MASIFAFFAN NAMIJI Complete
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:Jamilaumar351*
*DEDICATED TO:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi...!*
_Bismillahir rahmanir Rahim in the Name of Allah,The Most Beneficent The Most mercefull Praise be to Allah Lord of The Words..._
*001*
*ZARIA..*
Area:Tukur-Tukur...
'"Hafsah!...Hafsah...!Hafsah...! sunan danaji Megidana Abdullahi na Tsagamin shi da Asuban fari,wanda hatta mazan da suke wucewa ta kofar gidanmu in sun dawo Daga masallaci suna iya Jiyo kwakwazon Kiran Sunana da Abdullahi keyi muryansa Kakkausa kamar zata tsaga gidan.
Kaina na Dafe ina Daga Durkushe acikin karamin Kichen dinmu Dake tsakar Gida Ina Faman kunna Risho sai na kunna Lagwanin sai ya mutu da kanshi Tun Wajen 6 da wani abu na safe na Fito ina idar da sallar Asuba ban ma yi Tunanin komawa ba Saboda yau din Litini ne farkon Sati Su Amira nada Makaranta kada su makara Abdullahi ya Dora Laifin akaina Tunda tare yake Wucewa dasu in zai tafi aiki Bisa Mashin Dinsa mai Suna Wayyo Kudina.
Saurin Mikewa nayi Jin kiran yafara Kusantoni kada na Kular Dashi dogon Sikat din Jikina na gyara Lokaci daya da Hijabin danayi sallah wanda ban cire ba Jin garin yau din an Tashi da sanyi sanyin Damuna dayake Jiya an kwana Tsala ruwa,ina kokarin Shiga Dakin muka ci karo Dashi zai Fito,Da Sauri nayi baya ina Raba Ido Cikin Kulufuwa da Takaichi yake Jifanta da wani kallo kafin ya Daga Murya yana Fadin"Wani sabon Iskanci kuma kika samo Hafsah..!?
Muryanta cikin Sanyi nace"Name fa Abban Amira..? Harara ya wurgamin yana Fadin''Bansani ba..Nace bansani ba bandama Salon iskanci kira nawa nayi miki Tun ina Daga cikin Daki baki amsa ba sai da na Fito..? Yafada yana wani karkace tsayuwa Cikin Jin Haushinta,Ajiyar Zuciya ta sauke kafin ta kada kai kawai ta wuce shi Zuwa Cikin Dakin bayanta yabi yana Fadin"Hafsah ina mgana kina Tafiya..? Yafada cikin Mamakinsa.
Atsakiyar Falon Taja ta tsaya tana Fadin"A"a kayi Hakuri ba Tafiya nayi ba na Shigo Daki ne kada makota su jiyo Fadanka,mganar kuma Kira banji bane Lokacin danaji na amsa kenan zan taho Dakin sai ga ka kayi Hakuri.."Tafada Cikin Sanyin Murya Kawai Tsayawa yayi yana Kallonta cikin Fada,sai yanzu na karemai kallo Dogon Namiji ne mai Cikar zati da kamala mai Fadin Kirji da cikar Cikakken Da Namiji mai iko Ba fari bane ammh Wankan Tarwada ne,Fuskarsa bata da Tsawo sosai sai dai tana da Fadi kadan Hancinsa Dogo ne Turbarkallah Masha Allah Sajensa daya zagaye bakinsa shi yake karamai kyau da Kwarjini.
Abdullahi Usman Direba kenan Dan Misalin Shekaran Haihuwan 32 da biyu Aduniya Mai iko ne kuma mafadacin Namiji ne ga iyalansa bai da sauki ko kadan Ballatana Ragowa a kallan Farko in kayi mai bazaka taba Zaton Abdullahi ya iya Fada ba ammh Ranar dakayi katarin zuwa gidansa nan zaka ga Abunda ake Kira Tijara da kudinka Sai kayi Mamakin Dama Abdullahi na iya Dogon Mgana ne..?haka yake baka iya yankema Abdullahi Hukunci ga Dabi"unsa matarsa Hafsah ce kadai Zata iya Fadar Wanene Abdullahi 90%Cikin Halayyarsa wanda Mutane basu sani ba,sai yan"uwansa makusantansa.
Numfashi ya Sauke Lokaci Daya yana Fadin"Eh Lalle wato kada makota Sujiyo Fada na ko Hafsah..? Wato ga mafadaci ko..? Yo in gaskiya kikeso Uban wa ke sani Fadan in bake ba.Kullum kwakwalwarki bata Daukan Mgana Koda yaushe sai dai adinga nanata miki Mgana Daya,ko karatu ya isa ki gama Haddaceshi acikin kwakwalwarki ammh Ina baki da Buri illah Kiga Ina Mgana Shine Burinki sai anyi Mgana kiwani Langwabe kai kamar Wata marainiya kina Sharan kwallar karya.."Yafada yana kallonta tana goge kwallarta da gefen Hijabinta,Bata dagoba ta kara kwantar da Murya tana Fadin"Allah ya baka Hakuri.."
Tsaki yaja yana Fadin"Ameen...Sai ana mgana ki wani fama ma mutane kuka kina wani Allah baka hakuri"yafada yana kwaikwayan Muryanta cike da Haushi ita dai bata Dago ba kanta na kasa tana kallon Center Capet din Dake tsakiyar Dan madaidacin Falon nata wanda yaci Kujeru saiti Daya mai Dauke da Karama Mai zaman mutum biyu Guda biyu da kuma Mai zaman mutun uku guda daya na kuma mai zaman mutum biyu,Babu komai daga kujerun sai Tibin Bango Plasma dake kafe a bangon Dakin,wanda ya samu mahadin Dish din da suke kallo Dashi..
Hannu ya yarfa yana Kallonta yace"Kinga Malama ni ba Hayaniya na Fito nayi dake ba ina Takarduna wanda na Dawo dasu gida Daga wajen aiki Ranar Jumma"a saman Madubinki na ijiye kuma yanzu nazo zan Dauka bangani ba.."Cikin Sanyin Murya ta wuce Cikin Bedroom din tana Fadin"Suna cikin Dorowan gado ni na Dauke da zan gyara Dakin Jiya.."Binta yayi abaya Cikin Fada yake Fadin"Kinji ko..?kai Hafsah wai ke Wata irin macece..? Sau nawa zan gaya miki kidaina Tabamim kayana ko wani abu nawa in na ijiye da Hannuna Ehe..?
Yafada yana Tsareta da manyan Idanuwansa kamar ya maketa Baki ta saki kafin ta Bude tana Fadin"Haba Abban Amira ina Laifina anan?,na dauke maka ne saboda kada Amira ko Amir su dauka su bannata maka.."Tafada Cikin karya Murya Wani Dogon tsaki yaja yana fadin"Na sakaki..? Ki barsu su bannata mana bani na ijiye ba..? ko kinfini sanin akwai su Amiran ne..? Nifa wannan Sanaben naki sam baya Burgeni Hafsah in ma zaki chanza Ki chanza Tunkafin dare yayi miki,Dillah Malama daukomin Takarduna zan Fita dasu ne..!
Yafada yana Yarfa mata Hannu batayi musu ba ta Juya Ta Bude Drower din gadon ta Daukomai Takardun ta mikamai bayan ta Ramkwafa Fizgewa yayi cikin Fada yana Dubawa Zuwa chan yace"Allah ya Soki Wlh da wata Takarda ta bace sai kin Raina kanki..Daga yau sai yau karki kara Tabamin kayana Daga inda na ijiye am i Clear..? Yafada yana Taba kunnansa Numfashi ta Fesar tana Fadin"Naji insha Allahu haka bazata kara Faruwa ba.."Bai kalleta ba yawuce gefen gadon yana zama ita kuma ta Fice tana kada kai.
Kichen ta koma Sai lokacin ta Duba taga ba Kalanzir ne Da Sauri Ta Daga glan din kalanzir din nasu taji ba komai sai da gabanta yafadi sanin Halin Abdullahi yanzu kan mganar ba Kalanzir sai Ranta ya kara baci tayi Kokarin samun wata Dubara ammh Ashana taki kama Lagwanin Dole dai uwar naki Dakin ta koma tana Sunne kai yana Saka Takardun Cikin karamar bakar Jakarsa ta Briefcase ta Shigo yana ganinta ya Daga kai yana kallonta,Tunda yaga tana wani Sunne kai yasan akwai matsala Baki ya Tsuke yana kallonta yace"Da wani abu ne..?
Yafada kai tsaye Cikin Sanyinta tace"Eh...Eh...Dama da..."Dama mene in zaki yi mgana kiyi malama..! Ya katseta cikin Dauriya tace"Eh dama Kalanzir ne na duba naga babu wanda zan kunna Rishon dashi.."Tafada tana Sosa kanta Wani irin kallo ya sakarmata kafin kawai ya kada kai yana Fadin"Bazaki taba Chanzawa ba Hafsah narasa Wata iriyar macece ke..? Sau nawa zan gayamiki duk Abunda babu ki dinga Fadamin tun kofa da Nisa..? Yanzu ki duba agogo 7am ake nema kuma kina sane da cewa 7:30am nake fita na Biya na kaisu Amira makaranta kana na wuce wajen aiki, baki ma sa mana Ruwan wanka ba ballatana akai ga Abun karyawa.."yafada cikin bayyana Takaichin dake cin Ransa.
Kasa tasakeyi da kai kafin tace"Kayi hakuri Wlh Allah bansan babu sai ya..."Wannan ya Rage naki ga Naira Dari ki Dauka ki Siya gawayi kiyi amfani dashi Domin yanzu babu inda zan samu kalanzir sai dai in na tashi Daga Office na Taho dashi.."yafada yana Jefamata Naira Darin daya Dauko Daga Cikin Walet dinsa bata tsaya wata mgana ba ta Duka ta Dauka ta Fita zuwa Falo karamin Dakin dake kallon nasu ta Shiga inda suke ijiye kayan abinci sai kuma wata karamar katifa Inda Amir da Amira ke kwana Mirmishi ta saki kafin ta karisa ta zauna gefen gadon tana Dukan Kafar Amira Lokaci daya tana Fadin"Amira...ke Amira Tashi maza.."
Ido Amira yar Shekara Shida ta Bude tana kallon mamanta Cikin Sauri ta mike tana Fadin"Mommy ."Mirmishi Hafsah ta sakarmata tana shafa kumatunta tace"Tashi kiyi sallah kiyi Sauri kizo ki shiga gidan Asiya ki Siyomin gawayi yau mun Tashi kalanzir din mu ya kare sai Abbanku yatashi aiki zai taho mana Dashi.."Amira bata koma ba Tatashi tana Fadin"Mommy ina Abba...? Hafsah tana kokarin Tada Amir tace"Yana daki kije ki gaisheshi Dagachan sai ki shiga bayi kiyi awala kiyi sallah kizo ki siyomin ina Jiranki kinji ko..? Dakai ta ansa mata kafin ta Ruga ta Fita da Gudu Amir ta Tada daga Barci waje ta Fita dashi ta sakashi Bisa Foo yayi Fitsari,kana ta wanke mai Fuska ta mai alwala ta turashi Daki tace yaje yayi sallah ya wuce yana Dan Gudunsa na yara wanda shima Ashekaru iyakarsa Shekara uku da wani abu.
Kichen din ta koma tana Tunanin me zata yi musu na karyawa Sharp sharp,ganin Lokaci ya tafi ya sa ta Fito da Murhun gawayin nata tsakar gida saboda yasha Iska Duk da Tsakar gidan bai da girma ammh kana gani zaka Fahimci komai na gidan Muhallin mace Daya ne,Buhun gawayinta ta Zazzage duk da ya kare ammh ta samu Kadan tayi Sauri zubashi Cikin Murhun gawayi ta kwafkwafi Sauran kalanzir din glan ta kunna wuta dayafara kamawa Da mafici ta tada gawayin da Sauri ta Dora yar madaidaiciyar Tukunyarta Ta cika da Ruwa,Dayake suna da Rijiya Tun Jiya almajiranta yunusa ya cikamata babban Robanta da Ruwa.
Kwai ta fasa,lokaci daya tana yanka Albasa ta gama kenan tana Jajjaga kayan miya da kayan kamshi Wanda zatayi amfani Dashi Wajen Soya kwai da Dahuwar indomie,Sai ga Amira ta Fito tana sanye da karamin Hijabi bayanta ta Rumgume tana Fadin"Gud mrning mommy.."Tana Dariya ta Dakata da Abunda takeyi tana Fadin"Ehe Amirata ta zama baturiya kin gaida Abbanku toh yaji kin iya Turanci..?
cikin Farinciki Amira ta gyada kai tana kallon Mahaifiyarta Kumatunta Hafsah ta ja tana fadin"Gud girl...Maza muje na Bude miki gida ki siyomin gawayin kafin wannan ya mutu.."Tafada tana mikewa Daga kan kujeran Tsugunee,Taja Hannun Amira suka nufi hanyar waje ita ta cire sakatar kofar gidan kana ta Damkama Amira Naira Darin,Fita tayi da gudu itama kuma Hafsah ta tsaya nan tana Lekenta dayake gidan yana kallon Gidansu ne,ko minti goma Amira batayi ba sai gata ta Fito Dauke da kullin bakaken leda Guda Biyu masu Dauke da gawayi Da Sauri Hafsah ta tarbeta suka Dawo cikin Gida,cikin Sauri ta Dauki Wata Karamar Roba acikin kichen dinta ta Juye Ruwan zafi har ya fara Tafasa,ta shiga daki dashi Cikin Bedroom dinsu ta shiga inda Ta Iske Abdullahi na wasa da Amir cikin bayin takai Ruwan ta zubamai Rabi Cikin Botikin karfen dake bayi wanda yafi kama dana gargaji ko Tiolet dinsu na Tsuggune ne ammh mai Floshing din nan,ammh kuma bayin Shinfide da Siminti sai Tashin kamshin Detol yake yi Domin Hafsah akwai Tsafta kwata kwata bata da Kazanta.
Akwai Wata katuwar Bombi mai Cike da Ruwa,cikinta ta Debi Ruwa ta surkamai Ruwan wankan Daidai Misalin sanin Komai tama Abdallah bata iyamai,Sauran ruwan kuma ta kauda dashi gefe Ta Fito tana yarfa Hannunta Lokaci Daya take fadin"Abban Amira ga ruwan wankan chan.."Bai amsa mata ba ita kuma bata damu ba ta Fice sanin yajita Sarai,koda ta Fito Tsakar gidan Amira ta karisa jajjaga mata kayan kamshi da Hanzari ta Bude Ledan gawayin ta kara Ta Fifita yatashi taDauko wata karama Cikin Tukwananta ta Dora ta zuba Ruwa Daidai,Daki takoma ta Dauko Indomei guda Biyar wanda zasu ci da kuma wanda su Amira zasu tafi Dashi Makaranta.
Agurguje take komai sai da ta Zuba Indomie ta tura Amira ta Dubo mata ko Abbansu ya Fito Daga wanka ta Dawo tace bai Fito ba, bata damu ba ta cigaba da aikin gabanta Cikin Sauri ta Sauke Indomie ta Dahu ta maida kaskon Ta Zubo mangyada Cikin wata karamar Roba da Cokali ta fara So kwan sai da Tagama tas kana tatashi ta Shiga Kichen ta dauki basket din su Amira ta zuba musu harda kwan,ta mikama Amira ta kai Daki Sauran kuma ta Zuba cikin kula,Ruwan zafi ta maida Saboda Sauri bata saka Cittan da ta saba Dafawa dashi ba Sauri take ta kamallah komai kafin ta Shiga Daki,kawai suma su Amira wanka ya Rage Ruwan yana zafi ta Juye cikin Flaks kana ta maida Wani Ruwan wanka.
Tattarra komai tayi zuwa Cikin Daki saman capet din dake Tsakar dakin ta Jera komai Ta Zura da Gudu ta Dauko Pure water guda biyu ta fasa ta Durama su Amira cikin goransu na Cikin basket dinsu,ta koma kichen ta kwaso kanann kofuna ta Dawo daki ta jera kusa da Falks din Ruwan zafi Dayan dakin ta koma ta kwaso kayan tea dinsu tazo ta jera duka cikin Sauri kafin ta Nufi Cikin dakinsu nan ta Iske Abdullahi ya Fito wanka yar yayi ma Amir wanka ma,Da Hanzari tatura Amira cikin bayi ta Tubeta ta mata wanka ta Fito Amir ta fara Shafa ma mai Abdullahi kuma yana tsaye yana saka maballin Rigarsa,Amira ita ta shafama kanta mai Hafsah ta Fito musu da Uniform,Amira ta saka ma kanta ita kuma ta sakama Amir harda safa da Takalmi ta Dauko musu Jakunkunansu ta jasu zuwa Falo ta zaunar dasu ta hada musu Tea ta zuba musu Indomie da kwan ta Turama kowanne gabansa tana Fadin"Oya kowa yayi Bismillah kuma kuyi Sauri in ba Haka ba Abbanku yatafi ya barku.."Jin haka yasa suka Fara cin Abinci bayan sunyi Bismillah.
Tea din Amir ta Dauka tana Fifitamai sanin baya iya shan Abu da Zafi sai ga Abdullahi ya Fito Cikin Shigar Riga da wando kalan Navy blue,sunyi matukar mai kyau Ta kallesa tana Mirmishi ammh shi ko kusa Fuskarsa ba Walwala kusa da Amira ya zauna Jikinta na Rawa ta Shiga Kiciniyar Zubamai Indomie din Hannu ya Dagamata yana Fadin'Barshi..Bani Tea din kawai.."Jikinta a sanyaye ta Tsiyayamai Ruwan Tea din ta Tura gabanshi da wata Harara ya Rakata kafin yace",Oh ni kike so na hada Tea din kenan yau..?
Da sauri Hafsah tace""A"a ba nufina ba kenan naso ka Hada da kanka ne kada kace ina cika maka Siga.."Hararanta yakarayi kafin yace"Toh bazan hada ba..Kuma ki cika sigan ki gani.."Numfashi ta sauke kafin taja Kofin gabanta Madara ta farama Zubamai Cokali Biyu Zata Rufe kenan yace mata,"Kina Nufin Iya madarar da zansha kenan..? Wai ni Hafsah ke ki ke siyan kayan Shayin ne da kike min Ididdiga..?
Saurin Taran Numfashinsa,tayi da cewa'Bafa haka bane..Gudun nayi na Saka maka da yawa kace na Cika maka madara.."Wani kallon kasa kasa yayi mata kafin yace"Commom malama Karamin madara kina batamin Lokaci.."Numfashi ta Sauke Aranta tana fadin komai akayi maka koda na Gudun karkayi mgana ne sai ka Tanka,Madara da Bonviter din da yawa ta Zubamai Siga kuma ta sakamai kadan ammh duk da haka sai da yayi korafin ta bashi Tea ba siga Kai ta dafe kawai tana kallonsa Sigan ta Turamai gabansa Lokaci daya tana mikewa kallonta yayi yana Fadin"Ina zaki..? Ke bazaki karya bane..? Tana kokarin Shiga Uwar dakin tace"sai anjuma."Baki ya tabe kafin yace"Kanki.."yafada yana Zakuda kafada irin ko ajikinsa dinan.
Takwas daidai suka gama karyawa Shi ya fara mikewa yana kwalama Hafsah kira sanin Kiran yasa ta Fito da Sauri Lokaci daya tana Dauke da Jakarsa Karama baka da makullin mashin dinsa ta ramkwafa ta mikamai ya amsa Lokaci Daya yana ficewa,Ita kuma ta kama Hannun Amir yana Rike da basket dinsa Hakama Amira suka Fito Nan suka iske Har Abdullahi ya Fito da farar Lifansa dake Cikin wani Daki kwara daya dake gidan wanda ba"a gyara ba sai dai yana da kofa Siminti kasa ne kadai bai Dashi da Silin nan yake ijiye mashin dinsa in ya Dawo har Kofar Gida ta rakasu Daganan ya karbi Jakarsa yace ta koma bata Rufe gidan ba sai da taga Tashinsu Amir na gaba Amira kuma na baya Rike da kwandonsu ya tada mashin dinsu suka tafi tana musu Fatan Dawowa Lafiya.
Ajiyar Zuciya ta sauke kafin ta maida kofar gidan Ta Rufe,ta koma Daki ta zauna itama ta karya Saura kuma ta ijiyema Alamjiranta in yazo ta bashi,Kwashe komai tayi ta maida Muhallinsa Sauran kayan da aka bata kuma ta maida Kichen ta koma ta gyaro Dakunanta,Kayan su Amira kuma ta kaisu dayan daki ta Zuba cikin kwandom kayan wankinsu na Abdullahi kuwa ta Ninkemai ta Saka cikin Wardrope batayi wanka ba sai da ta wanke bayi kana ta Juyo Ruwan wankanta ta kashe gawayin ta maida kichen ta kulle kana ta koma Daki tayi wanka ta Shirya Cikin Riga da Sikat na wata atamfa mai kalan ja,Da baki Karamin Azkar dinta da wayarta ta Dauka tazo falo ta Zauna Bisa Kujera,tana kallon agogo har 9am tayi ammh Shuru Nepa basu kawo Wuta ba gashi tana son Tayi Blanding din kayan miya kishingida tayi kan kujera tana Tunanin in basu kawo ba in Yunusa yazo sai ya mikamata Nika Wayarta ta maida gefenta tafara Karanta azkar dinta hankalinta kwance.
_Hmmm ya kuka ji Salon..? Zai kayatar da ku..? Kuna so...? Kuna Bukata..? Cike Tagging dinki da kayattacen Sharhi..Ni kuma bazan yi kasa agwiwa ba wajen Baku Update akai akai da yardan Allah...Karku manta Kuyi Following dina ta sabon Account dina ta Wattpad@Jamilaumar351,Kana ku cike sa da Like da Vote Domin karfin gwiwana Son so Fisabilillah masoyan kwarai..._
*SHAKIRA...*💞
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated to: My Habibaty💞Aisha Idris Abdullahi*
*002*
"Tana cikin karatun azkar din ne Wayarta Dake gefenta ta Dauki Tsuwa ta Dakata ta Dauki Wayar sunan wanda Taga yana Kiranta ne yasa ta Saki Mirmishi Cikin Jin Dadi da wani Farinciki Ta Daga tana Fadin"Qawata.."
Dagachan Bangaren Subai"a tace"Ba wani kawarki Allah Hafsah Daga ke har yaya Abdullahi baku da kirki ace Har yau kwana na goma da Haihuwa ammh Daga ke harshi ba wanda ya Leko..? Haka ake Rayuwa..?Har Anty Zannira Dake kaduna tazo Ita da Mijinta ammh ke ban ganki ba,Ballatana Shi yaya Abdullahin..?
Hafsat ta Saki Mirmishi kafin Tace"Toh uwar korafi kin gama.
? Domin bana so na katse miki Hanzari ne Tunda kika Dauko Wannan Dogon Korafin naki sai kin idashi zakiji Dadi.."Subai"atu tace"Ba wani Sarkin korafi ko Gaskiya.."Hafsah tace"Ai bance ba gaskiya bane ammh sai ki Tsaya ki Saurari nawa uzurin ko.? Kinsan dai Haka kurum Tunda Kika Haihu Banaki Leko ki ba ko...?
Subai"atu Tace"Umh...Ina Sauraranki.."Hafsah tace"Wlh Tunda Kika Haihu nace ma Abban Amira zani Barka ammh baicemin komai ba Har suna yazo,Ranar suna kuma Wlh naso zuwa sai na Tashi bana jin Dadi,ga Amir nata Zazzabi Da Amai Shiyasa kika ga Baki ganni ba Ammh Insha Allahu Cikin Satinan ina Tafe karki Damu kawata.."
Subai"atu tace"Haka dai kikace Don ki Kare kanki da Mijinki bakomai..Sai na ganki.."Hafsah tace"Lah..Baki yarda ba...? Share zencen Subai"atu Tayi kafin tace"Jiya Ammi tazomin Barka Harda Abun arziki ki Tayani Godiya Qawata Allah ya saka da Alheri ya kara Tsawon Rai.."
Hafsah tace"Kajiki da wata mgana..?Don Uwa tama yarta wani abu sai ya zama Abun Godiya.."Subai"atu tace"Hakane kuma..ammh ai Godiya Abu ne mai kyau ko..? Ni ba wannan ba Ina Jiranki Allah kuwa Har Danki yayi Fushi Dake ya kwana Goma Aduniya baki zo kin ganshi ba ballatana Shi Yaya Abdullahin...." Hafsah tace"Kiyi Hakuri Insha Allahu Zamu zo.."
Subai"atu Tace"Toh Allah yasa."Daganan sukayi Sallama kowa ya Ijiye wayarsa Hafsah ta Gyara zama tana Sauke Numfashi Abun yazomata Cikin Ranta na Rashin kyautawarta ga Kawartata Subai"atu wanda kuma Ba Laifin Kowa bane sai na Abdullahi Domin Tunda akayi Haihuwar take mai nacin Tambayar ya barta Taje tama Subai"atu Barka ammh ya ki Kula Mganarta Har Suna yazo,Ranar sunan kuma Har yace ta Shirya ya kaita Ita da yara sai kuma yan Masifarsa suka Tashi Daga kawai Ta bata Lokaci wajen Shiryawa Shikenan yace ya Fasa kaita kuma Bai lamunta ta Fita ba Takaichi kamar ya kasheta,Tana ji Tana gani ya kwashi su Amira Zuwa Gidan Mama suka barta agida saboda Takachi Sai da tasha kuka,Ranta ya baci yasaa bata karamai mganar Zuwa Gidan Subai"an ba ta barshi ai Shima kanwarsa ne In Ya barta Taje Domin kanshi in ya Hanata Shima kanshi yayi mawa Ita miye nata aciki.
Gashi Abunda ke bata mamaki da Abdullahi yana da kyakyawan Mu"amala da kowa banda ita Shiyasa ko zata Shekara Fadin Aibun Abdullahi babu mai yarda,Ko Wajen iyayenta bata Isa ta Kushe Abdullahi ba,baya kwana Biyu baije Tudun wada ya Gaishesu ba,weekend kuwa Shi da yara a Cikin Zaria suke yinshi da Tudun Wada,Shiyasa komai zai mata Take Shanyewa sanin ko Zata Shekara Fada bamai yarda da Ita Saboda in ka Ganshi Bazaka Taba Zaton yana iya Doguwar Mgana ba ballatana Har ya iya wannan Hayagaggar,Abunda ke Daurema Hafsah game da Abdullahi Shine,Komai tayi mai Bata Burgeshi kuma komai tayi ba Daidai bane Duk ko iya Kokarinta na ganin ta zama mai Daidai acikin Idanuwansa ammh Abu ya Gagara Shekara Biyar da Auransu ammh ba wani Abunda ya Chanza Suna nan Jiya yau.
Ajiyar Zuciya ta Sauke jin Sallaman almajirinta yunusa,mikewa tayi ta Fito suka Gaisa,Rijiya ya Nufa ya Fara Zuba mata Ruwa Cikin Babban Roban Dake wajen,Ganin haka yasa ta Bude Kitchen ta Shiga ta Dauko kayan Miya ta Fara gyarawa Ta Tagama sai ta Saka Cikin Wata Robarta mai murfi tana cema Yunusa in ya Gama Zuba Ruwan ya mata Wanke wanke ya Dauki Nikan nan ya mika mata Gidan Nene mai nika yace mata Toh Daganan Ta koma Daki,Tana nan kwance Bayan Fitan Yunusa Zuwa Nika sai ga Nepa sun kawo Wuta ta Mike tana Fadin"Kash Nepa baku kyauta ba sai da yunusa ya tafi kai min nika kana kuka maido Wuta..?
Sai Lokacin kuma Abun yayi mata Shar cikin Ranta Da Sauri ta Mike tana Salati Cikin Ranta Tuna Abdullahi baya som Miyar Nika yafison kuma na Jajjage,ita kuma Abunda yaasa bata Jajjaga ba Taga kayan Miyan yana da yawa ne Bata iya zaman Jajjagasa Shiyasa takai Nika ajiyar rai ta Sauke afili ta Furta.."Fada ne da korafi yau zan Shashi Acikin Gidan nan Har sai na Godema Allah.."
Yunusa na Dawowa Daga kai mata Nika ya karbo mata ta Bashi Abun karyawansa Bayan ya gama ta Bashi Sakon Danmagaji tace ya Siyo mata kayan Lambu,Kabeji,da caras,sai Cocumber,Tana so tayi Cowslow ne kuma Ta Duba Cikin Fridge dinta Duka sun kare,Bama kadai Gareta sai kwai kudin Mota ta bashi Tace yayi Sauri ya Dawo yana Fita ta Dauki Tsintsiya ta Share Tsakar Gidan Tas ta kwashe Dattin Takai Bola aranta Tana Fadin kafin yunusa ya Tafi zai Zubda da Sharan Domin Ta Taru da yawa.
Yunusa bai Dade ba ya Dawo koda ya Komo har ta Gama Miyarta,Already dama Tana da Sauran Naman Jiya da Abdullahi ya Zo Dashi batayi amfani Dashi Duka ba sai tayi amfani da Sauran yau,Ruwan Farar Shinkafa ta Dora,Sauran gawayin Safe ne bai kare ba,Ta bama yunusa Hamsin ya karo mata kada ya yanke mata kuma Babu kowa Sallaman yunusa tayi ya Tafi makaranta yace mata yana da Rubutu sai Zuwa anjuma zai zo ya karbi abincinsa Dayake makarantar Allon nasu kusa ne babu Nisa Sosai.
Kokafin 12pm na Rana Hafsah ta Gama Komai Ta kwashe Cikin Kula,Cowslow ne din ne Bata Hada ba sai Zuwa anjuma Gudun karya ya Lalace,sai da ta gama yanka komai ta wanke ta Adanashi acikin Kitchen dinta,Dama ta saka Ruwan zafi Cikin Kittle ta juye tayi wanka Dashi ta Sauya kaya Zuwa Atamfar wata Doguwar Riga,Falo ta Dawo tazo ta kunna kallo Tashar africa Tv ta saka Tana kallon Wa"azi Domin Hafsah kallo bai Dameta ba har gwara ma India tana kallonsu akan Hausa Film.
Sallar azahar ne ya Tada ita ta Tashi ta Shiga Cikin Bedroom dinta ta Dauro alwala tazo Tayi Sallah,Ta idar da sallar kenan tana Addu"o'inta Taji wayarta na neman Dauki Daga Falo da Sauri ta Shafa Addu"arta ta Fito Falo ta Dauki Wayarta Ganin Sunan mai Kiran yasa sai da Gabanta ya Fadi Abdullahi ne.
Tana Gabda Katsewa Ta Daga Kiran Tana mai sallama Dagachan Bangaren Abdullahi yace"Yau kuma wani Salon Wulakancin kika sake samu Hafsah...?
Ido ta Runtse kafin tace"Wulakanci fa kace Abban Amira..? Kai tsaye yace"Eh mana Banda Wulakanci kinaji ina Kiran Wayarki ammh Saboda ki Kaini Bango sai da kika Ga Dama zaki Daga Kiran nawa."Batace komai ba kawai tamai Shurun jin Shurunta yasa yace kara Fadin"Au kina Jina ina mgana Shine kika min Banza.."Hafsah tace"Ba banza na maka ba Jira nake kagama Fadan naka sai na Baka Hakuri na kuma gayamaka Cewa Lokacin daka Kira ina Sallah ne.."Jin Haka kuma sai Jikinsa yayi sanyi Sai kawai yayi kwafa yana Fadin"Dama kiran Saboda Nace miki in Lokacin Tashinsu Amira yayi Daga makaranta ki Kulle Gida kije da kanki ki Daukosu mai Mashin dinsu yau bai Fita aiki ba yana Gida Baya Jin Dadi ni kuma aiki yayi min yawa Bazan samu Lokacin Zuwa na Daukosu ba.."Yafada Cikin Sanyin Murya Cikin Sanyinta tace"Shikenan...Allah ya kaimu zan je na Daukosu in Lokacin Tashinsu yayi.."
Daga Haka bai kara mgana ba Tana Shirin yanke wayar Taji yana Fadin"Akwai kudi a hannunki ne..?kai Tsaye tace mai"Eh akwai.."Bai Tsaya jin wani mgana ba ya katse Kiran Ajiyar Numfashi ta Sauke kafin ta Ijiye wayar nan saman kujera Ta koma ta Zauna tana kada kai,gefe Daya kuma Jifa Jifa Takan maida Hankalinta Wajen Tibi.
2pm na Rana Daidai ta Saka Babban Hijabinta ta Dauki Wayarta da Kudi Cikin yar karamar pos dinta ta Fito Bayan ta Kulle Gidan,Adaidaita ta samu ya Dauketa har makarantansu Amira wato Alhazawa Acadamey Zaria,Amira tana primary 1 ne Shi kuma Amir yana Nursery 2 ne,Shi karfe 1pm na Rana ake Tashinsu su Amira kuma 2:10pm ake Tashinsu,In Abdullahi yakaisu da Safe in an tashesu wani mai mashin nan yake makotansu Abdullahi ya Dauka yana Biya Duk wata yana zuwa yana Dawowa Dasu Amir zai Jira Har atashi su Amira a Daukosu Tare,Sai da ma ta jira aka tashesu kana ta Shiga cikin makarantar har ajinsu Amir suka gaisa da malamansu ta Daukoshi Dayake tana zuwa Daukosu Wani Lokacin in Wata mtsala ta Faru haka Amira kuma aharaban makarantar da Ganta Tashinsu kenan Ta Riko mata Hannu suka Tafi Mai adaidaitan nan nan dama tace ya Jirata ya maidasu sai ta Bashi kudinshi Gabadaya.
