Recent Updates

Nailah 10

 *


🌸NAILAH🌸*


   ~*(The abandoned flower🌹)*~




*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAY*



*PAGE 10*



Suna sauka direct babbar asibitin private ta abokin Abih wadda duk wani mai ji da kuɗi ko mulki suke zuwa aka wuce da Abban su, Ummi taso tsayawa a asibitin amma Abih yace suje su huta kawai dan ko sun zauna ma babu abinda zasu yi, zasu ƙara gajiyar da kansu ne, a nan Nurses kaɗai ke jinya shiyasa basa ma barin mutane zama idan aka wuce mutum ɗaya.




Da wannan aka wuce dasu gida kai tsaye lokacin har 11pm dan haka kowanne yana shiga gurin barci ya nema, da yake akwai wadatattun ɗakuna a gidan tuni Mommy tasa aka gyare ma Ommi ɗaya daga cikin ɗakunan da babu abinda babu a ciki na more rayuwa, ummi ta kwanta a nan ita da autarta da tun a jirgi tayi barci, Mariama da Asma kuwa ɗakin Nailah suka yada zango su duka suka kwana a gado daya karo na farko a tarihin rayuwarsu.




Gaba ɗaya gidan makara suka yi har saida gari ya fara haske Abih ya dawo daga masallaci yaji shiru sabanin kullum idan ya dawo ya kan ji motsin mutane shiyasa ya fahimci yau makara suka yi dan haka yana komawa ɓangaren sa ya shiga kiran wayar Mommy dan ba zai iya shiga kai tsaye ba saboda baƙi.




Itace duk tabi ta tado su sannan ta koma tayi sallar itama, duk yadda Ommi taso tana idar da sallah ta tuntuɓi Nailah da batun Mariyama bai samu ba dan tana gama sallar tun kafin ta ƙarasa Addu'o'inta bacci mai nauyi ya sake fizgarta.




Wannan karon ma sai 10am daidai kafin yan gidan suka fara fitowa dan baƙi kam basu ma nemi hanyar fita ba, Asma da tun ganin Mariama take neman ƙarin bayani itama, Nailah na fita ta kalli Mariyama tace "wai ya aka yi na ganki kamar daga sama? Ina mijin naki?




Mariyama da itama kanta buƙatar amsar take tace mata itama bata sani ba kawai ya kirata yace ya sake ta sannan ta ga Nailah tsaye da takarda a hannunta ta janyo ta suka taho.




Ihu Asma taso ƙwala wa sai dai tuna a gidan mutane suke ya saka ta saurin rufe baki da hannuwanta, murmushi sosai a kan fuskarta ta shiga fadin wai yanxu tsakanin ki da Allah babu igiyar aurenki a kan wannan koɗaɗden, kai ni kam dole in zuba ruwa kasa in sha, kamar da wasa ta shige toilet inda Nailah ta nuna masu suka yo alwala bayan sun gama zuba ƙauyanci da taɓe taɓe shima dan a gaban Nailah ne kaɗai, lokacin da suka shigo gidan jiya duk aljannar duniyar da suka gani basu wani nuna komai a kan fuska ba sai suka kama kansu kamar ba yau ne suka taɓa ganin duniya irin wannan ba.




Kamar da wasa ta ɗebo ruwan nan a hannuta ta fito ta zuba su a ƙasa inda tsaftataccen coffee brown ɗin tiles yake tas dashi kamar ba'a takawa ta duƙa ta sha daidai lokacin Nailah ta shigo ɗakin, ta kalleta da sauri tana faɗin Asma lafiyarki kuwa? 




Tana dariya ta ɗago tace bari kawai yaya Nailah ai wlh abinda yafi ma haka zanyi, wai fa Yaya Mariyama ta fita daga hannun wannan tsinannen, hakan na nufin ko mun koma gida ba zata koma gidansa ba, hakan na nufin ta fita daga wannan wahalalliyar rayuwar.



Nailah bata ce komai ba sai murmushin da tayi itama tace su taso su je su gaido Mommy sannan su wuce gurin umminsu.




Babu musu suka bi bayantar har ɗakin Mommy suka gaidata sannan suka nufi ɗakin da aka sauke Ummi, Ummi tana ganinsu ta sauke ajiyar zuciya dan dama a kage take itama taji dalilin ganin Mariyama, duk gaida ita suka yi, fatiya ma ta gaida Nailah da ita kadai keda arzikin ta gaida tan, dan kuwa su da ido ya saba gani ba wani gaida su zata yi ba gaskiya.



