Recent Updates

Rijiya ta Bada Ruwa Complete Hausa Novel

 


[7/20, 11:07 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...?*
     _GUGA YA HANA_
                              
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ* 

*WATTPAD@ Oum-Mumtaz123*
*INSTAGRAM @itz_me_real_oum_mumtaz.*  

           *charpter 1*

********Zaune take kan wani k'ayataccen kujera da ke cikin rantsattsen office nata sai faman juyawa take, gajiyayyun idanunta na kallon sama alamun ta yi zurfi cikin tunaninta!

Sanye take cikin wani rantsattsen kuma d'anyen leshi mai kyawun gaske d'inkin doguwar rigar buba mai ratsin ruwan zaiba!

Fara ce tas,kyakkyawa 'yar duma- duma saboda kallo d'aya idan mutum ya yi mata kai-tsaye ba za a ce mata siririya ba,ko kuma 'yar lukuta ita dai tsaka tsaki ce!

Kyakkyawa ce ma sha Allah na gaban kwantance! Doguwar fuskarta kuwa shimfid'e take da dogon hancinta da ya sake fito mata sihirtaccen kyawun fuskartata! Bakin kuwa jajayen labba ne masu dan fad'i kad'an wanda hakan kuwa sosai ya tafi da tsarin bakin nata! Itadunta sexy eyes ne wanda ke d'auke da eye lashes dogi kamar wacce ta sa mascara na asalin fulani!

Infact dai kawai mai karatu ya fasalta yanayin kyakkyawar matashiyar mai kimanin shekaru 24 da a duniya take! ya d'aya dilo a wurin _ALH ABDUL WAALI_

Wacce mutane da dama suka fi saninta da  __ZULAYKHA ALH ABDUL WAALI_.
Cike da tsananin kasala da ya zamto dabi'arta ta mike daga kujerarta ta alfarma zuwa bakin madaidaicin fridge din da ke gefe kad'an daga inda take a cikin office din nata,drinks ne makil kala-kala cikin pridge din tare da ruwa na gora samfarin faro,inda ta fiddo da robar freshyoo guda d'aya,wanda kuma ya fi komai yawa cikin pridge d'in.

Sai da ta sake ma kanta mazauni akan kujerar tata kamin ta balle bakin ta akan robar,ba ita ta sauke shi ba sai da ta shanye sa tas,inda ta sauke kakkarfar ajiyar zuciya tana yatsina fuska kamar wacce aka ma wani abu.

Tare da taimakon A.c d'in da ke cikin office d'in ne ya sa gumi ko kad'an bai sakko mata daga goshin ta ba akan abu mai sanyin data kora ma cikinta,wanda rabon da ta sama cikin ta wani abu tin yammacin jiya sai ruwa,ga shi kuma yanzu wajen karfe goma sha biyu na rana.

Wayarta da ke kan table nata ta d'auka samfarin iphone,fuskarta ce ta wanzu da wani lallausar murmushin da ya sa gefen kumatunta side d'aya ya loba(dimples),sosai kuma ta yi wani fitinannen kyau na ban mamaki.

K'ara wayar tata ta yi a kunnen ta a lokacin da ta latso number d'in da aka yi saving da _Abbana_ tana sakin murmushin da ke k'ara ma kyakkyawar fuskarta armashi.

Sai da wayar ta yi ring kusan shida kamin aka yi recieving daga d'ayan bangaren,wanda hakan ya sa Zulaykha fashewa da kukan da ka gani za ka tabbatar da cewa tsantsar na tabara ce ba wai kuka na gaske ba.

Daga ta can bangaren kuwa a rikice muryar dattijon ya ratso mata dodon kunnen ta inda yake fadin "afuwan yar albarka! afuwan 'yar albarka ki yi shuru kar ki sa Abbanki ma kuka kinji...?" Ya kare maganar cike lallashi,wanda hakan ya sa Zulaykha share d'an gulmammen hawayen ta daya zubo tana sakin murmushi zuciyarta cike da tsantsar soyayyar mahaifin ta da kaf duniya bata da tamkar sa.

Wata irin ajiyar zuciyar zuciya Abban nata ya sauke kamar wanda yayi gudun tsere daya sa ta sakin siririyar dariya cikin daddadar muryarta tace "kai Abbana kamar wanda ka yi wani aiki irin wannan ajiyar zuciyar?"

Shi ma dariyar ya sake daga bangaren sa ya ce "Kun ji min ja'irar yarinya...? Dan mai garinku ba ke ba ce kike neman saka Abban naki a uku umm...?"Ya yi maganar tasa me cike da tsantsar soyayyar da yake ma gudan jinin tasa.

"Abbana na yi kewar ka da yawa fa!" Zulaykha ta fad'a tana wani karya wuya kamar wacce ke gaban sa!  "Nima nayi kewar babyna sosai,da fatan kina kular man da kanki ko Mamana ?" "Sosai ma Abbana,yanzun ma kawai haka nan na ji ina son na ji muryarka ne kamin na yi sallah saboda na ga lokaci ya kusa!"

"Allah ya yi ma rayuwarki albarka 'yata! Allah Ya tsare mana ke daga sharrin mutum da aljan a duk inda kike!" Abban ya fad'a fuskarsa shimfid'e da murmushi a lokacin da yake ma 'yar tasa wannan kyakkyawar addu'ar,ita kuma Zulaykha sai "Amin-amin Abbana". Take ta faman maimatawa,tana mai jin nishad'i cikin zuciyarta.

Sun d'auki tsawon lokaci suna fad'a ma junansu dad'ad'an kalamai kamin sukayi sallama wanda idan mutum ya gan su a lokacin sai ya yi tsammanin cewa sun shekara ne ba su ga juna ba,bacin kuma yau d'in nan shida kansa ya kawo ta campanyn nata kamar yadda yake yi a kodayaushe saboda soyayyar da yake gwada mata mai tsayawa a rai ne da kuma ratsa jini da tsoka da ke sake kawo kusanci mai k'arfi tsakanin d'a da iyaye.

Wayan da ta yi da mahaifinta ne ya sa ta ji zuciyarta ta cika da farin ciki sai sakin murmushi take ita d'aya akai-akai kamar wacce aka ma albishir da gidan Aljanna!

Mik'ewa ta sake yi daga zaunen da take,wanda kuma dama babu gyale a jikin ta sai d'aurin dankwali na leshin da ke kanta,warware dankwalin nata ta yi da ya sa dogon gashin ta da ke nannad'e cikin d'ankwalin nata bayyana. Ma sha Allah na furta sabada yadda gashin kan nata ma abin kallo ne! Baki sid'ik da shi da ke d'aukar ido, ga kuma tsayi har gadon bayanta. wanda kuma daga gani sosai yake samun wadatacciyar gyara na ban mamaki.

Warwaron goal din da ke hannun ta ta cire su tare da zoben da ke mak'ale a yatsar ta sannan kuma ta cire takalmin kafarta a bakin toilet din da ke cikin office d'in ta shige da addu'ar shiga band'aki a bakinta.

Tsawon minti goma ta d'auka kamin ta fito,fuskarta,hannunta da k'afafunta digar da ruwa alamun alwala ta d'auro kenan. Bedroom d'in da ke cikin office d'in nata ta shige,inda ta dauki hijjap nata ta saka tare da shimfid'a sallaya ta fuskanci alk'ibila ta tada kabbarar sallarta a nitse!

Ninke hijap din ta yi tare da nad'e sallayar ta a lokacin da ta idar da sallah, ta fito daga d'akin,duk da ba ta ganin madubi hakan bai hana d'aurin d'ankwalin nata da ta yi kyau sosai ba,sannan ta bud'e k'aramar jikarta da babu wasu shirgi a ciki ta feshe jikinta da daddad'an turaren ta tare da gyara gashin girarta da suka tarwatse sakamakon alwalar da ta yi wanda ta sake fitowa face abinta kamar a sace ta a gudu.

Wayarta ta d'auka ta duba time ta ga har karfe biyu saura,wanda kuma an zarce lokacin da ake kawo mata lunch nata da mintuna  wajen 15.

Cikin takunta na k'asaitattun mata ta fito daga cikin k'ayataccen office d'in nata da ke upstairs,zuba ma ma'aikatan da ke kai kawo a down stairs ido ta yi daga inda take kamar mai son gano wani abu mafi mahimmanci.

Mik'a mata gaisuwa ma'aikatan ke yi a lokacin da ta gama sakkowa daga matattakalar benin,ko kallo ba su ishe ta ba,ballantana su saka ran za ta ansa masu,wanda kuma hakan sam bai dame su ba saboda sanin halinta na shariya da kuma taka duk wanda ta so a duk lokacin da ta ga dama idan ka shigar harkarta.

"'Yar gatan Abbanta an fito kenan". Wani kyakkyawan matashin ingarma dake sanye da suit mai ruwan toka ya fad'a a lokacin da Zulaykha ta zo giftawa daga inda yake zaune cikin k'aramin restaurant da ke cikin ma'aikatar,"um" kawai Zulaykha ta fad'a ba tare da ta ba sa amsa ba ta yi ma kanta mazauni akan wani kujera mai kyawun gaske.

Wata ma'aikaciya ce ta k'araso wurin jikinta na rawa ta tambayi Zulaykha abin da za ta kawo mata.

Tsawon mintuna 30 ta d'auka a wajen lunch din nata kamin ta kammala,inda suka fito tare da wannan guy d'in da ya yi mata magana a farkon shigowarta mai suna _MUSTAFA_ da ya kasance p a nata.

Tare suka haura zuwa office nata bayan ta d'auko wasu files a hannun cikin office nasa da ke makwaftaka da nata,inda ya ba ta ta yi duk wasu cike ciken da ya kamata tare da sake jaddada masa kud'ad'en da zai raba ma duk wani ma'aikaci da ma'aikaciya kamar yadda aka saba sannan suka yi sallama inda ta fito tare da jikarta da kuma wayarta zuwa  bakin wata mota madaidaiciya mai kyau,ita da kanta tayi driving zuwa gidansu da ke Maitama a garin Abuja.

*vote*
*comment*
*share*
[7/20, 11:07 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...?*
     _GUGA YA HANA_
                              
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ* 

*WATTPAD@ Oum-Mumtaz123*
*INSTAGRAM@itz_me_real_oum_mumtaz*      

           *charpter 3*

********Hausawa suka ce mata da miji sai Allah,wanda hakan take,domin kuwa Abba da Mami tare suka fito suna murmushin su suna zuba k'amshi alamun sun riga da sun shirya abin su tintini(na ciki na ciki),falon da suke zama tsakanin su iya ya su suka wuce inda suka tar da Zulaykha cikin shirin wani mini skirt bakid'aya tsaya mana a guiwarta,sai kuma rigarta long sleve da ya matikar mata cas-cas da ita sai baza k'amshi take yi kanta ko d'ankwali babu kamar yadda take zama idan tana gida sai dai ta raba gashin kan nata gida biyu da ke samun gyara sosai ba kad'an ba.

Game nata na candy crush take bugawa kamar wata irin yar tsana saboda yadda take yarintar tata ba zama mutum ya ce ta kai 24yrs ba sai irin 19-20,murmushi take ta faman dokawa alamun sosai game din ke tafiya da imaninta.

"'Yar Abba har an fito kenan"? Mami ta fada a lokacin da take ma kanta mazauni akan kujerar da Abba ya zauna yana kallon 'yar tasa kuma abar k'aunar tasa fuskarsa shimfid'e da murmushi saboda yadda ta masa kyau sosai ba kad'an ba kamar mahaifiyarta.

"Sannunku da fitowa" ta fad'a ba tare da ta d'ago kanta ba saboda yadda game d'in ya tafi da imanin ta bakid'aya,agogon da ke manne da bangon falon Mami ta kalla wajen biyar da rabi amma har yanzu shuru Musty bai iso gida ba,a ranta tana fatan Allah ya sa lafiya.

K'amshin turaren da suka ji ne ya tabbatar masu da wanda ya shigo tun kamin ya yi magana,"Mamina na dawo" Musty ya fad'a a lokacin da yake ma kansa mazauni akan kujerar da Zulaykha ke zaune na 3 seater.

Hararar wasa Abba ya aika masa ya ce "Wato kai kuma Mamina ka kawai ka gani ko Babana?" Sosai kai Musty ya yi cike da jin kunya ya ce "Afuwan Abba wallahi ba haka ba ne."

"Aishatu ji min ja'irin yaro idan ba haka ba to mene ne?" Abba ya fad'a yana sakin dariya saboda yadda ya ga Musty na ta faman sussunne kai kamar wanda ke gaban sirikinsa,ita ma Mami dariyar ta yi kawai ba tare da ta ce komai ba tana bin dan nata da wani irin kallo k'asa-k'asa ba tare da su Abba da shi kansa Mustyn sun lura ba.

Ihu Zulaykha ta sake kamar wata k'aramar yarinya tana faman burburwa a wajen d'aya su yin kanta bakid'ayansu,suna tambayarta lafiyarta kuwa? Duk hankalinsu ya tashi saboda yadda ta bi ta birkice masu.

Sosai ta sake masu kukan shagwaba harda gulmammun hawayen ta da ya sa Abba sake rikicewa yana kokarin tarota don kar ta fad'i. Sai da ta bi ta gama daga masu hankali bakid'ayansu kamin ta tsagaita da borin da take musu tana binsu da kallo daya bayan daya,inda ta ga fuskokin su duk cikin tashin hankali da ya sa ta fashewa da wani irin dariyar shak'iyanci da ba ko yaushe take yi ba tana faman nuna su da dogin yatsunta masu kyan gaske.

Wani irin tukukin takaici ne ya tokare ma Mami wuya saboda ganin yadda Zulaykha ke k'ok'arin raina masu hankali kamar ta ga wasu mahauka ta cike da hasala ta ce "Amma ke dai an yi sakarar yarinya wallahi!! Ai wannan naima kike k'i d'aga mana hankali da yammar Allah kuma ki samu a gaba kamar wasu sa'annin ki kina yi mana dariya saboda kin raina mana hankali?"

Tsagaitawa da dariyar Zulaykha ta yi tana kwabe fuska kamar za ta fashe kan an ce mata sakarar yarinya! Harara Abba ya watsa ma Mami ya ce "Akan wani dalili za ki ce ma Mamana sakarar yarinya? Allah fa idan ba ki kiyaye ni ba akan Mamana ranki idan ya yi dubu saina lalata shi Aishatu! Haka kawai yarinya da gidan ubanta ki bi ki hana ta sukuni ki ce ba za ki bar ta ta yi abin da ta ga dama ba! Ki daina mini irin wannan idan kina so mu shirya wallahi."

Sosai ran Musty ya 'baci akan abinda Abba yayi ma Mamin sa duk akan Zulaykha amman haka nan ya boye nasa bacin ran ya ce "Abba ka yi hak'uri dan Allah,kuma ke ma Mami ai bai kamata akan wannan karamin abin sai kin tanka ba,ko ba ki ga cewa har yanzu ita Ummin yarinya ba ce kuma kike k'ok'arin biye mata akan wannan k'aramin abin ba?"

Mami ba ta sake magana ba saboda ganin yadda d'an nata ke mata ido alamun karta sake magana, Abba kuma gefen Zulaykha ya zauna da ta fara matsar kwalla ya ce "Me ya sa me ki ne kike kuka Mamana?" Ya yi maganar cike da rarrashi!

Da ya sa Zulaykha turo ba ki ga ba ta ce "To ni Abba ba fad'uwa na yi a game dina ba." Sai kawai Abba ya yi dan dariya ya ce "Gaskiya waya ba ki kyauta mana ba da kika sa Mamana ta fad'i wannan game da ni d'in,amma dai sai na yi maganin ka."

Haka nan Abba kwatakwata bai ganin laifin 'yarsa akan duk wani abin da za ta aikata kai kyau da akasin haka da ya dasa ma Mami tsanar yarinyar har cikin zuciyarta.

Sosai Abba da Zulykha suka shiririce Abba na tarairayarta ita kuma tana zuba masa shagwa'ba son ranta har ma sun manta da Mami tare da Musty da ke cike taf a wajen saboda ganin yadda Abba yake masu rashin mutunci akan yarsa,haka nan suka wuce d'akin shi musty din dake da nasa side d'in daban kamar za su tashi sama.

********Mik'ewa daga durk'ushe da yake ya yi yana sharar kwalla na tausayin kansa da kuma ita karan kanta matar tasa da ke k'ok'arin aikata abin da za ta iya da-na-sani zuwa gaba.

Da kansa ya shiga madafar tasu duk da irin tarin da yake yi saboda rashin sabo ya k'arashe girkin duk da bai wani iya sosai ba ya kashe itacen tare da kau da abubuwan wurin ya mai da su mahallinsa kamar yadda yake ganin Alina na yi a baya.

Gwanin tausayi haka nan ya share gidan nan tas tare da wanke duk wasu kwanikan da ke wurin saboda kawai ya faran tama gimbiyar tasa rai,ya daibo ruwa a can borehole da ke unguwar tasu ya ciccika duk wasu kayan amfanin na ruwa sannan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ya shige d'akin nata,bacci ya tadda ta na yi akan katifarta da ke lailaye da zanin gadon da ya sha ruwa a duniya sosai.

Bai tashe ta ba ya cire kayan jikinsa sannan ya wuce bayi ya yo wanka,kamin ya shirya cikin wani kayansa na yadi da shi ma daga gani ya ga duniya amma kuma a wanke suke tsaf ya yi sallah na azahar da ta kufce masa,bayan ya idar shi ma ya cire rigarsa hadi da hayewa kan gadon ya fuskanci fuskar matar tasa da ke baccinta hankali kwance ya tsira mata ido cike da tsantsar soyayyarta ya fad'a tunanin rayuwarsu ta baya kamin akai ga wannan matsayin.

********"Hmm mai ake ciki ne yanzu akoi wani motsi ne?" Mami ta tambayi Musty da ke zaune bakin luntsumemen gadon nasa ransa na matik'ar tafarfasa kamar ya yi fiffike ya je ya kakkarya Abba kowa ma ya huta akan Zulaykha.

Ajiyar zuciya mai k'arfi ya sauke kamin ya janyo wayarsa da ke kan side bed drower ya ya yi danne-dannen sa cikin mintuna uku Mami ta ji karan sako a wayarta da ke hannun ta,alert ne na zunzurutun kud'i kimanin naira million biyar Musty ya yi ma mahaifiyar tasa transfer,nan take kuwa ta naimi duk wani bacin ran da ke tattare da ita ta rasa ta fara zunduma masa albarka kamar babu gobe.

Part nasu ta wuce bacin ta saita fuskarta kamar babu abin da ya faru suka yi kici'bus da Abba da ya fito da niyyar tafiya masallaci ta yi masa a dawo lafiya ta yi wucewarta d'aki ba tare da damuwar komai ba.

Bangaren Zulaykha kuwa gani ta yi bak'on ta ya zo da magriba,wanda hakan ya sa ta sake yin wani wanka ta tsaftace jikin ta sannan ta fito zuwa harabar gidan nasu da hasken lantarki ya yi masa k'awanya kamar rana,k'ark'ashin wata rumfa ta yi ma kanta masauki kan wata grasses tana kallon sararin samaniya kamar mai tunanin wani abu.

Wasu ma'aikata ne maza dake daga can wurin gate ke zaune kan benci su ukun su suke hirar su,ganin fitowar Zulaykha ne ya sa su mai da akalar hirar tasu akan gulman mai gidan nasu wato Abba da kuma 'yarsa akan rashin adalcin da suke tafkawa a gidan da kuma inda suke aiki mana k'asa da su.

*vote*
*comment*
*share*
[7/20, 11:07 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...?*
     _GUGA YA HANA_
                              
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ* 

*WATTPAD@ Oum-Muntaz123*
*INSTAGRAM @itz_me_real_oum_mumtaz*      

           *charpter 2*

********Wanka ta fara gabatarwa,sannan ta shafe jikinta da daddad'an lotion nata mai sanyin k'amshi had'i da fesa turaren ta body spray,sannan ta sanya riga da wando matsattsu da suka kama jikinta sosai,wanda hakan ya taimaka wajen bayyanuwar surar jikinta da kan iya girgiza zuciyan 'yan maza idan suka yi katari da shi.

Gashin kanta kuma ta raba su kashi biyu ta kuma tufke shi da ribbon,sannan ta fito daga d'akin nata hannun ta rik'e da laptop nata samfarin apple da kuma wayar ta samfarin Samsung da ba ta cika amfani da shi ba.

Zaune ta tadda wata hamshak'iyar mata akan wani kujera na alfarma da ke cikin babban parlon gidan nasu,wacce kallo d'aya mutum zai yi mata ya fahimci tsantsar wadatar da ke tattare da ita na arzikin duniya saboda yadda 'yay'an banki suka ratsa ta,tana sanye ne da wani d'anyen leshi y'an ubansu,sannan fuskarta kuma sanye yake da wani glashin ta mai karama idanuwa (medicated).

"Momina sannu da hutawa" Zulaykha ta fad'a a lokacin da ta yi ma kanta mazauni a gefen wannan matar data kira da Mamy , "yawwa sannu da dawowa uwar masu gidan,kin dawo lafiya?"  Matar ta tambayi Zulaykha da ke danna wayarta.
"lafiya" Zulaykha ta fad'a ba tare da ta kalli matar ba,wanda hakan ya sa matar yi ma Zulaykha wani irin kallo an kasar ido tana taunar labbanta.

Sun yi zaman kurame ne a wajen ko waccen suna famar danna waya inda daga k'arshe ma dannar system nata Zulaykha ta fara yi inda take ta faman settling na wasu files da Musty ya aiko mata tun daren jiya,bacci ne ya d'auke ta a wajen ba tare da ta ankara ba,wanda hakan ya sa Mami mik'ewa daga kan kujerar ta gyara mata kwanciyar ta badan ranta ya so ba,sai dan babu yadda ta iya,ta yi wucewarta d'aki.

******** Wata mata ce fara tas da ita kyakkyawa na k'in k'arawa ke tsaye bakin wani madafa ta langa- langa da hayaki yabi ya turni ke cikin madaidaicin gidan take ta faman zuba sababi da ke had'e da madarar tsiwa ma mijinta mai suna Waali da shi kuma yake rakube a gefe d'aya kaman wanda yake tsoron ta fuskarsa na bayyana tsananin tashin hankalin da yake ciki kamar ya yi kuka saboda soyayyar matar tasa da ke ta faman azaftar da shi da ya sa shi gagara d'aukan mummunar mataki akan ta dangane da irin cin kashi da take masa.

"Wallahi ni ban ta'ba ganin mutum mai mataccen zuciya irin taka ba Wali ,ga wannan shegen bakin talaucin naka da nake da tabbacin harda shi wajen ba da gudun mawar mutuwar zuciyarka,aure ne na ce ba na yi ka ba ni takarda ta in tafi inda ake maraba da ni,da za a ba ni na ci mai kyau,na sha mai kyau na kuma kwana a mai kyau idan da hali ma har na tsakuro maka wani abin da zai fishe ka a rayuwa amma kana man wannan bakin ciki mararan a filin Allah? Gaskiya ni kam na gaji ka san yadda za ka yi da ni ehe! Aure ne na ce a yi a a sauwak'e mini na huta da wannan azababbiyar talaucin da ya-k'i-ci-ya-k'i- cinyewa!"

Wannan matar ke fadi tana ta faman girgiza kwankwaso had'i da murguda baki ga kuma uban gumin da ke tsatstsafo mata ta farar fatar ta saboda hayak'in itacen daya tirnike gidan da kuma zafin ranar da ta hade wuri guda ya had'e kuma da yanayin zafin cikin garin Maiduguri da ake ya ba da wani irin fitinannen zafi mai gasa ma mutum aya a hannu.

"Haba ~ALINA~! dan Allah ki yi hak'uri akan wannan k'udirin naki,na san Allah ba zai barni haka nan ba,sabida ke ma shaida ce dangane da yadda nake ta fafutukar neman aiki amma abin ya-k'i-ci-ya-k'i- cinyewa saboda yanayin hali irin na k'asar mu! Idan kika matsa mini na sake ki ya kike so na yi rayuwa ne? Kin san ba ni da kowa! Mamana,Babana da kuma yan uwana duk ban da su sai ke kad'ai kika rage man idan ke ma kika kufce mini wa zan nuna ma duniya a mazaunin nawa Alina? Dan Allah ki rufa mini asiri na rok'e ki ba dan ni ba sai dan Allah ki dubi girman irin maraicin da zan afka idan ke ma kika guje ni"

Wali ne ya yi wannan maganar wasu irin hawaye masu zafin gaske na zubowa daga cikin idanunsa a lokacin da yake durk'ushe a wannan guri yana bai ma Alina hak'uri kan kar ita ma ta tafi ta bar sa maraicin ya yi masa yawa.

Tabbas idan ta ce ba ta ji tausayin sa a lokacin ba ta yi zuciyarta karya,amma kuma sai dai kwad'ayin son abin duniya da kuma hangen nesa na rud'ar ta, har ma yake ingizata izuwa ga hanyar da zata yi da-na-sani daga baya,wanda hakan ya sa ta d'an shafa kanta lafiya ta buga wani uban tsaki ta fad'a d'akin ta ba tare da ta sake wai wayar tuwon dawar da take yi ba cikin madafar.

********Sai wuraren la'asar kamin ta farka daga baccin da take yi wanda a lokacin ma wajen karfe hud'u da kwata,d'akin ta wuce sannan ta shiga bayi ta d'auro alwala tare da shifida sallayarta a d'aki ta tada sallar la'asar nata.

Dirin motocin da ta jiyo ne a lokacin da a idar da sallah ya sa ta fitowa da gudun ta saboda ta san Abbanta ne ya dawo gida,haka nan ta mak'alk'ale Abban nata tun daga filin gidan nasu da ke kawace da shukoki na fulawowi masu kyan gaske kamin suka shigo. A falo suka tarda mamy ta sake shek'o wani wankan sai zuba k'amshi take abinta fuskarta na fidda zallar murmushi tana yi ma mijin nata sannu da zuwa,sai kuma ta gintse sa a lokacin da ta ga yadda Zulaykha ta mak'alkale mahaifin nata kamar za ta koma cikinsa shi kuma yana biye mata.

"Maman Abbanta ki bar shi haka nan ya huta mana idan ya so sai ki dawo ku sake gaisuwar ko?" Mamy ta fad'a fuskarta da murmushi zuciyarta ba ki kirin kamar ya yi bindiga.

Aiko da shagwaba Zalaykha ta turo baki ga ba idanunta na tara ruwan hawaye wai akan mi Mami za ta ce tabar Abba ya huta bacin ta san yadda ta yi missing nasa da yawa.

Take kuwa Abba ya rik'e wa ya fara lallashin ta yana fad'in "yi shiru babynah,rabu da Mami yau tunda ta saman ke kuka sai na yi maganinta!! maza share hawayen ki"

Haka nan Abba ya samu da 'kyar Zulaykha ta yadda ta yi shurun kamin ya kallo inda Mami take da niyyar sauke mata bala'i amma kuma sai dai wayam bai ga komai kama da ita ba a wurin sai ma'aikatan suna cikin gidan da ke ta faman kai kawo saboda hada- hadar girkin dare.

K'wafa ya yi kamar wanda aka masa wani babban laifi kamin ya kama hannun Zulaykha har d'akin ta ya kai ta ya kuma tabbatar da cewa ta shiga wankan da ta ce masa za ta yi kamin ya wuce zuwa tasa turakar da ya tadda Mami ta cika ta yi fam kamar filowar da aka sama yis saboda haushin da su Abba suka ba ta yau d'in nan daga shi har yar tasa.

Harara Abba ya watsa mata ya ce "Allah idan ba ki kiyayi ba ta ma Mamana rai ba a cikin gidan za a jimu da ke _AISHATU_ dan kawai yarinya ta ma mahaifinta oyoyo sai ki bi ki wani nuna cewa kamar ba daidai ta yi ba? Kin fa san hali na akan Zulaykha Allah zan iya 'batawa da koma wane ne! Dan haka sai ki kiyaye ni na fad'a maki"

Abba ya yi maganar bakinsa har kumfa yake yi saboda masifar da ke cin shi wai an ta'ba masa 'yar lele! Hmm wani irin takaici ne ya lullube Mami ita ma cike da hasala ta ce "ai da ma dole ka ce haka Alhaji,idan ba haka ba kawai dan na yi magana na ce ta bar ka ka huta ka ci abinci idan ya so sai ku yi zaman naku shi ne na yi laifi ita kuma har da 'bare baki kuma a ce ba zan yi magana ba??? Akan ka aka fara haihuwa ne da ma duk wanda ka ga dama rashin mutunci akan yarka? Ko aka ce maka ni d'in ma ban san zafin haihuwar ba ne da kake k'ok'arin gaya mini magana?? Idan ka san haka nan za kana mini akan 'yarka mai zai hana ka sauwak'e mini na tafi inda za a yi maraba da ni ba wai a wulak'anta ni ba?"

Mamy ta karashe maganar cike da tsantsar masifar da ke cinta tintini dangane da Zulayka tare da mahaifinta. Abba kuwa kalamanta sun yi tasiri a zuciyarsa, amma kuma soyayyar da yake ma 'yar tasa ba zai sa ya iya goyon bayan wani ya bar nata ba ko da kuwa a ce ita ce mai laifi,dan haka sai kawai ya buga tsakin sa ya wuce ainahin bedroom nasa da ke mak'waftaka da na Mami.

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM Mumtaz ✍️*
[7/20, 11:07 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...?*
     _GUGA YA HANA_
                              
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ* 

*WATTPAD@ Oum-Mumtaz123*
*INSTAGRAM@itz_me_real_oum_mumtaz*      

           *charpter 4*

******** "Hmm,wallahi Alhaji na gidannan yanayin abin da bai da ce ba kwata kwata a cikin gidannan,kuna ganin yadda yake zuba ma mutane rashin mutunci a kan waccan yar tasa? Wanda kuma daga ciki har matar gidan da babu ruwan ta bai k'yale ba ballantana kuma oga Mustapha?"

'Daya daga cikin su ne ya cafe zancen da fadin "Ai idan ta wannan fannin ne da sauk'i ma! Kuna gani fa tsabagen mugunta da rashin imani irin na mutumin nan yanzu muna cikin watanni na biyar babu albashinmu bacin kuma yasan cewa kaf cikinmu babu wanda ba shi da iyali,kullum cikin aiko mana da sak'o yake wai mu yi hak'uri yana kokarin kashe wata 'yar matsala ne ba shi da kud'i alhalin kuma jiya-jiyan nan kuna gani ya saya ma 'yarsa mota ta kusan million asshirin bacin wanda yake saya mata duk kusan ko wani wata amma dan an ga mu ba mu da gata sai ana mana wasa da hankali"

Ya yi maganar cike da tsananin takaicin halin uban gidan nasu,dayan da tunda suka fara bai yi magana ba ne ya buga wani uban tsaki kamar harshensa zai tsinke shi ma cike da takaici ya d'aura da nasa fadin "Ai mutumin nan idan dai a haka ya ce zai ci gaba da tafiyantar da rayuwar sa ba zai gama da duniya lafiya ba daga shi har fitsararriyar 'yar Tasa! Akoi fa ranar da wata kanwata ba ta da lafiya shekarar da ta gabata na je wurin mutumin nan ina masa rok'o da magiya kan ya taimaka man da kud'in da zan kai k'anwar tawa asibiti idan ya so a cire cikin kud'in albashina,ya ce man na je waje na jira sa kan zai ba da a ba ni dubu hamsin d'in kamar yadda aka buk'ata a asibitin,wai kawai ina jira akawo man kawai na ga dubu biyar wai ya ce na yi hak'uri kud'in ba zai kai ba dake wurin sa? Wanda daga k'arshe ma sanadiyyar rashin aikin da aka ma k'anwartawa ne Allah Ya anshi rayuwarta!"

"Yo ai da ma haka nan halinsa yake,alk'awari da rashin cikawa kam ba daga baya ba,sai fa idan Hajiya Mami ce ta ji tausayinmu take dan taimaka mana da wasu yan kud'ad'e saboda kashe wasu larurinmu,ai matar nan sai da mu ce Allah ya saka mata da alheri ba dai kirki da hak'uri ba!"

Haka nan suka zauna suna ta sakin zance kan abubuwan da ake yi a gidan da bai kamata ana masu ba,d'aya kuwa cewa ya yi shi kam jira yake a biya sa kud'insa tas ya canza wurin aiki domin kuwa ba zai iya wannan kasada ba na zaman gawar shanu babu wani ci gaba.

Abba da Musty ne suka shigo gidan sanye da jallabiya bayan sallar isha'i,wanda suka tar da Zulaykha zaune a inda take tun d'azun ba tare da ta motsa ko nan da can ba. "Sannun ku da zuwa Abbana"  Ta fad'a a lokacin da ta gyara zaman ta daga kishingid'en da ta yi tana mai kallonsu da murmushi a fuskarta da ba kasafai yake ba ce wa ba!

"Yauwa sannu da hutawa Mamana, nan kike zaune kenan?" Abba ya fad'a yana mai shafa mata kanta fuskarsa da murmushi shi ma,"Ummi nan kike zaune kenan?" Musty ya katse masu 'yar guntuwar hirar tasu yana mai ma Zulaykha wani irin shegen kallo ba tare da sun lura da hakan ba saboda da hankalin su bai ta'ba kawo musu wani abu makamancin hakan ba ko da wasa.

Sun dan ta'ba hirarsu a wajen wanda suka d'auki tsawon lokaci kamin suka wuce zuwa cikin babban parlon nasu,sun tar da Mami da wayarta a hannun ta zaune kan luntsumemen kujerarsu ta alfarma da ke cikin parlon.

Kamar babu abin da ya faru d'azu sosai ta sake masu tana masu sannu da zuwa had'i da tarairayar Zulaykha da ke narke jikin Abbanta tana buga game d'in ta na gado.

Abinci Mami ta gabatar musu tuwon semo da miyar d'anyen kubewa da ya sha namar rago daga-daga a cikin miyar yana tashin k'amshin mai na shanu.
Sosai kuwa suka ba je cikinsu suka kwashi gara domin kuwa kaf gidan idan mutum na son ganin cin abinsu da yawa har haka to had'a musu kalar wannan abincin,bacin sun gama zama suka yi a parlo suna hirar su na yau da gobe kan lamarim duniya,sai wajajen 11 kamin suka yi sallama kowa ya wuce zuwa mak'wancinsa.

Sai da ta yi wanka ta kintsa cikin sexy sleeping dress nata had'i shafe jikin ta da daddad'an lotion da ke sake fito mana da madarar kyau na asalin kalar fatar ta,kamin ta d'auko wayarta daga cikin caji bayan ta lume cikin lallausar bargon ta,kan luntsumemen gadon nata.

Datar ta ta kunna inda ta laika shafinta na sada zumunta wato instagram. Saboda post da aka yi na pics tare da vedio take bi d'aya bayan daya tana kallo,idan kuma ta ga wanda ya birge ta takan musu like kamin ta wuce.

Cikin wani irin slow motion ta mike daga kwance da take zuwa zaune,hannun ta rike da wayar tata da ta tsura ma ido sosai saboda ganin sunan ~ZULAYM AHMAD SHUWA~ ya yi appearing a cikin jerin mutanen da suka yi post na photo.

Tsaye yake jikin wata langa-langa da gaba d'aya tsa tsa ya gama masa dameji saboda yadda ya ga duniya,jikin sa kuwa sanye yake da wani d'anyen yadi ruwan sararin samaniya mai saukin kud'i,inda kuma hannun sa ke rik'e da na wata kyakkyawar budurwa da ke gefensa suna kallon tsakiyar idanun junansu a lokacin da aka masu wannan photo duk,fuskarsu kuwa kallo daya idan mutum ya yi mata zai fuskanci cewa lallai ba k'aramin farin ciki suke ciki ba a dai-dai  wannan gabar.

Fari ne fat da shi tsayayyen namiji,mai faffad'an k'irji,idanunsa kamar sexy eyes,sannan kuma yana da dimple ta ko wanne gefe,ga kuma wani irin kwantaccen saje da ke lafe akan kuncinsa da ke shek'i irin na usil shuwa Arab.
La'b'ban bakin sa kuwa sun kasance pinkish colour ne sosai ba kad'an ba wanda haka kuwa ba k'aramin sake k'awata masa kyakkyawar fuskarsa ta yi ba,gashin girarsa ma kad'ai abar kallo ce saboda yadda yake bak'i sid'ik da shi da ya kusan had'ewa wajen guda da na d'ayan gefen,wanda idan mutum ya yi masa kallo d'aya tabbas ba zai so d'auke kansa ba saboda had'uwar tasa ta zarta zuwa duk inda mutum ke tunani!

Wani irin ajiyar zuciya mai k'arfi ta sauke had'i da lumshe tsumammun idanunta tana jin yadda zuciyarta ke dokawa kamar za ta faso k'irjin ta ta fad'o kasa. Sake ware idanun ta ta yi kan pic d'in a karo na biyu,inda ta ga ya ruwa kalmar "Alhamdu Lillahi" Daga can kasa.

Ta d'auki tsawon lokaci tana kallon mutumin da ta shafe kusan watanni biyu ba tare da ta sake kallon wani sabon post da ya dangance sa ba. Wanda har ta fid da rai da tsammani amma sai ga shi Allah cikin ikon sa a lokacin da ba ta yi tsammani ba ya sake dawo mata da "sanyin idaniyarta" Duk da tana da tabbacin shi wanda take hakan domin sa bai san da wanzuwar wata halitta mai kama da ita ba a fad'in duniya.

Tun wajen watanni takwas da suka wuce taga account nasa a shafin ta na insta garin shige-shigenta,harma takai ga tayi following nasa sabida yadda ya tafi da imaninta cikin lokaci kankani! Abin da ta fara yi shi ne bin post nasa tun daga farko tana kallo d'aya bayan d'aya tare da like saboda yadda yake birge ta.

Sannan kuma wacce ke jikin wannan hoton tabbas jikinta na ba ta tana da kusanci mai k'arfi da shi Zulaym din saboda duk cikin pic d'in da yake post guda daidai ne ba ta ciki,wanda kuma haka nan kawai Zulykha take ji yarinyar na masifar birgeta har cikin jini da tsokarta, duk da ma dai a wani gefe na zuciyarta tana kishi da yadda take ganin su kusan ko a wani lokaci tare da mutumin da tun a "Kallon farko" ta ji ya sace mata zuciyarta da bai sa ta kalli wasu mazajen a matsayin maza sai dai mata-maza.

Sai da ta gama tunane tunanenta tsaf,kamin ta koma wajen kwanciyarta bacin ta tofa addu'ar bacci ta rungume wayar tata,a haka nan wani daddad'an bacci ya yi awon gaba da ita mai cike da mafarkan Zulaym.

********'Yan asalin cikin garin Maiduguri ne a unguwar Madina,wanda akasarin mutanen cikin wannan unguwa kuwa yarensu shi ne Shuwa.

Waali da Alina na d'aya daga cikin mazaunan wannan unguwar tare da iyayensu da kuma yan'uwansu,wanda suka kasance yara wa da k'ani ne,wato 'ya'yan maza-biyu.

*vote*
*comment*
*share*

*OUM MUMTAZ✍🏿*
[7/20, 11:07 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA*      

           *charpter 5*

******** Washe gari.
Cike da tsantsar kasalar da ta rufe ta a daren jiya ta zuro kyawawan k'afafunta daga kan gadon,bacin ta tsurama agogon da ke manne a d'akin nata ido d'aya nuna mata k'arfe shida har da rabi,ga shi kuma ba ta yi sallar ta asuba ba,saboda makarar da ta yi.

A dan gaggauce ta ida mik'ewa kan k'afafunta zuwa cikin toilet,brush ta fara yi had'i da d'auro alwala ta zo ta gabatar da sallar ta raka'a biyu,ba ta tsaya yin doguwar addu'a ba ta mik'e had'i da tube kayan jikinta tas,ta d'auro wani ficicin towel ta shiga wankan da ya dauke ta tsawon 30mins.

Zama ta yi a bakin mirrow na d'akin da ke shak'e da kayayyakin ta na shafe-shafenta,sai da ta kammala kuwa tsaf,kamin ta gyara gashin kanta had'i da sake tifke shi wuri guda,wata doguwar riga ta atamfa ta zak'ulo daga cikin kayanta,sosai kuwa kayan ya zauna mata a jikinta ya yi das,daga sama ya kame ta,sannan kuma ta k'asa ya bage wanda aka fi sani da A shape.

In dai ta fannin d'aurin d'ankwali ne kam ba daga baya ba,nan da nan ta nad'a d'aurin ta mai kyawun gaske kamar irin na saya a kasuwa.
Wayoyinta tare da kwamutsan tafiya office ta d'akko su baki daya bayan ta saka wani takalmin ta na fashion mai dan tudu sosai take bulbula k'amshin turaren ta fuskar ta na ta faman shek'i duk da babu wani kwalliya idan aka d'auke powder,da kuma lipsglo.

Ta tar da Abba da Mami tare da Musty zaune kan dining suna breakfast,ko wannen su kuwa sai zuba k'amshi yake alamun su ma sun fito cikin shirin tafiya wajen aikinsu ne.

Side hug ta ba ma Abbanta 'bacin ta gaishe sa,kamin ta yi ma kanta mazauni akan kujerar da ke gefen sa ta had'a ma kanta tea a lokacin da take gaisar da Mamy tare da Musty.

"Ai na d'auka ba da wuri yau za ki fito ba Mamana" Abba ya fad'a a lokacin da yake kur'bar tea d'in da ke hannun sa yana sakar mata murmushi,ita ma murmushin ta mayar masa da martani a lokacin da take danna d'ankali a karamin bakin ta ta ce "A kwai wani abin da zan dubo ne yau ya sa zan shiga tin da wuri."

Had'a ido Mamy da Musty suka yi, a zuciyarsu,suna tunanin shin mai zai sa ta je wajen aiki? Duk da da ma sun san ba ta cika yin latti ba saboda tare suke tafiya kusan koda yaushe da Abbanta.

Sun kammala cin abincin nasu tsaf,ba tare da ko wannensu ya sake magana ba,Musty ne ya fara wuce wa wajen aikin bayan ya masu sallama had'i da ce ma Ummi "Sai kin iso"

Har bakin mota Mamy ta masu rakiya hannun ta rike da brief case na Abba,daya daga cikin mutanen daya dauka suke tsaronsa da kuma gidan nasa yana biyan su albashi dik karshen wata ya bud'e masu k'ofa.

Gidan baya suka shiga,sannan driver ya fice daga gidan tare da rakiyar motoci guda biyu masu d'auke da karfafan maza hannayen su kuwa rik'e take da bindiga,sai kuma a can baya d'aya daga cikin su ne ya biyo bayansu da motar Ummi saboda ba ta jiran Abba a lokacin dawowa.

Har cikin ma'aikatar tata Abba suka shiga da ita,sai mik'a masu gaisuwa ake cike da girmamawa,amma kuma fa a zuciya ban da tsine masu babu abin da suke yi saboda gani suke Abba ne ke d'aure ma Ummi gindi har take tafka masu rashin adalci. Domin kuwa albashinsu su ma sosai ake rage masu a wannan ma'aikatar akan wai za a biya su daga baya,ga shi kuma yawancinsu da wannan aikin suka dogara. Wanda kuma da yawa daga cikin su su ma sun ci alwashin ana biyan su kudin su sun bar aiki a wannan campanyn,kowa ya kama gabansa domin kuwa ba su iya zama inda babu cigaba.

Musty ne ya k'araso inda suke a matsayin sa na p a nata ya k'arbi abubuwan hannun ta ya wuce mata da su office,ita ma ta bi bayansa bacin sun yi sallama da Abba da take jin kamar wanda zai mata k'ololuwar nisa saboda shak'uwar su.

"ina so ka kawo man dik wasu information din kudin dake fita da shiga a asusun wannan campanyn." Zulaykha ta fad'a ma Musty da ke tsaye daga can gefe kad'an. "Ok" Musty ya ansa mata kamin ya sa kai ya fice.

Cikin abin da bai gaza mintuna goma sha biyar ba kuwa ya kawo mata duk wasu abubuwan da ya kamata,kuma ga shi nan komai dai-dai ne yadda ya kamata babu matsala ta ko wanne fanni.Wasu cike-cikenta ta yi akan wani file kamin ta mik'a masa ta d'aura da fadin "Ga shi nan,ko wanne ma'aikaci na k'ara masa albashin sa da kud'i naira dubu goma,sai ka had'a meeting ka shaida masu kamar yadda ka saba saboda ni ka san ba zan iya halartar irin wannan wuraren ba saboda ban son hayaniya! Kai kuma na k'ara maka naira dubu ashirin a kan naka."

Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar Musty,wanda har ma ya gaza 'boyuwa bisa ga kyakkyawar fuskarsa,yana zuba mata godiya kamar ya ari baki,nan ko farin cikin nasa da biyu ne.

Sai da ya fice daga office d'in kamin ta sauke ajiyar zuciya,tana mai imagining yadda ma'aikatan za su yi farin-ciki idan suka ji wannan batu na k'arin dubu goma-goma akan albashinsu.

Wayar ta da ke cikin jika ta d'auko,had'i da unlock na wayar ta shiga wajen gallery,Hoton Zulaym Ahmad Shuwa da jiya ta d'auka a insta ta tsura ma kyawawan lips nasa idanu tana mai jin wani irin yanayi mara misaltuwa na yawo a jikinta.

********Baban wali shi ne babba,sai kuma mai bi masa wato mahaifin Alina,inda suke zaman lafiya sosai da iyalan su,sannan kuma Wali da Alina su kad'ai iyayen nasu suka haifa,wanda hakan ya sa aka d'ai bi gatan duniya suka zu'ba masu duk da kasancewar su din ba wasu masu arzik'i ba ne na a-zo-a-gani amma Alhamdulillah tunda suna da na rufin asiri,domin kuwa Wali ma ya yi karatunsa a jami'ar Maiduguri fannin business,inda ita kuma Alina ta tsaya a matakin diphloma a Ramad da ke cikin Maiduguri.

Soyayya ce sosai tsakanin Alina da Waali tin suna kanana,wanda da suka girma sai abin ya sake kankama ya rikide daga soyayya ta 'yan uwan taka zuwa soyayya ta aure. Wanda hakan kuwa sosai ya yi ma iyayen dad'i.

Har ma aka saka lokaci na auren su tare da amincewarsu inda bayan aure a cikin gidan iyayen nasu aka ware masu nasu kewayen a can unguwar Madina,saboda har zuwa wannan lokacin Wali bai samu aikin gomnati ba,amma yana shiga kasuwa tare da iyayensu,wanda hakan ya sa abubuwa na rayuwar yau da kullum kan zo masa cikin sauk'i tare da matarsa,kuma 'yar uwarsa abar k'aunarsa.

The first matsalar da suka fara fuskanta a yanayin zaman takewar su daga Alina ne,domin kuwa ita da ma tun fil'azal irin yan matan nan ne masu matikar son abin duniya da suka d'auke ta da fad'i,wanda dama tun can da halin ta,abin da ya sa bai fito fili ba ne har aka shaida saboda yadda mahaifiyarta ke tsawatar mata ne in ba haka ba da kuwa ta yi ta'bargazarta tun tana budurwa kamin aurensu.

Sosai kuwa hankalin Waali yake tashi idan ta buk'aci abu daga wurin sa ga shi kuma ba shi da halin yi mata,wanda muddin bai yi mata ba a ranar wuni zai yi yana kwasan takaici saboda rashin kunyar da take shuka masa,amma ko daidai da rana d'aya bai ta'ba barin wata k'ofa da iyayen su za su gane ba sabida son da yake mata.

A sanadiyyar 'yan fashin da suka fad'o masu unguwa ne cikin dare suna bin gida-gida hadi da yashe su Allah Ya yi ma mahaifansu mazan cika wa saboda yadda suka ba da k'arfinsu akan k'in yadda a keta ma matansu haddi a gaban idanunsu,wanda hakan ya fusata 'yan bindigar suka sakar masu harbi da a wurin ba su sake motsawa ba sun ansa kira na Ubangiji.

