ROYAL CONSORT Complete Hausa Novel
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
(Historical fiction)
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Labarin ROYAL CONSORT labarine irinshi na farko a cikin labaran hausa novel,labari ne na tarihi amma wani bangaren labarin qagagge ne,labarin ya qunshi mulkin mallaka,tsantsar qauna,tasirin qarfin
iko,mugunta,rashin adalci,sadaukarwa da sauransu.❤️ Part 1 : Introduction
Masarauta ce mai fadi da girman gaske,domin zaifi sauqi a kirata da gari guda,masarauta ce mai tarihi da tsari mafi birgewa a yadda suke tafiyar da al’amuran mulki da rayuwar yau da kullum.
Sai dai matsalar guda d’aya ce tak,suna amfani ne irin tsarin nan na mulki da tantancewa tsakanin talaka da mai kud’i,hakan ne yasa kowa yake da kwad’ayin kasancewa a cikin mutane masu alfarma,domin kuwa hakan ne kawai zai iya tseratar da kai da ahalinka daga dukkan wata barazana.
Idan har mutum ya kasance da jinin talaka a jikin sa,to zai zama abin qyama ne a cikin al’umma,kuma ba zai samu sakewa ba sai dai a cikin talakawa ‘yan uwansa.
Wani ‘bangaren kuma zamu iya cewa duk wanda ya kasance a cikin wad’anda ake mulka to tamkar bawa ne a wajen sarki,domin mulkin mallaka akeyi,laifi kad’an ne ko wanda bai kai ya kawo ba zai iya sawa mutum ya rasa ransa.
Domin kuwa babu gwamnati balle kuma demokrad’iyya,masarauta ce take mulkin kowa da komai,kama daga jami’an tsaro,kotu,haraji,da sauran su.
kasancewar a haka suka tashi sukaga al’ummar su shiyasa basu d’auki hakan a wani nau’i na zalinci ba,sai dai sun yadda da cewar wajibi ne a garesu su yi wa sarki da iyalansa biyayya sau da qafa domin tsira da rayukansu.
Har ila yau a wannan masarauta,doka tana aiki akan kowa komai matsayinsa kuwa,matuqar dai an samu hujjar cewa an aikata laifin to kuwa ba zai tsallake hukunci ba,hakan yasa duk wanda ya aikata wani laifi zaiyi qoqarin ganin ya rufe kuma ya toshe duk wata hanya da za’a samu hujja a kansa.
Masautar tana da FADA guda biyu ne akwai fadar sarki mai martaba wato (Grand palace) inda nan ne sarki yake ganawa da fadawansa,da kuma fadar sarauniya,wannan fadar cikin gida ce da ake kiranta da (inner court) wannan fadar itace qarqashin ikon sarauniya (Queen) wato matar sarki ta farko,itace take mulkin cikin gida (pavillion of women: inda babu wani namiji da yake iya shiga sai da izini) a qarqashinta akwai sauran matan sarki da duk wata ‘ya mace da take cikin masaurautar,kama daga bayi (servants) har masu aikace aikacen cikin masarautar (Palace maids) haka nan kuma tana da office din bincike na musamman (office of investigation) wanda shima mata zallah ne a ciki da ake kiransu da (investigator ladies) wanda sunfi ko wacce palace maid matsayi a cikin gida saboda yanayin aikinsu yana buqatar baiwa da ilimi na musamman.
A tsarin wannan masarauta,Matar sarki ta farko ce kawai take da haqqin a kirata da sarauniya (Queen) inda duk wata mata da sarki zai samu bayan nan za’a kirata da (Consort) kuma suma ko wacce da matsayin ta daidai da yadda sarautar ta yazo,hakan yasa ba matsayin su daya da sarauniya ba,zasu kasance ne a qarqashinta kuma masu biyayya a gareta.haka nan kuma sarki yana da damar da zai nemi duk wacce yake so cikin palace maids ya mayar dasu qwarqwara (concubine)domin suna qarqashin ikonsa ne,hakan ne yasa basu da damar da zasu qulla alaqa ta soyayya da wani namiji domin hakan laifi ne mai girma.
Inner court din sarauniya tana da wasu jerin mata da ake kira da (court ladies) wanda su suka hada da sauran matan sarki,qwarqwarorinsa,da kuma palace maids da suke da babban matsayi a masarautar.
A tsarin masarautar duk wani abu da ya shafi inner court to fa sarki bashi da ta cewa a wajen,sarauniya zata sa ayi bincike kuma ta yanke hukunci,kuma idan har sarki yana buqatar wani abu da ya danganci inner court sai dai ya bawa sarauniya shawara ko kuma ya nemi alfarma a wajenta amma ba umarni ba,domin umarnin sarki baya amfani a inner court.
A cikin ‘yan matan masarauta akwai biyayya mai qarfin gaske,yadda ko yaya mutum ya fika sai kayi masa biyayya,kuma kaucewa wannan sharadin laifi ne mai girma. Kuma duk wata matar sarki babu wanda ya isa ya kirata da sunanta ko da kuwa iyayenta ne,domin doka zata iya hawa kansu,sai dai da sunansu na girmamawa.
A tsarin magadan sarauta kuwa,’ya’yan sarki maza ana yi musu sarauta kamar yadda yawancin masarautu sukeyi,babban d’a wanda mafi akasari shine yarima mai jiran gado(crown prince) sauran kuma duk wani d’an sarki namiji ana kiransu da (Grand prince)
‘Ya’ya mata ma suna da nasu yanayin sarautar saidai babu su a gadon sarauta.
Sarautar crown prince sarauta ce da ake bata matuqar muhimmanci domin a tsarin sarautar daga sarki(His majesty the king)sai mahaifiyar sa (queen dowager) sai sarauniya Her majesty The queen)sai crown prince,duk consorts suna kasancewa qarqashin crown prince ne duk da matan babansa ne domin yafi su kusa da sarauta,akwai biyayya a tsakaninsu ko da kuwa shi crown prince din consort ce mahaifiyarshi ba sarauniya ba.
A tsarin kayan sawa kuwa,sarki,sarauniya,da kuma crown prince suna rufa alkyabba a jikinsu a cikin kowane yanayi a cikin masarauta,kuma alkyabbarsu na d’auke da zanen dragon ne a jiki,wanda babu wanda yake da ikon saka alkyabba mai zanen dragon sai su ukun nan kamar yadda aka qawata karagar mulkin qasar (Royal throne) da wannan zanen dragon 🐉
Hakanan suma consorts da irin nasu design din alkyabbar,a doka su kad’ai suke iya saka alkyabba mai adon zaiba (golden and silver) inda mai adon golden a alkyabbarta tafi mai adon silver matsayi na sarauta,wanda ko wanda bai sansu ba,wannan kayan kawai zai kalla yasan matsayinsu.
Haka nan ko wane matsayi na court ladies akwai irin kayan dasuke amfani da ita,domin tantance kowa da matsayinsa a fadar.
Royalty 👸
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Page 3
Labarin hukuncin sarki ya isa kunnen kowa a cikin masarautar,ciki kuwa har da Her majesty The queen,da kuma mahaifiyar sarki (queen dowager) hakan kuwa ba qaramin girgiza su yayi ba,musamman mahaifiyar sarki da ko da yaushe fatan ta bai wuce sarauniya ta samu juna biyu domin ta haifa wa masarautar su magaji ba,tana fatan hakan tun kafin ranar da mai martaba zai yi tunanin yin wani auren,wato ya kawo consorts cikin masarautar,wannan dalilin ne yasa hankalinta yayi matuqar tashi qwarai da gaske yayinda ita sarauniya ba za’a ce bata damu ba,amma damuwar ta ba mai yawa bace domin ta dad’e da sanin cewar matsayinta na matar sarki a suna ne kawai amma bata da wani gurbi a zuciyar mai martaba,dama dalilin da yasa yake zaune da ita saboda mahaifiyar sa ne,kuma sannan da dalilin dokar qasa,domin sarauniya tamkar Uwa take ga al’ummar qasa,hakan yasa idan har ba wani gagarumin laifi da kai tsaye za’a iya kiran shi da ta’addanci ba,to ko sarki bashi da ikon cire ta daga wannan sarautar tata,ma’ana ba’a sakin aure a gidan sarauta.
Sarauniya HANEEFAH mace ce mai sanyin hali,bata da hayaniya ko kad’an,tana da matuqar dattako da sanin ya kamata,kasancewarta a matsayin sarauniyar garin JOSHUN kuma shugabar inner court bai sa ta kasance mai jin kai,ko kuma amfani da mulkin da take dashi domin cusgunawa bayin Allah ba,hakan yasa ta fita daban daga halayyar mutanen da suke cikin masarautar,mutanen da idon su ya rufe akan mulki suke mata kallon lusara,saboda tana da dukkan ikon da zata aiwatar da dukkan abinda taga dama,ko da kuwa sawa a kashe wanda taga haka kawai bata qaunar ganinsa ne,fad’a kawai zatayi a aiwatar da hakan.
Dowager queen ce a daki sai kai kawo takeyi cikin zurfin tunani,duk tunanin ta bai wuce yadda za’a yi taga ta dakatar da shigowar jalilah cikin masarautar ba,amma kuma ita kanta tasan cewar ta makara domin aikin gama ya riga ya gama,tuni ofisoshin da suke da alhakin ciccike takardun da zasu bawa jalilah lasisin shigowa cikin fadar suka gama aikin su,rana kawai mai martaba zai saka,ita kanta ta rasa mafitar abinda take shirin yi,wani murmushi ta saki da alama akwai wani abin da ta d’arsa a ranta tare da zama akan wata shimfida dake qasa kamar katifa,sai qaramin tebur a gabanta daidai yadda mutum zai iya dora hannunsa idan yana zaune a qasan.
A bangaren Shukra kuwa haka ta wuni a ranar sukuku har mutanen ma’aikatar su suka fahimci akwai wani abu da yake damun ta,hakan yasa kowa ya daga mata qafa ranar,ita kadai take zaune bayan sallar ishaa gari yayi duhu sosai,waigawar da zata yi ta hango wata algaita (Abin kidan sarauta) nan taake tunanin yayanta ya fado mata domin gwani ne wajen busa algaita,tashi tayi a nutse taje ta dauko algaitar,ta fita can wajen filin ma’aikatar su qarqashin wata bishiya ta zauna,a hankali ta fara busa algaitar hawaye na sauka daga idonta,domin babu abinda take tunawa sai rashin ahalinta da tayi da kuma kewar su da yake damunta,haka ta cigaba da busa algaitar yayin da kidan algaitar yake ratsa cikin masarautar har cikin kunnen mai martaba da dawowar sa kenan daga ran gadi tare da babban bafaden sa sai guards guda biyu domin yana fita ne cikin badda kama,yadda idan ba saninshi kayi sosai ba,zai yi wuya ka iya gane cewar sarki ne,dai dai lokacin da kidan algaitar ya sauka a cikin kunnensa yai daidai da tsayawa yayi cak ba tare da ya qara gaba ba,a nutse yake jin yadda sautin kidan yake fita cike da qwarewa da qayatarwa,juyawa yayi ya kalli babban bafadensa (chief eunuch) yace
“Kana jin abinda nake ji kuwa?” Murmushi C.E yayi tare da dan rusunar da kanshi alamar girmama wanda yake magana dashi sannan yace
“Ina ji mai martaba,idan kayi umarni sai aje a taho da mai busar yanzu”
Martanin murmushin mai martaba ya mayar masa tare da cewa
“A’ah ba yanzu ba,amma gobe ina son kaje ma’aikatar masu kid’an (bureu of music) kaje ka taho min da mai busar zuwa grand palace”
Dan rusunar da kai yayi alamar girmamawa don da alamu hakan ya zamar masa jiki,idan har zai yi magana da mai martaba sai an durqusar da kai.
Shukra tana zaune tana busa algaitar ta,kamar wacce aka zabura ta miqe da sauri ta tafi taje ta ajiye algaitar a inda ta dauko,daga bisani da dauki hanyar inda suke wanki,cikin sa’a kuwa tana zuwa ta taradda wasu ‘yan mata wanda shigen kayansu iri daya ne da nata amma nasu yafi nata tsafta da kyalli kuma kalar nasu shudi (blue) sabanin nata da yake brown ruwan qasa,da gudu taje ta qarasa gaban su ta tsaya,tsayawa sukai suna kallon yarinyar suna jiran suji da me tazo
“Barka da yamma my lady” abinda ta fada kenan cikin girmamawa (ta kirasu da MY LADY ne domin dokar girmama duk wanda yake gaba da kai a masarautar,su ‘yan matan nan palace maids ne,wato wadanda suke aiki a ainihin cikin masarautar bangaren ahalin gidan) kallonta suke sheqeqe sai guda daya ce a cikinsu tayi mata kallon arziqi,ita kadai ta iya amsa mata maganar da tayi
“Lafiya kika tsayar damu haka? Ko kinyi batan kai ne? Daga ganin kayan da suke jikin ki dai na tabbatar ke servant girl ce”
Kada kai tayi alamar “Ehh” sannan ta qara da cewa “Dama zuwa nayi don Allah neman wani taimako”
Zaro ido sauran ‘yan matan sukayi,suka kalli wacce ta fara amsa mata sukace
“Kina da lokacin wannan servant din kenan? To sai kin taho”
Kayan wankin da suka zo diba ne a hannunsu sukayi gaba suka barta ita da shukra a tsaye,matsowa tayi dab da shukra tace
“Fada min da me zan iya taimaka miki?”
Shukra ta sassauta murya tace
“Dama na san gobe ne asabar din qarshen wata da kuke aikin kwalemar cikin masarauta (monthly cleaning) shine dama nake son ko zaku taimaka min ina son na shigo na taya ku”
Kallon shukra take da mamakin me take son taje tayi a cikin masarautar amma dai bata tambaye ta ba,tace mata
“Ni ina aiki ne a quaters din ladies investigators ne,idan zaki iya zuwa da wuri gobe da safe amma kada ki bari kowa ya ganki,zan baki uniform dina sai muyi aikin tare”
Murmushi shukra tayi cike da farin ciki ta fara jero mata godiya,haka suka rabu tana mamakin abinda yasa shukra take son shiga cikin masarautar,haka tabar tunanin ta a ranta har ta qarasa inda zasu ajiye kayan wankin da suka dauko,tana jin qawayenta suna mata tsiyar ya ta qare da servant girl ,ita dai bata kula su ba ta shiga sabgar ta.
Shukra kuwa murna ce ta cika ta domin ta dade tana jiran wannan ranar da zata shiga domin dubawa ko zata hadu da court lady din da take nema,haka taje ta kwanta cikin dokin gari ya waye wataqila wannan shine mataki na farko da zata iya wanke sunan ahalinta da aka sa sunansu cikin ‘yan ta’addan qasar.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Page 2
❤️ Part 2 : slavery (bauta)
Shekarar 1432 AD.
Wata 'yar matashiyar yarinya ce da duka shekarunta ba zasu wuce goma sha uku ba,daga ganin kayan da yake jikinta dai baiwa ce,sai dai inda take ta kai kawo ne ban ga wata mace a wajen ba domin duka tarin maza ne,duk kowanne a cikin uniform din aiki,bayi maza,da kuma ma'aikatan da suke aikinsu a cikin wajen.
Aikinta takeyi cikin walwala da girmamawa,kuma suma da dukkan alamu kamar sunfi son tayi musu hidima a maimakon sauran bayi maza da ake dasu a wajen.
Ma'aikatar jin dadi da walwala kenan dake cikin masarautar qasar JOSHUN.
A wannan ma'aikatar akwai masu aikin kid'a,waqa,da kuma 'yan rawa mata da maza,wanda aikinsu shine nishad'antar da gidan sarauta a yayin da ake wani shagali a cikin masarautar. Ma'aikatar ta kasance ne a wani 'bangare a cikin masarautar,kamar yanda mukai bayani a baya,masarautar tana da girman gaske da duk wata ma'aikata tana cikinta ne.
Shukra ta kasance ita kad'ai ce baiwa mace a kaf fadin ma'aikatar,kuma ta kasance tana aikin share share,goge goge,wanki,taimaka wa ma'aikatan da kayan sawa,ko takalmi ko hula ko kuma daukan kayan aiki daga wani wajen zuwa wani.
Abinda yafi bawa kowa mamaki game da ita shine,ba'a san daga inda ta bullo ba,kawai wayar gari sukayi suka ganta a cikin ma'aikatar tun tana yarinyar da bata fi shekara 7 ba,amma tana qarqashin kulawar shugaban ma'aikatar.
A zaune take tana kallon wata farar takadda da dukkan alamu tunanin ta yayi matuqar nisa,leqawa nayi domin naga menene a cikin takaddar,wani zane ne mai matuqar qayatarwa,na malam bud'a (butterfly) anyi masa kalar ja mai dan turuwa(maroon) ta samanshi anyi abin maqalawa kamar abin maqala mukulli (key holder) ta qasanshi kuma igiya ce mai beza bazar bazar haka,abin sha'awa kamar ka dauka don kallon farko sai ka zata ba zane bane akan takadda tsabar yadda yayi kamar abin gaske ne a zaune a kan takaddar.
Wani matashin saurayi ne ya taho da gudu ya na qwala mata kira
"Shukrah shukrah " yana fad'a yana nufowa inda take a zaune,saboda yadda tai nisa cikin tunanin ta ne yasa bata san yana yi bama har sai da ya qaraso inda take ya tafa hannayensa a kusa da fuskarta sannan ta dan zabura ta kalle shi,cikin girmamawar da zata bawa wanda yafi ta a shekaru da kuma matsayi a ma'aikatar ta kalleshi tace
" yaushe kazo nan banji zuwanka ba?"
Gyada kai yayi sannan ya zauna a qasa yana fuskantar ta yace
"Shukra,duk cikin ma'aikatan nan kinfi kusa dani akan kowa,na dauke ki tamkar qanwata ta jini,amma ke naga alamar kwata kwata baki d'aukeni hakan ba" zare ido tayi ta bud'e baki cike da sakarci tare da cewa
"Ba haka bane maigida (boss kenan,domin shi ma'aikaci ne,ita kuma baiwa a ma'aikatar),babu abinda yake damuna,lapia qalau nake" ta qarasa cike da inda inda.
Kallon tuhuma ya bita dashi tare dasa hannu ya karbi takaddar hannun ta,ya dade yana nazarin abinda yake zane a kan takaddar kafin daga bisani ya dago kai ya kalleta,itama shi take kallo,yace
"Duk yadda akai akwai wani abu na rayuwarki da yake da alaqa da wannan abin saqala muqullin(key holder),amma tunda baki son ki fada ni ba zan yi miki dole ba,abinda nake so dake kawai shine ki rage zama ke kadai kina tunani don hakan zai iya zama illa ga nutsuwarki da ma rayuwarki gaba daya,ki manta abinda ya faru dake a baya domin ko baki fada ba,rayuwarki ta baya ce take saki a cikin wannan yanayin,ki fuskanci ta gaba"
ya qarasa tare da dora fuskar tausayi yana kallonta,murmusa wa tayi sannan tace
"Nagode maigida sameer,zan kiyaye hakan kuma yanzunnan zan fada maka abinda wannan zanen yake nufi a cikin rayuwa ta" ta qarasa tana wasa da 'yan yatsun hannunta tare da sunkuyar da kai qasa,shiru tayi na d'an daqiqai sannan ta fara da cewa
"Kwanaki kadan kafin nazo cikin masarautar nan,na rasa dukkan ahalina,dama ban tashi na samu mahaifiyata a raye ba,ina rayuwa ne tare da mahaifina sai kuma yayana,toh a wannan lokacin na rasa su gaba daya a lokaci daya,wanda alhakin mutuwarsu yana kan wasu mutane da ban san suwaye su ba,domin an d'ora musu sharrin laifin da basu jiba basu gani ba,hakan yasa Mai martaba sarki ya yanke musu hukuncin kisa" ta kai daidai nan yayinda kuka mai qarfin gaske ya qwace mata,shima fuskarshi fal tausayin yarinyar kuma ya kasa ce mata komai,don bai san dame zai fara ba,share hawayeta tayi sannan ta cigaba
"Wannan zanen key holder din da kake gani,na wata court lady ne,wacce na tabbar tana da alaqa da sharrin da aka yi wa ahalina,na taba haduwa da ita sau daya inda a wannan lokacin ne naga wannan abin maqullin a wajenta,kuma daga lokacin ban qara ganinta ba,na shigo cikin masarutar nan ne domin ina da yaqinin wata rana zan hadu da ita domin ta amsa min tambayoyina" ta qarasa hawaye na ta gangarowa daga idonta,bata damu da sharesu ba,domin ita kad'ai tasan irin quncin da take shiga a duk lokacin da ta tuna irin kisan rashin adalcin da aka yiwa ahalinta.
Cike da tausayinta ya kalle ta tare da cewa "kiyi haquri,ahalinki suna can suna hutawa in shaa Allah,kuma nayi miki alqawarin zan taimaka miki da duk abinda zan iya domin ki wanke baqin fentin da aka shafa wa ahalinki"
Kallon shi tayi da idonta da yake zubar da qwalla tace "Nagode maigida sameer,ba zan manta da karamcin ka a gareni ba" murmushi yayi yace "ba komai,dama manager ne yake nemanki nazo kiranki,amma ki zauna zan fada mishi ban ganki ba,in yaso zuwa anjima kya je ki gan shi" ya qarasa yana miqewa daga inda ya zauna,binshi tayi da kallo har ya bar wajen ba tare da tace komai ba,domin a halin da take ciki bata tunanin zata iya zuwa wajen manager domin yin wani aiki.
A cikin masarauta kuwa Hakimai ne jere a cikin fada,sun kai su 40,a gefe da gefen karagar mulki suke zaune a qasa kan carpet,goma a gaba,goma a baya,haka dayan bangaren ma goma gaba,goma baya.
A tsarin grand palace,hakimai sun rabu bangare hudu ne,akwai hakiman bangaren kudancin qasar,akwai na yammaci,akwai na gabashi sannan akwai na arewacin qasar.
Kasancewar babu gwamnati yasa masarauta ce take kula da komai na garin,saboda haka wadannan hakimai sune kamar ministers,akwai na bangaren ilimi,shari'a,tsaro,da sauran su.
Akwai zazzafar muqabala tsakanin hakimai na wadannan yankin basa shiri da wadancan yankin,kuma ko wanne yanki yana son wani nashi ya samu babban matsayi a kusa da sarki saboda su samu fad'a aji a masarautar.
A duk lokacin da sarki yake da wani hukunci da ya shafi masarauta,to suna da damar karba ko kuma yin tsokaci game da wannan hukunci kamar dai yadda akeyi a majalisa,dukkan hukunci yana zama cikakke ne tare da amincewarsu.
Kamar ko wane lokaci yau ma zaman fada akeyi,yayin da hakiman da suke a arewacin garin suke da jaa game da dawo da wata court lady da ta taba yin wani laifi aka koreta daga masarautar,yayinda ta kasance d'aya ce daga cikin ahalin hakiman kudu,su kuma hakiman kudu suna goyon bayan dawo da ita da za'a yi cikin masarautar domin su a ganin su wata dama ce a garesu.
Zazzafar tattaunawa ce a tsakaninsu yayinda mai martaba yana zaune akan karagar sa yana kallon kowa,ya riga da yasan menene a cikin rayukansu da dalilin da ya sa suke ta wannan cece- ku cen. Gyaran murya yayi da yasa kowa a wajen yin tsit,ya nisa tare da cewa
“Haqiqa mun fuskanci inda kowa a cikin ku ya dosa game da dawo da JALILA cikin masarautar nan,sai dai abinda zan fad’a muku guda d’aya ne,babu wani abu komai girman sa da zai hana dawowar jalilah cikin rayuwata”
Ya fad’a cike da iko da izzah ta cikakken basarake.
A lokacin na qare masa kallo sosai,matashi ne da ba zai wuce shekara arba’in da biyar ba,domin a cikin hakimansa akwai wad’and’a sun haife shi ma,sarki YA’AQUB NAUFAL kenan.
Yana da hasken fata sosai,idanunsa basu da girma can,sai dogon hanci siriri da ya ratsa fuskarsa,d’an sird’id’in saje ne a gefen fuskar sa sai dai bai barsu sun zubo har zuwa gemunshi ba,an katsesu ne daidai tsayin kunnensa,sai gemun da yake rage shi ba tare da yana barinshi yayi tsayi ba,a kallon farko zaka iya masa kallon sha-sha-sha ba don wannan alkyabbar mai zanen dragon 🐉 da yake sanye da ita ba,domin gaba d’aya bashi da suffar cikakkun maza,hakan ya samo asali ne daga sangarta shi da aka yi,ba shi da mu’amala da mutane,domin an raine shi tun yana yaro a matsayin yarima mai jiran gado,saboda haka karatunsa,da dukkan al’amuran rayuwarsa yana yinsu ne a cikin masarauta.
Tsit fadar tayi da jin furucin mai martaba,hakiman kudu har cikin zuciyar su sun ji dadin yadda sarki ya tsawatar kuka yayi amfani da qarfin ikon sa domin murtauke bakin hakiman arewa,wanda gaba dayansu sun cika da takaici akan dawowar jalila,domin kowa shaida ne akan irin son da mai martaba yake mata,kuma suna da yaqinin yana shirin dawo da ita ne domin ya aureta ta zama consort dinsa.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Page 5
Ranar da ya kama jalila zata shigo masarauta,a cikin bureu of music su sameer ne suke taya manyan masu kiɗa da mawaqa zuwa wajen taron cikar ranar haihuwar young prince,wajen gaba ɗaya kowa yana ta hada - hada,muryoyinsu kawai kake ji yana tashi"shukra miqo min hula ta" wancan yace "shukra ina igiyar rigata?" ita kuma tana ta kai kawo a tsakanin su tana yi musu duk abinda ya kamata.
Daga ɓangaren jalila kuwa an aika dogarai majiya qarfi da palanquin (wani abu ne da akeyi da katako kamar ɗan ɗaki,idan mace mai matsayi ce bata tafiyar qafa sai ta hau abin,maza majiya qarfi su dauko ta a kaita inda zata je) Yayin da ta gama shirin ta tsaf,cikin riga da skirt na silk sai alkyabba plain mara ado wacce ita special court ladies suke sawa,takawa takeyi cike da qasaita tazo har inda palanquin ɗinta yake,tsayawa tayi yayinda da sauri ɗaya daga cikin dogaran ya sa hannu ya buɗe mata qofar ta shiga ta zauna,ɗaukan ta sukayi har cikin masarauta kuma cikin quaters ɗinta.
Qarasowarsu keda wuya ta tarar da maids dinta su shida a jere suna jiran qarasowarta,suna zuwa bakin quaters ɗin dogaran suka ajiye palanquin ɗin yayin da senoir maid ɗinta ta matso ta buɗe qofar,qafa ɗaya ta fara zirowa waje,kafin ta fito da ɗayar qafar sannan ta fito da jikinta gaba ɗaya duk maids din da suke wajen da dogarai a tare duk suka rusunar da kansu tare ɗan lanqwasa wuyansu qasa kaɗan domin nuna girmamawa da dawowar ta cikin masarautar.
Kallon maids ɗinta tayi da murmushi a fuskarta kafin tace komai suka haɗa baki tare da cewa"Barka da dawowa cikin masarauta my lady" murmushin fuskarta ta faɗaɗa tare da ce musu "yauwa sannunku,kwana da yawa,da fatan na same ku lapia"
"Lafiyarmu qalau my lady,amma munyi kewar ku sosai da sosai" chief maid ɗinta ta faɗa cikin tsananin farin ciki,murmushi kawai tayi tare da fara tafiya,suna nan a tsaye har sai da ta gota su sannan suka bi bayanta a jere,chief maid ce a gaba,sai sauran maids din sunyi jerin biyu biyu suka bita a baya sai eunuch (dogari) guda ɗaya wanda shine kamar guard kenan da zai dinga bata tsaro (wannan tsarin haka yake ga sarki,sarauniya,mahaifiyar sarki wato dowager queen,consorts da kuma special court ladies,dole akwai maids da suke take musu baya,doka bata yadda da fitarsu su kadai ba duk inda zasu akwai masu bin su a baya) haka suka tafi suna biye da ita yayinda tayi hanyar quaters ɗin sarauniya haneefa.
A can quaters ɗin sarauniya hannefa kuwa,fitowarta kenan domin zuwa wajen birthday ɗin young prince,yayinda maids ɗinta suke tsaye suna jiran fitowarta a bakin qofar quaters ɗin,a jere suke a tsaye amma duk kansu a qasa,sun dan lanqwasar da wuyansu qasa,fitowarta keda wuya ta fara taka steps din da suke bakin wajen tana saukowa,suka biyota a baya,dowager queen ce tare da maids ɗinta suna take mata baya ta qaraso,da sauri sarauniya haneefah ta qaraso gaban dowager queen ta tsaya tare da rusunar da kanta har wuyanta qasa tare da cewa “Barka da zuwa queen mother” murmushi dowager tayi tare da dafa kafaɗar queen tace “da alama kin gama shiryawa ma,zamu iya tafiya” jerowa sukayi tare yayinda maids ɗinsu suma suka jero suka biyo bayansu suka ɗauki hanyar fita daga quaters ɗin queen,yayinda jalila itama take takowa ta inda su suke fitowa,gaba da gaba sukayi yayinda jalilah da maids ɗinta suka rusunar da kansu domin gaishe da queen da kuma queen dowager,jalila ce kawai ta ɗago kanta yayinda maids ɗinta har yanzu kansu yake a qasa,da murmushi akan fuskarta ta kalle su a jere sannan tace "Barkanku your majesty,Shigowata kenan nazo nayi paying respect a gareki” ta fada tana kallon queen Haneefah,queen dowager ce ta banka mata harara yayinda haneefah murmushi tayi har cikin ranta tare da cewa “barka da shigowa lady jalilah,kamata yayi kije ki huta ai yanzu,zaki iya komawa quaters dinki yanzu” jinjina kai tayi alamar gamsuwa tare da qara rusunar da kanta kafin ta juya,suma maids dinta suka juya suka bi bayanta suka bar wajen,kai tsaye quaters dinta ta koma.
Tana barin wajen dowager ta kalli queen haneefah tare da cewa “yarinyar nan tana wasa dani,don taga mai martaba yana kare ta,amma zanyi maganin ta,ke kuma harda wani sakar mata baki kina mata dariya” ta qarasa ranta a dan ɓace,murmushi haneefa tayi tare da cewa “Ni dawowarta bata dameni ba,domin nasan irin son da mai martaba yake yi mata ko ni baya min irin shi,bani da matsala matuqar dai zaman ta a nan zai bawa mai martaba farin ciki” ta qarasa fuskarta babu yabo babu fallasa,haka suka taho suna zantukansu har suka qaraso filin da ake birthday din,shigowarsu ke da wuya duk manyan baqin da aka tara a wajen,da sauran mutane da aka gayyato kowa ya miqe tsaye tare da rusunar da kansu qasa domin girmamawa a garesu,babban fili ne mai girman gaske,an qawata shi dogayen tebura ta kowanne ɓangare yayinda kujerun suke a jere,nan ne inda hakimai da ministoci da matansu da sauran manyan baqi suke zaune,yayinda aka shimfida wani carpet na alfarma a qasa shima gefe da gefe aka bar hanyar wucewa kawai,a kan carpet din wasu qananan pillows ne masu faɗi kuma basu da tudu sosai wanda a kansu ne ake zama,sai tebur dan qarami daidai yadda mutum zai iya cin abinci a inda yake zaune a qasa, can sama kuma matattakala ce sai qatuwar kujera mai kama da karagar mulkin qasar da adon dragon 🐉 a jikinta,hakan ya tabbatar min ta mai martaba ce ,inda nan na hango shi a zaune yana ta murmushi,queen ma tare da queen dowager nan suka hau yayinda queen ta zauna akan kujerar da mai martaba yake a kusa dashi,a gefen wannan kujerar tasu ne akwai kujeru a gefen dama da kuma hagu,ta hannun dama young prince da yau ake cika shekaru takwas a duniya a zaune cikin shiga ta alfarma,yayinda ta hagun queen dowager ta zauna,zamansu keda wuya duk sauran mutanen wajen suka zauna suma nan aka fara gudanar da taron.
Young prince ne ya taso daga kujerar da yake yazo gaban kujerar da mai martaba da queen haneefa suke ya rusunar da kanshi ya gaishesu,sannan sai ya yi qasa ya durqusa ya lanqwasa qafafuwansa ya zauna a kansu kamar dai zaman tsakanin sujjada biyu,nan ya sake yin qasa da kansa domin cika gaisuwar sa,mai martaba cikin murmushi ya fara da “ina taya ka murnar zagayowar ranar haihuwar ka,Fatan albarka da alkhairi a cikin rayuwarka” haka nan ma sarauniya ta sa masa albarka sannan ya miqe tsaye ya qara rusunar da kanshi ya koma ya zauna a kujerar sa.nan take aka umarci masu kiɗa da su fara nishadantar da mutanen da suke wajen,Cikin qwarewa suka fara kidan a tare,sautin kidan ya fara fita amma ba yadda ya kamata ba,melody din kidan kwata kwata ya kasa fita yadda ya kamata,wanda keyi musu umarnin tsayawa ne ya tsayar dasu sannan ya qara yi musu umarnin su fara,hakan ce ta qara faruwa har sau biyar,daɗin sautin kiɗan yaqi fita gaba daya,firgici ne ya bayyana a fuskokin ministers da hakimai da suke zaune kamar dai akwai wani abu da ya tsorata su a dalilin rashin fitar salon kidan yadda ake so.
A can bureu of music kuwa,su sameer basa cikin wanda suka zo wajen bikin birthday din,suna zaune wasu daga cikin fadawan sarki suka shigo tare da bada umarnin sarki na suje ayiwa jalilah kidan barka da shigowa,hakan yasa su sameer suka shirya suka tafi zuwa quaters din jalila,tana zaune a sitting room dinta chief maid dinta ta shigo da sauri tare da ce mata “My lady,masu kida ne daga mai martaba ya aiko ayi miki na barka da zuwa” farin ciki ne mara misaltuwa ya lulluɓe ta tare da tashi da sauri ta fito bakin qofar quaters dinta,nan ta hango su suna shirin zama tare da shirya kayan kidansu,kujera aka kawo aka ajiye mata a nan ta zauna har suka gama shirinsu tsaf suka fara kidan,sai dai irin matsalar da aka samu a can ita aka sake samu a nan,domin salon kidan baya fita kwata kwata,haka sukai ta gwadawa amma abin ya gagara,firgici ne sosai akan fuskokin maids dinta game da abin da suka gani yayinda ita bacin ranta kawai bata samu damar jin sauti mai dadi ba domin shauqin soyayyarta da mai martaba.
Da alama dai jalila bata san dalilin da ya sa sautin kidan yaqi fita a ranar da ta shigo cikin masarautar ba,amma na tabbata hakimai da kuma maids dinta sun sani domin yadda fuskokin su suka nuna kadai ya isa shaidar hakan,to ko me yake faruwa kuma?
Nima maryam na tambaya amma basu bani amsa ba.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Page 4
Washegari tun da sassafe chief eunuch ya turo mutane bureau of music domin a nemowa mai martaba gwanin busa algaita,yayin da shukrah tana can ta dauki hanyar shiga cikin gida domin zuwa taya bayin ciki aiki,hankali a tashe manager yake nemanta,hanyar fita daga wajen ya nufa,nan take ya hango bayanta tana tafiya hanyar shiga cikin gida,da sassarfa ya qarasa wajenta,yayi qasa da murya yace
“Ina kika shiga tun dazu ina nemanki? “ zaro ido tayi tana kallonshi don yanayin da yayi magana ya tabbatar mata ba lapiya ba,tace
“Ranka ya dade lapiya kuwa? Dama da ina fitowa naga dogarai suna shiga cikin ma’aikatar mu,Allah yasa ba wani laifin mukayi ba”
Kallonta yayi cikin damuwa yace
“Ai ke suka zo nema,mai martaba yaji busa algaitar ki jiya da dare,shine ya turosu su nemo wanda yayi busar” ya dan nisa sannan ya cigaba “Ban san ya zanyi ba idan suka san servant girl ce take amfani da kayan kidan masarauta,kashi na ya bushe” ya fada cikin damuwa,sameer ne ya qaraso wajen da qullin kaya a hannun sa,manager ya juya kalleshi tare da cewa
“Yauwa sameer kawo kayan nan” ya fada yana karbar kayan daga hannun sameer,tare da miqawa shukra yace
“Ga kaya nan,ki tafi can maqera da take wajen masarautar nan,suna buqatar mai taimaka musu da aiki kafin a gama nemanki sai ki dawo” rau rau tayi ido kamar zatayi kuka tare da cewa
“Amma ranka ya dade yanzu fa cikin gida zan shiga in taya su aiki,ai babu wanda zai gane ni”
“Kiyi maza ki fice daga nan ki tafi inda nace miki yanzunnan kafin ranki ya baci,ni zaki janyo wa masifa ace ina barin servants suna amfani da kayan masarauta? Maza ki wuce” ya fada mata a fadace tare da nuna mata hanya,sameer ne yace mata
“Kiyi haquri wani lokacin sai kije ki taya su aikin,amma yanzun tafiyar ki ita tafi muhimmanci saboda kada dogaran sarki su gane ki” gyada kai tayi fuskarta abin tausayi tare da juyawa ta bar wajen.
A cikin fada kuwa ana ta shirye shiryen dawowar jalila cikin masarautar,musamman uban gayyan mai martaba,yana zaune cheif eunuch ya shigo ya gaishe da mai martaba tare da cewa “Ranka ya dade ba’a samu mai kidan algatar ba,mun tambayi kowa amma basu gane waye yayi kidan jiya ba” cikin mamaki mai martaba yace
“Ikon Allah,amma kaima kaji kidan jiya ko? Da ni kadai naji sai nace gizo kunnuwa na suke yi min” murmushi chief eunuch yayi,mai martaba ya qara da cewa
“Dama ina son ko waye yazo yayi wa jalila ranar da zata shigo,domin tana son kidan algaita,kuma ina shirin tana shigowa zan bata matsayin CONSORT domin hakan zai qara qarfafa hakiman kudu sosai,domin ita din daya ce daga cikin ahalinsu” shi dai chief eunuch murmushi kawai yake yi,domin ya dade bai ga mai martaba a cikin farin ciki irin wannan ba.
A bangaren jalilah itama nata shirye shiryen yayi nisa,tana kuma cikin matuqar farin cikin komawa cikin fada domin tasan hakan yana nufin aure tsakanin ta da mai martaba abin qaunar ta,amma akwai abinda ko yaushe ta tuna sai hankalinta yayi matuqar tashi,wani bawan Allah da bata san waye shi ba tun shekaru bakwai da suka wuce ya fada mata abinda ko da yaushe idan ta tuna annurin fuskarta yake daukewa ta shiga cikin damuwa da rudewa,amma duk wannan ba zai mata magani ba,dole ta jira rayuwa ta gasgata ko kuma ta qaryata mata abinda mutumin nan ya sanar da ita.
Miqewa tayi ta dauko wani dan qaramin akwati,bashi da fadi sosai sai tsayi,budewa tayi nan take keyholder ya bayyana,irin wanda shukra take da zanen shi a hannunta,daukowa tayi ta riqeshi a hannunta tana dubawa a hankali tace
“Wannan abin shine mafi soyuwar kyauta a gareni,shine shaidar soyayya ta da maimartaba,ko da yaushe ririta shi nakeyi ina kaffa kaffa dashi amma gashi ya fara tsufa” ita kadai take fadawa kanta hakan,daga bisani ta miqe,ta dauki wata alkyabba plain ta saka a jikinta ta fito,kai tsaye maqera ta tafi da keyholdern ta a hannunta.
Tana shigowa maqerar duk ma’aikacin da ya ganta a hanya sai ya tsaya ya dan risinar da kanshi alamar gaisuwa,sannan ya wuce,kai tsaye wajen shugaban maqeran ta tafi,kanta tsaye ta shiga cikin office dinshi yana zaune,dago kai yayi yaga lady jalila ce,da sauri ya tashi daga inda yake yazo gabanta ya rusunar da kanshi tare da cewa
“Barka da zuwa my lady” murmushi tayi ba tare da ta amsa ba,taje kan kujerar da ya tashi ta zauna,har yanzu yana tsaye kanshi a qasa,ya qara rusunawa yace
“Wane irin taimako zan miki my lady?” Cikin qasaita ta kalleshi tare da cewa “Abin muqulli na ne ya tsufa nazo a sabunta min shi” ta fada tana miqa masa keyholder dinta tare da ajiye shi kan tebur din dake gabanta,cikin rawar jiki ya dago kanshi ya dauki keyholder din tare da cewa “At your service My lady” sannan ya juya ya fita,dawowa yayi da takadda sai kuma brush (kamar brush din da masu kwalliya suke amfani dashi,domin a wancan zamanin babu biro,ink ne ake narkawa sai a sa brush ayi rubutu) yana shigowa kanshi a qasa yazo daidai tebur din da jalila take,ya qara rusunawa tare da cewa “With your permission my lady” wato yana son ya zauna ne,amma sai da izinin ta,ba tare da ta kalli inda yake ba ta bashi amsa “Zaka iya zama” dan qarasowa yayi yaja kujerar da take kallon tata,amma sai ya mayar da ita gefe kadan sannan ya zauna,a hankali ya fara zanen keyholdern da ta kawo,tana zaune tana kallon me yake yi har ya gama zanenshi tas,zanen ya fito sak iri daya da wanda shukra take dashi a hannunta,tashi yayi domin tafiya can bangaren masu aikin sassaqa katako ya kai musu domin su yanka irinshi kuma suyi masa paint kalar maroon kamar yadda ya zana.
Cikin abinda bai wuce minti talatin ba aka gama mata komai aka kawo mata sabon da tsohon keyholder dinta,ta tashi ta bar wajen.
