Recent Updates

Nailah 9

 


*🌸NAILAH🌸*


   ~*(The abandoned flower🌹)*~




*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAY*



*PAGE 9*



Saida suka kimtsa aka ƙara shinfida wata tabarmar sannan aka shigo da su Abih dake ta mamakin mutanen wannan ƙauye yana ayyana to dama a ƙasar nan za'a iya samun garin da babu bakar fata ko ɗaya? Koda yake ai ƙauyen ne ya cika ƙauye gashi ba wani girma ne dashi ba, babu mamaki mutanen cikinsa duk ahali ɗaya ne idan aka bibiyi tarihi, to amma idan haka ne miyasa Nailah ta kasance mai duhun fata?




Bai gama tunanin ba fatiya ta shigo gidan da allo a hannunta mai nuni daga makaranta take.




Tsaye tayi bakin ƙofar tana kallon mutanen da ke zazzaune tsakar gidan sai kuma ta cire kai ta isa baƙin ƙofar ɗakin Ommi ta shige ba tare da ta tanka ma kowa ba.




Nailah dake shirya kayansu a cikin ɗakin jin an shigo ya saka ta maida dubanta kan fatiya tana kallonta na wasu lokaci sai kuma ta mike tsaye tana cigaba da kallonta da mamaki ta kalli Ommi, idan ta kalli fatiya sai ta kalli ummi, sai can ta fizgo maganar bakinta tace "ummi wacece wannan?



Ummi tayi murumushi tana shafa  gashin fatiya da tazo ta zauna a cinyarta tana tura baki gaba, saboda Allah wai ita da ummanta ake tambayar wacece ita, ita mai tambayar wacece ita to?




Ommi da har yanxu take ɗan murmushi tace " fattu ce mana, yar autar umminta"




Nailah ta sake maida dubanta kan fatiya ƙirjinta na bugawa ta matso ta rike hannun Ummi tana faɗin "Ummi kenan itama Abanmu baya sonta, ummi itama kullum sai an watsa mata ƙasa, ummi dan Allah karki ce min irin rayuwar da nayi take fuskanta, wlh ba zan iya jurewa ba.




Ummi ta ja kumatun fatiya da ta ƙure Nailah da kallon rashin sani tana murmushi tace "autana kinga yayarki ta birni, ai na gaya maki kinada yaya mai kalar fatarki ko? to itace wannan.




Nan da nan fatiya ta fara dariya ta nufi inda Nailah take tana bin jikinta da kallo sannan tana shafa tsadaddiyar suturar dake jikinta amma bata ce mata komai ba sai zama da tayi a gefenta ganin itama Nailar ta zauna.




Ummi bata ɓoye mata komai ba, ta sanar da ita duk abinda ya faru daga tafiyarta har zuwa yanxu da kuma rashin lafiyar da mahaifinsu ke fama da ita, yanxu haka yana ɗakinsa, kawai ya samu bacci ne shiyasa bata tado shi ba dan kamar ya samu hutu ne daga zafin ciwo.




Nailah tayi kuka, tayi kuka, ta kuma kara girmama lamarin Ubangiji, ta kuma gode ma Allah da fatiya bata tashi cikin irin rayuwarta ba, babban farin cikinta idan ta tuna ƙila Abanta ba zai kore ta ba ko taje ɗakinsa yanxu, amma kuma hankalin ta a tashe yake na jin bashi ta lafiya.




A yanayin ciwon da suka tardo Abba abin ya ɗaga hankalin Abih dan haka yace dole akwai buƙatar a kaishi asibiti a duba lafiyar shi dan haka zasu tafi dashi can, idan yaso sai su tafi harda iyalinshi baki ɗaya yadda zasu fi nutsuwa idan suna ganinshi.




Ko zaman minti sha biyar basu yi ba suka tambayi ko yanada wani makusanci da zai wakilce shi a can gidan hakimi inda za'a ɗaura aure yace masu Mlm Abubakar ɗin yaje kawai saboda shi bai tashi yaga kowa ba sai mahaifansa kuma sun jima da rasuwa, gashi Abih yace a yau ɗin nann za'a yi komai su juwa, dole Mlm Abubakar ɗin suka yafi tare da shi.





Ita dai Nailah tunda suka zo tayi noticing zallar farin cikin da ya kasa ɓoyuwa a kan fuskar Ommi sai ta barshi a kan kawai farin cikin ganinta ne, amma abinda ya fara daure mata kai sai taga Ommi tana yawan kallonta sai kuma ta saki murmushi ba tare da tace mata komai ba, dan haka ta ɗan fara tsarguwa.





Sai a lokacin ta fara tunanin wai miye ma ya kawo su ƙauyen nan harda su Abih da Sir da abokin Abih bayan su Mommy da Khairat? taya ma suka san asalin ta har suka kawo ta nan ba tare da ko sau ɗaya ta taɓa sanar da wani abinda ya shafi rayuwarta ba sannan suma basu tambayeta ba, taya Mlm. Abubakar yaje har inda take, waye yayi masa kwatance waye ya faɗa mashi inda take? Ya Salaam. Sai a lokacin duk waɗannan tunaninkan suka dawo mata a kai.





