana ƙara cigaba da istigfari a zuciyarta.

Farida ta ce " to kin ji mi tace?"

Kafin sister Munibat ta yi wani magana Halima ta amsa da cewa " za ki ce ba ki faɗi haka ba, ranan a masallaci. Idan kin manta ni ban manta ba"
Ta ƙarasa maganar tana matsowa kusa da ita kamar za ta maketa.
Jikin sister Munibat ya fara ɓari musamman da ta tuno abinda ya faru.

"Kin gani ai ta ka sa magana saboda ta san gaskiya ne, munafuka, kina jikinta kina zaginta"

Farida ta kalli sister Munibat ta ce " ki faɗa min gaskiya. Kin faɗi haka ko baki faɗi haka ba?"

Sister Munibat ta buɗe baki za ta yi magana sai hawaye.

"Shikenan! Kukan munafurci. Dama yare, yare ai sai a hankali, dukkan su munafukai ne"

"Yi min shiru" Farida ta daka ma ta tsawa. Ta kalli sister Munibat ta ce " kin bani mamaki. Ina ɗaukan ki da daraja ina mugun mutuntaki. I consider you an older sister"

Ta juya ta fita saboda ba ta da ƙarfin yin masifa.

.......

Ƙarfe bakwai na yamma sai ga sister Munibat a gidan su Farida. Duk hayaniyar da ake na lissafe-lissafe a tsakar gidan, Farida ba ta ciki. Ƙarshen sati aka ce za a kawo lefen Maijiddah.
Tana chan kwance ta gama murƙususu akan gado saboda ciwon ciki. Maijiddah na gefe tana yiwa wata ƙaramar ƙanwarsu kitso.

"Anty Farida ga ƙawarki ta zo" Sadiq ya faɗa lokacin da ya faɗo ɗakin da gudu

Da ƙyar  Farida ta ɗaga kai lokacin da sister Munibat ɗin ta shigo ɗakin su.

Sai da su ka gaisa da Maijiddah sannan ta zauna a gefen gado ta fiddo da ƙur'ani izub sittin ta ce " Sister Aisha na riga na yi alwala kafin na taho. Zan rantse mi ki akan abinda ya faru ranan da sister Halima ta ke faɗi"

Farida ta ɗan tashi jingine ta ce " bai kai har ga haka ba 'yar uwa. Ke dai ki gyara halin ki, zato zunubi ne ko da da gaskiya a cikinta. Sannan ki sani saka dogon hijabi ba shine ke nuna taƙawa ba"

"Na rantse da Allah sister Aisha ba abinda na faɗa ba kenan. Ranan da ba ki zo ba  farko-farkon fara aikin ki, inaga lokacin bikin gidan kun nan ne. Ana taɗi shine aka kawo maganarki, cikin maida zance sai na ce *' sister Aisha kam wani lokaci idan ta yi wani abu kamar 'yar ƙwaya'*. Na rantse da Rabbil Arshi iya abin da na ce kenan"

Ta ja numfashi ta ce "dan Allah ki yafe ni sister Aisha"

"Ba komai, ya wuce. Sai ki kiyaye gaba, ki dinga taka tsantsan da mutane, dan abu ɗaya za ka ce ace ka faɗi goma. Ita kuma Halima Baballe gobe sai na ci ubanta tunda haɗi ta ke son yi tsakanin mu"

"Kin yafe min?" Ta tambaya kamar za ta yi kuka

"Wallahi na yafe mi ki, nima ki yafe ni" Farida ta faɗa tana ƙara kwanciya akan gado...

............................

Washe gari ko office ba ta shiga ba ta biya office ɗin su Halima ta je ta ma ta wankin babban bargo, a yadda ta tsara ma ko rabi ba ta ma ta ba saboda har lokacin ba ta warke be. Sai da ta gama silleta sannan ta wuce office ɗin ta. Tana zuwa ta samu Sir Najeeb ya zo sai dai ko da ta shiga bai ma ta magana ba kan latti da ta yi ba. Ta lura tun jiya da ya zo ya ke wani shiru-shiru kamar akwai abinda ke damun sa. Sai dai ta ja bakinta dan kar ya sauke matsalar sa akan ta.

Yau Jumu'ah kuma yau ne za a kawo lefen Maijiddah da yamma. Da ke ranan Jumu'ah ana tashi ƙarfe uku ne maimakon huɗu da aka saba shiyasa ta ke ganin za ayi komai da ita.
Da murnan ta ta shigo kamfanin, yanzu kam ba kasafai su ke zuwa tareda Yakubu ba.

Tun daga shigowarta ake ma ta wani kallo ana ƙus-ƙus sai dai ba abinda ya dameta tunda ba akan kowa ta ke ba. Lifter ta shiga ya kaita hawa na uku.

Abin mamaki sai ta ga Anas da Yakubu suna magana a office ɗin ta, ga  Khalidah a gefe tana yamutse-yamutsen fiska.

"Sannun ku dai. Lafiya na ga wajen ya ɗau hayaƙi, Ya Anas me ke faruwa?"

Kallon tsana ya ma ta ya ce " na ɗauke ki a matsayin ƙanwata ashe kallon da ki ke min kenan?. Farida ashe za ki iya jefanmu da wannan mummunan ƙazafi. A dalilin me?
You know what?  kafin ma Najeeb ya koreki ni na koreki, ba ma buƙatar mai hali irin na ki a wannan kamfani" ya shige office ɗin Sir Najeeb cikin fushi.

Mamaki, fargaba da tsoro ya cikata. Cikin rashin fahimtar kalaman Anas ta ce " Yakubu mi ya faru? Mi na yi?".....

*NB: free page zai ƙare @pg 15 Insha Allah,  ga mai so zai iya biyan kuɗin karatu kafin lokacin.*

*ga mai son cigaban labarin zai biya #200 kacal ta wannan account ɗin 3099546325 Azizat Hamza, firstbank. Idan kuma credit card ne to MTN card na 200 za a turo wa wannan numbar 08137311900. Sannan za a turo shaidar biya (screenshot) na kuɗin zuwa numbar nan still 08137311900. Ko kuma ka biya #300 ka samu labarai biyu sakatariya ta da kuma tsohuwar soyayya**SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Free page*

0️⃣1️⃣2️⃣

"Asirin ki ya tonu, Munafuka 'yar matsiyata. Yau dai dole ki bar aiki anan tunda an koreki" Khalidah ta faɗa tana murmushi.

"Yakubu mi ya ke faruwa ne, mi na yi da har Ya Anas ke faɗin maganganu marasa daɗin ji haka?"

Anas ya miƙa ma ta wayar sa ya ce "ki kunna ki saurara"

Ta amsa wayar ta kunna recording ɗin ta fara ji.

Muryar mace ce ke magana tana faɗin

*"kinga Oga Najeeb ɗin nan, babban ɗan luwaɗi ne. Kin san a ƙasar waje ya taso, so ya jima da zama gay, shi ya sa ma ya ƙi aure har yanzu. Ance fa ya kusa kaiwa 40yrs amma ba aure. Hmmm wani abin al'ajabi da na gano shi ne.... Amma kar ki faɗawa kowa fa, Halima. Oga Najeeb da Anas su na neman junan su, a yadda na jiyo ma, wai sun yi aure a sirrance. A office su ke haɗuwa su ci amarcin su.  Ni Farida da ki ke ganin nan na taɓa kallon su sunayi da ido na. Bakiga yadda Anas ke zama boyi-boyi ba a gaban Najeeb , ai saboda shi ne matar Najeeb kuma mijin. Shi Anas fa ba wai son shi ya ke ba kawai kuɗinsa ya sa ya amince. Kin san Anas ɗan maigadin gidan su Najeeb ne"*

"Innalillahi. Yakubu ba muryata ba ne wannan. Wallahi ba murya ta ba ce"
Farida ta faɗa kaman za ta yi kuka.

"Ki ji ƙarya. Lokacin da ki ke hiran da Halima Baballe duk ta yi recording komai dan ma kar ace ƙarya ta mi ki. Kuma kin ji da kunnen ki"

Farida ba ta ce komai ba ta fita daga office ɗin da sauri.

.........

Lokacin da Anas ya shiga office ɗin Najeeb kuwa samun shi yai tsaye jikin window.

"Abokina ka yi haƙuri dan Allah, ban taɓa sanin Farida za ta iya faɗin maganganu haka ba. I'm so dissappointed in her. Kar ka damu, dana koma office ɗina zan typing takardar korarta"

"No need" Najeeb ya faɗi a hankali

"Ban gane ba? Kana nufin ba za a koreta ba kenan?"

Najeeb ya juyo ya kalleshi ya ce " ba muryarta ba ne. Its a trick"

"How?"

" ba muryarta ba ne, ba kuma yadda ta ke magana ba kenan."

Anas yai shiru saboda kansa ya ɗaure. Najeeb ya sake playing ma sa recording ɗin wanda Khalidah ta tura ma sa da sassafiyar yau tun ma kafin ya zo office.

Sai da ya gama ji Najeeb ya ce "barin ba ka satar amsa. Miss Salihu ba ta kirana da *Oga Najeeb*"

"Shit. Kuma fa haka ne" Anas ya faɗi ya na  buga goshin sa da taffin hannun sa.

"Kafin Miss Salihu ta fara aiki anan, i know her voice"

"Wallahi na tafka shirme Najeeb. Barin je na bata haƙuri"
..............

Farida na isa office ɗin su Halima ta samu tana tsaye da wasu tana mu su bayani kan recording ɗin da su ka ji. Farida na zuwa ta yaficota ta wanke ta da mari, kafin ta ankara ta ƙara ma ta na biyu. Kafin ka ce me sun kaure da kokawa...
Ruwan cikin Halima Farida ta zauna tana kirɓanta. Halima na ihu. Da ƙyar mazan da ke wajen su ka janye Farida da ga kan Haliman.

"Ku sake ni na ci uban shegiya annamimiya. Ku sake ni na watsar ma ta da haƙora shegiya Munafuka"

Halima ta samu ta tashi tana rufe hancinta wanda ke fidda jini jikinta na rawa.

Kici-kici ta ke tana ƙoƙarin ƙwacewa. Ana ba ta haƙuri amma ina sai masifa ta ke.
"Ku bar ni na nuna ma ta banbancin da ke tsakanin mu"

Tana  ƙwacewa ta yi kan Halima da gudu. Ta ɗaga hannu za ta kai ma ta duka aka riƙe hannun. Ta fara ƙoƙarin yakice hannunta amma ta kasa saboda riƙon da aka ma ta. Ta yi ta yi still ta ka sa dan haka ta juyo
"Ka sake ni na dak......" ta tsaya lokacin da ta ga Sir Najeeb ne riƙe da hannunta. Sake hannun yai ya ce " Miss Salihu to my office"

Ta juyo ta kalli Halima ta ce " wallahi ba ta tsaya anan ba. Sai na je har gida na ci ubanki, shegiya dama halin munafurcin da ya hanaki zaman gidan miji kenan"

Yakubu ya ɗauko ma ta gyelen ta da ke yashe a ƙasa ya miƙa ma ta. Wafcewa ta yi da ƙarfi tace " kai kuma zamu haɗu a gida"

Wucewa ta yi ta bar wajen tana cigaba da zage-zage....

Kai tsaye office ɗin Sir Najeeb ta wuce ranta cike da masifa. Ta san ba makawa takardar kora zai ba ta sai dai wannan karan za ta karɓa za ta bar Najeeb constructions amma sai ta wanke sunan ta.

Kaman ba abinda ya faru haka ta ganshi yana zaune yana duba wa su takardu.

"Sir Najeeb, na san ka ji abinda aka ce na faɗa amma ka sani ba muryata ba ce wallahi, ba ni ba ne"

Ɗagowa yai ya kalleta ya ce " Miss Salihu, let it be the last time da za ki maida Kamfanina wajen faɗa"

"Sir Najeeb, wallahi a liƙa min sharri kam ba zan zauna haka ba. Kowaye sai na ci kutumar uban sa, hakan ma sai hukuma ta shiga tsakani. Haka kawai dan an sanni da yawar surutu sai a kwaikwayi muryata a faɗi abin da ban faɗa ba"

Kafe ta da ido yai yana gani tana banbami kaman za ta ci babu.

Miƙa ma ta file yai ya ce " take this file to Anas, kuma ki sanar da Admin na HR inada zama da su anjima"

Mamaki ya kamata. Ta haɗiye miyau ta ce " ba korata za ka yi ba?"

"Ki na so na kore ki ne?"

Ta yi saurin girgiza kai ta ce " ba ka ji recording ɗin nan ba ne"

" muryan ki ne?"

" wallahi ba ni bane" ta faɗa da sauri

"Good.  Then get back to work"

Ta ɗau file ɗin ta ce " wani lokaci idan ka yi abu kaman Salihin mutum, Sir Najeeb"

"Miss Salihu!"

Ai da sauri ta bar gaban shi tana dariya.

...........

Zuwa ta yi ta ajiye file ɗin a table ɗin Anas ta juya za ta tafi saboda ba ta son ko haɗa ido da shi.

"Aisha dan Allah ki tsaya"

Ai dama jira ta ke yai magana ta fara masifa " Ya Anas dama zumuncin kenan, idan na yi laifi a tureni gefe kamar wata kayan wanki balle ma banyi laifi ba. Iya zama na da ku yau wata ɗaya da sati uku amma har ka ji a zuciyarka zan iya maka ƙazafi, ai ba zama mai kyau ake ba kenan..."

"Dan Allah ƙanwata ki yi haƙuri. I was blind by anger, maganganun sun girgizani sosai to the extend na ka sa ma tsayawa na lura cewa ba muryan ki bane. Im really sorry ƙanwata"

"Ba wani, kai dai tabarmar kunya kawai ka ke son naɗewa da hauka. Ni ka ma barni na faɗi abinda ke raina dan abinda zai sa na huce kenan"

"To faɗa ina jin ki"

Yadda yai maganar sai ta ɗan ji kunyar sa.

"Shikenan Ya Anas na haƙura amma tsakani da Allah na ji haushin abinda ka yi min"

"Dan Allah ki yi haƙuri my ƙanwa"...

Farida na komawa office ɗin ta ta ji saƙo ya shigo wayarta tana buɗewa ta ga numbar NJ, ta yi tsaki sannan ta buɗe saƙon

*bai kamata ki watsar da kan ki ta hanyar yin dambe da wacce ba ta kai ki daraja ba Aysherh, kin fi ƙarfin haka. Ko kin manta ke matar aure ce ..... N J*

"Mtsww, wannan NJ ɗin ma wallahi sai na binciko shi a wannan kamfani, mutum sai shegen na ci, kai ba za ka kira ba idan kuma an kira ba zai shiga ba" ... ta ajiye wayar ta cigaba da aikin da ta ke.


..............

Turo ƙofar aka yi da ƙarfi. Najeeb ya ɗago ido da sauri  don ganin wannan mai karambanin. Farida ma da ke jera wasu files a shelf ɗin Najeeb ta juyo da sauri.

"Najeeb wanni walaƙancin ne wannan? Ga wacce ta ma ka sharri amma ba ka ɗau mataki a kanta ba sai Halima. Ka manta Wannan Jakar har dukan Halima ta yi. You're supposed to sack her"

" ina ganin ba ki shiga office ɗin ki ba har yanzu. Go back to your office akwai saƙo da na sa aka ajiye mi ki"

"Najeeb i'm serious bai kamata ka kori Halima ba she didnt deserve it"

Ko kallonta bai yi ba ya ce " ki je office ɗin ki ki duba saƙona"

Ta juya a fusace ta bar office ɗin.
Farida ta fara dariya dan ta san saƙon, tunda ita ya ce ta typing suspension later ɗin Khalidan.
Ganin dariyan na ta ya ƙi ƙarewa ya sa ya daka ma ta tsawa.
"Miss Salihu!"

"Sorry Sir" ta faɗi tana ƙoƙarin gimtse dariyan...

Ta gama abinda ta ke amma ta fake dan tana son ganin reaction ɗin Khalidah idan ta dawo.
Ai kuwa sai ga Khalidan ta zo a rikice.
Ta cilla wa Najeeb takardar hannunta tana faɗin " Najeeb explain this"

" ba ki iya karatu ba ne ko me?"

"Najeeb one month suspension a kan me?"

Shiru yai bai kulata ba.

"Najeeb a wani dalilin za ka min haka"

Still Najeeb bai yi magana

"Najeeb magana fa na ke. I'm calling my Dad right now"

Tana ƙoƙarin kiran mahaifin na ta ta ji Najeeb yana magana.

"Alhaji Tukur na bawa 'yar ka Khalidah Siraj Tukur suspension na wata ɗaya, ko kana da ja akai?"

Saboda wayar a handsfree ta ke sai kawai Khalidah ta ji Babanta yana cewa "ba ni da ja My Engineer. Komai ka yi dai-dai ne"
Najeeb ya sa hannu ya katse kiran ko ɗagowa bai yi ba balle ya ga yadda Khalidah ta taƙune fiska.

"Shikechar inji wani almajirin mu. Asha hutun wata ɗaya lafiya ko, dama ance idan za ka gina ramin mugunta ka gina dai-dai kai" ta ƙarasa maganar tana dariya

Khalidah ta zo gaban Farida ta nunata da yatsa ta ce " sai na ga ƙarshen ki Farida, you'll see"

"Allah raka taki gona Anty Big"

Tsaki Khalidah ta ja sannan ta fice a office ɗin.

Tana cikin dariya Najeeb ya daka ma ta tsawa.

"Get out"
Simi-simi ta fita a office ɗin sa.

..............

An kawo lefen Maijiddah kuma ba ƙarya AbdulWahab ya kashe kuɗi wajen haɗa kayan nan.  A wajen ƙarɓan kaya ma Farida ta ka sa ta tsare dan ganin komai ya tafi dai-dai.

Anty Hanne ƙiri-ƙiri ta nuna kishinta a fili saboda kayan da akaiwa Maijiddah ko rabinsa ba aiwa 'ya'yanta da aka aurar ba.
Baaba Sabuwa kam farin ciki fal ranta.

Ranan sunday da dare AbdulWahab ya zo yiwa Maijiddah sallama da ke ya zo weekend.
Farida ce ta tsarawa Maijiddan kwalliya ta kuma zaɓa ma ta kayan da za ta sa.

Falon Baffa Musa aka saukeshi. Wannan zuwan sa gidan kenan na biyu tun haɗuwar su.

Tareda Farida su ka zo bayan sun gaisa da shi sannan ta fita ta basu waje.

"Ina yini" ta faɗa a hankali dan ita har yanzu ta kasa sake jiki da shi.

"Lafiya gimbiya ta"...

Hiran na su yawanci shi ya ke maganar dan Maijiddah kam kunya ta hanata sakewa.

Ya ɗan taɓa abinda aka kawo ma sa sannan ya tashi akan zai tafi.

"Allah ya tsare hanya, ya kai ka gida lafiya. Ka gaida su Baby da Alizah"

"Amin tawan. Shikenan gimbiya ba wani ɗan abu da za ki bani"

"Abban Alizah mi ka ke so"

Ɗan matsowa yai kusa da ita ya riƙe hannunta ɗaya yana ɗan murzawa. Ya sa hannu ya saukar da gyalen da ta yane kan ta da shi sannan ya tufke ɗankwalin,
warware gashin da ta tufke yai sannan ya fara shafa gashin wanda ya zubo har tsakiyar bayanta ƙanshin man da ta shafa wanda ke fitar da ƙanshin mint leaf kaman kuma lemon grass. Ya kai hancinsa yana shaƙar ƙanshin.
Hannunta da ke trembling cikin na sa da kuma yadda bugun ƙirjinta ya ƙaro saboda closeness na su ya sa ya saita kan sa yai gyaran murya bayan ya miƙe tsaye sannan ya ce " Allah ya kaimu kwana ashirin da tara gimbiyata"....

....................

Yakubu ta sa ya ciro ma ta kuɗi bayan ta ga cikakken alert ɗin ta wannan karan Sir Najeeb bai cire komai ba.
Karfe goma saura kwata ta shiga falon Baffa dan bai jima da dawowa ba, sai da ta ba shi lokaci kafin nan ya ci abinci.
Ɗan gefe da shi ta zauna suna gaisawa.

"Baffana na kai na. Allah ya ja zamaninka ya ƙara ma ka lafiya amin"

"Amin 'yar Baffa"

Hannu biyu ta sa ta miƙa ma sa kuɗi. "Baffa a sa mana albarka"

" wannan bai yi yawa ba Farida"

"Baffa na so ya fi haka ma sai dai ka san mu mata sai a hankali, kuɗin na wa na sayo gwanjo da su kuma ban gama haɗa kan kuɗin ba"

"Allah ya miki albarka Farida" ta amsa da amin.

"Dubu hamsin yai yawa Farida, ba dai duka albashin na ki ki ka kawo ba?" Baffa ya faɗa lokacin da ya gama irga kuɗin.

"A'a Baffa"

Shiru ne ya biyo baya na minti biyu kafin ta ce " Baffa dama na ce tunda wannan shekaran ka yi bikin su Salima ga na Jiddah nan da wata ɗaya mi zai hana nawan a barshi wata shekaran kaga kafin nan ka tara wani abu"

" A'a Farida, idan na yi haka na ci amanar mahaifin ki. Duk cikin 'ya'ya na ba wadda ta wuce shekara ashirin na aurar da ita, Maijiddah ce ma har ta kai ishirin ɗin. Idan ba ƙaddara da ta faɗa miki ba ai da tun shekaru uku da su ka wuce anyi bikin ki"

"Baffa Allah ba matsala ka bari irin watan uku na wata shekara sai ayi kafin nan komai ya dawo normal"

"A'a Farida ko da duka gonakaina zan sayar dan na samu kuɗin yi miki aure zan sayar. Ai idan na bari wata shekara sai duniya ta zageni. Idan ba su iyayen yaron sun ce bai gama shiryawa ba ai da tareda Maijiddan zan haɗaki"

"Baffa dai" ta faɗa kaman za ta yi kuka.

"Tashi ki je ki kwanta. Allah ya kaimu watan December"

"Baffa nikam..."

"Tashi na ce" ya faɗa da ɗan ƙarfi.

Ta tashi tana guna-guni ta bar falon.

Sai da ta fita Baffa ya ƙara godewa Allah domin halin Salihu na kyauta kam Farida ta ɗauko, dan lokacin yana raye bashida rowa ko kaɗan, zai iya bayar da abu shi ya rasa kuma hakan bai dame shi ba...

................

Lagos

Ranan Monday da safe ya isa Lagos, kai tsaye office ya wuce kasancewa dama shi ɗaya ya je ya bar su Alizah a gidan maƙocin sa kuma abokin aikin sa Mr AbdulRazaƙ.
Bai ɗauka Aneesa za ta zo ba tunda ya gaya ma ta zai je Kano kuma zai bar yaran a wajen maƙota.
Ƙarfe takwas da rabi na dare ya isa gidan Mr AbdulRazaƙ dan ɗauko yaranshi. Sai dai da ya je ake ce ma sa Aneesa ta zo ta ɗauke su.
A take a wajen ya kira Aneesa amma ba ta ɗauka ba. Hankalinsa bai tashi ba sai da ya je gida mai' aikin su ta ce Aneesa ta wuce da yaran Abuja. Yai ta kiran numbar Aneesan amma ba a ɗauka. Ƙarshe dole ya kira numbar ƙaninta Nazir  ya ce ya kaiwa Aneesa.

Minti biyar sai ga kiran Aneesa a wayarsa.

"Wannan wanni irin iskanci ne Aneesa za ki ɗauke min yara ba tareda kin sanar da ni ba"

"Iskanci kuma AbdulWahab, Ni da 'ya'ya na. For your information, kai da su Baby sai ka janye maganar auren ka. Ko kuma su zauna tare da ni anan amaryarka ta haifa ma ka wasu"

"Anny kin san yaran nan suna Makaranta fa"

"And so, zan sa su a wani anan"

"Look Aneesa, ki maido min da yarana gobe-goben nan ko kuma..."
Ƙiiit ta kashe kiran.*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Free page*

0️⃣1️⃣3️⃣

Kwana biyu Aneesa ba ta turo ma sa yaran ba dan haka dole ya kira Alhaji, mijin Maman Aneesan kenan, ya ma sa bayanin komai shi baya ma gari dan haka bai san su Alizah na gidan sa ba. Ya jima yana yiwa Aneesa faɗa akan ta ajiye aiki ta je ta zauna da yaranta amma ta ƙi. Kasancewa Maman ta ba ta bashi goyon baya ba shi ya sa yai shiru ya zuba mu su ido. Ya auri Hajiya Salma ne lokacin Aneesa na da shekara goma shabiyu ƙaninta kuma na shekara tara. Bai taɓa banbanta su da 'ya'yan sa na cikin sa ba,   makaranta mai tsada su ka yi da ta gama sakandare ya turata karatu ƙasar waje. 

Aneesa ta haɗu da AbdulWahab ne a cikin jirgi, daga Lagos za ta wuce Abuja. Sun kusan shekara biyu su na soyayya kafin su ka yi aure saboda dagewa da Aneesan ta yi akan za ta yi masters kafin ta yi aure. Bayan sun yi aure ta fara aiki da wani Kamfani a Lagos. Shekaru biyu da su ka wuce Kamfanin su ka buɗe wani branch a Abuja kuma su ka nemi Aneesa ta koma wajen. Ƙarin matsayi da albashi su suka ruɗi Aneesa ta tsallake mijinta da 'ya'yanta ta wuce Abuja. Abdulwahab ya yi faɗan ya yi fishin amma duk a banza. Haka ya kira Maman Aneesan ya mata bayani akan ba da yawunsa Aneesa ta koma Abuja ba. Buɗan bakin Maman sai ta ce "AbdulWahab idan ta ajiye aikin za ka iya ba ta dubu ɗari shida da hamsin a wata ne (650,000)?" Wannan maganar shi ya sa AbdulWahab ya sauke makaman yaƙin sa ya haƙura ba dan ya so ba,  sai dan inda ya ke ganin za a mata faɗan ma goyon bayanta ake. Bai faɗawa iyayen sa ba sai da ƙannensa su ka je ma sa hutu bagtatan su ka tarar Aneesa ba ta nan da farko ce mu su yai ta je gida ne kawai daga baya su ka gano komai, nan Hajiya Yelwa ta ce ba ta san zance ba ta ya za'ayi yana Lagos matar sa na Abuja wai sai ƙarshen wata za ta zo...

Alhaji yai waya ya ce maza  Nazir ya maida yaran Lagos. Kasancewa Aneesa ta fita wajen aiki sannan Mama ma ta fita ya sa ya ɗau yaran ba tareda wanni cikin su ya hanashi ba. Ya na samun tiketin jirgi sai Lagos. Baby da Alizah sai murna dan dama sun ƙagu su koma school sannan su ka Dad ɗin su.

...................

Shirye-shiryen biki ake ba kama hannun yaro, duk da dai abubuwan sun zo a tsukekken lokaci amma hakan bai hana Baffa ko Baaba Sabuwa yin ƙoƙari wajen yiwa 'yar su gata ba. Da ke AbdulWahab na da gida a Kano anan za a ma ta jeren kayan ta.
Farida kam abun ya haɗu ya ma ta yawa kwana biyu su na aiki sosai a kamfani da ke akwai wani sabon contract da Kamfanin ya samu ga kuma shirye-shiryen biki. Har ɗan rama ta yi saboda zirga-zirga. A cewarta Maijiddah tana da gidadanci ba kaman ƙannen ta da idon su ya buɗe ba, dan haka ta ke sa'ido akan komai saboda ayi komai na zamani...

Gulma kam a Najeeb constructions sai ma abinda ya ƙaru musamman da aka kori Halima sannan aka ba wa Khalidah suspensio.  Dayawa su na tafiya da cewa Najeeb da Farida su na soyayya ne musamman kasancewa har yanzu bai koreta ba duk da kuwa irin karya dokoki da ta ke. Sai dai duk gulman a bayan fage a keyi dan ba mai iya tunkaran Najeeb ko Farida. Irin dukan da Faridan ta yiwa Halima ma ya sa su ke tunanin ƙila Farida na da taɓin hankali...

Ɗan baccin da ba ta samu sosai cikin kwanakin nan saboda matsowar bikin Maijiddah shi ta ke yanzu a office. Sallaya ta shimfiɗa a ƙasa ta kwanta tana narkan bacci hankali kwance.

Ya kira telephone ba a ɗaga ba, ya kira wayarta still ba a ɗauka ba. Computer ɗin sa ya jawo ya duba ko ta fita ne sai ya hangota chan ƙasa tana bacci. Ya jima yana kallonta kafin ya tashi  ya ɗau key da wayarsa ya fita.

"Miss Salihu" ya faɗa da ɗan karfi lokacin ya tsugunna kusa da ita. Sai da ya kirata a na uku sannan ta tashi a firgice. Ganin shi tsugunne ya zuba ma ta ido ya sa ta ɗan goge fiskarta ta ce " sannu Sir Najeeb"

"Bacci a bakin aiki Miss Salihu"

"Yanzu sai ka ce acikin albashina. To ka yi haƙuri gajiya na yi"

Yadda ta yi maganar ya bashi dariya sai dai haɗa rai yai ya miƙe ya ce ta tashi za su fita.

Bin sa ta yi zuwa office ya nuna ma ta takardun da za ta ɗauka. Bacci bai gama saketa ba amma haka ta tattaro takardun ta biyoshi. Tsabar mugunta sai ya ƙi ya bi lifter ya bi stairs.
Suna saukowa ta fito da biro ta ɗan ƙara sauri ta caka ma sa biro a bayan wuyan sa. Hannu ya sa ya shafa wajen ba tareda ya juyo ba. Ƙaramar tsaki ta ja ta sake kai hannu za ta sake caka ma sa sai kuwa ƙiris ya juyo.
"Wayyo Allah na!....Wayyo!" Ta faɗi cikin ihu, ta zubar da files ɗin hannunta ta koma baya da gudu.

Irin yadda ya ga ta tsorata ta fita da gudu sai abin ya sa shi dariya. Sometimes ya kan yi tunanin yarinyar nan na da taɓin hankali...

Kai tsaye office ɗin Anas ta je. Tana magana tana haki ta ce " Ya Anas.... ka taimakeni... yau na tsokano tsuliyar dodo"

"Mi ya faru? Mi ki ka yi?"

Ba ta bashi amsa ba sai ma ta cigaba " wallahi ba zan sake ba. Ni ban ma san ya akayi na ma sa haka ba, dan Allah ka je ka bashi haƙuri"

"Me ki ka yiwa Najeeb"

Ta ɗan yi ajiyar zuciya ta ce "biro na chaka ma sa a wuyan sa"

"Biro" Anas ya maimaita sannan ya kwashe da dariya.

"Ya Anas ba dariya za ka yi ba fa, haƙuri za ka je ka bashi"

"Yanzu ke Farida a wanni dalilin za ki ma sa haka?"

"Kawai haushi na ji ya tashe ni a bacci kuma ya ce wai mu sauko ta stairs"

Cikin zuciyarsa ya ce "lallai Farida na jinjina mi ki"

A fili kuwa cewa yai " yanzu dai kin amince kin yi laifi?"

"Na yi. Wallahi na yi"

"Shikenan, mu je na same shi"

"A'a kai ka fara zuwa tukunna, ni zan jira ka anan"

"Ki zo mu je ba abinda zai mi ki"

Jiki a sanyaye ta bi bayan Anas su ka wuce office ɗin Najeeb.

A zaune su ka sameshi yana waya. Daga bakin ƙofa Farida ta tsaya dan idan ma wani abin zai ma ta za ta samu ta gudu da wuri. Anas ya ƙarasa wajen sa ya zauna yana ɗan dariya ƙasa-ƙasa.
Yana ajiye wayan Anas ya ce "Yallaɓai mun zo biko, ƙanwar mu ta yi laifi kuma ta gane kuskurenta. Ayi haƙuri"

Shiru yai na ɗan daƙiƙai sannan ya ce " ta gaya ma abinda ta yi?"

"Ta gaya min, kuma na ma ta faɗa sosai"

"Good, akwai psychiatrist da na kira yanzu, zai zo ya gwada min ita dan ban yarda da lafiyar ƙwaƙwalwar ta ba"

Daga inda ta ke tsaye ta ce " haba Sir Najeeb, psychiatrist kuma. Sai kace mai taɓin hankali"

Kallon Anas yai ya ce " idan aka tabbatar min da lafiyarta ƙalau, then she can work with me. Idan tanada matsala kuma sai ta je ayi treating ɗin ta, dan ba zan iya aiki da mahaukaciya ba"

"Sir ka rama abin da na ma ka idan haka ne" ta faɗi da ɗan ƙarfi

Shiru yai yana kallonta sai chan kuma ya ɗau biro ya miƙe tsaye. Tana ganin ya nufota da biro a hannu ta tsume, wai a dole ba ta damuba irin ta surrender ɗin nan. Sai dai saura taku kaɗan ya isota ta buɗe ƙofa ta fita da sauri.

Najeeb ya ce " you see, she's crazy"

Anas yana dariya ya ce " she's just funny. Dan Allah kar ka ma ta komai"...

Fitan Aisha Farida kam ai sai gida, dan ba ta yadda ta tsaya ba. Sai da ta je ta tuna ai ko wayarta ba ta tsaya ɗauka ba jakarta kawai ta ɗauka. Ta yi tsaki sannan ta yi amfani da wayar Jiddah ta kira Yakubu ta ce ya je ya ɗauko ma ta wayarta a office.

"Yanzu ke tafiya gida ki ka yi ba tareda an tashi ba, Sir Najeeb ya sani?"

"Ya sani mana, kai dai je ka ɗauko min wayata kawai"...

Najeeb ya fito daga office ɗin sa zai fita ya ji wayar Farida na ringing, ganin bai ga jakarta ba yai tunanin ta tafi ne. Zuwa yai ya ɗau wayar amma kafin ya ɗauka kiran ya yanke, take kuma aka sake kira sai ya ga sunan mai kiran an saving da *My Ray*. Tsaki ya ja sannan ya saka wayar a Aljihu ya fita.
Yakubu da ya zo bai ga waya ba ya kira Farida ya gaya ma ta. Ita kuwa ta rantse indai aka sace ma ta waya a Najeeb constructions to za ayi ƙaramin yaƙi dan kuwa ba za ta yadda ba sai an fito ma ta da waya...

..................

"Yanzu kinga wannan jakar, duk kayan ciki na ki ne. Na fi awa ɗaya ina zaƙulo waɗannan kayan a wajen ma su gwanjo. Wallahi ko manya-manyan boutique ki ka je ba za ki samu kaya ma su kyaun wannan ba, ai gwanjo rufin asiri ne. Sai ki samu kayan da har ki gama yayinsa ba za ki taɓa ganin irin sa ajikin wani ba"

Maijiddah ta buɗe jakar ta fara fiddo kayan da ke ciki. Duk wanda ta ɗaga sai ta yi saurin ajiyewa saboda yanayin kayan sun bata kunya.

"Jiddah ya na ga kina wani yanƙwane fiska kaman kin ga kashi?"

"Anty Farida wannan kayan ai...."

"Ai me? Na ce ai me?. Dan Uban ki ina siya mi ki mutunci kina cewa ke tsiya ki ke so. Wannan kayan da ki ke gani da su ake cin gari. Balle ke da ki ke da kishiya, kishiyar ma wayayyiya 'yar boko"

"To Anty kuma sai insa wannan kayan in fito?"

Wani kallon banza Farida ta ma ta sannan ta ce " idan kin ga dama ki sa, idan kin ga dama kuma ki ƙona su idan kin je chan. Ni dai na san watarana sai kin kirani kince Anty Farida zan iya samun irin kayan nan wallahi ko nawa zan biya ki nemo min su. Lokacin ni kuma sai na karɓi kuɗi mai tsoka a wajen ki kafin na nemo mi ki"

"Ki yi haƙuri Anty"

"Ba batun haƙuri ba ne Jiddah, so na ke ki waye ki shigo gari kema. Idan kin je kin mallake zuciyan maigidan gaba ɗaya. And Wallahi zan faɗa mi ki gaskiya ba da hijabi ko manyan kaya ake sace zuciyan miji ba"

"Anty Farida wani mai ƙatuwar mota yana kiran ki a waje. Maijiddah ke kuma wai inji Rashidan Bala wai za ta samu kitso?"

"Zo nan Sadiƙ" Farida ta faɗa tana kallon molelen kan yaron da ya sha aski.
Yana zuwa ta kama shi ta ma sa dundu uku a baya.
"Ban hana ku kiran Maijiddah da sunan ta ba? Eh. Mi na ce ku dinga ce ma ta?"

Yaron cikin kuka ya ce "Anty Maijiddah"

"Good boy. Yanzu ka je ka cewa Rashida, Anty Maijiddah ta dena kitso"

Yaron ya fita yana kuka yana ƙoƙarin sosa bayan sa....

Ba ta gane motar wayeba amma ta san koma waye to babba ne. Ba ta tunanin kuma Alhaji Hussaini ne, wanda ta haɗu da shi a wajen aiki ya zo wajen Sir Najeeb ya nace ya nemi numbarta, sai da ta sissilleshi sannan ya haƙura ya dena kiran ta.

Tana ƙarasawa jikin motar ta zagaya wajen driver ta ƙwanƙwasa glass ɗin saboda tinted ce ba ta ga wanda ke ciki ba. Ɗan sauke glass ɗin aka yi sannan  aka miƙo ma ta waya, tana ganin hannun ta ce "Sir Najeeb!"  sai kuma ta yi saurin rufe baki tunowa da ta yi da abinda ta yi a office yau.

Ƙarasa sauke window ɗin yai sannan ya ce " Miss Salihu karɓi wayan ki"

Ta yi saurin karɓan wayan sannan ta ce "na gode Sir" bai ce komai ba ya ja motar sa ya tafi...

"Kaman motar Sir Najeeb na gani ɗazu a ƙofar gida"

"Shine. Waya ta ya kawomin"

Da mamaki Yakubu ya ce " Sir Najeeb ɗin?

"Iyi"

"Sir Najeeb ya kawo mi ki waya har gida"

"To miye aciki, ni ba sakatariyar sa ba ce"

Shiru Yakubu yai yana tunanin ko dai gulman da ake yi a office gaskiya ne. To idan ba haka ba Sir Najeeb ɗin da ya sani a da kam bai damu da damuwar kowa ba, kan sa kawai ya sani. To idan kuma akwai abu a tsakanin su fa? Baba ya ce a ƙarshen watan December za ayi bikin Farida.
Farida ce ta katse shi da cewa "yawwa Yakubu ka san numbar nan?" Ta nuna ma sa numbar NJ. Ɗaukan numbar yai ya sa a wayarsa sai dai bai da irin numbar ma a wayarsa...

...................

Fitowar sa kenan daga wanka ya ganta zaune abakin gadon sa.

"What are you doing here?"

"Son, Kakan ka ya rasu da safiyar yau" ta faɗi cikin muryan kuka

"Allah ya ma sa rahama"

"Zan wuce Bahrain gobe. Za ka je?"

"i'm busy" ya faɗa a taƙaice

"Saboda ni ko saboda Sabreen ne ba za ka je ba"

"Enough Justice Nabilah. Ki fita min a ɗaki"

"Najeeb please" Mom ta faɗa kamar za ta yi kuka.

"Ke ko Sabreen, ba ku da wani matsayi da zai sa na yi abu ko kar na yi abu"

Hawaye ne ya gangarowa Mom ta yi saurin sharewa ta ce " sai yaushe za ka yafe mi ni"

"When you are ready to tell the truth"

"Najeeb!" Ta faɗa da ƙarfi.

"Oh, Justice ki na tsoron gaskiyan ne?"

Shiru Mom ta yi tana ƙoƙarin maida hawaye.

Sai da ya ga ta fice ɗakin sannan ya sauke numfashi, zama yai a bakin gadon lokaci guda jikin sa ya fara maƙyarƙyata, abinda ya gani shekaru ashirin da ɗaya da su ka wuce ya fara dawo ma sa. Duk yadda yai ya manta da komai ya ka sa. He was only thirteen amma yana iya tuna komai harta fiskar wanɗanda su ka ɗau gawan a ranan...

...............

Washe gari da wuri Farida ta je office ta ajiyewa Najeeb takarda a table ɗin sa.  Bai fi minti shabiyar da isowarta ba sai ga shi ya zo. Tana gaishe shi ma amma ko kallon ta bai yi ba. Sai da ta bashi minti biyar sannan ta bi bayan shi. Takardar ne a hannunsa lokacin da ta shigo.

"Sir na san na yi laifi amma ka yi haƙuri dan Allah"

Ya na so ya ma ta faɗa, ya na so ya nuna ma ta ko shi waye, amma ba zai iya ba saboda ransa da ke a ɓace saboda kuma...

Cillar da takardar ba da haƙurin da ta rubuto yai sannan ya ce " get back to work"

Ta yi mamaki da bai yi masifa ba ita kam hutarerenta ai. Har za ta fita sai kuma ta lura da yanayin sa kaman ba shi da lafiya ko kuma akwai abinda ke daminsa dan tsakanin jiya da yau ya chanja ma ta gaba ɗaya.

"Sir Najeeb ba ka da lafiya ne?"

"Get out Miss Salihu"

Simi-simi ta fita kar ma ta tunzura shi ya ce zai hukuntata.

Ya fara duba wasu takardu amma hankalinsa ya kau, tunanin kyakyawar fiskarta ya ke da murmushinta mai shiga zuciya. Ya missing ɗin ta sosai, *Aysherh* ya furta a hankali.

Ya na mamaki da Aysherh Farida ba ta da sanyi da haƙuri irin na Aysherh. Halin su ya sha banban duk da kuwa sunan su ɗaya....

***

Aisha Mustafah Jibo ta taso cikin soyayya da kulawar iyaye da 'yan uwanta. Kasancewarta kurmiya bai rage ma ta komai ba na jin daɗi a wajen iyayenta. Gata kam tana samu tun daga kan Alhaji da yayyanta ga uwa uba uwar da ta shayar da ita wato Hajiya Mama.

Karatu mai zurfi Alhaji Mustafah ke so Aisha ta samu saboda ya zamo ma ta gata ko ba sa raye, wannan ya sa ya turata ƙasar waje karatu wajen yayanta Adam. Komai cikin sauƙi Adam ya nema ma ta tundaga dreba zuwa ma su kula da ita a gida saboda shi da Nabilah ba zama su ke ba. Sabo mai ƙarfi ya shiga tsakanin Aisha da yaran Adam musamman Najeeb wanda ke da shekara tara a lokacin.  Kamar wata babbar yayarsu su ka ɗauketa hakanan itama ta kan zama yarinya acikinsu duk da ita ɗin ma ba wai ta girme su da yawa bane dan shekararta goma shabakwai.
Yaran da sun dawo daga makaranta su na maƙale da ita, za ka gansu da biro da takarda suna hira da Aisha ko kuma suna wasa. A hankali har su ka iya maganan kurame ya zamo idan za su yi magana ba sa buƙatar su rubuta sai dai su yi yaren kurame.
Shekaru biyu kenan da komawar Aisha wajen Adam. Duk hutun ƙarshen shekara ta ke zuwa gida amma su Alhaji da Hajiya Mama su na kawo ma ta ziyara lokaci zuwa lokaci. A wannan ƙarshen shekaran da ta je ta tarar Alhaji ba lafiya. Nan ta tubure akan ba za ta koma America ba sai dai ta zauna kusa da Baban ta.

Adam daga Belgium ya taho dubiyan Alhaji saboda a lokacin an maida shi chan. Zuwan sa kuwa ya tarar jikin Alhaji yai tsanani. Shi da su Sulaiman su ka fara yunƙurin yadda za a yi su turashi ganin likita a ƙasar waje sai dai shi Alhajin ya ce ba inda zai je. Ana gobe Adam zai koma Alhaji ya nemi alfarma a wajen sa duk da alfarmar ta zo ma sa bazata amma Alhaji ya fi ƙarfin haka a wajensa dan haka ba tareda ya ja ba ya amince. A yammacin ranan aka ɗaura auren Adam Usman Jibo da 'yar uwar sa Aisha Mustafah Jibo. Washegari ya koma saboda jikin Alhajin ya fara sauƙi dan an sallamoshi daga asibiti.
Kwana uku da tafiyar Adam, Alhaji ya rasu mutuwar da ta girgiza 'ya'ya da 'yan uwansa musamman Aisha.

Sai da aka yi da gaske kafin Aisha ta yarda ta koma karatu duk da kuwa ta san da auren Adam a kanta dan Alhaji ya gaya ma ta kafin ya rasu.

Larabawa da shegen baƙin kishi, tunda Adam yai wa Nabilah bayanin aurensa da Aisha sai ta tuɓure ma sa ta ce ita ba ta san zan ce ba. Sosai abin ya jawo rikici tsakanin su.
A da ba ta shiga harkan Aishan dan ba ta da lokacin ta amma tunda ta zamo matar Adam sai abin ya chanja, kullum cikin tsangwamarta ta ke. Ta kori dreba da mai kula da ita da Adam ya ɗauka ma ta, ta hana yaranta kulata amma Najeeb bai daina ba sai ma ƙara jin son Aishar da ya yi.
Lokaci guda Aisha ta chanja kullum sai ta yi kuka a ɓoye saboda indai Najeeb ya ganta cikin ɓacin rai to sai ya yi ta tambayar ta dalili haka shima ranan ba za a gane ma sa ba. 
Allah-Allah Aisha ta dinga yi ta gama makaranta ta bar mu su gidan ta koma Nigeria.
Shi Adam a nashi ɓangaren duk lokacin da ya zo yana ƙoƙarin ganin komai ya tafi dai-dai sai dai ita Aisha ba ta nuna ma sa tana cikin matsala haka nan Nabilah ma tana nuna komai na tafiya dai-dai.
Ganin ba abinda ya ke shiga tsakanin su ya sa Nabilah ta ɗan saki ranta kaɗan, sai dai shi a nashi ɓangaren ganin Aisha na karatu ya sa ya bari har sai ta gama tukunna ya tare da ita.

Wani hutu, Nabilah ta ɗau Najeeb da Najma ta wuce da su Bahrain wajen iyayen ta. Sai aka bar Aisha a gida.
Aisha tun tana tsoro har ta dena, kwana uku da tafiyar su Adam ya zo ya ɗauketa ya wuce da ita Belgium.
Ya kira Nabilah ne sai Najeeb ya ɗauka ya ke shaida ma sa ai sun bar Aisha ita kaɗai a gida kuma itama ta gama jarrabawarta.

A Brussels babban birnin ƙasar Belgium su ka sauka. Ba su tsaya ko'ina ba sai gidan shi. Haƙuri ya dinga ba ta na barinta da aka yi ita kaɗai.
Da dare ya zo dubata a ɗakin da ya sauketa sai ya samu tana kuka. Hankalinsa a tashe ya ce " Aisha mi ya same ki?"

Ya ɗauko biro da takarda ya ma ta rubutu. Ya miƙa ma ta biron akan ta rubuta ma sa amsa. Ta amshi biron  ta rubuta " ina so na je wajen Mama"

" ba kya son zama da ni ne? Kin tsane ni ko? Saboda ba na zama ina kula da ke" ta yi saurin girgiza kai bayan ta karanta.

Jawota jikinsa yai ya rungumeta sosai ya na ɗan bubbuga bayan ta a hankali har bacci ya saceta...

Wannan sati ukun da ta yi a Belgium cikin gata da kulawa ta yi su. Adam yana tare da ita koyaushe, harta office mafiyawancin lokuta da ita ya ke zuwa. Har 'yar ƙiba ta yi saboda kwanciyar hankali.

Da hutun ta ya ƙare ya maida ita lokacin su Nabilah sun dawo. Ita da ta dawo ba ta ga Aisha ba, ta ɗauka Nigeria ta wuce sai da ta ga Adam ya dawo da ita hankalinta ya tashi. Ta san yadda ta gansu akwai abinda ya shiga tsakanin su nan da nan ta nuna sai dai Adam ya rabu da ita ba za ta iya zama da kishiya ba ko kuma ya rabu da Aisha.

Rikici sosai su ka yi har ya ma fi na farkon lokacin da ya ce ma ta ya auri Aisha.
Ƙarshe ta ce za ta shigar da shi ƙara a raba auren tunda ba zai saketa ba. Ta chanja gida ta ɗau yaranta amma Najeeb ya gudo ya koma wajen Aisha.

Abu sai ƙara rikicewa ya ke, wata rana da ta zo ɗaukan Najeeb sai ta lura da ciki ajikin Aisha, wannan ya sa hankalinta ya kuma tashi. Ƙarshe ta shigar da Adam ƙara, ganin ya ba da haƙurin ta ƙi haƙura ya sa ya ma ta saki ɗaya dan mutum mai matsayi irin na sa ace yana hayaniya da matarsa a kotu ba dacewa bane...

Ma su aiki biyu Adam ya ɗaukawa Aisha dan su dinga kula da ita lokacin cikinta ya girma.

Lokacin da cikin ta ya shiga wata na takwas Hajiya Mama ta ce za ta zo ta zauna da ita, ta shirya zuwa sai aka ma ta rasuwa Babban yayan su ya rasu sai ta ɗaga tafiyar zuwa wa ta sati....

***

"Sir Najeeb, Sir Najeeb"

Muryan Farida ya dawo da shi daga dogon tunanin da ya ke.

"Sir ka na da meeting ƙarfe tara"

"Ok" kawai ya faɗi ya miƙe tsaye.

Yanayinsa kaɗai ya nuna ma ta akwai abinda ke damun Najeeb, kuma koma minene to yana da girma.*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Free page*

0️⃣1️⃣4️⃣

Tana zaune a office Faruƙ ya kirata wai gashi a kamfanin su.  Kwatancen office ɗin ta ta ma sa sannan ta ajiye wayar tana cigaba da aiki. Minti biyar kacal sai ga Yakubu da Faruƙ sun shigo.

"Farida haka yaron nan ya zama luƙeƙe. Kin san da farko ban ganeshi ba"

"Kai ma ka faɗa ai, wannan sai ya goyeni yai yawo da ni  duk faɗin garin nan bai gaji ba"

"Haba Anty, ɗan ni ɗin nan" Faruƙ ya faɗi yana dariya

Yakubu ya fita ya basu wuri, dama wajen Anas zai je ya haɗu da Faruƙ ɗin.

'Yan uwan biyu su ka zauna su na taɗi, su na yi su na dariya.

Wayar Farida ya ƙarɓa ya na duba hotuna. Ko ba a gaya ma sa ba ganin hotunan selfie da Farida ta yi da wani saurayi ya tabbatar ma sa shine Rayyan.

"Sis, wannan shi ne sirikin na mu ?"

"Kai ba na son gulma"

"Wallahi ba ku da ce ba,  wannan ai kin fi ƙarfinsa. Hmm ina tausaya ma sa wallahi, aka yi auren nan mijin ta ce zai koma dan ba zai iya da masifar ki ba"

"Buuuuyagi" wafce wayan ta yi tana faɗin " ka ji min rainin hankali, wato dai ni ka ke zagi ko" ta maki kafaɗar sa ta ce " Faruƙ yaushe ka raina ni haka?"
Yarfe hannu ta farayi shi kuma ya fara dariya. " jikin ka kamar wani katako, wai yaushe ka girma ne haka? Faruƙ"

"Serious Anty Farida ba ki dace da shi ba, kin ga lokacin Lukman..."

"Faruƙ!" Ta faɗa da ƙarfi.

Ya haɗa hannu ya ce "afuwan Anty na ta kai na"

Haɗe fiska ta yi ta tsume.
Faruƙ ya sa hannu ya fara tattaɓa kumatun ta yana tsokanarta kaman yadda yake yi lokacin suna yara.
"Anty kumatu, Anty Kumatuttu"

Ba ta san lokacin da dariya ya kuɓuce ma ta ba.
"Yaron nan ka mugun raina ni wallahi"

Yai dariya ya ce " na tuna da, lokacin idan na ce mi ki Anty Kumatu har maƙota sai anji faɗar mu"

Ta fara dariya sosai harda kama ciki.

Faruƙ ya cigaba " lokacin tunda na gano bakya son sunan sai na samu abun tsokala. Kin tuna lokacin da ki ka kwaɗa min tukunya har goshi na ya fashe?"

"Ai ranan Ummi ta zane ni kamar ba gobe" ta faɗa cikin dariya. Suna cikin dariyan kakkausan muryan Najeeb ya doki kunnen ta.

"Miss Salihu"

"Sir" ta faɗi tana miƙewa tsaye.

"To my office"

Ya jima tsaye yana kallon su tun daga lokacin da Faruƙ ya ke shafa mata kumatu. Zuciyar sa ta yi baƙi haka nan idon sa ya kaɗa yai ja, a take ƙwaƙwalwarsa ta tariyo ma sa sunan da ya gani ranan *My Ray*
Ta ya za ta kawo saurayinta har office tana iskancin da ta ga dama. Enough is enough dole ya taka ma ta birki. Abinda zuciyarsa ta tsayar kenan dai-dai lokacin da Faridan ta shigo.

"Ga ni Sir" ta faɗi a hankali

Da ƙarfi ya fara masifa "Miss Salihu yaushe ki ka maida office wajen soyayya da iskanci?. Listen young Lady, idan ba ki san yadda za ki kama kan ki ba go and get married. Ki dena mayar min da office wajen karuwanci. And i..."

"Sir Najeeb ba fa ni na kar zomon ba balle a bani ratayar sa. Daga ƙani na ya kawo min ziyara sai ka maidashi wani zancen banza wai karuwanci. Ba Karuwanci ba a'a Kwartonci"

Kalmar *ƙani na* da ya ji shi ya sanya duk wani masifar da ke cinsa ta washe, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kamar kiftawar ido, muryar sa da yanayin sa su ka chanja. Cikin sanyin murya ya ce "Miss Salihu, da ƙanin ki da saurayin ki, nan ba wajen ziyara ba ne"

Haushin sa da ta ji kaman ta makeshi takeji sai dai yanzu ba ta son samun matsala da shi dan ankusa biyan albashi, ƙaramin aikinsa ne ya cire mata wani kaso a ciki.

"Zan iya tafiya?"

Yai ma ta nuni da hannu. Sai da ta fita ya sauke numfashi. Cikin zuciyarsa yana cewa to ma miye ruwansa idan ma saurayinta ne?.


Tana zama ta yi tsaki " shi komai masifa, yai wa mutum kyakykyawar fahimta ba zai yi ba"

"Sis Ogan kin nan ya burgeni fa. Saurayi da shi amma ya mallaki babban kamfani kamar wannan, gaskiya na jinjina mi shi"

"Ko za ka je ya baka aiki ne. Nan za ka san wannan saurayin zuciyar dutse gareshi"

"Oh really"

"Hmm ai ni ma ba dan bana barin hau ta hauni ba da tuni an jima da fatattaka ni"

"Kai Masha Allah, wa su kam Allah ya basu duniya, ga shi handsome, ga kuɗi, ga class..."

"Zan make bakin ka Faruƙu"

Dariya yai ya ce " Jiya na yi mafarkin kin auri wani millionaire. Wai gamu a wani haɗaɗɗen mansion, wai nan ne gidan ki"

"To Sayyadi Sheikh Umar Faruƙ, ma su mafarkin waliyyai"

"Da gaske fa Anty Kumatu"

Ta ɗau wani littafi za ta buga ma sa ya kauce yana dariya...

...................

Wannan karan ba ta yi garajen barin wajen aiki ba dan ta san yana ɗaya daga cikin babban dalilin da ya sa Najeeb ya rage albashinta a watan farko da ta fara aiki. Ranan Laraba ta tambayeshi leave ɗin kwana biyu ya ce ya bata kwana ɗaya. As usual sai da ta yi ƙorafi amma bai kulata ba.
Wannan karan bayan Walima ba abinda za'ayi. Baffa yai iya ƙoƙarinsa wajen yiwa Maijiddah kaya, duk da bikinta ya zo ma sa cikin matsi.
Ranan Alhamis aka je yi ma ta jere, su Farida ne 'yan gaba-gaba wajen ganin komai ya tafi dai-dai. Gidan yana da kyau sosai, tana da ɗakuna biyu na ta sannan an ware ma ta kitchen daban sai dai store ne za su haɗa da Aneesa...

Gidan ya cika saboda gobe ne walima jibi Asabat kuma a ɗaura aure. Farida tun da su ka dawo daga wajen jere ba ta samu zama ba, shiga ta yi cikin ma su haɗa kayan waliman gobe ana aiki da ita.
Cikin ma su aikin cupcake ta ke ana yi ana hira. Chan wata 'yar uwar su wanda ita kan ta Faridan ba ta san takamaimai ta ina su ka haɗu ba ta ce " Ikon Allah, kaman ba yau aka yi hidiman bikin Farida ba, na tuna cake ɗin da aka yi ranan mai daɗi, su Talatun Haruna ne su ka yi cake ɗin nan ko?"

Farida ta fusata da wannan zance. Ta miƙe tsaye " Inna Tabawa ki ke ko wane. Wallahi ki riƙe girman ki, na ga take-taken ki tun awajen jere. Ba zan miki da daɗi ba"

"Daga magana. Ni na ce kiyi sosayya da ɗan shege" Taas Farida ta wanke ta da mari ai kuwa matan kowa ya tashi wasu su ka ja Farida gefe wasu kuma su ka tsaya da Inna Tabawa da ta ke ta zage-zage...

Kai tsaye falon Baffa Ummi ta shige da ita bayan an kawota wajen Ummin.

"Mi ye haka Aishah?, zafin kan ki har ya kai ki mari mace kamar Tabawa"

"Ummi so ta ke ta ci mutuncina cikin jama'a. Tun a wajen jere ta ke ta min habaici ina shareta. So ta ke wanda ma ba su san abinda ya faru ba su sani"

" shikenan?" Ummi ta faɗi ranta a ɓace

Farida ta kalli mahaifiyarta da mamaki ta ce "Ummi maganan Lukman fa"

" da ta yi maganan akwai abinda ya ragu ko ya ƙaru a jikin ki ne?"

Farida ta girgiza kai.

"To ni banga abin ɗaga hankali ba anan. Ƙaddarar ki ce ta zo da haka. Kuma Alhamdulillah Allah ya chanja mi ki da mafi alkhairi sai ki yi ta gode ma sa, ki share 'yan gulma da gulmar su"

"Amma Ummi..."

"Kul. Ba na son jin wani magana, ki je ki nemi abinci ki ci ki samu ki huta"...

Ɗakin su Yakubu ta shiga ta ke cin abincin, ba wai daɗin abincin ta ke ji ba sai dai saboda Ummi ce ta takura sai ta ci. Gaba ɗaya zuciyarta na ma ta ɗaci. Duk yadda ta so ta basar da abin ta ka sa, kawai sai hawaye. Ta ya za ta manta da wannan rana a rayuwarta, ranan da ya kamata ace ya zamo ranan farin ciki amma kuma komai ya zo ya dagule, ya zamo ranan shine rana mafi baƙin ciki a tarihin rayuwarta. Sai da ta yi kuka mai isarta kafin ta share hawaye ta tattara kwanukan ta fita...

...................

Anyi Walima lafiya, sai dai duk yadda Farida ta ci burin ganin anyi komai da ita abinda ya faru daren jiya ya kashe ma ta jiki. Da farko ma shiri ta yi kawai za ta wuce office amma amarya Jiddah ta hanata.
"Dan Allah Anty Farida kar ki tafi, ki taimakeni ki tsaya ayi komai da ke. Ke ce support ɗina Anty"

"Na san kin ji abinda ya faru jiya, ba na son tsayawa anan wata ta gayamin maganan banza mu kwashi 'yan kallo. I dont want to ruin your day"

"Anty dan Allah ki mance da komai, Allah ina buƙatar ki kusa da ni fiye da kowane lokaci"

Da ƙyar Farida ta haƙura ta tsaya. An ci kuma an sha sannan an kira Malami ya yi wa'azi.

Washe gari Asabat ƙarfe shaɗaya aka ɗaura auren *Hauwa Maijiddah Musa Wase da AbdulWahab Bello Hassan Kachako*

Ɗaurin auren da ya samu halarcin manya-manya mutane, ta ɓangaren Alhaji Bello Kachako da shi kan sa AbdulWahab ɗin.
Da dare aka kai amarya gidan ta wanda kwana biyu kawai za ta yi su wuce Lagos...

Gidan Amarya Maijiddah kam bayan kowa ya tafi aka bar amarya da halayenta.
Tun safiyar yau ta ke gudawa saboda tsoro da fargaba.
Akwai mafiya yawancin mutane da idan su na cikin damuwa ko tashin hankali ko tsananin farin ciki ko baƙin ciki za ka ga yanzu-yanzu cikin su zai hautsine su fara ziryan banɗaki.
Maijiddah was nervous tun wayewar garin yau, abu ne da ta jima tana roƙo sai gashi ya tabbata, wai ga ta amarya. Ta sha Flagyl kam har ba adadi duk dan ta samu sauƙin wannan abun amma kaman tunda Maghriba ta do so abin ya fara ƙaruwa. Yanzu haka kafin Farida ta tafi sai da ta tabbatar ta sha magani amma yanzu da ta ke ita kaɗai sai ta ke jin cikin ta na ƙugi yana kuma murɗawa.

Tana cikin wannan yanayi wanda ta kira da ƙarshen kunya aka shigo ɗakin. Buɗe ƙofar ɗakin yai daidai da kukan da cikinta yai "ƙululululu"

A hankali ya tako wajen da ta ke ya ajiye ledar hannun sa akan drawer sannan ya tsugunna gaban ta ya sa hannu ya ɗaga gyalenta sama yana mai yin Bismillah.
Jikinta rawa ya ke, sai zufa ta ke haɗawa. Na farko saboda tsoro na biyu kuma saboda yanayin da ta ke ciki.

"Alhamdulillah, finally Gimbiya Allah ya nuna ma na wannan rana"

Duk maganan da ya ke yi sama-sama ta ke jin sa. Kamar ta saki ihu ta ke ji saboda kunya da haushin kan ta. Ta ya za ayi daren farkon su ace ta ɓarke da gudawa, wannan abin kunyan har ina.

Hannunta ya kamo yana wasa da yatsunta bayan ya zauna kusa da ita.
"Bari mu yi sallah sai mu ci abinci, na san baki ci wani abin kirki ba yau"

A karo na ba adadi cikinta ya sake yin ƙugi, wannan karan kam AbdulWahab ya ji.

"Sorry princess yunwa ko?"

Idan ta cigaba da shiru za ta cutu haka nan da kunya ace ta gaya ma sa matsalarta sai dai ya za ta yi.

"Ki shiga ki yi alwala ni inada alwalata" ya katse tunanin ta

Ai da sauri ta miƙe ta shige banɗakin. Duk yadda ta so ta daure ta yi alwala amma hakan bai yiwuba dole dai sai da ta je ta zauna a toilet. Ƙarshen kunya sai ga shi ƙaran gudawan na fitowa da ƙarfi wanda tabbas ta san AbdulWahab da ke ɗakin ya ji.
Ta gama amma kunya ya sa ta kasa tashi ta yi flushing, ta jima tana zaune daga baya ta yi ta maza ta tashi ta flushing na shi sannan ta yi alwala. Sai dai ka sa fitowa ta yi daga banɗakin dan ba ta san da wanni ido za ta kalli AbdulWahab ba.

Jin shiru kuma ta ƙi fitowa ya ce " gimbiya ko na zo na fitar da ke ne?"

Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fito. Daga bakin ƙofa ta tsaya kanta a ƙasa ta ce a hankali " I'm sorry, cikina ne ya ruɗe Yaya"

Tasowa yai har wajen da ta ke tsaye ya kamo hannunta ya ce " There's nothing to be sorry about my dear, mun riga mun zama ɗaya ai"

Sai da ya zaunar da ita sannan ya ce "kinsha magani?" Ta ɗaga ma sa kai.

"Barin haɗo mi ki tea sai ki fara sha"
Fita yai daga ɗakin wanda cikin minti shabiyar da ya ɗauka sai da Maijiddah ta sake zagayawa banɗaki.

Lokacin da ya dawo ya sameta a ɗan kwance gefen gado. He know she's nervous shiyasa ta ke experiencing wannan abun. Ya tuna akwai wani abokinsa mai irin wannan, ko exam za su yi sai ya ɓarke da gudawa, a ranan da za su fara exam na Waec   shekaru da dama da su ka wuce sai da Hussaini ya makara saboda ruɗewa da cikinsa yai.

A yadda ya ganta she's already weak, idan yai yunƙurin yi ma ta wani abu that will label him a cruel man.
Taimaka ta yai ta tashi ta sha tea ya haɗa ma ta da kaza.
"Ki kwantar da hankalin ki ba abinda zan miki, ki ci ki samu ƙarfin jikin ki"

Shi da kan shi ya fara ba ta naman a baki har ta ƙoshi. Ya ce ta shiga ta yi wanka ta ce na yi.

"Kinga yanzu jikinki ya tsatstsafo da gumi saboda tea da ki ka sha. Ki je ki watsa ruwa"

Gaba ɗaya kunya sai ya sake rufeta. Ta tashi ta shiga ta sake wanka da ta fito ba ta same shi ba ya tattara wajen. Ta yi saurin buɗe closet ta nemo kayan bacci riga da wando ta sa, sannan ta ɗaura hijab akai.

Da ya dawo a zaune a bakin gado ya sameta.
"Hauwerh cire hijabin nan akwai zafi"

Ba mu su ta cire hijabin ta sunkuyar da kai tana wasa da bakin pyjamas ɗin ta.

"Ya cikin na ki?"

"Da sauƙi"

"Ki kwantar da hankalin ki ba abinda zai faru kin ji"

Ta gyaɗa kai.

"Now breath in and breath out"

Ba ta gane ba har sai da ya nuna ma ta yadda za ta yi da kan sa sannan ta yi yadda ya ce. Sai da ta yi kusan sau goma kafin ya ce ta kwanta.

Kafin ya shimfiɗa sallaya yai sallar nafila tuni bacci ya sace amaryar sa. Da ya idar sai ya gyara ma ta kwanciya sannan ya kwanta bayanta ya musu addu'a ya kashe wutan ɗakin...

Washe gari da kunyar sa ta tashi tunowa da tai da abinda ya faru jiya. Sai dai shi kam ko ajikinsa, nuna ma ta yai wannan shine amfanin auren domin sun riga sun zama ɗaya. Duk wani matsalarta na shi ne, haka nan duk matsalarsa na ta ne.

Da dare su ka je gidan su sallama, daga nan su ka wuce gidan su Maijiddan. A wannan lokacin Farida ta tambayeta ko gudawar ta tsaya kafin ango ya shigo. Maijiddah ta ce "inaa, Anty ni kam ai na sha kunya" a taƙaice ta gaya ma ta abinda ya faru Faridan ta yi  ta ma ta dariya.
Ba su jima ba su ka wuce saboda da sassafe jirgin su zai tashi.

Daren ranan ya gaya ma ta basic abubuwan da ya kamata ta sani gameda airport da jirgi. Sannan ya jaddada ma ta ba abinda zai faru yana tareda ita.
Ko breakfast ba ta iya yi ba saboda kar ta ci wani abu ya dameta. Ƙarfe tara jirginsu ya wuce Lagos. Kuma Alhamdulillah Maijiddah ba ta yi gudawa ba, sai dai ta tsorata kam lokacin da jirgin zai tashi, ba dan AbdulWahab na riƙe da hannunta yana kwantar ma ta da hankali ba ƙila da ta yi kuka. Sai da jirgi ya lula sama sannan ta ɗan samu nitsuwa kaɗan...

Asha amarci lafiya Maijiddah (banda gudawa plz😁)

.........................

Safiyar Monday Farida ta fito aiki duk da kuwa gajiya bai saketa ba, sai dai kamar yadda ta yiwa Maijiddah dariya sai gashi itama tana tsaka da aiki cikinta ya hautsina. Da farko sharewa ta yi tana mita " mutum ya yi ta ciye-ciyen mai kwana biyu ba dole ciki yai ta kuka ba"

Sai dai fa lokaci guda ta kasa yin komai ta tashi ta nufi office ɗin Najeeb da gudu dan nan ne kusa da ita sannan ta ɗauka baya office ɗin dan ya fita ɗazu ya je meeting. Abinda Farida ta manta shine ya riga ya dawo tuntuni.
Da gudu ta zo ta wuceshi yana zaune yana aiki, kafin ta ƙarasa ma ta saki tusa a hanya.
Yana shirin buɗe baki yai magana kan shigo ma sa office da ta yi da gudu ya ji ƙaran tusan da ta yi...

Hankali kwance Farida ta zauna ta zazzage kayan cikinta, dama tun ran asabat rabon da ta yi, ga shi ba ƙaramin abinci ta ci ba a bikin nan. Ta jima a ciki kafin ta wanke ta yi flushing, kasancewa banɗakin yai gum sai ta ɗau air freshner ta feffesa ta ƙara buɗe windown banɗakin da kyau saboda iska ya ratsa.

Ta fito tana ɗan daddanna ciki tana faɗin "kai abubuwan da na ci a bikin nan ai sai barka. Kashi rahama ne Allah, ka ji yadda na ji wani saƙayau lokaci guda"

Cak ta tsaya da tafiya lokacin da muryan da ba ta taɓa tunanin ji ba a wannan lokacin ya doki kunnenta

"Miss Salihu"

Kaman ta nitse cikin office ɗin haka ta ji sai dai ita Aisha Farida ce dole ta nuna dakewarta. Tukunna ma dama yana office lokacin da ta shigo? ko dai bayan ta shiga banɗakin ne ya shigo office ɗin.

"Miss Salihu whats the meaning of this?"

Da ƙarfinta ta waiwayo bayan ta sauke ƙaramar ajiyar zuciya. Ita ɗin expert ce wajen waskewa, ta ce

"Daɗin abin ma kowa yana yi, abinda na yi ba farau ba ne akai na. Ni'ima ce da ubangiji ya baiwa bayinsa dan ya nuna ma na mu ɗin ba komai ba ne. Da Sarki da shugaban ƙasa da maikuɗi da talaka, malami da jahili, mai kyau da mummuna, mace ko namiji, fari ko baƙi.  Dukkan mu muna da buƙatar wannan ni'ima. Abu ne ba babba ba yaro"

Ta ɗan haɗe rai ta ce " yanzu haka Sir Najeeb kai ma wannan ni'imar sai da ka yi ta kafin ka zo office yau, ko tun jiya rabon da ka yi?"

The girl is really crazy, taya za ta yi abin kunya and pretend kaman ba komai. Masifa ya ke so ya ma ta amma maganganunta sai su ka kusa sa shi dariya. Ya daure ya ce " Miss Salihu a wani dalilin ya sa ki ka yi min amfani da banɗaki?"

"Saboda ya fi kusa da ni mana"

"This should be the last time da za ki yi haka"

"Ok Sir"

Har za ta wuce sai ta juyo ta ɗan yi gyaran murya ta ce " Sir ina da magana"

Ido ya ɗaga ma ta alamar miye.

"Sir, tsakani da Allah tusar da na yi ɗazu ka ji ta?"

Kallon-kallo su ka tsaya yi. Har ga Allah tana son sani dan bayan ƙarar da tusar ta yi ba ƙaramin wari ne ya biyo bayan tusar ba.

"Get out of my offfice"...

*Tantaran taran taran...... kar ku manta free pages na Sakatariya ta zai ƙare @pg15 kuma yanzu ma aka fara labarin. Za ka biya 200 kacal domin cigaba da samun update na labarin ko kuma ka biya 300 ka samu harda labarin Tsohuwar soyayya. 'Yan Niger Insha Allah gobe zan sanar da ku yadda za ku biya na ku...#FARNAJ is waiting for you all*

Domin sanin yadda za ku biya ku min magana ta wannan numbar 08137311900*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Last Free page*

0️⃣1️⃣5️⃣

"Mama har yanzu bai kirani ba, ina ga bai san ma na yi yaji ba fa" Aneesa ta faɗa cike da damuwa a ran ta.

"Ya ki ke so na miki? Na kira AbdulWahab na ce ka zo ka bada haƙuri matar ka ta yi yaji ko ya?"

"Mama do something please, ba zan iya sharing mijina ba"

"An riga an ɗaura auren Aneesa live with it. Ke ne za ki san yadda za ki riƙe gidan ki ta yadda yarinyar ba za ta samu kan shi ba"

Aneesa ta ɗan ɓata fuska ta ce "Mama ta ya zan yi hakan bayan bana zama a Lagos"

"Za ki ajiye aikin ki kenan?"

"Hell no. Ta ya zan bar career ɗi na when i'm at its peak. Ko kaɗan"

Mama ba ta ce komai ba, to mi za ta ce. Itama mace ce da mijinta ba ya gabanta. Ta taso da aƙidar 'yan cin kai, yau tana Dubai gobe tana China wajen saro kaya, kasuwancin ta shine a gaban ta. Auren fari ta haifi Aneesa da Nazir, da ta auri Alhaji Abdullahi ma ɗa ɗaya ta haifa ta rufe haihuwa. Kuɗi kuɗi su kawai ta sa a gaba ba ta da lokacin kula da iyalin ta balle tarbiyyan yaran ta, shi ya sa ko kishiyoyin ta ba sa gaban ta, dama kuma kowa gidan ta daban...

.....................

Farida na zaune wani saurayi ya shigo neman Najeeb.
"Wa za a ce?" Ta tambaya lokacin da ta ɗau wayar.

"Ki ce ƙanin shi"

"Sir wai ƙanin ka na neman ka"

Ajiye wayar ta yi ta ce " ya ce ka shiga"

Ba a jima da shigar wannan  baƙon ba Anas ya zo shima ya shiga.

Dukkan su uku zama su ka yi ana taɗin bayan rabuwa.

"Big B tunda ka ƙi auruwa mu zamu shige gaban ka fa, dan na gaji da zama tuzuru"

"Shege yaushe ka dawo da za ka fara maganar aure. Anas see this small boy fa"

Anas dai murmushin ya ƙe yai dan ya san inda maganar za ta tsaya ba za ta ma sa daɗi ba.

Farida ta shigo ta samesu a haka, bayan Anas ba ta taɓa ganin Najeeb ya sake yana taɗi da wani ba. Sai dai kamar yadda wannan saurayin ya ce shi ƙanin sa ne ƙila su na da alaƙa tunda dai a yadda Anas ya gaya ma ta ƙanwar Najeeb ɗaya ce wato Najdah. Wata 'yar girman kan kaman yayan na ta.
Kai tsaye wajen Najeeb ta nufa a wajen kujerun da su ke zaune wanda anan ya ke saukan baƙin sa.

"Sir ga wannan ana buƙatar signature ɗin ka anan" ta faɗi lokacin da ta miƙa ma sa wasu takardu.

Ya amshi takardun ya fara dubawa.

"Kai Big B wannan hottie as a secretary ai za ta ɗauke hankalin ma su zuwa wajen ka"

Najeeb ya ɗago ido ya ma sa wani kallo wanda ya sa yai saurin chanja magana fa cewa.

"Ba wanda ta kai sweety na kyau ai. Najdah is the epitome of beauty ba ƙarya"

Gyaran murya Anas yai sannan ya ce "Musty zan wuce office, sannu da zuwa"
Musty ya miƙa ma sa hannu su ka gaisa. Idon Farida na kan Anas wanda ta ga ya chanja lokacin da Musty yai maganar Najdah. Tun farko-farkon fara aikinta ta san Anas ya na son Najdah, duk da kuwa Anas ɗin bai iya buɗan baki ya faɗawa Najdan ba har yau.

"Ya Anas dan Allah ka ɗan jirani minti biyu" ta faɗa tana murmushi.

Sauke idon da za ta yi domin ƙarɓan takardun da Najeeb ya gama signing sai ta ga idon shi chul akan ta. Ba ta san ma'anan wannan kallon ba amma ta fassara shi da cewa kallo ne da ke nuni da zan gamu da ke.
Da ta amsa takardun ta ce "Allah na gani ni ban ci bashin kowa ba, kurwata kur"

Har ta fita daga office ɗin bai daina kallon ta ba.
Musty cikin fake American accent ɗin sa ya ce " Your secretary is funny and cute"

"Ba ka daina halin na ka ba ko?"

"Sorry Babban yaya"

Tana fita ta tadda Anas na tsaye yana jiran ta. Gaba ɗaya fiskar sa ta chanja bisa yadda ta san shi da, shi ba kaman Najeeb bane kullum fiskar sa a sake ta ke gashi da son barkwanci.

"Yaya na ban gane wannan ɗan adawar ba fa, shi waye?"

Murmushin ya ƙe yai ya ce "ɗan ma su gida ne. Mustafah Sulayman Jibo kenan"

Kalmar da ya faɗa ta 'ɗan ma su gida' ya sa ta tuna da audion da aka ce ta yi kwanakin baya inda ake cewa shi ɗin ɗan Maigadin gidan su Najeeb ne, kenan da gaske ne.

"Ya Anas kar ka damu mu akai za mu dangwalawa. Idan da so ai ya share komai"

"Ki na ga Najdah za ta tsallake ɗan uwanta ta zaɓe ni ko kuma Daddy ne zai watsar da zumunci ya zaɓe ni?"

"Ya Anas da wannan ma amma tun farko kai ka yi sake. Da ka gina soyayyar ka a zuciyar ta da tuni an wuce wajen"

Girgiza kai yai ya ce " Farida ba za ki gane ba"
Wucewa yai ya bar office ɗin ran sa ba daɗi...

Najeeb na zaune da Musty ne amma hankalin sa na kan tunanin mai Farida za ta faɗawa Anas. The girl is mischievous, yanzu haka wani gulma ta ke yi.

A wajen cin abinci Farida ta samu Anas shi kaɗai, bai ordering abinci ba, ruwa ne kawai a gaban sa, yana zauna amma hankalin sa yai nisa cikin tunani.

"Ya Anas yau da garau-garau na zo, za ka ci" Farida ta ajiye kular tana ƙoƙarin buɗewa.

" 'yar uwa yau ba na jin yunwa" ya faɗi ba tareda ya kalli abincin ba.

"Allah sai ka ci, nan nan na hana Yakubu abincin nan na ce a yaya na zan kaiwa amma ka gwaleni ba ka isa ba"

Ta fara zuba abincin a plate tana faɗin "Ya Anas yajin ya ji maggi fa, ga man ma sai ƙanshin albasa ya ke"

Sai da ta gama haɗawa ta tura gefen sa ta ce " dan Allah ka ci"

Ba yadda zai yi dole ya ɗau spoon ya fara ci. Ita ma ta haɗa na ta ta fara ci. So ta ke ta ma sa maganar Najdah shi ya sa ta zo.

"And what is the meaning of this?" Muryan Najeeb ya gauraye ilahirin wajen.

"Anas miye haka?, babu respect tsakanin Oga da mere secretary. Ta ya za ka bari ta zauna a inda na ke zama na ci abinci. Are you trying to disrespect me kamar yadda ta ke disrespecting ɗi na"

"Najeeb is not..."

"Shut up" Najeeb ya katse Anas da tsawa. Wannan ya ja hankalin kowa ya koma kan su.

Ta shi Anas yai zai bar wajen. Farida ta ce "Yaya dan Allah ka tsaya ka ci abincin ka, ni barin bar ma sa wajen"

"Bar shi na gode Farida" ya faɗi sannan ya bar wajen.

"Girma ya faɗi, kuma wallahi an ji kunya"

Hannu Najeeb ya kai zai ma ta mari sai kuma ya tsaya yana huci hannun na reto a sama " I'm warning you Miss Salihu, ki kama matsayin ki ko kuma na nuna mi ki"

Haɗiye miyaun da ya tokare ma ta maƙoshi ta yi lokacin da Najeeb shi ma ya juya ya bar wajen. Ta gama sadakarwa Najeeb marin ta zai yi. Har ta hango yadda fiskarta zai koma idan da marin ya sauka a fiskarta.

Ranan dai ita ɗin ma ka sa cin abincin ta yi. Mi ya ke damun Najeeb da har zai yiwa Anas haka, hakan ma agaban jama'a wanda duk a ƙasan Anas ɗin su ke...

Kai tsaye office ɗin  Anas ta wuce da ga canteen. Yana zaune yana ta kan zane a takarda wanda da ka gani ka san yana zanen ne saboda huce haushi.

"Yaya na kar ka ce na cika gulma amma anya Sir Najeeb yana da lafiya kuwa. Gaskiya a binciki ƙwaƙwalwar sa"

"Lafiyar sa ƙalau Farida, kawai dai he has a rough life ne. Mahaifiyar sa then Sabreen, su suka maida shi haka"

"Sabreen?" Farida ta faɗa da alamar tambaya.

"Macen da Najeeb ya fara so ba"

"Dama duk girman kan Sir Najeeb ya taɓa soyayya? Abun mamaki"

"Kar ki damu da abinda ki ka ga ya yi ɗazu, anjima kaɗan za ki ga ya zo ba da haƙuri"

"Duk da haka Ya Anas, abinda yai bai ma ka adalci ba wallahi"

"Kar ki damu, abinda yai bai kai zuciyar sa ba"

"Wannan sirikin na ka Allah kaɗai ya san yanayin sa. Yau ka gan shi shiru anjima ya fara faɗa gobe idan ya fara banbamin  bala'i har wani spark bakin sa ya ke yi"

Ai Anas bai san sanda ya fara dariya ba "kai Farida kinada abin dariya ba kaɗan ba"

"Allah Ya Anas wani lokacin kaman majnuni ya ke, ka san lokacin da aka kidnapping ɗin mu haka mu ka kwana mu ka wuni bai min magana ba daga baya kuma bini-bini sai ya ɗaukeni"

"To waya sani ko ke ce ke sa shi haukan"

"Ni Aisha Farida! Rufa min asiri kafin yanzu na ga query letter"

Ta ɗan gyara zama ta ce " yawwa, da ma maganar Najdah zan ma ka"

Ya ɗago ya kalleta

"Mi zai hana ka faɗa ma ta kana son ta, you never know, sai ka ga an dace. Balle ni ina ganin tana son ka ma"

"Baba na gadi yai a gidan su har ya rasu, karamci na Daddy ne ya sa ya sponsoring karatuna tun daga primary har masters da na yi shi ya sa na zama abinda na zama a yau. Daddy is like my father amma kuma na san indai akan maganar Mustafah ne to zai zaɓeshi ya bar ni, domin Mustafah jinin sa ne"

" tsoro shi zai sa ka rasa masoyiyar ka wallahi. Ba ka taɓa ce ma ta kana son ta ba, ba ka gayawa Najeeb ba balle kuma Daddy, to dan Allah ta ya za su san kana yi balle har a dubi wanne ya fi dacewa da ita tsakanin kai da Mustafah"

"Ki bari kawai Farida. Gara na zauna a matsayina"

"Dan Allah kar ka bani kunya ma na"...

...........

Lokacin da aka dawo daga break ta koma office ɗin ta. Ko da aka zo neman Najeeb ta kira office ɗin sa amma bai ansa ba, ta shiga office ɗin amma baya nan. Har banɗaki sai ta leƙa amma shiru. Numbar sa ta fara kira amma ba ta shiga.
Daga ƙarshe dai ranan har aka tashi ba ta ga Najeeb ba. Haka nan ba ta san inda ya je ba dan da ta fita ƙasa ta tambayi security aka ce ma ta Najeeb ya fita da mota tuntuni.
A zuciyarta ta ce "ai dole ka gudu tunda ka yi abin kunya"...

Tunda ya bar canteen kai tsaye motar sa ya je ya ɗauka ya bar kamfanin, ya na shiga gida ɗakin sa direct ya wuce ya samu gefen gado ya zauna tare da dafa goshin sa. He cant believe wai shi ne yai wa Anas tsawa. Anas fa, Anas da duk faɗin duniyan nan ba shi da aboki kamar sa. Saboda me?
Shi kan sa bai san dalili ba, ya san ba laifin Anas a zaman da Farida ta yi a wajensa. Sai dai ya rasa dalilin da ya sa maimakon ma ya ji haushin Farida sai ya kasance ya fi jin haushin Anas akan ta.  Bai san ya za'a yi ya dena jin haushi ba duk lokacin da Farida ta ke tareda Anas.
Ya jima yana tunani a ran sa kafin ya tashi ya fara cire kaya dan ya watsa ruwa.

...............

Samun Anas ta yi akan dan Allah ya kaita gidan su Najeeb ta bashi wa su takardu sannan ta bashi saƙonnin wanda su ka zo ba su sameshi ba tunda wayar sa a kashe ya ke.  Yana sauketa a compound ɗin su ya juya ya tafi dan shima bai shirya fuskantar Najeeb ɗin ba, ko da kaɗan ne to ya ji haushin abinda Najeeb yai.

Ranan da su ka zo gidan da dare ba ta lura da gidan ba, saboda dare da kuma hali na gajiya da rashin lafiya. Amma yanzu kam ta ga yadda gidan ya ke da girma da kyau, sai da ta gama yabon kyaun gidan a zuciyar ta kafin ta wuce ciki. Doorbell ta danna tana jira a buɗe.

Najdah da Afrah ke cin abinci a dining saboda har yanzu Mom ba ta dawo daga Bahrain ba.

"Adama.... Adama ki zo ki buɗe ƙofa"

Adama ta fito da sauri ta nufi ƙofan.

"Sannu, wa ki ke nema?" Adama ta tambayi Farida da ke tsaye a bakin ƙofa.

"Ni sakatariyar Najeeb ne, na kawo ma sa saƙo yana nan?"

" ki shigo"
Ta matsa ma ta ta shiga.

"Adama waye?"

Kafin ta bada amsa Farida ta ce "Aisha Farida ce"

Sunan ba baƙon suna ba ne a wajen su duka biyun, dan sun san labarinta a Najeeb constructions. Ranan da su ka fara zuwa wajen Najeeb farko-farkon fara aikin Farida. Hana su shiga office ɗin sa ta yi ta sa su ka jira shi a office ɗin ta har sai da ya dawo. Ranan cikin shagwaɓa Najdah ta dinga complain wa Najeeb har da cewa "Big B, your secretary was rude to us". Daga baya Najeeb ya ce wa Farida duk lokacin da ƙanwar sa ta zo yana nan ko baya nan ka da ta hana ta shiga office ɗin sa.

"Ehen, duk haɗuwar ku na office bai isa ba sai kin biyoshi gida" Afrah ta faɗa tana huhhura hanci.

"Idan aiki na ya tsone mi ki ido, kya iya zuwa ki ƙarɓa"

"Mtsww" Afrah ta ja tsaki

"Mi ki ka zo yi?" Najdah ta faɗa ita ɗin ma fiskan ba yabo ba fallasa.

"Na kawo wa Sir Najeeb wa su files ne, sannan na zo neman bayanai gameda masoyina Anas kasancewa kin fini sanin shi"

"Masoyin ki Anas?"  Najdah ta maimaita

"Wanni Anas tukunna?" Afrah ta saka baki.

"Abokin yayanki ma na, ko kin san wani Anas ɗin bayan shi?"

Najdah ba ta ce komai ba sai haurawa da ta yi sama da gudu fuuuu itama Afran ta bi bayanta tana kiran ta.

Ganin su duka biyun sun bar wajen ya sa Adama ta je wajen SHS ɗin falon ta danna 6 muryarta na rawa ta ce "Ranka shi daɗe ga Sakatariyar ka ta zo neman ka"

Shiru kusan minti ɗaya ba a ce komai ba, har Adama ta fidda rai sai ga muryar sa ya na cewa  " send her to my room"

"Ina ne ɗakin?" Farida ta tambaya

"Idan kin haura sama shine ɗaki na ƙarshe a ɓangaren hagu"

Ok kawai ta ce ta haura saman. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin ta yi lokacin da ta iso. Ta tsaya na aƙalla minti biyu kafin aka buɗe ƙofar.

Sanye ya ke da jallabiya na 'yan Morocco kalar toka.

"What do you want?" Ya faɗi fiskar sa tamau.

"Ya Allah, wai haka gidan ma su kuɗi su ke ne, daga ka zo sai a fara tambayarka mi ka zo yi. To ni ba maula na zo yi ba ziyara na kawo"

Ƙofar ya jawo zai rufe ta yi saurin sa hannu ta ce " yi haƙuri Sir Najeeb saƙo na kawo"

Ya dakata da rufe ƙofar yana kallonta. Ta fito da wani file ta miƙa ma sa sannan ta ce " Sir MD na Hafzal suites ya zo neman ka ya ce da ka ji saƙon nan ka kira shi akwai magana mai muhimmanci da za ku yi sannan dan Allah ka bawa Ya Anas haƙuri abinda ka..." baam ya rufe ƙofar sa.

" Mr Egocentric" ta faɗa kafin ta juya ta fita.

A falo ta haɗu da Daddy shi ma ya shigo gidan kenan, har ƙasa ta rusunna ta gaida shi.

"Kaman na san fiskar nan"

"Yallaɓai ai ni ce sakatariyar Sir Najeeb wanda aka sace mu kwanaki"

"Oh Aisha ko?"

"E"

"Sannu ya Baban na ki"

"Ya na lafiya"

"Ki gaida min shi ko"

"Insha Allah zai ji"

"Gida za ki je ne?"

Ta amsa da E

"To to, Adama ki fita ki ce Iliya ya kaita gida ko"

"Na gode Daddy"

Ya fito da kuɗi a Aljihu ba tareda ya irga ba ya miƙa ma ta ya ce ta sha ruwa a hanya.

"Daddy ka barshi na gode"

"Idan ki ka yi haka ba ki ɗauke ni Daddy ba kenan"

Ai tuni Farida ta karɓa tana ƙara faɗaɗa murmushinta lokacin da ta ji kaurin kuɗin zai iya kaiwa dubu goma.

Ita kam bajau ɗin ta, ta tafi gida a mota mai kyau ga AC  ga dubu takwas da Daddy ya bata...

Ai ba ta gama zama ba Anas ya kira ta.

" 'yar uwa mi ki ka faɗawa Najdah ne? Ta kira ni wai muna soyayya da ke kuma na ɓoye ma ta bla bla bla..."

Sai da Farida ta yi dariya mai isar ta sannan ta ce " Yaya na kenan, idan akwai kishi to akwai so. Najdah na son ka, ka saurari plan ɗina ka ji..."

............

Su na cin breakfast a dining Najdah ta ce " Big B wai ashe Ya Anas da sakatariyar ka soyayya su ke"

Tea ɗin da Najeeb ya kai baki ya furzar da sauri.

"Anas ya gaya mi ki?"

"Jiya da sakatariyar ka ta zo ta ke gaya min. Big B, Ya Anas ya rasa wanda zai nema sai masifaffiyar yarinyar nan, that girl fa ba za ta rasa mu'amala da ƙwaya ba"

Miƙewa Najeeb yai bai ce komai ba ya bar dining ɗin.

Ranan da Anas da Farida ban san wanda ya fi shan masifar Najeeb ba. Abu kaɗan masifa, lokaci guda Najeeb ya dawo wa Farida Najeeb ɗin da ta sani farkon zuwan ta. " get out, fuct you, stupid, nonsense" waɗannan kalmomi da su na tsiro da sun tsiro a jikin Farida saboda tsabar yadda ta ji su a wajen Najeeb. Idan ta kawo takarda ya signing kuwa yana gamawa zai wurgeta da shi ba zai miƙa ma ta da hannu kamar yadda ya saba ba.

Anas ma ya ɗauka da Najeeb ya zo zai ba shi haƙuri a wuce wajen sai ya ga saɓanin haka. Yana tambayar sa abu maimakon yai magana sai ya fara ma sa tsawa...

Farida na tattara wasu takardu da Najeeb ya watsar Anas ya shigo office ɗin.

"Najeeb ka dubi wannan presentation ɗin nan na gobe. Wannan shi ne final edit da na yi"

Ko kallon laptop ɗin da Anas ya ajiye a gaban sa bai yi ba ya ce " kar ka damu kan ka, ba za ka yi presenting gobe ba"

"What"

"Ka jini da kyau"

"Najeeb are you serious? I've been planning for this pitch for a week now"

Da ƙarfi Najeeb ya daki table ɗin sa ya ce " Ni Najeeb Adam Jibo, CEO of Najeeb constructions na ce Architect Anas Ali AlMustafah ba za ka yi presentation gobe ba, ka na da ja?"

Da Anas mai saurin kuka ne da ya yi a wajen nan saboda wannan cin fuska da Najeeb ya ma sa. Sai dai ya daure ya ce " ba ni da ja, Sir Najeeb"

Wannan karo na farko da ya referring Najeeb da 'Sir' kenan, a cikin shekaru bakwai da su ka fara aiki tare.

Gwiwar Farida yai sanyi. Tausayin Anas ya mamaye zuciyar ta. Da ta na da iko da ta je ta wankawa Najeeb mari.

Wai a wani dalilin zai yiwa Anas haka, a wani dalilin?
(Ni dai da 'yan group ɗi na ma su albarka mu ka haɗa baki mu ka ce *a dalilin ki*)

*plz numbar da za a nemi yadda za'a shiga paid group ɗin sakatariya ta ita ce 08137311900, duk wani number da ba wannan ba scam ne. Kar ku manta, #200 ne kacal ko kuma ka biya #300 ka samu sakatariya ta da tsohuwar soyayya. Za ka iya biya ta wannan account ɗin 3099546325, firstbank,Azizat Hamza. Ko kuma ka turo katin waya zuwa ga wannan layin 08137311900. (Plz duk wani means of payment da ba wannan ba, babu hannun marubuciyar a ciki. Mutanen Niger za ku iya biya ta link da zan turo da yamma Insha Allah a wattpad account ɗi na 000Azee)*

............

"Yakubu dan Allah ka nemo min super glue mai kamawa sosai wanda baya saurin bushewa"

"Yanzu dan Allah mi za ki yi da super glue? Ke ba mai gyaran takalmi ko radio ba"

"Ni bana son sa'ido, ka nemo min kawai. Harda gum na ruwa ɗin nan. Yau na ke so ba gobe ba"

"Ke wallahi case ce, na ji zan nemo"

Farida ta yi murmushi

Da wurwuri ta zo office yau.  Tana daƙontar zuwan Najeeb dama ta gayawa security da zaran Najeeb ya ya shigo ya kirata.
Tana zaune kuwa security ya kira ya ce ga Najeeb ya shigo. Ta yi sauri ta shiga office ɗin sa ta samu kujeran sa ta fara matsa super glue ɗin da Yakubu ya kawo ma ta.
Za ta fito kenan ta yi kiciɓis da Najeeb zai shigo dama tuni ta sa tubes ɗin a jakarta.
"Good morning Sir"
Bai amsa ma ta ba ya wuce wajen zaman sa.

"Sir Ya Anas ya kawo flash ɗin da za ka yi amfani wajen presentation ɗin na ajiye a table ɗin ka"  wannan magana shi ya ɗaukewa Najeeb hankali ya zauna ba tareda ya lura da kujerar sa ba.
Tana gani ya zauna ta yi murmushi.

"Ki tabbatar duk wanda ke cikin team ya isa  conference room  kafin ƙarfe tara"

"Ok Sir" ta fita tana murmushi.

Flash ɗin ya ɗauka ya sa a laptop na shi yana duba presentation ɗin da Anas ya sha wahala ya tsara.

Ƙarfe tara saura minti shabiyar ya gama bitar abin ya kira Farida.  Ta san dole zai kirata domin ta ɗauka ma sa laptop da wasu files dama.

Ƙoƙarin tashi yai a kujeran ya ji ya ka sa tashi. Da ya tashi sai kujeran ta biyoshi.
"What's this" ya faɗi lokacin da ya ke ƙoƙarin raba takashinsa da kujeran amma hakan bai yiwu ba.

"Sir Najeeb ya dai?"

Farida ta faɗa kamar ba ta san mi ya ke faruwa ba.

Tsaki yai ya cigaba da ƙoƙarin raba jikinsa da kujeran.

