Recent Updates

Mummunan Zato Book 3

 

MUMMUNAN ZATO BOOK 3

       *📔📔📔 Page 1*


Da gudu ya fito yana kiran "Jabir! Jabir!!" Dai dai lokacin da Jabir ke fitowa daga garejin motoci, inda ya ajiye motar da suka shigo yanzun nan,ya ji muryar Ogan nashi cikin

wani firgici, da gudu ya nufo ƙofar falon inda suka yi kiciɓis da maigidan nashi ɗauke da A'isha ga jini na zuba. A guje ya koma ya fito da mota ya shiga suka fizgi motar a guje, duk da haka Uncle gani yake tamkar Jabir ba gudu ya ke ba, ya ce "Jabiru mu yi sauri fa,ƙila ma ta cika."



Suna isa da gudu ya ɗauke ta bai damu da jinin da yake zuba jikinshi ba, ya shiga asibitin yana kiran "Doctor! Doctor!?" Nurses ɗin da suka ganshi tuni suka nufi gurin da ake aje gadon da ake tura marasa lafiya, kafin su iso ai shi tuni ya kai Office ɗin Doctor. Bakin ƙofa suka ci karo da Likitan, shima ya firgita da ganin jinin. Nurse's suka iso tuni ya zube ta kan gadon, suka tura da gudu sai Emergency,shima ya bi su amma kafin ya shiga tuni an turo ƙofa, sauran Nurse's ɗin suka ce "Yallaɓai kayi haƙuri ka jira Doctor za ya yi aikinshi, lokacinne ya kalli jikinshi tun daga rigarshi har wandonshi jini ne. Nan take zuciyarshi ya yanke cewa cikinshi ya zube, ya dunƙule hannunshi ya kai ma bango duka ya kifa kai jikin bangon yana mai jin wani irin raɗaɗi a zuciyarshi.


"Oh Allah! Dama ba zan ga ɗan kaina ba?" Wata zuciyar ta ce "kada ka yi saɓo." Nan take ya ce, "Allahumma ajirni fi musibati." Sai ya saka dangana cikin zuciyarshi,ya yarda Allah da ya bashi wannan shi ne zai bashi wani,ya saka hannu cikin aljihun wandonshi ya ciro wayarshi,layin Alhajinmu ya kira, lokacin da yaji muryarshi yana cewa, "Abubakar ya ya?" Zuciyarshi ta karye ko yaushe in yana gaban mahaifanshi ko yana waya da su ya kan ji shi tamkar yaro ƙarami. Cikin rawar murya tamkar Zai fashe da kuka, ya ce "Alhaji A'isha tayi ɓari muna nan asibiti." Tamkar ya soka mishi ƙaho a cikin zuciyarshi, ya ce,me ka ce Abubakar? Kana nufin meɗakin ka ce ta yi ɓari?" Ya amsa da cewa "Eh muna asibiti." Jabiru yana ta kallon maigidan nashi cikin tausayawa. Bayan ya gama wayar da Alhajinmu ya kira Nafisa ya sanar da ita, Jabiru ya ce maigida ko zamu je ka canza kayan nan? Cikin ko in kula ya ce kada ka damu Jabir, bari mu ga yanda jikin A'ishan yake."


Sai ga Hajiya Jummai da Hadiza sun shigo da sauri, Jummai ta soma kuka tana kallon kayan jikinshi. "Alhaji me zan gani haka? Alhaji ba dai ɓari tayi ba?" Hadiza ma cikin matsananciyar damuwa ta ce "Mun shiga uku ni Dija, yanzun ina A'ishan ta ke?" Yanda suka nuna damuwarsu sai shi ne ya koma yana lallashinsu. A haka Alhajinmu ya same su can sai ga Nafisa, duk da kukan da Jummai ke yi da tagumin da Hadiza ta yi bai sa zuciyar Nafisa yarda da su ba, shiru-shiru Likita sai dai Nurse ta fito da gudu ta ɗauko wancan ta zo da gudu ta koma ciki, don haka sai ya soma fitar da rai da rayuwar A'isha. Nafisa ta zo ta dafashi, "Kayi haƙuri Bros, Allah yana tare damu, insha Allahu Allah zai isar mana komai." Ya saka hannun shi a kafaɗarta, amma bai iya cewa komai ba, sai dai girgiza kai kaɗan yake yi,jim kaɗan Likitan ya fito, Nurse's na biye dashi sun turo ta a kan gado Uncle ya nufo shi yana cewa, "Ya ya Doctor?" Likitan ya ce "jira ni" cikin Office ya shiga,ɗakin da za'a ƙwantar da ita, Nurse's suka turo ta ciki,sai da suka sa ta a gado tare da ruwa sannan Likitan ya ce, "Nurse ɗin su gyara ta da ƙyau, sannan kada su bari kowa ya shigo in da take. Ya fito ya nufi office ɗin shi inda ya samu su Uncle cirko-cirko a tsaye, ya shiga ya zauna yana cewa "Ranka ya daɗe bismilla,ku zauna." Ya ɗauki wani handkachief ya share zufar da ta zubo mishi a fuska, ya ajiye ya dube su. "Ranka ya daɗe yanzun dai muna buƙatar jini ne

" Alhajinmu ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce, "To sai a gwada mu,in bai yi ba sai a nemo." Likitan ya ce "Ranka ya daɗe ai kai ko ya yi ba zamu ɗibi naka ba saboda girma, sai dai na "Yallaɓai." Uncle wanda tunani da damuwa ta hana shi magana,ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, ya ce dama kai ba za'a taɓa jininka ba, sai dai nawa" ya ci gaba" Likita cikin ya fita ko?" Cikin ƙarfin hali Likitan ya ce, "Ba zan tantance ba yanzun,da so ma muke musha kan jinin da ke zuba." Uncle ya miƙe "muje gurin ɗiban jinin." Likita ma ya miƙe yana cewa, "Sai mun je an gwada." Ya ce jinina zan iya ba kowa, Likita ya ce "to shikenan,sai mu ɗiba mu gwada lafiyar shi, sannan mu tace."


Cikin ƙanƙanin lokaci suka ɗaurawa A'isha jini, duk mai imani in ya ga A'isha sai ya tausaya mata, don haka suka hana kowa zuwa gurinta.


Ƙwance take tamkar gawa, sannan jini ana sa wani, wani na fita. Alhajinmu da ya je ma da Hajiyarmu da labarin halin da ake ciki, bayan sallar isha'i ta ce da Alhajinmu su je ta duba ta.


Ta tsura mata idanu tana kallonta lokacin da Likitan suka shigo da Uncle, Alhajinmu ya dubi Likitan ya ce "Doctor wane ci gaba aka samu zuwa yanzu?" Likitan cikin karaya ya ce, "Sai dai godiyar Allah, amma lamarin ya ruɗani, don muna toshe nanne can na ɓallewa." Hajiyarmu ta matsa kusa da ita, ta kama hannunta ta dubi Likitan ta ce "Kai ɗannan gaya min gaskiya,ko dai yarinyar nan bata ne?" Likita ya ce tana da rai Hajiya bata rasu ba." Ta ce Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un, wannan kuma wanne irin ciwo ne haka?" Alhajinmu ya ce "Likita yanzun menene shawarar ka?" Likita ya ce "Addu'a kawai ce mafita,don ni ban taɓa karo da irin wannan matsalar ba."


Uncle ya jingina da bango don ya kula zaya iya faɗuwa. Duk da (AC) ɗin dake ɗakin bai hana shi zufa ta yi mishi wanka ba, Alhajinmu ya ce, "wannan sai dai mu ƙara,don kullum cikinta muke." Ya dubi Hajiyarmu "Ina ganin ko zan samu su Malam Yakubu ne?" Ta ce, "Za'a iya samun su ɗin, tunda suma waɗannan mutanan babu abinda ba sa saka ɗan Adam a ciki." Su Alhaji Bello sune suka yi ta ba Uncle magana, lokacin da yake cewa, shi dama tuni yasan A'isha ba zata tashi ba, saboda shi duk matar da ya aura mutuwa take. Yanzun me zai ce da Mustapha? Alhaji Bello da Alhaji Salisu suka ce, "ka daina wannan maganar, kada ka manta cewa, kai Musulmi ne."


Nafisa da Uncle suka ƙwanta gurinta,don anyi-anyi ya je gida ya ƙi, Hajiya Jummai ma da ƙyar su Hajiyarmu suka iya lallashinta, irin kukan da take yi ta so ta ƙwana aka lallaɓata suka tafi (kun ji makirci).


Tun shida na safe Alhajinmu suka iso da su Malam Yakubu, lokacin sun samu Nurse's suna gyarata, suna cire kayan shinfiɗar da na jikinta don haka dole suka jira, Nafisa ta fito ta sanar da su an gama, suka shiga addu'a suka soma yi suna tofa mata, cikin ikon Allah sai ta soma motsi,tana motsa ƙafa, ganin haka sai suka soma karatu,nan ta soma mutsu-mutsu, suka umarci Uncle ya riƙe ta kada ta faɗo. Suna ta karatu can ta soma gunji,suka yi, suka yi ko wanene ya yi magana, amma shiru. Sai dai can suka ga ta miƙe tana hamma, suka yi addu'o'i suka tofa mata, sannan suka ce ya fita ya dai ƙi yin magana ne. Sannan suka tafi da ƙudurin cewa zasu aiko mata magani, suka kuma sake bada shawara game da yawan karatu, sannan ta daina ƙwanciyar la'asar,in zata ƙwanta. To ta ƙwanta kamar da azahar zuwa la'asar, zatayi baccinta hankali ƙwance ga kuma lada.


Bayan tafiyarsu, Likitan ya iso,nan ya duba ta,ya cika da mamakin ganin ta tana numfashi, kuma numfashin ma irin na masu lafiya, Nan suka sanar da shi komai, ya ce "To mun gode ma Allah da yasa aka gano bakin zaren, yanzun in ta ɗan huta sai mu duba lafiyarta." Uncle ya yi hanzarin cewa, "Likita kana ganin za'a samu cikin nan?" Doctor ya dubeta cikin karaya, sannan ya kalleshi "Yallaɓai ba zan iya tabbatar wa ba, saboda ta zubar da jini har da guda-guda,ban sani ba ko har da ɗan tunda yanzun bai wuce ɗan guda ɗin ba."


Uncle ya yi ajiyar zuciya,dama shi tuni ya cire rai sai dai yana roƙo Allah ya bashi wani mai amfani.


Su Hajiya Jummai kowacce tana cike da murna, saboda murna kowace tana maƙale da waya tana sanar da duk wanda ta san zai taya ta murna. Jummai dai suna waya da Aminiyarta ta ce, "Ai ciki tuni ya jima da bin ƙwararon asibiti,kin ga yanda jini ke malala kuwa?" Kari ta ce, "Dama ba na gaya miki ba? Wani sa'in in kana son biyan buƙata sai ka bi ta irin waɗannan hanyoyin." Hajiya Jummai ta ce "Don wannan me sauƙi ne,ni da na kashe rayuka ma wannan har ya dame ni? Kedai Allah ya shige mana gaba." Karima ta ce, "Sai na zo jaje,ƴar iska ki ka ƙuƙe kina kuka,kai! Su Jummai makiran duniya." Jummai ta sheƙe da dariya ta ce, "Kin san Allah,kukan da nake yi a zuciyata ina yin sa ne saboda shegiyar ta ƙi mutuwa, amma ba don tausayi ba." Karima ta ce,"aini na sani,ke ce fa!" Ita ko Hadiza ko da ta sanar da Hajiya Lanti, sai ta ce "Dama ai boka ya gayamin hakan ce zata kasance, yanzu sai ki dage kafin ta dawo ta kuma ɗauka, kema ki dage ki ɗauka. Sannan yanzu wani farraƙu za'a haɗa min, ya ce aikin dai da tsada, amma ko sarƙarki ne za'a saida in yazo hannu sai ya maida miki." Ta ce, "To Hajiya zan yi duk yanda ki ka ce." Ta ce gobe zan zo jaje,in nazo sai mu yi magana in taho da sarƙar ko? Ta ce, "To."


Ƙarfe ɗaya saura, A'isha ta farka, miƙa ta yi gami da salati, sai ta ji hannunta da igiya. Cikin sauri ta kalli hannun nata,jini! Ta furta da ƙarfi Nafisa da ke zaune can gefe ta taso da sauri ta riƙe ta tana faɗin, "Sannu A'isha." Cikin tsananin tsoro ta ce, "Anty Nafisa me ya sameni?" Nafisa ta ce ba komai ki ƙwanta." Ta ce "Ina uncly?" Nafisa ta ce "Ya tafi masallaci." Ta koma ta ƙwanta shiru, sai ta soma tuno abinda ya faru da ita, ta tuna hayaƙinnan mara daɗi da ta shaƙa, ta tuna cewa ta ji wani abu yana bin ƙafafunta a lokacin ne ta kai hannunta sai ta ji an sa mata (always) a firgice ta tashi zaune tana cewa, "Anty Nafisa na yi ɓari ko?" Nafisa ta dafa kafaɗunta ,"kada ki damu A'isha, Allah da ya baki wannan shi ne zai ba ki wani ." A hankali ta koma ta ƙwanta, sannan ta runtse ido da ƙarfi gami da girgiza kai,a fili ta furta "Allahumma a jirni fi musibati,wakalifini kairan minha." Ta tausaya ma Uncle. Ta lumshe idanu, tana tariyo yanda aka yi cikin ya samu lokacin da zai fitar zuwa jikinta har tsoro ya bata, ta zata numfashinshi ne zaya fita, ma'ana ranshi ni zaya fita. Ita kanta ta ci baƙar wahala kafin ya samu hanya ma tukunna, hawaye ne suke sauka akan gefen fuskarta,sai ta ji saukar lallausan hannu a fuskarta,ko bata buɗe idanu ba ta sani Uncle ne. Ya saka ƴan yatsunshi yana share mata hawaye,ta buɗe idanu a hankali ya yi ɗan murmushi. "Beby kin tashi?" Wasu sababbin hawayenne suka sake zubo mata, ya ce "ki daina kuka Beby, insha Allah very soon za mu samu wani." A cikin zuciyarta ta ce, "Babu kamar ɗan fari."



########

[12/18, 08:23] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 2*




Likita ya turo ƙofa ya shigo tare da sallama, Uncle ya amsa tare da miƙa mishi hannu. Bayan sun gaisa ya isa gaban A'isha yana tambayar ko ta farka ne? Uncle ya ce "Ta farka yanzunnan." Bayan ƴan dube-duben da likita ya yi mata, sannan ya bata magani. Ta yunƙura ta amsa tana sha, bayan ya gama ya ce da Uncle yana Ofis. Tare ma suka jera bayan sun zauna, Doctor ya dubi Uncle ya ce, "Yallaɓai har yanzun ban gano cikin nan ba,zai iya kasancewa yana nan haka nan zaya iya kasancewa babu shi, saboda wannan ruɗanin ne ma na yanke shawarar ba zan mata wankin mara ba,in nufin wankin mahaifa,zamu bar ta ta ɗan ƙara samun lafiya a gama mata ƙarin jinin, sannan in an ƙwana biyu sai ta zo mu duba." Uncle cikin sadaƙarwa ya ce, "Babu wani abu, Allah ya shige mana gaba." Daga nan A'isha ta ci gaba da amsar magani, sannan jinin dake zuba ya tsaya ƴan jaje kam ga sunan, Hajiya Jummai ta kawo wannan ƙawa ta kawo wannan ƙawa, ana musu jaje tana hawaye sai sun fita ta yi ta dariya.


Satin A'isha ɗaya aka sallame ta, Likitan ya ce nan da sati biyu ta dawo, kafin ta koma ɗakin sai da Uncle yasa aka yi karatun Ruƙiyya,a cikin shi, bayan ƴan ƙwanaki A'isha ta gyare tamkar ba ta yi jinya ba,ranar da ta cika sati biyu, Uncle ya ce su koma asibiti ta ce ba ma sai taje ba, domin yau ta tashi da al'ada, wannan ko yana nufin ba ta tare da ciki. Cikin tausayawa kan shi ya ce "To Allah ya bamu mai amfani."


Haka dai zaman gidan ya koma mata babu daɗi,gurin Uncle kawai take samun sauƙi. Hatta da ƴan aikinsu ta kula da zata sauraresu, rashin mutunci za su mata. Uche ne kurum babu ruwanshi,sai ko sauran direbobin gidan,don haka ba ta saka kowa aiki ita take kayanta, duk ranar girkinta zata zage ta yi wa Uncle ɗinta duk kalar girkin da ranshi zaya ƙwanta ga kalolin abin sha. In ko suka zo ƙwanciya sai ya kusanceta sau biyu, wani sa'in har da safe yana mai fatan Allah yasa ya samu rabo. Cikin haka sai ƙwatsam! Aka wayi gari Hadiza ta ƙwanta riris,wai tana da ciki. Shi kanshi Uncle ba ya ce ga dalilinsa da yasa bai yi murna ba,watan bai ji abin a ranshi ba, sai dai duk da haka ya nuna kulawa gareta,sam bata yarda ya kaita asibiti ba, sai dai suje da Hajiya Lanti, kuma wai Likitanta daban bata son asibitin da suke zuwa,bai yi mamakin yanda suke amsar kuɗi daga hannunshi ba, domin Hadiza in yana ɗakinta kafin ya ƙwanta da ita sai ta sara mishi kuɗi ya biya, to ballantana tana da ciki. Jin wannan labarin ya saka Hajiya Jummai cikin ruɗu in da ta kuma bazama don zubar da cikin Hadiza kamar yanda take zaton ta fitar da na A'isha.


Ita ko A'isha ta yi wa Uncle murna har ranta, sannan ta samu damar zana jamb ɗinta,fatanta bai wuce ta haye ba. A'isha tana mamakin yanda har yanzun take jin wasu abubuwa irin na da watan kamar tana son kaza bata son kaza,sai kuma tashin zuciya wani lokacin wannan lamarin kan ɗan ɗaure mata kai, amma ta danganta hakan da cewa me yiwuwa saboda can da tana jin haka ne shi yasa ya zamar mata jiki, don haka sai kurum ta share. Hadiza dai ana nan anata langaɓe-langaɓe shin cikinne?.


Ranar Litinin da safe A'isha ta gama shiri kenan saboda tana so Uncle ya sauketa gidansu Nafisa, har sun fito sai taga sabuwar mai aikin da Hajiya Lanti ta kawo,ta shiga ɗakin Hadiza da gudu. Tana zuwa ta cewa Hadiza "Ga maigidanku nan za su fita da ƴar gwal" (Sunan da suke kiran A'isha dashi kenan). Nan ko ta ce "Tabawa bani wayar can in kira shi." Dama Tun da A'isha taga matar ta kallesu ta juya tasan cewa wani abu zai biyo baya. Har ya taka mota zai shiga sai wayarshi ta soma ruri, ya koma da baya ya ɗaga wayar tare da cewa "Ya ya dai Hadiza?" Cikin kuka ta ce, "Cikina na ciwo." Da sauri ya nufi cikin gidan,tana jin takunshi sai ta soma birgima. Nan duk ya ruɗe ya ce, "Ko muje asibiti ne?" Ta ce, "a'a Hajiyata ta mance ta wuce da magunguna na gida,ka amso min." Ya fita da sauri. A hannun Jabir ya amshi makullin ya ce yana zuwa. A'isha tana cikin mota ya ce ta koma gida yaje ya dawo, yaje ne ya amso ma Hadiza magani a gidansu. Ranta ya ɗan sosu, ta sani Hadiza ta yi haka ne don kada su fita da maigidan, ta daure ta ce to ko Jabiru ya kai ni da wata motar? Ga mamakinta sai ya ɗaure fuska,na ce ki koma ki jira ni ko?" Bata kuma cewa komai ba, ta fito da ƙudurin cewa ta fasa fitar in dai ta koma ciki to ba za ta fita ba.


Tabawa na tsaye tana gadi ta koma ciki tana dariya tana cewa, "wallahi gata nan ta dawo." Dariya Hadiza ta shiga yi sannan ta ɗauki wayarta da sauri ta kira Hajiya Lanti, ta zayyane mata komai, Hajiya Lanti ta ce"Haba yanzun ki ka soma ta ɓukawa,dama gurin mutumin nan da naje ya bani wani abu wai in bashi ya sha, to Allah yasa ya sha ɗin yanzun da ya zo zan bashi." Hadiza ta ce "To kawai sai dai in zaki sa a zoɓo." Ta ce, "To bari a nemo kafin ya zo. Sannan bana son kiyi saken da za'a gane ba cikin nan ba ne,kin ga ta haka ne zamu samu mu gama dashi." Hadiza ta ce, "kiyi sauri ki nemo zoɓon kafin ya iso, sannan ki nemi maganin da zaki bashi." Hajiya Lanti ta ce, "Kada ki manta fa mijinki wayayyen ɗan boko ne,za ya iya gane mu gurin magani, amma ki bar ni dashi." Ta kashe wayar ta shiga kiran ɗan Autanta Baba Sule,wai ya zo ya sayo mata zoɓo a maƙota.


Bayan sun gaisa sai ya sheda mata saƙon Hadiza sai ta ce kai wannan yarinya da shiririta take, maganin fa yana nan cikin durowarta ta gefen gado na kuma gaya mata shi ne zata taso ka don iya shege." Ya ce "Cikin ne ya matsa mata shi ne ma yasa nazo da kaina." Hajiya Lanti ta soma latsa waya "bari in kira ta mashiririciya." Ta kira ta ce"Hadiza kin manta na ce miki yana cikin durowa?" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "A to ni dai nasan na faɗa miki." Ta dube shi tana kashe wayar, "kaji wai sai bayan da ka taho ne sannan ta tuna, kuma ta sha ya faɗa ciwon cikin." Ya ce "Ai shikenan." Ta buɗe fridge ta ciro zoɓon ta tsiyaya cikin kofi. "Gashi ni muna ta magana ko ruwa ban baka ba." Tamkar kada yasha, amma sai ya ji ranshi na so,ya amshi na kofin ya ɗan sha,sam bai kai na Beby daɗi ba,ya dai daure ya sha kusan rabin kofin,ta yi murnar shan da ya yi don an ce ko ya ya yasha,matsalarta ɗaya ya yi bismilla.


A'isha tana shiga gida falonsu ta samu Hadiza da Tabawa suna tsaye, Hadiza da waya a hannunta,ganin A'isha ta shigo sai ta hau yin wayar ƙarya. Ta ce, "Hello ka wuce Darling? Yauwa amma don Allah kada ka je da wannan sarkin nacin,ok kama wuce kai kaɗai? To sai ka dawo mijina." A'isha duk tana jin ta, kuma ta yarda wayar suke yi,tana ta kici-kicin buɗe ƙofarta. Hadiza suka kalleta suka sheƙe da dariya, ita dai ta shiga ɗakinta ta faɗa kan gado, Uncle bai taɓa mata haka ba kuma bata taɓa zaton wata rana zata zo da Uncle zaya yi mata haka ba,ta jawo jakarta ta ciro wayarta. Nafisa ta kira,tana ɗagawa ta ce, "A'isha kun iso ne?" A'isha ta ciji leɓenta ta gefe, "Nafisa sai dai wani lokacin yau ba zan samu damar zuwa ba." Nafisa ta ce, "Saboda me A'isha, har kin sani jin haushi da ina ta murna zan samu abokiyar hira,wai ma me ya hana ki zuwa?" A'isha ta ce "Ba komai, da har mun fito da Uncle ya ce bari ya amso ma Hadiza magani." Nafisa ta ce "wai da gaske ne Hadiza tana da ciki?" A'isha ta ce "Gaske ne mana ana ƙaryar ciki ne?" Nafisa ta ce "A'isha kenan,baki san waye Hajiya Lanti da ƴarta Hadiza ba ne shi yasa ke ko Hajiyarmu bata amince cewa Hadiza ciki gare ta ba, amma ciki ɗan duma ne,yaɗo yake in ya fito ma ganshi." A'isha ta ce "Haka ne, yanzun dai ki min haƙuri, sai wani jiƙon." Nafisa ta ce, "Allah ya kai mu." Suna yin sallama Uncle yana turo ƙofa,ƙin kallon shi ta yi ya iso gaban gadonta, "Beby tashi muje."


Yana magana yana kallon agogon hannunshi,ji ta yi tamkar ta juyo ta ce ba zani ba, amma tana kallonshi sai ƙwarjininshi ya hana,ƙimarshi gareta ta wuce nan, cikin sanyin murya ta ce , "ka tafi Office ɗinka kawai Uncle,ka yi latti wata rana naje." Ya ce, "amma ni ne nace ki tashi muje." Ta ce, "Ka bar shi mun riga mun yi waya da ita." Ya zuba mata idanu sai ya ji ranshi yana zafi,wato ita wannan haushi ta ji kenan? Ya ɗaure fuska. " Kina nufin cewa haushi ki ka ji?" Ta girgiza kai, ya ce to in ba kin ji haushi ba, menene na cewa kin fasa? Kina nufin kada in amso mata magani? Ko don ba ke ba ce? Mamaki ya cika A'isha, ta shiga kallonshi a tsorace, muryarta tana rawa ta ce ba fa nufina kenan ba, ya katse ta, "Ke da Allah yi min shiru,ke in kina naki ciwon menene bana miki don kawai na amso mata magani za kiyi fushi? To ki fashe duk wadda na aje sonta nake don ki ji ki sani." Ya juya ya fita.


Kanta ya ɗaure matuƙa,lafiyan Uncle kuwa? Itama ta miƙe ta shiga zirga-zirga a tsakar ɗakinta, ba ta taɓa shiga cikin irin wannan halin ba, ba ta taɓa ganin Uncle ya faɗa irin haka koda ga wani ba bare ita. A ƙarshe ta ba wa kanta laifin cewa ƙila ya ji haushi ne ba ta bi umurnin shi ba,in ya dawo zata ba shi haƙuri. Ranar dai yini ta yi tana zubar da hawaye.


Shi ko yana fita ya shiga mota har zaya tada Jabir ya rugo da gudu ya ce, "Gani maigida, ya bashi makullin ya matsa gefen direba, maimakon baya da ya saba zama. Ya ƙwantar da naganshi a kujera ya yi ajiyar zuciya, ya lumshe idanu. Yana son tuno meke damunshi ne? Jabiru ma ya lura yau kam maigidan nashi ranshi ya na ɓace ne. Ko a Office bai ba wa sakatariyar sa damar ta shigo masa da kowa ba, duk da jiran da mutane suke mishi. Ya lumshe idanunshi yana karanta sunayan Allah,kusan minti talatin sannan ya soma ganawa da mutane. Kaɗan-kaɗan zuciyarshi ta soma sanyi, ƙarfe biyu yana zaune a ƙayataccen gidan cin abincin da nan ya kan ci abincin rana. Yana so ƙwarai ya sha zoɓon A'isha, ya ɗauki waya ya kira ta lokacin tana zaune kan sallaya har lokacin tana zubar da hawaye gaya ma Allah take yi da sauri ta miƙe ta ɗauki wayar, muryarta a dusashe ta ce, "Salamu alaikum." Ya amsa sai lokacin ya ke tunawa sun fa ɗan samu matsala da safe, take kuma ya ji a ranshi tamkar bai mata adalci ba, ya amsa da wa'alaikumus-salam , Beby zan samu zoɓon kuwa?" Ta ce, sai dai a dafa, ya ce to Uche za ya kawo min ko?" Ta ce eh, ta miƙe ranta ya yi ɗan sanyi ta shiga kujuba-kujubar dafa zoɓo.


Cikin mintina ƙalilan ta gama, musamman da ya ke tana da ƙanƙara ta kira Uche da wayarta. Tabawa ƴar rahoto tana kallon lokacin da Uche ya amshi ƙwando ya fita,ta shiga gurin Hadiza. "Antina wai menene ake fita dashi cikin ƙwando kullum?" Hadiza ta taɓa baki,zoɓo ne wahalalliya kullum sai ta dafa shi an kai ma maigidanmu." Tabawa ta ce, amma ya kamata a ɗauki mataki kan wannan zoɓon, Hadiza ta ce,ƙyale ta tayi,ni dai ba zan iya wahala ba. Tabawa ta gyara zama ta riƙe ƙugunta tare da miƙa kai ta ƙanƙance idanu, "Antyna an ce miki haka kawai Hajiya Lanti ta kawo ni aiki nan gidan? Ta cigaba to in baki sani ba bari na sanar da ke, sai da na ɗauki alƙawarin tarwatsa gidan nan tare da karɓar miki ƴanci gurin mijinki,ko kin san ni ce na kawo shawarar ace kina da ciki? Shin haka bai miki daɗi ba yanzun? Cikin mamaki Hadiza ta matso daf da Tabawa ta ce ,"Da gaske ki ke yi?" Tabawa ta ja tsaki "An ce miki a banza maza suke shakkar aurena? In da zaki ji tarihina tun ina ƴar ƙanƙanuwata sai kin sha mamaki, domin tun ina ƴar shekara uku na kashe auren wata da Ubana kan daddawa, sannan na hana duk matar da ya auro zama,to ki gaya min auran wa zan bari? Hadiza cikin jin daɗi take jinjina kai, sannan ta ce, "Tabawa nayi farin cikin samun ki, to yanzun me ki kace a batun zoɓo?" Tabawa ta ce, "Yauwa kin san takan zoɓon nan sai tafi ku ƙwarjini? Don haka ki bar batun zoɓon a hannuna kina nan za a gabza rigima takan tsinanne kuma a daina yin shege,in kun bar ni da yarinyar nan ba sai an kai ta gaban malami ba,tsabar kissa ma ta isheta, ita kuwa waccan tsohuwar guzumar biyu zamu haɗa mata." Hadiza cikin murna ta kai hannu suka tafa da Tabawa, tare da cewa. "Haka ni ke son ki ƴar gari."


Misalin ƙarfe shida saura ya shigo, Tabawa ce kurum zaune a falo tana kallon T.V da sauri ta miƙe tana mishi sannu Alhaji sannu da zuwa,ya ce yauwa ya nufi ɗakin jummy. Ta yi karaf ta ce "Ta fita Alhaji bata nan." Ya dubi Tabawa,a ranshi baya son irin waɗannan mutanan, ya nufi ɗakin A'isha,tana zaune kan kujera fuskarta na kallon T.V amma zahiri ba tasan me ake yi cikin aƙwatin ba, har yanzun in ta tuna kalaman Uncle suna soya zuciyarta,sam bata ji murɗa ƙofar shi ba, kuma bata ji sallamar shi ba. Ya tsura mata idanu ya ce "Beby." Ba ta ji ba,ya sake cewa "Beby." Da ɗan ƙarfi ya yi maganar, firgigit ta ce "Na'am."




######

[12/18, 21:24] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 3*




Ta dubeshi ta zamo ƙasa tana mishi sannu da zuwa. A sanyaye ya amsa ta miƙe kamar yanda ta saba,ta ɗauko mishi ruwa ta cika kofi ta miƙa mishi cike da girmamawa,ya amsa yana kallonta, ya zauna yana sha,yasha kusan rabi kafin ya dube ta, Beby ba ki da lafiya ne? Ta dube shi hawayan da take ɓoyewa suka sulalo, cikin rawar murya irin ta masu kuka ta ce "Uncle don Allah ka yi haƙuri." Ya matso ya ɗagata ya rungume yana shafa kanta,ina tsokanarki ne fa Beby,ba wai faɗan gaske nake miki ba, daina kuka ya shiga share mata hawaye,kusan minti biyar yana lallashinta sai da yaga tabbas ta haƙura sannan ta yarda kan cewa yana mata wasa ne sannan ya fita.


Tabawa tana son sanin me yasa Alhaji ke daɗewa a ɗakin A'isha, duk in ya shiga ba ranar girkinta ba? Kuma me yasa sauran ɗakunan baya daɗewa? Ɗakin Hadiza ya nufa wadda tuni Tabawa ta sanar da ita dawowarshi, ta kuma bata shawarar cewa tunda ita ce dashi ta aje ciwo ta tashi ta yi shirin amsarshi, ta kuma ce wannan garin maganin da na baki ki tabbatar cewa kin yi tsarki dashi." Ta juya da sauri zata fita don kada ya isko ta ciki,ta juyo ta ca "Af,na manta ki tatsi kuɗi dai." Ta fice dai-dai lokacin da shi kuma ya fito daga gurin A'isha kamar ya wuce sai kuma ya tuna ya bar ta babu lafiya,don haka sai ya shiga. Tana cire kaya zata shiga wanka zaninta na ɗaure a ƙugu ta cire riga ta juya tana mishi sannu da zuwa,ya dubi ƙirjinta ya kauda kai, ya ce kin samu sauƙi kenan? Ta yi fari tare da cewa sosai ma,ya ce mun gode Allah, bari in shiga in ɗan watsa ruwa kafin a kira magriba.


