Recent Updates

Mummunan Zato Book 2

 


____________________________

   *📗MUMMUNAN ZATO Book 2📗*


                       *NA*

*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*



              *page 1*



A hankali ta maida ƙofar ta rufe, sannan ta juyo da nufin ta ƙaraso cikin ɗakin. Idanu ta zare tare da dafa ƙirji, sannan ta ce "innalillahi" lokaci guda ta juya baya ta runtse idanu,duk ta yi haka ne sakamakon ganin Uncle ya fito daga wanka daga shi sai gajeren wando,yana goge jikinshi da tawul. Ta kama ƙofar zata buɗe, ya ce "Beby" ta ce "Umm." Ta ce "bari....em....bari na dawo in ka gama ban san kana ciki ba ne,don Allah ka yi haƙuri." Ya ce "Me ki kayi min? Ki zo kiyi aikinki,kin ji ko" ta juyo amma ƙasa take kallo tana tafiya ta ci karo da gado, da sauri ta ɗago idanunta ta sauke su akan gadon, cikin mamaki ta tsaya kallon gadon sam bai kai nata girma ba, kuma shinfiɗe yake da zanin gado an lailaye shi,ta ɗago kai ta kalli Uncle tayi sauri ta kuma sunkuyar da kai don ganin har yanzun bai saka riga ba, kuma bai damu ba sai shafa manshi yake yi. Cikin in ina ta ce "An....an ma riga an gyara ashe?" Ya dube ta,duk ta daburce. Ya ɗauki riga shirt fara mai gajeren hannu ya saka,ya tako zuwa gurinta.


Ya kamo hannunta ya zaunar da ita yana riÆ™e da yatsunta cikin nashi kanta yana kallon Æ™asa har yanzu bazata iya kallonshi ba saboda gajeren wandon bai rufe cinyoyinshi ba sannan duk cibiyoyinshi gashi ne, ya É—an murza mata yatsun "Beby bai haramta ki ga tsiraici na ba,ko ni in ga naki ba" ta dube shi da sauri ya ce "Yes saboda ni da ke halalin juna muke" Ta sauke kanta Æ™asa amma zuciyarta tana son ya fayyace mata komai don ita bata gane nufin shi ba,ya ce "yanzu dai Beby ni wanene a gurinki? Ma'ana menene matsayi na?" Ta dube shi sannan ta kuma sunkuyar da kai,a hankali ta ce "Miji" ya ce "me ake nufi da Miji? Ta yi shiru zuwa can ta ce "Wanda ya yi aure shi ne Miji"  Uncle ya yi É—an murmushi don jin shirmenta, ya ce to menene aure?"  Ta ce "Aure?" Ya ce "Umh" ta ce kamar  dai yanda ake yi mutane su taru a É—aura shi kenan sai kuma a kai matar" ya ce "to daga nan fa?" Ta É—an dube shi sannan ta rufe fuska, ya ce "Gaya min idan an kaita sai tayi me a gidan? Ta ce "zata rinka yin shara da wanke-wanke tanayin girki,ta rinÆ™a kula da yara.


Ya shafa hannunshi yana cewa, "Good, ashe kin sani? Ta yaya akeyi ta samu yaran?" Ta ce "Iye!' Ya ce "Ya ya za'ayi ta samu yaran?" Ta ce, "Ita ce zata haife su." Ya ce, "Haka nan zata haife su?" Ta ce "Eh,in cikinta ya yi girma." Ya gyara zama don jin sun gangaro inda yake son ji, ya ce "To ya ya akeyi ciki ya fito mata?" Ta ɗan yi jim,can ta ce, "Nima ban sani ba,ƙila wani abinci ake ci." Dariya ta kufce mishi, duk cikin matan da ya aura babu wadda ba ta san kan zaman aure ba kamar A'isha, duk da cewa akwai sa'arta cikin su, ya dube ta.


"Kina son ki san yadda ake a yi ciki?"


Kanta yana Æ™asa ta ce, "Eh" ya yi É—an murmushi ya ce, "In na tambaye ki abu É—aya yanzun ba ki san shi ba, idan baki san shi ba,zan  haÉ—a su in miki bayani. Amma in kin san shi to zan bar ki har ki sani da kanki,wato zai zama assignment,amma fa ba zaki tambayi kowa ba,kin yarda?" Ta ce"To ya ya za'ayi na sani in ban tambayi kowa ba?" Ya ce "Zaki sani,yau da gobe." Ta ce "To yi tambayar in ji". Ya ce "Kin san Haila? Da sauri ta saka kanta cikin cinyoyinta,don ya taÉ“o mata abinda ta fi jin kunya a rayuwarta,don in tana Haila ko Ummanta tana jin kunyar ta sanar da ita, sai dai ta yi ta nuÆ™u-nuÆ™u har Umman ta gano da kanta, ballantana Uncle wanda bata daÉ—e da saninshi ba,ba su yi sabon da zata yi mishi wannan maganar ba. Cikin dariya ya ce, gaya min mana Beby,kin taÉ“a yi ne? MiÆ™ewa ta yi har tana cin karo ta fita da gudu.


Ɗaki ta koma ta faɗa kan gado zuciyarta tana ta bugawa, ita dai tana matuƙar jin kunyar Uncle,shi bai sani ba ne zai mata wannan tambayar?.


Shiko dariya ya dinga yi,lallai dole ya haƙura da A'isha yanzu don ba ya son takura mata. Ya fi son a yi komai cikin sauƙi kuma cikin ilimi.


Jummai kuwa tana ɗaki cikin murna haka nan wani gefe sai ta ji ranta ya ɓaci, da tana da iko ko macen ƙuda ba zata yarda ta saukar mata a kan miji ba, balle mutum, shi yasa ta sha alwashin ko zata tafi tsirara ne sai ta halaka duk macen da ta ce zata zauna zaman aure da mijinta. Ta sani goben nan yarinyar nan ta zama gawa,don haka ita ranta kar yake, insha Allahu. Ƙwana ta yi tana kai-kawo cikin ɗakinta,don ba zata iya runtsawa ba.


A'isha tana zaune tana tasbihi , sai kurum taga an turo mata ƙofa da ƙarfi. Cikin tsananin firgita ta miƙe tsaye, ganin Hajiya Jummai tuni ta soma karato addu'a cikin zuciyarta. Hajiya Jummai ta yi sororo ganin A'isha tsaye. Ta ce, A'a, ihun wa nike ji? Sai na ji kamar kakari a nan ɗakin." A'isha ta ce, "Kai,anya nan ne?" Ta ɗan yi tsaki tare da cewa, "Gaskiya ba nan ba ne." Hajiya Jummai ta shiga waige-waige, zuciyarta tana mai tabbatar mata ihun A'isha ta ji, amma abin al'ajabi A'ishar ce gabanta tana mai tabbatar mata cewa ba a ɗakin ba ne. A'isha ta ce "Allah ba nan bane Hajiya." Sannan ta ɗan rusuna ta ce, "ina ƙwana Hajiya?" Tsaki mai ƙarfi taja sannan ta fita a fusace, tare da sakin ƙofar da ƙarfi. Aisha ta yi shiru,a ranta tana son sanin me hakan ya ke nufi? Daga baya sai kurum ta taɓe bakinta gami da ɗaga kafaɗarta alamar su dai suka sani,ta koma ta zauna tana nazarin hirarsu da Uncle ta jiya. Daga bisani ta miƙe ta nufi kitchen ba don Uncle ba ne ya yi mata wannan tambayar game da Haila da zata ce ɗan iska ne,Don dai ta san halin Uncle shi ba ya iskanci. Uche ta samu yana aikinshi, suka gaisa sannan itama ta shiga haɗawa Uncle abin karyawa. Uche yana ɗan taya ta,ɗakinta ta nufa da tiren, tana shiga ta same shi zaune bakin gado cikin shirin fita. Ta dubi agogo,taƙwas saura ƙwata, ta ce Uncle har ka fito?" Ta dire tiren a gabanshi ta shiga haɗa mishi tea. Ta miƙa mishi sannan ta soma zuba mishi dankali da kwai tana saka mishi bota jikin bread,ya ce har fa na manta ina karyawa a gida,bari na sakko ƙasa Beby" ta miƙe ta ɗauko dardumar sallah ta shimfiɗa mishi, ya zauna ya shiga karyawa, sannan ta zauna tana gaishe shi. Ya amsa cike da jin daɗi, sannan ya ce "Ya gajiyar gudu jiya daga tambaya Beby sai ki ka gudu ko?"


Cikin cinyarta ta saka kanta,ta ƙi ɗagowa me zai sa Uncle ya dinga irin wannan maganar? Ai wannan kamar na ƴan iska ne. Ita fa ko a school ba ta wannan hirar da ƙawayanta,nata ganin bai dace ba.


Ya ce "shin wai Beby menene abin jin kunya? Ta ce "Uncle don Allah ni dai ka daina wannan zancan." Ya ce "na daina Beby, shikenan?" Ta ɗaga kai alamun "Eh" ya ce "To oya ci abincin ki." Ta ce, Uncle nifa sai anjima zan karya, wannan duk naka ne" Ya ce,ya ya zanyi da wannan Beby? Ai babu tsari ga kowane musulmi ya zauna ya yi mugun ci, Manzon Allah (S.A.W) yana kasa cikinsa kashi uku ne, ɗaya abinci, ɗaya ruwa, da kuma ya shaƙi numfashi dashi,don haka kin ga tunda da shi muke koyi, sai mu ma mu ƙwatanta. Zaka ci ka ƙoshi amma ta yanda ba zaka kasa tashi ba.


Aisha ta ce, "Haka ne." Sai kusan tara ya fito daga ɗakin,yana son yarinyar ta shiga ranshi,ba ya gajiya da zama da ita yana son shirmenta,wani sa'in ta yi magana tamkar babba, wani sa'in kuma ta yi masa aikin ƙuruciya,waton shirme.


Kai tsaye ɗakin Jummai ya nufa,don yi mata sallama kamar yanda ya saba,in ba ya ɗakin ki zai zo ya yi miki sallama da safe in zai fita. Tana zaune abin duniya duk ya taru ya yi mata yawa, yanzun haka jin ta take yi tamkar ta yi hauka,don tsabar baƙin ciki. Ina ma kuka zai ƙwace mata ko zata samu sassauci. Sallamar maigidan ce ta dawo da ita cikin hayyacinta, tsayawa ya yi yana kallonta. Itama ta ɗago idanunta jajir tana dubanshi, ya ajiye jakar hannunshi ya nufi gurinta ya tsugunna a gabanta cikin sassanyar muryarshi, ya ce "Jummai" ya kamo hannunta, "wai shin Jummai me yake damunki ne cikin watannin nan duk kin rame kin lalace,dube ki don Allah sai ka ce wata tsohuwa?" Kalmar da tafi tsana kenan a kira ta da ita, wato tsohuwa. Hawayen da take ta so su zubo ko zata samu sauƙi suka ƙi zubowa, sai gasu yanzun sun zubo masu zafi ma,ta ce dole ne ka ce min tsohuwa tunda yanzun ka samu yarinya ƙarama wadda zata iya haihuwa,ba irina ba juya. Ya miƙe tsaye cike da jin haushi, "kinga matsalarki ko? Kin gani ko? Me yasa ne ke har kullum ba ƙya fahimta? Nifa ina son sanin matsalarki ne ba wai ina kushe ki ba ne,in baki son in san damuwarki Jummai ai sai in barki tunda ke ba ƙaramar yarinya ba ce. Ace kullum bawa ba zai sakawa zuciyarshi salama ba,koda yaushe sai baƙin rai. In kina da matsala ne ba sai ki faɗa min ba? Ta ce "Ni dai don Allah je ka kawai,ka bar ni inji da kaina." Ya ɗauki jakarshi tare da cewa, "Allah ya ƙyauta." Ya fita.


Ihu ta saka ita kaɗai,a ruɗe su Suwaiba suka shigo suna cewa, "Lafiya Anty Jummai?" Tana huci ta ce "ku bar ni zanci uban yarinyar can" Sofy ta ce, "Me tayi miki ne Anty? Yanzu mu je muci ubanta? Ta ce a'a ku bari ba yanzun ba,ni zan yi maganinta. (Waya ga sa kai a uku) Yinin ranar Jummai sun ƙule ita da Aminiyarta, suna neman mafita. Ta rantse ta kuma rantsewa cewa maigidan yana kusantar yarinyar gashi an ce zata mutu shiru bata mutu ba,ta dubi Kari,ko dai zan sa mata guba ne? Kari ta ce "a'a komawa zamu yi gurinsu." Ta ce dibi asarar da na yi ta kuɗi, amma ace maganin bai ci ba? Kari ta ce,mu koma musu kawai gobe ke in abin ma ya ƙi wallahi sai mu nufi Nijar,zan binciko miki wani malami ko ince Boka.


Sun bar zancan a kan zasu koma in basu ga dai-dai ba,su nufi jamhuriyar Nijar, Allah ka tsare mu,Amin.


A'isha ko sam bata ma san hidimar da suke yi ba. Ranar ƙuƙewa ta yi tana ta ƙoƙarin yiwa Uncle ɗinta gurasa da miyar taushe. Ta haɗa zoɓonta mai daɗi, Uche ne ya taimaka mata ,Marka mai aiki taje ta sanar da Hajiya Jummai ta same ta suna magana da Karima,don haka ta sanar da su Suby cewa, amarya ta samu sake, tana can kitchen ta girka banza da wofi. Nan ko suka nufi kitchen ɗin suka shiga buɗe mata kuloli, suna cewa, me wannan ƙwamacalar wannan ƙazamiyar ƴar ƙauyen ta ke yi ne haka?" Aisha ko da kallo ta bisu, Sofy ta ce, ashe ma abincinsu ne irin na ƴan ƙauye. Suby ta ce,ke gaja wa kikayi wa wannan ƙwaɗon? Ita dai kallonsu take yi ranta yana zafi,ta ce ina ruwanku da kayana? Duk suka haɗa baki gurin cewa,sai mu zubar dashi,dube ta ƴar matsiyata kawai, A'isha ta ɗauki kulolin ta ta nufi ɗakinta ta dawo ta ƙwashe sauran kayan,su kam sai dariya suke yi mata,suna cewa in dai Alhaji ki kayi ma wannan ƙazantar ba ci zai yi ba ƴar neman gindin zama,zaki gane kuranki. Tagumi ta zuba tana zubar da hawaye,tuni ta kula waɗannan za su takura mata.


Yau tun huɗu Uncle ya dawo, domin tunda ya kira A'isha sau uku bata ɗauka ba,ya soma tunanin ko dai bata da lafiya ne? Ita ko sam bata ma san inda ta jefa wayar ba, kuma damuwar da take ciki bata tuna mata cewa tana da waya ba, domin dawowarta a jiya ne ma ta ɗauki wayar. Amma ba sa zuwa makaranta da waya. Lokacin da ya shigo tana wanka,zama ya yi yaga fitowarta, da ɗaurin ƙirji ta rufa da tawul ta ɗan yi yaƙe tare da kallon agogo tana faɗin, har ka dawo? Shi ko ita yake kallo yana son gano halin da take ciki,jin bai yi magana ba ne yasa ta maida kallonta gareshi ya ce "Beby me yake damunki?" Ta zauna bakin gado cikin irin murmushin takaicin nan,ta ce ba komai. Ya dawo kusa da ita wani guri yana miki ciwo ko? Ta ce "a'a,me ka gani ne Uncle?" Ya ce, "Sau uku ina kiran wayarki ba ki ɗaga ba, sannan yanzun na zo sai na same ki ba yanda ki ke ba.


A'isha baki kai lokacin da zaki haɗiye damuwa ba,sanar dani matsalar ki?" Ta girgiza kai "Yi haƙuri Uncle,ka bar zancan,maganar waya kuwa ni na ma manta ina da waya saboda ka san zaman makaranta yasa na saba da rashin waya." Ya ce, "Ni fa Allah sai kin sanar da ni." Ta ce, "to ni ban san me zan ce maka ba." Ya ce, wani guri ne yake miki ciwo? Ta girgiza kai tare da cewa, a'a.




#######

[12/9, 07:33] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 2*




Ya ce, To mene ne? Hawayen da take maƙalewa suka soma zubowa,ta ce su Suwaiban nan ne, ya ce Suwaiba? Ta ɗaga kai "Me suka yi miki?" Ta ce, Ni dai kawai ka ce musu ba ruwansu da ni in ina abuna, tunda dai ni bana shiga cikin harkarsu, ya ce to kiyi haƙuri zan musu magana." Ta share hawayenta, ta miƙe ta kawo mishi ruwa mai sanyi,yana sha taa ce, "Yau fa na maka abinci,baza ka ci na Uche ba, Allah yasa zaka iya ci?" Ya ce, "Me yasa ki ka ce haka? Ta ce, saboda ban ƙware ba,ni kuma gani da son yin girki." Ya ce,zan ci koma ya ya ne,ai Beby kina da ƙoƙari, na san nan gaba zan huta da cin abincin masu aiki ko?" Ta yi dariya, ya ce, sannan kada ki ce na dawo da hannun agogo baya,shin me ya haɗa ku dasu Safiya? Ta ɗan ɓata rai ganina kawai suka yi ina girki cikin kitchen sai suka hau buɗe min suna zagina wai ƴar ƙauye ina haɗa ƙwamacala,na samu sake.


Suna ta yi min,ni kuwa na fita dan sun ce zasu zubar min." Ya ce, "Ke da wanene cikin kitchen ɗin?" Ta ce,ni da Uche ne,yana taya ni, ya ce to kiyi haƙuri.


Koda ya fita ɗakin Hajiya Jummai ya nufa,tasha adonta tamkar ba ita ce cikin damuwa ba ɗazun, shawarar Karima ta ɗauka wadda ta shawarce ta da cewa ta yi ƙoƙarin ɓoye sirrinta cikin ranta ta daina bari ana gane damuwarta. Ya dube ta "Jummai ina yaran nan ne?" Ta ce, "Sannu da zuwa,ka dawo?" Ya ce, "Eh" ta ce, "Su Suwaiba?" Ya ce "Eh," ta ɗauki waya ta kira Safiya ta ce,su zo ɗakinta yanzun. Koda suka shigo, ganin Uncle sai suka yi tsimi-tsimi ya ce kece ki ka tura su su je suyi wa A'isha rashin mutuncin nasu? Ta dube su,me ku ka je kukayi mata? Suby ce ta soma cewa,nima dai ban sani ba, Allah Anty sharri ne. Sofy ma ta ce, to mu yaushe ma muka ganta ni na ma san ta dawo ne? Bai yi magana ba ya ciro wayar shi ya kira Uche, ya ce ya same shi a ɗakin Hajiya Jummai. Nan a gabansu ya tambaye shi cewa ya gaya mishi gaskiya me ya faru tsakanin A'isha da su Suwaiba. Ya ɗan soma inda-inda, Alhaji ya ce, daina kallonsu,ni ne na ɗauke ka aiki kuma ni ke biyanka don haka bana son kana kallonsu,in zakayi magana." Nan dai Uche ya sanar da su duk yanda aka yi, duk da yana tsoron masifar su. Nan ko Alhaji ya soma faɗa,ya ce maza su fita hanyar matarshi, domin kan A'isha kowaccensu zata iya kama hanyar gidansu,a cewarshi don A'isha ba ta da gidan da yafi wannan, tunda nan ne gidan aurenta.


Hajiya Jummai ma dai ta daure ta ce musu su fita harkarta,ta yi musu faɗa a gabanshi, amma yana fita ta ce,lallai yarinyar nan har ta samu guri ta soma kai ƙara? Tabɗi,lallai zata san da wa take yi. Su Suwaiba ma sun sha alwashin cewa sai sun ƙuntata mata.


Ita ko bata san suna yi ba ma,don bai ce mata ƙala ba. Koda ya shigo rashewa ya yi a tsakar ɗaki nan kan sallayarta ta shiga jera mishi kayan gabanshi,ya buɗe babbar kular tare da cewa, tunda kin ƙi gaya min sunan abincin da ki kayi min bara na duba da kaina, ganin gurasa luhu-luhu ya sa shi sakin baki, sannan ya dube ta cike da mamaki, "Allah ke ce ki kayi wannan gurasar Beby? Ta ce,ba tayi ƙyau ba ko? Cikin fargaba take magana,ya ce ina dai mamakin iyawarki. Ya ɗauki ɗaya ya yaga,ya saka cikin bakinshi yana taunawa, ya ce Beby kin yi zaman Kano ne? Tana dariya ta ce, Uncle abinda ya yi Kano ai shi ya yi Jigawa,ya ce haka ne,ba zan ci gurasar nan ni kaɗai ba, bari na kira abokina wanda duk sa'ilin da ya shiga Kano sai ya shigo min da gurasa. Ya ciro wayarshi ya kira Alhaji Salis,ko gaisawa bai bari sun yi ba, ya ce mutumina don Allah ka zo gidana yanzun ka sha mamaki. Alhaji Salis ya ce to bari na ci abinci tukunna, Alhaji Saddiƙ ya ce,in ko kaci abinci za ka sha haushi,ai kurum ka iso da yunwarka."


Ya miƙe, matarshi Rabi'a tana cewa, ina za ka Salis? Ya ce ina zuwa, yanzun zan dawo. Ya fita da sauri.


Shi ko Uncle tuni ya soma ci,miyar ta ji naman rago ga kori tafiyayye tun daga Kano,Curry mai suna Amrif yana gyara girki sosai, Uncle kam babu baka sai kunne. Wayar Alhaji Salis ce ta katse shi,ya miƙe "Bari na shigo da shi,ban so ya katse ni ba."


Sun gaisa da Alhaji Salis, shima ya shiga mamakin ganin gurasa,bai tsinke da lamarin wannan ƴar yarinya ba, sai da ya soma ci. Faɗi yake yi zan turo Rabi'a insha Allahu,ki koya mata har da miyar duk ki nuna mata. Aisha kam sai jin daɗi take yi,ta zuba musu sassanyan zoɓon suka soma sha, Alhaji Salis yana cewa mutumina shi yasa naga ka soma yin tumbi ka ce gara ka ke ɗiba in zan samu wannan me zan yi da lemun kanti, sai dai don ra'ayi, amma ba don daɗi ba. Da suka gama za su fita, Uncle zai mishi rakiya sai da ya yi ma A'isha ƙyautar kuɗi ba tare da ya san ko nawa ba ne, saboda yaba matan da ya yi,suna fita ya dubi Alhaji Saddiƙ ya ce, "Abokina gaskiya Allah ya yi maka baiwa ai macen da ta iya girki baiwa ce, Allah kewa bawansa,gata ɗanya sharaf ko ta ina,kana morewa." Uncle ya ce, kai Salis,kana nan da halinka ko? Ya yi ɗan tsaki, gaskiya nima fa auren nan zan zo in ƙara, Uncle ya ce menene damuwar ka? Rabi'a tana kula da kai, ga kuma ƴan yaranka. Nima matsalar rashin ƴaƴa ne". Salis ya ce, to ai mutum yana son canjin gurin hutun,tunda ai matan sun bambanta." Uncle ya ce "Kai Salis, to ni har yanzun ban taɓa yarinyar nan ba, ina jin tausayinta,ta yi ƙarama."


Tabɗijam,in ji mata,Salis ya faɗa cikin mamaki,ai wallahi ba zan aje mace in sa mata idanu ba. Uncle ya ce, ni baka san dalili ba, "watan mutumina a duk lokacin da nayi yunƙurin kusantar yarinyar sai naga tamkar itama da zaran na kusance ta itama mutuwa zatayi. Sai kuma in ringa ji a jikina cewa dan ban kusance ta bane ta kawo yau.


Alhaji Salis ya ce, "kenan kaima kana yi ma kanka MUMMUNAN ZATON da mutane suke maka?" Ya matso ya dafa shi, Alhaji SaddiÆ™ daina zargin kanka,sa a zuciyarka, Allah ne ya amshi addu'armu,ka taki matarka sannan ka dage mu samu Æ´aÆ´a." Uncle ya yi Æ´ar dariya tare da cewa,ni nema zan dagen ko?" Nan dai suka yi sallama.


Koda ya dawo ciki,tuni A'isha ta gyara gurin tamkar ba aci abinci a gurin ba, tana zaune tana kallo. Ya ce, "Beby me kike son in baki tukuicin wannan girkin?" Ta gyara zama cike da zumuɗi ta ce,"Cika min alƙawarina kawai zakayi," ya ce wanne kenan? Ta ɗan karkatar da kai tana duban shi, ta ce wannan da ka ce zaka kai ni gida naga su Ummata har ma ka ce in na ƙwantar da hankalina. Ya yi murmushi, angama Beby, insha Allah next week can zamuyi week end. Ta shiga murna,shi ko kallonta yake yi, komai Beby ta yi birge shi take yi kuma ko yaushe ya kan yi sha'awar yin wasanni irin na ma'aurata, da ita sai dai hakan in ya tuna ya ya zata ɗauke shi,don tana girmama shi.


Sannan ya kan yi tunanin in har ya kai ga saduwa da ita to zata iya mutuwa. Na shi zaton rashin saduwar da bai da ita ba ne yasa har yanzu bata mutu ba. Yana ta tunani bai ma san ta gama komai ta zo ta zauna kusa da shi ba, tana ta kallonshi zuciyarta tana son gano me yake tunani, fuskarshi take kallo yana da ƙyau Uncle,ta raya ma ranta, gashi mai tsafta da son ƙamshi. Uncle ɗan gayu ne tsawonshi yana burgeta,ringing ɗin wayar shi ce ta dawo da shi daga tunaninshi da yake yi, itama haka. Firgigit suka dubi jt, cikin cinya A'isha ta saka kanta duk kunya ta rufe ta, Uncle ya kamata tana kallonshi.


Washegari Jummai ta zo tana son yiwa A'isha kashedin gulmar da ta soma kawowa gurin maigidan, sai kuma ta same shi a ɗakin,don haka sai ta juya zancan da cewa,dama nazo ne in baki haƙuri,kan abinda su Suwaiba suka yi miki, insha Allahu ba zasu ƙara ba. A'isha ta ce, "Ya wuce ma." Alhaji Saddiƙ ya ce, "Haba Jummai,ki daina damun kanki,ai ni ma dai nayi musu barazana ne, amma ba wai zan kore sun ba ne. Cikin sanyin jiki ta ce na gode, ta fita. Tana fita ta banko ma ɗakin harara, sannan ta ce da sannu zaku ga aya in dai nice Jummai.


Ranar juma'a, A'isha suka nufi jihar Jigawa cikin motar Uncle (Annaconder) Jabir direban shi na Ofis shi ne yake jan su. 


Yafi son tuƙin Jabir don ya san titi, suna zaune a bayan motar, harkokin shi kurum yake yi a cikin laptop tare da abokan kasuwancinsa, A'isha kam tagumi ta zabga, murna ce fal ranta Allah yasa Uncle ɗinta ya baro ta can har hutunta ya ƙare. Kai yau zata ga su Ummanta,can ta soma hamma, kafin sukai Kano tuni bacci ya yi awon gaba da ita, Uncle ya kalle ta,ta jingina kanta da gilashin mota,ya yi ɗan murmushi, sannan ya ajiye laptop ɗin shi gefe sannan ya kamata ya ƙwanto ta a jikinshi,yana ƙoƙarin gyarata ai tuni ta gyara kanta. Juyo da fuskarta tayi saitin mararshi ƙirjinta yana ƙwance saman cinyoyin shi har ma yana jin tudun ɗan ƙirgan danginta akan cinyarsa hannunta ɗaya yana kan kujera ɗayan ko yana ɗayar cinyar ta shi, sannan ta ɗan takure kamar tana jin sanyi. Nan take ya ɗauko babbar rigar shi ya rufa mata, sannan ya ce, "Jabir rage ƙarfin (A.C) ɗin nan. Jabir ya ce,to ranka ya daɗe, haka suka yi ta ƙwararar hanya har suka isa Kano, Uncle yana son fita ya ƙara masu Friend tsaraba Amma baya son ya tashi, Beby don haka sai ya ce Jabir su bi ta cikin gari kai tsaye ya wuce jifatu suna isa ya ɗibo kuɗi ba tare da ya ƙirga ba,ya ba Jabir ya ce ya shiga cikin jifatu ya lissafa mishi abubuwan da yake so.


Bayan ya dawo da kaya niƙ-niƙi, yaran shagon da wasu suka loda a bayan motar, sannan Jabir ya shiga. Ya juyo ya miƙa ma Uncle sauran kuɗin tare da cewa, gashi maigida, kuɗin sun rage. Kasa a aljihunka Jabir muje Allah dai ya sauke mu lafiya. Jabir ya ce Amin,. Sannan ya ce "Na gode maigida, Allah ya ƙara buɗi." Ya ce "Amin" suna tafiya ta sake yin juyi ta gyara ƙwanciyarta, sai dai numfashinta da ke sauka ka saitin cibiyarshi,yana sa shi jin wani yanayi, ya jingina kanshi da kujera ta baya, ya lumshe idanunshi, kasa daurewa ya yi,ya lalibo tafin hannunta ya saƙala cikin nashi. A hankali yake murzawa,nan ta yi miƙa tare da juyawa rigingine. Sai taji duk ta takura, don haka ta buɗe idanunta a hankali gami da lalubawa ta ji ko kan gado take. Sai taji ta damƙo cinya,da sauri ta tashi zaune ta kalli jikinta,tana rufe ne da rigar Uncle,nan take ta tuna cewa a cikin mota suke. Shi ko ya ce, sleeping Beby kin tashi? Kunya ce ta rufe ta, har ma ta kasa kallonshi, ta kifa kanta a cinyarta, ya ce, "Beby kenan, gaskiya kin shari bacci,ko dai jiya saboda murnar zuwa gida ba ki runtse ba ne?" A zuciyarta,ta ce "kamar Uncle ya sani, amma kunya ta hana ta ɗagowa a haka suka ci gaba da tafiya hannunta cikin nashi in ta ɗan ɗago da kai sai dai ta kalli yanda suke wuce ƙauyuka da dajika, da ya ɗan murza yatsun sai ta kuma sunkuyar da kai cikin cinyarta tana son yanda yake mata da yatsun in yana yi ta kan ji wani irin abu shi yasa ko ya riƙe hannunta bata ƙwacewa.


Jummai ko ba ƙaramin murna ta yi ba da wannan tafiyar tasu. A cewarta, Allah ne ya dube ta da idanun rahama ya sa su wannan tafiya, domin koda yaushe cikin lissafin ya ya zasu tafi Nijar ɗin suke tunda ƙwana za su yi ƙila ma ba ɗaya ba, kuma ta san Uncle ba zai taɓa barinta ta ƙwana bikin ƙawa ba,balle ta mishi ƙaryar cewa ƙawarta ce zata aurar da ƴa, dangin su ɗaya balle ta ce bikin danginta zataje,ya kuma san dangin ubanta duk ƴan Katsina ne, cikin wannan halin ne ya ce mata zai yi tafiya zai kai A'isha gida.