"Sir idan ka ja da ƙarfi zai yaga ma ka wando ka ga anyi ba ayi ba kenan. Tsuliyar CEO Najeeb constructions a waje" ta sa hannu ta ɗau flash ɗin da ke kan table ta ce " tunda takashin Oga ya maƙale a kujera sai na kaiwa Ya Anas kawai yai presentation ɗin tunda dama shi ya kamata yai tun farko"

Sai da ta fara tafiya ya ƙwalla ihun sunan ta da ƙarfi "MISS SALIHUUU"

Ta waigo tana fari da ido ta ce " SIR NAJEEB YA DAI"

*difdifdifdif..... anan na kawo ƙarshen free pages. Na yi ƙoƙari ai har page 15. Well, za ka samu cigaban labarin idan ka biya 200 kacal. Stay safe and Allah ya mana albarka ya rufa mana asiri duniya da lahira ta ku AZIZAT**SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣1️⃣6️⃣

Tana fita daga office ɗin Sir Najeeb office ɗin Anas ta wuce. Ta sameshi ya yi wani jugum da shi. Tabbas abinda Najeeb ya ma sa ya mugun kashe ma sa jiki.
Ajiye flash ɗin ta yi a gaban sa ta ce "Yaya na ga shi ka je ka yi presentation ɗin"

"Roƙonsa ki ka yi? Ko kawai ɗaukowa ki ka yi?"

"Ko ɗaya, Yaya na shi da kan sa ya bani ya ce na kawo ma"

"Ban yarda ba, Najeeb ba ya chanja magana da wuri. Kar ki damu ƙanwata, Najeeb shi ke da kamfani yana da ikon hana ni ko ya sa na yi abu"

"Ya Anas da gaske na ke fa, idan ba ka yarda ba ka zo muje ka tambayeshi"

Da farko dai Anas bai amince ba daga baya da ta takura sai ya tashi su ka fita, har lokacin dariyan Najeeb na cinta.

A ɓangaren Najeeb kuwa yayi nasarar raba jikin sa da kujeran amma kamar yadda Farida ta faɗi sai da wandon shi ta farke, wasu daga cikin pattern na wandon suna manne da gum ɗin a jikin kujera, wandon ya koma har ana ɗan ganin boxers na shi.

Najdah ya kira akan ta kawo ma sa kaya daga gida, ta ce ma sa tana school ai kuwa ya fara babbaleta da masifa abinda bai saba yi ma ta ba, idan ba masifa akan Mom ba, normally ba ya taɓa ɗaga ma ta muryarsa. Ganin yadda ya ke faɗa ya sa ta san lallai akwai matsala, dole haka ta bar class ta wuce gida.
Yana ajiye wayar sai ga Anas da Farida sun shigo, yai saurin komawa ya zauna akan kujeran dan kar Farida ko Anas ɗin su ga yadda bayan wandon sa ya koma a rarike.

"Sir Najeeb ina kai ka ce Ya Anas ya je yai presentation ko?"

Sai da ya ma ta kallon banza sannan ya kalli Anas ya ce " ka je ka yi pitch ɗin nan, its already time"

Anas da mamaki ya ce " miyasa ka chanja ra'ayin ka?"

"Oh please, just go"

"Ya Anas, Sir Najeeb ba shi da ja fa, kai ɗin ne dai za ka yi presentation ɗin"

Anas yai shiru yana nazarin Najeeb, akwai ɓacin rai mai tsanani a tattare da shi amma yanzu bai da halin tambaya saboda chanjawar da abokin sa yai. Ya karɓi flash ɗin daga hannun Farida ya juya. Farida ta bi bayan sa tana gwada irin tafiyar Najeeb. Sai da su ka kai bakin ƙofa ta juyo ta ce " Sir Najeeb asha zaman kujera lafiya" sannan ta sa dariya.

Bayan fitan su da kusan minti arba'in Najdah ta zo mi shi da wasu kaya daga gida.

" Big B mi ya faru ka ke ta min tsawa ɗazu?"

"I'm sorry baby, i was just pissed off ne"

"Barin koma school muna da class"

Ok kawai ya ce ya jira sai da ta fita daga office ɗin sannan ya wuce banɗaki ya chanja kaya.
Lokacin da ya ga wandon wani haushin Farida ne ya zo ma sa har wuya. He's 100% sure ita ta sa wannan abun a wajen, kuma ta yi ne domin ta hanashi presentation ɗin nan.

"All because of Anas" ya furta a fili.

Ya kalli kan sa a madubin banɗakin ya ce " Did she really love him?"

Wanni ɓangare na zuciyar sa yana cewa miya shafeka idan tana son Anas, wani ɓangare kuma na cewa bai dace su yi soyayya ba, Anas is a good person amma wannan Ayshern, bai san ma ya zai kwatantata ba.

Shi dai abinda ya barwa ran sa shine dole ne ya hukuntata. Ya rasa miyasa ya ke kasa aiwatar da komai a kanta despite the fact cewa ta raina shi kuma tana karya dokokin sa son ran ta....

Najdah daga office ɗin Najeeb sai ta wuce office ɗin Anas. So ta ke ta sake tambayarsa ko da gaske ne yana son Farida, domin ranan ba ta barshi yai magana ba ta kashe wayar.

Ganin baya office ya sa ta yi yunƙurin tafiya idan ya so sa haɗu daga baya, sai hankalinta ya je kan wani hoton sa da ke kan table. Ta ɗauka hoton ta ƙura ma sa ido. A cikin tarihin rayuwarta tana son baƙin namiji, ita baƙin mutum na burgeta. Farar fata gareta amma many a times tana envying skin ɗin baƙaƙen mutane.  Tun tana ƙarama ta san Anas, lokacin idan sun zo hutu Nigeria, su na tare koyaushe saboda tafi kowa kusa da Najeeb shi kuma shine kaɗai abokin Najeeb. Wani lokacin ko da Najeeb bai zo hutu ba to kullum tana tareda Anas, wannan ya sa ta shaƙu da shi tun a yarintar ta, shekaru uku da su ka wuce kuma ta fara jin wasu baƙin lamura game da shi wanda ita kan ta ba za ta iya fassara su ba. Ta ɗan shafa hoton sannan ta ajiyeshi.

Tana fitowa ta yi kiciɓus da Anas da Farida, da alama office ɗin na sa za su shiga amma maganar da su ke yi ya sa su ka tsaya a wajen. Dariya Anas ke yi sosai harda riƙe ciki. "Farida you are too much wallahi, abinda ki ka yiwa Najeeb kenan"

Doguwar tsaki Najdah ta ja wanda ya ja hankalin su.

"Najdah" Anas ya faɗa lokacin da ya juyo ya kalleta.

"An dai ji kunya" ta faɗa sannan ta bar wajen. Da sauri Anas ya bi bayanta yana kiran sunan ta.
Ta shiga lifter amma kafin ƙofar ta rufe Anas yai saurin sa hannu ya tare sannan ya shiga lifter ɗin shi ma.

"Najdah wai miya faru ne?"

"Dont pretend kamar ba ka san abinda ya faru ba. Sakatariyar Big B fa ka ke so. Sakatariyar sa"

A wannan dama da Allah ya bashi yau, dole ya cire tsoro kamar yadda Farida ta ce.
A hankali ya furta " to miye a ciki? Ita sakatariyar Najeeb ba mutum ba ce?"

Wannan karan kaman za ta yi kuka ta ce "Yaya yanzu duk faɗin garin nan ka rasa wanda za ka so sai ita, that cheap girl"

Ƙwarai ya gane kishi ta ke amma bashida 100% assurance cewa kishin sa ta ke, sai dai dole ne ya tabbatar wa kan sa domin shi ta ke kishin.

"Najdah wa ki ke so na so? Wa ki ke ga zai so ɗan Maigadi"

"Yaya you know we love you, ka riga ka zama ɗan uwan mu yanzu"

Matsowa yai kusa da ita ya riƙe hannunta ɗaya ya ce "so idan ɗan Maigadi ya nemi 'yar masu gida za ta amince?"

Jikinta yai sanyi haka nan kuma kusancin su da hannunta da ya riƙe ya sa ta fara jin wani baƙon yanayi ajikinta, zuciyarta na bugawa da sauri-sauri.

Zuciyar sa ce ta ce 'Anas is now or never'

A hankali ya kai bakin sa dai-dai kunnenta ya ce "i love you Najdah, only you"

Maganar yai dai-dai da tsayuwar lifter dan haka ta wafce hannunta ta fita da gudu. Bai bita ba, sai ma murmushi da ya fara yi saboda jarumta da yai yau, finally he said it...

Farida na zuwa office ɗin Najeeb ta tadda ya chanja kaya.

"Manyan mutane kenan, Allah ya ja zamanin ka CEO"

Fiskar nan ba fara'a ko kaɗan ya ɗago ya kalleta ya ce "your two weeks suspension starts now, Miss Salihu"

"Suspension"

Sai kuma ta yi shiru.

"Two weeks suspension is not all, bayan kin dawo za ki serving punishment na ki"

"Hutarere wallahi. Hutun sati biyu ai gaba ta kaini, ka ga zan fara azumi a gida kenan dan Jos zan wuce. Na gode Sir Najeeb Allah ya ƙara daraja"

"Leave" ya faɗi da ƙarfi

"Sir Najeeb ina da magana" ba ta jira ya ce komai ba ta ce "tsakani da Allah abinda ka yiwa Ya Anas bai dace ba, ka san yadda mutumin nan ke ganin girma da darajarka amma ka walaƙantashi. Irin walaƙancin kun nan na ma su kuɗi ya sa ya kasa furtawa ƙanwar ka kalmar so, kaima kuma da ke ba ka damu da shi ba, sai ba ka gano son da ya ke yiwa ƙanwar ka ba"

Ɗago ido yai yana mamakin maganganun ta.

"A rage girman kai Sir Najeeb. Shi girman kai rawanin tsiya ne"...

Bai san lokacin da ta fita daga office ɗin ba saboda ƙwaƙwalwarsa da ta tafi duniyar tunani.

Anas na son Najdah, how when,why?. Kenan ba Aysherh ya ke so ba?

Da sauri ya miƙe ya bar office ɗin...

Wasu takardu Anas ke dubawa lokacin da Najeeb ya shigo, da ka gan shi ka san yana cikin farin ciki.

"You love my sister?"  Ya tambayeshi lokacin da ya shigo.

"Najeeb..."

"Idan har kana son Najdah, why Miss Salihu again"

Dariya yai ya ce  "tsaya Najeeb, waya gaya ma ka akwai abu tsakanina da Farida? I love your sister, ita  kaɗai na ke so"

Ɗan ƙaramin tsaki ya ja sannan ya bar office ɗin.

Nan zuciyar Anas ta ɗauko kan zan cen.

"Najeeb kishi ya ke da ni. Haba, dole biri yai kama da mutum ai. I suspected this tuntuni, Najeeb is inlove"

Murmushi ya biyo bayan maganar da yai wa kan sa, duk wani abinda Najeeb ɗin ya ma sa sai ya ga ya washe ko kaɗan baya jin haushin sa. The fact that Najeeb has feelings for someone else bayan Sabreen ai abun farin ciki ne. After 8yrs of loneliness.

Cikin kwana biyun nan abubuwa sun chanja. Najeeb ya koma yana jin kunyar Anas saboda abinda ya ma sa duk da kuwa Anas ɗin ya nuna komai ya wuce.  Shi kan sa Najeeb ba zai iya faɗan dalili ɗaya da ya sa yai ma sa haka ba domin haushinsa ya ke for no reason amma kuma yanzu ya washe.

"Yau zan fara zuwa hira officially, sirikina ka gaya min tips wanni irin kaya Najdah ta fiso namiji ya sa"
Najeeb ya dundeshi ya ce "ɗan iska, ta fi son gwanjo"
Kalmar gwanjo da ya faɗi ya sa sunan Aysherh ya zo ma sa, kwana uku kenan da ba ta nan.

" abokina dan Allah kar ka manta a shigemin gaba wajen Daddy"

"Fuck you, Daddyn ne sai ni ne zan ma sa magana, kai ma ai ɗan sa ne you can talk to him about it"

"Ni ba marar kunya bane irinka ai"...

Anas na fita daga office ɗin sa ya tura wa Farida text akan an janye suspension ɗin ta resuming aiki gobe. Lokacin da text ɗin ya shigo Farida na bacci so ba ta gani ba.

Shigowar Khalidah office ɗin ne ya sa shi deleting ɗin text ɗin da ya ke shirin tura wa Farida ta ɗaya layinsa.

"Kwana na biyu da dawowa banga sakatariyar ka 'yar gold ba. Ko ka koreta ne?"

" get out"

"Maida wuƙar Najeeb. Na zo maganar project da ake yi a Kaduna ne"

Ya nuna ma ta kujera akan ta zauna...

Farida na ganin text ɗin Najeeb ta yi tsaki ta tura ma sa reply kamar haka

*Sir Najeeb ni ba zan dawo ba sai sati biyu sun cika, kana gani za a fara azumi nanda kwana biyu ka ce na dawo, gaskiya sorry*

Lokacin da ya  gama karanta text ɗin yai ƙaramar tsaki.

...................

Sati biyun dai ba ta yi shi ba, sati ɗaya ta yi ta dawo saboda yadda Anas da Yakubu su ka takura akan ta dawo.
Duk da an rage awa ɗaya cikin lokacin aiki, hakan bai sa ta jin haushin aikin ba yanzu saboda watan azumi da aka shiga.
8-3pm ba wasa ba ne a wajen Farida ga ɗan karen zafi da ake yi a garin na Kano, ga ruwan sama ma dai har lokacin da azumi ya kai goma ba wani alamunsa sosai dan sau ɗaya aka yi ruwa. Daga ƙarfe shabiyu za ka ga Farida ta yi laushi. Da ƙyar ta ke kaiwa lokacin tashi.

Yau ma wani aikin da za ta yi Najeeb ke ma ta bayani.
Burping ta fara yi akai akai har sai da Najeeb ya fusata ya ce " Miss Salihu will stop sounding like a frog"

(Burping kaman ƙwanafi kenan, ban san Hausa word na shi ba. Irin dai abinda ma su ulcer su ke yi ɗin nan ko kuma idan mutum ya cika cikinsa da abinci dayawa za ka ga daga maƙoƙoron ka kana fitar da sautin irgh irgh irgh )

"Sir Najeeb ba fa da gangan na ke ba, ulcer na ne ya tashi..." ba ta ƙare maganan ba ta kuma yi ya ce "Gosh! Miss Salihu get out"

Ba ta musa ba ta fita dan dama a gajiye ta ke...

Ya dawo daga sallar Azahar ya shiga office ɗin sa sai ya ji ƙanshin abinci. Abinci in his office a watan Ramadan? Ya juya inda ya ke jin ƙaran sokali and there he sees her. Ta barraje a ƙasa tana cin jollof ɗin taliya da macaroni.

"Since when did my office become your dining room?"

Ɗago ido ta yi ta kalleshi hannunta ɗauke da sokali totse da abinci.

"Ni ban ɗauka za ka dawo yanzu ba"

"Miss Salihu"

"Dan Allah Sir Najeeb ka barni, ka ga office ɗina kowa na shigowa ƙarangatsau, na ka office ɗin akwai privacy"

Zuwa yai ya zauna bai ƙara cewa komai ba. Lokaci zuwa lokaci yana ɗaga ido ya kalleta. Shi mamakin yadda ta ke cin uban abincin nan ya ke. Ko za a matse shi ba zai iya cinye abincin nan ba amma ita ya san zuwa anjima kaɗan za ta take shi.

Wata rana ana azumi goman ƙarshe, ranan anyi tsananin rana. Ƙarfe biyun rana sun je wani site Farida  tana tsaye tana jin maganganun su har ta koma ba ta jin komai sai yijib ta faɗi ta suma. Najeeb da mutanen da ke wajen su ka yi kan ta.
Wanni Emmanuel na shirin kai hannu zai taɓa ta Najeeb ya daka mi shi tsawa "dont touch her"....*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣1️⃣7️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

Bayan ta farfaɗo ya sa aka kawo ma ta ruwa, maltina da madara akan ta karya azumi.

"Kai za ka biyamin ai idan na karya" abinda ta faɗa kenan lokacin da ya miƙa ma ta maltinan.

Ranan daga wajen ma ya maida ita gida ba tareda sun koma kamfani ba.

Haka dai a dararance ta cigaba da azumi har aka ƙare. Ana gobe Sallah aka ba su hutun kwana uku akan rana ta ukun sallah za a dawo. Farida kam cewa ta yi ba ta san zance ba sati ɗaya za ta yi. Ta wuce Jos ta yi sallan ta achan, duk da Kano za ta ga hawan sallah amma wannan baya gaban ta ta fiso ta ji ta jikin Umminta. Ƙila ma daga wannan sallah ita da sallah a Jos sai ta Allah.

.................

Lagos

Sati uku Maijiddah da angonta su na kwasan amarci, ba ta da matsala dan yaransa ba ma su hayaniya sosai bane.

Iya Bose ke mu su girki, amma tana kwana uku da zuwa ta fara shiga kitchen tana taya Iya Bose sarrafa abinci duk da kuwa Iya Bosen ba ƙarya ta iya girki sosai. A wajen ta ta san favourite na mijinta ta kuma koyi yadda ake sarrafa su. Shi ba bayarabe ba amma yana son cin amala da sakwara, dan haka ta dage tana koyon su a wajen Iya Bose. Miya kam ta ga ikon Allah, domin ita dai a gidan su idan ba kuka, kuɓewa, ko alayyaho ba to ba wani special miya da ake yi. Akan yi miyar egusi wani lokacin saboda Baffa na so amma a wajen Iya Bose sai ta ga miyar egusin ma ba kala ɗaya ba ce. Haka ta dinga ɗaukan darasin girki a wajen 'yar tsohuwar matar nan.

Daren Jumma'a da ya cika sati uku da auren su sai ga Aneesa ta zo.

Suna zaune su na kallo da yara a falo ta shigo, yaran suna ganinta su ka fara ihun mommy mommy.
A hankali Maijiddah ta fara satan kallon Aneesan duk da kuwa ta taɓa ganin hoton ta, amma ganinta a fili sai ta ga ta ƙara zama ma ta wata Madam. A ƙalla Aneesa za ta kai 36yrs ko 37yrs, amma jin daɗi da kuma samun mayuka ma su tsada sai ya ɓoye shekarun ta.

Sai da ta raba su Baby da Alizah a jikinta sannan ta kalli inda Maijiddah ke zaune sanye da doguwar riga ta atampa ɗinkin ya amshi ɗan jikinta ɗas-ɗas da ita.

Sai da Aneesa ta ƙare ma ta kallo sannan ta ja tsaki ta ce "ashe househelp Sweetheart ya kawo min"

"Sannu da zuwa" Maijiddah ta ce da ita.

"Nonye, Nonye" Aneesa ta fara ƙwalla sunan nannyn su Alizah.
Matar ta fito da sauri.

"Welcome ma"

"Je ki gyara min ɗakin Seeetheart, na san by now it most be stinking of filth"

Nonye ta haura sama ɗakin AbdulWahab. Dama ita ke gyarawa sai dai zuwan Maijiddan ne ta hanata ta ce ta dinga gyara ɗakin yaran kawai da sauran wajen.

Kallon kirki Maijiddah ba ta samu daga wajen Aneesa ba. Aneesa ta haura sama don ta je ta shirya kafin AbdulWahab ya dawo.

Maijiddah kam sai duk jikinta yai sanyi. Tsoron Aneesan ne ya kamata ganin wannan kallo da ta ke ma ta. Ta na da ƙuruciya amma Aneesa ta fita wayewa da komai. Ba za ta iya haɗa kan ta da ita ba.

Ƙarfe tara saura sai ga AbdulWahab ya dawo daga office.  Yaran su ka fara sanar da shi gameda zuwan Aneesa. Bai yi mamaki ba dan rabon sa da magana da ita tun ranan da aka ɗaura aurensa da Maijiddah.

Maijiddah ba ta yi yunkurin raka shi ɗaki ba kamar yadda ta saba tunda Aneesa ta dawo.
Ɗakin sa ya je ya cire kaya ya watsa ruwa sannan ya fito bayan ya sa kayan gida.

"Hauwerh yau na yi laifi ne ko ya hanya ba a min ba?"

Rasa mi za ta ce ma sa ta yi dan gaba ɗaya zuwan Aneesa ya birkita ma ta lissafi.

Sai da ya zauna sannan ta fara serving na shi dama yara sun riga sun ci abinci,  ita ɗin ma saboda zuwan Aneesa ta ci abincin tareda yaran dan ba ta son hayaniya.
Da ta gama ta juya za ta tafi  ya riƙe hannunta " gimbiya ta zauna"

Ba ta musa ba ta zauna amma hankalinta ba a kwance ya ke ba. Ƙanshin turarukan Aneesa shi ya sanar da su isowanta falon. Irin kayayyakin da Farida ta bata a matsayin gudunmawa, irin sa ke jikin Aneesa yanzu. Wata arniyan riga ce ta saka wanda ya tsaya ma ta iya rabin cinyar ta, rigan ba ta da hannu, rabin nonuwan ta a waje. Tana catwalking har ta iso wajen su.

Kai tsaye ta mannawa AbdulWahab kiss a kumatu tana faɗin " Sweetheart sannu da zuwa. Shine har ka fara cin abincin ban da ni"

Da ƙyar Maijiddah ta sauke wani wahallen numfashi sannan ta tashi ta bar wajen. Ashe rashin ganin Aneesa a kusa ne ya sa take ganin kaman ita ba ta da kishi.
Kai tsaye ɗakin ta ta wuce ta ja ƙofa ta sa key. Maimakon bacci ya ɗauketa kamar yadda ta so sai bacci ya ma ta ƙaura. Ta ga yadda idon AbdulWahab ya chanja lokacin da ya ga Aneesa, to irin wannan shiga ai ko ita da ta ke mace ma ta yaba. Sai dai anya ita Maijiddah za ta iya saka irin waɗannan kaya kamar yadda Farida ta yi ta ja ma ta kunne?...

...............

Satin da Farida ta ce za ta yi shi ta yi duk da kuwa Yakubu ya kira ya ce Sir Najeeb ya yi faɗa akan wanda su ka ƙara hutu. Ita kam ba damuwarta ba ne.

Ranan da ta resuming aiki Najeeb bai yi faɗa ba, kodan ta ga kamar hankalinsa na kan wani aiki da aka damƙawa kamfanin na su satin da ba ta nan.  Sati biyu bayan sallah aka kawo sadakin Farida sannan aka sa rana uku ga watan december wanda yai dai-dai da wata uku ma su zuwa.
Farida ta so Baffa ya sa bikin irin wata biyar ɗin nan, dan ta samu ta haɗa wasu kuɗaɗe wanda za ta yi hidiman biki da su.

Sai da aka tashi daga aiki ta shigo office ɗin sa, lokacin ma shi duba wasu zane da aka submitting ma sa ya ke.

"Sir ga goron sa ranan aurena da akayi, na kawo ma"

Ɗago ido yai ya ga baƙar ledar da ta ajiye akan table.

Ƙura ma ta ido yai yana son gano wani abu a tattare da ita. She was excited as she talked to him.

"Sir idan ka ɗan ƙara haƙuri da ni, nan da wata uku zan bar aiki da kai"

Still bai ce komai ba
"Ka san anguwan da zan zauna ɗan karan nisa ne da kamfanin nan, ga kuma aikin ku 8am-4pm. Ina matan aure kam ba zan iya ba"

Duk maganganunta ba wanda ya tanka a ciki a dole da ta ga ba shi da niyyan yin magana ta haƙura ta ce "Sir Najeeb tunda ko fatan alkhairi ba za ka min ba. Sai da safe"  ta gyara zaman jakarta ta fita daga office ɗin.

Certainly Anas ya ce ma sa Farida is engaged tuntuni, amma shi bai ɗauki abin serious ba. Tukunna ma wani mahaukacin za ta aura da zai iya zama da ita. Ya kalli ledar da ta ajiye ya ji wani takaici ya shigeshi. Haka kawai ya tashi ya ɗau ledar ya je ya jefa a dustbin da ya gama ya shiga banɗaki ya wanke hannun sa. Da ya dawo ya zauna, ran sa ya riga ya dagule, aikin da ya ke son yi ma kasa yi yai dole sai tattarawa yai ya bar office ɗin shima.

.........

Its like tunda Farida ta yi maganan sa ranan ta sai Najeeb ya rasa kan sa. Mafiya lokuta idan Farida ta zo sai ya ji wanni haushin ta fiye da da, haka nan kuma ba shi da abinda zai ma ta. A da tana ɗan tsoron masifar sa amma yanzu kam kamar ma ta maida shi kakanta ne.

Yau ya dawo a gajiye ya tarar da Mom ta dawo. Kamar ko yaushe bai kulata ba, ita ne ta ma sa sannu da zuwa amma bai kula ta ba.

"Sabreen asked about you"

Tsayawa yai da tafiya ya juyo ya kalli mahaifiyar ta sa.

"Dont you dare, kar ki ƙara min maganar ta"

Juyawa yai ya wuce ɗakin sa.  Yana cikin banɗaki ya kunna shower ruwa na zubo ma sa ya fara tuno rayuwar sa da Sabreen.

Sabreen ta kasance 'yar uwar sa ce,  Mahaifinta da Mahaifiyar sa cousins ne. Ita ɗaya ce a wajen iyayen ta kuma mahaifinta yana da mahaukacin kuɗi. Shekara uku ya bata amma tun suna raya su ka shaƙu, duk lokacin da su ka je hutu ƙasar Bahrain to su na tare. Ko lokacin da ya ke fama da matsalar rasuwan Aisha, Sabreen ta kasance macen da ya ke son kasancewa da ita a wannan lokacin. Duk da alaƙarsa da Mom ya ruguje hakan bai hana shaƙuwar sa da Sabreen ya lalace ba. Shaƙuwa ce tun da ga yarinta ta girma ta zama soyayya. Saboda Najeeb Sabreen ta dawo America da zama wanda ya zamo musabbabin komai.

Sabreen tana da kyau kuma tana ji da kan ta. Bayan ta yi karatu a Newyork Film Academy ta nuna sha'awarta na acting film maimakon directing da ta ce za ta yi da farko. Sun riga sun tsara yadda rayuwar su za ta kasance idan sun yi aure. Matsayin mai bada umurni da ta ce za ta zama, Najeeb bai da ja akan haka, kuma tun kafin a sa ranan auren su ta riga ta fara aiki da Hollywood inda ta zama assistant director a wani romantic film da yai tashe a lokacin.

Shirye-shiryen biki ake yi wanda iyayen biyu ke ta sake kuɗi kamar ba su san wahalan neman sa ba. Mom a wannan lokaci tana so ta yi abin gwaninta ko Najeeb zai yafe ma ta amma kash abu bai yiwu ba.

Saura sati biyu a ɗaura aure Najeeb ya koma Bahrain saboda anan za a fara hidima kafin daga baya a wuce Dubai daga Dubai kuma a wuce Italy sannan a ƙare hidiman a  Singapore.

Lokacin Najeeb yana ji da kan sa matashi ɗan shekara ashirin da bakwai. Sai dai kash! Saura kwana biyar a ɗaura aure Sabreen ta gudu bayan ta ajiye wasiƙa akan Najeeb yai haƙuri tana son sa amma ba ta shirya aure yanzu ba. Wannan shi ya ƙara birkitar da al'amarin Najeeb. Cikin ƙanƙanin lokaci ya lalace ya koma mara haƙuri mara fara'a kwata- kwata.
Wannan dalilin ne ya sa ya dawo Nigeria ya buɗe kamfanin sa, kuɗin da ya ke da shi da kuma aron kuɗi da ya ƙarɓa a wajen Daddy da su ya haɗa ya tada Najeeb constructions har ta zama abun da ta zama a yanzu. Shekaru bakwai kenan da su ka wuce ana cikin na takwas. Ba abin da ya ƙara ɗasawa Najeeb tsanar Sabreen irin bayan wata takwas da guduwa da ta yi sai ga shi an saki film ɗin da ta yi cikin turawa har tana kissing ɗin wani ƙaton kafiri a cikin film ɗin....*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣1️⃣8️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*


Farida na zaune a office wani babban mutum ya shigo office ɗin. Cikin fara'a ta gaida shi saboda irin su ne idan sun zo wajen Najeeb su ke ba ta alkhairi idan za su tafi.

"Barka da zuwa ranka shi daɗe"

"Yawwa beauty, sannu da aiki"

"Wa za ace ya zo?"

"Alhaji Matawalle"

Ta ɗau phone ta kira Najeeb. Yana ɗauka ta gaya ma sa ga Alhaji Matawalle ya zo.
Tana ajiye wayar ta ce " ka shiga"

Sun ɗan gaisa kafin su ka fara tattaunawa kan abinda ya haɗa su. Kusan 30mins suna magana kafin su ka cimma matsaya ɗaya. Najeeb ya ƙarɓi takardun hannun Alhaji Matawalle yana dubawa kafin yai signing.

"Na ce ba, wannan sakatariyar kan nan..." bai ida maganar ba Najeeb ya ɗago ido ya ma sa wani kallo.

Maganar da Alhaji Matawalle ke son faɗa daban amma dole ya haɗiyeta ya buge da cewa

"matar aure ce?"

"Alhaji Matawalle  ka zo waje na ne ko wajen sakatariya ta ka zo?"

"Kai Allah yarinyar nan tana da kyau ga fara'a ga...."

Najeeb ya ture takardun hannunsa gefe ya ce " idan ka shirya aiki da ni sai ka dawo"

"Haba Najeeb, wanni irin magana ne wannan?"

"Ka jini da kyau Alhaji Matawalle, now leave"

"Shashashan banza shashashan wofi. Har ni za ka kora a office ɗin ka. Za ka gani"

Alhaji Matawalle ya ɗau takardun ya fita fuuuu...

............

Ranan Jumma'a bayan an dawo daga sallar jumu'ah Najeeb ya kira ta.

"Ki shirya, za mu je Lagos ranan monday"

"Haba yallaɓai ai ko ni buhun gawayi ce iya ka ci. Haka kawai ka ce in shirya mu je Lagos ba tareda na san abinda za muyi ba"

Ya ɗan yi shiru na wasu daƙiƙai kafin ya ce " akwai 2days bid da za'ayi a Lagos and its important for this company"

"Zan tambayi Baffa, idan ya barni to idan bai barni ba shike nan sai ka je kai kaɗai ko ka ɗau wani ku je tare" daga haka ta fita daga office ɗin.

Da dare ta samu Baffa Musa da maganar amma ya ce ba za ta je ba.

"Baffa ni da Oga na ne fa"

"Ogan na ki mijin ki ne da za ki bi shi har Lagos da sunan aiki, ku je kuna kwanan hotel"

"Baffa daɗina da kai gidadanci"

Daƙuwa ya ma ta ya ce  "zan ci uban ki Farida"

"Yo Baffa ai kai ne Uban nawa, sai ka ci kan ka, kawai"

Baffa ya taso zai mangareta ta fita daga falon da gudu tana dariya.

"Wannan yarinya wannan yarinya, Allah dai ya shirya min ke"

Baffa bai amince da tafiyar ba sai ranan Lahdi bayan ta ma sa alkawarin a gidan Maijiddah za ta kwana ba a hotel ba.

Ranan monday Najeeb da Farida su ka wuce airport da sassafe, wanda dreban Daddy ne ya kai su, ba su jima ba jirgin su ya lula sama.
Wannan karan ne farkon hawa jirgin Farida, ta dinga surutu tana cewa " dama ance albarkacin Kaza ƙadangare kan sha ruwan kasko, Sir Najeeb na gode Allah ya samu a damshin ku, irin wannan matsayi haka. Wa ya ga Aisha Farida ta shiga jirgi"

As usual bai tanka ma ta ba dan ba ya da abinda zai ce. The girl talks too much...

Kamar yadda aka tsara ɗin su na gama taron na ranan dreban gidan AbdulWahab ya zo ɗaukan ta.

Da za ta tafi ta ce "Sir Najeeb ka zo mu je a rage ma hanya"

Idon sa ne ya ba ta amsa ba baki ba. Ta san ma'anar Kallon na sa dan haka ta ce "Allah ya ba ka haƙuri, sai gobe"...

Gidan Maijiddah ya ma ta kyau ɗakuna shida ne a gidan. Uku a sama uku a ƙasa, ɗakin AbdulWahab Aneesa da kuma yara su ne a sama ita Maijiddah kuma na ta na ƙasa.

Saboda traffic ba su isa da wuri ba duk sai da ta gama gajiya kafin su ka iso.
Maijiddah a ɗakin ta ta sauketa, tana tsananin farin cikin ganin ta.

"Barin kawo miki abinci Anty Farida, kafin nan ki ɗan watsa ruwa, ga banɗakin" ta nuna ma ta ƙofar banɗakin da ke cikin ɗakin.

"O'o su Jiddah Amarya, muma dai za mu zo wajen"

Har Maijiddah ta kai bakin ƙofa ta ji Farida na salati. Ta juyo da sauri "Anty miya faru?"

"Jiddah ashe duk jan kunnen da na miki duk a banza. Dan Allah a ina kika samo wannan bujen kayan"

Maijiddah ta kalli kan ta, pakistan ta saka riga da wando amma wandon irin mai buje ɗin nan ne.

"Anty a cikin kayan lefe na ne"

"Ki na amarya auren wata biyu da 'yan kai, ki ɗauko wannan bujen wandon ki saka, dan Allah dan Annabi. Wallahi ko ni budurwa ba zan sa bujen wando haka ba balle ke matan aure, ga pakistan ma su pencil wanduna ba ki sa ba sai ki sa mai bujen wando. To maza ki cire kuma idan ba wai kin kai an shaping wandon ba kar ki ƙara saka kayan nan"

"Anty na ji, ki shiga ki yi wanka ina zuwa"...

'Yan kwana biyu da Farida ta yi a gidan Maijiddah ta sha faɗa kaman ba gobe, musamman da Jiddan ta ba ta labarin irin kayan da Aneesa ke sawa idan ta zo.

"Ke me ya hanaki sa irin kayan?"

"Anty Farida, a gaban yaran sa sai insa ƙananan kaya 'yan ficil-ficil ɗin nan. Idan uwar su ba ta da kunya ni inada shi"

"Lallai ke jaka ce Jiddah, dama ustazan nan yawancin ku sai a hankali. Wacce ayar ce ta hana ayiwa miji shiga ta ado da jan hankali"

"Anty Farida ba fa mukaɗai ba ne a gidan"

"Maza na shigowa ne?"

"A'a"

"To wallahi ki shirya zama boyi-boyi a gidan nan, very soon idan kin gama amarcin nan za a ajiye ki gefe saboda ƙauyanci da gidadanci da ya mi ki yawa"

Maganganun Farida shi ya ke ta yawo a ƙwaƙwalwarta lokacin da ta ke dudduba ƙananun kayan da Faridan ta ba ta lokacin auren ta.
Ranan laraba su Farida su ka tafi ita kuma Aneesa ta zo ranan Alhamis da dare. Duk cikin weekend ɗin nan a takure ta yi shi. Dama tsarin AbdulWahab ɗin ko na Aneesan ne ma oho, duk lokacin da Aneesa ta zo to yana ɗakinta har sai ta tafi, ita kuma sauran ranakun na ta ne.

Yau da safe Aneesa za ta koma Abuja. For once a rayuwarta tana so ta cire kunya da tsoro.

Ta tuno faɗan Farida lokacin da ta ce kunyan saka kayan ta ke ji.
"Shegiya kunya ya ƙare a abinda kukeyi da dare. Miye bai ganiba ajikin na ki da za ki dinga ɓoye ma sa"

Ta ɗauko micro mini skirt na blue denim jeans ta saka, cikin tops ɗin da Faridan ta haɗo da shi ta ɗauki wata fara wanda ta fi kama da vest amma V-neck gareta. Ta tsaya jikin madubi tana kallon kan ta, da ke guntuwa ce sai ƙananun kayan su ka amsheta sosai. Ta tufke gashinta da ta sawa ribbon ta nannaɗe shi kamar doughnut. Idan akwai abu ɗaya da ta san mijinta na so kuma ya ke ja ma sa hankali bai fi gashin ta ba. Dama Farida ta gaya ma ta kowanni namiji akwai abinda ya fi attracting na shi a jikin mace. Wa su ƙirji, wa su hips, wa su ƙafa wa su gashi da sauran su. To itakan ta san dogon gashin ta ne, AbdulWahab ba ya gajiya da shafa gashinta yana sa fiskarsa ciki yana shaƙar ƙanshin sa.
Takalmi mai ƙasan wedges ta saka dan ba ta iya tafiya da heel ba...

Su na cin breakfast a dining ta fito. Alizah ce ta fara hangota ta ce " Wow! Anty you look beautiful"

Ta ɗan yi murmushi ta ce "Thank you dear"

Sai da ta zauna Baby ta ce " i love your hair Anty"

Maijiddah ta yi murmushi, ta sa hannu tana wasa da gashin na ta ba tareda ta yi yunƙurin ɗiban abinci ba.

Normally idan Aneesa na nan ba ta zama ta ci abinci da su amma yau tana so ta rama abinda Aneesan ke ma ta ne.

Shi kam AbdulWahab tunda  ya ɗaga ido ya kalleta bai iya saukewa ba. Sandwich da ya riƙe tuntuni shine bai sauke ba kuma bai ci ba. Sai da Aneesa ta yi magana sannan hankalin sa ya dawo jikin sa.

"Sweetheart za ka dropping ɗina a Airport ko?"

" No Anny, zan makara idan na kai ki"

Ta gama gane mijin na tan ya ɗan bircike akan Maijiddan. Ta san mijinta na son ya ga mace ta sa sexy ƙananan kaya, shi ya sa duk lokacin da ta zo ta ke sawa dan hankalin mijinta ya tsaya a kanta, sannan a tunanin ta Maijiddah ba za ta iya saka irin waɗannan kayan ba dan tun day one da ta ganta ta ke ma ta kallon local girl. Sai ga shi kuma yau ta proving na ta wrong.

Nonye ta zo ta tafi da yaran bayan sun karya saboda makaranta da za su je. Su ma su Aneesan sun gama karyawan amma ta ƙi tashi saboda AbdulWahab ya ƙi ya ƙare cin abincin.

"Sweetheart time fa ya tafi"

Ya ɗan yi gyaran murya ya ce "yanzu zan gama. Yau na tashi da muguwar yunwa ne"

"Namiji munafiki" Aneesa ta faɗi a zuciyarta. Ta san dalilin Maijiddah ya sa shi ka sa ƙarasa abincin akan lokaci.
Ala dole ya tashi saboda Aneesa da ta tsaya a kan sa. Tare su ka fita daga gidan amma minti shabiyar kacal sai ga AbdulWahab ya dawo. Maijiddah na kan tattare dining ɗin ta ji an rungumeta ta baya. "Princess yau ba kya so na je office ko?"

" Yaya ni a su wa, ka je Allah ya kiyaye hanya"

"Wasa ki ke yarinya, wani office kuma bayan ban gaisa da gimbiya ta ba"  ya ɗauko wayansa ya ma ta hoto kafin nan ya ɗauketa cak su ka shige ɗakin ta wanda shine mafi kusa.

............

Wannan weekend ɗin ta je Jos kuma ba ƙaramin jin daɗi ta yi ba domin weekend ɗin ƙarshen wata ne, kaso mai tsoka ta ware cikin kuɗin ta ta tafi nemo sexy gwanjuna a kasuwa, tanaɗin biki takeyi tun kafin abin ya matso daf ta rasa lokacin zuwa Jos.

"Kin gaya ma sa kin taɓa aure?" Maganar da ta sa Farida ta ka sa kai lomar tuwon da ta yanko kenan.

"Ba na so a samu matsala kin san 'yan gulma, gara ki gaya ma sa tun kafin ya ji a waje"

"Ummi na ga ban tareba ai"

"Duk da haka, Farida ba na son a samu matsala a bikin ki irin na wancan karan. Gara duk wa ta ƙofa da zai kawo fitina a toshe ta tun kafin lokacin.

Da wannan zance ta koma Kano, zuciyar ta na tsoron abinda Rayyan zai ce idan ya ji wannan ba tu.

Sai da ta kwana biyu tana tunanin yadda za ta faɗa ma sa kafin daga baya ta yanke shawaran komai ta fanjama fanjam.

Tun kafin ya zo dama ta gaya ma sa tana da magana da shi. Dan haka da ya zo hira yau sama-sama su ka gaisa ya ce yana sauraron maganar ta.

"My Ray akwai abinda ya kamata ka sani gameda ni. It will come to you as a shock amma ka yi haƙuri"

"Ina jin ki"

"Na taɓa aure"

Ya zaro ido yana jiran ƙarin bayani.

"Yes, shekaru uku da su ka wuce an ɗaura aurena da Lukman, sai dai ko tarewa ban yi ba aka raba auren saboda matsalar da ta taso"...

Lokacin da ta gama bashi labarin Lukman yai shiru yana nazari daga ba ya ya ce " kin ga ke rabona ne, shi ya sa komai ya wargaje a lokacin"

Ta yi mamakin maganar sa dan ta ɗauka zai yi fushi saboda rashin gaya ma sa da ba ta yi ba da wuri.

*waye Lukman?*....*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣1️⃣9️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

Khairat Ilyas Magaji ta taso cikin gata da jin daɗi a gaban iyayen ta. Iyayen ta ita kaɗai su ka haifa wannan ya sa su ka ɗaura dukkan ƙaunan su a kan ta. Mahaifinta da Mahaifiyar ta dukkan su mutanen Kebbi state ne.
Tana ƙare secondary school mahaifinta ya turata karatu ƙasar South Africa inda anan ta haɗu da Lawrence su ka fara soyayya.

Lawrence  Schneider asalinsa Bayahuden ƙasar Germany ne amma a South Africa aka haifeshi.

Rashin isashshiyar ilimi na addini,rashin tarbiya mai kyau da kuma son zuciya su suka sa Khairat ta sakamar Lawrence ragamar rayuwarta har ta koma ko Sallah ba ta yi saboda idan Lawrence ya ganta tanayi yana fushi da ita.
Gidan da iyayen ta su ka kama ma ta, ya koma tamkar gidan ta da na Lawrence, domin kusan koyaushe anan ya ke kwana. A wani hutun dogon zango da ta zo Nigeria, lokacin shekararta na uku kenan a makarantar ta fara rashin lafiya. Aka ma ta treating ɗin shi sai kwana biyu kuma zazzaɓin ya sake dawowa. Wannan karan da su ka je asibiti aka ma ta gwajin ciki, sai ga shi result ya fito tana ɗauke da cikin wata uku.
Alhaji Magaji da matar sa ba su shiga tashin hankali ba sai da Khairat ta ce ai cikin na Lawrence ne.

"A Jew! Khairat ba ma Christian ba Jew. Wanda sun fi kowa tsanar musulmai" Alhaji Magaji ya faɗa cikin masifa.

Sun yi ƙoƙarin zubar da cikin aka ce mu su akwai haɗari saboda Khairat ta jima tana shan maganin hana ɗaukan ciki kuma ya sa mahaifarta yai rauni.

Lokacin komawa makaranta yai Alhaji ya hana Khairat komawa. Shi da kan sa ya je har South Africa neman Lawrence. Abin takaici a gidan da ya kamawa Khairat anan ya samu Lawrence yana hutawa da wata baturiyar karuwar sa.

Ko da ya shaidawa Lawrence Khairat na ɗauke da cikin sa dariya yai ya ce "who wants to have a baby with a moslem whore"

Alhaji dan takaici bai san lokacin da ya mari Lawrence ba. Abu kamar wa sa sai ga shi an kama Alhaji Magaji saboda ya mari Lawrence. Kasancewar sa baƙar fata ya sa abun ya kuma sawa kotu ta ɗau tsauri akan al'amarin. A ƙalla Alhaji Magaji sai da yai wata kusan uku a ɗaure kafin aka fitar da shi nan ma bayan ya biya tara wa Lawrence.

Wannan ya ƙunsawa Alhaji da matarsa baƙin ciki. Itama Khairat ɗin tunda ta ji abinda Lawrence yai sai jikin ta yai sanyi.

Duk min lalacewar ɗa dai na ka ne. Haka Khairat ta raini cikin shegen ta a gidan su har lokacin da ta cika watannin haihuwa. Wata rana da tsakar dare ta tashi da naƙuda iyayen ta su ka kaita asibiti. Ta jima tana labour kafin ta haifi ɗa namiji.

Nurse ɗin da ta sanar da su haihuwar Khairat ita ta cikata maganar da cewa Allah ya yiwa Khairat rasuwa.

Bayan an yi bakwai ɗin Khairat Alhaji ya fara shirye-shiryen barin Kebbi saboda gulmace-gulmace da ake yi akan mutuwar Khairat.

Garin Jos Alhaji ya dawo da iyalin sa, inda su ka cigaba da rainon Lukman tamkar ɗan cikin su. Tarbiyan da ba su bawa Khairat ba, shi su ka duƙufa su na ba wa Lukman.

Lukman Ilyas Magaji ya taso cikin tarbiyya mai kyau, ga shi dama yaron mai biyayya ne. Tun yana shekara shahuɗu yai haddar ƙur'ani, yana da ilimi na boko da addini.  Alhaji Magaji da Hajia Zainab su ya sani a matsayin iyayen sa har ya girma ya zama ƙwararren Likita.

Wata rana a asibitin Juth inda ya ke aiki aka kawo wata yarinyar cikin uniform mota ya bigeta. Wasu couples ne Mr and Mrs Owulum su ka kawota saboda su ne su ka bigeta da mota.
Yarinyar tun kan a fara duba ƙafarta ta fara ihu tana kuka tana faɗin Allah ya isa.

Lokacin da aka fara stitching kuwa tana kuka tana lissafta abinda Mr Owulum za su kawo.

"Wallahi Kaji goma za ku kawo, na gida biyar na Agric biyar. Kuma wallahi luƙa-luƙa dan ba na son ramammu"

Dr Lukman bai san lokacin da ya fara dariya ba. Ƙarin dariyan ma, Mr Owulum da matar sa ba sa jin Hausa. Ita kuma ta dage sai lissafo abubuwan da za a kawo ta ke yi.

Sai da a ka gama ya kalleta ya ce " Aisha duk lissafin nan fa ba su gane ko ɗaya ba, ba sa jin Hausa."

"Kan Uban chan! To wallahi  chicken, 10  big chicken Mr Igbo man"

Lukman mi zai yi ban da dariya. Kafin su tafi da ita sai da Lukman ya kusa fitsari a jiki saboda dariya.  Ko da ya je gida sai da ya bawa Mom da Dad labarin Aisha mai Kaji goma.
Washegari ma Mr Owulum ne ya kawota amma wannan karan har da Ummi da Nanna. Anan ya ke tambayar ta ko an kawo ma ta Kajin.

Ummi ta ce "ashe a gaban ka aka yi ko?"

Dr Lukman ya ce "na ga alama Aisha na son kaza"

Da za su tafi ya ce "Aisha Kaji nawa su ka kawo"

"Dan uban su shabiyu, shabiyu su ka kawo"

Dr Lukman yai murmushi.

Duk zuwan da za su yi sai Dr Lukman ya tabbatar shi ya duba ciwon Aisha. Bayan sati biyu da haɗuwar su wata ranan Jummu'a sai ga Dr Lukman a gidan su ya zo gaisheta. A wajen Mr Owulum ya samu
address ɗin ta.
Har cikin gida ya shigo ya gaida Baba da su Nanna da zai tafi Farida ta rakashi har wajen motar sa.
Ya shiga mota ya miƙo ma ta ledoji guda biyu.

"Dr green eyes har da wahala haka to an gode"

Dr green eyes ta ke ce mishi  tun ranan da ta fara ganin shi, kasancewa ƙwayar idon sa green ne, wanda ya samo asali daga mahaifinsa Lawrenc.

A hankali Farida da Dr Lukman su ka shaƙu har soyayya ta shiga tsakani. Ko da ta zana WAEC da NECO Lukman ne ya ƙara ma ta ƙarfin gwiwa akan ta ci gaba da karatu.  Da ba ta samu university ba ya ƙarfafa ma ta gwiwa akan kar ta zauna haka.

Lokacin da Farida ta ke aji biyu na diploma aka bayar da ita wa Lukman da zimmar tana ƙarewa za su yi aure.

Kowa ya san Alhaji Ilyas Magaji dattijon arziƙi ne, haka nan ɗan sa Lukman shima saurayi ne da aka ma sa shaida mai kyau a ko ina.

Rana ba ta ƙarya Farida ta gama diploma, aka fara shirye-shiryen bikin ta da Lukman.

A Wase za'ayi auren dan haka sati ɗaya kafin ɗaurin aure Farida ta koma chan. Mutanen Kano da Dukku duk sun hallara a wannan biki. Ba wanda ya fi jin daɗi ma kamar Baffa Musa saboda shi bai so har ta kai harka ba tareda an aurar da ita ba. Shi Mutum ne da bai yarda da karatun mace a gidan su ba.

Anyi kamu, anyi walima komai ya tafi lafiya. Ranan Asabat aka ɗaura auren Lukman Ilyas Magaji da Aisha Farida Salihu. Bayan an ɗaura aure ana ɗan gaggaisawa cikin 'yan uwan Alhaji Magaji da su ka zo daga Kebbi, wani ya fara magana da Alhaji Magaji bayan ya tabbatar a kusa da Baffa Musa su ke kuma maganar ta su ba a hankali su ke ba.
"Allah ya jiƙan Khairat, yau da kun ma ta tarbiya kaman yadda ku ka yiwa Lukman da Lukman bai zama ɗan shege ba"

Alhaji Magaji ya haɗe rai yana hararan ɗan uwan na sa wanda su ke 'yan uba.

Cikin rashin fahimta Baffa Musa ya ce " ban gane ba Alhaji Magaji. Wani irin ɗan shege?"

"au ba ku san Lukman ɗan shege ba ne? Lallai! Ai Lukman jikan Alhaji Ilyas ne, wadda 'yar sa ta haifa ma sa shi shege. Ance ma saurayin na ta ma wani bayahuden bature ne" Alhaji Kamalu yai wa Baffa Musa bayani.

Lokaci guda Baffa Musa ya hau faɗa yana masifa, kafin ka ce me wajen ɗaurin aure ya hautsine. Alhaji Magaji ba abin da ya ke sai hawaye.

Lukman na wajen masallaci  su na hotuna da abokan sa aka zo ma sa da wannan mummunan labarin. Da farko bai yarda ba sai da ya shiga masallacin ya ga Alhaji Magaji yana hawaye. Shi kuma Alhaji Kamalu yana ƙara zuba bayani kan yadda Alhaji Magaji ya sakalta 'yar sa Khairat har ya kaita ga karuwanci a ƙasar waje.
Lukman dai a take a wajen ya suma.

Amarya Farida tana cikin ƙawayen ta ana hira ana ma ta kwalliya. Sai tsokanarta su ke wai yanzu kam an ɗaura aure ta zama Mrs Lukman Ilyas Magaji.

Wajen ƙarfe sha biyu ta gota kaɗan labarin abinda ke faruwa ya iso mu su gida.

Wassu cikin 'yan uwan su mata su ka fashe da kuka ana ta kururuwa ciki har da Inna Tabawa.
Wannan hayaniya ya sa Farida da ƙawayen ta su ka fito daga ɗaki su na tambayar abin da ke faruwa.

"Wai ashe Lukman ɗan shege ne" wata ta faɗa da ƙarfi.

"Ɗan shege kuma?" Farida ta faɗa cikin rashin fahimta.

"Wallahi, ance uban sa ma kafiri ne. Yanzu haka su Baffa Musa sun ce sai ya sake ki dan ba za ki auri ɗan sheg..." ta tsaya da maganan lokacin da Farida ta yafuto ta tana dukan ta ta ko'ina.
Da ƙyar aka raba Farida da matar nan. Farida sai zage-zage ta ke tana faɗin ita ko Lukman ɗan Alade ne za ta aure shi.

Gidan biki fa sai ya zama tamkar gidan makoki. Zuwa ƙarfe tara na dare kafin su Baffa Musa su ka dawo kowa so ya ke ya ji mi ake ciki amma Bai yi magana ba cewa yai kawai a fara haɗa kayan lefen da aka kawo da duk wani abu da aka san daga gidan su Lukman aka kawo.

Farida ta yi kuka kamar idon ta zai zazzago. Zuwa tsakar dare zazzaɓi ya rufeta a inda ta ke zaune ta fara kakkarwa, ƙarshe ta faɗi ta suma...

A ɓangaren Lukman ma ko da ya farfaɗo sai da ya sake  suma sau uku. Zuwa yamma da jikin sa ya ɗan warware su Baffa Musa su ka zo gadon sa da buƙatar ya rubutawa Farida takardar saki, tareda cewa sun mayar ma sa da sadakin sa yana wajen Alhaji Kamalu tunda Alhaji Magaji ya ƙi ƙarɓa.
Lukman bai ce mu su ƙala ba sai hawaye kawai da ya ke ta yi.

Washe garin da wannan al'amari ya faru Baffa ya karɓo takardar sakin Farida wanda har lokacin tana kwance a asibiti.

Duk da 'yan uwan Lukman ba su buƙaci kayan da aka kaiwa Farida ba amma Baffa Musa sai da ya sa aka mayar mu su.

Wasa-wasa sai da Farida ta yi sati biyu a kwance a asibiti kafin aka sallamota. Tun daga  nan ta koma kamar ba ita ba, ba ta surutu balle hayaniya. Kano Baffa Musa ya so ta bishi a lokacin amma ta ƙi, ta koma wajen Ummin ta a Jos.

Bayan wata ɗaya da dawowanta Jos, Lukman ya zo ya ma ta sallama akan zai tafi Egypt ƙaro karatu. Ya ma ta fatan alkhairi tareda cewa har abada ba zai dena son ta ba. Duk yawan surutun Farida ranan ka sa cewa komai ta yi sai kuka.

"Aisha ina miki fatan alkhairi, ina kuma mi ki kwaɗayin ki cigaba da karatu, and above all" ya goge hawayen da ke shirin zubo ma sa.
"I want you to open your heart for someone else. I want you to always be happy no matter what"

Ta fi jin tausayin shi fiye da kan ta. Shekaru talatin da ɗaya ace rana tsaka kawai a  sanar da kai kai ɗin ba ka da asali, kai ɗin ɗan shege ne.

"Greeneyes, yanzu duk alƙawurran mu, duk burikan mu sun tafi a banza kenan?. Yanzu duk yadda mu ke son junan mu ba za mu kasance tare ba?"

Ajiyar zuciya yai ya ce " za ki samu wanda ya fini Aisha. Kyau, ilimi, dukiya da wayewa za ki samu wanda ya fini su. Za ki samu wanda zai so ki fiye da yadda na ke son ki Aisha. You never know, sai ki ga idon sa ma yafi nawa kyau"

Farida ta ɗan yi dariya ta ce " green eyes babu mai irin wannan siffan fa"

(Ni kam na ce ba ki je Kano ba ne😁)

Wannan ne ƙarshen Farida da Lukman. Tun daga ranan ba ta sake ganin sa ba har yau.
(Amma ta ga mai siffofin da Lukman ya bayyana😁)

Lokacin da aka fara saida form ɗin HND ta siya ta koma makaranta. 

Wannan kenan.

........................

Satin su ɗaya da dawowa daga Lagos aka aiko cewa sun winning bidding ɗin da su ka je, kuma an ba su dama su yi samfurin (modelling)  wannan gine-gine da za a yi.

Wannan karon kam ta ga seriousness sosai a kamfanin, domin ko yaushe ana kan meeting yadda komai zai tafi dai-dai domin aiki ne da za su yi wa federal government kuma ba ƙaramin miliyoyi za su samu ba idan su ka yi aikin.

Wani lokacin Sir Najeeb a office ya ke kwana. Cikin kwana biyar har ramewa Farida ta ga Sir Najeeb ya yi. Yadda ta ga kowa na kaffa-kaffa da shi haka ya sa itama ta ke taka tsan-tsan da shi.

Yau monday aka shirya meeting a conference room na su, duk wani babban Engineer ko Architect da ke aiki a Najeeb constructions sai da ya hallara.

Bayan an playing mu su power point da ke ƙunshe da zannen da aka yi. Sannan Najeeb ya zo gaban wani table mai faɗi ya ce "Ladies and Gentlemen. Ga biggest project  na mu na wannan shekara, project Alpha"

Lokacin da ya buɗe mayafin da aka rufe teburin da shi sai ga modelling ɗin ginin da za su yi. Har ta Farida da ba ta san komai akan aikin zane-zane da ƙere-ƙere ba sai da wannan modelling ya matuƙar burgeta.

Maganar Farida ta ranan ya tuno lokacin da ya ga Farida ta buɗe ido da baki tana ganin model ɗin.

Jawabin godiya ya fara bayan an gama kallo.

"Ina godiya wa team Alpha da su ka taimaka da bani ideas, wanda da su na yi amfani na fito da wannan zanen. Special thanks to Architect Anas, Architect Ifeanyi, Engineer Ɗayyabu, Engineer Mathew..." haka ya kira mutane goma da su ka yi aiki tare ya mu su godiya.

"Sir Najeeb ni ma a gode min, na yi ta aikin zirga-zirgan kai saƙo da ƙarɓo saƙo ai" muryan Farida ya ƙaraɗe hall ɗin. Nan aka fara dariya. Najeeb kam kallon " are you for real" yai wa Farida...

........

Tana shirin fita daga gida ta ji shigowar alert a wayan ta. Ta ɗauko wayan ta duba dan ta san ba ƙarshen wata ba ne. Dubawan da za ta yi sai ga alert ɗin miliyan biyu da ga VESTAC.Inc......*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣2️⃣0️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

Tana zuwa office ta samu ana ta shirye-shiryen baƙin da za su zo. Ba ta yi maganar kuɗi da kowa ba dan dama  Yakubu ta ke son tambaya ko ya san kamfanin VESTAC. Kafin ta tafi Bank ta bi bahasin wannan uban kuɗi da ba ta san ko ɓatan kai yai ya shigo account ɗin ta ba.

Ba ta ga Sir Najeeb ba, ta san shima yana chan yana ta shirye-shirye.

Sai ƙarfe tara da rabi Najeeb ya zo office. Wankan yau ma daban ta ke, ta san yana da kyau kuma ya iya wanka ba ƙarya sai dai yau wani extraordinary kyau ya ma ta na daban.

Minti goma da shigan sa office Anas ya zo ya wuce a bircike, ko amsa gaisuwan Farida bai yi ba.

Maganar da yaiwa Najeeb ne ya sa Najeeb ya tashi a hargitse yana faɗin What!

"Najeeb takardun zanen ba sa nan and the model is..."

Najeeb bai saurari ƙarshen ba ya fita da gudu.
Farida na zaune tana cin aya ɗanya da ta siya jiya ta ga Najeeb ya fito da gudu. Kasancewar ance Aya na sa ƙarin ni'ima ya sa ta lazimci cinsa ko kuma ta yi kunun aya ta sha tunda ta kusa shiga daga ciki.

Shima Anas bin bayan sa yai da gudun.

Yana tsaye gaban table ɗin yana kallon yadda aka faffasa model ɗin da ya sha wahala wajen haɗawa, and box ɗin da aka ajiye takardun zanen, shi ma empty ba komai a ciki.

Yana tsaye yana huci idon sa ya kaɗa yai ja hannun sa ya fara kakkarwa. Leɓensa na ƙasa ya ciza da ƙarfi amma still bakinsa bai bar rawa ba.

"Na sa an duba camera footage ɗin amma kuma tun jiya da rana baya aiki. It seems kamar an tampering na shi ne"

"Who is the last person to enter this place?" Ya faɗa cikin muryarsa mai fidda amo.

Anas yai shiru dan bai san ta yadda zai fara ma sa bayani ba.

"Who?" Ya sake faɗa da ƙarfi.

"Ba na tunanin za ta yi haka, CCTV footage ya nuna ta shiga ta duba model ɗin har ta ɗau hoton su sai ta fita daga nan kuma bai sake aiki ba"

"Who?" Ya faɗa wannan karan a hankali.

"Farida, your secretary"

Juyowa yai a hankali yana huci, yadda Anas ya ganshi sai da ya tsorata.

"Najeeb i'm sure ba ita ta faffasa abun nan ba, there's explanation to this"

"Sir Najeeb baƙin sun iso" wani staff ya shigo ya faɗa.

Kawai sai Najeeb ya fashe da dariya, dariya sosai har da ƙyaƙyatawa.

"Najeeb fa za mu yi?"

Cikin dariya ya ce " ya za mu yi? Hhhhhhhh. Dude she won, she succeeded. Abinda ta ke so kenan dama, to make me look stupid. Ka san mi ta yi ranan? Na san ta gaya ma ka ma, but let me tell you again. This crazy bitch puts superglue on my seat, and ...and do you know what she said?"
Ya sake fashewa da dariya " she said *Tsuliyar CEO Najeeb Constructions a waje* the bitch dare say that to my face. Yanzu na san mi ta ke nufi, she wants me to be humiliated, to look stupid"

"Najeeb plz calm down" Anas ya faɗa yana ƙoƙarin dafa abokin na sa.

"Calm down?"

"Za mu nuna mu su 3-D powerpoint ɗin sannan mu ba su haƙuri akan modelling ɗin sai gobe, then kafin goben...."

"If you are stupid i'm not Anas, we've lost this contract"

Ya mangaje Anas ya fita a wajen. Wajen baƙin ya je aka gaggaisa sama-sama. Anas na wajen yana tunanin mi Najeeb zai yi.
Kawai sai ya ce baƙin su biyoshi. Su na zuwa ya nuna mu su modelling ɗin da aka ɓata.

"I'm sorry but a bitch secretary i hired did this"

Nan su ka fara masifa " this is unprofessional, Mr Jibo taya za ka bari mu zo tundaga Abuja only to see a destroyed work"

Anas ya shiga ba su haƙuri yana ƙoƙarin nuna mu su hoton zanen a Tab ɗin sa amma ba su saurare shi ba. "We are highly dissappointed in you Mr Jibo"  babban cikin su ya faɗa sannan ya juya su ka tafi. Najeeb bai ce komai ba shi kuwa Anas bin bayan su yai yana ƙara ba su haƙuri amma ba su saurare shi ba...

Najeeb ya jima a ɗakin kafin ya fito, yadda ya ke tafiya kaɗai ka san yana cikin tsananin ɓacin rai.
Yana shiga office ɗin ta ya tadda Farida tana waya sai dariya ta ke.

Kallon tsana ya fara ma ta kafin daga baya ya nuna ta da ɗan yatsa " i will revenge Miss Salihu, bit by bit"
Tunda ta ga yadda ya shigo fiskarsa ba alamun wasa ko kaɗan ta yi saurin kashe waya tana sauraron mi zai ce dan ta ɗan tsorata da yanayin sa.

"Ni kuma mi na yi" ta faɗa lokacin da faɗi kalmar ɗaukan fan sa.

Ba a jima ba Anas ya shigo.

"Najeeb mutanen nan sun tafi, we lost the project"

Najeeb bai kulashi ba ya ma rigingina kansa jikin kujera yana kallon sama ya ɗan juyawa a jikin kujera a hankali.

"Najeeb lets investigate this issue. Ina da yaƙiƙin ba Farida ba ne ta yi wannan aiki"

"She did it" Najeeb ya faɗa a hankali.

Kafin Anas ya fito Yakubu ya zo office ɗin Farida yana ba ta labarin abinda ya faru. Farida ta dafe ƙirji tana faɗin " wayyo Allah, yanzu wahalan Sir Najeeb duk a banza"

"Farida mi ya sa ki ka shiga wajen nan?"

Ta ɗan rage murya ta ce " ba dai kana tunanin ni na yi wannan aika-aikan ba"

"Farida camera ya nuna ke ce ki ka shiga wajen nan na ƙarshe and ke yanzu ake zargi"

"Na shiga uku wata sabuwar sharrin da za a min kenan. Ni fa abin ne ya min kyaun na je na ɗau hoton sa. Ga ma hotunan a wayana" ta ƙarisa maganar tana ƙoƙarin buɗo hotunan a wayarta.

Anas ya fito ya same su, the same tambaya ya ma ta akan miya sa za ta shiga ɗakin nan, amsar da ta bawa Yakubu shi ta bawa Anas.
Anas ya girgiza kai ya ce " Farida akwai matsala fa, Najeeb yana zargin ki, kuma idan ba'a gano wanda yai wannan abin ba i'm sorry but abinda Najeeb zai iya mi ki ba zai tsaya a kora kaɗai ba"

"Wayyo ni Aisha, yanzu ba za a barni na rabu da Sir Najeeb lafiya ba"

Bayan sun bar office ɗin ta ta shiga office ɗin Najeeb, har lokacin yana zaune yana kallon sama.

"Sir Najeeb wallahi wallahi ban ruguza ma ka aikin ka ba, hoton abin kawai na ɗauka saboda ya birgeni" haka ta dinga zancen ta ita ɗaya ba tareda ya tanka ma ta ba, da ta gaji da kan ta ta fita daga office ɗin.

Wannan abu ya sa ta manta da batun miliyan biyu da ta gani a account ɗin ta da safe.

Zuwa rana duk Farida ta shiga damuwa, wannan ya shigo ya ma ta Allah wadai da halin ta wannan ya shigo yana son yi tsaigumi da gulma. Tun tana mu su masifa har ta gaji ta haƙura, idan mutum ya zo har ya tafi ba ta tanka ma sa.  Ranan fa gaba ɗaya kamfanin ya rikice. Rashin samun wannan contract zai jawo mu su asara sannan sunan Kamfanin su zai samu mummunan shaida a gari da ƙasar ma gaba ɗaya.

Lokacin da aka tashi Farida da ƙyar ta tashi ta tafi bayan ta leƙa Sir Najeeb wanda har lokacin ke zaune a kujera.

"Sir na san inada rigima amma wallahi ba zan yi abinda na san zai janyo wa kamfanin ka asara ba, tunda na san dukkan mu nan muna ci a ƙarƙashin ka" abin da ta faɗa kenan lokacin da za ta fita.

Ko da ta je gida ka sa taɓuka abin kirki ta yi. Jira kawai ta ke Yakubu ya dawo ta ji mi ke faruwa. Sai dai Yakubu bai dawo ba har chan dare lokacin ita kuma ta yi bacci.

Washe gari da sanyin jiki ta shirya ta tafi wajen aiki.
Ta fara zuwa office ɗin Yakubu amma ba ya nan. Haka ta wuce office ɗin ta tana fargaban mi za ta tarar.

Tana zuwa ta leƙa office ɗin Sir Najeeb amma ba ya ciki. Ta koma na ta office ɗin ta yi jugum. Ƙarfe tara saura Anas ya shigo, fiskar sa ba yabo ba fallasa.

"Yaya na ya aka yi?"

"Akwai babban matsala Farida. Kina cikin matsala, za'ayi board meeting a kan ki anjima. A ina ki ka san kamfanin VESTAC Farida?"

"VESTAC kuma?"

"Account details ɗin ki ya nuna kamfanin sun turo mi ki kuɗi miliyan biyu jiya"

Sai lokacin ta tuno da maganar kuɗi.
"Yaya ni ban san su ba, jiya nima na ga alert, abinda ya faru jiya ne ma ya sa ban yi maganar ba"

"Farida.." shigowar Najeeb ya sa ya katse maganar ya tashi ya bi bayan Najeeb ɗin.

"Allah ga ni gareka ni 'yar marainiyar nan. Wanda ya nufeni da sharri ka mayar ma sa ya Allah. Ya Rabbil Alaamin ka ceceni" ta faɗa a fili

Ba a jima ba Najeeb da Anas su ka fito, daga baya kuma Yakubu ya zo ya kirata.
"Farida ki yi ta addu'a kawai" abinda ya iya faɗa ma ta kenan lokacin da su ka baro office ɗin na ta.

Da Bismillah ta shiga hall ɗin.

Su kusan tara ne ko goma a wajen kowa yana zaune Najeeb na tsakiyar su.
Nu na ma ta kujeran da ke tsakiyar wajen aka yi ta je ta zauna. Kowa ya zuba ma ta ido. Ba ma kaman Najeeb da ke ma ta kallon tsana.

"Miss Aisha Farida Salihu, bincike ya nuna ma na ke ki ka lalata modelling da aka yi, ki ka sa aka sace takardun zanen. Mi za ki ce gameda wannan?"

"Ni ba abinda na yi, kawai dan na shiga na ɗau hoto. Ni ba abin da na yi"

Wani a gefe ya ce " Miss Salihu binciken mu ya nuna kin haɗa hannu da Kamfanin VESTAC domin ki lalata sunan kamfanin nan ta hanyar sace takardun zane da kuma faffasa modelling ɗin da aka haɗa"

"Ni ban san su waye VESTAC ba, jiya su ka turomin kuɗi batareda na taɓa sanin su ba"

"Ƙarya ki ke Miss Salihu, kin je bid ɗin da aka yi a Lagos tareda Mr Najeeb kuma kamfani VESTAC na ɗaya daga cikin wanda su ka je wannan bid ɗin, su na neman a basu wannan project"

" Allah ya isa na"

"Miss Salihu ga details na account ɗin ki, miliyan biyu sun shigo mi ki jiya daga Kamfanin VESTAC, mi za ki ce gameda haka? " wani acikin su ya kuma faɗi.

"Ni kam kun sani a gaba da tambaya kamar wanda na kai ziyara ƙabari. Ni ban san VESTAC ba balle na san dalilin da za su turomin kuɗi"

Wani daga cikin su ya ɗau waya yai kira ya ce " ku ce ya shigo"

Wani tsoho ne ya shigo, masinja ne a kamfanin tun farko-farkon buɗeshi, da ke a first floor ya ke aiki Farida ba za ta ce ta san shi ba  sai dai kaman ta taɓa ganin sa.

Ce wa aka yi ya shigo yai bayani.

Ya zo ya tsaya gefen Farida saboda kujera ɗaya ne a wajen ya ce " Ranka shi daɗe. Sakatariyar Oga Najeeb ta zo ta sameni akan an ba ta aiki amma ba ta san ya za ta aiwatar ba dan za a iya ganeta. Ta sanar da ni kamfanin Vekta"

"VESTAC" wani aciki ya gyara ma sa.

"Yawwa kamfani VESTAC sun ce ta lalata aikin da aka yi  ta kuma sace takardun zane saboda ba sa so kamfanin nan ta samu wannan aiki. Sun ce za su ba ta miliyan biyu. Ni kuma ta min alkawarin za ta bani dubu ɗari biyar aciki idan na yi wannan aiki"

"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun. Tsohon banza ka ji tsoron Allah. Ni yaushe ma na taɓa magana da kai"

"Na rantse da Allah, kai na rantse da mutuwata ita ta sani na je na ɓata abun nan na kuma sace takardun zanen, ba na baku takardun ba ɗazu"

Malam Muntari irin tsofin Najadun nan ne, wanda sun yi ƙuruciyar bariki tsufan su kuma ya zo ya zama a lalace.

"Malam Muntari munji bayanin ka za ka iya tafiya"

Sai da ya fita wani da ke gafen Najeeb ya ce " Miss Salihu kin dai ji abinda ya ce, mi za ki ce gameda abinda ya faɗa domin ki kare kan ki"

Ajiyar zuciya Farida ta yi sannan ta ce " ni ba abinda zan ce, tunda tsoho kamar wannan bai ji tsoron Allah ya faɗi gaskiya ba ai ba abinda zan ce. Allah ne shaida ta, ni ban san VESTAC ba, wannan tsohon kuma ban taɓa magana da shi ba"

"To Miss Salihu ki ɗan bamu Minti biyar"

Har ta zauna a lobby ɗin wajen ba ta daina maimaita kalmar Hasbunallahu wa ni'imal wakil ba.

Minti shabiyu ta yi a wajen sannan a ka kirata.

Tana zama wanda ke gafen Najeeb ya ce " Miss Salihu mun sameki da laifin ɓata sunan kamfani. Daga yau kin bar aiki a Najeeb Constructions sannan kamfanin nan tana bin ki taran miliyan biyu da rabi za ki biya cikin kwana talatin, idan ba ki amince da wannan hukunci ba ko kuma ki ka ƙi biyan wannan kuɗi to za mu shigar da ke ƙara kotu"

Kallon Sir Najeeb ta ke idon ta ya ciko da hawaye.  Shima ɗin kallon ta ya ke amma wannan karan ita kan ta ba ta san kallon tausayi ya ke ma ta ba ko kallon madallah.

"Sir ka na da abin cewa?" Wanda yai maganar ɗa zu ya tambayi Najeeb...

*Allah ya kaimu daren yau da rai da lafiya sai ku ji mi Sir Najeeb zai ce**SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣2️⃣1️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

"She stays" abinda ya faɗa kenan.

"Sir amma..."

"Za ta biya taran kamfani but she stays"

Daga haka ya tashi ya fita. Tana zaune a wajen ta kasa tashi, ji ta ke kamar an kafe ƙafafuwan ta a wajen. Tana ji su na wasu maganganu a kanta da Sir Najeeb amma kuma ba wannan ne damuwar ta ba. Ita da ta ke shirin aure  ina za ta samu 2.5M, 'yan kuɗaɗen ta duk ta yi amfani da su wajen siye-siyen abubuwan biki. Ummi da Baffa Musa da wanne za su ji, da siya ma ta kayan ɗaki ko da biyan miliyan biyu da rabi.

Har su ka gama fita ba ta tashi a wajen ba sai da Yakubu ya zo.

"Farida wani hukunci su ka yanke?"

Maimakon ta bashi amsa sai ta ce "Yakubu kai ma ka yadda ni na yi abun nan?"

"Na san duk tsiyar ki iya maganar baki ta tsaya, wannan ba halin ki bane"

"Yakubu 2.5M ina zan samu?"

"Malam Muntari ɗan giya ne, zai yiwu an biyashi dan yai miki wannan sharrin ne, amma Allah ya fisu koma waye ne"

"Ni kam aikin nan nawa ake bani da mutane su ka sa mun ido a kanshi haka?"

"Akwai Allah Farida, tashi mu tafi"

Office ɗin sa ya kaita ta zauna yana daɗa ba ta baki, sai da ya ga ta samu nitsuwa kafin ya rakata zuwa office ɗin ta.

Ta zauna ne amma kaman a ƙaya ta ke, ko da ta cigaba da aiki anan, hankalinta ba zai kwanta ba domin kowa da wannan abun za a dinga ganin ta.

Tana cikin wannan tunanin Anas ya shigo.

" 'yar uwa dan Allah ki yi haƙuri, wallahi ban yadda ke ki ka yi abin nan ba. Zan cigaba da bincike har sai na gano gaskiya"

"Ba komai Yaya na. Allah shi ne shaidata"

"Kin yi magana da Najeeb ne?"

"A'a"

"Barin sameshi"

Anas na shiga office ɗin ta yi ajiyar zuciya sannan ta jawo wayan ta ta fara dube-duben hotuna. Sai da ta kai kan hotunan modelling ɗin nan sannan ta tsaya. Hoto kawai ta je ɗauka ga shi ya zame ma ta jaraba. Tana kallon hoton ba ta san lokacin da hawaye ya fara zubo ma ta ba, hawayen da ba ta yi ɗazu ba shi ta ke yi yanzu...

"Na ji hukunci da aka yanke, amma Najeeb kai ka san Farida ba za ta iya samun 2.5M cikin 30 days ba"

Yai ajiyar zuciya ya ce "zan biya ma ta"

"No need"

"Ban gane ba?"

Najeeb yai dariya wanda ya fi kama da dariyar yaƙe.

"Ni ta yiwa laifi, so only i gets to punish her. Wannan duk formalities ne na Kamfani and i've cleared it up"

"Wait, ka biya ma ta 2.5M ɗin?"

"Ina da abinyi Anas, so get out"

"Najeeb are you inlove with her?" Tambayar da ta sa Najeeb ya tashi tsaye lokaci guda, cikin fushi ya ce "how dare you say that to me"

"Dude, abin ne da mamaki. Tunda Farida ta zo kamfanin nan ka chanja, when it comes to her ba ka iya taɓuka komai. What could that be if not love"

"Get out, get the hell out of here"

Anas dai ya fita ne amma zuciyar sa ta gama amincewa da Najeeb na son Farida. Its so obvious all this while bai gane ba...

"Wai wani irin magani ki ka yiwa Najeeb ne? Duk abinda ki ka yi sai ya shanye. Gaya min wani malamin ki ka riƙe?"

Takaici ma ya sa Farida ba ta tanka ma ta ba.

"Farida da ke na ke magana"

Wannan karan ba za ta ɗauki cin fuska daga wajen Khalidah ba.

"A wajen uwar ki na ke karɓan magani. Ki fita min a office kafin ki ga rashin mutunci"

"Its not over yet Farida" ta snapping a dai dai fiskarta sannan ta fita.

"Kai ya Allah daga wannan sai wannan. Ni da na san wannan cin fuskan zan fiskan ta a wannan kamfani da tun farko da Sir Najeeb ya koreni na tattara koli na na tafi"

Ba ta idda zancen zuci ba wayar ta ta fara ƙara.

Tana ɗauka ya ce " to my office"

Saɓanin ɗazu da ta ganshi a wancan hall ɗin yanzu fiskar sa ta sauya akwai ɗan fara'a a tattare da shi.

"Ki fixing meeting da team Alpha anjima"

"Sir Najeeb ba abinda za ka gayamin, ba za ka tambayeni gameda gaskiyar lamari ba"

"Miss Salihu, ba yau na fara gaya mi ki ba. Our relationship is strictly professional, anyi investigation kuma an sameki da laifi, kuma an hukunta ki. What else do you want me to say?"

"Sir Najeeb ko da na cigaba da aiki anan, daraja na ta zube, mutunci na ya zube"

"Wanni daraja ki ke da shi dama? You are just a secretary, my secretary"

"Shikenan tunda abinda ka ce kenan. Amma duk min daren daɗewa gaskiya za ta fito kuma da kai da sauran ma'aikatan na ka duk sai kun ji kunya"

................

Wata ɗaya kenan da ya wuce. Aiki a Najeeb constructions ya zamewa Farida sabuwa, zuwa kawai ta ke amma ba ta jin aikin a ranta. Ko da Anas ya ce ma ta Sir Najeeb ya biya ma ta kuɗin ba ta ma sa godiya ba. Ta so ajiye aikin amma sai ta yi tunanin idan ta bari to wanda basu yarda akwai hannunta a abinda ya faru ba ma za su yarda, shiyasa ta cigaba da zuwa. Dama niyyarta da zaran saura wata ɗaya auren ta za ta je ta rubuta takardar barin aiki.
Sir Najeeb bai chanja ma ta ba, yadda ya ke da ɗin haka ya ke, wani lokaci yai ihu yai faɗa wani lokaci kuma yai magana a hankali. Saɓanin da da ta ke maida ma sa magana yanzu kam ko mi zai ce ba ta kulashi.
Ta koma ba ruwan ta da kowa aikinta kawai. Ko sallah a office ɗin ta ta ke, balle wajen cin abinci kam ta dena zuwa...

"Sir ga resignation letter ɗi na" ta faɗi lokacin da ta ajiye ma sa takardar a gaban sa.

"Ok"  iya abinda ya faɗa kenan ko ɗagowa bai yi ba balle ya kalli idon ta.
Ta yi mamaki dan Najeeb ɗin da ta sani da ba zai yi shiru ba.

"Allah ya sada mu da alkhairi Sir Najeeb. Na gode da taimako da kulawar ka"

Cikin zuciyar sa ya amsa da amin.

*na riga na yi alkawari shiyasa na yi page ɗin nan. And na san ku na jira. Its very short so plz manage gobe da safe idan Allah ya kaimu sai mu cigaba**SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣2️⃣2️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

Waɗanda ta ke mutunci da su kawai ta je ta yiwa sallama. Lokacin tashi yai ta haɗa yanata-yanata ta tattara office ɗin,ta ɗauko office laptop da Najeeb ya ba ta dawo ma sa da shi.

"Sir Najeeb zan tafi, ka yafeni dan Allah, na san a zaman da mu ka yi na yi laifuffuka dayawa amma ka yi haƙuri. Allah ya yafemu gaba ɗaya"

Shiru ne ya ratsa office ɗin na lokaci mai tsawo. Tun tana ganin Sir Najeeb zai buɗe baki yai magana har ta cire rai ta fita daga office ɗin.

Sai da ta fita daga office ɗin sannan ya ɗago idon sa ya ce " i'm not done with you yet Miss Salihu"....

Office ɗin Anas ta je dan ta ma sa sallamar ƙarshe.

"Yanzu ƙanwata shikenan kin bar aiki da mu?"

"Yaya na ai ana tare ko da bana aiki anan"

"Gaskiya ban ji daɗi ba, yanzu idan ki ka tafi wa za mu samo ya replacing ɗin ki. Ke ce the second longest surviving secretary a wajen Najeeb"

"Ya Anas kenan, ai da ƙyar mu ka sha mu ɗin ma"

" ba wani, da ƙyar dai Najeeb ya sha a wajen ki"

Dariya ta yi sannan ta ce " ya Amaryar ta mu?"

"Tana nan sai rigima"

"Ta kaini rigima"

Anas ya zaro ido yana dariya "ai Farida idan ta kai ki rigima bulaguro zan yi a garin. Irin ki ai sai su Najeeb"

"Hmm Ya Anas kenan. Nikam ina abokin adawar ka? Ko ya janye ne?"

"Ai tunda Daddy ya sa min stamp na yaƙice shi. Ga shi dama gimbiyar wannan ɗan baƙin kaɗai ta ke gani"

"Allah ya kaimu lokacin biki Yaya na"

"Amin ƙanwata, kar a manta da IV ɗin mu fa"

"Ai kune ƙarɓan fari".....

...................

Shirye-shiryen biki ake ba kama hannun yaro saura sati uku aure aka kawo lefen Farida kuma gaskiya Rayyan ya yi ƙoƙari sosai.
Farida ta duƙufa da gyaran jiki da shirye-shiryen yadda  biki zai kasance.

Yau ana saura kwana goma sha takwas aure, Baffa Musa ya kirata.

"Wani shirme na ke ji za ki yi ranan Alhamis?"

"Baffa friends day za ayi ranan Alhamis tunda ka hana ayi kamu"

"Enemies day za ki yi ba friends day ba. Yanzu ke Farida ba za ki yiwa kan ki faɗa ba. Ayi miki walima  salamun  alaikum a kaiki ɗakin ki hankali kwance, sai kin bijiro da wani shirme"

"Baffa a cikin gidan nan fa za'ayi kuma iya mata ne ka san inada jama'a"

"Ungo na ki ke da jama'an na ki"

"Mun gode Baffa"

Taɓe baki yai kawai yana bin ta da kallo. Bakin tan nan yana fata ya zaunar da ita lafiya a gidan ta, ba ya kawo fitina ba.

"Baffa ina ka amince?"

"Ya na iya uwata. Allah ya kaimu lokacin ya kuma kaɗe fitina"

"Baffa thank you" ta faɗa tana tashi da sauri...


................

Duk yadda ta ke ji gameda auren sai da auren ya zama saura sati ɗaya sai jikinta yai sanyi. Haka kawai sai tsoro ya shigeta gani ta ke kamar za a kuma wani chakwakiyar kamar yadda aka yi lokacin Lukman.  Ummi ta zo amma su Nanna sai Alhamis za su shigo.  Ranan talata da safe ta wuce Najeeb constructions. Ta fara biya wa office ɗin Sister Munibat ta ba ta katin gayyata tareda cewa idan ba ta zo ba to sun ɓata.

"Sister Aisha kenan, ai indai ina da rai da lafiya to bikin ki da mu za ayi"

Farida ta ɗan harareta " kaman da gaske, kin sayi ashobe na kuwa?"

Sister Munibat ta fara sosa kai.

" hmmm ai dama na sani, Dan Allah ki daure ki zo"

"Insha Allah sister Aisha zan zo"


Daga wajen Sister Munibat ta wuce wajen Anas. Ta jima a wajen sa,  inda ya ke ba ta labarin sakataren da aka ɗauka bayan ta tafi.

"Farida kwanan sa huɗu ya ajiye aiki, wai ba zai iya ba"

"Ai Sir Najeeb idan ba jan wuya ba ba mai iyawa da shi"

"Jan wuya kamar ki ba"

"I'in ai mun sha fama da shi"......

Lokacin da ta shiga office ɗin sa yana jikin shelf ya na neman wasu files. Ta tsaya tana kallon yadda ya ke ta dibi-dibi a wajen. Da ta na nan yanzu da ita ke wannan aiki.

"Sir Najeeb mai ka ke nema?" Muryan da bai yi zatan jin sa ba ya ji a ta bayan sa. Bai san lokacin da ya sake file ɗin ya faɗo ba. Tsayawa yai yana kallonta, ta wani yi haske tana sheƙi, ga wani ƙanshi mai daɗi da jikinta ke fitarwa.
Tsugunnawa ta yi ta ɗauka file ɗin sannan ta miƙa ma sa. "Ga shi na ma ka aikin ƙarshe"
Bai amsa file ɗin ba sai ma juyawa da yai ya je ya zauna a kujerar sa.

"Iko sai Lillahi, daga ganin Sarkin Fawa sai miya ta yi zaƙi. Sir Najeeb ba fa aiki na zo ba da za ka min jan ajin da ka saba"

"Oh really"

"Gashi, dama IV na kawo ma ka" ta yi saurin ajiye file ɗin tareda ciro IV ta ajiye ma sa.

"Dan Allah a daure a zo. Duk da ma dai i'm just a secretary"

Ta ɗan yi dariya ta ce " was just a secretary"

"Congratulations Miss Salihu"

"Thank you Sir Najeeb"

Ya ɗan kurɓi coffee da ke gaban sa sannan ya ci gaba da latsa laptop.

"Sir Najeeb ina da magana. Dan Allah ka ɗan rage halin kan nan. Ka ga ba kowa bane zai iya jurewa. Ni ma da ƙyar na sha a wajen ka. Allah, watarana idan na koma gida daga office har ƙaramin zazzaɓi na ke saboda stress da zafin kai. Kai ba a maka gwanin ta sannan..."

"Out"

"Ka ga irin halin na ka ko"

"Miss Salihu get out"

Ta yi shiru tana kallon sa sai da ta ga zai sake ɗaukan  mug ɗin coffee ɗin sannan ta yi wuff ta ɗauke.
Ta kai baki da nufin ta kurɓe duka lokaci guda sai ta ji shi da zafi sosai. Ta ɗan kurɓi kaɗan ta sake kurɓa sannan ta ajiye ma sa.
Dariya ta yi saboda yadda ta ga ya zaro ido.

"Sir Najeeb tsokalar ƙarshe ne fa. Na tafi"

Harta juya sai kuma ta juyo ta ce "Sir Najeeb a yafe mu"...
Sai da ta rufe ƙofa ya ce "devil in a dress"  ya jawo wani dogon envelop ya buɗe, hotuna ne guda uku a ciki " happy never marriage Miss Salihu" ya faɗa a fili.

(🙄Sir Najeeb ya dai?)

.......................

Farida na komawa gida ta tarar da Maijiddah ta zo.

"Kai-kai Jiddah mi ki ke ci haka? Kin ganki kuwa"

"Kai Anty Farida"

"Zo zo mu shiga ɗaki ki gaya min sirrin"

Sai da su ka zauna ta ce " Jidddah ciki gareki, wannan ƙiban da walakin"

Maijiddah ta rufe ido tana murmushi.

"Masha Allah, Allah ya raba lafiya. Ina kishiyar ki? Har yanzu tana Abuja?"

"E, amma yanzu sau biyu ta ke zuwa a wata"

" 'yar kusun'wa, za ta ma ajiye aikin ta dawo gidan ta, ko kuma ta ji ta a silencer dan mune ma su gidan yanzu"

"Na gode Anty. Kayan da ki ka bani sun min rana"

"Zauna a wajen, ai mazan yanzu sai da shigar bariki. Nima na je Jos na kwaso nawa suna nan jingim"....

Biki na matsowa jikin Farida na ƙara sanyi kullun ta yi bacci sai ta yi mafarkin an fasa aurenta. Abin ya dameta ta gayawa Ummi, Ummi ta ce ta dinga addu'a. Itama ɗin Ummin Allah-Allah ta ke ayi bikin lafiya ba tareda wata matsala ba.
Ranan Alhamis aka je aka yiwa Farida jere a gidan Rayyan. Rayyan ya gina 3-bedroom flat mai kyau. Baffa yai ƙoƙari dan ya kashe kuɗi sosai wajen sayen ma ta kaya, 'yan uwan Ummi ma sun yi ƙoƙari gaskiya...

........... ..........

Ya na zuwa ƙofar gidan ya sa yaro ya kira ma sa maigidan. Da yaron ya fito ya ce yana zuwa...

Musabaha su ka yi da dattijon sannan su ka gaisa.

"Yi haƙuri ban ganeka ba"

Ya miƙa masa envelop sannan ya ce " ɗan ka zai yi aure ranan Asabat ɗin nan ko?"

"Insha Allahu"

"Matar da zai aura ba matar aure ba ce"

"Ban gane ba"

"Ka dubi cikin envelop ɗin nan za ka ga zahiri" daga haka  ya juya ya tafi.

.....................

Anyi friends day lafiya kuma ba laifi ƙawayen ta na Jos sun zozzo, anci an sha kuma an girgije.

Ƙarfe goma sha ɗaya na dare lokacin ba ta fi 'yan mituna kaɗan da kwantawa ba kiran Rayyan ya tashe ta. Tana ɗauka ya ce ta fito waje yana ƙofan gidan su.

"My Ray lafiya ka zo da daddaren nan?"

"Ki fito Farida akwai saƙon da zan ba ki ne"

Maganar saƙo da ya ce sai ta ji zuciyar ta ya buga. Ta tashi ta sa hijabi ta fito.
Akwai wa su baƙi da ke kwance a barandar tsakar gidan su na hira, da ke ba su jima da tattara tsakar gidan ba.

"Amarya ina zuwa haka?"

"Ƙofar gida zan je an kawo min saƙo"

"Samarin zamani dai, angon ne ya ka sa hakuri haka"

Ita dai ba ta sauraresu ba ta fita.

Wajen motar sa ta je ya buɗe ta shiga.

"My Ray minene, hankalina ya mugun tashi fa"

Da ke dare ne ba iya kallon fiskarsa ta yi sosai ba balle ta ga yanayin sa.

"Farida ashe za ki iya cin amana ta"

Dum ta ji ƙirjin ta ya yi.

"Wallahi ban ɗauka za ki min haka ba"

"Na shiga uku ni Farida ba dai za a kuma ba. Rayyan mi na yi?"

"Ashe soyayya ku ke da Ogan ki. Ashe duk yadda ki ke zagin sa a gabana iya fatar baki ta tsaya"

"Rayyan dan Allah kar ka sa zuciyata ta buga yanzu. Idan ma wasa ka ke ka dena please "

"Da kan sa ya je gida ya ce wa Baba ke karuwarsa ce"

"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun, Lahaula wala ƙuwwata illa billah. Sir Najeeb ne ya faɗi hakan?"

Miƙa ma ta wayarsa yai ya ce ga hotunan da ya kawo. Ina tunanin ma waɗannan lokacin da ku ka je Lagos tarene ku ka yi holewarku achan.
Ta amshi wayar ta fara kallon hotunan. Hoton farko tana zaune kan cinyar Najeeb ta sa hannayen ta a kafaɗun sa tana murmushi, ɗaya kuma suna tsaye ya rungumeta ta baya, lips ɗin sa a daidai wuyan ta. Ta swipping na gaba wanda tana kallo hawaye na ɗiga a jikin wayar. Suna rungume da juna bakinsu a haɗe kamar suna kissing.

"Ba ni bane, wallahi ba ni bane. Wannan sharri ne. Rayyan ka yarda da ni"

"Dama na zo na faɗa miki ne da kaina kafin gobe a zo gida a faɗa. Na fasa auren ki Farida, ina son ki amma ba zan iya auren ki ba. Najeeb yana da kyau yana da kuɗi, ko bayan mun yi aure idan ya neme ki za ki amince da shi. Ba zan iya aure da zargi a ciki ba"

Bakin ta ne ya fara rawa, tana so ta yi magana amma ko me ya taho zai fito sai ya maƙale a wuyan ta. *"Na fasa auren ki Farida"* shine maganar da ke ta maimaituwa a ƙwaƙwalwarta.

"Gobe za su zo su karɓi sadaki da lefe, sauran abubuwan na yafe. Na gode da Allah ya tona asirin ki kafin ma ayi auren, dama Umma ta sha faɗamin ba ta yarda da ke ba dan 'yan Jos ɗin nan yawancin ku 'yan iska ne"...

Ba ta san ya akayi ta buɗe ƙofa ba, ba ta san kuma ya akayi ta shiga gida ba. Zuwa ta yi ta zauna a bakin gado hawayen da ta ke yi ma ya tsaya. So take ta gane mafarki ta ke yi ko gaske ne.  Bacci kam ranan ba bu shi a idon Farida.

Washe gari da safe aka tashi da shirye-shiryen walima. Farida ta kasa magana ta kasa faɗan abinda ya faru jiya, ita har lokacin gani ta ke mummunan mafarki ta yi jiya da dare.

Zuwa ƙarfe goma sai ga Baffa ya shigo yana faɗace-faɗace. Kiran Ummi da Nanna da Baaba Sabuwa yai zuwa falon sa. The next thing da akaji sai kukan Ummi. 'Yan gulma su ka yi falon da sauri Baffa musa ya fatattake su.

"Amina ki dena kuka, ni ban yarda da abin da su ka ce ba, kuma koma hakanne dole sai na aurar da 'ya ta gobe. Ba zai yiwu a fasa aurenta har sau biyu ba, sai duniya ta zageni. Ni nawa 'ya'yan ina aurar da su lafiya ita kuma da ta ke amana gareni ake samun matsala duk lokacin bikin ta"

Nanna da ita kaɗai ce ba ta fara kuka ba ta ce "yanzu wa za ta aura?"

"Yakubu, Yakubu zai aureta, ku cigaba da shirye-shirye Allah ya kaimu goben"...

Farida na ɗaki har lokacin tana zaune jugum, Maijiddah ta yi tambayar duniyar nan amma ba ta kulata ba.

Ummi ta shigo ɗakin tana hawaye. Zuwa ta yi ta tsugunna gaban Farida ta ce "faɗa min gaskiya Farida, akwai abinda ke tsakanin ki da Ogan ki?"

Farida ta kalli Ummi da rinannun idanuwan ta ta ce "da gaske ne ko? Da gaske Rayyan ya fasa aurena?. Ummi banida sa'a a rayuwa kenan? Ummi ina son na yi aure, ina son na samu gidan kai na, ina so na haihu na tara 'ya'ya, ina so na samu ladan biyayyar aure, ina so na cika miki burin ki Ummi. Ummi ko dai aure ba ya cikin ƙaddara ta ne?"

Ummi ka sa magana ta yi sai kuka.....

Zuwa ƙarfe shabiyu 'yan gidan su Rayyan su ka zo karɓan kaya. Daga wajen ma su ke cewa aje a kwashe tarkacen da aka jera a gidan ɗan su. Abubuwa dai su ka rinchaɓe a wajen.

Kowa a gidan da abinda ke ran sa, wassu baƙin na shirin komawa amma da su ka ji Baaba Sabuwa ta ce aure ba fashi za ayi, sai su ka tsaya dan su ga ƙarshen Farida.

Farida tun safe ko sau ɗaya ba ta fito a ɗaki ba, ko wanka ba ta iya yi ba balle abinci kam ba a zancen sa.
Da yamma Yakubu ya dawo daga wajen aiki sai a lokacin ya ke jin labarin abinda ke faruwa. Baaba Sabuwa ce ta ma sa maganar auren Farida da ya koma kan sa. Duk da bai shirya aure yanzu ba sannan bai taɓa kawo auren Farida a ransa ba amma indai dan ya cececi mutuncin 'yar uwar sa ne to zai aureta da gudu ma. Abinda ya ƙara ɗaure ma sa kai baifi yadda aka ce wai 'yan gidan su Rayyan sun ce wai FARIDA karuwar Ogan ta ba ne. Ya san Farida kuma ya san Sir Najeeb, ko da dai chan ƙasar zuciyar sa yana zargin Sir Najeeb na son Farida amma bai kai har ace wai suna neman junan su ba.

Yana cikin wannan tunanin ya ji wayar sa na ringing. Yana dubawa ya ga Farida ai da sauri ga ɗauki kiran.

"Dan Allah Yakubu ka sameni a ƙofar gida"

Da sauri ya tashi ya fita.
Lokacin da ya ganta wani tausayinta ne ya kuma shigan sa. Lokaci guda Farida ta chanja ta zama wata iri, fiskanta ya kumbura ga idon ta da su ka ƙanƙance saboda kuka. Tunowa yai da shekara uku da su ka wuce exactly haka ta lalace lokacin da aka raba aurenta da Lukman. Gara lokacin da sauƙi tunda matsalar daga Lukman ne to yanzu fa.