Bayan sallar isha'i ya gama koman shi har yanzun zuciyarshi tana tana tausaya ma A'isha tana ƙara son Aisha tana muradin yarinyar sosai, ya kasa sukuni saboda ɓata mata ran da ya yi gani yake har yanzun tana can ranta ɓace, saboda bata iya fitina ba, ya ɗauki wayarshi ya kira ta ta ɗaga ya ce, "A'isha me ki ke yi ne yanzun?" Ta ce, "Ina kan sallaya ne ina Istigfari yau duk ban samu zama ba sai yanzun." Ya ce, "Allah sarki, Bebyn Uncle yau ya ɓata miki rai ko? Kiyi haƙuri..." Ta yi saurin katse shi da cewa,kar kace haka Uncle,kada ka bani haƙuri,ba ka min laifi ba,kai babba ne ba na zaton zaka yi abinda zaya sa har ka bani haƙuri,ta yi ƴar dariya,mun wuce gurin komai ya wuce, ya ce "shikenan Beby kiyi bacci tare da mafarki mai daɗi" ta ce kaima haka.


Sha É—aya da Æ™wata Hadiza ta shigo É—akin maigidan, lokacin yana zaune gaban laptop jikinshi sanye da fararen kar É—in kayan bacci, ya ji shigowar ta amma saboda bata yi mishi sallama ba sai yaÆ™i É—ago kanshi,ta zo ta zuba  yatsunta a kafaÉ—arshi, lokaci guda kuma ta sumbaci kumatunshi, har lokacin share ta ya yi,ta manna Æ™irjinta da bayanshi tsaf ya tsaya sannan ya ce wai Hadiza yaushe za ki koyi shiga wuri da sallama ne? Ta sa hannu ta matsar da laptop É—in,ta Æ™wanta a cinyarshi ni da É—akin mijina sai nayi sallama? Ya ce ko É—akinki zaki shiga ya dace kiyi sallama,tasoma yi mishi wasu salon nata da ta haddace su, na jan hankali,kafin wani lokaci ta zurma shi sai da suka yi nisa ya É—anÉ—ani maganin ta lura kuma ya soma zaucewa, sannan ta yakice shi ta É“ata rai, ya kasa É—aurewa ya soma lallashinta ta ce ita shikenan kullum sai dai ya Æ™wanta da ita ba ya bata komai,ta gaji, ranshi ya É“aci amma ba zaya iya haÆ™ura da abinda ya É—anÉ—ana ba, cikin zaÆ™uwa ya ce gaya min me ki ke so tunda ke ba zaman aure ki ke ba,babu yanda za'ayi in amshi haƙƙina gare ki sai na biya? Ta ce zaka sai min mota? Ya ce a'a ki je abinki, ta ce to in zaka bani dubu É—ari to in ba zaka ba ni ba shikenan. Ta kuma Æ™wanta,don ta sani dole ne ya dawo mata tunda shima ba baya ba, ballantana ya dangwalo wannan laÆ™anin nasu wanda suka yi wa laÆ™abi da sa maigida hauka, yanda kuwa ta yi tunanin haka ne kasa jurewa ya yi sai da ya nemo ta tare da amincewa zaya bata dubu É—ari, amma abinda ya ba shi mamaki irin daÉ—ewar da ya yi har kusan Asubahi ya kasa biyan buÆ™atar shi, sai da Æ™yar, tun a nan ya soma zargin ta yi amfani da wani abu tunda yasan kan shi.


Hajiya Kari ta kalli Hajiya Jummai," ke matsalarki kenan, kullum in an ce miki ga wani malamin sai kina gida ba su iya aiki ba,kin fi son na daji ko na ƙauye, alhalin irin ɓarnar da na gidan keyi,zaki sha mamaki" Jummai ta ce to ai ni sai in zata na cikin gari imani ne dasu ba za suyi maka wani abin ba, Karima ta ƙwashe da dariya sannan ta ce, "Bari in sanar da ke wani abu,kin ga wannan malamin da na ce muje gurinsa? Bata jira amsa ba ta ci gaba "Tantirin malami ne,kin san mun ci karo da gwamnan garin nan a gurin shi ranar da na je da daddare? Jummai ta ce, ke haba? Kari ta ce, wallahi ban ma gane shi ba shi kaɗai ya zo a sace, malamin ke faɗa min." Jummai ta ce in ko haka ne muje domin duk wanda ki ka ga ƴan siyasa suna zuwa gurinshi kin san ya yi ne. Karima ta ce haka ne, yanzun dai abinda nike so da ke in mun je ya buga bai ga mutuwar kishiyoyinki ba, to sai ki ce mishi ya yi miki na wani abin abu ko ciwo ko hauka,ko ki dinga haɗa su husuma da maigidan,ke kuma ki koma kiyi ta lallashin mijinki."


Jummai ta ce "ai ni na tsani in gansu ne a gidan,Kari ta ce in lokacin mutuwarsu bai yi ba ya za kiyi? Jummai ta ce haka ne, tunda gashi nayi-nayi ɗin sun ƙi mutuwa, musamman wannan A'ishan duk nafi jin haushin matsiyaciya, wallahi da za a bani bindiga ace in kashe wanda na fi ƙi ko? Wallahi Kari A'isha zan kashe ita ce mutum ta farko da ta karya min ƙwarina, irin kuɗin da na narkar kan ta mutu yarinyar nan ko ciwon kai bata yi ba, sai ma ɗaukaka da kullum take samu gurin miji, nasara ɗaya na san na samu kanta shi ne cire cikin nan nata." Karima ta ce, "yanzun dai in mun je gaban Malam ki baje kolin matsalolin ki. Jummai ta ce shikenan.


Misalin ƙarfe huɗu suka isa gidan Malam, Kari ce ta zaɓar musu wannan lokacin a cewarta ba'a cika samun layi ba, mutum biyu suka samu. Ɗaya a ciki ɗaya na zaune kan ɗaya daga cikin kujerun da ya jera a cikin zauran nashi,don zaman jiran shi. Suka dubi na zaunen suka ce da baƙi ne ko? Ta ce eh. Jummai ta kuma kallon matar lallai wannan mutumin da gani mai yi ne, tunda ta ga irin waɗannan mata.


Tunanin ta ya tsinke lokacin da taga waÉ—anda suka fito daga cikin É—akin Malamin suka kalli juna ita da Karima kamar yanda suma waÉ—anda suka fito daga É—akin Malamin suka kalli junansu, mai jira ta shige gurin Malamin daidai lokacin da Hajiya Kari ta ce (cikin kissa irin ta matan bariki) a'a Hajiya Lanti duniya ashe kema ki kan zo wurin Teacher? Lanti ta gyara zama cikin Æ™arfin hali ta ce, a'a ai mu sai da su muke iya kama gashin kuma ko'ina sai mu cinye mu bada siÉ—i." Karima ta ce,ana ki tunanin kenan, tunda dai jin ta take tamkar ta dawo ta koma. Hadiza kuwa ita ma duk ta warware kallon kallo suke yi wa juna, Hajiya Lanti ta kama hannun Hadiza suka tafi.  tana  cewa wa kada ki damu ni dama ai na daÉ—e da sanin  Jummai a wannan fagen sai dai ita da kanta ta sheda cewa ko gidan giya akwai babba,ta jima da sanin cewa ina samanta.


Ita ko Jummai ta kalli Kari ta ce, "Anya zamu shiga gurin Malamin nan? Kari ta ce, shiga kai,in kinji shiga ɗaya kenan." Ta ci gaba da cewa, "ke dai shawarata da ke ɗaya ita ce,ki saki kuɗi in har ki ka cire maƙo, to har sirrin su sai mun ji a gurin shi." Jummai ta ce kuma zai faɗa? Kari ta ce, sosai ma,in kin ji faɗi ɗaya kenan. Da zaki ji tawa ma tashin farko ki bashi kujerar Makka,kin san Allah da kin sha mamaki." Kafin ta ce komai har ta ciki ta fito,dan haka Kari ta yi saurin jan hannun Jummai suka shiga.


Yana zaune kan wani farin ƙaton buzu, gabanshi wani ƙaton carbi ne da wata ƙasa cikin faranti ko ina in ka kalla zaka ga kaya,ƙwalabe ne, litattafai ne da dai sauransu, suka zauna kan tabarma,ya ɗago ya zuba masu idanu zuwa can ya ce "Hajiya sannunku da zuwa,a tare suka amsa sannan suka gaidashi, Kari ta fara da cewa, " Na zata baka gane ni ba" ya yi ƴar dariya sannan ya ce me zai hana ni gane ki Hajjaju? Ina fatan dai aikin naki ya yi ƙyau, ta ce fiye ma da yanda na zata, shine dalilin da yasa na kawo Aminiyata domin tata matsalar ta doke tawa,Malam ya jinjina kai ya miƙa ma Jummai ƙaton carbi tare da cewa gashi ki ɗauki ɗaya, har sau uku tana zaɓa sannan ya bubbuga charbin a ƙasa ya riƙe shi jim ya ce Hajiya kina da abokan zama, kuma ba ƙya buƙatar zama da su ko? Ta gyara zama, hakane, ya ce ya ya sunannasu? Ya jawo tiren ƙasar gabanshi ta ce "Malam Hadiza da A'isha, amma nafi son komai ya fara takan A'isha,don tafi shige min gaba,na tsani yarinyar sosai. Ita ce ta soma karya min gwiwata, ta karya min shirina a cikin kishiyoyin da ake min ita ce ta fara kai labari har ma ta buɗe fagen da aka ƙara min wata kishiyar, cikin zafin rai ta ke maganar. Malam ya ɗaga mata hannu ya ce, bari mu bincike su mu gani, ya ɗan jima yana zane zananshi da ƙasa cikin farantin, ya yi ya share,yana girgiza kai har ya gama, ya ɗago kai ya dube su, dukkan su sun ƙagauta da son jin sakamakon. Ya yi gyaran murya ya zuba musu idanu tare da fara yi musu bayani kamar haka.


"Wato ita wannan A'ishan da ki ke faɗa ta banbanta da sauran mata da yawa, tauraronta yasha banban, wani tauraro gare ta mai ƙarfi wanda yana wahala in kin tara mata dubu da wuya ki samu ɗaya mai irin shi, duk wadda ta kasance tana da wannan tauraron yana wuya ayi mata sihiri ya kamata, sannan duk inda ta shiga zata kasance mutane na sonta don zata kasance mai ƙwarjini,kin ga ke nan dole ta fi ku samun shiga gurin maigidaku,da ma danginsa." Jummai ta soma share zufa, "to yanzun Malam ya ya za'ayi mata?" Ta ci gaba, "shi yasa nike ta tafka asarar kuɗina?" Malam ya ce, wannan shine gaskiyar magana, batun abinda zamuyi mata kuwa sai dai mu haɗa da maigidan naku in muka biyo mata ta bayan gida zai fi mana sauƙi, ita ko waccan yanzun zamu duba muku ita." Jummai ta yi karaf ta ce, "Malam ita ce muka ga sun fito daga nan ita da Hajiya Lanti." Ya zuba mata idanu, "kina nufin Hadizar Lanti ce ɗayar kishiyar taki?" Ta ce "Eh." Ya yi ɗan murmushi, "wannan nasan kowace ce bana buƙatar duba komai kanta."


Hajiya Kari ta ce," To amma hakan ba zaya hana ayi mana aiki ba dai ko?" Ya yi ɗan murmushi, "Sam illa dai wadda tafi ƙin jakarta aikinta ya tafi dai dai,in ko mutum ya so jakarshi nima in riƙe aikina." Jummai ta buɗe jakarta ta ciro ɗaurin ƴan dubu-dubu ɗai-ɗai ta dire gabanshi,sannan ta ce Malam me ya kawo Hadiza? Ina nufin da wace buƙata ta zo?" Duk da ba tace kuɗin na shi ba ne ya saka hannu ya ɗauki kuɗin ya juya su, sannan ya aje gefenshi ya ce,ta zo ne da buƙatar korarku,burinta shi ne ta mallake gidan da maigidan da dukkan abinda ya mallaka." Jummai ta yi murmushi, sannan ta ce, "Ni ko banƙi ace duk sun rasa rayukansu ba, amma yanzun Malam na baka zaɓi me ka ke ganin za'ayi musu? Sannan ina son duk aikinta kar a mata cikin da ta ce tana da shi a zubar, sannan in ta zo da wani bayani in sani, kullum a dinga yi min binciken kome suke ciki." Malam ya ciro kuɗin da ya ajiye a gefe ya ce duk a wannan kuɗin? Ta ciro irin su ta aje mishi sannan ta ce, "Me za ka bani in soma dashi yanzun?" Hajiya Kari ta ce, "Malam ka mata wanda zata san kai me yi ne ba irin waɗanda da an ce ga buƙatar da ake so sai su hau cewa Allah ya ce ba, yayi wata dariya sannan ya nuna Karima ya ce, "Ai ke kin sanni, wata roba ya ciro fara cikinta wata ƙatuwar tsoka ce gata nan kamar zuciya,ya miƙa mata kin san wannan? Ta girgiza kai,zuciyar mutum ce ta zaro idanu ya ce riƙe da ƙyau aikin wani da zan yi shi ne na fasa zan baki nasa a ciro min wata." Ta ce "a jikin mutanan ake cirowa? Ya ce to da ina za'a samu? Ta tsorata Malam da sassan jiki ka ke aiki? Kari ta katse ta tsoron me zaki ji bayan ke kanki rai nawa ki ka salwantar? Jummai ta ce amma ban taɓa amfani da sassan jikin mutum ba,Malam ya miƙa mata hannu bani in kina ganin ba zaki iya ba ne, ta ce, "zan iya Malam, yi haƙuri." Ya miƙo mata wata leda tare da cewa, "buɗe ki gani."


Wasu allurai ne cunkus cikin wani gari baƙi, ya ce " Guda ɗari ne da ɗaya, kullum ki dinga tsira ɗaya jikin wannan zuciyar,in zaki tsira ki ambaci sunan maigidanku sannan cikin zuciyarki ki ƙudurce cewa aikin yi ci, kada kiyi wasi-wasi da zaran kin yi wasi-wasi aikin ba zai ci ba, sannan aikin za ya yi tasiri ne kan maigidanku, duk wadda ki ka soma tsira alluran da nufinta cikin kishiyoyin to ita kaɗai ce zata samu matsala da mijin naku.


Sannan aikin mutum ɗaya ne,ɗayar za'a mata nata daban, ta ce to wannan na A'isha ne? Ya ce shikenan,in kun dawo zan baki na ɗayar, sannan kada ki ƙagara fa, don yanda kike soka allurar nan da ƙaɗan-kadan haka aikin zaya dinga ci da kaɗan-kaɗan,ta ce shi kenan, sannan kada ki ajiye inda za'a gani fa, ta ce to.


A'isha tana ƙwance sai zabga Game take yi, cikin wayarta sam bata ji shigowar Uncle ba,sai...




#######

[12/19, 15:33] Ummi Tandama😇: *📔📔 Page 4*




Sai da ta ji an ja mata yatsa da sauri ta tashi tana faɗin Hasbunallahu wani'imal wakil" Ganin Uncle yana mata dariya sai ta tashi tana dariya, ya ce,"Beby kin cika shegen tsoro." Ta miƙa mishi kofin ruwan cikin risinawa tare da ladabi ya amsa cikin farin ciki sannan ya zauna a hannun kujera yana sha,ta zuba mishi idanu, komai na Uncle birge ta yake yi, ya ɗago idanu ya kalleta ta yi murmushi shima yana murmushin ya ce kin san dame nazo miki? Ta girgiza kai, ya buɗe jakarshi ta Office ya fiddo takardu ya miƙa mata,sai ki zaɓi garin da ya yi miki, duk dai makarantun suna da ƙyau, cikin murna ta shiga dubawa ta dube shi cikin ɗoki Uncle zaɓa min Kano ko Sokoto,ko A.B.U za ni? Ya dinga yi mata dariya, kafin ya ce ke wacce ya fi ƙwanta miki cikin su? A'isha ta yi shiru alamun tunani,can ta ce Sokoto ko Maiduguri, ya ce gara ma Sokoto, amma Maiduguri ya yi nisa sosai, daga nan. To shikenan Uncle na gode, cewar A'isha kenan.


Cikin abinda bai fi sati biyu ba, Uncle ya É—auki A'isha, Jabir ne ke jan su sai Sokoto.


Masauki ya kama musu cikin wani shahararren Hotel. Suna sama Jabir kuma a Æ™asa, ya kama mishi Æ™wana biyu suka gama amma yanda Uncle ke samun kulawa gurin Bebyn tashi, sai ya kasance tamkar kada su dawo,don haka suka Æ™ara Æ™wana uku ita kanta A'isha ta rubuta waÉ—annan Æ™wanakin  cikin zuciyarta.


Bayan sun dawo sai kuma aka shiga shirin tafiya makaranta, sannan ta ziyarci Jigawa Æ™wananta biyu su Hajiyarmu da su Anty Fati duk tayi musu yini,nan ne ma Nafisa ta bata lambobin wasu Æ™awayanta,kan cewa zata haÉ—a su Æ´a Sokoto ne, kuma duk ba su da nisa daga makaranta. A'isha ta ji daÉ—i,dama bata san kowa ba, Nafisa ta sake tabbatar mata cewa zata ji daÉ—in zaman makaranta,don ita ma nan ta gama,ta ce mata waÉ—annan Æ™awayan nawa wayayyu ne musamman harkar riÆ™e miji,ba ma kamar Maimuna É—in nan , A'isha ta yi godiya tare da shan alwashin neman su, A'isha ka bata wasa da duk hanyar da ta ji an ce in tabi zata Æ™ara samun kusanta da mijinta matsawar ba hanyar saÉ“on Ubangiji ba ce. 


Komai na ƴan gata Uncle ya haɗa mata, wani gatan ma sai da suka isa garin Sokoto,dama gida ya kama mata, cikin makaranta ƙwanansu biyu a hotel yasa ana ta gyaran gidan sai ka ce gidanshi,kaya yasa aka siyo aka shirya gidan tamkar sabuwar amarya ya zuba mata komai sabo ga kayan wuta har da laptop ɗin ta sabo, ya shirge mata abinci, shima sai da ya ƙwana a gidan sannan suka je ya buɗe mata account, tamkar kada su rabu lokacin da zai tafi, A'isha har da kuka.


Ya samu dai ya lallasheta, tare da yi mata nasihohi, sannan ya tafi. Ta koma ciki tana kallon falon, yanda ya tsaru ta shiga bedroom ɗin ta faɗa kan gado,duk kewar Uncle ta dame ta,ita dai a rayuwa ta gode ma Allah,don bata isa ta ce ga abinda Uncle ya yi mata ba a tsawon rayuwarta a gidanshi,ta sani Uncle rainonta yake burinshi kullum ya faranta ranta,ya ji da ita daɗi, ya fidda ta tsara cikin ƙawayanta, Uncle koda wasa bai taɓa yunƙurin ɓata mata rai ba,ko ta ko'ina abinda take so shi zata ci shi zata sha shi zata sa hannun iyayanta. Ta kula ko gurin auratayyane burinshi yaga ta shiga nishaɗi, shi yasa itama ko yaushe ba ta da burin da ya wuce mishi biyayya tare da neman hanyoyin ji da shi daɗi daga ni'imar da Allah ya yi mata. Kafin ya isa gida sun yi waya kusan sau goma, shi ya kira itama ta kira,shi kanshi bai san ya yi kewarta haka ba sai da ya yi ƙwana biyun shi na sauran matan da ace tana nan da yau ita ce da shi,a zuciyarshi A'isha daban ce yana sonta,tana kula da shi tana da baiwar da ba duk mata ba,in yana kusa da ita ya kan manta da duk wata ƴa mace a duniya. Addu'a kullum yake mata, Allah yasa da ta da rahamarshi duniya da lahira. Haka dai ta dangana ta rungumi karatun ta ka'in da na'in.


Jummai da Hadiza kuwa, duk sun miƙa lamarinsu ga boka, ko in ce ɗan tsibbu. Jummai kam yanzun ta yarda Malamin nan zai share mata hawaye da A'isha ta jima tana sa ta zubarwa,ta gane hakanne lokacin da ta tinkari Alhajin da maganar son ya yi mata ginin da ya jima yana son mata a cikin gidan, daga baya ya share zancan. Alhajin bai Musa ba, ya ce zai sa a auna gurin duk dai da cikin gidanne. Malamin ya ce ta haɗa da ladabi da biyayya, don haka yanzun wani sabon ladabi ta samo.


Hadiza kam tafi ga magungunan mata irin waɗanda ke saka maza fitina, gashi ta ƙware gurin iya jan hankalin namiji,takan zuba mishi cikin ruwa ko abinci in ya ci kuma ta zo da salon tana jan hankali. Ba za ya iya haƙura ba,don haka sai ta sara mishi kuɗi haka zaya bata sannan ta yarda suyi auratayya wa'iyazubillah. Hadiza ba wai ƙyaƙƙyawa ba ce, amma irin matannan ne waɗanda suka san kan shawo kan maza,ta hanyar fizgar hankalinsu ta iya ƙwarƙwasa sosai, shi kan shi ya so ace A'isha ce ke mishi irin salon jan hankalin da Hadizan ke mishi.


Tuni an soma ginin Hajiya Jummai, gini ne za'ayi shi me tsari, shi kan shi ba zai ce ga dalilin da yasa ya ƙuƙe kan cewa sai an yi ginin cikin ƙanƙanin lokaci ba. Hadiza ta dame shi da son sanin wanda zai shiga ginin sai ya ce mata me rabo.


Yau kimanin ƙwana sha huɗu kenan A'isha ta yi a makaranta, har yau bata saba da kowa ba, kasancewar ta mara saurin sabo,gata miskila bata cika sakin fuska ba,ran da ta cika ƙwana huɗu ranar ta nemi Maimuna ƙawa Anty Nafisa izuwa yanzun sun saba sosai,in bata da lakca can takan je ta yi hirarta, Maimuna wayayyiyar ce ta gaske,tana ganin A'isha ta ga cewa A'isha ta yi mata,tana koyar da ita salo-salon yanda zata da kanta da mijinta,kai har da yarda zata dinga yiwa mijinta magana, tafiya da dai sauransu. Wani kunun Aya,dabino da cukwi da take bata mara suga sai madara,ga wata gumba da take dama ta da madarar shanu, A'isha da kanta ta ji tana sha'awar mijinta. Yau kam da ta je ƙin sha tayi ta ce, Anty Maimuna Uncle ba ya kusa gashi kina ta bani waɗannan abubuwan sai su dame ni fa, Maimuna ta ce ke baki san yanda zaki jawo hankalinshi ya zo gareki ba ko? Nan ta shiga tsara mata yanda zata yi, sannan ta bata garin bagaruwa ta ce ta ringa tsarki dashi in taji ranar zuwan nashi kafin ya iso.


yanzun haka da take ƙwance kan gadonta kusan ƙarfe goma tasan yanzun yana gida gaban laptop domin lokacin ƙwanciyarshi bai yi ba. Ta shiga murza wayarta shi take nema,jim kaɗan layin ya shiga ta juya rigingine, muryarshi ce ya ce "Beby" ta ce na'am Uncle ya ya ka ke? Ya ce lafiya lau ke fa? Ta ɗan runtse idanu ta buɗe sannan ta ce ina cike da kewar ka,ya cire gilashin idonshi tare da matsar da laptop ɗin, A'isha nima haka,ta ce,kai ai kana da wasu matan, ya ce, Beby basa min rainon da ki ke min, ba tonon asiri ba ne ko yi dasu,ke daban ce wancan satin fa da kin ganni al'amura ne suka yi min yawa, da kuma tunanin kada ki ce wannan Uncle ɗin ya nace min. Ta yi ƴar dariya cikin kissa sannan ta ce "Uncle ɗina kenan,kana ganin in da zaka zo kullum zaka gundure ni ne?" Cikin mamakin ta ya ce, Beby sai ina ga tamkar ba ke ba, Beby da ba ki iya gaya min yanda ki ka damu da ni ba, da zaran abubuwa sun yi sauƙi za ki ganni." Ta ce, to sai da safe, ya ce zan zo miki cikin mafarki kinji, ta ce sai na ganka. Sai ta samu kanta da sumbatar wayar tare da saurin kashe wayar. Sautin kiss ɗin ya daki dodon kunnanshi ya ratsa dukkan jikinshi. Haƙiƙa ta saukar mishi da kasala,yana jin ba za ya iya ci gaba da aikin gabanshi ba, dole ya rufe komai ya tashi. Ita kuwa juyi ta yi tana jinjina ma ƙoƙarin da tayi tasan in a gabanshi ne duk da Anty Maimuna tana bata ƙarfin gwiwar ta ringa mishi hakan ba zata iya ba.


Washegari wuraren ƙarfe shida lokacin ta fito daga lakca don ranar uku da mintuna suka shiga, ta buɗe gidanta ta shiga dama ta riga ta yi abincinta, magriba kawai zata yi sannan ta ci. Zaman ta kenan sai ta ji ana ƙwanƙwasa mata gida ta je ta buɗe. Wasu ƴammata ta gani su uku, suka nuna mata wani gida kusa da nata,ga gidan mu nan munce ne bari mu shigo mu gaisa, cikin fara'a A'isha ta ce ku shigo ta matsa suka shiga.


Abinka da wayayyun ƴan boko,nan suka sake, ita dai taje tayo sallah ta basu abinci suka ci har suna santi, nan suka sanar da ita sunayensu. Saliha da Amina,Kiristar kuma Linda ƴar kaduna ce,su kuma biyun nan Sokoto suke,suma course ɗin da take yi shi suke yi. Tana zaune dai ta ma kasa cin abincin don bata sake da su sosai ba,su ne dai sukayi tamkar dama sun santa, sai ta ji ana bugun gida, ta kalli agogo cikin zuciyarta ta ce to ko wanene kuma, ƙarfe baƙwai da rabi,ta fita tun kafin ta buɗe ta ji ƙamshinsa, cikin hanzari ta buɗe tare da cewa, Uncle tafiyar dare? Jawo ta ya yi zuwa jikinshi ya rungume, tare da faɗin I miss You Beby, ta amshi Jakar hannunsa "zo mu je Uncle kai kaɗai ne? Ya ce ni da Jabiru ne, sai da na kai shi masauki sannan nayo nan. Anan nayi magriba da isha'i, suna shiga falon ya yi turus yana kallon ƴan matan da ke zaune, fuskarshi da alamun tambaya, ta ce maƙotana ne suka shigo don mu saba,ta dube su ga Uncle ɗina, nan suka shiga gaishe shi kafin suka miƙe suka ce sai da safe A'isha Mustapha, ta ce na gode. Ya zauna nan ta shiga rawar jikin kawo mishi wannan da wancan,shi kam duk in da tabi kallonta kawai yake yi yana sonta.


Yana cin abincin suna hira tana mishi mitar zuwan ba zatan da ya yi mata, gashi bata mishi wani abu na musamman ba, ya ce shi ai ita ce ta musamman ɗin shi, cikin ƙwanaki ukun da ya yi a Sokoto ya kuma yarda A'isha ce kurum ta dace da rayuwarsa. Haka ya taho da kewar ta itama tana kewarshi, haka abubuwa suka yi ta faruwa lokaci ya dinga zuwa yana wucewa, Uncle yana ziyartar A'isha duk bayan mako ɗaya ko biyu.


Ƙwatsam! Wannan zuwa ya sameta ta tana fashin sallah, kuma ranar ta fara, da ƙyar ta lallasheshi ya yi ƙwana biyu tare da gamsar dashi ta hanyar wasu ƴan dubarun nata.


Wani sabon al'amari tun daga lokacin sati na huɗu kenan rabonshi da Sokoto, sannan wayar ma yanzun ba kamar da ba, kullum uzurin yake bata wai abubuwa sun mishi yawa gashi ana gyaran gida, daga baya ma in ba ita ce ta kira shi ba shi kam baya da lokaci. Abin ya soma ba wa A'isha tsoro,nan gefe kuma ga wata matsala da ke damunta. Motsi cikinta ke yi,ta sa rai ya zo ta sheda mishi, amma shiru suna daf da fara jarabawa abin ya matsa mata don haka ta kira Nafisa ta sheda mata,Anty Nafisa ta ce baki gaya ma Uncle ɗin ki ba? A'isha bata son saurin tona cikinta nata ganin gaske ne uzuri ya yi wa Uncle yawa ne, shi yasa har yanzun bai zo ba,ba zata yi saurin kai ƙararshi ba, ta ce abubuwa sun yi ma Uncle yawa bana son na gaya mishi zaya tada hankalinshi, ya ce zai bar aikin gabanshi ya taho. Nafisa ta ja tsaki,wane abubuwa ne suka mishi yawa baya ga komai da ya tsaida, Ya shiga harkar yiwa Jummai gini. Gabanta ya faɗi ta ce gini kuma? Nafisa ta ce bai sanar da ke ba kenan? A'isha ta ce, yace min dai yana gyaran gida. Nafisa ta ce, to ai gyaran kenan, Jummai ya fafaramma gini irin kuɗin da yake narkarwa a ginin sai kin gani yanzun ya gama kayan da za'a zuba ma daga (Chaina) za'ayo Odar su, A'isha ta ce to Allah yasa alheri." Nafisa ta ce,au! Ke bakiji haushi ba? Ta ce, to in naji ma Anty Nafisa ya ya zan yi? Tsaki Nafisa ta kuma ja,ke tafi can ke dai son miji ya yi miki yawa,ba ki iya ganin laifin shi. A'isha ta yi ƴar dariyar takaici, sannan ta ce to in ma naga laifinshi me ganin laifin za ya maganta min? Nafisa ta ce shi kenan mu dai mun ga laifin shi gidaje nawa gareshi cikin Katsina da kewayenta? Ya maidata wani mana za'a tsaya ɓarnar dukiya,kin san Allah, Alhajinmu da Hajiyarmu sun ji haushi, harkokin shi ma fa yaƙi ya maida hankali sai ka ce yau ya soma gini. A'isha ta ce Allah ya ƙyauta kuyi haƙuri kada suyi fushi da shi,tamkar Nafisa ta shiga ta waya ta doddoke A'isha don haushi, ta kula A'isha ba zata taɓa ganin laifinshi ba, don haka sai ta canza zancan da cewa,ki je asibiti mana? A'isha ta ce nima tunani na kenan, sai kuma naga ni ba ciwo cikin ke min ba, kuma ba wani guri ne ke min ciwo ba a jikina, sai naje na cewa Likita ina jin motsi? Nafisa ta ce kin ji irin haukan naki ba? Ki je ki yiwa Likita bayani,in yaso ayi miki (Scanning) a ga me ke damunki,in bai ga komai ba a koma Islamic." A'isha ta ce, shi kenan zan je, ki gaida min su Hajiyarmu."


Lamo ta ƙwanta tana tunanin me ya shiga kan Uncle ne? Don kawai yana yiwa Jummai gini sai ya share ta? Zata ce kada ya yiwa Jummai gini ne? Ba tare da ta gansu ba? Haƙiƙa ranta fa ya ɓaci sai dai bata son ta nuna ma ƴar uwarshi ne. Ta kira wayarshi abin al'ajabi ya ƙi ɗauka, har sau uku, sai ta tura mishi da text cewa,in ta mishi laifi ne don Allah ya yafe mata, rashin sa ya saka ta cikin damuwa,don Allah yaushe zai zo? Saƙon na isa sai kiranshi har tana murna ga zatonta sulhu zaya nema, sai kurum ya ce "ke kin fa matsa min da yawa......





######

[12/19, 22:33] Ummi Tandama😇: *📔📔 Page 5*




Ban cika son mace mai jarabar tsiya ba, duka-duka yaushe ne ban zo ba na shekara ne? Kin dameni don Allah daina kirana in na matsu zan neme ki da kaina." Kan A'isha ya yi matuƙar ɗaurewa,bakinta yana rawa ta ce, "Yi haƙuri Uncle nima ba wai na ce kazo ba ne,na zaci na maka laifi ne shi yasa." Tsaki ya ja kafin ya kashe wayar, wannan lamarin ya firgita A'isha sosai, baiwar Allah ranar sai dai bacci ɓarawo, amma bata runtsa ba. Maƙotanta su kansu cikin ƙwanaki sun fuskanci tana da damuwa koda suka tambaye ta sai ta ce musu bata jin daɗi ne. Anty Maimuna ma ta matsa mata dason sanin damuwarta, amma A'isha sarkin zurfin ciki ta yi ƙememe ta ce zuwan jarabawa ne. Yanzun suna karatu ba dare ba rana,Anty Maimuna ta ce to Allah ya taimaka.


