Recent Updates

Narjeesah Complete Hausa Novel


 💐💐 *NARJEESAH* 💐💐




DAGA MARUBUCIYA


_*NANA KHADEEJATU*_

*UMMU IHSAN*



          1&2

          

➿➿➿➿➿➿ Tsaye take a kaina sai masifa takeyi bama zata barni da abunda yake damuna ba. 



Kawai matar taci gaba da fad'ar, "yo in banda kin rai nani kin mayar dani ba'a bakin komai ba, dan bani ce na haife kiba, aini matar uban ki ce, kuma dolene na saka ki aiki kiyi mani, ko dan kin ga uban naki baya a raye ne iye? ".




Masifar tace ta ishe ni nace, "dan Allah Mama kiyi hakuri ki dubi halin da nake ciki ki dubi yanda nayi kumburi bayana ciwo yake yi mani gashi daket nake zama daket nake tashi, kuma fa ɗazun inno ta sakani wankin yara da nata kayan wallahi da zaune na ƙarasa shi ma". 



Mamar tace, "chan gareki wankin ɗan wankin da kika yi masu wanda bai wuce abun a zo a gani ba?  Ni ki tashi kiyi mani nawa aikin ki wanke mani zanen gado na guda biyu da labule na duk sunyi datti kuma idan kin ƙarasa ki ɗora mani girki, yau dambu ma zakiyi muna a gidan nan kafin su Halira su dawo makaranta suda suke da tarbiyya "yam mata ne su sai neman ilimi su basu biye wa kwaɗayi ma buɗin wahala ba, wanda ya biye wa kwaɗayi shike zaman gida baya fita dole ayi aikin gidan iyaye, waima mutum dan yasan ya kwaso mugun abu ai dole ne ya zauna gida yayi aiki ko zai samu zunubin sa ya ragu, amman ke kina wasa da ladar da zaki samu har laifin naki ya rage! ". 


Cike da jin zafin maganar da take sakar mani mai mugun ƙona mani zuciya jin na keyi da sa'a tace ba matar ubana ba wallahi da duk irin yanda nake jin jiki na sai na mareta, kawai nace da ita, "Ai kuwa wallahi a yanda nake jin nan ba zan iya yi maki wani abun ba, da ƙasan ciki na ma ciwo yakeyi da baya na! ". 

 



Hannu wa Mama ta fara tafawa tare da rafka uban salati ta ce, "ikon Allah wato yan zun dan kin ganki da wannan ƙaton cikin wanda ba'a san uban sa ba shine kike ganin kin girma baki da kunya har kike zagi na, to  mutanen gidan nan kuna jin abunda wannan marar kunyar take faɗa mani magana har da zagi, Yaya! Yaya!!  Kuzo ku gani kuma kuji da kunnen ku dan malam baya a raye shine zaki zage ni? dan kada ace nayi mata ƙazafi ".




Duk kan nin su matan gidan suka haɗu gurin ɗaya harda Umma na, tunda Umma na ta fahimci cewar dani ake wannan dramar sai ta koma gefe bata ce damu komai ba. 




Mama tace, "wai har nice zan saka Narjeesah  aiki taƙi aikatawa, wai bata iya wa? ". 



Inno tace, "Narjeesah kwana kin nan na lura dake fitsara kike ji, ke ce  zaki ɓata muna zaman lafiyar da Malam ya ɗauki shekaru yana ginawa, to a gaskiya ba zamu ɗauki wannan rashin mutum cin ba taya zaki zagi wadda take matsayin mahaifiyar ki? ". 




Ni kuwa shiru nayi ina sauraren su, abun da nakeji a jikina shine kawai yafi damuwa ta. 



Ki kayi kunnen uwar shegu damu, sai ka ce kin ga abokan wasan ki a gurin, "Mama ce  ke wannan maganar cike da annuri a fuskar ta harda murmushi take zaki tunda ta samu magoya bayan ta"




Tashi tsaye nayi na raɓasu na wuce da ket na ke ɗaga ƙafata har na ƙarasa ƙofar ɗakin mu na  shige nayi kwanciya ta, ina jin haushin kowa a duniyar nan. 




Yaya ce ta ce, "Wai nikam Umman yara ba zaki riƙa yiwa Narjeesah magana ba akan abun da ta tsira na yiwa Larai rashin kunya?  dan tana ɗauke da wannan cikin kuma ya tsufa ai ya kama ta tayi mata biyayya ko? Kuma ai tariƙa yawan motsa jikin ta ba wai ta riƙa biyewa jikin ta ba, saboda gurin haihuwa zata sha baƙar wahala ne".



Inno ta ce, "haba ai dai kowa yasan halin Umman yara indai akan Narjeesah ne tofa baza kiji, bakin ta ba, saboda ita sam bata ɗaukar Narjeesah a matsayin "yarta ta cikin ta saboda kasan cewar ta 'yar fari alkunya, ake yi mata inda dai su Mariya da Nusaiba ne tofa da kinji bakin ta har yafi na kowa, kuma amman banda Narjeesah shi yasa Malam ya cire Narjeesah  daga cikin ɗakin ta, ya mai da ita cikin ɗakin na, amman kuma yan zun duk ta sauya idon ta ya buɗe dama idon ta a buɗe yake ga shegen rashin kunya da fitsara". 




Ita dai shiru Umma tayi tana sauraren su tace, "to ya zanyi da ita ni wallahi nayi tsammanin da wani kuke magana bada ita ba". 



Shiru sukayi kowa ya kama gaban sa, Umma ce ta sameni a cikin ɗakin ta ina kwance ina haki kamar wadda taci gudu, kallo ɗaya tayi mani ta ɗauke kan ta, taje bakin gadon ta, mai rumfa ta zauna tayi shiru zuwa can ta ce, "Ke ki riƙa daurewa kina motsa jikin ki, nifa bana son kina yawan saka ni magana kuma ba cewa zakiyi ba zaki iya aikata mata aikin taba, sai dai kawai kice, tayi maki haƙuri zuwa anjima ba rashin kunya zakiyi ba kwana kin nan ina lura da yan da kike yiwa Larai rashin kunya to bana so kuma kada na sake ji ko na gani". 




Sai da Umma tayi shiru zuwa can nace, "shike nan dan kawai ina cikin wani hali sai ace nice zan riƙa aikin komai a gidan nan ita ce fa ke zagi na amman kinji ta lauye abun, to ina su Anty Asma dasu Balkisu kawai sai ace nice zanyi komai, in kuma ance su manya na ne , su Fauziyya fa? ". 



Shiru kawai Umma tayi bata sake magana ba, dama nasan ba zata ƙara maganar ba saboda bata magana fiye da biyu dani koda dagani sai ita ne uwa uba muna da yawa matsawar ana labari na saka baki na to ba zatayi magana ba har sai na tashi nabar gurin ko ita tabar gurin ina jin ciwon wannan abun fiye da zato, ace kai da mahaifiyar ka amman babu wata alamar shaƙuwa ko nuna soyayar ɗa da mahaifiyar sa.  



Aikin da banyi ba ke nan aikuwa dambun ta dafa na tsakin masara, ta baiwa kowa banda ni, ni kuwa dama koda nake da ciki da jarabar masu ciki ban fiye son abin da zanci a koma gefe ayi mani habaici ba, dan Umma tasan halina kai kowa ma yasan hali na, bana cin duk abunda ya kasan ce na gori ne, Inno  da kanta ta aiko kira na, da ket na tashi na fito a tsakiyar gidan suke zaune ta kalleni tace, "jeki ɗakina ki buɗe kular Yayan ku Deeni akwai alale na nan ki zuba wanda zakici, saura kuma ki ragawa Yayan naku saboda nasan yau sai dai ki zauna da yunwar ki, kije ki ɗora wa mutane aiki". 




Saboda nasan halin Inno kuma a ɗakin ta na tashi sam ita bata da rowa kuma koda bata shiri da kai sai ta taya maka ko miye a gaban ta, bata da muba, kuma babu ranar da zata goran ta maka, shi yasa na je na zubo alalen, a kusa da Inno na zauna na fara dubawa nayi shiru,  Yaya ce ta kawo mani, yaji da mai na ansa na zuba na fara ci, Anty Basira ce ta ce, "A'a kaga su Hajiya Narjees yau fa kinyi mani ƙatuwa da yawa wallahi wai miye sirrin ne? . 




Kallon ta kawai nayi, ban ce da ita komai ba, sai alokacin ne Yaya tace, "babu ko shakka Narjeesah haihuwa na kusa, kin kusa haihuwa dan wannan kum buri ya nuna cewar cikin yayi nauyin kuma sai ya zun ne na lura da cewar cikin yayi ƙasa sosai ". 




Mama tace, "to yan zun idan Narjeesah ta haifu a gidan nan ya ya zamuyi da mutane, kuma taya kuke ganin Narjeesah da abunda zata haifa su zauna da kwanciyar hankali kai gaskiya babu su babu kwanciyar hankali a garin nan dan haka gara ma tun yan zun asan abunyi dan ni babu ɗan da ya isa ya jami zagi, abunda yara na basuyi ba ke nan inda gidan mijin ta take ai da munyi firin ciki amman yan zun sai baƙin ciki muke ciki nikam ba zan yarda ba ehe ! ". 




Duka kallon Mama kowa keyi, wani kuka naji yana shirin zubo mani amman kuma sai na dake, naji ta bakin kowa. 



Cikin mamaki Inno ta ce, "wannan wace irin magana ce kikeyi hakan Larai? Da kika cewa yaran ki basu jawo maki zagi ba, ai itama Narjeesah "yar kice Narjeesah indai da gaske ne Malam son gaskiya kike yi masa ai irin son da Malam yake yiwa Narjeesah kema kiso ta". 




Yaya tace, "Larai sai dai idan kece zakiyi wa Narjeesah  rashin mutum ci tunda kin ga bata yi maki wani laifin ba, kika fara wannan maganar lallai ne Larai zuwa gaba kece zaki sauya zaman gidan nan! "




Haulatu ce "yar ɗakin Inno ta ce, "dan Allah  dan Allah a daina maganar nan mu bama so wallahi ai ita ƙaddara tana akan kowa ko? ". 




Da sauri Shamsiyya "yar ɗakin Mama tace, "ai dai ƙarya ce ake yiwa ƙaddara dan mutum inda baiyi niyar aikata hakan ba, da bai aikata ba, kuma mutum shine ya jawa kansa abun faɗa dan haka dole ne mu faɗa, cikin da ba'asan uban sa ba, gurin yawon lalata, aka janyo mugun abu mukam baza'a lalata muna gidan mu ba da mummunan iri ba, dolene asan abunyi, kuma in da Aure mutum yayi ai da yanzu mun fara shan jar miya, ni wallahi abun haushi ma, wai kamar Narjeesah "yar shekara goma biyar cikin ta sha shidda zata shiga, ace har ta iya lalata harda su guzurin ciki, muda muke yayun ta shekara biyar muka bata, amman bamuyi abunda tayi ba". 




Aunty Zuwaira yar ɗakin Yaya tace, "a gaskiya mukan an janyo muna rigima Narjeesah  kin shafa muna kashin kaji, gashi har sai da Bilya yace, ya fasa Aure na, sai da nayi ta masa rantsuwa da alkawarin ban taɓa aikata irin haka ba, nasan dai yan zun ya haƙura kuma zai turo iyayen sa, su kawo lefe dan haka asan abunyi dan ni kam bazan "yarda da a hana ni Auren wanda na mutu a kan sa ba". 



Rigima ce dai suka saka wasu na goyon bayan Mama wasu kuma ni suke karewa, ajiye alalen nayi cikin jin ciwon abunda suke faɗa a kaina nace, "kowa sai faɗar albarka cin bakin sa yakeyi to wallahi nikam ku barni naji da abunda yake damuna, haba dan Allah shin dame zanji ne?  Ko kuwa son kukeyi na haɗe zuciya ta na mutu haba! "  




Daket na tashi tsaye nabar masu gurin suka bini da ido,Mama ce tace, "oho maki ai kodai miye ba mune muka janyo maki ba, baƙin halin kine ya janyo maki yau inda malam yana raye ai da kece zaki kashe, ya haɗiye zuciyar sa ya mutu, tunda ga saka makon da kikayi masa shi ya fifita ki akan kowa amman kinje kinyo cikin shege". 



Su Inno baro mata gurin sukayi, Yaya kuwa zagin Anty zuwarah take, tana faɗar albasa batayi halin ruwa ba, wallahi idan ta sake ai banta ni sai tayi mata abunda batayi tsammani ba, Ita kuwa sai cika take tana batsewa. 



 Umma ce na samu zaune inda nabar ta, tana zubar da hawaye ina ganin ta,  tayi saurin gogewa, ta ɗauke idon ta, ni kuma sai nayi saurin shanye nawa kukan na zauna na fara karatun al, kur'ani mai girma dan na samu natsuwa, nida Umma na. 



Haka muke rayuwa a gidan mu, idan na fito tsakiyar gidan sai an sakar mani magana, ko habaici, na sani sanadiyar ƙyalen su da nakeyi na wannan lalurar ne, dan haka bana yawan fita. 



Wata rana daddare ina kwance can cikin barci na, naji kamar an tsun kuleni ai a zabure na tashi zaune, na yun ƙura in tashi tsaye kawai naji wani uban ciwo kamar zan mutu, addu'a na soma yi, Inno dake kwance a gadon ta na ƙarfe ta tashi zaune ta haska fitila tace, "ikon Allah Narjeesah abun ne ko? "




Da taimakon Inno da addu'a Allah ya sauke ni lafiya, duk wanda Allah ya baiwa ikon haihuwa lafiya farin ciki yakeyi da murna da godiya a gurin Allah maɗau kakin sarki, kuma duk wanda yaji wannan haihuwar farin ciki yakeyi da murna azo a ga jin jiri amman kash! wannan kam a guri na da "yan gidan mu abun baƙin ciki ne duk wanda yaji tofa sai ya zageni kuma a kira abunda na haifa da shege wanda sam ni ban ma san abunda na haifa ba mace ko na miji duk bani da masaniya akai. 



Tun ƙarfe ukku da rabi na dare na haifu amman har garin Allah ya waye ban ɗauke abunda na haifa ba, haka zalika ban sa abunda na haifa a ido na ba, yana gurin Inno da Yaya sune suke kula dashi Umma da Mama basu zo sun duba lafiya ta ba da abunda na haifa ba, kan kace ƙwabo gidan mu mutane sai shigowa gulma sukeyi da tse gumi, Inno da Yaya mamakin ta yanda akayi mutane suka sani sukeyi. 




Duk mutanen dake shigowa gidan basu sakani a idon su ba amman suna ganin abunda na haifa ni kuma ina kwance Inno ta shigo ta zauna a gefe na, tace, "Narjeesah  tashi zaune zamuyi magana dake ". 



A yanda naga yanayin Inno ba da wasa take maganar ba gashi ina jin ciwo kamar na mutu, a daddafe na tashi zaune na kafe ta da ido, Inno tace, "Narjeesah kin haifu Allah ya sauke ki lafiya baki dubi abunda kika haifa ba, baki ɗauka ba kuma baki tambayi abunda kika haifa ba, Narjeesah shin kina tunanin abunda kikayi kinyi wa ɗanki adalci ke nan?  Shin Narjeesah  kina nufin baki yarda da ƙaddarar data sameki bane ko miye? To bari kiji idan kuwa haka zaki tafiya  da rayuwar ki zaki ɗauki alhakin wannan bawan Allah Narjeesah ki godewa Allah a duk hanlin da kika tsinci kanki a ciki! "



jikina ne yayi sanyi, ta bani yaron daket na anshe sa, ina kallon fuskar sa sai da gaba na ya faɗi da sauri nace, "Inno anya wannan yaron mutum ne kuwa?"



Inno tace, "Narjeesah ke ke nan keda sai yanzun kika ganshi da alokacin da yazo duniyar nan ne kika ɗauke sa kallo ɗaya, sai kinja, *Innahu min Sulaimanu Wa Innahu  Bismillahir Rahmanin Rahim* saboda mugun kyaun da yazo dashi ka shi ƙaton gaske da nauyin sa, kamar balarabe duk 'yan gulmar da suka zo da zarar sun kalli yaron sai kiji sunyi shiru sai dai suce Allah ya raya". 



Bata yaron nayi ta ce, "ba zan ansa ba, sai kin bashi mamma yasha ai iya hakuri yayi hakuri ban ma taɓa ganin jin jiri mai hakuri ba irin wannan dan ha oya maza bashi yasha"



Nidai cike nake da mamaki irin wannan rayuwar da na tsinci kaina nakeyi, ace wai ni Narjeesah ƙaramar yarinya dani nice na zama uwa wai haihuwa wai kuma shayarwa zanyi, kai wai dai ko mafalki ne nakeyi?. 



Inno ce taga nayi zurfi cikin tunani kawai sai ta saka hannun ta ta fara ɗaga riga ta da sauri na dawo hayyaci na, na riƙe rigar nace, "Inno dan Allah ki bashi nonon Akuyar ki da tahaifu kwanan nan dan Allah kinji Inno? ". 



Sakin baki da hanci Inno tayi tana kallo na, kawai ta kwalawa Yaya kira, ai kuwa da sauri Yaya ta shigo tana tambayar lafiya?  Inno tace, ina fa lafiya wai Narjeesah ba zata shayar da yaron nan ba, sai dai abashi nonon akuya ta data haifu"



Salati Yaya ta saka tana kallona, shi kuwa yaron kamar yasan abunda akeyi ya fashe da kuka, jin yaron ya fara kuka ne yasaka Yaya tace, " ko kibasa yasha ko kuma yan zun nan ki haɗu da fushi na! "



Nasan halin Yaya ba ƙaramin aikin ta bane taci ubana a yanzun aikuwa da kaina ba sakawa yaron nonon a bakin sa ai kuwa kamar jara yake ya fara ja wani uban ihu nayi na janye shi, ina faɗar wallahi da zafi ciwo wallahi ". 



Zama naga Yaya tayi a kusa dani ta haɗe rai dole yasa na maida yaron yana sha ina yarfa hannu ba damar na janye sa, sai da Inno tace, "sauya masa ɗayan shima ya sha". 




Kuka na sanya yana sha hawaye na zubo mani wanda har sai suka tabbar da ya ƙoshi, yayi bacci sannan suka anshe shi, Yaya tace, Inno aje ayo mata wankan kodai naje nayo mata da kaina ne? ". 




Ai sai na ƙara saka kuka, basu saurare niba, Inno ta saka mani hijab muka fito tsakar gida muka shiga bayi, ina ganin robar wanka da ruwan yanda turirin zafi ke fita kawai naji kukan ma ya tsaya kallon Inno nakeyi, ita kuwa Inno wankan tayo mani da kanta ta gasani nikam jin nakeyi tawa tazo ƙarshe, ruwan da suka rage ta sakani na zauna sai da muka daɗe a bayin muka fito da Mama mukaci karo, aikuwa cewa tayi, "uwar shege anfito ke nan". 



Maganar ta daki zuciya ta tayi tsaye Inno kuwa tace, "mai ɗa goye baya cewa ɗan wani shege bai sani ba ko ya haifa" muka raɓata muka wuce, ashe taji haushin amsar da Inno ta bata, aikuwa Mama ta saka masifa tana faɗar ni wallahi babu abunda zaku iya yi mani duk taron ku mutanen gidan nan kuma ni ban haifi shege ba dan yara na duk sun girma ballema kice mani ina da yara a goye, ita dai ce da ta haifi shegen akafaɗa kuma na faɗa wata ta haifi shege". 




Duk abunda takeyi babu wanda ya kulata, saboda magagganu take saki wanda babu wanda yasan manufar ta, shi yasa kowa ya fita iskan ta. 




Da yamma zuwa ƙarfe biyar bayan anyo wankan marece ni kuwa ina gyara wa, Su Yayan mune  duk suka shigo cikin ɗakin Inno  su takwas duk maza mata ukku masu Aure da sauran wanda basu da Auren da ƙanen mahaifin mu da matan sa harda yaran sa duka, duk sukayi tsaye suka zuba mani ido. 



Ni kuwa na saka kayan da Yaya ta fito mani dasu harda hijab  na ɗauko mai zan shafa ke nan, sai na saki man domin na shiga tashin  tsananin tashi hankalin wanda ba'a sa masa rana, gashi mutanen duk fuskar su a haɗe take, Goggon muce ta shigo cikin ɗakin a har gitse ganin yaron a hannun Inno kawai cikin fushi tace..... 





*Comment And share* 




_*Yin comment din kune zai bani amsar  karɓuwar littafin*_


*Ummu Ihsan ce* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


💐💐 *NARJEESAH* 💐💐


*RUBUTAWA, DAGA ALƘALAMIN:-*   

            *NANA KHADEEJATU*   *_UMMU IHSAN_*



*YA  ALLAH  KAJIƘAN  IYAYE  NA  KAYI  MASU RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SU KA  SADA  SU DA  RAHMAR KA  ALLAH  KA  SANYA  SU DAGA  CIKIN  DAUSAYIN  ALJANNA  ALLAH DASU DA  DUK  KANNIN  YAN  UWA  MUSULMI BAKI  ƊAYA  AMIN YA ALLAH*



*_BISMILLAHIR RAHMANIN*


      *3&4*


➿➿➿➿➿➿➿➿


Tace, "wannan wace irin masifa ce?  A gidan ɗan uwana akan "yar da yafi ƙauna a rayuwar sa, wannan shine ake kira da baya ta haihu ke nan!  An maida gidan Yaya na gidan tara shegu, Narjeesah sai da kika ɓata sunan gidan nan, to wallahi ba zamu ɗauka ba, yan zun nan zamu ɗauki mata ki akan abun da kika aikata, kuma duk wanda yake da niyar aikata makaman cin irin abunda kika aikata, idan yaga hukunci da ya hau kanki sai ya gyara idan yaso yin hakan! "


Kawu Bala yace cikin masifa, "ai dama na daɗe da yanke hukunci shiru kawai nayi tagama haife abunda ke cikin ta, to bari kuji hukunci da na yake ku a gurin ku ya yi kuwa ko kuna da ja acikin sa? Yau ɗin nan za'a raba maku gado kowa ya kama kansa wanda suke da yawa kuma suke da abun siyen gidan nan ko kuma sukaci gidan nan su zasu zaune shi, saura kuma kowa ya kama gaban sa! "


Ai kuwa da sauri Mama tace, "nida  yara na mun yarda ku tambayi sauran yaran da kanku kada kubi ta iyayen su dan zasu hana su ƙwatar "yan cin su". 


Zuciya ta nake jin kamar zata fito daga cikin ƙirjina, sai dafewa nayi ina karanta duk abunda yazo baki na. 


Su Yaya Auwal suka ce duk abunda kuka yanke bamuda ja, da a bata muna sunan gida, gara kowa ya kama kansa"


Su Basira murna kamar su zuba ruwa ƙasa su sha, Inno dai kallon kowa takeyi yaran ɗakin ta sam sun nuna basu son ayi hakan, Amman ɗakin Yaya idan ka cire Yayar da yaron ta Mudarsir sune kawai basu yarda ba, sauran kuwa duk sun yarda mu kuwa muda ba'a bakin komai muke ba ba a bi ta kan muba kawai suka fita aka kira dillalai akayiwa gidan kuɗi akaje aka duba gonar Baban mu, suka je gurin malamai akayi rabon, muda muke zaune a gidan su goggo da Mama da sauran su Anty Asma dasu duk suna kasa sun tsare sunƙi fito cikin ɗakin, har su kawun suka shigo gidan. 


Kiran Umma na akayi da ƙanne na a take kawu ya fara magana wadda ban san ranar da zan iya man tawa da ita ba, yace, "to an raba maku gado daman nasan shi su Narjeesah suke jira ita da Umman ta, dan hakane suka tsiri ɓatawa gidan nan suna, to Allah ya fiku, ga abunda kuka samu dubu ɗari biyu da saba'in ku dukan ku, yan zun sai kuzo ku bar gidan nan ku kwashe kayan ku, yau_yau ɗin nan nake buƙatar kubar gidan nan! "



Inno tace, "wannan wane irin rabon gado ne haka da rana tsaka, kuma kuce ga abunda suka samu bayan baku sanar da abunda kowa ya samu ba?  Wallahi wannan ba adalci a cikin sa, indai ba zalunci kuka tsaro ba". 


Cike da masifa akayo kan Inno wadda su Yaya jafar suka dakatar tare da faɗa,  "sufa bazasu ɗauka ba kuma gaskiya Inno ta faɗa"


Rigima ce aka sanya kowa ya faɗi albarkacin bakin sa, Yaya tace, "kowa a sanar dashi abunda ya samu dan gaskiya nima ban yarda ba". 


nan dai aka ce, Mama mai "ya"ya maza su shidda mata ukku sune sukaci rabin gidan duk girman sa, Inno da take da "ya"ya maza biyar mata hudu, taci kusan rabin gidan kaɗan aka rage ɗaki ɗaya da zaure, sai aka baiwa yaron Yaya ɗaya wannan ɗakin da Zauren, sai aka koma gona, inda muda sauran su Yaya aka rabawa gonar. 


Umman muce ta shigo cikin ɗakin ba tare da tayi magana ba, kawai ta bashi hannun ta, a take duk suka zuba mata ido shi uban gayyar kuɗin ne ya watsa mata, wanda duk muka zaro ido waje muna kallon wannan wulakancin. 



Umma tace, "nagode sosai fa"  Sannan ta dubi tace "Inno mun gama shirya wa ga su Amrah can suna fitar da kayan mu ina ga ma sun kusa kwashe wa dan basu ɗaya bane harda yaran, unguwa zamu tafi duk wanda muka yiwa laifi to yayi hakuri". 


Babu wanda yayi magana daga cikin su, Umma ta dubeni tace, "Ke! kuma ki tashi ki baiwa masu gida gidan su ki fito ga mota can tana jiran mu". 


Kafeni da ido Umma tayi wanda a tarihin rayuwa ta shine na farko haka zalika a tarihin rayuwa ta wannan shine maganar da Umma ta taɓa yi mani a cikin mutane jikina sai rawa yakeyi, ashe bani ɗaya ba, duk wanda yake gurin yasan Umma yau anyi mugun cika ta, dan ita sam bakajin bakin ta koda kuwa kashe ni za ayi a gidan mu kuma bata taɓa yi mani magana ba, koda a cikin ɗakin mune ballema acikin mutane. 


Tsaye tayi, har sai da ƙanwata Amrah tazo a gaban Inno ta tace, "Inno bani ɗan albarka na nan gurin abun sona farin cikin rayuwar mu wannan yaron da kike gani ya shige a cikin zuciya ta, yaron nan daga gani mujaheed ne dan zaiyi taimakon addinin Allah da taimakon mutane, shi daga ganin sa ba zaiyi aiki da jahilci ba kuma, bazaiyi aiki irin na jallai ba". 



Dariya Inno da Yaya sukayi dan kowa yasan Amrah ta sakar wasu kawu Bala magane, Inno tace, "amman kuwa kin zaba masa sunan da ya dace dashi dan Allah ki riƙa kawo mani shi ina son shi wallahi har cikin raina, Allah sarki Allah ya rasa rayuwar musullunci" amin aka faɗa. 


Yaya tace, "kice dai a riƙa kawo muna shi duk da muma cikin satin nan zamu bar gidan nan amman ni kun san gidan da nake dashi wanda na bada haya a can zan koma, dan Allah ku riƙa kawo muna shi Allah ya rayasa Allah yayiwa rayuwar sa albarka Allah yasa ya zamo farin ciki a garemu baki ɗaya amin ". 



Amrah ta ansa ta goya shi,Nusaiba  na shigowa ta raɓa kowa tazo ta kwashe kayana da suke ɗakin Inno ta rufe jakar ta riƙa hannu na tabi ta gaban Umma dani muka fita, Inno ta share hawayen idon ta, tazo ta anshi kuɗin wanda kowa ya kasa ɗauka ya bata, ita ta ɗauka ta baiwa Umma, Umma ta ce, "to mu yafi juna Allah yasada mu da alkawarin sa"



Fita Umma tayi ta duba ɗakin taga babu komai tayi murmushi ta juya zata fita Inno da yaran ta, da Yaya da yaron ta suka rako Umma har gurin mota, Inno ta dam ƙawa Umma kuɗin wanda ta ɗaure da leda, Umma ta amsa, ta shiga cikin motar,  mu kuwa  a lokacin muna ciki, ga mutane ƙofar gidan kamar rana duk kuwa da cewar magriba ce, sai da motar ta tashi muka ɓacewa ganin su . 



Umma ce ta kalli Amrah tace, "Amrah kin sheda masa inda zai kai mu ko? "


Amrah ta goge hawayen da takeyi tace, Umma na sanar dashi amman Umma kina ganin su kawu Habu zasu yarda mu zauna a gurin su kuwa? Kin fa san halin sa da zafin zuciya ga rashin fahimta Umma ni wallahi tsoro nake ji". 



Umma dai kallon su kawai tayi ba tare da tace dasu uffan ba. 


Sai ƙarfe tara na dare muka ƙarasa unguwar su kawu Habu sai gaban mu ke faɗuwa, dan kowa a tsorace yake, sauka mukayi aka fara sauke muna kayan mu harda mai motar, Umma ta bashi kuɗin sa, muka shiga cikin gidan a tsakiyar gidan muka sami kowa da kowa, Kawu yace, "ina fatan dai ba cikin nan ne aka haife ba, kuma kuka dawo mani dashi gidan nan ku raine shi a gidana ba". 



Shiru Umma tayi kafin ta ce, "kayi hakuri kawu, ka barmu mu kwana anan da safe zamuje mu nemo gidan haya sai mu koma a can kaga dare ne yan zun ". 



Matar shi tace, "haka kawai zaku kwaso ƙafar ku harda kayan ku da shege ku zo muna gida cikin dare ai dai kwana ɗaya kika roƙa kuma shi zakuyi ehe! ". 



Umma dai batayi magana ba, ɗakin aka bamu ɗaya har kayan mu, nidai ban samu na rimtsa ba dan nasan nice duk silar faruwar hakan, Umma ce naga ta tashi tayo alwala ta fara nafila, da addu'a yaron ne ya motsa wanda yake kwance a jikin Amrah da sauri ta tashi ta kawo mani shi tace, "dan Allah bashi yasha kin ga yaron akwai hakuri". 


Ansar shi nayi na fara gir_giza shi amman kukan yakeyi fitila Umma ta hasko mani, tun da naga hakan nasan mi take nufi, gyara shi nayi na soma bashi, kawai muka jiyo masifar kawu Habu da matar sa, suna faɗar "wannan wace irin jaraba ce haba ya zaku sakawa mutane hawan jini ku hanasu kwana?  Nifa wallahi idan naga kun cika damuwar mu muda moƙwota sai dai muce kubar gidan nan ". 



Shikuwa bawan Allah harma ya koma bacci, suka gaji da masifar su sukayi koma ɗakin su. 


Tun da aka fito sallar Asubahi, muka gaisa da mutanen gidan muka fita ko karya wa bamuyi ba, muka fara neman gidan haya, har ƙarfe tara na safe bamu samu ba kuma bamu ci abinci ba, gashi ina jego, ganin hakan ne yasa Umma ta sai muna ƙosai da koko muka zauna Zauren wani gidan muka ƙarya muka tashi muka shiga yawon neman gidan haya, ga baki ɗaya sai da muka bar unguwar sosai zuwa sha biyu na rana Allah yasa muka dace kuma gidan babu kowa cikin sa ɗaki biyu ne da kichin da bayi, shekara ɗaya dubu, talatin haka muka biya anan aka barni nida yaron suka tafi gurin kwaso kayan. 


Zaune nake na buga uban tagumi ina kallon yaron wanda nake jin yan zun ina kaunar sa, to amman ya ya rayuwar mu zata kasan ce ne nida yaro na, zuwa gaba, har yaushe ne zan saka Umma na da yan uwana farin ciki?. 



Jin ana shigo da kaya yasaka ni dawowa hayyaci na, kawai na tashi na baiwa Nusaiba yaron ta ansa ta goya sa, ni kuma na taya saka kayan Umma ɗaki ɗaya muka saka mata gadon ƙarfen ta da da wadurof din ta da mu kuwa a ɗaya ɗakin muka saka gado ƙarami da katifa ɗaya, waje kuma aka saka durom naruwa da tukunyar ƙasa. 



Kichin Umma ta shiga ta gyara komai da komai, kayan miya ta fito dasu zata fara jajjage da sauri Amrah ta ansa ta ce, "haba Umma kibar shi muyi mana ai ke ya kama ta ace kin futa kawai". 



Umma ta ce, "naga kun gaji da yawa kibar shi kije ku futa, taliya ce kawai zan dafa muna". 



Dariya Nusaiba tayi tace, "Umma Allah ya raba mu da fu kina aiki muna zaune muna kallon ki da ran mu da lafiyar mu". 



Dole Umma tayi dariya wadda rabon da muga dariyar ta tun kafin cikin jiki na ya bayyana sai yau dan haka kowa sakin baki da hanci ya yi yana kallon Umma, itama sai ta daina dariya ta zo ta wuce ni ta shiga cikin ɗakin ta ɗauko tabarma ta shimfiɗa ta zauna, tashi nayi na shiga cikin kichin ɗin da kaina na fara gyara itace zan fura wutar Nusaiba tazo ta ansa tana faɗar kai Anty su waye suka taɓa barin mai jego na aiki, ai mai jego sarauniya ce ko ya ki ka ce, Anty ƙarama? ". 



Dariya Amrah tayi tace, "wato dai ba zaki sauya mani suna ba ko? "



Haka dai suke ta bidirin su abun su, suna gama dafa taliyar suka ɗora mani ruwan wanka, suka zuba wa Umma nata mu kuwa suka zobo muna guri ɗaya abincin muka ci sai da muka ƙoshi Amrah da Nusaiba suka fita suka nemo ganyen bedi suka kawo mani suka kwashe mani ruwan wanka naje nayo kamar yanda su Inno suka fara yi mani, cikin zuciya ta nace Allah sarki ashe dai su Inno gata ne suke yi mani da suke yi mani wankan nan yan zun gashi nice nake yi da kaina. 



Koda na fito Amrah ce na sama tana yiwa yaron wanka Nusaiba na ce mata, kiyi masa a hankali mana kada kije kisa sabulu ya shigar masa, ni wallahi inda nice nafi ki iyawa dan nataɓa yiwa Anty Basira wankan saifullah so da yawa". 



ai kuwa nikam dariya na zauna ina yi masu bayan sun gama yi masa wankan aka zo gashin chibi, Umma najin ihun yaron da sauri tasa hannu ta anshe sa ta fara faɗa, "kashe ɗan mutane zakuyi ne waye yace maku da zafi sosai akeyi, dallah ku tashi ku bani guri nayi masa ni bana son hauka! ". 



Ba niba hatta Amrah da Nusaiba sakin baki sukayi suna kallon Umma ni kuwa harda murza ido na keyi, fita iskan mu Umma tayi, kamar ba san mun tsare ta da ido ba, gashin tayi masa har sai da yayi bacci Amrah tace, "Anty kayan da zamu sakawa yaron nan fa?  Dan naga kamar kala biyu gare shi "yan gobe suna". 



Shiru nayi ban ce da ita komai ba, Umma ce ta tashi ta buɗe akwatin ta, ta ɗauko kayan jarirai har kala biyar kuma masu kyau da zanen goyo na saƙa da kayan sanyi saiti. 




Cikin farin ciki Amrah ta kwaso kayan tana tsalle, ita kuwa Nusaiba sai rawar jiki takeyi zata saka mashi kayan da sauri Amrah tace, "nifa zan shirya masa bara na ɗauko masa pampas din sa wanda na ajiye masa". 



Itama cikin kayan ta ta ɗauko pampas da wando na jarirai masu yawa da swafa da fula harda takalmi, itama Nusaiba tace ni dai bari ku gani, cikin kayan ta taje ta kwashe su, ta fara ɗauko mayukan shafawa da powder dasu turare ta kawo ta ajiye a gurin Amrah tace, "nima ga nawa kayan Baby boy a gyara muna abun mu mukam muna son shi". 



Ni kam cike nake da mamaki ba kamar Umma da zan iya cewa wannan shine karo na farkon da ta taɓa yin abun da faran ta mani rai sabo duk wani abun da yake da dan gata da farin ciki na Umma bata taɓa yin saba, ni ada nama ɗauka Inno ce ta haifeni sai da Inno tayi da gaske san nan na yarda da cewar Umma ce ta haife ni dan ko ɗin kin sallah bata yi mani amman Amrah da Nusaiba da Mariya 'yar ɗakin Inno dan kala biyar_biyar sai tayi masu harda takalmi kala ukku, ni kuwa Inno tayi mani ɗaya sai kuma idan Allah yasa mutanen arziki sun yi mani dan haka duk kowa ya fini yawan kayan ado, wata rana kuma idan antashi yin ankon biki idan ta kai ayiwa su Amrah ɗinkin biki, nike zuwa na anshe turmin zane ɗaya, idan taji sai ta kaiwa Inno ƙarata Inno kuwa tace, tayi mani magana da kanta mana, to anan ne nake samu nasara akan ta. 




Umma ce ta gyara masa tayi masa shiri mai kyau wanda abun ya yi ta bani mamaki, Umma kuwa basu yaron ta yi suka ɗauka suka fita, nima ina gama gyara wa, na fita cikin "yan uwa na ina kallon su na ce "Amrah Nusaiba " kun kam mala jarabawar ne ko kuwa?. 



Amrah tace, Anty nifa na ajiye 'kara tun bokon nan kamar yanda kika ajiye jss 2 kallon ta nayi cikin jin haushin maganar ta nace amman kuwa bakiyi mani adalci ba, ai ni kinga tawa ƙaddarar ke nan, dan haka dan Allah kuyi karatun nan kada ku manta burina bai wuce nayi karatu mai zurfin gaske ba boko da Arabi amman ku dubi yanda na kasan ce, to dan Allah kuyi hakuri kuyi karatun nan kunji!?. 



Shiru duk sukayi cikin tausayin halin da na tsinci kaina, sukayi mani alkawarin yin karatu. 



Haka dai mukaci gaba da rayuwar mu, a can makaranta su Amrah suka jiyo maganar Auren da za'ayi nasu Yaya Auwal dasu Surajo dasu Shamsiyya da Zuwaira dasu Balkisu wanda duk suna gaba na wasu shekaru biyar suka bani wasu shekaru ukku, bikin wanda aka ce a sanar dani kada na yarda naje gidan naɓata masu biki, 'yan gidan mu suka faɗawa mutanen gari kuma da Mariya da kanta tazo har gidan mu ita da wasu ƙannen mu, suka sanar damu wannan maganar. 



Ita dai Umma ta yarda taje gidan ita dasu Amrah inda suka dawo gidan kamar wanda aka koro. 



Hawaye na gani a idon su Amrah cikin tashin hankali na buɗe baki zan tambaye su, kawai naga Umma itama kukan takeyi, da sauri naje ina tambayar Umma hawaye na zubar mani amman Umma bata ce dani komai ba, tabbas nasan babban abune ko miye, daket Umma ta buɗe baki tace........ 





*Comment And share* 




*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


💐💐 *NARJEESAH* 💐💐



_*RUBUTAWA *_ 🖊

*NANA KHADEEJATU*

      *_UMMU IHSAN CE_*


*YA ALLAH KAJIKAN IYAYE NA KAYI MASU RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SU KA SANYA SU DAGA CIKIN DAUSAYIN ALJANNA SU DA DUK KANNIN MUSULMI BAKI ƊAYA AMIN YA ALLAH*


*_BISMILLAHIR RAHMANIN RAHIM_* 


                  *5&6*


➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿


Umma ta ce, "kada ku yarda naji wata magana ta fito daga cikin bakin ku har sai idan naso hakan, wannan umarni na ne! " kawai ta shige cikin ɗakin ta, ta saki labule. 


Tunda mukaji umarnin Umma sai duk jikin mu yayi sanyi babu wanda ya sake cewa komai tashi nayi nima kashige cikin ɗakin mu na kwata, ina nazari, tabbas duk abunda ya saka Umma kuka baƙara min abu bane, amman kuma Umma ta hana nasan ko miye wannan abun, kai koma miye babu shakka duk abunda ya faru nice sanadiyar komai ya Allah kadube mu. 




Duk yinin ranar bamu da wata walwala kowa a cikin damuwa yake har aka kwana biyu,  yau muna zaune muna fira ni dasu Amrah Nusaiba na goye da yaron yana bacci, sallamar su Inno ce ta katse mu, cikin farin ciki muka tarbe su Inno da Yaya da Mariya, Umma ce ta fito cikin ɗakin ta, tazo ta, tarye su da farin ciki, tabarma aka shimfiɗa masu suka zauna na kawo masu ruwa Amrah taje maƙota ta siyo masu zuɓo ta kawo masu, bayan sun sha aka gai da tambayar ya akaji da hidimar biki suka ce Alhamdulillah angama lafiya taro ya tashi sai dai abunda ya faru ne wanda basu ji daɗin saba. 



Umma tace, "ai komai ya wuce". 


Da sauri nace, Inno dan Allah miye ya faru a ranar dan Umma ta hana kowa ya sanar dani, sun barni cikin duhu da tunanin miye yake faruwa, bana bacci ina cikin damuwa, duk da nasan da cewar ba kowa bane ya janyo wannan matsalar ba sai ni. 



Inno ta ce, "ai koni ma ba zan iya sanar dake komai ba, da kuma wanda sukayi abun kasan cewar nafi kowa sanin halin ki Narjeesah idan kika san ko su waye da abunda akayi ba zaki ɗauka ba, kasan cewar ki mafaɗa ciya, daman cikin da kike dashi ne yasaka ki yin sanyi amman yanzun nasan zaki iya fafatawa da kowa". 



Yaya ta ce, "tabbas hakane Narjeesah zaki san wani abun amman banda wani abun, ranar a unguwar mu anyi faɗa sosai har makarantar islamiyar ku inda akace malan Abbakar shine ya yi maki ciki kasan cewar sa yana sonki tun kina ƙaramar ki, kuma Baban ku ya sani amman yace, sai in kinyi hankali kin ce kina son sa, to ganin irin yanda idan baki zo makaranta ba yake zuwa ya sakaki a gaba kije makarantar shine aka ce shine ya yi maki cikin yaron nan, shi kuma ya ƙaryara rigima har aka koresa a makarantar duk da kuwa kasan cewar mahaifin sa shike da makarantar". 



Hawaye naji suna zubo mani nace wallahi Inno bashi ne yayi wannan cikin ba kuma wallahi ko kalmar kebewa a wani gurin, ko a makarantar bai taɓa furta mani ba. 



Inno tace, "ana cikin wannan rigimar ne, wani mai mota yazo daga ganin sa anga dan shaye_shaye to shine ya ɗauki hankalin kowa inda ya ce, shine wanda ya yi maki cikin yaron nan kuma yazo ya anshi abun sa ne, saboda duk lokacin da ku ka tafi makarantar boko shike zuwa yana ɗaukar ki yana zuwa gidan sa dake har sai da kika ɗauki cikin sa, kuna tare shine ma yace ki zauna ki raini cikin zai Aure ki, to yan zun ya fasa Auren ki yaron kawai yake so ko kiba shi yaron da arziƙi ko kuma yazo da "yan sara suka sai dai su kashe ki da duk wanda yake tare dake su ɗauki yaron! ". 



Da sauri na tashi tsaye na fara ja da baya ina zubar da hawaye nace wallahi Inno da Yaya, wannan ba shine uban yaron nan ba, wallahi ba zan bada shi ba! . 



Inno da Yaya suma suka tashi tsaye suka haɗa baki gurin fad'ar, "to waye uban yaron nan tunda kin ce wannan bashi bane!?  Kuma kina nufin kin san inda uban yaron yake ke nan! ". 



Nace wallahi wannan ƙarya yake yi maku bani da wata alaƙa dashi, mutum nan ɓarawon yara ne kada ku yarda dashi. 



To wane ne uban yaron nan tunda kin san shi kuma a ina yake kuma ya ya sunan sa?  "Inno ce" ta jero mani wannan tambayoyin da suka riki tar dani a take na dabur buce na rasa ma wace irin amsa ce zani bata, gashi duk ankafe ni da ido. 



Sai da na haɗiye yawu masu ɗaci ga uwar zufar da take , zubo mani ta kowane saƙo na jiki na  nace, a gaskiya duk bani da amsar da zan baku daga cikin wannan tambayoyin amman gaskiyar zance "wannan mutanen ban taɓa sanin sa ba! "



Inno tace, to ya zama wajibi tsakanin yau ko gobe ki sanar damu Baban yaron nan, ko kuma kubar garin nan, sati ɗaya mutumen ya bada zai dawo kuma dawowar sa ba abu bane mai sauƙi dan da alama zai iya aikata duk abunda ya faɗa saboda a tare yazo da maso shaye_shaye harda takubban su"



Daɓas na zauna a ƙasa na fashe da kuka kamar raina zai fita, suma su Amrah kukan ne sukeyi sosai, Umma dai bata ce uffan ba, har su Inno suka dawo a kusa dani suna lallashin mu, kallon Inno nayi nace, "Inno dan Allah ku anshi adireshin sa da number sa ku ajiye mani ita har na tsayin wani lokacin". 



Insha Allah suka faɗa, Inno ce ta kawar da wannan kukan ta ce, yo ni wannan iyayen na daban kuke kuna nufin ba zaku bani maigidan ba na ɗauke sa, ba har sai na roƙa ko? ". 



Dariya mukayi, nidai shiru nayi Nusaiba ta sauke shi ta bata shi tace, "gashi nan Inno bama rowar ɗan baiwa". 



Dariya sukayi Yaya tace, "ni kuwa wane suna ne kuka sakawa angon namu dan naji har yanzun baku faɗa ba, kodai sunan bai da daɗi ne ace yaro wata biyar bamu san sunan shi ba? "



Dariya mukayi, "Nusaiba tace suna kam mai daɗin gaske sunan hafizai". 


Inno tace, "um kaji iyayen "ya"ya da kauɗin tsiya, wane suna ne wannan? ". 


Amrah tace, "Shuraim ke nan Inno yaro hafizi ga daɗin murya". 


suka haɗa baki gurin fad'ar, "kai masha Allah, Allah ya raya muna Shuraim yaro mai suffar larabawa da sunan larabawa abu ya yi kyau". 



Mariya ce ta anshe sa, tana kallon sa, tace, "kai Inno wallahi wannan bai kama da wannan ƙaton mutumen mai ƙaton hanci kuma gashi baƙin sa ya yi yawa kawai dai ɓarawon yara ne, a gaskiya a gudu da yaron nan daga garin nan ma baki ɗaya, saboda naji ana raɗe_raɗin cewar cikin dare za'a nuna masu gidan nan ni wallahi yaron nan tausayin sa, nakeji! "




Kallon_kallo muka shiga yi nida su Amrah cikin damuwa Amrah tace, "Insha Allah babu maiyi sai Allah, burin wasu ba zai cika ba"



Sai marece su Inno suka tafi, Umma ce taja Nusaiba suka fita, Amrah ta sameni a cikin ɗaki kwance ina tunani ta dafani, na ɗaga ido na kalleta na tashi zaune tace, "Anty nifa a tsorace nake da maganar da naji su Mariya na faɗa nifa ina ganin zan baiwa Umma shawara, ne yau mu nemi gidan da zamu je mu ɓuya a can". 



Kallon ta nayi, nace "Amrah "duk nice na janyo maku shiga cikin wannan hatsarin nifa ina ganin zan ɗauke yaron nan nabar garin nan gudun kada azo kashe ni a haɗa daku duka na bani, nayi sanadiyar mutuwar mahaifiyar mu daku kan ku, kuma aje a maida yaron nan wani irin mugun mutum". 



Rufe mani baki Amrah tayi ta ce, "Anty dan Allah hankalin ki ya dawo jikin ki, ai duk inda kika saka ƙafar ki muna sai mun saka dan haka zamu gudu tare mu tsira tare". 



Koda Umma ta dawo, ita da Amrah har mun gama abincin dare mu gyara ko ina, sannu da zuwa mukayi masu. 


Da dare bayan munci abinci muka rufe gidan tare dayin Addu'oi sosai muka ɗauro alwalar kwanciya muka rufe ɗakin mu nida Amrah, Umma da Nusaiba suka kwanta ɗakin Inno suka rufe, addu'a sosai mukayi, kafin mu kwanta na shafe Shuraim da addu'a wanda shi tuni yayi bacci. 