Ya ƙarasa wajenta yana faɗin "Farida dan Allah ki yi haƙuri, ki kwantar da hankalin ki komai zai wuce"

"Ka kaini gidan su Sir Najeeb" abinda ta faɗa kenan cikin muryarta da baya fitowa sosai saboda dashewa da yai...

Adama ce ta buɗe ƙofa lokacin da ta danna doorbell ɗin.
"Daddy na nan?"

"Eh ki shigo"

A tsaye ƙiƙam ta tsaya idon ta na kallon ƙasa, kan ta ke sarawa, duk yadda ta ɗaga kan sai ta ji wani raɗaɗi.

Mom ce ta fara saukowa ganin yadda Farida ta ke ya sa tasan yarinyar na cikin damuwa.

" 'yan mata ki zauna mana" ta faɗa da Hausanta da bai gama nuna ba.

Farida ba ta ce komai ba sannan ba ta zauna ɗin ba.  Kitchen Mom ta wuce ganin Farida ba ta cikin hayyacinta.

Minti huɗu sai ga Daddy ya sauko.

"Ina wuni Daddy" ta faɗa da disashshiyar muryarta.

"A'a Aisha Amarya?"

"Na'am Daddy"

"Lafiya dai ko?, shekaranjiya Baban ki ya kawo min katin biki, ina ce ba wata matsala ba ne ta taso ?"

"Daddy kai uba ne na gari amma ɗan ka bai ɗauko hali na gari ba. Najeeb ya min sharri, ya raba ni da farin ciki na. Ya sa min tabo  a rayuwata wanda ban san ranan da wannan tabo zai gogu ba. Ni marainiya ce, ba ni da gatan da ya wuce Allah, kuma na haɗa Najeeb da Allah. A kamfanin sa ban tsira ba, na bar aiki da shi ma ban tsira ba. Allah zai saka min"  ta fashe da kuka ta fice daga gidan da gudu. Daddy yana kiran ta amma ba ta tsaya ba. Daddy kan shi ya ɗaure dan bai gane ina maganganun Farida su ka dosa ba.

Tana fitowa ta tsaya ta goge hawaye  sannan ta fara tafiya duk da kuwa ba ta da  ƙwari a jikinta. Ta kusa isowa wajen Yakubu da ke jiran ta jiri ya ɗebeta ta faɗi ta suma. Yakubu ya yiwo kan ta da gudu...*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣2️⃣3️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*


Maigadi da dreba da su ke zaune a benchi su ka taso da gudu. 
Ce ma sa su ka yi ya kai ta mota yayinda Iliya dreba yai sauri ya shiga gidan don ya faɗawa Daddy.
Daddy na falo har lokacin yana waya da Anas.

Ya na ma sa bayani Daddy ya ce muje-muje.

Daddy na gaba Yakubu na baya ɗauke da Farida wanda har lokacin ba ta farfaɗo ba duk da kuwa sun yayyafa ma ta ruwa. Kafin su isa asibitin ta farfaɗo amma ba ta san inda ta ke ba....

Chan gida kuma Baffa ne ya ke ta faɗa kan miyasa za'a bar Farida ta fita a wannan halin. Maijiddah ne ta ce tare su ka fita da Yakubu. Sai a sannan yai shiru ya zaro wayar sa a aljihu ya fara kiran numbar Yakubun amma bai ɗauka ba.

"Shima ɗan gatan'wa, ko ina ya shiga oho"...

Ruwa aka ɗaura ma ta aka ma ta alluran bacci dan sun ce jinin ta ne ya hau. Sai da ta fara bacci tukunna Yakubu ya samu damar kiran gida ya faɗa mu su.

Daddy ya dubi Yakubu ya ce " mi ya ke faruwa ne? mi Najeeb ya ma ta?"

Da kaman ba zai faɗa ma sa ba,sai dai girman Daddy da kwarjininsa ya fi gaban ya ƙi ma sa magana.  Duk abinda ake ciki ya tsirge mi shi tundaga farko har ƙarshe.

Da ya gama bashi labarin Daddy ya ɗauko waya ya kira wata number.

"Anas ka na ina ne?"

Yakubu bai ji mi ake ciki ba ya dai ji ya ce "muna room 18 a sama"

Ba'a jima ba sai ga Anas ya shigo. Ganin Farida a kwance ya sa shi mamakin mi ya faru.

"Yakubu ya jikinta?, mi ya sameta?"

Da sauƙi kawai Yakubu ya iya ce masa.

"Ina ɗan banzan nan ya ke?"

Daddy ya tambayi Anas.

Ya gane Najeeb ya ke nema dan haka yai saurin cewa yana office nima daga office ɗin na ke.

"Har da kai ake rusa rayuwar mutane ko?"

Anas ya zaro ido ya ce "A'a Daddy"

Daddy ya miƙe ya ce "Yakubu Allah ya bata lafiya, ina nan dawowa anjima"

Yana Fita daga ɗakin Anas ga bi bayanshi da sauri.
A motan Anas ɗin su ka wuce Najeeb constructions.

Ya jima yana tunanin ko wani hali ta ke ciki. Wani ɓangare na zuciyar sa na faɗa ma sa bai kyauta ba wani ɓangaren na nuna ma sa ya yi dai-dai.
"She deserve it" ya furta a fili.
Yana ƙoƙarin duba wasu takardu da aka submitting ma sa tun da safe amma ya kasa fahimtar komai. Haka kawai zuciyar sa ke ma sa ƙunci....

A hanya Daddy ke sanar da Anas abinda Najeeb yai, Anas ya kaman salati yana salallami.

"Daddy ban san Najeeb zai iya yin haka ba especially saboda zargin da na ke masa akan yana son Faridan"

"Dan uban sa dan yana son ta sai ya mata sharri"

Anas dai shiru yai yayinda Daddy ke ta surfa ma sa masifa kaman wanda shi yai laifin.

Da ke an riga an tashi wajen shiru ka ke ji. Daddy da Anas su ka haura third floor.

Ya kifa kan sa akan kujera saboda wani zazzaɓi da ya rufeshi lokaci guda, ya rasa mi ya sa shi shiga wannan yanayi. He supposed to be happy ya rama kaɗan daga cikin asaran da Miss Salihu ta sa ya yi. But instead his sad.

Buɗe ƙofar office na shi da aka yi ya sa ya ɗago kan sa da sauri.
Ganin Daddy da Anas sai ya miƙe. "Dad " kaɗai ya iya faɗa kafin saukan mari ya sa ya haɗiye koma mi ya ke shirin faɗa.
A karo na biyu Daddy ya kuma marin sa, ji ka ke taas. Anas na gefe ya sha jinin jikin sa dan faɗan uba da ɗa sai Allah.

"I'm ashamed to call you my son"

"Dad" Najeeb ya faɗa a hankali

"Ashe tarin shekarun ne kawai akan ka ba hankali. Mahaukacin banza Mahaumacin wofi. Sai ka samu me idan ka hanata auren? Tukunna ma, miye dalilin yi ma ta sharri? Miye dalili? "

"she deserve it Dad, she wanted to ruin me. Na rasa big contract saboda ita saboda haka 2 project da mu ka fara su ka soke contract da mu. She tarnished my image and the repeatition of my company"

Wani marin Daddy ya kai ma sa. " i didnt know i have a monster son. Asaran kamfaninka yana dai-dai da ruguza mutuncin mutum kenan?. Shin ka yi tunanin halin da yarinyar nan za ta shiga? What if she died of shock, sai ka haɗa party kana murna ko"

Ya nuna shi da ɗan yatsa yace  " Anas, kalli banzan yaron nan fa,8yrs ago da Sabreena ta gudu ta barshi kafin auren su he almost died, he was depressed for months. Ya je theraphy section na watanni huɗu kafin daga baya ya warke ya dawo Nigeria. Do you know that this fool here yana shan antidepressant drugs har yau saboda baƙin cikin yarinyar nan. Amma shi ne ya ke da guts da zai je ya hana auren 'yar mutane"

"Najeeb" ya ka sa magana ma saboda baƙinciki da ya tokare ma sa wuya.
Daddy juyawa yai ya fita, Anas ya kalli Najeeb, kallon ka bani mamaki sannan ya bi bayan Daddy da sauri.

Gidan su Rayyan Daddy ya ce Anas ya kai shi. Da su ka je su ka sa a yi sallama da Baban Rayyan ɗin, aka ce mu su yana kasuwa.  Numbar sa su ka karɓa su ka kirashi jin sunan Alhaji Adam Jibo ne ya sa mahaifin Rayyan ya ce yana nan zuwa.  Haka su ka zauna zaman jiran sa, kafin ya dawo ma an fara kiran sallan maghrib su ka yi sallah a masallacin anguwar.
A ƙofar gidan aka shimfiɗa mu su tabarma lokacin da Baban Rayyan ya zo.

Daddy bai ɓata lokaci ba ya ma sa bayanin ko shi waye da kuma abinda ya ke tafe da su.

"Malam Abdullahi, wannan hoto da aka kawo muku ba tare su ka ɗauka ba, editting na shi aka yi, kasan yanzu fasahar zamani ba abinda ba ayi. Wannan yarinya ta na da tarbiya kuma kowa ya shaideta da haka. Duk abinda Najeeb ya zo ya faɗa muku to wallahi ƙarya ne, ya yi hakan ne dan ya cimma wani banzan burinsa. Ku yi haƙuri a maida maganar auren yaron ku da Aisha"

Yadda Daddy ya ke magana cikin kwantar da murya ya sa Malam Abdullahi yarda da maganar sa domin Daddy babban mutum ne a gari kai a ma ƙasar gaba ɗaya ba zai yiwu ya zo wajen sa dan kawai ya ma sa ƙarya ba.

"Alhaji na fahimceka, sai dai gaskiya al'amarin nan ya riga ya ɓaci. Ni da Alhaji Musa mun samu saɓanin  harshe a yau ɗin nan saboda wannan magana. Yanzu haka maganar da na ke maka an riga an dawo mana da sadaki da kuma kayan lefe da aka kai. Harta kayan yarinyar da aka kai gidan yarona sun je sun kwashe. Al'amarin ya ɓaci sosai gaskiya"

"Malam Abdullahi a duba dan Allah. Auren nan idan aka fasashi alhakin yarinyar nan zai bi Najeeb 'ya'ya da jikokin sa"

"Gaskiya zan faɗa ma ka Alhaji ko da za a dawo da bikin nan to ba gobe ba"

Shiru Daddy yai na tsawon lokaci kafin ya ce wa Anas su tafi.

...........................

Su Baffa da su Ummi sun zo asibitin da aka kwantar da Farida. Baffa kam a lokacin ma ya ƙara tabbatarwa kan sa ko mi zai faru to gobe sai ya aurar da Farida, domin idan gobe ta wuce bai san halin da Farida za ta shiga ba, balle ya san halinta yanzu sai ta ce ta haƙura da aure gaba ɗaya ta ce  karatu za ta cigaba da yi.

Bayan ya tabbatar da ankawo duk abubuwan da za su buƙata sannan ya musu sai da safe saboda ance sai gobe za a sallameta. Ya zo zai fita daga asibitin da shi da Yakubu su kuma su Daddy su ka shigo.

"Alhaji Musa dan Allah ka tsaya" Anas ya faɗa lokacin da ya ga Baffa Musa ya gan su amma sai ya kau da kai yai kamar bai gan su ba.

Baffa Musa ya juyo ya kalli Daddy yana ƙarasowa wajen su, girman sa ya sa ya fasa masifar da ya ke shirin yiwa Anas.

"Alhaji Musa dan Allah ko za mu iya magana da kai"

"Ni yanzu gida zan wuce Alhaji, ina sauri"

"Ba komai Alhaji Musa za mu bika gidan"

Baffa Musa dai bai so ba amma ba yadda ya iya. Haka su ka wuce gaba, su ma su Daddyn su ka bi bayan su.

Daddy da Baffa Musa ne a falon. Yayinda Anas da Yakubu ke ƙofar gida suna tattauna wannan abin al'ajabi mai kama da almara.

Duk girman Daddy da matsayin sa haka ya fara yiwa Baffa Musa magana cikin sanyi da harshe mai taushi.

"Alhaji Musa dan Allah ka duba wannan al'amari. Na yiwa Malam Abdullahi magana kuma ya ce za su duba, kar a fasa auren nan gobe dan Allah"

"Aure ai ba za a fasa shi ba, kamar yadda na gayyace ka da farko ba chanji. Gobe ƙarfe shaɗaya na safe za a ɗaura auren Farida da ɗa na Yakubu. Tunda sun shaƙu da juna idan anyi auren za su fahimci junan su sosai"

"Alhaji idan ka yi haka ba ka yafe ba kenan"

"Alhaji ko ka san ni ɗin nan ni na shiga na fita har na ga na amso takardar Farida saboda ɗan shege mu ka aura ma ta ba mu sani ba. Yanzu kuma ace duk walaƙancin da iyayen Rayyan su ka mana sai na ba su auren Farida. Wallahi ba zai yiwu ba, gara ayi tuwona maina kawai "

Daddy yai shiru yana tunani chan ya ce " Alhaji Musa ina neman alfarma a wajen ka"

Zumɓur Baffa Musa ya tashi lokacin da ya ji buƙatar Daddy.

"Wannan zancen banza kenan, ba zan taɓa yiwa Farida auren cin fuska ba. Allah ya kiyaye"

"Alhaji Musa ka taimakeni dan Allah, yaron nan inaga son ta ya ke shiya sa yai haka"

"Alhaji ka tashi ka tafi dan Allah, abinda ka ke buƙata ba mai yiwuwa ba ne"

Maimakon Daddy ya tashi sai ya sa gwiwowinsa a ƙasa yana roƙon Baffa Musa. Tuni Baffa ya fara ƙoƙarin ɗaga Daddy yana faɗin "haba Alhaji ka fi ƙarfin haka, dan Allah ka tashi"

"Yaron nan yadda ka ke so ka ga ka aurar da Aisha haka nima na ke so yai aure. Nan da 'yan kwanaki zai cika shekaru talatin da biyar a duniya kuma har yanzu ba shi da niyyar aure. Shi kaɗai ne ɗa na namiji Ba na fata ya ƙarasa rayuwar sa a matsayin tuzuri"

Baffa dai rasa mi zai ce zai yi dan kan sa ya kulle. Alhaji Jibo ya girmeshi a shekaru nesa ba kusa ba ya girmeshi a matsayi da komai amma shine ya ke roƙon sa har kamar zai yi kuka. Farin cikin Farida ya ke so amma idan ya amsa buƙatar Alhaji Jibo anya ba baƙin ciki zai shuka a rayuwar Farida ba....


............................

Bayan fitan su Daddy ya shiga wani tashin hankali, bai taɓa ganin Daddy cikin ɓacin rai haka ba, he only mean to punish her. So ya ke idan an fasa auren ta yi kuka ta ji baƙin ciki sai ya koma ya nuna wa mahaifin Rayyan gaskiyar lamari cewa hotunan nan aikin photoshop ne. But is he stupid or what, idan ya je will that undo what has already been done.
Ya kira Anas sau ba adadi amma ya ƙi ɗauka. Ya  fito da robar maganin sa ya ɗauko guda biyu sai kuma ya maida su. Ashe Daddy ya san halin da ya ke ciki all this while, shi bai san Daddy ya san da zuwan sa wajen theraphist ba, balle har ya san he has being on drugs all this while.
Duk da hasken da ke office ɗin na shi bai hana shi ganin duhu ba.
Mi ya sa koyaushe mace ce ke sa shi cikin ƙunci, first it was his Mom then Sabreen sannan wannan Miss Salihun.
Ya dafe goshin sa da ke sara ma sa kaman zai tsage...

..........

Bai san lokacin da ya isa gida ba balle ya san lokacin da bacci ya ɗaukeshi. Buga ƙofan sa da ake da ƙarfi ya sa ya farka. Tasowa yai da ƙyar ya je ya buɗe ƙofan.
Anas ya gani yana faɗaɗa murmushin sa.

"Maigida har yanzu ba ka tashi ba, yau fa ranan ka ce"

Najeeb ya juya ba tareda ya ce komai ba ya wuce banɗaki.

Anas ƙaramin walk in closet da ke ɗakin ya shiga yana duba kayan Najeeb ɗin.

Najeeb ya shimfiɗa sallaya ya gabatar da sallar asuba lokacin agogo ƙarfe bakwai saura kwata.

Anas ya fito da wasu kaya ya shimfiɗa akan gado  barin ga wanne zai fi fito da kai. Blue ko fari ko ash.

"And what are you doing exactly?"

" ina nema ma ka kayan da zai dace da kai a rana irin ta yau"

Wayar Najeeb ɗin ce ta fara ringing ya ɗauka da sauri ganin Daddy ne.

"I'm coming Dad"

Anas dai dariya ya fara ƙasa-ƙasa lokacin da Najeeb ya fita.

A ƙaramin falon Daddy da ke sama ya sameshi yana zaune yana waya.

"E ƙarfe shaɗaya ne, e masallacin wajen ne. Abin ne ya zo bagtatan ayi haƙuri" ya na gama wayar ya kalli Najeeb da ke zaune opposite da shi ya yi zuru-zuru da ido.

"Muhammad Najeeb" ya faɗa da sigar jan hankali.

"Ka kunna wuta a rayuwarka kuma ni nan na nemi hanyar kashe wutan. Idan ka amince ni Adam ni na haifeka kuma ka yadda ina da hakkin na samu biyayya daga gareka to yau ina umurtar ka da ka je ka shirya, ƙarfe shaɗaya za'a ɗaura auren ka da Aisha"

"What!"

"Ka jini da kyau kuma ba na buƙatar wani dogon bayani e ne ko a'a, idan ka ce e to ka yiwa kan ka adalci, idan kuma ka ce a'a to ka zaɓi samun wani uban daban kenan ba ni ba"

"Dad i'll sort this out, zan je na gaya mu su gaskiya. You dont need to do this"

"NAJEEB!"

Shiru ya ratsa falon.

"Yes or no?"...

...............

Yana shiga ɗakin ya fara kaiwa Anas duka ta ko'ina.

"Dude ba fa ni na ma ta sharri ba fa da za ka sauke a kaina. Abinda ka shuka shi za ka girba"...

Duk da kasancewa abu ne da ya zo cikin ƙurarren lokaci hakan bai sa wannan aure ya tara jama'a ba. Daga ɓangaren Alhaji Jibo zuwa na Najeeb wanda Anas ne yai ta inviting mutane. Ma'aikatan Najeeb constructions da ma su son gulma da ma su zuwa dan Allah da ma su zuwa dan su yi tsegumi da zunɗen Ogan na su duk sun hallara.

Ranan ta asabat wanda ya kafa tarihi a ɓangaren gidajen biyu wato iyalen Alhaji Jibo da na Alhaji Musa Umar Wase.
Ƙarfe shaɗaya da 'yan mintoti aka ɗaura auren Engineer kuma Architect *Najeeb Adam Jibo, CEO Najeeb constructions* 😁 tareda amaryarsa *Aisha Farida Salihu* (ex- secretary @Najeeb constructions😂)

Mutane kowa mamakin auren babban Mutum kuma ɗan manya kamar Najeeb Jibo su ke. Aure ba IV ba sanarwa a kafafen yaɗa labarai ba komai.
Abunka da masu arziƙi a hakan sai da aka haɗa reception bayan an tashi a masallaci aka wuce venue wajen da aka ci aka sha.

Ƙarfe ɗaya saura motar da ta ɗauko su daga asibiti ta tsaya a ƙofar gidan. Ita da Ummi da Maijiddah ne a motan sai ƙanin AbdulWahab mijin Jiddah da ya ɗaukosu kasancewa motar Baffa Musa ta shiga garari.

A hankali su ka shigo gidan nan aka fara guɗa.

"Ayyiriri amarya a gidan manya, tsatson fulani tsatson larabawa. Kyakykyawa mai kyawun hali. Taka lafiya amarya agidan Alhaji Jibo."

Chak ta tsaya lokacin da ta ji kalmar ƙarshe " Alhaji Jibo"

"Mu shiga ciki Farida" Ummi ta faɗa tana hanata damar tambayar ma'anar abinda ta ji...

Zuwa bayan azahar Farida ta shiga ruɗani. Zancen da ake ma ta mai kama da shirin film ta ka sa processing na shi a ƙwaƙwalwarta.
Ba abinda Ummi da Nanna ke ce ma ta sai ta yi haƙuri haka ƙaddarar ta ya zo. Kodan ganin ba ta kuka ne ya sa su ke ma ta wannan zancen banzan wai ta karɓi auren Najeeb Jibo a matsayin ƙaddararta.
Ita da tun jiya da dare da ta fara jin sauƙi ta yankewa kan ta hukuncin komawa karatu ta yi pdg ta yi masters na ta. Sannan ace yanzu an aurar da ita wa Najeeb. Mutumin da ya rusa ma ta auren ta da Rayyan.

Zuwa yamma Baffa Musa ya sa aka kirata. Nasihar dai da su Ummin su ke ma ta shi ma ita ya maimaita. Wai ta yi haƙuri.

"Farida ke 'ya ta ce, kuma ba zan ga abinda zai cutar da ke na tura ki ciki ba. Wannan al'amari rubutacce ne daga Ubangiji. Ki yi haƙuri ki yiwa mijinki biyayya ki kuma zauna agidan ki lafiya. Ki rage yawar magana dan Allah"

Jin Baffa kawai ta ke yi amma aure da Najeeb kam ba ta ga ta zama ba.

Ummi ce ta sa dole ta yi wanka duk da ta ƙi kwalliya amma ta sa wani leshi mai kyau wanda Ummin ne ta siya ma ta saboda wannan rana duk da kuwa a maimakon gidan Rayyan da za a kaita yanzu gidan Najeeb Jibo ne...

Ummi hawaye ta ke tana roƙon Farida ta zauna lafiya da mijinta. " Aisha idan ba ki zauna ba haka za ayi ta irga mi ki aure. Kinga nima tawa ƙaddarar yadda ta kasance, aure na huɗu. Ba na fatan ki zama haka, idan ki ka bi a hankali da sannu za ki gano kan mijinki har ku daidaita kan ku"  wannan nasiha na Ummi baƙaramin shigar Farida yai ba....

Ƙarfe takwas da rabi motocin ɗaukan amarya su ka zo. Ummi na kuka Farida na yi haka uwa da 'ya su ka rabu.
Kai tsaye gidan su Najeeb aka wuce da ita. Nanna da Baaba Sabuwa ne su ke tare da ita a mota ɗaya. Su suka ma ta jagora zuwa cikin gidan su mijinta. Su Mom da tawagarta sun ƙarɓi amarya lafiya kuma an karrama baƙin amarya daga ƙarshe aka kaita ɗakin Najeeb wanda anan za su zauna kafin Najeeb ya ƙarasa gyara gidan sa.
Anyi nasiha kuma anyi addu'a kafin wanda su ka kawo amarya su ka tafi.

Tun tana zaune tana jiran ko Najeeb zai zo har ta haƙura ta kwanta dan ba ƙaramin bacci ne a idon ta ba.
Washegari ba ta farka ba sai ƙarfe takwas na safe. Ta shiga banɗakin da ke ɗakin dan ta yi alwala nan ta ga ƙaton bathroom wanda sai ka kwanta ka yi minshari a ciki. Tsaf-tsaf ya ke sai ƙanshi, akwai bathtube na wanka sannan gefe akwai Inda aka kewaye da glass wajen shower kenan.  Ta gama kallon banɗakin kafin ta yi alwala ta fito.
Karfe tara sai ga Adama tana ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin.

"Amarya wai ki fito ki karya in ji Hajia" ta ce da ita.

"To barin shirya"
Ta yi wanka ta nemi atampa ta sa cikin kayan da aka kawo ma ta daga gida.

Lokacin da ta sauko sun gama karyawa tana saukowa tanajin Najdah na yiwa Mom ƙorafi " Mom wallahi i cant believe wai Big B ya yi aure, wai hakan ma da lousy secretary ɗin sa"

"Be happy for your brother, finally ya yi aure @35yrs"

"Mom ba ta dace da gidan nan ba..."

"E'e'em" Farida ta yi gyaran murya

Najdah ta ɗago ido ta kalleta. Farida ta ɗan risina ta gaida Mom. Mom ta ma ta ya kwanan baƙunta.

"Najdah take her to the dining plz"

Maimakon Najdan ta yi abinda Mom ta ce sai ta fara kiran Adama.

Farida dai ta taune ta haɗiye duk wani maganan da ke bakin ta, kar ace amarya daga kwana ɗaya ta fara faɗa da ƙanwar miji.

Da Adama ta kaita dining ɗin ɗiban abinda za ta ci ta yi ta koma ɗakin Najeeb ko na ce ɗakin su.

Baƙi sun zo ganin amarya kuma ta fita an gaggaisa. Yawanci 'yan uwa ne da abokan arziƙi...

Tana sallar Isha ya shigo ɗakin zama yai a bakin gado yana kallon yadda ta ke sallah. He cant believe he got married to this girl, a mere secretary.

Lokacin da ta idar da sallan ya kalleta da kyau sannan ya ce " Daddy na son ganin mu ƙarfe tara"

Zuwa yai ya zauna kan kujeran da ya ke aiki idan yana ɗaki, ya kunna laptop na shi yana duba wa su saƙonni.

"Sir Najeeb dama ka min sharri ne dan ka aureni?"

Yi yai kamar bai ji ta ba sai da ta sake maimaita tambayar sannan ya juyo ya ce " i wanted to punish you, i wanted you to cry, but it backfires on me. Na aure ki ne saboda Dad, only because of him"

Shiru ta yi tana nazarin kalamanshi tareda tunanin mafita a rayuwar ta ko na ce a rayuwar auren ta.

"Dad ba ya zama a gida, Baby na zuwa makaranta, Justice Nabilah ma ba ta zama. You'll feel bored at home"

"Ina ruwanka" ta faɗa da ƙarfi.

Juyowa yai yana kallonta sosai, har lokacin tana zaune akan sallaya.

"I'm offering you a job. Har yanzu ban samu secretary da zai maye gurbin ki ba, so  you can have your job back"

"Kan uba. Lallai ma Sir Najeeb ka raina ni"

"Well its just an offer, idan ki na so za ki iya fara aiki next week monday"

"Allah ya isa na Sir Najeeb, Allah ya isa bulluƙutu"......

(Mrs Najeeb Jibo, Najeeb constructions needs your service, Oya de go de go😁)*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi*

0️⃣2️⃣4️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*








Tare su ka shigo falon Daddy, ya na zaune yana karatun littafi su ka same shi.

Farida ta zauna ƙasa tana gaida Daddyn.

" 'yata tashi ki zauna mana"

"Daddy na fi jin daɗin ƙasan"

Daddy ya ajiye littafin ya ce

"Aisha, ina so na baki haƙuri kan yadda al'amura su ka kasance. Kin ga wannan da ki ke gani" ya nuna Najeeb.
"Babban banza ne, ba abinda ya sani sai kan sa. Ina roƙon ki dan Allah, ki yafe ma sa duk abinda ya mi ki"

"Daddy komai ya wuce, na yafe ma sa"

"Allah ya mi ki albarka Aisha. Sai ki riƙa haƙuri da shi domin shi ɗin wani bahagon mutum ne"

"Dad" Najeeb ya faɗa yana tsume fiska

"Ai gaskiya na faɗa, ko ba haka ba 'yata?"

"Haka ne Daddy, wallahi wani lokacin kaman majnuni" sai da ta yi maganar kuma sai ta ji kunyar abin da ta faɗa, ta fara rufe baki da hijabinta.

"To kinga duk waɗannan halayen na sa marasa kyau, ke ce za ki shafe su, ke ce za ki inganta rayuwar sa. Ina muku fatan samun zuri'a ɗayyaba"

Farida ta ɗago ido ta kalli Najeeb wanda ya watsa ma ta harara.

"Za ki yi haƙuri ku managing wannan gida zuwa wani ɗan ƙanƙanin lokaci kafin ya ƙarasa gyara gidan shi sai ku koma chan.  Ina so ki sake jiki damu domin nan gidan ki ne. Allah ya sa albarka a wannan aure na ku amin"

"Na gode Daddy, Allah ya ƙara ma ka lafiya ya ƙara arziƙi da buɗi amin"

"Duk abinda Najeeb ya mi ki ba dai-dai ba, kinga duk girman shin nan a gaban ki zan sa bulala na zane shi"

Farida ba ta san lokacin da ta kwashe da dariya ba ta ce " wayaga ana zane Sir Najeeb, har na hango shi yana tsala ihu"

Daddy ma ɗan darawa yai.

Najeeb kam haɗe rai yai yana yiwa Farida kallon za ki gamu da ni.

"Najeeb idan ba abinda za ka ce, za ku iya tafiya"

"Good night" ya faɗa ya tashi da sauri kaman wanda a ƙaya ya ke zaune da ɗin.

Farida ta bi bayan shi bayan ta yiwa Daddy sai da safe a nitse...

Tana shigowa ɗaki ta sameshi ya na kishingiɗe akan gado hannun sa ɗauke da waya ya na dannawa. Ƙarasawa ta yi ta cire dogon hijab da ta yi sallah da shi ta ninke ta kaishi saman bedside drawer.

"Ba a ajiye kaya anan"

"To hijabin sallah ne ai"

"Ba a ajiye kaya a nan Miss Salihu"

Dariya ta yi ta ce "yau na ji wani zance, Miss Salihu kuma? Jiya dai aka ce wai Najeeb Adam Jibo ya biya sadaki na naira dubu ɗari biyu, ko ba haka ba?. Gara ka san da me za ka kirani amma ba Miss Salihu ba"

Kallon ta ya ke yi itama ɗin ta zuba mi shi ido, doguwar rigan bacci ne a jikin ta wanda ya kai har ƙasa amma siririn hannu rigan ke da shi.

"Oh! so yanzu kin zama Mrs Jibo kenan? Congratulations"

"Ni kam Sir Najeeb mi ye acikin Aisha ko Farida da ba za ka iya kira na da shi ba?"

"Ki ɗauke kayan nan, ba a ajiye kaya a cikin ɗaki"

"To ka nuna min inda zan sa kaya na ne. Ina wancan wajen duk kayan ka ne a ciki, kaya sai ka ce wanda mutum ya buɗe boutique"

" This is my room Mrs Jibo, dole ki bi tsarin yadda ɗakin ya ke, ba na son datti, ba na son clumsiness. Kin ga yadda komai ya ke a tsare, haka na ke so komai ya kasance a inda ya ke. So ki ɗauke wancan tsummukoran a wajen nan"

"Hijabin nawa ne tsummokara, lallai"

Shiru ta yi tana kallon sa, ta ga ya maida hankalin sa kan waya.

Ƙaraman tsaki ta yi sannan ta ɗauki hijabin ta kai shi wajen closet ɗin.
Tana dawowa ta zauna bakin gado tana shirin kwanciya ya ce " and what are you trying to do?"

"Bacci ma na"

"A ina ɗin?"

" ni fa Sir Najeeb ka ƙyale ni tam. Idan ba haka ba na gayawa Daddy, ka san ya ce har zane ka zai iya yi a kaina"

" there's no way i'm sharing a bed with you ki na sakatariya ta. Ga chan sofa chan ki je ki kwanta akai"

"Da ka san ba za ka iya haɗa gado da ni ba miyasa ka aureni. Ni bance ka min komai ba dan na san abinda ka ke tsoro kenan" ta ƙarasa maganar tana kwanciya da kyau.
Ajiye wayar sa yai ya taso ya na ƙoƙarin ɗauketa daga kan gadon, ita kuma ta riƙe zanin gado tana " Allah ba inda zan je, ba zan kwana a kujera ba sai dai kai ka kwana"

Wuff yai sama da ita ya zo ya sauketa a kan sofar. Yana ajiyeta ta sake tasowa ta zo za ta kwanta, yasake ɗaukan ta ya maida ita kan sofa.
"Mrs Jibo, idan ba wani abin ki ke nema a wajena ba, sleep here"

"Tabɗijam, wallahi ko a makaranta ban kwana a kujera ba balle a nan. Wallahi ka barni na kwanta ko na gayawa Daddy"

"Go on, je ki gaya ma sa" har ta fara tafiya sai kuma ta juyo ta ce "ƙila ya yi barci yanzu"

Miƙa ma ta wata na'ura yai ya ce " za ki iya gaya ma sa ai ba sai kin fita ba, ga shi ki danna 2 ki yi ma sa magana zai ji ki a ɗakin sa"

Ita fa ta ɗauka wasa ya ke dan abin yai ma ta kama da wayar cellular ta ƙarɓa ta ce "ƙila ma ƙarya ne"

"Go on try it"

"Daddy ga Sir Najeeb ya hanani kwana a gado, ka zo ka ma sa magana" ta faɗa da ɗan ƙarfi.

Murmushi yai ya ce " stupid girl"

Minti biyu  kacal sai ga shi ana ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin su. 
"Najeeb be matured please, mi ye wannan shirmen"

Jin muryan Daddy ya sa Farida ta yi saurin kama baki tana dana sanin abinda ta ce.

"Sorry Dad, good night" Najeeb ya faɗa sannan ya kalli Farida da ke tsaye tana zare ido.

"On a second thought, za ki iya kwana akan gado but" ya nuna ta da yatsa "kar ki kuskura ki matso kusa da ni, i can bite"

"Ni ma kar ka kuskura ka matso kusa da ni, i can scratch"

Zuwa yai ya jera pillow biyu a tsakiyar gadon sannan ya kwanta.

"Wallahi wajen ka ya fi yawa, wannan ba tsakiya ba ne"

Sa hannu yai ya kashe wutan ɗakin. Dole ta laluba ta kwanta a haka.
Chan ƙasar ran ta tana tunanin anya akwai ranan da Najeeb zai iya jin son ta, ko da ɗan kaɗan ne? Anya za ta iya samun kan sa kamar yadda Ummi ta ce? Anya akwai ranan da za ta kwanta da shi ta yi rayuwar aure da shi?
Ta tuno abubuwan da ta yi ta sha da ci saboda samun amarci mai cike da tarihi tareda Rayyan, amma yanzu kam duk a banza. Tana cikin tunane-tunanen nan har bacci yai gaba da ita...

Ya na kwance ne amma ba wai ya yi baccin ba. He still wonders why everything turns out this way, jiya saboda bai san yadda zai haɗu da ita ba shiyasa ya kwana a office. Komai ya zamo ma sa wani iri, she's just his secretary and that's  what she'll always be 🙄
Bai taɓa hango rayuwar aure da wata ba idan ba Sabreen ba. Sun planning komai tare, tun daga irin gidan da za su zauna har zuwa 'ya'yan da za su haifa. Yara biyu Sabreen ta ke so, kuma shi su ka tsara za su haifa ( ka ji fa😁).  Ba su tsara zama a Nigeria ba saboda Sabreen ba ta so, a plan ɗin su Nigeria sai dai ziyara amma ba zama ba. But yanzu komai ya chanza and now auren Aysherh...

......................

Washe gari da asuba alarm ɗin Najeeb ya farkar da Farida, Ita kam ganin ƙarfe huɗu kuma akwai bacci a idon ta ya sa ta cigaba da bacci.

Ƙarfe biyar da rabi na ta alarm ɗin ya buga. Ta tashi ta hango Najeeb yana aiki a laptop ɗin sa. Cikin zuciyar ta ta ce "yanzu haka tun tashin sa bai yi sallah ba, shi komai aiki kaman machine"
Ta tashi ta shiga banɗaki fitsari ta yi sannan ta yi alwala ta fito.
Ta shimfiɗa sallaya ta tada sallah.
Da ta idar ta kalleshi har lokacin yana aiki.

"Sir Najeeb ina kwana"

"Morning" ya faɗa kaman ana roƙan sa amsan...

Tana azkar ɗin safiya ya tashi ya shiga banɗaki sai kuma ya fito ya ce "Mrs Jibo, next time ki ka yi amfani da toilet, you flush it immediately"

"Fitsari kawai fa na yi"

"Ba na son ƙazanta"

"Toh na ji, kuma ni ba ƙazama ba ce"

Ya jima a banɗakin har ta gama addu'o'inta ta koma gado ta kwanta bai fito.
Ya na fitowa ta bi shi da ido daga inda ta ke kwance, bathrobe ne ajinsa fari. Zuwa yai ya tsaya gaban mirror yana ƙoƙarin shafa mai. Duk abinda ya ke tana kallon sa har ya gama ya je ya shirya cikin wani grey  suit na kamfanin Dolce and Gabbana. Dole ta rasa gane wani irin turare ya ke amfani da shi saboda turarukan da ya fesa sun fi biyar. Lokacin da ya gama ya taje gashin kan sa sannan ya matsa wanni mai a hannunsa ya shafa a gashin.

Ya sake shiga banɗakin kafin ya fito ya ce " i know you are staring Mrs Jibo, idan kin tashi ki kira Adama za ta gyara ɗakin"

"Ni mi zan gani, ni ba kai na ke kallo ba"

"Mrs Jibo think about my offer" yana faɗin haka ya ɗau brief case na shi ya fita.
Agogo ta duba ta ga ƙarfe bakwai saura minti ishirin. Kai dole Sir Najeeb ya dinga zuwa da wuri, duk da kamfanin sa ne amma ba ya wasa da zuwa da wuri.

Bayan fitan sa sai da ta mori bacci sosai kafin ta tashi wajen ƙarfe goma ta fara gyara ɗakin...

....................

"Dan Allah wa ya ke zuwa wajen aiki ranan ukun auren sa. Haba Najeeb ko a week break ba za ka ɗauka ba"

"A week break? Bayan asaran da Miss..." " i mean Mrs Jibo ta jawo min"

Anas ya kwashe da dariya " Mrs Jibo, haba nawan, ba wani sweet pet name da za ka sa ma ta sai Mrs Jibo"

"Mrs Jibo ma ai matsayi ta samu"

"Akwai lokacin da za ka kirata sweetheart, my love..."

"Oh please Anas"

"Allah Wallahi. Yanzu dai akwai wani Korede da zai fara aiki da kai yau, i hope you'll like him"

"No need, Mrs Jibo za ta resuming monday"

"Wait, Farida za ta dawo nan?"

"She has no choice"

"Ka san mi ka ke faɗa kuwa? Yanzu fa Farida matar ka ce"

"So what?"

"Wallahi ba ka ma ta adalci ba Najeeb. Ita da ya kamata ya zama tana zaune a gida, ana treating na ta kamar queen, sai ka kawota nan, nan ɗin ma a matsayin secretary"

"Ba na buƙatar shawaran ka, hold it to yourself"

"Amma Daddy ya sani?"

"Anas ba ruwan ka da al'amarin rayuwata. Dont meddle with my family affairs"

Anas ya sa dariya  ya ce "sannu Mr Family man"

* ku yi haƙuri na yi update ɗaya yau, kuma ba shi da yawa. Bi izni kun fa ya kun, gobe Insha Allah 2 updates za ku samu. Thank you for your patience**SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣2️⃣5️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi*

Bayan fitan Anas da jimawa sai ga Khalidah fuuuu ta shigo office kamar wadda aka korota.

"Najeeb why?, why her?"

"Excuse me"

"Najeeb all this while da na ke zuwa wannan wajen ka ɗauka dan kuɗi na ke zuwa, ko an gaya ma ka ina son aikin wahala ne. Saboda kai na ke aiki a nan. Only for you"

"So?"

" Najeeb ka rasa wadda ta dace da kai sai Farida, miye ta ke da shi"

"Idan kin gaji da aiki za ki iya forwarding resignation letter ɗin ki, zan yi farin ciki da ƙarɓan sa"

"Najeeb dan Allah ka fahimce ni, Ina son ka, ina son ka fiye da yadda ka ke tsammani"

"Get out"

"Najeeb please"

"Out"

.......................

Bayan ta gama gyara ɗakin ta yi wanka ta shirya cikin atampa riga da skirt, ta sauko ƙasa dan yunwa ta ke ji. Gidan shiru sai ƙaran TV da aka bari a kunne.  Zuwa ta yi wajen dining ɗin ta zauna ta zuba abinci ta fara ci.
Adama ta fito daga kitchen za ta haura sama  Farida ta kira ta.
Sai da su ka gaisa sannan ta ce " mutanen gidan sun fita ne?"

"Eh"

"Ayya sannu da aiki"

"Na gode Anty"

"Anty kuma, ai sai ki sa na ji kunya. Ki kira ni Aisha ko Farida"

"Anty Farida dai"

Farida ta sa dariya.

"Dama na ce daga yanzu ba sai kina gyara ɗakin mu ba, zan dinga gyarawa"

"Na gode" Adama ta faɗa tana murmushi.

Da rana tareda Adaman su ka yi girkin rana, su na aikin tana ma ta tambayoyi gameda gidan. Su biyu ne ma su aikin ita da Tasallah. Tasallah kuma ta je gida an mu su rasuwa. Ita Adama matar Iliya dreba ne ita kuma Tasallah bazawara ce wanda aƙalla za ta kai shekaru arba'in zuwa arba'in da biyar.

Da su ka gama ta haura sama ta duba wayar ta ta ga miss call ɗin Maijiddah da text ɗin ta, inda ta ke sanar da ita ta isa gida lafiya.  Kiran Maijiddan ta yi amma ba ta ɗauka ba sai ta kira Ummi. Sosai su ka yi hira da Ummin wanda ta ke ta ƙara ma ta nasiha akan haƙuri...

Ƙarfe uku saura Mom ta dawo, bayan ta kimtsa ta ci abinci ta sa Adama ta kira ma ta Farida.

Farida na bacci ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofa kamar daga sama, ta tashi da ƙyar ta zo ta buɗe.

"Anty Farida Hajia na kiran ki"

"Ok tana ina? Tana falon sama"

"Ina zuwa"

Sai da ta wanke fiskarta sannan ta fito.

A ɗan kishingiɗe ta sameta  kan kujera ta yi nisa cikin tunani.

Farida ta ɗan yi gyaran murya ta ce " Mom barka da yamma"

Mom ta ɗago kai ta kalleta tareda ƙaƙaro murmushi.

"Sannu da zuwa Aisha"
Sai da Farida ta gyara zama sosai sannan ta ce "you're lucky Aisha, Kin san, Najeeb yana son sunan Aisha sosai"

"Ayya! Amma bai taɓa kirana da shi ba kuwa"

"He likes you. Na san bai gane hakan ba amma nan gaba zai gane"

Farida dai shiru ta yi tana sauraron wannan mata wadda ta ke uwar miji gareta.

Mom ta ɗauki wanni takarda da ke gefen ta ta miƙawa Farida ta ce " na rubuta mi ki abubuwan da ya ke so da wanda ba ya so. Zai taimaka mi ki wajen ganin kun fahimci juna da wuri"

"Na gode Mom"

Ta miƙa ma ta wani ƙaramin jewelry box ta ce "wannan kyauta ne da na ke son bawa duk matar da Najeeb ya aura"

Farida ta ƙarɓi box ɗin tana godiya.

"Open it"

Tana buɗewa ta ga sarƙa ce ta dimond sai walwali ya ke.

"Its pure dimond" Mom ta faɗa tana kallon yadda Farida ke kallon sarƙan

"Mom na gode, Allah ya saka da alkhairi. Haƙiƙa banida ma bakin godiya, this is too much Mom"

"Ba komai, just make him happy"

"Insha Allah zan yi ƙoƙari Mom"...

Farida na shiga ɗaki ta ɗau sarƙan nan ta gwada sawa a wuyan ta, tana duba kan ta a madubi. Wannan duk taron da ta je ta sa ka shi sai ta zama topic of the day. Tana cikin dubawa sai kuma ta ji jikinta yai sanyi tunowa da ta yi wanda aka bata sarƙan domin sa ba wai ya damu da ita ba ne.

Ta maida sarƙan inda ya ke sannan ta ɗauko takardan da Mom ta ba ta, ta fara karantawa.

  - ya fi son kala baƙi
  - ya na son cin fruits (musamman apple, inabi da lemu)
  - ya na son coffee
  - ya na son ƙanshi
  - ba ya son wari
  - ba ya son ƙazanta
  - ba ya son hayaniya
  - ba ya cin doya
  - ya fi son kifi akan nama
  - ba ya son jan abu....

Wayar ta da ya fara ringing ne ya sa ta tsaya da karantawa. Ta ɗauko wayan sai ta ga Rayyan ke kiran ta. Har wayan ta katse ba ta ɗauka ba.

"Mi kuma zai ce min" ta faɗa a fili yayinda kiran sa ya sake shigowa. Sai a kira na uku ta ɗauka.

"Rayyan lafiya ka ke kirana?"

Daga ɓangaren Rayyan ya ce "My Farida ban san ya zan yi ba, yanzu na ke jin wai hotunan nan haɗa su aka yi, wai Alhaji Jibo ya zo ya samu Baba ya nemi a maida zancen auren mu. I'm sorry dear, ki bani lokaci mu zauna mu yi magana"

"A ina za mu zauna? A saman kwano ko a saman bishiyan mangoro. Look Rayyan, kar ka ƙara kira na, ni matar aure ce"

Ta na kashe wayar ta cillata kan gado ta cigaba da karanta takardar da Mom ta ba ta.
...........................

Kusan ƙarfe biyar wa su baƙi su ka zo Adama ta zo ta kirata ta sauko ƙasa. Su biyu ne, ɗaya ta ganeta domin jiya ta zo, ƙanwar Daddy ce da su ke kira Hajia Fatima. Ɗayar kuma ba ta san ta ba.

Sai da su ka gaisa Hajia Fatima ta gaya ma ta sun zo ƙarɓan sizes ɗin ta ne saboda lefe da za'a haɗa ma ta.

Hajia Salma da su ka zo tare wadda ta ke amaryar Uncle Sulaiman ne ta ɗauko  Tab ɗin ta ta na rubuta sizes ɗin, tundaga na inner wears zuwa general measurement na ta.
Bayan sun gama aka buge da taɗi, su na haka sai ga Najeeb ya shigo.

"Yawwa ango dama kai mu ke jira"

"Ni kuma?"

"Yes, mun zo karɓan kuɗin haɗa lefe"

"What's that?"

"Ɗan iska, dan ka yi ƙwacen mata sai ba za ka ma ta kayan lefe ba. To ba zai yiwu ba"

Hajia Salma ta ce " Najeeb bar Hajia Faty da tsokala. Check za ka rubuta ma na za mu haɗawa Farida kayan lefe"

Sai da yai kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "how much?"
Hajia Fatima ta ma sa daƙuwa ta ce " ungo na ka da how much ɗin, blank check za ka bamu"

"Hell no, there's no way i'm giving you a blank check. Ki samu daman zuba jari a shagunan ki ko?

"Zan ci ƙaniyar ka Najeeb"

Najeeb ya zauna ya ciro check book na shi ya fara cikatawa Hajia Salma da Hajia Faty idon su ƙyam akan abinda ya ke rubutawa.

Hajia Fatima  ta ce "Allah ya sawwaƙa Najeeb, mi wannan zai yi? Ka san ina da ina zamuje kuwa? Kai ka na sa kaya designer ba ka so matar ka ta sa designer ne?"
Farida kam dai kallon su ta ke yi dan ba ta ga nawa ya rubuta ba.  Ƙarshe dai dole blank check ɗin ya ba su...

Yana shiga ɗaki ya ji wayar Farida da ke kan gado yana ringing haka kawai sai ya tsinci kan sa da ɗaukar wayan wanda kafin ta yanke ya ga sunan nan dai da ke tada ma sa hankali *My Ray* tsaki yai ya maida wayar ya ajiye.
Ya na cire kaya amma sai tsaki ya ke shi kaɗai.

Lokacin da ta shigo yana kan gado, ya kunna TV da ke ɗakin yana kallon tashar Aljazeera.

"Sannu da dawowa, ya aiki"

" your Ray ya kira ki"

Dam ta ji gaban ta ya buga. Ita wallahi ta manta ba ta goge numbar bane ɗazu.

"Sir Najeeb ba wai abinda ka ke tunani ba ne, Allah mantawa na yi ban goge numbar ba"

Bai ce komai ba sai ma remote da ya ɗauka ya fara chanja tasha.

Ganin yai shiru ta ce " Sir Najeeb ka yiwa Mom godiya ta min kyautar girma. She gave me a dimond necklace"

"Mrs Jibo" ya faɗa da sigar jan hankali.

"Kar ki ƙara yi min maganar matar nan"

Farida ta zaro ido "mahaifiyar ta kan"

"Idan ki na so mu zauna lafiya, to ki dena kawo min zancen ta"

" yau na shiga uku, Sir Najeeb...."

"Shhhhhhh"

Haɗiye maganar ta yi dan yadda ta ga ran sa ya ɓaci.

Zama ta yi a gefen gadon ta ce "Sir Najeeb zan yi aikin, amma sai ka amince za ka bani dama na wanke kai na daga zargin da ka ke min"

" good for you"

..........................

Zuwa yanzu ta gama gane yanayin gidan. Mom ba ta da matsala ko kaɗan hakan ya sa ta rasa gane dalilin da zai sa Najeeb ya dinga ma ta abinda ya ke yi. Najdah kam ƙiri da ƙiri ta ke nuna ba ta son ta. Ita kam ko ajikin ta, dan ba wannan ba ne a gaban ta.
Ranar asabat da ta cika sati  ɗaya 'yan gidan su su ka zo ma ta gaisuwa. Ta ji daɗi sosai kuma ta karrama su, gayya guda su ka zo dan duka matan Baffa Musa ne su ka zo da yaran su kusan su goma. Da za su tafi ta haɗa mu su tsaraba...

Anas tun ranan da Najeeb ya ma sa zancen zai dawo da Farida aikin t,  ya kira yana ma ta faɗa akan miya sa za ta amince da haka, ta nuna ma sa ba komai ita ke son komawa aikin...

"Sir Najeeb wai haihuwa ka ke a banɗakin ne? Tun ɗazu fa" ta cigaba da ƙwanƙwasa banɗakin.
Haƙura ta yi ta je ta zauna tana jiran sa, dama fitsari ne ya matseta.

Yana fitowa ta tashi da sauri ta shiga banɗakin.

Tunanin ko lafiyarta lau ya ke. If she's really pressed mi ya sa ba za ta je guest room ba.

Lokacin da ta fito ɗaure da towel ya riga ya shirya takalmi kawai ya ke sawa.
"Sir Najeeb ka jirani mu tafi tare dan Allah"

" i'm not your driver"

"Sir Najeeb ya ka ke so na yi, anguwar kun nan ba lallai mutum ya samu abin hawa da wuri ba"

"Akwai mota a gidan"

"Motan tuƙa kan ta za ta yi ne. Ni ban iya tuƙi ba"

Ya miƙe tsaye ya ce "good for you"
Har ya kai bakin ƙofa sai kuma ya juyo ya ce "idan kin je office ki yi aikin ki kamar yadda ki ka saba, cause our relationship is strictly professional"

"Na ji Mr professional"

...........

Ta ci sa'a da ta fito lokacin Mom za ta fita ta ce ta shiga ta kai ta. Da suna tafiya ta ce idan sun dawo ta zo ta karɓi key ɗin mota. Farida ta ce ba ta iya tuƙi ba, mom ta ce za ta sama ma ta dreba.
Lokacin da ta shigo kamfanin kowa kallon mamaki ya ke ma ta tunda dai kowa ya san ita Sir Najeeb ya aura. Kai tsaya office ɗin ta ta je, yana nan yadda ya ke ta ajiye jaka ta shiga office ɗin Sir Najeeb.

Yana waya lokacin da ta shigo dan haka ta samu waje ta zauna maimakon da da take tsayawa a gaban sa.  Sai da ya gama wayar ya kalli agogon hannun sa ya ce "8:44am Mrs Jibo"

Ta langwaɓar da kai ta ce "na tsaya na karya ne kuma kai ma ka san..."

"Shhhhhh, kin san ba na son latti. Today should be the last time da za ki zo min office a makare. Sannan ba na son personal excuses na ki a nan. Here, our relationship is..."

"Strictly professional na sani" ta ƙarasa ma sa.

"Good, akwai wassu saƙo da zan tura mi ki ki printing na su ki distributing na su according to their respective specification"

"Ok" ta tashi za ta tafi sai ya ce "ɗauko min wancan green file ɗin" ya nuna ma ta shelf ɗin da ke office ɗin. Ta je wajen sai ta ga file ɗin yana ta ƙasa ne ta tsugunna za ta ɗauka dai-dai idon sa ya kai wajen dan ya tabbatar file ɗin za ta ɗauka. Wandon jeans ta saka baƙi sai shirt mai dogon hannu ash color, ta yi rolling da baƙin gyale. Ɗan tsugunnon da ta yi sai rigan ya ɗan ɗaga. Ya rintse idon sa saboda wani abu da ya ji ya tokare ma sa maƙoƙoro.
Farida ta ɗauko ta ajiye ma sa.
Gyaran murya yai ya ce "Mrs Jibo, akwai dokar da ta ba da dama wa duk wata matar aure da ke son saka hijabi a wannan kamfani da ta sa, ba matsala"

"So?" Ta faɗa tana harɗe hannayen ta a ƙirji.

"It means, za ki iya saka hijabi ko mayafi babba tunda ki na da aure"

"I see, amma ka sani ko nawa mijin bai damu da sa hijabina da rashin sawata ba"

"Still Mrs Jibo, ya kamata..."

"Shhhhhh, Sir Najeeb our relationship is strictly professional" ta kwaikwayi muryan sa.

Ya ɗan ji zafi a ran sa amma ya dake da ce wa "ok get back to work"

Har ta buɗe ƙofa idon sa na kan bayan ta.  Irin kayan da ta ke sawa ne tun da, amma ya rasa dalilin da ya sa yanzu bai son ganin ta da wannan kayan...

Tana zaune tana typing Anas ya zo zai shiga office ɗin Najeeb sai kuma ya tsaya su na gaisawa. Labarin marukan da Najeeb ya sha a kan ta ya fara yi ma ta wanda ya sa ta fara dariya. Dai-dai lokacin kuma Najeeb ya fito, ba yau Anas da Farida su ka fara hira su na dariya ba amma yau gani yai dariyar ta yi yawa.

"Ango wajen ka na ke son zuwa amma tunda za ka fita barin jira ka a nan, idan ka dawo sai mu yi maganar"

Najeeb bai ce komai ba ya fita, bai yi nisa ba sai ya dawo, har lokacin magana su ke.
Yai gyaran murya ya ce "Mrs Jibo ki tuna min ina da meeting ƙarfe goma"

Ba tareda ta kalle shi ba ta ce to.
Ya sake fita amma ko taku biyar bai yi ba ya dawo.
"Mrs Jibo follow me"

"Ina zuwa"

"Follow me, now!"  ya daka ma ta tsawa. Shi kam Anas ya gane kishi ke ran sa, tun ɗazu da ya fito ya ga irin kallon da ya ke ma sa kaman zai mangareshi.

Farida ta tashi da sauri ta ce " ina zuwa Yaya na"

Sai da su ka fita Anas yai dariya ya ce "muje zuwa Najeeb, da kan ka za ka hanata aikin nan"*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣2️⃣6️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi*


Har su ka isa second floor bai ce ma ta komai ba. Bin shi kawai ta ke yi amma har su ka dawo ba abinda ta ma sa. Su na dawo wa ta ce "Sir Najeeb dama ba abinda zan yi shi ne ka hana mazauna na su samu hutu"

"Dama hutu ki ka zo yi ne?"

"Sir Najeeb its not fair, ina zaman-zamana kawai ka zo ka tasheni ,na yi ta bin ka kaman wanda aikin bodyguard ka ɗauke ni"

Kafin ya ba ta amsa wayarta ya fara ringing.

"Your Ray?"

"To ba shi ba ne, Yakubu ne"  ta faɗa tana picking call ɗin ta yi waje.

Shi ma ɗin ɗaukan waya yai ya kira Anas.  Lokacin da Anas ya zo ya ce "ango-ango, ka gama yawo da amaryar ta kan. Can we discuss business"

Najeeb ya ɗan gyara zama ya ce "wannan Architect Yakubu ɗin whats his surname?"

"Yakubu Musa Wase"

"Ok"

Anas ya kalli reaction ɗin Najeeb ya kwashe da dariya yace " ba dan ka ma sa ƙwace ba da yanzu shi ne angon Farida"

"Kar ka ƙara cewa na yi ƙwace. You and Dad force me into this marriage"

"Ayya! Ashe abinda ya faru kenan ko. Sorry Najeeb angon Aisha"

"Cut this bullshit, ya ake ciki?"

"Dama maganar hutun ƙarshen shekara ne, ta ya za'ayi a gama duk wasu major project da mu ke da su a ƙasa kafin lokacin?"...

Tana duba wasu takardu sai ga mutum ya shigo ma ta office da sallama. Ɗagowar da za ta yi sai ga Rayyan.

Ta miƙe tsaye da sauri. "Rayyan lafiya?"

"Kin ƙi ɗaukan waya ta Farida kuma na ji labari kin fito aiki"

"Wato stalking ɗina ka ke yi?"

"Farida ki zauna ma na mu yi magana"

"Wanni maganan za mu yi?, ni fa matar aure ce Rayyan"

"Exactly, matar Rayyan ya kamata ki zama ba ta Najeeb ba. Duk abinda yai ya yi ne da sanin kan shi dan ya raba mu. Idan ba rashin sanin darajan mace ba, ta ya zai auri mace kamar ki just one week ya dawo da ke aiki, aikin secretary"

"Rayyan dan Allah ka tafi. Ka ga miji na na nan"

"Miji? My Farida miji fa ki ka ce. Ina ki ka saka alƙawurran da mu ka yiwa junan mu. Tun yanzu har kin fara cin amana ta kenan"

"Yau na ga ta kai na, Rayyan duk alƙawarin da na ma ka ba wanda na saɓa aciki, Na yi alƙawarin mallaka ma ka zuciya ta da duk soyayyata idan mu ka yi aure. Kuma ba mu yi aure ba mi ya kawo maganar cin amana a nan?"

"Saboda yana da kuɗi ko?"

" yes, saboda ina da kuɗi"

Su ka jiyo muryan Najeeb a bayan su.

"Daɗin abin ma sai dai mutum ya bi gefe yai zagon ƙasa amma bai isa ya tunkari mace ya nemi soyayyarta ba" Rayyan ya faɗa yana yiwa Najeeb kallon banza.

Najeeb ya ƙaraso kusa da shi ya ɗan buga kafaɗar sa ya ce " mutumina ka ɗan je ka ɗauki darasi a kan virtual reality ka ji"

Ya miƙawa Farida hannun sa guda ɗaya ya ce " Mrs Najeeb Jibo shall we"

Farida ta haɗiye miyau saboda kan ta ya ɗaure amma indai dan ta yi abinda zai sa Rayyan ya fita a rayuwar ta ne to za ta yi. Duk da ta so Rayyan a baya, amma yadda ya shure watannin da su ka yi tare ya fasa auren ta ana saura kwana biyu ɗaurin aure ya sa tana jin ko da akwai burbuɗin son shi a tareda ita to za ta kaɗe shi ta huta. Ko da ba ta auri Najeeb ba Rayyan ya dawo, to ba za ta iya auren sa ba bayan ya riga ya watsa ma ta ƙasa a ido.

Ta sa hannun ta cikin na Najeeb tareda matsowa ku sa da shi, maimakon ya tsaya a haka sai ya jawo ta jikin sa sosai. Ya kalli Rayyan da yai mutuwar tsaye a wajen saboda kishi ya ce  " please feel free to visit Najeeb constructions some other time, yanzu Mr and Mrs Jibo za su huta. So get out"

Yadda ka san an sace balon-balon (balloon) haka gwiwar Rayyan ta yi sanyi. Yana son Farida sosai tun ranan da ya fara ganin ta a Keke kuma har yau yana son ta, hotunan da ya gani su suka birkita ma sa tunani ya rasa gane kan sa, musamman da ya kasance dama mahaifiyar sa ba son Faridan ta ke ba, ta dai haƙura ne a lokacin dan ba yadda za ta yi.

Juyawa yai zai fita dan bashida ta cewa a wajen. A yadda ya ke ganin su zai iya shaƙe Najeeb a wajen.

"One more thing, dont ever call Mrs Jibo again"
Rayyan ya ji wani abu ya suke shi a ƙirji. Ya haɗiye miyau da ƙyar sannan ya sa kai ya fita.

Rayyan na fita Najeeb ya ture Farida gefe.

Ta ɗan yi ƙara ouch.

"Sir Najeeb za ka karya min ƙafa"

Fiskar nan ba wasa ko kaɗan ya ce " kar ki sake kawomin tarkace office"

Ta gyaɗa kai saboda yadda ta ga ya ci serious.

Har aka tashi ranan Najeeb ba shi da walwala. Tana ganin ya fito zai wuce gida ta yi saurin bin bayan sa. Bai ma ta magana ba har su ka isa gida itama ba ta ce komai ba dan yunwa ta ke ji.

Shi ne ya fara shigewa ciki ita kan zuwa ta yi ta ɗebi abinci kafin ta haura sama da tray a hannunta.

Tana shiga ta gan shi tareda Najdah, Najdah na nuna ma sa hoton abu a wayarta wai ya zaɓa ma ta.

Sallama ta mu su amma ba ta ji an amsa ba, ko da kuwa an amsan to aciki su ka yi.

"Amsa sallama yana daga cikin haƙƙin musulmi akan ɗanuwansa musulmi"

Najdah ta ɗaga ido ta kalleta sai kuma ta sauke ido.  Shi kam Najeeb bai ce komai ba ya san  fitina ta ke nema and he's not ready for  that.

Ta ajiye tray ta shiga banɗaki ta watsa ruwa, lokacin da ta fito Najdah ta fita. Ba ta san mi ya sameshi ba amma ta ga ko kayan jikin sa bai cire ba ya miƙe akan gado yana kallon sama.

"Sir Najeeb ba ka da lafiya ne?" Shiru

"Sir Najeeb ka tashi mu ci abinci"

Ta gama duk surutun da za ta yi amma bai ce komai ba sai daga baya ya tashi ya shige banɗaki...

.....................

Sati ɗaya kenan da fara zuwa aikin ta, ba za ta ce komai na tafiya dai-dai ba ba za kuma ta ce akwai matsala ba. Yawanci ma Najeeb ba ya zama a office ya kan fita supervising ayyukan da kamfanin sa ke yi kuma ya ke so a ƙarasa kafin hutun ƙarshen shekara.

Safiyar yau da ta shiga kitchen ta samu Mom na decorating wani chocolate cake, sai ƙanshi ya ke yi.
"Mom wa ke birthday?" Ta tambaya.

"Ya kamata a ci taran ki tunda ba ki san birthday ɗin waye gobe ba" Mom ta faɗa tana murmushi.

"Najdah?"

Mom ta girgiza kai, Farida ta leƙa cake ɗin ta ga shekarun da aka rubuta "wai-wai ashe na babban mutum ne"

Mom ta yi murmushi ta ce " he likes chocolate cake"

Farida ta ce "Ayya, cake ɗin ya yi kyau kuma"

"Akwai surprise family dinner da za ayi gobe da yamma. But dont tell him, idan ya sani ba zai zauna a gida ba"

"Allah ya kaimu gobe Mom"

....................

Safiyar asabat bayan ya iddar da sallah bacci ya koma. Haka kawai ta tsinci kan ta da kallon kyakykyawar fiskar sa, ta jima tana kallon sa, she cant believe he's 35yrs. Gaskiya jindaɗi da hutu na ɓoye shekarun mutum...

Da ta ɗan tattare ɗakin sai ta fita dan ta taimakawa su Adama da aiki.

Lokacin da ta dawo ɗakin kusan azahar ya riga ya fita. Ta buɗe akwatin kayan ta tana duba kayan da za ta sa. Mom ta ce iyalen gidan Uncle Sulaiman za su zo ga su Hajia Fatima, dole ta yi shigar da ba za a raina ta ba. Tana cikin duba wannan ta ajiye ta sake dubawa ta ajiye  aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin,
Ta je ta buɗe ta ga Mom ne.

"Mom ki shigo"
Mom ta miƙa ma ta wani paper bag ta ce "ki sa wannan and please wear the dimond necklace"

Ta amshi bag ɗin tana ma ta godiya...
Ba ƙaramin kyau gown ɗin ciki ya ma ta ba tareda takalmi da purse wanda su ka shiga da kayan.

Ƙarfe huɗu ta fito bayan ta shirya cikin doguwar riga pink da  Mom ta ba ta. Lokacin gidan an fara hayaniya, ta sauko ƙasa tana gaisawa da su Hajia Fatima...

Ya na gidan sa Dad ya kirashi akan maza-maza ya zo gida. Ya san ƙila surprise party su ka shirya ma sa. But he has no choice ba ya iya yiwa Dad mu su. Haka ya rufe gidan ya shiga mota ya dawo. Tundaga motoci da ya fara cin karo da su ya san hasashen sa ya tabbata.
Da sauri ya haura sama yana avoiding wata ƙaramar cousin ɗin sa 'yar shekara biyar da ke cewa ya ɗauketa.
Zuwa yai ya shirya a gurguje dan text ɗin Najdah da ya gani akan ya zo Garden su na jiran sa a wajen.
Komai sauri-sauri yai tun daga wanka zuwa sa kaya. Yana buɗe ƙofa ya gan ta a bakin ƙofa. Daga sama har ƙasa ya kalleta, she look beautiful, ga dimond necklace da ta sa da ya ƙara fito da ita.

"A ka ce na zo na kira ka"

*this page is total crap. Ba proofreading ba editting. Ga shi ɗan kucil, ga shi ya zo very late. Ku yi haƙuri i got a bit distracted saboda rasuwan Anty na kuma Oga na. Allah ya gafarta ma ta amin*

* a surprise page gobe for team Najeeb**SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣2️⃣7️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi*

Da farko ya shagala da kallon ta amma tunda ya ƙyalla ido ya ga sarƙan da ke wuyan ta sai ya janye idon sa yana cewa "matsa na wuce"

"Sir Najeeb Happy birthday"

Bai amsa ba kawai wucewa ya yi. Ta bi bayansa tana cewa " Dan ma ka samu na wishing na ka Happy Birthday ɗin"  yana takun sa na ƙasaita ta na bin sa a baya, da ke heel ta sa sai ya zama ba ta iya sauri ba sai ta ɗan sa gudu-gudu sauri.

Sai da su ka kusa isowa wajen sai ya tsaya, tana iso shi sai yafara tafiya a hankali ta yanda za su jera tare.

Su na shiga wajen aka sa tafi. Wani cikin cousins ɗin sa ya ce " ka ga salon soyayyar manya. Har ta tafiyar su iri ɗaya ce"

Najdah ta zo ta kama hannun Najeeb ta ma sa jagora zuwa inda zai zauna. Yana zama itama Farida ta zauna gefen sa.

"Happy Birthday babban yaya" Uncle Sulaiman ya faɗa yana kallon Najeeb da ke kujeran su na opposite.

Daddy ya ce " kar ka kumbura ma sa kai, wannan taron domin 'ya ta aka yi ba shi ba"

Najdah ta ɗauko cake ta kawo gaban sa. Ta kissing goshin sa ta ce " Happy birthday sweet Bro"

Murmushi yai sannan ya amshi wuƙar yanka cake ɗin ya sa zai yanka.
Aminu babban ɗan Uncle Sulaiman ya ce " ka yanka tareda amarya ma na mu san yanzu kam ka bar tuzuran ci"

Juyowa yai ya kalli Farida wanda itama shi ta ke kallo.
" he's right, 'yata help him cut the cake" Daddy ya faɗa  yana kallon yadda Najeeb ya haɗa rai.

A hankali Farida ta ɗau hannun ta ta ɗaura akan na Najeeb. Ido ya ƙura ma ta ita ma cikin idon sa ta ke kallo. A. haka har wuƙar ya nitse cikin cake ɗin. Sai da aka fara tafi sannan su ka cire ido cikin na junan su.
Da ya yanka ma cewa aka yi Farida ta sa ma sa cake ɗin a baki bayan ta sa aka ce shima ya ba ta, relunctantly dai ya sa ma ta.

Ba a jima ba aka fara serving abinci ana yi ana taɗi ana dariya. Haɗa kujeru aka yi da table sai ya zama kaman a dogon table ake cin abinci. Sun jeru straight akan kujerun.

Anwar ɗan Hajia Fatima  ya tashi ya ce " aga aga?"

Aka amsa ma sa da aga

"Aga waye yai aure @35yrs?"

Aka nuna Najeeb.

Aminu ya tashi "Aga Aga" aka amsa da aga

"Aga waye yai ƙwacen mata?"

Aka nuna Najeeb, wassu na dariya ƙasa-ƙasa.

Wani kallo ya watsawa Aminun dan ya girmeshi kusan shekara shida amma shi ya yi aure harda yarinyar su ɗaya.

Aminu ya zauna yana dariya.

Anas ya tashi ya ce "aga aga?"

Da aka amsa ma sa ya ce "aga waye yai auren soyayya da sakatariyar sa?"

Wassu su ka nuna Najeeb wassu kuma wanda ba son auren Najeeb da Farida su ke ba, su ka fara hararan Farida, irin su Najdah da Afrah wanda tunda ta dawo daga weekend ta tarar da auren Najeeb ta tattara ta koma gidan Uncle Sulaiman.

"Barin nuna wani short video clip na wannan masoya, there first fight and probably there first love"

Idan da yadda Najeeb zai yi ya je ya make Anas a inda ya ke tsaye da ya je. Dan wani mugun kallo ya ka aika ma sa daga inda ya ke zaune.

Anas ya ɗaga Tab ɗin sa sama ya playing video ɗin. Video compilation ne na wajen da Farida ta fara zuwa aiki har ta hana Najeeb shiga office, da wajen da ya koreta ta ƙi tafiya har ta rungumeshi lokacin da ya kira security. Sai wajen da Najeeb ya zo ya zauna akan superglue. Tun a clip na farko aka fara dariya, Daddy har da tari tsabar dariya. Wassu da ke gefe su ka dawo wajen da za su ga video ɗin da kyau.
Lokacin da video ɗin ya ƙare Anas ya ce " Thanks to CCTV footage na kamfani mun samu wannan video na masoya mai cike da tarihi"

Najeeb ya rintse ido ya cize leɓen sa na ƙasa. Wannan embarrassment ɗin da me yai kama. A gaban su Daddy da ƙannen sa, dan duk wajen idan ka cire iyayen to ya girme mu su.

A lokacin aka fara cewa ya tashi ya duba kujeran da ya zauna ko akwai superglue a kai.  Wa su kuma su na kwaikwayon maganar Farida su na "Sir Najeeb ya dai?"

Farida kam idon ta na ƙasa saboda ta ji kunya. Duk uban mutanen da ke wajen nan sun ga asirin ta.

Uncle Sulaiman yana dariya ya ce " kai gaskiya Alhaji ka iya matchmaking. Ka haɗa Najeeb da dai-dai da shi"

Aminu ya ce " ai yanzu da take gidan sa idan yai mata laifi da ruwan borkono zai yi tsarki"

Anwar cikin dariya ya ce " sai ya zama tsuliyar Big B is on fire kenan"
Gaba ɗaya wajen kowa dariya idan ka cire Najeeb da ya cika yai fam.
Farida ma da ta sunkuyar da kai ɗan dariyan ta yi...

Ana cin abinci ana sake gulman abinda aka gani. " Hajia Fatima har da cewa immediately Anas ya tura ma ta video za ta forwarding wa Najma da su Uncle Abubakar da ba sa nan...

Daddy ya ce " kar ku sa 'ya ta a gaba. Idan ɓera na sata to daddawa ma na wari"

Yadda hannun Najeeb ke shaking, Farida da ke gefen sa sai da ta tsorata. Ta leƙa ta ga hannun sa ɗaya da ya sa akan cinyar sa ya tamke shi kamar mai shirin kai dundu amma still hannun na rawa, ɗaya hannun da ya riƙe tsokali da shi kuwa yai wa sokalin riƙon makami ne.

Ana cin abinci amma Najeeb ba ya ci. Farida ma tunda aka playing video ɗin nan ta ka sa cigaba da cin abincin.

Lokaci guda hayaniyar da ake ta tsaya chak. Wanda su ke opposite da su Najeeb su su ka ga matar da ta doso wajen da ake taron ita da Adama da ke riƙe da tray za ta kawo wani nau'in abincin.

Jin shirun yai yawa kuma su Daddy sun ƙurawa mai zuwan ido ya sa wassu daga cikin wanda ke zaune layi ɗaya da Najeeb su ka juya, cikin su har da Aminu.
Muryan Aminun ne ya fitar da sunan wacce ta doso wajen cikin takun ta na ainihin celebrity, yadda ta ke catwalking kamar a kan redcarpet ta ke za ta je karɓan Oscar award.

*"SABREEN"* ya faɗa da sigar mamaki

Jin sunan ya sa sauran su ka juya duk da ma ba kowane a wajen ya san Sabreen ba, balle labarinta.  Idan ka cire Najeeb da Farida duk sauran sun juya.

Najeeb na zaune, takaicin abinda Anas yai ya cika shi, chan ƙasan ran sa yana tsara irin yadda zai ciwa Anas mutunci idan su ka haɗu, ya ji muryan Aminu ta fitar da sunan da ya tsana a rayuwar sa*"Sabreen)*

Yadda wajen yai shiru ya sa yai tunanin ko dai Sabreen ɗin ne su ka gani ko kuma su na so su sake playing prank a kan sa da sunan Sabreen.

Sanye ta ke da wani arnen baƙin kaya. Gown ce wanda ta kamata ƙyamƙyam, sannan ya fidda duk wani sura na jikin ta. Hannu ɗaya dogo ne har zuwa wuyan hannun ta(wrist) ɗaya kuma hannun vest gareshi. Jikin rigan yana da adon duwatsu wanda sai kyalli su ke, ta ɗan yafa wani ƙaramin gyale wanda gyalen yadda ka san abin  tata haka ya ke, shara-shara da shi, gyalen ma an ɗan yane shi ne  kaɗan amma duk rabin gashin na ta na waje. Tana ɗauke da wani designer purse wanda aƙalla kuɗin sa a ƙiyasin kuɗin Naira zai kai miliyan huɗu. Murmushi ta ke har ta ƙaraso wajen.

"Hi everyone"  ta faɗi tana ƙarasawa wajen Mom da itama ke daskare akan kujera tana mamakin zuwan Sabreen, dan ba ta da masaniya akan zuwan na tan.
Ta kissing kumatun Mom kamar yadda Larabawa su ka fiyi idan za su gaisa da mutum.

"Masa'ul Khair Ammaty"  ta faɗa tana ƙara faɗaɗa murmushin ta tareda sauke idon ta akan Najeeb wanda tun zuwan ta wajen Mom idon sa ke kan ta.

"Happy Birthday Noory" ta faɗa tana gyara gashin ta da ya zubo ya ɗan rufe ma ta rabin fiska.

Najeeb ya miƙe tsaye ba tare da ya ce komai ba ya bar wajen. Yadda ya ke tafiya kawai ka san yana cikin ɓacin rai.

Da ƙyar Mom ta iya haɗa kalmomin bakin ta tambayi dalilin zuwan Sabreen Nigeria. Maimakon ta amsa ma ta sai ta tambayi Mom ɗin da cewa ko ba ta son ganin ta ne. Mom ta girgiza kai.

Hajia Fatima ne kaɗai a wajen ta iya cewa " 'yar burauba, kin ji yai aure za ki zo ki ɗaga ma sa hankali ko"

Ba ta ji mai Hajia Fatima ta ce ba amma ta san zagi ta yi.

"Let me talk to Noory" ta faɗa sannan ta kama hanya ta bar wajen still cikin takun ta na ƙasaita.

"Tashin hankali kenan, ana wata ga wata. Ke Aisha ki je ki hanata magana da mijin ki dan wannan yarinyar sheɗaniya ce"

Daddy yai ajiyar zuciya ya ce " 'ya ta ci abincin ki, ba komai"

Ala dole Farida ta fara cusa abinci a baki. Lokacin da Sabreen ta zo wajen Mom Farida ta gan ta sosai, lallai dole wannan mata ta girgiza rayuwar Najeeb. Farida ta raina kan ta a gaban wannan mata da Allah yai wa baiwar kyau haka...

......................

Yana zuwa ɗaki ya fara safa da marwa a ɗakin, miyasa lokaci guda abubuwa guda biyu su ka zo su ka haɗu ma sa. Ga abinda Anas yai ma sa which ya san 'yan familyn su wannan abun har bayan shekaru sai sun yi ta tsokanar sa da shi. Ga uwa uba Sabreen.
What did hell is she doing here? Ya tambayi kan sa.

8yrs, 2months and 11days da tafiyar ta. May be da ba ta gudu ba da su na rayuwa cikin jin daɗi da 'ya'yan su biyu ɗan shekara shida da 'yar shekara biyu, dan shekara huɗu su ka tsara za su bawa yaran na su rata (o'o ni Azizat🙄 Najeeb da Sabreen sarakunan tsari)
Sai dai komai ga rushe lokacin da ta gudu ta barshi da takaici.
Cikin shekaru takwas ya gina kan sa a matsayin CEO kuma Founder na babban kamfani. Yayinda Sabreen ta samu fitowa a fima-fimai 11 a cikin 8yrs. Ta dating Tom cruise ta dating wani ɗan ƙwallo, ta dating wani hamshaƙin mai kuɗi ɗan ƙasar Italy.  Shi gashi bai dating kowa ba amma an kakaɓa ma sa sakatariyar sa.
Cikin shi da Sabreen ba zai iya cewa waya fi wani samun cigaba da kwanciyar hankali ba a shekaru takwas.

Yana cikin wannan bulayin Sabreen ta buɗe ƙofa ta shigo. Ƙaran tafiyar ta ya ji ya gane ita ce.

"What do you want?"

"Noory i'm sorry"

Wani dariyan takaici yai ya ce ma ta " in 8yrs 2 months 11days ba abinda za ki ce sai I'm sorry? For kin maida ni mahaukaci ko"

"Noory" ta faɗa tana matsowa kusa da shi

"Go back to Hollywood" ya faɗa da ƙarfi

"I'm here to stay Noory, for you, for us"

"You're Crazy Sabreen"

Kuka ta fara mi shi tana faɗin cewa tana son shi har yanzu kuma ba ta taɓa dena son shi ba. Rasa ma mi zai ce ma ta yai ya fice daga ɗakin ya barta.  Ba zai iya tsayawa a gidan ba, not after all that happened.

Ranan dai wannan dinner ta zama wani iri, an dai ƙarasa da ƙyar, wanda su ka kawo gifts wa amarya da ango sun miƙa.  Daddy da su Uncle Sulaiman sun jima suna tattaunawa gameda zuwan Sabreen kafin daga baya kowa ya watse.
Da ƙyar Farida ta kai kan ta ɗaki dan gaba ɗaya ta shiga wani yanayi na ruɗu. Sabreen ta dawo, macen da Sir Najeeb yai dakon rashinta har shekara takwas, macen da Anas ya ce ma ta ita Najeeb ya fara so kuma ya so ta so mai tsanani. Idan Sabreen ta dawo miye amfanin zamanta tareda Najeeb tabbas nan ba da jimawa ba zai sallameta ya auri Sabreen.  Ta jima tana zaune akan gado tana tufka da warwara kafin daga baya ta tashi ta shiga banɗaki dan ta watsa ruwa...

Daddy yai ta kiran Najeeb amma ba ya shiga. Ya na son ma sa magana akan zuwan Sabreen dan ya san halin ɗan na sa. Daddy ba zai iya ƙin karɓan baƙuncin Sabreen ba saboda kamar 'ya ta ke a wajen matar sa.

Najeeb gidan sa ya je ya kashe wayoyin sa ya kwanta, ba wai bacci ya ke ba, ya kwanta ne yana tuno abubuwa dayawa da su ka faru musamman soyayyar sa da Sabreen. He gave her all his heart, he loved her with every beat of his heart. Ya ma ta alƙawarin samun rayuwa mai kama da aljannar duniya idan u ka yi aure amma...

Ranan bai koma gida ba dan ba ya son sake ganin Sabreen saboda yadda ya ke ji a zuciyar sa. Farida kam bacci ƙaurace ma ta yai. Makomarta ta ke nema a wannan lamari, idan tana ganin za ta iya samun soyayyar Najeeb to yanzu kam chances ɗin ta ya bouncing back to zero.
*Sabreen* ta maimaita sunan a karo na ba adadi...

.................

Washegari Lahdi Farida ba ta tako ko ƙofar ɗaki ba, a ɗaki ta wuni Adama ce ta ke kawo ma ta abinci har ɗaki, wanda abincin ɗan tsakura kawai ta ke iya yi. Rashin kwanan Najeeb a gida ya tabbatar ma ta nata zancen ya kaɗe domin ta san yana chan yana kitsa yadda zai yi aure na gani na faɗa shi da Sabreen.

Ga mamakin ta ƙarfe tara na dare sai ga shi ya shigo ɗakin, bai ce ma ta komai ba ya je yai wanka ya shirya cikin ɓakin pyjamas na shi ya kwanta.

Daga inda ta ke zaune ta ce "Sir Najeeb miye matsayi na yanzu?"

Bai kulata ba, shi idan ba dan Daddy ya ce lallai ya dawo gida ba da bai san ranan da zai dawo nan ba. He feels empty.

"Sir Najeeb magana na ke"

"Oh please Aysherh" ya faɗa ba tareda ya realising da sunan ta ya kira ta ba

Jin sunan ta for the first time a bakin sa sai ta tsaya ta na jin yadda sunan ke ringing a ƙwaƙwalwarta *Aysherh Aysherh Aysherh*

Ringing ɗin wayar ta ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, ta yi saurin zuwa ta ɗauki wayan sai ta ga Sister Munibat. Ta ɗauki wayan su ka gaisa, jin muryan ta kaman tana kuka ya sa ta tambaya ko lafiya. Sister Munibat ta sanar da ita mahaifinta ne ya rasu ta gayawa Sir Najeeb ba za ta zo aiki ba ta ɗau hutun sati ɗaya.

"Allah ya jiƙan sa, kar ki damu Sister zan faɗa ma sa. Daga satin nan ma za a shiga hutun ƙarshen shekara so kar ki damu. Allah ya ma sa rahama"

Da ta gama wayar ta fara gayawa Najeeb ko ya ji ta ko bai jita ba oho, dan bai amsa ba.

....................

Yau ma Mom ce ta kaita wajen aiki dan Najeeb tun ƙarfe shida ya fita. Su na tafiya tana ba ta haƙurin zuwan Sabreen tareda ma ta alkawarin duk yadda za ayi sai ta sa Sabreen ta koma inda ta fito.
Farida ta tambayeta ko miya sa ta ke supporting ɗin ta ba Sabreen ba. Mom ta ce "saboda  Sabreen is his past, ke ce present and future ɗin sa" da wannan ya sa Farida ta ɗan ji sanyi a ranta...

Tana aiki a laptop Sabreen ta shigo office ɗin ta still cikin shiga mai ɗaukan hankali.

Cewa ta yi za ta ga Noory. Farida ta haɗe fuska tana jin haushin sunan da Sabreen ke kiran Najeeb da shi.

"Sabreen ki ke ko Siren ne?Najeeb zaujy, Ana Zaujy Najeeb"  ta faɗa tana nuna kan ta.

Sabreen ta kwashe da dariya saboda shirmen larabcin da Farida ta yi. Ta san da zancen auren Najeeb kuma ta san wanda ya aura, but seeing Farida ya sa ta ƙara yarda Najeeb ba auren son ran sa yai ba, saboda Farida ba ta dace da irin matan da Najeeb zai so ba balle har yai tunanin yin rayuwa da su.

"Fuck off girl, i have his heart"

Tana faɗin haka ta shige office ɗin Najeeb.

"Shegiya karuwa" Farida ta faɗa tana tsaki...*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣2️⃣8️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©️
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900*

*a star is never perfect and the villain is not always that bad*


Ya riga yai nisa cikin tunani lokacin da ta shigo sai da ta kira shi sannan ya ɗago ido ya kalleta. Farin idon sa ya koma ja saboda rashin bacci da damuwa.

"Noory" ta sake kira da murya mai jan hankali

"Leave" ya daka ma ta tsawa.

Ba ta damu da abinda ya ce ba, ta samu kujera ta zauna.

"I'm here to stay Noory" ta faɗa tana ƙanƙanta ido kamar za ta yi kuka.

A da wannan muryan yana raunata shi, a da wannan murya yana ratsa duk jikin sa ya bi kowanni jijiya na jikin sa, a da wannan murya yana sa shi jin wani farin ciki mai wuyar bayyanawa.

"Look, ban san mi ya dawo da ke ba, kuma ba na so na sani, ko ma minene ina so ki sani cewa you're not welcome"

(Maganansu ingautsan Larabci da turanci su ke. And ni kuma😁)

"Noory listen to me please,  i love you, i still do"

"Get out"

"Noor..."

"Get out of here"

Ta san za a yi haka shi ya sa ta zo da shirin ta.

"Ba za ka iya korata ba"

Kallon mamaki ya ma ta at the same time sai maganan ta yai kama da abinda Farida za ta ce.

"Ina da 6% shares a kamfanin nan"

"6%" ya maimaita sannan ya sa dariya, tsayawa yai da dariyan lokacin da ta ce *"SABNAJ Inc."*

Farkon buɗe kamfanin sa kafin ta gama zama da ƙafarta, ya saida kaso ashirin da biyar a matsayin hannun jari ciki kuwa har da Sabnaj inc. Ya tuna lokacin kamfanin ta so siyan kaso shabiyar ne amma ya ƙi, daga baya aka koma kaso goma har kuma daga ƙarshe aka tsaida matsaya akan kaso shida. Abinda ya sani shine Sabnaj inc wata kamfani ce a ƙasar America.

"Yes Najeeb, i owned sabnaj"

"SABNAJ" ya furta a hankali. Sunan da su ka shirya sa wa kamfanin sa kenan kafin komai ya wargaje tsakanin sa da Sabreen.

"Sab for Sabreen and Naj for Najeeb. Do you still remember?"

Ta ya bai yi wani ƙwaƙwƙwaran bincike ba a lokacin har ya sayar da shares ɗin kamfanin sa ga Sabreen. Ko lokacin da kamfanin Sabnaj ta zo neman saka hannun jari bai yi niyyar karɓan su ba saboda yadda sunan kamfanin ya ke. Anas shi ya convincing ɗin sa akan ya amince mu su.

"Ina son na yi aiki a nan Noory, ina so na yi aiki kusa da kai. Na ɗau hutun acting na shekara biyu just to be with you. Na san kamfanin ka ta samu koma baya cikin watannin nan, i'm here to help"

"Nawa za ki sayar da shares ɗin ki?" Ya faɗa with serious face

"Ba zan sayar ba, i want to be with you"

"Miss Sabreen. Welcome to Najeeb constructions then"

"What!"

Murmushin yaƙe yai tareda sa hannun sa a haɓarsa ya furzar da iska a hankali ya ce " duk abinda ki ke tunanin samu a wajena ba za ki samu ba, nonetheless, i'm going to buy your shares. Now leave my office"

Murmushi ta yi ta ce " I'm going to fight for us Noory"

Tana tashi za ta fita ita kuma Farida ta shigo. Kallon-kallon su ka tsaya yiwa junan su. Kafin Sabreen ta janye kallon ta hanyar saka baƙin glass ɗinta ta fice daga office ɗin.

Farida ta ce "kurwata kur mayya"

Ƙarasawa wajen Najeeb ta yi wanda ke waya da Anas yana surfa ma sa masifa, dama tunda ya zo ba su haɗu ba. Yana ajiye wayan Farida ta ce "Sir Najeeb, wannan list ɗin da ka ce na yi akwai sunayen da ba su yi dai-dai da na cikin database ɗin ba ya za ayi?"

"Just do it anyhow?" Ya daka ma ta tsawa.

Jikinta ne yai sanyi, Najeeb ɗin da ta sani ba zai yi tsawa dan ɗan wannan abin ba.

"Sir Najeeb saboda Sabreen shine za ka min tsawa" ta faɗa a hankali

"Get out Mrs Jibo"

Wannan karan da ƙarfinta ta ce " Ba zan fita ba, ba zan fita ɗin ba. Ka gaya min matsayina? yanzu da wannan karuwar ta ka ta dawo, miye matsayina?"

Ɗago ido yai ya kalleta amma baice komai ba.

"Banda matsayi ko?, banda matsayin da ya wuce matsayin Sakatariyar ka ko?"

"Wanni matsayin ki ke so bayan wannan?" Ya maida ma ta martani.

"Amm..." sai kuma ta fasa maganar da za ta yi ta ce "na gode"
Juyawar da za ta yi ta ga Anas yana tsaye a wajen. Sauri ta yi ta bar office ɗin.

"Kai wanni irin mutum ne Najeeb, Farida matar ka ce fa yanzu"

"Sabreen ita ke da kamfanin SABNAJ"

"Wanni Sabnaj ɗin?"

"Kasan sarai abinda na ke nufi, also Sabreen wants to work here"

"shegiyar kuma ta nan ta biyo?"

" ba na son ganin Sabreen Anas"

"Its simple, ka siye shares ɗinta"

"Ta ƙi"

"Ka bar batun wannan, Najeeb yadda na sameku da Farida kwata-kwata bai dace ba. Kar ka manta matar ka ce fa"

"Matar da Dad ya sa dole na aura ba"

Anas ya harareshi ya ce "Matar da ka rusa shirin aurenta ba. I know you love her Najeeb, kar ka yi wasa da damar ka"

"Stop this nonsense Anas, ka san har yanzu ban yafe ma ka abinda ka yi ranan saturday ba"

"Ni dai na gaya ma ka" daga haka ya fita.

Samun Farida yai ta kwantar da kan ta a kan table tana hawaye.

"Farida" ya kira sunan ta a hankali.
Ta yi saurin ɗagowa tana goge hawayen.

"Dan Allah ki yi haƙuri"

Murmushin yaƙe ta yi ta ce " ba komai Ya Anas, ni dai abu ɗaya na ke buƙata a wajen ka"

Zama yai a kujera dan ya saurareta da kyau.

"Sharrin da aka min a wannan kamfani har ya sa Sir Najeeb ya ke ganin baƙina, ina so na wanke kai na ko ta halin ƙaƙa. After that, zan bar aiki a nan"

"I'm sorry 'yar uwa na ce zan sake bin bahasin case ɗin, abubuwa su ka shamin kai ban yi ba. But Insha Allah zan yi"

"Na gode"

"Farida" ya sake kiran sunan ta a hankali. Ta ɗago ta kalleshi.

"Najeeb na son ki farida, idan ki na son shi, ko da kaɗan ne, fight for him. Kar ki ga wai Sabreen ta dawo ki shiga ruɗu ko ki ɗauka shikenan ba ki da chance a wajen Najeeb. Ke ne ki ke da damar samun sa, har ki juyashi yadda ki ke so. But only idan ki ka cire shakka ko wani tsoro"

Maganganun Anas sun ba ta mamaki sosai, ta daure ta ce "Najeeb ba ya so na Ya Anas, ba zan iya ƙwallafa rai na a kan sa ba"

"Shikenan, ki zauna, ki zuba ido har Sabreen ta ci galaba akan ki. Idan hakan ta faru ina tabbatar mi ki da cewa ƙeyar Najeeb sai ya miki wuyar kallo"

Daga haka ya tashi ya fita.

Tunanin maganganun Anas ta shiga yi. Tana kokonton maganar amma wani ɓangare na zuciyarta na son gaskata hakan...

Ranan ba su dawo tareba saboda ta rigashi tafiya, ta barshi suna tattaunawa da Anas, ta san ba zai wuce akan fara aiki da Sabreen ta ce za ta yi da su bane.

A gajiye ta shiga gidan sai taga Sabreen da Mom su na hira a falo. Mom kawai ta gaisar ta wuce sama bayan ta aikawa Sabreen harara.

Tana ɗan jin ciwon ciki amma ba wannan ba ne a gaban ta yanzu. Mafita ta ke nema wa kan ta, ko da ba za ta samu Najeeb ba amma ba za ta bari Sabreen ta sameshi ba, dan Najeeb bai dace da karuwa ba. Ko yaushe ta fara damuwa da Najeeb oho...

As usual sai dare ya dawo, tana kwance akan gadon ya shigo. Ba ta kulashi ba dan ta kanta ta ke, tun da magriba ciwon cikin ta yai tsanani kuma ta duba ba ta da magani.

Bayan ya shirya ya sa Najdah ta kawo ma sa lemon tea. Ya zauna yana aiki a laptop yana sipping tea ɗin.

Tun ɗazu ta ke juye-juye a kan gadon bai lura da ita ba. Ta tashi zaune, ta yi rub da ciki, ta yi gotso duk saboda yadda ciwon mara da ciki ke jijjigata. Ƙarshe dai ƙasan gado ta sauko ta yi kamar sujjada tana ɗan jijjiga jikinta.

Ya gama abinda zai yi ya hau gado sai ya ga bai gan ta ba. Ɗazu dai ya gan ta a kwance kuma bai ji ƙaran buɗe ƙofar banɗaki ba balle yai tunanin wajen ta shiga. Ya share zancen ƙila kaya ta je chanjawa. Bai yi 5seconds da sake zancen ba ya ji nishinta.
Fara dube-dube ya ke har ya mirgino zuwa gefenta ya leƙa ƙasa ya ganta.

"Are you Ok?"

Girgiza kai kawai ta yi.

"Mi ya sameki?"

"Ina ruwan ka da ni. Ka damu da ni ne?"

Juyawa yai ya ƙyaleta.

Ta ɗan jawo pillow ta danne cikin ta da shi ta cigaba da nishi. Bata ankara ba sai ta ga ya kashe wutan ɗakin. Wani tuƙuƙin baƙin ciki ya zo ma ta har wuya, wato da gaske bai damu da ita ba.

"Wayyo Ummina, Wayyo Allah gatan marainiya. Wayyo Ummi"

Kunna wutar ɗakin yai ya tashi ya zo ya ɗauketa ya maidata kan gadon. Ya ce "mi ya ke damun ki?"

Ba ta kulashi ba ta cigaba da murƙusu a kan gadon. Lokaci guda ya tashi kaman an tsikare shi ya fita daga ɗakin. Minti biyar sai gashi ya shigo ɗauke da mug.

"Tashi ki sha magani"

"Ni ka bar ni, ka san abinda ke damuna ne?"

"Get up" ya faɗa da ɗan ƙarfi.

Ibrufen tab ya miƙa ma ta tareda ruwan ɗumi, ta amsa ta sha.

Ya ce " ki shanye ruwan"

Ta cigaba da shan ruwan ɗumin har ya ƙare. Ta miƙa ma sa mug ɗin ya karɓa ya ajiye a saman bedside drawer.

"Kwanta"

Kwantawa ta yi da bayan ta tana kallon idon sa. Rigan baccin da ta sa riga da wando ne masu laushi, wandon iya gwiwa ya ke.
Hannu ya sa ya kamo ƙafafuwanta biyu. Ta challa ƙara " Sir Najeeb me ka ke shirin yi?"

Wanni kallo ya watsa ma ta ta yi shiru. Ƙafafuwanta ya kama sannan ya tanƙwasu  ta yadda cinyoyinta sai da su ka taɓa cikinta gwiwan kuma na taɓa nonuwanta. Ya sake stretching ƙafafun sannan ya sake tanƙwasasu. Haka ya ke yi har sai da yai kaman sau goma sannan ya sauke ƙafafun, ya sake ɗaga ƙafa ɗaya ya tanƙwasashi gefe. Ƙafar ta yi kaman triangle, sannan ya tanƙwasa ta koma ɗaya ɓangaren haka yai ta yi har sau goma sannan yai wa ɗaya ƙafan ma haka. Hannu ya sa zai ɗaga hips ɗin ta sama Farida ta yi saurin cewa "Sir Najeeb ina abu fa, kuma ba a abu idan ana abu"

Ya gimtse dariyar da ta zo ma sa ya ce " Bakin ki ne abu ai, ni ma ba na abu idan ba na so na yi abu musamman ma da wadda ba ta da abu"

Ya tallafo hips ɗinta ya ɗan ɗaga sama sannan ya mai da su ya sake ɗaga su a haka sai da yai sau goma.
Yana sake wani form of stretching ɗin ta yi saurin cewa " Sir Najeeb ka yi a hankali wandona zai yage"

Tsayawa yai yana kallon ta. Sometimes yana mamakin wai yarinyar nan ta yi makaranta. Most at times tana yin wassu abubuwan kamar 'yar ƙauye.