Sun yi kuka iya kuka,tare da addu'ar Allah Ya bi masu hakkin su akan mutanen domin kuwa tuni sun tsere kamin 'yansanda su k'araso unguwar domin kawo masu agajin gaugawa.
Haka nan suka cigaba da kula da iyayen nasu da ke cikin tsananin damuwa dangane da mutuwar iyayen nasu. wanda zuwa wannan lokacin Alina ma ta jinginar da mugun halinta a gefe saboda alhinin rasuwar iyayen,wanda hakan kuwa sosai ya yi ma Waali dad'i.
[7/20, 11:07 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA*    

           *charpter 6*

********Janye idanunta da suka fara tara ruwan hawaye ta yi daga kallon pic na Zulaym  da ke tare da wannan yarinya da a kullum,kuma a koda yaushe,take ganin su tare ta yi,tana mai jin yadda zuciyarta keta faman kai kawo.

Flat ta kwantar da kanta bisa ga table d'in da ke gaban ta bacin ta ture kwamutsan kai a gefe guda,wasu irin zafafan hawaye ne suka safkowa daga cikin idanunta saboda wahalalliyar soyayyar mutumin da bai san zaman ta a fad'in duniya ba ya cika mata zuciya kamar wacce ba za ta kai labari ba.

Sosai take kuka k'asa-k'asa saboda jin yadda zuciyarta ke mata zafi dangane da ganin yadda duniyar Zulaym ke cike da soyayyar wannan yarinya da ko sunan ta ba ta sani ba,kishin wannan yarinya ya samu mahalli mafi girma cikin zuciyarta k'warai da gaske! Amma kuma sai dai soyayyar yarinyar da ke dank'are cikin zuciyarta tun a kallon farko da ta yi mata a photo bai gushe ba.

Sai da ta yi kuka ta gaji dan kanta kamin ta tsagaita tana mai jin tsananin ciwon kai na rufe ta,da k'yar ta samu damar gabatar da sallar azahar a wannan ranar saboda yadda kan ta ke masifaffen yi mata ciwo kamar ya rabe gida biyu dalilin kukan da ta yi.

Ga shi kuma babu wanda ya san halin da take ciki ballantana a kawo mata agajin gaggawa,ji da ta yi numfashin ta na k'ok'arin barin jikin ta ne ya sa ta danna k'ararrawa dake gefen ta da zai isar na sako na neman gaggawa zuwa ga office na P A da ke mak'waftaka da office d'in nata.

Sai kuma akaci rashin sa'a a lokacin,domin kuwa Musty bai nan,ya tafi cin abinci na lunch cikin restaurant da ke ma'aikatar,wanda hakan ya sa tun tana fahimtar inda take,har ta kai ta daina fahimtar komai saboda yadda zuciyarta ke faman ciwo kamar ranta zai fita,da kad'an-kad'an numfashin ta ya fara barin jikin ta har ma ya zamana komai ya k'are babu Zulaykha babu dalilin ta.

********Sunkuyar da kan sa ya yi a gaban mahaifin nasa da ke kallon dan nasa cike da tsantsar so da kuma kauna,fuskar dattijon kuma cike take da murmushi na zallar farin ciki kamar me?
"Ban fa ji abin da ka ce ba *Yaya*,ko za ka sake maimaita mani?"

*Babi* ya fad'a yana mai kafe dan nasa da ke ta faman sussunne kai kamar wani tsohon Bafilatani saboda kunyar sa,duk da kasancewar sa d'a namiji, gimtse dariyar da ke neman zuwar masa Babi ya yi ya ce "Kai nake sauraro fa Yaya?"

Sumar kansa da ke kwance lup-lup Yaya ya tusa hannun sa yana susawa had'i da hargitsa su,suna koma wa su sake kwanciya kamar ba a lokacin yake hargitsa su ba,kamar ya nitse cikin kasa,yau shi kam *HUSNA* ba k'aramin sashi a uku ta yi ba wallahi,da ya san haka ne da bai kawo kansa wajen Babi ba yau d'in nan sai idan ya shirya.

"So tunda da ma zuwa ka yi ka sa ni a gaba kana man susar kai kamar sabon kamu ka iya tashi ka yi tafiyarka ni ma ina da abinyi ko?" Babi ya fad'a a lokacin da yake k'ok'arin mik'ewa.
Cike da marairaicewa ingarman matashin da zai kai kimanin 34yrs a duniya ya rik'o k'afar mahaifin nasa,yana kwabe fuska kamar ya fashe cike da kasalalliyar muryarsa mai dad'in sauraro ya ce "Babi ka tsaya mana waii!"

Dawowa ya yi kuwa ya zauna had'i da fad'in "na ba ka mintu biyu ka yi magana da wuri saboda ina da wurin zuwa."

"Babi dama..dama...dam..." Katse shi Babi ya yi da sauri ya ce "Da ma me Yaya?"
"Husna ce ta ce wai in ce maka a yi a mana aure." Maganar ta fito a fusge ba tare da ya shirya ba, wanda yana gama fada da sassarfar sa kuwa ya ida ficewa daga d'akin mahaifin nasa bacin ya dire batun sa saboda masifaffen kunyar da ta kama sa.

"Ja'irin yaro!! Wannan kunya haka na rasa daga inda ka samo shi wallahi,a ce mutum sai kunyar tsiya kamar Fulanin farko?" Babi ke maganar yana mai sakin dariya saboda abin da Yaya ya gama fad'a masa a yanzu,wanda kuma ya jima yana mararin jiran wannan ranar dama.

Fitowarsa a d'akin ne kamar wanda aka hankado sa suka ci karo da *HUSNA* da duk abin da aka fad'a karaf a kan kunnen ta. Wani irin rikitaccen kallo ta jefa masa hawaye na taruwa cikin idanunta saboda jin irin sharrin da yaya ya mata wurin Babi.

Waigawa gefe da gefe ya yi,ya tabbatar babu mai kallonsu cikin gidan,bai bari ta yi maganar da ke k'ok'arin fitowa cikin bakin ta ba,ya toshe mata baki had'i da janyo hannunta suka fad'a d'akin sa da ke madaidaicin cikin gidan nasu saboda ganin ana k'ok'arin bud'e labulen d'akin *AMMA*.

Ai kuwa suna idasa shigewa cikin d'akin kamin ya ce wani ta fashe masa da wani irin kuka,da mutum na gani zai gano na tsantsar jin haushi ne mai tafe da zazzafar soyayya take masa. Marairaice fuska ya yi sosai had'i da rik'o dukkannin hannayen ta,yana lalumo cikin idanunta amma ta k'i yarda su hada ido. Saboda kukan da take masa,wanda mutum ko kana cikin d'akin ba za ka fahimci cewa kuka take yi ba,sai shi d'in da ake yi dominsa.

********A haka nan sukaci gaba da rayuwar su dadi da babu dad'i,wanda kuma a wannan lokacin ne Alina ta sake fito da mugun halinta na kwad'ayi da son abin duniya,duk abin da Wali ya kawo mata da sunan ya birge ta sai ta kushe abin da sunan sam bai birge ta ba,saboda ita ai ba haka nan ta saba gani ana kawa ma wasu k'awayen ta ba,ga shi kuma a wannan lokacin kamar abin sihiri sam babu riba mai kyau dangane da shagon war kasuwancin sa.
Wali yana sayar da takalma da ke cikin kasuwa ta Sunday market da ya gada daga wurin mahaifinsa.

A wannan lokacin ne kuma Maman Wali ta fara fama da matsala ta ciwon koda,an je asibiti an mata duk wasu abin da ya kamata saboda yadda abin ya girmama har ana k'ok'arin yi mata dacen ko da,kuma kodar Wali guda d'aya za a saka mata,sai dai kuma matsalar da suke ciki na rashin kud'in aikin ne ke masifar daga masu hankali,wanda sai an saka ranar da za a yi aikin sai kuma matsalar rashin kud'i ya sako su a gaba a sake dagewa.

Inda ta kai ta kawo sai da Wali ya ciyo ma kansa zunzurutun kud'i na ba shi da za a yi ma mahaifiyarsa aiki da shi,da shike Allah bai yi kan za a yi wannan aikin ba,shi da Iyami(mmn Alina) sun yanke kan washe gari zai je ya yi payment na kud'in cikin dare Allah Ya anshi ran mahaifiyar tasa.

Hankalin su Iyami a lokacin ba k'aramin tashi ya yi ba k'warai da gaske! Ba ma kamar Wali da ya zama marayan Allah gaba da baya,babu uwa babu uba,gashi kuma babu dangi! Wayan da suka rage masa a yanzu da zai iya buga kirji ya kira a mazaunin nasa matar sa ne da kuma Iyami.

A wannan ga'bar kam sosai Alina ta tausaya ma mijin nata,wanda ita ce ke kwantar masa da hankali idan hadi da tausar zuciyar sa,wanda kuma dama tun can fa tana son mijinta,kawai kwad'ayin abin duniya ne ke rud'arta tana yi masa iya shege son ranta.

An kai Mamansa gidan ta na gaskiya,inda aka yi zaman makoki na tsawon kwanaki bakwai kowa ya watse. Wanda a lokacin ne kuma abubuwa ke sake dame ma Wali ta fannin tattalin arzik'insa suna sake komawa baya,wanda hakan ya sa shi fara raba takardunsa wajen neman aikin gomnati ko Allah zai sa ya dace ta wannan fannin.

Shi ne ke kula da ci da sha na iyami tare da matar sa,da bayan mutuwan ta sake fito da sabon salon ta kullum cikin shuka masa rashin mutunci take,shi kuma bawan Allah ban da hak'uri babu abin da yake bata,saboda gani yake kamar rashin arzikin nasa laifin sa ne,ba Allah ba ne ya so ya gan sa a hakan. A halin yanxu shekara biyar kenan da auren nasu amma ko 'batan wata ba ta ta'ba yi ba.

Wannan kenan!

Ajiyar zuciya mai karfi ya sauke bacin ya gama tunanin asalin su daga shi har matar tasa,wanda shi bai san ta inda Alina ta d'auko wannan halin nata ba kwata-kwata.

Tsakin da ya ji k'asa-k'asa ne ya sashi kallo kyakkyawar fuskarta da sauri,zaune ya gan ta akan gadon nasu tana ta faman yatsina fuska alamun yunwa ce ke kwakular ta,amma tsabagen taurin kai irin nata ita ta rantse yau ba za ta ci tuwon dawa ba,in ba shinkafa da miya ba.

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[7/22, 8:36 AM] Mrs Sulaiman 💓:  

*RIJIYA TA BA DA RUWA*

           *charpter 7*

********Musty da dawowar sa daga restaurant,hannun sa dauke da laidar da yayo ma zulaykha order ya wuce office dinta,saboda jin shuru bata fito ba.A firgice ya yi fatali da laidar da ke hannunsa,had'i da kwalalo idanuwa waje saboda ganin Zulaykha da ya yi kwance shame-shame tsakiyar office nata,babu alamun numfashi tattar da ita,ga kuma wani irin fari sol da fatar ta, ta sake yi.

Bai yi watawata ba ya sungume ta a 360 ya fito daga office d'in,saboda ba ta da nauyi ko kad'an,uku-uku yake taka step d'in yana saukowa hankali tashe.
Ma'aikatan da ke harabar wurin kuwa duk tasowa suka yi saboda ganin yanayin da oga Musty ya fito da madam d'in nasu,suna tambayar sa lafiya?

Bai bi ta kansu ba,ya cilla ma d'aya daga cikin ma'aikatan nasu da ya k'ware a harkar tuk'i makullin motar sa.Fahimtar mai hakan ke nufi ne ya sashi take masa ba ya da sassarfa shi ma inda ya shiga driver seat, Musty kuma ya shiga baya tare da Zulaykha.

Figar motar ya yi kamar za ya tashi sama,inda ya wuce babban asibitin dake cikin birnin Abuja.
Da gaggawa kuwa aka an she su zuwa emergency aka shige da ita,wacce ko motsin ba ta yi har zuwa wannan lokacin.

Lambar Abba ya danna ma kira a lokacin da yake ta faman kai kawo bakin dakin da aka shiga da Zulaykha likitoci kusan guda hud'u sun dakufa a kanta sabida ceto rayuwarta.
Har wayar ta gama ringing Abba bai daga ba,wanda hakan ya sa Musty jan dogon tsaki yana ganin kamar da gangan Abbah ya k'i d'auka saboda ba Zulaykha ba ce ta kira sa. Bai hak'ura ba ya sake danna masa wani kiran,sai da ya masa kira kusan na shida kamin Abba ya d'auki a wayar a hasale cikin fada fada yace, "Haba Mustapha! Idan ka kira ni sau d'aya ko biyu ka ji ban d'auka ba ai ka yi tunanin wani abu ne mai mahimmanci ya rik'e ni,tunda dai ka san haka kawai da gangan ba zan k'i dauk'ar wayar ka ba ko??"
Abba ya fad'a a lokacin da ya fito daga cikin hole din da suke meeting bacin rai ya d'auki escuse.

Cike da 'bacin rai shi Mustyn ya ce "To shi kenan ka yi hak'uri!" Kit ya kashe wayar sa ba tare da ya ce ma Abba ga abin da ya faru ba ya fice daga asibitin bacin ya bama wanda ya kawo su kudin da zai hau a-daidaita-sahu,saboda shi gida ya nufa yanzu.

Shi kuwa Kabeer ganin abin da ya faru ne ya sa shi tsayawa a asibitin,ya shaida ma wata nurse kan bari ya je ya sanar ma mahaifinta halin da ake ciki,ta shaida masa babu damuwa.

A-dai-daita-sahu ya hau zuwa babban ma'aikatar Abba, dama yasani sabida dadewar da yayi yana aiki a k'ark'ashin sa. Bai samu ganin Abba ba saboda suna meeting da za su fito nan da mintuna 30,wanda hakan ya sa shi zama daga inda yake da yakinin zai ga fitowar Abban ba tare da ya sha wahala ba.

Bayan 32mins kuwa sai ga mutane nan sun fara fitowa daga hole din manyan mutane ne masu-fada-a-aji a fad'in kasar tamu,wanda kallo d'aya idan mutum ya yi masu tabbas zai gano tsagwaron wadata da ke tattare da su. Abba ya gano tare da wani babban amininsa sun fito a jere suna sake tattaunawa tsakanin su dangane da meeting d'in da suka yi a kan sake ha'bbaka kasuwancinsu.

"Barkanku da war haka yalla'bai fatan kun fito lafiya?" Kabeer ya fada a lokacin da ya iso zuwa inda su Abba d'in suke.
"Lafiya k'alau Kabeeru lafiya na ganka anan kuwa??" Abba ya fad'a a lokacin da yake sa'bar babbar rigar sa.
"A gaskiya ba lafiya ba yalla'bai! Domin kuwa zuwa na yi na shaida maka madam Zulaykha a halin yanzu tana asibiti rai a hannun Allah! Wanda oga Mustapha ya kira ka d'azu zai shaida maka kuma ban san dalilinsa na fasa fad'a maka ba"

Ai a wani irin firgice Abba ya ce "Kana nufin mamana ce ke asibiti..."K'warai ma kuwa yalla'bai!" Kabeer ya sake jadda ma Abba,had'i da fad'a masa asibitin da suka kai ta tare da Musty d'in.

***Kwantar da kanta ta yi kan damtsen hannun sa bacin ya lallashi sahibar tasa,tana sharar kwallar da ta kasa tsayar mata ta ce. "Haka nan kawai ka je ka had'a ni da Babi,wai na ce a mana aure,kuma bacin kai ka fara jangwalo mana zancen."

Husnah ta fad'a fuskarta cike da jin haushin cema Babi wai ita ta ce tana son a masu aure,bacin kuma shi ne ya matsa mata da zancen tunda ta farka daga gajeriyar jinyar da ta yo na watanni biyu ,wanda hakan ya sa ta ce masa shi mai zai hana ya fad'a ma su Babi din da bakin sa,amma ji yanzu ya je ya kunya ta ta a wajen Babi.

"To wai ni ma ba na ce ki yi hak'uri ba!!" Yaya ya fad'a 'bacin ya shagwabe fuska kamar wani yaron goye,wanda ya san hakan sosai yake sake narkar da zuciyar Husnah kan soyayyar sa,domin kuwa ita irin matan nanne mai son namiji shagwa'ba'b'be da zai zam to tamkar dan goye a gabanta.

Turo siraran la'b'banta ta yi gaba cike da sanyin murya ta ce "to na ce ai ni ma ya wuce ko Yaya?"  Tsadadden murmushi ya sakar mata da kaf cikin gidansu babu mai samun kwatan kwacin sa had'i da manna mata kyakkyawar sumba akan goshinta.

Nan take kuwa ta ji wani abu kamar almara ya tsarga mata tun daga tsakiyar kanta,har zuwa babbar yatsarta na k'afafunta,sake lumshe idanunta ta yi had'i da sake narke masa a jikinsa saboda jin dad'in yanayin da suke ciki a yanzu.

A 'bangaren Yaya kuwa Allah ne kad'ai yasan irin yanayin da ya afka a dai-dai wannan lokacin,amma kuma saboda jarumta irin tasa dole ya yi controlling na kansa,had'i da lalla'ba ta tare da gaya mata tsadaddun kalamai masu sanyaya zuciya kamin ta shige cikin gida,tana mai sake jin k'aunar yayan nata na yawo a sassan jikinta.

A lokacin k'arfe 1 ta yi,da sallama ta shiga dakin Amma ,inda ta tarda mahaifiyar ta-ta da girma ya fara kamata zaune kan abin salla hannunta rike da carbi,tana jiran lokaci ya ida cika ta gabatar da sallar azahar.

"Sannu da hutawa Ummana!"  Husnah ta fad'a a lokacin da take zuge zip na doguwar rigar atamfar da ke jikin ta,gyad'a mata kai Amma ta yi alamun ta ansa mata ba tare da ta mata magana ba,sallamar da ta jiyo daga tsakar gida ne ya shaida mata da dawowar su *Mima* daga makaranta.

Ba ta ma yi gigin tarbar su ba,bacin ta ansa masu sallamar da suka yi a lokacin da ta fito daga d'aki,jikin ta sanye da zanin wankan ta,inda ta d'auro hijjap babba akai,wanda ya saukar mata har k'asa.

Wani irin kallon uku-saura-kwata Hidaya da Hamad* suka yi ma d'akin Amma had'i da jan doguwar tsaki suka fada d'akin da ke mak'waftaka da na Amman,bakinsu d'auke da sallama.

"Allah ya shirye ku to."  Husnah ta fad'a a lokacin da take dosar hanyar bandakin nasu da ke tsakar gida,Mima da ke k'ok'arin shiga d'akin da su Hamad suka shiga ne ta dakata had'i da daga murya ta yadda Husnah za ta jiyo ta ta ce "Shiriya ta addinin musulunci idan ya kai har cikin zuciyarki."

Girgiza kai kawai Husnah ta yi ba tare da ta ba ma Mima ansa ba,had'i da shigewa band'akin bakinta d'auke addu'ar shiga.

A lokacin da ta shiga ne kuma *Waleed* ya shigo gidan shi ma,jikin sa sanye da uniform irin nasu Mima,Hidaya da kuma Hamad,alamun daga makaranta suka taso,inda shi kuma ya shige d'akin da Husnah ta fito bakinsa d'auke da sallama.

******** "Ko kai fa dan Allah! A ce mutum kullum tuwon dawa tuwon masara babu wani canji saboda a kan mu farau talauci? Ai idan kana kawo man ire-irensu shinkafa tare dasu macaroni Allah ba za a na jin kanmu da kai ba a mak'ota,ni ma in takaice maka ma ka jima ba ka yi masifar birge ni irin na yau ba *Yayana* "

Alina ne ke wannan maganar a lokacin da take ta faman aika shinkafa da miya a bakinta da ya ji nama akai,wanda saida Waali ya ciyo bashi ya kawo mata duk wasu cefane ta dafa shinkafa da miyar kamin ya samu kansa,shi ne take ta faman yi masa wannan Sambatun,shi kuma ba ma sauraran ta yake ba,tunaninsa kwacokan ya tattara ne izuwa tunanin hanyar da zai biyo wajen ganin ya biya Idi mai shago kud'in sa har naira dubu biyu da ya ranta,duk dan ya biya ma gimbiyar tasa buk'atarta na cin shinkafa da jar miya.

Ba su san daga inda ta shigo ba,basu ji motsin ta ba,sai ji kawai suka yi Iyami ta kwad'a ma Alina wani irin gigitaccen mari da ya sa ta fasa wani irin k'ara saboda babu karya marin ba k'aramin shigarta ya yi ba. Cike da tsananin bacin rai Iyami ta bud'i baki ta ce.

_comment and share plss_
[7/22, 8:36 AM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA*    

           *charpter 8*

********Rik'e da hannun Zulaykha Abba yake yana murza mata su,fuskar sa cike da tsananin damuwa a lokacin da ya iso asibitin har an fito da ita zuwa d'akin da za ta huta. Saboda sun yi nasarar dawo mata da numfashin nata da ya d'auke,a halin yanzu ma bacci take,inda dayan hannunta ke mak'ale da laidar da ake mata k'arin ruwa.

Cikin ciwon da bai gaza na awanni biyu ba sai ga ta ta zam to wata yar shafal da ita,hasken ta ya sake fitowa sosai. Sosai hankalin Abba ya tashi a lokacin da Kabeer ya fad'a masa,wanda babu 'bata lokaci suka wuce asibitin tare da amininsa da kuma masu take masa ba,shi ne fa ya same ta cikin wannan yanayi na barci d'in,sannan kuma dik wasu kudin da aka buk'ata a lokacin ya yi settling,'bacin ya kira Mamy ya shaida mata abin da ake ciki ne yake zaune hannunsa rike da na 'yar tasa da yake jin kamar za ta yo masa nisa,sai aminin nasa ne da ke zaune keta faman tausar sa,had'i da nuna masa mahimmancin d'aukar kaddara mai kyau da kuma akasin haka.(Abokin k'warai kenan).

*****   "Ai kuwa Allah shi kara akan abin da Alh ya yi maka yau! Idan ban da jaraba da kuma naci irin naka mai za ka yi da yarinyar da ubanta bai d'auki uwarka da kai kanka darajaba akan ta? Ban da shisshigi da tusa kai irin naka ko burburwar mutuwa ka gane wannan yarinyar na yi akan titi ai ba ka taimaka mata ba,saboda ubanta sam-sam mutum bai taba masa gwanin ta inda ta dalilin ta ne? Kai kuma ma ba wannan ba! Allah ko duniya sama da kasa za ta had'e ba za ka aure wannam yarinyar ba,gara ma tun wuri na sake jaddada maka saboda ka san da zaman hakan,bawai daga baya ka ce mani ba ka san zance ba!"

Mamy ce ke wannan maganar cike da tabbatar wa har cikin zuciyarta! Shi kuwa Musty da ke ta faman kai kawo cike da tsananin jin haushin Abba da ita kanta mahaifiyar tasa,sai faman sauk'e ajiya zuciyar yake,k'wafa ya yi had'i da ficewa a parlon mahaifiyar tasa ba tare da ya sake ce mata uffan ba.

*****    "Kai a gaskiya yau d'in nan ba k'aramin yunwa ba ce ta azalzaloni tun daga makaranta Ammana" Waleed yaro dan shekara goma sha hud'u ne ke wannan maganar,a lokacin da yake kai lomar joloup d'in shinkafa bakin sa.

Cikin muryarta na dattawa,matar da za ta kai kimanin shekaru hamsin a duniya ta ce "Kai! Amma a gaskiya yau yunwa bai kyauta ma magajin Babana ba,kuma Yayana na kaina!" Ta fad'a tana sakin wani irin murmushi da ke tattare da tsananin rauni ga duk wanda ya san mai ake kira da murmushin da ke fitowa daga k'asan zuciya,ko kuma wanda mutum kan iya-yinta iyakacin samar labbansa.

Da shike yaro k'arami ne,sai bai fuskanci komai ba,sai ma dariyarsa daya kwashe da ita,ya ce, "mene ne kuma magajin Babana Amma na ta kaina?" Tun kamin ta ba sa amsa,Husnah ta shigo d'akin nasu tana rawar sanyi saboda iskar bishiyar tsakar gidan nasu da ke ta faman hura mata farar fatar jikinta da ke jik'e da laima.

"Iyayen surutu an dawo kuma za a d'aura daga inda aka tsaya ko?" Husnah ta fad'a a lokacin da ta wani shige jikin amma kamar wacce za ta koma cikin ta,hak'oranta na had'ewa wuri d'aya muryarta na harhard'ewa.

Dariyar sa ya yi shi kuwa Waleed ya ce "Hmm! Su Aunty Husnah ba dai son jiki ba,ji yadda kika wani shige jikin Amma kamar za ki koma ciki! Wanda ko ni magajin Babanta da ke matsayin d'an auta ban yi hakan ba saboda wariyar launin fata da ake nuna mana."

"Waleed maza maza tashi ka je wajen Yaya ka ce ya ba ka guntun d'auri na maganin Husnah da ke wurin sa saboda na wajena ya kare." Ammah ta yi maganar cike da tsananin damuwa saboda gano kamar ciwon Husnah d'in ne ke k'ok'ari tashi,sanadiyyar sanyin da ya yi mata yawa.

Wanda shi ma sai a lokacin ya lura da yanayin da 'yar uwar tasa ke ciki,bayyi wata wata ba kuwa ya fice daga d'akin da gudun sa zuwa zaurensu,a inda d'akin Yaya yake.

*****    "Amma dai ban taba sanin cewa ba ki da mutunci har haka ba sai yau Alina!! Ashe abin da kike aikata ma mijin naki kenan a bayan idanuna,ba tare da-na-sani ba duk da kasancewar muna cikin gida daya? Mugun halin da shegen son abin duniyar taki dana rasa inda kika kwaso su,suna nan cikin jinin ki har yanzu ashe? Tir da irin halinki wallahi! Gwanda ma ki yi wa kanki fad'a,tare da karatun ta natsu tun kamin lokaci ya 'kure miki! Shashasha kawai wacce ba ta san inda yake mata ciwo ba."

Iyami ce ke wannan maganar cike da tsananin fushi da kuma 'bacin- rai d'in da tunda take Alinar ba ta ta'ba kunsa mata irin shi ba sai yau! Wanda dawowarta daga unguwa kenan yau,wata matar mak'watansu ta tare ta da zancen,tare da irin dibar albarkar da take ma Wali muddin tasa k'afar ta zuwa unguwa,wanda kuma ashe duk gidan da ka fad'a a unguwar za ka tadda ana mai da zancen ne,tare da nuna cewa ai laifin na Iyami ne da ba ta tsawatar ma 'yar tata,ya sa take ma mijin ta rashin kunya,wanda kuma baiwar Allah sam, ba ta san ma ana haka d'in ba sai da yau aka fad'a mata,da kuma maganganun da ta ji yo ita Alinar na fad'a ma Wali a yanzu,wanda hakan ya sa ranta ya yi masifaffen 'baci ba kad'an ba!

Sannan ta d'aura da fadin "Kai kuma wato ga ka sakarai saboda wata banziyar soyayya ka zuba ma yarinya ido,tana maka abin da ta ga dama? Duk ta bi ta gama raina ka ko? To wallahi kai ma ahir d'inka! Idan dai ka ce a haka nan za ka zaune kana ta faman wani lallaba ta kamar kwai,hakan shi ne zai 'bata damar ci gaba da kawo maka iskanci kala-kala. Gara tun wuri ka yi ma tifkar hanci kamin ka zo ka yi da-na-sani daga baya akan son zuciyarka."

Tana gama fad'ar abin da ya shigo da ita kewayen,ta sake sharara ma Alina mari mai rai da lafiya,kamin ta wuce zuwa nata 'kewayen cike da tsananin takaici na wannan halin 'yar tata.

Alina kuwa tun marin farko da Iyami ta mata,ta fashe da wani irin rikitaccen kuka kamar wacca akana wani abin kirki! Abinka ga farar fata,nan da nan fuskarta ta kad'a ta yi janur kamar wacca aka shafa ma jajjagen attarugu.

Wanda kuma mari na biyun da Iyami ta yi mata,shi ne ya sake hargitsa mata lissafi kukan nata ya sake samun matsuguni mai lasisi! Kuka take ba ji,ba gani,wanda hakan ya haddasa mata wani irin matsanancin zazza'bi lokaci da ta fara rawar d'ari!

Wali kuwa tun shigowar Iyami gidan ya dawo daga gajeruwar tunanin daya fad'a,sadda kansa k'asa ya yi a lokacin da Iyami keta faman balbale su! A lokacin da ta mari Alina ma kuwa ji ya yi kamar shi a aka mara har da dafe kumatunsa,yana rintse idanun sa! Tabbas yau da a ce ba Iyami ba ce ta aikata wannan marin babu tantama hukuma ce za ta raba su,saboda soyayyar da yake ma Alina ya zarce misali a rubuce.

Sosai ta sake ba sa tausayi,saboda yadda ya ga tana rawar dari ba ji ba gani,d'aukar matar sa ya yi zuwa cikin d'aki duk da tutture sa da take ta faman yi saboda wani masifaffen tsanarsa da ta mata dira cikin zuciyarta,dalili kuwa shi ne marin da mahaifiyar ta-ta ta yi mata a dalilinsa.

Haka nan suka kwana suka wuni gidan babu wani armashi,ga wani irin matsanancin zazza'bi da ya rufe ta tin jiya har kawo yau babu sau'ki,wanda hakan kuwa ba k'aramin d'aga ma Wali hankali ya yi ba! Haka nan yau ya wuni ko nan da kofar gida bai fita ba yana jinyar matar sa! Inda Iyami kuwa ta d'au fushi da yar ta-ta sosai ko leken inda take ba ta yi ba, duk da kuwa ita ma tana son ganin halin da tilor 'yar tata ke ciki amma haka nan ta yi mirsisi abinta!

Ba don komai ba sai don ta nuna mata kuskurenta,da kuma nuna mata amfanin da Wali ke da shi a cikin rayuwarta ko da kuwa babu aure tsakaninsu! Tausayin Wali take ba na wasa ba,saboda rashin uwa da uba a kusan lokaci da ya ba karamin abu ba ne cikin shekara guda,ga babu wasu dangi na a-zo-a-gani.

*vote*
*comment*
*share*
[7/22, 9:11 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BADA RUWA...!!*
    
                                 

           *charpter 9*

********Ba ita ta farfad'o daga gajerar jinyar da ta fada ba,saida tayi kwana biyu tana bacci sanadiyyar allurar data ke ansa wajen likitocin,inda Mamy ce ke kwana da ita tare da Abba da shima sam yace bai san zancen tafiya gida ba da Mamy tayi masa,sabida hankalin sa bazai taba iya kwanciya ba shi yana can gida yarsa na nan kwance rai a hannun Allah.
Musty ma dai kusan zance dashi ake jinyar zulaykha,domin kuwa har ya janye fushin da yake sanadiyyar abinda Abba yayi masa a wancan ranar,sabida soyayyar da yake ma Zulaykha tin kamin ta gama sanin ciwon kanta.

Inda aminan arziki dama na tsiya suke ta faman kai kawo zuwa asibitin sabida dubiyar mara lafiya,Mamy ma dai yanzu tayi sanyi sabida rashin lafiyar ita Zulaykhan,wanda kuma Musty ne idan ya samu lokaci yakan dan laika ma'aikatar tasu domin ganin abubuwan dake wakana bisa ga umarnin da Abba ya basa.

Tinda ta farka kuwa ta rama sallolin da suka kufce mata baki d'aya,wanda kuma jikin da sauki sosai,su Abbah sunyi-sunyi ta fad'a masu damuwarta amma ta k'ek'ashe k'asa tace ita babu abinda yake damunta,kawai ciwo ne daga Allah.Ba dan su Abbah sun yarda ba,saidon babu yadda zasuyi suka bar zance sabida likita ya shaida masu akoi abinda yake damunta daya sa hawan jini ke k'ok'arin kamata.

Sai da Zulaykha tayi sati guda cif cif a asibiti,kamin aka sallamo su suka koma gida,tare da rakiyar y'ar gidan aminin Abbah mai suna *JIDDAH*.
Wacce ta kasance matsayin babbar aminiyar Zulaykha,dikda kasancewar bada ko yaushe suke tare ba!
Jiddah kyakkyawar yarinya ce mai sanin ya kamata,sam itama bata da wani rawar kai a rayuwarta irin na y'an matan zamani,wanda hakan ne ma yasa amintakar su tazo daya tare da Zulaykha.

Bayan kwana biyu da komawar su gida.

"Wai ke matar nan miyasa kika wani dage sai kin tafi gida tin daga yau? bacin kuma Dad yace maki sai kinyi sati kamin ki koma gida." Zulaykha ce ke wannan maganar da take nade cikin bargonta,irin na duniyar kule,kanta ne kawai ke waje take ma jiddah magana dake kokarin saka wata doguwar rigar Zulaykha na shadda.
Ba tare da jiddah ta juyo ba itama tace "Allah kuwa baki isa ba ma yarinyar nan! Ai naga kin riga da kin gama warkewa daga ciwon naki da zaki wani ce sai na kai sati a nan,bacin kuma nasan Mom na can gida tana fama da kewata."
jiddah ke wannan maganar cike da jin dadi sabida tunowa tayi da mahaifiyarta da a kullum bata gajiyawa da ita ta ko wanne fanni.

Kanta dake waje Zulaykha ta idasa shigewa dashi cikin bargo, ba tare data bama jiddah ansa ba,wanda hakan kuma baisa jiddah tayi wani tunani daban ba,tana gama saka kayanta had'i da daukar jikarta tare dasu wayoyinta ta karaso bakin gadon da Zulaykha ke kwance,ta daddage ta lafta mata duka ta fice daga dakin da gudunta tana fadin ladar jinyarki danayi na fanshe tinda ke naga baki da niyya.
Alamu dai bayau suka sama irin hakan ba,kamar yadda dabi'ar abokai take na kaiwa aboki duka a un-espected.

Jin alamar jiddah ta fice daga dakin ne, ya sa ta mikewa zaune bayan ta yaye bargon daya lullube mata jiki,ta jingina bayan ta a jikin allon gadon nata,kanta a sama wasu irin zazzafar hawaye na zubowa daga cikin idanunta,alamun ta jima tanayin kukan a tin lokacin data lumar da kanta cikin bargo sabida jin Jiddah ta anbaci Mom dinta,itama tunowa tayi da tata mahaifiyar da batasan a wace duniya take ciki ba.
Abba ne ya shigo cikin dakin bakin sa dauke da sallama ya tadda yar lelen nasa cikin wannan yanayin daya masifar d'aga masa hankali.

********A kusan lokaci daya Yaya da Waleed suka shigo d'akin,hannunsa rik'e da wata laida dake d'aure da wani garin magani a cikinsa,hankalin sa a mugun tashe,yayo zuwa inda Ammah da Husnah suke,wanda har zuwa lokacin Husnah bata bar rawar darin da take ba,harma ya zarce misali.

Mika ma Ammah laidar dake hannun sa yayi,a lokacin da yayi nasarar raba jikin Ammah da ita Husnah,kamar jinjira haka nan ya dauke ta zuwa kan gadon Ammah yayi mata masauki amma taki sakin sa,saima sake shigewa jikin sa da tayi.

Babi ne ya shigo dakin,hankalin sa a mugun tashe,sakamakon kai masa rahoto da Waleed yayi kan ciwon Husnah ya tashi, bakin inda suke ya karasa,hadi da fara tofa mata addu'oi tare da shi Yaya din kansa.

Inda Ammah kuma ta daibo garwashin wuta,hadi da zuba garin wannan maganin,nan take kuwa dakin ya hargitse da wani irin hayaki mai fidda dumi dake ratsa sassan jikin d'an Adam.

Sun d'auki tsawon mintuna 30 cikin dakin batare da ko wannen su yace kala ba,hatta ga Waleed,dikda kasancewar sa yaro surutacce kaman akku,amma shima sam ya natsu a gefe yana kallon y'ar uwar tasa cike da t'sant'sar tausayinta.

Husnah kuwa da kad'an kad'an numfashin ta ya fara dawowa saiti sabida yadda dumin dake fita cikin garwashin ke faman ratsa mata jijiyoyin jikinta,dik wani rawar darin da takema a hankali-hankali ta daina su,ga wani irin fitinannen gumin dake karyo mata kota wata kofa ta jikinta,a haka nan wani gajiyayyen bacci yayi awon gaba da ita tana sakin ajiyar zuciya akai-akai.

Ammah dake kallon diyar ta-ta tin dazu hawaye na zuba daga cikin idanunta,Waleed na share mata su amma sam hawayen yak'i daina zubowa sabida matsanancin tausayin yar ta dake karairaya mata zuciya,ajiyar zuciya k'ak'k'arfa itama ta sauke tana janyo waleed din jikinta ta rungume sa,kamar zata maida sa cikin cikin ta.

"Allah mun gode maka" Babi ya fada,hadi da daurawa da fadin, "Hala dai kunbar yarinyar nan tayi wanka da rana fatsa fatso da kuma ruwan sanyi shiyyasa har ciwon nata ya tashi ko?" ya fada yana mai sakar ma da Ammah idanu.

Gyad'a masa kai tayi ba tare data bude bakin ta ba,wanda hakan yasa shi kallon Yaya yace, "Ka gyara mata kwanciyar ta,sannan ka lullube ta da bargo mai kauri kazo ka same ni a dakinah ina jiranka."

Yana gama fadar hakan yasa kai ya fito daga dakin,inda ya tadda su Mima tare dasu Hamad da  Hidaya, zaune kan tabarma karkashi bishiyar dirmi dake tsakiyar gidan nasu,sai hirar su suke cike da t'sant'sar nishadi,alamun babu abinda ke damunsu dikda kuwa sun fahimci cewa ciwon Asma'u ya tashi,amma ko a kwalar rigar su,wanda inda ace a baya ne tabbas da zuwa yanzu sun cika gidan nasu da kuka kamar su d'age gidan.

Inda daga ta can gefe wata mata ce zaune kan kujera yar t'suguno ta bakin madafa tana tankaden garin tuwo na masara,zata kai irin 54-55yrs a duniya mai t'sant'sar kama da Yaya kamar an t'saga kara,dikda kuwa tsufan data fara kamar tasu bata bace ba.

*AMMI* kenan,wacce ta kasance mahaifiya ga Yaya,Mima,Hidaya da kuma Hamad!

"Baku san yar uwarku bata da lafiya bane da bazaku iya shiga ku dubo yaya jikin nata ba?" Babi yayi maganar fuskarsa babu alamun wasa.

Wanda hakan yasa su fara kallon-kallo, hadi da fara gunguni k'asa-k'asa,suna kallon mahaifiyar tasu da tayi kamar bata filin t'sakar gidan. Sai da Babi ya daka masu wani shegen tsawa kamar ya cinye su danye kamin suka shiga taitayin su,wajen rige-rigen shiga d'akin Ammah. Harara ya cilla Ammi kamar tana ganin sa,bacin ita kuma batama san yanayi ba,sabida aikin da take ya dauke mata hankali,kamin ya buga wani uban tsaki ya wuce zuwa dakin sa dake ta can dungu yana kallo d'akin matan nasa sabida takaici.

Da suka shiga sun tarda Yaya na gyara ma Husnah rufar bargon daya lullubeta dashi,inda Ammah da Waleed ke zaune suna kallon su,cikin zuciyar Ammah kuwa sosai take sake girmama irin soyayyar dake t'sakanin Husnah da Yaya tin a ranar da aka haifo ta cikin duniya.

Harara Yaya ya cilla masu kamar idanunsa zasu zazzago k'asa,sabida yadda suka fado dakin babu ko sallama! Da shike sun san halin kayan su sam bashi da sauk'i sumi-sumi suka fice daga dakin,had'i dayin sallama,Ammah ce ta ansa masu,tana dariya cikin zuciyarta,domin kuwa dramer na gidan nasu a halin yanxu sam bai bata haushi,saima dariya sabida sanin da tayi cewa da ba haka suke ba,yanzun ma yanayi ne ya sauya,wanda hakan yasa dabi'un kowa dake cikin gidan sake sauyawa.

Da shike dodon nasu na cikin dakin,sai dik sukayi ma Ammah gaisuwar mara lafiyan a ladafce,kamin suka fito daga dakin suna ture-turen baki a lokacin da sukaji irin kwafar da Yaya yayo daga cikin dakin suna yatsina face.

Sallama yayi ma Ammah kamin ya fito daga dakin,gani yayi ashe har uku da wani abu yayi,wajen da Ammi ke tankade ya karasa bacin ya daura ma fuskar tasa gajeruwar murmushi.

******** Sai da Waali ya mat'sama Iyami,kamin tazo ta kewayen su zuwa duba jikin Alina,kallo d'aya Iyami tayi ma Alina ta gano shigar ciki dake tattare da ita,abin ku ga mutanen da,sosai zuciyarta ya cika da farin ciki sabida ta kusa samun jika,amma sai tayi gum da bakin ta,sabida sanin halin Waali da son haihuwa,ta tabbata idan yaji cikin dake jikin Alina bazai iya yin shuru ba,sai ya fad'a mata,inda ita kuma zatayi amfani ne da wannan damar tayi ta faman gara masa kai kamar ta samu gare-gare.

Tin daga wannan lokacin sai Iyami ta maida kewayen su Alina wajen zaman ta,wanda hakan yasa Alina shiga taitayinta,bata kawo ma Waali wargi akan dik abinda ya zartas a cikin gidan,sosai Iyami ke bama Alina kulawa da abinda ke cikin ta,inda take mata abubuwan da zasu kara mata kuzari,kuma cikin ikon Allah sam bata da wani laulayi sai uban bacci,wanda hakan yasa daga Waali har Alina basu lura da komai ba.

A lokacin da cikin nata ya cika wata biyar ne dik suka san da zaman wannan cikin,tabbas idan nace zan nuna maku irin farin ciki da Waali ya shiga ma bata baki ne da kuma cin lokaci! Bayan shekara biyar cif da auren su yau Allah ya basu abinda suka jima suna naima.

Alina kuwa da shike ja'ira ce,taso ta masu bori kan azubda cikin Iyami ta take mata birki! Tin daga wannan lokacin dik wani abu da Waali ya gani na kwadayi yana kan hanyar sayo ma Alina ne,koda kuwa bashi da ko sisi sai ya ciyo bashi ya sayo mata kayan dadi,sabida soyayyar abinda zata haifa masa ba kadan bane cikin zuciyarsa,idan yayi sallah har addu'a yake kan Allah ya basa diya mace sabida ya maida mata sunan mahaifiyarsa.
Bayan wata hudu.

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[7/22, 9:21 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BADA RUWA...!!*
    
                                   

           *charpter 10*

******** Sosai Abbah yabi ya rikice, yana tambayar ko wani ne a cikin gida ya b'ata mata rai? Amma tace masa babu komai,kawai tunowa tayi da mahaifiyarta! Wanda hakan yasa Abbah yi mata wani irin shegen kallo da babu shiri ta hadiye kukan nata,kirjinta na dukan tara tara. Kwafa Abbah yayi,ya fice daga dakin ba tare daya sake ce mata k'ala ba,wanda hakan yasa jikin Zulaykha yin sanyi bana wasa ba,harma taji rashin kyautatawarta akan fitowa fili da tayi ta nuna tana bukatar mahaifiyarta,bacin kuma shi bai rage ta da komai ba a fannin nuna t'sant'sar kulawa,gami da tsafta tacciyar kaunar da bata da algus.

Cike da sanyin jiki ta share hawayen dake kan fuskarta,tana mai jin haushin kanta ba kad'an ba,sandiyyar b'ata ma mahaifinta rai da tayi,akan matar da ta nuna bata kaunarta tin kamin ta fito duniya,zuwa ga ranar da ta haifo ta!
Bayi ta shiga tayo wankan ta fes,ta fito had'i da murza manta mai sanyin k'amshi,sannan ta shirya kanta cikin wata riga doguwa ta roba,da yabi ya lafe mata a lafiyayyen farar fatar jikinta,inda kuma yau y'an saka kallabi na kusa,dan haka saita saka hular rigar,had'i da feshe jikinta da turaren ta mai dad'in gaske! Wayarta guda ta d'auka,ta fito daga nata dakin cike da nat'suwa zuwa inda zata tarda mahaifinta,kasancewar yau lahadi ne babu zuwa wajen aiki.

Mamy ta tarda a parlo tare da Musty suna magana kasa-kasa,ganinta da sukayi ta shigo parlon ne yasa su yin gum da bakin su,dik suka bita dana mujiya daya sa taji wani iri.

Dan haka sai bata zauna ba,gaishe su tayi,had'i da fad'in, "Abbah na yana ciki kuwa Mamy??" wani irin kallo Mamy tayi mata na kasan ido,kamin ta waske had'i da fad'in, "Wato Abban naki ke kad'ai ko Ummi?? shi kuma Mustapha ba Abban sa ba??"

Dan daburcewa Zulaykha tayi kan maganar da Mamyn ta fada,sai kawai ta saki murmushin yak'e ba tare data ce kala ba,tana wasa da yatsarta dake cikin bakinta!
"Ki shiga yana ciki" ta tsinkayi muryar Musty na bata ansa,kamar jira take kuwa ta wuce harda da dan saurin ta,sabida jin yadda idanun Mamy da Musty ke mata yawo a jikinta dik ta tsargu.

"Mamy irin wayannan maganganun bai kamata suna fitowa daga bakin ki ba dai, ko ba komai dai kina da sanin cewa itace yarinyar da nake da muradin ta zam to uwar y'ay'ana ko??"

Wata shegiyar harara Mamy ta watsa masa,ba tare data ce masa ci kanka ba,ta mik'e fuu ta wuce zuwa nata dakin,shi kuwa tabe baki yayi,gami da zunkud'a kafada alamun ko a jiki na,kamin ya bama wandon sa iska zuwa nasa part din,yana kuma sake sawa cikin ransa babu wanda zai mallaki Zulykha a matsayin matar aure idan bashi ba.

Da y'ar karamar sallama ta idasa shigewa hadadden parlon mahaifin nata,da bashi da wani girma,domin kuwa baikai parlon farko girma ba,amma kuma yafi sa haduwa nesa ba kusa, ganin bata tarda sa a parlon bane yasa ta kut'sa kanta zuwa bakin bedroom,kwankwasa kofar tayi kusan sau uku amma bataji alamun da mutum bama,ballantana kuma akai ga bata iznin shiga,d'an turo kofar dakin tayi a hankali,hadi da laika kanta,inda idanunta suka sauka akan fuskar mahaifin nata,daya buga wani uban tagumi,ya lula duniyar tunani tin fitowarsa daga dakin Zulaykha,wanda dik bugun kofar da take masa baima san tanayi ba,sbd zurfin dayayi a cikin tunanin sa.

Nannauyen ajiyar zuciya ya sauke,had'i da lumshe idanunsa a lokacin da yaji Zulaykha a bayan sa,ta kwantar da kanta,hawayen idanunta na zuba akan gadon bayan sa,take yaji zuciyar sa ta karye!
Sake rint'sa idanun nasa yayi da suka kada,sukayi jawur dasu!

Mai do da ita ta gefen sa yayi,inda shima ya juyo yana kallon ta,yana jin zuciyarsa sam babu dadi kan kukan da take,kwantar da kanta yayi kan kafadar sa,yana bubbuga bata bayan ta alamun lallashi,wanda shima tabbas da ace zai samu wanda zai lallashe sa d'in yana so! Amma kuma yasan tabbas babu wannan a duniya kwata-kwata sabida shidin bashi da kowa a duniya sai yarsa k'wallin kwal guda daya wato zulaykha!!

******** "Sannu da aiki Ammi na!" Yaya ya fada a lokacin da ya karbi tankaden da mahaifiyar tasa keyi,wanda har zuwa lokacin murmushin dake kan fuskar tasa bai gushe ba! Sam fuskarta babu wata walwala a lokacin sabida shidin ma haushin sa take ji! tace, "yawwa." A tak'aice.