Idan bata manta ba Mommy tace Mlm Abubakar yana nufin sai tayi aure ko kuma sai ta kusa aure sannan zata koma gida, lokacin har Mommy ta roƙeta alfarmar yi mata zaɓin mijin aure ita kuma babu jayyaya ta amince dan dama batada wani saurayi ko wani wanda take so.




Idan sun barta ta zo hakan na nufi kenan.... kenan...



Ba shiri ta faɗa ɗakin da Mommy take ciki dan su a waje suke ita da Khairat da Asma suna shirin fita dan Khairat ke son ta ɗan zagaya cikin ƙauyen a karonta na farko da zuwa ƙauye.




Tana shiga taci karo da Arif dake tuƙuburin tunda suka zo Nailah bata tsayawa suyi ball kamar a gida, ko ta kanshi bata bi ba tana ayyana ai kanshi ne ball ɗin, in ba haka ba ina yaga wata ball a nan.




Ta isa inda Mommy take babu bata lokaci ta buɗe baki tace "Mommy wai miye muka zo yi nan? Itace kawai tambayar da taji zata iya yi a yanxu dan amsarta ta fi buƙata.




Mommy da dama ido kadai ta kawo ta zuba ma Nailah dan ganin iya gudun ruwanta itama kai tsaye cikin rashin nuƙu nuƙun da jan lamura tace "kin manta maganar da muka yi kenan"




Ko numfashi Mommy bata sauke ba Nailah tace "to waye? Mommy waye kika zaɓarmun? Miyasa ban ganshi a nan ba?



"Daddyn Arif mana, kuma dai ai kinga tare da shi muka taho"



Ƙitt numfashin Nailah ya tsaya na yan second kafin ta sulale ta zauna tana ma kanta fita da hannuwanta jin wani zafi ya taso mata cikin ƙankanin lokaci.




Yanxu nan abinda Mommy tayi mata kenan, yanxu Mommy da yayan Khairat ta haɗa ta, salon ya kama wuyanta ya murɗe shikenan ya kashe banza? Innalillahi.



Wani busasshen yawu ta haɗe a maƙoshinta sannan ta fizgo maganar bakinta daƙyar tace "yaushe za'a yi?" tana fatan ba yanxu bane dan ta samu damar tuburewa ta samo wanda yake daidai da ita su rufawa juna asiri amma ba Sir ba, ita ina zata kai shi.




Ba tare da damuwar komai bai Mommy tace "yanxu ma fitar da kika ga sunyi can gurin ɗaurin auren suka je, daga can ne ma mijin naki ya wuce dan yanada ayyuka a gabansa.




Ɗaurin aure! mijinta! Shine abinda Nailah keta maimitawa a zuciyarta sai kuma ta miƙe da sauri kamar an tsikareta ta fice daga ɗakin kamar zararra, Mommy ta bita da kallo tana taɓe baki a zuciyar tace "hmm daga ke har shi na wuce tunaninku wlh, kuma kina komawa ko kwana ɗaya ba zaki ƙara min a gida ba zaki koma can ku ƙarata" tayi maganar tare da amsa sallamar Ommi dake shigowa akai akai suna zantawa.



Nailah tana fita gurinsu Khairat ta koma tace Asma tazo ta raka su gidan Mariyama.



Asma ta dan yamutse fuska tace "nifa Ommi ta hana ni zuwa gidanta saboda matsala muke samu da wannan tsinannen mijin na Mariama.



Nailah ta dan yi shiru tace ban gane ba, mijin Mariyamar ne tsinanne?




"Eh mana, duk lokacin da naje sai munyi cacar baki, in ƙare maki har kusan dukana yayi rannan, ni kuma na hayo karti sukayi masa lilis shine bayan ya gama jinya sai ya rama dukan a kan Mariama kuma yace duk lokacin da nayi masa abu a kanta zai dinga ramawa shine Ommi ta hanani zuwa dan karma mu samu wata matsalar.



Cike da mamaki Nailah tace to duk mi ya kawo wannan? Mi yayi zafi Asma? Mijin yayarki ne fa.




Asma ta taɓe baki tana kauda kai gafe sannan ta juyo ta cigaba da faɗin "ba laifi na bane ba fa, gaba ɗaya mutumin bayada imani da tausayi ko kaɗan, babu wanda bai san irin azabtar da matanshi da yake yi ba, ga azabarsa ta duka ga ta kishiyoyinta da suma suka saka ta a gaba, baki ga yanda ta rame ba saboda wahala da rashin abinci kuma ba dan baida abincin bane kawai baya basu ne sai ya ga dama, sannan babban abinda yafi damunta shine yaƙi barinta ta haihu, duk lokacin da ta samu ciki sai ya zubar mata yace yara sun isheshi haka, tayi tayi, su Ommi ma sunyi iya yinsu ya sake ta amma yaƙi yace sai an biyasa sadakinsa kuma dubu hamsin yake so bayan kuma shi dubu goma ya bayar, kinga kuma Abanmu bayada lafiya ko gona ya daina fita babu hanyar samun waɗannan maƙudan kuɗaɗen shiyasa suka ce tayi haƙuri ta zauna har lokacin da Allah zai kawo mafita.