Sai da ya gama yi ma ta yoga dan ta samu relieve sannan ya kashe wuta ya kwanta.
A cikin duhun Farida ta dubi gefen sa ta ce "Sir Najeeb ya aka yi ka iya wannan abin, Allah na ji sauƙi sosai"

"Sleep Mrs Jibo" ...

...................

Kamar yadda Sabreen ta nema haka washe gari aka ware ma ta office a second floor. Da ta zo ta gani ta ce ba ta so sai a top floor inda office ɗin Najeeb ya ke. Anas ya ce sai dai ta yi manage ahaka zuwa kwana  biyu. Ba ta da haƙurin kwana biyu dan haka ta ce ba za ta zauna ba.

Kamar yadda Anas yaiwa Farida alkawari hakan ya sa ya kira Yakubu su ka fara reviewing ɗin case ɗin Farida da aka yi kwanan baya.

Najeeb ya jima yana zaune yana aiki, Sabreen ta sa shi a gaba da kallo. Ya ce ta tafi ta ƙi tafiya sai yai kamar bai san da zaman ta ba a wajen.
Farida ba ta office lokacin da Sabreen ta zo ta wuce. Ta dawo daga kai saƙo ta zauna tana yin aiki sai ta tuna ya kamata ta chanja pad. Ta ɗau jakar ta ta nufi office ɗin Sir Najeeb tunda banɗakin sa ya fi clean.

Yana zaune ya ji hannun Sabreen a kafaɗar sa. Ya juyo a fusace.
"Whats the meaning of this?"

"I know you missed my touch Noory" ta faɗa tana ƙara shigewa jikin sa.

"To karuwancin har a office" muryan Farida ta dakatar da ita.

Dukkan su su ka kalli Farida da ke tsaye ta sa hannu a kafaɗa.

"Miss celebrity you're stepping beyond your boundary" ta ƙaraso har gaban ta ta nuna ta da yatsa.
Kamar yadda ta ce mata she has his heart haka itama ta kwaikwayi maganan ta ta ce " fuck off old woman, i am his wife"

Sabreen ta cize leɓe tana huci.

"As as as, mai guri ta zo sai mai tabarma ta naɗe"

"Wow! I like your courage" ta faɗa tana haɗiye duk wani baƙin ciki da ta ke ji.
Har ta fita Farida ba ta bar cewa as as as ba.

Ta juyo ta kalli Najeeb da ya zuba ma ta ido yana ganin shaƙiyancin da ta ke wa Sabreen. Not minding ko waye Sabreen ɗin.

"An dai ji kunya, mace ta gudu ta barka shekara takwas amma ka gan ta yanzu jikin ka ya fara rawa kamar mazari"  ta yi wani juyi sannan ta wuce banɗaki.

....................

A hankali ta fara barbaɗa tankaɗaɗɗen yajin da ke hannunta, tun daga pillow zuwa duka bedsheet ɗin. Bedsheet ɗin ba fari bane balle a gane. Tana gamawa ta fice daga ɗakin ta maida roban yajin zuwa kitchen. Ta haura sama abinta.
Sabreen ta dawo tayi wanka ta shirya cikin rigan baccinta ɗan filili da shi. Ta kwanta akan gado. Juyawar da za tayi sai ta ji zafi a wuyanta da cinyoyinta da ke buɗe. Ta sa hannu ta sosa wuyar ai sai ya zama kamar ƙara zafi ta yi wa wajen. Ta yi wuf ta tashi tana sosa ko'ina ajikinta...

Farida ta baza kunne tana sauraron ko saƙonta ya kai inda ya ta ke so, saboda haka ma ba ta kunna Tv ba, Shi kuma Najeeb na aiki a laptop. Lokaci ɗaya su ka ji an kurma ihu.
Da farko Najeeb ya ɗauka ko ƙaran daga TV ɗin Najdah ne tunda ya ga Farida ba ta kunna Tv ɗin su ba. Ihu da ƙaran ya cigaba da ƙaruwa hakan ya sa ya miƙe zumɓur ya fita, Farida ta bi bayan shi da sauri.
Lokacin da su ka isa ƙasa su Daddy da Mom ma sun iso ƙasan su na kan Sabreen da ke ta soshe-soshe tana ihu...*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣2️⃣9️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900*

Sabreen na ganin Najeeb, ta yi kan sa tana sose-sose, ya riƙeta yana tambayar miya ke damunta amma ba magana sai kuka tana ƙara shigewa jikin Najeeb kaman jikin sa ne zai ma ta magani.
Mom ta tafi da gudu ɗauko car key. Chak ya ɗauketa za su fita dai-dai nan Farida ta sa kuka itama tana wayyo cikina wayyo cikina.
Najeeb ɗauke da Sabreen ya juyo ya ga Farida har ta kai ƙasa tana riƙe da ciki.

Dad ya ce ajiyeta ka ɗauko matar ka.
Sabreen ba ta ji mi aka ce ba amma ganin Najeeb na shirin sauketa sai ta sake ƙanƙame wuyan Najeeb tana kuka.
Chan gefe ma Faridan kuka ta ke yi Mom ta yi kan ta tana ƙoƙarin ɗagata tana tambayar miya sameta.
Tunanin Najeeb ko dai ciwon cikin period ne amma kuma she was normal throughout yau, tunda yau kwana na uku kenan da farawanta.

Farida cikin kuka ta fara cewa "Mom ulcer, ulcer na ne ya tashi"

Bai san ko maganar Daddyn ne ta shige shi ba, ko kuma dai ya zaɓi tallafawa Farida  ne akan Sabreen ɗin. Amma tsintar kan sa yai da sauke Sabreen ya nufi wajen da Farida ke murƙususun ƙarya a ƙasa. Daddy da Mom su ka tallafawa Sabreen su ka fita da ita. Daddy na cewa yai sauri ya ɗauko Farida. Faridan na hannun sa ya ce su tafi da Sabreen zai taho da Farida.
Ba tareda ya ji nauyin ta ba haka ya haura da ita sama dan ya ɗauko key ɗin motar sa, har da ce ma ta sorry.
Ya ɗauki key ɗin su ka fito still yana ɗauke da ita. Kafin su isa wajen motar sa motar su Daddy ta fice daga gidan. Sai da ya ajiyeta sannan ya zago da gudu ya shiga wajen zaman driver, yana ƙoƙarin tada motar ya ji ta ce "Sir Najeeb mu koma cikin gida, idan na sha Gestid ma zai lafa mun"

Kallon ta ya tsaya yi cike da mamaki da takaici, sai yanzu ya lura fiskarta ba ɗigon hawaye ko ɗaya. Lokaci guda zuciyar sa ta ankara da cewa lallai Farida na da hannu wajen abinda ya samu Sabreen, yanzu haka wani abin ta sa ma ta a ɗaki.

"You lied?" Ya faɗa da ɗan ƙarfi

"Sir Najeeb Allah Wallahi ina da ulcer, na ji alamun zai tashi ne shi ne ya sa na tareshi tun kafin ya zo"

Zaro ido yai waje lokaci guda kuma ya kwashe da dariya har da dukan steering.

"Now i'm very certain that you're crazy Mrs Jibo"

"Sir Najeeb da laifi idan mutum ya tari rashin lafiya ne?"

Sai da ya sha dariyar sa sannan ya ce " faɗamin gaskiya mi ki ka yiwa Sabreen?"

"Ni ba abin da na ma ta. Ance idan duka yai yawa na kai ake karewa. Da ka je kana dakon ɗaukar wata ƙatuwar banza ba gara ka ɗauke ni ba, har lada za ka samu a hakan fa"

"So, kin ƙirƙiri ciwo ne kawai dan na ɗauke ki?"

"Allankatafir ba haka ba ne. Ciwon a jikina ya ke tun asali"

" Ok ok, so yanzu mi za ki ce da su Dad? Su ma za ki gaya mu su taro ciwo ki ka yi?"

"Cewa zan yi na sha magani na warke"

"Ni kuma sai na kai ki asibitin, a taro miki ciwon da kyau"

Ganin yana ƙoƙarin ta da motar ne ya sa ta yi saurin buɗe ƙofa ta fita da gudu. Yana gani ta fita ya kwantar da kan sa ajikin kujera yana murmushi. Shi kan sa mamaki ya ke, a da ya tsani yawan surutun ta amma yanzu ya na jin nishaɗi idan tana yin wasu abubuwan.

Ya jima a cikin motar yana tuno wassu abubuwa da su ka faru a baya. Yana fitowa zai koma cikin gida Daddy ya kirashi yana tambayar ya aka yi ba su iso ba. Cewa yai cikin Faridan ya lafa ta ce ba sai anje asibiti ba.
Daddy ya ce "to Alhamdulillah, Allah ya ƙara lafiya"

Yana kashe wayar ya fara mamakin ƙaryar da yai saboda Farida.
Duƙunƙunewa ta yi ajikin bargo tana tsoron mi Sir Najeeb zai yi dan ta tabbata ya gane ita ta yiwa Sabreen wannan abu.
Yana shigowa ta sake duƙunƙunewa ta na rintse ido.

"Ki gayamin gaskiya mi ki ka sa ma ta?"

Ta yi shiru ba ta kulashi ba.
"Idan ba ki gayamin ba zan gayawa Dad ƙaryan da ki ka yi"

Ta ɗan buɗe idon ta ta leƙo shi yana tsaye yana kallon ta.

"Borkono ne, dakakken borkono na sa ma ta a bedsheet"

"You're a criminal Mrs Jibo, ya kamata a kama ki"

"Allah ya kiyaye"

Wucewa yai ya shiga banɗaki dan ya sake wanka...
Farida na ganin ya shiga banɗaki ta san ba fitowa zai yi da wuri ba ta yi wuff ta tashi ta fita daga ɗakin. Ɗakin Sabreen da ke ƙasa ta je ta cire bedsheet ta karkaɗe sannan ta juyashi baya ta shimfiɗa, filon ma ta ma sa haka sannan ta fito.

*(yau na ci yaji dayawa, hakan ya tada min ulcer na. That's d trigger for writing this scene😁. Ni ma daga yau irin na Farida zan na yi, zan dinga taro ulcer tun kafin ya tashi, saboda idan ya zo kar ya wahalar da ni😂)*

.......................

Su Daddy na zuwa aka duba jikin Sabreen wanda har ya feso da ƙuraje abinka da jar mace.  Magani aka ba su aka ce ta shafa. Mom ta karɓa ta shafa ma ta. Likitan cewa yai allergy ne ba komai ba.
Mom ta ce da sun koma gida za a chanja ma ta ɗaki tunda ta ce daga kwanciya a gado ta fara jin zafi da ƙaiƙayin.

Lokacin da su ka dawo gida ƙarfe shabiyu na dare ya wuce. Ɗakin Najma da ta ke sauka idan ta zo su ka wuce da ita. Mom ta je ta ɗebo ma ta kaya a wancan ɗakin da ke ƙasa.
Sai da su ka tabbatar ta kwanta a wannan gado lafiya kafin su ka bar ɗakin...

Farida ta yi bacci kafin su dawo amma Najeeb ya ji dawowar su, sai dai ko leƙowa bai yi ba.

Yau da asuba Najeeb ya fito daga wanka yana sa kaya sai ga siririyar tusa ta fito. Farida da ke shirin shiga banɗaki ta leƙo inda ya ke dan sarai ta ji tusan.

"Sir Najeeb ka ji abin da na ji kuwa?"

Yai gyaran murya ya ci gaba da saka belt ɗin da ya ke ba tareda ya kulata ba.

"Sir Najeeb fitar tusa na ji fa, kuma ba ni na yi ba. Ba ma irin warin tusa na bane"

Ɗagowa yai ya kalleta ran sa a haɗe.

"Ke wai bakin ki ba ya iya yin shiru ne?"

Ɓiiiit sai ga tusan ta kuma fitowa.

Ta kama baki tana faɗin "Lahaula! Sir Najeeb ashe kai ne. Ina ga basir ke damunka, ka nemi magani"

Hannu ya kai zai buge bakinta ta ja baya da sauri tana dariya. Sai da ta shiga banɗaki ta leƙo da kan ta ta ce "Sir Najeeb tusan ka irin ta yara. Kasan ance tusa kala uku ne akwai Ɓiiiit na yara, booooot na manya, alanrankiɗibobot na tsofi" 
Tana faɗin haka ta banko ƙofar banɗakin...

Ya na tsaye yana naɗa tie amma dariya ya ke ciki-ciki. Cikin zuciyar sa yana maimaita abin da ta ce. "Where on earth did she know all this" ya tambayi kansa.

Kafin ta fito ya riga ya shirya ya fita.  Lokacin da ya kai ƙasa ya haɗu da Daddy.
"Morning Dad"

"Morning ya jikin Aisha?"

"Da sauƙi" ya faɗa yana tuno abin da ya faru jiya.

"Allah ya ƙara ma ta lafiya, za ka koya ma ta mota ne ko za ka enrolling na ta a driving school? Ka ga ba daɗi Najdah na hawa mota ita ba ta da shi"

" Ehm Ehm..." ya rasa abin faɗa.

"Shikenan duk abinda ka yanke ya yi dai-dai"...

...................

Saboda abinda ya faru ranan Sabreen ba ta fita ba. Lokacin da Najdah ta dawo ne ta ke jin abinda ya faru a bakin Sabreen ɗin, saboda  ba ta kwana a gida jiya ba, gidan Uncle Sulaiman ta kwana.

Najdah ta tashi ta je ɗakin dan ta tabbatar da zargin ta. Sai dai Adama ta riga ta chanja bedsheet ɗin kuma an gyara ɗakin dan haka ba abin da ta gani.

Da ta dawo ta ce da Sabreen ta san wanda ya sa ma ta abu a gado. Sabreen ta zaro ido tana tambayar waye?...

...........

"Khalidah ban gane mi ya ke faruwa ba? Kin min alƙawarin zan samu wannan sakatariyar Najeeb ɗin amma daga dawowata ki ke min zancen banza wai Najeeb ya aureta. Ya aka yi haka? Ba kin tabbatar min plan ɗin mu zai tafi dai-dai ba. Zai koreta a aiki ni kuma na sameta"

" Alhaji matawalle ban san ya zan ma ka ba. Ba fa kai kaɗai ka ke jin zafin abin nan ba. Kai damuwarka ka kassara Najeeb ni damuwata na samu Najeeb. Kai buƙatar ka ta biya ka sa Najeeb ya rasa babban project wanda hakan ta jawo ma sa asara, ni kuma fa? Mai na samu banda ƙara haɗa Najeeb da sakatariyar sa"

"A'a Khalidah bayan kassara Najeeb kin min alƙawarin samun sakatariyar sa, Farida sunan ta ko?"

" Alhaji Matawalle ka fita a office ɗi na, ka bar ni da takaici da ƙuncin da zuciyata ke fama da shi"

"Kar ki kawomin zancen banza Khalidah, ba na neman abu na rasa"

"Ya zan ma ka ne? Ka je ka ɗauki Farida ma na idan ka isa"

"Haka ki ka ce ko" ya girgiza kai ya fita daga office ɗin.

Yakubu ya koma da baya lokacin da ya ga Alhaji Matawalle na shirin fitowa. Dama ya zo kawo wa Khalidah wa su takardu ne ya ji ƙarshen hiran na su. Jin sunan Farida ya sa ya fasa shiga office ɗin.

.......................

Wannan weekend ɗin da Aneesa ta zo ne ta lura da cikin jikin Maijiddah. Ba ta san lokacin da ta ce "Sweetheart yaushe wannan yarinyar ta samu ciki?"
AbdulWahab bai kulata ba ya cigaba da cin abincin da ya ke yi.

"Sweetheart magana fa na ke"

"So ki ke na bayyana mi ki abinda mu ka yi ta samu ciki? ko so ki ke ki san sau nawa mu ka yi kafin ta samu ciki?"

"AbdulWahab zai kai 4 months fa"

"Allah ya sauke min ita lafiya amin"

"Abinda ma za ka ce kenan? Bayan ka gama cin amana ta da yarinya ƙarama, wanda a haife ka haife ta har kana da bakin cewa Allah ya sauketa lafiya"

"Ya nuna ina da lafiya kenan, kuma kin ga ina da damar ƙaro irin Hauwerh biyu idan ina so, kin ga in shiga nan in shiga nan"

Aneesa ta cillar da cokalin hannun ta.

"Wallahi ba zai yiwu ba. Ba ka isa ba AbdulWahab"

"Ki cigaba da aiki a Abuja, zan cigaba da aiki a nan kuma da idon ki za ki dinga ganin sakamakon ayyuka na ma su kyau da tarin lada.  Alhamdulillah da na kasance musulmi, na ke da damar auren mace fiye da ɗaya. Kin ga musulunci ya min rana"

Juice da ke glass cup a gaban ta ta ɗauka ta watsawa AbdulWahab tana zage-zage. Bai ƙara cewa komai ba ya tashi ya bar wajen.

"Ka dawo ma na, ka dawo mu ƙarasa maganar, macuci kawai"...

Wannan weekend ɗin gaba ɗaya cikin faɗa su ka yi dan AbdulWahab dena shiga sabgar ta ya yi. Tana komawa Abuja ta sanar da Mama Maijiddah na da ciki, ga mamakin ta sai Mama ta ce "Allah ya raba lafiya"

"Mama kin ji mi na ce kuwa? Su baby da Alizah su na gab da samun step siblings"

"Na ji kuma na gane, idan kina son haihuwan ke ma sai ki dena planning  ki koma tara 'ya'ya rututu kamar Kaza"

Aneesa ta rasa bakin magana, dan inda ta dosa Mama ba ta bi nan ba.

A ranan da ta je office ta nemi a maida ita Lagos ko kuma ta ajiye aiki. Su ka ce za su duba.

.......................

Da ke tun ƙarfe ɗaya Najeeb ya fita kuma ya riga ya ce ma ta ba zai dawo ba sai yamma shi ya sa ta tattara ta fito dan ta koma gida. Tana fitowa ta hango Sabreen da wassu police biyu su na tahowa. Mamaki ya kamata ta ɗan tsaya dan ta yi gulman me ke faruwa.
Sabreen ta nuna ta tana faɗin "she's the devil, arrest her"

Farida ta zaro ido " arrest me for what?"

"Ran ki shi daɗe za ki bimu zuwa station mu mi ki wassu tambayoyi"

"Ƙwal ubanchan, na bi ku station a dalilin me. Kun san ko wacece?"

Ɗaya police ɗin ya kwantar da murya ya ce " dan Allah ki yi haƙuri mu je, mu ma daga sama aka samu"

Sabreen sai hararanta ta ke.

"Shikenan barin kira miji na" ta fito da wayarta daga jaka ta fara kiran Najeeb sai dai da ke inda su ke ba service sai bai shiga ba. Jikin Farida yai sanyi, ta tura ma sa text kawai ta bi police ɗin nan...

Bai duba wayar sa ba sai ƙarfe biyar da rabi bayan sun dawo kamfani. Yana duba missed call ya ga har da numbar Farida ga kuma text ɗin ta. Ya buɗe text ɗin ya ga ta rubuta *Sabreen ta arresting ɗi na*

"Arrest?" Yai saurin kiran numbar Faridan ya ji ta a kashe. Da sauri ya fara dialling numbar Anas ya na fita daga office ɗin da gudu...

Shi da Anas su ka isa gida dan numbar Sabreen ɗin da Najdah ta turo mu su an ƙi ɗaga kiran su.

Hankali kwance su ka samu Sabreen tana zaune a falo tana cin apple.

"Where's she?" Ya daka ma ta tsawa

" who?"

"Dont be stupid Sabreen, where is she?"

Juyar da kai ta yi gefe ba ta amsa ba.
Ƙarasawa yai wajen ya fincikota yai waje da ita Anas ya bi bayan sa...

............

Tun da su ka shiga mota ya ke faɗa abin mamaki Sabreen ta ce ba za a fitar da Farida ba saboda abin da ta ma ta...

'Yan station ɗin ma sai da su ka san sun taɓo matar babban mutum. Tun da su ka shiga Najeeb ke ta masifa. Anas ne ma ya ke ƙoƙarin bashi haƙuri dan kar a samu matsala a wajen.

Ba'a jima ba aka taho da Farida. Yana ganin ta ya ƙarasa wajen ta da sauri. Ya riƙe hannunta kawai sai ta faɗa jikin sa ta fara kuka.
Duk wani formalities Anas ne ya tsaya zai yi, dan Najeeb kan jan hannun matar sa yai su ka bar wajen. Sabreen ta bi bayan su tana faɗin ba zai yiwu Farida ta tafi haka ba bayan abinda ta yi ma ta. Najeeb bai kulata ba har su ka isa bakin mota. Zai taimakawa Farida ta shiga Sabreen ta riƙe ma sa riga, ta fara kukan munafurci.

"Noory she wanted to kill me, ita ta sa min yaji a gado jiya. I almost died Noory"

Bai yi yunƙurin yafce hannunsa daga riƙon da ta ma sa ba illa matsawa yai kusa da Farida ya ɗan sukuyo dai dai saitin fiskarta. Ba tareda wani tantama ba ya haɗe bakin su. Farida ta ƙwalalo ido saboda mamaki da shock da ta ji lokaci guda.

Sabreen ta sake rigan Najeeb tana kallon yadda Najeeb ke kissing Farida zuciyarta na tafarfasa, ji ta ke kamar zuciyar zai bulluƙo ya fito.

Farida ta yi saurin janye bakin ta saboda tunowa da ta yi a public place su ke. Da rinannun idanun sa da su ka ƙanƙance ya ce "kiss me"  ba ta san ya akayi ta jefar da kunyar ba kawai ta tsinci kan ta da haɗe bakin su not minding a inda su ke...

# Team Farida
# Team Najeeb
# Team Sabreen

Ina sauraron comments ɗin  ku.*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣3️⃣0️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900*



Murmushi kawai ta ke yi tunda su ka fara tafiya. Idon ta na gefen titi  amma hankalin ta ba a titin ya ke ba. Har yanzu tana jin  taste ɗin zaƙin bakin sa a nata bakin. Ba ta taɓa sanin haka kiss ke da daɗi ba sai yau. Lokacin su na soyayya da Lukman ya taɓa kissing hannun ta da goshi amma banda lip to lip kiss. Shi kam Rayyan ba su taɓa irin haka ba, Rayyan ya na tsoro da shakkar Farida shi ya sa ko hannun ta bai taɓa riƙewa ba sai dai ko a rashin sani.
Yau ta samu first kiss ɗin ta, kuma da Sir Najeeb, Sir Najeeb fa. Ta sa hannu ta rufe bakin ta saboda tsikar jikan ta da ya tashi lokacin da ta tuna abinda ya ce "kiss me".

"Did they hurt you?"

Ai ta tafi duniyar tunani ba ta ma ji abinda ya ce ba. Duk wani cin mutunci da ta shirya  za ta yiwa Sabreen lokacin ta na cell ta watsar da shi. Ƙwaƙwalwarta ba abinda ya ke tunowa sai wannan moment ɗin.

Chan ƙasan zuciyar sa ya ke neman dalilin da ya sa ya kissing ɗin ta amma ya rasa. Chan ya baiwa kan sa amsa da Sabreen. Yes ya yi haka ne saboda Sabreen, saboda ta gane cewa he's over her now. Amma must he resort to kissing her? Yanzu sai ta rena shi. Wata zuciyar ta ce but it was the best kiss you ever had. Ko dan ya jima bai yi kiss ba ne, dama da Sabreen ne kawai, no one else. First kiss na shi in 8yrs felt different. Kaman wani ƙaramin yaro haka ya lashe lips ɗin sa da harshe.  Garin haka ma saura kaɗan ya buge wani mai Keke.

Har su ka isa gida ba wanda yai magana. Farida ce ta fara shigowa dan ta fita ta bar shi a mota. Tana tafiya tana jin ta a sama fiskar ta ɗauke da murmushi.

Najdah ne da wata tsohuwa a falon lokacin da ta shigo. Ba ta ma lura da su ba sai da tsohuwar ta ce "amarya lafiya?" Farida ta juyo sai ta ga tsohuwar duk da kuwa kuɗi sun ɗan ɓoye tsufan, amma kuma a yadda ta gan ta za ta haifi Daddy.

Ta yi saurin ƙarasawa wajen ta ta tsugunna "Hajiyata dan Allah ki yi haƙuri ban gan ki ba ne"

"Na ga alama ai, kin tafi birnin soyayya ko. Ina angon"  kafin ta ba ta amsa sai ga Najeeb ya shigo.

Yana ganin Hajiya Mama ya washe baki " tsohuwa yaushe a gari?"

Yana ƙarasowa wajen ta ta ɗauki sandarta ta ɗaga sama za ta kwaɗa ma sa ya ja baya da sauri.

" ke fa tsohuwa kin dawo kenan za ki fara cin zalin mutane"

"Ungo na ka Najeebullahi, tun jiya na dawo amma shi ne ba za ka kawo min amarya na gan ta ba"

"To ke kiji da ƙafar ki ma na, amma sai shegen yawo"

Farida dai kallon Najeeb da Hajia Mama ta ke da su ke dramar su na Kaka da Jika. Najeeb was jovial amma ba kaman tsakanin sa da Mom ba wanda tun zuwan ta abin ke ɗaure ma ta kai.

Hajia Mama ta kalli Farida ta ce "kin ga mijin kin nan ke ce rufin asirin sa. Haka yai ta yawo ƙaton tuzuru da shi, sai da Allah ya kawo ki"

Farida ta yi murmushi.

"Sai ki kula da shi sosai dan ɗan duniya ne"....

Ta fito daga wanka bayan sallar Isha ta fara jin hayaniya a ƙasa. Ba ta tantance ko muryan su waye ba ne amma daga yadda maganar ta ke haɗakar larabci da turanci ta san ba zai wuce Sabreen ba ne...

"Big B mi ya sa ka ke bin bayan ta, kai kan ka ka san ita ta yi wannan abin and she needs to be punished for that"

" walau ita ta yi walau ba ita ba, dukkan ku biyu babu wanda ya ke da ikon arresting ɗin ta, especially you Sabreen. Ina so ki nisanci iyalina"

"Big B amma..."

"Najdah!" Ya daka ma ta tsawa. Kallon shi ta yi sannan ta haura sama da gudu.

Ya juyo ya kalli Sabreen ya ce "next time ki ka yi ƙoƙarin taɓa lafiyar mata ta, i wont take it lightly"

Cike da tuƙuƙin baƙin ciki ta ce "you dont love her, do you"

Haɗiye miyau yai sannan ya ce "go back to Hollywood you dont belong here"...

Ɗakin Najdah ya fara zuwa Lokacin da ya haura sama, amma ta ki buɗe ma sa ƙofa. Dan haka ya juya ya shiga ɗakin su.

Yana shiga ɗakin ya gan ta bakin gado tana kuka.  Jikin sa yai sanyi ya ƙarasa wajen ta yana tambayar minene dan a tunanin sa ko a cell ɗin an mata wani abu ne.

"Mi ya faru?"

Tana kuka tana jan majina ta ce "Baba ya rasu"
Kan sa ya ɗaure dan Anas ya taɓa ce ma sa Farida marainiya ce to yanzu kuma wani Baban ne ya rasu.

"Your father?" Ya sake tambaya.

"Kaka na ne"

Ya jawota jikin sa yana lallashin ta.

"Yanzu Ummi ta kira ni, dan Allah Sir Najeeb zan je Jos gobe"

Ya gyaɗa kai ya ce "its ok"

Sun jima tana kwance a jikin sa tana hawaye tana faɗa ma sa kyawawan halayen Baba.  Bai bar wajen ta ba sai da ta yi bacci, lokacin kusan sha biyu saura na dare. Da ya gyara ma ta kwanciya sannan ya je yai wanka ya shirya cikin kayan bacci sannan ya zo ya kwanta amma kafin yai bacci sai kusan ƙarfe biyu. Tunani ya cika ma sa kwanya.

Washe gari da sassafe ta shirya, ya sa Iliya ya kaita har Jos. Lokacin da motar ta bar cikin compound ɗin ƙarfe shida da rabi na safe. Yana shigowa cikin gida Daddy ya kira shi, da ya je tambayar sa yai gameda abinda ya faru jiya dan ya ji maganar a wajen Mom.
Bayan ya ma sa bayani sai Daddy ya ce " ka yi katanga tsakanin ka da Sabreen, ban hana ka ƙara mace ba idan ka ga ba za ka iya zama da Aisha ita kaɗai ba, amma ka sani. Ba zan taɓa amincewa da Sabreen a matsayin suruka ba. Ba wai dan ta rabu da kai ta dawo ba, sai dan ba zan bari ka haɗa zuri'a da macen da zata iya gurɓata ma ka rayuwa ba. Ina sane da lokacin da Mahaifiyar ka ta ke kuka kullum saboda Sabreen ta na shirin auren wani kafiri ɗan ƙwallon ƙafa har ta ke sukan addinin musulunci da ya hana aure tsakanin kafiri namiji da mace musulma. A hira da aka yi da ita shekaru uku da su ka wuce, cewa ta yi sallah na takura ta, wai anata abu ɗaya kullum ba hutu. Wannan ba macen aure ba ne. Idan har ka nuna za ka auri Sabreen to za ka yi nisa da ni da iyalina. Za ta zauna a nan ne kawai saboda alaƙa ta jini da su ke da shi da Nabilah amma bayan nan ba na so wani abu ya kuma shiga tsakanin mu"

Najeeb ya gyaɗa kai.

"Ya maganan gidan ka, anyi interior decoration ɗin?"

"An kusa a gama"

"Ok Allah ya nuna ma na"...

Yau dai throughout a office jin sa ya ke wanni iri. Musamman idan ya zo fita ya ga ba ta kan kujeran ta.

Da ke Jummu'a ne kuma ranan hutu ne an haɗa ƙwarya-ƙwaryan party amma bai iya tsayawa a wajen ba. Anas ne ya tsaya ya wakilce shi, daga sallar jummu'a gida ya wuce yana jin jikin sa ba daɗi. Ba wai ba shi da lafiya ba ne amma kuma jikin sa is weak.
Yana shiga ɗakin sai ya ji ɗakin ya ma sa faɗi kaman ba ɗakin sa ba, there's something missing. Ƙanshin ɗakin ya sauya tun zuwan Farida saboda haɗuwar turarukan sa da na ta kalolin turaren. Har ta fasalin ɗakin ya sauya. Ya tuna ranan da ya shigo ya ga tana chanja arrangement na wasu abubuwan a ɗakin.
"Sir Najeeb ɗakin ka yana buƙatan polish"

Ya tuna yadda yai ta gwaleta yana cewa ta hargitsa ma sa ɗaki.

Ya na shiga wajen closet ya tuna ranan da ya ke chanja kaya ta shigo lokacin gajeren wando na jeans ne a jikin sa ba riga.

" Sir Najeeb, idan ka na gida sai ka yi ta sa gajerun wanduna kaman wani ɗan firamare"

Yai murmushi tunowa da yai da kalolin tusa da ta lissafto ma sa ranan...

Lokacin da ya gama abubuwan da zai yi yana kishingiɗe a kan gado ya ji gadon ya ma sa daban. Tun da ta zo kullum za su kwanta akwai pillow a tsakanin su, jiya ne kawai su ka kwana ba pillow.
A hankali ya sa hannu ya fara shafa gefen da ta ke kwana wanda ya ke empty yanzu.  Ya tuno ranan farko da za su kwana a kan gadon faɗan da su ka yi, daga ƙarshe da tunanin kissing ɗin da su ka yi jiya bacci ya tafi da shi.

Washe gari da safe Daddy ya ce su je su yiwa Baffa Musa ta'aziya. Tare su ka je a chan ne ana taɗi wanda tsakanin Daddy da Baffa Musan ne dan shi banda ya haƙuri da ya ce bai kuma cewa komai ba. Cikin taɗin su Baffa Musa ke kawo rayuwar da Farida ta yi. Daga wannan gida zuwa wannan gida kafin daga baya ta zauna a wajen Kakannin ta.

Daddy ya tambayeshi ko miyasa bai ɗauki Farida tun da wuri ba. Baffa Musa ya ce "Hmm Faridan, tun tana yarinya ta ke da baki. Ko hutu aka kawota sai ta yi ta ƙorafi, Baffa garin ku akwai zafi, ba zan zauna ba"...

Lokacin da za su tafi Baffa ya ce da Najeeb " ka kula min da ita dan Allah. Ka da ranan gobe Ubanta ya ce ban riƙe amanar tilon 'yar sa ba"

Najeeb ya ce Insha Allah...

........................

Yau sati ɗaya kenan da ba ta nan. Cikin sati ɗayan nan ya rasa ganewa kan sa. Bai ma cika son fita ba, dama wajen aiki ke ɗebe ma sa lokaci to yanzu ana hutu. Sabreen washe garin da Farida ta tafi itama ta yi tafiya, bai san inda ta je ba kuma bai damu ba dan shi idan ta tashi ne to kar ta ƙara dawowa.

Yau da ya je wajen Hajia Mama ne ta ke cewa ya kira ma ta Farida ta ma ta ta'aziya.

Kwana uku da Farida ta yi a Jos ta yi su cikin rashin jin daɗi, na farko ga rashi da su ka yi, na biyu kuma Sir Najeeb da ya shareta. Kullum da tunanin sa ta ke kwana ta tashi, amma shi ko text bai ma ta ba balle ya kira ya ma ta ta'aziya. Duk da kuwa ranan da ta taho ta tura ma sa text akan sun isa lafiya amma ko reply bai yi ba. Wasu lokutan har mafarkin suna tare ta ke, haka kawai tana zaune sai ta ji kaman muryarsa a kunnen ta yana faɗin "kiss me" har tunanin ko ta fara hauka ta ke yadda waɗannan kalmomin biyu ke sa ta jin wani nishaɗi da farin ciki...

Tana ganin wanda ya kirata mamaki haɗe da wani farin ciki ya mamayeta, sai da wayar ta kusa katsewa sannan ta ɗauka.

"Sir Najeeb shi ne sai yau?"

"Aishatu, kuna lafiya ya haƙuri?" Muryan Hajia Mama ya doki kunnen ta maimakon muryan Najeeb...

Hajia Mama na kashe wayan ta kaiwa Najeeb sanda.
"Ashe ko ta'aziya ba ka je mu su ba. Kakan matar ta kan"

"Kai Tsohuwa, ba munje gidan uncle ɗin ta ba. Miye sai mun je har Jos. Will that bring back the dead?"

Hajia ta sa ke ɗaga sanda yai gefe da sauri yana dariya...

Kaman yadda Hajia Mama ta nema kuma ta sa Daddy ya ma sa magana dole ya shirya zai je Jos. Shi sau ɗaya ya taɓa zuwa garin kuma aiki ne ya kaishi.

Ya fito kenan ya tarar da Anas da Najdah a falo su na magana.
"Kai ba na son takurawa fa, she's still in school" Najeeb ya faɗa yana hararan Anas.

Anas ya ce " an gaya ma ka ni irin ka ne da sai na zauna har 35yrs. Ai ni kafin watan shidan sabuwar shekaran nan zan angonce"

"Shege, to Baby sai ta ƙare karatu tukunna"

"Wallahi ba ka isa ba, ka san tun yaushe mu ke shan ruwan kanwa kuwa"

"Ɗan iska, to ka bi ni a hankali ko in hanaka, dama Musty yana gaba dani saboda na hana shi, ka ga idan ka yi wasa sai na bashi ita"

"Kai na a ƙasa babban yaya, mu na neman tubarrakin ku"...

Sai da su ka jima su na wasa da dariya kafin daga baya bayan Najdah ta bar falon Anas ya shiga bayanin abinda ya kawoshi.

"Najeeb, Farida ita ke da gaskiya da kai da kamfani you owed her apology"

Najeeb ya gyara zama yana sauraron sa.

"Khalidah da Alhaji Matawalle su su ka kitsa komai. The money from VESTAC inc. Alhaji Matawalle ne ya sa aka tura   supported by Khalidah. Shi ya shirya yadda za a sace ma ka takardun zanen ka a kuma ɓata modelling da ka yi. On the other hand kuma Khalidah ita ta kawo shawaran a framing Farida. Duka evidences da mu ka haɗa yana nan" ya miƙa ma sa wata ƙatuwar envelope.

Idon Najeeb ya rine yai ja tsanar Khalidah da Alhaji Matawalle na ƙara shiga ran sa.

"Kai ka san wani mataki ko hukunci za ka ɗauka idan aka koma aiki ranan monday" ...

..............
Ba dan ya riga ya shirya tafiya ba da ba abin da zai sa ya tafi. Ƙusan ƙarfe uku ya isa Jos, address ɗin da Yakubu ya bashi ya bi, da tambaya kuma ya isa har layin su. Bai gama shan  mamakin layin ba sai da ya isa gidan. He cant believe a irin wannan gida Farida ta yi rayuwa. Ba wai dan bai saba ganin gidaje haka ba a'a sai dan yadda Farida ke gudanar da rayuwar ta with boldness and cofidence, ba ta shayin shiga ko'ina. A ko yaushe ji ta ke dai-dai ta ke da kowa, duk daraja ko kuɗin ka kuwa.

Yaro ya kira ya ce a ma sa magana da Farida dan tun a bakin layi ya ajiye mota saboda mota ba ta shiga layin.

Ana yiwa Farida kitso yaro ya shigo wai ana sallama da Anty Farida.

"Ni kuma? Waye?"

"Bai gaya min ba"

"Ya yake" Farida ta sake tambaya tana sawa ranta kwaɗayin ya kasance Sir Najeeb ne ya zo.

Yaron ya ce " fari ne, dogo, kaman balarabe ya ke amma ya iya Hausa" ai yaro bai gama bayani ba ta tashi daga gaban Umma Binta ƙanwar Ummi da ke ma ta kitso.

"Ka je da gudu ka ce ma sa ina fitowa yanzu"

"O'o amaren zamani kenan, Farida wannan zumuɗi haka"
Ai ba ta ji me Umma Binta ke cewa ba ta riga ta shige ɗaki za ta ɗau hijabi...

Ya bawa ƙofan gidan baya yana tsaye hannayen sa duka biyu su na cikin aljihu, hankalin sa ya tafi wajen wassu yaran Birom da ke wasa a ta wajen kwata yana mamakin yadda yaran ba sa ƙyanƙyamin wajen.
Yana sanye da baƙar shirt da baƙin hoodie jacket sai baƙin jeans.

"Sir Najeeb" muryan ta ya doki kunnen sa. A hankali ya juyo yana kallon ta, ba ta wani chanja ba sai dai idon ta ya ɗan nuna rama may be saboda kuka ne dan ya san ba ta wasa da abinci.

"Ashe za ka zo, shi ne ko ka faɗa min. Mu shiga ciki"

Sai da ya ɗau minti ɗaya ya na kallon ta kafin ya bi bayanta su ka shiga gidan...

Da ke kwana na tara kenan da rasuwan duk an watse sai iyalin sa kawai. A daddafe ya gaisa da su. Kusan awa ɗaya yai a gidan saboda yadda 'yan uwa da maƙota ke zuwa gaida mijin Farida wanda yawanci gulma su ke zuwa saboda su ga mutumin da ya sa aka fasa aurenta da Rayyan, su ga ya ya ke. Sai dai kowa ya zo da Masha Allah ya ke tafiya baki buɗe. Sun ga kyau, sun ga kuɗi, sun ga aji, sun ga ƙasaita...

Lokacin da zai tafi bayan ta raka shi wajen motar sa ya ce " za'a koma aiki monday yaushe za ki dawo?"

"O'o ni Aisha Farida, dan aiki kawai za a neme ni. Ni kam dole idan na koma a chanja min matsayi ya kamata a upgrading ɗi na, na bar matsayin sakatariya"

" ki na son ƙarin matsayi ne?"

"Haba Sir Najeeb wa ya ƙi cigaba a duniya"

Bai san ya ake zuwa gai da sarakai ba shi ya sa bai zo da komai ba. Ya dai bar musu dubu ɗari a gefen  ɗrinks ɗin da su ka kawo ma sa wanda ko taɓawa bai yi ba...

Har motar sa ta ƙule Farida ba ta bar wajen ba. Tana ƙissima abubuwa dayawa a ranta. Zuwan Najeeb ya sa Najeeb ya ƙara samun wani matsayi na daban a zuciyar ta...*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣3️⃣1️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900*

*yau na san team Najeeb sai sun min bulala😂. @team leader a ajiye tissue a kusa*

Yana hanya ta kirashi lokacin koma fita daga Jos bai yi ba. Ya saƙala bluetooth ya amsa kiran.

"Sir Najeeb shi ne har da ɗawaiyina haka. Mun gode Allah ya ƙara buɗi. Allah ya kai ka lafiya"
Amin kawai ya ce ya kashe kiran.

Da ya isa Kano yana so ya kira ta amma ya ka sa. Sai ya ɗauko wayar zai danna numbar ta sai ya fasa ya ajiye, ana huɗu da yai haka sai ga text ɗin ta ya shigo tana ma sa ya hanna da fatan ya isa lafiya.
"Na isa" kawai ya daure ya rubuta ya ma ta reply da shi. Maimakon ta haƙura a haka sai ta kuma turo da wanni text ɗin.
"Sir N mi zan taho ma ka da shi? ina son zuwa Wase gobe"

Bai san ina ne Wase ba, dan haka ya minimizing wayar ya browsing sunan nan ya gane wata ƙaramar hukuma ne a Jos.

Ya ma ta reply da "ok"

Ta sake turo wani saƙon " Sir N ba ka faɗi abinda zan kawo ma ka ba"

Ya na so ya ajiye wayar ya shareta amma zuciyar sa ta hanashi

"Kan ki" ya tura ma ta ba tareda ya gama tantance ma'anar faɗin hakan ba.

"Kan kifi? Sir N kan wani irin kifi"

Ganin reply ɗin ta ya sa shi murmushi. Ya ɗan jima kafin ya tura ma ta "Mrs Jibo sleep"

Good night kawai ta sake turowa daga nan ba ta kuma turo da wani saƙon ba. Shi ma ya ajiye wayar sa gefe ya kwanta.

.......................

Safiyar Sunday ya aika ma ta da Iliya driver akan ya je ya ɗauko ta. Ita kam tana chan tana kan haɗa kayan tsaraba da za ta zo da shi. Sai da Iliya ya kusa isa cikin Jos sannan ya kira ta ya ce ya kusa isowa.
Wani matsayi ta ke kuma hangowa kan ta idan ta koma Kano. Ya sa an kawota da mota ya kuma turo ma ta driver ya dawo da ita. Wannan karramawar sai Mrs Jibo ai...

Lokacin da su ka isa gida ana kiran sallar maghrib. Iliya ya je ga kira Friday su ka shiga da buhun dankalin turawa da ta zo da shi da kuma wata ƙatuwar jakan ghana-must-go.

Ɗakin Mom ta je dan ta gaidata ta samu ba ta nan, ta wuce ɗaki ta shirya ta yi sallar la'asar da magariba...

Ƙarfe tara ta sauko ƙasa dan ta nemi abinda za ta ci, ba komai a dining ɗin hakan ya sa ta shiga kitchen shi ma wayam. Yunwa ta ke ji dan haka ta tsaya ta girka noodles da soyayyan ƙwai, ta fito ɗauke da plate ɗin shi kuma Najeeb ya shigo.

"Sir Najeeb" ta kira sunan sa. Juyowa yai ya ganta tsaye riƙe da plate da cup

Sai da ya gama kallon ta daga sama har ƙasa sannan ya juya ya tafi. Ta bi bayan sa da baki buɗe.

A dining ta zauna ta ci abincin ta dan idan ta haura sama za ta ji ƙiwuyar saukowa, sai da ta gama ci sannan ta wuce ɗaki.

"Sir Najeeb irin ba ka ji daɗin ganina ɗin nan ba, ko sannu da zuwa babu"
Bai kulata ba hakan ya sa ta gane akwai abinda ke damun sa dan bayan bai kulatan ba fiskar sa ya nuna yana cikin damuwa.

"Sir Najeeb ba ka da lafiya ne?"

"Please stop talking" abinda ya iya faɗa kenan ya gyara kwanciya a kan gado.
Tabbas akwai abinda ke damun shi dan Najeeb ba ya bacci da wuri, sannan duk rintsi sai ya yi wanka ya sa kayan bacci kafin ya kwanta.

Kaman yadda ya buƙata ɗin, shirun ta yi tana tunanin ko me ke damun shi.
Har ta kwanta Najeeb bai tashi b, ba kuma baccin ya ke ba dan idon sa a buɗe lokacin da ta leƙa shi...

Washegari da ta shirya ta fito ne ta haɗu da Tasallah a kitchen wanda ke shaida ma ta Mom ba lafiya an ba t gado.
"Ayya ashe shiya sa jiya da na dawo na ji gidan shiru. Ya jikin ta?"
Tasallah ta ce da sauƙi. Maimakon office da ta yi niyyar zuwa sai ta wuce asibitin lokacin Iliya ya kawo Adama za ta ɗauki wassu kayan buƙatu sai su ka tafi tare.

Ta yi mamakin yadda Mom ta faɗa haka. A wajen Najdah ke cewa " tunda yanzu ke ki ke juya Big B sai ki sa ya zo ya ga Mom. Kin wani yanko ƙafa kin zo irin son a sani ɗin nan"

Farida ta kalli Najdan sannan ta kalli Mom da ke kwance tana bacci.

"Na san da cewa ba kya son ganina tareda yayan ki, amma ki sani shi ya kawo ni gidan ku ba ni na kawo kai na ba. Tun farko-farkon zuwa na ki ke ta ƙananun magana akai na, ban tanka mi ki ba. Kar ki sa na kalle ki da idon Aisha Farida dan ba za ki ji daɗi ba. Ki bini a hankali mu tafi a yadda mu ke yanzu"

Najdah ta yi tsaki, ta ɗau waya ta fara latsawa.

Farida ta fice daga ɗakin gudun kar ta fara masifa ta tada Mom daga bacci. Amma tabbas za ta ware lokacin Najdah nan ba da daɗewa ba...

Kai tsaye Najeeb constructions ta wuce sai dai da ta je office ɗinta kama baki ta yi saboda chanji da ta gani, office ɗin ta da na Najeeb ya koma kusan guda ɗaya, maimakon gini da ke tsakanin su yanzu wani tinted glass ne ya raba su wanda daga office ɗin sa yana iya hango komai a na ta office ɗin amma ita kuma ba za ta ga na sa ba.

" ba dai wannan Sir Najeeb ya ke nufi da matsayi ba"

Ba ta gama zama ba Najeeb ya shigo ran sa a ɓace. Yanzu ya fito daga board meeting.

"Sir Najeeb ashe Mom ba lafiya shi ne ba ka gaya mun ba"

"Get back to work Mrs Jibo"
Gwiwanta yai sanyi ba dai duk wani zumuɗi da zaƙalewan da ta ke yi a kan sa duk na banza ba ne.

"Noory" muryan Sabreen ya dawo da ita daga tunanin da ta ke.

Murmushi Sabreen ta yi ganin Farida a wajen. Da alama itama daga wajen da Najeeb ɗin ya fito ta fito.

Ganin Sabreen ya sa ta ma tuna da zancen ta, ita harga Allah ta manta da wata Sabreen.

"Noory, you are just taking it personal, i'm here to work"

"Kar ki sake kirana da wannan sunan. Here and anywhere else i am Najeeb to you"

Ta ɗan ji haushi saboda a gaban Farida ya faɗa. Amma ta dake ta ce "fine"

Farida ta fice daga office ɗin ta koma na ta duk da ta san daga inda ta ke su na kallon ta.

Wani yanayi ta tsinci kan ta ciki. Sabreen ta fara aiki anan, mi hakan ya ke nufi? Kenan watarana Sir Najeeb zai aiketa wajen Sabreen ko Sabreen ɗin ta ba ta saƙo dan ta kaiwa Sir Naheeb. Ba zai yiwu ba, dole ta ajiye aikin nan. Ba za ta yi aiki tana ƙarƙashin Sabreen ba, wannan cin fuska ne.

"Congratulations 'yar uwa. Finally gaskiya ta fito" muryan Anas ya doki kunnen ta.

"Wani gaskiyar?" Ta tambaya tana ƙoƙarin ɓoye damuwar ta.

Zama yai zai ma ta bayani sai ga Sabreen ta fito.

Tana ganin su ta yi wani murmushi sannan ta juya tana catwalking ta fita.

Anas ya juyo ya kalli Farida wanda itama bin bayan Sabreen ɗin ta yi da kallo.
Ya ce "asirin wanda su ka kitsa mi ki sharri ya tonu. Gaskiyar zance ta fito"

"Haba! Yaya na wani ɗan Alatsinen ne ya ke son ganin baya na"

"Wallahi Khalidah ce"

"Ban yi mamaki ba dan za ta rina"

Nan ga shiga labarta ma ta yadda aka yi gaskiya ta fito.
Da kotu za su shiga amma an settling case ɗin tsakanin Kamfani da su saboda Alhaji Matawalle ba ya so a je kotu domin ya na siyasa kuma ya na son fitowa takaran senator. Na biyu kuma Alhaji Tukur mahaifin Khalidah ba ya son wargaza alaƙar sa da Najeeb, 8% shares na shi a kamfanin shi ya san kuɗin da ya ke samu, shi ya sa shima ya zaɓi teburin sulhu.

Alhaji Matawalle zai biya kamfani taran miliyan ishirin ita kuma Khalidah za ta biya Farida miliyan biyu.

" 'yar uwa mun yi kuɗi fa. Dan Allah ayi kason da mu"

Farida murmushi kawai ta yi dan ba wannan ba ne damuwar ta.

Ranan duk wani ɗokin dawowa Kano da ta yi ta ji Kanon ya fita ma ta a kai. Da yamma bayan ta dawo Baba Sabuwa ke kiran ta akan 'yan uwan Najeeb sun kawo lefen ta yau da safe. Su kan su ba su san da zuwan ba ko karramawar kirki ba a mu su ba.
Farida kin ga kaya ki godewa Allah gaskiya domin an zuba dukiya a lefen ki. Yanzu ya za ayi? Za a kawo mi ki shi chan gidan kun ne ko ya?

"Baaba Sabuwa duk yadda ku ka yi"  ta faɗi hakan ne saboda ko kaɗan maganar lefen bai sa ta ji raɗaɗin da ta ke ji ya ragu a zuciyar ta ba...

........................

Yana shigowa Daddy ya kirashi tambayar sa yai ko ya je ya duba Mom ya ce bai je ba.

"Yanzu Najeeb ka kyautawa kan ka, da girman ka da ilimin ka amma ba za ka kyautatawa mahaifiyar ka ba. Duk abinda ta yi ma ka bai kai ace tana kwance a asibiti yau kwana uku ka kasa zuwa ka dubata ba. Najeeb tsinuwa ka ke nemawa kan ka?"

Maganganun Daddy su na shiga su na fita ta ɗaya kunnen ne, saboda ba jin su ya ke ba hankalin sa ya tafi wani wajen. Jini kawai ya ke gani malale a ƙasa ga kuma gawar Aisha...

Daddy ya gama ma sa wa'azi sai Najeeb ya tashi ya fita ba tareda ya ce komai ba...

Tuƙi ya ke amma zuciyar sa na tuno ma sa abun da ya faru shekaru da su ka wuce. Duk da yanzu ya girma kuma ya san ƙaddarar Aisha ne ta zo da haka amma wannan trauma ɗin da ya dasu a ransa tun yana yaro ya ƙi sake shi...

***

Cikin Aisha na wata takwas abin ya faru. Immediately Adam ya saki Nabilah ta tattare yaranta ta bar ma sa gida. Sai dai hakan bai sa Najeeb ya dena zuwa wajen Aisha ba. Idan ya taso daga makaranta chan zai wuce sai dare ya dawo. Mom ta ma sa faɗan amma baya ji.
Ana haka sai ɗaya daga cikin ma su kula da Aisha ta yi tafiya saboda Maman ta da ta mutu. Ganin haka ya sa Najeeb ya dawo wajen Aisha da zama duk da kuwa akwai Mrs Beverly tareda ita. A kwana na uku da ya koma wajen Aisha, Mom ta zo da ƙarfin tsiya ta tafi da shi gida ta hana shi zuwa wajen Aisha. Abu da renon turawa sai ya fara maida ma ta magana akan ba ta isa ta hana shi fita ba, Ya fita da gudu.
Mom ta nemi restraining order daga kotu akan ba ta yadda ɗan ta ya je gidan Aisha ba saboda tana tunanin Aisha za ta ma sa lahani. Da ke Najeeb under 18 ne sai ya zama dole yana ƙarƙashin kulawar iyayen shi. Ranan da letter ɗin ta fito haka Mom da jami'an kotu su ka je su ka ɗauko Najeeb tareda faɗawa security ɗin gidan ko da wasa kar ya bari Najeeb ya shiga gidan.

Daren ranan yai wani mummunan mafarki akan Aisha ta mutu hakan ya sa da safe ya kira Daddy da ke Belgium a kan ya sa baki yana son zuwa wajen Aisha.
Mom ta ce indai ya na America yara za su zo wajen sa amma Yaran ta ba za su je wajen Aisha ba. Da Najeeb ya fita school bai je ba sai da ya fara biyawa wajen Aisha ya ga tana lafiya kafin ya tafi.
Yammacin ranan da ya dawo ya samu Mom tana masifa akan Aisha ta dameta da kira. Najeeb bai kulata ba sai da Najma ta dawo ta ke ce ma sa yau ta ji tausayin Aisha domin ta kira kusan so biyar amma saboda ba ta magana ba ta iya ba da saƙon da ta ke son faɗa ba. Ƙila tana son ganin ka ne.

Hankalin Najeeb ya tashi, tunda su ka raba gida Aisha ba ta taɓa kira ba. Ta kira sau biyar kam yana nufin tana cikin matsala ne. Haka ya fita da gudu ya je ya ɗau keken sa ya tafi gidan Aisha duk da kuwa Mom tana ƙwala ma sa kira akan ya dawo.
Da ya je gidan tun daga falo ya fara kiran Aisha amma ba ta fito ba ya duba Mrs Beverly a kitchen ba ta nan sai ya haura sama da gudu. Kai tsaye ɗakin Aisha ya shiga. Amma mi sai ya ji kukan jinjira, yana duba gefen sa ya ga Aisha kwance ga jini duk ya ɓata wajen. Irin jinin da ya gani sai da wani jiri ya kusa kada shi ya dafe gini na wasu mintuna kafin ya ƙarasa wajen ta yana jijjigata amma ba ta tashi ba. Cikin kuka ya je ƙasa da gudu ya kira emergency line na police...

Yana tsaye aka zo aka ɗauke gawan Aisha, duk abinda idon sa ke sa ma sa shine Mom ce ta kashe Aisha. Ranan shima asibiti ya kwana dan yana tsaye a wajen bayan ansa gawar Aisha a mota ya faɗi ya suma...

Ko da bayan autopsy na Aisha ya fito kan ba kashe ta aka yi ba, haihuwa ta yi ita kaɗai jini ya tsinke ma ta kuma rashin Mutum a kusa da ita ya sa ba a kawota asibiti da wuri ba har ta mutu.
Najeeb bai daina ganin Mom a matsayin wanda ta kashe Aisha ba. He was very traumatized a lokacin da har ta kasance baya iya bacci sai da magani. Ya jima yana visiting therapist kafin daga baya aka ce ya dawo normal amma still a hakan bai koma dai-dai da Mom ba.
Rasuwan Aisha ya sa Mom ta saduda da rayuwa, ta nemi Adam ya maidata dan ta kula da Najdah...

"She wanted her dead all along, she's evil" abin da ya faɗa kenan ya buga steering ɗin motar. Idon sa na buɗe amma duhu ya ke gani, yana ƙoƙarin saita motar ta shi wata babbar mota ta zo ta buge motar sa, motar Najeeb ta yi sama sannan ta dawo ta faɗi ƙasa...

*sorry ba Morning post gobe sai da rana Insha Allah**SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣3️⃣2️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900*

*wannan page ɗin na ki ne ke kaɗai Anty nah Surayyah. Wishing you health, wealth, peace, grace, mercy and joy amin. Allah ya ƙarawa rayuwarki ta Oga da ta yaran ki albarka amin. Happy birthday🍾🥂🎂*

Tana zaune sai cika ta ke tana batsewa, abu ɗaya ta sani shi ne ta ajiye aiki da Najeeb sannan kuma dole ta rama abinda Sabreen ta ma ta. Ba za ta bar karuwan nan ta sha banza ba.
Tun tana duba agogo tana jiran Najeeb har bacci ya ɗauketa akan Sofa...

Daddy kam bayan fitan Najeeb kiran matar sa yai su ka yi hira, da ke jikin tan da sauƙi, dan likitan ya ce za'a iya sallamarta gobe.

Ƙarfe shaɗaya na dare wayar sa ta fara ringing, daga kan gado ya sa hannu ya lalubota ya ɗara a kunne dan ko gama gane numban da ya kira bai yi ba.
Abin da aka ce ma sa ne ya sa ya tashi zaune yana maimaita Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju'oun jikin sa na ɓari.
Ɗaukan key yai ya fita daga ɗakin da sauri duk da kuwa pyjamas ne a jikin sa...

Tunda aka shigo da shi ake ƙoƙarin tsaida jini, yadda jini ke zuba a jikin sa da ma  gefen kansa ka ce duka jikin sa zai tsiyaya zuwa ɗan ƙanƙanin lokaci.

Wani na ganin Najeeb Adam Jibo a jikin ID card ɗinsa ya gane ko ɗan waye, shi ya sa aka kira numban Daddy...

Yadda Daddy ke jinsa gani ya ke ba zai iya jira har Iliya ya taso daga BQ ya zo ya kai shi ba duk da an hana shi tuƙi da dare saboda idon sa.
Yana fitowa yana ƙwala sunan Malam Aminu maigadi akan ya buɗe gate, yadda ya ke kiran, shi kan sa Maigadi sai da ya tsorata... Ikon Allah ne kawai ya kai shi asibitin lafiya amma ƙila da shi ma hatsarin zai yi.

Yana zuwa aka ce har lokacin likitoci na kan sa. Jikin sa rawa ya ke bai iya zama ba yana safa da marwa zuciyar sa cike da addu'o'i. Tsabar rikicewa ko fitowa da wayar sa bai yi ba daga mota...

Anas ƙarfe huɗu da rabi na asuba aka kira shi, ya fito daga banɗaki kenan ya yi alwala ya ji kira kafin ya ɗauka ta katse. Ganin Daddy sai hankalin sa ya tashi, lokaci guda zuciyar sa ta raya ma sa ƙila Mom ce ta rasu. Duk da kuwa jiya da ya je dubata ya ga jikin ta da sauƙi sosai, to amma mutuwa ko da ciwo ko ba ciwo sai an tafi. Yana ƙoƙarin sake kiran Daddy kiranshi ya kuma shigowa ya ɗauka da sauri.

Maimakon Daddy ya ce ma sa wani abu ne ya samu Mom sai yai ma sa maganar Najeeb, Najeeb da su ka rabu lafiya ƙalau jiya.
"Daddy ya rasu ko?" Ya faɗa hawayen da su ka cika idon sa su na gangarowa.

Daga ɓangaren Daddy ya ce " a'a, yanzu likitocin su ka fito amma bai farfaɗo ba har yanzu"

Yai hamdala tareda cewa gashi nan zuwa...

Zuwa ƙarfe bakwai na safe asibitin ya cika da 'yan uwa. A wannan lokacin ne Uncle Sulaiman ya sa aka maida Daddy gida saboda ya chanja kaya.

.....................

Farida ba ta farka ba sai ƙarfe biyar lokacin da alarm ɗin ta yai ta ruri ba kakkautawa. Da ƙyar ta sa hannu ta jawo wayar ta katse alarm ɗin. Mafarki mai daɗi ta yi, itada Najeeb su na zaune a wani lambu, kanta na kan cinyar sa yana wasa da gashin ta.

" I love you Aysherh" ya faɗa idon sa cikin na ta.

"I love you too Sir Najeeb"

Hannun sa ya sa ya ɗan matse bakin ta ya ce "ba na hana Sir Najeeb ɗin nan ba"

"Sorry my champ"
Ta ɗan ɗago kanta ta kissing goshin sa sannan kumatun sa sannan hanci. Ganin ta tsaya ya sa yatsa ya nuna lips ɗin sa.

Ta girgiza kan ta. Ya ɗan yi ƙanƙan da ido alamar tausayi. Murmushi ta yi tareda haɗe bakin su...

Ta tashi jiki a mace ta shige banɗaki, wannan mafarki da ta yi ya sa ta sassauta jin haushin sa da ta ke ji.

Lokacin da ta zo gaban madubi, kallon kanta ta yi ta fara gwada maganan da za ta yiwa Najeeb ta yadda zai tabbatar ran ta ya ɓaci ya kuma ɗauki maganarta serious.
A hankali tana fari da ido ta ce "Sir Najeeb, gaskiya idan Sabreen za ta yi aiki a kamfanin ka to ni zan ajiye aiki na"
Ta yi tsaki ta ce ba haka bane barin sake. Wannan karan ta haɗa rai ta ce "Sir Najeeb zan ajiye aiki na"

Sai ta kwaikwayi muryan sa ta ce " good for you"

"Good for you kawai za ka ce min? Ka na tunanin idan na ajiye aikin akwai wanda zai iya yi ne?"

Da muryar sa ta ce "dayawa ma"

" Sir Najeeb, Allah ni kaɗai ce za ka iya jura. Ba wanda zai iya juran faɗan ka. Kai ba mace ba amma sai shegen mita"

"Aysherh" ta ji muryan sa a bayanta. Da sauri ta juya amma ba kowa. Ta rufe ido tana tuno kiss ɗin su na ranan...

Saboda ta tsara ba za ta koma aiki ba shiya sa da ta gama azkar ɗin ta ta sauko dan ta taya Adama aiki.
Tana saukowa ta haɗu da Daddy wanda shigowar sa kenan, ganin sa sanye da kayan bacci ga kuma damuwa shimfiɗe a fiskar sa ta yi tunanin ko wani abu ne ya samu Mom.

"Daddy ya jikin Mom" ta faɗa cike da tararrajin mi zai ce

"Alhamdulillah da sauƙi 'ya ta"

"Lah ba mu ma gaisa ba" ta faɗa tana tsugunnawa ta na mi shi ina kwana.

Tausayin ta ne ya kama Daddy. A yadda ya ga Najeeb ɗazu zuciyar sa ta karaya. Yanzu idan Najeeb ya rasu wanni hali Aisha za ta shiga? Auren da bai wuce sati shida ba.

"Aisha ki shirya yanzu, idan na fito za mu je asibiti Najeeb ba lafiya"

Dum ƙirjinta ya buga "Najeeb ba lafiya, mi ya same shi?. Allah sarki ashe shi ya sa bai kwana a gida jiya ba."  Tambayar da ke yawo a kanta kenan.
Amma duk yadda aka yi rashin lafiyar Najeeb mai tsanani ce dan kuwa Daddy ba zai damu har haka ba idan minor abu ne.
Komawa ɗaki ta yi dan ta ɗau gyale da jakar ta...

Iliya ne ya ke jan su, cikin motar shiru ka ke ji. Ganin yadda Daddy ke ta yawaita faɗin Lahaula Wala Ƙuwwata Illah Billah lokaci zuwa lokaci sai Farida ta ƙara tsorata da lamarin. Ba dai Najeeb ya rasu ba ne, idan Najeeb ya rasu ina za ta sa kan ta...

Sai da su ka isa asibitin sannan Daddy ya ce " 'ya ta ina so ki kwantar da hankalin ki dan Allah. Insha Allah komai zai zo da sauƙi, Najeeb ya yi hatsari jiya da dare"

Dafe ƙirjinta ta yi da sauri lokaci guda kuma numfashin ta ya tafi hucin gadi na 'yan wasu sakanni.
Hawaye ne su ka fara zirya a idon ta su na gangarowa.

"Ba kuka za ki ma sa ba, addu'a za ki ma sa Aisha"

Tafiya su ke amma ƙafafuwanta ji ta ke kaman ba ajikin ta su ke ba, she's not feeling them ko kaɗan.
Har su ka isa wajen su Anas hawaye ta ke. Yadda ta ga an cika wajen sai hankalin ta ya ƙara tashi.

Daddy ya tambayi ɗanuwan sa ko likitan ya ce wani abu. Uncle Sulaiman ya ce  sun ce ƙarfe tara za a ma sa CT-scan aga mi ya hana shi farfaɗowa dan sun ce su na zargin ƙwaƙwalwar sa ta kumbura ne.

Anas ya raka Farida gallery na theater room ɗin inda ta hango Najeeb kwance ansa ma sa life support system. A lokacin ta fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya. Anas ya ɗan dafa ta ya ce " dan Allah ki dena kuka addu'a za ki ma sa abinda ya ke buƙata kenan"

"Mutuwa zai yi ko?, mutuwa zai yi tun ban nuna ma sa yadda na ke son shi ba ko?, Ya Anas ba zan iya jure rashin sa ba"

Shi ma dai Anas daurewa kawai ya ke amma ya karaya da halin da ya ga abokin na shi....

Zuwa yamma an tabbatar mu su da cewa akwai jini da ya daskare a ƙwaƙwalwar Najeeb wanda idan ba acire ba ƙwaƙwalwar za ta yi ta kumbura ne har kuma ta iya jawo ta dena aiki gaba ɗaya wanda ƙarshen zancen dai mutuwa ce.

Abun ka da ma su dukiya tuni aka kira Dr Sajid Usman Abdallah dan ya zo ya jagoranci aikin da za a ma sa. ( ga wanda ba su san Dr Sajid ba an bar ku a baya 😂 ku karanta Mutum mugu ne. Yana nan a wattpad, za ku ga yadda Angon Zaytunah da Naziha ya sha goggonmayar rayuwa. Yai fama da zafin kishin Zayty da kuma rashin kamun kan ta. Sannan ya zo yai dakon soyayyar Ziha yarinyar da shekara ashirin da biyar cur ya ba ta, But aka ce love is blind☺)

Ranan Alhamis aka saka aikin kuma har lokacin Najeeb is in comatose. Kwana biyun nan Farida ta yi su ne akan sallaya. Kaso biyu cikin uku na daren sun tafi a sallah da roƙon Allah ne sauran kaso ɗaya kuma ya tafi a kuka da tunani.
Mom ma da aka sallamota wani tashin hankalin ta shiga dan sai da ta suma lokacin da ta je ta ga ɗan ta kwance a asibiti rai a hannun Allah...

Sun yi aikin awa shaɗaya akan Najeeb kuma Alhamdulillah an cire jinin da ya daskare ba matsala.
Sai dai Dr Sajid ya ce akwai yiwuwar Najeeb zai cigaba da zama cikin coma na tsawon lokaci. Amma, ba abinda ya fi ƙarfin addu'a...

Wata ɗaya kenan da ta wuce, wata ɗaya na kuka da roƙon Allah, wata ɗaya da tun ana cewa zai iya farfaɗowa gobe har aka zubawa sarautar Allah ido.
An tabbatar da case ɗin Najeeb ta shiga PVS (persistent vegetative state) yanzu kam sai randa ya farfaɗo kawai amma ba maganar ana tsammanta zai tashi nan kusa.

Duk wani wanda ya san Najeeb Adam Jibo sai da su ka tausaya ma sa. Shi ba mai bacci ba, shi ba mutuwa ba. Yana nan yana numfashi amma gashi a kwance ba abinda zai iya yi.

Wannan wata ɗayan da a ka yi Farida ta zama certified nurse a wajen kula da Najeeb. Tunda aka dawo da shi ɗaki na musamman da aka gyara saboda shi Farida ta koma kwana da shi. Duk yadda Daddy ya hana ta ƙi. Ita ke goge ma sa jiki safe da kuma yamma, har turaren sa ta je ta kwaso tana fesa ma sa. Ta ce Sir Najeeb ba ya son ƙazanta kuma yana son ƙanshi.

Zuwa yanzu ta rage yawan kuka da ta ke. Tana asibiti yanzu 24/7 duk da kuwa an ce ba sai an zauna da shi ba tunda ba wai tashi zai yi ya buƙaci abu ba kamar normal mai jinya. Idan ka ga ta je gida to ta je ɗauko wassu kaya ne. Kullum da safe da kuma dare sai Daddy da Mom sun zo sun duba ta tareda duba Najeeb da fatan cewa ko da na ɗan ƙaramin lokaci ne zai buɗe idon sa.

Farida ta chanja ta zama silent. Ko Sabreen ne ta zo duba Najeeb ba ta kulata, fita ma ta ke ta ba ta waje har ta gama tsiyarta ta tafi. Wanda iya ka daɗewar ta minti ishirin ne...

Yau ma ta na kwance gefensa tana ɗan shafa gashin sa da ya fara tohowa saboda lokacin da za a masa aiki aske gashin aka yi yai ƙwaranƙwal.
Taɗi ta ke ma sa kamar yadda ta saba yi.

"Sir Najeeb a ina ma mu ke"

Ta ɗan yi murmushi ta ce "yawwa na tuna, ranan da na fara jin wani abu gameda kai shine ranan da aka zo aka rescueing na mu daga hannun su Joseph. Ban ganewa zuciyata ba tun daga ranan. Ko da na dawo office kullum idan na kalli idon ka sai na ji wani abu ya taso min daga chan ƙasan zuciya ta,  shi ya sa ko ina magana da kai na ke avoiding haɗa ido da kai. Ko da yaushe ina ƙoƙarin yaƙi da zuciyata saboda wani sabon al'amari da ya dinga taso min da shi gameda kai ba mai yiwuwa ba ne, na dinga tabbatar wa kaina ka fi ƙarfi na, na dinga nunawa kai na, Najeeb Adam Jibo ya fi ƙarfin Aisha Farida Salihu. Amma ka san me? Bayan ƙaddarar aure ta shiga tsakanin mu sai...."

Sallamar Anas ya katseta daga labarin da ta ke wa Najeeb.

Sai da su ka gaisa ta ke tambayar sa ya aiki?

" 'yar uwa abubuwa fa ba daɗi. Riƙe kamfani kaman Najeeb constructions  sai ma su zafi irin Najeeb ɗin. Kin san Allah daga jin zancen halin da Najeeb ya ke sai kowa ya fara fidda asalin halin sa. Aka dena bawa aiki mahimmanci ana sako-sako da duk wani ayyuka da ake yi. Can you imagine wai anyi board meeting akan wai ba su yarda na jagoranci kamfani ba"

Farida ta zaro ido " to amma Ya Anas ba kai ke riƙeta ba idan Najeeb ba ya nan?"

"Haka ne amma kin san na 'yan kwanaki ne wannan. Najeeb bai taɓa tafiyar da ta wuce sati biyu ba. Yanzu kuma wata ɗaya da sati uku kenan ba ya nan. Farida abubuwa sun fara ja baya. Ba ni da zafi kaman Najeeb hakan ya sa kowa fara abinda ya ga dama"

"Amma ka gayawa Daddy?" Ta tambaya tana mamakin wannan al'amari, mutuwa Najeeb yai ba amma har an fara juya ma sa baya, Mutane kenan

"Mun tattauna da Daddy kuma ya amince da shawarar da na kawo, ya ce mu yi magana da ke ɗin"

Ta ɗan gyara zama dan ta fahimci zancen sosai.

"Farida riƙe Najeeb constructions ba zai tafi dai-dai ba sai iron man kaman Najeeb. Ki na da zafi, za ki iya taka kowa sannan za ki iya shugabanci. Kin zauna da Najeeb kin ga yadda ya ke gudanar da al'amuran sa i'm sure kin tsinci ilimin shugabanci a tareda shi. Farida ki koma aiki, wannan karan ba matsayin sakatariya ba sai matsayin CEO"

"Allah ya kiyaye Ya Anas. Wani zance ne wannan. Saboda ni ce na kawo son shugabanci duniya sai mijina na asibiti ba lafiya sai na tsallakeshi na tafi wajen aiki" ta goge hawaye ta ce " ina nan da shi anan har ranan da zai farfaɗo"

"Farida na san ki na so ki kasance tareda Najeeb, amma ba kya ganin kina da hakki akan kula da dukiyar sa. Barin gaya mi ki halin da mu ke ciki yanzu. Kamfanin da ta ke da major shares bayan Najeeb tana so ta janye hannun jarinta ko kuma mu mu sake sayar ma ta da kaso arba'in a ciki. Kin san mi hakan ke nufi? Yana nufin su na so su mallaki kamfanin ta ƙarfi, zai zama Najeeb 35% ne kawai na shi a ciki kuma kinga kamfani ta bar hannun Najeeb. Ke 'yar kasuwa ce kin san yadda za ki yi ki kawo cigaba a wannan kamfani ki kuma ceceta. Ni Architect ne ban da wani ilimi mai zurfi a wannan fanni. Najeeb da ki ke gani bayan karatun Engineering da Architecture da ya yi yana da degree a fannin kasuwanci sannan yana da certificates dayawa a ɓangarori ma su yawa musamman leadership. Hakan ya sa komai ke tafiya ma sa dai-dai"

"Ya Anas ba zai yiwu ba. A nemi wani ko cikin cousins ɗin Najeeb amma ban da ni. Ba zan iya ba"....

"Farida......"

.................................

Wata baƙar Marcedez benz ce ta shigo Kamfanin Najeeb constructions. Lokacin da motar ta tsaya an kai kusan minti biyu kafin aka buɗe ƙofa. Wata haɗaɗɗiyar mata ce ta fito daga ciki ta owners corner. Tun daga takun ta ka san mace ce mai aji da kuma girma. Kai tsaye ta shige kamfanin security ɗin wajen yana mata good morning ta amsa ma sa ta hanyar ɗaga hannu.
Anas ne ya nufota yana gaisheta lokacin da ta iso top floor ɗin. Tare su ka jera su ka wuce conference hall ɗin inda za ayi board meeting.

Kujeran da ta zauna an rubuta CEO a jiki waje ne da Najeeb ke zama lokacin yana da lafiya. Waje ne da bayanshi ba wanda ya taɓa zama a wajen idan ana taro haka.

Sai da ta ja numfashi ta sauke sannan ta ce *"suna na Aisha Farida Salihu, Mrs Najeeb Adam Jibo kuma acting CEO Najeeb constructions har zuwa lokacin da miji na zai samu lafiya ya dawo"*
Ta kalli fuskokinsu mai cike da tarin tambayoyi ta ce *ko da me ja?*....

*Tantarantarantaran. Daga secretary sai CEO wannan ƙarin matsayi har haka @team Farida kuna da aiki a gaban ku. @team Najeeb, sorry Najeebullahi ya tafi hutu, sai kun ganshi kawai dan nima ban san ranan dawowar sa ba😀**SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣3️⃣3️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900*

"Excuse me, ba za mu amince da wannan ba. Ta ya za ace za ki jagoranci kamfani kamar wannan ki na matsayin sakatariya. I bet wannan kamfani za
ta ruguje kafin nan da wata ɗaya. Duk da ki na matsayin matar Sir Najeeb hakan ba zai sa ki ma ye gurbin sa a wannan kamfani ba. You are incompetent and clueless"  wani a ciki ya faɗa yana huhhura hanci.

Ba tareda ta karaya ko nuna damuwa ba ta kalli mutumin ta ce " mi ye matsayin ka a wannan kamfani?"

Mutumin ya ɗaga kafaɗa ya na faɗin " I'm Festus Ogonna the F....."

"Get out!" Farida ta daka ma sa tsawa wanda kowa a wajen sai da ya sha jinin jikin sa, hatta Anas da ke gefe sai da ya ji wani dum. She sounds exactly like Najeeb.

"Mr Ogonna ba za mu iya zama da wawa kuma jahili ba. Tambaya ɗaya na yi ma ka amma ka fara ba da tarihin rayuwar ka. Who cares about your name?, a wannan kamfani matsayin ka shi ne identity ɗin ka and that's what i asked ba sunan ka ba"

Kallon-kallo aka fara yi, yadda ta ke magana da faɗa-faɗa ka ce kamfanin na ta ne tun fil azal.

"Get out!" Ta sake daka ma sa tsawa tana kallon sa ido cikin ido.

Mr Ogonna aƙalla zai kai 45yrs amma Farida ba ta kalli girman sa ba balle ta ji kunyar idon sa.

Mr Festus ya yi kasaƙe yana kallon ta. Ya buɗe baki amma ya kasa magana.

Phone da ke gabanta ta ɗauka ta danna wassu numbers. Ba su ankara ba sai ji su ka yi tana faɗin security su zo su fita da wani mahaukaci.

"You cant do this, you dont have the right" Mr Ogonna ya faɗa cikin masifa.
Farida na zaune ba ta ce komai ba sai ma duba takardu da ke gaban ta da ta fara yi. Mr Ogonna ya cigaba da kumfar baki yana  faɗawa sauran su sa baki, Farida ba ta da matsayin da za ta jagorance su balle har ta koreshi daga wannan meeting ɗin. Sai dai ba wanda yai magana. Sai kallon juna su ke su na magana da ido amma ba wanda ya furta wani abu.
Su na zaune har securities biyu su ka zo su ka fita da Mr Ogonna yana ta zage-zage.

Ta gane Mr Ogonna sarai, sau dayawa idan anzo meeting tun lokacin Najeeb yana ɗaya daga cikin wanda duk abinda aka faɗa sai ya kushe. Ya fi so ayi abinda ya zo da shi.
Najeeb bai cika sauraron sa ba, yana tashi zai yi magana Najeeb zai ce ya zauna. Wassu lokutan kuma sai ya bari ya gama bayanin sa sai Najeeb ya gwaleshi da cewa sun ƙayatu da labarin wasan kwaikwayon da ya gama ba  su.
Mr Ogonna irin ma su son cigaban kan su kaɗai ne. Ba su da wani interest akan aiki indai ba zai jawo ya samu wani matsayi ko wani kamashon kuɗi ba.

Bayan an fita da shi Farida ta sake tambayar su ko da mai ja, wannan karan ba wanda yai ƙwaƙwƙwaran motsi balle magana.

"Good, now what's next?"

Anas yai gyaran murya ya gabatar da matsalar da ke gaban su a yanzu. Maganan French investors ɗin su da ke son siyan kaso arba'in na kamfanin yai tareda neman minene mafita.

Farida ta bada dama a kawo shawara. A wajen kashi saba'in sun ba da shawaran a sayar da 40% ɗin sauran kashi talatin ɗin kuma su ka bada shawaran a kan kada a siyar a bari su janye 11% ɗin su. Duk da kuwa kamfanin za ta shiga wani yanayi amma idan aka jure aka kuma bi matakai masu tsauri za a farfaɗo daga faɗuwan da kamfani za ta yi. Cikin wanda su ka ba da shawaran a bari su cire hannun jari har da Anas. Bayan Mrs Najeeb Jibo ta gama sauraron su sannan ta ce
"11+40?"
Kallon kallon aka farayi dan ba a gane me ta ke nufi ba. Ganin ba ta kuma cewa komai ba ya sa wani ya ce "its 51"

"Exactly 51" ta faɗa tana buga table.

"Taya 51% zai kasance shares ɗin wassu turawa, mun amince mu sallama mu su kamfani kenan?. Ta ya za mu bar wa wassu turawa kaso mafi tsoka cikin wannan kamfani, bayan shekaru bakwai kenan ku na yiwa wannan kamfani hidima ace kun kasa riƙeta har sai wassu baƙin haure sun zo sun mu ku jagoranci. Miji na baya nan hakan bai sa komai zai tsaya ba, dukkan mu mu na da hakki akan wannan kamfani. Maganar ma a saida mu su shares ba ta taso ba. We will fight, we will fight with everything we've got. Tsoro ba na mu ba ne, the moment mu ka sa tsoro to mun faɗi, we will all fight this together"

Gaba ɗaya wajen aka sa tafi.

Anas yai murmushi tareda ma ta thumbs up...

A hankali ta buɗe ƙofar office ɗin, office ɗin na nan yadda ta san shi. Ba wani chanji illa kawai mai office ɗin da baya nan.  Ta ƙurawa kujeran sa ido tana ganin kaman Najeeb na zaune a wajen sai dai wannan karan maimakon yadda fiskan sa ke tsume koyaushe to yanzu murmushi ya ke ma ta.

"Sir Najeeb" ta faɗa a hankali.

"Aysherh" ta ga ya faɗa ma ta yana ma ta thumbs up.

"Farida" muryan Anas ya dawo da ita daga tunanin da ta ke.

Ta juyo tana kallon sa.
"Gaskiya kin yi ƙoƙari, sai dai da sauran aiki saboda jibi za su zo kuma ba mu shirya komai a kai ba"

"Ya Anas su zo ma na, su ɗin mala'ikun mutuwa ne da za mu ji tsoronsu?"

Anas ya girgiza kai.

"Wancan Mr Ogonnan ka sa a rubuta ma sa suspension na sati biyu. Ba ma son ɓata gari irin sa"

"Amma Farida ba kya ganin this is extreme".

Farida ta zauna akan kujera tana mai faɗin Bismillah a zuciyar ta.

"Lokacin da na ce ba zan karɓi aikin nan ba mi ka ce min?"

Anas yai ajiyar zuciya sannan ya ce "Shikenan Farida, zan yi yadda ki ka ce" 

" na gode Yaya na" fita yai daga office ɗin yana mai fatan zuwan Farida zai yi gyara ne ba lalata lamura ba.

Ta san dole za a samu matsala dama, shi ya sa tun farko ta ce ma sa ba za ta yi ba, saboda za su samu matsala da shi. Za ta iya bada umurnin da bai ma sa ba yai magana. A lokacin ya ma ta alkawarin duk abinda ta ce zai bi matuƙar bawai a harkan zane-zane ba ne tunda ba ta da masaniya a kan wannan harka.

Tana juyi a kan kujeran tana tuna hiran su da Daddy shekaranjiya.

" 'ya ta, Anas ya faɗa min ba za ki kula da kamfanin Najeeb ba, mi ya sa?"

Ta sunkunyar da kai ta ce "Daddy, aikin ya min girma kuma ban da ilimi a wannan harka"

Murmushi yai ya ce " Kamar ba Aisha Mai Gwanjo ba"

Farida ta yi saurin ɗago ido ta kalle shi cike da mamaki

Ya cigaba "Aisha mai turare, Aisha mai takalma, Aisha mai jakukkuna, Aisha mai zoɓo roto one in town.... and the list goes on. Aisha Baffan ki ya gaya min yadda tun ki na yarinya ki ka fara siye da sayarwa. Ko ba ke ba ce kina shekara tara ki ka saro goruba da taura ki ka zo da shi hutu kano, Baffan ki ya hanaki sayar wa ki ka ce ai ba za ki yi asara ba sai dai ya siye ya biya ki kuɗin hajar ki"

Farida ta sunkuyar da kai tana ƙoƙarin rufe fiskar ta da gyale saboda kunya.

"Lokacin da Najdah ke shekara tara ba abinda ta sani sai sakalci. "Lets go for ice cream Dad" ko "are we going to Disney this summer?" " Dad i want a pink teddy not brown" yai murmushin yaƙe sannan ya cigaba.
"Allah ya ba ki baiwa Aisha ki gode ma sa bisa wannan ni'ima. Ba zan takura mi ki ba amma ni akaran kai na ina so ki jagoranci kamfanin Najeeb, Allah kuma zai taimake ki a kan hakan"...

"Allah ka taimake ni bisa wannan jagoranci, ka bani ikon sauke nauyin da ya rataya a kai na, ka ba ni ikon yin gaskiya da adalci, Amin" abinda ta faɗa kenan kafin ta fara buɗe tarin files da ke gabanta.

.............................

Ƙarfe biyar da rabi ta isa asibitin, bayan an tashi sai da ta tsaya su ka tattauna da Anas kafin ta taho.
Tana shigowa ta samu Najma da Najdah a ɗakin.

"Sannun Anty, barka da yammaci" ta faɗa tana ajiye jakarta a kan ƙaramin fridge da ke ɗakin.

" an samu abinda ake so ko? Shi ne yanzu ba za a iya  zama da shi ba" Najma ta faɗa tana mata wani kallo.

"Big sis ai dama kukan munafurci ne,  neman attention ta ke yi kuma ta samu shine ta guje shi. I cant believe wai Daddy ne ya ce ta zama CEO ko mi ta sani oho"
Ta rasa cikin yayar Najeeb da ƙanwar sa wanne cikin su ta fi tsanarta. Mom da Daddy du ka sun karɓeta hannu bibbiyu kuma ba su da girman kai amma Najma da Najdah kam sai a hankali, ƙiri-ƙiri su ka nuna ma ta ba sa yinta, ba kamar Najdan ma.

Farida ba ta ce ƙala ba, ta ƙarasa bakin gadon da Najeeb ya ke kwance kamar mai bacci. Ta manna ma sa kiss a goshin sa ta ce " My Champ, ka ga na jima ko? Aiki ne ya min yawa. Ka san sai yanzu na gane ba ƙaramin wahala ka ke sha ba a office ɗin nan. Da ni kullum gani na ke kana zaune kan kujera mai laushi ga AC ba ka da wata matsala, ashe abin ba sauƙi.  Yau har irin zamanka na yi dan kawai na ba su tsoro, na nuna mu su cewa kana tareda ni. Kuma Wallahi sun tsorata. Ka san yanzu kai ni ne, ni ma kuma kai ne"

Najdah ta ja doguwar tsaki Najma kam ido da baki ta sake tana kallon ta. Ba su sha mamaki ba ma sai da ta ce "dan Allah tunda kun riga kun gaisa da shi ku bamu ware, miji da mata su na son keɓewa da junan su"

"Heeeee wonders shall never end, shegiya ke a suwa ki koremu a wajen ɗan uwan mu"

"Ni ɗin ce dai matar Najeeb"

Najdah ta kalli Najma ta ce " Big sis ki ji abinda ta ke faɗa fa, wai mu fita a ɗakin Big B"

Najma ta tashi ta ɗau jakar ta ta ce " ba laifin ta ba ne Najdah. Laifin Daddy ne da ya je ya kakaɓo wata 'yar ƙauye ya haɗata da Najeeb, har ta ke ganin matsayin ta yana dai-dai da namu"

Har su ka fita ko kallon su ba ta yi ba. Ba ta da lokacin su, idan fitina su ke nema su jira Najeeb ya warke su ga ikon Allah.
Ta zauna ta sa kanta a gefen sa ta na shafa hannun sa. Bai jima ba bacci ya ɗauketa a haka...

Da dare su Daddy su ka zo anan Mom ke ma ta sallama akan jibi za ta wuce za ta je Umurah ta yi wa Najeeb addu'a. Farida ta yi farin ciki da hakan tareda addu'an Allah ya kai ta lafiya ya dawo da ita lafiya.
Fitan su ke da wuya tana zaune ta zubawa Najeeb ido, ta kai hannu za ta kama hannun sa sai ta ga ya motsa yatsun sa biyu. Wani ihu ta ƙwalla tana kiran sunan  Daddy.

"My champ da gaske kai ka motsa yatsun ka? Da gaske yatsun ka ne su ka motsa?"

Ganin ba wani reaction da ya sake yi ya sa ta fita da gudu tana kiran su Daddy.

Sun yi nisa da ɗakin dan sun kusa fita a asibitin kafin ta taro su.

"Daddy ku tsaya Sir Najeeb ya motsa yatsun sa yanzu" ta faɗa tana haki.

Daddy da Mom ɗin kowa sauri ya ke ya je ya ga shalelen ɗan na su.

Koda su ka zo ɗakin Najeeb yana nan dai yanda ya ke.
Kallon da Daddy ya ma ta ne ya sa ta san ba su yarda da maganarta ba

"Allah Wallahi Daddy ya motsa yatsun sa, Allah"

Tana maganan tana hawaye. Mom ta kamo hannun ta ta ce " Farida it's ok, addu'ar mu kullum shi ne ya tashi ɗin. You're just hallucinating ki kwantar da hankalin ki, Bi izni kun fa ya kun zai tashi nan ba da daɗewa ba" jin haka Farida ta tubure akan wallahi Najeeb ya motsa yatsar sa. Ƙarshe dole aka kira likita wanda ya zo ya sa aka kunna mu su video footage ɗin wajen. Dama babban amfani na sa cctv cam ɗin kenan saboda a dinga bibiyar shi ko da zai iya motsawa ko ya farfaɗo ba tareda wani na wajen ba.

Lokacin da su Daddy su ka gani su ka gan hakan ne ta faru Najeeb ya motsa yatsun sa, farin ciki su ka ji marar misaltuwa tareda ƙara samun hope akan Najeeb zai tashi.

"Daddy zai tashi, yana so ya tashi Daddy zan ajiye aikin nan kar ya tashi ba na kusa da shi"  ta faɗa tana goge hawayen da ke zubo ma ta.

Daddy zaunar da ita yai yana ƙara ma ta nasiha akan tashin Najee.  Ko ta na kusa da shi ko ba ta kusa zai tashi Insha Allah, kuma zai fi jin daɗi idan har ya tashi ya ga ta kula ma sa da Kamfanin sa.
Ranan su Daddy ba su bar asibitin ba sai wajen ƙarfe sha biyu na dare.
Farida kam bayan sallah da ta tashi ta yi ba abinda ya sa ta ɗauke idon ta akan Najeeb gaba ɗaya daren ranan ji ta yi kamar zai buɗe ido ya ma ta magana. Ka sa bacci ta yi saboda kar ya buɗe ido tana bacci...

..........................

Su uku ne su ka zo domin yin wannan yarjejeniya. A ɓangaren team ɗin Najeeb constructions kuwa su biyar ne Madam CEO tana tsakiyar su.

Dogon bayani Mr Smith yai wanda du ka bayanan sa kan yadda su za su fi samun riba ne ba komai ba. Da ya gama Mr Nokovic ya karɓa ya fara magana amma shi maganar da yai akan wai ba su yadda da shugabancin Farida ba ne.

Da su ka gama ta su bayanin Farida ta karɓa ta fara bayani.

" a duk bayanan ku abu biyu na fahimta. Na farko ba ku yadda na zama CEO ba na biyu kuma ku na son cire hannun jarin ku"

Mr Nokovic ya ce " mu na son ƙara siyan hannun jari ba wai cire hannun jari ba"

"Oh really, ashe har kun tsorata kenan. Ni abinda na gani a rubuce shi ne kuna son ƙara siyan hannun jari ko kuma ku cire hannun jarin ku. So ni na riga na yadda maganan siyan hannun jari yanzu batun hannun jari da za ku cire za mu yi magana akai. So nawa za ku siyar ma na"

Kallon-kallon su ka farayi suna mamakin yadda lokaci guda ta juya abun kan su.

"Ba ni da lokaci da yawa, kaman yadda ku ka sani ina da majinyaci a asibiti wanda ke buƙatar kulawata"

"Mrs Jibo (ya faɗi jibon kaman wani *Jaebo*) mun san halin da kamfanin nan ke ciki ba za ta iya siyan shares ɗin mu ba."

Farida ta yi murmushin yaƙe ta ce " waya gaya mu ku Kamfani ba ta da halin siya. Ni nan ni zan siya kunga abu ya dawo gida kenan. So mu fara cinikin $200,000,000 mi ku ka ce?"

"Mrs Jibo" Mr Smith ya kira kafin ya ƙara da wani abu Farida ta ce " $205,000,000 wannan fa?"

Shiru su ka yi dan ba su zo don su siyar da shares ɗin su ba dama burga da barazana ne kawai.

"Ku na cewa ba ku yadda na shugabanci wannan kamfani ba a wani dalilin? Saboda ina mace?"

Mr Vladimir wanda bai yi magana ba tun ɗazu ya ce "mun yarda ki shugabanci wannan kamfani a bisa sharaɗi ɗaya"

Farida ta ɗan gyara zama ta ce " wanni sharaɗi"

Mr Vladimir ya ci gaba da bayani " akwai bidding da za ayi a Abuja nan da sati huɗu. Manya-manyan kamfanoni za su shiga wannan bidding su submitting picth ɗin su saboda duk wanda ya ci contract ɗin, its worth billions. Sau ɗaya wannan kamfani ta taɓa winning contract mai tsada kamar haka, but wannan ya ma fi wanchan da aka yi a Lagos.
Mu na so ki yiwa wannan kamfani register ki kuma jagoranci wannan kamfani har ta winning wannan contract ɗin. Idan Najeeb constructions ta samu wannan project, mu mun amince za mu sayar mi ki 5% na shares na mu amma idan wannan kamfani ta shiga gasan nan ta faɗi to za ki sayar ma na da 10% na shares ɗin ki"

"Idan kuma na ƙi shiga gasar fa?"

"Za mu cire duka 11% shares na mu wanda ka iya kassara wannan kamfani saboda halin da ta ke ciki"

Tsawon minti biyu ba wanda ya sake magana. Sai murmushi turawan su ke ganin sun sa ka Farida a wani hali.

" Najeeb constructions za ta shiga wannan gasa kuma za ta ci Insha Allah"

Anas ya kalleta yana faɗin "Farida akwai matsala, ba za mu iya..."

" Ni Aisha Farida Mrs Najeeb Jibo, na amince za mu shiga wannan gasa kuma za mu ci da yardar Allah"*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣3️⃣4️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*



***
Tana shiga office yana biyota.
"Farida kin san abinda ki ke faɗa kuwa, a halin da wannan kamfani ta ke ciki shine za ki samu cikin gasa.  Do you have any idea irin manya-manyan kamfanin da za su shiga wannan gasa, ko da Najeeb yana nan chance ɗin winning is very low balle kuma baya nan"

"Ya Anas so ka ke na ƙasƙantar da mu a gaban yahudawan turawan nan?"

"A'a so na ke ki cire girman kai, ki ce ba za mu yi gasan ba. Idan sun cire shares na su ko Daddy za mu iya neman taimako a wajen sa"

"Ya Anas kenan, mutanen nan sun san mi su ke fa, ɗaurin goro su ka ma na. By all means so su ke mu faɗi, mu ji kunya. Ni ban shirya turmusa wannan kamfani a ƙasa ba"

Wannan karan a hankali yai maganar ya ce " kin zaɓi a shiga gasan nan mu faɗi, Najeeb ya rasa 10% na shares na shi?"

" wanda su ke zama wani abu a rayuwa mutane ne that are willing to take risk. Ya Anas i'm a risk taker, ba na kallon 10% da za mu iya loosing, abin da na ke kallo shi ne 5% ɗin nan, kuma sai mun samu Insha Allah"

"Farida please, ka da ki yi haka. Ka da ki jefa mu cikin wani hali da zai kawo mu ga dana sani. Idan Najeeb ya tashi ya tarar ya loosing 10% na shi saboda ke he will never forgive you"

"Tun lokacin da ka hango nasara wa kan ka, to nasara tana tareda kai. Ya Anas za mu shiga gasan nan"

"Ba zan amince ba Farida, ba zan bari 7yrs of hard work ya crumbling a sati huɗu ba. Zan yi magana da Daddy za mu samu wata mafutar"
Har ya juya zai fita ta kira sunan sa " Ya Anas"
Daga bakin ƙofan ya tsaya bai juyo ba.

"Daddy kullum cikin kashe kuɗi ya ke, ta ya zamu tuntuɓe shi da maganan maƙudan kuɗi haka. Ka san ko nawa ya ke kashewa a  kowanni rana yanzu saboda Najeeb? Ka san ko nawa ya ke biya wa kowani kwana ɗaya da Najeeb ya ke yi a gadon asibiti. Da ceto rayuwan ɗan sa zai ji ko da ceto kamfanin ɗan sa?"

Anas bai yi magana ba ya fita daga office ɗin.
Ta jima a tsaye kafin daga baya ta je ta zauna, ba ta jima da zama ba  Mrs Confort Masoyi sabuwar sakatariyar ta ta kawo ma ta wassu reports da za ta duba. (yeeeh mu ma muna da sakatariya😂)...

Ranan gaba ɗaya Anas avoiding ɗin ta yai. Ita kan ta ta san cinye gasan nan abu ne mai matuƙar wahala amma kuma ba za ta janye ba, ai ance sai an gwada akan san na ƙwarai.


............................

Tun kafin ta tashi Daddy ya kirata  akan idan ta tashi daga kamfani ta zo ta sameshi a gida. Tunda su ka yi wayan ta san Anas ya mishi maganar gasa ne. Ta ƙudira a ranta idan Daddy ya ce ta haƙura da gasan za ta haƙura tareda kuma ajiye matsayin da ta ke yanzu.

