Recent Updates

Mummunan Zato Book 1

 


____________________________
   *📗MUMMUNAN ZATO📗*

                       *NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

             *Ɗandano page 1*

*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*

```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank       sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427  idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*

*Masu son  tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427*

Ya shigo gidan cike da fara'a yana faɗin "ina Umman yaran gidan nan ne?" Daga ciki ta amsa da cewa "gani Abbansu" ya iso cikin kitchen ɗin, tsaye take tana haɗa lemun soɓarodo yayin da A'isha ke jera ƙwanuka domin raba abinci, tace sannu Abba, yace yauwa ƙawallin Ummanta,ya dubi Umma "ina da babban baƙo fa" ita ma ta dube shi cikin kulawa"daga ina?"

   Ya fadada murmushin sa "zakiyi mamaki idan nace miki Alhaji Sadiq Usman kt ne" cikin mamaki take dariya " lallai munada babban bako yau kam zanga wannan Alhaji Sadiq naka" ya juya tare da cewa " muna falo na" tace "to".

Ta amshi rabon abincin daga hannun Aisha tace "kawo nan in zuba musu,ki kai musu abin sanyaya makoshi,kafin na zuba masu abinci ko? Aisha tace "to Umma" nan ta shiga hada kaya kan tire,lemun zobo ne mai dan karen sanyi tare da ruwan leda shima mai sanyi guda hudu sai kofuna guda biyu.

Tayi sallama falon Abba,inda suka kaure da hirar yaushe gamo? Suka amsa mata cike da fara'a ta shiga kan tebur ta daura tiren sannan ta dan jaa teburin zuwa gabansu,durkusawa tayi gwuiwa biyu a kasa tana zuba musu zobon cikin kofuna tana ce da bakon " Uncle ina wuni?"

Ya dube ta " lafiya lau yar Uncle "gabanshi ya yi wani mugun faduwa ya daure yace "yaya karatu?"

Tace "Alhmdllh, yaya hanya?" Yace "lafiya lau hanya,me sunan ki? Ta mike ta mika musu zobon sannan tace " sunana Aisha".

Ya dubi Abba yace " yanzu ya'yan ka nawa Mustapha?" Abba cikin fara'a yace "su hudu ne" Aisha fita sannan ta dawo ta kawo masu abinci Ummanta tana biye da ita cikin fara'a suka shigo ta gaisa da Alhaji Sadik Usman dan mutan KT,ta zauna tana zuba musu abincin tana cewa "yau dai naga Alhaji Sadiq KT"  Alhaji Sadiq ya dubi Abba yace " Friend kace kaima ko yaushe kana labari na?"

"Sosai ma" inji Abba ya cigaba da cewa "ai kai ba abokin da za a manta dashi bane"

Sukayi dariya.

___________
Kwance a masaukin baki na sukuni (Guest House) da ke nan cikin Dutse,Alhaji Sadiq ne zurfi ya yi cikin tunani,ko shakka ba ya yi Aisha yar abokinshi Mustapha ita ce yarinyar da duk sanda ya yi Istihara yake gani cikin mafarkinsa,kuma ita ce Malam Mamuda ya kwatanta masa cewar ita ce uwar ya'yansa.

Sai yanzu ya tuna wata tattaunawa da suka yi da Malam Mamuda ya sanar da shi cewa yarinyar da zata haihu da shi  tana wani gari ne mai nisa da Katsina,kuma a cikin Istiharar ta shi yana zaton akwai matsaloli can kasa cikin al'amuran,ya sani matsalolin ba za su wuce na kaddarar da ke faruwa kan duk matar da ya aura ba,ya sani ba kowa zai yarda ya ba shi auren yarsa ba matsawar yasan wane ne Alhaji Sadiq K.T.

Mikewa ya yi yana kai komo cikin masaukin nashi,ko dai ya sanar da aminin nashi matsalarshi? To in ya gaya mishi anya zai yarda ya ba shi auren yarsa Aisha? Me zai yi yanzu? Alwala ya yi cikin toilet ya fito ya cire kayan barcin shi ya maida jallabiya ya tada kabbara zabin Ubangiji ya shiga nema tare da addu'ar Allah ya kawo mishi mafita cikin lamuranshi,cikin barcinshi yake ganin yarinyar zaune tare da wasu yan yara guda biyu masu kyau da kuma kama da shi.

Da safe ya fito cikin yadin boyel fari tas,ya murza hula kube fari ya fi yawa jikin hular,takalmanshi sawu ciki ne suma farare kamshin sa tun fil'azal ya na tashi.

Alhaji Sadiq kyakkyawan Bakatsine ne,dogo mai cikar zati yana da kyau,tare da kwarjini,wankan tarwada ne fatar shi kurum in ka kalla ka san cewa ta goge da hutu,kamshinsa kawai zakaji ka san ya kama kasa,gidan Friend din ya nufa wanda ba ya da nisa daga masallacin dake bakin titi wato kan layin in an fito.

Aisha ce sanye da dogon hijabi ya fasa shiga layin ya tsaya,ya sauke gilashin motar,ya leko "ina za ki je ne Aisha?" Ta dubi gurin motar,ta dan saki fara'a.

"Sannu Uncle,Ina kwana?"

Yace "lafiya lau Aisha,ina zaki je?" "Zan je hadda ne."

"Ina Abbanki?"

"Yana gida,yanzun naji ya ce za yaje gurinka."

"To shigo in kai ki."

"Ba nisa Uncle,kuma gurin lungu ne mota bata shiga sai dai mashin."

Ya miko mata sabuwar dari biyar "ki hau mashin din" 

"A'a ka bar shi,Abba ya ba ni."

"Eh amshi nawa."ta amsa sannan ta ce "nagode" ya ja mota ya tafi.Tafiya take amma ranta cike da tunanin kyautar da ya yi musu ta jiya,dubu hamsin ya basu wai a sai musu sweet bai samu ya yi masu tsaraba ba.Kai gaskiya Uncle yana da kirki,ya burge ta musamman ma da ta ji taimakon da ya yi ma Abbansu,Allah ya ba shi haihuwa,ta kula burin shi kenan,in ta yi la'akari da yanda ya yi ta nuna sha'awar su.

Ya fito da mashin don zuwa masaukin Friend din nashi sai kuma ya hango motarshi tana shigowa cike da fara'a suka tari juna.Tafawa suka soma yi tare da kiran juna,Friend kamar yanda suke yi zamanin suna B.U.K "ina zaka da?" "Gurin ka na nufa" "da kaje ma sai dai mu dawo don kunu nake son sha,sukayi dariya sannan suka nufi cikin gidan,kunnun tsamiya Umma ta yi da kosai,ya ci sosai ya ce "kai na dade rabona da na ci wani abu kamar yau. Ina son wadannan abubuwan amma ba na samu"

"Ban gane ba ka samu ba iyalinka ba za ta yi maka ba?" Dan tsaki ya yi sannan yace "kasan matanmu mace tana ganin kana da hali shi  kenan sai ta kwanta wani kato dole za ka dauka yana muku girki kana biyan shi"

"Allah ya kyauta " inji Abba "amin dai" Abba yace "Yauwa inason in tambaye ka,shin ka taba neman taimako daga Malamanmu na addini domin samun haihuwa? Sannan me likitar suka ce kan matar ka?"  Alhaji Sadiq ya gyara zama ya sani yana da abokai da yawa,amma ko da wasa bai hada su  da Mustapha ba,dan shi yana da amana tare da zurfin tunani,in ya baka shawara za ya yi wuya kaga rashin fa'idar abin.Tuno hakan yasa shi sanar wa abokin nashi abinda ke ranshi game da matsalarshi,ya dube shi friend ka san wata matsala? Abin ala'ajabi duk inda muka yi yawon ganin likita sai ace Jummai ba za ta haihu ba,saboda ta yi amfani da kwayoyin hana daukar ciki kuma sun lalata mata mahaifa su ko Egypt da muka je cewa sukayi an taba mahaifarta ne sakamakon cire ciki da ta yi.Abin ya bani mamaki sosai,amma ta musa min,kuka sosai ta yi tare da ce min sun mata sharri ne ban da tacewa tunda yar'uwata ce dole ne na rufa mata asiri.

Abba ya ce "to me ya hana ka ka kara aure?"

Yayi dan guntun murmushi irin na damuwa din nan,sannan ya ce " Abokin Alhajinmu ya ba  ni auran yarshi Murja,karamar yarinya mai kyau da kyan hali,aka yi bikinmu,amma cikin rashin sa'a a ranar da ta cika sati biyu ta ce ga garinku nan? Tana sallar asubahi ya ci gaba,ranar da ta cika kwana arba'in da mutuwa aka daura min da kanwarta,abin al'ajabi kwanan ta goma ta ce ga garinku nan,cike da zargin wani abu Abba yace " ba a gwada ta aka san mene ne musababbin mutuwar ta ba?" "Likitoci sun gwada  ba wata guba ko duka ko irin toshe numfashi din nan sam,bayan yan watanni bayan rasuwar ta na hadu da wata yarinyar layin su Hajiyarmu,Jamila ta dawo Islamiya na tsaida ita,dabi'unta da yanayin maganar ta sun sata shiga raina,ta nuna min gidansu zuwana uku manya suka shiga maganar saboda an san juna tsakanin gidanmu da na su,Hajiya Jummai matata itace ta hada min akwatuna matsayin gudunmawarta,don itama tana son ta ganni da dan kaina kamar yanda kullum take min korafi.

Bayan biki na shiga yin amarci tare da sabuwar amaryata.

Ranar dana cika kwana bakwai na bar dakinta,ran kwana tara na dawo mata.Ina cikin yin auratayya da ita sai na ji yarinya bata motsi sai na tsaya na dubata,abin al'ajabi sai gawa."

Ya yi shiru,sannan ya furzar da wani huci mai zafi saboda tuno tashin hankalin da ya shiga ranar,ya dafa Abba sannan ya ce, "wallahi Mustapha ba zan iya shaida maka tashin hankalin da na shiga ranar ba"  Abba cike da mamaki yace "ikon Allah,ba ka samu malamai ba don taya ka addu'a? Duk da cewa mutuwa ta Allah ce".

Ya cire hularshi ya ajiye "me ka ji ma tukunna" ya cigaba "Alhajinmu da kanshi ya tashi muka je gurin Malam Mamuda,Malami ne mai takawa ba irin na tsibbu ba addu'a muka bukaci a taya mu da ita sai ya ce za yayi Istahara kan al'amarin ya bukaci mu tafi bayan kwana biyu uku mu dawo,sanda muka dawo cewa ya yi mu ma muje mu cigaba da addu'a,ya ga matsaloli da yawa,sannan kuma zan samu haihuwa ko nan kusa ko bayan shekaru.Sannan matar da zata haifa man yaran yarinya ce karama,kazalika akwai sanayya kuma tana nesa da garin katsina,yar fara ce mara jiki.jin haka na soma neman aure a wajan Katsina,farko na auri Rukayya a Kano,kwananta sha daya itama ta ce ga garinku nan,faruwar haka sai mutane suka shiga cewa kila ma arzikina da yake bunkasa ina cikin kungiyar asiri ne,wasu su ce yankan kai nake yi sai jama'an gari suka shiga tsorona har ma ba a barin yara su bi ta layin gidana,ban damu ba.

Wata rana na je Kaduna don siyan wasu injina da banki ya yi gwanjonsu,saboda bashin da yake bin wani kamfani.

Mun fito cikin kamfanin inda na dudduba injinan,wata yarinya na gani yar siririya ta min yanayi da yarinyar da Malam Mamuda ya ce min zata haihu min take na ce ke mai gyada kawo,wadanda muke tare sun sha mamaki ganinsu mutum kamar Alhaji Sadiq K.T ya sha karfin wannan gyadar,nace "gyadar ta nawa ce?" Ta ce "dari uku" na bata dari biyar,"je ki bawa almajirai sadaka,ta ce "to ba canji" na ce "ina ne gidanku in ba nisa je ki samo" ta ce "Badikko ne" na ce jeki na bar miki.

Bayan munyi sallama da Manajan Bankin duk da ya so mu tattauna sai na sallame shi na ce mishi nan zan kwana,gobe zan zo mu tattauna.Injina sun min,don haka inaso sai gobe zan zo na  shiga mota na ce da direba mu bi yarinyar nan,ya ce "Yallabai ban san in da ta yi ba ,na nuna mishi wani titi nan naga ta bi,mu bi mu na kan titin Ahmadu Bello way ne,ita kuma ta bi titin da zai kai ta gidan Gwamnatin Kaduna ne.

Muna bi kuwa sai ga ta can ta yi nisa, kadan-kadan muke bin ta har muka ga gidan su,ba tare da bata lokaci ba nasaka direbana ya yi sallama da Maigidan,na gabatar da kaina matsayin mai son 'yarsu kuma na yi musu bayanin daga inda nake.

Ban samu matsala ba,cikin wata biyu suka bani auren yarinyar,abinda ya tsaya min a rai shi ne,yarinyar ba ta sona sam,sai ina ganin zata so ni nan ba da jimawa ba,da zaran ta haihu.Yarinyar nan kwananta tara itama ta rasu.

Na tsorata kuma daga kanta na yi alkawarin na daina aure,kuma na hakura da haihuwar,haka muka ci gaba da zama ni da Jummai.Hamshakiyar mace ce mai son hutu,tana da masifa tare da raini ga talaka....

######
[12/8, 08:05] Ummi Tandama😇: ____________________________
   *📗MUMMUNAN ZATO📗*

                       *NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

             *Ɗandano page 2*

*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*

```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank       sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*

*Masu son  tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427

Hamshaƙiyar mace ce mai son hutu, tana da masifa tare da raini ga talaka amma game da zamantakewata da ita tana min biyayya. Mun shafe ku san shekara Bayan rasuwa Hafsat,wata rana naje Zariya sai na yi shawara na ƙarasa Kaduna in gaida Iyayen Hafsat, domin duk matan da na aura ban yada iyayensu ba, duk sanda muka fitar da zakka ina aika musu, haka nan Azumi ko sallah.

Cikin yardar Ubangiji na gaishe su tare da musu ihsani,sai na ɗauko hanyar tafiya daidai shataletalen Bankin Habib nan Shehu Musa Ƴar'adua House, tsautsayi kurum ban san ya ya aka yi ba kurum na buge wata yarinya,tana ɗauke da tiren ƙwai duk da ba taji ciwo ba,sai da na kai ta asibitin Fotifo don su dubata, sannan na kai ta gidansu da ke Abakwa.

Wannan ne silar auren Amina itama sai ta bi ƴan'uwanta,kai wannan yasa nima na san babu lafiya,mata shida? Jummai kam kuka take tana ƙara wa tana faɗin wannan sai wani ya ce da sa hannun ta,na ce babu saka hannun ki Jummai ba ke ki ke halitta ba, kuma ba zaki iya kashewa ba so kada ma ki saka ma ranki wannan."

Ya dubi Abba "My Friend ka san wani abu?" Abba da tsananin al'ajabi ya hana shi magana ya ce "ina jin ka sai ka faɗa". "wallahi sai da nayi aure tara ban da Jummai fa, kuma ban taɓa maida wata ɗakin wata ba,sai dai itama na bata wani ɗakin. Ta taran ma an kai ta kamar yau, washegari ta yi sallar Asubahi ta koma ta ɗan kwanta ashe ƙwanciyar kenan.Tun sannan na haƙura domin sai na ke ganin kamar ni ne ma ke kashe su,ji nake kamar sun rataya a wuyana. Ranar na je gaida Malam Mamuda ya ba ni addu'o'i tare da nafilfili sannan ya bani Istihara na je na yi da kaina tunda na soma Istihara ɗin nan wata yarinya na ke gani yawa yawan mafarkan da nake yi na kan ganta da yara,na kan ce to ni dai na haƙura ba zan kuma taƙalo wani aure ba.

Abba ya yi nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya ce, "shin Friend ba ka zargin maiɗakinka ko? Kasan mata sun tsani ba haihu ba wasu su zo su haifa.Alhaji Sadiƙ ya girgiza kai sam ba na tunanin haka zahiri Jummai tana da masifa tare da rowa, wulaƙanci da sauran wasu halaye, amma ba ta shige-shigen malamai ina ganin maƙonta ma ba zai barta ta iya bawa malamai kuɗi ba, nafi tunanin ko ina da wasu iskokai ne. Abba ya ce"kenan nima ina ganin friend lokaci ya yi da zan ga irin taimakon da zan maka na daɗe inason in ga nima na maka wani abu amma hakan bai samu ba, saboda duk wani da zan yi tunanin baka kafini ta ko'ina nima lokaci ya yi da zan nema *maka* mafita gurin Ubangijinmu."

Alhaji Sadiƙ ya ce "na ji daɗi sosai Friend Allah ya ja mana gaba,sai dai ka san irin gurin Malaman da za ka gurin su saboda aƙwai masu kauce hanya" Abba ya ce "kada ka damu ni kaina bana ra'ayin su" Alhaji Sadiƙ ya ce "dama kuma ina son maka albishir da cewa in har mun gama daidaitawa kan maganar kamfanin da na yi maka maganar shi a Jigawa, zan damƙa kula da gyaran shi a hannunka, sannan in an kammala gyaran ina mai farin cikin shaida maka insha Allahu kaine za ka zama Manajan kamfanin"kallon shi kurum Abba ke yi ya ma rasa me zai ce, Alhaji Sadiƙ ya yi murmushi ya tuno sanda suke makaranta duk in kaga ya yi shiru yana mishi irin wannan kallon to ya yi mishi alkhairi,don haka ya dafa shi tare da faɗin"a'a Friend kada ka ji komai" Abba ya miƙe tare da tuno baya.wannan kalmar Sadiƙ ke furtawa in yaga yayi shiru ya kasa godiya sai ya ce dole inji komai Friend sai yaushe ne ni zan taimaka maka? Haka shi kuma kan ce lokacin yana zuwa,sai kuma suka saka dariya, tare da tafawa saboda sun tuno baya, sannan Abba ya ce"nagode Friend, Allah ya shige mana gaba, kuma kaima Allah ya cika burin zuciyarka," "amin" inji Alhaji Sadiƙ.

A gajiye ya fito daga cikin motar,yana saka ƙafa cikin falon Hajiya Jummai tana isowa gurin, rungume shi ta yi tare da faɗin "Oyoyo Abubakar Sadiƙ ɗin a" shima matseta ya yi a jikinshi yana shaƙar daddaɗan ƙamshin ta.

"Na yi missing ɗin ki da yawa"

Cikin jin daɗi ta ce, "har ka kai ni?" Ya kalli manyan idanunta "Na ma fiki,yau fa kwanana huɗu a Jigawa" tace "to zamu gani anjima" ya shafi wani sashe na jikinta tare da faɗin "kin min tanadi kenan? Ta ja shi ciki "kai dai muje ka yi wanka ka cika tunbinka, daga nan sauran labari ya biyo baya" Suna cin abinci ne yake bata labarin nemo abokinshi da ya yi, ta washe baki "kai na yi murna, yaushe ne za ka koma? Nima da na bika mun saba da Iyalinshi,ya ji daɗi don ba zata za ta mishi maganar da mahimmanci ba,don haka sai ya ce, "kada ki damu,ai tunda Allah yasa yanzun mun gano juna, mutuwa ce kurum zata raba mu.Shi yasa ma kamfanin da na je maganar shi, Allah ya yi mun daidaita ranar Monday zan tura musu kuɗin su, shi na ba kwangilar gyara kamfanin tare da ɗora shi Manaja in komai ya kammala. Nan take yaga fuskar ta ta sauya, sannan ta ce " ba fa a yiwa ɗan adam saurin yarda,yanda mutanen duniya suka lalace da son kuɗi"

Ya aje cokalin hannun shi Sannan ya dube ina zaton na jima ina miki bayani  halayen dattako tare da riƙe amanar da Friend ya ke da shi kar ki ji komai." Ta yatsina baki bata kuma magana ba,shi ko miƙewa ya yi don ya shiga ɗakinshi,ya warware gajiya. Yana shiga wayar shi ta soma tsuwwa,ya duba. Murmushi ya yi tare da ɗaga wayar.

"Friend na iso har na yi wanka, kuma na ci abinci yanzu ma ƙwanciya zan yi" a can Abba ya ce" to Alhamdulillah,na barka lafiya ka huta."

Umma ta dubeshi "Abban yara mene ne abin damuwa kan wannan? Ai abin murna ne sai muyi ma Allah godiya." Ya ce"haka ne Umman yara,ina tunanin amana ne,kin san amana tana da wahala,sai dai Allah ya taya mu riƙo" ta ce"Amin".

A'isha ta shigo da sallama ta zauna cike da fara'a,"Abba nagode da siyayya, gaskiya ban taɓa sa'ar samun guzurim zuwa makaranta kamar wannan ba." Ya yi murmushi,"Uncle ɗin ku ne ya ba da yace ai miki siyayya, " ta ce kai gaskiya Uncle akwai shi da kirki,ina jin tausayin shi gashi Allah be  Baby ba" Umma ta ce"Allah zai ba shi insha Allahu" Abba ya miƙe domin zancan su ya yi mishi tuni ne da wani al'amari da ke gabanshi.

Zaune ya ke gaban Malam Dari,ya koro ma Malam Dari bayani kan matsalar abokin nashi,shi kan shi Malam Dari ya jinjina matsalar, sannan ya ce zai yi wasu bincike a kai, bayan ya tambayi sunan abokin Abba,ya ce mishi Alhaji Sadiƙ Usman,Malam Dari ya ce ka bani zuwa gobe ko dai ma jibi ka zo kaji batu,,ya miƙe bayan ya ajiye mishi dubu ɗaya, tare da faɗin "Ga sadaka" Malam Dari ya ce "to Allah ya karɓa,kuma ya shige mana gaba."sai na ganka" "to" inji Abba "sai na zo ɗin kenan."

___________________________
Ya yi parking a harabar gidan mahaifan nasa,ya fito ɗaukacin masu hidima a gidan suna ta isowa don gaishe shi,shi kuma ya shiga amsa musu ya shiga yi musu ihsani, kamar yadda ya saba, duk sanda ya zo, sannan kai tsaye ya nufi falon Hajiyar mu.

A zaune ya same ta kan kujera.Dirariya mace mai kyaun haiba, tare da taƙawa.tana da son addini,kana ganin ta ka san itace mahaifiyar Saddiƙ, tana taimako musamman asibitoci zuwa masallatai, cike da fara'a ya shiga ya zauna gabanta ita da shi suna yiwa juna kara nauyin shi kasancewar shi ɗan fari shi kuma bai shaƙu da ita ba,shi yasa ya ke jin nauyin ta, yanda ya zauna gabanta da ace akwai mutane a gurin tashi zatayi.

Ya dube ta, sannan ya sunkuyar da kai. "Ina kwana Hajiyar mu?"

Ta amsa da "lafiya lau, ashe ka dawo?" Ya ce"eh,na dawo jiya ban samu shigowa in duba ku jiyan ba, dafatan za ku min afuwa?" Ta dube sannan ta kauda kai, tunda dai an iso lafiya Alhamdulillah,ina kuma fatan tafiyar ta yi nasara?

Ya yi murmushi.

"Nasarori ma kuwa, domin bayan nasarar sayan kamfanin na haɗu da Aminina Mustapha Gumel, wanda ko yaushe ya ke raina." Ta dube shi tare da faɗin"ikon Allah! Lallai tafiya ta yi nasara, domin ba ta manta yanda koyaushe yake ɗalibta da batun Mustapha Gumel. Ya ce"Alhajinmu yana nan?" Ta kalli gefen ɗakinshi, "yana ciki amma yanzun zai fito."

rufe bakinta ya yi daidai da fitowar Alhajinmu,miƙewa tsaye ya yi tare da faɗin,"sannu da fitowa Alhajinmu" ya amsa da cewa"yauwa Abubakar Saddiƙ ,ka dawo lafiya" daidai sanda ya zauna,shima Saddiƙ ya zauna inda dama yake "lafiya lau kuma anyi nasara" ya shiga yi mishi bayanin yanda kamfanin yake girmanshi zuwa kyan injinanshi tare da gyare-gyaren da za a yi, sannan ya bashi labarin haɗuwarshi da abokin nashi tare da hukuncin da ya yanke.Alhajinmu ya ce," to Allah ya yi jagora?". Hajiyar mu ta yi gyaran murya, alamun zata yi magana, sannan ta ce "Fatima ta ce a gaya maka alkawarin motar da ka yi mata, Nafisa kuwa tayo waya daga can makaranta ka tura mata kuɗi don kuɗin ta sun ƙare."

Ya yi murmushi.

"Nafisa ƴar auta, ta dai kusa gama karatun nan ta huta."

Alhajinmu ya ce"ai ni na ƙosa ta ƙarasa karatun nan,na fi son auren ta." Sadiƙ Ya ce"insha Allahu zata yi Alhajinmu."  dube shi "Dama na jima ina zargin kai ke ɗaure mata gindin ƙin auren nan ko?" Ya yi ƴar dariya , "ba haka ba ne Alhajinmu, Allah za ta yi ka san shi aure lokaci ne, kuma insha Allah kwanan nan zata yi" Ya miƙa ta Saddiƙ ni zan fita zuwa ofis, da akwai masu jirana." Cikin tausayawa Alhaji Saddik ya dubi tsohon nasa, sannan ya ce"ya kamata Alhajinmu ka zauna ka huta da zuwa ofis ɗin nan tunda ina kula da kusan duk harkokin ka,na fi son ka huta."