Cikin haka ne A'isha ta samu ziyartar asibiti inda ta samu ganin Likitan mata. Bayan ta gama mishi bayani ya tambaye ta ko tana da ciki ne? Ta shaida mishi ita kam bata da komai,don haka ya bukaci ta ƙwanta kan gadonsu na likitoci don yi mata (Scanning). Bayan ya gama bai ce mata komai ba, sai da ya fitar da sakamako ya dube ta, "kina da miji?" A'isha ta ce "Eh." Ya miƙa mata sakamakon, tana buɗewa idanunta na sauka kan (EDD) ta maimaita kalmar a fili (EDD) kuma? Ta dubi Likitan ta ce,kana nufin ciki ne da Ni? Ya ce wata baƙwai ta zaro idanu tare da ɗora hannunta kan mararta, sannan ta ce Likita ka kuwa duba sosai? Ya yi ɗan murmushi,a katin ki naga cewa ke ɗalibarmu ce amma kin kasa gane kina ɗauke da ciki,kina nufin ko kaɗan ba wata alama da ki ka gane kina ɗauke da ciki?" A'isha ta girgiza kai tare da cewa, "Ina al'ada duk wata sannan wata bakwai ɗin da ka ke magana nayi ɓari lokacin wata uku."


Ya zuba mata ido, "Ya ya abin ya faru wancan lokacin? Ta bashi labarin a taƙaice, ya ce to wankin cikin da baayi miki ba shi ne dalilin da ba a wanke ɗan ba, Allah ya sa zaya taka doron ƙasa, sai dai zaya iya kasancewa watannin cikin ya koma baya. Yanzun dai cikinki wata bakwai da sati ɗaya.


Jugum A'isha ta yi tana tunanin wannan lamarin na Ubangiji,lallai wannan shine mafi girman abinda ya fi bata mamaki,iyaka tsawon rayuwarta, sannan ta yi murna mara adadi kuma ta san wannan labarin in ta bawa Uncle shi zai kawo karshen rashin jituwarsu, ko ta ce fushin da yake yi da ita, wanda bata san silarshi ba. Ta jawo wayarta ta shiga neman shi da glo ɗin shi har sau biyu tana rurinta tana katsewa bai ɗaga ba hakan (MTN) ɗin shi jikin ta ya yi sanyi, amma duk da haka ta daure ta kira (Seltel) ɗin shi daf da zata katse ya ɗaga, gabanta na faɗuwa ta yi sallama,rai ɓace ya amsa sallamar, kafin ta yi magana ya ce wai lafiya ne? Ta ce a'a dama ina son muyi magana ne. Ya katse ta da cewa,bani da lokaci, sannan ya yi tsaki ya kuma kashe wayar. A'isha ta zabga uban tagumi nan take kanta ya shiga sarawa,kuka mai ƙarfi ne ya ƙwace mata,ta yi shi har ta gaji babu mai lallashi. A'isha ta zama tamkar wata zararriya wa zata tunkara da matsalarta? Zuciyarta ta ce mata Ubangijinki, ranar kuwa ƙwana ta yi kan sallaya tana kaiwa Allah kukanta, zuwa safe ta ji ɗan dama kuma ta yanke hukuncin har ma cikinta batun cikin jikinta dama Ubangiji shi ne ya ɓoye kayanshi, ko Nafisa ba zata faɗa mawa ba, haka ta ci gaba da rayuwarta cikin makaranta.


Jummai kuwa ta samu yanda take so,da tace kaza za ya yi mata, gini kuwa an gama an kuma danƙara kaya na iyayan kuɗi sannan ta shirya walimarta ta gani ta faɗa suka shige ita da Suby da Sofy Sai gefen maigidan. Hakan ya yi matuƙar tunzura Hadiza nan ta tada bala'in cewa ba zata yarda ba, rigimar ta kai su ga manya inda Alhajinmu ya ce tunda ya yi wa Jummai dole ne sauran matan ya yi musu, dole yasa aka bige gefen Hadiza da nashi da na Jummai na da aka hau yiwa Hadiza nata amma A'isha dama ko ƙasa da sama za su haɗe ba za ai mata wani gyara ba. Ya dai sa an ragi falon an bar mata ɗan ƙarami ya zuba mata tsofaffin kujerun falon. Rashin kunyar da Hadizan ta mishi lokacin ya isa sakinta, sai dai ɓarin da tayi ne yasa ya bar ta ko Allah zai sa ya kuma samun wani rabon daga gare ta, don shi ya yarda har ga Allah ciki ne kuma ya amince cewa ɓarin ta yi irin kuɗin da ya kashe lokacin da suka zo da batun ɓarin suna da yawa, sannan sun hana shi zuwa asibitin a cewar su ba sai ya je ba,daga ƙarshe ma da suka ga ya matsa kan cewa zai je sai suka dawo da ita gida, Likitan da suka naɗa na ƙarya ya ci gaba da zuwa duba ta.



****    ****    **** ****


A'isha tana matuƙar tausayawa kanta don zurfin cikinta ya hana ta sanar da wani bare a tausaya mata,don haka ta shiga rama ta koma sirit sai nono sai ko cikinta wanda ya bayyana lokacin Anty Maimuna ta yi ta yi da A'isha ta sanar da ita matsalarta, amma ta ƙi cewa kurum take karatu ne don bata son tambaya ma ta rage zuwa gidan, cikin haka ne suka samu hutu na ƙwana goma jal, tamkar kada ta tafi Katsina, amma ya zamar mata dole tunda bata da kuɗi duk sun ƙare komai nata ya yi ƙarƙaf, ta yi ta kiran Uncle a waya don ta sanar da shi a zo a ɗauke ta, amma yaƙi ɗaga wayar. Abin ma ya daina bata mamaki ya shiga bata tsoro,bata son kowa ya san halin da take ciki, don haka ta ƙi kiran kowa ta nufi tasha.


Sun iso Katsina biyar saura,nan ma ta ɗauki shatar Taxi zuwa gida, har cikin harabar gidan ta ce ya shiga. Maigadi na ganinta ya buɗe Gate ɗin gidan,tana fitowa Uncle ta gani tsaye jikin mota yana waya, Jabiru yana riƙe da jakar Uncle ɗin ta Office da alama dawowarshi kenan daga Office ya bi motar da kallo don ganin wanene ya shigo masa cikin gida da Taxi? Ranshi ya yi mugun ɓaci lokacin da suka yi arba da A'isha, sai ya ji tamkar ya hau ta da duka,nan take ya ɗauke kanshi daga kallon gurin da take. Ganin haka bai bata mamaki ba, domin nata zaton na ma zaya kore ta ne, ta ciro kuɗi ta bawa ɗan Taxi ta saɓa jakarta tare da jan akwati, sai lokacin ta soma tambayar kanta wane gefe zata nufa, domin gaba ɗaya fasalin gidan ya canza, tana kallonshi ya nufi sabon ginin wanda take zaton shi ne na Hajiya Jumman.


Ƙofarsu ta da ta nufa duk da ta kula nan ma akwai ƴan gyare-gyaren da aka yi,taja ƙofar a kulle take gam don haka ta shiga ƙwanƙwasawa. Jim kaɗan ta ji muryar Tabawa tana tambayar wanene? A'isha ce ta ce,nice Tabawa buɗe. Ganin A'isha sai ta hau sheƙa dariya,dama ke ce haka? Ta taɓa baki,ai yanzun ƙofarki ta koma can, ta nuna gefen gareji, A'isha bata gane ba, amma yarda Tabawa ke tuntsire dariya shi ne ya sa ta saɓa kayanta ta nufi gefen gareji. Sule mai bawa fulawa ruwa ya nufo ta da sauri yana yi mata sannu ta amsa mishi, ya ɗauki akwatin tare da cewa ai Hajiya an samu ƴan gyare-gyare ne a gidan suna isa ƙofar tana kulle ya ce bari in amso miki makullin gurin maigida, da gudu ya nufi sasan Jummai.


Ya samu maigidan nashi yana shirin shiga wanka in da Jummai ke ta faman riritashi tamkar Æ™wai, ya yi sallama Sofy ta zo menene? Ya ce maigida nake nema,taje ta sanar da shi. Jummai ta  fito tace menene? Wanka zai yi, ya ce ranki ya daÉ—e zan amshi makulli ne na gefen gareji, ta yi guntun murmushi sannan ta juya.  ya fito fuskarshi É—aure hannunshi riÆ™e da makullan, gashi ka bata sakaryar yarinya kawai,Sale ya amsa ya fita daidai sanda Alhajin ya ci gaba da cewa don iskanci sai ta kama shigowa motar haya Taxi har  cikin gidana? Jummai ta taÉ“a baki wannan tsageruwar yarinyar mara kunya mene ne ma ba zata yi ba,ya katse ta da É—aga hannu saurara min tsagerancin me Beby ta yi miki? Nan ta tuna da sharadin boka da ya ce kada ta yarda ta kushe A'ishan a gabanshi, yin haka zaya ringa lalata aikin dole sai ta saka kissa cikin lamarin. Aikin da kissa zai tafi ba da hassada ba, don haka sai ta wayance da cewa ba Suwaiba ka ke nufi ba? Ya girgiza kai ni ban ce miki Suwaiba ba, kuma bana son in Ina ma wata faÉ—a a dinga sa min baki ta dafashi muje kayi wanka mijina,ni kaina ban za ci kana nufin Bebynka ba, ina zaton Suwaiba ce shi yasa,ni ko me A'isha zata min na tsageranci,yarinyar da magana ma bata dame ta ba,ai ita ce ta dawo? Lallai ina mata Sannu da zuwa,tsaki yaja sannan ya nufi gurin wanka.


A'isha ta buɗe ƙofa ta shiga, tsayawa ta yi tana kallon ɗan tsuku kun falon, kujerun suna da ne cikin falon sai ko T.V ta tura ƙofar ɗakinta ta shiga duk ko'ina ya yi ƙura,bata gaji ba ta tuɓe ta shiga gyaran ko'ina, da falo ta soma har ga Allah ita waɗannan dakunan sun ishe ta, ina laifi mutum mai zaman kabari ya samu ciki da falo a gidan duniya ai ya ishe shi rayuwa, ta goge komai sai abinda ke bata mamaki shi ne ba taga kitchen ba. Me hakan ke nufi? Ita dai tasha alwashin ba zata taɓa mishi zancan ba,zata fito da kayan girkin ta ko a ƙofar ɗaki ne ta saka risho, ta yo wanka bata shafa mai ba saboda zufa ta zumbula doguwar riga ta zo falo ta zauna, yanzun matsalarta yinwa ta miƙe ta fita harabar gidan, duk mazan ƴan aikin sun tafi gida sai Baba maigadi kurum. Ta isa gurin shi ta ce don Allah Baba duk su Sule sun tafi ne? Ya ce sun tafi Hajiya kina son wani abu ne? Ta ce biredi nake so, da kayan tea, ya ce to bari a karɓo miki dama ɗari biyar ɗin kenan ta miƙa mishi gashi duk yanda ya kama ka sai min,ta koma ciki. Can ta fito don tago ko ya dawo dai-dai lokacin da aka soma kiran magriba. Ya miƙo mata saƙon daidai lokacin da Uncle ɗinta ya fito,ya bi ledar da kallo ita dai ta amsa ta juya bayan ta ce ta gode.


Uncle ɗin nata ya bita da kallo tafiyarta irin ta masu ciki ya raya a ranshi ya isa gurin maigadi Baba ina ka je ne? Ya ce Hajiya na siyoma kayan shayi. Kayan shayi? Eh, inji Baba maigadi. Uncle ya kaɗa kai ya nufi masallaci. Ranshi ɓace,me yasa A'isha ke sha'awar wulaƙanta shi a idanun duniya ne? Ɗazun Taxi ta shigo mishi da ita har cikin gida yanzun kuma kayan tea ƙulli-ƙulli kamar gidanshi, motocin shi nawa? Sannan shaguna nawa ke gareshi cikin plaza, daban-daban? Ya yi ƙwafa.


Ita kam ta samu ta jona ruwa ya tafasa tasha tea ɗin ta ta ƙoshi, ta yi sallolinta, ta ƙwanta don ta huta. Sai dai maimakon bacci sai ta soma karanta matsalolinta. Tuni ta nemi bacci ta rasa, don haka sai ta miƙe ta soma da yin alwala, ta shiga kai kukanta ga Allah domin iyaka tunanin ta shi ne kurum zai yi mata maganin dukkan wannan halin da ta shiga.


Uncle É—in ta kuwa don takaici ya kasa cin duk kayan alatun da Hajiya Jummai ta shirya mishi, zuciyarshi sai Æ™ara zafi take game da Beby. Jummai tasan komai,don tun lokacin da ta ji dawowar A'ishan sai ta zuba rushi cikin kasko  ta kara hantar nan mai cake da allurai, shi yasa zuciyar maigidan Æ™ara zafafa,kamar yanda Malamin ya tsara mata, ta dube shi maigidana wai me ke damunka ne? Ya ce wallahi Jummai A'isha ce ta bani haushi. Ta ce haba Alhaji me A'isha zata yi maka ka ji haushi, irin haka bayan ka sani cewa yarinya ce? Ka dai same ta ne ka nuna mata baka son shiga motar haya tunda Allah ya hore maka, ya dubeta, to bayan ma wannan ina fita sai naga wai ta aiki Baba maigadi siyan biredi da madaran Æ™ulli dibi wannan cin zarafin? Hajiya Jummai ta ce,lallai bata Æ™yauta ba, amma ka mata uzurin cewa daga tafiya ta dawo,kai itama da rashin dabara take maimakon ta zo nan ta amshi abinci in tana jin yunwa ne? Ya ce girman kan nata zai bar ta ne? Ya sake yin Æ™wafa, zuciyar Jummai kar da murna, ta ce to kaje can gurinta don yau ita ce da kai tunda tafiya ta dawo. Ya ce bar ta ba zan je ba. Ta haÉ—a fuska wallahi sai kaje don bana son shiga haƙƙin wani, Allah ma ya sani. Ya ce kina korata ne? Ta ce a'a ni dai nafi son ko lahira mijina ya tashi daga cikin maza masu adalci, ya ce haka ne zata ci albarkacin ki ne zan je amma ba don ita ba, ta miÆ™e ta zo ta Æ™wanta a bayan shi na gode mijina nasan kai nawa ne daga duniya har abada, tashi ka je bari na bika da abincin,ya ce bar su kawai ya fita ta bishi da kallo fuskarta É—auke da murmushin cin nasara tasan in ya yi arba da ita wani sabon haushin nata zai ji kamar yanda Malam ya tsara mata.


Yana ta bugun Æ™ofa ba ta ji ba sai daga baya, da sauri ta sallame ta nufi Æ™ofar, ta buÉ—e lokacin ya cika tamkar zai fashe "waton wani sabon salon wulaÆ™ancin ne haka,da kimarshi da komai a ce yana bugun Æ™ofa Æ´an aikin gidanshi suna ji,ya dubeta a zafafe, watan kina jina ina ta faman bugun Æ™ofa ki ka min banza ko? Cikin sanyin murya ta ce kayi haÆ™uri Uncle wallahi ban ji ba, ina sallah ne ta kau ce ya shige ya kalli falon ko'ina ya taÉ“a baki sannan ya shiga bedroom É—in zuciyarshi na zugi so kurum yake yaga abinda zai yi faÉ—a a kanshi ta buÉ—e fridge da nufin ta bashi ruwa amma sai taga wayam ta manta É—azunnan ta gyara shi babu komai ciki, ta dube shi yi haÆ™uri Uncle,ba ni da ruwa cikin fridge, ya katse ta nace nazo shan ruwa ne? Ta girgiza kai, ya zauna kan kujerar madubi ita kam gabanta ne ke ta faÉ—uwa, ta cire hijabinta tana ninkewa, ya zuba mata idanu can ya ce "ke." da sauri ta dubeshi "mene ne a jikinki? Ta kallo cikinta kunya take ji ta ce mishi ciki ne don haka sai ta sunkuyar da kai tana É—an murmushi  da Æ™arfi ya ce "dake fa nake magana?...




######

[12/20, 19:35] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 6*




Ta dube shi cikin in ina ta ce shi ne dama nake ta kiranka ina son nayi maka bayanin baka saurareni ba, ya ce bayanin me? Ya ci gaba da magana cikin ɗaga sauti kada ki ce min kina da ciki, ta zaro idanu gabanta na faɗuwa, ya ce ko shi ke gare ki? Ta ɗaga kai. Ya miƙe da sauri ina ki ka samo shi? Jin furucin shi yasa ƴan hanjinta juyawa me Uncle ke nufi? Bata ankara ba sai ta ji ya cakumi wuyan rigarta, abinda za ki min kenan ko A'isha ya ɗan tausasa murya,kin dai san zuwana gurinki na ƙarshe kina haila ko? Muryarta tana rawa ta ce eh, amma bai san sanda ya ɗauke ta da wani wawan mari ba,amma me? Ya hankaɗata kan gado kin cuceni don ina neman ƴaƴa ido rufe shi kenan sai a kawo min shege? A'isha kin yi kuskure yanzun so nake ki gayan uban da ya yi miki cikin? Kuka take yi sosai tamkar ranta zai fita, ina ma ta mutu ta huta da wannan baƙin cikin? Ya ce zaki gaya min ko sai ranki ya yi mugun ɓaci? Jin shi yake tamkar ya shaƙe ta ta mutu ya huta, ya dubeta a zafafe,kiji nan kafin da safe kiyi ƙoƙarin sanar da ni kowanene ya yi miki wannan cikin,ya juya fuu ya fita tare da bugo ƙofar.


Ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un,wane irin mummunan zato ne wannan Uncle za ya yi min? Ta ci gaba da kuka,ya ma ƙi ya saurare na, yau shi ne har da marinta,to ko dai ya daina sonta ne? Shin dama haka ne maza ke yi? To in haka sukeyi me yasa Abbanta ba ya yi wa Ummanta haka? Ta tsorata da lamarin Uncle bata san me zai mata ba washegari cikin kishiyoyi,gara ta san nayi tun yanzun.


Fitar Uncle Tabawa ta miƙe cikin motoci domin tana laɓe tana sauraron duk hidimar da ake yi,jin Uncle zai fito ta ruga ta ɓoye,da gudu ta nufi Hadiza tana faɗin. "Antina zo ki ji." Ta shiga rattafo mata duk yanda ta ji, ta ce matar so har da mari ta sha,kin san ta dai dai wundon su na uwar ɗakin na maƙale, ciki tayo can a makaranta an zo a yaudareshi sai kuma Allah yasa ya gane. Hadiza ta ce kai Tabawa? Tabawa ta ce na taɓa kawo miki wani labari daga baya ki kaga ba haka ba ne? Hadiza ta dafa ta,ko sau ɗaya ba'a taɓa haka ba . Tabawa lallai ki ce lokacin fitar wannan matsiyaciyar matar ya yi,dama nafi jin haushinta sai inji da waccan guzumar ta bar gani yanzun tana jan zare na barta da ma in gama da wannan ne kai naji daɗin wannan labarin Tabawa zan baki goro da safe amma yanzun bari in je gurinta a zuwan na zo in yi mata sannu da zuwa ne, Tabawa ta ce kin yi daidai tama san an sani.


Lokacin da Hadiza ta shigo ta same ta tana kuka da sauri ta ƙaraso, lafiya A'isha? A'isha ba taji shigowar Hadiza ba sai dai ta ji magana akan ta, ta ce cikina ke ciwo. Hadiza ta ce assha to bari in kira Alhajin a waya. A'isha ta ce ai ya sani ya tafi ya zo min da Likita,harara Hadizan ta sakar mata shi ne zai je yazo da Likitan? A'isha ta ɗaga kai, Hadiza ta ce, Allah ya sawaƙe ta fita. Ta je gurin Tabawa tana cewa Tabawa gaske ne kuwa labarin da ki ka bani? Tabawa ta ce me ki ka gani ke? Hadiza ta bata labarin yanda suka yi, Tabawa ta ce to ke da kin zauna ne ta faɗa miki? Ko ance miki kowa ma irin ki ne? Hadiza ta ce ƴar iska ni zata yi wa bariki,ai muna cikin gidan ma ga yanda za a ƙwashe.


Shi kam fitarshi ke da wuya ya nufi sasan Jummai,tana zaune tana tunanin kada dai ta tura shi yaje kuma komai ya daidaita tsakaninsu? Kai ina ba zai yiwu ba, domin ta yarda da Malam É—ari bisa É—ari. Sai ko ga Alhaji ya shigo tamkar wani bijimin zaki, da sauri ta miÆ™e Alhajina lafiya? Ya zauna yana huci, ta ce kayi haÆ™uri ko mene ne ya ce wane haÆ™uri zan yi? Ya ci gaba, wallahi ba zan haÆ™ura da cikin da ba nawa ba, Jummai ta zaro idanu tare da dafa Æ™irji ban gane ciki ba? Ya ce A'isha mana yarinyar nan zuwana na Æ™arshe gurinta fashin sallah na samu tana yi, yanzun sai gata ta zo min da uban ciki don ina neman haihuwa shi kenan sai a kawo min shege? Zufa ce ta shiga keto ma Jummai,domin tana tsoron kada a juya a sake juyawa cikin ya zama na shi,ai ko da ta shiga uku. 


Ta juyo tamkar ta zuga shi, amma Malam ya ce mata babu wannan aikin ta ba zai tafi da zuga ba sai da kissa ta daure ta ce to Alhaji ko dai zuwan naka na ƙarshen ne ta samu cikin? Ya dubeta ta tana hailar ne za ta samu cikin? Jummai ta kuma jan dogon numfashi,ka dai a hankali, ya ce ke ni fa ba batun hankali cikin wannan lamarin, ta ce to ni bana sone ka ce zaka rabu da ita,ga mamakinta sai ta ji ya ce babu batun rabuwa amma sai na ji uban da ya yi mata wannan cikin,shiru Hajiya Jummai ta yi ilahirin jikinta kuwa rawa yake yi. Ta daure ta ce in ka samu wanda ya yi cikin tunda mu musulmai ne sai ka tuntuɓi malamai, ya dube ta ke ce kika fini sanin yanda zanyi? Ta ce a'a ya ce ki bar ni ya miƙe ya nufi gefenshi. Da kallo ta bi shi,takan rasa gane kanshi wasu lokutan itama ɗaki ta shiga ta kira Karima Aminiyarta, don jin wane mataki ya kamata ta ɗauka don cikin nan ba ƙaramin firgita ta ya yi ba.


Tsam, ta miƙe ko jakar ratayawa bata ɗauka ba domin tasan babu ko taro ciki, ta nufi barin gidan tun kafin gari ya waye ya yi mata tijara, gidan Anty Nafisa ta yi nufin zuwa saboda yanzun dare ne.


Da safe sai ta amshi kuɗin mota a hannunta ta nufi garinsu. Kafin ma ta iso babban titi ta samu mai mashin cikin mintuna suka isa gidan Nafisa sai da ya jira ta shiga ta amso mishi kuɗin. Mamakin ganin A'isha ya hana Nafisa zama har A'ishan ta dawo daga gurin mai mashin ɗin in da suka shiga ɗakin baccinta suka zauna bakin gado, Nafisa ta zuba ma A'isha idanu lafiya kuwa? A'isha ta nisa hawayen yana zuba daga idanunta,ta shiga rattafo ma Nafisa halin da take ciki da kuma wanda ta shiga yanzun nan,baki Nafisa ta saki tana kallon ta, lamarin kamar almara, ta ce shi da kansa Brother ya ce ba cikinsa ba ne? A'isha ta ce wallahi ya ma ƙi ya tsaya ya saurareni, balle ma yasan ga yanda Ubangiji ya juya lamarin cikin. Nafisa ta ce ni ko naji mamaki, amma yanzun yanda za'ayi bari in kira Anty Fatima ba zaki tafi gida ba,nan take ta shiga kiran layin Anty Fatima ko gaisawa ba su yi ba ta shiga sanar da ita abinda ya faru, cikin tsananin mamaki Anty Fatima ta ce,kada ki bar ta ta tafi zan zo da safe.


Ranar dai A'isha bata runtsa ba,Æ™wana ta yi kan sallaya tana me zubar da hawaye, tare da sanar da Allahu matsalolinta. Ko kusa bata so ta tsani Uncle shi yasa take yawan ba shi uzuri, yanzu da haka zuciyarta na bata tabbacin in yaji yanda lamarin ya kasance za ya yarda da ita,Æ™ila ma ya bata haÆ™uri. 


Shida daidai na sai ga Anty Fatima, ta tausayawa A'isha matuƙa yanda taga yarinyar ta ƙare ta fita daga hayyacinta. Nan Fatima ta shiga faɗa tana cewa, lallai Brother irin tsirfar da ya kama kenan Nafisa ta ce kin san ba haka yake ba,ni dai na ce ba haka aka barshi ba. Fatima ta ce shi dai ya sani yanzun dai ki tashi muje gidan Hajiyarmu ke Nafisa tunda mijinki ba ya nan ki zauna duk yanda aka yi zaki ji. Nafisa ta ce muje kurum babu wata matsala zan masa waya ai baya gari ne. Fatima ta ce shikenan mu je, cikin matar Anty Fatima suka tafi. Hajiyarmu ko tashi daga kan sallaya bata yi ba,ta ji sallama ta ɗago idanu ta dube su, suka zauna kan kafet suka jira har ta shafa, sannan ta dubesu ta ce lafiya? Nafisa ta ce da sauƙi, Hajiyarmu kallon A'isha kurum take yi. Anty Fatima ta ce wallahi Hajiyarmu Brother ne ya taso A'isha fa, gidan Nafisa ta ƙwana,jiya,-jiya daga dawowarta daga makaranta har an soma tsiya. Nan ta shiga rattafo ma Hajiyarmu Nafisa tana ƙara bayani, Hajiyarmu tayi shiru ɗakin ya yi tsit suna sauraron hukuncin da zata yanke. Ranta ɓace amma ba kasafai mutane suka cika gane ɓacin ran nata ba sai ƴaƴanta, ta dube su Nafisa ke da Fatima ku tashi ku koma gidajenku ita A'isha ku barta nan suka ce to, suka miƙe suka fito bayan sun yi musu sallama.


A'isha tana can maƙale gefe, Uwani ta shigo ɗauke da karin kumallon Hajiyarmu, ta dire a gaban Hajiyar, Hajiyarmu ta ce A'isha me ki ke son ci?


A'isha ta ce, sai anjima yanzun bana jin yunwa, to kurum Hajiyarmu ta ce bayan fitar Uwani, Hajiyan ta ce A'isha ki zama jaruma ba ki ga komai ba game da halin namiji,in zaki bincika duk matan duniya komai matsayin mace komai mulkin ta zata sanar da ke cewa ta yi kuka saboda namiji,wata ta yi shi a fili wata kuma ta yi shi a ɓoye, ta share hawayenta ta zauna a ɗakinta kema ina so ki saba na sani kina da haƙuri, to ki ƙara. Sannan ki dage da addu'a wata rana za ki ci ribar haƙurin ki, da addu'o'inki bana so ki sama ranki cewa an mishi asiri ne da sauransu,ki yarda a ranki cewa jarabta ce daga Allah, sannan ko a waya bana son mahaifanki su san ga halin da ki ke ciki,ki zama mai ɓoye sirrinki zaya kasance ki sanar da su hankalinsu ya tashi ke kuma nan ku zo ku shirya da shi kin ji duk abinda na faɗa? Kan A'isha yana ƙasa ta ce,eh insha Allah zan kiyaye. Hajiyarmu ta ce na gode yanzun ina son ki ci abinci kinga ba ke kaɗai ba ce, sannan ki yi wanka,matso nan ki zuba abinda ranki ke so, sannan ta miƙe in kin gama kiyi wanka bari in hau gurin Alhaji, A'isha ta ce to.


Cikin natsuwa ta yi wa Alhajinmu bayanin komai,shiru ya yi na tsawon lokaci, can ya nisa ya ce "Shikenan ki barta a nan kada a neme shi." Hajiyarmu ta ce, "Ni lamarin shi yanzun yana bani mamaki, haka kurum duk ya bi ya ruÉ—a kanshi, ya hana kan shi sukuni." Alhajinmu ya ce,ki bar ni dashi kawai wannan karon, zan taka mishi birki, Hajiyarmu ta ce bari in shirya maka abin kari, ya ce inda tuwon nan nafi son shi, ta ce da akwai bari inje in É—umama maka,ta fita shi kuma ya ci gaba da nazarin matsalar É—an nasu,ko harkokinshi yanzun ba kamar da yake tafi da su ba,lallai dole ne ya zauna da yaronnan in har yana da wata matsala ne mu sani.


Daren Alhaji Saddiƙ bai runtsa ba,ya yi duk iyaka nazarin da ya kamata ya yi amma zuciyarshi ta ƙi yarda cewa A'isha zata aikata wata alfasha,ya tambayi kanshi cewa to ko cikin ruwa tasha? Domin dai ya tabbata zuwanshi na ƙarshe tana Haila. Hajiya Jummai ta so ta lallasheshi amma ya dakatar da ita kan cewa ta barshi ba ya so a dame shi.



****     *****     *****


Yana dawowa daga sallar Asubahi, gefanta ya nufa dole ne ta mishi bayanin inda ta roro wannan ciki? Ko tana nufin taje jami'a ne idanunta sun buɗe? Da wannan tambayar ya tura ƙofar ko ina ya duba bai ganta ba don haka sai ya za ci tana bayi,shirun da ya ji ya yi yawa ne yasa shi duba bayin,bata ba dalilinta, ya tsaya shiru sai kuma ya fita gurin Baba maigadi ya nufa,bai amsa gaisuwar da Baba maigadin ke masa ba, tambaya kurum yake masa,Baba ko kaga fitar Beby? Baba maigadi ya ce gaskiya ba wanda ya fita yau, sai dai kuma jiya da dare Hajiyar da ta dawo ta fita, amma bata dawo ba, ya ce ita nake faɗa,tun jiya kenan ta fita? Baba ya ce,ƙwarai kuwa ya juya cikin sasan Jummai zuciyarshi tana harbawa, to ina wannan yarinyar ta nufa? Me take nufi? Ya zauna bakin gadonshi ya lalubo wayarshi ba za ya iya tuna rana ta ƙarshe da ya kira wayarta ba,nan ya lalubo lambarta ya shiga kira, sai ta yi tayi har ta yanke ba'a ɗaga ba, shi bai ma san bata ɗauki wayar ba ya fito ya shiga mota sai da ya hau titi sannan ya soma tunanin ina ma zaya nufa ne yanzun? Ya kira Nafisa don yasan yanda suke,ya ce mata sister ko A'isha ta zo? Nafisa ta ce, a'a ta dawo ne? Ba tare da ya bata amsa ba ya katse wayar, gidansu Hajiyarmu ya nufa babu kowa cikin falon kai tsaye ya nufi ɗakin Hajiyarmu daidai lokacin da A'isha ke shan wani ɗan kunun gyaɗa da ta tarfa cikin kofi don dai kada Hajiyarmu ta ce bata ji maganar ta ba,yana ganin ta sai ya ji wani sabon ɓacin ran.


Ke me ya kawo ki nan gidan? Kina zaton za'a tursasa ni ne in amshi cikin da ban san daga ina yake ba? Ta zuba mishi idanu, muryarta na rawa ta ce, "Uncle da ace zaka saurareni da ka gano yanda Ubangiji ya zo da al'amarin. Ba zan saurari shirme ba, kuma ina so kiyi maza ki fita daga nan gidan, muryar Hajiyarmu ta katse shi gidan ai bana zaton naka ne ko? Ya juya da sauri, kada ku yarda da dukkan abin da yarinyar nan zata gaya muku."


Hajiyarmu ta ce, "to ubana." Jin haka yasa shi yin shiru tare da kauce mata daga hanya. Ta nuna ƙofa sai anjima ko? Zai yi magana ta haɗe fuska,sai ya fita domin babu shaƙuwa tsakanin su ko in ce suna jin nauyin juna.


Saman Alhajinmu ya wuce, Alhajin yana cin tuwanshi, Uncle ɗin ya shigo da sallama,kan kafet ya zube ya dubi Alhajinmu ga mamakin shi sai yaga fuskar Alhajinmu tamkar hadarin mangariba murtuk, iya tsawon rayuwarshi bai taɓa ganin Alhajin cikin wannan yanayin ba,nan take fargaba gami da tsoro suka shige shi cikin sanyin jiki ya zauna kan kafet ya soma da gaida Alhajin a dake kuma ba tare da ya dube shi ba ya amsa zai tashi Alhajin ya dakatar dashi da hannu.