Daga office maimakon ta wuce asibiti kaman yadda ta saba sai ta wuce gida. Tasallah ta samu a falo tana goge-goge ta tambayeta ko Daddy na gida ta ce ma ta yana nan. Kai tsaye sama ta haura ta wuce falon sa. Da sallama ta shiga falon ya amsa ma ta yana kora ruwa, da alama magani ya sha dan ga tulin magani a gaban sa.

Sai da ta gaishe shi sannan ta ma sa ya jiki. Ba ƙaramin zabgewa yai ba, to ba dole ba shalelen ɗan sa yana kwance a asibiti shi da mai mutuwa banbancin su kaɗan ne.

"Aisha ya aikin?" Ya katse shirun na su

"Alhamdulillah Daddy"

"Allah ya taya ki riƙo" ta amsa da amin.
"Ki na cin abinci kuwa? na ga kin rame"

"Ina ci tareda Sir Najeeb mu ke ci"

Daddy yai shiru bayan yai addu'an Allah ya bawa Najeeb lafiya.

"Aisha, Anas ya zo wajena ɗazu da rana kuma ya min wassu bayanai, na saurare shi kuma na fahimce shi. A wani ɓangaren kuma ke ma na fahimci inda ki ka dosa. Alhamdulillah dukkan ku manufar ku ɗaya ne, sai dai ra'ayin ku ne ya banbanta kan yadda za ku cimma wannan manufa"

"Daddy zan haƙura idan ka ce na haƙura amma gaskiya ba zan cigaba da zama a matsayina ba bayan hakan"

" ba zan ce ki haƙura ba amma ina da tambaya. Idan da ace Najeeb ne a wannan yanayi ki na ga zai shiga gasan nan ko ba zai shiga ba?"

"A sanin da na yiwa Sir Najeeb Wallahi zai shiga gasan nan"

Daddy ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ya ce " ki je ki yi abinda ki ka ga Najeeb zai yi, Allah na tareda ke. Idan ki na buƙatan taimakona ko shawara kan wani abu feel free ki min magana yadda Najdah ta ke matsayin 'ya ta haka na ɗauke ki"

Godiya ta ma sa sannan ta tashi ta shige ɗakin su. Ɗakin na nan yadda ya ke abu ɗaya ya rasa shine mazaunan ciki.

Tana tsaye gaban mirror ta rage kayan jikin ta tana kallon yadda ta rame ta yi baƙi.

"Aysherh ba na son ƙazan ta" ta ji muryan Najeeb a bayanta. Ta juyo ta ɗan harareshi ta ce "ni ba ƙazama ba ce"
Sunkuyo da kan sa yai ya shinshina gashin ta sannan ya ɗago yana fifita hanci yana faɗin " kin san ba na son wari Aysherh"

Ta juyo a harzuƙe zata fara masifa ta ga wayam ba kowa. Dama idon ta ke ganin kamar Najeeb na wajen, abinda ke sa ta nishaɗi kenan saboda ganin Najeeb da ta ke yi a idon ta, koyaushe yana tare da ita.

Da sauri ta wuce banɗaki ta fara wanke gashin ta wanda rabon shi da ya ga proper wanki tun zuwan ta Jos. Ta shampooimg kanta tana dirje dattin gashin da na scalp ɗin ta. Da ta wanke kumfan sannan ta saka instant conditioner yai  minti biyar kafin shima ta wanke, sai a sannan ta fara wanka da shower gel ɗin Najeeb mai shegen ƙamshi.
Lokacin da ta fito ita kan ta sai kan ya ma ta saƙayau. Bayan ta drying na shi da hand dryer sannan ta shafa ma sa leave in conditioner. Zama ta yi ta yiwa gashin twist manya guda takwas. Ta kalli kan ta a madubin ta ga ta yi kyau saboda rabon da gashin ya ga gyara tun tana Jos. Cikin ran ta tana faɗin ai dole Champ ya ce ba ya son wari, kan ta cikin wata biyu ban da ruwan alwala da kuma ruwan wankan tsarki bai ga ruwan wanki ba. Tana shiryawa Tasallah ta zo ta tambayeta ko ta kawo ma ta abinci ne yanzu. Ta ce ta haɗa ma ta za ta wuce da shi asibiti...

Lokacin da ta je asibitin ta samu likita na duba Najeeb.

"Ya jikin na shi?"  Ta tambaya lokacin da ta ƙaraso.

Likitan ya amsa da sauƙi

Sai da Farida ta samu waje ta zauna sannan likitan ya juyo ya kalleta bayan ya gama duban na'uran da ke kula da Najeeb.

"Aisha, ki cigaba da addu'a amma halin da Najeeb ke ciki komai zai iya faruwa. Wassu kan ɗaukan shekaru ma su tsawo ba su farfaɗo ba wassu daga haka su ke mutuwa, wassu kuma idan sun farfaɗo ma za ka ga sun samu matsala da ƙwaƙwalwar su ko kuma ka ga sun..."

"Na sani likita, tunda Najeeb ya shiga wannan halin na fara karance-karance akan wanda su ka shiga hali irin na shi kuma na gane komai. Ina da yaƙinin cewa mijina zai tashi nan ba da jimawa ba. Zai tashi mu yi rayuwan aure mai cike da soyayya da ƙauna, zai tashi mu haifi 'ya'ya kyawawa kaman sa, zai tashi ya kirani Mrs Jibo, zai tashi na nuna ma sa yadda na ke tsananin son sa" hawaye ya ƙwace ma ta.

"Ki yi haƙuri Aisha, Allah ya na tareda ke. Akwai wani likita da ke zuwa visiting doctor a nan kwanan nan ya dawo Nigeria kuma gaskiya ana yabon ƙwazon sa. Yana aiki ma da Dr Sajid so inaga idan ya zo gobe zai duba mijin ki. Mu ji wanni shawarwari zai bayar"

"Na gode Doctor amma idan ya zo ka kirani, zan so na ji mi zai ce da kunne na"

"Insha Allah zan kiraki" daga haka likitan ya fita.

Farida ta taso ta ƙarasa gadon Najeeb. Ɗankwalin ta ta cire ta kai gashinta dai-dai hancin sa ta ce "my champ na wanke gashin baya wari yanzu, ka ji ƙanshin sa. Do you like it?"

Ta sumbaci idon sa da ke rufe ta ce "ko za ka mutu a haka ba zan gujeka ba, zan jira ka. Zan cigaba da jiran ka har iya ƙarshen rayuwa ta. I love you, I love you so much. Ka tashi ka ji, ka tashi mu yi abubuwa, saboda kanada abubuwa ma su saka abubuwa kuma nima inada abubuwan da za su saka yin abubuwa. Ka tashi ka kissing ɗi na irin na ranan, ka tashi kamin tafiyar ka mai ɗaukan hankali ɗin nan. Ka tashi ka min dariyan ka mai daɗi"...

.........................

Washe gari ta zo ta tarar da abun mamaki, tana office Mrs Comfort ta shigo wai Anas yana kiran ta ana meeting a conference room.
Ba tareda ɓata lokaci ba ta wuce hall ɗin. Tana zuwa ta tadda an cika, duk wani mai babban matsayi yana wajen, abun takaicin ma har da Sabreen.

Anas ne ya raising motion kan ƙin amincewa da yai da shiga gasar da Farida ta sa.
Zaro ido tai lokacin da ya ce  ko ta janye gasan nan ko kuma ya ajiye aikin sa.

"Ya Anas ya za ka min haka?" Ta faɗa idon ta ya ciko da hawaye. Ba ta ɗauka abin zai kai haka ba. Jiya sun rabu da Daddy akan zai yiwa Anas magana to mi kuma ya faru.

Sabreen ta ce Anas ba zai ajiye aiki ba idan ya ajiye kuma za ta cire shares ɗin ta. Ta sake cewa Farida ta ajiye aikin ko kuma dukkan ma'aikata su yi yaji.

"Its your lost Farida, dont destroy my Noory's company"

Sunkuyar da kai ta yi tanajin maganganun su. Ta jima a haka kafin ta ɗago, ga mamakin ta sai  ta ga Najeeb yana kallon ta yana murmushi.

"Its not easy ko?, haka nima na ke fama da su, but you have to be strong, you have to stand by what you believe. Kin san ya akayi na gina wannan kamfani cikin shekara bakwai ta zama haka?"
Farida ta girgiza ma sa kai

"Saboda idan na sa abu a raina sai na ga na cimmaci na ke ajiyewa. Na gaya miki mi za su yi idan ki ka janye gasar nan?"
Ta ɗaga ma sa kai

"They will consider you weak and incompetence. Za su ce ki sauka daga matsayin ki za su ce ba abinda ki ka iya. Anas is good amma yana da tsoro da rauni. But you" ya nunata da yatsa "My Miss Salihu My Mrs Jibo My Aysherh ba ki da tsoro ba ki da rauni"

Firgigit ta yi lokacin da Anas ya ce " muna sauraren ki Aysherh"

Tashi tsaye ta yi tana shanye duk wani damuwa da ke ranta.

"Ya Anas za ka iya ajiye takardar a wajen sakatariya ta, za ta shigo min da shi office. Sauran da za su shiga yajin aiki kuma Bismillah sai na ji ku. Ma su son bin bayan ya Anas kuma takardan ajiye aikin ku duk ku ajiye wa sakatariya ta"

Ta maida kallon ta ga Sabreen ta ce "ke kuma zan fi kowa farin ciki idan ki ka cire shares ɗin ki a wannan kamfani"

"Ga wanda ya goya min baya wajen ayi gasa kuma. Zan sa a ajiye box a ƙasa kowa ya jefa ƙuri'ar sa ciki. Ba suna za ka saka ba ko matsayi, kawai ka ɗau takarda ka rubuta *i support* ka jefa ciki. Na barku lafiya"
Daga haka ta ɗau wayar ta ta fita. Anas dai mutuwar tsaye yai a wajen. Hall ɗin ya kaure da kace na ce.

Ko zama ba ta yi ba Sabreen ta shigo. " ba ki isa ki yi haka ba. Ba ki da matsayin da za ki kafa doka ki ce dole sai an bi ba"

Farida ta sa dariya ta ce " na samu matsayi tun ranan da aka ɗaura aure na da Miji na Najeeb. Love of my life, my heartbeat, my champion, my handsome.." mari Sabreen ta kai ma ta Farida ta riƙe hannun.

"Ka da ki kuskura ki taɓa ni, ko kuma na sa a yanke mi ki hannu. Duk wanni matsayi da ki ke da shi outside Nigeria ya ke da tasiri. This is Nigeria ba wanda ya damu da wata karuwar Hollywood a nan. Ki tattara ki koma inda ki ka fito ko kuma idan na waiwayeki ba za ki ji daɗi ba" ta tura hannun gefe.

Yadda ta ke magana da masifa ya sa Sabreen ta ɗan ji tsoro.

"Now get out of my office"
Yadda ta yi tsawan tamkar Najeeb ne ke wannan tsawa.

Sabreen ta ce " we'll see" sannan ta fita.

Daga fitan ta Yakubu ya shigo.

"Haba Farida, ta ya za ki yiwa Anas haka. Anas ya mi ki halacci ta ya za ki ma sa haka?"

Wayar ta ne ya fara ringing ta duba ta ga Doctor Sadiq ta ɗauki kiran tana faɗin to gani nan zuwa. Tana gama wayan ta kalli Yakubu ta ce.

"Barinje na yi magana da likitan mijina, duk wani ƙorafin ka zan saurara idan na dawo"

Yakubu yai galala da baki yana kallon 'yar uwartasa yadda ta koma Najeeb sak.

Jaka kawai ta ɗauka ta fita ta barshi a office ɗin...

............

Kai tsaye ɗakin Najeeb ta wuce lokacin da ta iso. Ba kowa a ciki dan haka ta kira likitan ta gaya ma sa cewa ta iso. Kusan minti goma sai ga doctor Sadiq ya shigo tareda wani likitan.
Idon sani ta gani, idon da ba za ta taɓa mancewa ba.

"Dr Lukman ga matar patience ɗin na mu" ya kalli Farida ya ce "Aisha ga Dr Lukman wanda na miki maganar sa jiya"

"Green eyes" ta faɗa bakin ta na rawa...

*na gode da kulawar ku, sai kunjini Insha Allah**SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣3️⃣5️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*

"Kin san shi ne?" Dr Sadiq ya tambaya. Ba ta bashi amsa ba sai kawai kallon Lukman da ta ke, bai chanja ba ya de ɗan ƙara ƙiba da kuma gemu amma bayan nan yadda ta sanshi haka ya ke.
Lukman ya katse shirun da cewa " ka san na zauna a Jos, itama 'yar Jos ce"

Dr Sadiq ya ce ok barin barku. Sai da ya fita sannan ya kalli Farida da kyau. Although kayan jikin ta sun nuna tana cikin jin daɗi amma yanayin fiskarta ya nuna saɓanin haka.

"Aisha ya ki ke ya mai jikin?"

Da ƙyar ta haɗiyi miyau ta ce " lafiya Alhamdulillah"

Ƙarasawa yai gadon Najeeb duk da ma dai kafin zuwan Faridan shi da Dr Sadiq sun shigo sun duba shi, sai dai ɗazun rashin sanin ko waye ya sa bai damu da kallon ya patient ɗin ya ke ba. Masha Allah ya faɗa chan ƙasar zuciyar sa lokacin da ya ƙare ma sa kallo.

"Yaushe ka dawo?" Farida ta tambaya tana matsowa kusa da shi.

" shekara ɗaya da ya wuce"

"Ok"

"Sai dai tun lokacin da na dawo ban je Jos ba gaskiya"

Farida ba ta ce komai ba sai bin hannun sa ta ke da ido yadda ya ke tattaɓa jikin Najeeb.

"Kinga Allah ya amsa addu'a ta ko? He's handsome"

Maimakon ta bashi amsa sai ta ce "ka na ga zai tashi nan kusa?"

"Na duba records ɗin sa kuma na ga cewa ya taɓa motsa hannu sau ɗaya which is good news gaskiya. Insha Allah zai farfaɗo Aisha, dole ma ya tashi ya kula min da ke"

Sai alokacin Farida ta yi murmushi...

Daga asibiti dreba ya mai da ta kamfani. Tana zuwa sakatariyar ta ta miƙa ma ta resignation letter ɗin Anas. Har ga Allah ta ɗauka Anas ba zai yi haka ba. Dama so ta ke ya gane da gaske ta ke ba za ta janye ƙudirinta ba. Amma sai gashi ya ɗau abin da zafi.

Yakubu ta kira akan ya zo office ɗin ta. Bayan ya zo dai faɗa ya fara ma ta kan abinda ta yiwa Anas ga shi yanzu ta sa Anas ya ajiye aiki.
"Sai mu ga yadda za ki kula da kamfanin ba tareda Najeeb ko Anas ba"

"Akwai Allah Yakubu, da Allah na dogara kuma shi zai taimakeni"

Tashi yai zai bar office ɗin ta ce ya tsaya.

"Yakubu ka na tareda ni?"

"Farida zan ba ki goyon baya akan wani abu amma ba wannan ba"

"Ba ka yadda da ni ba ne kenan?" Ta faɗa tana matse hannayen ta.

"Mi ki ka sani gameda wannan gasa?"

"Ban san komai ba amma idan kuka min bayani zan fahimta"

"Farida abu ne mai wuya..."

"Dan Allah kar ka gujeni kamar yadda Ya Anas yai" ta faɗa tana narai-narai da ido. Ajiyar zuciya yai sannan ya ce...

..........................

Washe gari da ta ke tunanin za'ayi yajin aiki shiru ka ke ji kamar shaho ya ci shirwa. Kowa ya kama aikin gaban sa. Ba ta jima ba Sakatariyarta ta kawo ma ta box ɗin da aka ajiye tun jiya wanda ke cike da takardu.

"Ki je ki ware min wanda su ka supporting da wanda ba su yi ba ki gayamin percentage ɗin"

Mrs Comfort ta amsa da to ta fita.

Bai fi minti talatin ba Mrs Comfort ta dawo da result
"Madam, 65% sun supporting sauran 35% kuma ba su yi supporting ba"

" 'yan iska kawai, na gode Mrs Comfort. Yanzu ki je ki aikawa Mr Ogonna saƙo kan cewa na janye suspension da na ma sa kuma ya resuming aiki gobe"

Mrs Comfort na fita ta cigaba da duba wani littafi da ta ke ganin Najeeb na yawan dubawa lokaci zuwa lokaci idan baya aiki. Sai yanzu ta fahimci Najeeb mutum ne mai tsari. Waɗannan wa su details ne na yadda ya cimma wa su manyan projects na shi...

"Ina shegiyar ta ke?" ta jiyo muryan Najdah tana daka wa sakatariyarta tsawa.

"Ohooo! so wuyan ki yai ƙwari har za ki ce Ya Anas ya ajiye aikin sa? Who are you? Mi ki ka ɗauki kan ki ne. Idan akwai wanda ya dace ya riƙe kamfanin Big B to Ya Anas ne ba ke ba. Gold digging bitch"

Farida ta yi juyi kan kujera sannan ta ce " idan kin gama haushin na ki dan Allah a gaida min Daddy dan ban samu  zuwa gida jiya ba. Miji na baya so na bar gefen sa"

Najdah ta harzuƙa ta je gaban Farida ta sa hannu ta fara janta. Wallahi ki tashi a kan kujeran nan, ba ki dace da shi ba..." saukan mari ta ji a fiskarta wanda ya sa ta yi saurin riƙe gefen fiskan ta.

"You slapped me!"

"Idan ba ki fita harkata ba Najdah sai na sa an zane min ke. A kan ki aka fara auta ne da za ki bi ki rena mutane. Ni sa'ar ki ce? Na ce ni sa'ar ki ce?"

Farida ta koma ta zauna da kyau sannan ta ce  " ki rufe min ƙofa idan kin fita...

Najdah was so shocked da ƙwaƙwƙwaran motsi ta kasa. Ta  jima tsaye kafin ta fita daga office ɗin... sai da ta fita Farida ta kalli wani hoton Najeeb da ke kan table ɗin ta ce "My champ ka ga za su haukata ni ko, Ina zaman zama na su ka ce na karɓi wannan matsayi kuma yanzu na karɓa ana min mugun kallo"...

"Najdah is my favourite sister mi ya sa ki ka mareta?"

"Ka na ganin rashin kunyar da ta min fa, dama tun ba yau ba ta ke gayamin maganganun da ta ga dama ina shareta"

"Ohooo ni da ki ke min rashin kunya kullum na taɓa marin ki?"

'Yar dariya ta yi ta ce "Haba my champ ni yaushe na ma rashin kunya, faɗi gaskiya dai" zuwa yai gaban ta ya ja hancin ta da ƙarfi.

" ouch! My champ da zafi fa" ta faɗa tana hararan sa...

"Madam na gama aikin" muryan Mrs Comfort ya dawo da ita daga duniyar tunani.

...........................

"Daddy she slapped me fa. Daddy ka yi wani abu please"

"Na san idan ba ki ma ta rashin kunya ba ba abinda zai sa ta mareki. Ki fita a maganan kamfanin Najeeb. Karatu ne a gaban ki yanzu"

"Daddy abinda za ka ce kenan, mu zuba ma ta ido ta ɓata komai ko? I will never do that" ta tashi ta bar falon da sauri.

Waya ya janyo ya yiwa Farida text akan ta zo idan ta tashi...

Anas ne ya fara zuwa kafin Farida ta zo. Ta samu Daddy yana mishi faɗa kan ajiye aiki da yai, dan shi bai gaya ma sa ba ɗazu Najdah ke gaya ma sa da ta kawo ƙaran Farida...

"Ni ban amince da wannan ba Anas. Idan ku ka raba kan ku kuna ga kamfani zai cigaba ne? Ka koma aikin ka, idan ba za taimaka ma ta har ayi gasan ba, ka cigaba da kula da sauran harkokin ai"

"Daddy ka yi haƙuri dan Allah. Kawai dai..."

"Ba na son jin wani ƙarin bayani. Gobe idan Allah ya kaimu ka koma aiki"

"Insha Allahu Daddy"
Juyawa yai kan Farida ya ce.

"Ku haɗe kan ku Aisha, saboda a samu cigaba mai inganci. Allah ya shige mu ku gaba" ta amsa da Amin...

Tana cikin yiwa Najeeb taɗi sai ga Lukman ya shigo da sallama. Ledar hannun sa ya ajiye wanda ke cike da fruits.
"Barka da yammaci Aisha" ya faɗa lokacin da ya ƙaraso wajen ta.

"An wuni lafiya?"

"Lafiya, ya mai jiki?"

"Da sauƙi Alhamdulillah"
Shiru ne ya ratsa ɗakin na 'yan mintuna kafin Lukman ya ce " zan wuce Abuja gobe amma Insha Allah zan dinga neman ki na ji ya mai jikin"

"Na gode" ta faɗa tana maida kallon ta ga Najeeb...

Bayan ya fita ta kalli Najeeb  sai ga hawaye ma su ɗumi shaar su na zubowa.

"Kukan na miye? Tukunna ma waye wannan?" Najeeb ya faɗa yana haɗa rai

"Lukman, Dr Lukman sunan shi"

"Ina jin ki, miye alaƙar ku?" ya faɗa yana ɗaga  ma ta gira. Nan ta fara bashi labarin soyayyar su da Lukman da yadda ƙaddara ta raba auren su.

"So kukan anga tsohon zuma kenan"

Kaman da gaske da Najeeb ɗin ta ke magana ta fara girgiza kai...

............................

Anas dai ya dawo amma kowa harkan sa ya ke. Ya ce ba zai sa hannun sa a maganar gasa ba. Farida ma ba ta damu ba tunda ya cigaba da ayyukan sa...

Mr Ogonna ya shigo yana washe ba ki " Madam an gama duk wani shiri, umurnin ki kawai ake jira"

"Ok, ka sa kowa ya hallara a hall" ...

Details ɗin tsarin gine-ginen da za a yi ta nuna a projector.
"Ba ni da masaniya kan harkan gine-gine amma kuma akwai wanda su ka jima a harkan kuma za su taya mu zaɓe. Akwai kyauta mai tsoka ga duk wanda aka zaɓi zanen sa. Sannan duk wanda ya shiga gasan kuma ko da ba a zaɓe shi ba, aikin sa ba zai tafi a banza ba domin akwai kyauta na musamman da za a bashi."

"Mr Ogonna zai gaya mu ku sauran baya nan" ta yi hakan ne saboda jiri da ta ji yana ɗiban ta. Da sauri ta bar wajen saboda za ta iya faɗuwa a wajen idan ba ta yi a hankali...

A ƙasa ta zauna dirshan saboda yadda ta ke jin kan ta na sarawa. Ta sani stress ne da yunwa ba komai ba. Gaskiya sai yanzu ta ganin jarumtar Najeeb, despite all this stress ba ya wani cin abinci mai yawa. Ta jima a zaune a wajen har sai da ta ɗan samu nitsuwa kafin ta je wajen fridge ɗin office ɗin ta buɗe. Maltina ta ɗauko ta fara sha saboda ko za ta samu ɗan ƙarfin jikin ta...

............... ..............

Wanda su ka shiga gasan zane da Farida ta haɗa, kowa ya shiga aiki tuƙuru wajen ganin zanen sa ya fi na kowa fitowa, kwana biyar aka ba su kowa ya kawo zanen sa. Anas kan ido ya zuba ma su dan bai yi kaman ya san ana wani abu makamancin wannan ba.
Su Mr Ogonna kam ganin Farida na tsoma shi cikin harkoki sai ya zaƙe yana ƙoƙarin ya ga an gudanar da komai lafiya saboda ya san ya kusa samun ƙarin matsayi.

Ranan da za a fitar da wanda ya ci kuwa ga mamakin kowa sai su ka ga manyan professors ne har uku a wannan ɓangaren Farida ta kira wanda connections ɗin Daddy ne ya sa su ka amsa wannan gayyata.

Cikin mutum sha uku da su ka submitting zanen su kowa ya yi ƙoƙari sai dai mutum huɗu aka fitar wanda na su ya fi fice. Arch Hassan yai na ɗaya sai Arch Bashir na biyu sai Arch Yakubu na uku da kuma Arch Thomas na huɗu, na biyar kuma Arch Bazu.
Bayan an ba su kyauta sannan taro ya watse. Farida sai da ta sake tattaunawa da professors ɗin nan kafin su ka tafi. Ranan da aka yi wannan abin ma Anas ko wajen bai leƙo ba, hakan ya sosa ran Farida amma ya za ta yi tunda yanzu gaba ya ɗaura ma ta ba gaira ba dalili...

Da yamma waɗanda su ka yi na ɗaya zuwa na uku su ka hallara a gidan Daddy. Chan wajen gazebo su ka haɗu su ka tattauna yadda za a haɗa kai a sake gyara zanen Arch Hassan, wanda although ko shekara bai yi da fara aiki da Najeeb constructions ba yaron ƙwaro ne kuma ana ji da shi. Sau biyu Najeeb na sa shi a team da su ka yi zanen wani project da aka ba su tare...

Duk wani aiki da su ke yi a ɓoye su ke saboda gudun munafukai. Dukkan su ukun sun haɗa kai kuma sun fito da abinda ya bada mamaki. Wannan karan ba wanda ya ga wannan zane a kamfanin.

........................

Baffa Musa ne ba lafiya shi ya sa ta je gida, rabon da ta je gidan ma ta manta. Jikin sa ya fara sauƙi dan kwana ɗaya yai a asibitin aka sallameshi, sai dai bai fara fita kasuwa ba.

"Farida kin gan ki kuwa?" Baffa Musa ya faɗa ganin yadda Farida ta dawo.

" anya za ki cigaba da wannan auren. Ance ma su laluran sa fa sai su ƙare rayuwar su a haka, wassu kuma ba su jimawa su ke mutuwa cikin dogon baccin na su"

Girgiza kai ta farayi tana hawaye.

"Wata uku da wani abu, anya zai tashi. Ƙarshen zuwa na fa yadda ya ke haka ya ke ba chanji"

"Baffa zan jira shi, ko shekara nawa ne, zan jira shi" ta faɗa tana fashewa da kuka. Tausayin Faridan ne ya kama shi. Shi yana ganin tunda ba auren soyayya su ka yi ba dama za ta iya haƙura da auren. Amma abinda idon sa ke gani yanzu ko da ace da Farida ba ta son mijin ta, to yanzu soyayyar sa ya ma ta mugun kamu. Dama miji da mata sai Allah...

***

"My Champ gobe za mu je Abuja, please be with me. Anas ya cire hannun sa ya bar min komai. But Alhamdulillah da taimakon Allah komai ya zo min cikin sauƙi". Ta ɗauko wayarta ta fara buɗe wajen hotuna sannan ta nuna ma sa hoton wani zane. "My love ga zanen mu, Allah shi ne gatan mu. Please be with me ka ji" ta manna ma sa kiss a lips ɗin sa...

Ta jirgi su ka tafi Abuja inda su ka sauka a gidan Uncle Abubakar, Daddy ne ya buƙaci hakan. Farida , Yakubu da Hassan kaɗai su ka tafi, su za su representing  Najeeb constructions.

Kwana uku za a gabatar da wannan bid ɗin. Saboda ba su yi register da wuri ba sunan kamfanin su ya faɗo a rana ta uku...

Lokacin da aka kira Najeeb constructions Farida ne ta fara tashi ta yi ƙaramin bayani kafin Hassan da Yakubu su ka buɗe modelling na su, su biyun ne su ka bada bayani kan yadda na su zanen ya ke da inganci da kuma sauƙi wajen tsari, tareda nuna yadda kamfanin su zai ba da mahimmanci wajen ganin ginin zai tafi dai-dai da yadda aka tsara.

Farida na zaune ne amma hankalin ta ba ya wajen tana kallon yadda Yakubu da Hassan ke bayani amma kunnen ta ba maganganun su ta ke ji ba. Addu'a ta ke yi a zuciyar ta, dan ta san idan su ka faɗi ba ƙaramin kunya za ta sha ba, sannan ga Anas wanda zai ma ta madallah Allah shi ƙara.

Ji ta yi an kamo hannunta, ta ɗaga ido da sauri dan ta ga waye, idon ta ya sauka kan Najeeb wanda ya ke ma ta murmushi.
"Take it easy Aysherh, I'm with you"  murmushi ta farayi hawaye na sauko ma ta...*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣3️⃣6️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©️
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*

Ranan Jumma'a aka ce za a sanar da wanda ya ci wannan gasa. Sun bar wajen da ɗan hope a zuciyoyin su, base on yadda aka yi mu su tambayoyi da kuma nuna jinjina garesu.

Su na zuwa gida lafiyar gado ta bi. Ɗakin Afrah aka ba ta su Yakubu kuma ɗakin baƙi. Tana kwance zazzaɓi mai zafi ya rufe ta. Tana kwance sai rawan ɗari ta ke Najeeb ya shafa fiskarta ya ce "sorry love, zazzaɓi ko?"
Ta gyaɗa ma sa kai. Ɗaukan jakan ta yai ya fito da wayanta da ke ciki ya danna numban Yakubu ya sa ma ta a kunne.

" Hello, Yakubu dan Allah ka  zo banda lafiya" ta faɗa tana tura wayan gefe.
Najeeb ba ya wajen ita ɗin ce dai ta ɗauko wayan.

Bai jima ba Yakubu ya shigo ɗakin, har lokacin tana rawan sanyi. Dai-dai lokacin wayan Faridan ya fara ringing Yakubu ya ɗau wayan ya ga Dr Lukman.
Amsa kiran yai su ka gaisa ya ke ce ma sa Farida ba lafiya zazzaɓi na damunta. Lukman ya ce ya turo ma sa address ɗin gidan zai zo.

Da su ka gama wayan ya kalli Farida ya ce " za ki iya jiran Dr Lukman ko kuma mu kai ki asibiti?"

Da ƙyar ta iya cewa za ta jira shi. Yakubu ya fita ya je ya sanar da mai aikin gidan akan ta haɗawa Farida tea...

Lokacin da ta buɗe ido Najeeb ta gani zaune yana karanta wani magazine.

"Sir Najeeb" ta faɗa a hankali

"Kin tashi, ya jikin?"

"My champ zan sha ruwa"  ta faɗa tana ƙoƙarin tashi duk da kuwa hannun ta da canula an ɗaura ma ta ruwa.

"Kwanta za'a kawo miki ruwan"
Riƙe rigan sa ta yi da ɗaya hannun da ba canulan ta ce "kar ka tafi ka barni my champ, zan mutu idan ka barni, please my love"

A hankali Lukman ya gyara ma ta kwanciya ya ce " ba zan bar ki ba"
Sai da ya ga ta sake komawa da bacci kafin ya fita daga ɗakin. Har yanzu yana son Farida, duk da kuwa ya sani sarai ya rasa Farida har abada. But seeing her like this breaks him. Tana tsananin son mijin ta, son da ta ke mishi ko lokacin da su ke soyayya bai yi tunanin ta ma sa rabin son da ta ke wa bawan Allah nan ba.

Sai yamma lis kafin Farida ta farfaɗo da kyau, ta dena ganin duk wanda ya shigo a matsayin Najeeb.
Bayan Isha ta fito falo saboda ta gajiya da zaman ɗaki da ta yi, kuma yanzu tana ɗan jin ƙarfin jikin ta.

Yakubu ne ya ce ma ta Mr Hafiz Olabode ya kira ta kuma ya ce su haɗu gobe ƙarfe tara na safe.

Yakubu ya ƙara da cewa "Mr Olabode yana ɗaya daga cikin wanda za su judging pitch ɗin nan. Na san ƙila cewa zai yi ki bashi wani abu dan ya voting zanen mu. Kin san yanzu komai ɗan bin ƙafa ne, ka bribing officials na Gomnati a baka contract"

Hassan ya ƙara da cewa "mu addu'a za mu musu amma gaskiya bribe ake bayarwa, wanda ya fi ba da kaso mai yawa a bashi"

Farida kan jin su ta ke amma ita kaɗai ta san mi ta ke ji...

Washe gari  tareda Yakubu su ka je wani classy restaurant da Mr Olabode ya ce su haɗu. Ɗan gefe da su Yakubu ya zauna.

Yadda su Yakubun su ka faɗa hakan ta ke Mr Olabode ya ce ma ta zanen kamfanin su na ɗaya daga cikin wanda ya burge su, sai dai idan tana so sun cinye komai gaba ɗaya to ta yi abinda ake yi.

Kai tsaye ta ce " ba kuɗin da zan bayar"

Mr Olabode yai murmushi ya miƙo hannun sa ya ɗaura akan na ta hannun yana faɗin "who is talking about money, when this heavenly beauty  here is everything..."
Saukan mari da ya ji ya sa sauran maganan su ka kafe a bakin sa.

Ba ta tsaya haka ba ta ɗau juice ɗin da ke gaban ta ta watsa a fiskan shege. Ta ɗau jakarta ta fita ta bar Mr Olabode da buɗe baki.
Yakubu na jin ƙaran mari ya kalli wajen da su Farida ke zaune. Tana tashi ya bi bayan ta da sauri.

"Kuɗi ya ce ki bashi ko?"

"Wani kuɗi kuma, kana ganin baƙin kwarto a wajen"

Yakubu ya ce "Allah ya shige ma na gaba amma na karaya"

"Indai har sai mun ba da cin hanci da mu ci gasan nan to na haƙura. Mu koma gida kawai, ma san yadda za mu ɓullowa su Mr Vladimir"...

Yammacin ranan Lukman ya zo duba ta. Ya ji daɗin yadda ya ga ta murmure sosai. Da ya je ma ya samu tana ta masifan abinda Mr Olabode ya ma ta ne. Wai har Mr Olabode mai kaman angulu shi ne zai kalleta ya tsaya yana ma ta maganan banza.    Uncle Abubakar ya ce " to ai yadda ƙasar na mu ta koma kenan. Give before taking ake yi"

Farida ta ce "dole ai ba za mu taɓa cigaba ba. Cin hanci da rashawa ya mana katutu"...

Sai da ta rako shi bakin mota sannan ya ce " so, yanzu gobe ba za ku jira ku ji result ɗin ba"

"Dr Lukman kenan, ka na ga bayan abin da na yiwa Mr Olabode za ma a saurare mu balle kuma ace mu mu ka ci gasa"

"You never know Aisha, ai ba shi kaɗai zai judging ba. Dan Allah ki je, ko da ba ku samu ba dai ya nuna kuna da jarumta you stayed till the end"

"Shi kenan" amma da ni na cewa su Yakubu gida za mu wuce gobe"...

Bayan Lukman ya shiga mota ya tafi sai ta ga Najeeb na tsaye ya harɗe hannun sa a ƙirji fiskar sa ba walwala.

"My champ lafiya ka haɗe rai? Ka min murmushi dan Allah"

"Aysherh ba na so, na ce ba na so" daga haka ta dena ganin sa ko na ce ya ɓace ma ta a idon ta...

Washe gari Jumma'a su ka je inda ake taron. Wassu ba su zo ba dan yanayin yadda ka ke jin kanada hope shi zai sa ma ka tsaya tunda dai mutum ɗaya ne zai ci.

Farida na zaune hankalin ta kwance ga Najeeb na gefen ta hannun su sarƙe cikin juna. Sai Yakubu da Hassan da kowannen su ya sha suit kaman a ranan za su yi pitching zanen su.

Mai gabatarwa ya gabatar tareda nuna jinjina ga duk wanɗanda su ka shigar da zanen su haƙiƙa kowannen su ya yi ƙoƙari. Amma akwai wani zane guda ɗaya  wanda ya ɗau hankalin mu ba wai dan ya fi na kowa ba sai dan yadda tsarin zanen ya tafi da zamani kuma still its just simple tradional design. Haƙiƙa wanda su ka tsara zanen nan sun yi ƙoƙari. Mafiyawancin lokuta abun da bashida yawan ƙyale-ƙyale shi ke ɗaukan hankali. To mudai wannan zanen ya ɗauki hankalin mu. Harta baturen da ke cikin mu Mr Briston ya yaba da wannan zane matuƙa kuma a karan kan sa ya bada kyauta ta musamman ga wanda su ka yi wannan zane. Kafin na cika ku da surutu za mu kira Mr Briston ya faɗi kamfanin da su ka lashe gasan nan.

Duk yadda Farida ta so daurewa sai da ta dinga jin ƙirjinta na bugawa da sauri-sauri.

Baturen Mr Briston ya hau stage ya fara bayani da turancin sa da ta ke kama da ta hanci ta ke fita.
Farida ba jin komai ta ke ba dan kunnen ta ya toshe a wannan lokacin.

Firgigit ta yi lokacin da muryan Mr Briston ya doki kunnen ta yana faɗin "we've selected the design presented by Najeeb Constructions company. I here by called on the team leader Mrs Farida Jibo of Najeeb constructions to come..."

Yakubu ne ya dafa kafaɗar Farida yana faɗin Alhamdulillah, 'yar uwa Alhamdulillah.

Ƙwaƙwalwarta ba abinda ke yawo ciki sai 'Najeeb constructions company'

"Farida ki tashi, ki tashi ana kiran ki" muryan Yakubu ya dawo da ita daga  nisan kiwon da ta yi.

Sai da ta miƙe tsaye Najeeb da ke wajen ya kalleta ya ce "ni ba na son ƙauyenci, walk with class and elegance Mrs Jibo"

Hannun ta ya kama ya ce mu je na raka ki. Tafiya su ke tana jin kan ta a sama, ga shi sun lashe gasa ga Najeeb a kusa da ita.
Yakubu da Hassan kam kallon yadda 'yar batalikan nan ke tafiya su ke. Tana tafiya kaman wanda ta ke jin tsoron taka ƙasa...

Akwai daɗi fa ka representing mijin ka a wani waje, musamman wajen da ake ganin kaman matan aure ba su da wani daraja da ya wuce su zauna a gida su yi girki.

Yakubu da Hassan kuwa Mr Briston kyautar kuɗi naira dubu ɗari biyu ya basu.

Ba ta taɓa jin daɗin a kirata da Mrs Jibo ba irin yau. Ko ina ta juya sai congratulations Mrs Jibo ake ta faɗi. Su na barin wajen Daddy ta fara kira dan tun jiya da ya kirata ya tambaya ko akwai wani haske, ce ma sa ta yi ita ta haƙura za su dawo gida kawai.
Daddy ya ji farin ciki sosai. Na farko 5% zai dawo hannun Najeeb sannan ga yadda kamfanin za ta sake samun ɗaukaka a ƙasar...

Da dare text ɗin Anas ya shigo
*congratulations, ba ni da bakin magana Farida. Kin ƙara tabbatar min da maganar Najeeb da ya ke yawan gaya min cewa 'duk inda akwai tsoro to babu nasara a wajen' Allah ya dawo da ku lafiya*

Farida ta yi tsaki ta ce daga baya kenan, wai anyi sadaka da bazawara. Haushin sa ta ke ji yanzu ko da ace bai so ta shiga gasan ba amma tunda ta riga ta shiga sai ya sa hannu ya taimaka wajen ganin an yi iya ƙoƙari akan abin. Amma ya bar ta tana ta wahala ita kaɗai.

Ba su dawo ba sai ranan Tuesday saboda sai da su ka tsaya ranan monday aka yi cike-ciken contracts document.
Daga airport da aka zo ɗaukan su cewa ta yi a wuce da su asibiti, kafin ta ga kowa sai ta ga lafiyan mijin ta.

Tare su ka wuce asibitin dan su ma rabon su da Najeeb ya fi wata ɗaya.
Tana shigowa ɗakin ta ga Sabreen tana kissing goshin Najeeb har da hawayen munafurci a idon ta tana faɗin.

"Noory i have to go, i'm sorry, but this movie means alot to me. I've always wanted to work Keanu Reeves and now i got the chance. Please forgive me. I'll come back for you after the shooting...."

Farida ta kama hannunta ta ja ta gefe. "Ba ya son jin komai daga gareki, so just go"

"If he wakes up Aisha, i'm going to do anything just to get him back. I promise"

"mtsssw aikin ɓur inji tusa. Ki wuce ki bamu waje karuwan banza karuwan wofi"

Sai da ta ɗau jaka ta tafi su Hassan su ka fara dariyan maganar ta.

Farida sai da ta goge wa Najeeb fiska kafin ta kissing ɗin sa tanajin haushin kissing ɗin da Sabreen ta ma sa.

"My Champ we got the contract, thank you for being with me"

Jin Farida ta manta da su a ɗakin ya sa su Yakubu su ka ma ta sallama su ka fita wanda ko iya amsawa ba ta  yi ba dan hankalin ta gaba ɗaya na kan hiran da ta ke yiwa Najeeb...

*i'm not feeling well, ba lallai ku samu update na dare ba amma zan ƙoƙarta*

*plz ranan da na yi magana akan mutane su acting maturedly wajen fita da labarin nan da su ke. Ba wai ina nufin na basu go ahead ko kuma license na fitar wa ba ne. Dan Allah kar ku forwarding min labari. Mu ji tsoron Allah plz abinda zan iya cewa kenan**SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣3️⃣7️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*

*na gode da addu'o'in ku Allah ya ƙara ma na lafiya gaba ɗaya.*

Tana tareda Najeeb, Anas da Daddy su ka shigo ɗakin.

"Masha Allah 'ya ta Allah ya mi ki Albarka" Daddy ya faɗa lokacin da ya ƙaraso.

Ta amsa da Amin tana murmushi.

"Son ka ga abinda matar ka ta yi ko? She is a fighter, she's a winner. Matar ka iron lady ce. Ka tashi ka ji, ka tashi ku gina rayuwar ku tare"  ya kissing goshin sa yana shafa gashin sa.

"Daddy Mom ta dawo?"

"Sai next week" ya amsa ma ta.

"Allah ya dawo da ita lafiya"

Su ka amsa da Amin.

Anas kam kunya ta hanashi magana sai kau da kai ya ke. Daga baya Daddy ya bar su ya ce zai je yai magana da likita.

"Ya hanya" Anas ya katse shirun na su.

"Alhamdulillah mun je lafiya mun dawo lafiya. Sauro bai cize mu ba haka Cinnaka ba ta cize mu ba balle ayi tunanin mun wahala. Kuma dai girma ya faɗi"

"Farida dan Allah ki yi haƙuri. Na san ba ni da hujja akan abin da na aikata amma ki yi haƙuri ki yafe mun"

"Ya Anas a nan ka zo ka roƙe ni Allah Annabi akan na zama CEO amma mi ka yi bayan na zama CEO. Ka bauɗe min, ka ƙi goya min baya har ka na ganin gara ka bar aikin da zama na CEO ko?"

"Ba haka ba ne Farida, kawai dai ba na so kamfani ta shiga matsala ne"

"Da kyau, saboda ga Aisha Farida mai farar ƙafa ko?"

"Duk abinda ki ka ce i deserve it. Ban riƙe amanar abokina ba, i'm truly sorry"

"Ka san mi ake cewa namiji matsoraci? To Ya Anas kai matsoracin namiji ne kuma ragon namiji. Idan ba ka dena sa tsoro a lamurran ka ba to ba inda za ka je a rayuwa. Kuma ko a gidan ka za ka samu matsala. Kana ganin da ina da tsoro zan kai yadda na kai da Najeeb, ka san da ni matsoraciya ce da tun ranan da Najeeb ya  koreni da na bar aiki a kamfani kenan. But i fight back, na nuna ma sa ni ba ƙwallo ba ne da zai dinga bugawa duk lokacin da ya ke so. Ka san miyasa Najeeb ya ka sa korata? Because he needs me. Najeeb na son mutum mai zafi, mutum da ba ya da tsoro ko kaɗan"

Ya ji haushin kiran sa rago da ta yi amma kuma gaskiya ta faɗa, sau tari ta inda su ke samun matsala da Najeeb kenan.

"Ki yi haƙuri dan Allah"

" na ji haushi kuma har yanzu ina jin haushin ka. Ka bani lokaci na huce tukunna"

"Ba komai, amma dan Allah ki yafe min"

"Na yafe"

Ba su sake wani maganan ba har Daddy ya dawo su ka tafi.

"My champ ka ga abokin ka ko, ka ganshi ko" ...

......................
Washe gari tana shigowa kamfani aka fara tafi, ana ma ta congratulations. 
Duk wanɗanda su ke ma ta wani gani-gani to yanzu sun sha jinin jikin su. Madam Farida kamar yadda yanzu aka fi kiran ta ta zama Boss lady. Tundaga lokacin da ta ƙarɓi matsayin CEO kowa ya shiga taitayin sa saboda ita ma zafi gareta kamar Najeeb. Wani zubin ma gara Najeeb ɗin dan shi idan ya ma ka tsawa shi kenan amma wannan sai ta bika da baƙar magana wani lokacin idan ta yanko ma ka magana sai ka ji kamar ka kama kai ka rusa kuka.
Ga wanda ya bita sannu kuma tana da sauƙin kai...

Su Mr Vladimir bayan ya tabbata Farida ta leading team kuma anci gasa ba ƙaramin baƙin ciki su ka yi ba. Neman sulhu su ka fara yi dan kar su rasa 5% da au ka yi alƙawari amma kuma Farida ta ce bata san zance ba. Su su ka faɗi sharaɗi kuma dole su bi shi yadda ya ke. Haka dai ba tareda sun so ba su ma sa hannu a takardar da ke shaidar sun ba da 5% shares ɗin su a Najeeb. Ranan Farida sai da ta yi hawaye saboda hango farin cikin da ta yi a idon Najeeb idan ya farfaɗo ya ji abinda ta yi...

......................

Gidan AbdulWahab kam yanzu zaman lafiyan ba kamar da ba. Tunda Aneesa ta dawo Lagos da aiki sai komai ya chanja. Kullum cikin taƙalar Maijiddah ta ke yi, duk da ma yanzu Maijiddan ta dena tsoron ta kuma ta na ɗan maida ma ta magana amma still wassu lokutan shiru ta ke ma ta. Aksarin lokaci Maijiddah tana burin inama ace itama ta iya magana kaman Farida da za su dai-dai ta tsakanin ta da Aneesa.

Haka kawai ta hana yaran shiga harkan ta, duk da yaran na so amma abinka da uwa da ɗa sai ya zamana ta yi musu tsawa shikenan. Ɗan gara ma Alizah wani lokacin tana ƙin bin umurnin Maman na su.

AbdulWahab na iya ƙoƙarin yin adalci tsakanin su duk da ma yanzu Maijiddah ta fara ganin chanji a tattare da shi lokacin da Aneesa ta dawo. Tana renon cikin ta lafiya  amma wani lokacin gani ta ke tunda Aneesa ta dawo kaman yanzu AbdulWahab ya rage ba ta kulawa da kuma ɗokin cikin da ta ke ɗauke da shi.
Cikin ta na wata bakwai Aneesa ta fara laulayin ciki. Ta gano hakan ne ranan su na zaune suna cin abinci ta fita da gudu tana amai a banɗakin da ke guest room.
Daga baya kuma Aneesan ta fara tsirface-tsirfacen abubuwa irin na ma su ciki.

Lokaci guda hankalin AbdulWahab ya koma kan Aneesa. Ranan su na cin abinci da ke Maijiddan ne ta yi girki, Aneesa ta fara kushe abincin akan an hana ta yawan cin mai a asibiti kuma ga shi abincin Maijiddan ya cika mai.

"Sweetheart ba ka gaya ma ta abinda likita ya ce ba ne?" Ta faɗa tana kallon Maijiddah.

"Anny zan gaya ma ta ba yanzu ba akwai yara a nan"

"Na san ba za ka iya gaya ma ta ba. To Malama Maijiddah ciki ne da ni kamar yadda ki ka sani, kuma likita ya ce saboda mahaifata tana da rauni na guji aikin wahala da yawan stress na kuma rage cin wassu abubuwa saboda kar cikin ya zube. Sai ki kiyaye nan gaba"

Maijiddah ta buɗe baki da hanci tana ganin wannan cin fuskan. Ƙarin haushin ma AbdulWahab bai yi magana ba.
Ajiye cokali ta yi ta bar wajen. Da ya ke kwanan ta ne AbdulWahab da ya zo sai ya ke ƙara gaya ma ta report ɗin da likita ya ce gameda cikin Aneesa.

Haushi ya kawo ma ta har wuya, ka sa shiru ta yi ta ce "amma Abban Alizah ni ma fa ciki gare ni kuma ko da babu likitan da ya gindayamin sharaɗi, dai a matsayin da na ke yanzu ina buƙatar kulawa ta musamman"

"Hauwerh dont get me wrong please, ba wai ina nufin ke baki buƙatar kulawa ba ne..."

"Sai yanzu na gane gaskiya. Dama saboda matar ka ba ta nan ka auro ni, to yanzu ta dawo ban da matsayi ko?"

"Shhhhh, kar ki sake faɗin haka Hauwerh ki na da matsayi babba a rayuwata"

" a rayuwar ka haka ne amma a zuciyar ka Anny ce kaɗai"

Kamo hannun ta yai ta wafce hannun.

"Plz Gimbiyata, ki yi haƙuri. Ki na da matsayi a zuciyata da rayuwata gaba ɗaya"

Ranan dai AbdulWahab da ƙyar ya shawo kan amaryar sa...

.....................

Ko mi zai  ma ta ba za ta koma Lagos ba. Gara ya dinga zuwa yana dubata duk ƙarshen wata.  Ta bar mu su waje su sakata su wala yadda su ke so. Sai da motar su ta ɗau hanya sannan ta jingina kanta da seat tana hawaye. Babbar motar Macapolo ta shiga da zai je Kano daga Lagos. Duk da kasancewa dare ne hakan bai sa ta ji wani fargaba ba. Su na tafiya tana tuno maganganun AbdulWahab...

Sai da su ka dawo daga asibiti sannan ya je ɗakin Maijiddah dan ya bata haƙuri tsawan da ya ma ta ɗazu. Ya sani sarai bai kyauta ma ta ba. Duk abinda ya faru bai kamata ya gaya ma ta magana haka ba.
Wayam ɗakin ba kowa. Ya duba ko ina ba ta nan. Mai aikin su dama ba ta nan ta yi tafiya. Fita yai ya je ya samu mai gadi inda ya sanar ma sa Maijiddah ta fita. Faɗa ya fara ma sa akan miyasa zai barta ta fita ita ɗaya da tsohon ciki. Maigadi ya ce shi ya je ya samo ma ta taxi ma domin kuka ta ke yi ta ce an musu rasuwa ne za ta je gida kuma kai ka ce ta tafi saboda kun fita da Madam Babba.
Tsaki yai ya koma ciki. Ya kira numbarta sau ba adadi amma a kashe. Ba dai Maijiddah gida ta tafi ba.
Aneesa na kwance sai nishi ta ke ita a dole ta yi ɓarin ciki kuma kishiyar ta ce sanadi. AbdulWahab ya shiga tashin hankali sosai ina ya san zai nemi Maijiddah da daren nan...

Washe gari da safe ya samu labarin ta shiga mota ta tafi Kano. Kiran Hajiyar sa yai dan ya ji ko ta iso sai ya ga Hajiya ba ta ma sa maganar ba sai ma tambayar sa da ta ke ina Maijiddah. Sai alokacin ya waske da cewa ai tana hanyan Kano ma yanzu.

"Ko kai fa amma ka ce wai ta zauna a chan ta haihu"

Dama Hajiya Yelwa ta nemi ya bar Maijiddah ta haihu a kano ya ƙi shiyasa ba ta kawo komai aran ta ba.

Ƙarfe goma na safe su ka isa Kano inda direct gidan su mijinta ta wuce. Yanayin yadda Hajiya Yelwa ta ganta ya sa ta gane ba tafiyar jirgi ta yi ba.

"Lafiya Hauwa na ga kin kumbura, duba ƙafafuwan ki"

"Ba komai Hajiya zama ne kawai ya sa yai haka"

Hajiya Yelwa ta kira AbdulWahab tana ma sa faɗa akan barin Maijiddah da yai ta zo ita ɗaya sannan a mota ba a jirgi ba.

Hamdala yai lokacin da ya ji Maijiddah ta isa gida lafiya. Ya bawa Hajiya haƙuri akan ayyuka su ka ma sa yawa.

"Hajiyata ki ɗan bawa Hauwa wayar na kira numbar ta baya shiga ina ga wayan ya mutu ne"

Hajiya ta miƙawa Maijiddah wayar wanda ganin idon Hajia ya sa ta karɓa.

"Haba Hauwerh kin min adalci kenan, idan wani abu ya same ki fa."

"Na isa gida lafiya a gaida marar lafiya" ta kashe wayan saboda Hajia ta fita a ɗakin...

Kwanan ta na uku sai ga AbdulWahab. Tana zaune tana cin abinci a ɗakin Hajia sai ga shi ya shigo.
Ganin sa da ta yi sai da ta ɗan yi jim amma ta dake.
Zuwa yai ya zauna gefen ta ya kamo hannunta ɗaya ya ce "Gimbiya ta haka kike da zuciya dama. Haba dan Allah, kin san ina son ki kuma ba zan taɓa yin abinda zai ɓata miki dai ba"

"Amma ai ka yadda ai lokacin da matarka ta ce na  tureta ta faɗi. Na yi sanadiyar rasa cikin ɗan Lele ko"

"Na san na yi kuskure Gimbiyata a min haƙuri"

Namiji dai da daɗin baki haka ya gama kwantar ma ta da hankali da kalamai ma su daɗi. Dole dai ta miƙa wuya ta haƙura ƙarshe ma ita ta koma tana bashi haƙurin kan tahowa da ta yi cikin dare ba tareda ya sani ba...
Washegari ya tafi dan ya san tunda ta riga ta zo sai ta haihu tunda dama tun farko Hajiya Yelwa ta nemi hakan...

.......................

Sati biyu da zuwan Maijiddah kano ta haifo santalelen ɗan ta mai kaman uban sa. Haihuwan nan ya sa Aneesa ta tada daru akan AbdulWahab dole ya bi ma ta hakki tunda Maijiddah ce ta yi sanadiyar zubewar cikin ta. Shi kam bai biye ma ta ba dan sai a lokacin yake ganin wautarsa ranan. Domin ya san Maijiddah ba ta da faɗa kuma yadda ta ke ɗan jin tsoron Aneesa haka kawai ba za ta tureta ba dan dai maganar fatar baki. Balle Maijiddah na da tsohon ciki ita kuma Aneesa cikin ma wata biyu ne.
Ana saura kwana biyu suna ya tattaro yaran sa su ka zo Kano. Aneesa kam Abuja ta wuce ta ce ba za ta je sunan ba...

Daga gidan suna ta wuce asibiti.

"My Champ ka ga babyn Maijiddah kuwa? Wallahi kyakykyawa da shi. Ka tashi muma mu yi abubuwa na samu ciki na haifi Baby mai kaman ka. Ka ji miji na"
Ta ƙara kissing hannun sa tana faɗin "sunan Babyn na su Muhammad Al'amin, nima My Champ ina son suna Muhammad. Sunan ɗan mu na farko kenan Insha Allah"...

Ƙarƙashin jagorancin Madam Farida Najeeb Constructions ta samu cigaba sosai kuma an samu gyararraki kan abubuwa dayawa.
Yau ma wassu baƙi ta ke meeting da su da su ka zo daga Kaduna.

Tana shiga office ɗin ta Anas ya shigo.
"Farida ba ki sa hannu a wannan takardan ba"
Ya miƙo ma ta wani takarda. Ta ƙarɓa ta yi signing sannan ta miƙa ma sa.

Tana zama sai ga kiran sakatariyar ta.

"Hello Madam, Mr Rayyan Abdullahi is here to see you should i send him in?"

"Rayyan Abdullahi?"...

Mi Rayyan zai zo yi wajen ta. Rabon ta dashi tun ranan da ya zo office ɗin ta Najeeb ya ma sa kora da hali...*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣3️⃣8️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*

"Faridah" muryan Rayyan ya doki kunnen ta. Ta ɗan ɗago ta kalleshi, kallonta ya ke yi mai cike da ma'anoni.
Da yatsar ta ta ma sa nuni da ya zauna ba tareda ta kalle shi ba. Har ya zauna bai ɗauke idon sa a kan ta ba. Ita kuwa tunda ta ɗago sau ɗaya ta maida kan ta ga  takardun da ta ke dubawa.

"Farida" ya sake kira

Ta ɗago kai tana juya biron da ke tsakanin yatsunta biyu.
"Mr Rayyan what can i do for you?"

"Farida ni ɗin, ni ɗin ne Mr Rayyan" ya faɗa yana nuna kan sa.

" ok to Malam Rayyan mi zan iya ma ka"

"Lallai duniya!"

"As you can see aiki na ke yi. Idan ba ka da abin faɗi dan Allah ka ƙara gaba"

Jijjiga kai yai sannan ya ce "ya jikin Mijin ki?"

"Alhamdulillah da sauƙi"

"Stop pretending Farida, waye bai san halin da Najeeb ya ke ba a garin nan. He's being in coma for months now, ba alaman zai farfaɗo balle..."

"Balle me? Balle me?" Farida ta daka masa tsawa.

"Kwantar da hankalin ki Farida ba faɗa na zo ba. Ina so ki sani cewa har yanzu ina son ki kuma ina son auren ki. An sa aure na da mai sunan ki nan da 2 months. Amma na roƙi Umma ta bar ni na aure ki bayan na auri 'yar uwata Aishatu kuma ta amince. Kin ga by the time kin gama iddah sai mu maida auren mu"

"Ban san ka da shan giya ba Rayyan, ko dai ka fara ne bayan rabuwar mu?"

"Farida ke kan ki kin san har yanzu ina son ki..."

"Rayyan idan ba giyan wake ka sha ba ya kamata ƙwaƙwalwar ka ta gaya ma ka ni matar aure ce, ni matar Najeeb ce"

"Wanni Najeeb ɗin, Najeeb da ke chan kwance kamar gawa. How long has it being, kusan 8 months fa"

"Yes Rayyan. Yana chan kwance for 7months 9 days, kuma zan jira shi ko da zai ɗau shekaru kafin ya farfaɗo. I love him and i will wait for him till the end of my life. Get that into your thick skull Rayyan"  ta faɗa tana miƙewa tsaye.

"Far..."

"Leave!" Ta daka ma sa tsawa

"Farida ki..."

"Get out! Ka fita na ce!" Yadda ta yi tsawan wannan karan sai da ya ɗan tsorata.

Ba tareda ya sake yunƙurin magana ba ya tashi ya fita.

Zama ta yi ta fashe da kuka. Miyasa kowa ke ganin Najeeb ba zai tashi ba, miyasa su ke ganin a haka zai ƙarasa rayuwar sa. Haka jiya da su ka yi waya da Ummi ta ke ce ma ta ance ba lalle Najeeb ya farfaɗo ba, ko za a raba auren su. Miyasa ita ba ta gaji da jiran sa ba amma su sun gaji. Akwai wanda ta farfaɗo daga coma bayan shekara ishirin, ko da Najeeb zai shekara ishirin a haka za ta jira shi. Balle ta san ya na chan ya missing ɗin ta yana ƙoƙarin dawowa gareta...

.....................

A gajiye ta shigo ɗakin na su saboda aikin abincin sadaka da su ka yi. Duk Jummu'a ita ke zama da su Adama su girka jollof rice da naman rago su sa a take away guda dubu a kai wa almajirai da mabuƙata. Kullum sun sa ana mu su sadakan kunu da ƙosai da Masa.
Mom ma ba a barta a baya ba wajen sadaka. Ranan su Adama su ka tayata fitar da kusan duka kayayyakin ta da ke closet, wassu kayan ma ba ta taɓa sakawa ba, ga su kaya ne ma su matuƙar tsada, ta sa aka rabar sadaka. Mutum goma ta biyawa Umurah da lokacin azumi. Shi Daddy kam ba irin sadakan da yai Allah ne kaɗai ya san adadin sa. Ba wai dama ba ya taimako ba ne, amma abinda ya faru ya sa ya ƙara buɗe hanyoyin taimakon al'umma...

A Desk ɗin sa da ya ke zama yai aiki idan yana ɗaki ta zauna. Wani brown envelope ta gani, ta jawo shi. Wayoyin Najeeb ne guda biyu a ciki. Sai yanzu ta tuna cewa ita ɗin ce ta saka a wajen ranan da Anas ya kawo ma ta. Anas ya sa an buɗe wayan domin a duba wassu saƙonni. Ko lokacin da za aje Bank da Court wajen authorizing signature ɗin ta ya zama bayan Najeeb da Anas har da na ta signature ɗin wajen sarrafa abubuwan Kamfani har da wayan nan aka je. Ta tuna sai da ta yi rantsuwa a kotu sannan aka gama haɗa komai, abin tausayin ma maimakon signature ɗin Najeeb dole thumb print na sa aka sa.
Ranan da Anas ya kawo wayan tunda ta ajiye su a kan table ɗin ba ta sake bin kan su ba.

Ta ɗauki babban wayan ta kunna. Hoton sa ne a screen ɗin duk da ma screen ɗin ya ɗan tsatstsage. Ta ƙurawa hoton sa ido, ta sa hannu tana shafa kyakykyawan fiskar sa. Ta shiga gallery tana kallon hotuna wanda yawanci hotunan zane-zane ne, sai wani folder wanda hotunan Najdah ne da hotunan sa wanda su ka ɗauka da Anas wassu kuma da Daddy. Allah sarki ya yi hoto da yawancin 'yan uwan sa amma ba hoton Mom ko guda ɗaya a wayan da ta gama ta koma kan text messages ta ga duk yawanci alerts ne sai saƙonni na ma'aikata ko clients.
Ɗaya wayan ta kunna, wannan kam da ta shiga gallery ɗin hotuna biyar kacal ta gani aciki. Hoton farko na Mom ne tana budurwa kaman ma ranan aure ne dan ta sha ado na gwalagwalai da dimond ga shi kayan da ta sa wani kaman bridal dress ne kalar pink. Sai ɗaya hoton kuma Mom ne da wani ɗan yaro a gaban cake. Ta zooming hoton sosai sai ta ga a jikin cake ɗin an rubuta *Najeeb is one*. Dariya ta fara tana ganin yadda Najeeb ya ke so cute har da murmushin sa a hoton.
"Ayya! Miji na yana ɗan yaro"

Ta jima tana kallon hoton kafin ta tura zuwa hoto na gaba. Wannan hoton family picture ne kaman a Birthday ɗin Najma ne lokacin tana shekara shashida. Mom, Daddy, Najma, Najeeb da kuma wata budurwa wanda ba ta gane ko waye ba ce. Hoto na huɗu ma na wancan budurwan ce, tana murmushi ta sa graduation gown ta ɗaga hulan sama. Cikin ranta ta ce kowaye ce wannan tana da muhimmanci a rayuwan Najeeb, cikin ran ta ta ke tunanin ko budurwan nan babban yayar su Najeeb ɗin ce? To amma kuma Anas ya ce 'ya'yan Daddy uku ne. Hoto na biyar da ta gani sai da ta miƙe tsaye. Ƙwaƙwalwanta ne ya shiga tunani, jijiyoyin jikinta suka fara guje-gujen kai saƙo domin su taimakawa ƙwaƙwalwar ta yi bincike cikin gaggawa. 

"Na tuna, Wallahi na tuna" ta faɗa da ƙarfin ta...

Watarana sun fita supervision aiki wani waje.  Tana gefen Najeeb yana magana da wassu sai ga wani mai saida cucumber a wheelbarrow. Wassu ma'aikata su ka nufe shi su na siya. Yadda mai cucumber ke yanka ta yana zuba yajin ƙuli sai ta ji yawun ta ya tsinke.

"Sir Najeeb ina zuwa" ta faɗa tana barin wajen da sauri. Zuwa ta yi aka yanka ma ta cucumber ta ɗari, ga albasa da aka yanka siri-siri da shi abin gwanin sha'awa. Tun a wajen ma ta ke ta haɗiyan miyau. Ta ƙarɓi ledan ta bi bayan Najeeb da ɗan sauri-saurin ta saboda ya nufi wajen da motar sa ta ke. Tana shiga motar ta buɗe ledar, ƙanshin albasa da ƙarago ya cika motar. Maimakon ya tada motar sai ya tsaya yana kallon ta yadda ta ke sa hannu tana cin cucumber.
"Kai! yajin nan ba ƙaramin maggie ya ji ba" ta juyo ta kalli Najeeb da ya zuba ma ta ido.
"Sir Najeeb za ka ci ne?"

"Miss Salihu..." sai kuma yai shiru ya tada motar

"Sir Najeeb ka san ba na iya juran yunwa, ga shi tun ɗazu mu ke ta yawo cikin rana"

Bai kulata ba ya maida hankalin sa ga tuƙi da ya ke yi.

"Sir Najeeb Allah ka ci, kasan ance maza su dinga cin cucumber saboda yana ƙara mu su ruwa" ta yi saurin riƙe bakin ta jin abinda bakin ya riga ya faɗa

Ɗan juyowa da yai ya kalleta ya sa ta ce "Sir Najeeb ka ji mi na ce ne?"

"Wani irin ruwa?" Ya faɗa ba tareda ya kalleta ba.

"Nima ban sani ba, kai namiji ne ai ka san irin ruwan ai"

"Ke kuma mace da ki ke ci mi zai ƙara mi ki?" Ya faɗa yana kallon ta.

Basar da zancen ta yi ta ce "tunda ba za ka ci ba shikenan"

Wajen traffic light da su ka tsaya ta cigaba da cin abinta. Hoton da ya ɗauka daidai ta kai cucumber baki ne.

Rungume wayan ta yi tana dariya. Wani daɗi takeji a duk ilahirin jikin ta, rabonda ta ji daɗi haka tun ranan da su ka ci gasa. Kai ya ma fi. Hoton ta a wayan Najeeb, duk da ma ta san ya ɗau hoton ne dan ya dinga dariya saboda ga bakinta cike da abu kuma ga shi ta kai hannu tana son ƙara cusa wani cucumber.

"I love you Najeeb, I love you" yanzu kam ta yadda ko ba so bane to Najeeb yana jin wani abu gameda ita...

Wajen message ta shiga tana duba saƙonnin wayan wanda ba su da yawa kaman ɗaya wayar.
Text ɗin da ta ci karo da shi an tura wa wani number da aka saving da *Aysherh* ne ya tsaya ma ta a rai. Duka texts ɗin sai da ta bisu ta karancesu. Ta gane text ɗin amma kanta ne ya ɗaure. Numban Ayshern ta duba wanda ya sa numfashin ta ya tafi hucin gadi na 'yan daƙiƙai.

" N-J, Sir Najeeb shi ne N-J" ta faɗa tana dafa ƙirji.
Sai yanzu ta gane shirmenta na baya. Tana ta neman ma su suna da ya fara da N a kamfani bayan ga mai Kamfanin nan da ke da sunan NJ
"N-J, Najeeb Jibo" ta furta tana dariya kaman wata zararriya.

Its true kenan abinda Anas ke faɗa. Najeeb has feelings for her. Zama ta yi tana tuno abubuwan da su ka faru tsakanin su tun daga farkon fara aikin ta da shi har ƙarshen haɗuwar su.  Duk wani abu da zai yi hinting feelings ɗin Najeeb sai da ta zaƙulo shi...

Tana cikin mota ma sai murmushi ta ke wani lokaci kuma sai ta yi dariya. Hatta Dreban ta Abdullahi sai da ya tsargu ko Madam ɗin na sa ƙalau ta ke yau ɗin.

"Hajiya amma dai lafiya?"

"Lafiya Malam Abdullahi" ta amsa tana sake duba hoton da Najeeb ya ɗauketa.

Ba su yi nisa da gida ba Daddy ya kirata akan ta zo gidan Hajiya Mama. Ta so ta ƙarasa asibiti ta ga mijinta ko da na minti ɗaya ne amma dole ta bari ta gama da komai dan ƙilan idan ta je wajen sa ba za ta iya barin gefen sa ba yau.
Cewa ta yi Abdullahi ya kai ta gidan Hajia Mama...

Ta san Hajia Mama ba lafiya tun kwanaki to amma kusan sati kenan da aka sallamota daga asibiti. Rabonta da 'yar tsohuwan ma kusan kwana takwas, tun tana asibiti rabon ta da ita.

Gaskiya 'Yar tsohuwa na jin jiki dan yadda ta ganta ba ƙaramin bushewa ta yi ba. Tana kwance akan gado su Mom, Daddy, Uncle Sulaiman da Hajia Fatima su na kewaye da ita.

Har ƙasa ta tsugunna ta gaida su, kafin Daddy ya ce "Mama ga Aishatun na ki ta zo"

Hajia Mama ta ɗan miƙa hannu tana yiwa Farida alamar ta zo. Farida ta ƙaraso ta tsugunna a bakin gadon tana riƙe hannun Hajia Maman.

"Aishatu ce ko?"

Hajia Fatima ta ce "e ita ce, ba kin ce a kira mi ki matar Najeeb ba"

"Najeebullahin ya tashi ne?"

Farida da idon ta ya ciko da hawaye ta ce "zai farfaɗo Insha Allahu Hajia"

Hajia Mama ta ɗan yi murmushi, ta san Allah bai bata haihuwa ba amma ya bata 'ya'ya da jikokin da za su tuna da ita bayan rai yai halin sa.

Akwai wani awarwaro kaman bangle na zallan azurfa da ke hannun Hajia Mama. Ko su Daddy da shi su ka tashi su ka gan ta. Ba su  taɓa gani ta cireshi ba.

Hajia Mama ta sa hannunta ta cire awarwaron azurfan ta miƙawa Farida.
"Mutane dayawa sun nemi na bar mu su wannan awarwaron amma na ƙi, kin san miyasa na baki?"

Farida ta girgiza hawaye na zubowa a idon ta.

"Na yiwa Najeebullahi alƙawarin zan bawa matar sa awarwaron nan..."

Tari ne ya ƙwace ma ta. Ta jima tana yi kafin ta cigaba.

"Kyautar budurci ne, tundaga ran da Alhaji ya sa mi ni a hannuna ban taɓa cire shi ba sai yau. Ki riƙe shi da daraja"

"Insha Allah Hajia" ta faɗa tana sa awarwaron a hannun ta.

"Allah Sarki Najeebu na. Allah ya tashe ka"

Kowa a wajen sai hawaye.

Mom ta taso ta durƙusa gefen Farida da ke sheshsheƙar kuka.

"Hajiya" Mom ta faɗa cikin raunatacciyar murya

"Nabilatu ce"

Mom ta gyaɗa kai.

"Ki yafe min dan Allah. Najeeb ya yi gaskiya ni ba uwa ta gari ba ce, ranan da Aisha za ta rasu ta kira ni sau biyar, kuma daga jin yadda take nishi na san tana jin jiki amma kishi ya rufe min ido ban je na taimaketa ba, ban kuma kira an je an taimaketa ba har ta haihu ita kaɗai ta rasu ba kowa a wajen ta. Ki yafemin"

"Allah Sarki Najeebu ashe dai dalilin da ya sa ya ke gudun ki kenan. Na yafe miki, ai dama sababin mutuwar Aisha rubutacce ne tun kafin ta zo duniya. Allah ya yafe mu gaba ɗaya. Na yafe wa kowa"

..................

Duk wani ɗokin zuwa asibiti da ta ke sai ta ji ya fita a ranta. Tana so ta tsaya da tsohuwar nan wanda ta ke cike da tarin barkwanci.
Ranan ba ta bar gidan ba sai taran dare. Da ta je ma kuka ta dinga yiwa Najeeb tana nuna ma sa awarwaron da Hajia Mama ta bata...

Da asuba bayan ta yi sallah ta yi azkar ta ɗau alƙur'ani ta zo saitin kunnen Najeeb tana karanta ma sa kamar yadda ta saba. Da ke asabar ne ba za ta je aiki ba. Kusan ƙarfe shida da rabi sai ga kiran Mom akan Allah ya yiwa Hajia Mama rasuwa tsakar daren jiya, tun daga wajen ta fara hawaye...

Tareda ita aka yi karɓan gaisuwa har na kwana uku. Cikin kwanaki ukun nan sau ɗaya ta ke zuwa duba Najeeb...

7days later

Daren ranan jummu'a tana zaune akan kujera tana karatun ƙur'ani bacci ya sace ta. Tana bacci ta yi mafarki Najeeb ya farka yana kiran sunan ta. Da murmushi ta buɗe ido lokacin da ta farka. Haka kawai sai ta tsinci kan ta da zuwa dubashi ko dai da gaske mafarkin ta zai zama gaskiya.
Ƙura ma sa ido ta yi, kaman a mafarkin sai ta ga gashin idon sa yana ɗan rawa, chan kuma sai idon ya buɗe, ido ta zaro ganin idon sa ya buɗe. Sake rufe idon yai ya sake buɗewa a karo na biyu a karo na uku kam da ya buɗe bai sake rufewa ba.

Farida da ta yi suman tsaye na ɗan daƙiƙai ka sa yarda da abinda idon ta ga gani ta yi ta fara murza idon ko dai har yanzu bacci ne a idon ta. Ganin idon sa a buɗe ta mari kumatun ta da ƙarfi dan ta tabbatar dai ba mafarki ta ke ba. Bakin sa ta ga yana motsawa kamar zai yi magana amma bakin ya ma sa nauyi. A hankali ta ƙarasa wajen sa hannun ta na rawa ta kai yatsar ta kaman za ta sa a idon sa sai ta ga ya fara ƙyafƙyafta idon.

"Sir Naj..." maganar bai ƙarasa fitowa ba ta faɗi wajen a sume...

*Team Najeeb ku sha rawan shoki wannan page na ku ne*

*ku yafe min dan Allah ban turo da rana ba kaman yadda na ce**SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣3️⃣9️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

   𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*

Yana son ɗaga hannun sa amma hannun ya mai nauyi banda yatsun sa da su ke motsi ya kasa ɗaga hannun sama. Da farko baƙi ya ke gani daga baya kuma ya ci karo da idon mutum. Ba zai iya cewa ya san mai idon ba hakanan kuma ji ya ke kaman ya jima yana kallon mai idon. Ƙaran na'ura da kuma abubuwan da ya ga an jona ma sa a ƙirji ya tabbatar ma sa a asibiti ya ke. Ƙoƙarin tuno dalilin da zai kawo shi asibiti ya ke amma ya kasa. A hankali ya fara ƙoƙarin tursasa ma ƙwaƙwalwar sa domin ta gano abinda ya kawo shi asibiti. Yana so yai magana amma ya kasa, haka ya cigaba da kallon sama still yana ƙoƙarin gano miya faru da shi da kuma inda ya ke.

Tun ƙarfe huɗu na dare sai ƙarfe biyar da kwata ta farfaɗo. Initially ƙwaƙwalwarta bai tuno ma ta miya faru ba, amma cikin rabin sa'a da ta tuno abinda ta gani sai ta yi wuff ta tashi.
Har lokacin idon sa a buɗe ya ke.
"Da gaske Sir Najeeb ka farfaɗo?" Ta faɗa tana shafa fiskar sa.
Da yana da bakin magana da zai tambayi dalilin taɓa shi da ta ke.
Dariya ta ke, murmushi da kuma kuka duk a haɗe. Ta jima tana kissing kumatun sa duka biyu kafin daga bisani ta ankara ko Sujudish shukri ba ta yi ba.
Ta gyara ɗaurin ɗankwalin ta sannan ta yi kabbara ta yi sujjada. Bayan ta ɗago da gudu ta je wajen jakarta ta fito da waya, ba za ta iya barin ɗakin nan ba. Idan ta fita zai iya rufe idon sa ya ƙi buɗewa.
Numban Daddy ne a kusa dan haka shi ta kira, har wayan ya katse ba a ɗauka ba. Ba ta yi ƙoƙarin sake kira ba sai ta kira numban Mom. Sai da ta kusa yankewa kafin aka ɗauka.

"Hello Mom ya tashi, ya tashi mom. Idon sa a buɗe har yanzu, Mom ku zo ya tashi" wassu maganganun ma ba ta san ta yi su ba dan abin na ta har da shirme.

"Najeeb ya buɗe ido?" Mom ta tambaya da mamaki

"Yes Mom wallahi idon sa a buɗe  ya ke har yanzu"

"Muna zuwa yanzu ki kira likita" har za ta ajiye wayan sai ta kuma cewa "Aisha dan Allah ki turomin hoton ɗana na gan shi"

"Yanzu ma kuwa Mom"

Tana katse kiran ta shiga camera ta fara video ɗin Najeeb.
Shi kan kallon ikon Allah kawai ya ke yi yana ƙyafta ido. Bai san me wannan matar ke yi ba, ihun da ta ke ma ya sa bai gane maganganun da ta ke faɗa.

38sec video ta turawa Mom wanda ta ke saukowa daga stairs. A ƙasa ta haɗu da Daddy daya dawo daga masallaci.

"He's awake, our son is awake" ta faɗa tana fashewa da kuka.
Karɓan wayar da ta ke nuna ma sa yai ya kunna video ɗin, and there it is, idon ɗan sa Najeeb a buɗe har yana ƙyafta ido.

"Alhamdulillah, Alhamdulillah" ya faɗa yana mai sujudi. Mom ma ganin haka ita ma ta bi shi ta yi sujjadar...

Tana turawa Mom video ta fara kiran numbar Dr Sadiq da ke shima na masallaci bai ɗauka ba, sai ta kira Dr Johnson, shi kam ya ɗauka amma ya sanar ma ta baya asibitin ta kisa Dr Usama. Duk ma su kula da Najeeb tun daga doctors zuwa nurse tana da numbobin su. Hatta cleaner da ke zuwa gyara ɗakin musamman idan bata nan tana da numban su...

Kusan minti shida sai ga Dr Usama ya shigo.

"Doctor ka gani ko, ka gani idon sa a buɗe ko?"

Wanni na'ura ya ɗauko mai kaman torchlight ya fara haska idon Najeeb da shi. Farida na gefe tana sauke numfashi.
Duk wani response na ido Najeeb ya yi. Ya ci first step a cikin glasglow coma scale da ake yiwa wanda su ka farfaɗo daga coma.

"Ka na jina?, are you hearing me?" Dr Usama ya faɗa

Najeeb sai motsi ya ke da baki amma maganar ta ƙi fitowa.

"Idan kana jina ka motsa hannun ka" ya faɗa yana kallon hannun.
Najeeb ya fara motsa hannun sa a hankali.

"Alhamdulillah" Dr Usama ya faɗa.

"Dr Usama ya baya magana?"

"Malama Aisha kenan watanni fa yai a kwance ba magana ba motsi, a hankali komai zai dawo dai-dai. Alhamdulillah ma tunda har ya fahimci mai na faɗa"

"Allah ya baka lafiya miji na" ta faɗa tana goge hawaye.
Ƙarfe shida ta gota kafin su Daddy su ka iso.

Har lokacin Dr Usman na wajen tareda Dr Wunmi. Duk abinda su ke a kan idon Farida. Ta ƙi matsawa ko nan da chan.

Daddy dai ya yi ta maza bai yi kuka ba amma Mom kam kuka ta fara ganin yadda ake Ƙoƙarin juya kan ɗan ta saboda wuyan da ya riƙe. Ƙwanciya waje ɗaya tsawon watanni ba wasa ba...

Su ukun suna tsaye a kansa sun ƙura ma sa ido, yadda su ke kallon sa ka ce jaririn yaro ne sabon haihuwa.
Ƙarfe takwas aka ce za'a ma sa Computerize Tomography Scan (CT-scan)
saboda a gano ko akwai matsala a ƙwaƙwalwar. Najeeb ma idon ya zuba mu su. Daga ya kalli Daddy sai ya kalli Mom da ke hawaye sai ya kalli Farida da ta kasa rufe baki.

Yanda ya ke jan numfashi ma ka san a wahale ya ke yi.
Duk cikin su ba wanda ya matsa daga gefen sa har aka zo aka fita da shi. Sai da aka tafi da shi tukunna Daddy ya kira Najdah ya faɗa ma ta sannan ya kira ƙanin sa...

Kafin a gama yi ma sa komai 'yan uwa sun cika wajen. A kwance aka turo shi aka dawo da shi ɗakin.  Kowa sai tausayi yadda ya ke abin tausayi. Ga baki amma ba magana.
Likitan ne ya kira su gefe yana briefing na su akan abubuwan da za su yiwa Najeeb saboda taimakon sa har ya warware. Kafin result ɗin scan ɗin sa ya fito kar a dinga hayaniya a wajensa kuma mutanen da su ka fi kusa da shi ne kaɗai za su tsaya kusa da shi dan idan yana ganin baƙin fuska zai confusing ɗin sa...

Kwana biyu kafin aka fara ɗaura Najeeb akan wheel chair, har lokacin baya magana sai dai wani lokaci idan likitoci na tambayar sa yana gyaɗa mu su kai tunda kan ya fara motsawa yanzu. Da ke an hana hayaniya, banda wanda su ke kusa da shi ba wanda ya ke zuwa wajen sa.
Farida kam duk da yanayin da ya ke ciki na rashin magana da rashin iya motsa jiki tafi kowa farin ciki saboda yanzu idon Najeeb a buɗe su ke, zai kalleta za ta kalle shi.
A rana na biyar ya fara iya ɗaga hannun sa har ana bashi abu yana iya riƙewa kuma har lokacin ba magana.

Bayan CT scan da aka ma sa sai da aka kuma yin MRI wanda aka tabbatar mu su Najeeb yana da severe traumatic brain injury. A yadda su ka mu su bayani Najeeb zai jima kafin ya iya yin komai da kan sa hakanan kuma zai iya manta wasu abubuwan gaba ɗaya, wasu abubuwan kuma sai a hankali zai dinga tuno su.
Farida kam ta dena zuwa office, ko da abu ya taso sai dai Anas ya kawo ma ta ta yi cike-ciken da za ta yi a asibitin. Yanzu kam ita da Mom su ke kwana da shi. Har gara itama ta dena kuka yanzu, amma Mom idan ta ga ana ma sa neuropsychological assessment ko excercise sai abin ya dinga sa ta kuka. Hatta juya kai sai da aka koya ma sa.
In every theraphy section da aka yi ma sa Mom da Farida su na manne da shi. A kwana na sha uku aka fara koya ma sa tsayuwa. Sai a bashi abu ya dafa ya tsaya idan ya daɗe sai a zaunar da shi kafin a kuma ɗaga shi a haka ake yi har sai an ga ya gaji kafin a bar shi haka nan.

Ranan da aka fara bashi abinci, amai ya dinga kwarawa ƙarshe jikin sa ya fara jijjiga da ƙyar aka samu jikin sa ya dawo normal. Sai da ya kwana biyu ana bashi maganin da zai sa shi iya cin abinci kafin da ya ci bai amayar ba. Mom ce ke bashi abincin amma yana ci kaman wani ɗan koyo.

A rana na goma sha tara ya fara magana. Mom na sallah ita kuma Farida na zaune a kujera tana karanta ma sa labari taji kaman magana. Maganar ta fito kaman mai koyon magana ko na ce irin maganar wawaye.
"Yuu a yuu?"

Ta yi saurin ajiye littafin ta kai kunnen ta saitin bakin sa dan ta ji da gaske Maganar yai.

Maganar ta sake fitowa kaman ta da. Da farko ba ta gane me ya ce ba sai a na biyu da ya maimaita ta gane cewa "who are you" ya ce.
Dam ta ji ƙirjin ta ya buga.
"Sir Najeeb ba ka gane ni ba?, Aisha Farida, Miss Salihun ka"

Mom ta dafa kafaɗarta ta ce "Aisha ki kwantar da hankalin ki, kin ji dai mi likita ya ce" sai a lokacin ta ji zuciyarta ya yi sanyi.

"Whhhhere...Whhha" sai yai shiru saboda maganar da ta maƙale ma sa.

Mom ta fara shafa kan sa tana cewa " its ok son, a hankali maganan zai fita"

Da therapist ɗin da ya ke ma sa rehabilitaion theraphy section ya zo su ka gaya ma sa ya yi magana. Sai ya fara ma sa wassu tambayoyi, wassu ya amsa da ƙyar wassu kuma shiru yai.

Tambayar farko sunan sa ya tambaya. Bawan Allah Najeeb kam da ƙyar ya iya furta "YaaJeeb"  Najeeb ɗin ya ke son faɗa amma saboda bakin sa da be koma dai-dai ba maimakon N to Y ne ta fito.

A kwana na ashirin da shida ya fara gwada tafiya da taimakon sanduna biyu.  Yanzu maganan sa ta ɗan fara kyau ba kaman ranan da ya fara magana ba...

Fiskar Daddy Dr Kenneth wanda ya ke shi ne rehabilitation therapist ɗin sa ya nuna ya tambaya ko ya gane shi.

"Dad" ya faɗa a hankali.

Ya nuna Mom ya tambayeshi, ya jima yana kallon ta kafin ya ce "Mom"
Hawaye da Mom ke ƙoƙarin ɓoyewa ns su ka fara zubowa. Shekara nawa rabon da Najeeb ya kira ta da wannan sunan.
Najdah aka nuna ita ma ya furta "baby"
Ƙirjin Farida bugawa ya ke da ƙarfi-ƙarfi yadda ka san zuciyar ta ne zai fito.

A karo na uku ya sake tambayar shi ko ya san Farida amma bai yi magana ba. Najma ya nuna ita ma ya kira sunan ta Najma.

Wannan karon hawayen da Farida ke ɓoyewa kan su ke zirya a idon ta.
Najeeb ya zuba ma ta ido yana son gane a ina ya san ta amma ya kasa, kuma idon na ta ya ma sa kama da idon da ya ke yawan gani cikin baccin sa.

Hannu ya ɗaga ya nuna Farida da yatsa ya ce "who is she?"

(Team Farida ku kama 'yan Team Najeeb. Su suka bribing ɗi na😂)*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣4️⃣0️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©️
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*

*jiya na ga comments ɗin ku na kuma sha dariya. Princess Salma shugaban 'yan team Farida, ina mai ban haƙuri😀. No brain injury is the same haka healing process ɗin ma ba ɗaya bane. Normally waɗanda su ka farfaɗo daga coma su na shiga wani yanayi da ake cewa traumatic brain injury. Ya danganta idan aka gwada mutum a samu ko mild ne ko acute ko kuma severe. Ko da wanda aka yiwa induced coma ba sa farfaɗowa a take su dawo normal. Wassu idan su ka farfaɗo manta komai su ke tundaga magana zuwa tafiya zuwa duk wani abu da su ka iya da. A hankali-ahankali ana sake koya mu su sai brain ɗin su ya dinga picking da sauri, waɗansu abun ma kafin a nuna musu sai su tuna da kan su. Najeeb ya fara tuna 'yan uwansa ne saboda sun fi kusa da shi. It will be odd ace daga farko-farko ya gane Farida tunda ba wai sun jima tare ba ne. Koda ya ke Najeeb ɗan duniya ne zai iya ganeta ma ya waske😂 i dont know, ba ri mu bi su mu ga ya za ta ƙare*

Najdah ne ta yi saurin cewa "she's your secretary" Daddy ya buge bakin ta.
Najeeb cigaba dai da kallon Farida yana son fahimtar miye ma'anar secretary da kuma dalilin da ya sa ita wannan secretary ɗin ta ke tareda shi koyaushe.

Dr Kenneth ya ce "za ka tunata a hankali. Yanzu ka tuna ya aka yi ka zo nan?"

Najeeb ya girgiza kai still idon sa na kan Farida da idon ta ke cike da hawaye amma tana ta dannesu kar su zubo.

"Ba ka san ya aka yi accident ɗin nan ya faru ba?" Najeeb ya sake girgiza kai.

"Ka tuna wani abu a iya kasancewar ka cikin yanayi  na coma?"

"I dont know, there was darkness, then voices then her eyes" ya faɗa yana nuna Farida

"Za ka iya tuna voice ɗin da ka ke ji?"
Najeeb ya girgiza kai.
Dr Kenneth ya miƙa ma sa wani littafi ya ce duk abinda ya tuna ya rubuta a ciki.

Kafin Dr Kenneth ya fita sai da ya tabbatar mu su da kada su dinga damun sa da tambayoyi, su bari a hankali zai dinga tuno komai. Za dai su iya dinga yi ma sa labarin abinda ya ke so ko kuma su dinga nuna ma sa abubuwan da zai sa ƙwaƙwalwar sa ta yi saurin dawowa dai-dai...

Najeeb ya buɗe littafin ya fara zane. Idan akwai abinda ya farayi bayan ya fara iya riƙe biro to zane ne. Dan har yanzu ma rubutun sa bai dawo dai dai ba.

Dukkan su su ka zuba mishi ido su na ganin yadda ya ke zanen wani gida. Duk da freehand sketch ne hakan bai hana gidan ya fito da kyau ba. Da ya gama sai ya zana wata mace a bakin gidan tana murmushi wanda yanayin fiskar ya ɗan yi shige da fiskan Farida.

Farida kam ba zanen ta ke kallo ba tana tsaye ne amma ta yi nisan kiwo. Tunanin ta bai wuce ya za ta ji idan aka ce kwata-kwata Najeeb ya manta da ita kuma ya kasa tunowa da ita.

"Aisha" mom ta faɗa tana dafa kafaɗarta. Ta ɗanyi firgigit ta kalli Mom, Mom ta nuna  ma ta Najeeb.
Idon ta ya sauka akan Najeeb da ke miƙa ma ta takarda. Hannu na rawa ta karɓi takardar. Duban zanen ta yi sai ta fashe da dariya wanda ya sa hawayen da ta ke ta ɓoyewa su ka samu damar saukowa.
Shima Najeeb ɗin murmushin yai.

Ba abin da ya fi ɗaukan hankalin Farida irin abinda ya rubuta a ƙasar zanen *Plz smile*

"Allah sarki yanajin ta ajikin sa ne fa" Daddy ya faɗa yana shafa kan ɗan na sa.

Najdah ta cika ta yi fam, tana ta hararan Farida ta gefen ido.

Mom ta ajiye album a gaban sa ta buɗe tana faɗin duk wanda ta tuna a ciki ya faɗa. Hoton baby tana jinjira ne a farko, ya fi minti biyu yana kallon hoton kafin ya ce Baby. Gaba ɗaya sai su ka sa dariya.
Hoto na gaba kuma na shi ne yana ɗan shekara huɗu anyi hoton a wani amusement park ne yana cikin motan wasan yara.  Wannan kam bai ɗau lokaci ba ya nuna kan sa. Hoto na uku hoton shi da Sabreen ne lokacin da Sabreen ta yi graduation ɗin gama high school. Ya jima yana kallo, ya gane ta amma sunan ya maƙale ma sa. Kusan minti huɗu ya ce "Sa Sa Sabreen"...

Har lokacin da Farida ta zame jiki ta bar ɗakin ba su ankara ba. Tafiya ta ke amma ba abinda ke yawo a ƙwaƙwalwarta irin sunan da Najeeb ya ambata.
Wato ya iya tuna Sabreen amma ita bai tuna ta ba, Sabreen fa!...

Hoton Aisha aka buɗe ma sa lokaci guda idon sa ya fara kawo ma sa hoton ta kwance cikin jini. Dafe kan sa yai yana numfashi da ƙyar nan kuma seizure ya kama shi ya fara jijjiga. Su Najma su ka fita kiran likita, bayan seizure ɗin ya tsaya Dad ya gyara ma sa kwanciya ya maida shi kwance ta gefen sa...

...................

Tana zuwa ɗakin su gado ta  hau, kukan ma da ta ke son yin ma ta kasa. Zazzaɓi ne ya rufeta tun tana rawan sanyi har bacci ya tafi da ita. A ƙalla ta yi awa uku tana bacci kafin ringing ɗin wayar ta ya tashi.

Ta ɗau wayar tana mai goge gumin da ke goshinta da ɗaya hannun.

"Aisha ki na ina?"

"Ina gida Mom"

"Yaushe za ki dawo?"

"Sai dare"

"Ok"

Sai da ta ajiye wayan ta tashi da ƙyar. Ko'ina a jikin ta ciwo ya ke a haka ta shige banɗaki dan ta yi wanka...

Da dare da ta isa ta tarar da abun mamaki. Mom na tsaye gaban Najeeb tana hawaye tana bashi haƙuri, shi kuma ya kauda kai gefe.
Daddy baya nan dan ya bar asibitin tun da yamma. Najdah ne a wajen bayan Mom, itama Sallah ta ke yi.

Mom ta zagayo gaban Najeeb ta tsugunna har ƙasa. Da gudu Farida ta ƙarasa wajen tana ƙoƙarin ɗaga Mom.
"Mom so ki ke ki ja ma sa bala'i. Bai kamata ki tsugunna ma sa ba"

"Ki bar ni Aisha, ya tuno abinda na yi ya ce baya son ganina. Plz ki ce ya yafe min, ba zan iya rayuwa ba tareda ina kusa da shi ba"

Farida sai da ta tabbatar ta ɗaga Mom kafin ta sa hannu ta fara goge ma ta hawaye.
"Dan Allah ki dena kuka, kukan ki masifa ce a gareshi"
Da ƙyar Mom ta iya haɗiye kukan ta yi shiru.

Farida ta juya ta kalli Najeeb da ya ƙura ma ta ido, cikin ɗaga murya ta ce "kai Sir Najeeb, ka kiyayi fushin mahaifiyar ka. Kar ka ga dan kana cikin wannan yanayi ana tausaya ma ka ka maida mu bamu san mi mu ke ba, ka sanni sarai zafi gareni, kuma idan ba ka shiga taitayinka ba duk abinda ke cikin ƙwal..."

"To kashe ma na shi. Munafuka, kin san yana cikin wani hali amma ba za ki bari hankalin sa ya kwanta ba, kashe shi tunda abinda ki ke so kenan, dan ki gaji dukiyar sa ko"

"Najdah!" Mom ta daka ma ta tsawa.

"Mom ki ga abinda ta ke ma sa fa, anan ɗazu ya shiga wani hali saboda wani abu ya tuno amma yanzu ta dinga ma sa masifa kaman wani ɗan ta"

Shikan ido ya ke bin su da shi.  Yadda Farida ke masifa haka ya dinga ji ƙwaƙwalwarsa na tuno ma sa wassu masifan da ta yi a baya. Abin ya confusing na shi, domin yana ta ƙoƙarin gano a ina abubuwan nan su ka faru kuma yaushe su ka faru.

"Ki tafi ki bamu waje zamu iya jinyar sa" Najdah ta faɗa tana kallon Farida ido cikin ido.

"Yarinya kenan, ki je ki yi aure za ki fahimci minene tsakanin miji da mata. Jinya kuma ko uwar da ta haifeshi ba ta ma sa ɗawainiyar da na ma sa ba."

"Mom kin ji maganar banzan da ta ke yi ko?"

Mom ta ce "gaskiya ta faɗa. Babu wanda yai wa Najeeb hidima kaman ta, kuma ba abinda za mu saka ma ta da shi sai addu'a. She's the only one that never stop believing in him kuma na tabbata da ya yi shekaru a haka to a hakan Faridan za ta jira shi"

Najdah haushin maganan Mom da ta ji ya sa ta je ta ɗau jakan ta fuuuu ta fita ko sallama babu.

"Koyaushe haka ki ke da faɗa?" Najeeb ya tambaya yana kallon Farida

"Haka na ke, a haka ka sanni dan haka idan za ka tuno ka tuno, idan ma ba ka tuno ba to zamu cigaba daga inda mu ka tsaya"

"Son please forgive me" Mom ta faɗa tana haɗa hannun ta alamar magiya.

"Ka san Allah Sir Najeeb ba inda za ta je sai ka ce ka yi haƙuri"

Dariya yarinyar ta bashi.
"A matsayin ki na wa?"

Confidently ta ce "a matsayina na matar ka"

"Mata na?" Ya tambaya looking confused

"Yes ni matar ka ce" ...

.........................

Bai gama yadda da maganar Farida ba sai da Washegari da Najdah ta zo ya tambayeta ya aka yi ya auri Farida ba Sabreen ba. Da ke tana jin haushin Farida ba ta faɗi laifin Sabreen ba, sai ta ce Daddy ne ya aura ma sa Farida kuma ba son ta ya ke ba.
Maimakon ya bibiyi miya faru. Sai zuciyar sa ta fara kawo ma sa soyayyar sa da Sabreen, take kuma tausayin Sabreen ya kama shi. Sai dai kasancewa bai gama gane abinda ya faru da shi ba ya sa yai shiru...

Duk da ya tuno abinda ya haɗa su da Mom amma tundaga ranan da Farida ta ma sa masifa sai ya dena ɗaure ma ta fiska amma dai still ya kasa sake jiki da ita.