Shukrah kuwa tana can tana ta aikin ta a wani waje da suke hada wani abu da farin dutse,farin dutse ne ake fasa shi sai ayi masa wani shape cikin gwanancewa domin yana da matuqar amfani wajen fitar da sautin kid’a,ji tayi an bude qofar wajen a hankali an shigo cikin sanda,dago kanta tayi don taga waye mai shigowar,wani ma’aikacin su ta gani,shi har yanzu bai kula da mutum a wajen ba,a hankali cikin sanda yake tafiya yana kalle kalle,sai da yazo dab da ita yana ta kallon baya,juyowar da zaiyi ya ganta sai ya zabura,zare ido yayi tare da cewa “kin tsorata ni sosai,me kike a nan” cikin sakarcin ta tace masa “aiki aka saka ni nayi polish din wadannan duwatsun” murmushi yayi yace mata “yi tafiyarki kawai zan qarasa” zaro ido tayi tace masa “an ce fa na gama kafin 5 na yamma” dan sassauta murya yayi yace mata “Ehh kiyi tafiyar ki,kinga tunda na fiki iyawa ma ai zan fiki saurin gamawa” tana jin haka cikin murna kuwa ta fito,fitowar ta kenan manager ya hango ta,da hannu yai mata alamar tazo,ta qaraso gabanshi ta rusunar da kanta qasa tare da cewa “barka da yamma my lord” murmushi yayi tare da cewa “kema sannunki,ga takaddun zanen aikin da akayi yau,ki dauka kije rijiyar da ake hada wuta ki zuba su a qona” qara rusunawa tayi tare da cewa “Yes my lord” sannan ta wuce da sauri ta shiga office din,takaddun ta gani a cikin wani bakitin qarfe,ta dauko ta nufi hanyar rijiyar dasu,zuwanta ke da wuya ta fara zazzage su tana kawar da fuskarta saboda hayaqi,sai da ta gama zazzage su tas sannan ta juya tana kallon yadda suke qonewa,wata takadda ta hango da maroon din kala,da sauri ta sa hannu ta zaro gefen da bai fara qonewa ba na takaddar,a qasa ta ajiye ta ta fara tattake inda wuta take ci,nan da nan wutar ta mutu ta qara daukowa tana kallo,sak irin zanen da yake hannunta,dan yatsan ta ta saka ta lakuto ink 🖋️ din da akayi zanen dashi,ta ga danyen ink ne ko gama bushewa baiyi ba,ai da gudu ta bar wajen zuwa inda kayanta suke,waccar takaddar ta hannuta ta dauko ta hada su taga babu bambanci,ta qara fitowa a gigice sai wajen masu sassaqa katako,nuna musu abin tayi wani ma’aikacin wajen yace mata “Wanda yayi aikin ya tafi garinsu yau,sai wani satin zai dawo aiki” fitowa tayi ta nufi office din manager,tana haki ta shiga tare da cewa “My lord Dn Allah wannan zanen na abin muqulli waye ya kawo shi” kallonta yake cike da mamakin dalilin da ya sata wannan gudun,kawai dai ya bata amsa “Na wata court lady ce ta kawo akayi mata sabo” runtse ido tayi gam cikin takaici,ya qara ce mata “me yasa kike tambaya?” juyawa kawai tayi ta bar office din ba tare da ta ce mai komai ba.
Dakin da aka bata ta koma ta zauna,da zanen duka guda biyun tana kallon su qwalla na cikowa a idonta,a zuciyarta take fadan
“Yanzu shekara bakwai kenan da rasuwar babana da yayana amma na kasa yin komai cikin tsawon shekarun,ga dama na gani yau amma ta kufce min,naso zuwa cikin fada na taya su aiki amma shima na kasa samun damar” ta sunkuyar da kanta haqaye na zuba a idonta ba tare da ta samu damar share su ba.
“Shukrah,Shukrah “ taji ana qwala mata kira,
Muryar sameer ne,da sauri tasa hannu ta goge idonta,ta dan saisaita kanta,shigowa yayi ya tarar da ita zaune a qasa da takaddu biyu a hannunta,zama yayi shima tare da duba abinda ke hannunta,kallon yanayin ta yayi,yace “kinzo nan babu mai kula da ke kika shigo nan kina aikin kukan ko? To ki shirya mu tafi yanzu” wata qwallar ce ta zubo mata ba tare da ta sani ba,kafin tace komai sameer ya qara cewa “A ina kika samo irin wannan zanen da kike dashi kuma?” Share hawayen tayi
“A nan wata court lady tazo aka yi mata irin shi” ta fada a taqaice,cikin murmushi yace mata “kin hadu da ita kenan? Itace wacce kike nema ko? Kin samu abinda kike buqata a wajenta?” Duk ya jero mata tambayoyin,kwabe fuska tayi tace “Ni ban ganta ba,mai aikin sassaqa katakon kuma ya tafi,manager ne ya fada min na wata court lady ne” sameer yai saurin cewa “meyasa shi managern baki tambaye shi wacece ba? “
Tace “ba zai san wacece ba tunda bashi yake yi ba,wanda yakeyi din kuma lokacin da na ga abin ya riga ya tashi kuma sai wani satin zai dawo aiki,kaga kuwa ba zan samu sanin wacece ba” gyada kai sameer yayi sannan yace mata “kiyi haquri yanzu ki tashi mu tafi ko?” Ba tare da tace masa komai ba ta miqe ta hada sauran kayanta ta qulle a abinda tazo dashi ta fito suka tafi.
A bangaren jalila kuwa tana komawa gida (tana zaune ne a wajen mariqin ta,minister na tribunal) ta tarar dasu suna magana a farfajiyar gidan minister da babban danshi mai suna jameel kamar cikin rashin nutsuwa,qarasawa tayi kusa dasu tare da cewa “lafiya kuwa na ganku haka? Ko wani abin ne ya faru a gidan?”
Juyowa sukai a tare gaba dayansu suka kalleta,jameel ne ya ce mata “mun fahimci kamar dowager queen tana da wani qulli da ta shirya ranar da zaki shiga cikin masarauta” cikin rashin fahimta tace “me kake nufi da haka?”
“Ta shiryawa young prince(qaramin qanin mai martaba ne) taron murnar zagayowar haihuwar sa,kasancewar shi dan consort din da tafi tsana ne yasa bata taba bashi muhimmanci irin wannan ba,shiyasa muke tunanin akwai wani abu da take shiryawa,kuma ko menene yana da alaqa da ma’aikatar kida(bureu of music)”
Jinjina kai tayi cikin zurfin tunani ba tare da tace komai ba,jameel ya qara cewa “ ko zaki canza ranar ki qara ko kwana biyu ne saboda mu kaucewa ko ma me suke qullawa” girgiza kai tayi tace “A’ah bana son na kaucewa ko me suke qullawa,domin idan na kauce dole zasu qara qulla wani,a zaman da nayi a baya a masarautar na san yadda komai yake gudana,idan baka iya siyasa ba,ba zaka iya rayuwa ba saboda haka daidai nake da ita”
Sai a lokacin hakimi ya ce “Wannan haka yake jalilah,shiyasa na san duk inda zaki shiga ba zaki bani kunya ba”.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Whattpad :Oum_tasneeem
Page 6
‘Yan surutai ne suka fara tashi qus qus daga Ɓangaren hakiman arewa,mai martaba ne yayi wa chief eunuch alama da hannu nan take ya juya shima ya bawa na bayansa umarni,shi kuma ya juya ya sauka daga kan inda suke zuwa inda shugaban masu kiɗa yake,magana yayi masa a kunne ya juyo ya dawo inda yake,yayinda shi kuma shugaban masu kida ya fara yiwa mutanen sa alamun su tashi da su da kayansu su bar wajen.
Mai martaba yayi hakan ne domin hana cece-kucen da zai tashi a dalilin matsalar da aka samu,sai ya kasance kowa jikinsa babu dadi hakan yasa aka tashi taro kowa ya watse.
A wajen jalila ma hakan ce ta kasance domin kiɗa yaqi daɗi,hakan yasa ta sallame su suka tafi.
Minister of state affairs ne a durqushe gaban queen dowager,dukkansu babu mai cewa komai,shi ne yayi qarfin halin cewa
“Yanzu shikenan mun shiga uku an kawo mana annoba cikin masarauta Your Majesty” ya fada muryarsa cike da takaici,murmushi queen dowager tayi tare da kallon shi tace
“Ai jalila da ni take zancen,da qafarta zata gudu daga cikin masarautar nan don sai nasa zaman gidan nan ya gagare ta” ta qarasa cike da mugun nufi a ranta,minister da yake cikin alhini yayi mata kallon rashin fahimta,yana qoqarin bude baki yayi mata tambaya ta dakatar dashi da hannunta sannan ta dora da cewa
“Da me kuke tunani? In zauna in nade hannu na jalila tazo ta haifar wa mai martaba da,inaaa ba zai yiwu ba ace jininta zai hau kujerar mulkin garin nan,sannan abu na gaba ina umartar ka da ka rufe bakinka gum,bana buqatar maganar nan taje kunnen kowa ko da kuwa sarauniya haneefa ce”
Gyada kai yayi alamar ya ji ba tare da yace komai ba,ya miqe tsaye ya rusunar da kanshi ta gefen da queen dowager take sannan ya fice yana ta saqe saqe a ranshi.
Cikin masarauta yau ta rikice,kowane lungu da saqo duk inda ka leqa bayin gidan na munafurcin ai jalila annoba ce,domin a camfin su babbar annoba ce ace sautin kida yaqi samuwa toh lallai akwai wani mugun abu da zai faru,haka aka cigaba da yadawa har yazo kunnen jalila.,hankali tashe take qwalawa chief maid dinta kira
“Halisa,halisa,halisa” da gudu ta fado dakin domin daga jin kiran da ake mata ba na lapia bane,tazo ta durqusa a gaban uwar dakinta tare da cewa
“Gani my lady,lapia kuwa?”
Cikin muryar tashin hankali jalila tace
“Ki fada min wace magana naji tana yawo a cikin gidan nan? Me hakan yake nufi?”
Halisa da bata tsammaci jin maganar jita-jitar dake ta yawo a gidan a kunnen uwar dakin tata ta dan sunkuyar da kai tare da cewa
“Rqnki ya dade…” shiru tayi ta kasa qarasawa
“Ki fada min nace “ jalila ta fada cikin tsawa,halisa da ta firgice da jin tsawar ta fara magana cikin rawar jiki
“Ki gafarceni my lady,kasancewar a yau an rasa melody 🎶 na kida,yaqi fita yadda akeso ne yasa….” Qin qina ta fara
“Yasa meee? “ jalila ta tambayeta cikin qaguwa da jin abinda halisa zata fada mata
“ shine ake alaqanta hakan da dawowarki cikin masarauta yau da annoba (bad omen)” ta qarasa tana mai qasqantar da kanta,dafe kai jalila tayi a cikin zuciyarta tana fadin
“Wannan shine shirin queen dowager kenan,don nasan ba aikin kowa bane face nata” a fili kuma ta kalli halisa tare da cewa
“Ayi min shirin zuwa GRAND PALACE sannan ku sanar musu da zuwana” tana gama fadin haka ta juya ta zauna a mazauninta da yake wajen tare da fadawa zurfin tunanin mafitar halin da zata iya shiga a dalilin wannan abin,domin indai har masarautar da ta sani ce,ta san ministers din arewa sai sunyi wa mai martaba petition (qara) game da ya qara duba hukuncin sa na shigo da ita masarautar kuma tasan matuqar dai suka fishi hujja to sai abinda suka ce domin zasu bada hujjar suna kare qasar su ne daga annoba.
Tana cikin wannan tunanin ne Taji shigowar halisa,rusunar da kanta tayi tare da cewa
“Shirye shirye sun kammala my lady,babbar fada suna shirin zuwanki”
Alkyabbar ta ta dauka wacce take plain ce babu adon komai a jiki ta yafa sannan suka fito,maids dinta da suke tsaye a bakin qofa ne suka bi bayansu har grand palace,a bakin grand palace suka tsaya yayinda aka yi mata iso zuwa ga mai martaba,qofa aka bude mata ta shige su kuma maids dinta suke jeru a gefen qofar da ta shiga suna jiran fitowar ta.
A can bureu of music kuwa sun duqufa wajen gani dalilin da yasa yau melody din kidan su yaqi fita,tare da damuwa a cikin ransu,domin su masu yadda ne da camfi qwarai da gaske hakan yasa suke ganin kamar wani mugun abu zai faru a cikin garin ne shiyasa aka samu matsala da melody din,shukra ce ta kalli manager tare da cewa
“Amma ranka ya dade,baka ganin ko matsala aka samu da wani abin daga cikin kayan kidan?” Kallon banza ya watsa mata tare da cewa “har yaushe wannan yarinyar ta fara aikin zama mai gano matsalolin kayan kida?”
Sameer ne ya qunshe bakin shi da dariya,yayin da ya kalli manager yace
“Yallabai ka qyale shukra da shirmen ta kawai” dan qasa yayi da murya kuma ya qara matsawa kusa da kunnen manager tare da cewa
“Ana ta cewa hakan yana da alaqa da dawowar lady jalila ne,haqiqa ita din annoba ce ga masarautar nan”
Manager da ya dauki maganar da muhimmanci amma yana tsoron wani ya jisu suna yi ya toshe bakin sameer tare da rada masa
“Idan ka bari wani ya jika kasani a bakin ranka ne”
Shiru sameer yayi tare dan yin murmushi,ya kalli shukra yace mata
“Tashi muje waje”
A hankali suke takowa har bakin qofar office din manager,shukra ce tace
“Nifa yallabai ina ji a raina kamar akwai wani abu da yake faruwa,don ni gaskiya ban yadda da camfin nan ba”
Sameer ne ya kalle ta tare da cewa
“Ke dai rigimar ki yawa ce da ita shukra,abinda kika ji ana fada gaskiya ne,lady jalila ce annobar da tasa hakan ya faru,don hakan alama ce qarara da take nuna faruwar wata annoba tun zamanin iyaye da kakanni”
Gyada kai shukra tayi tare da cewa
“Zan gwada dubawa na gani,ko zan samu wani abin da zan kafa hujja dashi,kuma kafin kace min komai ni bana buqatar taimakon kowa,amma zan qoqarta don har naji lady jalila tana bani tausayi duk da ban santa ba”
Kafin sameer yace wani abu shukra tayi gaba ta barshi a wajen,kallo ya bita dashi yace
“Shukra kenan,Ina fatan kada ki janyo mana abinda ba zamu iya ba”
Shukra kai tsaye dakin baccinta ta nufa tare da canja kayan jikinta,domin idan ta fita da kayan da take sawa duk wanda ya ganta zai gane cewar ita baiwar masarauta ce,hakan yasa ta canja domin tana son ta fita wajen masarautar ta dan sha iska.
A grand palace mai martaba ne yake kwantar wa da jalila hankali,cikin tattausan lafazi yake ce mata
“Bana son ki dinga damuwa akan abubuwa irin wannan,kin ga dawowar ki kenan bamu hadu domin muyi wa juna farin ciki ba sai dalilin bacin rai”
Marairaicewa tayi tare da cewa
“Your majesty ina tsoron ministers din north zasu iya yi akan wannan issue din,na san zasu daga maka hankali akan sai ka qara korata daga masarautar nan” ta fada kamar zata yi kuka
“Jalilahh” dago kanta tayi jin yadda ya fadi sunan nata cikin nutsuwa,bata ce komai ya cigaba
“A wannan karon babu abinda zai raba ni da ke,kin shigo kenan cikin masarautar nan kuma nan da kwanaki kadan zan mayar dake mallaki na domin in qara baki kariya ta musamman,domin matuqar na daga darajar ki a cikin masarautar nan to babu mai iya nuna miki yatsa,abinda nake so dake shine kawai ki qara haquri”
Cikin wani yanayin damuwa da cakude da farin ciki jalila ta murmusa tana kallonshi tare da cewa
“Na yadda da kai your majesty kuma na yadda da son da muke wa junan mu,zan jira har ranar da zaka alqawarin ka”
Ta qarasa cikin murmushi
“Yauwa my lady jalilah,ya kamata ki zama jaruma sosai,domin zama matar sarki sai jarumar mata”
Dariya sosai maganar shi ya bata domin cikin barkwanci ya fadi hakan,hakan yasa ta sake sosai suka cigaba da hira,daga bisani ta tashi ta fito maids dinta suka bi bayanta suka koma quaters dinta.
Mai martaba shima daki ya shiga ya cire dragon robe dinshi (kamar alkyabbar da take nuna shi sarki ne) ya dauko normal robe da kowa yake sawa ya dauko wata baqar hula malafa mai dan shara shara abin kyau ya saka a kanshi,yana gama shiryawa tsaf ya fito bakin grand palace,chief eunuch yana ganinshi a haka ya san yau akwai yawon rangadi kenan (lokaci zuwa lokaci mai martaba ya kan shiga gari cikin irin kamannin da babu wanda zai gane shi,kuma baya fita guards din masarauta sai dai private guards wanda suma basa saka uniform dinsu sai dai su saka kaya irin wanda kowa ke sawa,kuma suna gadin shi ne daga nesa nesa,kasancewar a wancan zamanin babu camera ko wayar daukar hoto yasa idan har ba kusa sosai kake da sarki ba toh mutanen gari basu san fuskar shi ba)
Guards din ma suna ganin haka,suka bar wajen,chief eunuch ne yayi aike a sanar da orivate guards cewar zasu fita da mai martaba,yayin da kowa ya hallara suka dauki hanyar fita daga masarautar da qafa.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Whattpad :Oum_tasneeem
Page 7
Shukra tana cikin tafiyarta tana ta kalle kalle don ta dan jima bata shigo cikin gari ba,nan take yarintar ta ta ringa zuwar mata a cikin tunanin ta,duk inda ta wuce sai ta tuna wani abu da ta taba yi a wajen,a cikin haka ne ya buge wani mutum bata sani ba,juyowa tayi da sauri jin ta buge abu ta ganshi fuskar nan a murtuke yana kallon qasa,idonta takai inda taga yana kallo nan taga wasu fararen duwatsu ne suka zubo daga cikin wata jaka da take hannun sa,da sauri ta tsugunna ta fara kwashewa tana cewa
“Kayi kin afuwa,kayi haquri ban ganka bane”
Tana bashi tana kwashe mai duwatsun sa,daga bayansa wani mutum ya taho da alama tare suke dashi
“Mutumina me ya hada ka da yarinya?”
Dago kai shukra tayi domin taga mai magana,lokaci daya ta qura masa ido tana son ta tuna a ina ta taba ganin fuskarsa,yayinda shi kuma tuni ya gane ta,basarwa tayi ta cigaba da taince fafaren duwatsun tana mayarwa cikin jakar har sai da ta tsince su tsaf suna tsaye,mutumin da yazo daga baya ne yake ta rarraba ido yana Allah Allah su bar wajen don da dukkan alamu shujra bata gane shi ba,hannayenta ta dago zata karkade sai taga burbushin farin abin da ta kwashe,nan take mamaki ya kamata da sumulmulallun duwatsu zasu yi burbushi haka,hannunta takai zuwa baki ta dandana abinda yake hannunta
“Gishiri “ ta furta da qarfi tare da tofar da yawu,a birkice suke kallonta,wanda ta zubar wa da kaya ne ya zaro wuqa a qugunshi,ganin haka shukra ta juya da gudu suma suka bita a baya,gudu takeyi sosai ba tare da ta san laifin da tai musu suke binta ba,lungu lungu take shiga har tazo wani waje kamar akurki ta shige ta buya,tana shiga su kuma suna qarasowa wajen suka tsaya suka rasa inda tayi cikin haki wanda ya gane fuskar shukra yacewa dayan
“Wannan yarinyar fa idan bamu samota ba tona mana asiri zatayi,na gane ta servant girl a bureu of music,kuma ranar da mukai akin nan tana cikin maqerar don a hannunta ma na karbi aikin nayi” ya qarasa cike da firgici da kuma takaici,dayan ne yace
“Kai kabi nan hanyar,nima zanbi nan,sai mun nemo ta mu gama da ita”
Haka suka rabu kowa yabi hanyarsa daban suna neman shukra,sai da ta tabbatar sun yi nisa da wajen sannan ta fito tana karkade kayanta,wani mutum ta hango yana tahowa ta dan tsorata har ta kasa motsi,zuwanshi kusa da ita ta gane ba su bane,a daidai lokacin kuma suka dawo ashe wayo sukai mata,ganin wannan mutumin da yazo wucewa ta kusa da ita sai suka zata ko tare suke da shukra,takobi suka ciro masu tsayi sosai suka nuna su da ita,take wanda yake tare da shukrah ya rikice har ya fita shiga tashin hankali,kallonta yayi yace
“Menene haka? Suwaye su? Me mukai muku? Ni ban san wannan yarinyar ba fa”
Duk a tare ya jero wadannan tambayoyin cikin tsananin firgici,shukra ce ta duqusa qasa cikin hikima kamar ta sadida,da sauri ta damqi qasa a hannayenta tare da watsa musu a ido,hannun mutumin nan ta kamo da gudu suka bace a wajen kafin su gama share qasar idonsu sun bace musu.
Gudu sukeyi sosai yayinda ya fara haki amma shukra janshi take,tsayawa yayi tare da tsayar da ita itama yace
“Nifa na gaji,daga ganinki fitinanniyar yarinya ce,me ya hada ki da wadannan mutanen?”
Kallonshi take cike da mamaki tare da cewa
“Karka qara ce min fitinanniya,dan gudun da mukayi shine ka gaji? Ka tashi mu qara gaba kafin su qara biyomu ko na tafi na barka a nan”
Bata fuska yayi
“Toh ni ai tunda nake a rayuwata ban taba gudu irin wannan ba shiyasa”
Shukra mantawa tayi da halin da suke ciki ta sheqe da dariya tare da nuna shi da hannu
“Na san dai daga ganin kayan daje jikinka kai dan gata ne,amma dan wannan gudun kace baka taba yi ba? Raina min hankali kawai kake so kayi”
Bai bata amsa ba suka hango mutanen da suke biyosu amma wannan karon suna da yawa don sunkai kusan su shida,da sauri ta jawo hannunsa suka maqale a jikin katanga yadda ba za’a gane da mutum a wajen ba saboda duhun dare,har suka zo suka gifta su tare da shigewa gidan da su shukra suka buya a jikin katangar shi,da yake guntayen katanga ne ana iya hango farfajiyar gidan,shukra ce ta dan dago kanta kadan tare da leqawa cikin gidan,ganinsu tayi sun je wajen wasu buhunhuna masu yawa sun fara jidarsu suna zagayawa cikin gidan inda bata iya hangowa,suna tafiya suna maganganunsu,wanda yace ya ganeta ne yake cewa dayan
“Muyi maza mu zubar da wadannan sauran abubuwan tunda sun gama amfani,dama ni kudin da na samu sun ishe ni na gina sabuwar rayuwa ba tare da na koma aiki a maqera ba,ai godiya mai yawa ga queen dowager”
Dayan ne ya bashi amsa da cewa
“Gaskiyar ka fa,gara muyi sauri mu zubar dasu a daren nan kafin yarinyar nan ta koma masarauta ta tona mana asiri,don matuqar aka gano mu muka lalata salon kidan masarauta to zamu biya da rayuwarmu ne”
Mamaki ne da firgici kwance a kan fuskar shukra,ta juyo ta kalli wanda suke tare
“Mallam ka taimaka min da wani aiki mana,mutanen nan ina ganin basu da gaskiya,naji suna maganar lalata salon kida kuma dama ina son bincike akan hakan,ko zaka taimaka min ka haura nan mu shiga gidan nan”
Cikin wani irin yanayi da ba zata iya fassara shi kai tsaye ba yace
“Haura katanga? Ba zan iya ba gaskiya,ni ban taba haura katanga ba a rayuwata”
Dariya ta sheqe da ita tana nuna shi irin ya sharo mata qarya dinnan
“Kai….. kai baka taba haura katanga ba…” ta cigaba da dariyarta “Amma dai wasa kake ko? Ko kuma kawai kace ba zaka taimaka min ba” idonsa a kanta ya qara jaddada mata
“Da gaske ni ban taba haura katanga ba,katangar gidan mu tsayi ne da ita da mutum ba zai iya haurawa ba kuma a cikin gidanmu nayi makaranta da komai shiyasa ban iya ba”
Shiru tayi kamar mai nazari a yayin da take qara jiyo maganar mutanen sama sama a cikin gidan,kallonshi ta qara yi tare da cewa
“To ni ka juya na taka bayanka sai na hau,ka jira ni a nan na dawo kada ka tafi ko ina”
Da qarfi yace mata
“Ke kin isa ki taka bayana ki hau katanga? Kinsan wanene ni?”
Haba kai kuwa,kana ganin masu laifi kuma kaga babu mai taimaka mana a nan,ka juya mana in hau in shiga na gani”
Ta fada masa tare da marairaice fuska,qara bude idonsa yayi a kanta sannan yace
“Ni bari inje in samo mutanen da zasu taimaka mana mu fita daga yankin nan,don gaskiya ni ban saba haka ba”
Kallon shi take cike da takaici a ranta tace
“Mutum sarqeqen na qato amma sai lalaci fal cikinsa,bai iya tabuka komai….”
Katse mata tunani yayi da cewa
“Ki tsaya inje in nemo mana jami’an tsaro yanzu zan dawo” bai jira amsarta ba ya fara takawa a hankali ya bar wajen,leqawa take tayi a hankali tana hangosu har lokacin suna ta kwashe buhunhunan daga inda suke,ya kai minti kusan bakwai sai gashi ya dawo,cikin sanda ya qaraso inda take a hankali shima ya fara leqa su tare da ce mata
“Ki zo mu tafi nasa a kirawo ‘yan sanda su zasu zo su tafi dasu”
Harara ta daka masa tare da cewa
“Ni ba zan bar nan wajen ba har sai naga abinda suke yi,wata tana can cikin qunci anyi mata sharrin ta zama annoba kuma naga abinda zai wanke ta kace na jira jami’an tsaro? Tunda kace ba zaka durqusa min in hau ba zanje in shiga ta qofa kawai” ta qarasa tana mai miqewa sosai ta fara tafiya,da sauri yace
“Ahhahh ki dawo zan durqusa ki hau tunda ni ban iya hawa ba”
Durqusawa yayi daidai katangar ta sa qafarta a gadon bayansa tana qoqarin haura katangar
“Ka dago sama,sama”
Ta fada,yayinda fuskarsa tuni ta nuna alamu na jigata,gumi kawai yake yi,da quar ya samu ya qoqarta ya dan dago ta haura katangar ta barshi nan a tsaye.
Wani matashi ne yake shiga babbar headquater ‘yan sanda ta garin da wani abu a hannunsa,katako ne abin da rubutu a jiki sai qasan akayi igiya mai beza bazar bazar haka,yana shiga da gudu fili ne fetal sai gine ginen katako irin na wancan zamanin,wajen zagaye yake da sandunan aci bal bal wanda sune suke bawa wajen haske,kai tsaye wajen wasu ‘yan sanda da ya gani a tsaye ya nufa yana haki
“Barkanku ranku ya dade,ina da saqo zuwa ga babban sufeto(inspector general )”
Cikin sa’a yana cikin mutanen da suke tsaye,a nutse ya kalli mutumin tare da cewa
“Lafiya? Daga ina?”
Abinda yake hannunsa ya miqa masa da sauri,ido ya zaro tace da cewa
“Imperial dispatch seal” ya kai kallonshi ga matashin tare da cewa
“Waye ya baka wannan?”
“Wani mutum ne ya bani yace in kawo nan” ya bashi amsa kai tsaye,IG ne ya qara cewa
“Ina ne inda yace maka?”
“Bayan hauren maqera” ya qara bashi amsa
IG ne ya kalli wani dan guntun a kusa dashi yace
“Gather all force,mai martaba yana cikin hadari”
“Yes sir” ya fada tare da barin wajen don tqjo da sauran ‘yan sandan da suke available.
Har yanzu bamu shiga cikin labarin ba gadan gadan,ku kasance tare dani domin jin yadda zamu warware komai.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Whattpad :Oum_tasneeem
Page 8
Cikin sanɗa take takawa har ta samu wajen laɓewa tana kallonsu a kusa kusa,suna ta ɗibar abin suna kaiwa bakin wani kwalbati da ya biyo ta cikin gidan,tana tsaye tana kallonsu ta jiyo hayaniyar mutane,qara ɓuya tayi amma sai taga ‘yan sanda ne suka shigo,nan ta samu qwarin gwiwar fitowa da gudu yayin da hankalin mutanen ya tafi kan hayaniyar tayi saurin ɗauko duwatsun guda biyu tafita da gudu,inda ta barshi ta koma har lokacin yana wajen a zaune yana jiranta,hannu ta miqa masa da duwatsun tace
“Kaga abinda nake son naje na ɗauko nan,ni dai ban taɓa ganin irinshi ba amma yana da ɗanɗanon gishiri”
Kallonta yake cike da mamaki don shi duk a baya ya ɗauki maganarta shirme ne,a hankali ya miqa hannu ya karɓa yana dubawa,yace
“Tabbas wannan salt stone ne,haka yake kamar dutse amma gishiri ne,ana tsoma shi a ruwa yake narkewa,amma fa yana da tsada don daga can qasar SIN (china) ake kawo shi”
Kafin shukra tace komai kamar wanda ya tuna wani abu,ya qara ce mata
“Kince sune a cikin nan da yawa? “
“Ehh ai yan sanda ma sunzo,ashe dai akwai abinda zaka iya yi? Ko dai kaima dan sandane?”
Bude baki yayi yana kallonta cikin rashin sanin abinda zai ce mata,cikin in ina yace
“Ehh ɗan sanda ne ni,bangaren binciken sirri”
Tace “ohh ho,shiyasa ma kasan da irin wannan abin,ni zan tafi”
“Zaki iya tafiya ke kadai? Ba kya jin tsoro”
Kallon ka raina ni ta watsa mai tare da cewa
“Kai da baka iya gudun ceto ranka ko kuma haura katanga bane kake tambaya ta ko ina jin tsoro,kai dai zan tambaya ko kana jin tsoro”
Bata tsaya jin abinda zaice ba tayi gaba ta barshi a nan,murmushi yabi bayanta dashi yana kallonta har ta ɓace masa.
Wucewarta ke da wuya chief eunuch da IG na police suka qaraso inda yake a zaune a qasa,tsayawa sukai a tare suka qqqrusunar da kansu a tare suka ce
“Da fatan kana lafiya mai martaba”
Miqewa yayi tare da zagaya hannunsa baya ya sarqe su,take fuskarshi ta sarauta da izza ta bayyana ba wacce ya gama shashanci da shukra ba,yace
“Lafiya qalau,ina son a nemo min wacece yarinyar nan,naga alamun yarinya ce mai hazaqa,sannan kuma a binciki wadannan mutanen cikin gidan nan domin ina da yaqinin suna da hannu cikin abinda ya faru da kayan kidan masarauta” ya qarasa yana dan fara takawa don barin wajen.
“Angama your majesty” tare suka amsa,chief eunuch ne yabi bayanshi suka fara tafiya yayinda IG ya koma cikin gidan da ake kama masu laifi.
Washegari da safe shukra da saurinta ta tafi wajen manager tare da bashi duwatsun nan
Cikin nazari manager yake kallon dutsen “wannan ai dutsen gishiri ne”
Gyada kai tayi tare da cewa
“Haka wani dan sandan sirri ya fada min jiya da daddare,dama tun farko na fada maka akwai wata matsala,amma kowa ya gasgata camfi”
Miqewa yayi ba tare da yace mata komai ba ya fita tabi bayanshi,dakin da ake ajiyar kaya suka nufa,da shigarshi ya fara binsu daya bayan daya yana sa harshe,cikin cikakkiyar gamsuwa ya juyo ya kalli shukra tare da cewa
“Gaskiyane wannan duk salt rock ne,amma yaya akayi haka? Bayan daga maqera ake hada su a kawo mana,kuma daidai lokacin da ake hada mana wadannan ai kina can maqerar”
Dogon nazari ta shiga,da sauri ta daga masa hannu tare da tuno wani abu
“Hakane,hakane hakane a cikin mutanen da na gani jiya da daddare akwai wani mutum,a jiyan ban gane shi ba sai yanzu da kayi maganar maqera,ina cikin yiwa duwatsun da aka hada polish ya shigo kamar baya son kowa ya ganshi yace min in tafi zai qarasa aikin,kuma jiya shi na gani da daddare ashe shiyasa yake ta bina suna son su kashe ni saboda kada na tona musu asiri ne”
Bai samu damar bata amsa ba suka ji shigowar yan sanda gadan gadan cikin ma’aikatar,fitowa sukayi daga dakin ajiyar kayan,manager ne ya qarasa har gaban IG tare da rausunar da kanshi yace
“Barka da zuwa my lord”
Gyaɗa kai kawai yayi tare da cewa
“Muna buqatar duba ɗakin ajiyar ku”
Hanya manager ya nuna masa,yana gaba IG na binshi a baya har dakin ajiya
“Ku shigo” IG ya fada da qarfi,yan sandan da suke biye dashi ne suka shigo cikin tsare gida suka fara ɗibar fararen duwatsun suna fita dashi,sai da suka kwashe tas sannan suka fice suka bar ma’aikatar,IG ne yace wa manager
“Shikenan,idan muna buqatar wani abin zamu qara dawowa”
Rusunar da kanshi manager yayi alamun “Good bye” har IG ya wuce sannan ya ɗago kanshi,sauri yakeyi domin yaje ya samu sameer don yafi kusa dashi akan kowa a wajen yayinda IG yana fita ya ci karo da shukra,qura mata ido yayi har ya bar wajen yana jinjina kai.
Manager,sameer da shukra ne a zaune a office din manager cikin takaici ya kalli sameer yace
“Da tun farko mun dauki maganar shukra da yanzu mune muka gano gaskiyar nan kuma wata qila his majesty yayi mana tukuici mai girma amma tana fada mana muka watsar muka qi ji” karkada kai sameer yayi tare da cewa
“Hakane my lord,da yanzu mu ne da credit din nemo gaskiya don nasan mai martaba zai ji dadi sosai domin an wanke lady jalila daga zargi” haka dai suka ci gaba da tattaunawar su,yayinda a can ma’aikatar bincike (bureu of investigation) ake bawa mutanen da aka kama da salt tock dinnan azaba,azaba akeyi musu sosai amma sunqi fadin wanda ya saka su aikin,hakan yasa aka yanke musu hukuncin kisa domin dokar qasar ce indai talaka ne yai laifi komai qanqantar sa toh sai dai ya biya da rayuwarsa.
Lady jalila tana zaune har yanzu cikin alhini don bata san wainar da ake toyawa ba,chief maid dinta ce ta shigo da sauri tare da cewa
“His majesty is here”
Lady jalilah ta dago idonta ta kalleta tare da miqewa daga wajen zamanta da sauri ta tafi tana tattare alkyabbar ta zuwa bakin qofar quaters dinta
“Barka da zuwa your majesty” ta fada tare da dan rusunar da kanta,juyawa tayi ta fara tafiya domin komawa ciki,shima yabi bayanta,yayinda maids da chief eunuch suka tsaya a wajen domin jiranshi,wajen abin zamanta inda ta tashi kai tsaye ya tafi ya naɗe qafarsa ya zauna,yayinda ita kuma ta zauna tana fuskantar shi,kafin su daidaita zamansu ma chief maid dinta ta kawo musu shayi yana ta tururi da qananan kofuna irin na gidan sarauta ta ajiye a tebur din da ya raba tsakiyar su.
Gyara zama mai martaba yayi,yana kallon lady jalila cikin damuwa yayinda ita kuma tana qoqarin zuba masa shayi a kofin da ta ajiye a gabanshi,cikin nutsuwa ta gama zuba mai tare da dauka da hannu biyu ta miqa masa cikin girmamawa,karba yayi tare da cewa
“Na kawo miki albishir din yanzu an wanke ki daga zargin da mutanen masarautar nan sukeyi miki” kallon shi take yi cikin rashin fahimta,kafin ta kai ga cewa wani abu yace
“Jiya da daddare na hadu da wata yarinya wacce ita tayi leading dina har inda aka kama masu laifin,an samesu da salt rock wanda shi sukai amfani dashi a maimakon farin dutse har hakan ya zama matsala,kuma na tabbata ko waye ya sasu aikin nan yayi hakan ne domin kiyi baqin jini,amma burinsu bai cika ba”
Cike da farin ciki ta fara cewa
“Amma naji dadi your majesty,yanzu zan iya fita nayi yawo a cikin masarautar nan,naji dadi matuqa da ya kasance an samu masu laifin,ita yarinyar fa?”
Ta tambaya,murmushin da yake qara fitar da haibarsa yayi
“Nasa IG ya nemo min wacece ita amma yarinyar tana da yarinta sosai,gata da qarfi ta iya gudu,har katanga fa ta hau ina kallo,gaskiya tana da qarfin hali kuma kasancewarta mace hakan ya qayatar dani”
Ya qarasa cikin dariya mai sauti
“Kuma fa bansan sunanta ba har muka rabu amma dai nace mata ni dan sandan sirri ne” ya qara fada yana kuma qarfafa dariyarsa,jalila ma dariyar ta taya shi,suka gama shan shayinsu ya tashi ya tafi.
Komawar mai martaba grand palace kenan aka sanar masa da zuwan IG,iso akayi masa ya shiga ya zauna a inda mai martaba yake ganawa da mutane,shigowar mai martaba ya sa ya miqe tsaye tare da rusunar da kanshi,cikin murmushi mai martaba yace
“Babban dan sanda zaka iya zama,ka samo wani labari game da yarinyar nan?”
Cikin nutsuwa IG yace
“Ehh your majesty,servant girl ce a bureu of music “ ya bashi amsa yana qoqarin zama akan kujera,cikin mamaki mai martaba yace
“Ohh a cikin palace dinnan take ma,amma servant mace a bureu of music dama suna da mata ne?”
IG ne ya ce “A ah ita kadai ce mace kuma babu wanda yasan lokacin shigowarta,kawai wayar gari akayi aka ganta tana aiki a wajen tun tana qarama”
Kada kai mai martaba yayi daga bisani ya miqe tare da cewa
“Ba komai,zanga abinda ya kamata ayi mata domin itace silar da muka gano gaskiya ya kamata mu saka mata da wani abin” ya fada yana shigewa daki,shima IG tashi yayi ya bar grand palace tare da komawa bakin aikinsa”
Abinci aka fara shigowa dashi bureu of music,abinci na alfarma a cikin irin kwanukan da yayan sarauta suke cin abinci,kuma abinci irin wanda yayan sarauta kawai suke ci kala kala iri iri har da lemuka,wasu ma babu wanda ya taba shan irinsu a ma’aikatar,haka fadawa sukai ta shigo dashi a irin dan qaramin tebur dinnan da ake cin abinci a qasa suna ajiyewa,sai da suka gama shigowa dasu tsaf sannan wani bafade ya kalli manager ya rusunar da kanshi yace
“Saqo ne daga mai martaba a kawo wa dukkan ma’aikatan da suke cikin bureu of music saboda tukuicin abinda shukra tayi”
Murna ce ta cika wajen da sowa domin kowa ya fito ganin kalar abincin da ake shigowa dashi,murmushi manager yayi tare da yi musu godiya,shukra da take gefe a tsaye ta kalli manager tare da cewa
“Amma to ya akayi mai martaba ya san nice,ko dai dan sandan sirrin nan ne ya bashi labari?”
Manager ya jinjina yarintar shukra tare da cewa
“Ai na tabbata shine kam ya bashi labari”
Cikin farin ciki kowa ya zauna suka fara cin abinci mai rai da lafiya,sameer,shukra da manager a tebur daya suke cin abincin,tun daga wannan lokacin suka dinke su ukun ya kasance sun zama tamkar ‘yan uwa.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Whattpad :Oum_tasneeem
Page 9
Minister of State affairs ne cikin tsananin tashin hankali yake tahowa quaters din queen dowager,chief maid dinta ce tai masa iso a zabure ya shiga tare da durqusawa ko dan rusuna mata baiyi ba alamun gaisuwa
“Minister lafiya kuwa na ganka haka?”
Cewar queen dowager,tashin hankalin da ke fuskarsa ne ya canja ya koma mamaki tare da ce mata
“Your majesty ke ya kamata na tambaya ya na ganki haka?”
Murmushi tayi tare da bashi amsa
“Ai ni bani da matsalar komai,idan ma akwai to bata wuce kasancewar jalila ta kubuta daga tuggun da na qulla mata ba”
Jinjina kai minister yayi tare da cewa
“Hakane your majesty,amma nayi mamakin yadda duk wandanda aka kama basuyi magana ba”
“Ban tari numfashin ka ba,amma kana tunanin zanyi abinda idan ta ɓaci zai dawo kaina ne? Hahaha “ tayi dariya sannan ta cigaba
“Ai duk wanda zai min aiki sai na tabbatar zai iya bada rayuwarshi saboda yi min biyayya shiyasa ko da aka kama su banji komai ba”
Kada kai yayi cike da gamsuwa da qara girmama qarfin rashin imani na queen dowager,mutum har kusan bakwai sun mutu saboda asirinta ya rufu amma ko a jikinta
“Idan baka da wata maganar zaka iya tafiya,jalila kuma in ta san wata bata san wata ba,mu zuba ni da ita” tayi qwafa,minister dai jan qafafuwansa yayi ya bar quaters din jikinsa a sanyaye.
A daren ranar shukra,manager da sameer suka fito wajen fada domin shan iska,dukkaninsu cikin shiga irin ta mutanen gari,babu wanda zai gane ma’aikatan masarauta ne suna tafiya a cikin kasuwa suna hirar su suka hango wani shago da ake saida lemuka da shayi irin na gargajiya haka,akwai tebura da kujeru a wajen shagon inda zaka iya zama kasha a nan,isar su wajen yayi daidai da zuwan wasu mutane suma,daya daga cikinsu yana ganin shukra yayiwa wanda suke tare alama da ido man da nan suka watse shi kuma ya qaraso inda su shukra suke,shukra ce ta fara lura da zuwansa wajen,cikin murmushi da tarin farin ciki ta ce
“Yallaɓai dansanda yau ma mun sake haduwa”
Murmushi yayi mata mai qara fitar da kyawun fuskar sa,cikin rada yace mata
“Yaya sunanki yan mata?” Rufe fuska tayi saboda taji kunyar yadda yayi maganar itama a hankali ta mayar masa
“Sunana shukra “
“Hmmm suna mai dadi….”
“Shukra waye wannan kuma” muryar manager ta katse su,shukra ce tayi saurin juyawa inda yake
“Shine dan sandan sirrin da muka hadu dashi jiya” ta bashi amsa kai tsaye,A tare sameer da manager suka gaishe shi ya kalli shukra
“Tare kuke dasu? Me kuke yi a nan?”
Sameer ne ya cafe maganar “Ehh tare muke yallabai,munzo shan lemo ne ko zaka zauna kaima musha tare?” Murmushi yayi tare da cewa “toh ba matsala” tare da zama,ganin haka suma suka zauna,nan aka kawo musu lemon kwakwa,na abarba,na tsamiya,da dai sauransu suka fara sha suna hirar su sama sama,sameer ne ya kalli manager tare da cewa
“Yallabai baka ganin dan sandan nan yana maka kama da mai martaba?” Manager ya kalli mai martaba cikin tsanaki daga bisani yace
“A ah mai martaba ai yafi wannan kyau,shi kyakyawane sosai”
“Da gaske yallabai,mai martaba yafi wannan kyau?" shukra tayi saurin tambaya,sameer ne ya bata amsa da
“Ehh ai kinsan yallabai manager ya taba ganin mai martaba lokacin wata liyafa amma daga nesa nesa”
“Uhm uhm uhm” mai martaba yayi gyaran murya,shukra ce ta juyo ta nuna shi da dan yatsa tare da cewa
“Kai kaine jiya ka bawa mai martaba labarin ni na samo mutanen nan ko? hhat ya aiko mana da abincin alfarma Ai ka sanshi kenan? Wai kyakyawa ne har yafika kyau?”
Muryarsa ce ta fara rawa,ya daure yace
“Ta yaya zan fadi hakan da bakina?"
“Ehh?” Shukra ta tambayeshi,kafin ya samu amsar da zai bata manager yace mata
“Ke meyasa to kike ta tambaya,kina son kyakyawa kamar mai martaba ne?” Tabe baki skukra tayi tare da cewa
“Chabb me zanyi da namiji kamar mai martaba,ni bana son namiji ya fiya haske,kuma nafi son mai qwanji tsayayyen namiji “ dariya manager da sameer suka sheqe da shi yayinda mai martaba ya tamke fuska,gudun kada su gane wani abin kawai ya taya su dariyar,haka suka cigaba da hirar su har dare ya dan fara nisa su sameer suka tashi suka tafi,yayinda chief eunuch suka bullo daga inda suka ɓuya domin raka mai martaba zuwa gida.