Don murna har da turamen zannuwa ta ba A'ishan,wai gashi ta kaima mahaifiyarta,da zasu tafi kuwa rakiya har mota. Dama sun gama shirya ta su tafiyar ita da Aminiyarta,don haka suna tafiya itama ta suri jakarta ta kira direban su ta ce ya kai ta gidan Aminiya wato Hajiya Kari, daga can suma suka nufi Nijar.


A'isha da gudu ta shiga cikin gida, tana kiran Ummata! Ummata! Tsalle ta yi tare da ɗane Ummar tata wadda ke ta kujuba-kujubar haɗa musu abin sauka, kafin su iso. Gefanta Hauwa ƴar maƙotansu da ke taimakon ta da aiki ce, Umma ta ce "yau ku ji mu da ɗiya, A'isha an girma ba'a san an girma ba?" Cikin murya shagwaɓa ta ce, "Kai Umma wanne girma nayi? Umma ta tsaya tana kallon ƴar Tata, duk da bata ƙara girma ba ta ɗan ciko,idanu sannan fatar ta ta murje gwanin sha'awa, sannan ta ƙara haske. Ta ce, "To ina ki ka bar maigidan naki?" Ta ce Uncle yana waje Abba fa? Umma ta ce "tunda ya fita sallah bai shigo ba,muje ki amshi makullin sashen baƙi ki je ki buɗe mishi kafin Abban naki ya zo," ta ce to,da gudu ta sheƙo tazo tana buɗe ƙofa, shi kam Uncle kallonta ma yake yi yana dariya......




#######

[12/9, 21:27] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 3*



Bai taɓa ganin tana murna irin haka ba,ta buɗe sannan ta iso gurinshi "zo ka shiga Uncle" ta shiga ya bi ta, ta ce "Uncle bari na kawo abinci." Ya ce "Haba Beby daga zuwa? Bari dai mu sauke nauyin dake kanmu,watan mu yi sallah. Ya zauna tare da ɗaukan waya bari na ce Jabir ya shigo shima tunda da toilet nan sai mu yi sallah ta ce, to ya ce yau kam Beby sai murna ko? Anga Umma, ta fita tana dariya.


Bayan su Abbanta sun dawo nan ya shiga gurin amininshi sirikin shi kuma maigidan shi ta fannin aiki,nan suka shiga hirar yaushe gamo A'isha ce ta kawo musu abinci ita kuma ta koma gida yau kam murna ba sauƙi gata cikin family ɗin ta tana cin abinci ƙwano ɗaya da Ummanta, gefanta ga su Jafar da Munnir ƙannanta, dole ne ta yi murna domin ba ta yi zaton zata sake zuwa wannan gidan ba,ga zatonta ta yi banƙwana da gidan har abada. Yini sukayi zaune da Ummanta duk inda Umma ta yi A'isha tana biye da ita, tana ba su labarin makarantar su,ƙawayanta su Samira da kuma tsaruwar makarantar,wata dirama kuma sai da dare,ta haye gadon Ummanta ta ƙwanta, Umma ta dube ta, tashi mana A'isha ki je gurin mijinki,ta tashi zaune in je in masa me? Umma ta ce kin ji shirme bangane ki je ki masa ba,ta koma ta ƙwanta nafa riga ya na kai musu abinci, Umma ta ce to ba za kiyi mishi sai da safe ba? Ta ƙara jan rufa tare da cewa zai kira waya.


Shi ko suna can suna shan hirarsu da Abba, goma dai-dai sun gama kallon labaran ƙasa. Abba ya miƙe tare da bashi hannu gami da cewa friend mu ƙwana lafiya,bari na turo maka A'ishan, wani iri Uncle ya ji, ya ce a'a friend ka barta ta kwana gurin Ummanta, Abba dai bai ce ƙala ba, ya wuce yana shiga ɗakin Umman ya same ta ƙwance, Umma kuma tana ƙoƙarin shiga wanka, ya ce Ummansu ya ya zaki riƙe ƙawallin ta ki ki hana ta zuwa gurin mijinta?" Ta ce,ka ganta nan ba yanda ban yi ba,ta tafi ta ƙi wai zasu yi waya, gashi nan har ta yi bacci, ya ce A'isha! A'isha ta ce,Umm, cikin yanayi na bacci ya ce ke tashi maza mijinki yana kira,ta zuro ƙafafunta ƙasa sannan ta ce wash Allah na, duk gajiyar hanya ta isheni,ta fita ta nufi ɗakin baƙi,shi Jabiru yana can gurin Yaya Abdulrahman, ta ƙwan-ƙwasa ƙofa tuni shi Uncle lokacin ma ya kulle ƙofa yana saka kayan bacci duk jin shi yake a takure shi yasa ya so ya sauka a Hotel amma Abba ya ƙi shi nauyinsu yake ji ya zo ya buɗe ƙofar ya ce a'a Beby ba kiyi bacci ba? Cikin yanayin shagwaɓa ta ce, "To ba kaine kasa Abba ya tasoni ba,?" Ya ce muje in rakaki ki koma, har bakin ƙofar ya rakata. Koda ace yana ƙwana da ita to ai ya haƙura a gidan su komai fitinar shi ya shafi kumatunta sai da safe Bebyna,ta ce to mu ƙwana lafiya.


Ɗakin Ummanta ta shige ta haye gado sai da Umma ta fito bayi ta ganta ƙwance ta ce, a'a dawowa kika kuma yi? A'isha ta ce don Allah Umma ki bar ni Allah kuwa shine ya ce ba kirana yake yi ba,in zo in ƙwanta, Umma ta ce to ai shi kenan.



Su Hajiya Jummai,ƴan Nijar tunda take bata taɓa shan wahala irin ta yau ba. Musamman da yake motar haya suka bi, amma ita wannan baya gabanta,tata damuwar bata wuce su isa yau lardi ba, inda zasu samu bokan da aka yo musu ƙwatance,tata damuwar kenan. Sai guraran goma saura suka shiga ƙauyan. Yanda aka ƙwatanta musu haka suka bi. Sun iso gidan bokan wanda yake gida ne na kara,an sauke su da hura. Bokan Bororo ne, irin masu kitson nan haka ma matarshi sam baya jin Hausa don haka dole su ƙwana a nan kamar yanda ya ƙwatanta musu,in gari ya waye za'a samu wanda zai musu tafin ta,sai dai daga Jumman har Karimar sun ƙwana ne cikin ƙyan-ƙyamin gidan da komai ma,don ma sun riƙe ruwa, can hantsi ya ɗaga me yin tafinta,ya zo nan suka sanar da shi buƙatar su, Jummai ta ce tazo ne saboda tana son a kashe kishiyarta, sannan ta ringa juya mijinta yanda taga dama, sannan tana son in da hali ta haihu, bayan mai tafinta ya sanar da shi komai sai ya tambayi sunan kishiyar da mijin,nan ta sanar da shi, bayan ya zuba tsafin ya kuma zubawa, ya ce kafin wannan ta kashe wasu rayukan ko? Mai tafinta ya tambaye ta, bata ji shakka ba,ta ce ƙwarai,ya girgiza kai sannan ya ce, to aikinta yana da matuƙar wahala,don ita wannan ta sha banban da sauran tana da kariya sosai, sannan yaga wasu abubuwa da take yawan kira tana samun tsaro daga abin bautarta. Sannan koda yarinyar zata mutu to fa ba ƙwana kusa ba,don tana da tsawon rai. Koda aka mata bayanin ta hau zufa ta ce ka gaya masa in ma batun kuɗi ne kada ya damu,in har za'a kashe min ita ko nawa ne zan bada, kace da shi tun daga Katsina fa muke don munji labarin aikinshi yana ci tamkar yankan wuƙa. Kada ya nuna kasawar shi mana, inji Karima. Jin haka sai ya ce shikenan. Nan ya shiga haɗa musu kalolin nashi surkullen, sai da suka sake ƙwana sannan suka kamo hanya.


Shiko Uncle duk jin shi ya yi takure, shi yasa gari yana wayewa ya ce to fa shi zai yi haramar komawa,in an yi kwanaki zai dawo kafin hutunsu ya ƙare, da ƙyar Abba ya yarda, don cewa ya yi su juya tare ai an gaisa, lokacin da ta je ɗakin don suyi sallama,tuni ya gama shiri,yana shafa turare.


Cike da murna ta shiga tana cewa, Uncle wai zaka tafi? Ya ce "Eh, Beby shi ne ki ke murna? Don zan tafi ko?" Ta É—an canza fuska zuwa yanayi na tausayi, ta ce "Ayya, Uncle ba wai don zaka tafi ba ne,naga ba mu yi zaka barni ba ne" Ya ce "Naga ya dace ki É—an yi Æ™wana biyu ne,zan yi kewarki da zoÉ“onki da ruwan da ki ke bani kullum." Ta yi Æ´ar dariya, "Nima ai zan damu da rashin ganinka." Cikin mamaki ya ce, "Don Allah da gaske ne za ki damu da rashin ganina?" Ta rufe fuska, ya kama hannunta yana murzawa, zan rinÆ™a kiranki ko yaushe kin ji? Ta ce to Uncle,yasa hannu cikin aljihu ya ciro kuÉ—i dami ya miÆ™a mata gashi saboda kashewa. Ta zaro idanu,haba Uncle, sun yi yawa gaskiya ba zan amsa ba,ya ce riÆ™e in zaki dawo sai ki sayi me kika ce sunan? Corry É—in nan? Ta ce Amrif an fi samun shi a Kano ne, ya ce to in zamu koma in nazo sai mu tsaya mu siya. Ta ce, "To." Ya ce,in kin dawo ke ce zaki cigaba da min girki, kafin hutunku ya Æ™are,ki fa koyo wasu ina son irin su É—anwake,waina,burabisko,dambu kin dai ga ne,abincinmu na gargajiya ko? Ta ce "Eh,ai dama fa duk fa na iya su, yasa tafukan hannunshi ya riÆ™e kumatunta,ki kula da kanki,kin ji Bebyna? Ta ce, to sai naji wayar ko? Ya ce, to Bebyna ya shiga ya yi sallama da Umma tana ta godiya, Abba da A'isha zuwa su Abdulrahman da su Jafar sun yi mishi rakiya har mota. Jabir ya ja mota suka yi gaba,ga mamakin A'isha sai ta ji wani irin kewar Uncle cikin zuciyarta, ta ce Allah ya sauke mata da Uncle É—inta lafiya. Lokacin da Alhaji SaddiÆ™ ya iso gida yamma ta yi kis,don ma basu tsattsaya a hanya ba, rashin samun Jummai a gidan ya yi mugun É“ata mishi rai,shi dai wannan É—abi'a me yaÆ™i da addini,da matan  zamanin suka É—auka tana É“ata mishi rai, ace mace ba zata nemi iznin miji ba,in zata fita saboda rashin sanin hukuncin musulunci,ko a waya ba zata kira ta nemi izini ba,ya samu su Suwaiba sun cika gidan da kiÉ—a tare da Æ™awayansu,sun sha wanduna suna ta rawa ga Æ™walaban totolyn emzolyn nan zube a Æ™asa, ranshi ya Æ™ara É“aci ya shiga ya tarwatsa su tare da yi musu tatas. Ya ce, ina Jumman da ta É—aure muku gindi? Cikin maye Sofy ta ce,ta yi tafiya tun jiya, al'ajabi ya cika shi,ya nufi É—akinshi ranshi yana matuÆ™ar zafi. Ya zauna bakin gado ya soma kiran layin ta, ga mamakin shi tama Æ™i tafiya,a Æ™arshe ma sai aka ce a kashe layin yake.


Wasa-wasa har wayewar garin ba ta babu labarin ta, kazalika ci gaba da neman layinta ko zai samu,shiru kai daga baya sai ya soma tunanin ko dai ta ɗan fita unguwa ne, ta samu matsala ko mota ta kaɗe ta haka? Yin wannan tunanin ya saka shi kiran danginsu, har da nata wato makusantanta,yana sanar dasu rashin ganinta tun jiya. Ya san ba nisa tayi ba,don ba ta fita da mota ba, kuma bata saba tafiyar ƙwana ba ma in dai ba ƙasar ta bari ba, komai dangatakar ku da ita ba zata taɓa zuwa ta ƙwana don zumunci ba,nata ganin ƙasƙanci ne ta ƙwana gidan da suka fi su kuɗi, amma gata can ai ta ƙwana a bukka,nan fa hankula suka tashi.aka shiga neman asibitoci,ranar basu iso ba sai daf da magriba,kai tsaye gida kowacce ta nufa, lokacin da ta iso gidan yana cike da dangi shi kuma yana daga harabar gidan in da wani ɗan sandan ciki yake neman ƙarin bayani daga bakinshi.


Sai kurum gata ta shigo, ganin maigidan yasa ta ji faÉ—uwar gaba,don sam ba tayi zaton zai riga ta dawowa ba, amma da yake tana zaton yau ya dawo,tun da haka suka yi dashi, sai ta isa gurinshi tana cewa "Sannu da zuwa Alhaji, har ka iso? Na É—an fita ne" bai iya ce mata komai ba, sai dai ya dubi wannan (C.I.D) É—in ya ce shi kenan ma gata nan ta dawo.


Suka yi sallama ya tafi, shi ko ƙin shiga ma gidan ya yi,yana tsaye cike da mamakin baƙin halayen da Jummai ta zo mishi da su yanzun yi,abin har ya kai ta da yin ƙwanaki. To ina taje? Ya na nan har aka kira sallah, ya shige masallaci, ita ko tana shiga cikin gidan ta same shi cike da dangi ana ta jaje. Turus ta ja ta tsaya, tana son sanin wanene ya mutu? Shin ko dai A'isha ce har ta mutu kafin ma ta dawo? Ta yi amfani da maganin? Kai in ko haka ne lallai zata sake komawa ta mishi sabon biya,don ya cancanta,haba shiyasa taga Alhaji a waje babu fara'a,ya ma kasa amsa ta,ta dubi jama'a sannan ta ce, "Haɗarin mota ne?" Nan kuma sai taji sun ɗauki salati, suna tambayarta a ina abin ya faru? Sai kuma ta yi sororo tare da cewa,wai dama me ya tara su haka? Nan suka shaida mata labarin ɓatanta,nan fa ta hau masifar cewa inji uban wa? Ita da taje biki? Shi ne za'a ce wani ta ɓata? Wata Yarsu ta ce, to mu dai maigidan ki ne ya yi waya tun jiya kuma sai nemanki ake yi cigiya gidajen radiyo da na talabijin. Ta ja tsaki, "To ni biki naje, shima bayanan ne kuma na kira shi a waya ban samu ba." Nan dai kowa ya tashi yana Allah to ya kiyaye gaba, gaskiya ta ji haushi don duk tasa ma ranta cewa A'isha ce ta mutu.


Sai bayan da kowa ya tafi sannan ta kira su Suwaiba,tana tambayarsu yaushe ne Alhaji ya dawo? Suka shaida mata tun jiya, kuma ya tambaye su sun ce ta yi tafiya. Cikin É—ar-É—ar ta zauna,shi kam bai ma shigo gidan ba da ya yi isha'i gidansu Hajiyarmu ya nufa, don ya sanar da su dawowar Jumman,nan har yake yiwa Hajiyarmu complain É—in halayen da Jummai ta shigo da su, ya ce ada bai san ta da duk waÉ—annan halayen ba, sai yanzun. 


Hajiyarmu kuwa haÆ™uri ta bashi tare da cewa, zatayi mata magana. Sai sha É—aya saura sannan ya nufo gida,tana ta gadin zuwan shi,don haka tana kallon shigowarshi, sanda ta shiga É—akinshi yana watsa ruwa,ta zauna. Yana fitowa da ya ganta fuska ya É—aure tamkar bai taÉ“a dariya ba,ta rasa ta ina zata soma mishi magana,can dai ta daure ta ce, "Alhaji ka min haÆ™uri,na san ban Æ™yauta ba, amma wallahi na kira wayarka taÆ™i shiga,dama wata Æ™awata ce dake Kaduna ta ke aurar da Æ´arta," ya ce "to yanzun sai ki koma Kadunan," ta zaro idanu, Haba don Allah,ka yi haÆ™uri Alhaji, nayi laifi, ya eh da haka ni ne dama sarkin haÆ™uri shiyasa sai ki min abu ki ce inyi haÆ™uri to na gaji ba zan É—auki yawon gantali ba, don haka sai ki koma". 


Tayi saurin zubewa gwiwa biyu a ƙasa,don Allah ka rufa min asiri, insha Allahu ba zan ƙara ba,don Allah.


Ya ce ,don Allah ni tashi ki bar min ɗaki,shashasha wadda ba ta san darajar kanta ba,bare na aurenta,ke kenan yi nan yi nan,gara ma kin canza hali,don wallahi ba zan ɗauki wannan rainin wayon ba. Ta fita dai tana mai jin zafin abinda ya yi mata, amma cikin ranta tana cewa,ƙwanan nan zaka zama zauna nan in Allah ya yarda,duk wannan cin mutuncin da ya yi mata sai ta rama.


Shi ko ƙwanciyarshi ya yi tare da yi mata addu'ar Allah ya shirye ta, ita ko A'isha tana can gurin Ummanta, suna shan hira, tana ba Umma labarin yanda Uncle ya ke kashe mata kuɗi,ko da Ummanta ta ce, to suna zaman lafiya da abokiyar zaman tata? Cewa ta yi suna yi har ma take bata labarin zannuwan da ta ba da a kai mata, Umman ta fahimci ƴarta bata zuwa gurin mijinta a cikin hirar tasu, inda take cewa, ita sau ɗaya ta taɓa zuwa ɗakin Uncle ya ce ta gyara mishi shimfiɗa, sai kuma taga shimfiɗar a gyare.


Umma ta ce,ai yanzun ke don rashin hankali ba zaki shiga É—akin mijinki ba duk ranar girkin ki ki gyara safe da yamma?" A'isha ta yi shiru, Umma sai faÉ—a take mata, ta ce "Lallai yarinya in ko haka za kiyi,za kuwa ki zama koma baya gurin mijinki,ai wannan gyaran É—akin shi ne zai sa yaji dake fiye da yanda ki ke labari yanzun, duk irin biyayyar da zaki mishi na banza ne in har ba zaki gyara mishi shimfiÉ—a ba."




######

[12/10, 19:21] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 4*




Aisha ta ce , to Umma shi ne fa ya ce wai ba zan iya ba,wai sai nan gaba. Shiru Umma ta yi don ta san A'isha yarinya ce, amma har da ma shirmenta,in ban da haka yara ma ƙanana waɗanda ba su kai ta ba sun san aure bare kuma ita? Sam ta kula A'ishar ma bata gane me take nufi da gyaran shimfiɗa ba.


Aisha ta ce, to in na koma ai zan ringa yin gyaran.


Kafin ranar dawowarta, Umma ta zaunar da ita ta koya mata shan kayan marmari masu saka ni'ima a jikin mace,duk da yanda Umma ta nuna mata cewa su kankana,shan rake,aya,ayi kununta da dabino shan romon kaza da sauransu,suna saka mace tayi ni'ima. A'isha ba ta gane wacce irin ni'ima Umma ke nufi ba,ga nata zaton jikinta zai yi fresh ko ƙiba zatayi ko ko fari, Umma take nufin zata ƙara? Oho. Ita dai tana can ta soma amfani da su, sai wasu tsumi da dai sauran abubuwan sha na mata, waɗanda basu da illa.


Itama nata gefen Hajiya Jummai ta gama aiwatar da komai nata,wato guzurin Nijar, don haka jiran sakamako kawai take yi.


Ana saura sati É—aya hutun A'isha ya Æ™are, Uncle ya yi mata waya cewa yana nan bisa hanya,don haka ta soma shiri da ya zo zasu juya. Tamkar kada ta tafi ta ji, sai dai wata damuwa tun jiya ta soma jin wata faÉ—uwar gaba har ta sanar da Umma. Umma ta ce, tayi ta addu'a itama zata taya ta. 


Sun tsaya a Kano sun yi siyayya, Uncle dai sai tuni yake mata da Amrif Cory, dariya ta ringa mishi, shi kam ya ce na yaba da ƙamshinsa gami da ɗanɗanonsa, duk tsarabar da A'isha ta zo da ita gurin Jummai ta kai ta ce gashi nan ta raba ta ba kowa.


Hajiya Jummai ta ce, a'a bani da wanda zan ba tsaraba,ki dai aikawa da su Hajiyarmu,ni kuma bari in É—an samu riÉ—in.


A'isha ta ce, to da kanta ta ce don Allah Uncle ya kaita ta ba su Hajiyarmu tsarabar su. Sun yi godiya mai tarin yawa, a nanne ma take jin zancan auren Nafisa, lokacin da Uncle suke magana da Hajiyarmu, ashe wani abokin Uncle zata aura, mai suna Alhaji Bello,yana da mata ɗaya da ƴaƴa uku,fatan A'isha Allah yasa lokacin bikin suna hutu, har ma tayi wa Uncle ƙorafin hakan, Uncle ya ce kada ta damu,in tana da rabon za'ayi tana nan to za'ayi cikin hutun. Lahadi tana zagayo wa Uncle ya haɗa komai na makarantar A'isha ya maida ita. Sun maida hankali kan karatunsu yanda ya kamata.


Jummai kuwa, kullum cikin zuba idanu take yi taga ta ina aikinta zai fara? Amma shiru. Nan fa hankalinta ya sake tashi, ta shiga surutu ita wane laifi ta yi? Duk abinda ta yi ba ya ci,da yake an ce duk abinda ka ke yi shi kake zaton kowa yana yi,don haka sai ta bar abin kan cewa suna tufka mata asirine, shi yasa. Yin wannan hasashen yasa ta garzaya gidan Aminiyarta don neman wata mafitar.


Aisha ta zamar mata annoba, bala'i. Aminiyarta ta ce,sake neman wani gurin zamu yi da zai yiwu ni dai da mun dangana da Indiya, can ne ƙarshen tsafi ba ki gani ko cikin fina-finansu? Jummai ta ce,don Allah kuma gaske ne yana yi?" Karima ta ce ,"Zauna nan,ai in zaki miƙe,miƙe sahibata wani aikin sai Indiya,ko Chaina, kafin ma mu dawo tun muna can za'a ɗauki ran banza mu huta."


Jummai ta ce,ba zuwan ba,ba kuma kuɗin nake ji ba,don sai na iya sa duk wani abu nawa a kasuwa in amshi kuɗin,matsalata mutumin gidana, kin san cewa har zuwa yau ba mu koma normal da shi ba? Tun zuwanmu Nijar ɗin nan har yau,na kasa gane kanshi. Sai ya yi ta dakemin yana shan ƙamshi.


Karima ta ce, "ke Aminiyata nemi kuɗi in ma bai barki ba ni sai in je miki. Menene amfanin Amintakar? In ana zuwa lantsandan gaban lahira inji ƴan magana to zani,in samo miki mafita game da kishiya. Ai ki daina damuwa,mu za'a gaya wa Boka? Jummai ta yi ajiyar zuciya, daɗi ya rufe ta,a duniya bata da tamkar Karima, ta ce, "Aminiyata Allah ya ja mana ƙwana,ni na san bani da masoyiyar da ta kai ki duk duniya."

    Ji toshewar basira.


In sun samu hutu.

A'isha duk ranar girkinta,ta kan shiga ɗakin Uncle ɗin ta gyara mishi gado har ma da sauran gurare, sannan ta saka mishi turaren wuta mai ƙamshi, amma bata kwana tunaninta ma bai kawo mata ta ƙwana ɗin ba, har ƙwanakinta na hutu suka cika ya yi mata komai ta koma.


A'isha ta maida hankali kan karatunta, bata wasa sai dai zama da su Samira ya yi matuƙar wayar mata da kai. Su kan zauna suyi hirar samarinsu kamar yanda ƴan mata kan yi. Amina kam kullum bakinta yana ba su labarin Kabir,Samira ma bata da zance sai na Adam.


Kowacce in tana labarta yanda take ji game da abin ƙaunar nata, A'isha kam baki take saki ta yi ta kallonsu. Samira ta ce, A'isha wai ke kullum tamkar ba ki waye ba, haka ki ke jin kike wai baki da saurayi ne? A'isha ta girgiza kai tare da cewa,ni bani da wani saurayi.


Amina ta ce,ni wallahi ban da ina da Adam ɗina ko da sai na ce don Allah ki haɗa ni da Uncle ɗinki mana? Samira ta ce,ai gayen ya yi ne, A'isha ta yi ɗan murmushi, sannan ta ce,shi Uncle ba fa yaro bane. Samira ta ce ji wannan ai ba yarinta ake kallo ba a maza,ƙwalitis ake dubawa, shi Uncle ɗin ki yana da duk ƙwalitis ɗin da ake so ga namiji."


Aisha ta ce,ni ban san wani ƙwalitis ba fa da kuke magana" Dariya suka shiga yi mata, A'isha ta ce,kun ji lokacin sallah ya kusa, ya kamata mu soma shirin shiga Masallaci."


Duk lokacin da suke ire-iren wannan hirar, A'isha kan tambayi kanta, menene wannan ɗin da su Samira suka damu kan su dashi? Ita dai ta san burgewa kamar Uncle in ya yi ƙwalliya,yana matuƙar birgeta, bayan wannan ba ta san komai ba.


Ƙwanci tashi su A'isha an shiga (SS3) duk da batayi wata ƙiba ba, amma ta ƙara tsawo.


Ƙirjinta kuma ya bunƙasa har yana ɗan rinjayarta, shi ne ma sanadin yin ɗan rusunawarta wanda wasu ƴan makarantar nasu suka fassara shi da yanga, zuwa yanzun ta san mene ne aure,me ake yi in anyi shi? Sai dai ita mai tsananin tsoro ce.


Shi kuwa Uncle har yanzun ba ya tunanin taɓa ta, domin yanzun ya gama yarda cewa ƙwanciyar da yake yi ne da ƴaƴan jama'a suke mutuwa, duk da yana tsakanin buƙatar hakan, saboda yanzun Hajiya Jummai,damuwarta ma tai yawa,don ta ce an sa mata hannu na asirin da tayi bayi ci,tana nan dai tana fafutukar haɗa kuɗin zuwa Indiya ko Chaina.


Aisha wadda yanzun shekarun ta sha baƙwai kenan ta samu shekara biyu gidan Uncle ɗinta.


Ganin haka ya sanya jama'a suke ta kai-kawo kan cewa Alhaji SaddiÆ™ dai yanzun mata sun daina mutuwa a gidanshi, sai dai haihuwa shiru,don haka mutanen da a baya suke zaginshi sai kuma suka shiga kawo mishi tallar Æ´aÆ´ansu.


Nuna musu yake yi ba shi da ra'ayin sake aure,don haka su yi haƙuri.


Yau bayan tashinsa daga Office,gidan Hajiyarmu ya nufa, ya samu Alhaji Sunusi wan mahaifinshi,amma ƴaƴa maza suke. Alhajinmu yana jin maganar Alhaji Sanusi sosai, domin yanzu ku san shi kaɗai ne ya rage mishi a maza, cikin dangi. Alhaji Saddiƙ ya zauna suka gaisa,ya juya ya gaida Hajiyarmu, Alhaji Sunusi ya ce wannan zuwan naka ne fa Abubakar, Uncle ya dube shi tare da gyara zama sannan ya ce, to ina jin ka Baba. Alhaji Sunusi ya yi gyaran murya sannan ya ce, maganar Hadiza ce ta kawo ni, Uncle ya dube shi wace Hadiza fa? Alhaji Sunusi ya ce,ai ba ka ma san ta ba? To Hadiza ta gidana, tun lokutan baya na sani kaima ka sani tsayawa ta yi tsayin daka kan cewa kai take so, amma a lokacin kowa yaƙi saboda kai ba a son ra'ayinka ba,to sakamakon haka har izuwa yanzun taƙi kowa ta ce ita dai sai kai, gashi an tashi bikin ƙannanta su Hussaina shi ne muka yanke shawarar aura maka ita kawai.


Uncle ya dubi gefen da Hajiyarmu take zaune,tana ta nazarin littafin ƙawa'idi, ya sani tana jin su sai dai ba zata taɓa magana ba. Sannan duk ƙwaƙwarka ba zaka iya gane me ke fuskarta ba, ma'ana zancan ya yi mata daɗi ko ko akasin hakan, sannan ya dawo da dubansa ga Alhaji Sunusi wanda ya san yanzun nan zasu hau sama su faɗo in dai ya bashi amsar da ke bakinsa, ya ce Alhaji ai ko lokutan baya na san anƙi in auri Hadiza ne saboda matsalar da ke tare dani, ta mutuwar matana, yanzun kuma an yarda ne saboda an ga nayi aure matar bata mutu ba,don haka ni dai a bawa Hadiza haƙuri, ta nemi mijinta kawai."


Alhaji Sunusi ya ce, inji wa ya ce maka don wannan matsalar ne? Mu dai burinmu mu ga Æ´aÆ´anka."


Alhaji Saddiƙ ya ce, "Gaskiya ba ni da ra'ayin mace fiye da biyu, kuyi haƙuri."


Ran Alhaji Sunusi ya soma É“aci, don haka cikin fusata ya ce, "Abubakar ba wai na zo neman izininka ba ne, umarni na zo baka domin ko mahaifinka ne na bashi umarni baya tsallakewa,in ma mahaifiyarka ce zata zuga ka to ku sani daga kai har ita aure babu fashi."


Uncle ya ce, "Allah ya huci zuciyarka,ba ruwan Hajiyarmu cikin wannan zancan, Hajiya da ke jin su ta rufe littafin hannunta, sannan ta dubi wan mijin nata ta ce, Yaya Allah yasa alkhairi, kuma yasa muna da rai za'ayi." Jin haka yasa gaban Alhaji Saddiƙ ya faɗi, ya sani zancan ya tabbata tunda Hajiyarmu ta amince, Alhaji Sunusi ya miƙe yana cewa, "Duk yanda muka yi zaku ji gurin Alhajin gidan nan." Ya tafi.


Shiru Alhaji Saddiƙ ya yi,yana kallon ƙasa,shi da yake tunanin lokaci ya kusa da zai daidaita tsakanin shi da A'isha,don yin zaman aure cikakke, sannan sai kuma a kawo mishi batun wani auran? Shi fa ya sani ya so ya auri Hadiza a lokacin yana cikin tsananin son haihuwa, amma yanzun sam babu Hadiza a ranshi, duk da ko can da ɗin ma ba itace ta ƙi shi ba, dangin mahaifinshi ne suka ƙi, musamman Hajiya Lanti da Alhaji Sunusi mahaifanta yanzun kuwa ya sani ganin daɗewar A'isha a gidanshi ne yasa su amincewa.


Hajiyarmu ta katse shi da cewa,ka ci gaba da addu'a,zamu taya ka. Ka zama mai biyayya sannan ka shiga shirin bikin,to kurum ita ce kalmar da ta fito bakinshi, ya miƙe tare da cewa,ni zan ƙarasa gida. Duk ƴan ƙwanakin yana cikin damuwa.