A kwanan sa na talatin da bakwai da farfaɗowa sai ga Sabreen.  Shi da Farida da therapist ɗin sa ne a chan wani fili, yana gwada tafiya da walking stick ɗaya maimakon biyu da ya ke amfani da su da.

Najdah da Sabreen ne su ka nufo su. Sabreen na ƙara tabbatar wa idon ta ga Najeeb nan a raye kuma yana tafiya ta yanka da gudu ta je ta faɗa jikin sa.

"Noory you're back, i miss you Noory, i miss you"

Ji ta yi an damƙi gashinta da ƙarfi, dama ɗan gudun da ta yi ya sa gyalen da ta yafa ya faɗi.

"Ah Ah...Noory help"  Sabreen ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwatan kan ta. Amma ba ƙaramin damƙa Farida ta yiwa gashin ba.

"Wallahil Azim ko ki koma inda ki ka fito ko na lahira ya fiki jin daɗi. Idan ba hauka ke kan ki to nawa sun fi na ki"

Ganin yadda idon Sabreen ya firfito, goshinta yai ja, jijiyinta su ka mimmike ya sa Dr Kenneth ya fara bawa Farida haƙuri akan ta sake ta za ta illata Sabreen.

Najeeb kam tsayawa yai a gefe yana kallon ikon Allah.
Da ƙyar Farida ta haƙura ta sake Sabreen wanda ta faɗi ƙasa tana numfashin wahala, har da hawaye.

Cikin zuciyar sa ya ke tunanin ashe Najdah ta yi gaskiya da ta ce ma sa Farida is mentally not stable.

Zuwa yai zai taimakawa Sabreen ta tashi. Farida ta riƙe shi " inka ɗaga ta na mutu kafira"
Bai ɗaga tan ba sai ma Dr kenneth ne da Najdah su ka ɗaga ta...

Ranan dai Sabreen ba ta sake dawowa ba sai washegari.
Duk zuwan ta gaishe shi sai dai ta zo da Najdah dai-dai lokacin da Mom ko Daddy ke wajen sa. Shegiya ta ji damƙan manya😂...

Har yanzu dai bai gama tuno komai ba, yadda memory ɗin ke dawo ma sa tsilla tsille ne ba direct ya ke tuno abu ba. Wani lokaci sai anyi magana sai abinda aka faɗa ya triggering ma sa wani memory.

Yau ma magana ya ke da likitan sa a office likitan ya excusing kan sa yana amsa waya. Juyawar da zai yi ya kalli Tv da ke ɗakin likitan sai ga Sabreen a cikin TV. A church su ke ana ɗaura ma ta aure da wani, bayan priest ya ce you may now kiss the bride sai ga shi ɗaya actor ɗin ya kama waist ɗin Sabreen su na kissing. Najeeb ya rintse ido wassu abubuwa na dawo ma sa....*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣4️⃣1

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*

Dafe kan sa yai yana jin wani irin zogi. Komai ne ke son dawo ma sa lokaci guda. Likitan ne ya lura da yanayin sa.

"Are you Ok?"

Da kyar Najeeb ya ɗago kan sa idon sa sun yi ja.

"Mr Najeeb ka dinga yi a hankali, kar ka takura wa kan ka, ahankali za ka tuno komai"

Najeeb ya gyaɗa kai...

Tun bayan abinda ya tuno gameda Sabreen ƙoƙari ya ke ya tuno ya su ka yi zaman auren su da Farida. Although Najdah ta gaya ma sa ba auren soyayya su ka yi ba, he still wants to remember something gameda auren su. Yawancin abubuwan da ya ke ɗan tunowa gameda ita time to time bai wuce aikin su tare a office ba. Tun ranan da ya tuno abinda Mom tayiwa Aisha ya ke ƙoƙarin ɓoye wasu abubuwan da ya tuno. Ko ranan da ya tuno accident ɗin da yai bai gaya mu su ba, he pretends bai tuna ba.

Farida ce bashi abinci, su biyu ne a ɗakin. Duk da yanzu yanada ƙarfin jiki sosai zai iya cin abinci da kan sa amma Farida sam ta hana. Dole sai dai ita ta feeding ɗin sa, su yi ta daru akan rashin son cin abincinsa. Yana cin kaɗan idan ya ce ya isa Farida za ta hau shi da faɗa. Wani lokaci idan ta takura ya kan  ƙara kaɗan amma ma fi yawancin lokutan kau da kai gefe yakeyi ya ƙi ci.

Yau ma ɗin ita ke bashi abinci.
"Aysherh" ya kira sunan ta. Ranan da ya fara kiranta da wannan suna ya ga farinciki da ɗoki tattare da fiskar ta, har da cewa "My Champ sake kira dan Allah"

Lokacin da ya tambayeta ko ya ya ke kiranta da kafin wannan abu ya sameshi ƙin gaya ma sa ta yi, tace ya kira ta da Aishern kawai. Shi kam sai ya ke ji kamar ba Aysherh ya ke kiranta ba. Sunan a bakin sa ya yi daban, like there's more to sunan Aysherh da ya ke kira.

Yayi gyaran murya ya ce "Ehm Aysherh...Ehm....did we?" Ya sake gyaran murya
"Have we.....?"

"Ina jin ka mijina" ta faɗa tana goge ma sa baki da tissue.

Wannan karan daurewa yai ya ce "lokacin da mu ka yi zaman aure da ke muntaɓayin wani abu?"

Dariya ne ya cika ta amma ta gimtse ta ce "wani abu kuma?"

Sai da yai gyaran murya kafin ya ce "abun aure"

"Abun aure ai dayawa My Champ. Wanne a ciki?"

Ya marairaice ido ya ce "please Aysherh. Kin san abun da na ke nufi fa"

Daɗi kashe ni. Abin da zuciyarta ya faɗa kenan, wai Najeeb na hira da ita, hiran ma irin hiran su ta da.

"I'm serious Aysherh"

"Abubuwan aure ai dayawa My Champ. Akwai cin abinci tare, wanka tare, wasa da dariya tare, akwai kuma abubuwan da ake yi da dare, ko kuma ayi abun idan ɗaya ya ji abu sai ya taƙali ɗayan sai a haɗu ayi abubuwa. So wanne aciki ka ke tambaya?"

Maganan nan ya tuno ma sa da wassu abubuwa amma har yanzu bai iya tuno ko sunyi abun da shi ya ke tambaya ba.

"So, we did everything that couples do?"

"Mun yi komai hadda gyara"

Zaro ido yai lokaci guda kuma ya sa hannu yana tare gaban sa.

Farida ta fashe da dariya tana faɗin "to na nawa kuma. Bayan angama ganin komai"

Har lokacin bai ɗaga hannun sa ba ya ce " you're lying"

Tana cikin dariya Anas ya shigo.

"Wannan dariya haka, Farida ko dai ya tuno komai ne?"

Farida ta girgiza kai. As usual ya kawo ma ta wasu documents ne ta duba.

Anas ya gaida Najeeb wanda har lokacin yana kare gaban sa da hannu.

"Abokina ya dai?  ko wani abu ya samu wajen ne?"

Pillow ya jawo ya sa a wajen kafin yai wa Anas wani mugun kallo.

"Mutumina ka godewa Allah da ya ba ka jarumar mace. Ba dan ita ba da kamfanin ka ta samu matsala"

"Ko a wanni duniyan ne secretary ta ke zama Oga oho?"

Ya kalli Farida da ido ya ce "what did you know Miss Salihu?"

Farida ta zaro ido, shi kuwa murmushin yaƙe ya mata ya maida hankalin sa kan Anas.

Abubuwa dayawa ne ke yawo a cikin ƙwaƙwalwarta. Kenan Najeeb ya tunata, komai ya tuna? ko kuma dai ba komai ba.

"Alhamdulillah mutumina. Ka tuna Miss Salihun ka, the stubborn Miss Salihu"

"Ko ba Miss Salihu ba ne ta sa min superglue a seat?"

Anas ya kwashe da dariya. Ita kuwa Farida jikinta ne yai sanyi.
Najeeb ba wai ya tuna abin ba ne da kan sa. Ranan ne Najdah ta nuna ma sa video ɗin da Anas ya nuna mu su ranan birthday ɗin sa, yana gani kuma wassu abubuwa su ka dinga dawo ma sa gameda Farida, musamman lokacin su na office...

Bayan Anas ya tafi, Farida ta ce " My Champ ka tuna komai ne?"

"The last time i remember ba da wannan suna ki ke kirana ba. What changed?"

Da gayya ya gaya ma ta haka, shima rama abinda ta ma sa ɗazu yai.

"Saboda..." sai kuma ta kasa magana.

Ranan gaba ɗaya gwiwarta yai sanyi. Duk yadda ta yi dan ta fahimci ko ya tuno komai na rayuwar su amma ta ka sa. Sai ya dinga gwaleta idan ta tambayeshi...

Washe gari da safe ƙarfe goma sai ga Lukman. Bayan ya yiwa Najeeb ya jiki sai ya ke faɗa ma sa cewa gaskiya ya riƙe Farida da kyau domin ta ma sa abinda ba ko wacce macce ne za ta iya yi ba.

"Oh! and how do you know?"

Lukman ya ƙaƙaro murmushin dole ya ce "saboda na gani da ido na"

"Nagode da gaisuwa, Dr Lukman right?"

Lukman ya gyaɗa ma sa kai tareda barin ɗakin, chan ƙasan zuciyarsa kishi na cin sa...

"Shi kuma wannan daga ina ya ke?" Ya tambaya yana tsare Farida da ido

Ba tareda ta kalli idon sa ba ta ce "he's my ex husband"

"Ashe ma bazawara na aura ban sani ba"

Ɗago rinannun idanunta ta yi tana ma sa wani kallo. Abinda ma zai ce ma ta kenan wai bazawara. Anya za ta taɓa samun matsayi  a wajen Najeeb musamman yanzu da bai gama gane kan sa ba...

...............................

Bayan anyi sunan ɗan Maijiddah da kwana uku AbdulWahab ya koma Lagos. Bai samu Aneesa a gida ba, dama ta ce ma sa Abuja za ta je. A washe garin ranan da ya dawo ta dawo. Ita ba ta ma san ya dawo ba...

Tana zaune a falo tana kallo   tana cin pringles sai ga kiran wata ƙawar ta.

Bayan sun gaisa ƙawar ke tambayarta ya kishiyar ta.

" shegiyar fa haihuwa ta yi, namiji kuma"

Ɓangaren ƙawar ta ke ma ta faɗa akan ta yi sake da har ta bari Maijiddah ta haihu a gidanta.

"To ya zan yi Binta, kwanan  baya har cikin ƙarya na ce ina da shi dan na samu attention ɗin AbdulWahab kuma na samu a lokacin. Daga baya na mata sharri akan ta tureni cikin ya zube. Da farko ya yarda daga baya ya ƙaryata zancen. I really dont know what to do again..."

Ko mi ƙawar ta ce oho. Aneesa dai cewa ta yi "ni kin san ba na son shige-shigen nan. Ka je ma duk su ci kuɗin ka a banza ba biyan buƙata"

Jayayya su ka fara yi da ƙawar akan zuwa wajen Boka, daga ƙarshe Aneesa ta kashe wayan tareda cewa za ta yi tunani akai.

"Nonye....Nonye"
Ta fara kiran mai aikin ta. Jin shiru ya sa ta miƙe tsaye, ai kuwa da sauri takoma ta zauna daɓas tana riƙe baki.

"Sweetheart" ta faɗa baki na rawa.

Yana tsaye ya harɗe hannuwan sa a ƙirji yana kallon ta, idon sa yai wani irin ja.

"Aneesa why? Why? Ki rasa abinda za ki yi sai ƙarya"

"I can explain AbdulWahab, please" ta faɗa tana haɗa hannuwan ta biyu.

"Wajen Boka ko, ki je Allah ya bada sa'a" yana faɗin haka ya haura sama.

Jikin ta na rawa ta tashi ta bishi da sauri...

Buga ƙofar sa ta ke yi amma bai kulata ba balle ya buɗe, ta zauna a bakin ƙofar tana ba shi haƙuri tana hawaye...

Kwanaki uku su ka gifta amma kalma ɗaya ba ta ji daga bakin AbdulWahab ba. Ta yi kukan ta bada haƙurin amma bai ma kulata ba balle ta san ko ya yafe ko bai yafe ba.
A rana ta biyar ya ce ma ta idan har ta zaɓi zama da shi to za ta ajiye aikin ta ta zauna ta kula da shi da kuma yaranta, amma idan ta zaɓi aikin ta to zai sawwaƙe ma ta.

It was a very tough decision for her. Tana son AbdulWahab tana kuma son aurenta. Duk da dai ta san ba ƙaramin asara za ta yi ba idan ta ajiye aiki amma kuma ba za taɓa zama bazawara saboda aiki ba. Ta kira Mama neman shawara, inda Maman ta ce ma ta ta zaɓi abinda ta ga ya fi ma ta, amma ta sani ba za ta taɓa samun wani miji kamar AbdulWahab ba musamman ma a shekarun da ta ke yanzu.
Ƙarshe dai shawaran da ta yankewa kanta shine ta ajiye aiki...

Duk da ta ajiye aiki hakan bai sa AbdulWahab ya koma ma ta kamar da ba. Cewa ma yai ta je ta bawa Maijiddah haƙuri. Girman kai ba zai bar ta ba, ta girmi Maijiddah sosai,  kusan shekara shashida ta bata. Da ta ga uwar bari dole dai sai da ta kira Maijiddan a waya ta ba ta haƙuri. Maijiddah kam ta yafe tuntuni tunda mijinta ya gane gaskiya kuma ya yarda da ita ai an wuce wajen... kafin Aneesa ta samo kan mijinta sai da ta kai wajen wata ɗaya...

.................................

Yau aka sallami Najeeb daga asibiti bayan kwanaki hamsin da huɗu da yai da farfaɗowa. A report ɗin da su ka bayar sun nuna cewa ba shida matsala, a hankali zai dawo da dukkan ƙarfin sa, haka kuma bisaga tambayoyi da kuma shaidar 'yan uwansa sun tabbatar da cewa ya tuno kaso tamanin na rayuwar sa ta baya kuma a hankali zai ƙarasa tuna komai...

Gefen sa na dama Farida ɗayan kuma Najdah a haka su ka fito daga asibitin Daddy da Mom kuma na gaba farinciki yana nan tattare da fiskokin su. Motar Farida su ka shiga, yadda Najdah ke maƙalewa Najeeb ba dan su Daddy na wajen ba da ta gaya ma ta maganar banza.

Maimakon Najdah ta bi motar su Daddy sai ta shiga tasu motar.
Su uku ne a baya sun sa shi a tsakiya.
"Dan Allah ki fita ki bamu waje, mata da miji suna son ganawa da junan su"

"Wayaga mata. Ba inda zan je. Yaya na son kasancewa da ƙanwar sa"

"Tunda sirrin miji da mata ki ke son gani, Bismillah"  ta faɗa tana hawa kan cinyar Najeeb, kafin ya ce wani abu ta haɗe bakin su, yana so ya tureta daga jikin sa saboda Najdah da ke motar amma gangan jikin sa ya betraying ɗin sa. Maimakon ya tureta sai ma ƙara matseta yai a jikin sa, yayinda kuma hannunsa duka biyu su ka fara yawo tsakanin bayan ta zuwa hips ɗin ta.

"Dreba tsaya zan fita" Najdah ta faɗa tana jan tsaki.
Sun fito daga gate ɗin asibitin kenan ko nisa ba su yi ba.
Ya samu waje yai parking

"Karuwa kawai" ta faɗa tareda banko mu su ƙofar motar.
Abdullahi dreba ya fara dariya ƙasa-ƙasa yana faɗin "to kema miji ya kwanta a asibiti tsawon watanni ba lafiya, yanzu ya samu lafiya ki zo ki liƙe ma sa, ai duk abinda ki ka gani ke ki ka jawo"

Lokacin da ta ji Najdah ta fita ta fara ƙoƙarin janye bakinta.
"My Champ" ta faɗa cikin sarƙewan numfashi tana nuna ma sa ƙeyar dreba wanda bawan Allah kam kiɗa ma ya sa a motar ya ƙure volume sosai, dan kar kunnen sa ya jiyo ma sa ba dai-dai ba.

Kallon-kallo su ka fara yiwa junan su, idon Najeeb yai wani ja guguwar sha'awa ta bugeshi.
Ya san a mota su ke amma kuma duk wani ƙoƙarin hana jikin sa aikata wannan abu ya ka sa, jikin sa har rawa ya ke yi. Ƙoƙarin tashi ta ke yi daga jikin sa gaba ɗaya. Ya maidata da sauri, "My Ch..." Najeeb bai bari ta ƙarasa ba ya jagoranci wannan kiss ɗin, wannan karan da zafi zafin sa ya ke yi, ya cire ɗankwalin ta ya sa hannun sa cikin gashin ta yana shafawa. Kafin ta ankara yai wani juyawa da ita sai gashi tana ƙasa yana samanta still bakin su haɗe da na juna. Ta san glass ɗin motar tinted ne amma kuma ko da Abdullahi dreba bai juyo ya leƙa su ba, ya san dole su na aikata wani abu a bayan motar.

Ƙoƙarin zuge zip ɗin doguwar rigarta ya ke ta yi saurin riƙe hannun sa. "A mota mu ke My Champ" ta faɗa lokacin da bakin su ya rabu. Ya jima yana kallon idon ta kafin ya tashi daga kan ta. Itama ɗin tashi ta yi ta ɗau ɗankwalin ta tana ɗaurawa. Tunda ya juyar da kam sa gefe bai sake juyowa ya kalleta ba, numfashi kawai ya ke saukewa da sauri sauri. Ita kan kwantar da kanta ta yi a kafaɗar sa tana ayyana abubuwa dayawa a ranta...

Najdah kiran Mom ta yi akan su dawo su ɗauketa, da ke motar su ta riga ta yi nisa.
Cikin Daddy da Mom ba wanda ya tambayi dalilin da ya sa ta sauka a motar su Farida. Tunda dama tun farko bai kamata a ce ta shiga ba. Ta zauna a gaban mota sai tsaki ta ke yi tana ƙara jin tsanar Farida. Ita fa tun day one da ta ga Farida yarinyar ba ta mata ba, balle yanzu da ta ke jin ina ma tanada yadda za ta yi ta raba Najeeb da Farida saboda tsanar da ta ma ta...

*Barka da safiya, Allah ya sada mu da alkhairin da ke cikin wannan rana amin**SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣4️⃣2️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*

Motoci ne cike maƙil a compound ɗin gidan lokacin da su ka shigo.
"Ya na ga gidan ya cika haka?"

Juyowa ya yi ya kalleta kallon irin kin fini sani ai.

Wayarta ta ɗauko ta kira numbar Mom.

"Mom gidan a cike sosai kaman wanda ake biki?"

"Dear, Walima ce za'ayi"

"Oh"

"Gamunan ma mun iso"

Katse wayan ta yi tana jira motar su Daddy ta shigo.

"My Champ" ta kira shi a hankali

Ɗaga ma ta gira yai.

"Wai an shirya ma ka  Walima. Yadda aka cikan nan na san za ayi hayaniya, ko mu wuce kawai ka je ka yi wanka ka kwanta?"

Girgiza ma ta kai kawai yai.
Sai da Mom ta zo ta ƙwanƙwasa mu su window kafin su ka buɗe ƙofa su ka fito. Yana fitowa daga motan ya fara kallon gidan na su. Tabbas ya tuna gidan, hakanan kuma ya tuna cewa shi ya zana gidan, lokacin ma yana degree ɗin sa na farko ne.

Wannan karon Daddy ne ya kama hannun sa su ka nufi hanyar garden inda aka shirya Waliman.
Farida kam cikin gida ta wuce bayan sun yi musayar harara ita da Najdah.

Tana shiga ta tadda baƙi sun cika falon ƙasa, kusan ba zai fi mutum biyu ta gane a ciki ba sauran duk baƙin fiska ne a wajen ta. A tsanake su ka gaisa kafin ta haura sama.

Wanka ta yi da ruwan zafi saboda jikinta da ke ma ta ciwo. Bayan ta fito ta shafa mai ta ɗau wata atamfar ta riga da skirt ta sa. Dariya ta farayi lokacin da ta kalli kan ta a madubi ta ga yadda kayan ya ma ta ruwa. Gaskiya yanzu kam ta yarda ta rame sosai. Cire kayan ta yi ta je ta ɗauko wani Anarkali gown kalar abin cikin ƙwai, zanen adon flowers da ke jikin kayan kuma ja. Ba wani kwalliya ta yi ba powder ce kawai da kwalli, sai ta ɗan goga jan lipstick kaɗan a lips ɗin ta. Tana yafa gyalen tana murmushi. Ta ya ba za ta yi farin ciki ba, taya fiskarta ba zai zamo ma'abocin murmushi ba akoda yaushe. Kaman yau fa ta ke cikin nishaɗi saboda first kiss ɗin su, gashi duk da matsaloli da su ka fiskan ta, duk da ƙaddara da ta afka mu su. Allah ya sake dawo da wani ranan da su ka sake sharing kiss. Akwai lokutan da ta ke jin kaman ba zai tashi ba amma sai ta dake ta dinga maimaitawa kanta cewa ita da Najeeb akwai rayuwa mai tsawo a gaban su, rayuwa mai tarin farinciki da annashuwa, rayuwa da za su ga 'ya'ya da jikokin su.
Wani abu ta tuno da ya sa ta rufe fiskan ta tana murmushi. Tana kuma fatan Allah ya sa wannan rana ta iya jurewa ta daure ta faranta ma sa rai sosai...
Kiran Ummi ne ya katse ma ta dogon tunanin da ta tafi.

"Mun iso gidan na ku ki fito ki shigo da mu"

"Ummi na yaushe a gari? Shi ne ba ki ce za ki zo ba"

"Ba na son surutu ki fito yanzu, ba ni ɗaya ba ne harda su Baaba Sabuwa"

"Yeeeeh, ganinan zuwa"...

Taro ne da ya haɗa manya-manyan mutane, 'yan uwa da abokan arziƙi. Wanda aka gayyata da wanda su ka zo gayyar soɗi duk an cika garden ɗin maƙil. Manya manyan tents huɗu aka kafa amma sun cika maƙil har ma wassu ba su samu wajen zama ba. 
Abinci kam Masha Allah domin anyi varieties kala-kala, caterers aka ɗauko su ke serving mutane abincin.

Malami aka kira ya fara buɗe taro da addu'a kafin Daddy ya yi jawabin godiya da kuma farinciki da ya ke ciki a yau. Daddy yai hawaye lokacin da ya ke bayyana halin da su ka shiga da Najeeb ya shiga coma, tun ana irga kwanaki da satuttuka aka koma irga watanni, daga ƙarshe ma da Allah ya tada shi sai da aka yi kusan wata biyu cur kafin ta kai har yau yana tafiya normal, yana magana yana kuma gane mutane, gaskiya abin godiya ne. Bayan ya gama jawabi aka kira Najeeb. Najeeb ya karɓi mic yai taƙaitacciyar jawabi wanda godiya ce ga dukkan wanda su ka taya shi da addu'a da kuma wanda su ka dinga ware lokutan su mai muhimmanci su na zuwa dubashi a asibiti bayan sun san ba ganin su zai yi ba balle ya ji su. Har ya miƙawa MC mic ɗin sai kuma ya ƙarɓa ya ce "Aysherh Farida Salihu should please come here"

Farida na zaune kusa da su Ummi ta ji abinda ya ce. Dama tunda ya fara magana hankalin ta ke kan shi.

"Mrs Jibo" ya sake kira.

Duƙar da kan ta ta yi tana ƙoƙarin danne hawayen da ke shirin zubo ma ta.

"Farida ba za ki je bane?" Muryan Ummi ya doki kunnen ta.

"Mrs Jibo please come out" ya sake maimaitawa.

A hankali ta ke tafiya kan ta a ƙasa, ba wai kunyan mutanen wajen ta ke ji ba. Abubuwan da su ka faru ne su ke mata zirya a ƙwaƙwalwar ta.

Tana isowa wajen da ya ke ta ɗaga ido ta kalleshi, shi ma ɗin ita ya ke kallo. Hannunta ɗaya ya kama ya jawota kusa da jikin sa sosai.

"Ga wanda ba su san wacece wannan ba, ko su ke tunanin minene alaƙata da ita. To dai Aysherh Farida Salihu sakatariya ta ce"

Wurin ne ya ɗau hayaniya, domin dayawa sun san Farida matar sa ce.

Ɗan murmushi Najeeb yai wanda ya ƙara bayyana kyaunsa.
Ƙirjin Farida ya fara bugawa da sauri-sauri.

"Then she became my wife. Auren mu bai cikata wata biyu ba na yi hatsari na shiga coma, i was unconcious for months. Kun san mi ta yi?"

Aka haɗa ba ki aka ce a'a

"Ta jira ni, ta kula min da gida da dukiya, ta aiwatar da duk wani responsibility da mata za ta yiwa mijin ta. Ba ta gujeni ba, ba ta ƙyamace ni ba, ba ta kuma nemi rabuwa da ni ba in my vulnerable state. Ba ko wace mace ba ce za ta iya abinda Aysherh ta yi. Ina so ku sani cewa Aysherh jaruma ce, she always fight and she always win"

Ya kalli Farida da ke kallon ƙasa idon ta na hawaye, ya sa hannu ɗaya ya goge ma ta hawayen da ke fiskar ta.

"Thank you Aysherh, Thank you for everything"

Fashewa ta yi da kuka me haɗe da dariya, Ya jata jikin sa ya rungumeta. Gaba ɗaya wajen aka sa tafi...

Anyi ruwan hotuna kam kamar ba gobe har sai da Najeeb ya gaji da tsayuwa. Ƙarshe da ya ji hajijiya na kama shi ya excusing kan sa ya bar wajen.

Yana ƙoƙarin shiga gida sai ga Sabreen ta biyoshi.

"Noory"

Juyowa yai ya kalleta yana jin haushinta na taso ma sa tun daga ƙasan zuciyar sa.
Lokacin da ta iso ya yi ƙoƙarin sake fiskar sa ya ce "Sabreen"

"Noory na san na yi laifi a baya kuma kana fushi da ni amma ka sani har yanzu ina son ka. Ba zan taɓa son wani kamar yadda na so ka ba. I love you Noory, Please give me another chance"

Kamar ya shaƙota ya haɗata da gini ya ke ji amma ya dake ya ce "i still have feelings for you Sabreen, but you know i have a wife now"

Marairaice murya ta yi ta ce ba ta damuba ta ƙara da cewa "I want to be your wife too, ko da ta biyu ce ba matsala"

Najeeb yai murmushi ya ce ta bari idan komai ya lafa zai wa su Daddy magana.

Murmushi ta yi ta zo za ta rungumeshi ya ce "we'll talk later"

Har ya shige ba ta bar murmushi ba. Ba ta ɗauka Najeeb zai ƙarɓi bukatan ta da wuri haka ba...

Yana shiga ɗakin su ya ga komai na nan yadda ya ke, ya kalli kayan da ta bari a kan gado riga da skirt na atamfa wanda ta sa da fari kafin ta chanja su.

"Clumsy Aysherh, will she ever change?" ya furta a fili...

Farida kam sai da ta ga bayan taro, domin jama'a sun ma ta chaa kowa yana jinjina ma ta kan namijin ƙoƙarin da ta yi.  Tun daga 'yan uwan Najeeb na ɓangaren Daddy da su ka zo daga Gombe zuwa 'yan uwan Mom da su ka zo daga ƙasashe daban-daban. Mom ta nuna ma ta yayun ta biyu maza da kuma cousin ɗin ta mahaifin Sabreen. Farida kam baki har kunne domin kyauta kam ita kan ta ba ta san iyakan abinda ta samu ba...

Ƙur'ani ne a hannun sa yana karatu lokacin da ta shigo ɗakin. Yadda ta ke jin jikinta idan ba ta je ta watsa ruwa ba ba za ta ganema kan ta ba.

"Aysherh"

Ya kira sunan ta.

Ta juyo ta kalleshi har da lumshe ido.

Yatsa kawai ya ɗaga ya nuna ma ta kan gado. Bin yatsar ta yi da kallo har idon ta ya sauka kan kayan ta da ke kan gado.

"Ba na son ƙa..."

"Na sani- na sani. Kawai dai su Ummi da su ka kirani ne ya sa ban ɗage kayan a wajen ba, Mr ba na son ƙazanta"  tana faɗa tana tattara kayan.

"Kai fa ka dawo kenan ka yi ta yiwa mutane gadara da ɗaki, bayan ɗakin na mu ne mu biyu"

Bai kulata ba ya cigaba da karatun da ya ke yi...

Bayan ta fito daga wanka ta  sa wata ƙaramar riga wanda ko rabin cinyar bai gama rufewa ba. Ƙaton hijabi mai hannu ta sa ta zo ta ɗau sallaya ta tada sallah. Lokacin da ta idar ba ya ɗakin. Ba ta san ya aka yi zuciyar ta ya raya ma ta kaza ya je nemowa ba. Haka kawai ta tashi ta fara duba hammata da gabanta ko ta yi waxing na shi da kyau, ba ta so ya kalleta ya faɗa ma ta kalmar da ke baƙanta ma ta rai ɗin nan "Mrs Jibo ba na son ƙazanta yanzu kuma Aysherh ba na son ƙazanta"
Ta girgiza kai ganin komai na nan tsaf-tsaf ba ta jima da gyara wajen ba.
Ta fesa turaruka a ɗan filingin kayan na ta, sannan ta shafa turarukan jiki.

"Aishatu anya wannan uban turarukan bai yi yawa ba?"  Ta tambayi kan ta tana shinshina jikin ta...

Wajen Daddy ya je a chan ɗakin sa, shima dawowan sa kenan daga rakiyan baƙi.

"Dad you called me"

"Ya ƙarfin jiki?"

"Alhamdulillah"

"Son abu biyu ya sa na kiraka. Na farko lokacin da ba ka da lafiya Anas ya turo magabatan sa kuma na bashi Najdah. Mun saka biki ƙarshen shekara lokacin ta ƙare karatun ta.  Alhamdulillah along the line sai ka farfaɗo, saboda hankalinmu na kan samuwar sauƙin ka shiyasa mu ka jingine maganan aure a gefe. Amma yanzu tunda ka samu lafiya sosai me ka ke gani mu ɗaga bikin ne ko kuma a bar shi a date ɗin da ɗin?"

"Duk abinda ku ka ga ya dace ni bani da abin cewa"

"Abu na biyu shine maganar mahaifiyar ka. Najeeb dan Allah ka gyara tsakanin ka da mahaifiyar ka. Ta yi kewan ka sosai, na san yanzu ba kaman da bane tunda har kana kiran ta da kalmar uwa. Amma still ka raɓeta ka samu albarka ajikin ta. Uwa fa Uwa ce Najeeb..." haka Daddy ya cigaba da yi ma sa nasiha mai ratsa jiki

Ya jima yana hawaye kafin daga baya ya bawa Daddy haƙuri tareda alƙawarin zai gyara...

Ya so ya samu Mom a wannan dare sai dai kuma bai san waɗanne kalmomi zai yi amfani da su ba, shiyasa ya haƙura har sai ya samu nitsuwa sosai...

Ana murɗa ƙofa ta yi saurin rufe idon ta kamar mai bacci. Tana kwance ne tun ɗazu tana jiran kaza😂 da kuma abinda ake yi bayan kaza sai dai Najeeb bai shigo ɗakin da wuri ba.

Jin bai zauna akan gadon ba ya sa ta ɗan buɗe ido ɗaya ta leƙa shi. Mug ne a hannun sa yana shan tea, ta sake buɗe ɗayan idon ta duba gefe da gefen sa da kyau ko za ta ga leda ko take away ba ta ga komai ba. Tana bin sa da ido har ya ƙarisa shan tea ɗin ya shiga banɗaki yai wanka.

Pyjamas ya sa ma su laushi baƙaƙe kamar yadda ya saba, ya zo ya kwanta gefen ta. Kashe wuta yai ya jawota jikin sa sannan ya fara bacci bayan ta ji bakin sa na motsi alamar addu'a yai. Ta jima tana ta tunani kafin bacci yai gaba da ita ba tareda abin da ta hasaso ya auku ba. Ba maganar kaza ba maganar abubuwa...*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣4️⃣3️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*

Washe gari ma baƙi ne su ka yi ta zuwa gaisuwa, tun da safe har yamma. Kafin su samu sarari ma sai da aka yi kwana huɗu da dawowar shi gida...

Da sassafiyar Jummu'a ya shigo ɗakin mahaifiyar sa. Dad bayanan ya tafi wani taro a Minna.
Tana zaune akan sallaya tana jan carbi ya shigo.
Gwiwowin sa ya sa a ƙasa ya ɗaura kan sa a kafaɗar ta.
"Mon ki yafe min dan Allah, for years i treated you..."

"Shhhhhhh" ta dakatar da shi, hawaye ne ke zubowa a idon ta wani na bin wani.

"Son na yafe ma ka. Ba laifinka ba ne kaɗai, har da ni. You were young, you're traumatize, maimakon na ja ka ajikina na nuna ma ka kulawa sai na barka hakanan har abin ya zo ya girma a ranka. I'm sorry son"

Ita hawaye shi hawaye. Uwa da ɗa sun jima rungume da juna kafin daga baya Najeeb ya janye jikin sa ya ce "Mom zan sake yin wani laifin. Ki yafemin kafin lokacin"

"Son minene?"

A hankali ya furta Sabreen...

.............................

Farida ta shiga kitchen tana ƙoƙarin haɗa Alala saboda sha'awarta da ta tashi da shi yau da safe sai ga Najdah ta shigo kitchen ɗin. Da alama shigowa ta yi dan ta ɗauki wani abu, ba gaisuwa balle sannu da aiki. Farida ma ta yi kamar ba ta gan ta ba.

"Adama, Adama, Adama" Najdah ta fara ƙwala kiran sunan baiwar Allah.

"Wai ke wacce irin daƙiƙiya ce. Kin dai ga ba ta kitchen ɗin nan dai ko, sanin kan ki ne sarai tana shayarwa yanzu. Ki dinga kiran ta kamar wata 'yar cikin ki. Matar nan idan ba ta baki shekara goma ba za ta baki takwas amma ki wage baki ki dinga kiran sunan ta kamar wanda ku ka yi wasan ƙasa tare. Adama...Adama"

"Kin ga bana son shishshigi Farida, ban yi da ke ba dan haka kada ki shiga harkata"

"A hakan za'ayi auren, yarinya ba tarbiya ba komai"

"Uban ki da uwar ki ne ba su koya min tarbiyan ba"

Maimakon Farida ta  bata amsa sai ta zo ta kama hannun ta.

"Ki sake ni, ki sake ni Farida"

Jan ta ta ke yi Najdah na tirjewa, amma da ta ga uwar bari sai ta haƙura ta bi ta dan taga iya gudun ruwan ta, ta san ƙarshe wajen Mom za ta kai ta.

Ba ɗakin Mom su ka shiga ba sai ɗakin su Faridan.
Yana zaune akan kujera yana ƙoƙarin duba wassu takardu, yana so ya fara fita aiki ranan monday, tunda yanzu ya gane kusan komai gameda ayyukan sa.

Buɗe ƙofar da aka yi ya sa shi juyowa. Yanzu su ka gama daru da Farida kafin ta fita akan wai ta chanja ma sa tsarin da ya jera kayan sa.

Gaban Najeeb su ka tsaya kallon su ya ke yana so ya gano mi ke faruwa.

Farida ta zage hannu ta falle Najdah da mari. Shi kan sa Najeeb sai da ya tsorata da marin nan.

"Matar yayan ki na ke Najdah, ni ba kishiyar ki ba ce. Idan ba za ki bani girma da matsayi da Allah ya bani a kan ki ba. To kuwa ki shirya dan kafin ayi bikin ki sai na gyara miki zama a wannan gida"

Ta juya ta kalli Najeeb ta ce " ka gayawa ƙanwar ka cewa ba na son raini, ko kuma idan na sa ma ta ƙahon zuƙa a gidan nan sai na zuƙeta zuut"
Ta juya ta fita ba tareda ta jira amsar da zai bata ba.

Najdah ta tsugunna a gaban Najeeb riƙe da fiskarta tana kuka.

"Big B she slapped me. Ba yau ta fara ba, she's being doing this for along time now"

Dafa ƙafarsa ta yi ta ce "Big B ka rabu da ita, she's not good for you wallahi ba ta son ka kuɗin ka kawai ta ke so"

Duk surutun Najdah bai ce komai ba kawai kallon ta ya ke. Bai rarrasheta ba dan haka da kanta ta bar kukan ta share hawayen ta.

"I love her Najdah" ya furta a hankali.

Najdah ta ɗan zaro ido dan ta yi mamakin kalaman Najeeb. Ita tunanin ta duk yadda ta dinga gaya ma sa aibun Farida lokacin yana asibiti abin ya shigeshi.

"Why? Big B why her? Akwai mata dayawa da ke son ka wanda su ka fi Farida komai. A hankali za ka ga wadda ta dace da kai"

"Because i love her"

Najdah ta haɗe rai.

"Ina son ki Baby, you're my dearest sister. Na san abinda ki ke so na yi bai wuce na zaɓa tsakanin ki da Aysherh ba. Kar ki nemi hakan a wajena domin za ki sha mamakin wanda zan zaɓa"

"Big B..."

"Na yadda bakya son ta, ba ta kuma burgeki amma ina so ki ba ta girma a matsayin ta na wacce na ke so"

"Big B you're confused, har yanzu ba ka san wacece Farida ba, har yanzu ba ka tuno rashin mutuncin da ta yi ta shuka ma ka ba. The girl is just a gold digger"

Najeeb yai murmushi ya ce " ki na son Anas ko?"

Najdah ta yi shiru.

"Ba kya tunanin yadda ki ka ƙi ɗan uwan ki Mustafah ki ka amince da Anas haka ƙannen Mustafah za su dinga ganin Anas a matsayin wanda ke son yin auren jari"

"Accept this simple truth Baby. I love Aysherh. Bana tunanin kina yiwa Anas rabin son da ta ke mini"

To mi za ta ce ma sa? wani ƙorafi za ta kuma yi?.tunda wanda ta ke tunanin zai ɗau mataki akan Farida ya nuna ma ta  yana tsananin son Farida. Gwiwa a sace ta tashi ta fita daga ɗakin...

.............................

Yana ɗaura tie ta shigo ɗakin ɗauke da tray. Ta riga ta shirya tuntuni, fita ta yi ta ƙarɓo mu su breakfast.
Bayan ta ajiye tray ɗin ta ƙaraso gaban shi. He looked so handsome a grey three pieces suit ɗin kamfanin Brioni Vanquish II.

Hannu ta sa tana gyara ma sa tie ɗin.

"You look great My Champ"

"I think the right word is handsome" ya faɗa yana kissing hannun ta.

Murmushi ta yi ta ce"Mu je ka ci abinci"

Tea kawai ya sha sai ya ɗan tsakuri soyayyan dankali. Farida kam bayan toasted bread da ta ci guda biyu sai da ta ci soyayyen ƙwai da potato fries ɗin sosai.

Kallon yadda ta ke cin abincin ya ke yi yana sipping tea. Lokaci guda ƙwaƙwalwar sa ta tuna ma sa ranan da Farida ke cin cucumber a mota, yai murmushi.

"Na sani za ka ce wannan matar ta cika ci ko. Ba na juran yunwa ne ga ulcer da ta haɗumin biyu"

Kalmar ulcer da ta faɗa ya sa shi tunowa da ranan da ta sawa Sabreen yaji a gado har ta yi ƙaryar ulcer. Dariya ya farayi saboda tunowa da yai da abinda ya faru.

Tsayawa ta yi tana kallon yadda ya ke dariya, ya mata kyau sosai...

Driver ne ya ja su dan a asibiti sun hana shi tuƙi, atleast sai ya ɗau lokaci. Ita kuma Farida har yanzu ba ta iya tuƙi ba...

Su na fitowa daga mota ya bi building ɗin kamfanin da kallo, akwai so many memories a wannan waje wassu ya tuna su wassu bai tuna su ba. Tafiya su ke a hankali dukkan su biyun kowa da abinda ya ke saƙawa a zuciyar sa.
Dai-dai sun zo ƙofar shiga ya saka hannunsa cikin na ta. Kallon sa ta yi ya ɗaga ma ta gira...

Suna shigowa aka fara tafi, wajen ya sha decoration na flowers ga ƙatuwar banner da aka rubuta *Welcome back Mr and Mrs Najeeb Jibo*
Mutane dayawa da basu halarci waliman gidan su Najeeb ba su ka zo su na musabaha da Najeeb su na ma sa fatan alkhairi. Unlike Najeeb ɗin da yana amsa musabahar ne fiskar sa shimfiɗe da murmushi hatta ma su ƙananan matsayi kamar masinja ko cleaners sai da su ka gaisa da Najeeb.

Anas ne ya ja su suka je wajen da aka ajiye mu su cake, shi da Madam ɗin sa su ka haɗa hannu su ka yanka. A baki ya sa ma ta itama ta sa mishi a baki.
Sun ɓata kusan awa ɗaya a wajen kafin su ka shiga lifter zuwa third floor.

"Ga Mrs Comfort Masoyi ita ce sabuwar Sakatariyar ka"

Mrs Comfort ta rusuna ta gaishe da Najeeb.

Da Bismillah ta shiga office ɗin. Abin mamaki sai ta ga office ɗin ya chanja ma ta. Rabon da ta shigo office ɗin tun farfaɗowan Najeeb. Sau ɗaya ta zo ta yi meeting da wassu 'yan china da su ke son siyan hannun jari amma ba ta basu dama ba.

Office ɗin ne aka raba biyu an saka glass an raba tsakani.

Ba ta san anyi gyaran nan ba hakanan ba ta san wayayi ba.

Waya ta ɗauko tana ƙoƙarin kiran Anas Najeeb ya karɓi wayan.
"I made the changes" ya faɗa yana kama hannun ta su ka shiga ɗaya ɓangaren da aka raba. Bai ajiyeta ko ina ba sai kan kujera.

"You're good in marketting strategies, abinda ya sa ki ka iya bunƙasa kamfanin nan kenan. Ba zan iya yin aiki ni ɗaya ba, kafin na gane kan zaren aikin sai an ɗau lokaci. But with you beside me komai zai zo da sauƙi"

"My Champ..."

"Shhhhh" ya sa hannu ya rufe ma ta baki.

"We're going to work together now and always"

Faɗawa jikin sa ta yi tana kuka.

Ya fara bubbuga bayan ta yana lallashinta...

Shirye-shiryen bikin Najdah aka fara dan an mayar da date ɗin bakwai ga watan January kusan wata ɗaya da sati ɗaya kenan yanzu. Tun daga ranan da Najeeb yai wa Najdah magana ta dena shiga harkan Farida, magana ba ta haɗasu hakanan ba ta iya ma ta kallon banza kamar da...

Najeeb da Farida tare su ke fita aiki su dawo tare. Kusan komai ma ita ke jagoranta dan har yanzu wassu abubuwan sun sha ma sa kai.
Ana saura sati huɗu aure Mom ta sa aka fara yiwa Farida gyaran jiki tareda Najdah, wata mata ce aka kawo daga Sokoto. Farida dai dan Mom ta takura ne amma da ba abinda za ta yi, shi mutumin da za ayiwa gyaran jikinma domin shi har yanzu bayan kiss ɗin cikin mota ba abinda ya kuma yi. Daga ya rungumeta tsam ajikinsa idan za su kwanta sai wani lokaci ya kissing hannun ta ko goshi. Ita idan ba dan ranan a mota ta ji tudun abun shi ba, da sai ta ce ko ba shi da lafiya ne.

Da ke an ɗau hutun ƙarshen shekara ba sa fita aiki yanzu. Daga gida sai gida, ita Najdah har haushin Mom ta fara ji saboda yadda Mom ke wani ɗari ɗari da Farida, duk abinda aka mata na gyara sai ta ce a yiwa Faridan irin sa...

Saura kwana goma shashida a ɗaura aure sai ga Sabreen. Farida tun washegarin da aka yi walima ba ta sake ganin Sabreen ba. Da ke ba ta gabanta shiyasa ba ta tambayi ina ta je ba. Yadda ta ɗauka ma shine Sabreen ɗin ta bar ƙasar kenan har abada, amma da ya ke ba ta da kunya sai ga ta ta dawo. Ta san dai ba wai dan bikin Najdah ta zo ba, wani neman fitinan ne kawai...

Suna zaune a falo dukkan su, lokacin da ta shigo tareda tawagarta su uku. Biyu larabawa ne suma ɗaya kuma baturiya ce.

Najdah da Farida na zaune ƙafafuwan su na cikin ruwan ɗimi wanda aka cikashi da kayan ƙanshi.
Sabreen ta zo da gudu ta rungumi Mom tana kissing ɗin ta. Sai da ta gama shiriritar ta kafin ta nuna team ɗin da ta kawo. A matsayin ma su taimaka ma ta.

Ta kalli wata dattijuwa aciki wacce za ta kai 50yrs ta ce "this is Sarah, ita ce za ta kula da gyaran jikina" sai ta nuna ɗaya matashiyar wacce ba za ta wuce 25-26yrs ba. "Wannan ita ce  Arfa, ita ce za ta dinga min kwalliya" ta nuna baturiyar ta ce "Najdah i brought her specially for you. Sunan ta Jean ita sexologist ce, i know you're a virgin, so she'll help you get rid of the fear and educate you on how to..."

Hahhahaha ta fashe da dariya.

Mom ce ta iya ce mu su sannu da zuwa ta ƙara da cewa " Najdah da Farida ga Sabreen itama ta kusa zama amarya"

Kaman bugun guduma haka Farida ta ji saukan maganan Mom " Sabreen ta kusa zama amarya. Amaryar wa?"

Ka sa zama ta yi a wajen ta cire ƙafafuwan ta acikin ruwan ta sa room slippers ɗin ta da ke gefe ta bar falon ba tareda ta ce komai ba. Ta sani Najeeb baya
nan, tun safe ya fita shi da Daddy. Waya ta ɗauka ta fara kiran sa amma bai ɗauka ba. Abu ɗaya ta sani idan har Sabreen za ta auri wani ba Najeeb ba to ba abinda zai sa ta baro chan ƙasar su ta zo nan ta zauna da niyyar wai ta zo gyaran jiki. Mi ke shirin faruwa?

Ranan har yamma ba ta kuma fitowa ba. Zazzaɓi ne ma ya rufeta. Tana nan haka Najeeb ya shigo ɗakin da sallama.
Ba ta kulashi ba har ya gama abinda zai yi ya zo ya kwanta gefen ta. Ƙanshin jikinta na ratsa duk wani jijiyar jini a jikin sa.

"Mi ya faru na ga ko sannu da zuwa ba ki min ba"

Idonta da su ka yi ja ta ɗago ta kalleshi ta ce "mi Sabreen ta ke yi a gidan nan?"

Ɗan dafe kan sa yai yana danne dariyar da ta taso ma sa.

"Oh sorry" ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce "i'm going to marry Sabreen, rana ɗaya za a ɗaura mana aure da su Anas. You see Aysherh ki na da kyau kuma kin min abinda ba zan taɓa mantawa da ke a rayuwata ba. You'll always be my first wife amma kuma Sabreen will always be my first love"

Dariya Farida ta fara dan maganar Najeeb bai kama hankali ba kwata-kwata.

"Wasa ka ke yi Najeeb, kuma ba na son irin wasan nan, zuciyata za ta iya bugawa"

"I'm serious Aysherh. Na san Sabreen ta yi ba dai-dai ba a baya amma yanzu ta chanja. She loves me"

"Da Sabreen da soyayyar ta sun ci kutumar uban su. Wai Najeeb me ka ɗauke ni ne. Shashasha ko? Wallahi ba zan yadda ba. Yau ko mata uku za ka auro ka auro amma banda Sabreen. Wai tukunna kan ka ɗaya kuwa. Sabreen fa, Sabreen da ta gudu ana saura kwanaki a ɗaura mu ku aure, Sabreen da ta shiga harkan film tana sheƙa ayarta yadda ta ke so, Sabreen da kana kwance baka da lafiya ta shure ƙafa ta tafi ta barka wai za ta je ta yi film da Kwano Reeves ne ko Keanu Reeves ne ma..."

"I know, na san komai Aysherh but kin san soyayyar farko ba ta taɓa gushewa"

Hawaye fal a idon ta ta ce "ni tawa soyayyar fa? Duk son da na ke nuna ma ka a banza kenan, ba ka ɗauke shi a bakin komai ba ko?"

"Aysherh i have feelings for you amma kin san Sabreen..."

"Ya isa haka!" Ta daka ma sa tsawa.

"Ni ba zan zauna da kai ba matuƙar za ka auri Sabreen. Idan ma ba za ka iya zama dani ni ɗaya ba, ka nemi wata mana. Ko acikin cousins ɗinka ka aura amma banda Sabreen. Wallahi ba zan zauna da Sabreen ba"

"Aysherh please, na yafewa Sabreen ke ma ki yafe mata" ya faɗa yana kamo hannunta. Tureshi ta yi ta tashi ta je wajen closet ta fara haɗa kayan ta. Zan bar ma gidan ka, zan bar rayuwan ka, ka zauna da Sabreen ita kaɗai tunda matacciyar zuciya gareka"

"Kin san ina buƙatar ki, Kamfanina tana buƙatar ki. Please Aysher"

"Kai wanni irin mutum ne Najeeb. Ba ka sona, ba ka  tausayina, ni dai kawai na zauna da kai saboda amfanin kamfani"

"Ba haka ba ne Aysherh please ki fahimceni"

Tsugunnawa ta yi a wajen tana kuka. Zuwa yai zai rarrasheta ta buge hannun sa ta ce ya bar wajen ta. Yana tsaye a gefe har ta gama kukan ta ta tashi ta shiga banɗaki ta jima a banɗakin dan aƙalla ta kai kusan minti talatin kafin ta fito. Direct gado ta je ta hau ta kwanta ta rufe dukkan jikin ta...

Yana jin kukan ta a ransa, he wants to tell her it was all a trick amma ya san halin ta, idan ya gaya ma ta komai za ta nuna rashin damuwa, hakanan kuma abinda ya shirya ba zai tafi dai-dai ba dan Sabreen za ta iya ganewa.*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣4️⃣4️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*


Ba baccin daɗi Farida ta yi ba, bacci ne ta yi na wahala. Da huturun sanyi aka tashi da asubahin ranan. Da ƙyar ta tashi ta shiga banɗaki ta yi alwala. Sanda ta farka Najeeb ya fito kenan yana shirin fita masallaci.
Tana idar da sallah ta nemi wata ƙatuwar rigan sanyinta wanda aƙalla ya yi  shekara shida da ta ke amfani da shi. Rigan sanyin doguwa ce mai hula, dan idan ta sa yana wuce gwiwanta. Ko lokacin tana Jos idan ana tsananin sanyi idan ta sa shi ta sa dogon wando da socks shikenan ta yi maganin sanyi. Tana son rigan saboda Ummi ce ta siya ma ta...

Daga sallaya gado ta koma, kan ta ke wani mugun sara ma ta, ga cikinta da ke ta kukan yunwa.
Ba bacci ne a idon ta ba, asali ma jiyan ba ta kwanta da wuri ba. Yadda cikinta ke juyawa ya sa ta tashi dan ta sha gestid ko za ta ji sauƙi duk da kuwa ta san ciwon cikin ba na magani ba ne na yunwa ne. Tana tsaye a wajen dressing mirror tana shan maganin Najeeb ya shigo.
Ta yi kaman ba ta ganshi ba, maimakon 10ml da za ta sha sai ta ƙara wani 10ml ya zamo 20ml, tana tsayen ma wani jiri-jiri ta ke ji.

Yana tsaye yana kallon ta. Har ta ajiye maganin ta je ta hau gado. Bai ce ma ta ƙala ba, zuwa yai ya buɗe fridge ya ɗauko apple guda biyu da su ka saura a ciki. Dama shi kam bayan ruwa to fruits kawai ya ke sawa a ciki.
Sai da ya zauna gefen ta sannan ya ce "Aysherh tashi ki ci apple, bai da ce ki sha magani ba tareda kin ci wani abu ba"

Shiru ta yi ba ta ce komai ba.

"Aysherh"

A harzuƙe ta tashi ta na masifa "ina ruwan ka da ni, na ce ina ruwan ka dani. Na ci abinci, ban ci ba, wannan ba matsalar ka ba ce"
Juyawa za ta yi ta kwanta ya ce "Aysherh amma rigan sanyin kin nan gwanjo ce ko? As in Okrika, fairly used cloth..."

"Eeh shi ne, gwanjo ne, amma ka san me? ta fi designer cardigans ɗin da ka ke sawa. Tunda shekara da shekaru tana min maganin sanyi"

"Oh really, kinga banbancin ki da Sabreen kenan. Sabreen ba za ta taɓa saka irin wannan kaya ba"

"Mugu, butulu, ka bi ka damu mutane da Sabreen Sabreen, daɗin abin ma karuwa ce. Karuwa mai lasisi ma. Idan ita ba ta sa gwanjo ni a ina sa gwanjon ka ganni ka ɓata min aure saboda ka aure ni. Ka ga gwanjo kuwa sun min rana"

Sake miƙa ma ta apples ɗin yai wannan karan ta wafce a hannun sa.

Sai da ya ga ta fara ci sannan ya ce " Sabreen ta tuba Aysherh. Kuma Allah Gafurun Rahimun ne zai gafarta ma ta"

"Allahu Akbar, Ashsheikh Najeeb Adam Jibo Rahimahullah. Aje dai a ƙarata da ragowar kafirai" fa faɗa tana hararar sa

"Yawwa Uwargida na, Aysherh mai gwanjo"

Dundu ta fara kai ma sa da apple ɗin a hannunta tanayi tana kuka, dayaga abin na yi ne ya tashi a gadon da sauri yana dariya...

...............................

Ƙarfe shaɗaya ta fito dan ta maida plates ɗin abinci kitchen. Sabreen ta gani da tawagarta a falo su na duba wassu jewelries.

"Aishah" Sabreen ta kira sunan ta.

Farida ba ta juya ba, ta dai tsaya. 

Sabreen ta taso ta zo gaban ta riƙe da sarƙa. Ta kai hannu za ta gwada sarƙan a wuyan ta Farida ta buge hannun.

"Kar ki taɓa ni!" Ta faɗa da tsawa.

"I wanted to give it to you Ayshah, i mean no harm"

"I dont want anything from you, you whore" ta faɗa tana barin wajen.

Sabreen ta yi murmushi dan ta san kishi ke cin Faridah...

Daga kitchen ɗakin Mom ta wuce. Mom ɗin ma jewelry box ta buɗe tana ware jewelries da za ta bawa Najdah da wanda za ta bawa Farida.

Da sallama Farida ta shigo, ko gaisuwa babu ta tsugunna a gaban Mom ta ɗaura kan ta a cinyarta tana kuka.

"Miya faru?, Aishah talk to me, miya same ki?" Dan ta tsorata da yanayin ta.

"Mom dan Allah ki ce Najeeb kar ya auri Sabreen, Mom mutuwa zan yi idan ya aureta. Mom dan Allah"
Tana maganan tana kuka.

"Farida, Najeeb yana son ki. He loves you so much"

"Mom ƙarya ne baya sona, idan yana sona ba zai ce zai auri Sabreen ba. Mom yaushe ma ya samu lafiya da har zai yi zancen aure. Wallahi idan har ya aureta ba zan zauna da shi ba" ta sake fashewa da kuka

"Farida sai ki barwa wata mace mijin ki, mijin da ki ke tsananin so"

"Mom ba zan iyaba, mutuwa zan yi, Mom please ki ma sa magana"

Tausayin Faridan ne ya kamata. Tsoron ta kar garin neman gira a rasa ido. Ya sa ta yanke shawaran gaya ma ta gaskiya.

"Barin gaya mi ki abinda ke faruwa, amma ba na so ki nuna kin sani"

Farida ta girgiza kai tana share hawayen da ke shimfiɗe a fiskarta...

...........................

Bisa shawaran Mom ta fara attending class ɗin da Miss Jean ke yiwa Najdah. Ranan da ta zo kunya ne ta cika ta, da ƙyar ta iya ƙarasa class ɗin. Baturiyar matar nan ba kunya ba komai ta ke bubbuɗe mu su abubuwa, tun daga sizes na girman abun zuwa yadda su ke idan suna cikin aiki. Bayan an gama bayani aka koma kan su mata. Da Faridan da Najdan dukkan su ashe shatara su ke cikon ishirin. Sun Jahilci abubuwa dayawa gameda jikin su da kuma yadda za su sarrafa mazajen su saboda kar a samu matsala...

A ranan lecture na biyu Jean ta fara nuna mu su different sex positions. Farida ganin abun na wuce gona da iri ya sa ta tashi za ta fita, sai ga Sabreen ta shigo.

Ɗan dariya ta yi ta ce "you're still a virgin? You mean Noory never ..."  sai ta sake kwashewa da dariya.

Haushi ya cikata har wuya, ba dan ta san gaskiya ba, da yanzu  ba abinda zai hanata marin Sabreen.

"Dont be shy Ayshah. Na san kin fi Najdah buƙatar lectures ɗin nan. Domin sai kin yi da gaske kafin ki samu kan Noory idan mu ka yi aure"

Farida ta cize leɓen ƙasa tana huci. Sabreen zuwa ta yi ta gayawa Jean saƙo sannan ta fita. Sai da ta fita Farida ta koma ta zauna, duk da dai tana jin kunya haka ta daure tana ƙaruwa da bayanan Miss Jean...

Najeeb kan bai fahimci komai ba saboda Farida ba ta nuna ma sa ta san plan ɗin shi ba. Har yanzu ba ta sake mishi fiska, maganan kirki ba ta shiga tsakanin su...

Wasa-wasa ranaku su ka dinga tafiya har ya saura kwana huɗu ayi aure. Gidan na su ya fara cika da mutane. Da ke Najeeb ya cewa Sabreen baya son hayaniya shiyasa ba ta nuna zaƙewa kan wassu lamuran ba. Dama itama ta ce tanason auren ne a sirrance dan kasancewarta celebrity idan maganar auren ya fito fili za ayita cecekuce, tafiso ko da za ayi gulma to ya zama bayan auren ne...

Ba wassu 'yan uwa ba ne su ka zo daga ɓangaren Sabreen mahaifinta ma tun zuwan sa Walimar Najeeb da ya koma ciwon sa ya tashi, yana chan London ana kulawa da shi. Sabreen independent woman ne. Da 'yan uwa, ba 'yan uwa za ta yi aure ba abinda ya shafeta. Ƙanin Mahaifinta ne ya zo sai kuma yayan Mom da yayar Mahaifiyar Sabreen...

Daddy ya ce baya son hayaniya saboda albarkar aure ake so ba komai ba. Najdah ta so ayi dinner amma Daddy ya hana. Shi Daddy tun ciwon Najeeb yai wa kan sa karatun ta nitsu wajen almabazzaranci da kuɗi. Da da ne ba ƙaramin bidiri za ayi a bikin ba, dan ko lokacin auren Najma ansha shagali sosai...

Daddy bai san mi Najeeb ke shiryawa ba sai da ƙanin Baban Sabreen ya ma sa maganar sadakin Sabreen. Abun ya ɗaure ma sa kai, a take a wajen ya kira Najeeb.
Da Najeeb ya zo haƙuri ya bayar tareda nuna mu su cewa ya yi hakan ne saboda ya kowa wa Sabreen hankali.
Daddy ya rufe shi da faɗa yayinda Hajj Khalid Abu Nasir ya fahimci Najeeb ɗin. Tunda shi kan sa ya san lokacin da aka kashe maƙudan kuɗi wajen shirya bikin su amma Sabreen ta gudu ta bar su da abun kunya. Hakanan bai taɓa goyon bayan shiga film da Sabreen ta yi ba...

Ranan Jumu'ah bayan an yi sallar Jummu'a aka ɗaura auren *Architect Anas Ali Almustafah da Najdah Adam Jibo* biki ya samu halartar manya-manyan mutane...

Sabreen wani farin wedding dress ta saka wanda ta aje maƙudan kuɗi aka designing purposely saboda ita. Ta sha ado na dimond da gwalagwalai. Hakanan make-up artist da ta zo da ita Arfa ta rangwaɗa ma ta kwalliya, ba ƙarya ta yi kyau sosai.

Wanda su ka dawo daga wajen ɗaurin aure ne su ka fara labarin yadda taro yai taro. A wajen Mouna ƙanwar mahaifiyar Sabreen ta ji aure ɗaya aka ɗaura, auren Najdah da Anas. Mamaki ya sa ta wuce ɗakin Sabreen wanda ke ta ɗaukan selfie cikin kayanta na aure kafin su zo su yi hoto da angonta...

Maganar da Mouna ta gaya ma ta ne ya sa jikinta ya fara rawa. Waya ta ɗauko da sauri ta kira uncle ɗin ta wanda ya ƙara jaddada ma ta auren Najdah kawai aka ɗaura ban da na ta. Wayar hannun ta ya suɓuce ta yi durƙushe a ƙasa kanta na ma ta wani nauyi, zuciyarta na cigaba da bugawa da ƙarfi-ƙarfi kaman wanda zai bulluƙo...

Manage this plz banda chaji.

* ku wanke idon ku da kyau gobe za'ayi abubuwa😂**SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣4️⃣5️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*

Duk yadda ta daure ma zuciyarta ta ka sa saboda wani ƙunci da ya cika ma ta zuciyar.
"Ahhhhhhhh" ta fashe da kuka

"Noory dont do this, dont do this to me plz" sunbatun da ta farayi kenan tanayi tana kuka.

"Mahlan yaa Sabreen, Mahlan binti" Mouna ta faɗa tana ɗan bubbuga bayan ta.

Lokaci guda ta yi wuff ta miƙe tsaye tareda tattare rigarta da ya baza waje ta fita da gudu, su Mouna su ka bi bayan ta...

Ɗakin Mom ta shiga ba ta nan dan haka ta sauko ƙasa da gudu tana kiran Noory.

A falon ƙasa ta yi kiciɓus da Najma. Najma cikin sanin miya faru ta fara tambayan lafiya, Noory kawai ta iya furtawa.
Najma ta ce bayanan. Sabreen ta fita da gudu tana kiran Noory...

Yana wajen reception Najma ta kira shi akan ga Sabreen tana ta kuka tana neman sa. Ya san za ayi haka, hankalin sa kwance ya ce a bashi 30mins yana zuwa. Shi yadda ya tsara ma baya so ta gano shi har sai dare idan ya zo da niyyar zai ɗauki amarya. A yadda ya sharara ma ta ƙarya cewa yai shi zai zo ya ɗauketa su je gidan sa inda anan za su ci amarcin su. Ai raka amarya ƙauyenci ne, ita kuma Sabreen ba 'yar ƙauye ba ce...

Zuwa yanzu kusan kowa agidan ya san abinda ke faruwa. Sabreen tana zaune tana kuka, fiskar nan duk ya chaɓe, kwalliyar da aka wa idon duk ya zazzago sai idonta ya zama kaman wani horror.
Sai lallashinta ake, wanda ba su san mi Sabreen ta yiwa Najeeb ba su ka fara zagin Najeeb, wassu har cewa su ke ƙila ƙwaƙwalwarsa ce ta motsa tunda ance tun rashin lafiyan da yai ƙwaƙwalwarsa ba ta dawo dai-dai ba. Ka ji mutane fa...

Farida tun da sassafiya da su ka tashi ta fara wani tsumewa ita a dole yau za a mata kishiya. Da Najeeb ya ɗau wanka ya sha manyan kaya zai tafi ta ce ma sa "Allah ya taimaki angon Sabreen"
Yai dariya kawai ya fita. Kwanciyar ta ta yi, sai ƙarfe goma sha ɗaya ta tashi. Bayan ta yi wanka ta shirya sannan ta fito. Ƙasa ta sauka dan ta nemi abinci dan tsayawa sai Adama ko Tasallah sun kawo ma ta har ɗaki ba adalci ba ne dan ta san aiki ya sha mu su kai..
Bayan ta karya Mom ta kirata, da ta je kaya ne ta bata wanda za ta sa a yau ɗin, ta karɓa tana godiya...
Tana ɗaki ta idda sallar azahar kenan ta ji ihun Sabreen. Jin hayaniya ya fara yawa ya sa ta sauko dan kar ayi show ɗin ban da ita...

Ba ƙaramin cika aka yi a falon ba. Kowa da abinda ya ke cewa zuwa yanzu Sabreen ta dena ihun kuka. Hawaye ne kawai ke zuba a idon ta...

Har lokacin kayan da ya sa ya je ɗaurin auren ne a jikin sa amma babu malun-malun ɗin. Bai yi mamakin ganin yadda mutane su ka cika falon ba dan yasan mata da gulma. Najma da Mouna ne ke gefen Sabreen su na ƙara lallashinta.
"Ga Najeeb ɗin" Najma ta faɗa lokacin da ya shigo.
Zumɓur ta miƙe ta nufe shi.

"Noory why? Why?" Ta faɗa  tana dafe ƙirjinta da ke ma ta zafi.

Ɗan murmushi yai sannan ya ce "Why? Sabreen ki na tambaya na Why?. The same why da ki ke tambaya shi na yi ta tambayan kai na 9yrs ago. We were inlove remember, we made so many promises. Sabreen why? Abinda na yi ta tambayar kai na kenan. It took years kafin na amince wa kai na cewa ni ko soyayyata ba komai ba ne a wajen ki. That being an actress ya fi ni muhimmanci a wajen ki. That having a role in a movie ya fi aure na a wajen ki, That the love we shared was fake, that everything about you is fake"

Sabreen ta tsugunna a ƙasa tana ƙara danne ƙirjinta saboda gani ta ke idan ta cire hannunta ƙirjin ne zai fito saboda yadda ya ke bugawa da ƙarfi.

"Kina ji kaman zuciyar ki za ta fashe ko? Thats exactly how i felt and even more, na tsani kowa na tsani komai, na zamo tamkar mahaukaci. Sai da na yi watanni bana cikin hayyacina Sabreen. Ba na iya bacci sai na sha magani ba na iya cin abincin kirki. Years went by and i couldnt love again, kyawawan mata, mata ma su matsayi da ƙasaita fiye da ke sun nemeni amma idona ya rufe, ba na kallon kowa sai ke. In those 8years da na yi ta yawo da dakon soyayyar ki not once ki ka waiwaiye ni, not even once Sabreen. You're busy creating your fake life, kin manta da ni gaba ɗaya. In 8yrs  kin je an mi ki butt enlargement, kin je an miki plastic surgery an gyara miki wide lips ɗin ki, in 8yrs kin dating manya-manyan mutane guda uku, in 8yrs kin zubar da ciki that almost killed you because you nearly bled to death. In 8yrs kin renouncing addinin ki saboda kina son auren wani ƙaton kafiri. In 8yrs..."

"Noory stop, plz stop" Sabreen ta faɗa tana kuka tana riƙe ƙafar sa.

"Sabreen ban miki haka dan na punishing ɗin ki ba sai dan na nuna mi ki cewa rayuwar ki tana tafiya ne base on movie scripts and you need to wake up. A year ago da ki ka dawo kin ce kin ajiye film saboda ni, kin ce kina so ki zauna kusa da ni ki samu soyayyata a karo na biyu, but few months bayan na shiga coma ki ka tattara kayan ki ki ka koma Hollywood saboda an baki role tareda Keanu Reeves"

ƙaramar dariya yai kafin ya ce "And the stupid thing shi ne a gaba ɗaya film ɗin sau uku ki ka fito, Sabreen kin tafi kin barni saboda kawai ki yi fita uku a film. I think ba ki shirya wata rayuwa ba bayan film, so go back to Hollywood, i dont need you, nobody needs you here"

Ya yafce ƙafarsa daga riƙe shi da ta yi.Har ya juya zai fita sai kuma ya juyo ya ce "actually ya kamata na gode miki ne ma, because you left i finally found true love, and i finally know real love. So thank you Sabreen"

Wannan karan gaba ɗaya ƙasa ta yi kamar wata mai sujjada tana buga ƙasa tana kuka. Wassu sun ji tausayinta wanda ba su gane maganganun Najeeb ba kenan saboda ingautsan Larabci da kuma turanci da ya yi. Amma wanda su ka fahimci mi ya faɗa ba su ji tausayin Sabreen ba"

Farida na ganin yadda Sabreen ke kuka sai ta ɗan ji tausayin ta, ko ba komai ta san ya ake ji idan ranan auren mutum  ya zo aka samu matsala aka fasa auren, she felt it twice, so ta san zafin abin. Juyawa ta yi jikinta a sanyaye ta bar wajen...

...... .......... .......

Da yamma ta ci kwalliya su ka fita aka yi ta ɗaukan hoto, kaman ba abinda ya faru haka aka cigaba da hidima. Ango da tawagar sa sun zo an yi hotuna. Najeeb ma ya je ya chanja kaya ya zo aka fara hotunan da shi.
Wani hoto da za su yi su biyu ya ɗan rankwafo kan sa dai-dai kunnen ta ya ce "ki shirya yau za mu yi abubuwa"
"Wane ni Aisha, abubuwa ai sai Noory da Sabreen ɗin sa"
Ya ɗan cizi kunnen ta ta yi 'yar ƙara...

Daren ranan ƙarfe takwas aka shirya amarya Najdah za a kaita ɗakin ta. Farida ta gama shiryawa akan za ta raka amarya sai ga kiran Najeeb tana ɗauka ya ce ta sameshi a ɗaki. Tana ƙunƙuni ta wuce ɗakin.
Gani ta yi shi kam ko shiryawa bai yi ba jallabiya ce ma a jikin sa.

"Ba za ka zo ka raka ƙanwar ka ba, Anas fa yana buƙatar abokin da zai taya shi siyan baki"

"Ni idan na tafi wa zai tayani nawa siyan bakin?"

"Kai ka sani, ni kam bari mu je kai amarya dan yanzu tana wajen Daddy ba za su jima ba za su tafi"

Hannun ta ya riƙe ya ce "wani raka amarya kuma, bayan ga mijin ki nan yana buƙatar rakiya"

"Allah ka bar ni na je, ai sai a ga baƙina idan ban je ba ƙanwar miji guda"

"Na ƙi ɗin, serious Aysherh akwai inda za ki raka ni"

"To ka bari idan mun dawo daga kai amarya"

Ya lakuci hancin ta ya ce "No, yanzu za mu je mu dawo, ƙila ma har mu dawo ba a tafi da amaryan ba"

"Serious?"
Ya gyaɗa ma ta kai.
Fita yai bayan ya ce ta sameshi a wajen mota.

Ba abinda ta ɗauka sai purse da waya, ta gyara gyalenta ta fita...

Motar ta ce dai da Daddy ya bata anan ta sameshi, Ta shiga baya ta zauna saboda Abdullahi dreba ne zai kai su.
Sai da su ka haɗa ido ta ga yadda Najeeb ke mata murmushi tukunna ta ankare da abu biyu na farko ɗazu da yamma Najeeb ya ce yau za su yi abubuwa, na biyu kuma idan ba Sallah ba Najeeb ba ya fita da Jallabiya yanzu kuma Jallabiya ce a jikin sa.

"My Champ mu koma gida na yi mantuwa"

"Kar ki damu ba daɗewa za mu yi ba"

"My Champ wayata, na manta da wayata"

Dariya ya suɓuce ma sa ya ce " ko dai kin manta wayar a hannun ki"

Ta dubi hannunta sai ga wayar, ta san dama ta fito da waya amma ta manta wayar na hannunta lokacin da ta yi maganar ta manta waya.
Haɗe rai ta yi ta juya gefe ba ta sake magana ba. Yadda ya ke murza yatsun hannunta a hankali ya sa tsikar jikin ta ya fara tashi, darussan Miss Jean na yawo a ƙwaƙwalwarta. Tunaninta kar fa abun Najeeb ya zama irin wanda Miss Jean ta mu su bayani, har ta ga Najeeb da BLTD yana shigarta. Kai anya za ta iya, duk da Miss Jean ta mu su bayanin cewa idan aka bi wassu procedure zafin da za ta ji ɗan kaɗan ne, ƙila ma zafin ma ba za ta ji ba.
Kai amma yadda ta ga zanen ƙaton abun nan da Miss Jean ta nuna mu su za'a samu matsala idan irinsa ya shigeta...

Duniyar tunanin da ta tafi da lissafe-lissafen da ta ke yi ya sa ba ta ankara ba ta ji ƙaran buɗe gate. Ta ɗaga kai ta ga ƙaton gidan da su ka shiga. Tunaninta hotel ne, haushi ya kamata idan ma za su yi abu sai a gadon hotel haba.

"My Champ dan Allah ya za ka kawoni hotel"

" waya gaya mi ki hotel ne"

"To gidan waye?"

"Shhhhhh ba na son yawan tambaya"

A bakin gidan Abdullahi ya tsaya, wanda tsakanin gate da inda gidan ya ke ma tafiya ce mai tsayi dan idan ka fito da ƙafa daga ƙofar gidan zuwa bakin gate a tafiyar sauri sai ka yi minti biyu kana tafiya kafin ka iso gate ɗin.

Najeeb ne ya fara fitowa, ita kan ta dake cikin mota tana ganin ikon Allah. Zagayowa yai ya ɗauketa "ka barni zan fito da kai na"  bai saurareta ba ya ɗauki a barsa su ka wuce gidan.  Wassu numbers ya danna ƙofar gidan ta buɗu.

"Mu shiga da Bismillah" ya faɗa yana kallon ta.
A fili yai na shi ita kuma ta yi a zuci.
"Aysherh anya kin yi?"
Ta zumɓuro ba ki ta ce "na yi a zuciya fa"
Ganin sun ƙutsa kai cikin gidan kai tsaye ta ce
"Yanzu idan mutanen gidan su ka ganmu ahaka ya ka ke so na ji, dan Allah ka saukeni"

"Mune mutanen gidan ai"

Ya faɗa yana kissing goshinta. Sama ya haura da ita wanda mamaki ya sa ba ta ƙara cewa komai ba.

Wani ƙaramin falo su ka shiga ba shi da wani tarkacen furnitures a ciki, komai a wajen fari ne, ya ajiyeta akan kujera.
"Close your eyes"

"Idan na rufe ido ka yanka ni fa, daga rufe ido sai na ganni a lahira, ba zan rufe ba"

"Ke kam ba daɗin ki ba, daga zuwa soyayya sai a zarce gidan gaskiya"

"To ba zan mutu yanzu ba Malam, sai na ga 'ya 'ya na"

Yai murmushi ya ce " mu je to ki karɓi saƙo, idan ki ka ci sa'a ma wannan shekaran sai ki fara ganin 'ya'yan na ki"

"Ni dai ba haka na ke nufi ba"

Hannu ya sa ya toshe ma ta baki " mu je ki ga wani abu to"...

Tana tsaye amma sanyi da ƙanshin ɗakin ya cikata har wani laƙwas jikinta yai saboda kasala da ta ji ya sauka ma ta.

"Janjanin ya isa haka ka buɗe mun ido na ga inda mu ke"
A hankali ya cire hannunsa daga idon ta.

Wani makeken gado ta gani a gabanta wanda aka zuba real roses a kai.

Hannun sa a kan ƙugunta ya ce " do you like our bed?"

"Ni dai ka maida ni gida zan je kai Amarya" ta faɗa cikin shagwaɓa.

"Yanzu ma a gidan amaryan  ki ke"

"Ba wani, ni dai ka maida ni gida"

"Yanzu ma a gidan ki ke"

"Ni dai..."

"Kin san idan ki na yawar maganan nan, all i wanted to do is to kiss you. Should i?"

Ta sa hannu ta toshe bakin tana sake wani munafukin murmushi...

Cewa yai ta rage kayan jikin ta ta yi wanka.
"To inada wassu kayan ne idan na cire wannan?"

"Idan ba wassu kayan you can sleep naked ai ba matsala"

Dundan cikin sa ta yi ta gudu. Shi kuwa ya fara dariya.

Banɗakin ma wani abun kallo ne, da tana ganin na ɗakin su na chan gidan Daddy yana da girma amma wannan ya kusa biyun wanchan. Jacuzzi bathtube  ta ke son shiga amma ganin ba ta gane kan abin ba ta je wajen shower wanda ya ke da warm and cold. Ta sakarwa kan ta warm ɗin...

Aƙalla ta yi minti ishirin a banɗakin kafin ta fito. Baya ɗakin amma ga hijabi da wata rigan bacci a kan gado. Idan ba maimaita kayan da ta zo da shi za ta yi ba saka rigan baccin nan shine option ɗin ta.  Ta ɗau rigan ta sa ka wanda ta ke tunanin ko a ina Najeeb ya samo wannan rigan oho. Ta saba saka ƙananan kaya idan su na tare amma banda irin wannan, domin wannan kam sai a hankali. Ta warware hijabin ta sa wanda ya kai ma ta har ƙasa. Maida towel ɗin da ta yi amfani da shi ta yi banɗakin kafin ta fito kuma  ya dawo ɗakin.

Hango ledodi uku ta yi a kan ƙaramin center table da ke ɗakin yana ƙoƙarin ajiye plate da spoon da forks.

"Come here my love"

Ƙirjinta ne ya fara ɗan bugawa da sauri-sauri.

"Barin yi alwala" ta faɗa ta shige banɗakin da gudu wanda a zahiri ta yi alwalan lokacin da ta yi wanka. Ta jima tana saita nitsuwarta kafin ta fito bayan kaman 5mins. Miss Jean ta ce "dont panic or else ko ba zafi za ki ji zafi"...

"Akwai fried chicken, akwai grilled chicken. Wanne za a fara serving na ki?"

Dariya ta fara saboda wani farinciki da ke mamaye da ita...

Duk yadda ta ke ɗokin cin kazan nan sai ta ji ta kasa sakewa ta ci shi da kyau, Najeeb ke ba ta a baki. Da ta ce ma sa ya isheta sai yai murmushi ya ce "ni dai na san Aysherh na ba ta ƙoshi da wuri ban san miya chanja ba yanzu"

Murmushin ya ƙe ta yi. Dan duk yadda ta ke ƙoƙarin kauda tsoron da ke ranta ta kasa.  Da tana ɗokin wannan rana and now that komai ya fara zama gaskiya sai ta ji tsoro da fargaba na ƙoƙarin cika ma ta zuciya.

Wanka ya shiga shima bayan ya tattare wajen. Ita kan har ya fito ba ta iya taɓuka komai ba haka nan ba ta cire hijabin ba...

Sallaya ya shimfiɗa bayan ya sa silk pyjamas na shi navy blue, wannan karan ba baƙi ba kamar yadda ya saba sa baƙaƙe..
Sallah ya ja su raka'a biyu, bayan ya idar ya mu su addu'a sosai. It took him 8yrs ya sake aure bayan maganar auren su da Sabreen ta tashi. And it took a year kafin wannan rana ta zo ma sa, finally zai kasance da matar sa kuma abar son sa...
Tashi yai bayan ya gama addu'an ya je ya buɗe wata drawer ya ɗauko wata file. Gaban Farida ya durƙusa wanda ke zaune tana jan carbi tun bayan sallan da su ka yi😂.

Buɗe file ɗin yai ya fiddo da wassu takardu guda uku ya miƙa ma ta. Karɓa ta yi tana jiran ƙarin bayani, biro ya miƙa ma ta ya nuna ma ta chan ƙarshen takarda ta farko ya ce " sign here"

Muryanta na rawa ta ce "my champ minene?"

"Just sign" ya faɗa yana murmushi. Ba ta tsaya karanta mi aka rubuta ba ta signing a wajen. Sauran takardu biyun ma sai da ta sa hannu. Da ta gama ya karɓi takardun ya maida su cikin file ya ce " Aysherh Farida Salihu. Yanzu haka kina da 25% shares a Najeeb constructions"

Zaro ido ta yi tana mamaki.
"Ni?"

"You deserve it and even more"

Magana ta ke son yi ya haɗe bakin su...

It was a different kiss a different feeling. Kowanni jijiya a jikinta na amsa wannan saƙo. It took him less than 3sec ya cire hijabin jikin ta. Ɗaukan ta yai sai kan gado still bakin su haɗe da na juna...

Zama su ka yi akan gadon yana gaya ma ta kalamai ma su daɗin ji while working his hand all through her body. Ya ɗauko ɗaya daga cikin rose ɗin da ke gadon ya fara goga ma ta a fiska.
"I love you Aysherh" ya faɗa yana shafa ma ta rose ɗin a lips ɗin ta.

"I love you too" ta faɗa da ƙaramar murya

Bai yi ƙoƙarin cire rigan jikin ta ba sai da ya ga ta gama sake jiki da shi. Lokacin da ya cire ɗin ma ba ta yi ƙoƙarin kare jikin ta ba, she just lay flat amma idon ta a rufe ya ke.
Kissing ɗin dukkan gaɓoɓin jikinta ya ke har ya kai wajen cinyoyinta, Was she nervous? Was it intentional? Amma dai sai ga tusa ta fito.

Rintse ido ta yi da ƙarfi kunya ya cikata " Allah na riƙeta, na riƙeta amma munafuka sai da ta fito, i'm sorry"

Ƙara kissing ɗin ta yai a wajen ya ce " kar ki damu my Love mun zama ɗaya"

"But it was embarrassing"

Bai amsa ma ta ba ya cigaba da sarrafata a hankali...
Miss Jean ta gaya ma ta idan ta sake jikin ta komai zai zo da sauƙi shiyasa ko Lokacin da ya ɗan ɗaga ƙafanta sama  ba ta kame jiki ba ta bashi full access.
Pillow ya sa ata bayan shi saboda ya samu full support sosai.
Ta riga ta jiƙe he sees it and he feels it. Bai shiga ciki ba ya fara goga ma ta abun a bakin wajen.
"Plz ka min a hankali, na san an daɗe ana shan kanwa"

"Ni kuma na san matar da na aura jaruma ce" ya faɗa yana kissing ɗin wuyan ta har lokacin bai sa abun a ciki ba. Lokacin da ya ɗago ne yai addu'ar saduwa sannan ya sa abun a ciki, bai shiga a lokacin ba sai a na biyun da ya sake turawa da ɗan ƙarfi.

"Wayyo, wayyo, dan Allah ka cire, dan Allah"

He was going in gently amma fa lokaci guda shi kan sa ya kasa sarrafa kan sa, he wanted to go easy amma kaman ba shi ke controlling kan shi ba a wannan lokacin, he was going fast and with full speed...

Yaƙushi da cizo ba wanda tabon sa bai fito a soft skin ɗin sa ba. Ta yi kuka har da mai kamar busar sarewa. Miss Jean kuma ta sha tsinuwa ba kaɗan ba, dan a ganin Farida ƙatoton ƙarya ta mu su lokacin da ta ce zafin  da za su ji kaɗan ne.

Najeeb ma sai da hawayen daɗi ya zubo a idon sa. Finally zai buga ƙirjin sa ya ce "i'am now a man"...*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣4️⃣6️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*

It took a very long while kafin yai release. Ya kwanta gefenta yana maida numfashi, ya juyo ya kalleta idon ta a buɗe, amma idon yai jaa ga hawaye da majina duk sun ɓata fiskar, lips ɗin ta na ƙasa yai jaa sosai saboda cize leɓen da ta rinƙa yi.
Goshinta ya ɗan tallafo ya kissing ya ce "Thank you Aysherh, thank you my Queen. Jazakillahu Khairan my love"

Ba abinda ta iya cewa sai ma wani hawayen da ya fara zubowa. Sa harshensa yai ya fara lashe hawayen ta sa hannu ta makeshi.

"Ashe har yanzu da ƙarfin ki, barin je second round kawai"

Buɗe baki ta yi za ta yi magana amma ta kasa.

Murmushi yai yace "once upon a time bakin Aysherh ya mutu"

Hannu ta ɗaga ta ma sa daƙuwa.

Ya kama dariya, yana miƙewa tsaye tareda yin miƙa. Farida ta bi bayanshi da kallo. Ɗakin da ɗan haske dan ɗazu da su ka hau gadon Najeeb ya rage hasken wutan zuwa dim ne. This is the first time da ta ke ganin mijinta naked. Ashe kullum da ta ke ganin shi cikin kaya ya sa ta renan ma sa. Standing there naked ta ganshi a namijin sa. Hararan bayan sa ta ke yi har ya wuce banɗaki...

Sai da ya heating ruwan a jacuzzi tube sannan ya fito cikin zuciyar sa yana tunanin anya ruwan bai yi zafi dayawa ba. To amma ya karanta cewa a hot sit bath zai sa mace ta ji sauƙin zafin.

Har lokacin daya ƙaraso tana kwance, ta so tashi amma ƙafafuwanta sun ƙi bata haɗin kai. Ɗazu kam ta sadaƙar Najeeb karya ma ta ƙafa zai yi yadda ya dafe su ya ke shiganta da sauri-sauri. Duk shegiyar Miss Jean ne da ta shalala mu su ƙarya cewa idan su ka ɗaga ƙafa zai sa a disvirgining na su da sauƙi. Bayan wahala ga wahalan ɗaga ƙafa. Tana cikin saƙa da warwara ta ji ana ƙoƙarin ɗaukan ta. Ta fara ƙoƙarin riƙe zanin gado amma ina tuni Najeeb yai wuff da ita...

Ihu ta saka lokacin da ya sa ta cikin ruwan zafi. Tana ƙoƙarin tashi ya maidata.
Da dashashshiyar murya ta ce "ka cire ni dan Allah,  zafi" bai kulata ba  "ɗuwawu na zai mele, wallahi ya ma fara dafuwa, ka cireni dan Allah"

Aysherh kenan, amidst pain ma dai bakin ba zai yi shiru ba.
"I'm sorry my love, za ki ji daɗin jikin ki anjima"

Haka ta dinga kuka har ruwan yai sanyi...
Bayan ya gama gasa ta ya taimaka ma ta ta yi wankan tsarki sannan ya ɗaukota, a ɗan bakin gado ya zaunar da ita amma kafin ya dawo ta kwanta. Saboda ana sanyi sai da ya shafa ma ta mai kafin ya sa ma ta kayan baccin sa ma su kauri.  Kan kujera ya maidata sannan ya je ya yaye bedsheet ɗin ya ɗauko wani ya shimfiɗa...

Magani ya bata tana kumfar baki ta sha da ƙyar sannan ya maidata kan gado ya ja ma ta bargo.  Bayan yai wanka yai alwala  ya gabatar da sallah raka'a biyu yana ƙara godewa Allah da ya sa duk wani pressure bai sa ya resulting to zina ba. It wasnt easy amma Alhamdulillah ya tsira ko da da ƙyar ne...

Jawota jikin sa yai lokacin ta jima da fara bacci. He still wish he can go in again saboda yadda ya ke jin sabon ƙarfi na taso ma sa amma kuma dole yai haƙuri...

Safiya...

A hankali ta fara buɗe idon ta da takejin sun ma ta nauyi. Idonta cikin na sa ya ma ta ƙuri da ido yana kallon ta yana murmushi.
Ita ne ta janye idon ta tana ƙoƙarin juyawa ɗaya ɓangaren.

" wakey-wakey its already past seven"

Ta rintse ido tana tuno wahalar jiya.
Ganin ba ta da alamar tashi ya sa ya ɗauketa, tana ta ƙoƙarin tirjewa.

Wannan karan ma shi ya taimaka ma ta ta yi wanka ta yi brush ta yi alwala.

Sai da ta fara sallah ta kai ruku'u ta ji ƙafafunta suna ma ta wani zogi. A daddafe ta samu ta idar da sallan. Ta koma kan gado ta kwanta dan har yanzu jikinta ciwo ya ke.
Lokacin da ya shigo ɗauke da tray ta kalleshi daga sama har ƙasa tana ƙaramin tsaki a ranta. Ba dole ta wahala ba irin kayan da ya ajiye under that jallabiya ai ba kaɗan ba. Dama Miss Jean ta ce most at times za ka siraran mutane sun faye samun babban abu.

Ƙarasowa yai kan gadon yana ajiye tray ɗin gefe.

"Good morning my Queen, ya jikin na ki. I made breakfast for you"

Ta ɗan tallafo kai ta ga tray ɗin, omelette ne sai apple da grapes a gefe da tea.

"Ka yi wa kan ka breakfast dai ba ni ba, wannan ne zai ishe ni"

Ya taƙali hancinta ya ce "na san matata akwai ci, but manage this please, na sa a kawo miki special breakfast daga gida, ki ci wannan kafin nan"

Yunwa ta ke ji dan jiya ba wai ta ci kazan nan sosai ba ne. Kwaɗayin kazan ma ta ke ji yanzu.
Ta tashi zaune ya ɗaura tray ɗin a kan cinyar sa ya na sa ma ta grape ɗaya a baki ta fara taunawa tana jin daɗin sa...


...........................

Karfe tara saura na dare aka kai amarya Najdah zuwa ɗakin ta. Bayan nasiha da 'yan koke-koke aka watse aka bar Najdah ita ɗaya a ɗaki.
Ƙarfe goma saura kwata ango ya shigo ɗaki. Tana zaune bakin gado kan ta a rufe. Ya zauna gefen ta yana mai sallama a karo na biyu, Najdah ta amsa ƙasa-ƙasa.

"Masha Allah" ya furta lokacin da ya ɗaga veil ɗin ya ga kyakykyawar amaryar sa. Sai da su ka haɗa ido kafin ta yi saurin sauke idon ta tana murmushi.

"Najdah ban san da wani irin baki zan gode mi ki ba. Kin so ni, kin amince da ni a talaka na duk da kin fito daga gida mai girma gida mai daraja"
Ya ɗaga hannun ta ɗaya ya kissing...

Kazarta ya fito da shi a cikin foil paper sai tiriri ta ke.
"Bismillah"

Ta girgiza kai "Dear ka manta bana cin abinci idan dare yai nisa"

"I know, amma wannan kazar daban ne, ki ci ko kaɗan ne"

Ta kai hannu za ta ɗau cinya, ya riƙe hannun ya ce "barin fara samun lada tun daga yanzu"

Ya sa hannu ya yago nama ya fara ba ta a baki... cinya ɗaya ta ci ta ce ya isa sai da ta ɗan kora da fresh milk kafin ya tattara wajen.

Bayan kowannen su ya yi wanka ya yi alwala sannan su ka gabatar da sallah raka'a biyu na godiya. Anas yai wa amarya tambayoyi kuma Alhamdulillah ta san basics na abinda ya shafi tsarki da alwala da sallah...

Hannunta ya kamo ya fara murzawa a hankali, dama hannun gasu da laushi saboda hutu abin ya zo ya haɗu da gyara kuma.  A hankali ya kai bakin sa kan nata ya fara kissing ɗin ta yanayi yana shafa breast ɗin ta... zuwa lokaci kaɗan ya cire after dress da ta sa ya saura rigan bacci. A kan gado su ka ƙarasa cire kayan...

Ana kiss ana sucking breast Najdah ta fara jin daɗi ta sake jiki har tana ƙanƙameshi. Amma da ya introducing abun shi sai ga shi ta challa ƙara. Kuka ta ke tana roƙon shi amma ina ya ɗimauce hankalin sa baya jikin sa... Sai da ya sauka a kanta ya ga ashe ta jima da suma gaba ɗaya tausayinta ya kamashi. It wasnt his first time amma ya so da ita ya fara, har yau yana dana sanin haɗuwa da Zulfa.
Ya je masters na shi a Canada ya haɗu da Zulfa student ce amma su mazaunan wajen ne saboda ita a Canadan ma aka haifeta. Sun ɗan shaƙu da ita tun lokacin da su ka fara haɗuwa. Duk da ya san yarinyar ba ta da kamun kai amma hakan bai sa sun dena friendship ba. Sun jima suna tare ba abinda ya taɓa shiga tsakanin su sai da ya ƙare karatu yana shirin haɗa thesis na shi watarana tsautsayi Zulfa ta rinjayeshi shi kuma sheɗan da son zuciya ya sa ya biye ma ta. Sai da haka ta faru tsakanin su sau uku kafin ana ukun ya daure ya yaƙi zuciyar sa. Ranan da Zulfa ta zo ya ma ta faɗa tareda shi kan sa, sai da su ka yi kaca-kaca kafin su ka rabu...Duk da dai daga baya Zulfan ta yi ta bibiyan sa amma shi ne ya daure ya gina katanga tsakanin su ya dena shiga sabgarta har ya gama abinda zai yi ya dawo Nigeria...

.........................

Sabreen ta jima a ƙasa tana kuka kafin lokaci guda ta tashi ta haura sama. Kayan ta dama a haɗe su ke ta ɗau handbag ɗinta da akwatin kaya ta sauko ƙasa. Su Mouna da su Najma su na ba ta haƙuri amma ko kula su ba ta yi ba. Ganin su na so su hanata fita ya sa ta ce ko su bar ta ta tafi ko kuma ta shiga ciki ta kashe kan ta. Wannan furuci ya sa su ka haƙura su ka bar ta ta fita. Tana jan akwati tana tafiya tana hawaye. Ta sani ko mi ya faru yau ita ta ja wa kan ta. Tana son Najeeb anna tafiye son kan ta da yawa, she was always selfish. "Chasing my dream, following my heart" shi ya kawota inda ta ke yanzu.
Tana tafiya tana tuna rayuwar su ta baya. Ƙuruciyar su da adulthood na su. Ta tuna ranan da su ka fara sharing kiss. It was the day da ta gama highschool.  Ta tuna how he's blushing saboda wannan ne first kiss na shi duk da ita ba shi ne first kiss na ta ba saboda tun tana 14yrs ta samu first kiss na ta da wani crush ɗin ta a class ɗin su.

Najeeb loved her, supported her. He's the only man da ya ke da damar yin komai da ita amma bai yi ba. Every other man yana samun dama the next thing shi ne ƙoƙarin shigar da abun shi cikin abun ta. Amma Najeeb, Najeeb, ta goge hawaye tana tuna kalaman sa idan watarana sun yi kiss mai nisa har ta fara ƙoƙarin jan hankalin shi.

"Lets just do it Noory"

"No princess we'll do it, at the right time"

"Za mu yi aure fa, so miye dan mun fara yanzu?"

Najeeb murmushi zai yi ya ce " lets wait for the right time. Its coming very soon"

Ga shi wannan very soon ɗin bai zo ba har yau, all because of her.

Ta so auren Najeeb, everything was going perfect until lokacin da aka kirata akan za a bata role na wani  movie idan za ta yi, ta sani ba wanda zai barta ta ajiye aure saboda film hakanan ta sani idan ta riga ta auri Najeeb ba zai taɓa barin ta ta yi acting ba. Just aikin assistant director da ta ke yi ma ya bari ne saboda ya san ta jima tana son aiki da Hollywood...
Ta so dawowa daga wannan film ɗin guda ɗaya amma bisa rashin sani contract ɗin da ta signing na shekara biyar ne. Gashi kuma watarana bayan sun gama shooting sun je wani party da co'actor ɗin ta, shi ya bige da shan giya, ita ba ta sha giya ba amma just coke da tasha sai ya bugar da ita. Ba ta san ya akayi ta ƙare da James Anderson a ɗaki ba. Da ta yi ƙoƙarin ma sa barazanar kai ƙaran shi sai ya nuna ma ta ba wanda zai yarda da ita saboda da ƙafarta ta zo gidan shi. Wannan abu ya ƙara dagula ma ta lissafi saboda abinda ta ke tattali shekara da shekaru saboda Najeeb sai ga shi wani ya samu a banza. Daga baya ta yi ƙaran James for rape amma kasancewa shi babban actor ne kuma ɗan asalin ƙasar America sai court ta ruling on his favour, har ta kai ma sai da ta biya tara saboda acewar su ta ɓata ma sa suna.

Tun daga James Anderson rayuwar ta ta sauya. She have sex whenever she wants to, tana shan giya kai har ƙwaya ta sha. Sai da ta shekara shida kafin ta dawo dai-dai ta dena shan giya da ƙwaya bayan dogon theraphy section da ta rinƙa zuwa akai-akai.  Being a celebrity is not easy. Fans su yi ta tunzura ka. Fans ne su ka yi ta tunzura ta har ta je aka gyara ma ta shape ɗin bakinta saboda fans sun ce tana da kyau amma lips ɗin ta sun yi manya. Daga lips kuma ta yi butt enlargement...