Cikin jin daɗi Alhajinmu ya ce "kada ka damu Saddiƙ,nima ina jin tausayinka ne abubuwa sun maka yawa,ni dai roƙona ga Ubangiji koda yaushe bai wuce Allah ya baka mai rama maka, inason naga zuri'arka."

Zan can Alhajinmu ya taɓa shi,don haka shima sai ya yi shiru yana jin wani abu a iranshi sai yana jin tamkar ya yi shela ya gaya wa matan duniya cewa duk wadda ta haihu da shi zai raba dukiyar shi ya bata rabi, Hajiya dake zaune tafi su damuwa tana matuƙar son ta ga ƴaƴan ɗan su namiji guda ɗaya,shi kaɗai ne namiji gun su sai ƙananan shi mata guda uku,Sadiya ta na auren ɗan gidan Sarki, Fatima tana auren shugaban ƙaramar hukuma.sai auta Nafisa ƴar lelen yayan ta Saddiƙ,yana matuƙar son Nafisa,sai dai kuma sam ba shiri da matarshi Jummai, duk da kasancewar ta ƴar uwar su. Ya fito don raka Alhajinmu wurin mota sannan ya dawo gurin Hajiyar mu don ƙara gaisawa duk da ba wata hira suke yi ba,yana son ya ganshi zaune gaban ta sai ya dinga jin shi tamkar ɗan yaye.

*Page 3*

Abba zaune gaban Malam Dari,suka gaisa da masabaha,sannan Malam Dari cikin al'ajabin abinda binciken shi ya nuna mishi,ya soma magana.

"Malam Mustapha,bayan kai abokin ka yana da wani Amini a garin nan?"

Ya girgiza kai,"ba shi da wani aboki da ya wuce ni." Ya gyara zama " abinda na gani cikin Istaharata shine,zai auri yar Amininshi da ke nan garin,abinda na yi ta bincike. Nayi bincike zata mutu ko bazata mutu ba,zata haihu ko bazata haihu ba? Allah be sa na fahimta ba,amma lallai yarka ce mata ta goma  sha daya da zai aura,kuma kila ta zama uwar ya'yanshi,Allah shi ne masanin gaibu."

Zufa ce ta keto mishi ko ta ina. Ya yi shiru yana mamaki,can ya ce "Malam...." Malam Dari ya katse shi da cewa Istihara ce,in kana shakku kaima bari in baka kaje ka yi ta,ka yi ta da kyau insha Allahu ko cikin mafarki ne Allah zai nuna maka."

Bayan barin shi gidan Dari,guri ya samu ya zauna don jikinshi ya yi sanyi,shi kan shi ya kasa sanin dalilin da ya sa shi shiga cikin tashin hankalin duk da hana zaton baya rasa nasaba da mutuwar da duk matar da Alhaji Sadiq ya aura take yi. Yana son yin nazari kan lamarin,da kyar dai ya isa gida.Umma taso ta gane yana cikin damuwa ganinshi da ta yi wani iri,amma  dage mata ya yi kan cewa babu komai kanshi ne ke dan ciwo yama sha magani,sallah yake son ayi ya samu ya dan huta kila bacci ne.

Bayan ya yi nafilar sannan ya gabatar da addu'o'in kamar yanda Malam Dari ya yi mishi bayani. Ya kwanta shiru maimakon bacci sai tunanin yanda zai yi,shi dai damuwarshi daya kada ya bashi itama ta mutu. To zai iya hana Saddik wani abu nashi? In ko ya yi haka bai yi butulci ba kuwa?Me zai sa ya manta da abinda Aminin nashi ya yi mishi a baya? Sai dai kuma yana tausayin Aisha,don yarinya ce karama,kashinta bai yi kwari ba. To ko dai ya yi shiru ne tunda Aminin nashi bai san komai game da maganar Malam Dari ba? Nan take wata zuciyar ta soki hakan,da cewa ka sani ko tun can Katsinan an gaya mishi cewa yarka ce zai aura? Nan take ya yardar ma kanshi cewa ga shi ma ya misalta mishi cewa tsakaninsu da nisa,tabdi! In ko Sadiq ya sani dole ne ma ya hakura da Aisha,ya aura mishi koda hakan ya na nufin itama zata bi 'yan'uwanta,wato matan da ya yi ta aure suna mutuwa. Da wannan tunanin bacci ya yi awon gaba da shi.

Aisha ya gani cikin mafarkinshi goye da yaro,sai dai ba ta walwala,tana tafiya da alama cikin tashin hankali ta ke. Firgigit! Ya farka ya na addu'o'i,ya koma ya kwanta yana tausayi 'yar ta shi.Karama ce Aisha 'yar shekaru sha biyar,ga ta siririya,damuwar Aisha ita ce karatu. Tana da burin zama likita,ko yaushe ta zo hutu daga makaranta sai tace Abbanmu don Allah ka cika min alkawarin da kai mini wanda ka ce insha Allah sai na zama likitar mata,ni ina son na taimaki musulmi,ya kan ce insha Allah zaki zama,Aisha kin ma zama in dai kin dage da karatu,wannan burinta ne tun tana yarinya,gashi Allah bai yi ba. Tunda a daren ya yanke hukuncin ba yar da Aisha ga Amininsa,sai dai ya kwana addu'a,Allah yasa ita ce uwa ga yaran shi,Aminin nasa.

Da safe gurin karin kumallo bayan sun gama ya sallami 'yan mazan sannan ya dubi Ummar su "ina kawallin ta ki ? Ta ce "ta na dakina,tana gyarawa." Ya ce " da ta bari ta karya ai ko?" Umman ta dube shi "ka manta yau alhamis ? Aisha tafi mu kokarin Azumin nan na Litinin da Alhamis,tun dan zazzabin da ka yi kwanaki ni da kai muka saka shiririta cikin azumin"'. Ya gyara zama "shi yasa ina matukar son Aisha ,duk da haka kuma gashi lokaci ya yi da zamu rabu,ta dube shi da sauri "ban gane zaku rabu ba? Ya dan yi jim sannan ya ce "Aure zan mata" da sauri ta mike,"Aure! Aure dai? Ya yi karfin hali,"mene ne to na daga hankalin?". Ta zauna cike da damuwa,tare da fadin "dole ne na tada hankali,to ko dai kana tsokanata ne?" Ya dube ta" kin ga  na taba miki irin wannan maganar?" Ta girgiza kai tare da shafe zufar da ke keto mata, "amma Abban yara Aisha ba ta isa aure ba,gata dama ita ba kiba ba baka ganin da kwara?".

Ya girgiza kai ba wani kwara a  cikin aure,bautar Ubangiji ne,bana son ki nuna damuwarki,har ki karya mata gwiwa ina son mu lallashe ta nasan zata damu ko don yanda take matukar son karatu,ki bani goyon baya,nima inason na rama akhairan da Aminina ya jima yana min ne,wato Alhaji Saddik." Ta dube shi.Tsura mishi ido ta yi "Alhaji Saddik za ka ba ta?" Ya ce "shine" shiru ta yi yace "me ki ka ce?" Ta girgiza kai " babu komai,sai dai tausayin ta,yarinya ce ga shi kuma suna katsina ba kusa ba ne" ya ce"kada ki damu,aure babu in daba ya ksi mutum,batun yarinta kuwa duk ba komai bane,shekara kusan sha biyar ai ta girma,jiki ne ba  ta dashi.Nasan Friend za ya kula da ita,yanzun kira ta in sanar da ita" Cikin jimami ta ce " To Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Ta tashi ta kira Aishan,kallon ta yake yi a ranshi shima yana kara tausaya mata,saboda sam batada kauri don tsinken hannun tamkar na yara kanana.

Ta zauna kusa da Umma ,kuma ganin Abban nasu ba da alamun wasa ba,yasa ta nutsu ta san magana ce mai mahimmanci zai mata,kila batun komawarta makaranta ne nan da kwana hudu,ya katse mata tunaninta da fadin "Aisha" ta amsa "na'am Abba." Ya ci gaba "ina son zan miki wata magana,sai dai ina shakka." Cikin mamaki ta dube shi,sannan ta ce "Shakka Abba?" Ta ci gaba "bazan so in zama 'yar da iyayenta za su rinka shakka a kanta ba,domin bani da burin bijire ma umarnin ku,ko haninku,ka fadi ko ma me ka keson fada ba tare da shakka ba." Ya numfasa tare da jin dadin maganar ta,sannan ya furta zancan zan miki aure ne." A tsorace ta dube shi,domin batayi zaton faruwar haka ba,amma sai ta dake ta kuma hadiye wani abu da ke taso mata ,ta ce "to Abba." Ya ci gaba "kuma Alhaji Sadiq wanda yazo daga katsina,shi na zaba miki." Kanta na kasa ta ce "to" Ta dube shi kamar zata yi magana,amma tana jin da ta bude baki hawaye zai zubo mata,don  haka sai ta yi shiru.

"Ki yi magana mana." In ji Abba,don ya fahimci tana son ta yi magana ne ta fasa.Sai ta yi dan murmushi sannan hawayen data ke makalewa suka zubo,ba ta share ba,ta ce "dama zancan karatu ne zan yi sai kuma na tuna cewa ai babu sauran karatu."

Tausayinta iyayan suka ji,Abba ya ce " insha Allahu za ki ci gaba,yanzun ma zaki koma kafin mu tsaida lokaci,ina so  ne dai ki sani,ta ce "to" ya ce " tashi kije,Allah yayi miki albarka."

Wanka ta shiga,amma zama ta yi a bayi ta kasa wankan,tunaninta shin mene ne dalilin Abba na aurar da ita bayan ya yi mata alkawarin zama Doctor? Kuka ta yi sosai cikin bayin,tana tausayin kanta, Ta sani duk yanda aka yi Abba yana da dalili mai karfi  na yin hakan gare ta,sai dai ta sani ba yana nufin cutar da ita ba ne,ba ta taba soyayya ba,ballantana ta ce bata son shi,ta sani dole ne ta girmama shi musamman in ta tuna taimakon da ya yi ma mahaifinsu,gashi mai kyau da kuma tsafta,ma'abocin kamshin turaruka,ta tuna san da yazo suke falo kamshinsa ya cika gidan ko ina,sam bai yi kama da shekarunsa ba tamkar wani matashi dan shekara talatin,daga karshe dai tayo wankanta ta fito,ko a daki lallashinta Umma ta kara yi,kan cewa kada ta damu.

___________________________
    Hajiya Jummai tana zaune bakin gadonta kafarta daya kan daya,tunanin ta yana can Jigawa ita kam sam ba ta so ba,Alhaji ya yanke hukuncin bawa abokin shi Manajan wannan kamfanin ba,bayan ta jima tana mishi maganar kaninta,bataso ta ga wani kusa da dukiyar mijinta domin duk abinda ya tara nata ne,tunda ba d'a gareshi ba,don haka dole ta kula da dukiyar ta,ta san kuma  tunda shine gaba da ita zai rigata mutuwa,dole ma ta san matakin dauka kan wannan kamfanin bari dai ta bari a gama gyaran.

Dai dai yayi parking wayarshi ta soma tsuwa,ya duba Friend ya furta,sannan ya dauka.

"Assalamu alaikum,Friend mun wuni lafiya?"

"Lafiya lau Friend.Alhaji Saddik ya fada.

"Yarana suna lafiya?"

"Lafiya qalau,batun aiki ne nake son ce maka an kusa kammalawa,sannan sai batun taimakon da na ce maka zan nemo game da matsalarka.  Da fatan kana da lokaci zan maka bayani." Alhaji Saddik ya ce " ina jinka,ni kadai ne." Abba ya ci gaba...

[11/30, 07:51] Ummi Tandama😇: ____________________________
   *📗MUMMUNAN ZATO📗*

                       *NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

             *Ɗandano page 4*

"Bayan Istihara mun ga alkhairin aurenka da wata yarinya,zan so ka samu lokaci ka zo," Shiru Alhaji Sadiƙ ya yi,can ya ce, "Friend na haƙura da duk wani aure yanzun, mutane sun camfani da yawa,ba na son ƴaƴan mutane su yi ta mutuwa a hannuna....." Abba ya katse shi "kai dai in ka samu lokaci kazo." Yace,"shikenan,na gode."

Sai da ya sauka masauki ya huta sannan ya yi ma Friend ɗin shi waya cewa yana nan a Dutse fa, Abba yace "ka min bazata fa,to bari inzo in same ka inda ka sauka wancan karon ne?" "Eh,nan ne" inji Alhaji Sadiƙ. Ya idar da sallar la'asar yana jan carbi, Abba yayi sallama ya shigo, Alhaji Saddiƙ ya tare shi cike da fara'a tare da yi wa juna musabaha, suka zauna. Sun gaisa Alhaji Saddiƙ yace "Friend ina yaran nawa,sun koma karatu hutu ya ƙare ko?" Abba yace, "Sun koma,ya ya Madam?" "Tana lafiya" inji Saddiƙ, tace in gaishe ku,(ya  ari bakinta ya ci mata albasa). Ya ci gaba,"Naso ince ka zo min da zoɓon nan da nasha a gidan ka"Abba ya yi ƴar dariya,"ai na zata gidan ma zamu je yanzun," inji Abba, "Na fi son mu gama magana a nan shi yasa na sauka,yi man bayani Friend danni fa bana son yanda ƴan garinmu suka shiga tsorona,nan ma in shiga wannan halin" Abba yace "bari dai in baka labarin komai ."nan ya koro mishi bayanin yanda suka yi da Malam Dari, Alhaji Saddiƙ bai ji mamaki sosai ba, saboda ya san ita ce shima ya sha ganin ta cikin mafarkinshi.

Ya dubi Abba, "Friend ban sha mamaki ba, saboda ran da naga yarinyar nan na san cewa ita ce nake gani cikin mafarkina, amma hakan ba zai sa in aureta ba,sam ba zan zama sanadin mutuwar ƴarka ba,bayan haka ma da kunya in auri ƴarka,ai ƴata ce, kuma da kunya sa......." Abba ya ɗaga mishi hannu alamar yayi shiru, sannan ya ce "amma ka san cewa bai saɓa ma Shari'a ba ko? Hasali ma wata sunna ce mai ƙyau ta Manzon Allah (S.A.W) muka yi koyi ko? Ka manta Sayyidina Abubakar (A.S) babban abokin Manzon mu ne, sannan ya aura mishi ƴarsa Nana A'isha, Allah ya yarda da ita,Tana da ƙarancin shekaru, shi kuma ya soma manyantaka,sam wannan ba abin kunya ba ne kamar yanda wasu ke faɗi."

Alhaji Saddiƙ ya ce "Friend yariyar nan ƙarama ce, bayan haka mu duba irin yanda mata suke mutuwa a gidana...."  Abba ya sake katse shi da cewa "kai ne ka ke kashe su?" Alhaji Saddiƙ ya girgiza kai, "To!" Inji Abba,"ƙwanansu ne ya ƙare itama in nata ƙwanakin suka ƙare ko ba a gidanka ba dole ta tafi, batun ƙanƙanta kuwa wannan ba wani uzuri ba ne, iyayenmu ko shekarunta ba su kai ba,me ya same su? In dai baka sonta ne shi kenan."

Alhaji Saddiƙ ya dafa kafaɗar Abba "ba za ka taɓa haihuwar ƴa in ce bana sonta ba,na amsa kuma ban san bakin da zan iya maka godiya ba, saboda kai masoyina ne, cikin kowanne hali,in ba mai sonka ba,wanene zai yarda ya kai ɗansa mahalaka,don ni da kaina sai in rinƙa ganin tamkar gidan nawa mahalaka ce, Allah ya yi maka sakamako ya sa itace sanadiyyar warwarewar al'amurana."

"Amin" inji Abba. "To yanzun yaushe ka ke son matarka?"

Alhaji Saddiƙ sai ya samu kan shi da jin nauyin Abokin nashi,ya yi shiru, Abba ya dube shi "Don Allah Friend kada ka ji komai,ba wata kunya" Alhaji Saddiƙ ya ce "abin ne sai yana ba ni mamaki, ashe zaka haifi ƴa ni kuma in aura?"  "To ai abin Allah ne," inji Abba,"yanzu dai yaushe ne za ka turo sai a saka rana in ta dawo hutu ayi bikin in ya so zan roƙi alfarma koda je ka ka dawo ce don Allah ka yarje mata,don tana son karatu,burinta shine ta zama Doctor."

"Don wannan kada ka damu Friend, insha Allahu ba tun turowa daga naje zan masu Alhajinmu bayani." Daga nan suka ci gaba da hirar aikin gyaran kamfani, bayan sun gama tare da cewa su zo su je gidan nashi, Alhaji Saddiƙ yace"an ya sai nake ganin yanzu kamar gidan zai min wuyar zuwa" Abba ya miƙe "to tashi muje ku gaisa da yarinyar,don tuni na yi mata bayani" Alhaji Saddiƙ ya dubeshi da sauri "Ta amince?" Abba ya yi murmushi "A'isha ba ta musu ko gardama,ƙwarai zaka ji daɗin zama da ita,ko dana sanar da ita ba ta yi musu ba, amma ta yi zancen karatunta,in kaje yanzun ka ga sai ka shaida mata karatun nata yana nan, insha Allahu" "to na gode,sai dai in har bata so dole ne mu bar wannan maganar," murmushi kawai Abba ya yi, sannan ya miƙe tare da faɗin "shiryo mu je, bari na yi waya" ya fita. Umma ya kira ya ce mata ga su nan zuwa su da Alhaji Saddiƙ, kuma yana buƙatar zoɓo mai ɗan sanyi.

Falon Abba suka shiga Umma ta leƙo sun gaisa tare da tambayar Iyalan nashi da kuma su Hajiyarshi,ya ce duk suna lafiya,ta koma kicin inda A'isha ke harhaɗa abinci kan babban tire. Umma ta ɗauka tare da faɗin "Shiryo musu zoɓon bari na kai wannan." Tana direwa Abba ya dube ta, "Ni fa dake zaki haɗa min,Ummansu shi Friend sa mishi nashi shi ɗaya, wannan zuwan ba nawa bane,na ƙawallinki ne." Murmushi Umma ta yi,ba ta ce komai ba ta fita. Ta isko A'isha kicin tana ƙoƙarin fitowa,ƙasa-ƙasa ta yi mata magana.

"Ki natsu ban da wauta, Alhaji Saddiƙ zai yi magana da ke,kada ki ba Abbanku kunya." Ta ce "to" dama tsaf take. Ta nufi falon Abba,ta yi sallama ta shiga.

Daddaɗan ƙamshin sa ya gauraye falon, ta ɗan saci kallon inda yake yana sanye da wani farin shara-sharan yadi wanda har ana iya ganin bes ɗin shi ta ciki. Ƙyan yadin ne ya bayyana tsadar shi,hular shi ƙube ce wadda aka yi ta da farin zare. Ta dire tire sannan ta zauna ƙasa,kanta sunkuye ta ce, "Ina yini Uncle?" Tun shigowarta ya ke kallonta, duk da cewa sanye take cikin hijabi bai hana shi ganin rashin jikinta ba, shi kanshi tausayinta ya ji ya amsa da cewa, "lafiya lau ƴar Abbanta." Ta miƙe ta soma ɗauko plate don zuba mishi cous-cous, ya ce "bar shi Nana A'isha,ba ni zoɓon nan nasha bana jin yunwa," ta ce "to" ta soma zuba mishi cikin kofi ta rage tsawo ta bashi,hakan ya burge shi, sannan ta koma mazaunin ta ya dube ta,ke ce kikayi wannan zoɓon?" Ta ɗaga kai alamar "Eh" ya kuma kafa kofin a bakin shi ya shanye ragowar na cikin kofin.

"Kice zaki dinga haɗa min in kin koma gidana can Katsina? Ko ba za ki je Katsina ba?" Cikin cinyoyinta ta tura kanta,ya ce "Gaya min in ba ki son zuwa don bana son ki takura." Ta ɗago kanta ta ɗan dube shi "in dai zan dinga  zuwa makaranta ai ba komai," ya ce "da gaske ki ke yi?" Ta ɗaga kai ya ce, "To za ki yi karatunki in ma makarantar da ki ke,ki ke so zan bar ki kiyi abinki,yanzun yaushe zaki koma?" Ta ce"jibi" ya ce "to shikenan,in na kai jibi a garin nan sai na kai ki." Ta ce,"To" bai san me zaice mata ba ma,yana jin nauyin yi mata magana, hannu yasa cikin aljihun rigarshi ya ciro bandir ɗin ƴan Naira ɗari biyu "Gashi kiyi shopping" ta ce,"A'a,ka barshi na gama shopping ai" ya yi yayi taƙi amsa,ta nufi cikin gida. Abbanta ya ce har kun gaisa?" Ta ce "Eh," ta shige ɗaki bakin gadonta ta zauna. Mutumin yana burge ta, ya iya gayu mai ƙyau da shi, tunda ya ce zatayi karatu ba ta damu ba, sai dai zata yi kewar Ummanta da Abba.

Washegari tafiyarshi ta kama,don haka ba zai samu kaita makaranta ba, Abba ya ce kada ka damu,dama da akwai motar da ke kai su, kuma ita ce ke ɗauko su. Ya ciro ƙwalin waya ƴar mai ƙyau ƙirar (Nokia), "Gashi ka ba ƴar gidan tawa in dai babu damuwa, saboda kasan ba zan dinga samun zuwa ba, duk da na san ba za ta da ita makaranta ba,in ta dawo ma ringa gaisawa,don na bata kuɗin ne taƙi amsa shiyasa na siyo mata da na fita ɗazun," Abba ya ce "ita da zata koma makaranta ka sai mata waya?" Alhaji Saddiƙ ya ce ka dai bata ƙila ma zata fi amsa min magana a cikin wayar," "shikenan" inji Abba, Allah ya biya maka da gidan aljanna,bari na turo ta kuyi sallama," "a'a ka barta tana jin nauyina yarinyar tana da kunya bana son matsa mata," "shikenan". Suka sake yin musabaha, sannan ya shiga mota sai Kano,ya bar motar a gidanshi na nan Kanon, sai ya hau jirgi.

Labarin da Alhaji Saddiƙ ya zo ma su Hajiyarmu da shi sun ji daɗi, amma suna fargaba sai dai Alhajinsu ya kawo shawarar a miƙe da roƙon Allah,tun kafin bikin,ya ce zai samu malamai kuma zai sanar Masallatai a saka su a cikin addu'a.

Nafisa auta itama cewa tayi Yaya Saddiƙ nima insha Allah zan soma tsayuwar dare tun daga yau. Ya dube ta "kin yi alƙawari fa?" Ta ce "insha Allah,Yaya zan cika" shima dama Allah ya ke gayamawa kullum sai dai ya sha alwashin dagewa.

Ya dubi Hajiyarmu wadda har yanzun ba ta ce komai ba, sannan bai karanci wani abu game da zancan a fuskarta ba,ka ra Hajiyarmu ta yi don haka bata furta komai ba. Amma zancan ya yi mata daɗi, duk da tana fargaban abin, ganin kallon da yake mata yasa ta ce "Allah yasa ma abin albarka."

Yayi ajiyar zuciya tare da miƙewa,can ƙasan zuciyarshi kuwa cewa ya yi "Amin Hajiyarmu".

Nafisa kuwa, dariya ta yi.

Sau da yawa tana mamakin yanda Hajiyarmu da Yaya Saddiƙ suke jin nauyin juna,tamkar surukai. Yace "to ni zan tafi,ban riga na sanar da Jummai ba tukun, sai na koma yanzun."

Nafisa ta ce, "Yaya don Allah kada ka gaya mata".

Kafin ya yi magana, Hajiya ta ce "Don me? Ke Nafisa kin cika fitina," shiko ƴar dariya ya fita yana yi, Nafisa ta bishi tana cewa "Yaya bani lambar A'isha,zan kira ta," ya ce "ayya Nafisa, A'isha yarinya ce ƙarama, gobe ma zata koma makaranta (S.S 1) take a Munjibir, kuma ba wai shekarunta ne suka kaita (SS) ɗin ba, ƙoƙari ne,she is fifteen."

Dariya ta yi.
"Yaya kana son ƙananan yara."

Ya ce,"to Nafisa ƴar abokina ce, shi ya bani duk da yasan matsalar gidana,ki bari in lokacin ziyarar ɗaliban makarantar ta zo in kina gari sai muje ko?"

Ta ce, "to Yaya," Ta koma ciki,shi kam ya shige mota. Ya lura kowa yana son Aisha a dangin nashi, yanzun saura Jummai.

***    ****    ****    ****
Umma ta ce, "Ga wayarki can jikin chaji in ji Uncle ɗin naki, har ma da layi ya saka miki." Ta kalli wayar, "kai tana da ƙyau wayar, sai dai na san Abba ba zai bari na riƙe waya ba, kuma makaranta ma ba zasu bari ba ai".

Umma ta ce,"to ai Abban naki ne ya kawo" ta ɗauki wayar tana jujjuyawa,ga ta ƴar mai ƙyau,na gode. Umma ta yi dariya.

"A'isha kenan,dama ga ki da son yin (Game)."

Tayi dariya,ta zauna tana cewa, "Bari na gani zan gane kan wayar kuwa?" Ba tako gane ba, sai da Yaya Abdurrahman ya shigo, sannan ya koya mata.

Bayan sallar Isha'i,sun ɗan taɓa hira ta ce "bari na ƙwanta Umma,don gobe tashin wuri zan yi saboda komawa makaranta."

Jafar ya ce, "Yaya A'isha ko dai kina son ki buga (Game) ne da wayar?"