A'isha tana school, Hajiya Jummai kuwa damuwarta ta sha ƙarfin tashi,don haka ita bata ma kula da me yake ciki ba, ganin haka yasa yau ya shiga har cikin ɗakinta tana ta waya ne da Hajiya Kari,kan cinikin wani gidan ta wanda shi ne kurum ya rage mata. Saboda tsabar ba ta cikin natsuwa sam bata ma san ya shigo ba, sai da suka gama sannan ta gan shi ta ɗan razana don ta san yaji me suke zantawa.


Ya zauna kusa da ita, ya maida hankalinshi kanta cikin sanyin murya, ya ce "Jummai wai menene matsalarki? Me ke damun ƙwaƙwalwarki? Ta dube shi da idanunta da suka yi jajir duk kwanakin nan haka yake ganinsu, ta ce ba komai me ka gani? Ya ce,haba Jummai, duk wanda ke gidan nan ya san kina cikin matsala, ta ce ni dai bana cikin wata matsala, ya ce to shikenan, yanzun menene dalilin ki na saida gida? Ta ce, matsala gare ni, kuma na san in na ce ka bani ba bani zakayi ba,don haka gara na saida ƙadarata, ya ce wacce irin matsala ce? Ta yi shiru tana son ta tuno me zata ce?.


Ya sake tambayarta, ta ce,zan je ne in dama dai wani likita zan gani a Indiya, saboda matsalar haihuwata,don naga wata mai irin matsalata kuma ta haihu,na gane in na ce zan tambaye ka ba yarda zaka yi ba cewa zaka yi ina ne ba mu je ba ance ba zan haihu ba."


Ya dube ta cike da zargi, sannan ya ce, "Ki bari zan shirya muje tare." Ta ɗan zaro idanu,ni dai ka bar shi kawai inje ni kaɗai, tunda kaga kai baka da wata matsala." Ya miƙe yana cewa, "Jummai waɗannan sabbin halayen da ki ka ɗauka sam ba zan ɗauke su ba, tunda ki ka bar gidan nan har ƙwana biyu ba ki gidan danginki ba ki gidan nawa, zuciyata ta soma zargin kin canza layi.....



#####

[12/11, 17:18] Ummi Tandama😇: *📗📗Page 5*




Sakamakon yawo da kawayan banza,to ba za kije ba,kuma kada inji kin saida wannan gidan,ta ce ai ba gidanka ba ne,ya ce to shikenan. Amma ki sani halayanki sun gundure ni,baki zaman gida ke ba ma'aikaciyar gwamnati ba,kullum sai shegen yawo,ni kaina yaushe rabon da ki shigo dakina? Koda kin zo baki iya tsinana min komai,sai dai ki min jungum kina tunani,don haka ni ba karfe ba ne ina da bukatar kulawa. Aisha tana makaranta,ke kuma baki da lokacina." 


Ta dube shi a hasale,to ka dauki mataki mana." Ya fita yana fadin "shikenan."


Gidan su Hadiza ya nufa yau,saboda yana son bin umarni,sannan Hajiya Jummai ta bashi haushi. Daga waje ya tsaya ya aika kiranta. Hajiya Lanti ta ce,maza a bude mishi kofar falo ya shiga. Hadiza kuwa murna tamkar me,don tana bala'in son shi,ba wata hira sukayi ba. Bayan gaisuwa ya ce,mata shi fa yazo ba ta hakuri ne,da zata daure ta nemi miji. Nan ta soma kuka tare da rokonshi,ya ce mata shi kenan sai dai fa ta san yana da mata har biyu,kuma suna zaman lafiya don haka kada ta yi kokarin rusa mishi tsarin gida. Ta ce,in Allah ya so ba wannan. Nan dai suka yi sallama ya tafi.


Tun daga ranar bai sake zuwa ba,sai dai ya kan kira ta a waya. Kafin wani lokaci labari ya watsu cikin dangi,Nafisa da bata so ba,don gaskiya tana ganin za'a kwari Aisha ne,tunda duk cikinsu ita ce karamar yarinya,haka ma su Aunty Fatima suke cewa.


Shi ko da ya tuno cewa bai sanar da iyalanshi ba,duk sai ya damu,musamman Hajiya Jummai,yanda ta daga hankalinta lokacin auren shi da Aisha,amma don Aisha yasan ba zata damu ba,tunda ita yarinya ce sannan ba ya tunanin ta ma san mene ne ma auren,don haka bai damu ba. Sai dai yana tunanin ya ya zai tunkari iyayanta da batun auren shi?  Ko me Friend zai kawo a ranshi in ya ji batun auran?  Kullum ya kan yiwa kanshi wannan tambayar.


Hajiya Kari ce ta jiyo zancan auran a gari,jin wannan labarin daga gidan mitin din su na gungun mata aiko gidanta ba taje ba,gurin Hajiya Jummai ta nufo,ta same ta zaune tana aikin gyaran kumbunanta. Hajiya Kari ta ce,ke Aminiya,dama wata ta taso shine baki sanar da ni ba?" Hajiya Jummai ta ce "Um zo zauna dama ina nemanki." Kari ta ce, kice muna kukan targade sai kuma ga karaya ta samu? Hajiya jummai ba tare da damuwa ba a zatonta fa zancan hana zuwa Indiya ne sai ta ce ai kan batun nike neman ki wai ni zan yi mishi dabara,sai kuma na rufta.Ya hana tafiya yanzun ya ya ki ke ganin zamu yi? Hajiya Kari ta ce,ke da Allah can,ba wannan zancan nake miki ba, ina miki zancan auren shi, ashe aure zai ƙara? Hajiya Jummai ta yi mutuwar tsohuwa a zaune, kusan minti biyar Hajiya Kari ta girgiza ta sannan ta ce, "Aminiyata me ki ke tunani ne haka?" Hajiya Jummai ta ma rasa ta cewa, zufa ce kurum take keto mata, duk kuwa da (AC) da ke ɗakin.


Can ta ce, "ko dai ba kiji dai-dai ba Karima?" Hajiya Kari ta ce, "Ki dai bincika." Ta suri jakarta tare da cewa, sai naji wayarki,don jin gaskiyar lamarin." Ta fita ta bar Aminiyarta cikin hawan jini.


Inda Hajiya Karima ta bar Hajiya Jummai,tana nan a gurin, har ƙarfe tara na dare. Ta rasa wane irin tunani ma zata yi? Wayarta ce ta shiga ruri, ashe maigidan ne cikin ƙarfin hali ta miƙe. Ta same shi da laptop yana harkokinshi,ta shigo ta zauna, jikinta ba laka, ya dube ta.


"Jummai ba ki jin daÉ—i ne?"


Ta ce, "shi ne dalilin kirana don ka san ko ina jin daÉ—i ko bana ji?"


Ya ce, "A'a." Ta ce "To yi maganar ka." Ya ce, "To dama kan batun aure ne da aka bani, cikin cijewa ya yi maganar, ya ci gaba su Baba Alhaji Sunusi ne suka ba ni mata," zaraf ta miƙe kana nufin Hadiza? Ya ce, ita, tayi wani guntun murmushi, sannan ta ce, "Allah ya bada Sa'a." Ta fita ya bita da kallo ya san gatse ta yi da ta ce Allah ya bada Sa'a.


Ya lumshe idanu, ya gama da nan sauran A'isha, duk da ba ya jin ta yasan ita ba zata ce komai ba.


Ranar ko runtsawa Hajiya Jummai bata yi ba,ta ma rasa me zata yi taji sanyi? Ta san Hajiya Lanti kamar yunwar cikinta, duk cikin dangin maigidan nata ɓarayin mahaifinshi ba mafaɗaciya irinta. In ma asirin ne take taƙama dashi ta san zasu goga,don haka dolenta ta nutsu kada ta yi saurin nuna za ta ɗauki wani mataki kan Hadiza,ta sani su Hajiya Lanti lashe money ce,ta jima tana son ƴarta Hadiza ta auri Alhaji Saddiƙ,don dukiyarshi. Wannan lokacin bata damu da cewa ƴar ta mutu ko tayi rai ba,in har za su samu kuɗi Hajiya Lanti gogaggiya ce ta samu duniya, ita ce mace mai faɗa a ji cikin matan Alhaji Sunusi,ku san ita ce ke juya gidan son ranta. Ta taɓa jin labarin ta gurin Boka na kan dutse. Lokacin da taje da buƙatar mallakar mijinta a hannu,Boka na kan dutse ya shaida mata cewa,wata Hajiya Lanti ita ce mace mai tsananin Sa'a, wadda ta samu mallaka ta ƙarshe a gurin Aljanunmu.


Tun daga kanta har zuwa yau ba mu kuma ba da irin wannan mallakar ba, bata samu matsala a gurin gano kowace ce Hajiya Lantin ba, sai dai ta gano dangin mijinta ce, don haka ta haƙura da ta so su haɗa ƙawance da ita, da irin waɗannan tunane-tunanen ne gari ya waye mata.


Ita ko A'isha ba ta san me ake ciki ba, suna ta fama da jarabawar da ke fuskanto su lokacin bikin Uncle baifi sati biyu ba, da yake Uncle bai É—auki bikin da wani muhimmanci ba, ya yi zuwa gurin A'isha ya kai nawa, amma bai ce mata komai ba game da bikin nashi,hasalima shi mantawa yake yi da batun wani auran shi. Bai ma san dalili ba,in dai yana tare da A'isha ya kan manta da duk wasu lamura na shi, ballantana ma yanzun da ta mallaki abin kallo.


Yana son ganinta cikin kayan makaranta,ko na zaman cikin makaranta , har dai ace bata saka hijabi ba,ƙirjinta yana mishi ƙyawun kallo. Sirantakarta ce kurum yake ganin matsala sai dai yana son yanda take da tsawo,dan tsayinta na sa shi jin alfaharin kasancewar ta matarshi,yana son taɓa jikinta sai dai yanda take ba shi girma na saka shi yaji nauyinta.


Wani daÉ—i yake ji duk lokacin da ya riki tafin hannunta, ta tsaya mishi cikin zuciya kuma bai rufe mata ba,yana yawan shaida mata yanda yake jinta cikin zuciyarshi, wanda ita kuma haka yana saka ta jin daÉ—i har ma tayi kewarshi,in ya yi kwanaki bai zo ba.


Yau saura sati ɗaya bikin shi,ya yi dai ta maza ya kira Abbanta a waya ya shaida mishi cewa an bashi mata,wan mahaifinshi ya cigaba da cewa Friend wallahi ba da son raina zan yi auren nan ba, zan yi ne kawai don bani da yanda zan yi, maganar ta biyo ta gurin Hajiyarmu da Alhajinmu ne. Abba ya ce, "Haba Friend,ai ko kai ne ka gani ka ce kana so koyi kayi da sunna, ina fata dai A'isha bata ɗaga hankalinta ba? Don ka san mata ba su da hankali, yanzun sai taga cewa ita ba'a yi mata daidai ba, bayan Allah ne da kanshi ya umurce mu, Uncle ya ce, "Ai ita wannan baiwar Allah ce, wallahi friend tunda yarinyar nan ta zo gidana ko sau ɗaya ban taɓa ganin fushinta ba, kullum cikin fara'a take. Abba ya ce, Alhamdulillah, sai in mun zo insha Allah zan zo ɗaurin aure."


Uncle ya ce "To shi kenan, sai ka zo kenan."


Washegari Sunday (lahadi), Uncle gurin Beby ya nufa, suna zaune suna fuskantar juna, ta rasa dalili in tana kusa da Uncle sai ta samu kanta cikin wani yanayi da ba zata iya cewa wane iri ba ne.


Ya dube ta da murmushi, Beby kullum ƙara ƙyau da girma ki ke yi,ta ce ko dai tsawo? Ya ce,kinsan cewa tsawonki yana ɗaya daga cikin abinda yasa nake sonki? Ta rufe fuska da dogayen tafukan hannunta, sannan ta ce, wai da gaske kana sona? Ya ce, sosai ma, kada ki ga yanda na ƙosa kuyi hutu wannan karon domin na san yanzun kinsan abinda ake yi a samu ciki ko? Cikin cinya ta saka kanta, sannan ta ce ni ban sani ba fa,ya ce to ai koya miki zan yi,kina so? Ta girgiza kai alamun a'a,ya ce amma da ai kin ce in nuna miki kenan kin bincika kamar yanda na ce,kafin ta yi magana wayarshi ta soma ruri,yana cirowa yaga Hadiza ce, bayan sun gaisa take cewa wai ƙawayanta zasu zo amsar kuɗi gurinshi zasu zo ko gurin abokanshi? Ya ce, mata ba ko ɗaya,su gaya mata ko nawa ne sai tayo mishi waya zaya aiko a kawo mata, ta ce shi kenan. Ya dubi A'isha wadda zuciyarta ke son sanin wacece Hadiza? Ya ce Beby dama na zo ne da magana sai kuma na manta kin san cewa in ina kusa da ke ina manta komai da komai ne? Ta yi ƴar dariya tare da cewa, wace magana ce? Ya ce, "Beby mata aka bani." Ta kafa mishi idanu,ko ƙiftawa sannan ta ce,ban gane ba? Sai kuma ya samu kanshi da ɗari-ɗarin gaya mata, sai dai dole ne ma ya daure ya sanar da ita saboda ance magana zarar bunu, kuma ya riga ya furta. Ya ce, "kin san Baba Alhaji Sunusi?" Ta girgiza kai ni ban san shi ba,ya ce kin san Hadiza? Haushi ya ma hanata magana, kallonshi kawai takeyi,ya ce ita ce aka bani ƴar wan Babanmu ce,yau saura ƙwana shida bikin."


Idanu A'isha ta zaro, saura ƙwana shidda? Ta taɓe baki, sannan ta miƙe tsaye tare da cewa, "Allah ya ba da zaman lafiya." Ta nufi cikin makaranta,sam bai za ci haka daga gareta ba, ita ko ko gani batayi, ta isa ɗakinsu kan gado ta ƙwanta, ga mamakin ta sai kurum ta ji hawaye suna ƙwaranya a kan kumatunta.


Wato ita Uncle zaya yi wa haka? Wai an bashi mata kenan, ita ba son ta yake ba,dama bai wani damu da ita ba,shi kenan yanzun zaya daina gaya mata kalamai masu daɗi, haba ita ta sani in ba baya son ta ba ai bazai kasa kula ta ba,bai taɓa neman ta ba haba ya ci ace tun tuni ma ta gano wannan matsalar, amma ba komai yaje ya yi ta yin auran, Umma ta ce,in bana gyara mishi shimfiɗa sai ya ƙara aure, duk hutu sai ta gyara mishi ɗaki amma hakan bai sa ya sota ba. Tana cikin wannan halin su Samira suka shigo, cikin sauri suka isa gurinta, nan suka shiga tambayarta abinda ya same ta. Sun ruɗe ƙwarai,domin ba su taɓa ganin A'isha musty cikin wannan halin ba.


Samira ta ce,"A'isha Musty me ya same ki ne? Don Allah tashi ki ji mu." Jin lallashin da suke mata ya saka ta kukan sosai,ba ta iya cewa komai ba,sai da tayi ma isarta sannan ta share hawayenta. Samira ta ce,me ya same ki? Wane ne ya ɓata miki rai? Ta ce, Uncle ɗina ne. Amina ta ce,me ya yi miki suka haɗa baki gurin cewa, Uncle ɗin ki dake matuƙar ji da ke? Ta ce,wai fa aure zai yi, dariya ta kama su,don zai yi aure ke ba abin murnarki ba ne? Ta yi shiru ita ta manta ma da ba su san cewa Uncle mijinta ne ba,don haka sai ta ce ai ba zaku gane ba ne, duk yanda muke da Uncle wai ace sai yau zai gayan bikinshi saura ƙwana shida bayan duk sati sai ya zo,ni kun ji damuwata." Suka ce ki mishi uzuri,ki ka sani ko abin ne yazo mishi ba cikin shiri ba?" Ta ce,Umh, daga nan ba ta sake cewa ƙala ba, domin ta gane ba zasu fahimce ta ba.


Tun daga ranar ba ta da sukuni, duk bayan awa ɗaya sai ta lissafa sauran ƙwanakin da suka rage na bikin Uncle ɗin nata,su ko su Samira mita suke mata kan cewa ta yi wa Uncle ɗinta afuwa, tare da ba shi uzuri. Ita ko Amina cewa take ina ma ba lokacin makaranta ba ne,su zo mata biki har ma su ga Antin tata,wato amaryar Uncle ɗin nata,a cewarsu ta yi dacen miji. A'isha kan ja tsaki tare da cewa, "Allah ya sutura,ta zama Antynta,su kuma suce dole ne tunda tana auren Uncle ɗinta. Aisha kan yi tsaki ta yi shiru kurum.


Shima Uncle na shi gefen yana cikin damuwa, wato damuwar Beby ita ce ta É—aga hankalinshi. In ya tuna yanda ta wuce yana kiranta Beby-beby tamkar ba ta ji shi ba haka ta yi. Dama Beby tana fushi? Itama kishi kenan gare ta? To me yasa ba ta kishi da Jummai sam? Koda yaushe tunanin A'isha ke ranshi, tamkar ya ce ya fasa auran yake ji. Cikin haka aka shiga bikin.


Abba ya shigo Katsina,ana gobe ɗaurin aure ka ji daren da ya hana mutum huɗu bacci, A'isha ƙwana tayi sallah tare da addu'o'i, tafi maida hankali ne ga roƙon Allah ya rage mata kishi cikin zuciyarta. Jummai kuwa ƙwana ta yi neman mafita inda ta farka da mummunan ciwon kai...




########

[12/11, 21:33] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 6*



Hadiza kuwa ta ƙwana da farin cikin samun mijin nunawa Sa'a ga kuɗi ga ƙwarjini,shi kuwa Uncle tunanin Beby ne ya hanashi bacci,ya ƙosa gari ya waye sati ya je school ɗin shi da Abbanta.


Aisha ta farka damuwar da ɗan sauki,ta yi tunanin gara ta rungumi ƙaddara tunda auren babu fashi,sai dai matsalarta ɗaya,dama Uncle ba ya son ta? Ta kan ba kanta amsa da cewa eh,tunda gashi ya yi wata a madadinta. Tana son samun natsuwa badan komai ba sai don jarabawar da ke tunkaro su,nan da satin da zasu shiga,ta sani ƙarƙari nan da sati uku za su yi hutu maimakon Uncle ya bari sai sunyi hutun ya yi auran. Sai kuma tayi tsaki ta ce, ita dai tana son cire batun auren nan na Uncle daga zuciyarta.


An É—aura auran Uncle da Hadiza da misalin Æ™arfe É—aya da rabi na ranar asabar, bayan an tashi daga sallah,ko jiran walimar abokan da  nashi suka shirya bai yi ba,yaja Abba da cewa su zo suje gurin Beby a makaranta, Abba ya ce a'a ka barta kawai,ni yanzun zan É—auki hanyar garinmu."


Uncle ya ce "friend dole muje ka ganta,zata ji daÉ—i saboda wancan hutun nan kaita gida ba." Abba ya ce,shi kenan muje.


Suna kan hanya, Nafisa ta kira shi tana cewa, "Brother,tun jiya na ke son ganinka,ya ce gamu nan zamu je gurin mutuniyar ki ne makaranta." Nafisa ta ce,ku gaishe ta,sai ka dawo zamu haÉ—u." Shima yana son ganinta tun bayan bikinta bai ganta ba.


Sanda suka iso makarantar, lokacin tana ƙwance. Tun safiyar yau gabanta ke mugun faɗuwa, musamman in ta tuna sauran ƴan awanni a ɗaura auran Uncle ɗin ta, lokacin da take zaton cewa lokacin ne ake ɗaurin auren sai ta samu kanta da kasa koda zama ne, saboda faɗuwar gaba, tabbas dole ne a ce an zo yiwa duk matar da mijinta zai ƙara aure dannar ƙirji,dama haka ake ji? Kafin ta ba kanta amsa, sai ga sallamar Momy ɗin da ke kula da gefen su, ta ce ƴar gidan Uncle ki zo inji shi. Wani sabon takaicin taji ya rufe ta,ta ce Momy ki ce mishi bana jin daɗi ba zan iya fitowa ba. Momy ta ce,da kin daure kin ɗan lallaɓa A'isha, ta ce,ki dai gaya mishi.


Momy ta tafi tana cewa,zaki sa hankalin Uncle ɗin ki ya tashi kenan. Da yake kusan yawancin malamai zuwa ɗaliban makarantar sun san shi a duk lokacin da makarantar take buƙatar wani abu da zarar ya samu labari zai ba da, haka nan tunda A'isha ta shiga wannan makarantar,bai taɓa biyan school ɗin ta ita kaɗai ba, sai ya haɗa duk ajin ya biya, shi yasa A'isha Musty ta yi suna cikin makarantar ga ƙoƙari.


Lokacin da Momi taje musu da batun A'isha ba ta ji daɗi, sai hankalinsu ya tashi. Uncle ya ce, sosai ne? Me ya same ta? Momy ta ce da ɗan sauki Abbanta ya ce kice ta ɗan lallaɓo Abbanta ne. Koda Momy ta shaida mata saƙon da sauri ta tashi zaune tana cewa, su biyu ne? Momy ta ce eh.


A'isha ta zura hijabi suka tafi, Abbanta yana zaune shi ko Uncle yana tsaye ya kasa zama. Ta shigo da sallama suka amsa, Uncle ya nufo gurinta yana cewa, Beby me ke faruwa da ke ne? Bata ko kalle shi ba ta nufi Abba,tana cewa, Abbana yaushe ka zo? Ya ce, jiya na zo, yanzun nan kuwa ina kan hanya ne dama na zo É—aurin auren friend ne,ta ke ta canza fuska, tare da canza magana,ta ce Yaya Umma fa? Ya ce,da tare zamu zo sai kuma su Jafar ba su ji daÉ—in jikinsu ba.


A ranta ta ce,lallai Umma, wato da auren Uncle za ta zo? Ta ɗan taɓa baki sannan ta rusuna ta gaishe su, suka amsa. Uncle ya sake tambayarta,me ya same ta? Ta ce,mura ce,kuma ta samu sauƙi. Wayarshi ta yi ringing,ya ɗan fita don amsawa. Ai nan take zuciyar A'isha ta yanke mata hukuncin cewa amaryar tashi ce ta kira shi,don haka sai ranta ya kuma ɓaci. Abbanta ya kula,don haka ya ce, "A'isha ki fa ƙwantar da hankalinki,ki kuma zauna lafiya da maigidan ki, kada kiyi kishi irin na jahilan mata, kiyi kishi irin na mata Annabinmu Muhammad (S.A.W) na san kina da labarin yanda suka yi nasu kishin kin ji ko? Ta ce, to Abba. Uncle ya dawo ciki, Abba ya miƙe yana cewa, to ni zan yi harama fa. Ya fita Uncle ya dube ta.


"Beby na miki laifi ko?" Ta girgiza kai,ni ban ce ba, ya ce, amma kin nuna beby,kin kuwa san halin da ki ka bar ni a ciki ina kiranki ki kayi banza da ni? Ta dube shi, sannan ta sunkuyar da kai cikin zuciyarta ta ce, kaima ka san kuwa halin da ka sani? Amma a fili sai ta ce to yi haƙuri," tausayinta ya ji ya ce "kiyi haƙuri kema Beby ban san cewa abin zai ɓata miki ranki ba da ko da aka matsanta min auren nan da ban amince ba. Ta kalli fuskarshi nata ganin yana mata daɗin baki ne don ya lallashe ta, amma sai ta ce saboda ni zaka ƙi koyi da Manzon Rahama? Idanunshi suna kallon nata ya girgiza kai, sannan ya ce, "Shikenan na gode, amma babu fara'a? Ta yi ajiyar zuciya tare da lumshe idanu,sai nan ta girgiza kai tare da cewa, kada ka damu zaka samu wani lokaci,ya fito tana biye da shi, sai yana tuhumar kanshi ko dai ya cutar da ita ne? Ita kuma zuciyarta ba zata iya dariya ba,don haka bata jin cewa zata iya yin wata fara'a, ta leƙa Abbanta a mazaunin kusa da direba, ta ce "ka gaida su Umma da su Jafar, insha Allahu wannan hutun zan zo." Ya ce,to shikenan sai mun gan ki ta kalli gefen Uncle ta ɗaga mishi ƴan yatsunta guda uku, alamar bye-bye. Ɗan murmushi kurum ya yi sannan ya furta da leɓunanshi a hankali,wai ƴar rigima. Abba yana kallonsu amma ya yi tamkar bai san suna yi ba. Uncle ya ja mota suka tafi. Cike da takaici ta juya yanzun waton Abba, saboda shima ba wani sonta yake yi ba, yafi son Uncle shi ne har da zuwa don za ayi mata kishiya? Ya sani Umma ba zata zo ba koda lafiyar Jafar ƙalau tunda ciwon ƴa mace na ƴa mace ne.


A'isha ke nan.


Hajiya Jummai kuwa duk da ƙoƙarin da tayi don ta danne amma hakan ya faskara, duk wanda ya kalle ta ya san tana da matsala,wai don ma ƙawayanta sun sakata a tsakiya suna tausarta, mamakin ta shi ne dama aƙwai rana da zata zo har ta kasa maganin kishiya da kuɗin ta da komai? Ashe lokaci yana zuwa da zata zauna da kishiyoyi biyu? Su ƙwana su tashi a gadon mijinta? Lallai duniya mai juyi,ta yi tsubbun ta yi tsafin,ta ci nasarori shin me yake shirin faruwa da ita ne? Waɗannan tunane-tunanen su ne suke sakata yin jingum,suke hanata bacci, kuma su ke barazanar saukar mata da ciwon zuciya, domin ba ta shirya ma zuwan wannan rana ba,sai dai tana da burin ɗaukar kowane irin mataki bari dai taro ya watse. Manyan mata kenan.


Bayan shagali, Amarya ta tare a gidan ta,ko'ince a ɗakinta, wanda ke nan cikin falon gidan Alhaji Saddiƙ, da ɗakin na baƙi ne amma yanzun an gyara ma baƙi wani, amarya ta ci gayunta ga tanadi kala-kala da aka yi don birge ango,ta ɓangaren jiki an sha nasha an cusa na cusawa,ban da na su kalolin asiran wanda Hajiya Lanti duniya ta shirya mata,wato mahaifiyarta Hajiya Lanti lashe money. Tun tara angon yana gida amma ko a ranshi ba ya da ra'ayin zuwa gurin amaryar tashi.


Flashing ɗin da ta gallaɓe shi da shi ne ya saka shi kiran wayarta,yana tambaya ko lafiya? Ta ce,taga bata ganshi ba ne ya ce mata shi tuni yana gida, sannan ya kashe ita ko bayan feshe jikinta da tayi da turaruka sai ta nufi ɗakin angon cikin wata shegiyar rigar bacci.


Hajiya Jummai tana leƙenta ta window har ta shige,nan ta zube kan gado tana son koda kuka kai ko hawaye ne ya ɗan fito ta samu rahama, amma abin ya faskara. Ita ko amarya ta samu ango yana shafa'i da wuturi, komawa ta yi ta ɗauko hijabi, bayan ya idan sannan ya ce ta zo suyi sallah irin ta ma'aurata. ango da amarya ranar an darji amarci, duk da da farko ya yi fargaban kada ta mutu,don yana ɗaya daga cikin abinda ya hana shi kusantar A'isha kenan, har yanzun.


Cikin satinshi da zai yi a ɗakin amaryar,ya sha shagali, har ma yaji tamkar kada ya bar ɗakin nata. Hadiza ko gaban waye tana nuna rashin kunyarta matsawar maigidan yana kusa da ita. Shi ko namiji dama ɗan son a ririta shi ne, don haka sai yake jin shi tamkar yanzun ne ya yi auren fari. Duk yanda Hajiya Jummai ta ɗauki abin da sauƙi, sai ta samu ya wuce da tunaninta,don haka sai ta kuma bazama neman wata sa'ar.


A'isha ko tana makaranta daran amarcin su Uncle,haka ta ƙwana raya halin da suke ciki a zuciyarta, wani satin da ya zagayo, Uncle ya zo gurinta, ta isa gurinshi fuskarta a tsare cikin girmamawa, kamar ko yaushe ta gaishe shi, ya amsa yana mai kallonta, ganinta ya yi ta rame mishi, ya ce Beby don Allah ki cire komai cikin zuciyarki,a gurina har ya ban ga ƴar da ta shiga raina ba tamkar ki ba,ta dube shi da son ta fahimci gaskiyar maganar shi,sai taga ya yi mata ƙyau fuskarshi har wani ƙyallin goshi yake yi, daga ka ganshi kaga sabon ango. Zuciyarta ta yi wani iri,lallai Uncle yana shanawa, shi ne yanzun zai mata daɗin baki.


Ta sunkuyar da kai,ya ce "ina don zanyi tafiya jibi ranar Monday,zan je Phoenix,saboda wani kasuwanci da zamu bunƙasa a can, ina zaton zan kai sati biyu ko in wuce."


Ta ce, Allah ya taimaka,ya kuma ba da sa'a, akan abinda aka je nema, ya ce na gode da addu'ar ki,shiru na ɗan lokaci Hadiza ta kira shi da ya ɗaga wayar sai ya ce, ya ya ne? Cikin shagwaɓa ta ke cewa,my love kana ina ne? Ya ce, ina makarantar su Beby ne, menene? Kishi ta ji ya cika zuciyarta, ballantana in ya ce Beby,komai Beby ita ta ma ƙosa taga wai ya ya wannan Beby take ne? A'isha dai tana jin shi,ya ce, "kin yi shiru na ce menene? Ta ce, missing ɗin ka nayi dama, ya ce "ok ina zuwa kin ji? A'isha tamkar ta miƙe domin ta gane da amarya yake hira,ta dai daure. Yana gama wayar ta miƙe ta ce,sai ka dawo kenan, lokacin yin kitsonmu ya yi. Ya riƙo hannunta irin sallamar da zamu yi kenan? Ji tayi tamkar ta fisge hannunta,ya ci gaba.


Beby zan tafi, ina kewarki,zan so ace tare muka tafi."


Cikin gatse ta ce,"To ba ga amarya ba." Sai bai fahimci gatse ta yi mishi ba, ya ce,"kin amince in tafi da ita?" Haushi ya kama A'isha, ta ce yardata ka ke nema? Ni kuma a wa?" Ya ce,ni fa duk abinda zai maido min da walwalarki shi nake son yi,a zuciyarta ta ce,ka ce dai kana son abinda zai baƙanta min rai,ya ce kin ji ni me zan miki ki huce? Ta ce,wai to ni ce maka aka yi ina fushi? Ya ce, amma ai da ba haka ki ke ba,ta ce to yanayin rayuwa ne yazo da haka, don haka mu duka sai mu ɗauki haƙuri da juna. Ya saki hannunta tare da cewa shikenan,ni zan wuce Beby sai na kira waya" Ta rakashi kamar yanda ta saba, suka yi sallama a gun mota.


A'isha ta koma ciki, zuciyarta da damuwa. Nata ganin Uncle ya samu wadda ta fita yanzun zaya daina damuwa da ita, shi ko ya tafi ne cike da kewarta tare da son ganin ta dawo tamkar da.