Amsawa  Nailah tayi tana shafa kanta cikin so da ƙaunarta, Asma ta mangare keyarta tana fadin ke mu baki gaida mu?



Janyo auta ummi tayi da ta wani zunbure baki zata yi abinda Asma zata jibgi kayanta irin yadda suka saba a gida sai kace wasu sako da sako, koda yake hake dan ita ke bi mata amma ai akwai nisa a tsakaninsu dan Asma gurin 12yrs ta bama fatiya, tsakanin Nailah da Asma kuma 3yrs, A tsakanin Mariyama da Nailah ne tayi su kusa da kusa dan shekara ɗaya da watanni Mariama ta bama  Nailah.




Bata so su nuna hali a gidan mutane dan haka tace, ke Asma bana son cin zali fa, dama kin koya mata gaida ki ne ban sani ba?



Zata sake magana me aiki da shigo da katon tray a hannunta na breakfast, tunda Mommy da jisu shiru ta san ba lallai su saki jiki su yi a dining ba sai ta sa aka kawo masu nan kawai, fita mai aiki tayi ta kara dawowa da wani tray din ta fice, sai a lokacin duk suka kai dubansu inda kamshi ke dukan hancinansu tun kafin a bude kulolin.



Saida suka kammala breakfast din sannan ummi ta kalli mariyama, haka yasa itama mariyamar da sauri ta maida kallonta kan Nailah wanda ya saka ummi dole itama dawo da nata kallo kanta, fuskarta na nuna yanayin bukatar karin bayani.




Nailah ta gane abinda kallon ummi ke nufi dan haka ta fada mata duk yadda suka yi tun daga zancen da taji daga bakin Asma har yadda suka yi da tsohon mijin mariyama da sakin da komai




Sai a sannan ummi ta sauke boyayyar ajiyar zuciya tace "Allah yasa yakan shi yafi Alkhairi, a kullun rana ta Allah bata taba mancewa da rayuwar da yarta take ciki ba, tana jin radadi a zuciyarta amma babu yadda ta iya dan haka sai ta bar lamarin ga Allah ta cigaba dayi mata Addu'a da fatan Alkhari, sai gashi Allah yayi nasa ikon a kankanin lokaci, a ƙasa da yini daya ya rabota da walahar da ta sha a shekaru ukku na aure, lallai Allah mai amsa Addu'ar bayinsa ne, bawa ya dogara ga Allah yayi ta Addua sannan yayi hakuri tabbas zai ga budi da kwanciyar hankali masu wanzuwa da yardar Allah.




Mommy ce tazo dakin suka gaisa da Ummi sannan ta faɗa mata su shirya za'a kaisu asibiti su gano Abba.



Kwana biyu da zuwansu aka yi musu jagora zuwa ƙayataccen gidan da Abih ya basu yace su zauna kafin Mlm sagir ya samu lafiya a san abin yi, gida ne da ya ƙunshi komai na more rayuwar duniya da nutsuwa, babu abinda babu daga kan furnitures har suturun sakawa sannan ko wace an ware mata ɗakin ta, fatiya ce kawai ummi bata barta ita ɗaya ba.




Ummi gani take hidimar da ake masu har taso tayi yawa, auren ɗiyarsu ne fa kawai aka yi, godiya da addu'a kam babu irin wadda Abih da iyalinsa basu sha ba a bakin Ummi musamman da Nailah ta faɗa mata irin dawainiyar da suka yi da ita.




Zaman su ummi a gidan Abih shine kaɗai ya hana Mommy tattara Nailah ta miƙata gidan mijinta dan haka suna komawa sabon gidan a daren ranar aka yi ƙayatacciyar walima wadda ta samu ziyarar manya da yaran manya sannan aka kaita bayan nasihohin da ta sha daga kowane ɓangare, ita Husna dama tuni ta dawo, Nailah da taƙi yarda a barta ita kaɗai sai aka haɗo ta da Arif, taso har fatiya ma a haɗo mata ummi tace ba zata bada ɗiyarta ba gaskiya, idan ma zuwan ne sai ta kwana biyu tukunna.



A hankali ake ta jinyar Abba da aka gano hawan jini ne yayi masa mugun kamu dan haka ake ta bashi kulawa kuma yana samun sauƙi sosai dan yanzu har tashi yana iyawa da kanshi.