Can cikin dare muka fara jiyo, motsin ana shirin cire muna ƙofa ta shigowa cikin gidan, ai kuwa duk muka tashi zaune a tsorace addu'a muka somayi, ai kuwa dukan ƙofar akeyi da ƙarfin gaske kuma da makamai ake dukan ƙofar da sau muka diro ƙasa, nasa hannu, na ɗauke Shuraim na goye shi nasa wani zane na taresa dashi, sai muka lallaba, a hankali muka buɗe ƙofar ɗakin mu muka fito anan ita Umma suka fito sai jikin mu ke rawa, addu'a duk wadda tazo bakin mu ita muke yi. 



Gashi har ƙofar ta fara alamar da kuwa, ta maƙotan mune aka saƙo tsani, da sauri muka ja da baya dan mun riga da mun san tamu tazo ƙarshe, hannun Amrah naja da niyar mu koma cikin ɗaki mu rufe amman kuma idan mun gudu su Umma fa, duk mun ruɗe dawowa gurin Umma mukayi nace, Umma dan Allah ki yarda mu koma cikin ɗaki ɗaya, mu ruf...  Ban kai ga ƙarasa wabane, wasu maza guda biyu ne suka diro ta inda aka saƙo tsanin. 



Zaro ido mukayi waje da sauri suka nufo mu mukam mun sadaƙar, har gaban mu suka tsaya cikin rawar jiki suna yi suna kallon ƙofar mutumen ya ce, "kuzo dan Allah mu taimakeku, kafin su shigo ciki dan sunada hatsarin gaske, akwai wanda zasu tarye ku a waje! "


 Da gudu muka nufi gurin dan Amrah ta gane mutumen, naji tace, " to Baban Ahmad"


Abu ga tso wai mune da hawan tsani wanda ko amafalki ban taɓa tsammani haka ba, Umma aka fara ɗorawa kamar walkiya ta haye saman katangar gidan wasu suka taryeta sai, su Amrah suka turani, ni kuwa ina cewa ku fara fita, mutane suka ga zamu saka har a samemu kawai wannan ɗaya mutumen ya ɗagani sama ya taka matattakar tsani nin ya fitar dani, aka anshe ni sai Nusaiba sai Amrah sai mutanen suka ɗauke tsanin suka diro mukuwa tsuru_tsuru a cikin gidan kawai suka bud'e muna wata ƙofar muka faɗa wani gidan inda matan gidan suka maza suka tura mu wani ɗakin suka rufe, Shuraim ne na sauke da sauri gashi ta ko ina jikina rawa yakeyi. 



Fitila aka kunna, Allah sarki bawan Allah idon sa biyu yana kallo na, zama nayi a gefen matar dake cikin ɗakin na bashi mama, ya fara sha, matar tace, "Allah ya ƙara tsare gaba ". 



Mukace amin, anan muka zauna sai da asubahi aka buɗe kofar ɗakin muka fito, mukayi alwala mukayi sallah tare da godiyar Allah da ya tseratar damu dan wannan ikon Allah ne. 



Sai garin Allah ya waye sannan muka fito gidan muta yi masu godiya wadda bamu san irin ta ba, a ƙofar gidan muka riski su Baban Ahmad mukayi masu godiya, suka ce babu komai ai yiwa kaine, wallahi wannan mutanen miyagune, suka bamu shawarar ya kamata mubar gidan. 


Tun a ƙofar gidan ne zaka fahinci cewar da sun same mu a gidan nan da sunga bayan mu dan ƙofar sai an sauya wata. 



Cikin gidan duk sun har gitse  muna kaya amman basu ɗauki komai dan babu abun ɗauka a gidan. 


Umma kam fita kawai itada Nusaiba kamar jiya, mu kuma muka gyara gidan da ɓarnar da akayi muna, muka ɗora abun karyawa koda muka gama Umma bata dawo ba zama mukayi muna ta jimamin abunda ya faru a daren jiya. 



Umma ce ta shigo tare da wasu mata suka shiga cikin ɗakin ta suka fito, suka dawo cikin d'akin mu suka fita Umma ce ta dawo da kuɗi a hannun ta masu yawa, kallon ta mukeyi nida Amrah, sanin cewar idan nayi magana Umma ba zata bani amsa bane ya saka na ƙyafaci Amrah, da sauri Amrah tace, "Umma kuɗin miye haka? ". 



Bata kuɗin Umma tayi Amrah amsa, Umma ta ce, "na sayar kayan ɗakin mune harda katifu kuma kwanonin sai a zuba su a buhuwa, yau nake son mubar garin nan saboda hankali na bai kwanta da wannan mutanen ba dan nasan zasu iya sake dawowa, yauma Allah ne ya kawo muna ɗauk,  kuma kunji mutane sun bamu shawarar mubar gidan nan da wuri, gudun samun matsala, gashi ana ta sanar damu cewar yau kada mu kwana a gidan nan, shine ni kuma na ce  abunda zamuyi kawai shine yau bar garin nan". 



Ajiyar zuciya muka sauke a take muka hau shiri, Amrah na goye da Shuraim har muka gama komai muka rufe gidan muka baiwa maƙota makullin saboda wanda zasu ɗauke kayan su idan suka kwashe idan ansamu wanda zasu zauna sai basu su ƙarasa wata bakwai wanda ba muyi ba. 



Ƙarfe biyar na marece muka isa tasha, mudai Umma muke bi duk inda ta dosa, motar kaduna muka hau ta biya kuɗin sai da Umma tayo muna siyayya muka ɗauki hanya, kasan cewar duk bamu san gurin waye zamu je b, amman bana jin zafin wannan tafiyar, har su Amrah fuskar su a sake take, Shuraim ya hannu na, yana bacci saboda su Amrah a matse suke, shi yasa na anshe sa. 




A gaskiya tafiyar dare babu daɗi ko kaɗan, zafi ne ya dami Shuraim ya saka muna kuka na rasa ya zanyi masa, Amrah ta amsa Umma ta ansa Nusaiba ta ansa adawo mani dashi, ni kuma na rasa miye zanyi masa ma wanda zai daina wannan rigimar. 



Wani bawan Allah ne da yake a jikin glass ɗin motar yace, "baiwar Allah kodai zafi ne ke damun sa,na buɗe maku glass ɗin kaɗan gudun kada mura ta kama shi? ". 



Godiya nayi masa ai kuwa yana buɗe windon tuni ya koma baccin sa, ajiyar zuciya muka sauke, sai da naji iskan yayi yawa nace ya rufe muna mun gode. 



Biredi da lemo muka sha da tsire,tafiya mukeyi tun daga jigawa dutse zuwa kaduna, jigawa dutse ma a Kauyen gumil dake cikin garin jigawa. 



A tasha muka sauka muka da misalin ƙarfe shidda da rabi na safiya. 



Wata unguwar mukaji ana faɗa unguwar kawo, a can muka sauka, Umma ta tsayar damu taje tayo tambaya aka yo mata kwatance, tayi godiya tazo tace, muje, cikin ikon Allah, bamu wani sha wahala ba, muka isa gidan da Umma ke nema, da sallama muka shiga gidan matar ta amsa ta fito, tana ganin Umma ta washe baki tana faɗar lale_lale maraba da zuwan ku haba, Aysha yau kam kin wanke tarin laifin ki a gurina, maraba ku ƙaraso daga ciki mana". 



Cikin falon ta muka sauka kayan mu muka baro su a tsakar gidan, Allah yasa da nefa duk sai muka baje a saman ledar tsakar ɗakin muna futuwa, a take taje ta kawo muna abinci da nasha, nida su Amrah ne mukaci muka ƙoshi, ba mayi wani baƙunta ba, Umma ma haka, dan ma ina zaune a gurin bata wani saki jikin ta ba Shuraim ne ya motsa ya fara kuka, Nusaiba ta sauke shi ta bani, matar ta kafe ni da ido musamman ma da taga na fara shayar da yaron riƙe baki tayi ta kafeni da ido. 




Ganin hakan ne ya saka Umma tambayar ta buta zatayi alwala, da sauri matar ta, tashi ta kawai wa Umma ruwan wanka tace, ta fara yo wanka tukun na. 



Murmushi Umma tayi taje gurin wankan matar ta ce, "Narjeesah wai ku kuwa har yanzun baku daina yin Aure da wuri haka ba?  Kuma fa naga mahaifin ku baya da wannan ɗabi'ar kodan anga baya raye ne shine akayi maki Auren wuri? ". 



Kallon_kallo muka shiga yi mu ukku, Amrah ce, "eh ke dai bari kin gafa da ƙurciyar ta anyi mata Auren wuri shine fa mijin yaje ya shawo iskan sa, yazo ciki wata biyar ya sake ta a gaban mu harda su Inno kuma saki ukku, shine ta reni cikin gidan mu, wai yan zun da yaga yaron ya fara wayau wai shi sam bai san lokacin da yayi sakin ba, ina mai baki labari zarya kullum da safe da rana da dare, shine wai kowa sai ta koma ko kuma tabashi ɗan sa". 



Wani uban ashariya matar ta saki, tace, halan ce masu akayi bata da gata ne, kodan sunga Aysha tana share tane, ai Aysha dama ita kunya ne da ita da kawaici ai kuwa tunda kuka baro masu garin nan ba zaku koma ba wallahi bari uwar taku tazo, to wai ma ke da nasani uwar masifa da surutu ya ya akayi kika dawo haka? ". 



Dukan mu ta bamu dariya, sai da muka dara nace, "Mama ni wallahi sai yanzun ne na gane ki ashe wai gidan ki muka sauka". 



Dariya tayi tace, "ja'irar yarinya, idan mai gidan nawa ya ƙoshi bani shi". 



Shuraim ɗin na bata, Umma kuwa tun lokacin da Amrah take, sheƙa ƙarya ta fito riƙe baki tayi tana mamakin a ina Amrah ta iyo ƙarya haka, shigowa cikin ɗakin tayi, nima naje nayo wankan su Amrah ma duk sunyi wankan muka ranka sallolin da bamuyi ba, mamar ce tayiwa shuraim ɗin wanka, mukam bacci muka ranka har shuraim ɗin, Umma kam babin firar yaushe rabo suka dasa. 



A gaskiya zaman gidan Mama Luba akwai farin ciki dan ɗaki biyu ta bamu Umma ɗaya mu ɗaya, satin mu biyu a gidan ta baiwa Umma shawarar mufara kasuwan ci, to wace sa'na arce zamu fara?. 



Tace da Umma "ko abinci ne ki fara sai dawa inada shago a kusa da shagon da nake ɗinki, mai sai da abincin tayi Abuja ne dan haka ke zaki iya, dan Allah Aysha kada kice ba zaki iya ba, saboda yaran ki matane, da suje su siyar da abinci ko wani abun daban gwara ke kiyi hakuri kiyi wannan sana'ar". 



Shiru Umma tayi tana, tunani zuwa can tace, "babu komai na yarda zanyi nasan duk abunda kika sani wanda zai sa naci gaba shi kike bani shawara akai baki taɓa bani mummunar shawara ba, dan haka na yarda ɗari bisa ɗari". 



Mukam duk jikin mu yayi sanyi bare ma lokacin da muka gano wurin ranar da Umma ta fara yin abinci a gurin, gidan muka dawo muka saka kuka, kamar wanda akayi wa mutuwa, a ranar koda suka dawo gida sam basu gane kan mu ba. 



Babu wanda yabi takan mu dan sun fahimci komai, Umma ce naji tana faɗar Alhamdulillah kasuwa tayi kyau , sai farin ciki sukeyi. 



Da haka dai har muka saba itama Umma ta saba, cikin ikon Allah Umma da tayi abinci nan da nan ya ƙare, sai Mama Larai ta baiwa Umma shawarar itama ta kama gidan haya dan itama haya takeyi Umma bata kawo komai ba, takuwa yarda, a haka har Umma ta samar muna gidan haya, amman nesa da unguwar da Mama Luba take. 



Umma kam, sai sam barka a da kuɗin abincin ta mukeci muke sha, kuma muke biyan haya hankali kwance. 



Cikin ikon Allah har muka shekara biyu a garin shuraim na daɗe da yaye sa, shegen wayau ne dashi shekarun sa, biyu da wata shidda a yanzun amman idan ka ganshi zaka ɗauka ya shekara ukku a duniya sai uban surutu. 



Umma ce mu kaga kwana biyu bata dafa abinci ba, shine muka kasa hakuri tunda munga lafiya lau take, amman da alama tanada damuwa gashi ni ban isa in san damuwar ta ba, zaune muke da Amrah da Nusaiba na ce, "Amrah miye yasaka ba zaki tun kari Umma ba kiji damuwar ta, tunda kin san nice babba amman bani da wannan ikon dan Allah kije ki tambayar muna ita ". 



Tashi Amrah tayi ta sami Umma zaune ta doka uban tagumi shi kuwa shuraim yana zaune a ƙafar ta na wasa da motar da ta siya mashi, da remote a hannun sa. 



Amrah tace, "Umma dan Allah mike damun kine?  Kuma kwana biyu bakiyi abinci ba lafiya dai? ". 



Ajiye zuciya Umma ta sauke tace, "Luba ta hana ni ɗan makulli tace, itama abincin ta dawo wa saboda ɗikin da takeyi babu kasuwa amman taga siyar da abinci akwai kasuwa harda riba, kuma tace kada mu sake zuwa inda take gashi na kashe kuɗi na, nayo cefane, yan zun ya ya zamuyi ne, gashi wannan lokacin ne zan nemi kuɗin hayar gidan nan! "



Zaro ido waje mukayi nida Nusaiba uwa uba Amrah da take zaune ta kafe Umma da ido. 


Fitowa nayi inda muke ɓoye nida Nusaiba na ce, "Umma ni zan...... 





*Comment and share*



*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹



💐💐 *NARJEESAH* 💐💐




_*Rubutawa daga alkhalamin*_🖊

*NANA KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_* *SADAUKAR GA DUK KANNIN  MASOYANA  NA*



*ELEGANT ONLINE WRITERS*



            *7&8*


➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Umma ni zan iya fitar maki dashi a bakin titi ko ƙofar gida, tunda kema kina iya bakin ƙoƙarin ki na ganin kin ciyar damu da halak, dan haka ki bani wannan damar dan Allah Umma". 



Shiru tayi duk muka zuba mata ido Amrah ta ce, "Umma ki yarda damu zamu iya wannan aikin dan Allah, mudai kawai ki bamu dama yan zun mu soma aiki kawai". 



Nusaiba ta ce, "Umma ya kamata ki fahimci cewar baki da masoya na gaskiya idan ba muba, baki da wani ɗan uwan da zai so ganin ci gaban ki sai mu, kuma baki da wani abokin shawara wanda ya kai mu, mune kawai yafi chan chanta ki baiwa yarda da amana ɗari bisa ɗari". 



Umma kuwa ta ce, "kuje ku ɗaura girkin ni zan iya fitar da abuna kawai ni dai fatana ku koma makaranta dan ku sami ilimi domin ilimi shine farkon abunda ya kamata na koyar daku nema ba kuɗi ba". 



Sanin halin Umma magana ɗaya takeyi ne yasaka muka fita muka fara haramar ɗaura girkin kowa da abunda ya keyi, nike wanke kayan miya, Amrah ta ɗaura dafuwar shinkafa, Nusaiba ke dafuwar wake da taliya, ina gama wanke kayan miyan Nusaiba taja hannun Shuraim suka nufi gurin markaɗen kayan miyan ni kuma naci gaba da aikin da takeyi, koda ta dawo na komawa aiki na itama taci gaba da yin nata, kudi Umma ta fito dasu tace, "waye zai je sayen nama dan na kira mai naman nace ya ajiye muna na dubu ukku, sai aje a anso daga nan asiyo kayan lambu a yanka shi daga can ayi sauri a dawo". 



Kallon Umma mukeyi, Amrah ta ce, "Umma nikam yau duk a har gitse nake ba zan iya fita ƙofar gida haka ba, sai dai ko Nusaiba "



Nusaiba ta ce,"Umma kin san bana shiri da mai naman nan saboda ce mani yake nice matar sa, har mutane yake nunawa cewar Umma ta bashi ni, kuɗin Aure na kawai zai kai dan haka ni kam ba zan iya zuwa ba". 



Dariya muka saka wa Nusaiba muna zolayar ta, "aa Nusaiba kice zamuci nama sosai a gidan ki, tunda kin zama matar mai nama"



Ture baki tayi, na tashi ina dariya na wanko hannu na, na ashi kuɗin na ɗauko mayafi na, zan fita, shuraim yafasa uban ihu da sauri kowa yake kallon sa ana faɗar lafiya? Umma ta ce, "wannan yaron anyi ja irin yaro, nan mu da kake gani halan ba mutane bane ko cin yeka zamuyi ne? Da sha shancin banza". 



Sai a lokacin ne muka fahimci son yakeyi ya biyo ni. 


Dariya su Amrah keyi, Nusaiba ta ce, "jirgin yawo abun nema ya samu, to tashi ku tafi kasan halin Anty zata iya tafiyar ta, tunda kana yi mata kukan banza". 



Dariya ya saki da gudu ya ƙaraso inda nake wai kuma sai na ɗauke sa, dariya nayi na ce, "ashe dai baka shirya tafiya ba, yaro nikam da kake gani na a nan ba zan iya ɗaukar ka ba, yaro sai dai kayi zaman ka" 




Tunda yaga na juya zan tafiya ta, da sauri yazo ya kama hannu na ya riƙe muka fita yana yi masu bye_bye, aikuwa duk inda muka wuce, sai an bimu da ido, har na fara tsar guwa, a kusuwar kuwa Mai naman ne yaƙi shanye raɗa yake tambaya ta, ina matar sa, ni kuwa na share sa saboda ni kwata_kwata yanzun maza na ajiye su guri ɗaya azzalumai ne kawai. 


Ya yi ta magana yaji shiru, da yake mun saba zuwa nida Amrah da Nusaiba wata rana nida Amrah kawai wani lokacin kuma ni ɗaya shi yasa yasan hali na, dan haka bai damu ba, da share san da nake yi. 


Yana bani naman hannun shuraim naja muka nufi gurin mai sai da cucumber carrots cabbage na soya harda green beans da dai sauran su, ya wake ya yanko mani, ya zubo mani a Leda mai zane, ya zubawa shuraim lemo da ayaba da abarba yanka ɗaya_ɗaya godiya nayi masa muka fito ka suwar muka dawo gida abinci dai aka gama komai, Umma ta fita dashi cikin ikon Allah har ana nema. 



Tun daga wannan ranar ne Umma a gidan ta abincin yake ƙarewa. 


Mama Luba ce, tazo gidan mu cike da masifa wai Umma ta muna fuce ta, duk ta janye mata customer, wallahi tayi alkawarin sai Umma ta zubar da hawayen ta indai har tana cikin garin nan kuma tana siyar da abinci ". 



Kallon ta mukayi bamu ce dasu uffan ba dan ko Umma murmushi tayi bata ce da ita komai ba,har ta ƙarasa zazzaga masifar ta, zata fita Umma ta ce, "Luba saboda ke nazo garin nan kuma ke ce kika bani shawarar yin wannan abincin, banso yiba sai da kika roƙeni, kece kika bani gurin fara wannan aikin daga baya kuma kika zo kika hanani kika ce na baki shagon ki, na baki abun ki, shine kika zo yan zun har gidan mu kike futa mani irin wannan muya gun kalaman, to naji Luba ki bani nan da kwana biyu, kizo unguwar nan kuma ki bin cika a garin nan idan har kin tsinci takalmin da na bari a garin nan kije kiyi abunda kika ga dama dashi! ". 



Fuuuuu taja iska ta fita  kallon Umma mukeyi cikin mugun tashin hankali, nace, Ummmma... Kina... Nufin. Zamu.. Zamu bar.. Garin.... Garin nan ne to muje ina!?. 



Amrah ta ce, "Umma kina nufin cewar tsoron ta zamuji ne, to muje ina wai, ko zamu koma garin mune inda ake farau tar rayuwar mu!? "



Kallon mu Umma tayi ta ce, "tabbas mutun abun tsoro ne, kuma zuciya mugun nama ce, hassada mummunar abuce, kada ku yau dari zuciyar ku, saboda idan kun lura da yanda take wannan maganar sam bataji bata gani huɗubar shaiɗan ce kawai keyi mata yawo a jinin jikin ta". 



Nusaiba ta ce, "to Umma ina zamu a yanzun zun nan shike nan mu kullum cikin gudun hijira muke? ". 



 dariya Umma wadda tafi kuka ciwo tace, "Yaro yarone tabbas duk ku yara ne, kuje ku fara shiri zan zo da dillalai su saye kayan mu saboda tafiyar nan bata yuyuwa da kayan nan namu". 




Hannun shuraim taja suka fita mukam duk jikin mu a sanyaye yake, yanda Umma ta ce, muyi hakan mukayi, koda dillalai suka zo suka siya kayan har tukunyar da muke abinci dasu da katifu, suka bita kuɗin suka kwashe kayan ya ge daga mu sai suturar mu da wasu tarkace ba masu yawa ba, gurin wanda take ansar kayan abincin taje ta biya su, cike da alhini suka rabu, ta biya kuɗin da ake biyar nu na haya, ta dawo da sauran kuɗin. 



Da dare sai dai muka shimfiɗa tabarma mukayi shimfiɗa muka, kwanta duk muka kasa yin bacci sai juye_juye mukeyi, har Asubahi, muka tashi mukayi sallah, mu ka fito neman abinci, tea muka dafa muka sha muka wanke kayan muka kwashe komai muka ɗaure a buhu, muka fito da komai a tsakiyar gida duk kowa ka duba zaka fahimci yana cikin damuwa in banda shuraim dake ta haukar sa ko ince shirmen sa, daɗi Kawai yake ji yau zai hau mota. 



Sallama mukayi da maƙota muka baiwa mai gidan makullin sa, muka hau mota sai tasha, garuruwa ake faɗa mudai Umma muke bi rasa motar da zamu shiga mukayi, wani mutum ne yazo ya ishe mu da surutu, "Hajiya wallahi motar Yola bata da wata matsala dan daga ganin ku, ku mutanen Yola ne, Allah Hajiya wallahi maganar gaskiya wannan drivar ya iya tuƙi yasan takan aikin sa, dafe goshi Umma tayi ta ce, "muje malam haba! ". 



 

Dariya mukayi duk da irin halin da muke ciki, ai kuwa da gudun sa yake ɗauke buhu huwan har da akwatin mu, mu kam sai bin sa mukeyi da ido, sai da ya kwashe komai muka bisa a baya muka shiga cikin motar, kamar mune kawai ake jira, muna shiga motar na tashi, shuraim kuwa a ƙafar Nusaiba yake zaune sai surutu sukeyi, ni kuma tunda muka shiga cikin motar nan nake jin gaba na na dukan ukku_ukku, addu'a kawai nakeyi duk na zama wata irin ta daban, Amrah ce ta dubeni ta dafa ni na ɗago ido na kalle ta. 



Ta ce, "Anty lafiya dai duk naga kin sauya mani kala ba kamar yanda muka fito daga gida ba yan zun kin fi shiga cikin damuwa". 



kallon ta nayi na gir_giza mata kai alamar babu komai na rufe ido na. 


Tafiya mukeyi ina ƙara shiga cikin damuwa, sai na kauda kaina gefe na fashe da kuka, wanda ni kaina ban san dalilin yin sa ba, kawai naji muryar Amrah ta ce, "Anty na sani kuka kikeyi ni ba zaki iya ɓoye mani komai ba, amman kuma na fahimta sosai kukan zuwar maki yayi, dan Allah ki daure ki daina kukan nan haka, kafin Umma ta san halin da kike ciki ko Shuraim". 



Ɗaga mata kai nayi ba tare da na juyo ba, tafiya kawai muke yi, har muka isa garin yola koda muka sauka a tasha bamu san inda zamu ba, wata motar kawai muka shiga aka sauke mu a cikin garin. 



Goya Shuraim nayi saboda ya gaji kuma yunwa yakeji guri muka samu ajikin wata bushiyar mangwaro muka zauna a kusa da wata hanyar manya_manyan gidaje, shimfiɗa mukayi,  mukayi sallar ƙasaru, daga nan muka buɗe abinci muka fara ci amman ni sam hankali na yana gurin wata hanyar da wata motar ta fito a can gaban mu, ba wannan hanyar da muke kusa da ita ba. 



Tashi nayi na ce, "Umma" zan je wan can gurin na gani. 



Amrah ce ta ce, "muje na taka maki, nima nagano abunda kika tsare da ido tun ɗazun". 


Murmushi nayi, nace, "Amrah "kedai kice gudu kikeyi na ɓata kije nema na baki san inda zaki same ni ba. 



Dariya mukayi zamu tafi Shuraim ya taso ya riƙe mani hannu nace wallahi rigimar ka yawa ne da ita, nida zani gurin can ba wani nesa ba. 



Dariya Amrah tayi, ta riƙe hannun sa ɗaya muka tafi, hanyar nake bi da ido duk da marece ne, wata bushiyar lemon tsami na kafe da ido a take gaba na ya faɗi, da sauri hawaye suka soma zubo mani, babu tsayawa, cikin tsananin tashin hankali Amrah take gir_gizani tana tambayar miye na gani, kuka na fashe dashi matsanan cin kuka na fashe dashi, na durkusa, ƙasa ina kuka, tambayar duniyar nan Amrah tayi mani amman na kasa bata amsa shima Shuraim ganin kukan da nakeyi ne ya saka shi fashewa da kukan ya rungume ni ta baya. 




Da sauri Amrah taje ta kira Umma da Nusaiba suka kwaso kayan mu suka sameni a yan da Amrah ta barni. 


Nusaiba ma cikin kukan take tambayar mike faruwa amman duk na kasa basu amsa Umma kuwa juya muna baya tayi, har sai da su Amrah sukace idan ba zan dai na kukan ba, suma ba zasu daina ba, dan dole tasa na goge hawayen duk da basa barin zubar, na ce, "Amrah kuzo muje ba zamu kwana a nan gurin ba, duk da ban taɓa tsammani haka ba ko mafalkin hakan ba, kuma ina roƙon ku da ku zuba mani ido kawai". 



Sukam duk basu fahimci inda maganar tawa ta dosa ba, goya Shuraim nayi ina takawa a hankali kamar wadda ƙwai ya fashe wa a ciki tafe muke ta gefen hanyar muna ta wuce manyan gida jen dake unguwar, bayan wani ƙaton gidan wanda irin su basu wuce biyar ba, amman kam unguwar akwai gida je masu kyau kuma unguwar ta tsaru, ta jikin wata "yar ƙaramar hanya mukabi ta bayan wannan gidan, muka iso gaban gidan. 



Nusaiba ta ce, "kai Anty Narjeesah uban waye zai iya bamu gurin aiki idan ya kalli shigar mu da kayan mu, kuma wannan gidan ai sai masu yanka kan yara dan Allah mu rufawa kanmu asiri! ". 



Kyaleta nayi, na matsa a jikin get ɗin na durkusa, ƙasa na tona wani rami wanda yake da dutse a gurin na janye dutse, wani ɗan akwatin ƙarfe na ɗauko wanda yake rufe a cikin wata 'yar jaka, na buɗe makullai ne a cikin gurin sai da na duba da kyau na ɗauki ɗaya, naje na ɗorawa Amrah akwatin wadda ta saki baki da hanci tana kallona ko ƙyaftawa babu,  a hannun ta, na juya naje na saka ma kullin na buɗe ƙofar sai da na rufe ido na, a lokacin da gidan ya buɗe, tsaye nayi a gurin duk jikina a sanyaye yake, Nusaiba ce ta dafa ni na jiyo na buɗe ido na na kalleta zata magana nace, "Nusaiba" bana son tambaya a halin yan zun dan haka ki ɗauko kayan mu mu shiga daga ciki. 



Sanin halina da yanda nayi mata magana ne ya sakata aikata abunda na faɗa, da tsoro_tsoro suka shiga cikin gidan harda Umma ni kuwa sai da na daɗe a gurin da addu'a na ɗaga ƙafata na shiga cikin gidan tare da zubar da hawaye, rufe ƙofar nayi da makulai na ƙara gyara get ɗin gidan, motoci ne guda biyu a harabar gidan duk a lullube suke, abun duk yayi datti bana wasa ba, shuke_shuke ma wasu duk sun bushe wasu sun fito ciyayi duk ko ina in banda cikin barandar gidan. 



Wuce su Umma nayi, na dake zuciya ta, naje na buɗe ƙofar da ɗaya makulin na tura ƙofar na jiyo nace "Bismillah Amrah". 



Nice na fara shiga ina shiga na kunna wutar gidan a take gidan ya ɗauki haske ta ko ina gashi gidan babba ne kuma a cikin babban falon gidan duk kujeru ne ta ko ina ga kayan more rayuwa. 



Kowa ni yake kallo tare da neman ƙarin bayani, ni kuwa na share na ce, kuzo mu gyara gurin da zamu zauna kafin zuwa safiya kowa ya kama nasa ɗakin duk da nasan Nusaiba da Amrah ɗaki ɗaya zaku ɗauka Umma ɗaki ɗaya, ni kuma ɗaki ɗaya nida Shuraim. 



Amrah ta ce, "ok Anty Narjeesah Allah ya taimake mu baki ɗaya ". 


Kowa ya ce, "amin"


Makuli ɗaya nasake amsa gurin Amrah naje na buɗe wata ƙofar wanda gurin yake kichin ne da gurin ajiye kayan share_share da goge_goge, ɗaukowa nayi nazo na basu muka fara gyara ko ina, A cikin falon sai da muka gyara Umma da Shuraim suka zauna, a kujera, lokacin sallah ne yayi nazo muka fita gurin fanfo mukayo alwala mukayi sallah nadade ina addu'a har sai da nayi sallar isha'i natashi gurin abinci muka ci kowa da abunda ya ke saƙawa, bayan mun gam. 



Amrah ta ce, "dan Allah Anty Narjeesah yaushe ne kika taɓa zuwa garin nan kuma har kika san wannan gidan dan duk abunda kika aikata a tun daga ɗauko makullin gidan nan da buɗe sa da shigowar ki da da yanda kike komai hankali kwance da sanin ma'ajin komai haƙiƙa babu ko shakka kin san abunda mu bamu sani ba"



Nusaiba ta ce, "tabbas Anty Narjeesah akwai abunda kike ɓoyewa wanda mu bamu sani ba dan Allah ki sanar damu dan muna cikin duhu, ki fitar damu haske ". 



Amrah ta ce, "Anty Narjeesah tun lokacin da muka tun karo garin nan kike ciki ƙunci da damuwa, kuka kuwa tun a cikin mota kike yin sa har zuwa lokacin da muka shigo cikin gidan nan, miye shi wannan damuwar da kukan kuma ta ya ya kika san garin nan kika san gidan nan batare da sanin muba". 



Shiru nayi jin wannan tambayoyin masu kama da saukar kibau a ƙirjina na, kuka na saka suka ishe ni da tambayar da ƙarfi na rufe ido na cike da masifa nace masu, Gi... Da... Na... NE nan halak malak!. 



Duk suka tashi tsaye suka gir giza kai suna faɗar, gidan kine kuma? ta ya ya zaki faɗi hakan ..? 





*Comment And Share*



*Ummu Ihsan ce* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


💐💐 *NARJEESAH* 💐💐



*Rubutawa*

*NANA KHADEEJATU*

           *_UMMU IHSAN_*


*ELEGANT ONLINE WRITERS*


_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_



               9⃣⏮🔟

➿➿➿➿➿➿➿➿➿  Nace dasu babu ko shakka wannan gidan nawa ne, kuma Abu na biyu da zan sanar daku shine bazan ƙara amsa maku wata tambayar ba dan gane da wannan rikitaccen al'amarin, saboda dalilin masu yawa". 



Amrah ta ce, "Anty Narjeesah ki sani mune 'yan uwan ki baki da kamar mu a nan duniyar Umma kuma itace ta haife ki baki da wata uwa a duniyar nan wadda ta dace da tasan sirrin ki bayan ita, kasan cewar babu wani bare a cikin mu, miya sa ba zaki iya sanar da mu sirrin kiba?". 



Kallon Amrah nayi cikin matsanan cin kuka na ce, "Amrah" duk  ku kun yarda da cewar Umma ce ta haifeni amman ni har yan zun ina da shakka akan hakan, miyasa kuka damu da damuwa ta bayan wadda ta can_can ci da tayi mani irin wannan tambayoyin ko fiye da hakan sam batayi ba! "



Umma bata sona, da Umma tana sona da tun kafin na san kaina ita na fara sani, saboda miye zan sanar da sirri na ga wanda bai son jin hakan!? "Amrah Nusaiba "ku jini da kyau wallahi kamar yanda tun farkon lamarin ban sanar da kowa ba, to yan zun ma, baya ga sanar daku cewar wannan gidan nawa ne ba zan ƙara cewa komai ba, akai har sai ranar da Umma ta buɗe bakin ta, ta tambaye ni da kanta, tana son sanin gaskiyar lamarin ni kuma nayi alkawarin a ranar ko ɗigon gaskiya bazan ɓoye mata ba! "



Duk sai suka maida idon su akan Umma wadda tayi kamar bata gurin kamar bata san mike faruwa ba, gyarawa Shuraim kwanciyar sa ma takeyi. 


Gir _giza kaina nakeyi kawai na wuce su naje na kwanta akan kuje ɗaya na rufe ido na. 



Nusaiba ta ce, " Umma dan Allah ki.. Kallon da Umma tayi mata ne ya sakata yin shiru, Amrah ma ganin yanda Umma tayi wa Nusaiba itama sai taje ta kwanta, haka muka kwana kowa babu daɗin zuciya. 



Tun da mukayi sallar asuba bamu koma ba, da garin ya soma haske muka tashi muka soma gyara gidan, Amrah da Nusaiba  ganin irin dukiyar da aka zube a gidan sai da suka tsorata kasan cewar mu a gidan talakawa muka tashi kuma ƙauye, Umma dai har yan zun bata ce damu komai ba, ko cikin dorowa da zamu saka kayan mu cike muke da mamaki har dani saboda kayan da muka gani, zanen gado ya kai bakwai, kuma shaddodi atamfofi les matiriyas iri daban_daban. 


Rufewa mukayi mukaje muka ajiye kayan namu a inda suke sai dai muka gyara komai, bayi da muka shiga duk sai da na koyar dasu komai muka fito. 



Nusaiba ce taje ta koyar da Umma komai akwai ɗakin da ban buɗe ba wanda bani da niyar buɗe sa, ko kaɗan bana son kallon ƙofar ɗakin. 



Sai da muka gama, muka shiga cikin kicin ɗin muka gyara ko ina, store ne na buɗe gurin yayi uban datti sai yanar gizo_gizo, attishawa kawai mukeyi, windo muka buɗe gurin ya ɗauki haske ta ko ina kuma na kunna glub, buhu huwan shinkafa muka gani da kwalayen taliya da indomi da kus_kus da semo cike muke da mamaki wanda su kansu su Amrah sun tabbar da nima ina cike da mamaki. 



Amrah ce ta ɗauki taliya ta ɗebi indomi ta fita, mu kuma muka gyara muka goge muka rufe, girki Amrah ta ɗora a rishon da muka zo dashi, ɗaki muka nufa kowa yayo wanka sai da muka fito Amrah taje tayo Nusaiba ce ta zubo muna taliyar mu ukku, Umma ita ɗaya, shuraim shi ɗaya ai kuwa yaƙi ci ya dawo jikin Nusaiba ya zauna yana ci, sai muka gama ne muka wanke kayan da muka ɓata muka fita yawon duba gari amman bada Umma ba. 



Haka mukeyi kullum har muka saba da gidan da unguwar muka daina jin tsoron komai. 



Watan mu ukku yau a garin nan duk mun ciko mun murje sam bamu da wata damuwar hankalin mu a kwance, shuraim ya cika shekara ukku cif sai shegen surutu kamar Aku. 



Zaune muke a kujera muna labari mu ukku Shuraim yana jikin Umma yana yi mata kukan shagwaba, ita kuwa ta biye masa tana lallashin sa. 


Dariya mukeyi Amman ƙasa_ƙasa gudun Umma ta san su muke yiwa dariyar,ƙwan_ƙwasa get ɗin ne aka soma yi, muka saurara muji nan ne ko kuwa, sai da muka tabbar da nan ɗin ne muka soma kallon_kallo, Umma ta ce, "a dubo mana kukayi Zaune". 



Tashi mukayi muka shiga cikin ɗaki muka ɗauko mayafi, muka fita da gudu Shuraim ya kama hannu na, muka fita, a lokacin duk ana ƙwan_ƙwasa ƙofar buɗe wa mukayi, "yam matane su ukku a tsaye, da murmushi a fuskar su, hannu na basu nace, "Assalamu  Alaikum" muka gaisa dasu, haka su Amrah sukayi masu. 



Dariya sukayi, ɗaya tace, haba "yan uwa sai kubar mu a waje, ba zakuyi muna karramawa ba irin ta baƙin ku ba? ". 



Murmushi nayi nace, na ɗauka tambaya kukeyi ne shi yasa Amman kuyi hakuri ku shigo daga ciki". 



Tare muka shiga dasu har cikin falon suka gai sa da Umma, nace su zauna bayan sun zauna ne Amrah ta kawo masu ruwan sanyi suka sha. 


Bayan sun shane ɗayar wadda tayi magana ɗazun tace, "Suna na Aysha Umar" da sauri muka kalli juna, duk suka bimu da ido suna kallon mu. 



Tace, "sunan nawa babu daɗi ko? ". 


Da sauri nace aa keko mai babba suna kiyi hakuri zamu kira ki da Humaira dafatan bamu ɓata maki suna ba". 


Dariya sukayi dukan su, tace, "ashe babba suna ne to na yarda". 


Ɗayar kuma tace, "ni kuma Hindu" ɗayar kuma tace, Halimatus Sadiya". 


Humaira ta ce, "mu ba baƙi bane a unguwar nan ba, kuma yan zun haka ana cikin hidimar bikin Hindu ne, to da an gama da sati ukku sai bikin Halima, ina fatan daku za'ayi komai dan muna yawan ganin ku kuna zaga unguwar nan bakwa shiga gidan kowa". 



Dariya mukayi nace insha Allah zamu halarta, ni ce Narjeesah wannan ƙanwata Amrah itace ke bina shekara biyu na bata, sai Auta Nusaiba gata nan ". 



Suka ce wow, "wannan big boy din fa? . 


Amrah ta ce, "yaron Anty Narjeesah ne". 


Humaira ta ce, "my boy yaushe zaka zo gidan mu ne? ". 


Dariya yayi kawai bai ce dasu uffan ba gurin Umma ya komawar sa. 


Fira mukayi sosai sai da la'asar muka rakasu kowace har ƙofar gidan su, gida muka dawo mukaci da har kar gaban mu kwata_kwata mun manta da maganar bikin da aka gayya ce mu, sai ranar kamu, su Humaira suka zo gidan mu ni kuma ina sama a kwance kaina ke ciwo Umma suka gaisa da ita, suke tambayar ta,  "Umma kodai kece kika hanasu su zuwa bikin nan" . 



Umma kuwa ta ce, "aa rufani ku sayani yaran nan, ku shiga ciki ita tana nan amman Amrah da Nusaiba sun fita da Shuraim na aike su". 



Da sallama suka shigo cikin ɗakin, zaune na tashi Hindu sai harata takeyi, dariya nayi na ce, "afuwa Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida". 



Dariya sukayi Hindu ta ce, "idan na kashe ɗan masu gida ai ke ce zaki fara bada shawarar a kaini kotu a ɗaureni ko kuma ki fara yaɗani a duniya". 



Dariya duk mukayi, na ce, "dan Allah kada kuce komai wallahi mantawa mukayi yau kuma kaina ke ciwo "



Hindu ta ce, "wallahi babu wani batun hakuri sai kin tashi mun tafi. 



Dariya mukayi dole na tashi na ɗauki gyalena daman ban wani daɗe da fitowa wanka ba na saka kaya amman banyi kwalliya ba, ciwon kai kawai yafi damuwa na, fitowa mukayi Umma bata nan tana ɗakin ta, na shiga nace "Umma zan tafi bikin can idan sun dawo su sameni a can dan Allah ". 



Ai kuwa Umma bata ce dani komai ba, har nagaji da tsayi, na juya zan wuce ke nan ta ce, "Adawo lafiya kuma a kula da kyau". 


Jin tayi shiru da sauri na jiyo ina kallon Umma wadda taci gaba da aikin gaban ta kamar ba itace tayi magana ba. 



Cike da farin ciki na fito gurin su nace muje, tafiya mukeyi amman zuciya ta sai mai_maita addu'ar Umma takeyi farin ciki kawai nakeji wannan shine karo na farkon da Umma ta taɓa yi mani abunda nake so, kuma nake mafalki.  



A gidan su Humaira muka sauka gaskiya Maman Humaira da yan uwan ta, basu da matsala gasu dai masu kuɗin gaske amman basu da wulakanta mutane, a ɗakin Humaira muka yada zango hum Humaira kam badai gayu ba, budurwa ce "yar gayun gaske nikam akan gadon ta na faɗa nayi kwance, yan mata kuwa gayu kawai suke ɗauka, Halima ce ta dube ni ta ce, "Narjeesah ki tashi ki gyara zamu gurin saloon ne fa kuma ke kin wani kwata, dolene fa ki ajiye ciwon kan ki a gefe sai angama biki ehe". 


Dariya mukayi nace, waye zai iya ajiye ciwo ke mu banda abinki? "


Tace, "to kisha magani kuwa" kallon ta nayi na ce, "ke kisha mani maganin mana idan kin sha mani zan warke". 


Dariya ta saka mani tace, "malama ki fito fili kawai kice bakya shan magani nafi gane hakan". 


Dariya mukayi dukan mu, duk kowa yana gama gyara wa, Angon ya kira waya yace, "a fito ga motoci nan. 



Tashi mukayi zamu fita, Humaira ta janye ni ta maidani ɗakin ta, ta zaunar a kujerar madubi ta ɗauki kayan kwalliya ta soma yi mani dariya kawai na keyi nace, Humaira nifa bana kwalliya sam". 



Tace, "haba malama ai kuwa tunda kina tare dani dole sai kin iya dan ni jinki nakeyi kamar uwa ɗaya uba ɗaya muke, to waima ni kam haka kike zama ba bu kwalliya kamar ba mace ba? "



Dariyar Hindu muka jiyo a bayan mu tana faɗar da kyau my Humy wallahi yi mata raɗau da kwalliya ". 


Jefe ta nati da marfin foda ai kuwa da gudu ta fita tana dariya. 


Sai da Humaira tayi mani kwalliya mai kyau bamai yawa ba, mai tarkace, muka fito Halima ce ta dube ni ta ce, "wow ko kefa malama Narjeesh, wallahi kin fi kowa kyau a gurin nan harda Amaryar, jakar hannun Hindu na amsa na jefe ta dashi da gudu ta fita tayi waje". 


Maman Humaira ce ta ce, "Allah dai ya shirye ku, kuyi ku tafi dan Allah kun bar mutane nata jiran ku". 


Amrah da Nusaiba ne suka shigo da sallamar su, da sauri ƙanwar Humaira ta kama hannun su, suka shiga cikin gidan Humaira kuma ta ɗauki Shuraim suka fita muka bisu a baya, gidan su Hindu muka nufa inda motocin ƙawayen Amarya duk sun shege motoci mu kuwa, wata haddiyar motar ce, muka nufa, Halima ce ta shiga gidan gaba mu kuma muna gidan baya harda Amaryar". 



Tunda muka shiga cikin motar babu wanda ya ce uffan, Halima kuwa fira sukeyi da mutumen, har dasu dariya sukeyi, mu kuwa har muka ƙarasa ba muyi magana ba. 



A bakin wani haɗaɗɗen guri suka ajiye mu, kawai muka shiga ciki gurin salon ne da gyaran jiki, wanke kai kawai da ƙafafun mu akayi muna muka fito suna ɗaukar mu sai holl muku nufa duk an ƙawata shi, ta ko ina yaji gyara sosai, shiga mukayi gurin na zauna a kujerar da aka tanadar wa manyan ƙawayen Amarya nida Humaira da Shuraim Halima kuma suke ƙara gyara wa Amarya, haka akayi komai da zamu koma Angon da kansa ya ɗauke mu muna tafe suna fafa tawa da Humaira, yana ce mata azzaluma ita kuwa tana ce masa zata saka a ƙara masa sati biyu, mukam dariya mukeyi. 



Halima ta ce, "to kai idan ta saka aka ƙara sati biyu ka ce abokin ka ya ƙara wata biyu sai ayi bikin ". 



Dariya mukeyi harda Angon da sauri Halima da Hindu suka ce "ƙarya kike yi ai kin mafi Angon zumuɗin bikin tunda yau saura kwana ishirin da biyu". 


Shiru tayi, nidai suna burge saboda na lura suna ƙaunar junan su, Halima ta ce, "nifa wallahi banƙi jinin a ɗaga wannan Auren ba". 


Humaira tace, "komai abun ki Aure kamar anyi sa an gama ne". 



Muna isa gidan aka fara kiran sallah da sauri muka fita daman ƙofar gidan su Humaira muka sauka muna shiga cikin gidan naja su Amrah muka tafi gida, tun da safe sai gasu Humaira mukaje gurin kitso da lalle akayo muna, tunda muka dawo gida, hima dai akeyi tare damu, aka ɗaura Auren aka kai Amarya ɗakin ta. 



Alhamdulillah anyi biki lafiya an gama lafiya, sai himar bikin Halima ta kunno kai bamu dai wani futa ba, rabon cimgam muka tafi, munsha yawo muka dawo munje gurin saloon mun dawo sai dai wannan bikin za'ayi dinier banyi niyar zuwa ba, amman ganin du sun ɓata ran su dole na yarda zanje harda ankon bikin akayi muna mu duka kuma bada ko naira namu ba. 



Kallona Humaira tayi tace, "Nikam har yanzun banji kin sanar dani komai ba kina da Aure ko babu ina Baban Shuraim amman fa ban ce dole sai nasan komai a kan kiba, kada kiyi fushi idan har wannan abun sirrin kine dan Allah kada ki sanar dani kinji Narjeesh? ". 



Dariya nayi ban ce da ita komai ba tace, "na fahim ta, amman nikam bari kiji, Narjesh kin ganni nan kwata_kwata bani da saurayin da nake saurare saboda na tsani yau dara, duk wanda yazo guri na sai na fara tambayar sa miye ya kawo sa guri ba da zarar ban gamsu da baya nin mutum ba nakan da katar dashi, shi yasa aka ce korar samari nakeyi ". 



Dariya nayi nace "mutum sai Allah kinji Humaira Allah ya kawo maki miji na kwarai musha biki, ranar nice kan gaba ". 


Firar mu mukeyi muna aikin gyara kayan miya tunda akayi abinci muka baiwa mutane tare da Hindu muke komai shirin zuwa gurin dinier mukayi sosai, nikam duk sai naji kamar kar naje, amman duk sun hana ni suna tsare dani, da nace zan je na dubo Shuraim sai Humaira ta ce, "Shuraim kam yana gurin mijin Hindu wato Aliyu". 



Cike da mamaki na ce, "kuma ya yarda yaje gurin sa? ". 


Hindu ta ce, "to da miye nufin ki malama? Ai Shuraim yaron mune ba naki ba". 


Dariya kawai nayi na ce, "Allah yaron baida yarda ne kun dai san halin sa ni mamaki ne nakeyi". 


Dariya sukayi, motoci aka kawo muka tafi, tafe muke ni dai ba zan ce ina jin daɗin wannan dinier ba ko akasin hakan. 



A gurin dinier ma kujera na samu na zauna nesa dasu saboda yanda naga wasu yam matan nayi abun baiyi mani ba, Humaira ce ta zo inda nake tace, "Narjeesh wallahi kin bani wahala ina ta neman ki kizo ku gaisa da Angon dan ya iso shida manyan abokan sa harda wani babban baƙon sa naji ana faɗa". 



Oh Humaira ke kinje kun gaisar ne nikam, tace, "ban jeba tare zamu je dake nima bada son raina nake son zuwa ba saboda ban wani saba da wannan angon ba, Aliyu munfi sabawa dashi, kuma shine ya aiko Hindu ta kira mu ". 



Tashi nayi muka Jera muna tafiya sannu a hankali kamar wasu marasa lafiya Hindu ce ta taryemu tana dariya ta ce, "wai lafiyar ku kuwa twins sister na?  Naga duk jikin ku yayi sanyi". 