Ran da Jummai zata fita daga girki, Alhajin ya sanar da ita cewa,yana son tafiya da Hadiza tafiyar nan da zai yi. Nan Hajiya Jummai ta shafa ma idanunta toka, ta shiga masifar cewa, ita bata yarda ba, don ya ga komai ya ce tana shiru shine zai zalince ta,to ita fa bata amince da wannan zancan ba.


Shiru ya yi yana kallonta,ga mamakinta sai taga ya miƙe tare da cewa, tafiya da Hadiza babu fashi, saboda matanshi uku ba zai tafi shi kaɗai ba,ta ce to dole sai da Hadiza? Ya ce,to gaya min da wadda zan tafi, A'isha tana makaranta,ke kuma ina ne ba mu je da ke ba? In bazaki manta ba,lokacin da aka ɗaura mana aure dake ko sati ɗaya ba muyi garin nan ba muka bazama duniya, wata shidda muna yawon amarci. Cikin waɗannan wa ya samu haka? A'isha ko airport ta taɓa zuwa ne?"


Hajiya Jummai ta fito tana cewa,na barka da Allah. Da kallo ya bita, ita wannan watau rashin mutuncin da take yi wa wasu shi ne ya soma zuwa kaina,ya yi ƙwafa,ko a jikinshi ya ɗauki amaryarshi suka nufi Phoenix.


Harkokinshi suna tafiya yanda yake so gefe kuma ga amarya.


Hadiza irin matan nan ne masu fi'ilin tsiya da ƙwarƙwasa,gata da son komai ace ita ce gaba, sannan tana da son ƙyale-ƙyale. A da Hadiza baƙa ce, amma yanzun fara ce tas,sai dai in ka kalli ƙafar zaka gane farin na mai ne. Tana da ƙiba kuma bata da tsawo,ga tumbi. Gaskiya sun yi soyayya ko ince suna soyewa. Tana matuƙar son Alhaji Saddiƙ.



#######

[12/12, 13:22] Ummi Tandama😇: *📗📗Page 7*




Ta fi son ace daga ita sai shi bata son ganin kowace mace kusa da shi, shi yasa take jin haushin wannan shegiyar Beby É—in da bakin shi ke yawan kira, don ta kula yanda yake yawan cewa Beby ko Jummai ba ya kira haka,tana burin maye gurbin Beby É—in nan.


Tun saura ƙwana huɗu a yiwa su A'isha hutu, makarantar kamar yadda ta saba ta samo tura ma dukkan iyayan ɗaliban nasu text cewa rana kaza ne za'ayi hutu, lokacin da saƙon ya isa ga wayar Uncle ba layin ba ne cikin wayarshi, tunda baya ƙasar ma. Kan wayar da layin ke ciki ma bada ita ya tafi ba, don haka bai samu saƙon ba, ballantana ya ce aje a ɗauke ta, ƙa'idar makarantar ba sa ba da ɗalibai sai dai in iyayansu ne ko waɗanda suka ɗauki nauyinsu. Sam Uncle bai san taƙamaiman ranar hutun ba, don haka koda ranar hutun ta zo A'isha ba taga anzo ɗaukarta ba,a ƙarshe bayan kowa ya watse nan shugaban makarantar suka shiga neman shi a cikin waya. A'isha ta ce, musu ya yi tafiya baya ma ƙasar gaba ki ɗaya. Don haka sai suka ba da ta gidan wata Malama da ke nan cikin makarantar.


Wannan lamarin ya ƙara sa A'isha yarda da cewa yanzun Uncle ya daina yi da ita, ya daina sonta inda da ne ba yanda za'ayi ya share ta, yanzun ya samu wata wadda ta fita, sanadin wannan yasa A'isha zama miskila.


Gidan Malama Salamatu, gida ne mai tsari da tarbiyyar Islama, tana da yara Æ´an biyu sa'annin A'isha, suna son Aisha sai dai ta kasa sakewa da su,ba ta cika magana ba, sai dai sun kula tana da yawan ibada. Malama Salamatu ma ta yaba da A'isha.


Ranar da ta cika ƙwana biyu ne ya ga saƙon ta cikin Internet ɗin shi, lokacin yana zaune yana duba saƙonni. Hadiza kuma an dage ana ta danƙara uwar ƙwalliya, faɗin innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un ɗin da ya yi shi ne ya saka ta juyowa ta dubeshi,nan ya ɗauko wayarshi ya shiga neman layin Hajiya Jummai. Hajiya Jummai ta ɗauka lokacin ma tana gidan Kari, ya ce Jummai an ɗauko beby daga makaranta ne? Ta taɓa baki sannan ta ce, wacece haka? Cikin sauri ya ce "A'isha fa" ta ce,sallahu ka bari cewa a ɗauko ta? Sannan ta kashe wayarta, ta tsani wannan A'isha ballantana in yana faɗin Beby ɗin nan, ta ce ɗan rainin wayo, Kari ta ce,hala mutumin naki ne?" Ta ce shi ne mana,kin ji shi ne? A firgice wai an ɗauko A'isha daga makaranta? Karima ta ce, na kula duk da ya yi auran nan hankalinshi ya fi tafiya ga wannan A'ishan.


Jummai ta ce, shi yasa na tsane ta, har na fi jin kishinta akan Hadiza, duk da nasan Hadiza da uwarta Lanti ba ƙyalle ba ne? Kari ta ce"ai dole ne kifi jin kishin A'isha, tunda wanda ake kishin domin sa ya fi sonta,(ta ci gaba da cewa) ko me ya gani jikinta? Yarinya ba ƙugu ba sharaɓa babu nonon kirki. Koda yake kin san ƴan ƙauyan nan fa suna da mugayan malamai, sai a mallake miki miji a kan Naira ɗari ko ɗari biyu."


Tsaki Jummai ta ja,ai ba'a ƙwana a gado kullum, kuma nima na san ba don sun min asirin da duk abin da nayi kada ya ci ba wane su, shi yasa yanzun nake son in an gama aikin nan, ba makamin nan ya ce zai karya asirin da suka yi mini ba? Yana karyawa zan ɓalle tsiya nima duk in ga bayansu,don duk sai na kashe su,ni kishiya in ba a lahira na aikata ba ko mai nayi mata ban huce ƙwanciyar da tayi na gadon mijina ta ɗanɗani kalar soyayyarshi ba,ta sha min zumar da ba kowane namiji ne ya iya ba da ita ba". Kari ta yi dariya, tare da cewa, shegiya mutuniyata,in na tuna baya,ba ki da ƙyau, amma tunda naga Alhajinki ya riƙe ki daga wasu mazan na san ba ki da sauƙi. Jummai ta ce,ai wallahi duk mazan da aka yi harka a can da ba su san komai ba,ke dai bari kawai." Suka tafa tare da sakin dariya.


Shi ko Uncle tsaye ya miƙe rike da waya yana jan tsaki layin Jabir ya nema, bayan ya ɗauka ya ce Jabiru don Allah maza-maza gobe da asubahi ka nufi makarantar su Beby,sun yi hutu ba'a ɗauko ta ba." Jabir ya ce,ko aje yanzun ne? Uncle ya ce a'a bana son tafiyar dare,kai dai don Allah kayi sammako. Sannan ya kashe wayar, ya dubi Hadiza wadda ta cika ta yi dam sakamakon yanda yake kiran Beby, ta ce to ita bata san hanya ba ne? Da bazata koma gida ba? Ya dube ta cike da haushin abinda Jummai ta mishi, sannan ya ja tsaki ya fita, takaici ya rufe ta,lallai zata ɗauki mataki a kan A'isha.


Daran dai Alhaji Saddiƙ sun yi ƙwanan doya da manja ne, shi da amarya.


Washegari Jabir yana idar da sallar Asubahi ya ɗauki hanyar makarantar su A'isha. Maigadin ya yi wa bayani tare kuma da neman taimakonshi,kan cewa gurin wa zai je yanzu? Maigadin ya ce "Gaskiya gara ka koma in dai ba sunanka aka saka ba kan cewa,kaine zaka ringa zuwa ɗaukar ta ba,don ba zasu ba ka ba, lokacin da Jabiru ya kira maigidanshi ya shaida mishi yanda suka yi da maigadi,shiru ya yi lokacin yana shirin zuwa mitin ne ya ce, "Jabiru ka koma gida nima zan taho yau insha Allahu,in na ɗaukota na dawo." Furucin ya firgita Hadiza saboda ɗauko ta daga makaranta za su koma gida? Ta hura hanci gami da girgiza kai, dole ma tasan me wannan yarinyar take taƙama dashi.


Ƙarfe taƙwas na dare suka sako ƙafa cikin gidan,ban da wayar shi da yake son ɗauka da ke cikin gidan,da baza ya shiga gidan ba,ko ta kan Hadiza be bi ba ya barta da ƴan aiki suna ta ya ta ɗiban kaya,ya yi cikin gidan,kai tsaye ɗakinshi ya nufa,ya ɗauko wayar da number ɗin (P.C) ɗin su A'isha ke ciki matsalar babu caji. Batir ɗin ta,ta hannunshi ya cire ya saka sim ɗin ya fito ya leƙa gurin Jummai kamar yanda ya zata bata nan sai su Suby ya nufi waje. Yana fita su Hadiza na shigowa, ya ce mata sai ya dawo bata amsa shi ba dama bai jira amsar ta ba ya tafi abinshi.


Jabir ke jan motar har suka iso, ya kira (P.C) a waya in da ya tabbatar mishi cewa tana nan gidan wata Malama nan cikin makarantar yanzun zai yiwa Malamar waya,ya ƙara da cewa ba ya gari ne da yazo, amma su shiga Malamar zata fito, har ƙofar gidan Malama Salamatu wani malami ya kai su, sannan ya yi musu sallama a gidan lokacin A'isha har sun ƙwanta batayi bacci ba amma ta yi shiru cikin tunanin Uncle da abinda ya yi mata,sai taji ƙwanƙwasa ƙofa gami da sallama,ta amsa, sannan ta tashi ta buɗe Malama ta ce an zo ɗaukar ki A'isha kunna wuta. A'isha ta kunna wuta tare da cewa da wannan daren Momy? Haka ta ji ƴan biyu suna kiranta don haka ɗan zamanta a gidan itama take mata duk abinda taga yaran suna yi. Ta ce eh, fito da jakarki,ta koma ta kinkimo jakar Momy ta amsa tare da cewa ɗauko ɗayar, A'isha ta ce gashi su Hassana suna bacci ba mu yi sallama ba,ta ce ba komai zan sanar da su,in hutu ya ƙare ki ka dawo ina fata zaki zo? Ta ce insha Allah, har mota ta rakata. Sun gaisa da Uncle ya yi mata godiya sosai sannan ya yi mata alkhairi kamar yanda ya saba babu ƙirgawa. Aisha dai ta shige bayan mota ta yi shiru sam bata son komawa gidan rayuwar ƙwana uku a gidan Malama Salamatu ta yi mata daɗi.


Jabir na jan mota suna zaune a baya ƙala dai bata ce mishi ba tunda ya shigo motar suka ɗau hanya kasa jurewa ya yi ya lalibo hannunta ya saƙala yatsunshi cikin nata,bata hanashi ba sai dai bata kalleshi ba yanayin salon da yake yi gurin murza hannun nata kansa ta ji wani irin yanayi. Saitin kunnanta ya rusuna, ya raɗa mata cewa ki yi haƙuri Beby, nayi laifi,ba tare da ta dube shi ba ta ce name? Ya ce na manta na tafi na barki,ta girgiza kai tare da ɗaga kafaɗu,ai ba komai, rashin sakin fuskarta shi ne ya hanashi yi mata hira shiru har suka shiga harabar gidan sai dai hannunshi yana cikin nata. Jabir yana tsayawa ya fito ya buɗewa maigida ƙofa, Uncle ya ce kai mata kayan ciki Jabiru. Tana ƙoƙarin buɗe ƙofa ya jawo hannunta tsaya mana Beby ta koma ta zauna. Ya fuskance ta sosai, Beby kiyi haƙuri,ta ce me kayi min ne Uncle wai shin? Ya zuba mata idanu. Kina nufin ban miki komai ba? Ta girgiza kai tare da cewa, a'a. Ya ce,to in haka ne meye ki ka canza min,ki ka dake min ba kamar da ba? Na shiga wani hali Beby,hakan yana soya raina fa. Sai a nan ta dubeshi zuciyarta na gaya mata cewa da gaske ne zancan da yake miki da bai manta da ke har na tsawon kwana uku ba, duk da an mishi text amma a fili sai ta ce, kayi haƙuri to yanayin rayuwa ne ka san ya kan canza wata rana ƙila zan daina ya sake yin ƙasa da murya tare da cewa,haba Beby,wata rana fa ki ka ce? Ta ɗaga kai ya ce kenan ni da farin ciki sai wata rana kenan? Ta ce, Uncle ai kai ba zaka zama cikin baƙin ciki ba saboda kana da amarya in ba kaga fara'a ta ba ai zaka ga tata. Ga mamakin ta sai taji ya ce, haka ne, amma sai dai ni nafi son ganin taki ɗin,ta yi shiru,ya ce kin ji me nace? Ta dube shi duk da a duhu ne amma tana iya ganin annurin angonci a fuskarshi, kuma gashi ya tabbatar mata cewa yana ganin fara'ar amarya. Ƙila da amaryar ce zata ɗaure fuskar da sai yafi haka ruɗewa, ya ɗan matsa hannunta da ke cikin nashi,ta yi firgigit ta kalli gurin da yake, ya ce na sani kina tunanin abinda na yi miki ne ko? Ya ci gaba da sam ban za ci yin auran nan nawa zai ɓata ranki ba, da ban yi ba, ba tasan sanda ta ce Uhum ba, saboda ta san labari Uncle ya ke,wai kace baka san ran mace zai ɓaci ba,za ka yi mata fa kishiya ne, amma ka ce baka san yin hakan zai ɓata ranta ba, wannan ma hira ne,shi kam da ya fuskanci ba zata lallasu ba, sai ya ce shikenan mu shiga ciki.


Addu'a ce a bakinta, har ta buɗe ɗakinta, ta shiga. Da wanke toilet ta soma sannan ta kakkaɓe gadonta,ta kulle ƙofarta ta ƙwanta, cikin bacci ta ke jin ƙwanƙwasa ƙofa,ta kalli agogo sha biyu,a ranta ta ce to wanene? Maida kai ta yi ta ci gaba da baccinta, don bata zaci Uncle ba ne, tunda ba ya ƙwana ɗakinta ko ma ya ƙwanan baya kula ta.


Washegari da aiki ta tashi, ta yi sallar Asubahi,ci gaba ta yi da aikace-aikacenta, ta share ko'ina ta goge ta kunna turarukan wuta ko'ina ya ɗauki ƙamshi,ta faɗa toilet ta yo wanka ta fito tana yin filla-filla da kayanta. Nan ta dinga ɗago kayan da Uncle ya yi mata, lokacin yana ji da ita, ta cire su gefe. Sannan ta ciro zannuwa da lesuka tun na cikin aƙwatinta,ta zube su duk zata ba da a ɗin ke mata su ne. Yanzu tana son English wears gashi ba ta sa su ba, duk sun mata kaɗan. Sai wani (3)ne da t-shirt ɗin shi ta saka,ta cire saura ta zuba su cikin wata leda da niyyar zata ba Mima ƴar gidan Anty Sadiya, wanda zata ɗinka ɗin ma Anty Nafisa zata yi ma waya ta bada a ɗinko mata, tunda ba ta san inda zata kai ɗinkin ba, duk zamanta a gidan ba tayi wani ɗinki ba, sai dai Uncle ya siyo mata (r) kawai, zama da su Samira ya sa ta iya zama gaban madubi, duk da basa yi a makaranta, amma suna labarin mahimmancin yin ƙwalliya a gurin mace,su kan ce mata mace doki ce sai da gayu,su kan yi labarin cewa in sun yi aure zasu ringa yin ƙwalliya ga mazan nasu. Amina kan ce ai in auranta ya kusa ƙananan kaya zata shiga kasuwa ta jibgo, A'isha tana gaban madubi tana tuna hirarsu,nan ko ta zage ta zabga ƙwalliya ta saka sarƙa (passion) har da ta ƙafa da ƴankunne zobuna da warwaro da ta kalli kanta a madubi sai da ta furta ni ce kuwa? Ta gyara gashinta,tana cikin saka wayarta a caji taji ƙwanƙwasa ƙofa,ta zo bakin ƙofar ta ce, "Wane ne?" Muryar Uncle taji ya ce,ni ne Beby buɗe min,ta buɗe fuskarta ya soma kallo a ranshi ya ce jiya i yau waton babu fara'a kenan.


Ta kauce ya shiga sannan ta kulle ƙofar cike da mamaki ya bita da kallo ta burge shi fiye da tunaninta,sumar kanta da ke ƙwance a dokin wuyanta ta tsuma shi, kamar yanda ta saba ta tsugunna ta gaishe shi duk da ba fara'a ya ji daɗi ya amsa tare da cewa lafiya lau Beby,kai amma fa kin yi ƙyau, shiru ta yi tana zaune nan inda ta gaishe shin, tana wasa da zoben dake ƙaramin yatsanta,ya dubi ɗakin a zuciyarshi ya ce yarinyar tana da tsafta sosai, ya ce Beby ina so in Zauna da ku in kin gama yanzun cikin falona, ta ce, to ina zuwa.


Duk sun hallara a falon A'isha kurum suke jira. Hadiza takaici Hajiya Jummai takaici gashi su kansu sun ƙi kallon juna tsakanin Jumman da Hadiza sai ƴan harare-harare. Aisha kamar ta saka hijabi sai kuma ta fasa,ta ɗauki hula baƙa kalar wandon tasa, gashinta kuma ya bazu a bayanta,silifas baƙi ta saka sannan ta ɗauki wayarta ta nufi falon.


Hadiza da ta ƙosa taga A'isha sai da numfashinta ya kusa ɗaukewa lokacin da A'ishar ta shigo da sallama, Uncle ne kurum ya amsa. A'isha ta ƙara tsare gida, ganin amaryar ta su duk suna zaune ne kan kujera mai zaman mutum uku sun sa shi a tsakiya.



 

########

[12/13, 07:51] Ummi Tandama😇: *📗📗Page 8*




Aisha me ladabi sai kurum ta zauna kasa a gabanshi ta kalli hajiya Jummai ta ce,Hajiya ina kwana? Itama ta cije ta ce,lafiya lau Aisha kin dawo kalau? Ba tare da ta dubu Hadiza ba,ta ce ina kwana? Yi tayi tamkar ba ta ji ta ba,sai da Uncle ya ce ana gaishe ki,cikin yatsina ta amsa,shi ko sai kallon Aisha yake yi,ta dube shi ta ce Uncle gani.


Hadiza ta kuma cika da mamaki ta maimaita kalmar tace Uncle? Lallai wannan yar bariki ce,dubi yanda tayi wata shiga tana ta yatsina sai kace yar wani da wata ga wani ladabin kinibibi za a wani zauna gabanshi,maigidan ya yi gyaran murya ya ce,dalilin tara ku a nan shi ne,ina so in kara tunatar daku cewa yanzun kun zama ku uku don haka sai ku yi ta hakuri da juna,musamman ke Jummai,tunda ke ce babba,ku ma dole ne kuyi mata biyayya ban da raini,sannan ga masu aiki nan ni nake biya,don haka na kowane in ma basu isa ba a nemo wasu,haka nan duk mai wata bukata sai ya tambaye ni ,game da kwana kuma sai kuyi shawara dai dai ko bibbiyu?."


Hajiya Jummai ta ce,bibbiyun za'ayi, Hadiza ta dube ta gami da tabe baki ta ce,bibbiyu? Gaskiya ba zan iya kwana hudu ban gan shi ba,Hajiya Jummai ta dube ta,ko Aisha mamaki ya cika ta,wannan tana nufin tafi kowa son shi kenan? Jummai kuwa cewa tayi sannunki da karfin hali,kina nufin kin fini son shi ne? Hadiza ta ce kina shakka kenan? Wani murmushi Jummai ta yi irin wanda ya ke nufin baki san da wadda ki ke magana ba. Sannan ta ce kin tafka kuskure,amma za ki ga aya.


Aisha ko wayarta ta ciro ta shiga yin game,jin suna ta musu ne ya dakatar dasu da cewa,kai ku min shiru,an ji naki ra'ayin kema anji naki,Beby ke me ki ka ce? Hankalinta ya tafi ba taji ba,ya sake cewa, "Beby." Ta dubeshi "Na'am,Uncle me ka ce?" Haushi ya cika su Hadiza,ya ce ke me kika ce game da kwana?  Ta girgiza kai uncle bani da zabi,ya sanyaya murya saboda me? A ranta ta ce ko na zaba me kwana da kai zai kare ni dashi? Amma a fili sai ta ce ,ba komai ni kaga ba zama nake ba,ya ce a a wannan ba dalili ba ne,ta kara sanyaya murya,Uncle Allah na yafe musu,su yi yanda suke yi,ta mike ta tafi. Ya bi ta da kallo sannan ya ce,ba zai yiwu ba. Hadiza ta ce,me zai hanashi yiwuwa darling ba itace ta ce ba. Jummai ta ce kawai ka bar ta tunda ita ce ta yafe ya ce to in ita ta yafe ni ban yafe ba,baku ganin cewa yarinya ce sai mu taru mu cutar da ita? Ya mike ina zuwa, Hadiza ta ce yanzun binta za kayi? Ko sauraronsu baiyi ba,ya tafi.


Hadiza ta miƙe ranta ɓace tana cewa,tabɗi, wallahi ba zan zauna ba ƙaramar yarinya tana juya mu son ranta,ɗazun ya taramu fiye da minti goma muna jiranta yanzun kuma ta tafi ya bita, bayan da ta zo ɗin sai da ta gama yiwa mutane kallon banza," Haka ta wuce tana mita.


Jummai kuwa kasa magana ta yi ita mamakin ta wai ita ce haka, ita ce kuwa? Ita ce Jumman da tasha alwashin kai duk mai Æ™ararran Æ™wanan da ta aurar mata miji lahira? Yau ita ce da kishiyoyi biyu? Ba dan bata da kuÉ—in da zata biya ayi mata aikin ba,ba don babu malamai ba sai don me? Tana son jin amsar wannan tambayar. 


Aisha kuwa tana shiga ɗakinta kan kujera ta faɗa ta ɗauki ƙafarta ɗaya ta ɗora kan gado, tana karkaɗawa, wani irin zugi take ji a cikin ranta. Wai duk yanda take jin Uncle,a ranta waɗannan matan sun fita? In ma Jummai ta furta za ta iya yi mata uzurin daɗewar su tare, amma Hadiza fa da tazo jiya-jiya,ba ta yarda ta fita son Uncle ba,to abinda tafi son sani yanzun ta ji duk suna son Uncle to shi Uncle ɗin wa yafi so?.


Muryarshi ce ta katse ta, inda ya ce, "Beby ban yarda da hukuncin ki ba,ko kina tunanin ba zan miki komai ba, dole ne kema yanzun ki ringa kwana dani. Ya zauna bakin gado ya ɗora hannunshi kan ƙafarta wadda ke kan gadon ta ce "mai yasa ya dace ɗin? Ya ce Beby me yasa kikeson dafa ni cikin ruwan sanyi ne? Ya murza yatsun ƙafarta. Beby kina ji na?" Ta ce "Uncle, Allah ba haka ba ne,kaga ni zan je gida ne ma ko ba zaka kai ni ba?" Ta zuba mishi idanu, ya yi ɗan murmushi ba zan kai ki ba, sai in kin yarda da batun cewa za ki dinga gyara shinfiɗata, duk bayan kwana biyu ko huɗu. Ta ce, to naji na yarda duk ƙwanakin da ka yanke ya yi min. Ya sunkuya ya sumbaci ƙafar dai-dai tafin ƙafarta, wani abu ta ji zir har cikin kanta, har sai da ta yi girgiza tare da yin ajiyar zuciya. Lokaci ɗaya kuma ta sa tafin hannunta ta rufe fuskarta. Ya ce "Beby ina son abubuwa a tare da ke, cikin su har da wannan kunyar ta ki." Ya miƙe yau fa kece da gyara shimfiɗa, don jiya kin ƙi ki buɗe min ƙofa, kuma gobe zan koma in ƙarasa harkokina a can Phoenix,ko zamu je?" Ta ce, a'a ka dai koma da amarya kawai,ya ce Beby kenan ƴar daru, ta ce yanzun har wani daru gareni? Ya ce ai ke darunki daban ne,babu faɗa babu hayaniya cikin ruwan sanyi ne. Ya fita yana cewa, haka ne ko?" Ta ce haka ka ce.


Tana kishingiɗe tana kallon (Zee Aflam) fim ɗin soyayya suke yi,in tana kallon finafinan soyayya sai ta rinƙa jin yana taɓa zuciyarta, ta sani tana son Uncle ta girma ne cikin son shi,ba wani namiji dake birge ta in bashi ba. Amma shi tana shakkar son da yake mata,ta san dai so ƙwaya ɗaya ne tak, kuma nata shi take yi ma wa,to shi fa wa yake mawa cikinsu? Matarshi da suka yi auren saurayi da budurwa, kuma zamanin ƙuruciya? Ko ita da ya aura tana yarinya ya kuma kasa haɗa shimfiɗa da ita? Ko amaryarshi da ya ke shanawa da ita? Saboda son ta fa wata ƙasar zai je sai da ya tafi da ita, ita ko ko nan da can bata taɓa zuwa ba, daga gida sai makaranta, sai ko garin su in taje hutu. Unguwar ta kuwa ba ya wuce gidan Hajiyarmu,Anty Sadiya ko Anty Fatima. Gidan Nafisa ma ba taje ba, tunda tana makaranta aka yi bikin yanzu dai take son zuwa kafin ta tafi hutu Jigawa. Jin da tayi an dafa mata cinya shi ne ya dawo da ita daga tunanin da take yi, da sauri ta dubi ko wane ne don ta ɗan razana, ganin Uncle ta yi cikin kayan bacci ya zauna kusa da ita, gabanta ne ya sake faɗuwa, amma da ta tuna cewa tana al'ada sai kurum ta ƙwantar da hankalinta, ta ce sannu da shigowa Uncle,ta miƙe ta kawo mishi zoɓo cikin zumuɗi ya amsa tare da cewa, Beby ƴar albarka, har kin min zoɓon? Ya cika kofi ya soma sha idanu lumshe sai da ya sha yafi rabi sannan ya dube ta, nayi missing ɗin zoɓonki sosai Beby, ta ce, to yanzun zaka sha har ka gaji.


Ya kalli wuyanta kullum yana sha'awar shafa wuyan nata,leɓunanshi suna ƙwadayin sumbatar wuyan ya ce, Beby yau dai za ki yi gyaran shimfiɗa ko? Ta kasa kallonshi, amma ta ce to, ya miƙe da jug ɗin zoɓon a hannunshi ina jiran ki,ta ce to.


Tana son kallon fim ɗin nan amma haka ta haƙura ta miƙe ta ƙara fesa ɗan turare ta nufi ɗakinshi. Tana kama ƙofar, Hadiza na fitowa daga ɗakinta. Ta yi saurin zuwa gurin ƙofar tana ke! Ke!! Tsaya ina za ki shiga? Aisha ta dube ta sannan ta shige, itama Hadizan ta shigo,ban gane ba, tunda ka yarda cewa ƙwana ɗai-ɗai ne to ai yau ni ce da ƙwana." Ya dube ta wa ya ce miki ta ƙwana nan jiya? Hadiza ta ce, to an hana ta ne? A'isha ta yi sororo tana kallonsu,bata da lokacin hayaniya, don haka sai ta nufi bedroom ɗin shi da niyyar ta yi abinda ya kawo ta,ta fita watan gyaran shimfiɗa.


Aiko sai Hadiza ta yi caraf ta cafke mata hannu cikin É—aga murya take cewa, Malama kada ki shigar min É—akin miji,don yau nawa ne,ran A'isha ya É“aci, ta tsani ayi mata ihu,don haka sai ta fisge hannunta ta juya tana jin lokacin da Uncle ya ce wa Hadiza dama haka halinki ya ke? Beby zo nan." Ya miÆ™e yana kiranta,ai wannan tuni ta kai É—akinta, ta zauna kan gado ta riÆ™e kai ta tsani ayi mata ihu a kai. Ita ba ta iya masifa ba,bata saba ba, amma duk ba wannan ya fi bata takaici ba irin yadda Hadiza take nuna mata kan Uncle ba zata barta taji da kishin dake cin zuciyarta ba. 


Shi kuma Uncle saboda yafi son Hadizan ya kasa hanata. Ya tura ƙofar ya shigo, ya tsaya a gabanta ya maida hannuwanshi baya,ya ce "Beby tashi kizo mu je." Ranta ya kuma ɓaci,tamkar ta dubeshi ta ce ba zan je ba. Amma kimar shi ta wuce haka,koda ba zataje ɗin ba ba zata iya yi mishi rashin kunya ba,don haka sai ta girgiza kai "kayi haƙuri Uncle, ba zani kuma shiga ɗakinka ba, cikin sanyin murya ta ke magana.


Ya jawo kujerar madubi zuwa gabanta, ya zauna,ya kira sunanta cikin tattausar murya, ya ce A'isha sai yaushe zamu yi zaman aure? Da farko na barki ne saboda kasancewar ki ƙaramar yarinya, yanzu kuma kin girma ya kamata mu canza,shiru tayi mishi, ya ce kin ji ni? Ta sunkuyar da kai,ni dai kurum kai min alfarmar cire ni cikin masu zuwa ɗakinka." Ya taso ya dawo kusa da ita ya zauna, amma Beby ni kin amince in dinga zuwa naki ɗakin ko?kai kurum ta ɗaga mishi ya ce shikenan zan ƙwana nan kenan ko?" Ta ce "In kana ra'ayi."


Duk da cewa bai so ba lokacin da ya ce tazo su yi sallah don yiwa Allah godiyar zuwan wannan rana sai ta sanar da shi cewa tana fashin sallah, amma ya ji daÉ—in yanda suka yi bacci tana lafe a jikinshi.  Sannan ya yi wasanni da ita,ita kanta irin yanda yake mata É—in yasa ta jin daÉ—in cewa itama mace ce.


Sai dai washegari ta kasa kallonshi,in ta tuna jiya duk ya kalle mata jiki, musamman ƙirjinta da take jin kunyar ko a riga taga mutum na kallon mata su, shi kam farin ciki ya farka da shi tamkar ya biya buƙatarshi da ita. Tana gama abinda zatayi ta ce tana son zuwa gidan su Anty Nafisa, ya saka Jabiru ya zo ya kaita mana? Sai cewa ya yi ni zan kai ki Bebyna, tana wanka ta dinga kallon guraren da Uncle ya yi ta mata wasanni da su, ta yi murmushi in tana tuna yanda taga Uncle ya fita cikin hayyacinshi sai taji wani alfahari, ashe itama mace ce.