Zuwan yanxu sati biyu kenan da tarewar Nailah a gidan Eeyad amma har a wannan lokacin ba zata ce sunyi maganar fatar baki ba, sai Sa'a ma suke haɗuwa da juna saboda idan ya fita office tun safe baya dawowa sai kusan 5pm, itama kullum da safe Khairat ke zuwa su wuce makaranta tare idan suka dawo kuma wanka kawai take yi ta koma asibiti wani lokacin ma direct can take wucewa bata dawowa sai dare, tana dawowa kuma zata shige ɓangaren ta shikenan har safe, kuma lokuta da dama da gangan take keeping kanta busy dan kar su haɗu da shi, idan kuwa har suka haɗu to by mistake ne, a nan xaka ga zare idanuwa, kamar yadda bahaushe yace zuru bata cin zuru dan kuwa baya ce mata ufan bata ce masa ufan bayan gaisuwa sai kallo kawai.




Husnah kam dama ba wani haɗuwa suke ba kwata kwata, Arif ne ma idan Nailar ta tafi aisbiti yake zama a ɓangaren ta kafin Nailar ta dawo.




Yau da ya kasance Juma'a ƙarfe ukku suka taso daga makaranta Khairat ta biyo ta ajiye ta a asibiti sannan ta wuce, a nutse ta isa ɗakin da Abba yake ta shiga, yana ganinta murmushin fuskarsa ya ƙara faɗaɗa.




Itama murmushin tayi ta ƙarasa inda yake tana gaida shi da tambayar jikinshi ya amsa mata da yana jin sauƙi sosai Alhamdulillah, abubuwa ne cunkushe da ƙirjinsa da ba zai iya faɗa a fatar baki ba, hakanan sai dai yayi ta binta da kallo yana mata Addu'a da sa mata albarka a zuciyarsa.




Yau taji bata son zama a asibitin dan haka ta bar Asma kaɗai dake gurin ta koma gida ta ɗan huta dan yau test suka yi mai zafin gaske, har bakin asibitin Asma da dukansu suka fara murmurewa da yanayin hutu, musamman fatarsu da ta ƙara wani fari da yake farinsu ba mai ja bane, irin snow white ɗin nan ne me kamar madara, ta raka Nailah ɗin ba tare da damuwar komai ba Nailah ta tari napep ta wuce, Asma kuma ta juya dan komawa ciki.




A nutse take tafiya har ta shiga cikin asibitin tana nufar ɗakin da Abba yake bata ankara ba taji ta daki mutum da ɗan karfi har saida shima takardun hannusa suka zube.




Ɗagowa tayi da sauri da shirin yin masifa jin tsawar da ya daka mata yana faɗin kkkee bakya gan.... 




Sai dai shima bai ƙarasa maganar ba yayi shiru yana binta da kallon mamaki sai kuma ya saki fuska yana nunata yace "ke mi kike yi a nan"




A yanayin da yayi maganar yayi ta ne ga wadda ya sani sosai ko ma  makusanciyarsa, ita kuma wannan ko mai kama dashi bata sani ba dan haka take binshi da kallon mamaki da rashin sani.



Yadda take masa kallon rashin sani sai shima ya ɗan ƙara kureta da ido yana so ya gane banbancin da saida ya nutsu sosai ya gano, ita Zarah ai ta ɗan fi wannan girma dan a yanxu shekara ta ashirin da biyar take, wannan kuma da gani ba zata wuce ashirin ba, sannan wannan bata ida kai Zarah tsawo da cika ba.




Daƙyar ya haɗiye yawun dake maƙoshinsa sannan ya bata hanya alamar ta wuce, babu bata lokaci ta ratsa shi ta wuce, shikam yana ganin ta wuce ya bita a baya da sauri har ta shiga dakin da Abba yake.



Asibitin basu yarda su bada information ɗin wani ba dan haka bai nemi sanin patient dinta a gurin kowa ba sai ya tura ƙofar ya shiga tare da sallama a bakinsa.



Abba da Asma suka amsa a tare, amsawarsu kuma yayi daidai da zubewar wannan bawan Allahn da yayi ido biyu da fuskar Abba a sume.



Nailah saida ta biya ta dauko fatiya sannan ta wuce gida.


Tana komawa abinci kawai taci tayi wanka ta kwanta ko ta kan Arif dake rigimar ta yi mashi homework bata bi ba, ba ita ta tashi ba sai gurin 4:30pm, Sallah tayi sannan ta fito falo ta iske su Arif da fatiya suna kallon cartoon, bata tambaye su wa ya kunna masu ba tace su je suyi sallah sannan ya dauko homework ɗin.