Kiran wayanta aka fara yi hakan ya sa ta dawa daga dogon tunanin da ta tafi. Tana zaro wayan ta ga Larry ne manager ɗin ta.*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣4️⃣7️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*

Sabreen na ɗauka wayar Larry ya fara magana cikin masifa. Ba ta gane mi ya ke faɗi ba amma ta ɗau abu ɗaya, wato ta duba whatsapp na ta ya tura ma ta saƙo.
Ta cire wayan a kunne tana ƙoƙarin duba mi Larry ya turo ma ta.

Ba ta yi mamaki ba ganin video clip ne na wajen da ta ke durƙushe a ƙasa tana kuka yayinda Najeeb ke kwararo bayani, sai ɗayan kuma wajen da ta riƙe ƙafan Najeeb tana ba shi haƙuri.
Ta sani cikin su Jean, Arfah da Sarah da ta zo da su ne wani ya ɗau wannan video ɗin. But at the moment da video ɗin da wanda ya ɗau video ɗin duk ba sa gabanta. Babban damuwarta shi ne Najeeb, ta sani daga wannan rana ta rasa Najeeb  rasawa ta har abada kenan.
If only ba ta gudu ba, da yanzu suna nan tare cikin farinciki.

Larry ya cigaba da kiran ta amma ta ki ɗagawa. Su Mom da Mouna ma sun yi ta kira amma ta ƙi ɗagawa.
All she needed is a quite place  where she can cry her eyes out...

Receptionist da ya ga Sabreen sai da ta bashi tausayi. Wedding dress ne a jikinta amma kuma babu farinciki a tattare da ita ko kaɗan.
Ya miƙa ma ta key ɗin ɗaki tareda cewa "sorry Madam" ko kallon sa Sabreen ba ta yi ba ta ƙarɓi key ta ja akwatin ta. Da ace akwai yadda za ta samu jirgi da zai ɗauketa a wannan lokaci yai nisa da ita da Nigeria da za ta biya ko nawa ne ta samu wannan Jirgi. Amma dare ne kuma yau Friday ne.
Receptionist ɗin ya bi bayan Sabreen da kallo wanda ke tafiya a ƙafa ba ko takalmi ga takalman tana riƙe da su a hannu. Tunanin shi ya bashi ƙila ta zo daga wata ƙasa dan ta auri ɗan Nigeria ne shi kuma ya ƙi ta, ƙila ma irin online dating ɗin nan su ka yi...

Sabreen na shiga ɗakin hotel ɗin ta rufe ɗaki ta durƙusa a wajen ta fara kuka. Tana son ta yi kukan rayuwan ta, tana so ta yi kukan rashin masoyin da ta yi. Wannan karan da gaskiya ta ke son ajiye film na har abada bayan sun yi aure da Najeeb. Tana so ta zauna da shi, ta nuna ma sa kulawa, ta nuna ma sa tsantsan so.  Yadda ta ke ta kukan tana dafe da ƙirjinta sai ga tari ya ƙufce ma ta. Hannunta da ta ke tare tarin ne ta ga jini, she's coughing blood, nishi ta ke yi a hankali. Ko da za ta mutu she has to ask Noory for forgiveness. Ta tashi da ƙyar tana dafe bango idon ta na ganin bibbiyu. Da ƙyar ta buɗe ƙofa ta fito daga ɗakin tana furta Noory a hankali. Ko ta ku biyar ba ta yi ba ta faɗi a wajen...

.............................

Da sauri Anas ya miƙe daga kan gadon ya shiga banɗaki da gudu. Ruwa ya ɗebo a wata roba ya fito da gudu jikin sa na rawa. A hankali ya ɗeba ruwan ya shafa ma ta a fuska nan da nan ta ja dogon numfashi.
"I'm sorry baby love, i'm  very sorry" ya faɗa kaman zai yi kuka.

Wani matsanancin zafi da ta ke ji daga ta ƙasanta ya sa ta sake fashewa da kuka. Ji ta ke the pain was unbearable.
Anas ya fara hura ma ta iska a kunne yana ce ma ta sorry.  Ganin kukan ba mai tsayawa ba ne ya sa shi tashi dan ya haɗa ma ta ruwan zafi...

"Sannu kin ji, i'm sorry my love" ita kam kukanta kawai ta ke yi duk da ma ruwan zafin da ya saka ta ya sa ta ɗan farajin sauƙin zogin da gabanta ke yi, ba kamar da farko ba.

Da ƙyar ya samo pcm a na shi ɗakin ya kawo ma ta dan ta sha. Shan maganin ma sai da ta ma sa kuka...
A hankali ya dinga bubbuga bayan ta har baccin wahala yai gaba da ita tana kwance a jikin sa...

...............................

Farida ta zage ta cinye omelete ɗin nan tas, saboda ita ne ma ya haɗa ƙwai huɗu, shi kam ba zai taɓa iya cinye ƙwai huɗu a lokaci guda ba. Yana mamakin ma yadda duk yawan cin ta ba ta yi ƙiba ba.

"Alhamdulillah ba laifi ka iya soya ƙwai" ta faɗa tana kora sauran tea da ke mug ɗin ta.

Ganin yadda ya ke kallon ta ya sa ta ce "mi ye?" Da ɗan ƙarfi

"I love you"

"A hakan shi ne jiya ka kusan kashe ni"

Ya shafi kumatun ta ya ce "sorry my Queen, ni ma ba a son rai na ba ne"

"Kaman da gaske, abunda duk sauran Sabreen ne"

Dariya yai ya ɗau tray daga kan gadon ya ce " kaman sauran Wannan likitan na gani jiya ko? Tunamin ma sunan shi?"

Ta jawo pillow ta wurgeshi da shi ya goce yana dariya...

Bayan ya dawo ɗakin ya ce ta fito ya nuna ma ta gidan ta kuma ga ɗakin ta.  Kukan sakalci ta sa mi shi wai ba za ta iya tafiya da ƙafarta ba. Haka ya tsugunna ta hau bayan shi ya fita da ita daga na shi ɗakin. Ko'ina su ka zaga a cikin gidan, gidan ba ƙaramin burgeta yai ba. Ɗakin ta ya yi kyau sosai, akwai walk-in closet a ciki wanda ya ke cike da kaya.

"My champ ina da kaya a gidan su Daddy fa"

"Tuna min wa ki ke aure ma?"

Ta ɗan ranƙwashi kan sa a hankali ta ce "Mai girma Sir Najeeb, my Hero my Champion, my Mr BLTD"

Sanda su ka sauƙa falon ƙasa su ka ji doorbell ɗin na ƙara. Still Najeeb na goye da Farida ya je ya buɗe ƙofan.
Tasallah ce ɗauke da kwandon abinci.

"Alhaji an tashi lafiya?"

"Lafiya" ya faɗi a hankali yana matsa ma ta dan ta shigo.

Daga bayan Najeeb Farida ke yiwa Tasallah ina kwana.

A kan dining ta jera food warmers ɗin. Suna tsaye ta gama ta zo za ta tafi Farida ta ce "Baaba Tasallah ya su Mom?"

"Hajiya na lafiya, amma jiya a asibiti su ka kwana wannan ɗiyar yayanta ba lafiya"

"Wacce ɗiyar yayantan?"

Tasallah ta ce " wannan Sabeera ko Sareena ne ma. Wacce de ta ke tafiyan magen nan"

"Sabreen?"

"E ita"

"Mi ya sameta"

Tasallah ta ce ba ta sani ba.

Bayan Tasallah ta fita dukkan su shiru su ka yi kowa da abinda ke saƙawa a ransa.
Tasallah kam ta fita tana mamakin Najeeb da Farida. Ko kunyar ta ba su ji ba haka su ka tsaya ƙato na goye da ƙatuwa. Chan zuciyar ta ya ce to ai duk cikin so ne...

Farida ce ta fara katse shirun da cewa "my Champ mu je sama ka kira Mom mu ji labarin mai jiki"

Ok kawai ya faɗa ya haura sama da ita chan ƙasan zuciyan ta yana addu'ar Allah ya sa Sabreen ta samu sauƙi dan ya san saboda shi ta shiga wannan hali.

Farida ce ta kira Mom ɗin tana tambayar ya jikin Sabreen, Mom ta ce da sauƙi domin ta farfaɗo yau da safe amma an ma ta alluran bacci tana bacci.

Farida ta ce "Allah ya ƙara sauƙi" Mom ta amsa da amin.

"Aishah" Mom ta kira sunan Farida a hankali

"Na'am"

"Dan Allah ke da son idan kun samu dama ku zo ku duba Sabreen. She's in pains kuma ɗazu da ta farfaɗo sunan Son ta ke ta kira"

Wani tukuƙin kishi ne ya tasowa Farida. Lokaci ɗaya ta hango Sabreen da Najeeb. Kunnen ta ne ya fara jiyo ma ta kalaman Mom tana faɗin " Ayshah mi yi haƙuri an ɗaura auren Sabreen da Najeeb saboda zuciyar Sabreen za ta buga idan ba ta samu Najeeb ba"

"Ayshah ki na jina?" Mom ta maimaita a karo na uku. Sai a lokacin ta ɗan dake ta ce "ba matsala za mu zo"

Tana ajiye wayan ta haɗa rai ta ce "Mom ta ce ka je ka duba Sabreen anjima"

"Na ji mi ta ce fa, cewa ta yi mu je mu biyu"

"Ni ba inda zan je. A gaida marar lafiya daga nan a kai goro"

Sai da yai dariya mai isar sa kafin ya kai bakin sa zai kissing ɗin ta ta juyar da kai. Ɗan cizon kunnen ta yai ya ce "wannan kishin haka, kin san ke kaɗaice sakatariyar zuciya ta"

Ta ɗau hannu za ta kai ma sa duka ya riƙe hannun ya jawota jikin sa yana dariya...

Karfe biyar saura na yamma su ka isa asibitin. Lokacin Sabreen ta farfaɗo amma ba ta magana ko na ce ta ƙi magana da kowa. Jininta ne ya hau kuma likita ya ce idan ta cigaba da sa damuwa a ranta za ta iya samun heart attack. Magana ma ƙarin damuwa ne a gareta shiyasa ta ƙi magana. Noory kawai ta ke son gani.

Za su ɗakin da aka kwantar da Sabreen su ka haɗu da Dr Lukman. Najeeb yanata wani shan ƙanshi lokacin da Lukman ya miƙa ma sa hannu. Hannun sa sarƙe cikin na Sabreen ya ciro hannun sa da ƙyar ya miƙa ma sa su ka gaisa...
Farida ne ta iya ce ma sa sun zo duba mara lafiya ne. Amma Najeeb bayan gaisawa bai iya furta komai ba...
Bin bayan su yai da kallo yana ganin yadda Farida ke tafiya ya ji wani abu ya ɗarsu a zuciyar sa...*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣4️⃣8️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*

Sabreen na ɗauka wayar Larry ya fara magana cikin masifa. Ba ta gane mi ya ke faɗi ba amma ta ɗau abu ɗaya, wato ta duba whatsapp na ta ya tura ma ta saƙo.
Ta cire wayan a kunne tana ƙoƙarin duba mi Larry ya turo ma ta.

Ba ta yi mamaki ba ganin video clip ne na wajen da ta ke durƙushe a ƙasa tana kuka yayinda Najeeb ke kwararo bayani, sai ɗayan kuma wajen da ta riƙe ƙafan Najeeb tana ba shi haƙuri.
Ta sani cikin su Jean, Arfah da Sarah da ta zo da su ne wani ya ɗau wannan video ɗin. But at the moment da video ɗin da wanda ya ɗau video ɗin duk ba sa gabanta. Babban damuwarta shi ne Najeeb, ta sani daga wannan rana ta rasa Najeeb  rasawa ta har abada kenan.
If only ba ta gudu ba, da yanzu suna nan tare cikin farinciki.

Larry ya cigaba da kiran ta amma ta ki ɗagawa. Su Mom da Mouna ma sun yi ta kira amma ta ƙi ɗagawa.
All she needed is a quite place  where she can cry her eyes out...

Receptionist da ya ga Sabreen sai da ta bashi tausayi. Wedding dress ne a jikinta amma kuma babu farinciki a tattare da ita ko kaɗan.
Ya miƙa ma ta key ɗin ɗaki tareda cewa "sorry Madam" ko kallon sa Sabreen ba ta yi ba ta ƙarɓi key ta ja akwatin ta. Da ace akwai yadda za ta samu jirgi da zai ɗauketa a wannan lokaci yai nisa da ita da Nigeria da za ta biya ko nawa ne ta samu wannan Jirgi. Amma dare ne kuma yau Friday ne.
Receptionist ɗin ya bi bayan Sabreen da kallo wanda ke tafiya a ƙafa ba ko takalmi ga takalman tana riƙe da su a hannu. Tunanin shi ya bashi ƙila ta zo daga wata ƙasa dan ta auri ɗan Nigeria ne shi kuma ya ƙi ta, ƙila ma irin online dating ɗin nan su ka yi...

Sabreen na shiga ɗakin hotel ɗin ta rufe ɗaki ta durƙusa a wajen ta fara kuka. Tana son ta yi kukan rayuwan ta, tana so ta yi kukan rashin masoyin da ta yi. Wannan karan da gaskiya ta ke son ajiye film na har abada bayan sun yi aure da Najeeb. Tana so ta zauna da shi, ta nuna ma sa kulawa, ta nuna ma sa tsantsan so.  Yadda ta ke ta kukan tana dafe da ƙirjinta sai ga tari ya ƙufce ma ta. Hannunta da ta ke tare tarin ne ta ga jini, she's coughing blood, nishi ta ke yi a hankali. Ko da za ta mutu she has to ask Noory for forgiveness. Ta tashi da ƙyar tana dafe bango idon ta na ganin bibbiyu. Da ƙyar ta buɗe ƙofa ta fito daga ɗakin tana furta Noory a hankali. Ko ta ku biyar ba ta yi ba ta faɗi a wajen...

.............................

Da sauri Anas ya miƙe daga kan gadon ya shiga banɗaki da gudu. Ruwa ya ɗebo a wata roba ya fito da gudu jikin sa na rawa. A hankali ya ɗeba ruwan ya shafa ma ta a fuska nan da nan ta ja dogon numfashi.
"I'm sorry baby love, i'm  very sorry" ya faɗa kaman zai yi kuka.

Wani matsanancin zafi da ta ke ji daga ta ƙasanta ya sa ta sake fashewa da kuka. Ji ta ke the pain was unbearable.
Anas ya fara hura ma ta iska a kunne yana ce ma ta sorry.  Ganin kukan ba mai tsayawa ba ne ya sa shi tashi dan ya haɗa ma ta ruwan zafi...

"Sannu kin ji, i'm sorry my love" ita kam kukanta kawai ta ke yi duk da ma ruwan zafin da ya saka ta ya sa ta ɗan farajin sauƙin zogin da gabanta ke yi, ba kamar da farko ba.

Da ƙyar ya samo pcm a na shi ɗakin ya kawo ma ta dan ta sha. Shan maganin ma sai da ta ma sa kuka...
A hankali ya dinga bubbuga bayan ta har baccin wahala yai gaba da ita tana kwance a jikin sa...

...............................

Farida ta zage ta cinye omelete ɗin nan tas, saboda ita ne ma ya haɗa ƙwai huɗu, shi kam ba zai taɓa iya cinye ƙwai huɗu a lokaci guda ba. Yana mamakin ma yadda duk yawan cin ta ba ta yi ƙiba ba.

"Alhamdulillah ba laifi ka iya soya ƙwai" ta faɗa tana kora sauran tea da ke mug ɗin ta.

Ganin yadda ya ke kallon ta ya sa ta ce "mi ye?" Da ɗan ƙarfi

"I love you"

"A hakan shi ne jiya ka kusan kashe ni"

Ya shafi kumatun ta ya ce "sorry my Queen, ni ma ba a son rai na ba ne"

"Kaman da gaske, abunda duk sauran Sabreen ne"

Dariya yai ya ɗau tray daga kan gadon ya ce " kaman sauran Wannan likitan na gani jiya ko? Tunamin ma sunan shi?"

Ta jawo pillow ta wurgeshi da shi ya goce yana dariya...

Bayan ya dawo ɗakin ya ce ta fito ya nuna ma ta gidan ta kuma ga ɗakin ta.  Kukan sakalci ta sa mi shi wai ba za ta iya tafiya da ƙafarta ba. Haka ya tsugunna ta hau bayan shi ya fita da ita daga na shi ɗakin. Ko'ina su ka zaga a cikin gidan, gidan ba ƙaramin burgeta yai ba. Ɗakin ta ya yi kyau sosai, akwai walk-in closet a ciki wanda ya ke cike da kaya.

"My champ ina da kaya a gidan su Daddy fa"

"Tuna min wa ki ke aure ma?"

Ta ɗan ranƙwashi kan sa a hankali ta ce "Mai girma Sir Najeeb, my Hero my Champion, my Mr BLTD"

Sanda su ka sauƙa falon ƙasa su ka ji doorbell ɗin na ƙara. Still Najeeb na goye da Farida ya je ya buɗe ƙofan.
Tasallah ce ɗauke da kwandon abinci.

"Alhaji an tashi lafiya?"

"Lafiya" ya faɗi a hankali yana matsa ma ta dan ta shigo.

Daga bayan Najeeb Farida ke yiwa Tasallah ina kwana.

A kan dining ta jera food warmers ɗin. Suna tsaye ta gama ta zo za ta tafi Farida ta ce "Baaba Tasallah ya su Mom?"

"Hajiya na lafiya, amma jiya a asibiti su ka kwana wannan ɗiyar yayanta ba lafiya"

"Wacce ɗiyar yayantan?"

Tasallah ta ce " wannan Sabeera ko Sareena ne ma. Wacce de ta ke tafiyan magen nan"

"Sabreen?"

"E ita"

"Mi ya sameta"

Tasallah ta ce ba ta sani ba.

Bayan Tasallah ta fita dukkan su shiru su ka yi kowa da abinda ke saƙawa a ransa.
Tasallah kam ta fita tana mamakin Najeeb da Farida. Ko kunyar ta ba su ji ba haka su ka tsaya ƙato na goye da ƙatuwa. Chan zuciyar ta ya ce to ai duk cikin so ne...

Farida ce ta fara katse shirun da cewa "my Champ mu je sama ka kira Mom mu ji labarin mai jiki"

Ok kawai ya faɗa ya haura sama da ita chan ƙasan zuciyan ta yana addu'ar Allah ya sa Sabreen ta samu sauƙi dan ya san saboda shi ta shiga wannan hali.

Farida ce ta kira Mom ɗin tana tambayar ya jikin Sabreen, Mom ta ce da sauƙi domin ta farfaɗo yau da safe amma an ma ta alluran bacci tana bacci.

Farida ta ce "Allah ya ƙara sauƙi" Mom ta amsa da amin.

"Aishah" Mom ta kira sunan Farida a hankali

"Na'am"

"Dan Allah ke da son idan kun samu dama ku zo ku duba Sabreen. She's in pains kuma ɗazu da ta farfaɗo sunan Son ta ke ta kira"

Wani tukuƙin kishi ne ya tasowa Farida. Lokaci ɗaya ta hango Sabreen da Najeeb. Kunnen ta ne ya fara jiyo ma ta kalaman Mom tana faɗin " Ayshah mi yi haƙuri an ɗaura auren Sabreen da Najeeb saboda zuciyar Sabreen za ta buga idan ba ta samu Najeeb ba"

"Ayshah ki na jina?" Mom ta maimaita a karo na uku. Sai a lokacin ta ɗan dake ta ce "ba matsala za mu zo"

Tana ajiye wayan ta haɗa rai ta ce "Mom ta ce ka je ka duba Sabreen anjima"

"Na ji mi ta ce fa, cewa ta yi mu je mu biyu"

"Ni ba inda zan je. A gaida marar lafiya daga nan a kai goro"

Sai da yai dariya mai isar sa kafin ya kai bakin sa zai kissing ɗin ta ta juyar da kai. Ɗan cizon kunnen ta yai ya ce "wannan kishin haka, kin san ke kaɗaice sakatariyar zuciya ta"

Ta ɗau hannu za ta kai ma sa duka ya riƙe hannun ya jawota jikin sa yana dariya...

Karfe biyar saura na yamma su ka isa asibitin. Lokacin Sabreen ta farfaɗo amma ba ta magana ko na ce ta ƙi magana da kowa. Jininta ne ya hau kuma likita ya ce idan ta cigaba da sa damuwa a ranta za ta iya samun heart attack. Magana ma ƙarin damuwa ne a gareta shiyasa ta ƙi magana. Noory kawai ta ke son gani.

Za su ɗakin da aka kwantar da Sabreen su ka haɗu da Dr Lukman. Najeeb yanata wani shan ƙanshi lokacin da Lukman ya miƙa ma sa hannu. Hannun sa sarƙe cikin na Sabreen ya ciro hannun sa da ƙyar ya miƙa ma sa su ka gaisa...
Farida ne ta iya ce ma sa sun zo duba mara lafiya ne. Amma Najeeb bayan gaisawa bai iya furta komai ba...
Bin bayan su yai da kallo yana ganin yadda Farida ke tafiya ya ji wani abu ya ɗarsu a zuciyar sa...*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣4️⃣9️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*

Ido ya zaro waje yana faɗin "really?"
Ta gyaɗa ma sa kai.

"Alhamdulillah, Alhamdulillah. Thank you my Queen"

Ɗaukan ta yai sama yana juyi da ita.

"My Champ saukeni Hajijiya na ke ji"
Bai sauketa ko'ina ba sai a wajen kujerun da ake zama dan hutawa.

Yana riƙe da hannun ta ya ce "ban san da mi zan fanshi wannan good news ɗin ba. Ask me anything my love"

Hannunta da bai riƙe ba ta kai saitin kirjin sa ta ce "ka mallaka min zuciyar ka ni kaɗai, i want your heart to beat only for me. Abinda na ke so kenan"

Sai da ya kissing goshin ta kafin ya ce "zuciyata ta jima da zama mallakin ki. I love you Aysherh only you"

Haɗe bakin su ta yi tana faɗin "i miss you"

A hankali ya zare suit ɗin jikin sa ya fara ɓalle buttons ɗin shirt ɗin ciki.

"My Champ mu na office ne fa" ta faɗa in between kisses.

"Wait here" ya faɗi tareda tashi ya je wajen table ɗin sa. Waya ya ɗauka ya kira Sakatariyar shi.

"Ki sa ka do not disturb tag a jikin ƙofa"

Bai jira mi za ta ce ba ya katse kiran. Wani remote ya ɗauka ya kulle ƙofar shiga office ɗin wanda ko mutum ya zo shiga babu yadda zai yi sai dai an buɗe ta ciki.  Ya rage wutan office ɗin kafin ya ƙarasa wajen Madam ɗin sa.

A hankali su ka fara gudanar da abubuwa akan kujera. Nishin da Najeeb yai lokacin da wani daɗi ya ziyarce shi ya sa Farida faɗin "za a jimu fa"
"Soundproof" kawai ya iya faɗa ya cigaba da shiga ciki ciki...
Sai lokacin ta tuna da mafi yawan lokuta da ta ke son jin gulma amma ba ta iya ji ba saboda duk abinda ake a office ɗin ba ka jin sa a waje, Lokacin da ta ke Miss Salihu...

Yana kwance ya miƙe akan kujera ita kuma tana kwance a kansa su na maida numfashi, kayan su na yashe a gefe.

" ina so ya kasance namiji mai kamannin ka"  Farida ta faɗa hannunta na wasa da nipples ɗin sa.

"Ina son mace mai irin jarumtar ki. A no nonsense cute princess"

"De ka ce mai baki kamar ni, ta dinga cika ma ka kunne da surutu"

"Ina son ta kasance mai komai irin na ki, everything na ki"

"I love you" Farida ta faɗa tana kissing ƙirjin shi...

Anas ya zo zai shiga office ya ga tag ɗin da aka sa *do not disturb*

"Naomi mi Najeeb ke yi a ciki?"

Naomi ta langwaɓar da kai ta ce "Madam ce ta zo"

"Madam....He's wife?"

Naomi ta amsa da yes.

Anas yai murmushi ya juya yana cewa nima ba zan dawo da amaryata aiki anan ba kuwa...

Banɗakin da ke office ɗin su ka shiga su ka yi wanka, da ke garin akwai zafi shiyasa Farida ta daure ta yi wanka da ruwan shower ɗin wanda ba irin na gidan su ba ne mai ba da ruwan sanyi ko ruwan ɗumi, wannan ruwan sanyi kawai ke bayarwa.

Bayan sun kimtsa ne Najeeb ya ƙarasa duba wani aiki, ya yi su a gurguje cikin minti shabiyar. Sannan su ka fito daga office ɗin maƙale da juna.

Farida ne ta cewa Naomi sun tafi sai gobe. Naomi ta bi bayan su da kallo.

Office ɗin Anas su ka je, Anas sai dariya ya ke mu su, har da tsokala wai zai bawa Najdah aiki a office ɗin sa, saboda aci soyayya a gida da office.

Daga wajen Anas su ka fita daga kamfanin sai gida. Tana shiga falo ta cire gyale da ɗankwalin ta wanda ya jiƙe saboda wankan da su ka yi ɗazu kan bai gama bushewa ba ta ɗaura ɗankwali, dan ma gashin da kitso ba wai a tsefe ya ke ba.

Tasallah ta leƙa a kitchen ta ma ta sannu da aiki sannan ta haura sama.

Yana tsaye yana waya ta shigo. Zuwa ta yi ta rungumeshi ta baya. Yadda ya ke wayan ta tabbatar da Daddy ya ke magana. Minti ɗaya kafin ya gama wayan.

"Miji na da Daddy ka ke magana?"

"Yes Love, he's so excited that ya kusa ganin 'ya'ya na"

"Yanzu ba ka ji kunyar gaya ma sa ba?" Ta faɗa tana ƙoƙarin cire ma sa riga.

Dariya yai ya ce "wani kunya kuma my Queen"

"Dan Allah ya ka gaya ma sa? Cewa ka yi Dad matata tana da ciki? Ko cewa ka yi Dad Aysherh na da ciki?"

Jawota jikin sa yai ya ce "cewa na yi Dad abubuwan da mu ke yi da wife ɗina an samu sakamako mai kyau kum...."

Toshe bakin sa ta yi ta fara dariya...

.............................

Rintsawar kirki Naomi ba ta yi ba daren ranan. Ta jima tana kallon hotunan Ogan na ta a waya. Ta sani Ogan ta ya ma ta nisa hakanan ga matar san nan da alama masifaffiya ce. Ta tuna ranan da ya fara resuming aiki tana zaune ta hangoshi yana tahowa. Tafiyar sa kaɗai abun kallo ne, balle shigar sa. Ta dulmiya da kallon sa har ya zo ya buɗe office ya shiga ba tareda ta iya buɗe baki ta gaida shi ba.

Sai da ta ji ya rufe ƙofan ta yi saurin miƙewa tsaye tana sake kallon kan ta a screen ɗin wayarta. Wig ɗin da ke kanta ta sake bazawa da kyau kafin ta ƙara goga janbaki a lips ɗinta sannan ta shiga office ɗin.

"Good morning Sir" ta faɗa tana jiran ya amsa.
Bai yi kamar akwai mutum a wajen ba ya cigaba da latsa system ɗin da ke gaban sa.

"Oga i'm Naomi Masoyi your new secretary"

"Get back to work then" ya faɗa ba tareda ya ɗago ya kalleta ba.
Ranan ba ta tunanin duk shige da ficen da ta ke tsakanin office ɗin sa ya ɗaga ido ya kalleta.
Washe gari ma cikin ƙananun skirt ɗinta ta zaƙulo ta sa ta tafi office, skirt ɗin rabin cinyar ta ya tsaya. Yadda jiya ta kasance hakan ma ta kasance yau ko sau ɗaya ba su haɗa ido ba. Tana ma sa magana bayan ya ce ta tafi ya daka ma ta tsawa, sosai ta tsorata da shi duk da ma ta samu labarin halinsa sai dai ance tunda yai rashin lafiya ya rage faɗa.

Sati ɗaya da ya fara zuwa aiki gaba ɗaya ta shiga wani hali. Soyayyar Ogan na ta ya ma ta wani mugun kamu. A kullum ta kalleshi ƙara dulmiya ta ke cikin son sa. Ta rasa ya za ta yi da wannan so da ka iya jawo ƙarshen aikinta. Wanda shi ke ciyar da su yanzu. Ta gama service ba aiki, tana manage a wani shago inda ta ke salesgirl kafin mamansu ta yi hatsari...

Mahaifin su Pastor John Masoyi ya jima da mutuwa kusan shekara shabiyar kenan. Shi mutumin Ɓilliri ne da ke jahar Gombe amma matar sa Comfort 'yar Tafawa Ɓalewa ne da ke Bauchi. Sun haɗu a wani church seminar ne da aka yi a Kaduna tun lokacin bai ma zama Pastor ba.
A BUK yai karatu, bayan ya yi service ya samu aiki a wani Kamfani daga baya kuma ya ajiye aikin bayan ya tsunduma cikin harkan Choci.  Mrs Comfort 'ya'ya uku ta haifa ma sa. Elizabeth ce babba sai Naomi da ƙanin su Abel.

Kasancewa Pastor John ya mutu ya barta da yara ƙanana ya sa ta nemi aiki ta samu a wani babban Kamfani. Da albashin ta ke ciyar da yaranta ta kuma kula da ɗawainiyar su.
Elizabeth tana dawowa daga makaranta  ta yi hatsari ta mutu lokacin ajinta Biyu a Unimaid.
Ya saura Naomi da Abel.

Koran ma'aikata da aka yi a Kamfanin da Mrs Comfort ke aiki ya sa ta rasa aikin ta, kafin daga baya ta samu aiki a Najeeb constructions.

Naomi typical catholic church girl ce until lokacin da ta fara Jami'a ta haɗu da Daniel wanda cikin watanni kaɗan ya rabata da duk wani shiru-shiru da rashin wayewa da ta ke yi. Sun shekara uku su na gurzan junan su wanda har cire ciki ta yi sau biyu. A shekara ta huɗu ne su ka rabu bayan ta kamashi a kan ƙawarta su na abubuwa. Tundaga Daniel ta cire soyayya a ranta amma ganin Najeeb ya sa ta faɗa wani yanayi wanda ko lokacin suna tareda Daniel ba ta ji irin sa ba. Soyayyar Najeeb ce ta ma sa babban kamu.

.............................

Ba ta jima da zama ba su ka shigo hannun su cikin na juna. Ta yi saurin miƙewa tsaye tana gaishe su. Farida ce kawai ta iya amsa ma ta shima ɗin kaman ana roƙonta.

Wassu files Naomi ta kawowa Najeeb dan yai signing, daga ɓangaren Farida ta hango shigar Naomi da kuma yadda ta yi bending tana nunawa Najeeb wani abu a takardar da ke hannun sa. Shirt ne da pencil skirt ta sa. Pencil skirt ɗin ba ƙaramin matseta yai ba, dan tafiya ma da ƙyar ta ke yi, rigan kuma ta buɗe buttons uku na sama har ana ɗan hango bra ɗin ta.

Ba ta ankara ba ta ji an damƙi gashin ta. Sai da ta jita a ƙasa sannan ta ɗaga ido tana kallon angry Farida tsaye da gashin wig a hannun ta.

"Ke karuwa ce? Ko kwartuwa ce? Wannene a ciki?" Ta faɗa da tsawa.

"I'm sorry Madam, I'm sorry"

"Dan uban ki miyasa za ki bar nonuwan ki a waje? Nan hotel ne? Ko aiki ki ke a hotel?"

Naomi ta birkice tana ta bada haƙuri.

"Albarkacin Mrs Comfort ki ke aiki anan, idan ba za ki kama kan ki ba, za ki yi gaba dan ba zan yi aiki da karuwa ba"

Ta cilla ma ta gashin wig ɗin ta ce " ki je ki sake reviewing dresscode na wannan kamfani. The next time ki ka sake shigan banzan nan za ki gane kuren ki. Now get out"

Naomi ta ɗau gashinta ta yi waje da gudu.

Najeeb na kallon su bai ce komai ba, Farida ta juyo tana huci.

Najeeb ya taso ya kama hannunta, sai da ya zaunar da ita a kan kujerar sa sannan ya ce "My Queen kin san fa yanzu ba ke ɗaya ba ce. You have to take things easy"

"Take it easy? bayan ga sakatariyar ka tana girgiza ma za nonuwanta"

Najeeb ya fashe da dariya ya ce " My Queen anya ba za ki haƙura da zuwa aikin nan ba"

"Wallahi sai na zo. Da ba na nan fa inaga sai dai ka ɗaga ido ka ga ta buɗe ma ka rugujajjun nonuwanta"

Najeeb mi zai yi banda dariya...

Manage this plz*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣5️⃣0️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*

Naomi ta sa hannu ta fara shafa ƙirjin Najeeb. Bai motsa ba bai kuma hana ta ba. Ganin bai yi masifa ba yasa wanni daɗi ya ziyarci zuciyar Naomi. Ta kwantar da kai jikinsa tana cigaba da shafa shi. Najeeb dai yana tsaye kaman gunki bai iya aiwatar da komai ba.

"Sweetheart ka yi haƙuri ka ji"
Najeeb ya tsinci kan sa da gyaɗa ma ta kai...

Farida ta ji farin ciki sosai da amincewar Lukman. Tanada yaƙinin Sabreen za ta amince da shi musamman idan Najeeb ne ya ma ta maganar.

"Barin kira mijina yanzu na san ya kusa dawowa"
Ta ɗau waya ta fara kiran numban Najeeb. Sau uku tana kira sau uku wayan na tsinkewa ba tareda an ɗauka ba.
Duk da gabanta ya faɗi da hakan amma ba ta nuna ba.

Ta yi murmushi ta ce "ƙila wayar ba ta kusa da shi ne, bari mu ɗan hira shi"

Lukman ya miƙe tsaye ya ce "Aishah zan wuce, kawai duk yadda ku ka yi da shi sai ki sanar da ni"

"Insha Allahu wannan karan za a dace"

A zuciyar sa ya amsa da amin amma a fili murmushi kawai yai.

Har ga Allah tausayin shi ta ke ji. Lukman ya haɗu ta ko'ina musamman ma da ya kasance mutum ne da ya ke da tarin ilimi a ɓangaren addini, hakanan yana da kyawawan halaye...

Ta cigaba da kiran Najeeb amma shiru. Hakan ya sa ta kira Abdullahi. Bugu ɗaya ya ɗauka. Ta tambayeshi ko har yanzu Najeeb bai gama abunda ya ke bane. Abdullahi ya ce yanzu ma muna hanyar gida ne.
"Gida kuma?" Farida ta faɗa cikin rashin fahimta.
"Hajiya ai daga kamfanin ne ya ce mu wuce gida" ya amsa ba tareda ya fahimci mi ke faruwa ba.
Farida ta kashe kiran ta cigaba da kiran Najeeb amma still bai ɗauka ba.

Jakarta ta ɗauka ta fito.
"Ma, za ki fita ne?" Naomi ta faɗa tana murmushi.
Farida ba ta kulata ba ta cigaba da tafiya, har ta kai ƙofa sai kuma ta juyo ta ce "Naomi miji na ya zo ne?"

Naomi ta yi saurin cewa "No ma"
Farida ta fita cike da tunani a ranta...

............................

Tunda ya fito daga cikin Kamfanin ya ke jin shi kaman marar lafiya. Yana ganin kiran Farida amma ya ka sa ɗauka. Daga an kira wayan idan ya duba ya ga My Queen sai ya maida ta ya ajiye.
Ko wanka bai yi ba da ya shiga ɗaki ya kwanta a kan gado. Jin jikinsa ya ke kamar ba shi ba, kamar akwai abinda aka cire ma sa a jiki.
Yana kwance a haka har Farida ta shigo. Ganin sa kwance da kayan office a jiki ya sa ta san ba lafiya ba. Duƙawa ta yi ta cire ma sa takalman sa kafin ta ƙarasa dai-dai kan sa tana faɗin " miji na lafiya? Are you Ok?"
Bai ce komai ba sai ma juya ma ta baya da yai.
Tunanin ta ko ciwon kan sa ne ya tashi. Dan tunda aka sallameshi daga asibiti yake fama da ciwon kai amma ya fi tashi ma sa idan ran sa ya ɓaci ko kuma he's stressed. Likita ya ce a hankali ciwon kan zai tafi gaba ɗaya, amma kuma ya dinga samun isashshen bacci, sannan duk lokacin da ya jima yana aiki to ya tabbatar ya ware lokacin da zai kwanta dan ya huta. Hakanan ya guji duk wani abu da zai ɓata ma sa rai.

"My Champ dan Allah mi ya sameka? Wa ya ɓata maka rai?"

" ba na son surutu" ya faɗa a hankali

"Shikenan tunda ba za ka gayamin miya faru ba, amma dan Allah ka tashi ka rage kayan jikin ka za ka fi jin daɗin baccin"

Mirginawa yai ɗaya ɓangaren ba tareda ya amsa ma ta ba.
Ganin dai ba tashi zai yi ba ya sa ta tashi ta fita tunanin ta idan ya huce zai gaya ma ta koma minene.

Ɗakin ta ta wuce ta je ta yi wanka ta chanja kaya. Sai da ta kira Ummi su ka gaisa kafin ta wuce kitchen dan ta taya Tasallah aiki...

Su na jera abinci a dining ya fito ya sha wanka. Baƙin riga da wando ya sa sai ya ɗaura farin blazer a kai.

"My Champ fita za ka yi ne?"

"My Champ...My Champ" ta cigaba da kira har lokacin da ƙofar ta rufu. Baki tasake tana bin ƙofar da kallo. Ya kalleta sun ma haɗa ido kuma ya ji maganar da ta yi amma ya shareta.
Mi ke faruwa, abinda ta tambayi kan ta kenan.

Tun tana jiran shi nan da awa biyu har ta koma cewa nan da ƙarfe takwas na dare zai dawo amma shiru. Ta kira duka nambobinshi amma a kashe.

Tana kwance a kan kujera da ke falon ta ji takun sa. Ta yi firgigit ta tashi dan dama ba wai ta jima da bacci ba ne, baccin ma rabi da rabi ta yi.

"My Champ, My Champ" da sauri ya dinga taka stairs ɗin har ya ƙule ma ta.
Agogon falon ta duba ta ga ƙarfe goma har da rabi. Tunda su ka dawo gidan su bai taɓa wuce ƙarfe tara a waje ba...
Tashi ta yi ta bishi dan ba ta ga ta zama ba. Yana banɗaki lokacin da ta shigo. Itama banɗakin ta je za ta shiga dan ta taya shi wanka    ko za su shirya daga nan amma ta ji banɗakin a rufe. Mamaki ya kamata dan indai wanin su ya shiga banɗaki yo baya rufewa tunda su biyu ne a gidan Tasallah ɗakinta na ƙasa.

Ta zauna a bakin gado tana jiran fitowar sa. Tana zaune ya fito, ya shirya yai ɗan shafe-shafe da feshe-feshen sa ya zo ya kwanta.
Mamakin yadda yai kamar babu mutum a ɗakin  ya sa Farida ka sa magana. Ganin ya ja bargo ya kwanta ya sa ta lalubo sauran maganan da ke bakin ta ta ce "My Champion dan Allah ka yi haƙuri, idan ma wani laifin na maka ka yi haƙuri ka yafemin. Dan Allah miji na ka min magana. Ka gaya min laifina" tana maganan ne kaman za ta yi kuka

"Idan ba za ki iya kwantawa shiru ba, to ki koma ɗakin ki"

Kan ta ya ɗaure. Najeeb ba zai taɓa gaya ma ta haka ba, ko lokacin da ba sa shiri ma duk shirmen ta ba ya cewa ta bar ɗakin.

"Miji na dan Allah, hankalina ba zai kwanta ba idan ban san laifin da na yi ma ka ba"

tsaki yai ya tashi ya ɗau pillow ya koma kan kujera ya kwanta.

Haushi ya cikata. Idan ma laifin ta mishi bai ci ya ma ta wannan walaƙancin ba. Ta ja tsaki itama ta kwanta, a zahiri ranta na raya mata kar ta kuma bashi haƙuri zai zo da kan sa ya bata amma kuma chan cikin ranta tana tsoron wannan chanji bagtatan da Najeeb yai ma ta. Ta dinga tariyo abubuwan da su ka faru ko za ta tuna wani furuci ko wani abu da ta ma sa da zai iya ɓata ma ta rai amma ba ta gano komai ba. They are just fine, tun jiya har safiyan yau, infact san da zai fita a office ma sai da ya kissing ɗin ta sannan ya kissing cikin ta amma komai ya wargaje ne tun daga tafiyan sa. To ko a inda ya je ne aka ɓata ma sa rai? To ai koma wani ya ɓata ma sa rai bai kamata ya sauke fushin a kanta ba musamman saboda condition ɗin da ta ke ciki.
Da ire-iren waɗannan tunani ne bacci ya sace Farida.

Da asuba ma gum ya ma ta ba magana. Bayan ya dawo daga masallaci ta gaishe shi amma bai amsa ba. Haka kawai jikinta yai laushi ta fashe ma sa da kuka. To her uttermost shock maimakon ya rikice ya fara ba ta haƙuri sai ya shige banɗaki ya barta zaune tana kuka.

Innalillahi kawai ta ke ta maimaitawa a fili.
Najeeb ne zai ga tana kuka ya share, yai kaman bai ganta ba, gaskiya da matsala.

Ta zauna har ya fito ya fara shirin fita office still ignoring her. Tsoro da fargaba su ka cika ma ta zuciya.
Ba ta san ma ya za ta fassara wannan yanayi ba. Wannan yanayi mai kama da mafarki ko almara.
Wai Najeeb ɗin ta ke ma ta wannan walaƙancin. Yadda ta ke zaune tana kallon sa haka ya ƙarisa shiryawa ya fita daga ɗakin. Tunda su ka shirya ya dena fita da sassafiya haka, tunda tare su ke fita office ɗin, amma sai ga shi bayan ma yai fitar sassafiya bai ma damu ya san ko wani hali ta ke ciki ba balle ya ji ko za ta fita office ko ba za ta je ba.

Farida ta jima zaune a kan sallaya ta rasa ma abinyi Allah kawai ta ke kira a ranta. Dan wannan sauyi ya fi ƙarfinta, nan gaba kaɗan za ta iya shiga wani hali...

Shi kuwa Najeeb yana shiga mota ya ce Abdullahi ya kai shi gidan su Naomi. Tun jiya Abdullahi ya shiga ruɗu, ya kai Najeeb kamfani inda ya ɗau Naomi su ka fita, wani haɗaɗɗen restaurant su ka je daga nan ya kai su wata babbar shopping Mall inda su ka fito da kaya niƙi-niƙi. Gidan su Naomin ya kai su ta shiga ta ajiye kaya sannan ta sake shiryawa cikin wassu matsatstsun kaya ta fito.
Sunan hotel ɗin da Naomin ta faɗa ne ya sa shi sake maimaita sunan da ɗan ƙarfi alamun mamaki.
Najeeb ya ce ya kai su inda ta ce. Lokacin kusan shida na yamma ta wuce, har ma wassu wajen ana kiraye-kirayen sallan magriba. Sun kusa isa hotel ɗin Daddy ya kira Najeeb akan ya zo yanzu-yanzu.
Najeeb ya cire kuɗi ya bawa Naomi akan ta je ta jirashi. Idan ya dawo daga wajen Daddy zai zo.
Bai bar wajen Daddy ba sai ƙarfe tara na dare. Har sun kama hanyar hotel ɗin Naomi ta kirashi akan ta koma gida an kirata mamanta ba lafiya. Wannan ya sa su ka dawo gida...

Naomi ta shiga mota tana zuba murmushi. Cikin kayan da su ka siyo jiya ta sa wani shegen gown ɗan guntu da shi. Har gashin wig  da ke kamta ta chanja shi.  Ta kamo hannun Najeeb tana kaiwa kan nonuwanta tana shashshafa su. Najeeb bai hana ta ba bai kuma yi yunƙurin yin wani abu ba. Kallon ta ya ke yi zuciyar sa na raya ma sa abubuwa dayawa. Naomi ta kai baki za ta kissing Najeeb Abdullahi ya ce " Alhaji yau Hajiya ba za ta aiki ba ne?"

Naomi ta koma baya tana hararan ƙeyar Abdullahi ita shaɗaf ta manta da wani driver. Abinda ya cika ma ta zuciya  shine yadda za ta ji idan Najeeb ya shigeta. Yau kan ko ma wani irin uzuri ne ba za ta yadda ba sai ta san yadda za su je hotel su je su yi abubuwa...

Farida kam wani zazzaɓine mai zafi ya rufeta.
Kusan ƙarfe shaɗaya sai ga Sabreen ta kirata.

"Mi ya sa za ki min haka? Ba na son shiga rayuwar kowa Ayshah"

Ta sani ƙila Lukman ya kira ta ne dan jiya ta bashi numbar Sabreen ɗin.

Ta danne duk wani baƙin ciki da ke ranta ta shiga ba ta labarin Lukman a taƙaice. Ta ƙare da cewa " Sabreen kince kina son gyara rayuwar ki. Shiyasa na miki kwaɗayin ki kasance tareda mutumin da zai taimaka miki wajen cimma burin ki. Lukman mutum ne da zan iya bugan ƙirji na ce shi ɗin namiji ne na gari wanda ya san kima da darajar mace. Wanda ya ke da ilimi ya ke kuma ƙoƙarin amfani da wannan ilimin da Allah ya bashi. Amma idan kina ganin na miki shishshigi a rayuwar ki to kiyi haƙuri"

Shiru Sabreen ta yi na kusan rabin minti kafin ta ce za ta yi tunani a kai. Farida ta kashe wayar tana fatan Sabreen ta amince da Lukman. Bayan wayan su da Sabreen shiryawa ta yi dan ta je gida. Ko idan ta ga Ummi hankalin ta zai kwanta har ta iya tambayarta shawara bisa yadda za ta ɓullowa wannan baƙon lamari da ta tsinci kan ta a ciki...*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣5️⃣1️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*

Naomi ta sa hannu ta fara shafa ƙirjin Najeeb. Bai motsa ba bai kuma hana ta ba. Ganin bai yi masifa ba yasa wanni daɗi ya ziyarci zuciyar Naomi. Ta kwantar da kai jikinsa tana cigaba da shafa shi. Najeeb dai yana tsaye kaman gunki bai iya aiwatar da komai ba.

"Sweetheart ka yi haƙuri ka ji"
Najeeb ya tsinci kan sa da gyaɗa ma ta kai...

Farida ta ji farin ciki sosai da amincewar Lukman. Tanada yaƙinin Sabreen za ta amince da shi musamman idan Najeeb ne ya ma ta maganar.

"Barin kira mijina yanzu na san ya kusa dawowa"
Ta ɗau waya ta fara kiran numban Najeeb. Sau uku tana kira sau uku wayan na tsinkewa ba tareda an ɗauka ba.
Duk da gabanta ya faɗi da hakan amma ba ta nuna ba.

Ta yi murmushi ta ce "ƙila wayar ba ta kusa da shi ne, bari mu ɗan hira shi"

Lukman ya miƙe tsaye ya ce "Aishah zan wuce, kawai duk yadda ku ka yi da shi sai ki sanar da ni"

"Insha Allahu wannan karan za a dace"

A zuciyar sa ya amsa da amin amma a fili murmushi kawai yai.

Har ga Allah tausayin shi ta ke ji. Lukman ya haɗu ta ko'ina musamman ma da ya kasance mutum ne da ya ke da tarin ilimi a ɓangaren addini, hakanan yana da kyawawan halaye...

Ta cigaba da kiran Najeeb amma shiru. Hakan ya sa ta kira Abdullahi. Bugu ɗaya ya ɗauka. Ta tambayeshi ko har yanzu Najeeb bai gama abunda ya ke bane. Abdullahi ya ce yanzu ma muna hanyar gida ne.
"Gida kuma?" Farida ta faɗa cikin rashin fahimta.
"Hajiya ai daga kamfanin ne ya ce mu wuce gida" ya amsa ba tareda ya fahimci mi ke faruwa ba.
Farida ta kashe kiran ta cigaba da kiran Najeeb amma still bai ɗauka ba.

Jakarta ta ɗauka ta fito.
"Ma, za ki fita ne?" Naomi ta faɗa tana murmushi.
Farida ba ta kulata ba ta cigaba da tafiya, har ta kai ƙofa sai kuma ta juyo ta ce "Naomi miji na ya zo ne?"

Naomi ta yi saurin cewa "No ma"
Farida ta fita cike da tunani a ranta...

............................

Tunda ya fito daga cikin Kamfanin ya ke jin shi kaman marar lafiya. Yana ganin kiran Farida amma ya ka sa ɗauka. Daga an kira wayan idan ya duba ya ga My Queen sai ya maida ta ya ajiye.
Ko wanka bai yi ba da ya shiga ɗaki ya kwanta a kan gado. Jin jikinsa ya ke kamar ba shi ba, kamar akwai abinda aka cire ma sa a jiki.
Yana kwance a haka har Farida ta shigo. Ganin sa kwance da kayan office a jiki ya sa ta san ba lafiya ba. Duƙawa ta yi ta cire ma sa takalman sa kafin ta ƙarasa dai-dai kan sa tana faɗin " miji na lafiya? Are you Ok?"
Bai ce komai ba sai ma juya ma ta baya da yai.
Tunanin ta ko ciwon kan sa ne ya tashi. Dan tunda aka sallameshi daga asibiti yake fama da ciwon kai amma ya fi tashi ma sa idan ran sa ya ɓaci ko kuma he's stressed. Likita ya ce a hankali ciwon kan zai tafi gaba ɗaya, amma kuma ya dinga samun isashshen bacci, sannan duk lokacin da ya jima yana aiki to ya tabbatar ya ware lokacin da zai kwanta dan ya huta. Hakanan ya guji duk wani abu da zai ɓata ma sa rai.

"My Champ dan Allah mi ya sameka? Wa ya ɓata maka rai?"

" ba na son surutu" ya faɗa a hankali

"Shikenan tunda ba za ka gayamin miya faru ba, amma dan Allah ka tashi ka rage kayan jikin ka za ka fi jin daɗin baccin"

Mirginawa yai ɗaya ɓangaren ba tareda ya amsa ma ta ba.
Ganin dai ba tashi zai yi ba ya sa ta tashi ta fita tunanin ta idan ya huce zai gaya ma ta koma minene.

Ɗakin ta ta wuce ta je ta yi wanka ta chanja kaya. Sai da ta kira Ummi su ka gaisa kafin ta wuce kitchen dan ta taya Tasallah aiki...

Su na jera abinci a dining ya fito ya sha wanka. Baƙin riga da wando ya sa sai ya ɗaura farin blazer a kai.

"My Champ fita za ka yi ne?"

"My Champ...My Champ" ta cigaba da kira har lokacin da ƙofar ta rufu. Baki tasake tana bin ƙofar da kallo. Ya kalleta sun ma haɗa ido kuma ya ji maganar da ta yi amma ya shareta.
Mi ke faruwa, abinda ta tambayi kan ta kenan.

Tun tana jiran shi nan da awa biyu har ta koma cewa nan da ƙarfe takwas na dare zai dawo amma shiru. Ta kira duka nambobinshi amma a kashe.

Tana kwance a kan kujera da ke falon ta ji takun sa. Ta yi firgigit ta tashi dan dama ba wai ta jima da bacci ba ne, baccin ma rabi da rabi ta yi.

"My Champ, My Champ" da sauri ya dinga taka stairs ɗin har ya ƙule ma ta.
Agogon falon ta duba ta ga ƙarfe goma har da rabi. Tunda su ka dawo gidan su bai taɓa wuce ƙarfe tara a waje ba...
Tashi ta yi ta bishi dan ba ta ga ta zama ba. Yana banɗaki lokacin da ta shigo. Itama banɗakin ta je za ta shiga dan ta taya shi wanka    ko za su shirya daga nan amma ta ji banɗakin a rufe. Mamaki ya kamata dan indai wanin su ya shiga banɗaki yo baya rufewa tunda su biyu ne a gidan Tasallah ɗakinta na ƙasa.

Ta zauna a bakin gado tana jiran fitowar sa. Tana zaune ya fito, ya shirya yai ɗan shafe-shafe da feshe-feshen sa ya zo ya kwanta.
Mamakin yadda yai kamar babu mutum a ɗakin  ya sa Farida ka sa magana. Ganin ya ja bargo ya kwanta ya sa ta lalubo sauran maganan da ke bakin ta ta ce "My Champion dan Allah ka yi haƙuri, idan ma wani laifin na maka ka yi haƙuri ka yafemin. Dan Allah miji na ka min magana. Ka gaya min laifina" tana maganan ne kaman za ta yi kuka

"Idan ba za ki iya kwantawa shiru ba, to ki koma ɗakin ki"

Kan ta ya ɗaure. Najeeb ba zai taɓa gaya ma ta haka ba, ko lokacin da ba sa shiri ma duk shirmen ta ba ya cewa ta bar ɗakin.

"Miji na dan Allah, hankalina ba zai kwanta ba idan ban san laifin da na yi ma ka ba"

tsaki yai ya tashi ya ɗau pillow ya koma kan kujera ya kwanta.

Haushi ya cikata. Idan ma laifin ta mishi bai ci ya ma ta wannan walaƙancin ba. Ta ja tsaki itama ta kwanta, a zahiri ranta na raya mata kar ta kuma bashi haƙuri zai zo da kan sa ya bata amma kuma chan cikin ranta tana tsoron wannan chanji bagtatan da Najeeb yai ma ta. Ta dinga tariyo abubuwan da su ka faru ko za ta tuna wani furuci ko wani abu da ta ma sa da zai iya ɓata ma ta rai amma ba ta gano komai ba. They are just fine, tun jiya har safiyan yau, infact san da zai fita a office ma sai da ya kissing ɗin ta sannan ya kissing cikin ta amma komai ya wargaje ne tun daga tafiyan sa. To ko a inda ya je ne aka ɓata ma sa rai? To ai koma wani ya ɓata ma sa rai bai kamata ya sauke fushin a kanta ba musamman saboda condition ɗin da ta ke ciki.
Da ire-iren waɗannan tunani ne bacci ya sace Farida.

Da asuba ma gum ya ma ta ba magana. Bayan ya dawo daga masallaci ta gaishe shi amma bai amsa ba. Haka kawai jikinta yai laushi ta fashe ma sa da kuka. To her uttermost shock maimakon ya rikice ya fara ba ta haƙuri sai ya shige banɗaki ya barta zaune tana kuka.

Innalillahi kawai ta ke ta maimaitawa a fili.
Najeeb ne zai ga tana kuka ya share, yai kaman bai ganta ba, gaskiya da matsala.

Ta zauna har ya fito ya fara shirin fita office still ignoring her. Tsoro da fargaba su ka cika ma ta zuciya.
Ba ta san ma ya za ta fassara wannan yanayi ba. Wannan yanayi mai kama da mafarki ko almara.
Wai Najeeb ɗin ta ke ma ta wannan walaƙancin. Yadda ta ke zaune tana kallon sa haka ya ƙarisa shiryawa ya fita daga ɗakin. Tunda su ka shirya ya dena fita da sassafiya haka, tunda tare su ke fita office ɗin, amma sai ga shi bayan ma yai fitar sassafiya bai ma damu ya san ko wani hali ta ke ciki ba balle ya ji ko za ta fita office ko ba za ta je ba.

Farida ta jima zaune a kan sallaya ta rasa ma abinyi Allah kawai ta ke kira a ranta. Dan wannan sauyi ya fi ƙarfinta, nan gaba kaɗan za ta iya shiga wani hali...

Shi kuwa Najeeb yana shiga mota ya ce Abdullahi ya kai shi gidan su Naomi. Tun jiya Abdullahi ya shiga ruɗu, ya kai Najeeb kamfani inda ya ɗau Naomi su ka fita, wani haɗaɗɗen restaurant su ka je daga nan ya kai su wata babbar shopping Mall inda su ka fito da kaya niƙi-niƙi. Gidan su Naomin ya kai su ta shiga ta ajiye kaya sannan ta sake shiryawa cikin wassu matsatstsun kaya ta fito.
Sunan hotel ɗin da Naomin ta faɗa ne ya sa shi sake maimaita sunan da ɗan ƙarfi alamun mamaki.
Najeeb ya ce ya kai su inda ta ce. Lokacin kusan shida na yamma ta wuce, har ma wassu wajen ana kiraye-kirayen sallan magriba. Sun kusa isa hotel ɗin Daddy ya kira Najeeb akan ya zo yanzu-yanzu.
Najeeb ya cire kuɗi ya bawa Naomi akan ta je ta jirashi. Idan ya dawo daga wajen Daddy zai zo.
Bai bar wajen Daddy ba sai ƙarfe tara na dare. Har sun kama hanyar hotel ɗin Naomi ta kirashi akan ta koma gida an kirata mamanta ba lafiya. Wannan ya sa su ka dawo gida...

Naomi ta shiga mota tana zuba murmushi. Cikin kayan da su ka siyo jiya ta sa wani shegen gown ɗan guntu da shi. Har gashin wig  da ke kamta ta chanja shi.  Ta kamo hannun Najeeb tana kaiwa kan nonuwanta tana shashshafa su. Najeeb bai hana ta ba bai kuma yi yunƙurin yin wani abu ba. Kallon ta ya ke yi zuciyar sa na raya ma sa abubuwa dayawa. Naomi ta kai baki za ta kissing Najeeb Abdullahi ya ce " Alhaji yau Hajiya ba za ta aiki ba ne?"

Naomi ta koma baya tana hararan ƙeyar Abdullahi ita shaɗaf ta manta da wani driver. Abinda ya cika ma ta zuciya  shine yadda za ta ji idan Najeeb ya shigeta. Yau kan ko ma wani irin uzuri ne ba za ta yadda ba sai ta san yadda za su je hotel su je su yi abubuwa...

Farida kam wani zazzaɓine mai zafi ya rufeta.
Kusan ƙarfe shaɗaya sai ga Sabreen ta kirata.

"Mi ya sa za ki min haka? Ba na son shiga rayuwar kowa Ayshah"

Ta sani ƙila Lukman ya kira ta ne dan jiya ta bashi numbar Sabreen ɗin.

Ta danne duk wani baƙin ciki da ke ranta ta shiga ba ta labarin Lukman a taƙaice. Ta ƙare da cewa " Sabreen kince kina son gyara rayuwar ki. Shiyasa na miki kwaɗayin ki kasance tareda mutumin da zai taimaka miki wajen cimma burin ki. Lukman mutum ne da zan iya bugan ƙirji na ce shi ɗin namiji ne na gari wanda ya san kima da darajar mace. Wanda ya ke da ilimi ya ke kuma ƙoƙarin amfani da wannan ilimin da Allah ya bashi. Amma idan kina ganin na miki shishshigi a rayuwar ki to kiyi haƙuri"

Shiru Sabreen ta yi na kusan rabin minti kafin ta ce za ta yi tunani a kai. Farida ta kashe wayar tana fatan Sabreen ta amince da Lukman. Bayan wayan su da Sabreen shiryawa ta yi dan ta je gida. Ko idan ta ga Ummi hankalin ta zai kwanta har ta iya tambayarta shawara bisa yadda za ta ɓullowa wannan baƙon lamari da ta tsinci kan ta a ciki...*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣5️⃣2️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*


Aure Rahama ne, musamman idan ka samu kwanciyar hankalin mijin ka. Ummi har wani ƙiba ta ƙara ga haske da ta yi, annurin fiskar ta ya ninka na da.

Kunun Aya da Ummin ta yi ta kawowa Farida. Farida ta ƙarɓa ta tsiyaya a kofi. Ta riƙe ƙofin amma ba ta kai baki ba. Zuciyarta ne ya tafi ga abinda ke faruwa da ita tsakanin jiya da yau.

"Farida lafiya?" Ummi ta tambaya ganin 'yarta ta yi nisa  cikin tunanin da ta ke.

"Dan Allah Hajiyata ina da tambaya"

"Minene?"

"Shin dama akwai lokacin da Namiji zai juya ma ka baya ne bayan kuna zaune lafiya?"

"Kin yiwa mijin ki laifi ko?"

"Ummi ba abinda na ma sa fa, idan ma akwai to ni duk iya tunani na ban gano ba. Ummi na bashi haƙuri amma ko kallo ban isheshi ba"

Ummi ta yi shiru tana nazartar Farida wanda damuwa ya bayyana ƙarara a fiskarta.

"Yanzu haka cikin yawar maganar ki ki ka gaya mi shi abinda ya ɓata ma sa rai"

"Najeeb bai taɓa fushi dan na gaya ma sa magana. Ba halinsa ba ne"

"Yanzu dai idan kin koma ki tsugunna har ƙasa ki bashi haƙuri. Ko ma minene Insha Allah za ki ga ya sauko"

So ta ke ta yiwa Ummi bayanin yadda Najeeb ya iya ganinta tana kuka amma ya wuce bai nuna ya damu ba. Amma kuma kar hakan ya sa Ummi ta shiga damuwa.
Ta daure ta ce "Insha Allah zan yi hakan"

"Dan Allah ki riƙe addu'a sosai. Domin addu'a da haƙuri su ke riƙe aure"

Farida ta ce "na ji Hajjaju na"

Ƙoƙarin sake fuska ta yi dan kar Ummi ta sa damuwa a ranta...

................................

Shigar su ɗakin hotel ɗin Naomi ta shiga cire kayan jikin ta. Najeeb na tsaye bai iya yin komai ba.  Sai da ta gama fidda komai na jikinta sannan ta fara jujjuya jikinta tana faɗin " ya ka ga sexy body. Ko'ina a cike ya ke fam domin ka"

Idon sa yai ja zir yana fidda numfashi da sauri-sauri. Idon ta ke sa shi samun nitsuwa, idon ta ke sa ya ji sanyi a ransa. Amma yanzu da ta ma sa tsirara sai ya ke jin wani ƙunci da baƙin ciki, kan sa ne ya hau sarawa ya dafe goshin sa yana jin kan kaman zai tsage biyu.

"Sweetheart mi ya faru? What's wrong? Are you sick?" Naomi ta faɗa tana ƙoƙarin riƙe shi. Gaba ɗaya rikicewa yai yana jin kamar idan ya sake goshin sa kan shi fashewa zai yi.

Ganin yadda ya ke yi ya sa Naomi ta tsorata, ta shiga maida kayan ta...

...............

Tun kan su isa asibiti Abdullahi dreba ya turawa Farida text akan Najeeb ba lafiya su na hanyar asibiti.

Ta fito daga wanka kenan  ta ji ƙaran shigowar saƙo. Da sauri ta je ta ɗau wayar saboda tunanin ta Najeeb ne ya ma ta reply ɗin texts ɗin da ta tura ma sa ɗazu.
Tana ganin Abdullahi hankalinta ya tashi. Ta buɗe saƙon da sauri.

*Oga ba lafiya muna hanyar asibiti*

Innalillahi ta faɗa tana kiran numbar Abdullahi...

Su na zuwa asibitin aka shiga da shi emergency saboda kafin su isa asibitin ya riga ya suma.

Naomi jikinta ɓari ya ke yi. Tsoro biyu ne a ranta, na farko kar asirin da ta ma sa ya zama ya karye na biyu kuma kar Najeeb ya mutu domin za ta shiga hali na ƙunci ga zargin ta da mutane za su yi...

A birkice Farida ta shigo asibitin. Ganin Abdullahi da Naomi su na tsaye cirko-cirko ya sa zuciyar ta ya karaya.

"Malam Abdullahi mi ya samu miji na? Ina ya ke?"

"Hajiya dan Allah ki kwantar da hankalin ki. Insha Allahu ba abinda zai sami Oga"

"Ina ya ke?" Ta faɗa da ƙarfi.

Kafin Abdullahi yai magana aka buɗe ƙofan ɗakin da ya ke. Da sauri ta ƙarasa gaban likita tana tambayar lafiyar Najeeb.

"Hajiya yana bacci yanzu. Sai dai dan Allah ku dinga kiyaye ɓacin ransa, yanzu haka jinin sa ne ya hau sosai"

"Can i see him?" Ta faɗa da raunatacciyar murya.

Likita ya ce e amma ta bari za a chanja ma sa ɗaki yanzu.

Su na tsaye aka fito da shi akan gadon marasa lafiya, aka turashi zuwa ɗakin da aka ba shi.
Farida da Abdullahi su ka bi nurses ɗin har ɗakin da aka maida shi, yayinda Naomi ta juya da baya ta tafi. Ta ji kaf abinda likita ya ce, amma zuciyarta ta rasa gane ko mi ya sa ran Najeeb ya ɓaci har ta kai ga haka. Normal su ka je hotel ɗin, infact da murmushi a fiskar sa lokacin da su ka shiga ɗakin. Tana cikin keke tana tariyo duk abinda ya faru tun safiyar yau. Ba wani abinda zai ɓata ma sa rai sai dai.... karaf ta tuna dai-dai lokacin da Najeeb ya fara chanja fuska. Tabbas tsiraicin ta da ya gani ne. Idan har saboda ba su yi aure ba ne ya ke jin ba zai iya kusantar ta ba to tabbas za ta gaya mi shi su yi aure nan ba da jimawa ba...

Awa uku kafin Najeeb ya tashi, lokacin duk 'yan gidan su sun zo har da Sabreen. Kowa tambayar abinda ya faru ya ke amma Farida ba ta da bakin magana tunda itama ba ta sani ba. Tunaninta ko saboda ita ne ya shiga wannan hali. "My Champ laifin mi na ma ka ne?" Ta faɗa a zuciyarta.

Daddy ya tambayi Abdullahi ko daga ina su ke. Ya san matuƙar ya faɗi gaskiya to iyayen Najeeb za su shiga tashin hankali musamman ma Farida da ciki gareta.
Ya chanja maganar da cewa sun je wani site ne yai magana da ma'aikatan da ke wajen to da su na dawowa shi ne ya fara riƙe kan sa yana nishi sama-sama.

Daddy ya ce " Allah shi kyauta, amma daga yanzu duk wannan aikin fita supervision ɗin ya isa haka.  Anas ko wani daban zai dinga zuwa"

Lokacin da ya farfaɗo garau ya ke jin sa sai dai rashin ganin Naomi a wajen ya sa ya ji ba daɗi. Yana son tambaya amma Mom da Farida sun ƙi bashi dama kowa nan da nan ya ke da shi. Ya haƙura ya zuba mu su ido.
Chan dare aka sallamesu saboda ya ce ba zai kwana ba, shi lafiyarsa lau...

Su na cikin mota amma ba wanda yai wa ɗan uwansa magana. Farida ta kamo hannun sa ta kai kan cikin ta tana faɗin "baby ya missing ɗin ka sosai"
Zare hannunsa da yai daga kan cikinta ya sa ta zaro ido. Tana binsa da kallon mamaki, juyar da kan sa yai yana kallon titi.
Hawayen baƙin ciki su ka fara zubo ma ta.
"Wai mi ke faruwa ne?" Ko lokacin da bai gane ta ba a asibiti farkon farfaɗowan sa ai ba ya ma ta wannan walaƙanci balle yanzu da su ke tsaka da soyayya. Wai har cikin da ke jikinta ma bai damu da shi ba.

Ba ta kuma yunƙurin yin wani abu ba har su ka isa gida. Ido kawai ta ke binsa da shi duk abubuwan da ya ke yi.
Tana ganin ya zauna a bakin gado yana shirin kwanciya ta zo gaban sa. Tsugunnawa ta yi ta riƙe gwiwowin sa duka biyu.

"Na roƙe ka da girman Allah Ubangiji Mai Rahama. Ka yafe min mijina, na yadda na yi ma ka laifi a rashin sani amma ka yafe min. Horon rashin magana da halin ko in kula ya min tsauri. Mijina abin so na, abin muradi na. Kai kaɗai ka mallake zuciyar Aisha Farida. Ba ni da tamkar ka kuma ba zan taɓa samun tamkar ka ba, ka yi haƙuri dan Allah ka gaya min mi na maka ka kuma yafe min. Idan ka cigaba da haka ciwon zuciya zai kasheni...." kuka ya kufce ma ta.

Duban ta ya ke yadda ta ke ta sheshsheƙar kuka, maimakon ya ji tausayin ta sai ma ran sa ya ɓaci.
Da kakkausar murya ya ce " you liar, ba ki da wani bayan ni? Oh really! Shi ne daga fita na ki ka kira tsohon saurayin ki ya ɗebe mi ki kewa kafin na dawo ko?"

Shiru ta yi tana rarraba ido dan ba ta gane maganar sa ba.
"Tsohon saurayina kuma? My Champ...."

"Oh please! Ba na son jin komai ki je ki yi duk abinda ki ke so"

"Wai Lukman ka ke magana? Haba My Champ, haba. Tsakanina da Lukman ya zama tarihi"

Miƙewa yai ya ɗau pillow zai fita ta riƙe ƙafar sa.

"Dan Allah ka tsaya na ma ka bayani. Wallahi ba abinda ka ke tunani ba ne"

Turata gefe yai ya fice abinsa.
Farida ta fashe da wani sabon kukan. Ba abin da ya fi damunta irin wai duk hukuncin nan  akan zargi ne. Ta ya zai zargeta, wani irin so za ta nuna ma sa ta tabbatar babu wani namiji a rayuwarta da ya wuce shi.  Tafi minti talatin tana kuka kafin ta tashi ta shige banɗaki ta ɗauro alwala.

Bayan ta yi sallah ta zauna a sallayar tana kuka tana gayawa Allah buƙatunta. Ta jima tana addu'a kafin ta naɗe sallayar ta je ta kwanta. Ba abinda ke ranta irin cin uban Naomi da za ta yi gobe, tunda ita ce 'yar burauban da ta haɗa ta da mijinta, ta ma ta ƙaryan mijinta bai zo ba ranan. Ashe ya zo har ya ganta da Lukman.
Ta jima tana saƙa da warwara kafin bacci yai gaba da ita.

.........................

Washegari tun da sassafe ta kira Sabreen akan dan Allah ta shirya za ta mata wani taimako. Sabreen ta amsa da ba matsala.

Karyawan kirki Farida ba ta iya yi ba. Zuciyarta ke tafarfasa yana zafi. Ba ta san sadda ma Najeeb ya fita ba tana tsammanin ƙila lokacin da ta koma na ta ɗakin ne...

Kamar jiya ma dai Najeeb cewa yai ya kai shi gidan su Naomi. Jin haka ya sa Abdullahi ɗaura aniyar dole ya sanar da Farida, domin gaskiya akwai lauje cikin naɗi a wannan al'amarin.

Naomi ta yi farin cikin ganin Najeeb garau ba kamar jiya da ya ke rai a hannun Allah ba. A cikin motan hannunsu sarƙe cikin na juna har su ka isa kamfani...

Suna isowa sai ga Anas shima motar sa ta yi parking.  Da sauri ya fito ganin Najeeb da Naomi sun fito mota ɗaya.

"Najeeb... Najeeb" Anas ya kira shi da ƙarfi da ke sun riga shi fitowa a mota.

Najeeb ya juyo ya kalli Anas. Kallon tuhuma Anas ke wa Najeeb ɗin har ya iso.

"Good morning Sir" Naomi ta gaishe da Anas tana murmushi.

Ko amsawa bai yi ba ya ce ta basu waje. Naomi ta yi gaba tana tafiya tana yauƙi.

Anas ya kalli Najeeb ya ce "mi ke faruwa Najeeb? Mi ya sa za ku taho tare kai da sakatariyar ka? Ina Farida?"

" Dude ka ci sa'ido. Ina Baby? Fatan ka na kula min da ita sosai"

"I'm serious Najeeb. Mi ke faruwa?"

Najeeb ya ɗan buga kafaɗar sa ya ce " kar ka cika ni da surutu we have board meeting today"

Girgiza kai Najeeb ya fara yi yana neman yaƙi da abinda zuciyar sa ke raya ma sa. Najeeb ba zai taɓa haka ba, ba halin sa ba ne, No.
Ya jima tsaye kafin ya bi bayan Najeeb wanda tuni ya shige ciki...

Ƙarfe tara da rabi Farida da Sabreen su ka iso Kamfani. Tun a mota Sabreen ke tambayar Farida me ke faruwa amma ta ka sa gaya ma ta. Cewa kawai ta yi za ta ba da wani shaida ne.
Farida kam cikin zuciyar ta ayyana yadda za ta yi ƙuli-ƙulin Kubra da Naomi ta ke yi...

Kai tsaye sama su ka wuce. Sabreen na ta cewa ta yi a hankali saboda condition ɗin ta.

Su na isa office ɗin kuwa Naomi na fitowa daga office ɗin Najeeb.
Belt ɗin Najeeb da ta sa a jaka ta ciro, ta yi kan Naomi da sauri. Naomi ba ta ankara ba ta ji saukar belt a bayan ta. Dama ta gan su, ta kau da kai ne kawai, saboda yanzu ta gama convincing Najeeb akan ya aureta kuma ya ma ta alƙawarin zai auretan. Tunda za ta zama matar Najeeb mi zai sa ta wani tsaya ba wa Farida girma...

Farida ta sake warɓa ma ta belt ɗin tana masifa "shegiya mai kaman Aladu, ke ce sheɗaniyar da ki ka haɗa ni da miji na ko"

A na huɗu da ta kai ma ta dukan ne Naomi ta riƙe belt ɗin tana huci.

" 'yar iska ramawa za ki yi? Bismillah, rama" ta jawo gashin Naomi ta falla mata mari. Naomi ta challa ƙara tana kiran sweetheart.

"Kan Uban chan, mijina ne sweetheart ɗin ki" ta sake yowa kan ta. Naomi ta shige office ɗin Najeeb da gudu.

"Ayshah take it easy" abinda Sabreen ke ta faɗa kenan.

Farida ta cire gyalenta ta miƙawa Sabreen ta ce " yau yarinyar nan za ta san da wa ta ke ja, sai na chanja ma ta kamannin ta"...

Numfashin ta sai da ya kusa ɗaukewa saboda abin da idon ta ya ci karo da shi. Najeeb ne tsaye gaban Naomi yana goge ma ta  hawaye da hankerchief ɗin sa.

"My Champ" kawai ta iya faɗa bakin ta na rawa.

Ya kalleta da idon sa da su ka rikiɗa su ka koma ja....*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣5️⃣3️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*



"Mi ya sa ki ka dake ta"
Najeeb ya faɗa da ƙarfi.

Mamaki, tsoro, kishi, baƙin ciki su suka haɗu su ka hana Farida Magana.

"Sorry, sorry dear" ya faɗi yana bubbuga bayan Naomi.

Sabreen ma dai mamakin ne ya cikata. Da ƙyar ta iya cewa " Noory what's this?, what's happening here?"

"This should be the last time da za ku taɓa min ita, she's very special to me, duk abinda ya taɓani ya taɓa ta"

Maganar da yai ya sa hawayen da Farida ke tarewa su ka fara zubowa.

"Najeeb akan wannan Kafirar ka ke min walaƙanci tun shekaranjiya? Akan wannan fasiƙar?"

"Please ku bar min office ba na son hayaniya" ya faɗa tareda kwanto da kan Naomi jikin sa.

"Noory what's wrong with you?" Sabreen ta faɗa ganin yadda Najeeb ya bada hankalin sa kwacokam a wajen Naomi.

Zuciyar Farida kaman za ta bulluƙo tsabar yadda ta ke bugawa da ƙarfi-ƙarfi. A hankali ta tako gaban su tana kallon cikin idon Najeeb.
Naomi ta sake narkewa jikin Najeeb tana kukan munafurci.

"Wallahi yau ka ce kana son Sabreen za ka dawo da ita rayuwar ka. Zan yi kuka, zan ji baƙin ciki, amma daga baya zan rarrashi kai na na amince ma ka. Amma wannan?"
Ta faɗa tana nuna Naomi.

"Ba zan taɓa amincewa ba har abada"

"Fine, dama ba amincewar ki na ke nema ba. Infact we are getting married soon"

Ta buɗe baki za ta yi magana amma sai hawaye. Ta juya da sauri ta fita, Sabreen ta bi bayan ta da gudu...

Ganin halin da ta ke ciki ya sa dole Sabreen ta raka ta gida. Kuka ta ke cikin motar kaman ranta zai fita. Da ƙyar Sabreen ta dinga rarrashin ta saboda abin cikin ta...

Kwanciya Farida ta ce za ta yi hakan ya sa Sabreen ta ma ta sallama tareda cewa za ta gayawa Mom abinda ya faru dan abin ya ɗaure ma ta kai...

Sabreen na tafiya Farida ta shiga haɗa kayan ta.

...........................

"Wato dai ba za ki gaya min mi ya dawo da ke gida ba ko"
Farida ta juyar da kai ta cigaba da hawaye.

"Ki tashi ki koma gidan ki kafin Baban ku ya dawo"

"Ummi kafira ce fa, wai kafira zai aura. Akan ta ba irin walaƙancin da bai min ba. Ni na haƙura, ya je ya auretan zai gani ai"

"Najeeb ɗin?"

"Ummi cikin ido na fa ya kalla ya ke faɗa min wai zai aureta. Ko na amince ko ban amince ba babu ruwan sa aurenta zai yi" ta fashe da kuka.

Ummi ba ta yi ƙoƙarin hanata kukan ba sai ma nazarin maganganun Faridan da ta fara yi wanda ta ke ganin ba lafiya ba. A yadda ta karanci Najeeb yana tsananin son Farida ba zai taɓa ma ta walaƙanci haka kawai ba musamman yadda ta ke da cikin nan.

Rarrashin Faridan ta shiga yi saboda cikin jikin ta...

Sabreen na zuwa ta sanar da Mom abinda ya faru. Mom ta ka sa gaskata hakan, ta ɗau waya ta shiga kiran Najeeb amma bai ɗauka ba.  Mom ta ce ba ta ga ta zama ba dole su je har kamfanin ta ji bahasin wannan sabon salo na shi...

Da su ka je ba su same shi ba. Shi da Naomi sun fita. Mom ta je office ɗin Anas shima baya nan ya fita. Haka su ka dawo gida tana jira Daddy ya dawo ta sanar da shi komai...

Farida kashe wayarta ta yi lokacin da ta ga Anas ya dameta da kira. Bayan ta yi sallar Azahar ta samu ta kwanta saboda baccin da ba ta samu ta yi jiya ba.

Anas kuwa ya ga lokacin da Najeeb da Naomi su ka fita. Yana kiran Najeeb amma ya ƙi kula shi. Farida ya shiga kira amma ba ta ɗauka ba, ƙarshe ma aka kashe wayar.  Hakan ya sa ya je ya shiga mota ya wuce gidan su. Da ya isa gidan Tasallah ke gaya ma sa Farida ta tafi gidan su kuma yanayin kayan da ta ɗauka kaman yaji ta yi.
Hankalin Anas ya kuma tashi yana tunanin mi ke faruwa tsakanin wannan masoya.
Gidan su Farida ya wuce direct. Da ya isa ya aika yaro akan ya kira ma sa Farida inji Anas. Yaron da ya shiga ya samu Ummi ya gaya ma ta.  Ummi ta aiki Zainab ƙanwar Maijiddah akan ta cewa Anas Farida ba ta jima da bacci ba. Za ta kirashi idan ta tashi.

Anas dai ya tafi ne amma ya so ya ga Farida ya tambayi mi ke faruwa. Yana hanya saƙon Mom ya shigo akan idan ya tashi a waken aiki ya zo gida...

........................

Bayan la'asar ta farka. Kuma Alhamdulillah zuciyarta yai sanyi.

Sai da Ummi ta tabbatar ta ci abinci sosai sannan ta shiga ma ta nasiha tareda faɗa ma ta illar baro gidan ta da ta yi.

"Ummi to na koma na ma sa mine? Bayan ya samu 'yar ma su fitsari a tsaye yace yana so"

"Farida kenan, har yanzu da sauran ki. Wa ya gaya miki zaman aure zaman jin daɗi ne na dindindin. Ki koma gidan ki ki cigaba da yiwa mijin ki addu'a har Allah ya warware mu ku matsalar da ku ke ciki. Ni ina tunanin ba haka yarinyar nan ta bar shi ba. Amma addu'a ya fi ƙarfin ko wani sharri dan haka shi za ki riƙe"

Maganganun Ummi ya sa jikin Farida yai sanyi. Sai yanzu ne zuciyar ta ya fara wannan tunanin. Ƙila Naomi ta yiwa Najeeb wani abu ne...

Cikin ruwan zamzam da su ka zo da shi daga saudiyya Ummi ta ɗauko ta kawo ma ta. Sai a lokacin Faridan ma ta tuna su ma na su da su ka zo da shi bai ƙare ba. Ta amsa tana yiwa Ummi godiya.

"Kar ki saka damuwa a ranki dan Allah, ki riƙa tashi da dare kina yiwa mijin ki addu'a, sannan wannan ruwan zamzam ɗin ki dinga haɗa ma sa a ruwan shan sa, abinci dama shayin da zai sha. Ki riƙa tofe makwancin sa da kuma inda ya saba zama da Suratul Falaƙi da Naasi saboda suna maganin asiri da sheɗanu"...

Ƙarfe bakwai saura ta isa gida. Kunna wayarta da ta yi ta ci karo da saƙonni. Biyu daga Anas sai ɗaya daga Mom sai ɗaya daga Lukman inda ya ke ma ta godiya domin Sabreen ta amince da shi. Na ƙarshen ne ta ga Abdullahi dreba inda ya ke cewa "Hajiya dan Allah akwai maganar da na ke son gaya mi ki gameda Oga".

Ta turawa Lukman saƙon taya murna kafin ta kira Abdullahi. Da ke yana tareda Najeeb a mota sai bai ɗauka ba. Da aka sake kira sai ya ɗauka ya ce " ina tuƙi Hajiya, mun ma kusa isowa gida"

Farida ta sauke ajiyar zuciya lokacin da ta kashe kiran.
Numbar Mom ta kira dan saƙon na ta cewa ta yi ta kira ta dan Allah.

"Ayshah ki na lafiya?"

"Lafiya Mom" ta amsa tana ƙoƙarin saita maganarta.

"Anas ya ce min kin koma gidan ku, dan Allah 'ya ta ki dawo, zan zo gidan na ku gobe"

"Mom na dawo ma, yanzu haka ina gidan"

"Allah ya miki albarka"
Farida ta amsa da amin...

Bai fi minti shabiyar ba sai ga Najeeb ya shigo gidan. Tana zaune a falo tana kallo ya shigo, a zahiri za ka ga kaman kallon ta ke amma ba kallon ta ke ba, hannunta akwai carbi tana jan Ya Hayyu Ya Qayyum.

Ba ta ma sa magana ba haka ya hau sama da gudu kaman zai tashi sama.
Tana ganin ya shiga ta kira Abdullahi akan ya shigo...

Duk yadda ta yi ya zauna a kan kujera ya ƙi. A ƙasa ya zauna su ka gaisa.

"Malam Abdullahi ina fata lafiya?"

" Hajiya dan Allah ki yi haƙuri da abinda zan gaya mi ki"

Farida ta ce ba komai.
Nan ya shiga gaya ma ta abinda ya lura tsakanin Najeeb da Naomi. Ya faɗa ma ta jiya da ya kai su hotel ne Najeeb ya fara ciwo amma da lafiyar sa ƙalau. Ya ƙara da cewa " Hajiya kar ki tsorata amma akwai asiri ajikin Alhaji. Wannan cegiyar arniyar ta yiwa Alhaji asiri"

Duk da gaban ta ya faɗi amma hakan bai sa ta ji tsoro ba, dan tunda Ummi ta ba ta shawarwari ta sa a ranta sai inda ƙarfinta ya ƙare akan yiwa Najeeb addu'a.

Ta yiwa Abdullahi godiya ta sallameshi...

Sai da ta leƙa ɗakin sa ta ga yana bacci kafin ta wuce na ta ɗakin. Ɗazu ta tsiyayi ruwan zamzam a hannunta ta tofa ƙula'uzai a ciki sannan ta yayyafa a gadon sa da duk kujerun sa...

Ƙarfe biyu da rabi ta tashi ta fara gabatar da sallah tana addu'a ba ta kwanta ba har asuba. Ƙarfe shida ta fito ta taya Tasallah haɗa ma sa breakfast duk da ma Tasallah ta ce tea kawai ya ke sha yanzu.  Acikin tea ɗin ta tsiyaya ma sa ruwan zamzam kaɗan wanda shima ta tofeshi da addu'o'i...

Da za ta haura sama ta ce da Tasallah ta kai kuɗi gidan da ake musu kunu da ƙosan sadaka lokacin da Najeeb bai da lafiya su ma ta sadaka.
Ita kan ta Tasallah ta san akwai matsala a gidan dan masoyan da kullum su na manne da juna sai ga shi yanzu ko kallon kirki ba sa yiwa junan su.

Saboda bacci da ke idon tana shiga ɗaki bacci ta yi. Ba ta farka ba sai ƙarfe tara. Ta yi wanka ta shirya ta sauko. Kaman yadda Tasallah ta ce tea ɗin kawai  ya sha ya fita.
Ta zauna a dining ta ci abinci sosai, ba wai dan daɗi ba sai dan ɗan da ke cikin ta.

Ƙarfe shaɗaya ta wuce gidan su Najeeb. Mom ta riƙa ba ta haƙuri tareda da nuna ma ta Najeeb yana cikin matsala dan jiya sa'insa su ka yi da Daddy akan ya ce zai auri Naomi.

Cikin kuka ta ce " he has never raised his voice to his father, amma jiya..." kuka ya kufce ma ta.

"Mom dan Allah ki dena kuka, addu'a za mu dinga ma sa har Allah ya kawo ma na ƙarshen wannan bala'i"...

Ta jima a gidan dan sai bayan Azahar ta tafi.
Anguwar su ta wuce amma ba ta kai gida ba ta tsaya a gidan su Saminu. Saminu abokin Yakubu ne amma tun secondary school ya lalace da shaye-shaye. Yanzu haka ba shi da aikin yi sai maula gidan 'yan siyasa, idan lokacin zaɓe ya zo sune 'yan bangan siyasa.
Duk da halin su da ya banbanta amma ba su dena mutunci da Yakubu ba. Lokaci zuwa lokaci yana zuwa wajen Yakubu ko kuma su haɗu a majalisa.

Da ta je gidan dai cewa aka yi Saminun baya nan amma an bata numbar shi.

Tana fitowa daga gidan ta kira numbar ringing ɗaya kuwa aka ɗauka.

"Kai ɗan dambulan 'wa ina ka shiga, na je shagon ka ban sameka ba" abinda Saminu ya fara faɗi kenan.

"Haba Saminu a bi a hankali mana"

Jin muryan mace ya sa Saminu ya fara washe baki yana faɗin sorry Hajiya.

"Suna na Farida ƙanwar Yakubu ɗan gidan Alhaji Musa Wase"

"Kai kai ashe Hajiya Farida ce. Ki gafarceni dan Allah na ɗauka wani banzan yaro ne"

Farida ta ce ba komai

"Ina son ka min wani aiki ne ka ɗan samu wani abokin ka sai ku zo. Za ku samu 'yan chanji na siyan kati"

Saminu ya sa ihu yana faɗin koma minene za su yi...

Farida ta yi murmushi ta ce "Naomi miji na ki ke so ko?. Fine, za ki same shi da kyau"...

...............................

Tana zaune tana duba kayyayakin da su ka siyo ɗazu ta ji wayarta na ringing. Da sauri ta ɗauka dan tunanin ta Najeeb ne ganin sunan Madam Farida ya sa ta yi tsaki. Ko me ta ke nema a wajena oho.
Kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma ta ɗauka.

"Naomi Naomi, Naomi Masoyi. Naomi matar Najeeb ko. Fatan kina lafiya? Ina son ganin ki ya za ayi ne?"

Naomi ta ja tsaki ta ce " ba za ki ganni ba. Na san plan ɗin ki bai wuce ki dake ni ba"

Farida ta yi dariya ta ce "Allah ko? To barin zo sai mu ga ko dukan na ki da gaske zan yi"...

Naomi ta kashe wayan tana tsaki. Baifi minti goma ba sai ga shi Mrs Comfort na kiran ta akan ta zo ta buɗe ƙofa ana ƙwanƙwasa ƙofa.
"Mama ina Abel, ya je ya buɗe mu su"

Mrs Comfort ta ɗaga tana faɗin " wai ba za ki fito ba. Abel baya nan fa"

Naomi ta yi tsaki sannan ta fito.

Mrs Comfort na zaune a kan keken guragu tana karanta bible Naomi ta zo ta buɗe ƙofa. Naomi ta zaro ido lokacin da ta ga Farida tsaye bayanta kuma wassu samari biyu ne wanda da ka gan su ka san a buge su ke.
Ta ja da baya da sauri tana faɗin Mama.

Suna shigowa Farida ta ce "Saminu rufe min ƙofa dan Allah"

Naomi gefen Mrs Comfort ta tsaya jikin ta na rawa.

Farida ta kalli Falon na su da kyau sannan ta ce " Mrs Comfort ban san ko da sa hannun ki Naomi ta asirce min miji ba, har ta ke son auren shi"

Mrs Comfort ta zaro ido, Ita da ta tsani musulmai shi ne za ta bari 'yarta ta yi tarayya da musulmi. Ta dai lura da yawan kayyakin da Naomin ke zuwa da su kwana biyun nan, kuma ta yiwa Naomin magana amma ta ce saurayin ta ne ke siya ma ta.

"Ni ban san komai ba. Naomi wai mijinta ki ke so?"

"Madam Farida ki fita a gidan mu ko na kira police"

Farida ta kwashe da dariya ta ce " ina da numban comissioner of police zan baki sai ki gaya mi shi ƙorafin ki amma kafin nan..."

Ta kalli Saminu  ta ma sa ishara da ido. Shi da ɗayan da su ka zo da ake cewa Maska su ka yi kan Naomi. Naomi ta yi hanyar ɗaki tana ihu amma ko takun kirki ba ta yi ba, Maska ya cafko ta.

Kujeran da ke wajen ɗan ƙaramin dining ɗin su Saminu ya ɗauko. Aka zaunar da Naomi ana ɗaureta bayan sun fara rufe bakin ta saboda kuka da ihu da ta ke yi.

"Tsirara za ku ma ta"  Farida ta faɗa da ƙarfi.

Maska ya yaga vest ɗin da ke jikinta, mini skirt ɗin ma ya yage ta ya saura daga ita sai pant.

"Shi ma ku cire" Farida ta faɗa ba alamar wasa a fiskarta.

"Plz Madam Farida, i beg you. Naomi za ta bar mi ki mijin ki dont kill her" Mrs Comfort ta faɗa tana kuka.

"Ni ba kisa zan yi ba, zan dai ɗanɗana ma ta kaɗan daga azabar da za ta ji duk ranan da ta sake neman mijina ne"

Ta kalli Saminu ta ce "bar ma ta pant ɗin, zai ma sa cirnakun su ci gindinta sosai"

Handglove ta cire ta miƙawa Saminu. Saminu ya ce " Hajiya barshi zan sa hannu kawai"

"A'a ka dai saka ɗin"

Ya karɓa handglove ɗin  yana sawa. Daya gama Maska ya fito da wata leda wanda kwalbar Bama mayonnaise ne aciki cike da cirnaku baƙaƙe da jajaye.

Saminu ya ɗebo cirnakun nan ya sa hannu cikin pant ɗin ta ya zuba su. Har da cuccusawa cikin abun ta.
Da ya gama ya zuba sauran a cinyayyen gashinta, dama ta riga  ta cire wig ɗin da ke kan ta. Sauran ya sa a bayanta....

* ma su cewa asiri ya karye da wuri to Insha Allah page ɗin dare na ku ne*

*not edited, not proof read, dan haka za a iya ganin typing errors**SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣5️⃣4️⃣

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900 ya biya #200 ta account no 3099546325 ko kuma idan ba hali, then MTN card ta wannan numban 08137311900*

Naomi sai zazzare ido ta ke yi tana kici-kici akan kujera, idonta yai ja ga gumi da ke ta tsatstsafowa a jikinta. An ɗaure hannu da ƙafa ga bakin ma an kulle ba halin kuka.

Mrs Comfort ta turo kekenta zuwa wajen Farida da ke tsaye tana kallon Naomi.

"Plz Madam Farida, i beg you in the name of the Almighty God stop this. Naomi za ta bar mijin ki i promised you that"

Jin yadda Mrs Comfort ke roƙo tana hawaye ya sa ta ɗan ji tausayin ta.

Ta ciro Shentos insecticide a jaka ta miƙawa Saminu.
"Fesa ma ta su mutu, tunda uwarta ta roƙi alfarma"

Saminu ya ƙarɓa ya fara fesa wa Naomi a kanta da bayanta. Yana shirin feshe wajen abun ta, Farida ta ce "tsaya-tsaya Saminu. Cire ma ta pant ɗin za su faɗo"

"Hajiya ki bari na fesa a wajen za su fi mutuwa da wuri"

Farida ta girgiza kai. Saminu ya cirewa Naomi pant ɗin wanda ke cike da cirnaku wasu sun mutu wasu kuma suna ta mutsu-mutsu a jiki.  Cikin minti ɗaya kusan duk cirnakun sun mutu saboda ƙarfin maganin. Wanda su ka tsira ma to sun nakasa sosai.

Farida ta kalli  Mrs Comfort ta ce "ki jawa 'yar ki kunne, duk abinda ta yiwa mijina ta warware idan ba haka ba. Nan gaba ba'a cirnaku kaɗai zan tsaya ba, sai ta ƙwammace ba ta zo duniya ba"

Ta cilla ma ta wani tube na magani ta ce " idan ta wanke jikinta da kyau ta shafa wannan. Zai taimaka wajen rage raɗaɗi"
Ta kalli su Saminu ta ce su kunce ta. Ana kunce bakin Naomi ta ɓarke da kuka, ihu ta ke kamar wadda aka aikota saboda azaba.  Ana gama kunceta ta fita da gudu sai banɗaki, tana zuwa taga ba ruwa a ciki ta fito ta wuce kitchen da gudu tana sosa gabanta da bayanta zuwa kanta duk lokaci guda. Suna ji ta buɗe randan ruwa ta fara kwararawa kan ta tana yi tana kuka...

Farida ta kalli Mrs Comfort ta ce "ki jawa 'yar ki kunne ko kuma jikinta ya gaya ma ta" daga haka su ka fice a gidan.

Gaba ɗaya ruwan randar ta ƙarar a jikinta still ba ta ji sauƙin komai ba. Sai ihu ta ke yi, Mrs comfort ta ɗau waya ta kira Abel ƙanin Naomi akan maza-maza ya zo gida.
Naomi ta zama tamkar mahaukaciya a cikin gidan, ta shiga nan ta fita chan, ta kasa zama ta kasa kwanciya sai kuka da soshe-soshe...

Ƙarfe shida na yamma Naomi na kwance tsiraran ta tana hawaye tana nishi sama-sama, gefenta ƙawarta Maureen ne ke ma ta fifita a gabanta. Maganin da Farida ta bayar aka shafa ma ta, ya ɗan taimaka wajen samun sauƙin raɗaɗin da ta ke ji. Ilahirin jikinta duk ya cika da tabon cizo.

"Na God go Punish that woman" Maureen ta faɗa tana tsaki

Mrs Comfort da ke gefe tana ganin 'yartata ta ce "ba laifin Madam Farida ba ne. Laifin Naomi ne, mi ya kaita soyayya da musulmi hakan ma married man"

"Mama ki dena faɗin haka. Ko ma mi Naomi ta yi ba ta chanchanci wannan punishment ɗin ba. This is pure cruelty"

Mrs Comfort ta girgiza kai tana tunanin idan Naomi ba ta ji sauƙi ba za su wuce asibiti kawai...

.............................

Hankali kwance Farida ta koma gida, zuciyarta saƙayau, ko ba komai Naomi za ta yi jinyar kwana biyu.
Ƙarfe shida saura sai ga Anas da Najdah sun zo ma ta.
Anas dai haƙuri ya ba ta kan wannan magana tareda nuna ma ta suna tareda ita ɗari bisa ɗari.
"Akwai wani Malami da na yiwa magana ya ce zai tayamu da addu'a. Insha Allah za mu ga ƙarshen wannan al'amari"

Farida ta ce " Ya Anas na gode sosai Allah ya saka da alkhairi"

Najdah ta cire girman kai ta ce " Anty Farida, Big B yana son ki sosai, ba zai taɓa walaƙanta ki cikin hankalin sa ba, Please kar ki yi fushi da shi"

" Na gode Najdah, ku dai cigaba da tayamu da addu'a"

Najdah ta ce Insha Allah.