Riga da siket ne a jikinta na pink ɗin atamfa ƴar Holand,ta ɗora baƙar after dress mai shara-shara, ta saka baƙin takalmi, fuskarta tasha fenti. Ta kalli madubi cikin zuciyarta ta ce, wasa-wasa fa nima nayi. Ina da ɗan kyauna dai dai gwargwado. Ta saka turare mai sauƙin ƙamshi, saboda ta san tare da Uncle zasu fita, kuma gidan Nafisa zata je da ba za ta saka turare ba, saboda bin umarnin da Manzonmu ya yi mana kan cewar bai halatta ba ga mace ta saka turare in zata fita. A wata ruwayar ma an ce in har ta saka to in ta dawo tayi wankan janaba.


A'isha ta fito tana kulle ɗakinta a ƙasa kuwa kusa da ita,jakarta ce baƙa da kuma ledarta mai ɗauke da kayan da zata kai ɗinki, Uncle ya fito ya yi ƙyau cikin suit baƙaƙe tamkar matashin saurayi,daga ɗakin Hajiya Jummai ya fito ya kalleta da murmushi,ta sunkuyar da kai shi Uncle ba ya irin kunya ne? Ta raya a zuciyarta,ya shiga gurin Hadiza ya ce mata,ya tafi. Tana ƙwance kan gadonta ko kallonshi batayi ba, ita dole tana fushi an ci amanarta, shi kam bai saurari amsarta ba,ya fita abinshi.


A'isha ta duƙa ta ɗauki jakarta, ya iso shi kuma ya ɗauki ledar tayi saurin dubanshi gami da zaro idanu,ya ce muje,ta ce to kawo ledar. Ya ce zan riƙe miki ne ta girgiza kai,don Allah kawo na riƙe Uncle ba girmanka ba ne. Ya matso kusa da ita saitin kunnanta ya raɗa mata inji wa ya ce ba girmana ba ne? Ko ke kanki ba sai in ɗau abina ba,ta ce haba dai? Ya ce to bari ki gani,ya kai hannu ta ja baya tare da cewa,ana fa kallonka,ya ce na san su Suwaiba a gurin sai naƙi wasa da Bebyna? Ta ce to muje, suka jera yana riƙe da ledar, suna fitowa nan ma'aikatan tun daga kan mai ba fulawa ruwa zuwa direbobin sun zo don su amshi ledar amma duk ya hana su, sai dai jakarshi ta Ofis ce ya ba Jabiru.


A'isha ko hakan ya yi matuÆ™ar bata mamaki, shi da kan shi ya buÉ—e mata Æ™ofa ta shiga sannan shi kuma ya koma can gefen inda Jabiru ya buÉ—e mishi,yana zama cikin hannunshi ya saka nata.  Yanayin susar da yake mata a hannu ya sa tajin kasala, har ma bata san lokacin da idanunta suke lumshewa ba,sai da suka hau titi sannan ya ce, "Jabir mu fara zuwa gidan Nafisa mu sauke Beby,ya ce to maigida. Hannu yasa ya kwanto da ita kafaÉ—arshi,a hankali ya raÉ—a mata cewa, jikinki yana da laushi Beby, ina son Æ™amshinki, É—an murmushi ta yi tun jiya yake faÉ—in wannan kalmar.


Wayarshi ce ta shiga ruri,ya ciro ta daga aljihun suit ɗinshi, ya kalli fuskar wayar ya shafa kumatunta tare da cewa, Abbanki. Da sauri ta ɗago daga kafaɗarshi tare da cewa, don Allah? Bai bata amsa ba sai dai taga ya ɗaga wayar yana cewa, "Assalamu alaikum, Friend an tashi lafiya? Bayan sun gaisa ne yake shaida mishi cewa dama batun bikine zai sanar da su na yarinyar ƙanwar Umma da za'ayi ranar juma'a mai zuwa ɗin nan,in sun samu zuwa to,in ma basu zo ba ba matsala.



########

[12/13, 17:32] Ummi Tandama😇: *📗📗 Pages 9*




Aisha duk tana jin su, bata san sanda ta dafa bayan Uncle ɗin ba,tana faɗin "Ɗan bani don Allah Uncle ba ni Abban." Tana magana tana girgiza shi, cikin yanayin irin na shagwaɓaɓɓu, ya ce to gama Beby ɗin,da zumuɗi ta amsa,ta ce Abbana ina ƙwana? Bayan sun gaisa ta ce, bikin Naja ko na Sauda? Ya ce na Naja ne za'ayi ranar juma'a,cike da zumuɗi ta ce zan zo insha Allahu, Abba ya ce a'a in mijinki ya ce a'a ba komai dama dai don ku sani ne,ta ce dama zan zo hutu,ya ce to sai kunzo bawa maigidan naki,ta ce to ka gaida min su Umma." Ta miƙa ma Uncle,suka koma kuma kan batun kasuwancinsu, daga bisani kuma suka yi sallama kan cewa sai sun zo. Suna isowa gidan Nafisa, suka shiga harabar gidan suka sauke ta,ta ce "Uncle ba zaka shiga ba?" Ya ce, nayi latti, idan na dawo ɗaukanki zan shiga, ta ce to. Ya miƙo mata ledar, tare da cewa,sai na dawo,ta ce to ka dawo lafiya,ta nufi hanyar da take zaton nan ne ƙofar falon. Shi kam zamanshi ya gyara tare da yin ajiyar zuciya,sakin fuskar Beby a yau ya samu ƙwanciyar hankali.


Ta ƙwankasa ƙofar ana ukun ne Nafisa ta iso,ta leƙo sannan ta buɗe cike da zumuɗi,tana cewa Bebyn bros ce? A'isha ta shiga tana cewa,amare, Nafisa ta amshi ledar tana cewa, kawo in taimake ki. A'isha ta ringa juyi cikin ƙaton falon mai shegen tsari tana cewa, wow Anty Nafisa falonki ya tsaru,gaskiya maigidanki ya iya zaɓen guri.


Nafisa ta ce, maigidana ko maigidanki? Ai da gidan da abin da ke ciki har shirya gidan duk Uncle ɗinki ne. A'isha ta sake kallon falon "kai gaskiya Uncle ya San tasta, mutumin nan ya haɗu da yawa fa, shiyasa kome ya zaɓa zaka ganshi ya haɗu. Nafisa ta zuba mata idanu tana dariya cikin mamaki ta ce, A'isha yaushe ki kayi baki haka? Wasa mijinki ki ke yi, ta ce Allah Anty Nafisa kinsan gaskiya na faɗa, domin Uncle ko kaya ya saka sai kiga tamkar don shi aka ƙera su. Nafisa ta riƙe haɓa tana cewa, lallai A'isha kin shigo gari yarinyar,ta ja hannunta,to zo mu shiga cikin ɗaki. A ɗakin ma haka A'isha ta yi ta santin gadon da sauran kayan tare kuma da koɗa Uncle ɗin nata,ta zube kan gado tana kallon Nafisa tana cewa "Anty Nafisa ga shi kema kin yi ƙyau, Nafisa ta zauna tare da dafa A'isha wai yaushe ki ka zama haka ne? A'isha tana dariya ta ce,me nayi wai? Sannan suka gaisa ta ce, ina Bros? Aisha ta ce, tare muke, ya yi latti ne shiyasa ya wuce, amma in ya dawo za ya shigo. Ya ya maigidanki?" Nafisa ta ce, yanzun za ki ganshi yau yana gidan uwargida ne.


A'isha ta taɓa baki gami da cewa, don ma ku biyu ne, da ace kamar mu ne daga can gidan sai ya wuce wani gidan,don ma Allah yasa gida ɗaya muke. To yanzun kuma ke kaɗai kike kuma Anty Nafisa? Ta ce "eh mana, sai dai ƴan aiki na" Nafisa ta dafa A'isha tare da cewa,sai kurum ki kaji auren Uncle ɗinki? A'isha ta gyara zama tare da cewa,hum ai na ji mamakin auren Uncle,in kin ji takaicin da nayi sai da na kai zuciyata nesa, sannan fa na iya zana jarabawa.


Nafisa ta miƙe,bari inje in kawo miki abinci, A'isha ta riƙe ta,ban daɗe da karyawa ba,bari sai anjima. Nan fa zan yini sai naci abinda nake so " Nafisa ta zauna tana cewa, "ai dukkanmu babu wanda ya so auren bros,ke shi kanshi ma fa ba wai yana son auren ba ne, don dai babu yanda zai yi ne."


A'isha ta ce,ni barni. Yana sonta har fita ya yi da ita waje."


Nafisa ta ce,"Amma dai kin san yafi son ki ko gaban waye yana faɗa." A'isha ta ce, "Gaskiya ni ban gaskata ba." Nafisa ta ce, "saboda me?" Aisha ta ce don yana musu abinda ba ya min." Nafisa ta gyara zama "me kenan? A'isha ta taɓa baki, duk garin nan Anty Nafisa ke kaɗai ce nake gaya miki matsalolina,ni ko ba wai na matsu ba ne,kuma ba jaraba ba ce,hasali ma matsayina na budurwa kuma yarinya na san bai dace in yi wannan zancan ba. Amma zan gaya miki ne ba wai don ki faɗa ma Uncle ba,sai don ki yarda cewa Uncle yafi son matanshi fiye da ni,kin san cewa Uncle bai taɓa taɓa ni ba?."


Nafisa ta zaro idanu,"kai haba?" A'isha ta ce wallahi, amma amaryarshi har da fita ƙasar waje da ita." Nafisa ta ce,wai har yanzun? A'isha ta ce, Allah kuwa,ba wasa nake ba, da yana cewa ban isa ba, yanzun fa? A'isha ta ce God forbid,ai sai ya zata na matsu ne, Nafisa ta ce amma ai addini bai hana ba, kuma in da baki damu ba yanzun ai kin kai ki damu ɗin, tunda ba dutse bace ke, A'isha ta ce koda zamu tabbata a haka ba zan taɓa ce mishi ƙala ba, tayi ƴar dariya tare da cewa kuma shikenan sai ince Uncle me yasa baka ƙwana da ni? Suka yi dariya tare, A'isha ta ce Allah ko ke ce Anty Nafisa na san ba zaki ce ba. Nafisa ta ce bazan ce ba, amma zancan zan maka fuska. A'isha ta ce, "Ni fa ban damu ba,ni da ina makaranta ma,in ya saba min naje makaranta na damu fa? Haka dai suke ta hira har suka zo kan batun su Hadiza nan Nafisa ta shiga ba A'isha labarin wacece Hadiza,ta ce daga Hadiza har Jummai sun auri Bros ne, saboda kuɗi,kuma dukkansu babu wadda bata buga duniya ba. Kuma shi Bros da Hajiyarmu sun ƙi yarda cewa Jummai tana da hannu a cikin mutuwar kishiyoyinta, A'isha ta ce nima haka kawai sai inji zuciyata tana zarginta musamman da wannan ƙawar tata Hajiya Kari.


Nafisa ta ce, kamar kin sani ke dage da yin addu'a, amma batunki da Bros zamu ga yanda zamu yi yanzun dai ki barshi ya gama amarcin da Hadiza, yanda in ya juya kanki zai san kuna da banbanci. Haka ta yini suna hira suka shiga kitchen.


Biyu dai-dai mijinta, Alhaji Bello ya shigo. Nan A'isha ta saki baki tana kallon yanda Nafisa ta ruga da gudu ta rungume mijinta,ta ma manta da wata A'isha a gidan, sai da ya tafi sannan Nafisa ta samu natsuwa. A'isha ta ce tabɗi,Anty Nafisa kina sha'aninki, ina ma zan iya na dinga yiwa Uncle ɗina haka? Ta ce kin ko san da kin ƙara haskawa cikin zuciyarshi. Hadiza zata iya shi yasa ki kaga tana ɗan jan hankalinshi. A'isha ta yi ɗan tagumi ta tsurawa mirrow ido tana tunanin shin zata iya? Ta dubi Nafisa ta yi ɗan tsaki ina jin nauyin Uncle shi ne matsalar amma ina son in burge shi. Nafisa ta ringa yi mata dariya.


Biyar dai-dai Uncle ya kira Nafisa,wai ga shi a ƙofar falonta, suka fito suka buɗe mishi ya shiga. Nafisa ta yi kicin, A'isha kuwa kamar yanda ta saba, ruwa ta kawo mishi ya amsa yana kallon fuskarta, sannan ya ce A'isha Allah ya shayar da ke ruwan Alkausara, yanda ki ke gusar min da ƙishina, shiyasa ko bana ƙasar nan duk lokacin da naji ƙishi,sai kin zo raina kuma sai na miki addu'a. Daɗi ta ji sosai sannan ta ce, "Allah yasa in sha tare da kai Uncle." Ya ce, "Amin Bebyna."


Nafisa ta iso da abinci,ya ce wa zai ci? Tayi turus kai mana Bros ya ce ni kam sai kuma nan da tara na dare. Na riga na ci na rana. Yanzun Beby ta fito mu wuce gida. Bayan sun fito, Nafisa ta ce to telan fa bai san measurement ɗin ki ba, A'isha ta ce,zan aika da kayana sai ya yi min girman su, masu ƙyau inji Uncle. Nafisa ta ce kada kaji komai Bros, bayan sun shiga mota ta miƙo ma A'isha tsarabar da ta bata, tare da ki fa yi amfani da shi yanda na miki bayani, A'isha ta ce to na gode,sai mun yi waya.


Bayan Jabir ya É—auki hanya ne sannan Uncle ke cewa, tsarabar me ki ka samo Beby? Ya kai hannu gurin ledar, kawo in gani. Ta yi saurin É“oye ledar ba fa wani abu ba ne,ya yi É—an murmushi tare da cewa, "Mata ba ku rabuwa da tarkace."


Tun fitar su A'isha, Suwaiba da safiya suka shiga gurin Jummai,suna bata labarin abinda A'isha da maigidan sukayi har ma da ƙarin gishiri,wai ya rataya jakarta. Jummai ta ce jaka fa ku ka ce? Suka ce jaka mana, kuma ta ratayawa ko kunya da girmanshi da komai,tsaki ta ja ni ku daina gaya min tunda ku baku da fus cikin gidan,ba ƙwa taimakaman da komai. Safiya ta ce in mun yunƙura zamu daki banza sai ki ce a'a," ta ce Allah wadaran halinku tunda ba ku da wata dabara sai ta duka,ku fitar min daga ɗaki, ance muku yanzu ana ya yin duka ne? Sai dai na ƙarƙashin ƙasa. Suwaiba ta ce to ba sai ki nuna mana yanda zamuyi ba? Ta ce,ai yanzun duk zamanku tare da ni ba ku ɗauki wani darasi ba? Allah wadaran zamanku tare dani, ta miƙe ta nufi toilet tana masifa,shegu kun iya yawon bin ƙana nan yara suna rarake ku, amma baku iya sanin yanda za ku zauna da mutane ba, yanda za ku ƙuntata ma yarinya, ya gagare ku.


Ranar dai haka ta yini cikin ƙuncin zuciya, gefen Hadiza yau kam a cike da A'isha ta yini ga takaicin jiya,nata ganin ya danne mata haƙƙinta, sannan yau ba girkin A'isha ba, amma ya fita da ita don itama tana kallonsu ta window ɗinta, nata ganin ya fi son Aisha. Ƙaramar yarinya tana juya shi son ranta,don haka koda lokacin ƙwanciya ya yi,ya yi sallama da sauran matan nashi ya shige ɗakinshi ba tare da ya shiga gurin Hadiza ba,don ta san ita ce dashi,ƙin zuwa ta yi, dole tana fushi, shima bai neme ta ba, kuma ko washegari bai leƙa inda take ba,hakan ya ƙona zuciyarta.


Ranar Alhamis suka sauka Jigawa,niƙi-niƙi da tsaraba,ga kuma gudunmawa. Aisha ta tattala dubu biyar ɗinta zata bada, sai kuma ta ji Umma da Abba suna mata godiya,wai Uncle ɗin ta ya bada dubu hamsin, talatin nata, ishirin na shi. Tun ranar A'isha suka wuce Gumel, ita da Umma,su Abba sai gobe in sun zo ɗaurin aure. Inna Rabi ta ji daɗi sosai da wannan gudunmawa,nan A'isha ta zama tauraruwa gidan bikin kowa sai birge shi ta ke yi.


Washegari ana gama ɗaurin aure Uncle ya yi mata waya cewa ta leƙo suyi sallama shi zai wuce, lokacin suna cikin gidan maƙota, tare da su Naja da ƙawayanta. Nan ta fito ta same shi cikin mota,ta shiga ta zauna ya rufe. Sannan ya ce Beby ƙwana nawa za kiyi? Ta ce, duk sanda ka ce Uncle zan shirya in jira ka. Ya ce, to zamu yi waya? Ta ɗaga kai alamar eh,ya sa tafukan hannunshi biyu ya ɗago fuskarta. Kallo ɗaya ta mishi ta lumshe idanunta,tana jin nauyinshi. Cak numfashinta ya tsaya lokacin da taji saukar leɓunanshi kan nata leɓunan ƙamshin turaranshi ne ya doki hancinta.


A hankali ta buɗe idanunta,na shi idanun a lumshe ƙyakƙawar fuskarshi irin ta fulanin Katsina KT cike da annuri. Ba zato shima ya buɗe nashi idanun zata rufe nata, da idanu ya yi mata alamar kada ta rufe. Suka zuba ma juna ido, Kasa jurewa ya yi ya jawo ta zuwa jikinshi, sannan ta yi ajiyar zuciya tare da runtse idanunta sakamakon jinta cikin wani yanayi, muryarshi a sarƙe ya ce Beby yaushe zan zo in tafi da ke zanyi kewarki da yawa. Ta ja numfashi muryarta ƙasa-ƙasa ta ce,nace duk randa ka zo. Ya ɗagota tare da cewa shi kenan sai nazo kanta yana ƙasa don kunya ta ce, to . Ya ɗauki kuɗi daga gaban motar ya ce gashi,ta dube shi ka fa bani kuɗi jiya, ya ce ki ƙara Bebyna, sai mun yi waya? Ta ce,eh ya kuma kama tafin hannunta ya sumbaci tsakiya,tsigar jikinta ta yi yar,ta kalleshi, sannan ta fita daga motar. Ta koma ciki bayan ta ɗaga mishi hannu alamun bye-bye.


Kano ya Æ™wana,sannan washegari ya nufo K.T lokacin da ya shigo gidan tsit, wannan lamarin yana taÉ“a zuciyarshi, kullum ya shigo gida tamkar ya shigo maÆ™abarta. Ya buÉ—e É—akinshi ya shige kan kujera ya zube, sannan ya jingina da bayan kujerar,kai wannan abu yana damun Æ™wanyar shi, duk gidan abokanshi in sun shiga,ya kan ji hayaniya sa'an nan Æ´aÆ´an su kan shigo suna oyoyo, saÉ“anin gidanshi kullum shiru mata biyu a ciki amma ko T.V da wuya, ya shigo ya taras an kunna kowace tana É—aki tana Æ™wance, ya ja tsaki shi yasa in A'isha tana makaranta ko son tuno gida ba ya yi,ita kaÉ—ai ce wadda in ya kalleta ya ke jin annuri. 


Ta tare shi da ruwa mai sanyi ko zoɓon nan nata mai daɗi, ya kai hannu kan leɓunanshi yana son tuno yanda ya ji lokacin da leɓunanshi suka mannu da nata,ya sauke ajiyar zuciya, sannan yasa hannu cikin aljihu ya ciro wayarshi. Layin A'isha ya nemo lokacin tana shafa mai,ta fito wanka, tana cikin ɗakin inna Rabi, cikin uwar ɗakanta, da sauri ta ɗaga wayar.


Ta ce, "Assalamu alaikum! Uncle ina ta neman layinka network ya ƙi shiga, ya yi ɗan murmushi gani na sauka gida yanzun nan, ta ce ina ka ƙwana? Ya ce Kano mana,ta ce ka sauka lafiya?" Lafiya lau Bebyna,ki kula min da kanki. Tayi murmushi,nima haka. Ya ce ke ma me?" Ta ce, yanda ka ce,ya yi ƴar dariya, zanyi yanda ki ka ce,kafin ki dawo ki cigaba da kula dani...



#######

[12/14, 07:15] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 10*



Ta ce na manta kana da wasu masu kula da kai É—in har su biyu, ya ce "ai Beby yanda kowa ke kula dani daban, sannan in muna tare da ke ki ringa ji a zuciyarki ba kowa cikin duniyar nan daga ni sai ke,kin ji ko?" Ta ce to Uncle, ya ce yauwa Bebyna, bari na watsa ruwa, ta ce to. Suka yi sallama.


Ya yi shiru, ya kula A'isha tana matuƙar son shi, kunya ce kurum ke ɗawainiya da ita, shi yasa shima yake jin nauyin yi mata wasu abubuwan, amma yanzu ya san ya ɗauko gangarar cimma burinshi.


Bayan ya yi wanka ya fito zuwa (Dinning table)  bayan ya yi wa Uche waya kan cewa ya kawo mishi abinci, ya dubi Uche ba kowa a gidan ne? Uche ya ce Madam ta fita, amma bai ga fitar amarya ba. Zuciyarshi ta tafi ga tunanin yaushe rabon da ya samu kulawa daga Jummai? Ba zai iya tunawa ba, domin tun lokacin da ya zo mata da labarin auranshi da A'isha, ta canza har yau bai gane kanta ba. A fili ya ce, "Allah ka shirya wannan baiwa taka." Yana rufe baki tana shigowa,ta nufo shi "ka dawo ne? Wallahi nima na je gida ne na duba Innarmu." Idanu kurum ya zuba mata.


Ta ja kujera ta zauna,ba ka yarda ba ko? Ta soma magana cikin karya murya, irin ta wanda ke cikin damuwa ɗinnan, ta ce ni yanzun ai ko zan haɗiyi Alƙur'ani ka daina yarda da magana ta, duk abinda na faɗa ƙarya ka ke ɗauka, tun da ka samu yara masu jini a jika, ni ko na tsufa."


Ya ajiye cokalin hannunshi.


"Jummai don Allah ki zauna ki yi tunani, irin yanda ki ke tafiyar da gidan nan matsayinki na uwargida ya dace? Ni kaina yanda ki kayi watsi da duk lamurana,ki ka kama ƙawayan bariki masu kai mutum ga halaka,yawo tamkar an yi miki ƙauri da kan kare. Da na miki magana sai ki kawo duk maganar da ta zo bakinki ki caɓa min." Ya nuna tebur ɗin gabanshi "Look at, yanzu tafiya fa na dawo ku biyu cikin gida amma sai kuku shi ne mai kawo min abinda zan ci, shima ɗin sai da na roƙa. A ce kamar ni bani da wata ƙima cikin gidana?"


Ta ce, "To kai ne ai duk ka canza min, yanzu A'isha ce a gabanka." Ya ce,"Ita ce take ganin girmana, amma fa duk wanda na kawo na ajiye ai so ne ya kawo haka ba wai ƙi ba. Ni dukkanku ina sonku,ki kula da wani abu A'isha, yarinya ce kuma ba mazauniya ba ce,ku ko kullum muna tare da ku, amma duk da haka sai ƙorafinku ya tsaya a kanta? Kun yi mata adalci kenan? Shiru Jummai ta yi, amma a zuciyarta faɗi take yi, adalcin banza,za ku gane kuskuranku. A fili kuwa sai ta ce, to shikenan, kayi haƙuri yanzu me kake so inyi? Cike da jin daɗi ya ce, ina so ne ki canza ki koma Jumman da na sani da, kici gaba da kula da ni tare da yin riƙo da muƙaminki na uwargida sarautar mata, kada ki yarda ki yi watsi da shi, wata ta samu. A'isha ki ɗauke ta ƙanwa, bata da raini zata girmamaki, ta kuma sunkuyar da kai tare da cewa , insha Allahu zan yi yadda ka ce." Ya ce, "To na gode, sai batun yarannan su Suwaiba ya kamata su fito da miji ko ya ya ki ka gani?".


Ta ce, "Haka ne,nima fama nake da su,samarin na su duk ƴan yara babu mai shirin yin aure yanzu,ka yi musu magana da kanka,ni sun riga sun gama raina ni." Ya ce, "Shikenan, zan gan su." Sai suka ci gaba da hira tana gaya mishi cewa kayan shafanta gami da turarukanta sun ƙare, ya ce, to za ya bata ta saya. Da yake ranar ita ce dashi,ta kula da shi yanda ranshi ya gamsu cewa ta gane kurenta, ta yarda da dabarar da zasu sake tunda magani ya ƙi sai a koma kissa, don haka ko gurin ƙwanciya ta yi mishi ba zata, sannan ta sake ba shi haƙuri.


Hadiza tana ƙwance suna waya da Hajiya Lanti mahaifiyarta, tana kuka tana sanar da ita cewa, Saddiƙ ya mata wulaƙanci saboda wannan A'ishar,tun suna can ƙasar da suka tafi ya dawo don kawai ya ɗauko ta daga makaranta, sannan tunda ta dawo sai abinda ta ce.


Haka ya ɗauki ƙwanana ya kai mata, na yi magana ya fi ni fushi, yanzun da haka zancen da nake miki yau ƙwananshi biyu,ya ɗauke ta sun tafi ko'ina ni,ni ban sani ba. Sai yanzun na ganshi suna zaune da waccan tsohuwar Hajiya Jumman,ko tun yaushe ya dawo be neme ni ba? Oho."


Hajiya Lanti ta ce,da Allah ni rufe min bakinki, kin bani kunya, kishiya ki ke wa kuka, sai ka ce ba nonona ki ka sha ba? To bari ki ji in zaki dage ki dage, kuɗi za ki ƙwaƙwalo in bazama kin tsaya yin zuciya,an ce miki fada ko kishi ne silar kawo ki gidan nan? In baki sani ba, bari ki sani, na shiga na fita na kutso ki Wannan gidanne don kawai ki wawuro min dukiyarshi,ke dai dage ki samu ciki kada ki tsaya kishin banza." Hadiza ta ce, "Hajiya ni dai na fi son ki samo min taimakon da hankalinshi zai dawo kaina." Ta ce, kuɗi za ki kawo Hadiza." Ta ce, "zan kawo." Hajiya Lanti ta ce,a to, Hadiza ta ce to dama gobe ni ce da girki,in sauke kenan in daina fushin?.


Lanti ta ja dogon tsaki, "in ba iskanci ba dama ina ke ina fushi? Sauke ki kuma bashi haƙuri yaƙi ɗan zanba ne Hadiza,kin ji ko?" Ta ce, "To Hajiya sai kin zo."


***     ****     ****    ***


Satin A'isha biyu, Uncle ɗin ta ya yi mata waya cewa, gashi nan zuwa. Ta ce Uncle sauran fa sati ɗaya mu koma makaranta,ka bari mana sai ana sauran ƙwana uku". Ya ce, "Lallai ma Beby,waton ba kiyi missing ɗina ba ko?" Ta ce, "Nayi mana Uncle." Ya ce, "To gaya min da me ki ke tunani?" Ta ce,Da abubuwa da yawa nake tuno ka, ya ce gaya min ɗaya.


Ta yi shiru, ya ce ina jin ki mana." Ta ce, "Ka bari dai ai zan gaya maka in na dawo." Ya ce, "ke ɗin? Kin kasa gaya min yanzun a waya sai a gabana ne za ki iya? To ni bari na faɗa miki ɗaya,kina ji na? Ta ce, Eh." Ya ce, da lallausar fatarki, da kuma zazzaƙan leɓanci..." Da sauri ta kashe wayar tare da rufe fuska sai ka ce a gabanta yake. Shi ko dariya yake mata, ta kunna wayar ta tura mishi saƙon cewa "Uncle kai fa babba ne,ba ka jin kunya?" Ya duba saƙon, sai ya tura mata cewa,a cikin soyayyar ma'aurata Beby ba jin kunya wani abu ma sai in kin dawo." A ranshi ya raya cewa, bari na kashe maganar, sai ya rubuta cewa Beby shin za ki iya gaya min ya ya kike ji a duk lokacin da jikina ya haɗu da naki? Ya tura mata,aiko ya kashe magana don tana karantawa ta kashe wayar gaba ɗaya. Ta ƙwanta tana tunanin shi, Uncle tamkar zuga shi ake yi.


Umma da Abba sun yiwa A'isha nasiha a lokacin tahowarsu, Umma ta ce,"Ni dai A'isha ina ƙara yi miki nuni ne da haƙuri, musamman kasancewar ku,ku uku gidan mijinku. Ki kama kanki da bakinki, kada ki yarda ki haɗa kai da wata don kawai ki musguna ma wata,gara ace ke ake cuta ba ke kike Cutar ba. Sannan ki riƙe mijinki."


Abba ya É—ora da cewa,"ki zamo mai yi masa biyayya ki zamar masa wadda zata kai shi gidan Aljanna,ba wuta ba."


A'isha a cikin aurenki ki sa ma ranki cewa, bautar Ubangiji ki ke yi, kada ki kalli ƙyale-ƙyalen duniya da abinda ke cikin ta. Ta ce,"To Abba insha Allahu zan yi yanda ku ka ce."


Jabiru Sarkin tuƙi ya ɗauki hanya da su,yayin da suke zaune a baya suna ƴar hira. Lokacin da suka iso gida ta yi mamakin ganin Hadiza ta zo mata sannu da zuwa, cikin dakewa ta amsa,yau kam Hajiya Jummai tana gida. A'isha taje ta gaisheta, itama cikin sakin fuska ta amsa. A ran A'isha ta ce, ina ma ace har zuciyarsu, saboda gajiya A'isha ko tashi daga kan sallaya bata yi ba, bacci ya yi awon gaba da ita. A haka Uncle ɗinta ya same ta,bai tashe ta ba cak ya ɗauke ta ya ɗorata kan gado.


Hijabin kurum ya zare mata daga ita sai ɗaurin ƙirji, da alama ma wanka ta yi kafin sallar,zama ya yi ya zuba ma fuskarta idanu, komai na yarinyar yana son shi.


A hankali ya runƙufo ya sumbaci leɓunanta, sannan ya miƙe don yin shafa'i da wuturi, sannan ya zauna gaban laptop kafin lokacin da zaya ƙwanta. Ya so ƙwarai ya sami hutu da ƴar Bebynshi, amma ta gaji sai dai ya mannata a jikinshi suka ci gaba da bacci.


Washegari girkin Hadiza, da rana A'isha ta yi zoɓo don ya yi waya za ya aiko a ɗauka, Hadiza tana zaune a babban falo taga Uche ya zo ya amshi ƙwando kamar ta yi magana ta dai share.


Da yamma da ya dawo bayan ya shiga gurin Jummai, ya fito ya shiga gurin Beby, duk da cewa duk inda ya shiga lokacin shigowa gida ko lokacin fita ba ya zama, amma ya kan ɗan yi jum gurin A'isha saboda yana shan ruwa ko zoɓo.