Babu musu suka miƙe suka yo alwala suka dawo falon, a nan suka yi sallar  sannan ya kawo mata homework ta dinga gwada masa har ya gama.




Suna gamawa ya fara mata nacin suje suyi ball tunda yau babu Islamiyya.



Bata musa ba dan itama kwana biyu tayi missing ball ɗin sosai, dan haka suka fito ƙayataccen compound ɗin gidan su duka ukku suka hau buga ball ɗin cikin nishaɗi.




Gaba ɗaya ta manta a inda take ta manta tare da su waye take, ball ɗin kawai take bugawa tana dariya cikin farin ciki, bata samu yin wasan yarinta ba dan haka yanxu idan tana yi take maida dukan hankalinta a kai.




Dai dai ta jefa kwallo a ragar su Arif ta dan yi baya tana masu gwalo taji bayanta ya bugu da jikin mutum, ba shiri tayi saurin juyowa saida ta ɗaga kanta sannan ta samu kallon fuskarsa da idanunsa ke kanta itama yana mata wannan kallon da har yanxu ta kasa gane masa.




Rawa lips ɗinta suka ɗauka tana son yin magana sai dai bata kai ga furta komai ba taga ya janye jikinshi daga nata.



Sai lokacin ta lura dasu Arif da fatiya wadda tuni ta saba da Eeyad dan kullum sai yaje ya duba Abba sannan yana zuwa har gida ya gaida ummi shiyasa ta sanshi sosai kuma ta san shine mijin Nailah.



Rugowa suka yi da gudu suka rungume shi ya shiga shafa kawunan su kafin a nutse yana bin Nailah da ganin hankalinsa ya koma kan yaran ta juya da sassarfa harda gudu gudu ta shige ɓangarenta illahirin jibgegen ƙugunta sai juyawa yake yana masa daƙuwa.



Da sauri ya rumtse idonshi ya buɗesu a hankali sannan ya kalli ball ɗin da suke yi ya dauke ta yayi ɗakinsa da ita, su Arif ganin haka yasa suma suka bi bayan Nailah su gaya mata Daddy fa ya ɗauke ball taje ta anso masu.




Kamar karamin abu na neman xama babba, duk marecen nan har zuwa dare azabar da Arif ke mata kenan taje ta anso masu ball, ta bashi haƙurin tayi dabarar ce mashi Daddy ze maido da kansa, karshe ma sai tace bari a sawo mashi wata amma yaron nan yace bai san wannan ba tashi kawai yake so, tace kuma yaje ya amso da kanshi yace shi wlh ba zai je ba sai ita zata je ta anso, sau ɗaya ta taɓa ganin irin wannan rigimar tasa lokacin suna gidan Mommy, yau gashi itama ya saka ta gaba da masifa, dan haka ta sadakar ta dauko wayarta ta dannan kiran lambarsa a karo na farko.



Har ta katse ba'a daga ba sai a kira na biyu ne ya ɗauka tare da Sallama



Kaɗan ya rage ta daburce ta samu ta saita kanta tare da amsa sallamar, sai kuma cikin rawar murya tace "Arif ne, ball ɗin su shine" gaba daya ma ta rasa ta yadda zata faɗa mashi Arif ke son a bashi ball.




Can ɓangaren Eeyad tun kafin ma ta fara magana yayi hasashen abinda zata faɗa dan haka a taƙaice yace "ki zo ki karɓa" yana gama faɗi ya katse kiran bai jira amsarta ba.




A nutse ba da tunanin komai ba Nailah ta miƙe ta ɗora zunbuleliyar hijab bisa kayan baccin da ke jinkinta ta nufi ɓangaren sa tana duba saƙon password ɗin ƙofar ɓangaren nasa da ya turo mata.




Dukda dare ne amma ba zaka fahimci hakan ba sai ka ɗaga kanka zuwa sararin samaniya saboda fitlun dake tsaitsaye a ko ina masu masifar haske, tana isa ƙofar ta saka password ɗin nan take ta buɗe ta shiga kai tsaye lokaci ɗaya ta lumshe ido tana shaƙar daddadan kanshin daya daki hancinta mai haɗe da sanyi A.C duk da bata nutsuwar da zata karema falon kallo amma ta gani kuma ta yaba.........✍🏽

No comments