BAYAN WATA DAYA DA DAWOWAR JALILAH
muryarta a sama take magana
“Ba zai taba yiwuwa ba aure tsakaninka da jalila,ka dai barta matsayin qwarqwarar tunda kana sonta amma matsayin CONSORT? sam wannan matsayin bata dace da shi ba,gara ka canja shawara tun wuri” queen dowager ce take sanar da mai martaba hakan,yayinda suke ganawa a quaters dinta,shiru yayi cikin dogon nazari yayinda ita kuma sai huci take,cikin rarrashi yace
“Tabbas jalila zata zama CONSORT domin tayi abinda ya kamata a bata wannan matsayin” ya fada cikin dakewa,kallonshi take cikin wani irin yanayi
“Menene abinda tayi da har kake fadin ta cancanta da ka bata matsayin CONSORT?”
Ta tambayeshi cike da qaguwar jin amsar da zai bata,sai dai taji abinda bata taba tsammani ba a wannan lokacin,cikin dakewa yace
“Saboda jalila tana dauke da juna biyu,kuma nawa ne” maganar ta dirar mata tamkar diran kibiya a cikin zuciyarta,cike da rikici take kallon shi yayinda bakinta ya kasa furta komai,idonta suka fiffito cike da firgici tace
“Me…me… kake nufi da tana da juna biyu? Zata haifi da a gidan nan? Jalilan? Sam ba zan jure ganin gudan jininka ya fita ta tsatson su jalila ba,ko ka manta jinin lowborn yana yawo a jikinta?"
Cikin hikima da sanin halin mahaifiyar shi yace
“Tabbas tana da juna biyu,kuma kasancewar ta da juna biyu hakan yasa dokar qasa ta bata wannan matsayin ko da ina so ko bana so,kinga wannan ba doka ta bace kuma ba zabi na bane,tsarin dokar qasa ce”
Alama tayi masa da hannu akan ya tashi ya tafi
“Na barki lapia” ya fada tare da juyawa ya bar quaters din nata.
Tunaninta cak ya tsaya domin sunyi mata bazata,kuma tasan a wannan qadamin babu abinda zata iya yi akan hakan,dole ko tana so ko bata so mai martaba zai auri jalila ya mayar da ita cikakkiyar matar aure,wannan tunanin shi ya hana zuciyarta zama lapia kwata - kwata.
Takadda likitan masarauta ya rubuta da take tabbatar da juna biyu da jalila take dauke dashi,sarki ma ya rubuta tashi takardar,queen hanifa wacce itace nadin sarautar CONSORT yake qarqashin ikonta itama ta rubuta tata takardar,daga nan aka tattara takaddun aka kai wa office of investigation na cikin inner court domin tabbatar da babu wani haufi game da jalila,ladies investigators sukayi approving daga bisani aka dawo da takaddun wajen queen haneefa domin ayi musu stamp,stamp ta buga a takardar tare da bawa office of state record suyi copying komai su ajiye na record su dawo da original takardar nadin sarautar.
Inda bangaren iyayen jalila,mahaifinta ya rasu sai qanin mahaifinta,da kuma uban riqonta (minister of tribunal) sune suka bada aurenta ga mai martaba,akayi daurin aure kamar yadda al’adarsu ta tanadar.
Quaters din queen haneefa ne ake ta faman decorations da gyara da saka kujerun zama da tebura,yayinda tayi shiri cikin kayan sarautar ta wanda sai za’ayi wani sha’ani irin wannan take sa su,Alkyabba ce ta musamman,wacce aka qawata kafaɗunta da zanen dragon 🐉 kaya ne masu matuqar nauyin gaske da wani gyaran gashi da akai mata wanda aka nannade shi ya fito ta tsakiyar kambun mulkin da yake saman kanta (crown 👑) tayi matuqar kyau qwarai da gaske,suma maids dinta ba regular uniform dinsu suka saka ba,suma sunyi kwalliya ne,haka nan suma special court ladies,jalila ce ta taho cikin itama irin tata shigar ta mulki,itama da kambun mulki a kanta amma ba irin na queen hanifa bane,maids dinta da sukayi shiga irin ta maids din queen haneefa ne suka rako ta,tare da riqe gwiwar hannayenta ita kuma ta hada tafukanta biyu a saman cikinta a hankali sannu sannu take tafiya cikin izzar sarauta,su kuma maids dinta suna qara daidaita mata tafiyarta daga gefe,ganin tahowarsu yasa queen haneefa ta tashi tsaye daga kan karagar mulkin da take zaune tazo daidai qarshen matattakalar da jalila zata tsaya,chief secretary na masarautar ne a gefen damanta riqe da faranti (tray) wanda a kanshi takadda ce da aka liqe bayanta da fata (leather) mai adon flower 🌸 qasa da samanta kuma aka sa mulmulallen katako yadda za’a iya rieqewa a karanta,daga bisani kuma aka nannade ta kamar nadin tabarma,iya katakon kawai ake gani aka dora akan tray din.
Jalilah tana zuwa daidai gaban queen haneefah ta dan rusunar da kanta alamun gaisuwa sannan tayi qasa ta durqusa ta zauna akan qafafuwanta kamar zaman sallah,chief secretary ne ya dauki takaddar tare da miqawa wanda yake kusa dashi tray din,takaddar ya bude tare da karanta ta kamar haka
_Royal consort Jalilah_
_duba da dabi’u na gari da kika nuna a cikin masarautar nan_
_da kuma kasancewar kina dauke da gudan jinin mai martaba_
_Hakan yasa aka baki matsayin ROYAL CONSORT ta mataki na uku (third rank)_
_da kuma matsayin daya daga cikin mataimakan sarauniya na musamman a inner court_
_hear and obey_
Nan da nan wajen ya dinke da “congratulations your Highness lady jalilah”
Yayin da chief secretary ya qara nannade takardar tare da miqawa queen haneefah,nan ita kuma ta miqa ta ga lady jalila,daga inda take zaune a qasan ta miqa hannunta bibbiyu ta karba tare da cewa
“I hear and obey your majesty” fuskarsu dauke da murmushi har da queen haneefah.
Maids din lady jalilah ne suka taimaka mata ta tashi daga inda take zaune,rusunar da kanta tayi ga sarauniya haneefah tare da nufar inda kujerar zamanta take ta zauna,daga nan aka cigaba da liyafar,an ci an sha sannan kowa ya watse zuwa quaters dinshi.
Oum tasneem ✍️
❤❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Whattpad :Oum_tasneeem
Page 10
Washegari maids din jalilah ne suke ta zirga zirga wajen ganin an qara qayata mata quaters dinta,tunda yanzu ta samu qarin matsayi,itama ta shirya cikin shiga ta alfarma,da ka ganta kaga matar sarki,dukkan kayanta da kuma alkyabbar ta silk ne mai zanen flowers a jiki,sabanin daa da take saka plain silk,hairpin dinta mai kalar golden wanda a lokacin baya fari take saka wa,komai dai ya canja domin a yanzu ko da wanda bai san wacece ita ba idan yaga suturar ta da kuma irin fulawiwin da suke jikin alkyabbarta zai tabbatar da cewa matar sarki ce,kowa farin ciki yake taya ta amma ita fuskarta babu yabo babu fallasa,tana zaune a sitting room tayi nisa a cikin tunani chief maid dinta ta shigo,rusunawa tayi tare fadin
“Barka da war haka your highness”
(Yanzu zasu koma kiranta da your highness saboda qarin matsayin da ta samu)
Dago kanta tayi tare da sauke idonta akan chief maid din ba tare da ce komai ba,qara rusunawa tayi
“Your highness kina da baquwa”
Kasancewar jalila ta san da zuwan ta yasa ba tare da ta tambayi wacece ba tace
“A shigo da ita”
Qara rusunar da kanta tayi,sannan ta juya ta fita,fitar ta ke da wuya,wata mata da ba zata wuce shekaru 40 ba ta shigo cikin shiga mai kyau,fuskarta cike da farin ciki itama jalila ta miqe daga inda take zaune suka rungume juna,cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa jalila tace
“Nayi kewarki mahaifiya ta,kuma gashi yanzu ina cikin yanayin da nake matuqar buqatar ki a kusa,ina fatan kin dawo garin nan kenan ba zaki koma ba”
Murmushi mahaifiyar jalila tayi,tare da shafa fuskar ta
“Na dawo gareki your highness,zan baki duk irin gudunmawar da ta dace,domin ina alfahari da haihuwa irin taki” dariya jalila tayi cike da farin cikin ganin mahaifiyarta,qarasawa sukai wajen zaman jalila ta zauna yayinda mahaifiyarta ta zauna tana fuskantarta.
Jalila shiru tayi da alama ta fara nutsawa duniyar tunani,mahaifiyarta Haj jameela tana nazarinta daga busani tace
“Ke kuwa me yake damunki a wannan yanayi da ake ciki na farin ciki? Kuma kinsan shiga irin wannan yanayin bashi da kyau ga mace mai juna biyu?”
Cikin yanayin mai wahalar fassarawa tace
“Mama ni bani da komai fa,mai martaba yayi haka ne domin queen dowager ba zata taba yadda ya aureni haka kawai ba”
Tashin hankali ne da fargaba suka bayyana a kan fuskar hajiya jameela,take ta fara jefo mata tambayoyi
“Ta yaya mai martaba yayi hakan? Yaya akayi da likitan masarauta? Shin mai martaba ya zubar da qimar sa har haka wajen aikata irin wannan laifin? Idan abin nan ya fito fili shi kanshi ba zai tsira ba” ta qarasa cikin matuqar tashin hankali,jalila ce ta ruqo hannun ta cikin sigar kwantar da hankali tace
“Ki kwantar da hankalinki ko likitan masarauta bai san bani da ciki ba,domin mai martaba ne ya duba slippery pulse (wata hikima ce da likitocin wancan zamanin suke jin bugun zuciyar ɗan da take ciki ta hanyar jin bugun zuciyar uwar,suna iya tantance ko akwai na yaro ko babu,ta hakan suke gane mace na dauke da ciki ko kuma babu) da kanshi,kuma ya fadawa likitan masarauta ya rubuta report din domin ba zai yadda wani qato ya taba ni ba”
Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa
“Amma har yanzu akwai wata matsalar ai your highness”
(Ko iyayensu basu da damar kiransu da sunan su matuqar suka taka matsayin matar sarki)
Haj jamila ta cigaba
“Shi ciki ai da kanshi yake bayyana kanshi,idan lokacin fitowarsa yayi akaji shiru fa? A lokacin zamu shiga matsala kwarai da gaske”
Jalila ce ta tare ta
“Nima mama abinda yake ta damuna kenan amma shi mai martaba ko a jikinshi,kamar bai san girman abinda ya aikata ba”
Haj jamila ta dan jima cikin tunanin neman mafita kafin daga bisani tace
“Your highness,mafitar mu guda daya ce,akwai wasu sassaqen itatuwa da ake amfani dasu wajen habbaka saurin daukar ciki,ina ganin su zansa a kawo miki,kinga idan kika samu ciki nan kusa,komai zai zama daidai”
“Amma mama ta yaya zamu shigo da magani cikin nan? Bayan kinsan cewar babban laifi ne shigo da wani magani daban daga wajen masarautar nan,domin duk abinda muke buqata akwai a asibitin ciki,idan aka san munyi hakan shima zai zamar mana matsala”
Jalilah ta fada cike da damuwa
“Haba your highness,amintacciyar baiwa zamu samu da zata iya yi mana aikin shigo da maganin ba tare da kowa ya sani ba,cire tsoro zakiyi ki samar wa kanki mafita,domin kinsan irin gidan da kike zaune,yanzu bakya tunanin mai zai faru duk ranar da queen dowager ta gano akwai irin wannan matsalar?”
Haj jameela ta fada cikin qoqarin ganar da jalila abinda ya fi musu amfani a halin yanzu,gyada kai jalila tayi sannan tace
“Shikenan mama,akwai yarinyar da nake tunanin zata iya yi min wanann aikin,zamu gwada hakan mu gani”
Murmushi haj jameela tayi tare da cewa
“Yauwa ko ke fah? Ai yanzu mafitar mu kawai zamu nema,kinga har yanzu kece a turakar mai martaba,gara muyi yadda zamuyi ki samu juna biyu a cikin wannan lokacin,ko shi kanshi sai kin qara matsayi a zuciyar sa”
Murmushi jalila kawai take saki jin an ambato mata zata qara matsayi a wajen mai martaba.
Haka suka cigaba da hirar su har sanda haj jameela tayi mata sallama ta tafi gida.
A bangaren shukrah kuwa shaquwa mai qarfi ce ta shiga tsakanin ta da mai martaba ba tare da ta san shi ne ba,yana jin dadin yadda take nuna yarintar ta da kuma yadda a karo na farko wani mutum a garin yana masa magana kai tsaye a matsayin ba kowa ba,domin shi tun daga haihuwarsa har girmansa ya zama sarki girmamawa ce tsakanin shi da kowa a qasar ko da kuwa shekarun mutum sunkai 100 ne,hakan yasa yake jin kamar wani ‘yanci ya samu wanda da bashi da shi. Hakanan manager da sameer suma lokaci zuwa lokaci suna haduwa da mai martaba a wajen masarauta,su zauna suyi hira,su sha shayi tare ayi wasa da dariya.
Chief maid din lady jalila ce tare da wasu maids din suka shigo bureu of music,wajen manager suka nufa tare da isar masa da saqon lady jalila,shukra tana bakin rijiya tana hada kayan wanki zata fara wankesu maids din suka iso tare da manager,manager ne ya kalleta sannan ya kalli chief maid din tare da cewa
“Wannan itace yarinyar da ake magana,amma dai ba wani laifin tayi ba ko my lady?” Ya tambayeta fuskarsa da dan alamun damuwa,murmushi chief maid din jalila tayi
“Ahh babu komai,ba laifi tayi ba akwai wani abu da zata yiwa her highness ne”
Boyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke tare da maida kallonshi inda shukra take tsugunne,tare da zuba musu ido cikin rashin fahimtar inda zancensu ya dosa,yanayin ta ya karanta kafin ya bude baki yace mata
“Her highness lady jalilah ce take nemanki” zare ido tayi cikin kaduwa tace
“Lad….ladyyy jalilah kuma? Me nayi?”
Murmushi yayi mata tare da cewa
“Babu abinda kikai mata,amma dai ki tashi kije ko ma menene zaki ji” jikinta a sanyaye ta miqe tare da nufar dakin da take kwana,farar takaddar da take da zanen butterfly dinta ta dauko tare da budewa,runtse ido tayi tare da fadin
“Allah ka taimakeni yau idan na shiga cikin masarauta yau na gamu da court lady din da nake nema”
Saurin miqewa tayi tare da mayar da takaddar ta ajiye a inda ta dauko ta,fitowa tayi inda maids din lady jalilah suke suka tafi tare har quaters din ta.
Daga Shigowar shukrah ta sauke idonta akan lady jalila ta gane ta,farin ciki ne ya lullube ta cikin ranta take cewa
“Ina da tabbacin wannan itace court lady din da nake nema,idan ma ba ita bace toh kamar tayi yawa,duk da shekara bakwai kenan…..” kafin ta qarasa tunanin ta muryar chief maid din lady jalila ta katse ta
“Me kike yi a tsaye,greet her highness”
Daidai lokacin itama jalila ta dawo daga nata tunanin,wanda bata san dalilin da ya sa tunanin ya fado mata a daidai wannan lokacin ba,tunanin ta kuwa bai wuce wani mutum da ta taba haduwa dashi har ya fada mata abinda yake daga mata hankali duk lokacin da ta tuno shi,a hankali ta furta
“Kamar yadda yace duk irin daukakar da zan samu tabbas ni zan zamo inuwar ta (shadow)”
Diriricewa shukra tayi tare da rusunawa sosai tamkar zata kai qasa
“Barka da hutawa your highness”
Murmushi jalila tayi tare da cewa
“Zaki iya zama” a inda take tsaye kawai ta nade qafarta ta zauna a qasa tare da tunanin dalilin kiranta da kuma ta inda zata fara tambayar lady jalila maganar keyholder dinta,muryar lady jalila taji
“Shukrah ko? Na san zakiyi mamakin dalilin da ya sa na kira ki nan” ta dan nisa,ba tare da shukra tace komai ba ta ci gaba
“Na ji qoqarin da kikayi wajen gano gaskiya akan sharrin da aka so a qulla min,na kuma gode sosai,kuma idan ba damuwa ina son in saki wani aiki ne domin aikin yana buqatar sirri,shin zaki iya?”
Daga yadda take zaunen ta qara rusunar da kanta tare da cewa
“Ki fadi dukkan umarninki your highness,zan kasance mai biyayya a gareki”
Murmushin jin dadi jalila tayi tare da cewa
“Akwai saqo da zaki karbo min a wajen mahaifiya ta,sassaqen itatuwa ne kuma kinsan an haramta shigo da magani daga waje,saboda haka sai kinbi a hankali kuma ki tabbatar babu wanda ya ganki yayin da kike shigowa dashi”
Maganar jalila ta dan firgita shukra amma duk da yake yarinya ce,amma tana da qarfin zuciya,fuskarta babu yabo babu fallasa ta rusunar da kanta
“An gama your highness”
Ta fada tare da miqewa ta bar quaters din,sukuku ta koma bureu of music ko sameer bata sanar dashi abinda jalila ta saka ta ba,ta shirya ta cire uniform dinta na bayi tare da sa normal ta dauki hanyar fita daga masarautar.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏻❤️
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Whattpad :Oum_tasneeem
Page 11
Queen dowager ce a kwance a dakinta cikin wata doguwar rigar bacci,gashinta ma a warware,kitse jelar gashin kawai akayi yayinda queen haneefah take zaune da wani baho a gabanta da kuma duster tana tsomawa tana matsewa tare da gogewa queen dowager jiki,dayan bangaren kuma royal doctor ne a tsugunne kanshi a qasa,sai royal nurses guda biyu a bayanshi suma sunyi irin zaman da yayi.
fuskar queen haneefah fal damuwa ta furta
“Sannu maama,Allah ya baki lapia”
Cikin jin jiki dowager tace
“Yauwah sannu queen,nagode da kulawarki,Allah yai miki albarka”
Murmushi queen haneefa tayi duk da damuwar bata bar fuskar ta ba tace
“Ai aiki na ne na kula dake maama,kiyi shiru Allah dai ya baki lapia”
“Ameen ta furta can qasa qasa” tare da lumshe idonta bacci ya dauketa sanadiyyar maganin da aka bata yanzu.
Shukra tana tafe har unguwar da aka kwatanta mata nanne unguwar su lady jalila,tambaya tayi aka nuna mata gidan,da sallamarta ta shiga gidan,wata maid ta tarar a tsakat gidan tana ta kai kawo,jin sallamar shujra yasa ta tsaya don ganin mai shigowar,a hankali shukra take turo kai cikin gidan da ganin maid din ta dan rusunar da kanta kadan tare da cewa
“Barka da warhaka,her highness lady jalila ce ta turo ni” da jin haka maid din murmushi kawai tayi ba tare da ta cewa shukra komai ba ta nufi qofar sitting room haj jameela,jim kadan suka fito tare,shukra da ganin ta ta rusuna tare da cewa
“Barka da war haka,sunana shukra” wani kallon wulaqanci haj jamila ta bita da shi tare da cewa
“Fuskar ki ta nuna min hakan,ba sai kin gabatar da kanki ba”
Nan take shukra ta sha jinin jikinta,haj jamila da maid dinta ne suka fita shukra tabi bayansu har wajen mai magani.
Da zuwansu gidan mai maganin haj jamila ta shiga ciki ta bar shukra da kuma maid dinta a tsakar gida,da shigarta mai maganin ya miqe daga inda yake zaune tare da rusunawa ya gaishe ta
“Barka da zuwa madam”
Ba tare da tace komai ba ta nemi waje ta zauna,shiru ne ya ratsa tsakaninsu kafin daga bisani tace
“Ina fatan maganin ya kammala ko?” Ta fada tana me dubanshi,gyaran murya yayi
“Ehh ana hadawa amma sai zuwa qarfe takwas na dare zai kammala”
Gyada kai tayi tare da cewa
“Ina tare da yarinyar da zata karba,ka tabbatar ba’a samu wata matsala ba,kuma idan har buqata ta biya kana da kyauta mai tsoka”
Washe baki yayi cike da farin ciki yace
“Ai ba za’a samu matsalar komai ba madam”
Tsam ta miqe ba tare da ta qara ce masa komai ba ta fito inda ta tarar da su shukra,sai da tazo dab da shukra sannan ta rage murya tare da cewa
“Ki jira zuwa qarfe 8 sai ki tafi da saqon,Ki tabbata ba’a samu ko wace irin matsala ba,kuma kada ki bari kowa ya ganki,ina fatan kin fahimta”
Cike da ladabi shukra tace
“Na fahimta madam”
Barin shukra tayi anan suka wuce ita da maid dinta.
Waje shukra ta samu ta zauna domin jiran saqon wani mutum ya shigo karbar magani,har ya karbi maganin shi zai wuce daidai inda take ya yarda qulli daya,shukra ce ta tsugunna tare da dauko qullin tace
“Baka ji ba”
Juyowa yayi ya kalleta tace
“Ka yar da wannan” ta fada tana miqa masa qullin maganin da ya yar a qasa,saurin karba yayi tare da cewa
“Aff ban kula bane,nagode sosai”
Murmushi shukra ta yi da ya saka ya tsaya ya qura mata ido kamar mai nazarin wani abu,a haka ya fara tafiya yana tafiya yana waigen shukra kamar dai da wani abin da ya gani a fuskar ta.
Tana nan a zaune har aka kira sallar maghreeb,tambaya tayi inda zatayi sallah aka bata,a nan ta zauna har akayi sallar ishaa ta qara tashi tayi,ta idar tana zaune wani yaron mai magani ya zo inda take tare da sanar da ita maganin ya zama ready,tashi tayi tare da bin bayansa har wajen mai maganin,a daidai lokacin da yake qunshe itatuwa,saiwa da kuma sassaqen magani a cikin wata leda daga nisani yasa zani yai masa daurin da akewa qunshin kaya,inda aka daure ya miqa mata ta karba ta tashi ta bar wajen tare da nufar hanyar komawa cikin palace.
A bangaren mai martaba yau yana police bureu wajen IG din police cikin shigar da ya saba yi idan zai shiga cikin gari,suna zaune suna hirar daren da suka kama mutanen da suke dauke da salt stone dinnan mai martaba yace
“Ai a wannan daren na hadu da wani abin mamaki,a karo na farko naji kamar nima mutum ne kamar kowa,babu durqushe durqushe,babu magana dani ana qin kallon idona”
Cike da mamakin kalamansa IG yace
“Your majesty me hakan yake nufi?”
Cikin murmushin da yake tabbatar da yana jin dadin labarin da yake bayarwa yace
“Yarinyar da ka nemo min kace a bureu of music take,kai ranar har fa gadon bayana ta taka ta hau katanga” ya qarasa tare da fitar da sautin dariya sosai cike na nishadi,haka dai suka cinye lokacin yana ta bashi labarin shukra da yadda suke haduwa bayan nan da irin yadda yake jin dadin hira da ita har qarfe takwas tayi suka tashi domin komawa palace.
Zuwan shukra bakin palace yayi daidai da bugawar agogo qarfe tara saura kwata 8:45pm,kasancewar qarfe tara daidai ake rufe qofofin masarauta yasa tara saura kwata ake fara tare duk wanda zai shigo sai ya bada name tag dinshi (abinda suke amfani dashi dauke da sunan ko wane mutum,kuma yanayin design din abin ne zai nuna iyakacin matsayinka da kuma inda kake aiki a cikin masarautar,kamar ID card kenan a wancan zamanin) layin da shukra ta hango a bakin shiga ya tabbatar mata an fara night search,kuma ta san idan har zata bi ta qofar to sai an bincika me take dauke dashi,da yake gwana ce wajen haura katanga sai ta koma da baya ta koma bangaren katanga da babu kowa,ɗage qafafuwanta tayi tare da ajiye qunshin kayan a kan katangar sannan ta fara qoqarin hawa,tana ta faman hawa wajen daidai lokacin da mai martaba,chuef eunuch da kuma private guards din mai martaba suka qaraso wajen,bata ji takun wucewarsu ba,sai chuef eunuch ne yaji motsinta,tare suka waiga da mai martaba,ganin shukra ce mai martaba yace su wuce kawai,chief eunuch ne yai saurin cewa
“Amma fah laifi babba take qoqarin…..” katseshi mai martaba yayi tare da cewa
“Nace ku wuce mu tafi ko?”
Haka suka wuce suka bar wajen,tana ta qoqarin hawa har yanzu bata samu hayewa ba taji a bayanta ance
“Me kike qoqarin yi haka?” Da sauri ta juyo a razane,mai martaba ne a tsaye ya harde hannuwansa biyu a bayansa,daidaita tsayuwarta tayi tare da cewa
“Yallabai me kake anan a wannan lokacin?” Murmushi yayi tare da cewa
“Ke za’a yiwa wannan tambayar shukra,tunda kin kasa haurawa ki wuce mu tafi”
Zare ido tayi tare da cewa
“Guards fa suna bakin qofa,kuma yanzun ma tara ta riga ta wuce” ta fada tare da kwabe fuska cike da shagwaba,murmushi yayi wanda bai san yana iya yin irinshi ba yace mata
“Ke dai ki wuce nace,don yau dai ba zan tsugunna ki hau gadon bayana ba,sabida haka kawai ki wuce mu tafi”
Ba tare da tace komai ba tabi bayanshi suka qarasa har bakin qofar da ta tarar da palace guards a cike dazu suna search,cike da mamaki tace
“Yanzunnan fa naga guards a cike anan wajen,kuma mutane sunyi layi suna dubasu”
Juyowa yayi ya kalleta tare da cewa
“Ehh da suna nan amma yanzu na sallamesu gaba daya”
Murmushin jin dadi tayi tare da sauke ajiyar zuciya ta kalle shi tace
“Kai abota da dan sanda akwai dadi gaskiya” ta fada cike da murna,shagala yayi da kallonta har sai da tace
“To yallabai ni na tafi,kaima ka tafi gida kaji?”
Murmushi yayi tare da cewa
“Toh shukra nima zan tafi gida,sai da safe”
Godiya ta qara yi masa ta wuce ta shige ta tafi,sai da ta tabbatar yayi nisa sannan shima ya shiga,kai tsaye makwancin sa ya nufa inda ya tabbatar lady jalila tana jiran dawowar sa.
Mutumin da suka hadu da shukra a gidan mai magani ne,a tafe yake har ya kai gida,da sallamar sa ya shiga gidan,wani mutumi ne wanda zai girme shi da kadan a tsakar gidan ya amsa sallamar,miqa masa maganin yayi tare da cewa
“Yallabai yau naga wata yarinya a wajen mai magani,kuma naga albarka da daukaka sosai a fuskarta”
Murmushi dayan mutumin yayi tare da cewa
“Ka dai ce kawai kaga kyakyawar yarinya,amma yaushe har ka fara karantar fasalin fuskoki? (Facial features)Tun yaushe nake fama da kai ka kasa iyawa sai yau kuma?” Ya qarasa yana mai fadada murmushin sa,cikin sarewar gwiwa matashin yace “da gaske nake fa yallabai,da gaske naga daukaka sosai a fuskarta,amma kuma da alama akwai matsaloli da dama da suke bibiyarta” tabe baki wancan mutumin yayi ba tare da yace komai ba,da ganin haka shima matashin ya kama bakin shi yayi shiru domin da alama maganar shi ba mai karbuwa bace a halin yanzu.
Shukra kuwa ko da ta shigo a hankali take tafiya,wata zuciyar ce tace bari taji wanne irin itatuwa aka bata ta shigo dasu? Qunshin kayan ta kai daidai hancinta,tare da jijjiga kai alamun gamsuwa,ta qarasa har cikin quaters din lady jalila ta miqa su ga chief maid dinta sannan ta juyo zuwa bureu of music.
Toh fah masu karatu,nasan tambayoyinku suna da yawa.
Shin abinda mai duba fasalin fuskar shukra ya fada zai zama gaskiya?
Shukra ta fahimci irin abin da aka bata ta shigo dashi ko kuwa?
Shin haduwarta da mai martaba a wannan daren ba zai zamar mata matsala ba?
Ku biyo ni dai domin jin amsoshin ku.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏻❤️
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Whattpad :Oum_tasneeem
Page 12
Washegari da safe lady jalila ta tashi da wani irin yanayi da kowa ya kasa ganewa,aikawa tayi a kira mata shukra,a kan hanyar su ta shigowa cikin quaters din suka ci karo da chief maid da tray a hannunta,abinda shukra ta kawo ne akan tray din,a dayan bangaren kuma wuqaqe ne,har sunyi gaba shukra ta juyo tacewa chief maid din
“My lady wannan ba leonuri herba (motherwart in english,ban san sunanshi da hausa ba) bane da na kawo jiya?” A razane chief maid ta jefo mata tambaya
“Ya akayi kika san haka? Kin bude abinda aka baki kenan kafin ki kawo?”
Girgiza kai shukra tayi tare da cewa
“A ah ban bude ba,qamshin ta na gane,kuma na san qarfe yana rage qarfinta (anti metal properties) gara kisa kaba amma kada kisa qarfe”
Jinjina kai chief maid din jalila tayi tare da qara jeho wa shukra tambaya
“Amma ya akayi kika san duk ilimin wannan abubuwan?”
Rusunar da kanta tayi tare da bata amsa
“Saboda ma’aikatan bureu of music suna dan yin rashin lapia da ba’a rasa ba,shiyasa nake karanta littafan magunguna domin samar musu magani”
Ba tare da ta qara ce mata komai tayi gaba,ganin haka yasa itama shukra tayi hanyar shiga wajen lady jalilah.
Shigarta ta tarar da ita a inda ta saba zama,tsayawa tayi tana fuskantar ta tare da rsusunawa ba tare da ta ce komai ba,da murmushi jalila take kallonta tare da ce mata
“Zauna shukra” duqusawa shukra tayi ta zauna akan qafafuwanta,jim shiru ya ratsa tsakaninsu,daga bisani jalila tace
“Na san zakiyi mamakin kiranki da na qarayi yau,na kiraki ne domin na baki haquri don na san na baki aiki mai matuqar wahala wanda zai iya saki a hadari” gyada kai shukra tayi bata ce komai ba,ganin haka jalila ta cigaba
“Ina son ki yafe min da qoqarin sa rayuwarki a cikin hadari da nayi”
Girgiza kai shukra tayi tare da cewa
“Ba komai your highness” ta fada a taqaice,da murmushi jalila take kallonta tana qara jin yarinyar tana burgeta,sallama tayi mata ta tashi ta tafi,a bakin qofa shukra suka gamu da haj jamela,cikin girmamawa ta gaishe ta ta wuce.
Haj jameela na shigowa ta tarar da jalila a inda shukra ta barta,zama tayi a inda shukra ta tashi,kafin jalila tace wani abu haj jameela ta fara magana
“Your highness wace iriyar magana nake ji daga wajen chief maid dinki?” Jalila ta bude baki zata yi magana kenan chief maid ta shigo da faranti sai wani qaramin bowl 🥣 da magani a ciki yana ta tururi,ta ajiye kan qaramin tebur din da ya raba jalila da haj jameela,haj jameela ce ta qara cewa
“Maza ki shanye,domin babu wani maganin da zai yi sauri boosting din fertility dinki (haɓaka damar daukan ciki) kamar wannan”
Jalila ta kalli chief maid dinta tare da cewa
“Shekarar ki nawa kina tare da ni?”
Cikin ladabi tace
“Na kusa shekara shida”
Harara jalila ta watsa mata tare da cewa
“Shekara shida kuma har yanzu baki sanni ba ko? Dauke wannan abin kuma ki batar da duk wata shaidar shigowar sa a cikin masarautar nan”
Da mamaki haj jameela take kallon jalila
“Jalilah cewa fa kikayi a zubar,kin san tsadar maganin kuwa? Da kuma hatsarin da aka shiga kafin a shigo miki da shi?”
“Hatsarin lda aka sa yarinyar nan ne yasa nace ba zan iya wannan abin ba,na kwana ina tunanin yadda na sa rayuwarta a hadari saboda biyan buqata ta,ba zan iya ba mama,hankali na yaqi kwanciya”
A dai dai lokacin wata a cikin maids dinta ta shigo a rikice tare da cewa
“Your highness an samu gagarumar matsala”
Gaban jalila ne yayi mummunar faduwa,Cikin razana ta kalli yarinyar tare da cewa
“Fada min yanzun nan,me yake faruwa”
❤️❤️❤️❤️❤️
A grand palace,mai martaba cikin razana ya kalli chief eunuch tare da cewa
“Kace an sa guba a tonic (hadin magani) din queen haneefah?”
Gyada kai chief eunuch yayi tare da cewa
“Hakane mai martaba,an gane hakan ne ta hanyar cokalin qarfen da aka saka da ya canja kala,Abin farin cikin ma shine bata kai ga shan tonic din ba” (a wancan zamanin suna gane akwai guba a cikin abinci ne ta hanyar amfani da qarfe,idan har akwai gubar qarfen zai canja kala kamar an zuba masa hypo,idan kuma babu toh ba zai yi komai ba)
Mai martaba shiru yayi na dan wani lokaci kafin yace
“Na bada umarnin a binciki duk herbs din da suke royal phamacy da masu haqqin shigo da su cikin masarauta,da masu siyar da maganin cikin gari,da kuma royal doctors”
Rusunar da kanshi chief eunuch yayi tare da juyawa ya bar wajen ya bar mai martaba cikin tunanin wane mai burin mutuwar ne ya aikata hakan?
❤️❤️❤️❤️❤️
A royal pharmacy kuwa a na can ana taqaddama da alhini,kowa hankalin shi a tashe yake da abinda ya faru,chief eunuch ne ya qaraso ya kalli royal doctor tare da cewa
“Ina son jerin magungunan da ake bawa queen (tonic prescription) da kuma ainihin wanda aka dafa mata yau”
Cikin ladabi ya nufi inda suke ajiye takaddu ya dauko wasu takaddu sunkai guda bakwai (A yadda tsarin masarautar yake,ba sai basu da lafiya ake basu magani ba,akwai tonic da ake basu kullum domin qara musu lapia,haka shima mai martaba yana da wanda yake sha kullum,a misali itatuwan da zasu qara musu lafiyar zuciya,lafiyar ido,ko kuzarin jiki da sauransu)
A hankali cikin tsanaki yake duba takaddun,nannade su yayi tare da juyawa ya bar wajen.
Royal guard office ya nufa,ya samu chief of royal guard tare da bashi umarnin mai martaba na a bincika duk masu saida maganin cikin garin,hakan yasa aka baza royal guards ko ina a cikin garin domin bincikar record din magungunan da suka bayar a cikin satin.
Bincike dai yayi bincike har zuwa inda shukra taje karbo magani,amma da zuwansu sai gawar mai maganin suka tarar,hakan yasa suka dauko gawar suka taho da ita masarauta domin bincike,a dakin da aka tanada domin binciken gawa a cikin police bureu suka ajiye gawar,tare da miqawa ‘yan sandan wajen ragamar binciken gawar,littafin record din wanda suka karbi magani a wajensa kuwa suka miqashi ga office of investigation.
Jita jita ce ta fara yawo a cikin masarautar ba tare da ansan daga inda ta fito ba,na cewar lady jalila tasa an shigo da magani daga waje domin ta kashe sarauniya haneefah,kuma ta sa an kashe mai maganin saboda asirin ta ya rufu,fitowar wannan jita jitan yasa rikici da dama a cikin masarautar,cikin wanda suke cikin rikici kuwa har da shukra,domin wanda ya fitar da jita jitar bai bar shukra ba,sai da sunanta ya fito. Duk inda hankalin jalila yake ya kai qololuwar tashi,kasancewar abinda take tsoro shi ya faru.
A cikin binciken da ake a royal pharmacy aka gano dalilin da yasa tonic din queen haneefa ya zama mai cutarwa,kuma ba guba bace aka saka,wani ganyen magani ne da ake kira da pinnelia,kuma idan ya hadu da wani itace na cikin ainihin tonic din sai su hadu su bayar da guba,amma dukkansu ba masu cutarwa bane akan kansu har sai an hada su.
Kasancewar lady jalila matar sarki yasa babu wata bayyananiyar hujja da za’a bincike ta,hakan yasa aka kamo shukra zuwa office of investigation wanda yake cikin gidan mata kasancewar sunanta ya fito cikin record book din wadanda suka karbi magani a wajen mai maganin da aka samu gawar shi.
Da farko tambayoyi aka fara yi mata,da yake office din mata ne,chief madam investigator,irin kayanta daya da chief maids na cikin palace wato green colour (kore) kuma itace shugabar office of investigation,sai mutum uku da suke biye mata a matsayi,suma irin kayanta ne a jikinsu amma ash colour(ruwan toka)sai ladies investigators wanda ‘yan mata ne matasa su kuma doguwar riga ce tasu mai kalar pink,kuma yawansu zai kai su ashirin,duk aikin cikin masarautar aikin ladies investigators shine yafi ko wane aiki daraja saboda sai ‘ya’yan manya a garin ake bawa wannan aikin,wanda suka samu ilimi mai kyau.
Shukra a zaune akan kujera da tebur a tsakiya,sai wasu kujerun guda uku a zagaye da tebur din,duk da hankalinta a tashe yake amma tana da qarfin halin da zaka kasa gane yanayin da take ciki,chief madam ce ta shigo,a bayanta ladies investigators ne guda biyu,a kujerar da take fuskantar shukra ta zauna yayinda yan matan suka zauna a sauran kujerun guda biyu da suka rage.
Kallon shukra take a cikin ido tare da cewa
“Ina fatan zaki bamu hadin kai,ki amsa mana tambayoyin da zamuyi miki domin kema ki samu sauqin uqubar da zata iya biyo baya matuqar kikai mana taurin kai”
Ta qarasa maganar har yanzu idonta yana cikin na shukra,sunkuyar da kai shukra tayi ba
tare da tace komai ba,chief madam ta fara tambayoyin ta da cewa
“Shin ko kinsan shigo da magani daga waje haramtacciyar doka ce a cikin masarautar nan?”
Gyada kai shukra tayi tare da cewa
“Yes my lady,na san da haka”
Chief madam ta qara jefo mata tambaya
“Me yasa kika aikata hakan,bayan sanin cewar babban laifi ne hakan? Kuma waye ya saka ki aikata hakan?”
Cikin dakewa da tattaro qarfin halinta gaba daya tace
“Leonuri herba ne na karbo domin hadawa wasu cikin ma’aikatan bureu of music maganin mura,da ciwon kai kuma babu wanda ya sani aikata hakan,nayi ne akan kaina”
Cike da mamaki investigators din suke kallon ta domin sun san qarya take,kuma sun kasa gane dalilin da zaisa ta dauki wannan laifin mai girma saboda jalila,meyasa zata yi hakan?”
Ba yadda basuyi da ita ba amma shukra taqi fadan abinda suke buqatar ta fada,kawai ta furta sunan jalila suke buqata amma shukra taqi,hakan yasa suka tafi sashe na gaba bayan tambayoyi wato uquba da azabtarwa.
Labarin rashin maganar shukra ya bawa jalila mamaki qwarai da gaske,domin bata taba tunanin shukra zata iya kare ta haka ba,hakan yasa hankalinta ya tashi jin za’a fara azabtar da shukra saboda taqi magana,yayinda haj jameela da chief maid dinta suke ganin ba abin damuwa bane akan wata servant girl,ko da an yanke mata hukuncin kisa ai ba matsala bane tunda dai ita jalilan ta tsira.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏻❤️
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Whattpad :Oum_tasneeem
Page 13
Tun yammacin da aka fara azabtar da shukra babu tausayi babu imani,daureta akayi akan kujera a bakin office din chief madam inspector,ba ruwa babu abinci tana zaune amma babu wata uquba bayan wannan,har yanzu amsarta daya ce cewar babu wanda ya sata shigo da magani cikin masarautar.
Sameer da manager hankalin su yayi qololuwar tashi kuma gashi babu abinda zasu iya yiwa shukra a wannan halin,tahowa sukayi qofar office of investigation,idan masu karatu basu manta ba,office of investigation yana cikin gidan mata ne inda ba’a shiga sai mai martaba kawai sai kuma wanda aka bawa izinin hakan,cike da tashin hankali manager ya kalli sameer yace
“Ya kamata mu bar wajen nan kafin wani ya ganmu”
Sameer ba tare da ya juyo ba ya mayar masa da amsa
“Yallabai shukra fa tana ciki,ko ma yanzu sun kashe ta oho”
Hannu manager ya saka ya doke bakin sameer tare da cewa
“Kul ka qara fadan haka,amma dai ina jin tausayin yarinyar nan don babu wanda zai damu don ta amsa laifin da ba nata ba”
A quaters din lady jalila itace zaune a inda ta saba zama sai mariqinta minister na tribunal yana fuskantar ta,cikin tsanaki tace
“Hakan nake nufi minister,zanje na miqa kaina a office of investigation “
Cikin razani bakinshi na rawa yace
“Your highness idan kikayi haka zaki sa mai martaba cikin wani hali,za’a dinga cewa an kama matar da ya fiso da qoqarin kashe sarauniyar shi,kuma a wannan lokacin ko shi ba zai iya yi miki komai domin dokar qasa ba zata bashi wannan damar ba,ki duba dai your highness”
A tsanake tace masa
“Kayi haquri amma abinda zanyi kenan,ba zan iya zuba ido ana qzabtar da yarinyar da bata ji ba bata gani ba,ni matar sarki ce basu isa suyi min yadda sukai mata ba,kuma tunda nasan ban sa an shigo da pinellia ba,na san gaskiya zatai halinta”
Haka minister ya cigaba da bata baki,ba tare da ta qara ce masa komai ba har suka gama magana ya tafi.
A quaters din queen dowager jikinta da sauqi,mugun nufi ya sata ta qarfafa jikinta ta shirya tsaf cikin kayanta na alfarma,da kuma alkyabbar ta mai dragon 🐉 a zaune take a sitting room dinta,a gabanta kuma minister of state affairs ne a durqushe,cike da ladabi yake ce mata
“Your majesty komai ya kammala”
Fuskarta cike da mugun nufi tace
“Ka tabbatar wannan karon ba’a samu matsala ba”
Qara rusunawa yayi yace
“Komai yana tafiya daidai yadda muka tsara your majesty ki kwantar da hankalinki”
Jinjina kai tayi ta maida idonta kallon waje daya,tana kimtsawa kanta abinda ita kadai ta san menene.
A office of investigation chief madam ce take cewa shukra
“Da alama bakya son rayuwar ki,ki fadi abinda ake buqata ki bar wajen nan kema ki huta amma kinqi ko?”
Shukra ta bude baki cikin yunwa da qishirwa tace
“Magana ta daya ce,banyi hakan akan unarnin kowa ba kuma babu pinellia a cikin abinda na shigo dashi” ta qarasa da qyar.