Take kuwa Yaya yasha jinin jikin sa,sabida yasan tat'suniyar gizo bata wuce ta koki! Gum yaja bakin sa ya t'suke,yaci gaba dayi mata tankad'en daga durk'ushen da yake,wanda har a jinin sa yake jin kaifin irin kallon da mahaifiyar tasa ke jifan sa dashi,wanda yasan ba kallon komai take masa ba,sai kallon wanda baya kishinta kwata-kwata a matsayin ta na mahaifiyarsa.

"Jarababbe kawai" Ammi ta fada a lokacin da take mikewa daga inda take ba tare data sake masa magana ba. Dariya ce ke son kamasa,amma haka nan ya gint'se abarsa sabida gudun sake tafka wani laifin,yana mai ci gaba da tankade mata garin nata,fes kuwa ya gama,had'i da rufewa kirif a cikin kafilas d'in,ya karkade hannayen sa da suka baci da gari,ya d'aga murya ta yadda zata jisa yace "Ammina na gama maki tankad'en na wuce masallaci"

Can ciki Ammi dake cikin dakin ta tare da y'ay'anta,tana juyo sa tace "To Allah ya tsare man ku baki daya."

Tare da Babi suka dawo daga masallaci sallar la'asar,inda a dawowar su gida suka tarda har Husnah ta farka,tana sanye da wani rigarta na sanyin daya hurata ba kadan ba,sabida yadda yayi mata girma,wanda asalin rigar ta Yaya ce amma yayi mata kyautar sa.

Ammah,Waleed tare da Husnah na zaune daga kofar dakin su akan tabarma,sai kuma su hidaya dake karkashin bishiyar dirmi su ukun su,suna assigment nasu da aka basu a school,wanda shima Waleed Husnah ce ke koya masa.

Ammi kuwa tana can cikin madafar su ta langa langa tana had'a masu abincin dare sbd yau itace take da girki.

Kamar yadda Babi yace yana naiman Yaya din kuwa,tare dashi suka sake fitowa daga gida,inda suka tari abin hawa akan babban hanya zuwa cikin garin Abuja daga Suleja.

******** Bayan wata hudu.

Zuwa wannan lokacin sosai cikin Alina ya girma,domin kuwa ta shiga cikin watar haihuwarta yau ko gobe! wannan acikin wayannan watannin babu irin cin kashin da Waali bai fuskanta ba daga wurin Alina,ga wani irin dan iskan bashin dake kansa dik ata sanadiyyarta! Wanda tasan yanayin samun sa,amma haka nan sai ta murzama idanunta toka tace ita ga abinda take so,bawan Allah kuwa da shike ya kwalllafa ransa akan wannan cikin jikinsa na mazari zaije ya kawo mata koda kuwa bashi da ko sisi! Iyami tayi fadan,ta kuma yi nasihar amma dik a banza domin kuwa Alina kam tayi nisa sam batajin kira! Ga wani dan iskan rashin kunyar data tsiro dashi cikin gidan,na yau daban,na gobe daban! Amma haka nan Waali ke kauda kai kamar baiga abubuwan da take masa ba.
Wanda abin nata da har yakai ya kawo ta matsa ma Waali kan lallai lallai sai ya saketa dik randa ta haifa masa wannan banzan cikin nasa! Badon yanajin zai iyaba,sai don a zauna lafiya yace mata yaji ya yarda.

sannan kuma bugu da kari akoi wani dan iskan mai kudi da yazo masu bakunta a unguwar tasu magidanci,shine yabi ya sake zuzzuge Alina,sabida tin kallon farko da yayi mata ta sace masa zuciya,wanda ita kuma ta masa alk'awarin aure tana haihuwa sabida ta gansa Alaji mai kudi! Kuma dik wannan abu da ake har zuwa lokacin Iyami bata da labari sabida a munafurce sukeyin dik wani shirye shiryen su!
Yau ta kama ranar laraba!

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*

[7/23, 11:51 AM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BADA RUWA...!!*

*©️OUM MUMTAZ✍️*
    
                              

           *charpter 11*

******** Tin daga wannan ranar sai ya zamana Zulykha kan tunowa da mahaifiyarta akai-akai,wanda idan ta kwanta bacci har mafarki take da ida,tana fadi mata kalmomi na zalla da kuma madarar kaunar da take mata,had'i da kewarta data lullube ta.
Amman koda wasa bata sake tinkarar Abbah da zancen ba,sabida nuna bacin ransa da yakeyi karara a dik lokacin da tayi gigin sanar masa wani abinda ya shafi mahaifiyar ta da ko sanin ta ba tayi ba.

A fannin tafiya wurin aiki kuma yanzu ma'aikatar Abbah take tafiya tare dashi bisa ga umarnin sa,wanda ya kasance nata kuwa sai ya daura Oga Musty akai,inda yanzu komai da zai shiga ya fita cikin kamfanin sai da saka hannun sa! Amma kuma umarni bada ga wurin sa yake ba,daga sama ne,wato wajen mai asalin kamfanin Zulaykha!

Inda kuma abubuwa suka sake tab'arb'arewa,kullum cikin zagi had'i da tsinuwa Ummi da mahaifin ta ke kwasa a wajen ma'aikatan,kan wai sun tauye masu hakkin su,basu biyan su albashin su yadda ya kamata! Sannan har wasu daga cikin su suka bar zuwa wajen aikin tare da fadin Allah ya isar masu kan dik wasu kudaden su da aka tauye masu ba tare da an biya su ba!

Shi kuwa Musty da Mamy ko a kwalar rigar su,duniya sabuwa ta sake bude masu ne sabida wannan damar da aka basu! Haka nan a fannin ma'aikatan cikin gida ma,wasu da suka ga basu iyawa da wannan cutar sai suka sallami kansu tare da fadin a lahira za'a biya su hak'kin su da akayi ta faman tauye masu na tsawon watanni wajen shida.
inda wasun su kuwa,suka ce babu inda zasuje,sai sunga abinda ya ture ma buzu nadi cikin wannan gidan!

Dik wannan budirin da akeyi kuwa,sam Abbah da ita Zulaykha d'in basu da labari! Basu ma san maike tafiya ba,sabida irin sakacin da sukayi na yadda da mutunen da bai cancanta su basu dikkan yardar su ba!
wannan kenan.

******** "Oyoyo takwara na sannun ku da zuwa! Sannu da zuwa!" Wani babban mutum ne da a kalla zai kai irin shekaru tamanin a duniya ke wannan maganar! Wanda t'sufa k'arara ta bayyana tattare dashi sabida yadda shekarun sa suka ja!

Dikda kuwa tsufar data riske sa hakan bai hana shi mikewa daga zaunen da yake ba,hannun sa rike da sandar sa,dake taimakon sa wajen tafiya ba tare da gargada ba, da sassarfa kuwa Yaya ya karaso zuwa inda wannan tsohon yake,ya basa kyakkyawar runguma yana fadin "T'soho na mai ran karfe gani nan yi a hankali kar garin murna na ganin takwara yasa ka karashe kakkarya mana guntun kafafun naka."

Wannan maganar da yayi ne yasa Babi dake gefe yana kallon dan uwan nasa da kuma dan nasa dake kaunar junan su sosai sakin dariya, shima kuwa tsohon nan sake rungume d'an gidan k'anin nasa yayi,yana fadin, "ai kuwa dai dan albarka! Kamani mu karashe wurin zamana sabida k'afafun nawa sun fara matsamin."

Tare da Babi suka kama *Yaya babba* zuwa kan wani cushion din da a kullum zaka same shi zaune yana jan carbin sa! Suna yi masa sannu,Babi ya daura da fadin, "ai da baka tashi ba Yaya sabida matsalar nan ta k'afar ka."

"Kayya! Gwanda ka barni na taka da kafafu na *Amadu* ! Sabida ni kaina nafi son ina take su, suma suna jin irin radadin da suke k'unsa man!Balle ma kuma kaima kasan idan ba takwara bane yazo ai ban mikewa daga inda nake ko kuwa?"

Girgiza kai Babi yayi,ba tare da ya bama yayan nasa ansa ba yace, "mun sameku lafiya? yaya iyalin?"

"lafiyan su qlaou alhamdulillah,ina su *Kausara* sarkin rikon tsiya tare dasu *Halimatu* da kuma sauran yaran?"

"Dik suna lafiya Yaya, kuma sunce a mika masu gaisuwa!" Fadar Babi cike da girmamawa. Wani irin dariya Yaya Babba ya sake kamin yace, "Nasan dai Kausara ba za ta ce a gaida ni ba,sai dai ita Halimatun,bana raba d'ayan biyu"

A tare Babi da Yaya karami suka kwashe da dariya sabida jin abinda Yaya Babba ya fada,wanda kuma gaskiyar ya fada,da ace a baya ne idan Ammi tasan wajen sa za'a zo harda guzirin su goro zata bayar a kawo masa bama gaisuwa kawai ba,amma sanadi daya zo ya ratsa sai kuma gaisuwar ma ta daina aiko masa!

Sosai suka gaisa abin su,cike da tsantsar kauna da kuma fahimtar juna dake tsakanin su! *Hajjo ce* ta shiga parlon mai gidan nata,itama dai tana dingisa kafafu sabida matsalar tasu kusan iri d'aya ne tare da mai gidan nata! itama ma kam ta tsufa sosai,sabida za ta kai shekaru 70 a duniya.

"Oyoyo mai gida na,kana ina ne." Hajjo take fada a lokacin da take idasa shigowa cikin parlon,ai kuwa babu shiri ya mike daga zaunen da yake da sassarfa ya karasa inda take yana sakin dariyar shekiyanci yace "gani nan kuwa my wife a kusa dake"

Tare da taimakon sa suka karasa zuwa inda su Babi suke,ya zaunar da ita a gefen Yaya Babba,sannan shima ya zauna a wajen kafafun ta yana mata matsar kafa,Babi kuma yana daga wajen kafar Yaya!
Sabuwar gaisuwa suka sake yi inda take tambayar su wajen mutan gida,suka shaida masu kowa lafiya.

Gyara zama Babi yayi,ya kalli Yaya yace "ka bamu wuri ko mallam?" Ba tare daya musa ba kuwa ya mike ya fice daga parlon yana shafa sumar kansa dake kwance lup-lup gwanin birgewa,ba kamar idan ya tashi hargitsa su ba.

Bai tsaya daga bakin kofa ba ya kusa kansa zuwa cikin gidan dake da girma sosai, inda ya shiga parlon da yake jiyo hayaniya bakin sa dauke da sallama.

Wata matace zaune kan kujera da zata kai kimanin 35yrs,tare da wani magidancin mutum da zai iya kaiwa 55 da kuma wasu yara guda biyu mace dana miji da suka cika parlon da hayaniya daga can gefe suna wasan su.

Jin muryar da suka jiyo ne yasa su dakatawa daga hayaniyar da suke dik suka shiga taitayin su sabida sanin halin Yaya da rashin son hayaniya.

Wannan magidancin mai suna *Abubakar da suke kiransa da Dad* ne ya mike hadi da bude ma Yaya hannayen sa alamun yazo gare sa,fuskarsa shimfide da zallar murmushi!

kamar wani karamin yaro haka ya karaso zuwa inda yake ya fada masa jikin sa, bubbuga bayan sa Dad yayi,hadi da fadin "sannu da zuwa Baban mu! Fatan kazo lafiya?"

Sai da suka zauna kan kujerar sosai kamin yace, "lafiya kalau Dad,ina su Mom tare dasu Hauwa'u sarkin surutu??"

Dariya Dad yayi yace, "Dik suna nan lafiya kalau,amma fa suna fushi da kai sabida gudun su da kayi baka zuwar masu ziyara."

Shima dariyar ya sake kamar bashi ba yace, "su Hauwa'u Jiddah manyan mata,ina nan zuwa kace mata karsu damu,insha Allah zanzo kwanan nan!"

"Ina wuni uncle yaya?" wayannan yaran suka hada baki wajen gaisar da Yaya, sai da ya wani dan tsuke face wai shi gudun raini yace "lafiya"

Kallon gefen da *khadeeja* ke zaune yayi,inda yaci karo da fuskarta,tana wurga masa harara kamar idanunta zasu zazzago k'asa.

"Malama Dije wannan kallon fa kamar zaki cinye ni?" Ya fada yana mai dage mata gira guda,wanda hakan yasa ta daukar pillow din dake gefenta ta jefa masa,aikuwa babu shiri ya goce yana mai sakin dariya kamar bashi ba!

"Dad ka jimin wannan matar da rashin kunya ban shiga shirginta ba,ita tana kokarin shiga tawa ko??" girgiza kai kawai Dad yayi cikin murmushi yace "kunfi kusa ai Yaya"

Turo baki gama yayi ya tashi daga gefen Dad zuwa inda anty (khadeeja) take,ya zauna a gefenta yace "Mutuniyas ya ake ciki ne,naga sai faman harara ta kike tinda na shigo?"

Tab'e baki Anty tayi cikin sanyin murya tace, "ba dole na harare ka ba,daga shigowan ka har ka kora man yara waje sabida cin zalin su da kakeyi,idan sun ganka kamar sunga dodo."

Wanda shi sai a lokacin ma ya lura ashe har yaran sun bama wandon su iska, sai kuma yaji babu dadi har cikin zuciyarsa,amma sai ya waske kawai yace "To dama so kike na sakarma yarana fuska su rainani?"

Rank'washi ta sakar masa akai tace "Dan baka son raini sai kuma akace ka zamar masu dodo!"

Tab'e bakin sa yayi yace "kyadai ji dashi ai,niba wannan ne ya kawo ni ba! ina wuni Anty?"

Sai a lokacin ta saki fuska sabida jin ance mata Anty,kuma ba kowa ne ya fadi hakan ba sai Yaya tace "lafiya kalau kanina! Yasu Ammi da sauran mutanen gida?"

Aikuwa take Yaya da Dad suka fashe da dariya sabida yadda take wani murmushin son girma! Bama idan tana tare da yaya! Wanda gani take kamar ta basa wasu shekaru masu yawa,nan kuwa shekara guda d'aya ne tal ta basa,tana da 35yr,yana da 34!

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[7/23, 11:51 AM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BADA RUWA...!!*
     

*©️OUM MUMTAZ✍️*

           *charpter 12*

******** Yau ta kama ranar laraba.

Waali ne ya shigo gidansa da gajeruwar sallama d'auke a bakin sa,wanda kallo d'aya idan mutum yayi masa,zai fuskanci zallar damuwar dake tattare dashi,ga wani irin rama da yake ta faman zubawa a t'sait'saye sabida damuwar da suka masa yawa bana wasa ba!

Alina ce zaune daga bakin dakin ta,ta mikar da kafafunta inda gabanta kuwa wata laida ce ta bank'ararriyar kaza dake ta faman tururi yana tashin kamshi! Yagar kazar ta takeyi hankali kwance,tana korawa da hollandia!

Da mamaki Waali ya idasa shigowa cikin gidan nasa,sabida abinda idanunsa ke gane masa,domin kuwa shi kam a iya sanin sa dik wasu basissikan da yake ciyowa kansa wajen sayo ma Alina kayan dadi bai taba sayo mata irin wannan kazar ba,sabida kazar sai wane da wane ne kan iya sayan ta bawai yaku bayi irinsu ba!

Zama yayi a bakin tabarmar cikin tuhuma yace, "Alina a ina kika samo kudin sayar wannan kazar kuma?"
Banza tayi masa kamar bata san da ita yake ba,tana mai ci gaba da yagar kazar ta kamar wata koron yunwa!
Cikin kaushin murya yace, "Ba da ke nake magana ba?"
D'an dakatawa daga cin kazar tayi,had'i da yi masa wani irin kallo na shek'ek'e cike da fit'sara tace, "Ina ruwan ka da inda na samu kud'i,tinda kai ka kasa yima matar ka abinda take so?"

Da shike dama yau din zuciyarsa a kusa yake,abinka ga mutumi wanda bai sabayin fushi ba dama ance ka guji ranar da yayi fushin ba zaka ji da dadi ba! Ware muryar sa sosai yayi cike da tsananin hasala ya buga mata tsawar data kusan zautar da ita yace "uban waye ya baki kud'i kika sayi kaza nace!!!!!"

Jikin Alina ne ya dauki rawa sabida sabon yanayin data gani a wajen mijin nata da ba ta saba ganin haka ba! Ta matsa baya tare da laidar kazar ta!

Wani wawan fusga yayi ma laidar dake hannunta,hadi dayin cilli tashi sama,saiga kaza kuwa ta dawo kasa,cikin kwatamin dake daga can wajen makwararin wanke wanke!

Wani irin ihu Alina ta sake kamar wacce aka yanki namar jikinta sabida ganin inda kazarta ta fad'a! Dikda cikinta dake mata kugi akan yanayin da Waali ke ciki ba,hakan bai sata yin wani uban tsalle ba sai gata ta diro a gabansa taci masa kwalar rigarsa cike da t'sant'sar masifa da kuma bala'i gami da tsiwa tace "wallahi Waali baka isa ba!! Nace baka isa ba! Wallahi saika biyani kazata kona tara maka jama'a tinda bakai ka sayo man ba,baza ka hana ni ci ba!!"

Abinku ga zuciya na kusa,wasu irin tagwayen maruka ya fara jere mata su a fuska,cike da tsananin hasala da tinda yake a rayuwarsa bai tab'a yi ba!

Amma da shike taurin kai na mata yawo cikin kwanya,k'in sakin sa tayi,bakinta bai mutu ba,saima uban ashariya dake sakin masa marasa dad'in ji! Wanda har mak'wafta ana juyo su,abinku ga geto area nan da nan mutane suka cika cikin gidan yan gulma,amma aka rasa wanda zai shiga tsakanin wannan fadan,sai faman Allah shi kara ake ma Alina akan irin jibgar da take sha a hannun Waali a dai-dai wannan lokacin yana saita fad'a masa uban daya bata kudi ta sayi kaza tana bazata fad'a ba!

Iyami kam baiwar Allah tin farkon fad'an nasu tana jinsu daga kewayen ta,amma haka nan taki fitowa daga d'akin nata sabida tasan yau Alina takai Waali iya mak'ura ne daya sa shi laftar ta baji ba gani! Wanda kuma tasan muddin taje ta kwaci Alina a hannunsa ba tayi masa adalci ba! Hakan yasata k'in fitowa ma daga cikin dakinta,dikda hayaniyar mutane da take jin ya cika gidan,kuka take a wannan lokacin sabida bak'in ciki da kuma takaicin halin diyar ta,da batasan inda ta kwaso su ba, wannan shi ake cewa ka haifi d'a,baka haifi halinsa ba,kuma albasa batayo halin ruwa ba!

Wannan magidanci mai kudin dake sake hurema Alina kunne ne ya fad'o cikin gidan tare da yan sanda kamar wanda aka koro su! Wanda a wannan lokacin kuwa sosai Alina taci na jaki a hannun waali kamar bazai barta da rai ba! Inda yan sandan sukayi kansu da kyar aka banbare ita Alina din daga hannun Waali! yan sandan suka rirrike sa,had'i da koran dik mutanen dake cikin gidan! Har zuwa lokacin kuwa ko leke Iyami batayi ba,saima kukan ta daya t'sananta sabida bakin ciki gami da takaici!

"Wallahi aure na da kai ayau dinnan ya kare! Domin kuwa ni ba jakar ka bace da zakayi man irin wannan dukan!" Alina ta fada,tana mai sharb'ar majina,fuskar nan tayi daga daga da hawaye,tare da majina,ga shatin hannayen Waali da sukayi mata b'aro-b'aro akan fuskarta!

Abin takaici da bakin cikin daya sake rufe zuciyar Waali shine ganin wani gardin banza ya d'aga masa matar sa yana goge mata fuskarta da tufafin dake sanye a jikinsa! Wani kukan kura yayi cike da tsantsar zuciya dashi kansa baisan yana dashi ba,yayi wurgi da Alina gefe,had'i da shak'o wuyan Alajin ya rufe sa da duka kamar Allah ne ya aiko sa! Domin kuwa dama yau kamin ya shigo gida sai da wani mai shagon unguwar su ya tare sa,yana fada masa yasa ido akan matar sa,da kuma bakon mai kudin daya zo unguwar su! Domin kuwa dazunnan ya ga mutumin da ita Alina a k'ofar gida ya bata wani bakin laida da baisan minene a ciki ba,bai gama yarda da abinda aka fada masa ba sai da yakai ga shigowa cikin gidan nasa,wanda hakan kuwa sosai yayi masifar daga masa hankali! har zuciyan yan maza ta mot'sa!

Da kyar kuwa Alh yasha a wannan lokacin,tare da taimakon yan sandan! da Alh ya biya su kud'i sbd su daure masa Waali tinda yasamu labarin irin kilar da yake ma Alina a yaudin!

" *idan kaci ka dan halak!! haihuwar uwarka Zulai! da ubanka Aminu! Kuma ka tabbatar da cewa ta hanyar sunna suka haifeka bata hanyar fasikanci ba!!! Ina so kamin saki daidaya har guda uku batare daka sake motsawa daga nan ba ABDULLAHI!!!!*"
Suka tsinkayi muryar Alina dake ta faman sauk'e numfarfashi sabida azabar k'ullewar da mararta tayi mata a dai-dai wannan lokacin!

Da wani irin gudu Iyami ta fito daga cikin dakin nata,har tana tuntub'e ta dirk'usa a gaban Waali da hannunsa ke daure cikin ankwa ya gagara motsawa daga inda yake! Kansa na k'asa,idanunsa na fidda wasu irin zafafan hawaye! Tabbas a yau dinnan yayi nadamar auren Alina da yayi! Had'i da kuma danganta ka ta yan uwa daya had'ashi da ita!

Rike k'afafun Waali iyami tayi tana sakin kuka harda majinah tace " *Na roke ka da girman Allah ka sauwake ma wannan yarinyar mara neman albarka ubangijinta Abdul! Ka sake ta! Ka nuna mata cewa tabbas kai d'in d'an halas ne!! Ba wanda aka same shi ta hanyar fasik'ancin ba kamar yadda ta ambata!!*

Wani irin murmushi mai tsananin ciwo Waali ya sake kamin ya kalli side din da Alina ke kwance cikin wani irin sanyin murya kamar ba tasa ba yace " *DIK MUTANEN DAKE WURIN NAN! INA SO KU SHAIDA CEWA NI ABDUL WAALI AMINULLAH! _NA SAKI MATATA ALINA SAKI DAYA! NA SAKE TA SAKI BIYU...! NA KUMA SAKE TA SAKI UKU!!!_ DAGA YAU HAR DUNIYA TA NADE BABU NI BABU ITA DA DIK WASU ABINDA YA SHAFE NI A FANNIN AURATAYYA!! ALLAH YA HADA KOWA DA RABON SA!!!!*

Wani irin mugun sanyi jikin yan sandan dake wajen yayi su kansu! Cike da t'sant'sar tausayin Waali! Da kuma tir da halin mace irin Alina,dikda basu san mainene musabbabin fad'an nasu ba! Amma a yanayin da suka ga Waali tabbas sun shaida shine mai gaskiya! Babban d'an sandan dake wurin ne ya cilla ma Alaji kudin sa! Had'i da bama yaran sa umarnin su kwance ma Waali hannayen sa! Cikin kankanin lokaci kuwa suka kwance masa hannunsa! Inda ya dirkusa har kasa yana sakin wani irin murmushi dake tarwatsa zuciya!

Mikar da Iyami dake ta faman kuka kamar ranta zai fita yayi bayan yan sandan sunyi ficewar su! Sannan Alaji ma ya fice daga gidan cike da matsanancin farin ciki ba tare da damuwar abinda yan sandan suka masa ba, sabida ganin wannan ranar kamar an masa albishir ne da gidan aljannah!

Share mata hawayen ta yayi, hadi da sakin mata murmushi da iyakacin sa akan lab'b'anta ne yace,  "To mainene kuma na kuka Iyami? Dan Allah kibar zubdar mana da hawayenki mai daraja! Fatana kawai ki mana addu'a Allah yasa hakan shine yafi mana alkhairi baki dayan mu!!

Da kyar Waali ya samu ya lallaba Iyami da numfashinta ke faman sama da kasa! Kamin tayi shuru! Kallon side din da Alina ke sheme a kasa tayi! wacce keta faman hada zufa tace, "Ke kuma tinda haka nan kika zaba ma rayuwarki! Zaki ga sakamakon abinda kikayi ma Abdu ganin idanunki tin anan duniya kamin aje ga lahira! Badai ke kince kwadayi ba?? To kuwa tabbas da izinin Allah saikin sauka a tashar walak...!"

Taushe mata baki da Waali yayi ne yasa ta kasa karasa maganar dake fitowa a bakinta! Har kewayenta ya kai ta,had'i da kwantar da ita kan yar katifarta! Ya sake lallaba ta,kamin ya fito a dakin,wanda shima kawai k'arfin halin ya key, da ace shima zai samu mai rarrashin sa tabbas iya so! Amma kuma wanene? A kuma ina ne? wayannan sune bai sani ba!

Kewayen su ya koma, inda ya tarda wata t'sohuwar ingozama dake unguwar su,tare da wacce ke taimaka mata kan Alina data gama ficewa cikin hayyacinta sabida nakudar da ta sako ta a gaba gadan-gadan baji ba gani!

Bai karasa inda suke ba,yaja ya tsaya daga can gefe! Tabbas a wannan ranar Alina ta dandana gudarta ta! Tsawon wunin wannan ranar ta dauka kamin Allah ya takaita mata wahalarta ta samu kanta!
Su ingozama ne suka gyarata,tare da abinda ta haifa! Kamin suka tafiyarsu,Bacin Waali ya masu godiya!

Sai wajajen k'arfe 8 na dare Alina ta farka! Abin bak'in ciki da takaici, ko ta kan yarinyar data haifa batabi ba! Ballantana tasan kalar data haifa ta harhada kayayyakinta cikin akwati! Tasa kai ta fice daga gidan ba tare da sanin ko wannen su ba!

*vote*
*comment*
*share*
[7/24, 9:04 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BADA RUWA...!!*

*©️OUM MUMTAZ✍️*

           *charpter 13*

***** Dawowar Waali daga kasuwa wajen sayayyar da yayi ma y'ar tasa ya fara jiyo kukan yar tasa na masa maraba tin Shigowarsa, da gudun sa,gami da sassarfa ya k'arasa idasa shigewa cikin d'akin!
Kallon d'akin yayi gaba daya babu Alina babu labarinta, sai y'ar tasa dake ta faman callara kuka kamar tasan abubuwan dake faruwa cikin duniyar iyayenta!
Daukar y'ar tasa yayi ya rungumeta! Kamin tayi shuru! Luf tayi a jikinsa tana sakin ajiyar zuciya alamun ta jima tana kuka! Wani irin tausayinta ne ya kamasa!  

Dik inda yasan zai samu Alina cikin gidan ya duba,babu ita babu dalilinta! Wanda hakan yasa shi dawowa dakinta yaga ashe har kayan ta ma rabi da kwata babu! hakan kuwa daya gani ya sake tabbatar masa da hasashen sa na cewa Alina tasa kafa ta gudu tabar jinjirar data haifa ayau yau ba tare da tayi tunanin abinda zai iya zuwa ya dawo mata ba sabida son zuciya da kuma kwad'ayin abin duniya!

Kewayen iyami yayi da nufin sanar da ita halin da ake ciki, amma kuma sai me? Abinda ya tarar ne yayi masifar d'aga masa hankali fiye da misali! Domin kuwa dai bai tarda iyami a duniya ba,Allah ya anshi abinsa!

Wani irin kuka Waali ya fashe dashi! Mai cike da zallar damuwa da kuma bakin ciki! Had'i da t'sant'sar t'sanar Alina sabida yasan itace silar komai akan dik wasu abubuwa da suka faru ayau dinnan sabida dogon buri irin nata a cikin duniya!

Cikin kankanin lokacin rasuwar Iyami ya karade cikin unguwar tasu a wannan daren, tare da guduwar da Alina tayi tabar karamar jinjirar data haifa a wannan ranar! Wanda dik wanda yaji abinda ya faru yakanyi ma Alina Allah wadai!
A tsakankanin wannan lokacin kuwa sosai Waali yayi wani rama mara kyan gani,domin kuwa dashi da yarsa sun tabbata marayun ta ko wanne fanni!

Washe gari da safe akayi ma iyami suturarta aka mika ta gidan ta na gaskiya! Ba tare da an b'ata lokaci ba Waali ya saka gidan nasu a kasuwa dikda yana da sanin cewa itama Alina tana da nata kason,amma kuma yasan hakan da zayyi yafiye masa koma a rayuwa!

Y'ar sa kuwa da nono akuya yake shayar da ita,yaki barin kowa yayi masa rainon ta! A ranar da akayi sadakan bakwai a ranar ya rada ma y'arsa suna *ZULAYKHA* wato mai sunan mahaifiyarsa dayake da burin sawa!
Gidan yazamana daga shi sai y'arsa da wani irin shakuwa na ban mamaki ke sake shiga tsakanin su!

A lokacin da *Ummi nah* (kamar yadda yake fada mata) ta cika sati uku a duniya, ya samu wani Alh zai sayi gidan nasu, aikuwa an ma gidan tayin mutunci, domin kuwa mak'udan kud'ad'e mutumin yasa ya sayi gidan,wanda haka kuwa yayi ma Waali dadi sosai ba kad'an ba!
First abinda ya farayi shine raba kudin tsakanin sa da ita Alina din kamar yadda musulunci ya tanada, Inda nasa kason yafi nata yawa kasancewarsa d'a namiji!

Sannan ya saida shagon sa dake kasuwa, dik wasu basis sikan dake kansa saida ya sauke kamin ya tattara ya nasa da nasa yayi ma garin Maiduguri hijira na har abadan da yake jin bazai taba sake taka kafafun sa cikin su!
Tare da yarsa suka bar gari da itama sam bata yarda da kowa idan ba mahaifinta ba zuwa garin Kano ta dabo tumbin giya,koda me kazo an fika!

*Bangaren Alina kuwa*

Ashe dama sun hada plan tare da wannan Alh,saida ta faki idanun yan unguwar tasu kamin tayi wuf ta fada motar da Alh ya shaida mata zasu gudu da ita,dake ta can gaba da gidan su kadan, A cikin wannan daren suka bar cikin garin Maiduguri zuwa Ben sheik! Inda washe gari suka d'auki hanya tare da Alh ,da kuma driver nasa zuwa can garin Zamfara kamar yadda Alh ya fad'a mata can suka nufa!

Sunsha tafiya kuwa ba dan kad'an ba,kamin suka isa can cikin dare! Abinda zai bama mutum mamaki da halin Alina sam ita bata tunanin jinjirar yarta data baro tare da mahaifiyarta take ba,sai tunanin abin duniyar da zataje ta tarar acan garin Zamfara din,tana jin zuciyarta wasai sabida rabuwa da talauci da tayi na din-din-din!

Wani tangamemen gida na alfarma dake cike da securities kota ina taga motar tasu ta shiga,wanda hakan yasa ta sake jinta a duniya sabuwa kanta na huruwa ta shigo gidan masu kud'i,shiko Alh sai sake wani lallab'ata yake kamar ya samu k'wai!

Gidan kam ya tsaru ne iya tsaruwa! Dikda kasancewar gidan ba cikin gari yake sosai ba! Wanda tinda motar su ta shigo cikin gidan taga yadda ake ta faman daga ma motar tasu hannu alamun girmamawa!
Tinda suka zo wannan gidan kuwa nama ta yau daban,ta gobe daban,kama daga kan su kaza,talo talo da dai sauransu! Wanda wani naman ma idan aka kawo mata ci kawai take sabida kwadayi ba tare da sanin ta maicece ba!

Shi kuwa Alaji a ranar da suka cika kwana uku da zuwa gidan aka daura masu aure da Alina, tufafi kam Alina sai da ta ture su masu tsadar gaske! Cikin lokacin kankanin Alina ta koma hajiya Alina cikin gidan, ga wani uban respect da ake bata a matsayinta na matar Alh!

Hakan yasa take sake gaskata cewa ta cutu iya cutuwa a zaman aurenta da Waali na shekaru biyar, sai a yanzu ne ta fuskanci cewa lallai tayi aurenta da suka fara angwance wa da Alh dinta da babu abinda ya rage ta sai zallar soyayya!

Dik wannan bidirin da akeyi Alina batasan kowa daga cikin family na Alh ba sai ma'aikatan gidan, Amma hakan sam bai dame ta ba,tin tana cin mai maiko,ta kwana a mai kyau,ta kuma sha mai kankara!
Cikin lokaci kalilan tama manta dasu Iyami tare da yarta harma da Waali a duniyarta baki daya!
Bayan wata biyu!

******** "Ya mukaji da karin hakuri kuma yar uwa??" Yaya ya fadi yana mai kallon Anty da suka sha hirar su sosai, wanda zuwa lokacin Dad ma ya fice daga parlon zuwa can wajen su Babi sbd kiran dasuka aika aka masu!

"Alhamdulillah ,sai godiyar Allah Yaya!"  ta fada tana mai dan share kwallar data fitoh mata daga cikin idanunta! "Allah ya jikan musulmi! Idan kuma tamu tazo Allah yasa mu cika da imani!!!" "Ameen summa ameen!!"

"Wai kasan mai Ya Yusuf(Dad) yazo man dashi kuwa dan uwa?"  Gyara zama mai kyau yaya yayi cike son jin abinda Dad din ya fada yace, "Ah-ah sai kin fad'a!!"

Kamar karamar yarinya haka nan ta turo baki gaba tace, "Wai fa so yake nayi aure tin daga yanzu, kuma ma fa Kai ma kasan kwata kwata rasuwan su Baban su *NURAAZ😻* (sunan wani littafinah kenan ga wanda suka karanta ina fatan baku mance dashi ba😉) bai wuce shekara guda ba amma Dad yake son matsa man wai yana son na auri amininsa! Nida kwata-kwata ma banso na sakeyin aure har karshen rayuwata."

Wani irin kallon shek'ek'e Yaya yayi mata mai kama da lallai bansan baki da hankali ba sai yau! Itama hararar sa tayi sabida dama sukam kamar masu ganin hanjin juna ne tace, "Dallah wannan wane irin kallon rashin kunya ne Mallam??"

Gint'se fuska yayi kamar basu suka gama wasa da dariya yanxu ba yaci serious face wanda hakan yasa itama maida fuskartata serious yace "Amma dai kam idan kikace haka Allah anyi babbar kwabo Khadee ,ke dama a tunaninki haka su Dad zasu zuba maki ido suna kallon ki ba tare da kin sake yin wani auren ba sabida tsoron ki sukeji?? Hmmm toh wlhi gwandama tin wuri kiyima kanki fada kisan inda yake maki ciwo kamin lokaci ya k'ure maki! Kinfa riga da kinsa cewa wannan auren da Dad ke kokarin yi maki shine cikar mutuncin dik wata diya mace mai daraja amma kike k'ok'arin butulce ma ubangiji akan ni'imar da yake k'ok'arin sauk'ar maki? Nidai shawarar da zan baki a matsayi na,na d'an uwanki shine ki amshi zabin da Dad yayi maki hannun bibbiyu,sabida da-ke-da-ni dik munsan cewa bazai taba maki zab'in tumin dare ba!"
Sosai Yaya ya kashe ta da kalaman da nan da nan taji harma ta amince da auren da Yayan nata ke kokarin yi mata tare da amininsa!

Su Babi basu baro cikin Abuja a ranar ba,sai da aka saka bikin Yaya da Husnah nan da sati uku masu zuwa idan Allah ya kaimu! Inda suka koma ma su Ammi da Ammah da t'sarabarsu da suka samu daga su Hajjo! Harma da guzurin gaisuwa ta musamman da Yaya Babba ya aiko ma da Ammi (Kausara) ta bakin Yaya K'arami! A lokacin da sakon gaisuwar ya sameta kuwa abin mamaki sai gata da kyalkyalewa da dariya sabida tasan ba banza ba Yaya Babba ya aiko mata da gaisuwa ta musamman.

Kowa dake gidan ranar yaga chanji a wajen ta,domin kuwa idan ta tuno da gaisuwa Yaya din daga lokaci zuwa lokaci takan sakin murmushi yau babu daure fuskar data sabayi a y'an kwanakinnan!

Ranar Husnah da Yaya kamar zasu had'iye junan su da soyayya sabida sunsan auren gata za'ayi masu! Domin kuwa ba k'aramin k'aunar Yaya da Husnah akeyi cikin wannan family din ba fiye da kima!

Cikin k'ank'anin lokaci amarya Ma'u fatar ta, ta fara sauyawa sabida gyaran da take sha ciki da bai wurin mahaifiyar ta! Wanda kuma Ammi ma sosai ta sauko daga fushin da take da yan gidan tare da yaranta da dama suna taya uwarsu kishi ne aka fada cikin harkan biki gadan-gadan babu kama hannun yaro!

Dad ne yayi ma Husnah kayan d'aki! Tare da kuma muhallin da zasu zaunaa a cikin garin Abuja.
Dikda Yaya na aiki amma Dad ya hanasa yace shi zai masa a mat'sayin gudun mawa!

Babi kuwa babu abinda yake masu banda addu'a tare da saya masu kayan gara a matsayinsa na uban amarya,domin kuwa sadaki ma Yaya Babba ne ya dauki nauyin yima takwaransa ba kowa ba! Wanda nikam nace wannan shi ake kira da auren gata!

A t'sakankanin wannan lokutan kuwa sai da Ammah ta koka bana wasa ba! Sabida halarcin wayannan mutanen a gareta bazai tab'a goguwa ba, Su anty khadee da itama suka dai-daita da aminin Dad zuwa yanxu sune k'irjin biki! Komai ya kammala gida yayi kyau domin kuwa an zuba dik wasu abubuwan da suka dace cikin gidan!

Su Mima sune k'annen ango,kuma k'annen amarya,inda Jiddah ma yar gida Dad ta tare a can sulaija, dik da daga abuja tazo da suka hadu da yan uwa da abokan arziki! Sai murna ake! Ansha shagali kam a satin auren daya gabata! Inda wayewar garin ranar friday bacin an tashi daga sallar juma'a dubban jama'a suka shaida daurin auren *ZULAYM AHMAD SHUWA* tare da matar sa *ASMA'U IBRAHIM SHUWA* bisa sadaki naira dubu dari da hamsin!
    
                              
*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[7/24, 9:19 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BADA RUWA...!!*

*©️OUM MUMTAZ✍️*
                                 

           *charpter 14*

******** Sauk'owa take daga matakalar jirgin sama daya sauka a cikin filin babban jirgi wato international airport dake garin Abuja! Wanda ya kwaso su daga kasar Dubai, sanye take cikin wata doguwar riga ta abaya mai kalar shud'i irin sararin samaniya,watoh sky blue! Wanda akayi ma gaban rigar ado duwatsu mai kyan gaske!
Ta yane kanta da babu kitso da siririn mayafin daya kasance mahad'in rigar ce! Farar fuskarta kuwa shimfide take da zallar farin cikin dawowarta kasarta ta gado wato Nigeria,wanda tayi tafiya zuwa kasar dubai a makwannni biyu da suka gabata,wajen yin sayayyan kayayyakin ta na ado da kwalliya.

Hannun ta kuwa rik'e yake da wani madaidaicin akwati maicin kaya kala uku! Inda idanuta suka sauka akan mahaifinta dake ta faman rarraba idanuwa sabida son gano ta inda yar lelen nasa zata b'ullo! Domin kuwa ba karamin kewarta yayi ba sanadin wannan tafiyar,da tinda suke bata yin tafiya ta kwana wani wuri ba tare dashi ba,wanda ko shine zayyi tafiya zuwa wani gari ko kuma kasa to k'afarta k'afarsa ne,domin ko bai yadda yaje wata uwa duniya ba,ba tare da d'iyar tasa ba!
Jin irin kyakkyawar rungumar da aka basa ne,ya shaida masa yar lelen sa ya iso! Sosai Abbah ya nuna murnar sa ta dawowar Zulaykha tin a filin jirgi kamin su idasa zuwa can ainahin gida!

Inda acan ma kuwa Zulaykha ta samu tarba na musamman,wanda ta tabbatar ba aikin kowa bane,saina mahaifinta! Sai nan-nan da ita Musty yake yi kamar zai maida ta cikin sa,dik kuwa da irin uwar hararan da yake ganin Mamy na aiko masa amma haka nan yayi mirsisi abinsa kamar bai san tanayi ba!

Tayi wanka,taci abinci gami da fiddo ma kowa tsarabar data kawo masa,inda na Abbahn ta yafi na kowa!
Wanda hakan kuma ya sosa ma Mamy rai,wai Zulaykha bata dauke ta mahimmanci ba,kamar yadda ta dauki mahaifinta(kujimin k'ok'ari fa☹️ a gun matar nan).

Washe gari.

Zulaykha ce zaune tsakiyar kan luntsumemiyar katifarta,ta tankwashe kafafunta! hannunta rike da waya tana karanta wani littafi mai suna ~RAYUWAR DARAKHSHAAN~ wanda wannan marubuciyar data saba kashe ku da dadadan littafan ta irin su :
_nuna so gaban kishiya._
_zatoh._
_ayshat._
_ta'ummu ka(aure saida kaka)._
_nigeria ko niger(wacece bora)._
_hamdeeyerh._
_nuraaz(treasure of noor)._
_silar al-majiranci._
_Aymana (romantic story_
_kunji munafuki_
tazo tayi _rayuwar darakhshaan_!
ina a halin yanxu take kawo maku daddadan labarinta mai taken ~RIJIYA TA BADA RUWA~ ba kowa bace wannan marubuciyar wayannan face littafan "OUM MUMTAZ"😉

Sosai littafin ke taba mata zuciya sabida ganin irin wofantar da shaan da iyayenta keyi! Wanda kuma hakan yasa ta tuno tata mahaifiyar!

K'iran daya shigo wayar dake hannun ta ne,yasa ta dakatawa daga karatun da take,hadi da sakin karamin murmushi sabida ganin wacce ke k'iranta!
Kamin ya yanke tayi recieving,had'i da manna wayar tata a kunnen ta tace, "Amincin Allah ya tabbata a gareki aminiyar arziki,fatan kina lafiya?!"

Daga ta can bangaren Jiddah dake gidan kakan ninta tace, "Tare dake my k'awalli! Fatan kin dawo lafiya??"

"Lafiya kalau wallahi! Ya kuma gajiyar zirga-zirga?" Zulaykha ta tambaya sabida auren Uncle na Jiddah d'in da akeyi! wanda bata samu damar halarta ba,sabida tafiyar da tayi!

"Zirga-zirga kam munata fama ai! Yanzu haka ma an daura auren ne! muna jira su dawo daga can inda aka d'aura auren sabida hada gagarumar dinner din da zamuyi anan abuja din,dafatan kema zaki zo ko?"

D'an murmushi ta daura akan fuskarta,dikda yadda yau ta tashi cikin tsananin faduwar gaba da bata san dalili ba tace, "Anya kuwa zan iya fidowa Jiddah? nida wai yau da nake son na huce gajiya amma kike son fito dani ba tare dana shirya ba?"

"Kunji ki da wata magana! Huce gajiyan menene zakiyi? keda ba tafiyan mota ko kafa kikayi ba saina jirgi? Allah kinsan nifa banson wannan lalacin naki!"

A tare suka kwashe da dariya,sabida jin yadda jiddah ke magana kamar wacca ta samu y'arta! "To ki tanadar man kaya bari nayi wanka nazo na sameki! kika ce kina gidan su Kaka ko?"

Cike da zumudi Jiddah tace "yeah! yeah! Ina can wallahi, kuma idan kayane kisha kurumin ki, dama dik wasu kayan dana dinka kema saida na maki naki, kawai suprising naki nake sonyi ne, dan Allah kiyi sauri kinsan nayi kewarki sasai!"

Bata bama Jidda ansa ba ta katse wayar,tana sakin dariya sabida tasan idan ta biye ta surutun Jiddah bazata barta haka nan ba! Wanka ta sheko abinta,bacin ta fito mai kawai ta shafa ma fatar ta, sai ta saka wandon jeans,tare da t shirt nasa ta zumbula hijap har k'asa, wayoyin ta ta kwasa tare da key na motar ta ta fito daga d'akin da d'an saurinta!

A parlo ta tarda Mamy na danne dannen wayarta kamar ko yaushe! Sai kuma ma'aikatan dake ta faman kai kawo! Abbah da Musty kuwa sun tafi sallar juma'ah! inda daga nan zasu wuce suleja wajen daurin auren kanin Dad din Jiddah kamin su wuco gida!

"Mamy na tafi wajen su Jiddah! idan Abbah na ya dawo ki gaisar man dashi! Kuma kice masa ban kirasa bane sabida nasan yana cikin taro! bye"

Tana gama fadar hakan da sassarfarta ta fice daga parlon sabida ganin har wajen 3 ma tayi,Mamy tabi bayan ta da wani mat'siyacin kallo, had'i da jan doguwar tsaki taci gaba da latse-latsen wayarta.

Lafiyayyar motar ta ta fada mai kyawun gaske! Hadi da bama motar wuta ta fice daga gidan bacin mai gadin su ya bude mata gate! Sosai take sharara uban gudu akan babbar kwaltar! Wanda hakan yasa cikin kankanin lokaci ta unguwar su Kakannin Jiddahn.

******** Banda washe baki babu abinda Yaya yake yi a lokacin daya ji mai sanar wa ya gama tabbatar masa da cewa an daura masa aure,tare da sahibar sa,kuma muradin zuciyarsa bacin tsawon lokaci daya dauka yana dakon soyayyarta.

Inda suke ta faman gaggaisa da y'an uwa tare da abokan arziki! Daga nan suka wuce wani madaidaicin hole da abokan sa suka kama akayi walima yasu yasu da abokan ango, inda basu suka bar wajen ba sai goshin magriba, wanda shima sun dawo ne dinne sabida su sake shiryawa wajen tafiya gagarumin dinner din da d'an Yaya babba mai bi ma Dad ya shirya masu a wani dankareren hole, wanda shi bama a kasar yake ba, dirar sa kenan a wayewar garin yau d'in!

Bangaren amarya kuwa banda kukan rabuwa da yan gidan nasu babu abinda take yi,bama kamar Ammah da basu tabayin cikakken sati guda basu tare ba, itama Ammah d'in kawai karfin hali take,amma kuwa tabbas tana cikin alhini na rabuwa da gudar jinin nata da zatayi zuwa cikin garin Abuja!
Su Mima ma dai kam banda rawar kai tare da karadi babu abinda akeyi na auren Yaya da kuma Anty Husnah! Kamar yadda suke kiranta kenan bisa umarnin Yaya tin basu kai haka ba!

Waleed da Hamad suma y'an shekaru goma sha hud'u a duniya,ba karamin gayyatar abokan su sukayi ba! Wanda dama abokan nasu kusan daya ne! sai sab'a babbar riga suke kamar wasu manyan mutane!

Bangaren Jiddah kuwa tare da Asmy y'ar gidan kanin babanta suna daga gefen amarya dikda sun girme mata da kusan shekaru hudu! inda suma suka shiga cikin kawayen ta dasuka zo gayya suka saje abinsu.

Uwar ango Hajiya kausara (inji yaya babba) wato Ammi itama ba'a barta a baya ba! Bakin nan sam yak'i rufuwa sabida ganin ranar auren danta na fari,data jima tana tsumayi yau Allah ya nuna mata shi da ranta da lafiya.
Ana kiran sallar magriba motocin da zasu wuce da amarya can Abuja suka iso tare da wasu dangin da suke bangaren gidan yaya babba!

A lokacinne kuwa suka ga tashin hankali,sabida yadda Husnah tabi ta kanainaye Ammah kan ita,ta fasa auren baza akaita wani waje ba! Da k'yar da sid'in goshi su Anty khadeeja tare da Mamar Asmy suka raba su anata faman zolayarta kan ai itace tace tana son auren,ba wani ne ya masu dole ba!