Sun ɗan jima kafin su ka tafi. Su na ma tunanin Najeeb zai dawo ya same su amma har su ka tafi bai dawo ba...

A ɓangaren Najeeb kuwa zuciyarsa tafarfasa ya ke lokacin da ya isa gidan su Naomi ya isketa kwance. Maureen ce ta kira shi ta sanar da shi komai.

Lokacin da Mrs Comfort ta ga Najeeb ya shigo gidan su hankalin sa a tashe ta fara tunanin kaman maganar Farida gaskiya ne. Idan ba haka ba Sir Najeeb ɗin da ta sani ɗan ƙwalisa mai ji da kan sa ba zai taɓa kallon Naomi ba balle ya damu da ita ko kuma ya so ta.

Tana gani ya ɗauki Naomi a hannun sa su ka fita tareda Maureen. Tana faɗin su tsaya amma ba wanda ya kulata cikin su...

Da su ka je asibiti gado aka ce ta kwanta sannan Likita ya duba ta daga sama har ƙasa. Da ya gama examining na ta ya nemi bahasin abinda ya faru har cirnaku su ka cize ta haka musamman a ta wajen abun ta. Maureen ta fara koro bayani akan ai wata Ogar Naomin ce ta sa ma ta cirnaku a jiki.

"Saboda me? Wannan ya kamata akai case ɗin nan gaban 'yan sanda" Likitan ya faɗa cikin faɗa.
Maureen ta ce yanzu ma daga asibitin police station za su wuce.

Magani ya rubuta mu su na sha da na shafawa sannan aka sallamesu bayan ya rubuta mu su report da za su kai police station.

Daga asibiti Najeeb ya ce Abdullahi ya kai su police station. Abdullahi dai mamaki ya cika shi dan bai gane wannan al'amari ba daga asibiti sai police station. Ya dai cika umurni ya wuce da su...

Ganin report ɗin da su ka kawo da kuma testimony da Naomi da Maureen su ka bayar ya sa aka haɗa su da police biyu dan su je su arresting wannan muguwar mata da aka kira da Madam Farida.
Cikin su Naomi ba wanda ya ambata cewa Madam Farida matar Najeeb ne. Shi kuma Najeeb yana zaune kaman wawa duk abinda Naomi ta faɗa to daidai ne...

Motar su na gama motar police na baya har su ka isa gida. Abdullahi dai bai san mi ya ke faruwa ba.

Maureen sai kumfar baki ta ke tana faɗin "today she go no say our madness pass her own"
Naomi kam maƙalewa ta yi jikin Najeeb wanda ke ta ce ma ta sorry...

Bayan tafiyar su Anas, wanka Farida ta yi ta gabatar da sallar Isha. Tana ma kan sallayar tana addu'a Tasallah ta shigo ɗakin da gudu tana haki.

"Baaba Tasallah lafiya?" Farida ta faɗa ganin yadda ta tsorata.

"Folisawa a falo, Folisawa suna neman ki Hajiya"

"Police kuma"

Tasallah ta gyaɗa kai.

"To ki je ina zuwa"

Tasallah ta fita, still tana tsoro dan ganin Najeeb ne ya zo da su ya sa ta ƙara tsorata da lamarin.

Farida ta cire hijabin sallar ta ta je ta ɗauko ƙarami ta saka dama gown ɗin material ne a jikin ta.

Najeeb da su Naomi na zaune a falon su kuma police ɗin su na tsaye.
Ganin Naomi ya sa ta gane dalilin zuwan police.

"Suna na Sergeant Iliya. Mu na tambaya ko ke ce Madam Farida Salihu?"

Farida ta kalli Najeeb wanda ko wajen da ta ke tsaye bai kalla ba sannan ta kalli sergeant ɗin ta ce "eh ni ce"

"Madam you are under arrest"

Farida ta yi murmushi ta ce  "mu je ko"

Tasallah da ke chan wajen dining ta fashe da kuka tana faɗin "Alhaji ka yi wani abu dan Allah. Za su tafi da ita"
Ko gizau Najeeb bai yi ba balle ya sa baki.

Maureen na faɗin "evil woman. You'll rot in jail for this"

Haka Farida ta bi bayan su suka fita. Tasallah na ihun matar gidan ne fa mi ta yi.
Ganin ba wannan ba ne zai fishsheta ya sa ta nufi ɗaki ta ɗau wayarta ta kira Mom...

Ganin gidan Najeeb ya ƙara haukata Naomi. Duk ciwon da ta ke ji sai ya zamana ta watsar da shi gefe, babban burinta shi ne yadda za ta mallaki wannan gida ita kaɗai...

...........................

Tun kan su isa police station ɗin Daddy ya fara kiraye-kirayen waya. Su na zuwa ma ba wani dogon bayani kawai sake Farida aka yi. Domin Comissioner of police ne ya kira ya ce a saketa.
Abinda ya ƙara sa Daddy ya tsorata da lamarin shine jin cewa Najeeb ne ya zo ya bada report sannan ya ce a arresting Farida. Gaskiya Najeeb yana buƙatar addu'a.
Farida kam har su ka iso gida ba ta ce ƙala ba. Mom ce ma ke ta aikin ba ta haƙuri.
Daddy ya ce wa Mom gobe Tasallah ta kwasowa Farida kayanta. Daga yanzu a nan za ta dinga kwana tunda abin ya kai ga haka kar su wayi gari Najeeb ya kashe Farida.

Farida sai da ta shiga tsohon ɗakin su sannan ta fashe da kuka. Tun ɗazu ma tanajin kukan, kawai ta daure ne saboda su Mom. Wai ita ce yau Najeeb da kan shi ya ke kawo ma ta police har gida.
Najeeb ɗin da lokacin da Sabreen ta sa aka kamata haka hankalin sa ya tashi ya zo police station yana masifa kaman zararre. Ta tuna first kiss ɗin su a ranan. Shi ne yau Najeeb ke gani ana tafiya da ita amma ko ajikin sa, kai duniya!...

..........................

Washegari kamar yadda Daddy ya ce haka Tasallah ta ɗebo wa Farida wa su daga cikin kayan ta. Daddy ya ce ta fita hanyar Najeeb kar ya illata ta tun da abin ya kai ga haka.

Addu'a aka ci gaba da yiwa Najeeb dan addu'ar ce kaɗai garesu. Tasallah ba ta fasa sawa Najeeb ruwan zamzam a abinci ba kaman yadda Farida ta buƙata...

A ɓangaren Naomi duk faɗa da wani masifa da Mrs Comfort ke yi ba wanda ya shigeta. Tun da su ka shiga ɗaki ita da Maureen su ka fara shirya yadda za su kawo ƙarshen Farida saboda ma kar a samu matsala a gaba...

Bayan kwana biyu

Maureen da Naomi su ka sake duƙufa gaban Boka Ifagbemi.
Lokacin da Naomi ta gama kwararo buƙatunta Boka ya kece da mahaukaciyar dariya. Sai da yai mai isar sa sannan ya ce "a kasheta? Ko kin manta annurin matar sa ya ke gani a idon ki, ko kin manta duk ranan da Matar sa ta mutu zai dena miki kallon so?"

"To Baba ya za ayi tunda idan aka kasheta maganin zai warware?"

Boka ya fara buga ƙirji yana surkulle sannan ya ɗago ya kalli Naomi ya ce "akwai abinda za a yi amma da ɗan wahala"

Naomi ta ce ko minene za ta yi.

Boka ya miƙa ma ta wani ƙaramin ƙwarya ya ce " ki samu gashinta ko farcenta ki sa a cikin wannan ƙwarya sai ki rufe. Da ƙarfe ɗayan dare ki toni rami ki sa wannan ƙwaryan a ciki sai ki saka saurayin kare wanda bai taɓa hawa mace ba akan ƙwaryan ki bisine tare. Yadda karen nan ya danne ƙwaryan nan haka za ta ƙarasa rayuwarta a kwance ba za ta taɓa tashi ba har sai idan wani ne ya tone ramin ya ɗaga karen daga kan ƙwaryan shi ne za ta tashi"

"Baba taya za mu gane saurayin kare da be taɓa hawa mace ba?" Naomi ta faɗa cike da fargaba.
Boka ya kwashe da dariya...

Sai da ya gama mu su bayani ya ce " ikilo pataki. Kar ki yarda wani mutum ya gan ki lokacin da ki ke businewa"

Naomi da Maureen su ka haɗa kai wajen cewa wannan mai sauƙi ne...

..........................

Bayan sun dawo Kano tunanin samun gashin Farida ko farcenta ya sa su ka shiga ruɗani dan da sun ɗau abin da sauƙi. Daga baya Maureen ta ba ta shawara akan su je gidan ko za su samu. Hakan kuwa aka yi. Naomi ta tambayi Najeeb ya kai ta gidan shi. Ba tareda ya musa ba ya amsa ma ta.
Suna zuwa ɗakin Farida ta ce ya kaita. Tasallah ganin tare su ke da Najeeb ya sa ba ta iya hana Naomi ba...

Su na zuwa wajen dressing mirror ɗin ɗakin ta je tana dube-dube. Ta jima tana dubawa ko za ta ga gashin Farida ko da tsilli ɗaya ne amma ba ta gani ba. Har za ta tafi ta lura da wani baƙin Comb da ke wajen da kyau ta ga akwai tsillin gashi guda biyu a jiki ta yi murmushi ta cire su...

Bayan kwana ɗaya...

Tun da yamma ta je bayan gidan su ta tone shi da ɗan zurfi. Ta sa kwali da buhu ta rufe wajen.

Ƙarfe ɗaya saura ta ɗau ƙwaryan da Boka ya bata ta fita.  Karen da ta siyo na kwance a wani keji gefen ramin da ta tona. Dama tun da yamma ta ma sa alluran bacci saboda Boka ya ce ba matacce za ta sa ba.

Lokacin da ta sa ƙwaryan a cikin ramin dai-dai agogon hannun ta ya cika ƙarfe ɗaya na dare.  Ta cicciɓi karen za ta sa a cikin ramin  aka dallota da torchlight.

"Anty Naomi what are you doing there?" Muryan ƙaninta Abel ya doki kunnen ta....Skt 55

Naomi ta ɗago ido ta kalli Abel da ke nufo wajenta. Lokaci guda ta ji wani abu ya shiga kunnen ta, ta fara girgiza kai da sauri-sauri.

"Anty Naomi..." kafin ya ƙarasa maganar sa Naomi ta cilla ma sa Karen da ke hannun ta, ya goce da sauri har torchlight ɗin hannun sa sai da ta faɗi.

"Yirrrrrrrrrr, Ah Ah Ah, Chinkokoko kokokokoko Chichichichi..."  waƙar da Naomi ta fara kenan tanayi tana rawa.

Abel ya tsaya yana kallon ta tareda kiran sunanta amma sam ba ta san yana yi ba sai tiƙar rawa ta ke yi, tana yi tana dariya.
Ganin fa ba dena rawar za ta yi ba, ya je ya kamota da ƙarfi yana faɗin "stop this nonsense please"
Naomi ta yi wani kuka sannan ta wancakalar da Abel ta baya ya faɗi ƙasa yana haki, "i'm coming oo i'm coming oo" abinda ta ke faɗi kenan kafin ta ranta a guje. Shi kuwa Abel ya fara ƙwala wa Maman su kira...

Ƙarfe ɗaya saura na dare ta tashi fitsari. Ganin idan ta koma bacci za ta iya kasa tashi ƙarfe biyu kamar yadda ta saba ya sa ta yi alwala kawai ta fara sallah.  Ba ta kwanta ba sai ƙarfe uku da rabi bayan da ta ji ƙafafuwanta sun ma ta nauyi...

....................................

Karfe biyar alarm ɗin ɗakin ya fara bugawa. Ya sa hannu ya laluba agogon ya kashe alarm ɗin. Idon sa a rufe ya fara jawo pillow jikin sa saboda yadda ya ke jin daɗin baccin. Daga saman pillow har ƙasansa ya shafa kafin ya ankara pillow ya rungume ba matar sa. Ya sa hannu ya fara laluba gadon ba tareda ya buɗe ido ba. Sai da ya ga hannunsa ya kai ƙarshen gado bai ji laushin mutum ba, sannan yai saurin buɗe idon sa tareda kai hannun sa wajen switch ɗin wuta ya kunna shi. Ɗakin ya ƙaraɗe da haske, yadda hannun sa ya lalubo ma sa babu hakanan idon sa ya gano ma sa babu.  Tunanin sa banɗaki ta shiga dan haka yai murmushi haɗe da miƙa yana addu'ar tashi daga bacci a zuciyar sa.
Ya ziraro dogin ƙafafuwan sa ƙasa hannun sa akan idanun sa yana murza su saboda nauyi da su ka ma sa. Sai da yai minti biyu zaune kafin ya miƙe tsaye ya fara ƙoƙarin cire kayan baccin sa...
Lokacin da ya shiga banɗakin ma dai wayam ne ba kowa a ciki. Ya girgiza kai yana sawa a ransa ƙila ta je cin abinci ne dan 'yan kwanakin nan har dare ta kan tashi ta ce yunwa, ta je ta yi girki ta ci.
Akwai ranan da ƙarfe ukun dare ta tashi ta je ta fara wanke wake wai ƙosai za ta ci. Ƙosan ma na manja irin wanda maƙociyar su Iya Abosede ta ke yi a Jos.

Cikin bacci ya farka da niyyar su yi abubuwa saboda kafin su kwanta ba su yi komai ba saboda ciwon kai da ya takura shi, ya ga gadon wayam. Ƙarshe a kitchen ya samu matar sa tana ta faman wanke wake.
Sai da ya tsaya a bakin kitchen ɗin ya ƙare ma ta kallo kafin ya ƙaraso wajen ta.

"My love mi ki ke yi da daren nan please?" Ya faɗa yana rungumeta ta baya.

"Ƙosan manja na ke son ci shine na ce barin zo na haɗa shi da sauri"

"Queen ki bari da safe sai ki yi mana, kin san ƙarfe nawa yanzu?"

" kar ka damu yanzu zan haɗa, na ma gama wanke waken saura marƙaɗe"

Ya sani ba haƙura za ta yi ba dole haka ya tsaya kusa da ita har ta markaɗa waken a blender ta zo ta soya ƙosan cikin manja. Duka duka ƙosan ma guda shida ne wanda ta yi su manya.

A kitchen ɗin ta zauna ta fara ci, tana ci yana kallon ta. Lokacin da ba ta da ciki ma ya aka ƙare da ciye-ciye balle yanzu da abun nema ya samu.

"My Champ ka taɓa ka ji, yai daɗi sosai Wallahi"

Ya girgiza kai ya ce " ƙosan mangyaɗa ma bana ci balle na manja. Ki ci da kyau Maman princess"

Tana ci tana lashe manjan da ke yatsunta.
"Ka san da yanzu na yi da niƙaƙƙen waƙe da ba zai taɓa yin daɗi kamar wannan ba. Amma this one is fresh and yummy"

Gyaɗa kai kawai ya ke dan ba wai yana gane maganganun ta ba ne. Haka ya tsaya har ta take ƙosan nan gaba ɗaya...

Yai wanka ya ɗauro alwala ya fito, ya sa jallabiyar sa ya sauko ƙasa ganin har lokacin ba ta ɗakin. Duhun da kitchen ɗin ya ma sa ne ya tabbatar da babu mutum a ciki, amma duk da haka sai da ya kunna wutan kitchen ɗin, still ba kowa. Ya kashe wutan ya fita yana sawa a ransa tana ɗakin ta ne. Ya wuce masallaci dan gabatar da sallar Asuba.

Bayan an idar da sallah ya tsaya ya ɗan yi azkar sannan ya fito. Musabaha su ka yi da Alhaji Abubakar maƙocin sa inda Alhajin ke tambayar ko ya yi tafiya ne kwana biyu baya ganin yana fitowa asuba.
Najeeb ya girgiza kai tareda ƙoƙarin nemo dalilin da zai sa ba zai fito sallan Asuba ba bayan yana gida. Dalili biyu ne za su iya sawa, ko dai ya makara bai tashi ba ko kuma ana ruwa. To duk babu ko ɗaya aciki domin zai iya cewa tun da su ka dawo anguwar indai yana gida to baya fashin fita sallar Asuba, hakanan ko ruwan farko ba a fara a garin ba balle ya ce ruwan sama ne.
Bai ma san lokacin da Alhaji Abubakar ya tafi ba saboda nisan tunani da yai.
Yana tafiya abubuwa da dama na ma sa yawo a kwanyar sa.
"Its not possible" ya faɗa da ƙarfi lokacin da kwakwalwarsa ta tuno ma sa da mafi yawancin abubuwan da su ka faru cikin abinda bai wuce sati biyu ba.

Yana shiga gidan ya fara kiran sunan ta da ƙarfi.

"Alhaji Barka da Asuba" Tasallah ta faɗa wanda fitowanta kenan daga ɗaki za ta je ta fara haɗa ma sa breakfast saboda fitar sassafiya da ya ke yi.

"Ina Aysherh?" Ya faɗa da muryan da ta ke tattare da damuwa. Ba abinda idon sa ke gani kamar Aysherh a tsugunne gaban sa tana kuka.

"Alhaji ba kai ka sa folisawa su ka zo su ka tafi da ita ba kwanaki"

Yadda ka san guduma aka kwaɗa ma sa a kai haka ya ji saukar maganar Tasallah.

Maganar da ta yi ya sa ya tuno abinda ya faru ranan. Numfashin sa ne ya fara ɗaukewa ga wani duhu-duhu da ya ke gani. Ya fara ƙoƙarin dafa bango saboda kar ya faɗi amma bangon ya ma sa nisa, ƙarshe dai da shi da hannun duk ƙasa su ka yi. Tasallah ta fara Salati tana kiran Alhaji.
Dafe ƙirjin sa yai saboda zafi, ga uwa uba kan sa da ke sarawa.
Idon sa a buɗe ya ke amma baya ganin komai sai duhu.

Salatin da Tasallah ke yi ya sa shi ya fara maimaita kalmar Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun. Ya jima yana maimaita kalmar  kafin ya fara jin sauƙin ƙuncin da ya ke ciki.  Tashi yai a hankali ya rasa ma ina zai je waje zai fita ko sama zai haura.

"Aysherh Aysherh Ay..." bai ƙarasa na ukun ba ya faɗi ƙasa yigif...

............................

Bayan ta yi sallar Asuba sai da ta jima tana addu'o'i kafin ta ɗauko Ƙur'ani ta fara karantawa. Kusan ƙarfe takwas sannan ta ajiye ƙur'anin ta yi addu'a ta naɗe sallayar. Sai da ta je ta yi fitsari kafin ta zo ta kwanta tunda ba abinda za ta yi kuma ba yunwa ta ke ji ba. Tana kwance ne dai amma baccin ya ƙi zuwa, kewar mijinta ta ke yi sosai.  Ba ta san yaushe wannan abu zai zo ƙarshe ba amma ta sani duk min daren daɗewa za a sami nasara tunda Allah su ka riƙe shi kaɗai. Ba dan kisa babban laifi ba ne da ba abinda zai hana ta je ta shaƙe wuyan Naomi har sai ta mutu.
Ta ƙara lissafta kwanakin da ta yi ba tareda zaman lafiya da mijinta ba. Kwanaki goma shauku ne rus yau ne ma cikon na sha ukun. Tunda ta dawo gidan Daddy kuwa ko zuwa bai yi ba balle kuma kira. Mafiya yawan lokuta takan wuni da waya a hannu ko za ta ga kiran shi ko text amma shiru. Dama tun ranan da ya faɗawa Daddy zai auri Naomi da su ka yi baran-baran har yau baya zuwa gidan.
Tana cikin wannan tunanin Aka fara buga ƙofar ta.
Yes ta faɗi tana miƙewa dan ta buɗe ƙofar.
Lokacin da ta buɗe ƙofar kafin ma ta ce ƙala Mom ta rungumeta tana faɗin "Alhamdulillah Allah ya amsa roƙon mu"

Ba ta fahimci mi Mom ke nufi ba ko kuma dai ta fahimta ba ta gaskata hakan ba ne kawai.

"Ɗazu Tasallah ta kirani wai Son ya faɗi, dreba ya wuce da shi asibiti. Ni da Daddy mu ka fita ɗazu mu ka je asibitin. He's back Ayshah. Mijin ki na neman ki, he wants to see you"

Tabbas ɗazu da tana azkar ta ji fitan su Mom amma ba ta kawo aranta wannan ne dalilin ba.

Hawayen daɗi ne su ka fara sauko ma ta, Mom ta sa hannu tana goge ma ta su tana faɗin " ba kuka za ki yi ba, farinciki za ki yi Ayshah. Allah ya dube mu da rahama. Wassu su kan shiga wannan yanayi su jima a ciki, a ɗau watanni ko shekaru ana ta roƙon Allah kafin daga baya a samu sauƙi amma mu Allah ya mana gata cikin ƙanƙanin lokaci ya bawa Najeeb lafiya"

"Alhamdulillah, Alhamdulillah" Farida ta faɗi tana murmushi.Skt 56

Lokacin da su ka shiga ɗakin yana kwance yana bacci an ɗaura ma sa ledar ruwa. Daddy ke gefen sa yana kallon ɗan na sa yadda abubuwa da dama su ka dinga faruwa da shi a rayuwar sa. Kowa da tashi ƙaddarar, shi kam Daddy bai fuskan ci irin waɗannan ƙalu bale ba kamar na ɗan na sa.  Tunda ya mallaki hankalin sa, idan ka cire mutuwar Aisha baya tunanin akwai lokacin da ya shiga yanayi na ƙunci sai a kan Najeeb. Shi ne yai rayuwar kaɗaici shekara takwas saboda ya rasa Sabreen, shi ne aka kidnapping, shi ne yai accident yai kusan wata tara kwance a asibiti shi ne ya ɗau watanni kafin ya dawo dai-dai, shine kuma mace ta ma sa asiri har ya ke ƙyashin matar da ya ke mutuwar so. Kai Alhamdulillah, dama dole ne mutum ya fuskanci jarrabawa a rayuwar sa.
Yai wa ɗan na sa addu'ar Allah ya sa ya ci dukkan jarrabawar sa ta duniya.

Mom ta ce " ya yi bacci ne?"
Daddy ya ce " Likita ne ya ma sa allurar bacci saboda ya samu ya huta"

Farida ta gai da Daddy tareda ma sa ya mai jiki. Daddy ya amsa da cewa "Aishah kin ga al'amari na Ubangiji ko. Allah ya share ma na kukan mu, sai mu dage da addu'a kuma, kar mu taɓa sakaci da addu'a"

Farida ta amsa da Insha Allahu. Kallon Najeeb ta ke tundaga gashin kan sa har tafin ƙafar sa. Ya mata kyau sosai amma kuma ya rame...

Najeeb bai farfaɗo ba sai kusan ƙarfe ɗaya na rana. Yana buɗe ido ya ga matar sa zaune. Kamar wadda aka tsikara haka ya tashi zaune da sauri. Ganin ta haɗa rai lokacin da su ka haɗa ido ya sa ya tashi tsaye ya iso wajenta. Tana zaune akan kujera ko gizau ba ta yi ba balle ta tashi sai ma juyar da kai da ta yi.
Tsugunnawa yai a gabanta yana kallon gefen fiskarta.

"Na sani abinda na yi is unforgivable. Na sani kina da hujjar da za ki yi fushi da ni. Amma Dan Allah my Queen ki yafe min, I love you, only you"

Juyowa ta yi ta kalli ƙwayar idon sa wanda ke nuna tsananin so da begen ta. Ba abinda ta tuna irin yadda ta tsugunna gaban sa tana hawaye tana roƙon sa amma yai watsi da ita.


"I forgive you"  ta faɗa a hankali. Ya taso da sauri zai kissing ɗin ta ta sa hannu ta tare bakin sa ta ce " i forgive you amma kuma..."

..........................

Kafin a samu a kamo Naomi sai washe gari a chan wani bola tana kwance duk kayan jikinta a yayyage. Kai tsaye gidan Pastor Chukudi aka wuce da ita, wanda ya ke shine pastor ɗin church ɗin da su ke zuwa. Maureen ce ta faɗi silar haukan Naomi shiyasa aka wuce da ita gidan Pastor ɗin. Ita kan ta Maureen ta tsorata da yadda ta ga haukar ƙawar na ta, acewarta su koma wajen Ifagbemi ya basu magani amma Mrs Comfort ta ce ba za su aikata saɓo biyu ba. Ga saɓon zuwa wajen Boka dan asiri ga saɓon neman magani a wajen boka. Ita ta yarda Jesus zai warkar da 'yarta.

Annointed water da oil kam Naomi ta sha su kamar ba gobe amma shiru ka ke ji kaman an suka dusa. Ba sauƙi balle ayi tunanin za ta warke. Da dare Pastor Chukudi da tawagar su su wuni akan Naomi suna ma ta holighost fire amma su na yi tana ƙara rikice mu su...

.......................

Cikin kwana biyu Najeeb ya fita hayyacin sa. Farida ta ƙi dawowa. Ta ce ta yafe ma sa amma ya bata lokaci ta yi tunani. Mom ma ta goya ma ta baya akan ya barta ta huta.

Yau ma dai gidan ya zo roƙo amma ba ta nan, Adama ta ce sun fita da Sabreen.

Ya zauna a falo yana jiran dawowar su duk da kuwa Adaman ta ce ba su jima da fita ba.
A falon Daddy ya dawo ya sameshi lokacin har ya fara bacci. Jin takun mutum ya sa ya farka.
Gaishe da Daddyn yai yana faɗin yana son magana da shi. Daddy ya ce ya biyo shi. A falon Daddy su ka ya da zango inda Daddy ke tambayar ko lafiya.

"Dad ka sa baki dan Allah. Ta ce wai sai ta haihu kafin ta dawo. 3 months yai yawa, ba zan iya jure rashin ta ba"

Daddy yai murmushi ya ce " so ka ke na sa ta tayi abinda ba ta so?"

"No Dad amma idan ka ma ta magana wallahi ba za ta ƙi maganar ka ba"

" Son kenan, wannan tsakanin ka da iyalin ka ne ba ni da wani hurumi a ciki. Ka bata lokaci kaɗan za ta sauko, she went through alot saboda kai dan haka ka bi ta a hankali"

Najeeb ya haɗa rai dan bai ji daɗin maganar Dad ba, maimakon ya supporting ɗin sa sai ya ke maganar wai ya amince da hukuncin da ta yanke...

Lokacin da su ka dawo ma haka ta wuce shi, yana magana ko uhum ba ta ce ma sa ba ta haura sama.

"Sabreen please help me talk to her"  ya faɗa yana haɗa hannu.

Kaman Daddy itama cewa ta yi ya ba wa Farida lokaci.

Ɗakin su ya wuce ko zai samu daman magana da ita amma ya samu ta kulle ɗakin.

"My Queen please ki bari na ganki ko na minti ɗaya ne"

Tana zaune akan gado tana jin magiyar sa amma ko ajikinta duk da chan ƙasan ranta tana son kasancewa da shi amma ba za ta janye ƙudirinta na son horashi kaɗan ba. Haka ya gama magiyar sa ya bar wajen....

Bayan kwana biyar da haukar Naomi Pastor ya bada shawaran a je a bawa wanda ta yiwa magani haƙuri saboda idan su ka yafe hakan zai sa Naomi ta samu sauƙi.
Mrs Comfort, Pastor Chukwudi da Saint Janet suka je gidan su Najeeb. Maigadi ne ya sanar da su Farida tana gidan au Najeeb, su ka karɓi address a wajen shi su ka wuce chan...

Mrs Comfort kuka ta dinga yi wiwiwi a gaban su Farida tana roƙon su gafartawa Naomi. Daddy  ya ari bakin Najeeb da Farida ya ce sun yafe, Najeeb ya haɗe rai dan shi plan ɗin shi ma sai Naomi ta je jail.

Pastor ya mu su godiya sannan su ka tafi.  Duk da wannan yafiya da aka yi bai sa Naomi ta warke ba. Kwana biyu da dawowar su daga gidan su Najeeb ta tsere daga gidan Pastor ta shiga gari.  Wasa-wasa aka baza neman ta amma har sati guda ba labarin inda ta ke...

.........................

Shirye-shiryen bikin Sabreen ake yi duk da kuwa Sabreen da Lukman ɗin sun amince akan ba za ayi hidima ba amma Mom da Farida sun ƙi. Wata guda aka saka har yanzu kuma saura sati uku.

Fitowarta kenan daga wanka ta kalleshi zaune akan gado. Mantawa ma ta yi ba tarufe ƙofan ba.
"Ni fa ba na so ana shigo mini ɗaki ba izini"

A hankali ya taso ya zo ya tsugunna gaban ta ya kamo hannunta biyu ya riƙe gam. Kallon sa ta ke yi yadda idon sa yai ja.

"Aysherh I cant, ba zan iya ba. Kafin 3 months ɗin nan zan iya mutuwa idan ba kya tareda ni. Please ki manta da komai ki dawo gida mu cigaba da rayuwar mu. I promised to make it up to you, ba zan sake ɗaukan sakatariya ma ce ba, yalla yarinyace ko tsohuwa. Zan dage da addu'an dare saboda kar wata ta kuma samun galaba a kaina. Zan yi duk abinda ki ka ce amma please come back to me. I love you"
Ya kai hannun ta kan kirjin sa ya ce " My heart beats for you Aysherh, only for you. Ki taimakeni ki taimaki zuciyata kar rashin ki kusa da ni ya min illa. Na ɗauka zan iya jurewa amma Wallahi ba zan iya ba, its being 2 weeks amma gani na ke kamar 2 years ne. I miss you Aysherh, I miss us. Please my Queen..."

*team Farida kun karɓi haƙurin Najeeb ko ya?*Skt 57

"Ka yi haƙuri amma ba zan koma yanzu ba" ta faɗa a hankali duk da kuwa maganganun sa sun karya ma ta zuciya.

Ya cize leɓen sa na ƙasa yana huci, bayan 'yan daƙiƙai ya miƙe tsaye ya ce "tunda abinda ki ke so kenan zan jira ki"...

Ba ta iya ɗaga ido akan sa ba har ya fita daga ɗakin.
Anya ta ma sa adalci kuwa? Ta tambayi kan ta. Sai dai kuma ta rasa gane amsar da za ta bawa kan ta...

Yinin ranan sai sintiri ta ke tsakanin falo da ɗaki amma Najeeb bai dawo ba. Washe gari ma bai zo gidan ba...

Su uku ne a dining su na cin breakfast lokacin da Najeeb ya shigo. Kwana biyu kenan bai zo gidan ba.
Wajen Mom ya je ya gaisheta, ta shafa gashin sa tareda ma sa peck a goshi.

Ya duba Sabreen ya ce "amarya ya shirye-shirye"

Sabreen ta yi murmushi ta ce "shiri ai sai su Mom da Ayshah, su ke ta komai"

"Allah ya kaimu lokacin"

Mom ta amsa da amin yayinda Sabreen ta sunkuyar da kai tana murmushi.

"Zan wuce Abuja, i'll be there for two days"

Mom da Sabreen su ka ma sa addu'ar Allah ya kiyaye.
Farida tunda ya zo ta ke binsa da ido amma bai ko kalli wajen da ta ke ba.

Ganin ya juya zai tafi ya sa ta yi saurin sake mug ɗin tea da ta riƙe, Mug ɗin ya faɗi kan tile ya ɗan fashe.

"Ouch...Ouch ... Wayyo zafi..." Farida ta faɗa saboda tea ɗin ya ɗan fetsu ma ta.

"Sannu Ayshah, sannu, ba ki ji ciwo ba ko?" Mom ta faɗi tana ƙoƙarin riƙe hannun Farida.
Farida kam idon ta na kan Najeeb wanda ta ke tunanin zai zo da gudu ya dubata. Sai taga saɓanin haka tsayawa kawai yana kallon ta.

Ɗan gyaran murya yai ya ce " na tafi"

Farida na jin haka ta fashe da kuka.
Sabreen mi za ta yi banda dariya. Mom ma dariyan ta ke son yi amma ta gimtse.

Har ya fita Farida bata dena kuka ba. Sabreen ta ce  "someone is missing her husband"

Farida ta kalleta ta galla ma ta harara. Mom kam yi ta yi kaman ba ta san sunayi ba, Adama ma ta kira akan ta zo ta tattare wajen da Mug ɗin ya fashe...

Ƙarshe haushi ya sa Farida tashi daga wajen ba tareda ta gama cin abincin ba...

...........................

Tana jiran kiran sa ko text amma shiru. Baƙin ciki ya tokare ma ta maƙoshi, kowa ma haushin sa ta fara ji a gidan. Sabreen kuwa indai su ka haɗu sai ta tsokaneta akan Najeeb.

Ranan da zai dawo ta samu Mom a ɗakin ta da su ka gaisa ta ce "Mom zan je na ɗau wassu kaya a chan gida"

Mom ta yi murmushi dan ta gano Ayshah na son komawa gidan ta ne. Ta ce " 'yata ni inaga horon ya isa haka, Son zai cutu idan ki ka cigaba da zama a nan"

"Amma Mom..."

Mom ta katseta da cewa "ki yi haƙuri ki koma kin ji"

Farida ta yi ajiyar zuciya ta ce "shikenan zan koma saboda ke"

Mom ta ce na gode. Sai da Farida ta fita sannan Mom ta yi murmushin manya...

Farida ta kira Adama ta tayata haɗa kaya, da su ka gama ta kai ma ta su cikin mota. Da ta shirya ta je ta yiwa Mom sallama sannan ta shiga ɗakin Sabreen. Waya su ke da Lukman lokacin da ta shigo, tana kallon ta da jaka ta sa dariya har da hawaye.

"Ni ba na son gulma, Mom ce ta ce na koma" Farida ta faɗa tana haɗa rai.

Sabreen ta ce " to Allah ya kiyaye hanya sai mun zo karɓan tsaraba"...

Saloon ta fara wucewa aka ma ta gyaran gashi da lalle sannan ta wuce gida. Ko'ina na nan tsaf-tsaf saboda Tasallah ba ta wasa da gyaran gidan.

Lokacin da ta shiga ɗaki wanka ta yi ta feshe jikin ta da turaruka.
Ƙarfe biyar na yamma Abdullahi ya faɗa ma ta zai je ya ɗauko Najeeb a airport yanzu kuma ƙarfe huɗu da kwata.
Gyara ɗakinta ta yi kafin ta wuce na shi ɗakin. Yana nan a gyare amma sai da ta cire zanin gado ta sake sa wani sannan ta shiga banɗaki dan ta wanke...


Tun ƙarfe biyar da kwata ta ke tsaye jikin balcony  na falon sama tana jiran dawowarshi amma Abdullahi bai shigo gidan ba sai ƙarfe shida saura minti goma. Tana ganin ya fito daga motan ta yi saurin barin wajen. Ɗakin sa ta shiga ta fara gyara arrangement na turaruka da mayukan sa...

Ta ji shigowar sa amma ta dake ba ta kulashi ba ta cigaba da gyaran har da faɗin " duk an bar ɗaki a hargitse. Komai gashi nan ba tsari kaman ba mutum ke kwana a ɗakin ba"

Yana tsaye yana kallon ta bai ce komai ba duk da kuwa farin cikin da ya mamaye zuciyar sa.

Ya ajiye jakar sa ya shige banɗaki ba tareda ya ce ƙala ba. Tana binsa da wutsiyar ido har ya shige banɗaki.

Ta ɗan yi ƙaramar tsaki  ta ce " koma ya nuna ya gannin nan"
Ta zauna bakin gado tana jiran sa. Ya jima a banɗakin kafin ya fito sanye da bathrobe fari.

"Ni fa kar mutum ya ga na zo ya nemi yi min walaƙanci Mom ce ta ce na zo."

Shiru Najeeb bai ce komai ba. Ta ɗaga ido ta kalleshi yana tsaye gaban mirror yana shafa jikin sa da mai.

"Allah na gani sai na tafi tunda ba a son ganina, dama ba wai da son rai na na zo ba"

Najeeb ya ajiye man da ke hannun sa ya je ya buɗe ƙofar ɗakin ya ce " a gaida Mom da su Sabreen. Allah ya kiyaye hanya"

"Kuturun Uban chan. Au'uzubillahi har ka sa ina zagi"
Ta tashi fuuuu ta ce " zan tafi ɗin koma ba za ka sake ganina ba"

Sai da ta zo shigewa ta ƙofan ya riƙe hannun ta.

"Ni ka sake ni in tafi, ka sake ni na ce"

Ya jawota jikin sa yana kallon ƙwayar idon ta. Itama ɗin kallon sa ta ke ƙirjin ta na bugawa da sauri-sauri ba abinda jikinta ke muradi irin tajita kwance kan faffaɗan ƙirjin sa.

"My stubborn Mrs Jibo. Na san duk maganan nan cika baki ne kawai, you miss me, i see it in your eyes"

"Ba wani. Ni dama taimakon ka zan yi tunda Mom Allah Annabi ta roƙeni akan na dawo"

"Oh really?" Ya faɗa tareda sunkuyo da kan sa, ganin yana matso da bakin sa kusa da nata bakin ya sa ta lumshe ido tana jiran haɗuwar bakin su.

Maimakon kiss a baki sai ya kissing kumatun ta. Ta buɗe ido a hankali gaba ɗaya ta yi laushi saboda wani mugun sha'awar sa da ke taso ma ta.

Murmushi ya ma ta ya sake matsowa da bakin sa wannan karan kam tuni ta yi saurin matsawa da nata bakin, bakin su ya haɗe waje guda...
Sun jima suna aikawa junan su hot kiss kafin ya jawota zuwa kan gadon. . Wata ɗaya da 'yan kwanaki rabonta da shi, ba ƙaramin missing ɗin sa ta yi ba. Yadda ya ke sarrafata haka itama ke mayar ma sa da martani, sun jima su na gogar junan su saboda an jima ba a gamu ba...

Bayan komai ya kankama da su ka yi wanka Najeeb ya ce " ki shirya na maida ki wajen Mom na haƙura ki huta a chan"
Duka ta kai ma sa ya goce yana dariya...

..........................

Rayuwan masoyan gwanin sha'awa, kullum su na manne da juna. Duk dare sai sun tashi sun gudanar da sallah sun roƙawa junan su addu'an samun zaman lafiya da kuma samun 'ya'ya ma su albarka. Duk Jumu'ah Farida ba ta fasa yin sadaka ba...

Ranan Asabat aka ɗaura auren Sabreen da Lukman. Daddy ne ya zama alwalin Sabreen  'yan uwanta sun zo ba laifi, wannan karan har mahaifiyarta sai da ta zo. Anyi walima kuma anyi family dinner a gida. Washe gari Sunday kuma aka wuce da Sabreen Abuja. Farida ta so zuwa amma Najeeb ya hana saboda yanzu ta yi nauyi.

Duk cikin 'yan uwanta babu wanda ya nuna damuwar sa da asalin Lukman, su daɗin su ne ma Allah ya shirya mu su Sabreen har kuma ta yi aure hankali kwance...

.......................

Wanda su ka kawo Sabreen mutum huɗu ne Mom ce da Najdah sai Aunt Mouna da wata cousin ɗin Sabreen ɗin Nihaya. Ba su fi awa biyu a gidan ba suka koma bayan sun yiwa Sabreen 'yan nasihohi.

Ƙarfe biyar Lukman ya shigo gidan na su. Cike da farin ciki, finally shima ya zama ango...

Ƙarfe takwas saura su ka gabatar da sallan Isha tareda sallar godiya sannan Lukman ya gabatar ma ta da kazarta. Tare su ka ci kazar su ka ƙoshi sannan Lukman ya tattare wajen...

Kunyar Lukman ta ke ji, ta sani ita ba irin matar da ta dace da Lukman ba ne. Ya fi ta daraja da kima duk da kuwa ta fishi asali.

"Ka yi haƙuri ba nida abin da kowane ango ke farin cikin samu a rana irin ta yau. Na yi rayuwa marar daɗi a baya, na zubda mutuncina a idon duniya, na ɗauka rayuwa mai kyau na ke yi, rayuwa ta 'yan ci da jin daɗi amma a gaskiya rayuwar ƙunci na yi a baya. Ka yi haƙuri dan Allah. Ina godiya da Allah ya bani kai. Ba ka dubi yawan shekaruna ba, ba ka dubi rayuwar bariki da na yi a baya ba amma ka amince da ni ka amince na zamo sashen rayuwar ka. Thank you Lukman"

"Shhhhhh" ya faɗi tareda haɗe bakin su...

Sabreen ta sha gyara sosai, duk da ta saba amma Lukman ya bata mamaki saboda yadda ya birkitata da salon sa takejin ba ta taɓa tarayya da wani da yai kusan sa a iya sarrafa mace ba....Skt 58

*ina roƙon duk wanda ya karanta wannan shafin yai wa Mijin Maman Durratu addu'a, Allah ya jiƙan sa da rahama, ya haskaka ƙabarin sa, ya gafarta ma sa ya kuma bawa iyalen sa haƙuri da juriyan rashin sa, Amin.  Wanda su ka rigamu gidan gaskiya Allah ya jiƙan su da rahama, muma idan tamu ta zo Allah ya sa mu cika da imani amin*

Yau tun safe ta ke jin ta ba dai-dai ba. Ta dai daure ta cigaba da ayyukan da ta saba. Yana fitowa daga wanka ta riga ta cire ma sa kayan da zai sa. Ita ta shafa ma sa mai sannan ta taimaka ma sa ya shirya. Tana gyara mi shi tie ɗin ya ce "my Queen lafiya? You look dull this morning"

"Just ƙafafuwa na ke ciwo" ta faɗa dan kawai kar ta tada ma sa hankali

"Ko za mu je ki ga likita?"

"No, zai yi sauƙi zuwa anjima"
Ta ɗan bugi ƙirjin sa kaɗan ta  ce " mijina ka ga yadda ka yi kyau. Dan Allah ban da dogon hira da mata, banda lumshe mu su ido, ban da yi mu su murmushi,  ka ji nawan"

Ya ɗan ja kumatunta ya ce "na ji your highness zan kiyaye duk abinda ki ka ce"  light kiss ya manna ma ta a baki kafin ya ja hannunta su ka bar ɗakin...

Tafiyar Najeeb office da awa uku Farida ta fara naƙuda. Ɗanliti sabon dreban ta ya wuce da su asibiti. Tun a hanya Tasallah ta kira Mom ta gaya ma ta.  Su na zuwa asibitin ko minti arba'in ba ta cika ba ta haihu.
Abin ya zo ma ta da sauƙi gaskiya, kuma Alhamdulillah ba wata matsala...

Tana kwance an kaita ɗakin hutu Mom na gefe tana kallon jaririn mai kama da uban sa. Cikin zuciyarta ta ke godiya wa Ubangiji da ya sa ta ga ɗan Najeeb.
Mom ta miƙawa Farida jaririn tana faɗin "he look just like his father"

Farida tana kallon jaririn tana godiya bisa wannan ni'ima da Allah ya ma ta...

Bayan minti talatin da haihuwar kafin Najeeb ya iso asibitin. He cant believe it sai da ya ga jaririn, Mom ce ta kirashi ta ma sa albishir da haihuwan. Bai kawo haihuwa ba tunda ya bar Farida lafiya gashi kuma EDD ɗin ta saura kwana shida. Sai dai al'amari na Allah yafi gaban kowa.

Ya ɗau yaron yana murmushi tareda kissing goshin yaron. Alhamdulillah ya ke ta maimaitawa a fili, bakin sa ya ƙi rufuwa saboda farin ciki.

Ƙarfe huɗu da rabi aka sallame su daga asibitin su ka dawo gida. Kafin dare gidan na su ya cika da Jama'a. Kowa na zuwa ganin babyn Farida.

................................

Gidajen biyu sun kasance cikin farinciki bisa wannan ƙaruwa da aka samu. Da farko Mom ta so Farida ta dawo wajenta amma gogan sam bai ba da dama ba.

Mom za ta je gidan su tun safe sai dare ta tafi. Ita ke yiwa Farida wanka. Ummi ma kullum sai ta zo duba Farida da jikar ta.

Kafin ranan suna gidan an cika shi da tarkacen yara. Wassu abin ma jaririn kafin ya iya amfani da su sai ya shekara uku amma an siye su tun yanzu.

Ranan suna yaro ya ci sunan *Muhammad Yaman*
(Finally Farida an zama Umm Muhammad🤓)

Mutane ba kaɗan ba su ka halarci waliman wannan suna, tun daga mutanen Gombe zuwa na Wase da Jos kowa ya karkaɗe jiki ya zo. Sabreen da Lukman ma saura kwana ɗaya suna su ka dira a Kano. Yaro ya samu kyaututtuka ba adadi.
Sorveniers sa aka raba ba za su irgu ba. Saboda gudun evil eye, sunan yaro kawai aka sa babu hoto. Washe gari aka yi abincin sadaka aka kai Iskalin Almajirai sunfi ishirin...

Rayuwa ta cigaba da tafiya hakanan soyayyar Najeeb da Farida tana tafiya gwanin sha'awa. Baby Yaman ba ƙaramin gata ya ke gani a wajen iyayen sa ba, ga uwa uba kakannin sa. Kowa son ɗaukan sa ya ke idan aka fita da shi, amma miskilin yaro ba kowa ya ke yarda ya ɗauke shi ba. Ko Tasallah da ƙyar ya ɗan saba da ita ya dena kuka idan ta ɗauke shi...

Kamfanin Najeeb sai daɗa bunƙasa ta ke yi, yanata samun buɗi ta ko'ina...

Wannan zuwan Farida gida lokacin Yaman yana ɗan wata huɗu ta lura da cikin Ummi. Ko ya akayi ma ba ta lura da shi ba sai yanzu oho dan aƙalla cikin zai kai wata shida.

"Ummi dan Allah ki haifo mace na samu ƙanwa nima"

Ummi ta ma ta daƙuwa, Farida ta sa dariya, dan ta gane Ummi kunyar cikin ta ke ji...

....................

Aneesa da Maijiddah sun saita kan su, sun dena kishin hauka. Aneesa ta yadda duk makaman yaƙinta, sosai ta ke kula da miji da yaranta tunda yanzu ba inda ta ke zuwa. Ciki ma ta ke da shi amma ta kasa sanar da Abdulwahab dan kar yai zaton ƙarya ta ma sa irin wancan karan.

Daren wata Monday AbdulWahab yana ɗakinta ya ke ma ta maganar wani abokinsa da ya buɗe sabon kamfani, yana yi ma sa tayi akan ya bar Aneesa ta jagoranci ɓangaren sales and marketing saboda experience da ta ke da shi.

"Mi ki ka gani?"

"Duk abinda ka ce Sweetheart" ta faɗa tana kai hannunsa daidai cikinta. Jin ɗan tauri-tauri da cikin yai ya sa shi duban Aneesan da kyau yana neman ƙarin bayani. Ta ɗaga ma sa yatsu huɗu tana murmushi.
"Da gaske?"

Ta gyaɗa ma sa kai. Ya jawota jikin sa sosai yana hamdala...

Bisa amincewar AbdulWahab ta fara aiki wanda 8am-2pm za ta dinga yi duk rintsi zuwa uku da rabi ta dawo gida randa ba ta samu traffic sosai ba ma kafin ƙarfe uku ta iso gida.  Cikin be zo ma ta da wani laulayi ba shiyasa ta ke gudanar da lamuranta cikin sauƙi. Ita kuwa Maijiddah sosai Al'amin ɗinta yai wayo, kowa na son yaron a gidan ba ma kamar yayunsa Baby da Alizah, indai su na gida sun dinga faɗa akan sa kenan kowa na son ɗaukan sa...

Bayan wata biyar Aneesa ta haiho yarinyar ta mace. Yadda bata wahala a renon cikin ba sai ya zamana ta wahala wajen haihuwa, dan awa takwas ta yi tana labour ƙarshe sai da aka sa mata ruwan naƙuda kafin haihuwan ya taso gadan-gadan.

Itama wannan jaririyar a Kano aka yi sunanta, yarinyar ta ci suna Khadijah su ka sa ma ta inkiyar Mujahida...

............................

Ummi ma ta haihu namiji amma kwanan sa biyu yaron ya koma. Farida sai da ta yi kuka ranan tamkar ita ta yi haihuwan.
Baffa Musa ma ya ji mutuwar yaron dan yadda ya ke ji da Ummi to haka ya ke jin son abinda za ta haifo ma sa. Sai dai ƙaddara ce da ta riga fata...

Yau Jumma'a da wuri ya dawo daga office. Ɗakinsa ya fara shiga amma ba ta nan. Ya rage kayan jikin sa sannan ya wuce ɗakin ta. Abin mamaki sai ya ganta durƙushe bakin gado tana kuka. Da sauri ya ƙaraso wajenta dan tunanin sa wani abu ne ya samu Yaman.

"My Queen mi ya faru? Ina Yaman?"

Ɗaga hannu ta yi ta nuna wajen gadon yaron. Ya ƙarasa gadon da sauri, ya kalli Yaman na bacci hankalin sa kwance, sai a lokacin ya ji hankalin sa ya kwanta. Ya shafa kan yaron sannan ya koma wajen Farida da ke kuka.

Ya jima yana rarrashin ta kafin ta yi shiru ta miƙa ma sa PT strip ba tareda ta ce ma sa ƙala ba. Bai gane ba ya tambayeta " what is it?"

Ta ɗago jajayen idanun ta ta kalleshi ta ce " i'm pregnant"

Allahu Akbar Najeeb ya faɗa tareda yin sujjada a gefenta. Har ya ɗago ba ta dena kallon sa ba.

"Kai i'm happy Aysherh, kin min komai a rayuwa ban san mi zan miki na saka miki ba"

Hararansa ta yi ta ce "it seems ka manta shayarwa na ke. Yaman is only 7months"

"So?"

"Da ke ba kai za ka yi wahalan ba ai"

Jawota jikinsa yai ya ce " Aysherh aren't you happy, mutane nawa su ke neman haihuwa ido a sama amma Allah bai ba su ba. Amma ke kin samu kina kuka, let me ask you something. Kuɗin kula da su ne ba mu da shi ko kuma me ne?"

Plz manage thisSkt 59

Maimakon ta bashi amsar maganar sa sai ta fashe da kuka. Har cikin ransa ya ke jin haushin kukan ta, dan shi bai ga abin kuka a nan ba.

"Ban yi aure da wuri ba Aysherh, i had my first child at 37yrs. Ina da abokai da 'ya'yan su na fari suke shekara goma, takwas, bakwai. Kai Cousin ɗina Bilyamin da ke Gombe, shekara ɗaya aka haife mu, but his first daughter will be thirteen this year. Ba kya son haihuwa da ni ne?"

Shiru ta yi dan ba ta da abin cewa. Ita dai ta san tana son hutu, haihuwa ba wasa ba ne.

"Shekarun baya cikin wauta na tsara wa kai na iya 'ya'ya biyu na ke so. Amma yanzu i've changed, ina son 'ya'ya dayawa. Allah ya kawo mana ko nawa ne, da taimakon Ar-Rahman za mu kula da su, mu tarbiyantar da su bisa tafarkin addini, za mu yi komai dan mu inganta rayuwar su in har muna raye"

"Dole ka ce in haihu dayawa ai, salon nan da 'yan shekaru kaɗan idan na gama yin laushi ka je ka ce za ka auro wata sabuwa tunda na tsufa. Wallahi lokacin ne za ka san Aisha Farida ka auro"

Lallai Farida har yanzu da sauran shirmenta, abin da ya ke hanga daban abin da ta ke hangowa daban. Cigaba da magana da ita a wannan lokacin ma shirme ne.
Miƙewa yai ya je ya ɗau Yaman da ke bacci ya ce "ka da abinda ya samu baby na Aysherh. Or else..." ya sa kai ya fita ba tareda ya jira mi za ta ce ba.

Ranan gaba ɗaya ɗauke ma ta wuta yai dan har raba wajen kwana su ka yi, ya kwana a ɗakin sa ita ma ta kwana a na ta.

Washe gari ma ko kulata bai yi ba. Tana gaishe shi ma sama-sama ya amsa ma ta. Haka su ka ci breakfast ba tareda wani ya yi wa ɗan uwan sa magana ba. Yana gamawa ya tashi ya fita...

.............................

Yau kwana biyu kenan ma'auratan ba sa wani magana da junan su. Najeeb na dawowa daga office zai maƙalewa Yaman yana wasa da shi. Idan ya lura yana jin yunwa kuwa Tasallah zai kira ko matar Abdullahi su miƙawa Farida.

Najeeb na dawowa daga sallar Maghrib ya ga su Tasallah na fito da kayan Yaman ana sawa a boot ɗin mota. Farida na tsaye ɗauke da Yaman wanda ya sha kayan sanyi ma su kyau saboda yanayin garin akwai sanyi, itama Faridan da ganin shigarta fita za ta yi. Bai ce komai ba ya tsaya yana kallon ikon Allah. Farida ma kau da kai ta yi kaman ba ta gan shi ba tana jira su  Tasallah su ƙarasa fito da kayan.
Sai da su ka gama Farida ta ce " ba'a manta komai ba ko?"

Tasallah ta ce duk kayan da ta ce a ɗauko an ɗauko.
Farida ta sa kai ta shiga mota dreba ya ja mota su ka fita a compound ɗin. Najeeb na tsaye a wajen yana ganin ikon Allah. Ran sa kuwa yai matuƙar ɓaci, mi Farida ke nufi da shi.

Ya isa cikin gidan da ƙyar saboda ciwon kai da ya fara ji saboda ɓacin rai. A hankali ya ke maimaita Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun saboda ya samu nitsuwa...

........................

Farida kam gidan su Najeeb ta wuce da Yaman. Da ta je a falo ta samu Mom da Najdah suna hira, itama ta zo gida.

"Oyoyo angona" Mom ta faɗa tana ƙarɓan Yaman a hannun Farida.

Shigowa da kaya da Danliti ya farayi ne ya sa Mom tambayar ko lafiya.

"Na kawo miki ɗan yaye ne"

"Ɗan yaye?" Mom ta faɗa tana sake kallon Yaman da ke hannunta. Yaron da watan shi bakwai da sati biyu ne a duniya.

"Mom yaron bai damu da nono ba, shima rashin son cin abinci kaman uban sa. Shi ne na ce gara na yaye shi"

"Amma Anty Farida da kin bari ya cika shekara ɗaya, Yaman fa bai da wani ƙwari" Najdah ta faɗa tana kallon Yaman ɗin da ke murmushi saboda Mom da ke ma sa wasa.

"Kema kina hanya ai za ki ji yadda ake ji. Allah ya kaimu nan da wata biyu lafiya"

Najdah ta yi shiru dan itama fama ta ke yi da kanta. Ta wahala sosai da wannan cikin tun yana ƙaramin sa har yanzu kuwa.

"'yata ki bari Yaman ya kai 10 months mana, Najeeb ma a wata goma na yayeshi"

"Mom ki yi haƙuri dan gaskiya na yaye shi daga yau"

Mom ta kalli Faridan da kyau ta yi murmushi dan ta lura kaman Faridan na ɗauke da ciki ne...

Sai bayan sallar Isha Farida ta dawo gida. A falon sama ta samu Najeeb yana zaune sanye da baƙar jallabiya yana jan carbi.

"Barka da hutawa" ta faɗa tana ƙoƙarin tafiya ɗaki tunda har yanzu ba wai sun shirya ba ne.

"Aysherh" ya kira sunan ta a hankali.

Tsayawa ta yi tana jiran mi zai ce.

"Zo ki zauna?"

Ba musu ta dawo ta zauna a gefen sa.

"Ina ki ka kai min ɗa na?"

"Gidan kakannin sa"

"Why?" Ya faɗa yana ma ta kallon tuhuma.

"Na yaye shi ne, shi ne na kai mu su shi"

"Da izinin wa?" Ya faɗa da ɗan ƙarfi.

"Kai ne fa ka ce kar abinda ya samu cikin ka, lafiyata da lafiyar Yaman ya sa na yaye shi dan na kula da wanda ke cikina yanzu"

"And you made the decision without me"

"Ya ka ke so na yi, fushi ka ke da ni, ba ka min magana balle na gaya ma ka zan yayi Yaman"

Yana son yin magana amma idan yai hankalin sa ne zai tashi saboda ɓacin rai da ke cin sa.

Miƙewa yai ya ce " tunda banida matsayin da za a yanke shawara tare da ni, shikenan ki yi duk abinda ki ke so. Wanda ya ke cikin ki ma idan ba kya son sa ki yi waje da shi kar ya takura ki ya sa ki tsufa da wuri"...

"Ba haka ba ne My Champ, Wallahi..." ta tsayar da maganar saboda wucewa da yai ɗakin sa ba tareda ya kalleta ba...

Yadda ya ke magana ta san ran sa a ɓace ya ke. To ba ya ma ta magana ya yake son ta sanar da shi shawaran da ta yanke...
............

Waɗannan kwanaki huɗun sun fi kowani rana zafi a gareta. Idan ka cire lokacin da Naomi ta ma sa asiri, Najeeb bai taɓa shareta kaman na wannan kwanakin ba. Ba ya dawowa daga office sai ƙarfe goma ranan da ta je office kuma yadda ka san kwandon shara haka ya maidata ko kalma ɗaya bai ma ta ba. Lokacin da ta ke bashi haƙuri ma miƙewa yai ya bar ma ta office ɗin.

Shi kam Najeeb daga office gidan su ya ke wucewa ya je ya zauna da ɗan sa. A kwana na biyu Mom ta ma sa maganar ko zai tafi da Yaman ne, ya ce ta bar shi Farida na da ciki shiyasa ta kawo shi...

Ba abin da ya kai zaman lafiya tsakanin miji da mata daɗi. Farida har rama ta yi saboda fushin da Najeeb yai da ita. Yana dawowa da dare zai shiga ɗaki ya kulle sai kuma da safe.

Yau kam ta watsar da duk makaman yaƙin ta, ta ɗaga farar tuta. Tana son mijin ta, ga shi ko cikin ne ko minene dai 'yan kwanakin nan da su ka yi ba sa tare ba ƙaramin kewar shimfiɗar mijin ta ta ke yi ba.

Zuwa ta yi aka ma ta ƙananun ƙitson bare-bari saboda Najeeb ya fi son ya ga ta yi ƙitso compared to barin gashin haka nan ba kitso, aka ma ta jan lalle mai kyau ya fito da kyaun ƙafarta da hannun ta.

Ta haɗa madara zuma da lalle ta shafe jikin ta da shi, da yai awa ɗaya ta shiga banɗaki ta kakkaɓe sannan ta yi wanka da shower cream mai ƙanshi.
Dama tunda rana ta blending kankana da apple da lemon ta sa a fridge yai sanyi. Da ta gama shiryawa ta sa dogon hijab ta sauƙa ƙasa ta je ta ɗauko juice ɗin ta, tana zaune bayan sallan Isha tana shan juice ɗin tana kallon wayarta ko za ta ga saƙon sa amma shiru. Tun ƙarfe biyar ta tura ma sa text akan dan Allah ya dawo da wuri, sai dai bai ma ta reply ba.
Ƙarfe tara da rabi ta ji horn ɗin mota ta yi hamdala a zuciyarta...

.......

Ya fito daga wanka kenan ya ji ana buga ma sa ƙofar ɗaki. Ya sani sarai ita ce amma ya share. Ganin ancigaba da bugun ba a daina ba ya sa ya je ya buɗe.
Tsaye ta ke ta sha light make up a fiskarta, jikinta na fidda wani ƙanshi mai jan hankali, tana sanye da doguwar night robe baƙa.

"Yes, what can i do for you?" Ya faɗa yana kallon ƙwayar idon ta.
Ba ta yi magana ba, ta sa hannu ta zarge igiyar robe ɗin da ta sa, a hankali robe ɗin ya sulluɓo ƙasa.

Idon sa ne ya fara tracing ɗin jikinta tun daga sama har ƙasa. Haɗiyar miyau kawai ya ke saboda yadda ran sa ke ayyana ma sa abubuwa dayawa. Wata arniyar lingerie ta saka, wato yadda ka san an sa igiya an matse ƙasan breast ɗin ta haka nonuwanta su ka ɗago sama su ka cika tam cikin raga-ragar rigan. Riga ce da ta bayyana ko'ina a jikinta.

Da wata mitsitaiyar murya ta ce " in shigo?"

Gyaran murya yai yana ƙoƙarin saita nitsuwar sa, kusan 3 seconds kafin ya matsa daga bakin ƙofar ta shigo. Yana ƙoƙarin janyo ƙofar ya ji ta kwanta a bayan shi.

"Mijin na, abin alfahari na, jarumin namiji" ta faɗa tana wasa da kunnen sa duka biyu. A hankali ya juyo saboda gwiwowin sa da su ka yi sanyi.

"Mi ki k..."

"Shhhhh, ni ce da magana ba kai ba"  ta faɗa tana sa yatsar ta ɗaya akan lips ɗin sa tana wasa da shi. Ɗaya hannun kuma ƙasa ta yi dashi tana gaisawa da abunsa da ke ƙoƙarin leƙowa waje ta cikin towel ɗin da aka rufe shi.

"Na yi ba dai-dai ba. Ka na da dukkan dama akan Yaman da ni kai na, ka yi haƙuri dan Allah. Ka yafemin My Crown, My King, My Hero, My Mr BLTD"

Zai yi magana ta rufe bakin sa da na ta. Yayin da hannun ta ya ratsa cikin towel ɗin yana yiwa BLTD wasa.

"Aysherh you know..." ya faɗa lokacin da ya samu damar breaking kiss ɗin.

Hawayen da ya gani a idon ta ya sa ya kasa ƙarasa maganar.

"Ka yafe min dan Allah" ta faɗa da muryan kuka.

Sake haɗe bakin su yai su ka cigaba da abubuwa, tuni Farida ta warware, dama hawayen na kissa ne...

...........................

Wannan cikin kam ya sa Farida cikin yanayi na saurin fushi da faɗa.  Da farko farkon cikin dai abin da ɗan sauƙi amma cikin na ƙara girma abin na ƙara gaba. Ba sa sati ba su yi ƙaramin faɗa da Najeeb ba. Ga shegen kishi, sau biyu ta ke zuwa office a sati amma da ƙarfi ta maida shi duka kwana biyar ɗin. Indai ta ga mace ta shigo wajen Najeeb to haka za ta je ta zauna da su ayi duk maganan da za a yi a gaban ta. Tun Najeeb na tanka ma ta har ya haƙura ya daina kulata dan ya lura idan ya kulata ma shine ke ƙara ma ta ƙarfin gwiwa...

Bayan wata biyu da sati ɗaya Najdah ta haifi ɗan ta namiji. Ranan suna aka yiwa Najeeb takwara. A gidan sunan kuwa sai da Farida ta yi halin ta. Fauziyya sabuwar ma'aikaciya ce a Najeeb constructions, Architect ce da ta yi karatu a South Africa, asalin iyayen ta Nupawan Minna ne, amma sun jima suna zaune a Kano. Yarinyar ba ta da girman kai ga ta da yawan fara'a. Guruwa ce dan first class ta fita da shi.

A matsayinta na ma'aikaciya a Najeeb constructions ta zo sunan Najdah tunda Anas Ogan ta ne. Amma daga zuwan ta Farida ta fara yaɓa ma ta magana. Wai ta zo shishshigi da neman suna. Fauziyya ba ta kulata ba haka ta ajiye ledar da ta kawo ta fita ko babyn ba ta ɗauka ba...

Abun bai tsaya a nan ba, da dare da Farida ta dawo gida  haka ta kama yiwa Najeeb faɗa wai ya turo budurwarsa ta zo ta yi gaisuwa.

"My Goodness Aysherh. Fauziyya is a staff @ the Company. Ta je gaishe da matar Ogan ta miye laifi a ciki?"

"Ni dan Allah ka koreta, ba ta min ba. Idan ta zo wajen ka ta dinga buɗe haƙora kenan tana ma ka tallan open teeth ɗin ta dan wannan ya fi ƙarfin wushirya"

"Fauziyya is good, wata Biyu da ta fara aiki da mu i saw potential in her, i saw raw talent. Kuma kin san ba na ɗaukan ma'aikata sai ma su ƙwazo"

"Ni gaskiya ka koreta, ba ta min ba. Idan ba za ka iya ba ni zan koreta"

Rasa abin cewa yai ya tashi a falon ya ba ta waje...

Kwanaki su na tafiya, lokaci na gudu. Fauziyya kam tana shan magana a wajen Farida sai dai abu bai kawota office ɗin Najeeb ba. Yarinyar ba ta taɓa tankawa Farida ba, tana mugun respecting ɗin ta. Domin ta ji labarin bajintar da Farida ta nuna lokacin da Najeeb ya ke kwance a asibiti...

..............

Yau ma Najeeb shiryawa ya ke zai je wani taro Kaduna. Saboda faɗan da su ka yi ɗazu ya sa bai ce ta haɗa ma sa kayaba ya fara haɗawa da kan sa.
Har ta shigo ta zauna bai yi alamar ya gan ta ba.

"Wannan karan ma da Fauziyyar za ka tafi?"

Ya cigaba da abinda ya ke ba tareda ya tanka ma ta ba.

"Tambaya fa na ke dan na ga Fauziyya ce 'yar gaban goshi a Kamfani yanzu"

" Aysherh please, ba na son tashin hankali"

"Wallahi indai da ita za ka je sai dai mu tafi tare. Ba za ayi irin tafiyar ku Portharcort ba"

Sai a lokacin ya ɗago yana kallon matar ta sa. Cikin ya sa ta yi ƙiba ga baƙi da ta yi. Ba kaman lokacin cikin Yaman ba da ta yi haske ta yi kyau, wannan kam banda faɗa ba abinda ya ke sata whilst cikinta na farko ya sa ta cin abinci kamar gara.

"Queen Aysherh, my heart belongs to you, my love is only for you. Mun je Portharcort as a team ba wai na ɗau mace na tafi Portharcort ba. Ni, Yakubu, Hassan, Peter and Fauziyya. As a team Aysherh, ki dena yi min mummunan fassara"

Ta turo baki ta ce " to ai a hotel kuka kwana, Allah kaɗai ya san mi ya faru a wajen"

Maganar ta ma sa ɗaci, amma ya shanye dan yana ƙara magana ɗaya anan sai ta Allah, dan Farida idan ta fara masifa ka ɗauka dukan sa za ta yi. Yai shiru kawai yana sauraron maganganun ta wanda su ka fi kama da tuhuma...

..........

Washegari da sassafe ya fita, ruwan tea kawai ya sha ya fita har ya kusa kai wa bakin ƙofa ya dawo ya manna ma ta kiss a goshi ya ce " sai na dawo"

Sai alokacin Farida ta saki ranta ta ce " Allah ya kiyaye hanya ya dawo da kai lafiya" ya amsa da amin sannan ya fita...

Shiru- shiru har ƙarfe uku Najeeb bai kira ba bai kuma turo text ba. Ina Kano da Kaduna ace tun bakwai saura da ya tafi bai isa ba. Da farko ta ɗauka ko dan maganar jiya ne amma yanzu kam hankalinta ya tashi dan duk faɗan da su ka yi ko text zai tura ma ta ya ce ya isa.
Ta fara kiran numbar sa switch up, ta kira numbar Abdullahi dreba shima switch up. Nan jikinta ya hau rawa ta shiga kiran Mom. Tambayar Mom ta yi ko Najeeb ya kirata ta ce ma ta a'a.
Cikin kuka ta ce "Mom ki tambayamin Daddy ko sun yi magana da shi"...

Zaune su ke a falon kowa yai jugum saboda rashin sanin halin da Najeeb ya ke, da shi da dreban sa duk wayoyin su a kashe.
Daddy dai baya nan dan ya fita kai report ko zai ji labari ko anyi hatsari hanyar Kano to Kaduna.

Najma na jijjiga ɗan ta Bobo da ke kuka wayar Farida ta fara ringing Farida ta yi saurin tashi ta ɗau wayar da ke kan centre table. Ganin My Champion ke kira ya sa ta fara murmushi.

"My Champ saura kaɗan na mutu yau, ina ka shiga? Are you Ok"

"Yana nan lafiya idan har kun amince da sharuɗɗan mu" muryan wani ƙato ya doki kunnen ta.

"Waye, mi kuka yiwa mijina? Ina mijina?" Tambayoyin da ta fara jerowa kenan.

Jin maganarta ya sa Mom tashi da sauri ta amshi wayar ta sa a speaker tana faɗin " ina Najeeb?, mi ku ke so"

Mutumin yai wata mahaukaciyar dariya sannan ya ce " Najeeb Adam Jibo yana nan lafiya until kun fanshi ran sa a wajen mu"

" what do you want?" Mom ta faɗa tana danne hawayen ta.

"200million" ya faɗa a taƙaice.

"Ka bawa ɗana mu yi magana"

Mutumin ya sawa Najeeb waya a kunne.

"Mom i'm ok, ku kwantar da hankalin ku." Jin kukan Farida ya sa shi cewa  " My Queen dan Allah ki dena kuka"

Mutumin ya ƙarɓe wayan ya ce " kun ji shi dai yana raye, nan da 24hrs idan ba mu ga kuɗi ba za mu aika shi lahira" daga haka ya kashe wayan.

"Hello Hello" Mom ta faɗa amma shiru, sake kiran numbar ta yi amma ta ji shi a kashe.

Farida ta dafa kafaɗan Mom tana faɗin "Kashe shi za su yi ko? Kashe min shi za su yi ko?"

Ƙoƙarin faɗuwa ta ke yi Mom ta riƙota tana kiran sunan ta amma....

*Jirgin SAKATARIYA TA yana shirin sauka jama'a,  jirgin ya yi wata ɗaya da 'yan kwanaki yana lulawa a sararin samaniya kuma Alhamdulillah yana daf da sauka da daren yau Insha Allah. Da fatan Team Najeeb da Team Farida za su yi cincirindo a filin jirgi su ga saukan mu sannan su bamu masauki mai kyau. Wanda su ka supporting ɗina by paying to read this novel Jazakumullahu khairan. Wanda su ka karanta ta bayan fage kuma...*Skt 60

Haihuwa ne ya taso wa Farida gadan-gadan bayan sun kaita asibiti wurjanjan. Ba ƙaramin wahala ta sha ba kafin ta haihu dan sau biyu tana suma a wajen. Lokacin da 'yar ta fito gaba ɗaya ta gama galabaita jinin ta ya hau sosai, ga azabar haihuwa ga kuma tashin hankali.

Saboda yadda ta rikice dole sai da su ka ma ta allurar bacci.
Tun a asibiti Mom ta kira Daddy ta sanar da shi halin da ake ciki daurewa yai ya ƙaraso asibitin dan hankalinsa ya mugun tashi.
Lokacin da ya iso Mom na ɗauke da jaririyar da ke kama da uwar ta sak. Ya karɓi jinjirar yana ma ta addu'a...

Bayan an tabbatar ma sa da lafiyar Farida ƙalau sannan ya bar asibitin saboda ya je ya sanar da jami'an tsaro...

Wannan karan waɗanda su ka kama Najeeb da Abdullahi ba ƙananun kidnappers ba ne domin duk yadda ake ƙoƙarin gano inda su ke abin ya faskara. Washe gari Daddy ya je bank aka fara ƙoƙarin cire kuɗi, abu da manyan mutane cikin abinda bai fi awa uku ba aka gama haɗa 200million...

......................

Ummi ce ke zaune gefen Farida tana riƙe da baby tana ɗan shafa bayanta saboda kuka da ta ke yi. Yarinyar ba dai kuka ba, ga shi uwar ta ko ta kan ta ba ta yi, damuwar da ke ranta ya isheta.

"Farida ki karɓe ta ki ba ta nono dan Allah. Ba ta da wani ƙwari fa"

"Ummi idan su ka kashe shi mutuwa zan yi, ba zan iya rayuwa babu shi ba" ta faɗa hawaye na bin kumatunta.

"Ba na son kina magana kamar wacce ba ta da imani. Rayuwa da mutuwa duk a hannun Allah ya ke kuma zai kuɓutar da mijin ki Insha Allahu. Tashi ma za ki bata nono dan Allah"

Da ƙyar Farida ta iya miƙewa zaune tana jin duk gaɓoɓin jikinta na ma ta ciwo, ta amshi jinjirar daga hannun Ummi ta fara ba ta nono har lokacin ba ta dena zub da hawaye ba.
Ummin ma tausayin 'yartata ne ya cika ta amma dole ne ta dinga ƙarfafawa 'yarta gwiwa saboda halin da ta ke ciki...

A kwana na uku da haihuwar aka sallameta su ka dawo gida. Yau ɗin ne kuma kidnappers ɗin su ka ce za su sake Najeeb dan jiya aka aika mu su da kuɗin su. Ƙarfe goma Mom, Farida da Ummi su ka iso gidan wanda ke cike da 'yan uwa. Kowa a wajen yana jimamin abinda ya faru ne ana kuma jiran dawowar Najeeb...

A hankali Mom ta taimaka ma ta ta zauna a bakin gado, har yanzu ba wai tana da ƙarfin jiki ba ne kawai dai dauriya ta ke yi.

"Mom zan sha ruwa" ta faɗi  tana ƙoƙarin kwantawa akan gadon.
Mom ta ce tana zuwa. Ummi ta kwantar da baby a gefen Farida tana faɗin "ta ma yi bacci ashe"

Tun safe ake jiran dawowar Najeeb har yamma shiru.
Ihun da gidan ya karaɗe da shi ne ya farkar da Farida da ke bacci. A hankali ta buɗe ido tana maida hankalin ta ga abinda ta ke jiyowa. Jin ana kabbara da faɗin Alhamdulillah ya sa ta miƙe tsaye zumɓur ta fita da gudu duk da kuwa yadda jikin ta ya ke very weak.

Tun daga stairs ta hango shi yana murmushi, an yi cirko-cirko ana kallon shi ana kabbara, gefen sa Daddy ne riƙe da hannun sa ɗaya, shima ɗin fiskar sa ɗauke da murmushi. Tun da ta gan shi ta rage saurin da ta ke yi ta koma saukowa a hankali. Hajiya Fatima ce ta fara kallon ta ta ke cewa " Farida Alhamdulillah kin ga sun sake shi ko"

Tsayawa ta yi tana ƙarewa mijin na ta kallo, kayan jikin sa ne tun na ranan da ya fita, kayan sun ɗan yi bututu, akwai tabon ciwo a goshin sa da gefen bakin sa.   Sai duhu da yai da alama bai ga ruwa ba a 'yan kwanakin nan.

Ɗago ido da zai yi ya kalleta tsaye ta zuba ma sa manyan idanun ta. A hankali ya cire hannun sa daga jikin na Daddy ya taka zuwa wajenta yana zuwa ya rungumeta tsam ajikin sa kamar zai shigar da ita ƙirjin sa ne. Sun jima a haka kafin Farida ta iya cewa "it's a girl, your princess is born"

"Alhamdulillah ala kulli Haal" ya furta ya na sauke ajiyar zuciya.

Aƙalla sun yi minti biyu rungume da junan su. Hawayen da ya gani a fiskarta ne ya sa shi sa hannunsa duka biyu yana goge ma ta su yana faɗin "Queen ba na son kuka please" sake shigewa ta yi jikin sa tana murmushi...

.......................

Su na shiga ɗaki ta sa key ta kulle. Kafin ma ta gama kullewa ya je wajen gado ya ɗau 'yar sa da ke kwance tana bacci. Ya kissing goshin ta yana yi ma ta addu'o'i.

"She's beautiful, just like you"
Ya faɗa yana kallon Farida. Ganin ba shi da niyyar ajiye yarinyar ya sa ta amshi 'yar a hannunsa ta ce mu je na ma ka wanka. Ta maida yarinyar kan gado kafin ta ja hannunsa su ka shiga banɗaki. Ita ta sa hannu ta cire ma sa duk kayan jikin sa wanda ta san daga yau sun gama aiki dan ƙona su za ayi. Yana tsaye yana binta da kallo ta fara murza ma sa shower cream a jikin sa tana dirje dukkan jikin sa da shi. Da ta gama ta kunna shower ya wanke duk kumfan. Ta tsiyayi shampoo ta sawa gashin sa tana dirza ma sa especially scalp ɗin sa, ɗan rankwafowa yai da kan saboda ta samu daman wankewa da kyau cause ya fi ta tsayi. Sai da ta wanke shi sau biyu a bakin shower kafin ta tara ma sa ruwan zafi a bathtube ta ce ya shiga ciki. Ya ji daɗin ruwan zafin da ya shiga dan dama jikin sa na ma sa ciwo.

"I'm sorry my Queen" ya faɗa ganin hawaye da ta ke yi.

"Ni ce zan ba ka haƙuri miji na. I'm sorry you are married to a crazy woman"

Dariya ya fara yi yana faɗin "and i love my crazy wife"

Dariya itama ta yi tana cigaba da yiwa kafaɗun sa massage...

..........................

Duk ƙoƙarin 'yan sanda ganin an kama wanɗanda su ka kidnapping Najeeb abin ya ci tura. Kidnappers dai sun tafi da miliyan ɗari biyu wanda biya kam sai dai a lahira.

Ranan suna anyi ƙasaitacciyar walima, duk da anyi shagali amma bai kai lokacin sunan Yaman ba. Ko dan saboda abinda ya faru, oho.
Yarinya dai ta ci sunan Mom, an raɗa ma ta *Nabeelah Zafreen*

Wannan karon a gidan Daddy aka yi suna, infact sai da aka yi sati uku da sunan ma kafin su ka koma gidan su.

.........................

Yau Monday ta fara fita aiki bayan Zafreen ta cika wata biyu a duniya. Tana duba wassu takardu Zafreen da ke kwance a gadon yara da ke office ɗin ta hau kuka.

"Kayya 'yar nan Allah ya miki albarka, shegen kukan kin nan ban san ya zan yi da ke ba." Ta faɗa tana ɗaukan yarinyar.

Wayar office ɗin aka fara kira ta ɗauki kiran.

"Hajiya, Architect Fauziyya na son ganin Ki" muryan Kabiru sakatare ya doki kunnen ta.

Kabiru ƙanin mahaifiyar Anas ne. A ƙalla zai kai shekaru talatin da takwas zuwa da tara. Sakandare kawai ya karanta, yana aikin masinja a wata makaranta kafin Anas ya ma sa maganar aiki a Najeeb constructions tunda Najeeb ya rufe ɗaukan sakatariya ma ce. Wata ɗaya ana ma sa training na aiki kuma ya ɗauka sosai gaskiya, kafin ya fara yi mu su aiki.

Farida ta ce "ka ce ta shigo"...

Najeeb ba ya gari ya tafi Lagos wani taro.

Fauziyya ta gaida Farida a ladafce kafin ta ce " Ma ya jiki?"

"Da sauƙi" Farida ta faɗa fiskarta a sake dan yanzu ta yi wa kan ta faɗa. Dama cikin Zafreen ne ya sake tunzura ta.

Fauziyya ta fito da IV daga jakarta ta miƙawa Farida. Farida ta amshi IV ɗin tana karantawa. Ta ɗago ido da sauri ganin sunan da ke jiki.

Fauziyya ta yi murmushi ta ce " Ma, you have every reason to be jealous, ko ni na ke auren Sir Najeeb ba ƙaramin kishin sa zan yi ba. He's handsome, rich and successful. Amma ki sani ban taɓa son mijin ki ba, tun kafin na fara aiki anan an riga an ba da ni, lokaci kawai mu ke jira and now the wedding is in 12 days"

Cike da kunya Farida ta ce " ba dai za ki bar aiki da mu ba"

"No, i love my job, kuma dear ya amince na yi aiki anan matuƙar za a maida lokacin tashi na ƙarfe ɗaya ko biyu"

"Kar ki damu za a rage miki. Wannan kamfani yana buƙatar ma su ƙwazo irin ki"

Fauziyya ta miƙe tana faɗin " na gode Ma"

Farida ta ce " dan Allah ki yi haƙuri abinda ya faru baya"

Fauziyya ta ce ba komai ya wuce...

..........................

Tun da su ka dawo daga sunan Zafreen ta ke jin jikin ta ba daɗi. Ba ta son gayawa Lukman saboda kar hankalin sa ya tashi. Ciwon kai idan ta ce tana ji ranan za ka ga Lukman ya rikice yana ƙoƙarin ba ta kulawa na musamman. Yana son ta sosai yana kula da ita, she's really lucky da ta aure shi. Ya iya soyayya ga iya kula da mace, ba shi da zafi kwata-kwata. Cikin zaman auren su za ta iya irga lokutan da ta ga ransa a ɓace hakanan ana ɗaukan wassu awowi za ka ga ya sauko ya koma normal. Itama ɗin ba ƙaramin tattalin sa ta ke ba, cikin 'yan kwanakin nan ma tunanin samun haihuwa ta ke dan ta san shine kaɗai abinda za ta yi ta sa Lukman farin ciki, ga shi har yanzu shiru. Wani lokaci sai ta ga ko dan shekarun ta ne, amma kuma ai ma ta na haihuwa har a fifties na su balle ita da ke talatin da biyar.

Ta tuno da lokacin da  ake tsakiyar shooting wani film hajijiya ya kwashe ta ta faɗi, da aka kaita asibiti aka ce tana da ciki. Baƙin cikin da ta ji a lokacin ba zai misaltu ba. Bayan kwana uku ta sayi wassu pills ta sha ranan ta yi bleeding kamar jinin ta zai ƙare. Ƙarshe sai da ta yi jinyar sati biyu a asibiti Ta rintse ido tana hawaye....

Lukman na fitowa daga asibiti ya haɗu Da Dr Jennifer wanda ta koma Dr Aisha. Ta jima da barin aiki da asibitin da ya ke, few months bayan ta yi aure.

Gaisawa su ka yi sama-sama har zai tafi ta tsayar da shi akan tana son magana da shi.

"Faɗi maganar ki da sauri dan my wife na chan gida tana jira na"

Jikinta yai sanyi da jin kalaman sa amma ta daure ta shiga koro ma sa bayanin yadda mijin ta Dr Faisal ya walaƙantata ya hana ta aiki ga shi ba ya wani kula da ita, ga matan sa da su ka sa ta a gaba akan ita yare ce kuma kafira wacce ta gama yawon titi. Walaƙanci dai iri-iri, yanzu gashi ko wata shida ba ta cika da haihuwa ba ya saketa.

"Sorry ko, ya sunan babyn?" Lukman ya faɗa cikin halin ko in kula.

"Fatima amma ta rasu few days bayan sunan ta"

Lukman ya ce " Allah ya sa me ceto ce amin. Barin je gida kar wife ɗina ta jini shiru"

Ya wuce ya bar Dr Aisha cike da tarin nadama, yau da Dr Lukman ta aura ta tabbata ba zai taɓa walaƙantata haka ba, he'll love her and cherish her for the rest of his life, sai ga shi ta ƙi auren ɗan shege ta auri ɗan asali kuma tana nadama...

Lukman na zuwa gida ya samu Sabreen na kela amai a banɗaki. He's being suspecting pregnancy 'yan kwana biyun nan amma saboda rashin samun isashshen lokaci ya sa bai damu ya tsaya ya tabbatar da zargin sa ba. Bayan ya taimaka ma ta ta gyara jikin ta sannan ya fara duba ta. Daga idanun ta zuwa tafin hannunta kafin ya ɗaga rigarta yana sa hannu a mararta da cikin ta.

"What is it?" Sabreen ta tambaya ganin taɓe-taɓen yai yawa.

With excitement a fiskar sa ya ce " Lets confirm first"

Sai da ya tabbatar ta samu ƙwarin jiki kafin ya fita ya je ya siyo PT strip. Da ya dawo su ka gwada.

Ɗaukan ta yai sama yana juyi da ita yana dariya bayan ya ga reading ɗin strip ɗin ya bada positive...

..........

Kwanci tashi cikin Sabreen ya cika wata tara inda ta sha wahala wajen naƙuda ƙarshe aka ce ba za ta iya haihuwa da kanta ba aka cire ma ta kyakykyawar jaririyar ta. Yarinyar sak ubanta hatta green eyes ɗin sa sai da ta ɗauka, idan ka ɗebe farin Sabreen da ta ɗauko ba abin da ta bari na Lukman.

Murna wajen Lukman ba a magana. Finally shi ma ya samu 'ya, 'ya ta sunnah.

Kwana biyu kafin suna Najeeb da Farida su ka dira a Abuja, tareda yaran su Yaman da Zafreen wanda ƙiriniyar yarinyar yafi ƙarfinta. Yayinda Yaman ya ke so quite ita wannan tun aciki ta ke sa uwarta masifa da ta fito ma tun tana 'yar jinjira ta ke nuna iya shegen ta balle yanzu da ta fara wayo. Idan mutum ya ɗauketa ba ta so har cizo tana yi.

Ranan suna gaskiya anyiwa Sabreen da Lukman kara domin kuwa an zo dayawa, 'yan uwan Lukman ta ɓangaren mahaifiyar sa duk sun zo, ga 'yan uwan su Najeeb da su ma su ka cika wajen.

Tsakanin ma'auratan su ka yanke shawaran sunan da za a sawa yarinyar. Farida kam ba ƙaramin mamaki ta yi ba da Najeeb ya kira ta daga masallaci yana faɗin sai ta kawo kuɗin suna domin an samu *little Aisha Farida*

Bayan sun gama waya ta je ta ɗauki 'yar tana ma ta addu'a. Sabreen da ke kwance sai murmushi ta ke yi...

..........................

Rayuwa na cigaba da tafiya shekaru sun fara ja domin kuwa an samu haɓaka na arziƙi da iyali.
Najdah da Anas sun sake haifan mace inda su ka sawa 'yar su sunan *Aisha Amira* aka yiwa marigayiya Aisha takwara.

Farida ta sake haihuwan namiji bayan Zafreen ta cika shekara biyu  su ka yiwa Daddy takwara *Adam * suna kiran sa da *Aasim*

Sabreen ma ta sake haihuwa bayan Little Farida, shima ɗin CS aka ma ta dan ance da wuya ta iya haihuwa da kan ta. Sun samu *Muhammad Mubarak*

Baffa Musa da iyalen sa na zaune lafiya kowacce ƙoƙarin faranta ran ɗan tsoho ta ke. Amma alamu sun nuna Amina ta ci galabar sace zuciyar wannan tsoho, ilimi da wayewa sun sa duk abubuwanta sun banbanta da na sauran matan. Ba ta ganin tsufan sa kwata-kwata, duk ranan girkin ta haka ta ke birkitashi da salon ta na matan zamani wanda ya ke sa ya ji ina matan sa su ka shiga lokacin da sauran mata ke koyan dabarun sarrafa miji. Abubuwan da ya ke yi yanzu da wanda Ummi ke ma sa ko lokacin yana matashi bai samu wannan gatan ba.

Yakubu ma shekara ɗaya bayan haihuwar Zafreen ya angonce da amaryar sa Halima.

A ɓangaren Aneesa da Majiddah ma sun haɗe kan su suna zaune lafiya. Duk da Aneesa na zuwa aiki hakan bai hanata samun lokacin miji da 'ya'yanta ba. Bayan Mujahida haihuwa ta tsaya ma ta amma Maijiddah ta samu Yusuf bayan Al'amin ga kuma tsohon ciki da ta ke da shi yanzu. Shi kam AbdulWahab sai dai yai ta hamdala kawai domin kuwa kwanciyar hankali da nitsuwa sun samu gindin zama a gidan shi...

............

Zama aure sai haƙuri, akwai soyayya, akwai faɗa, akwai matsaloli amma idan kuka san yadda za ku dinga tafiyar da lamuran ku sai ya zamana duk inda matsala ta kunno kai za ku samu mafita cikin ƙanƙanin lokaci.

Najeeb da Farida su na nan su na soyayyar su, su na abubuwan su ma su sanya farin ciki da jin daɗi. Idan ana aiki a office jiki ya buƙaci abubuwa, sai a kashe wuta a rufe ƙofa a cigaba da abubuwa kawai 😂
It wasnt a perfect life, they werent perfect. Su na faɗa suna samun saɓani kuma suna soyayya. Ba abinda su ka maida hankali akai kamar tarbiyyan yaran su da kuma tsare gidan su da yawan addu'o'i da yawan sadaka da kuma taimakon mabuƙata. Shiyasa lokacin da Sabreen ta buɗe Foundation ɗin ta, duk wata su na zuba maƙudan kuɗi a ciki saboda a samu a tallafi mabuƙata...

Mrs Comfort ta mutu kafin Naomi ta samu lafiya, ta samu lafiyan ne bayan Boka Ifagbemi ya mutu. Chan wani ƙauye a Owerri Naomi ta tsinci kanta lokacin da hankalinta ya dawo jikinta. Mutanen ƙauyen su ka ce ai tafi shekara biyu tana hauka. Su su ka haɗa ma ta kuɗi su ka bata kaya ta shiga mota sai Kano. Da ƙyar ta samu ƙaninta Abel saboda ya riga ya tashi a gidan su na da.  Bayan ta samu masauki a gidan Pastor kafin aka sanar da ita mutuwar mahaifiyarta ta yi kuka kuma ta yi baƙin ciki sosai. Daga ƙarshe dai da ita da Pastor su ka je gidan su Najeeb inda ta ba wa Najeeb da Farida haƙuri. Sun riga sun yafe ma ta tuntuni, haka ta tafi tana kuka. Neman Maureen ƙawarta ta shiga yi inda ta gano ta bi wani chief ne hotel aka neme ta aka rasa har yau. Zance dai da ya fi tabbata shi ne an tsafe Maureen ne. Naomi ta yiwa kan ta karatun ta nitsu ta koma zama a gidan Pastor tana yiwa church ɗin su hidima alƙawari ma ta yi za ta zama Nun saboda ma kar ta yi haƙuri. Pastor dai ya ba ta shawaran ta ƙara tunani a kai....

Rayyan kam ya rasa Farida har abada. Matar sa Aisha tana ƙoƙarin kyautata ma sa, sai dai har yau akwai ƙaramin gurbin Aisha Farida a zuciyar sa. Suna zaune da matar sa da 'ya'yan su uku Kamal, Abdullahi da Zainab

.......... .......... ........

Gaba ɗayan su su ke airport ɗin. Ƙarshen shekara ne inda iyalen uku su ka shirya zuwa Maldives da kuma London dan yin hutun ƙarshen shekara.
Lukman da Sabreen suna tare da Little Farida 'yar shekara uku sai Mubarak ɗan shekara ɗaya.
Najdah da Anas ma na tareda Najeeb Bobo da kuma Amira 'yar shekara biyu.

Sai zugan FARNAJ
Yaman ɗan shekara biyar
Zafreen huɗu
Aasim biyu da kuma babyn da ke cikin Farida ɗan wata biyar...

..............

...Maldives 2017...

Wajen beach ɗin ya cika da mutane kala-kala. Kowa ka gani yana sha'aninsa ne a wajen.

Wani mutum ne ya hango Zafreen da Little Farida su na wasa a wajen yashi yaran sun burgeshi. Shima tareda ɗan sa Nasir su ka zo beach ɗin tunda mai ɗakin sa shekararta ɗaya kenan da rasuwa.

Jin suna ingautsan Hausa Larabci da turanci ya sa su ka ƙara burgeshi. Ya ƙarasa wajen su riƙe da hannun ɗan na sa ɗan shekara bakwai.

"Hey pretty" ya faɗa yana kallon Little.

"Ya sunan ki" little ta kalleshi daga sama har ƙasa kafin ta ce " Aisha Farida Lukman Magaji"

"Wow what a cute name"

Kafin ya tambayi Zafreen ta yi caraf ta ce " my name is more cute than hers"

Ya ce " Oh really and whats your name?"

"Nabeelah Zafreen Najeeb Adam Jibo, see i have the most cutest name in the world and i'm also a princess" ta faɗa tana cuno baki

Yai ƙaramar dariya ya ce "where are your parents?"

Dukkan su biyu su ka ma sa nuni da inda iyayen na su su ke.

Mutumin yai murmushi tareda nufo su Najeeb saboda kodan yaran da su ka burgeshi yana son ƙulla ƙawance da iyayen su tunda shima ɗan Nigeria ne...

Bilal yana magana da su Najeeb inda ya introducing kan sa a matsayin Engineer Bilal Bello Bukar sai ga Bobo ya zo da gudu yana kuka.

Wajen Anas ya nufa yana kuka sosai. Sai ga sauran yaran suma sun iso wajen da gudu.
Anas ya tambayi ɗan na sa ko mi ya faru sai Bobo ya nuna Zafreen.

Farida ta kalli Zafreen wanda ta yi tsaye ƙyam da ita ba ko tsoro a idon ta.

Farida ta ce " mi ki ka ma sa?"

Zafreen ta sa hannu a ƙugunta tana faɗin " ce min yai 'yar lukuta, and mommy i'm not fat"

Farida ta harareta ta ce " bakin ki ne i'm not fat ai, zo nan na cire bakin rashin kunyar na ki"

Najeeb ya ce "princess zo nan" Zafreen ta je wajen Najeeb da gudu tana dariya.
Little Farida ne ta faɗi abinda Zafreen ta yiwa Bobo. Marin sa ta yi sannan ta watsa ma sa yashi a fiska.

Kowa ya juyo yana kallon Zafreen wanda ko'ina ta je sai ta nuna halinta na rigima, ƙiriniya da masifa.

Farida ta ce "wannan 'ya wannan 'ya"

Najeeb ya harareta ya ce " Thank God princess gado ta yi"

Gaba ɗaya wajen aka sa dariya. Farida kuma ta haɗe rai, ƙarshe ita ɗin ma ta joining na su aka cigaba da dariyan ana yi ana tuna baya..

*Anan jirgin sakatariya ta ya sauka*

*Alhamdulillah*

*The end*

*Anan na kawo ƙarshen labarin Romantic Comedy mai taken SAKATARIYA TA, da fatan kun ji daɗin karanta shi. Kura-kuren da na yi Allah ya gafarta min. Duk da ya kasance RomCom hakan bai hana shi zuwa da darussa na rayuwa ba. Rayuwar gaba ɗaya cike ta ke da ƙalu bale. Labarin Najeeb da Farida was not perfect and soyayyar su ma ba perfect ba ce, dukkan su suna da flaws na su. Amma su kan yi ƙoƙari wajen saita tsakanin su cikin ƙanƙanin lokaci. Yayinda Najeeb ke da sanyi ita Farida 'yar zafi-zafi ce*

* labarin sakatariya ta labari ne akan yadda wata sakatariya ta sace zuciyar Ogan ta. Note that, in reality mafi yawanci secretaries mata za ka ga suna ƙoƙarin shiga rayuwar Ogan su, idan Ogan bai kai zuciya nesa ba su zo su fara yin abubuwa tsakanin su and mafiyawanci za ka ga Ogan magidanci ne. Akwai wassu secretaries kuma wanda su ke munafukai ma su haɗa guri, akwai wanda su ne ke hana ruwa gudu a kamfani ko wajen aiki. Akwai wanda kafin ka ga Oga ko file ɗin ka ya je wajen Oga to sai ka bada cin hanci. Ga su nan dai birjik. Da sakatare namiji da sakatariya mace akwai na banza akwai kuma na ƙwarai. Whether namiji ne ko mace mu ji tsoron Allah a duk inda mu ke aiki sai ka ga an samu cigaba mai amfani*

*ban yarda wani ko wata ya sayar min da labarin nan ba, ko kuma a karanta shi a youtube channels. Ko a yaɗa shi ta ko wanni fanni. Akwai wanda sun fara haɗa documents na labarin nan, su ma su sani ba da yarda na bane. Akwai wanda su ka yi ta sharing labarin nan bayan sun san na kuɗi ne. Har wassu idan an mu su magana su ke maida martani da furuci mai muni. Gaskiya ba ku kyauta ba.*

*Alhamdulillah na samu alkhairi dayawa dalilin rubuta labarin nan, wanda su ka biya jazakumullahu khairan, wanda bayan sun biya sun haɗa da wani ihsanin kuma ina godiya Allah ya saka muku da mafificin alkhairin sa.*

*zan cigaba da labarin Tsohuwar soyayya daga gobe Insha Allah. Wanda ba su samu daman biyan sa ba, akwai free story da zan yi immediately bayan Tsohuwar soyayya za su iya jiran wannan idan har Allah ya sa muna cikin ma su rai da lafiya*

*Suna na Azizat Hamza ina yiwa dukkan masoyana fatan alkhairi. Ma'assalam*

No comments