“Nice nan na saka ta shigo min da maganin”
Dukkansu suka kalli daga inda maganar ta fito,da mamakinsu lady jalila ce,chief madam da sauri ta qarasa inda take ta tsaya,dan rusunar da kanta tayi kamar an mata dole tare da cewa
“Your highness kinsan me kike fada kuwa?”
Gyada kai jalila tayi tare da buga mata harara
“Tabbas na san me nake fada,ko ba abinda kike son kiji yarinyar nan ta fada bane? Shine na fada miki da bakina,sai ku sake ta ta tafi domin bata da laifi”
Chief madam ta kafeta da ido babu ladabi tace
“Hakan yana nufin office dinmu zai bincike ki fah kenan your highness”
“A shirye nake da hakan shiyasa kika ganni a nan”
Umarni chief madam ta bayar a saki shukra a kuma raka lady jalila inda za’a yi mata tambayoyi,shukra cikin galabaita ta daga kanta ta kalli jalila
“Me yasa kikai haka your highness? Ni da ke mun san bamu shigo da pinellia ba,meyasa zaki dauki laifin da ba ke kika aikata ba?”
Murmushin takaici tayi ta kalli shukra tace
“Nayi hakan saboda ba zan iya jurewa kina cikin wannan halin saboda ni ba,ko ba komai ni zan samu sassauci ko don kasancewa ta CONSORT a cikin masarautar nan,kuma in har kin yadda bani da laifi komai daren dadewa gaskiya zata fito,ki yafe min akan wahalar da kika sha saboda ni”
Tana gama fadar haka ta shige ciki ta bar shukra a nan,kunce shukra akayi,cikin warfin hali take takawa cikin rakiyar special lady investigator mai ash uniform guda daya (Basma) da kuma lady investigator mai pink uniform guda daya(Aliya) sameer da manager da suke tsaye a bakin wajen suka jiyo motsin tafiya,buya sukayi da sauri yayinda su shukra suka qaraso bakin qofar,cikin girmamawa shukra ta daure tayi da rusunar da kanta
“Nagode” ba tare da sunce mata komai ba suka juya zasu koma ciki maganarta ta tsayar dasu
“Amma ne zai faru da lady jalila?” Ta fada cikin nuna tsantsar damuwar ta
Aliya ce ta kalleta kamar zata kai mata duka tace
“Ina ruwanki da abinda zai faru da ita,ke dai tunda kin tsira maza bace daga nan” ta qarasa cikin fada,shiru shukra tayi su kuma suka koma suka barta a tsaye a wajen,duk abinda akeyi a kunnen su sameer da manager da suke labe,suna ganin investigators din sun bar wajen suka fito kowannen su da saurin shi ya qaraso inda shukra take tsaye,cikin farin cikin ganinsu gaba daya ta jefo musu
“Me kukeyi a nan? Saboda ni kuka zo?”
Manager ne ya bata amsa da
“Ko bacci bamu iya yi ba jiya saboda fargabar halin da kike ciki,basu ji miki ciwo ba ko?”
Jikinta yake bi da kallo wai yana neman ko sunji mata ciwo,sameer da yake tsaye bai ce komai ba ne ya miqo mata gorar ruwa,da sauri ta karba ta fara sha kamar bata taba sha ba,tausayinta ne ya rufe su gaba daya suka zuba mata ido,sai da ta sha yadda ya ishe ta sannan ta sauke gorar daga bakinta tare da kallon sameer tace
“Nagode yallabai,nagode da nuna damuwarku a gareni”
Manager ne ya cafe
“Kema sai ki daina janyo mana magana da rashin jin ki da karambani” shiru tayi tare da sunkuyar da kai
“Ni tunani na ma wane irin hali lady jalila zata shiga”
Sameer yai saurin cewa
“Ai da sun gama yi mata tambaya zasu barta ta tafi tunda matar sarki ce ai ba zasu riqe ta ba kuma gashi ma tana da juna biyu”
Jinjina kai manager da shukra sukayi,suka fara tafiya domin komawa bureu of music.
Suna qarasawa abinci ta samu mai rai da lafiya sun tanadar mata,ta zauna taci mai isarta,iya gata taga gata a ranar domin shaquwar su ta qara habaka sosai.
Lady jalila a kan teburin tambayoyi,chief madam inspector ce (lady sumayya) tana zaune akan kujerar da take fuskantar jalila,cikin girmamawar da bata kai har zuciyar ta ba tace
“Your highness ina fatan zaki bamu hadin kai domim amsa dukkan tambayoyin da zamuyi miki”
Cikin qasaita jalila tace
“Tsawon wani lokaci tambayoyin naku zasu kai?”
Lady sumayya tace
“A bisa tsari suna kaiwa tsawon awa daya”
Jinjina kai jalila tayi alamun gamsuwa,miqewa lady sumayya tayi tare da kallon special investigator da take kusa da ita mai ash uniform(Nadeeya) da kuma lady investigator mai pink din uniform (Afrah) sannan tayi hanyar fita,nadeeya da afra ne tabi bayanta,kafin su qarasa bakin qofar office din sumayya ta tsaya ta kalli nadeeya tare da cewa
“Ke nadeeya kije ki samu basma ku tafi quaters din lady jalila ku bincika komai a wajen,kada kubar komai baku duba ba,mu kuma zamu tsawaita lokacin tambayoyin har ku gama abinda kukeyi zamu riqeta a nan” ta fada a cikin sigar bada umarni,cikin girmamawa nadeeyah ta rusunar da kanta tare da cewa
“Yes my lady”
Chief madam ta juya ta kalli Afrah “ke kuma muje duk abinda ta fada ki dinga rubutawa,kuma ki tabbatar bakiyi rubutu da sauri ba”
Rusunar da kanta afrah tayi tare da cewa
“Yes my lady”
Chief madam sumayya da afrah suka koma ciki yayinda nadeeya kuma ta fita neman basma.
Jameel ne cikin tashin hankali yake shigowa dakin mahaifin sa,a zaune ya tarar da mahaifinsa nasa a inda ya saba zama yayi zurfi cikin tunani,zama shima yayi a qasa tare da cewa
“Abba kaji abinda yake faruwa kuwa? Jalila fa ta kai kanta office of investigation “
Jinjina kai ba tare da yace komai ba kuma bai juyo ya kalli jameel ba,ba komai yake tunawa ba sai lokacin da jalila take fada masa zata miqa kanta saboda wata baiwa,jameel ne ya qara cewa
“Abba kamar baka jin abinda nake cewa”
“Ina ji mana,yanzu me kake so muyi jameel? Jalila ta san cewa dukkan yankin mu sun dogara ne da qarfin ikonta a cikin masarauta kuma ta aikata hakan,yanzu idan muka ce zamu shiga muma zata iya jan mu ta goga mana laifin,saboda haka abinda yafi kawai shine mu qyale ta taji da abinda ta daukowa kanta”
Cike da mamaki jameel yake kallon mahaifin nasa,yace
“Haba Abba,ko ba komai jalila fa ‘yar dan uwanka ce,ni dai a ganina mu nemi yadda zamuyi mu dorawa wani laifin amma jalila ta kubuta,ko da wannan baiwar ce shukra tunda mayar da laifin kanta zai fi sauqi tunda itace ta shigo da maganin”
Shiru tribunal minister yayi yana nazarin maganar da jameel yake fada,cikin qara gamsar dashi jameel ya qara cewa
“Ina jin a jikina akwai wani abu da son qullawa jalila a cikin masarautar nan,domin kuwa mai bada maganin nan shi kadai ne shaidar cewa bata karbi pinellia a wajenshi ba kuma kaga an kashe shi saboda wata manufar”
Gyaran murya minister yayi tare da cewa
“Zancen ka gaskiya ne jameel,idan muka bar jalila ta fadi to muma mun fadi,zamu san yadda za’ai a mayar da laifin kan yarinyar yadda ko jalila ba zata iya kareta ba”
Cikin gamsuwa jameel yace
“Nagode da ka fahimceni Abbana”
Murmushi yayi masa tare da shafa fuskar sa yace
“Idan ban fahmce ka ba,wa zan fahimta babban mutumi?” Murmushi jameel ya mayar masa tare da tashi ya bar dakin.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏻❤️
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Whattpad :Oum_tasneeem
Page 14
Duk tsawon lokacin da suka dauka a qarshe dai aka gama yiwa lady jalila tambayoyi,afrah ce ta kalli lady jalila cikin girmamawa tare da cewa
"Your highness zan aika a kirawo maids dinki su raka ki quaters dinki" lady jalila ta miqe tsaye ba tare da ta kalli afrah ba tace
"A ah ki barshi,na san guda biyu suna jirana a waje,zamu tafi tare da su" tana magana tana takawa zuwa hanyar waje.
A daidai wannan lokacin an birkita ko ina a cikin quaters din lady jalila ba tare da saninta ba,ladies investigators ne masu pink din kaya ko ina a cikin quaters din suna ta bincike bincike,wata murya ce mai tashi tace
"Ga shi nan na samo" dukkansu suka dakata da abinda sukeyi tare da mayar da hankalinsu inda maganar take fitowa,wata yarinya ce lady investigator Sameerah,Basma ce ta qaraso inda take da sauri,sameerah ta rusunar da kanta tare da miqawa basma abinda ta samo,hakan yasa suka bar binciken tunda sun samu abinda suke nema. Maids din lady jalila suna ta kuka saboda qarshen wulaqancin da akai wa iwar dakinsu na binciken rashin mutunci,kuma gashi ance an samo abinda suke da yaqinin babu shi a cikin quaters din,tabbas wani makircin ne ake qoqarin qulla mata.
Fitowar lady jalila daga office din ta kalli gefenta da dayan gefen taga babu qyallin maids dinta ko daya,cike da mamaki a fili tace
"Me hakan yake nufi? Ya kamata ace suna jira na a nan,ko meyasa suka tafi?" Kafin ta gama tunanin abinda ya faru ta jiyo muryar lady sumayya tana cewa
"Ni nace su tafi su barki,domin da yiwuwar ba zaki tafi a daren nan ba" ta fada idonta cikin idon lady jalila,mamakin hakan ne ya cika jalila ta ce
"How dare you " cikin zare ido ta cigaba
"Ki dinga kallon cikin idona kina min magana babu ladabi?" lady sumayya ta dan saukar da idonta qasa ba tare da tace komai ba,shiru ne ya ratsa tsakani suna tsaye sai ga investigators basma da Aliya sun taho da faranti da bowl a kai,bowl din kuma pinellia ce da aka samo a quaters din jalila a cikin ta,suna zuwa daidai inda chief madam sumayya take suka tsaya da farantin a hannunsu,sumayya ta kalli jalila tare da cewa
"Wannan shine sakamakon binciken da akayi a quaters dinki kuma an samu pinellia da aka sawa queen haneefah a cikin tonic dinta har ya zama mai cutarwa"
Cikin firgici lady jalila take bin sumayya da kallo,daga bisani ta mayar da kallonta kan basma da aliya ba tare da tace komai ba,nan take zuciyarta ta bata anyi amfani da miqa kanta da tayi an qulla mata wani makircin,chief sumayya ce tace
"My lady zaki iya komawa ciki,domin yanzu you are under arrest da samun cikakkiyar hujjar qoqarin halaka uwar qasarmu,queen haneefa" idon jalila ne ya cicciko da ruwa,ta juya ta koma cikin office din,kan kujerar da ta tashi ta koma ta zauna,itama sumayya ta shigo ta zauna a wacce take fuskantar jalila,cike da rashin ladabi tace
"Muna tuhumarki da qoqarin halaka queen haneefah,ko zaki fada mana dalilin da ya sa kikai yunqurin aikata haka?"
Jalila idonta cike da ruwan da bata basu damar zubowa ta kalli sumayya
"Ban san abinda kike fada ba,domin babu abinda kuke fada a cikin quaters dina,ban san abinda kuke cewa ba,sharri ake son ayi min"
Ta qarasa maganar cikin murya mai rauni
"Amma ga abinda aka samo a quaters dinki,wannan ma kadai ya isa hujjar abinda muke thumar ki dashi" sumayya ta fada tana nuna mata bowl din da aka zuba ganyen pinellia a ciki,jalila ce ta zare ido tare da cewa
"Ki iya bakinki,ki san da wa kike magana cikin rashin da'a"
Cike da tsiwa sumayya tace
"Ke zaki iya bakinki saboda kina nan ne a matsayin mai laifi"
Jalila shiru tayi ba tare da ta qara cewa komai ba,haka nan ta kwana a office of investigation.
Washegari da safe mai martaba yana fitowa chief secretary ya kawo takaddun da suke buqatar ya duba ya kuma yi musu stamp,wanda yake buqatar yanke hukunci a yanke,a cikin takaddun yaci karo da takaddar da ta fito daga office of investigation na tuhumar da akewa jalila da kuma shaidar evidence da aka samu a quaters dinta,a razane ya dago ya kalli chief secretary da yake tsaye daga bisani ya mayar da kallonshi kan chuef eunuch tare da jefa mai tambaya
"Me wannan yake nufi? Jalila tana office of investigation? Sunyi arresting dinta sun samu hujja a quaters dinta? Wannan shine abinda kake boye min tun jiya kenan?" Duk a tare ya jefo tambayoyin,yayinda duk su biyun shiru sukayi tare da qara sunkuyar da kansu qasa,sassauta muryar sa yayi tare da cewa
"Ina magana duk kunyi min shiru,kuna tunanin idan na sani tun da wuri zan shiga sha'anin matan inner court ko? Babu abinda zan iya yiwa jalila amma ya kamata a sanar da ni tun jiyan" har yanzu babu wanda ya motsa a cikinsu bare suce wani abu,don dama sun san hakan zata faru duk lokacin da ya ji labari,miqewa yayi daga wajen ya bar takaddun ba tare da qarasa duba su ba ya koma cikin daki,zagaye dakin yake tayi cikin zurfin tunani,shi ya san jalila ba zata taba aikata haka ba,kuma tunda aka samu hujja to babu makawa sai ya yanke mata hukunci domin laifin yunqurin kashe sarauniya laifin cin amanar qasa ne,ta yaya zai iya yankewa macen da ya fi so a duniya hukuncin da ya san cewar bata da laifi a kai? Yaya zai yi ya samo hujjar da zata nuna bata da laifi? Wannan tunanin yayi tayi ba tare da yasan mafita ba domin dokar qasa zata iya daure kowa har da shi kuwa.
Gaba daya masarautar ta dauki labarin anyi arresting lady jalila ana jiran mai martaba ya yanke mata hukunci,wanda suke alhini suna yi,masu murna ma sunayi.
Shukra ma tana cike da jimami har yamma da sameer yazo ya sameta tayi tagumi
"Shukra meyasa kike damun kanki akan abinda baki da maganinshi?"
Dago idonta tayi ta kalli sameer,kamar zata yi kuka tace
"Da ni da kai mun san cewar lady jalila bata da laifi,hujjarta daya kuma an kashe shi mai bada maganin"
Sameer ya jinjina kai tare da cewa
"Hakane kuma kinga babu abinda za'a iya yi da gawa" kamar maganar ta tsikari shukra ta miqe da sauri,da gudu ta shiga dakin ajiyar su ta fito da wasu kwalabe,sai wani yadi ta qaraso inda sameer yake ta shimfida yadin ta jera kwalaben sannan ta daure,kallon rashin fahimta sameer yake mata
"Menene wannan? Me zakiyi dashi?"
Ba tare da ta kalle shi ta cigaba da daure kwalaben cikin yadin
"Zan sa gawar tayi magana ne,don hakan ne kadai shaidar lady jalila"
Dariya sameer ya barke da ita har da durqusawa qasa yana nuna shukra da dan yatsan sa yace
"Amma kin haukace ko? Kisa gawa magana?" Ya fada cikin dariya tare da riqe cikinshi,ko ta kanshi bata bi ba ta dauki kayan da ta daure ta fita ta bar masarutar,office din 'yan sandan sirri ta nufa a bakin qofa ta tarar da sojojin da suke gadi,zata kutsa kanta kenan suka ce mata
"Ke !! Me kike yi anan wajen?" Cike da ladabi tace
"Shugaban 'yan sandan sirri nake nema,ban san sunan shi ba amma" kallon kallo sukayi daga bisani dayan yace mata
"Kinga kama hanya ki bace daga nan"
Cikin raunin murya tace
"Ku taimaka ku kirawo min shi,ku ce masa shukra ce zai gane"
Dayan da tun dazu baiyi magana ba yaji tausayinta,miqewa yayi ya shiga ciki,jim kadan ya fito ya kalle ta
"Kinga ki kama hanyarki ki tafi,yace bai sanki ba"
Zare ido tayi tace "kuma kace masa shukra ce?"
Basu qara ce mata komai ba suka share ta,ganin tana zaman bata lokacin ta ne yasa ta bar wajen tana tunanin lallai dan sandan sirrin nan yayi mata rashin mutunci,sai yau da tazo neman taimakon shi.
Daga nan police bureu ta nufa,tana zuwa bakin qofar wajen taga 'yan sandan da suke gadin wajen a tsaye suna ta kai kawo,labewa tayi a jikin wata katanga tana hangosu,tsoro ya cikata sosai,tana ta tsaye ta rasa yadda zatayi ta shiga wajen,da taga ta gaji da tsayuwa ta juya da niyyar tafiya daga wajen wata zuciyar tace mata
"Meyasa kike jin tsoron yin abinda kikayi niyya,bayan lady jalila tana can cikin wani hali" wannan tunanin ya sa ta ta juyo ta tafi kanta tsaye zuwa 'yan sandan da suke gadin.
Ps: ku riqe sunayen duk ladies investigators da na lissafa domin nan gaba kadan labarin zai dawo office of investigation kacokam.
Oum tasneem ✍️❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏻❤️
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Whattpad :Oum_tasneeem
Page 15
A grand palace mai martaba yana zaune gaban takaddun da aka kawo masa da safen,amma ba duba su yake ba,dayan bangaren kuma pinellia da aka samo a quaters din lady jalila ne a cikin bowl,yayi nisa cikin tunani can ya dan nisa tare da gyaran murya yace
"Waye a nan?" Cikin dan daga sautin muryar sa,chief eunuch dake tsaye a bakin qofa ya shigo cikin hanzari,tsayawa yayi a gaban mai martaba ya rusuna tare da cewa
"Kana nemana ne your majesty?"
Fuskarshi babu yabo ba fallasa yace
"Ka kirawo min chief secretary,ina son na bada Inperial order" (Imperial order- umarnin masarauta kenan wanda babu wanda zai masa shamaki)
Rusunar da kai chief eunuch yayi tare da juyawa ya fita.
Bayan minti goma komai ya kammala mai martaba ya fito cikin rakiyar chief eunuch da maids dinsa suka nufi office of investigation,da zuwansu ladies investigators suka fito,chief sumayya a gaba,Basma da nadeeyah a bayanta,sai Aliya,sameerah da Afrah suma da suka ware bangare guda,a tare suka rusunar da kansu a gaban mai martaba tare da cewa
"Barka da zuwa your majesty"
Bai amsa musu ba kuma bai daina yi musu kallon tuhuma ba,wucesu yayi yana qoqarin shiga cikin office din da jalila take,da sauri nadeeya tace
"Your majesty za'a sanar da ita zuwanka" dakatawa yayi har yanzu bai ce komai ba,nadeeya tazo ta wuce ta gabansa ta shige cikin office din,ladies investigators din da suke wajen ta kalla tace musu
"Ku bamu waje" nan da nan suka fice,ta ce
"Your highness kina da baqo"
Kafin jalila ta amsa mata ta dan daga murya
"Zaka iya shigowa" rufe bakinta ke da wuya mai martaba ya danno kai cikin office din,ganin shi yasa jalila tashi daga kujerar da take zaune cikin nutsuwa da cikakkiyar haiba kamar ba wacce take cikin tashin hankali ba,ba tare da ya kalli inda nadeeya take ba yace
"Zaki iya bamu waje"
"Yes your majesty" ta fada tare da rusunar da kanta sannan ta bar wajen.
Tana fita ya zauna a kujera,itama jalila ta koma ta zauna,kallonta yakeyi cikin tausayawa,daga bisani yace
"Kina nan cikin nutsuwarki da kamala kamar kullum,daman na san ke ba irin matan da zasu bare baki suna kuka suna ihun basu da laifi bane" murmushi kawai tayi ya cigaba
"Na san cewar baki da laifi,ina tsantar nadamar dawo dake cikin masarautar nan,sanin da nayi miki mace mai aji ba zaki taba zubar da qimar ki kiyi abu irin wannan ba,amma a matsayina na mijinki na yarda dake sai dai kuma a matsayina na sarki hakan ya tilasta ni yadda da hujjoji ne kawai"
Murmushi tayi mai ciwo tace
"Nagode da ka yadda dani,kuma na dade da sanin cewar wanda nake so ba qaramin mutum bane irin kowa,zuwan da kayi nan ma a matsayin mijina kazo ba a matsayin sarkin qasar nan ba,hakan kadai ya ishe ni" ta fada tare da sunkuyar da kanta tana wasa da 'yan yatsun ta,idonshi ne ya cika da qwalla cikin rashin sanin abinda ya kamata yayi ya kalleta
"Za'a miqawa tribunal alhakin binciken,zasu bayyana gaskiyar abinda ya faru,kafin sannan ki qara haquri na kasa kareki" ya qarasa maganar hawaye ya taru taf a idonshi,qiris suke jira su zubo,ba tare da ya jira me zata qara cewa ba ya miqe ya fita domin baya son taga raunin sa.
A cikin police bureu,wata amalanke ce aka shigo da ita da kaya a kai,assistant lieutenant na police ne ya ke bawa yaran umarni
"Ku sauke wannan kayan a kaisu dakin da ake ajiye gawawwaki" juyowa sukai tare da fadin
"Yes sir" tare da rusunar da kansu suka fara aiwatar da abinda yai umarni,lura yayi da wani saurayi wanda shi bashi da uniform a jikinsa kuma bai taba ganinshi a wajen ba yace
"Kai,waye kai? Me kake anan?" Kafin saurayin yayi magana daya daga cikin police din yace
"Sabon mai binciken gawa ne (corpse handler) yau ya fara aiki" jinjina kai assistant lieutenant din yayi,shi kuma saurayin yayi saurin rusunar da kanshi cikin girmamawa yace
"Nine sabon corpse handler,sunana Abdullahi Sulaiman" jinjina kai ya qara yi alamun gamsuwa ba tare da ya amsa ba.
Shukra tana waje tare da masu gadi,daya daga cikinsu ne yace mata
"Me kika zo nema nan?"
Cikin qarfin hali tace
"Zuwa nayi zanga IG akan case din lady jalila"
Kallon tuhuma sukai mata,kafin suce wani abu assistant lieutenant yana qarasowa wajen domin fita zai tafi,jin abinda take fada yasa yacewa masu gadin su barta ta qaraso wajenshi,tambayoyi ya fara yi mata,suna shigowa cikin wajen,shukra tace
"Office of investigation sun yi arresting dina nima,kuma ance idan akwai abinda na manta zan iya zuwa kowane lokaci shiyasa nazo na fadawa IG" a tsanake yake kallonta tare da cewa
"Amma ai can zaki koma ki fada musu ba nan ba,amma dai ki tsaya a nan bari in fadawa lieutenant" barin ta yayi a wajen tare da juyawa,ai tana ganin ya juya itama ya juya ta fara shiga cikin wajen tana labewa idan taga mutane suna tahowa,a haka har ta bulla inda wasu dakuna suke a jere,a hankali tace
"Dakin ajiyar gawar zai kasance a cikin dakunan ne" a hankali take leqawa daya bayan daya har tazo kan inda gawar take,a hakali ta bude qofar ta shigo,gawawwaki guda uku ta gani an lullube su da farin qyalle,ta shiga budewa ana biyun taga fuskar mai maganin,cikin hanzari ta ajiye abinda yake hannunta ta fara budewa,abubuwan da suke cikin kwalba ta fara zazzagowa a hannunta tana shafawa a 'yan yatsun gawar tana cewa
"Ai idan ya taba pinellia hannunsa zai nuna har yanzu" gama rufe bakinta kenan taji motsin alamun wani zai shigo,sauri tayi ta kwashe kayan ta shige qarqashin dan siririn gadon da gawar take,kasancewar duhu ya fara shiga,babu wanda zai kula da mutum a wajen,Abdullahi sabon corpse handler dinnan ne ya shigo,wani abu ya shigo dashi a faifai ya ajiye kan wani tebur,daga nan ya nufi inda wasu tsofaffin littattafai suke ya fara bincikawa cikin sauri kamar wanda baya son azo a kamashi,hankalinshi yayi nisa cikin binciken da alama har yanzu bai ga abinda yake nema ba,shima jin motsin za'a shigo yai saurin matsawa daga inda litattafan suke,wani abokin aikinshi ne ya shigo,nan take ya wayance,wancan ya ajiye abinda zai ajiye suka fita tare,duk abin nan da ake shukra tana jin motsin su amma bata samu damar ganin fuskar ko daya a cikin su ba.
Suna fita ta fito ta cigaba da abinda take yi,sai da ta shafa abinda tazo dashi a kwalba a dukka yatsun gawar,ta dan bashi 'yan mintuna sannan ta sa farin qyalle ta goge,tana kallon qyallen fuskarta cike da farin cikin samun abinda tazo nema ta nade kayanta ta nufi hanyar fita,cikin sanda take tafiya kamar daga sama taji ance
"Dakata a nan" gabanta ne yayi mummunar faduwa,bata juya ba domin daga bayanta ake maganar,IG ne na plolice,ya fara magana
"Ya akayi mace ke fitowa daga dakin ajiye gawa?" A hankali ta juyo ta kalleshi,da sauri yace
"Ke? Ba kece servant girl dinnan ta bureu of music ba? Me kikeyi a wajen nan a wannan lokacin?"
Rarraba ido ta fara yi tana kallon shi,ya ce
"Ba magana nake miki ba ? Me kike a nan wajen?" Ganin ba zata yi magana ba ya dan daga murya tare da cewa
"Waye a nan?" Bai gama rufe baki ba lieutenant da assistant lieutenant suka bullo,AL ne yake kallon ta tare da cewa
"Ke ba kece yanzu kika min qarya ba kika gudu"
Rau rau tayi ido har yanzu ta kasa cewa komai,daurewa tayi ta kalli IG tace
"Dama zuwa nayi neman evidence a jikin gawar"
Kallon rashin fahimta suke mata dukkansu,sai IG ne ya qara cewa
"Wace irin hujja kike nema? Wannan wane irin shirma ne?" A firgice ta qara cewa
"Ina neman hujjar da zata wanke lady jalila ne domin ba tada laifi kuma mai maganin ne kadai shaidar ta" IG ji yayi a ransa hankalinsa ya kwanta da yarinyar,nan yace mata
"Biyo ni" tafiya ya fara yi yayinda suka bi bayan shi ita da leiutenant da assistant.
Jameel ne durqushe gaban mahaifinshi,dukkansu sunyi jugum suna tunani,cikin sanyin murya jameel yace
"Yanzu Abba na sa a nemo yarinyar nan amma ance tun da yamma ba'a ganta ba,gashi lokaci yana qure mana,mai martaba ya bada imperial order a miqawa tribunal alhakin binciken,yanzu haka gobe da safe za'a miqa lady jalila tribunal" ya qarasa maganar cike da rashin sanin abinda ya kamata yayi,babanshi ne yace
"Ka baza yaran ka a nemo ta a daren nan domin a san abinyi,dole mu fitar da lady jalila daga halin da take ciki kuma dole sai mun samo servant girl dinnan" jinjina kai yayi daga bisani ya tashi ya fita.
Duk inda mutanen sa suke tunanin zasu ga shukra amma sun neme ta sun rasa hakan ya qara sa su a rudani matuqa.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏻❤️
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Whattpad :Oum_tasneeem
Page 16
Isar su shukra dakin ajiyar gawar dukkansu suka shiga tare da tsayawa a gaban gadon da aka ajiye gawar,IG ne ya kafa mata ido tare da cewa
“Fada min wace iriyar hujja kike tunanin zaki iya samu?”
Shiru tayi tana rarraba ido,lieutenant ya kalli IG tare da cewa
“Yallabai yarinyar nan kawai ka kulle ta ,bata da gaskiya”. Hannu IG ya daga masa alamar ya dakata da magana,har yanzu idon shi yana kan shukra da ta kasa cewa komai,cikin sanyin murya yace
“Ki yadda dani,zan fahimci duk abinda kike son fada,ki fada min me kika zo nema a nan”
Bayyanannuyar ajiyar zuciya shukra ta sauke ba tare da tace komai ba ta ajiye ta fara kwance kayan da suke hannunta,kwalba guda daya ta dauko ta nuna wa IG tare da cewa
“Yallabai wannan vinegar ce,nayi amfani da ita ne na shafa a hannun gawar nan domin akwai wani reaction da pinellia da vinegar suke bayarwa,yau tsawon kwana uku da mutuwar sa,amma indai ya taɓa pinellia to vinegar nan zata nuna mana” cike da mamaki yake kallonta tare da jinjina kai yace
“Amma ta yaya vinegar zata nuna ko ya taɓa pinellia?”
Cikin qarfin gwiwa shukra ta cigaba da bayani
“Idan aka shafa vinegar a hannun,za’a bashi ɗan mintuna sai a saka farin qyalle a goge,idan ya taɓa pinellia to farin qyallen zai fito da kalar pink,idan kuma bai taɓa ba,ba zai bada wani colour ba” cikin matuqar burgewa IG yake kallon shukra,Jinjina kai sukai gaba dayansu cike da gamsuwa,IG ne yace
“Zamu kawo pinellia sai mu gwada domin tabbatar mana da hujjar da kika zo da ita”
Rusunar da kanta tayi a gabanshi ba tare da tace komai ba,
Hannu ya miqa mata tare da cewa
“Bani vinegar,yanzu zanje na samu mai martaba “ kwalba daya shukra ta miqa masa a cikin kwalabe uku,ya kalli lieutenant yace
“Kayi maza ka aika jami’ai a samo pinellia domin akwai amfanin da zamuyi da ita idan na dawo daga wajen mai marataba,rusunar da kanshi yayi a gaban IG tare da cewa
“Yehhh” (yes sir in korean)cikin sautin amsar umarni.
Bayan tafiyar IG da minti 10 shukra tace wa lieutenant
“Yallaɓai ko yaushe IG zai dawo?” Kallonta yayi cike da birgewa yace
“Ai ki koma bureu of music kawai,duk yadda ake ciki bayan ya dawo zamu sanar dake” jinjina kai tayi alamar gamsuwa,ta juya zata tafi ta jiyo muryar shi yana cewa
“Dare yayi ko na sa guards su raka ki?”
Dan rusunar da kanta tayi tace
“A ah ba komai zan iya komawa,ai na saba fita a iron wannan lokacin” ta qarasa tana murmushi,shima murmushin yayi mata tare da cewa
“Toh shikenan sai kin ji mu” qara rusunar da kanta tayi sannan ta juya ta tafi.
Jalila a office of investigation a zaune tayi zurfi cikin tunani amma a nutse take,kamar babu wani abu da yake damunta amma kuma cikin zuciyarta wani tarnaqin baqin ciki ne da tashin hankali na yadda yau ita ce aka wulaqanta aka ciwa mutunci har ladies investigators ma su samu damar fada mata abinda suka ga dama,tunanin ta ne ya katse daidai lokacin da chief sumayya ta shigo,daga idonta tare da binta da kallo har ta zauna tana fuskantar ta,cikin gadara da rashin ladabi chief sumayya tace
“Mai martaba yayi umarnin a miqawa tribunal alhakin binciken laifin da kika aikata” jalila bata ce komai ba,ganin haka ta cigaba
“Ke kuwa me ya kaiki kika aikata irin wannan laifin? A matsayin mu na wanda muke kula da case dinnan muna ganin hakan abin kunya ne” Ran jalila idan yayi dubu ya baci,cikin tsanaki take kallon sumayya,tace
“Ni kike fadawa irin wannan magnaganun? Ehh na yadda abin kunya ne amma a gareku,a sanina office of investigation suna daukar matan da suka fi kaifin basira da ilimi ne,amma yau na fahimci cewa hakan bashi da amfani,ba shi kuma da tabbas,ina tunanin yadda zaku jagiranci inner court nan gaba a rayuwa”
Murmushi sumayya tayi tare da cewa
“Kinyi matuqar birgeni da a cikin wannan yanayin ma kina tunanin me zai faru da inner court,amma a halin yanzu abinda ya kamace ki shine ki kula da halin da zaki shiga ba rashin tabbas din office of investigation ba”
Jinjina kai jalila tayi tare da cewa
“Ba zan manta da kalaman ki ba chief madam inspector” ta qarasa cikin tsuke fuska,chief sumayya ta kalli ladies investiga din da suke tsaye su biyu tace
“Ku kula da ita sosai kafin gobe da safe tribunal su aiko masu rakata can” rusunar da kansu sukayi tare da cewa
“Yehh ma-ma-neem” (yes my lady in korea- zamu dan fara sirkawa da words dinsu domin jin dadin masu karatu) sannan ta fita daga office din ta bar jalila a zaune cikin takaici.
Shukra tana cikin tafiya take jin kamar ana binta,juyawa tayi da sauri taga ba kowa,ta cigaba da tafiya amma har yanzu taji kamar alamar ana binta,juyawa ta qara yi taga ba kowa,ga wajen babu mutane,rungume kwalaben da suke hannunta tayi ta fara gudu,sai ga wanda yake binta shima ya biyo ta gudu,tana shan wata kwana taga wasu sun biyo ta gaban ta,ta juya zata canja hanya amma wasu ma suka tare mata hanya,a tsorace tace
“Me nayi muku? Su waye ku? “
Babu wanda ya kula ta a cikinsu,sai daya daga cikinsu ne da babbar murya yace
“Ku damqe ta mu tafi” jikin shukra ne ya fara rawa,mutum biyu suka zo suka rirrriqe mata hannaye,tana ta qoqarin qwacewa amma dai qarfin ba daya bane,hakan yasa ta fara kuka,kamar daga sama suka ji mutane sun diro da qarfi,kowa hankalinsa ya koma wajen,mai martaba ne ya ɓullo daga kwanar da shukra ta biyo nan da nan guards dinnan suka bawa wanda suka riqe shukra umarni
“Ku sake ta matuqar kuna son ku tsira da rayuwar ku “ ogansu ne ya kalli guards din cikin rashin fahimta tare da cewa
“Ba zamu saketa ba,ku din suwaye? Kuyi abinda zakuyi”
Mai martaba ne yayi gyaran murya,cikin kaushin murya yace
“Ku sake ta aka ce ko? “ ganin an tsaya taqaddama ogan ya kama shukra ya sa mata wuqa a wuya,cikin dabarun guards din mai martaba suka karbo shukra suka kame ‘yan iskan da suka kamata,daddaure musu hannaye suka yi suka gurfanar da su a gaban mai martaba,a dai dai lokacin da hankali tashe yake kallon shukra
“Babu abinda ya same ki ko? Basu yi miki komai ba ko?” Girgiza kai shukra tayi tare da cewa
“Ehh lapiyata qalau,babu abinda sukai min”
Daya daga cikin guarda din sarki ne yace
“ya za’ayi dasu?” Mai martaba ya kallesu yace
“Yan iskan hanya ne,ku kaisu police bureu a hukunta su” tisa qeyarsu akayi shi kuma mai martaba suka tafi tare da shukra.
IG yana isa grand palace chief eunuch ya tabbatar masa mai martaba baya nan,domin ya tafi police bureu domin ya gana da shi,hakan yasa ya juyo domin dawowa police bureu.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏻❤️
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Whattpad :Oum_tasneeem
Page 17
Mai martaba da shukra suna tafe a cikin gari suna hirar su,ya kalli shukra yace
“Ke dai da alama ba kya jin magana,ba na ce miki ki daina yawo da daddare ba? Yanzu da ban zo ba fa? “
Rusunar da kanta tayi tare da cewa
“Nagode yallaɓai ka ceci rayuwata,amma yau na fito ne domin yin wani aiki mai muhimmanci”
Mayar da hankalinsa yayi gaba ɗaya kanta tare da cewa
“Wane irin muhimmin aiki ne wannan?”
Zaro ido tayi tana nuna shi
“na tuna,Ai har nemanka naje yi saboda aikin amma mai gadin yace min kace baka sanni ba”
Da sauri kamar an tsikare shi yace
“Ina kikaje nemana??”
Tace
“Office din ‘yan sandan sirri mana? Ba nan ne wajen aikin ka ba? Amma suka ce min wai kace baka sanni ba”
Cikin rashin sanin abinda zai ce mata ya fara in-ina,can ya samo abinda zaice
“Ai ina jin wajen ɗayan shugaban suka je,kinsan mu biyu ne shuwagabannin wajen,kuma wancan office ɗinsa yafi kusa da qofar shigowa” murmushi shukra tayi cike da shashanci tace
“Auu hoo,shiyasa ashe suka ce yace bai sanni ba,ni kuwa har na zata ko ka manta da sunana ne” ta qarasa har yanzu da murmushi akan fuskar ta,shima murmushin ya mayar mata tare da cewa
“Yauwa baki faɗa min muhimmin aikin da kika ce kinje yi ba” ɗan ɓata fuska tayi
“Kasan office of investigation sunyi arresting ɗin lady jalila,kuma akan abinda bata aikata ba shine naje samo hujjar da zata nuna bata da laifi” ji yayi kamar an soke shi jin sunan lady jalila,cikin sanyi yace mata
“Toh yanzu me kika samo?”
Nan ta kwashe duk bayani duk faɗa masa,har da tafiyar IG wajen mai martaba,jin haka yasa guard dinsa guda ɗaya ya rakata har cikin bureu of music shi kuma ya juya ya tafi police bureu.
Da zuwansa shima IG ya dawo daga masarauta kuma an kawo pinellia da qwararren mai binciken gawa,mai martaba ne yayi umarnin a maimaita irin yadda shukra tayi,aka qara yi bai bada kala ba,sai yayi umarnin IG ya taba pinellia sai shima aka shafa mai vinegar,ana saka farin qyalle aka goge sai gashi kalar pink ta bayyana,murmushin nasara ne duk ya bayyana a fuskokinsu,mai martaba ya jinjina kai tare da kallon IG yace
“Kuma da gaske yarinyar nan ce ta bayyana wannan hujjar?”
Jinjina kai IG yayi cike da girmamawa yace
“Nima ina mamakin hakan your majesty,tabbas ita ta bayyana hakan”
Washegari da safe,a office of investigation,chief sumayya ce sai Sameerah da Aliya a bayanta,sun taho daga bangaren da ɗakunan baccinsu yake zuwa cikin office,wata tawagar investigators ne suka taho,wacce take gaba kayanta iri daya sak da na chief sumayya,ganin yadda chief sumayya da tawagar ta suka dakata suka tsaya cak a inda suke tare da rusunar da kansu a tare hakan yasa na gane mai tahowar wata babba ce a wajen,qarasowarta wajen chief sumayya tace
“Barka da shigowa Director”
Suma wanda suke bayanta haka suka furta a tare,hakan ya tabbatar min da cewar ita wannan matar tafi sumayya matsayi a wajen,wato itace director ɗin office of investigation gaba ɗaya,fuskarta ɗauke da murmushi ta kalli sumayya tare da cewa
“Ina fatan lady jalila ta shirya domin tafiya ofishin tribunal” itama sumayyan murmushi tayi tare da rusunar da kanta tace
“Ta shirya ranki ya dade,guards din tribunal kawai muke jira wanda zasuyi mata rakiya zuwa can” jinjina kai director tayi cike da gamsuwa tace
“Office of investigation kunyi qoqari matuqa a qarqashin jagorancin ki kun kammala case mai wahalar ganewa,idan komai ya lafa zamuje tare domin ki gana da queen dowager”
Murna ne da tsantar farin ciki ya bayyana a kan fuskar sumayya,cike da zumuɗi tace
“Ranki ya dade da gaske zanje wajen queen dowager?” Murmushi director tayi mata na tabbatar wa da abinda ta fada sannan ta yi gaba ta tafi ta bar su sumayya a wajen.
Sameerah ce ta qaraso gaban sumayya tare da ce mata
“Congratulations my lady,ba qaramar karramawa bace zuwa ganin queen dowager”
Ta fada itama cikin tsantar farin ciki,sameerah ce ta qara qasa qasa da muryarta
“Dama aikinmu dole yasa queen dowager farin ciki tunda dama tana neman yadda zatayi da jalila kuma gashi ta samu,wataqila ke zaki zama next director a office dinnan”
Sumayya ce itama ta mayar mata cikin rada
“Ke ki daina gaggawa,mu fara zuwa ma mu gaisa da its kafin ki fara tunanin zama director “ ta qarasa cike da murmushi da yake nuni da tsantsar farin cikin da take ciki.
Tana shiga cikin office dinta taci karo da nadeeyah da basma wanda a qa’ida su suke biye mata a matsayi,tashi sukayi cikin girmamawa da rusunawa suka gaishe ta sannan suka koma suka zauna,cike da ladabi nadeeya tace
“Ranki ya dade akwai abin dubawa da muka ga ya dace a qara bincikawa a al’amarin nan”
a take farin cikin da ke fuskarta ya gushe,ta kallesu a tsanake tare da cewa
“Kamar ya a sake bincike? Ban gane ba”
Har basma zatayi magana,nadeeya ta katse ta da cewar
“Ranki ya dade bayan an sallami yarinyar nan shukra,ta sameni take fada min lallai fa lady jalila bata da laifi,hakan yasa na nemi taimakon basma muka tafi kasuwa inda ake dealar itatuwan,mun duba littafin da suke record kuma mun tabbatar sama da shekara uku ba’a siyar wa wannan mai maganin itacen pinellia ba,shiyasa muke tunanin idan aka sake bincike za’a iya gane inda matsalar take”
Chief sumayya tayi kasake tana jinta,sai da ta gama tsaf sannan tace
“Toh kuma sai akace don bai siya pinellia ba shikenan ba zaiyi amfani da ita ba,mu mun gama bincike kuma babu abinda zai sa mu sake wani bincike a halin yanzu,bayan ana ganin mun qara ɗaga darajar office of investigation har ana tunanin queen dowager zatayi mana tukwuici shine zaku kawo mana wani zancen banza?”
Basma cikin murya mai sanyi tace
“Ranki ya dade idan mukai haka za’a hukunta wanda ba shi yayi laifi ba,alhalin mai laifin yana nan yana yawo a cikin masarautar nan”
Wata gigitacciyar tsawa chief sumayya ta buga mata
“Ai sai kuma ku yi!!! Na fada muku ku ajiye wannan shirmen zancen da kuka samo domin bincike ya qare”
Kafin su nadeeya su farfado daga tsawar da aka daka musu,sameerah ta shigo da gudu har tana tuntube,da dukkan alamu cikin tashin hankali take
“My lady ki fito kiga me yake faruwa a waje”
Zumbur chief sumayya ta miqe da sauri tayi waje,haka nan nadeeya da basma suka bita domin ganin me yake faruwa,chief sumayya ce cike da mamaki tace
“Kamar royal guard nake gani,ina tribunal guard din kuma?”