Haka nan motocin daukar amarya suka kama hanyar Abuja akabar su Ammah da Ammi da kewa,Hamad,Waleed,Mima da Hidaya gaba dayan su dama sunbi ayarin y'an d'aukan amarya ne sabida dinner din daza'ayi.

Gida ya rage y'an t'sirarrun mutane ne,Ammah ta kule uwar D'aka sai kuka take kamar yarinya,wasu na mata fadan kukan da take,wasu kuma kan mata dariya sabida koni kaina abin yaban dariya🤦🏼‍♀️

Gidan Yaya Babba aka wuce dasu sabida can ne matsayin gidan su ango,inda acan Suleja kuma yake matsayin nasu amarya,domin kuwa Babi ne ya karbi waliccin Husnah,inda Yaya Babba kuma ya karbi na takwaransa,dikda tsufar da yayi hakan bai hanashi taburewa kan lallai-lallai sai yaje wajen daurin auren ba!

Sun samu tarba ta musamman kuwa daga wurin su Mom din Jiddah tare da wasu mata na yan uwa, Inda sai a lokacin ma kamin Yaya yasa amaryar tasa a cikin idanunsa da aka kirasu a dakin Yaya Babba!

Haka nan yakejin shima zuciyarsa sam babu dadi, kamar ya sungumi abarsa yaje ya lallashe ta,amma babu yadda ya iya kasancewarsa mutum mai tsananin kunyan na gaba da shi.
Sosai aka masu nasiha mai rat'sa jiki,ta yadda zasu zauna lafiya ba tare da wata tashin tashinah ya bullo daga wurin d'aya daga cikin su ba.
Inda daga nanne kuma yan uwa da abokan arziki tare da kawaye aka dunguma zuwa gida amarya tare da rakiyar wasu goggon ninsu,a lokacin kuma wajen karfe takwas da rabi ne na dare.

Sun tadda su Jiddah a gidan tare da Zulaykha da ta natsu a gefe kamar t'summa a randa sabida yadda takejin zuciyarta ta kasa natsuwa waje guda. Amma sabida jidda haka nan ta dake.
Inda tinda akace mata yan kawo amarya sun iso,ta gagara motsawa daga inda take,gida kam sai son barka! Domin kuwa kuwa ba karamin kokari Dad yayi ba,wajen tsarin gidan,tare da kuma da kayayyakin daya zuba masu,masu kyau da inganci! Inda kayan kitchen ne kawai Ammah tayi ma yar tata kamar yadda iyaye mata suke ma yayansu.

*vote*
*comment*
*share*
  
[7/25, 12:28 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BADA RUWA...!!*

*©️OUM MUMTAZ✍️*
                           

           *charpter 15*

******** Bayan wata biyu.

B'angaren Hajiya Alina kuwa duniya ce sabuwa ta bud'e mata,sabida yadda take fantamawa abinta cikin kud'i da kayan alatu na more rayuwa babu ji,babu gani! Domin kuwa sosai Alh ke sake jikata da nairori tana wadak'arta yadda take so! Kuma dik wannan bidirin da ake ko nan da kofar gida Alh bai taba barinta ta taka ba! Wanda a cikin wannan wata biyun rabo ya ratsa tsakanin su,domin kuwa tana da shigar karamin ciki na wata biyu cif cif! Wanda hakan kuwa ba karamin abin farin ciki bane a wurin Alh ,sabida yadda yake gano burin sa na gaf da idasa cikewa babu sauran gurbi.
Wanda zuwa wannan lokacin hatta ga yan aikin gidan saida suka san da zaman wannan cikin,sabida yadda Alh ke bala'in ji da ita,kamar t'soka d'aya a miya.

Akoi wata dattijuwar mata data kasance d'aya daga cikin ma'aikatan gidan,tausayin inda Alina ta jefo kanta kawai take! Domin kuwa ta tabbata cewa da ace tasan Alh wani irin mutumi ne a duniya tabbas ko mai kama da ma'aikacin gidan sa aka nuna mata saita sume tana farfad'owa.

Tabbas ta lura kwadayi ne da kuma son abin duniya irin namu na mata ke neman kaita ya baro ta,wanda ita d'in ma hakance ta kasance mata tin tana budurwata! Wanda har kwanan gobe na duniya takanyi nadama hadi da kuka akan irin k'ask'antaccen rayuwar data kefa kanta,dik don sabida abin duniya.

Gidan Alh babban gida ne mai fadin gaske! Wanda ko ta wani kusurwa ke cike da murdaddun mazaje masu jini a jika dake dauke da manya-manyan makamai masu had'arin gaske.

Sannan kuma akoi flat-flat a cikin gidan da akalla suka kai kusan guda goma,masu zaman kansu! Wanda tin zuwan Alina wannan gidan kuwa bata tab'a taka k'afarta zuwa ko ina na cikin gidan ba,sai nata flat d'in da Alh ya ajiyeta tin farkon zuwanta,amma hakan kwata-kwata bai dameta ba.

Bayan wannan kuma akoi wasu flate guda biyu masu girman gaske dake dauke da dakuna mabanbanta,wanda suka kasance na ma'aikatan gidan,d'aya na mata d'ayan kuma na maza.

Rayuwa na gangarawa,lokuta na tafiya,wanda zuwa wannan lokacin cikin alina yayi wani irin girma na ban mamaki haihuwa yau ko gobe,wanda ko tafiya k'wak'k'wara Alina bata iyayi,komai sai anyi mata wanda kuma har zuwa wannan lokacin ko dai-dai da rana d'aya tunanin mahaifiyarta,tare da yarta data tsallake ta tafiyarta bai zo mata cikin kwakwalwarta ba,sabida formating na kwakwalwarta da Alhaji yayi na karfi da yaji da hanyar gagarumin t'safi.

Yau Alina ta tashi da ciwon nak'uda babu ji babu gani,hankalin kowa a mugun tashe yake cikin gidan,sabida yadda aka kwana aka wuni ana abu daya,ga kuma Alhaji shi a dokarsa yace babu kai matar sa asibiti da sunan haihuwa. Inda ya saka wannan dattijuwar dake tausayin Alina mai suna *Baba Rabi* ta karb'i haihuwar kamar yadda take karb'ar na sauran matan nasa,wanda Alina sam-sam bata da san ma inda kanta yake ba.

******** A wata unguwa na talakawa likis Waali ya samu wani gida d'an k'aramin mai d'aki d'aya tare da band'aki ya saya cikin kudin sa tin a ranar daya sauka cikin garin kano tare da taimakon wani dattijo da suka hadu tin a motarsu daga can Maidugurin. Alhamdulillah Waali ya ambata a lokacin da yaga gidan dake matsayin mallakin sa.

Da shike akoi RIJIYA a cikin gidan,wannan dattijon ne da suke mak'waftaka dashi ya aiko jikansa ya kawo masu bokiti yaro d'an shekaru 6.

Da shike akoi wasu abubuwan su na amfanin gida na yau da kullum daya kwaso daga can gidan nasu,sai baisha wani wahala ba a ranar,domin kuwa hatta ga kayan abincin su daya rage sai da ya kwaso su.

Wanka yayi ma y'ar tasa,tare dashi kansa da ruwan cikin RIJIYAr,dikda irin kukan da yar tasa keyi gwanin ban tausayi,kasancewarta sabuwar haihuwa. Inda ya had'a mata madararta a fida irin na yara tasha ta koshi,kamin shima yasama cikin sa cake tare da zob'on daya saya akan hanya,yanayin sallar isha'i ya shimfida masu karamar katifarsa dayazo dashi irin na yan boarding school mai cin mutum daya,sannan ya daura masu net suka shige bayan ya rufe masu kofar su ta ciki.
Akan cikin sa ya daura yar tasa inda ya tofe masu addu'a,cikin kankanin lokaci kuwa baccin gajiya yayi awon gaba dasu dikkansu.

Washe gari da safe Waali yaji ana buga masu kofa,cike da mamakin wanda yazo masu kuwa ya bude kofar gidan,tare da Ummi dake kan kafadar sa tana sharar baccinta hankali kwance,wanda a daren wannan ranar sosai tama sa rigima wanda sai kusan asuba tayi baccinta.

Wata matashiyar budurwa ya gani da zatayi sa'a da Alina a shekaru kofar gidan,sai faman harare-harare take,fuskar nan ram da kwalliya na kwalli da jan baki kaca-kaca kota ina,sam babu kyan gani. Ga yanda ta d'ano bakin nan gaba yawa k'arin kunama.

"Malama lafiya kuwa?" Wani tab'e baki tayi cike da rashin kunya tace "Mallam dallah kauce man na shige! Ni ba Malama bace,yanzu ma badan Baba ya matsa man sai nazo na maka shara ba ai da bazaka ganni ba!"

Ta fada tana mai bangaje Waali ta kutsa kanta cikin gidan,shi kuwa ya bita da kallon mamaki baki sake! Amma kuma da yayi tunanin wane Baba take nufi,sai ya tuno tsohon jiya da sukazo tare.

A ransa kuwa mamaki yake ta yadda akayi wannan fitsararrar ta zamana y'ar gidan wannan tsohon mai sanin darajar d'an Adam, girgiza kai kawai yayi,had'i da rufa mata baya yana girgiza kai.

Share-sharen gidan take,sai faman mita da tsaki take zubawa akai akai! Shi kuwa Waali banda kallon ikon Allah babu abinda yake yau dinnan a ransa fadi yake na rayu tsawon shekaru da wacce ta fiki fitsara.

Cikin awa d'aya wannan budurwar fes ta kammala share dik wani lungu da sako dake cikin gidan,had'i da jere kayayyakin data gani a inda suka dace,ba tare data ma Waali dake ta faman jijjiga yarsa sallama ba tayi tafiyarta! Harda ladan bugo masu kofa kamar zata balle sa.

Kamar jiya yauma dai da ruwan sanyi sukayi wanka,wanda yauma saida yarinyar tasha kukanta,sabida babu abinda tafi bukata a wannan lokacin sama da ruwan dumi,bawai mai sanyi ba.

Inda ya hada mata garin madarar ta,saida ya tabbatar ta koshi,kamin ya d'auki zanin dayake nannade ta ciki yayi mata goyo mai rai da lafiya kamar bana miji ba,ya bude k'ofar gidan da niyyar fita, sukayi clashing da jikan Baba wanda ya kawo masu bucket jiya(kamar yadda yaji yarinyar dazu ta fada) hannun sa rik'e da wani kwano na samira, mikama Waali yayi bacin ya gaishe sa yace "inji kaka yace akawo maka"

Waali kuwa cike da jin dadi yace "Kace masa na gode sosai."   Wanda dama fita zayyi domin neman abinda zaici koda kosai ne irin wanda ake sayarwa da safe.

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[7/25, 12:35 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...!!*

*©️OUM_MUMTAZ✍️*
                                

           *charpter 16*

********A lokacin ne kuma gidan ya idasa b'arkewa da hayaniya,sabida akoi kawayen amarya irin y'an kaud'i na bani na iya.
Su Jiddah ne tare da Zulaykha da wasu k'awayen su na nan Abuja suka sake tarban su cike da karramawa,wanda har zuwa lokacin Husnah na nannad'e cikin lafaya sai sharar k'walla take gwanin ban tausayi,Zulaykha taso taga fuskar amaryar da tazo domin ta amma bata sami damar hakan ba,sabida shirye-shiryen tafiya dinner da yan matan suka kacame dashi,inda itama amarya aka d'auko _munash beauty_ tazo ta sake fesa mata kwalliya mai kyan gaske.

Kowacce daga cikin su kam masha Allah babu na kushewa,inda Amarya kuma kwalliyar ta, ta fita daban dana kowa sbd nata d'in special ne.

Zulaykha da Jiddah ba k'aramin kyau sukayi ba,suma sun fito fes fes abin su,cik'as d'aya shine na rashin kwalliyar da Zulaykha tayi,wanda ko kwalli bai ga fuskarta ba,sabida dama ita tin can ba mutum bace mai son shafe-shafe,natural beauty nata take a yawancin lokuta,sabida ko powder irin na y'an mata bai ganin fuskarta.

Amma kuma hakan bai sa ta zama koma baya ba cikin su,kasancewar ta jik'ak'k'iyar shuwa arab gaba da baya.

A lokacin da suka fito madaidaicin harabar t'sakar gidan sun tadda motar da za'a d'auko amarya ne kawai,inda motar da k'awaye zasu shiga suna ta waje.

Zulaykha da Jiddah kuwa,Jiddah ce tayi driving nasu a motar da ita Zulaykha tazo dashi,sun isa hole d'in kuwa cikin k'ank'anin lokacin a cikin jerin motocin aboka nan ango.

Waje kam masha Allah,domin kuwa komai yayi dai-dai (inji wani mawak'i😻),cike da nat'suwa da kuma waye wa irin ta y'an Abuja aka fara gudanar da wannan k'ayataccen dinner,tinda Zulaykha ta d'aura idanun ta akan fuskan amarya da ango a lokacin shigowar su cikin hole d'in ta naimi dik wani natsuwa,gami da courage d'in da tazo dasu sun tafi,sabida abinda idanunta suka gane mata yafi k'arfin abin da k'wak'walwarta kan iya d'auka a dai-dai wannan lokacin! Nan take idanun ta suka kad'a sukayi jazir! Dik magana gami da jijjigata da jiddah kanyi akan su shiga filin rawa amma ta gagara mot'sawa,bata sa tsawon lokacin data dauka cikin wannan mummunar yanayin ba sai ji tayi an d'auke ta kamar wata babyn robber an fice da ita daga cikin hole d'in.

Wanda kuma har an kammala k'ayataccen dinner d'in,dik Zulaykha bata cikin hayyacin ta,wanda haka yasa hankalin jiddah ya tashi ba kad'an ba,k'anin Dad d'in su jiddah dake da wajen 39-40yrs,wanda ya kama masu wannan hole d'in kenan,shine yayi jihadin d'aukar Zulaykha daga wajen bacin an gama tattaunawa,wanda kuma sam ita Zulaykha bata ma san anayi ba,sabida yadda tayi loosing na hankalin ta a wannan lokacin.

Can gidan su Ummin jiddah dake cikin tashin hankali take ma uncle d'in nata kwatan ce,a lokacin wajajen k'arfe goma tayi na dare,inda suka dannan horn,leko kai mai gadi yayi,ya gano jiddah,wanda hakan yasa bai b'ata lokaci ba ya wangale masu gate d'in,cike da natsuwa  ~uncle jafar~ yayi parking na motar tasa a parking lord.

Abbah kuwa gaba d'aya hankalin sa ya karkata ne izuwa ga ita Zulaykha d'in da har zuwa lokacin bata dawo ba,dik yabi yasa kansa a damuwa,haka nan yake ji a jinin jikin sa kamar wani abu mara dad'i ya faru da y'ar tasa,dikda yana da sanin inda take amma ya gagara zaune ya gagara t'saye tinda yaga wajen karfe tara tayi bata kira ba,bacin kuma bata dawo ba,sannan kuma tin d'azun yake k'iran layin ta amma bata dauka ba,zirga-zirga yake ta faman yi cikin parlon sa yana kai kawo,Mamy kuma na zaune can d'akin ta ko a kwalar rigarta.

Musty ne ma dai shima yabi ya damu,inda yake taya Abbah d'in jaje shima yana daga zaune akan kujera,HORN d'in motar Zulaykha da suka jine ya sasu rige-rigen fitowa da sassarfa har suna bige junan su! Daga Abbah har Musty d'in cak suka tsaya suna kwalalo idanu waje sabida ganin Zulaykha da sukayi hannun Uncle j d'in babu alamar numfashi tattare da ita,ga kuma jiddah da hannun ta ke rike da kwamut'san Ummin fuskarta na bayyana irin tashin hankalin da take ciki.

********Tasha azaba kam iya azaba a wannnan ranar,domin kuwa saida ta kwan ta sake yini kamin Allah ya t'sauwala mata wahalar ta! Banda masha Allah babu abinda Baba Rabi ke an bata a lokacin da ta gama karbar haihuwa ta Alina d'in tare da wata dattijuwa sabida 3ples din da ta santalo jazir dasu,kalar fatar uwar su.

Goya Baba Rabi ne kawai Alhaji bayyi ba a lokacin da ta ke shaida masa haihuwar matar tasa,t'sabagen farin ciki da ta cika masa zuciyar sa,take labari ya karad'e cikin babban gidan lungu da sak'o,wasu kanyi farin ciki,masu hankalin cikin su kuwa kanyi bak'in ciki k'warai da gaske,sabida sanin makomar yaran da basu ji ba,ba kuma su gani ba,kamar yadda suke gani Alhaji bai d'auki rayukan jarirai a bakin komai ba,indai akan abin duniya ne babu abinda bazai iya ba.

Yaran sai callara kuka suke gwanin tausayi tinda suka b'illo duniya,sabida rashin d'umin jikin mahaifiyar tasu da itama take ta kanta,domin kuwa baccin wahala take ta faman yi mai cike da wasu irin mafarkar marasa dad'i,sai faman had'a gumi take.

Baba Rabi dake kula da Alina sosai take matik'ar tausaya mata ba kad'an ba,tayi farin ciki da wannan haihuwa kwarai,domin kuwa kaf cikin matan Alh dake cikin gidan babu wacce ta tab'a  haifan y'an biyu ballantana akai ga har uku,saidai kuma kash!!! Idan ta tuno makomar rayuwar yaran takan ji bak'in ciki fiye da tunanin mai tunani!

Kallon yaran Alhaji yake cike da tsantsar k'aunar su a lokacin daya shigo,harma yakan ji cikin zuciyar sa anya kuwa zai iya aiwatar da k'udirin sa da yayi zaman jira na tsawon shekaru 25???

Baba rabi a zuciyar ta banda addu'a babu abinda take,kan Allah yasa kar Alhaji ya butulce ma uban giji akan kyautar yara d'ai d'ai har guda uku da yayi masa cikin lokaci guda!

Alina tasha bacci ba kad'an ba,inda still Baba Rabi ce ke kanta har ta farka,inda ta taimaka mata wajen kimt'sa jikin ta ta fito fes abinta,kallon yaran nata dake dunk'ule wuri guda suna bacci tayi fuskarta cike da tsantsar farin ciki,wanda ganin yaran nata da tayi cikin k'oshin lafiya yasa ta naimi dik wasu ciwon jikin da take tattare da su ta rasa!

Wato wani irin kauna ce fiye da kima dangane da yaran ke sukar zuciyar ta! kauna ta tsakanin y'ay'a da iyayen su,wanda har ma ya zarce hakan,ni ban ma san ta yadda zan maku baya ni ba!

Mace guda d'aya ce,sai maza guda biyu! Sosai suke samun kulawa daga ta ko wanne b'angare na cikin wannan gida har na tsawon sati guda! Inda ranar suna na zagayo wa aka rad'a masu suna _BASSAM da BAZAM_ sai kuma d'iya macen _BASMA_!

Wasu irin mutane takan gani suna shigowa kallon yaran nata da sam sam hankalin ta bai kwanta da su ba,inda dik wanda ya shigo sai ta ga yabi yaran nata d'aya bayan d'aya an shafa masu kai da sunan zuwa barka! Haka nan take jin wani irin mat'sanancin fad'uwar gaba na riskar ta a dik lokacin da taga wani bak'on fuska yazo da sunan ganin yaran nata,ga babu halin ta hana sabida gudun matsala t'sakanin ta da Alh.
Zuwa can dare da misalin karfe goma Baba rabi tare da Alina suka keb'e,tsawon awanni suka d'auka suna tattaunawa wanda ni kaida banjin abinda suke fad'a.

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[7/25, 9:32 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...!!*
 

    *©️OUM_MUMTAZ✍️*

           *Charpter 17*

******** Komo wa cikin gida Waali yayi,inda ya zauna bakin katifar tasa,ya bud'e kwanon,d'umame ne na tuwon masara da miyar kuka sai tiriri yake alamun da zafi zafin sa,tas Waali ya cinye babu ko ragi sabida dama akoi kwantacciyar yunwa a jikin sa,inda yasha ruwa yayi ma ubangiji hamdala.

Abubuwan da ya dace ya sake yi wajen mai da komai mahallin sa yayi,inda ya fito daga cikin gidan tsakiyar layi yana ta faman kalle-kalle,kowa sai harkokin sa keyi,wasu kanyin k'us k'us idan sun ga namiji da goyo,kuma bak'on fuskar da basu sani ba suyi wucewar su,idanun sa ne ya sauka akan mutumin da suka jiya zaune daga can k'ark'ashin wata bishiya kan tabarma,sai kuma wannan yaron dake wasan sa daga gefe!

Ajiyar zuciya ya sauke yana mai jin dad'in ganin sa,sabida dama so yake ya sayo dik wasu abubuwan da bashi da su na amfanin yau da gobe da baza'a rasa ba.

Har k'asa ya t'suguna ya kwashi gaisuwa cike da girmamawa gami da mutuntawa,inda Baba ya ansa masa cikin sakin fuska had'i da tambayar sa ya kwanan bak'unta? ?? Gaishe sa wannan yaron yayi yana mai lek'a fuskar Ummi dake bacci bayan mahaifin ta hankali kwance,murmushi yayi cike da jin dad'in ganin yarinya k'arama yace "Kaka kaga wata yarinya mai kyau!"

Dik dariya sukayi,inda daga baya ya kunto masu da Ummi dake ta faman fiddo harshe waje alamun ta farka,addu'a sosai Kaka yayi mata kamin Masta ya leko fuskarta yana tayi mata wasa!

Inda daga k'arshe Waali ya shaida ma Kaka abinda ya fito dashi,wani matashin saurayi Kaka ya had'a su bacin ya karb'i Ummi daga hannun sa idan sun dawo sai ya karbe ta,domin kuwa zata sha wahala ne idan yaje kasuwa da ita yadda take a danye danyen ta,saida ya dama mata madarar ta ya bama Baba kan idan ta fara kuka a bata kamin suka masu sallama suka wuce kasuwa.

Sosai Waali yayi masu sayayya bana wasa ba,aljihun sa kuwa ta girgiza amma hakan ko a kwalar rigar sa,inda ya sayo har irin kayan trader dinnan da suka tashi,kayan wasa da kayan sawa masu sauk'in kud'i dik ya sayo ma abar kaunar tasa,Allah-Allah yake dama suyi su tafi sabida baro y'ar tasa da yayi a wani waje,wanda suka dauki wajen awanni hud'u kamin suka fito daga kasuwar da kaya nik'i-nik'i,shatar mota suka yo har kofar gidan,inda wasu yara dake tare da Masta suka fara shigar masu da kayan cikin gida,Waali bai samu ya gama jere komai ba sai wajajen la'asar,sosai yayi ma wanda ya raka sa godiya had'i da basa d'ari biyu ya huce gajiya,aikuwa mutumin da murnar sa ya wuce gida,domin kuwa a wannan lokacin kudi akoita da guntuwar darajarta kamin ta idasa karyewa.

Gidan Baba d'in da d'azu ya nuna masa kamin su tafi ya dosa da suke makwafta ka,kukan Ummi da yayi masa sannu da zuwa ne tin daga k'ofar gidan ya sa shi shigewa ba tare da na masa izni ba sabida tashin hankali,Baba ya tarda tare da mara kunyar y'ar tasa ta d'azu dik sunbi sun rikice sai faman lallashin ta suke amma yarinya kamar ana sake kunnata,ga Masta shima fuskar sa dik ta nuna irin damuwar da yake ciki sabida kukan da Ummi kanyi.

Basu ji alamun shigowar ba,sai ganin mutum sukayi gaban su kamar wanda aka cillo sa daga sama,wanda hakan ya sa su sakin ajiyar zuciya,bayyi wata wata ba ya karb'i yar tasa a hannun AISATA dake ta faman zagaye da ita,kamar anyi ruwa an d'auke sukaji miki'it babu wannan kukan da Ummi take yi sai faman sakin ajiyar zuciya sabida yadda taci kukan ta.

Rungume y'ar tasa yayi cike da t'sant'sar tausayin ta,inda yayi ma su Kaka godiya gami da wuce wa gidan nasa bacin ya karbi feeder na madaran Ummi!

Wanka ya farayi mata da ruwan d'umi daya d'aura kan risho kamin ya fita,inda ya dama mata kunu mai kyau da ruwan dumi,sosai kuwa yarinya tasha sabida uban yunwar dake dankare cikin ta,domin kuwa dik yadda su Aisata suka so tasha ko kad'an ne fir yarinyar nan taki sai uban kuka kamar wacce ake yankar namar jikin ta.

Cikin k'ank'anin lokaci tayi bacci,inda ya kwantar da ita a cikin nata net d'in bacin ya shirya ta ,sai shima ya shiga wankan ya fito ya saka wasu kayan sa kamin ya tada kabbarar sallah,saida yayi azahar da la'asar tare da magriba kamin ya tashi a wurin.

Taliya dafa dika yayi ma kansa,tas ya koshi abinsa,babu abinda yake buk;ata a lokacin kamar yayi bacci,amma sai ya d'auki y'ar tasa kan kafad'a ya fice da ita zuwa gidan Kaka,saida ya k'wank'wasa k'ofa aka basa izinin shiga kamin ya kutsa kansa da sallama d'auke a bakin sa,sai a lokacin ya kare ma gidan kallo,dake dauk'e da d'akunan bacci guda biyu,sai kuma bayi,inda daga can gefe kad'an kuma akoi wata karamar runfa dake d'auke da murhu guda biyu,sai kuma tukwane da d'an sauran kwanika da baza'a rasa ba.

Har k'asa ya kwashi gaisuwa,inda Aisata da Masta ma suka gaida shi ya ansa masu hadi da sake masu godiya bisa ga kulawar da suka bama y'ar tasa,nan ya shaida ma Kaka batin sayo kayan trader da yayi! Basu dai rabu ba,sai da suka tsaida dik yanda saye da sayar war tasa zata kasance ya wuce gidan sa cike da farin ciki da kuma jin dad'i na sabuwar rayuwar da zai shimfida a inda bai da kowa daga shi sai gudan jinin sa da kaf duniya bai had'a ta da kowa ba.

******** Can cikin bedroom nata Uncle j yayi ma Zulaykha masauk'i bisa ga umarnin Abbah da kwata-kwata bai cikin hayyacin sa,Musty ya k'ira Mamy,wacce ta d'an nuna damuwar ta,inda ta samu towel ta tsoma cikin ruwan dumi ta fara shashshafa ma Zulaykha a fuskar ta bisa ga umarnin uncle j kasancewar sa likita ne mai zaman kansa!

Dik cirko-cirko sukayi cike da damuwar dalilin daya sa Ummi cikin wannan yanayin,bacin kuma lafiya k'alaou suka shiga hole d'in suna walwalar su,saida uncle J yaga ta fara sauk'e numfashi hankali-hankali alamun tayi bacci kamin ya ce abar dumama ta haka nan yayi masu sallama ya wuce Abbah yayi ta masa godiya,inda Jiddah kuwa bata tafi ba a ranar,kwana tayi a gidan bacin ta kira mahaifiyar tata,ta shaida mata Zulaykha bata jin dad'i.

******** An kai amarya gidan ta tin a daren ranar,inda kawaye da ma wasu yan uwa dik sun kwana a gidan kamar yadda al'ada ta tana da,ango kuma da aboka nan sa suka wuce can inda zasu kwana.

Washe gari.

Bayan sallar isha'i akayi rakiyar ango bacin d'an nasiha da kuma addu'oi aka masu sallama aka bar amarya da angon ta da kewa harda guntun kukan ta na gulma irin dai yadda amare keyi kamar basu suka ce suna son auren ba.😏😏

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[7/25, 9:40 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...!!*

    *©️OUM MUMTAZ✍️*
      

           *Charpter 18*

******** Wani irin gumi ne ke t'sat'st'safo ma Alina a lokacin da ta gama jin labarin da Baba Rabi ta bata mai tarwatsa k'wak'walwa.

Sosai ta shiga cikin mat'sanancin ciwon kai gami da tashin hankali mara misaltuwa,dafe kan ta tayo,dik wasu memories nata da tayi loosing sun fara dawo mata cikin k'wak'walwarta daki-daki,
sosai gaban ta yayi wani irin mummunar bugawa,a lokacin da k'wak'walwarta ta hasko mata d'anyen haihuwarta data tsallako ta bari dik dan sabida abin duniya da ba mai dore wa ba!! Mahaifiyar ta Iyami ne ta sake fad'o mata cikin k'wak'walwarta,gami da d'an uwan ta,kuma mijin ta mai k'aunar ta da dikkan nin zuciyarsa,amma ta watsa masa k'asa a ido dik dan sabida _KWAD'AYI_ !

Wani irin rikitaccen kuka ta fashe dashi mai cike da t'sant'sar nadama da kuma dana sani! Baba Rabi kuwa tuni ta fice daga d'akin simi-simi sabida kar Alhaji ya gano su ta cikin madubi ta shiga uku,domin kuwa babu tantama idan yasan cewa ta fad'a ma Alina ko shi wanene tin kamin ya cika kud'irin sa karshen ta ta bak'unci lahira a yau yau d'innan! Sai dai kuma abinda bata riga ta sani ba,tin farkon fara zancen su! Har suka dasa aya akan idanun Alh ne! Tare da mutane marasa tsoron Allah ire-iren sa da suke k'ok'arin aiwatar da idasa cike nasu k'udirin ta hanyar aika Alina barzahu su bama dodon tsafin su jinin ta!

Wani irin gagarumin b'acin rai ne ya ziyar ce su baki d'aya,a lokacin da suka ga Alina ta k'ank'ame yaran ta baki d'ayan su tana bulbulawar ruwan hawaye,sannan kuma tana tofa masu dik wasu addu'oi da suka zo bakin ta,wanda hakan yasa dik wasu power nasu ya fara raguwa! Hakan ko ba k'aramin sake b'ata masu rai yayi ba,cikin abinda bai gaza minti d'aya ba,sai ga Alina rungume da yaran ta,tare da Baba rabi durk'ushe gaban way'annan munatanen da suke zindir haihuwar uwar su!

"Kin aikata gagarumin kuskure a rayuwar ki Rabi! Wanda hakan da kika aikata dai-dai yake da kawo k'arshen shan ruwan ki a duniya! Tabbas yau ba sai gobe ba!!! Yanzu ba sai anjima ba zaki bak'unci lahira! Zaki je ki tadda masu bakin akku irin naki da basu iya shuru su k'yale akan dik abinda zasu gani cikin gidan nan! Wanda nake tunanin hakan shine hukunci mafi sauk'i da zan iya yi maki!"

Alhaji ne ke wannan maganar cikin tsananin b'acin rai da yasa har halittar jikin sa ke fara canzawa daga na d'an Adam zuwa wata halitta ta daban! Take jikin Alina da Baba Rabi ya fara d'aukar b'ari suna sakin gigitaccen kuka mai tada hankalin mai sauraro! Dik wata addu'ar data zo bakin ta Alina yi take babu k'ak'k'autawa,tana rungume da yaran ta tamkar zata mai da su cikin cikin ta!

Allah sarki Baba Rabi! Banda karkarwa babu abinda jikin ta keyi,ga kuma addu'ar da itama take da buk'atar yi hakan ya gagara,domin ko abinda yasa Alina Allah ya bata ikon yin addu'ar sabida tonuwar asirin su ne da tayi kamin su kai ga cimma manufar su akan ta!

Take cikin wannan d'akin ya kacame da wani irin gurnani mara dad'in sauraro ga cikakken d'an Adam.

Sai kuma wasu irin dariya mai tafe da kuka mara sa dad'in ji daga mabanbantar murya daya karad'e cikin wannan d'akin kamar zai t'saga bango!!! Wani irin duhu ne ya mamaye d'akin da ko tafin hannun ka bazaka iya gani ba,wanda hakan ya sake razana Alina matik'a! A dai-dai wannan lokacin banda kaico da masu halin kwad'ayi irin nata babu abinda takeyi! Bata t'sagaita da yin addu'ar dake fitowa daga bakin ta ba, sai dai kuma yanzu idanunta a bud'e yake tana lalumar gefen da Baba Rabi take da k'afafun ta amma wayam bata ji ko alamar numfashi ba,ballantana mutum!

Wani irin haske ne ya mamaye cikin wannan d'akin mai kashe idanu da sai da Alina ta lumshe idanun ta kamin ta bude su bayan tsawon lokaci!

Wani irin zaro idanuwan ta tayi waje cike da t'santsar firgici har tana naiman hant'salawa sabida abinda idanunta ke gane mata! sake murza idanuwanta tayi da kyau domin tabbatar da abinda idanun nata ke gane mata! Ai wani irin cilli tayi da yaran kamar wasu kiyashi sai gasu sun baje a k'asa,a wani irin gigice ta mik'e da niyyar zuwa inda ta gano Baba rabi tare mahaifiyarta rayaye jikin gini tsirara haihuwa uwar su suna kallon ta,suna kuma girgiza mata kai alamun karta k'araso inda suke,kamar abu a iska, sai ji kawai tayi anyi wani irin cilli da ita daga sama zuwa k'asa da yasa ta callara wani uban ihu tace "IYAMI!!!!!"

********Washe gari da safe.

Zulaykha taji dad'in jikin ta ba kad'an ba,amma kuma sam ta kasa yima kowa magana tinda ta farka,sai dai ta lumshe idanun ta idanun ta na hasko mata fuskar Yaya da Husnah a daren jiya dake ta faman walwali had'i da fidda annuri alamun suna cikin t'sant'sar farin ciki maras misaltuwa sukan ziyar tar kwakwalwarta.

Babu yadda Abbah,Jiddah da kuma Musty basuyi da ita ba,kan ta fad'a masu damuwar ta amma sam tak'i tace masu k'ala sai dai ta bisu dana mujiya! Tana ji cewa a cikin jinin jikin ta ko mutuwa zatayi da son wannan bawan Allah n bazata tab'a barin duniya tasan halin da take ciki ba koda kuwa hakan zai zama ajalin ta!

Wasa-wasa dai sai da Zulaykha ta shafe t'sawon sati guda kamin ta gama dawowa cikin hayyacin ta,wanda kuma Jiddah ta wuce gidan su tin bayan kwanaki uku da suka gabata sabida ganin jikin nata da sauk'i,sannan kuma dik wannan tsawon kwanakin Abbah ya  tare ne a wajen y'ar sa yana bata dik wasu kulawan da suka kamata a mat'sayin sa na uba,kuma sannan mahaifiya!
Musty ma dai ba'a bar sa a baya ba,dik da shine yake fita wurin aiki amma yana bata dik wasu kulawan da suka kamata!

Mamy ce ma dai gashi dai,ba laifi tana d'an bata kulawar dik da ba wani har can ba amma hausawa suka ce da babu gara babu dad'i wai.

"Mama nah akoi maganar da nake so muyi dake dama idan babu damuwa!!!" Abbah ya fad'a yana blushing kamar wanda ke jin kunyar y'ar tasa,Zulaykha dake kwance kan cinyar Abbah nata ta d'an saki k'aramin murmushi had'i da gyara  kwanciyar ta da kyau tana mai fuskantar mahaifin nata tace "karka ji komai Abbah nah,ka fad'i dik abinda ke cikin ranka zuwa gare ni,a kuma dik lokacin da kaga dama Abbah nah,sbd nid'in a karkashin ka nake ba sai ka nemi izini nah ba a dik lokacin da ka son yin magana da y'ar ka!!"

Cike da jin dad'in maganganun d'iyar tasa Abbah yace "To - to-to y'ar albarka nako ji dad'i sosai da wannan kalaman naki! Ina so na sanar dake ne dama idan Allah ya yarda cikin ikon sa nan da 1month zan kawo maki sabuwar Mommy cikin gidannan"

Cike da t'sant'sar mamaki Zulaykha ta zaro idanuwa waje tana kallon mahaifin nata da shima ke kallon ta domin ganin a yanayin da zata amshi batun nasa!

Mik'ewa daga kwancen da take Zuly tayi tana gyara zaman ta da kyau cike da tsantsar farin ciki daya gazo b'oyuwa akan fuskar ta tace "gaskiya na matik'ar jin dad'in haka nan Abbah nah! Allah yasa mutuniyar arziki ce da zata zauna damu zuciya daya tamkar uwar data t'suguna ta haife ni babu t'sangwama!!!"

Tayi maganar tana mai tunano wasu irin hali na i don care da Mamy ke nuna mata a lokuta da dama,tinda ta kawo kai wanda bata san dalilin canzawar tata ba sabida da ba haka nan takeyi mata ba!

Sosai kuwa Abbah yaji wani irin tausayin ta,had'i da sake d'aura d'amarar sake yin wannan aure da Dad d'in Jiddah yayi masa magana akan auren k'anwar sa wato Anty Khadeeja.

*vote*
*comment*
*share*
  
[7/27, 7:50 AM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...!!*

*©️OUM_MUMTAZ✍️* 
        

           *charpter 19*

******** 'Bangaren ango da amarya kuwa sosai suke rakashewa suna zuba amarcin su babu ji babu gani! Kowa k'ok'ari yake wajen ganin ya faran ta ma d'an uwan sa rai ta hanyar t'saftatacciyar soyayya da babu algus,wanda suka gina zaman rayuwar auren su bisa ga koyi na fiyayyen halitta Annabi Muhammad(S A W).

Sam Yaya bai son abinda zai tab'a masa ASMA'Un sa ko na misk'ala zarratin! Wanda itama haka nan take,dik wasu hakkokin sa daya rataya a wuyan ta tana k'ok'arin sauk'e wa kamar yadda shima bayyin sanya sai na d'an abinda ba'a rasa ba!

Sannan kuma a lokuta da dama su Hidaya tare da sauran yaran gidan nasu dama na gidan y'an uwa kan kawo masu ziyara,haka nan suma suna kaima y'an uwa da abokan su nan Abuja da Suleja ziyara ba kad'an ba.

A gefe d'aya kuma har an riga an gama settling na auren Anty khadeeja da Dad yayi masa zance nan da wata d'aya.

Mat'salar Yaya guda d'ayace!!! Sam sam bashi da sakin fuska ga yaran y'an uwa ko kad'an! Dik inda yaro koman k'ank'antar sa yakai ga son Yaya ya d'auke sa to kuwa tabbas karya ce,sai ma dai kora su yana daddaure fuska,wanda hakan ya sa yaran ke shayin sa ba kad'an ba!
Wanda dama hakan ne shi ke had'a sa da Anty khadeeja da suka kasance abokan shawarar junan su tin suna k'anana har kawo girman su!

Ita akoi ta da son jan na k'asa da ita a jiki,bacin shi kuma sam-sam ba haka bane,a lokuta da dama takan fad'a masa cewa, "A yadda kake hantarar mana yara kaima zan so naga yaya zakayi a lokacin da ka haifi na kanka idan aka nuna ba'a yin su a gaban idanun ka!!"

Idan yaji hakan kuwa sai dai yayi dariya kawai ba tare daya bama maganar tata mahimmanci ba,inda Yaya babba ke d'aure masa k'ugu yace, "Kar a takura ma mai sunana fa." Hakan na damun Husnah da itama Allah ne ya d'aura ta akan sa tin tana k'ank'anuwar ta bata shak'u da kowa ba kaman sa,amma yanxu auren nan da sukayi yasa ta jin dad'i tana ganin komai ya kusa zama dai-dai,idan har ya haifi d'an kansa tana da tabbacin zai san mahimmanci da kuma dad'in yara ba kad'an ba,sabida babu wanda zai haihu yace "ba ya son abinda ya haifa"

Abin farin cikin daya iske su kuma a yanzu shine shigar k'aramin ciki da Husnah ke dashi,wanda kowa ke cikin farin ciki da wannan kyauta amma banda Yaya daya so a zubda cikin wai don sabida bai shirya haihuwa ba,yafi son sai sun kai irin 5yrs da aure d'innan,wanda hakan ya mugun b'atama Husnah rai amma ko kula sa ba tayi ba,ta kuma riga da tasa a ranta bai isa yace zai zubdar mata da ciki ba sabida ganin take-taken sa hakan yake so ayi,gashi kuma ita bata san ko iya wannan bane kad'ai nata kwan a duniya da Allah yayi mata yakai ta ya baro ta akan wani shirme na social life wai,wanda take da tabbacin koman daren dad'ewa idan akace yau bata haihuwa koman son da Yaya kanyi mata sai ya sake dank'aro mata kishiya,wanda ita kuma sam bazata so hakan ba,kasancewar ta mace mai zazzafar kishi akan Yayan nata tin bata kai haka ba.

Yaya kuwa ganin baiga fuska bane yasa shi shafa mata lafiya,amma kuma kullum cikin yin muzurai yake kamar wanda akayiwa laifi yana daure ma Husnah fuska ba kamar a baya ba,kuma dik wannan iya shegen da yake t'sulawa babu wanda ya sani daga shi sai matar tasa da ita kuma bata so asan da zancen sabida Yaya gani zayyi kamar takai karar sa ne,wanda kuma sai da Ammah ta hane ta da fidda sirrin t'sakanin ta da mijin ta idan hakan bai kama ba.

Wannan canjin da take gani daga mijin nata kuma sosai yake damun ta,amma bata san ta yadda zata masa bayani da zai fuskanci gaskiya ba,dik dama tana da tabbacin sarai yasan abinda yake so suyi d'in haramci ne amma yake son takewa sabida son zuciya da kuma d'aukar zugar abokai da suke fada masa idan ya sake ya fara haihuwa tin daga yanzu ya gama t'sofewa kamar wanda t'sufa da rashin t'sufar a hannun su yake.

******** Sam Alhaji ba mutum bane,gagarumin mat'safi ne fiye da kima daya fito daga jinsin aljanu,wanda wasu aljanun da kan su na sara masa a wannan fannin!
sannan kuma dik wannan bidirin da yake na t'safi bai aiki da aljanu ire-iren sa sai da bil adama! Wannan ya tara gagaruman jahilai a karkashin sa cikin jinsin mu da suka d'auki duniya da abinda ke cikin ta da fad'i,sukan yi masa sadaukarwa na jinin iyayen su,matan su,yayan su,yan uwan su da kuma way'an da basu da alak'a domin yayi siddabarun sa dashi shi kuma yakan buga masu kud'in t'safi kamar na hauka cikin k'ank'anin lokaci!

Yayi aure da dama cikin jinsin bil adama suna haifar masa yara shi kuma yakan shayar da kansa jinin ki bacin kin haihu,inda daga karshe kuma sai ya fed'e ma jariri ko jaririyar da aka haifa masa yayi amfani da sassan jikin su wajen ganin ya inganta t'safin nasa ta yadda zayyi karko.

Kuma dik matan da yake aura kwad'ayi ne ke fusgar su izuwa gare shi domin ko bai zuwar masu a siffar wani abu mara kyan gani sai a siffar bil adama!
Baba rabi ma na d'aya daga cikin wannan matan daya bugu su a dalilin son abin duniya tin tana budurwarta,har kawo girman ta,wanda itama dalilin daya sa bai kashe ta tintini ba sai don bata tab'a haihuwa dashi bane wanda sam hakan bai cikin nasa t'sarin na t'safi, a ranar da mace ta cika sati guda cif cif da haihuwa yake idasa cika kudirin sa babu daga kafa balle kuma wani abu wai shi tausayi,kuma dik macen data shigo cikin wannan gida daga ranar zayyi mata formating na cikin wawalwarta ta yadda zama ta manta ita wacece ko kuma daga ina ta b'illo? suwa ta baro? Dik wannan sai ya tabbatar daya gama goge mata wannan haddar!

Batin Alina kuwa tin a ranar da aka haifo ta garin bincike-binciken t'safin sa aka tabbatar masa da cewa jinin ta,na mahaifiyarta da kuma na abinda zata haifa masa da kaf matan daya ke haihuwa dasu babu wacce zata haifa masa kamar yadda ita zata haifar masa,wanda kuma sune matakin sa na nasara na karshe da zai zama gagarumin mat'safi da dik duniyar aljanu zasu san da zaman sa,mai matik'ar girma da kuma iko.
wanda hakan yasa Alina tin tana k'ank'anuwarta yake bibiyar dik wani mot'sinta a tafin hannun sa,sai kuma abinda ya sake sashi farin ciki shine na ganin halin ta na kwad'ayi yasan bazai sha wahala ba wajen cimma burin sa,kasancewar a t'sarin kalar nasa t'safin sam-sam babu tilastawa,dan haka dik wacce yake aura ya kuma kashe ita ke kawo kanta da kafafun ta har inda yake,shi kawai nasa ya saye su ne da abin duniya kamar yadda ya sake saye zuciyar Alina a lokacin daya bayyana a gareta.

A daren ranar da suka gudu da Alina,a washe gari wannan ranar yasa aka ciro masa mahaifiyar Alina daga cikin k'asa,wacce a wajen duniya rasuwa tayi daren jiya d'in,nan kuwa basu san cewa hakan dik cikin set-up na Alhaji bane.

Inda ya keb'eta a wani d'aki yake shayar da ita with thick blood na bil adama tare da d'anyen nama! Wanda jiran wannan ranar yake domin ya idasa cika kud'irin sa akan Alina da mahaifiyarta tare kuma da yaran da aka haifa masa.

Tonon asirin da Baba rabi tayi masu kamin su cika kudirin su kan iya ruguza masu dik wani t'sare tsaren su,wanda hakan yasa suka yanke mata wannan danyen hukuncin,kaf cikin mutanen dake d'akin manya manyan k'asar mu ne dama wayan da ke mak'waftaka da mu idan aka d'auke ainahin Alh daya kasance shine boss nasu!!

(Kar na ja masu karatu dayawa,wannan shine tak'aitaccen bayani dangane da wannan Alhaji).

Sam Alina ta gagara mot'sawa daga inda take balle ta iya kaima mahaifiyar tata d'auki sabida d'ad'd'aure mata jijiyoyin jikin ta da wannan halitta yayi dake mat'sayin Alhaji da wai har tayi kwanciyar aure dashi!

Jikin ne ya fara karkarwa tana faman girgiza kanta a lokacin da taga Alhaji ya kafa bakin sa akan nonuwan mahaifiyarta dake kallon y'ar tata itama tana t'siyayar hawaye mai cike da t'sant'sar tausayin kanta da kuma y'ar tata da ba komai bane ya jawo mata hakan illah kwad'ayi dai!!

*vote*
*comment*
*share*
[7/27, 8:29 AM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...!!*

*©️OUM_MUMTAZ✍️*
    
                              

           *charpter 20*

******** An d'aura auren Abbah da Anty khadeeja daya samu halartar mutane da dama,dikda ba auren fari bane,inda akayi gagarumin tashin hankali da Mamy ba kad'an ba,sai da Abbah yayi mata baraza da dat'se igiyoyin auren dake t'sakanin su kamin ta shafa masa lafiya!

Su Zulaykha ma ba kad'an taji farin cikin wannan auren ba,wanda kuma ba komai ne ya jawo hakan ba,illah Allah-Allah da take kan Allah yasa  haifa ma Abban ta wasu yaran da zai na kallon su a mat'sayin nasa dangin ba wai ita kad'ai ba da idan yau ta Allah ta kasance akan ta tasan babu wanda mahaifin nata kan iya yin tutiya da shi a mat'sayin nasa.

Flat na Anty khadeeja ma daban ne,kamar Mamy,sannan kuma Abbah ya buk'aci da tazo da yaran ta idan har dangin mahaifin su sun yarda shi yayi alk'awarin zai rik'esu t'sakanin da Allah tamkar yaran sa daya haifa.

Anty Deeja na da saukin kai ba kad'an ba itama,wanda hakan yasa tasu tazo d'aya da Zulaykha,wanda kusan kullum tana can part d'in suna hirar su sabida rashin tazarar shekaru masu yawa dake t'sakanin su,wanda hakan ko sosai yake sake tafarfasa ma Mamy zuciya fiye da tunanin mai karatu!

Har zuwa wannan lokacin Zulaykha bawai ta manta da batun Yaya bane sam!! Hasali ma ranaku d'ai-d'ai ne bata zama yin tunanin sa na musamman,tinda ta san dangantakar dake t'sakanin su da jiddah aminiyarta,bacin wannan ma tana da labarin irin son da yake ma matar tasa uwa t'soka d'ai a miya!