Bamu bata amsa ba, taja hannun mu sai gurin mijin ta, yana ganin mu ya taso yazo ina muke ya ce, "haba dan Allah kuje ku gaisa da Angon da abokan sa mana, kuma munada babban baƙo amman yana can gurin saboda yan mata ya koma can". 


Ni kuwa nace, "hala ma mayen mata ne shi?"


Dariya sukayi ya ce, "kai wannan ai babu wata mace a gaban sa sai matar sa, muje kawai ". 


Mere baki nayi hannu na Shuraim ya kama yana tsalle_tsalle gurin Angon da abokan sa mukaje muna ganin Angon muka gaisa, dashi ya amsa ba yabo ba fallasa abokan sane suka fara tsokanar mu, bamu biye masu ba, har mun juya zamu wuce Angon ya ce, "Humairah kuje ga babban aboki na can gurin ku gaisa dashi". 


Ba Humaira ba ko ni da naji yanda ya kira sunan nata sai da muka jiyo da sauri muka kalli junan mu, kai tsaye nace, "ai ba sai mun jeba saboda mutane sunyi yawa ni zan ma koma can baya na ɓuya Humaira kuje ki gaisa dashi". 


Kai tsaye ta ce ba zan je ba, Angon ne ya nuna rashin jin daɗin sa a fili yace, "ok nagode da karramawar da muka samu a gurin ku". 


Hannu na dana Humaira Hindu taja tace, to honey muje ka raka mu naji kace jami'an tsaro ne dashi". 


Harda Angon tare muka tafi muna tafe, Shuraim yana riƙe dani, 'yan mata muka gani sai iyayi sukeyi, wasu har gurin sa suka nufa amman an hanasu su ƙarasa gurin, mu kuwa muna tafe nace, "Hindu Humaira banga fa Halima ba wai tana ina ne? ". 


Humaira ta ce, "wallahi tun ɗazun nake neman ta, harda wayar ta na kira bata zuwa, duk shi yasa na shiga cikin wannan yanayin". 



Hindu ta ce, "to ina Halima zata tafi bayan itace ta, taramu a gurin nan ". 


Angon ya ce, "wallahi na ɗauka tana can gurin da aka kira mani ku, to amman ina ta tafi ne? ". 



Wayar Humaira ce tayi ƙara tana duba ta sauke ajiyar zuciya ta ce, video coll Halima Allah dai ya shirya muna ke, ɗaukar wayar tayi, kawai sai ga Halima muna gani ba'a cikin holl din ba. 



Halima tayi dariya ta ce, Humaira ki saurare ni da kyau kiji, da hankali na nake komai, ina fatan kin san da sanin cewar Yazeed abokin Jafar wanda zan Aura ko? Wanda yake mutum makusan cin Jafar ko nace aminin sa, wanda yake zuwa guri na yace Jafar ne ya aiko sa guri na, har ka kace kin tsane sa, yana son ya ɓata Aure na da Jafar ne, to ki sani soyaya mukeyi dashi kuma shi nake so ba Jafar ba, yan zun haka ma nabishi mun tafi a ɗaura muna Aure dashi, shi kuma Jafar yayi hakuri Allah ya bashi wadda ta fini". 



Da sauri na anshi wayar nace, "Halima baki da hankali ne wai, taya zaki yanke wannan ɗanyen hukuncin kada ki biye ruɗin zuciyar ki mana? "



Halima ta ce, "ki baiwa Humaira shawara, nasan zata ɗauka, ki sani na baiwa Humaira miji ta Aura kece aminiyar ta dan haka kiyiwa Humaira adalci tayi Aure ga farin masoyi nan wanda take son na Aura wanda take fushi da nurul ƙalbina Yazeed a kan sa, lallai Humaira mutum ce kuma adilah". 



Hindu ta ansa tace, "Halima ki dawo hayyacin ki dan Allah ". 


Halima ta ce, "Hindu nayi nisa bana jin kira, ku baiwa Jafar dasu Mama hakuri kuma kuyi recordin ɗin abun da nake faɗa yan zun ". 


Jafar ne ya anshi wayar ya ce, "saboda miye zaku yau dare ni keda yazeed miye laina dan nace ina sonki kuma baku tashi yau dara ta ba sai ranar dinier? ". 



Halima ta ce, "Jafar yan zun ni matar abokin ka ce, dan haka bara na bashi shine dai_dai da kai". 



Yazeed yace, "Kayi hakuri amini na haka Allah yaso Halima ba matar ka bace mata ta, ce". 



Halima ta ce, "nasan kuna recording ɗin komai Baba da Mama ku yafeni abunda nayi maku bana son Jafar a yanzun dan haka ku maida masa da kayan sa, na barku lafiya". 



Kashe wayar tayi, kowa ya shiga cikin damuwa Humaira kuka kawai takeyi, ta ce, "Hindu ban faɗa maki ba, ban yarda da alaƙar Halima da wannan wawan ba? "


Hindu ta ce, yan zun fa kawai musan abunyi kawai kowa ya rasa mafita, kawai wayar Jafar tayi ƙara yana dubawa, ya baiwa Aliyu sai Aliyu ya ce, "muje gurin Mutanen nasan shi yanada mafita". 



Haka mukaje gurin tun kafin mu ƙarasa naji zuciya ta kamar zata faso ƙirji na ta fito sai dukan ukku ukku takeyi da sauri da sauri rufe ido na nayi muka ci gaba da tafiya muna zuwa naja nayi tsaye batare da na kalli mutanen gurin ba, Aliyu ne ya bashi labarin akasin da aka samu da duk yanda akayi kallon mutanen kawai yake. 


Dafe zuciyar sa yayi da sauri, ya tashi tsaye duk suka zuba masa ido, cike da mamakin sa, kallon inda ya kafe da ido sukayi ga mamakin su nice yake kallo gashi nima nayi tsaye na juya baya, ina dafe da ƙirji na. 



Shuraim ne ya gudu yaje ya rungume sa, ya ce, "na kamaka wallayi". 


Cike da mamaki aka maida ido a kan Shuraim da wannan mutanen, kawai ya saka hannu wansa ya ɗauke sa ya rungume sa a ƙirjin sa, suna sauke ajiyar zuciya sun ɗauki wasu lokuta a haka kafi ya ƙara duba fuskar Shuraim ɗin ya yi masa murmushi. 


Ni kuwa jin shirun ya yi yawa sai na maida ido na akan, su Humaira sai naga tana kallon wani gurin nima sai na ɗaga ido na abunda nagani ne ya fir gitani Shuraim ajikin wani mutum kuma sun kafe juna da idon sai murmushi sukeyi iri ɗaya. 



Aliyu ne da Jafar suka ce, "man ya zamuyi da mutane zauna wa yayi da Shuraim a jikin sa, ya riƙe dashi, yana kallon sa, kawai naje kusa dashi nasa hannu na ɗauke Shuraim na juya zan wuce, naji an riƙe Shuraim a fusace na juya zanyi masifa kawai naga ashe....... 




*Comment And share* 



*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


💐💐 *NARJEESAH* 💐💐



*Rubutawa*

*NANA KHADEEJATU*

           *_UMMU IHSAN_*


*ELEGANT ONLINE WRITERS*


_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_



               1⃣1⃣⏮1⃣5⃣



➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Kai sai naga Ashe Shuraim ne ya riƙe masa hannu cikin jin haushin sa kawai na doke hannun sa, ya saki mutumen, ya fashe da kuka, sukam kallon mu kawai sukeyi, da sauri naja hannun Humaira da Hindu muka bar gurin, muna fita na sauke ajiyar zuciya na maida hankali na a gurin Hindu nace, "Hindu ya kamata Humaira tayi kamar ita ce Halimar saboda kada mu kunya ta wannan bikin musam ma abokan Angon nan da yan uwan kamar Halima ko ya kuka gani?  Tunda kaya iri ɗaya ne kuka saka kwalliya kaɗan ce ta ban banta, sai na baki wannan gyalen nawa yafi naki girma yanda babu wanda zaga fuskar ki bare yasan wace ce a gurin ki duba yanda ake ta cigiyar Amarya kuma dare kayi fa". 


Da sauri Hindu tayi na'am da shawara ta, mukayi wa Humaira kamar Amaryar mukaje muka zaunar da ita akan kujerar Amaryar, tafi kawai akeyi, Hindu ce taje ra sanar dasu abunda muka tsara suma daket Jafar ya yarda  suka rakoshi ya zauna a gefen Humaira, kiɗa aka sanya aka fara yin dinier cake aka ce a zo a yanka, Humaira taƙi tashi sai da na roƙeta da ket ta tashi a hankali take tafiya gurin yanka cake ɗin sai da Aliyu da wannan baƙon nasu sukayi tsaye wa Jafar ya riƙe wukar muka, taku rawa Humaira itama ta riƙe wukar suka yanka, Dj yace, sai su ciyar da junan su, hakan duk ka ƙiya ni kaina banyi tunanin hakan ba, da ket muka samu ya saka wa Humaira abaki itama ta saka mashi, tafi akayi suka koma suka zauna haka dai akayi ta dinier har aka gama komai, motoci ne suka zo suka fara kwashe mutane Humaira na can tana kuka bayan ta gama gaisa wa da mutane da abokan Angon. 


Mota zan shiga na juya banga Shuraim ba inada  na barshi a kusa da Humaira da sauri kira Amrah da Nusaiba da suke jira na cikin kuka nace dasu banga Shuraim ba. 

Hindu ta ce, "Narjeesah wane irin baki ga Shuraim ba, bayan a hannun ki na gansa". 


Nace wallahi a nan yake zaune kusa da Humaira, na barshi zan samar muna mota,  cikin kuka nake magana. 


Ai kuwa atake kowa ta shiga neman Shuraim babu shi babu labarin shi, kuka kawai mukeyi nida su Amrah harda Humaira gashi dare yayi har kusan ƙarfe ɗaya, Jafar ya kira duk motocin da suka fita sunce basu ga yaro ba, su kam". 


Neman duniya an yiwa Shuraim amman ba'a samesa ba, dole sukayi ta bani hakuri suka ce nemo mani shi, gida muka koma a ƙofar gidan mu suka sauke muka shiga gidan, Umma tana ta duba inda zata ga Shuraim amman bata gansa ba gashi duk idon mu yayi jawur dashi. 


Da gudu na shige cikin ɗaki na, nayi kwance ina kuka, Umma kuwa cewa  tayi, "kun baro sa a can ko?  To kuwa kun kyauta, taya ma zakuje ku saki ƙaramin yaro a can cikin taron mutane kuma cikin dare gashi ba yarda yakeyi da mutane ba, wallahi badan kada ayi biyu ba, da sai ku. Koma cikin daren nan kun nemo sa, yo wannan ai sakarcin banza ne! ". 


Faɗa kawai Umma keyi ta inda ta shiga ba tanan take fita ba, ganin yanda Umma tayi fushi ne take ta faɗa kowa ya gudu cikin ɗakin sa, kuma kowa kuka yakeyi, alwala na ɗauro a ranar ban rintsa ba, kaina kuwa saboda ciwo kamar zai watse, da safe abun karin kumallo ne aka kawo mani bana iya saka komai a bakina Humaira ce ta shigo itama idon ya kumbura, ta gaida Umma, Umma ta amsa ta kafe ta, da ido har ta tashi ta shiga guri na, Umma ta dakatar da ita, ta dawo ta zauna abinci Umma ta zuba mata ta tsare ta, tace, "ki cinye sa ki bani kwanon nan shi nake jira". 


Humaira juya cokalin takeyi ta kasa saka loma ɗaya a bakin ta, Umma na ganin abunda takeyi tace da Nusaiba jeki ki ce ta fito ina kiran ta"


A tare muka fito da Nusaiba ina fito wa na kafe Humaira da ido, a kusa da Humaira na zauna cokali Umma ta bani tace, " kwanon kawai nake buƙata". 


Duk kan mu juya cokalin kawai mukeyi, har abincin ya fuce, Maman su Humaira ce ta aiko kiran mu tare muka tashi su Amrah suka raka mu, Maman Humaira ce ta ce, "kuzo muje gidan su Halima ana can ana neman ku". 


Tare muka tafi gidan yan biki cike da gidan ɗakin Mommy muka shiga Maman Halima, ita ma tace kuzo muje inda ake neman ku"

Muna shiga cikin ɗakin mutane muka samu a gurin harda su Jafar mahaifin Halima ne ya buɗe taron da addu'a sannan yace, "naga saƙon Halima kuma muna godiya sosai da abunda ta aikata muna, zata kuwa gani ga kwaryar shanta". 


Sannan ya dubi mahaifin Jafar ya ce, "malam dan Allah kuyi hakuri laifin ɗan yau ne ba namu ba, mu bamu ƙi mu haɗa zuriya da ku ba, amman haka Allah ya so ga kayan ku da kuka kawo sai ayi lissafin abunda taci wanda  babu shi anan ciki! ". 


Mahaifin Jafar ne ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "tabbas bamu ji daɗin abunda ya faru ba, amman babu komai ƙuruciya ce kuma ni kam ba zani anji komai ba daga hannun ka tunda daga kan sadaki har komai, kai mahaifin Jafar ne, zaka iya nema masa mata aduk inda kake so kuma nasan zaka zaɓa masa ta kwarai dan haka wuƙa da nama duk suna hannun ka". 


Mahaifin Halima ya ce, "ina godiya da wannan karamcin amman ku baiwa Jafar hakuri kuma ku bashi damar fitar da wadda yake so ni nan zan masa waliccin Auren nata". 


Jafar yace, "bani da wani zaɓi duk zaɓin da kukayi mani yayi "


Mahaifin Halima ne ya kalli mahaifin Humaira ya ce, "to malama Abdullahi gani nazo da ƙoƙon bara na, ina son ka baiwa ɗana Jafar Auren "yarka, Humaira". 


Da sauri muka haɗa ido da Humaira wadda tuni ta soma zubar da hawaye, kuka ta fashe dashi ta kwanta a jiki na. 


Baban Humaira ya ce, "da Humaira da Halima duk naka ne kamar yanda zakayi hukunci akan Halima haka zakayi sa akan Humaira dan haka wuƙa da nama suna hannun ka". 


Murmushi mahaifin Halima yayi ya ce, "Humaira zan tambaye ki ki sanar dani tsakanin ki da Allah, shin kina da wanda kike so ko babu, ina son ki sanar dani gaskiya bana son ki ɓoye mani komai ". 


Kasa magana Humaira tayi sai kuka takeyi, kowa ya zuba mata ido, mahaifiyar Humaira ce tace, "Narjeesah ke nasan kin san sirrin zuciyar Humaira kada ki ɓoye muna komai shin Humaira nada wanda take so ko babu? ". 


Shiru nima nayi har sai da mahaifin Halima ya ce, "ki bada amsa dan duk gurin nan mun yarda dake". 


Kallon Hindu nayi ta matso kusa dani ta kafeni da ido alamar nayi magana, da ket na buɗe baki kasan cewar murya ta bata fita naci kuka tun jiya har yau, nace, Humaira bata kula kowa ma, ita a tsarin rayuwar ta bata son samari barkatai". 


Shiru duk sukayi zuwa can Baban Halima ya ce, to Alhamdulillah, shin Humaira zaki iya yarda ki Auri Jafar a matsayin zaɓi na? "


Kallon Humaira akeyi har yanzun dai kukan takeyi, sai aka dawo da tambayar a kaina, Hindu ta gyada mani, kai. 


Nace, "ku iyayen mune zaɓin da zakuyi muna shine mafi can_canta mubi dan haka mun yarda da zaɓin ku". 


Hamdala sukayi dukan su, anan aka maida sadakin Jafar akan Humaira suka ga addu'a akace yau za'a ɗaura Auren duk sai da muka zaro ido har Hindu, sai kuma aka koma zan cen neman Shuraim da aketi har gidan redio an bada ciya da gidan tv, da unguwar ni.


Baro ɗakin mukayi muka dawo gidan su Hindu Maman Hindu tayi ta bamu baki, kowa faɗar yakeyi duk sune silar ɓatan yaron nan, hankalin kowa a tashe yake, haka aka ɗaura Auren Humaira da Jafar, Humaira har yanzun kukan takeyi. 


Nima kukan ɓatan Shuraim na keyi a ranar ne aka kai Humaira ɗakin ta, muna kaita na baro gidan muka dawo gida, yau ma da kukan na kwana, zazzaɓi  mai zafi ne ya kamani, gashi idan ina ciwo komai bana iya ci, duk nabi na rame na susuce. 


Har cikin sati biyu babu Shuraim babu labarin sa, nikuma har yanzun banyi lafiya ba kullum cikin ciwo, Humaira ce ta aiko kira kashe na tara, Umma ce yau ta ce, "ke ni gaji da wannan aiken ki tashi kije kiji kukan ta". 


Tashi nayi, na shirya cikin riga da siket na shadda lemon green na ɗora gyalen a kafaɗa ta yau ban yafa har a kaina ba, Amrah ma shadda ce marun Nusaiba ma shadda ce pink, fitowa mukayi zamu tafi Aliyu ne ya gan mu yazo gaida su Mommy daman ya saba yin hakan, tsayawa yayi yace, muje ya kai mu yasan dai gidan su Humaira zani yasan ba gidan sa zani ba". 


Kaina na dafe da yake yi mani ciwo sosai nace, "wallahi ko ita Humaira wannan shine aike na tara tun ranar da muka kai ta ban koma ba, sai  yau gashi har yanzun bani da lafiya ". 


Tausayi na bashi ya ce, "wallahi har yanzun bamu daina neman Shuraim ba, dan yaron nan idan muka daina neman sa ba muyi maku adalci ba, saboda ata dalilin mune aka ɗauke sa, to taya zamuje muyi farin ciki ku kuyi kuka kin kuwa ba zai yuyu ba, har gidan Humaira ya kai mu nace masa wani satin insha Allah zamu je gidan sa. 



Muna shiga cikin gidan da farin cikin Humaira ta, tarye mu kallon ta kawai nake duk tabi ta rame ta sauya kamar ba Humaira 'yar gayun nan ba, zama mukayi ta kawo muna abun sha su Amrah suka sha, kallon Humaira kawai nakeyi, tayi murmushi ta ce, "kada kice dani komai malama aike yafi nawa sai yau kika ga damar zuwa? ". 



Murmushi nayi na ce, "Humaira kema kin san abun da yake damu na". 


Humaira ta ce, "nima shine damuwata wallahi kullum da shi nake kwana nake tashi, na rasa ma wace hanyar ce zamu bi mu nemo sa? ". 



Amrah ce ta ce, "Anty zamu ɗan fita mu dawo "Humaira ta ce, babu inda zaku bari mu baku guri kunna masu kayan kallo tayi, ta basu remote tace, kuyi kallon ku, kichin ta shiga ta kawo masu kayan motsa baki muka basu guri sai dariya sukeyi wai mun gano manufar su. 



Cikin wani ɗakin muka shiga, muka yada zango, bayan mun zauna ne nace , "Humaira ya gidan ya mai gidan da fatan dai kun sasanta kanku "


Humaira ta nisa tace, "wane sasanta kai kuma Narjeesah kin fa san ba son junan mu muke yi ba, zuciyar sa tana akan Halima kuma ni har yanzun ganin nakeyi dawowa zatayi ga masoyin ta to sakin jiki na miye? Inje in saki jiki a kaini a baro sai na faɗa son sa Halima na dawowa ya koma mata ni ya sako ni ko ya kike nufi? ". 



Dariya nayi harda dafe ciki na ce, "haba da ranki ya daɗe har sai da kika sa nayi dariya wadda rabon da nayi ta tun ranar da mukayi abinci yan zuwa dinier, sai yau, to ke kice hauka ce kike zaune kikeyi a gidan mijin ki, haba Humaira kefa ce, kike son miji wanda zai baki kulawa, kuma mai  hankali gashi Allah ya baki amman kike wasa da damar ki dan Allah kiso mijin ki, ki dawo da hankalin sa a gareki ki cire masa tsoron mara da yashe sa, wallahi Humaira kina da abunda ba kowa ce mace bace ta tara suba, koda a gurin tsatar ki da ilimin ki kawai aka tsaya uwa  uba natsuwa, Humaira ki yiwa kanki faɗa mana". 



Shiru Humaira tayi Jafar dake tsaye a bakin ƙofar tun ɗazun, yayi murmushi ya ƙaraso da sallamar sa yana dariya ya ce, "madam yau ke ce a gidan namu to munyi farin cikin zuwan ki, duk da muna fushi dake, a ce sai yau kika dawo gidan nan ". 


Dariya nayi na ce, "ranka ya daɗe ba wata lafiya ce dani ba wallahi ko yan zun haka kaina ciwo yakeyi ". 



Ya ce, "wallahi kina da gaskiya ɓatan yaro ai babban abune wallahi tunda mutum bai san irin halin da yaron yake ciki ba". 


 

 Ya dubi Humaira ya ce, "Madam baƙona ya iso yana ƙofar gidan nan yan zun ya kira ni, Allah yasa akwai abunda za'a tarye sa dashi dan wallahi nima bai sanar dani zuwan nasa ba, sai da yazo ƙofar gidan nan ". 



Humaira ta ce, "ok babu damuwa bari mu haɗo masa abunda akwai idan baya cin sa, sai a sama masa wani abun da ban ". 



Tashi tayi tace, "muje ki taya ni" kwanciya ta nayi na ce "wallahi ba zanyi ba, nima ta kaina nake da nakejin yana ƙara mani ciwo ga bugun zuciya ta ya ƙaru". 



Ido suka haɗa da Jafar da sauri tabar gurin shi kuma yace, naje na shigo da baƙo na". 


Da sauri na ce, badai a nan cikin ɗakin ba". 


Dariya ya yi ya fita ni kuma nayi kwanciya ta, abinci ta ajiye a cikin ɗakin na ɗaga ido na na ce, "ba dai nan zaku kawo wani can ba? ". 



Dariya tayi, na ce, "nikam zan gudu kuwa dai_dai lokacin suka shigo cikin ɗakin, ƙirji na ne naji kamar zai fashe, ko kallon inda nake baiyi ba, na koma na kwanta na rufe ido na Aliyu naji yana faɗar badai ciwon kan bane, Narjeesah? ". 



Kallon sa nayi kawai na tashi zan bar ɗakin na ɗauki gyalen nawa, na riƙe a hannu na bar masu ɗakin su Amrah na yiwa nace, ku tashi muje gida sunyi baƙo kuma ni bani son ganin sa, ban san dalilin hakan ba". 



Tashi sukayi Aliyu ya ce, "baƙon mu zai rage maku hanya" da sauri na juya na kallesa nace, bana so ya tafiyar sa". 


Dariya sukeyi, Amrah tace, "Yaya Aliyu mun yarda zamu je tare da baƙon mu dan har naji baƙon ya kwanta mani tunda har zai kai mu  gida ". 


Tsaki nayi na ce, "ai sai kuje tunda mayun mota kuka dawo". 


Dariya sukayi suka dawo suka zauna nayi_nayi dasu mu tafi amman suka ƙi tafiya har sai da Jafar yazo ya ce, "ku fito yana jiran ku, zai kai ku gida, amman fa tare yake da masu bashi kariya, dan kada kuje ku ji tsoro " da dariya yake maganar ya kallon fuska ta Humaira ma dariyar takeyi Aliyu ya saka ni gaba yana dariya har muka fita ƙofar gidan da gaske kuwa mutanen yau sun fi wanda na gani ranar dinier din nan, muna zuwa suka buɗe muna mota ɗaya. 



Tsaye nake su Amrah duk sun shiga sai da Aliyu da Jafar sukayi da gaske nazo shiga suka rufe ƙofar suka buɗe mani gidan gaba, kamar nayi kuka na shiga cikin motar kawai naji ƙamshin da bazan taɓa manta irin sa ba, a take hankali na yayi mugun tashi, muka ɗauki hanya muna tafiya wanda yake tuƙin motar ne ya dubi su Amrah ta madubi ya buɗe bakin sa ya ce, "mike damun wannan yarinyar da ai ban san lokacin da na wani irin juyowa gabaki ɗaya nace,... 



Sauke ni a nan malam kaji ko? Shima da sauri ya ɗaga ido sa ya waro su waje ya kafe ni da ido ya ce, "what!!  Wani wawan burki ya taka ji kake ƙiiiiiiii ya ce, "kina nufin cewar wannan yaron ɗan ciki nane!!?. 



Cike da zafin zuciya na ce, "baka da ɗa kuma ka daina alakan ta ɗana da sunan ɗan kane, yaro na bai da uban kuma kai ba kowa bane a gurin sa!!! "



Tsawa ya daka mani ya ce, " rufe mani baki anan malama!  Kuma kada ki yarda ki sake dan gata yaro na da wani ban za can!! ". 



Cike da masifa da rashin tsoro nace, "an cevShuraim ba ɗan ka bane, Shuraim bai da uba!! "



Yace, "ƙarya kikeyi Shuraim ɗana ne baida wani uban bayan ni!! ". 


Su Amrah duk sun shiga cikin ruɗani, da sauri ta buɗe motar ta kira yaron sa saboda yadawo a kujerar da ake ɗora yara ya baro gurin tuƙin, saboda masifa, bamu ma san wani ya shigo motar ba, jan motar yayi Amrah nayi masa kwatan ce, har ƙofar gidan ya yi parking ya fita ya rufo motar mu kuwa masifar mukeyi ba bu ji ba bu ga, 



Da gudu Nusaiba taje ta kira Umma sai ga Umma ta fito nima fita nayi shima fitowa yayi nasha ɗamara da gyale na, nace wallahi baka da ɗa a tare dani, kuma sai nayi ƙarar ka kotu sai an bi mani haƙƙina! ". 



Shi kuma ya ce, "idan kika sake alaƙan ta yaro na da wani ban za can sai kin bin ciko mani shi, munyi shari'a dashi koda duk dukiyar dana tara zata ƙare!! ". 



Umma ce, ta daka muna tsawa tace, "ya Isah! haka dan Allah kuke shirin tara wa kan ku mutane! koda ya ke ai ma na fahim ci komai, wannan shine Baban Shuraim dan ga kamar su nan dash! Ku shigo daga ciki muyi magana ". 



Da sauri nace Allah ya raba Shuraim yayi kaman ce ceniya da wannan mugun! ". 


Shima ya ce, wallahi ɗa nawa ne, ehe! ". 


Hannun mu Umma nawa dana shi wannan shine lokacin na farko a ta rihin rayuwa ta da Umma ta taɓa riƙa hannu na mukayi tafiya muna shiga a falon gidan muka zazzauna Umma ta ce, " *NARJEESAH!!* yau ina son sanin sirrin da kike ɓoyewa yau nake son sanin taya kika sami cikin Shuraim har zuwa yau ɗin nan, yau nice da kai na na kira Sunan ki karon farko da nake son jin damuwar ki dan haka gareki". 



Cikin farin ciki da baƙin ciki na ce "Alhamdulillah Umma yau ne karon farko da zan fara faɗar abunda ya faru, sirrin da ban taɓa sanar wa kowa dashi ba, saboda a ayi sani da duk abunda ya sami ɗa uwar sace ta farkon da zata fara sani, to ni kuma tawa uwar tayi ban za dani tayi kamar babu ita a duniyar nan shine nima na ɗauki alkawarin sai uwata ce kawai zata san sirri na to yan zun tun da uwata ta damu da damuwa ta, zan sanar daku komai". 




"Umma a yau zan sanar dake gaskiya abunda ya faru a shekarar da nake zana hara bawar shiga j ss 3,............ "



*Allah kajiƙan iyaye na kayi masu rahma ka saka su cikin aljannar ka ta firdausi dasu da duk kannin yan uwa musulmi baki ɗaya amin*



*Comment And share* 



*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹   



💐💐 *NARJEESAH* 💐💐




*Rubutawa*

*NANA KHADEEJATU*

           *_UMMU IHSAN_*



*ELEGANT ONLINE WRITERS*



_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_



               1⃣6⃣⏮2⃣0⃣




➿➿➿➿


Amrah ta ce, "amman kafin ki fara Anty Narjeesah taya ya akayi kuka haɗu da wannan mutanen amman abun  mamaki ke baki san shiba kuma kun haɗu dashi tun ranar da akayi dinier kuma a guri ɗaya kuke dashi amman duk baku nuna kun san junan ku ba, sai yau ko yau ɗin sai da yayi magana kika nuna kin san shi shima hakan ce a a gurin sa a gaskiya kun saka mu a cikin duhu miyasa hakan? 


Murmushin takaici nayi nace, "ban san shi ba kuma ban taɓa ganin sa ba"



Amrah ta maida duban ta a gareshe ta ce, "bawan Allah kai kuma fa taya kake cewa Shuraim ɗan kane bayan ita bata san ka ba? "

Ya ce, nima ban taɓa ganin taba, amman kuma Shuraim ɗana ne wannan shine gaskiyar magana! ". 



Su Umma duk sun shiga cikin duhu, tashi tsaye ya yi ya ce, "Umma ni zan tafi ina da uzuri ne, amman gaskiya zan sanar maki, ita ɗin mata tace, akwai Aure a tsakanin mu, kuma Shuraim ɗan mu, ɗan halak ne shi ba shegeba dan nine mahaifin sa, kiyi hakuri Umma na barku lafiya kuma a kila da igiyar Aure na duk da bata san ni nima nima ban san taba, amman muna da Aure nida ita". 



Kawai ya fita, da sauri na ce, "Allah ya raba ni da Auren mugu irin ka azzalumi! ". 



Aliyu da Jafar da matan su su Humaira da Hindu suka shigo, suna kallon mu, Umma ta ce, gara da kuka shigo, ina fatan kun ga mutumen da ya fita? ". 



Gyaɗa mata kai sukayi anan Amrah ta labar ta masu komai bata boye, masu ba, kowa tambayar yakeyi taya ya hakan ta faru kuna da Aure a tsakanin ku harda ɗa ɗaya amman baku san junan ku ba, sai a murya gashi kun haɗu ya kai sau nawa?. 


Umma tace, "ke muke saurare"? 


Kallon su nayi na ce, Zakuji labarina yanzun kuwa". 



Sunana Narjeesah Isah Musa, mahaifina malam Isah Musa mutume ne ɗan kasuwa Allah yayi sa da zafin nema, matan sa huɗu Maryam itace uwar gidan sa amman muna kiran ta da Inno sai Larai itace ta biyu muna kiran ta da Mama sai Atika ta ukku muna kiran da Yaya, sai Aysha wato Umma itace cikon ta huɗun". 



Zama akeyi na haɗin kai dan basa faɗa ko kaɗan idan ka cire Mama wadda take da zafin kishi da son abun ta da nuna nata_nata ne, ga shegiyar rowar tsiya, gashi itace da manyan "yaya a gidan, sam sauran halin su ya ban banta dana sauran mutanen gidan, haka yaran ta duk halin ta sukayo dan duk ta ɓata su. 


Yaya ma cikin yaran ta Mama ta ɓata mutum biyu saboda suna zama a ɗakin ta ne, Yaya kullum cikin nasiha take da nuna masu halin da suka tsira bai da kyau, mata ne su gidan wasu zasu amman inaa.. Duk wanda yayi nisa baya jin kira"




Nice ta fari a gurin Umma dan haka ban samu kulawar ta ba ko kaɗan dan ni sai da na yi wayo nake yarda da cewar Umma ce ta haifeni amman sam ni bana yarda a tunani na Inno ce ta haifeni dan ma Inno tana yi mani yaƙi a gurin Umma tana amsar mani abu koda rabo ne na cikin gidan idan Umma tayi rabo, to nawa sai dai Yaya ta ɗaukar mani ko Inno amman ita bata cewa ga nawa, Umma bafulatana ce, kunya ne da ita ba ta wasa ba, kasan cewar bana samun kulawar ta ne Baban mu, ya maida ni ɗakin Inno. 



A cikin gidan mu nice, wadda Allah ya ɗora soyayya ta a cikin zuciyar mahaifin mu, komai ya samu Narjeesah baya son gani na a ciki damuwa koda kuwa kaɗan ne, bawai yana fifita ni bane aa dai duk abunda ya samu nice zai kira na kaiwa duk wadda take aiki, gashi na taso da masifa ga faɗa sam bana yarda acuce ni, idan aka kaiwa Umma ƙarata, bata kula mutum sai dai mutum ya gaji da tsayin sa yayi gaba, sai da mutane suka fahimci cewar Inno ce, inna ta, kawai sai suka daina kaiwa kashe dina, idan Baban mu yana nan sai dai ya bada haƙuri ya ce, na daina ba kyau. 


Baban mu ya Auradda da manyan mu, su Anty Basira su ukku har sun haifu daga mai biyu sai mai ukku, sai maganar Auradda su Anty Shamsiyya da Zuwairah da Hanan wanda suka bani shekaru biyar, wato shekarar su ashin ni kuwa sha huɗu ke gareni ke nan. 


Wata ranar laraba ce, Baban mu zai tafi kasuwan cin sa, a ranar na tashi bani da lafiya, duk bana jin daɗi kuma ban san abunda yake damuna ba, yau rakiyar Baban mu naji ina son yi haka nabi sa harda su yaya Auwal wato babban Yayan mu na ɗakin Inno. 



Tun da muka isa tasha Baban ne yaja hannu na gefe yake tambayar mike damu na nace,  masa babu komai kawai dai ban san abunda yake yi mani ciwo ba, kuma ni jin nakeyi bani da lafiya. 



Ya ce, "Allah sarki Narjeesha ki yi hakuri halin Umman ki nata ne, ba aro tayi ba, ki rage damuwa da abunda takeyi maki na rashin kulawa wata rana zata sauya, kuma ki sani sirrin ki naki ne kada ki yarda ki sanar da wani abunda yake damun ki ko ya sameki, ko waye kada yasani, indai ba wadda ta haifeki ba, taso jin damuwar ki, kada ki faɗa kiyi ƙoƙarin ganin mahaifin ki ta janyo ki a jikin ta, kuma ina son ko miye ta fara sanin sa kafin kowa ya sani, dan uwa itace Babbar masoyiyar mutum ta nan duniya, saboda haka kije kiyi ƙoƙarin ganin ta saurari kukan ki, ko ba a yan zan ba". 




Ni kam saboda ƙuruciya ta, sam ban wani fahimci komai ba, daga cikin maganar sa, addu'a kawai nakeyi masa ta Allah ya kai shi  lafiya ya dawo dashi lafiya, haka su Yaya Auwal addu'a ce, sukayi masa, muna tsaye har motar su ta tashi ta tafi, sannan muka dawo gida, zuwa marece, su Yaya Auwal suka dawo, cikin tashin hankalin ni kuwa dama ina kwance bani da lafiya jikina rawa, yakeyi har sai da Inno tayi marufa, Yaya ce ta kira ta ta fito kowa yana tambayar lafiya, kawu Bala ne ya shigo shima cikin tashin hankali, ya ce, "sai haƙuri Malam Isah sun sami hatsarin mota, motar da suke ciki babu wanda ya fita, sun ƙone ƙurumus! ". 



Faduwa wasu daga cikin mu sukayi atake gidan ya kacame da kuka, ni kam fito wa nayi ana biyar layi ɗaya bayan ɗaya, na ce, sam wannan maganar ba gaskiya bane, ni ban yarda ba, ruɗewa nayi kamar wata mahaukaciya, somewa nayi, ban sake sanin kaina inda yake ba sai da safe. 




Tunda na tabbatar da cewar gaskiya ne, Baban mu ya mutu shike nan nadawo kurma bana magana bana cin abinci kullum cikin kuka sai da aka haɗani da addu'a aka samu nadawo dai_dai tun daga wannan ranar ne Mama ta fara rigimar gado itada su kawu dasu goggo, amman saboda babu wanda ya goyi bayan hakan sai aka bar maganar. 





Tunda muka koma makaranta daman burina bai wuce nayi karatu mai zurfi ba, boko da islamiyya har na ce sai nayi aiki saboda karatu, shi yasa bana fashin zuwa makaranta, gidan mu da unguwar mu sai suyi ta dariya wai sai sun ga yanda zan yi karatun mai zurfin tukun, ni kuwa sai nayi ta masifa, amman  makarantar islamiyya idan ban haddace karatuna ba, malam Nura ne ke zuwa ya saka ni gaba, sai naje makarantar, idan ba haka ba bana zuwa.  



A lokacin da nake shirin shiga jss 3 ne na haɗu da wannan iftala'in tare muka tafi makaranta nida su Hanan wanda suke ss2 a lokacin shikerata sha biyar ne, sai da muka gama jarabawar mu, muka fito misalin ƙarfe biyu da rabi na rana, bani mance wa munyi jarabawar Maths ne duk mun gala baita, ajin mu shine na ƙarshe da fitowa, na fito ina tafiya ni ɗaya a bakin titi duk nagaji yunwa nakeji kawai na zo zan raɓa wasu motoci da suke a gefen titin saboda idan nabi ta gaban motocin zan hau titin ne kuma mashin zai iya bigeni ko mota ko keke, gashi yau sam hankali na ba kwance yake ba. 



Na wuce mota biyu lafiya lau nazo a mota ta, ukku, kawai aka kamani aka jefani cikin mota baƙa itace ta ukkun, rufewa kawai akayi a kaja motor da ƙarfin gaske, ihu na zun duma, kafin na rufe baki har an watsa mani wata, powder a take naji garin na juya mani, zuwa can sai bacci ya ɗauke ni. 


Ban tashi falkawa ba sai a wani gurin, tare da wasu mutane manya_manya,  



Wasu kuma malamai ne dan naga littafai ne a gaban su suna karatu, da sauri na tashi zaune ina dube_dube, 


 Nidai ganin nakeyi  ba'a gidan mu nake ba, wasu matane suka zo inda nake, da sauri naja da baya sai ji nayi antaro ni ta baya, da sauri na juya na ɗaga kaina wata matar ce, zata kai sa'an Inno, da sauri na dun ƙule jiki na guri ɗaya, wannan matan ne suka riƙoni sai cikin wani ɗakin a gaban wasu limamai ina jin sun fara magana, 



 Sai  naji sam wannan ba hausa irin tamu bace, dan hausar su bata fita kamar Umma na. 



Mutumen yace, "yarinya kiyi hakuri ki anshi jarabawar ki, idan kina son ki tsira da mutumcin ki to ki yarda a ɗaura maki Aure a yanzun idan kuma bakya son wannan Auren anshrya maida ke karuwa, to ni kuma mutumen daya turo nu yace, kiyi hakuri ki anshi wannan Auren dan kuwa mukam mu sai da mukayi istahara akan Auren kuma munga babu wata illa idan kin yarda da ƙaddarar Allah to ki ashi Auren nan da hannu biyu ". 


Kallon sa nayi na ce, "bawan Allah kadubi girma Allah ka tausaya mani ni marainiya ce kuna ƙaramar yarinya ce!"



Murmushi mutanen ya yi yace, "shekarun ki nawa ne yan zun? ". 



Da sauri nace, "sha biyar". 

Ya ce, "shin kin mance, cewar NANA Aisha yardar Allah ta tabbata a gareta, shekara nawa akayi mata Aure? Shin ke nan ke a yanzun uwa ce ko? To kiyi hakuri ki ɗauki Auren nan kada ki bari ayi zina dake". 




Kalamai masu shiga jiki akayi mani, dole na yarda na amshi sadakin dubu sittin aka ɗaura Auren wanda nake jin kamar wuta aka ɗaura mani a jiki tashi sukayi bayan sun gama saka mani albarka da adduar kariyar Allah da wasu ruwan addu'a da suka bani, nasha ina kuka, suka fita, wasu matan ne suka kawo mani wani abun kamar zuma da kuka na nake sha saboda muguwar yunwar da nakeji ga tsoro ta ko ina, bacci ne ta ɗauke ni ban sake sanin inda kaina yake ba. 


 

A cikin  wani ɗaki mai duhun gaske na tsinci kaina, hannuwa na a ɗaure haka ido na da baki na, na rasa ya ya numfashi na zai iya fita a sauƙaƙe. 



Jin motsi nayi a kusa dani, a take nayi yun ƙurin guduwa, kawai naji an janye mani ƙafa, na faɗi ƙasa Ashe akan katifa ne, ƙafa ta aka raba biyu, aka ɗaure a wani gurin da ban san miye ba, sai kawai naji saukar mutum a jiki na, Ashe ma ko kayan jiki na an cire, hannu na duk suna a ɗaure haka nayi ta dukan mutumen amman ina koda ba a ɗaure nake ba ƙarfin mace dana namiji ba ɗaya ba, kawai ya afka mani. 




Tabbas wannan itace baƙar rana a gareni yau nice akayi wa fyde tabbas babu wani bam banci wannan fyde ne! .  




Sai da na kusa sumewa aka ƙyaleni, zuciya ta naji tana batun bugawa, naji duniyar ta isheni naji na tsani kaina da kowa ma na cikin duniyar nan!.  



Bayan wani lokacin haka aka sake afka mani, haka dai nayi ta kukan zuci wanda yafi wuta zafi, da ƙuna,  bayan kamar wani lokacin sai naji an fita, kuma an dawo, sautin murya naji, kamar haka:-




"Yarinya badan mace ɗaya bace, tsari na ba dana, ajiye ki koda a wani guri ne,  kodan wannan abun da nayi maki, amman yanzun ga kuɗi nan, masu yawa ki nemi lafiyar ki, kuma kije ayi maki wankin mara, bana bu'katar ganin fuskar ki, kema ba zaki ga tawa fuskar ba, kisani nayi maki nisa, har abada, kuma bazan sake ki ba, kije kawai haka nan dan ni bana iya sakin mace, idan lokacin da mace takeyi, ya kai zaki iya neman wanda zai rabaki da Aure na, koda yake baki san sun nan mijin ba, zaki iya samun duk sunan da kika fi tsana a duniyar nan, kice shine mijin ki, sai a taimaka maki amman kafin ki nadawo zaki iya aikata hakan idan kuma Allah yasa nadawo cikin rayuwar ki, tofa babu wannan zan cen ya roshe, 




Ga sabuwar waya nan nasan baki da ita dan na lura kuruciya na damun ki, kasan cewar ki mai tarbiya yasa har na kusan ceki, duk da banga fuskar ki ba, nasan baki son rasa wannan darajar taki, shi yasa kika tsaya baki damu da wata duniyar ba da ruɗin duniya, yanzun kije na baki wayar nan, da ƙuɗi gasu nan a cikin ƙaramin akwati sannan kuma harda wannan gidan duk sun zama mallakin ki da motoci guda biyu dake cikin gidan nan ke da duk wani abunda yake gidan nan. 



Na baki dan kiyi jinyar jikin ki, duk da kin iya boye mani budurcin ki, ni mijin ki kawai nasan sirrin ki,  duk da baya a gaba na. 



Ni ma sakani akayi ina tare da security masu duba ko na cika aiki na ne?, 




Babu wanda yasan da cewar wannan gidan nawa ne, amman ke haka kawai, naji na baki shi a kyauta. 




Kuɗin nan kuma nasan zasuyi maki amfani, zan buɗ maki baki, kiyi magana nasan kina da buƙatar ki zageni, kuma idan kika sake kikayi mani mugun zagi him! ". 




Allah Allah nakeyi ya buɗe mani baki, dan yanda zuciya, ta take ingiza ni jin nakeyi kamar na haɗe zuciya, na mutu. 




Hannun sa ya saka ya bud'e mani baki, ai kuwa abunda na fara faɗa shine, Allah ya isa na mugu azzalumi, kuma kamar yanda ka batawa marainiya budurcin ta, Allah yasa  wannan abun ya hanaka jin daɗin rayuwa, Allah ya isa na, kuma wallahi na tsaneka na tsani duk wani abunda yake naka ne, ka ɗauki tsiyar ka, bana buƙatar komai naka, nagode wa Allah da yasa banga wannan mummunar fuskar taka ba, azzalumi kawai". 




Ya ce, "ya Isah haka! idan kika sake zagi na, sai na ƙara maki abunda nayi maki, koma fiye". 




Na ce, "azzalumi kawai, mai cutar karamar yarinya wadda take da buri masu yawan gaske inyi karatu inyi aiki inyi kuɗi masu yawa na ginawa Umma gida da Inno da Yaya banda Mama dan na rama abun da take yi mani na rowa da hassada". 




Naji yayi yace, "ko yanzun ma zaki iya cika burikan naki, duka tunda ba kashe ki nayi ba". 




Da ƙarfi nace, "Allah ya isa na!, ka ruguza mani komai amman sai na rama wallahi ko ba yau ba, na murguda masa baki duk da kuwa kasan cewar baki". 



 Fita kawai naji anyi, ina ɗaga hannun na naji, a kwance harda ƙafa ta, hannu na saka na yaye abunda aka rufe mani fuskar ddashi, sai da na  runtse idon, saboda haske.  



Ina duba jikin na, na fashe da kuka na janyo dan kwalin da na gani gefe na rufe jikin na dashi. 



Kuka kawai nakeyi da takaicin yanda naga, jikin na, Ashe bani da komai a jikin na, kuma glub kunne haske ta ko ina. 




Allah ya isa kawai nake ja masa, na ɗauki alwashin sai na rama. 



Tashi nayi daket da jan ƙafa ina cije baki, na shiga gurin da naga an rubuta toilet na duba banga bokitin wanka ba, sai bahon wanka, tunowa nayi da wani siries din film a take nakoyi komai nayo wanka na fito, 




 Sallah nayi ban ma san adadin sallar da banyi ba, nidai nayi ta kwana biyu, abinci naga an ajiye mani, naci, nadawo tunanin abunda zan sama a gida idan na koma gida, bacci ne ya ɗauke ni, ina tashi da zazzaɓi na tashi, naje nayo wanka haka dai na kasan ce har tsayin kwana biyu ni ɗaya ina jin na sami sauƙi na fito sanye da kayan jiki na, ƙasa na sauka na falon gidan na kalla har kichin naje bayan na fito ne, na kashe komai na gidan mai aiki da wuta, makullai kawai na ɗauka da nagani a cikin wani ɗan akwatin ƙarfe, na fito gidan na rufe a harabar gidan, motoci biyu na gani na buɗe get ɗin na rufe naje na binne akwatin na ɗora dutsi natashi na fara dube_dube gabas kudu yamma arewa ina tunanin ina ne hanyar gidan mu?. 



Kawai  na saka kai ina tafiya ina wai wayen gidan dana fito, a gurin bushiyar lemon tsami, na tsaya ina futawa na ƙara ɗaukar hanya ke nan, wata motar tazo taja wani wawan burki a gaba na, kafin na gudu han an turani cikin motar an shaƙa mani wani abun bacci ya kamani ban tahi falkawa ba, sai a cikin ɗakin Inno. 



Ɗakin naji yana juya mani, na dafe kaina, da ƙarfin gaske, Inno da Yaya ne keta tofa mani addu'a, har nadawo cikin hayyacina, kuka na fashe dashi dan nasan, asiri na ya tonu, Kuka kawai nakeyi, tambayar duniya sunyi mani nace masu babu komai, kuma ni ban san komai ba. 



Kyaleni sukayi, koda na fito tsakar gida cewa akeyi yawo na naje, nadawo, tun ina damuwa har na daina damuwa, ranar na tambayi Inno yaushe ne nadawo gida, shine take bani labarin anyi nema na ba dare ba rana duk ba a ganni ba,  har kwana bakwai nikam tsoro ne ya ƙara kamani, kuma da aka tashi gani na a cikin layin mu ka tsince ni bana cikin hayyaci na har sai da na kwana ɗaya a gidan na falka. 



Nan ma Inno tayi tambayar duniya amman nace mata nima ban sani ba, bayan wata biyu ciwo ya kamani ni har ma na manta da abunda ya faru dani saboda hauka irin tawa, na ɗauka cewar komai ya wuce ashe matsala babba na nan, ciwo nakeyi kamar zan mutu, Mama ta ce, " da alama dafuwar ta nuna, ciki ya bayyana idan ba a yarda ba aje asibiti ayi awo ai kuwa cikin satin akaje asibiti rest din farko ciki wata biyu, aikuwa ƙarya tawa nayi, abu kamar wasa ƙaramar magana sai ta zama babba, duk inda akaje ciki wata biyu wasu harda sati ɗaya suke faɗa. 