Suna Dawowa Amira ta Cire Uniform Dinta ita kuma Hafsah ta Cire ma, Amir suka sauya zuwa kayan Gida Sai Lokacin ta Hada Cowslow din ta Zuba musu Farar Shinkafar da miya sai Cowslow din suka Hadu Sukaci Gabadayansu suka Sha Ruwa,Bayan sun gama ta tattara komai Zuwa Kitchen,Ta Zubama Abdullahi nashi Cikin Kololinsa Coslow dinshi kuma Bata Hadamai ba sai indan ya Dawo kada ya lalace iya wanda zasuci ta Hada musu sai na Wanda ta Zubama Yunusa Wajen la"asar sai gashi ya Dawo ya sake Zuba mata Ruwa ya mata wanke wanke ta Bashi abincinsa ya Tafi Bayan ya mata Sallaman sai da Safe.
Su Amira ta Shirya suka Tafi Islamiya nan kusa dasu suka Barta Ita kadai acikin Gida,ganin haka kawai sai ta Tsiri wankinsu Amira daya Taru na Abdullahi da nata Dama wanki yakan kai musu in sun Taru,Suma nasu Amiran yace tabar wankewa zai Dinga Hadawa dasu yana kai wanki tace ya bari ta Dinga wanke musu kayan yara ne kada su Dinga bacewa wajen Wanki Shiyasa ya Bar mata na yaran Tana wankewa da kanta,Mganar Gaskiya Banda Fadan Abdullahi da Korafinsa bai da wani illah Daidai gwargwardo yana iya Bakin Kokarinta akanta da ya"yanta,ga lalurori akansa nashi dana kannensa Da kuma na Mama Don ma Allah na Rufa Asiri ammh bazaka Taba kallon Hafsah kace tana Cikin Wahala ba Abdullahi gwarzo ne kuma Tsayayye ga Lamarin Gidansa.
*******
Karfe 7:30pm Abdullahi ya Shigo Gidan kan Mashin Dinsa,Lokacin Hafsah Sun idar da Sallar mangariba Ita dasu Amira tana Biya musu karatun Qur"ani Amir najin Karan Mashin din Abbansu ya Ruga da Gudu Zuwa Waje yana Kiransa Aran Hafsah kuwa tace kila ya Biya Gidan mama ne Domin Ta Duba agogo taga Bakwai ta wuce ta kuma Tattabata 6pm yake tasowa Daga Office.
Tana Kokarin mikewa Bayan tace ma Amira ta Nade Darduman Taji yana Kiranta da Sauri ta Fito Tsakar Gidan tana amsawa yana Zaune Bisa Mashinsa Dinsa bai ma kai ga Shiga da mashin Din ba Ciki ya Dauki Amir ya Dora agaban Mashin Dinshi nashi Hannanunsa Guda Daya kuma Dauke da Ledoji Guda 2,Da Sauri Hafsah ta karisa tana mai Sannu da Zuwa kamar Abun arziki ya Dago ya amsa yana Tambayanta ya Gida tace lafiya ne Ta mika Hannu zata karbi Ledan Hannunsa ya Kalleta yana Fadin"ai na zata bazaki karba bane.Ni kike jira na kai miki Shi inda ya Dace.."Bata tankamai ba sanin Halinsa ta karbi Ledan Zuwa Kitchen ganin Kalanzir ne Aduka Ledojin Guda biyu din.
Galan din kalanzir din ta Dauka ta Juye su Duka aciki kafin ta,wanke Hannunta lokacin har Abdullahi ya Shiga da Mashinsa dinsa Ciki,Ya Shiga Daki itama sai Tabi bayansu ta iskeshi Zaune kan kujera yana ma Amir wasa Amira na gefensa Itama tana Ma Amir din wasa,da Sallama ta Shigo Abdullahi ya Dago ya amsa mata ta wuce Bedroom dinsu ta Sake mai Ruwan wankansa ta Surkamai Har Lokacin suna da Wutar Nepa,tana Cikin Tailet din ya Shigo yana Nade hannun Rigansa Ta Dago tana Fadin"Bakai Sallah bane Bisa Hanya..?
Tafada Tana Zubamai Ruwa Cikin Botar dake Tailet din bai kalleta ba yace"Gidan Mama na Biya ta Tsaidani da mgana Ban samu nayi sallar ba.."Daga haka Bai kara mgana ba ta mikamai Butar tana Fadin"Ga Ruwa wanka nan fa.."Da kai ya amsa mata ita kuma ta Fice Daga Toilet din ta koma Falo taDauke mai karamar Jakarsa ta Shigo Dashi Cikin Bedroom din Gudun Fitinarsa yasa ta ijiye mai nan saman Gado ta Fita Zuwa Kitchen Ta Hadamai Coslow dinsa ta kwaso Abincin nashi Zuwa Falo ta Jera atsakiyar Falon,saman Center Carpent din Dake Tsakiyar Dakin.
Bayan yayi Sallar mangariba ne yayi wanka ya Dauro alwala,ya Fita Zuwa masallaci Shida Amir Sai bayan daya Dawo ne ya Zauna Hafsah ta Zubamai abinci,Hafsah taji mamaki da Har Abdullahi ya kusa Gama Cin Abinci baiyi korafinsa Daya saba ba,Bata gama mamaki ba Taji mganarsa.."Miyar nan Tayi Dadi Hafsah.."
Ya Fada yana kara Zuba Miyar saman Farar Shinkafar Dake gabansa Kallonsa tayi Kafin tace"Ko..? Inaga ka Fara santi ne ko a saka maka waigi ne..? Wani kallo ya watsa mata kafin yace"ai ke za"a sakama waigi Hafsah Saboda Taurin kanki Bansan meyasa kika Rainani ba..Sai na Shekara ce miki ga Abunda nake so ammh ke kullum sai dai na Hakura Nabi Ra"ayin ki ko..?
Cikin Mamaki Hafsah ta kalleshi kafin tace"Me kuma ya Faru Abban Amira..? Kai tsaye yace mata"Bansani ba...nace bansani ba.."Cikim zafin Rai ganin haka yasa ta Kauda kanta Tana Fadin"Allah baka Hakuri.."Daga haka Taja Bakinta tayi Shuru Ta maida kanta wajensu Amira inda Amiran ta Dage sai ta ma Amir Homework shi kuma yana ta Rigiman bazai bata ba tabar mai kayansa Har ya gama Cin Abincin bai kara mgana ba,sai dayasha Ruwa kana yace"Miyar tayi Dadi Sosai..Ammh da miyar Jajjagece sai tafi Haka Dadi ammh Dayake Allah ya Hadani da marajin Mga Irinki Hafsah ai irin Ra"ayinki kikayi kin kyauta.."Kanta na kasa batayi mgana ba sai ma Mirmishi Data saki yana kallonta ammh Girman kai ya Hanashi ya kara mata Mgana ya Tsalleke ya koma Bisa Kujera yana Fadin"Kinga malama Bani Remot Don Allah.."Jin haka yasa tatashi ta Dauko ta mikamai ya karba yana Kokarin Chanza Tasha ita kuma Tatattara komai Zuwa Kitchen,ta saka komai Cikim Muhallinsa,ta kulle Kitchen din Takoma Daki yana Falon ta Wuceshi Zuwa Ciki Ta Shiga Tailet ta Sake Ruwan Data saka a kittle tayi wanka Dashi Har ta Fito bai Shiga ba ta Shirya Cikin Wasu Riga da wando wadanda suka kamata Sosai suka kuma Fitar mata da Suran Jiki bata saka Kallabi ba illah ta saka Band ta kama Gashinta takulle Baya Tana Cikin Shafa Humra Taji Muryan Abdullahi na Kiranta Daga Falo.
Da Sauri ta karisa Falon Gudun kada tayi Laifi Har ya Dago da Niyar Fara mata Korafin nashi sai kuma ya kasa Ganin Irin Shigar Daukan Hankalin Datayi Daman kuma Abdullahi na son ganin Hafsah Cikin English Wears,Fasa mata Fada yayi sai ma yace Cikin Sanyin Murya.."Kizo ki kaisu wajem kwanciyarsu Sunyi Barci.."Ya fada yana Nuna mata Amira Datayi Barci nan kasa sai Amir Dake kan Jikinsa,To tace ta Sunkuya ta Fara Daukan Amira ta kaita Cikin Tailet ta saka tayi Fitsari Tazo takaita Dakinsu kana tazo ta Dauki Amir,Tunda ta kusantoshi kamshin Humaranta Suka Taimaka wajen Sakashi Cikin kasala da Sha"awa Sai Binta yake da kallo har takai Amir Ya kwanta Shima tayi musu addu"an Barci ta kashe musu Wutar Dakin ta Fito.
Ta gaban Abdullahi tazo Zata wuce Cikin wata Kasalalliyar Murya ya saka Baki ya Kirata.."Hafsah...! Cak ta Tsaya kana ta waigo tana Kallonsa dakai yayi mata mgana kafin yace"Zo mana.."Jin haka yasa tasan kwanan zencen Cikin yanga ta karisa Gabansa Tana Shirin zama gefensa yasa ka Hannun ya Jawota ta Fada Bisa Kirjinsa Dukkansu atare suka Saki Numfashi mai karfi Hannuwansa Duka Biyu ya saka ya Rumgumota yana Shinshinar Wuyanta Nokewa Tayi ta na kara Shigewa Jikinsa Cikin Shauki da Soyayyah.
Cikin Wuyanta ya saka Kanshi yana Shinshinar kamshin Turaranta kafin ya Dago yana Fadin"A gayamin sunan wannan Turaran mai bala"in kamshi wanda yasa Take naji Sha"awar Matata ya Kamani.."?
Hafsat tayi Mirmishi Batace komai ba kara matseta yayi yana mata Rada Cikin kunni Zillewa Tayi Tana yar Dariya Cikin kunya Shima kuma ya Sake Rikota yana Fadin"Hafsatuna ta sanni Fiye da kowa aduniyar nan...Tasan in ta Batamin Rai ta lallasheni ta Hanyoyi Dadama,kamar irin ta wannan Hanyar.."Yafada yana Sakarmata Kiss Saman Goshinta,itadai sai Mirmishi Take ta lafe Bisa Kirjinsa Ganin haka yasa ya yunkura yamike da ita kam Jikinsa kafin Taji ya Dagata Cak yana Fadin"muje kan gadonmu kila achan zaki fi Min Bayanin Wani irin Turare ne wannan."
Daman Tunda Taga ya Sauke kai Tana son yana Bukatarta,kanta kawai ta maida kan kirjinsa Lokaci Daya tana Zagayo da Hannuwanta ta Wuyansa Tana Jinsa Ya sauketa kan Gadon ya kuma Bita suka kwanta Rike da juna yana Shafa wasu sassan Jikinta itama bata bashi kunya ba ta Juyo itama Ta Hade Bakinsu Waje Daya Lokaci Daya itama tana Sarrafashi kamar yadda yake Sarrafamata ta ko"ina.
*Hmm yanzu Salon ya Fara..Kudai kucike wajen da Kayattacen Sharhi Hade da Votings da Comments da Kuma Likes Ni kuma zan Faranta muku wajen baku update koda yaushe...*
*Shakira...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Dedicated To:My Habibaty💞Aisha Idris Abdulllahi..!*
*003*
*TUSHE...*
"Abdullahi Usman Direba Shine Babban d'a Namiji na Farko agidan Marigayi Alhaji Usman Direba wanda asalinsa Haifaffan Garin Zaria ne,kuma Tashin Zaria a anguwar Babban Dodo Dake Cikin Birnin Zaria.
Alhaji Usman Direba kafin Rasuwarsa ya kasance Mutum ne mai Dabi"ar Aure Saki ya saki mata Sunfi Biyar Ciki harda mahaifiyar Abdullahi,Wato Hajara wacce ta kasance Haifaffiyar garin Zamfara ce Dake Babba birnin Jahar Gusau,A birnin Tarayyan Nageria,Wanda suka Hadu da ita wajen Wani bikin wani abokinsa Da yajema Biki nan garin Zamfara Shikenan Soyayyar ta Kullu Har takai su ga Aure,Hajara itace Matar Usman ta Farko,Auren Saurayi da Budurwa Sukayi.
Alhaji Usman Direba ne,wanda yake jan Babban Mota ta Kamfanin Dangote,Kuma Alhamdulillah ko acikin Direbobin Alhaji Usman na Dabam ne,Domin kowa Sana"ar ta karbeshi Cikin Lokaci kadan ya Tara Abun Duniya kuma yaje Ya Sauke Farali ne kafin yayi Auran Fari,kuma sai da ya Gina Babban Muhallinsa anan Babban Dodo Dake garin Zaria Lokacin Duka iyayansa Sun kare,Dama su Biyu Mahaifiyarsa ta Haifa Shida kanwarsa Habiba toh Tayi Aure a Danja Dake Jahar katsina.
Ya samu Lakanin Alhaji Usman Direba ne saboda kwazonsa ga aikinsa kuma yafi Jin Dadi in ka Danganta Sunansa da Usman Direba Fiye da ka Kirasa Usman dinsa kai Tsaye Shiyasa Usman Direba yabisa Duk wanda ya sanshi da wannan lakanin nashi ya sanshi har yabar Gidan Duniya.
Ya auro Hajara Cikin Soyayya da kauna,Aka kuma kawomai Ita Zaria,agidan Daya gida Yan"uwan Hajara da Dangin Hajara Suka Tafi suna ta son barka Suna Fadin Hajara ta Dace,Hajara batayi Zurfi a karatun Bokonta ba iyakarta Jss3 ta Dakata da karatun sai dai Tana da Ilimin Addini Daidai Gwargwardo.
Zamansu ya Fara ne Cikin kwanciyar Hankali da kuma Soyayyah,Har na Tsawon wata Daya da wani abu Komai tace tana so Cikin Rawan jiki yake mata da Tattali sai dai Lamarin ya Sauya ne Lokacin da Hajara Ta Fara Laulayin Ciki kuma sukaje asibiti aka Tabbatar musu Da Tana da Shigar Ciki na Tsawon Sati Uku da wani abu wannan Dalilin Shine Sanadiyar Tabarbarewar zamansu wanda har yakaisu ga Rabuwa da Juna na Har Abada.
Hajara tayi mamakin Sanda Usman Direba ya nuna bayason Cikin Jikinta atakaice dai bai Shirya Haihuwa yanzu ba,ya Tada Bala"in sai an Zubar da Cikin nan ita kuma Hajara tace bai isa ba yayi Bala"in yayi barazanar Duk abanza Hajara tace bamai Zubar mata Cikinta,ganin haka sai ya Chanza Salo ya Daina sakarmata Fuska ba kalma mai Dadi,sai Harara da Habaice Habaice da Mganganu marasa Dadi,Daga karshe sai ya Fara mata Horon Yunwa Duk Hajara ta lalace ta Rame ga laulayin Ciki ga kuma Horo da yunwa Wajen miji kuma ba wani Saussauci Ballatana jin Dadin Dalilin Haka Rana tsaka Hajara ta Gudu ta koma Garinsu Wajen iyayenta ta kuma Fadamusu Duk Halin da akeciki Iyayenta kuma suka ce tayi zamanta agida kuma ciki Insha Allahu sai ta Haifeshi.
Wannan tafiyar ta Hajara itace Tafiyar ta Har Abada Daga Gidan Usman Direba Domin bata Dawo ba Sai dai Taga sakon Takardan Saki,Domin Tunda tatafi bai Bita ba kuma iyayenta suka ce bazata koma ba sai yazo har garin,shi kuma yaki Zuwa kanwarsa Habiba Taje har gidansu Hajara tana Rokon iyayenta da su barta ta Dawo ammh sukace Sai Usman yazo,Dole ta koma ba jin Dadi Domin Usman yamata Rantsuwa bazai je ba,Domin ma Ta gane Hajara bata gabanshi sai kawai ya Shiga neman Aure Wata Biyu da Tafiyar Hajara yayi Sabuwar Amarya mai Suna Sahura Ita yar zaria ce,Ranar kuma da aka Dauramai Aure ya Turama Hajara Sakinta Uku ta Cikin Akwatin Sirrin Wayarta Ranar tayi kuka kamar Ranta zai Fita ta kuma yi Nadamar wannan Auren na Usman wanda bai da wani Amfani iyayenta su suka Karfafamata Gwiwa suka kuma ce Tana Haihuwan Cikin Usman Bayan ta yayeshi Zasu maidashi Gidan Ubanshi Domin Itace Tasu bashi ba.
Kusan Abunda ya Faru da Hajara ne ya Faru da Sahura itama Auren ba Dadewa sai ga Ciki nan fa ya Tada Bala"i sai an Zubar tace bai isa ba Itama dai Bata Zauna ba ya Saketa ya Tura ta Gida da Ciki,Ba Dadewa kuma ya Sake Auran Wata Bazawara Karimatu sakin Wawa toh itace ma Tayi karfo Domin Daman Tunkafin ta Shigo Gidan ta samu Labarin Irin Halinsa sai ta Shigo da Shirinta na zama Dashi Domin bazata so ya saketa ba Tunda gaskiya Usman yana Kokarin kyautata iyalansa Shi matsalanshi Daya Rashin Son Haihuwa.
Ya auri karimatu ba Dadewa Aka kai ko masa Hajara ta Haifi Danta Namiji,Habiba tazo har gida ta Shaidamai cewa Mahaifiyar Hajara takirata ga waya tana Shaidamata Sai tayi ta gaske ya Bata Kudi 50k tatafi Dashi wanda za"ayi Hidimar suna da Shakika Ranar da Zata tafi ta matsamai wani Suna za"a sakama yaron Cikin Bacin rai yace asakamai kowani Suna Habiba dai Haka taje Zamafara ba wani kwarin Jiki takai Kudin Daya bata tana ta Ban Hakuri Iyayen Hajara basu bi takan Habiba ba,Domin komai Sunyi ma yarsu Usman yaci Darajan Musulunci ne da kuma Yaron Daya Hadasu kuma ko Sisin Habiba basu karba ba sukace ta maida mishi,sun dai karbi Atamfa da Rigan yaron data Rantse musu ita ta Siya da Kudinta Gudummmuwarta ne kana suka karba.
Sun basu Hakkinsu sukace wani Suna Za"a sakama Jaririn wanda yazo Duniya yana kama da Mahaifinsa sak sai dai ya Dauko Hasken Fatan Hajara,Habiba tace a sakamai Sunan Mahaifinsu Abdullahi batare da tayi wani Tunani ba,Haka ko akayi Ranar suna akayima Yaro Shakika yaci Sunan Abdullahi kwana Biyu Habiba tayi ta Dawo Danja Batare ma Data Biyo Zarian ba Saboda yadda yayanta ya Bata Haushi da Takaichi.
Hajara ta Cigaba da Kula da Danta da Taimakon iyayenta Abdullahi nada wata Shida Sahura ma ta Haifi yarta mace Wacce taci Suna Zanniratu,wanda itama sai da Mahaifinta ya zo yama Usman Tijara kana yaje yaga yarinyar ya mata Huduba kuma ya saki bakin aljihu akayi Hidima Da Shawaran karima da kuma Tsoron kada Mahaifin Sahura yakai kotu kamar yadda yace,Dole ya yardan ma kansa zai Dinga aika kudi Gidansu Sahura Duk Wata kudin Shayarwa Hajara kuwa ko ta kanta Bayabi Saboda yaga iyayenta Sun sakamai Ido.
Zamansu da Karima ya Daure Saboda Bata yarda tayi Ciki Ba ballatana Goyo,,ammh duk da Haka ko Shekara basu yi da Aure ba ya kara Auren wata Bafullatana Hure,wacce ita ba komai ya Rabasu ba sai Barauniya ce tana mai sata yasa ko Wata Biyu bata yi ba ya Saketa Daga ita sai Kuluwa Itama dai tana Samun Cikin ya kadata Gida,Ita Allah ya Tsareta Cikin sai ya Zube bata sha Wahala ba Sosai,Yayi Aure Aure bai san iyaka ba kuma Duk Da Ciki yake sakinasu,karima ce dai Matarsa Domin bata yarda tayi Ciki ba Ballatana Goyo Shiyasa Duk wacce ta Shigo Fita take ta Barta.
Wasa wasa sai da Usman Direba ya Tara ya"ya Biyar wadanda ya Saki iyayensu kuma aka Haifan masa,ana ciresu anono ake kawomai Cikin Gidansa Abdullahi na Cikin Jerin Wadanda iyayensu mata ke Dawo Dasu Gidan Ubansu,Ganin haka yasa Karima ta Daka Tsalle tace bai isa ba ba Yaron da zata Rike balle tama mata Wahalan Da,ita tana Zaune bata Haihu ba,Usman bashi da yarda zai yi Domin ya"ya dai nashi ne, kuma in bai karbesu ba Duniya zata kara Tur Dashi akan Wanda daman takeyi Ganin Haka ne yasa ya yarda Ita karima ta Haihu wannan Dalilin ne yasa Karima ta yarda zata Rike ya"ya Biyar din da aka Dawo Dasu gabanta Bayan Taje asibiti an Cire mata Abunda aka samata Saboda kada ta Dauki Ciki.
Acikin yaran Biyar da aka Dawo Dasu Abdullahi ne Babba sai Zanniratu,sai Subai"a,sai Auwal,sai Mariya sai karamarsu Hauwa Jidda kuma yawancin yan kai Daya ne Domin Abdullahi da Zannira da Suba"i Tsakaninsu yan shekara da yan watanni ne,,Cikin ikon Allah karima ta ma yaran Rikon Tsakani ga Allah Domin bata nuna ba ya"yanta bane komai ita take musu ganin haka yasa Usman yaji Dadi komai ya samu Na karima ne Saboda Farantamai Datakeyi.
Sai dai har wajen Shekara Biyar Karima Haihu Shuru Hankalinta ya Fara tashi ta Fara Damuwa Taje asibitoci da Dama ammh har tsawon wasu Shekaru Shuru,tayi kuka sosai kuma Tayi Tunanin Hakkin iyayen su Abdullahi ne ya kamata Domin Tana gani Usman yake Rashin Mutumcinsa da adalcinsa bata taba Hanasa ba,kila Allah ya Barta ne Domin yana Nuna mata Isharansa Shima Usman din yaso Haihuwan da karima ammh Allah ya Hanasu Dukkansu sun Gane kuskuransu alokaci Daya wannan Dalilin Yasa karima ta Rumgumi ya"yan Kishiyoyinta ta Rike gam Domin itace Uwarsu ayanzu Shima Usman yayi Nadama Sosai ya yi kokarin Bin Matan nashi Daya saka sai Dai Sahura kadai ya samu ya Roketa Gafara Har Lokacin batayi Aure ba Hajara kuma koda yaje zamfara Iyayenta suka ce ta Dade da Aure a garin Gusai Dole ya Dawo Mahaifiyar Subai"a kuma Allah yayi mata Rasuwa Itakuma Mahaifiyar Auwal,Ta Koma Niger wajen Yayar mamanta da Zama Mahaifiyar Hauwa Jidda kuma Tatafi Saudiya neman kudi Ganin haka yasa ya Dawo Domin ingantama yaransa Rayuwa Habiba tafi kowa Murnan Haka tana kuma tayashi Addu"an Allah ya yafemai kurakuransa.
Duka ya Sanyasu makarantan kudi ne,Abdullahi da Zanniratu suna Lawal aliyu ne,su kuma Sauran sai ya sakasu a Comtemporary life Sch Shi kuma yakai kaisu a motarshi in yana Gida in kuma Baya gari sai su Hau mashin Din Haya Domin yana Barin musu Ishashen kudi a Hannun Karimatu.
*****
Bayan Shekara Ashirin da Takwas..
Shekarun sun ja abubuwa Dadama sun zo sun Shude ciki harda Rasuwar Alhaji Usman Direba wanda yan Fashi suka Tareshi a Hanyar Abuja suka Kasheshi Shida yaron motarsa Har Lahira,lokacin Abdullahi nada Shekaru Ashirin da Biyar aduniyar har ya kamallah Secondry Sch Dinsa yana Diplomansa a Poli Dake Cikin Zaria,Zanniratu kuma Tuni tayi Aure a Kaduna Har ta Haihu,Subai"a ne tana Shakaran Karshe a matakin Sankandiri sai su Auwal da Jidda da Suka Farkon Zangon karshe na Karatunasu.
Mutuwarsa ta Girgiza Iyalansa Gabadaya,jigon Gida ya Dawo Duka Hannun Karima wacce Suke Kira da Mama,Allah yasa Alhaji Usman yabar kaddarori da Dama Ciki harda Babbar Mota Daf,Tashi da kanshi da kanta da Gidaje da Filaye,Su aka Raba aka Saida wasu Domin inganta iyalansa Dashi aka Cigaba da Biya musu kudin Makaranta Har Suka kamallah.
Zuwa Lokacin da Abdullahi keda Shekara 28 aduniya ya zama Saurayi Kin kowa kin Wanda ya Rasa,Abdullahi Namijine, mara Hayaniya,mai kwazo da kuma Kokari,bayason Wasa acikin Lamarinsa kuma baya Harka da mai Son Wasa,,Mutum ne mara son Raini ga Son Girma yana da isa da Iko da kuma Takama,sosai yake da Dadin zama,yana Girmama Mama Duk da ba ita ta Haifeshi ba,kuma Duka kannensa suna Girmamasa,Domin ya Tsare Gidansa Baya Sakarmusu Ballatana Suga wajen Rainasu,Mama kuma Duk Cikinsu Tafi son Abdullahi Domin Jajirtattace ne kuma Tsayayye ne kan komai Haka Goggonsu Habiba Itama akoda yaushe wajen Yabon Abdullahi Take Shima kuma Dan Gidanta ne, Domin Duk Sati yana Wajenta Achan yakanyi Weeked Dinsa in babu karatu A makaranta Dayake Allah bai bata Haihuwar Da Namiji ba sai mata Kuma Duk Sunyi Aure sai Autar ta Kadai ta Rage batayi Aure ba.
Bangaren Hajara kuwa Wacce Abdullahi da Sauran ya"yanta ke Kiranta Umman Sadiq,Wacce take zaman Aurenta agarin Gusai tana Auran wani Dan kasuwa kuma Alhamdulillah suna Zaune lafiya ta Haihu Dashi,ya"ya Hudu Uku maza Daya mace Babba Shine Abubakar Saddiq,sai Halifa sai Umar Autansu ne Fatima Suna Kiranta Zahra,Abdullahi yana Zuwa wajen Ummansa in sun samu Hutu Lokaci bayan Lokaci kuma suna Mgana awaya Sosai Kannenasa Duka sun saba Dashi.
Abdullahi ya gama karatunsa na Diploma sai ya Dora Hnd dinsa,yana kamallah sai ya samu wani karamin aiki a Kango Dake Zaria yana aiki a wani karamin Office anan Cikin kongo zaria yana Diban Albashinsa da bai gaza Dubu 70 ba,Dashi yake Taimaka kannensa da kuma Mama da Sauran Bukatu,Da albashinsa kuma ya Fara Gina Gidansa a Tukur Tukur Dake Zaria Lokacin ne kuma akayi Bikin Subai"a Inda a wannan Sha"anin Auren ne ya Hadu da Hafsat wacce kawa ce ga Suba"an tare sukayi makaranta da Ita.
Hafsat Haifaffiyar Garin Zaria ne a Anguwar Tudun wada Zaria Hafsat Itace ya ta Biyu a Gidansu Kuma ta karshe bata da kani ko Daya,Daga ita sai yayarta Hadiza wacce take Auran wani mai Kudi a Garin kano,Dan kasuwa ne,tsakaninta Da yayarta Hadiza Shekara Takwas Domin Har Hajiya Zinaru da Alhaji Hamza mai Guga Har sun Fidda rai da kara Haihuwa sai kuma Allah ya Basu Hafsah Daga Baya wacce tatashi Cikin Gata.
Hafsah yarinyace mai Sanyin Hali da Hankali Tashinta Cikin Gata baisa ta zama Sangartattaciya ba sai dai Sanyin Halinta uwa uba kuma tana da kawaichi da Hakuri,Hafsat Tana da kyau Sosai Domin Farace mai kunya Tana da Kokari Shiyasa a kananun Shekarunta Har ta kamallah Nce Dinta tana da Shekara 22 a Duniya,Hafsat bata cika Fita zuwa Gidajen kawaye ba Daga makaranta sai gida sai ko Inda Taje gidan yayarta Hadiza Hutu agarin kano achan take ma Kwana Da yawa Har sai Hutunasu ya kare take Dawowa Zaria.
Hafsat da Subai"a sunyi aji Dayane a makarantarsu ta Comtemporary,Da Farko ba kawaye bane Daga Baya ne suka Zama Good Friend Da Hafsat Saboda Sanyin Halinta da ita kanta Subai"an Data nemi Hafsatn Ta yarjemata suyi kwawancee Wannan Dalilin ne yasa Suka Fara Mutumci sai kuma Suka koma kawance ganin itama Subai"an bata da wani Banzan Hali Subai"a Tazo Gidansu Hafsat ba Adadi ammh Ita Hafsan Sau Daya Tataba zuwa Gidanasu Subai"an Sanda mama bata da lafiya Taje gaishesu,Sai dai Subai"an tagaji da Korafi Harta Ammin Hafsat sai da ta mata Tsiyan bata Zuwa Gidansu Subai"an
Dalilin Bikin Subai"an wacce Zatayi Aure acikin Zaria Zata Auri Dan Gidan mallawan Zazzau,Shine Dalilin Dayasa Dole Hafsat tayi Hakuri ta Shiga Sha"anin Bikin Tunda Subai"an ta sakata Dan Dole,Tare sukayi Hidimar Raba cingam kuma sukake Gudanar da Wasu Shirye Shiryen Bikin,kuma Hafsat da Abdullahi basu Taba Haduwa ba Domin Sanda zata zo Gidansu Shi Baya nan yana wajen aiki,sai dai Ita Hafsan tana ji Subai"an na yawan Zencen yayanta Abdullahi.
Basu Fara Haduwa ba sai ana Gobe Bikin Subai"a da suka Dawo Daga Gidan kunshi Suka Iske Abdullahi akofar Gidan suna Hira da wani abokinsa Nazifi,Wata Soyayyah ce ta kulla da ganin Farko da sukama juna Hafsat taji Jikinta ya amsa Tare da Zuciyarta,Shima Haka a Bangaren Abdullahi haka ya Wuni yana Fama da Faduwar Gaba Daya Tuna da Hafsat Haka Itama Abagarenta Haka ta koma Gida Jikinta Duk a sanyaye Domin Taki yarda ta kwana agidansu Subai"an Duk da Ammi ta barta.
Washegari Sai suka Hade wajen Dinner,wanda Abdullahi bai so Zuwa ba ammh Mama ta matsamai da lallashi Ita da Zanniratu yasa ya yarda yaje wajen sai wani Bata rai yake Shida abokinsa Nazifi yaje,Suna Gefe suna kallon Kowa Daidai Cikin kalle kallen nashi ne suka kara Hada ido wannan karon Dukkansu basu Dauke ido Da kan Juna ba,Nazifi ne ya ankare da Halin da suke Ciki ya kuma Bama Abdullahi Shawaran ya Tunkari Hafsat kada ya bari Garin kallo Ruwa kwado yamai kwafa.
Lokacin da Abdullahi yanemi Kebewa Da Hafsah bata ki ba,Kuma sanda ya Furtamata kalmar so nan ma batayi gaddama ba Domin a kallon Farko Zuciyarta ta aminta Dashi kafin atashi wannan Dinner Duka Zuciyoyinsu sun Aminta da Juna sanda Subai"a tagama Fahimtar Abunda ke Faruwa Farinciki ya Cika Ranta Domin Zata so Yayanta ya samu mace irin Hafsat.
Ranar Hafsah gidan Subai"a ta kwana Washegari ne ta koma Gida Cike da Farinciki,wanda yakasa Boyuwa saman Fuskata Ammi ta Tasata Da Tambaya Cikin kunya ta gayama mata komai ita kuma ta Shiga Tsokanarta,bata kasa a gwiwa ba Alhaji Hamza na Dawowa ta Sanar Dashi komai Shi kuma ya Kira Hafsah yace in Abdullahi ya Kirata tace yana nemansa.
Haka ko akayi Abdullahi ya gana da Mahaifin Hafsah kuma ya gamsu Dashi Lokaci Daya ya Bashi Daman ya nemi Hafsat,Cikin Soyayya da Muradi suka Fara Gudanar da Soyayyarsu Cikin Son Juna da kauna Zuwa Lokacin kuwa kowa Daya Shafi Abdullahi da Hafsat ya gama Sanin Soyayyarsu Hatta Umman Sadiq Taji labari wanda Abdullahi yaje har chan yamata Bayani kuma tayi Farinciki da Hakan watansu Hudu da Haduwa Alhaji Hamza yace Abdullahi ya turo magabatansa,Cikin Lokaci kankani akayi komai aka gama Aka Sanya Ranar Wata Bakwai masu Zuwa A inda aka bar Abdullahin zai kama Haya kafin ya karisa Gidansu.