Bayan ya fito ne ya nufi ɗakinshi kamar yadda ya saba, sai mai girki ta bi shi. Wani sabon salo wai sai Hadiza ta shigo wai ta zo (danning) inji darling don su ci abinci, kamar kar taje amma jin cewa Uncle ke kira sai ta fito. Ba shi a gurin sai Hadizan kaɗai, sai ga Hajiya Jummai,jim kaɗan shima ya fito. Ya kallesu, kowacce fuska a ɗaure in ban da A'isha wadda hankalinta ke kan T.V Hadiza ta ce, tana son ya haɗa su su dinga cin abinci tare, sai shima ya ga da hakan zata yiwu,da zai so. Don haɗin kansu yake nema ba rabuwar kansu ba. Ya yi musu sallama su suka amsa. A'isha ta ƙara da cewa sannu da fitowa." Ya ce,"yauwa Beby." Ya dubi Hadiza "Na ji daɗin wannan zaman, Allah yasa ya ɗore" duk suka ce, "Amin." Nan Hadiza aka buɗe abinci, maigidan aka soma zuba mawa, sannan ta tura ma saura plate kowa a gabanta,wai ta zuba abinda ta ke so.


A'isha ba gwanar cin abinci ba ce,don haka kawai sai ta ɗan zuba romon farfesun kazar dake gurin tasa cokali tana sha. Ya dubi plate ɗin beby wannan ne abincin? Gira ta ɗaga tare da yin murmushi, Hadiza ta ce, shi yasa baki yin ƙiba ko? Kullum kamar a hure ki ki faɗi, tana magana tana dariya, A'isha ta fahimci magana ta gaya mata da wasa,don haka ba tare da ta dube ta ba tace, "ai ƙiba ciwo ne,ke baki sani ba ne." Hajiya Jummai dai tana ji ba ta ce ƙala ba, kuma abincin da tasa sai juya cokalin take yi tana mamakin,yau ita ce zaune da kishiyoyi biyu? Abin tamkar cikin mafarki.


Shi ko sam bai ma fahimci suna jefa ma juna magana ba ne, musamman da yaga Hadiza tana fara'a ta yi maganar. Sannan A'isha bata nuna wani fushi ba. Hadiza ta ji haushin kalmar A'isha, amma bata da ta cewa, A'isha ba ta jima ba ta miƙe, Uncle ya ce, har kin ƙoshi? Ta ce, na ƙoshi Uncle." Ta dube su sai da safenku, dukkansu sun amsa ne a maƙoshi,ko mene ne yasa dukkansu suke jin zafin ta? Ta tafi ya bita da kallo, komai na Beby yana birge shi, musamman tafiyarta cikin natsuwa, tamkar mai tausayin ƙasa, wani sa'in shi kanshi sai ya dinga ganin tamkar yanga take yi. Hadiza ce ta buga cokali akan plate ya yi ƙara, sannan ya dawo daga tunanin da ya tafi, cikin ɓacin rai ta ce "ko yaushe in A'isha na guri kowa banza ne?" Ya ce "haka ki ke gani?" Ta ce, "Eh mana." Ya ce, shikenan. Ranta ya sake ɓaci, ta ce "sai ka ce wata ƴar gwal?" Bai kula ta ba, shima ya miƙe ya nufi ɗakinshi suma suka watse kowace zuciya na raɗaɗi. Washegari ma A'isha ta wuce makaranta, ta bar su suka ci gaba da neme-nemensu.


Wannan karon A'isha sun buÉ—e wuta,don daga wannan hutun sai na fita.


Hadiza dai kowane wata ana jiran a ji ciki shiga, amma shiru. Zaman su da Hajiya Jummai zama ne na ba ruwan wani da wani, sai dai ana gumawa juna ta ƙarƙashin ƙasa. Cikin haka wata ranar Lahadi maigidan nasu ya tashi da matsuwa ta buƙata, Jummai ke dashi to amma jiyan tana fashin sallah,yau kam Hadiza ce a daddafe ya kai magriba, inda so samu ne ma tunda rana ya biya buƙatarshi, ana idar da sallah ya shiga gida,kai tsaye ɗakinshi ya shiga,ya ɗauki waya ya kira layin Hadiza,sai da ta ɓata lokaci sannan ta shigo.


Ya nufe ya dafa ta, sannan ya cire ɗanƙwalin da ke kanta na shaddar da ke jikinta, doguwar riga. Abubuwan da ya soma yi mata su ne suka fahimtar da ita abinda ya ke so. Nan take mulkinta ya tashi ta ƙwace daga rungumar da ya yi mata.


"Ba ka sanin darajata sai in kana buƙata,to gaskiya nima yanzu lokacina ne, kuma ba zan yi abinda ka ke so yanzun ba." Idanunshi da suka yi jajir, ya dube ta, "Don Allah Hadiza ki bani haƙƙina, wallahi na matsu da yawa,ki min taimako.



#####

[12/14, 18:12] Ummi Tandama😇: *📗📗Page 11*




Ta sake taɓa baki dama ina da rana?" Ya ce, kada fa ki manta,duk matar da ta gujewa kiran mijinta, tana ƙwana ne cikin tsinuwar Allah da Mala'iku." Ta juya mishi ƙeya kai ka san wannan Ni ban san shi ba, ya ce in ma kuɗi ki ke so zan baki Hadiza, ya zo ya rungume ta ta baya. Ya dace a ce ina da mace fiye da ɗaya, amma ina cikin wannan bala'in?" Ta fisge mai Beby yau ina Bebyn taka? Ya ce, duk ba wannan ba ne,don Allah fa na ce. Ta ce, wallahi ni fa ba yanzun ba,yau ma ƙwata-ƙwata bana jin yi, amma tunda ka matsu goman dare ka zo sai mu yi ciniki a ɗakina kuma nima ni ke so yanda ka kewa Bebyn taka ita ƴar gwal bata bin miji sai dai ya bi ta. Ta dube shi, goma na dare ina jiranka sai ka zo da kuɗi." Ta fice abinta, ya bita da kallo yana haɗiye miyau,jin shi yake tamkar ya kama ta da ƙarfin tsiya.


Kan gadonshi ya zube rigingine mararshi har ta soma ciwo. Ya miƙe tsaye ina zan kai wannan matsalar tawa? Gaskiya kafin goma na dare zan sha wahala. Ya raya a zuciyarshi,ya kalli agogo baƙwai ma yanzu ta yi, ya janyo wayarshi.


Jabir ya kira bayan ya ɗaga ya ce,kana ina ne Jabiru? Ya amsa da cewa, ina nan gidanmu maigida,ya ce na san zan takura maka, amma in zai yiwu ina son ganinka yanzun. Ya ce,ba komai maigida gani nan zuwa. Kamar minti goma ya kira shi gani na iso maigida. Ya ce, yauwa Jabiru ina fitowa. Turare kurum ya ƙara fesawa, sai kuɗi da ya ɗauka ya saka su cikin aljihunan nashi guda biyu,ya ɗibi wayoyinshi ya fita.


Tuni Jabir ya fito da mota, suka fita titi ya É—an juyo ina zamu ne maigida? Ya ce,mu je makarantar su Beby. Da sauri ya ce "lafiya dai ko?" Ya ce,a lafiya lau." Ya ciro waya ya soma neman shugaban makarantar, bayan sun gaisa ya ce zan zo in tafi da yarinyar nan ne zuwa da safe. Mahaifiyarta ce ta zo yau kuma sammako zasuyi, Allah yasa ba matsala? Shugaban makaranta ya ce, da matsala, sai dai tunda kai ne zan iya yi maka alfarma, amma fa da safe a tabbatar da cewa ta dawo da wuri, saboda ta samu shiga aji. Alhaji SaddiÆ™ ya ce, don wannan duk ba damuwa insha Allah zata dawo da wuri, ya ce to bari in yi waya cikin makarantar.


Lokacin da suka shigo cikin makarantar, A'isha suna dawowa daga (Dinning) suna tafe suna yi wa juna ba'a irin ta ƙawaye. Samira tana ƙwaiƙwayon tafiyar A'isha.


A'isha ta yi murmushi ko da haka ni ke tafiya da sai na fi awa ban kai ko nan da masallaci ba." Amina ta ce,ba haka take yi ba,kunga yanda take yi nan. Sallamar da aka yi musu ne ta dakatar da su, mai sallamar ta ce cikinku wacece A'isha Mustapha? A'isha ta dube ta, gani nan, ta ƙara da cewa lafiya? Lafiya lau,kina da visitor. Ta dafa ƙirji,ni kuwa? Ta ce ba ke ce A'isha Mustapha ba?" Amina ta ce ki je ki gani mana. Cikin fargaba ta ce,na bani ni A'isha,wa zai zo gurina da daren nan? Samira ta ce, Uncle ɗin fa? Cikin damuwa A'isha ta ce, Uncle ya zo jiya fa. Suka ce muje mu raka ki, kasancewar kowane gurin gal yake da haske,tamkar rana. Tun kafin su ƙarasa ta ce Uncle ne don ta hango motar sannan ga Jabiru a tsaye, ta ce ina zaton ba lafiya ba,ban ga Uncle ɗin ba Samira,Suka ce to bari mu koma sai kin dawo ma ji ko mene ne. Ta ce to.


Tana isa gurin cikin firgici ta ce,"Jabiru lafiya, ina Uncle ɗina?" Ga zatonta wani abu ne ya sami Uncle ɗin. Jabir ya nuna mata mota, ya ce yana ciki, shiga." Ta kai hannu zata buɗe bayan motar,sai taga an buɗe mata, daga ciki ta a shiga da sauri lokacin ne kuma wutar motar ta haska, ta kalleshi "Uncle lafiya?" Ya jawo hannunta lafiya Beby, amma ba lau ba. Ta zaro idanu me ya faru? Abbana ne ko ummat? Ya ce, a'a ni ne. Ta soma leƙa ƙafafuwanshi me ya faru da kai? Ganin yanda ta ruɗe kuma jawota jikinshi taimako nazo nema gurinki, domin yanzun duk duniya kece kurum ki ka rage min da zaki iya yi min wannan taimakon, ta ce mene ne shi? Ya ce, zan gaya miki in har zaki taimaka min,ta ce zan maka shi, matsawar ba zan shiga haƙƙin Ubangiji ba." Ya ce, na gode Beby, bari muje. Ya danna wani guri Jabiru ya zo ya shiga motar yaja suka fita daga cikin makarantar suna hawa babban titi ya ce, Jabiru ya samu guri ya yi parking Uncle ya saka hannu cikin aljihun wandonshi ya ciro kuɗi ba tare da ya ƙirga ba,ya miƙa mishi.


"Jabiru gashi ka isa gida kayi haÆ™uri zan bi wani guri ne." Jabiru ya ce,a haba ba komai sai da safe kenan." Ya fita Uncle ya koma gurin zaman direba ya ce dawo nan Beby, ta koma har yanzun kanta a daure bata fahimci me yake nufi ba. Tun da ta ga irin tuÆ™in da yake yi ta fahimci yana cikin wani yanayi ne, don gudu yake yi da su sosai, cikin zuciyarta,to ni A'isha lafiyar Uncle Æ™alau kuwa? Ina zai kai ni ne? Tana cikin wannan tunanin ne ta ji sun tsaya sai ta gansu sun shiga wani Æ™aton (gate), ga motoci cike a gurin. 


Ya yi parking ya fita da sauri bari in zo. Ta dubi ginin sai taga an rubuta (Guest Inn) ya dawo zo mu je. Cikin tsoro ta ce,"Uncle me zamu yi a Hotal?" Bai bata amsa ba, ya kamo hannunta zo mu je. Suka nufi ciki,a zuciyarta ta ce, to ko dai Uncle za ya sai da ni ne? Ko dai gaske ne yana yankan kai É—in ya É“oye min ne?".


Ƙofar wani ɗaki suka tsaya,yasa makulli ya buɗe, suka shiga ya maida ya rufe. Ta kalli fuskarshi duk ya canza, idanunshi sun kaɗai sun yi jajir,ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un." Cikin ranta,ganin ta firgita da yawa ya kama hannunta suka zauna gefen gado, lokacin mararshi ta ƙulle tam,a cikin sarƙewar murya yake cewa,taimakona za ki yi Beby,don girman Allah. Tun jiya na shiga wannan halin, wata muguwar sha'awa ta kama ni, in ban fitar da ita ba sai ina jin kamar zan mutu, Jummai tana fashin sallah, Hadiza ta kafa min doka cewa sai ƙarfe goman dare sannan sai na bata kuɗi, duk da cewa haƙƙina ne, kuma yau itace da ƙwana da ni,Beby ban taɓa zina ba ban san yanda zan nemi matan banza ba, shi yasa na ce ke ce kawai zaki taimaka min, don komai zai iya faruwa da ni in har na bar abin nan ban fitar dashi ba.


Ya cire mata hijabi yana cewa, don Allah Beby,kin yarda?" Cikin tsoro ta ɗaga kai, sannan muryarta na rawa ta ce,zan yi fitsari ya miƙe da sauri ya nufi ƙofar da yake zaton banɗaki ne,ya ce zo kiyi, bayan ta fito,a tsorace take ta tsaya tana yarfa hannu irin na tsorata ɗin nan dan ganin ya raba jikinshi da tufafin shi, ya ce kada ki ƙi yardar min Beby,zo nan, hawaye ya soma zubo mata tana cewa, to,to da zafi? Ya ce,ba zafi zo mana. Ya nufo ta ta bi can gefen tana kuka ya dawo ya zauna bakin gado ya dafe kanshi yana kiran sunayen Allah. Ta haɗa yatsanta na tsakiya da babban tana ta buga su cikin tsoro,tana cizon leɓenta ta zo kusa dashi ta ce gani Uncle, jikinshi yana wani irin rawa ya kamata ta ya zauna.


A hankali ya raba ta da Uniform ɗin da ke jikinta, ya ƙwantar da ita. Sannan wasu abubuwa suka ci gaba da biyo baya, wanda shi kanshi ba zai ce daɗi ya ji ba,don ciwo sosai mararshi ke yi lokacin da abin zai fita. Ya yin da ita kuma ta jure ta daure sai ta gama duk yanda take hango wahalar bata kai nan ba, sai dai fa tasha wuya,kusan awa ɗaya yana fama kafin ya samu gurin sauke wannan aikin da ya tasa mishi. Kusan minti biyar ya kasa ko motsi, da ƙyar ya mirgina gefe. Itama shiru ta ƙwanta, Uncle ya ce mata,ba zafi gashi ita dai ta ji zafin. Muryarshi ƙasa-ƙasa ya ce, Beby-beby, ta ce Um,ya ce na gode Allah ya saka miki da alheri, rufe ni sanyi nake ji zaki iya tashi? Ta yi ƙarfin hali ta yunƙura ta rufa mishi bargo, ita kuma ta rufa da zanin gado.


Ta ƙwanta shiru tana tunanin dama haka ake yi? In ko haka ne waɗanda suke cewa aure da daɗi ba su gane ba,bata ƙara tsinkewa da lamarin ba sai da gadon da suke ƙwance ya soma rawa da sauri ta juyo gurin da yake ƙwance wata irin rawar sanyi Uncle ke yi. Ta ce, Uncle ta tsorata tuni ta tashi zaune dama haka ka ke yi? Ya ce, "a'a" ta ce, yanzun ya ya za'ayi? Ya ce je kiyi wanka,kin iya?" Ta ce a'a ya ce,kin iya na haila? Ta ce,eh, ya ce to irin ɗaya ne,niyya ce banbanci,kin ji in kin sa kaya sai ki kira min Likitana. Da ƙyar take tafiya itama yana kallonta tausayinta ya ke ji. Ta kunna ruwan zafi ta gasa jikinta ta yo wankan sannan ta maida kayanta. Ya ce,ta ɗau wayar zata ga Doctor Isma'il ta kira shi ta ce ya zo gidan saukar baƙi na Daɗin Kowa a nan zaya same shi, haka ko kusan minti ashirin da biyar don da ƴar tazara tsakanin da gidan likitan. Ya kira ta gaya mishi lambar ɗakin. Bayan ya yi wa ma'aikata bayani sai aka rako shi har ɗakin saboda tabbatar da batun Likitan.


Uncle bai ɓoye wa Likitan komai ba, ya faɗa mishi sanadin zazzaɓin. Likitan ya ce,yana ganin ya tara sha'awa ne shine dalili,ya bashi magunguna. Uncle ya ce itama ka bata magani don (V) ce. Kunya duk ta cika A'isha,Likitan ya ce,"To" maganin kashe raɗaɗi da na rage gajiya ya bata, Likitan ya ce su ƙwanta su samu bacci, sannan ya tafi. Suka ƙwanta bayan ta kashe dukkan wayoyinshi.


Tana ƙwance take tunanin abubuwan da suka faru yanzun nan, abinda ya fi bata mamaki, duk da halin da Uncle yake ciki bai hana shi karanta addu'ar saduwa da iyali ba.


Ya ɗauki kanta ya ɗora saman ƙirjinshi,a hankali ya ce, "Na wahalar da ke ko Beby?" Ta girgiza kai, alamar a'a, sannan ta ce Uncle ka yi bacci ka ga fa ka sha magani. Ya ce, To na gode, Allah ya saka miki da aljanna A'isha." A haka bacci ya yi gaba da su.


Hadiza kuwa tana komawa ɗaki,ta shiga murna ta san ko nawa ta ce zai bata yadda ya matsu ɗin nan,ai dubu ɗari zata ce,in ba zai bada ba ya haƙura. Wata zuciyar ta ce, to in ya haƙura ɗin fa? Gara dai ki ce hamsit, ta ce kai bazan rage ko sisi ba. In bai yarda ba kuwa ba dai guri ɗaya zamu ƙwana ba? Sai nayi sanadin da zai kasa haƙurin, kafin goma ta yi duk shirin da tasan zata ƙara jan hankalinshi, amma har goma da rabi bai shigo ba. Sai ta yanke shawarar ta bishi kada ya yi wannan fushin nashi tayi asarar kuɗin da zata samu.


Ta murɗa ƙofar a datse take ta buga shiru, har sha biyu tana sintiri tsakanin ɗakinshi da nata,daga ƙarshe ta koma neman layinshi duk a kashe suke. Ta zauna kan gado cike da cizon yatsa, yanzun haka yana can zai kai ma wata karuwa a banza,a fili ta ce,kai ni ma banza ce wallahi,na tsaya sokwanci gashi abinda ya same ni babu kuɗin,babu ƙwanan girkin. Haka ta yi ta juyi ita ɗaya har gari ya waye.


Shidda ya farka, zazzaɓin ya sauka illa jikinshi da yake ji babu ƙwari sosai. Motsin shi ne ya farkar da A'isha tana buɗe idanu sai suka haɗa ido, da sauri ta sa hannu ta rufe fuskarta. Wata matsananciyar kunyarshi take ji,ya yi murmushi "Beby yanzun ai babu batun kunya." Ya tashi yaje ya yi wanka tare da yin alwala, ya yi sallah harda Isha'in,yana zaune yana Istigfari, ta miƙe tana kare fuska ta nufi bayin ta yi wanka sannan ta yi alwala zuwa ta yi itama ta tada sallah, jikinta ba ya mata ciwo, sai dai tafiyar ta ce in tana yi sai ta ɗan ringa jin zafi don haka sai tana ɗan buɗe ƙafa kaɗan.


A bayan shi ta zauna,don haka tana jin irin addu'ar da Uncle ya ke mata,sai ta samu kanta da yin alfaharin kasancewar ta mai kamun kai. Ta kawo budurcinta ga mijinta, gashi yana mata addu'a, Allah ya haɗa ta da dukkan rahamarshi, kuma ya albarkace shi da zuriya ta tsatsonta. A zuciyarta ta ce ina ma duk wata ƴa mace zata nemarwa kanta wannan mutuncin gurin mijinta? Kun san girman addu'ar miji a kan matarshi? Ya juyo yana dubanta, ita kuma kanta yana ƙasa tana wasa da yatsun ƙafarta,ya ce "Beby" ba tare da ta dube shi ba,ta ce "Na'am" Ya ce,me zaki ci? Ta ce,ba komai,da dai zaka maidani makaranta saboda yau zamu fara jarabawa. Ya ce, to amma kin ci wani abu ko? Ko ruwan tea. Ta ce, to, nan ya yi waya aka kawo musu karin kumallo, lokacin baƙwai saura suka ɗan sha ita dai ta kasa kallonshi. Sannan suka miƙe, ya sake rungume ta yana yi mata godiya har ta soma tambayar kanta cewa,shin Uncle ya manta cewa ita halaliyarsa ce,zai ta yi mata godiya haka? Suka fito suka shiga mota ya kai ta har ciki,yana tsayawa ta fita, ta zo saitin shi ba tare da ta dube shi ba,don kunya ta ce Uncle Allah ya ƙara sauƙi, ya ce amin ya miƙo mata kuɗi "riƙe waɗannan." Ta girgiza kai "Ranar sati da kazo ka bani kuɗi,ko taɓa su ban yi ba." Ya ce,"to ba ki son komai?".



######

[12/14, 21:49] Ummi Tandama😇: *📗📗Page 12*




Ta É—aga kai,ya ce, to je kiyi shirin shiga aji." Har zata wuce,ya ce "Af,na manta Beby,me za ki gaya wa abokananki? Ta É—an saci kallonshi, gida zan ce musu naje,ya ce yauwa kada ki gaya musu komai fa,kin ga wannan sirrinmu ne ni da ke, Allah ya tsine ma wanda ya tona kin ji." Ta É—aga kai, ya ce to bye-bye,ta É—aga mishi hannu sannan ta tafi. Kallo ya bita dashi. 


Tafiyarta ta canza,ya ji tausayinta sosai, ya ja mota. A zuciyarshi kuwa ya ajiye A'isha cikin wani ma'adani a yanzun yana ganin duk matan duniya in ya cire mahaifiyarshi to babu kamarta, insha Allah zai riƙe amanarta.


***     ****    ****


Gidan shiru kamar ko yaushe, ya shiga ya ƙwanta duk da tarin aikin da ke jiranshi a Office. Wasa-wasa zazzaɓi ya dawo. Matan gidan ba su san yana ciki ba,sai da Likita ya zo bayan ya yi mishi waya cewa ya same shi gida.


Safiya ya samu a falo ya ce mata ya zo duba maigidan ne,ta ce baya nan. Likita ya ce, bincika dai shi ne ya yi min waya."


Gurin Hajiya Jummai ta je, ta ce "Hajiya Doctor ɗin Alhaji ne,wai ya zo duba shi." Ta ce, "Ce masa aka yi Alhaji ba shi da lafiya?" Ta ce, oho. Hajiya Jummai ta fito suka gaisa, tana mishi wannan kallon rainin. Ya ce, Maigidan na zo dubawa,ta ce to ban yi zaton ya ƙwana gidan ba ma."


Doctor ya ciro waya ya kira layin Alhaji,ya ce "Gani na zo an ce ba ka gida." Ya ce, "Doctor shigo ɗakina ina ciki, sai ka baƙo.?"


Hajiya Jummai ta ga Likitan ya yi ciki, ta bi shi tana faɗin ba fa ya nan,bai ko saurare ta ba,ya shige. Itama ta bishi, ganin maigidan cikin bargo yana rawar sanyi ya sa tayi turus nan dai likitan ya duba shi. Ashe wasa farin girki, jiki ya yi jiki dole ya koma asibiti, kasancewar bai taɓa ciwo irin haka ba, sai hankalin iyayanshi ya tashi, musamman Alhajinmu, wanda ya ke ganin nan duniya ba shi da tamkar Abubakar,ɗan shi guda namiji tamkar da dubu.


Su Hadiza da Hajiya Jummai,ana ta zirya. Hajiya Jummai ba ta son ya mutu ba tare da ya saki su Hadiza ba, ita kuma Hadiza nata ra'ayin bata son ya mutu ba tare da ta yi ciki ba,don haka suke ta fatan ya samu sauƙi.


Nafisa ta dubi Fatima ta ce "Anty Fati ko dai za'a je a zo da A'isha ta ganshi ne?"


Hajiya Jummai da ke zaune kan shimfiÉ—a ta ce, "In an zo da ita iyaka fa ta mishi sannu, zata cire mishi ne?" Fatima ta ce, "Ai kuma sannu da daÉ—i, duk yana jin su dai ya farka daga bacci basu zaci ya farka ba. Ya ce, "Nafisa kada ku sanar da ita, Beby tana da ruÉ—ewa, gashi suna jarabawa ne, suka ce to.


Hajiya Jummai dai ƙala bata ce ba, sai baki da ta taɓa.


Satin shi ɗaya aka sallame shi,ya ji sauƙi sosai,damuwashi wannan satin duk bai ga Beby ba, tunda suka rabu kowa da jinya bai san halin da take ciki ba. Yana son ya je amma kar ya karya musu doka da yawa,don haka sai ya haƙura sai wani satin.


Ita kam A'isha kullum da zazzaÉ“i take Æ™wana, amma ta cije ko  su Samira bata bari sun gane ba, illa dai sun kula bata cika walwala ba,tun daga ranar da aka zo aka kaita gida ta Æ™wana da ta dawo ta ce musu mahaifinta ne yazo za ya yi sammakon tafiya shi ne aka zo aka kaita. Komai A'isha ta ci sai amai, tun tana yi a É“oye har su Samira suka gane. Sai ta ce musu haka take yi in shawara ta kama ta, sun yarda a kan haka suka ce ta je Clinic ta ce musu a'a,na asibiti ba ya mata in ciwon ya tashi sai dai in na gida,tana jiran Uncle É—inta ya zo sai ta faÉ—a mishi ya samu ya amso mata,duk da yarintarta ta fahimci cewa tana da shigar ciki, domin lokacin al'adarta ya wuce da Æ™wana shida, sannan (Science class) take duk an yi musu bayanin wannan. Sannan tana zuwa Clinic zasu gane cewa tana da shigar ciki.


Abinda ya dinga bata mamaki in ta tuna da haka ake cikin daga zuwa É—aya?


Ranar Asabar tana ƙwance laga-laga a kan gadonta wayewar gari amanta na huɗu kenan,su Samira sun sata a gaba kan cewa sai fa ta tashi sun je Clinic ita kuma ta ce su jira ta san zuwa rana Uncle ɗin ta zai zo sai ko ga ƴar aike wai tazo inji Uncle ɗin ta.


Haka ta miƙe tana bin bango,su Samira sun so su riƙe ta amma sai ta ce su barshi. Yana jingine jikin motarshi shi da Jabir suna magana, sai ya hango ta tana haɗa hanya, da sauri ya nufo ta yana faɗin "Beby lafiya kuwa?" Ya riƙe ta zuwa bayan mota, ya ƙwantar ya shiga yana tambayarta a ruɗe,ta ce tun ranar nan ban ƙara lafiya ba, kullum ciwo. Ya ce innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un nima fa satina ɗaya ƙwance a gadon asibiti." Ta ɗago kai ta dube shi, duk ya rame ta ce,sannu! Shi ne ba'a faɗa min ba?" Ya ce ai ni na hana, ashe kema kina nan kina fama,kin je Clinic?" Ta ce a'a,ya ce saboda me? Ta ce,ni bana son allura ne kawai, ya ce to yanzu haka za ki zauna? Ta ce, saura paper biyu mu gama jarabawa in na dawo gida sai mu je asibiti. In na je na nan ƙila su ƙwantar da ni,ba zan samu yin sauran papers ɗin ba. Ya tsura mata idanu ko dai mutuwa yarinyar zata yi? Shi yasa fa duk shekarun nan ya ƙi ya kusance ta don yana tsoran haka.


Ya ce, Beby ni dai da mun je, kin gan ki kuwa? Ta ce gobe da jibi ne zamu yi sauran papers ɗin,in ya so sai ka zo ranar Laraba ka musu bayani sai mu tafi. Ya ce,ni barinki cikin wannan halin shi ne matsala ta, ta ce kada ka damu,satina fa biyu cikin wannan halin, to dan ƙwana biyu? Ya yi shiru yana kallonta,can ya ce shi kenan zan zo labarar. Ta yunƙura ta tashi zaune tana ƙarfin hali dan kada ya ƙi yarda. Ta fito ta ce,sai kazo ya ce,to, yabita da kallo shi dai kawai don dai taƙi ne.


Cikin mota suna tafiya tunani yake,ko dai wani ciwon ne ya ɗurawa ƴar mutane? To shi wannan wace irin ƙaddara ce? Allah ka min da sauƙi, cikin ƙwana biyun ta koɗu,ta dai samu ta zana jarabawar, amma fa cikin jin jiki.


Tun misalin baƙwai ya isa makarantar,kai tsaye gurin (P.C) ɗin ya nufa, ya tambaya ko yaran sun gama zana jarabawa? (P.C) ya tabbatar mishi da cewa sun gama. Ya ce, to dama ya zo ne ya tafi da A'isha, saboda ba ta da lafiya, kuma gashi bata son shan magani dole sai an sa idanu kanta (P.C) ya ce,babu matsala,nan ya ce bari ya yi waya da waɗanda suka dace.


Aisha tana ƙwance saƙon ya zo mata, cewa an zo ɗaukar ta, kasa tashi ma ta yi, sai da taimakon su Samira sannan ta tashi ta riƙe ta suka je,ya tare su. Ko lokacin amai take ji, zuciyarta tana tashi ya kamata cikin mota ya saka ta,su Samira ne suka ƙwaso mata kayan,ya yi musu ihsani, suka yi sallama tare da fatan samun lafiya gare ta, sannan ya shiga mota.


Suna cikin tafiya ta kasa jurewa,nan fa amai ya zo mata ta ko dinga sheƙa shi tamkar ranta zai fita, daga nan asibiti suka nufa. Cikin sauri ya shiga ya yi wa Nurse's magana,gadon ɗaukar marasa lafiya suka ɗauketa a kai, har lokacin amai take zabgawa. Uncle ɗin kuwa duk ya gama ruɗewa, ya kira Alhajinshi yana sanar dashi cewa A'isha babu lafiya, kuma babu yanda take ma'ana, jiki ya yi tsanani,ya kira Nafisa da Fatima har da Sadiya, kafin ka ce haka kuwa,tuni Nafisa ta iso,su Fatima suma sun zo, Alhajinmu shima sai gashi ya ce me ya same ta? Uncle ya ce, Likita na tare da ita.


Jim kaɗan Likitan ya fito Nurse's na turo ta a gado. Nan suka bi su zuwa ɗakin da aka ƙwantar da ita, ruwa aka ɗaura mata tare da yin allurori cikin ruwan,nan da nan ta soma bacci. Likitan yana fitowa Alhajinmu ya bishi zuwa Ofis, shi da Uncle ɗin. Likitan ya ce,su ƙwantar da hankalinsu, insha Allah komai zai zo da sauƙi, yanzun dai zasu yi mata gwaje-gwaje daban-daban, tunda bata cikin hayyacinta da zata iya musu bayani, sannan sun ce daga makaranta take. Suka ce to bayan sun fito ne Alhajinmu ya yiwa ɗan nashi nuni da ya ƙwantar da hankalinshi ya san cewa rayuwa da mutuwa duk daga Allah ne.