Tabbas na shiga cikin matsanan cin damuwa da tashin hankali, na rasa ya ya zanyi da rayuwa ta ne inji daɗi, kullum cikin kuka nake tun daga wannan ranar ne, Mama da iyalan ta da yaran Yaya su biyu suke zagi na aka bi duniya dani, kawu kuwa dasu goggo cewa sukayi babu wanda zai haifa masu shege a cikin dan gin su, itama Umma kawun ta da matar sa sun zo sunyi rashin mutuci, harda su cewa a zubar da cikin aikuwa su Mama dasu kawu suka dage sai an zubar dashi, ni kuwa tunowa da nayi cewar fa wannan cikin ba shege bane da uban sa duk da ban san waye uban nasa ba, to wallahi ba zan yarda ba. 



Aka kaɗa aka raya naƙi yarda su yaya Halilu harda dukan tsiya sukayi mani amman naƙi yarda shine suka ce, zasu barni amman nasani duk ranar dana haihu to sai nabar masu gida Inno kuwa tace, babu inda zani ai gidan uba nane dan haka ciki itama bata yarda a zubar dashi ba, rigima sosai akayi a gurin. 



Tun daga wannan ranar ne na daina shakkar a zageni mutum na zagi na sai na sakar masa magana, su yaya kawai nake tsoro, aiki kuwa ina shan sa hardai Mama wadda take bani aikin wahala kuma ina yin sa, gashi duk abunda ta dafa duk yan da nake son abun nan bata bani, kuma nikam bana ma biye wa abinta saboda bana son gori dan tace ita bazata iya bani abunta ba, saboda ita ba zata iya ciyar da shege ba, da uwar shege, a ranar dana haihu kuwa a ranar aka koremu, wai anyi rabon gado bamu da gado cikin gidan sai gona, wadda aka siyar aka bamu dubu ɗari biyu da saba'in"


Kallon su Umma nayi dasu Jafar nayi murmushi wanda yafi kuka ciwo na ce, "Umma kinji yanda akayi wallahi ni ban san fuskar sa ba, muryar sa kawai na sani koshi dan munyi musayar magana ne! "



Hawaye masu zafi nake sharewa. 



Umma dai shiru tayi cike da mamaki tace, "ki sani baiwa ina shareki bane, wallahi ko bacci banayi saboda ke, kullum na kwanta da tunanen wane hali kike ciki nake kwana nake tashi, kuma ganin ki ɗakin Inno duk da kasan cewar tana sonki ina kula da yanayin da kike ciki, rashin kunyar miye zan nuna dan an taɓaki ai duk wanda ya nuna yafika son ɗanka to kai yake so, mahaifin ki yana kula da tarbiyyar ki, haka Inno to ni kuma saboda rashin godiyar Allah kulawar miye kike so nabaki eye! ?  Itafa duniya kaƙi naka duniya taso shi kaso naka duniya taƙishi, dan haka ni ina godiya da kulawar da kike samu, a gurin wannan mutanen. 




Kuma ko a gidan mu haka na taso Mama na ko kallon inda nake batayi saboda alkunya, amman mutane suna kula dani sosai  dan haka ni ba ƙin ki nakeyi ba ina son ki, kuma daga yau ina son duk abunda yake damun ki, kizo ki sanar dani, saboda alfarmar da mahaifin ki yayi ta nema a kanki kuma nima yan zun na gane sakaci na ne da rashin kulawa dake yasaka wasu abubuwan suka faru dake da kuma ƙaddarar rayuwar ki". 




Duk shiru mukayi muna sauraren Umma har ta gama maganar tayi shiru sai hawaye nake sharewa. 




Murmushi Amrah tayi tace, "Yaya Jafar Yaya Aliyu Anty Hindu Anty Humaira, zan ƙarasa maku labarin nan ta labarta masu komai har zuwa yau ɗin nan, cike suke da al'ajab. 



Aliyu ya ce, "to ke nan Narjeesah matar Salman ce ko? kuma Maman Shuraim ko? ". 



Ɗaure fuska nayi nace, "ni kotu zan kai shi ko kuma ya bani takarda ta, kuma duk da haka sai an bi mani haƙƙina! ". 




Jafar ne ya ce, "Narjeesah Salman mutumen  kwarai ne, amman duk da haka akwai gagarumar matsala! ". 



Kowa faɗar,  " Matsala! Matsala!! Matsala!!!  Kuma?  in banda Aliyu, dan da alama yadan komai. 



Jafar ne ya sharce zufar da ta zubo masa yayi yace, "eh matsala babba ma kuwa dan baku san waye Salman ba, amman yan zun zaku sani, keda kike cewar zakiyi ƙarar sa ki saurara da kyau kiji wane ne Salman da har kike takun saƙa dashi, ke da kanki zaki baiwa kanki amsa". 


Salman........ 




*Comment And share* 



*UMMU Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹




 💐💐 *NARJEESAH* 💐💐



*Rubutawa*

*NANA KHADEEJATU*

           *_UMMU IHSAN_*


*ELEGANT ONLINE WRITERS*


*Alhamdulillah  Am back*


_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_



               2⃣1⃣⏮2⃣5⃣

➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Salma Muhammad Yunus, ɗane a gurin Alhaji muhammad Yunus  ɗan gidan Mai martaba, Yunus, mahaifin Salman bayan kasan cewar sa ɗan Sarki tofa shi jakadan nageria ne a ƙasar london, a can aka haifi Salman amman mahaifin sa yana nan nageria, kuma mahaifin Salman yake jira ya zo ya anshi sarautar sa dan shine ake so a masarautar shi kuma yace baya buƙatar sarauta sai dai a baiwa Salman shima Salman ya ce, baya so sam, to har yanzun rigimar da akeyi ke nan. 


Salman ɗan gata ne gaba da baya, mahaifiyar sa, Hajiya Lamrat "yar gidan sarauta ce, ita kuma babbar masarauta a can london ɗin aka Auro ta, shi yasa Salman baya son zuwa nageria sai da Mai martaba ya nuna ɓacin ransa akan rashin zuwan Salman gurin sa, sannan iyayen suka shiryo suka zo, Salman yanada ƙanwa Salma da Autan su Muhseen, wannan zuwan nasu a nageria shine na farko a tarihin rayuwar su, Salman da ƙannen sa. 


Tunda Salman yazo nageria sam baya da farin ciki shida ƙannen sa, suka takurawa iyayen su akan su zasu koma koda ba tare da iyayen su bane, amman Mai martaba, yace shi bai san zan cen ba, sai dai iyayen su koma, abakin aikin su abar masa yaran nan sai sun saba zama tare dasu, a take duk suka a za rigimar sam su basu yarda ba, an wani zo an takura masu, jin furucin su Salman ne ya ƙara har zuƙa mai martaba inda ran sa yayi munmunan ɓaci, a take ya baiwa mahaifin su umarnin bai son ya sake kwana ƙasar nan, yau_yau ɗin nan yake da wannan ɓukatar, iyayen su Salman badan sun soba, dole sukabi umarnin Mai martaba suka tafi a ranar. 


Tunda iyayen su Salman suka bar su, shike nan suka rufe kan su a cikin ɗaki basu basu sha, kai sam basa ma fitowa, har sai da Mai martaba da kan sa yaje yana dukan ƙofar tasu akan su fito zaiyi magana dasu amman kamar bada su yake ba. 


Fruit, ɗin dake cikin ɗakin shi sukeci, da swan saboda sam basu iya cin abincin yan nageria ba, dan haka su basu jin komai sai kewar iyayen su da mahaifar su, sai da Mai martaba ya saka aka ɓalle masa ƙofar ya shiga cikin ɗakin shida matan sa, da ƙannen mahaifin su, Salman, a zaune suka samesu kowa ne su ya yi uban tagumi, kowa da ƙana nan kaya harda Salma ita da take mace a cikin su, kuma a lokacin tana da shekara goma sha bakwai ne, shiyasa hankalin su yaƙara tashi, su Mai martaba a tsaye suke akan su, amman sunyi kamar basu san da zuwan su ba. 


Mai martaba ganin yayi idan ya cika matsa masu tofa abin caɓe masa zaiyi, kawai sai ya zauna a kusa da Salman ya dafasa, a lokacin shi kuma Salman ya yi niyar tashi yabar gurin amman kuma ƙwar jinin Mai martaba sai ya hana shi aikata hakan amman bai kallesa ba, kallon su Salma da Muhseen yayi yaga duk sun juya masu baya kawai, ya yi dariya ya ce, "haba ku kuwa miye nayin fushi dan naso ganin ku a tare dani? Ashe laifine, dan na ce ina son na sabu da jikoki na? To kuyi hakuri dama sati ukku kawai nake son kuyi a nan sai ku koma ƙasar ku inda kuka saba, amman yan zun na janye wannan maganar idan naga duk kun saki jikin ku damu duka zan baku damar tafi, can ku futa inda ba'a takura maku kamar ni". 


Duk jikin su sanyi ya yi, ganin haka ne sai ya baiwa fulani damar taje gurin su Salma ta fito dasu shi zai fito da Salman, da ido yayi mata nuni a take ta fahimci maganar sa, kawai ta riƙa hannun Salma da Muhseen suka tashi suka bi bayan ta shi kuma Mai martaba ya riƙo Salman suka fito a falon sa ya zaunar dasu, ita kuwa fulani gyale ne ta yafawa Salma a jiki ganin yanda shigar ta, duk ta fito da tsiraicin ta, Salma duk taji wannan mayafin ya ƙara takura mata kawai ta fashe da kuka ta faɗa jikin Salman, a take ya rungume ta ya doddoka bayan ta, alamar rarrashi, haka Muhseen shima lallashin ta yakeyi har yana share mata hawayen idon ta, duk sai suka ƙara shiga cikin damuwa. 


Mai martaba tashi ya yi cikin fushi ya kira ɗansa, a waya yafara yi masa masifar yabar yara sun lalace, shi ba zai ɗauki wannan sakarcin ba, dole sai ya gyara masu tarbiya ko yana barin su, su koma gurin su, hakuri yake baiwa mahaifin nasa, Amman Mai martaba baima saurare sa ba ya kashe wayar, ya saka aka kawo masu abinci, aikuwa ko kallon abinci basuyi ba, sai kowa ya tafi ya basu guri bisa ga umarnin Mai martaba. 


Mahaifin sune ya kira su video coll ai kuwa suk suka sakar masa kuka, Salman ya ce, "wallahi Dad yau gudowa zamuyi wannan wane irin mutane ne wanda basu san "yancin ɗan adam ba, gaskiya nikam na gaji Salma ku tashi ku shirya yau zamu bar wannan baƙar ƙasar". 



Tsawa Dad ɗin su ya sakar masu wanda har sai da suka zabura suka saki wayar wannan shine karon farko da hakan ta taɓa faruwa dasu, duk duka koma jikin Salman suka shige, suka bar wayar a gurin, mahaifin nasune yaci gaba da faɗar, "taya zaku zagi ƙasata ƙasar da aka haife ni, da ku a tunanin ku bana son ƙasata ne nake zaune a ƙasar wasu can, to ku sa ni  nima zaman dole ne nakeyi anan ɗin kuma dolene ku zauna anan ku saki jikin ku da iyayena da yan uwana da dangi na, kuma ni kaina wannan lokacin na ajiye masu aikin su nima nawo gida, idan yaso sai kuci gaba da zagin ƙasar taku dan kuma kuna da alaƙa da ita tunda nida na haifeku, a nan aka haife ni, dan haka dolene ku saba kuma kubi umarnin mahaifina!! ". 


Kawai ya kashe wayar, ganin wannan abun sukeyi kamar a film, a take Salma tace, "bros ba zamu zauna anan ba kuma gashi an sauyawa Dad tunanin sa ya daina son mu nikam zan koma gamany ne idan yaso duk sanda suka dawo da son mu su nemen! ". 


Shima Muhseen wanda yake biwa Salma ɗan shekara goma sha huɗu, yace, ", zan koma school ɗina ne, ba zan je gurin su Dad  ba dan haka tare zamu tafi ". 


Murmushi Salman yayi yace, "da dare zamuyi wannan tafiyar ". 


Aikuwa sai da dare ya tsala kowa yayi bacci, masu tsarin gidan ne kawai suke ido biyu, Salman Salma Muhseen duk suka ja jakar su, suka fito ko tsoro babu, kawai suka sa kai batare da sun kalli mutum ɗaya ba daga cikin masu gadin gidan har sun isa bakin ƙofar fita sun fara farin ciki harda tafawa, kawai Salman yayi turus haka su Salma da Muhseen suka zubawa ƙofar ido. 


Ƙarasowa yayi inda suke ba tare da yace dasu uffan ba kawai yaja hannun su ya ƙarasa fita dasu a cikin wata mota aka ɓude masa ya saka su a ciki shima ya shiga daga ciki aka rufe, yaye mayafin fuskar sa yayi, atake suka haɗa baki gurin faɗar, "grandpa!! ". 


Murmushi kawai yayi masu ya bada umarnin tafiya, aka ja motar, sai tafiya sukeyi, cikin wata unguwar da wasu mutane duk a waje suke kwana, saboda gida jen su duk sun rishe, wasu zane ne suka ɗaura suka killace, parking akayi a hankali ya sauka daga cikin motar ya fara jawo hannun Salma da take ita ce a kusa dashi, sai kuma yaja hannun Salman da Muhseen, duk suka fito suna dube_dube gashi dare ne unguwar sai ɗoyin kwata ke tashi, bayan motar aka buɗe aka riƙa sauke kwalayen taliya indomie shinkafa irin buhun nan masu ɗaukar kwano huɗu, ƙanan jarkar manja man gyaɗa magi gishi, sai amblant, layi Mai martaba yake bi yana ajiye masu kayan a gaban su tare da amblant ɗin, su Salman kuwa cike suke da mamaki, wata mata ce ana ajiye mata kayan zasu tashi da sauri ta riƙewa Mai martaba ƙafa, ta fashe da kuka, Mai ne ya ɗuƙa yace, "mike faruwa ne daga ganin wannan kukan kin daɗe kina yin sa" 


Tashi zaune tayi tace, "dan muna talakawa shine aka maida mu bayi babu mai kulawa da halin da muke ciki, maru nd gareni mata biyu dan rashin imani anzo an ɗauke mani su duka duk anyo masu ciki, ɗayar gurin haihuwa ta haɗu da lalurar yoyon fitsari kuma, mutanen ya ce, ba zai iya ɗaukar nera ya bamu ba mu nema mata magani ba, kuma bamuda wanda ya isa ya kamasa da laifin cikin da yayi mata kuma ya saka ɗan sa ya ɗauke ƙaramar itama yan zun haka tana ɗauke da cikin ɗan sa, munje police, an koro mu, to shine "yar tawa tace zata kashe kanta, nikuma na hane ta da aikata hakan shine suka gudu suka barni, wai basu kashe ni da baƙin cikin suba! ". 


A take jikin kowa yayi sanyi a gurin, Salman ya ce, baku da human right ne a ƙasar nan? ". 


Shiru Mai martaba ya yi kukan tsohowar na damun su, Salma tace, "yaran naki kin san inda suka tafi ne?". 


Kai ta gyaɗa masu ta ce, "ance mani an gansu, amman na kasa zuwa inda suke gudun kada su bar gurin ". 


Salman ya ce, "zamu zo da safe amman kiyi shiru da bakin ki". 

Tashi sukayi suka ƙara sa gaba, haka sukayi ta cin karo da masu matsala, matsalar wani dattijo ta ƙara sanyaya masu gwiwa, saboda yaran sa ukku biyu maza ɗaya mace, ne gobe za'a yanke masu hukuncin kisa, saboda sun sace wa Mai gidan da suke yiwa aiki maƙudan kuɗade, a take hankali kowa ya tash. 


Muhseen ne ya ce, kuma an tabbar da sune suka aikata hakan? "


Dattijon ya ce, "harda shedu suna su wanda suka ce, sun gane su da idon su suna aikata hakan, kunga kuwa ni babu abunda zan iya faɗa duk wanda mukaje gurin sa ya taimaka muna sai ya ce, shi sam baya iyawa, wani mane yace, zai taimaka muna amman sai mun bashi miliyan ɗaya,  ni kuwa ko abincin da zamuci wahala yake yi muna nida mata ta da ƙana nan yara na, wani kuma ya ce,zai taimaka muna ashe ƙarya yakeyi, wannan mutanen ya turo shi, muna zuwa kotu, yace shi ba lauyan mu bane lauyan mutumen ne! ". 


Tashi tsaye sukayi Salman ya ce, "zamu zo da safe insha Allah ". 

Gida suka koma har ɗakin da suka baro Mai martaba ya raka su,suna shiga suka rufe ƙofar, suka kunna glub, duk suka zazzauna a ranar basuyi bacci ba, tun da asuba Salman da Muhseen suka nufi masallacin gidan kowa ya gan su a wannan nan lokacin sai yayi mamakin hakan amman su basa kula kowa har akayi sallah sai da safe suka fito bayan sunyi azkar". 


Darect gurin Mai martaba suka nufa a cikin falon gidan inda kowa yake kawo masa gaisuwa, kowa ka gani cike yake da mamakin ganin Salman da Muhseen, Mai martaba suka nufa suka rungume sa, suka sumbace shi, zasu juya ne ya janyo su jikin sa, shima yayi masu yanda sukayi masa, yace, "Allah ya yi maku albarka ". 


Amin kowa ya ce cike da farin ciki, Salma ce ta fito itama da shagar ta ta ƙananan kaya amman wannan da ɗan damar su, ta zo ta rungumi Mai  martaba ta sumbace shi, shima ya ce, "Allah ya yi maki albarka ". 


Ta dawo gurin su Salman suka rungume juna, suka sum baci juna, ta koma jikin fulani ta sumbace tayi kwance a jikin ta, zama su Salman sukayi ƙasa a kusa da ƙafar Mai martaba, bayan sun zauna ne, ƙanen mahaifin su wata, shattima ya ce, "Alhamdulillah abu ya yi kyau sannu a hankali komai zai tafi dai_dai ". 


Duk sukayi dariya, abinci aka kawo kowa da abunda ya ke ci, Salman da Muhseen Salma suka tsare kowa da ido cike da burgewa, sai da fulani ta ce, "ku ba zakuci komai bane? ". 


Salma ta ce, "yau fa duk azumi mukeyi yau Thursday kasan cewar Dad da Mom sunayi shi yasa duk mun saba a kowa ne Monday da Thursday ". 


Jin jina kai Mai martaba ya yi haka fulani da murmushi ɗauke a fuskar ta, wata budurwa wadda suke sa'a ɗaya da Salma ta ce, "shike nan ma kuwa daman naji labarin Uncle duk abunda ya keyi yana kaman ce ceniya da Mai martaba, gashi kuwa yau mun fara sani muma dan haka fulani ba zaku sake yin wannan azumin bada ni ba ". 


Dariya akayi masu, Salman da Muhseen Salma ne suka tashi suka shiga ɗakin su, kowa ya fito a gyare Salman da Muhseen duk sun yo shigar su irin ta cikakken turawa, sunyi stoking, sai duk suka burge kowa Salma kuwa doguwar riga ta saka har ƙasa amman ta sako gashin kanta a ƙafaɗar ta, babu ɗan kwali sai fula facing cap, da haka a hannun ta, irin ta ma aikata, haka su Salman suke, kallon su kawai akeyi. 



Mai martaba ne ya tashi ya ce, "kuzo muje daga ciki". 


Murmushi kowa keyi da mamakin taya akayi Mai martaba ya shawo kan, wannan yan rigimar nasa, koda yake Mai martaba Allah ya yi masa baiwa wadda ba kowa ne yasan da hakan ba. 


Ɗakin Mai martaba suka shiga anan ne shima ya shirya ya kira waya, ya yi magana sannan suka fito yana gaba suna biye dashi, fadar suka nufa, sai gaisuwa ake kwasa, kowa ya kalli, su Salman sai ya sake kallon su, motoci aka fito dasu, aka jera shiga sukayi su Mai martaba da tawa gar sa, su Salman suka shiga wata motar ta daban, suka ɗauki hanya, motocin Mai martaba hanyar su, daban suka ɗauka, haka su Salman, wani ƙayataccen gida suka nufa, suna yin parking suka zauna direban ne ya fito shida wani bafade da suke tare suka shiga, basu wani daɗe ba, suka fito sukayi masu iso. 



Wannan dattijon ne da wannan tsohowar da wasu mutane su ukku a zaune saman kujera, hannu suka baiwa Salman da Muhseen Salma kuwa hannu ta ɗaga masu ta ce, "Hi". 



Gurin zama aka basu suka tattauna tare da sake yiwa wannan dattijon tambayoyi yana amsa masu, haka wannan tsohowar, magana suka sakeyi da wannan mutanen, sukayi basu hannu sukayi masu sallama suka fita daga cikin gidan mota suka shiga suka nufi wani gurin basu daɗe ba, suka ɗauki hanya sai wata unguwar, a bakin wani gidan suka faka motar, bafaden ne ya fito yayi sallama aka amsa mashi mai gidan ne ya fito bayani yayi masa tare yake da baƙi mutumen ya ce, "nasan da zuwan su kace dasu si shigo". 



Tare suka fito suka shiga cikin gidan iso mai gidan ya yi masu har cikin ɗakin sa, wannan tsohowar ce, da wasu matasan mata zaune sai kuka suke wata mata tana gefen su, zama su Salman sukayi, suka fara yi masu tambayoyi suna amsawa, daga nan suka fito suka ɗauki hanya sai wata babbar kotu, suna isowa yayi dai_dai da mai shari'a yana yanke hukunci kamar haka:-ni alƙali Muktar na kotun mages tree na yanke wa wannan yaran Haruna Nuhu Musa Nuhu Saude Nuhu hukuncin.. Da sauri, Salman ya ce, "ya mai girma mai shari'a ayi hakuri da zuwan mu a makare suna na Salman Yunus muhammad, loya ne ni mai zaman kan sa, ina tare ne da loyan Human right daga hukumar human right ta duniya, mune wanda zamu Kate wannan mutanen da ake ƙara, takardu ya baiwa wani maga takardar kotu, a take ya ansa ya baiwa wasu suka duba aka baiwa alƙali ya duba, umarni ya basu da su ƙaraso ciki su zauna, zama sukayi si biyu, shi kuma Muhseen ya samu guri ya zauna. 



Lauyoyin gurin duk haushin shigowar su Salman sukaji, mutumen da yake ƙarar su, jin yakeyi kamar ya tashi ya kashe su Salman, su kuwa bayin Allah kuka ne kawai sukeyi, mutane kuma masu kallo gyara zama sukayi dan kowa son yakeyi yau ayita ta ƙare, bayan Salman ya zauna shida Salma, alƙali ne ya baiwa Salman damar fara aikin sa, aikuwa Salman ya tashi tsaya, rigar lauyoyi ce ya saka, yaje gaban su Haruna ya kafe su da ido ya yi murmushi san nan ya ce, "Sunan ka muke son sani ". 



Kallon Baban su da innar su sukayi ganin sukayi suna hawaye suna ɗaga masu kai, aikuwa ya ce, "Haruna Nuhu" kowa gurin cike yake da mamaki dan tun da aka fara shari'a dasu wannan zaman shine na biyar sai yau suka taɓa magana shi kanshi alƙalin sai da ya jin jina. 


Salman ya ce, "shakurun ka da aikin ka please". 


Amsa masa ya yi shekaru na ishirin da shida, ina yin wanko da guga ne a gidan Alhaji  Ƙasimu, shekara ta ukku a gidan sa ina aiki". 



Murmushi Salman ya yi ya dawo gurin ɗaya ya tambayi sunan sa, sai ya ce, "Musa Nuhu shekara ta ishirin da ukku, ina aiki ne a gidan Alhaji Ƙasimu, nine wanda yake yi masa gyara da kula da fulawar sa, shekara ta biyu ina wannan aikin". 



Itama Saude ta amsa masa amman ita abinci ne kawai take dafa masu, shekara ta ishirin dai_dai". 


Salman ya duba alƙali da mutane ya ce, "ya mai girma mai shari'a ina son kotu ta bani dama nayi magana da Alhaji Ƙasim"



"Kotu ta baka dama" fitowa yayi yana tafe yana hura hanci ga uwar zufar dake zubar masa ta ko ina, yana tsayawa, Salman ya kafe sa da ido, ai kuwa duk ya daburce, murmushi Salman ya yi ya ce, "koto zata so sanin Sunan ka"



Kallon Salman ya yi, ya fara gyara babbar rigar sa, ya ce, "ba kotu ke ce ke son sanin sunana ba, kai ne kake son sanin suna na kaida ba ɗan nageria ba, su yan nageria ai sun san ko waye Alhaji Ƙasimu a ci dukiya! ". 



Tun kafin Salman ya yi magana alƙali ya ce, "ina mai horon ka da ka guji kaucewa umarnin kotu nan kotu ce, ba gidan ka ba, dan haka dolene kayi biyayya ka yi duk abunda aka umurce ka idan ba haka ba akwai hukunci mai tsana nin da zai iya hawa kanka". 


Salman ya ce, "nagode ya mai girma mai shari'a" kallon sa ya mai da aka Alhaji Ƙasimu. 

Shiru ya yi ya sharce zufa ya ce, Sunana Alhaji Ƙasimu aci dukiya shahararren mutum wanda ya tara dumbin duk... ". 



Salman ya ce, "dakata malam iya Sunan ka kawai muke son ji, kuma munji shin da gaske ne kamar yanda suka faɗa shekarun da suka ɗauka a gidan ka, haka ne? ". 



Cikin gadara ya ce, hakane kuma tun lokacin basu taɓa shiga can cikin gida na ba, saboda bana son sa ido, ehe!". 


Dariya mutane suka fara a ɓoye lauyoyin sane da sauri ɗaya ya tashi ya ce, " ya mai girma mai shari'a taya lauyan wanda yake kare wanda ake ƙara yake daburta mai ƙara? "


Salman ya kafe sa da ido shima a take ya tsuke bakin sa, ya koma ya zauna yana goge zufa, alƙali ya ce, ai ba matsa masa akayi ba, kuma ba tukura masa akayi ba, tambaya ce yake amsawa dan haka ƙorafi bai ƙarbu ba, sai a ki yaye loya, Salman ya duba yace, ci gaba "



Murmushi Salman ya yi, ya ce, "nagode ya mai girma mai shari'a ". 


Salman ya ce, "kace basa shiga cikin gidan ka, amman duk shekarun da sukayi a gidan ka antaɓa kamasu da wani laifin ne makaman cin sata? ". 


A a yace, kuma ni har ma mantawa nakeyi dasu a gidan, sai da akayi mani wannan satar ne, nagane ashe su ɓarayi ne kuma ni ina da shedun da suka ga lokacin da suka fito da kuɗin suka gudu". 


Salman ya ce, "wato dai kai baka ga lokacin da suka fito da wannan maƙudan kuɗaden naka ba". 


Ya ce, "eh kai nifa nagaji da wannan tambayoyin naka ne shi yasa nake sanar da kai gaski, kuma lauyoyin dana ɗauka duk sun kasa bani taimako, to gaskiya tunda ba lahira muke ba, zan sanar dakai wanda suka gan su da idon su, Mai gadi na Lado sai yara na maza guda biyu Ashir da Yasir, sune suka sanar dani a lokacin da nake haukar neman kuɗin nawa". 



Kiran su aka ba Salman damar yi ya kuwa kira su, kallo ɗaya Salman ya yi masu, a take ya fahimci basu da gaskiya, Salman ya ce,"mai gadi kaine cikin ma'akatan gidan kaga lokacin da suka fita da kuɗin ko? ". 




Tsuru_tsuru sukayi mai gadi sai soshe_soshe yakeyi, kowa ya kafesa da ido kawai ya fashe da kuka yace, "nidai ban ga lokacin da suka fita da kuɗin ba, kuma nima kashedi akayi mani akan nace sune, idan ban ce sune ba, kashe ni zasuyi, shine nazo nabada sheda suka bani kuɗi nera dubu hamsin ne suka bani, kuma wannan da muke tare sune suka fito da jakar kuɗin cikin dare kasan cewar ni ne mai gadin gidan dan haka ne, nima na gan su! "


Kuka yake, su kuwa tsuru_tsuru sukayi sai zarar ido sukayi, tambayar farko suka bada tabbacin sune suka saci kuɗin suka sayi mota suka ɓoye sauran kuɗin kuma sun kashe wasu, sun ɓoye wasu".  



Hamdala kowa yakeyi shi kuma Alhaji Ƙasimu aci dukiya mutuwar tsaye ya yi jin cewar yaran sane ɓarayin ba yaran wasu ba, dan haka mai ɗa goye baya cewa ɗan wani shege, sai yan zun yasan fassarar wannan karin maganar. 



Salman ne ya kalli mai shari'a ya ce, ya Mai girma mai shari'a ina son kotu tayi dubo da aikin da wannan bayin Allah sukeyi a gidan wannan mutanen kamar yanda suka faɗa da yanda mai gidan ya faɗa da yanda shedu suka faɗa, duk da kasan cewar sheɗun sune suka aikata hakan, da wannan nake son kotu ta wanke bayin Allah nan nagode ya mai girma mai shari'a ". 



Yana zama alƙali yayi rubuce_rubuce ya ce, ko akwai wani mai magana daga cikin lauyoyin ne? "

. shiru sukayi Salma ce ta tashi tsaye ta ce, "Suna na Salma Yunus muhammad nice lauyan da human right ta turo akan wannan ƙarar kasan cewar duk wani haƙƙi na ɗan adam muna da alƙa dashi, muna neman haƙƙin wannan bayin Allah da aka zalun ta, aka yi masu ƙazafi aka kai su gidan yari suka sha kunun gidan yari, da duka idan aka dubi yanda suka dawo ga tabon duka nan ta ko ina da wannan ne muke jan haƙƙin su a gurin mutanen da ya kawo su, wanda shine sanadiyar komai, nagode ya mai girma mai shari'a " 


Zama Salma tayi kowa mamakin yakeyi yanda akayi su ba hausawa ba, amman suke jin hausa kamar mi sai dai hausar tasu bata hau bakin su ba, da kyau, dan suna yin magana zaka gane turawa ne, su. 



A take alƙalu ya yanke hukunci ya ɗaure su, ya wanke bayin Allah nan ya nemeni haƙƙin su akan Alhaji Ƙasimu aci dukiya saboda shine ya ɗaure su, kuɗi akace ya basu kowa ɗubu ɗari da hamsin dubu ɗari huɗu da hamsin ke nan. 



 a take ya ce su bishi gida su ansa hannu da hannu. 


Kotu ce ta tashi da sauri Salman yaje ya yanki wani sammacin aka baiwa yaron alƙali yaje ya kai, ya tafi, fito wa sukayi shida Salma suna riƙe da hannu juna, gurin Muhseen suka nufa da sauri ya rungume su yana yi masu barka da samun nasara akan wannan shari'ar, jikin motar su suka nufa anan ne lauyoyin suka zo suka basu hannu Salman ne kawai ya amsa Salma kuwa kai ta ɗage, fadawa ne suka zo kiran su, cike da mamaki kowa yake kallon yanda fadawa suke duƙawa suna gaishe su, tafiya sukayi gurin da mai martaba yake tare da tawa gar sa da wannan dattijon da iyalan sa, suna yi masa godiya duk wannan lauyoyin suna biye dasu, su Salman na zuwa aka basu guri kawai suka je suka rungume kakan nasu tare da sumbatar sa, nuna masu yayi masu godiya kawai Muhseen ya ce, "mu bama buƙatar godiyar ku kuje kuyi ta muna addu'a ita ce kawai muke buƙata". 


Hannu su Salman suka ɗaga masa, aikuwa sun sha addu'a haka suka tashi suka rafi, ɗan saƙon ne ya dawo tare da mutanen da akaje nema suna zuwa suka shiga chamber, anan ne aka sa santa suka ce sun yarda da cikin sune suka ɗauki nayin memawa ɗayar lafiyar ta, da kula da abunda ta haifa, itama ɗayar zasu kula da lafiyar ta da cikin ta har ta haihu tayi yaye dasa hannun kotu,  kowa abun yayi masa, da daɗi, godiya da addu'a sun shata sosai. 



Gida suka koma tun daga wannan ranar ne kullum cikin dare sai sunbi Mai martaba sun jiyo koken jama'a suna tsaya masu, cikin kwana ki ƙan ƙani sunan su ya baza gari kowa zuwa yakeyi da buƙatar taimakon su, suna taimawa, amman mai gaskiya kawai suke yiwa wannan idan kazo da rashin gaskiya yi sukeyi kamar basan da zuwan kaba, idan ka gaji dole ka tashi ka tafi, sai aka maida su garkuwar talakawa, Sunan su ya zaga ta ko ina, duk Nigeria an san dasu, anan ne mutane keyi ta kawo masu, gari mata da maza, yan mata kuwa kowa, Salman yake son Aure dan dai kawai babu damar ganin sane, samari da manyan mutane kuwa Salma suke son Aure amman sam basa kila kowa. 



Watan su Salman biyar basu koma london ba, iyayen su sunji kewar su, har gaji kawai suka shirya zowa Nigeria, barare da sun kira sun sanar da zuwan nasu ba. 



Yau su Salman ne zaune a cikin "yan uwan su, dan yan zun sun saba da su, Salma kuma ta fara saka doguwar riga amman har yan zun bata wani saba, dan zafi takeji idan ta saka, sallamar su, Dad da Mom ɗin sune suka shigo cikin falon aikuwa kowa da farin ciki ya tashi suke tarbon su, su kuwa farin ciki sukeyi suna rungume jinin nasu, kallon su Salman sukayi da suketa harkar gaban su, Salman yana danne_dannen laptop Salma  ma laptop ɗin ce a hannun tana aiki, shi kuwa Muhseen waya ce a hannun sa ya saka earpiece akunne sa, cike da mamaki kowa yake kallon su, fulani kuwa cewa tayi, "Salman Salma Muhseen bakuga iyayen ku bane? ". 



A tare suka ɗaga kai suka dubi fulani, suka maida idon su akan aikin su, cikin sanyi jiki Mom ta ce, "my ɗear baku san da zuwan mu bane a nan way kuka share mu?. 



Ɗaga idon sukayi suka ɗaga masu hannun "hi Mom hi Dad" suka tashi bar gurin iyayen bin su sukayi da ido suna shiga cikin ɗakin su, su Dad suka zauna daɓas cikin damuwa. 



Fulani ta dubesu ta ce, da alama kunyi wa yaran ku, laifi amman zasu sauko ne, tunda gashi sun sauko yan zun sun saba da kowa". 



Uncle ɗin sune yake ƙara sheda masu aikin da sukeyi anan shine ya hana su koma gurin su ba, Mai martaba ba, Dad ya ce, eh duk abunda akeyi ina sane saboda ina magana da Mai martaba a kullum, kuma tun lokacin nake sheda masa yaran nan sam ko mun kirasu a waya ba wani magana mukeyi dadu ba daga gai suwa basa ƙara cewa damu komai! ". 



Tausayin su sukaji ya kama su, a ce kai da ɗan ka, amman babu wata magana daga gaisuwa har tsayin wata biyar , lallashin su akayi sai da suka haƙura aka cika masu gaban su da kayan ciye_ciye. 



Salman da Muhseen da Salma kuma suna shiga cikin ɗakin suka fara dariya harda tafawa ajiye kayan sukayi suka, zauna Salma ta ce, "kagafa Dad wai har ya manta irin tsawar da ya daka muna wai mun zagi ƙasar sa, ai ga munan mun zauna ƙasar tasu, kuma ba zamu koma ba". 



Dariya duk sukeyi, Muhseen ya ce, kuwa ma yan zun ma yawon zaga gari nake son yi, duk da ranar naji Dad da Mai martaba suna magana akan bikin ɗan gidan Mai girma governor ashe abokin Dad ne, shine naji yana faɗar ba zai samu damar zuwa ba, sai dai mu muje mu wakilce sa". 



Salman ya ce, "sai dai ku kuje ni kun san babu inda zani, saboda ni ban cika son yawan damuwa ba, ba kowa nake son hulɗa dashi ba, gaskiya kuma kun fi kowa sanin haka, kune ƙanne na wanda nasa daku, duk da a gida ma, ba wani cika shiga lamarku nayi ba, kasan cewar bana son haya niya kwata_kwata". 



Dariya duk suka sanya masa, sukaci gaba da aikin su, da sukeyi a computar su. 



Tun lokacin da Mai martaba yaga gudan jinin sa ya dawo, shike nan farin cikin sa yakasa ɓoyuwa, sanar dashi damuwar su sukayi, murmushi ya yi yace, ai tunda kun dawo sai ku jawo abun ku a jikin ku, ku tashi ku shiga cikin ɗakin su" 


  


cikin sanyin jiki suka shiga cikin ɗakin gurin Salman suka fara dosa domin shine babba sauran kuma biyayya sukeyi masa a tsakiyar su suka saka Salman, shi kuma yana ganin hakan ya shagwabe fusa ya kwanta, jikin Mom ya saki laptop ɗin sa ajiki sa, Mom tace, "son fushi dai fushi dai abu yakai some 6moth ya kama ta kuyi hakuri haka nan, duk irin son da muke yi maku, ku a tunanin ku, shike nan Mai martaba zai nemi alfarma muƙi yimasa ne?  Haba son kudu ba fa, munyi kewar ku, sosai ko a waya baka sakar muna jiki duk kun bi kun hanamu kwanciyar hankali, iye?  Nifa na haifeku ni mayi haƙuri nabi umarnin kakan ku amman ku sai kusa na kasa yi masa biyayya bayan tamkar mahaifi yake a guri na? ". 



Dad ne ya ce, "ni kuma fa baiwa nayi maku tsawa bane dan kuji haushi bafa dan kawai kuyi saurin fahim tane nayi maku hakan amman shine kuka ɗauki fushi damu". 



Tsakanin ɗa da iyaye sai Allah atake suka shawo kan su, sukaci gaba da farin ciki tare dasu. 



Bikin da su Dad sukace ba zasu zoba, sai gashi dasu za ayi Dad ɗin sune yaje dasu gidan governor, anan suka haɗa kan iyalen su, inda anan muka haɗu da Salman kasan cewar Khalid ɗan gidan governor abokin mune tare muka tashi dashi munyi karatu dashi tub daga secoundary har i zuwa university couse ɗaya mukeyi dashi har muka dawo gida nigeria, muka fara aikin likitanci, sai dai ba garin mu ɗaya ba, muma bikin sa ne muka zoyi, kasan cewar Salman sa'an mune, sam bamu wani sha wahalar zama abokai ba, kasan cewar mu bama da hatsaniya dan duk abunda abokan ango sukeyi, badamu ba, zuwa gurin Amarya da ƙawayen ta, sai da ma za'a gurin dinier ne, angon ya nuna fushin sa, akan dole nida Aliyu da Salman  sai munje gurin dan yasan halin iri ɗaya ne, ganin yanda ya kafe dole muka shirya mukaje, koda mukaje gurin bamu shiga ba muna cikin motar, waya yayi ta kira saboda anfara shagali bai saka mu a idon saba. 



Dole muka ɗauki wayar sa kasan cewar yayi kiran wayar mu har ransa ya fara ɓaci mu muna kallon sa, dole muka fito uban yan naci ya kira mu. 



Bamu wani jima a gurin ba, saboda yanda "yamta ke ta zuwa gurin gurin amsar number waya dole muka dawo cikin motar, har aka tashi muka koma gida, tunda aka kai Amarya muka anshi number wayar Salman, muka baro kaduna muka dawo nan yola, tun daga wannan lokacin ne abota mai ƙarfin gaske ta shiga tsakanin mu, ko ince aminta har muka san junan mu da aikin juna da sirrin juna, kowa idan wani abun ya shige masa yakan kira ɗan uwan sane, kwata_kwata bama yin abu ko miye dan muna mu biyu sai mun saka Salman aciki shima haka, a dangin sa duk ansan mu haka ma dangin mu kowa yasan Salman. 



Numfa sawa Jafar ya yi ya ce, "babbar damuwar da Salman ya fara fuskata a rayuwa wadda ta zame masa ƙalubalen rayuwa take ci masa tuwo a ƙwarya har yanzun wadda wannan ya shafeki Narjeesah shine zaki sani a yanzun kasan cewar, har yan zun baki san waye Salman ba shine.... ". 




*Comment and share*



*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹



 💐💐 *NARJEESAH* 💐💐



*Rubutawa*

*NANA KHADEEJATU*

           *_UMMU IHSAN_*


*ELEGANT ONLINE WRITERS*


_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_


*Ya Allah kajiƙan iyaye na kayi masu rahma ka sada su da rahmar ka dasu da duk kannin yan uwa musulmi baki ɗaya amin*



               2⃣6⃣⏮3⃣0⃣


➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Narjeesah Salman sai da ya zamo fittacen lauyan da ƙasa take alfahiri dashi ya kasan ce mutum mai gaskiya  wanda akeji dashi ta ko ina a faɗin ƙasar nan ".  



Rayuwar Salman ta fara sauyawa ne saka makon haɗuwar sa da yar mataimakin shugaban ƙasa, Haulart, Haulart ta shiga rayuwar Salman ne da ƙarfin gaske, wanda muka rasa taya hakan ta faru kasan cewar bamu sani ba, dan bai sanar damu ba sai ranar ɗaurin Auren sa, wanda ta kasan ce iyayen Salman da "yan uwan sa sai ranar suma suka san da zan cen, dan haka Auren bai wani samu shagalin biki ko ɗaya ba, dan yace wa su Mai martaba kada ayi taron komai dan shima Auren zuwar masa yayi da rana tsaka. 




Tunda aka ɗaura Auren Salman da Haulart suka bar ƙasar sai da suka shafe shekara biyu suka dawo garin Abuja suka sauka, Salman ya sauya, baya neman kowa nasa, daga shi sai matar sa kawai suke bidirin su. 



Matsalar farko da ta fara fuskar tar Salman rashin haihuwa wanda alokacin kowa yasan Salman baya cikin hayyacin sa, dole Mai martaba da kanshi ya nemi Salman kuma yayi masa nasiha da ya dawo hayyacin sa, ya waiwayi iyayen sa, da suke fushi dashi, cikin ikon Allah kuwa Salman yayi abunda Mai martaba ya umurce sa, dashi kowa yaji daɗin sauyawar Salman, kuma fa duk wannan halin da Salman ya shiga, yana nan yana aikin sa akan gaskiya da sanya marasa gata a cikin lamarin sa, ƙungiyoyi ya kafa sosai na kula da gajiyayyu da marasa ƙarfi, da marayu, da malamai hidima sosai yakeyi masu, wannan shine ya ƙara wa Salman daraja a idon mutane, 



Ganin har shekara ukku Salman da matar ta basu haifu ba, suka fara shiga damuwa kasan cewar Salman shine ya shiga damuwar da yawa sai suka fara zuwa ganin likitoci amman abun mamaki duk ƙasar da sukaje result ɗin Salman yakan nuna cewar Salman kwata_kwata baya haihuwa matar sa ita kuma lafiyar ta, ƙalau, wannan abun ya ɗaga hankalin kowa ba kamar Salman wanda ya shedawa iyayen sa, zai rabu da matar sa, dan gudun kada ya cutar da ita, sunji tausayin Salman sosai kuma sunji daɗin Salman zai rabu da wannan "yar isakar matar wadda tunda sukayi Aure da Salman sau ɗaya suka taɓa ganin ta har su Mai martaba. 




Tunda Salman ya shedawa Haulart hukunci da ya yanke tace, sai Salman yayi nadamar rayuwar sa, shida iyayen sa, duk sai sun zubar da hawayen su, ai kuwa tun daga wannan ranar Salman bai sake fita koda ƙofar gidan sune sai da jami'an tsaro wanda mahaifin matar sa, ya haɗasa dasu, ga baki ɗaya Salman ya manta kowa nasa, baya tuna koda sunan iyayen sa, haka iyayen suka tsani ace sun haifi ɗa mai suna Salman. 




Abu kamar da wasa ƙaramar magana ta zama babba daga baya ma baya iya kallon ko wace mace, saboda duk maccen da zatayi wa Salman magana zai ganta a gaban sane kamar suffar alade, Haulart ce kawai yake ganin ta a matsayin mace kuma cikkakkiyar mace, wannan abun har iyayen sa, sun shiga daga cikin abun ƙin sa, akwai ranar da Salmah ta haɗu da Salman a wunin wani aikin da ya haɗasu a tare, kasan cewar sun san Salman yan zun baya ko tuna sunan su, ta matsa a kusa dashi ta ce, "bros nasan baka son ganin fuska ta, nima haka, amman kasani muna kewar ka muda iyayen mu, bro duk wanda ya aikata hakan a gare mu ba zamu taɓa yafe masa ba, na barka lafiya ". 



Tunda Salma ta ambaci sunan sa, kansa yake a ƙasa bai ɗago ba, har tabar gurin, a ranar da ciwon kai ya kwana mai tsananin gaske, sai da ya kwana, biyar yana jinya sannan ya samu sauƙi, tun daga wannan ranar ne yake yi muna sallama a WhatsApp wanda rabon da yayi muna hakan har mun manta dukan mu, to anan ne yake sheda muna yana barar addu'ar mu, kuma muje ga iyayen sa, mu sheda masu halin da yake ciki da yanda yake jin kowa a garesa inba Haulart ba, to anan ne kowa yasan mike faruwa, shine muke bashi shawarar duk lokacin da muka gama magana dashi ya goge farar da yake yi damu, cikin ikon Allah kuma babu abunda ya sake faruwa muna yawan magana dashi kuma yakan turo muna da kuɗi muci gaba, da kulawa da har kokin sa, na yau da kullum, tare da sadaka da neman addu'a a bakin mutane da dama da malamai. 





A wata ranar laraba ne yake sheda muna, yana cikin tsananin tashin hankalin, domin yana jin a jikin sa cewar akwai akwai macen da yakejin zata iya shiga rayuwar sa, kuma Haulart ta tada masa hankali akan cewar, ko wace mace ce sai ta ne mota, shi bai san a ina tasan da wannan zancen ba, dariya mukayi dan mun ɗauki abun kamar almara fa shirme, amman sai ya matsa muna akan muje mu sanar da Mai martaba dan abun bana wasa bane, jin hakane mukaje har gurin mai martaba muka bashi wannan labarin, a take  mukaga hankalin sa yayi mugun tashi, a gaban mu ne ya saka aka kira masa malamin masarauta, ya labar ta masa kuma cikin ikon Allah ya ce, a bashi kwana biyu zai je ya dawo masu da amsa, mai matarba, ya hanamu komawa, dole muka zauna har zuwa kwana biyu. 



Anan ne Malamin yasa aka kira mu, bayan mun zauna ne, yace, "tabbas wannan yarinyar itace haske a cikin rayuwar Salman kuma akwai rabo mai tarin yawa a tsanin su, kuma yan zun haka akwai rabon da yake a kusa_kusa dan haka duk yan da za'ayi a ɗaura Auren Salman da yarinyar nan saboda akwai igiyar Aure a tsanin su kuma igiya ko ɗaya ba zata tsinke ba, duk da kasan cewar su nesa da juna. 



Yana gama bayanin ne duk mun kasa gane wannan bayanin kawai ya ce, kada ku sanar da kowa gaskiyar wannan lamarin har Salman ɗin a take ya sanar da mai matarba cewar, a riƙa bibiyar rayuwar Salman da matar sa daga ɓoye, haka kuwa akayi mai gadin gidan Salman shi aka baiwa wannan aikin har da wayar da zai riƙa kira yana sanar da abunda yake faruwa, da yake mutumen yana da hali mai kyau shine yayi ta sheda wa Mai martaba abunda ke faruwa. 




Bayan wata biyu Mai martaba ya kira mu yake sheda muna cewar Salman zai zo gurin mu duk yanda akayi mu hanasa tafiya har sai idan shine ya kira mu ya bada umarnin barin sa ya tafi, ya tambaye mu cewar ko Salman yanada gurin sauka a garin mune, muka sheda masa cewar eh amman bamu san unguwar da zai sauka ba, dan yana da gidaje a garin mu harda motoci dan haka yanada masauki. 



A gidan Salman kuwa wani irin ciwo ne ya taso masa, wanda yayi kamar zai mutu, sai shure_shure yakeyi ma aikatan gidan ne suka samesa a hakan da sauri suka kira wayar Haulart duk da kuwa irin tsoron ta da sukeyi, sukayi shahadar kiran ta, sai da taga damar ɗauka ta ɗauki wayar cikin masifa, take tambayar su miye?". 