######

[12/20, 23:02] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 7*



Ya koma ya zauna cike da tunanin me zai biyo baya,ya san Alhaji tamkar yunwar cikinsa, dattijo ne mai sauƙin kai mai zafi kuma ga wanda ya taɓa shi, sai da ya gama karyawar shi tsaf sannan ya dube shi jeka ɗauki matarka kuje gurin Doctor gani nan zuwa,za ya yi magana Alhajin ya katse shi da cewa, kada ka ce min komai bana son ji, Uncle ya miƙe ba tare da cewa ƙala ba, ya fito yana tunanin shin me yarinyar nan ta faɗa ma mahaifansa ne da zafi irin haka? Na shi ganin ai ita ce da laifi,laifin ma mai girma.


Ɗakin Hajiyarmu ya koma shima ranshi a ɗaure ya ce ke taso, Hajiyarmu ba ta ce ƙala ba, ganin haka sai A'isha ta miƙe ba tare da tasan inda za suje ba,ko cikin mota ƙala bai ce mata ba ita kuma ba tace mishi ba, sai dai taga sun tsaya asibiti. Tun kafin su iso Likitan yasan da zuwansu don sun yi waya da Alhajinmu, don haka suna zuwa Likitan ya shiga yiwa A'isha tambayoyi.


Tun yaushe rabonki da al'ada? Uncle ya zuba mata idanu yayinda shi kuma Likitan yake ƴan rubuce-rubuce, ta ce yau ƙwana shida kenan, Likitan ya ajiye biron hannunshi ya ɗora hannuwanshi kan teburin shi tare da maida hankalinshi kacokan gurinta,kina nufin duk wata kina al'ada? Ta ce eh, cikin ya shiga ne bayan wanda ya fita anan watanni bakwai da suka wuce? Babu wanda ya ji takun sawun Alhajinmu sai kaɗai muryarshi suka ji ya ce ai cikinne bai zube ba, dukkan su suka juya suka dubeshi,ya ƙaraso yana ce ma Likitan shi yasa na ce ka ciro fayal ɗin ta ka duba sannan ka duba ta, Likitan ya bashi gurin zama sannan ya ci gaba da aikinshi, Uncle kuwa jinsu kurum yake yi yanzunne ya gano zancan da ta shirya wa tsofaffin nashi suka hau kai suka zauna, bayan tambayoyi da bincike gami da aune-aune sai kuma ya kira wani Likitan daban shi kuma (scan) ya yi mata sai da ya fitar da sakamakon sannan ya ba Doctor ya fita nan dai Doctor ya tattara bayanai ya tabbatar musu cikin nan shi ne dai bai faɗi ba, sannan yana cikin ƙoshin lafiya. Uncle ya yi zaraf ya ce, "Likita dama in mata suna da ciki suna fashin sallah ne?" Likitan ya zauna ya yi mishi dogon bayani tare da tabbatar mishi cewa akwai matan, kuma itama hakanne ya faru gareta, duk da yanda yake jin tsanarta cikin ranshi amma wani sashen na zuciyarshi na murna da wannan labari.


Ƙwarai ya so ya tafi da ita gida, amma sai Alhajinmu ya ce ya kai ta gidanshi can gurin  Hajiyarmu, duk da ba taga canjin komai daga gare shi ba,ta ji daÉ—in yanda ya amince da cikin koda suka dawo har yanzun Hajiyarmu bata sakar mishi fuska ba, ya fito ya nufi gida.


Hajiya Jummai ta ƙosa ya shigo domin ta ji me yake faruwa, da kanta ta taka har gefen A'isha, amma bata nan lamari fa zaya jagule mata in bata yi Sa'a ba,ga Hadiza kuwa murna ce fal zuciyarta,tasan ƙarshen A'isha ne ya zo,wa ya sani ma ko tun jiyan ya danƙara mata saki? Inji Tabawa, Hadiza ta ce Allah yasa hakanne. Lokacin da maigidan ya dawo bai ce komai ba, Jummai kuwa ta yi ta maza ta daure bata ce mishi komai ba har sai da ya yi wanda ya zauna cin abinci, ita kuma tana kusa da shi tana zuba kissa da salo,can ta ce waini Alhaji daga masallaci ina ka nufa? Ya dubeta, gidan su Alhajinmu naje. Suna lafiya? Ya ce lafiyarsu lau, suna gaida ku." Ta yi shiru don tana son sanin ta ina zata fara batun A'isha? Can sai ta kira Uche wanda yanzun ta ɗauke shi zuwa sasanta, ta ce shirya breakfast ka kai wa A'isha ko? Uche ya ce to zaya tafi sai Alhaji Saddiƙ ya ce bata nan,da sauri ta sha mur sai ka ce gaske,bata nan ina ta je Alhaji kada dai ka ce min ka saki yarinyar nan? Ya dubeta dama na ce miki zan saketa ne? Cikin sanyin jiki ta girgiza kai alamar a'a, ya ce to ƙyamin wannan tambayar, kiyi harkar gabanki wannan ba matsalarki ba ce,ta karkata kai Allah ya baka haƙuri ni kaina bazan so ka rabu da ita ba,dama ganin yanda ranka ya ɓaci ne. Ya miƙe tsaye ya nufi ɗakinshi ba tare da ya ce mata ƙala ba.


Lamarin fa ya dagule wa Jummai lissafi,in maigidan ya yi kamar zaya juyu son rai sai kuma ya murɗe, tana fa so ta san shin ina aka ƙwana ne batun cikinnan? Dole ta je gurin Malam yau saboda ya yi mata bayani filla-filla, Lallai kam zata ga boni in har su Hajiyarmu suka ji batun ciki.


Ɗakin A'isha yana daf da na Hajiyarmu,tuni tasa aka gyare shi A'isha tana ciki a ƙwance tunanin rayuwa kawai take yi, ashe akwai wani lokaci da zai zo Uncle ɗin ta ya juya mata baya? Musamman irin wannan lokacin da ya kamata ace ya jata a jiki,ya so ta ya riritata, amma ba komai ta sani jarabta ce ta Ubangiji yana jaraba bayinsa ta kowace hanya, ta yarda itama yana jarabata ne don ya gwada imaninta, Uncle kuwa tana ta ƙara ba shi uzuri ba ta so ta tsane shi.


Yau ƙwananta uku a gidan tana cin gyaɗa dafaffiya da ta ce tana so Hajiyarmu tasa aka dafa mata, Nafisa ta shigo da sallama tare da ƴar tsokana tana cewa mai ciki Uhum ga ni nan tafe, A'isha ta yi murmushi ta ce Anty Nafisa ce yanzun? Ta zauna tare da ɗiban gyadar tana cewa tun ɗazun na zo ina gurin Hajiyarmu ne, A'isha ta ce ina yini? Suka gaisa ta ce Yaya Bebynmu? A'isha ta yi ɗan murmushi ta juya zancan da cewa yau fa sauran sati ɗaya mu koma makaranta, Nafisa ta ce har an gama yajin aikin? A'isha ta dubeta da sauri ba yajin aiki mukayi ba. Nafisa ta ce to tabbas ni naji da kunnena makarantarku suna barazanar tafiya yajin aiki,in har ba a biya musu buƙatunsu ba. A'isha ta ja tsaki, Allah yasa kada a tafi. Nafisa ta ce amin, Brother ya zo kuwa?


A'isha ta yi guntun murmushi, ina ganin abubuwa sun mishi yawa ne shi yasa, Nafisa ta kalleta cike da tausayawa,ke dai A'isha ba ƙya son laifinsa ne, amma in yana gari kullum sai ya zo gidan nan, yanzun dan kina nan ne shi yasa ya daina zuwa. A'isha ta ce to ni me zan ce? Nafisa ta ce, Allah duk da ke ma shiyasa yake miki wannan abin,ni duk son da nake maka wallahi in ka taka ni zan nuna maka kuskuran yin hakan. A'isha ta ce to Anty Nafisa kin san ko na mishi wani laifi ne? Ai da baya min haka, sai in ga tamkar nayi butulci in har na manta irin rainon da Uncle ya yi min a baya. Nafisa har da tagumi tana kallonta, kafin ta ce A'isha ke kam ban ma san irin ki ba,ko son shi ne ya yi miki yawa? Oho, A'isha ta yi guntun murmushi, sannan ta ce ke ba ki son Uncle Bello? Nafisa ta ce so kai amma fa bashi zai hana in ya min wulaƙanci in kasa ramawa ba.


A'isha ta tsura ma ƙasa idanu,son kawai take ta tuno ta ya ya zata iya yin sa'insa da Uncle ɗinta? Ko rama wulaƙancin da ya yi mata? Nata ganin yana mata hukunci ne sakamakon wani laifi da tayi mishi, damuwarta ɗaya shine ya sanar da ita wannan laifin ko zancan ciki ta mishi uzurin rashin sani ta kalli Nafisa tare da girgiza kai ni kam Uncle yana da wata irin ƙima a idona,ba zan iya ɓata mishi rai matsawar ina sane ba, kuma ko yanzun nasan duk yanda aka yi ina da laifin da nayi mishi mai girma,tsaki Nafisa ta ja sannan ta fita daga ɗakin,yarinyar ba zata gane cewa maza ba'a musu haka ba.


Daren ranar Alhaji Saddiƙ ya zo da daddare falo ya samu iyayan nashi cikin girmamawa ya zauna ya gaida su, Alhajinmu ya fi sakar mishi fuska,shima ɗin ba kamar yanda ya saba ba, ita ko Hajiyarmu da ƙyar ta amsa kalma ɗaya daga cikin jerin gaisuwar da ya jero mata,nan ya shiga kame-kamen cewa ya yi tafiya ne shine dalilin rashin zuwanshi, sannan in ya nemi Alhajinmu a waya bata shiga,sai Alhajinmu ya canza maganar da cewa ɗazun kaga baƙi a Office ɗinka? Ya ce ,eh sun zo mun kammala da su, zuwa satin sama zamu tura musu da kuɗi in mun ga kayan nasu. Alhajinmu ya ce, shikenan,ya yi ɗan jim sannan ya ce, A'isha na ciki? Hajiyarmu yi tayi tamkar bata ji shi ba,isowar Uwani kenan ta dire mishi ruwa ta ce eh tana ciki,ya miƙe ya shiga, daidai lokacin da A'ishan ke kan sallaya hannuwanta a sama idanunta suna zubda hawaye,tana cewa ya Allah kai ne mahaliccina da kai na dogara, kai ne kaɗai zaka sama min mafita cikin lamarin nan nawa da mijina. Ya Allah daidaitamu cikin gaggawa, Allah ka shafe wannan matsalar tamu,nan ta shiga kiran Ubangiji cikin sunayen shi keɓatattu,yana tsaye yana kallonta har ta shafa sam bata san da mutum ba, ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya shiga cikin ɗakin,ta bishi da kallo har ya zauna ta miƙe ta nufi ƙofa,ya danne wani abu da ke taso mishi ya ce ina zaki? Ta ce zan kawo maka ruwa ne, ya girgiza kai yanzun nasha a falon su Hajiyarmu, ta dawo ta zauna kan sallaya sannan ta ce ina yini? Ya amsa cikin cijewa domin lokacin wani irin haushinta zai ce ko tsana ma? Bai san ya ya zai kira abin ba, duk da ƙoƙarin dannewar da yake yi fuskarshi ta canza, ya daure ya ce ya ya jikin? Ta ce Alhamdulillah, ta sake duban fuskarshi gabanta ya faɗi saboda ganin irin yanda ya ɗaure, duk da haka ta daure ta ce, "Don Allah Uncle kayi haƙuri,bisa ga laifin da nayi maka,koda dai ban san laifin ba,ya miƙe tare da juya mata baya,ba abinda ya kawo ni yanzun ba kenan nazo ne na duba ki sannan ki min lissafin abinda ki ke buƙata ke da Bebyn."


Ta tsura ma bayanshi idanu bata gajiya da yaba mishi cikin kowace Irin shiga, muryarta a sarƙe ta ce sai dai ka tambayi su Anty Nafisa, ya juyo duk abinda suka zaɓa miki ya yi? Ta ce eh, sai dai batun komawata makaranta, ya kuma dubanta yaushe ki ka dawo? Ta ce, Uncle mu ba ayi mana hutu, ya juya baya domin in yana kallonta sai yaji ranshi ya fi ɓaci,ya ce makarantar ku sun tafi yajin aiki,ko dama ba a tafi ba bazan bari ki haihu can ba." Ya nufi waje ni na wuce hope ba wata matsala? Ta ce babu,ka sauka lafiya, har ya kai bakin ƙofa ta ce, "Na manta Uncle." Ya tsaya ba tare da ya juyo ba, ta ce wayata da kayana. To, kurum ya ce ya wuce, don ya ƙosa ya bar ɗakin, haka kurum yake jin tamkar ya make ta,yana barin ɗakin sai ya ji shi sakayau, ga mamakinshi da ya fito sai yaga mahaifan nashi sun canza mishi, da alama shigarshi gurin A'isha ya yi musu daɗi,nan ya nufi gidanshi.


Haka A'isha ta ci gaba da zama gidan surukanta gata na duniya tana ganin shi matsalarta ɗaya ce, Uncle ɗin ta wanda har yanzun yake nuna mata tsana da tsangwamma. Lura da ya yi cewa su Hajiyarmu ba su da matsala in dai suka ganshi ya zo da gurin A'isha shiyasa shi kuma kullum zai zo da safe in ya taso Office ma ya sake biyowa,duk kuwa da kasancewar dole yake ganinta,na ta gefen kuwa ta kan ji daɗin hakan duk da ba wata magana mai daɗi ko kulawa yake mata ba, sai dai ta lura yana matuƙar ƙaunar cikin in tayi la'akari da yanda ya narko ma Anty Nafisa kuɗi wai su je suyi siyayya, sai ga Anty Nafisa niƙi-niƙi,wai ta zo suje siyan kaya,da taƙi zuwa sai da Hajiyarmu ta ce ta kimtsa su tafi dama Likita ya ce ta ringa motsa jiki,ko a can idanu ta zuba Anty Nafisa ta ringa jidar kaya tamkar hauka, kuma bayan sun dawo washegari sai ga Nafisa da wasu shirgin kayan wai na Bebynta ne ta fara siya kafin ta yi ɓari, A'isha ta ce Anty Nafisa maimakon ki ajiye su tunda dai zaki samu wani, Nafisa ta ce don zan samu wani sai naƙi yiwa ɗan bros ɗina hidima? A'isha in baki sani ba yaron da Brother zaya haifa, shi ne gaba da duk wasu ƴaƴa da zamu haifa,koda gurin mahaifanmu, ballantana mu. A'isha ta yi ɗan murmushi ita kanta tasan hakan da Nafisa ta faɗa gaskiya ne.


Ga su Jummai kuwa gata nan zaune gaban Malam tana sanar da shi damuwarta, ta ce Malam da farko fa har ya ce cikin ba nashi ba ne, amma yanzun ya dawo ya amshi cikin, kuma sai faman zumuÉ—i yake yi kan cikin nifa na fi so inga an yi waje da cikin. Malam ya na jin ta kuma yana zuba aikinsa, ya dubeta kafin duk wannan aikin ina cikon kuÉ—ina? Ta jawo jaka tana cewa, matsalarka kenan, kuÉ—i,ya ce kina zaton zan zauna ne in ta aikata saÉ“o a banza? Ba duniyar bayan dama na san a lahira sai dai in ana bada haya mu kama? Hajiya Jummai ta ce,ni dai gashi nan ya ya batun aikina yanzun? Ya ce sauÆ™i ne, amma in kin tafiyar dashi yanda na baki, cikin É“arin jiki ta ce zan tafiyar malam,kai in ka faÉ—i abu matsawar an yishi babu mishkila aikin zaya tafi daidai, yanzun ka faÉ—a min duk dokar da ka ke so in kuma in cika aiki, ya dubeta ta na farko dai cikin nan sai an haife shi, sai dai in an haife shin asan yanda za'ayi da shi, sannan kamar yanda na taÉ“a gaya miki duk wadda ta soma haihuwa a gidan ita ce matar da zata zama uwar Æ´aÆ´anshi, sai dai in za kiyi Æ™oÆ™ari in ta haihu ki kawo mana mahaifarta."  Hajiya Jummai ta shiga share zufa, zuwa can ta ce tabÉ—ijan aiki, Malam ya ce ba wani aiki ba haihuwar asibiti ba ne? Da zaran kin samu masu amsar haihuwar kin jona su da É—an wani abun zasu É—auko miki, ta ce to in kuma gida ta haihu fa? Ya ce ya ya kike yi kamar ba mace ba? Bana jin tunda sheÉ—an ya sara muku za'a samu wanda yafi ku iya makirci,ke cikin irin taki kissar ba zaki iya É—auko mahaifar ba? Ta yi jim sannan ta ce zan Æ™watanta sai dai baka sanar da ni me za'ayi da mahaifar ba,don na fi zage dantse.



#######

[12/21, 08:48] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 8*



Ya ajiye allon dake hannunshi in har ki ka samu nasarar kawo min mahaifarta kin haye,don ina mai tabbatar miki ke kanki sai kin haihu, ita kuwa zamu ruɓar mata da gabanta yanda ma mijin ba zai je kusa da ita ba, sannan zamu maida ita juya har tsawon rayuwarta ba zata kuma haihuwa ba. Cike da farin ciki mai tsanani Hajiya Jummai ta ce ni ko ko tawane hali zan nemo mahaifarta zan dai haihu ka ce ko? Ya ce cire shakka, ta ce aikinka ba shakku a ciki, gafarta malam sai dai in ba a dire maka kuɗi ba, ya ce ashe kin gane kuɗin aikinki dubu ɗari da saba'in za ki bada in kin kawo mahaifa sannan zaki ba da kuɗin, ta ce aikin ma ya yi sauƙi na gode zan ƙoƙarta,kun ji matan da suka ɓata suka bar Allah da Manzo (S.A.W) Allah ka shirye mu.


Hadiza ma halin da ta ke ciki kenan, ya ya za'ayi taga bayan A'isha,ga ƙaryar ciki da ƙaryar ɓari,ga kuma amsar kuɗi hannun miji kafin ya yi auratayya da ita, duk sun haɗu sun firgita shi, shi da kanshi Alhaji Saddiƙ ɗin in ya zauna sai ya yi ta tunanin yanda aka yi yanzun baya gane kanshi, kuma yana da yawan addu'a ga ƙyautata ibada, haka nan mahaifanshi biyu suna tsaye kanshi da addu'a.


Wata tsurfa da Jummai ta É—auka shi ne kullum zata zo gidan su Hajiyarmu dama-dama take da A'isha tare da nuna kulawarta ga A'ishan,tun A'isha tana É—ari-É—ari da ita har ta saki ranta. Su Nafisa ne dai ma suke cewa A'isha tayi hankali da Jummai,in Hajiyarmu ta ji sai tayi musu faÉ—a tare da cewa wato zunubi ne koda ya kasance gaskiya ne, A'isha kam ta É—auki nasihar surukar tata kan cewa kada ta saka batun su Nafisa cikin ranta, ta zama mai zama da kowa cikin zuciya É—aya. Wannan ne ma yasa har  hira sukan yi da Jumman, tunda dama ba su taÉ“a faÉ—an sa'insa ba, ita dai in taga Jumman ne sai gabanta ya ringa faÉ—uwa,sai ga Jummai an je kasuwa an jido kayan beby na mahaukatan kuÉ—i an zo ana nuna ma maigidan, shi ko baki ya taÉ“a dan duk wanda za ya Æ™yautatawa A'isha shi ka baya birge shi, duk da wasu lokutan yana ji cikin zuciyarshi cewa ba ya Æ™yautata mata da ya so ya yi nazari kan abinda ya ke mata sai ya ji tamkar ana raÉ—a mishi a cikin kunnanshi ce wa ita taja duk abinda kai mata,in ya tambayi kanshi cewa da tayi ma ka me? Sai yaji zuciyarshi ta soma zafi ranshi ya shiga tafasa saboda kisisinar Jummai har faÉ—a suke yi da Alhajin kan A'isha, wata ranar juma'a ya shigo ganin su Hajiyarmu bayan sallar juma'a kamar dai yanda ya saba yi kowace ranar juma'a cikin É—akin Hajiyarmu ya samu Jummai rashe-reshe tana shan farfesu,ya shiga yana cewa Æ´ar gidan Hajiya wai me take baki ne, kullum kina nan? Cikin murmushi ta ce ina zuwa taya A'isha rainon É—anmu,ka dai san yanda na matsu mu ga Bebynmu.


Hajiyarmu tana kan sallaya duk da ta idar da sallar tuntuni tana ta addu'o'i,ya gaishe ta cikin girmamawa, ya sani Jummai zata yi ta jan shi da hira ne shiko ba za ya sake ba gaban Hajiyarmu, don haka sai ya miƙe. Ya samu A'isha zaune kan sallaya duk ƙafafunta sun kumbura, cikin ya yi ƙato ita kuma ga ta duk ta sirance ta ƙare yana son ya tausaya mata, amma ya kasa maimakon haka ma sai haushin ta. Ya juya mata baya kamar ko yaushe wannan ɗabi'a tana mugun baƙanta ran A'isha,ya ya Uncle zaya dinga juya mata baya? Nata ganin tamkar rahamar Allah ta juya baya daga gare ta ne, muryarshi ta katse ta kina bin dokokin Likitan kuwa? Cikin rawar murya irin ta me kuka ta ce eh,ya ce wai ke baki da wani aiki sai na kuka? Salon wani ya ji ya ce ina cutar da ke ko? Ta share hawaye sannan ta ce Uncle ina kukan baƙin ciki ne tare da yin tir ga rayuwata,na aikata laifin da mijina ya kasa yafe min, duk da ban san laifin ba. Ya juyo,na ce kin min laifi? Ya sake kauda kai daga gare ni baki min komai ba. Ta miƙe ta zo bayanshi sannan ta durƙusa gwiwowinta ƙasa, Uncle don son da Ubangiji yake yiwa Manzonsa ka taimake ni ka sanar dani laifin da na yi maka, kada ka barni cikin duhu, nasan laifin mai girma ne domin idanunka ba sa son kallona,haka zalika kafi son juya bayanka daga gare ni, ta kama ƙafafunshi "Uncle don girman mahaliccinmu ka yafe min." Ji ya yi tamkar ta zuba mishi wuta a daidai inda ta riƙe, cikin wata matsananciyar tsawa ya ce "Sakar min ƙafa,kina hauka ne? Jummai ta shigo da sauri tana faɗin, "Lafiya,me ya faru?" Domin tsawar da ya daka ilahirin wanda ke kusa ya ji, itama A'isha cikin masifar tsoro ta sakar mishi ƙafar,don makirci Jummai sai ta ɗaure fuska tare da ɓata rai ta soma cewa, "haba Alhaji, gaskiya abinda ka ke yi ya wuce min sherin,me yarinyar nan ta yi maka da ka ke mata wannan tsawar? Duk lokacin da nazo gidannan cikin damuwa nake ganin yarinyar nan kuma na san kai ne zaka sakata cikin wannan halin. Ya dubi Jumman,ita kin san abinda ta yi min ne? Ta ce ban sani ba amma ai komai na duniya ɗan haƙuri ne ko? A'isha ta iso gurin Hajiya Jummai cikin matuƙar son ta san laifin da ta yi mishi,ta ce Hajiya don Allah ki tambaye shi me na mishi? Hajiya Jummai ta dubeshi, Alhaji ka sanar da yarinyar nan laifinta domin gaskiya kana cutar da ita." Ya dube su ya yi shiru kamar yana son tunowa, can ya ce to wai ni na ce ne ta min laifi? Ni batayi min komai ba, duk abin da suke yi Hajiyarmu tana kallonsu sai lokacinne ta yi magana cewa, kurum ta yi A'isha taho muje. A'isha kam ta bi Hajiyarmu zuwa ɗakinta, Hajiya Jummai ta ce to ka gani ga shi ma har Hajiyarmu tana fushi da kai, ranta ya ɓaci bata son yanda ka ke yiwa yarinyar, tsaki kawai yaja sannan ya fita.


Koda Jummai ta shigo ɗakin Hajiyarmu nata zaton za ta samu suna tattauna batun Alhajin, amma sai ta samu Hajiyarmu tana waya, A'isha kuwa tana duba littafin Hisnul Muslim, ta zauna tana ƴan mitoci gaskiya Alhaji baka ƙyautawa.


Hajiyarmu ta gama waya, Jummai ta ce Hajiyarmu ya kamata a yiwa Alhaji magana baya ganin ba ita kaÉ—ai ba ce? A'isha bata da matsala ya ya zaya ringa matsa mata? Hajiyarmu ta ce ya yi dai mu gani, rayuwa ce amma cikin ran Jummai dam da murna sannan tafi kowa sanin dalilin da yake wannan abin ga A'isha ita dai burinta shi ne A'isha ta haihu gabanta ko daga ita sai ita,ta samu mahaifa ta ida tarwatsa rayuwar yarinyar.


Tana gama waya da su Ummanta, ta kishingiɗa. Allah sarki! Su Abbanta sun zata har yanzu tana cikin ƙwanciyar hankali ne,sai dai tasha alwashin ba zata taɓa sanar da su ba, domin ko me zata ce Abbanta ba zai yarda ba,ƙila ma reshe ya juye da mujiya,wato laifin ya dawo kan ta. Cikin wannan tunanin ne taji tamkar an mintsine ta a baya,dama duk ƙwanakin a zaune take ƙwana in zata iya kuma ta yi ƴan nafilfili a haka ta yi sallar isha'i. Hajiyarmu ta shigo tana ce mata,kin ci abinci? A'isha ta ce,na ci zan ma ƙwanta ne. Hajiyarmu ta ce kina jin daɗin jikinki kuwa? A'isha ta ce eh babu damuwa Hajiya, fitar Hajiyan ke da wuya ciwo ya dawo sabo, ita kaɗai ta dinga kai kawo sam bata za ci haihuwa ba ce,ga nata zaton irin ciwon dai da ta saba ji ne yau da kullum,ya yi ya lafa,ya yi ya lafa cikin dare,biji-biji tayi zuwa lokacin ta gama yanke hukunci mutuwa zata yi,taso ace Uncle yana kusa ko zaya tausaya ya yafe mata laifin da ta mishi wani irin ciwo take ji wanda bata taɓa jin ko labarin shi ba,nishi yazo mata ta ji tana nishi mai tsanani tare da salati sai taji tamkar ana buɗe ta sai kurum wani ruwa tare da yaro jim kaɗan sai ga wani abu shima ya faɗo ashe mahaifa ce. Yaro ya shiga yanka ihu ita kuma ta koma gefe tana nishi.


Cikin bacci Hajiyarmu ta yi mafarkin wai ga A'isha an banÆ™are ta za'a yanka mata ciki, ta farka da salati dama duk dare tana zuwa duba A'isha kusan sau uku,ta kan ganta zaune ko kuma tana nafila,tana nufo É—akin ta ji kukan baÆ™on duniya, da sauri ta shiga tana cewa ni Æ´asu ke Æ´an nan shi ne kina naÆ™uda ba zaki yi magana ba? Gashi ni yau sai Allah ya sauko min da bacci sannu kin ji? Ina kayan haihuwar? Ta nuna mata inda suke inda Nafisa ta ajiye su ko da yaushe tazo gidan tana shaidawa A'isha cewa tana jin burin É—in ciwo to ga kayan da zata É—auka nan,reza ta ciro ta yanke cibi sannan ta sa zani ta É—auki jaririn lokacin da take karanto addu'ar da zata tofa ma yaron, idanu ta zuba mishi gabanta ne ya faÉ—i domin yaron tamkar mahaifinshi lokacin da ta haife shi,kamannin ya yi yawa sosai,nan kuma sai ta samu kanta da jin nauyin yaron,don haka sai ta matso ta ba A'isha shi a inda take cikin jin nauyi. A'isha ta amshe shi nan da nan Hajiyarmu ta tashi duk Æ´an gidan suka shiga aiki, Uwani ita ce ta wanke yaro tas yayin da Baraka ta shiga gyara gurin Hajiyarmu kuwa gurin Alhajinmu ta nufa,kan sallaya ta same shi. Ya kalli agogo na jira ki sai naji shiru, shi ne na ce Hajiyar gidan nan yau batayi da ni, ya yi maganar cikin tsokana, ta ce Allah sarki,ba haka ba ne É—an bacci ne ya sace ni ba  farka ba sai da nayi wani É—an mafarki haka ina tashi sai kukan jariri na ji,yarinyar nan ashe naÆ™uda take yi ba ta faÉ—a ba, ita kaÉ—ai ta haihu, da sauri ya miÆ™e A'isha? Ta ce eh,nan ya shiga murna yana cewa alhamdulillah,ya so zuwa É—akin Hajiyarmu ta ce ana gyara su ne.


Zuwa wayewar gari ko'ina labari ya je ban da gidan Uncle,domin daga Alhajin har Hajiyar babu wanda ya sanar dashi,su Nafisa kuwa an zo ana ta murna da ko tuno shi ba su yi ba, maijego tamkar ba ita ba,ta shirya tsaf asibiti za su je don Likita ya duba su . Ita da Nafisa suka nufi asibitin. Likitan ya duba su kuma ya tabbatar da lafiya suke. Aka yi wa yaron (Bcg) suka dawo,Likitanne ya kira shi lokacin yana shirin fita zuwa Office,suna gaisawa Likitan ya yi mishi barka,nan take Alhaji ya shiga tambayar Likitan ta haihu ne? Cikin mamaki Likitan ya ce ba ka sani ba kenan? Shi yasa banga ka biyo su ba? Ya ce Likita suna nan ne? Doctor ya ce a'a sun zo na duba sune gida ta haihu ko da ya gama shirinsa sai ya sake shiga bayinsa ya yo alwalla, nafila ce ya yi raka'a biyu yana yiwa Allah godiya, fuskarshi fal annuri ya fito ya dubi Hajiya Jummai Beby ta haihu,jin zancan ta yi tamkar saukar aradu, amma ta dake ta ce me ta haifa ne? Ya ce ban sani ba sai naje zan ji, ta shiga É—akinta da gudu ta janyo gyalenta muje tare. A zuciyarta kuwa cewa take Allah ya bata Sa'a ta É—auko mahaifa.


Sun samu ɗakin cike da jama'a ƴan barka, Uncle ya shiga mutane suna mishi barka, Hajiya Jummai cikin nuna zumuɗinta ta shiga ina ɗan nawa? Allah sarki,ko ƴa ce? Aka ce mata ɗa ne, Nafisa ta ce gashi nan mai kama da mahaifinshi,yaron na hannun Jummai Uncle ya tsura mishi idanu,wani farin ciki yake ji tamkar yau aka haife shi,ya miƙa hannu Jummai ta ɗora mishi yaron,nan take ya yi wa yaron huɗuba tare da addu'o'i,ko Nafisa ba ta furta ba lallai yaron hotonshi ne ji yayi tamkar kada ya bada yaron ya zauna yana ta kallonshi kawai, kaɗan-kaɗan mutane suka ringa fita har su Nafisa. Yana ɗago kai tuni sun watse sai matan nashi kurum, ya dubi A'isha a ranshi yana so ne ya yi mata sannu amma yana kallonta sai ya ji tamkar ya ɗauke ta da mari, Nan take fuskarshi ta canza ya kuma juya mata baya, zuciyar A'isha ta sosu amma sai ta danne, ta ce Uncle Ina ƙwana? Da ƙurar kuma can ƙasan maƙoshi ya amsa,ta ce ka faɗa ma su Abbana? Hajiya Jummai ta ce sai dai yanzu ya faɗa,mu ma ba yanzun muka ji haihuwar ba,wai tun yaushe ne haihuwar? Kan A'isha yana ƙasa ta ce da dare ne. Uncle ya ce to kin ji abu da dare amma an kasa sanar dani. Hajiya Jummai ta ce Alhaji sai ka amshi mahaifar mu je gida ka rufe ko? Ya ce haka ake yi? Ta ce eh mana,ai ba'a wasa da ita,ya dubi A'isha sannan ya kauda kai, ina mahaifar? Ta ce sai dai a tambayi Hajiyarmu, Jummai ba ta san sanda ta furta Allah yasa ba su rufe ba, sai kuma ta riƙe bakinta saboda katoɓarar da ta yi, ya dubeta in an rufe a nan laifi ne? Ni fa bana son canfi,ta ce a'a ina fa laifi wai mu ma muce an taɓa rufewa a gidanmu.