Ta ce,"Jafar ka raina ni ko?" Ta shige ɗakinta, gado ta haye tana buga (Game) ɗin (Bounce) kusan goma na dare wayar ta shiga ringing,ta saba da wayar Umma don haka ba taji komai ba,ta ɗauka. Da ƴar zazzaƙar muryarta ta ce,"Salamu alaikum"  ya amsa da "wa'alaikis-salam, A'isha ce?" Gabanta ya faɗi saboda ta gano Uncle ne,ta amsa "Eh." Ya gyara ƙwanciya, "kin san mai magana?" Ta ce "Eh," ya ce to wanene?" Ta yi shiru ta rasa me zata ce,kina jina? Ta ce Umh,ya ce kiyi magana mana A'isha...

#######
[11/30, 21:03] Ummi Tandama😇: ____________________________
   *📗MUMMUNAN ZATO📗*

                       *NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

             *Ɗandano page 5*

Ya ce kiyi magana mana A'isha,wa ke magana da ke? Ta daure ta ce, Uncle ne. Yayi murmushi, "zan zama mijinki kuma kina ce min Uncle? Gara kin kira sunana" ta ce "bazan iya kiran sunanka ba". "To ki samin wani sunan mana ban da Uncle". Ta yi shiru, ya ce "to ba mu gaisa ba" ta yi maza ta ce "Ina yini?" Ya ce "lafiya lau Nana A'isha Saddiƙa,ya ya su Abbanki da Ummanki?" Ta ce"suna lafiya." Ya ce "za ki jini ina kiranki da sunaye duk na ki ne", ta yi shiru, shima ya kan rasa me zai ce mata,can ya ce, to bani labari" ta ce "Na me?" Ya ce, "Na komai mana" ta yi shiru,ya ce "To bani na ƙawayenki na makaranta."

Tamkar ya mata susa,ta ce "ƙawayena biyu ne,da Suwaiba Shehu Ringim,sai kuma Zainab Shitu Katsina, duk suna da kirki."

"Ashe har da ƴar garinmu? Ki ce shi kenan in kin zo Katsina kina da ƙawa, sai kuyi ta wasanku ko?".

Kalmar ta bata dariya, har ma ta ɗan dara kaɗan, sannan ta ce "wasa kuma?" Ya ce, "Eh mana,ko baƙwa wasa a makaranta?" Ta ce "sai ka ce ƙananan yara?" Ya ce "Au,na manta ashe fa ku manya ne,ni da har ina son in saya miki kayan wasa su Tedi, haka su Cartoons." Ta ce "Haba dai?" Ya ce, "To shi kenan bari in bari sai kin haifa mana Beby sai in saya mata ko?"

Zancan ya yi mata nauyi, har ma ta kasa magana,ya ce "A'isha" ta ce "Umh" "kin ji me nace?" Ta ce "Um," "to kin yi shiru" ta ce "Uncle Ina jin bacci," ya ce"shikenan yi baccinki, sannan ki yi mafarki mai ƙyau na ƙyawawan yara masu kama dani" ya kashe wayar.

Shiru ta yi tana mamakin zancan da Uncle ya yi mata,ta yi addu'a ta shafa ta runtse idanu, har bacci ya yi gaba da ita.

Hajiya Jummai wadda ta jima tsaye kanshi tana sauraron surutun da yake yi, sai jikinta ya hau rawa,ta san tabbas da budurwa yake magana, kenan Alhaji aure yake nema? Cabdi! Daga gani kuma ko ma wacece yana sonta,dubi yanda yake wani kashe murya tamkar shima ɗan matashin saurayi ne? Lallai yana neman tada zaune tsaye ne, amma don ta san in har ta nuna ɓacin ranta yanzun ba zata san komai game da yariyar ba,don haka sai ta sako makirci da kisisina.

"Alhajina kai kuma da wa kake samartaka a waya?"

Cike da walwala ya dube ta,sanye take da rigar bacci mai santsi, ɗan gashin kanta da ya rage ta tufke shi da ƙyar ma yake tufkuwa saɓanin da da take da gashin da yawa, tsabar ƙalƙalin da take ma gashin duk ya karye.

Ya miƙa mata hannuwanshi alamun ta zo, sai ta basar ta zauna gefenshi, ta kuma cewa da shi.

"Kai da wa kake waya?"

Ya ce, "ƙanwarki to be insha Allah." Ta danne wani abu da ke son taso mata.

"A ina ka samo ta? Nifa ina jin tsoron ka ƙara aure yanzu in ina tuna baya."

Ya ce"to ni kaina a tsorace nake,ƴar abokina ce na Jigawan nan,wato Mustapha Gumel."

Ta miƙe da sauri tare da faɗin "Dama na san za'ayi haka,wato yaga kuɗi za'a ɗora shi manajan kamfani ba dole ba, kai ma in baka so cutarshi ba ai sai ka gaya mishi cewa gidanka duk wadda ka auro mutuwa suke yi."

Ya dube ta, "To menene na tada jijiyar wuya? Har kina gaya min cewa In ba na so cuta ba, wato ni ne macucin ko?"

Shiru ta yi ranta yana tafasa.

Ta miƙe tsaye "wallahi wannan karon ba zan yarda ba,ban amince da auranka ba, shiyasa ka ke waya har kana wani cewa zata haifa maka yara? Sai dai ka zaɓa ko ni ko ita, haka kawai kana auro matan suna mutuwa,ƙila ma ana can ana zagina ana cewa nice ke kashe su to ba zan iya ba."

Ya dube ta,"zan auro ta, itama ta zo ta mutu,batun yarda kuma bana neman yardarki tunda bake bace Hajiya Sa'adatu uwata ba,kin ji ko? Batun kamfani kuwa da kike magana naga ba naki bane,bana kuma son shiga sharo ba shanu,in ma kyauta na bashi ba ruwanki sannan ki sani rashin mutuncinki da ki ka iya kada ki yarda ya zo kaina."

Fuu! Ta fice ta bar mishi ɗakin, kallo ya bita da shi, cikin mamakin ɗaga hankalin ta da tayi. Sam bai za ci haka daga gareta ba, saboda duk auren da ya yi a baya bata taɓa nuna damuwarta ba sai wannan.

Ita ko cikin ɗakinta safa ta ringa yi tare da marwa, lallai ta kula Alhaji da gaske auren nan zai yi,ta soma magana, wallahi-wallahi ba zan gushe ba zan cigaba da ɗaukar alhakin rayukan duk wadda ta yarda ta yi kishi dani, shima wannan karon ko nawa zan kashe sai nasa an kama min shi, aikin banza kawai in ko ba zai gaji da aure-aure ba nima ba zan gaji da aikawa da duk matar da ya aura barzahu ba."

Ta ɗauko wayarta, Hajiya Kari ta soma nema,tana ta ringing ba ta ɗaga ba,ta ja tsaki itama ƴar iska ko gidan uban wa ta shiga ni ban ma sani ba,Ta Kuma kira, cikin yanayin bacci ta ɗauka, tare da faɗin "lafiya Hajiya Jummai?" Ta ja tsaki "to kasa sarkin bacci in ce dai kin wartsake? Magana zamu yi."

"Ina jin ki" inji Kari, "kin ji na da wannan sarkin ɗaukakkiyar" "Wa fa?" Inji Kari, "Alhaji mana, aure ya kuma ƙirƙirowa, duk abinda ya faru baya bai ishe shi saduda ba." Kari ta ce, "ke ki bari, aure kuma ya ƙara lakatowa?" Jummai ta ce, "ke dai bari, sai ma kin ji yanda ya wani canza murya yana magana da ita a waya, ina zaton da farko ma bai yi niyyar sanar dani ba, kawai na kama shi suna waya."

Hajiya Kari ta ce, "To ya ya kikayi?" Ta ce, "buɗe wuta mana, yanzun nan in gaya miki kaca-kaca mukayi da shi". Hajiya Kari ta ce, "Kash! Ai ke kin ji matsalar ki,ke da zakiyi kwanto kamar yanda muka saba,me ma kika sani game da yariyar?" Hajiya Jummai ta ce, "Me kuwa? Abinda na sani kawai ya ce min ƴar abokinsa ce,kishi ya rufe ni na hau masifa." Hajiya Kari ta ce, "lallai kin so ki kwafsa,ko sunanta ba muji ba, saboda haka da safe ko kuma yanzu ki je ki bashi haƙuri ki ce masa zafin kishi ne, daga nan sai ki bugi cikin shi muji komai."

Hajiya Jummai ta ce, "sai dai goben, amma yanzun kamar ba zai saurareni ba,na san shi sarai ina ganin wannan karon ko boka na dutse ba zai iya aiki kan Alhaji ba, zan nemi wani tunda har yau bana juya shi yanda nake so,sai yanda ya ce, dole haka za'ayi."

Hajiya Kari ta ce, "kada ki damu, zan zo gobe sai mu yi magana a tsanake, amma don Allah ki kwantar da hankalinki" ta ce "zan yi ƙoƙari."

Yana saka kaya ta shigo da sallama. Ta ci gayu cikin shadda mai kalar ja, ƙyan shaddar da tsarin ɗinkin shine ya toni asirin tsadar kayan,ƙamshinta ya cika ɗakin,cike da salo ta iso gurinshi ta amshi (Nect tie) ɗin tana gyara mishi tare da faɗin, "ka ganka kuwa Alhajina? Kai ka yi ƙyau." Bai ce mata komai ba, haka nan bai saki fuska ba, kuma bai katse ta da gyara mishi (Nect tie) ɗin ba, sai da ta gama yana kallonta,ta ɗauko turarenshi Matador ta fesa mishi kaɗan, sannan ta ce sauran ka (break) ya ce na ƙoshi,ta dube shi da sauri ban gane ka ƙoshi ba? Kana nufin ba zaka ci ba zaka fita?"

Ya soma tafiya,tasha gabanshi cikin yanayin tausayi,ta ce "Haba Alhajina, kayi haƙuri na san ban ƙyauta ba laifin kishi ne, sonka ne ya sani na yi maka haka." Ya tsaya yana dubanta, sannan ya ce "Don kina kishina sai ki min rashin kunya? Har kina gaya min cewa ni macuci ne?" Ta zube ƙasa guiwa biyu.

"Kai min afuwa,ba zan sake ba." Ta soma hawaye, mai tausayi ne musamman ga mata,don haka ya ce "naji tashi shi kenan, amma kada ki sake,batun Break kuwa na yi latti,in na dawo zan ci na dare" cikin shagwaɓa ta ce,"ka kula min da kanka." Ta rakashi zuwa ƙofar falo,yana fita ta ce,zaka sani ne, tunda ka ce mata kasa gaba.

Hajiya Kari ta dubi Hajiya Jummai.

"Ina jin ki."

"Wai kin san da ya ya ma ya faɗa min sunanta?" Ta ɗan dakata,kafin ta cigaba "sai da siyasa,na ce haba Alhaji ko baka huce ba ne? Kana ji ina tambayarka sunan ƙanwar tawa amma ka min banza."

"To me zan ce miki" haka fa ya ce min sai daga baya yake ce min "A'isha." Yaƙi gaya min ma lokacin bikin."

Hajiya Kari ta ce, "ki bar shi,ai dai in lokacin ya matso dole muji, tunda mun samu sunanta shi ne kawai abin buƙata, yanzu kuma mun ji."

Yanzun sai mu sa ranar tafiya maguzawan, "To yaushe ne zuwan? Inji Hajiya Jummai,ta cigaba "Kuma sai dai mu je da direbanki, kamar kowane lokaci" "Eh,ai ina sane ba zamu bar wata kafa ko ya ya take wadda zata tona mana asiri ba,ke dai ki shaƙi kuɗi don bokan dutse yanzun idanunshi sun buɗe da son kuɗi,da, ko akan dubu biyar ma sai ya yi kisan rai." Jummai ta ce,"A sosai ma kuwa, ɗan iska ni har yau ma ban sai mashi motar da yake naci ba". Hajiya Kari ta ce "ke dai bar ɗan iska ko ina ruwan wanda ke cikin daji da mota?" Jummai ta ce,"nima shine na gani, shiyasa na share shi,rabo na da zuwa gun shi tun aikin ƙarshe da ya yi mana,na matar ƙarshe da Alhaji ya aura." Hajiya Kari ta ce, "ƙyale shi wannan karon sai ki sai masa ko ƴar starlet" Hajiya Jummai ta ce "hakan za mu yi" nan dai suka ci gaba da shirya ranar da zasu tafi.

Da gudu suka rungume juna suna murna.

*A'isha Mustapha kin ɗan rame." Inji Suwaiba Ringim.

"Nayi rashin lafiya ne, Zainab K.T bata iso ba?"

Sam, A'isha ba tayi niyyar sanar da Aminan nata batun auren nata ba, saboda kunya take ji, duk cika bakin da takeyi na cewa ita karatu zatayi kamar ba gobe,don Doctor zata zama yanzun ma har Doctor Aisha suke ce mata,in ko suka ji ta san zata sha tsokana, sai dai su shafa su ji bata dawo ba, Zainab ma ta iso kuma sun duƙufa karatu babu wasa.

Alhaji Saddiƙ ya yaba da yanda Abba ya tsaya tsayin daka, aikin kamfanin ya kammalu. Guri ya yi ƙyau duk mutane sun yaba,don haka shima bai yi wasa ba wurin kawo duk wani abu da kamfanin ke buƙata don fara aiki.

Alhamdulillah,tuni kamfani ya soma aiki, Abba kuwa ya samu kujerar manaja, yanzu sunturi yake yi tsakanin Dutse da Jigawa, Alhaji Saddiƙ ya ce mishi ya nemi gida nan Jigawa sai a siya, sannan ya saya mishi ƴar mota,ba a jima ba suka samu gidan suka dawo Jigawa.

[12/1, 19:47] Ummi Tandama😇: ____________________________
   *📗MUMMUNAN ZATO📗*

                       *NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

             *Ɗandano page 6*

Aisha tana makaranta ba ta san ana yi ba.

Gurin Abba Alhaji Saddiƙ ya ji cewa satin da zamu shiga ne visiting day ɗin su mutuniyar shi,ya ce "To Friend ka bari ni zan je mu da Nafisa" Abba ya ce,"shiyasa na sanar da kai don tasan cewa magana tana nan.

Waya ya yiwa Nafisa cewa,ta shirya zasu je visiting tana jin haka ta soma murna. Sun ɗau hanya in da Yahaya direban shi yake jan su. Aikin shi yake yi a bayan mota cikin laptop, harkokin business ɗin shi yake ta yi. Nafisa ko sai dai kallon ƙauyuka take yi, sai da suka isa garin Kano sannan suka tsaya bakin Sahad Store ya yi mata tsaraba mai ban mamaki, sannan suka ɗauki hanyar Munjibir.

Da tambaya suka isa makarantar,Henesy baƙa wul tana ta sheƙi,ta ɗauki hankalin da yawan ƴan makarantar,gilashinta masu duhu ne,don haka suke ganin mutane. Ya dubi direbanshi ya ce "Yahaya fita ka samo mana ofis ɗin (PC) ɗin makarantar."

"To ranka ya daɗe" inji Yahaya.

Jim kaɗan ya dawo.

"Ranka ya daɗe ga ofis ɗin can, har ma na yi mishi bayanin cewa maigidana yana son ganinshi,kuma ya ce mu shigo" "To ai shi kenan." Inji Alhaji Saddiƙ, tare da Nafisa suka fito. Ƙwarjinin Alhajin ya sa ya zama abin kallo gurin ɗaliban tare da masu ziyara. Kai tsaye ofis ɗin (PC) ɗin suka nufa,suna shiga shima (PC) din ya miƙe tare da ba Alhaji Saddiƙ hannu,don daga ganin shi ya jiƙe da Naira. Sun gaisa, sannan suka zauna kan wasu kujeru da ke gefe,ya nuna ma Nafisa wata kujera ya ce, "Bismilla Malama" shi ko Yahaya cewa ya yi,bari ya koma gurin mota.

Alhaji Saddiƙ ya ce,"mun zo ziyarar yarinya ne."

"Ya ya sunanta?" Inji P.C.

"A'isha Mustapha, daga Gumel ta jihar Jigawa."

P.C ya ce,(S.S) take ko JS?"

"S.S one." Inji Alhaji Saddiƙ.

"Ok" ya miƙe yana fita ya kira shugabar ɗalibai ya aike ta neman A'isha,ya dawo ya ce bari a kira ta.

Alhaji Saddiƙ ya ce,"Ba komai" ya zauna tare da cewa, "Ranka shi daɗe ƴar ka ce?" Alhaji Saddiƙ ya amsa da cewa "Eh,ƴar abokina ce", wayarshi ta shiga ruri,ya ɗauka yana magana.

Shugabar ta gano A'isha ne tare da ƙawayanta Zainab da Suwaiba,in da Yayan Zainab ya kawo mata ziyara daga Katsina, ta ce kece A'isha Mustapha ko?" Ta amsa da "eh,ni ce."

"To ki zo inji P.C"

A tsorace ta ce,"lafiya?"

Nima ban sani ba" ta ce "Ina jiran ku" ta nufi ofis ɗin shugabar ce ta shiga,ga ta nan Sir,ya ce ta shigo, nagode miki ta fita sannan ta ce A'isha ta shiga, ita kuma ta tafi. Tana shiga ta ji hancinta ya shaƙi daddaɗan ƙamshin turaren Uncle,gabanta ya faɗi amma ta daure ta shiga,sanye take da wando da riga haɗe da gyalen su, kayan mutanen Pakistan masu kalar sararin samaniya, kai tsaye teburin P.C ɗin ta nufa, inda ta gaishe shi cikin harshen Turanci, sannan ta ce gata,ya nuna mata Alhaji Saddiƙ da ke waya.

"Ga masu visiting na ki." Ya miƙe "Bari na barku, ku gaisa ko?" Ya fita.

Duk sai taji kunya ta rufe ta, har ma ta ja gyalenta ta rufe gefen fuskarta. Ta dubi Nafisa,ga zatonta matarshi ce. Cike da dariya Nafisa ta ce, "zo mu gaisa A'isha." Ta isa gurinta ta zauna, sannan ta ce "Ina yini? Ya ya hanya?" Nafisa ta ce "lafiya lau,hope kema kina lafiya?" A'isha kanta a ƙasa ta ce "lafiya ƙalau." Nafisa ta ce "Hajiyarmu da Alhajinmu sun ce mu gaishe ki" A'isha ta ce, "ina amsawa, na gode."

Dai-dai sannan Alhaji Saddiƙ ya gama waya ta ɗan saci kallonshi da gefen ido. Wata jiƙaƙƙiyar shadda ya saka kalar ƙasa,ya yi ƙyau sosai ta zamo daga kan kujera don ta gaishe shi.

"Ina yini Uncle?"

"Bana cin miƙe A'isha, daga nan za ki gaishe ni?".

Ta saka gyale ta rufe fuskarta, sannan ta miƙe taje gefenshi ta tsugunna,muryarta ƙasa-ƙasa ta sake gaishe shi. Ya amsa yana dariya.

Nafisa ma dariya take yi, sannan kunyar A'isha ta burge ta, A'ishan ta mata ƙyau,sai dai yarinya ce ƙwarai, ya ce "Nafisa yau dai ga ki ga A'isha" Ya dubi A'isha ya ce, "Ga ƙanwata Nafisa." Ta kuma duban Nafisan.

"Sannu da hanya"

"Yauwa," Nafisa ta amsa da fara'a.

A'isha ta miƙe tana kallon Nafisa, "Bari na kira ƙawayena." Har za ta fita, ya ce "Zo" Ta dawo ta tsugunna.

"Wa zaki ce musu ya zo?"

Ta rufe fuska,tana ɗan murmushi. Ya ce, "Umh,wa zaki ce musu? Ko har kin basu labarina ne?" Ta girgiza kai, sannan ta ce, "Ce musu zan yi Uncle ɗina ne." Ta miƙe ta fita da sauri. Dariya Nafisa ke musu, ta ce "Yaya Saddiƙ duk da A'isha yarinya ce kun matuƙar dacewa, Allah dai ya yi mana jagora tare kuma da shige mana kan matsalarmu." Ya ce "Amin sister."

Ta je gurin su Suwaiba ta kira su, ce musu ta yi Uncle ɗinta ne daga Katsina, suka shigo suka gaishe shi,ya tambayi sunayen su suka gaya mishi,ya ce "Har da ƴar garinmu? To sannuku,ku dage da karatu ko?" Suka ce, "To mungode" ya ce "nima na gode." Suka fita suna mamakin dama A'isha tana da Uncle a katsina, Amma ba ta taɓa gaya musu ba? Zainab kam so take ta tuna inda ta san shi.

Nafisa ta miƙe, "A'isha bari na bi ƙawayenki na ɗan miƙe ƙafa,"  A'isha ma ta miƙe ta fito, kira ta ƙwalawa su Zainab.

"Ga baƙuwa ko zaku je school shop."

Suka ce, "To" ta dawo ofis ɗin ta zauna, ya dube ta "Ya ya bayan rabuwa?" Ta ce "Da godiya, shi Abbana ba zai zo ba?" Ya ce,in gaishe ki ba zai samu zuwa ba, saboda aikin shi ya koma Jigawa. Kuma yanzun Jigawan ku ke" ta dube shi, "Mun tashi daga Dutse?" Ya ce "Haka ne,to yanzu yaushe ne zakuyi hutu?" Ta ce, "Nan da sati biyar zuwa shida." Ya ce, "To so nake a shirya komai kafin kuyi hutu, cikin hutunku za'a ɗaura aure tare da bikin." Gyale taja ta rufe fuskarta. Ya ce, "Me kika ce?" Ta ce, "Duk yadda ku ka yi,ni dai karatuna na fi ji" Ya ce, "wannan babu komai, sai makarantar da ki ke so ita zan kai ki" ta ce "Bari na samo maka wani abu." Ya ce, "No,bar shi am ok." Ya dubi agogo bari muyi sallah mu zo mu tafi." Ta ce, "To."

Bayan sun yi Sallah,ya dawo ya yi ma P.C alkhairi mai yawa,P.C ya rako shi har gun motarsa. A'isha taje ta kira su Zainab su yi sallama,har ma ta ce ma Sani Yayan Zainab,ya zo ya bi su Uncle ɗin ta mana tunda suma Katsina za su je.

Sanda suka iso gurin motar Yahaya,yana ta aikin jibge ƙwalaye a ƙasa daga boat ɗin motar,Sani yaja baya ya tsaya yana mamakin ganin Alhaji Saddiƙ K.T. mutumin da ya yi kuɗi da jinin mutane, yanzu kuma dabarar da ya sake kenan? Ta shigowa makarantu yana son shan jinin ƴan makaranta? Sun gama sauke kayan suka shiga mota.

Alhaji Saddiƙ ya miƙa ma Nafisa bandir ɗin kuɗi yace ba ƙawayan nata. A'isha ta leƙo tana cewa, "Nafisa ku sauka lafiya,ku gaida ƴan garin." Ya ce, "Ni fa ko Nafisa kaɗai ki ka sani?" Nafisa ta ce, "yauwa ga Yayan Zainab shima Katsina zai je". Alhaji Saddiƙ ya ce, "To ya shiga mu je." Ta zo gurin su, ina Sanin?" Yana daga bayansu ya ce,"A'a su tafi ni dama sai gobe ina da aboki nan cikin Munjibir,ta je tace su tafi su Zainab ma suka je sukayi godiya.

Suna tafiya sai ya zo gurin su ya nuna A'isha, "wannan mutumin ne Uncle ɗin ki?

Zainab ta ce, "Ka san shi ne? Nima ina ta mishi kallon sani."

"Sani ya ce, "kin san shi mana, Alhaji Saddiƙ Usman K.T ɗin ne baki sani ba."

Zainab ta dafa ƙirji da ƙarfi.

"Kana nufin me kuɗin jini?" Ya ce "shi ne mana."

A'isha ta zaro ido,me kuɗin jini kuma?" Sani ya ce, "tabɗi,ke da baki san halin Uncle ɗin na ki ba? Koda yake ai basa cin na gida sai bare."

Jikin A'isha ya soma rawa, cikin matsanancin tsoro ta ce, "Don Allah ku gaya min gaske ne?" Zainab ta ce, "kada ki damu zan baki labari,ku zo mu ƙwashe kayan nan." Ta ce, "ai ni bazan ɗauki wani abu ba har sai naji labarin Uncle." Suwaiba da Zainab har ma da Sani suka shiga ƙwashe kayan. Zama tayi bakin gado tana tunanin baƙon al'amarin, har suka raka Sani suka dawo.

Zainab ta zauna kusa da ita, A'isha dama baki sani ba,shan jini suke yi,An ce aure-aure ya ke yi, duk wadda ya aura ba ta sati biyu take mutuwa,aurenshi goma, uwargidan ce kaɗai bai cinye ba, ke yanzu fa ba a bin layin gidan shi,don ance kana cikin tafiya a layin wani abu zai ja ka zuuu sai dai ka ganka a cikin wani ɗaki a gidan,ke kina ganin gidan kin san ana cin mutane a cikinshi, ko ba ki san gidan ba?"

A'isha cikin tsananin tsoro ta ce "ban taɓa zuwa ba".

Suwaiba ta ce, "Tab! Amma ya yi ƙyan banza." Zainab ta ce "kinga gidan ne wani mahaukacin gida ga bishiyoyi."