_UNCLE J_ kam bata ma san ina ya samu number wayar ta,wanda suke d'an tab'a chart dashi dik da shashshare sa da take kasancewar sa mai mata harda d'an su guda d'aya!

Wanda ita kuma sam sam a t'sarin ta ma bata son ta auri mai mata! Ta gwammaci idan ma za'ayi mata kishiyar ita ta fara shiga gidan,idan yaso ko uku ne ma ya auro daga baya bai dame ta ba,kamar ita ace taje ta tadda su,wanda hakan yasa take baya baya da uncle j d'in,tin da ta fuskanci manufar sa amma sam baiji,saima k'ara lik'e mata da yake kamar chewing gum,dik da kuma kasancewar sa mazaunin k'asar Australia da su sukayi believing da zama da mace guda har k'arshen rayuwar su.

A lokuta da dama idan taje kwanciya bata da abin yi sai kallon pic na Zulaym Shuwa! Wanda kuma shi a nasa b'angaren sam sam bai san da zaman wata halitta mai kama da tata ba a duniya!

Wata ran takan yi kuka to her own satisfaction kamin ta share hawayen ta,wanda hakan kesa ta kwana da ciwon kai mai t'sananin gaske,amma kuma koda wasa babu wanda ta tab'a bama wani k'ofa da zai fuskanci halin da take ciki,hatta ga mahaifin ta da bata had'a sa da kowa ba a duniyar ta.

Bangaren Mamy da kuma Oga musty kam duniya ce ta sake bud'e masu sabuwa a fannin zubin adashen da suke babu k'ak'k'auta wa,inda kuma Allah ya isa gami da tsinuwa a kullum Abbah da Zulaykha sai sun sha ta yafi cikin kwando amma sam su basu da labari.

******** "Kiyi addu'a y'ata! Kiyi addu'a,domin kuwa ita addu'a makamin mumini ce! Ina ji a jinin jiki na akoi guntun rayuwar da zakiyi mai t'sawon gaske a gaba! Kije ki naimi yafiyar d'an uwan ki da kuma y'arki! Kar ki bari way'annan azzaluman suci nasara akan mu! Ki tashi kije!! Ki tashi kije nace!!!!"

Iyami ce ke wannan maganar cikin t'sananin galabaita da kuma zabar zuk'ar ruwan nonon ta da wannan halitta keyi dake mat'sayin Alhaji tin iya k'arfin sa,wanda tin ruwan nona na zuwa har saida ya fara zuk'ar ainahin jinin jikin ta ta wannan hanyar,wanda kuma wannan maganar da tayi shima dik cikin iko ne na uban giji!

"Ku d'aure man ita!!!!" Alhaji yayi maganar cike da t'sananin t'sawa da sai da d'akin da suke ya girgiza!! Amma kuma aka rasa mai tinkarar inda Alina take sabida karanto addu'ar da take ta faman yi tana kallon mahaifiyar ta amma ta gagara mot'sawa daga inda take.

Tas Alhaji ya gama zuk'ar jinin Iyami ta wannan hanya jikin ta ya saki alamun rai yayi halin sa! The same thing na abinda yayi ma iyami haka nan yayi ma Baba Rabi dik akan idanun Alina da ta zama butum-butumi tinda aka kashe mata mahaifiyar ta akan idanun ta!

Kamar wanda aka hankad'a sai gata tayi wani irin sukuwa gaban Alh daya d'akko wani abu mai t'sinin gaske bacin an mik'o masa jinjirar ta guda wato Basma dake ta faman callara kuka!

Amma kuma saidai cilli d'aya Alh yayi mata da k'afar sa sai gata can mak'ure jikin bango idanun ta ya kafe akan Alh da kuma yar tata dake ta faman cilla uban kuka gwanin tausayi.

Babu d'igon tausayi ballantana kuma imani haka nan tana ji tana gani aka k'wak'ule ma y'arta idanuwa akan idanunta,aka farke mata ciki! Aka ciro kayan cikin ta aka kuma wurgar da gangar jikin ta inda ya sakeyi ma sauran yaran nata irin abinda yayi ma wannan jinjirar agaban idanun ta ya kuma zauna ya cinye abubuwan nan t'saf yana lasar baki!

Wato fa akace wai shima kuka rahma ce ga d'an Adam! wanda Alina ta yarda da hakan tabbas a wannan ranar! Fit ta naimi da tayi kuka amma ta rasa wai ko zataji saukin rad'ad'in da take jin cikin zuciyarta ya ragu.

Wani irin shegiyar dariya ALH ya kece da ita,inda d'akin ke ansa kuwa tare da muryoyin way'anda ke tare dashi suma suna taya sa cike da t'sant'sar kafirta kamar ba jinsin su ake wulak'antawa haka nan ba dik dan sabida kwad'ayi da kuma son abin duniya!!!

"Daga yau! Daga kan jinin ki da zan shayar da kaina! Suna na zayyi fice cikin duniyar mu da jinnu da dik inda aka ambaci sunana sai an girgiza sabida k'arfin ikon da naki jinin dana ahalin ki zai k'ara man akan dikkan lamura nah zuwa kan dangi nah da dik wanda ke kewaye dani!!!"

Alh yayi maganar cike da dariyar keta,wanda hakan yasa Alina ta samu damar raba jikin ta daga jikin ginin da Alh ya manna ta bayan ta karanto addu'ar "SUB HANAKA INNI KUNTU MINAZZALUMIN!!" wanda take ta faman maimatawa cikin zuciyarta har ta fito fili! Take kuwa d'akin da dik wani abinda ke cikin ta suka fara k'arar rakin fashewa sabida komai daya danganci wannan gidan t'sagwaron t'safi ne.

"Ki dakata! Ki dakata da wannan abinda kikeyi!!"

Alh keta faman ambata sabida yadda shi karan kansa fatar jikin sa ta fara sullubewa yana zama ruwa iya zuba a wajen!!"

Suratul jinni kawai Alina data fara dawowa cikin hayyacin ta ta cafko tin iya k'arfin muryarta da Allah ya bata tana sakin rikitaccen kuka bacin ta tamke idanun ta gagam!

Ta d'au t'sawon lokaci tana karanta wannan surar da komai na cikin gidan keta faman babbakewa yana ci da wuta,tin tana iya jin ihun bil'adama dake cikin wannan d'akin cikin fitar hayyaci har takai ta kawo taji anyi wani irin wulli da ita cike da t'sananin hasala,wanda ba kowa bane mai wannan aikin face Alh dake cikin mummunar yanayi sabida yadda ayar Allah ta narkar masa da sassan jikin sa da baza su sake amfanar sa da komai ba!

A dai-dai time d'in da yayi cilli da ita gidan ya kama da wani irin tafasashshen wuta mai t'sananin azabar gaske ko ta ina! Amma kuma dikda haka dik mutanen da suke wucewa takan wannan hanyar babu abinda suke gani,kasancewar gidan yana daga kan hanya ne!

Motoci ne matafiya dake wucewa ta kan hanyar suka fara guje-guje suna bama motar su wuta sabida ganin yadda aka wat'sa abu cikin t'sararin samaniya,bacin ya kai k'asa kuma sai suga mutane ne! Tashin hankali ne sosai ya barke akan hanyar dake t'sakanin Abuja da Kaduna.

Wata motace da tazo wucewa ta wajen dake tafiya cike da t'sant'sar nat'suwa dikda guje-gujen da mutanen kan hanyar keyi,matashin saurayi ne da ak'alla zai bama 30yrs baya daya zo saitin dai-dai wajen kawai kamar ba d'an adam ba sai ganin mutum yayi ta fad'o a kan glass na gaban motar sa.

wanda hakan ya sa shi cin wani irin wawan birki a mugun razane.

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*

[7/29, 1:41 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...?*  

   *©️OUM_MUMTAZ✍️*                      
   

           *Charpter 21*

******** Tin daga wannan ranar a hankali rayuwar Waali tare da y'ar sa ya fara gangarawa cikin garin Kano ta dabo tumbin giwa,inda kuma shak'uwa gami da zumun ci na sake k'ulluwa t'sakanin su da gidan Kaka Baban Aisata,inda yaji asalin su ashe suma y'an asalin garin Maiduguri ne KANURI,inda zama ne ya kawo su nan garin Kano d'in sabida guje ma t'segumi na mutane akan iftila'i na cikin gaba da fatiha d'in da Aisata tayi ya fad'a masu.
Wanda hakan yayi sanadiyyar rasuwar mahaifiyar ta,inda suka tattaro yana su yana su suka dawo nan d'in bacin ta haihu,wanda ba kowa bane wannan yaro illah Mastaa.
Ummi kuwa sosai take samun wadatacciyar kulawa daga Aisata,Masta,Kaka da kuma uwa Uba mahaifin ta,wanda hakan yasa cikin k'ank'anin lokaci tayi wani irin girma na ban mamaki ga kuma k'oshin lafiya.

Babu wanda ta sani sama da mahaifin ta dik da irin kulawar dasu Aisata ke bata amma ko bata sake masu kamar yadda take sakewa da mahaifin ta, a gefen kasuwan ci na saida kayan trader da Waali keyi kam sai dai ya d'aga hannu yace "Allah na gode maka!"
Bashi da wani mat'sala daga shi har y'arsa sai na kewar ahalin sa daya t'sallako ya baro mahallin su a can jihar Borno!  A kullum dare da kuma waye wa ta duniya t'sanar Alina da mai hali irin nata na dad'a bunk'asa ne cikin zuciyar sa,wanda yake jin ko duniya da abinda ke cikin ta zasu k'are wannan t'sanar da yayi mata bazai tab'a gogewa ba!

A lokacin da Ummi ta cika 1yr da sunan "Abbah na" bakin ta ya fara bud'ewa cikin gwaran ci kamar yadda a kullum ta duniya Waali ke sata a gaba yana koya mata ambatar wannan sunan da Allah ya sa ta fara anbatar hakan kuma cikin ikon sa.
"Mamy" sunan da take kiran Aisata kamar yadda Mastapha ke kiran ta.

A fannin kasuwan cin Waali kuwa sai abin da yaci gaba,inda yazo ya koma cikin babbbar kasuwar dake cikin Kano bacin ya bud'e babban shagon sa da yake saran takalma daga manyan shaguna yana sayar wa bacin ya d'aura ribar sa kamar yadda sukeyi da iyayen sa tin acan Borno kamin k'addara ya kawo sa nan garin d'in.
Kuma sosai yake samun ci gaba,wanda kuma Aisata ce ke kulawa da ita Ummi d'in babu t'sangwama balle kuma hantara,wanda hakan yasa yarinyar bata da damuwa ko kad'an,kayan wasa iri-iri kuwa babu wanda Abbah nata bai saya mata.
Yau sun tashi ne da tashin hankali na rasuwar Kaka bacin gajeruwar jinyar da yayi na t'sawon kwana uku.

******** "Yaya ga can lunch naka fa na kammala ko na kawo maka nan ne,naga kamar baka son mot'sawa daga inda kake???"  Husnah ce ke wannan maganar a lokacin da take t'saye daga bakin kitchen tana fuskantar Yaya dake kwance kan kujera 3seater yana lat'sar wayar sa,jikin sa sanye yake da wani 3quater sai kuma riga armless,wanda hakan yasa murd'ad'd'en surar jikin sa ta cikakkun maza sake bayyana matik'a.

Batare da ya d'ago ya kalle ta ba,ya girgiza mata kai alamun bai jin yunwa,nannauyar ajiyar zuciya ta sauke cike da rashin jin dad'in halin rashin damuwa da yake nuna mata ta tako zuwa cikin parlon,inda tayi ma kanta gurbi a kan k'irjin sa kamar zata shige jikin sa bacin ta lumshe idanun ta tana shak'ar daddad'an k'amshin turaren sa da taba gajiya da shak'a tinda ta samun wannan cikin.

Ba tare da ya mata magana ba ya sake gyara mata kwanciyata a jikin sa ta yadda zata fi sakewa ya ci gaba da danne-dannen sa,wanda hakan ya sata sake shigewa jikin sa sosai kamar mage tana sakin ajiyar zuciya.

Abinda take masa ne yasa shi sauk'e wayar tasa a gefe guda,inda lek'o k'ansa ta inda fuskarta yake,waro idanu yayi cike da damuwa a fuskar sa sabida ganin kuka fa ashe take yace "lafiyar ki kuwa dear!?"
kamar dama jira take ta fashe da kuka sosai,wanda hakan ya sa shi mik'ewa da ita suka idasa shige bedroom d'in dake mat'sayin mallakin ta.

******** "Mamy da Abbah na tafi gidan su Jiddah wai zan rakata gidan y'an uwan su sai na dawo!" Ummi ce ke wannan maganar a lokacin da take zaune kan kujerar da Abban nata yake ta jinginar da kanta a kafad'ar sa.

D'an bubbuga bayan ta Abbah yayi yace "toh a dawo lafiya Mamana,amma fa karki dad'e sosai kina jina ko??"

"Insha Allah Abbah na!" ta fad'a a lokacin da take mik'ewa,"Mamy sai na da wo." ta fad'a a lokacin da take ficewa daga flat d'in nasu zuwa na Anty khadeeja,zaune ta tadda ta a parlo da kuma su Nuraaz da Aymana suna kallo .
Suna cikin gaisawa suka ji sallama Jiddah,wanda hakan yasa basu wani b'ata lokaci ba nan d'in suka fice bacin sun ma Anty Deeje sallama,a motar Jiddah yau suka fita,inda suka kama hanyar Suleja kamar zasu tashi sama.

******** A mugun t'sorace yake,amma hakan bai sa shi fasa fitowa daga cikin motar tasa ba jikin sa na karkarwa,sai da ya tabbatar da cewa dik guje-gujen da ake akan hanya an d'an ragu,kamin ya waiga gefe da gefe ya tabbatar babu wanda hankalin sa ke kansa,dikda a d'an t'sorace yake,hakan bai sa shi dakatawa daga tinkarar gaban motar tasa ba,zuciyar sa take tayi mummunar bugawa sabida kallon mace da yayi t'sirara haihuwar uwar ta kwance shame shame jini na zuba akan goshin ta,ta inda glass d'in gaban motar tasa ta fasa mata.

Wata zuciya na ce masa yayi cilli da ita cikin sauran gawarwakin da ke zube akan hanyar ya gudu kamin y'an sanda su zo,inda wata zuciyar kuma ta kwab'e shi da hakan da bai san dalili ba,kamar wanda ake tunkud'a shi ake basa umarni ya bud'e boot na motar sa da akoi wani troley nasa da kuma wani babban bargo ya ciro bargon,saida ya nannad'e ta cikin bargon kamin ya saka ta cikin boot d'in bacin ya maida kayan sa dake ciki gefe yana ta faman waige-waige kaman mara gaskiya,da wani irin mugun gudu shima ya bar wajen sabida jin jiniya na y'an sanda da suka samu labarin abinda ke faruwa.

Kan kwaltar shall dik wasu motoci kowa ya fece abinsa,sai motocin police keta faman kai kawo tare da likitoci da aka kawo ambulance daga kaduna,inda aka kwashi gawarwakin mutanen dake wajen aka wuce asibiti da su,ma'aikatan kuwa sai faman al'ajabi suke sabida ganin manya-manyan y'an siyasa na k'asar tamu da aka san da zaman su,d'ai-d'ai ku ne sabbin fuska,cikin k'ank'anin lokaci labarin abubuwan dake faruwa ya cika states na 9ja kan asirin wasu masu mulkin ta tonu,wanda mutane da dama kan masu tofin ala t'sine,an k'ira iyalan ko wanne daga cikin bayan an gama dik abubuwan da ya kamata aka basu gawarwakin suka tafi dashi.

Nan da nan kuwa aka mance ma da shafi kansu a rayiwa sabida dama basu ajiye wani abu mai kyau da in an gani za'a ringa tunawa da su ba,balle kuma ayi masu addu'a.

(Sun zo a banza zasu koma a banza😭Allah ka cire mana kwad'ayi da kuma son abin duniya da zai kai mu ga aikata aikin da nasani ranar gobe k'iyama🤲🏻🤲🏻🤲🏻🤲🏻🤲🏻😭😭😭😭).

Sosai yake sharara uban gudu akan titin da ya sada shi da cikin garin Kaduna babu b'ata lokaci,unguwar Gomna road ne dama inda zaije wajen mahaifiyar sa domin kai mata ziyara daga can Abuja d'in,kasancewar yau ranar friday ne.

Ya jima zaune cikin motar yana ta faman sauk'e numfarfashin gajiya kamin ya samu da k'yar ya fito daga cikin motar tasa yana sharar zufar da ta jik'e masa jikin sa ba kad'an ba.

Sallama ma da k'yar ya samu damar yin sa a kan fatar bakin sa,inda ya tadda mahaifiyar sa zaune kan sallaya akan baranta t'sohuwa tukuf da ita tana ta faman jan charbi.

Zubewa yayi a gaban ta yana mai jin wani irin zazzafar hawaye na zuba daga cikin idanun sa da bai san na minene ba?

"Lafiyar ka kuwa HIMU?? Wani abu mummuna ya faru ne akan d'aya daga cikin ku kake irin wannan kukan?"

Da k'yar ya samu damar t'saida kuka nasa kamin ya shaida mata dik abubuwan daya faru akan hanya har kawo tahowa da yayi da macen da baida sanin cewa mutum ce ko aljan? Rayayya ce ko kuma matacciya...??

_SO MASU KARATU DAGA NAN LABARIN ~ALINA~ ZAI D'AN DASA AYA,ZAN SHIGA LABARIN WANNAN MATASHIN DA AKA KIRASA DA HIMU,DOMIN JIN CIKAKKEN TARIHIN SA IDAN YASO IDAN AKAZO DAI DAI WANNAN GAB'AR DA MUKA T'SAYA LABARIN ITA ALINA D'IN DA KUMA NASA ZASU TAFI AKAN GAB'A GUDA INSHA ALLAH🥰🥰🥰💃_

*vote*
*comment*
*share*
  
[7/29, 1:55 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...?*  

*©️OUM_MUMTAZ✍️* 
                        
   

           *Charpter 22*

******** Sun shiga rud'u iya rud'u gami da tashin hankali,domin kuwa mutuwar Kaka ba k'aramin girgiza mazaunan unguwar yayi ba,kasancewar sa mutum ne shi mai sauk'in hali da sanin yakamata,tare da taimakon na k'asa dashi,dikda cewa ba wai k'arfi ne dashi ba,amma dai yana k'ok'artawa dai-dai gwargwadon iko,Aisata da MUSTY ma ba k'aramin tashin hankali suka shiga ba daya zarta na kowa.

A ranar da ya rasu aka mik'asa gidan sa na gaskiya,Waali ma ba kad'an yayi kukan rasuwar Kaka ba a wannan ranar sabida yadda ya zaunar masa mat;sayin mahaifi akan lamuransa na yau da gobe tin sauk'ar sa cikin garin KANO.

Ummi kuwa na wajen Aisata da mutuwar mahaifin nata ya girgiza ta ba k'arami ba,inda Musty ma sosai yaci kukan sa sabida yadda ya fara wayo a lokacin yasan cewa dik wanda y mutu bazai tab'a dawowa ba.

Saida akayi kwana bakwai da rasuwar Kaka kamin aka daina zaman k'ofar gidan kowa ya wat'se sabida dama mutanen da akayi zaman tare ne bawai dangi na jini ba.

Tin daga wannan lokacin sai ya zamana dik wasu larurorin Aisata da d'anta Musty Waali ya d'aukar masu,domin kuwa yanxu sun zamto kamar wa da k'anwa ne,ga kuma Ummi dake sake girma abinta kyawunta t'sant'sa na sake fitowa kamar y'ar turawa.

Manyan unguwa ne suka had'u akan Waali wajen basa shawarar auran Aisata sabida yanayin kusancin dake t'sakanin su,zuciya bata da k'ashi,ba fata ake ba,shaid'an kan iya k'awata masu junan su koda a gaba ne,gwanda su tari abin tin daga yanxu.

Ba don Waali na da niyyar sake aure a rayuwar sa ba,sai don gujema abinda manyan suka hango masu yasa shi amincewa da auren Aisata d'in,ko ba komai ta wannan hanyar zai iya saka ma MARIGAYI da taimakon sa da yayi a baya.

An d'aura auren Aisata da Waali wanda kuma UMMI da MUSTY kan k'ira su da MAMY,ABBA. A lokacin da Ummi ta kai 4yrs ne kuma arzikin Abba ke dad'a bunk'asa babu ji babu gani,kasuwanci yaci uban na da da,domin kuwa har daga wani gari yakan saro takalman sa ya maida shagon nasa babban BOUTIQUE da ake ji dashi cikin kasuwar.

Sannan kuma ya zuba yaran da zasu na kular masa dashi,Mamy da d'an ta ma sunyi b'ul-b'ul dasu abinsu gwanin sha'awa sbd yadda Abbah bai rage su da komai ba na jin dad'in rayuwa.

Soyayyar dake t'sakanin Abba da Ummi kuwa saima abinda yaci gaba ba wai baya ba,Abba yasa su a islamiya ita da Musty wanda zuwa lokacin sun tashi daga wannan unguwar sun koma RIJIYAr zaki a wani gidan su mai d'an girma amma ba har can ba.

Sannan kuma yasa su a makaranta ta private mai kyau da suke tafiya tin safe basu dawowa sai yamma,Akoi wani abokin Abba da suka had'u a yawon kasuwan ci mai suna _YUSUF_ wanda shi kuma mazaunin garin Abuja ne tare da matar sa,da kuma y'arsa guda d'aya mai suna JIDDAH. Sannan kuma iyayen sa mazaunan Abuja d'inne amma asalin su y'an garin KADUNA ne.

Daga abokan taka na kasuwanci aka koma aminta mai lasisi,wanda kuma cikin k'ank'anin lokaci Waali yayi wani irin kud'i harma ya zarta abokin sa Yusuf d'in (Dad na Jiddah kenan).

Wanda hakan yasa Dad yima Abba kwad'ayin zaman cikin Abuja dik da yadda take da t'sadar rayuwa,Abbahl kuwa bai musa ba,inda ya sayi wani babban filin sa acan cikin garin Abujan unguwar Maitama ya dank'ara uban ginin sa na gani na fad'a kamin ya kwashi iyalan sa bayan ya d'aura way'anda ya yarda dasu akan kasuwancin nasa.

Komawar sa cikin garin Abuja kuwa Mamy da MOM matar Dad suka zamto k'awaye dik da ba wani har can ba,sannan kuma Ummi da Jiddah ma haka nan,sai Musty da shi kuwa kan t'saya masu a harkar karatun su mat'sayin sa na yayan su.

Abba da kuma Dad ne suka had'a hannun jari su biyun su suka bud'e wani babban kamfanin su na saida takalma na fata a cikin garin ABUJA mai suna _~Z and H NIGERIA LIMITED~_ .

Sun kuwa bud'e wannan campany d'in da k'afar dama,domin kuwa cikin Abinda bai gaza shekaru biyar ba,sunayen su ya shige da fice a k'asashen k'etare bama Nigeria kad'ai ba,kud'i yaci uban nada,wanda hakan ya fara saka Mamy fara jin takaici kan miyasa Abbahl d'in bai saka Musty a mat'sayin magajin sa ba sai UMMI(kuji min kokari)

Yara suna girma suna sake yin wayo,wanda tin Ummi na k'arama MUSTY yake son ta tin bata kai haka ba,ya riga su kammala secondry school inda Abba ya kaisa k'asar china yayo k'aratu a fannin business kamar yadda shima yayi,kuma yake da burin y'ar sa ma ta gado sa.

A lokacin da suka kammala sec sch dik wani abu da ake kira da budurci ya gama bayyana tattare da su baki daya,inda kuma Dad d'in Jiddah ne ya nema masu admission a BUK kano suna karanta course d'aya business sabida a commercial class dama suka zauna sec sch nasu.

Kud'in Alina da Waali ke d'an jujjuya mata daga lokaci zuwa lokaci ya fara gina ma Ummi wani madaidaicin kamfani shima na sarrafa takalma ne kamar nasu,amma bai kai shi girma ba.

Dawowar su hutu na farko ne ta fara fuskantar hali na i don care daga Mamy d'in ba kamar da,da take ji da ita ba. Wanda ita kuma sam bata san mainene silar haka din ba.

Lokacin da Musty ya dawo sai suke tafiya wajen aiki tare da Abba wanda kuma Mamy bata so haka d'in ba,taso ace shima Abba ya bud'e masa campany kamar yadda taga yana yi na UMMI.

Musty kuwa hakan sam-sam bai wani dame sa ba,lokacin da suka kammala degree nasu fannin business suna da 22yrs,inda Abbah zai tafi k'asar India domin kafa wata kamfanin su shida Dad d'in acan da ak'alla zai d'au t'sawon shekara guda,tare da Mamy Abbah ya tafi,da kuma JIDDA da UMMI d'in sabida suyi masters nasu a fannin business d'in na t'sawon shekara guda daya tal.

Watan su shida acan Abba da Mamy suka dawo,sannan Dad da Mom na JIDDA suma sukaje suka idasa watanni shida din kamin suka tarkato tare da su UMMI d'in da suka kammala karatun su suka dawo gida.

A lokacin ne kuma Abba ya d'anka ma ZULAYKHA (UMMI) ragamar kula da kamfanin ta daya bud'e mata da dukiyar mahaifiyarta,wanda hakan kuma ya sa Musty saka rai shima za'a bashi nasa amma yaji shuru,hakan ya sosa masa rai amma sai bai nuna damuwar sa ba,inda ya buk'aci da a had'a shi waje guda da ita Ummi sabida bazai so ace wasu mazan na kalle masa ita ba,har Abbah yace zai bashi manajer na campanyn amma yace sam shi saidai ya zauna a mat'sayin P A nata ta yadda zasu rink'a kasancewa tare a ko wani lokaci.
Sosai Mamy taji haushin hakan kuwa,ta ringa masa masifa kamar zata cinye sa d'anye amma shikam ko a jikin sa.

Jiddah kuwa mahaifin ta bashshi da ra'ayin barin ta yin aiki har sai tayi aure idan mijin ta ya aminta sai ya d'aura ta akan nasa kasuwan cin zuwa gaba,dan hakan ita kusan koda yaushe tana gida ne abinta daga gidan kakan nin ta da kuma y'an uwan su babu inda take zuwa.

Musty da Ummi tare suke dawowa daga wajen aiki wasu lokutan,wajen zuwa kuwa kullum tare suke fita da Abba ya ajiye ta a nata shi kuma ya wuce nasu wajen.

Batun arxikin sa da ya baro acan KANO ma ba'a magana sabida yadda arziki keta faman shigo masa ko ta ina babu ji babu gani sai dai ya d'aga hannu yace Alhamdulillah.

Musty ba k'aramin birge JIDDAH yake yi ba,amma kuma bata bari kowa yasan hakan ba,sabida ganin yadda yake masifar son aminiyar ta tin suna k'ananu.

Mamy kuwa kullum cikin fad'a ma Musty take kan bazata barsa ya auri ZULAYKHA ba amma bai yadda ba koma saurararta bayayi tinda yaji shid'in menene asalin sa.
Abbah ma kuwa tin gama war su Zulaykha makaranta ya bata tarihin rayuwarta kaf a lokacin da ta buk'aci hakan babu abinda ya rage mata. Tayi kuka iya kuka a lokacin da taji halin wacce ta t'suguna ra haife ta,amma hakan baisa ta t'sane ta ba,sabida mahaifiya ta wuce gaban wasa koman lalaci.

Mat'salar kud'i kuwa da ake dannewa ma'aikata hakkin su ba aikin kowa bane saina Mamy da Musty,wanda a bayyane kuwa hakan Aikin Abba ne da Zulaykha dayasa kullum cikin t'sine masu ake,wanda kai t'saye zan iya kiran hakan da suna *RIJIYA TA BA DA RUWA*
_guga ya hana_  inji hausawa.

Ma'ana kuwa.........🖊️

*vote*
*comment*
*share*
  
[7/29, 2:05 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...?*

*©️OUM_MUMTAZ✍️* 

_WANNAN LITTAFIN TIN DAGA FARKON SA HAR K'ARSHEN SA NA SADAUKAR DASHI GA ~MSS FLOWER🌸🌸~ MARUBUCIYAR :_
~LAFAZI~
~AR SO~
~SARKI~
~GUMBAR DUT'SE~
_SON SO FISABILILLAH❣️💃🥰❣️❣️_                             
   

           *Charpter 23*

******** "Miyasa kika fiye rigima ne da taurin kai yanxu my dear" Yaya ya fad'a yana mai sake shigar da Husna jikin sa,gami da goga mata lafiyayyen sajen fuskarsa akan fuskarta da yasa jikin ta sakewa,tana lumshe  idanunta da suka d'an canza launi daga farare zuwa d'an jaaa.

Cikin murya can k'asa-k'asa tace "Ayya dai Yaya! Wallahi kaine gaba d'aya kabi ka chanza man tin da batun wannan cikin ya shigo,harma gani nake yanzu baka k'auna ta kamar yadda kake so na a baya,sabida sai ya zamana cewa mutum bai k'aunar ka ne,bazai so had'a jini da mutum ba,wanda kuma gashi ni yanzu hakan kake nuna man a fili baka k'aunar had'a zuri'a dani da nake kyautata zaton ka daina k'auna ta ne yanzu kamar baya."Ta idasa maganar tana mai fashewa da kuka mai matik'ar tab'a zuciya,da yasa jikin Yaya yin sanyi ba kad'an ba,tausayin ta ne ya sake samun mat'suguni cikin zuciyar sa da yasa shi sake rungumeta da kyau yana faman lallashin ta had'i da gaya mata kyawawan kalamai masu sanyaya zuciya da nan take taji damuwarta ta yaye, alamu sun nuna ya safko daga wancan akidar tasa mara tushe.

Sai da suka yi wanka suka fito abin su suna ta faman zuba k'amshi kamar babu abinda ya faru,wanda tin daga wannan ranar Yaya ya fara bata wani irin kulawa na musamman da yasa hankalin Husnah sake kwanciya.
Sosai yake tattalin ta da abinda ke cikin ta babu ji,babu gani dikda kuwa har cikin zuciyarsa wannan ra'ayin nasa na k'in son haihuwa na nan bai goge ba.

****** A k'ofar gidan sukayi parking na motar,inda suka fito hannun Jiddah rik'e da wata babbar bak'ar laida da Zuly ta kama mata gefe guda.
Waleed ne ya fito daga gidan nasu zai tafi shago sayo biscuit ya ci karo da su Jiddah d'in dake kiciniyar shigowa da laidar.

Washe baki yayi idanun sa na kan Jiddah cikin muryar sa data fara bud'ewa sabida yanzu suna cikin 15yrs shida Hamad yace, "sannun ku da zuwa Anty Jiddala kuma my daughter ta ta kaina."

"Yauwa Baffa Walidi sannu ko?" ta fad'a tana mai dire masa laidar gaban sa,b'ata fuska yayi kamar zai fashe ya kallo inda Zuly ke t'saye ta k'ura masa ido sosai tinda taga fitowar yaron da bata tab'a ganin sa ba sai yau yace "Anty mai kyau jimin wannan matar daga zuwan ta zata wani ceman Baffa kamar ta samu t'sohon Abujan can(Yaya Babba)."

D'an saita kanta Zuly tayi ta b'ata fuska had'i da hararar Jiddah d'in tace "Ki kiyayi ni fa jiddala." Itama tayi maganar cike da t'sokala da yasa suka fashe da dariya baki d'ayan su.

Sosai Waleed ya birge Zuly dikda cewa yau yau d'innan ta fara sanin sa,inda ya karb'i abin nasu ya shige dashi zuwa cikin gidan yana ci gaba da t'sokalar Jiddah tana biye sa,ita kuma Ummi sai faman murmushi take suka rufa masa baya,da sallama d'auke a bakin su suka shigo cikin gidan inda suka tarda su baki d'ayan su yaran zaune kan tabarma suna ta hirar su gwanin birgewa kowa fes-fes dashi babu k'azan ta.

Ammi dake d'aki ta juyo hayaniyar yaran ta fito daga d'akin ta da murmushi a fuskarta,har k'asa suka kai suka kwashi gaisuwa wajen AMMI dake tambayar su mutanen gida.

"Hala wannan itace Zulykha ko Jiddah?" Ammi ta tambaya tana mai k'ure fuskar ita Zulyn da kallo kamar mai son gano wani abu,wanda hakan yasa Ummi d'in dik taji ta takure tana ta faman sunkuyar da kai kamar mara gaskiya.

Murmushi Ammi tayi tace, "Ga dikkan alamu d'iyar tamu akoi kunya ba irin su Oh-oh ba kuwa" B'ata fuska Jidda tayi wai ance mata bata da kunya dik suka saka mata dariya.

"Ammah bata gida ne banji mot'sin ta ba." Hidaya ce ta ansa ma Jiddah da fad'in ta tafi unguwa ko minti goma ba'ayi ba kuwa."

"Allah ya dawo da ita lafiya" suka had'a baki wajen fad'a Ummi da Jiddah.  Da sallama Waleed ya shigo gidan yana mai rairawa wak'ar sa kan bazai samma kowa ba sabida karma su tambaye sa kan ya sammasu alamun y'an rowa yau sun kusa-kusa,dariya dik sukayi masa inda Ummi keta faman kallon sa sabida yadda yaron ke birgeta tana sakin murmushi.

Ruwa Hamad ya sayo masu mai sanyi ya kawo masu,inda Mima ta k'arasa girkin da takeyi ta zubo masu a babban tray baki d'ayan su harda Ammi.

Gaba d'aya Ummi a takure take da zaman Ammi d'in sbd sanin da tayi cewa itace mahaifiyar Zulaym Shuwa sabida t'sant'sar kamar da sukeyi da junan su ko ba a fada ba.

Sai da rana ya tardo inda suke kamin suka koma d'akin Ammi d'in da hirar tasu. Sosai suka sha fira a gidan,inda wuni ranar cur sukayi sa wanda wani irin shak'uwa ne na ban mamaki ya shiga t'sakanin Ummi da Waleed a wannan ranar,da zata tafi ma yace zai bita idan yaso sai ya kwana a wurin Anty khadee amma Ammi tace bai isa ba,ya bari idan Ammah ta dawo sai ya tambaye ta yaje ko a weekend ne,haka nan suka tafi Waleed sai faman gunguni yake an hana shi bin Anty mai kyau..

Itama Zulyn sai taji babu dad'i amma haka nan ta share kawai suka tafi bacin sun ma Ammi d'in bayanin kayan da suka kawo masu ita da AMMAH daga HAJJA.

Saida ta ajiye Jiddah a gida kamin ta wuce nasu gidan ana k'iran magriba suka had'u da Abbah tare da Musty zasu wuce masallaci.
Flat na Mamy ta wuce da sallama a bakin ta,bata tarda ta a parlo ba,don haka sai ta wuce d'akin ta,wanka ta fara yi kamin ta d'auro alwala ta gabatar da sallar magriba,ba ta mot'sa a wurin ba,saida tayi sallar isha'i kamin ta shirya kanta cikin sleeping dress nata ta fito zuwa parlon su data tarda Mamy,Abbah,Musty,Aymana,Nuraaz da Anty Khadee zaune kan dining har sun fara dinner.

Da shike tasan tayi laifi sai taki zuwa gefen Abbah tayi zaman ta daga can kujerar da ba kowa kasancewar yanzu dining d'in mai d'aukar kujeru goma sha biyu ne,don haka akoi enough wajaje.

Kowa cin abincin sa yake,amma banda ita dake ta faman wasa da yat'sun hannun ta kanta a k'asa alamun bata da niyyar cin abincin,daga lokaci zuwa lokaci takan sakin murmushi ita kad'ai idan ta tuno da rigimar da Waleed ya tada mata d'azu kaman wani k'aramin yaro.

Sai da Anty khadee da Musty suka tambaye ta bazata ci abinci bane? Ta daga masu kai batare data bude baki ba tana kallon Abbah ta wut'siyar ido sabida ganin yadda yayi kicin kicin da fuska kaman bai ganta ba kwata-kwata. Dik dan akan takai magriba a waje bacin kuma yace karta dad'e.

Sumi-sumi ta wuce d'akin ta bayan ta masu sallama kan zata kwanta,Anty Khadee ma ta wuce nata flat din tare da yayan ta,Musty ma ya wuce aka bar Mamy da Abba tinda dama yau girkin na Mamy ne,shiysa akayi dinner a part nata kamar yadda Abba ta t'sara masu baki daya.

Mamy ma bata b'ata lokaci ba ta wuce d'akinta aka bar Abbah shi kad'ai zaune kan kujera yana kallon news,nan kuwa ba kallon bane ya dauke masa hankali,sai tunanin rashin cin abinci da Ummi din tayi yana t'soron kar ulser ta kamata.

Da kansa ya had'a mata shayi mai kauri daya sha madara da milo ya wuce zuwa dakin nata,zaune ya tadda ta kan gadonta cikin shirin bacci da wayarta a hannun ta tana kallon pics din da sukayi a gidan su Waleed dazu.

Bakin gadon nata ya zauna cikin sassauta fuskar tasa da tin dazu take a hade yace, "Oya karbi ki shanye ki bani cup dina Ummi na"

Babu musu kuwa ta ansa tana sha a hankali-hankali, inda gefe guda kuwa hankalin ta na kan wayarta,wajen kallon wani pics da sukayi gaba ki dayan su harda Ammi din suna dariya.

*vote*
*comment*
*share*
[7/29, 2:17 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...!!*

*©️OUM_MUMTAZ✍️* 

_WANNAN LITTAFIN TIN DAGA FARKON SA HAR K'ARSHEN SA NA SADAUKAR DASHI GA ~MSS FLOWER🌸🌸~ MARUBUCIYAR :_
~LAFAZI~
~AR SO~
~SARKI~
~GUMBAR DUT'SE~
_SON SO FISABILILLAH❣️💃🥰❣️❣️_                            
   

           *Charter 24*

******** YUSUF SHUWA. Shine cikakken sunan mahaifin su d'an asalin garin Kaduna tare da matar sa ASMA'U da suke k'iranta da UMMA.

Suna da rufin asirin Allah dai-dai gwargwado,domin kuwa basu naimi ci,sha ko sutura da kuma buk'atun yau da gobe sun rasa ba,sana'ar Yusuf shuwa tin tasowar sa itace saida kayan masarufi a cikin kasuwar garin Kano.

Shekarar auren su guda suka haifi d'an su na fari da yaci sunan mahaifin baban sa ZULAYM,tin daga nan kuma basu sake samun wani cikin ba,har sun fidda rai da sake samun wani haihuwa kwat'sam saiga wani cikin a lokacin da Zulaym yakai 19yrs,wanda yake shekarar sa ta 20 cif cif aka haifo masa k'ani da yaci sunan baban maman sa wato AHMAD.

A lokacin ne akayi ma YAYA aure tare da wata y'ar uwar sa mai suna HAUWA'U da shi kuma Ahmad kan k'irata da HAJJA,don haka sai sunan ya zamana kowa ya santa dashi harma Hauwa'u d'in ya bace.

Hajja tare da surukar tata wato UMMA da kuma mahaifiyar ita kanta Hajja d'in mai suna HIDAYA tare suka samu ciki a lokaci guda.

Ahmad na da 5yrs Umma ta kuma haihuwar wani d'a namijin da yaci suna IBRAHIM suna kiran sa da HIMU.
Hajja ma d'a namiji ta haifa da yaci sunan mahaifin mijin nata wato YUSUF(dad) kenan.
Sannan mahaifiyar Hajja kuma ta haifo d'iya mace da taci suna KAUSAR,a wajen haihuwar kausar d'in mmn Hajja ta rasu,don haka sai Hajja d'in ta hade dan nata wato Yusuf da kuma k'anwarta Kausar take kula dasu amma bata shayar da ita.

Daga kan HIMU kuma UMMA bata sake haihuwa ba,don haka sai suka tattara kulawar su baki daya kwacokan akan yayan nasu,yara kuwa sun taso ne cikin t'sant'sar k'aunar junan su fiye da tunanin mai karatu,YAYA shine sunan da suke k'iran Zulaym babban yayan su dake matik'ar kulawa da k'annen nasa fiye ma da yadda mahaifin su zai kula dasu.
Hajja ta sake haihuwar d'a namiji sunan sa AHMAD shima suna k'iran sa da AMADU,Bayan shekaru ta sake haihuwar wani d'a namijin da yaci suna JAFAR.Wanda cikin wanna shekarun kuwa abubuwa da dama sun faru,ciki harda rasuwar YUSUF wato baban su HIMU.

Sosai kuwa mutuwar tasa ta matik'ar girgiza su a wannan lokacin,amma da shike sudin musulman kwarai ne,kuma sun yarda da fad'in ubangijin mu kan _KULLI NAFSIN ZA'IKATIL MAUT_ sai suka d'auki dangana suke binsa da addu'oin dacewa.

Cikin hakan kuwa harda girman su Kausar,inda UMMA da kanta ta hada auren AHMAD(maibin bayan yaya) da KAUSAR. Kuma Alhamdulillah zaune suke lami lafiya.

YUSUF(Dad), AMADU da HIMU tare Yaya ya kaisu makaranta acan garin Zaria daga cikin Kaduna , AHMAD dama ya rigasu zuwa don haka tin kamin bikin sa da kausar ya kammala nasa karatun,sai ya zamana YUSUF,HIMU da AMADU ne kawai ke can makarantar.

A lokacin Jafar yana k'arami sosai domin ko bai wuce 4-5yrs ba,kuma a lokacin ne KAUSAR ta haifo d'an ta na fari kyakkyawa son kowa k'in wanda ya rasa,ranar suna na zagayo wa yaro yaci sunan Yaya wato ZULAYM suna k'iran sa da YAYA shima kamar yadda takwaran nasa ya buk'ata.

Wanda kuma dama shekarar da ta gabata HAJJA ta sake haifo diyar ta mace mai suna KHADEEJA abokiyar fad'an Yaya k'arami.
Da shike tazarar shekara guda ne t'sakanin YUSUF da AMADU tare suka kammala makaranta dikkan su uku.

Acan Zaria d'in inda sukayi makaranta YUSUF da AMADU suka samo matan auren su da suka kasance wa da k'anwa FATIMA(mum) da MARYAM(um-asmy).

Anyi aure an gwangwaje lafiya kalau inda suka tare da amaren su acan garin Abuja,dikda kasuwan cin takalma da shi yusuf d'in kanyi acan kano.

Auren su da shekara guda suka haifu kusan lokaci guda,wanda dai-dai wannan lokacin dama shekaru sun dan ja,sabida shekaru YAYA K'ARAMI yana cikin na goma cif-cif aka haifo HAUWA (sunan Hajja Dad ya sama y'ar tasa wato JIDDAH),inda shi kuma Amadu ya sama y'arsa ASMA'U suna kiran ta da (Asmy).

Kasuwancin Dad yayi tsamari da har takai suka hada hannun jari da abokin sa wato WAALI(na riga da na fadi maku yanayin dangantakar dake tsakanin WAALI da DAD dama tuntuni.)

JAFAR(uncle j daya dauko Zulaykha daga wurin dinner) ya samu schoolar ship na makaranta acan AUSTRALIA bayan sunyi exam shida Yaya Karami,amma shi Allah baisa ya samu ba,a lokacin ne kuma Yaya Babba suka tattara kwamutsan su zuwa garin Abuja,babu yadda bayyi da kanin sa Ahmad(BABI KENAN!) kan su zauna gidan sa ba,amma yaki yace sam dawainiyar zatayi yawa dik irin kokarin da yake akan su tin suna kanana.

UMMA kam dama cewa tayi bazata bar kaduna ba,idan har sun damu da ita d'in suna zuwa inda take amma ita da garin KD sai dai mutuwa,don haka sai ya zamana idan YAYA yazo satinnan,sai BABI yazo sati na gama,still kuma wani satin sai shi HIMU da yak'i aure yana nan gidan yayan nasu yazo mata.

Kullum yanzu damun sa da ake ya fidda tasa matar aure ne,BABI kuwa gidan sa a mashigar Abuja wato sulaija yayi ginin sa sabida cikin Abuja akoi t'sadar rayuwa ba kad'an ba.

Wanda a wayewar garin yau HIMU na kan hanyar sa ta zuwa wajen mahaifiyar tasa kaddarar haduwar sa da ita Alina ta faru,shine ya karaso gida wajen mahaifiyar sa da ita! wannan shine tushen labarin su.

_MASU KARATU YANXU LABARIN ALINA DA KUMA WANDA YA KAWO TA GARIN KD ZAI FARA TAFIYA AKAN MIZANI GUDA INSHA ALLAH❣️❣️❣️❣️❣️_

****** MA'ANA......✍🏽✍🏽

Bak'in cikin da Mamy ke ciki kan miyasa Abba bai bud'e ma nata d'an campanyn sa daban bane yasa ta fara ingiza Musty d'in wajen nuna masa kan cewa ai dama tin can Abba ba k'aunar sa yake ba,gwanda ma tin wuri ya farka yasan inda dare yayi masa shima ya wawu shi dukiya ya gina kansa,ta yadda ko yau akace Abba d'in ya fad'i ya mutu yana da wani abin,tinda yana da sanin cewa bashi da gadon Abba.

Ai kuwa maganar ta tayi tasiri cikin zuciyar sa,don haka sai suka had'e kai batare da kowa ya sani ba,suke cin dunduniyar Abbah d'in ta k'asa batare da sun ankare da su ba.

Da shike Musty shine PA na Ummi yasan dik wani shige da ficen kud'in wannan campany d'in,don haka sai yayi amfani da wannan damar wajen ganin sun kwashi dukiya son ransu,dalilin da ya kuma saka suka ci nasara akan Ummi sosai fiye da nata mahaifin shine: ita ta kasance yarinyar da bata fiye son hayaniya da shiga jama'a ba,sannan kuma ta bama Musty dikkan yardar ta,sai ya zamana komai za'a wanzar cikin kamfanin ita a rubuce zata danka masa wanda shi kuma sai yayi sa a aikace,hakan yasa yake amfani da wannan damar da har ya rage ma ma'aikatan nasu albashin su kan za'a basu daga baya idan komai ya zama dai dai,A hka watanni suka d'an jaa amma shuru sukeji kamar an shuka dusa babu wani batu na biyan su kudin su,gashi kuma kamar sammu aka rasa wanda zai tinkari ita Ummi din da batun,saidai su tinkari musty da shima kan sake basu hakuri,harma yayi masu ihsani da wasu kudaden da sunan shi ya basu,don haka sai suke ganin bak'in Ummi,kullum cikin Allah ya isa take,tare da fadin dik ranar da aka biya su hakkin su to kuwa tabbas sun sallami kansu da kansu babu su babu aiki anan sbd baza su iya zama inda bazasu samu ci gaba ba. (wannan na daya daga cikin abinda yasa sunan littafin ya zamana _RIJIYA TA BA DA RUWA...! ~guga ya hana~_)

......

A b'angare guda kuwa acan gida Mamy ce ke tafiyar  da komai cikin iyawa ba tare da sanin Abba ko Ummi ba,da shike ta hannun ta Abbah ke bada dik wani kudin da za'a sallami ma'aikata na cikin gida sai tayi amfani da wannan damar wajen hana ko wannen su albashin sa,wanda kuma a zahirance fadi masu take Abba ne bai bata k'udin ba shiysa bata sallame su ba,toh sud'in ma dai tin suna hakuri akan hakan sai ya zamana abin ya fara gundirar su,dalilin ma da yasa suke sake ganin bak'in Abba shine yadda yake treathing akan dik uban da ya taba masa y'ar tasa,koda kuwa a gaban waye ne,wanda ko Mamy idan tayi bai kyale ta sai ya babbake ta a gaban koma waye.

Sannan kuma wani zubin takan d'an raba masa 2k ma ma'aikatan,kan su dan rage hanya kamin Abbah ya bata kud'in nasu da sunan ihsani,sosai kuwa ma'aikatan gidan ke kallon kima da kuma mutuncin mamy da Oga Musty kamar yadda suke kiran sa.