Abubuwan da suka Biyo Baya kafin Aure,Abubuwa ne masu dadi Sosai,Domin Zumunci ya kulli Tsakanin Umman Sadiq da kuma Ammi,Kuma abubuwa suna Tafiya Daidai,Soyayyarsu Kuwa ba wani Targadan Domin Abdullahi mutum na gari kuma alokacin bai Taba nuna mata yana da Halin Fada ba wanda kuma Kowa baisanshi Dashi ba andai sanshi da Bayason Raini ko Kadan da kuma Tsare Gida Uwa uba kuma Rashin yalwar Fara"a ga Fuskarsa.
Biki ya karato kuma anyi Duka Shirye Shiryen Daya kamata wani Flat Abdullahi ya kama Ahaya a Gaskiya layaout suka Fara Zama Shida Hafsat Cikin Soyayyah da Muradi mai Girma zamansu ya Fara Cikin Farinciki ne Gefe Daya kuma yana ta kokarin Karisa Ginin Gidanashi Domin Bayaso Hafsat tayi Haihuwan Fari suna Gidan Haya.
Rana Daya Ko nace Rana Tsaka Abdullahi ya Farama Hafsah Wannan Halin nasa na Fada da Mita da korafi,Tun bayan da Alhaji Hamza ya samoma hafsah Koyarwa a wata Private School,Ammh sai Abdullahi ya Hana ya kuma Bada Idanuwansa Toka yace bai amince Hafsat Tayi aiki ba,Alhaji Hamza bai ja Mganar da Nisa yace Hafsat tayi Hakuri da aikin Duk da ta sakarai Ammh Tayi mamakin Yadda Abdullahi ya Hanata yin aikin Alhalin bata Zaci haka Daga Gareta.
Shi kuma Abdullahi ba komai yasa ya Chanza ba sai Zugan Abokinsa Nazifi wanda yaji labarin Case din aikin Da mahaifin Hafsah ya samo mata da kuma Hanawa da yayi Nazifi Shi yabama Abdullahi Shawaran Sakarma Hafsan da yakeyi ne yasa Take Tunanin komai Zata iya yi Ya kamata ya Fara Nuna mata Shima Namiji ne,ya daina Sakarmata akomai yadaina Nuna ta iya ko tayi Daidai Haka kadai zai sai Su Daidaita ta kuma Dinga Shakkarsa ta kuma gane Shine Mijinta tana karkashinsa ne,Da wannan Shawaran Abdullahi yayi amfani ya sauya Takun zamansa Da Hafsah Daga Zaman Soyayyah da kulawan da kauna mai Tsanani,ya koma zaman Kadahan kadahan Masifa,korafi,da kuma Mita komai kuma akayi ba"a mai Daidai Hafsah ta Daina Yin wani Abu Na Burgewa ga Abdullah ba, komai tayi Sai yayi korafi kuma ya Nuna Batayi mai Daidai ba.
*Shakira...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty❤️Aisha idris Abdullahi..!*
*004*
"Nazifi bashi da Mugun Hali ko kyashi ko Hassada ko kuma wani Dalili nabama Abdullahi wannan Shawaran,Sai dai Abu Daya Shine Hallayarsu ta Bambamta na Farko Nazifi yana da Leken Leken mata da kuma Buri yana son Mace mai kyau mai aji da kuma Dukiya ko ita ko Iyayenta ma"ana dai yana Burin Auran Jari da kyau arayuwarshi.
Kuma ya samu Domin ya Riga Abdullahi Aure ma,Da wajen Wata Biyar in da Allah ya Cikamai Burinsa ya Auri Diyar masu Kudi ga kyau ga Diri ga Tarin Dukiya Mai Suna Sakina,Sakina Diyar wani Hamshakin Dan Siyasa ne agarin kano Babanta Har Sanata yayi kafin Ya Sauka ya Rike Yan majalisu Dadama,Ma"ana dai yayi Gwargwarmayan Siyasa Sosai,Ya"yansa Dukkansu sai ya kwafasu yake Aurar dasu,Sai sunyi masters Sun samu aiki yake Aurar Dasu,Kuma sai ya kaisu Hajji kana,Sakina Ta karanta aikin Gidan Jarida wato Mass.Com,Akasar London ma ta Hado Masters Dinta akan Harkan Jarida har ma ta Fara aiki da Gidan Jarida na Bbc ta bari ta Dawo Gida Saboda Zencen Auranta da Nazifi Daya taso.
Nazifi Yayi karatunshi har matakin Digree Engenearing ya karanta aka samu sa"a ya samu aiki Ahukumar nepa ta Jahar kaduna,Asalinsu yan Sokoto ne zama da Sana"a ya kawo mahaifinshi nan zaria har ya Auri mahaifiyarsu wacce suke kira Inna Abu,Kamar Abdullahi Shima Nazifi Shine Babba Agidansu yana da kanne mata da Maza ammh Dayake mahaifinsu Alhaji Wada,Dan kasuwa ne Sosai yana da Rufin Asirinsa ba laifi Shiyasa komai yazoma Nazifin Cikin Sauki.
Sun Hadu da Sakina a Fbuk ne Suka Kulla Soyayyah mai Zafi Ganin Dukkansu Zabin Juna,Sakina Tana son Namiji mai kyau Itama Dogo,mai ingarman jiki da Fadin mazantaka mai kuma ilimi da Haiba Saurayi mai Jini a Jika Domin ba laifi Nazifi gaye ne na Nuna Sa"a Itama Sakinar tayi Daidai da Ra"ayinsa Tun Tana london suka Fara Soyayyah Bayan Tazo Gida Hutu yazo suka Hadu suka kuma Yaba da Juna Cikin Lokaci ta gabatar Dashi Wajen mahaifinta Shi kuma ya Amince Domin baya ma ya"yansa Dole Abunda suka kawo suna so in dai na kwarai ne toh yana Aura musu Toh hakan ta Faru da Nazifi iyaye suka Shiga Cikin mgana akayi komai Cikin Girma Duka Duka Bikin Wata Biyu aka saka Dayake Nazifin yana da Gida Akaduna sai Abun yazomai da Sauki.
Farkon Auransu Nazifi ya zama Dan Gata kuma Abun kwatance Domin Sha Tara na arziki Mahaifin Sakina yayi mai ya Bashi Motar Hawa,da kuma Gida Lafiyayye anan garin kadunan ganin Haka yasa Nazifi ya kulle Gidansa Ya koma Gidan da Uban matarsa ya bashi Wanda Sai dai Abdullahi ya nunamai Rashin Dacewar haka ammh yaki ji Ransa na wajen Burinsa wanda baida Amfani.
Kayan abinci kuwa na kusan Shekara aka Cika musu Store kayan Aure kuwa Gida sai wanda yagani Saboda kyau da kawatuwa,Da Farko zamamsu ya Fara Cikin Soyayyah da kauna sai Daga Baya komai ya Chanza Zani,Domin Sakina dai Tafi karfin Nazifi ta Fara Nunamai Tana Bukatar Rayuwar yanci ne da kuma Sakewa,Domin Tana Takama Tana da komai Ubanta Nada kudi Ita kuma tana da Ilimi Farkon Samun mtsalansu Aikin Da Mahaifinta ya sama mata agidan Tibi na NTA Abuja bama Tare da an Tuntubi Nazifin ba,Wanda dama kafin Auransu da Sakinar sai da Alhaji Wada ya Kira sa yajamai kunni da kuma Fadan kan Gidan Dayaje ya Nemi Aure kamar sunfi karfinsa ammh ya Nuna Babu Abunda zai Faru Sakina na Sonshi akwai yaga karshen so Daya nuna Bazatayi aiki ba Babanta da kanshi ya Kirashi yamai wankan Tsarki ya kuma ce Dole Sakina tayi aiki Dama ai ya sani amfanin karatun nata tayi aiki Dashi ko kuwa in ta Zauna zai kare mata Lalurorinta ne Shima yana nema yadai Ci Zarafin sa Sosai Shida iyayensa Irin dai basu da komai Ranar Nazifi bai iya barci ba Saboda Bacin Rai ita kanta Sakinar bata Saurareshi ba Kano ta Tafi sai ta kwana uku ta Dawo bayan Tagama Duka Shiryen Shiryenta Har Gidan da zata Zauna achan Abujan ya kamallah Domin bazata Dinga Zuwa tana Dawowa ba Nazifi yana ji yana gani Sakina ta Fara aiki bada izininsa ba kuma in Tatafi sai tayi Sati Biyu bata zo kaduna ba in kuma tazo Bata wuce kwana uku ta koma Nazifi ya Shiga Damuwa Sosai ya Fara lalacewa,kuma ya kasa Iya Fadama kowa sai Abokinsa Abdullahi wanda kuma yace Allah ya kara Dama kowa ya Siyi Rariya yasan zata Zubda Ruwa.
Da Farko Sakina ta nuna ma Nazifi ya Dinga zuwa mata Abuja Weeked in ya samu Lokaci Domin Har ga Allah tana son Mijinta sai dai Rayuwarta da Goal dinta na Rayuwa na gaba da komai,Sai yaki ya Fara Fadan Ta Raina mai yawo,ita kuma sai ta kyaleshi Daga Baya ganin zai iya Fadawa Halaka yasa yake Kokarin Zuwa mata Weekend Duk Sati,Ganin haka sai Taji Dadi ta kara Sangarcewa in bashi yazo ba sai tayi wata bata Shigo Kaduna ba Tun Nazifi na Boyewa ma iyayensa Har Labari ya kai musu Inna Abu tace Allah kara Alhaji wada ne kadai yace Allah ya kyauta Domin koma miye ya Faru Nazifi shi ya Deboma kansa Ruwan Dafa kansa da kansa.
Wannan Dalilin ne yasa Ba Abdullahi kadai Nazifi kebama Shawaran ba"a Sakarma ma Mace ba Abokansu Dadama yana Fadama Haka masu karamin Tunanin Irin na Abdullahi sai su yarda da Batunsa Duba da ganin Irin yadda Rayuwar Nazifin ta Dawo Yana da mata kamar bashi dashi Shiyasa yanzu yama Daina Kwana akadunan kusan kullum yana Hanyar Zaria zuwa kaduna Bambamcin Shine kawai Auren ammh bawani Ci gaba,Abdullahi Nadaga Cikin abokan Nazifi makusantansa wadanda suke da Labarin Irin Abubuwan da suka Faru Dashi Shiyasa Daya bashi Wannam Shawaran bai yi wani Dogon Tunani ba ya yarda da Mganarsa Domin baya kaunar yayi Sakem da Mace zata maidashi wani Salallamame Ita da iyayenta ba gwara ya kame kawai Shima ya zama namiji Domin ya Tabbata bazai Taba yarda Hafsah tamai Irin Abunda Sakina Take ma Nazifi ba Shiyasa ya Sauya alaqan zaman nasu Kuma yake ganin Riba da Daidai kan Abunda yake mata Shine zai sa Ya zama Namiji acikin Gidansa mai iko kan komai.
*******
Acikin wannan Halin ne Hafsah ta samu Cikin Hajara wato Amira Ammh samuwar Cikinta sai ya Rage wani abun Tunda Abdullahi na son Hafsah Sosai kuma yana Tsausayinta Lokacin kuma Cikin yazo mata da laulayi Sosai Don har Asibiti ta kwanta,Tasha Lodojin Ruwa Lokacin har Umman Sadiq tazo Dubata itace Dataga Halin da Hafsah ke Ciki tama Abdullahi mgana kan Ya maida Hafsah gaban mahaifiyarta ta kula da Ita Bai so ba Domin ya nuna Rashin Amincewarsa ammh sai Umman Sadiq tafi karfinsa Dole ya amince Ammi ta Dauki Hafsah Zuwa Gida,Tana kula da Ita Nazifi bai sani ba sai Daga Baya ya Dinga Zuga Abdullahi da Cewa yayi kuskure Shikenan kuma Komai iyayentavzasu Juyashi Shi kuma Bashi da yadda zai yi Umarnin Umman Saddiq ne kuma Yana jin kunyar Ammi gaskiya bazai iya mgana ba Dole Nazifi ya sakamai ido Sai da Hafsah Tayi wajen Wata Biyu a Gida kana ta Dawo Gidanta Lokacin Taji Sauki Sosai tayi Kiba Cikin ya karbeta Tayi Bul Bul Ganin haka yasa Abdullahi ya lallaba yana ta amfana Da Ni"imarta Ba Fada sai dai Abunda Ba"a rasa ba.
Abdullahi yaso Hafsah baza ta Haihu a gidan Hayan da suke ba sai kuma Allah bai yarda ba anan ta Haifi Santaleliyar yarta mace mai kama da Ubanta da Uwarta sak,Asibitin Chika ta Haifeta ta kwana Washegari suka Dawo Gida Mamace ta kwana Dama da Ita,Tun Kafin Hafsah ta Haihu Dama ya gayamata bazata Wanka Gida ba,bayaso Shiyasa da Ammi ta Fara mganar Komawarta Gida Jego ta Cemata Abdullahi ya hana da Farko Ammi taso tamai mgana sai Alhaji Hamza ya Hanata yace ta Barshi ai Mijinta ne Shike da Hakki akanta Abunda ya yanke Shine Daidai Hajiya Hadiza ma Datazo Tana Fadan meyasa Hafsah bata Dawo Gida ba,Ammi ta Fadamata Dalili,jin haka yasa tace Ammi ta samo Wata ko Cikin yan'uwanta Taje ta zauna da Hafsah Din Tunda Mama ce ke ta Zirga Zirga Zuwa Safe da yammh Tana ma Hafsah wanka ita da Jinjiran Jin Haka yasa Ammi tama wata Matar Yayanta mgana wanda Dama yayan nata ya Dade da Rasuwa Asibi Ita ta je ta Zauna da Hafsah,ammh sai da Ammi ta Kira Abdullahi ta gayamai Shi kuma ya amince.
Anyi Shagalin Suna Cikin Farinciki da Annushuwa Raguna Biyu Abdullahi ya yanka yarinya yaci Sunan Umman Saddiq Hajara kenan,su Subai"atu ne kan Gaba kan komai Zanniratu ma tazo Daga kaduna da Kayan Barkanta,Umman Sadiq kuma Kishiyarta Da suke Kira Iyami ce tazo ita dasu Sadiq dasu Zahra,Hafsah tayi Goshi Domin Harta Sakinar Nazifi Tazo Sunan da yammah da Leda Cike da kaya Dayake Sakinar bata da laifi akwai da Sakin Fuska ba Ruwanta Bayan Aurensu da Abdullahi Sunje kaduna Sau Daya Lokacin sun sameta Tana Gida Itama tazo Sau Daya sai wannan Shine Zuwa na Biyu.
Duk nan suka kwana wasu kuma Gidan Mama suka koma suka kwana wasu kuma Wajen Ammi musamman ma yan"uwanta,Maijego tayi Goshi ita da yarta Hajarah wacce ake ma alkunya da Amira,Hafsah tacigaba da wankan Jegonta Cikin kulawa Da kuma Taimakon Asibi wacce ku kula dasu Ita da Amira a zaman Asibi Awajen Hafsah Bata koma ba sai da yabon Abdullahi da kyakyawan Hallayarsa acikin Bakinta,Domin ko Korafinsa ne yatashi baya yadda yayi shi Gaban wani ahalin Hafsh sai dai kaji kowa na Yabonshi Sosai ta koma da Kayan arziki da Abdullahi ya Hada mata Wanda Abun yayi ma Ammi Dadi Sosai Ta kuma Kara Godema Allah Data samu Suruki Irin Abdullahi.
Bayan Haihuwar Amira Haka zamansu ya Cigaba da zama Dai Kadahan kadahan Zuwa Lokacin Tuni Hafsah ta saba da Sabbin Halin Abdullahi tayi Tambayan Duniyan in Wani Laifi tayi mai ya gayamata yace bata mai komai ba Dole ta kawo Ido ta sakamai iyaka in ya Fara Fadansa ta Bashi Hakuri Taja Bakinta tayi Shuru wani Lokacin ko Suna Cikin Dadi Dashi sai ya samo Abunda zai Mata Fada akanshi Wanda ma bai kai yayi mgana ba Tun yana Damunta Har ya Daina ma Damunta Tunda ta lura Abdullahi ya Chanza ba kuma zai Daina Wannan Fadan nashi da Korafinsa ba.
Amira na da Wata Shidda Abdullahi ya kamallah Ginin Sabon Gidansa Dake Tukur Tukur Zaria suka koma akuma Lokacin ne ya siya Sabon mashinsa,wayyo kudina Sunyi Walima Sosai da Saukar al"qurani na Tarewa,Komawarsu Sabuwar anguwa tazo musu da Ssuye Sauyen Rayuwa Sosai Ciki harda Da karin Bunkasan Abdullahi ya samu karin Girma awajen aiki har ya Bude Shagon Provisio a kasuwar Tudun Wada Dake Zaria Auwal ke zama mai ashagon Shi da wani yaro Sani Auwal sai in ya Tashi Daga makaranta yake zama nan poli Shima yake Karatunsa kuma Abdullahi ne ke Dauke da Nauyinsu Shida Jidda da mariya.
Sai da Amira ta samu Shekara uku da Haihuwa kana Hafsah ta Haifi Usman wanda suke ma alkunya da Amir,Zuwa Lokacin kuma Babu Abunda ya Sauya zani,Sai ma ya karu Domin abaya Abdullahi baya Hanata Fita in Bukatar Hakan tataso ammh yanzu kai Tsaye zai ce bazata ba ko Ina ne kuwa,Gidan Mama kuwa in bashi yayi Ra"ayi ya Dauketa ba Ya kaita ba Bazai barta Taje ba Hakama Tudun Wada ammh Shifa yana zuwa akai akai Shi dasu Amira,Bangaren Nazifi da Sakina ma ba wani Chanji Gashi Har yanzu Haihu Shuru,Nazifin ya Fara Damuwa Domin yana Bala"in Son yaga kwansa a Duniya ammh Daya ma Sakina Mganar sai tace bata Shirya Haihuwa ba yanzu Sai nan Gaba Gabadaya Duk ya Rame ya Lalace wani Lokacin dama Burikanmu Suna iya Jefamu ga Halaka bamu sani ba.
Mariya da Jidda sun zama yanmata,Mariya Sch of Heatlh Takeyi nan Jama"atu Sch Of Health Kofar Kibo,Sai Jidda Dake Shekaran karshe a matakin Sendondry,Suma Dukkansu Suna Karkashin kulawar Abdullahi Domin Baya musu da wasa Musamman ma Jidda da Batajin Mganar kamar Sauran Abdullahi kadai Take Shakka.
Amira aka Fara sakawa a makaranta Kafin Amir ya Shekara Biyu a sakashi Suna Zuwa Tare,Da Farko Abdullahi ke Daukosu in sun Tashi Daga Baya kuma sai ya samar musu mai mashin nan kusa Dasu yana zuwa yana Daukosu Bayan Haihuwar Amir Sunje zamfara Shida Hafsah sukayi kwana uku Suka Dawo Lokacin kuma da Saddiq yayi Sauka ma Taje ta kwana Daya ta Dawo Tana zuwa in wani Abu ya Faru Hafsah Bata Da matsalan kowa game da Dangin Mijinta,Kowa na Girmamata baga Umman Saddiq ba,baga Mama ba,kowacce Tana ji da Ita haka kannen Mijinta baga Masu Auran ba baga yanmatan ba Kowa Anty Hafsah in Tana da matsala Guda Daya baya Wuce masifar Abdullahi da Korafinsa na Fama.
*****
Ganin yau sun Tashi Cikin Farinciki babu Yan masifan da Fadan a kusa yasa yana goge mashinsa dinsa Ta Rako su Amira da sukayi Shirin Makaranta ta kallesa Tana Fadin"Abban Amira Don Allah yau ka bar ni naje Gidan Subai"a na mata barka,Ta Kirani Jiya Tana ta Nuna Rashin Jin Dadinta kan Rashin Ganinmu Dagani har kai."
Dagowa yayi yana kallonta Lokaci Daya yana Ggyara zaman Tek tile din Gaban Rigansa kafin yace"Wato Nine bansan inda kaina ke min Ciwo ba ko..? Ita Don Ubanta Subai"an yaushe Rabonta Dana ga kafarta acikin Gidan nan Shine Domin bata da kunya Har Tana da Bakin mgana..! ?
Kan Hafsah na Kasa tace"Kai ma kasan Mahmud kulle fa garesa Abban Amira.."Taran Numfashinta yayi da Fadin"Oh Wato Shine ya san Ciwon kansa Bandani ya Hana Matarsa yawo acikin Gari sai ni gani Sakarai na barki kije ko..? Dariya ta kusa kama Hafsah ta Danne ta kafin tace"Kadai yi Hakuri naje din Abban Amira Tunda Harta Haihu Banje barka ba banje Suna ba..",Ido kawai ya sakar mata Ganin Haka yasa ta Lamgwabe kai Tana Fadin"Don Allah...Don Allah plz kar kace A"a.."Tafada Tana Sakarmai kyakyawan Idanuwanta wanda suka Taimaka wajen kashemai Jiki Karamin Tsaki ya saki kafin yace"Ki Shirya ki Tafi..ammh ban amince ki Kai mata yammah ba..Kowa ta zauna Gidan Mijinta.."
Dariya Ta kama Hafsah,Sai da Ta Murmusa kamata yayi Tana Dariya Da Sauri yace"Zan Sauya Ra"ayina yanzu matukar kina min wannan Dariyar taki.."Jin haka yaasa ta kame Bakinta kawai Tana kauda kai Kwandon abincin Amir ne a hannunta Amira na Rike da nata ta Rakasu Har Kofar Gida,Ya Dorasu kan Mashin Din Ita kuma ta mikama Amira kwandon Amir tana Fadin Allah ya Kiyaye Abdullahi ya kalleta yace"Basai kin Tsaya yin Girki ba..zan gayama mai mashin Dinsu in ya Daukosu ya kaisu Wajen mama..Ke kuma ki Dawo Da Wuri kibiya ki gaida mama in na Tashi aiki zan Biya na Daukoku mu Dawo Gida.."
Da Sauri Hafsah tace"Angama Ranka ya Dade...."Tafada tana mai Mirmishi Duk yadda yaso kar ya Nuna sai da ya Nuna Jin Dadinsa Kafin ya Kada kai kawai Yaja mashinsa Ita kuma Tana Binsu da Daga Hannu.
Gidan Ta maida ta kulle Cikin Farinciki yau dai Allah ya Dorata kam Abdullahi,Sama sama Ta karya da Tea da Bread da Soyayyan kwai,Tayi Sharan Daki Ta gyara ko"ina Sai ga Almajirinta yunusa yazo tace ya Zubamata Ruwa in yagama sai ya karya kana ya wanke mata kwanukan ita kuma ta Shiga wanka Koda ta Fito Har ma Yunusan ya gama yana Sharan Tsakar Gidan,agurguje ta Shirya Saboda Zumudi ta saka wani Sabon Less Dinta wanda Abdullahi ya Dinga mata Riga da Sikat,Babu Abunda zata ce ma Abdullahi sai Godiya Domin ko matar Wani Hamshakin mai kudi bata ta taba Nuna mata saka kaya ba Baya da Korin Iyalansa ta wannan Bangaren ita dasu Amira Duk wata sai ya Siya musu Sabbin kaya.
Leshin yada da kalan Marun ne ajikinsa Shiyaasa ta saka marun Din Hijabinta ta Dauki Jakarta mai kalan marun sai Takalminta wani mai Tudu sanin Halin mijinta yasa batayi kwalliya ba Hoda kadai tashafa sai kwalli,Sai Liptick,Wardrope Dinta ta Bude ta Dauki Daya Daga Cikin Atamfofin da Anty Hadiza ta kawo mata ta saka Cikin Leda wanda zata kaima Subai Tunda wannan karan Shi bai Siyama Subai"an komai ba,Batamai mgana ba gudun karya ce ma Tafasa Zuwan.
Kashe Wutar Duka Dakunan Tayi Kana Ta Rufe Kofar Bedroom dinta da Dakinsu Amira ta Fito,Yunusa Tagani yana Jiranta nan ta gayamai yatafi kawai anguwa zata tafi sai Dare zata Dawo Naira 100 ta bashi Tace ya Siya wani Abu da Rana yaci ya karba yamata Godiya ya Tafi Ita kuma Ta saka key ta kulle kitchen din,Ta Fito Ta kulle Gidan da makulli ta taka Zuwa Bakin titi nan ta samu Abun Hawan da zai kaita Har Bambamli inda Gidan Mijin Subai"a yake,Tana so ta bata mamaki ne Shiyasa bata ma Kirata ba Sai dai Ta Kira mama Tun Tana Gida ta Fadamata yau gidan Subai"a zata Wuni za"a kawo mata su Amira in an tasosu Daga makaranta Mama tace bakomai Dama suna da kaya nan gidan Maman Shiyasa ma Hafsah bata Daukan musu kaya ba.
Mai napep bai Direta ko"ina ba sai kofar Get din Gidan Subai"a,ta Sauko ta Biyashi Kudinsa ta isa ga get din ta Kwankwasa maigadin yana lekowa ya ganta ya Bude mata Kofa yana mata Maraba ta amsa Cikin Fara"a ta Shiga Haraban Gidan kenan suka Ci karo da Mijin Subai"a ya Fito zai Fita nan ta Tsaya Suna gaisawa Cikin mamaki yake Fadin"Anty Hafsah idanuwanki kenan ko..? Har Sweetheart ta gaji da korafin Rashin Zuwanki ta Hakura.."
Hafsah tace"Na wanke wannan Korafin gani yau Wuni zan muku.."Cikin fara"a yace"Masha Allah aikuwa mun gode yaya Abdullahi ya Mana kara Karisa Ciki zan Fita zuwa Gidanmu ammh bazan Jima ba zan Dawo.."Hafsah tamai addu"an Dawowa lafiya ya wuce ya Shiga Motarsa ita kuma ta Karisa Kofar da Zata Sadata da Cikin Falon Gidan.
*Anitha...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Dedicated To:My Habibaty💞Aisha idris Abdullahi..!*
*005*
"Da sallama abakin Hafsah ta Shiga Babban Falon Gidan na Subai"a Dayake mijinta Dan Babban Gida ne kuma yana da aiki mai kyau Medical lap ya karanta Babban Ma"aikaci ne a asibitin Chika Dake samarun Zaria.
Babu Kowa afalon sai Jaririnta mai Suna Salim Dake kwance Bisa Kujera Cikin Towel yana ta Barcinsa Kusa Dashi Hafsah ta karisa Tana Fadin"Tsiyata da Qawata wauta yaushe zaki bar Karamin yaro Shi kadai Cikin Falo ke ki tafi naki Sabgar..? Ga Iska ko ta ko"ina nata Kadawa Cikin Falon.."
Tafada Lokaci Daya Tana karisawa ta kashe Fankar Falon ta kuma Dauki Rimot din A.C ta kashe kana ta Sauke Jakar Hannunta da Ledan ta zauna ta Sunkuci yaron Bisa Hannunta Tana kallonsa sai Sharan Barcinsa yake Hankali kwance yaci wasu kayan Sanyi masu kyau sai Tashin kamshi yake yi Yaron sak Babanshi ne Hasken Fatan Subai kadai ya Debo.
Bata Jima Zaune ba sai ga Subai Ta Fito Daga Cikin Bedroom Dinta Tana wani Taku Daidai da Waya a Hannunta mamaki ya sandarar da ita ganin Hafsah zaune Dauke da Salim Baki ta saki Tana kallonta tama kasa karisowa Dariya ta kama Hafsah ta Bude baki Tana Fadin"Rufe baki Kuna ki Karaso sakarya Uwa kawai.."Da Sauri Subai ta karisa Gareta ta Fada gefenta Ta Rumgumeta tana Fadin"Innalillahi kai Qawas kin Bani Mamaki ne sai na ganki kamar Daga sama Wlh.."...
Tafada Cikin Wani Farinciki Daya kasa Boyuwa acikin Ranta Hafsah Ta Saki Mirmishi kafin Tace"Mamakin dama nake so na Baki Shiyasa ban Hidi miki gani Tafe ba..Sai nazo na iske kin bar yaro shi kadai Cikin Falo kuma kin kure Fanka da A.C ko..? Jego kike yi ne Subai ko kuwa Danyan Iskancin Jego ko..?
Wata Dariya Subai ta saki kafin tace"Kaji yar rainin wayau..Wai ke Hafsah kemin Fadan Yara..?Don Kaniyarki Koda kika yi Aure na Haihu so banga me zaki Fadamin ba.."Tafada tana Dariyarta Harara Hafsah ta sakarmata kafin tace"Waya gayamiki bata Daganan Wlh..banga alaman kin san komai ba Tunda kika bar Jariri Dayan Haihuwa Shi kadai kuma kika sakarmai sanyi ba zaki sani ne in sanyi ya kamashi ke zaki Dinga jelan zuwa Asibiti Allah na Tuba bama Fata.."Subai tace"Naji Zan gyara Mu bar mganar..Allah laifin Honey ne shi fa na barmawa na Shiga wanka Kinga sai ya ijiyeshi nan ya Fice abunshi.."Hafsah tace"Mun hadu dashi da zan Shigo Har muka gaisa Shima yana tamin Tsiya ke Subai kiji Tsoron Allah kin gama Barbadini a Duniya ko..?
Wata Dariyan Iskanci Subai ta kara Saki kafin tace"Yo Uban wa yaja ma kansa..? In da kinzo ai bazakiji korafi na ba ballatana Honey yaji Wlh ya san baki zo ba Daga ke har shi Uban gayyar wanda baki san laifinsa Yaya Abdullahi.."Hafsah tace"Kya dai ji Dashi Malama Na dai wanke Duka laifin gani nazo yau nan zan Wuni musha Fira.."Subai tace"Allah naji Dadi Sosai..Dama kamar kinsan ina nemanki.."
Hafsah tace"Lafiya kuwa..? Subai tace"Da sauki mu gaisa Tukunnah..Zamuyi Zencen Daga Baya.."Daganan suka Fara gaisawa da Tambayan gida da yara,Hafsah tace"Ina muhsin da Muhsina..? Subai tace"Suna Makaranta sai anjuma zasu Dawo..Ina su Amira Nayi ma Yaya Abdullahi mganar su zo min Weeked kuma naji Shuru.."
Hafsah tace"Ban ma sani ba Wlh...Wanchan weekend din a Tudun wada sukayi shiyasa ammh Insha Allahu zasu zo.."Subai tace"Allah ya yarda.."Daganan suka cigaba da Hiransu ta kawaye Hafsah ta bata Atamfar Data zo mata Dashi Ta karba Tana mata Godiya Cikin Fara"a Take fadin"Masha Allah matar Babban Yaya harda Wata Dawaniya Salim yayi Goshi Allah ya saka da alheri.."Hafsah Ta karba da Ameen.
Tare Sukayi Girkin Rana Suna yi Suna Hira Acikin Hirar ne Subai take gayama Hafsah wannan Shekaran Mahmud yace zata Dora karatunta,Hafsah ta kalleta Cikin Fara"a tana Fadin"Kai kai na tayaki Murna kawas wlh..Kinyi Sa"a ke mijinki ya barki zaki Dora karatunki Allah ya Bada sa"a yasa afara Cikin Nasara.."
Subai tace"Ameen kawata kema kici gaba da naci in kinci Sa"a kila yaya Abdullahi ya barki kicigaba kinga sau mu Dora tare,kinga ma kin Fini Fita da sakamako mai kyau aji Biyu Direct zaki samu Kawata.."Hafsah tace"Hmm bari kawai Kawas..kin fa san Halin yayan naki wlh bazai bari ba.."
Subai tace"Gaskiya ne ai yaya Abdullahi sai ke kawata...Yana da Wani Budadden Hali ne da Shegen Miskilanci zama Dashi sai mai Hakuri ammh ai illimi ba laifi bane in ya barki kin Cigaba kika samu aiki yau ai Ribarsa ne.."Hafsah tace"Kul karma ki bar yaji ki kina Fadin haka wlh sai ya Saba miki Shida yace Ko Da Kwalin Digree gareni Wlh Tunda na Aureshi bazai min amfaani ba Mace bata karatu Gidansa kuma bata aiki.."Subai tace"Uhum..Gaskiya yaya Abdullahi nada Tsauttsauran Ra"ayi kamar ba Dan Boko ba.Su mariya suna Complain dinsa Takura musu yake sosai sunce kila har gwara lokacin mu ni da Anty Zannira nace ba gwara wlh muma munsha wannan Saka idon da Takuran na Yaya Abdullahi.."Hafsah tace"wannan kuma bai yi laifi ba matsayin Uba yake gareku.."Hararanta Subai Tayi Ita kuma Hafsah ta sakamata Dariya.
Sai da suka gama Abincin suka ci sukayi Salla kana suka Zauna zaman Hira Subai na Dauke da Salim tana bashi Nono tace"Honey yayi nisan zango kinga har yanzu bai Shigo ba...?Hafsah Tace"Kuma yace min gida zai je bazai Dade ba zai Dawo ba.."Subai ta tabe baki kafin tace'"Ai bazasu barshi ya Taho ba..Wannan Shegiyar yayar nashi Bazata barshi ba Dama tace na mallakeshi bayajin mganar kowa sai Tawa.."..
Hafsah tace"Subhanallah Wacce Daga Ciki kuma..? Subai tace"Anty Uwani babar yayarsu mana..Wlh kawata Matarnan ta Fara Shigarmin Hanci da Majina na Ta isheni.."Tafada Cikin Damuwa da Bacin rai Hafsah tace"Toh duk mai ya kawo haka..?