A'isha sai kuka,lallai Allah ya so ta tana zuwa gida zata sanar da Abbanta. Duk kayan da ya kawo ta ce bata so,ta ma fita hayyacinta cikin ƙwana uku ta ƙwanta ciwo,ƙwananta biyu ta ɗan samu sauƙi. Amma duk ta rame su Zainab sun yi ta matsa mata da son jin gaskiyar lamarin ta da Alhaji Saddiƙ don sun ga yanda ta ɗauki abin da zafi ƙwarai. Ta gaji ta gaya musu cewa Babanta ya riga ya bashi ita,sun jajanta mata tare da kuma bata shawarar ta tashi tsaye da addu'a, Allah ya shiga tsakaninta da sharrinshi. Sun ce suma za su taya ta.

A daddafe dai suka yi jarabawa, Abba da Abdulrahman ne suka zo ɗaukanta, Abba ya dube ta, "A'isha ciwo ki ka yi haka? Na ganki ne babu ko ƙyan gani?" Hawaye ya soma zubo mata, cikin sanyi murya ta ce "Abba nayi ciwo ne sosai."

Sun isa Jigawa misalin ƙarfe biyar na yamma,suna tsayawa A'isha ta fito tana kallon sabon gidansu,ga dai gida mai kyau amma ta kasa jin farin ciki, kuma ta yarda cewa iyayenta suna cin kuɗin ƴarsu ne. Nan take hawaye ya soma zubo mata,ta shiga ciki.

#######
[12/2, 08:00] Ummi Tandama😇: ____________________________
   *📗MUMMUNAN ZATO📗*

                       *NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

             *Ɗandano page 7*

Abdulrahman yana biye da ita da kaya, cikin wani tsararren kitchen ta hangi Umma, Umma tana juyowa ta yi arba da ƴarta, da sauri ta fito tana cewa ga ƴan makaranta ga ƴan makaranta." A'isha ta faɗa jikin Umma tana kuka.

Ramarta ta tsorata Umma, ta ce, "A'isha kin yi ciwo ne?" Dai-dai nan Abba da Abdulrahman suka shigo, Abba ya ce, "ƙawallin taki ta bani tsoro, Ummansu kin ga yanda ta ƙare?" Umma ta ce "Shine ai,wane ciwo ki kayi haka?" Cikin kuka A'isha ta ce, "Nima ban san ciwon ba,ni dai duk jikina ne bana jin daɗin shi. Suka shiga falo kan kujera ta ƙwanta tana ƙara kallon yanda aka tsara falon da kuɗin jini, duk sai ta samu kanta da ƙyanƙyamin komai na gidan. Umma ta zubo mata abinci ta tasa shi ta kasa ci, har dare Umma ta yi tayi A'isha, amma ta ƙi cin komai. Hankalin Iyayen ya tashi, cikin dare zazzaɓi ya rufe ta saboda tsananin damuwa da kuka, dole da safe suka nufi asibiti, duk binciken likitan bai gano komai ba, sai damuwa. Don haka yasa mata ruwa tare da allurai don ta samu bacci.

Ƙwananta biyu aka sallame ta, tunda ta dawo ko yaushe jugum ba ta magana. Umma ta matsa mata da tambayar abinda ke damunta,don likitan ya ce tabbas akwai abinda ke damunta. A'isha tana son sanar da Umma amma tana tsoron kar ta gaya wa Abba, shi kuma ya yi faɗa. Ko ma ya yi fushi da ita,don haka ta yi shiru.

Abba yana zaune yana cin abinci, ya tasa ta gaba wai itama sai ta ci nata. Umma ma ta shigo ɗakin na A'isha, wanda ya ji uwar katifa sai (T.V) ance ba za'a cika ɗaki da kaya bane tunda cikin hutun nan ne za'ayi bikinta, Umma ta zauna tana cewa,ka ce kana nan na fito ban ganka ba,ya ce "eh, ina nan gurin A'isha so nake ta ci abincin a gabana in gani," Umma ta ce "to nima dama na zo ne in tsare ta, yarinya duk tasa kanta a uku" ta dubi A'isha wadda take ta ƙoƙarin ganin ta ci abincin,ko don hankalin iyayenta ya ƙwanta, ta ce, "To ko saboda aurenki da Alhaji Saddiƙ ne?" Da sauri ta kalli Abba, wanda ya tsura mata ido, sannan ta girgiza kai, "Ba haka ba ne Abba" ya ce "ai bani ne na tambaye ki ba, Ummanki za ki bawa amsa, tunda ni dai ai mun gama magana,jiya ma nake sanar da shi dawowarki, sai dai ban sanar dashi ciwon ki ba, saboda zai ce zai bar aikinshi ya zo,ya ce dai zai zo kafin su kawo kaya."

Umma ta ce "bari na saka mata wayarta ma a caji, saboda ƙila zai neme ta. A'isha ta yi ajiyar zuciya,lallai ya kamata ta sanar da Umma, domin dai ba su san komai kan Uncle ba. Sai da Abba ya fita sannan A'isha ta dubi Umma, ta ce "Umma zan gaya miki abinda ke damuna, amma sai kin yi min alƙawarin ba zaki sanar da Abbanmu ba" cikin fargaba Umma ta ce, "Sanar dani,ba zan gaya mishi ba." Ta soma hawaye, "Umma ashe Uncle ɗan yankan kai ne? Ashe duk kuɗin shi na jini ne?" Umma ta daburce tare da cewa "Wane Uncle ɗin?" A'isha ta ce, "na Katsina, kinsan ƙawata ƴar Katsina ce nan dai ta koro ma Ummanta labarin da ta ji game da Uncle ɗin nata, Umma ta shiga damuwa,zufa ta shiga keto mata duk da cewar da takeyi anya kuwa A'isha zancan nan gaskiya ne? Duk suka yi shiru kowa yana tunaninshi, can dai Umma ta yi ƙarfin hali ta ce "A'isha wannan zancan ba na shiru ba ne, dole Abbanki ya ji, domin dai duniya yanzu babu gaskiya, kuɗi suna kai mutane cikin halaka, sannan kai ka yarda da mutum shi ko yana da nashi burin a kanka".

A'isha ta soma kuka tana faɗin,  "Don Allah Ummata kada ki sanar da Abba,ba zai taɓa yarda ba saboda ya yarda da Uncle ni dai na haƙura zan auri Uncle ɗin tunda dai dama na san ƙarshena mutuwa zan yi."

Abba da ke ƙoƙarin shigowa ɗakin tun ɗazun,ya ji A'isha tana sanar da Ummanta A ranshi ya ce, "shikenan sun ji zancan da ya ke ɓoye musu,ya zama dole ya shiga ya sanar da su gaskiyar lamarin domin ya yarda Alhaji Saddiƙ ba zai mishi ƙarya ba,ba zai cuce shi ba,ba zai ci amanar shi ba, kuma ba zai kasance ɗaya daga cikin masu shan jini ba.

Da sallama ya shiga duk da baya da kuzari amma ya yi ƙarfin halin cewa "kuna hira ne? Umma cikin damuwa ta ce "wane hira Abbansu zauna ka ji". Ya zauna tare da faɗin "lafiya dai ko? Umma ta ce "da sauƙi dai,dama Abbansu dama ashe irin sana'ar da yake yi kenan?" Abba ya ce "wa?" Ta ce "Alhaji Saddiƙ mana ta shiga jero mishi bayani yanda A'isha ta sanar da ita. A'isha dake ƙwance jikin Ummanta tana kuka,ta ce "Abba ka min afuwa na sani ranka ba zai so ba, amma duk da haka zan aure shi.

Abba ya ce "ku kwantar da hankalinku ni kaina na san wannan labarin kuma shi da kansa ya yi min bayanin zargin da jama'a suke masa. Tabbas tun daga kan Hajiya Jummai duk Mata da ya aura mutuwa take yi, gaske ne ya yi aure kusan tara ko goma ne? Duk sun rasu," A'isha ta zaro ido, Abba ya ci gaba da cewa, "ina so ku sani cewa, dukkan mai rai mamaci ne, haka nan matansa da suka riga mu gidan gaskiya,ku yarda wa'adinsu ne ya zo, batun yana yankan kai babu gaskiya cikin zargin da mutanan unguwar suke mishi."

Umma cikin matsananciyar damuwa ta ce, "to yanzun Abbansu matan nasa suna mutuwa haka za'a bashi A'ishan?.

Ya ce, "Haba Fatima,ya ya ki ke dawo da hannun agogo baya? Na gaya miki na sake gaya miki aure babu fashi, mutum baya mutuwa face ƙwananshi ya ƙare. Ya fita yana cewa "ki zo."

Ɗakinta ya shiga, Umma ta biyo shi jikinta babu ƙwari. Ya dube ta yace, "Haba Fatima,me zai sa kiyi min haka? Ke kin san son da nake ma A'isha,kin sani ba zan cutar da ita ba, aure bautar ubangiji ne, zan yi murna a ce ta mutu tana ibada,don haka ki natsu kuma ki ƙwantar da hankalin ki,ki bani goyon baya. Ki yaƙi shaiɗan mu tattaushe ta,nima wallahi ƙarfin hali nake yi,in tana ganinmu cikin damuwa zata kasa ƙwantar da hankalinta kullum zata zama cikin fargaba."

Umma ta ce, "Shikenan, zan yi yanda ka ce," ya ce "yauwa, addu'a kurum ita ce magani,ki tsaya tsayin daka da addu'a,ba dare babu rana. Itama A'ishan ki tsaya kanta ta dage da yin azkar safe da yamma. Cikin fargaba ta ce "To."

Sanda Umma ta shigo ɗakin A'isha, ta samu A'ishar tana zaune gabanta wayar ta ce tana ta ruri tsabar tsoro ya hana A'ishar ɗaga wayar Umma ta kalli fuskar wayar Uncle ɗina haka taga an rubuta nan take ta gane,ta cewa A'isha an sa shi mana? Ki natsu ki ƙwantar da hankalinki,ki mishi magana cikin natsuwa,kada ki ɗaga mishi hankali,kin ji?" Ta ce "Ina jin tsoron shi ne Umma" Umma ta ce "Daina tsoron shi, shi ba mugu bane sharri ne mutane suke masa, ɗauki wayar." Ta kai hannu zata ɗauki wayar, ta katse a karo na biyu.

Ya sake kira a karo na uku, Umma ta ɗauki wayar ta miƙa mata, hannunta yana rawa ta amsa ta danna green ta sa a kunne. Cikin muryar nan tashi mai natsuwa da hikima yace, "amincin Allah ya tabbata a gareki Humaira Beby". A'isha ta dubi Umma,harara Umma ta zabgo mata, sannan ta fita can gefen. Ya ce "kina jina ƴar Abba?" Ta daure, sannan ta ce, "Ina yini Uncle?" Ya ce, "lafiya lau,kin dawo lafiya?" Ta ce, lafiya lau, ya ce "Masha Allah" a zuciyarta kuma faɗi take, Allahumma kafihim bima shi'ita,tana maimaitawa tana sake faɗa,ya ɗan yi gyaran murya,ya ce "A'isha ina labari?" Ta yi shiru,ya ƙara sanyaya murya,ya ce "A'isha kina ji na?" Ta ce, "Umh" ya ce, "zan zo week end,tun Friday kin ji? Kamar ta ce A'a, sai kuma ta ce Umh, ya yi ƴar dariya sannan  ya ce "to Bebyna,me da me zan kawo miki?" Ta ce,babu komai.ya ce Shikenan, sai na zo, tace, "To ka gaida Nafisa" cikin jin daɗi ya ce "ita kaɗai ban da Hajiyarmu?" Da sauri ta ce "har da su." Ta ƙosa ƙwarai ya gama maganganunshi, kamar ko ya sani, ya ce "to bari na ƙyale ki sai kin ganni ko?" Ta ce Uhum, ta riga shi kashewa,ana shi gefen bai damu ba zaton shi kunya ce.

Daran juma'a,sam A'isha bata runtsa ba, tama rasa tunanin da zata yi, duk da lallashin da Umma take mata, bayan sun karya, Umma ta matsa mata suka shiga kitchen don girka abin tarbar baƙo.

Sun gama sha biyu da rabi nan Umma ta bar ta ta haɗa mishi zoɓo da sauran kayan sha. Ta shigo falo ta ƙwanta kan kujera, Umma ta fito don zuwa kitchen ta ce har kin gama?" A'isha ta ce,eh, Umma ta miƙa mata waya ga shi yana ta kira ni ina wanka." A'isha ta amsa Umma ta koma ciki.

Wayar ta soma ringing. Ta tsurawa wayar ido, ita dai kullum ƙara tsoron shi ma take yi, amma ba ta da yanda zata yi dole ta ɗaga wayar tare da addu'a a can ƙasan zuciyarta. Sannan ta ce, "Salamu alaikum" ya ce "wa'alaikumus Salam, Beby ina ki ka shiga ne? Ina ta kiran wayarki?" Ta soma magana cikin in'ina, "ina....am......wannan ne a kitchen ne," ya yi ƴar dariya, "ni kike yiwa girki kenan?" Ta yi shiru, ya ce "ok,shiru yana nufin eh ne,to na gode. Yanzu haka na shigo Jigawa, masauki kawai zamu je, sai na iso kenan" ta ce,to, Ya kashe wayar.

Ta tsaya tana kallon wayar,daddaɗar muryarshi har yanzun tana yi mata gizo, murya mai cike da kamala kamar yarda fuskarshi take nunawa ta tuno suffarshi a fili ta ce lallai Uncle bashi da makusa in ban da na mugun halinshi koda dai su Umma suna ƙaryatawa.

Ta fito wanka tayo alwalla tana idar da sallar azahar mai ta shafa sama-sama saboda zafin garin ta zazzago farar hoda a hannunta,ta ɗan murza a fuskarta ko madubi ba ta duba ba,dama ita bata ƙwalliya. Don haka ba ta ma duba madubi,kai ita fa ko kaya bata da zaɓi duk wanda Abbanta ya sai mata sun yi,don tana saka kaya ne don suturta jiki ba wai don gayu ba, ta ɗaga aƙwatinta ta ciro kayan da ke sama. Wata atamfa ce ta mutanan Ghana, fara ce ta saka taje ta ɗauko abincinta,ta zauna tana ɗan cakula tana dai cin abincin ne amma hankalinta duk yana kan Uncle ganinta ƙila ma tun yau zai gama da ita. Jafar da Munnir suka shigo,suna cewa Umma ga Uncle ɗin mu ya zo yana waje yana waya. Umma ta ce, "tare da Abbanku su ke?" Suka ce "a'a shi kaɗai ne, amma Yaya Abdulrahman yana gurinshi, ta ce "Abbanku yau ina ga aiki ya mishi yawa ne,ko gida bai dawo ba, ina ganin daga Office ɗin ya wuce Masallacin juma'a.

Jafar ya fita waje,jim kaɗan ya dawo. "Umma Yaya Abdulrahman,ya ce ki bada makullin ɗakin baƙi" taje ta ɗauko, A'isha kam tana zaune kamar gunki tana jin su. Yaya Abdulrahman ya shigo, "Umma Uncle yana ɗakin baƙi ya ce yabi ta Ofis ɗin Abba,sun tafi masallaci, shima yaje ya yi sallah ya koma Ofis ɗin basu dawo ba shi ne ya zo nan gida". Umma ta ce, "bai kira wayarshi ba?" Yana ta kira bai samu ba sai yanzun. Umma ta ce, "To ai shi kenan, tunda ma ya sameshi. Ta leƙo falo "A'isha tashi ki je ki shirya mishi abinci,ki kai mishi." Jiki babu ƙwari ta tashi ta fita.