Ya nuna murnarshi sosai a gaban mahaifan nashi da ƙannanshi, in da har yake tambayar ƙannan nashi me ake buƙata game da jariri da mamanshi? Nan take Nafisa ta shiga lissafi har da na tsiya, lokacin da Uncle ya sanar da mahaifanta sun yi murna sosai, Abbanta ya ce Friend na tayaka murna sosai, Allah ya raya mana ya ce Amin friend,na gode ina fatan za ku zo kada ka ce min don A'isha tana ƴarka ba za ka zo ba, dariya Abban ya yi kafin ya ce ban ɗaukar maka alƙawarin zuwa ba, sai dai ko bayan suna zan zo insha Allah. Dangin A'isha suma labari ya karaɗe ko'ina,ba labarin ciki sai na haihuwa, lokacin da labarin ya samu Hadiza tamkar zata suma don itama da yawa Malaman nasu sun sheda mata cewa duk wadda ta haihu cikin su shi kenan ita ce kurum zata yi ta haihuwa, kuma ta yi rantsuwa kan cewar in dai ba ita ce zata haihu ba, to sai dai kowa ya rasa cikin da yake cewa ba na shi ba ne shine zai amsa? In ko haka ne itama sai ta nemo shi wajen ai ba an fi su sanin kan bariki ba ne.






#########

[12/21, 18:37] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 9*




Hajiya Jummai ita dai damuwarta ta samu mahaifa, don haka lokacin da Alhaji zai fita bin shi ta yi gurin mota, faÉ—i take shin Alhaji ka amshi mahaifar? Ya dubeta,au Ina zuwa,ya koma ciki sai dai ya kasa tambayar mahaifiyarshi saboda nauyin da ke tsakaninsu,ya ce Nafisa zo mana,a gefe ya ke cewa ta tambaya mishi ina mahaifar don ya je ya rufe. Lokacin da ta yiwa Hajiyarmu batun sai ta bata amsa da cewa zasu yi ta ajiyar mahaifa ne ba za su rufe ba har zuwa yanzun? In kuma ya fi son ya rufe da kanshi to sai ya jira mahaifin nasu in ya shigo sai ya ce ya tono mishi yana son ya rufe da kanshi ne,yana jin lokacin da take faÉ—a wa Nafisa wannan batun,don haka sai ya juya kurum yasan har yanzun mahaifiyar tashi tana ciki da shi.


Jummai ta dube shi ka amso ne? Ya ce sun rufe tuni, ta zaro ido har ma ya tsaya yana kallonta, sun rufe? Ta ɗora hannu akai tare da cewa kash! Ta dubeshi ɗan jira ni in ɓari inzo muje gida, da sauri ta suri gyalenta ko sallama ba ta yi wa mutane ba ta wuce. Yana ƙoƙarin tada mota ta fito, sannan abinda ya dinga ba shi mamaki yanda duk surutun da yake yi bata san ma yana yi ba,ga uwar zufa da take zabgawa sai ka ce wadda ta haɗiye kunama. Suna isa gida tun kafin ya gama parking ta buɗe mota kaɗan ya rage ta faɗo, ta fita da sauri sauri gudu-gudu tana shiga falonta suna cin karo da Aminiyarta Hajiya Kari, ta ce Jummai tunda na samu labarin haihuwar matar mijinki na ce bari in zo kada kiyi sakaci, Jummai cikin wani huci mai tsanani ta ce na nawa kuma,ai an riga an gama sun rufe ta. Karima ta yi saurin cewa, sannu Alhaji dan ganin ya riga ya shigo kuma ga Jummai da shegen ɓarin baki, sannan ta yi mishi barka,cike da murna ya amsa tare da godiya, ya kalli Jummai ya ce, wani abu na damunki ne? Ta share zufa ta ce me ka gani? Ya ce duk kin canza irin kamar kina cikin mawuyacin hali? Ta kuma share wata zufar haba dai mu yau da muke cikin farin ciki? Ta yi ƴar dariyar yaƙe,ai mu yau dai babu bacci, ya tsura mata idanu Jummai wannan zufar fa? Ta ce tsabar farin ciki ne, sai ta soma matso hawaye shekaru nawa ba mu taɓa jin kukan ɗa ba cikin gidan nan sai bana, dole in yi zufa, Karima ta ce haba Jummai ai godiya zamu yi wa Allah ba kuka ba, Alhajin ya dafa kafaɗarta, Jummai na san dole ne kiyi murna, sannan ina miki albishir da zaran an tashi ya ye shi ke ce zaki ɗauke shi kiyi rainonsa har abada, ta dubeshi cikin muryar kuka tana cewa na gode Alhaji ni dama nasan ɗan ka ɗana ne Allah ya raya mana shi, suka ce amin ya ce bari in je in ɗauki wasu takardu ina da baƙi a Office suka ce to ya fita. Hajiya Jummai ta ɗora hannu a kai zata zunduma ihu Karima ta saka tafin hannunta ta rufe ma Jummai baki, sannan ta ci gaba da cewa kina hauka ne? Na kula garin taɓargazarki wata rana za ki tona kanki,ɗazun kin ƙwaci kanki yanzun in yaji ihunki ya dawo me za ki ce?


Cikin kuka Jummai ta ke faɗin na shiga uku ni Juma, yanzun shi kenan ni ko me nayi babu nasara cikinshi,na fi wata ina zirya gidan su Hajiyarmu na ringa daure zuciyata ina zama tare da tsinanniyar yarinyar nan ina kashe ma tsinanen cikinta kuɗi duk don in samu mahaifar nan amma haƙana bai cimma ruwa ba, Kari ta ce naji yi shiru ki shirya yanzun da ya fita muma sai mu nufi gurin Malam mu ji ta bakinshi.


Ya dubeta kin isa a yi miki jaje, domin in baki dage ba ƙila lokacin rushewar al'amuranki sun zo,yarinyar nan ita ce zata yi ta haihuwa dama kin yi nasara ne haƙiƙa da kin dace, cikin jimami ta dubeshi to ni yanzun yaya zanyi? Ya ce sai mun bincika ta ce yanzun in je in zura idanu kenan? Ya ce in kina da wata dabara sai ki je ki ƙwatanta, kafin mu mu binciko. Tamkar zata yi hauka ta baro gidan Malamin, Karima tana tausarta tare da lallashinta, tana nuna mata cewa ta yi a hankali kada mutane su gane halin da take ciki.


Gidan masu jego kuwa, al'umma sai tantsowa suke yi, wasu ma ba a san su ba,ƙwananta uku ƴan Jigawa suka iso, murna gurinta ba a magana har da su Jafar da Munnir aka zo,sai da Hajiya Lanti da Tabawa suka taushi Hadiza sannan ta zo barka, Hajiya Jummai ma ta cije ta sake zuwa ana gobe suna, yanda taga ana sauke kayan ciye-ciye da shaye-shaye ga gidan ya cika da jama'a sai hankalinta ya kuma dungunzuma ta bar gidan suna. Tafe a mota direba na janta tana surutai ita kaɗai.


Ranar suna yaro ya ci suna Usman,waton sunan Alhajinmu, labarta yanda sunan ya kasance ma ƙauyanci ne. Sun samu alkhairi mai yawa daga abokan Uncle har da masu ba shi motar zuwa makaranta. Hadiza dai babu wanda yasan tafiyarta. Jummai ma tunda ta yi arba da maijego tun daga ƙasa har sama take kallon A'isha kaya ƙarshen tsada ga gwala-gwalai tun daga yatsun ƙafa har zuwa na hannu,na wuya kam ai ba a magana, sai ta juya gida. Taro ya tashi lafiya danginta sun koma gida suna sambarka, haka suka ci da wankansu, A'isha tana matuƙar mamakin yanda dangin Uncle suke tsananin son yaron wanda Nafisa ta yi wa laƙabi da Abbul khairi, Hajiyarmu ce kurum ke karantawa bata ɗaukarshi, hakan ne ma yasa A'isha sam in Hajiyarmu tana ciki bata ɗaukar yaron ta bashi nono, sai ta dinga kara itama musamman tun bayan suna Alhajinmu ya ce su A'isha su dawo ɗakin Hajiyarmu. Matsalar A'isha ɗaya, Uncle wanda har yanzun bata cikin ƴan kayan shi duk da cewa wani lokacin abun yana damunshi, A'isha har ta soma ƙyau ta ci tasha duk abinda ranta ke so kuma Hajiyarmu ta ce kada ta damu da matsalar Uncle tana zaune za ya zo ya kawo kanshi.


Misalin ƙarfe huɗu saura ya fito daga sallar la'asar ya shiga gidan mahaifan nashi don yaga Abbul khairi. Yana shiga gefen Hajiyarmu sai ya soma jin kukan yaron, da sauri ya nufi ɗakin domin ji ya yi tamkar an watsa mishi ruwan zafi, kuma ƙila ɗakin babu kowa, amma ga mamakin shi yana shiga sai ya samu A'isha tana zaune tana cin abinci, Hajiyarmu kuwa tana sallah daga bakin ƙofa ya tsaya yana kallon A'isha,ji ya yi tamkar ya shiga ya hau ta da duka, waton tana zaune ma tana cin abinci? Ta bar yaro,ya ɗauki yaron ya fita a falo ya tsaya yana jijjiga yaron, zuciyarshi na ce mishi A'isha bata son yaron kamar yanda Hajiyarmu bata so shi ba lokacin yana yaro kai har zuwa yanzun a fili ya ce tab in dai haka ne gara ya kai ɗan shi gidan raino. Hajiyarmu ba ta tsaya doguwar addu'a ba,ta dubi A'isha,amso shi ki bashi ya sha, ta dubi Hajiyarmu tamkar ta ce a'a amma bata iya jan musu da Hajiyarmu, ta miƙe ta fita yasa kai zai fita daga falon zuwa inda zuciyarshi ta raya mishi watan gidan rainon yara sai ya ji muryar A'isha, Uncle ya juyo wai ka kawo shi in ji Hajiyarmu, ya zuba mata harara,ai dama nasan ba son shi ki ke ba, in dai irin rainon da Hajiyarmu ta yi mun ne zaki mishi gara na kai shi gidan rainon jarirai. Ta zaro idanu, yi haƙuri Uncle don Allah, ya dube ta ba zan amince da nufinku ba, duk cikin al'adun Hausa Fulani wannan al'adar ce bata yi min ba,babu hadisi ko aya da ta nuna cewa iyaye su dinga jin kunyar ƴaƴansu, tun ina ƙarami babu irin wuyar da ban sha ba,dan kawai ina ɗan fari da kaina na dinga addu'a Allah yasa mahaifina ya sake aure,ƙila matar zata kula dani,gara na kaishi in da zan zuba kuɗina a luran min dashi.


Dukan su ba suji shigowar Hajiyarmu ba, sai kurum suka ji ta ce A'isha koma ciki barshi ya kai shi ta kama hannun A'isha tamkar ta ƙwace, amma ba zata iya bijirewa ba, ta bi ta suka shiga ciki, A'isha tana zama bakin gado yana shigowa ya miƙa mata shi. Ta kalli Hajiyarmu sai tayi mata alama da kai,don haka sai ta amshe shi shi ko ya fita. Hajiyarmu ta dubeta kada ki dinga barin shi yana kuka, mijinki za ya iya raba ki da ɗanki, domin nasan da zaran ya sanar da mahaifinshi wannan matsala za ya gaya masa,baya kan ƙudirinshi,kin ga ku, ƴan zamani ne ki kula da ɗanki kin ji ko? A'isha ta ce to haka suka ci gaba da wankan su.


Satin su shida suka soma fita asibiti suka soma zuwa sannan gidan Anty Sadiya sai gidan su Fatima da kuma su Nafisa. Ranar da suka je gidan Anty Nafisa cewa ta yi to A'isha an gama wanka lafiya yanzun kuma sai azo a soma shirin gyaran jiki, A'isha ta taɓa baki um wane gyaran jiki bayan har yanzun Uncle yana fushi da ni? Nafisa ta ce ni fa nawa ganin tsakanin ku aka shiga, A'isha ta ce Anty Nafisa wanene zaya shiga tsakaninmu? Ni dai nafi zaton cewa na mishi wani laifi ne. Anty Nafisa tunda kuna shiri don Allah ki same shi ki tambayan min shi mana? Nafisa ta ce kada ki damu, insha Allah komai zai daidaita, yanzun dai bari na yi wa Hajiya Aliya waya can kaduna don gyara ki zan miki sosai, A'isha ta ce kin yi sabuwar Aminiya kenan? Ta ce"a'a dama muna tare lokacin da zan yi aure don dai kina makaranta ne baki ganni ba gyaran sati ɗaya naje tayi min amma ni kaina nasan nayi ne." A'isha ta ce ni da nike saran cikin watannan za'a buɗe mana makaranta ko da nayi wani gyara sai inga kamar a banza ne. Nafisa ta ce A'isha ban san ki da jan zance ya yi tsawo ba, A'isha ta ce to nayi shiru,nan take ta yi waya da Hajiya Aliya mai Zahra Global,suka gaisa Nafisa ta ce ƙanwata ce zata koma gidan mijinta daga wankan gida ina son ayi mata gyara ne sosai,Aliya ta ce wannan ba matsala zan aiko muku da duk abin da ya dace tare da bayani a rubuce, sannan zan miki ƙarin bayani ta waya, suka yi sallama A'isha dai idanu ta tsura ma Nafisa ba zasu ga ne bane,sun san irin wulaƙancin da Uncle ke mata kuwa?


Yanzun dai lamura sun juyawa Jummai,ƙwana take zaune tana saƙe-saƙen zuci, yanzun ita ce dai Jummai ita ce duniya ta yi wa haka, ashe akwai ranar da zata zo da kuɗin ta amma ta kasa samun biyan buƙatarta,shin Malamai sun daina aiki ne? Rayukan da ta kashe a baya ba kuɗinta ba ne ya biya mata buƙata? Yanzun ma tana da kuɗin amma malamai da bokayan su kasa,an ya kuwa ba zata ɗauki hukunci a hannunta ba? Wannan tunanin da shi take ƙwana kuma da shi take ta shi rashin barcin nan shi ne mafarin birkita lissafin ta.


Hadiza kuwa na ta ganin yanzun zata soma tashenta na shiga bokaye, tunda A'isha ta haihu. Su kuwa su Hajiyarmu sun duƙa addu'a fatansu Allah ya juyo da hankalin ɗan nasu ga matarshi, domin gaban kowa ya nuna tsana A'isha, kuma koda wasa bai taɓa batun komawarta gidanshi ba,hakan nan suma ba su ce mishi zasu maida ta ba, maimakon haka ma yanzun sun fi yi mata shirye-shiryen komawa makaranta don an dawo daga yajin aiki.


Sun yi shawarar haɗa ta da Uwani don kula da yaron tare da nemo mata ƴar aiki ƙarama. A'isha ta so zuwa gida, amma Abbanta ya ce a'a ta koma makarantar ta in ta kuma samun wani hutun ta zo tunda shi ya zo Ummanta kuwa suna waya koda yaushe,gurin Alhajinmu Uncle ɗin ta yaji batun komawarta makaranta,nan take ya yi kicin-kicin ya haɗa rai amma bai ce ƙala ba, duk da mahaifin nashi ya lura da hakan bai nuna ya gane me ɗan na shi ke nufi ba tunda dama ya dai sanar da shi ne amma ba wani gana neman izinin shi ba ne. Koda yaje gida ranar bashi da walwala gefen Hadiza yake ya shiga bai same ta ba sai Tabawa,nan take ya ƙara ɗaure fuska, ina Hadizan? Ta ce Um ta tafi gaisuwar mutuwa ne. Ya ce,a ina? Ta ce unguwarsu nan maƙotansu,tsaki yaja kafin ya fita ya tsani halin da wannan matan suke yi na fita babu izini, Allah ya sani shi ba zai yafe ma dukkan wadda ta fita babu izini ba, gefen Jummai ya nufa so yake ya watsa ruwa yaje gidan Nafisa,saƙo zai bata zuwa gurin mahaifiyarsu, ya sani in ta amince Alhajinmu ba zaya yi wuyar fahimta ba.


Lokacin da ya kira Nafisar ya sheda mata cewa zai zo don yana son ganinta sai ta ce itama tana son ganin shi dama ɗakin Jummai ya soma shiga tana zaune ta zabga tagumi duk ta yamutse ta yi baki yace Jummai lafiya wai duk ƙwana kin nan kin yi wani iri, ta ce (cikin rawar murya) ni wallahi duk duniyar nan ta isheni, ina ga dai an sa min hannu ne komai nayi sai ya lalact, cikin rashin fahimtar zancan ta ya ce me ki kayi ya lalace? Nan kuma sai ta dawo hankalinta ta gane da wa take magana, sai ta ce ni dai Alhaji to kalleni fa, Allah asiri ne to komai na duniya baya min daɗi ya zauna gefenta,haba Jummai ina Tauhidinki ya je ne? Kullum kin fi son ki ji ki cikin jin daɗi da walwala? Ki sani Ubangiji yana jaraba imanin bayinsa ta kowace hanya,shin baƙya ganin kema imanin ki ake taɓawa? Sai ta miƙe tsaye imani? Ni fa babu wani imani asiri ne. Tsaki yaja ya miƙe ya fita fasa yin wankan ya yi ya nufi motarshi,yana tuƙi yana tunanin matsalar mata ita ce ajalinshi, ya fito ya shiga cikin gidan, ita ce ta fito ta buɗe mishi ƙofar falo, ya shiga ciki yana cewa Sister na gaji da halin da gidana yake ciki na gaji da halin matana,mata uku amma ba wadda zan tunkara in ji sanyi? Mata fitina ne bala'i ne shin ku ma dama haka ku ke yiwa mazajanku? Dole ne ace mata kun fi yawa a wuta. Nafisa ta iso kusa da shi ta nuna mishi kujera zauna Bros kada ka faɗi zauna mu tattauna insha Allah zaka samu sauƙi.




#######

[12/21, 22:31] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 10*




Ya zauna ta ɗaga waya ta kira mai yi mata hidima, ta sanar da ita cewa ta kawo abin sha mai san yi tana da bako,ta haɗo da zoɓo ta ce to sai da ya cika kofi da zoɓon ya shanye tas,ya dubi Nafisa da gidan Hajiyarmu nasha zoɓon nan da na ce Beby ta yi shi. Nafisa ta ce wannan ma ita ce ta yi shi shekaran jiya da tazo. Ya ɓata rai shi ne ki ka ba ni? Nafisa ta dubeshi,Bros ka ce kana son ganina dama nima Ina son mu tattauna wata matsala, ya ce ina jin ki, ta ce ko dai ina jin ka fara sanar da ni taka matsalar Bros.


Ya gyara zama Nafisa wallahi na gaji da abin da matan nan suke min musamman A'isha. ta gyara zama me A'isha ta ke maka haka da zafi? Ya yi shiru yana son lakubo laifin da take mishi, amma ya kasa. Ya lumshe idanu, Sister na kasa tuna laifin da take min amma nafi jin haushinta. Nafisa kinga dai ke ƙanwata ce kuma ƙarama daga cikin ƙannena, ina miki rantsuwa da Allah ba zan tuna ɗaya daga cikin laifukan da A'isha take min ba, amma ina tsakanin jin haushin ta." Nafisa ta ce "Brother nima dalilin da yasa ni ke son ganinka kenan, to wannan abin ba sihiri ba ne kuwa? Ya girgiza kai tare cewa, a'a Nafisa kada ki zama cikin marasa yarda da ƙaddara komai ace sihiri Nafisa ta ce amma kasan gaskiya ne sihiri ko? Ya ce na sani amma wannan mu bar shi a ƙaddara, yanzun a taki shawarar mece ce mafita? Nafisa ta ce Yauwa nawa ganin dama lamuranmu ga Allah suke,to mu sake miƙa wuya gareshi, sannan mu samu malamai na ƙwarai su taya mu da addu'a, Brother ka rage bacci ya ce haka ne,kin san ni ne? Ta girgiza kai, ya ce a ƙasan zuciyata ina jin zafin abinda nake yi wa yarinyar, amma tsananin haushinta ya sha ƙarfina, sannan ƙarin damuwata wai yanzun shirin komawa makaranta su Hajiyarmu suke mata ga yaro bai yi ƙwari ba,dama saƙon da zan miki ga Hajiyarmu ki ce mata ban amince ba, sai yarona ya yi ƙwari."


Nafisa ta yi Æ´ar dariya, "Bros ba zan iya yiwa Hajiyarmu batun A'isha ba,don zata ce bakinmu É—aya da kai, kuma kaima a shawarce kada kayi mata magana, don kaima jiranka take yi ta warware ka, zuba musu idanu kafin lokacin da zamu samu warware matsalar ka." Ya ce shi kenan, bari in tafi ta ce dama kenan matsalar A'isha ce damuwarka?" Ya ce kusan haka ne, sauran ma da tasu matsalar amma bata shan kaina Kamar ta A'isha.


Ta fito da kasko yau Æ™wana biyu bata kara hantar a rushi ba,kai anya ma maganin yana yi kuwa? To ta gane tunda A'ishan ta haihu sai É“arin kuÉ—i kawai yake yi sannan in kana son gura ta yi tsawo to sai dai in labarin Abulkhairi zakayi mishi,bari taje ta aiki su Suby su É—ibo mata rushin wuta gurin matar maigadin maÆ™otansu,yau zata zafafa mishi zuciya, rufe ta samu Æ™ofar ta soma mitar cewa  Æ´an iskan yara yanzun haka sun bar gidan zan zo in san yanda zan yi da ku baza ku Æ™ara min hawan jini ba,bayan wanda nike da shi Allah ma ya sani. Tana tura Æ™ofar me zata gani? Suwaiba da Safiyya tare da wasu Æ™awayansu guda biyu tsirara haihuwar uwarsu suna aikata masha'a da junansu, sannan tsakar É—akin ga Æ™walabe nan na pakalin, totolyn da kuma wata Æ™waya wai roci. Jummai bata san lokacin da ta saki kaskon hannutaba tare da faÉ—in na shiga uku me zan gani? Wannan iftila'in da  ya faÉ—a mata ta gani da idanunta shi ne sanadin fashewar kaskon ta gami da zubewar gantar ta har ta manta da batun kasko,da me ya fito da ita daga É—aki ma,wata sabuwar damuwa ta shiga gami da tashin hankali mai tsanani,komai yana da sanadi wannan shi ne sanadin da Alhaji SaddiÆ™ yana zaune cikin Office É—in shi yaji shi tamkar yana jin Æ™ishi, sai da ya shanye goran swan water babba guda É—aya mai sanyi ya jingina yana mamakin kanshi, domin ya sani sai ya tashi daga Office bai shanye goran ba,jin zuciyarshi ya yi tamkar an wanke wani nishaÉ—i gami da annashuwa, ya rasa jin shi yake tamkar sabo yau akayi sht,nan take ya miÆ™e ya nufi fita daga Office É—in cikin zuciyarshi yana son ya ji shin shi ne kuwa? Sai yake ganin tamkar wani zai kalleshi ya kira shi da wani suna ba nashi ba.


Gidan Nafisa ya nufa bai shiga ciki ba a harabar ya tsaya ya kirata da waya,ta kalli mijinta ta ce "Dear,Bros ne wai ba zai shigo ba sauri yake yi." Alhaji Bello ya ce to ki je mana zan fito mu gaisa nima,tana isa gurin shi da fara'arta me zai hana ka shigo Bros sai kurum taji ya ce kalleni Sister ni ne kuwa? Ta zaro idanu ban gane ba kamar ya ya kaine? Ya ce ji na nike tamkar ba ni ba, ta ce kuma? Gaskiya ka tsaya da addu'a tsayin daka ya ce ina yi daidai gwargwadon hali, Alhaji Bello ya iso gurin yana cewa Alhajin Allah haÉ—uwa ta yi wuya, Alhaji SaddiÆ™ ya ce a'a dama kana ciki ne? Ya ce dawowata kenan garin, Alhaji SaddiÆ™ ya bashi hannu suka gaisa, ya yi yayi su shiga ciki amma ya ce sauri yake yi.


Cikin Æ™wanakin Alhaji SaddiÆ™ yana jin canje-canje  tare da shi, sai dai rashin lafiyar Hajiya Jummai ya hana shi nutsuwa sosai, zuwa aka yi aka sameta tana Æ™wance cikin matsanancin hali a Æ™ofar É—akin su Suwaiba, waÉ—anda su lokacin tuni sun bar gidan. Bayan gwaje-gwaje Likitan ya tabbatar wa maigidan nata da wata Æ™anwarta cewa jininta ya yi matuÆ™ar hawa fiye da da, sannan wasu alamomi sun sa mun yi mata gwajin suga, mun kuma gano tana dashi,ga kuma ciwon ta na tun farko waton zuciya,don haka tana cikin haÉ—ari,in dai zata dinga sa damuwa cikin zuciyarta. Alhaji SaddiÆ™ ya tausaya mata tare da buÉ—e bakin aljihunshi don ganin ta samu lafiya, dangi suna ta zuwa dubara yawancin su sukan ce sai dai suje don mijinta amma ba wai don halinta ita kanta ba domin ba tsarin ta ba ne zuwa duba mara lafiya ko gaisuwa,ko barka, duk yanda ku ke in ba irin Æ™awayansu ba.


A'isha tare da Hajiyarmu suka zo, sun same ta zaune ta jingina da filo fatan acca take ci watan tuni ta soma amfani da abincin masu shuga, cikin zuciyarta tamkar ta shaƙe A'ishan dan takaici,nan ta ture ƙwanon gabanta gefe tsani wannan tsinanniyar yarinyar,da ƙyar ta amsa gaisuwar su, maigidanne ya shigo yau ƙwana uku A'isha bata sa shi a idanunta ba,tun ranar da ya zo ya sake yi mata kashedi game da yaron shi kuma ya yi mata rantsuwa da Allah cewa in har ya samu labarin cewa ta tafi makaranta ta banzatar mishi da yaro zata sha mamakin hukuncin da zai yanke mata.


Bayan ya rage tsawo ya gaida gyatumarshi ta tambayi mai jiki ya ce da sauÆ™i, A'isha tamkar ko yaushe cikin girmamawa ta gaishe shi tasha mamakin yanda ya amsa cikin sakin fuska, idanunshi suna kallonta sannan ya iso kusa da ita yana cewa, kawo Alhajin nawa,wato Abulkhairi ta kunto shi daga bayanta ta miÆ™a mishi,yau idanunshi sun fi son kallon Beby fiye da yaron shi, itama ta lura da hakan ko in ce kusan duk Æ´an É—akin sun kula da hakan ne ma yasa Hajiyarmu miÆ™ewa tare da cewa juma Allah ya Æ™ara sauÆ™i, sannan ko tana buÆ™atar wani abu ne ta faÉ—a a kawo mata? Jummai wadda ta zurfafa tunani gurin tuno kaskon ta wanda sai yanzun ta tuno da shi a'a kawai ta ce ma Hajiyarmu ba tare da taji me tace ba, Hajiyarmu ta nufi fita tana cewa A'isha goyo shi mu je. 


Ta dubi Uncle ɗin nata zamu tafi ya yi ɗan murmushi, Beby ki zauna mana in kaiki,ta tsura mishi idanu,yaushe rabon da ta ji wannan sunan daga bakin shi? Yaushe rabon ta da ganin murmushin shi tare da muryarshi nan mai daɗin sauraro, ta sauke ajiyar zuciya, kayi haƙuri direba ya kawo mu ya ce to juyo in sa miki shi,ta juya mishi baya yana sa mata yaron ta goya shi da ƙyau ya ce kin yi ƙyau da goyon, murmushi kurum ta yi bata ce ƙala ba ta dubi Hajiya Jummai mun tafi Allah ya ƙara sauƙi,bata amsa ba sai hannu ta ɗaga mata. Shi kuma ya bi ta a baya sun fito daga ɗakin ya ce Beby ta ɗan tsaya amma bata juya ba, yaushe za ki koma makaranta? Ta dube shi sannan ta dubi ƙasa,jibi ya zuba mata idanu. Ta yaushe zaki koma ɗakinki? Ta ce sai dai ka tambayi Hajiyarmu, ta ci gaba da tafiya, daga nan ya tsaya yana kallonta, har ta ɓace ya yi ajiyar zuciya tare da juyawa.


Kuka rurus ya samu Jummai tana yi, ya iso gurinta a tsorace lafiya kuwa Jummai? Ta soma tari cikin kukan faɗin "shi kenan ni yanzun ba ni da amfani tunda cututtuka sun min katutu shi ne kana ganin A'isha ka bita." Ƙanwarta taja tsaki, gaskiya Jummai in ba zaki ƙwantar da hankalinki ba zan tafi ba zai bita ba ba matarshi bace? Alhaji Saddiƙ ya ce haba Jummai,haba Jummai!! Wai shin ƙaramar yarinya zaki koma ne? Kin san fa halin da ki ke ciki, A'isha baƙuwa ce a gare ki? Don Allah kiyi ƙoƙari ki zama mai natsuwa don ki samu lafiya. Indo ƙanwarta ta ce ina zata ƙwantar da ranta ba saka damuwar ce tasa ta cikin wannan halin ba? Ita dai jin su take yi ba zasu gane halin da ta ke ciki ba ne. Alhajin fita ya yi cikin damuwa.


Yinin ranar A'isha ce a cikin zuciyarshi har zuwa dare. Ya fito wanka ƙananan kaya ya saka jeans blue da shirt fara turarenshi na ko yaushe ya saka, Hadiza ta shigo sanye da riga da sket na lallausan leshi mai ruwan madara. Ta dube shi Darling ka gan ka kuwa? Sai ka ce saurayi ɗan shekara ashirin? Ya dubeta kada ki maida ni baya mana. Ta ce Allah kuwa, ya ƙwashi wayoyinshi da makullin motarshi ta kalli agogo ina zaka yanzun tara ta kusa? Kuma ga abincin ka fa,ya ce zan ci gidan Hajiyarmu yau tuwo nake son ci kin san basa rasa tuwo,ko dan saboda Alhajinmu, ta ɓata rai shi kam bai kula ba ya fito abin shi ta biyo shi an kusan fara news fa, ya ce ai zan kalla a can ta tsaya tamkar hawaye ya zubo mata don takaici tasan gurin A'isha zai je ba wai don mahaifanshi ba, ta yi tsaki ta juya ciki.


Hajiyarmu tana kula da A'isha, tun da taga fara'ar maigidanta ta fara sukuni, yanzun ma su suna falo ne suna kallon labarai amma ita ta shiga ɗaki ta ƙwanta alhalin ba wanda ya kai ta son labarai. Ita kam A'isha so take ta keɓe kanta ta yi tunanin shin Uncle ya yafe mata ne? Ko ko don yaga Hajiyarmu ne? Kai a'a ba don haka ba ne tunda ko a cikin gidan ya kan yi mata wulaƙancin da ya so, tana ganin Allah ne ya amshi addu'arta ya juyo mata da tunaninshi gareta. A fili ta ce Allah yasa haka ne, lokacin da take wannan tunanin shi kuma ya iso falon har yasa Baraka ta kawo mishi tuwo, bayan sun gaisa da iyayan nashi ya kasa cin tuwon na kirki domin waɗanda ya zo domin su bai gansu ba, daga bisani ya miƙe yana kallon gefen da Alhajinmu yake yana cewa bari naga Abulkhairi ba su ce mishi ƙala ba ya nufi ciki,ƙamshin turaranshi shi ne yasa ta buɗe idanunta da ke lumshe fuskarta kurum yake kallo ga nashi zaton bacci take yi ganin ta buɗe ido sai ya yi murmushi, Beby dama idanunki biyu? Ta tashi zaune fuskarta babu yabo babu fallasa, ta gaishe shi. Ya amsa sannan ya isa gurin ɗan shi yasa hannu ya ɗauke shi yana kallon fuskarshi kafin daga bisani ya sumbaci gashin yaron tare da manna shi a ƙirjinsa yakan ji wani irin daɗi duk lokacin da ya rungumi ɗansa,yana addu'a ga duk wanda bai samu ɗa ba, Allah ya bashi A'isha tana kallonshi zuciyarta na yaba ƙyawun shigar shi, da ƙyan haibar shi banda ta san shi da in aka ce tayi mishi shekaru zata ce ashirin da biyar, ya dawo da dubanshi gare ta, sai ta ɗauke kanta yayin da suka haɗa idanu, ya matso daf da ita Beby wai me yasa naga kin kasa sakewa da ni ne? Ta ce ba komai, shi da kanshi ya sani abubuwan da ya yi mata can baya bai ƙyauta ba Sai dai shi ba zai ce ga dalilin da yasa yake yi mata hakan ba, ya ce Beby ɗazun na ce yaushe zaki dawo ba ki ce min komai ba, ta ce Uncle ka manta ne? Na ce sai dai ka tambayi su Hajiyarmu, ya ce kin dai san in dan ta su ne zaki yi ta zama ne ba zasu dawo min da ke ba, ta yi guntun murmushi a ranta ta ce kuji Uncle da wani zan ce mutumin da ke guduna. A fili kuwa sai ta ce, sun ga baka buƙaci hakan ba ne shi yasa ya ce Beby kenan cikin ruwan sanyi ki ke dafa mutum ni dai ki dawo gida kawai,ta tashi zaune Uncle jibi ne fa zan koma makaranta to menene ma zai sa in dawo tunda ba zama zan yi ba, ya yi shiru can ya ce ni fa don dai kawai su Hajiyarmu ne amma Allah da ba zaki koma yanzun ba sai yarona ya yi wayo bana son aje baa luran min dashi. Shiru ta yi mishi ya ce to in zaki shiga aji dawa zaki dinga barin shi? Ta dube shi da Uwani zamu tafi har ma da wata yarinya saboda aikin gida, ya ɗan taɓa baki da bana gari ma da sai dai in dawo in samu kin tafi abinki, ta ce Uncle naga kamar kafi buƙatar hakan ne shi yasa tunda tuni ka fitar da kanka daga cikin lamarina, ta sunkuyar da kai, wallahi a shekarar da ta wuce in wani ya ce min zan tsinci zuciyata cikin garari ba zan amince ba, domin na san uban goyona mai amana ne da halin dattako kuma zaya jure duk wasu laifuka da ƙuruciya zata aikata matsawar ba alfasha ba ce, sai gashi yana zarginta da alfasha wanda ke ɓata aure, ya ɗaga mata hannu, zuciyata bata zargeki ba Bebyna ko da baki ya furta zuciya ta ƙi amincewa, Beby an wuce gurin bana son ki dawo da hannun agogo baya, kuma kamar yanda nike fada koda yaushe ni baki yi min laifin komai ba....