Yakan yi masu alkawarirrika a lokuta da dama,kuma tabbas yana cikawa,amma kuwa saidai alkhairan da yake masu bai isa wajen su Mamy kan dakile wa,wani zubin kuma sai ta rage ta basu abinda bashi ne ba,wanda hakan ya faru akan ma'aikacin da yace Abba ya basa 5k maimakon 50k din kamar yadda sukayi.

(haka din ma zamu kirashi ne da RIJIYA TA BA DA RUWA kamar yadda sunan littafin yake,ina fatan masu tambayar ma'anar RIJIYA TA BA DA RUWA  kun fara d'aukar haske😂).

So sai kuma ya zamana auren Anty Khadee da Abba yayi wasu abubuwan sun soma faruwa cikin gidan,da yasa hankalin Mamy fara tashi,sabida ganin asirin ta na gab da tonuwa ita da d'an nata!! Wannan shina takaitaccen tarihin ZULAYKHA ABDUL WAALI!!

_ALINA ITACE MAHAIFIYARTA_

_WAALI KUMA SHINE MAHAIFIN TA WATO ABBAH_

_BARI KUMA MUJI YAYA RAYUWAR ALINA ZAI KASANCE A HANNUN HIMU DOMIN MU SAMU LABARIN NAMU YA TAFI BISA MADAI DAI CIYA HANYA✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽_

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[8/1, 10:48 PM] Mrs Sulaiman 💓:  

*RIJIYA TA BA DA RUWA...!!*

 
*©️OUM_MUMTAZ✍️*

_WANNAN LITTAFIN TIN DAGA FARKON SA HAR K'ARSHEN SA NA SADAUKAR DASHI GA ~MSS FLOWER🌸🌸~ MARUBUCIYAR:_
~LAFAZI~
~AR SO~
~SARKI~
~GUMBAR DUT'SE~
_SON SO FISABILILLAH❣️💃🥰❣️❣️_                          
   
           *Charter 25*

******** Hankalin UMMA idan yayi dubu ya tashi a wannan lokacin,cike da kid'ima suka fita daga cikin gidan tare da Himu,tare suka kinkimo Alina dake nad'e cikin bargo da bata san ma inda take ba,zuwa cikin gidan nasu da zuciya d'aya,dikda t'sufan daya kama UMMA sosai hakan bai sata zama ba,saima wankan da tayi ma Alina da kanta,sannan ta saka mata kaya dikda yayi ma ALINA d'in yawa amma dai yafi zama haka nan!

Sannan ta gyara mata kwaciyarta suka tofe da addu'a ba kad'an ba,wanda kuma zuwa lokacin wani bacci ne yayi gaba da Alina mai cike da mafarkai barkatai marasa kan gado! Sai a lokacin UMMA da kuma d'an nata suka gaisa,sannan shima yayi sallah suka ci abinci,wanda suka zauna hira a k'aramin parlon nata,anan suka ga an hasko abinda ya faru cikin akwatin talabijin!!
Sosai suka jinjina wannan abin,wanda har cikin zuciyar su tunani suke kan mai yakai d'iya mace wannan wurin?? Fatan su dai Allah yasa kar Alina ta cuce su idan ta farka,kasancewar rayuwar mu ta yanzu taimako ma ya zama abinda ya zama.

A gigice dik sukayi kan Alina sabida ganin yadda ta farka cikin mummunar yanayi kamar wata mahaukaciya sabon kamu,sanadiyyar mafarkin da tayi da Alh yana mata ihu kan ta zama silar ajalin sa!
Da k'yar suka samu damar controlling nata ta hanyar addu'ar da sukayi cikin ruwa suka d'ura mata,sannan kuma suka shafe mata jikin ta dashi! Sai faman rarraba idanun ta take ga dikkan alamu hankalin ta ba jikin ta yake ba,sabida maganar da sukayi tayi mata amma sai dai tabi su da ido alamun bata ma san mai suke fad'i ba,wanda muddin ta rint'sa idanun ta hoton lokacin da Alh ke fard'e mata y'ay'an ta da kuma hanyar da yabi wajen raba mahaifiyarta da duniya ne ke fad'o mata,sai kuma daga nan ta razana!

Ga kuma wani masifaffen ciwon kai da ya sako ta a gaba,sabida fad'owar da tayi akan motar shi Himun!
Saida Himu da kansa yayi mata d'uren kunun hat'sin da UMMA tayi sabida yadda taki cin dik wani abinda suka ajiye mata,saidai ta bisu dana mujiya!

Ana yin sallar isha'i yaje chemist ya taho tare da yaron shagon da ya kasance nurse ne,ciwon dake goshin ta aka wanke mata had'i da dressing na wajen wanda nan d'in ma da kyar aka samu akayi sabida yadda take ta faman fisge-fisge.

.........

Kwanan wannan ranar gaba d'ayan ta UMMA da HIMU sun yi ta ne cikin hidimar Alina da ta kwana cikin mawuyacin hali suna kulawa da ita.
Washe gari kuwa da safe bayan HIMU ya tafi sallar asuba yayi ma limamin nasu bayanin suna da mara lafiya a gida,da suke buk'atar taimakon sa! Wanda hakan yasa tare suka zo da wani malamin da shima d'an unguwar ne,a lokacin UMMA ma ta idar da sallar asuba,sannan kuma Alina ma ta samu baccin da bata samu yi daren jiya ba!

Karatu suka farayi mata baji babu gani a wannan lokacin har wayewar gari kamin suka samu ta mot'sa daga inda take kwance! Wanda nan take suka fuskanci bawai aljanu ne da ita ba,illa firgicewa da take ta faman yi akan wani abinda ta gani da idanun ta!

Bayan sun tafi liman ya aiko masu da wani ruwan zam-zam cikin gora kan su tabbatar da sun bata tasha,da zarar ta farka da yaddar Allah komai zai zama dai-dai!

Ai kuwa suna bata d'in ta kwanta wani nannauyen bacci yayi gaba da ita, wanda cikin baccin nata sai faman had'a zufa take baji ba gani! T'sawon lokaci ta d'auka tana bacccin kamin ta fardad'o,wanda kuma cikin ikon Allah garas ta farka babu wani alamu na tab'in hankali kamar yadda ta fara da farko! Sai kuma ta fashe da wani irin rikitaccen kuka da ya sake tadar ma dasu UMMA hankali ba kad'an ba, sunyi lallashi iya lallashi da kuma bada baki kamin suka samu kanta! Sallah suka fara saka ta tayi,kamin suka bata abinci taci,had'i da bata magungunan ta na jiya tasha nan da nan kuwa wani baccin ya sake gaba da ita,sabida akoi maganin bacci cikin magungunan nata.
T'sawon kwana uku su UMMA suka d'auka suna bata t'saftatacciyar kulawa kamar jinin su babu kyara ko t'sangwama dik da har zuwa lokacin ko sunan ta basu sani ba!!

UMMA ta k'ira YAYA kan tana naiman sa shida BABI,wanda kuma a ranar suka kamo hanya zuwa Kaduna,sai kuma suka tarda bak'uwar fuska,nan UMMA ta masu bayani kamar yadda HIMU yayi mata,wanda a ranar kuwa suka saka ta a gaba tana kuka da komai ta basu tarihin rayuwarta kaf,babu dad'i babu k'ari!
Tare kuma da jaddada masu nadamar ta k'warai da gaske,ta kuma buk'aci da su taimaka mata da kud'in mota zuwa maiduguri sabida dubo y'arta da kuma yayan ta! Washe garin ranar BABI ya koma suleja,inda YAYA da HIMU kuma tare da UMMA suka wuce Maiduri tare da Alina!

Wanda basu suka isa ba,sai magriba,don haka sai suka samu masauki a hotel tinda dama YAYA kam yana da arziki babu laifi,washe gari da safe waja jen k'arfe sha d'aya suka tafi unguwar su Alina d'in tana masu kwatance har k'ofar gidan sabida bata manta komai ba!
Kan kace me?? Mutanen unguwa suka ankare da Alina wanda nan da nan aka taru a wajen ana mata tofin ala t'sine tare da Allah ya wadai da masu irin halaiyar ta tinda gashi a ta sanadiyyar bak'in cikin ta mahaifiyar ta tabar duniya! Sannan kuma Waali da y'arsa sun shiga duniya da ba'asan inda sukayi ba bayan ya saida gidan su!

Ai kuwa ba k'aramin tashi hankalin ta yayi ba,jin cewa ba'a san inda Waali da y'arta suke ba,wanda ta fara tunanin k'ila sud'in ma ALH ne ya kashe mata su kamar yadda ya kashe mata mahaifiya akan idanun ta.
Sun bar number na wayan su kan don Allah dik ranar da WAALI ya waiwaye su su k'ira su shaida masu,sabida zasu tafi tare da Alina can KADUNA,sanna kuma suka basu adress nasu!

Haka nan suka koma babu wani daddad'an labari suna ta lallashin ta tare da nuna mata kuskurenta akan abinda ta aikata.
HIMU da YAYA sun koma ABUJA,sannan suka bar ALINA tare da UMMA  kamar yadda ta buk'ata.

…………

Tin daga wannan lokacin sai ya zamana dik wasu aikace-aikacen gidan Alina ce ke ma UMMA da ta d'auke ta mat'sayin mahaifiya,bata barin UMMA tayi ko dai dai da nad'e sallayar da tayi sallah,gashi kuma HIMU da kansa ya aiko ma UMMA kud'i ta saka ta a ismiyya wanda hakan ko sosai yayi mata dad'i!! Rana ku d'ai-d'ai ne Alina bata kuka idan ta tuno da WAALI tare da y'arta da bata san ma sunan ta ba!

Cikin k'ank'anin lokaci Alina ta saba da family na UMMA baki d'ayan su kowa ya santa itama ta sansu sabida zuwar masu da ta tab'ayi,sosai kuwa YAYA K'ARAMI jinin su ya had'u da ita,wanda yasa akai akai yake kaima UMMA ziyara idan sunyi hutu,wanda kuma da ba haka bane,sai ya zamana UMMA takanyi masa t'siya kan wai kodai za'ayi y'ar gida ne irin lik'ema y'ar kyakkyawa haka.

Tayi sabo da mutane sosai kuwa,t'sawon shekaru biyu suka d'auka tare da Alina,wanda kuma har zuwa lokacin babu wani kyakkyawan labari game da bayyanar Waali da kuma y'ar tata.
Soyayya ce mai k'arfi ta k'ullu t'sakanin HIMU da ALINA wanda kuma hakan yayi ma su UMMA dad'i ba kad'an ba,an saka ranar auren nasu,inda YAYA shine yayi mata komai na auren kamar yadda ake ma y'ar gata,shima gidan sa da ya gina a suleja ne,wanda suke makwaftaka da BABI,katanga ce kawai ga raba su!
Anyi aure lafiya an wat'se an bar UMMA da kewa wacce girma ya riga da ya kamata.

*vote*
*comment*
*share*
  
[8/1, 10:55 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...?*

*©️OUM_MUMTAZ* 

_WANNAN LITTAFIN TIN DAGA FARKON SA HAR K'ARSHEN SA NA SADAUKAR DASHI GA ~MSS FLOWER🌸🌸~ MARUBUCIYAR:_
~LAFAZI~
~AR SO~
~SARKI~
~GUMBAR DUT'SE~
_SON SO FISABILILLAH❣️💃🥰❣️❣️_                             
   
           *Charter 26*

******** Ai kuwa sosai mutunci mai kyawun gaske ya wanzu t'sakanin KAUSAR (AMMIH) da HALIMATU (ALINA) kwarai da gaske,ga kuma yadda gaba d'aya ma YAYA ya tattare kayan sa zuwa gidan Uncle d'in nasa sabida yadda jinin su ya masifar had'uwa! A kuma dai-dai wannan lokacin ne Allah yayi na UMMA rasuwa,mutuwar data girgiza family na YUSUF SHUWA ba kad'an ba,sbd rashin mahaifiya,wanda ita kanta Alina ma mutuwar ta kusan zautar da ita.

Tin daga lokacin da UMMA ta rasu sai ya zamana YAYA babba shine bangon su,wanda dik wani abinda zasu zartas t'sakanin su shine mai cewa eh ko ah ah a mat'sayin sa na magajin uba! Kuma suma sosai suke girmama shi tinda dama a haife ma zai iya haifar tasu.

AMMIH kuwa ta maida AMMAH(Halimatul Alina) mat'sayin kanwar ta,kuma abokiyar shawarar ta akan abubuwa na yau da gobe! Shekara na zagayo wa AMMAH ta haifi d'iyar ta mace mai kyan gaske son kowa k'in wanda ya rasa,wanda tin ranar da aka haife ta YAYA yabi ya kanainaye ta ya hana kowa ya d'auke ta in ba shi ba! Ranar suna na zagayo wa aka rad'a ma yarinya suna ASMA'U (HUSNAH) mai sunan MARIGAYIYA UMMA kenan!

Wanda dik wani d'awainiyar Husnah na wajen Yaya ne,sam
-sam bai son abinda zai tab'a ta tin tana k'ank'anuwarta!
Kowa kuwa son ta yake cikin dangin baji ba gani! A lokacin da ta kai 2yrs ne AMMIH ta haifo d'iya mace bayan t'sawon lokaci,wacce taci sunan HAJJA suna k'iran ta da MIMA!
Bayan wani 2yrs d'in ta sake haifar d'iya mace mai sunan mahaifiyarta HIDAYA!
Wani 2yrs d'in na zagayo wa cikin month guda suka haifu tare da Ammah! Wanda a wannan lokacin suka haifo yara maza dikkan su,AMMAH ta sama
WAALI takwara ne,wato ABDULWAALI,amma suna k'iran sa da WALEED! Inda yaron AMMIH kuma sunan sa AHMAD wato HAMAD!! Daga kansu kuma basu sake haihuwa ba wanda suka zamtoh sune y'an auta! Watoh fa akace jini ba wasa bane muddin ya shata layi,domin kuwa wani irin masifaffen kamar WAALI WALEED ya d'auko kamar shine mahaifin sa! Wanda hakan yasa a kullum idan Alina ta kalli fuskar Waleed d'in takan tuno da Waali da kuma d'iyarta,takan kuma yi addu'a da fatan Allah ya k'addara saduwar su kamin ta Allah ta kasance mata ta naimi yafiyarsu!
Takan k'ira Waleed da yayana kuma magajin ubana a lokuta da dama da su kuma basu san ma'anar haka d'in ba!!!

Wanda kuma a lokacin ne akayi auren KHADEEJA autar YAYA da suka kasance sa'anni da yaya domin kuwa shekara guda ta basa kwata kwata!!! wanda itama harda guzirin yaron ta guda watoh NURAAZ.

HUSNAH kuwa tin tana k'aramar ta tana da problem na jinnu,sannan kuma tana da skiller da yasa kwata kwata bata son sanyi ko kad'an,sai kuma abin ya had'u mata guda biyu dake matik'ar bata wahala!
Shekaru na jaa,lokuta na tafiya,wanda abubuwa da dama sun faru cikin wannan shekarun masu dad'i,da kuma akasin haka! Batare da doguwar jinya ba shekaru uku da suka gabata Allah yayi ma HIMU rasuwa,wanda mutuwar tasa ta kusan zautar da Alina tare da yaran ta harma da sauran dangi!!!

Sannan kuma sanadiyyar hakan ne YAYA ya had'e aure t'sakanin BABI DA AMMAH sbd gujema yaran k'anin nasu rayuwar agolanci a dik lokacin da suka wayi gari mahaifiyar su tayi auren wani gidan!! Wanda saida YAYA yakai ruwa rana da AMMIH kamin ta saduda,amma kuma ta rik'e su a zuciya,sabida gani take kamar bai k'aunar ta kamar baya shiysa yayi mata kishiya da girman ta da kuma wacce tasan komai na sirrikan ta! A tak'aice dai kishi ne kawai ke azalzalarta,wanda hakan har ya kusan shafar dangantakar dake t'sakanin yaranta da kuma su HUSNAH d'in,domin kuwa wani irin rikitaccen rashin kunya suke zabga ma ALINA da HUSNAH,su kuma hantari Waleed idan babu idon Yayaaa ko Babi a gidan.

Girman Yayaaa da HUSNAH shak'uwar dake t'sakanin su ne ta rikid'e izuwa zazzafar soyayya da babu algus! Sosai yake masifar sonta tin tana k'ank'anuwarta,da kuma ta girma sai abin ya girmama fiye ma da baya! Cikin wannan lokutan UNCLE J ya kammala karatun nasa,sannan kuma ya naimi aiki acan kuma sun basa tare da albashi mai t'soka,ya kuma yi aure tare da wata abokiyar karatun ta mai suna RUSHNI da ta kasance cikakkiyar ba indiya ce gaba da baya,amma kuma musulma ce!

Wanda auren nasu ma saida aka kai ruwa rana kamin both family nasu suka amince sabida rashin dai dai tuwar al'adar dake t'sakanin su,wanda a halin yanxu ma suna da yaron su namiji guda,wanda daga kansa basu sake wata haihuwar ba,hakan kuwa dik cikin nasu t'sarin ne!

Sannan kuma mijin Anty Khadee Allah yayi masa rasuwa ya barta da yara guda biyu Nuraaz da Aymana,wanda shine har Dad na Jidda yayi mata tayin auren aminin sa WAALI.

Ga kuma HUSNAH da Yayaaa k'ark'ashin inuwar aure guda mat'sayin mata da miji da ya kasance shine mafarkin su. Ga kuma mat'salar su dake t'sakanin su sabili da rashin son haihuwa da Yayaaa keyi!

Shin ko yaya zasu kasance?? Shin burin ZULAYKHA (UMMI) zai cika na auren ZULAYM AHMAD SHUWA dake mat'sayin mijin k'anwarta da suka kasance uwa d'aya,wanda kallo guda tayi masa cikin photo yayi nasarar sace zuciyarta dik da tarin masoyan da take dashi ciki harda d'an gidan Yaya wato UNCLE J...? Ya kuma had'uwar Alina da kuma Waali zai kasance bayan t'sawon shekaru 24 da suka d'auka basu tare da junan su...? Ina kuma labarin soyayyar da Musty kema Ummi? Shin mahaifiyar sa zata bari burin sa ya cika ko kuwa zata hana shi kamar yadda ta saba fad'a masa...? Waima shin ina su dangin mahaifin Musty ne? Kuna gani kuwa akoi uban da zai so ya aura ma y'arsa yaron da aka same shi ta hanyar da babu aure sannan kuma bashi da dangi...?
Tambayoyin akoi kaca kaca,wanda kuma nasan zaku so ku sami amsar tambayoyin ku! wanda idan kuwa kuna son hakan sai kun fara k'arfafa man gwiwa ta hanyar zuba sharhi zaku ci gaba da samun post akai akai kamar yadda kuka ga nakeyi akan Book d'innan.

_So masu karatu da fatan kun fahimci cikakken labarin wannan ahali guda biyu? daga yanxu zamu fad'a cikin labarin gadan gadan insha Allah🌸🌸🌸🌸🌸_

…… ……

K'ura ma fuskar Waleed Abbah yayi na cikin hoton a lokacin da ya karb'e wayar daga hannun ta sabida ta shanye shayin cikin lokaci k'ank'ani,ganin yadda mood na Abbahn nata ya chanza lokaci guda ne yasa ta mat'sowa had'i da kwantar da kanta a jikin sa,cikin muryar k'asa k'asa tace " Abba na kaima kaga yadda wannan yaron yake kama da kai ko??"

Cikin d'an muryar sa da ta fara shak'ewa Abbah yace "wannan d'an gidan wanene a ina kika samo shi?" da shike Ummi bata san komai dangane da gidan su Yaya d'in ba,saita masa bayani iya sanin ta "Kaga wannan kyakkyawan matan? itace maman way'annan dikkan su,kuma akoi ma wani yayan su da yayi aure kwanaki shima d'an ta ne,wanda har kuka je d'aurin auren!!" cikin son gaskata kalaman ta Abbah yace "kin tabbata Mamana?" "kwarai ma kuwa Abba na!" Ta kuma tabbatar masa da hakan iya gaskiyarta,domin kuwa dik tunanin ta Ammah d'in da suke ta faman ambata itama y'ar Ammih ce.

... ...

Washe gari da safe,tare da Abbah Zuly suka fita wurin aiki kamar ko yaushe!! Inda Musty ma ya wuce wajen nasa aikin dake kan kujerar Ummi d'in a halin yanzu.

Acan gida kuwa bayan fitar su Abbah abinda ya faru shine.........✍🏽

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[8/2, 6:14 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...?*

*©️OUM_MUMTAZ✍️* 

_WANNAN LITTAFIN TIN DAGA FARKON SA HAR K'ARSHEN SA NA SADAUKAR DASHI GA ~MSS FLOWER🌸🌸~ MARUBUCIYAR:_
~LAFAZI~
~AR SO~
~SARKI~
~GUMBAR DUT'SE~
_SON SO FISABILILLAH❣️💃🥰❣️❣️_                          
   
           *Charpter 27*

******** Ashe tin daren jiya ma'aikatan gidan da abin ya isa sukayi zaman meeting yasu-yasu,ta yadda zasu k'watar ma da kansu hak'k'in su na ganin an biya su albashin su da aka danne wata da watanni!!!
Hankalin su Mamy da Anty Khadee dake gida ba k'aramin tashi yayi ba,sabida ganin yadda suke ta faman rurrushe masu windows nasu cikin hargowa suna fad'in sai an biya su hak'k'in su ko su tada unguwar! Mamy batayi gigin k'iran wayar Abbah ba koda wasa,sabida tasan muddin indai yaji labarin to kuwa tabbas sun kad'e yau har buzun su yau kashin su sai ya bushe k'ik'ir,danna ma Musty dake office k'ira tayi,wanda shima ta jiyo sa cikin hargowa da hayaniya,sanadiiyar wirge wurgen da ma'aikatan keyi suma sai an biya su kud'in su sun tada zanga-zanga!!

Hankalin Mamy kam sake tashi yayi fiye ma da baya,ta rasa mai ke mata dad'i! Da kuma ta inda zata fara taren abin kamin Abbah ya ji labari! Anty khadee dake can ta kulle kanta a d'aki ita ta k'ira Abbah cikin tashin hankali ta shaida masa kan ga nan ma'aikatan gida nata faman faffasa dik wani abin da suka samu a gida kan sai an biya su hakkin su,wanda ita kuma bata san manufar hakan ba!!

A lokacin Abbah da Dad suna tare ne,Dad ne ya k'ira commisioner of police ya shaida masa kan yakai yaran sa gidan Alh Abdulwaali babu lafiya emergency,sbd yadda Abbah ma dik yabi ya rikice yama gagara mik'ewa ballantana yayi yunk'urin yin wani k'wak'k'waran abu!
Tare da taimakon Dad suka fito daga office d'in yana ta faman rirrik'e shi,wanda hakan ya jawo hankulan ma'aikatan kamfanin da aka samu wanda ya kaima Ummi rahoto kan gacan Abbahn ta ya gagara tafiya sai da taimakon yallab'ai Yusuf kamar baya cikin hayyacin sa.

Ai kuwa da gudu gudu sosai ta fito daga office d'in nata,wanda ba tare data ankare ba dogon takalmin dake k'afarta taja ta sai ji kake timmmm!! Wanda hakan yasa ta callara wani uban ihu cike da t'sananin azaba da ya sake hargit'sa ma'aikatan baki d'aya! Abbah dake can tare da Kabeer da yazo ya shaida masa kan abin da ke faruwa acan ma'aiakatar tasu ne ya sake d'aga masa hankali fiye da tunanin mai tunani,sai kuma ihun d'iyar tasa da ya karad'e illahirin harabar ma'aikatar tasu,bai san lokacin da ya k'arasa wajen ba ma ya ciccib'eta a mugun gigice kansa na barazanar t'sagewa gida biyu.

Dad ne ya amshe ta ya sata cikin mota ya umarci su Kabeer su wuce hospital da ita,shi kuma ya kamo Abbah suka fad'a mota zuwa ma'aikatan Ummi d'in domin jin ba'asin zanga zangar!!! Masu t'saron Abbah na take masu baya,da dik wanda ya gansu a lokacin sai ya kaice masu a hanya sabida yadda suke banbara uban gudu kamar babu gobe!

A lokacin da suka isa ma'aikatar hankalin Abbah da shi kansa Dad d'in idan yayi million a ya sake tashi k'warai da gaske,domin kuwa sun tarda matasan nan sunyi b'arna ba kad'an ba,wanda hakan yasa Dad sake k'iran commisioner of police kan a sake aiko masu da yara nan ma sabida ga abinda yake faruwa!! Dik yadda su Abbah suka so suyi calming na mutanen nan amma fir suka k'i,saima hayayyak'o ma Abbah da sukayi,kan ai shine ya d'aure ma y'arsa gindi take abinda taga dama yau idon su idon ta sai sun koya mata hankali!! Banda karkarwa babu abinda jikin Musty keyi,sabida yasan tabbas yau kam dubun su ta gama cikewa fes-fes daga shi har Mamyn nasa data tinzira shi yake wannan aika aikar.

Abbah kuwa sam k'wak'walwarsa ta toshe...yama gaza gane inda zantukan nasu suka sa gaba...masu kama da k'anzon kurege!!!
Isowar y'an sandan da suka fara k'wamushe su ne yasa wajen sake b'arkewa da hayaniya fiye da baya,a kuma lokacin ne Abbah ya samu nasarar saka Musty dake ta faman had'a zufa cikin idanun sa! Dad ne ya umarci Musty d'in tare da wasu ma'aikatan da babu su a masu aika aikar su biyo su,da kuma wasu y'an sandan zuwa cikin wani babban hole da aka tanade shi musamman domin irin wannan had'uwar ta gaggawa idan ya kama.

Wani daga cikin ma'aikatan ne ya shaida masu abinda ke faruwa a lokacin da Abbah ya buk'aci jin ta bakin su!!! "Wato yallab'ai a gaskiya abinda ake cikin wannan ma'aikatar kwata kwata baya dacewa, domin kuwa ita madam Zulaykha a watannin baya da suka gabata wajen wata takwas zuwa tara kenan ta rage ma dik wani ma'aikaci dake kamfanin nan salary wajen kaso 15 cikin d'ari, wanda hakan ya mugun d'aga mana hankali muka tinkari yallabai Mustapha da maganar sabida sak'on daga wurin sa ya iske mu, amma sai ya bamu hak'uri tare da tabbacin insha Allahu zai san ta yadda zai biyo mata har ta biya mu dik wasu kudaden da ya zamtoh hakkin mu, to a gaskiya yau da gobe tafi k'arfin wasa, tin muna jurewa muna magana ta k'asa-k'asa har hakurin mu ya fara gazawa muka fara tunanin hanyar da zamu bi wajen ganin mun karbo hakkin mu, tinda kullum yallabai cikin shaida mana kwana kusa zasu biyamu abin yaci tura,wanda hakan ya fusata wasu daga cikin mu suka tada zanga-zanga kan sai an biya su hakkin su ko kuma su tada wajen kowa ma huta...……"

Shuru wajen ya d'auka na wasu y'an dak'ik'u, wanda a dai-dai wannan lokacin da masu karatu zaku t'saga jikin Musty to kuwa babu abinda zaku gani sai magudar zawo a wando sabida tashin hankali🙈....Abbah kuwa ransa idan yayi dubu a dai dai wannan lokacin ba karamin baci yayi ba,wani shashi na zuciyarsa na k'ok'arin k'aryata abinda aka fada akan yar tasa sabida sanin halin ta da yayi ciki da bai,wanda kuma wani b'arin na fadi masa da cewa ai dan yau ka haife sa ne baka haifi halin sa ba!!! Wanda kuma a gefe guda Dad ma ya t'sunduma tunani ne cikin wannan lamarin ne gadan gadan.

'Dan sandan dake daukan details kan zantukan da ma'aikacin keyi ne ya sake jefo masa tambaya, "ina shi yallabai Mustaphan naku yake yanzu??"  "Gashi nan ranka shi dade." Kallo daya police din yayi ma Musty ya hango tsagoron rashin gaskiyar dake tattare da yaron! Cikin t'suke fuska police d'in yace, "Mallam Mustapha ko zaka iya yimana bayani dalla-dalla dangane da abinda ya faru ta yadda zamu fi fahimta???" Zufa ne sharkaf ya sake jik'a rigar Musty ya fara zuba i ina yama rasa ta inda zai fara bayani!! Wanda hakan yasa  daya daga cikin police din kallon Abbah da ya lula duniyar tunani da kuma Dad dake ta faman kallon Musty cike da nazarin sa yace, "yallabai zamu wuce da wayannan can offishin namu,sannan kuma muna da buk'atar ganin ita mamallakin kamfanin sabida muna so muyi mata wasu y'an tambayoyi dangane da case dinnan! Don haka yanxu zaku tafi da wasu daga cikin yaran mu suzo mana da ita,mu zamu wuce da wayannan din"

Tsakanin Abbah da Dad babu wanda ya musa,inda suka wuce tare da motar police guda sauran kuma suka kwashi su Musty bayan an rufe gate na ma'aikatar zuwa police station......!

………………

Asibiti su Abbah suka nufa,wanda suka tarda har zuwa lokacin likitoci basu fito akan ta ba,sabida buguwar da kafarta tayi hakan yayi sanadin yi mata karaya cikin kashin ta. Kabeer dinma dashike dashi za'a tafi station din sai ya zauna asibitin tare da yan sandan,kan idan aka gama da ita zasu wuce aje a karashe case din!
Wanda daga nan kuma su Abbah suka maida akalar tafiyar tasu zuwa can unguwar Maitama domin gano yadda Al'amarin can d'in yake!
Acan kuwa abinda ya faru tin bayan shaida ma Abbah abinda ya faru da Anty khadee tayi shine……✍🏽

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[8/2, 6:32 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...?*

*©️OUM_MUMTAZ* 

_WANNAN LITTAFIN TIN DAGA FARKON SA HAR K'ARSHEN SA NA SADAUKAR DASHI GA ~MSS FLOWER🌸🌸~ MARUBUCIYAR:_
~LAFAZI~
~AR SO~
~SARKI~
~GUMBAR DUT'SE~
_SON SO FISABILILLAH❣️💃🥰❣️❣️_                          
   
           *Chapter 28*

******** A lokacin da y'an sandan suka k'arasa gidan Abbah d'in ba k'aramin b'arna suka tarda ma'aikatan sukayi ma gidan ba,sabida hatta ga windows na motocin sun faffasa cike da t'sananin fusata da yasa Mamy kanta gagara fitowa tayi ta kulle kanta a d'aki tana zuba zawo na tashin hankali,ita kam Anty Khadee banda addu'ar neman t'sari kan wannan haukar tasu babu abinda take cikin d'akin ta tare da fatan Allah yasa kamin yaran ta su dawo daga makaranta su Abbah su d'au mataki gudun kar a illata mata su (uwa mai dad'i,a dik halin da take ciki kyakkyawa da mummuna to kuwa tabbas bata tab'a mancewa da abinda ta haifa😘).

Da k'yar suka samu nasarar dakatar dasu ta hanyar fet'sa masu tiyagas suke kame su,suna antayawa cikin motocin su tas suka kwashe su hatta ga mai gadi suka gark'ame su kamin Mamy da Anty khadee dake a t'sure har yanzu suka firfito suna zare ido!!!

Wanda saida suka tabbatar da sun kwantar masu da hankali kamin suka tafi da yaran bayan sun d'auki dik wasu bayanan da suka kamata,suka kuma bar masu wasu y'an sandan guda biyar a bakin gate da zasu kula da masu shige da fice zuwa wani lokacin idan k'ura ta lafa.

A cikin wannan yanayin su Abbah suka iso,wanda su Aymana ma already sun dawo gida dama,wanda hakan yasa Abbah tare da Dad basu wani zauna ba,sallah kawai sukayi ko cin abinci basu yi ba suka wuce station tare da su Mamy baki d'aya da taso zille ma tafiyar.

Inda suka tarda harda Ummi dake zaune kan kujera kanta k'asa zuciyarta kamar ta faso k'irjinta sabida jin laifin toye hak'k'in ma'aikatan ta da ake tuhumarta da shi tinda aka kawo ta station d'in ta gagara magana!!! Sai uban kuka da take sharb'a kamar babu gobe sabida bak'in ciki da takaici.

Banda wani irin mummunar kallo babu abinda Abbah ke wat'sa ma Ummi tin wajen zaman da aka basu da suka k'araso cike da t'sananin jin haushin ta,da kuma takaicin dake cin zuciyarsa tin-tini!! Mamy na zaune wajen t'sam kamar t'summa a randa k'yat take jira ta fesa da gudu sbd yadda k'irjinta ke dukan uku uku sbd tasan mai ta aikata,ga kuma Musty da shima ke zaune rik'e da kansa ya rasa maike masa dad'i kwata-kwata,wani irin nadamar biye ma hud'ubar mahaifiyarsa ne da kuma d'acin ta ke taso masa daga can k'asan zuciyarsa kamar ya mutu ya huta don bak'in ciki da kuma takaici.

Dad nada niyyar ficewa ya wuce gida tinda abin kamar family issue ne amma Abbah ya buk'aci kan ya zauna babu damuwa.
Biyu daga cikin ma'aikatan kamfani da kuma biyu daga cikin ma'aikatan gida mata biyu da maza biyu da zasu wakilci y'an uwan su aka ciro daga cell zuwa gaban Cm_p domin aji ba'asin wannan masifar.

……...……

Wani irin shiru cikin station d'in ya d'auka a lokacin da way'annan bayin Allah suka gama koro bayani dalla-dalla aka rasa wanda zai fara bud'e baki t'sakanin Abbah da UMMI banda ido da suka sakar ma Musty dake jin kaf duniya babu wanda yakai sa muzanta a yau d'innan!!!

"n.i..ce nas...s aka rage Albash...in su Ya Musty...?" Ummi ta fad'a cikin rawar murya dake tafe da wani irin hargit'sat'st'sen kuka mai matik'ar tab'a zuciyar mai sauraro!!

"Tabbas nid'in a yau na nuna ma duniya cewa ni ba d'an halak bane batare da an buk'aci hakan daga gare ni ba!!" Musty ne yayi wannan maganar cikin t'sananin bak'in ciki da kuma takaicin halayyar sa yana mai fashewa da wani irin Kuka kamar ba namiji ba! Sannan kuma ya d'aura da fad'in "tabbas dik abinda way'annan bayin Allah suka fad'a gaskiya ne babu k'arya kan rage masu salary nasu da akayi,amma kuma fa ita mamallakiyar ma'aikatar wato Zulaylha AbdulWaali bata da masaniya akan dik wannan abubuwan dake faruwa! Hasalima watanni biyu zuwa Uku da suka gabata ita da kanta tayi mawa dik wani ma'aikaci dake aiki k'arin salary na naira dubu goma goma,ni kuma ta k'aramin naira dubu ashirin amma kuma naci amanar ta na gagara yin aiki da zuciya d'aya t'sakani da Allah!"

Shiru Musty yayi,yana kallon tafin hannayen sa cike da d'acin zuciya da kuma muzanta da yasa CM gyaran murya yace, "Muna jinka ci gaba"

Saida ya jim kamin yaci gaba da shaida masu dik wasu shawarwari da suka yanke da mahaifiyar sa da irin yadda suke cin hakkin jama'a tinda dama basu san zafin naima ba saina hassada da kuma rashin godiyar Allah!!"
Kowa dake wajen jinjina kai yake kawai cike da d'imbin mamaki na wannan al'amari mai kama da ta t'suniya ko kuma suce shirin film.

Wani irin kallo Abbah ya aika ma Mamy dake ta faman share zufa akai-akai da yasa hanjin cikin ta kad'awa ba k'arami ba sabida mugun t'soron Abbahn daya dirar mata lokaci guda!!! "Abinda zaki saka man dashi kenan Aishatu? Nace abinda zaki saka man dashi kenan?"  Yayi maganar cikin t'sananin t'sawa da hargowa daya sa Mamy hant'salawa zuwa bayan C_M jikin ta d'aukar b'ari kamar mazari! Dad ne ya rik'e Abbah da k'yar tare da wasu police d'in sabida k'ok'arin da yake wajen ganin yayi nasarar jibgar Mamy!! Ummi ta jima da sanin irin k'aunar da Musty ke mata,wanda wani zubin in ta zauna ita kad'ai takanyi tunanin zata iya yin rayuwar aure dashi sabida bashi da wani aibu ko nakaso idan aka cire rashin asalin sa,wanda kuma shima idan mutum mai hankali ya auna zai gano cewa bashi da wani laifi dangane da rashin asalin nasa,tinda bawai anyi shawara dashi bane kamin a haifesa,amma kuma saidai kash! Wannan abinda ya faru yasa taji wani irin mummunar t'sanar sa ya sauk'ar mata cikin zuciya,da take jin ko dik duniya da abinda ke cikin ta zasu taru akan ta bazata tab'a yadda ta aure shi ba!

Anty Khadee kam da yaran ta sun zama y'an kallo ne kamar wasan kwaikwayo suna kallon ikon Allah! Da k'yar aka samu Abbah ya zauna mazaunin sa tana dafe kansa dake barazanar t'sagewa kamin CM ya yanke hukuncin da yake ganin shine dai-dai babu batun zuwa kotu.

Mamy da Musty zasu biya each and every ma'aikaci dake cikin wannan station d'in cikin sati guda wato kwanaki bawai,sannan kuma baza'a kulle su ba,amma fa idanuwan y'an sanda na kansu ta yadda idan ma suka aikata wani mummunar abu ta hanyar samun kud'in sun sake d'aura ma kansu laifi ne,wanda a wannan gab'ar kuwa baza suyi masu sassauci ta wani sanayya ba,yanxun ma dalilin da yasa bazasuyi masu terere ba sbd girma da kuma mutuncin da Abbah ke dashi cikin garin ne in ba haka ba tabbas abinda za'ayi masu sai ya zarce wannan d'in.

Sosai su Dad sukayi ta bama Abbah hak'uri kamin ya yadda akan bazai sallami Mamy da d'an ta ba bayan rubuta yarjejeniya akayi masu bayani  tare da tabbacin cewa dik wani abinda suka fasa both gida da kamfanin idan aka kawo kudin nasu sai an gyara idan yaso sauran a raba masu! Wanda hakan kuma yasa suka fara jin haushin kansu ba kad'an ba gashi yanzu suma da tasu asarar🤣😂.

Haka nan suka tattara suka koma gida,inda Ummi kuma suka wuce asibiti da Anty Khadee sabida yadda ita Ummin keta faman d'ingisa k'afar tata dake masifar yi mata ciwo tare da taimakon Anty khadeen,wacce dama y'an sandan ne suka taho tare da ita bayan ta farfad'o batare da an duba mata k'afar tata ba.

Tin a hanya banda bombomi da masifa babu abinda Abbah keyi,cike da takaicin Mamyn.
Da isar su gida kuwa Dad ya masu sallama ya wuce gidan sa,sabida lokacin kusan k'arfe takwas na dare ne.
Wanka Abbah yayi bayan yayi sallar la'asar,magriba da isha'i ko cin abinci bayyi ba ya fito daga gidan nasa batare da yabi ta kan su Mamy ba zuwa wani had'ad'd'en restaurant yayi masu order na abinci da su drinks da dik wasu abubuwan da ya kamata asaima mara lafiya ya wuce zuwa asibitin bayan ya kaima Aymana da Nuraaz nasu da suke ta kallon su hankali kwance,tinda su ba gama gane mai duniya ke ciki sukayi ba.

B'angaren Mamy da Musty kuwa tinda suka dawo gida...……...……✍🏽✍🏽

_GARI YAYI ZAFI😂🤣_

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[8/3, 2:18 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...?*

*©️OUM_MUMTAZ* 

_WANNAN LITTAFIN TIN DAGA FARKON SA HAR K'ARSHEN SA NA SADAUKAR DASHI GA ~MSS FLOWER🌸🌸~ MARUBUCIYAR:_
~LAFAZI~
~AR SO~
~SARKI~
~GUMBAR DUT'SE~
_SON SO FISABILILLAH❣️💃🥰❣️❣️_                          
   
           *Charter 29*

******** B'agaren Mamy da Musty kuwa tin da suka dawo gida banda kuka da kaicon ta babu abinda Mamy keyi,wanda kuma Musty ya gagara bata hak'uri, banda zuba mata idanu babu abinda ya iya yi. Tabbas ance uwa ta wuce gaban kowa,wanda ba don haka ba da yau babu abinda zai hana ya faffala ma wannan matar data kaisa ta baro.....

Cike da bak'in ciki gami da takaici cikin chunkushashshiyar murya yace, "Nifa ba kuka nasa kizo ki zauna kiman ba!!! Shiga d'aki zakiyi ki fiddo da dik wasu kud'ad'en da kika san ina kawo maki tinda dama ba amfani muke dasu ba,sabida babu abinda muka naima muka rasa cikin gidannan,kwad'ayi ce kawai take sa muke kwasan kud'ad'en bayin Allah da suka sako mu inuwa"

Sharce majinar dake sauk'o mata tayi ba tare da tayi magana ba ta mik'e zuwa d'akin ta,few minute ta fito daga d'akin hannun ta rik'e da wayarta ta samu guri ta zauna.
Cikin mintuna da bai wuce guda goma ba ta juye ma Musty kud'ad'en cikin account nata tas babu ko d'igo zuwa cikin nasa cike da wani irin nadama mara misaltuwa.

Haka nan suka kwana cikin rashin dad'in rai,washe gari da sassafe wajajen k'arfe takwas Musty ya tafi station akayi masa iso wajen DPO,wanda dama anyi dik wasu lissafe-lissafen daya kamata tin jiya babu ragin ko k'wandala hakkin mutane a cikin account nasa sai halalin sa da yake d'auka na salary nasa kamin yaji kamar an sauk'e masa wani gundumemen dut'se daga t'sakar kansa,har wani fresh air yake ji yana shak'a.

Gida ya wuce inda ya tarda Mamy cikin shirin zuwa asibiti domin dubo Ummi d'in da suka kwana acan,harda girki kuwa mai rai da lafiya ta masu,da yaso yak'i zuwa amma ta tursasashi,sabida su wanke bak'in fentin da suka lafta ma kansu! Wanda suka tarda jikin ma da sauk'i,amma daga ita har Abbah babu wanda ya sakar masu fuska hakan yasa jikin Mamy sake yin sanyi,wanda suka zauna jugum-jugum sai ga Dad tare da MUM da kuma Jiddah sun zo su da kayan breakfast suna tambayar ya mai jiki,sai kuma a lokacin suka saki fuska harda cin abincin da su Jiddah suka kawo wanda ko kallon na Mamy babu wanda yayi idan aka d'auke Anty Khadee da taji Mamyn ta bala'in bata tausayi sbd yadda taga uban zabgewar da tayi cikin kwana guda.

Shi kam Musty yasan tabbas yayi ma kansa,kan soyayyar da yake ma Ummi yasan idan ba wani ikon Allah ba kam tabbas shi da ita saidai hange daga nesa.
Wajajen azahar aka sallamo su suka dawo gida,wanda aka sake yin zama na musamman tare da Dad da ya sake tausar zuciyar Abbah,tare da yima Mamy da kuma Musty nasiha mai rat'sa jiki daya sa wani nadamar sake rufta masu,inda Allah ya taimaka ma Dad ba irin mutane masu baki sakaka bane,don haka babu wanda yasan abinda ya faru idan aka d'auke way'anda abin ya shafa.

Har k'asa Musty ya duka ya sake basu hak'uri akan abinda sukayi masu shida mahaifiyar sa,suka kuma tabbatar mashi da sun yafe masu har cikin zuciya kamin aka wat'se zuciyoyin su wasai amma banda Musty da tunanin ta yadda zai had'u da dangin mahaifin sa yake ta faman k'ullawa da kwancewa.

...……...

"Ni dai wallahi yau sai naje wajen Anty Khadee Ammah nah"  Waleed ya fad'a cikin b'ata fuska cikin marairacewa kamar ya fashe da kuka yana faman cuno baki gaba.

Tagumin da Ammah tayi ta janye cikin gajiyawa da magiyar da Waleed d'in ke mata tin ranar dasu Jiddah d'in suka tafi tace, "ka fita fa daga ido nah kamin na sab'a maka a gidannan ko?"

Ai kuwa kamar jira yake irin k'ananun yaran nan ya fashe mata da kukan iya hege yana ta faman tirje-tirje da k'afafuwa!!

Wawuro maficin dake gefen ta tayi,da yasa shi ficewa da gudun sa yana shidai sai yaje gidan Anty Khadee ko ayi yak'i yau a gidannan!

Kicib'us sukayi da Yaya da yanzu suke rafka sallama tare da Husnah da matashin cikin ta yayi mata das dashi suna baza uban k'amshi abinsu gwanin birgewa!!! Dakatawa daga biyo Waleed d'in Ammah tayi tana murmushi cike da jin dad'i tace, "Maraban ku da zuwa..."

Da d'an sassarfa Husnah ta k'arasa zuwa wajen Ammah d'in ta fad'a jikin ta da yasa Ammih fitowa daga d'akin ta tare dasu Mima sabida jin hayaniya a t'sakar gidan nasu!!!
Wanda hakan yasa suka kaure da hayaniya cike da farin ciki suna masu oyoyo,wani irin farin ciki ne ya kama zuciyar Yaya sbd ganin yadda gidan nasu ya koma happy family kamar baya!!! D'akin Ammih suka wuce,Waleed na lik'e da Yaya yana kora masa rok'o kan dan Allah su tafi tare dashi yana son zuwa gidan Anty khadee wajen Nuraaz!!!

Nan suka wuni suka shiririce abin su gwanin birgewa har zuwa yamma da Babi ya dawo aka zauna dashi shima suka sha hirar su,sai can bayan isha'i kamin suka tashi tafiya,da yasa Waleed tada masu bori don dole aka tafi dashi tare da Hamad da shima yace sai ya bisu!!!

Gidan Dad suka wuce,da suka samu tarba ta musamman dikda basu san da zuwan nasu ba,su Hajiya Jiddah sai faman surutu take zuba masu wanda saida Yaya ya kora ta kamin suka sami lafiyar kunnen su,a lokacin wajajen k'arfe tara na dare ne,don haka sai kawai Yaya ya wuce dasu gidan sa baki d'aya kan gobe idan yaso sai suje mata sabida yanzu babu dad'i dare yayi sosai,ba don sun so ba haka suka bishi sabida sanin halin sa na rashin maimaita magana idan ya fad'e ta!!!

"Akoi wata kyakkyawa dana gani yasin ta fiki had'ewa Anty Husnah!" Waleed ya fad'a cikin shek'iyanci a lokacin da suke zaune parlo wajajen goma na dare! Harara ta wat'sa masa batare data basa ansa ba Hamad yace, "ba wani nan,ni ban tab'a kallon wacce takai Anty Husnah kyau ba,bamu son fyori!!"

Ai kuwa wani irin want'salowa gaban Hamad Waleed yayi,cikin son tabbatar masa da abinda yake fad'i yace, "Wallahi da gaske nake,kardai kace man har ka manta da Anty mai kyau d'innan na ranan??"

Shiru Hamad yayi alamun son tuno wacce Waleed d'in ke kira da Anty mai kyau amma ya gagara tunowa.
Gyara zama da kyau yayi yace, "Wai har yanzu baka tuno da wannan wacce suka je gida da Anty Jiddah ba har suka kai bayan la'asar da muka sha game da wayar ta?"

Ai kuwa shima gyara zama yayi mai kyau yace, "Ayyooo!!! Ai saika man bayani ta yadda zanfi saurin tafiya gana kai kuwa,ba wai kana yiman kwane-kwane ba!!! Ai kuwa tabbas wannan kam k'arshe dama zan samu ire-iren su su zan zuba guda hud'u reras idan na tashi yin aure nah wallahi"

Yaya da tinda suka fara magana ko kallon su bayyi ba,balle kuma yasa masu baki ya d'aga fararen idanun sa fes ya sauk'e kan fuskar su cikin t'sare gida sabida jin bayanan da suke,ai kuwa nan take dik sukayi mit kamar babu su a wajen suna t'sili-t'sili da idanuwa! Girgiza kai kawai Yaya yayi cikin d'aure fuska tamau yace, "Ku wuce kuje ku kwanta kamin na tattaka ku a gidannan!!!!"