____________________________
   *📗MUMMUNAN ZATO📗*

                       *NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

             *Ɗandano page 8*

*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*

```ACT}:--1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account ɗin namu ya samu matsala ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*

*Masu son  tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427*```

Babban tire ne ta shaƙe shi da kuloli masu ɗauke da kalolin abinci. Sai plate da cokali, da sallama ta shiga,ƙasan zuciyarta kuma tana maimaita addu'ar Allahumma kafihim bima shi'ita.

Ya yi matuƙar ƙyau cikin shadda mai tsada kalar ja mai duhu,hular da takalman duk kalar jan ne,ƙamshin daddaɗan turarenshi ya cika falon. Duk da tsoronshin da take ji bai hana zuciyarta yaba ƙyanshi ba. Ta dire tire kan tebur ɗin, gabanshi ta jawo teburin sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce sannu da zuwa Uncle, ya ce "yauwa ƴar Bebyn Uncle,I hope kina lafiya?" Ta ce "lafiya lau,ya ya su Nafisa da su Hajiya?" "Duk suna gaishe ki, cikin jin daɗi yake bata amsa, domin yarinyar ta shiga ranshi har yana mamakin yanda wasu lokutan ya kan shagala da tunaninta,ya kan ji kewar ƴar siririyar muryarta, da Beby face ɗin ta, abinda bai taɓa yi kenan a kan mace ba, duk matan da ya aura baita jinsu kamar yanda yake jin A'isha ba,a ranshi. Ta cika kofi da ruwan zoɓo mai sanyi ta miƙa mishi cike da ladabi, ta koma gefe ta zauna, ya ce "No, come on hau kujera ki zauna,ta ce nan ya yi Uncle, ya ce to nima bari na sakko ƙasan, ta yi sauri ta hau kan kujerar ta ɗan ɗofanu yana ƴar dariya shima ya gyara zaman shi.

Sannan ya soma shan zoɓon ta gefen idanunta ta ke kallonshi. A ranta ta ce "Oh,ga mutum har mutum, amma cikin zuciyarshi gara kura da shi. Ya katse shirun da cewa "Beby in Allah ya gwada mana ki ka koma gidana, ina son kina min wannan zoɓon kin ji?" Ta ɗaga kai alamar ta ji ya ce "to abincin fa zo ki zuba min," ta ce to, tana buɗe kular farko yaga saƙwara fara ƙar-ƙar, ya ce "ai shikenan Beby yau kuwa har in tafi ita zan ta ci.

Nan ta zuba mishi da miyar agushi, ga nama manya-manya,ya cika cikinsa dam,ko magana ba ya iya yi, sai da ya gama sannan ya dube ta yana goge fuska da fari ƙar ɗin handkachief ya ce, Beby kin ganni babu ba ka sai kunne ko? Ta sunkuyar da kai.

Ya ce,"Beby sai naga kamar kin rame min a ido hakane?" Ta ce na ɗan yi mura bayan haka kuma ga makaranta," ya ce "kin manta ɗayar ga kuma maganar aure". Ta rufe fuska, ya yi ƴar dariya sannan ya ce zan sa su kawo kaya da zarar na koma gida nan da sati biyu zuwa uku,kin zama ƴar mutanen K.T? ko?" zancan ya daki zuciyarta, nan take ta raya ma ranta haka yana nuna nan da sati huɗu zuwa biyar zata baƙunci kabarinta, tunda an ce matan nashi ba sa wuce sati biyu zuwa uku suke mutuwa.

Ya katse ta. "Ko ya yi nisa a rage?" Da sauri ta girgiza kai,ya ce "a barshi haka?" Ta ɗaga kai alamar Eh. Nan ya ciro mata tsarabar ta, abubuwan ci ne tare da turaruka har da wata ƴar Tedi ta wasan yara. Ya miƙa mata ledojin ya ce "to duk da kin ce baki son tsaraba gashi nan ki basu Jafar ke kuma ga naki" ya miƙa mata Tedi.

Baki ta saki tana kallonshi, shima ita yake kallo tamkar masu kallon soyayya, sannan cikin sanyin murya ta ce "Uncle me zan yi da wannan?" Ya ce "wasa mana" ta ce, "am not a small girl," ya ce haba? Ta sunkuyar da kai tace,da gaske,ya ce shikenan to ki ajiye min in kin haifa mana Small boy sai ki na bashi yana wasa," ga mamakin shi sai ya ji tace "in kuma na mutu fa?"

Da sauri ya dube ta,a ranshi ya soma zargin ko taji cewa matanshi suna mutuwa ne? Amma a fili sai ya ce,"nima ina yawan tuna haka, sai dai duk sanda na tuna cewa zan iya mutuwa ko ke ki mutu ban ga ɗan kaina ba, ina shiga wani mawuyacin hali, zuciyata tana sonki da yawa." Ta sunkuyar da kanta ƙasa,ko dai mummunan zato ne a ke mishi? Ko dai zargi ne? Ƙwanan matan nasa ne suke ta ƙarewa? Ya katse mata tunani da cewa, "ki na tsoron mutuwa ne? Ko kina zaton in kin aureni zaki mutu ne?".

Cikin dabara ya sako mata tambayar,don yana son ji ko ta samu labarin matanshi suna mutuwa ne? Nan take ta gane nufinshi,don haka sai ta ce "a'a bana tsoron mutuwa,sai dai kullum tunanina yana kan ayar da ke sanar damu (kulli nafsin za'ikatul mauti), kaga dukkan Musulmi yana da ƙyau ya dinga tunawa ranshi zata ɗanɗani mutuwa, sannan in ajali ya yi kira ko ince in ajali ya zo ba za'a ƙara ma mutum ko second ba.

Alhaji Saddiƙ ya dube ta cike da farin ciki,ya ce haka ne Beby, lallai kina da kaifin basira. Haka nan duk bawan da yake yawaita tunanin mutuwa zata iya riskarshi a kowane lokaci,za ki sameshi yana mai matuƙar kiyaye dokokin Ubangijinshi, ina saka rai kema kina ciki? Ta sunkuyar da kai tare da faɗin insha Allah ya ce, to ba zaki taɓe ba.

Sannan ya canza zancen da cewa,me kike shiryawa bikin? Ina nufin waɗanne shagulgula za kiyi ke da ƙawayanki? Saboda in na tafi ba zan dawo ba, sai ɗaurin aure, shiyasa nake son in sallame ki."

Ta dube shi,a ranta ta ce, inyi shagalin me? Bayan ni ƴan ƙwanaki ne suka rage min,a fili kuwa sai ta ce, "ba zan yi komai ba." Ya ce, "Haba! Ko walima?" Ta girgiza kai tare da ƙoƙarin maida ƙwallar da ke son zubo mata. Ta ɗan saka hannu ta ja hancinta kamar tana mura, sannan ta ƙago murmushi ta ce "kasan Uncle bani da ƙawaye bayan haka ma ni ban cika son hayaniya ba,so kaga gara na barshi ko?" Ta faɗa tare da duban shi,ya ce "shikenan Bebyna" ya saka hannu cikin aljihun ya ciro rafar ƴan ɗari biyar guda biyu dubu ɗari kenan,"gashi gudunmawata," zatayi magana ya tare ta da cewa, "kul ki kakiyi magana, ke dai ce ne Allah ya cika mana burinmu,a ranta ta ce Amin in ba shanye mini jinina ba ne. Ya ce zaki shiga gida ko? Da sauri ta ce,eh tare da kallonshi ya yi ɗan murmushi sannan ya ce, "kin ƙosa ki tafi ko?" Ta sunkuyar da kai tare da girgiza kan alamar a'a, ya ce "to ga kayanki nan ƙwashe. Ta miƙe tare da ƙwashe kayan ta ce mun gode. Ya ce,ba ki ɗauki Tedi ɗin Small beby ɗin tamu ba,ta kalli Tedin sannan ta ɗauka ya ce in Abbanki ya shigo sai ki ce ina jira, sannan ki bar wayarki a kunne kin ji?  To tace,ta fita.

A gadon Ummanta ta zube kayan tare da zama gefen gadon ta rafsa tagumi. Umma ta fito daga (toilet) ta tsaya tana kallon kayan da iyayen kuɗin da ke zube a kan gadonta, ta ce "A'isha waɗannan kayan fa?" Ta ce "Uncle ne ya ce in kawo ma su Jafar?" Ta ce, "wannan kuɗin fa?" Me yasa ki ka amsar masa kuɗi?" Ta ce "Umma nayi-nayi ya bar su yaƙi wai cewa ya yi gudunmawa ya bani don na ce mishi ni ba zan yi shagalin biki ba.

Umma ta ce duk da haka da dai baki amso ba, A'isha ta dubi Ummanta ta ce, "ki aje a gurinki ni sai in dinga ganin tamkar yana biyan kuɗin jinina ne da zasu sha....." Ke! Tsawa Umma ta daka mata, sannan ta ce "A'isha bana son jin irin waɗannan surutan daga bakinki kenan kema kin yarda da mummunan zargin da al'umma suke ma mutumin da zai zama mijinki? Duk kin bi kin ɗaga hankalinki, maimakon ki tsaya kan addu'a Allah yasa ki shiga gidanki cikin Sa'a ko? Ta miƙe ranta ɓace ta fita falo ta bar ta ɗauke da tagumi tana nazarin yanda ma za'ayi ta iya ƙwantar da hankalinta.

"Sofy! Sofy," Hajiya Jummai ce ke ƙwala ma ɗaya daga cikin ƴammatan da take ɗaukowa cikin danginta kira. Sofy ta zo cike da yatsina, ta ce "gani Anty Jummai," ta ce suby fa? Sofy ta yi wani luu da idanu, sannan ta ce tana bedroom in kirata ne?" Jummai ta ce, "eh kirata aikenku zan yi yanzun ku fito cikin shiri." Suka fito cikin riga da wando ya ɗame kowacce cikinsu, Sofy ce ma ta ɗan yafa wani ɗan kucilin gyale, Jummai ta dube su kun yi ƙyau, sai dai kema Suby je ki yana ko ɗan irin na Sofy ɗin kin san Alaramma yana gari. Haka take kiran Alhaji Saddiƙ in zata yi wani abu daya hane ta. Ko in ya yi mata nasiha, to ranar yini zata yi tana ce mishi Alaramma,ko Alagafarta. Soby taje ta ɗauko tana mitar ita bata son wani yafe-yafen gyale duk takura ne, Jummai ta ce "ya ya zakiyi tunda kina gidan Ustazai,ka ce shi yafi kowa sanin Allah" ta ce "ga wannan ta miƙa musu wani ƙullin abu cikin tsumma,ku kai ma Hajiya Kari,ku ce mata ga ƙasar ƙafar nan za kuma mu yi waya.

Sofy ta ce, "motar wa zamu ɗauka tunda ta mu tana gurin gyara?" Hajiya Jummai ta soma masifa, "ku hau mashin ba zan ba ku motata ba,ku je ku buga min ku ja min asara." Suby ta ja tsaki tayi gaba tare da cewa, "Sofy ta baki kuɗin mashin ɗin, amma ai ba mutuncinmu bane hawa acaɓa." Hajiya Jummai ta ce "shegun yara kada ku yi mutuncin mana, tare da jeho musu ɗari biyu Sofy ta ɗauka tana mita haka suka tafi suna zaginta, da cewa masifaffiyar mata.

Sofy ƴat ƙanwarta ce,Suby kuwa ƴar autar su ce,yaran sam basu da tarbiyya,ba sa shakkar kowa sai maigidan. Hatta Hajiya Jummai maida mata magana suke yi. Foly suke zuwa da ke nan Katsina. In kin ga yanda suke ɗaukan kai da shan ƙamshi zaka zata ƴaƴan shugaban ƙasa ne. Alhaji Saddiƙ kaɗai ke taka musu birki in yana gari.

Hajiya Kari da Jummai cikin motar Hajiya Kari, ita da kanta take jan motar suna hirar yanda zasu tsara mutuwar Amaryar ta Alhaji Saddiƙ,waton A'isha.  Hajiya Jummai ta ce "kin san Allah Hajiya Kari, (ta cigaba) wannan karon sati ɗaya nake son a aika yarinyar nan barzahu, domin duk cikin matan da ya yi,yayin auren ban taɓa jin kishin wata ba kamar wannan". Kari ta dube ta "menene na ɗaga hankali,yarinyar da ƴan ƙwanaki za ta yi ta sheƙa barzahu, har ki ke damun kanki." Jummai ta yamutsa baki,"ina mugun jin takaicin yanda ya damu da yarinyar, duk abokansa ya bi ya sanar da su alhalin da a ɓoye yake aurensa, sai in amaryar ta mutu sannan su ji, amma wannan fa shi da kanshi yake buga musu waya yana cewa,zai yi aure su taya shi da addu'a,ke wani takaici ma sai suna waya da yarinyar in kin ji yanda yake ƙara saisaita murya zaki sha mamaki." Hajiya Kari ta ce, "dama ga muryarshi kamar ta mata,anya ma ba salabane yake yi kuwa?" Jummai ta ce,"shi dai ya sani,ni yanzun damuwata ba ta wuce ya Boka na kan Dutse ya ganni ba. Kari ta ce "a'a kada ki damu,zai ganki ɗan iska nufin shi zai rama wulaƙancin da mukayi mishi na aikin ƙarshe da ya mana na ƙin sai mishi motar da ki kayi?" Jummai ta ce "shiyasa yanzun na taho mishi da makullin motar su Suby,don ba zan sai mishi sabuwa ba,yana kan tsauni ban da iskanci me zai yi da wata mota?" Kari ta ce "saka ai mata penti ki bashi ya ƙarata da ita". Jummai ta ja tsaki,"Ni tunanina me zan ce ma Alaramman nawa in ya ce ina motar su Suby?" Kari ta ja tsaki, "Jummai kina bani haushi,mu da muka nufi gurin masu biyan buƙata cikin gaggawa shakkar me zakiyi,ai ki sa a rufe mishi baki yanda ba zai tuna motar ba,su kuma shegun yaran masu ɗan iskan rawar kan tsiya sai kurum ki ringa haɗa su da na Mashinko direba ya dinga kai su."

https://hikaya.bakandamiya.com/muazzam-babi-na-daya/

*💃💃💃💃💃Wata garabasa sai tsarin bakandamiya ki sayi littafi daya ki samu damar karanta littafai sama da arba'in,akwai litattafan manyan marubuta kamar su RUFAIDA UMAR,LUBNA SUFYAN,MAIMUNA IDRIS SANI BELI,FATIMA DAN BARNO da sauran su,yi kokari kada wannan garabasa ta wuce ki akan naira 500 kacal,wacce take bukata ta yi magana ta wannan number 09068032427*

____________________________
   *📗MUMMUNAN ZATO📗*

                       *NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

             *Ɗandano page 9*

Jummai ta ce, "sun raina Tinau direba, kullum rigima shi yasa fa Alhaji ya sai musu ta su", Kari ta ce "ƴan iska to su fito da miji mana ki musu aure,ki huta can sa ƙarasa karatun a ɗakunan su" Jummai ta ce "yaushe suka nutsu har zasu samu mazan ƙwarai? Sai dai masu rarake su kuma ƙanana sa'o'insu.

Kari ta ce,"nima gidana matsalar kenan,Safina tamkar ƴar Akuya ko ince karya maza wannan ya aje wannan ya ɗauka". Jummai tasa dariya, sannan ta ce bata yar ba,kin tuna lokacin muna school?" Kari ta ce "kema ai Allah ne yaso ki gurin cire cikin da Mr.Joseph ya yi miki,mahaifarki ta nakasa,da ba don haka ba ƴarki ko ɗanki ba ƙaramin tataccen ɗan iska ko ƴar iska za'ayi ba."

Jummai taja tsaki "bar tuna min ɗan iska Mr.Joseph, shi ne ya yi min sanadi da ko ƴan iskan na samu ai da ban Yi wahalar ɗaukar rayukan jama'a ba,tun da nasan don rashin ƴaƴa ne yake ta wannan aure-auren." Kari ta ce, haka ne. Suna ta ƴan hirarrakinsu, har suka isa ƙauyen da zasu je, hanya ce mara ƙyau mai cike da ƙwazazzabai tare da dutsina.

Suna isa suka fito suka rufe motar, sannan suka soma hawa dutsen wata ƴar bukka ce a saman dutsen nan suka nufa ashar suka zunduma ita ce sallamar shiga gurin Bokan dutse,shima daga ciki ya ce maraba da ƴan tselan uwa,ku shigo dan abu takazar ubanku.

Suka samu guri gefe suka zauna. Ya dubi Jummai da jajayen idanunshi,kafin ki ce komai ki fara cika min alƙawarina,don tsakaninmu babu ƴar ɗaga ƙafa yanzun ga wuri ga waina zamu dinga yi, tunda ke na lura ƴar rainin hankali ce. Dodo ya ce in kin sake kuskure alƙawarinsa za ki sha mamaki."

Ta buɗe jakarta tana cewa,"kai ko gashi ka cika gajen haƙuri, gashi" ta miƙa mishi makullin motar, ya ce "riƙe tukunna ina motar?" Ta ce "a'a tana can ni ba zan iya jan zuwa gurin nan ba, kuma bana son in ce direba ya jawo asirina ya tonu,ko ba haka ba ne? Yace don wannan babu ji ko su Ifiritu sai su ɗauko, amma sabuwa ce ko?" Suka dubi juna ita da Kari, har suna haɗa baki gurin cewa dal ma kuwa,ya ce shi kenan. Ya shiga haɗa wasu abubuwa yana surkullenshi har ya gama ya ce,to ke ma fa kina da aiki a gabanki, domin wannan aikin ya banbanta da na baya.saboda ita wannan yarinyar tana yawaita ambaton Ubangijin musulunci, saboda haka sai mun dage."

Jummai ta ce,gara kam a dage Boka, saboda wannan in son raina ne ta mutu a ranar da aka kawo ta.

Hajiya Karima ta ce "in ma ta mutu ranar ya kiyaye aure," Boka ya ce "ba zata mutu sanda ku ke so ba, domin Aljani ba zai samu aiwatar da aikinsa ba, sai lokacin da take fashin sallah, saboda tana tsananta ambaton Ubangiji.

Tana yawan kusanta kanta da Ubangiji, sannan ke kuma zaki daina sallah daga yau har sai lokacin da Dodo ya ce kici gaba da yi. Ya miƙa mata wani ruwa gashi nan ki yayyafa cikin ɗakin da za'a saka amaryar, kullum sau uku a rana har tsawon kwana baƙwai. Ya bata wani ɗan gwangwani,ki binne shi a ƙofar ɗakin amaryar in ana sauran sati ɗaya bikin," ta ce "Boka ko'ina tiles,ya ya zan yi in saka?  Ya ce "ruwan ki in kin matsu ki sa a fasa, sannan zaki dawo in ana sauran ƙwana tara bikin" ta ce "to sai batun mijina ya ya zanyi na sameshi a hannuna?  Ya ce"wannan ba zan gaji da gaya miki ba,ba zaki taɓa samun shi yanda kike so ba, kasancewarshi mai tsayuwa akan duk dokokin Ubangijinshi, sannan tun yana ƙarami iyayanshi suna matuƙar tsaye kan shi, duk bokan da ya ce zai kama miki shi to ƙarya yake yi ba zai iya ba, sai dai ki haɗa da kissarku ta mata,to zuciyarshi tana da tausayin mace, amma ba dai asiri ba,in ma ya kamashi ba za aje ko'ina ba, zai karye.

Jummai ta ce, "shikenan zan ga me zanyi. Suka tashi suka fita yana me ƙara tuna mata ban da Sallah ban da Sallah. Wa'iyazu billa,kaji mushirikan mata.

Alhaji Saddiƙ ya dubi Fatima, "Sister ki duba dai ko za'a ƙara wani abu"  cikin dariya ta ce, "sun yi fa Brother,sai dai in kana son ka ƙara zaka iya." Nafisa ta ɗaga wani takalmi mai igiya ta baya ta ce, "haba Brother wallahi wannan takalmin ya yi ma A'isha kaɗan na yara ne fa?" Ya dube ta kaji ki to ai itama yariyar ce,she is fourteen or fifteen,sa'ar ƴarki ce fa sister" ya dubi Fatima. Nafisa ta ce "amma ai tafi Nana tsawo," ya ce "to ai Kuma Nana ta fita ƙiba ma," ya miƙe yana cewa, "kisa direbanku ya ƙwasa ku kaima Hajiyarmu,in ta ce komai ya yi shikenan,sai kusa ranar tafiya tunda gaba ɗaya yau sauran kwana sha shida bikin. Suka ce "To" bayan ya fita suka soma dariya Fatima ta ce "ni nama rasa me zan ce ma Brother babu fa brezia ko ɗaya,ya dai saka pants da skat zuwa su bess, amma babu bra. Nafisa ta ce "nufin shi bata da nonon sakawa ne ko?" Suka sa dariya, Fatima ta ce "kin san shi da kanshi ya siyo undes ɗin, zannuwa da sauran kayan duk ni ya ba zaɓi amma ko takalma sai gashi da su" Nafisa ta ce "shikenan in ta zo gidan ya siya," suka soma shirin ƙwasar kaya don zuwa gidan Hajiyarmu.

A'isha tana ƙwance kan katifa, zuwa yanzu ta gama sadaƙarwa ta dangana ta kuma ɗauki ƙaddara, sannan ta amince ƙwananta ne ya ƙare. Don haka ko yaushe zaka same ta da casbaha tana ja. Istingifari ta ke yi, domin Allah ya yafe mata zunubanta.

Wayarta da ke gefanta ce take ruri, bayan ta ɗauka tare da sallama, ya amsa, sannan ta ce, "ina ƙwana Uncle? Ya ce lafiya lau Beby, baƙin sun taso na san yanzun ma sun sauka a Kano, saboda jirgin Kano suka hau, ta ce "Allah ya kawo su lafiya," ya ce "Amin" ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Beby duk abinda be yi ba cikin lefen ki gaya min kin ji ko? Saboda bata son dogon bayani sai kurum ta ce "To" ya ce "shikenan sai na kira ko? Ta ce,to na gode, ya ce nima haka.

Gidan cike yake da ƴan'uwa ta gefen Umma da kuma gefen Abba. Shi yasa yawancin baƙin duk ƴan Gumel ne, sai ƴan Garki, sun zo ne don karɓar lefe kamar yarda akayi waya aka sanar da su. Anyi girke-girke don tarbar baƙin Katsina. Su kan yiwa amarya tsiya da cewa duk gudun auren ne ta ƙara ramewa, ita dai tana kallon su tana kuma jin su,nata addu'a ne a zuci, Umma ma dai tana ƙarfin hali ne domin kada ta karya ma A'isha guiwa.

Sun iso cikin motoci guda uku fararen Acadami su uku motar farko matan abokanshi ne na Kano,ta tsakiya kuma kaya ne a ciki, sai direba ta bayan mata huɗu ne Fatima a gaba, sai Nafisa sai kuma ƙanwar Hajiyarmu, da ƴaƴarta Talatu.

Ƴan unguwa da suka taru da kuma ƴan'uwa sun sha mamakin ganin kayan da aka kawo, suma sun sha tarba kuma sun ga karamci sun kuma yaba. Nafisa kuwa ɗakin A'isha ta shige lokacin A'isha tana wanka. A'isha tana fitowa taga Nafisa zuciyarta tana son Nafisa. Ta saki murmushi tare da cewa "dama har da ke aka zo? Ta ce,eh mana aini Brother ya yi ma ƙawance. A'isha ta zauna tana shafa mai, Nafisa na kallonta, lallai kam yanzun nononta suke fita ashe ya kula ne. Ta ce, Nafisa ya ya Hajiya fa dasu Aunty Fatima?" Nafisa ta ce, "ai tare da Anty Fatima, muka zo Hajiyarmu kam tana gaishe ki ba ki ce ina Uncle ba? A'isha ta ɗan yi murmushi kawai.

Nafisa ta ce, "Naga kin rame ne" A'isha ta ɗan yi murmushi, sannan ta ce "Na sha jinya fa tun a school har yanzu." Nafisa ta ce Allah sarki, to Allah ya ƙara lafiya. Amin inji A'isha, tare da zura wata duguwar riga, sannan ta soma ɗaura ɗan ƙwali. Nafisa ta ce Allah yasa ki haifa mana Beby mai irin gashin nan naki. A'isha dai ta sunkuyar da kai, Nafisa tayi-tayi ta zo su gaisa da su Anty Fatima, amma ta ƙi,Fatiman ce ma tace ai nima ƙanwar ta ce, bari naje mu gaisa,Talatu ma tabi Fatima dan su ga A'isha.

A'isha ko rufe fuskarta ta yi, har dai suka gaji suka tafi, Nafisa ma nan ɗakin ta ci abincinta, Abba yayi-yayi su ƙwana amma suka ce a'a, Kano zasu ƙwana don zasu shiga kasuwa goben da safe,sai su wuce. Da zasu tafi an basu tukuici suma yanda ya kamata. Nafisa ta raɗa ma A'isha a kunne, cewa ki rage bacci,ki tsaya kan addu'a.tsayuwar dare zaki dinga yi kina roƙon Allah alkhairin da ke cikin auren ya kuma kare ku da duk masu sherri da hassada kin ji ko? A'isha ta ce, na gode Nafisa zan kiyaye insha Allah.

Ya fito daga wanka,wankan da ya zama mishi ƙa'ida, duk dare koda da ya yi shi ne zai kusanci matarshi ya fi gane yayin in yaso ya sake. Matsawar bai yi wankan nan ba,to ko ba zai samu bacci ba, kasancewar yanayi ne na zafi shiyasa. Yana fitowa ya warware (AC) turarukan shi na ƙwanciya ya faffesa, sannan ya saka kayan baccin shi riga da wando.

Ya zauna bakin gado yana son jin muryar A'isha ne kawai,yau ƙwana biyu kenan ba su yi waya ba,bai san mene ne yasa yake son Yarinyar ba,yana tsoron fa kada Yarinyar ta mutu tamkar sauran matanshi. Ya soma neman layin yarinyar,yana yi yana kallon agogo goma ta gota a ranshi, ya ce ko kin yi bacci zaki tashi. Dai-dai lokacin ko ita tana kan darduma, nafila take yi sanda ta sallame sannan ya sake kira.

Ta ɗauko wayar ta ɗaga tare da sallama, ya ce "oh sorry Bebyna, na tashe ki kina bacci ko?" Ta ce, "a'a bana bacci, ya ce me ya hana ki? Ta yi shiru, ya ce to ko abinda ya hana ni bacci ne kema ya hana ki? Ta ce um,ya yi ƴar dariya kin san abinda ya hana ni ne? Ta ce a'a, ya ce in gaya miki? Ta ce eh,ya ce ni tunanin kine ya hanani ke fa? Ta yi shiru ya ce Beby kina ji na kuwa? Ta ce,ina jin ka,ya ce oh gaya min, ta ce ni ina sallah ne, ya ce good,me kike roƙo? Da sauri ta bashi amsa da cewa cikawa da imani da rahamar kabari, tare da samun Aljanna maɗaukakiya." Ya ce "Umhum? Yana son jin ƙarin bayani, ta ce "Shikenan nake roƙo," ya ce "batun aure fa baƙya yi mana addu'a? Shiru ta yi jikin shi ya yi sanyi ya ce A'isha in tambaye ki wani abu? Ta ce eh, ya ce zaki sanar dani gaskiyar maganar? Ta ce,in har na sani ba, ya ce "kin ji wasu maganganu ne a kaina?" Ta ce kamar me? Ya yi ɗan jim sannan ya ce koma na me? Ko kirkina ko akasin haka?.

Ta rasa me zata ce ya ce ina jinki nasan duk mai irin sunanki in dai ta ci sunan bata ƙarya. Sanar da ni. Ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce "Uncle duka biyun na ji da kirkin da kuma akasin hakan. Ya ƙwanta rigingine jikinshi ya yi matuƙar sanyi sannan ya ce "Beby tsorona ki ke yi ko? Kin tsane ni ko? Kina zargina kema ko? Na sani na dai na burge ki ko? Muryarshi ta soma rawa, shi kenan ba zan matsa miki ba Beby zan barki kema kina tsoron haka bana son ki mutu domin kin shiga raina sosai" ya kashe wayar ya jefar da ita a kan gado sannan ya ɗauko filo ya rufa akan fuskar shi tare da matsewa yana jin wani pain a cikin ranshi.

*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*

```1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account ɗin namu ya samu matsala ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*

*Masu son  tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427*

____________________________
   *📗MUMMUNAN ZATO📗*

                       *NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

             *Ɗandano page 10*

A ɓangaren A'isha kuwa duk sai ta ji babu daɗi har ma ta yi da ta sanin amsa shi, sai ma duk ta ji tausayin shi ya kamata,ta ji kamar yana kuka. Abbanta zai ji daɗi in yaji labarin nan kuwa? Ƙila ma ya ce ba zai yafe mata ba. Da sauri ta tashi ta duba agogo,sha ɗaya saura, ta ɗauki ɗari biyu ta fita, da sanɗanta ta fice bakin titi ta siyo kati ta dawo ta shige. Sai da ta kulle ƙofarta ta hau katifarta ta loda katin, gabanta yana ɗar-ɗar ta soma kiran layin shi kasancewar wannan ne karo na farko da ta taɓa kiran shi.

Dai-dai lokacin shi kuma yana ta neman layin Abba don ya shaida masa ya haƙura da auran, amma wai layin is switch off,sai ga call ɗin A'isha Beby kamar yanda ya rubuta a cikin wayar tashi. Ya tsura ma sunan ido, kada dai idanunshi ne suke mishi gizo? Ya dai ɗauka ba tare da yin magana ba,ta ce "Uncle" ya ce "Na'am"  ta ce "nifa ban zarginka,don Allah kada kayi fushi dani ko da na samu labarin tun a school ne na san dai an confuse amma ba dai na yarda bane,don Allah in nayi laifi kayi min afuwa." Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce "ba ki da laifi Beby, domin nima sai da nace a'a Abbanki ya ce babu damuwa, amma bari kiji wani abu,kin ga ke yarinya ce ko? Amma zan rantse miki da wallahi-wallahi ban taɓa shan jini ba, duk wani laifi game da sicret cold zargi ne,ban san shi ba, batun mutuwar matana ƙarar ƙwana ce kurum,kin yarda da haka? Jikinta a sanyaye ta ce na yarda,ya ce "to Beby ki ƙwantar da hankalinki, addu'a za ki dage da yi Allah ya zaɓa mana abin da ya fi zama alkhairi kin ji ko?" Ta ce "to,kaima ka daina fushin? Ta ci gaba kada fa ka sanar da Abbana," ya yi ƴar dariya bana fushi da ke, kuma insha Allah ba zan taɓa yi ba, itama ta yi ajiyar zuciya, sannan ta ce "to sai da safe,ka kwanta. Ya ji daɗin kalmarta, sannan ya ce "to zan yi yanda ki ka ce,kema ki ƙwanta tare da mafarki mai daɗi na twins ma su kama da face ɗin ki,ta kashe wayar da sauri.

Hajiya Jummai ta kalli kayan, sannan ta kalle shi.

"Me ka ke nufi da waɗannan kayan?" Ya dube ta "Na ki ne mana" ta taɓe baki, "Ni fa gaskiya duk zannuwan nan ba suyi min ba,babu kala ta, maimakon ka bani kuɗin na saya da kaina? Kuma ina son canza kayan ɗakina, sannan ga su Suby." Ya ce, "Jummai, gaskiya ni dai ba zan bada kuɗin wasu kaya ba,kin san nawa na siya waɗannan kayan? Game da gyaran ɗaki dai zan baki dubu ɗari,su Suwaiba kuwa dubu hamsin zan bada kada a kuma damuna,cefanen gida kuwa mun gama magana da Uche,ya rubuta komai." Ta sake fusata, domin ta kula ma ƙwangilar da take so ta yi bazata samu ba kenan, komai ƙit da ƙit? Ta dube shi "don kurum zakayi aure, sai ka dinga komai faɗa-, faɗa? Ga wani maƙo da ka koya,da Uche ne yake faɗin abinda ake so?" Ya ce,"to ke ko yaushe baki gida kin ma fi ƙarfin ki ce min zaki guri kaza,koda a waya ne sai dai na dawo baƙya nan, lokaci ya ƙure min dole na sauke abubuwan dake gabana, Uche kuwa shi ne yake girkin nan,don haka shi ne yasan abinda za'a nema.

Ta ce, "Kana lokaci ya ƙure,ba saura sati uku bane bikin? Ta ce, "batun lefe fa? Sai ka kawo a haɗa" ya ce ai lefe ya daɗe a gidan su amarya." Ta miƙe cike da masifa.

"Lallai Alhaji Saddiƙ aurenka na wannan karon ya banbanta da na baya, wannan karon aƙwai ƴar zargi." Ta soma kuka, "maƙiyana sun samu galaba,wato lefen ma ban isa ko gani inyi ba, na gode." Ta fita tana cewa gara daka nuna min babu ruwana abinda babu ruwan mutum ai daɗin ji ne da shi. Ya bita da kallo,wato ita bata san ma ta mishi laifi ba,bare ta bashi haƙuri ko ta mishi bayani shi ne ta zo tana tuhumar shi,ya samu labarin ta saida motar da ya siya ma su Safiya da Suwaiba, domin wanda ya gyara motar ne yake sanar dashi lokacin da ya je ɗaukar tashi motar. Da be ga ta su Suwaibar ba yace sun zo sun ɗauka ne? Sai yaron mai gyaran motar ya ce, a'a wani ne yazo ya ɗauka, kuma ya gaya mishi cewa Babanshi ne ya sayi motar.  Alhaji Saddiƙ shi dai alwashi ya sha ba zai ƙara sai wa yaran koda mashin ba.

Hajiya Jummai ta kalli Hajiya Kari.

"To kin ji yanda muka ƙwashe da Alhaji,babu abinda ya fi bani haushi wai har an kai lefe bani da labari saboda rainin hankali, ke kayan faɗar kishiya ma shi ya siyo min, saboda haka ina son mu koma gurin Boka, gashi bakon ya ce in biki ya rage ƙwana goma in koma,to gashi yau sauran ƙwana taƙwas. Tunda jiya tara ya ce min ne ko nawa ne ma oho."

Hajiya Kari ta ce, "To gobe sai mu je,in ce dai kin binne abin da ya baki?" Ta ce "ina fa ni ban fa san taƙamaiman lokacin ba sai jiya,na san zai kama zigar waɗannan ƴan iskan ƙannan nashi ne"  Hajiya Kari ta ce "Bari mu gama da amaryar, har su ba za'a barsu haka ba, sai mu shiga tsakaninsu." Hajiya Jummai ta ce, "Da ko kin taimaka min,ba ma dai irin tsinanniyar Nafisan nan, gashi yafi ji da ita duk cikin su."

Ta binne surkullen da aka bata,ta kuma yayyafa na yayyafawa kamar yadda aka umarce ta. Sannan ta nutsu don tana son samun kuɗi a hannunshi, duk da wannan karon ya tsuke mata bakin aljihunshi, ta samu dai-dai gwargwado.

Lokaci na ta zuwa gida kam ya sha fenti da gyara, yanda ya ba ta kuɗin canjin kayan ɗaki, haka ya ba su Fatima da Sadiya da Nafisa kuɗi su siyo na ɗakin A'isha, sannan shima nashi gefen sai da ya canza komai. Nan fa ta tada balli kan cewa shin wannan amaryar ta fi sauran ne yake ta faman kashe kuɗi har da sa mata kayan ɗaki? To ba zai yiwu ba,ya ce Jummai ki daina tada jijiyar wuyanki akan abinda ba za ki hana ba,yarinyar nan ko ba ni ne zan aureta ba kusan dole ne in mata kayan ɗaki, ballantana gidana za'a sa,kina cewa ba zata yiwu ba,za ki hana ne? Kema fa na baki haƙƙinki."