Itama Hajiyarmu ta damu taga wani daga cikinsu don taji labarin jikin,da ta gaji sai ta kira Nafisa ta ce,wai shin Nafisa ya ya jikin yarinyar nan? Nafisa ta ce, jiki kam tana jin shi Hajiyarmu, yanzun dai ana mata ƙarin ruwa, sannan sun ɗibi jininta za su yi mata gwaji. Ta ce, to Allah ya sawwaƙe


Shi kam Uncle yana nan duk inda Likitan yabi yana biye dashi,don son sanin matsalan A'isha,bai ga wasu cututtuka ba, amma ya fi zaton ciki ne,don haka sai ya shiga wannan gwajin. Sun tafi sallar azahar, Likitan ya shigo yana cewa, ina maigidanta? Fatima ta ce, ya je sallah, ya ce in ya dawo yana neman shi a Ofis, suka ce to.


Nafisa ta ce,ni matan Bros suna bani mamaki,dubi har yanzu babu wadda ta leƙo" Fatima ta ce ,ai dama ke kina sa ran zuwansu ne? Gaya min cikinsu wace ce ta kirki? Hadizan Hajiya Lanti ko Hajiya Jummai? Ni dai na ce Allah yasa ba wani ciwon suka sakawa ƴar mutane ba tunda dukkan su ba wadda ta dogara ga Allah."


Sadiya ta ce, "Shi yasa yanda na tsani mutuwa ta haka na tsani auren shi da Hadiza,kina ganin yanda Hajiya Lanti mahaifiyarta ta ke juya Baba Sunusi,sai ka ce remote,shima Bros É—in suna samun guri haka za su maida shi."


Fatima ta ce, "Insha Allahu ba zasu samu haka ba,ta Allah ba tasu ba."


Ya shigo da sallama, ya dubi gadon da A'isha ke ƙwance, sannan ya ce har yanzu bata farka ba? Suka ce eh, Likitan ya ce ma in ka dawo ka je." Ya ce, to kun yi sallah?" Suka ce, yanzun dai zamu yi.


Fuskar Likitan cike fara'a yake kallon Alhaji Saddiƙ, ya miƙa mishi hannu.


"Ina matuƙar taya ka murnar cewa, matarka tana ɗauke da ciki ƙwana goma sha baƙwai."


Idanu Uncle ya tsura ma Likitan, jin zancan ya yi tamkar cikin mafarki. Likitan ya jijjina mishi hannu.


"Ranka ya daÉ—e wannan shi ne sakamakon da muka gani cikin gwaje-gwajen da muka yi."


Cikin wani farin ciki mai tsanani ya rungume Likitan yana cewa, "Na gode, Allah alhamdulillahi" Da sauri ya fita ya nufi ɗakin da A'isha take kwance, har yana cin tuntuɓe. Ya shiga ko ta kan Nafisa bai bi ba ya isa gaban gadon ya tsaya, idanu ya zuba ma A'isha.


Ya kama hannunta ya riƙe gam,a zuciyarshi yana raya dama ɗan shi ne zai fita ranar? Ya gode Allah da bai sa yaba Hadiza ba, ya gode Allah da ya tsareshi bai zama mazinaci ba,bare ya ba wata karuwa. Cikin kiɗima Nafisa ta girgiza shi.


"Brother lafiya ka ke hawaye?"


Sam bai ma san yana hawaye ba.


Fatima ta fito da gudu daga banɗaki, tana cewa "Me ya faru na ji kin ce yana kuka?" Sadiya kam tana sallah, amma duk hankalinta na gurin,sai kawai gani suka yi ya juyo ya rungume Nafisa yana magana cikin rawar murya,tamkar kuka zai ƙwace mishi. Yana cewa, "Sister A'isha tana ɗauke da cikina!!"


Duk su ukun har da mai sallar suka furta cewa ciki? Ya yi ajiyar zuciya, ashe zan ga ɗan kaina? Murna suka shiga yi tare da yi wa Allah godiya. Nan suka shiga kiran iyayansu. Nafisa ce ta yi dacen kiran Hajiyarmu tana ɗagawa Nafisa ta ce Hajiyarmu A'isha na da ciki,Bros zai samu ɗa." Kalmar ta doki zuciyar Hajiyarmu, har ta kasa magana. Nafisa ta ce kin ji me na ce?" Hajiyarmu ta ce, "Allah ya inganta, ya bata lafiya." Ta ce,"Amin" Nafisa tana kashe wayar, Hajiyarmu ta miƙe ta ɗauro alwala ta zo ta soma nuna murnarta gurin Ubangiji, lokacin da take godiya ga Allah har da hawayen ta.


Uncle shi ne ya sanar da Alhajinmu wanda shima ya katse duk harkokin da yake yi a wannan lokacin ya sake nufo asibiti. Lokacin da ya iso, Uncle ya koma masallaci, inda ya zube cikin sujjada yana yi wa Allah godiya. Lokacin da ya dawo ɗakin su Alhajinmu, suna cikin ɗakin har da Likitan. Alhajinmu nan take ya yi wa Likitan ƙyautar mota, ya ce yaje gidan motocinsa da ke kan titin Isa Kaita ya zaɓi duk wadda yake ganin ta mishi. Kai yau kam duk wanda ke da dangantaka da su, sai da ya san A'isha na da ciki.


"Kai Nafisa, har da ƙawayanta ta ringa kira tana shaida musu, cikin ne da ita. Amma yanda suke murnar na A'isha abin da mamaki...



######

[12/15, 19:45] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 13*




Lokacin da Alhajinmu ya iso gida har lokacin Hajiyarmu tana zaune kan sallaya amma yanzun tana jan carbi ne, cikin tsokana ya ce ke ban ganki a asibiti ba, tunda na san dai kin samu labarin matar É—an naki tana da ciki."


Ta sunkuyar da kai, "Me zan je in musu? Na san duk Æ´an'uwanshi suna can." Ya zauna, "Naga fuskarki, ta nuna murnarki, tayi É—an murmushi kana son jin ta bakina ne kawai,to na ce Allah ya inganta mishi, shikenan? Ya yi dariya na sani duk cikin Æ´aÆ´aki kin fi son Abubakar,don haka yau babu wanda ya kai ki murna. Ta yi É—an murmushi.


"Gaskiya ka faɗa." Ya sheƙe da dariya," Ashe dai kina son shi ki ke share shi? To yau zan gaya mishi ya daina min mita kan cewa shi baki son shi,shiru ta yi mishi.


Ku tambaye ni lokacin da ake wannan murnar ina su Hajiya Jummai da Hadiza suke? To sai in ce muku suna gida, labarin ya ishe Hadiza ne ta bakin mahaifiyarta wadda Alhaji Sunusi maigidanta wanda Alhajinmu ya yi mishi waya ya sanar dashi, cikin murna ya zo gidanshi ya sanar. Nan fa Hajiya Lanti ta ji tamkar labari mutuwarta ya zo mata dashi. Nan ta kira Æ´arta tana son jin gaskiyar lamarin.


Haƙiƙa Hadiza ta ruɗe da jin wannan labarin, sai dai ta ce wa Hajiya Lantin tana shakka domin a saninta dai A'isha tana makaranta. Hajiya Lanti ta ce,an ce tana asibiti. Hadiza ta ce, zan dai bincika,nan take ta ɗauki waya ta kira maigidan.


"Assalamu alaikum,darling kana ina ne?" Ta tambaye shi.


Cikin murna ya ce, "muna asibiti da A'isha,na manta ban sanar da ku ba, A'isha tana nan asibiti."


"Me ya same ta?"


"Ciki ne." Ya bata amsa a taƙaice.


Ya kira layin Jummai lokacin tana lissafa kuɗin da zata kai ma wasu malamai guda biyu, ɗayan yana mata aiki kan Hadiza, ɗaya kuma kan A'isha. Ta ɗaga wayar cikin raha ta ce, "Maigidana na kaina." Ya ce, "Jummai yau dai Allah ya amshi addu'armu." Ta ce, "Ta me fa?" Ya ce,"A'isha tana da ciki." Da sauri ta miƙe tsaye, "Ci me?" Ya ce,"Ciki." Ta yi ƙoƙari ta saisaita numfashinta,"kai Allah mun gode maka,kuna asibitin ne? Ya ce eh,ta ce gani nan zuwa,ya ce dama na sani Jummai za ki yi murna,ta ce ai faɗa ma ɓata baki. Ya kashe wayar.


Jikinta har rawa yake wajen neman number Hajiya Karima,daƙyer ta samu taga number saboda fita hayyacinta da ta yi,tana ɗauka ta fashe mata da kuka "Na shiga uku!, Shikenan tawa ta same ni,ni nasan tawa ta ƙare."


Hajiya Kari ta ce,"Sakinki aka yi? Ta ce,wane saki ba gara a sake ni É—in ba da wannan takaici! A'isha fa ke da ciki."  "Ciki?" Inji Kari, Hajiya Jummai ta ce "Ciki kuwa," Hajiya Kari ta ce, to share hawayenki,ba sai mun barshi ba, sannan zai zo duniya,tankaÉ—ar da É—an iska zamu yi ya bi sokawe kawai,ai haka zai zauna yanda baki haihu ba babu shegiyar da zata haifa. Ki shirya zama guri É—aya a tsautsayine. Hajiya Jummai ta ce, to sai na ganki Aminiya ta, mai maganin kuka na."


Suna gama wayar,ta zabga tagumi a yanzun babu abinda ya fi dacewa face ta bar batun fitarsu, ta koma kan batun cikin nan. Don haka ta soma tattara kuÉ—in guri É—aya,tana yi tana magana ita kaÉ—ai cewa take yo in ma ta fitar da ita alhali ga ciki ai nayi ta banza, tunda É—an shi da ita zai zo duniya. Kaji masu ja da ikon Allah.


A'isha sai da tayi baccin wajen awa biyu sannan ta farka,Uncle dake zaune kujerar gefen gadon ya yi tagumi yana kallon ta,jin hannunta a riƙe ne yasa ta buɗe ido ta kalli ko ina, sannan ta kai dubanta ga Uncle ɗinta wanda ya ke kallonta cike da murmushi, ta ce har yanzun muna asibitin? Ya ce,eh muna asibiti, ta ce Uncle baka je Ofis ba? Ya ce, Ofis sai da lafiya ai Beby. Ta kalli ƙarin ruwan suna min ƙarin ruwa ne? Ya ce eh,ta ce gashi ina son inyi sallah. Ya ce za kiyi Beby,bari ki ɗan ƙara jin ƙarfi. Ta ce to. Ya ƙara matsowa kusa da ita,"kin san ciwon da ke damunki? Ta ce, a'a ya saka hannunshi cikin tafin hannunta ya ce "Beby ashe ɗana ne nake ta neman inda zan saka na sha wuya, Allah ya dube ni da rahamarshi ya sa ni na ɗauko ki tun daga makaranta na saka cikin mahaifarki. Beby don murna yau ji nake tamkar yau aka haife ni, nima zan zama uba,kina ɗauke da cikina ƙwana goma sha baƙwai." Ta juyar da fuskarta gefe don kunya.


Ya miƙe tsaye "Beby kina jin kunya ne? Yana magana yana ƙoƙarin leƙa fuskarta. Tasa hannu ta rufe fuskar, ya ce a'a Beby kada ki cuci ɗanmu,kada ki mishi yanda Hajiyarmu ta yi mini har yau na kasa yarda cewa tana sona kin ji? Ta ɗaga kai alamar eh, amma kanta na ta can gefen, ya ce to gaya min ki yi murna? Ta kuma ɗaga kai,kina son Bebyn? Ta kuma ɗaga kanta, ya ce na gode. Bari na ce ma Likita kin farka,bai ce dasu Nafisa ta farka ba,ya nufi gurin Likitan tare suka shigo da Likitan ya duba ta tare da tambayar inda ke yi mata ciwo,ta ce babu, sai dai jikinta Duk a gajiye,sannan bakinta babu daɗi, kuma tana jin yinwa sai dai ta san in ta ci zata yi amai ne.


Likitan ya ce, yanzun dai faɗa mana me ki ke marmari? Ta yi shiru tana tunani,can ta ce tuwo da miyar kuɓewa,tuwon garin masara. Uncle ya ce,to bari na sanar da Nafisa ta je tayo miki yanzun kin ji? Ta ɗaga kai. Likitan ya ce ya kamata dai ta sha ko ruwan tea ne haka saboda cikinta ya warware.


A'isha ta girgiza kai, tare da cewa,ba zan sha ba,in na sha tea bakina tsami yake yi, Likitan ya ce za ki jira har a kawo tuwon? Ta ce eh, Uncle suka fito da Likita. Lokacin ne ya ce musu ta farka suka shigo.


Nafisa tana cewa,"Maman biyu, Maman biyu" A'isha ta rufe fuska, Uncle ya shiga ya dubi Nafisa "Sister ki je ki yo mata tuwon garin masara da miyar kuɓewa,ya dubi Beby ɗin ya ce, wace irin kuɓewa? Ta ce ɗanye. Nafisa ta suri jakarta,ta ce bari naje na cika aikin Bebynmu. Ta fita tana cewa, sai na bi ta gidan Hajiyarmu na amshi garin,don ba ni dashi a gidana.


***.     ****        ****


Hajiya Jummai suka yi sallama ita da Hajiya Kari,ɗakin cike da dangin maigidan nata aka amsa musu. Ta shigo tana cewa, sannunku, sannunku fa. Ina A'ishan? Suka ce ga ta nan a ƙwance. Hajiya Kari ta ce sannu kin ji, Allah ya inganta miki. Hajiya Jummai ta ɗora hannunta a goshin A'isha tana cewa Allah mun gode maka, ashe mu ma zamu ga ɗanmu? A'isha ko jin hannun ta yi tamkar an ɗora mata dutse, ita tun fil'azal in dai Hajiya Jumman nan ta zo inda take gabanta sai ya yi ta faɗuwa,don haka yanzun ma addu'a take yi cikin ranta.


Hajiya Jummai kuwa saboda tsabar makirci sai ta kama kuka tana faɗin, ni ƴa su wannan yarinya kin share mana hawaye, shekaru sha baƙwai! Babu ɗa cikin gidanmu." Anty Sadiya ta ce, Jummai ki daina kuka, insha Allah sai kun samu dozin.


A ran Jummai ta ce,tir da maganarki tsinanniya amma a fili sai ta ce,amin Sadiya. Karima ta ce,ƙya koka Aminiya,kukan farin ciki ne" Fatima ta ce, "Nafisa ta daɗe ko in kira ta ne?" Anty Sadiya ta ce,ai Bros ya bita. Rufe bakinta ke da wuya sai gashi da sauri yana ɗauke da cooler, Nafisa tana biye dashi, itama ɗauke da ƙwando da su plate, Jabiru ya shigo ɗauke da ƙwalayan ruwan (EVER) da kalolin juice,ya ajiye ya koma ya shigo da manyan ledoji cike da tarkace


Hajiya Jummai dai suna gefe suna kallon ikon Allah,suna taɓa baki tare da girgiza kai ƙunci cikin zuciya kuwa ba a magana, shi ko maigidan sam bai ma kula da su ba.


Ya ja kujera ya zauna gaban gadon, ya ciro  waya ya kira Likitan yana shaida mishi sun kawo mata abincin, Likitan ya ce, gashi nan zuwa. Ya shigo Nurse's ke biye da shi É—auke da Æ™wanonin silver, Likitan ya dube ta da murmushi ya ce, sannu Madam. A'isha dai hannunta na kare a fuskarta,ya ce da Nurse's É—in bata ta wanke bakinta,ta shi ko? Ta yunÆ™ura kafin ta ankara tuni Uncle É—in ta ya É—agata zaune yasa filo ya jingina ta, kunya duk ta rufe ta. Ya amshi Æ™wanan daga hannun Nurse É—in ya ce Nafisa bani ruwa É—aya a can cikin Æ™walin,ta miÆ™o mishi ya ajiye Æ™wanon kan cinyarta ya buÉ—e ruwan,ta ce kawo zan iya da kaina. Likitan ya cire mata ruwan da ake Æ™ara mata. Ta kuskure bakinta, Nafisa ta miÆ™o mata tuwon nama ya yi wa tuwon zube, Uncle ya amsa ya ajiye mata a cinyarta,ta taÉ“a baki ta ce,a cire naman,ya ce to Nafisa cire mata naman. Aka cire ta kuma cewa a rage tuwon. Ya ce,ki ci iya cinki, in kuma ba zaki iya ba, bari na baki ko? Ta ce, a'a zan iya sai dariya su Nafisa suke mata.


Ta soma ɗan ci loma ta uku ta ajiye ta ce ta ƙoshi,ya ce, haba Beby ɗan ƙara mana,ta ci kaɗan nan fa zuciyarta ta soma tashi. Da sauri ta miƙa mishi ƙwanan kafin ta ce wani abu tuni ta soma sheƙo amai. Kai kawai ya riƙe yana kallonta,kowa sai sannu ya ke mata,su Hajiya Jummai dai ana ta kallon ikon Allah,da ƙyar aman ya tsaya.


Nurse suka shiga gyara wurin. Ya ba Nafisa makullin É—akin A'isha ya ce, "Ki É—auki mata kaya ta cire wannan Uniform É—in ta amsa ta fita.


Bayan an gama gyara komai, dole sai dai ruwan aka maida mata,jim kaÉ—an bacci ya É—auke ta don ya yi mata allurar bacci, cikin ruwan.


Koda aka kira sallar magriba, Uncle ya ce to duk su koma gidajensu. Nafisa ta ce wa zai zauna da ita? Ya ce, shi ne suka sa dariya, tare da cewa, "haba dai" ya ce Allah kuwa. Nafisa ta yi wa mijinta waya ya ce gashi nan ma cikin asibitin. Shigowarshi Katsina kenan daga Kaduna,ko gida bai je ba.


Bayan sun gaisa ya taya abokinshi murnar samun Æ™aruwa. Nafisa ta nemi iznin zama da A'isha, jin cewa Alhaji SaddiÆ™ ne zai zauna, Alhaji Bello ya ce, ya yarda Nafisa ta zauna tunda su Fatima duk suna da yara. 


Hajiya Karima ta kira Jummai gefe ta ce,sakarya ki zauna da ita mana in yaso na amso magani sai mu kaÉ—ar da shegen cikin tun daga nan. Hajiya Jummai ta ce,jinina zai iya hawa ba zan baki a É“oye ba, matsawar zan cigaba da kallon yarinyar da kuma rawar jikin da Alhaji ke yi kanta,wai baki ga dauriyata ba ne wannan zuwan da nayi ma? Ni dai gobe mu shirya mu bazama."


Ƙarfe taƙwas daidai su Hadiza da Hajiya Lanti suka shigo,su da shirinsu ma suka shigo. Hadiza tana ɗauke da kula anyo farfesun kayan ciki wanda ya ji haɗin magungunan salwantar da ciki. Cikin raha Hadiza ta shigo, ina A'ishan ƴar'uwa rabin jiki, lokacin ta farka tana ƙwance.


Nafisa kuma tana sallar Isha'i, shima Uncle yana masallaci. Hajiya Lanti ta ce sannu Æ´ar nan,kin ji Allah ya raba ki lafiya. Mun yi murna mun yi farin ciki." Nafisa ta idar suka gaisa ta ce, Nafisa ke ce gurinta? Nafisa ta ce,eh, Hajiya Lanti cikin makirci ta ce,haba dai ga Æ´ar'uwarta ba sai ta zauna ba? Kema sai ki koma gidanki,ki ji da kanki" Hadiza ta ce,ai kam ki tafi kawai". Nafisa ta ce, a'a ai babu komai maigidana ne ya ce in zauna. Hajiya Lanti ta ce, to shikenan.


Hadiza ta buɗe kular hannunta, ta ce ga farfesu na ɗan yo miki ko za kiji daɗin bakin ki." Ƙamshin shi ya doki hancinta, ta ce to na gode." Nafisa ta taso tana cewa,anya za ta ci? Komai ta ci fa sai amai. Hajiya Lanti ta ce "Wayyo, amma kuma kin san ciki sai ki ga in ta ci wani abin ya zauna,in tana so a barta ta ɗan taɓa" Nafisa ta ce to." Ta kalli A'isha za ki ci ne? Ta ce eh, Hajiya Lanti da Hadiza suka kalli juna, suka yi murmushi. Nafisa ta lura da hakan da suka yi don ta gani,don haka sai ta tsargu da wannan girkin,don haka sai ta ce to bari Uncle ɗin yazo ya kira Likitan don ya ce duk abinda ta ce zata ci sai yazo tukunna.




#######

[12/16, 08:36] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 14*




Hajiya Lanti ta ce,ke rabu da su, waɗannan likitocin masu tsirfar tsiya,ba ni plate nan ki gani in bata. Nafisa ta ce,ki dai yi haƙuri mu bi dokarsu kada ta ci ta kuma yin aman su ce sun faɗa mun ƙi ji. Hadiza ta ce, haka ne kuma a bari ɗin. Tana magana tana taɓa Hajiyar alamun ta bari.


Uncle ɗin ne ya yi sallama ya shigo da sauri Hajiya Lanti ta ja baya tana faɗin sannu da shigowa Alhaji, ya amsa da cewa yauwa sannu da zuwa. Suka gaisa har tana durƙusawa. Ta ce,ya ya me jiki? To Allah ya inganta mana yasa a sauka lafiya, ya ce Amin nagode. Hadiza ma cike da fara'a ta gaishe shi, tare da yi mishi murna. Ta ƙara da cewa, insha Allahu ƴan biyu zata haifa,sai a bata ɗaya. Ya ce, Allah ya bi bakinki Hadiza. Hajiya Lanti tana dariya tana cewa,kai waɗannan yara.


Ita dai A'isha tana ƙwance tana jin su. Ya matso kusa da gadon ya duƙa ya ce "Sannu Beby" a hankali ta ce,zan ci naman da su Hadiza suka kawo,da hanzari ya ce Nafisa zuba mata,me su Hadiza suka zo dashi? Wai zata ci. Nafisa ta ce, sai in Likitan ya zo,ɗazun ya ce kada ta kuma cin wani abu sai in yazo. Hajiya Lanti ta ce,ni dai na ce da kun bata,ba lallai ne tayi aman ba. Nafisa ta ce bari dai in kira Likitan.


Uncle ɗin ya tashi, bari in kirashi ta ce zauna kawai Bros,bari na kirashi,ta fita. Ko da ta samu Likitan cikin Office ɗin shi, suka gaisa ta ce mishi,ta zo ne don Allah ya yi ma yayansu magana ba kowa ba ne zai kawo abinci ta ringa ci, saboda yanda ya daɗe babu haihuwa, wasu za su yi baƙin ciki,da samun cikin musamman kishiyoyinta,don haka ya zo yanzun ma an kawo wani nama wai zata ci, kuma ita bata yarda da naman ba,don haka tana son ya hana ta ci. Da hanzari Likitan ya miƙe tare da cewa, Madam nima nayi wannan tunanin,ba zan so wata matsala ta faru ba,na gode da wannan taimakon da ki kai min."


Likitan ya shigo suka gaisa da Uncle ɗin,ta hanyar riƙe hannu. Ya ce,ka ce inzo? Uncle ya ce eh, wani nama ne aka kawo shine take son ci. Likitan ya ce, "Yallaɓai ba zata ci komai ba yanzun ba sai zuwa da safe, saboda wannan ruwan da muke ƙara mata yana tare da abinci,ba ma buƙatar ta ci komai yanzui."


Fuskar su Hajiya Lanti Nafisa ta kalla, sai ko taga sun kalli juna da É“acin rai. Likitan ya fita tare da cewa,in ka fito ina Ofis,ya ce to Doctor nagode."


Hajiya Lanti ta ce, to ni zan tafi ke zaki jira mijinki ne? Ta ce , to. Tana dubanshi ya ce to jira sai muje É—in. Hajiya Lanti ta ce to bani cooler in tafi da ita mu ma ci can ko? Hadiza ta ce to ko Nafisa tana so? Nafisa ta ce a'a nagode." Ta É—auki kular,wai bari ta rakata ta hau mota. Nafisa ta ce , to.


Suna fita shima ya nufi gurin Likita, Nafisa ta koma kusa da A'isha ta ce,ke wace irin wawiya ce zaki ce za ki ci? So kike ɗan cikin muna murna kisa ayi watsi dashi? Baki san su Lanti ba ko? Kar su kuma kawo wani abu ki ce za kici kin ji ko? Ta ce,to. Shima Uncle ɗin naki yasan komai don dai su maza ba su cika ɗaukan irin waɗannan abubuwan da mahimmanci ba ne, likita ya ce baya son kowa ya kawo abu ace ki ci, ya yi taka tsantsan, duk abinda tace tana so ta ci to ya kasance shi ne zai sa waɗanda zuciyarshi ta yarda da su su dafa mata. Uncle ya ce shikenan. Likitan ya ce ko gidan mahaifiyarka kawai ya fi dacewa a dinga kawo mata duk me zata ci,ya ce ƙwarai kuwa na gode insha Allah zan kiyaye.


Hadiza kuwa suna tattaunawa da mahaifiyarta kan cewa, duk wannan Nafisar ce ta É“ata musu shiri, Hajiya Lanti ta ce,ni ba wannan ne matsalata ba, damuwa ta kuÉ—in da na kashe gurin amso wannan maganin. Kai ina ma wannan cikin jikinki yake,kinga tun cikin asibitin nan sai mun Æ™washi kuÉ—i. Hadiza ta ce,ke dai bari, Hajiya yanzun ya ya zamu yi da wannan abin? Lanti ta ce wa? Ai tunda ranta na so sai ta ci shi, gobe zan É—inÉ—ima tunda yau ne aka ce kada ta ci saboda ana mata Æ™arin ruwa, gobe da sassafe in zaki taho ki biyo ki amsa.  Ki zo mata dashi,sai ki ce wani ne ki kayi. Ta ce, to shi yasa ai na ce su bari na tafi da shi tunda ba zasu ci, tunda ba nice nazo dashi ba,na su zaton ke ce ki ka dafa. Haka ne inji Hadiza, zan biyo, suka yi sallama,ta dawo Hajiya Lanti kuma ta hau mota.



****    *****.    ****


Goma dai-dai Uncle ya kula Nafisa tana hamma, A'isha tuni ta yi bacci,don haka ya miƙe ya je bakin A'isha ya tsugunna ya sumbaci kumatunta, sannan ya zo gurin Nafisa ya ce "Sister tashi ki je ki ƙwanta kema sai da safe." Hadiza ma tayi musu sai da safe, sannan suka fita.


A cikin mota take ce mishi "Darling amma ran A'isha ya biya da naman nan ko in yo mata wani gobe tunda tana so? Gashi ance mace mai ciki in ta buƙaci abu a bata in dai da shi kada ta haifi ɗanta da tabo." Ya yi ɗan murmushi, "inji hadisin hausawa ko?" Hadiza ta ce, "Allah gaske ne." Ya ce,to ki kawo mata, amma fa ba lallai ba ne ta ci tunda Likitan bai ce da safe zata ci wani abu,kai ko dai ki barshi kawai ma." Hadiza ta ce, a'a zan mata ko bata ci ba na san mutanan gurin za su ci, ya ce shikenan.


Ranar Æ™wana Uncle ya yi yana sallah, ya kasa bacci. Washegari tunda Asubahi ya kira Abbanta. Bayan sun gaisa, Abba ya tambaya ko lafiya? Uncle ya ce, A'isha ce bata jin daÉ—i ba, tana asibiti. Abba ya ce, "assha gado aka bata kenan?" Uncle ya ce wallahi, amma da sauÆ™i ba sai kun zo ba. Sannan ka taya ni addu'ar Allah ya sauke ta lafiya. Abba ya ce,ashe? Lallai nayi murna Friend, Allah ya bamu masu albarka. Uncle ya ce Amin. Daga nan ya nufi asibitin don yaga yanda suka Æ™wana. Zaune ya same ta tana sallah, gaskiya yaji daÉ—i sosai,ya zauna har ta idar ta juyo ta dube shi, ina Æ™wana Uncle? Ya  ce lafiya lau Beby ya ya jiki? Ta sunkuyar da kai ta ce,da sauÆ™i. Ya ce ina Nafisa? Ta ce ta shiga wanka. Ya ce,to daÆ™yau,kema kin yi ne? Ta ce eh, nayi shi ne na ji É—an Æ™arfi. Ya ce su Abba suna gaishe ki,ta ce gaya musu ka yi bani da lafiya? Ya ce eh mana, har ma nace musu kina da ciki." Ta saka kanta a gwiwarta tare da faÉ—in haba dai don Allah. Ya ce to mene ne? Ta ce,ni ina jin kunya yanzun su Hajiyarmu sun ji? Ya yi murmushi.


"Sun ji mana,tun lokacin da Likitan ya sanar damu."


Ta ce, "Shi kenan ba zan kuma zuwa gidan ba" ya ce "Don me?" Ta dube shi, yanzun kowa ya san abinda na yi na samu cikin kuma? Ya yi dariya, sannan ya ce, a'a ba wanda zai sani,ke da ki ke makaranta, wasu za su ce a ruwa ki ka sha." Ta É—an yi murmushi don ganin ya maida ita doluwa,ta ce "Ai na san ba'a sha a ruwa." Yasa dariya.


Nafisa ta shigo tana cewa "Bros ka zo kenan?" Ya ce, "wallahi ya ya kuka kwana?" Ina ta tunanin dare? Nafisa ta ce bacci sosai mu ka yi kaga gashi har ta yi wanka,ta yi sallah. Ya ce aiko naga da sauƙi yanzun me zaku ci inje gidan Hajiyarmu in sa ayo muku? Nafisa ta ce,Mama two me zamu ci? Ta ɓata rai Anty Nafisa bana so, Uncle ka ce ta bari fa, cikin murmushi ya ce , Sister bama so gaskiya, ya dubi A'isha ƙyale ta Beby gaya min me zaki ci? Ta ce,da zan samu waina ko irin ɗan waken nan? Ya ce zaki samu ya miƙe, har ya fita. Ya dawo zaki ci farfesun irin na jiyan a zo miki da shi? Ta ce a'a, ya ce shi kenan.


Hadiza ta zo lokacin suna karyawa. Hadiza ta aje mata kular a gaba gashi kin ji ƴar'uwa na yi miki wani ne. A'isha ta ce na gode, yanzun kam na ƙoshi amma anjima zan ci. Ta miƙa ma Nafisa ta ce Anty Nafisa gashi ki sa can gefe kada ku ci min fa. Nafisa ta ce, to A'isha Hadiza kam daɗi ne ya rufe ta.


Hajiya Jummai kam an bazama nema,an nemo kuma an samo,ana kan aiwatar wa. Satin A'isha ɗaya a asibiti, ta samu sauƙin aman. Sai dai kasala tare da tsirfa iri-iri har yau abinci in ba daga gidan Hajiyarmu ba ne bata ci. Hajiyarmu kuwa ko yaushe mai aikin ta tana kicin tana dafa duk abinda A'isha ta buƙata, sannan addu'o'i ko yaushe tana nan tana tofa mata su cikin ruwa tana sha. In za'a kawo abinci sai an kawo, shi kam Uncle shi ne mai jinya, duk wadda yake ɗakinta zai je ya bata haƙƙinta in ya kintsa jikinshi zai dawo gurin A'isha.


Ya lura da ita, musamman saboda dare Hajiya Jummai ce ta so ta nuna rashin amincewarta ya ce haba Jummai,in kin lura A'isha tana buƙatar kula,ba fa wai ta samu sauƙi ba ne, dole sai da mai kula in kuma da wanda ya dace ya kula da ita,to ni ne. Ta dai ƙyale shi ne kawai.