Subai tace"Ohon mata bai wuce Rainin arziki mana Dama Tana ta Fadin wai yaje ya kwaso musu Diyar Direba mai Auri saki,gidanmu gidan Takalawa kuma matsiyata ai kinsan Tana India wajen jinyar mijinta akayi mganar Aurenmu da Honey kuma tana chan akayi Auren Toh Tunda ta Dawo Shikenan Idonta ya kawo kaina Matarnan bansan me na Tsareta mata ba in da Honey zai Bi nata mganar toh da yanzu ya Rabu dani.."
Subai ta karishe Mganar Cikin Taruwar kwalla Hafsha tace"Innalillahi Abu baiyi Dadi ba wannan ai Tozarci ne..Toh in ya sakeki ta aura mai wa..? Subai tace'Kanwar mijinta mana..Samira ta Fadamin kanwar mijinta wacce take karatu a lagos ita keson Honey kamar ta mutu Ita Anty Uwani taso ta Hada Abun Shi kuma yaki ya Nuna Baya Ra"ayi sai kuma Rashin lafiyar mijinta ya taso suka Tafi India Ciwon Sugar yake Fama Dashi Chan suka Rikesa wajen Shekara koda ta komo anyi Auren mu nan fa sai Bala"i take Daga karshe tace sai ya auri yarinyar shi kuma ya kiya Kinji fa Dalili yanzu Duk inda muka Hadu ta Dinga sakarmin mgana kenan Hafsah.."Tafada Hawayen Idanuwanta suna kawowa,Matsowa Kusa da Ita Hafsah Tayi Ta Dafa kafadanta Tana Fadin"Kiyi Hakuri kawata Bai kamata ki saka wannan Abun Aranki ballatana Har ya Dameki ba Kedai Allah ya gani Mijinki na Sonki Saboda haka ki Fidda kanki Cikin mganarsu ki barshi Shida yar"uwansa ne babu Ruwanki..".
Subai ta Sauke Salim kan Cinyarta ta mika Hafsah Shi Tana Fadin"Wlh kawata in Cin Mutumcinta Baya Taba Ahalina da asalina Ko Damuwa Banyi ammh Cim mutumcin nata ya wuce kaina ya koma kan Ubana Dayake kasa Baisan meyake Faruwa ba,Ranar sunan wannan yaron fa Ya"yanta da Surukanta suka zo Gidanan baki ji Abunda suka Dinga Hidima su mariya ba wai Babanmu Auri saki ne Bakincikinsa ma ya kashe Uwata wai kuma Dukkanmu suna da Labari ba wacce uwarta ta Haifeta Gidan Ubanta Duk Daga Baya aka maidomu Don Allah Hafsah ya Dace nayi Shuru da wannan Cin Mutumcin da Tozarcin..? Tafada Idanuwanta suna kara Zubar kwallah.
Hafsah tace"Gaskiya bai Dace ba kam..Ammh Shawarata gareki ki saka musu ido ko Mahmud din karki Fadamawa..In kika yi musu Banza kika Nuna bama kisan Sunayi ba Wlh su da kansu in suka Gaji zasu Daina.."Subai tace"Ina Wlh ban iya wannan Shegen Hakurin irin naki Hafsah..Sai da na gayama Honey Kuma ya Bisu har gida yaci musu Zarafi itama Anty Uwani sai da sukayi ba Dadi Dashi aie..Zan iya Hakuri Da komai ammh banda Zagin mu iyaye ai iyaye bai fi Iyaye kuma Ban Taba Cin Zarafin nashi iyayen ba kin ga kuwa Bai kamata na Zauna ana cin Zarafin nawa ba Har sai da Umminsa tazo Har Gidan nan tana Bani hakuri kuma tamin alkawarin Uwanin bazata kara ba.."Hafsah ta Rike baki kafin tace"Ke kawata Fitinarki nada yawa fa.."
Subai tace"Ah naki wasa ne Wlh kuka na sakamai Wiwi na Hada kaya nace ni Gidanmu zani Shine Hankalinsa ya Tashi ya Kira Ummi ta waya gayamata Shine tazo Taban Hakuri ta kuma Min alkawarin insha Allahu haka bazata Kara Faruwa ba.."Hafsah tace"Ke yanzu da ya barki da Danyen Jegon zaki komama Mama Gida..?
Subai tace"Kina wani Zence kawata..ai nasan bazai barni na Tafin bane.."Tafada tana Dariya Hafsah tace"Karyan Tsiya kike Subai Karki dai ki kuma irin Haka ba Dadi kin Dagama bawan Allah Hankali haka kurum.."Subai tace"An bari matar yaya ammh gwara da nayi ba gashi an ma Abun Tufkar Hanci ba.."Hafsah tace"Hakane..Allah ya kyauta na gaba Rayuwar ne sai Hakuri.."Da haka suka Cigaba da Hiransu Hankalinsu kwance sunayi Suna Shakiyansu da Suka saba in ka gansu zaka Fahinci ko Daman Chan suna da Shakuwa da kuma kyakyawan Fahimtar juna.
Basu Fahimci Lokaci yaja ba sai da Direbam gidansu Mahmud ya Dawo Daga Dauko su Muhsin Daga makaranta Suna Zaria acadamy ne,Tare da Yan Gidansu Mahmud din kannensa da kuma ya"yan yayyinsa Toh Duk mota Daya kai kaisu kuma ta koma ta Daukosu ta maida kowa Gidansu,Suna Dawowa suna ta murnan ganin Umma Wato Hafsah kenan suna Tsalle Tsalle abinci kadai sukaci sai kiran Sallar La"asar,sukayi salla kuma aka kwashesu Zuwa islamiya Itama Hafsah bayan ta idar da salla tace zata tafi Gidan Mama Subai Tace bata isa ba Ai Wuni tace mata zatayi Bazata tafi yanzu ba.
Hafsah ta kalleta tana Fadin"Yanzu Fisabilillahi Ban miki Wuni ba..? Tun karfe nawa nake gidanka ga..? Nafa gaya miki Su Amira na Gidan Mama kuma yayanki yace chan zai Je ya Daukomu mu koma Gida in yaje ban Dawo ba kema kin san Hali Dagani har ke Sai mun raina kanmu.."Subai ta Dauke Jakarta da Hijabinta tana Fadin"Eh din naji..Wlh Baki tahiya yanzu sai anjuma in Honey ya Shigo ya Sauke ki Gidan mama.."Hafsah Tayi tayi Subai"a ta bata Hijabinta da Jakarta taki sai ma ta kai Cikin Bedroom Dinta ta Kulle da makuli ta Fito Tana Dariya Hafsah ta Shaka Duk Ranta ba Dadi sanin Halin Gogan nata yanzu Ranta zai baci in batayi wasa ba.
Mahmud bai Dawo Gidan ba sai gabda mangariba Koda ya Dawo Hafsah ta gama Sadakarwa Kawai yau Ita da Abdullahi sai ta kauda kai kawai koda ya Shigo ya ganta nan Subai"a ke bashi labarin Abunda ta aikata Shima Biye mata yayi,sai da yayi Sallar mangariba suma sukayi Subai"a ta matsa mata sai da taci Dinner kana Ta Dauko mata Jakarta da Hijabinta tana Duba Wayarta Sai da Gabanta ya Fadi 7missed calls na Abdullahi harda Kiran Mama gabanta ya Fadi Jikinta ya kama Rawa Cikin Firgici tace"kingani ko Subai..? Yayanki sai kiran wayata yake harda Kiran Mama Wlh kila ma ya Dawo yaje chan bai ganni ba.."
Subai tace"Kwantar da Hankalinki Tare Dani zamu Rakaki har gidan mama.."Saboda Haushi ko Kulata Hafsah batayi ba ta Fice Subai ta Bita da Dariya Kaya ta Sauya ta Dauko mayafinta ta Nado Salim cikin Towel ta Fito Haraban Gidan inda Mahmud ke jiransu,Su muhsin basu Dawo ba kila suna wajen Ummi,Hafsah tana so tama Subai fadan Fita tana Jego ammh Hankalinta ba"a kwance yake ba yasa bata mata mgana ba suna ma Cikin motan sai kiran Abdullahi take yaki Daga Kiranta sai Cikinta kawai ya Kulle Zufa ya fara ketomata.
Subai"a nata Jefata Cikin Hirarsu ita da Mahmud hankalinta Baya Jikinta sai dai kawai tayi musu yake,Suna kawowa Kofar Gidan Mama da Abdullahi suka Fara Cin karo Shida Auwal suna Tsaye suna mgana Wutar motar ta Haske musu Fuska Subai tace"Hafsah mun Shige su ga Yaya Abdullahi nan wlh..."Ai Hafsah bata tsaya ma Sauraran Subai"a ba ta Balle Murfin Mota ta Fice motar ko Gama tsayawa batayi ba Subai"a ta Bita da kallo tana Girgiza kai Mahmud yace"wai duk Tsoron Fadan yayan namu ne Haka..?
Subai tace"Bama itaba nima kaina sai yanzu nake Nadamar Biyoka Har ni nan bazan Sha Daga Fadan yaya Abdullahi ba wlh.."Mahmud yayi dariya yana Kallonta Hafsah kuwa tana Fitowa Daga Motar ta nufi su Abdullahi Shi kuma Daman yana Ganin motar ya gane na Mijin Subai"a ne Ransa yabasa Cewa Hafsah suka Kawo dama Tun kafin mangariba ya taso Daga wajen aiki yana zuwa Mama tace Hafsah bata kariso ba Tukunnah Ransa ya baci ya dauki waya ya Kirata bata Daga ba gabadaya Zuciyarsa ta Fara tafasa kawai ya Fita zuwa masallaci sallar mangariba bayan sun idar ne yaga Kiranta yaki Dagawa suka Taho tare da Auwal Daya gani a masallacin suna mgana kan Shangonsa Dake Tudun wada sai gasu Hafsah.
Tunda ta Nufosu ya Hade Ransa tamau ba alamun Fara"a Auwal ne yana Hangota ya washe baki yana Fadin"la..yaya Abdullahi gama Anty Hafsah nan.."Yana jinsa kawai sai ma ya Juya ya Shiga Cikin Gida ya barsu nan Hafsah ta Bisu da kallo kafin ta kalli Auwal tana amsa gaisuwansa Cikin Firgici take Fadin"Yayanku ya Dade da Dawowa ne..?
Auwal yace"Wlh Anty Hafsah bansani a masallaci muka Hadu nima dawowata Shago kenan Dayake daga makaranta na Wuce.."Hafsah ta kada kai tana fadin"Allah sarki..ya karatun..? Yace"Alhamdulillah Anty..mun godema Allah..'Hafsah tace"Allah taimaka Bari na Shiga Ciki.."Daga haka ta Shiga Ciki Shi kuma ya karisa wajen su Subai da Mahmud Dake Tahowa ya amshi salim suna gaisuwa kafin suma su Shiga Cikin Gidan.
Hafsah tana Shiga Gidan ta Iske Abdullahi cikin Dakin Mama Su Amira najin sallamanta suka Rugo da Gudu suna mata oyoyo ta Rikesu Tana Fadin"yan Gidan mama yau kunsha ma mama wuni ko..? Tafada tana Sallama Dakin Mama wanda ke Haske da kwan Fitilan makarfi Domin Babu Wutar Nepa,Mama Dake Zaune kan Daya Daga Cikin kujerun Falon ta amsa sallaman Tana Fadin"Hafsah kin kariso..?
Tace"Eh Mama.."Tafada tana Satan kallon Abdullahi dake Zaune Akasa gefen mama kansa na kasa yana latsa wayarsa Gefensa Chan Nesa ta zauna Tana gaida mama ta amsa Tana Fadin"Ya dawo yana Tambayanki nace baki kariso ba Tukunnah...Kila Subai"atu ta Rike ki..'Hafsah tayi yake kafin tace"Eh Wlh Mama tun bayan La"asar na Shirya tahowa Subai ta Hanani Mama.."Tafada Tana kallon Abdullahi wanda ko kallo bata Isheshi ba.
Mariya ce ta Fito Daga Uwar Dakin Mama Tana Fadin"Anty Hafsah ina wuni.."Hafsah ta Dago Tana Fadin"Lafiya lau mariya ya Gida..? Ya kariniyan Su Amira..? Mariya tayi Dariya kafin tace"Mama ce tayi fama nima sai Yammah na Dawo daga makaranta.."Hafsah Zatayi mgana kenan Abdullahi yace ma Mama"Mama wai meyasa kike Barin Jidda Tana kaiwa Dare a waje ne..?
Mama tace"Wlh ba laifina bane Yayansu Kanwar mamarta ta aiko Taje yau suna Tariyan sabon Gida Tun Safe tatafi kuma har yanzu bata Dawo ba kila chan zata kwana.."Abdullahi yace"Wani irin chan zata kwana..? Banda ta Raina mutane in zata kai Dare ko kuma zata kwana Bata iya Kiran waya ta sanar..? Kuma ni wlh bana som wannan Yawom na Rashin Dalili Mama..".
Mama tace"Sai dai fa kayi Hakuri gani nayi Hassana ce ta aiko Taje Shiyasa nace ta Shirya taje Bakomai Da nan da chan Duk Dayane in ta kwana ai ba wani abu bane.."Kai Tsaye Abdullahi yace" Da abu mana Mama...Chan ai ba Gidansu bane bamai kwabamata Abunda taga dama zatayi Dama ai Jidda bata Jin mgana Ki kirata awaya Mama Kice nace mata komai Dare ta Dawo Gida wlh ko na saba mata.."Mama tace"ai Shikenan bari na kirata na gaya mata.."Daga Haka kawai ya mike Daidai Lokacin dasu Subai suka Shigo Gidan da sallama Mama ta amsa Auwal ne kan Gaba wajen Shigowa Dakin Dauke da Salim sai Subai"a da Mahmud suna Binsa a baya baki Mama tarike kafin tace"Me zan gani haka..? Subai"a da Danyen Jegom kike wayo..?
Subai"a Tayi Dariya Mariya ta Fito tana mata oyoyo kamar yadda su Amira suka Riketa suna mata oyoyo Mahmud ya Gurfana yana gaida mama ta amsa Cikin Sakin Fuska kafin ya waiga yana Fadin"Yaya Abdullahi mun wani lafiya..'?
Ya fada yana Mikewa Lokaci daya Yana Mikamai Hannu ya karba sukayi musabaha bayan sun gaisa Subai"a na Dari Dari tace"Yaya Ina wuni.? Wata uwar Harara ya Sakarmata kafin yace"Ke ashe baki da Hankali bansani ba..? Wani irin Sakarci ne zaki Fito kina jego ana mgana kina ma Mutane wannan Shashashar Dariyar nan taki koda yake ba laifin ki bane na wannan Mijin naki ne daya koma Mijin Hajiya.."
Yafada Fuskarsa ba Annuri Subai"a ta Sadda kai batayi mgana ba Mama tace"Ka yi mgana dai kila taji haka tarika wannan Fitan Lokacin haihuwar muhsina Wlh ki kya kanki da wayon nan Subai"a kina da Karamin Yaro.."Mahmud yace"Baza"a kara ba Mama yanzu ma Antynmu matar yaya muka Rako.."
Abdullahi ya kada bai kara Mgana ba ya kalli Hafsah yana Fadin"Ki Dauko su mu tafi.."Daga haka ya waiga yana cema Mama"Mama sai da safe zamu Tafi.."Mama tace"Allah tashemu lafiya.."Hafsah ta mike itama tama Mama sallama Lokaci Daya tana cema Su Amira su Dauko Unifirm dinsu da Sch bag dinsu sai kwandonsu Mariya ta Dauko musu kayan makaranta wanda ta wanke da Jakunkunansu ta basket dinsu Tabama Hafsah,Subai"a ta taso ta Biyo Hafsah har Haraban Gidan Tana Fadin"Kawas sai da safe.."Wata Uwar Harara Hafsah ta sakar mata kafin tace"Zaki sani ne.."Dariya ta mata kawai nan sukayi sallama Mariya da Auwal suka rakasu har waje Amir Shi ya zauna agaban mashin din ita kuma ta Hau Baya ita da Amira ta Rike Ledan da Sch Uniform dinsu yake Ciki da Sch Bag dinsu Basket dinsu kuma na Hannun Amira su Mariya na Daga musu Hannu Abdullahi yaja Mashin Din suka Wuce.
Tunda suka Hau Titi kala Abdullahi bai ce ma Hafsah ba itama Batacemai,sai Sharara Gudu yake Bisa mashin Daga gani Ransa yana bace ne Hafsah ta Fara tsorata da Gudun da Abdullahi yake Cikin Sanyin Murya tace"Don Allah Abban Amira kayi a hankali kada ka kadamu.."Kamar ta kara Zugashi ne ya kara sakarma Mashin din wuta sai kawai ta kame kanta ta koma tana sallami Cikin Ranta gefe Daya kuma Tana karanta Hasbunallahi wani"imal wakil.
*Shakira..*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Dedicated To:My Habibaty💞Aisha Idris Abdullahi...*!
*006*
"Ajiyar Zuciya ta Sauke Lokacin Data ga sun kawo kofar Gida bai ce mata komai ba ya karkata mashin din ta Sauka Bayan ta Sauke Amira,harma wajen sauka ta Sarke kafarta tayi kamar zata Fadi ya saka Dayan Hannunsa ya Riketa,ammh bai kalleta ba dayaji ta Tsaya da kafafunta sai ya saketa ya Sauke Amir kasa wanda ya Fara Barci bai Jira cewar ta ba kawai ya kara Tada mashin din nasa ya juya ya koma Da kallo ta Bishi acikin Ranta kuma Duk Babu Dadi tafi kowa sanin Illar Fushin Abdullahi karshenta Itace zata sha Wahalansa.
jakarta ta lalubo ta Dauko key din Gidan wanda ke Hade Dana Sauran Dakunan,da Fitilar wayarta tayi amfani ta Haska ta Bude Gidan Bayan tabarma Amira Rikon ledan kayan makarantarsu,Suna Shiga Gidan Nepa na maido Wuta,Ta Bude Dakinta suka Shiga ta Kunna Wutar Ciki dana waje haske ya Bayyana ko"ina Amir ta kallah wanda ta Rikeshi a Jikinta Barci yaFara Daukansa.
Kumatunsa ta Shafa kafin tace"Amir kana jin yunwa.? Kai ya Girgiza mata alamun A'a Amira ce tace"Umma mun koshi Munci Tuwo agidan Mama.."Hafsah ta mike tana Fadin"Kama Hannunsa ku Shiga bayi kuyi Fitsari kuzo ku kwanta.."Batayi gaddama ba ta ijiye ledan kayansu akasa Ta kama Hannun Amir Zuwa Cikin Dakin Barcinsu hafsah inda Tailet din yake Ciki,Suka Shiga tayi Fitsari ta saka Amir yayi ta kamo Hannunsa suka Fito,Hafsah ta kamasu Zuwa Dakin Barcinsu ta kwantar dasu Tayi musu addu"an Barci ta Tofa musu Ta ja musu Bargo ta Fito Falo ta zauna kan Kujera ta zabga Tagumi ganin har Tara ta wuce Abdullahi bai Dawo ba Dakyar ta iya Tashi ta Kwashi kayansu Amira da suka Dawo dasu takai musu Ciki ta Fada Tailet tayi Alwala Bayan ta saka Ruwa a kittle sanin Abdullahi in ya Dawo zai yi wanka tazo tayi salla Ta idar kenan tana Zaune kan Sallaya taji Shigowar Abdullahi da Karan Mashin Dinsa tayi Zumbur ta mike ta Fito Tsakar Gidan ko Hijabinta bata Cire ba.
Yaga Fitowarta ammh sai yayi kamar bai ganta ba ya Bude Dayan Dakin ya saka Mashin din nasa ya Fito Hannanunsa Dauke da Ledoji Guda2,Ya Raba ta gefen Hafsah ya Shiga Dakin Tabi bayansa saman Capet nan kasa ya Zube Duka ledojin Dake Hannunsa ya kama Hanya ya Shige Bedroom Hafsah tayi sakale Tana Binshi da kallo Jiki a sanyaye ta karisa ga Ledan ta Bude,Daya maganin Sauro ne sai mayan Bicuit Guda Biyu nasu Amira ne,Dayan ledan kuma Gasashiyar kaza ce Guda Biyu sai Tiriri suke da alaman yanzu aka gama gasasu,Dauka tayi ta matsar gefe Ta Dauki ledan mganin Sauran zuwa Ciki Sai suka ci karo ya Fito Daga Tailet Dauke da Botikin wanka na karfe Kadan ya Rage basu bangaji Juna ba Hafsah tayi Saurin Matsawa Baya Shi kuma ya Rabata ya Wuce Hafsah sai dai Tabishi da kallo kawai gefe Daya na Zuciyarta na addu"ar Allah ya saukar da wannan Fushin Data gani a Kan Fuskar Abdullahi.
Bayanshi Tabi Bayan ta Ijiye ledan maganin Sauron Abunda tagani ne ya Bata mamaki Abdullahi ya zage yana Cika Botikin Daya Fito Dashi Da Ruwa a Rijiya Cikin mamaki ta karisa Tana Fadin"Abban Amira me zakayi da Ruwa kuma..? Alhalin Duka Bombin Tailet Cike suke da Ruwa Hakama na wajen nan.."In Iskar Dake wajen ta Tankanta toh Abdullahi ya Tankata,yayi mata Banza bai Dakata ba sai da ya Cika Botiki tsaf kana ya Dauka da Hannunsa tana Tsaye ya wucewa Zuwa Ciki da Sauri tabi Bayanshi Har Cikin Tailet din Abunda ya Bata mamaki bai Juye Ruwan Kittle ba Taga kawai ya Fara Kwabe Rigar Jikinsa alamun wanka zaiyi baki sake take Binshi da kallo Shi kuma yaki yarda ya kalli Barayinta ganin bata Niyyar Fita yasa ta Tube Duka kayansa ya Wurga Cikin kwandon tara kaya wanki ya Fara watsama Jikinsa Ruwan sanyi.
Batazata iya Juran ganinsa Haka ba Koda suka Haihu har sau Biyu Tana da kunyar ganin Tsaraicin wani kawai sai ta kada kai ta Fito Zuwa Cikin Bedroom din Hawaye sun kawo Cikin idanuwanta gefen gadon ta zauna Kawai Tana Tunanin mafita da kuma makomar wannan Shariya ta Abdullahi wanda komai nata yanzu baya Bukata,Tana nan zaune ya Fito Daure da Babban Towel ta gabanta ya wuce zuwa Jikin Wardrope ya Bude ya Dauko Jallabiyansa Baka ya saka kana ya koma Toilet din da Towel Din Dake Hannunsa,sai chan kuma ya Fito gaban madubi ya koma ya Fesama Jikinsa Spry, Tana kallonsa ya koma Bisa gado ya kwanta Bayan ya kashe wayarsa,Har kuma ya kwanta sai kuma ya mike yaje ya Kashe Wutar Dakin ya koma ya kwanta Harda Jan Bargo kamar bai sam da zaman mutum a gefen gadon ba.
Ganin haka sai Jikin Hafsah yayi sanyi Cikim karfin Hali da Shawaran Zuciyarta ta Mike ta isa Kusa Dashi dan Dukawa tayi tana Fadin"Abban Amira.."acikin Taushin Murya da kuma Lallashi Tsit yayi kamar bai jita ba sanin yana Jinta yasa tacigaba da Fadin"Don Allah kayi hakuri kan Abunda ya Faru yau..Wlh ba laifina bane laifin Subai"a ce Zan taho Tun bayan La"asar ta Daukemin Jakata da Hijabina taki Barina natafi..Allah ba laifi bane.."Ta karishe Fada Cikin Rawar Murya kamar zatayi kuka Shurun ya sake mata sai ma kawai Taga ya gyara kwanciya ya Juya mata Baya bata Hakura ba Ta kara Bude baki tana Fadin"Kayi Hakuri...Ba..."Bata karisa ba Taga kawai yayi Zunbur ya mike Har sai da Ta Tsorata tatashi da Sauri kawai sai taga ya Dauki Filo da Blanket din kawai ya Bar mata Dakin Galala Hafsah ta Bishi da kallo kafin ta Hadiye wani miyau mai Zafi wanda ya wuce ta Cikin mangwaronta bai Shirya ba.
Bayaansa Tabi Cikin sanyin Jiki nan ta iskeshi kwance kan Doguwar kujera,yayi kwanciyar Rigingine yana kallon Celling gefe Daya kuma ya goya Hannayensa Akan Kirjinsa ya kuma Lumshe Idanuwansa kamar mai Barci Hafsah tayi kasake kafin ta karisa Tana Fadin"Ka tashi ka koma Ciki Don Allah..kasa ina jin wani iri Abban Amira.."Ko alaman yajita ma bai yi ba,Balle ta saka Ran zai amsata Ganin haka yasa ta kara marairaicewa Lokaci Daya tana Riko Blanket din Daya Rufu Dashi Tana Fadin"Kaji..Don Allah ka tashi ka koma ci..."Bata karisa ba Taji ya Daka mata wata Gigitattaciyar tsawa Wanda sai da ta sa ta afirgita ta saki Bargon ta koma Baya Cikin wani Zafin nama ya Tashi zaune yana kallonta kafin yace"Kinga malama indai bakina so na barmiki Gidannan bane ki Tafi ki bani Wuri i don"t want to see u in my Side plz.."Yafada Cikin Kakkausan Murya mai nuna Bacin Rai..
Hawayen Idanuwan Hafsah suka Zubomata ta saka Hannu ta Share Cikin Muryan Rauni da karaya tace"A"a bari na tafi Dakinsu Amira na kwana..Allah ya Huci Zuciyarka.."Tafada Lokaci Daya tana Hucewa Cikin Sharan Hawaye ya Bita da kallo acikin Ransa kuma sai yaji Tsausayinta kamar ya Tsaidata sai Wata Zuciyar ta kwabesa Da cewa gwara ka kyaleta ta gane Kuraanta in kayi Saurin saukowa shikenan ta samu Dama gaba sai Tayi Abunda ma yafi haka da wannan Shawaran ya kwashi kayan kwanciyarsa ya koma Cikin Dakin yana sakin Tsaki.
Ita kuwa Tana Shiga ta Fada Gefen Amira kan katifa lokaci Daya Tana Fashewa da wani Irin kuka mai Tada Hankalin mai Sauraro Dama Abunda Ta gudanar ma kanta kenan Tana ta Fadama Subai ammh Taki yarda da Ita gashi dai Abunda ta Gudanar kuma ya Faru har ma ya Zarce Tunaninta,kuka take mai Cin Rai,da kuma Rauni Bata san iya Adadin Lokacin Data Dauka tana wannan kukan ba Sai da Tagaji tatashi Zuwa Falo nan ta iske bayanan gabanta ya Fadi Tana Tunanin Allah sa ba gidan ya Bar mata ba kamar yadda ya Fada,sadaf sadaf ta Leka Bedroom din chan ta Hangoshi yana Barci yayi kwanciyar Ruf da Ciki,ya saka Filo a gefensa ya Rike blanket din Daya Rufu Dashi ma ya Jaye gefe ganin haka yasa ta Shiga Ciki a Hankali Tana bin Hasken Farin watan Daya ke Shigowa ta Labulan Window Bedroom din,Blanket din Taja ta gyaramai,kawai sai ya motsa ya maida kansa yana kallon sama Acikin Barci ganin haka yasa tayi Saurin Fita Tana Maida Numfashi,Waje ta fita Tayi alwala kana tazo ta kulle kofar Sai Lokacin Taga agogo karfe 1:30am na Dare,Dakin su Amira ta ta wuce Ta Shinfida Sallaya ta Tada sallah da Hijabin Jikinta sai da tayi Raka"a Tara ta Cike da Shafa"i da Wuturi Ta Dade tana addu"an Allah ya Saukar da Fushin da Abdullahi yayi akanta Allah kuma ya Huci Zuciyarsa sai wajen uku saura na Dare ta Sulale nan saman sallayar Barci ya kwasheta Batare Data sani ba.
****
Washegari ma Abun bai Chanza Zani ba Domin komai Datakemai Yau din bai nemi Taimakonta ba,Ta Juyemai Ruwan wanka ammh yakiyi Dashi sai yaFito kamar Jiya yaja Ruwa arijiya Ruwan sanyi yayi wanka Dashi,Breakfast ma nan ya bar mata kayanta,Har tagama Shiryasu Amira tana Sharan kwallah ta sani Abdullahi nada Fada Ta saba tayi laifi ammh bai Taba mata irin wannan Horon ba sai tama gwammace Dama Fadan yayi mata da wannan Shurun Ranar laifinta ya Shafi su Amira bashi yakaisu makaranta ba Briefcase din kawai ya Dauka da Key din Mashin Dinsa ya Fice Bai ce mata komai ba Sai tayi Tunanin kila ita zata kaisu makaranta Amira Har Kofar Gida Tabishi Tana Fadin Abba yau bazaka kaimu makaranta bane,Ita ya fadama mai mashin dinsu zai zo ya kaisu ita Amiran ke Fadama Hafsahn din,Ba Jimawa sai ga mai mashin dinsu yazo ya Daukesu zuwa makaranta...
Abdullahi yana Office wajen karfe 2pm na Rana Nazifi ya Kirasa yana Tambayansa yana ina ne..?yace yana Office ne..Yace gashi nan zuwa,Ba jimawa sai gashi yazo bayan sun gaisa ne Abdullahi yaga Nazifin Duk ya Rame kuma afirgici yake kamar Baya cikin Natsuwarsa Yasa ya kalleshi Cikin mamaki kafin yace"Abokina lafiyarka kuwa na ganka Duk afirgice..?
Nazifi yayi ajiyar Zuciya kafin yace"Hmm bari kawai iskancin Sakina ne Duk yabi isheni Wlh..."Abdullahi yace"Topha..Me kuma ya Faru yanzu..? Nazifi yace"Miye ma bai Faru ba,Jiya Na Dawo Daga Abuja ammh ina gaya maka Mutumina Sai da mukayi kacha Kacha da ita har dai ta kai ga sai da ta kureni na Daga Hannu na mareta.."
Abdullahi yace"Subhanallah Mari..? Gaskiya baka kyauta ba bai kamata ka Daga Hannu ka Mari matarka ba komai ta maka kuwa abokina.."Nazifi ya saki Tsaki kafin yace"Yo In ma Bugu ne ta kama Bani Bugunta..Yarinya ta maidani kamar wani yaron Gidansu Saboda mene..? Ita ke Aurena ko ni ke Auranta..?
Abdullahi yace"Duk wannan bai Taso ba...kowa ya sani kai ne Shugabanta,ammh bazan Fasa Fada maka baka kyauta ba Babu kyau kuma ba Mazantaka Bane,Namiji ya Daga Hannu ya mari matarsa gaskiya ba Dacewa bane.."Nazifi yace"Wlh ni kuma In dai mace zata kawomin Rainin da Sakina ta kawomin yau sai na Bigeta bama Marinta ba.."Abdullahi yace"Koma dai menene Hakuri ake Mutumina Mata sai a Hankali kowa ka karkace su Domin su Gyara Kara Bankare suke Abun ne sai Hakuri kawai.."Yafada Batare Daya Damu ya Tambayi Nazifin meya faru ba.
Nazifi ya gyara zama yayi yana Fadin"Ina gayamaka Mutumina Shekaranjiya naje Abuja Tunda naga wajen Sati uku Rabonmu da Juna,Ita batazo ba Nima Fushi nayi naki zuwa,Daga baya kuma sai nahuce na Bita Chan Mun kwana lafiya lau sai Jiya da Safe kawai naga tana Shiri Dana Tambayeta sai take Fadamin wai Wata Seminar zata lagos Kuma zatayi wajen kwana Hudu,Abun Takaichin ma ba Neman izinina take ba gayamin take don na Tambaya karim ma Abun Haushin ma atafiyar ita kadai ce mace Duka Uku wasu gardawan Maza ne wadanda ba Muharramanta ba,Don na mata Mgana Shine ta tasomin Daga karshe Ni kuma nace na Hana Tafiya,Shine fa ta Faramin Borinta Data saba na kuma ce Wlh bazata jeba,kasan Saboda Raini yarinyar sai kawai taci kwalata Tana Fadin na Bata makullin Gidan Dana Dauka na rufe Kofar Falon saboda karta Fita ina gayamaka Mutumina,Sakina Hardamin Gorin gida da Dukiya,Ni kuma Raina ya baci na Tsinketa da mari na Tureta Gefe na Fito na Barta aranar na kamo Hanyar zaria Bansa yadda ta kare ba.."
Abdullahi Da yayi Sagale yana kallon Nazifi ya saki Nunfashi yana Fadin"Tabdijam...Abu kam baiyi Dadi ba ammh agaskiya Abokina saken kane Tun Farko Sakina ta Rainaka Kana Bani wannan labarin acikin Raina ina Tunanin in nine Wlh mace taci kwalata ina Fada tana Fada yadda na Tsani Raini da sa"in sa Wlh sai na Barta kwance Duk ko ina Daukan Namiji mai Dukan mace Sakarai.."Nazifi yace"Hmm Nima na yarda da Haka Shiyasa nake baka Shawaran kar kayi saken danayi abaya Nima Daga saken ne Komai ya kwacemin shiyasa nake gayama kowani Namiji ya zama Jajirtattace kuma Masifaffe agidansa Hakanne kadai zai sa ya samu lafiya ya kuma sa mace ta Dinga Shakarsa.."Abdullahi yace"Da wannan don wannan kuma ka Fadi gaskiya..Toh yanzu ina ita Sakinar..? Tatafi lagos din ne..?