Su Hajiya Karima ne suka tausasheta da cewa yarinyar da ba mazauniya ba ki ke damun kanki? Gawa ce fa.

Ita ko A'isha, amarya duk ta gama sukurkucewa,iyayanta ma suna daurewa ne kurum,tuni ƴan'uwa da abokan arziki sun cika gida don yin biki.

Ranar ɗaurin aure ta kasance asabar,don haka ƴan ango sun iso juma'a domin ana gama ɗaurin aure za'a ɗauki hanya da amarya. Alhaji Saddiƙ ya kasa zuwa ɗaurin auren,waya ya yi wa Friend ɗin shi kan cewa ba zai samu zuwa ba,don ba ya jin daɗi. Lafiyar shi lau sai dai yana ganin kamar za'ayi ta nuna shi,ko kuma Friend ya shaidama ƴan'uwanshi halin da ake ciki,ko su iyayan in sun ganshi su dinga mishi kallon wanda zai yi musu sanadin ƴarsu da dai sauran tunani kala-kala.

Daren juma'a aka sanya amarya a lalle,ba ta saka kowace ƙawa ba, sai dai ƴaƴan ƴan'uwa sa'anninta. Da dare suna ƙwance a kan katifa zuciyar A'isha cike da tunanin gobe zata rabu da Ummanta da Abbanta,ƙila ma rabuwar kenan. Hawaye ne suke bin gefen kumatunta, wayarta tana ta ruri. Naja ta ce Amarya wayar ki na neman agaji, A'isha tasa hannunta ta lalubo wayar,muryarta a dusashe ta ɗaga wayar tare da cewa "Assalamu alaikum, Nafisa ce?" Ta ce "amaryar mu,na so in zo ban samu zuwa ba, sai dai in kin zo gobe mun haɗu, " ta ce "to ina yini ya ya su Hajiya? Nafisa ta ce, kowa lafiya, gama Hajiya nan,sai dai nasan ba zata ɗaga wayar ki ba saboda Brother ɗinmu ɗan fari ne,tana mishi kara.

A'isha ta ce,to ki gaida ta,ta ce to ga Uncle ɗin naki dama yazo ne nace ya kira min ke gobe. Ta ɗan yi ƙasa da murya kada ki manta da addu'o'i daren yau, saboda Allah ya yi mana jagora a cikin ɗaurin auren da za'ayi a gobe. Shiru kawai A'isha ta yi mata, sai kawai ta ji Muryar Uncle yana cewa, Beby kina jina? Ta ce eh, zuciyarta kuwa sake karyewa ta yi hawaye ya shiga sintiri a kumatunta, ya ce na kasa zuwa ne Beby sai ina ganin tamkar ban yi wa mahaifin ki adalci ba, ina jin nauyinsu, kukan da take maƙalewa ya kufce mata, ranshi ya daɗa tsinkewa, ya ce "A'isha kiyi haƙuri daina kukan zan yi miki magana ne," ta share hawayen ta sannan ta yi ƙoƙarin tsaida kukan ta ce, ina jin ka, ya ce ina son ki tashi daga wannan kukan ne kiyi alwala, nafila za kiyi tare da addu'o'i kin ji ko? Alkhairin da ke tare da auren,ki tsaida zuciyarki,ki daina wasi-wasi,ki saka a cikin ranki cewa duk yanda Ubangiji ya yi dake dai-dai ne,kin amince?" Ta ce "Uncle dama ni bani da wani zaɓi sai wanda Allah ya yi min, sannan zan yi duk yanda kace." Ya ce yauwa Beby sai da safe.

Tsam,ta miƙe,Naja ta bita da kallo,ta shige (toilet) ta ɗauro alwala.

Naja ta dube ta, Angon yayi lallashi kenan mu ko munyi mun gaji kin ƙi kiyi shiru? Ɗan murmushi ta yi sannan ta ce,Naja kenan ba zaki gane ba ne, sannan ta tada sallah. Sai ya kasance wannan dare duk wanda yasan halin da ake ciki tsakanin Katsina da Jigawa idanunshi biyu ya kwana, kuma tsaye gaban Ubangiji, ana ta kai kuka. Zuwa wayewar gari kowa ya tattara komai ya miƙa wa Allah, sai sauraro duk sun nutsu da cewa duk abinda Allah ya yi daidai ne.

A'isha kam sai ta wayi gari zuciyarta sake duk ƙuncin da take ji ya washe, sai dai ɗan abinda ba za'a rasa ba. Hakan ya yiwa Umma daɗi har ta isko Abba cikin ɗakinshi,tana shaida mishi cewa...

____________________________
   *📗MUMMUNAN ZATO📗*

                       *NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

             *Ɗandano page 11*

               *ƘARSHEN FREE PAGES*

*Alhamdulillah ƙarfe free Pages kenan idan baki siya ba kiyi ƙoƙari ki mallaki naki akan farashin masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*

```1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account ɗin namu ya samu matsala ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*

Shaida mishi cewa yau kam A'isha ta saki ranta,suna cikin zantawa sai ko ga A'isha ta yi sallama domin gaida Abbanta, bayan ta gaisheni ne ya ce "yauwa ƙawar Ummanta dama ina son in kira ki domin inyi miki nasiha duk da cewa tun da bikin nan ya matso muna tayi miki,na farko dai nasihar da zan miki ita ce, zaman aure ya banbanta da zamanki na gida,don nan iyakaci kici abinci ki ƙwanta da dai sauransu. Yanzun kam da zaran an ɗaura aure Akwai wasu haƙƙoƙi guda goma da suka hau kanki na mijinki.

Na farko shine ki yi masa biyayya duk abinda ya ce kiyi,ki yi masa, matsawar bai saɓawa addini ba, kamar yanda ki ka sani babu biyayya ga abokin halitta don saɓawa mahalicci.

Kima zama mai tsafta kamar yanda ki ka ga Ummanki tana yi, tsafta bata jiki kurum ba har da muhallinki.

In kuma ya kira ki zuwa shinfiɗarshi kada ki bijire.

Ta dubi Abba da sauri kamar tana neman ƙarin bayani, domin A'isha yarinya ce sannan ba wai suna zama da ƙawayanta suna hirar samari ko ta aure ba ne,haka nan bata da wata ƙawa wadda ta yi aure ballantana ma taji labarin zaman auran, kazalika ita ba ma'abociyar karance-karance ba ce, ita ana ta zaton in an mata aure zata na girki tana kai ma mijin ruwan wanka tasa mishi na buta kamar yanda ta gani Ummanta tana yi, sai ko gyaran ɗakin Abbanta da Umman bata bari wani ya yi sai ita.

Abba ya katse mata tunani da cewa, ma'ana in ya neme ki kada ki guje shi, Umma ta ce,nima na miki duk nasihar da ta dace,na sani ke dama mai biyayya ce,ki girmama ƴan'uwansa,ki ɗauki mahaifiyarsa tamkar taki, haka mahaifinshi, matarsa ki yi mata biyayya."

Hawaye suna zuba daga idanunta, ta ce insha Allah zan yi Abba da Umma, suka sa mata albarka tare da yafe mata,ta miƙe ta fita suka bita da kallo cikin tausayin ta yayin da ita kuma ta wuce cikin tsananin damuwa.

Ƴan ɗaurin aure sun hallara in da aka ɗaura aure. Maroƙiya ta shigo tana rangaɗa guɗa, A'isha dai-dai lokacin tana wanka wanda Umma Rabi ta matsa mata ta yi umma Rabi ƙawar Ummanta ce,tun suna dutse tana fitowa ta ji gidan ya kaure da guɗa, duk sai taji wata fargaba a cikin zuciyarta. Inna Uwani Ƙanwar Umma, ita ta ciro mata wani leshi baƙi mai ado, ruwan lemon zaki tasa ka,sun bata siket da bes da kuma pant duk baƙaƙe.

Aunty Hasiya mata ƙanin Abba ta ce ni ban ga ma rigar nono ba cikin kayan? Umma ta ce ba a saka ba, Umma Rabi ta ce to me za'a sakama ƙirjin ba komai, ita dai A'isha tana jin su, Ummanta ta ce kin ji saka kayanki ki tafi nan duk iyayan banza ne suka taru. Ta gama shirinta ta fita, bayan an ɗan natsa da gama ɗaurin aure sai kuma aka shiga shirin tafiya Katsina,kai amarya. Duk wanda ya cancanta ya yi wa amarya nasiha ya yi mata,dangin Uwa da na Uba. Idanu ta zuba ma Ummanta a zuciyarta tana raya cewa, ta yi wa mahaifiyarta kallon ƙarshe. Haka nan aka fita da ita tana ta rusa kuka.

Abbanta da sauran mutane suna waje gurin mota suna ta ce waɗanda zasu je Katsinan,don kowa yana son zuwa, kuma tafiya ta gari ba kusa ba,don haka suka ce dole ne wasu su haƙura ba kowa da kowane zasu je ba, an fito da ita tana cin kuka ganin Abbanta sai kuma ta ƙwace ta nufi gurinshi.

Ya riƙe mata hannu yana cewa haba menene haka kuma? Ganin yanda take rusa kuka har ma wasu daga cikin dangi suma sun soma taya ta, sai Abban ya kama hannunta ya ce,zo muje, ɗakinshi suka je ya zaunar da ita ya shiga lallashinta da cewa menene na damuwa bayan ta yi musu biyayya sannan ya san Friend ɗin shi zai kula da ita, zatayi karatun ta duka biyun, kuma suma da an ƙwana biyu za su zo shi da Ummanta. Ya miƙe ya ɗauko alƙur'ani izifi sittin da fiƙihu da Tauhidi ya ce ki riƙe wannan kin ji A'isha?" Ta share hawayenta tasa hannu biyu ta amsa tare da cewa , to Abba da gaske za kuzo? Ya ce in Allah ya so, tashi muje ga mutane can sun shiga mota ke dama ake jira. Allah ya yi miki albarka zan kira ki in kun isa,ta ce to. Abba da kanshi ya kai ta har mota inda ta zauna tsakiyar Inna Uwani da kuma Aunty Rabi matar ƙanin Abba. Suka nufi Katsina bayan ta yiwa gidan su kallon ƙarshe, tare da duban Abbanta da Yaya Abdulrahman Munnir da kuma Jafar.

Alhamdulillah ƙarfe free Pages kenan idan baki siya ba kiyi ƙoƙari ki mallaki naki akan farashin masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*

```1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account ɗin namu ya samu matsala ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*

[12/4, 20:23] Ummi Tandama😇: *📗 Page 12*

Can katsina kuwa, gidan Alhaji Saddiƙ yana cike da danginshi, na gefen Hajiya Jummai da kuma ƙawayanta. Amma shaƙiƙan ƴan'uwanshi irin su Fatima, gidansu Hajiyarmu suke yin bikin su. Kuma a nan suka yi girkin saukar amarya domin suna isowa direbobin zasu kira su a waya kamar yanda suka shedawa direbobin.

Gefen Hajiya Jummai kuwa tana ɗaki tsakiyar aminanta suna ta tofin Ala tsine ga Alhaji Saddiƙ ɗin da ƴan'uwanshi da kuma amarya da danginta. Tuni suka sa ma amaryar suni mai ƙararran ƙwana.

Yamma ta yi sanda motar amarya ta iso, tunda suka shigo Katsina direbobin suka yi waya suka sanar da su Hajiyarmu. Nan take su Fatima Anty Sadiya su Nafisa da sauran dangi suka ciko mota da kuloli ɗauke da nau'ikan abinci kalolin abin sha, suka nufo gidan Brother ɗinsu. Suna shigowa kallo ya koma kan su nan dai aka je aka tsegun tama Hajiya Jummai ita da ƙawayenta suka fito falon suka shiga yada habaici, domin tsarin gidan ƙaton mahaukacin falo ne mai ɗauke da ɗakuna huɗu, falon ya shiryu da kalolin kujeru na alfarma gefe-gefe.

Kusan seti uku ban da (dinning), ɗakin Hajiya Jummai sai na su Suby sai ko na A'isha, yanzun ɗayan na baƙi ne, sai hanyar da zaka bi don zuwa gefen shi yanda ya shirya kujerun falon yana nufin kamar kowace mace da nata, domin kalar kujerunki kalar labulanki kuma suna daf da ɗakinki kayan kallonki kuma suna nan a gurin, domin tsakanin kowane ɗaki zuwa wani ɗaki da ɗan tazara.  Akan kujerun A'isha suka zauna babu jimawa sai ga motocin amaryar sun iso,suka fito suka tari amarya,in da Nafisa taje ta rungumo A'isha tana cewa amaryarmu sannu da zuwa. Ta laluba kunnan A'isha tana cewa kada ki manta ki shiga gidanki da ƙafar dama tare da addu'o'i,kai A'isha ta ɗaga. Dama tun kafin su shigo gidan take zabga addu'o'i,suna shigowa sai wata cikin matan ta soma rangaɗa guɗa.

Hajiya Jummai ta miƙe zumbur tana haki,su Hajiya Karima suka riƙe ta tare da cewa,haba-haba Hajiya Jummai ai an wuce nan,me yasa ki ke tada hankalinki? Kada idanunki su rufe ki manta matsayinki, ta sauke huci, da zuwa zan yi in ɗauke matar da ta zabgo min wannan guɗar a cikin gidana da mari suka ce a'a Hajiya Karima ta jata cikin toilet me zai sa ki nuna kanki? Kada ki manta da zaran ya sadu da ita ta zama gawa kamar yanda yake faruwa da sauran matan,nuna musu faran-faran yanda za'a tafi ana yabonki,me yasa wannan karan duk ki ka kasa control ɗin kan ki ne?.

Ta dubi Hajiya Karima nima ba zan ce ga dalili ba, sai dai ina samun kaina da matsanancin Kishin yarinyar. Na tsane ta fiye da sauran kuma naga Alhaji ya fi nuna ɗokin aurenta fiye da sauran na baya. Hajiya Karima ta ce don Allah manta da kishin nan gawa ce fa, yanzu dai zo muje mu taryesu ki canza kayanki kiyi sabuwar shiga,mu rufa miki baya ki gaishe su kada ki nuna mata kishi don Allah, ta ce shikenan suka fito. Nan ko take ta zabga wani uban sun less mai shegiyar tsada, suka rufa mata baya zuwa ɗakin amarya.

Lokacin wasu suna sallah yayin da wasu ke cin abinci, A'isha dai lokacin tana zaune bakin gado. Nafisa tana kusa da ita tana waya, tamkar mutuniyar ƙwarai ta durƙusa tana gaishe su ƙawayanta ma suka gaishe su,ta ce ina ƙanwar tawa? Umma Rabi ta ce gata nan ta ƙudundune kai, Hajiya Jummai ta ce zamu ganki ne har mu gaji suka ce ƙwarai kuwa, Nafisa dai ko kallon ta batayi ba, amma don makirci har da cewa Hajiya Nafisa waton yau ana gurin amarya kenan ko?.

Nafisa ta gama waya amma sai ta cigaba da magana tamkar ba ta gama ba, don kada ma suyi magana da Hajiya Jummai. Suna fita kuwa su Umma Rabi suka soma yabonta kan cewa gaskiya wannan mata tana da kirki, Allah ya haɗa kansu. Nafisa dai bata ce komai ba,don ba wai suna zarginta da kisan matanshi ba ne, a'a shirine kawai basayi da ita,su kuwa suna komawa ɗaki Hajiya Karima ta ce,ni ban ga mutum ba a nan? Jummai ta ce,ai shine duk da tana rufe amma yarinya kamar ƴar kalan hanji? Wata da suke kira Hajjaju ta ce don rashin tausayin namiji sai fa ya ce zai neme ta ko? A, sosai ma, inji Hajiya Jummai, duk matan haka yake auro su amma ba ya ɗaga musu ƙafa, wannan ma ba zai kalleta ba,bugu da ƙari ma ni nafi son ya take ta. Hajiya Karima ta yi saurin ƙwabarta da cewa to ke dai ya isa zancan haka,mu dai Allah ya bada zaman haƙuri ki dai kauda kanki kawai,ta yi haka ne saboda wannan kashe-kashen sirrinsu ne sauran ƙawayan ba su sani ba. Nan take Jummai ta gano kuskuran da ta so tayi don haka sai suka shiga wani zancan.

A'isha tana zaune kan sallaya ta idar da sallar isha'i, Nafisa ta durƙusa ta ce sai da safe tunda kin ƙi cin komai sai dai zan faɗa ki da Uncle ɗin naki cewa tunda ki ka zo kin ƙi shan ko da ruwa ne.

A'isha ta dube ta,haba don Allah kar ki gaya masa. Umma Rabi ta ce ai gara dai ki sanar da shi ɗin. Nafisa ta fita tana cewa to sai da safenku, suka ce to ki gaida Hajiyarmu mun gode sosai,ta fita Inna Uwani ta ce yanzun A'isha haka za ki ƙwana da yinwa? Ta dube ta Allah Inna ni bana jin yunwa fa.

Hajiya Jummai ta shigo da sallama, fuskarta ɗauke da fara'a ta ce,sannunku, sannunku fa suka ce yauwa ta ce duk kun yi sallah kenan? Suka ce mun yi Hajiya. Ta ce,to bari a kawo muku abinci, suka ce wallahi duk mun ƙoshi,kin gan shi can ma wani ne ko buɗa shi bamu yi ba,ta ce to shikenan ku zo muje in kai ku masaukin baƙi,in ya so sai amaryar da ƙawayanta su ƙwana a nan. Suka ce to, suka miƙe suka bi ta sai sa'anninta uku aka bari.

Ita dai tana zaune kan sallaya,ɗakin baƙin yana da girma ga ƙaton gado sannan ga wasu manyan katifu guda biyu an baje duk sun sha shinfiɗa. T.V na bango ne a ɗakin kamar dai na falon sai dai shi ƙarami ne,ga (AC) ga kuma bayi. Ta buɗe wordrobe ta ciro musu manyan barguna kasancewar lokaci ne na sanyi, sannan ta ciro parnpas ta ce, masu yara gashi nan suyi musu nafkin,ta kunna musu T.V tashar da ake yin wasan Hausa,wato fim ɗin Hausa. Ta ce,in zaku yi bacci sai ku cire soket ɗin, kada ku manta da yiwa yara addu'a kun ji ko? Ku karanta musu ƙulhuwallahu,falaƙi da Nasi ƙafa uku-uku, da kuma ayatul kursiyu duk ku shafe jikinku da shi dana ƴaƴanku, suka ce to mungode fa Hajiya, Allah ya saka miki da alkhairi,ta ce haba ba komai sai da safenku,ku huta gajiya suka ce to Allah ya bamu alkhairi,ta fita ta ja musu ƙofa,su kuwa suna ta yabonta da cewa Allah ya saka mata tana da kirki,lallai A'isha ta yi dacen dangin miji da kishiya,ita kuwa fita ta yi tana cewa ƴan iska ba zaku gane ba ne sai kun zo zaman makoki.

Ita ko A'isha tana nan zaune kan sallaya ta zuba tagumi, yayin da su Naja suka yi ɗai-ɗai kan gado har sun soma bacci saboda gajiya zuciyarta ta nata neman dalilin da yasa ɗazun da Hajiya Jummai ta zo musu sannu da zuwa gabanta ya yi mugun faɗuwa, yanzun ma haka. Tana sallama ta ji gabanta ya faɗi,in ko haka zata ci gaba da ji lallai zata bani tunda guri ɗaya suke. Ta soma tambayar kanta da cewa menene ma na jin tsoron ta ko faɗuwar gaba dan ta ganta? Mace mai karamci da mutunci.

Ƙwanƙwasa ƙofar tare da buɗewa ne ya katse ta,a hankali ya yi sallama tamkar yana ciwon baki,ko kuma baya son ya tashi ƙaramin yaro. Kanta na ƙasa ta amsa, amma bata ɗago kai ba,ya tako har gabanta ya tsugunna,sam bata ma san ya iso ba, sai dai ta ji yace Beby (a hankali) ta ɗago idanu ta zuba mishi. Yana sanye da wandon jeans baƙi da rigar sanyi tafkekiya ta saƙar baƙin zare da fari, sai ta ganshi tamkar ɗan matashin saurayi,ko kusa ba ya kama shekarunsa,ƙyawun fuskarshi ya sake fitowa saboda ƴar rama da ya yi,ta sauke idanunta ƙasa, hancinta yana ci gaba da shaƙar ƙamshinsa,ya yi ɗan murmushi yanda Bebyn tasa ke dubansa, cikin yanayin damuwa ya ce Beby baki ci abinci ba, saboda me? Ta gyara zama bana jin yunwa ne Uncle, ya ce Nafisa ta ce min kina cikin damuwa ko ruwa ba ki sha ba,why Beby? Kina fargaba ko? Ta ce ba haka ba ne Uncle, ya ce to gaya min ya ya ne? Ta rasa me zata ce, ya ce ok,kina tunanin cewa in kinci wani abu na gidan nan shi ne zaki mutu ko? Da sauri ta dube shi, Uncle ba na nufin haka, ya ce to in ba ƙya nufin haka ki ci wani abu in gani, ta ce to,ya ce me ranki yake so a kawo miki shi yanzun? Ta ce komai ma zan ci ba sai na daban ba, maimakon tsugunnon da yake sai ya zame ya zauna sannan ya kira wayar Uche. Ya ce ka kawo min kaza mai zafi in kuna dashi a kitchen da maltina ko fresh milk ya kashe wayar ya dubi gefe,su Naja ƙawayan naki sun yi bacci da sun taya ki ci ko? Itama ta dube su,sun gaji ne, ya ce dole su gaji don da nisa. Uche ya ƙwanƙwasa ƙofa, ya miƙe yaje ya amso tiren ya dire a gabanta sannan ya zauna, "ci in gani" nauyinshi take ji don haka sai ya kauda kanshi gefe ya ciro wayar shi ya soma neman wani layi, aka ɗauka suka ci gaba da hirar kasuwancinsu.ita ko nan ta soma cin kazar nan wadda ta ji haɗi ta kuma gasu, ta ci sosai ta sha maltina kaɗan sai ruwa. Ya dube ta har kin ƙoshi? Ta ce,eh ya ce yauwa to tashi kije ki ƙwanta zuwa ƙarfe uku in gajiyar mota ta barki sai ki tashi kiyi alwala ki yi nafila ki tsananta roƙon Allah ya albarkaci aurenmu, ta ce to, kanta na ƙasa ta tashi ta hau gado ta kwanta tsakiyar su Naja ya ce sai da safe,kizo ki rufe muku ƙofa kiyi addu'a fa,ta ce to.  Bayan ta karanta ƙulhuwallahu,falaƙi da Nasi,ta tofa cikin tafukan hannayanta sannan ta shafa tun daga kanta da fuskarta har da sauran gaɓobin jikinta,ta yi haka har sai uku ta karanta Ayatul kursiyu.....

######
[12/5, 20:22] Ummi Tandama😇: *📗Page 13*

Amanar rasulu, sannan ta karanta da sunanka ya Ubangijina na ƙwanta kuma da izininka ne nake tashi in ka riƙe raina da (mutuwa) to ka ji ƙanta in ka sake ta ya Allah ka kiyayeta da abinda ka ke kiyaye bayinka salihai da shi, sannan ta ce:--

Allahumma innaka kalaƙta nafsi wa'anta tawaffaha naka mamatuha,wama hayaha in ahyetaha,fahfadha wa'in amattaha,fagfirlaha. Allahumma inna as'alukal afiya,tana koyi da Manzon Allah (S.A.W) in tazo ƙwanciya sai tasa hannunta na dama ƙarƙashin kuncinta ta ce:--

Allahumma ƙiyni,azabaka yauma tab'asu ibadaka. Sau uku, sannan ta ce bismikallahumma a mutu wa'ahaya. Lokacin ta soma hamma sosai don haka sai ta tsaya nan gurin ta kuma ƙwanta.

Shigar Alhaji Saddiƙ ɗakin da fitarshi kai har zuwan Uche duk a kan idanunta ne. Hajiya Jummai ta yi ƙwafa sannan ta ce lallai ban da yarinyar nan mutuwa zata yi ƙila da na ƙunshi takaici gidannan,dubi yanda mutumin nan ke ta faman sintiri a ɗakin yarinyar nan tun baƙi na nan,ta ciji yatsa tare da cewa kash, da na sani da har ƙawayan nata na ce su je can shi ko nasan da nan zai ƙwana ba kuma zai bar ta ba,in ya so tana mutuwa suyi zaman makokinsu gaba ɗaya an huta,su koma Jigawa su dawo, amma tunda an riga an yi haka shi kenan,sun dawo ɗin tunda ya kama su ne.

Washegari tuni tasa Uche a dama koko ga ƙosai. Rahina mai aiki tana ta suya. Sai ga ƴan aikin Hajiyarmu tare da Nafisa ɗauke da ruwan zafi gwangwanayan madara milo suga da kuma ƙatuwar kula mai ɗauke da soyayyan dankali da kuma ƙwai.  Sanda su Sofy da Suby suka shigo ɗakin babu ko sallama suka aje bokitin koko sun same su suna ta wadaƙarsu da shayi sororo suka tsaya sannan suka fita suka koma gurin Jummai in da take ce ma Rahina rage ƙosai ƴan ƙauyan banza shiyasa na ce ayi musu koko tunda shi suka sani, Suby ta ce Hajiya ai ba zasu sha koko nan ba, domin tea da ƙwai suke ta bikin sha.