Kullum sai Ummanta da Abbanta sun kira ta sun tambayi jikin umma ta kan bata shawarwari masu kyau game da rainon ciki. A daddafe cikin ya yi wata biyu, suka yi waya da Samira inda Samira take cewa wannan satin ne za'a koma makaranta, ta ce, ina sane ni da nasha ciwo kamar ba zan tashi ba tun daga wannan dai ciwon? Samira ta ce ayya amma me yasa ba a samun wayarki? Ta ce,ke dai bari,ni da tunanina manta da batun wata waya, sai dai mun haɗu a makaranta. Samira ta ce to shikenan, Allah ya sawwaƙe, A'isha ta ce Amin.


Koda Uncle ya dawo ta ce mishi an koma makaranta, sai ya ce mata wace makaranta? Beby gaskiya ba zaki koma makaranta da ciki ba." Ta dube shi cikin rashin walwala ta ce, Uncle kana nufin ba zan zana (S.S.C.E) ba? Ya ce haba Beby,ke sai ma ance miki,kina ganin yanzun ban bari ki yi nisa da ni? Ta ce, gaskiya ba zan so haka ba, wata uku fa kawai ya rage min in gama duka,don Allah Uncle ka daina wannan maganar." Ya ɗaure fuska wata shekarar kin zana, ganin yanda ya ɗaure fuska, abin da bai taɓa mata ba,sai ta yi shiru ta kifa kanta kan filo, shi kuma ya fita abinshi. Kuka ta ringa yi wiwi,na ta ganin Uncle bai mata adalci ba, ita a nata son ran ta koma makaranta tunda ba wanda ya san tana da ciki, har ta gama.


Da daddare ko da ya shigo ta bashi ruwa, sai dai ba ta cikin walwala,ya amsa yana sha yana kallon fuskarta, wadda ta kumbura ta yi dam. Ya aje kofin da sauri,me ya samu fuskarki Beby? Ta sunkuyar da kai babu komai, ya ce ban yarda ba kin yi kuka ko? Ta ɗago ta ce mishi, a'a sai hawayen da take maƙalewa suka zubo ya kama hannunta suka zauna, yanzu saboda na ce ba ki komawa makaranta ba shi ne ki ke kuka? Beby na fiki son karatun ki domin alƙawari na ɗauka cewa zan tsaya har sai kin ji da kanki cewa kin gaji da karatu, amma yanzu koda ba ciki duka-duka yaushe aka sallamo ki daga asibiti? Ba ki gama murmurewa ba" Ta ce, Uncle ko a makaranta fa zan kula da kaina." Ya yi shiru yana kallonta,sam baya so ko kaɗan ya ga yarinyar cikin damuwa, ya ce to daina kuka za ki koma, amma sai kin ƙara murmurewa, sannan in naga kina cin abinci. Ta ce, to Uncle zan dinga ci. Nan fa A'isha ta dinga ƙarfafa jikinta don kawai ta samu ta koma makaranta, sai dai duk da haka cikin nata mai saka laulayi ne da tsirfar zan ci kaza ba zan ci kaza ba,ga saurin fishi. Wata rana tunda safe ta ce da Uncle idan zai dawo ya zo mata da agwaluma, ya ce ni kam ina zan ga wata agwaluma? Ba na zaton cewa duk Katsina za'a samu agwaluma, amma zan sa a duba. Yinin ranar neman agwaluma gurin mutum huɗu ya baza,neman agwaluma. Ita kuma tana ta yi mishi waya a ƙarshe washegari a Kano aka siyo cikin baƙar leda ya tashi Jabiru ya dawo gida lokacin ƙarfe uku na rana ya same ta tana shan ƙanƙara ta fiya wota, ya ce Beby me yasa kike shan ƙanƙara? Kada in sake gani ta ce, to da ya aje mata ledar agwaluma komawa ya yi gefe yana kallonta, da gudu ta tashi ta ɗauko ruwa a firij ta wanke ta soma sha hannu baka hannu ƙwarya. Tausayinta ya cika shi, ya ce Beby bana son wannan gudun da ki ke yi,kin ga cikin ki bai yi ƙwari ba,ta ce na daina.


Washegari kuma ta ce zogala, gidansu Hajiyarmu ya yi waya aka kawo mata shi da yawa,ta yini ci. Irin waɗannan abubuwan suke sa Uncle tunanin yanda zata zauna a makaranta,ba za'a bari a zo kullum ba,week end ɗin da yake zuwa sun gaya mishi don shi ne, sannan ita abin tattalin shi ce,a yanzun saboda mutane da yawa suna bashi shawara kan cewa ya kula da ita sosai, saboda maƙiya ko ɓarayi masu yin garkuwa da mutum don su amshi kuɗi irin waɗannan abubuwan suna sa shi tunanin barin ta ta koma, amma ya san makarantar su akwai tsaro, sannan albarkacin addu'ar da yake yi ko yaushe Allah zai kare mishi ɗan shi.





######

[12/17, 11:31] Ummi Tandama😇: *📗📗Page 15*




Cikin wannan halin wata rana A'isha tana Æ™wance da daddare, Uncle yana É—akinshi,yau Hadiza ce da girki,tasan komai dare zai dawo É—akinta,don haka ba ta murÉ—a key ba. Shiru-shiru har É—aya ta wuce, ita ko bacci na cin ta, don haka ta rufe Æ™ofarta,ta Æ™wanta tana karanta addu'ar bacci ta gama bata gama ba oho bacci ya yi awon gaba da ita. Can cikin baccinta sai  wata Æ™atuwar mage ta nufo ta, nan suka soma gabza dambe ta nayi tana karanta duk addu'ar da ta zo bakinta,mage Æ™oÆ™ari take ta cafko mata cibiya, Allah bai bata Sa'a ba, suka yi wa juna kaca-kaca duk ta yayyaÆ™ushe A'isha, itama ta ji ma magen ciwo. A tsorace ta farka da addu'a, sai me,magen ta gani a kan durowar gefen gadon ta murtukekiya. Ta yi wani tashi ta nufo ta,da matsanancin tsoro ta Æ™wala ihu tare da kai ma magen nan duka da filo,ta miÆ™e tana waige-waige saboda bata san in da magen ta shige ba,ta nufi Æ™ofa da gudu tana salati, tana buÉ—e Æ™ofa Uncle yana fitowa, shima da gudu saboda duk wanda ke gidan ba zai ce bai ji ihunta ba.


Hanyar fita ta nufa ya yi sauri ya riƙo ta, ta sake ƙwala wani ihun tana ƙoƙarin fizgewa. Abinda ya bashi mamaki, wani mugun ƙarfi ya ji ta yi. Ta ƙwace zata fita, ya kuma damƙo ta da ƙyar,ya kai ta ƙasa ya danne ƙafafunta da hannuwanta. Nan ya shiga tofa mata addu'o'i, sai ta yi laƙwas. Ya ɗauke ta zuwa ɗakin yana shiga ta soma ihu da sauri ya fito da ita kan kujera ya ƙwantar da ita yana tofa mata addu'o'i.


Hajiya Jummai tana leƙensu ta window, haka Hadiza daga falonshi ta leƙen su. Hajiya Jummai ta fito da sauri tana cewa, "Lafiya Alhaji?" Ya ce, wallahi nima ihunta na ji. Ta zo ta tsugunna tana cewa, A'isha me ya faru ne? Ina, A'isha sai wani gunjin kuka take yi. Addu'a dai yake ta tofa mata, Hadiza ma ta fito suka zauna cirko-cirko. Jummai tana ɗan mutsu-mutsunta da baki tana tofa mata amma a zukatan su farin ciki suke yi, kowacce tana zaton nata asirin ne ya ci, kafin safe ta yi wani sharaf ta daina gunjin kuma bata ko motsi.


Tun cikin daren ya kira Alhajinmu ya sanar mishi, ya ce mishi ko su wuce asibiti? Alhajinmu ya ce, a'a ya bari sai zuwa da safe. Suna idar da sallar Asubahi sai ga Alhajinmu,ba za ya iya tuna zuwanshi na ƙarshe gidan ba sai ko yau.


Lokacin da ya iso su Uncle ɗin suma fitowar su kenan daga Masallacin. Duk ya yi zuru-zuru yana sanye da farar jallabiya. Alhajinmu ya zuba ma A'isha idanu, inda take ƙwance kaman ruwa. Ya dubi ɗan nashi ya ce, Abubakar wai ya ya abin ya faru ne? Uncle ya ce , nima ban sani ba, ihunta kawai na ji na fito, da na kamata ma zan maida ita cikin ɗakinta sai ta fara ihu.


Hajiya Jummai ta ce,ko mafarki ta yi ne,ni ƴasu?. Uncle ya ce in kaga yanda muka dinga cin dambe da ƙyar na kai ta ƙasa, na soma karanta mata addu'o'i. Alhajinmu ya nufi hanyar fita, Uncle ya bishi.


Bayan sun fito suka tsaya a harabar gidan, ya dube shi.


"A gaskiya Abubakar al'amarin yarinyar nan ba na zaton na asibiti ne, Malamai zamu samu. Uncle ya ce , to yanzu ya ya za'ayi? Alhajinmu ya ce, yanda za'ayi shi ne,a saka ta a mota mu tafi da ita can gidanmu, Allah ya yi mana jagora.


Haka Uncle ya ɗebo ta yaraf,ya ƙwantar bayan mota. Hajiya Jummai ta ce, asibitin za'a ko? Ya ce, a'a bai tsaya wani dogon bayani ba ya wuce ya shiga mota, don hankalinshi ya tashi na ƙarshe. Jummai da Hadiza suka tsaya jikin motar suna to Allah ya sawwaƙa. Alhajinmu ya shiga gaban motar, direba ya ja suna cewa Allah ya sauwaƙe." Alhajinmu ne ya ce,ku koma gida kun ji? Kada ku damu, Allah zai kawo sauƙi.


Hajiyarmu tana zaune cike da zullumin wane hali ƴar mutane take ciki? Jiran dawowar maigidanta kawai take yi,ta ji labarin jikin, sai ga su sun yi sallama. Uncle ɗin yana rungume da ita, tamkar babu rai, ta miƙe cike da sallallami, tana cewa,ya ya haka? Uncle ya zube ta kan kujera. Hajiyarmu ta isa gurinta tana tofa mata addu'a, Alhajinmu ya ce ina ganin lamarin kamar na jinnu, shi yasa na ce mu yi nan da ita. Yanzu zan je gurin Malam Yakubu ne yazo ya duba mana ita, suka ce to. Uncle ya zauna yana gaida mahaifiyarshi, Hajiyarmu ta amsa cike da jimami, sannan ta ce ya ya akayi haka? Nan ya shaida mata duk yanda ya sani, ta tausaya sosai. Ta kuma ci gaba da addu'a, Alhajinmu ya shigo shi da malam Yakubu,da kuma wani Malam Sufi,suka zauna suna tofa mata addu'a, tana nan dai yanda take can Malam Sufi ya soma karanto alƙur'ani mai girma cikin Suratul Baƙara,nan ta soma motsi ya matso kusa da ita yana yi cikin ɗaga murya, sai kuma ta soma gunjin kuka cikin wata irin murya. Malam Yakubu shima ya amsa. Ai tuni ta soma fizge-fizge, suka ba da umurnin a riƙe ta, Uncle ya riƙe ta gam,tana fizge-fizge. Suka ce wane ne? Wata ƙatuwar murya ta soma magana,ni ne. Kai ne wa? Ni ne umm! Umm! Suka ce kayi magana kaine wa? Ya ce sunana Sulaiman, suka ce me ya kawo ka jikinta? Ya yi shiru,nan Malam Sufi ya ci gaba da karatu, shi kuma Malam Yakubu yana mishi tambaya,ba za kayi magana ba? Ya ce,kuna ƙona ni fa zan fita, to faɗa mana me kazo yi jikin wannan baiwar Allah? Ya ce turo ni aka yi,an umarce ni ne da inzo in sakar mata jini in fitar da cikin ta. Suka ce kai Musulmi ne? Ya ce eh,ka yarda da Allah da ranar tashin alƙiyama? Ya ce eh, na yarda,to me yasa kazo ka cutar da ita? Ya ce,an sani ne. To wa ya saka? Ya ce Ubangijina,shi Malami ne ni da mahaifana muna ƙarƙashin ikon shi ne. Suka ce to yanzu zaka fita ne ko mu ci gaba da karatu? Ya ce,zan fita. Suka ce to fita ta baki ko ta hanci,sannan ka ji tsoron ranar tsayuwa a gaban Ubangiji ko da ba jinsin ku ɗaya da ita ba, akwai hisabi tsakaninku ko? Ya ce,eh, suka ce to maza ka fita. Nan take ta yi atishawa mai ƙarfi sau biyu. Jim kaɗan ta buɗe idanu, ta tsura ma silin ɗin ba. Uncle ya ce, A'isha? Jin muryar Uncle ɗin ta, sai ta yunƙura,ya riƙe ta ya tada ita zaune ta ringa kallonsu cikin mamaki. Ta dubi Uncle, me ya faru Uncle? Ya ce ba komai,sai sannu suke mata. Alhajinmu mamaki yake tamkar tatsuniya. Hajiyarmu kam har da hawaye don tausayi,nata ganin ba su yi mishi adalci ba,ko waye ya turo su? Yaro shekara da shekaru sai yanzun ya samu rabo amma har ya tsole ma wani idanu, Uncle kam burinshi ta tashi,shi dai lamarin shi ya bar wa Allah, addu'a yake yi kullum Allah ya shige mishi gaba, kuma ya kai ƙararshi gurin Allah duk wanda ya ke son ganin bayan ƙwanshi a duniya.


Sun bada magunguna irin su habbatus sauda, zaitun, sai garin itacen magarya,sun ce ta ringa yin azkar safe da yamma, sannan ta zama mai yawan jin alƙur'ani.


Alhajinmu da Uncle sun musu rakiya tare da godiya gami kuma da yi musu alkhairi mai yawa. Hajiyarmu ta matso kusa da A'isha wadda ta jingina da kujera duk gaɓoɓin jikinta ciwo suke mata,ta so ta san yaushe ta zo gidan su Hajiyarmu? Ta ce,ƴan nan sannu kin ji, A'isha ta ɗago kai ta ce ko zaki yi wanka ne? A'isha ta girgiza kai alamun a'a, sannan ta ce bacci nake ji,ta ce to yi ƙwanciyarki nan bari in ɗauko miki filo. Luba mai aiki ta shigo tana cewa Hajiya an gama a kawo?, Hajiyarmu ta ce, a'a bari su Alhajin su shigo,je ki kawo mata filo, kafin ka ce haka tuni bacci ya yi gaba da ita. Uncle sai da Hajiyarmu ta matsa mishi sannan ya tafi gida.


Su Jummai rai fal murna, addu'a take Allah yasa rai ya yi halinsa,lallai zata koma gurin wannan makamin don za'a dashi,tashin farko aiki ya soma ƙyau? Hadiza ma tana baje kan gado suna waya da Hajiya Lanti tana cewa,ai gaskiya malamin nan ya yi ne, ina ga aljannu ma ya haɗa ta da su,fatana dai Allah yasa cikin ya zube,tunda kinga damben da suka sha da maigidan? Yanzun dai ya fita da ita. Hajiya Lanti ta ce, Allah yasa asibiti suka je,kin san Aljani yana son a yi gabas shi yana yamma, ana maganin asibiti shi yana nan yana ɓanna. Suka sheƙe da dariya. WANDA YA YI NISA BA YA JIN KIRA.


Lokacin da Alhaji Saddiƙ ya shigo gidanshi, abinda bai taɓa gani ba wai yau Jummai da Hadiza ne zaune suke hira. Hakan ya yi mishi daɗi,ga nashi zaton jikin A'isha ne ya sa su zubar da komai, domin ya lura sun tausaya ma A'isha.tare suka miƙe suka nufo shi, suna cewa ya ya me jikin? Ya ce,jiki da sauƙi, Hadiza ta ce, wane asibiti aka kaita? Ya ce, tana gidan Hajiyarmu, ta dawo cikin hankalinta ma, yanzun na barta tana bacci. Jummai ta ce Alhamdulillah, amma Alhaji babu abinda ya samu cikin ko? Ya ce bana zaton ya samu matsala, ta ce amma mun gode Allah,ni dama damuwata kenan. Hadiza ta ƙara da cewa mun yi arziƙi, Allah dai ya kar lafiya,ya nufi ɗakinshi su kuma kowacce ta shige ɗakinta ba haka suka so ba,jikin A'isha yana yin sauƙi sosai ɗakin Hajiyarmu take ƙwana,zuciyar A'isha na matuƙar son Hajiyarmu,duk sanda ta farka kan sallaya take ganin wannan baiwar Allah, gashi suna jin nauyin juna balle ta tambaye ta cewa tana bacci kuwa? Sai dai duk lokacin da ta farka ta ga Hajiyarmu tana ibada, itama sai ta tashi ta hau yi. Wannan abin yasa itama Hajiyarmu jin A'isha a ranta. Ta yarda yanzun wannan yaron ya samu mata, irin matar da ta ringa mishi addu'a tun yana yaro.


A'isha na da kunya da son addini, tana jin nauyin surukanta, sai dai hakan ba ya hana ta zo ta zauna kusa da Hajiyarmun,in ko Uncle ɗin ta yazo ba ta iya yi mishi magana gaban Hajiyarmu, kuma takan miƙe da kanta ta shiga kitchen ta kawo mishi ruwa mai sanyi,ta bashi cikin girmamawa. In ko ya ce Beby ban ci abinci ba yau ta kan je ta kawo mishi ba tasa me aiki hakan yana yi wa Hajiyarmu daɗi, ba kamar Jummai ba duk da tana ƴar uwarta, ko ruwan gidan su bata sha, sannan gabansu zata yi ta yiwa mijinta yatsine-yatsine,bata la'akari da cewa su iyayan shi ne.


Uncle in zai je Ofis zaya biyo haka in ya dawo, waya kuwa sai ya kira ta fiye da sau goma a rana. Ita dai kullum zancan ta ya barta gidan Hajiyarmu,ta fi jin daÉ—i. Shi kuma sai ya ce a'a,ko hirarta ba ya samu sosai, ballantana ya É—an shasshafa jikinta ya ji daÉ—i, sai ta ce duk me ya ke so zai mata ai gidansu Hajiyarmu ma gida ne, ya ce abinda in nazo sai ki zauna kusa da Hajiyarmu,ko magana da Æ™yar ki ke amsa min, ta ce to in ban da abinka Uncle,da so ka ke inyi ya ya? Ya ce ka ji Beby da wani zance,ke baki da irin wayon nan ne naku na mata? Sai ki shige É—aki ki zauna ni kuma na biyo ki, ta ce kai. Cikin mamaki ni dai ina jin nauyi, ya ce to ko irin rakiya É—in nan cikin mota? Ta t, Uncle kenan,ni dai ina jin kunya, ya ce to ba zan iya barinki ba kenan ki zauna,nan da Æ´an Æ™wanaki zamu koma gida." Cikin shagwaÉ“a ta ce, kai don Allah Uncle É—ina. Ya ce Allah Bebyna. Ta ce, to in ka zo in baka ganni a falo ba ba sai ka shigo É—akin ba. Ya ce,kin ga ina shigar ma Hajiyarmu É—aki ne,bare ma in miki wani abu ciki? Ta ce to to ai dai haka kakeyi ba? Ya ce,in ba mutane ba, amma in da mutane sai ta ce min in fito mata daga É—akinta tun ina Æ™arami fa.  Ina ga Hajiyarmu ba ta sona shi yasa nake tausayin kaina, gashi ban dace da matar da zata rungume ni ba.


A'isha ta tausaya mishi, sannan ta ce haba Uncle, ya ya zaka ce haka bayan ga ka da mata uku? Ya ce, duk ba ku damu da ni ba. Hajiya Jummai bata ma zauna ba, ballantana ta san matsalolina. Hadiza ko son abin duniyarta yasa na kasa sakin jiki da ita,ke ko Beby kunyarki ta yi yawa, ta ce to zan rage yace to na gode. 


Satinta biyu gidan Uncle ya ce ma Alhajinmu tunda ta samu sauƙi yana so ta koma. Ranar da A'isha zata tafi har da kukanta,wai ita tafi son gidan Hajiyarmu, Hajiyarmu ɗin ce ta bata baki kan cewa ta ɗaure ta koma ɗakinta. Ta yi mata nasiha kan cewa ta ƙara dagewa gurin addu'a.



Su Jummai sun zo duba ta sau ɗaya, ganinta cikin hayyacinta yasa su cikin baƙin ciki, duk da suna ɓoyewa junansu mugun halinsu, ma'ana babu wadda ta nuna ma ƴar uwarta cewa tana shiga gurin bokaye, sai dai duk suna zargin junansu. Daga nan ko basu ƙara zuwa ba har kau da ta dawo gida. Sun dai shigo ɗakin sun yi mata Sannu, A'isha ta amsa tare da yi musu godiya.


*📗📗Page 16*



Wani lamari na Allah, A'isha sai ta samu sauƙi sosai, Uncle ya kai ta gurin Likita,ya duba ta ya kuma tabbatar musu ciki yana nan lafiya lau. Ya keɓe da Likitan ya tambaye shi ko zaya iya saduwa da ita babu matsala? Likitan ya ce babu wata matsala,don haka ranar suna dawowa daga asibitin misalin ƙarfe huɗu na yamma,nan ko ya sa ma ƙofa key, ya kuma shiga yi mata wasanni, duk da tana fargaban wuyar da ta sha, kuma tana tunanin ita zata ƙara sha,bai sa ta nuna fargaba ba. Sai gashi itama bata sha wuyar da tayi tunani ba,haka nan tun daga ranar itama ta shiga sahun matan gida, sannan yanzun ne ta san me ake yi wa kishin?.


Don haka ta Æ™ara yarda zata Æ™yautata mishi,duk ranar da ita ce da shi ta kan shiga kitchen ta yi mishi girki da kanta,ga zoÉ“o mai sanyi, sannan duk lokacin da ya buÆ™ace ta ba ta É“ata rai,ko jan aji tana ba shi dukkan goyon bayan da ya dace, shi yasa ta Æ™ara É—aukaka cikin ranshi, ta kuma zarce duk matan nashi, har ya dinga Allah-Allah girkin  ya zagayo kanta, haka nan duk abinda ta ce yanzun nan za'ayi shi,ko da ta yi mishi batun makaranta ta ce tuni an wuce ta a karatu, sai ya ce za ya samu (P.C) É—insu ya ga me zasu yi, koda ya samu (P.C) da batun cewa bata da lafiya ga jarabawa yana son su yi mishi taimako kullum za a ringa kawo ta ko kuma in suna da abu mai mahimmanci (P.C) ya yarda. duk da ba hakan ya taso ba,taji daÉ—in samun hakan,nan ko ta shiga zuwa makaranta.


Su ko su Jummai, sai suka shiga cewa don yaga tana da ciki shi yasa ƙarara ya ke nuna tafi kowa kuma ko gaban wane ne. Don haka kowacce ta tsaya ɗacin ran ba ya sonta, ta shiga fushi, tare da shiga faɗi tashin neman asiri. Hakan da suka yi na yin watsi da shi ya bashi damar more amarcin shi da A'isha, wanda bai yi a baya ba.


Duk ran girkin ta ya kan makara Ofis kuma ya dawo da wuri. In ya kalli madubi sai ya ce Beby kin sani na yi ƙyau fa,ko ba ki lura ba ne? Sai ta ce ai kai Uncle kullum mai ƙyau ne, komai naka yana da ƙyau. Ya ce har da ƴar Bebyna? Ta ce ai ni ba'a saka ni cikin jerin masu ƙyau, ya ce inji wa? Kina kallon madubi kuwa? Ai Beby har yau ni ban ga me ƙyanki ba, cikin haka suka soma jarabawa, dole ta zauna a ɗakinsu na cikin makaranta saboda suna karatu ita da su Samira,su Samira sun dame ta wai wane irin ciwo ne wannan da ya sakata yin shegen ƙyau haka? Ga wasu (hips) da ta yi,ƙirji kuma ya ƙara cika ta ce zaman gida ne kawai,ai ba za'a haɗa zaman gida da makaranta ba,sai dai cikin ranta ta saka duk ranar da suka yi banƙwana zata sanar da su cewa ita matar Uncle ce, haka suka ci gaba da jarabawa har suka gama. Ranar da aka yaye su,sun yi hotuna tare da canja lambobin waya,su da ƴan ajinsu, lokacin da za su rabu, Uncle ya zo tafiya da ita. Samira Suka ce in za ta yi aure ta faɗi musu,sai ta ce musu sai dai in zata haihu. Ta gaya musu cewa dama ta ɗauki alƙawarin yau zata sanar da su cewa Uncle mijinta ne. Dukkansu baki suka saki cike da mamaki. Ta ce musu yanzun haka ma ina ɗauke da ciki wata uku, zan sanar da ku in na haihu,ku kuma ina jiran bikinku don Allah da zarar ya zo in sani,nan suka yi banƙwana suna kewar juna.


Ta dawo gida suka ci gaba da zama da mijinta lafiya. Uncle na kula da ita sosai, sannan ba ta damuwa da lamarin su Hajiya Jummai, musamman da suka haɗe kai da Hadiza. Sun haɗa kansu, sai su zauna falo suna zuba mata habaici tare da su Suwaiba, musamman ranar da ya kasance ita ce da girki,nan fa za su yi ta surutunsu na cewa salon banza ana yi wa miji girki alhalin ga mai girki sai wannan ta ce ba dole ba ke ko abar wani ya yi ana son a zuba asirin mallaka duk da dai ba ta kula su kuma bata taɓa gaya mishi ba, cikin wannan halin ne wata ranar Litinin yana ɗakinta misalin ƙarfe ɗaya da rabi, haka kawai ya bar komai ya zo wai ya ganta da yaronshi, tana ƙwance kanta na kan cinyarshi, ya shafi cikin ta ya ce, Beby naga cikin ya ƙi ya yi girma ya fito ki dinga tafiya da ƙyar da ƙyar,na ƙosa in ga lokacin. Ta ce Uncle to cikin ƙwata-ƙwata watan shi uku fa, ya ɗaga rigarta mararta a shafe tamkar ba ta da komai, ya ce ni dai wannan cikin naki wane iri ne? Bai ƙara komai ba Beby? Kafin ta ba shi amsa sai ga Hajiya Jummai ta banko ƙofa babu ko sallama, ta ce ashe gaske ne,dama an ce kana zuwa kana cin amanar mu, tunda ai naga yau ba ita ce da kai ba, kuma yanzun ba lokacin dawowarka ba ne ka sato jiki ka dawo. Kallonta kawai yake yi sai da ta kai aya sannan ya dube ta ya ce,haba Jummai,me zai sa ki tsaya kina zubar da girmanki a gurin wannan ƴar yarinyar,ya kamata ace yanda take baki girmanki ki riƙe shi ni a zatona kece mace ta farko da za ki kula min da A'isha,da halin da take ciki,in na tuna yanda a baya ki ka fi ni son ki ga na samu ɗa, sai naga akasin haka, maimakon haka ma sai ki ka yi watsi dani da lamarina, kuma ki ka nuna tamkar kina faɗa da Ubangijinki, saboda ya bani ƙyauta, shawarar da zan baki,ki sake hali ki rabu da mugayen ƙawaye za su kai ki su baro. Ta soma kuka,ai ni yanzu komai ya zo bakin ka gaya min zakayi tunda mahaifata ba zata iya ɗaukar cikinka ba.


A'isha ta ce, to kiyi haƙuri Hajiya, Uncle ka koma Ofis shi kenan. Jummai ta daka mata tsawa ke makira, yi min shiru ba ke ce sanadin canza min halin miji ba,an je makaranta an roro ciki an zo an manna mishi, shi kuma da yake yana neman haihuwa ido rufe ya amsa jiki na ɓari,in da ka iya cikin me zai hana Hadiza kai mata in ni ba zan haihu ba.....ya katse ta da tsawa mai tsanani. Jummai kina hauka ne? Wace magana ki ke yi haka? Ya kama hannun A'isha wannan yarinyar ƙaramar yarinya ta fi min duka manyan matan da na aura, wannan yarinyar ita ce mace mai daraja ta farko a idanuna ni nan nine na yi mata ciki tunda kin tono bari in sanar da ke. A ranar da na kauda budurcinta a ranar cikina ya shiga jikinta, dan haka ki kama bakinki Jummai.


Ta fita tana masifar cewa eh dole ka ce kai,ni dai ban yafe satar min ƙwana da ake yi ba.


A'isha tana zaune ta zabga tagumi mamaki take yi wannan kuma wanne irin sharri ne? Hawaye suna zubowa daga idanunta,ya zo yana  bata baki ta ce ka tafi Uncle ba komai. Ya ce, Beby ki zama mai haÆ™uri, ina nufin ki Æ™ara kan naki, ta share hawayenta tana murmushi ka koma Ofis Uncle, ya dinga bata haÆ™uri har sai da ta tabbatar mishi da cewa ita fa hayaniyar da suka yi ne wato sa'in'sar da suka yi ne yasa ta hawaye, nan ya fita yana shi mata albarka, A'isha ko ta maida Æ™ofa ta rufe.


Bayan sallar la'asar Wani bacci A'isha ta ringa ji,ta ƙi ƙwanciya saboda ta san cewa baccin la'asar ba shi da ƙyau,ko a musulunce, ta zauna tana kallo wai don kada baccin ya ɗauke ta. Da yake an ce gwanin sata ne baccin, sai ko ya sace ta har ma bata san lokacin da ta ƙwanta ba.


Can cikin baccin sai take jin numfashinta yana yin sama, ta soma kokowa da numfashinta, buɗe idanunta ke da wuya sai taga hayaƙi ta kowanne bangon ɗakin,nan ta shiga salati da ƙarfi tare da ihu, amma muryarta ba ta fita. Nan fa hayaƙin ya cika ɗaki, ya toshe mata numfashi.


Biyar dai-dai Uncle ya shigo gidan, ya nufi ɗakin Beby domin zuciyarshi ta kasa nutsuwa,yana shiga ya same ta kan gado tana ta mutsu-mutsu, numfashinta yana wuya ko sauka ƙirjinta ba ya yi, bakinta na ta motsi. Amma ba a jin me take cewa, sannan shi bai ga hayaƙin ba, ya ɗauke ta yana jijjiga ta,yana cewa Beby! Beby!! Ai ina ta daina ma motsin ta yi lagaf ƙasan zaninta kuma wata laima ya ji mai ɗumi,tana sauka a hannunshi, da sauri ya duba kun san me ya gani? Jini. Da ƙarfi ya furta jini?.



Tabbas jini ne, sai mun haÉ—u cikin kashi na uku don jin shin cikin da ake nema shekara da shekaru a ka sha wuya kanshi,ya zube? Asirin Hajiya Jummai zai tonu? Da sauran wasu abubuwan. Daga taku har kullum Halima K/Mashi.


Na gode




No comments