Ya k'arashe maganar cikin kakkausar murya da yasa su bajewa lokaci guda har suna rige-rige sabida sanin halin sa t'saf zai mazge su idan ya mik'e!!!!

"Yaya wai akoi wacce tafi ni kyau???" Husnah ta fad'a tana mai narke masa cike da wani irin abu mai d'aci dake taso mata can k'asan zuciyarta tinda Waleed ya d'auko maganar Anty mai kyau da bata ma santa ba ita kam.

Murya can k'asa-k'asa ya rad'a mata cikin kunnen ta yace, "karya suke,kaf cikin duniyar nan babu wacce takai My Ma'u kyau" wanda hakan yasa ta lumshe ido cike da t'sananin jin dad'i ta wulla bakin ta cikin nasa suka fara aika ma da junan su zazzafan sak'onni cike da t'sananin shauki da kuma begen junan su.

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[8/3, 2:18 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...?*

*©️OUM_MUMTAZ* 

_WANNAN LITTAFIN TIN DAGA FARKON SA HAR K'ARSHEN SA NA SADAUKAR DASHI GA ~MSS FLOWER🌸🌸~ MARUBUCIYAR:_
~LAFAZI~
~AR SO~
~SARKI~
~GUMBAR DUT'SE~
_SON SO FISABILILLAH❣️💃🥰❣️❣️_                          
   
           *Chapter 30*

******** WAshe gari da misalin k'arfe goma na safe,Yaya ya ajiye Husnah,Waleed da Hamad k'ofar gidan Abbah kan idan ya taso daga wajen aiki shima zai shigo su gaisa.
Idan kuka fuskar Waleed kamar gonar auduga sabida yadda yake ta faman d'auki na ganin Anty mai kyau,d'aya daga cikin sabbin ma'aikatan da aka kawo ce bayan ta kaima mai gadi abinci daga part na Anty Khadee ta masu jagora!!

Da sallama suka kut'sa kansu cikin parlon,Husna ce a gaba sai Hamad tare da Waleed da suka take mata baya!
"Sannun ku da zuwa k'annen arziki yanxu kuke tafe?" Anty Khadee ta fad'a cike da t'sant'sar farin ciki a lokacin da ta fito daga kitchen sabida jiyo mot'sin su!

"Ai kuwa dai mune da zuwan safiyar nan an sako mu a gaba Anty" Dariya dik suka shek'e dashi Anty Khadee tace, "Babu wani sako ku a gaba da akayi,kuka san ko zamuyi y'ar gida ne da Anty mai kyau d'in da ake ta faman ambata? Ai jiya da dare munyi waya dasu Babi sun kuma shaida man na t'sammaci zuwan Alhaji mai gida yau"

Nan dai suka sake gaggaisa sosai,Aymana,Nuraaz da Ummi ne suka fito daga kitchen da in kuka gansu sai kun rik'e baki sbd yadda sukayi butu-butu da fulawa!

"Bak'i mukayi ne Anty? Sannun ku da zuwa fatan kunzo lafiya?" Ummi ta ce ma Husnah da itama kanta saida ta yaba da kyawun halitta irin na Ummi d'in,abinda ya farkar da ita shine muryar mahaifiyar ta da ta jiyo tattare da Ummin babu banbanci ko na sisin kobo!

"Lafiya klaou Anty mai kyau" ta ba ta ansa tana k'wak'ulo murmushin yak'e sbd yadda take jin gaban ta na t'sananin bugawa!

"My man's kunzo lafiya ko??" Ai kuwa mat'sowa Waleed yayi yace, "suwal muka zo Anty nah,tin jiya naso a kawo ni amma mijin waccan t'sohuwar ya kasa ya t'sare!"

Da mamaki kuwa UMMI tana dariya tace "wanene kuma mijin t'sohuwa ni Zuly?"

"Wai fa Yaya yake nufi?" Hamad ya bata ansa shima yana sakin dariya,wanda hakan yasa Husnah d'aure fuska tace, "kamar a kunnen sa yau d'innan!!" wanda ma tin kamin ta gama rufe bakin ta suka bi suka rikice sunaa bata hak'uri kan karta fad'a masa su shiga tara!!

Sosai kuwa suka sha hirar su,wanda tin Husna da Ummi na baya baya da junan su cikin k'ank'anin lokaci suka saki jiki suna zuba charpter kamar dama sun jima da sanin junan su,inda suka shiga kitchen suka k'arasa girkin ma tare tana ta t'sokalar ta da maman unborn!

Bayan sallar azahar sun gama cin abincin su Ummi ta kwashi Hamad dasu Waleed tare da Aymana da kuma Nuraaz zuwa wajen shak'atawa domin su sha iska!

Husnah taso binsu sabida yadda take jin dad'in kasancewar su tare amma Anty Khadee tace "bata isa ba" sabida sanin halin Yaya bazai ga laifin Husna ba sai nata.
Sun sha yawo bana wasa ba kuwa,basu suka dawo gida bai sai bayan sallar la'asar wajajen k'arfe biyar na yamma!

Inda suka tarda sabuwar motar yaya fake cikin harabar gidan nasu,da yasa Waleed dafe k'irji had'i da fad'in, "Shikenan kuma! Yanzu nasan yau kam harara saimun ture!" Nuraaz da bai cika yawan magana ba cikin sanyin murya yace, "Hala har yanxu bai canza halin sa na t'sare mutane ba?"
"Ai abin ne ma yana girma yana sake yin linkaya in fad'a maka!!" Aymana da Ummi kuwa dariya suka shek'e dashi,dik da yadda k'irjin Ummi ke masifar bugawa bana wasa ba!

Da sallama suka shigo parlon,inda saida Ummi takai ga dafe k'irjin ta batare da kowa ya lura ba,sabida ganin Yaya da tayi a yau ido da ido sai da wani irin mik'i da soyayyar sa ya sake samun mat'suguni cikin zuciyarta tare da zazzafan kishi sabida ganin yadda Husnah ta masa rashe-rashe tana zuba masa shagwab'a shi kuma sai biye ta yake,ga kuma Anty Khadee zaune gefe sai t'siya take masu.

Mik'ar da Husnah Yaya yayi yana gyara mata zaman gyale kanta,batare da ya ansa gaisuwar dasu Hamad ke masa ba yace, "Sai ku wuce mu tafi a yawo!"  "Ka bar su su huta mana sarkin azarbabi sai ku tafi idan anyi sallar magriba!"

Ai kuwa harara ya dalla ma Anty Khadeen da yasa Ummi cikin sanyin murya da tin d'azu tayi ma kanta mazauni kan kujera tace, "ina wuni?" Kallon inda aka gaida sa yayi a karkace da yasa k'irjin sa bugawa cikin basarwa yace, "lafiya" daga nan yaja bakin sa ya t'suke ya kad'a kan su baki d'aya suka fito,inda sukayi clashing da Abba wajen da sukayi parking shima ya dawo tare da masu t'saron shi!

D'an risinawa sukayi suka gaida shi ya ansa masu cikin sakin fuska tare da tambayar su mutanen gida,wanda sai a lokacin Yaya ya tabbatar da abinda ke masa yawo tin farkon had'uwar sa Abbah kamar yasan wani mai kama dashi,sai yanxu da ya gan Waleed jere da Abbah d'in yasan inda yake masa kallon sani! Sai kawai ya basar bai bama hakan mahimmanci ba!

Abbah kuwa harda bama su Waleed money sabida yadda yaron ya masifar birge shi ba kad'an ba,ya kuma jii k'aunar sa har cikin zuciyar su! A lokacin da idanun sa suka sauk'a kan fuskar Husnah sosai gaban sa ya fad'i,sbd ganin wani irin mugun kamar marigayiya Iyami shimfid'e kan fuskar ta! Wanda kuma zuciyar sa ta fara zarga masa wani abun,amma sai kawai ya share tinda dama ance ai kowa yana da masu kamannin sa guda bakwai a duniya !

Choculate dasu ice cream d'in da suka sayo Ummi ta bama su Hamad bayan ta raga ma su Aymana nasu! Inda suka rabu cike da t'sant;sar kewa,suna gama ficewa daga cikin gidan suka kama hanyar suleja sabida mayar dasu Waleed d'in gida kamar yadda sukayi ma su Ammah alk;wari!
Basu suka dawo cikin gidan nasu ba sai wajajen k'arfe tara na dare!

B'angaren Ummi kuwa komai yinsa take cikin k'arfin hali har sukayi dinner,inda tin bayan da tayi shirin kwanciya tabi lafiyar katifar ta banda kuka babu abinda take,sabida ganin wani irin soyayyar Husnah cikin idanun Yaya ta tabbatar zayyi wuya ta samu koda gurbi guda ne cikin zuciyar sa!

Washe gari misalin 10:00am.

Ringing d'in da wayar ta keyi da naiman agaji ne ya farkar da ita daga baccin da bata samu damar yi daren jiya ba,sakamakon kwana da tayi tunani da kuma kukan son ma so wani...!
A kasalance ta zuro da hannun ta na hagu zuwa inda take da tabbacin ta ajiye wayar tata batare data bud'e idanun ta ba,ballanta kuma tasan wanda ya k'irata,tayi recieving!

Muryar wanda ta jiyo ne daga cikin wayan yasa ta d'an yamut'sa fuska ta kuma gyara kwanciyar sannan ta bud'i baki da k'yar tace, "Mun tashi lafiya uncle??"

Daga ta can b'angaren Uncle J dake k'asar Australia yace, "lafiya kalai preety na,yasu Abbah da kuma sauran mutanen gida...?"

"Dik lafiyan su,ya aiki?" 

"Alhmdlh my dear!"

Daga nan dai suka t'sunduma cikin firar tasu gadan-gadan,wanda yawanci ma shine ke magana,sai dai ta ansa masa da eh ko Ah ah...! Sannan kuma yawancin hirar tasu da suke na magiya ne kan ta basa damar turo da iyayen sa a naima mashi auren ta amma take gara masa kai sabida sanin da tayi cewa a zuciyar ta akoi wanda take so,amma kuma idan ta zauna tayi dogon nazari tana ganin kamar hakan bazai haifar mata da d'a mai ido ba,da ace ta nacema mutumin da babu d'igon soyayyar ta a zuciyar sa ita kuma tana son sa,gwanda ta bama wanda ke k'aunarta dama dikda bata son sa,tasan with time komai zai zama tarihi ne kamar ba'ayi ba!!

Gashi wanda a baya take ganin zata iya bashi damar auran ta ko da kuwa ace bata k'aunar sa ya b'ata rawan sa da t'salle(musty kenan) .So don haka kawai sai tayi deciding ta kuma bama Uncle J dama tinda taga kaf cikin maneman ta shine matured one dikda a cikin burikan ta babu t'sari na auren mai mata,and kuma datayi sake reshe kama ganye kam gwanda tasan inda dare yayi mata.

Inda a wannan ranar saita Ummi ta kuma tabbatar ma da Uncle J damar ya turo magabatan sa sabida ita ma ba dut'se bace,tafiya ake shekarun ta na sake jaa gwanda kawai tayi ma kanta fatan Alkhairi ba wai bin muradin zuciyar ta ba...!

Hakan kuwa ta kasance.........🧕🏼

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*

[8/3, 6:51 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...?*

*©️OUM_MUMTAZ* 

_WANNAN LITTAFIN TIN DAGA FARKON SA HAR K'ARSHEN SA NA SADAUKAR DASHI GA ~MSS FLOWER🌸🌸~ MARUBUCIYAR:_
~LAFAZI~
~AR SO~
~SARKI~
~GUMBAR DUT'SE~
_SON SO FISABILILLAH❣️💃🥰❣️❣️_                          
   
           *Chapter 31*

******** Hakan kuwa ta kasance......!

Domin kuwa bayan sati guda dayin wayar tasu Babi dake mat'sayin Uba kuma waliyyi wajen Uncle J kamar yadda YAYA BABBA ya nad'a shi da kuma Dad d'in Jiddah tare da Baban Asmy da wasu mutane guda biyu suka zo har gida naima wa Jafar auren Zulaykha...!
Wanda in tak'aice ma masu karatu,basu suka baro gidan Abbah ba saida aka t'saida ranar biki nan da 3month kamar yadda suka buk'ata!

A kuma wannan ranar Ummi tayi kuka iya kuka sabida jiyo k'amshi rabuwar ta da muradin zuciyar ta na sake kusanto ta,sai ya zamana Mamy da ta ladaftu ba kad'an ba a wajen Abbah tare da Anty Khadee da abin ya masifar yi mata suka had'u suna lallashin ta,had'i da kwantar mata da hankali gudun kamuwa da wani ciwon.

Ranar dik wanda ya kalli fuskar Abbah sai ya tabbatar da irin farin cikin da yake ciki sabida murnar auren d'iyar sa k'wallin k'wal a duniya...!
B'angaren Uncle J kuwa dik budirin wannan naiman auren nasa da yake sam sam ba'indiyar matar sa bata da labari,sabida bari yayi bazai fad'a mata ba sai nan gaba idan abin yayi sauran kadan!

A gefe guda kuwa kusan ko da wani lokaci suna lik'e da waya shida Ummi da itama k'arfi da yaji take k'ok'arin koya ma kanta soyayyar sa amma abin yaci tura!
Bayan sati guda da tambaya tare da saka rana Ammin su Yaya,mom Jiddah,Um-asmy tare da wasu matan daga cikin dangi suka kai kayan godiya kamar yadda al'ada ta tanadar,kowa kuwa sai son barka yake  sabida ganin Ummi da sukayi sosai ta kwanta masu a zuciya!

Ammi ma kuwa kamar ta goya ta a baya,sabida Allah nah gani tin ranar da ta fara d'aura idanun ta akan yarinyar sosai take masifar birge ta sabida sanyin ta da kuma rashin son hayaniya irin na d'an ta.
Inda ko ta wani b'angare guda biyu aka fad'a harkar biki gadan gadan babu kama hannun yaro,Mamy gyaran Ummi ciki da bai kasancewar ta cikakkakiyar kanuriya a ranta tana mai jin ina ma ace d'anta ne zai aure Ummin amma tasan hakan bazai tab'a faruwa ba,har duniya ta nad'e! Musty dama shikam yajima da yi ma gidan Abbah k'aura zuwa Borno sabida naimo uban sa da kuma dangin sa sabida yasan ko ba a goran ta masa a yanzu ba,to kuwa tabbas a lokacin da yazo naiman aure sai ya fuskanci gagarumin k'ask'anci.

Inda Anty Khadee kuwa Uncle J ya aiko mata da kud'in da zasu sayi lefe da dai sauran abubuwa...!
Wato a b'angaren Abbah idan kuka ga yadda yake narka uban dukiya wajen saya ma y'ar sa set na d'aki da parlo bugun zamani sai kunsha mamaki,kaya ne na kece raini fiye da tunanin mai tunani, gasu kuma masu quality bawai local ba

A lokacin saida Ummi tayi kukan rashin dangi ba kad'an ba,domin kuwa har aka shiga cikin satin biki idan kazo gidan bazaka samu wani dangi ba sai k'awayen Mamy wanda suma basu da wani yawa tare da Anty Khadee da ita kuma kan wuni acan gidan su tin auren yayan ta za'ayi...!
Takan yi Allah wadai da mahaifiyar ta,sabida gani tayi inda ace maman ta batayi abinda tayi ba,babu abinda zai sa Abbah ya bar gidan sa na haihuwa batare da tunanin komai ba!

Jiddah tare dasu Asmy sune k'irjin biki,da kuma wasu dayawa daga cikin k'awayen su da sukayi mata kara,domin ko tin satin bikin da ya kama wuni suke mata tin safe sai dare suke wat'sewa a barta da aminiyarta!

Ana gobe d'aurin aure ango ya d'ira tare da tasa tawagar ta can suka had'e dana nan Nigeria aka tafi wani babban hole da sukayi dinner a ranar,sabida ana d'aura aure ango ya masu booking na flight zasu wuce.

A wajen dinner da Ummi ta d'aura idanun ta akan Yaya da kuma Husnah wacce cikin ta ya zama babba sosai haihuwa yau ko gobe saida taji wani irin mashi ya chaki zuciyar ta mai kama da kishi,sabida ganin yadda suke ta faman tarairayar junan su! Wanda UNCLE J da ganin amaryar tasa ya kusan zautar dashi saida ya rasa gane kanta sabida yadda tafara rusan kuka baji ba gani, daga wajen dinner wuri ya rikice da hayaniyar mai ya samu amarya take irin wannan kukan,amma babu wanda yasan tak'a maimai abinda ke damunta, Haka nan dai kowa ya wat'se ana ta k'ananun maganganu kan kodai auren dole za'ayi mata take irin wannan kuka!?

Sosai UMMI ta masifar bama Yaya haushi a lokaci,sabida yadda yaga tana reacting alamun bata son d'an uwan nasa ne ko kuwa shi bai gane mata ba,Husnah kuwa haka nan take jin wani irin fargaba da kuma tashin hankali da bata san ma'anar haka d'in ba, Su oga Waleed kuwa anyi b'arin naira d'ari-d'ari wajen dinner kamar babu gobe wanda da k'yar suka ciyo ta a aljihun Dad!!

Watoh dik wannan budirin da ake sam sam Ammah bata san wacece amaryar Uncle J ba koda kuwa a photo ne! abinne ya zamtoh kamar almara,idan zataga pics d'in ko wani abinda ya danganci amaryar sai kuma wani abu daban ya d'auke mata hankali!
Haka nan uncle J tare da tawagarsa suka maida amare da k'awayen ta gida kamin aka wat'se!

A wannan ranar ma kuka iya kuka UMMI tayi shi bana wasa ba,gaba d'aya ta d'aga masu Abbah tare dasu Mamy hankali anyi lallashin duniyar nan tak'i yin shuru,wanda hakan yasa suka zuba ma sarautar ALLAH ido har bacci yayi nasarar sace ta a wahalce wajajen k'arfe d'aya na dare,don haka sai Abbah ya buga gargad'in kar wanda ya tashe ta idan ba ita ta farka don rad'in kan ta ba.

RANA BATA K'ARYA ......!

Tin daga farkon layin su Abbah har zuwa babban harabar gidan dake cike da mutane bila'adadin an kafa wasu manya manyan rumfuna tare da shimfid'a manya manyan carpet cike yake da manya manyan k'asar nan harma da way'anda suka kasance ba nan k'asar suke ba sbd halartar d'aurin auren y'ar gidan Alh Abdul Waali guda d'aya tilo!! Kar kuso kuga bakin Abbah sabida yadda ya gagara rufuwa a wannan lokacin sai faman gaisawa suke da mutane inda da ango ma ya k'araso tare da tasa tawagar idan kuka ga yadda yayi wani masifar kyau abin kam sai son barka!!! Inda hannun sa ke sark'e dana Yaya da shima kayan sa exactly irin na Jafar sabida shi da kansa ya d'inka masu a mat'sayin gift nasa sai faman maik'o gezner da babban riga!!

Waje ya d'auki zafi sabida yadda aka fad'a harkar d'auri aure gadan gadan,Dad d'in Jiddah shi Abbah ya bama wakilci na y'ar tasa dikda kasancewar sa waa ne a wajen angon uwa d'aya uba d'aya...! Inda Babi ma ke daga gefe mat'sayin waliyyi na ango tare da sauran y'an d'auri aure,sai kuma Yaya dake lik'e da anko wanda yafi kusanci da Mahaifin nasa!!

Wani irin hargit'sat'sen k'ara ne ya rat'sa dodon kunnuwar ilahirin jama'ar dake wurin da yasa kowa ya fara zuba salati yana sanar da ubangiji sbd ganin motar data k'aryo ta cikin gidan gadan gadan,babu shiri kuwa mutane dik suka tarwat'se daga wurin sai kuwa ga motar ta bigi jikin gini da yasa glass d'in dake jikin motar tarwat'sewa lokaci guda...!

Wani irin gumin tashin hankali ne ya karyo ma UNCLE J cike da t'sant'sar tashin hankali ya zaro idanun sa waje s sauk'ar da idanun sa sukayi akan fuskar matar sa  dake kaca-kaca da jini sakamakon glasess na motar daya wat'so mata  a jikin ta lokacin data faka motar ta fito daga cikin motar cike da t'sananin galabai ta hannun ta rik'e da wani irin wuk'a mai shegen yalk'i da kallo d'aya mutum zai masa ya tabbatar da cewa ba k'aramin kaifi zayyi ba...!

Kowa dake wajen tambaya yake kan wannan kuma daga ina take amma an gaza mai basu ansa!! "My love pls ki ajiye wannan wuk'ar dake hannun ki na rok'e ki da Allah!!" Jafar ya fad'a yana mai durk'ushewa akan gwiwowin sa kamar ya fashe da kuka dayasa mutanen wurin suka gama fahimtar ko ita wacece...!

"J kaci amana ta!! Wannan itace sakayyar soyayyar da zaka nuna man dama? aure kake k'ok'arin k'arawa batare da ka sanar dani ba sabida kai d'in butulu ne??"

Rushni ke maganar tana mai sake rushewa da kuka ba kad'an ba!! Inda a lokacin mutane da dama daga cikin su kan bama Jafar rashin gaskiya,cikin t'sananin b'acin rai Dad yasa kowa ya samu waje ya zauna banda Jafar dake ta faman lallab'a Rushni amma ta ki yadda ta kafe kan lallai lallai sai an fasa auren nan,sabida su a al'adar su ta India namiji mijin mace guda d'aya ne.

Tin mutane na faman lallashin ta har ta fara basu haushi da yasa su Dad ci gaba da gudanar da daurin auren su! Wanda hakan yasa ta fasa wata gigitacciyar k'ara tare wani irin yanka hannun ta da nan take gurin ya hargit'se da salati suna sanar da ubangiji! Cikin t'sananin kukan masifa tace, "Wallahi ko kace ka fasa auren nan ko kuma na kashe kaina anan gurin J" girgiza mata kai jafar ya fara alamun bazai iya ba,ai kuwa ta wani dagewa ta sake yanko namar cinyar ta dikda irin t'sananin azabar dake rat'sa mata sassan jikin ta amma gani take hakan nafila ne akan ayi mata kishiya!!!

Abbah da dik yabi ya rikice tare da sauran mutanen wajen aka fara  fad'in a fasa wannan d'aurin auren kar azo ayi dana sani daga baya,ta d'aga hannu da niyyar sake dab'a kanta wuk'a a cikin ta cikin rikicewar kwakwalwar jafar yace "WALLAHI NA FASA WANNAN AUREN DON ALLAH KI DAKATA...!!"

Kallon sa tayi dikda t'sananin jirin dake kwasar ta tace, "A d'aura ma yarinyar aure da koma wanene a yanzu yanzu idan dai baso kuke na kashe kaina ba...!"

Babi da ransa ke masifar b'ace had'i da tausayin UMMI da ROSHNI d'in baki d'ayan su ya kalli Yaya yace, "Akwai kudi ne a jikin k?" Ba tare da damuwar komai ba yace, "I akwai." "zai kai nawa??" "60k." "mik'o man."

Ai kuwa babu musu ya bama Babi kud'in cike da mamakin abinda zayyi dasu! Sai dai kuma bai gama dawowa daga d'an gajeriyar tunanin daya afka ba yaji muryar mai shela na tabbatar da cewa " _AN D'AURA AUREN ~ZULAYM AHMAD SHUWA~ tare da MATAR SA ~ZULAYKHA ABDULWAALI~ BISA SADAKI NAIRA DUBU 60_ "

Wanda hakan yayi dai-dai da lokacin da ROSHNI ta sulale sumammiya daga inda take da yasa Jafar yin kanta da masifar gudu yana kuka sharshar da hawayen sa.

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[8/3, 7:56 PM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...!*

*©️OUM_MUMTAZ*

*Chapter 32*

Wani irin buga t'salle k'irjin Zulaym yayi kamar ya faso k'irjin ya fad'o k'asa,a mugun razane yayi ma Babi daya d'auke kai kamar bai ga yanayin da yaron nasa ya shiga ba da kallo!! Ganin yadda jikin Zulaym ya d'auki mugun rawa ne yasa Dad rik'o hannun sa yana girgiza masa kai alamun kar yayi wani abinda ba shine ba!!!!

Cike da t'sananin tension Abbah da bai so ayi hakan ba ya kallli Abbah daya bama Babi auren Zulaykha,sannan kuma ya kalli mawuyacin halin da Yaya ke ciki,ga kuma Babi da yak'i kallon shashin da Yaya d'in yake suna gaisawa da mutane tare da masu fatan Alkhairi akan wannan auren da akayi na bazat!!

A ransa kuwa ji yake wani irin girma tare da kima da kuma darajar ahalin Babi ya rufesa lokaci guda,sabida t'samo dashi daga tafkin k'unyar da Jafar yaso jefa sa da yayi,dikda yasan fin k'arfin shi Jafar d'in matar tasa tayi.

Sallama Dad yayi ma Abbah kan bari yaje anjima zai dawo idan komai yayi settling,inda yake rik'e da hannun Yaya dake cikin mawuyacin halin ba kad'an ba! Idan kuka ga yadda idanun sa suka kad'a sukayi jazur sai kusha mamaki...!!
Baban Asmy ne keyin driving,sannan kuma Dad tare da Yaya suna baya inda ya d'aura kansa bisa k'afad'ar Dad yana jin yawun bakin sa na k'ok'arin kafewa sabida ganin wannan aure da aka lak'aba masa mai kama da almara.

Gidan Yaya Babba dake cike da taf da mata y'an biki kama daga kan su Ammah,Ammih,Um-asmh ,Mom,Anty Khadee da dai sauran su suka shiga bayan sun sa Yaya dake ta faman tangad'i t'sakanin su,suna rirrik'e shi.

Kowa tambaya yake da guntuwar gulmar sa kan lafiya?? Amma ko kallo basu isha su ba,suka wuce parlon Yaya da suka same sa sanye cikin manyan kaya yasha binjimar sa yana jan charbi tare da wani abokin sa da shima sosai girma ya kama sa suna b'allan goro!

Sosai tausayin Yaya ya kama YAYA Babba ya soma lallashin sa had'i da basa baki tare da nuna masa mahimmancin karb'ar k'addara da kuma biyayya ga za6in iyaye !
Sannan kuma yake tofe sa addu'oi da yasa nan take yaji wani irin nat'suwar da ya rasa ta na wucin gani na ziyartar ko wane lungu da sak'o na sassan jikin sa.

Y'an cikin gida mata kuwa sunyi cirko-cirko kowa na son sanin abinda ya faru,sabida ganin su Dad da sukayi d'azun sun tabbatar da cewa ba lafiya ba! Ai kuwa suna nan suna k'ananun maganganun nasu saiga Waleed tare dasu Hamad,Nuraaz da sauran bataliyar su sun shigo gidan sabida dawowa da ake ta faman yi daga d'aurin aure! Waleed da bakin sa sam bashi da sakata ne ya tak'ark'are baki had'i da zubo ma matan gidan Abinda ya faru wajen d'aurin aure tiryan-tiryan batare da ragi ko na sisin kwabo ba...!

Wani irin salati da sallallami gidan ya rud'e dashi sabida jin wannan bayani mai kama da wasan kwai kwayon daya afku cikin gidan...!! Babi da wasu mutane suka shiga wajen YAYA babba had'i da masa bayani inda ya nuna hakan ba damuwar komai bane tinda jihadi sukayo Allah bazai barsu haka nan ba! Wanda kuma a lokacin sosai ransa yayi wani irin b'aci akan abinda surukar tasa tayi dikda dama yasan aikata hakan kad'anne daga cikin halayen india da basu san wai wata abu kishiya ba.

Aikuwa cikin k'ank'anin lokaci labari ya iske en cikin gida baki d'aya da saida gaban Ammah ya fad'i sbd tuno wani irin hali d'iyar ta zata shiga idan taji wannan labari kishiya da rana t'saka!!!! Addu'a take Allah yasa kar tazo gidan amma kuwa sai addu'arta bata karb'u ba,domin kuwa a lokacin da ake t'saka da gulmace-gulmacen abin saiga ta da sallamar ta,tana jan cikin ta da yayi wani irin girma ba kad'an ba da k'yar take ciccilla k'afafun ta.

Nan kuwa kowa keta faman binta da kallo ana zancen ta k'asa k'asa da yasa taji dik ta muzanta,don haka sai kawai ta tashi cikin jama'a zuwa d'akin Hajja da itama keta faman jimamin abinda ya faru cikin d'akin ta tare da tata tawagar.

Kwanciya tayi ta juya masu baya tana mai jin yadda zuciyar ta kwata-kwata bata da nat'suwa tinda ta tako kafar ta cikin gidan.
Inda take ta faman k'iran wayar Mijin ta amma ansa d'aya ake bata shine "no answer"   Haka nan ta wuni a kwance cikin rashin dad'in rai da kuma damuwar rashin samun mijin nata a waya da hankalin ta sosai ya karkata izuwa ga sanin halin da yake ciki.

Ammih ma da taji labari sosai taji gaban ta ya fad'i sabida sanin halin yaron nata da tayi ciki da bai,da kwata-kwata bashi da ra'ayin zama da mace sama da d'aya,tana kuma guje masa aikata rashin adalci da ranar lahira zai iya tashi da shanyayyen gefen jikin sa guda.

...……...……...……...

A b'angaren gidan Abbah kuwa...!

Bayan an gama cuku-cukun d'aurin aure kowa ya soma kama gaban sa,Abbah bai samu damar shiga cikin gida ba,saida ya tabbatar da ya gama sallaman bak'in baki d'aya,inda ya wuce part na Mami daya tadda cike yake da bataliyar ta na k'awaye...!!!!

"Aishatu ina su Mamana ne?" Abbah ya tambayi Mamy bayan sun keb'e a wani d'aki. "Ai kuwa suna can b'angaren Khadeeja tare da k'awayen ta." Ta basa ansa tana kallon yadda fuskar ke cikin damuwa da yasa ta gaza hak'uri ta tambaye sa abinda ya faru,ai kuwa tiryan-tiryan Abbah ya k'oro jawabi da yasa Mamy buga wani uban tagumi cike da t'sant'sar damuwa akan abinda kan iya zuwa ya dawo idan Ummi ta samu bayani!!

Ummi kuwa da bata jima da farkawa a bacci ba na can tare dasu Jiddah dake ta faman k'ok'arin ganin sun shirya ta amma sai iya shege take masu kan ita babu wanda zai tab'a mata fuskarta da wayannan abubuwan jagwalgwalen...!

"Bari na k'ira Uncle J wata k'ila idan shi yazo ya lallab'a ki zaki fi t'sayawa tinda nasan war haka an riga da an shafa fatiha." Wani dum gaban Ummi da tinda ta farka take cikin farin yayi sabida ambatar sunan Uncle J da Asmy tayi tana jin wani irin zafi har cikin ranta batare da sanin dalilin hakan ba.

Abbah ne tare da Mamy suka aiko aka zo masu da Ummi zuwa part nasa da babu cikowar jama'ah...!!! Nan suka zaunar da ita tare da mata nasihar karbar rayuwar ta a dik yadda tazo mata,sabida ubangiji da yasa hakan ya faru shi yafi ta sanin asalin dalilin hakan.

A lokacin da Ummi taji sunan wanda aka aura mata maimakon Uncle J kad'an ne ya hana bata mik'e ta taka rawa ba,sabida t'sananin farin cikin faruwar hakan da kuma jin dad'i...! A gefe guda kuma wani irin t'soro ne ya kamata,yanzu idan shi Zulaym Shuwa d'in ya tab'ure masu kan shi bai son ta yaya kuma makomar rayuwar ta zata zamtoh?! Wanda hakan yasa nan take taji dik murnar ta ya koma ciki,saima kukan da ta sakar ma su da sunan na rabuwa da Uncle J ne,nan kuwa su basu san na wani abin ta daban bane...!

...……...……...……...

B'angaren Uncle J kuwa tare da wasu abokan sa suka kai matar tasa dake sume tana ta faman zubda jini asibiti cike da t'sant'sar tashin hankali da nan da nan aka wuce da ita emergency aka shiga bata dik wasu taimakon da suka dace da condition d'in da take ciki!

Inda aka samu daidaiton numfashin ta,tare da sank'ama mata jini tare da drip sai kuma allurar bacci(😆yasin halin india ne wagga abu,wata ma tsaf sai ta kashe kanta akan saurayi sabida gidahumanci😆).

Wajajen k'arfe takwas na dare Yaya ya k'ira Jafar kan yazo ya same shi tare da matar sa da yasa don dole aka rubuta masu sallama a daren bayan dogon gargad'in gujema abinda zai famar mata da ciwon ta zuwa gidan nasu!

Anan ya tadda Yaya Babba,Babi,Dad,AMADU,Hajja,Ammih,Ammah,Mom,Um-asmy sai Yaya tare da Husnah dake wajen k'afafun Ammah tana ta kallon Yaya da sai yanzu ta sashi cikin idanun ta wanda kuma idan ba gizo idanun ta ke mata ba,gani take kamar dik yayi zuru dashi lokaci guda...!

*vote*
*comment*
*share*
[8/4, 9:54 AM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...!*

*©️OUM_MUMTAZ*

*33*

Cike da t'sananin bacin rai bayan kowa ya zauna an nat'su Yaya babba ya kalli side d'in da Rushni ke jingine cikin harshen hausa tinda dama ta koyi hausan ya ce,"Amma dai a gaskiya kin matik'ar bani kunya yau d'innan Rushni! Kishi hauka ne? Ko kuma akanki aka fara yin kishiya da zaki je ki zubda man da mutuncin gida na wajen taron jama'a...? gaskiya baki kyauta mana ba,sannan kuma baki kyauta ma kanki ba akan haka d'in da kikayi gashi dik kinbi kin jima kanki rauni,yanzu idan t'saut'sayi ya gifka kika halaka kanki mai zaki je kice ma ubangijin ki a mat'sayin ki na musulma?"

Share hawayen dake zubowa cikin idanun ta tayi,cikin muryar dake nuni da cewa tana jin jiki tace, "PAPA wallahi ba laifi ba bane,laifin J ne da bai fad'a man zai k'ara aure ba tintini sai kawai jiya da daddare wata cousine sister nah ta k'irani daga INDIA tana tambaya ta wai dama mijina zai k'ara aure shine ban fad'ama family na ba? Wanda hakan ya sani tambayar ta dalilin ta na fad'ar hakan,inda ta turo man wano short vedeo din da akayi sa wajen dinner da har ya zaga duniya. Hakan ne yasa naji raina ya b'aci sosai inda nayi booking na jirgi a daren jiyan sabida inzo naji dalilin sa b'oye man kan zai k'ara aure,cikin sa'a kuwa na samu wanda zai tashi k'arfe Uku na dare wanda ban d'auko komai nawa ba sai fad'a ma wani Uncle d'ina dake nan Nigeria yana aiki a airport d'in kan ya naima man mota gani nan zuwa,inda jirgin mu na s'auk'a na bincike adress na gidan su yarinyar da zai aura tinda naji a yau ne za'a d'aura auren ba'a riga an d'aura ba,tare da taimakon Map dana saita akan motar nazo gidan har mai afkuwa na afku. Amma ina naiman afuwar ku akan abinda na aikata nayi nadama insha Allahu makamancin hakan bazata sake faruwa ba."
Ta k'arashe maganar tana mai fashewa da kuka sosai sabida azabar dake ziyartar kwanyarta akan lahanin da tayi ma kanta...!

Ai kuwa take kowa dake wurin ya fara k'ananun maganganu yana baima Jafar daya sunkuyar da kansa laifin mafarin faruwar komai ba...!

"Ai kuwa Allah shi k'ara gwanda ma da kika mashi hakan wallahi,ai wallahi koni akayi wa hakan sai inda k'arfi na ya k'are,don kawai sabida zalinci zai wani maki kishiya batare da sanin ki ba? Ai kuwa in dai nice akayi wa hakan abinda aka maki abinda zanyi sai ya zarta naki...!" Ai kuwa gwab'e ma Husnah baki Ammah tayi cike da t'sananin kunya da kuma tashin hankali sabida jin zantukan da yarinyar tata keyi cikin fusata sabida maganar da take directly daga cikin zuciyarta ke fitowa sabida mantawa da tayi a inda take kasancewarta mace mai zafin kishi.

Kowa dake wajen sosai ke kallon Husnah data tak'ark'are tana zuwa zance hatta ga Yaya da zuciyarsa ke bugawa  kan kalamana da tace inda itace sai tayi abinda ya zarta wanda Rushni tayi!! Ganin irin kallon da kowa ke mata ga kuma bangajar da Ammah ta kawo ma bakin ta tagane irin katob'arar da tayi,wanda hakan yasa taji wani mat'sanancin kunya ya rufeta sosai ba kad'an ba...!

"Tashi kizo kusa dani Mamana." Yaya babba ya fad'a yana mai yafito iya Husnar da hannun sa,ai kuwa babu musu ta mik'e da k'yar zuwa inda yake sabida nauyin da cikin nata keyi ta samu waje ta zauna,tana kuma lura da irin kallon da mutanen wajen ke binta dashi data rasa gane na mainene...!

Cikin sigar dabara Yaya babba ya kama hannun ta ya ce, "yanzu kina nufin yau idan takwara ya k'ara aure batare da sanin ki ba kema abinda zaki aikata sai ya zarce wanda y'ar uwarki Roshni tayi uwata?" Cike da jin kunyar mutanen dake wajen ta rufe fuskarta da tafin hannun ta tinda dama Yaya babba sun maida shi ne kaman kakan su tace, "Nasan ma Yaya bazai tab'a man haka ba."  "So idan kuma yau akace Mahaifin ku Babi ya aura masa wata yarinyar batare da sanin ki da kuma takwara na ba laifin wa zaki gani anan? Kuma shin zaki iya illata kanki!" A wannan lokacin sosai taji gaban ta ya fad'i,wanda hakan yasa ta samu nat'suwa k'irjin ta na bugawa tace, "Nasan Babi yana k'aunata tabbas bazai tab'a had'ani da abinda zai iya cutar dani ba sabida shid'in garkuwa ne gare ni tare da mahaifiyata da kuma k'anina...!"

Murmushi sosai dik y'an cikin parlon sukayi sabida jin dad'in kalamanta inda Yaya yaci gaba da fad'in, "To ina so kiyiwa maganar da zan fad'a maki kyakkyawar fahimta,ki gane cewa komai na duniya dake faruwa Rubutaccen Al'amari ne da ubangiji ya riga daya gaba t'sara kayan sa tin kamin asan za'a halicci wani halitta...! Don haka ina so ki kwantar da hankali,ki kuma fahimci dik bayanin da zan maki ki dube sa da kyakkyawar fahimta ba wai don bama sonki bane hakan ya faru saidon dama hakan Tin ran gini tin ran zane ne...!"
Haka nan taji k'irjin ta na mat'sanancin bugawa sabida k'wak'walwarta data fara hasaso mata abinda ake shirin fad'a mata da d'azun taji ana ta gulmar amma bada bama zancen nasu mahimmanci ba...!

Tiryan-tiryan Yaya babba yayi mata bayani ta yadda zata fahimta batare da t'sikewar zuciya ba har k'arshe! Kowa dake wurin zuba ido yayi sabida aga irin reaction d'in da zatayi inda ita kuma tayi k'asa da kanta dikda yadda takejin numfashin ta na k'ok'arin fin k'arfin ta ta bud'i baki da niyyar yin magana amma saita gagara,wanda hakan yasa Yaya ya rufe taron bayan doguwar nasihar da yayi masu tare da umartar Hajjo ta kula da yanayin ita Husna d'in sabida gudun faruwar mat'sala.

A tak'aice ranar Husnah kwana tayi cikin mawuyacin hali da bata bar kowa ya fuskanci halin da take ciki ba sai mahaifiyarta wato Ammah da tayi ma y'ar tata farin sani ciki da bai...! Inda itama saida suka kebe a daren ta sake kwantar mata da hankali sosai,inda Ammih ma ta d'aura da nata kowa dai nata fadin albarkacin bakin sa amma ita bata cema kowa k'ala ba,saida ta bisu da ido...!

Yaya kuwa tin rabuwar su a parlon YAYA bata sake sashi cikin idanun ta ba har zuwa lokacin,dikda yanayi na rashin dadi da Jafar ke ciki,hakan bai sa shi taya d'an uwan nasa murna tare da fatan alkhairi ba,ya karbi kaddarar sa a yadda tazo masa tinda Allah bai nufa cewa Zulaylka matar sa bace!

Tin a daren ranar yayi masu Booking na jirgi washe gari da sassafe suka d'aga daga Nigeria tamu ta gado,zuwa k'asar Australia...!

Acan b'angaren gidan Abbah kuwa labarin daurin auren daya fasu da asalin ango zuwa kan dan uwan sa ya riga daya gama karade dik wani lungu da sako,masu gulma nayi masu jaje nayi kowa dai na tofa albarkaci bakin sa...!
Suna da niyyar maida kaya Dad ya shaida masu ba sai sun dawo dashi ba,shi Jafar d'in ya barma d'an uwan sa komai da komai mat'sayin gudummawa,wanda hakan yasa Zuly jin tausayin J d'in dikda bata son sa...! Da shike dama bawai dangi bane sai dik aka wat'se a ranar gida ya zamana shiru kamar ba gidan biki ba,sai Asmy da Jidda tare da wata k'awar su ne kawai ke nan gidan tare da Ummin,Mamy kuwa sosai ta kasa ta t'sare ta hana Ummi fita daga d'akin ta,su Jidda ma don dole suke nan !

Asmy a daren itama ta tafi gida tare da Umaima k'awar tasu kenan aka bar Jiddah dake mat'sayin babbar k'awa ita kad'ai...! Anty Khadee kuwa ita da Jiddah sosai suke nan nan da Ummi kamar t'soka daya a miya!

Acan gidan YAYA kuwa washe garin ranar Husnah ta tashi da mat'sanancin nakuda tin cikin dare amma abu yaki ci yaki cinye wa sabida edd nata bai cika ba,kawai tashin hankali ne da yayi mata yawa ya tasar mata da nakudar babu shiri,idan kuka ga yadda Yaya ya birkice masu kan shi sai ya saki Zulaykha a ranar sai kusha mamaki,fadi yake ai dik ta sanadiyyar auren ta da aka lika masa batare da anji ra bakin sa bane ke neman illata lafiyar matar sa!! A ranar saida YAYA ya nuna masa bacin ransa sosai kamin ya sarara masu aka kwashi Husnah dake matik'ar galabaice zuwa asibiti...! Inda tasha Allurai da dik abubuwan da suka dace ayima nai nak'uda amma shuru kake ji kamar an shuka dusa...! An wuni ana abu d'aya hankulansu dik a matik'ar tashe yake gidan baki daya,sai aka kawo ma Yaya takadda yasa hannu za'a shiga mata C S sbd zata iya gamuwa da yoyon fitsari idan basu dau mataki ba! Haka nan yana kuka da komai yayi signing cikin k'ank'anin lokaci  aka kammala komai aka shiga da ita therter room...!

T'sawon awa daya da rabi wata nurse ta fito daga ciki hannun ta nannade da baby girl dake ta faman callara kuka kamar ana yankan nama jikin ta...! Gaba daya mutanen dake wurin suka fara hamdala ana rige rigen karbar yarinyar fuskokin su na washewa cikin tsananin farin,inda Ammah kuwa sai faman leka bayan nurse d'in take ko zataga fitowar diyar tata amma wayam...!

"Ya jikin matata kuma?" Yaya dake k'ank'ame da yarinyar kamar za'a kwace masa ita ya tambaya...! sunkuyar da kai NURSE d'in tayi cikin muryar rauni tace "am sorry to say......maman baby ta ansa k'iran ubangiji😭😭😭😭😭"

*vote*
*comment*
*share*
[8/4, 10:42 AM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...!*

*©️OUM_MUMTAZ*

      
*34*

A wani irin mugun tashin hankali daya zarta tunanin mai tunani Yaya da dama kwata kwata bai cikin hayyacin sa ya saki yarinyar dake hannun sa tana callara kuka ya kaima wannan nurse d'in wani irin mugun naushi inda Allah ya taimaka da mugun azama Dad ya fisgeta tayi k'asa wanda hakan yasa shi kaima jikin ginin da suke t'saye naushi da nan take hannun sa ya fara bleeding,cikin wani irin hanzari Anty Khadee da itama tana wajen ta taro jaririyar datake ta faman tsala ihu baji babu gani sabida gigitar da kwakwalwarta yayi!

Wani irin azababben mari Ammih ta wat'sa ma Yaya da bai gama dawowa cikin nat'suwat shi ba cikin t'sananin t'sawa da takaicin sa ta fara zuwa masa masifa babu ji babu gani akan gangancin da yake so yayi da rayuwar k'aramar yarinyar da yau yau aka kawo ta duniyar! Wanda shi kuwa Yaya baima san tana yi ba sabida suman tsayen da yayi tin lokacin data mare sa,inda kwakwalwarsa keta faman son yin aiki daya kamata amma ya gaza yin hakan!

Kafafun sa da suka masifar yi masa tsami ya fata jansu kamar wanda aka watsama ruwan kankara zuwa dakin da yake da kyautata zatohn zai samu ASMA'Un sa! Ai kuwa sosai zuciyarsa ta buga wani irin tsalle sabida ganin mutanen da suka zo asibiti tare dasu nata faman share kwalla sun saka wata dake kwance kan katifar fuskarta lullube cikin wani shudin bedshet ko fuskar ba'a gani!

A lokacin tunani ya farayi,wanda idan zuciyar sa na aiki dai dai,ya kuma daura maganar da wannan likitar ta masu dazu kenan wannan gawar ta Ma'un sa ce...!?

Wani irin kuzari ne ya saukar masa lokaci guda da yasa shi isa zuwa gadon dasu Mom suka saka gaba suna famar hawaye,hannayen sa na masifar rawa ya yaye wannan lullubin da akayi,wani irin murmushi ne ya subuce masa sabida ganin fuskar Husnah dake fidda wani irin annuri fuskarta da murmushi kamar a kira sunan ta,ta ansa.

Bata fuska yayi sosai sannan ya kalli mutanen dake masa kallon tausayi ya ce, "So wai dik wannan kuka na mainene? Ni dama nasan waccan shegiyar likitan k'arya take da zatace man Ma'u na na rasu,bayan kuma munyi ma junan mu alkawarin kasancewa tare da junan mu har abada."

Kowa dake wajen zuba masa ido yayi ganin da sukayi alamun ya zauce ne idan ba haka ba yana kallon gawa kwance a gaban sa yana karyatawa...?

Shigowar su Dad da wasu likitocin ne ya hargitsa ma Yaya kwakwalwa yana masu borin kar katon daya kuskura ya taba masa matar sa amma basu bi ta kansa ba sabida already an riga da an gama dik wasu cike cike a halin yanzu ma ambulance aka kawo zasu tafi da ita gida!

Ai kuwa sai gani sukayi Yaya ya zube warwas a k'asa babu alamun numfashi tattare dashi a lokacin da yakuma tabbatar da cewa Ma'un sa is no more. Baban Asmy kawai aka bari asibitin kan da zarar ya farka sai suma su biyo su gidan Yaya Babba sabida can zasu wuce a halin yanzu, ai kuwa tin kamin su k'arasa labarin ya iske gidan da nan take kuwa ya barke da wani irin koke koke babu kakkautawa,Ammah da itama tana gidan kuwa ta gagara gaskata abinda ake fadi na rasuwar diyar tata sai a lokacin da aka shigo da ita da yasa su Waleed tare da sauran yaran dake gidan fara kuka cikin tsananin tashin hankali sbd ganin gawar Anty Husnah!

Cikin kankanin lokaci kuwa saiga gidan YAYA BABBA ya cika makil da mutane dikda kasancewar goshin magriba ce a lokacin! Wani irin kuka Ammah keyi mai matik'ar taba zuciya a lokacin da tasa gawar diyar tata a gaban ta da sai uwa ce kawai kan iya fahimtar wannan yanayi da Ammah ke ciki idan akace diyar ki ko danki sun ansa kiran ubangiji...!