######

[12/22, 12:13] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 11*




Amma da mamaki ace don jin daɗin kanka ka juya baya gareni,kafin ya ce wani abu sai kurum suka ji muryar Hajiyarmu tana cewa in nan zaka ƙwana mu kulle ƙofa ya dubi agogon hannunshi sha biyu saura,lallai lokaci ba wuya ko kuwa don yana tare da masoyanshi guda biyun ne?.


Bayan fitarshi ne Hajiyarmu ta kalleta sanyinki ya yi yawa A'isha,me zai sa ki saurareshi shi da ya nuna baya ƙaunarki? Kanta a ƙasa ta ce Hajiyarmu in ma na ɗauki zafi dole in sauke domin daga gare shi zan samu aljanna, Hajiyarmu tana mamakin A'isha in da mata da yawa za su ɗauki halin A'isha haƙiƙa za su zauna lafiya da mazajansu kuma su ci ribar aure, ta ce haka ne amma mazan ku na yanzun sai kuna ɗan nuna musu kuskurensu,na ce baki sakir mishi fuska yanzun ba nan gaba zaya ji shakkar yi miki irin haka. Ta ce haka ne sai dai yana da ƙyau in bashi uzuri kasancewar bai taɓa aikata min ƙwatanƙwacin haka ba, sai wannan karon, sannan yana da ƙimar da ba zan iya rama abinda ya yi min ba, Hajiyarmu ta ji zuciyarta ta ƙara ƙaunar A'isha, ta ce to Allah ya daidaita ku,mu dai addu'armu kenan, sannan in ya yi ba daidai ba mu tsawata, sannan ki lura da ɗan ki kin ji ko. A'isha ta ce, to ta lura tana matuƙar son jikanta nata tana da kara ne.


Tafiya ta kama shi ranar da A'isha zata koma,bai so haka ba,ya so Æ™warai ya zama cikin masu rakiya in yaso ya Æ™ara wanke kanshi gurin Bebyn tashi, ya dai yi sallama da su kan cewa sai ya zo insha Allahu da zaran ya dawo daga Egypt. Nafisa ta zo da safe dan su yi sallama A'isha ke cewa ina son ki zo ki sha labari don ba za ya yiwu ta waya ba, Nafisa ta ce bani  labari. A'isha ta labarta mata yanda suka yi da Uncle É—in ta, nan Nafisa ta yi murna sai dai itama ta yi wa A'isha tsiyar cewa ta cika son miji daga sakar mata fuska shi kenan ta shiga wage mishi baki, A'isha ta ce to ni ya zan yi? Anty Nafisa kin san Uncle ya wuce wasa a gurina, domin sai fa ya É—aga Æ™afa sannan zan shiga aljanna,ya zan yi wasa da dama ta? Nafisa ta yi dariya kina burge ni A'isha Allah ya sani ma in gwada irin halinki. Itama A'isha dariya ta yi.


Yana ƙwance yana nazarin yarinyar ya sani sarai cikin ruwan sanyi A'isha magana ta gaya mishi, ita kowace irin mutum ce bata fushi? Gaskiya ba zaya gaji da godewa Allah ba,muryar Hadiza ce ta katse shi. Gaskiya ni na gaji, kullum sai ka tafi gurin A'isha ka raba dare ko ka je asibiti ni ce ban san haƙƙina ba don kaga ina haƙuri? In zata dawo ne A'ishan ba gwara ta dawo ba, amma sai a dinga shiga cikin haƙƙina ranar girkinta da ranar da ba tata ba.


Ya miƙe zaune to tunda kin gaji sanar dani yanzun me ki ke son in miki? Ta zunɓuro baki ta dawo a raba ƙwana mana, ya ce na ƙi ta dawo ɗin sai ya ya kuma kike so? Ta kalleshi,ai ni banida alfarmar da zan faɗi abinda ni ke so ayi wannan sai A'isha. Ya ce ƙwarai kuwa domin bata da san kai a rayuwa in kuma abinda ya kawo ki kenan to fita ba ni da lokacin ɓacin rai yanzun ya juya bayanshi, tunda ta wanke gaba ta baka a zoɓo kuma ta haihu ai gare ka babu kamarta, murmushi ya yi a fili kuwa ya ce mahaukaciya kawai, ta fita tana ƙunƙunai.


Haka lokaci ya yi ta tafiya A'isha tuni tana makaranta kuma ta dage ma karatunta, yayinda Uwani ke lura da Abulkhairi, kullum kuma tana ɗaga wayar Uncle ɗin nata a ƙalla sau huɗu a rana ko fi ma,don haka hankalinta ƙawance ta murmure gwanin sha'awa da ita, ranar suna waya da Nafisa take cewa Anty Nafisa Uncle yana son kawo min ziyara ina dakatar da shi da cewa karatunmu ya ɗau zafi in ya zo bazai samu kulawarmu sosai ba, sai nace ki bani kayan nan na gyaran jikin kafin ya zo, gefe kuma ina tsoron kada na kuma ɗaukar wani cikin ga Abulkhairi ga karatuna, Nafisa ta ce zan tura miki da kaya ta tasha gobe, akwai na sha sunanshi hurul'in da na matsi sannan turarukan shafawa da na tsuguno sai man gyaran jiki da sabulun shi sannan lalle na wanka da kuma haɗi na musamman irin wanda ta ke yi don Amare duk nasa ta haɗo min su, zaki gan su kawanne da sunanshi wanda baki gane ba ki kirani ko ki kira Hajiya Aliya zan turo miki lambarta, batun ciki kuwa a sakar ma ɗan uwana jiki ya huta haihuwa muke buƙata kema kin sani, A'isha ta ce haba Anty Nafisa baki tausayin Babanki? Abulkhairi bai yi ƙwari ba Nafisa ta ce za ya yi ne ma suka sa dariya sannan suka yi sallama.


Hajiya jummai kuwa yau in ciwo ya lafa gobe zai tashi domin ta kasa ƙwantar da hankalinta guri ɗaya, shi kanshi Likitan ya gaji da ita don haka yana ganin ta ɗan samu sauƙi sai kawai ya sallame ta ya ce zaya dinga zuwa gida yana duba ta,Indo ma tayi murna don tana so ta tafi, kuma halin ƴar uwarta ya isheta a gidan ma a daddafe ta yi sati ta haɗa yanata yana ta tayi tafiyarta sai ƴan aiki da kuma ƙawayanta da ke tururuwa suna cika gidan kullum kuma abin takaici har yau ba su daina ƙalla banza ƙwance wofi ba,burinsu wai su fitar da A'isha kuma wai A'ishan asiri ta yi mata wannan ciwon nata wai Hadiza ma tana jeho mata asirai kin ji fa.


A'isha suna hanyar su ta zuwa aji ita da wasu abokan karatunta, suna tafe suna hirar Abulkhairi ne, Hafsa Sulaiman tana cewa yaron ya fi ki ƙyau sam bai yi kama da ke ba. A'isha ta ce Abbanshi ya biyo sun yi kama sosai,Hauwa'u Hamza ta ce to kuwa Baban nashi yana da ƙyau kenan,don nima bana gajiya da yaron, kafin ta yi magana sai wayar Uncle ɗin ta ta shigo ringin ɗin shi na musamman ne don haka cikin sauri ta soma lalubo inda wayar take,cike da kissa ta ce Hello Uncle ɗina,ya gyara zama Bebyna, suka gaisa yana tambayar ina Babanshi ta ce suna gida tare da Uwani yanzunni ina hanyar zuwa aji ne ya jingina da kujera,na kasa komai Beby ina cike da kewarki ke kuma na kula baki son in zo inda ku ke, ta ce wacece ni Uncle da zan hanaka zuwa gurin mu ya ce in gaske ne in zo yau? Ta ce Uncle kaɗai shigo week end duk ƙwanakin nan bama samun lokacin kanmu, ya ce shi kenan zan dai samu tarba ta musamman ko? Don maƙogwarona ya bushe da yawa ina jin ƙishi, ta ce faɗi duk me ka ke so zan maka ya ce ke kurum kin wadatar dani, ta ce Uncle dama ni ai taka ce ko yaushe sai dai in kai ne ka ƙi hakan ya ce Bebyna kenan kin dai warware ni a hankali to kaina dai bisa wuya, sai na zo ta ce to shi kenan muna kallon hanya.


Hafsat ta ce A'isha Musty dawa ki ke waya haka kina faman salo sai ka ce kina gabansa cikin dariya ta ce yanzun don Allah har wani salona yi? Da Uncle ɗina fa nake waya, Hauwa'u ta ce kai wannan salon ina jin dai da Abban Abulkhairi ki ke wayar, ta ce au baku yarda ba cewa da Uncle ɗina nike yi ba? Hafsat ta ce Uncle ɗin nan da kike kira yana ji dake kema haka, A'isha ta ce haka ne baki faɗi ƙarya ba Uncle yana ji dani tamkar rai, Hauwa'u ta ce yana da mata? A'isha ta ce matansa uku ɗan sa ɗaya. Hafsat ta ce aiko in bakin ci Sa'a ba matansa sai sun tsaneki, cikin dariya ganin ta shigar da su sun shiga ta ce suma ji dani suke yi, suka ce lallai,kin dace nan dai suka ƙarasa ajinsu don ɗaukar darasi, A'isha kenan tunda saƙon da Nafisa ta aiko mata dashi ya shigo hannunta ta soma amfani da su cikin ƙwana uku ta canza ta zama tamkar wata amarya abokanan karatunta kuwa kowacce sai ta dinga ce mata ana karatu ana rama ke kuma kina ƙara ƙyau dan Allah menene sirrin? Dariya kurum take musu tare da cewa suna dai zolayarta ne. Hatta Anty Maimuna ƙawar Anty Nafisa sai da ta dinga yiwa A'isha nacin son ta san man da take shafawa ta ce sunanshi Zahra Global in kina so zan yiwa Anty Nafisa magana.


Tunda ya yi waya cewa yana hanya duk ta rasa sukuni, ta ƙosa su fito daga lap,tana shiga gida kuwa yau ko ta kan Abulkhairi bata bi ba suka shiga aiki su da Tani mai aikinta,girka wannan sauke wancan har suka gama, ta haɗa mishi mutumin nashi wato zoɓo sannan ta shiga wanka.


Ƙwalliya sosai ta zauna gaban madubi ta yi tare da saka turarukan jiki masu ƙamshin daɗi. Atamfa ce ƴar Holand ja ɗinkin riga da siket sun zauna dam a jikinta tamkar a jikin nata aka ɗinka su. Hatta Uwani sai da ta ce kin yi ƙyau ƴannan wannan kaya sun karɓe ki, tana cikin shirya Abulkhairi ta ji ana ƙwanƙwasa gida. Kafin ta yi magana ta jiyo Uwani tana cewa Tani taje ta duba,don haka ta ci gaba da saka mishi kaya,ƙamshin shi ta ji ta amince shi ne ya iso cikin sauri ta ƙarasa tana cewa Abulkhairi kayi ƙyau babana" juyowannan da zata yi sai suka haɗa ido da Uncle ɗin nata yana tsaye yana kallonsu cike da sha'awarsu, A'isha ta ce la Uncle har ka shigo? Ya iso gabanta na iso Beby ya ɗauki Abulkhairi ya ɗaya shi sama yana mishi wasa ita kuwa tuni ta shiga gyara mishi gurin da zai zauna don cin abinci, ta amshi Abulkhairi, Uncle kawo shi kaci abinci bari in kai shi gurin Uwani ya ce a'a barshi nan abincinma nan za'a kawo min,nan take ta baza capet ta shiga jera mishi kuloli sai da ya zauna kafin ya fara cin abinci ta shiga gaishe shi tare da tambayar jikin Hajiya Jummai,su Hajiyarmu da sauran jama'a ya ce duk suna lafiya, Jummai dai jikin nata sai a hankali, da zoɓon ya soma sannan ya shiga cin abincin ya ma rasa me zai ci duk ranshi yana so rabon da ya yi ci irin wannan har ya manta, ya ce Beby kin ga kin sani yau har na wuce ƙa'ida,na ci na kasa tashi, ta yi murmushi Uncle kenan to ai ni nafi son haka.


Taƙwas da rabi daidai lokacin da ya dawo daga masallaci sallar Isha'i, ya ce Beby ba zan ƙwana a nan ba shi yasa muna isowa nasa Jabiru ya je ya kama min masauki ta ce don me? Ya ce ga su Uwani ko ba haka bama kin san ba ni son cikin makaranta, ta ce to ya za'ayi yanzun? Tashi zakiyi mu tafi, ta ce da Abulkhairi? Ya ce eh mana, ta ce can zan ƙwana kenan? Ya ce to ya ya kike nufi da? Ya ci gaba,kina nufin ni kaɗai zaki bari inje in ƙwana? Ta ɗan yi taƙwa-taƙwa da fuska haba Uncle gidannan fa dasu Uwani shi kenan sai nabi ka can da safe kuma idan na dawo da wane ido zan kallesi? Ya ɗaure fuska koda nan na ƙwana abin da kike gudun su kalle ki dashi in kin bini dashi dai zasu kalleki,kin gane? Beby duk mace mai miji in dai tana tare da shi an san me suke yi, balle ni da na ɗan ƙwana biyu ban abinnan ba, ya ƙarasa da ƴar tsokana ta ce Allah Uncle gaske nake faɗa zan ji kunya, ya ɗauki Abulkhairi muna jiranki cikin mota ki zo muku da duk abinda za ku buƙata, zuwa gobe.


Ta bisu da kallo ɗan murmushi ta yi sannan ta shiga haɗa musu kayan bacci da sauransu, ta kunna tiraran tsugunno ta yi tare da ƙara kimtsa jikinta, ta saɓa jaka tare da zura hijabi ta fito, Uwani suna kallon T.V su da Tani ta fito ta ce Uwani zamu in nan cikin gari kome sunan unguwar? Gidan dai wani ko abokinshi ne? Ku dai kulle gidan in mun dawo to sai mu buga. Uwani ta ce to ƴan nan a sanyin nan? Da kun bar Alhaji nan tunda shi bashi da rigima, ta ce yama riga ya fita da shi sai dai mun dawo. Tani ma ta ce sai sun dawo.


Cikin mota ta same su yana ta mishi wasa, ta shiga tare da tura baki Uncle ka sani zula ƙarya, ya ce kin so ne me ki kace? Ta sanar da shi yace in suka zauna jiranki fa? Ta ce shi ne ai ko in koma ince mun fasa sai ka shigo mu ƙwana ciki kawai, kafin ta rufe baki ya tada motar.


Cikin Reception suka ga Jabiru yana zaune yana kallon ƙwallo cikin T.V, ya tare su tare da amsar Abulkhairi, shi ne ya yi musu jagora zuwa ɗakin daga bakin ƙofa suka yi sallama tare da miƙa musu yaron.


A'isha tasha mamakin yanda Uncle ya ke ta rawar jiki tamkar yau ya soma sanin mace, ta dai sha wuya sosai shi ko sai kace bame mata biyu ba, haka ƙiri-ƙiri ya ƙi su tafi gida ranar tana ji tana gani dole ta kira wayar Uwani ta ce mata sun yi wata ƴar tafiya kada su ji shiru, cikin satin da lahadin wata rayuwa suka yi mai tsayawa cikin zukatansu, ranar Lahadin ma sai dare sannan ya kawo su gida shi kam Asubanci zasu yi don komawa KT,lokacin da zasu yi sallama ta kuma maimaita mishi batun da ta ringa mishi naci tun da suka je hotel ɗin bai ce mata ƙala ba.


Ta ce don Allah Uncle kaga Abulkhairi be yi ƙwari ba, kuma ga karatuna. Nan take ya gumtse fuska Beby na fi son in kin faɗi abu nayi shiru ki ringa ƙyale ni, ke kina ganin ko'ina shaye-shaye zan yarda da wani tsarin iyali? Ki kalleni fa ki gani a shekaru na sai yanzun Allah ya bani ɗan fari, amma har in soma butulce ma Allah? Please bana son in kuma jin makamancin wannan zancan, kanta na ƙasa ta ce to, sallamar ma ba cikin daɗi sosai suka yi ta ba,in ba dan A'isha ba ce ma ƙila da wata ce tazo mishi da wannan batun sai ya mugun saɓa mata yanda ta kula da irin ɓacin ran da ya nuna cikin dare sai da ta kuma kiranshi ta bashi haƙuri kan cewa ya yi haƙuri ta ga ranshi ya ɓaci da batun da tazo masa dashi, ya ce ya wuce shi bai ƙima ace yanzun tana da wani cikin ba, dariya kurum ta yi amma cikin zuciyarta cewa take yi Allah ka tsare ni.





#######

[12/22, 20:35] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 12*




Tana ta gudu gyale a hannu takalmi a hannu tana zunduma ihu cikin Æ™ungurmin dajin mai tsananin duhu,yaran ta ke gani cikin wani muguwar kama mai ban tsoro, dukkan su suna furta mata kalmar fansa! Fansa!! Ko'ina cikin dajin amsawa yake yi, gudu take yi tun Æ™arfinta duk ta gaji sai ta hangi wani rami nan take yi ta yanke shawarar tsundumawa cikin, tana faÉ—awa sai taji ta kan macizai da kunamu, ihu ta saki mai tsanani sai ta farka a tsorace ta tashi zata gudu Alhaji SaddiÆ™ ya riÆ™e ta da Æ™arfi yana cewa Jummai lafiya? Masu aiki ma suka shigo da gudu saboda ihun da suka jiyo,faÉ—i take gasu nan,su murja ne da Hafsatu zasu kashe ni wai zasu É—auki fansa su Jamila ne, da taimakon Æ´an aiki ya samu ya dannata kan gado zuwa wani lokaci yana tofa mata addu'o'i sannan ta lafa sai kuma kuka tana faÉ—in na shiga uku ni Jummai. Ya ce me yake faruwa ne ki min magana mana ta ce su Jamila ne zasu kashe ni suna ta bina, ya ce wacece Jamila? Matanka mana da suka mutu, shiru ya yi ya zuba mata idanu, cikin zuciyarshi kuwa tunani yake yi me zasu É—auki fansa yake nufi? Amma sai ya dubeta ya ce to kici gaba da addu'a ya miÆ™e ya fita cikin É—aurewar kai,baya son zargi don haka sai kawai ya shafe batun daga zuciyarshi sannu a hankali mafarkin ya zamo wa Hajiya Jummai Æ™a'ida in dai har zata rufe idanu da sunan ko gyangyaÉ—i ne ba ma bacci ba,tuni Æ´an aikinta kunnuwansu sun soma sabawa da jin ihun Hajiya Jummai cikin dare da rana, ita kuwa tuni rashin bacci ya yi biji-biji da ita tamkar zautacciya ta dawo ko yaushe tana surutai waÉ—anda in ka saurare su asirin ta kawai take tonawa,ko yaushe tana faÉ—in kada ku kashe ni sun ce zasu rama na shiga uku na kuyi haÆ™uri wannan yasa Alhaji tsare Jummai da son jin me ke faruwa ne? Kuma me zasu rama? Cikin kuka ta ce ka taimake ni nice na kashe su dukkansu nan ta zayyane mishi duk yanda komai ya faru,kuka da hawaye Alhaji SaddiÆ™ ya yi sannan ya je yazo da Alhajinshi don jima kunnanshi shima, Alhajinmu kasa magana ya yi sai da yaje gida sannan ya iya furta ma Hajiyarmu labarin itama girgiza mahaifan Jummai sun yi baÆ™in cikin jin wannan zancan, Alhaji SaddiÆ™ ya samu mahaifan nashi don son sanin menene mafita shi dai ta gefen shi ya gama zama da ita, ashe duk ita ce silar  da jama'a suke mishi mummunan zato kai Allah ya isa Jummai na tsane ki har abada, mahaifinshi dai ya ce in yaga bazaya iya zama da ita a haka ba to ya sauwaÆ™e mata domin kam dan cutarwa an cutar da shi Hajiyarmu kuwa shawartar shi ta yi da cewa in ya saketa to don Allah yabar ta a muhallinta wato gidan shi kenan, ya amince da hakan don haka yana shiga gidan É—akinta ya nufa zaune ya sameta gefenta Hajiya Kari ce tana cewa, haba Jummai yaya zaki saki baki ki yi ta tona ma kanki asiri? Alhajin da basu san da shigowar shi ba ya ce ko bata fada ba dole ne wata rana asirin ya karye, domin ta É—auki rayukansu ba tare da haƙƙinsu ba,shawarata gare ku ke da ita in kuna son samun sauÆ™i gobe kiyama ku kai kanku kotun musulunci domin a zartar muku da hukuncin da ya dace da laifukanku,in kuma kun fi son Allah ya yi muku nasa hukuncin da kansa to kuyi shiru ya ja numfashi sannan ya ci gaba da cewa Jummai am sorry to say na sake ki saki biyu in kina so za ki ci gaba da zama cikin gidan nan sai dai ni yazama dole in barshi.


Wani irin ihu ta saki mai ƙarfi tana cewa ka taimake ni kai ne kaɗai ka rage min saboda sonka ɗin ne fa na aikata duk waɗannan laifukan shi ne yanzun za kayi min haka? Ya ce ke kika zaɓo hakan, wacece ke da zaki ce ba za'ayi miki kishiya ba saboda kin ƙwashe kayan ki daga gaban Manzo,ya dubi Karima ku saurari ƙarshenku yana zuwa. Yasa kai ya fita abinshi, Jummai an shiga sabon ruɗu, hauka hauka ne ya sameta nan take. Lamari fa ya ta'azzara su Jummai yau gashi an kai ga rufe mata ƙofa domin zabura take zata gudu tana faɗin ga sunan baƙin wani kashi da ke jikin Jummai tuni ta yi mishi fizgar kaza,ya zama abinci sai dai a kulla ƙwano da igiya a tura mata Alhaji Saddiƙ tuni ya tattara su Hadiza da wasu daga cikin ƴan aikin gidan suka koma wani gidan shi da ke can cikin G.R.A. Hadiza a baɗini murna take amma a fili kuka rurus ta ringa yi wai ita dole nan me imani, shi ko Alhaji tuni ya dawo rakiyar su shi dai tsoron lamarin mata yake bashi domin bai taɓa zaton Jummai zata iya kashe koda ƙiya shi ba bare mutum. Shine dalilin da ya ji mata sun fita ranshi, hatta A'isha da bata san ma meke faruwa ba duk yasa su gefe shi ne dalilin da hankalin A'isha ya yi matuƙar tashi ga zatonta abinda ya faru ƙwana kin baya ne zai kuma faruwa cikin sauri ta kira Nafisa da kukanta tana cewa Uncle ya yi watsi da ita kota kirashi ba ya ɗaga wayarta,nan take Nafisa ta ce daina kuka mijinki yana cikin ruɗani ne sannan ta sanar da ita dukkan abinda ya faru. A'isha tasha mamaki lallai dole ne maigidan nasu ya shiga rudani.


Karima kuwa taje tazo da bokansu don ya yiwa Jummai magana,suna shiga inda take ta riƙe shi fatar jikinshi ta shiga yaga tana surutai Karima ta yi baya da gudu,tana fita mashin ya yi ciki da ita nan take wuyanta ya karye shi ko boka da ƙyar ya ƙwaci kanshi ya fito jina-jina ya fita da gudu, ganin ƙofa buɗe itama Jummai ta yi ficewarta ta shiga gari tana fallasa dukkan abinda ta yi anyi watanni kusan uku kafin Alhaji Saddiƙ ya gano kanshi, ya zaunar da Hadiza ya yi mata nasiha tare da nuna mata cewar ta dauki ishara daga abinda ya faru kan Jummai, ta nutsu ta dawo cikin hankalinta domin itama zai iya kasancewa da ita, Hadiza kam ta ɗan yi nazari game da batun maigidan nata lallai haka zancan yake. Amma Hajiyarta har yanzun tana nuna mata cewa aikin da suke yi ne nasara ta samu, sannan ta ƙara miƙe ƙafa gidan miji ya zama nata, haka nan kada ta damu da zancan A'isha ita ma data dawo za su saukar mata da nata aikin don haka sai hankalinta ya kasu gida biyu, amma wata safiyar asabar da Hadiza ta nufi gidansu don duba jikin mahaifinta,taga Jummai wasu ƙarti suna dambe zasu saka ta a mota don kai ta gidanta gefe kuma ga mijin nasu da alama shi ne ya bada umurni sai ta ƙara tsorata don haka ranar da kukanta ta dinga roƙon mijin nasu wai ya yafe mata insha Allahu ta daina kuma zata zauna da shi fisabilillah, to kun ji Allah yasa gaske ne.


Tun zuwan farko da ya yi gurin su A'isha bai sake samun sukunin zuwa ba sai wannan karon ita ko taso hakan saboda dama tana tsoron ciki, zuwan ba zata ya yi mata dawowarta kenan daga lecture ta samu Uwani tana tuƙa tuwon shinkafa, cikin jin daɗi ta ce Allah sarki Uwani,ke da kanki? Uwani ta ce ƴan nan na gaji da cin shinkafar nan tuwan semo ɗin nan naku baya ɗaukana shi yasa na ce bari dai ki gani, cikin dariya A'isha ta ce nima fa ƙuiya ce dani ina son cin tuwon wace miyar ki kayi mana? Ta ce a'a ga dai tumatur ɗin nan yana dahuwa. dama kiyi mana miyar ganyan nan me ƙara jini, ta ce ogun? Uwani ta ce shi kuwa, A'isha ta shiga haɗa miyar ji suka yi ana ƙwanƙwasa ƙofa,Tani ce ta buɗe su Hafsat Sulaiman ne, suna ganin tuwo suka ce sun zo a Sa'a. Uwani tana ta musu tsiya da cewa sai yau ƴaƴan nan ƙwana biyu kun mana yaji har dake uwata, ta ce ma Hauwa'u. Hauwa'u ta ce karatune ya yi zafi Uwani,sunan mahaiyarta ne Hauwa'u, A'isha kuwa sunan ƴarta ne ta fari ƴar ma ta rasu amma bata faɗa don kara,kai dai dai da laraba bata cewa saboda a ranar Laraba ne ta haifi ƴar sai dai ta ce ranar samu.


Duk sun zube a falo suna Æ™wasar tuwo, A'isha ko ta ce sai ta yi wanka wai warin zufa take, mai kurum ta murza ta zuro doguwar riga baÆ™a ta zauna tana shayar da Abulkhairi sai kuma suka kuma jin Æ™wanÆ™wasa gida, A'isha ta ce maÆ™otana ne suma su shigo mu Æ™ara yawa yau gidana ya yi albarka, na gode da Uwani ta yi tuwon nan mai yawa,tuni Tani ta je ta buÉ—e Æ™ofa tun kafin ya iso falon Æ™amshin sa ya shigo da sauri ta miÆ™e har ta tsorata Æ™awayan nata tare da cewa Uncle da sauri ta fita, suka kalli juna fuskarshi tana É—auke da murmushi ta É—an sakar mishi irin hararar nan ta masoya cikin shagwaÉ“a ta ce Uncle ba notis? Ya Æ™araso ya cafki yaronshi cikin jin daÉ—i, sannan ya ce bana so in kira ki ce min karatu ya yi yawa gashi ina cike da kewarku,kin san saboda sauri ban zo da Jabiru ba, jirgi na biyo, ta ce sannu da zuwa Uncle shigo,yana shiga ya samu É—akin da jama'a sai ya ce muna  da baÆ™i kenan? Ta ce eh,Æ™awayena ne ta gabatar mishi da su da kuma sunayensu, sannan su kuma ta ce musu ga Uncle É—ina dai yau kun ganshi suka ce lallai kam suka tashi wai za su tafi ya yi ciki tare da cewa suyi zamansu ganin yanda A'isha ta hana kanta sukuni yi wannan yi wancan Hafsatu ta ce kai Hauwa'u ina zaton Uncle É—in nan nata shi ne mijinta baki ga kamar su da yaron ba? Ta ce na lura kuma fa haka ne don yanzun haka ma ta kan ce wa mazan su kai amma A'isha ta samu cikin Æ™wali da harmun kama Hafsa ta ce sosai kuwa, amma fa tayi dace mutumin ya haÉ—u Allah da Uncle É—in ta ne na gaske sai na ce don Allah ta haÉ—a mu, suna cikin hirar sai gata za ta je kicin Hauwa'u ta ce ji mana A'isha Musty ta zo tana dariya Hauwa'u ta ce Uncle É—in ki ya yi kasuwa Hafsa ta ce ki shigar da ita, A'isha ta ce wuu ba zai Æ™ara ba, matan shi sun ishe shi, cikin dariya Hafsat ta ce Æ´ar wulaÆ™anci  dama Uncle É—in ne Abban Abulkhairi shi ne kike ta samu cikin Æ™wali ko? A'isha ta juya tana dariya ganin sun harbo jirgin ta.


Ta yi murmushi ganin yanda yake cin tuwon hannu da baka hannu ƙwarya, ta ce Uncle da alama ka jima ba ka ci tuwo ba ko? Ya dubeta "Beby ba ma tuwo ba,na jima ban ci abinci ba, tun da matsalolin Jummai suka tsananta wata rana ma yini nake ban sha ko ruwa ba, lamarin ya girgiza ni sai tayi tamkar bata ji labarin ba ta ce jikinta ne ya yi tsanani? Ya dubeta kina nufin baki san me ke faruwa ba? Ta ce, "Uncle ina zan samu labarin Katsina, ina Sokoto?" Ya ce na zaci Nafisa ta tsegunta miki, ta ce muna waya amma ba ta ce min ga wata matsala ba, ya yi shiru can ya girgiza kai Beby na ƙara tsorata da lamarin mata, kuma na amince sharri tare da kaidin mata ya ɗarar ma na sheɗan, kazalika dole ne su fi yawa a wuta." A'isha ta ce "haba Uncle ya ya ka ke wannan zantuka ba duka aka taru aka zama ɗaya ba,wai ma duk me ya kawo wannan batun? Nan ya bata labarin komai, duk da cewa Nafisa ta bata labarin da take jin shi yanzun sai da ya girgiza ta, ta zuba tagumi cikin hawaye shi kam nasiha ya shiga yi mata da cewa A'isha na sani ke cikin mata daban ki ke,kin samu tarbiyya tare da yin gadon halayen mahaifanki, amma ina so ki ƙara zama cikin mata salihai,abin koyi kada ki amince ruɗin duniya ya ja ki ga halaka, duk duniyar guda nawa ce? Duk sonka da ita wata rana sai ka barta, tare da duk abinda ka tara daga kai sai halin ka zaka tafi, abinda Jummai ta kasa ganewa kenan, yanzun wa gari ya waya? Mai sammako inji ƴan magana, A'isha ta nisa ta ce to yanzun tana ina? Ya ce tana nan gidan sai dai ba a buɗe ta don ƙwanaki da ta ƙwace sati huɗu ana nemanta sai da ƙyar aka ganta hauka tuburan fa. A'isha ta ce, Allah ya bata lafiya, sannan don Allah ina roƙon mata arziƙin ka yafe mata ta ji da na sauran,ya tsura mata idanu sannan ya yi murmushi, A'isha ina son halayan ki to har zuciyata ta ci albarkacin ki na yafe mata nawa laifin, shi kenan? Ta ɗaga gira suka yi ƴar dariya.