Cikin tsananin tashin hankali direba ya ce, "ranki ya daɗe wallahi yallaɓai ne bai da lafiya sai shure_shure yakeyi! "


Kashe wayar tayi cikin minti talatin ta iso gidan ita da  guard ɗinta, da sauri ta shigo cikin falon turus tayi ta kafesa da ido tana ya tsinar fuska, wani uban ashariya ne tayi, cike da masifa ta kira waya, ana ɗaukar wayar tace, "abunda aka faɗa ya tabbata, kuma ance ko na barsa ya aikata ko ni na mutu, gashi ina da tsananin kishi, amman tunda ni rashin aikata abun zai shafa, to nayi ƙoƙarin samo yarinyar da aka ce, har ankai photon ta, a gurin bokon kuma ya sheda muna cewar ita ce, kuma nasa an sato yarinyar har ankawo ta wata hotel, kuma yan zun zan saka akaisa a ƙofar hotel ɗin a jiye sa a hakan kamar yanda aka ɓukata, nikuma zan koma na cika ɗayan aikin ". 



Magana akayi mata, daga can ɓangaren, kawai ta kashe wayar da gudun ta ta fita, tare da body guard dinta ta shigo su huɗu suka ɗauki Salman suka fita dashi, maigadin ne ya kira Mai martaba ya sheda masa, ai kuwa aka bisa daman shima nashi ma aikatan suna biye da duk wani motsin Salman da matar sa. 




Ban san ya akayi ba, nu dai Kawai mun ya ankawo Salman tare da jami'an tsaron sa, airport mukaje muka ɗauko su, a hotel suka sauka, sai da ya kwana biyu ya fara magana, kuma tun daga lokacin bamu sake zuwa inda yake ba saboda umarnin Mai martaba, sai dai ya kiramu yace, Salman zai koma mu kaisu airport, tun daga lokacin Salman bai sake zuwa nan garin ba sai wannan karon . 




Amman fa matar sa wani sabon salon ta ɗauka duk wata macen da ta samu labarin cewar Salman ya kalla sai taga bayan ta, da sai an nemeta an rasa, kai abun ma harda abokan Salman bata bari ba, amman ban san miye yasaka mu bata rabamu da Salman ba, har tsayin wannan lokacin duk da tasan da cewar muna tare dashi, saboda duk inda Salman ya saka ƙafa tanada masaniya, akai abu kamar aljana". 


kuma har yan zun sakamakon Salman baya haihuwa yake nunawa, amman kuma sai gashi Shuraim yazo a matsayin ɗan Salman, wanda kusan kullum matar Salman har a internet tana posting din Salman da result ɗin rashin haihuwar sa, anayi mata like, wannan abun ba ƙaramin ɓatawa Salman da "yan uwan sa yakeyi ba him! " 



Nisawa jafar yayi ya ce, "NARJEESAH kinji tarihin Salman kuma har yan zun Salman tutar sa a gurin kowa tsaye take, koda kinyi ƙarar Salman ba zaki samu biyan buƙata ba, sai in da Matar sa zaki kai ƙarar sa" 



Kowa shiru ya yi Amrah ce, ta ce, "Antyn Nargeesah dan Allah kada ki kai ƙarar Salman saboda idan har mutane suka kalli Shuraim duba na hankali zasu fuskaci cewar ɗan Salman ne, to masu kawo wa Salman hari kina ganin kamar yanda muka rasa sanin inda Shuraim yake ba zasu ji daɗin kashe muna yaro ba?, ki duba da kyau kada kiyi abunda zai janyo mu rasa ganin Shuraim




Kallon su nakeyi zuwa can nace, "wallahi nikam nadawo ai nahin Narjeesah ta marar ɗaukar reni masifaffiya, kuma ni ban wani ji tausayin wannan mugun ba, koda banyi ƙarar sa ba, sai na rama abunda yayi mani! "



Dariya sukayi Nusaiba ta ce, "da mun bani har mu, dan nikam ba zan iya mantawa da halin ki ba, Anty Narjeesh". 



Hindu ce ta ce, to yan zun a ina ne zamu nemo Shuraim? dan da alama Shuraim baya gurin Salman dan naga hankalin sa a tashe yake ". 




Umma ta ce, "ku jira sa yazo muji ta bakin sa, idan Shuraim yana hannun sa, sai hankalin mu ya kwanta". 



Kowa ya yi na'am da maganar Umma. 



Nace, dan Allah Jafar da Aliyu ku saka mugun nan ya bani takar data, dan nikam ba zan iya zama dashi ba". 



Kallona sukeyi suna dariya, Humaira ta ce, "ai lokacin da muka haɗu dashi munji yana faɗar akwai igiyar Auren sa a kanki kuma ba zai iya tsinke ta ba, kuma acikin labarin da kika bada ya ce, idan kika yarda ya dawo cikin rayuwar ki, kin makaro". 



Tsaki kawai nayi, na share su fira muka chanza saboda sun ga bana son maganar Salman, sai dare suka je gida bayan sun zaga iyayen su, da iyayen Halima. 



Yau ma kasa bacci nayi, tun da safe Amrah da Nusaiba suka kawo mani abun kari amman na sheda masu sai zuwa anjima dole suka ɗauke, suka fita sai ƙarfe goma na fito tsakiyar falo na ƙara gaida Umma na zauna ina kallon labaran da Umma take kallo, Amrah da Nusaiba suka fito suka zauna muka fara labari Umma ganin mun cika ta da surutu ne ya saka tabar gurin ta koma warta cikin ɗaki. 




Labari mukeyi na yaushe ne zamu je gurin Inno mu dubo ta ita da Yaya sai dai muna gudun haɗuwar mu da wannan mutumen wanda ya so sace, Shuraim yana jariri,. 



Amrah tace, Aunty gashi kuma, Shuraim ɗin baya hannun mu, da munje kawai tun da mun gano mahaifin Shuraim ko". 



Nusaiba ta ce, "Allah yasa da Daddyn Shuraim zamu yaga ɓarawon yara ya kaisa kotu ayi muna maganin sa". 



Harara na ɓallawa Nusaiba na ce, "uban waye zai je da wannan mugun garin mu, kisa ya raina ni, wallahi ni, bazan yarda yama ga fuskar hakuri a gareni ba dan banda shi kuma bana jin tausayin sa, ko na ƙwayar zaira ai bani ce, na saka ya aurowa kansa annobar da tafi ƙarfin sa ba ehe! ". 




Gimtse dariyar su, suke yi Amrah ta ce, "Anty nifa wallahi matar Salman nake son gani kin san ko dan saboda miye? "



Gir_giza mata kai mukayi ni harda su mere mata baki, tace, "saboda yan da result ɗin Salman na asibiti yake nuna cewar baya haihuwa kwata_kwata gashi kuma ansamu akasin hakan shin wai nikam anya ma kuwa ita mutum ce, kuwa, shin tanada tunani kodai kwanyar kifi ne da ita?  Shin da tasa aka nemoki ta ƙarfin gaske ta haɗaki da mijin ta, idan har da gaske takeyi, tana kishin kamar yanda tace, to ai koda umarnin duniyar zai bata, ba zata ji wuyar yin saba, irin yanda ta baro gidan ta, garin su, ta ƙetaro cikin local, ta satoki bataji wahalar komai ba, kuma ta haɗaki da mijin ta abanza da yofi, duk dan cika umarnin bokan ta, gashi kuma ya shirga mata uwar ƙarya". 



Dariya Nusaiba keyi harda dafe ciki da kwan tawa, Nusaiba ta ce,  "itafa mutuwa take tsoro ba wai kishin mijin ta bane ya sakata aikata hakan ita da bokan kida humai ne na bugawa a jarida, tunda sun bari har Salman ya kusan ci wata mace, ta daban bai karya tsafin nasa ba, da yace, zata mu ba". 




Nikam ban ce dasu uffan ba, har suka gama, zuwa nayi na ɗauko abin karin kumallo na na karya, na, mukaje kowa yayi wanka muka saka ankon Humaira, muka fito zamu gidan, su Hindu, gurin Umma muka nufa muka sanar da ita, ai kuwa Umma ta soma faɗa, mutum da Auren sa akan sa, yake wannan shigar mayafi a kafaɗa, kuma anbi jiki da turare, kuma bada izinin miji ba, za'a fita ko? ". 




Duka Umma muka tsare da ido Umma ta ce, "ni ku tafiyar ku ku bani guri kukayi mani tsaye kamar wasu itace". 



Dariya mukayi muka fito nikam na ce muje dai nikam bazan wani takura kaina ba". 



Tafiya mukayi, mun fito daga cikin gidan ke nan, sai ga motoci har ukku ajere parking sukayi a gaban mu, sakin baki mukayi, ganin mutane sun fito harda mace, sai Salman, a take su Amrah suka saki murmushi ni kuma na ɗaure fuska na ɗauke kai na juya zan tafiya ta kawai naga mutum a gaba na, saura kaɗan nafaɗa a jikin sa, da sauri nayi baya, cike da masifa nace, Malam miye hakan? " 



Kowa kallon mu yakeyi harda su Amrah, wannan budurwar ce, mai kama da Salman da namiji suka iso gurin kallo ɗaya nayi masu, na gane su waye, wato Salma da Muhseen ne, hannu ta bani tana dariya, tace, "madam kiyi hakuri mu ɗan gaisa mana, sai ki kaini masauki nasan zakiyi tarbon baƙi ko? ". 



Kamar ba zanyi magana ba, kuma dai naga ai ba ita ce tayi mani laifin ba, nace, "da ace ke ɗaya kika zo da kin ga yanda ake tarbon baƙi dan kin zo gidan karamci amman sai kika zo da mugun mutum kin kuwa ansamu naƙasu anan gurin". 



Murmushi tayi ta ce, "to ai dai mu baƙin kine kuma ga Muhseen bro ɗina ne ku gaisa". 



Kallon shi nayi banyi magana ba, shiko dariya yake gimtsewa, Amrah ce ta ce, dasu "bisimillah ku zamu mu shiga daga ciki". 


Kallon su nayi na ce, "idan kika kaisu suka gaisa da Umma ki fito mu wuce, dan ni kam va zan shiga ba, tafiya ta kawai zanyi, kuma ki shaidawa mutum ya dawo mani da yaro na ehe! ". 



Da sauri duk suka bini da ido Salman ya ce, wai kina nufin har yan zun Shuraim baya hannun ki, kuma kike zaune hankali kwance? "



Da sauri na dawo da ido na akan sa, nace, "kana nufin Shuraim baya hannun ka da gaske na rasa shi ke nan innalillahi wa inna lillahir rajiun, na shiga ukku ni Narjeesah waye wannan azzalumin da ya rabani da farin ciki na, Salma ce, ta dafa ni cikin kaɗuwa tace, "bani photon yaron na gani ". 



Nusaiba ce, ta basu wayar da sauri Muhseen ya ansa ya Cuba photon Shuraim da sauri Salma ta ansa, shima Salman ansar wayar yayi ya juya cikin tsananin tashin hankalin, da sauri Salma ta ce, "kiyi hakuri yau muma zamu fara namu bin ciken yan zun kuwa zaki iya komawa cikin gidan ki zauna ga wannan wayar zan riƙa kiran ki muna magana ". 




fasa fitar mukayi muka dawo cikin gidan muka zauna jagwab, kuka mukeyi har Umma ta fito ta same mu a hakan, zama tayi ta ce, "kuka ba shine mafita addu'a ita ce mafita a gare mu dukan mu". 



Su Salman kuwa wata unguwar suka nufa sunayin parking suka fito da gudu suka shiga cikin gidan, saman kujera suka zazzauna Salma kuwa kaiwa takeyi tana dawowa, tana cizon baki, ta duƙule hannun ta ɗaya tana ɗan dukan tafin hannun ta, 



Muhseen ya ce, "sister babu wanda zai ɗauki yaron nan face, masu bibiyar bro, amman wallahi, duk wanda ya yi wannan aikin da wata manufar yayi ba wai dan ya san da sanin cewar wannan yaron yana da alaƙa dashi ba". 



Salma ta juyo ta fuskan cesu tace, "bros nikuma nawa hasa shen ba kowa bane ya ɗauki wannan yaron ba, face, ya fahimci yanda kayi saurin yarda da yaron har ya raɓeka, bayan kowa yasan cewar kai ba ma'abuci dariya bane ballema mutum yayi tunanin kana ƙaunar yara har haka ba, dan haka zamuyi bin ciken mu ta ƙar ƙashin ƙasa, dafatan zaka bamu haɗin kai kasan cewar ka babban lauya kuma wannan case ɗin kai ya shafa ba lallai bane ka iya aikin nan ba, dan haka ina son duk abunda kaga, mahaifiyar yaron nan tayi kayi mata uzuri kuma kasani ko ma miye da sa hannu na". 




Kallon rashin fahimta sukeyi mata, amman sai ta sakar masu murmushi tace, "ku yarda dani bros". 




Gyada mata kai kawai sukeyi, amman duk basu fahimce taba, cikin wani ɗakin ta shiga ta kira waya ta ɗan daɗe tana magana, kafin ta fito ta zauna tana kallon su". 




Zaune muke bayan na gama yiwa Umma bayani, shiru tayi tace ke da Amrah ne zakuyi wannan tafiyar kuma duk zaku iya kuwa? "



Amrah tace, "addu'ar ki kawai muke buƙata ". 



Addu'a Umma tayi mana, ita da Nusaiba suka rako mu, har ƙofar gida muka ɗauki hanya......... 





*Comment and share*




Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹



 💐💐 *NARJEESAH* 💐💐



*Rubutawa*

*NANA KHADEEJATU*

           *_UMMU IHSAN_*


*ELEGANT ONLINE WRITERS*


_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_



               3️⃣1️⃣⏭️3️⃣5️⃣


➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Tafe muke a hanya nida Amrah muna janye da trolley din mu guda biyu da muka ɗauko daga cikin kayan da suke ajiye a waydrop wanda duk Daddyn Shuraim ne ya ajiye su, to a cikin sune muka ɗauki biyu daga ciki. 



Tafe muke hankali kwance illa jimamin barin gida da su Umma mukeyi, muna ƙarasa wa a bakin titi mota na jiran mu, muna zuwa aka buɗe muna muka shiga muka ɗauki hanya sai airport koda mukaje komai angama, muna shiga kawai mukeyi jirgin ya ɗaga sai Abuja, tunda muke a rayuwar mu wannan ne karon farko da muka shiga filin jirgi harma muka hau jirgin a gaskiya munji daɗin hakan. 



Muna sauka muka fito wani mutum ne ya tarye mu, muka shiga cikin motar da yazo da ita, muka ɗauki hanya, a gaskiya Abuja babban gari ne, tafe muke muna kalle_kalle a wayan ce, saboda tsaro, badan tsoro ba. 



Wata unguwa ce muka shiga gidan kam ɗan madai daici, dashi yayi kyau yana ajiye mu yayi gaba abun sa, mukam tare da kayan mu muka shiga cikin gidan, babu kowa a cikin falon gidan muna ta sallama sai daga baya wata, mata ta fito da fara'ar ta tana yi muna lale mar haban da zuwa, ajiyar zuciya muka sauke, nida Amrah. 



Matar ta ce, "ku shigo daga ciki mana kuka wani tsaya nan kamar wasu baƙi". 



Dariya mukayi muka ƙarasa shiga cikin falon gidan akan kujera muka zauna muka gaisa da matar wadda a ƙalla zata kai sa'ar Inno, bayan mun gaisa ne aka ciki muna gaban mu da abinci dana sha, kai komai sai sam barka, ƙasa muka zauna mukaci muka ƙoshi, aka kwashe kayan matar tace, "to ku tashi na nuna maku ɗakin ku, kuyi wanka ku futa, ko? "


Murmushi mukayi mata, muka ɗauki kayan mu muka shiga cikin ɗakin da takaimu ta fito, a bakin gadon muka zauna muna sauke numfashi, Amrah ce, ta fara shiga wanka ta fito nima na shiga tare da ɗauro alwala muka sauya kayan jikin mu mukayi sallah muka zauna muna futawa, har mukayi sallar magrib da isha'i muka fito falon muka ƙara gaisawa da matar har take cewa"Amrah kodai anan zaki zauna dani kin ga ni ɗaya ce a gidan nan yara na duk sunyi Aure su ukku mata, Abida Asiya Lamra, sai maza ne kawai suka rage mani kuma duk suna gurin aikin su, kin ga na samu wata Autar mata ko? ". 



Dariya mukeyi tun lokacin da ta fara maganar itama tana dariya Amrah tace, "eh fa zan kuwa zauna dake Ummi kin ga sai Anty Narjeesah da Auta Nusaiba su daina yi mani dariya suna cewa ni kam basu san a wane matsayin nake ba, niba ga yar fari ba, kuma niba Auta ba". 



Dariya muke yi harda tafawa na ce, "Amrah ai dai mun riga ki sanin matsayin mu, nifa wallahi yau naga, kin zama wata  irin shagwaɓaɓɓiya da ke sai uwar shagwaɓa kikeyi, kai mun gode Allah da yasa ba kece Auta ba da mun shige su wallahi ". 


Dariya mukeyi, fira sosai mukayi da Ummey kamar ba gobe, kwanan mu ukku a gidan mun saki jiki da Ummey sosai, yau ne mukayi shirin zaga gari ni da Amrah direba ne ya jamu sai wani haɗaɗɗen hotel muka isa, yanayin parking muka fito nida Amrah, munyi shiga ta alfarma, wani gurin futawa ne muka nufa muka nemi kujera muka zazzauna Amrah taje tayo muna order abin sha ni kuma ina zaune ina dan na wayar hannu na, Amrah ta dawo ta zauna, muka soma fira, muna ɗan kallon gurare kaɗan_kaɗan, har aka kawo muna abin sha, wasu matane su ukku suka zo a kusa da kujerar mu suka zauna, kowa ce daga cikin su, tayi shiga ta kece raini, ɗayar ma harda gilas a idon ta ga manyan wayoyi a hannun su, da sauri ma'aikata gurin suka soma kawo masu gaisuwa tare da abinci da lemo, suna ajiyewa suka bar gurin, sai a lokacin ne wasu daga cikin ma zauna gurin suka fara kai masu gaisuwa mukam ikon Allah muke kallo. 



Bamu ƙarasa mamaki ba, naga ɗayar tayi nuni da gurin da muke zaune, ai kuwa da sauri wata yariya tayo gurin mu, muna ganin hakan muka ɗauke idon mu, daga gurin su, muka fara kallon wani gurin, budurwar ta ce, "am excuse me please ana son ganin ku a gurin can". 



Kallon juna mukayi nida Amrah  na ce, "kije kice wa mai neman mu munje gurin koyon sallama ". 


Zaro ido waje tayi tace, "pleace kuyi hakuri kuje basa son gar dama". 


Amrah tace, "iyayen kine a gurin halan da naga kina jin tsoron kai masu Saƙon da aka baki? "



Shiru tayi cikin sanyin jiki ta juya ta kasa sanar dasu Saƙon dana bata, amman ta makaro dan sunji abun da na faɗa da sauri suka juyo suna kallon mu, mu kuwa fira mukeyi nifa Amrah ƙasa_ƙasa, sake aiko wata sukayi tana zuwa ta ce, "ance kuyi wa kanku adalci kuzo da kanku tun kafin a ɗauko ku ". 



Dariya mukayi nida Amrah harda tafawa muka share "yar aiken, ganin haka ne ta koma ta ɗurƙusa ƙasa, ta fara basu hakuri, a take wasu mutane na zaune a gefen mu, wanda suke kallon duk abunda yake faruwa suka fara zuwa gurin mu, suna bamu baki wai muyi hakuri muje gaisuwa ce kawai zamu kwasa a gurin su, nikam na ce, "abunda sukayi niyar bamu su riƙe abun su, kuma abincin da suke ciyar damu daga yau kada su ƙara bamu shi, su barmu da yunwa da dattin talauci ko kuwa Sis? ". 



Amrah tace, "kwarai ma kuwa kai nifa har kunya kuke bani irin wannan rawar jikin kamar kun ga wasu doddani, yo in banda dodo miye ake gani aji irin wannan tsoron haka? ". 



Na ce, "yar uwa gane mani hanya dan Allah ". 



Cikin sanyin jiki kowa ya tafi ya bar mu, ganin hakan ne da jin abunda muka faɗa wanda muke ɗaga murya yanda zasu ji ne ya saka suka taso a fusace sukayo kan mu, suna zuwa sukayi muna tsaye a kai suka riƙe ƙugu. 



Murmushi nayi, na ce, "yau wa kina jina kuwa idan har kin han go shi kiyi ƙokarin sanar dani inda yake zaune da inda yake har kokin sa a wannan garin sannan zan turo maki kuɗin da zaki riƙa baiwa masu bibiyar maki labarin halin da ake ciki, da yarinyar da suke yawon hotel da gidajen futu, da sauran su ke harma da iyayen yarinyar da kakanin ta, ƙannen ta, abokan ta, ina fatan kin fahimci baya nina, dai ko?  Zan baki photon yarinyar nasan shi kin san sa baki da buƙatar photon sa, sai dai kuma zan baki saboda yaran da zasu taya ki aikin ". 




Dariya Amrah tayi tace, "na fahimce ki, duk da nasan ba nice mace ta farkon da kika fara baiwa wannan aikin ba, amman kuma taya kike tunani zai bar wata shedar da zai bar maki, tunda yafi kowa sanin halin ki, akan sa? "



Dariya nayi na ce, "da ace yasan zan bishi a garin ko a ƙasar nan da tuni ya bar wannan ƙasar saboda tsabar sanin halin nawa, na naci da bin diddigi a kan lamur ran sa". 



Wata daga cikin matan ne, ta ce, "idan kun gama shirya cutar "yar mutane sai ku ajiye ku saurari masu garin da irin hukunci da zamuyi maku akan wannan rashin kunyar da kukayi muna". 



Tashi tsaye mukayi na baiwa Amrah hannu na ce, "Allah ya baki sa'ar wannan aikin sai mun sake haɗuwa a nan gurin saboda naga akwai sirri gurin ranar Sunday da misalin ƙarfe biyar da rabi na yamma, dan Allah banda afrikan time". 



Sara mani Amrah tayi mukayi mubiha, ta juya ta fita nima na raɓa ta gefen su nayi tafiya ta, sakin baki da hanci sukayi suna kallon mu har Amrah ta fita ni kuma na ɗan tsaya amsa waya, sai da na baiwa Amrah kusan minti goma nima na ajiye wayar na fita a cikin mota muka haɗu da Amrah muna ta dariya, direba ya ɗauki hanya muka zaga garin muka koma gidan Ummey. 



A can kuwa wannan matan cike suke da mamakin su waye mu a garin nan da mukayi masu wannan iskancin, ai kuwa suka gasa zama gurin kowa ce, a hasale taja motar ta, suka bar hotel ɗin. 



Salman ne zaune shida Salma da Muhseen a gidan Umma Nusaiba ce, ta kawo masu abinci da ruwa, taje kiran Umma, kasa cin komai sukayi, har Umma ta fito ta zauna suka gaisa, cikin kulawa, Salma tace, "Umma dan Allah ko zamu iya ganin Maman Shuraim kuwa? ". 



Shiru Umma tayi, Nusaiba ta ce, "ayyah ai Umma ba zata baki wannan amsar ba, nice kawai zaki samu amsa dan gane da Anty Narjeesah". 



Murmushi Salma tayi Muhseen ya ce," saboda miye ba zamu sami amsa ba a gurin Umma akan maganar da ta shafi Anty Narjeesah? "  


Dariya Nusaiba tayi tace, "kaima yau Anty kake cewa Anty Narjeesah? to ai kuwa zaka sha labarin Anty Narjeesah ko Umma? ". 



Tashi Umma tayi tabar gurin, Nusaiba tasa dariya ta ce, "Umma ki zauna mana muyi labarin harda ke". 



Umma ta ce, "Auta kema kinyi koyi da halin Amrah ko?  Allah idan kika dameni sai na fasa maki baki"Umma na gama maganar tayi tafiyar ta. 


Dariya sukeyi banda Salman da yayi murmushi yana kallon Nusaiba. 


Nusaiba ta nisa, ta ce, "am yauwa Anty Narjeesah da Amrah basa nan yau kwanan su biyu da tafiya". 


Da sauri Salman ya ce, "what...! Kina nufin cewar da Auren nawa ta je wani gurin kuma harda su kwana ba tare da neman izini na ba? ". 



Sakin baki duk sukayi suna kallon Salman cike da mamaki, shi kuwa masifa yaci gaba dayi, Nusaiba ta ce, "ikon Allah to yan zun dan mutum yayi tafiya kawai sai a kama masifa, kamar yana gurin ashe dai nikam zan ga irin hakan da ido na biyu, to kai inda a gaban Umma ne hakan zakayi ta masifa mai laifin daban wanda akeyi wa masifar daban?  Nikam gaskiya ba zan iya zuwa gidan ka ba". 



Dariyar ƙurciyar Nusaiba sukeyi harda Salman ɗin Nusaiba ta bala'in bashi dariya amman kuma haushin Narjeesah yake ji taya zatayi masa wasa da Aure bayan ta zauna har a gano inda Shuraim yake, ya ɗauke su ya tafi dasu gidan Mai martaba, amman wallahi idan ta dawo sai ta raina kanta. 



Muhseen ya ce, "harda wannan Yayar taki a kayi tafiyar kuma yaushe ne zasu dawo? "



Nusaiba ta ce, "nima ban sani ba amman idan sun dawo zan sanar daku, dan inda suka tafi babu service ". 



Dafe kai Salman ya yi yace, "ok yan zun ko kin san garin da suka tafi da gidan? ". 



Nusaiba ta ce, "nifa daman ban fiye zuwa wani gurin ba, ina zama ne tare da Umma na, shi yasa ake cewa na cika shagwaba, dan bana son nayi nesa da Umma na, a toh". 



Dariya sukayi Salma kuwa ta ce, "Amman zaki zo bikin Aure na, dan har anfara shagalin biki, maganar ganin Shuraim da Maman sane da ɓatan Shuraim ne ya saka na dai na zama, yau saura kwana biyu ɗaurin Auren kin ga kuwa, ya kamata a ce matar Yaya Salman tana kusa, yanda zata ga kowa kuma tasan kowa kuma kowa yasan ta, amman tunda bata nan ita da Amrah ke kizo ayi dake sai ki wakilce ta". 



Shiru Nusaiba tayi, Muhseen ya ce, "bafa sace ki zamuyi ba, kin ga da Antyn mu tana nan ai nasan da zaki zo ko? ". 



Dariya sukayi Salma kuwa ta ce, "ki kirawo muna Umma mana". 



Nusaiba tare da Umma suka fito Umma ta zauna, Salman ya ce, "Umma dan Allah ana bikin Salma ne shine nake son ki bar Auta taje dasu Humaira wannan bikin dan Allah ". 



Murmushi Umma tayi tace, "babu damuwa ai Nusaiba ƙanwar kuce, zata je, amman ta cika laƙuwa da yawa, sai kunji ta bakin ta, ta yarda da kanta, dan gudun kada sai an shirya tafiya ta ce, ita ta fasa zuwa". 



Dariya sukayi Nusaiba ta ce, "Umma zanje ai". 



Sunyi farin ciki suka tashi sukayi masu sallama suka tafi suna fita Nusaiba ta ce, "Umma ba zani ba wayau ne nayi masu, gudun su dameni da magiya". 



Dariya Umma tayi tace, "ai kuwa dai sai kinje kije kiyi shiri dan ina ga gobe ne tafiyar ". 


Zum ɓuro baki Nusaiba tayi tana shura ƙafa, Umma kuma ta share ta. 



A ranar su Salman suka dawo fada inda fadar take cike da mutane 'yan biki direct cikin gidan suka shiga sharp_sharp suka shirya aka soma hidimar dasu  harda iyayen su duk suna a gurin da sauran yan uwa na gurin mahaifiyar su na can ƙasar London wato dan gin Mom ke nan. 




Amrah ce ta gama shirin ta na zuwa royal hotel da shigar ta ta kece raini, tana fito wa, na soma yi mata iya shege, "wow kaga Hajiya Amrah ikon Allah Hajiya Amrah babbar mace, kai Allah dai yaja da kwana, matar babban mutum". 



Na ƙarasa maganar ina dariya, kwaɓe fuska Amrah tayi ta zauna tace, "Anty Narjeesh wallahi zaki daina ko na fasa zuwa ma ". 



Ummey ce ta fito tana dariya ta zo ta dafa kafaɗar Amrah tace, "ke kyaleta kinji Amrah na, indai dan wannan abun ne da takeyi maki sha kurumin ki, ai Daddy Shuraim ne zai shigar maki wannan rigimar ". 



Ai kuwa a take na haɗe rai na ɓata fuska, suna kallon fuska ta suka soma dariya Amrah harda dafe ciki, ta ce, "yauwa Ummy kin kuwa bani satar amsa, Anty Narjeesh ta Yaya Salman ". 



Da gudu nayo kanta, ai kuwa ta fita gidan da gudu sai gurin mota, ina dariya suka fita ni kuma na shiga gurin wankan ina fitowa nayi kwalliya na saka shadda ta ash color na fito, turare na feshe jikina dashi na fito da mayafi na, a hannu, makulin mota Ummey ta bani ta ce, "ke kiyi amfani da wannan kuma ga Ashiru nan yana jiran ki tun ɗazun". 



Ansa nayi ina godiya na fito da sauri Ashiru ya tar yeni da fari ar sa, muka gaisa muka shiga ya jamu sai royal hotel, inda mukayi parking anan ne naga motocin wannan matan da masu basu kariya wato masu tsaron su, murmushi nayi, na Ashiru ne ya buɗe mani motar na sauko na fara taku, duk inda nabi na wuce, idon mutane, akaina jin nakeyi kamar na ɗora hannu na akai na fasa ihu Amman na dake na shiga gurin waya na kira Amrah ta ɗaga, ta ce, na ƙaraso. 



Gurin Amrah na nufa, su kuwa da ido suka bini duk da kuwa ko wace, idon ta na a wayar ta amman hankalin su yana a kai na, murmushi nayi kujera Amrah ta ja mani na zauna da bisimillah, lemo ta bani na ansa na ce, "na gode" na ajiye na kalle ta a goggo hannun ta, ta kalla nayi murmushi na ce, "kinyi ta jira na kuma kinyi ta kiran waya ta, am sorry wani abun ne ya taso mani shi yasa ban samu lokacin ɗauka ba, ko na kira ki, to ya labari ina fatan kin nemo mani tarihin ko wace yarinyar ce? ". 



Murmushi Amrah tayi, ta bani wani envelope na ansa da sauri zan buɗe Amrah tace, "kiyi a sannu mana, kibi komai a hankali zaki fi fahim ta ". 



Kallon Amrah nayi, nayi mata murmushi nace, "da ace kin san yan da zuciya ta takeyi a halin yan zun da baki ɓata bakin ki ba, akai". 



Buɗewa nayi ina duba bayanin komai sai da na kai ƙarshe nace, da sauri "ƙarfe nawa ne yan zun pleace ". 



Ta ce, "shidda da kwata"


Cikin zafin nama na tashi harda gudu nake haɗawa nafi ta sai gurin Ashiru da sauri na ce, kayi sauri muje, da sauri na sanar dashi titin da zai kaini ai kuwa da mugun gudu yaja motar muka fita, tafe muke  da gudu ina duba a gogon hannu na, wani irin burki ne Ashiru ya taka, da sauri ya fito ya buɗe motar nima na fito ina duba agogon hannu na, a take na soma masifa, "haba wannan wane irin hauka ne kasan kuwa irin barnar da kayi mani yan zun, kasan mota nan bata da lafiya kabari na fito da ita, da ba sai na shiga wata, motar ba, gashi yan zun  ka sakani cikin damuwa ba zan same suba, oh sheet! "




Na dafe goshi sai go and come nakeyi, wayar Amrah na kira, tana ɗaga wayar nace, sun bar ƙasar sai nan da sati biyu kuma zan sake ganin sa, dan haka zan koma gida ne, sai na sake shiri, zasu haɗu dani ne, kiyi mani bucking ɗin jirgi zan bar garin nan da daren nan kawai! ". 



Kashe wayar nayi na dawo nayi jin gene jikin motar, ina dafe da goshi na, naji an doka mani uban horn, kallon gurin nayi bayan motar mune na ɗauke ido na, naci gaba da cizon yatsa. 



Fitowa sukayi suka nufo ni, dafani ɗayar tayi na ɗaga ido cike da mamaki ina kallon su ɗaya bayan ɗaya, murmushi suka sakar mani, ɗayar kuma ta kawo ruwan swan ta bani, masu sanyi kamar ba zan ansa ba, amman kuma sai naga sun kafeni da ido na ansa na  buɗe robar nasha, ina ajiyewa na fara sauke ajiyar zuciya. 



Murmushi suka sakar mani a tare, sai ɗayar ta bani hannu tace, "Sarah ko kuma kice, Mrs Naseer". 


Ɗayar ma ta ce, "Nafisah ko kuma kice Mrs Nazeer". 



Ɗayar ta ce, "Zeenat ko kuma Mrs Yaseer". 



Ta ƙarshen ta ce, "Mrs brr or haulman nice duk faɗin ƙasar nan mai wannan Sunan, couse suna ne dana mijina, am naga kamar mijin kine yayi maki halin nasu na maza rashin gaskiya, amman nikam miyasa kikayi masa wannan saken da yawa har haka? ". 



Kallon ta, nayi da kyau ban ce dasu uffan ba. 



Dai_dai isowar Amrah, daket nace dace, "Nice meet your's sorry fa kunga ina cikin damuwa amman idan na rage damuwar sai mu haɗu daku yan zun zan koma gidan miji na ne ". 



Murmushi suka yi, Mrs barr, tace, "idan ba zaki damu ba zan so muje dake gida na, duk da ni bana barin ko wace, karya tazo mani gida ke harda, wannan da kike ganin mu a tare dasu kasan cewar tare mukayi karatu dasu, kuma mazajen da suke Aure fitattu ne, a ƙasar nan shi yasa ƙawan cemu yakai har wannan lokacin gashi duk halin mu ɗaya illah wannan da kikaji ta sanar dake sunan ta Mrs Yaseer amman duk da hakan bata shiga hurumin da banata ba, so ke naji ina son kije gida na ki futa kafin na baki wata mafitar wadda zakiyi mani godiya ina fatan zaki karɓi wannan buƙatar tawa". 



Ban ce da ita uffan ba, har sai da suka haɗa baki gurin roƙo na, nace dasu, haba, taya zan biki gidan ki, wata kila ma mijin ki yana, gida, idan dai har dan shi kika hana kowa zuwa gidan ki to ya zakiyi da ni nida baki san inda na fito ba? ". 



Kallon_kallo suka shiga yi, sai sukayi dariya, Nafeesa tace, "a yanda kika mutu da kishin mijin ki, har kika biyo bayan sa, kika kashe kuɗi gurin neman labarin sa, to duk wani namijin baya a gaban ki, kin ga kuwa koni ce zan iya yarda kibi ni har gida na, bani da shakku a kan ki". 



Dariya nayi na ce, "ok to ku dai yi mani wannan hakurin idan nadawo zuwa jibi zan sauka a gidan naki, koshi dan naji zaki bani mafita ne kawai, kin san akan mijina babu abunda ba zan iya ba". 



Cikin farin ciki muka rabu dasu tare da musayar number, motar Amrah nabi, muka tafi airport koda mukaje muka shiga daga ciki, muka bi ta wata ƙofar Ashiru muka gani, ya ɗauke mu a mota sai gida. 



A can gidan Umma kuwa sai da Umma tayi da gaske san nan Nusaiba ta yarda tabi Jafar da Aliyu Humaira da Hindu suka nufi gurin bikin Salma suna tafe, suna yiwa Auta tsiya su Jafar na tare mata, ita kuwa ta kyalesu ta turo baki gaba, ita ala dole fushi takeyi dasu. 




Zaune nake ina, yiwa Ummey yan kan farce, Amrah nayin game a waya ta, kira ya shigo da sauri Amrah tace, "Anty Narjeesh Mrs Nazeer na kiran ki ". 



Dariya nayi na ce, "kyale ta soma kira" kiran ne ya ƙara shigowa sai da ya kusa tsinke wa na ɗauki wayar na kara a kunne na, ta ce, "sai Mrs Nazeer uwar gida kuma Amarya daga ke ba ƙari". 




Cike da wani irin farin ciki ta ce, "ramki ya daɗe ya kike ina fatan dai komai ya zama dai_dai, ina nufin kin rage jin haushin kowa ". 



Dariya nayi na ce, "da sauƙi dai kam amman har yan zun ina jin haushin wasu". 



Ta ce, "to share kawai madam gobe ne zaki zo ko? To ki zo da yam ma, saboda Mrs barr taje unguwa amman zata dawo gobe kasan cewar a hotel ta sauka kuma jirgi zata, biyo ko kuma kizo gida na kawai idan ta iso sai na saka direba ya kai ki ko ya kika gani ne? ". 



Murmushi nayi, na ce, "kodai na bari a ƙara kwana biyu saboda bani son na takura wa kowa gashi ita bata nan ke kuma na zo na ɗaura maki nauyi". 



Dariya tayi tace, "ina ma zaki zo tun yau ai da naji daɗi, wallahi". 


Dariya kawai nayi zuwa can na ce, "sai goben dai Mrs Nazeer idan na sauka a airport kizo ki ɗauke ni, amman fa tare da wannan yarinyar zan zo sai ki ware muna ɗakin da zamu sauka gudun haɗuwar ta, da mijin ki, kin san mace, komai ƙuruciyar ta namiji na iya ƙyasawa da ita, dan kin gan mi nan akwai zafin kishi ". 




Ajiyar zuciya ta sauke tace, "to sai kin zo babu damuwa ni nasan gurin da zan ajiye ta, kuma zanyi wa Mrs barr magana nasan ba zaki samu wata matsalar ba indai akan wannan ne". 



Sallama mukayi naci gaba da aiki na, haka kuwa tun da safe ita ce, ta tayar dani daga bacci, dole tasa na tashi muka fara shiri tare da parking ɗin kayan da zamuyi amfani dasu, zuwa tara da rabi Ashiru ya zo mukayi sallama da Ummey muka nufi airport, zuwa ƙarfe sha ɗaya na kira Mrs Nazeer ai kuwa da farin ciki ta zo ta ɗauke mu sai katafaren gidan ta, duk ma'akatan gidan nata maza ne sai "yam mata, masu ƙananun shekaru daga sha biyu sha ukku suke nan, 




Wani haɗɗen falo, kafin kace wani abu har an cika muna gaban mu da abinci irin da ban_daban, sai da muka futa sannan muka ci abinci da abun sha, wata yarinya ce, ta kira tazo, ta durƙusa ƙasa idon ta a ƙasa tace, "gani ya shugaba ta". 



Dariya naso nayi amman na dake, Mrs Nazeer ta ce, "jeki ki kai wannan baƙuwar can kusa da part ɗin ku kuma duk abunda take buƙata ki tabbar mata da kin yi mata shi, kada ki yarda ta nemi abu ta rasa". 



Da sauri ta gyaɗa kai, tashi Amrah tayi taja trolley ɗin mu tabi bayan wannan yarinyar, mu kuma muka saka fira inda take tambaya ta, labari na da suna na, nayi dariya na ce, "to yan zun ya ke nan Mrs barr ta ce, kada na yarda ku rigata jin wannan ". 



Dariya ta saka ta ce, "kai wato dai wannan Haulman ɗin ta riga mu a komai kuma tafi mu sa'a to mun yarda maji daga baya, amman kin san wani abu kuwa". 



Gir_Giza mata kai nayi, ta ce, "kin ƙara burgeni fa, wallahi, saboda tun yanzun kin fara riƙon sirrin mu, tun da gashi Haulman bata kusa kin faɗi sharaɗin ta, ɗaya daman haka muke so, shiya sa, har yan zun muke tare da Mrs Yaseer saboda tasan komai namu sirrin mu babu wanda bata sani ba, amman har ila yau bata taɓa fitar da sirrin mu ɗaya ba, a gurin kowa, dan haka kici gaba da hakan ". 




Dariya nayi muka ci gaba da fira, har sai da Mrs barr ta kira ta ce, mu ƙaraso gidan ta, ta dawo tun ɗazun tana fatan dai Mrs Nazeer bata san komai a kai na ba"



Dariya mukayi haka muka bi ta gurin ɗakin da aka kai Amrah gurin akwai nisa da inda muke, kanar ba gida ɗaya ba, muka kira ta muka fita da direba ta haɗamu tare da sha tara ta arziki, na ce ba zan amsa ba, Amrah ta matsawa ita ce ta amsa, mukayi sallama, direba ya ɗauki hanya sai gidan Mrs barr, him to ai sai naga gidan Mrs Nazeer ba wani gidan bane tun lokacin da muka iso bakin get ɗin gidan nake ji wani irin bugun zuciya sai da na rufe ido da addu'a ɗauke a baki na muka lula cikin gidan, get ukku a na huɗun ne muka tsaya, da sauri wasu ma'aikatan gidan suka zo suka buɗe muna. 



Kallon Amrah nayi naga duk a tsorace take sai da na dafata nayi mata murmushin ƙarfin hali sannan ta, fita nima fita nayi baki na ɗauke da addu'a kayan mu aka amsa aka shiga dasu, muka ma muna biye da masu yi muna iso har cikin gidan, faɗar haɗuwar falon ɓata lokaci ne . 




Muna isa tsakiyar falon kamar ance mu kalli gurin tv turus mukayi muka zaro ido waje cikin rawar murya na ce..........




*Comment and share*


*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹



 💐💐 *NARJEESAH* 💐💐



*Rubutawa*

*NANA KHADEEJATU*

           *_UMMU IHSAN_*


*ELEGANT ONLINE WRITERS*


_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_



             3️⃣6️⃣⏯️4️⃣0️⃣

  

➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Cikin rawar murya na ce, "Amrah kin ga wani irin surprise kuwa, wannan tar ba haka, kai am very happy fa, har naji na rage yawan damuwa ta". 


Ba komai bane a burin photon mune nida Amrah a lokacin da muka haɗu a royal hotel haɗuwa ta biyu muna murmushi a jikin photon an rubuta, *your welcome pretty and friend* da zaiba, kula ga flowers masu masifar kyau a gurin. 




Kallon gurin kawai mukeyi, mun shagala da kallo, takun takalmi ne, na jiyo a bayan mu, ana sauko wa daga step juyowa mukayi, da murmushi ɗauke a fuskar mu, itama da murmushi ta ke tafe, tayi shiga ta kece raini. 



Ta ce, "ku ƙasa ku zauna mana kamar wasu baƙi?"


Bayan mun zauna ne a saman manyan kujerun gurin da suka kusa make falon duk kuwa da irin girman sa, bayan mun gaisa ne kukun tane ya fara kai komo a gurin, abinci dana sha kamar hauka, har sai da nace, ya isa hakan, muka ɗan taɓa kaɗan, bayan mun ƙarasa ne tace, "please muje daga ciki na kaiki ki futa dan ina son yin magana ne da ƙawata, so sirri ne zamuyi" . 



Tashi Amrah tayi dan taga irin kallon da takeyi mata, tare suka bar gurin, ta ɗan jima kafin ta dawo a kisa dani ta zauna tace, "yauwa sunan ki da labarin ki sister nake son ji domin nasan irin taimakon da ya kama ta na baki ". 



Kallon ta nayi murmushi na sakar mata sai kuma na ɗaure fuska na ce da ita, "Mrs barr zaki ji suna na da labari na, domin nasamu mafita da sauri dan jina nakeyi kamar saman ƙaya nake, mafitar da zaki bani kuwa ita ce ta sakani naji ƙwarin gwiwar zuwa gurin ki, dan ina son yau idan nasamu mafita nayi amfani da damata gudun a bari ya huce". 



Ajiyar zuciya ta sauke tace "to kafin nan naji sunan naki dana mijin ki da fari". 



Dariya nayi nace, "NARSAL, shine suna na dana mijina, bana saken furta wa kowa Sunan mijina saboda, ina jin kishin wani ya mai_maita Sunan da bakin sa ". 



Dariya tayi tace, "amman Sunan yayi daɗi kjn kuma burge ni da kishin da kike yi da badan nasan yanda nake jin kishin mijina ba, da nace, kin fini haukar kishi amman nj nasan kishi gaskiya ne, to yan zun dai muje ga labarin Auren ku". 



Kallon ta nayi na sauke ajiyar zuciya na ce, "Munyi Auren soyayya ne nida shi kulawa muke baiwa jjnan mu, har mukayi shekara da Aure, to a watanni baya da suka wuce, yace, dani haihuwa yake so shi, nikuma ban shirya hakan ba gaskiya ina yar yarinya dani yasa na tsofe da wuri, shine yace zai nemi Aure ba ƙaramin tashin hankali na shiga ba, aikuwa duk budurwar da ya nema, da Aure har gidan su nake zuwa da wuƙa da guba, nace, su shirya kwasar gawar yar su, idan suka yarda aka ɗaura Auren ta da mijina dan mijina nawa ne ni ɗaya, aikuwa sai a fasa, abun yana yi masa, ciwo duk yan da, ya ɓoye mani zan cen Auren sa, sai na gano sa, to shine ya sauya yake biyar matan titi, ni kuma babu ruwa na da karuwar waje dan matsayin kishiya na ɗauke ta, nasha korar masa matan bari ki shine yan zun, ya gudo wannan garin, kuma gashi har naga nasara, amman ta kubce mani" na ƙarasa zan cen da dafe goshi na. 




Ta ce, "tab ai kuwa kin kawo kukan ki inda za'a share maki, ki kwantar da hankalin ki, zan kaiki inda ko sunan mace, yaji ko muryar ta, indai ba ke bace, zai iya ɗaukar ta matsayin mugun abu ke koda uwar sa ce, magana kuma sai kin basa, umarni, yan kin shigo cikin tafiyar mu, amman yan zun zan saka a kaiki gidan Mrs Yaseer da Mrs Naseer, Mrs Yaseer nake son ki jawo muna hankalin ta, a matsayin ki na baƙuwar mu nasan kina da dabarar yin hakan ". 




Kallon ta nayi nace, "zan yi wannan ƙokarin amman ke baki bani labarin nasarorin da kika samu ba, ballema naji daɗin yin amfani da wannan nasarorin naki gurin shawo kan Mrs Yaseer ko ya kika gani? ". 



Itama ni take kallo, tana saurare na har sai da na dasa aya. 



Nisawa tayi tace, "ba zan ji shakkun sanar dake ba, NARSAL amman a takaice ne zan sanar dake ". 


Gyaɗa mata kai nayi, a take ta soma bani labarin ta, har ƙarshe, ai kuwa tsalle na doka na ce, "dole ne nayi aiki da wannan damar yan zun ma kuwa, amman yau zaki kaini gurin ko? ". 



Dariya takeyi har da tafawa ta ce, "kai NARSAL kin ƙara burgeni tashi dai kije ki gani wan nan Mrs Yaseer ɗin ko zata bamu haɗin kai, amman kiyi amfani wayon ki". 



Tashi nayi, muka fito a jikin motar muka sami Amrah shiga kawai mukayi, direba yaja mu sai gidan Mrs Yaseer ai kuwa da farin ciki ta tarbemu, ta shigar damu cikin falon ta, turus mukayi, ganin mijin ta, zaune yana aiki da laptop ɗin sa, ɗago idon sa yayi muka gaisa dashi a daddare, tashi yayi ya bamu guri muka zazzauna. 



Kayan motsa baki ta saka aka kawo muna, mukayi godiya kallon Miss Yaseer nayi naga ni take kallo, nayi murmushi na ce, "to ke ba sai ki sanar damu Mai gidan yana nan ba, kin fa mun zo mun takura masa fa? "



Dariya tayi ta ce, "to dan Mai gidan yana nan sai akace ko wane baƙin ne bana son su gan shi? ". 



Cike da mamaki muke kallon ta Amrah cike da dariya tace, "to ke ba kya gudun nayi maki snatched ne madam, kowa ce, na ɓoye mijin ta ke kina nunawa? "   


Dariya tayi tace, "ai kuwa tunda mijina ba mugun abu bane sai na nunawa kowa shi Aure fa mukeyi ba zina ba, ballema naji kunyar nuna shi, a gaban idon kowa ". 



Dariya mukayi, ta ce, "nasan kin zone kiji ta baki na, kija ra'ayi na, na yarda muje gurin da zamu halaka baƙi ɗaya". 