Daga Nailah har Khairat jikinsu rawa yake na jin wani sabon bala'i kuma, da rawar jikin Nailah ta miƙe tana faɗin muje yanxu Asma ai nasan Ommi ba zata hana ki raka mu ba.




Babu musu suka fice tsabar ruɗewa ko Ommi basu sanarwa ba, suna isa ƙofar gidan gaban Nailah ya faɗin ganin duk lalacewar gidansu yafi wannann sau dubu gashi suna tinkarowa sai warin kashin shanu da na tumaki babu daɗin shaƙa.



Suna shiga suka iske ta tsakar gidan a bakin murhu tana ƙoƙarin hura wuta da iskar bakinta idanunta sunyi ja, sallamar da taji ya saka ta ɗagowa da sauri idanuwanta suka sauka a kan Asma da waɗanda suke tare, kafin ta iya tantance su Nailah ta ƙarasa gurinta da sauri ta riƙo hannunta tana ƙarema farar fuskarta mai kama da Omminsu sak kallo, idanuwanta na ɓuɓɓugo da ruwa.





Mariyama da ko mutuwa tayi ta dawo ba zata manta fuskar Nailah ba ta ɗago ramammun hannuwanta ta ɗora a fuskar Nailah tana shafawa tace "Nailah kece?



Girgiza mata kai Nailah tayi tare da rungume ta tana sauke idanunta a kan kishiyoyinta da suka fito suka yi tsaitsaye suna kallon Nailar cikin mamaki dan duk tsararrakinsu ne a lokacin baya.




Suna sakin juna suka wuce ɗakin Mariyamar da ƙiris ya rage Nailah ta fashe da kuka, Khairat kam tuni take ɗan share hawaye lokaci lokaci dan tsananin tausayin wai ɗan Adam ke rayuwa a cikinsa, sun jima sosai har suka tafi mijin nata bai shigo ba dan haka Nailah ta ƙuduri aniyar zata neme shi suyi magana irin wadda yafi fahimta da yardar Allah





Sai bayan Magrib aka zo da motocin ɗaukar su dan a can Tayra zasu iske su Abih su wuce gaba ɗaya, harda motar da aka saka Abba shi kaɗai dan ko tashi zaune baya iyawa.



Ganin haka ya saka Nailah saurin fita daga gidan ba da sanin kowa ba ta koma gidan Mariyama bayan ta ɗebo kuɗin da a ƙalla zasu kai dubu ɗari biyu, cikin Sa'a ta iske shi ba tare da wata doguwar magana ba ta gaya mashi bukatar da ta kawo ta babu alamun sassauci ko wasa a muryarta, dan ta ɗauki niyar ko bai karbi kuɗin ya saki Mariyama ba sai ta makashi kotu ko kuma ta haɗa shi da sojojinsu Abih su canja mashi kamanni, ba zata taɓa tafiya ta bar Mariyama a wannan rayuwar ba da yardar Allah.



Jiki na rawa ganin kuɗin da bai taɓa ganin tsabarsu a ido ba ya karɓa ya shige ɗakinsa mintina kaɗan ya fito da takarda ya bata sannan ya kira Mariama da bata san da zuwan Nailah ba ya ƙara shaida mata ya sake ta saki ukku.




Mariyama bata gama tantance abinda ke faruwa ba Nailah ta ja hannunta suka fice dan akwai hijab a jikinta kuma bata tunanin akwai abinda Mariyama zata buƙaci ɗauka a cikin ɗakin da babu komai sai tabarma sai dai saboda ƙara tabbatarwa Nailah ta kalleta tace "akwai abinda zaki ɗauka a cikin gidan ne?



Girgiza kai Mariama tayi tana cigaba da kallon Nailah cikin mamaki da rashin sanin abin yi ta cigaba da bin bayanta kamar itace ƙanwar.





Koda suka isa Nailar kawai ake jira gashi ƙauyen babu network ko ɗis balle a kira ta, ganinsu tare da Mariama ya saka Ommi saurin ɗagowa tana ma Nailah kallon ya haka?



Bata iya bata amsa ba sai buɗe baki da tayi kawai tace "Ommi zanyi bayani idan mun sauka InshaAllah"




Itama Ommi shiru tayi, ganin kowa ya gama shiga drivers suka ja motocin suka nufi airport inda tuni Eeyad daya koma Azhar tun ɗazu ya turo masu jirgi wanda zai kwashe su duka ba tare da wani ɓata lokaci ba suka ɗaga zuwa babban birnin......✍🏽

No comments