Kafin ya dawo sai da A'isha ta tabbatar da cewa babu sauran wata damuwa cikin zuciyarshi na shi ganin har wata ƴar ƙiba yayi, A'isha kuwa dariya ta ringa yi mishi lokacin da ya iso gida Hadiza ta tare shi da nata salon tarairayar.


Yau da gobe lokaci yana tafiya,ƙwanaki na shuɗewa haka satittika da kuma watanni har su A'isha sun sami ɗan hutu suna ƙarshen shekara, sun iso gida cike da ɗokin ganin ƴan'uwa.




#######

[12/22, 23:34] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 13*





Uwani garin su zata wuce don duba dangi haka ma Tani, Aisha kuwa gidan su da suka koma aka wuce da ita,tsarin gidan yafi nasu na da, haka nan kowace da gefenta babu abinda zai haɗa wata da wata, komai sabo ya zuba mata, Hadiza har da yin girki don taran A'isha. Tabawa kuwa ta turo baki ta ce in dai kishiya ce fa baza kiyi gwaninta ba, Hadiza ta ce don Allah Tabawa ki ƙyaleni,ni na gaji da halinku, Tabawa ta kuma taɓa baki,nan gaba za ki kuma neman mu,kin kama tashar daji in dai kishiya ce,ta fita waje.



Cikin ƙwanakin suna zaman lafiya da juna, Hadiza ko yaushe tana shigowa gurin A'isha musamman in ba ita ce da miji ba, sai dai ganin yanda A'isha ke kula da mijinta da yanda shi kanshi ke ji dasu ita da ɗan ta sai ta kasa daure ma zuciyarta,in ta koma gurinta sai ta yi ta ƙunci wannan damar Tabawa ta sake samu ta dinga zuga Hadiza tare da cewa in fa Aisha na gidannan ta bar Samun soyayyar mijinta har abada, sai dai ƙunci ya kashe ta, Hadiza ta ce bana son in koma gurin maƙaryatan Malaman nan ne,sun jima suna ce min A'isha zata fita ba zata haihu ba menene, menene,sai gashi duk babu abin da ya faru,a ƙarshe ma ita ce ta haihu. Tabawa ta ce tuni da kin yarda tun dawowarta da tuni mun soma shirya mata kissa, tunda ba ki son Malaman, Hadiza ta ce kada ki shirya min ramin da zan rufta, Tabawa ta ce kajiki da wani tunani, duk abubuwan da muka shirya can baya wanne ne ki ka rufta? Hadiza ta ce shikenan.


A'isha tana kallon su tana dariya, Uncle ne shi da ɗan shi suke rigima, ya rarrafa ya janyowa Uncle ɗin waya daga chaji ya jefar sannan ya hau kan kujera ya zauna kan laptop ya hana Uncle ɗin aiki, ya dubi A'isha Beby zo ki ɗauki yaron ki ya hanani aiki, A'isha ta ce tayaka fa zaya yi Uncle, ya dubi yaron Babana je ka gurin Mominka, A'isha tana tasowa yaron ya ƙanƙame uban ta koma tana musu dariya, ya ce kina dariya ne ma ko kin ƙi ɗauke shi in gama ko? Shima ya yi ƴar dariya tare da rungume yaron dama muna magana ne kan tafiyar ki aikin hajji, tunda ba zaki riƙe shi mu gama ba shi kenan. Asha wasa ko yaron Baba?" Da sauri A'isha ta tashi ta cafke yaron zo kada kasa in ga samu in ga rashi, ta zauna kusa da shi tare da dafashi gaske ne Uncle ɗina? Ya ce kalli ki gani lis ɗin sunayan waɗanda zasu tafi aikin hajji ne sunan waye farko? Ta kalli screen ɗin laptop ɗin, Beby ta gani farko cikin murna ta ƙwantar da kanta a kafaɗarshi tana cewa na ji daɗi bari na gani su waye sauran nayi musu albishir koda in samu tukuici, daga sunanta sai nashi ta dubeshi kai fa duk shekara sai ka je ya ɗora yatsanshi kan leɓanta ke zan raka ta ci gaba da dubawa, sai sunan mahaifanta biyu da yayanta Abdulrahman sai Nafisa da Uwani mai aikinta sauran kuwa bata san ko su waye ba,ƙila cikin danginsu ne. Ta dube shi ban san da wane baki zan maka godiya ba Uncle, ya ce kawo kunnanki ki ji dame za ki bani tukuici, ta miƙa kunne ya raɗa mata, dariya ta shiga yi sannan ta ce ka samu ban ga Hadiza ba, ya ce kin san dai ance Hajji kiran Allah ko? Ta ɗaga kai ya ce to Allah bai kira ta ba, A'isha ta ce to Allah yasa tana da rabo nan gaba, ya ce Amin.


In kin je me zaki roƙa? Ta ce Sa'a a karatuna sai kuma gamawa lafiya, tare da samun ƙyaƙƙyawan ƙarshe. Ya ce ni duk shekara haihuwa nake roƙo, ta dubi Abulkhairi da ke bacci a jikinsu, sannan ta ce Uncle ba gashi ka samu ba, ya ce ni da nike son dozin biyu Beby kina da sauran aiki fa, ta ce wai ba zan iya ba ana shan wuya fa sosai,ni dai wannan ya isheni, ya zuba mata ido, Beby ba ki yin tsarin iyalin nan ko? Ta ce me yasa ka ce haka? Na gane shiru, ta ce Allah tunda ka ce baka so an wuce gurin, ya ce shi kenan. Ta miƙe da yaron a kafaɗarta bari in shinfiɗar da shi ka ƙarasa ina zuwa yau zaka sha tukuici, murmushi ya yi tare da cewa Beby.


Tabawa wadda ke maƙe tana kallo tare da sauraron duk abinda ke faruwa tsakanin ma'auratan, ta riƙe baki sannan saɗaf-saɗaf ta bar gurin tana tafe tana tafa hannu gami da riƙe haɓa, irin na wanda ya ji ko ya ga abin mamaki, har Hadiza ta soma bacci Tabawa ta tashe ta,tashi-tashi Antyna wato ma bacci ki ke yi ke,ni ina can gurin neman zaman lafiyarki. Ta ce Tabawa na ƙi bacci tunda ke kin je kin yi zamanki? Ta dafa ta na taɓa ki da alheri kin san me na jiyo? Hadiza ta ce sai kin faɗa, Tabawa ta taɓa baki irin na wanda ya kawo gulma to ke me son bawa kishiya amana to gata can ita dake makaranta an biya mata Makka tare da iyayanta har fa da wata ke da ke nan kullum sai ya ɗaga ƙafarki ko oho,don kinibibi har tana cewa Hadiza fa? Cike da al'ajabi ta ce to shi me ya ce? Tabawa ta taɓa baki,ɓata rai ya yi tare da cewa,wai kiran Allah ne, wato ke bai kira ki ba, Hadiza ta ringa girgiza kai lallai gaskiyan su Tabawa ne ba aba wa kishiya amana.


Ranar kam ƙwana ta yi babu bacci,ko da ya shigo da safe lokacin da zai fita ta cije sun gaisa amma shi kanshi ya lura tana cikin damuwa, ta so mishi magana amma Tabawa ta ce in ta mishi magana ba zata ci ribar zance ba,tunda ranar zata amshi girkin ke ki kasan yanda za ki riɓa ce shi ki ji komai, amma ita ki bar ni da ita zan shirya mata gadar zare kuma zata faɗa, akwai batun da sukayi na ji.


A'isha ce a gaban Uncle ɗin ta da ke ɗauke da Abulkhairi yana cewa Beby tana duka fa? A'isha ta ce Ni ba zata min komai ba, ya ce ki dai leƙa ta window ne tunda kin dage sai kin gaishe ta. Yanda A'isha taga Jummai kuka sosai ta ringa yi,lallai wannan shine in kasan farkonka baka san tsakiya ba, ƙarshe dai dama mutuwa ce ta yi baƙi ta rame, jikinta babu sauran gashi,ga ciwuwwuka da ta jiwa kanta fuskarta tamkar ta ƙone ɗakin sai wari yake yi,da ta kalli ƙafafun ta kuwa ai sai ta kuma sa kuka dan ganin yanda wasu manyan tsutsotsi irin na toilet mara tsafta ɗin nan suna fita daga jiki, gashi sai surutai take yi in ka saurara zaka ji tana faɗin duk abinda ta aikata ne. Ta kalli A'isha ta window inda take kuka ta miƙe tsaye sai ta hango Alhajin,nan take sai ta soma dariya, Alhaji ka gansu ne? Zo ka zauna,in maka abinci? Hawaye ya kuma zubo ma A'isha, ta ce sannu Hajiya, Allah ya baki lafiya, ta maida kallonta ga A'isha ta tsura mata ido tamkar tana son tuno da ita,can sai ta ce ina yini? Sannunku tare ku ka zo? Tana ta gaida A'isha cikin kuka A'isha ta ce Uncle gurin babu tsafta ya kamata a gyara mata gurin. Ya ce Beby wa kika ga zaya iya shiga wannan gurin,duka fa take yi da cizo duk wanda ta kama sai ya yi jinya, abinci ma fa sai dai a ɗaura igiya, gidan mahaukata ma sun ƙi amsarta don ranar da muka kai ta mutum biyu ta sumar,zaman ta nan shi ne ƙwanciyar hankalin al'umma. Yaja hannunta zo mu tafi, ya lura in bai jata sun bar gurin ba sai ta ja ma kanta ciwo don kuka, ya ce ishara ce Beby Allah ya saukar mata, saboda masu hali irin nata,duk wanda bai yarda da ƙaddara ba ya zaɓi son zuciyarshi ina mai tabbatar miki da sannu zaya ga aya ta sauka a kanshi.


Cikin motar da ƙyar ya shawo kanta ta yi shiru. A'isha ta ƙara tsoron Ubangiji tare da tsinkewa da lamarin duniya,lallai kam duniya budurwar wawa ce, kuma duk wanda ya ɗau ɗamarar zamanta ya wahala, domin wanda ba a haifeshi bama jiranshi take yi,yazo ya ci yayin shi ya wuce, Allah kasa mu fi ƙarfin zukatan mu,Amin. A'isha ta ringa damun Uncle ɗin ta da son zuwa Jigawa, dole ya bar komai suka tafi. Mahaifanta sun yi murna da ganinta da ɗan jikansu. Haka nan sun sha mamaki lokacin da Alhaji Saddiƙ ya basu labarin Jummai sun jajanta mishi game da al'amarin haka nan sun yi godiya mai tarin yawa a lokacin da A'isha ta sanar da su batun aikin Hajjinsu,babu ma kamar Yaya Abdulrahman,tamkar anyi mishi albishir da gidan Aljanna,ga kuma tsaraba aka yi ta rabawa dangi na ko'ina da ina,da zasu tafi mahaifan nata suka yi mata nasiha tare da nuna mata cewa ta bi mijinta sau da ƙafa, kada ta biyewa ruɗin duniya da kayan cikinta, suka ɗauko hanya suka dawo gida.


Dawowarsu da ƙwana ɗaya suka soma zirga-zirgar gidan Nafisa, ta haifi ƴarta mace basu sami hutu ba sai da aka yi suna ta samu ƴarta Asma'u,sunan mahaifiyar Alhaji Bello,suna ce mata Husna, A'isha sun sake haɗuwa da Hajiya Aliya ta zo sunan ƴarta,Anty Nafisa nan ta buɗe bakin jaka ta ƙwashi kayan gyaran jiki, A'isha tana iyaka ƙoƙarinta don ganin ta ƙyautata wa mijinta, shima yana nuna sonta ko gaban wanene, wannan dalilin shi ne ya ƙara tunzura Hadiza sai ya kasance duk ranar girkinta ta dinga ƙorafi kenan ita baya sonta,ya fi son Aisha,kaza-kaza, shi kuma nuna mata yake cewa A'isha tana da biyayya tare da ladabi, itama in har ta bishi haƙiƙa zata iya kamo matsayin A'isha a cikin zuciyarshi duk ran girkinta ta dinga cika kenan tana kumburi ita a dole ba ayi mata adalci. Hutun A'isha ya ƙare ta tattara ta koma makarantarta tare da su Uwani,nan fa Hadiza ta soma tsiro mishi da kalolin tsirfa musamman in ya buƙace ta nan zata tirje ta ce dan yaga A'isha bata nan i, haka kawai ita da shan wahala A'isha ke morar shi, nan nema ta sako maganar batun Hajji da ya biya mata da iyayanta, shi ko ya ce ya biya kuma babu wanda ya isa yasa shi fasawa, kuma ta fitar mishi daga ɗaki taje ta riƙe kayanta,tun daga lokacin ya share lamarinta ko kanta ta kawo ɗakinshi baya sauraron ta daga baya dai ta bashi haƙuri tare da ɗaukar masa alƙawarin ba zata ƙara ba.


Ƙwanci tashi asarar mai rai, A'isha ta kuma zuwa hutu yaronta lokacin yana tafiya ya ƙara ƙyau tare da birgewa,kowa ƙaunar yaron yake yi. Hajiyarmu ta ce ba za a koma dashi ba yayeshi za'ayi. A'isha ta ce dama in zasu tafi aikin aikin Hajji nan zata barshi in ta dawo ma ba dashi zata koma ba, ta yi karatunta cikin nutsuwa, shi kuma Uncle ɗin cewa ya yi insha Allah kafin ki koma sai da wani cikin,shiru tayi mishi ya ce baki fata kenan? Ta ce ina fata mana amma sai na gama karatu bai ce komai ba cikin zuciyarshi kuwa sai ya ɗan zargi wani abu,an ya A'isha bata shan komai? Amma sai ya share wannan zargin, baya son ya zargi abu.


Dukkan É—aukacin musulmi suna ta shirin tafiya aikin Hajji, haka ma su A'isha da mahaifanta, kasancewar wannan shine karo na farko da zata aikin hajji duk ta bi ta hana kanta sukuni burinta kawai shi ne ta ganta gaban ka'aba, Nafisa kuwa kasancewar taje ba sau É—aya ba ba so biyu ba sai dariya take yiwa A'isha.


Tabawa ta kalli Hadiza kada ki nuna musu damuwarki bar su in sun tafi can zasu ƙwaɓe ƙila ma ya sako ta tun can ke dai kiyi ƙoƙarin zuba waɗannan ƙwayoyin cikin kayanta. Hadiza ta ce ƙwayoyin mene ne? Tabawa ta ce " Na hana ɗaukar ciki ne,in ma mace tana da cikin zubewa za ya yi." Tsaki Hadiza ta ja, Tabawa kin cika abin haushi, to kuma ce miki aka yi ita mahaukaciya ce tana ganin ƙwayoyin cikin kayanta sai ta hau sha ko? Tabawa ta dafats,saurara mana ke dai ba zaki ci ribar zance ba wallahi, ce miki aka yi zata sha? Mijinku kawai ake buƙatar ya gani,in ya gani kuwa kin san dai yanda yake son haihuwa, rigima ce zata ta shi, ballantana dama na gaya miki yana zargin tana shan wani abu, nasha jin yana ce mata ba dai ta yin tsarin iyali ko? Hadiza ta ce kai Tabawa, Allah ya biyaki sai dai ban san ya ya zanyi in sa mata ba. Tabawa ta sakar mata harara in nemo maganin in kawo miki sannan sai na koya miki yanda za ki sa? Hadiza ta ce taimakamin don Allah, Tabawa ta ce to kin dai san ita sakarya ce yanzun zata yarda da mutum, zuwa zakiyi har ɗakinta ki shiga da sakin jikinki da kuma sakin fuskarki ki ce kin zo ne kuyi sallama sannan don Allah ta yafe miki duk abinda ki kayi mata, to a nan zaki shammace ta ki saka mata. Na ce zan zo miki da lokacin da ya dace ki shiga sai na leƙo tukunna kin san za a sane in da zaya gani ba inda zata gani ta zubar ba, Hadiza ta ce to ina jiran ki sarkin ƴan leƙen asiri. Tabawa ta ce kuma ki sani in bom ɗin nan da muka ɗana ya tashi da A'isha za ki bani ƙyauta ta musamman, tare da yi mini ƙarin albashi, don na lura da ke in dai ba roƙon ki aka yi ba baki ƙyauta ba ki yin sadaka don tsabar rowar tsiya, Hadiza ta ce na ji zan miki uwar ƙwaɗayi,don ke ko komai zaki yi don ki samu kuɗi ko da halaka ne. Tabawa ta fita tana cewa,na ji dai ai halina ɗaya da uwarki, Hadiza ta ce iye? Lallai kinga gadon baccina, Tabawa ta yi wucewarta ta bar Hadiza tana surutai.


Washegari da misalin ƙarfe sha ɗaya lokacin maigidan ya fita zuwa Office. Tabawa ta shigo tana cewa ina Hadizan? Zo ki shiga yanzun wata jaka ta na nan cikin ta zaki sa, saboda ta haɗa suturarsu ciki,za yayi amfani da shi kinga zaya gani in ya zo ɗaukar kayanshi. Hadiza ta ce tana ciki kuma? Tabawa ta ce tana ciki mana kefa sokuwa ce yanzun sai ki ce sai na gaya miki yanda za ki yi ko? Hadiza ta ce ba wani sokonci,ban ga ji makirci ba, ba dole sai an nuna min sannan zan iya ba? Tabawa ta ce amma ai kin gaji asiri, makircin ma ƙila ta gurin uba ne ba'a gada ba, ta ci gaba da cewa yanzun in ki ka je kusa da jakar zaki zauna ki ba jakar baya kan gado kuma jakar take, tashi kiyi azama kada ta fito daga uwar ɗakan ta dawo falo.




######

[12/23, 11:57] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 14*




Aisha tana ta haÉ—a kayan Abdulkhairi,in Babanshi ya dawo za su kai shi gidan su Hajiyarmu, tare da yi musu sallama, domin tashin Asubahi za su yi, sai ta ji sallamar Hadiza cikin sakin fuska ta amsa tare da faÉ—in shigo, bakin gado ta zauna tare da ba jakar baya kamar yanda Tabawa ta yi mata Æ™watance. A'isha ta bar aikin da take yi don su gaisa, bayan sun gaisa Hadiza ta ce, ashe kuma tafiya ta zo? A'isha ta ce wallahi kuwa, yanzun nake cewa bari in gama in shigo muyi sallama." Hadiza ta ce, "Ina Abulkhairi?" A'isha ta dube ta yana bacci a falo, ba ki ganshi ba? Hadiza ta ce ban lura ba, to Allah yasa aje lafiya a dawo lafiya, kusa mu cikin addu'a. A'isha ta ce insha Allah ai naso  ace dukkan mu ne zamu je, Hadiza ta ce to ai kin san an ce Hajji kiran Allah, kafin A'isha ta ce wani abu cikin Sa'a sai wayarta ta soma ruri,da sauri ta nufi falo domin ringing É—in na musamman ne,don Uncle É—in ta ne,hakan ya yi wa Hadiza daÉ—i, don haka tana fita ita kuma ta danna maganin ciki ta rufe ta koma ta zauna A'isha ta shigo tana waya, Hadiza ta bita da kallo tana cewa Uncle babu sauran nono fa,ya ce bana turo a kawo ba? Ta ce bai zo ba, bari na tambayi Hadiza." Ta dube ta Jabiru ya kawo nono? Ta ce a'a. A'isha ta ce bai iso ba in yazo zan dama in bashi ya ce to Beby. A'isha ta aje wayar ta dubi Hadiza Na barki ko? Hadiza ta ce sai ka ce wata baÆ™uwa? Suka yi shiru kasancewar ba su saba ba, can dai Hadiza ta miÆ™e bari in koma sai kun dawo, A'isha ta ce haba dai zan shigo kafin mu wuce." Hadiza ta ce, "to sai kin shigo, ta fita cikin murna ta isa sasanta zaune ta samu Tabawa ta zuba ma T.V idanu, Hadiza ta kalli T.V É—in wasannin turawa ake yi a tashar MBC max ta ce Tabawa duk kallon ne haka sai ka ce zaki shiga T.V É—in kuma,abin haushin ma ba wai kina jin me suke cewa ba ne. Tabawa ta ce Um ni dai ba ina binsu da idanu ba,to kin dai saka ko? Hadiza ta ce na sa mana da Allah ya taimake ni in gaya miki sai ga kira wayarta ta hau ringing tana fita na tura. Tabawa ta ce ya yi Æ™yau, yanzun sauran mu jira sakamakon da zai biyo baya, Allah dai yasa ya gani,amin.


Da ace A'isha tana tara sani da Ubangiji, da ba ta bari jakar kan gadon  ta ba har zuwa yanzun da suka dawo daga kai yaron nasu gurin Kakanninshi da sunan yaye.  A'isha ta dawo da alhinin rabuwa da É—an wanda ko yaushe suna tare musamman irin wannan lokacin,wato dare.


Uncle ɗin nata shi ne yasa hannu ya ɗaga jakar da nufin saukewa ƙasa,yana cewa Beby yau kamar kina jin kasala ne zan ce ko mene ne? Ta dube shi,me yasa ka ce haka? Ya ce na gane gadonki duk tarkace, ta kalli gadon Uncle jaka ce fa kawai, ya ce me kika zuba ne cikin jakar na ji ta da nauyi sosai? Ta ce ni me ma na saka ne? Kayanmu ne kawai fa,zai buɗe ta ce don Allah Uncle ka bar ta da ƙyar fa na shirya su, ya ce ni fa kada ki ɗaukar min abinda ba zan yi amfani da shi ba,ya soma ciro kayan ciki yana cewa Beby da duk ni kika ɗibar ma wannan bolasas ɗin? Yana dariya, ta ce ai na zaci zakayi amfani da su ne,shiru ta ga ya yi yana karanta wani ɗan ƙaramin ƙwali mai ɗauke da wasu ƙananan rubutu,yana gamawa ya ɗago idanu yana kallonta, yanda taga fuskarshi yanda taga idanunshi yasa ta razana ta nufoshi lafiya Uncle mene ne? Ya kuma kallon ƙwalin sannan ya ce dole ki ce kada in buɗe jaka,da ƙyar ki ka shirya, saboda kin san me ki ka taka, ya ajiye ƙwalin kan kayan ya miƙe ya fita. Gabanta na faɗuwa ta nufo gurin ƙwalin ta soma ɗauka, ta zaro idanu lokacin da ta fahimci kowane magani ne. Tuni zufa ta soma tsattsafo mata, to wanene ya kawo mata wannan maganin ɗaki? Duk da ta sani ba zai taɓa yarda da ita ba akan cewar ba ita ce ta kawo maganin ba.


Ta sameshi a cikin falo yana ta zirga-zirga bata taɓa ganin shi cikin wannan halin ba, ta ta tsaya ta daure ta ce "Uncle...." Ya juyo tare da ɗaga mata hannu,ba ki da wata kalma da zaki furta min, shi yasa bana so zuciyata ta zargi abu domin a ƙarshe zaya zama gaskiya. Amma Beby kin bani mamaki ya sake juya mata baya da duk matan duniya zasu taru su ce min suna da amana zuciyata ba zata taɓa yarda da su ba,ya girgiza kai A'isha ke ce kurum zuciyata ta aminta da ke,ke ce kika sani gardamar cewa mata suna suka tara, A'isha ke nake tunawa in gode ma Allah,don a zatona kin cike gurbin kowace mace a gurina, sai gashi kin yaudare ni kin ci min amana kin ƙara nuna min cewa halin mata ɗaya ne. Ya ƙara saitin muryarshi lokacin da zai ce dame za ki kare kanki? Cikin jakarki da kika zauna ki ka shirya kayan da kanki naga maganin tsarin iyali, ta ya ya zaki gamsar dani cewa ba ke ce ki ka sa ba? Ya tsura mata idanunshi da suka yi jajir. Ta girgiza kai babu amma wallahi Uncle ba ni nasa ba, kuka ya ƙwace mata, kuma lokacin da nake shirya kayan ban gan shi ba,ya ce to wa ya sa miki? Cikin kuka ta ce Allah shi ne mafi sani, shi ne kuma shaida ta.


Ranshi ya sake ɓaci Beby nafi son mutum in yayi laifi ya amsa laifinshi fiye da ya nemi raina hankalina,tuni na jima da fahimtar cewa kin fi son karatunki fiye da auranki ko? Shi ne dalilin da yasa ba ki so ki haihu, ashe Jummai bata isa ta zama wa'azi a gare ki ba ko? Na gode, ya nufi waje. Nan A'isha ta zauna ta shiga rera kukan baƙin ciki, ta sani an yi wannan ne don a haɗa ta da mijinta,ganin kuka ba zai zama mafita gare ta ba, sai kawai ta miƙe ta koma ɗakin baccinta, alwalla ta ɗauro ta hau yin nafilfili don gaya ma Allah.


Shi kuwa rasa ina za ya dosa ya yi,mota kurum ya buɗe ya zauna ya kifa kanshi kan kujera, yanzun wane mataki ya kamata ya ɗauka kanta? Ina ma zata ɗaukar mishi alƙawarin ta daina shi kam yanzun Allah ɗaya mace zata gaya mishi ya yarda,don in zata shekara tana rantsuwa cewa ita mai gaskiya ce za ya yi wuya ya yarda,bai san tsawon lokacin da ya ɗauka yana tunani ba, har zuwa lokacin da ya fita ya nufi cikin falon ya dubi agogo ɗaya da rabi na dare. Ya ƙwanta kan doguwar kujera,haƙiƙa wanda ka yarda da shi ka amince mishi ya ci amanarka lallai abin yana da matuƙar ciwo.


A'isha wadda itama ta kasa bacci har lokacin tana zaune kan sallaya ta ji motsin shi, don haka ta miƙe da nufin amsa laifin da ba nata ba. Bai ji shigowar ta ba sai dai jin shashshekar kukanta lokacin da zata tsugunna kusa da shi, ya dube ta sannan ya ɗauke kai, cikin muryar da ta ci kuka ta soma gajiya ta soma magana, "Uncle na sani cewa ba zaka yarda da abinda zan ce maka ba, amma gaskiyar magana shi ne ban aikata wannan laifin ba, amma tunda bani da mafita na amshi laifina, ni ce na aikata." Ta ci gaba da kuka, amma ka yafe min, insha Allah ba zan kuma aikatawa ba. Ya dubeta, "Na sani za ki kuma domin baki gama karatun ba, ta girgiza kai ba zan kuma ba insha Allahu don Allah ka yafe min.


Ya yi wata doguwar ajiyar zuciya, shi kenan Allah yasa. Ta share hawayenta, to tashi kaje ka ƙwanta, ya girgiza kai,nan ma ya ishe ni. Zata ƙara magana ya ɗaga mata hannu sannan ya ce koma ciki kawai, ta miƙe ba ko musu ta shiga ciki. Haka suka yi wannan tafiya cikin rashin walwala don ya kasa sakin jiki da A'isha,mahaifanta ta Kano za su tashi don haka ba su haɗu da su ba lokacin tafiyar,sun ci gaba da gudanar da aikinsu yanda ya kamata, lokacin da A'isha ta ganta gaban Ka'aba sai ta ji tamkar ba gaske ba,nan ta shiga kaiwa Allah kukanta.



****    ****    ****   ****

Sun dawo da ƙwana uku, lokacin su Tabawa suna cikin falo suna musu da Hadiza kan cewa Hadizan ba tasa ba gashi sun je sun dawo babu wata matsala? Ita ko Hadizan cewa ta yi sai dai in mugunta Tabawa ta yi mata ba da jar jakar zasu tafi ba. A'isha ta yi sallama ta shiga, duk basu jita ba sai da tayi sau uku sannan suka dawo cikin hayyacinsu, tsaraba A'ishan ta basu suka shiga godiya,suna zaro idanu ga nasu zaton ta ji su, ita kuwa sam bata san kanme suke musu ba kuma bata iya shiga shirgin da babu ruwanta.


Tsananin ihun Jummai shi ne ya firgita dukkan ma'aikatan da ke gidan, musamman masu mata abinci, don haka duk suka cikawa rigunansu iska, wato suka tsere duk masu maƙotaka da gidan sun ji ihun wanda ta ɗauki ƙwanaki uku tanayi,ranar na huɗu sai suka ji shiru. Bayan wasu ƙwanaki biyunne al'ummar layin suka shiga kiran layin wayar Alhaji Saddiƙ suna shaida masa ya zo ya yi musu agaji domin matsanancin wari ne ke fitowa daga tsohon gidanshi da ya tashi, shi kanshi da yazo ya kasa shiga sai da ya nemo waɗanda suka shiga gidan don duba abinda ke faruwa. Jummai ce ta mutu kuma ta kumbura dam! Ko wanka ba'a yi mata ba don duk in da aka taɓa a jikinta saluɓewa yake yi, sai dai ruwa aka yayyafa mata aka yi mata sallah aka kaita da halinta, aka turbuɗe, Allah yasa mu yi ƙyakƙyawan ƙarshe Amin.


Ranar da aka yi ƙwana uku A'isha ta koma makaranta ta ci gaba da karatunta. Hadiza kuwa dama haka ta fi burin gani, wato ita ɗaya a gurin mijinta, kuma har yau Hajiyarta tana nan kan bakanta na nemawa ƴarta asirai ƙauye da birni,sai dai in ta kawo mata ne wani tayi amfani da shi wani kuma in ta tuna da Jummai da kuma yanda ta ƙare sai ta yarda, cikin haka ne ma maciji ya sare ta a wani daji cikin wani ƙauye mai suna tsamiya. Da ƙyar ta samu waɗanda suka taimaka mata suka kawo ta gida, wannan saran macijin shi ne silar yanke mata ƙafa, sannan ga ciwon ɓarin jiki da ya sameta daga faɗuwa zata dogara taje bayi.


Wata ziyara da Uncle ɗinta ya kai mata a makaranta,roƙonta ya dinga yi kan cewa in har yanzun tana kan bakanta na shan ƙwayoyin nan don Allah ta daina,shi ko biyanta ne ma in tana so zaya iya yi saboda ta yarda ta haifa mishi yara, ta yi kuka sosai tare da sanar da shi cewa tunda yana zarginta har yanzun tana mai shawartarshi ya je ya ƙari aure ko Allah za yasa matar ta haihu, kallonta ya tsaya yi kafin ya ce shi kam ya gama aure, ya tsorata da lamarin mata baki ɗaya, tunda ya sani duk halin su ɗaya,in kuma ba yana neman wadda zata kai shi kabari ba ne. Shiru A'isha ta yi domin tana hankalce da shi tun lokacin da yaga ƙwayoyin nan komai tayi mishi bata birge shi, ita kanta fata take Allah ya bata ciki ƙila shi ne kurum zai sa ya huce. Har dai ya dawo hankulan su ba'a natse ba.


Lokacin da ta kuma samun wani hutun ta zo gida, washegarin ranar ya ɗauko Abulkhairi yaron na da wayo bai manta da mahaifiyarshi ba, yanzun ya tattara dukkan soyayyar shi ya maida ta kan ɗan nashi, nashi ganin daga mahaifanshi sai ko ɗan nashi sune masoyanshi na gaskiya,abin ya ɗaga hankalin A'isha, domin tunda ta dawo ko sau ɗaya bai nuna sha'awarshi kanta ba, ya kan saka ɗan shi gaba ne su sha baccinsu kuma da safe shi ne yake yiwa yaron duk abinda ya dace uwa tayi mishi,daran ranar da ta cika ƙwana huɗu da dawowarta ita ce dashi,suna ƙwance ya saka ɗan nasu tsakiya ta kalleshi jira kurum take yi ɗan nasu ya yi bacci zata mishi magana gara ma ita in ya yi mata amma Hadiza fa me ta mishi? Domin ta kula cewa Hadiza ma hakan yake mata har ma tana zargin dawowar A'ishan ne yasa ya juya mata baya, sannan koda gurin Hadizar yake ta daina shiga ɗakinshi ta koma ƙwana nata ɗakin.