Afrah da take tsaye ce tayi saurin qarasowa wajen chief sumayya
“My lady sun ce sunzo ne qarqashin umarnin mai martaba domin tsaron lafiyar lady jalilah”
Cike da rudani ta kalli afrah kafin tace wani abu sai ga royal chief secretary ya taho da sauran sakatarorin cikin masarautar suna dauke da tray wanda takadda ce a kai,shigowar su yasa dole director ta office din ta fito daga office,suna qarasowa dukka ladies investigators din suka rusuna don girmama su,domin da an ga chief secretary toh anga umarnin mai martaba,hannu ya miqa aka miqo masa takaddar da suka zo da ita,kai tsaye ya miqawa director din,a hankali ta bude takaddar ta fara karantawa,tashin hankali da firgici ne qarara ya bayyana akan fuskarta har takai qarshen takaddar,juyawa tayi tare da miqawa chief sumayya,tashin hankalin da sumayya ta shiga yafi wanda director ta shiga sai aka shiga kallon kallo a tsakaninsu,sauran ladies investigators da suke tsaye basu san me yake faruwa ba duk sun shiga rudanin shin me yake shirin faruwa a safiyar yau?
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏻❤️
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Whattpad :Oum_tasneeem
Page 18
A ɓangaren queen dowager bata san me yake faruwa a office of investigation ba,jikinta yayi qwari sosai tayi shigarta kamar yadda ta saba cikin alkyabbarta ta alfarma,tana zaune inda ta saba zama a sit room dinta,ɗan ɗaga murya tayi
“Waye a nan kusa?” Ta fada tana mai kallon qofa,chief maid dinta ce ta shigo da sauri tare da rusunar da kanta tace
“Ranki ya dade,kamar kina kirana ko?” Jinjina kai tayi
“Ehh ni na kiraki,kuyi shiri yanzu zamu fita” cewar queen dowager,qara rusunawa chief maid din tayi
“Ranki ya dade,ina zamu je a wannan lokacin?” Dago kanta tayi ta kalleta tare da bata amsa
“Ba yau da safennan za’a miqa lady jalila zuwa tribunal ba? Ya kamata naje rakiya saboda darajar qawancen da ke tsakanin mu” ta qarasa cikin shu’umin murmushi,amsawa chief maid din tayi tare da fita domin shirin fitar su.
Lady jalila tana zaune tayi nisa cikin tunani taji shigowar mutum,ɗagowar da zatayi taga chief maid dinta ce,da sauri chief maid din ta qaraso gaban lady jalila,cikin fuskar alhini tace
“Maa- maa” (your highness)
Murmushi jalila ta yi mata tare da cewa
“Me ya kawo ki nan a wannan lokacin,na zata kuma kuna karɓar hukunci saboda laifin uwar dakin ku” rusunar da kanta tayi,qwalla ta tsatstsafo a idonta,daga bisani tace
“Mun sha wahala my lady,amma wannan ba komai bane domin muna can amma zuciyar mu a cikin tunanin ki take,da fatan kina lapia”
Jinjina kai kawai jalila tayi alamar “Eh “ cike da tausayin ma’aikatan nata,
“Your highness yanzu zaki fita daga wajen nan domin an samu hujjar cewa baki da laifi” zumbur lady jalila ta miqe daga inda take zaune,idonta suka fiffito take kallon chief maid dinta cike da mamakin furucin da yake fitowa a bakinta daidai lokacin da ta riga ta yanke tsammanin fita daga wannan matsalar,cike da rikici tace
“Me kike nufi da hakan? Hujjar cewa bani da laifi? Ta yaya kenan?”
Rusunar da kanta tayi
“Yarinyar nan shukra itace ta samo hujjar,kuma mai martaba ma da kanshi ya tabbatar da hakan,saboda haka yanzu chief secretary ya shigo cikin nan wajen tare da royal order domin a wanke ki daga laifi” wani farin ciki ne mara misaltuwa ya bayyana a kan fuskar jalila,da sauri tayi hanyar fita waje chief maid dinta ma tabi bayanta,tana fitowa ta tarar da duk ma’aikatan office of investigation sunyi layi kamar ‘yan assembly suna jiran fitowar ta,director da chief sumayya da green din uniform dinsu a gaba,nadeeya da basma da ash din uniform dinsu a baya,sai sauran ladies masu pink din uniform kusan su 30 suma a baya duk sunyi layi layi kamar assembly dayan bangaren kuma maids din lady jalila da suka zo yi mata rakiya,a daya bangaren kuma royal guards ne da suka zo tsaron lafiyar jalila,sai kuma su chief secretary da sauran sakatarorin masarautar suma a gefe guda.
Tana fitowa ta tsaya kan step din office da ta fito,dukkan mutanen wajen suna qasa da ita,director ce ta fara magana
“Ki yafe mana your highness,haqiqa munyi babban kuskure,ki yafe mana” ta fada tare da rusunar da kanta har wuyanta qasa sosai alamun neman afuwa,chief sumayya ce da idon ta yai qifi qifi itama ta rusuna tare da cewa
“Haqiqa mun aikata mafi munin kuskure,ki yafe mana your highness” ta qarasa tare da qara rusunar da kanta qasa sosai,sauran ladies dinne gaba daya suka rusunar da kansu tare da fadin
“Forgive us your highness”
Cikeda nutsuwa jalila ta sauko daga inda take tsaye sai da tazo daidai inda sumayya take
“Bana jin hakan zai yiwu” ta dan ja numfashi yayin da wajen gaba daya yayi tsit suna sauraron abinda zata fada,suna da tabbacin a halin yanzu idan kashe su tace tana so ayi to fa hakan zai tabbata shiyasa duk a tsorace suke da lamarin
“Ina tunanin ai ba ni zaku bawa haquri ba,qaramar yarinyar da ta gano abinda ‘ya’yan manya,masu ilimin bincike irinku suka kasa ganowa,lallai kun kasa akan aikin ku,kun kuma nuna baku cancanta ba” ta qarasa tana kallon cikin idon sumayya
“Ya kika ji lady sumayya? Slave girl ta fiki sanin ilimin bincike,a yanzu ina ganin ina da damar da zan damu da makomarki a nan gaba ai ko?tunda kince bani da damar hakan a matsayina na mai laifi” shiru sumayya tayi sai qara sunkuyar da kai da tayii,cikin tsawa lady jalila tace
“Ko ba haka kika ce ba!!!?” Sosai lady sumayya ta firgita da yanayin jalila domin daga ganinta tana cike da tsananin bacin ran maganganun da ta dinga fada mata,qara hada baki sukai gaba dayansu tare da cewa
“We made a terrible mistake your highness,please have mercy on us” ba tare da ta qara cewa komai ba ta fara tafiya,tsakiyar su ta nufa,a take suka dare gida biyu,sukai gefe da gefe suka bude mata hanya har yanzu kansu a qasa yake har ta bar wajen tare da maids dinta da suke take mata baya sai kuma royal guards.
Fitar ta keda wuya director ta juyo kan sumayya
“Sumayya kin bani kunya,kun jawowa office dinmu abin kunyada ɓacin suna,mu da ake ganin duk masarautar nan babu masu aiki da hankali irin mu,babu wanda ake girmamawa irin mu, amma yanzu kun ga abinda kuka jawo”
Shiru sumayya tayi cikin qunar rai ba tare da tace komai ba,fuuu director ta wuce ta koma office dinta.
Suna fitowa daga office of investigation kai tsaye jalila ta nufi quaters dinta,daidai zata shiga qofar sit room dinta ta juyo ta kalli chief maid dinta
“Aje a kirawo min shukra,ina son ya kasance ita na fara gani”
“Yeehh maa-maa” (yes your highness )
Ta fada tare da juyawa ta nufi bureu of music domin kiran shukra.
Aliya ce a tsaye tare da wasu ladies investigators,da yake aliya irin matan nanne giant masu jiki da tsayi hakan yasa suke dan jin tsoronta,cike da bacin rai take magana
“Yanzu kuga abinda yarinyar nan ta jawo mana? Yanzu duk masarautar nan za’a daina ganin qimar mu kamar da,tunda yanzu wannan slave girl din ta jawo mana abin kunya” Afrah tana tsaye a gefe tana jinsu itama ranta babu dadi amma bata tofa komai ba,domin tana da nutsuwa da hankali sosai,bata da son hayaniya.
Nadeeya da basma ne suka qaraso wajen,jin abinda aliya take cewa ne yasa basma yi mata magana
“To ku aikin ne kukayi da kuka zauna kuna ta babatu akan yarinya? Shin kun ma yi yunqurin cewa bari ku bankado gaskiyar? Zaku bar nan wajen ko kuwa?” Ta qarasa cikin fada,hakan yasa dukkansu suka watse daga wajen.
Lady sumayya a office ita da ‘yar jelar ta wato sameerah,kusan duk inda zaki ga sumayya to sameerah tana biye da ita,kuma ba komai ne yasa sameerah take hakan ba sai don neman gindin zama da munafurci,sumayya ce take magana cike da bacin rai
“Ta yaya za’a ce duk shekarun da nayi ina aiki a office dinnan sai yau ɗaya zan wulaqanta saboda wata slave girl?” Ta qarasa tana huci kamar zata kai duka,sameerah tace
“Calm down my lady,kiyi haquri” sumayya dai jinta kawai takeyi,nan take taji duk duniya babu wanda ta tsana kamar shukra da jalila.
A quaters din lady jalila,chief maid sun dawo tare da shukra,inda ta bar shukra a bakin sit room din lady jalila domin zuwa yi mata iso,bayan tayi mata iso ta rako ta har cikin dakin,shukra ta zauna sannan ta fito,shukra ce ta rusuna yadda take a zaunen tare da cewa
“Your highness da fatan kina lapia” murmushin jin dadi jalila tayi tare da cewa
“Gani a zaune a quaters dina cikin qoshin lapia saboda abinda kika aikata,haqiqa naji dadin qoqarin da kikayi shiyasa nace ke zan fara gani domin na gode miki” murmushi shukra tayi tare da cewa
“Ba komai your highness,kema ai kin cece ni daga wajensu,kina da matuqar karamcin da zaki sa kanki a cikin matsala domin ki ceci wacce ba kowa ba kamar ni” murmushi jalila tayi har haqoranta suka fito tace
“Na rasa da wane kalamai zanyi amfani wajen nuna miki godiyata da abinda kikai min shukra,amma duk abinda kika fada ba gaskiya bane,ke ‘yar baiwa ce,ki daina cewa ke ba kowan kowa bace,idan kika sa a ranki zaki iya zama komai,to zaki ga cigaba sosai a rayuwar ki,ina son ki fada min ko akwai wani abu da kike so daga wajena da zan baki tukwuici”
Shiru shukra tayi tana tunanin ko zata iya fadan abinda ke ranta,yayinda jalila kallon burgewa take binta dashi,can dai ta daure tace
“Ranki ya dade alfarma daya nake nema a wajenki” jinjina kai jalila tayi yayinda shukra ta cigaba da magana
“Your highness ina son ganin keychain dinki” ta fada cikin qasa qasa da murya,murmushin lady jalila ne ya fadada tace
“Keychain dina?” Jinjina kai shukra tayi,cikin nutsuwa lady jalila ta tashi ta bude wani cupboard a can bangaren daman dakin,wani dan qaramin akwati ta dauko mai dan tsayi ta ajiye a gaban shukra,gyada mata kai tayi alamar “ta bude”
Hannu shukra ta miqa hannu cikin sanyin jiki ta bude qaramin akwatin,keychain din lady jalila ne ya bayyana mai alamar butterfly,fuskar shukra ba yabo ba fallasa ta dago ta kalli jalila tare da cewa
“Amma your highness,tun yaushe kike da keychain dinnan?” Sai da lady jalila ta dan nisa kafin tace
“Tun ina yarinya,ina sonshi sosai shiyasa nake ririta shi” jinjina kai shukra tayi tare da cewa
“Nagode,dama abinda nake son gani kenan”
Lady jalila tayi saurin cewa
“A ah shukra,duk da ban san dalilin da ya sa kika nemi ganin keychain dina ba,amma wannan bai isa tukwuici ba,zan duba abinda ya kama ayi miki” godiya shukra tayi tare da tashi ta fita tana tunanin keychain din da ta gani.
A quaters din queen haneefah tana zaune cikin shiga irin wacce ta saba ta alfarma,tana zaune ta nade qafarta a zaune,da chief maid dinta a zaune tana fuskantar ta,cikin sanyi da ya zama yanayinta tace
“Kin aika cakes da snacks din da nace quaters din lady jalila?” Gyada kai tayi tare da cewa
“Na aika an kai mata,domin mai martaba yana can lokacin da naje shiyasa ban samu ganin ta ba, amma idan zan iya tambaya meyasa kikai haka? Bayan laifin da ta aikata miki?”
“Yi min shiru” ta dakatar da ita,shiru chief maid din tayi,queen haneefah ta cigaba
“Bana son in qara jin wannan zancen a bakin ki,lady jalila ta shiga wani yanayi saboda abinda bata aikata ba,ki aika mata saqon fatan alkhairi daga gareni” rusunar da kanta tayi alamar taji
“Naji ance slave girl ce ta nemo hujjar ko?”
Cewar queen haneefah,
“Ehh your majesty,slave girl ce wacce ta samo gaskiyar wancan salt stone din” chief maid din ta bata amsa
Jinjina kai queen haneefah tayi yayinda yanayin ta ya canja,tace
“Hatta slave girl din lady jalila ma ‘yar baiwa ce,ga kuma soyayyar mai martaba,haqiqa jalila tana da abubuwa da dama da nake jin dama ni nake dasu” ta qarasa cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa,chief maid dinta tayi mata kallon tausayawa ba tare da tace komai ba.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏻❤️
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Whattpad :Oum_tasneeem
Page 19
Manager ne da sameer suna zaune suna ta shashanci,wai suna jiran suga wannan karon wane irin tukwuici za’a bawa shukra,sameer ya kalli manager
“Yallabai ina jin wannan karon ma za’a kawo mana abinci na alfarma irin wancan” manager ya kwabe fuska tare da cewa sameer
“Gaskiyarka fa,ni tun yanzu ma ba zan qara cin komai ba,sai kayan alfarma sun iso”
Da sauri sameer ya cafe
“Ai nima dani za’a yi yajin aikin cin abincin,don cikinmu ya shirya karbar kayan dadi” dukkansu suka tuntsure da dariya,shukra suka hango tana shigowa da wani qullin kaya mai girma a hannunta,da gudu suka nufi inda take shigowa sameer yana cewa
“Yauwa shukra kin dawo daga wajen lady jalila,bari muga me aka baki?”
Manager ya dora “Ehh bamu mu gani,silk ne ko keychains din ‘ya’yan sarauta?” Tana qoqarin yi musu magana amma basu bata dama ba,saurin karbar kayan suka yi yayinda duk sauran ma’aikatan suka yo cincirindo zuwa wajen domin suga me ta kawo,suna bude qullin suka ci karo da kayan takalman su da ta dauko domin ta wanke,kallon kallo suka fara yi,manager ya kalle ta yace
“Wai bata baki komai ba?”
Kafin ta bashi amsa sameer yace
“Kai dai mu cigaba da yajin aikin cin abincin,kasan dafa irin wannan abincin yana daukan lokaci watakila sai gobe “ jinjina kai manager yayi cikin gamsuwa da maganar sameer yace
“Haka ne kam,ke kuma ki ajiye takalman nan kije ki huta don zirga zirgar da kika je jiya” ya qarasa maganar shi yana kallon shukra,murmushi kawai tayi ta kwashi kayan ta bar wajen.
Da daddare,Mai martaba shi da lady jalila a tsaye a wani hawan bene inda mai martaba yake hutawa,duk masarautar babu bene mai tsayin shi,hakan yasa idan ya hau barandar wajen yana iya hango ko’ina na cikin masarautar,shiru sukayi babu me cewa komai suna kallon taurari a sararin samaniya,kowa da tunanin da yake ran shi,yayinda maids dinsu suna can baya baya yanda ba zasu iya jin me suke fada ba sai dai in sun daga murya,mai martaba ne ya katse shirun da cewa
“Lady jalila kina fushi da ni ne?”
Murmushi ne ya bayyana akan fuskarta ba tare da ta kalleshi ba tace
“A’ah ko kadan bana fushi da kai,kamar dai yadda na fada maka ne,zuwan da kayi ka ganni ma kawai ya wadatar” ta qarasa har yanzu fuskar ta da murmushi,juyowa yayi ya fuskance ta sosai
“Gaskiya yarinyar nan shukra tayi qoqari,domin duk saboda itane komai ya zo cikin sauqi,hakan abin birgewa ne sosai”
Itama juyowa tayi ta kalleshi
“Gaskiyane your majesty,shiyasa nake ganin zamanta a matsayin slave girl kamar zai zama asarar qwaqwalwarta da basirar ta” shiru ta danyi,shima mai martaba bai ce komai ba ta cigaba
“You majesty ina da wata alfarma da nake son na roqe ka”
“Alfarma wace iri? Game da shukra?” Cewar mai martaba,jinjina kai tayi ba tare da ta ce komai ba,ya cigaba
“Ki fadi duk abinda kike so ayi mata,za’a yi mata my lady” ya fada cike da barkwanci,murmushi hakan ya bata ganin yanayin da yayi maganar.
Shukra a bureu of music ma’aikatan suna cin abincin dare,ita kuma sai kai kawo take tana harhada kayan da sukai amfani dasu,wani cikin ma’aikatan ya kalleta
“Yanzu duk irin qwaqwalwa basirar yarinyar nan,haka zata qare tana kai kawo na share share da goge goge”
Wanda yake maganar dashi ne yace
“Gaskiyar ka fah,domin a qasar mu matuqar dai aka haifeka a matsayin lowborn toh baka da wata nasara a rayuwa” haka suka cigaba da tattaunawar su game da shukra.
Sai da ta gama ayyukanta tsaf,ta zo ta zauna a step din da ake shiga dakin ajiyar kayansu a bureu of music tana tunanin rayuwa,nan take tunanin Keychain dinnan ya fado mata,tabbas zanen butterfly ne amma ba kalar nata ba,ba ma iri daya ne da wanda take nema ba,domin wanda take nema din na katako ne,wanda lady jalila ta nuna mata kuma na roba ne,wancan kalarsa maroon ne,wannan kuma multi colour ne ma’ana kala kala da yawa ne aka hada,a nan take ta sawa ranta lady jalila ba ita bace court lady din da take nema.
Lady jalila a quaters dinta tana zaune har yanzu kana ganinta zaka san irin farin cikin da take ciki,don murmushi ne shimfide akan fuskarta,chief maid dinta da take zaune tana fuskantar ta tace
“Amma my lady,shin meyasa zaki zabi yiwa shukra irin wannan tukwuicin?” Murmushin fuskarta ne ya qaru
“Matuqar dai mai martaba ya amince,to kamar anyi an gama ne”
Rusunar da kai chief maid din tayi
“Your highness nasan shukra yarinya ce ‘yar baiwa mai kuma basira,amma yin hakan zai jawo cece kuce a masarautar nan domin abu ne wanda ba’a taba yin shi ba”
Fuskar lady jalila ta canja nan take ta kalli chief maid dinta
“Wannan ba hurumin da zaki fadi ra’ayinki bane,don haka ki iya bakin ki” rusunar da kanta tayi ba tare da ta qara cewa komai ba,lady jalila ce ta qara cewa
“Ya labarin yayana?”
“Mun samu labarin ya baro qasar china ta jirgin ruwa,zuwa gobe zai qaraso cikin garin nan” cewar chief maid
Lady jalila da murmushin fuskarta ya dawo tace
“Na matsu ya dawo na nuna masa shukra,yana da baiwar gane halayen mutane,ban san me tunaninshi zai bashi a kanta ba” ta qarasa cikin tsantsar farin ciki,domin a halin yanzu ji take kamar shukra ta zama wani bangare na jikinta.
Washegari da safe,a can cikin gari sameer ne a tsaye kamar mai jiran wani abu yana ta kai kawo a qofar wani gida,yana magana shi kadai
“Wannan mutumin ba zai zo bane? Kada fa a kawo abincin ina nan,gashi nan yau saboda shi nazo gida na kwana ban kwana a bureu of music ba” yana ta maganganun shi shi kadai,ji yayi daga bayansa ance
“Barka da safiya” da sauri ya juyo,bai damu da amsa gaisuwar ba yace
“Kaine wanda zaka kama haya?”
“Ehh nine” cewar abdullahi,sabon mai binciken gawa da ka akawo police bureu (corpse handler)
Sameer ne kawai yayi gaba tare da shigewa cikin gidan,shima abdullahi ya bishi a baya,wani daki suka nufa,sai da suka shiga sameer ya kalli abdullahi
“Kaga dakin nan,duk garin nan bazaka samu daki mai kyaun wannan ba da irin kudin da zaka biya,kuma ka kula sosai bana son qazanta kaga ni ba zama nake ba domin ni royal musician ne kamar yadda kake gani” ya qarasa yana mai nunawa abdullahi uniform din dake jikinshi,jinjina kai abdullahi yayi baice komai ba har sameer ya gama surutunsa mara kan gado ya fita daga dakin,ajiyar zuciya abdullahi ya sauke tare da cewa
“Me yasa zan fado hannun royal musician da zai dinga tuna min da Abdulshakur?” Saurin kawar da tunanin yayi tare da fara kunce kayan da ya shigo dasu yana ajiyewa domin ya huta kafin ya tafi wajen aiki.
Sameer yana fitowa qofar gida zai tafi masarauta,wani saurayi da ba zai wuce shekarunsa ba yayo kwana da gudu ya bangajeshi,yana huci saboda gudun da yasha yacewa sameer
“Ka taimakeni dn Allah,ka taimakeni” sameer ya saki baki yana kallon ikon Allah,kafin ya ankara ya ciro kudi masu yawa ya sa a hannun sameer,tare da shigewa cikin gidan neman wajen buya,shigarsa ke da wuya wasu mutane suka qaraso suka kalli sameer
“Kai kaga wani saurayi yanzunnan? Ni ina da tabbacin ma gidannan ya shiga”
Da sauri sameer yace
“Bai shiga nan ba,ni banga kowa ba”
Naushi mutumin ya kawowa sameer,sameer ya goce nan da nan tsoro ya shige shi,kamar daga sama suka ji ance
“Kai dakata” suna juyawa abdullahi ne yaji hayaniya ya fito,ya qaraso wajen yayinda sameer yayi saurin matsawa,abdullahi ne sukai fada da mutanen har suka gudu suna fadin
“Yaya za’ayi mutun yayiwa matata fyade kuma yasa ayi mana duka” haka dai suka tafi,ganin yadda abdullahi ya iya fada sosai yasa sameer ya sha jinin jikinshi.
Saurayin da ya buya ne jin anyi wa mutanen duka ya fito daga inda yake,Yayan lady jalila ne.
Kafin yaje gida har labarin abinda ya aikata yaje kunnen mahaifiyar shi da kuma mariqin Jalila,minister na tribunal,jameel da yake zaune a gaban mahaifinshi yace
“Abba idan har jaleel zaiyi amfani da matsayin ‘yaruwarsa ya dinga irin wannan abin lallai hakan zai zamar mana matsala” jinjina kai baban yayi tare da cewa
“Duk da hakan zuwan nashi yana da amfani don haka ka nema masa matsayin da zai dace da shi”
“Yehhh aboujii” (yes father) jameel ya fada tare da tashi ya bar wajen.
Jaleel yana isa gida haj jameela tayi mai ta tas akan abinda akace ya aikata,bayan ta gama yi mai fada har suka gangaro kan hirar shukra da abinda tayi wa jalila na bajinta,haj jameela ce tace,
“Kaje kana bin matan mutane,ga yarinyar nan jalila tace zata aiko ta yau”
Da sauri yace
“ita slave girl din? Zata zo gidan nan yau?” Kafin ma haj jameela ta bashi amsa suka jiyo tana sallama,fitowa sukayi dukkansu tsakar gida,kallon tsanaki jaleel yakeyi mata ba tare da yace mata komai ba ya kama hanyar sa ya fice domin tafiya ganin ‘yar uwarsa,ita kuma shukra ta bada saqon da zata bayar ta tafi.
Shigowar jaleel cikin masarautar kai tsaye quaters din lady jalila ya nufa,jin labarin isowarshi yasa ta fitowa har da dan gudun ta ta sameshi cikin matuqar farin ciki tace
“Orabeuni” (elder brother in ancient korean language) shima murmushi ne a kan fuskar shi,ya rusunar da kanshi tare da cewa
“Your highness” dariya tasa sosai har haqoranta suka fito,shima dariyar yayi tare da binta suka shiga sitroom din ta.
Zama sukayi kamar yadda yanayin zaman masarautar take,tana zaune ta nade qafarta a qasa kan abin zamanta yayinda shikuma yake zaune yana fuskantar ta da qaramin tebur din da ya raba tsakaninsu,cikin farin ciki tace
“Yanzu yaya meyasa daga dawowarka har ka fara jawo magana,maimakon ace ka nutsu sosai?”
Murmushi yayi “ke yarinya ce,ai nafi son kowa ya dinga ganin kamar ni wawa ne kuma soko,shashasha yadda ba za’a dinga sa min ido ba akan duk wani abinda zan aikata,kowa zaiyi tunanin bani da hankali ai” cewar jaleel,murmushi jalila tayi tare da cewa
“Hakane,lallai wannan shine lokacin da muke ta jira kuma gashi yazo” kallonta yayi cikin rashin fahimta,ganin haka ta cigaba
“Ka manta alqawarin da na daukarwa kaina ranar da na fara shigowa masarautar nan? Nayi alqawarin sai na kai qololuwar matsayi a cikinta,kuma yanzu lokacin zama muna kallo ya qare,saboda haka na samu wata yarinya mai tsantsar basira da hankali kuma mai iya riqe sirri,ina ganin zata yi mana amfani sosai,Ina ta Allah Allah ka dawo domin na nuna maka ita,ban san me zaka ce a kanta ba”
Da sauri yace
“Ko dai yarinyar nan ta bureu of music?”
“Har kaji labarin ta?” Cewar lady jalila
“Ehh ba labarinta ba,na ganta ma”
Da sauri jalila tace
“Yauwa fada min toh,ya kake gani?”
Shiru yayi ba tare da yace komai ba,tambayar shi ta qara yi,nan ma yai mata shiru,nan take ta sha jinin jikinta,cikin damuwa tace
“Yaya ka fada min me kayi tunani game da ita?”
Dago kanshi yayi ya kalleta
“Na tabbata yarinyar ‘yar baiwa ce,kuma da basira amma hakan ne dalilin da zaisa ki guji janyo ta jikin ki” da sauri jalila tace “saboda me?”
Sauke ajiyar zuciya yayi
“Saboda yarinyar tana abubuwa masu kama da irin naki,lowborn ce kamarki,wacce tunaninta,hankalinta,da kuma basirarta yafi qarfin matsayin rayuwarta kamar yadda kema daga haka kika fara,kuma har kika kawo zuwa wannan matsayin,shin me zaisa ita ki bata fiffiken da zai sa ta tashi sama?”
Shiru lady jalila tayi tana tunanin maganar yayanta,amma ita sam bata tunanin hakan zai iya zamar mata matsala.
Mai martaba ne zaune a grand palace yayi zurfi cikin tunani,ba komai yake tunawa ba sai maganar da sukayi da lady jalila,yana tuna lokacin da lady jalila take ce masa
“Mai martaba ina son ka bawa shukra damar da zatayi amfani da basirar da Allah ya bata kuma mutanen qasarmu ma su amfana da hakan,ina son kayi mata tukwuici daidai da abinda tayi “ da yaga tunanin ya ishe shi haka,ya tashi ya canja kaya domin fita cikin gari ko hakan zai rage masa yawan tunani,kuma ya tsayar da matsaya game da shukra.
Shukra a kasuwa wajen masu siyar da irin abin zare da yadiddika,ta kalli mai shagon tace
“Kaga ka bani zaren da zaiyi daidai da belt din royal musicians”
Dakko wani tray yayi tare da miqo mata dauke da zare kala kala akai,hannu ta kai tana dubawa daya bayan daya,tazo kan na tsakiya shima ya dora hannunsa a kai,da sauri ta dago don ganin waye,da sauri tace
“Yallabai,kaine anan?” Cike da murna,da murmushi shima yace
“Ashe shukra ce,kinzo aike kenan kema?” Gyada kai tayi tana murmushi,abinda bata siya ba kenan ta bishi suka fara hira,suna tafiya a cikin kasuwa tace masa
“Ai mutanenka (manager da sameer) suna nan sunqi cin abinci suna jiran ko za’a kawo musu irin na wancan lokacin,ni kuwa ina ta tunanin mai martaba ba lallai ya qara yi mana karamci irin wancan karon ba” murmushi kawai yayi tare da ce mata
“Ai kuwa mun hadu dashi,kuma banga alamun ma yana shirin yi miki wani abin ba” da sauri ta kalleshi
“Da gaske kake? Chab lallai su sameer suna ruwa” ta qarasa cikin dariya sosai,shima dariyar yayi
“Ko dai ranki ya baci da na ce miki mai martaba ba zai baki komai ba?” Da sauri ta fara yarfe hannu
“A ‘ah ko kadan,banji haushi ba,ni dama ban sa rai ba,su sameer ne dai suna can suna fama da yunwa suna jira”
Ce mata yayi
“Toh tunda baki ji haushi ba muje ni in baki tukwuicin,dani da mai martaba ai duk daya ne,ko ni na baki ko kuma shi ya baki ai duk daya ne ko?” Gyada kai tayi suka nufi wajen wani mai siyar da kayan kwalliyar mata,wani awarwaro ya dauka tare da miqa mata
“Duba wannan kiga?” Karba tayi
“Yayi kyau sosai” kafin ta qarasa gani ya qara miqo mata wani awarwaron,ta karba
“Shima wannan yayi kyau” juyawa yayi ya cewa mai shagon,mun dauki duka biyu ,zare ido shukra tayi tare da kallonshi
“Kanka daya kuwa? Kasan kudin wadannan abubuwan? Ni dai bana so sunyi tsada sosai”
Da sauri yace mata
“Kar ki damu ai ina da kudi da yawa da yawa”
Mamaki ne ya bayyana akan fuskar ta,ya biya kudin sukayi gaba,tun da safen nan har yamma suna tare suje nan suje can,sai da zasu rabu yace mata
“Shin kina da burin zama wata nan gaba al’umma?” Yanayin ta ne ya canja daga murmushi zuwa damuwa
“Idan ma ina da wannan burin na tabbata ba zai taba cika ba,sai dai ko a rayuwa ta gaba domin ni lowborn ce,a wannan duniyar tamu mutane iri na basu da damar da zasu cimma wani buri nasu” tausayinta ne ya cika mai martaba,cikin sanyin murya yace mata
“Kada ki damu,ba sai a rayuwar gaba zaki samu cikar burinki ba,tunda kin cika nawa burin,toh nima zan cika miki naki” ya fada cike da qarfin gwiwa,shukra da kwata kwata bata fahimci me maganar shi ta qarshe take nufi ba amma kawai ta share,haka suka rabu ta koma bureu of music shi kuma guards dinsa suka fito suma suka koma palace.
Yana dawowa palace quaters din lady haneefah ya nufa,yana zuwa bakin qofa zai shiga maids dinsa suka tsaya domin jiranshi ya fito,nan ya kalleni tare da cewa kema ki jirani sai na fito sai ki cigaba da daukan rahoton 😂😂 hakan yasa ban san abinda suka tattauna ba,haka royal secretary da sauran sakatarori sukai ta zurga tsakanin quaters din queen haneefa da office of record da kuma office of properties,har dare suna abu daya,suna ta yawo da takaddu da nima kaina ban san na menene ba.
Washegari da safe,shukra tana bakin rijiya tana wanki,sameer ne da gudun tsiya ya qaraso inda take yana ta haki,cikin daga murya yace
“Shukra,ki bar duk abinda kikeyi kizo yanzu yanzu,anzo nemanki daga office of properties “ kallon rashin fahimta tayi masa,kafin ta furta wani abin ya qara ce mata
“Ba lokacin tambaya bane yanzu,don ni kaina ban san me ya kawo su ba,kizo mu tafi kawai” hakan yasa ta bishi a baya suka taho bakin office din manager,dukka ma’aikatan wajen sun hallara kowa yana mamakin me yasa aka zo neman shukra,matan da suka zo tare da su ne suka shimfida wani carpet aka dora pillow irin wanda suke zama akan shi,hakan yasa duk ma’aikatan suka yi layi a bayan inda aka sa carpet din tamkar ‘yan assemby,haka shukra tazo ta samesu,isowar ta wajen wata mace cikin baqin da suka zo ta kamo kafadarta tare da zaunar da ita a kan carpet da pillow din da aka ajiye,kowa bakinsa a sake suke kallon abinda ke faruwa,kowa ya matsu yaji menene dalilin zuwansu da kuma karrama shukra haka.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏻❤️
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Whattpad :Oum_tasneeem
Page 20
A office of investigation chief sumayya ce da dukkan ladies investigators da kuka sani a bayanta suka taho a sukwane cikin tashin hankali suka nufo inda director take tsaye bayan ta rako tawagar ‘yan office of properties wanda daga wajenta suka wuce bureu of music wajen shukra,sumayya cike da damuwa tace
“My lady ki taimakemu ki janye amincewarki akan wannan lamarin,wannan abu ne da bai taba faruwa ba a cikin qasar nan,tozarcin da zamu ji a ranmu har sai yafi na abinda shukran tayi mana,mutuncin office dinmu zai zube” ta qarasa cike da matsananciyar damuwa,director da ta kasa hada ido da kowannen su,itama fuskarta da damuwa sosai tace
“Bamu da abinda zamu iya yi,domin anyi hakan ne da izini da kuma sa hannun queen haneefah,kuma a matsayinta na shugabar inner court ba zamu taba tsallake unarnin ta ba,amma nima ina tunanin mu gwada zuwa wajen ta din ko za’a dace”
tana gama fadar haka tayi gaba ita da wanda suke binta a baya suka bar wajen.
Chief sumayya,nadeeya,basma,afrah,aliya,da sameerah sukai tsaye duk jikinsu a sanyaye,haqiqa lady jalila ta shammace su akan shukrah don sunsan wannan shine kawai abinda zatayi ta hukunta su cikin ruwan sanyi,chief sumayya ce tayi qwafa ba tare da kowa ya san abinda take tunani a cikin ranta ba tayi gaba sameerah ta bita,yayinda sauran suka tsaya suna jajantawa juna.
A bureu of music dukkan ma’aikatan wajen sun matsu suga saqon menene aka zowa da shukra haka,yayinda itama take tsugunne akan pillow da carpet din da aka shinfida a kasa,tana fuskantar ‘yan office of properties,hannu shugabansu ya miqa aka miqo masa takadda da take ajiye akan tray a hannun wata mata da suka zo tare,hannu ya saka ya bude ya fara karantawa kamar haka
Slave shukra Anas Malak zatayi biyayya ga unarnin office of properties.
A yau 11 march na shekarar 1432.
Baiwa shukra zata shiga cikin inner court.
Zata shiga cikin office of investigation a matsayin lady investigator.
Ya zama dole kiyi riqo da biyayya ga dokoki da kuma cika haqqin aikin ki ga wannan qasa tamu da kuma a matsayinki na lady investigator.
You will hear and obey.
Wato tun daga kan manager,sameer,da kuma dukkan ma’aikatan kallon kallo suka shiga,domin ko a tarihi basu taba jin yadda baiwa ta shiga inner court cikin office of investigation ba,abin mamaki ya zama har shukra ta kasa cewa komai sai kawai nuna kanta take tana cewa
“Ni? Ni? Ni din? Lady investigator? Office of investigation? Gaba daya ta rude,ta rasa me zatayi,wanda ya gama karanto mata takardar ne yace
“Slave shukra,hear and obey” da sauri ta nutsu na miqa hannunta biyu biyu ta karbi takardar tare da cewa
“I hear and obey my lord” nan take wajen ya cika da shewa ta ko ina,ma’aikatan bureu of music ba komai ne yake basu mamaki ba illa yadda akayi wannan abu ya faru,sun san ba saboda dalilin abinda tayi ne kadai ba,domin idan ana son bata tukwuici kudi ya kamata a bata da abubuwan alfarma amma tunda aka ɗaga darajar ta lallai akwai sa hannun wani babba( ni dai maryam nace baku san qawar mai martaba bace kenan ko? 😂😂 toh aikin sa ne)
Kafin ki ce me labari ya karaɗe ko ina ai slave girl shukra yanzu ta zama court lady investigator,ana ta taya ta murna a cikin bureu of music kowa da abinda yake faɗa na alkhairi,wasu suce dama bata dace ta zama slave ba,wasu suce yau sunga ikon Allah a tsarin rayuwar su indai aka haifeka a talaka mara galihu to a haka zaka qare rayuwarka sai gashi shukra ta samu ɗaukaka.
A office if investigation director ta kira meeting din kowa da kowa,ta kalli basma da nadeeya tace
“Ku zaku kai takaddar da na rubuta na cewar ba zamu karbi shukra ba zuwa office of properties,ni kuma ni da sumayya zamuje mu samu queen haneefa don its kaɗai take da damar dakatar da faruwar hakan”
Labari dai har kunnen uwar masarauta wato queen dowager,tana zaune a quaters dinta aka kawo mata rahoto,tare da faɗin director da chief na office of investigation sun tafi quaters din queen haneefa domin su gamsar da ita ta janye kawo shukra cikin office dinsu,hakan yasa itama queen dowager ta tashi ta nufi quaters din queen haneefa,da zuwanta ta tarar da chief sumayya a bakin qofa yayinda director take ciki suna magana da queen haneefah,shigowar queen dowager daidai lokacin da director take cewa
“Your majesty ya kamata ki duba lamarin mu,lady jalila tana son ta tozarta mu ne shiyasa ta nemi a kawo mana slave girl cikinmu,kuma kasancewar office dinmu shine yake juya dokokin inner court,matuqar aka fara kawo mana wanda basu isa ba hakan zai zubar da qimar mu sosai” kafin queen haneefa tace wani abu suka ji muryar queen dowager tana cewa
“Meyasa kike dogon tunani akan haka my queen? Kiyi maza ki aiwatar da hakan domin ba zai yiwu akai musu slave girl ba” cikin sauri queen haneefa ta tashi daga inda take zaune tare da cewa
“Mother” queen dowager taje ta zauna a inda haneefah ta tashi yayinda ita kuma ta zauna ta gefen tebur din da yake wajen,ta kalli queen haneefah tare da cewa
“Tunda akayi haka ba tare da an tuntube ki ba ya kamata a wannan lokacin ki dakatar domin kina da dukkan ikon yin hakan a matsayinki na shugabar inner court “ cikin sanyin da ya zama yanayinta tace
“Amma maamaa ni na riga na bada izini na akan hakan,anyi dukka hakan ne abisa izini na,kuma banyi domin lady jalila ba,nayi ne saboda na gamsu da cancantar yarinyar”
“Amma dai kinsan lowborn slave ce ko?” Cewar queen dowager
“Ehh maamaa amma ban duba wannan ba,domin doka ta bawa lowborn dama su zama palace maids” cewar queen haneefah
“Amma your majesty wannan dokar ta dade da daina aiki,an dade ba’a bawa lowborn damar zama palace maids” director ta fada,cikin dakewa da jin izzar sarauta queen haneefa ta kalleta tare da cewa
“Nan ba inda zaki fadi ra’ayinki kuma abi hakan bane,maganata ta qarshe kenan,da izini na aka kai shukra office dinki,ina fatan zaki bi abinda nake so” nan da nan director tayi shiru da bakin ta,ganin zuciyar queen haneefa ta riga ta gama yadda da hakan yasa queen dowager ma bata da ja.
Shukra cikin farin ciki ta nufi quaters din lady jalila domin tayi mata godiya,tana shiga ta tarar da ita a zaune cikin murmushi tace
“Shigo mana,zo ki zauna” a hankali shukra ta qarasa ta zauna,kafin tace komai jalila tace
“Ganin yanayinki ya tabbatar min kin karbi saqona” jinjina kai kawai shukra tayi alamar “Ehh “ ba tare da tace komai ba,jalila ta cigaba da magana
“Kamar har yanzu kina cikin mamaki shukra,meyasa? Bakya murna da tukwuicin da nayi miki ne?” Sai yanzu shukra ta tattaro qarfin halin yin magana
“Ina farin ciki your highness amma ina ganin ta yaya za’ayi slave girl irina ta zama palace maid a office of investigation,har yanzu na kasa yadda” maganar shurkra yasa lady jalila faɗaɗa murmushin ta tare da cewa
“Kina da baiwa da ba kowa yake samun irinta ba,hakan yasa kika samu wannan matsayin ba tare da duba irin yanayin da aka haife ki a ciki ba na lowborn,kina ganin yadda kika samu nasarar warware abubuwa manya har sau biyu wanda tarin maza da mata na police bureu da office of investigation suka kasa warwarewa” godiya shukra tayi sosai,lady jalila tayi mata fatan alkhairi ta tashi ta tafi.
Queen haneefa bayan dowager ta tafi tana zaune tana tunanin ranar da mai martaba yazo wajenta
*flashback*
Mai martaba yana zaune a mazaunin queen haneefa,yayinda ita kuma tana zaune tana fuskantar shi da qaramin tebur din da ya raba tsakaninsu,tana cikin matuqar farin cikin zuwanshi quaters dinta don rabon da ta ganshi har ta manta,labarin shukra yake ta bata its kuma tana ta dariya,da yadda suka haɗu da farko da yadda suke haɗuwa duk bata san shi sarki ne ba,daga qarshe yayi gyaran murya tare da cewa
“Nazo ne domin na nemi wata alfarma a wajenki duk da nasan tana da matuqar wahala”
Cike da ladabi da kuma murmushin da har yanzu yake kan fuskar ta tace
“Wace alfarma ce wannan your majesty?”