Nazifi ya Tabe baki yana Fadin"Ohon mata..Tun jiya ina Hanyar Zaria naga Kiran Tsohonta naki Dagawa nasan ta Kirashi ta gayamai karya da gaskiya Shi kuma mai ya' ya ya kirani zai Rainamin wayau naki Daga Kiran,yau kuma Tun Safe Baba ya kirani yace nazo yana nemana Ina zuwa sai yake Min Fada wai Baban sakina ya Kirashi yana ta Fada yana ikirarin sai yamakani kotu na Dakarmai yarinyar har sai da ta Suma..."Abdullahi ya Zaro ido Lokaci Daya yana Fadin"Innalillahi kaji wani Sharri.."
Nazifi yace"Wlh..ai ya saba dama yarda da mganar ya"yansa...Ita zata kara mganar shi kuma ya hau kai mana Nadai ma Baba Bayani Daga karshe yayi tamin Fada kadai san Halinsa.."Abdullahi yace"Kai Abu dai bai yi Dadi ba sam..Allah dai ya kyauta kai Mata Duk haka suke in kayi sake Shikenan Nima Tun Jiya ko mgana bana ma Hafsah saboda ta gama Batamin rai wlh.'"Nazifi yace"Ahaf..Ai na gayamaka Wlh in baka zama Masifan kanka da Gidanka ba Sai kafini zama Abun Tsausayi meya Faru ne Hala..? Abdullahi ya sauke Numfashi da kamar Bazai gayamai ba sai kuma ya fadamai Kadan Daga Cikin Abunda ya Faru Nazifi ya karkace kai kafin yace"Wlh kamin daidai...gwara ka mata haka ai da gangane tasan ai kace mata ta koma Gidan Mama akan Lokaci Salon Raini ne kawai sai an yi mgana su kwashe sukai Gida iyayensu su mara musu Baya Allah dama Gida ka aikata Kila achan tafi gane Kuranta.."Abdullahi yayi ma Nazifi wani kallo kafin yace"Kawai sai na aikata Gida saboda wannan karamin laifin..? Ina fa som matata bawai bana sonta bane kuma Itama tana sona tana kuma min biyayyah daidai gwargwado da kuma Gudun Bacin rai kawai na yarda Kuskure aka samu zan Hora ta kawai da irin Horona ammh ba mganar Turata Gida Mutumina Haba dai Iyayenta ba irin iyayen sakina bane suna da Dattako sosai ba zan iya wani Abun da zan Tozarta musu ya' ba gaskiya.."
Nazifi yace "Ai Shikenan Tunda kace Haka gani nayi Turasu gidan yafi Firgitasu da kuma su Dawo Cikin Hayyacinsu lokaci Daya.."Abdullahi yace'Naki din..? Kai Gida ka Tura sakina Duk da Irin Dibar albarkar Datake maka.? Nazifi yace"Ban taba Tura ta ba ammh zan Turata kwananan wlh.."Abdullahi ya saki Dariya kafin yace"Dan Rainin Hankali...Oh Shine ni kuma da matata bata taba Maidamin mgana sai na Turata gida ko..? Anki din toh.."Sai Nazifi ya maida mganar Dariya Sun Dade suna Hira kafin Nazifi yamai sallama ya tafi.
Da yammah da Abdullahi ya taso Daga wajen aiki Gidan Mama ya wuce yaci Tuwo Dawa miyar kubewa chan yayi sallar mangariba da Isha'i,Har kuma Lokacin Jidda bata Dawo ba Ran Abdullahi ya baci ya Shiga Fada Sosai Mama tana Bashi Hakuri kafin tace"Wlh yayansu na Kira Hauwa"u da kaina Nace mata kace ta Dawo gida sai kanwar uwar ta karbi wayar ta Rokeni na Bari gobe da safe zata Turota yanzu Dare yayi ne kaji yadda mukayi da ita Na dauka Tun safe zata Turota ammh har yanzu Shuru bata Dawo ba.."
Auwal na Zaune yana cin Tuwo yace"Mama bafa zata dawo ba wlh..Dama Yarinyar nan batajin mgana ta samu sake chan bamai gwabamata Dama ai bazata Dawo ba Wawiyar yarinya kawai.."Mariya na zaune tace"Kai ya Auwal kai fa Dan Zugi ne.."Da maficin gabansa ya Jefeta yana Fadin"Kimin Shuru wlh ko nayi kasa Kasa Dake yanzu nan.."Baki ta Tura tana kunkuni Dakatawa Yayi da Cin Abincin yana Fadin''Ammh Mama kina kallonta ko..? Wlh in ta kuskura ta Zageni saina mata Dukan Tsiyan sai ta manta Sunanta karyan Iskanci take ai Duk sune su Jidda marasa kunya.."Mama tace"Kai kuma dan Zafin Rai ba..ke Mariya kar in kara jin Bakinki anan wajem.."Tashi tayi Fuu ta Shige Uwar Dakin Mama Tana Kunkuni Auwal ya Rakata da Harara Abdullahi na Zaune yana Laluban Lambar wayar Mariya wacce Jiddan ta ari wayar Tatafi da ita, Daga ganinsa Ransa a Bace yake ya Hade Girar sama Data kasa Fuskarnan ba Fara"a ko kadan ko Ta kansu Auwal bai bi ba.
Ana Cikin hakane sai ga sallaman Jidda Ta Shigo Dakin Mama da Ledan kaya Riki Riki,Tana sanye da Doguwar Rigar atamfa mai launin ja Harda mayafinta karami ta Sagaloshi ta Wuyanta ta Shigo da Fara"arta tana Fadin"Mama mama..Anty Mariya na Da..."Mganarta ta makalene ganin Abdullahi zaune kusa da Mama sun Hada Ido Hudu Dashi kawai sai Jikinta ya kama Rawa sanin Hali Kauda kanta tayi Gefe daya tana kallon Auwal dake auna mata Harara Mama ta Kalleta tana Fadin"Jidda sai yanzu..? Na dauka tun safe innar taki zata Turoki Ga yayanku nan Tun jiya yake Fada rashin Dawowarki Wlh.."
Jidda Ta Bude baki tana Fadin"Allah mama zan taho Anty Lariyace tace na Tsaya zan karbi sa..."!Ki koma Inda kika Fito sai su Rikeki achan.."Mganar Abdullahi ta katseta wanda ya Fada Cikim kaushi da Fushi Lokaci Daya yana mikewa.
Jin Haka yasa Jidda ta sadda kai kasa Tana Fadin"Don Allah ya Abdullahi kayi Hakuri bazan kara ba.."Wani tsawa ya Dakamata yana Fadin"Yimin Shuru..In kika kara mgana anan wajen sai nazo na Tattaki mara kunya..Tun jiya da kika Fita Daga Gidanan sai yanzu kike Dawowa kuma Saboda Rashin kunya da wani Ficicicin mayafin wanda Dashi da Babu Duk Daya Don kaniyarki Shi kika saba sakawa anan..? Nace shi kika saba sakawa anan gidan..?
Ya karishe Fada Cikin Tsawa Da Sauri Taja baya kafin tace"A"a yaya..Bazan kara ba..'Tafada kamar tayi kuka yatsa ya Nuna ta Dashi kafin yace"Wannan ne na karshe da zan kara zuwa Gidan ace min wai kin tafi wani yawon wofi mara amfani in ma Fitan ta kama Dole akirani awaya a sanar dani in na amince aje in ban amince ba kowacce ta zauna agida bana son Shashanci banza da Yawo mara amfani kinji ko baki ji ba..? Da kai ta amsa kafin tace"Naji yaya.."Bai tsaya wata mgana ba kawai ya Wuce ta gabanta taja baya da Sauri sai da ya saka Takalminsa kana yace"Mama na tafi sai Allah ya kaimu.."
Mama tace"Allah taahemu lafiya ka gaida Hafsah da Megidana.."Bai amsa ba ya Fice Daga Gidan Cikin Fushi Auwal Dake zaune ya Saki Dariyar da Dama yake Riketa Tun dazu Jidda da Hawaye suka kawomata ta kalleshi kafin ta kalli Mama tana Fadin"Mama kinganshi ko..? ta karishe fada kamar zatayi kuka Mama tace"ina Ruwanki kuma Dashi..Kyalesa Hauwa"u na yakinan manta da wannan Babban gwabon.."Tafada tana yafito da Hannu Auwal kuwa sai kara tsintsira Dariya yake mariya na Ciki tana jindu Taki Fitowa Gudun kada Ahada da ita acikin Ranta kuwa Fadi take Anty Hafsah na Hakuri Wlh.
*Assalamu Alaikaum my Follow pipu's Hop kuna Lafiya..? Ya kokari kuma..? Allah ya taimake mu Ameen Ina son Don Allah nayi muku wani karin Bayanine kan Wannan Littafin Dana ke kam Rubuta muku mai Suna Masifaffan Namiji..! Ina so ku Sani Dan adam Tara yake bai Cika goma ba Duk zamowarka gwani akwai inda zaka kuskusre Allah ne kadai ke iya yin Dadai kuma yayi Abun ya zama Daidai akoda yaushe Shi kadai ne baya kuskure ammh mu mutane akoda yaushe Cikin kuskure muke,Toh irin wannan Kuskuran nayi Wajen Da zan Rubuta Shekarun Abdullahi maimakon na Saka 35 sai na saka 32 kumin afuwa Shekarun Abdullahi 35,yayi Aure yana da Shekara 28 ne,Hajara Amira kenan Tana da Shekara 6, ne Yayinda Amir Usman kenan yana da Shekara 3da wasu wattani kenan,a lissafi Suna da Shekara 7 da Aure kenan Tsakaninsa da Hafsah, sai kuskure na Biyu da muka samu Shine wajen da nace Mahaifin Abdullahi ya saki Hajara ta wayar hannu,Toh an samu akasi ne,lokacin wayar Hannu bata Fito ba Shekara Talatin da wani Abu baya Sai mu barshi a Ya Tura mata sakon Sakin ne ta Tarkada har garinsu gusau,Ina Fatan awannan Bayanin nawa kun Fahimce ni..? Ina godiya Sosai Gareku,na Tabbata ba kuna Karatun littafin Janafty da baki bane kawai kuna Hadawa da Duka Zuciyarku Shiyasa kuka gano wannan kuskuran da aka samu,kuma Hakan ya Faru ne saboda karancin Lokacin da nake Dashi,in nayi Typing bana samun Lokaci da zan zauna na Maimaita har nayi Editing dinsa Ballatana in naga kuskure na gyara ammh Insha Allahu zan yi Kokarin na Dinga Bin baya ina Dubawa...Ina Matukar godiya gareku Allah ya bar zumunci Masoyan kwarai..Allah ka barmu da Masoyanmu Duniya da Lahira...Ameen ya Allah...*🙏
*Janafty..*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..!*
*007*
"Yadda ya Fita Daga Gidan Mama ransa bace haka yaje ma Hafsah Cikin wannan Fushin da Bacin Ran,Koda yashigo Tana Zaune afalo Su Amira suna Homewark dinsu yau batayi Girki Da Daddare ba Sauran Abincin Rana ne ya Ragu basu Cinye ba sai Sauran kazan Jiya Wanda Tunda taga megidan bai kula ba tasan bazai kula ba,Kuma koda ma Tayi abincin baya ci ballatana ma yabi ta kanta.
Kansa Tsaye ya Shigo Falon ko Takalmin kafarsa bai Cire ba,Sawun Cikinsa Dasu ya Shigo Har Tsakiyar Falon su Amira suka Tashi suka Rikesa suna masa Oyoyo,Kan Amira ya Dafa Shi kuma Amir ya Dagasa sama yana mai waasa,Hafsah Dake gefe ta mike tana Fadin"Sannu da zuwa.."Dama bata san ran zai amsa ba,kuma bai amsa ba Din yaja Ya"yansa Zuwa Ciki,Komawa tayi ta zauna kan Daya Daga Cikim Kujerun Falon Ta Zabga Tagumi kawai Domin Abun na Abdullahi ya Fara isarta.
Chan sai gasu sun Fito da Robobin Ice cream a Hannunsu Kowa Dai dai,Dama taga ya Shiga da wata Bakar Leda,Suka zo suna Nuna mata tace tagani susha abunsu sun zauna suna Cikin Sha sai Fada ya kaure Tsakanin Amir da Amira ta Tabamai Ice Cream dinshi Shi kuma ya Cika Fitina ya Fara Dukanta Hafsah na zaune ta Dakamai Tsawa yaki Sauraranta kawai sai tace"Amira in ya kara Dukanki ki Mareshi Tunda Bayajin mgana.."
Ita kuma Amira yana kara Dukanta ta saka Hannu ta makeshi ya kara Sakin kuka Ashe Duk Abdullahi na Ciki yana Jinsu Bai Fito ba sai da yaji Amiran ta Daki Amir din kana ya Fito da Sauri Cikin Bacin rai Har ya Sauya kaya ya saka Dogon wando baki da kuma Wata karamar Riga Fara,Kirere ya tsaya gaban Hafsah yana Fadin"Waya Dake shi..?
Hafsah ta Dago ta kalleshi kafin tace"Dukan Amira yake yi na Hanashi yakiji ni kuma nace in ya kara Tabata ta Dakeshi.."Tsayawa kawai yayi yana mata wani Irin kallo wanda sai da Hafsah ta sadda kanta kasa Tana wasa da Zoben Hannunta,Bai mata mgana ba illah Amir Daya Dauka yana Lallashinsa kafin ya kalli Amira yana Fadin"Mamana karki kara Dukansa kinji ko..?.
Kai ta Gyadamai Cikin Taushin Murya yace"Komai zai miki kar ki yarda wani ya kara cewa ki Dakesa ki Dakesa Kinji ko..? Kaninki ne kece Babba Watarana sai Labari.."yafada yana Hararan Hafsah wacce Tasan da ita yake Bata tankamai ba yaja hannun Amira Zuwa Ciki suka Barta nan da kallo ta Bisu tana Sauke ajiyar Zuciya.
Ranar dai su Amira wajen Abdullahi suka kwana ita kadai ta kwana Cikin Daki Abun yana Damunta ammh bata da yadda zatayi Tunda Ko zatayi mganan Duniyan nan Abdullahi baya Tankamata gashi ita kuma Bata da Dabi"ar Gayama wani Sirrin Mijinta balle ta gayama wani ko Zai bata Shawara,Subai'a ma ta Kirata tana Tambayanta Komai Lafiya ita da Abdullahi sai kawai tace mata komai ya wuce saboda bata Cika son Fadin wani Abu Daya Dangancin Auranta ba.
*****
Cikin wannan zaman Doya da Manjan Tsakanin Abdullahi da Hafsah wanda tayi iya yinta Domin Taga komai ya Daidaita ammh Abu ya gagara,sai kawai ta Zubama Sarautar Allah ido ta barma Allah komai.
Yau Takama Jumma"a ce,Bayan su Amira sun Dawo makaranta Mai mashin dinsu ya sake kwasansu zuwa Gidan Mama tare da kayansu da kuma Uniform din Haddarsu ta asabar da Lahadi Tunda chan Abdullahi ya sakasu Ranar jumma"a suke Tafiya chan Gidan Mama sai Lahadi kuma da Daddare Abdullahi ke zuwa ya Dawo Dasu.
Tun Bayan Tafiyarsu Gidan yayi ma Hafsah Shuru sai kawai ta Tsiri wankin kayan yaran da kuma nata,Sai Gabda mangariba ta gama tana gamawa ta Fada wanka Jikinta yayi mata wani Nauyi,bayan ta gama wanka sai ta Dauro alwala ta Fito ta Shafa mai ta saka Riga da Sikat na wani Boyel wanda Abdullahi ya Dinkamatashi Lokacin da zasu kaduna Zanniratu ta Haihu,Akamata Dinkin Buba,kayan sun mata kyau alokacin Haka Abdullahi ya Dinga yaba kyan Datayi Shiyasa ta sakasu yau zata jawo Ra"ayinsa Batayi kwalliya ba ta bari sai ta Idar da sallah Tukunnah.
Ta Shinfida Sallayar ta Tada sallar Raka"ar Farko Taji wayarta Dake Falo ta Dauki Ringing,Tana sallah Tana ji ana ta Kiran Wayar nata Haka Kurum taji gabanta ya Fadi Dakyar ta salallame sallar ta Fito Falo da Sauri Saman Daya Daga Cikin kujerun Falon ta ijiye wayar Dazu da sukayi mgana da Umman Sadiq Daga gusau,Da sauri ta Dauka Ganin Ammi ce ta Kirata Har sau Biyar yasa Jikinta Haka Kurum ya Fara rawa Ballatana ma Tun Dazu take Kiran layin Daddy bata Shiga Daga Baya kuma sai Taji wayar tana kashe Ta kuma Kira Ammi Har sau Hudu bata Dauka ba Tun Lokacin Jikinta ya bata ba lafiya.
Kiran tabi baya sai da wayar ta kusa katse kanta kana Ammi ta Daga Kiran Cikin Sanyin Murya tace"Autana ina kika Shiga kika bar wayarki ina ta Kiranki Shuru..? Yadda Hafsah taji Muryan Ammi yasa Kafarta ta Fara rawa Da sauri ta nemi gefen Kujera ta zauna Tana Fadin"Ammi kin kirani ina sallah ne..? Lafiya naji muryanki wani iri..? Ina Daddy nayi ta Kiran wayarsa Tana kashe kema na Kiraki baki Daga ba? Wani Abu ya Faru ne..?
Ammi tace"Auta irin wannan Jerin Tambayoyi wanne kike so na Fara amsa miki..? Hafsah tace"Duka Ammi..."Da Sauri kamar ta kagara taji ko lafiya ajiyar Rai Ammi ta Sauke kafin tace"Dama ba wani abu ne,Daddynku ne ba lafiya Tun Jiya Da Daddare Hawan Jininsa ya Tashi Haka muka kwana da Safe muka tafi asibiti a almadina muka Wuni yau sai yanzu muka Dawo Gida.."Da sauri Hafsah ta mike tana Fadin"Innalillahi Ammi Shine baki kirani kin gayamin ba.."Tafada Cikin matsanancin Damuwa.
Ammi tace"Shi ya Hana yace kar na Kiraku keda Hadiza Yasan ku da Rudewa yanzu hankalinku zai Tashi,Jikin da Sauki Gashi har mun Daawo Gida,lokacin muna asibitin ne ban Daga Kiranki ba Bayan mun Dawo ne na kiraki baki Daga ba sai na Kira Mijinki yanzu muka gama mgana Dashi ma.."Hafsah tace"Wayyo Daddy..Ammina ya Jikinsa..? Yaji Ssuki..? Yana iya cin Abinci..?ko barci yake ji..?
Ammi Tayi Dariya kafin tace"Kai Autana Irin wadanan Tambayoyin fa..? Ki bari in kikazo kya gani Abdullahi yacemin yana Hanyar zuwa Gida zai Daukoki ku Taho tare.."Hafsah tace"Ammi ki gaida Daddy sai munzo..Don Allah ki bashi abinci ya koshi.."Ammi tace"Ohoni Da ke da Hadiza bansan wanne yafi wani Son Daddyn nan ba itama dana Kirata Fadi take Ammi yaci abinci..? Yayi barci..? Ya jikinsa..? Ki bashi abinci karki barshi da yunwa hala kunfi son Mijina ne da kuma yadda zan kula Dashi.."?Ammi ta karishe Fada Cikin Zolaya tana Dariya ganin yadda Mahaifinsu Hafsah ke ta Dariya Shida kaninsa Alhaji Mustapha..."
Tura Baki Hafsah tayi kafin tace"Mudai mun fi Son Daddynmu.."Ammi tace"Ehe lalle Bari kizo sai Daddyn naku ya zaba ko ni ko kuma ku.."Daga haka ta yanke Kiran tana Mita Ita kadai Alhaji Hamza Dake Zaune kan Gado acikin Dakinsa zama irin na marasa Lafiya Bayansa Kaninss Alhaji mustapha ya karamai Filo,Farin Dattijo ne mai kima da Dattako Dan Kimanin Shekaru 63 aduniya Fuskarsa tana Cike ne da yalwar Fara"a da Haiba.
Cikin Muryan Ciwo yace"Banda Abunki Zinariya wazai Hada mata da ya"ya..? Kowa matssyinshi Dabam ko Mustapha..? Alhaji Mustapha na Dariya yace"Haba ina ma za"a Hada ai sai ana son mata ake son ya"yanta.."Mirmishi tayi kafin tace"Allah Baban Abdul Iyayin yaran nashi ne ya Isheni kowacce ta Isheni da Ammi Don Allah ki ba Daddy abinci ya koshi.."Tafada Tana kwaikwayon Muryansu Dariya ta kama Alhaji Mustapha da Alhaji Hamza ganin yadda Ammin tayi.
Hafsah kuwa Bayan Ammi ta kashe wayarta sai ta Sulale kan Kujera ta zauna Tsausayin Daddynta ya Isheta sai ga Hawaye Sharr sun zubomata ta Tuna Shekaranjiya da Damuwa ta mata yawa Shi ta Kira suka Sha Hira yana ta Zoyalarta Dayake sunan Marigayiya Ayya aka samata Mahaifiyarsa Shiyasa yafi sonta daji da ita komai ya samu Mamana Shiyasa Tun tana Gida akwai Shakuwa Sosai a tsakaninsu Wani Lokacin Ammi tayi ta Fadan Irin Koda yaushe yana Tare da ita tana fadin watarana Aure Hafsah zatayi ta barshi Tunda Dukansu mata ne sai yace ba komai mijinta zai Dinga kawota ina ganinta Domin zan gayamai matarsa Ba irin Sauran mata ne bane, Autan Hamza ne kuma Uwa take garesa,In ya Fadi haka Daga Ammin har Hafsah dariya sukemai aikuwa Lokacin da Hafsah ta kawo Abdullahi sai da Alhaji Hamza ya gayamai Ya kular mai da Mamansa da kuma Autansa Hafsatu.
Tana Cikin wannan Tunanin ne taji Sallaman Abdullahi acikin Falon Tayi Zurfi Cikin Tunani batama Ji Shigowarsa ba,Dago ido Tayi ta kallesa yana Sanye Cikin wata Blue din Shadda mai kyau da yarari da kuma Tsada Riga da wando Dinkin zamani kafarsa na sanye Cikin Budadden Takalmi Haka Kansa sanye Cikin Hula kube mai kyau da Tsari.
Ganin Fuskar Hafsah tana Hawaye sai da gabansa ya Fadi Dayake aikwai wuta shiyasa ya samu Damar ganin Hawayenta Cikin mamaki yama manta da Fadansu da Fushinsa yace"Hafsah lafiya kike kuka..? Jin Haka yasa Zuciyarta ta kara Rauni kamar wacce aka ce Daddyn nata ya mutu ne kawai ta mike ta isa ga Abdullahi sai Ji yayi kawai ta Fada Jikinsa ta Rumgumeshi Lokaci Daya tana sakin mai kuka.
Da Sauri ya Tallabeta jin yadda ta Sakarmai Jikinta Hannuwansa Shima ya saka Duka Biyun ya Zagayen kugunta Dashi yana Sauraran Kukanta Cikin Sanyin Murya yace"Wannan kukan fa..? Wani Abu ne ya faru..? Cikin Kuka tace"Abban Amira Daddy ba lafiya yau Ammi tace ma a asibiti suka wuni.."Tafada tana kara Shigewa Kirjinsa.
Ajiyar Zuciya ya Sauke jin Abunda tace da Farko Hankalinsa ne ya tashi yana tsoron ko wani Abu ne ya Faru Bayanta ya Shiga Bubbugawa alaman Lallashi yana Fadin"Shiii..Ya isa...Meye Abun kuka kuma..? Munyi mgana da Ammi tace min da sauki kuma ma yanzu dawowar danayi Domin na Dauke ki muje mu Dubashi ne.."
Ya fada Cikin Sigar lallashi Saurin Dagowa Hafsah tayi Tana Fadin"Yauwa..Toh muje.."Tafada Cikin Rudewa kallonta yayi kafin yace"Haka zamu tafi Fuskarki Duk Hawaye..? Jin haka yasa ta kwashi Gudu zuwa Daki ta Shiga Tailet ta wanko Fuskarta ta Fito Falo ta Dauki wayarta tana Fadin"Na wanke Hawayen Abban Amira...'"yana tsaye yana kallonta Cikin mamakin ganin kamar bata Cikin Natsuwarta ganin haka yasa yace"Dauko key din Gidan.."
Da sauri ta koma Daki ta Dauko ta mikamai ya karba suka Fito Daga Dakin Shi ya kulle Dakin ya Hada Harda Kitchen kana suka Fita waje dama bai Shigo da Mashin dinsa Ciki ba Tana tsaye ya saka key ya Kulle Gidan kana ya Hau mashin din yamata key ya karkatamata yana Fadin"Ki Rikeni in zaki hau Domin naga har yau baki kware wajen Hawa mashin ba Duk da ita mijinki ya mallaka.."Bata ma Tsaya Sauraransa ba,kawai ta Dafashi da Hannuwanta Duka Biyu ta Haye Mashin Din yaja suka Fara Tafiya Sun Hau Titi kenan iska ya Fara kadawa Cikin wani yanayi wanda ke saka Masoya Cikin Wani Shauki wanda su kadai ke iya ganin irin yanayin.
Jim wannan iskar yasa kawai Hafsah ta kwanto Jikin Abdullahi ta Nannadeshi ta Saka Hannuwanta Duka Biyu ta zagayo Dasu ta Cikinsa lokaci Daya ta maida kanta Bisa Bayansa ta kwanta tana maida Numfashi Gabadayansu atare Suka saki Numfashi saboda yadda Jikinsu ya Hadu waje Daya Cikin wani irin kasala da wani irin Soyayyah wacce Sai ma"abota Soyayyah da kuma Kauna kadai ke iya ganewa Abdullahi ya lumshe ido ya Bude Cikin sanyin murya yace"Hausi kina so ki sakamu muyi Hatsari ne..?
Yafada Cikin Wata murya mai Cike da Shauki,Cikin Shagwaba Hafsah tace"sanyi nake ji toh..."Tafada Cikin Tabara da Sangarta,Kafin ta kara Fadin"Ko in tashi ne..? Tafada tana kokarin Sakinshi da Sauri yace"Kwanta abunki wazai Hana Hafsatu Kwanciya Jikin Abdullahinta.."kalamansa sun sanyayamata Rai Sosai har bata san Sadda tayi mirmishi ba kafin ta Furta.."Allah nagode maka Daka Saka Mijina ya yafemin Laifina..."
Jin haka yasa kawai sai ya dan Murmusa sai Lokacin ma ya Tuna da Suna Fada,Har suka kai Tudun wada Layin Bare bari Gidansu Hafsah ba wanda ya kara mgana sai dai zuciyoyinsu Dake Bugawa Lokaci Daya Har Cikin Haraban Tamgamemen Gidansu Hafsah Abdullahi ya Shiga da mashin dinsa Gidansu Hafsah Gidane Daya amsa Sunansa Gida mai kyau da Tsari,Haraban Gidan Motocin Alhaji Hamza wajen Guda Hudu sai ta Ammi Guda Daya hudu kenan.
Karkatamata Abdullahi yayi ya taimaka mata ta Sauka ta tsaya ta Jirashi har ya kafa mashin din,Sai da suka gaisa da Baba megadi kana suka Nufi Cikin Gida afalon Gidan babu kowa Hafsah ta kalli Abdullahi tana Fadin"kila Ammi tana Shashen Daddy bari na Shiga na gaya mata.."kai ya gyada mata Kafin ta Wuce Wani Shashe Dake Cikin Falon Shi kuma sai ya samu Daya Daga Cikin kujerun Falon ya zauna Chan sai ga yar aikin Ammi ta Shigo Falon ganin Abdullahi yasa ta rankwafa tana gaisheshi ya amsa cikin kauda kai,Ruwa ta kawomai da Lemo ta ijiye Dayake a koshe yake bai ko kalli Barayin ba.
Hafsah kuwa da Gudunta ta karisa Shiga Dakin Daddynta Tana Fadin"Daddy...! Daddy...! Take Fada Lokaci Daya tana Shiga Bedroom din na Daddy Ammi Dake Tsaye Gefen Alhaji Hamza Tana Bashi Fruit,Alhaji mustapah kuma na Gefensa zaume suna Hira Sai ga Hafsah ta Shigo kamar Daga sama Tana Kiran Daddynta.
Alhaji Hamza ya Dago kansa yana Fadin"Gani nan Mamana..."Yake Fada yana miko mata Hannu Da Sauri ta karisa Gabansa Har tana Ture Ammi Wacce ta sake baki Tana kallonta Kusa Dashi ta zauna ta Riko Hannunsa tana Fadin"Allah Sarki Daddyna..Duk ka Rame sannu.."Take Fada Hawaye suna gangaro mata Alhaji Hamza ya Saka Hannu yana Sharema Hafsah Hawaye Lokaci Daya yana Fadin"Toh kuma miye na kuka Mamana..? Baki ganni ba naji Sauki Sosai nama warke har Gudu zan iya yi..'"
Yafada Cikin Zolaya Mirmishin Hafsah tayi kafin ta yada kanta Gefen kafadarsa Tana Fadin"Allah Baka lafiya Daddyna."yana Mirmishi yana Shafa kanta yana Fadin"Ameen Ameen Mamana..."Ammi Dake Tsaye tatabe baki Tana Fadin"Masu Daddy manya..Shi kadai kika gani..? Ga Babanki mustapha zaune kin Wucesa ko..?
Sai alokacin Hafsah ta ga Alhaji Mustapha,Kunya ta kamata ta tashi Tsaye tana Rufe Fuska,Tana Fadin"La Abba Wlh ban ganka ba..Ina Wuni ya gida..? Yasu Mama maimuna Da Hajiya gaje..? Yana Dariya yace"Ina fa zaki ganni Mama ai sai kin gama da Daddyn naki..lafiya kalau ya Megidan na ki..?Hafsah tace"Lafiya lau Abba tare ma muke Dashi..".
Baki Sake suke Kallonta Ammi tace"Tare kuka zo Dashi..? Toh kika barsa a ina..? Hafsah tace"Yana Falo nace bari na Shiga na gayamiki.."Salati Ammi ta saki kafin ta sakarma Hafsah Dakuwa Tana Fadin"Kinci Gidanku Hafsah yanzu Fisabillahi Kin zo Tare da mutum ammh ki barsa afalo ke ki Shigo Ciki..? mintinki nawa Da Shigowa..?
Tura Baki Hafsah tayi kafin tace"Toh ba mantawa nayi ba..Na Zagu naga Daddyna.."Ammi ta Zabgamata Harara Alhaji Hamza Ya kalli Ammi yana Fadin"Ki mata ahankali mana Baki ga yarinya bace..Mamata maza kije ki Shigo Dashi Abdullahi ai dan Gida ne.."Ya fada da Sigar lallashi Baba Mustpha yace"Yaya wa kenan yarinya..? Ya"yanta Biyu fa..?
Alhaji Hamza yace"Ah to ko ko ya"yanta goma ne Mamata ayarinya nake Daukanta Ko Zinaru a yarinya nake Daukanta Ballatana Mamana.."Ammi ta Saki Mirmishi kawai Baba Mustapha din ma Dariya yayi Hafsah ma sai da ta Dara kana ta Fice Daga Bedroom din.
Zaune ta iske Abdullahi yana ta latswa Wayarsa Zuwanta yasa ya Dago yana kallonta Cikin kunya tace"Kayi Hakuri Abban Amira ganin Daddy yasa na manta Dakai afalo.."Mikewa yayi yana Fadin"Bakomai..Tunda Daddynmu ne.."Yafada Cikin Zoyala Gaba ta Shige Ya Bita abaya Har Zuwa Shashen Daddy.
Da Sallama Abdullahi ya Shiga Bedroom din Daddy,Hafsah na gaba yana Binta abaya Har gaban Gadon Daddy,Ammi ya Fara gaisawar Bayan ya Duka har kasa Ammi ta amsa tana Fadin"Kayi Hakuri Abdullahi Shirmen matarkace maimakon Tun Shigowarta tace tare kuke bata ce ba,Sai da ta gama Hira da Daddynta,Sai ma da Baban Abdul ya tambayeka ne kana tace Tare kuka zo.."
Abdullahi ya Dukar Dakai Kawai yana Mirmishi Daddy yace"Kedai Zinariya kina son Rura wata Wutar..Abdullahi da Mamana Duka Daya ne.."Abdullahi yayi mirmishi kafin ya Dago kansa yana Fadin"Daddy ina Wuni ya karfin Jikin..?
Daddy ya miko Hannu yana Fadin"Ya ka nan Abdullahi...Kazo ka zauna kusa dani kamar yadda Mamana keyi Duka Daya na Daukeku.."Baba Mustpha yace"Tabbas..Wannan haka yake.
"Abdullahi ya mike yana gaida Baba Mustpaha ya amsa yana Tambayansa su Amira Ammi tace"Suna Gidan mama gobe suna da Hadda.."Baba Mustpha yace"masha Allah..."