Hajiya Jummai ta dube su,a ina suka same shi? Sofy ta ce,oho ƙila daga gidan waɗancan tsegumammun ne, gidan su Hajiyarmu. Hajiya Jummai ta suri ƙwanon ƙosai ta nufi ɗakin baƙin,tana shiga sai ta saki fara'a sannunku da tashi baƙi, suka ce yauwa ina ƙwananmu? Bayan sun gama gaisawa sai ta ce, to ga ƙosai nan da koko in zaku ƙara dashi, domin naga abin marmari ne na ce ayi muku, suka ce to mun gode, sai dai gashi duk mun ƙoshi gara ma ƙosan ma ɗan taɓa, Allah dai ya baku zaman lafiya.

Hajiya Jummai ta fita tana faɗin amin a baki, amma a cikin zuciyarta tsine musu take yi.

A ranar ne aka yi buɗar kai suka gyara mata ɗaki sosai, sannan suka shirya ta suka kaita gidan Hajiya Babba inda suka danƙa amanarta gurin Hajiyan, sannan suka dawo in da dangin nashi suka tara mata kuɗi daga nan aka kaita gurin Hajiya Jummai wadda ke hakimce tare da ƙawayanta, itama ance ga amana nan ta kuma ce ta amsa tare da cewa Allah ya taya ta riƙo,wata cikin ƙawayan nata ta ce ba a karɓar amanar kishiya fa Jummai. Hajiya Jummai ta ce ke daina gaya min wannan zancan,ai jahilan mata ne suke wannan abin yarinyar nan na ɗauke ta ƴar'uwa Allah yasa ki haifa mana ƴan dagwai-dagwai a gidan nan, suka ce amin,ta miƙo rafar ƴan ɗari bibbiyu to gashi ƙanwata. Nan aka shiga godiya kowa yana yabonta cikin dangin amarya.suka maida ita ɗakin ta,nan suka ƙara yi mata nasihar ta bi mijinta da matarsa, sannan ta bi danginshi ga dai shi ta gani kowa sonta yake yi. Suka shiga shirya kayansu,nan fa A'isha ta soma kuka suna ta lallashinta.

Hajiya Jummai ta fito da tiraman zannuwa goma sha huɗu ta basu wai suyi tsaraba, nunawa ta yi itace ta basu alhalin Alhajin ne ya bada kuɗin da zannuwan,tirmi ishirin, sannan ya bada ne kan Naira dubu uku uku ta siya ƴan dubu da ɗari bibbiyu,su dai suna ta godiya. Lokacin da suke shiga motoci ne a harabar gida motarshi ta shigo, kusa da su ya ce direban ya tsaya ya fito,yana cewa ina ce sai gobe ko jibi zaku tafi? Suka ce an gama komai Alhaji gara mu je gida dama ƙwana ɗai-ɗai muka ce zamu yi,ya ce to Allah ya kaimu da alkhairi, kuma ya sauke ku lafiya. Ya dubi direbanshi bani kuɗi nan in da na zauna,shi kan shi bai san ko nawa bane ya dai san ƴan dubu ɗai-ɗai ne. Suka ce har da wahala haka? Dama  ka barshi gashi ma Hajiya ta bamu zannuwa, ya ce ku ƙara, suka ce to mungode Allah ya sa muzo suna haka, ya ce amin. Nan dai suka ɗau hanyar Jigawa suna yabon waɗannan mutanan.

Shi ko ɗakin amarya ya nufa domin ya san yanzun tana cikin damuwa,hakan ce kuwa ya taradda tana ƙwance tana ta shirga kuka na fitar hankali. Da sauri ya isa gaban gadon,ya zauna a bakin gadon, tashi mana Beby ta so ki gaya min zaki bisu ne? Tashi inji" ta tashi zaune,ya ce kina son ki bisu ne? Ɗaga kai ta yi alamar eh, yace"to taso ki ɗakko hijabinki" ta share hawayenta,ta zauna tana ajiyar zuciya. Ta kasa tashi,ya ce "to muje Beby kada su tafi," ta ce "Abba zai min faɗa har da Umma" ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce to kiyi shiru,in naga kin kwantar da hankalinki zan ɗauke ki muje in kaiki,in da ni ne zasuyi miki faɗa? Ta ce a'a ta sake yin ajiyar zuciya sannan ta ce in dai ba zaka ce musu ina kuka ba,to baza su yi min faɗa ba,ya ce ai kafin muje ma kin daina kukan ko baki daina ba? Cikin shashshekar kuka ta ce na daina, wasu hawayen suka sake zubowa,ya ce a'a to gashi kina yi kuma? Ta ce to na daina, ya ce wai ba ki son gidan ne? Ko kina ganin za ki mutu ɗin ne? Ta ce ba haka bane, ina tuno su Umma ne da su Jafar.

Ya ce,ba ki ce da Abdulrahman ya gaida su ba ne? Ta ce na gaya mishi,ya ce to ki daina kukan kin ji ko? Da ƙyar dai ya shawo kanta ta yi shiru kusan awa ɗaya da rabi yana lallashi, lokacin ne aka yi kiran magriba sannan ya fito bayan tayo alwalla,sai da aka yi issha sannan ya dawo lokacin ma yayo wanka yana sanye da jallabiya mai ruwan toka mai gajeren hannu.

Yana riƙe da jakar laptop da wayoyi ya shigo ɗakin da sallama,tana zaune kan sallaya kanta yana ƙasa kewar gida ce ta cika ta har ma hawayenta suke zuba. Jin sallamarshi ta miƙe da sauri tare da share hawayenta. Ya tsura mata idanu, sai ta sunkuyar da kai ya isa kujerar da ke gefen gadon ya aje kayan hannunshi sannan ya zo kusa da ita. Beby! Beby! Har yanzu dai kukan ne? Ta ce a'a ai na daina,ya kama hannunta ya zaunar da ita bakin gado, sannan ya ce sanar dani me ke saka ki kuka ne? Ta ce, tunanin gida kawai nake yi,ya ciro waya bari na kira Abban,bata san lokacin ta riƙe hannunshi da sauri ba,ta ce Uncle don Allah yi haƙuri kada ka kira shi zai min faɗa,ya ce to shikenan kin ci abinci? Ta ce na ƙoshi ne. Nan dai ya yi wa Uche waya ya ce kada ya shirya mishi abinci a dinning,ya kawo mishi ɗakin amarya,nan yasa ta shinfiɗa mishi babbar darduma.

Uche yana kawo abincin ya shirya mishi a kai ba tare da neman izini ba,ya ce zo nan muci abinci,ta kalleshi ganin fuskarshi ɗinke sai ta je,ya jawo plet  ta amsa cikin natsuwa ta buɗe kulolin,tuwan shinkafa ne da miyar agushi, sai dafadukan taliya mai haɗe da kayan lambu.

Ta ɗago ta dube shi, kafin ta yi magana ya duk wanda ki ka ga ya yi miki a ranki sa mun. In to bashi ranka ke so ba fa? Ka ci dai duka, cikin natsuwa ta ke maganar ya ce ɗaya zan ci kuma ke ce zaki zaɓar min da abinda ya dace in ci matsayin abincin dare, ba ta kuma cewa komai ba ta janyo plet ɗin ta saka tuwo da miya sannan ta saka cokali ta aje mishi a gabanshi. Ta tsiyaya mishi ruwa da jus,itama kaɗan tasa tuwon tana yin loma ɗaya sai ta ji babu wani ɗanɗano duk da ƙamshin da ya cika ɗakin amma haka ta daure tana ɗan tsakura. Amma shi yana ta cin abinsa da alamu ya saba da shi, wayoyinsa suka soma ringing lokaci ɗaya ta miƙe ta ɗebo mishi su, sannan ta koma gefe ta sha ruwa ta zauna tare da tsura ma guri ɗaya idanu da alamun ta faɗa cikin tunanin nata,kusan minti talatin yana amsa wayoyi, sannan ya kira Uche ya kwashe kayan ya dubi A'isha, "Beby tunanin ko?" Ta sunkuyar da kai ya miƙe ya isa gurin T.V wanda ke manne a jikin bango ya kunna sannan ya shiga neman tasha,MBC 3 yasa sannan ya dube ta ga irin naku ko Beby? Ta kalla Cartoons suke yi na Tom & Jerry tana son cartoon,sai dai ta kula shi Uncle ya maidata wata ƴar mitsitsiyar Yarinya. Nan ko ta gyara zama ta shiga kallonta, shi ko ya jawo laptop ɗin shi ya shiga al'amuranshi na kasuwanci daga bisani ta ji bacci yana fizgarta,don haka ta hau gado bayan tayo alwala ta zauna ta jero addu'o'inta sannan ta kwanta bacci kuwa ya yi gaba da ita,sam bata tare da fargaba irin na amaren nan game da angwayensu, uku dai-dai ta farka har lokacin yana gaban laptop alwalla tayo ta zo ta soma na filfilu, hankalinshi ya yi nisa sai daga baya ne ya ji motsinta, nan shima ya yo alwalla.

Hajiya Jummai tana da tabbacin ango ya kwana ɗakin amarya fatan ta dai Allah yasa sun sadu .

Da safe har ɗaki A'isha taje ta gaida Hajiya Jummai ta same ta tare da su Sofy, cikin fara'a ta amsa ma A'isha, sannan ta ce dasu Sofy ba za ku gaida Antyn taku ba? Har suna haɗa baki gurin jan tsaki, haka da A'ishan ta gani yasa ta gaishe su ba su amsa ba, A'isha ta fito tana tunanin su kuma waɗannan su wanene? Tana shiga ɗakinta ta soma gyaran gado,ta gyara ko'ina sannan ta shiga toilet tana wankewa ya shigo cikin shirin fita motsin da ya ji a bayin ya sa shi tsayawa ya san tana ciki,jim kaɗan ta fito. Ya ce na zaci wanka ki ke yi? Ta ce a'a ina wanke bayin ne. Ta durƙusa ina ƙwana?  Ranshi ya yi fari sannan ya ce lafiya lau tashi na gode. Ya ci gaba ni zan fita ne don Allah kada ki yi kuka ko tunani sannan ki ci abinci kuma wannan aikin da ki kayi yanzu akwai masu gyaran ɗakunanku. Zan sanar da ke komai sai in na dawo yau da yamma zan haɗa ku da Jummai, ta ce to, har ya soma tafiya ta ce Uncle ka....sai kuma ta yi shiru,ya dawo har kusa da ita, nayi me? Sanar da ni mana. Ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta sannan ta ce ina nufin kayi break fast ne? Ya yi murmushi, abinda Hajiya Jummai ba ta taɓa damun kanta a kan ya yi ba kenan, haka gaisuwar da A'isha ta yi mishi ya sa shi jin cewa shi ɗin maigida ne. Ya ce A'isha bana yin break a gida saboda baƙwa karyawa da wuri ni ko bana son mutane su yi ta jirana a Ofis," ta ce "to acan ana saida abu ne? Ya ce zan sha copee a Ofis da rana kuma muna kusa da gidan cin abinci," ta ce "to sai ka dawo Allah ya bada Sa'a" ya ce amin Bebyna,na gode miki kiyi kallonki kin ji? Zan kira ki" ta ce to,ya fita ta bishi da kallo. A zuciyarta tana tunanin duk in da Abbansu za shi komai sauri sai Ummanta, ta mishi Abinda koda ba zai ci ba saboda sauri zai riƙe.

######
[12/6, 07:59] Ummi Tandama😇: *📗 Page 14*

Shi ko ya fito ne yana jin daɗin yanda A'isha ta nuna kulawarta kanshi, ƙaramar yarinya kenan. Sai sha ɗaya sannan aka kawo mata abin kari tea kawai ta iya sha domin hatta dankalin ɗanɗanonsa bai mata ba.

Misalin ƙarfe ɗaya da rabi tana zaune kan abin sallah tana karatun Alkur'ani tun bayan da ta idar da sallar azahar, Hajiya Jummai ta shigo tare da ƙawarta Karima, ta miƙe tana musu sannu duk cikin fara'a suka amsa. Karima ta ce wayyo ashe ma yarinya ce ƙarama.

Ita dai A'isha kanta yana ƙasa. Jummai ta ce eh, yarinya ce,sai wayar Jummai ta soma ringing sai ta fita ina zuwa bari in yi magana Alhaji ne ya kira ni ku gaisa ina zuwa,tana fita Karima ta matso kusa da A'isha, "yarinya ni dai zan miki nasiha ne ki riƙe mijinki ki mishi biyayya, kada ki zama cikin irin matan nan masu gudun miji,kin ga haihuwa yake so kiyi maza ki cika mishi gidan da ƴaƴa kin ji?" Zancan ya yi ma A'isha nauyi,don haka ta kasa ɗago kai, sai dai ta kaɗa kai alamun to. Ta ƙara ƙasa da murya,kin ga dai kishiyarki aminiyatace ko? To wannan ba zai sa in kasa gaya miki gaskiya ba, ita bata so kowace mace ta haihu tunda ita bata haihu ba,don haka zatayi ta zuga mijinku kan cewa kada ya kusance ki,ke yarinya ce in kin ji tana haka ki mata shiru, amma da lokacin ƙwanciya ya yi ki tafi gurin mijinki kin ji? Sai Hajiya Jummai ta turo ƙofa tare da sallama, sai Karima ta ja baya alamun bata son Jummai ta ji, amma yanda A'isha taga sanda suka haɗa ido suka yi wata alama da gira sai jikinta ya bata cewa ƙila sun shirya wani abu ne.

Yinin ranar ta amsa wayar Uncle kusan sau taƙwas, duk dai dan yaji halin da take ciki. Ta kira Umma da Abba da kuma Yaya Abdulrahman, shida saura ya shiga ɗakinta amma daga gani ya fara zuwa ɗakinshi, domin ya canza kayan shi daga suit zuwa jallabiya fara kar. Ta ce sannu da dawowa,an dawo lafiya? Ya ce lafiya lau Beby,ba dai wata damuwa ko? Ta ce eh,ya ce to bari muyi sallah, ta ce to. Wanka tayi tasa riga da siket na atamfa,bata damu da yin wata ƙwalliya ba, domin shafa wannan shafa wancan ba damuwar ta bane. Ta yi sallah tare da nafila raka'a biyu,ta zauna tana yin azkar ɗin yamma. Ayatul kursiyu ake fara karantawa, sannan falaƙi da Nasi da ƙulhuwallahu, sannan ta ce "am saina wa amsalmulkulilahi Rabbana as aluka khairan mafiy hazihil lailati wa khaira ma ba a daha,wa'a uzubika min sharri mafi hazihillailati wa sharri ma ba a daha, sannan ta ce:-

Allahumma bika amsaina wa bika asbahna,wabika nahya wa bika na mutu,wa ilaikal masir.

Allahumma anta rabbii laa ilahaaha illa anta kalaƙatani,wa'ana abduka wa anna ala ahdika wawa'aduka mastaɗa'atu a'uzubika min sharri ma sana'atu abu'u laka bi ni'imatika alayya wa abuu'ubi zanbi fagfirlii fa innahu la yagfiruz zunuba illa anta.

Haka ta yi ta kawo addu'o'i har zuwa isha'i ta yi sallah tare da yin shafa'i da wuturi,tana zaune tana tasbihi, Uncle ya shigo da sallama. Ta amsa, sannan ta yi mishi sannu da shigowa, ya amsa ya ce in kin gama zo muje,dama ta gama ta yi addu'o'inta ta shafa shima ya shafa tare da cewa Allah ya karɓa ta yi ɗan murmushi sannan ta ce Amin. Ya ce me kika roƙar mana? Ta dube shi, sannan ta sunkuyar da kai ta ce alkhairi, ya ce kin sani a ciki? Ta dube shi, "na manta" ya ce "to daga yau in kin yi sallah ki dinga saka ni cikin addu'arki, Allah yana saurin amsar addu'ar mace a kan mijinta, haka nan ta mijin akan matarsa. Ta ce to, ya juya zo muje, ta bishi suka ratsa falon shiga cikin wani labule, sai ga gurin cin abinci,dinning ne na glass mai kujeru shida,can gefe ga wani mai kujeru taƙwas,gurin ya tsaru gwanin sha'awa.

Hajiya Jummai ta shigo ta wata ƙofa bata hanyar da suka biyo ba, ashe kitchen ne, da fara'a ta shigo,ta dafa A'isha wadda tunda ta shigo ta soma jin wata muguwar faɗuwar gaba,ta rasa dalili duk lokacin da Hajiya Jummai ta zo inda take sai gabanta ya dinga wata muguwar faɗuwa.

Hajiya Jummai ta ce, ƴar ƙanwata kin fito? Cikin in-ina A'isha ta ce, in in ina  yini? Jummai ta zauna tana cewa, lafiya lau, Alhaji Saddiƙ ya yi murmushi sannan ya ce,gata nan sai kunya da tsoro,dubi yanda duk ta rikice daga shigowar ki.

Jummai ta ce, daina tsorona ko kunyata,ni ƴar'uwarki ce kin ji ko? Ta jawo plate ta soma zuba ma Alhaji shinkafa fara da miyar ganda,ta tura mishi, ita ko cous-cous ta zuba sannan ta ce me zaki ci ne ƙanwata? Shiru A'isha ta yi Uncle ya ce zuba mata shinkafa itama. A'isha dai tana jin su ba ta ce komai ba, domin ita ƙamshin abincin ma bai mata ba,tana ɗan tsakura tana korawa da ruwa kaɗan kaɗan,ya dube ta Beby ba ki cin abinci fa, ta ce ni dama bana cin abinci sosai. Jummai ta ce ki ci fa nan gidanki ne.

Bayan sun gama, ya dubi Jummai ya ce, to Jummai ga dai ƙanwa nan sai kiyi ta haƙuri da ita saboda yarinya ce, duk da na san A'isha tana da hankali da biyayya, duk in tayi ba dai-dai ba ki gyara mata, sannan ki nuna ta ga ma'aikatan gidan nan, ta ce insha Allah.

Ya dubi A'isha, Beby kin ga ƴar'uwarki nan kiyi mata biyayya sannan da akwai masu aiki babu abinda za ki yi hatta gyaran ɗakinki da wankin bayinki duk za su yi akwai mai girki,wato Uche kenan. Sai dai duk abinda ki ke so ƙya iya sanar dashi ga kitchen ɗin nan,za kuma a zo a saka miki wayar cikin gida a ɗaki saboda kiran masu aiki,in kin yi baƙi haka,ko dai wata matsalar,aikinki ɗaya ne jal shi ne gyaran ɗakina,wato shinfiɗa ta, to amma na ɗauke miki wannan tukunna don ba zaki iya ba.

Ta dube shi kamar zata yi magana, amma sai tayi shiru,na ta ganin menene abin wuya a gyaran gado? Nata ganin komai girman gado zata lailaye shi. Jummai ta ce, gaskiya kam, amma dai ka raba mana kwana saboda ko bata gyara maka shinfiɗar ba, saboda ƴan matsalolin ta kaga sai ka rinƙa ji,ya ce haka ne.

Bayan sun gama jawabansu, tana dai jin su,ta ƙosa ta koma ɗaki don jinta take tamkar kan ƙaya,ba don komai ba sai don Jummai,don haka ta soma hamma,ya ce je ki ƙwanta ai kafin ya rufe baki har ta miƙe ta nufi ɗakinta.

Jummai ta dube shi, Alhaji ni ko nawa ganin ba yi bane kace zaka ƙyale ta,ka san yaran yanzun da wayonsu sarai,mu da muke son yara ka tsaya renonta? Ya yi shiru, sannan ya ce ni abubuwan ne sun min yawa dubi fa yarinyar zan cutar da ita,ƙirjin ma babu komai sannan sai in dinga ganin tamkar in na ƙwanta da su ne suke mutuwa,shi yasa nake tsoro.

Jummai ta zaro idanu "kada fa asirinta ya tonu,ta ce mishi haba dai to da haka ne dani yanzun sai dai labarina ka daina wannan tunanin." Shiru ya yi yana nazarin maganarta,sai dai shi kam nashi ra'ayin ba zai taɓa ɗanɗana nauyin juna ba yanzun a tsakaninsu,yana ganin in ya ɓullo da haka ɗan sakin jikin da take mishi zata daina, amma sai ya bar wannan a ranshi don sirrinshi ne. Ya dubi Jummai ya ce haka ne,shi kenan sai ku riñƙa yin ƙwana bibbiyu in na gama ƙwanakina cike da jin daɗi ta ce Allah ya taimake mu ya bamu Sa'a, ya ce amin.

Abinda ya soma ɗaga hankalin Jummai shi ne,yau satin amarya biyu, kullum tana jiran ta ji Alhaji Saddiƙ ya ce jama'a ku zo, har yau shiru. In ta kira Karima ta mata magana sai ta ce bata da haƙuri ne sun taɓa yin wannan abin ya yi musu gaddama? Ta ce ko dai har yanzun bai ƙwanta da ita bane? Jummai ta ce oho amma yau zan bugi cikinta. Matsiyaciyar yarinya kina ganinta haka na kula zata yi salo don yanzun kin san kullum daga Ofis sai ya aiko an karɓar mishi wani zoɓo da take mishi?" Kari ta ce daina bani labari, zan dai zo gidan gobe.

A'isha kam yanzun tafi ƙosawa da karatunta,don haka sai ta ɗebo littattafan ta na makaranta tana ta karantawa, Uncle ya shigo ta ajiye ta miƙe tare da yi mishi sannu da zuwa,da sha'awa ya dubi takardun me ki ke karantawa ne Beby ? Ta ce ina ɗan duba books ɗina ne na school,ya ce kin tuna min,an kusa a koma hutu ko? Ta ce ni da jiya ma zan koma Sunday. Ya zauna kina son makarantarki ne ko in samar miki wata? Ta yi shiru sannan ta ce duk yanda kace bani da zaɓi Uncle,daɗi ya ji sannan ya ce to shikenan,nan da ƴan ƙwanaki zaki ƙara zama student ko Bebyna? Ta yi dariya har kumatunta suka loɓa. Abinda yake burge shi sosai.

A'isha tana ta gyaran ɗakinta domin tunda take sau ɗaya ƴar aikinta ta taɓa zuwa ta gyara mata daga nan bata dawo ba,don haka sai ta ci gaba da aikinta,dama ba ta ɗauke shi aiki ba,ta gama ta jona na'urar da ake saka turaren wuta,ta zuba nan fa ƙamshi ya soma tashi. Hajiya Jummai da Hajiya Kari suka yi sallama,ta amsa nan take gabanta ya shiga faɗuwa ta soma karanta Allahumma kafihim bima shi'ita,domin yanzun addu'ar da ta koma karantawa Jummai kenan.

Suka shigo ta zauna ƙasa ta sunkuyar da kai,su kuma suka zauna bakin gado. Ta gaishe su kanta yana ƙasa suka amsa cikin fara'a, sai kurum suka ji an bugo ƙofa a tsorace A'isha ta ɗago kai. Suwaiba ce cikin rashin kunya ta ce Hajiya ki zo kinyi baƙi,me kike yi ne ɗakin wannan ƴar ƙauyen? Jummai ta miƙe tana cewa ubanki nake yi kin ji ko? Ta bita suka fita. Hajiya Kari ta girgiza kai tare da cewa, Allah wadaran irin wannan tarbiyya da Jummai ta koyawa yaran nan, ta dubi A'isha ƴar nan sai fa haƙuri kin dai ga abinda nake gaya miki nan,ta sake matsowa gaya min yanda kuka yi da Alhajin naki,baki dai gudun shi ko?" A'isha ta ɗaga kai amma zuciyarta cike da tsanar matar, ta ce yauwa ƴar nan,to ya ya kukeyi ɗakinshi ki ke zuwa? Ran A'isha ya ɓaci ta yi mata banza tana ta tambayarta A'isha tayi shiru, da ta matsa mata sai ma ta saka kuka.

Hajiya Karima ta ce yau na shiga uku daga tambaya? To yi haƙuri,wayar A'isha ta soma ringing ta share hawayenta ta ɗaga Uncle ne ya ce na turo direba, ya amshi zoɓon nan na ji shi shiru, ta ce bai zo ba ko ƙila yazo bai samu wanda zaya aiko ba, ya ce to bari na kira Uche ya amsa ya bashi,ta ce to sai ka dawo, ya ce ba wata matsala ko? Ta ce a'a babu komai ta ajiye wayar bayan ta kashe ta kalli in da Karima take, tana nan zaune ba ta koma ta kanta ba, sai kawai ta shiga haɗawa Uncle ɗinta zoɓon da ta riga ta haɗa cikin wani ɗan ƙyakƙyawan ƙwando,yau har da cin-cin da diblan ta haɗa irin na bikinta ta zuba cikin wani ɗan ƙwanon tangaran saiti ne da jug ɗin ta zuba kofunan jug ɗin Uche ya ƙwanƙwasa ƙofar ta buɗe mishi sannan ta bashi tana juyowa taga Hajiya Kari ta miƙe ta ce, to sai anjima tunda kin ƙi mu yi hira A'isha can ƙasan maƙoshi A'isha ta ce to ta shige toilet.

########
[12/6, 16:20] Ummi Tandama😇: *📗 Page 15*

Cike da al'ajabi Kari ta isa ɗakin Hajiya Jummai da sauri, Jummai ta miƙe ta ce ta sanar dake komai? Karima ta ce, ina fa, wannan yarinyar tana da shegen wayo, na lura muna mata kallon biri ne ita kuma tana mana kallon ayaba.

Jummai ta dafe ƙirji ya ya ku kayi ne? Karima ta zauna,yarinyar da na matsa mata sai kurum ta saka min kuka,can kuma in gaya miki sai Alhajin ya kira ta,zo kiga kashe murya don sanabe Uncle ma take ce mishi an haɗa su soɓo da cincin an kai mishi.