“Ina roqon alfarmar shigo da shukra cikin inner court a matsayin palace maid amma a office of investigation,kinga kenan zata zama lady investigator “ shiru queen haneefa tayi tana nazari,kafin tace komai ya qara cewa
“Nayi hakan ne saboda ina ganin ta cancanta,domin na gani da idona duk abubuwan da tayi ba labari aka bani ba,amma fah alfarma ce kawai,kina da damar da zaki qi karbar ta domin ke kike mulkin inner court” cikin murmushi take kallonshi tare da cewa
“Your majesty na yadda zan shigo da shukra cikin inner court kuma office of investigation,domin tunda ka yadda da qoqarinta nima na gamsu da hakan”
Daidai nan ta dawo daga tunaninta,kafin ta qara fadawa wani tunanin chief maid dinta ta shigo domin sanar da ita zuwan lady jalila,umarni ta bayar kan a shigo da ita ciki,chief maid din tana fita lady jalila ta shigo,tana shigowa daidai inda queen take zaune ta tsugunna har qasa ba tare da ta zauna ba,hannayenta a gefe suna taba qasa,sai ta sunkuyar da kanta qasa,queen haneefa tana kallonta ko motsi bata yi ba,sai da jalila ta danyi ‘yan sakanni a haka sannan ta qara tashi tsaye ta matso daidai inda ake zama ta zauna,cikin girmamawa tace
“Barka da hutawa your majesty” har yanzu queen haneefa bata ce mata komai ba domin kishin da izzar mulkin sun motsa,cikin nutsuwa jalila tace
“Your majesty nazo ne domin nayi miki godiya akan karamcin da aka yiwa shukra….” Kafin maganar bakinta ta gama fitowa queen haneefa tace
“Babu buqatar godiya,domin nayi abinda ya kamata nayi ne,kuma banyi hakan domin ke ba,nayi ne don yarinyar ta cancanta” rusunar da kanta jalila tayi,sannan tace
“Your majesty ina qara baki haquri da cece- kucen da hakan ya jawo a cikin inner court,ina fatan zaki yafe min kuma ki bani dama zan kula da komai,domin komai ya dawo daidai” murmushi queen haneefa tayi
“Zaki kula da komai? Lallai naga alamun al’amuran inner court sun fara zama masu muhimmanci a wajenki,ina ganin kamata yayi ki cire kanki a ciki,don duk cece kucen da akeyi ana yinshi ne domin na ga damar shigo da shukra cikin inner court amma ba don ke ba domin ni kadai nake da ikon yin hakan,toh saboda me zaki bawa kanki laifi?” har yanzu kan jalila a qasa yake,queen haneefa ta cigaba
“Abinda ban so ya faru ba guda daya ne,alfarmar da kika nema a wajen mai martaba tasa ana ta maganganun cewar kina da wani buri nan gaba a inner court,bana son sake jin haka,meyasa ba zaki janye kanki ba ki barni zan kula da komai”
Jalila cikin sanyin jiki tace
“Ina ta tsoron zaki yi min faɗa akan laifin dana aikata,ban san kin damu dani har haka ba your majesty,amma duk da haka a matsayina na daya daga cikin masu babban matsayi a inner court,ta yaya zan janye jikina in zuba ido? Hakan kamar yana nufin gujewa haqqin da aka dora min ne,kin riga kin san bani da wani buri nan gaba a inner court,kinga kuwa babu abinda zai dameni,saboda haka ba zan watsar da haqqin da ya rataya a wuyana ba your majesty”
Kallonta queen haneefah take ido cikin ido,har ta qarasa maganarta,sallamar ta tayi ta fita,tana fita chief maid dinta ta shigo ta zauna tare da cewa queen haneefah
“Your majesty kinga abinda nake fada miki ko? Shiyasa ban so kika bada izinin shigo da yarinyar nan ba,yanzu lady jalila zata dinga jin anyi mata hakane domin tana da alfarmar mai martaba”
Ajiyar zuciya Queen haneefa tayi tare da cewa
“Kina tunanin bani da wayo ne? Ina sane da duk abinda take yi”
Lady jalila tana komawa quaters dinta ta tarar da zuwan minister na tribunal da jameel babban danshi,gaishe ta sukayi yayinda ita kuma ta nemi waje ta zauna,minister ne ya kalleta tare da cewa
“Your highness na san cewar dole sai kina da damar juya office of investigation ne zaki samu qarfin iko a inner court amma sai mun bi komai a sannu” murmushi tayi tare da cewa
“Kada ka manta,ina da jinin lowborn a jiki na,ko ka manta? Office of investigation suna zabar 'yan mata ne daga gidajen masu kudi da iko na qasar nan,hakan yasa sai dai suyi min biyayyar dole amma a ransu suna jin cewar qarfin ikon iyayensu yafi qarfin nawa,shiyasa na kai musu ita domin su san mutun iri na zai iya shiga cikinsu kuma yafi su iya komai”
Jameel ne yace
“Amma your highness idan yarinyar nan tayi kuskure guda daya komai fa zai dawo kanmu kuma zamu wulaqanta saboda haka”
“A’ah jameel na tabbata zatayi abinda ya kamata,ku yadda dani”
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏻❤️
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Whattpad :Oum_tasneeem
Page 21
❤️ Part 3:The lady investigator
A bureu of music shukra ta kasa tsaye ta kasa zaune domin tana tsoron zuwa wajen queen haneefa yasa ta yadda da buqatar ‘yan office of investigation na qin karɓarta,har sai da manager yazo yace mata ai basuyi nasara ba kuma queen haneefa ta bayar da cikakkiyar amincewarta,sai sannan ta saki jiki sosai su sameer suna ta tsokanarta suna ce mata “My lady” tana cewa su daina fada,sameer ne yace
“Chab rufa mana asiri mu ai yanzu bamu isa mu kira ki da shukra ba,bari ma ki gani” nan da nan yaja baya ya hada hannayensa a kan cikinsa,ya rusunar da kanshi qasa tare da cewa
“My lady” haka duk sauran mutanen da suke wajen suma sukayi,dariya ya bawa shukra,haka ma sauran mutanen wajen kowa yana cikin farin ciki.
A halin yanzu matsayin shukra ya zarce kowa a bureu of music har manager,saboda haka yanzu babu wanda zai qara kiranta da sunanta,sai sun girmamata da my lady.
Manager ne yake tahowa inda suke da wasu ma’aikata a bayanshi dauke da tebur din abinci masu yawa,haka suka zo suna ta jerawa,shukra tace
“Yallabai wannan na menene?” Kafin manager ya bata amsa sameer yace
“haba shukra,ba kya gani walima zamuyi” da sauri ya rufe bakinsa, “ina nufin my lady” juyawa tai ta kalli manager hawaye ya cika a idonta,jinjina mata kai yayi cike da farin ciki shima idonshi ya cika da ruwa,wataqila wannan shine zamansu na qarshe don zata bar wajen kenan har abada,haka suka zazzauna kowa ya fara cin abinci,kowa cikin farin ciki gwanin sha’awa.
A police bureu suma IG ne sai lieutenant da assistant suke hirar shukra,a lokacin ne ake hirar yadda aka kai mata official decree of appointment harda cikakken sunanta Shukra Anas malak,jin haka yasa IG fadawa tunani shekaru takwas da suka wuce,kamar yasan wata qaramar yarinya mai irin wannan sunan,amma ita waccan SHUKRIYYA ANAS MALAK ne sunanta,ya kwashe shekaru kusan hudu yana nemanta daga baya ya haqura,amma ya za’a yi ta kasance a cikin masarauta,kuma baiwa? maganar assistant lieutenant ce ta katse masa tunaninsa
“Yallabai,kana da baqo a waje,wani shashashan yaro yazo nemanka”
Tashi IG yayi tare da fitowa waje domin ganin me neman shi,tsayawa yayi yana kallon yadda jaleel yake shashanci da masu gadin wajen cikin uniform dinshi na ‘yan sanda,da rank din lieutenant,har bai ma kula da isowarshi wajen ba,cikin rashin daraja suka gaisa,IG ya bashi warning akan cewar idan yana da hankali da iya aiki zasu zauna lapia domin an kawo shi ne ba akan qa’ida ba,alfarmar minister of tribunal ne,kuma matsayin lieutenant aka bashi daga sama,IG ne ya kalli assistant lieutenant yace
“Ya fika matsayi a rank amma ka fishi matsayi a sanin makamar aiki,saboda haka ka kula da training dinshi” yana gama fadar haka yayi gaba ya barsu,assistant lieutenant yana yiwa jaleel magana amma ko kula shi baiyi ba ya fara tafiya yana zagaye wajen,abdullahi ne ya bullo shi da wani dan sanda da littattafai a hannunsa,abdullahi cikin girmamawa yace
“Yallabai ko zaka bani litattafan sai naje na ajiyesu a inda ake ajiyewa” kallon abdullahi yayi yace
“Zaka iya jerasu kuwa?” Dariya yayyi
“Zan iya yallabai,duk da ban iya karatu ba amma zan iya gane harufan da zan jera” miqa masa littattafan yayi tare da cewa
“Ka taimakeni kuwa abdullahi domin ina da abubuwan yi da yawa” abdullahi juyawa yayi ya nufi inda suke ajiye litattafan su,da sauri ya ajiye wanda ya shigo dasu ya fara dudduba sauran wanda suke wajen cikin sauri domin kada wani ya shigo ya tarar da shi yana bincike,magana kawai yaji a kanshi
“Sannu da aiki ko?” A razane ya dago kanshi,jaleel yace
“A ah kada ka damu,cigaba da abinda kake yi,nima ai ka taimakeni a baya ko?” hannu jaleel ya kai kan littafin da abdullahi ya bude,a fili ya karanta
“LABARIN BAYIN DA SUKAYIWA MASU KUDIN QASA KISAN GILLA” ya kalli abdullahi
“Lallai kana karanta labari mai qayatarwa”
“Karatu kuma? Ta yaya zanyi hakan? Nazo mayar da wasu litattafai ne kuma na kasa gane inda zan ajiye su” cewar abdullahi,murmushi jaleel yayi tare da cewa
“Kaine Gwani wajen iya faɗa,kuma mai ɓoyayyen tarihi,lallai kana buqatar ka ɓoye ko waye kai,ba zan cewa kowa naga kana karatu ba tunda ka nuna musu baka iya ba” Cike da razani abdullahi yake kallonshi,baice komai ba jaleel ya qara cewa yana miqa masa littafin
“Karɓi ka cigaba da karatun ka,ni na tafi,yi karatun ka kaji?” Cikin sanyin jiki abdullahi ya karbi littafin shi kuma jaleel ya fita.
A daren ranar bayan an gama walima an ci an sha an gama komai,shukra tana ta tattara komai nata domin tafiya gobe da safe,sameer ne da manager a tsaye suna kallonta,ta dago ta kalli sameer tare da miqo masa wani
“Yallabai ga wannan,shayinka ne domin yawan murar da kakeyi,ka kula sosai tunda kaga yanzu bana nan” tsayawa yayi yana kallonta,shi bai karba ba,kuma bai ce mata komai ba,hawaye ne suka cika mai ido,manager ne ya kalle shi
“Sameer menene haka?” Cikin sanyin murya sameer yace
“Sai yanzu na yadda lallai shukra tafiya zatayi ta barmu” manager ne ya harare shi
“Kamar wacce zata tafi nisan duniya? Naga dai inda zata je ma duk cikin masarautar nan ne” manager ya fada shima idonshi yana cika da qwalla,sameer ne yace
“Duk da ba barin masarautar zatayi ba,amma a nan bureu of music kamar dangi daya muke,tana tafiya kuwa ganinta ma wahala zaiyi mana” ya qaraso daidai lokacin da hawayen da yake boyewa ya sauko kan fuskarsa,shukra shiru tayi itama zuciyarta ta karye sosai,manager ne ya dauko algaitar da ta taba busawa har mai martaba yaji kidan ya miqa mata
“Ki tafi da wannan,kinga shikenan ba zan dinga yi miki fada ba don kina amfani dashi” hannu tasa ta karba a hankali,itama hawaye yana zubo mata,ba tare da ta ce musu komai ba ta fita daga wajen ta nufi waje,zama dukkansu sukayi akan kujera kowa yana kuka sosai kamar yara.
Zuwa tayi ta zauna a bakin dakin ajiyar kaya,tana shafa algaitar nan tana tunawa da yayanta,wanda a da royal musician ne kafin a kashe su shi da babanta,a hankali ta bude bakinta ta fara magana tana kallon taurari a sama
“Abbana yau zan bar bureu of music”
“Zan shiga cikin office of investigation “
“Duk da ina tsoron abinda zanje in tarar,amma zan gwada”
“Kana fada min cewar zama lowborn ba’a haihuwa ko dukiya bane”
“Idan zuciyata ta zama mai kyau,hakan yana nufin nima highborn ce”
“Ina kewarku kai da yayana”
Ta qarasa hawaye yana zubowa a idonta,haka ta raba dare a zaune a wajen kafin taje ta kwanta tayi bacci.
Washegari da safe,ladies investigators ne a jere kan layin assembly,yayinda chief sumayya take zagayawa tana duban tsafta ranta a matuqar bace,dai dai kan aliya har ta wuce,ta dawo baya,wani zare ne a gaban rigarta,chief sumayya tasa hannu ta zaro zaren tare da yarwa a qasa,tace
“Zare ya kunce a gaban rigarta,qarin night duty guda 3 ga aliya” nadeeya da take binta a baya ce ta rubuta abinda ta fada suka cigaba da zagayawa,sameerah ce tazo ta gabansu tare da cewa
“My lady,slave girl dinnan ta qaraso” bacin ran dake fuskar sumayya ne ya qaru
“Je ki taho da ita” juyawa sameerah tayi suka taho tare da shukra,shukra cike da girmamawa ta rusunar da kanta tana gaishe su,sai dai babu wanda ya amsa mata,’yan kan assembly kuwa duk suka bita da harara suna takaicin yanzu matsayinsu daya da wannan,sumayya ce ta kalli nadeeya
“Ki tafi da ita,ayi mata abinda ya kamata“
“Yes my lady” nadeeya tace tare da yin gaba,shukra ta bita a baya,sun bar assembly ground din sukayi hanyar dakin kwanan su,wasu bayin wajen suka hadu dasu da suke sanye da kaya irin na shukra,nadeeya ta tsayar dasu
“Ki bisu su baki uniform kuma su nuna miki dakin ki”
“Yes my lady” su shukra suka amsa ita da bayin guda biyu.
Shukra ta shirya tsaf cikin uniform dinta,navy blue din skirt da pink din riga,sai headband mai kyau da tambarin office of investigation a kai,a gaban madubi take tana kallon kanta tace
“Yanzu ni palace maid ce” tana ta murmushi,slave girl din da ta kawo ta ce ta shigo,tace
“My lady kin gama?”
Shukra ta kalleta,ta dan rusunar da kanta tare da cewa
“Ehh na gama” zare ido slave din tayi tare da cewa
“Ki taimaka ki daina girmamani my lady,hakan zai iya jawo min matsala” sai a lokacin shukra ta tuna ai yanzu ita za’a girmama,tace
“Toh shikenan,muje” ta fada tare da dan rusunar da kanta,slave dince a hankali tace
“Ai kin qara yi” kafin nan ta fita ta bar shukra a tsaye,a hankali ta fara magana
“Yanzu nima ya zama dole na dinga magana da bayi kai tsaye ta sigar basu umarni,kai zan iya kuwa? Wannan wani sabon yanayi ne” ta fada tana runtse ido,domin har rashin sabo da hakan ya fara damunta tun yanzu.
Tana shigowa assembly ground din kowa ya watse sai wa’yanda suke tsaye suna dan surutun su,nan aka fara nuna ta da baki suna ta binta da harara,sameerah ce ta fito daga office din sumayya tace
“Ki biyo ni muje wajen director” shukra ta dan rusunar da kanta tare da cewa
“Yes my lady” harara sameerah ta watsa mata
“Kar ki qara ce min my lady” shukra taji kunya sosai domin ita mantawa takeyi,suna tafe har office din director,suna shiga ta gaishe da kowa a wajen ta samu waje ta tsaya,director ce ta kalleta
“Yanzu ya kamata kisan cewar ke ba lowborn bace,lady investigator ce,kuma hakan yana nufin qarin girma,mutunci,da girmamawa,ki bi dukkan dokokin mu domin zama lapia”
Rusunar da kanta tayi
“Yes my lady” shukra ta fada,director ta kalli sameerah
“Ku tafi da ita” sameerah ce tayi gaba shukra ta qara binta har office din da sauran ladies din suke zaune,suna shigowa kowa ya bisu da kallo,shukra ce gaishesu duk suka qi amsawa,nan da nan suka fara ficewa daya bayan daya har ya rage daga ita sai Afrah,cikin nutsuwa ta kalleta
“Kada ki sa rai akwai wanda zai miki kirki a cikinmu,kuma kada ki zata wai don kina ‘yar talakawa ne,a ‘ah sai dai kawai dukkanmu muna jin takaicin yadda kika kama qafa da masu mulki domin zuwa inda yafi qarfin ki” tana gama fada mata haka itama ta fice ta barta,nadeeya ce ta shigo,ganin yadda kowa ya fito tasan saboda zuwan shukra ne,dafa kafadar shukra tayi
“Kada kiga laifin ‘yan matan nan,dukkansu tun suna qanana ake kawo su domin sai sun samu aqalla shekara goma suna training na shan wahala kafin su samu irin matsayin da kike kai yanzu,shiyasa suke jin haushi domin suna ganin ke kinzo a bagas ne,kuma matuqar baki gamsar da kowa cewar kin cancanta ba,babu wanda zai daukeki da muhimmanci” murmushi shukra tayi
“Nagode my lady,ke kadai kika fada min abu mai dadi,kuma nayi alqawarin zanyi qoqarin gamsar da kowa cewar na cancanta.
Suna fita dukkansu office din chief sumayya suka nufa,aliya ce tace
“Yanzu chief haka zamu zuba ido muna kallon wannan qasqantacciyar a cikin mu?” Sameerah ta cafe
“Ni yanzu har kunyar kaina ma nake ji,duk ajina ya zube tunda yanzu matsayin mu daya da wata baiwa” aliya ce ta qara cewa
“Gaskiya zanga zanga ya kamata muyi,mune wanda muka fi kowa muhimmanci a inner court,idan aka ga munqi yin aiki,dole queen haneefah ta duba lamarin nan”
Sumayya ce tayi gyaran murya dukkansu sukai shiru
“Duk babu buqatar yin hakan,domin ba zan barta da dade a nan ba” hakan kawai ta fada ba tare da wani qarin bayani ba,amma duk zuciyar su ta gamsu don sunsan halinta sosai,matuqar dai tace zatayi abu,to sai tayi.
Chief maid din queen dowager ce ta shigo
“Your majesty chief sumayya tazo”
Dago kai tayi ta kalleta
“Je ki shigo da ita” juyawa chief maid tayi suka dawo tare da sumayya,tana shigowa cikin sit room kai tsaye inda dowager take zaune taje,a hankali ta durqusa qasa,ta tokare jikinta da hannayenta da suka taba qasa,tare da rusunar da kanta sosai,da dauki sakanni a haka sannan ta tashi ta matso dai dai pilon da yake ajiye a qasa domin zaman baqi ta zauna,duk abinda take idon dowager yana kanta
“Kece chief madam investigator sumayya kenan”
“Ehh ni ce your majesty” sumayya ta bata amsa,murmushi dowager tayi tare da cewa
“Ina sauraronki” rusunar da kai sumayya ta qarayi tare da cewa
“Your majesty akan yarinyar nan da aka kawo mana,nasan kema ba’a son ranki bane aje akwai wani wanda yake da alaqa da lady jalila a cikinmu” jinjina kai dowager tayi sumayya ta cigaba
“Ni ina da yadda zanyi ta bar wajen a cikin kwana uku ba tare da mun karya doka ba,domin ba korar ta zamuyi ba,da kanta zata kori kanta”
“Ta yaya kenan?” Dowager ta tambaya
“Kasancewar a dukkan irin wannan lokacin na shekara akwai taron da mukeyi a office of investigation” sumayya ta fada,dowager ce tayi saurin cewa
“Taro a irin wannan lokacin? Kina nufin taron….” Kafin ta qarasa sumayya tace
“Ehh shi dai your majesty,ina tabbatar miki da lady jalila da duk masu goyon bayanta zaau wulaqanta” jinjina kai dowager tayi cike da gamsuwa,nan suka cigaba da tattaunawar su yadda abubuwan zasu kasance.
Chief sumayya tana fitowa daga quaters din queen dowager kai tsaye training center ta nufa,inda ake koyawa ladies investigators karatu,tana ta rarraba ido dai taga bata ga shukra ba,nadeeya da tazo gabanta ta tsaya ta kalla
“Ya banga shukra ba?” Nadeeya cikin girmamawa tace
“Na ga yaune ranar ta ta farko,shine nace taci abinci sai ta huta a daki” harara sumayya ta watsa mata
“Waye ya sa ki hakan? Ai itama yanzu lady investigator ce,ya kamata ace ta fara shiga cikinsu” Nadeeya sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba,sumayya ta daga murya tana kallon saitin da sameerah take
“Sameerah,jeki dakin shukra ki taho da ita,ai itama investigator ce kamar kowa,ya kamata tazo daukar karatu”
“Yes my lady” Sameerah ta fada tare da rusunar da kanta a gaban sumayya sannan ta wuce kiran shukra,yayinda duk sauran suka bi bayan sameerah da harara domin basu ji dadin abinda chief sumayya tayi ba,su sunfi jin dadi da aka ce kada tazo cikinsu.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏻❤️
ROYAL CONSORT
Korean inspired novel
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Whattpad :Oum_tasneeem
Page 22
Sameerah tare suka dawo da shukra wajen karatun,yayinda aka fara bitar karatu,kowa da littatttafan sa a gaba,a zaune suke a qasa,sai qaramin tebur daidai yadda hannunsu zai kai rubutu,sai tawada (ink) da abin rubutu (brush) wanda dashi suke amfani domin yin rubutun,littafin doctrine of the mean (kamar constitution na qasa) ake karanta musu suna cikin duddubawa,malamar tana karantowa suna duba littafin,chief sumayya ce tazo daidai inda shukra take ganin ta tasa pejin da ake karantawa,durqusawa tayi ta budo mata shafin sannan tace
“Nan ne inda ake karantawa” tare da nuna mata kan layin inda ake karantawa,kallon kallo suka fara yi a tsakanin su ganin wani sabon mutunci da lady sumayya take yiwa shukra.
Washegari da safe shukra a tsugunne a bakin rijiya tana wanki,slaves din da suke aiki a wajen ne suka zo da gudu
“My lady,bai kamata kina wankin nan ba,domin aikinmu ne” dago kanta tayi ta kallesu
“Na tashi ne kuma naga babu abinda zanyi shiyasa,ku barshi kawai na qarasa” shukra ta basu amsa
“A ah my lady,idan aka ganki kina wanki hakan zai iya zamar mana matsala” miqewa shukra tayi daga wajen,ta dauraye hannayenta,har zata tafi ta juyo fuskarta da murmushi ta e
“Tunda ku kuna min magana bari in tambayeku mana?” Daya daga cikin bayin ne tace
“My lady kiyi tambayar ki”
“Na san dai ladies investigators suna aiki sosai,amma meyasa tunda nazo banga kowa yana aiki ba,kuma da na tashi daga bacci ma banga kowa ba,duk ina suka tafi?” Murmushi baiwar tayi
“Ai my lady a wannan lokacin na kowace shekara ladies investigators suna jarrabawar qarshen shekara,shiyasa yanzu kowa yana shirin yin jarrabawar ne,domin gobe ne ma zasuyi ta”
Jinjina kai shukra tayi sannan tayi musu godiya ta bar wajen.
Chief sumayya ce a office din director,tare suke da nadeeya da basma,director ta gama jin abinda ya kawo ta tsaf
“Yanzu kina nufin kina son shukra tayi wannan jarrabawar?” Director ta tambaya
“Ehh my lady,tunda itama yanzu lady investigator ce,ya kamata ayi mata yadda akewa kowa domin haqqinta ne hakan” sumayya ta fada,murmushi director tayi tare da cewa
“Gaskiyarki,ni banyi wannan tunanin ba,duba da cewar jiya jiya tazo,amma ayi hakan kawai” sumayya cike da murmushi tace
“Nagode ranki ya dade,ni zan taimaka mata wajen karatun jarrbawar” jinjina kai director tayi,sumayya suka juya suka fita itada su basma,office dinta ta wice yayinda su basma suka tsaya domin tattaunawa.
Basma ce ta kalli nadeeyah cikin zare ido tace
“Me chief take nufi da tana son shukra ta yi jarrabawa? Ai baza ta iya yin ta ba”
Nadeeyah cikin jimami,domin ita hankalinta ya kwanta da shukra tace
“Wannan wani abu ne kawai da chief take shiryawa domin korar shukra daga office dinnan,zatayi hakan ne ta koreta salin alin ba tare da wani ya zarge ta ba”
Basma ce ta kalleta cikin rashin fahimta
“Ban gane tana son ta koreta ba” nadeeya ta kalleta
“Haba basma,kin manta dokar jarrabawar ne? Ana bada maki ne kamar haka PASS,CREDIT da kuma DISTINCTION kuma kinsan mutum idan bai samu credit ba to shikenan ya rasa matsayinsa na lady investigator kenan” basma cikin damuwa tace
“Na kuwa tabbata yarinyar nan ba zata samu ko PASS din bane,shiyasa sukayi hakan domin su koreta”
Shukra tana tsaye a gaban sumayya a office dinta,domin ta aika a kirawo ta domin yi mata bayanin zata dauki jarrabawa gobe tare da kowa,cike da damuwa shukra ta kalleta
“Amma my lady ni da ban san komai ba,ya zanyi?” Murmushi sumayya tayi
“Kada ki damu shukra,kawai ki rubuta iya abinda kika sani,kada ki takurawa kanki kinji?” Jinjina kai shukra tayi,tayi wa sumayya sallama ta tafi.
Ranar har dare ya ratsa tana zaune a wajen karatu tana karanta wani littafi,ana jin muryar ta tana haddar “yawan palace maids din da suke cikin masarautar nan
14 attendants
20 sewing
23 embroidery
2 academy
2 treasurers
13 kitchen
11 beverages
12 laundry
Tana ta karantowa ba tare da ta duba littafi ba,daga baya ta duba taga akwai inda tayi kuskure,haka dai ta cigaba da karatunta a cikin daren,domin shiryawa wannan jarrabawa.
Washegari da safe kowa ya zo cikin aji sun zazzauna,qus qus suka fara ganin shukra itama a cikinsu,Afarh da take kusa da shukra ce ta kalleta
“Me yasa kika zo yin jarrabawa?” Juyowa shujra tayi tare da ce mata
“Chief sumayya ce tace inzo nayi,kuma tace na rubuta abinda na sani kawai” qasa qasa suke magana,afrah ta qara ce mata
“Da alama baki san me wannan jarrabawar take nufi ba” shukra ta zaro ido tare da cewa
“Kamar ya ban san me take nufi ba?” Afrah tace
“Idan baki samu makin da ya kai credit ba,lallai zaki bar office dinnan ki koma bureu of music a matsayin slave girl dinki da kika baro” nan da nan gaban shukra yayi wata mummunar faduwa,cike da damuwa tace
“Amma ni chief bata fada min haka ba,kuma bata nuna min abinda ya kamata na karanta ba,ni dai na karanta elementary reading kawai” jinjina kai afrah tayi tare da cewa
“Lallai shukra kina ruwa” kafin shukra tace wani abu suka ji shigowar chief sumayya,da su basma da nadeeya a bayanta,tsayawa tayi a gaban su tare da cewa
“Da fatan kun shirya,abinda zakuyi jarrabawa a kanshi shine DOCTRINE OF THE MEAN zaku karanta da kanku ba tare da duba littafi ba” gaba daya wajen suka kama qus qus domin littafin yana da wuya sosai,yana da wahala,amma hankalin shukra yafi na kowa tashi,don tun ranar da ta shigo aji sau daya taga ana karanta shi ai bata qara bi ta kanshi ba,nan da nan ido ya raina fata,daga idonta tayi tana kallon chief sumayya,taga itama idonta yana kanta tana mata kallon “zanga yadda zakiyi” shukra ji tayi kamar ta fashe da kuka a wajen,domin ta san ta ma fadi jarrabawar nan kawai,tana cikin wanan halin ta tsinkayi muryar chief sumayya
“Ina fatan kowa ya shirya wannan jarrabawa,kamar yadda kuka sani ne,duk wanda bai samu CREDIT ko sama da haka ba,zai fadi jarrabawa,kuma hakan yana nufin rasa matsayinsa na lady investigator,domin office of investigation abin koyi ne ga dukkan inner court shiyasa ya zama dole mu horar daku domin ganin kun fi kowa a cikin inner court,ina fatan kowa zaiyi abu mai kyau”
Wata mata ce ta taho da wani qaton bowl a hannunta,takaddu ne a ciki duk a na nannade su,chief ta dauko guda daya ta daga sama
“Wannan sune farkon layin da kowa zai karanta,zaku dinga dauka sai ku bude,duk abinda mutum ya dauka,to zai karanta har qarshen sa da ka,don haka yanzu zamu fara” kiran sunansu aka fara yi mutum bibbiyu,su zo kan tebur din akwai kujerun su na zama,sannan su dauki takaddar,idan suka bude sai su karanta,a take za’a fada miki ko kin wuce ko kin fadi,haka ake ta kiran sunayensu suna zuwa suna yi.
Slave din da shukra tayi wa tambayoyi ne a baki rijiya da gudu ta taho quaters din lady jalila,wata attendant dinta ta tarar a bakin qofa,cikin damuwa da gaggawa tace mata
“Nazo wa da lady jalila da labari ne,ya kamata ki sanar da ita yanzunnan,a office of investigation suna can sun saka lady shukra yin jarrabawa” ai da sauri labari yaje kunnen lady jalila,ta kalli baiwar nan tare da cewa
“Me kika ce? Sun sata yin jarrabawa? Ya za’ayi tayi jarrabawa yanzu,shekaran jiya fa ta shiga wajen,ya za’a yi su hada ta da wanda sukai shekara guda suna shiryawa karatun jarrabawar” cikin bacin rai sosai take magana,tare da fara tunanin abinda ya kamata tayi.
Dai dai kiran sunan Afrah tare da shukra aka kira su,suka zo suka zauna,afrah ce ta fara har ta gama,chief sumayya tace
“Afrah - pass” da yake dama duk cikinsu afrah tafisu qoqari,hankali da kuma nutsuwa.
Shukra ce ta miqa hannu ta dauko takadda tare da budewa,tsayawa tayi tana kallon takaddar domin bata iya ba,chief sumayya tace
“Karanto mana” dagowa tayi ta kalleta cikin fuskar tausayi,chief kuwa ta samu yadda take so ta qara cewa
“Ki karanta nace” ajiye takaddar shukra tayi ta fara karantawa,maimaita iya inda aka rubuta a takaddar take, ba tare da ta qara da komai ba,tana ta maimaitawa cikin rashin sanin abinda zatayi,tausayinta duk sai ya cika su nadeeyah da basma domin sun san mugunta dama aka so ayi mata,muryar chief ce take cewa shukra
“Sqi maimaita waje daya kike,ki cigaba mana” kallonta shukra tayi
“Cigaban? Cigaban?” Sumayya cikin dakewa tace
“Ehh cigaban,karanto cigaban”
Rusunar da kai shukra tayi tare da cewa
“Forgive me my lady,amma ban iya cigaban ba”
Sameerah ce ta harareta,aliya ma haka amma ita ta dan ji tausayinta,amma taji dadi tunda zata tafi ta barsu dama bata dace da wajen ba,chief sumayya ce tace
“Shukra - fail” da sauri shukra ta dago kanta ta kalli sumayya,itama ita take kallo cikin rashin tausayi,nadeeya ta sauke ajiyar zuciya domin ba haka taso ba,ta tausayawa shukra sosai haka basma ma,amma babu abinda zasu iya yi,sauran ladies investigators kuwa kowa yana ta murmushin jin shukra ta fadi.
Bayan an gama jarrabawar shukra ce take ta bin chief sumayya a baya tana cewa
“Na roqeki chief ki qara bani wata damar” tsayawa tayi ta juyo tare da kallon shukra
“Wai ba nace ki daina bina ba? Kawai ni nayi qmfani da doka ne,saboda haka ki daina bina”
Shukra ta taugunna tace
“Amma my lady kinsan ban taba karanta littafin nan ba,kuma ke kika ce min na yi jarrabawar nan daidai abinda na iya,ko dai anyi hakan ne dama domin a kore ni daga nan?” Kallonta sumayya ta tsaya yi domin tayi mamakin qarfin halinta,tace
“Ni kike fadawa haka? Bayan na riga na fada miki cewar kawai munbi yadda dokokin suke ne,mu a nan muna girmama doka,ko kina tunanin zamu baki wata alfarma ne a wajen jarrabawa? Yadda akayiwa kowa haka kema akayi miki tunda duk matsayi daya kuke”
Shukra da har yanzu take a tsugunne tace
“Ki taimaka min my lady,ki bani wata damar” cikin daga murya sumayya tace
“Ki dakata haka,idan har kin dauki kanki cikakkiyar lady investigator,to abinda ya kamata kiyi shine ki bi doka ki bar cikin wajen nan salin alin,sai ki jira fitowar sakamakon qarshe amma zamanki a nan ai ya qare” tana gama fadar haka ta yi gaba tabar shukra nan,itama shukra daga murya ta fara yi yadda zata jiyo ta
“Ki taimaka min my lady,hakan ba’a yi min adalci ba,ku qara bani wata damar” ko juyowa chief bata yi ba ta yi gaba abinta,a wajen shukra ta durqushe ta saki kuka mai ban tausayi.
A office dinsu ladies investigators suka shiga kowa da murmushi akan fuskar shi,sameerah tace
“Ni dama nasan chief ba zata taba barin yarinyar nan ta zauna ba,ashe dama abinda ta shirya kenan,yanzu ba shikenan ba mun rabu da ita ba,ko tana so ko bata so dole ta tafi”
Haka kowa yayi ta tofa albarkacin bakinshi,afrah ce tace
“Amma abinda baku sani ba shine,ba shukra bace tayi abin kunya,mu aka jawo wa abin kunya” sameerah ce ta kalle ta
“Kamar ya kenan? Kina taya ta baqin cikin zata tafi ne?” Afra tace
“Abinda nake nufi shine,duk wanda yaji wanan abin yasan an shirya hakan ne,sai a fara kallon office of investigation kamar shashahai kima marasa adalci,akwai wasu hanyoyin da za’a iya bi a koreta amma ba ta haka ba”
A office din chief sumayya su nadeeyah da basma a zaune suna bata baki akan bai kamata ayiwa shukra haka ba,kallonsu take cikin dakewa tace
“Ni dai kawai nabi doka ne,kuma ai kunsan yadda dokar take ko? Nadeeya ce tace
“Amma my lady ya kamata ce an fara mata training tukunna,a halin yanzu fa zuwanta kenan babu training din da ta fara karba”
Sumayya ce ta harareta “shin akwai wata dokar da tace lallai sai mun jira an fara mata training,alhali lokacin jarrabawa yayi?”
Basma ta sa baki
“Amma my lady ba yadda za’ai kayi tunanin yari zai iya gudu,bayan ko rarrafe bai fara ba”
Ran chief sumayya ne ya baci,ta kallesu su biyun tare da cewa
“Ni dai nabi tsarin doka ne,kuma na gama magana ta qarshe” da fadan haka ta tashi ta fita ta barsu a office din,basma ce ta kalli nadeeya
“Yanzu nadeeya yaya zamuyi,haka zamu bar yarinyar nan ta tafi? Ba’a yi mata adalci ba” nadeeya da gaba daya yanayin fuskar ta ya canja zuwa bacin rai sosai tace
“To yaya zamuyi basma?”
Lady jalila tana zaune cikin matuqar bacin rai da ba’a taba ganinta a cikinsa ba,chief maid dinta ce tace mata
“My lady ya kamata kiyi wani abu,domin idan sukayi sa’ar korar shukra toh kema suna wasa ikon ki ne,za’a rage ganin girmanki a cikin masarautar nan” cike da bacin rai jalila tace
“Ai ban taba tunanin zasu iya zubar da girmansu suyi irin wannan abin ba,amma babu abinda zanyi”
“Babu abinda zakiyi your highness?” Chief maid ta tambaya
“Ehh babu abinda zanyi wa shukra a halin yanzu,domin idan na taimaka mata ta tsallake wannan,wani abin zasu qara qirqirowa,tunda ita take zaune dasu ya kamata tayi qoqarin magance wannan matsalar da kanta,mudai mu bita da addu’a a wannan yanayin,domin nasarar ta itace tamu,faduwarta kuma faduwarmu ce”
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤
ROYAL CONSORT
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Page 23
Shukra tana zaune tana kuka,kamar wacce ta tuna wani abu,tayi sauri ta goge hawayenta,nan da nan ta samu qarfin gwiwar tashi,da sauri take tafiya har tazo library,dube duben wasu litattafai ta fara yi har ta samu wanda take nema,budeshi ta fara yi tana neman wani shafi,murmushi tayi tare da cewa
"Yes,na samu"
Cike da qwarin gwiwa ta fito daga library din,director ta hango suna tafiya chief sumayya tana binta a baya,da gudu ta qarasa wajensu tare da cewa
"My lady,ku taimaka ku saurareni,akwai abinda nake son fada muku" director ce ta tsaya,shukra tazo gabansu ta rusunar da kanta sosai tare da cewa
"My lady,littafinnnan na rules (dokoki) nake ta karantawa tun ranar da nazo shine na ga inda yake nuna an bada jarrabawar nan ba akan qa'ida ba" littafin ta miqo tare da nuna musu layin domin su karanta,sannan ta cigaba da cewa
"A littafin dokoki an rubuta cewa za'a bada jarrabawa ne akan topic din da akayi a shekarar da ta gabata,amma littafin DOCTRINE OF THE MEAN da aka yi mana jarrabawa akai,sati biyu da suka wuce aka fara karanta shi,hakan yasa ba zai iya zama topic din jarrabawa ba" sumayya da tunda shukra ta fara magana ranta ya fara baci,huci kawai take yi tace
"Me kika ce?" Shukra ta kalleta tare da cewa
"Na tabbata kin zabi wanan littafin ne domin kinsan ban taba karanta shi ba,kuma ba'a yi min adalci ba a kan hakan,shiyasa dokar ta bada damar a sake min wata jarrbawar" saukar mari kawai taji a kan fuskarta,chief sumayya tana huci tace
"Ke kin isa ki koya min dokokin office of investigation?ganin dama ta ne na zabi duk inda nake so na bayar ayi jarrabawar akai...." shukra ce ta katse ta
"Amma my lady......"
"Rufe min baki,mutuniyar banza,shashashar yarinya" ta katse ta tare da qara miqo hannu zata qara marinta,director ce ta sa hannu ta tare ta,hakan yasa ta ja baya tare da cewa
"Yes my lady" director ta kalli shukra tare da cewa
"Kince an bada jarrabawa ba daidai ba,ke wace irin yarinya ce mai tsaurin ido? Yanzu me kike so a yi miki? Kina tunanin ko kin karanta littafin zaki ci jarrabawar ne?" Rusunar da kanta shukra tayi tare da cewa
"My lady anyi tsawon sati biyu ana koyar da littafin nan,ina ganin nima idan aka bani sati biyun......" katseta director tayi
"A baki sati biyu? A yanzu hakan ma ai mun bata kwana daya a kanki,wulaqancin da muka samu ta dalilin ki ya isa haka,don haka ki tattara salin alin ki bar cikin office dinnan don nan wajen bai dace da irin ki ba" suka wuce suka barta a wajen.
Sameer ne ya shigo office din manager ran shi a bace yana ta qwala wa manager kira
"Wai kiran na menene ne?" Manager ya tambaya yana kallon inda sameer yake shigowa
"Yallabai mummunan labari ne,ina tunanin shukra ta kusa dawo mana bureu of music" cikin razana manager yace
"Kasan me kake fada kuwa? Me zai dawo da ita?
Sameer ne ya fada masa duk abinda yake faruwa,nan da nan hankalin manager ya tashi sosai,tausayinta ya lullube shi.
Shukra a nan bakin main qofar shiga office of investigation ta zauna tana roqon su (idan kana da wata buqata ko kuma kana son a yafe maka a kan wani laifi,suna yin haka,sai ka zauna qafarka a nade kamar zaman sallah a bakin quaters din wanda kake meman alfarmar shi,ko kwana nawa zakayi,ba ci ba sha duk iska,duk damuna har sai sun fito sunji tausayinka sunyi maka abinda kake nema,hakan yana daya daga cikin al'adunsu) haka shukra ta zauna har yamma,ga hadari ya hado sosai,nan da nan aka fara ruwa mai qarfi tare da iska.
Mai martaba ne ya fito daidai lokacin da aka fara yayyafi,a bakin grand palace cikin shigar shi ta dragon robe maroon kamar yadda yake sawa idan yana cikin masarautar,cikin yayyafin ya fito ya tsaya yayi nisa cikin tunanin da shi kanshi bai san tunanin me yake ba,amma yadda ruwan yake sauka yake kallo,chief eunuch ne yace masa
"Your majesty ya kamata ka koma ciki domin iskar ta fara yin qarfi sosai" shiru yayi masa bai amsa ba,fuskarshi da alamar damuwa.
Shukra tana tsugunne ruwan yana ta qara qarfi,ladies investigators Suna hangota daga inda suke tsaye,har ta basu tausayi,nadeeyah ce ta fito da lema a hannunta,tazo daidai inda shukra take tasa mata lemar tare da cewa
"Ki tashi daga nan wajen,domin zamanki a nan wajen ba zai canja komai ba" shukra ta dago idonta da suka qanqance ta kalli nadeeya
"Ba zan iya tashi daga nan wajen ba har sai anyi min adalcin daya kamata,zaki iya tuna ranar farko da nazo nan? Wata lady investigator (Afrah) tace min ba ni ce basa so ba,kawai suna jin takaicin yadda na kama qafa da masu alfarma domin samun abinda yafi qarfina,hakanan kema kika fada min idan har ban tabbatar da cewar na cancanta ba,babu wanda zai kalleni da daraja,kinsan yadda kalaman nan suka qona min rai? Saboda dukkan abinda kuka fada gaskiya ne"
"Amma shukra......." Kafin nadeeya ta qarasa magana shukra ta katse ta
"Toh a ganinki me lowborn iri na zata iya yi? Gaskiyane ina son zama mai amfanar al'umma ta,ina son na zama mai masara kamar dukkanninku,ina son na zama mai amfani ko da sau daya ne,shin hakan laifine? Ina son na nunawa kowa cewar kasancewa ta lowborn,amma zuciyata ba lowborn bace,na tabbata zan iya cimma wani abu mai muhimmanci,abinda kawai nake buqata shine a bani dama,ko da ta lokaci qanqani ce,amma idan aka koreni a haka,tabbas zan tabbata lowborn"
Tausayinta ne gabadaya ya cika nadiya,haka ta taho ta barta a wajen a tsugunne ruwa ya cigaba da dukanta,office dinsu ta dawo ta zauna tayi nisa a cikin tunani basma ta shigo,kusa da nadeeya tazo tare da dafa kafadar ta
"Lafiya nadeeyah? Tunanin me kike haka?" Juyowa tayi ta kalli basma tare da cewa
"Basma,tun yaushe rabon da ayi mana promotion? Zaki iya tunawa?" Fuskar basma ce ta canja a take tace
"Me yasa kike tambaya? Chief sumayya class mate dinmu ce,amma yanzu ta fimu matsayi,so an dade ba'a yi mana promotion ba,amma meyasa kike tambaya yanzu?" Nadeeya ce ta juyo ta kalleta
"Basma yanzu idan aka ce za'a qara dadewa ba'a yi miki promotion ba,shin hakan zai dameki?"
Basma cike da mamaki tace
"Wai nadeeya me yake damunki yau dinnan ne?"
Nadeeya tayi ajiyar zuciya tare da cewa
"Ina son mu tinkari director da kuma chief akan lallai san an yiwa yarinyar nan adalci,domin ba mu kadai ba,kowa ya san cewar babu adalci a cikin abinda akayi mata,idan munyi nasara shikenan,amma idan bamuyi nasara ba nasan muma zamu fuskanci hukunci,shin zaki iya sadaukar da promotion dinki domin mu taimaki shukra?" jinjina kai basma tayi domin nuna amincewarta.
Shukra har akayi ruwa aka dauke tana wajen,har tsayin dare gari ya waye,sai da safe su nadeeya sukaje domin magana da su director da chief.