Da mamaki muke kallon ta, gashi ta ɗaure fuska ba alamar wasa, a tattare da ita, taci gaba da faɗar, "kada kuyi mamakin taya akayi nasan hakan, to a zahirin gaskiya tun farkon ganin ku da nayi da kuma yanda nake a natse ina iya gano cewar ke da wannan yarinyar Yaya da ƙanwa ne, kuma tun daga lokacin da na fahimci hakan sai na ƙara zurfafa tunana, a kanki da abunda kika zo nema, 




Tabbas abunda kika zo nema yana nan a kusa dake ki natsu da kyau kada kuyi garaje, kibi komai a sannu zaki fahimci gaskiyar abunda kike son sani, yan zun ki tashi ku tafi kada ku daɗe anan dan kuna cikin tarko ne amman kisan abunda kika faɗa a kai na Allah ya bada sa'a". 




Kallon ta nayi nace, "to kin san da hakan miye yasaka kike biye dasu, kuma kin san cewar hakan yanada illah babba, sannan a iya sani na, biyayya da ƙasda kai a gurin miji da nuna masa kulawa, tsabta tattalin iya girki iya ado kwalliya nuna masa yafi kowa a gurin ki, girma mawa, farin cikin sa shine naki baƙin cikin sa kin fisa shiga damuwa, samun sa shine naki rashin sa, tare kuke da muwa kina kwantarwa mijin ki hankali tare da addu'a sune suke saka, miji yaso mace, har yaji  baya iya haɗata da kowa ce mace, to sakacin na miye? ". 


Dariya tayi ta ce, "shi yasa nace dake keda yar uwar ki, kallon farko na fuskaci akwai abun da kuke nema, ku tashi kuje ". 



Tashi tsaye mukayi, Amrah ta ce, "naga alamar sun tsoratar dake da yawa, kuma na fahimci cewar ke mace, ce mai sanin ya kamata Allah ya ƙara danƙon soyayya keda Yaya na ". 


Da Amin muka amsa muka fito da mijin ta muka haɗu ya ce, "har kun fito Mrs Salman?  To Allah ya bada sa'a". 



Ganin irin yanda muka zaro ido waje nida Amrah kawai yayi murmushi ya raɓamu ya wuce war sa, ssi da ya shige ciki sannan muka dawo da idon mu a kan ta murmushi kawai tayi muna, tayi gaba abinta, tayiwa direban ta, maganar inda zai kai mu, tunda wancan direban yayi tafiyar sa. 



Jikin mu a sanyaye muka shiga motar ita kuma ta komawar ta cikin gidan ta, muka ɗauki hanyar gidan Mrs Naseer, itama da farin ciki ta tarye mu, amman har yan zun nida Amrah bamu ce da junan mu uffan ba, ganin yanda muka shigo cikin yanayin damuwa ne, ya saka Mrs Naseer tace, "I hope everything is fine, kodai Mrs Yaseer tayi maku wani zan cen ne akan mu? "



Gir giza mata kai nayi, na sauke ajiyar zuciya nace, "Mrs Yaseer tayi nisa bata jin kira mijin ta ya kafe ta, ya hure mata kunne bata jin zata iya aikata irin hakan, ke a gaban idon mu ma cewa yayi baya hana ta kwashe_kwashen abokai ba?  Shifa baya son ganin ta da ƙawa ko ɗaya fa, dan haka mu tashi mubar masa, gidan sa, haka kawai daga ganin mutum baƙuwar fuska sai ya yarda dashi? ". 



Zaro ido waje tayi ta ce, "a gaskiya bai kyauta ba, amman ni banga wani laifin sa ba, ke nima fa nayiwa kaina karatun ta natsu, ba zan koma aikata irin aika_aikar da mukayi ba, abaya ba, dan haka kema ki janye kanki daga aikata irin wannan mugun nufi da kika tsirowa kanki"



Kallon ta nayi nace, "ke koda ni ɗaya ce a wannan tafiyar tunda nayi niyar cika burina sai ya cika, ba zan janye akan baka na ba, kuma ki rubuta ki ajiye ni NARSAL sai na baku mamaki ". 



Na kalli Amrah na ce, "ke tashi muje ". 


Da ido ta bimu sake da baki, Amrah tace, "idan ke gwiwar ki ta kwance, to mu yan zun muka ɗaura ɗamarar tun karar filin daga, dan nima sai na shiga a cikin wannan tafiyar mun bar ki lafiya ". 



Fita mukayi sai kiran mu take tana mu tsaya, amman muka shareta muka nufi direban ta, nayi masa bayanin inda zai kai mu, aikuwa muna shiga yaja mu sai gidan Haulman direba ko parking bai gama gyarawa ba, na fito nayi cikin gidan da sauri, ai kuwa a tsakiyar falon muka sameta ta da sauri taja hannu na ta zaunar dani, taje ta ɗauko ruwan Ever ta bani nasha, ta zauna tayi murmushi tace "ita fa Mrs Naseer da wasa take yi maki, dan ta gwada ki ne taga ni, kodai Mrs Yaseer ta sauya maki tunani ne". 



Kallon mamaki nakeyi mata, ta ce, "kwarai kuwa, ni nasan halin kowa daga cikin su, dan haka ki kwantar da hankalin ki, ke gama labari mai daɗin ji, yau da dare zamu tafi gurin nan ina fatan yan zun hankalin zai kwanta". 



Murmushi dayi wanda har haƙora na suka bayyana, na ce, "haba yan zun naji zance nikam". 



Dariya tayi tace, to jeki na nuna maki ɗakin da zaki zauna kafin na zo da dare misalin ƙarfe sha biyu na dare, sai ki shirya da kyau ". 



Dariya nayi nace "Aa yau zan kwanta ne tare da wannan yarinyar saboda tsaro kin san yan zun akwai waya hannun ta, kada muyi sakaci". 



Ta ce, "yauwa shiyasa kike ƙara shiga raina dan akwai ki da saurin fahim ta ". 



Ɗakin da Amrah take ciki anan na shiga kwance na sameta, nima na zauna a kusa da ita, ita kuma ta ce, "idan kuna ɓukatar wani abun kuje kichin da kanku kuma idan kuna son miƙe ƙafa ku shiga duk inda kuke so, ni zan shiga daga ciki zanyi bacci na tun yanzun ". 



Dariya mukayi ta juya ta fita, ni kuma wanka na shiga na sauya kayan jiki na, haka ma Amrah, zaga gidan muke son yi, ai kuwa muka fito nida Amrah mun sha yawo kafin mu dawo cikin ɗakin, waya na ɗauka na shiga cikin bayi, na kira mukayi magana na fito, nida Amrah mukayi sallar magriba muka zauna akayi isha'i mukayi, muka kwanta can misalin ƙarfe goma da rabi, muka tashi nida Amrah muka fito ta bayan wani corridor da muka gani da addu'a ɗauke a bakin mu, muka fita, ta jikin flowers muke bi cikin sanɗa cikin ikon Allah sai gamu a jikin ƙofar mai gadin gidan wanda Miss Yaseer ta bani a rubuce, a test message ɗin da tayo mani, 



Ƙwan ƙwasa ƙofar ɗakin mukayi aka ɓude da sauri muka shiga cikin ɗakin aka rufe ana rufewa ta jikin window na hango security suna dube_dube, ajiyar zuciya muka sauke a tare glub ne aka kunna ɗakin yayi haske ta ko ina, mutum ne muka gani zaune akan sallaya ya bamu baya, kuma sallah ce yakeyi, kallon sa mukeyi amman gaban mu faɗuwa yakeyi, nikam harda dafe zuciya ta ina karanto duk addu'ar da tazo baki na, sallame sallar yayi, addu,oi yakeyi sai da ya jima kafin ya tashi tsaye ya ɗauki sallayar ya fara lunkewa, juyowar da zaiyi kawai muka saki baki da hanci muka zaro ido waje muna nuna mutumen da hannu, 




Shima mu yake kallo ya zaro ido yana, kallon mu cike da mamaki kawai ya dafe kai yayi luuuu.... Ya tafii... Zai faɗi ƙasa kawai, aka taro sa kafin mu ƙarasa kaiwa gurin har numfashin sa ya ɗauke ɗab. 



Cike da tsoro da kukan daya kubce muna, nida Amrah mukayi kansa, shi kuwa wanda ya taro sa, shine yayi dubarar ɗauko buta, ya ɗebi ruwa a hannun sa ya shiga yayyafa masa, ai kuwa cikin ikon Allah sai gashi ya fara buɗe idon sa ya sauka akan wanda ya yayyafa masa ruwan ya kafe sa da ido yace, "Da gaske Salman abunda nake gani da ido na Narjeesah ce, da Amrah a gaba na ko kuwa mafalkin da na saba yin sane? ". 



Jikin sa muka faɗa cikin kuka na ce, "da gaske ne Baban mu nice Narjeesahr ka, tare da Amrah a gaban ka, ba mafalki bane, daman sai da na faɗa masu cewar baka mutu ba, amman suka ƙaryata ni". 



Shafa kaina ya keyi, nida Amrah, Amrah ta ce, "Baba mi yasa ka ƙi dawowa a cikin mu gashi gidan mu duk ya watse, akan yarka abar kaunar ka da jarabawa ta faɗa mata, amman idon wasu ya rufe Baban mu, Anty Narjeesh tasha wahala sosai nasan da kana a kusa ne da wanda ya isa ya aikata muna irin wula'kancin da akayi muna Baba! ". 



Share muna hawaye yakeyi ya ce, "yan zun ba lokacin labari bane, saboda ƙurewar lokaci nima yan zun ne ganin ku nadawo cikin hayyacina da kyau na gane waye ni kuma na gane garin dana fito da iyalai na". 



Da sauri na tashi zaune kallon Salman nayi sai yan zun ne, na ma gane shi ashe shine ya riƙe Baba ya hana sa faɗuwa ƙasa, ai kuwa muka haɗa ido na banka masa harara, shi kuma yayi murmushi, yayi ƙasa da muryar sa, yace, "wato kin kawo kanki gida na bama kijira har a kawo mani ke, kin ga yaro ɗan shala son kowa ƙin wanda ya rasa, kin biyosa har gidan sa". 



Kallon kama raina mani da wayau na bisa dashi, nayi ƙasa da muryar ta nace, "malam kama shirya bani takarda ta, dan ina gama haɗa aikin da nazo yi a gidan ka, zan koma ƙauyen mu". 



Harara ya watsa mani nima ramawa nake yi Amrah ce, tayi gyaran murya tana dariya ƙasa_ƙasa, kallon ta mukayi a tare sai muka ga  ita da Baban duka idon su na akan mu, waskewa nayi, nace, Baba wane gurin ne aka ɓuye Shuraim? ". 



Da sauri ya ce, "shin Amrah wane Shuraim Narjeesah na take faɗa ne? ". 


Salman da sauri ya ce, "Abba ɗan mune nida ita, wanda muka haifa, shine aka kawo a gidan nan "



Sakin baki mukayi nida Amrah muna kallon sa cike da mamaki cikin jin haushin sa, nace, "ai daman kasan inda aka kawo sa, kayi kunnen uwar shegu dashi, ka barni ina ta wahalar da kaina har da kuka, kullum cikin kuka". 


Na ƙarasa maganar ina murguda masa baki. 


Cike da masifa ya taso mani, nima nataso masa, Amrah tace, "dan Allah ku bar wannan rigimar haka nan mu fuskan ci ƙalubalen dake gaban mu, kuma a gaban Baba kuke wannan rigimar taku da bata ƙarewa". 



Sannan ta ce, "Baban mu yaron da aka rufe a gidan nan wanda Miss Yaseer ta baka kulawa da cin sa, da suturar sa, shine muka zo nema a gidan nan, kuma yaron su Yaya Salman ne da Anty Narjeesh wanda yake tsakanin su". 



Cikin sauri Baban yace, "ku tashi da sauri muje ku gani kafin a riga mu ɗaukar sa". 


Da sauri Salman ya ce, "ba zasu riga mu garesa ba, dan na zuba mata maganin bacci, kuma tayi baccin, sai dai masu yi mata aikin, masu tsaron gidan nan, amman nasan yanda zanyi dasu". 



Tashi mukayi muka buɗe ƙofar cikin sanɗa muke tafiya muna kusa da shiga cikin ɗakin ne aka taƙa muna bindigogi ai da sauri nadawo bayan Salman na rungume sa, na rufe ido gam, saboda nafi kusa dashi Amrah kuma ta shige jikin Baba, wani daga cikin wanda suka taƙa muna bindigogin ya ce, "ku juya ko kuma mu kashe ku mu kashe banza". 



Ai kuwa da sauri Salman ya juyo ni nadawo gaban sa ya riƙe ni, ya kalle su, ɗaya bayan ɗaya, ya ce, "to ku aikata mana kuga abunda zai faru, kuma kubar gidan nan tunda ba gidan uban ku bane, jahilci banza da yofi! "



Ai da sauri suka juya suka bar gurin cikin tsananin tashin hankali, sakin sa nayi ina sauke ajiyar zuciya haka Amrah cikin ɗakin muka shiga kwance yake cikin duhu sai da muka kunna fitilar waya muka hango shi kwan ce cikin sanyi sai rawar sanyi ya keyi, ai da gudu muka isa, gurin sa har muna rige_rige hawaye keta ambaliya a idon kowa rungume sa muka, cikin kuka da tausayin yaro na na ce, "Shuraim tashi ka gani ga Mommyn ka a tare da kai, da Anty Amrah da Daddyn ka da kakan ka, kaji yaro na!? "



Buɗe idon sa yayi, ai kuwa ya fashe da kuka ya shige cikin jiki na ya rike ni da ɗan ƙarfin sa, ya na kuka kamar ran sa zai fita, nima ƙara shigar dashi nayi jiki na, sai kuka mukeyi sai jiki na ke rawa, amsar sa Amrah tayi ta rungume sa, itama kukan takeyi haka, Salman ansar sa yayi, idon sa yayi ja saboda tsananin ɓacin rai, jijiyar kansa duk sun tashi sunyi ruɗu_ruɗe, haka Baban ya anshe sa ya rum gume sa a jikin sa. 



Mun kusa awa ɗaya a gurin, Salman ya buɗe bakin sa da ket ya ce, tashi muje na raka ku ɗakin da zaku zauna ba tare da kowa ya san mike faruwa ba, kai kuma Baba ka koma bakin aikin ka insha Allah ba zasu fahimci komai ba".



Ɗaukar Shuraim ɗin yayi ya janyo hannu na, ya ce, "muje Amrah ". 


Muka fito waje ta wata ƙofar yabi damu, ai kuwa sai cikin gidan har ƙofar ɗakin da muke da kayan mu a cikin sa, yazo zai wuce da sauri na ce, "wannan shine ɗakin da kayan mu suke ciki". 



Kallon Amrah yayi ya nuna mata ta buɗe, ai kuwa ta buɗe muka shiga daga ciki a, tsakiyar gadon ya kwantar da Shuraim nima ya janyo hannu na, ya ce, ki kwanta, anan sai ki san dabar da zakiyi kafin ta shigo cikin ɗakin ki fito falon ki zauna, Amrah ke kuma ki kula da motsin Shuraim kin dai san wane mataki, ake cikin sa yan zun gashi yan zun ƙarfe biyu ta kusa na dare, kar ku ɓata lokaci please". 



Gyaɗa masa kai mukayi, ya juya ya fita, muka rufe ɗakin muka kwanta, muka sanya Shuraim a tsakiyar mu, muna shafa sa har yayi bacci. 



Waya na ɗauko nayi ta kiran layin Mrs barr amman ba'a ɗauka ba, Mrs Nazeer na kira, tayi saurin ɗauka, na ce, "kin kira layin Mrs barr kuwa?, nifa nayi ta kiran ta, har yan zun babu reply, to kodai kunyi tafiyar ku ne kun bar ni". 


A cikin damuwa nake maganar gashi murya ta muryar kuka ce, dan har ta soma shaƙewa. 



Da sauri ta ce, "nima fa tun ɗazun nake kiran ta, babu, reply anya dai ko mijin ta ya dawo ne, ta manta da maganar cika alkawarin bokan, ai kuwa kada tasa mu tafka asara, ki kira muna Mrs Naseer mu gani ko suna tare? "



Kashe wayar mukayi, na shiga kiran wayar Mrs Naseer itama sai da nayi mata kira ukku ta ɗaga, na ce, "haba taya zakuyi tafiyar ku, kubar mu, nida Mrs Nazeer, sai kiran wayar Mrs barr mukeyi taƙi ɗagawa kema sai da nayi kira ukku zaki ɗauka, da kun san ba zakuyi dani ba, da baku sa na kwaɗai tuba, da wannan aikin haba dan Allah! ". 



Cikin tashin hankali tace, kika ce bata ɗaga wayar ki keda Mrs Nazeer anya kuwa tana lafiya dan ban taɓa ganin ta kasa cika wannan alkawarin ba, bayan daga wannan ta gama wahala nifa inada shakku a kai, indai ba ta ɗauki wayar ku ba, to batada lafiya, nima bacci ne ya sace ni dan ina zaune ina jiran ta kira ni, amman shuru kake ji kamar anshuka dusa, gaskiya da alamar tambaya "!?. 




Kashe wayar mukayi muka ci gaba da kira ba amsa har Asubahi Amrah kuwa murmushi takeyi, tana ƙara gyara wa Shuraim kwanciyar sa, alwala muka ɗauro muka fara nafila, har aka kira assalatu, mukayi raka atainin fijri, mukayi sallar Asubahi, mukayi lazumi da azkar, sannan na fito cikin falon gidan nayi zaune na buga uban tagumi, sai kusan ƙarfe takwas ta fito a har gitse bata ma lura dani ba zata raɓani ta wuce nayi saurin shan gaban ta. 



Na ce, "madam miye ya same ki ne mukayi ta kiran ki duk hankalin mu a tashe? "



Dafe kai tayi ta zauna daɓas a ƙasa tace, "nashiga ukku ni Haulart na rasa wannan damar ban san miye ya same ni ba, nayi wannan kuskuren nayi bacci mai mugun nauyin gaske, kira mani su a wayar ki suzo yau a gidan nan mu san abunyi, tun kafin guguwar nan ta taso ta dun ƙule guri ɗaya ta haifar da illar da aka ce, zata shafemu dukan mu! ". 



Gir giza mata kai nayi, na ce, "duk suna a hanyar zuwa gidan nan saboda kowa da far gaba ya kwana saboda kiran da mukayi ta maki harda Mrs Yaseer a ciki ". 



Shiru mukayi dukan mu ƙofar aka buɗe Miss Nazeer Mrs Naseer Mrs Yaseer a tare suka shigo a har gitse dukan su, indon su na akan Haulart saboda yan da duk ta birkice. 



Mrs Nazeer ce ta ce, "Bafa zama zamuyi ba, kawai shawara ce, zamuyi mu samu mafita "



Mrs Naseer ta ce, "mafita kam babu ta, ta tashi kawai ta shirya mu ɗauki saƙon mu doshi cikin dajin nan wannan shine mafitar kawai ". 



Ai kuwa duk sunyi na'am da wannan shawarar  da sauri ta shiga cikin ɗakin ta har tan tun tuɓe da capet, ko wanka batayi ba, ta chanza kayan jikon ta, ta fito ko mayafi babu. 



Kallon su nakeyi cike da mamaki Mrs Yaseer ta ce, "kinyi brush kuwa?. 




Cike da masifa Haulart ta ce, "ke brush ya dama ni damuwa ta, ta fiye mani komai malama, kallona sukayi suka ce, muje, kada ki sa mu ƙara ɓata lokaci ". 



Waya tace tayi ringing na ɗauka, nayi shiri na ajiye wayar na kalle su da kyau na ce........ 





"Comment and share*


*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹



 💐💐 *NARJEESAH* 💐💐



*Rubutawa*

*NANA KHADEEJATU*

           *_UMMU IHSAN_*


*ELEGANT ONLINE WRITERS*


_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_



               4⃣1⃣⏭4⃣5⃣


➿➿➿➿➿➿➿➿➿ kafin na furta wata kalmar, Mrs Yaseer ta dakatar dani gurin faɗar, "kamar motar mijin ki nagani a waje shida yaran sa, kodai ido nane yake yi mani gizo? "



Cikin da mamaki Haulman ta ce, "barrister ka? ki kagani kuwa? ". 



Da sauri Mrs Nazeer ta ce, "kina nufin cewar baki san ya dawo ba ko miye? "


Cikin fushi ta ce, "taya zan san ya dawo ne, bayan nayi nauyin bacci amman wallahi sai ya haɗu da fushi na, bari nadawo gurin da zani zai gane kuren sa wallahi, ke kuma NARSAL tashi muje dallah! "



Dariya nakeyi harda dafe ciki na gir giza kai na, nace to ina ajiyar taki ne ko duk fushin yasa kin manta ne". 


Tsaki kawai tayi tace, "nama manta ne" da sauri ta nufi hanyar kichin, ni kam da ido nabi bayan ta dashi, tayi kusan mintina goma sai gata ta dawo a har gitse cikin tsananin tashin hankali, ta ɗora Hannuwan akai duka biyun ta kwatsa uban ihu tana faɗar, "na shiga ukku na lalace sun sace, mani shi sun gudu dukan su, ban same su ba! " 



Tafaɗi ƙasa tana shure_shure ƙafafuwan ta, a ƙasa, kowa cike da tashin hankali suke faɗar su waye ne wai!?. 



Ƙofar da ta fito take nuna masu, duk suka saka salati suna faɗar, "mun shiga ukku dai zaki faɗa" duk sukayi zaune daɓas a gurin da suke, ai kuwa wata irin uwar dariya ce, na kece da ita har ina tafa hannu, na tashi tsaye ina kallon su ina ci gaba da dariyar, ai kuwa suka tsare ni da ido cike da mamaki in banda Miss Yaseer. 



Takowa nayi har inda suke ina fara zagayen su duk su ukkun, ina tafa hannu, sakin baki da hanci sukayi suna kallona harda murza ido. 



Sai da na gama zagayawa na tsaya a tsakiyar su, nace, "to yau dai anyi walkiya an haska kowa, yau ne zaku girbi abunda kuka shuka, Miss Nazeer Mrs Naseer Haulman, ina son ku bani aron ɗan sauran hankalin ku da ya rage  a nan, tun kafin ya ƙarasa ɓacewa". 



Kallon su na sakeyi ɗaya bayan ɗaya, na sauke mayafin nawa na ɗaure a ƙuna, na ci gaba da faɗar, "Amrah...! "Da ƙarfi yanda zata jini, na ce, "ki shigo daga ciki mana". 



Ai kuwa duk suka maida idon su gun da Amrah ta fito ai duk sai suka tashi a tsaye suna sauke ajiyar zuciya, harda su faɗar wai har hankalin mu ya kwanta a gaskiya ki daina yi muna irin wannan wasar yan zun ba lokacin wasa bane, da sauri Mrs Naseer tayi niyar tun karar gurin su Amrah wadda take ɗauke da Shuraim a hannun ta, 




Da sauri na dakatar da ita gurin faɗar, "dakata saurin miye kikeyi ne, ai bari kiji ƙarshen zan cen wanda kike ɗaukar sa da wasa, wannan yaron da kuke gani da kun san waye shi da hankalin ku yafi hakan tashi ba kamar Haulman "



Sake ɗaure fuska nayi ganin irin kallon da suke bina dashi naci gaba da faɗar "yan zun lokaci yayi da wannan guguwar da kuke tsoro zata haɗu guri ɗaya" Shuraim na kalla ina murmushi na ce, my lovely Son Come with me, "


Ai kuwa da gudu ya sauka jikin Amrah yayi kaina da gudun gaske ya ce, "Mommy I miss you ". 



Da sauri na ɗaga shi sama ina juyi dashi muna dariya ina faɗar ɗan farin fitilar gida, ɗan farin mai maye gurbin soyayya ko wace, iri ce, ina son ka ɗana ɗan albarka ". 



Dariya mukeyi, cikin giɗima da fir gita suka haɗa baki gurin faɗar, "ɗan kiii.....!  Kuma!?  Ta ya ya hakan ta faru ne!?.... Kodai kinyi hauka ne!? ". 



Kallon ban za nayi masu nace, "eh amman ba irin taku haukar ba, yan zun ɗan wannan abun har ya isa ya firgita ku hakan kuma harda zufa, ina ga nace, daku Shuraim ɗan manyan mutane ne, ɗan masu mulki masu, gari ba irin muƙamin iyayen wasu ba, wanda suke ƙare rayuwar su a gidan yari ba? "  



Sannan na ce, Shuraim ina Daddyn ka su gan shi, ko da yake nasan yana kusa bisimillah ". 



Ƙofar falon suka maida idon su dan ganin mai shigowa, kawai suka ga Salman ya shigo, suka ƙara kafe ƙofar da ido ko zasu ga wani ya sake shigowa amman sai sukaga babu kowa a bayan sa, sai suka maida idon su a kaina suna yi mani kallon raini. 



Dariya nayi nace, "Shuraim Daddy...! " na nuna masa, ai kuwa da gudu yayo kan Salman, shi kuwa ya durƙusa ƙasa, ya tara masa hannu ya ɗauke sa, ya shigar dashi cikin jikin sa, yana juyi dashi, suna dariya. 



Ai sai Haulman ta daka masa uwar tsawa kamar wani bawan ta, ta ce, "wannan wane irin salon wulaƙanci ne, malam ku ajiye wannan diramar haka, kuma wallahi sai ka gamu da matsanan cin fushi na! ". 




Dariya ya yi, ya tako yazo inda nake, ya haɗani da Shuraim ya rungume mu, ya sakar muna pick ni a goshi Shuraim a kumatu, wani irin uban ihu Haulman ta saka, tayo kan mu amman kafin ta ƙaraso, taji muryar Salma na faɗar kada ki kus kura ki kai gurin da suke wallahi idan kuma ba haka nan ba, jikin ki ne zai gaya maki! "



Da sauri suka maida idon su akan Salma, sai suka ga Muhseen a tsaye yana murmushi shida Salma, Muhseen ya ce, "bisimillah ku shigo daga ciki ". 



Ai kuwa Mai martaba ne ya fara shigowa shida fulani da Mom da Dad, sai Naseer da Nazeer da Yaseer, da Jafar Aliyu Humaira Hindu Auta Nusaiba sai Baban mu, hannu duk suka ɗora akai cikin fir gici, suka faɗi zaune sai jikin su ke rawa. 



Salma ce tayi gyaran murya tace, "Narjeesh kici gaba please ".   


Ni kuwa muna can muna halin da muka saba, mintsil sa nakeyi, harda cizo idan na faki idon mutane, shi kuwa magana yakeyi ƙasa_ƙasa, "yarinya komai abun ki tunda kika kawo kanki gida na ba zaki koma zuwa wani gurin ba, ehe! Kima zauna a kusa da mijin ki uban "ya"yan ki, wata kila naɗan sama maki guri a zuciya ta". 



Tsaki na doka masa wanda ya fito fili, Amrah tace, "Auta jeki gurin su, kiyi masu magana suna can suna aikata halin su". 



Ai kuwa da gudu tayo kan mu ta rungume ni ta baya, tana faɗar, "Anty Narjeesh nayi kewar ki keda my Shuraim". 



Sai alokacin ne ya sakeni na jiyo na run gume Nusaiba muna dariya Shuraim da sauri ya ce, "Anty nima ban ganki ba, ki ɗauke ni ki goya ni kuma ki rama mani dukan da wan can tayi mani taci zali na, harda baki na ta doke har da jini da hannu na, kuma bata bani abinci bata, goya ni inyi ta kuka kuma bana buga boll bana, yin komai...! "




Hannun sa yana kan Haulman yana nuna ta da yatsan sa, da sauri Nusaiba ta ɗauke sa ta fashe da kuka tayi gurin Amrah dashi, itama Amrah kukan takeyi shi kuwa Baban ganin Nusaiba bata gane sa bane ya saka shi kamo hannun ta ya zaunar a kusa dashi, ya anshi Shuraim yana goge masu hawaye yana lallashin su. 



Kallona, na maida akan, su Haulman naci gaba da faɗar, "Haulman kike koma waye, nasan yan zun kin fahimci wani abun, amman bari kiji yanda abun yake, na shigo cikin kune da tsabar wayau na da ɗaukar fansa, da ceto yaro na, Haulman tun kafin nazo garin nan nasan ki da ƙawayen ki da halin ku baki ɗaya, sai dai sam ban riga da nasan halin Miss Yaseer ba, sai da naji daga gareku, him!  Haulman kama Dila sai an shirya tunda shi sarkin dabara ne, shi yasa sai da na shiryo na shigo cikin ku, 



Tun ranar da kika sanar dani cewar Sunan ki Haulman ne, na fahimci Sunan ki ne dana Salman, ma'ana Haulart Salman, shine kika haɗa farkon sunan ki da ƙarshen sunan Salman, wato Haul Man, ni kuwa shi yasa na , buɗe sunan naku wato Haulart Salman, nayi dariya nima shine na sanar dake, NARSAL wato, Narjeesah Salman, kin ga na ɓatar dake, tun daga nan nabaki labarin dana ƙir ƙira, da kaifin basira ta, dan na daki cikin ki, naji sirrin ki, kuma Alhamdulillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu, nasan komai naki kuma na sami yarina ƙarin farin ciki harda mahaifina na". 




Na nuna Baban mu, da hannu na, da sauri Nusaiba ta kafe sa da ido ya sakar mata murmushi ya rungume ta, haka gurin kowa yake mamakin taya hakan ta faru. 



Kallon Yaseer nayi nace, Yaseer a jiya dana tafi gidan ku, kai da matar ka, ban san tan da akayi kuka gane wace, ce niba, kuma narasa taya akayi har kuka san shiri na wallahi badan matar ka, tayo mani test ba, akan kada na yarda da nadamar Miss Naseer ba, da kun saka asiri na ya tuno, amman Allah ya kyauta, Haulart ni ban taɓa kawo wa kaina cewar zaki iya sace, Shuraim ba, saboda nasan baki san niba, baki san wace ce niba haka Shuraim duk da kuwa kammanin Salman da ya ɗauko, na manta cewar kina bibiyar duk wani motsin Salman, kuma na manta cewar zaki iya aikata komai akan Salman, sai da aka lurad dani hakan na fahim ta, koshi kuwa sai da su Jafar suka tuna sar dani cewar har na manta yanda akayi kika sato ni kika haɗa da mijin ki har zan kasa fahim tar, aikin ki? ". 




Cikin da razana take kallona, nayi dariya na ce, "kwarai kuwa ban san kammanin ki ba, amman nasan labarin ki, sai da Salma ta turo mani photon ki dana kwayen ki iri daban_daban da bayanin garin ku da shige da ficen ku, da gurin da kuke zuwa, da yanda al'adar ku take, dan haka ne, aka shirya mani wannan tafiyar wadda ban san wanda ya biya kuɗin jirgi da direban da suke zirga_zirga damu, ke harma da gidan da muke zaune, nidai nasan Salma ce ta tsara, amman ita da waye shine ban sani ba, Salma ya abun yake, a ina kika sami wannan shawarar? 




Dariya Salma tayi tace, "am dafatan duk kuna biye damu, to a zahirin gaskiya kowa yasan bana shiri da matar Yaya Salman ballema nasamu photon ta, dan bana jin zan iya ajiye photon ta, a waya ta, haka zalika ni ko kallon ta bana son yi ballema naji labarin ta, to abunda yasaka na ce, ita ce zata iya aikata hakan saboda, nasan yanda take bibiyar rayuwar bro, kuma nasan yanda bata son ya raɓi kowa ne, ɗan adam nasan zatayi tunanin yana da alaƙa dashi duk da, kuwa a lokacin shi kan sa bro da Anty Narjeesh basu san, alakar dake tsakanin su ba, har sai kusan ɓatan Shuraim da kusan wata ɗaya koma fiye, tun lokacin da bro ya sanar dani komai, kuma ya tabbar mani da cewar ya ɗauki Shuraim a ranar kuma a ranar aka nemesa aka rasa, to kawai na fahimci cewar aikin Haulart ne, shi yasa na nemi shawarar wanda zan Aura a lokacin, shine ya taimaka mani, haka, Muhseen shima ya bada tashi gudumawar, a gurin wanda zan Aura ne nasami photon su da bayan su cikin sauƙi ba tare da nasha wata wahalar ba, amman kuma ma sauki da direbobin da ke zirga_zirga da ku da gidan da kuke zaune ba aiki na bane, aikin Muhseen ne, Muhseen kai muke saurare". 




Gyaran murya Muhseen yayi yace, "a lokacin da na fahimci miye Sister Salma take shirya wa ita da Narjeesh, shine na, sanar da direba na ya ɗauko su a hanya ya kaisu airport, kuma a hannun Salma na anshi photon su Anty Narjeesh naje, gurin abokin karatuna a airport domin ina son yayi masu komai a cikin sauri kuma Alhamdulillah nasami yanda nake so, haka na kira abokina kuma amini na, Al'amin akan buƙatar su Anty Narjeesh su zauna a gurin Ummeyn su, kuma yayiwa abokan mu bayani sune zasu riƙa kaisu duk gurin da na kira na faɗa ina  bukatar aikaisu, ai kuwa haka, suke bin umarnin na, sun bamu haɗin kai ɗari bisa ɗari, harda su sauya suna akan sunayen "yan kauye wannan ke nan". 




Salma taci gaba da faɗar, "tun daga lokacin muka fahimci su Anty Narjeesh sun sami nasarar shiga a gurin su Haulart muke neman yanda zamuyi, su sami ɗaukar Shuraim, gashi mun sami labarin tafiyar dare ne, duk hankalin mu a tashe yake, mun rasa mafita, gashi duk mun haɗu a guri ɗaya nida Muhseen da Yaya Jafar da Yaya Aliyu da ita Anty Narjeesh da Amrah da muke waya, dasu, suna sanar damu halin da ake ciki, na tabbar da cewar Shuraim yana gidan kamar yanda Miss Yaseer ta sanar da ita, gaskiyar lamarin, ai kuwa kamar daga sama, Bro ya fisge wayar ya kashe idon sa yayi mugun ja saboda ɓacin rai, duk sai da muka tashi tsaye, muna zarar ido, cikin ɓacin rai yace, "haba taya zaku riƙa ɓoye mani halin da ake ciki bayan mata ta da ɗana da "yar uwar ta suna cikin hatsari, kuma kun san irin matsanan ciyar damuwar da nake ciki,?  A gaskiya kun ɓata mani rai ku tashi muje gurin su Mai martaba dan duk abunda ake faɗa tun daga farko har ƙarshe munji komai! ". 



Haka muka doshi ɗakin Mai martaba duk da kuwa yawan mutanen biki da suka cika ko ina na cikin gidan, a can ne, Mai martaba yayi muna faɗa sosai shida Dad shine muka shirya zuwa Abuja kuma Alhamdulillah mun iso da wuri, bamu san lokacin da Bro ya baro mu ba, amman ya kiramu yace, na kira Anty Narjeesh akan cewar duk abunda sukeyi su isa ɗakin Mai gadi, a cikin daren, to kunji abunda ya faru". 



Murmushi nayi nace, "Allah sarki sannun ku da ƙoƙari" anan ne Daddyn Shuraim ya ce, "a lokacin dana zo gidan, sai na shigo cikin sanɗa batare da kowa ya ganni ba in, banda yara na, masu, kare lafiya ta, shine na shiga cikin gidan na zubawa Haulart maganin bacci a cikin ruwan lemon da ta a jiye ta shiga toilet, ina kallon ta ta jikin labule har ta shanye duka anan ne bacci ya ɗauke ta, ni kuma na baro ɗakin naje ɗakin mai gadi dan jiran zuwan su, ai kuwa suna zuwa na ɓude masu ƙofar na ɓuya, kasan cewar yasan da zuwan nasu tun kafin nazo, to anan ne, suka gane cewar mahaifin su ne, kuma shima ya ƙarasa dawowa cikin hayyacin sa" 


A Nan ne yaci gaba da basu labarin har zuwa yan zun da komai yake faruwa a gaban kow. 



Cikin sauri Miss Naseer ta nufi gurin Miss Yaseer da niyar dukan ta, cikin tsawa mijin ta ya ce, "haba dai tun kafin kiji naki saka makon, to tun da kin so jin naki tarihin bari kiji". 



Turus tayi tana kallon mijin nata, kamar wata hauka sabon kamu, 


Ya ce, "to duk abunda kika ji Salma ta faɗa nine wanda take magana a kai kuma nine na basu information a kan ku, kuma nine na basu tarihin ku, da halayyar ku, kuma Yaseer da Nazeer dani kai na duk kowa ya bada gudu muwar sa, a cikin wannan aikin, kuma Salma da kike gani ita ce nayi niyar Aure ita ce muka haɗu da ita a shari'ar da sukayi ta farko wadda na bata, rigata, ta rufe jikin ta, saboda kallo ɗaya nayi mata, a lokacin suna baƙin zuwa wannan ƙasar, kuma ni ban san ya ya, akayi ba kika shigo rayuwa ta, har na Aure ki, dan haka yan zun ina yi maki albishir da cewar, an ɗaura Aure na nida Salma yan zun haka, ita a matsayin mata ta, take". 




Wani irin uban ihu tayi ta zube a ƙasa sai ihu take zubawa tana ba zai yuyu ba. 


Kukan mutum ukku da ihun su kawai kake jin yana tashi a gidan dan duk sun cika wa mutane kunne, ihu Nazeer ya ce, "Shin yan zun guguwar ta zo ne ko da sauran ta? ". 



Da sauri Miss Nazeer ta ce, "aa kada ka ce komai a gurin nan na roƙeka da ka tausaya mani! " sai gir giza kai takeyi. 



Wata uwar tsawa ya daka mata ya ce, "yan da kika rabi da iyaye na, mata ta da yarana da kowa sukaji baƙin ciki kema sai kinji fiye da hakan shegiya muna fuka azzaluma! ". 



Mai martaba ne yayi gyaran murya ya buɗe taron da addu'a, bayan ya ƙarasa ne, ya ce, "tabbas Allah shine mai iko akan komai, gashi Allah ya baku aron dama kunyi watsi da ita, to bari kuji Salman da wannan yarinyar Narjeesah ni ne, na saka aka ɗaura masu, Aure tun lokacin da tsafi gaskiyar mai yin sa, ya saka, aka sato yar mutane da niyar cin zalin ta, na riga su, a gurin domin nine na saka aka bar hotel ɗin da aka yada su, kuma wannan yaron da ake rigima a kan sa, ɗan halak ne gaba da baya" anan ne Mai martaba ya basu labrin komai har zuwa yau ɗin nan. 



Ham dala kowa keyi duk da ni da su Yaya Jafar dasu Amrah dasu Humaira da su Salma mun san da wannan zan cen wanda basu sani bane kawai suke cike farin ciki, saɓanin mutum ukku, wato Haulart da  wanda a tare suka wani ƙurma uban ihu suka bushe da dari suka fara yaga kayan jikin su, sukayi waje da gudu suna ihu, duk abunda suka gani sai sun daka, cige gashin kan su sukeyi, wata irin uwar guguwa ce ta taso, ta tur nuƙesu tayi sama dasu.     



Mutane kuwa kowa yayi ta kan sa da gudu. 



Nan nauyar ajiyar zuciya kowa ya sauke, Mai martaba ne ya ce, "to kun dai ga ƙarshen masu shirka, duk wanda yace, tukunyar wani ba zata tafasa ba, to shi tasa tukunyar ko zafi ba zatayi ba, dan haka muji tsoron Allah a duk inda muke, ku kuma Allah ya saka maku da alkhari, gabaki ɗayan ku, Salman kuna sakaci da addu'a duk da nasan ka da ƙoƙari, kuma ita ƙaddarar mutum duk inda yake sai abun nan ya shafesa, sai dai saboda addu,oi abun ya zowa mutum da sauƙi, Allah ya ƙara bamu kariyar sa baki ɗaya ". 




Amin, duk aka amsa Mai martaba ya sake cewar, ku tashi kowa yaje ya shirya yau zamu bar garin nan, kema Salma bikin da ya rage sai kuje ku ƙarasa, Narjeesah da mahaifin su, a maida su gidan su, dan hankalin Umman su ya kwanta". 



Kowa ya amsa da "Insha Allah". 


Dad ne yakewa Shuraim wasa, yana faɗar, "abokina zaka bimu ko? ". 


Ai kuwa da sauri ya tashi ya gudo ya haye jikin Amrah ya ce, "gurin Umma zani, ita ne mai yi mani wasa, tana siya mani kayan  wasa kuma tana sakani nayi bacci na mai daɗi... "



Ai kuwa dariya aka saka masa, tashi mukayi, cikin farin ciki nida Nusaiba mukayi waje, Amrah tana riƙe da hannun Shuraim sukaje suka janyo trolley ɗin mu, suka fito shima Baban mu, ya ɗauko kayan sa, duk kowa yayo waje, motoci aka shiga, nida, Humaira Hindu Amrah Nusaiba Shuraim mota ɗaya Yaya Jafar Aliyu Baban mu mota ɗaya, Salman Salma Muhseen Dad Mom motar su ɗaya, Mai martaba mota ɗaya Naseer Yaseer Nazeer Miss Yaseer motar su, ɗaya. 




Haka muka ɗauki hanya sai gidan su Ummey muka ɗauko kayan mu, mukayi mata, sallama muka rabu cikin jimamin juna, tana tsokanar Shuraim, haka muka nufi airport, jirgi muka hau dukan mu, yan yola, cikin ikon Allah muka sauka lafiya, yaron Yaya Jafar ne yazo da motoci muka shiga sai ƙofar gidan mu, ai kuwa Shuraim da Nusaiba da gudu sukayi cikin gidan, mu kuwa dariya mukeyi masu, muka mara masu baya. 




Umma ce zaune tana famar kiran wayar mu amman shuru, duk hankalin ta, ya tashi kamar daga sama taji muryar Shuraim yana kiran Umma..... Umma...., ai kuwa da sauri ta buɗe idon ta ganin Shuraim ya shigo da gudun sa, ƙofar falon ma da ƙarfin sa, ya turo yayo kan Umma cike da farin ciki ta cafe sa, ta rungume tana dariya Nusaiba ba ce, ta shigo itama ta rungume Umma tana dariya, ahaka muka same su. 




Hindu ta ce, "kai Umma sune kawai kike yiwa oyo amman banda mu". 


Sai a lokacin ne Umma ta ɗago idon ta, ta kallemu taga kowa ya zauna yana murmshi, ta ce, "to bayan kun nemo muna wannan mai saka mutane kuka ya hana su cin abinci? ". 



Dariya mukayi Humaira ta ce, "ai dole ne muyi kuka Umma, kema fa kawai kinyi dauriya ne, amman fa abun babu dama". 



Dariya Umma tayi tace, "Humaira ungo wannan na ce gidan ku". 



Dariya muka shiga yi, a dai dai lokacin da su Yaya Jafar da Yaya Aliyu da Baban mu suka shigo bakin su ɗauke da sallama, amsawa Umma tayi ai tana ɗaga ido, kawai sukayi ido biyu da Baban mu, cikin wata irin zabura Umma ta tashi tsaye, ta zaro ido tana murza idon ta ta gani ko mafalki ta keyi ne, da sauri muka ƙarasa inda take muka riƙe ta, sai jikin ta, ke rawa bakin ta sai mur_mar yakeyi ta kasa furta kalma ɗaya. 



Nusaiba ta ce, "Umma a zahiri ne ba a mafalki bane , Baban mune da kan sa, wanda kowa aka sanar dashi mutuwar sa, ashe yana a raye wasu ne dai suka mutu". 



Zaunar da Umma mukeyi Amrah tace, "a gidan Daddyn Shuraim muka samesa a lokacin baya cikin hayyacin sa, sai da idon sa ya sauka akan Anty Narjeesh san nan yadawo daga cikin hayyacin sa". 



Kuka Umma ta fashe dashi, shima Baban kukan yakeyi ganin hakan ne ya saka Yaya Aliyu ya ce, "dan Allah ku dai na kukan nan haka, kada ku saka kowa ya kama kukan, tun da Allah yasa Baban yana a raye kuma an samesa ai sai godiyar Allah ". 



Share hawayen su, sukayi, kowa yayi shiru sai Shuraim ne ke wasa a jikin Umma yana jan jelar gashin Umma, yana dariya. 



Tashi Umma tayi tace ku tashi Amrah keda Nusaiba ku kawo abinci muje na nuna maku, komai". 



Abincin aka kawo bayan anci ansha ne, Amrah ta labar tawa Baban komai wan da yayi kuka sosai, shi kuma ya ce, sai sun koma gida zai basu labarin abunda ya sani game da hatsarin, kowa yayi na'am da hakan. 



An ajiye maganar tafiya gobe laraba da safe, ai kuwa su Yaya jafar sukace duk tare za'ayi wannan tafiyar dasu, dan haka sukayi sallama suka tafi tare da matan su, mu kuwa cikin farin ciki muka kwana ga Shuraim a jikina. 



Yau tun da mukayi sallar Asubahi, bamu kwanta ba, muka shiga haɗa kayan tafiya, Umma kuwa suna kichin ita da Auta da Shuraim. 



Bayan mun gama shirin mu, mun ci abinci su Humaira suka zo daga baya su Hindu suka zo, muka shiga fitar da kayan mu, motar Yaya Jafar muka shiga muka ɗauki hanya..... 




*Comment and share*



*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹



 💐💐 *NARJEESAH* 💐💐



*Rubutawa*

*NANA KHADEEJATU*

           *_UMMU IHSAN_*


*ELEGANT ONLINE WRITERS*


_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_



*Hahhhh😂🤣 Narjeesah team kun fa sakani dariya, a page biyu, 36/40 41/45, haba dai har kun manta cewar mutuniyar taku, irin gidan da ta fito gidan mata huɗu gidan makirci?  Tafa san ta kan kishi da iya zaman da mutane, kuma, cikin Shuraim shine ya saka ta, ta dawo wata irin shiru_shiru da ita, amman kowa yasan Narjeesah bata dama, haka Amrah, dan haka nasan yan zun kun gane dalilin da yasa, sukayi, acting ta maida Sunan ta NARSAL*



*Ina godiya sosai da Comment ɗin ku da sharhin ku, kuma ina ƙara godiya da addu'ar ku, sosai*


               4️⃣6️⃣⏯️5️⃣0️⃣



➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Tafe muke a cikin motar Yaya Aliyu Hindu na gefen sa, nida Amrah da Shuraim muna a baya,  kowa ka kalli fuskar sa, a cikin farin ciki yake. 


Yaya Jafar kuma shine ke driving Humaira tana gefen sa, Baban mu da Umma da Nusaiba suna baya, kowa yana cike da farin ciki idan ka kalli fuskar sa, amman Baban mu ba zaka gane wane yanayin yake a ciki ba. 


Shuraim sai surutu yakeyi, yana faɗar, "yeeee!  Mun hau mota zamuje yawo, Uncle ka siya mani giwa da zaki inyi wasa dasu, mu shiga ta cikin wannan jejin muyi ta faɗa, da... Da...  Dami ma ake ce masa Anty? "


Dariya mukeyi, Yaya Aliyu ya ce, "nikam ba zan iya siya maka giwa da zaki ba, amman inda kace, na siya maka doki ka hau zan iya kayi ta su guda" da dariya ya ƙarasa zancen. 


Haɗe rai Shuraim yayi Hindu ta, juyo tana dariya tana kallon Shuraim ta ce, "kada kayi fushi nawan bari na anshi wayar sa na kira maka Daddyn ka, nasan shi zai siya maka su, ko? ". 


Kwallar idon sa ya goge ya gyaɗa mata kai, Yaya Aliyu ya ce, "kai my boy badai kuka kake yi ba, to yi hakuri da wasa nakeyi maka, zan siya maka duk abunda kake so, kaji yaro na? ". 


Maƙe kafaɗar sa yayi, mukam dariya mukeyi masu, Hindu ce, ta ɗauki wayar Yaya Aliyu ta kira number Daddyn Shuraim, ai kuwa ringing biyu, ya ɗaga suka gai sa, take sanar dashi Shuraim ke magana, ya ce, da ita "bashi wayar ki saka mashi Hans free". 


Hans free ta saka mashi, ta bashi wayar, shi kuwa ya amsa, yayi kwanciyar sa, a jiki na, ya fara faɗar, "Daddy ina kwana? " dariya ya yi yace, "lafiya lau my lovely son,  ka tashi lafiya ya Umma na, dafatan ta tashi lafiya da Baban mu da su Amrah da waye ma? ". 



Dariya Shuraim yayi yace, "lafiya lau Daddy baka ce, da Mommy na ba, kuma muna cikin mota zamuje wani gurin, kana zuwa muzo mu tafi da kai ko? ". 