Kusa da Daddy Abdullahi ya Zauna Daddy ya Riko Hannunsa yana Fadin"Abdullahi ya gida..? Ina Matata take ne..? Kardai Taji Tsoron Fadan Zinariyata taki Dawowa.."Abdullahi na Dariya yace"Haba Daddy ai ita bata Tsoro Amaryan taka Suna gidan mama gobe suna da Hadda,ammh kasha kuruminka Zata zo ta Gaisheka da kayan Dubiya.."Daddy ya saki Mirmishi yana Fadin"Yauwa yanzu naji Batu."Ammi dai na gefe tana Mirmishi ita da Hafsah Nan Daddy suka kara gaisawa da Abdullahi sosai ya masa ya Jiki yace da Sauki,Shi kuma yana ta Tambayansa Wajen aikinsa yana Bashi amsa.
Ammi da Hafsah fitowa sukayi Falo suka barsu suna Hira,Ferfesun kayan Ciki Ammi ta Tasama Hafsah tana ci suna Hira Har Hadiza ta Kira waya sukayi mgana da Hafsah,Tace gobe itama tana Tafe Sai wajen goma da wani Abu Kana su Hafsah suka Bar Gidan Shima sai da Daddy yace su tashi su Tafi Gida Dare yayi,Baba Mustpah ya Rigasu Tafiya Kula Guda Ammi ta Cikama Hafsah kula da Ferfesun kayan Ciki tace in sunje Gida suci Ita da Abdullahi Daddy ma Fadi yake Zinariya kin Zuba musu kuwa..? Ki zuba musu su Tafi Dashi mana Ammi Da tagaji tace mai"Wai Shin ko zaka tashi da kanka ne ka Zuba musu..? Sai yayi Dariya yace"Kedai zaki Zubamusu Zinariya.."Daga Abdullahi har Hafsah Dariya suka saka inda sabo Abdullahi ya saba ganin Diramar Ammi da Daddy kan ya"yansu Domin Shima kamar Dan Gida ne Shiyasa ko Nazifi yace Wani Abu kan iyaye masu kudi sai ya karyata Domin iyayen Hafsah Mutane masu Dattako ba irin irin iyayen Sakina ba
Kamar Tafiyar farko wannan karon ma kara Nademai Tayi Suna Tafe iska na Hurasu Cikin wani Shauki da Muradi mai Girma.
*NOTE:Labarin Masifaffan Namiji Labari ne da zai Taba Bangarori Da yawa,Labarine da zai yi Duba zuwa ga Abubuwan Dake Faruwa a gidajen Auranmu, Labari ne da zai Dubi Bangaran zamantakewarmu Labarine da zai Dubu bangaran Rayuwar mu ta yau da kullum,Labari ne da zai yi Duba kan Yadda Iyaye da Yayyi suke da Rawa mai girma wajen Tarbiya da kuma Tsaron ya"yansu....Fatana Kada ku gaji ko kuma ku nuna gazawarku wajen Comments,Sharhi,Likes,Vote,Ni kuma na ijiye muku alkawarin Samun Daily Update Insha Allahu ..*
*Shakira...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Dedicated To:My Habibaty❤️Aisha Abdullahi Idris..*!
*Jinjina Tare da godiya mai yawa garesku Masu Sharhi,Hakika naga Soyayyarku ga wannan labarin na kuma ji Dadi,Masoyan Audu how far?🤣Team Hafsatu..? Abdullahi na godiya da Caccakarsa da akayi tayi yace na Fada muku kowacce ta zauni Gidan Mijinta in Budurwace itama ta zauna agida banda Fitar Rashin Dalili🤣My Wattpadian Fans..? Abdullahi na kai gaisuwa fa🖐️yace ku daina sa mai ido Shi da matarsa yafi kowa iko a kanta...Allah ya bar zumunci Ameen So So So mara iyaka..*
*008*
"Ahaka suka isa Gida,ita ta Sauka Ta Bude Gidan Tana Rike da karamar Kular da Ammi ta saka musu Ferfesun kayan Cikin,Shi kuma ya Shiga da Mashin din Cikin Gida.
Tare suka Bude Dakin Suka Shiga,Hafsah ta Bude Kitchen ta Dauko Filet tazo ta Zubama Abdullahi yaci kadan sunayi suna Hira Jefi Jefi Duk game da Ciwon Daddy ne,Bayan ya gama ya Shiga Toilet yayi wanka yau dai yayi wanka da Ruwan Zafin Data saka a Kittle Dashi yayi wanka Bayan ya Fito itama Hafsah ta Shiga Tare sukayi Sallar Isha"i Shi yaja musu Jam"i.
Bayan Sun kamallah sukayi Shirin kwanciya Kowannensu ya Saka kayan Barci Abdullahi ya saka Riga da wando na Pjm ita kuma Hafsah ta Saka Wata Rigar Barci Mai kalan pick,wacce iyakarta Gwiwa Kuma SharaShara ce Ana ganin komai na Jikinta wanda pant kadai ta iya sakawa.
Abdullahi na kwance yana Kallon Hafsah Dake gaban madubi Tana Fesa Turare,ya Daga kansa yana Fadin"Ni kam Hausina yau kuma Audin naki kike jama Aji..?
Hafsah ta saki Mirmishi kafin tace"Wace Hausi ta jama Mai Babban Suna aji..? Ganinan Tafe gareka Mijina.."Tafada Cikin wani Shauki da Soyayyah Mirmishi ya sakarmata Hanyar Fita Falo ta Nufa ya Dago yana Fadin"Ina kuma Zaki..?
Hafsah tace"Kicthen zan Rufe sai na Kashemana wuta na Rufe Kofa..."Da Sauri ya tashi zaune Lokaci Daya ya Sauko Daga kan Gadon yana Fadin"Karki Fita ahaka..Bari ni naje na kulle ina key din..? Hafsah tace"Yana kan Fridge afalo.."Fita yayi ta Bishi da kallo acikin Ranta tana addu"an Godiya ga Allah Daya Saussauta Fushin Abdullahi akanta.
Kitchen din ya Fara kullewa kana ya Shigo Falon ya Kashe kwan Waje kana ya Kashe na Falon ya Rufe Kofar da key,kana ya koma Cikin Bedroom din ya iske Hafsah har ta kwanta Taja Blanket,ta Rufe Jikinta Dashi Mirmishi ya saki kafin ya Kashe Lantarkin Dakin ya hayo Gadon Cikin Bargon Ya Riko Hafsah Lokaci Daya ya sakata acikin Jikinsa,Atare suka saki ajiyar Zuciya Domin Dukkansu sunyi kewar Jikin Juna.
Yana ta Bayanta ne ya saka Kanshi Cikin Wuyanta yana Hura mata iska Cikin wani Salo Zillewa tayi Tana kamkame Hannuwansa,Cikin Wata irin Murya,tace"Abban Amirah...!
Taja sunan cikin wani yanayi Kamar mai Rada Cikin wani Salo kuma Cikin Shakewar murya kansa na Cikin Wuyanta Yana Fadin"Hmm...Uhm...!Hafsah ta Juyo da Kanta Suna kallon Juna Lumshe ido yayi kafin ya kara Budewa Cikin Wani irin yanayi mai kama da Sha"awa yace"Uhm ina Jinki..." Menene..?
Yafada yana Kara Tusa kansa Cikin Kirjinta Hannuwanta ta Zagaya abayansa Tana Shafashi kafin ta Fara mgana"Don Allah kayi Hakuri Bisa Duka Laifin Dana aikata maka...Wlh bada Son Raina bane Abban Amira ka yafemin...."!Ta karishe Fada kamar zata saka kuka Kamkameta yayi Cikin Sakin Numfashi kafin yace"Ya isa...!yake Fada lokaci Daya yana Yawo da Hannuwansa a Dogin Wuyanta.
Cikin Muryan Rauni Hafsah tace"Kana Fushi dani Abban Amira...Ka sakani ku..."Shiii..."!Abdullahi yace mata Lokaci Daya yana Dora Bakinsa saman Bakinta ya Sumbata kafin ya Dago kansa yana kallon Cikin kwayan Idanuwanta Da dan Hasken Farin Watan Daya ke Shigowa Ta Cikin Labulen Window Dake Bude.
Hannu ya Saka yana Shafa Fuskarta kafin yace"Kinsan meyasa nayi miki wannan Hukuncin..? Bai bata Zarafin mgana ba ya Cigaba da Fadin"Saboda na nuna miki kuskusranki,Kuma Abu mai Girma mafi Muhimmanci Shine Bana son Watarana ki Raina ni ko kuma Watarana Na zama nine a kasanki bana son awayi gari Watarana nagaya agidana kuma aki amfani Dashi Bana so ki Rainani Hafsatu Shiyasa wani Lokacin zaki ga na koma Miki Masiffan Namiji ba Laifina bane kema Ba naki bane kawai bana son Watarana ki zama ina Fada kina Fada ko kuma in Bada Umrni ya zama abun Banza..."Yafada Cikin Wani Raunin Murya
Hafsah tamai kuri da ido Kafin ta Murmusa Hannunsa Dake yawo saman Fuskarta ta Damke tana Fadin"Taya Hafsatu zata Raina Gwarzon maza kamar Abdullahi..?Taya kake tsamamin Zan iya Raina ka..? Kana Tunanin akwai Watarana da zata zo naji kai ba Shugaba na bane..? Ko kana Tunanin irin Tarbiyan Dasu Ammi suka Bani kenan..?Ta karishe Fada Cikin Sanyin Murya.
Rumgumeta yayi yana Fadin"Ko Daya bana Tamtama ga Tarbiyanki kuma Bana ja da cewa ke macece ta gari..Kawai dai bazan iya sakin Jiki bane..Sai dai kawai ki kara Hakuri wani Lokacin ina da Fushi da Kuma Zuciya.."Hafsah ta Kara kamkameshi Tana Fadin"Bakomai Mijina...Ina Sonka kuma zan Cigaba da zama Dakai a yadda kake...Ina mai Tabbatar maka Ni Hafsah bazan Taba Raina ka ba koda yaushe kai Shugabane akan Hafsah.."Tana Rufe baki Taji ya Rufe bakinta Danashi Ya fara Kissing dinta,itama sai ta Tallabe kanshi Tana taimakamai suna Kissing din Juna Cikin Fitan Hayyaci Lokaci Daya kuma Hannayensu na kara kaina Cikin na juna,Chan kuma Abdullahi ya Zuro Hannu yaja musu Bargo har kansu sai dai kawai naga sun Dungule waje Daya Suna Cigaba da Bama Junansu da Jikinsu hakkinsu......
****
Haka suka kwana Cikin Farinciki da Annushuwa,Sun kwana Suna Raya wannan Daran mai Cike da Soyayyah da Muradi mai Girma,wanda suka sakashi Cikin Darare masu matukar albarka da Alheri da Tarihi acikin Dareren da Suka gudana acikin Tarihin Auransu.
Wuni Sukayi Ranar Asabar agidan Suna Shan Soyayyarsu Abdullahi ko nan da chan bai Fita ba sai dai in zashi masallaci,Yana gida kusa da Hafsah yau ba Fada ba Korafi sai ma wani Tattali da Soyayyah Dayake Nuna mata kamar ya Hadiyeta Batayi mamaki ba Sanin Abdullahi haka yake wani Lokacin kamar mahauniya wajen Chanza launi in yau anyi Dadi Dashi Bai zama lalle Gobe ayi Dadi Dashi ba.
Wajen karfe 2pm na Rana Bayan Hafsah tagama Abinci Fatan Wake Tama Daddy da hanta sai kayan Fruit Abdullahi ya Dauketa suka Tafi Gidansu Hafsah Suka kara Duba Daddy da Jiki Chan suka Wuni sai gabda mangariba ya Daukota Suka Dawo Gida,Shi daman yana kaita bai Jima ba ya barta nan ya Shiga Cikin Gari ganin Anty Hadiza tazo da kuma wasu Daga Cikin yan"uwan Daddy da suka zo Dubashi.,Alhamdulillah Sun samu Jikin Daddy da Sauki Sosai yama Warware Ganin ya"yan nashi Suma Cikin kwanciyar Hankali musamman yar Lelensa Hafsatuwa.
Ganin gidan su kadai ne Shiyasa Hafsah bayan Sun Dawo ta Tsuke Cikin Wata Riga wacce iyakarta Asirin Nonuwanta kadai ta Rufe,cibiyarta Duka da Cikinta suna Waje sai wani karamin Wandon Jeans wanda iyakarsa Rabin Cinyarta ya Rufe Komai daga Sama zuwa kasa yana Bayyana ne,Kanta kuma tayi Tsifa ta Tara gashinta waje Daya ta Daureshi da Band ta sakeshi kawai Tana yawo haka gashi tayi aiki da Turare ko'ina ta Gifta sai kamshi ke tashi Abdullahi ya Rude da Dressing din Hafsah wanda Dama Shi aduniya yana Son yaga mace da irin wannan Shigar yawancin kayan ma Shi ya Siyo mata,Da Farkon kunyar sakawa take sai da Anty Hadiza tayi wani Zuwa Gidanta ta gansu Cikin Wardrope dinta bata sakawa ta Fara mata Fada Rashin amfani Dasu Da ita da Subai"atu babu Abunda zata ce musu sai Godiya Domin Suna bata Shawarwari da kuma Karin Haske game da Abunda ya Danganci Zaman Aure.
In yaran na nan Sai Da Daddare take sakamai irin kayan Lokacin sun kwanta suna Dakinsu Weekend ne in yana Gida take Chakaremai wani Lokacin ko Ransa na bace ne ya Dinga Satar kallonta kenan Har Daga karshe dai ya saki Tsiyan nashi ya More kallonnashi Dakyau Abu Guda Daya Dake kara Burgeta kan Abdullahi duk Abunda ya gani na kwalliyar mata sai ya Siyo mata yace wannan zai yi ma Hafsatuna kyau matuka,in kuma ya Siyo ta sakamai ya Dinga ya bata mata kenan yana Kuranta kyan Datayi acikin Idanuwansa Shiyasa Sau Tari bata Dora Fushi ko Masifar Abdullahi awata gagaruman mtsala tafi Dora hakan da Shi yanayin Halittarsa kenan kuma ita bazata iya Taba Chanzashi ba sai ta bar ma kanta Mijinta yana Sonta itama tana Sonshi Zatayi kokari wajen kyautatamai Daidai gwargwardon iyawarta.
Da daddare ma hanata yin wani Abincin yayi ya Fita yaje ya Siyo musu kaza da kuma kayan Fruit suka ci suka Sha Hafsah na kan Jikinsa Tare suka Ciyar da Juna,Ya Dauko Yankan kankana ya sakamata abaki kenan Shi kuma sai ya Bude Bakinsa alamun ta sakamai Shima make kafada tayi alamun ta Shagwaba ganin haka yasa ya kama kanta kawai ya Tura Harshensa Cikin bakinta ya Fara wasa da kankanan aciki itama sai ta Biyemai suna ta Gutsiran kankanan a Hankali Gefe Daya kuma Suna Wasa da Harshensu Lokaci Daya sai da suka gama Cijye kankanar nan Tas kana kuma Suka Zarce da kissing din Juna Cikin wani yanayin Muradi mai Girma sunyi Nisa basa jin kira kawai sai Kiran Wayar Abdullahi ya katse musu Hanzari Hafsah ce ta Fara Janye Kanta Lokaci Daya da Jikinta Tana kallon Abdullahi wanda ya koma ya Jingina da kujera yana maida Numfashi Idanuwansa suna Lumshe kamar mai Barci.
Cikin Sanyin Murya tace"Ana kiran Wayarka fa Abban Amira..."Dakyar ya iya Bude ido yana Fadin"Mikomin wayar.."Tashi Tayi da Sauri ta mikamai wayar dake Chan gefensu,Ya karba sunan wanda yaga yana Kiran nashi ne yasa ya Gyara zama yana kara Bude idanuwansa Cikin Girmamawa ya Daga Kiran da Sallama tare da gaishe da wanda ya Kirashi Ganin Haka yasa Hafsah ta Duka Tana Tattara Kasusuwan kazan da suka ci suka Zuzzubar a kasan Cafet kamar wasu yara ta Tattara Fruit ta Hada da Filet din ta kai Kitchen Gabadaya ta bar Abdullahi ya samu Damar amsa wayarsa.
Baba Wada Daga Chan Bangaren yace"Lafiya lau Abdullahi ya gida ya yara da kuma ita iyalin naka...? Abdullahi yace"Duk suna Lafiya Baba.."Baba Wada yace"Masha Allah...Dama Abunda yasa na Kira Rokonka zanyi Abdullahi Don Allah ka Taimaka Gobe Tun Safe ka Shirya Nazifi zai zo ya Daukeka kuje Chan kano Tare Wajen iyayen mai Dakinsa ku basu Hakuri,Wauta ne dai Nazifi ya Riga yayi,sai Hakuri Tunda Tun Shekaranjiya Mahaifin Sakinar ya kara Kirana yana gayamin Sakina ta dawo Gida tace bazata koma ba kuma ga Duk alamu yama Goyi bayan yar"sa yace yazai zai maka Shi Nazifi kotun Bisa Dukan yar"sa da yayi.."Abdullahi yace"Ashh Abu bai yi Dadi ba..Ai ya kamata ya Kira Shi Nazifin yaji nashi Bangaren in adalci yake so yayi.."
Baba Wada yace"Abdullahi kenan ai wannan sai Dattijo wanda yasan Dattako ba irin Gidan da Nazifi yaje ya Dauko Aure ba Dama na gayamai Duk wanda ya Siyi Rariya yasan zata Fidda Ruwa akoda yaushe ina gayamai ya kamata ya rika Koyi Dakai Bai Dubaka yagani ba Duk da iyayen mai Dakinka suna da Halinsu ammh kaga ai Dattijom arziki ne Alhaji Hamza Dalilin Zuwa neman Auranka har yau muna gaissawa ta waya kuma Duk inda ya ganni sai ya tsaya mum Gaisa da ita kanta mai Dakin nashi Komai da ita ake Gudanarwa an zama Daya ammh Shi ka Duba inda yakai kanshi Ai daman wanda ya Hau Motar kwadayi karshensa Tashar Wulakanci ne.."Abdullahi yace"Sai Hakuri Baba....Insha Allahu in Allah kaimu goben sai muje..Allah ya kyauta na gaba.."Baba wada yace"Ameen..Nagode Abdullahi ka gaidamin da Amaryata Hajara da kuma Abokina Usman tare da ita mai Dakin naka.."
Abdullahi yace"Zasu ji Baba.ammh amaryanka da Abokin ka Suna nan tare Dakai Suna Gidan mama sai gobe da yammah zasu Dawo.."Mallam wada yace"Hakane fa...Na manta Karshen mako me suna zuwa makaranta Shikenan zan Shirya Dakai naje har gidan naji Dalilin karima na Kin barina naga Amaryata.."Abdullahi na Dariya sukayi sallama da Baba wada mahaifin Nazifi wanda dama Haka yake Mutum ne na gari ga Dattako Da sanin yakamata ga kuma Barkwanci.
Yagama wayar kenan sai ga Hafsah ta Shigo Kallonta Abdullahi yayi kafin yace" Ahaka kika Fita waje..? Kallon kanta tayi kafin tace"Eh.."Wani kallo yayi mata Kafin yace"Ammh dai baki da Hankali ko..? Yanzu fa Dare ammh Shine zaki Fita ahaka ina laifinki ki saka Hijabi Hafsah ko Domin idanuwan Wadanda bama Gani,."Sai Lokacin Hafsah ta gane laifinta ta kuma san bata kyauta ba ko ba Domin komai ba sai Domin Tsarin Jikinta kuma ta manta ne Datashi Fita wani karamin gyale kawai ta yafa ma kanta.
Kai ta Sadda kasa kafin tace"Kayi Hakuri na manta ne ammh Haka bazata kara Faruwa ba."Mikewa yayi yana Fadin'"Tsiyana Dake da Abun bada Hakuri da bana bada Hakuri sai kin Bani Hakuri meyasa kike Hakane..? Nifa ba saboda komai yasa nayi mgana ba, sai Saboda yau ba fata ake ba Dalilin Haka wata lalura ta sameki kinga wa gari ya waya kenan..?
Hafsah tace"Hakane...ammh ai Shima Bada Hakurin ba laifi bane ko Abban Amira..? Kai Tsaye ya kalleta zai yi mgana kenan Wayarsa ta fara neman Dauki kawai sai ya Daga mata Hannu ya Juya ya Nufi Hanyar Bedroom din Lokaci Daya yana Daga Wayar da Fadin"Hello Mutumina.."Tunda Taji haka ta gane Nazifi ne Domin Shine kadai abokin Abdullahi na kusa wanda suke Kiran da juna da Irin Sunayen nan.
Tsayawa tayi afalon ta Kankanta komai kana ta kashe kwan Falon ta Kulle Kofar key dama already ta Kullo Kitchen dinta kana ta Bishi Cikin Bedroom din ta isleshi Zaune yana Duba wani Abu Cikin Sytem dinshi Tailet kawai ta Wuce ta Tube kayanta ta Fara wanka Bata Dauki Lokaci ba ta gama kana ta Dauro alwala Har ta Fito bai gama ba kawai sai ta Zura wata Rigar barcinta Ja Doguwa mai Zanen baki Tana da igiyiya ne ta gaba wanda ake Daurewa ko Botir Bata Dashi Sallaya ta Shinfida ta saka Hijabinta tayi sallar Isha"i ta Dora da Shafa'i da Wuturi Sai da ta Idar kana Abdullahi ya Kashe System dinsa ya Shiga wanka da Kallo Ta Bishi ganin yanayin Fara"arsa ta Sauya Daga Shigowarsa Daki Baya Rasa Nasaba kila da wayar da sukayi da Nazifi ko kuma Daga wajen aiki ne Bacin Ran nashi.
Koda ya Fito wanka Har ta kwanta Tana kallonshi ya isa Gaban madubi yana Fesa Spary Wardrope ya Bude ya Dauko Wata Bakar Jallabiya ya sanya Shima Sallayar ya Shinfida ya Tada Sallar Shafa'i yayi da Wuturi ya Dade yana Addu"a kafin ya Shafa Lokacin Tuni Har Barci ya Fara Daukan Hafsah kashe Wutar Dakin yayi kana Shima ya Raba gefenta ya kwana yana Shafa Kumatunta Lokaci Daya yana Fadin"Hafsatuna...Hafsatuna kin yi Barci ne..?
Sama sama Taji Shi ta Bude Idonta Jinta Cikin Jikinsa yasa ta Juya Suna kallon Juna kafin tace"Barcin ne ya Daukeni Bansani ba..am Sorry.."Hancinta ya lakuce kafin yace"Bakomai..Dama zan gayamiki ne gobe Tun 7am Nazifi zai zo ya Daukeni zamu je kano in Allah ya kaimu.."Cikin mamaki tace"Kano kuma Abban Amira..? Kai ya Dagamata yana Fadin"Eh..Gidan Surukansa zamu Sun samu matsala da Sakinar ne ta koma Gida.."Yafada yana Kokarin Warware Band din data Daure Kanta Dashi Daga haka kuma bai kara cewa komai ba Saboda daman Shi bamai wannan Surutun bane ko Hafsah ta sani Abdullahi bashi da Surutun barkatai Shidai Abunda ya Shafeshi yafi maida kai akanshi.
Tana jinsa yana waasa da gashin kanta yana kuma Tura Hannuwanshi Cikin gashin nata Dayake tana da Suma kuma bata Dade da zuwa gyaran kai ba,lumshe ido tayi kafin tace"Ayyah Abu bai yi Dadi ba..Allah ya kyauta ya kuma kaimu Goben Allah kuma yakai ku lafiya ya Dawo mana Daku lafiys.."Kiss ya bata a goshinta kafin ya Rumgumeta yana Fadin"Ameen ya Allah Matata..."Tana jinsa ya warware igiyar Rigar barcin yana Tusa Hannuwansa Duka Cikin Rigarta Itama Tallabanshi tayi Lokaci Daya ta Hade bakinsu waje Daya Daga haka dai bai mata komai ba ya Dai dan Rage zafi kadan sai kuma ya kara sakata Cikin Jikinsa yana Fadin"Oya yi barcinki yau Babu Abunda zan miki"Mirmishi kawai ta saki Ta Rufe idanuwanta Domin Tabbas Dama Barci nacin idanuwanta.
*****
Washegari Tun karfe 7am da wani abu na safe sai ga Nazifi acikin Gidansu ya ci Shadda Mai Ruwan Toka sai maiko take da yarari Abdullahi ma Tuni ya Shirya Domin Tunda Hafsah ta tashi sallah bata koma ba sanin yace mata zasu yi Tafiya,Nan gidan Nazifi yayi Breakfast dinshi yana bama Abdullahi labarin ba"a Zaria ya kwana ba yanzu haka Daga kaduna yake,Abdullahi natamai Dariya yana Zolayansa da mai Gida Uku,Hafsah dai na Ciki tana Jinsu Dayake itama bamai Son Hayaniya bace Daga gaisuwa ta Shige Ciki ta barsu nan har tayi wanka tazo ta Shirya Cikin wani less basu gama Breakfast din nasu ba Tana Saka Dankunne akunnenta kenan Taji Abdullahi na Kiranta ta amsa Cikin Hanzari ta karisa saka Dan kunnen ta kuma Zari mayafinta ta saka ta Fito Falon
Tsattsaye ta Gansu Abdullahi ya kalleta yana Fadin"Mikomin wayata kiga mu tafi kada muyi yammah Bisa Hanya.."da Sauri ta Juya Zuwa Cikin Bedroom ta Daukomai wayarsa tazo ta mikamai Tana Fadin"ka ko saka Turare Abban Amira..? Kai ya Dafe yana Fadin"Inafa na saka na manta wannan Dan Wutar Cikin yazo Tun safe ya Dameni.."Yafada yana kallon Nazifi wanda ke latsa waya Dagowa yayi yana Hararan Abdullahi kafin yace"Kaji Sharri..Ba gidan ka kwana ba wani ya Hana tun jiya ka Fito da Turaran da zaka Fesa.? Kinga Hafsah Don Allah kyalesa haka mu Tafi,wazai sakama Turare shi da ba neman Aure zashi ba in kuma kina so Daga zuwa Bikon Wata ya Dawo da mganar wata kuma Shikenan..'Yafada yana Dariya.
Hafsah tace"Naji ba komai...Komai dai menene bana son Arainamin Mijina muje Ciki na Fesa maka Turare harda ma Hula domin wannan Hular bata Dace da wannan Shaddar ba.."Tafada tana kama Hannunsa Shi kuma Abdullahi ya Bita yana Fadin"Yauwa Hausina..Matata har agidan Aljannah.."Yafada yana waigen Nazifi yana mai Dariya Harda gwalo.
Hular ta sauyamai ta Daukomai wacce tayi Shige da kalan Shaddarsa mai kalan Sararin samaniya,ta kuma Jikanshi da Turaransa na azzaro Visit,Kallonsa tayi ganin yadda yayi wani kyau kamar Zarah Cikin wata Cikin Shagwaba tace"Lala...Kaga yadda Mijina ya Hadu kuwa..? Nidai ina Tsoron kada mganar Nazifi ta zama gaskiya.."Dariya ta kama Abdullahi kawai sai yajata Jikinsa ya Rumgume yana Fadin"Karki biyema Mganar Nazifi kinsansa magulmaci ne yau ko Aure zan kara matata ai kice wacce zan Fara sanarmawa kafin kowa balle ma ba mganar karin Aure a Tsarina bansani ba ko zuwa gaba.."Ya karishe Fada yana Hura mata iskar Bakinshi kan Dogin wuyanta Zillewa tayi tana Dariya ya taka zai Rikota Kawai Sukaji Hon din Motar Nazifi na neman Toshe musu Dodon kunne Kai Abdullahi ya Dafe kafin yace"Kai Wanchan gayen dan Wutar Ciki ne..Kasan kana son matar taka ka bari ta tafi gida kawai ni ina son yau na zauna naga kwalliyar Hausina Dakyau dakyau ammh yazo ya Takuramin.."Yafada yana wani Bata rai Daidai Lokacin da Nazifin ya kara sakin Hon.
Dariya ta kama Hafsah bata karisa ba Abdullahi ya Rikota ya kara sakata Cikin Jikinsa Na dan wani Lokaci kafin yayi mata Kiss Saman kanta yana Fadin"Miss u...Take care of ur self for me kinji HAFSATUNA.!
Yafada Cikin wata Murya Mirmishi ta sakarmai kafin itama tayi Dage Domin ya Fita Tsawo ta sakamar sumba bisa karan Hancinsa Tana Fadin"Insha Allah U Too..Abdullahi Mijin Hafsatu.."Mirmishi ya sakarmata kafin ya Riko Hannunta har Tsakar Gidan ta Rakashi kana suka saki juna ya Fita Tana Dagamai Hannu,jikinta Duk yayi sanyi Tafiyar ne tazo ba wani Shiri.
Yana Fitowa Nazifi ya saki Tsaki kawai Abdullahi ya Bude gaban Mota ya Shiga yana Fadin"Mallam karfa ka Takuramin wlh..Kaja Tsiya sai na koma Abuna.."Ko kallonsa Nazifi bai yi ba ya Fizgi Motan da Gudu sai da Abdullahi yayi gaba ya Dawo Cikin mamaki ya kalli Nazifi yana Fadin"Shin wai ni nace ka mari Sakinar ne har tatafi Gidansu..? Yau ga Shawarakin Banza Yana neman Hushe haushin wata akaina..'Ba Abdullahi kadai Daya Fada ba Hatta Nazifin sai da ya kyalkyace da Dariya suka Hada Hannu suka Tafa suna Cigaba da Dariyansu irin na Shakikan abokan da Shakuwa da yarda da Juna ke Tsakaninsu.
*Janafty..*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:@JamilaUmar351*
*Dedicated To:My Habibaty Aisha Idris Abdullahi..!*
*009*
"Koda misalin karfe 10am da wani Abu na safe,tayi ma su Abdullahi a Babban Falon gidansu Sakina Dake Kofar Nasara acikin Birnin kanon Dabo Tumbin Giwa.
Tun Zuwansu Megadi ya Shiga Ciki ya sanar da isowarsu Shi yayi musu Jagora zuwa Cikin Setting Room din,Suna nan zaune mai aikinsu ta Shigo da kayan Tabawa ta kuma sanar dasu Hajiya da Alhaji suna sama su Dan Jirasu suna Saukowa yanzu.
Nazifi ya karkata kai yana Tambayan Sakina Mai aikin tace musu Sakina ta Fita tare da,kawarta Rukayyah zuwa wajen Shopping,Daga haka ta Fice ta Barsu nan,Abdullahi Dake gefe kawai sai ya Maida kansa jikin Cussion din Kujera Lokaci Daya yana Bin kayattacen Falon da kallo Wanda yaji kayan alatun Rayuwa Duk da ba wannan ne Zuwansa na Farko ba ammh yana da Tabbacin an sauya kayan Falon Domin bai taba manta Zuwansu na Farko Dashi da Nazifi Tun Lokacin kafin Auran su da Sakinar ne.
Tun suna Hira Jefi Jefi Har suka Gaji Kowa ya Fiddo wayarsa yana Latsawa ba wanda ya Lekosu Ran Abdullahi ya Fara baci ya Tsaki Siririn tsaki yana Kallon agogon Fatan Dake Hannunsa Cikin kosawa yace"Mutumina ka ko kalli agogo karfe nawa yanzu..?
Nazifi Dake latsa wayarsa ya Dago yana kallon Shima agogon Fatan Dake daure a tsitsiyan Hannunsa Cikin waro ido yace"Kai pass 11 fa mutumina Nake gani.."?
Abdullahi ya sauke Numfashi yana Fadin"Ko dai masu Gidan basu san da zuwanmu bane..? Nazifi yace"Wani irin basu sani ba...Baba ya fadamin ya fadama Mahaifin sakinar muna tafe yau insha Allahu Wulakanci ne kawai da Rainin arziki irin wanda Nake gaya maka.."Ya karishe Fada Cikin Bacin rai da kosawa Lokaci Daya kuma yana Lalubar Lambar sakina wacce bai yi Niyyar ma Kiranta ba kwata kwata Domin Tun Bayan Abunda ya Faru basu waya da Juna ba bai Kiranta ba bata taba kirashi ba.
Lokacin da wayarsa ta Shigo Wayar sakina Daidai Lokacin da tayi Hon kofar makeken Gidansu Cikin Bakar Motarta Camry,Rukyyah kawarta na gefenta Suna Taba Hira Jefi Jefi,Bata Duba wake kiran nata ba Sai da Ta Daidaita Motar a parking space kuma alokacin ne ta ci karo da Motar Nazifin Batayi mamaki ba Domin Da Safe Abba ke sanar da ita zuwan Nazifin yau in Allah ya yarda.
Lokacin Data Dauko wayar har kiran nashi ta katse Ganin irin Mirmishin Data saki ganin Shine mai Kiranta yasa kawarta Rukky tace"Yadai Qawata..? Sakina tace"Wannan dan Wahalan ne mana...."Rukky tace"Wa.? Nazifi..?
Sakina tace"Shi mana Bana gayamiki Abba Dazu yake gayamin sunyi mgana da Babansa yabada Hakuri ba kuma yace yau zai Turo Shi Nazifin yazo ya bada Hakuri Da kanshi ba.."Rukky tace"Dama ai na gayamiki Zai zo da kafarsa..Waya Fada mishi ana Taba mace irinki wacce ta mallaki Komai na Rayuwa a zauna lafiya..? Ai Dolensa yazo yayi ladabi ya bada Hakuri Don Ubansa.."Wani kallo Sakina ta watsa mata kafin tace"A"a nan fa Daya Rukky Bana so komai zaki yi karki zagi mijina Domin bazan Dauka ba...Har yanzu ina Son kayana Atoh..."Rukky tace"Allah baki Hakuri Qawata kaina Bisa Wuya.."Tafada tana Dariya Itama Mirmishin Sakinar ta saki kafin ta kashe motar su Bude Murfin Mota suka Fito Booth ta Bude Rukky ta tayata Daukan Ledojin Datayo Shopping Domin gobe zata koma Abuja wajen aikinta.