Jummai ta ce,ni yanzu zama bai ganni ba,Kari shirya kawai mu nufi maguzawa in ko Boka na kan Dutse ya yi kuskuran aikin nan ne to ya cuceni,Kari ta ce daina wannan zancan kema kin san ba zaya ƙi yin aikin nan ba sai dai in tanan ne aka samu mishkila, amma yanzun ki bari sai gobe mu je muji dalili. Jummai ta ce bana bacci fa Karime, kullum sauraron ganin gawar yarinyar nake yi. Kari ta ce ki dai haƙuran ma goben.

Washegari tun safe ta fice ta riga maigidan fita, gidansu Kari ta nufa, shi dama ba'a ɗakin ta ya ƙwana ba, amma ga tsarin shi ko ba kece da shi ba zai shigo har ɗaki ku gaisa. To ya shigo ɗinne su Suwaiba suka ce mishi ta fita. Ya kalli agogon hannunshi,baƙwai da ƙwata ya dube su ina taje? Suka ce ba su sani ba,ya yi tsaki sannan ya fita. Ya samu A'isha tana gyaran gadonta, ya ce a'a Beby ina mai aikin naki ne? Ta ce Uncle ni na ce ta barshi bana son zama bana aikin komai shi ne dalilin,ya ce good,ta rusuna ta gaishe shi, ya ce zai fita,yau dai ta daure ta ce to Uncle kace ma Uche in aiki ya yi mishi yawa ni zan dinga taya shi, domin bai dace kana fita baka karya ba, kallonta ya dinga yi some times tana ɗaure mishi kai in tayi wata maganar domin sai ya ji tafi Jummai wadda ta haifeta hankali. Ya ce Beby kina son in dinga karyawa a gida ne? Ta ɗaga kai alamar eh,ya ajiye jakarshi ta Ofis ya zauna kan kujera je kitchen ki haɗo min ko menene zan ci,ta ce to amma kana ganin Anty Jummai ba zata ga kamar na canza mata tsari ba? Nan ma kallonta yake yi,ya girgiza kai sai ta saka takalmi to bara na zo ta fita ya bita da kallo zuciyarshi tana ta kai kawo an ya kuwa in ya ce zai bar A'isha sai zuwa wani lokaci ba zai ƙwaru ba? Shi yana mata kallon yarinya amma komai nata irin na masu hankali. Koda yake haka Allah yake ikonshi, sai ka ga yaro da hankalin manya.

Ita ko tana shiga kitchen ta samu Uche yana ta aiki suka gaisa nan ta tsaya tana kallon na'urorin girkin da yake amfani da su. Ta ce,ya ɗora mata ruwan zafi, sannan ta ɗebi dankali zata fere da wuƙa nan ya amsa yasa na'urar fere-fere nan da nan sai ga shi cikin lokaci ƙanƙani ya gama nan dai ya dinga taimaka mata ta shirya mishi abin kari mai sauƙi tunda sauri yake yi ta cika tire.

Ta zauna gabanshi tana cewa Uncle yi haƙuri na tsaida kai, ya ce Beby kenan,nan ta haɗa mishi tea tare da baje mishi dankali da ƙwai, duk da yana cewa tea bai dame shi ba,ya sha sosai, har ma ya gano ba wai baya son tea ɗin ba ne,ba a iya haɗawa bane. Ya dubi A'isha ya ce Beby kin san da can ina shan tea lokacin ina gidan Hajiya, daga baya sai na ji ban son shi,ta ce la ban sani ba shine kasha da ka gaya min me ka fi so da nayi maka shi. Ya ce a'a wannan ya yi min daɗi ina son irin shi, amma yaushe za ki min irin kunun gyaɗannan da Ummanki take yi? Ta ce gobe in ka fita ka ce Uche ya zo zan rubuta abubuwan da zana yi amfani da su sai ya siyo zan maka gobe,ya ce na gode.

Sun isa maguzawa kai tsaye suka zarce gidan bokan dutse,sun samu wasu halakakkun ƴan'uwansu a gurin, sai da suka jira suka fito sannan su kuma suka shiga. Yana kallon su ya soma sheƙa dariya tare da cewa, kowane shege ya ci tuwo damu miyar ma ba zai sha ba, Hajiya Jummai ta kalleshi,na kan dutse me ka ke nufi? Kari tayi saurin cewa ba dai ka ɓata mana aiki ba? Ya kuma ƙwashewa da dariya,na san dole ku dawo domin na san ba zaku ga da ƙyau ba. Jummai ta zaro idanu ya ce ke ƴar tselan uwar menene na zare idanu,kin maida ni kidahumi tunda ina daji ban san komai ba,kin kawo tsohuwar mota buga-buga an kawo min,to nima shi yasa na ce zaki gani, zufa ta shiga ketoma Hajiya Jummai, ta ce kash, to yanzu ya ya za'ayi ne? Ya ce ki zube kuɗi in miki aiki, ta ce haba na kan dutse, wannan aikin ai na biya ka na motar ne kurum aka sami akasi, ya ce ban san akasi ba,ta ce to naji yanzu nawa zan ba da? Ya ce sai kin zube min dubu ɗari biyu,shiru tayi abin duniya ya ishe ta,ta dubi Karima,to yanzu ya ya kenan? Kari ta ce kawai ki nemo kuɗi kin san na dutse bai san Allah ba bare a roƙe shi," ta ce to shikenan zamu dawo ta miƙe cikin damuwa,Karima ma ta miƙe suka fita. Cikin mota Hajiya Jummai sai mita take yi har da kukanta don baƙin ciki Karima ta ce ɗan iska ko yaushe ma ya san mota da har yasan an yi mata ƙwasƙwarima ne? Jummai ta ce bar matsiyaci ni yanzu ma kuɗin cikin account ɗina da ƙyar in ya kai dubu ɗari, Karima ta ce ki ƙwaƙula jikin shi mana. Hajiya Jummai taja tsaki tare da cewa, kada ki ban haushi Hajiya Kari kina yi kamar baki san halin shi ba? Kin san fa dole sai ya san me zan yi da kuɗi kafin ya bani,ta ce ke ja can, inji Kari wani sa'in sai ki ringa yin abu tamkar wawuya,ba za ki iya ce mishi biki ko sunan ƙawa ba? Ta ce, to zan dai ƙwatanta in bai bani ba sai na saida abin hannuna (warwaro) in yaso shima sai nasa a min aikin da na tambayi kuɗi zai bani,Kari ta ce kin yi tunani haka za'ayin ma kawai. Cikin satin zuwan Hajiya Jummai maguzawa uku, kuma ta kai duk abinda boka na kan dutse ya buƙata ta koma tana sauraron abinda zai biyo baya.

A'isha tana zaune tsakar ɗakinta kallon Cartoons take yi a tashar mbc 3 amma zuciyarta tana can ga tunanin Uncle ɗinta Wanda ya tafi Angeles ta ƙasar Amerika,don kasuwancinsu tafiyar ta ƙwana uku ce yau zai dawo gashi har yanzun bai iso ba, kuma tun safe ya ce sun taso,baya da abokin hira hasali ma tunda Uncle baya nan ba ta fita, domin su Suwaibar nan dariya suke mata tare da yi mata ba a wai ƴar ƙauye, ita ko Hajiya bata zama ma bare ta ƙwaɓa musu,don haka sai ta daina ma fita tunda tana da komai kuma Uche in ya gama abinci zaya kawo. Kasa ɗaurewa ta yi ta jawo wayarta ta shiga neman layin shi na can, cewa akayi ba zai je ba ta ajiye wayar ta saka kanta cikin guiwa. Sam bata ji turo ƙofa ba,bare taku sai dai taji an dafata a bayan ta. Firgigit ta waigo cike da tsoro, tare kuma da faɗin innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un. Ganin Uncle sai taji wani shegen daɗi cikin fara'a take cewa har ka dawo? Sannu da zuwa ya ce yauwa sarkin tsoro, ta ɗan rufe fuskarta sannan ta ce zauna,ta nufi ɗan fridge ɗin dake ɗaki ta ciro mishi ruwan swan tare da kofi.

Ta tsiyaya mishi ya amsa ba tare daya zauna ba, har zai kai ruwan bakin shi yana cewa yauwa Beby. Ta ce Uncle ka zauna mana, Manzon Allah (S.A.W) ya ce kada ɗayanku ya sha yana daga tsaye. Uncle ya zauna yana cewa,na gode Beby, kin tunasar da ni,ya sha ya aje kofin bari nayi wanka ko? Kai ta ɗaga shi kuma ya fita dama yau gurin Jummai yake.

A'isha kam baki tasa ki tana kallon tsarabar da Uncle ya kawo mata,shin an ya ma Uncle yana sane ya kawo mata kayan nan kodai yayi mantuwa ne? Ba wai da yawan kayan ko tsadar su ba, a'a illa ganin ƴan bulawus ne na yara tare da takalma sawu ciki, sai rigunan jeans da wandunansu, wani abin dariya har da Tedi,ta tasa kayan tana kallo tana juyawa,ƙofarta aka buɗo tare da sallama,ta amsa, Nafisa ce ta miƙe da sauri tana cewa "Anty Nafisa sai yau? Ta zauna tana cewa yauma nazo in yi muku sallama ne, A'isha ta dube ta haba? Ina za ki? Zan koma ma makaranta mana, A'isha ta cika da mamaki, ta ce dama ba ki gama ba Anty Nafisa? Nafisa ta ce sauran wata shida in kuma na tafi ba zan dawo ba, sai na gama. A'isha ta ce, Allah sarki,za ki bar Hajiyarmu ita ɗaya dama Uncle ya maida ni can kafin ki dawo, yanda A'isha ta karya murya,ta yi maganar ya yi matuƙar bawa Nafisa dariya, ta ce ban da shirme irin naki yaushe ki ka ga matar aure ta bar ɗakinta,ta koma wani gida? Ta ce can ma fa gida ne don Allah ki gaya ma Uncle dama fa ban taɓa zuwa ba tun lokacin da su innata suka kai ni.

Nafisa dariya take yi tare da ƙara yarda,lallai A'isha ƙaramar yarinya ce, Uncle ya shigo da sallama. A'isha zumbur ta miƙe tsaye tana mishi sannu da zuwa. Ya amsa yana duban ta yauwa sannu Beby,ya zauna bakin gado yana kallon Nafisa,auta kin zo ne? Tana dariya ta ce eh jiya Hajiyarmu ta ce kazo bana nan gidan Anty Fatima na ƙwana ya kuma sai ga tsaraba, A'isha ta isa fridge ta ɗibo goran ruwa da na jus ta tsiyaya ta miƙa mishi ya ce yauwa Beby shi yasa ko'ina na shiga da naji ƙishin ruwa sai kawai na tuno ki. Nafisa ta ce a'a da yake kai Uncle ɗinta ne amma ni ai bata bani ba. Cikin tsokana Nafisa tayi maganar, A'isha ta dube ta tare da cewa,ayya Anty Nafisa ba haka ba ne,ko fa gaisawa ba mu gama ba fa don Allah,ta ɗauko wani kofin tana zuba mata. Nafisa ta ce,ba wani shima Uncle ɗin naki ai tun kafin ma ya gama zama ki ka bashi. Ta miƙa mata ruwa to gashi yi haƙuri shi dai Uncle dariya ya ringa musu, A'isha ta ce sha to,ki gani nima ga tsarabata.

Nafisa tana ɗaga kayan ta shiga gumtse dariya don kada Brother ya ci ƙaniyarta, amma wannan kayan da bai wuce su Maama su saka shi ba yaran Anty Sadiya.

A'isha ta ce kuma zai min dai dai Anty Nafisa? Uncle ya katse ta da cewa,baki gwada ba ne Beby? Nawa kema ki ke za suyi miki mana.

Nafisa ta kasa daurewa sai da ta dara sosai ma. Ya ce, menene kuma na dariya? Ta ce Brother na tuna ne ta wayance da cewa, A'isha ce wai na ce nazo muyi sallama, sai ce min ta yi wai don Allah in ce maka ka maida ta gurin Hajiyarmu ta taya ta zama kada ta zauna ita kaɗai, Uncle ya yi murmushi.

A'isha kenan haka suka ringa tsokanarta suna mata dariya ita ko ta dage tsakaninta da Allah in za'a kaita gidan Hajiyarmu tana so. Cikin ƙwanakin Uncle ya matsama Aisha dole take saka kayan kowanne da ɗan takalmin sa,in tasa ta kalli madubi sai ta ganta tamkar irin yaran shahararrun masu kuɗin nan waɗanda ake bala'in ji dasu.

Sai dai iyakarta ɗaki, shi ko nashi ganin nawa take bata wuce sa su ba. Yau ma riga da wando ne masu ƙyau na jeans sai dai tana sawa ta saka hijabi. Tana so ne in Uncle ya shigo yau ta ce tana son yin kitso,aiko yana shigowa koɗa ta ya soma yi,kai kai kai Beby kin ganki kuwa? Ta saka tafukan hannunta ta rufe fuska ya ce iyyeh cire hijabin in gani? Ta cire ya dinga koɗata sai dariya take yi. Can ta ce Uncle ina son yin kitso, ya dubi agogo zo muje in kai ki,ta soma murna yau dai zata fita,ta ce in cire kayan ko Uncle? Ya ce bar kayan ki saka hijabin. Iyakarshi gwiwa ta saka takalmin kayan mai ƴar igiya suka fito ya rufe ƙofar.

#######
[12/6, 22:08] Ummi Tandama😇: *📗 Page 16*

Ɗakin Hajiya Jummai suka nufa,tana zaune ta doka tagumi,jin sallamar maigidan ta yi wata gwauruwar ajiyar zuciya. Ya ce,ina ne ake yin kitso Jummai?" Ta ce waza ayima kitso? Ya ce Beby ce,ta nanata sunan cewa Beby? Wacece haka? Kafin ya bata amsa A'isha ta shigo da sallama. Ran Jummai ya dugunzuma amma sai ta daure ta ce um kuje saloon ni dai can nake zuwa. Ya ce muje Beby, A'isha ta ce sai mun dawo Hajiya, Jummai ta ce "um hum" da ƙyar ta amsa,gaba ta shiga shi ke jan motar dan direba ya taso ya ce barshi malam Sale, in ka gansu zaka za ci ƙaramar ƙanwarshi ce ko kuma ƴarshi ta fari. Wani ƙaton comflek ya kaita sannan ya sadata da wani shahararren shagon gyaran kai, hannu ya riƙe mata yau ce rana ta farko da ya taɓa taɓa jikinta, shima ɗin ba wai don yaji wani abu bane a'a ya yi haka ne kawai don wani nishaɗi da yake cikin ranshi, yana son tafiya da yara, kasancewar shi sanannan mutum mai shagon da ƴan aikinta suka shiga yi mishi gaisuwa irin wadda ake yiwa manyan ƙasa. Ya ce,ga Bebyna tana son a gyara mata gashinta, mai shagon da kanta ta cire mata hijabi ta ce mai za'a saka miki? A'isha ta ce a'a kitso nake so,matar ta ce, to amma sai an ɗan wanke shi ya yi datti.

A'isha ta ce to amma kada a ƙona min gashina, Uncle ya ce kuyi mata yanda take so ku kula da ita,zan je na dawo,ya dube ta zan je in dawo,ya kalli mai shagon ku bata take care please,ta ce kada ka damu nan suka wanke mata kai suka gyara mata ƙunba suka yar fa mata kitso, har da wankin ƙafa dan ma sunyi taƙi ta ci wani abu.

Bayan ya kirata ta ce an gama ya iso,ba tare da ɓata lokaci ba suka ce mishi dubu uku, shi kam bai ma san me ya ɗibo ya basu ba, daga nan haka ya shiga yawo da ita guraren kayan ƙwalama da na wasan yara. Har dariya ma abin yake bata. Sai da suka biya gidansu wani abokinshi Alhaji Najib, matarshi mai kirki Hajiya Ummi, ita ma ba wata babba ba ce yaranta biyu amma tana da Uwargida yaranta biyar. Zuciyar A'isha ta ƙwanta da Ummi,sun ɗan yi hira sannan suka wuce gida, da ledoji ta shiga gidan shima ya shigo da wasu na Hajiya Jummai ne itama ya siyo mata abubuwan da take so.

Tana zaune a falo ita da su Safiya, suna yin sallama Suwaiba ta yi sauri tasa remote ta rage radio da ya cika gidan da kiɗa sannan kowace ta shiga neman ɗanƙwalinta, ita ko Hajiya Jummai sai ta kau da kai tamkar bata san sun shigo ba, gurin ta A'isha taje ta yi mata sannu da gida, sai ta wayance da cewa ai bata gansu ba, har sun dawo? A'isha ta ce eh,ta nufi ɗakinta. Zaman A'isha na ɗan kwanakin ta gama yarda Uncle ɗinta shi ba mugu ba ne ba ya shan jini haka nan ba ɗan yankan kai ba ne, ta yarda matan shi na baya ƙwanan su ne ya ƙare.

Shi ko nashi ɓangaren zuciyarshi ta amince da cewa kusantar matan da yake yi ne sanadin mutuwar su, domin ga A'isha, tafi wata ko zazzaɓi don haka ko sha'awar kallonta da auratayya ma ba yayi. Ita ko Jummai jin shirun nan ya yi matuƙar ɗaga hankalinta.

A'isha tana zaune Uncle ɗinta ya shigo cikin tsokana ya ce Beby duk school ɗin da naje ban samar miki Form ba sun ƙi ɗaukarki, jikinta ya yi sanyi ta ce, to Uncle bari na koma makarantar da nake, ya yi dariya ya miƙo mata form din Ulil Albab,ya ce amma fa ta ƙwana ce,zamu je gobe su yi maki interview,tsabar murna bata san lokacin da ta rungume shi ba tana murna, tare da zabga godiya, cikin satin ya gama mata komai bayan sun mata interview,sai suka maida ta (SS1) maimakon (SS2) da take inda A'isha ta ji daɗin makarantar haɗe take da islamiyya.

Ranar da ta halarci makarantar ta ruɗe da ganin tsarin makarantar duk abinda ake sai wa ɗangata Uncle ya sai mata. Sannan ya yi mata nasihar ta kula da kanta kuma ta kama bakinta kada ta ce ita matar aure ce, tunda makarantar bata matan aure ba ce,ta kula da addininta. Ta yi abinda ya kaita, Ummanta da Abbanta duk suma sun mata nasihar, ko da ta je yiwa Jummai sallama ko kallonta bata yi ba, haka ta fito jiki ba ƙarfi,su Sofy da Suby kuwa dariya suka shiga yi suna cewa ci baya.

Tun zuwan A'isha makaranta ta samu ƙawaye kasancewar ta mai ƙwar jini. A'isha irin mutanen nan ce waɗanda nan da nan sun shigar ma mutum rai,hulɗar ta dasu Samira Kabir Malumfashi, Amina Sani Katsina,Zainab Tahir Kaita, ya sata ƙara wayewa, kasancewar su ƴaƴan masu da shi. Itama tun daga shopping ɗinta suka gane ƴar wani don ɗin ce, suna karatu sosai don makarantar babu wasa.

Ranar da ta cika sati uku, Uncle ya kawo mata ziyara lokacin suna zaune da su Samira suna tsifar kai, domin duk ranar Lahadi suke yin kitso, wata mai kula da gefen su ta zo, ta ce cikinku wacece A'isha Mustapha? Ta dube ta cikin razana ni ce,ta ce to kizo kina da visitor, tun kafin ta isa gurin da aka tanada don ganawa da maziyarta, ta gama yanke hukuncin cewa Uncle ne. Don haka ko da taga shi ɗin ne bata wani ji mamaki ba,ta yi murna da ganinshi sosai,ta rusuna ta gaishe shi ya amsa shima yana mai tsokanarta da cewa, wato kinfi son school fiye da gida ko? Tana dariya, ta ce me yasa haka Uncle? Ya ce,naga kin ɗan yi ƙiba ne,ta sake yin ƴar dariya sannan ta ce ina su Hajiyarmu da kuma Hajiya? Ya ce suna lafiya sun ma ce in gaida ki. Ta ce Anty Nafisa fa? Ya ce tana lafiya, kullum mukayi waya sai ta tambaye ki,ta yi ƴar dariya. Ya ce kin yi ƙawaye yanzun na sani ko? Ta ce eh to sai dai ƴan ɗakinmu kuma suna da kirki bari na kira maka su,ya ce to Bebyna kira su.

Ta je ta kira su wai su zo su gaisa da Uncle ɗin ta,ya gaisa dasu ya yaba dasu har ranshi ya kuma yi masu ƙyautar da tasa su doguwar godiya, sannan ya ce ku dage da karatu ku dinga taimakon junanku ta gefen karatu kun ji ko? Suka ce to Uncle mungode,ya ce yauwa ban da faɗa. Bayan tafiyarsu ne ya tambaye ta koda matsala? Ta ce babu komai suka fito ta raka shi har cikin mota,yau ce rana ta farko da ya saka tafin hannunshi cikin nata ya haɗa su ya murza ta dubeshi, sannan ta sunkuyar da kai amma sai tana jin wani yanayi mai wuyar fahimta. Tamkar yana isar da wani saƙo ne daga jikinshi zuwa nata. A hankali ta zame yatsun ta daga nashi, shima jikinshi babu ƙwari ya miƙo mata kuɗi,ta kasa kallonshi sai dai cikin siririyar murya ta ce bani fa da matsala Uncle, ya ce na sani Beby ki dai amsa.

Ta samu su Samira suna labarin Uncle ɗin, A'isha wai mutumin nan ya yi wallahi, A'isha ta ce kamar ya ya kenan? Amina Sani ta ce komai ma, A'isha yana da yara? A'isha ta ce a'a matarshi bata taɓa haihuwa ba. Zainab ta ce ayya ni kam ƙyawunshi ne ya kasa tsere ma idanuna, amma ku fulani ne ko? A'isha dai ta ce eh, ranar dai sun kuma yarda A'isha ƴar gata ce,kusan duk sati uku Uncle yana zuwa duba A'isha, sannan cikin makarantar akwai wayar da ɗalibai suke amfani da ita yana kira haka ma Abba yana kiranta.

Cikin haka sukayi jarabawa suka sami hutu, inda Uncle ya zo ya ɗauke ta Hajiya Jummai kuwa wadda rashin mutuwar A'isha yasa ta yi wurjan-wurjan, tamkar ta zare saboda tashin hankali,tana jin cewa yau A'isha zata dawo bata yi ƙasa a guiwa ba gurin fito da dukkan asiran da ta tanada na gurin bokaye daban-daban ta shiga zuba su wasu na binnewa ne wasu kuma na yarfawa,kai har toilet ɗin A'isha sai da ta saka asiri cewa tayi wai ya buɗe ɗakin za a share mata, kafin ta iso,shi ko har da sa mata albarka.

Yanda yaga A'isha ta ɗan murmure har wasu ƴan mazaunai ta yi sannan ƙirjinta ya ɗan yi tudu ta riga sai kurum ya samu kanshi da sha'awar kusantarta. Ya kasa manta yanayin da ya ji a ranar da ya riƙe hannunta.

A'isha ba ta manta da addu'ar shiga gida ba,da ta ɗaki tana aje jaka ta shige toilet ɗauke da addu'a a cikin bakinta, ta yo wanka ta fito. Uche ya gabatar mata da abinci. Bayan sallar isha'i tana zaune Uncle ya shigo ya zauna bakin gadonta yini ya yi yana tunanin ta ina zai ɓullo mata? Ko ya sanar da ita ƙudurinshi game da ita? Kai in ya yi haka ƙila ta daina ganin girman shi,to ko ya....ta katse shi, lafiya Uncle? Ya ce zaki iya gyara min shinfiɗata? Ta yi ƴar dariya haba dai shinfiɗa kawai zan kasa gyarawa kuma na ke gyara nawa ma? Ya ce kin san fa gado na ba irin naki bane yana da girma,ta ce zan iya,ya ce to kiyi shirin baccinki kawai sai kije ki gyara min hope zaki iya? Ta ce why not, Uncle zan iya mana. Sam bata san nufin shi ba,don haka sai da ta gama shirinta tsaf na bacci har tana Uncle ya kawo min dabara ina dawowa sai in ƙwanta yau dai zan ga kalar wannan gado da Uncle ya ke cewa ba zan iya gyara shi ba. Hajiya Jummai tana zaune a falo lokacin da A'isha ta fito sanye da kayan bacci riga ce doguwa in and out. A'isha ta yi mata sannu, sannan ta wui. Sam A'isha bata san kishi ba sannan bata san ƙudirin Uncle ɗin nata ba,don haka kai tsaye ta shige ɗakin tare da sallama.

Jummai tana kallonta,kishi da baƙin ciki ya sa ta faɗawa ɗakinta da gudu,nata ganin A'isha ta yi haka ne don ta ɓata mata rai don ta nuna mata itama ta san daɗin namiji.amma da ta tuna bokan gindin tsamiya da na kan dutse bakinsu ya zo ɗaya,kan cewa in dai tayi amfani da maganin da suka bata ya yi amfani da ita ya koma ya yi da A'isha to an gama komai, kuma ita ta yi duk yanda zatayi yau da asuba ya kwanta da A'isha lallai ta san gawar A'isha kawai za'a ɗauko, domin bata da ja da maganar bokayen nan guda biyu dan sune abin dogaronta, wa'iyazu billa,shin hakan ta kasance?......

Mu haɗu a littafi na biyu.

Taku:-
K/Mashi.

No comments