Shima dariyar yayi, ya ce, "Shuraim ai Mommyn ka bata son tafiya fani, kaga bata sanar dani ba, ko?  Amman zan zo yaro na dami kake son na zo maka dashi ne? "



Cikin sauri Shuraim ya ce, "Daddy zaki da giwa, da doki mai tashi sama"



Ai kuwa kowa ya saka masa dariya shi kuwa Salman ɗin ya ce, "to kai kuwa yaro na a ina ne, zaka ɗaure giwa da zakin ka kuwa san Mommyn ka tsoron su takeji ko?  Kuma gashi har doki mai tashi sama, ina fatan dai zaka hau dokin". 



Cike da jin haushin su, na ce, "ai da yake shi mutum baya tsoron zakin dolene a cikawa mutane baki, kuma kada a sake sakoni a cikin shirmen ku ehe! ". 



Dariya yakeyi ta cikin wayar, haka su Amrah, Shuraim ne ya ce, "Daddy ka kawo mani mage ƙarama mai kyau ". 



Da sauri na ɓalla masa harara, na ce, ki nemi gidan uban da zai kai maka ita, ku ajiye, kai wallahi kun fa fara cika ni, zan baku mamaki, idan baku fita hanya taba". 



Yaya Aliyu ne, ya ce, "to ke Narjeesh wannan faɗan kuwa, kamar yana a gaban ki, firar suce sukeyi a tsanin ɗa da mahaifin sa, sai kuma kiji haushin su? "



Ni kuwa na ce, "to baka jin sune suke sako suna na a cikin zan cen su?  To kayi masu magana mana su dai sakani a harkar su, ehe! "



Dariya sukayi shi kam firar shirmen su sukeyi kuma duk abunda nake faɗa, a kunnen sa, ne yaƙi magana sai ma cewa yayi, "Shuraim ka kirani da wayar Mommy ka yan zun sai muyi firar mu ko? Ka baiwa Uncle wayar sa kaji yaron kirki? ". 



Dariya yayi ya baiwa Hindu wayar ta kashe suna dariya, kallona ya keyi yana son na bashi wayar amman na ɗaure fuska, kuka ya saka, na kallesa, na daka masa tsawa, "rufe mani baki daga nan ko yan zun nayi maganin wannan rashin kunyar, anƙi a baka wayar, tunda da kuɗin ku na siya, ko kuma ta mutum ce, na ɗauka dole sakani abunda banyi niyar aikata wa ba, kuma ba zaka kira shi da wannan wayar ba, sai dai ku zauna kurame ni babu ruwa na, a ciki" ina zare masa ido. 



Ai kuwa cikin jikin Amrah ya faɗa ya saki kuka yana kiran "Dadd... Daddy", share sa nayi kamar bana a kusa. 



Amrah ce ta shiga lallashin sa, da taga yaƙi yin shirun ne, ta rasa ya zatayi, zuwa can tayi kamar zatayi kuka, ta ce, "Anty Narjeesh dan Allah ki aro muna wayar taki, mu kira masa Daddyn nasa, tunda ba kece zakiyi maganar ba, kinji Anty Narjeesh wallahi har jikin sa ya fara zafi". 



Shareta nayi, itama tayi shiru Hindu ta ce, "shima dai Salman yaso ya haɗa wannan rigimar ne, yasani sarai, Narjeesh ba zata bada wayar ta ba, amman ya saka Shuraim a ciki dan ya fahimci rigimar sa, ke kuma dan Allah ki basu aron wayar tunda ba cinye wa  za suyi ba". 



Kamar nayi kuka na zaro wayar a jaka ta na bashi, ai sai kukan ya dawo dariya idon sa da hawaye amman dariya yakeyi. 



Suma ajiyar zuciya suka sauke suna dariyar, Hindu ce ta anshi wayar ta saka number ta kira, ta saka murya ta bashi da farin ciki ya amsa, ya fara magana amman bayaji saboda munzo gurin da service yake rawa, dole ya haƙura, zuwa can yayi bacci, sai a lokacin ne Yaya Aliyu ya ce, "Narjeesah wai miye ya saka kika saka yaron nan kuka kuma ba zaki lallaba sa ba, kodai irin yanda Umma takeyi maki zaki yi masa ne? ". 



Na ce, "to ya zanyi masa, ai dai kasan ni bana son lambar wayar wani ta shiga cikin waya ta, sabo bana buƙatar ya takura ni, tunda ba shine ya siya mani wayar ba". 



Ya ce, "amman kin san zai iya siya maki wadda tafi wannan ko? "


Na ce, "aa ni ban sani ba dan ban buƙata ba, kuma ban roƙa ba". 



Hindu ta ce, "hahh wata rana zaki buƙata Miss Salman Allah dai ya ƙara danƙon soyayya dan wannan zazzafar soyayyar tana tafiyar dani ne fa". 



Tsaki kawai na sakar masu ban sake bin ta kan su ba, tafiya kawai mukeyi , amman mun tsaya a hanya munyi sallah munci abinci mun riƙo wani, na guzuri sai gab da magriba muka iso garin namu, ham dala muka shiga yi mun shigo garin dutse, a wani hotel muka sauka, muka kwana, tun da safe muka ɗauki hanyar shiga garin gumel, mun iso cikin garin gumel lafiya muka ɗauki hanyar shiga ƙauyen mu. 




Tafe muke wasu zafafan hawaye ne, suka shiga zubo mani, ina tuna irin fitowar da mukayi a lokacin, kallon Amrah nayi naga tana wani makirin murmushi, ta ce, "Alhamdulillah Allah mun bar garin nan da far gaba da tashin hankali da tunanin makomar gurin da zamu sake sabuwar rayuwa, sai gashi yanzun zamu shiga garin nan da ƙarfin mu, kuma cike da farin ciki, da tarin nasa rori". 



Kwatan ce hanyar da zasu bi Amrah takeyi, har muka iso ƙofar gidan mu, mukayi parking, duk muka furta "Alhamdulillah", 



Bamu fito ba muna daga cikin motar, kusan mintina biyar, idon mutane, yana akan mu, Yaya Auwal ne ya fito daga cikin gidan yana kallon motocin, a kuwa nida Amrah da gudu muka buɗe ƙofar motar muka fita da gudu muka faɗa jikin sa, muna hawaye, cike da mamaki da farin ciki ya ce, "Alhamdulillah Alhamdulillah Amrah Narjeesah kune nake gani da ido na?  Ina Umma ina Auta Nusaiba ina yaron nan Shuraim? ". 



Yaya Aliyu ya ce, "to taya zasu iya amsa maka duk wannan tambayar lokaci ɗaya, ka bari ku shiga daga ciki ku zauna mana ". 



Dariya Yaya Shuraim ne ya ƙaso gurin yana faɗar "Mommy waye ya dakeku kuke kuka, na kira Daddy na, nasar dashi yazo da Bindigar sa ya rama maku? ". kamar zaiyi kukan shima




Da sauri Yaya Auwal ya janye mu daga jikin sa, ya matsa, ya ɗauki Shuraim yana dariya yayi cikin gidan dashi, mutane kuwa tuni labarin zuwan mu ya riski kowa. 



Inno ce ta fito tana gyara ɗaurin zanen ta, ta ce, "dama nadan duk daren daɗewa zaku dawo, toni yan ban zanga kuzo na rungume ku mana". 



Ai da gudu mukayi kanta har da Auta da ƙaraso gurin mu, rungume ta mukayi, kuka ta fashe dashi taja hannun mu kukayi cikin gidan, kallon gidan mukayi duk an sauya masa tsari icce dalbejiyar mu yana nan, amman ɗakin Umma babu shi kwata_kwata wasu ɗakuna ne akayi daga baya, a tsakiyar gidan cikin inuwar icce inno ta saka akayi muna shimfiɗa muka zazzauna, Shuraim ne suke fira shida Yaya Auwal yana bashi labarin Daddy sa, suna dariya Inno kallon mu takeyi ta kalli Shuraim. 



Ta ce, "wai nikam Amrah yaron nan ne yayi wannan wayon haka? "



Dariya mukayi Yaya Aliyu ne ya ce, zan je nadawo Shuraim kayi mani rakiya mani"



Da sauri ya tashi yana murna, Inno ta ce, "kuce ɗan naku swai_swai ne jirgin yawo to ayo muna tsara dai". 


Dariya mukeyi Shuraim ya ce, "zanyo maki tsaraba mai yauwa ko Uncle? "


Dariya yayi masa ya shafa kansa, Inno ta ce, to da kuɗin waye zakayi mani wannan tsabar mai yauwa, dan nasan kai dai ba kuɗi ne da kai ba, baka da ko naira".  Tana yi masa dariya 



Fuska ya ɗaure ya ce, "Uncle Daddy na yanada kuɗi masu yawa ko?  Kuma shine zai bani kuɗi nayo maki tsarabaaa". 


Dariya akeyi masa antaru a gurin harda maƙota da yan gidan wanda bamu sani ba, baƙin fuska, Humaira da Yaya Jafar suka shigo da sallama da sauri Shuraim ya nufesu yana yi masu oyo kuma sai dawo "mun riga ku, wallahi"


Ɗaukar sa Yaya Jafar yayi ya shillashi sama, suna dariya. 


Humaira a kusa da Inno ta zauna tana gaisawa da ita, ta ce, "wash Allah na gaji, Inno a bani filo na kwata naɗan futa". 



Cike da mamaki Inno ta kalle ta ta ce, "da alama jiki na ne yake wahalar mani da 'yata ". 



Dariya muka shiga yiwa Humaira Inno tayi mata tonon silili, rufe ido tayi, kawai aka kawo mata fillon ta ce, "to malama Narjeesh matar shugaba Salman ". 



Duka na kai mata, Inno ta tare, tare da faɗar "kada ki kusa dukan ta a gaban idona, Allah zan saɓa maki". 



Baki na turo na tashi daga gurin nace, "ai inda Yaya tana nan da sai ta shigar mani, nima". 



Dariya suka saka mani, ina hara rar su, harda kyabci nakeyi masu. 


Su Yaya Aliyu kam tafiya sukayi, sai ga Yaya ta shigo tana faɗar "Inno da gaske dai sune suka zo"



Da gudu mukayi kanta mu ukku run gume ta, muna dariya, itama kukan ta saka tana faɗar, "miyasa kuka daɗe baku wai waye muba, ne duk kun tafi kun bar mu da tunanin rasa sanin inda kuka shiga, munyi nema munyi cigiya gashi Allah ya dawo muna daku cikin ƙoshin lafiya, ina Umman Nusaiba, ina fatan tana lafiya naga anfito da yaro ƙarami baƙi nakuwa san cewar shine yaron da kuka tafi dashi yana jin jiri"




Dariya muka shiga yi, hannun mu taja muka ƙarasa  muka zauna sai tambayar mu take "kuna lafiya ya bayan rabuwa, Narjeesah duk kun sauya muna kamar ba ku ba"



Humaira ta ce, "Yaya ai ita Narjeesah Daddy Shuraim ne yayi mata wannan gatan bakiga irin yanda suke zuba soyayya ba, ke da zamu zo harda kukan rabuwa sukayi harda cewa tayi wai ita ba zata zo ba, sai dai mu muje ita ba iya barin mijin ta, ya zauna shi ɗaya". 



Ido na zaro waje na ce, "ke Humaira Allah Yaya kada ku yarda da uwar sharrin nan, Allah ƙarya takeyi maku! "



Hindu ta ce, "Inno da gaske ne bata son mu faɗa ne kawai amman ko yan zun hankalin ta yana gurin gurin sa da kuka suka rabu dashi ". 



Tagumi na zuba ina kallon su, Anty Basira ce da Shamsiyya da Hanan Haule, Hannatu Yaya Halilu Yaya Hamza, Yaya Mudarsir Anty Asma duk sune suka shigo cikin gidan kamar wanda aka koro su, zuwa can kafin su zauna sai ga goggo da Kawu Bala har yan cin tun tube da babbar rigar sa, kamar zai kife, Mama ce, ta fito tana ɗir gisa ƙafa duk tayi baƙi ta fita hayyacin ta. 



Su Humaira duk sai suka maida hankalin su akan wannan mutanen dake ta shigo wa, mu kuwa kallon kowa mukeyi ɗaya bayan ɗaya. 



Kawu Bala ne ya ce, "kamar dai naji ance, wai su Nusaiba ne suka dawo kodai mutane basa gani da kyau ne kuma basu dai ji abunda ake faɗa da kyau ba, har kasuwa akaje aka sheda mani, ɗan achaɓa ne ya kawo ni gidan nan". 



Duk a daburce yake magana, Hanan ce tayi dariya ta ce, "wallahi sune suka dawo Narjeesh Amrah Nusaiba kun dawo kamar wasu "ya'yan turawa" tana dariya tayo kan mu ta zauna a kusa damu tana cike da farin ciki ta ce, "ina Umma da Shuraim? ". 



Humaira ta ce, "ko bamu tambaya ba nasan wannan ita ce Hanan". 



Dariya mukayi tashi Hanan tayi, ta ƙarasa gurin su, aikuwa sai fira kamar sun daɗe da sanin juna. 



Kallon Inno nayi batare da na kula da kowa ba a gurin na ce, "Inno tare muke da Umma da kuma wani babban al'amarin daya shafe mu baki ɗaya". 



Cike da mamaki kowa yake kallon mu, suna mamakin wane babban al'amari ne da yashafi kowa a zuri,ar mu? 



Kawu Bala ne ya ce, "badai wani cikin ki sake yowa ba, ko wannan ce ma tsaurin idon tayo shi, to ba a gidan ba, dan kun san baku da gado a cikin sa". 


Da sauri Hindu ta ce, "gado kam ai ya tashi tunda mamalkin gidan da ransa bai mutu ba, nifa wallahi ba zan iya jurar abunda su Narjeesah suka jura ba, ehe! ". 



Humaira ta cafe tace, "waifa gado ina ma wani gadon yake ne, malamai bari kuji, ita fa Narjeesar nan da kuke gani zaune a gaban ku, ku kiyaye sakin duk maganar da tazo a bakin ku, saboda idan masu tsaron lafiyar ta, sukaji zasu iya datse wa mutum halshe dan haka mutum ya kiyaye, kawu Bala kaida goggo da Mama kubi a sannu dai ehe! "



Kowa kallon su Hindu yakeyi cike da mamaki, goggo ta ce, "to da alama dai ankai maku ƙarar mune dan naji kuna furta Sunan mu kamar a bakin ku aka zana shi ki? ". 



Amrah tayi dariya ta ce, "wato dai mu bamu da aiki sai tara "yaya kun maida mu fasiƙai, to Alhamdulillah duk cikin mu babu wanda ya taɓa zubar da cikin shege kuma, yan zun da mutum yasan wace ce Anty Narjeesh da ɗan mu Shuraim da zufa tayi ta zubo masa! "



Ni kuwa nayi saurin faɗar ku ce, dasu da sun san abunda muka zo masu dashi da wasu sun kusa sumewa, marasa gaskiya kuwa za suyi ta kan su, Inno da Yaya duk abunda kuka gani kada ku firgita kuyi aiki da hankalin ku, komai a zahirin gaskiya yake tafiya kuma, mutuwa bata ɗauka sai lokaci yayi, haka zalika ko wane bawa da irin tasa ƙaddarar wasu suyi imani da ita ƙaddarar wasu kuwa suyi biyu babu, Nusaiba jeki kice da Umma kowa ya hallara a gidan nan! "



Ai kuwa da gudu Nusaiba ta tashi ta fita, kowa yana jiran dawowar ta, Inno ta kasa haƙuri ta ce, "kodai masu neman Auren kune? "


kawu ya ce, "ashe dai kun ƙaro fitsara eh lallai kam na fahimci komai ". 



Goggo ta ce, "wato rashin kunya kuka dawo kuyi muna ku nuna muna baku shiryu ba kuma duniya bata hora kuba ko su kuwa wan can fitararrin daga ina kuka samosu ko suma abokan fitsarar taku ne? "



Sai a lokacin Mama tace, "sune ma dan wannan rawar kan nasu yayi yawa, ai kuwa abunda kika aikata zasuji babu wani rufin asiri". 



Yaya tace, "ai dai masu goyon shegun suna da yawa, dan haka baki da bakin yiwa Narjeesah gori dan kema kin goya shegu, ga kuma wani cikin nan wanda bamu san uban saba, a gurin yarki, kin ga kuwa dama can mun sanar dake mai ɗa goye baya cewa ɗan wani shege bai sani ba ko ya haifa, ashe kuwa ya baki ya boka, kin haifa shegen ke nan". 



Tsit kaji bakin Mama tayi ƙasa da kanta. 


Dariya Amrah da Humaira da Hindu sukeyi harda tafawa. 


Sallamar Umma ce ta katse masu tattaunawa suka maida idon su, akan Umma cike da mamaki suke kallon yanda Umma ta sauya ta zama wata Hajiyar da ita, sakin baki sukayi wasu ma murza ido sukeyi. 



Inno ta ce, "Allahu akbar kabira, Umman yara kece kika dawo haka ikon Allah to lale maraba da zuwa, sannu da zuwa sannu da zuwa " cike da farin ciki suka rungume juna. 



Ita kuwa Yaya hannun Umma ta riƙe tana kallon ta, tana godiya a gurin Allah subhanahu wata'ala. 


Umma tayi murmushi tace tare muke da baƙi fa, dan Allah ku zazzauna hannun Inno da Yaya ta kama suka nufi gurin su Humaira suka zauna, 



Nusaiba ce tare da Baban mu suna riƙe da hannun juna suka shigo Yaya Jafar Yaya Aliyu suna biye dashi. 



Hailala da salati gurin ya ɗauka sai murza ido sukeyi ai kuwa da gudu Yaya Auwal ya matsa yana taɓa jikin Baba sai da ya tabbar shine ba mafalki bane yakeyi ai kuwa ya rungume shi, ai sai ga Hanan itama ta faɗa jikin sa, sai kuka yadawo sabo. 



Kawu Bala ne ya ce, "wannan ai ba gaskiya bane waye ya taɓa mutuwa kuma ya dawo sai dai ko fatalwa ne eh lallai kuwa ni ban yarda da wannan lamarin ba! "



Goggo ta kasa tsayuwa ta zube a gurin bata numfashi haka Mama faɗuwa gurin tayi, su Yaya Halilu kuwa suman zaune sukayi hada su Anty Asma. 




Hamdala Inno tayi tace, "ikon Allah tabbas wannan Malam Isah Musa, dan naji a jiki na, mai gidan mu ne ya dawo ran sa, Allah mun gode maka". 



Yaya tace, "hakane Inno wannan uban "yayan mune Allah ya dawo muna shi, yara kun tashi daga marayu kun dawo masu uba, mu kuma mun dawo matan Aure Allah da ikon sa yake". 



Tashi nayi natako nazo nace, "muje ka zauna Baban mu ka futa sai ka bamu labarin abunda ya faru a shekarun baya"



Hannu na ya riƙe muka je muka zauna muka saka shi a tsakiyar mu, duk kowa yayi shiru muna jiran muji daga garesa, harda maƙota masu kallon Ikon Allah, duk suna a gurin. 



Wayar Yaya Jafar ce tayi ƙara, da sauri ya kalli Baban ya ce, "sun neman izinin shigowa"


Murmushi Baban yayi ya maida idon sa akan Yaya Mudarsir ya ce, "kaje ku shigo da baƙi". 



Tashi yayi ya fita, sai gashi sun shigo tare zaro ido waje nayi, na buɗe baki zanyi masifa, da sauri Humaira tayi wa Inno da Yaya raɗa a kunne da sauri suka ce, "A hir ɗinki Narjeesah Allah kikayi wata magana a gurin zamu swaɓa maki ". 



Zuɓurar baki nakeyi gaba, ina ɗaure fuska, Shuraim kuwa ƙafata, yazo ya haye Salman a kusa da Yaya Jafar ya zauna, Muhseen kuwa a kusa da inda muke  zaune ya zauna  ya ce, "Anty Narjeesh bakiyi maraba da zuwan mu ba ne? ". 



Gir giza masa kai nayi nace, "kai nayi maraba da zuwan ka amman banda wan can mutumen ka duba yanda yake harara ta" 



Ɗaga ido sukayi shida Amrah ai kuwa harar ta, suka kamasa yana yi dariya sukeyi ƙasa_ƙasa. 



Gyaran murya Baban yayi yace, "To Alhamdulillah Allah shine mai tsara yanda yaso a duk lokacin da yaso, to gashi Allah yayi dawo wata a cikin iyalai na, kuma gashi nasami sauye_sauye da dama kuma abubuwa duk sun birkice, motar da muke ciki ce, tayi hatsari ba tare da mun san miye musabba bin ba, amman kuma ni a cikin jeji aka jefa ni, motar ta kama da wuta, kaina ya bugu da icce nikam ban sake sanin inda kaina yake ba, na dai falka ne na sami kaina a asibiti kuma na manta kaina da Sunana kawai dai na rasa Yaya zanyi na tuna inda na fito, koda aka sallame ni daga asibiti wannan yaron ne na gani a kaina, kuma shine ya ɗauke ni ya kaini gidan sa, naci gaba da jinya ta har nasami sauƙi amman kuma, hal zuwa lokacin bana iya tuna waye ni, ganin haka ne ya mai dani asibiti aka ce, idan naga abunda nafi ƙauna zan iya tunawa, gidan su muka dawo ya bani aiki wanda na nema duk da kuwa cewar gidan sa cike yake da ma'aikatan kaki da marasa kaki ya bani gadin get ɗin ƙuryar gidan sa, kasan cewar get huɗu a gidan nasa". 



Kallon Salman sukeyi wanda idon sa yake a watar sa kamar baya gurin. 


Baban ya ce, "sai shekaran jiya ne Allah ya kawo mani Narjeesah da Amrah, muka haɗa ido dasu ne, a lokacin ne, nafaɗi ƙasa, kaina na juya mani, a take na some a gurin, ina farkawa na fahimci cewar nawo cikin hayyaci na". 



to kunji abunda ya faru. 


Zufa su kawu suke gogewa, kallon Baban Inno tayi tace, "Alhamdulillah barka da dawowa Malam, sai kuma abunda ya faru bayan baka nan" a take Inno ta labarta masa komai. 


Ai kuwa kallon kowa yakeyi a gurin yana gir giza kai, ya ce, "wato koda mutuwar ce, haka zakuyi wa iyali na, wula'kanci, Narjeesah!  Narjeesah!! Narjeesah!!!  Kuna nufin ita ƙaddara bata isa ta faɗa a kan ta bane ko miye kuke nufi? Ai ada na ɗauka, koda a ce da gaske cikin jikin Narjeesah da gan ganci ta same sa irin yanda kukafi kowa sanin ina son ta, to kuma zaku sota kuma zaku janyo ta a jikin ku, a hankali kuna nuna mata, laifin ta, 




To yan dai bari kuji waye wannan Shuraim ɗin yaron Narjeesah wanda kuka tsana kuka kureta ida da 'yan uwan ta, harda mahaifiyar ta, suka rasa matsu gunni, kuka basu wasu 'yan kuɗi, wai gadon da suka samu ke nan, to kun ga wannan yaron Shuraim? "



 Ya  janyo hannun Shuraim ya zaunar dashi a jikin sa ya ce, masu "yaron nan ɗan halak ne kuma wannan yaron da kuke gani Narjeesah ta hanyar sunna suka sami cikin sa, kuma, shi jika ne, a gurin sarakai kafin nan Aliyu ku sanar dasu waye mahaifin Shuraim"




Gyara zaman Yaya Aliyu yayi yace, "Shuraim" labarin komai ya basu har sace sa zuwa yan zun, san nan ya sake kallon su, ya ce, "kun ga wannan"



Ya nuna Shuraim yace, "ga Salman nan shine uban Shuraim halak malak". 



Dukan su  mamaki sukeyi wai a ce Shuraim ɗan gata gaba da baya, sukayi muna wannan walaƙancin haka?. 


Salman kuwa haushin su yakeji, Inno ce da YAya da su Yaya Auwal Hanan da wasu daga cikin yan uwa na kawai yaji baya jin haushin su, tashi kawai yayi ya bar gurin yayi waje kamar wani kubu buwa. 



Da sauri su Yaya Aliyu da Jafar suka mara masa, baya. 



Inno ce  ta ce, "Malam Shamsiyya da Atika ciki biyu sunayin kuma suna haifewa, ita Shamsiyya wannan cikin na jikin ta shine na ukku, duk da anso zubar dashi amman abun ya faskara". 



Cike da mamaki Baban ya ce, cikin fushi, wato........  





*Comment And share* 

 


*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹



 💐💐 *NARJEESAH* 💐💐



*Rubutawa*

*NANA KHADEEJATU*

           *_UMMU IHSAN_*


*ELEGANT ONLINE WRITERS*


_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_


                5⃣1⃣⏭5⃣5⃣

               

➿➿➿➿➿➿➿➿➿ "wato sune "ya'yanso ko?  Basa laifi, ai ni a ganina duk yara na ɗaya suke a gurin ku kamar yanda nake ji a zuciya ta, Bala kai da ƙanwata da  ke Larai  kun cutar dani kun raba mani kan "ya"yana manya basa tausayin naƙasa dasu, ni kuma ba haka nabar ku ba, amman babu komai kunyi son ranku, duniya ce, gashi nan tun yanzun kun fara gani!". 


Kawu Bala yace, "kayi hakuri ɗan uwana sharrin sheɗan ne hakan ba zata sake faruwa ba "



Goggo ta ce, "haba ɗan uwana ai wallahi mu bamu da niyar watsaye maka zaman lafiyar da ka ɗora iyalan ka, shi yasa ma bamu siyar da gidan ba". 


Tsaki Muhseen Humaira da Hindu sukayi, ni kuma na ce, "andai ji kunya wallahi, a ce ya'yan ɗan uwan ka, kayi mugun tsana to taya ma zan yarda in saki jiki daku, kudai kawai a daiyi zumunci". 



Baban murmushi yayi, ya ce, "ba kuda bakin kariyar kan ku amman ina mai jin takaicin abunda kuka aikata mani, domin ni kuka to zarta ba wani ba, ke kuma Larai kin girbi abunda kika shuka ko?  Nafi kowa sanin irin yanda kike ƙin Narjeesah amman na ɗauka ko da bayan rai nane zaki iya renin duk nin abunda na bari a baya na, amman ba bu komai a ga su Shamsiyya nan sun bar maki darasi,  Narjeesah ƙarama ce, akan su Shamsiyya amman babu tausayi babu tausayawa keda yan uwa na da sauran yara na aka kora mani iyali, saboda idon ku ya rufe akan dukiya, to gani nadawo kowa ya dawo mani da abunda yake hannun sa indai nawa ne! "



Shiru duk sukayi sai zarar ido sukeyi da soshe_soshe. 



Muhseen ne ya ce, Anty Narjeesh nifa haushin mutanen nan nake ji wallahi, musam man yan zun dana ƙa jin haushin su"



Dariya mukayi na ce, "duk alamun rashin gaskiya ya bayyana a gare su, sai wani kame_kame sukeyi"



Fira akeyi tsakanin Inno da Yaya da Umma na yaushe gamo har suke sanar da ita cewar ai su yayan mu sunyi Aure, wannan sabon ɗakin da muke gani na sune, da matan su, Yaya Auwal ne da Yaya Anas ne basu yi Auren ba, saboda sun ce, sai Mun dawo ko suna dawowa cikin natsuwar su, haushin kansu sukeji, saboda kasa iya tsare muna wannan fitinar data faru da rashin adalci, sun je neman mu gidan da muka zauna ko suna da labarin garin da muka nufa?  Maƙota sukace basu da labari, shine bayan kwana biyu suna neman mu basu same mu bane shine suka tuna da ƙawar Umma baba Luba, to sunyi nasarar zuwa gurin ta, sun gano gidan ta, amman kuma itama ta ce, dasu neman ku takeyi ta nemi yafiyar ku, domin saboda ita kuka zo garin amman hassada ta saka ta koreku, gashi ita bata da labarin, wasu 'yan uwan ku, bayan kawu, haka suka dawo jiki babu lakka, to shima dai kawun Umma yana cikin tashin hankalin rasa, rike ammar da aka bashi saboda tsabar son zuciya , kun fa ji abunda ya faru ". 



Amrah ta ce, yauwa Inno ina mutumen da ya tashi sace muna Shuraim ya turo muna yan daba, wanda shine silar barin mu garin nan? "



Ai kuwa da sauri Mariya ta ce, "number shi tana nan na amsa, mayar sa ta kusan bakwai neman ku, shi da yan daban sa, ala dole sai anfito masa da ɗan sa, bari na ɗauko maku number "



Tashi tayi ta shiga cikin ɗakin Inno mu kuwa  murmushi muke sakar wa juna, Muhseen ya ce, "kamar ya ke nan?"



Nusaiba ta ce, "bari na baka labarin abunda ya faru" ai kuwa harda zufar sa cike da masifa ya anshi number wayar ya tashi ya fita waje Yaya Auwal ya mara masa baya. 



A can ƙofar gida suka sami su Daddyn Shuraim tare da Shuraim ɗin yana maƙale da hannun sa, sai rigima ya keyi, duƙawa Salman yayi ya ɗauke sa, ya ce, "my friend miye ne mi kake so ne wai, wannan rigimar ta miye? ". 



Dariya Shuraim ya yi ya ce, "Daddy ka bani sharabar da nace, maka ance na kawo idan kazo, kuma na ce shan bata". 



Dariya suka saka masa, "a'a Shuraim yau kuma maganar ma irin ta shagwaba ce akeyi, to Allah ya taimaka man bashi tsarabar sa da sukayi rigima shida Inno ya kai mata"



Salman ya ce, "Aliyu yaron nan harda su cika baki yayi wa matan nasa ke nan?  Eh lallai nabaka goyon baya, ka kai masu kada matan su kira ka miji marar cefane ". 



Dariya aka saka Jafar ne ya buɗe motar yana dariya ya fara ɗauko masa ledodin masu zane kuma cike suke baya iya ɗaukar su, gashi leda ukku ce, riƙo masa sukayi har cikin Zauren gidan namu, suka rage yawan kayan suka bashi da ket yake tafiya su kuwa dariya sukeyi masa, da sallama ya shigo cikin gidan sai uban nishi yakeyi, duk muka amsa muka bishi da ido. 



Dariya mukeyi ganin yanda yake ta uwar zufa, ya raɓa ta gefen mu yayi gurin Inno yana cewar, " wai...!  Wai..!  Na gaji Inno ga sharabar ki na kawo maki, kuma bari na kawo maki sauran, Anty Nusy muje ki tayani ɗauko mata shauyan". 



Kowa sakin baki yayi yana kallon sa musam man yan da ya riƙe kun kumin sa, yana sauke numfashi, tashi Nusaiba tayi tana yi masa dariya ta ce, "wallahi Shuraim ka cika ran ganci yaro daga ɗaukar wannan yan kayan sai uwar zufa kakeyi da sauke numfashi a cikin wahala? ". 



Baki ya turo mata yayi gaba abin sa ya ce, "ban ma so kada kizo nama fata dake". 



Auta ta ce, "Ai kuwa yaro sai nabika dan kaji daɗin kai ƙarata a gurin Daddyn ka ko? " 


bin bayan sa tayi a cikin Zauren ne ta gan su ta anshi kayan tare da neman ta kira masu ni, a tare suka dawo ɗauke da kayan a gaban Inno suka ajiye, Inno ta ce, "Shuraim wannan aikin ai yayi yawa ko?  Nifa da wasa nake yi "



Humaira ta ce, "Inno ko yan zun idan kina buƙatar wani abun kiyi bayani dan yaron namu akwai lafiyar kyauta". 



Dariya akeyi a gurin Yaya tace, "a a iyayen sa dai suke wannan aikin "



Hindu da Humaira da Amrah harda Auta shiga chapta da su Inno, zuwa can Auta tace, "Anty Narjeesh Daddyn Shuraim yana neman ki a waje". 



Ɗaure fuska nayi, kawai na share ta, kowa ya maida hankalin sa a kaina, Inno da Yaya cikin hasala su kace, "anya Narjeesah ba kiji mijin ki na kiran ki bane ko ya ya? "



Umma tac, "humm...! 


Hindu da Humaira suka ce, "Inno sai kunyi da gaske fa, dan har yan zun haushin sa, takeji bayan kuma ta riga da tasan ƙaddarar suce a hakan bayan ma ta gode Allah da Mai martaba da yasa da Auren su wannan abun ya faru "




Ɗaure fuska Inno tayi, tace, kina tashi ko sai nasamu wani abun na jefeki dashi, ja'irar yarinya kawai "




Cin no baki nayi gaba, na tashi na ɗaure fuska na fita, waje. Baban mu ne yayi dariya ya ce, "Narjeesah manya in banda harkar ƙuruciya ina ke ina Salman keda Allah yayi maki babbar kyauta, ai kuwa kada kiyi wa kanki mugun abu, koda ace Salman a iya taimako na ya tsaya ai zaki so ki faran tawa wanda ya ceci rayuwar mahaifin ki a lokacin da kika kusa rasa shi, koda kuwa wannan farin cikin naki shine ya rage maki"



Amrah tace, Baba tanafa son shi, haushin da take ji idan Haulart tana yabon shi da mugun abunda takeyi masa, har jikin ta ke rawa sai nayi da gaske gudun kada ta bari kishi ya saka ta, ɓata muna aiki, kai Baba a ranar da muka shiga cikin gidan kasa bacci tayi, sai yawo takeyi a tsakiyar ɗakin da aka ware muna, sai faɗar take, wallahi ita sai ta ramawa Daddyn Shuraim wannan cin kashin kajin da akeyi masa"



Kun san Allah ce mata nayi, "Anty Narjeesh miye naki a ciki kedai mu ɗauki Shuraim shida yake namu kawai ". 



Anty Humaira kin san yan da ta taso mani kamar ta dakeni ta ce, "ke mahaukaciyar ina ce halan, uban ya'yan nawa zaki ce na barshi a cikin wannan halin tare da wannan mummunar mata?  To wallahi ni bazan iya barin shi tare da wata ba, sai dai ke ki ɗauki Shuraim ɗin ku tafi ni kubar ni na kwaci "yan cina ehe! ". 



A da ido kawai nake bin ta, na zama wata wawuya dani, amman idan suka haɗu sai haushin wannan lokacin ya taso mata, sai ta murje idon ta kamar ba ita ba". 



Dariya suka saka, "Yaya ta ce, ai kuwa zamu riƙa takura mata da lurad da ita kada taje tayi saki na dafe "



Amrah tace, "shima fa halin su ɗaya wallahi idan suna a kusa da juna faɗa kawai ke shiga tsakanin su, amman idan bata a kusa himm..! "



Nusaiba ta ce, nice zan baki wannan labarin domin yayi maya ta kai goma neman ta, har sai da ya riƙa zuwa shida Salma da Muhseen, sune suka tambayi inda taje, mukace, bamu sani, ba cike da masifa ya ce, "da Auren nawa zata tafi wani gurin ba tare da izini ba? "


Nan dai sukayi ta bada labarin irin halin, su Inno da Yaya sukayi wani shiri akan mu. 


Ni kuwa ina kaiwa zaure na haɗu da shi, shima cikin fushi ya janyo ni, jikin sa, ya riƙe ina ta son na kwace jiki na na kasa, yace, "uban waye ne uban sa a garin nan da zai ce zai rabani da ɗana! ? "



Na ce, to malam sake ni mana, nama ɗauka gamo ne nayi, ashe akan wan can shegen mutanen ne"


Ƙin sakin nawa ya yi, "na ce nifa ban ma taɓa ganin saba sai yaran sa, Amrah da Nusaiba ne suka taɓa ganin sa, sai Mariya, ko farmakin da suka kawo muna a cikin dare bamu gan su ba, dan maƙota sune suka ce ce mu". 



Ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "to kuwa zai gamu da gamon sa, tun da ya firgita mani rayuwar iyalina, sai na ɗauki fansa, muje cikin mota muyi magana saura kiyi mani musu, ni kuwa na baki mamaki dan wallahi har cikin gidan zan shiga na ɗauko ki a jikina ". 



Kallon sa nayi nace, "ai dama nasan zaka iya aikata hakan muje ni kada ka kunya tani dan ni nasan darajar mutane ". 



Sakina yayi ya riƙe hannu na, muka jera muka fita, kallon mu mutane kawai suke, abokan Baban mu ne suka aika kiran sa, ya fito yayi ta gaisawa da mutane, tafiya mukayi, har jikin motar daya zo da ita muka shiga nida shi su Jafar kuwa a can cikin majalisar samari muka hango su. 



Shiru mukayi nida shi babu wanda ya ce, uffan har tsayin wani lokacin motocin su na can gefe sun faka. 


Wata mota ce gob3 ta iso ƙofar gidan mu a tsiyace, duk taci uban ta, ta bubbuge ta tsofe, sai mashin kusan bakwai, duk mutanen dake bisa moshin ɗin da na cikin motar ɗauke suke da makamai, sauka sukayi, suka fara ihu, na cikin motar ne suka fito suna busa taba, sigari. 



Zaro ido waje nayi ina kallon ikon Allah, shi kuwa murmushi yakeyi wayar sa kawai yake shafawa, cike da tsoro na ce, "Daddyn Shuraim wannan mutanen fa irin sune suka tashi kashe mu, harda su Umma ". 


Kallo na ya yi yace "to ke kuma keda kika je kikayo rigima kika ɗauko Shuraim yau kece da tsoro?  Ki fita kawai ki zama jaruma dan sun sami labarin zuwan ki, kin ga yan zun ma sun zo ɗaukar Shuraim ne". 



Dariya nayi nace, "to su ɗauke sa mana, ai yanzun bani ce kawai abun zai shafa ba, dan gasu Yaya Jafar da Yaya Aliyu da Muhseen can idon su saboda harara kamar su fito waje, kai ni kallo ne kawai nawa". 



Shima kallon su Yaya Aliyu yakeyi, ai kuwa bai san lokacin da ya kama dariyar su, ba. 


Ƙofar gidan mu suka suka yada zango, Yaya Auwal ne dasu Humaira Hindu da Amrah da Nusaiba su Mariya suka fito suna ƙare masu kallo, wani mummunan mutum ne ya tsaya a gaban su, ya ce, "ina take ina yaro na da aka gudu dashi?  Dan yau ba babu wani tausayi ko ɗauke ƙafa, sai naje da yaro na, kuma sai nayi gun duwa_gun duwa da naman duk wanda ya hana mu ɗaukar ɗana! "




Cikin irin maganar yan tasha, da shaye_shaye yake maganar, dariya Yaya Auwal yayi ya dube shi ya ce, "daga cikin wannan wace, ce, uwar yaron naka duba da kyau dan duk suna da yaro a wannan lokacin? "



Kallon kun raina mani hankali yakeyi masu, sai kuma ya tsare Humaira da ido ya ce, "ke kin ɗauka zan manta kine, to kin gama guje_gujen naki kin dawo ina yaro na yake ne? dan yau ko ki bani na tafi dashi ko nayi filla_filla da naman ki"




Mutane cike da mamaki suke kallon wannan mahaukacin mutumen kace, yaro naka ne amman kuma baka san uwar yaron ba, wata dariya ce, naji Salman nayi, harda dafe ciki da sauri nake bin sa da ido, cike da mamaki nake kallon sa dan yau shine farkon ganin sa yana yin irin wannan dariyar. 



Buɗe motar yayi ya fito nima fitowa nayi su Yaya Jafar dasu Muhseen dasu Baban da yan gidan cikin gidan mu da maƙota duka gurin muka dosa, Humaira kuwa cike da haushi ta ce, "amman dai kai kam anyi jahilin mutum, a ce kai saboda tsabar jahilci da ƙarya da rashin hankalin wato kama rasa sanin wace haukar zakayi sai ta satar yara ai kuwa da kasan ko suwaye a gaban ka da kasan irin masifar da kajefa kanka, da kayi kuka da dana sani na shekara ukku zuwa huɗu dan ba ƙaramin bala'i ka jefa kan kaba, amman na lura da kai da wanda ka kwaso suka biyo ka daƙiƙaine wawaye, kida humai kun zo ku saci, yaro, yaron ma wanda baku san ɗan waye ba, to ina taya ku farin cikin zaman gidan yari tare da horo mai tsanani, dan naga ku mahaukata ne, baku ma gane ko miye nake nufi ba, Muhseen bashi yaron shi! "



Mutumen ya ce, "amman wallahi kin sa'a kina da kyau kuma har yanzun ina son ki, kuma naji kin ce a bani yaro na, amman da kin gane waye kikeyi wa maga haka, kai bani ɗana" yana mai kallon Muhseen kamar yanda Humaira tayi. 



Dariya Muhseen ya yi ya ce, "Salman kazo yana neman ka". 


Aikuwa shima mutumen ya bushe da ƙatuwar dariya ya ce, "kunji sunan yaro na, wai Salman amman kin kyauta kin saka mashi suna mai daɗi". 



Wasu mutane ne wanda ban san lokacin da suka zoba, suka biyo bayan Salman yana ɗauke da Shuraim a kafaɗar sa, suna zuwa Salman yayi murmushi ya ce, "Shuraim duba ka gani su waye wannan mutanen? "




Ai kuwa Shuraim yana haɗa ido da wannan mutanen ya kwasa wani uban ihu wanda sai kowa ya rufe kunnen sa, da sauri Hindu ta janyo hannu na na ƙaraso a kusa da Salman na anshi Shuraim ɗin ina jijjiga shi dan yayi shuru, yana yayi shirun na sauke shi na riƙo hannun sa na ƙasa gurin na ce, "lallai yan zun nasan kowa ya fahim ci waye kai a wan can lokacin da naso su fahimci halin da nake ciki akan cewar ban san kaba, bani da wata  alaƙa dakai duka basu yarda dani ba, sai gashi sabo da satar yara ta zama sana ar ka, ka saka aje har gida a kashe mu A ɗauko maka yaron, Allah ne ya kare mu, ya nuna maka shine ya haliccemu, mu dakai ya kuɓutar damu, a hannun ka, muka bar garin mu mahaifar mu saboda kai, shine yan zun dan ɓatan basira kazo ƙarasa nufin ka, kuma baka ma san uwar da ta haifi yaron ba, mutane yan zun kowa ya shaida him lallai duniya! "



Zan ƙara magana Mariya ta ce, "to andai ji kunya duk wanda ya baka shawarar nan kwanyar kifi ne dashi, kaga wannan ba ita ce kake nema ba wannan ce kake nema, ga kuma yaron nan " 


Ta nuna Humaira dani da Shuraim, sannan tace dashi, "kazo kana wani zaƙewa da hura hanci kai ala dole aji tsoron ka, to ga uban yaron nan a gaban ka shine Salman ɗin da kaji a na faɗa, wawa kawai ". 



Salman kallon wannan mutanen yayi wanda suke bayan sa, "da sauri suka kewaye su, suka fito da bindigogin su, suka ɗora a kan yaran sa, dashi kansa aka nuna masu aid card, tare da faɗar kidnappers, your under arrest "



Dur ƙusawa ƙasa sukayi suka ɗora Hannuwan a ƙeyar su, sai kuka wasu sukeyi, dariya aka sanya masu, Salman ya ce, "mu haɗu daku a kotu, nine mijin Narjeesah kuma nine mahaifin Shuraim Salman Muhammad Yunus ke nan, jika a gurin Mai martaba Sarki Yunus, kuma ni loya ne mai zaman kan sa, wanda ƙasa take alfahiri dani, mahaifina kuma Muhammad Yunus ambassador ne, ina fatan ka fahimci ɗan waye kake son yin kidnapped ɗin sa, ku tafi dashi ". 



Magana mutumen yaso yi gurin bada hakuri amman babu wanda ya kula sa, hannu na Salman ya kama muka nufi cikin gidan haka su Humaira su Yaya Jafar suka tasa su a gaba sai cikin gida. 



Kowa dole ya watse mutane cike suke da mamakin a ina na haɗu da Salman gashi, koda ganin Shuraim an san ɗan sane, a cikin gidan kuwa muna shiga na nufi cikin ɗakin Inno nayi kwanciya ta, tsakiyar gidan sai firar haukar wannan mutanen sukeyi su Salman kuwa suka bar garin suka bar mu, tunda na samu labarin basa nan na fito akaci gaba da fira dani. 




Kwanan mu biyar muka shirya muka nufi gidan Kawun Umma, zo kuga yanda ake yin ina nakan a za daku, jin sukeyi kamar su goye Umma sai hakuri suke bata, har dare muka kai, sannan muka dawo gida. 



Yau tun da safe aka fara kawo mani tantabu masu romuwar magani, ai kuwa nace, Inno a gaskiya daga ganin wannan abun zaiyi ɗaci, nikam ba zan ci ba, haka kawai naje na ɓata baki na". 



Inno ta ce, "ci kuwa kamar anyi an gama ne, da alama kin soma man tawa da halina, ko? "



Jan kwanon nayi a gaba na, na soma ci ina zubda hawaye, su kuwa dariya sukayi Hindu ta ce, "kada ki ci ƙashi malama kuma kisha romuwar da yawa kinji matar Salman " ta kashe mani ido ɗaya. 


Harara na zabga mata, sai da na ƙoshi na fara yun ƙurin amai sannan aka ajiye sai zuwa anjima, tsimi Yaya  ta kawo ta tsare ni babu musu nasha dan nasan halin Yaya. 



Haka sukeyi mani kullum wata rana harda su Humaira a gurin ci, ko sha. 



Kwanan mu goma sha biyu a gidan mu, Mariya tayi muna zanen lalle ja, da baƙi, Hanan tayi muna kitso, gyaran jiki kam kullum sai anyi maganin mata sun ishe ni, da kayan fruit da su Yaya Auwal suke kawo wa ni abun harma tsoro nake ji gashi a jiki na tabbas naji chanji sosai. 



Turare humra kayan ƙamshi kuwa kawo wa akeyi yan uwa da abokan arziki, yau muna zaune a ɗakin Inno harda su Baba da su Yaya Auwal ana fira nake cewa, "Yaya Auwal dan Allah su Inno su tashi garin nan su koma gidan mu da yake a garin Yola inda muka fito wallahi babban gida ne kuma akwai ɗakuna da yawa, ko Amrah? "



Cike da farin ciki Amrah tace, "wallahi Yaya gidan zai ishi kowa dan kowa zai samu nasa ɗakin ". 



Hindu da Humaira da Auta suka ce "Allah da yafi kam dan zamu fi jin ɗadin ganin ku a tare da mu, dan kada abari zumunci mu ya lalace ". 



Shiru duk sukayi Umma ta ce, "Inno to ku yarda mana tunda gashi wannan gidan yan zun yayi kaɗan saboda yara sun fara zama a cikin gidan su". 



Yaya tace, "a gaskiya hakan ba zaiyuyu ba saboda gidan Shuraim ne da Nargeesah taya zamu yarda muje gidan yara mu zauna haba dai ku duba ku gani ". 



Da sauri nace, "Allah Baba ku yarda na mallaka maka gidan Yaya Auwal kuma na mallaka maka mota ɗaya a cikin motocin nawa, dan Allah kuyi hakuri ku yarda". 



Cike da mamaki suke kallo na, Amrah kuwa da Humaira da Mariya da Hanan rungume ni sukayi, suna dariya Anty Asma tace, dan Allah Baba ku anshi wannan kyautar da tayi maku Allah nikam naji daɗi sosai ". 



Yaya Auwal kuwa cike da mamaki yake kallon kowa a gurin wai kyautar mota kodai mafalki ne yakeyi?. 


Baban mu ya ce, zamu ansa mana Narjeesah amman sai kin anshi tayin mu bada tursa sawa ba, tukun". 



Da sauri nace, "Allah zan yarda da duk abunda kuka umarce ni, tunda har kune iyaye na kuma Inno da Yaya basu gujeni ba, har bayan rashin gatan da nayi da ƙaddarar da ta afka mani, lallai ni kam mai biyayya ce a gare ku". 



Jikin kowa sai da yayi sanyi amman Inno ta daure tace, "Narjeesah kiyi wa kiyiwa Shuraim gatan komawa gidan Salman ku riƙe yaron ku da kyau yanda zaiyi farin ciki mai ɗaurewa". 



Da sauri na ɗago ido ina kallon Inno da duk wanda yake cikin ɗakin naga duk idon su yana a kaina, duƙar da kaina nayi ƙasa da ket na buɗe baki na ce, "indai wannan shine burin ku na amin ta, wallahi Allah yasa hakan shine mafi alkhari! "



Amin duk suka amsa cike da farin ciki Yaya tace, "to yau she ne kike son mu koma gidan Narjeesah? "



Da sauri na ce "Yaya duk ranar da kuka shirya, zamu iya tafiya ". 