Ta dubeshi, Uncle Ina son muyi magana, ya ce ina jin ki, ta ce Uncle duk ka canza min tamkar ba kai ba, ya dubeta ya lumshe idanu, dole ne in koya ma kaina yanda zan cire mata daga raina, saboda me? Ya tashi zaune, Allah ya ce matayanku da ƴaƴayanku maƙiya ne a gareku, ta dubeshi sosai amma kuma ya ce idan kukayi haƙuri kuma ku ka gafarta musu lallai shi Allah mai gafara ne a gareku, sannan in ni na maka laifi ita fa Hadiza? Kada ka tauye haƙƙinta domin Allah ba zai barka ba, ya ce to naji na kuma gode ya koma ya ƙwanta. Cikin sauran ƙwanakin da suka biyo baya ya ɗan canza musu dukansu, ranar Lahadi ba shi da Office an tashi da ruwan safe. Ranar yana manne da Bebyn tashi, Abulkhairi kuwa yana can gurin Tani ta mishi wanka yana ta rigimar za ya ci Indomie, suka nufi kitchen tare, Uncle yana raɗa ma Bebyn tashi cewa yau insha Allah sai ya samar ma Abulkhairi ƙani, ta sake rungume shi, Allah ya bamu mai albarka, Allah ya amsa.


Cikin shirin tafiya masallaci sallar azahar ya shigo ɗakinta, fitowarta daga wanka kenan, ya dubeta da murmushi na zaci zan sameki kina bacci? Ta ce haba dai sallah zan yi in sama maka abinda za kaci, ya fita yana cewa da kin ƙyauta, ina Babana mu je masallaci? Ta ce yana falo.


Ta gama shirya tebur ɗin da kalolin abincin da ta yi su cikin lokaci kaɗan, sannan ta nufi ɗakinta don ƙara gyara jikinta, ta kalli agogo ta sanya tsayin la'asar ne ta ci gaba da shafe-shafenta a gaban madubi, Abulkhairi ya shigo da gudu hannuwanshi cike da kalolin sweet da cakulet..




#######

[12/23, 21:20] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 15*




Yana cewa gashi Ummi Abbana ne ya bani ta ce cin zaƙin nan ya yi yawa sufa ka ci kafin ka fita,ta amshe muje ka ci abinci,ya soma kuka ta ɗora shi saman teburin cin abincin zauna nan in sa maka abinci,tun daga harabar gidan yake jiyo kukan yaron, da sauri ya shigo me ya samu Babana ne? Ta dubeshi Uncle cin zaƙin Abulkhairi ya yi yawa fa,shi ne na amsa na aje ya iso yasa hannu ya ɗauke shi kasan in da ta ɓoye? Ya ɗaga kai alamun Eh, ya ce muje in ɗauko maka, cikin marairaita ta ce, yanzun Uncle ɗauko Mishi za ka yi? Ya ce haba Beby zaƙin nan da maiƙo shi ne ya kawo kakanninmu da iyayanmu birni bar shi ya ci ko Babana? Ya ce eh, tagumi tayi ta rakasu da idanu har suka shige ɗakin ta kai tsaye ya nuna durowar madubin ya jawo yana ƙwaso mishi gabanshi ya faɗi lokacin da ya kuma arba da ƙwalayan.


Shirun da taji ya yi yawa shi ne dalilin da yasa ta bin shi domin tuni yaron ya fito da kayan zaƙinsa a hannu, zaune ta same shi bakin gado ya riƙe kai da sauri ta isa gurinshi, Uncle lafiya kanka ne yake ci....?" Hannu yasa tare da ɗauke ta da wani mari mai saka mutum yaga wuta, ya miƙe tsaye ki haɗa kayanki ki tafi garinku ki je kiyi boko tunda shi ki ka fi so fiye da auranki,ku na.....ba tasan lokacin da ta daka tsalle ta faɗa jikinshi ba, kada ka furta Uncle,ban maka abinda zaka sake ni ba, ta soma kuka mai tsanani, ya isa gurin durowar ya ciro ta gaba ɗaya ya yarda ita ƙasa,kin ce kin daina gashi Allah ya kuma nuna min ki sani duk macen da bata son ta haihu da mutum to ko shakka babu bata son shi ne, kuma bata ƙaunarshi,kin fi ƙaunar boko, ta tsura ma ƙwalayan idanu, wasu hawaye masu zafi suka soma sunturi a kumatunta,haƙiƙa na cancanci ka rabu dani tunda na kuma aikata laifin da na ɗauki alƙawarin tuba daga gare shi ta miƙe ta soma haɗa kayanta, shi kuma ya fita ya ɗauki ɗan shi ya fita rai ɓace suka yi waje.


A'isha kuwa tuni ta soma haɗa kayanta,tana gamawa Jabiru ya shigo, maigida ya ce zamu yi tafiya ko? A'isha ta yi ƙarfin hali ta ce eh, yawan kayan da yaga ta fito da su kuma ba yaron shi ne yasa shi tambayar anya Hajiya lafiya? Ta ce lafiya lau,nan ya shigar da kayan bayan mota suka ɗauki hanya, lokacin da suka kusa isa garin na Jigawa tuni ta tsure ta shiga tunanin me zata ce da mahaifan nata anya kuwa zasu yarda da ita? Lallai maza ba su da tabbas dubi abinda ya dinga yi mata can baya ta daure ta haƙura ta yi ta bashi uzuri amma shi gashi ya kasa bata, cikin wannan halin suka isa Jigawa duk da gudun da Jabir ya yi sai da suka yi dare a hanya suna isowa ƙofar gidan A'isha hankalinta ya ƙara tashi,layin nasu shiru saboda dare ya soma yi amma yaya Abdulrahman yana zaune a ƙofar gidan saboda garin da zafi,don tun yamma suke saran za'ayi ruwa amma har lokacin shiru sai dai zafin da garin ya yi. Ya tsura ma motar idanu lokacin da ta tsaya ganin A'isha ta fito ya taso yana jiran yaga fitowar maigidan,ganin Jabiru ya fito sai Abdulrahman ya isa gurinshi, Jabiru lafiya kuwa da darennan? Jabiru ya miƙa mishi hannu tare da cewa lafiya lau, suka gaisa A'isha kuwa tuni ta yi cikin gidan cikin sanyin jiki Abdulrahman ya biyo ta ya sani ba lafiya bane domin tunda aka yi mata aure wannan ne karo na farko da ta zo batare da maigidan nata ba,tuni mahaifan nata sun rufe ƙofa, Abdulrahman ne ya ƙwanƙwasa,Abban su ne da ke zaune yana nazarin wasu takardu ya ce wanene? Abdul ya ce ni ne,Abban ya buɗe yana cewa ba ka ƙwanta ba? Ganin A'isha ya sa shi tsayawa yana kallonta, jikinta ya kuma mutuwa, Abbanta ya ce ke da maigidan ne? Ta ce a'a Abdulrahman ya ce ita da Jabiru ne bari inje in kai shi masauki,Abban ya juya ya koma in da ya taso ya zauna A'isha ta shiga ta tsugunna daga gefe ya dubeta, ina yaron? Hawayen da ta maƙe ya soma sintiri akan kumatunta, ya tattara hankalinshi gare ta me yake faruwa na ce? Cikin kuka ta ce Uncle ne ya ce in dawo gida, ya maimaita kalmar ki dawo gida? Ta ce eh, ya ce lallai kin aikata mishi laifi mai girma, ita dai ta ci gaba da kuka, ya ce shiga ciki Ummanta tana shafa'i da wuturi, tana jin su amma bata san dawa yake magana ba,ganin A'isha ta kaɗu sosai, ta aje hijabi tana cewa dama ke ce? A'isha ta zauna bakin gado tana kuka,umma ta ce me ya faru? Cikin kuka ta ke sanar da Mahaifiyarta duk yanda abubuwan suka faru, Umma ta ce har da sakaki? Umma ta jinjina kai amma kin tabbata baki aikata ba? Ta ce wallahi Umma ba ni na kawo maganin ba ma, ta ce to shi kenan bari mu saurari sarautar Ubangiji."


Shi kuwa Abbanta take ya kira layin abokin nashi duka suna rufe hakan ya yi matuƙar ɗaga hankalinshi, amma ya haƙura sai zuwa da safe. Yana yin sallar Asubahi abinda ya fara yi shi ne neman layin aminin nashi,daidai lokacin shima yana zaune kan sallayarshi,kiran na sirikinshi, kuma amininshi ya shigo. Alhaji Saddiƙ,yasa hannu ya ɗaga wayar,sai da suka gaisa tare da tambayar lafiyar iyalai sannan Abban ya ce Friend sai kuma naga A'isha jiya ita da Jabiru, ta shigo tana min kuka tana sanar da ni wai ka ce ta dawo gida,da shiga ciki kuma mahaifiyarta ta ke sanar da ni har da saki, Alhaji Saddiƙ ya ce ta tsorata ne zan yi magana sai ta yi zaton ko kalmar saki zan furta amma a zahiri ni ne na turo ta gida amma ban sake ta ba, Abba ya ce tayi maka halinsu na mata kenan wato shirme? Alhaji Saddiƙ ya jingina bayanshi da bango sannan ya ce wato Friend tun daga abinda Jummai ta shammace ni ta aikata min cikin gidana sai na shiga tsoron mata da kaidin su. Na samu kaina cikin ƙin amince musu sai A'isha a ganina ita ce kurum tasha banban da sauran mata,ƙwatsam wata rana sai take shawarta ta damu yi tsarin iyali saboda yaro da kuma karatunta,na nuna mata ban amince ba donni yanzun na soma samunta ta ce shi kenan zance ya wuce, ashe yarinyar nan ta hau shan maganin hana ɗaukar ciki ban an kara ba sai lokacin da zamu yi tafiya zuwa aikin Hajji,na ganshi cikin kaya hankalina ya tashi amma ta bani haƙuri tare da ɗaukar min alƙawarin ta daina,na haƙura kawai sai gasu jiya cikin durowarta da yawa ta ɓoye, wato abinda na lura tafi son karatunta bisa haihuwar shi ne yasa na ce ta zo gida don kusan me yake faruwa,in tafi son karatun babu damuwa sai in sawwaƙe mata Allah ya raya wanda muka samu, kuma ba shi ne zaya shiga tsakanin hulɗarmu ba, haka nan zana ci gaba da ɗaukar nauyin karatunta.


Abbanta wanda ya yi shiru yana sauraron shi kasa magana ya yi har sai da abokin ya kai aya, sannan ya ce ka jira ni muna tahowa yau insha Allah, batun ya sha ƙarfin ayi shi cikin waya, lokacin da Abba ya baiwa Ummanta labari ta dubi ƴar tasu ta ce,dama kin taɓa shawartar shi da batun tsarin iyalin? Ta ce eh, Umma ta ce ai ke ce ki ka aikata shi ne zaki ce baki ma san wanda ya kawo miki maganin ba,don kin raina mana hankali, A'isha ta yi shiru ta sani Allah shi ne kurum shaidanta, kuma shi ne zai fidda ta daga cikin wannan halin,don ta zama dole gareta ta kuma amsa wannan laifin a karo na biyu, Abbanta don tsabar takaici ya kasa ce mata ƙala, ya dai ce da Ummanta zai maida ta Katsinan.


Lokacin da zasu tafi Umman ta yi mata faɗa tare da nasiha ta kuma kafa mata dokar cewa in har ta kuma aikatawa mijinta laifin da ya koro ta, to ta nemi wata uwar ba ita ba,ko cikin mota Abba yana gaba ne suna hirarsu da Jabiru, amma ita tana ƙwance bayan mota abin duniya ya ishe ta, sai dai tana kaiwa Allah kukanta, Allah ya toni asirin wanda ya aikata mata wannan sherrin don kawai ya raba ta da mijinta.


Hadiza da Tabawa duniya sabuwa, domin duk abinda ke faruwa suna laɓe kuma akan idanunsu A'isha ta tafi gida, tamkar su haɗa fati don daɗi, ta rungume Tabawa tana yi mata godiya. Tabawa ta hau yiwa kanta kirari,sai ni ƴar Audu naga ta kowa tawa ta yi wuyar gani, sai ni Laraba Tabawa ranar samu, ta dubi Hadiza ban taɓa ƙulla makirci ya ƙi shiga ba, kuma asirina bai taɓa tonuwa ba,ba kuma zai taɓa ba,ya ya batu na ƙarin albashi? Tare da ƙyauta ta musamman? Hadiza ta ce duk kin samu bugu da ƙari zan shiga in fita gurin kanainaye maigidan da kissa shekara mai zuwa ni da ke muje aikin Hajji mu ma kamar yanda A'isha ta je da mai aikinta Uwani, Tabawa ta ce da kin ƙyauta,ni kuma da na dinga shirya miki kissoshin da mijinki shi da ƙara aure har abada, ita kuma wannan A'isha ta tafi kenan,ki yi yanda ki ke so ke kaɗai cikin gidanki, kuma gurin ƙyaƙkyawan mijinki, ta kalli hoton shi da ke manne jikin bangon falon ta ce wannan maigidan naki da ƙyau yake,ba don ban yi boko ba da nima sai na gwada sa'ata, Hadiza ta ɗaure fuska, Tabawa kina hauka ne? Hurumina fa kike so ki shiga kenan? Ta ce Allah ya baki haƙuri kin san bama zai yiwu ba.


Sun iso gidan lokacin babu kowa Hadiza da Tabawa sun je kasuwa sai ko maigidan wanda ya dawo don jiran aminin nashi,tuni yasa Uche ya shirya musu abinci sai dai ban da Jabiru da ya amshi nashi ya fita babu wanda ya saurari abincin domin Abban ya ce yau zaya juya suyi abin da ya kawo su,a gaban A'isha Uncle din nata ya karanto ma Abban nata dukkan abubuwan da suka faru ciki har da marin da ya yi mata,Abban ya dubi A'isha ya ce kin tabbata hakan ya faru? Ta ce eh,ya faru Abba sai dai wallahi ba ni ce na kawo maganin ba, Abbanta saboda tsabagen haushi bai san sanda ya miƙe ya ɗauke ta da mari ba yasa hannu cikin aljihun shi ya ciro dorina wadda ya yo guzurin ta tun ɗaga gida ya shiga zabga mata, abinda bai taɓa mata ba ko lokacin da take yarinya. Cikin sauri Uncle din nata ya isa gurin Aminin nashi ya kuma samu sa'ar riƙe bulalar ya ce haba Friend wannan bai dace ba,ai Beby ta wuce duka.


Abban yana haki ya ce bata wuce ba, kuma daga yau bata babu boko na hana, ta zauna ta nemi aljannarta,bokon banza da iyakar shi duniya zata kashe aurenta saboda shi? Abu na gaba kuma ban yafe miki ba in har kika kuma shan wannan maganin sannan ki nemi wani uban ba ni ba,ke hanyar Jigawa ma kada ki yarda ki biyo ta, ya maida bulalar shi cikin aljihu ya nufi fita, Uncle ɗin ya bi shi don Allah ka tsaya ka jini, ya ce ba zan tsaya ba na kula kai ne ka shagwaɓa ta in ta ɓata maka tafi ƙarfin duka ne? Kasan sa mata tukunna ta san kai ba abokin wasanta ba ne da zata aikata laifin sannan ta raina ma mutane hankali wai ba ita ce ta kawo maganin ba, to ba sai ta faɗi uban da ya kawo ba? Uncle ɗin ya bishi suka fita ya yi yayi dashi ya bari sai gobe ya tafi ya ce shi sam bai shigo Katsina da nufin ƙwana ba, Kano zai ƙwana, dole ya kira wani direban domin Jabiru yana buƙatar hutu, ya shiga ya kaishi Kano.


Lokacin da ya shigo gidan har lokacin Aishan tana tsugunne a gurin tana kuka,sam bata ga laifin mahaifin nata ba domin ya yi mata haka ne domin gyara,in ma laifin ne tafi ganin na Uncle ɗinta wanda ya kasa yin haƙuri da ita koda kuwa ta aikata laifin da ake zargin ta dashi, ganin Uncle ɗin ya nufo gurinta sai ta miƙe da hanzari ta nufi ɗakinta tare da maida ƙofa ta rufe. Ya yi ƙwanƙwasawar duniya ta ƙi ta buɗe, ya yi lallashin haba Beby yi haƙuri ki buɗe mana,taƙi dole ya ƙyale ta,sai in ta huce ya san fushi ta yi domin kuwa bata da taurin kai tun zamanta da shi yau ce rana ta farko da yaga fushinta.


Wasa-wasa har washegari ba ta fito ba,ya zaci in ya tafi aiki zata buɗe, amma da ya dawo ya tambayi Tani ta tabbatar mashi bata fito ba, ita kuwa sallah kawai ke ɗagata daga gado, aikin kuka kawai take yi bai ɓata lokaci ba gurin nemo masu saka ƙofa suka cire mishi ita ya jingine ta gefe ya shiga tana ƙwance ruf da ciki ta kifa kanta kan filo ya ɗago ta Beby yi haƙuri tashi zaune,ji ya yi jikinta zafi rau, gashi fuskarta ta kumbura dam saboda kuka, ya yi lallashin duniya ta ƙi shiru,dole ya kira Nafisa cikin waya cewa ta zo da matsala. Tabawa tana kallon Nafisa ta fito cikin motarta ta shiga sheƙa dariya taje gurin uwargijiyarta tana cewa Antyna ga waccan uwar iya yin nan bata san wadda take son bata nan ba, suka yi ta dariya domin basu san cewa ta dawo ba, Tabawa ta ce na rasa zaman da yake yi a sasanta, Hadiza ta ce naci ne irin nashi, kuma zai haƙura da ita da kanshi.


Nafisa ta zuba wa Aisha idanu, me ya faru haka jikinta duk tabon bulala? Uncle ya ce Sister ki dai lallasheta,nasan zata gaya miki komai, ina zuwa,ya fita Nafisa ta ce A'isha rigima ku kayi da Brother ɗin?" Tana buɗe baki sai kuka ya ƙwace mata, muryarta ta ƙi fita, cikin kuka da dasashewar murya take sheda ma Nafisa yanda lamuran suka faru. Nafisa ta tausaya mata kuma ta amince cewa A'isha ba zata aikata hakan ba, ta ce maza kenan, amma shi Bros ya mance haƙurin da ki kayi dashi baya sannan babu binciken da ya yi,dan ya ganshi a sasanki ai gidan da mutane kuma yafi kowa sanin cewa Hadiza zata iya aikata abinda yafi ga wannan la'ananniyar mai aikin tata sai ka ce irin karuwan nan na maraba, ta dubi A'isha tashi ki shiga kiyi wanka tana fitowa zazzaɓi ya rufe ta,sai rawar sanyi take yi, Nafisa ta ce shirya muje asibiti, ya shigo ta ce dole zamu je muga Likita, jikinta sai rawa yake yi, ya ce to kuje ko in zo muje, ta ce bari kawai muje mu dawo..




#######

[12/24, 09:00] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 16*



Amsoshin da ta bawa Likitan sune suka sa shi ya ce ba zai bata magani ba har sai ya yi mata gwajin fitsari sannan ya yi mata wasu gwaje-gwaje ya fitar da sakamakon ciki wata biyu. Nafisa ta dube ta kin ga Ishara ko? To da yaja garin duka cikin ya zube da ya huta. A'isha kuwa shiru kawai ta yi fatanta Allah ya tona mata asirin wanda ya ƙulla mata sharri,ya bata magungunan da suka dace suka nufo gida.


Yana zaune yana kallon Aljazira suka shigo,su Hadiza basu ga fitar su A'isha ba sai dawowarsu suka gani, Tabawa ta ce"innalillahi, wannan tsinanniyar bata tafi daga garinnan ba ko ko dawo da ita aka yi?" Hadiza ta ce wannan fa kada tasa nima in yi kisan kai, wallahi na tsane ta, amma Tabawa dole ne ki samo wata dabarar."


Shi ko ya biyo su har cikin ɗaki, A'isha ta ƙwanta har yanzu in ta kalleshi ranta na zafi, ta lumshe idanu ya ce kun samu magani Sister? Ta ciro sakamakon daga cikin jakarta ta miƙa mishi ya amsa yana dubawa ya kalli Nafisa, wadda ke kiran layin Hajiyarmu, ya ce Sister yana nufin Beby tana da ciki? Kafin ta bashi amsa Hajiyarmu ta ɗaga wayar nan Nafisa ta shaida mata ciwon A'isha ta kuma shaida mata cewa ciki gare ta wata biyu, Hajiyarmu ta ce Allah ya bata lafiya, haka ta yi kiran sauran ƴan'uwa tana shaida musu, shi kuwa gaban A'isha ya zauna, Beby don Allah ki yafe ni lallai yanzun na amince ba laifinki ba ne ya miƙe ya nufi ɗakinshi ya ciro ƙwalayen maganin yaba Nafisa kin gan su nan har da alamun wanda aka sha a ranar sannan karanta ki gani da tasha da cikin ya fita tunda sun rubuta hakan, Nafisa ta gama dubawa ta ce kasa idanu sosai musamman kan wannan Tabawar, ya jinjina kai shi kanshi baya ƙaunarta, amma yanzun ba shi da hujja, sai dai zaya sa idanu.


Nafisa tana gidan har dare sannan ta ƙara bawa A'isha haƙuri ta tafi shi kam har lokacin bai ga fuska gurin Aishan ba, gashi ranar gurin Hadiza yake,yana nan har sha biyu sannan ya nufi gurin Hadiza yana fitowa har ya gota ya nufi ɗakinshi sai yake jin magana ƙasa-ƙasa ɗakin Hadiza labulen window ya ɗaga,suna zaune kan gado Tabawa tana cewa ina zaton bata da lafiya ne fa dama tsinanniyar zata mutu da mun huta. Hadiza ta ce lallai wallahi da sai nayi party, yanzun wane kalar makircin za'a shirya mata tunda wannan na maganin sai mun ƙarasa shi, ta ce ai ba wahala zamu yi gurin shiga sasanta ba,kin san ita idan mijin na nan bata da lokacin kowa sai na shi, to bari zamu yi sai ranar da miji ke gurinta in ya kama week end sai mu samu wani ya haɗa mana layar ƙarya asa sunan ki da nashi ace an shiga tsakanin ku a zuwan ita ce tayi sai musa a inda zai gani kin san zai kai a buɗe mishi, to daga nan sai muyi yin wasu dabarun zai yarda tunda zai zarge ta yanzun ma dama cikin zargin take. Hadiza ta ce hakan ki naga zai yiwu? Ta ce to gidan da na soma aiki mata shidda muka kora da wannan dabarar, Hadiza ta ce shi kenan Allah yasa wannan karon mu dace ko da yake wancan karon ma mun dace tsabar naci ne da kuma ƙwadayi. Tabawa ta ce ina kallon lokacin da ya ɗaura mata mari da yaga maganin amma don rashin zuciya ta dawo ina zato har da saki ya yi mata, Hadiza ta ce ke in mungwada komai be yiwu ba Allah zan sa mata guba ne kawai. Tabawa ta ce kin Istigfari daga baya shi kenan kin huta,ya saki labulan ya zo ya turo ƙofar,dukkansu suka waigo ya ce to duk na jiku, Allah ba azzalumin sarki ba ne,yau gashi ya toni asirin ku ya juya ya fita ya barsu cikin zufa da tashin hankali shi kaɗai cikin ɗakinshi,ya zurfafa cikin tunani har hawaye sai da ya yi saboda tausayin Beby har amsa laifin nan don kawai tsabar bata son tashin hankali,ga dukan da ta ci bada laifinta ba,nan kuma gashi suna shirya mata sabon makirci ciki har da yunƙurin kashe ta lallai zama da Hadiza hatsari ni tunda har ta furta zata aikata gara ya ɗau matakin kada gidanshi ya zama sansanin ɗaukan rayukan jama'a.


Da safe kuwa ya miƙa mata takardarta,saki uku don ma kada ace ya yi haƙuri Allah yaga zuciyarshi. Da safe da ya fito bayan ya dawo daga masallaci ya gama duk shirye-shiryen shi zai fita zuwa Office zaune ya samu Hadiza da Tabawa tana bata shawara kan cewa taje ta bashi haƙuri, ya yi sallama sannan ya miƙa mata takardar, gashi kada in dawo in same ku cikin gidana, ya fita ya bar ta tana ihu tare da roƙonshi har gidan Aisha wato sasan A'isha ta bishi tana ba shi haƙuri kukan ne ya tashi A'isha daga bacci tun bayan da tayi sallar Asubahi,yana shiga ɗakin A'isha ta bishi ta tashi zaune a razane tana kallonta, ya ce na ce ki tafi me zan miki,saki uku ne ki je gaba kiyi kisan ba gidana ba na gaji, A'isha ta ce haba Uncle me zai saka yanke wannan hukuncin? Ya zauna kusa da ita wannan shi ne mafita,ya koro mata komai a gaban Hadiza haƙuri ta shiga bawa A'isha tare da cewa ta taimaka mata don Allah, A'isha ta ce Uncle me kaga za'ayi? Ya ce gidan su kawai zata sannan ya rusuna gaban A'isha, Beby don Allah ki min afuwa bisa abubuwan da na miki ba da laifinki ba, cikin sauri ta miƙe ta ce Uncle don Allah ta shi don Allah kada ka kuma min haka na sani kana da hujja sai dai na gode Allah da ka gane cewa ba laifina bane, sannan kayi saurin yiwa Hadiza saki uku,ka sani ko sanadin wannan ta shiryu? Ya ce sakin za ya fi sa ta shiryuwa in tayi wani auren gaba in zatayi irin wannan sai ta tuna da sakin sai ta fasa. A'isha ta dube ta kije gidan ƙila manya ba zasu rasa yanda za'ayi ba, Itama dai tasan ta faɗi haka ne saboda Hadiza ta tafi,ta kuwa miƙe ta nufi gidan nata ganin zai yiwu a maidata.


Bayan fitarta A'isha ta dubeshi baka ƙyauta ba Uncle,ai sai kayi mata ɗaya shi ne na gargaɗi in yaso sai ayi mata nasiha baka gudun Allah ya jarabce ka da sonta? Ya ce insha Allah na rabu da ƙaya ne, Hadiza ba zata taɓa hankali ba. A'isha ta ce gashi ka saba da mata uku, ya ya zakayi da ni ɗaya dole kenan sai ka sake aure? Ya kalle ta Beby ni kam kin isheni zaman duniya, ta ce yanzun shi kenan nayi missing ɗin makaranta ta kenan,ya ce in ji wa? Ta ce ka manta abin da Abbana ya ce? Ya yi ɗan murmushi ai dole ne muje mu wanke ki gurinshi ta ce yaushe? Ya ce da zaran kin soma jin sauƙi.


Mahaifin Hadiza da kanshi ya samu Alhajinmu da batun ya ce be sani ba, amma bari ya kira Abubakar É—in, Alhaji SaddiÆ™ kuwa ya zayyano musu duk yanda al'amarin ya kasance, Alhajinmu ya ce laifinka a nan saki uku da kayi,Babansu Hadiza ya ce ai ana gyarawa inji wasu Malaman.


Alhajinmu ya ce a'a duk wani Malami da zai ce ana gyara saki uku wannan yana faɗin son zuciyarshi ne kawai, abinda wasu Malamai suka dogara da shi,shi ne lokacin da Manzon Allah ana saki uku a koma,to lokacin Umar Allah ya yarda da shi,sai ya hana saboda yanda maza suka maida saki uku kowa saki uku, shi ne wasu Malamai suke maidawa saboda Manzon Allah bai hana ba amma ya umarce mu da cewa muyi biyayya da Sahabban sa, domin su sun ɗora ne daga in da ya tsaya don haka muyi haƙuri Allah ya haɗa kowannansu da rabon shi na alkhairi in kuma da rabon zasu zauna can gaba sai su zauna. Baban Hadiza ya ce ka dai ɗaure mishi gindi ne. Alhajinmu ya ce to ni dai akan su koma saki uku gara na ɗauki laifin da ka ɗora min, ya tashi ya yi saman shi haka taron ya watse kowa ya kama gabanshi shi kuwa Uncle ya yi matuƙar farin cikin faruwar hakan.


Sun je Jigawa ƙwanansu ɗaya inda Uncle ɗin ya wanke Bebyn tasa gurin mahaifanta har sai da suka tausaya mata Uncle da kanshi ya sanar da Abban cewa zata koma karatunta, sai dai zata bar Sokoto zata dawo Kano ko Zariya.


To Zariya ta samu lokacin da zata tafi ta ce ba girmanshi ba ne zama babu mata, ya ce hakan ya fi mishi ƙwanciyar hankali, zai dinga zuwa mata week end haka rayuwarsu ta ci gaba cikin sha'awa, ta haifi ƴar ta mace wadda ta ci sunan Hajiyarmu, suna kiranta Ummulkhairi.


Ƙwanci tashi babu wuya a gurin Allah,yau ga su A'isha ana rantsar da su matsayin likitoci Æ™wararru, dukkansu suna sanye da kaya na musamman lokacin Æ´aÆ´an A'isha huÉ—u ta Æ™ara Abubakar sunan Uncle suna kiranshi Khalifa, sai takwararta A'isha suna kiranta Humaira. Ta samu lambar yabo da Æ™warewa ta musamman, Uncle É—in ta da ke zaune cikin É—inbin jama'ar da suka halarci gurin. Alhaji Bello ya  ce kai Alhaji SaddiÆ™ ban da na san A'isha zan Æ™aryata ita ce me Æ´aÆ´a huÉ—u, Alhaji SaddiÆ™ ya ce abinda zuciyata ke faÉ—a min kenan,taro ya tashi in da suka yi hotuna da danginsu da Æ™awaye, su Abdulrahman da amaryarsa da su Jafar duk sun zo su Anty Nafisa kuwa sai rabon abubuwa da aka buga suke yi taro ya tashi suka shiga shirin zuwa gida.


Sati ɗaya da gamawarsu ya ɗauki A'isha tare da yaransu wai za su masa rakiya,sai gasu gaban wani katafaran gini mai hawa biyu, maigadi ya buɗe musu suka shiga, tun daga yanda aka tsara falon ƙasan ta gane cewa asibiti ne. Sun hau ko'ina da ina, duk abinda ake nema a cikin asibiti akwai shi a nan. Sai da suka fito falon ƙasa ya miƙa mata makullai tare da takardun asibiti ya ce Beby wannan ita ce gudunmawa ta gare ki. Ta zuba mishi idanu ta rasa me zata ce kawai sai ta rungume shi tare da sumbatar ko'ina a jikinshi sai kawai su Ummulkhairi suka soma tafi suna dariya suni ta murna da yaran.


Shi ne ya ɗauki nauyin nemo mata Likitoci waɗanda suka karanci fanni daban-daban sannan ta samu aiki a babban asibitin gwamnati na jihar ta Katsina domin taimakon talakawa musulmai. Domin ta sani ba kowane zai zo asibitin na taba mai suna (AishSadik Hospital)ita ce tasa mishi suna, haka nan A'isha ta ci gaba da aikinta tare da kula da Uncle ɗin ta da kuma ƙyawawan ƴaƴansu, Alhajinmu girma ya sa shi dole ya ajiye aikinshi duk Uncle ke kula da komai shi kuma ya huta rayuwarsu mai ban sha'awa.


Yasa hannu ya zare farin gilashin idanunsa ya bita da kallo, maimakon kallon (CNN) da yake yi,ta yi Æ™yau cikin doguwar rigarta atamfa Æ´ar Holand,Æ™irjinta cike tamkar ba ta taÉ“a shayarwa ba,yanzunne take cikin shekarunta ashirin da biyar in bai manta lissafi ba yanzunne komai nata ya Æ™ara zaunawa musamman Æ™ugunta,lallai shi kan ya gode mahaliccin shi da wannan baiwa ga kuma Æ´an yaranshi, bai san ta iso gurin ba sai  kawai ya ji ta hura mishi idanu, firgigit ya yi tare da jawo ta jikinshi, ta Æ™wanta a cinyoyinshi tana kallon fuskarshi ya ce Beby kullum Æ™ara Æ™yau ki ke yi da Æ™uruciya bana gajiya da kallonki. nima ai bana gajiya da kallonka, ya ce in yaran nan sunyi hutu ya kamata mu É—an fita ko na sati uku ne zuwa waje suyi mana rakiya Æ™ila ma su samu Æ™ani ko Æ™anwa, ta ce ai sun kusa hutun nan da sati mai zuwa.


A birnin na Misira waton Egypt wata rayuwa suke yi tamkar sababbin aure,sam ya manta da Jummai da mummunan zaton da ta saka shi a baya, yanzun sai farin ciki tare da godiya ga Allah da baiwar da ya yi mishi na samun mace jaruma mai haƙuri da biyayya,haƙiƙa da duk mata zasu ɗauki halin haƙuri da sauƙin kai irin nata, da mace-macen aure ya ragu. Tabbas haka ne, Allah Ya bamu haƙuri domin Allah yana tare da masu haƙuri.




ALHAMDULILLAH!


Na gode ƙwarai

Taku ko yaushe, Halima Abdullahi K/Mashi.

No comments