Cikin Gida suka Shiga,Dakin Sakinar suka yada zango Direct Sakinar bata zauna ba kayan Hannunta kadai ta ijiye ta kalli Rukky tana Fadin"Bari na leka saman Abba..Kila bai sauko wajen Nazifin bane inaga Dalilin Kiran kenan.."Da kai Rukky ta amsa mata ita kuma ta Fice da Sauri Zuwa sama Inda Dakunan Barcin iyayen nata yake.
Bata kai ga karisawa ba suka ci karo da Mahaifiyarta Cikin Mamaki Hajiya ke fadin"Lafiyar ki kuwa..? Har kun dawo Daga Shopping din..?
Sakina tace"Eh Hajiya ina Abba yake..? Hajiya tace"Yana Dakinsa yana Shiryawa wani Abu ne..? Baki Sakina ta Tura kafin tace"Hajiya bai san Nazifi yazo bane..? Wani Harara Hajiyar ta sakar mata kafin tace"Ya sani sai me..? Ke wai meke damunki ne Mutumin Daya Daga Hannu ya mareki ke har yanzu yana Ranki..? Mahaifinki yanci yake son kwatar miki ke kuma kina wani Sakarci.."
Kai Sakina ta Dukar Tana Fadin"Nifa Bance komai ba Hajiya...Kada dai yaga an Shanyashi ne kuma ina jin kamar ba Shi kadai bane.."
Hajiya tace"Hmmm Sakina kenan..Kina da Wahala in Namiji zaki Dinga ma Haka wuce ki Sauka kasa ga Abban naku nan Fitowa ai gwara amishi haka yasan kina da Darajarki ammh har yaushe Kamar wannan yaron da bai Wuce dan aikin Gidanki ba zai Daga Hannun ya marar mana ke mu kuma sai mu Zura ido..? wlh dole ya gane bai da wayau in sakarci ne ke damunsa.."Ta karishe fada Cikin zafi Da kuma Bacin rai.
Sum sum Sakina ta Sauka kasa tana Waiwayan Hajiya wacce ta Juya zuwa Dakin mahaifin sakina tana Cigaba da Fadan yadda Sakina take nuna son Mijinta karara
Nazifi kuwa ganin ya kira Sakina bata Daga ba yasa bai kara Kiranta ba,Abdullahi kuwa Ya gaji da zama bini Bini sai ya Duba agogo yana sakin siririn tsaki Shi kanshi Nazifin Ransa ya gama Baci Cikin kunar rai yake fadin"Abdullahi kaga Abunda nake Fadama ko..? Wlh na yardan ma kaina nayi sakacin da Sakina da iyayenta suka Rainani yanzu Fisabillahi meye amfanin wannan Wulakanci ko dai basu san waye yazo ba ya dace suyi mai Abunda suka mana..? Ya fada idanuwansa suna Chanza launi alamun bacin rai.
Numfashi Abdullahi ya Fesar yana Fadin"Abun dai ba Dattako aciki..Arzikin kadai ake Tutiya Dashi ba kima..Ai ko bakomai sai su Duba kai Surukinsu ne har yanzu akwai Aure tsakanin ka da yar"su...'Nazifi ya kada kai bai ce komai ba Saboda Takaichin Abun yana cin Ransa.
Shuru ya kara Biyo Bayan maganganunsu kafin Chan Abdullahi ya muskuta Ruwan Gora da aka ijiye musu basu Taba komai ba ya jawo ya Tsiyaya a wani karamin Kofi yasha Sai da ya koshi kana ya Sauke Kofin kasa yana Hamdala acikin Ransa,Cikin Kosawa ya sake Kallon Nazifi bayan ya kai Duba zuwa ga Agogon Hannunsa yana Fadin"Kai Nazifi wannan zaman ni kam ya isheni wlh...12 fa yanzu Fisabilillahi Ko da bamu da Abunyi sai mu zauna Haka balle ma sun sani mu da aikin yin mu Dukkanmu.."
Nazifi ya saki Huci kafin yace"Wlh Ba domin ina Tsoron Fadan Baba ba,da Tuni yanzu mun kusa ida Zariya kajima na Rantse maka sai dai su Fito suga mun kara Gaba Wulakancin ya isa Haka.."Abdullahi yace"Nifa nama ga Kokarinka in nine yadda nake da Zuciya da Fushi da Tuni na sakar musu yarsu Su jika susha Bazan iya Daukan wannan Iskanci ba..."Nazifi yace"Shiyasa nake gayamaka karka yarda kayi irin sakacin danayi Mutumina Abunda kake yi Shine Daidai.."
Abdullahi yace"Ai ni Matata ba irin Matarka bace..Iyayenta suna da Kudi ammh kuma susan Dattako..Wlh ba karya ko ganin Ido ba Hafsatu bata taba sa"in sa Dani ba kuma ban taba saka mata Doka ta karya ba Ballatana har na Dinga Fada tana Fada ina wannan karya ne Nida kai Nazifi akwai Bambamci ka yarda bakayi Sa"a ba kawai.."Nazifi ya goge Zufa yana Fadin"Ok ban yi Sa"a ba ko..? Toh ka yi sake ka gani Wlh sai ta maka Abunda Sakina ma batamin ba.."
Abdullahi yace"Ai banki Taka ba Mutumina kaima ai mganarka nakan Hanya ko yayane gwara ka Rika Nuna ma mace kai ne Shugabanta yafi ka zauna Komai sai Abunda ta tsara maka."Nazifi ya Bude Baki zai yi Mgana kenan Sai ga Alhaji Badamasi mahaifi ga Sakina ya Sawo kanshi Falon Cikin Shigar Shadda harda Babbar Riga Tun da ya Shigo kamshin Turaransa ya gauraye Falon.
Da Hanzari suka Mike Tsaye suna Kallonsa Kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon ya Zauna ya wani Harde Kasa Dukkansu sukayi suna Gaisheshi ya amsa Fuskarsa ba Walwala Dukkansu sukayi Shuru suna jiran Suji me zai ce musu,Sai da ya Dauki Dogon Lokaci kafin yayi gyaran Murya yana Fadin"Ashe mahaifinka kadai keda Kima acikin Idanuwanka ko Nazifi..?
Yafada Cikin Gadara da wani Rainin Wayau,Abdullahi ya Dago ya kalli Nazifi Shima ya kallesa kafin Nazifi ya Dago kansa yana Fadin"Ba haka bane Abba....Wlh...! Ba haka bane to ya ne..? Ya katseshi Cikin dan bacin Rai Lokaci Daya ya Cigaba da Fadin"Kira nawa nayi maka kana gani baka Daga ba..?kuma koda baka gani ba in kazo kagani bazaka iya kirana Back kaji Dalilin Kiran nawa ba..?
Ya karishe Fada yana Kallonsu Dukkansu Abdullahi kuwa mamaki ya Cikasa sai kallon Alhaji Badamasi kawai yakeyi Nazifi na bashi labarin Rashin Kirkin Surukansa bai taba zaton Abun nasu yakai haka ba Nazifi kuwa Ransa Dama chan yana bace ne yasa kuma ga wannan mganganun,sai kawai yayi mai Shuru jin Shurun yasa Alhaji Badamasi ya Cigaba da Fadin"Koda yake ai bazaka Daga Kiran ba kasan Abunda ka aikata Kasan Allah ba Domin mahaifinka ya Kirani yana Bani Hakuri ba da Tuni sammaci ya iskeka Domin bazan Lamunci wani Sakarai Dagachan bangaren yana Dukan min ya"ba wanda ko Ni Dana Haifeta ban Dake ta ba ballata wani Chan Bare bazai Sabu ba.."Yafada Cikin Nuna yadda Abun ya batamai rai.
Nazifi dai kansa na kasa bai ce komai ba ganin Haka sai Abdullahi ya Dago kansa yana Fadin"Abba hakuri za"ayi Abun duk bai kai haka ba..Kuma in Nazifi nada Laifi itama Sakinar Danata Laifin ko miye bai dace Tana karkashinsa Ta Dinga Nuna kamar ita ke Auransa ba Yakamata Shima Abba aduba wannan mtsalar.."Yafada kansa Tsaye da mamaki Alhaji Badamasi ke kallonsa Domin don sani ya san Abdullahi Domin ko gaisuwan Surukai tare suka zo ammh bai Taba tsammanin Haka yake da Tsaurin ido ba.
Alhaji Badamasi yayi Shuru kafin yace"Naji mganarka ammh ai banga Bambamci ba Domin yasan Diyar wanda ya Aura..Sakina tayi karatu bama a kasar Nageria ba Taya yake Tsammanin zata zauna bazata yi aiki ba..? Kuma in ta samu aikin yasan yanayin irin wannan aikin Tunda yaji yagani Dole kuma yayi Hakuri da yanayin Tsarin Tunda Shi yaji kuma ya gani.."Ya fada Cikin Halin ko in kula Abdullahi suka Kalli Juna Shida Nazifi kafin Abdullahi ya kada kai yana Fadin"Duk da Haka dai Abba ya kamata adubi..Shi Aure ba Abun wasa bane Ibada ne wanda in Suka Rabauta kansa Dukkansu sai Su samu aljannah ta wannan Hanyar Abun Dubawar Shine koma miye ai Shine mijinta ya kamata ta Rika bashi Girman da Allah ya Riga ya bashi.."Alhaji Badamasi yayi kasakai yana Kallon Abdullahi da Sauraransa aransa yana Fadin wannan yaron ya Cika iyayi da Sanaben Tsiya ba Tsoro acikin Ransa ballatana wani Fargaba.
Cikin Dakewa yace"ok...Shikenan.Dukkansu sai su Taru su gyara...ammh Dole ya barta In wani aikin ya taso bana son wani Hayaniya Tunda yasan yanayin aikin Matarsa.."Nazifi ya Kada kai yana Fadin"Ayi hakuri Abba Insha Allahu haka bazata kara Faruwa ba.."Alhaji Badamasi yace"Shikenan ya wuce Tunda kazo ka bada Hakuri...ammh mgana ta karshe Kar ka kuskura ka sake Saka Hannu kace zaka Daki sakina in wannan karon na kauda kai In ka sake wlh zan Rufe ido naci Mutumcinka.."Yafada Cikin kakkausan Murya.
Nazifi ya Dake yana Fadin"Naji Abba ammh itama Sakinar ku ja mata kunni ai yakamata amatssyina na Mijinta in wani Tafiya ya kamata ta Dinga neman izinina ba Wai ta Rika Bani Umarni ba.."Yafada Shima Cikin Dacin Rai,Alhaji Badamasi bai ce komai ba ya Daga wayarsa kawai ya Kira Hajiya tana Dagawa yace"Ki Turomin sakina Shashen baki yanzu nan.."Daga Haka ya katse Kiran Falon ya Dau Shuru na wani Lokaci.
Ba"a Jima ba sai ga Sakina tayi Sallama acikin Falon Tana sanye da Doguwar atamfa na wani material da mayafi,Sau Daya Nazifi ya kalleta ya kauda kai Bai kara ba itama kallonsa tayi Dagashi Har Abdullahin kana ta isa kusa da Abbanta ta zauna Tana Fadin"Gani Abba..Hajiya tace kana son ganina.."
Da Hannu ya Nuna mata Nazifi yana Fadin"Mijinki ne yazo ban Hakuri da Bikon ki,na jamai kunnan kar ya kara Dukanki in kuma ya kara zan Dauki mataki Sai kuma Shima ya kawo nashi Korafin kan baki Neman izininshi kan wasu abubuwan sai dai kawai ki Rika sanar Dashi Kai Tsaye.."Sakina ta Dago kanta tana kallon Nazifi wanda yayi Saurin Dauke kansa Jim tayi kafin tace"Abba ina Fadamai..Ko wannan ma Tafiyar na sanar Dashi Shine yace Bazani ba kuma in zai Fadi gaskiya ina nataba zuwa Ban gayamai ba..?
Tafada tana kallon Nazifi wanda Shima ya kalleta ido Cikin ido na wani Lokaci Abba yace"Toh kai kaji Abunda tace Cikinku bansan waye mai gaskiya ba..? Ba Nazifi kadai ba Hatta Abdullahi sai da ya Dago kansa yana kallon Daga Uban har yar yana Jinjina kai Cikin Dacin Rai Nazifi yace"Me zan karu dashi in nayi miki karya Sakina..Tun da mukayi Aure Baki Taba bani Girmana a matsayina na mijinki ba ki Bude baki yau wata Tafiya ta kamaki kice min Nazifi Ranar kaza zamu Tafi kaza ina neman izininka..? In kuma kin Taba sai ki sanar dani..?
Ya karishe Fada yana Sakarmata Idanuwansa Itama kallonsa Take kafin ta sadda kai Kasa tana wasa da gefen Mayafinta Alhaji Badamasi Daya gano yarsa bata da gaskiya Cikin Borin kunya yace"Shikenan..Ke sakina ki gyara Kinji ko..? Daga Abdullahi har Nazifi da kallo suka Bisa kawai Ganin yana Shirin mikewa yasa Nazifin yace"Abba ina da wata mgana..?
Komawa yayi ya zauna yana Fadin"Ina Sauraranka kayi Sauri Domin ina da Taro zan Fita ne.."Kai Tsaye Nazifi yace"Bazan Hana Sakina aiki ba..Ba kuma zan Hanata taka duk inda take so awannan kasar ba saboda ni nayi sake Haka ta faru..ammh ta sani Dolenta ta Rika zuwa Gidana na Kaduna tana Weekend dinta Bai zama Dole ina matsayin mijinta kuma ace Kullim sai dai ni na Rika kwasan Jiki ina Binta ba mganar gaskiya na gaji bazan iya ba.."Sakina ta Dago tana kallonsa kafin tace"Wani gida aciki naka ko wanda Abba ya bamu..?
Kai Tsaye yace"Nawa dai..Shine ai mallakina wanda Abba ya baki kuma wannan mallakin ki ne.."Cikin Zafi ya Fadi mganar wanda yasa Alhaji Badamasi yayi Tsai yana kallon Nazifin Ganin yadda ya Hade rai Allah na ganin Bashi da Burin ganin Auran sakina ya Mutu Domin Duk Cikin ya"yansa Sakina tafi kowa Dacen Mijin kwarai sauran Daga yan Iska sai Marasa Tarbiya gadai Dukiyar ammh ba Tarbiya Shi kuma Nazifi gashi dai bamai kudi ba ammh dai Akwai Hankali da Tarbiya Shi kuma Abdullahi yaji Dadin Mganar Da Nazifi yayi domin Shi ya bashi Shawaran ya kamata ya Bar gidan da mahaifin sakina ya basu ya koma nashi Shine Mutumcinsa.
Kafin Sakina ta samu Damar mgana Abba ya Rigata da Fadin"Shikenan zata Dinga zuwa ba Shikenan ba..."Yafada Cikin Son kauda zencen kan Nazifi na kasa yace"Shikenan Abba.."Alhaji Badamasi ya mike yana Saba Babban Rigansa Lokaci Daya yana Fadin"Sai kuje kuyi ta Hakuri..Kadai ji Abunda na Fada maka Banason na karajin Zencen Duka.."Nazifi yace"Insha Allahu.
Sakina tayi zaraf tace"Abba ina son yayimin lamani sai bayan na koma Abuja Ranar sati sai na koma Kaduna din.."
Kafin ma Abba yayi mgana Nazifi ya Rigashi da Fadin"Allah kiyaye Hanya...."Jin Haka yasa Alhaji Badamasi bai kara mgana ba Su Abdullahi suka mai sallama ya Fice Daga Falon,Ganin haka yasa Abdullahi ya mike yana Fadin"In kun gama ina Mota.."Daga haka kawai ya Fice Domin mganar gaskiya ya gaji da zaman Gidan.
Da kai Nazifi ya amsa mai kafin yace"Ok Nima ganinan Zuwa..."Daga haka ya maida kallonsa kan Sakina Wacce ta kafeshi da ido Tana kallonsa ganin Duk ya Rame ganin Sun kwashi Wajen Mintuna Biyar ba wanda yace ma Dan"uwansa komai yasa Nazifi ya Mike yana Fadin"Mu zamu koma Tunda baki iya gaisuwa ba ko..?
Itama Mikewar tayi Tana Fadin"Baka so na gaisheka bane..
kai da kake Kallona kana Kauda kai.."Yana Shirin mgana yaji wani masallaci Dake Kusa da Gidansu Sakina ana kwala Kiran Sallah ido ya Fiddo yana Fadin"Har Azahar tayi..? Lalle mun kwashi zaman Rashin Dalilin agidan nan...Toh mu zamu Dauki Hanya...Gobe zan Koma Bakin aikina."Daga Haka kawai ya saka kai ya Fice Cike da mamaki take Binsa da kallo kafin Daga Bisani ta tabe baki ta Shige Cikin gida aranta tana jin ko ahaka aka Tsaya ita keda Riba.
Yana Fitowa basu Tsaya ba kawai ya Bude Bangaren Direba ya Shiga ya Zauna Dama already Abdullahi na gefen mai zaman Banza Motar ya Tada lokaci Daya ya saki Hon megadi ya wangale musu get suka Sulala waje Sai da suka Daidaita Motarsu kan Titi ne kana Abdullahi yace ma Nazifi.."Har kunyi sallaman ne..?
Tsaki Nazifi yaja kafin yace"Wani sallama Fitowa nayi na barta ta Tsaya mulkinta kila Jira take itama na Bata Hakuri kamar yadda na bama Ubanta.."Ya karishe Fada Cikin bacin Rai kai kawai Abdullahi ya kada kafin yace"Ka tsaya muyi sallah in kaga masallaci kan Hanya Lokaci yayi.."Ok kawai Nazifi yace Daganan kowa yayi Shuru yana Sake sake Cikin Ransa.
Sakina kuwa Hajiya Fada ta Hau ta dashi Lokacin Data Tambayeta ina su Nazifin tace sun tafi nan ta Fara Fadan Rashin kunyansa tayi yawa Har ya iya zuwa bai Shigo ya gaisheta ba Sakina dai ba Mgana kai kawai ta Dukar dac kai toh me zata ce ko ita din ma Nazifi bai ma kyakyawan kallo ba Ballatana Har taga wajen cewa ya Shigo ya Gaida Hajiya Sumi Sumi tayi ta wuce Dakinta Daman Abba yana Dawowa ya Fita Zuwa Wajen Taronsu na yan Siyasa..
Duk yadda Rukky taso Sakina ta Fadamata yadda sukayi Afalon Abba kiyawa Tayi Saboda Ta tsani Rainin Hankali Rukky ba Tun yau ba ta lura tana Raina mata Nazifin ta,Tun Lokacin Auransu take Fadin ba, ajinta bane Tafi karfinshi Ballatana yanzu da suka samu mtsala sai kara Ruru wutar take tana kar Sakinar ta koma alhalin ita har yanzu bata samu wanda zai kwashetanta ba Ita tana Jiran mai kudi kuma ba wanda yazo Talakawan ma Data Raina ba wanda yazo,Kawar Sakina ne tun Suna Yara ammh ahakan ma Suna da Bambamcin Ra"ayi sai da Sakina taci Uwarta ta Damata agirman kai da kuma Takama da Isa da komai.
*Shakira...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Janafty*💞
*Dedicated To:My Habibaty❤️Aisha Idris Abdullahi..*!
_Wannan Shafin Sadaukarwa ne gareki Babbar Yayata Wato *ANTY MARYAMA*, Alherin Allah ya kai miki adukkan inda kike Ameen..._
*010*
"Basu Shigo Zaria ba sai Bayan Sallar Mangariba Saboda sunyi Tsaye Tsaye Kan Hanya,Sun Tsaya sun Yi Sallar azahar suka dau Hanya,Lokacin Sallar La"asar ne suka Tsaya sukayi Salla suka ci Abinci nan suka Bata Lokaci kuma Duk da basu yi Gudun da sukayi ba Lokacin da zasu je.
Direct Gidansu Nazifin suka Fara isa Abdullahi shi ya korama Mallam Wada Duk Abunda ya wakana kai kawai ya girgiza kafin yace"Allah ya kyauta na gaba..Sai ka kiyaye ka dai ji da kunnanka Abunda Nima ya gayamin..Bazan so ace yau na saka Baki ka Saki matarka ba Domin lokacin da ka ganta kuka Daidaita kanku bansani ba...ammh dai nasan dai na Fita Hakkinka wajen nuna maka Kuskuranka na Auran ya'yan masu kudi ka nuna min ba matsala Babu Abunda zai Faru Toh yanzu kuwa Dole kayi Hakuri ka Zauna da ita Ayadda kake Tunda dai kai kaji kuma ka gani..."
Inna Abu Dake zaune ta Tabe baki kafin tace"Shi ko kunya bayaji.Matarsa bata Darajasa bama Ballatana ta Daraja mu iyayensa da kannensa da yan"uwansa...Me ake da mata Irin Sakina Wlh Mallam Rabonta da Gidanan Tun Lokacin da kayi Ciwon kafar nan wajen Shekara.."Mallam wada ya kada baki yace"Wannan Duk Ba Abun Damuwa Bane Abu in batazo ba kanta Tayi mawa..Yara nawa garemu wadanda kullum ke kan Hanyar Zuwa gaishemu,Surukai nawa garemu masu ganin kimar mu,akwai wadanda ma bamu Haifa ammh suna bamu Girmanmu Saboda haka bai kamata ki Damu kanki da wannan ba..Nidai Mganata ta karshe dashi Kar naji kar na sake ganin ka saka Hannu ka Daki yar mutane Ballatana har Mahaifinta ya Kirani yana gayamin mganar Banza.."
Abdullahi yace"Haba Baba kai kuma sai ka kyaleshi..? Mallam wada yayi Dariyansu na manya kafin yace"Toh Abdullahi in ban kyaleshi ba Dukkansa zanyi..? Ko nima na Biye mishi muyi ta sa"in sa,Banga Laifinsa ba Domin Duk Abunda ya Kirani ya gayamin ba kowa ya jamun ba sai Nazifi toh akan me zan damu kaina.?Yafada yana kallon Abdullahi da Nazifin Duka atare.
Inna Abu Tace"Ina fa Mallam Abun ne na Hausawa da suke Fadin dan kuka Shi ke jama Uwarsa Jifa..."Mallam wada yace'Shine ma Abu."Daga Nazifin har Abdullahi ba wanda ya kara Mgana Gwarama Abdullahi Sudan Taba Hira da Baba wadan Nazifi kuwa kala bai ce toh me zai ce..?bayan duk Abunda Baban ya Fada gaskiya ne Dama Abunda ya Gudanmai kenan shi Alokacin bai gani Idanuwansa Sun Rufe da Soyayyar Sakina da kuma Cikar Burinsa da Muradinsa.
Daga gidan su Nazifi masallaci suka wuce sukayi sallar Mangariba sai Suka Shiga Gidan mama sai ya samu ma Su Amira Auwal ya Tafi kaisu bai ma Dawo ba Zama sukayi suka gaisa Da mama Shi da Nazifin Tana Tambayansu Daga ina Abdullahi yace Daga kano Daganan bata kara Neman jin ba"asi ba Domin ba Abunda ya Shafeta bane Mariya ce kadai agidan ita ta Zubo musu Tuwon Dawan Datayi Miyar kubewa Bushashiya sanin Abdullahi masoyin Tuwon Dawa ne ana kawowa Abdullahi ya kalli Nazifi yana Fadin"Mutumina gafa Tuwon Dawa..?
Yamutsa Fuska Nazifi yayi kafin yace"Kai kaci..kayi Sauri ina so na ijiye ka a gidane kaduna zan koma adaran nan.."Abdullahi yamike yana Fadin"Kaduna.?haba ka bari gobe da safe mana.."
Nazifi yace"Gwara na tafi yau din kawai Kaji mutumina."Abdullahi bai sake mgana ba ya Fita waje ya wanko Hannunsa ya Dawo Daki,Ya zauna Lokaci Daya ya Tankwashe kafa ya Bude kulan Tuwon Dana Miyar kamshi na Tashi na kashi da manshanu Domin Abdullahi yadda agidanshi bai Ciyar da iyalansa Cimar Banza Hakama Kannensa da Mama Suma Suna Cin Cima mai kyau Domin Duk wata yadda zai siya kayan abincin Gidansa haka zai Siya na Gidan Mama haka kuma zai Damkamata kudi a Hannunta,Daga chan bakin Titi akwai wani mai nama wanda Abdullahi yama mgana Su Mama zasu Dinga karban na miya in Wata yayi ya Biyashi da Gudu yayarda Sanin Abdullahi bazai Taba mai wasa da kudi ba.
Yana cin Tuwon suna Dan Taba Hira da Nazifi wayarsa tayi Kara Ya Dakata da cin Tuwon ya Ciro wayar nasa Dake gaban aljihu da Hannu Daya yaga Sunan *MY WIFEY..* ya fito baro baro Ajiyar Zuciya ya Sauke yana Fadin"Nayi laifi ban kira Hausina ba Tun Dazu da mukayi mgana muna Hanyar Dawowa..."
Yafada Lokaci Daya yana Daga Kiran Dagachan Bangaren Hafsah tace"Hello Abban Amira kun iso ne..? Cikin Sanyin murya yace"Mun iso yanzu ba Dadewa Hausina..Muna gidan mama da Nazifin yanzu zai maidoni inda ya Daukoni.."Yafada yana Kallon Nazifi Lokaci Daya da Dariya Hafsah tace"Shikenan sai ka Dawo..Su Amira ma Auwal ya kawosu yanzu ma ya Fita.."Kai ya kada yana Fadin"Haka Mama tace ya kyauta..Sam na manta Dasu kafin na Fita ban kirashi dama nace in yadawo kasuwa ya Maidosu gida ba.."Hafsah tace'Nima Asha"afan nayi..Gashi mama Ta saka ya maidosu aie.."Cikin gamsuwa yace"Ta kyauta..Sai na iso.."Daga haka ya yanke Kiran Hararansa Nazifi yayi yana Fadin"Mallam zakayi ka gama na kaika gida ko kuwa na kara gaba..?
Abdullahi yace"Wani ka kara gaba..?dama agidan Mama ka Daukoni..? Wlh ko lagos zaka kwana yau ba kaduna ba sai ka maidani Inda ka Daukoni kajima na Rantse maka.."Nazifi bai kara mgana ba ya maida Hankalinsa kan wayarsa Shima Abdullahin ya Cigaba da cin Tuwonsa.
Sallamar Jidda ce ta katse musu Shuru Atsakar gida Mama ta amsa wacce ke dan kai da kawo Cikin Bacin rai Mama tace"Ina kika Tsaya jidda..?Daga ki mika ma Baba ayyah Rariyanta Shine sai kije ki share kafa kiyi zamanki sai bayan mangariba..?
Jidda ta kada kai Tana Fadin"Mama gidansu Rumana fa na Shiga.."Mama tace"Au..Toh zaki Bayani ne yayanku na ciki.."Sai Lokacin ta Lura da Takalma Sawu Ciki guda Biyu bakake,ido ta zaro Tana Dafe Kirji kafin ta samu Zarafin mgana ba,Abdullahi Dake Cikin Daki yadan Daga murya yana Fadin"Shigo nan don Ubanki Jidda.."
Yafada cikin zafin rai da Wani bacin rai na yadda Jidda take neman ta Fita zakka acikinsu,Jikinta a sanyaye ta Shiga Dakin tana kallon mama wacce ta Juya ta Shiga Kitchen tana Fadin"Ni bar kallona..Jidda sam bakijin mgaa na mariya tafiki gudun Zuciya wlh."
Akofar dakin ta Coge tana wani Raba Ido Nazifi ta gaisar ya amsa yana kallonta kafin ta maida kallonta kan Abdullahi tana Fadin"Ina wuni yaya.."Ko kallonta baiyi ba sai cin Tuwonsa kawai yakeyi Ganin haka yasa Jikin Jidda ya Fara rawa Domin ta Tuna kwanaki sai da yaja mata kunni kan ana aikanta tana Biyawa Gidan kawaye musamman ma Gidansu Rumana wacce dama ya Rabata da ita saboda Rumanar yar Duniya ce gata bata da kunya Duk haka yan Gidansu suke kuma yajama Jidda kunni kan Ta rabu da ita ita kuma Taki Domin kawartace Sosai Ajinsu Daya a makarantar Boko da islamiya.
Mariya ce ta Fito Daga Uwar Dakim Mama da Hijabin Datayi Sallah zata Wuce Abdullahi ya Kirata ta waigo tazo Hannu ya nuna mata yana Fadin"Kwashe wannan kayan na koshi.."Ba musu ta Durkusa ta Tattara kololin ta Fita Zuwa waje suka Hada ido da Jidda Ta sakarmata gwalo ita kuma ta Harareta mikewa yayi ganin haka yasa Jidda ta Fita da Sauri tana Rawan Jiki ta zata zai Daketa ne sai taga kawai ya Nufi bakin Robam Ruwa ya Diba ya wanke Hannunsa Tas yana Fadin"Mama tun yaushe kika aiki yarinyar nan.?
Mama ta Fito Daga kitchen tana Fadin"Tun wajen Biyaar na yammah fa ammh sai yanzu ta Shigo Gidan.."Bai ce komai ba sai da ya gama wanke Hannunsa ya Dago da kansa yana yarfe Ruwan Hannunsa Lokoci Daya yana Fadin"Ke zo nan..' yafada yana kallon Jidda wacce ke Tsaye tana ta Raba ido.
Cikin Tsoro ta kariso Gabansa Tana wani Fiki Fiki da ido Cikin Fushi yace"Daga gidan Uban kike..?Da mama ta aike ki tace ki biya wani waje ne..?Yafada yana Kallonta Lokaci Daya yana kara mata da Harara,Kai ta Fara Sosawa Ta kasa mgana Wata Tsawa ya Dakamata wanda ba ita kadai hatta mariya sai da Tsawar ta Razanata ta makale acikin kitchen tana leken Ya Abdullahi Dake Tsaye a tsakar Gidan yana Faman Huci,cikin Fushi yake Fadin"Bada ke nake mgana ba..?
Baya Jidda taja Cikin Rawan Jiki Dana Murya take Fadin"Dama..
da..ma..Bata je Makaranta Ranar jumma"a bane Shine na Shiga na gani ko lafiya.."karamin Tsaki yaja kafin yace"Saboda Nan ne inda Mamar ta aike ki ko..? Kin Raina maman ko..? Shiyasa duk inda ta Ijiye ki baki iya zama sai kin Chanza Directiom kinfi son Kullum adinga Bin Ra"ayin ki kuma azura miki ido ana kallonki ko..?
Yafada cikin Tsawa Muryanta ta Fara Rawa kamar tayi kuka tace"A'a..."Nuna ta yayi da yatsa yana Fadin"Saka gwiwoyinki a kasa Don Ubanki yau sai kin Raina kanki Duk wani Tashen iskancinki sai na Sauke ki mishi Gobe in Aka aike ki Daga Gidan da Mama tace ki Tsaya baza ki iya karawa gaba ba.."Yafada yana waiwaigen neman Abun Duka.
Da Sauri Jidda ta Zube har ta Fara Hawaye sanin Halin Ya Abdullahi Tsaf zai saka Sanda ko Bulala ya mata dukan Tsiya ko agefen Kwalan Rigansa Tana Kuka take fadin"Don Allah ya Abdullahi kayi Hakuri Na Rantse Har ga Allah bazan kara ba.."Wani karamin icce ya Dauko ya Nufeta Dashi yana Fadin"Nasan sai kin kara Hauwa"u...."Da sauri tace"Wlh bazam kara ba kaji ma na Rantse yaya.."
Mama na gefe tace"Rantsuwar banza ce kike yi Jidda da kukan Tsoro ammh baki da gudun magana sam.."Abdullahi yace"Kyaleta Mama ni yau zam kawo karshen Taurin kanta Don Ubanta maza ki kwaben Hijabin Jikinki Kinsan Allah yau sai Fatar Jikinki ta Daga saboda Duka kila Daga yau zaki kiyayi Tsayawa inda aka aike ki da kuma Rabuwa da wannan Yarinyar mara Tarbiya da Tuntuni na Raba Tsskaninki da ita.."Jin haka yaasa Jidda ta kara Rushewa da kuka tana Rokon Abdullahi da yayi Hakuri ammh yaki Sauraranta yace tayi maza ta Cire Hijabin Jikinta.
Hatta Mariya da suke Takun saka da Jidda sai da taji Tsausayinta Shiyasa arayuwarta tana Gudun Abunda zai saka ta Shiga Tarkon ya Abdullahi,Mama kuwa ita kanta Tsausayin Jiddan ya kamata sai dai bata isa ta Hana Abdullahi Daukan mataki kan Jidda ba Tunda batajin mgana Ba sau Daya ba ssu Biyu ba yasha mata Fada kan Shigen yawon Bin Gidajen kawaye in Mama ta aiketa da kuma Kawance da yarinyar nan Rumana ammh Jidda bata jin mgana sam.