Cikin sanyin murya Mama tace, "nikam nasan bani da masauki a gidan saboda abun da na aikata maku, sai nace Allah ya kaiku lafiya Allah ya sanya alkhari ". 



Nidai ban ce komai ba Umma ta ce, "Larai ai duk abunda ya faru yari ga da ya wuce, miye amfanin dawo da abunda ya wuce baya, kin fi kowa sanin yanda muke da yanda malam ya koyar damu yafiya da maida komai ba komai ba, dan haka abar komai dan Allah a fuskanci gaba, kawai, anriga da an zama ɗaya, babu yanda za'ayi ". 



Kuka Mama ta fashe da shi ita da yaran ta, Anty Basira ce ta ce, "Umma mun gode da haƙurin ku haƙiƙa ke mace, ce, abun koyi a cikin duniyar nan muna godiya da halaccin ki a gare mu ". 



Inno ce tayi murna da wannan sabuwar rayuwar ta ce, "to Narjeesah muna godiya sosai zamu tashi wannan gidan mu barwa sauran yaran mu da sukayi Aure, ke kuma da mun koma zaki bi mijin ki, ku ɗauki ɗanku ku tafi dashi Allah yayi maki albarka ya huci zuciyar ki, ya ƙara maku haƙuri ya baku zuri'a ta gari mai albarka, mun gode sosai Narjeesah yar Albarka keda sauran yan uwan ki da abokan ku duk Allah ya albarkace ku da iyalin ku baki ɗaya ". 



Duk muka amsa da, "Amin " Baban mu kuwa farin ciki kawai yakeyi, su kawu da goggo kuwa, hawaye suke sharewa. 



Haka akaci gaba da fira, kullum cikin farin ciki muke shirye_shiryen tafiya akeyi mutane sai zuwa taya murna sukeyi Shuraim kuwa tun da safe idan yaci abinci akayi masa wanka bana sake saka shi a idona sai dare idan yayi bacci. 



Yau tun da safe Humaira take sanar damu su Salman suna a hanya, tun a lokacin nake jin wani irin, ganin idan fa yazo zan bar su Umma dasu Amrah da gani sai Shuraim, kawai naji kuka ya zo mani. 



Sun fahimci abunda nakeyi wa kuka dan haka suka shiga bani baki. 



Ƙarfe goma na safiya suka iso nasan kuwa a garin mu suka kwana, tare da motocin ɗaukar kaya suka zo, ai kuwa aka shiga fitar da kayan mota ake saka su, gidan gaba ki ɗaya muka fito motoci muka shiga, aka rufe gidan muka ɗauki hanya........ 




*Comment and share*




*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹



 💐💐 *NARJEESAH* 💐💐



*Rubutawa*

*NANA KHADEEJATU*

           *_UMMU IHSAN_*


*ELEGANT ONLINE WRITERS*


_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_


 🔚


5⃣6⃣⏭️6️⃣0️⃣

               

➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Alhamdulillah mun iso lafiya cikin amin in Allah, tun lokacin da muka ɗauki hanyar unguwar mu, su Mariya aka fara buɗe ido, suna kallon yanayin unguwar, bamu tsaya ko ina ba, sai bakin kofar gidan mu,  su Yaya Aliyu basu ma shiga cikin gidan ba, sukayi tafiyar su, mu kuwa fitowa mukayi, muka dum fari bakin get ɗin mu, na fara ƙoƙarin buɗe get ɗin, duk da ido suke bin mu cike da mamakin ganin irin wannan haɗaɗɗen gidan. 



Kasa hakuri Yaya tayi tace, "anya kuwa Narjeesah gidan ne kuwa? "



Murmushi na sakar mata, ban bata amsa ba, har na buɗe gidan Shuraim da gudu ya  riga kowa shiga, su Yaya Auwal suka ɗauki kayan suka mara masa baya, Umma kuwa ita ta yiwa su Inno jagora suka shiga cikin gidan kwasar kaya muka tsaya yi, na baiwa Auta makullin ƙofar falon, ai kuwa da sauri ta shiga ciki dan ta buɗe masu ƙofar, muka ɗauki kayan muka mara masu baya, a bakin kofar falon na ajiye masu na dawo na rufe get ɗin, na juya na shiga cikin falon. 



Koda na shiga duk sun baje a tsakiyar falon wasu a kujeru wasu a ƙasa, nida Amrah Nusaiba da Humaira da Hindu muka haye sama, ɗakin Umma muka shiga muka kwashe mata kayan ta, muka dawo dasu cikin ɗakina, muka shirya mata komai nawa kayan kuwa a akwati suka zuba su, da kayan Shuraim. 



Bayan mun ƙarasa ne, muka fito muka shirya wa Inno nata, ɗakin inda muka kwashe kayan Umma, a ɗakin kusa da Inno muka shirya wa Yaya nata, haka Mama ma mukayi mata, muka sauko Amrah ce ta sanar dasu, suje ta nunawa kowa nasa ɗakin, haka kuwa akayi Mariya a ɗakin su Amrah aka kai nata kayan, su  Zuwaira Shamsiyya nasu ɗakin daban. 



Su Yaya Auwal kuwa a ɗakin ƙasa suka zaɓa sai farin ciki suke yi Baban mu ma ɗakin sa yana sama yana daga gefen nasu Inno. 



Kai Alhamdulillah gidan kam sai sam barka kowa ka gani a cikin farin ciki yake, kamar wanda akayi wa albishir da kujerar makka. 



Bayan komai ya dai_dai tane, su Humaira suka tafi, gidan iyayen su, mu kuwa duk yam matan a kicin muka haɗu domin shirya abinci, saboda basu san takan komai ba hakan ya saka muka dage gurin koyar dasu, bayan mun kam mala ne, Zuwaira Basira da Shamsiyya suka ni a gaba suna ƙara neman yafiya a gare ni, nikam na ce dasu, "na riga da na yafewa kowa dan Allah abar tuna baya". 



Godiya sukayi mani, haka muka yini cikin farin ciki muka tashi cikin farin ciki, su Mommyn su Humaira da Hindu da Haleema, duk sun zo tare da yaran su, sosai suka nuna farin cikin su da jin daɗin su, akan dawowar familyn mu guri ɗaya. 



Bayan kwana biyu, muna zaune anata fira, nace, Yaya Auwal gafa motoci nan guda biyu a harabar gidan nan muje ka zaɓi wadda kake so, ɗayar kuma su Yaya sai ku san yanda zakuyi da ita, dan nikam na mallaka maku ita halak malak amman Yaya Auwal shi ɗaya yake da wadda ya zaɓa"



Cike da farin ciki muka doshi harabar gidan ai kuwa Anty Asma da Anty Basira suka zaɓar masa, shi kuwa kukan farin ciki yakeyi musam man lokacin da na bashi makullin motar su kuma na basu makullin ɗayar. 



Yau ne a tarihin rayuwa ta naji Mama ta kama hannu na, ta rungume ni, tana zubar da hawaye tana faɗar, "haƙiƙa ɗan hakin da ka raina shine yake tsone maka ido, haƙiƙa ko wane ɗan adam Allah ya rubuta masa arzikin sa, a haƙiƙa zafin nema baya kawo samu, tabbas hassada gamai rabo taki ce, na yarda da wannan Narjeesah tun daga lokacin da Allah ya nuna mani, cewar bani da dubara kuma babu wanda yake tserewa ƙaddarar sa, kuma yan zun na ƙara yadda da cewar, mutum yana tare da arzikin sa, Narjeesah gashi Allah ya nuna mani da ido na, cewar ke ɗin dai da nake fatan naga kin dauwa ma a cikin baƙin ciki, sai gashi Allah ya nuna mani, ke baiwar sace, shine mai tsara komai akan bayin sa, gashi dai a ƙarƙashin ki yau muka dawo, ina riƙon Allah da ya yafe mani, 





kuma kema ki yafe ni, kada kiga laifin yan uwan ki na rashin sonki nace na ɓata ki a gurin su, ada ina dariyar kinyo cikin shege duk da na fahimci kin ɓiye wa kowa gaskiya ne, kuma ni kaina na fahimci cewar cikin jikin ki, ba shege bane, tun lokacin da na fara shegan ta cikin na fahimci hakan amman a lokacin bana sonki da farin ciki shiyasa nayi ta, zagin ki ina saka kowa ya kyace, ki, Narjeesah tabbas duk wanda yace tukunyar wani ba zata tafasa ba, to shi tashi tukunyar ko zafi ba zatayi ba, kuma tabbas na yarda da cewar mai ɗa goye baya cewa ɗan wani shege dan bai sani ba ko ya haifa, sai gashi ina zagin ki ashe nima a cikin ɗaki na, akwai shegu har huɗu, dan Allah kiya feni wallahi haƙin kine yake bibiyar rayuwar mu... 



Kuka mai cin rai Mama ta fashe dashi tana mai dur ƙusawa a ƙasa saman kafafuwan ta, da sauri na ɗago ta, nace, "Mama na daɗe da yafe maki Allah ya yafe muna baki ɗaya ". 


Riƙa ta nayi muka dawo cikin gidan a gurin Umma taje neman yafiya kuma Umma tun kafin tayi maga ta ce, ta yafe, haka su Inno duk sun yafe kowa ya yafi kowa, sai zaman lafiya akeyi, da godiya  a gurin na, sai da na fara jin haushin hakan har ina ɓuya, sai da suka nemo ni. 



Satin mu biyu da dawowa aka sake gyara mani jiki tare da kitso da lalle, kullum cikin nasiha su Inno Mama da YAya sukeyi mani, mai shiga ciki, tattalin miji tsabar ƙirsa iri daban_daban wani lokacin har kunya suke bani, gyaran jiki kam ciki da waje, komai zam_zam sai sam barka. 



Yau muna zaune Yaya ta bani zuma ina sha mukaji tsayuwar motoci, Shuraim kuwa da gudu ya sauka jikin Inno yayi waje yana kiran "Daddy Daddy " 



Duk mun ɗauka shirmen sa ne, kawai naji muryar Salma tana faɗar, "Antyn mu Narjeesh nayi fushi gaskiya" 


A da sauri na tashi na tar yota muka baje a falo suka shiga gaisawa da mutanen gidan, na ce, "Inno Gaggon Shuraim ce, kan war Daddyn Shuraim ce, fa". 



A da sauri su Shamsiyya dasu Mariya suka zazzauna a kusa da ita sai gaisuwa akeyi, Amrah ta kawo mata abun taɓawa, fira kawai mukeyi, Daddyn Shuraim ne ya shigo ɗauke da Shuraim suna dariya Muhseen yana biye dasu, su Mom ne suka shigo harda Dad, da sauri muka tarbe su, suka zazzauna suka shiga gaisawa dasu Inno, Baban mu ne, ya fito cikin farin ciki, suka gaisa dasu Dad, Umma kam ana gama gai sawa ta bar gurin, sai su Inno ne a gurin, Mom tace, "to mufa yau mun zo tafiya ne da 'yata da jikan mu da fatan zaku yarda da ƙoƙon barar mu". 



Dariya aka shiga yi, nikam jinin jiki na, nasha, Dad ya ci gaba da faɗar, "kuyi haƙuri da abunda ya faru gashi dai suna da Aure amman ba'ayi biki ba, duk da mukam a can london mun sha bikin mu babu ango babu Amarya, gashi kuma shima Shuraim ba ayi hidimar bikin haihuwar sa, ba, amman idan ranar cikin shekara biyar ya zo da haihuwar zamuyi masa bikin sa, dafatan zaku duba yanda abun ya kasan ce, ku daure ku bamu, wannan kyakykyawan irin naku mai albarka,  dan ci gaba da samun yaɗo". 



Dariyar manya su Baban mu sukayi, Baban ya ce, "to Alhamdulillah Narjeesah dai ta kuce daman iyayen ta, sun gama shiri, suna jira ne kawai daga gareku, kuma tun da Allah ya kawo ku, sai muce, Allah ya dai daita hankalin su, ya bada zuri'a mai albarka ". 



Da amin aka amsa, Yaya tace, "to Salman Narjeesah abunda nake so daku shine, dan Allah ku zauna ku fuskan ci matsalar ku, kada ku yarda ko da Shuraim ne, ya gane cewar bakwa shiri a tsaka nin ku, ku zauna lafiya ku iyaye ne, kuma yan zun kun fara girma tunda Allah ya mallaka maku Shuraim, tarbiyar sa idan ta gyaru daga gare ku ne, idan kuma aka samu akasin hakan, Allah ma ya kyauta duk akan ku haƙƙin yake, dan Allah ku zauna lafiya Allah ya zaunar daku lafiya ya baku zuri'a mai albarka ". 



"Amin" aka amsa sosai akayi muna nasiha mai shiga jiki, aka ce, naje nayi sallama da Umma su Amrah su kwashi kayan mu, su fito dasu waje. 


Haka naje gurin Umma ina kuka nake neman yafiyar ta, ta janyo hannu na, ta zaunar dani a jikin ta, atake naji wani irin farin ciki ya mamaye ni, ta ce, "bani da matsala da irin tarbiyar da kike dashi, kuma nasan bayanin da zanyi maki su Inno sunyi maki fatana kawai shi, kiyi hakuri ki rungumi mijin ki da ɗanki, kada aji kanku, ina son naji kyakykyawan albshir nan da wasu watan ni daga gareki idan kikayi mani wannan saka makon to ki sanya a ranki, har ƙarshe rayuwa ta, ina cikin farin cikin da kika saka ni a cikin sa, kije Allah ya albarkacin ki da zuri,ar ki baki ɗaya ". 



Amin na ce, na ƙara run gume Umma yau nice Umma take baiwa umarni  tare da sanar dani burin ta,? A take na saka a raina Insha Allah, Umma zata dauwa ma da farin ciki, indai daga gare ni ne. 



Tashi mukayi ta rako ni har gurin su Inno, ai kuwa duk kowa ya tashi tsaye suna dariyar farin ciki, da yabon wannan ranar wanda Baban mu da kasan ya ɗaga hannun sa a sama yana mai nuna godiyar sa a gurin Allah da ya nuna masa wannan ranar, ai kuwa kowa cike da farin ciki yake, hannu na da hannun Salman ta haɗa tayi muna addu'a sannan ta ce, "ku tafi Allah ya kare gaban ku da bayan ku ta kare idon maƙiya a kanku ya albarkacin zuri,ar ku baki ɗaya ". 



Haka kowa yake amsawa da Amin cikin tarin farin ciki. 



Har a gurin motoci suka rako mu ina zubar da hawaye muna shiga cikin motar, Inno ta rufe aka tayar da motar muka ɗauki hanya, Shuraim sai farin ciki yakeyi idan ya dubeni ya dubi Daddyn sa, sai yayi dariya"



Tafiya mukayi sosai babu mai magana a cikin mu, sai airport abun mamaki jirgin tafiya london kawai muka shiga, muna sauka motoci ne irin na alfarma suka ɗauke mu, nikam cike da al'ajab nake ƙarewa ko ina kallo a wayan ce, bamu tsaya ko ina ba sai  a wata haɗɗiyar unguwa, kai Alhamdulillah a gaskiya kam london tayi ba ƙarya, nikam tun ina sa ran akawo, har bacci ya ɗauke ni, kawai can a cikin barci na, naji kamar ina a jikin mutum ai da sauri na buɗe ido na. 



Ai kuwa na zaro ido waje da sauri na ce, "dan Allah ka ajiye ni, baka ganin mutane a gurin kuma gashi a tare muke dasu Mom? "



Dariya ya sakar mani ya ƙara shigar dani jikin sa, ya ce, "oh ashe dai ba tare nake da kurma ba, ai na ɗauka ke kurma ce, malama, kuma su Mom kam sun nufi nasu gidan mu ma, yan zun mun kusa isa namu gidan Shuraim yana gurin su, kuma nan ƙasar ba wani abu bane dan miji ya ɗauki madam ɗin sa, babu ruwan wani da wani, dan haka ba zan sauke ki ba, ke wai ma anya kuwa kina cin abinci kuwa"!?. 



Nasan ba zai sauke ni ba, dan haka na saƙalo hannu na a wuyan sa, na maƙala, na ce, "aa bana cin abinci kullum sai an rufe ni a ɗaki ake cin abinci "



Ya ce, "haba dai nikam na sani, amman malam maka am, na ɗauki babbar mace amman har Shuraim ya fita nauyi? "


Da sauri na ce, "ai da gaske?  "



Ya ce, "anya ma kuwa zakiyi kukan amarci kuwa? Nifa naga idon ki a tsai tsaye sai rainin dake tsakanin mu, anya kuwa ba, tun yau zamu fara amarci ba? ". 



Rufe ido na nayi, shi kuwa ya samu gurin tsokana ta, har muka iso bakin get ɗin gidan da zamu shiga sai bashi girma mutane keyi, manya da yara, sunayi masa barka da zuwa, yam mata da samari ma, barka sukeyi masa, tare dani, ina jin su nayi kamar bacci nake yi har muka wuce gurin mutane muka iso bakin nasa gidan, aka buɗe muna ƙaton get ɗin muka shiga cikin harabar gidan, sai a matakalar da zamu taka na ƙarshe ya ajiye ni ya buɗe gidan muka shiga ina daga bayan sa, ya kunna glub a take gidan ya haske ko ina, kwashe kyallayen da aka rufe kujerun mukayi, nikam kwanciya ta nayi, ina kallon sa ya gama kwashe komai shima ya zauna a kujerar da nake kwance, a kusa dani. 



Shiru mukayi zuwa can mu ɗan futa na tashi na ce, "mu fara gyara gidan sai muyi wanka muyi sallah mu nemi abincin da zamuci ko? ". 



Dariya ya yi yace, "nima hakan naga zai fi". 



Ai kuwa a take muka hau gyaran gidan har ɗaku nan na ƙasa da sama, da kichin da bayi duk sai da muka tsab tace komai, san nan, na haɗa masa ruwan wanka ya shiga ni kuma na dawo falon na kunna kalli sai da ya fito ya saka kayan shan iska, nima na shiga nayo wankan na fito ke nan, naga ya a jiye mani kayan da zan saka na shan iska ina ɗaukar rigar da guntun wandon, na ajiye na ce, "kam lallai ma, taya zan iya saka wannan yan iskan kayan na fito falo, na zauna?  Ni kam ba zan iya ba, haba kamar wata yar iska dai! ? ". 




Hijab na saka, gashi towel ɗin ƙarami ne, baya rufe mani cinya ta, ai kuwa na soma faɗar "Daddyn Shuraim! Daddy Shuraim..! Kazo Allah ni ba zan yarda ba, haka kawai a ce, na rasa kayan da zan saka sai wannan kayan haba ɗan Allah, kuma kace naje na zauna kamar wata marar kunya? "



Ido rufe nake ta masifa, shi kuwa ya shiga cikin ɗakin ya harɗe hannayen sa, yana bina da ido, ganin ba zan dai na masifar bane, kuma ba zan buɗe idon bane, ya saka shi yin wani makirin murmushi, ya matso dab dani, ya fisgen hijab ɗin, ya riƙe a hannun sa, ya zuba mani ido kallona ya keyi tun daga sama har ƙasa, ko ƙyafta ido ba yayi. 



Ni kuwa mutuwar tsaye nayi, cikin fir gici na, buɗe ido na zaro su waje, ganin abunda ban shirya ba, a kuwa da gudu na juya zan faɗa toilet na rufe kawai, taku biyu yayi ta tare ƙofar shiga bayin na faɗa jikin sa, ai ban san lokacin da na kwatsa masa wank uban ihu ba, sai da ya rufe mani baki da hannun sa. 



Ya ce, "wallahi idan baki saka wannan kayan ba, yau sai dai ki zauna da wannan towel ɗin kuma ba zaki saka wannan hijab ɗin ba, ke nama fasa kada ki saka wasu kayan kiyi zaman ki a hakan kin fi ma burge ni, wallahi ". 



Ai tun da naji yayi rantsuwa kuma dai naga ya ɗaure fuska kawai, na ce, "dan Allah Daddyn Shuraim kayi hakuri Allah zan saka kaga bama zanyi sallar ba, kaje kayi sallar kawai ni na yarda in dan wannan kayan ne Allah ". 



Dariya ya yi, ya ce, wato dai aboki na ne ya zo, ashe dai nan da wata tara zaki sake haifo mani yan biyu, ko ƙuratul aini? ". 



Jin nakeyi kamar na nutse saboda tsabar kunya amman Daddyn Shuraim ya sauya mani lokacin ƙan ƙani, kwata_kwata, ya ajiye kunya a gefe, sai zuba mani fitsara yakeyi. 



Kuka na fara harda hawaye, ya ce, "ashe ko dai zan cire wannan towel ɗin yan zun sai naga yan da ake kukan shagwaɓa". 



Ai haɗiye kukan nayi, na ce, "nifa kukan yunwa ne nakeyi ba wani kukan ba". 



Dariya yayi yace, "haba dai ƙurratul aini, ai nasan halin basajar ki, yan zun jeki ki saka kayan bara na kawo maki pad da fant, na tausaya wa yar yarinyar nan, kai na gode wa Allah fa, na Auri yar shekara sha shidda gani da ɗa kusan shekara biyar kuma ita matar yan zun zata cika shekara ishirin kai nikam ɗan baiwa ne, yan zun take zama cikak kiyar mace, wayo Allah na....!, kai ƙurciya zallar ta ". 



Rasa bakin magana nayi, daman tsokana ta ce, yakeyi kuma tsokanar ta samu shiga, dan hawaye naci gaba dayi". 



Da dariya ya mai dani gefe, ya je ya ɗauko kayan ya bani ya fita yana dariyar keta gashi da hijab ɗin ya fita, hawayen na shiga sharewa, shigo wa ya sake yi ya bani leda ya fita yana, lasar baki yana shafa sajen sa, da harara na bisa har yaja ƙofar. 



Haka na shiga na shirya, na saka kayan rigar mai haɗe, da gidan  bra, kuma hannun bra ne da ita, iyaka cibiya, ta tsaya, sai wandon iya karsa, cinya, kasa fito wa nayi, nayi zama na a cikin bayin gajiya yayi da jira na, yazo ya buɗe bayin ya shigo yaja hannu na muka fito waje bai bari muka haɗa ido dashi ba, muka dawo cikin falon ya zauna akan kujerar ya zaunar dani akan ƙafafuwan sa, ya janyo abincin da yayi order aka kawo masa, ya buɗe ya soma bani, a baki, ganin bai ma damu yanda nake shigewa cikin jiki na ba saboda kunya, sai da ya tabbar da na ƙoshi ya bani ruwa, sannan ya soma ci, har ya ƙoshi. 



Ya ce, "to ki tashi kije ki shirya sai ki dawo muyi fira kuma idan baki dawo ba, da kaina zan je kin dai san sauran ". ya kanne ido ɗaya. 



Tashi nayi jiki babu lakka na nufi cikin ɗakin, naje nayi sha, fa mai na fesa turare da humra nayi, sai yar powder da jan baki, na tashi gashi ina jin kunyar sa, haka na fito na samesa yana kallon labarai, naje na zauna a kusa dashi yasa hannun sa, ya dawo dani sosai a jikin sa, mukaci gaba, da kallon a tare, har naji bacci, a jikin sa na kwata ya gyara mani kwanciya, a take nayi bacci. 



Shi kuwa koda ya gama kallon ya kashe kayan kallon, ya ɗauke ni, ya kaini, ɗaki ya kwantad dani shima ya shiya ya kwanta yayi muna addu'a, nikam saboda tsabar gajiya bacci sosai nasha, sai a suba na falka, ina buɗe ido kawai na tsinci kaina, kwance a jikin mutum da sauri na yuƙura zan gudu ya janyo ni nadawo ya ce, "gudun na miye madam?  Bayan duk kin bi kun shure ni da ƙafafuwan ki, kin zubo mani yayun bacci "



Nikam ban san lokacin da na ce, "wallahi ban yarda ba, ina da ja ni bani da nauyin bacci kuma bana saleɓa, kai sai dai idan kaine kake yi, ni rabu dani, naje na gyara jiki na, malam, haka kawai kazo kana yi mani cin kashin kaji? ". 



Dariya ya yi, daman burin sa ke nan yaga ina masifa, kuma iyakar gaskiya ta na keyi, tashi nayi nace, "ka bani kayan da zan sauya ni kam, wallahi ko kuma ka nuna mani inda suke kaji? ". 



Ya ce, "aa malama zo ki doke ni, ki ɗauki kayan kin ji...?  Matar Salman?  Uwar ya'yan Salman yar yarinyar Salman, mai ƙuruciya, shagwaɓaɓbiya t.... Maman Shuraim ƙurratul aini, nikam yau dai da kai na zan yo maki wankan nan fa bari na tashi dai na cire maki wannan kayan ". 



Ai at 3√6o na faɗa jikin sa, na rufe ido na shige jikin sa, sai dariya yakeyi, ganin ya samu abunda ya keso naji, kunya, sannan ya ce, "ni tashi mani a jiki kada ki karya ni, kin ga kayan ki can a wan can seat ɗorowar, kuma sau ran kan yan suna a ɗaya dorowar, maza jeki ki fito kizo muyi baccin safe". 



Kayan naje na ɗauka, na ce, "halan kayi sallar ne da zaka sake yin baccin? ". 



Ya ce, "kina can kwance kiji fata mai laushi a baki sanin na tashi ko ban tashi ba, amman zan rama nikam dan ba zan yarda ba ". 



Kyalesa nayi na shiga ciki bayin nayo wanka, da brush na shirya na fito, koda na fito yayi bacci, nadawo na kwanta a gefen sa, na kwanta sai bacci. 



Sai sha biyu muka fito muka nemi abunda zamuci, bayan mun ci, muka fito muka nufi falo, ya ce, "muje ki sauya kayan nan mu fita ki gano gari". 



Cike fa farin ciki muka dawo cikin ɗakin ya ɗauko mani sweater da dogon wando, da gyale nayi rolling ɗin gyalen, shima irin shigar mu ɗaya, har ta kalmi,  muka fito, hannu na a cikin nasa hannun, muka fita yawon shaƙatawa, kai nikam sai dai na ce Alhamdulillah. 



Birnin london kam mun zaga shi sosai nida Salman tattali da soyayya da kulawa duk ina samu, a gurin Salman, ga tsokana kamar miye?  Wata rana har sai taga ina kuka yake dawowa yayi lallashi, babu abunda na nema ba rasa a gurin Salman, gidan su Mom munje ya kai sau nawa, a gurin su ma nida Shuraim gata suke nuna muna, har gurin dan gin Mom ya kaimu, a masarautar su Mom kuwa kwana biyu ne kawai muke tsallakewa. 




Zaune muke nida Daddyn Shuraim ina sha masa ƙamshi shi kuma sai famar dariya yakeyi, ya ce, "ke kuwa wannan haɗe ran fa ba zai hana anjima na sake yi maki wani wa'azin ba, keda naga harda su kabbara kikeyi mani, saboda tsabar ɗaukar wa'azi, ai my love, kin iya bada hankali gurin ɗaukar wa'azin Mr Salman Daddyn su Shuraim da 'yan uwan sa ". 




Filo na jefa masa ya ci, gaba da dariya, yana tsokana ta, na ce, "yau ma nawa ga wata ne? "


Ya ce, "oh zaki fara lissafin cikin wata nawa ne? Yau dai kwana ɗay... "


Da sauri na haye saman jikin sa, muka shiga ko kawa, dashi ina son rufe masa, baki, shi kuma yana son ƙasawa, sai da muka gaji muka baje a gurin. 



Haka dai rayuwar mu, taci gaba tafiya cikin kulawa, da tattali da ƙaunar juna muna kiyaye duk wani abun da zai bamu matsala a zaman mu dashi, cikin ikon Allah watan mu biyar a ƙasar, wata ranar labara na tashi da ciwon ciki mai tsanani, a ruɗe ya ɗauke ni, ya kaini asibiti gwajin farko, aka sami kyakykyawan result, Allah ya bamu ƙaruwar cikin wata, ukku, da sati biyu, murna a gurin mu ba a faɗa, su Mom ya kira ya sanar dasu, ai kuwa koda muka dawo gida a nan muka same su harda Muhseen Mom Dad Shuraim, 



dan Salma ta daɗe da komawa Nigeria, sai tambaya ta sukeyi miye zan ci, ko miye nake so, kuma sun ce, kada ya yarda ya cika matsa mani da takura mani, duk abunda nake so, yayi mani ko a kira su a sanar dasu Shuraim kuma ya ce, ba zai koma ba, a nan zai zauna ai kuwa korar sa, Salman ya yi, wai kada ya takura mani ya riƙa saka ni yawan magana, nikam dariya suke bani, kuma da yaga Shuraim yayi fushi sai ya fasa barin a tafi dashi, dole aka bar sa, daman sun san ba zai bari a tafi dashi ba, dan mun sha zuwa ɗauko ana hana mu. 




Haka dai akaci gaba da tarairayya, ta, har Allah yasa cikin ya kai watan haihuwar sa, har kwakin haihuwar da aka bamu ya wuce, zama daket tashi da ket, Shuraim wata rana har kuka yakeyi, idan yaga ina son tashi tsaye na kasa, Salman kuma jin yakeyi kamar cikin ya dawo a jikin sa, wata rana shi da kansa yake ɗauka ta ya tayar dani tsaye mu fara tafiya saboda motsa jiki. 



Yau kam tun da na tashi nake jin ba dai dai ba, ciwo_ciwo sama_sama, tun ina jin kamar da wasa har na kasa hakuri, nace, "Shuraim kira wo mani Daddyn ka, wash...! "



 

Ai da gudu suka iso baiyi wata_wata ba,  yazo ya ɗauke ni, Shuraim ya buɗe muna motar muka shiga, sai asibiti ai da sauri muka ƙarasa, yana yin parking, ya fito ya ɗauko ni, abu da ƙasar waje kawai sai ga ma'aikatan asibitin sun zo da gadon ɗaukar masu ciki, suka bar su a nan baya aka shiga dani, aka hana su shiga sai go and come sukeyi tare da addu'a Shuraim kuka kawai yakeyi. 



Cikin ikon Allah ko a awa ba'ayi ba Allah ya sauke ni lafiya, aka sami yan biyu namiji da mace ai kuwa zo kuga irin yanda su Salman suke tsalle da hamdala, ɗakin da aka kaini futu suka shiga, idon su, a kaina, sai da suka tabbar da lafiya ta lau sannan suka ɗauki yaran sai dariya sukeyi, sai alokacin ya kira Mom yake sanar da ita, ya kira Dad da Muhseen da Salma sai ya kira Yaya Auwal dasu Jafar, kai Salman kusan sai nace, zaucewa yaso yi sai da na anshe wayar dan photo yake ɗaukar yaran iri daban_daban yana posting ɗin sa. 




Mom na zuwa ita dasu Dad kowa guri na ya fara zuwa sai da sukaji lafiya ta, sannan suka ɗauki yaran wanda Muhseen da Shuraim suka kan kane gurin sun hana kowa ɗauka, Mom ce ta anshe yaran ta kore su, awar mu shidda aka bamu sallama bayan a duba lafiya ta da lafiyar yaran,  muka dawo gida ai kuwa sai shirye_shiryen zuwa gida Nigeria akeyi wanda Mai martaba ya bada umarni, sake shirya wa mukayi, dan Muhseen ya tafi da Shuraim airport mune kawai ake jira, haka muka fito cikin farin ciki muka nufi airport ɗin, bamu wani jima ba jirgin mu ya ɗaga sai Nigeria. 



Da misalin ƙarfe biyu na dare muka iso, ai kuwa motocin Mai martaba ne suka ɗauke mu sai fada, muna isa bakin kofar faɗar kamar rana haka muka sami gurin cike da mutane, fulani ce da kanta ta janyo hannu na, muka shiga cikin gidan wani ɗakin ta nufa dani, muna shiga tace, "ki kwanta kiyi bacci ki futa har zuwa da safe kinji jika ta? ". 



Murmushi na sakar mata tare da gyaɗa mata kai na, ta juya ta fita ni kuma baccin gajiya ne ya ɗauke ni akan wannan gadon na alfarma, ban falka ba, sai gurin ƙarfe takwas na safiya, ina falkawa sai a idon fulani ai kuwa da kanta ta kaini bayi, tayo mani wankan da ba zan taɓa manta irin saba, a rayuwa ta, muna fitowa ta shirya ni da kanta, aka kawo yaran duk an gyara su, sai uban ƙamshi suke zuba wa, harda Shuraim a biye dasu, shayar dasu nayi, aka fara jero mani abun kari nama rasa wane zan ci wane zan bari, Mom ce ta shigo cikin ɗakin da kanta ta soma ciyar dani har sai da na ƙoshi. 



Anan ne Fulani da Mom suke sanar dani cewar, Mai martaba ya ce, zamu zauna ne a fara yin walima sannan mu tafi gurin su Umma na, dan za'a haɗa ne da bikin naɗin sabon sarki. 



Na ce, "babu damuwa duk yan da kuka tsara mu masu biyayya ne". 



Ai kuwa sun ji ɗaɗin wannan maganar tawa, har sai da suka nuna farin cikin su. 




Tun daga wannan ranar fulani da Mom sune suke kulawa dani har zuwa yau da mukayi kwana shidda kuma yau ne walimar, walima ce, wadda ta tara manyan malamai sarakai masu mulki da masu muƙamai talakawa da masu kuɗi, samari da yam mata, yara da manya, tsoho da tsohuwa, su Salma da su Humaira dasu Amrah tun daga lokacin da suka zo jiya basu futa ba, sai kai komo suke yi, anyi walimar lafiya an watse lafiya. 



Sai shirye_shiryen zuwa gida kawai mukeyi, muna gamawa, aka ɗauke mu cikin motoci na alfarma muka nufi garin Yola domin ƙarasa wannan gagarumin bikin, cike da ɗoki nake son na buɗe ido na, naga irin farin cikin da Umma na zata nuna mani da na cika mata burin ta, su Hindu da Salma sai tsokana ta, sukeyi, ina share su. 



Saboda tafiyar Asubanci ce mukayi kuma bamu tsaya ko ina ba, zuwa ƙarfe goma muka iso, ƙofar gidan mu, muna sauka da sauri nabar yaran hannun su Amrah nayi cikin gidan da gudu ina kiran Umma..!  Inno...! Yaya....!  Gani nazo na ganku". 



Dariya suka sakar mani cike da farin ciki, Mama ta rungume ni, ta ce, tunda ni badani ba, a cikin mutanen da kike kira ni na fara tarbon ki. 



Da sauri na rufe ido alamar naji kunya nace, "Afuwan Mama duk cikin mararin ganin kune". 



Inno ce, tace, "munyi farin ciki da ganin ki, amman ki daina gudu ba kyau". 



Dariya nayi na faɗa jikin Inno, haka su Amrah suka same mu, Yaya ma rungume ni tayi, yan gidan kuwa, gurin ɗaukar yaran suka nufa idan wannan ya ɗauka sai wannan ya ɗauka, nikam hayewa sama nayi, na nufi cikin ɗakin Umma, ai kuwa tare da mutane na sameta, suna jin sallama ta, duk suka taryeni tare da yi mani barka, duk suka fita, aka barni nida Umma sai Mama Luba, jikin Umma na faɗa ina dariya ta fara shafa mani kaina, tana murmushi, Baban da ya shigo cikin ɗakin ya ce, "wa nake gani kamar Narjeesah na? ". 



Ai da sauri nayi kansa na faɗa jikin sa ina dariya sosai mukayi farin ciki a cikin ɗakin Mama Luba ce, ta ce, "Narjeesah Ashe ansami ƙaruwa Allah ya raya, am sai kuma gashi kin sameni a cikin gidan ku, dan Allah ki yafe ni laifin da nayi maku na cin mutumci ta korar wula'kanci sai gashi kuna barin garin komai nawa ya lalace hayar ma dana ke biya na kasa biya, ke daga ƙarshe ma na rasa komai nawa sai bara nadawo ina yi a rin wannan rayuwar ne, Allah ya kawo mani Umman ku, ita ce ta zo dani har ta bani kuɗin ɗaukar wani gidan hayar, tare da kuɗin siyen kayan ɗaki da sutura, haƙiƙa gaskiyar magana na yarda hassada ga mai rabo taki ce, ku yafe ni ". 



Murmushi nayi, na ce, "nikam na yafe maki bana iya riƙe kowa a zuciya ta, Allah ya yafemuna baki ɗaya ". 


Kowa ya ce, "Amin". 


Cikin falon muka dawo Baban mu kuma ya fita, muka soma fira da su Amrah har nake tambayar ta sauye_sauyen da nagani, ta ce, "duk aikin Yaya Salman ne, dan dashi da Shuraim duk ƙarshen wata, suna zuwa su kwana biyu, shine ya baiwa Umma dasu Inno jarin miliyan biyu_biyu, su Yayan mu kuwa, aiki ya nema masu, mukam dubu ɗari biyar_biyar ya baiwa mata mu dogora da kan mu, yara dubu hamsin_hamsin, 




Sai kuma provision ɗin da buɗawa Baban mu, sannan ya baiwa duk su Yaya mota, harda Baban mu ai kin ga gidan cike da motoci, sannan wan can gidan na gumel ya gyara masu shi, harda su get, su Yaya suna ajiye motocin da ya basu ke harda moƙota duk sun sheda, dasu kawu, wai duk kina nufin cewar baki da labari? "



Kallon ta nayi cike da mamaki nace, "ke ni wallahi duk ƙarshen wata suna yin tafiyar kwana ukku ko huɗu amman ban taɓa sanin nan suke zuwa ba, saboda ya ce, dani wani aikin ne suke zuwa yi, wata ƙasar ". 



Amrah tace, "shi yasa nake ƙara godewa Allah da ya sanya kika zamo alkhari haka Shuraim zuwan sa, a rayuwar mu alkhari ne, wannan maganar haka kowa yake faɗar ta, harda wanda suka jahilci abun a can baya ". 



Haka dai mukayi ta fira, su Mommyn Humaira duk suna gidan harda moƙota, gidan ya cika sosai biki akeyi sosai ƙaton sa aka yanka da rago huɗu, wai harda na bikin Shuraim za'a haɗa, mukam dariya mukeyi, matan su yayan mu duk suna nan harda Mrs Yaseer a cikin yan bikin, kayan barka kuwa kamar wani company, kai komai cikin nasara akayi sa, yara sun ci sunan Mai martaba muna kiran su, da Sultan da Sultana, kwana biyu mukayi ana bikin saboda naɗin sarautar Daddy wanda Salman yayi masa wayo ya amsa. 



Taro ya watse lafiya inda muna zaune dasu Humaira wata ce, ta shigo tace, tana son ganin mu shine, su Mariya suka kawo ta gurin mu, kallon ta, mukeyi a take duk muka tashi tsaye nida Hindu da Humaira, Hindu ta nuna ta, ta ce, Haleema ke ce, daman kina nan!? "



Ta ce, "ina nan ku zauna daman nasan zan sameku a tare". 



Zama mukayi muna kallon ta, duk tayi baƙi ta fita hayyacin ta, Haleema yar gayu ta dawo wata bakar tsohowa dan daga gani tasha baƙar wahala a rayuwar ta. 



Ta ce, "nabi ruɗin zuciya ta, na Auri wanda zuciya ta, take mararin sa na bar tsohon zaɓina, zaɓin iyaye na, nayi Aure batare da yardar suba, bada sanin suba, ga yaudar Jafar da nayi, duk haƙƙin sune ya hanani sukuni, munyi zaman soyayya nida zaɓi na, sai gashi watan mu biyu, mun fara samun matsala inda yake bani maganin hana ɗaukar ciki tun ina sha cikin farin ciki har na ƙosa dashi na daina sha, kwatsom ciki ya shige ni, nayi ciwo mukaje asibiti kwajin farki aka tabbar muna da ina ɗauke da cikin wata, biyu, tun daga cikin asibiti ya ɗaure fuska yace, a zubar dashi a take nasha jinin jikina, na fara cewa ba za'a zubar dashi ba, 




Tun  a asibitin ya soma duka na, har muka dawo gida da belt yake duka na, yana taka cikin ai kuwa yayi sa'ar zubar dashi tun daga wannan lokacin ya dawo kulawa dani, saboda son da nakeyi masa, bana jin haushin sa, kwatsam na sake samun wani cikin, shima ya ce, a zubar a wannan lokacin kam na hana, har dukan da yayi mani cikin bai zube ba, sai ya riƙa zuba mani magani a cikin abinci da abun sha ba tare da sani na ba, 




Aikuwa gurin zubewar cikin na kusa rasa raina, asibiti sun so ƙin yi mani aiki, da ket suka anshe ni, tun daga wannan lokacin muka dawo kamar wasu maƙiya a take ya tsiro mani da asalin halin sa, na rashin kulawa da kawo yan matan sa, a cikin gidan, idan nayi magana sai duka, kai da abun ya dameni, sai na fara tunanin, cewar ko dan anyi wannan Auren ne bada albarkar iyaye ba ne, shin ya kawo wannan rashin jituwar, ke wata rana ina ina aikin tunanin makomar rayuwa ta shine ya shigo tare da worgo mani takardar saki, inda na shiga kaduwa, tare da tarin nadamar wannan Auren da nayi, yan zun haka yau zan koma a gaban iyayena,




 Bayan  na zauna a gidan wata ƙawata, na cika iddah, shine yan zun nace, bari na zo na sameku tunda na sami labarin anyi bikin haihuwar da Nargeesah tayi, shekaran jiya, shine nasan zan sameku a tare, dan Allah Humaira kiyi hakuri ki dawo mani da Jafar nasan da sanin cewar kin Aure sane saboda ni na guje sa badan kuna shiri da juna ba, wallahi nayi maki alkawarin zan kula dashi, kuma zan anshi yaron da kika haifa zan riƙesa tamkar yaron da zan haifa da ciki na!". 




Ta fashe da kuka nukam kallon ta kawai mukeyi, zuwa can na ce, "to nidai ban san miye zan ce dake ba, amman ina iya faɗar Allah ya kyauta kuma Allah yasa yanda muka hana iyayen mu kuka muma, ya'yan mu kada su saka mu kuka, dan son zuciya ɓatan ta". 



Hindu ta ce, "a nufin ki muji tsoron gujewa aikata son zuciyar mu, ko kuma kin kawo muna kukan ki ne?  Dan na kasa fahimtar komai ". 



Humaira ta ce, "Haleema ke nan to yan zun kam na fahimce ki, wato tunda ga Humairar mahaukata, ai dole ne naci gaba da baki farin ciki na, kina saka ni kuka, kuma dolene yi maki duk abunda kike so, to bari kiji wani abun, Haleema ni da kike gani a yan zun na wuce da sanin ki, wato nasa daukar da ɗana Haniff na baki, uwa uba soyayyar mijina, duk dan ke kiyi farin ciki, to lallai ne sai yan zun na tabbar da kina hauka ne Haleema, ina son Jafar ko nace dake abu Haniff, bana jin zan iya barin wata mace ma ta raɓesa da sunan soyayya ballema ace Aure, ni Ummu Haniff nayi maki nisan da ba zaki iya hango koda wutsiya ta bane, Yaya Jafar nawa ne dan ni akayo sa, ai kin riga da kin koya mani son Jafar dan haka, ba zan ce, ba zanyi zumunci dake ba, amman kada ki yarda zuciyar ki ta ƙara raya maki cewar ni Humaira zan sake sadaukar maki da farin ciki na, eh lallai ne na Auri Yaya Jafar bana son shi shima baya sona, amman kuma abun al'ajab anan kuwa shine a yanzun nida Yaya Jafar mun afka a tafkin soyayya mai zurfin gaske, wanda ko masoyan da sukayi Auren soyayya ba zasu kaimu shauƙin junan mu ba, dan haka ki iya halshen ki Haleema "



Haleema sakin baki tayi tana kallon mu, su Yaya Jafar da suka shigo tun ɗazun ne ya ce, "Haleema kike koma waye, oho!? ban damu ba, Humaira ita ce rayuwa ta ai sai yan zun ma da kika dawo na sake gane hakan, Ummu Haniff ita ɗaya ce, a zuciya ta, dan haka ki ja jikin ki, Humaira taso muje gida dan yau ina jin idan na tsaya a gidan nan za'ayi abun kunya". 



Haniff dake rarrafe ne ya rarrafa yayi gurin Yaya Jafar ya ɗaga shi sama yana yi masa wasa, tashi Humaira tayi suka tafi bayan tayi sallama da kowa haka Hindu tare suka fita itada yaya Aliyu, haka Haleema taja ƙafar ta, tana kuka tabar gidan. 



Bayan kwana biyu Inno ke tambaya ta, wai kuwa Salman yana gari kuwa? Dariya nayi nace, "baya nan ai Dad ne ya saka shi ya kammala masa wani aikin a london to da fushi ya tafi shi yasa, suka daina jin sa, ni ce, ma nake kiran sa, ina saka shi ƙara jin haushin tafiyar". 



Dariya aka saka Inno ta ce, "ai kuwa zan rama masa, bari dai zaki gani"



Ban damu ba dariya ma Kawai nake yi, haka har mukayi kwana arba'in da biyu, gyara kam nasha shi, kitso da lalle akayi mani na yawon arba'in, sai gashi Inno da Yaya suka ce, zan je na yiwa Mai martaba barka da wannan matsayin da Allah ya bashi, suka haɗa mani kayan da zamu dasu, suka rakani har mota, ina shiga da Shuraim ya zauna aka ɗora masa Sultana a ƙafar sa, ni kuma Sultan ne a jiki na, muka ɗauki hanya, sai airport inda Yayan mu, ya kaini, muka shiga jirgin, muka ɗaga, sai garin Abuja. 



Muna sauka sai alokacin ne na tuno ashefa Abuja muka zo to miye yasaka Yaya Auwal yayi muna bucking na jirgin Abuja?  Run gume ni akayi ta bayana, ai da sauri nake ƙoƙarin kubcewa, ina jiyowa sai akan Salman ido na ya sauka ya rungume Hannuwan sa, yana kashe mani ido ɗaya yana ɗaga gira ɗaya, ya ce, "ya dai madam, kin yi mamaki ne?  Ai daman nace zan rama gashi dai su Inno sun tayani ramuwa"



Haushi naji na ce, "haba dear ban fayi yawon arba'in ba fa, ni wallahi ba a kyauta mani ba". 



Dariyar shakinyan ci yakeyi ya anshi Sultan yaja hannun na, Shuraim a cikin motar muka same sa nima ya saka ni, ya shiga aka rufe motar muka ɗauki hanyar gidan sa, sai fushi na keyi shida Shuraim sai dariya sukeyi wai ashe haka na iya smile, bai sani ba, Shuraim duba ka gani, yau tafi kullum kyau ko? "



Da sauri Shuraim ya ce, "Daddy fuskar Mommy idan tayi fushi tafi kyau, gashi har da baki take turowa kamar na Baby Sultana tana son nono". 



Doke masa baki naso yi Salman ya tare masa, ya ce, "kai hubby harda dukan nan irin na naji daɗin yanda ake yabo na? ". 



Ai kuwa kukan shugaba na fashe dashi dan duk sun cika ni, sai suka dawo lallashi na har nayi shiru, wani haɗaɗɗen gida Salman ya kai mu, tsayawa faɗar kyauwan sa, ɓata lokaci ne, dan yafi wan can tsohon gidan ba, komai bane akan wannan. 




Kai Alhamdulillah soyayya muke kwasa da kulawa nida yara na, sai sam barka, arzikin Salman ƙaruwa yakeyi sai dai muce Alhamdulillah. 



Bikin su Yaya Auwal aka haɗa dasu Amrah da Mariya amman banda Nusaiba inda Amrah ta Auri Muhseen ashe sun daɗe suna soyayya ni ce, ban sani ba, sai da abun yazo, a gaskiya munsha shagalin biki. 




Nida Salman zama mukeyi, na amana da ƙaunar juna, tarbiya muke baiwa yaran mu ukku babu abunda muka nema muka rasa. 


*Alhamdulillah*


 

  

*Nima dai anan nake cewa Allah ya yafe muna kura kuren da naikata a cikin wannan littafin da laifuka na baki ɗaya, Allah ka jiƙan iyayena, Allah ya yafe masu ya kai haske kabarin su tare da yan uwa musulmi baki ɗaya amin* 




*Sai Allah ya sake haɗa mu a cikin littafi na gaba Ummu Ihsan ce keyi maku fatan alkhari*



*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 

No comments