A zazzaune suke,nadeeya da basma cikin girmamawa suke son su nusar da chief sumayya da director kan cewar ya kamata ayiwa shukra adalci,sumayya ta kalleta
"Waye zai ga laifin office of investigation? Bayan kuma kunsan kawai mun bi abinda doka tace ne"
Nadeeya ce ta amsa mata da
"Amma chief idan har dokar za'a bi ai ba za'a basu jarrabawar akan abinda aka koyar a cikin shekarar nan ba,sai dai ta baya,domin haka dokar jarrabawar take" director ce ta daka wa nadeeya tsawa,kafin tace wani abu sameerah ta shigo da gudu tana cewa
"My lady,ya kamata ku fito kuga me yake faruwa a waje" ba tare da dogon bayani duk suka tashi suka fito,shukra ce a kwance a qasa ta suma,sai Afrah da Aliya da suke jijjigata,taqi motsi,hakan yasa Afrah ta kalli aliya
"Aliya ki dauke ta ki kaita quaters dinmu,ni zanje in kirawo likita" ta fada tare da tashi ta tafi da gudu domin kiran likita.
Queen haneefah da take tsaye tana kallon abinda yake faruwa ta qaraso tare da maids dinta,hakan yasa director,chief sumayya,nadeyya da basma duk suka rusunar da kansu domin gaishe ta,director ce tace
"Your majesty,me ya kawo ki nan a irin wannan lokacin?" Kallon tuhuma kawai queen haneefa take binsu dashi,wucewarta tayi har cikin office dinsu,hakan yasa suka biyo bayanta,zama tayi kan kujerar director,yayinda su kuma suka zauna a sauran kujerun da suke wajen,kallonsu ta farayi da harara daya bayan daya,hakan yasa kowa ya sha jinin jikinsa
"Ban yi tunanin kama ku da laifin duk kuskuren da kukayi a baya ba,saboda a cigaba da ganin darajar ku amma har kune zaku shirya abinda kuka ga dama domin kuga kun bijirewa umarni na ko? " director ce tayi saurin cewa "your majesty,ba haka ba....."
ta fada tana qara rusunar da kanta,katseta queen haneefah tayi
"Rufe min bakinki a nan,yau nazo ne domin kama ku da dukkan kusakuren da kuka san kun taba yi,na yanzu da na baya,kuma zan hukunta ku akan haka" tsoro ne da firgici ya bayyana akan fuskokin director da chief sumayya,yayinda su nadeeya fuskar su babu yabo ba fallasa,kowa yayi shiru,queen haneefa tace
"Idan likita ya gama dubata,ta dan samu qwarin jikinta a turota quaters dina ina son ganinta,ku kuma ku jira hukunci na"
Miqewa tayi ta fita,maids dinta da suke tsaye a waje suka bita a baya suka bar wajen.
Shukra bata farka ba sai da gari yayi duhu,afrah ce a zaune a wajenta,ta bude ido a hankali ta kalli Afrah,bakinta ta bude
"My lady" afrah tayi saurin cewa
"Ya jikin naki? " shukra ce ta fara kallon inda take a kwance
"Ya akayi na ganni a nan?"
"Suma kikayi,Allah ya taimaka babu abinda ya sameki bayan haka,akwai inda ya kamata kije,zaki iya tashi?"
Gyada kai shukra tayi,afrah ta tashi ta fita,suka dawo tare da nadeeyah,domin ita queen haneefa ta dorawa alhakin kawo shukrah wajenta,suna zuwa bakin qofar quaters dinta,chief maid dinta tace shukra ta shiga,nadeeya ta jirata ta fito.
Shukra tana shiga ta rusunar da kanta sosai tare da cewa
"Na gaisheki your majesty,ni ce shukra Anas Malak" murmushi queen haneefa tayi tare da cewa
"Zo ki zauna shukra,a yadda kanta yake a durqushe ta qaraso wajen zama da yake fuskantar queen ta zauna,queen ce ta fara magana
"Naji duk abinda ya faru game da jarrabawar ku,kuma zan dauki mataki a kansu,amma kina ganin idan aka baki lokaci zaki iya cin jarrabawar? " shukra ta dago kanta ba tare da ta hada idonta dana queen ba tace
"Zan iya your majesty,idan aka qara bani dama zan ci jarrabawar da izinin Allah" murmushi queen haneefa tayi tare da cewa
"Tunda na fara jin labarin ki nake son ganinki,amma sai na ganki ma kinfi yadda na zata qanqanta" murmushi shukra tayi har sautinsa ya fito,queen ta qara cewa
"Shikenan shukra,za'a qara baki dama domin kiyi jarrabawar,amma ki tabbatar kin dage sosai domin kici jarrabawar,domin wannan karon idan kika fadi to ya zama dole ki bar office of investigation " jinjina kai shukra tayi,tare da yi mata godiya ta tashi ta fito,tare da nadeeyah suka koma office of investigation,kowa ya tafi daki ya kwanta.
Washegari da safe,dukka ladies investigators suna tsaye a wajen assembly,sun jeru akan layi,yayinda basma da chief sumayya suke saman step suma a tsaye,wata mata ce ta fito daga office din director,da green din uniform irin na director da sumayya,nadeeya ce take binta a baya,suka zo dai dai tsakiyar da director take tsayawa ta tsaya,nadeeya ce tace
"Ku gaishe da sabuwar director" hakan yasa dukkansu har su basma da sumayya suka rusunar da kansu domin gaisheta,kallonsu take daya bayan daya har tazo kan sumayya
"Lady sumayya" ta kira sunanta,sumayya ta dago ta kalleta,
"Kece wacce take kula da al'amuran administration na wannan office din ko?"
"Yea my lady" sumayya ta bata amsa
Sabuwar director ta cigaba
"Toh ba zan iya barin mutum mai son zuciya irinki ya cigaba da riqe wannan matsayin ba,saboda haka daga yau wannan alhakin ya koma kan nadeeya,zata dinga tuntubar ki akan abinda ya shige mata duhu,duk da kasancewar har yanzu kece chief ba ita ba" wani qololon baqin ciki ne ya tokare sumayya,ganin an mayar da ita mara amfani,sai dai matsayin chief din kawai,hakan zaisa yaran su raina ta ai,haka dai ta daure tare da cewa
"Yea my lady" tana ta dacin rai.
Director ce tace
"Ina yarinyar nan ta bureu of music" nadeeyah ta daga murya ta kirawo shukra
"Shukra Anas,ki fito gaba" hakan yasa shukra fitowa daga layin da take tazo gaban ta rusunar da kanta ta gaishe da director,director ce ta qara cewa
"Rukayya,kema matso nan" wata 'yar budurwa ce da bata fi sa'ar shukran ba ta fito tazo ta tsaya kusa da shukra,director ta qara cewa
"Wannan 'yar yayana ce (niece) tare muka zo da ita,ita da shukra zasu qara yin jarrabawa nan da kwana uku"
Haka dai ta faffada musu dokokin ta na aiki,da sauransu sannan kowa ya watse suka kama aiki.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤
ROYAL CONSORT
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Page 24
Mai martaba cikin fara’a yake tambayar chief eunuch
“Kace an qara bata damar yin jarrabawar?” Shima chief eunuch da murmushin ganin yadda mai martaba yake fara’a yace
“Ehh your majesty,zasuyi jarrabawar ne nan da kwana uku”
“Kwana uku? Kamar kwanakin sunyi kadan,ko yaya zatayi da karatu ita kadai?” Shi dai ya rasa meyasa yake tsananin farin ciki ko da tuna shukra yayi,shiyasa da ruwa yake dukanta yaji a jikinshi,har shima ya shiga ruwan ya dakeshi ba tare da ya san dalilin da yasa yake tsaye a cikin ruwan ba,sai daga baya da ya samu labarin yadda shukra ta kwana a bakin office of investigation,har yaje wajen queen haneefah domin ta shiga maganar,da murmushi akan fuskar sa yace
“Ina tunanin ranar da zata san ni sarki ne,kai bana son ma ta sani don nafi jin dadin zama da ita yadda ta dauke ni a haka” shi dai chief eunuch tun yanzu ya fuskanci mai martaba yana qaunar shukra ne ba tare da shi kansa ya fahimci hakan ba.
Cikin kwanakin shukra ta dage karanta littafin DOCTRINE OF THE MEAN sosai,ba dare ba rana,ana i’gobe zasuyi jarrabawar da daddare tana zaune tana ta karatu a fili,mai martaba ne yazo wajen ya dade a tsaye yana kallonta bata sani ba,daga bisani ya matso kusa da inda take,jin motsi ya sa ta dago kanta,ganin wanda yake tsaye tasa murmushi
“Yallabai kaine a nan?”
Murmushin shima yayi mata
“Ehh nine,na jiyo mutum yana karatu tsakar dare ne,ashe kece” bata fuska tayi zuwa kalar tausayi tare da cewa
“Jarrabawa zanyi gobe,kuma ina tsoro sosai ban sani ba ko zan iya ci” shima bata fuska yayi yadda tayi
“Kina tsoron ko zaki ci? Anya kuwa shukran ce? Har kika karaya haka? Ai kuwa akwai abinda nake son na fada miki saqon mai martaba ne,amma ki taso daga nan,domin akwai sanyi sosai” da sauri ta kalleshi
“Saqon mai martaba kuma? Me yace ka fada min?”
“Ki taho mu bar nan tukunna sai na fada miki” haka ta bishi a baya suna tafiya har cikin wani library mai shegen kyau,tsarin komai a ciki ma abin kallo ne,baki bude shukra ta kalleshi
“Yallabai nan din ina ne ka kawo mu?”
Murmushi yayi
“Nan royal library ne” hannu tasa tare da rufe bakinta cike da tsoro tace
“Amma yallabai,nan fa wajen karatun sarki ne da ahalinsa kadai,idan wani ya ganmu fah?” Dariya sosai ta bashi yanayin yadda tayi maganar,sai da yayi dariyarsa mai isar sa
“Kada ki damu,yau ai night duty nake anan shiyasa babu mai zuwa” da sauri ta tare shi
“Amma ya za’ayi dan sandan sirri yayi night duty a cikin palace?” Diriricewa yayi ya rasa me zai ce mata,da qyar ya lalubo abin fada
“Ai da yake ni shugaba ne shiyasa kullun ni nake night duty a nan” jinjina kai shukra tayi
“Au hooo amma ban taba tunanin ana haka ba” gudun kada ta qara jefo masa wata tambayar yasa yayi saurin cewa
“Maza ki zauna kiyi karatunki a nan cikin nutsuwa kuma kinga nan babu sanyi” gyada kai kawai tayi tare da zama a kujerar da ya nuna mata,shima zama yayi a wata kujerar tare da ce mata
“Kika ce kina tsoron ko zaki iya cin jarrabawar? Gashi kuma mai martaba ya fada min yana da tabbaci da qwarin gwiwar zaki ci” zare ido tayi tana kallonshi
“Mai martaban ne yace haka?”
Jinjina kai yayi
“Qwarai kuwa,da kanshi ya fada min haka,kinga kuwa idan yaji kin karaya tun yanzu ai ba zai ji dadi ba,kuma zaki bashi kunya” jinjina kai tayi tare da cewa
“Kuma haka ne fa,da gaskiyar ka yallabai,zan dage sosai naci jarrabawar nan ko don kada na bawa mai martaba kunya” murmushin jin dadin maganar ta yayi tare da cewa
“Yauwa haka nake son ji” janyo littafin nata yayi
“Kinga haddace duka littafin DOCTRINE OF THE MEAN ba zai yiwu a cikin kwanakin nan da kika yi ba,bari in duba miki wasu wuraren da zaki haddace da daddaren nan,ki dai tabbatar kin iya sosai don wata qila su iya zama tambayoyin jarrabawar “ jinjina kai tayi tare da cewa
“Amma ni fa nayi karatu sosai,kawai dai bani da wanda zan karantawa yaji ko nayi daidai shiyasa nake jin kamar karatun bai zauna ba,amma kawo na gani” haka ya ajiye littafin yadda itama zata dinga ganin inda yake nuna mata,ya nuna mata wurare kusan guda shida a take ta haddace su yace ta karanto masa yaji,haka ta karanto masa har asuba suna wajen suna karatu cikin nishadi da farin ciki,daidai kiran sallar asuba ya tashi suka fito,ta wuce office of investigation shi kuma ya wuce grand palace.
Bayan gari ya waye,kowa ya hallara a wajen jarrabawa,gaba daya ladies investigators din suna wajen,yadda akayi waccan haka aka tsara wannan,su biyu ne akan benchin shukra da ruqayya,takaddun da aka rubuta abinda zasu karanta aka ajiye musu a gabansu,nadeeya ce tayi saurin cewa
“Rukayya ta fara” hakan yasa ruqayya ta miqa hannu ta dauki takaddar ta bude,a hankali ta fara karantowa,abinda yake cikin takaddar take ta maimaitawa kusan sau hudu,sai da nadeeya tace
“Ki cigaba ki karanto har qarshe sannan kuma kiyi bayanin ma’anar sa” gyada kai ruqayya tayi cikin sanyin jiki ta fara cigaban kamar bata da tabbacin ko daidai take yi ko ba daidai ba,haka dai ta kai har qarshe ta gama,nadeeya tace
“Ruqayya - pass” ta kalli shukra
“Saura ke” hannu shukra ta miqa ta dauki takaddar,tana budewa mamaki ya cika ta,murmushi ne a kwance a kan fuskarta tare da sa tafin hannunta ta rufe bakin ta cikin tsananin farin ciki,a ranta tace
“Wannan yana cikin wanda yallabai yasa na haddace jiya” bata gama maganar a ranta ba taji muryar nadeeya
“Zaki iya karantawa?” Nadeeeya ta tambayeta cikin tausasawa,da sauri shukra ta daga kanta sama,tare da sauke ajiyar zuciya,a nutse ta fara karantowa cikin qwarin gwiwa da murmushin farin ciki har qarshe ta dire tare da bayani,mamaki ne fal akan fuskar chief sumayya da kuma baqin cikin ba haka taso ba,yayinda nadeeya da basma suma mamakin suke amma cike da farin ciki,nadeeya tace
“Shukra - pass” jin haka yasa shukra jin dadi matuqa,a nan take maganar yallabai dinta ta fado mata,a hankali tace
“Yanzu na san yallabai zaiyi alfahari dani domin ban bawa mai martaba kunya ba”
Yayinda labari ya isa kunnen su sameer da manager suma murna suka taya shukra sosai,hakan yasa da daddare suka fita cikin gari domin su sha shayi su dan sha iska,daga nan suka wuce gidan sameer,cikin dakin abdullahi sameer yaja manager,suna shiga manager ya bi dakin da kallo,daga bisani yabi sameer da kallon tambaya,sameer ne yayi saurin cewa
“Yallabai tunda mutumin nan yazo gidannan a tsorace nake da shi,da farko na zata wawa ne,amma ganin dukan da yayiwa wasu mutane da suka biyo yallabai jaleel hakan ya bani tsoro sosai,kuma da alamu akwai wani abu da yake boyewa baya son a sani game da shi” manager ne ya dungure masa kai tare da cewa
“Idan har kana jin tsoron shi haka,ai sai ka koreshi daga gidanka kawai,tunda ba tare kuka gina gidan ba” zaro ido sameer yayi tare da cewa
“Ai gara na zauna lapia da shi,wata qila idan ma mugun ne ai ya sarara min tunda zaman lafiya mukeyi dashi” ya fada kamar zaiyi kuka,manager dai bai qara ce masa komai ba,ganin haka sameer ya fara bincike bincike a dakin yana cewa
“Bari kaga in dudduba ko zan samu makami,kada wata rana ina kwance da daddare ya kawo min hari” dariya sosai manager yake masa,ganin yadda ya haqiqance yana duba kayan mutum bayan baya nan,sai da ya gama dubawa tsaf sannan ya juyo ya kalli manager
“Kaga ni dai ban samu wani makami ba amma dai hankalina yaqi kwanciya” jijjiga kai manager yayi tare da juyawa zai fita daga dakin don ba zai iya zama ganin shashancin sameer ba,har yaje bakin qofa sameer yace
“Yallabai kaga” juyowa yayi don yaga mai sameer yake nuna masa,wani farin yadi ne an daure shi da zaren kaba,matsowa ya fara yi don shima ya dan tsorata da abin,da sauri sameer ya fara kwancewa,wani siririn yadi ne ya bayyana kamar dankwali da mazan garin suke daurawa a kai amma baya rufe tsakiyar kai gaba daya,wani irin zane ne a jiki kamar LOGO a jiki daidai inda ake daurawa a goshi,zanen yayi kama da lauje guda biyu,da aka hade su ta tsakiya,sameer ne yayi saurin cewa
“Ka gani ko yallabai? Wannan zanen yayi min kama da abin marasa gaskiya,daga gani wannan mutumin dan wata muguwar qungiyar ne” jinjina kai manager yayi tare da cewa
“Haka ne fa,da gaskiyar ka,yanzu yaya zamuyi mu gane me wannan abin yake nufi?” Sameer ne yayi saurin cewa
“Wajen shukra zamu tafi,tunda ita yanzu lady investigator ce,hakan ba zai yi mata wuyar bincikowa ba” manager yace “haka ne,sai ka ajiye,gobe da safe ka kai mata” hakan kuwa akayi,suka gyarawa abdullahi dakinshi tsaf tamkar dai yadda suka shigo suka tarar da shi sannan suka fita suka koma bureu of music don ba a gida zai kwana ba.
Washegari da safe,a office dinsu shukra dukkansu ne a tsatstsaye kowa da abinda yakeyi,sameerah ce ta kalli shukra
“Shukra ko zaki duba wadannan litattafan sai ki jera su a tsari ki mayar inda suke?” Cikin murna shukra tace “Ehh zan iya,bari nayi” nan da nan ta fara dudduba littattafan domin hada su ta ajiye a ma’ajiyar su,daya bayan daya suka fara fita daga wajen har ya kasance daga ita sai Afrah a tsaye a wajen,shukra ce ta juya ta kalli inda afrah take
“Kingani ko? Yanzu sun fara yi min magana,har ma aiki suka fara sani in taya su” ta fada cikin farin ciki kamar wani abin arziqi aka sata tayi,afrah ce ta kalleta ta gefen ido tare da cewa
“Toh yanzu ke murnar me kike? Kawai don ance ki mayar da littattafan da ba ke kikai amfani dasu ba? ai hakan raini ne ba girmamawa ba,meyasa basu mayar da kansu ba?” Shukra ita dai hakan bai dameta ba,sai ma zancen da ta sauya
“Yauwah my lady naga kowa ya fita yana shiri,yau me akeyi a nan ne?” Afrah da take karanta wani littafi,ba tare da ta kalli shukra ba ta bata amsa
“Yau ‘yan police bureu da tribunal zasu zo domin yi mana training akan investigation (bincike) ne,shiyasa kowa yake shiri domin yau samari masu ji da kansu da kuma matsayi zasu zo” murmushi shukra tayi daidai lokacin da ta gama jera littattafan,kafin tace wani abu afrah ta ajiye littafin dake hannunta ta fice,hakan yasa itama ta bar wajen,quaters din su suka koma inda taga dukkan ‘yan matan suna gaban mudubi,suna kwalliya,masu sa powder nayi,masu sa lip gloss ma nayi domin babu jambaki mai kala a tsarinsu,ita abinma mamaki ya fara bata yadda taga kowa yana ta gyare gyaren jiki don samari zasu shigo office dinsu,nadeeyah ce da basma cikin uniform dinsu suma sun fito daga daki,suka ci karo da ‘yan matan kowa tana kwalliya,nadeeya ce tayi saurin cewa
“Kalli abinda yaran can sukeyi,bari naje…..” kafin ta qarasa basma ta katse ta
“Haba ke kuwa,ki qyale su mana,ba’a barin su suyi kwalliya lokacin aiki ,amma yanzu tunda training ne,ki qyale su mana” ta fada tana murmushi,kallonta nadeeya ta tsaya yi,kafin tayi murmushi
“Ai kyace a qyale su tunda kema ai kin shafa powder ko?” Zaro ido basma tayi tare da jin kunya,tace
“Toh ai kinsan IG din police zai zo ko? “ dariya sukasa gaba dayansu tare da barin wajen.
Gida biyu aka raba ‘yan matan,kowa da inda zasuyi training din,’yan tribunal zasu koyar da rabi yayinda ‘yan police bureu zasu koyar da rabi,a cikin ‘yan police bureu da aka taho office of investigation har da abdullahi domin zasuyi topic din binciken gawa ne,saboda haka zai taimakawa IG don ganin sun fahimci darasin sosai,yayinda ‘yan tribunal kuma jameel ne dan gidan tribunal minister wato mariqin lady jaleela,da wani abokinshi suka je,shukra ta kasance a bangaren wanda zasu dauki darasin ‘yan tribunal,yayinda afrah kuma take cikin wadanda zasu dauki darasin ‘yan police bureu,hakan yasa shukra basu hadu da sabon mai binciken gawa ba wato abdullahi,amma su afrah sun ganshi.
Bayan an gama training dinne,su sameer suka nemi ganin shukra,a bureu of music taje ta samesu,suna hangota tana tahowa sameer yace da qarfi
“Gaskiya uniform din ladies investigators yayi miki kyau sosai my lady” yana murmushi,itama murmushin ta mayar masa daidai lokacin da ta qaraso gabansu tare da gaishesu,sameer ne yayi saurin ce mata
“Shukra wani taimako nake nema a wajenki domin ke kadai ce zaki iya yi min shi” cikin damuwa shukra tace
“Wane irin taimako ne wannan yallabai?” Abin da ya dauko a dakin abdullahi ya ciro a aljihun shi ya riqe a hannunsa tare da cewa
“Akwai wani sabon mai binciken gawa a police bureu da yake haya a gidana,to naga kamar alamun rashin gaskiya a tare da shi,shine na kawo miki wannan ko zaki bincika min me hakan yake nufi” ya qarasa tare da miqo mata abin,da sauri shukra ta karba tare da zare ido tana kallon logo din da yake jikin abin,cikin razani ta dago ta kalli sameer “kace sabon mai binciken a police bureu?” daga kai sameer yayi,alamar “Ehh” kafin ya bude baki yayi mata qarin bayani shukra ta fella da gudu ta bar wajen,qwala mata kira suka fara yi,amma inaa tayi nisa.
Police bureu ta nufa kai tsaye,da yake akwai uniform a jikinta shiyasa babu wanda ya hana ta shiga,daga ganinta tana cikin tashin hankali,wani security ta tsayar tare da tambayar shi
“Dn Allah sabon mai binciken gawar da aka dauka aiki a wajen nan nake nema” kafin ya bata amsa sai da ya rusunar da kanshi alamun girmamawa sanadin kayan da ya gani a jikinta,sannan yace
“Abdullahi kike nufi,Baya nan my lady,sun fita shi da IG har yanzu basu dawo ba amma ina tsammanin sun biya wani wajen ne” da sauri ta kalle shi sosai tare da cewa
“Sunanshi abdullahi?” Jinjina kai yayi tare da cewa
“Ehh abdullahi sulaiman sunanshi,amma meyasa kike nemanshi my lady?” Ai daga inda yace sunanshi abdullahi sulaiman shukra bata qara jin komai ba,don gaba daya hankalinta baya jikinta,ganin ba zata qara kulashi ba yasa yayi gaba abinshi,yayinda ita kuma tana tsaye ta kafe idonta waje daya qwalla na zubo mata wanda da alamu bata san suna zuba ba.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤
ROYAL CONSORT
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Page 25
Har dare sameer da manager suna nemanta amma basu ganta ba,hakan yasa sameer dawowa gida kuma har lokacin abdullahi bai dawo ba,yana tsaye yana ta kai-kawo a tsakar gidan yaji shigowar abdullahi,turus yayi ganin sameer a gidan,sameer ne yace masa
“Yau baka dawo da wuri ba,lapia kuwa?”
“Lafiya qalau,na biya wani waje ne” abdullahi ya bashi amsa
“Toh sai ka shiga ka kwanta”
“Toh yallabai” abdullahi ya fada tare da shiga dakinsa,yana shiga ya fara bin dakin da kallo ya san an taba masa kaya,hakan yasa ya duba abinda yake tunanin shi za’a dauka kuwa yaga baya nan,fitowa yayi ya murde hannun sameer ta baya tare da cewa
“Ina headband dina? Me kayi dashi?” Cikin jin zafin yadda abdullahi ya murde masa hannu ta baya yace
“Kayi haquri dauka nayi na bawa wata lady investigator saboda ban yadda da logo din da yake jiki ba” da sauri abdullahi yace
“Lady investigator kuma?”
“Ehh kamar qanwa take a wajena,amma ina bata ta gane LOGO din da yake jiki ta fella da gudu ta tafi nemanka kuma har yanzu ban ganta ba” jin haka da sauri ya saki hannun sameer ya juyo daidai fuskarsa tare da cewa
“Kace ta gane LOGO din da yake jiki?” Gyada kai sameer yayi
“Ehh shukra ta gane logo din” jikin abdullahi ne gaba daya yayi sanyi,da qyar yace wa sameer
“Kace sunanta shukra?”
Gyada kai sameer ya qara yi
“Ehh sunanta kenan,shukra Anas malak”
Qwalla ce kawai ta cicciko a idon abdullahi,yacewa sameer
“Taho muje ka kaini cikin palace din,ni zan nemo ta”
Suna zuwa cikin palace,bureu of music suka fara zuwa,manager ya shaida musu yanzu shukra ta bar nan kuma ta tafi gidansu ne nemanshi,hakan yasa suka qara juyowa suka dawo.
Da zuwanta ta tarar babu kowa a gidan,tana ta bude bude,ta shiga nan ta shiga can,tsayawa tayi tana tunani
*FLASHBACK*
tana yarinya qarama suna tsaye da abdullahi a tashar jirgin ruwa da je garin,irin headband din da sameer ya samo a dakin abdullahi ne a hannunsa yana nunawa shukra
“Shukriyya,kada ki manta da wannan zanen (logo) domin matuqar dai kina tare da wannan abin to komai dadewa zan dawo gareki” gyada kai tayi tare da cewa
“Ba zan manta da hakan ba,amma kwana nawa zakayi ka dawo?” Murmushin jin tausayinta abdullahi yayi tare da cewa
“Duk dadewar da zanyi,nayi miki alqawarin zan dawo gareki,ki kula da kanki”
Motsin da taji ne ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi,juyowar da zata yi suka hada ido da abdullahi,hannunta ne ya saki kamar babu jini a jikinta ta daskare a tsaye a wajen,matsowa yake yi kusa da ita yana cewa
“Shukriyya,Ke ce? Shukriyya” hawayen farin ciki ne kawai ya lullube fuskar ta,sheshsheqar kuka ta fara,hakan yasa yayi saurin qarasowa gareta tare da rungumeta sosai a jikinsa,a hankali ta bude bakinta tare da cewa
“Orabeuni” (Babban yaya in korean)
Dagota yayi daga jikinshi yana kallon fuskarta tare da cewa
“Qara fada shukra,ni ne” hawayen bai daina zuba a idonta ba tace
“Dama kana raye? Zaka dawo gareni Yaya Abdallah?”
“Ina nan Shukriyya,dama na fada miki duk dadewar da zanyi nayi miki alqawarin zan dawo gareki”
Tuni suka manta da sameer a wajen,hakan yasa shima ya basu waje,nan gaba ya nemi qarin bayanin alaqar da ke tsakaninsu,waje suka samu suka zauna,shukra da har yanzu da hawaye a fuskarta tace
“Yaya duk lokacin da zanyi wa su Abbana addu’ah ina hadawa hadda kai domin ban taba tunanin kana nan a raye ba,na zata ni kadai ce na rage bani da sauran dangi a duniya” murmushi yayi mata shima da hawaye a fuskarshi tare da cewa
“Na dade ina nemanki shukra,amma ban sameki ba,duk cikin garin nan babu inda ban zagaya ba amma ban sameki ba”
Shiru shukra tayi ba tare da tace komai ba,abdullahi yana mata kallon tsanaki ganin yadda ta girma,tare kuma da farin cikin qara ganin qanwar tasa,jan hanci tayi da ya taru da majina
“Yaya kullun ina tunaninku,da Abba da yaya Abdulshakur,ina ma ace zan qara jin muryoyinsu suna kirana shukriyya?” Tausayinta ne ya lullube shi,dafa kafadarta yayi
“Shukriyya Abba zai yi matuqar farin ciki a duk inda yake domin kema kina cikin farin ciki,kuma nayi masa alqawarin zan kula dake,zan zame miki garkuwa” haka suka yini tare,da yake tunda zata shigo cikin gari ta cire uniform dinta ta skaa normal kaya,hakan yasa babu mai ganeta suka cigaba da zama a cikin gidan tare da hirar yaushe gamo har dare,a nan ta kwana sai da asuba ta koma office of investigation.
A office of investigation Aliya ce take ta hargagi akan bata ga shukra ba,kuma ga aiki sunayi yayi musu yawa,da yake dakinsu daya,sai masifa takeyi kamar zata ari baki,sameerah ce tace
“Dama matsalar ‘yan alfarmar nan kenan,ko ina ta tafi ma?”
Aliya ce tayi saurin cewa
“Rabu da ita,zata dawo ta sameni ne” ta gama fada cikin masifar da take yi ta bar wajen.
Rukayya da yake itama sabuwa ce masifar da Aliya tayi ya bata tsoro sosai,tace wa sameerah
“Wai meyasa take wannan fadan haka?”
Da sauri tace mata
“Ke baki san Aliya ba ko? Ai ita ce mai qarfi kuma ‘yar ta’addar Office of investigation” dariya sauran da suke wajen suka saka,don kuwa yadda take masifar nan ai tayi kama da’yar ta’addar.
IG na police ne a tsaye a gaban mai martaba,da damuwa a fuskar mai martaba yake tambayar sa
“Kace akwai wanda kuke zargi a cikin baqin da zasuzo daga china?”
“Ehh your majesty,dan asalin garin nan ne,amma an bashi matsayi babba a china,hakan yasa yake taimaka musu wajen shigowa da makamai cikin qasar mu,da kuma fita da abubuwan mu masu muhimmanci ta barauniyar hanya,sunanshi KiIM YOUNG DAL” jinjina kai mai martaba yayi bayan jin bayanin IG
“Yanzu me kake ganin ya kamata muyi?”
Gyara tsayuwarsa yayi,sannan ya cigaba da bayani
“A baya mun fara bincikarsa cikin sirri kuma mun tabbatar yana aikata hakan,sai dai bamu da bayyanannuyar hujja,shiyasa wannan karon idan suka qaraso zamuyi aiki tare da office of investigation da kuma tribunal domin samun hujja akan shi da ma sauran masu hannu a ciki” jinjina kai mai martaba yayi
“Hakan yayi,sai ku fara shiri kuma ku tabbatar ba’a samu wata matsala ba”
A office of investigation kuwa sun taru a wajen da suke assembly na safe,Sameerah ce cikin farin ciki take cewa
“Yanzu mune zamu shiga quaters din baqin nan a matsayin maids dinsu kenan?” Aliya ce ta cafe zancen
“Ehh mana,a haka zamu gane duk wani motsin su,kuma mu samo hujjar da ake nema ba tare da sun san mu investigators bane” shukra da take sauraronsu ta kalli Afrah tare da cewa
“Ni dai ban sa rai ba gaskiya,ko ya kika gani?” Murmushi kawai afrah tayi mata ba tare da ce mata komai ba,suna haka su nadeeyah da basma suka fito daga office din director,hakan yasa duk suka nutsu,basma ce ta bude takaddar da take hannunta tare da cewa
“Kowa ya saurara,duk wacce taji sunanta ta fito gaba” Aliya ce ta kalli shukra tare da cewa
“Ai naji kina tambaya,to kada ki ma sa rai,don an fi son masu qwazo da qoqari sosai,kinsan kaf cikinmu daga Afrah a qoqari sai ni”
Basma ta kira sunan Afrah,sameerah,sai wasu guda biyar,duk suka fito,a qarshe tace
“Sai kuma ta qarshe…” Aliya ce ta yi ready din fitowa,tana murmushi kawai taji basma tace
“Shukra” murmushi shukra tayi tare da murna ta kalli afrah da ta qaraso inda suke
“Kinga ni ko? Sunana ta kira” murmushi afrah tayi tare da cewa
“Ina miki murna shukra”
Tare suka yi dariya har sautin ta ya fito,yayinda aliya ta cika tayi fam,da sauri ta tafi zuwa office don ganin basma
“Yanzu my lady ya za’a yi min haka,a zabi shukra a kaina,bayan kaf cikinmu daga afrah sai ni a qoqari?” Bata fuska basma tayi
“Ai ba qoqari muka duba ba”
“Ba qoqari kuka duba ba,to me kuka duba kenan?” Aliya tayi tambayar
“Ehh mun duba kyawun fuska ne” basma ta bata amsa
“Kyawun fuska my lady?” Aliya ta fada tare da bata rai sosai,jinjina kai tayi ta juya ta fita ba tare da qara cewa basma komai ba.
‘Yan matan sun shirya tsaf cikin uniform din ladies-in-waiting (maids din da suke yiwa mutanen masarautar hidima ta yau da kullum,kuma suke binsu a baya duk inda zasu je) shigen irin uniform dinsu ne amma wannan farar riga ce a ciki mai dogon hannu,sai ta sama mara hannu light blue,sai ratsin dark blue a wuyan rigar,sunyi kyau sosai,nadeeya ce ta dauko wani qaramin madubi ta miqawa shukra
“Karbi wannan mudubin,shine abinda muke magana da junan mu idan muna aiki cikin badda kama,afrah zata yi miki bayanin yadda abin yake” karba shukra tayi tare da rusunar da kanta tayi godiya,basma ce tayi musu sauran bayanai tare da basu damar zuwa domin tarbar baqinsu.
A gidan minister na tribunal jaleel ne shi da mutumin da suka zo daga china wanda ake zargin yana harkar safara ba bisa qa’ida ba,kuma ake neman hujja a kan shi,jaleel ne ya fara shiga wajen minister,sukayi gaisuwa kafin daga bisani jaleel yace
“Ranka ya dade na kawo maka wata harka ne mai gwabi,kuma akwai qaruwa sosai a cikin ta”
“Wannan wace irin harka ce jaleel? Kasan bana son shashancin nan naka” girgiza kai jaleel yayi tare da cewa
“Idan kaga wanda nake tare da shi zaka fahimci yau ba shashancin ne ya kawo ni ba” kafin minister yace wani abu jaleel ya dan daga murya tare da cewa
“Zaka iya shigowa” Kim Dal ne ya shigo kanshi sanye da hula malafa da ba’a iya gane fuskar shi,zama yazo yayi kusa da jaleel,ya rusunar da kan shi alamun gaisuwa ga minister,jaleel ne ya fara bayani
“Wannan shine Kim Dal,kasan kusan duk kudin da zai fita daga qasar nan domin kasuwanci da china yana shiga kuma ya fita ne ta hannun sa,kuma yana da niyyar bamu wani abu daga cikin ribar da yake samu domin qarfafa hakiman kudu,hakan kuma zai qarfafa ikon lady jalila”
Jinjina kai minister yayi
“Amma jaleel baka ganin harkar nan akwai kasada kuwa? Idan aka samu hujja a kanmu zamu shiga uku a qasar nan tare da tsatstsauran hukunci “
Dariya jaleel yayi
“Haba ranka ya dade,Wannan mutumin fa ya dade yana harkar nan,kuma babu wata matsala,kuma kaga tunda kaine mai masaukin baqin china da suka zo tare da shi ai komai zai tafi daidai” jinjina kai minister yayi cike da gamsuwa da abinda jaleel yazo dashi,sai yanzu Kim Dal yayi magana
“Amma yallabai,wani hanzari ba gudu ba,ladies in waiting da aka kai mana,ina zargin akwai wani abin rashin gaskiya a tattare dasu” kallon tsanaki minister yayi masa
“Gaskiyane,wadannan yaran ladies investigators ne,kuma sunje neman hujja a kan ka ne,kuma suna aiki ne tare da tribunal da police bureu,amma tunda yaron wajena jameel shine director na tribunal,zamu shirya yadda binciken su ba zaiyi wani tasiri ba” cike da gamsuwa kim Dal da jaleel sukayiwa minister godiya suka tafi.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤
ROYAL CONSORT
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Page 26
Afrah ce tsaye itada shukra a bayan dakin baqin,cikin qaramar murya afrah ta miqowa shukra wata takadda
“Karbi wannan shukra,maganganunsu ne kiyi maza ki kaiwa lady nadeeya,ko za’a samu wani abu mai muhimmanci a ciki” karbar takaddar shukra tayi z
“Amma afrah kina jin yaren chineese ne har kika iya fahimtar maganganun su?” Murmushi tayi mata tare da cewa
“Ina ji kadan kadan” sallama sukayi,shukra ta tafi office of investigation kai saqon takaddar.
Washegari da safe dukkan baqin da akayi suka tafi gaisawa da mai martaba domin cin abinci na musamman,hakan ne ya bawa su shukra damar bincike a cikin dakunan da aka sauke baqin,babu wanda ya samo komai,sai shukra da ta samu wani rubutun kalmomin chineese a wata siririyar takadda kuma anyi rubutun ne a tsaye,yayinda fadin taddar zai iya daukan kalma daya ne kawai tak,Zuwa tayi ta nuna wa afrah,afrah ta karanta da yake tana fahimtar yaren chineese amma babu ma’ana,kawai wani surkullen rubutu ne mara ma’ana,hakan yasa sukayi shawara da shukra akan ta mayar da takaddar domin bata da amfani,hakan kuwa akayi ta mayar ta ajiye a inda ta dauko.
A ranar bayan baqi sun dawo daga wajen mai martaba ne kawai suka tara ‘yan matan tare da bincike quaters dinsu tas,mudubi suka samu ‘yan qanana a cikin kayan kowaccen su,hakan ya tabbatar musu da cewar investigators ne,nan da nan labari ya cika masarautar cewar an aikawa baqin sarkin china investigators saboda ba’a yadda dasu ba,kuma matuqar maganar taje kunnen sarkin china toh qasar JOSHUN zata ahiga cikin tashin hankali,domin qasar tana qarqashin mulkin mallakar china ne,abubuwa da dama basa yiwuwa sai da sahalewar
Masarautar china,haka kuma suna da damar sauke ko dora wanda suka ga dama akan mulki,hakan yasa ake yi musu biyayya sosai.
Da labari yaje wajen IG da hanzari ya taho zuwa quaters din masaukin baqi,jameel ya tarar a wajen wanda shine director na tribunal,cikin tashin hankali yake tambayar jameel
“Ya akayi suka gane yaran nan? Kuma wane hali yaran suke ciki?” Jameel cikin halin ko in kula yace
“A halin yanzu bamu da tabbacin komai” takowa IG ya fara yi domin shiga wajen,jameel ya tare shi
“Kasan idan wakilin sarkin china ya san cewar ana binciken nan ne tare da police bureu da kuma tribunal to tashin hankalin da qasar nan zata shiga sai yafi na yanzu,domin yanzu Office of investigation kawai aka sani a cikin lamarin nan,to shigar mu ba zai haifar da da mai ido ba” lura da cewar maganar jameel gaskiya ce,yasa IG dakatawa daga shiga wajen,juyawa yayi domin zuwa wajen mai martaba,wata qila su samu mafita.
Washegari da safe,su nadeeya suna office suna alhini tare da tunanin halin da yaransu suke ciki,suka ga shigowar su shukra,su 8 reras ‘yan china sun sako su,domin a cewar su ba zasu hukunta yaran ba,kawai dai zasu koma garinsu ne a ranar ba tare da sun gama abinda ya kawo su ba,domin dama a qa’ida duk shekara suke zuwa masarautun da suke qarqashin ikonsu domin qarfafa alaqa da kuma tattauna cigaba,hakan ne ya tayar wa mai martaba hankali matuqa domin hakan zai bada matsala a tattalin arziqin qasar,hakan yasa ya shirya tsaf domin zuwa har inda suke a quaters dinsu ya samesu,ya amsa laifin da sukayi kuma ya basu haquri,tare da umartar ‘yan bureu of music da su shirya domin zuwa nishadantar da baqin tare da mai martaba.
A yayinda a office of investigation kowa yake alhinin abinda ya faru dasu,domin binciken ya lalace kenan,kuma ba za’a samu abinda ake so ba tunda an riga an gano su,shukra kuwa babu abinda yake ranta sai wannan takardar da ta gani,ita dai zuciyarta tana ta bata cewar akwai wani abu mai muhimmanci ga bincikensu a cikin takaddar,amma kuma rubutun sam bashi da ma’ana,tana zaune ita kadai tana tunani,kawai wani tunanin ya fado mata,da gudu ta tashi ta nufi police bureu wajen abdullahi,tana shiga da gudu taci sa’a kuwa dab da yana fitowa daga office din lieutenant,hakan ya sa ya jawo ta zuwa office din da suke zama,cikin nutsuwa shukra tayi masa bayanin abinda ta gani,sai da ta gama bayaninta tsaf,sannan yace mata
“Tsaya mu gani” tashi yayi yaje ya dauko takadda,ya yanka ta a tsaye sannan ya dauko wani dogon katako mulmulalle ya nade takaddar a jiki,iya inda ya nado ta gabanshi ya dauko brush din rubutu tare da fara rubutu daki daki,daga sama zuwa qasa,duk layi daya kalma daya,sai da ya gama tsaf sannan ya warware,sai ya kasance rubutun akwai space sosai tsakanin kalma da kalma,sai kawai ya cike space din da duk kalmar da tazo masa kansa,sai da ya hama tsaf ya daga takaddar ya nunawa shukra
“Kamar haka takaddar take?” Saurin daga kai shukra tayi
“Sak kuwa yayana,sak haka take,shin me hakan yake nufi?”
Mulmulallen katakon ya dauko,ya qara nade takaddar a jiki tare da cewa
“Kina ganin wannan katakon ko? To dashi kadai ake iya karanta irin wannan wasiqar sirrin,kinga idan kika nada gaba,kika nadoshi ta baya,tunda takaddar siririya ce,zata nannade gaba daya a jikin katakon ne,to idan kika gama,zaki ga kalmomin da suka bayyana a gaba,ki bar na bayan katakon,idan kika karanta zakiga sun bada ma’ana” ai shukra sosai ta fahimta,ba tare da ta tsaya yi masa bayani ba ta fita da gudu,direct ta wuce bureu of music,manager ta samu tare da roqonshi ya barta taje tare da su,tunda mai martaba ya gayyacesu,zatayi shiga kamar yadda take baiwa a da,domin akwai abinda ya kamata tayi,kuma babu hanyar da zata iya shiga wajen sai da taimakon shi
“Abin da kamar wuya shukra,me zai hana kije ki sanar da manyanki a office of investigation?” Manager ya tambayeta
“Haba manager,masifar da suke ciki ma,da muka zama silar lalacewar binciken nan ai ta isa haka,babu wanda zai qara kasada da rayuwarsa da matsayinsa akan abinda bani da tabbas akai,nu dai ka taimaka min ka shiga dani” shukra tayi masa bayani game da qara roqonsa,
da qyar ta samu ya yadda zai tafi da ita amma sai tayi taka tsan tsan,don yasan ko bai barta ta bishi ba sai ta samo wata hanyar da zata shiga,don yasan irin karambanin ta kuma idan ta sa abu a gaba to tabbas sai taga qarshen shi.