Ammih kuwa ba kankame da jaririyar itama tana sharar kwalla na rashin Husnan da kuma maraicin da wannan jaririya zata fuskanta,ga kuma halin da suka baro yaran ta na kila wa kala a asibiti.

Sai da Yaya babba dasu Babi suka shigo har cikin gida suka tsawatar masu kamin suka bar wannan kururuwar suka kama karatun qur'ani mai girma!

Hajja da wata tsohuwa data kasance yar uwar su da kuma Ammah da itama tayi tawakkali ta mika lamuran ta ga Allah ne ta samu dangana suka hadu sukayi ma Husnah wanka a wannan daren inda aka kintsa ta,aka barta zatayi kwanan keso!

Jinjirar kuwa tana karkashin kulawar Ammi dama,don haka dabibo ta fara bata tare da ruwan zam zam!
Sai wajen karfe daya na dare Abbah ya samu kira daga Dad ya shaida masa abinda ya faru,ai kuwa washe gari da sassafe ya kada kan Mamy da Ummi suka wuce gidan rasuwar da suka tarda shi makil da jama'a!

YAYA kuwa da shike an masa allurar bacci har sai washe gari ya farka,ai kuwa sosai ya birkice masu kan sai sun kaisa inda matar sa yake,inda kuma Baban asmy bai bata lokaci ba ya karba masu sallama tinda dama Babi ya kirasu kan su dawo sbd lokacin jana'iza ta kusa!

Wanda dik wani wanda ke dangantaka da Husnah aka shiga daki parlon Yaya Babba da gawar Husnah din ke ciki sukayi tayi mata addu'oi hadi da naima mata gafarar ubangiji!

Wanda kuma sai a lokacin Yaya ya kuma tabbatar da cewa Ma'un sa ta tafi tabar sa da kewarta,a lokacin ji yake inama shima mutuwar tazo ta dauke sa a binne su makotan juna da Husnar sa...?

A lokacin da suka fito daga parlon Yaya din yayi dai-dai da lokacin da su Mamy suka shigo gidan,ai kuwa karaf idanun Yaya d Ummi ya sarke cikin na junan su da yasa jikin sa fara daukar wani irin mugun rawa zuciyar sa cike take taf da tsanar ta da yake jin cewa cikin ransa a ta dalilin auren ta ne Husnah ta tafi ta barsa.

Kamar wani mayunwacin zaki haka yake yin kanta da yasa mutanen dake wajen fara sallallami sbd fahimtar abinda Yaya din keda niyyar aikatawa.
Wani irin azababben shaka yakaima wuyan Ummin cikin fitar hayyaci yana furta, "Kema sai na kashe ki naga bayan ki tinda a ta dalilin ki na rasa matata kema bazan barki da rai ba yau dinnan saidai a hada ku a tafi tare yaso nima sai a kashe ni!"

Dik yanda aka so kwatan Ummi a hannun sa an gagara a wannan lokacin,wanda kuma Ammah tin a lokacin data sauke idanun ta akan fuskar Ummi din taji wani irin masifafen fadin gaba ya kamata,haka nan taji wani irin bushewa da kuma taurin zuciya ya risketa da yasa ta daukar wani itace dake daga can kasa batare da ansan isowar ta wajen ba kawai sai wani irin hargitsatstsen karar Yaya da sukaji kansa na zubda jini sanadiyyar rantaba masa wannan itacen da Ammah tayi bisa ga tsakiyar kansa tana kuka sosai ba kadan ba tayi kan Ummi dake ta faman shure-shure cike da tsananin azaba, wanda hakan yayi  dai-dai da lokacin da manyan dake waje suka shigo sabida labarin abinda yake faruwa yakai masu ciki kuwa harda Abbah da jikin sa ke masifar rawa sabida jin da yayi cewa ana kokarin kashe masa yarsa.

Ai kuwa take gidan rasuwan ya barke da wani irin hayaniya mai wuyar fassarawa!! "Kashe man d'an nawa kike son kiyi ne Halimatu...?" Ammih ta fada cikin tsananin karaji da yasa Ammah dagowa itama a mugun fusace tace, "Baki ga yaron naki shima kokarin aika kisan kai yake bane kausa......!" maganar da take kokarin karasar wa ne ya tsaya cak,sakamakon saukar da idanuwan ta yayi cikin na mutumin da shekaru 25 zuwa da shida bai isa yasa ta mance da kamancece niyar sa ba,koman tsanani koman wahala,mutum da har kullum ta duniya a sallolin ta guda biyar idan tayi sallah bata gajiyawa da kai kukan ta gare shi kan Allah ya sada su kamin ta Allah ta kasance a gare ta kodon ta naimi yafiyar sa dana diyar sata sallaka ta baro sbd zalintar rayuwar su da tayi!

"YAYANA...!" Ammah ta fada cikin wani irin slow murya dake nuni da tsananin alhinin da take ciki!

A tin kallon farko ya shaida ta! Amma kuma hakan bai sashi jin cewa zai iya saurarar dik wani soki burut'sun dake fitowa ta bakin ta ba! Wanda shikam a wajen sa ganin ta da yayi din ba koman komai bane!

Da shike yaga yanayin gidan sai bai bama ambatar sunan sa da Alina keta faman yi ba! Ratsa wa yayi ta cikin mutanen zuwa inda yar sa ke yashe a kasa ga kuma Mamy dake kokarin ganin ta mika da ita cike da tausayin ta amma ta gagara!

Bai kalli kowa dake wurin ba ya sanya hannayen sa bayan ya mat'sar da Mamy ya sungumi abar sa ya sabata a kafata,sannan ya kamo hannun Mamy dake ta faman share kwalla suka fice daga gidan batare sa sun cema kowa kala ba!!

Wani irin mari YAYA BABBA da tsuma sosai ya kama sa yake kifama Yaya abinda tinda yake a rayuwar sa bai taba aikatawa ba! Domin kuwa tsawon cikin rayuwar sa Yaya bai taba mata masa rai ba irin na yau dinnan!!
Nan kuwa gida ya dauka da kananun maganganu,ga Alina dik tabi ta rikice tana kuka akan sai tabi su Abbah amma su hajja dasu Mom sun rirrike ta.

Haka nan aka fice da gawar Husnah bayan an sallace ta a kofar gida aka wuce da ita zuwa gidan ta na gaskiya,a cikin makabartar da kyar aka samu damar fito da Zulaym sabida yadda ya kifu akan yana ta faman kwararo mata addu'a na neman dacewa har gaban abada tinda ya fara dawowa cikin natsuwar sa sakamakon marikan da tasha.

Inda ana dawowa gida kuma aka shiga zaman karban gaisuwa,an jera tsawon sati ana zaman makoki saida akayi zaman bakwai kamin kowa ya kama gaban sa sai ya zamana sauran yan gida kawai! Sannan an rada ma yarinya sunan mahaifiyarta Asma'u ana kiran da Husnah!

Zuwa lokacin idan kukaga yadda Yaya da Ammah suka koma sai kun tausaya masu! Sosai suka zabge sabida damuwar data masu yawa! Inda washe gari kuwa Yaya babba ya aika a kira masa Abbah da kuma su Ummin!

......

Cike taf parlon Yaya babba yake da yaran sa,jikokin sa,kannen sa suma da nasu iyalin ga kuma Abbah shima da nasa iyalan!!
inda Yaya babba y fara magana......

*vote*
*comment*
*share*
[8/4, 10:52 AM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...!*

*©️OUM_MUMTAZ*

      
*35*

"A madadin kowa da kowa dake cikin wannan wuri dama wayanda basu halarta ba ina mai baka hakuri akan abinda wannan shashashan yaron ya aikata satin daya wuce ABDU..." YAYA babba ya fadi maganar yana kallon Abbah da kansa ke kasa,sakamakon kunyar surukan taka daya shiga tsakanin su.

Cikin murmushin da bai kai har ciki ba Abbah ya ce,"Babu komai wallahi Baba,na kuma dauki abinda ya aikata ne sakamakon bai cikin hayyacin sa a lokacin sabida mutuwar mata a daidai lokacin da ba'a taba tsammani ba nasan dole sai ya taba sa sosai." Abbah ya fada cikin sanyin murya.

"To Alhamdulillah sai kuma abu na gaba don Allah ina neman Alfarma idan babu damuwa jibi nake son Ita matar tawa ta tare a gidan ta wanda nake da tabbacin hakan shine zai saka masu kusanci a tsakanin su da har zasu fahimci junan su cikin kankanin lokaci batare da anja da nisa ba..."

"Ban ki ta taka ba Baba,amma tinda gashi shi wanda ake maganar tarewa a gidan nasa a tambaye sa idan ya amince banda matsala ko yanzu ne ma..." Abbah dake cike da haushin Yaya ya fadi maganar yana mai sakar ma Zulaym din idanuwansa da yasa shi yin kasa da kansa babu shiri kamar wani munafuki sabida kunyar dattijon daya kama sa sosai ba kadan ba. Inda cikin zuciyar sa kuwa fadi yake ko don yafi cin Uban Ummi da lasisi ai dole zai amince ta tare a gidan nasa idan an tambaye sa sabida ya huce takaicin sa.

Tunanin sa ne ya katse a lokacin da muryar YAYA ya ratsa masa dodon kunnen sa da yake fadin, "To kai kaji dai abinda mahaifin matar taka ya fadi ai ko? Shin ka amince ne ta tare a gidan ka ko kuwa?" Cikin kasa da murya sosai Zulaym dake shafa sumar kansa da kwata-kwata babu kyan gadi sakamakon rashin gyaran da yake fama dashi satinnan yace, "na amince ta tare Yaya" Nan kuwa akayi hamdala sannan BABI yasa Zulaym ya durkusa har kasa gaban kowa da kowa ya baima Abbah da Ummi hakuri akan rashin hankalin da yayi. Hmm dik wannan budirin da akeyi tinda suka shigo parlon kan Ummi ke kife akan cinyar mahaifin ta batare data daga idanuwan ta ba,ballantana taga iya adadin mutanen dake cikin parlon ta nausa duniyar tunani,ga wani irin tafasar zuciya dake riskar ta a dik lokacin da ta tuno cewa wai Husnah ce ta rasu. A yan kwanakin nan har kwanan ta uku a asibiti sakamakon shakar da tasha a hannun Zulaym,wanda hakan yasa ta cin alwashin tabbas saita nuna masa yayi da yar halak. Kamar wacce aka tilasta aka ta daga da fuskar ta da babu ko digon kwalli karaf kuwa idanun ta ya fada cikin na Ammah da tinda aka shigo wajen take son ganin fuskar Ummin amma bata samu dama ba,sabida kanta dake kasa.

Wani irin mugun rawa jikin Ummi ya fara sabida kallon fuskar wannan matar,ga wani irin mikewa da take jin tsikar jikin ta nayi sabida yadda ta kafe ta da idanuwa ko kiftawa batayi. Mikewa Abbah yayi da baison Alina ta nuna tasan shi ma cikin wannan jama'ar sannan ya mikar da Ummi da sam taki yadda ta kalli side din da Ammah din take dikda yadda zuciyarta ke azalzalarta da aikata hakan kamar magnet. Gyara mata hijap nata Abbah yayi cike da tsantsar soyayyar yar tasa ya kalli mutanen dake cikin parlon yace, "To jama'atul musulmin mu zamu wuce gida! Allah ya jikan Asma'au, idan tamu tazo kuma Allah yasa mu cika da imani..." da shike dama dik sun riga da sun gama tattaunawar su sai suma suka masu fatar a sauka lafiya.

Ai kuwa wani irin rikitaccen kara Ammah da saki da mugun gudu zuwa wajen su Abbah da suka kusa ficewa daga babban parlon ta wani irin fisgo Ummi da hannun su ke sarke da Abbah hadi da manna ta a kirjin ta tsam-tsam kamar wacce zata maida ta cikin ciki,tana wani irin kuka mai matikar taba zuciyar mai sauraro hadi da sakin tagwayikan ajiyar zuciya cikin kukan nata sabida yadda taji wani irin feeling mai masifar karfi dangane da yarinyar ko tantama bazatayi ba,ballantana kaffara akan cewa wannan diyarta ce,kodaga yanayin mugun kamar da take da kanwar mahaifiyarta marigayiya Iyami.

Ummi kuwa da bata san a wace duniyar take ciki ba sai tayi lamo a jikin Ammah hadi da lumshe idanun ta,tana saurarar yadda kirjin ta keta faman sama da kasa. Wani irin natsuwa ne ke shiganta from no where da zata iya rantsewa da Allah tinda take bata taba jin makamancin sa ba a dik lokacin data rungumi wani mahaluki idan aka dauke mahaifinta Abbahn ta.

Mutanen dake cikin parlon kuwa daskare wa sukayi suna kallon ikon Allah aka rasa wanda zai fara bude bakin sa ballantana yace uffan sbd ganin wannan abu haka kamar a cikin shirin film.

Wani irin fisga Abbah yayi ma Ummi a mugun zuciye daya sa ta dawowa cikin hayyacin ta a mugun tsorace ta kankame mahaifin nata sabida jin yadda yake wani irin karkarwa jikin sa na tsuma!

"Wallahi saina rike ta a jiki na idan har kai bazaka iya bude baki kace kasanni ba YA WAALI...!" Alina/Ammah ta fada cikin tsananin kuka da tashin hankali tana sake wawurar Ummi amma Abbah yaki bata damar hakan sabida yadda ya maida Ummi ta bayan sa hadi da harde hannayen sa akan kirjin sa ya zuba ma Ammah idanuwa fuskar sa cike da wani irin kwantaccen bacin rai da tinda yake bai taba sanin yana dashi ba!!

Mutanen dake cikin parlon kuwa daga kan YAYA BABBA,DAD,BABA da BABI da kuma AMMIH daskarewa sukayi a wajen sabida jin sunan daya fito daga bakin Ammah da kuma ba kowa bane sai Alh Abdulwaali da sukayi shekara da shekaru dashi cikin rashin sanin cewa shine mutumin da suke naima matsayin wa a wajen Alina.Inda sauran yaran dake wajen kuwa da shike basu san takamaimai abinda ke faruwa ba sai dik suka baza ido da kunnuwa suka ikon Allah.

"karki kuskura ki taba man yata da wannan kazamin hannun naki!!!" Abbah ya kwasa mata tsawa da yasa ta sakin kuka itama cikin tsananin hargowa da kuma kuka tace "wallahi saina taba ta tinda nima 'YATA CE...!!!"

Wani irin murmushin takaici Abbah ya saki kamin ya kalli tsakiyar cikin idanun ta fuskar sa babu alamun rahma sannan yace, "Da a lokacin zaki gane ke karamar tsagera ce HALIMA...!!" (da shike halima shine sunan ta na yanka)

Da shike zuciyarta a a daskare take sai kawai ta mika hannun ta hadi da wani irin janyo Ummi dake tsananin kuka sabida yanayin da taga mahaifin ta a ciki da bata taba gani ba!

Wani irin salati mutanen dake cikin parlon suka saki cike da tashin hankali sabida wasu irin tagwayen mari da Abbah ya sauke ma Ammah har guda uku reras da sai gata ta zube a kasa numfashinta ya tsaya cak!! Yin kanta gadan gadan yayi a mugun zuciye da niyyar ya tattaka ta amma hakan bayyu ba sakamakon rike shi dasu DAD tare da Baban Asmy sukayi inda Babi kuma yayi kan matar sa tare da Zulaym suka dagota,hadi da zaunar da ita kan kujera cikin gaggawa Ammih ta ajiye little Husnah kan cinyar Yaya babba da gudu gudu ta kawo ruwa mai sanyi aka shafa ma Ammah a fuskar ta,wanda hakan ya sata sakin wani irin ajiyar zuciya hadi da fashewa da wani irin kuka mai fallasa raunin dake cikin zuciyarta tana kallon Abbah dake ta faman bubbuga bayan diyar sa dake tsananin kuka fuskar sa dinnan sam babu alamun wani abu wai shi murmushi ballantana akaiga dariya.

"Kai kai kai...! Amma a gaskiya banji dadin wannan abu da kayi ba Audu,yanzu kai in banda sakarci da girman ka da komai amma ka bige da saka hannu jikin diya mace da sunan duka? kaina nake tunanin mai hankali ne da idan kaga wani na aikata hakan zaka hane shi da aikatawa" YAYA babba ne ke wannan maganar muryar sa cike da damuwa da kuma tausayin su dikkan su biyu....

Abbah dake kokari wajen ganin yayi cooling zuciyarsa yayi kasa da kansa batare da yayi magana ba,sabida yasan muddin ya budi bakin sa a dai-dai wannan lokacin furucin sa bazai ma kowa dadi ba,sabida yadda yake cikin fushi mai tsanani.
"Mainene dangantakar ki da Audu ne Halimatu...?"

Ai kuwa batare da jinkirin bata lokaci ba ta sake bada labarin su ita da waali tiryan-tiryan kamar yadda ta fadi masu a baya babu ragi babu dadi tana kuka sosai.
Su Zulaym kuwa da dik basu san wannan labari ba suka cika da al ajabi da kuma sake gaskata cewa lallai duniya ba a bakin komai take ba.
Kamar yadda ta basu labari haka nan WAALI ma ya daura da nasa da kuma labarin rayuwar da sukayu da yarsa.

Wanda aka hadu aka rufta ma Waali sosai da nasiha da wa'azizzika dangane da mahimmancin hakuri da kuma nuna masa cewa ko don rabon haihuwar Waleed da marigayiya daya gitta tsakanin su ai yasan rabuwar su dama rubutaccen al'amari ne daga Allah.
Gashi harda guzirin Jika ma kodon haka ma ai ya isa mutum mai hankali darasi! wanda hakan yasa zuciyar Abbah yin sanyi sosai ba kadan ba.
Inda aka shirya komai da komai amma dik yadda Ammah taso Ummi ta sake da ita sosai abin yaci tura sai faman nokewa take a wajen mahaifin ta cike da tausayin sa,inda a wani gefe guda kuma takan rayawa a zuciyarta cewa ashe jini daya ba wasa bane,ko don soyayyar Husnah dake dankare cikin zuciyarta tin a ranar data soma ganin ta a picx tare da  Zulaym da shima a ranar yayi nasarar sace zuciyarta! Ga kuma Waleed uwa uba irin shakuwar data shiga tsakanin nan da nan ashe dai sun rayu ne cikin mahaifa guda...?

An sake yima juna ta'azziya sosai akayi koke-koke,dik yadda Ammah tasa UMMI ta kwana a wurin ta amma taki,ta makale ma Abbahn ta badon taso ba sai don dole ta hakura.
Kowa dai zuciyar sa a yanxu wasai take saina damuwar mutuwar Husnah da ta soma bin jinin jikin su.

Bayan kwana biyu...

Cikin wannan kwana biyun an cire dik wani abinda yake mallakin Husna an masa kudi aka rabama magadan ta...! Sannan kuma an jere kayan Ummi  a gidan da har ila yau takaicin Ummi ne ke zuciyar zulaym idan ya tuno kalaman da yaji Dad ya fadi ranar da akayi wannan zaman.

"Yanzu fa dik wannan abin ya faru tsari ne na ubangiji,kaga dik mu mun daura ma kanmu alhakin rasuwar baiwar Allah n nan,ashe dai zama ne mai tsayi da zai wanzu tsakanin Zulaym da Ummin ubangiji yayi hikimar dauke ta tinda akoi haramci na zaman kishi tsakanin wayanda suka hada uwa daya uba daya,ko kuma uwa daya ko uba daya."

Bayan amarya ta tare...✍🏽

*vote*
*comment*
*share*
[8/4, 11:48 AM] Mrs Sulaiman 💓: *RIJIYA TA BA DA RUWA...!*

*©️OUM_MUMTAZ*

      
*36*

Kowa ya watse an bar Ummi zaune bisa tsakiyar gadon ta tayi shiru alamun zurfafa cikin tunanin ta,kuma ba komai take tunawa ba sai yadda take masifar kaunar wannan bawan Allah Zulayma,amma ta lura shikam idan ma akwai wacce ya tsana a rayuwar sa bai wuce ita bace sbd gani yake da rabon zaman ta tare dashi ne ya rasa Husnah! A dan daburce ta dago idanuwan ta kuwa ras ya sauka akan Zulaym daya banko kofar dakin nata ya shigo jikin sa sanye da boxes daya fallasa gargasar jikin sa da kuma surar sa mai girgiza zukatan magauta. Babu shiri Ummi tayi kasa da kanta jikin ta na daukar rawa kamar wanda taga dodon ta sabida yadda murdadden jikin nasw ya girgizata kamar wani dan wrestling.
Zama yayi kan kujerar dake gaban mirrow ya daura kafa daya kan daya hannun sa rike da wani glass cup da akoi ruwa a ciki,inda ya ajiye akan mirro sannan ya balli kwayan wasu magunguna guda biyu dake hannun sa ko wanne dai daya,yana aika ma Ummi da wani irin kallo daya sa hanjin cikin ta kadawa kamar zata arce.

Saida yasha maganin kamin ya mike daga zaunen da yake ya fice daga dakin zuwa nasa a zuciyar sa kuwa Allah ne kadai yasan maganin mai yasha!  Wanda takura masa da Ammih tayi ne yasa shi zuwa gidan a yau badon ya so ba, wanka yayi,hadi da feshe jikin sa da turarikan shi masu dadin kamshi daga lokaci zuwa lokacin yakan sakin wani irin shegen murmushi da kallo guda idan mutum yayi masa zai kuma tabbatar dana mugun ta ne.
Still yanzun ma boxes ne a jikin sa ya doso dakin nata yana ta faman gaggantsarewa alamun wani irin abu ne ke taso masa from no where yana sakin hamma da kuma tandar baki.

Kamar wacce ke jiran ace mata cas tace as,haka Ummi ta zabura daga zaunen da take zuwa can lungun gadon ta sabida ganin yadda Zulaym ya banko kofar dakin da kuma yadda yake doso zuwa inda take kamar mayunwacin zaki...

"Zonan don ubanki!" Zulaym ya fada cikin kakkausar murya da zuwa wannan lokacin wani irin gumi ne ke yanko masa,ga wani irin tsuma da jikin sa keyi! "Kayi hak...u r..." ai kuwa kasa karasa maganar tata tayi sabida yadda yayi mata wani irin warta da hannun sa guda batare da jinkirin komai ba jikin sa ta tsuma ya tattare mata lafayar da take sanye dashi hadi da yin sama da  zanin dake jikin ta,sannan ta janyo pantis nata kasa,ya kuma afka mata cike da tsantsar rashin imani da kuma tausayi a cikin wannan suturar da aka kawo ta,kamar wanda ya samu karfe.

Tin a lokacin daya fisgota,tafara kokarin kwacewa cike da tashin hankali take girgiza masa kai amma sam baijin ta! A lokacin da ta fahimci abinda yake da niyyar aikata mata wani irin rikitaccen kuka ta fashe dashi sabida tashin hankali...

A lokacin daya ratsa kansa zuwa cikin jikin ta kuwa cak! Komai ya tsaya da aiki a jikin ta na wucin gadi sbd jin wani irin abu mai kama da icce nata famar shiga da fice a jikin ta yana kuma yi mata rauni da nan take ta naimi wannan kukan ta rasa shi sai wani irin mazari jikin ta ya fara ihun ma ta gagara yinta...tin tana iya fahimtar abinda yake aikata mata har koman ta ya tsaya cak...!

Shi kam Zulaym da yasha pills na karin sha'awa sosai ya mugun fita hayyacin sa babu ji babu gani yake ta faman aiki babu digon tausayin ta ko kadan cikin zuciyar sa! Wanda Ummi tin tana kirga iya adadin sumar da take tana farfadowa cikin azaba har ta saduda kawai tana jiran mala'ikan daukar rai ya dauki rayuwar ta...

Tinda karfe goma Zulaym da ya haike na yar mutane bashi bane ya dawo cikin natsuwar shi saida a kalla ya shafe kimanin awanni hudu raa ras sakamakon pills din daya dura ma kansa! Wanda zuwa wannan lokacin idan kuka ga irin tabargazar daya aikata ma baiwar Allah zai kun zubda mata hawaye sabida rashin tausayin da Zulaym ya gwada mata kaman ya samu wacce ta jima da sanin harkar,nan kuwa yarinya ya samu sabuwa fil a laida da bata taba yin wani ganganci da budurcin nata ba!!
Gata nan kwance a wajen cikin jini sosai babu alamun numfashi tattare da ita,kayan nata da bai cire mata a farko ba zuwa yanzu gaba daya sunyi hanyar garin su baima san lokacin daya cire mata su ba.

Mikewa yayi daga kanta bayan komai ya lafa jikin sa kaman wanda aka zare ma lakka haka nan ya idasa mikewa ya zare jikin sa daga nata yana kallon fuskar ta dake bushe da jirwaye na hawaye ga wasu kuma na koron wani alamun idanun ta biyu ne,wani irin abu ne yaji ya chaki zuciyar sa da har saida ya dafe saitin hadi da lumshe idanun sa na yan wasu sakanni,kamin kuma ya bude su tar akan fuskarta ya sake zuba masu...

A hankali ya soma bin kyakkyawar fuskar ta da kallo,zuwa kan lallausar bakin ta dake ta faman motsi masu kyan gaske,har idanun sa ya gangaro zuwa kan dukiyar fulanin ta da suka kada sukayi jazir dasu a tsaitsaye suna kallon sa sakamakon yadda ya murza mata su bana wasa ba... A lokacin ne kuma wani irin tsoro mai tsananin gaske ya rufta masa sbd arba da yayi da private part nata dake bace sosai kaman wanda aka yanka karamar dabba...

"wayyo Allah na shiga uku mai ka aikata yau Zulaym..." ya fadi maganar a mugun gigice ya mike daga kwancen da take yana na girgizata hadi da kiran sunan ta, "don Allah kiyi hakuri ki bude idanun ki wallahi sharrin shaidan bada gangan na aikata hakan a gare ki ba, wayyo Allah na kar yar mutane ta mutu a hannu na."

Ya fada a kidime yama rasa taimakon gaggawar daya kamata ya bata,sai kuma can kamar wanda aka minstina ya mike a zabure zuwa cikin toilet ya jona heater sbd akoi wuta a lokacin,ai kuwa cin kankanin lokaci ya tafasa ya juye a jacuzi ya hada dai dai yadda ya kamata sannan ya fito hadi da daukar ta zuwa cikin toilet din. Wani irin ajiyar zuciya mai karfin gaske ta saki hadi da son mikewa a zabure sakamakon yadda taji ruwan ya wani irin ratsa mata sassan jikin ta... sosai ya sake shiga tashin hankali ga wani irin tausayin ta daya dabai baye shi lokaci guda sabida ganin yadda ruwan ya chanza launi.

Bashi ya daina tsoma ta a ruwa yana fiddo da ita ba,saida ya tabbatar da cewa ruwan ya daina chanza kala kamin yaji hankalin sa ya dan kwanta.
Inda kuma a cikin wannan daren yayi mata wanka soso da sabulu... Dik abubuwan da yake mata tana jinsa amma ta gagara bude idanun ta sbd wani irin zogin da zuciyarta ke mata harma ya zarce wanda kasan ta keyi mata ga yadda fatar idanun ta suka tasa sosai ko bude idanun ma bazata iya ba.

Da kyar ya samu ya shawo kanta tayi wankan tsarki wanda kuma har zuwa lokacin ta gagara bude idanun ta,ta daura akan mutumin data kaunace sa fiye da ko wane da namiji a duniya idan aka cire mahaifin ta amma sai gashi da abinda zai saka mata ranar da aka kawo ta cikin gidan sa matsayin matar sa ta sunna...! Maganar fatar baki ma ta gagara hada su shine ke kidan sa ya kuma yi rawar sa,inda shima yayi wankan kamin ya fito da ita daga toilet din,nannade ta yayi cikin wani lallausar bargon ta,yakai ta parlo kan 3seater sannan ya koma dakin ya yaye bedsheed din dake kaca kaca ya jefa cikin machine ya tattare dakin sosai ya kuma shimfida wani sabo da ya gansu reres cikin worldrop nata,ranar fa baccin ne ma ya kaurace ma idanun sa sabida tashin hankali yayi abu da niyyar ya kuntata mata,kuma yaci nasarar hakan amma gashi shima a kuntacen ya kwana dik da wani sashe na zuciyarsa cike yake da nishadin da dik wani da namiji yake shiga idan ya samu matarsa a cikakkiyar mace.

Da shike yasan ta kan aikin gida sosai sabida taya Husna da yake yanzu ma har su borner ya jona cikin dakin da nan take ya dauki wani irin kamshi da kuma sassanyar raba daya dauka sanadiyyar kunna Ac din da yayi.

Wani riga mai laushi armless iya gwiwa ya ciro mata,sannan ya fito zuwa parlon da har zuwa lokacin itama baccin ya gagara zuwar ma idanun ta,sabida gani take da zarar ta rufe idanun ta Zulaym zai sake aikata mata makamancin abinda yayi a baya.

Daukar ta yayi zuwa cikin dakin ya zura mata rigar,tare da shafe ta da mai nata na lotion daya gani kan dressmirrow.

Sannan ya shimfida mata sallaya ya saka mata wani hijap har kasa ya zaunar da ita kan sallayar cikin muryar dari-dari ya ce,"Kiyi sallah kinji harma an shiga tintini." sbd harga Allah shifa wannan shurun nata sosai yake masifar daga masa hankali ko zagin sa ne ma shi ya yarda tayi inda zaisa zuciyarta ta huce.
Sannan shima ya tafi dakin sa ya sanya jallabiya bayan ya sake dauro alwala ya tada kabbara sallah.

A gurguje yana idar wa ya shiga kitchen ya daura ruwan zafi ya hada mata shayi mai kaurin gaske daya sha madara da bornvita zuwa dakin, inda ya barta ya tarar da ita jingine jikin gadon ta kuma har yanzu idanun ta biyu ta zuba ma wuri guda ido kamar mai son gano wani abu.

Wannan tea din daya kawo mata a lokacin daya mika mata batayi musun karba ba sabida da hankalin ta tinda tasan ko bata sha ba kanta ta cuta ba wai shi Zulaym din ba,tana gama sha ta ajiye kofin a wajen gumi sai faman karyo mata yake,wanda hakan yasa shi cire mata hijap din ya kwantar da ita ya kuma kara mata gudun Ac kamin ya fice daga dakin da nan take wani irin azababben bacci yayi awon gaba da ita...


*vote*
*comment*
*share*
[8/4, 12:03 PM] Mrs Sulaiman 💓: *OUM_MUMTAZ*

*RIJIYA TA BA DA RUWA...!*

_Finally daga wannan page din na kawo karshen littafin nan wato RIJIYA TA BA DA RUWA(guga ya hana) abinda na rubuta dai dai ina rokon ubangiji ya bani ladar shi,wanda kuma nayi kuskure wanda na sani dama wanda ban sani ba ina rokon ubangiji ya yafe man🙏🏼🙏🏼sannan kuma dik wanda na bata ma rai tin a lokacin dana fara rubuta littafinnan har kawo yau dana kawo karshen sa shima a yafe man don Allah, ubangiji ya yafe mana baki daya ameen ya hayyu ya qayyum😍😘😘🥰🥰🙏🏼🙏🏼_

      
*37*

Kamar a cikin mafarki take jin dan surutu kasa-kasa a kanta,ga kuma yadda take jin wani dan zafi zafi na ratsata da yasa ta bude idanunta tar ta sauke su akan wata matashiyar mata dake sanye da fararen kaya alamun likita ce,sai kuma ta maida idanun nata ta sake budesu but still dai wannan matar ta gani da yasata yamutsa fuska ta dafe goshin ta dake barazanar tsagewa murya can kasa kasa tace "wacece ke...?"  sister Rk da Zulaym ya kira ne har gida tazo duba ta takai duban ta ga fuskar Ummin dake matikar kumbure cike da tausayawa tace "Masha Allah sannan baiwar Allah kin farka ma ashe..."  "Uhum" kawai tace mata batare data bude baki ba,sabida yadda kwakwalwarta ta shiga tariyo mata irin cin zarafin da Yaya yayi mata.
A wannan ranar dai sosai Yaya ya afka cikin wani irin nadamar da bai taba yi ba,inda akama Ummi dinki sakamakon... da akayi da ita ta hanyar d bata kamata ba.

Dik wannan budirin da ake kuwa Ummi ta gagara sanin takamaimai hanyar da ta dace ta daura abinda Yaya yayi mata,a lokuta da dama idan ta dago kanta tana kama shi iya satar kallon ta da sai itama ta tsinci kanta da zuba masa idanun ta sbd yadda fuskar sa take babu wanda zai taba tunanin wannan fuskar zata iya aikata abinda yayi a daren jiya...

Haka nan kwanaki suka dan fara gangarawa babu abinda ya chanza tsakanin zaman su,shi a nasa wajen yana kokarin wajen ganin ya wanke bakin pentin daya lafta ma kansa a wajen ta amma sam sam taki basa fuska ballantana ma ya samu kwarin gwiwar tinkarar ta da batun bada hakuri,sabida tabbacin da take dashi wannan abinda Zulaym yayi mata ko wayanda ake ma fyade albarka kenan.

A haka nan tana shan magungunan ta,tana kuma shiga ruwan zafi kamar yadda sister Rk ta bata shawara har ta warke tsaf abinta kamar wacce batayi wani abu wai shi ciwo ba,kuma a cikin wayannan kwanakin tana iya bakin kokarin ta wajen ganin komai ya dai daita tsakanin ta da mahaifiyarta.

Abinda yayi mata dadi sosai bai wuce lokacin da ta cika wata guda ba dasu Jidda suka kawo mata ziyarar bazata kamar yadda suka saba yi mata idan zasu zo basu fadi mata sai kuwa gashi sunzo mata da labari mai dadi dangane da saka date na ranar bikinta da akayi da Musty wanda ya samo dangin mahaifin sa da suma wasu family ne manya masu hannu da shuni dake maiduguri,kuma har zuwa lokacin mahaifin sa nan nan da ransa! Gashi kuma Asmy ma nata saurayin ya fito wanda hakan yasa aka hade auren nasu rana guda.

Nan suka shantake suka sha hirar su har zuwa yamma da Yaya ya dawo,wanda sosai ya fada shima wannan lokutan sabida stress da yayi masa yawa ba kadan ba... ga kuma soyayyar Ummin da tayi masa mugun kamu cikin zuciyarsa amma yana shakkar tinkarar ta da wani batu na soyayya Sabida yasan ya cutar da ita, zai yi wuya ta aminta da cewa yana sonta.
Ummi kuwa dik wani abinda tasan duty nata ne a cikin gidan tana iya kokarinta wajen ganin ta sauke su,kama daga kan girki da tattare gida da dai dik abubuwan da suka kamata amma banda zama wuri guda tare da shi.

_Bayan wata biyu_

Zuwa wannan lokacin anyi wata uku kenan da tarewar Ummi,kuma har zuwa wannan lokacin babu abinda ke shiga tsakanin su sai gani sai hange daga nesa...lolz..

Amma fa kuwa sosai Zulaym ya mugun shan jiki ba kadan ba,ga kuma yadda yake jin wani irin azababben feeling nata na kama shi a dik lokacin da yayi arba da ita sbd yadda take masifar tsukewa da sha gayu dare da rana kamar ma wani abin da gayya takeyi...

...... Zaune take kan royal cushion nata kafa daya kan daya tana girgiza su cike da wani irin salo da kana gani zaka san cewa na manyan mata yan gayu ne da suka san sirrin naira,kunnen ta manne yake da wayar ta,tana sanye cikin wani riga iya rabin cinyar ta mai spaghetti hand ga kuma rabin beatiful breast nata gaba daya waje yake yana zuba sheki da daukar ido,chewing gum ne a bakin ta tana tauna wa kamar wacce ke taunan paracetamol sbd tsantsar iyayi irin namu na mata😆

"Mamy pls ki aika akawo man irin wancan turaren da kike amfani dashi akoi kamshi sosai..." ta fadi tana kyabe face kamar wacce zata fashe...

"To karki damu in Allah ya yarda nida kaina zan kawo maki tinda ke kam kin mijin ki nasan bai son kina fita..."   Mamy ta bata ansa daga dayan bangaren cikin raha...   "uhimmm" kawai tace kamin sukayi sallama inda tana dago kanta karaf idanun ta ya fada cikin na Zulaym da tin shigowar sa gidan yayi mutuwar tsaye a inda yake sabida yadda ta masifar tafiya da imanin sa tana naiman zautar dashi batare daya shirya ba.

Ji tayi wani irin maganadisu na janta zuwa gare sa amma haka nan ta dake ta janye nata idanun sbd yadda take jin jikin ta wani iri...(true love bai taba gushewa fa koman lalaci merh people😆😆)

Wani irin ajiyar zuciya mai karfin gaske ya sauke,kamin ya janyo kafafun sa da suka masifar yi masa sanyi ya doso inda take gadan gadan. Wanda hakan yasa taji wani irin ras da gaban ta ya bata sakamakon tuno ranar da aka kawo ta daya doso inda take gadan gadan! Saidai kuma fa yanayin tafiyar da yake a wannan ranar da ta yau akoi bambanci ba kadan ba.

Wanda hakan yasa ta sakin silent ajiyar zuciya ta maida hankalin ta kan wayar ta dikda babu abinda take fahimta sabida kusancin da suke sake samu tare dashi.

A bazata taji ya saka tattausan hannayen sa bisa nata da ya sata lumshe idanun ta babu shiri jikin ta ya soma daukar rawa. So take ta mike daga inda take amma ta gagara sbd yadda ya zuba gwiwowin sa a gaban ta ya kuma rike mata both hannayen ta babu ta yadda za'ayi ta saukar da kafafun ta ballanta ta mike idan bashi ne ya bata damar hakan ba...

"Tabbas nidin na cika azzalumi a gare ki matata! Na ci mutuncin ki ta yadda babu mahalukin da a kaf cikin duniya zaiso ai diyar sa ta cikin sa sbd yadda idanuna suka rufe na gasa gaskata abinda yake rubutaccen al'amari ne daga lillahi! Yau ni Zulaym Ahmad shuwa gani a kan kafafu na gaban ki ina rokon arziki a wajen ki don Allah ba don hali ba ,ba kuma don na isa ba,ki gafarce ni ki yafe man akan dik muzguna maki din da nayi daga ranar da aka daura mana aure wanda na sani da wanda ban sani ba don Allah......" Zulaym ne ke wannan maganar gwiwowin sa a kasa muryar sa cike da wani irin rauni hannayen sa guda biyu hade🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼 alamun neman gafarar ta...

Ummi da ta rasa abinda ke mata dadi sabida yadda taji abin wani irin banbara kwai babba kamar Zulaym durkeshe a gaban ta da sunan yafi sai tayi kokarin mikewa amma sai ya saka hannayen sa ya mayar da ita daga zaunen cikin yin sake raunata murya yace, "Bazan iya barin ki ki mike anan wurin ba har sai kin fadi mani matsayin laifi na gare ki don Allah kin yafe man."

Runtse idanun ta tayi sosai sabida yadda kusancin ta da Zulaym din ya haifar mata wani irin azababben feeling da ta jima tana dannewa ta gyada masa kai batare data iya bude bakin ta ba...

"Nagode kwarai da gaske da wannan yafiyar da kika man! Insha Allahu zaki sameni a matsayin mijin da zai zamto abin tinkaho da alfahari a wajen ki! Ba kuma zan sake yin wani yunkuri da zai zamtoh cutar wa a gare ki ba sbd NA JIMA DA KAMUWA DA KAUNAR KI ZULAYKHA...! INA SON KI HAR CAN CIKIN KARKASHIN ZUCIYA TA! INA SON KI I LOVE YOU SO MUCH...!"

Wani irin madarar sanyi ne ya gangaro daga cikin makogwaron ta zuwa cikin zuciyarta ya wanke mata shi tas! Akan abinda Zulaym din yayi mata zuwa cikin cikin ta har babbar yatsan ta, ta jiyo ta a cikin wani irin duniya mai cike sa shauki tare kuma da begen da masoya kan afkawa a dai dai wannan lokacin............

Finally yau gata ga mutumin da take kwana da kuma tashin a kowacce rana cikin ko wane second da kaunar sa zaune a gaban ta yana zayyano mata kalaman kauna a gare ta...? Wannan rana zata sako ta cikin ranaku mafi mahimmanci a rayuwarta da bazata taba mantawa dashi ba...!

Tallafo fuskar ta da hannun sa yayi suka zuba ma kwayar idanun junan su wani irin kallo dake aika sako directly from their heart...!

Ganin yadda dik tabi ta zama sokuwa ta shashance da kallon sa ne yasa shi hure mata idanun nata da yasata yin kasa da kanta cike da kunya......!

Wani irin murmushi ne ya subuce masa sabida wani irin sanyin dadi daya zuba cikin zuciyar sa "ashe dai haka baiwar Allah keda saukin kai amma ba zalince ta mafi muni?" Zulaym ya raya maganar cikin zuciyar sa yana kallon ta da take ta faman wasa da yatsunta kanta a kasa.

Da wani irin salo ya dauke ta zuwa cikin bedroom din nata dake ta faman zuba kamshi na turaren wutan yan borno da Mamy ke sayo mata inda ya wuce da ita zuwa toilet!!  Dik da yadda take nonnokewa a wannan ranar haka nan sukayi wanka tare da mutumin data tabbata rashin hakuri bazai iya bata shi ba kamar yadda wasu matan da idan suka so namiji suke addabar kansu da cewa lallai lallai shima sai yaso su a wannan lokacin,da basu san ita zuciya ba''a taba yi mata dole ba, Kuma komai dan hakuri ne.

Ai kuwa wannan ranar saida Yaya ya tabbatar da cewa ya gama kashe boss ya kuma tabbbatar ma da gangan jikin ta ma irin kaunar da yakeyi mata har cikin zuciyar sa sbd yadda ya gwada mata wasu irin salon sa masu matikar girgiza zuciyar yammata,dik wani kuncin daya kunsa ma zuciyarta a cikin first night nasu a wannan ranar saida ya tabbatar ya goge mata memory dinnan tas...! Wanda itama kuwa ta baje tata manhajar daya tabbatar masa sa da yadda take kaunar sa mararan dikda bata furta masa hakan a baki ba...

BAYAN WASU SHEKARU.........

A cikin wayannan shekarun anyi auren Jiddah da Musty da shima yayi wani irin kudi na ban mamaki suna zaune a Kaduna! Sabida campany nasa na kansa da mahaifinsa ya mallaka masa halak malak ki bayan babu ransa sbd yasan bashi da gadon sa...wanda zuwa lokacin harda guzirin yaran su guda uku cif cif...
Asmy ma da nata angon itama yaran ta uku kamar na Jiddah suna zaune a cikin garin Abuja.........
Mima da Hidaya ma sunyi auren su ko wacce na gidan Mijin ta harda yaran su bibiyu...
Ga kuma su Waleed da suka zamtoh manyan samari a lokacin masu tafiya dai dai da zamanin su...............

Allah yayi ma YAYA BABBA rasuwa sakamakon gajeruwar jinyar sa yayi,wanda labarin hakan daya riski hajja ne itama ta yanki jiki ta fadi tabi bayan mijin ta aka binne su  kabarin dake makwaftaka da juna...

Gidan Abbahn Ummi  kuwa shima a cikin wannan shekarun Allah ya azurtashi da samun haihuwa tare da Anty Khadee,wanda kuma a karon farko ta haifa masa yaran sa maza har guda uku,inda kuma data sake haihuwa ta haifo masa mata tagwaye wanda farin cikin da Abbah da kuma yarsa suka shiga a lokacin bazai rubutu ba kawai mai karatu ya kiyasta kayan sa...

Aymana yarinyar Anty khadee ma tayi auren ta da Sadeeq nata da yan gidan su ke kira da Hamma sadeeq (Aymana ta koma ma hamma Sadeeq kamar yadda sukayi aure a littafi na na AYMANA (Romantic story...) ga dik wannan bai karanta ba dadi ya barshi a baya⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️)

Bangare gidan Hajiya Zulaykha Alh Abdulwaali kuwa......

Wani irin soyayya suke competition suke bugawa tsakanin ta da mijin ta kuma uban yayan ta wato Zulaym Ahmad shuwa babu kama hannun yaro.

A cikin wannan shekarun kuwa yaran su guda huda ne,mata biyu maza biyu + Little Husnah data zama yammata su biyar kenan.
Batun fita aiki company kam dama ya Zulaym ya soke shi sabida masifaffen kishi irin nasa wai shi bazai yarda matar sa tana shiga cikin maza suna chudanya ba...

...... Wasu beatiful yara ne yan 4yrs mace dana miji zaune tsakiyar wani kayataccen parlo keta faman tsala ihu suna kiciniya akan wani toy na baby ko wannen su na kokarin wajen ganin ya kwace amma sun gagara da yasa su sakin kuka...

Daga wani kofa dake manne da parlon wata kyakkyawar yarinya yar 8yrs ta fito da gudu gudun ta har tana tuntube wani yaro sa'an ta mai kama da ita na take mata baya shima sbd jiyo ihun kannen nasu...

"Kice abani kayana intyyyyy..." yarinya macen ta fada cike da fitina tana faman turje kafafuwa alamun itace fitinanna kuma bata da gaskiya...

Shi kuwa dayan yaron da shima ke kuka tsakanin sa da Allah yace "baan bayay ba nikam..." wai bazai bayar ba shikam...

Sai inty da BOBO (mai mata hudu na littafin kunji munafiki😆😆😹kenan) suka tsaya sororo sabida sun san kannen nasu da shegen fitanar tsiya...

Wata yarinya ce ta fito daga wani dakin yar 15yrs zuwa inda suke da gudu gudun ta tayi sama da yaro namijin da yafi yin kuka tana lallashin sa "wayyo yaron Ammie don Allah kayi shuru karka sa inji kunya kana ma kanwar ka kuka kaji.." ai kuwa bata rufe baki ba yaro yayi shiru kamar anyi ruwa an dauke yana sakin ajiyar zuciya akan kukan da babu hawaye.

"Ni kam hayaniyar mai nene yake min welcome tin daga waje ne ni yaron Babi."

Wani yong alaji da zai kai irin 50yrs ya fadi daga bakin kofa,amma sbd yanayin yadda kudi ya zaunar masa sai a dauka irin 40yr ke gare sa...

maida masa abinda ke faruwa Little Husnah tayi da yasa shi daukar hararar yarinyar data kankame toy din bakin nan gaba tana jiran ace mata fim tace masu as...

A haka Ammien su ta fito daga dakin ta tana bulbula wani irin kamshi cikin wani dankareren les yan uban kamar wacce zata gasar kyau

"Your highly welcome my exellency..." Ta fadi hakan tana ansar jikar hannun sa da murmushi akan fuskarta mai kyau.

"kina jin yarana suna rikici amma bazaki fito kiji ba'asi ba wai don Allah..." 

Turo baki gaba tayi cike da shawaba tace, "Amma kaima kasan halin yaran nan yanzu ina gama raba su shikenan kuma zasu ci gaba dayi ne,shiysa na barsu idan sun gaji sa daina don kansu ai."
Tayi maganar tana hararar _Madiya_ dake jiran fim ta fashe sbd masifar ta suma kansu iyayen nata sun sara mata.

"Abieeeee  auke ni yima..." tayi magana cike da fitina sabida an dauki dayan ta ita ba a dauke ta ba.
Mikama little dake ta faman dariyar yaran Haidar Abien nasu yayi kamin ya dauki Madiya ya cilla ta sama da nan da nan tayi jifa da toy din da ake fada akansa tama manta dashi tana zuma dariyarta ...

"Abieeee! a shauke ta a auke ni nidaii" Haidar ya fadi yana tsala nashi ihu da yasa su fashewa da dariya baki dayan su sbd kullum da irin dramer din da yaran nasu keyi is so funny...

_Alhmdlh ala kulli halin..._

*vote*
*comment*
*share*

No comments