Shukra ta shiga masaukin baqi tare da su manager da sameer da sauran mawaqa na bureu of music cikin shiga irin ta bayi wacce ta saba yi a da kafin ta zama palace maid,kuma har ta samu nasarar shiga dakin da ta dauki takaddar wancan karon,wani mai kida ne na bureu of music da yaga lokacin da suka wuce shi kuma yana tsaye,yake cewa na kusa dashi
“Kalli waccar yarinyar kamar shukra fah”
Juyawa dayan yayi
“Ya za’ayi kaga shukra anan? Bayan yanzu investigator ce?” Dayan ya bashi amsa
Kallon bayanta suke sosai da yake sun riga sun danyi nisa,wanda ya fara ganin nata yace
“Ka san ni na dade ina son yarinyar nan,ba yadda za’ayi na kasa ganeta ko da kuwa wane irin kaya tasa,kuma ka duba ka gani ai babu mace ko daya a servants din bureu if music sai ita kadai” jinjina kai dayan yayi tare da cewa
“Gaskiyane,ai itace ma,toh amma me zai kawo ta nan bayan ita lady investigator ce? Kuma cikin kayan bayi?” Wani dan china da ya kasance a cikin baqin da ya dade a bayansu yana jin abinda suke fada ya matso gabansu tare da cewa
“Kuka ce kunga lady investigator a cikin kayan bayi ta shigo nan?” Diriricewa sukayi,suka tambayeshi a tare
“Shin kana jin yaren korea ne? Har kaji me muke fada?” Bai amsa musu ba yayi maza ya hada kan sojojin su ya basu umarnin su shiga bangaren dakin baccinsu su kamo yarinyar da take ciki,kasancewar wakilin sarkin china da sukayiwa rakiya yana tare da mai martaba acan dakin ganawa da baqi na cikin quaters din,shukra tana can tana ta bincike bincike bata san me yake faruwa ba,littafin elementary learning da ta samu takkadar a ciki ne a hannunta ta jiyo daga waje ana cewa
“Ku shiga ku bincika ko ina ku kamo yarinyar nan” jin haka ta hanzarta ta bubbude littafin tare da daukar takaddar,ta nannade skirt dinta ta fara gudu,hangota sukayi tana gudu nan da nan suka bita a baya,gudu take tayi daga gani ta qware a gudun,ta shiga can ta fita can ba tare da tasan inda take shiga ba,suna ta binta a baya har ta bullo wani fili,royal guards ne gaba daya birjik a wajen,sun jeru a qame kamar basu taba motsi ba,yayinda mai martaba yake fitowa daga dakin ganawa da baqin tare da wakilin sarkin china ya rako shi,shukra tana shigowa ta tsaya qarewa wajen kallo domin ganin sojojin mai martaba ta tabbatar sarki yana wajen nan,idonta ne ya sauka akan mai martaba,ai da sauri ta qarasa wajenshi ta tsaya a gabanshi tare da cewa
“Yallabai me kake anan wajen? Gara da na ganka,ka taimaka min wasu mutane ne suka biyo ni” ganin baice mata komai ba,kuma ya dake ganin jama’ar da suke wajen,wani royal guard ne ya yanquro zai kama shukra,chief eunuch ya dakatar dashi kasancewar ya san wacece shukra,mai martaba ma yayi masa alama da hannu akan kada ya taba ta,matsawa yayi tare da rusunar da kanshi yace
“Yea your majesty “ jin abinda ya fada yasa shukra a gigice ta kalli mai martaba tare da cewa
“Me yasa ya kiraka Your majesty?” Matsawa tayi da sauri daga gabanshi ta qare masa kallo tas,sai lokacin ta lura da dragon 🐉 robe din da yake jikinsa,a ranta tace
“Lallai sarki ne kawai yake sa dragon robe kuma kalar maroon” kafin ta gama tunani sojojin china suka shigo wajen
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤
ROYAL CONSORT
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Page 27
Tsayawa tayi tana qara bin ko ina da kallo,a hankali hankalinta ya dawo kan royal guards da suke tsaye a wajen,wannan ma wani qarin tabbacin ne,royal guard din da yake kusa da maimartaba ne ya bawa sauran umarni
“Ku kama wannan yarinyar,zata iya cutar da mai martaba”
“Yea “ sauran suka amsa a tare da tahowa don tafiya da shukra,mai martaba ne ya daga hannu,da qarfi yace
“Ku dakata,na santa” jin hakan yasa suka rusuna tare da cewa
“Yhea your majesty” sannan suka koma inda suke a tsaye suka qame,duk abinda akeyi shukra kawai ido take binsu dashi domin tana ganin kamar a mafarki duk abubuwan suke faruwa,sojojin china da suka biyota ne suka taho daidai gaban mai martaba suka rusuna,babban su wanda shine yake gaba,sauran sun tsaya a bayanshi ne yace
“Mai martaba ka gafarceni,zan tafi da wannan palace maid din,domin lady investigator ce ta shigo quaters dinmu domin wani dalili nata” yana gama fadar haka,ya bada umarnin a kama ta a tafi da ita
“Ku dakata nace” mai martaba ya fada cikin tsawa,har sai da shukra ta daga ido ta kalle shi,royal guard din da yake kusa dashi shi kuma ya daka mata tsawa
“How dare you? Kike kallon mai martaba ido cikin ido” da sauri tayi qasa da kanta,tare da ranqwafar da wuyanta,chief eunuch da yake tsaye duk yaji babu dadi domin ya san mai martaba ma don babu yadda zaiyi ne,gyaran murya mai martaba yayi
“Yanzu a gabana ina tsaye zakuyi arresting palace maid dina? Tunda palace maid din masarautar mu ce,ku barmu domin muyi binciken abinda ya kaita wajen,kuma zamu hukuntata yadda ya kamata idan mun kama ta da laifi” rusunar da kai sukayi tare da bashi haquri,alama yayiwa police officers din da suke tsaye a bayanshi,da hanzari suka matso kusa,yace
“Ku tafi da ita” shukra da har yanzu take jin kamar babu jini a jikinta ta fara tafiya,’yan sandan suka sata a gaba,suna tafiya tana waiwayen mai martaba har suka bar wajen.
Manager da yaji labarin sojojin china suna bin lady investigator da gudu ya rikice sosai ya shiga tashin hankali,sameer ne ya taho wajenshi da gudu,manager yacewa sameer
“Me ya sami shukra? Sun kama ta?” Cikin alhini sameer yace
“Basu kamata ba amma an tafi da ita police bureu” juyawar da sameer zaiyi ya hango mai martaba a tsaye a inda shukra ta barsu,nuna wajen sameer yayi tare da cewa manager
“Yallabai wancan kamar dan sandan sirrin nan ko? Ka ganshi” manager da ya juyo shima yana kallon mai martaba yace
“Kai ba shi bane,wannan mai martaba ne” sameer ya kalli manager
“Mai martaba kuma?”
“Ehh mai martaba ne,ba kaga alkyabbar sa ba,dragon robe ne a jikinshi “ manager ya fada yana qara nunawa sameer inda mai martaba yake tsaye,daidai lokacin da ya juya baya ya bar wajen,jinjina kai sameer yayi
“Tabbas dragon robe ce a jikinshi,mai martaba ne,ka san ni ban taba ganin shi a kusa kusa haka ba,amma abin bai baka mamaki ba? Kamar su tayi yawa sosai” haka dai suka cigaba da alhinin tsananin kamar da mai martaba yakeyi da abokinsu dan sandan sirri.
Mai martaba suna fitowa daga wajen ya tsaya ya daina tafiya,ganin haka chief eunuch yace
“Your majesty ya za’a yi da shukra?” Mai martaba da damuwa ta cika fuskar shi ya ce
“A kirawo police IG,na tabbata tana da qwaqqwarar hujjar da yasa ta shigo wajen nan”
“Yea your majesty “ chief eunuch ya bashi amsa,wucewa yayi domin komawa palace.
A office of investigation,’yan matan suna zaune gaba dayansu Aliya ta shigo da saurinta
“Wai da gaske ne abinda nake ji shukra ta samo hujja mai muhimmanci?” Rukayya ce ta bata amsa
“Ehh da gaske ne,an ce wasu kalmomi ne na china kuma ba kowa yake iya gane me suke nufi ba” Afrah da take zaune tace
“Lahh abinda shukra ta nuna min,nace ta mayar basu da amfani” sameerah ce ta kalli Afrah
“Lallai ta qara takar sa’a kenan” Afrah ta miqe tsaye
“Ta yaya zaki ce ta taki sa’a,taga abu mara ma’ana,ni banyi tunanin zai iya zama wani abu ba,amma ita ta dage har sai da ta fitar da abu mai ma’ana a ciki,kuma kice sa’a ce?” Shiru Sameerah tayi,Afrah ta cigaba
“Wannan halin naku shi zai kaiku ya baro,wai ta taki sa’a saboda kawai ba zaku iya yaba mata akan qoqarin da tayi ba” kowa tsit yayi a wajen don kuwa gaskiya Afrah ta fada,baqin ciki kawai sukeyi.
A office din director kuwa,lady sumayya ce cikin bacin rai take fadawa director
“Yarinyar nan fa yin kanta tayi ba tare da izinin kowa ba,ko da ta samu abu mai muhimmanci amma mu bai kamata ace mun zuba ido ba,ya kamata a hukunta ta domin tayi gaban kanta….” basma ce ta katseta
“Duk da gaban kanta tayi amma ta cece mu ne gaba dayanmu daga abinda zaije ya dawo idan labari ya jewa sarkin china cewar an tura ladies investigators a matsayin ladies-in-waiting domin suyi binciken qarqashin qasa,yanzu kuwa ana samun hujja a kan wanda ake tuhuma ai komai ya qare,kuma muma mun tsira daga mu har mai martaba” harara sumayya ta aika mata,basma ta sunkuyar da kanta,director ce tace
“Yanzu ina yarinyar take”
“Naga kamar bata cikin nutsuwarta,shiyasa nace taje ta huta” nadeeya ta bata amsa.
Shukra da gabadaya ta rasa ma wane tunani zata yi,tana zaune ta lumshe ido ita kadai take magana da kanta
“Dama shi ne? Shi ne ? His majesty The king” bude idonta tayi,da sauri ta qara lumshe su tare da cewa
“Na shiga uku na,yanzu tunda na san shine mai martaba lallai sai ya hukunta ni akan rashin girmama shi da na dinga yi,ina magana dashi kamar naga sa’a na,dama mai martaba ne? Shikenan tawa ta qare”
Nan da nan ta fara tunanowa tun ranar da suka fara haduwa,ta tuna ya taba ce mata
“Ya bata imperial order” (Dokar karagar mulki wacce sarki ne kawai yake bada ita) da lokacin da yace mata bai taba hawa katanga ba,da lokacin da yace mata yayi umarni a turo ‘yan sanda,kuma taga ‘yan sandan da suka zo ba ‘yan sandan sirri bane ‘yan police bureu ne,ta tambayeshi yace mata
“Ai duk qarqashin ikona suke” da lokacin da yace mata zai bata kyauta a maimakon mai martaba,ai kyautar shi da ta mai martaba duk daya ne,da lokacin da ya kaita royal library tayi karatu,da lokacin da yace mata ya kori masu gadin dare na qofar fada saboda ta wuce don ba zai iya qara tsugunnawa ta taka shi ta haura katanga ba,abubuwa da yawa suka dinga dawo mata,a hankali ta furta
“Lallai ni shashasha ce,ashe akwai abubuwa da dama ya kamata na fahimta,amma meyasa yace min shi dan sandan sirri ne?” A take ta tuno lokacin da take daka matsa tsawa sai dai ya zabi daya,ko ya haura katanga,ko kuma ya duqusa ta taka bayanshi ita ta hau.
“lallai na shiga uku na lalace,duk mai martaba na dinga yiwa haka? Lallai sai yasa anyi min kisan da ko gawata ba za’a gane ba”
Muryar sameer ce ta ratsa kunnen ta
“Shukra shukra” shi da manager da gudun su suna nemanta,idonta a lumshe suka tarar da ita,duk kiran da suke qwala mata kamar bata ji,hannu sameer yasa ya bugi katakon da ta jingina dashi,a hankali ta bude ido,manager ne yace mata
“Lafiyarki kuwa? Ana can ana ta cewa an kama lady investigator a quaters din baqi,har mai martaba ma yaje wajen” da sauri tace masa
“Kaga mai martaba?” Sameer ne ya saki murmushin jin dadi
“Abin mamaki ko? To idan kika ganshi kamar abokin mu dan sandan sirri” rintse ido shukra tayi jin abinda sameer ya fada,ganin bata ce komai ba ya cigaba
“Da gaske fa,idan baki kula sosai ba sai kice mutum daya ne” har yanzu bata ce komai ba,manager shima yace
“ yanzu fa mutane sai su dauka abota nake da mai martaba,don kamannin su babu maraba” shukra da sai yanzu ta bude idonta tace
“Ai shi ne,wannan mutumin da kuke magana shine mai martaba” tuntsire mata sukayi da dariya,sameer yace
“Mai martaban ne kike ganin shi a arha ko? Lallai kin samu matsala,kama ce kawai”
“Da gaske nake,har magana munyi dashi,Wallahi shine mai martaba,alhinin da kuka sameni inayi kenan,ji nake kamar zanyi hauka” zamewa sameer yayi qasa yai zaman dirshan tare da cewa
“Mai martaba ne nasa shi shan shayin dole,na dinga dura masa nace masa kuma dole sai ya shanye,na bashi ganda nace ya cinye a cikin kasuwa,na shiga uku” manager da ya fisu qarfin hali yana tsaye yace
“Ni da muka taho tare na sarqe mai hannunshi ciki nawa,nai ta ɗaka masa duka a qirji,yana ta cemin indaina dukanshi,ba’a taba dukanshi ba,na ce masa,na dakeshi din” shukra ce tace musu
“Dukkanku ai naku mai sauqi ne,ni fa….taka….takashi nayi a baya na hau Katanga” dukkansu sun shiga tsananin tashin hankali,idan kaga fuskarsu sai kace saqon mutuwa aka aiko musu.
Mai martaba yana zaune a grand palace da takaddar da shukra ta samo a qauters din baqi da IG ya kawo masa,sun duba yadda suka karanta sunan wani qauye ne da yake bayan gari kuma kusa da gaɓar ruwa,hakan yasa mai martaba yayi umarnin suje su bincika qauyen ko zasu samu wata hujja a wajen,yana zaune da abin a hannunsa yana kallo,a hankali yace
“Me yasa zamu hadu da ita a haka? Me yasa? Kai ban so haka ba,yanzu yaya zata ji? Kamar ta yadda dani ni kuma na ha’ince ta ko?” Shi kadai yake maganganun sa.
Su shukra da duk tsoro da alhini ya cika su suna nan inda suke zaune,wasu ladies-in-waiting suka qaraso wajen,ta bayan shukra suka shigo shiyasa basu kula da zuwansu wajen ba,ta gaban ce tace
“Kece Shukra Anas Malak ta Office of investigation?” Juyowa shukra tayi tare da cewa
“Yes my lady” matar ta qara cewa
“Ki biyo mu a baya,domin mai martaba ya nemi ganinki” ai manager da yake tsaye qafarsa ta kasa daukar shi,kamar zai fadi dai yai saurin qarfafa jikinshi,a ranshi yace
“Shikenan ta faru ta qare,an fara da shukra saura mu” sameer kuwa ido yayi qifi qifi a zaune.
A can qauyen da aka tafi bincike,IG yana bakin ruwa yasa aka bincike jiragen ruwa da zasu bar garin,ba’a samu komai ba,lieutenant ne ya qaraso tare da cewa
“Yallabai duk inda zamu duba mun gama dubawa bamu samu komai ba” jinjina kai yayi
“Bani taswirar qauyen na gani (map) “ bude takaddar da map din take akayi,kulkin da yake hannunsa yasa ya nuna wani waje
“Nan wajen ya kamata ace akwai gidan ajiyar kaya “ da sauri lieutenant yace
“Ehh Assistant sun tafi shida jaleel suna wajen”
IG ne yayi gaba suka bishi a baya,suna isa wajen daidai lokacin da jaleel yake cewa
“Tunda bamu samu komai ba ya kamata mu bar binciken nan haka,mun duba ceiling,mun duba rijiyoyi amma bamu samu komai ba” jin haka IG yace
“Toh ku wuce mu tafi kawai” cikin jin dadi jaleel yabi bayanshi haka sauran ‘yan sandan ma suka fara tafiya,IG ne ya tsaya cak tare da juyowa yana qarewa wajen kallo,jaleel ya fara rarraba ido,juyowa IG yayi ya koma ya fara zagaye wajen a hankali yana qarewa ko ina kallo,hakan yasa duk suka biyoshi a baya,daidai wani gini ya tsaya tare da cewa assistant lieutenant
“Kace baku samu komai a cikin dukka ginin ba?”
“Ehh yallabai,na tabbatar babu komai a ciki” jinjina kai IG yayi tare da matsawa kusa da ginin da dora hannunsa,alamun sabon ginin qasa ya gani domin hannunsa ya lakuto taɓo,kulkin da yake hannunsa yasa ya fara dukan wajen,har sai da yayi rami,dama sabon gini ne ko bushewa baiyi ba,idonshi ya saka ya leqa,nan ya hango kayan bindigogi manya manya,da wasu akwatuna da bai san menene a ciki ba,juyowa yayi ya kalli lieutenant
“Kaje yanzu yanzu a sanarwa wakilin sarkin china cewar mun samu qwaqqwarar hujja akan Kim young Dal”
“Yes sir” lieutenant ya fada tare da barin wajen,cikin jaleel ne yayi wata irin murdawa,domin a tsorace yake amma ko kaɗan ba zaka gane hakan a fuskar shi ba,IG yasa sauran suka sauke ginin aka fiffito da duk kayan da suke ciki,kayan makamai ne masu matuqar yawan gaske.
Mai martaba a tsaye a grand palace,ya goya hannayensa sai kai da kawowa yake yana zagaye wajen,ɗaga murya yayi
“Waye a nan?” Chief eunuch ne ya shigo tare da rusunawa ,mai martaba ya tambaye shi
“Wai yaushe zata qaraso ne? Na jita har yanzu shiru” qara rusunawa yayi
“Ka gafarce ni your majesty,saboda ana bin matakan tsaro ne” jinjina kai yayi tare da yi masa alama da hannu ya tafi.
Shukra tana quaters din ladies in waiting na grand palace,a tsaye take ta daga hannayenta sama suka caje ta tsaf suka tabbatar babu wani mugun abu a tattare da ita,babbarsu tace musu
“Ku shiryata,ku bata kaya ta saka” ta fice
Wani kwali suka dauko,suka fito da kaya daga ciki suka miqawa shukra,kallon su ta tsaya yi
“Menene wannan?”
“Kaya ne,ba zaki iya zuwa ganin mai martaba da wannan uniform din naki ba,dole sai kin canja” karbar kayan shukra tayi,kaya ne irin wanda special court ladies suke sawa,ta saka riga da skirt sunyi mata kyau sosai,fitowa sukayi tabi wanda zasuyi mata rakiya zuwa wajen mai martaba,suna tafe a hanya tana zancen zuci
“Ko me yasa yallabai….au mai martaba yake nema na? Ko zai gafarta min ya yafe min idan nace masa ban san shi sarki bane?” Suna tafiya tana ta kalle kalle domin kyawun grand palace ba na wasa bane,bata taba gani inda aka qawata waje kamar haka ba,tana ta kalle kallenta amma gaban ta na dukan shida shida,domin bata san me mai martaba zaiyi mata ba.
Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤
ROYAL CONSORT
©️ marriam mayshanu…. ✍️
Page 28
Jaleel ne tsugunne a gaban tribunal minister,a daya gefen kuma jameel ne da yake jefa wa jaleel harara
“Yanzu wannan makaman da aka kama,idan wajen bincike sunan Abbana ya fito fah?” Ya jefowa jaleel tambayar,wata dariya jaleel yayi yana nuna jameel din cikin nishadi tare da cewa
“Nace ka qyaleni zanji da hakan,babu wani abu da zai faru” shi dai minister bai ce komai ba,shiru kawai yayi yana sauraronsu,amma cike yake da tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo,sallama jaleel yayi musu ya fita,yana fita jameel ya matso kusa yana fuskantar mahaifinsa
“Yanzu Abba haka zaka bari wannan shashashan yaji da matsalar nan? Bayan duk shi ya samu a cikinta? Yanzu idan aka samu labarin abinda kuka qulla kai da Kim Young Dal fa? Me kake tunanin zai iya faruwa?” Gyaran murya minister yayi
“Jameel ka kwantar da hankalinka,kuma idan ban bawa jaleel damar ya gyara abinda ya lalata ba yaya kake so muyi? Dole mu zuba masa ido muga abinda zaiyi,domin shi ba shashasha bane kamar yadda kake zaton shi” duk da dai jameel bai gamsu da hakan ba amma haka ya haqura,yayiwa mahaifinshi sallama ya tashi ya fita.
Mai martaba yana zaune duk hankalinshi ba a kwance ba,yana ta tunanin me zai ce wa shukra,shi kadai yake magana da kanshi
“ko dai ce mata zanyi banyi niyyar nayi mata qarya ba? Ba da gangan nayi ba,a’ah a’ah ba haka ba,ce mata zanyi….” Maganar chief eunuch ce ta katse shi
“Your majesty ta qaraso,a ina kake buqatar ganinta?”
Dan zabura yayi daga inda yake zaune,kafin yace
“Ka kaita dakin da nake ganin baqi na musamman” dago kai chief eunuch yayi cike mamakin abinda yaji,abinda bai saba yi ba,da ido mai martaba ya bashi tabbacin haka yake nufi,hakan yasa ya juya domin kai shukra inda ya kamata.
Suna tsaye a waje,cikin rakiyar ladies in waiting da suka rakota,ga jerin royal guards da suke gadin grand palace,tana tsaye ta rusunar da kanta,ita kadai take magana da kanta
“Ce masa zanyi KING a’ah your majesty ya kamata nace,ko kuma royal highness,ko dai imperial majesty?” Cikin rikita ta rasa inda zata sa kanta,taji muryar chief eunuch,zuwa yayi gabansu ya tsaya tare da cewa
“Ki biyo ni” bin bayanshi tayi har dakin da mai martaba yake ganin baqi na musamman,kalle kalle take tayi yadda aka tsara dakin gwanin sha’awa,akwai wajen zama na mai martaba sai dan qaramin pillow a qasa wajen zaman baqo,ta can gefe taje ta tsaya,jiyo muryarsa tayi
“Tana ciki?” Chief eunuch ya amsa masa da
“Ehh tana ciki your majesty” hakan yasa ta rusunar da kanta sosai,ta ranqwafa kamar zatayi ruku’i amma bata kai qasa sosai ba,yayinda ya sa hannyenta biyu akan cikinta,leqowa mai martaba ya fara yi,ganin yadda tayi yasa shi saurin qarasowa ya zauna a mazaunin sa,kallonta yayi da ko motsawa batayi ba yace
“Zo ki zauna” sai a lokacin ta dago kanta,amma ta kasa hada ido dashi kuma bata motsa daga inda take tsaye ba,cikin taushin murya ya qara ce mata
“Zo ki zauna nace” a hankali ta fara daga qafarta tazo dai dai inda yake tana fuskantar shi,tsugunnawa tayi da sauri akan gwiwoyinta tare da rusunar da kanta tace
“Royal Majesty!!!!” Da qarfi,ta cigaba “ka yafe min ban san kai sarki bane,tunani na bai taba bani hakan ba,na san na cancanci mutuwa akan abubuwan da na aikata maka,amma ka taimaka ka ceci rayuwata a karo na farko ba zan qara ba” da qarfinta take maganar kuma cike da tsoro,sai da ta gama tsaf sannan mai martaba ya tuntsire da dariya har da hantsilawa gefe,sai da ya daidaita kansa sannan yace mata
“Ke dalla can,tashi ki zauna sosai,dama halinki ne bani dariya,ina ta tunanin me zan fada miki kika zo kika wani ce ROYAL MAJESTY” ya qarasa yana qara tuntsire mata da dariya,mamaki sosai hakan ya bata,ta dago kanta ta kalleshi,suna hada ido nan da nan ta sauke kanta qasa tana rufe idon,shi ya cigaba da magana
“Ai ni ya kamata na baki haquri,ke kuma kinzo kina sani jin kunya”
Qara rusunawa tayi hannayenta a qasa tace
“Dama ba kirana kayi ka hukunta ni ba?” Da mamaki yake kallonta
“Hukuntaki kuma? Meyasa zanyi haka? Ai nine nayi miki qarya nace miki ni dan sandan sirri ne,naso fada miki gaskiya amma sai nake jin dadin yadda kike mu’amala dani kuma har ta kawo mu ga haka,saboda haka kada kiyi fushi dani,ba da niyya nayi hakan ba” a firgice ta dago kanta
“Mai martaba ka daina fada min haka,ni wacece da na isa nayi fushi da kai?” Leqa fuskarta yayi
“Da gaske? Ina ta tunanin zaki ɗaka min duka ne saboda nayi miki qarya?” Da sauri tace
“Duka…duka mai martaba,don Allah ka daina fadar haka,idan royal guards suka ji yanka ni zasu yi” dariya ya sheqe da ita
“Ba zaki iya dukana ba? Amma ai kin taka gadon bayana kin hau katanga” ai kamar ya tunzura ta da sauri ta dago kai ta kalleshi,fuskarta har yanzu cike da tsoro tace
“Your majesty,a wancan lokacin ban san kai sarki bane,ka gafarce ni”
“Yauwa,yanzun ma zaki iya yin kamar har yanzu baki san ni sarki bane? Ki dinga magana dani yadda kikeyi da,ki daina wannan durqusawar ki dauka kawai ni dan sandan sirri ne a wajenki ba sarki ba” kallonshi take da mamaki
“Your majesty” yana kallon yadda takeyi hakan yana burge shi yace
“Kinsan meyasa ban fada miki gaskiya tun da wuri ba? Saboda ina tunanin zaki yi abinda kike yi yanzun,ina tunanin zaki daina sakewa a kusa dani kamar yadda kike yi yanzu,na san abin ba mai sauqi bane a gareki tunda kin riga kinsan ni sarki ne,amma saboda wani dalili nawa ina buqatar ki cigaba da kallona kamar da,mutum ne kamar kowa ba sarki ba a duk lokacin da kike tare da ni”
Hankalinta ne ya dan kwanta,tsoron da take ji ya fara raguwa,a hankali tace
“Amma your majesty,ban isa nayi maka yadda kake so ba,domin dokar qasar nan….” Kafin ta qarasa cikin dakakkiyar murya yace
“Kin isa kiyi hakan,ke qarewarta ma umarni na baki,it’s an imperial order kuma ki karya imperial order kin san mai zai biyo baya,kin ji me nace? “
Idonta ta dago ta kalleshi ido cikin ido,kwarjini yayi mata a cikin dragon robe da yau ne ganinta na biyu dashi a haka,hakan yasa ta qara sunkuyar da kanta,leqa fuskarta ya fara yi yace
“Dago dai” ta dan dago kadan,ya qara cewa
“Dago dai” ta qara dagowa kadan,haka har ta dago fusukarta sosai ta kalleshi,yana ta mata dariya,amma ita ta kasa sakewa,har yanzu mamaki bai bar ta ba,haka ya cigaba da surutun sa amma taqi sakewa har ya sallameta ta fito,a hankali tana ta qarewa wajen kallo har ta fita daga grand palace,a inda ta fita ta barshi a zaune murmushi ne akan fuskar shi yana tuna yadda ta dinga yi mai yace
“Ina fatan tayi saurin komawa yadda take da,ta dauke ni mutum kamar kowa”
A quaters din lady jalila,chief maid dinta ce ta shigo da gudunta,ta rusuna a gabanta tare da cewa
“Your highness akwai labarin da nake tafe dashi” da ido lady jalila tayi mata alamar ta zauna domin ita ba mai yawan magana bace domin akwai aji,tana zama ta fara da
“Your highness naji labarin mai martaba ya kira wata palace maid zuwa grand palace domin ganawa da ita a dakin baqi na musamman,da na tambayi wacece sai ake fada min shukra ce” zaro ido waje lady jalila tayi
“Me kika ce? Mai martaba ya kira shukra grand palace?” Ta tambayi chief maid dinta,jinjina kai tayi cikin bayar da tabbaci
“Ehh ranki ya dade,shin ko menene dalilin kiranta grand palace?” Sauke ajiyar zuciya lady jalila tayi bata qara cewa komai ba,domin ita dama ba’a fiya gane tashin hankali akan fuskar ta ba,ko da kuwa tana cikin matsala,amma tana tunanin meyasa mai martana yake daukaka lamarin yarinyar nan haka? Lallai akwai alamar tambaya.
Jaleel ne a tsaye cikin duhun dare tare da Kim young Dal,cikin tsananin tashin hankali kim yake ce masa
“Da gaske police bureu sun samu hujja akaina?” Jinjina kai jaleel yayi
“Haka ne,amma kada ka damu,saboda irin wannan ranar nake da abokai masu babban matsayi,zamu gama da wannan matsalar sannan naji da yarinyar nan shukra,amma yanzu ga yarona nan,ku tafi tare dashi,zai kaika inda zaka buya,idan kuma wani abu ya faru zai taimaka maka ka bar qasar nan”
A police bureu IG ya hada kansu domin tafiya kamo Kim,cikin ayarin su suka tafi har quaters din aka sauke baqin china,da zuwansu aka ce musu ai ba zai yiwu su kama shi ba domin wakilin sarkin china ya tafi magana da mai martaba,IG ne ya tambaya
“Kamar yaya ba zamu iya kama shi ba?bayan muna da hujja kuma da takaddar izinin kama shi(arrest warrant)” kafin a bashi amsa jameel ya fito daga cikin quaters din
“Suma suna son su miqa mana shi amma ba zasu iya hakan ba” IG ya daga kanshi ya kalli jameel,tare da tambayarsa
“Kamar yaya suna so amma ba zasu iya ba?”
“Saboda ya kashe kansa,sauran bayanin kuma wakilin sarki yaje ganin mai martaba domin bashi cikakken bayani”
A grand palace cikin mamaki mai martaba yake kallon wakilin china
“Kace ya kashe kanshi?”
“Qwarai kuwa,ya kashe kanshi a cikin qasar ka” wakilin china ya fada,tare da miqawa mai martaba wata takadda
“Ya bar wannan takaddar ne da ya rubuta cewa ya kashe kansa ne domin duniya ta yadda bashi da laifi,sharri kawai ake nemanshi dashi” karbar takaddar mai martaba yayi nan take yanayin fuskar shi ta canja zuwa bacin rai,yana gama karanta takaddar ya nannadeta ya ajiye akan tebur din dake tsakiyar su,wakilin china yace
“Nayi shiru lokacin da kuka tura mana ladies investigators ban ce komai ba,na qara yin shiru lokacin da yarinya daya a cikinsu ta shigo mana a boye,amma wannan karon da aka dorawa dan rakiya ta sharri tabbas zan dauki mataki tunda har hakan ya kai ga rasa ransa domin ya kare kansa ya kuma tabbatar bashi da laifi” mai martaba cikin bacin rai yace
“Aka yi masa sharri kuma? Bayan hujja da muka samu akan shi?”
“Hujja? Kana nufin wannan saqon takaddar sirrin da palace maid dinku ta samo? Ta yaya zan yadda dama can ba ku kuka tsara hakan ba? Tunda dama kuna zargin Kim Young Dal?” Wakili ya fada,
“Wakili!!! Kana daukar abin nan da nisa,ta yaya zamu shirya haka kawai domin muna son mu kama shi?” Mai martaba ya fada masa cikin bacin rai,amsa wakili ya bashi da
“Tabbas hakan zai iya zama shirin ku ne,kuma matuqar labari ya kai wa sarkin china,to matsalar sai tafi haka girma,domin Kim dan asalin qasar nan ne,amma yanzu ya zama dan qasar china,kuma yazo ya kashe kanshi a qasarku” mai martaba ne ya dan sassauta murya
“Toh yanzu me kuke son ayi muku?” Ajiyar zuciya wakili yayi tare da cewa
“Ina son ka bani yarinyar nan your majesty,ina da damar da zan bincika na gani ko shiri ne kuka yi domin ganin kun kama Kim da laifi,zan tafi da lady investigator dinnan china domin na yi mata tambayoyi da azaba har sai ta fadi gaskiya your majesty” Ran mai martaba idan yayi dubu to duk sun baci,fuskar nan babu annuri ko kadan ya kalli wakili cikin daga murya yace
“Kalle ni nan Wakili! Me kake fada haka? Na dauki yarinya na baku ku tafi da ita qasar ku? Bayan bata da laifin komai?” Ganin yadda ran mai martaba ya baci Wakili ya miqe tare da cewa
“Ka dai qara tunani,domin idan ba hakan akayi ba,tabbas qasar JOSHUN zata samu babbar matsala da sarkin china.
Washegari a office of investigation,suna tsatstsaye kowa da abokin hirar sa shukra ta shigo,magana ta fara yi musu tana gaishe su kowa yayi mata banza,cikin mamakin hakan ta qaraso inda Aliya,sameera da ruqayya suke tsaye tace
“Sannunku,kun tashi lapia?” Juyar da kansu sukayi ba tare da sunce mata,gaba tayi ta wuce su tare da tsayawa tana tunanin dalilin hakan,sai ga Afrah nan,da sauri ta qaraso inda shukra take suka gaisa sannan tace wa shukra
“Kiyi sauri kije office ki samu Lady nadeeyah”
Shukra da ta dan tsorata tace
“Lady nadeeyah kuma? Lafia?” Murmushi Afrah tayi wanda daga ganinshi na yaqe ne,sannan tace
“Idan kinje wajenta zakiji ko menene” da sauri shukra ta wuce,Afrah ta bita da kallon tausayi.
Da shigarta office din,nadeeya da basma ne a zaune a kan kujera,bayani sukayi mata akan buqatar Wakilin sarkin china na tafiya da ita qasar su,cikin razana tace
“Suna son su tafi dani china! Na shiga uku!” Babu wanda ya qara ce mata komai domin suma su biyun suna cikin tashin hankali sosai,don haka kawai yarinyar ta kwanta musu a rai musamman nadeeyah,tana qaunar shukra sosai har cikin ranta.
A majalisar sarki an zauna zama na musamman akan wannan matsalar,dukkan hakimai suna zaune a qasa a jere kamar yadda suka saba zama,tribunal minister ne yake cewa
“Mai martaba,dole ne mu nemi hanyar da zamu gusar da bacin ran su,domin dorewar zaman lapia tsakanin qasashen namu guda biyu” mai martaba da har yanzu ran shi a bace yake yace
“Kana nufin mu miqa musu yarinyar su tafi da ita kenan?”
Minister of state affairs yace
“Your majesty,daya daga cikin ‘yan rakiyar Wakili ya kashe kansa fah!kuma hakan zai bamu matsala sosai da sarkin china,ka taimaka ka miqa musu ita kawai sannan…..”
“Bana buqatar ji!!!” Mai martaba ya fada cikin gigitacciyar tsawa
“Ya isheku haka! Yarinyar nan da ake magana a kanta ba ita tayi laifi ba,aikin ta kawai takeyi,ta yaya zaku bude baki kuce na miqata zuwa wajensu?” Shiru dukkansu sukayi,tribunal minister yace
“Amma mai martaba idan ba’a yi hakan ba,ta yaya za’a yi maganin wannan matsalar? Wakili ba zai bar garin nan ba tare da ita ba,idan kuma ya zauna mana,zasu turo sojojin su daga can qasarsu domin suyi gadin shi da mutanensa,hakan kuma zai iya zama yaqi tsakanin mu dasu,ta yaya zamu iya hana hakan faruwa? ka qara duba lamarin nan your majesty” dukka wajen suka hada baki tare da saukar da kansu qasa a yadda suke a zaune,suka ce
“Ka qara duba lamarin nan your majesty! Ka qara duba lamarin nan your majesty!! Ka qara duba lamarin nan your majesty!!!” Huci kawai mai martaba yakeyi yana kallonsu daya bayan daya.
A quaters din queen dowager,chief maid dinta ce tazo tana bata labarin dalla-dallah tun daga farkon farawar lamarin har zuwa yanzu da mai martaba yace ba zai bada shukra a tafi da ita ba,tabe baki tayi
“Yanzu ya gwammace ya jawo wa qasar nan rikici da tashin hankali akan wata palace maid wacce ba kowan kowa ba?” Queen haneefah da take gefe tace
“His majesty ya yanke hukuncin da ya dace Mamaa,wannan palace maid din itama ai ‘yar qasar sa ce,kuma haqqine a kansa ya kareta “
Harara queen dowager ta miqa mata,amma ba tare da kallon idonta fuska da fuska ba,tace
“Ta yaya zaki fadi haka a cikin wannan halin da ake ciki? Yarinya ita kadai ta addabi dukkan garin nan,kowa hankalinsa a tashe?”
Basma ce ta shigo office da gudu,inda nadeeya da Afrah suke tsaye suna jimamin abinda yake shirin faruwa,kallonta sukayi domin yanayin da ta shigo kawai ya nuna musu ba lapia ba,kafin suyi magana tace
“Hakimai gaba daya sunayiwa mai martaba zanga-zanga akan ya miqa shukra” Afrah da sauri cikin bacin rai tace
“Ta yaya zasuyi zanga-zanga don a miqa wacce take yiwa qasa aiki?” Basma ce ta bata amsa
“Ai su hakiman basa bawa palace maid wata daraja,su kawai damuwar su bacin ran sarkin china” nadeeyah da jikinta gaba daya yayi sanyi tace
“Ta yaya zasuyi haka? Ina ganin ana son a hukunta shukra ne saboda qwazo da qoqarin ta,zan je na samu IG saboda naji ainihin abinda yake faruwa” basma tace
“Zan biki muje”Afrah ma tace
“Muje”
Hajiya jameela ce ta shirya tsaf domin zuwa cikin masarauta don ganin lady jalila,ita da maid dinta suka fito daga daki a tsakar gida suka tarar da jaleel,kallon yanayin shigar da tayi ne yasa yace
“Maama,ina zuwa haka?” Ba tare da ta tsaya ba ta bashi amsa
“Zanje wajen jalila,na san wannan halin da ake ciki na yaqi ko yau ko gobe kuma gashi akan yarinyar da ta shigo da ita Office of investigation,nasan hankalinta ba a kwance yake ba,tana buqatar wani a kusa da ita” tsayar da ita jaleel yayi da murmushi a fuskar shi tare da cewa
“Haba maama,in dai don wannan ne ai ba sai kinje ba,duk wannan abin da kike gani nine nan na shirya shi” da mamaki hajiya jameela take kallonshi
“Kai !!! Me ka aikata haka?” Murmushi ne har yanzu akan fuskar shi
“Tun ina yaro nake sawa kowa yake min kallon shashasha,sai na basu mamaki,amma fa lady jalila bata sani ba don ban sanar da ita ba,kuma ina yin wannan ne saboda ita don bata san hatsarin wanann yarinyar shukra a kusa da ita ba” tsabar mamaki kasa cewa komai tayi,kawai ta tsaya tana kallonshi.
A gida sameer yake bawa Abdullahi labarin abinda yake faruwa,domin duk abinda akeyi bai sani ba,da sauri ya tashi domin neman shukra,a bakin qofar quaters din baqin china ya ganta cikin kayanta irin dai wanda talakawan gari suke sawa,yadda aka jera sojojin china,ga kuma sojojin JOSHUN suma a jere suna fuskantar su kamar dai masu shirin yaqi,ta bayanta ya tsaya tare da cewa
“Shukra” juyowa tayi cikin tsoro,ganin Abdullahi ne yasa ta sauke ajiyar zuciya,hannun ta ya jawo har zuwa gidan sameer,suka shigo daki ya fara tattara kayan duk da ya san nashi ne,ganin haka shukra ta jefa masa tamabaya
“Me kenan kake yi?” Ba tare da ya kalleta ba,kuma bai daina abinda yake yi ba ya bata amsa
“Ya kamata ki bar qasar nan,saboda a halin yanzu kina cikin hatsari” Da sauri cikin daga murya tace
“Orabeuni !” (Yaya!)
Juyowa yayi a wannan lokacin ya kalleta
“Naji abinda yake faruwa shukra,Wakilin china ba zai haqura ba har sai ya sameki”
“Amma ni palace maid ce,kuma palace maid basa guduwa,hakan babban laifi ne” shukra ta fada masa
“Kina nufin ki zauna,a basu ke su tafi dake china ko? Idan suka tafi ke kashe ki zasu yi” ya fada mata qwalla tana cika a idonsa,jikinta ne yayi sanyi ganin qwallar da take idonshi,ganin bata ce komai ba ya cigaba da magana
“Kawai kiyi yadda nace,yau da daddare zamu bar garin nan,saboda haka ki shirya kawai” yana gama fada mata haka ya cigaba da hada kayansa,tana masa magana amma bai qara kallon inda take ba balle ya amsa mata tunda ya gama magana.
Mai martaba yana zaune shi kadai a grand palace,gaba daya ya shiga rudani na rashin sanin abinda ya kamata yayi,chief eunuch ne ya shigo,ya rusuna tare da cewa
“Your majesty,her highness lady jalila tazo ganinka” dago kai yayi
“A ce mata ta shigo” ya fada a taqaice,chief eunuch yana fita ita kuma ta shigo,tana shigowa ta tsaya tana qare mai kallo,gaskiyane yana cikin damuwa,dago kai yayi ya kalli inda take nan take damuwar shi ta koma murmushi mai kyau,ta rusunar da kanta tare da cewa
“Your majesty” tasowa yayi zuwa inda take,zama yayi a kujera itama ta zauna a dayar kujerar da take wajen,tare da zagayayyen tebur a tsakiyar su,shi ya fara magana
“Na san kinzo ne saboda kin damu da halin da shukra take ciki ko?” Jinjina kai tayi
“Hakane your majesty,na san kana buqatar wanda zakayi magana dashi shiyasa nazo,kuma ina ganin kamar duk laifina ne,da ban kawo ta cikin Office of investigation ba da duk hakan bata faru ba”
“A ah ba laifin ki bane,itama ba laifin ta bane,laifi nane domin bani da cikakken iko da kuma isa a qasata,amma ba zan taba basu ita ba haka nan kuma ban san yadda zanyi na tsayar da bala’insu da yake tunkarar mu ba” cike da mamaki lady jalila tace
“Kana nufin ko me zai faru ba zaka basu ita ba?” Jinjina kai yayi cikin tabbatar wa
“Tabbas ba zan taba basu ita ba,domin hakan ba adalci bane,ba zan taba bari ta dauki nauyin laifin da bata aikata ba ita kadai” ganin yanayin da yake fuskar shi yasa lady jalila ta sha jinin jikinta sosai,domin taga alamun ainihin kulawar da yake bawa shukra a ido da kuma kalaman mai martaba,hakan yasa cikin sanyin jiki tayi masa sallama ta fita,tana fita ya kirawo chief eunuch tare da ce masa
“Kaje ka duba min wane hali shukra take ciki? Na san hankalinta a tashe yake,kuma hakan yana damuna “ rusunawa yayi tare da cewa
“Yes your majesty “ sannan ya fita domin zuwa isar da umarnin mai martaba.
3,600 words
Oum tasneem ✍️
No comments