Nazifi ne yaji magiyar tayi yawa ya Fito yana Fadin"Kai Mutumina Don Allah ka kyaleta..Tunda ta amsa laifinta kuma ta baka Hakuri karka Daketa plz."Cikin Bacin Rai Abdullahi ya Kalli Nazifi yana Fadin"Kana fa ganin Dabi"un Yarinyar nan..? Rawan kanta zai saka Wlh na kusa kasheta da Duka.."Nazifi ya karisa Kusa da Abdullahi yana karban Sandan Hannunsa Lokaci Daya yana Fadin"Cool ur mine Mutumina...Kamata afuwa Ko saboda ni don Allah.."
Yafada yana kallon Abdullahin wanda yake ta sakin Huci Shi kadai,Ajiyar zuciya ya sauke bai yi mgana ba Nazifi ya waiwaya ga Jidda yana Fadin"Maida Hijabin jikinki..."Da sauri ta maida hijabin Jikinta din wanda ta Riga ta Cire Har Farar T.shirt din Jikinta ya Bayyana wanda ya Bayyana Sirrin Kirjinta,Kau da kai Nazifi yayi da Sauri yana jin wani yanayin da bai Taba ji ba Duk da Duka Kannen Abdullahi ba wacce bata tashi agabansa ba.
Fushin Abdullahi ya sauka yasa Cikin Sanyin Murya yace"Daka bari na mata Dukan mutuwa Abokina..Bar ganin Tana wannan kukan bai Hana gobe ta kara maimaita laifinta.."Nazifi ya Juya batare daya ma Abdullahi mgana ba,Ya kalli Jidda yana Fadin"kinga tashi Tsaye.."Ba musu ta mike tana Share Hawaye Mama dake gefe tace"Da baka kwace ta ba Nazifi..Daka bari ya Mata ko kadan ne.."Nazifi yace"Haba mama...Har da ke Autan ki ce fa..'
Mama tace"Autan ne batajin mgana Nazifi yayansu ne Daidai da maganinta Tunda Daga Mariya har Auwal Ta Raina su Basu isa suyi mata mgana taji ba.."Nazifi ya sakarma Jidda ido kawai yana kallonta Lokaci Daya yana Nazarinta Ganin tana ta Share Kwallah da gefen Hijabinta yasa yace"Hauwa"u...!!!
Ya kirata Cikin wani Sauti Wanda yasa ta Dago Jajayen Idanuwanta Tana kallonsa Cikin wani yanayin da ita kanta batasan Dalili ba Taji kawai yaya Nazifin yau yana mata kwarjini Duk da Daman babu wani wasa Tsakaninsu Dalilin yana abokin Babban Yaya agaresu Cikin mutuwar Jiki ta Sadda kanta kasa Ta Kasa Jure kallonta.
Shima anashi Barayin Hakane Wani Iri yake ji acikin jikinsa game da idanuwanta,Cikin Dakiya yace"Kin dai gani yau na kwace ki hannun Yayanki...Gobe kuma Bana nan in kika Kara kinsan Abunda zai biyo baya ko..?Nida kaina bazan Hanashi Hukuntaki ba Tunda bakijin mgananr na gaba Dake.."
Jidda tace cikin Raunin murya"Bazan kara ba Ya Nazifi..
"yanayin yadda ta Fadi sunan nashi ya kara kashemai jiki ammh sai ya basar Cikin son Girma yace"Kinyi alkawari..?
Ya fada yana kafeta da idanuwansa Bata Dago ba ta Daga kanta tana Fadin"Insha Allahu nayi alkawari Ya Nazifi...!!!!Lumshe idanuwansa yayi kafin ya Bude yana Fadin"Naji Dadin haka..Plz ki zama mai jin mgana kada na sake Dawowa gidanan naji ance Jidda tayi wani laifin kuma kiyi Respect din Na gaba dake,Mariya da Auwal They elder dan u in suka gayamiki gaskiya u hv to Listem to Them yau in basu ba kina da wasu Shakikan yan"uwan da zasu Fada miki gaskiya ne..?
Jidda ta girgiza kai mirmishi Nazifi yayi kafin yace"Yauwa..Toh Maza ki Dauki Buta kiyi alwala ki Shiga Daki kiyi sallah sai kizo kici abinci ko..? Kai ta Fara Dagawa kafin tace"Nagode ya Nazifi..Allah ya saka da alheri.."Tafada tana Wucewa Bakin Fanfo inda Jerin,butoci yake ta zari Daya Lokaci Daya tana Cire Hijabin jikinta ta sagale Jikin igiya ta Fada Bayi Da kallo Dukkansu suka Bita Barin ma Nazifi Daya zama wani Mutum mutum na ganin Irin Dirin da Allah ya bama Jidda wanda bai taba lura ba sai yau.
Kallonsa ya maida kan Abdullahi kafin yace"To Babban yaya..Case din ya mutu sai kazo na ijiye ka Gida na kara gaba.."Abdullahi baiyi mgana ba ya Duka yana Saka Takalminsa Shima Nazifin ya Duka yana Saka nashi atare suka Dago suna ma Mama sallama sai Lokacin Mariya ta Fito Daga kitchen tana Fadin"Ya Abdullahi zani Gidan kawata wacce Muke karatu tar..."
Bazaki ba.."Bata karisa mgana ba ya Katse mata Hanzari batare Daya Jira Rokonta ba Kawai ya Fice Nazifi na Dariya ya Rufamai Baya Shi da kanshi yasan Halin Abdullahi kaifi Daya ne wani Lokacin ma yana Fa ganin kokarim Hafsah duk da baya ganin Hakan Abdullahi keyi wani illah ne,ammh fa Duk da Haka Abubuwan na Abdullahi sun Tarar da Halinsa na rashin son Daukan Raini da kuma Wulakanci ga kuma Fada da Fushi.
Akofar gida suka Hadu da Auwal nan ya gaishesu Cike da Ladabi nan yake Fadama Abdullahi yana Bukatar kudi zai siya Handout na makaranta Abdullahi bai yi gaddama ba ya Zaro 5k cikin Walet dinsa ya mika ma Auwal din Ya karba yana ta mai Godiya Yana wajen Har Motar Nazifi ta bacema ganinsa yana Daga masu Hannu Cikin Farinciki ya Shiga Gida yana nuna ma Mama kudin da Abdullahin ya bashi Mama itama tayi ta saka albarka.
Ganin Jidda sai wani kumbure kumbure take ne yasa Auwal din ya Tambayi Ba"asi mariya ta koramai Abunda ya Faru kallonta yayi harda Cizon yatsa yana Fadin"kash...Banso Ya Nazifi ya Karbeta ba naso yau ya Abdullahi ya Chasamin wata Hallita Naga karshen Rashin kunya da Taurin kai.."
Yafada yana Dariya Jidda Dake Zaune saman Cafet a dakin mama tana Yanke kumban kafarta ta Dago tana kallonsa kafin ta maida kallonta kan Mama wacce ke kokarin Zura Hijabi zata yi sallah tace"Mama..Mama kinga ya Auwal ko..?.
Tafada Cikin Shagwaba Mama ta kalli Auwal tana Fadin"Toh Baban Banza Baban gwabo..Ina Ruwanka da ita..? daga kai har Mariya kar wanda ya kara Tankamin Autata Tunda bata Kulaku ba ki kyaleta,kuma sai ka tashi Zuwa salla gashi chan ana Kira a wasu masallatan.."
Ta Fada Lokaci Daya tana Tada Sallah Auwal Yar dariya yayi kawai batare da yayi mgana ba ya Tura Kudinsa alijuhu ya Zura Takalminsa ya Fice Mariya kuma tatashi ta Shige Dakinsu wanda ke kusa da Na Mama Duk cikim Falo Daya,Wanda abaya Ciki da Falo ne Abdullahi yasa aka gyarashi aka Hade da wani Daki aka Fitar ma da Mama babban Falo da Uwar daka sai kuma aka Fitar da wani Daki Shima nasu Mariya,Duka Dakunan suna da Bandaki aciki sai Dakin kusa da na Mama ciki da Falo ne shima agyare yake Nan Zannira ke sauka in tazo ganin gida ko kuma in anyi baki Domin Har katifan kasa akwai acikin Dakin,Daga Wajen Kofar gida kuma Dakin Auwal ne,Gidane babba sosai katon Madafinsu ga kuma Wawaken Filin Tsakar gida ga Tailet din waje na Bahaya da kuma Fitsari.
******
Nazifi yana ijiye Abdullahi a kofar gida bai Shiga ba sukayi sallama ya koma,Yana Shiga Gidan su Amira suka Rugo suna mai oyoyo harda Hafsah wacce ta Chaba ado Daga wajen ya miika mata wayarsa da Kuma Links din Rigarsa bayan ya amsa sannu da zuwanta yace"Bani Ruwa abuta nayi alwala kafin na Shiga Ciki."
Da Sauri ta koma Daki ta Daukomai yayi alwala kana suka Dunguma Dukkansu Zuwa Ciki agida yayi sallarshi kana ta gabatar mai da abinci Tuwon Shinkafa miyar Shuwaka Dayake Cimarsane sai yaci kadan yace ta bari da safe ta Zafafa mai ya Riga yaci Tuwon Dawa wajen Mama Daga haka yaja ya"yansa Zuwa Ciki yana Biyema Shirmensu.
Da sukayi barci da kansa ya Daukesu Zuwa Wajem kwanciyarsu ya kwantar,Yayi musu addu"a,Ya koma Bedroom dinsu ya kwanta ita kanta Hafsah bata Damu kanta ba ganin yanayinsa kar tayi mgana Allura ta Tono garma,Sai dai tayi mai uzuri da gajiyan tafiya da kuma Zuwa Office washegari nan kuwa batasan bacin Ran da suka kwasa agidansu sakina ne bane,da kuma na Jidda bai gama sakinsa ba.
*Anitha...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Janafty*❤️
*Dedicated To:My Habibaty💞Aisha Idris Abdullahi..*
_*Na Sadaukar da wannan Shafin kachokan zuwa gareki FAUZIYA S MADAKI..❤️,Janafty na Matukar Godiya da karamcinki gareni..Nagode kwarai Allah ya bar zumunci*_
*011*
"Washegari ma Haka ya tashi Ba Fara"a sosai Tunda Hafsah Taga haka sai ta kama kanta sanin in ya tashi da irin wannan yanayin Ita yake saukemawa aikuwa Duk Kafa kafanta sai da ta samu nata Rabon.
Jakar yaran na makaranta ya Duba yaga an basu Homework kuma ba"ayi musu ba nan fa ya fara ma Hafsah Fadan Tana da Careless kan ya"yanta Tunda har za"a basu aikin gida Tun Ranar jumma"a ammh tana gayamai bata san am basu yi ba Shuru kawai tayi mai saboda tasan ko tayi mgana bazai saurareta ba ammh laifin na Amira ne domin ita tace an basu Homework Ranar jumma"a Da suka Dawo Daga makaranta sai tace taja Amir ta koya mai suyi Homework Din tare,Tunda Gobe zasu tafi gidan Mama ba Lokaci ashe Amira bata Kama ma Amir din sunyi ba,gashi yanzu Fada ya koma kanta.
Haka ya fice Ranshi bace ko Cikakken kari bai yi ba,Kuma ranar bai Dawo Gidan da Wuri ba sai Dare Nan ne ma yake Fadamata Daga Tudun wada yake Ammi da Daddy na gaisheta sai Lokacin Taga sakin Fuskarsa.
Ranar sati ta zagayo Ranar asabar da kanshi ya kaisu Amira Chan Makarantarsu Ta hadda Daganan kuma ya Biya Gidan mama bai Dawo ba sai pass 12 bai jima da Shigowa ba sai ga Nazifi yazo Daukansa,Dama ko da yazo yana wanka ne,Yana Fitowa ya Shirya a gurguje,ya saka Kaya yace Hafsah ta bashi wasu Takardu Daya bata ajiya ta Dauko ta bashi suka Fice bashi ya Dawo Gidan ba sai wajen karfe Goman Dare agajiye ya Dawo wanka kawai yayi yaci abinci Hafsah tamai Tausa barci ya kwasheshi bai mata bayani ba sai da Safe Lokacin suna karyawa.
Ashe Fitar da sukayi Jiya Filinsa na Gaskiya ya saida wanda suka Siya Tare da Nazifi Kusa da kusa sai shi ya saida nashi Ya cika da kudin Hannunshi ya Siya wani Babban Fili a GRA,shine basu Dawo ba sai Dare sai da akayi Cike ciken Takardu da kuma sallaman Dilallai.
Hafsah ta kallesa tana Fadin"Meyaasa ka saida wanda kuka siya da abokinka Abban Amira..? Yana kurban Tea din Dake Hannunsa yace"Saboda na Gra din yafi Girma Sosai zai isheni na gina 3Flat harda Wadatar Filin Ijiye mota ina so in Allah ya yarda bayan na gama Ginin Gidan mun koma sai na Siya mota ko..? Wanchan kuma bai da Girma Sosai da kadan yafi wanda muke Cikin nan fa.."Kai Hafsah ta gyada kafin tace"Da wannan dan wannan kuma..Allah ya sa albarka Allah kuma yabada ikon Ginawa.."Ya amsa mata da Ameen nan suka cigaba da karyawan Jefi jefi suna Taba Hira.
Bayan yayi wanka Taga bai da Shirin Fita ta kallesa yana Zaune gefen gado yana latsa wayarsa tace"Yau Nazifin ba zai biyo maka ku fitan bane..? Bai Dago ba yace"Ai tun jiya ya koma Kaduna...Sakina ta je mai weekend.."Yar Dariya Hafsah tayi kafin tace"a"a lalle Dole kuwa bazaka ganshi ba kila sai Wani Weekend din."Tabe baki Abdullahi yayi kafin yace"Allah sa tayi mai zuwan ko na marmarina ne,Jiya muna Wajen Siyan Filin nan na Gra ta Kirashi tace ta tadawo bata ganshi ba,Shine bama mu gama Dashi ba nace ya tafi kawai ma karisa awaya kawai.."Hafsah tace"Ka kyauta.."Daga haka ta Dinke bakinta Shima gogan bai ce mata komai ba sanin Halinsa yasa ta Tura Kofar Tailet ta Shige Tana so ta wankeshi kafin ta Fara aikin waje.
Ranar litina kuma Yana office Mijin Zanniratu ya kirashi yana Shaidamai Haihuwan zannira ammh aiki aka mata Tana asibiti an ciro mata yarta mace,Barka Abdulllahi yayi da kuma Sakon sannu ga ita Zannira suna gama waya ya Kira Mama yana Fadamata tace itama yanzu Suka gama waya da mijin Zannira din nan Mama tace yakamata ko Mariya atura taje ta zauna da ita kafin adawo da ita gida Tunda Jidda na makaranta,tana Shekarar Karshe a sakandiri ita kuma Mariya Karatu suke basu da Test shiyasa.
Nan Abdullahi ya amince yace Mariyan ta Shirya tatafi in da akwai kudi hannun mama ta bata tatafi kafin yazo Mama tace Shikenan suka yanke Kiran nan da nan Mama ta Umarci mariya ta Shirya tatafi kaduna ta zauna da yaran Tunda ita Zanniratun tana asibiti,Murna ta kamata Dama ta takura zaman Gida baka zuwa ko"ina nan da nan ta Shirya kanta ta Shirya kayanta,Mama Ta bata 2k tace ta Rike Ahannunta in kuma ta isa takira waya Dayake Abdullahi ya siya mata Wayar hannu Vivo tana Karawa da ita.
Wajen la"asar ta Kira Mama tace ta isa,yanzu ma Mijin Anty Zanniran zai kaita asibitin nan Mama tace in sun isa ta kirata ta hadata da Zannira din ta mata Barka Bangaren Hafsah kuwa Subai"atu ta kirata tana shaida mata Haihuwar ta kuma Tambayeta yaushe ya Dace suje Barka su Duba Zannira din Hafsah tace"Duk lokacin da kika ga ya kamata.."Sai subai tace Jibi in Allah ya yarda ta Shirya zata Biyo da Direbanta ta Dauketa sai suje suyi mata Barka su Dawo kafin Suna kuma yazo Da haka suka Rabu da Subai suna gama waya ta Kira Ammi ta shaidamata ita kuma tace bari ta Kira Mama ta mata barka.
Bayan Abdullahi ya Dawo da Daddare Taji bai mata mgnar ba yana cin Abinci ta kallesa Tana Fadin"Ashe kuma Zannira an sauka Abban Amira..? Ya Dade bai bata amsa ba tama Zata bai jita bane tana Shirin maimaita Tambayar tajisa yana Fadin"Eh dazu da safe megidanta ya Kirani yana gayamin anyi mata C.s ne.."Hafsah tace"Wh haka Subai take Fadamin dazu..Allah sarki Allah Bata lafiya Subai tace zamu barka Jibi kafin suna ya zagayo.."
Yana jinta kamar bazai Tanka ba sai kawai taji yace"Ok.."Daga haka bai kara mgana ba yacigaba da cin Abinsa Gefe daya kuma yana Kallonsu Amir da Amira Dake yin Homework dinsu Hafsah kuwa murna ta kamata ganin Abdullahi ya amince batare Daya yi wata mgana ba Sai da kuma wani Shashe na Zuciyarta na gayamata ai Zannira kanwarsa ce zai so taje ta gaisheta.
Ganin Haka yasa bata kara mai mganar ba sai Ranar tafiyar,Tun safe tatashi da Shirinta sai dai me Bai Fita da Wuri ba su Amira ma mai mashin dinsu ya kira yazo ya Daukesu yace bada Wuri zai Fita office ba yau mamaki ya kama Hafsah sai kuma ta Shanye mamakin Tunanin kila suna da Taro ne,Domin wani lokacin in suna da Taro yakan kai 10 da wani Abu agida kafin ya Fita,Tuna haka yasa bata damu ba Cikin Lokaci tagama Komai na Gidan ta yi wanka ta Shirya Cikin Wata Atamfarta mai kyau da Garari mai kalan green,Sai ta saka Hijabinta gree da Takalminta baki jakarta ma Haka,Gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta ta madubi Abdullahi na Gefe kan gado yana ta Danne danne kan Laptop dinsa Jifa Jifa yana Maida kallonsa kan Hafsah wacce ke ta Shiri acikin Ransa kuwa mamakinta ya kamashi tana nufin wai wannan gayamai datayi Shine azuwan neman izini..? Saboda ta Rainashi bata Daukeshi da Daraja ba kenan toh sai yagani in zata iya zuwa batare da Cewarsa ba.
Bai gama wannan Tunanin Zuccin ba yaji wayarta ta Shiga neman Dauki da Ido Daya ya maida kallonsa kanta yaga ta Daga wayar Lokaci Daya tana Rataya Jakar hannunta Cikin Fara"a take fadin""Uwar muhsin har kin iso ne..?
Dagachan Bangaren Subai"a tace"Eh gani kofar gida...ko sai na Shigo ne..? Hafsah tace"Toh da dai kin Shigo kun gaisa da yayan naki.."Subai Ta rike baki kafin tace"Wai kina Nufin wai yana nan bai Fita office ba..?Hafsah tace'Eh inaga sai anjuma zai Fita.."Tafada tana kallon Abdullahin wanda yayi Saurin Dauke kai kamar bai san kan me suke mganar ba nan kuwa Hankalinsa kacokan yana kan Hafsah.
Subai tace"Nifa bawai na Shigo bane kinsan Halin yaya sai ke Wlh Qawata.."Dariya Hafsah tayi Tana Fadin"Ki fada.Yana jinki Wlh.."Jin haka yasa da Sauri Subai ta katse wayar Lokaci Daya tana Saba Saleem akafadarta ta Fito Daga Motar kirat Jeep tana Fadama Direban bari ta Shiga su Fito tare da Hafsah din yace bakomai Hajiya.
Ko Minti Biyar ba"ayi ba sai ga Subai"atu tayi sallama a tsakar gidan,Hafsah Dake Ciki tayi Wuf ta Fito tana amsa sallamar nata Lokaci Daya tana mata Maraba Falon Subai ta Shigo Tana Fadin"Mu shigo ko mu koma.."Hararanta Hafsah tayi kafin tace"Ku koma mana yar rainin Hankali.."Tafada tana Karban Saleem Dake hannun Subai din kan Daya Daga Cikin kujerun Falon suka yada zango suna gaisawa kafin Subai ta Fara waige waige tana Fadin"Ina ya Abdullahin..? Ko iskanci ne Saboda dai na Shigo..?
Hafsah tace"A'a wlh..Yana Ciki bari na Shiga namai mgana.."Tafada tana Tashi sabe da Saleem ta Shiga Dakin inda ta barshi nan ta iskeshi Cikin kulawa tace"Abban Amira bakaji Shigowar Subai bane..?
Hankalinsa na Bisa Syestem dinsa yace"Naji....!! tazo lafiya..? Yanayin yadda ya amsa mata yasa kawai tasha Jinin jikinta Jiki a sanyaye ta Juya Tana Fadin"Ta Shigo ne ku gaisa wucewa Zamu yi.."Bai ko Dago ya kalleta ba Har ta Fice,Ba Dadewa Shima yabi bayanta Suna cikin Mgana da Subai ya Fito Cikin Jallabiyarsa mai Ruwan kasa,Da Sauri Subai ta gyara tana Fadin"Ina kwana yaya..?
Yana Tsaye yace"Lafiya lau ya yaran..? Yafada yana mikama Hafsah hannu ita kuma ta sai ta mikamai Saleem Dake hannunta Karbansa yayi yana Fadin"Yayi yawo sosai.."Subai tace"yaya yayi fa 3month.."Tafada tana kallonsa da Mirmishi yana Tsayen ya sake Fadin"Duk da haka dai Subai"atu...yau kin zo mana Wuni ne..?
Daga ita har Hafsah Da kallo Suka Bi Juna kafin Subai ta maida kallonta kan ya Abdullahi Tana Fadin"Wuni kuma yaya..? A"a ba wuni nazo ba..Hafsah bata gayamaka ba,? Abban Muhsin ne ya bamu Direba zai kaimu Kaduna muje mu Dubo Anty Zannira kafin Ranar suna.."Kai Tsaye yace mata"Eh ta Fadamin mana.."
Cike da mamaki Subai ta kalli Hafsah kafin tace"To yaya ai yau ne zamu je din...Shiyasa na Fito da Wuri saboda mu Dawo da wuri kaga Hanya bakyau.."Mirmishi yayi kafin yace"Ok Nidai cikin Zencenta naji tana Gayamin Zaku Tafi Barka kaduna...."
Jin Haka yasa Hafsah tace"Ammh Abban Amira na gayamaka."Tafada Cikin Raunin murya kai Tsaye yace"Wa kika gayamawa..?ni...?Kika dai yi Zencenki ina jinki,na dauka kinaa mganarki ne kawai Domin wannann Zence ne na mata ban Daukesa aneman izinin ba.."Yafada yana Mikama Subai Saleem wacce tayi Jugum Tana kallon Ikon Allah.
Idanuwan Hafsah ya kawo kwallah Cikin wani Rauni tace"Na dauka danaji kace Ok ka amince naje din ne.."Karamin Tsaki yaja kafin yace"Saboda kin Rainani ko..? Haka kurum Saboda Subai"atu ke Auranki sai ta Shiryamiki tafiya ke kuma ki Hau ki zauna Batare dani mijinki kin Tuntubeni ba kuma da kike mganar kin gayamin Daga Ranar kin karamin mgana..?Kin sameni kin ce Abban Amira muna so zamuje Mu gaishe da Zanniratu kafin suna..? Kin sameni..?
Yafada yana Tsare ta da ido Jikin Hafsah yayi sanyi kawai sai ta Dukar dakai Hawayen idanuwanta suna kawowa Subai kuwa addu"a take aranta Allah sa kada Fadan ya Dawo kanta Tabe Baki yayi ya juya yana Fadin"Kinga kenan baki da Tafiya sai ki bari Ranar suna sai ki Tafi..Shima in kikamin irin wannan Tafiyar kinsan Allah bazaki ba.."Yafada kai Tsaye yana Shirin Shigewa Bedroom
Da Sauri Subai tace"Don Allah yaya kayi Hakuri munji munyi kuskure bazamu kara ba..Ammh Don Allah yanzu kabari muje mu Dubata bazamu yi Dare ba da yardan Allah...."Waigowa yayi Lokaci Daya yana Hararan Subai din Wacce ta sadda kai kasa gabanta na Faduwa cikin Gadara yajuyo yana kallon Subai"atu Lokaci Daya yana Fadin"Kinsan Allah.? Bafa zataje ba ayau..Sai dai in ku Rushe tafiyar yau wlh...In kuma bazaku Rusheta ba ki kama Hanya ki Tafi Tunda ke kin gayama Mijinki kuma ya barki har ma yabaki Direba kinga ke sai ki kama Hanya ita kuma Ranar data Shirya tafiyan in ta nemi izinina na barta sai tatafi taje ta gaisheta ta mata barka ta Dawo.."Daga haka bai kara komai ba ya Shige Ciki.
Hafsah Data ke Rike Hawayenta sai gasu sun Zubo Sharr,Subai ta kalleta Tana Fadin"Wai ke baki Fadamai bane..? Hafsah ta Dago idanuwanta cike da kwallah tace"Wani irin ban gayamai ba.? Ina Ranar da mukayi waya da Daddare bayan ya Dawo muke tadin Haihuwan dani Dashi anan ne toh nake gayamai mun yi waya Yau zaki Biyomun mu tafi muyi mata barka yace min Toh kinji Dalilin Daya saka ban karamai mgana ba.."Ta fada Lokaci Daya tana Share kwallar Idonta.
Subai ta saki ajiyar Zuciya Tana Fadin"Toh yanzu ki Tashi ki Bishi ki gani ko zai yarda mu tafi gaskiya in bamu je ba bamu kyauta ba Duk da Mariya na chan Jiya Mama da Inna Abu fa sukaje suka Dubata suka komo.."Hafsah tace"Karma na batamiki Lokaci Subai ki tafi kawai kice ina mata barka Duk da daman na Kirata awaya na mata sannu..Ranar suna in yabarni sai na taho..
Subai tace"Kina ganin in kika lallasheshi bazai yarda ba.."Hafsah tayi yaken Dole lokaci Daya tana Fadin"Hmm Kema Subai da wata mgana kike ina ce kin Rigani sanin Halin yayanku kaifi Daya ne in yace Abu toh hakan take ba Chanzawa Tunda yace bazani ba Toh fa din bazani ba Sai dai wani Lokacin kawai..'Subai tace"Kai kai..Ya Abdullahi Danja ko Daru ne ma Zance.."Sai da ta Fada kana ta koma tana Rufe baki Lokaci Daya Tana kallon Hanyar Bedroom din Hafsah idanuwanta Duk suna waje
Mikewa tayi tana Saba Saleem Lokaci Daya Tana Fadin"Zan tafi Hafsah in naje zan gayamata kin so Zuwa yayanmu yayi Tsiya.."Tafada tana yar dariya Hafsah ma yaken tayi ta mike tana Fadin"Allah kaiku lafiya ya Dawo daku lafiya..ki gaishemin da ita Don Allah."Subai tace"Zataji insha Allahu sai ki lallabasa ya barki zuwa suna mu Tafi Tun ana gobe mu dawo Washegarin suna.."
Kai kawai Hafsah ta Kada kafin tace"Wa..? Lalle nema ina ma laifin Ranar suna mu kwana Daya bazai barni ba zai ce Ko Biki ne iyakarta kenan.."Subai tace"Gaskiya Qawata ina jinjina miki wajen Fama da yayanmu Wlh bazan iya ba.."Tafada tana Bata rai Hafsah batayi Mgana ba illah kada kai kawai datayi.
Tsakar gida suka Fito Subai na kara Saba Saleem Bisa kafadarta Tana Fadin"Lokacin muna gida munci Ubanmu ammh Mariya tace Har gwara kila lokacinmu yanzu basu da wani Motsi ko Fita Zakayi sai da izininsa Auwal ya Fadamin Jidda ce kecin kwal ubanta a wajensa.."Ta karishe tana yar Dariya Kada kai Hafsah Kawai Hafsah tayi tana Fadin"Ai fa..Sai ta rika kiyayewa kamar kowa.."
Har Kofar gida Hafsah ta Raka Subai Tana Dagamata Hannu,Har Motarsu ta bace ma ganinta kana ta koma Cikin Gida,Tana Shiga Suka ci karo da Abdullahi ya yo Shirinsa na zuwa Office sabe da Jakar Breifcase dinsa,Ko kallonsa batayi ba kawai ta saka kai ta Shige Dakin su Amira ta Shige ta Haye yar katifarsu kawai ta fashe da kukan Data ke ta Rikewa tun dazu Labulan Dakin ya Daga yana kallonta Cikin mamaki,sai da yadan Jima kafin ya kada kai yana Fadin"In kin gama kukan Jin Dadin ni na Fita.."Daga haka kawai ya sauke Labulen ya Fice Tana daga kwance ko Dagowa batayi ba Ballatana ta amsa mai.
Tana jinsa ya bude Dakin da Mashin Dinsa yake ya Fito Dashi ya Goggoge ta kafin ya Fice Tana Jin Tashin Mashin din nashi da kuma Tafiyarsa ammh bata Daga ba,Sai da tayi kukanta ya Isheta kana ta Share Hawayenta Tana Nan kwance Taji wayarta na Ringing Daga Falo ta Fito ta Dauki Wayar ganin Umman Sadiq yasa ta gyara muryanta ta Daga Kiran suka gaisa nan take tambayanta su Amira tace suna makaranta,ita Hafsah ke gayamata Haihuwan Zannira Umman Sadiq din tace ai mama ta Kirata ta gayamata in ta samu Dama Zatazo tayi barka Zahra ce batajin Dadi nan Hafsah ta mata ya Jiki basu Dade suna mgana ba sukayi sallama.
Agaskiya Hafsah tayi Dacen Surukan kwarai baga Mama ba baga Ummin sadiq ba wanda Duk kwannan Duniya sai ta Kirata taji ya suke..? Matar bata da matsala ne sosai,Abdullahi ma Suna yawan mgana Sosai,Duk da in ba ya Fada ba ba wanda zai ce Ba Mama bace ta Haifesa ba Saboda bai Taba nuna wani bambamci tsskanin Mama da Umman Sadiq ba,Gidan kakaninsa kuwa yana Zuwa Sosai yaje ya Wuni ya Dawo,koda bazai kwana ba Harda Nazifi sun sha Zuwa in sukaje yaBiya yaga Umman Sadiq sai dai in sun Daawo Hafsah taga sako inji mama kana zata san sun je gusai aranar.
Har yammah Hafsah bata saki ba ko Girki batayi ba,Complex ta jikama su Amira suka Sha Bayan sun Dawo Daga makaranta Subai"atu kuwa ta isa kaduna Lafiya ta samu ma an sallami Zanniratun ta koma Gida,Da taga Subai ita kadai sai da ta tambayi Hafsah Wanda daman Ita Subai din ta mata waya kan tare zasu zo nan Subai take basu labarin Abunda ya Faru baki Zanniratu ta Rike kafin tace"Na Shiga goma ni Zanniratu dama wai Har yanzu Ya Abdullahi bai chanza Halinsa ba..?
Mariya na gefe tace"Sai ma Abunda ya karu Anty...Kinsan Allah da bai amunce ba da ko ke bazan zo na zauna miki ba.."Zanniratu tace"Lalle ya Abdullahi isar nan da ikonsa Na nan Tare dashi Haka Aliyu na ke Fadin Yayan naku ya cika Fadin rai da isa ni kuma nayi ta karesa Duk da dai nasan gaskiya ya fada,nima Jiya Daya Kirani yayi min Barka Kunsan me yace min..?
Gabadayansu suka Girgiza kai Cikin Takaichi tace"Wai ina Dauka sai cemin yayi mai cikin Haihuwa..Nace kamar ya Ya Abdullahi..? Bude bakinsa sai cewa yayi Wai na cika haihuwa duka duka yaushe nayi Auran har nayi ya"ya har Biyar..?Subai da mariya suka saka Dariya kamar Cikinsu ya kulle Mariya tace"Kadan Daga aikin Ya Abdullahi kenan Anty Zanniratu..
"
Subai tace"Yau ai naga lukutar masifa..Kiri kiri yace Hausi baza je ba....Sai dai in mu sauya Ranar Tafiya.."Zanniratu tace"Allah sa ya Barta zuwa suna Toh.."Subai tace"Yace in ta nemi izini ya yarje zata zo...In kuma ta karamai irin na wannan karon yama Rantse bazataje ba...."Mariya tace"Kuma ya gama mgana Wlh..Kaifi Daya nan ba"a sauyata.."
Zanniratu tace"Ni wlh na zata ya sauya..ashe Hali na nan..Don ma Hafsah mai hakuri ne da yanzu anji kansu.."Mariya tace"In batayi Hakuri ba ya zatayi Anty..? Ya Abdullahi ya wuce Duk Tunaninki kan Ra"ayinsa da Jin kansa da isarsa uwa uba kuma Masifarsa kowa neman Tsari yake da Ita Har ya Auwal kuwa.."
Zanniratu tace"Allah ya kyauta..ni Lokacina Abunsa bai kai Haka ba Ko domin ina kiyaye masa ne,Ammh nifa Lokacin kan Samari munsha Fama dashi Sosai Sai da nayi Aure kuma Komai ya kare.."Mariya tace"Yanzu ai Jidda ce ke shan Wahalarsa.."Nan ta Shiga Basu labarin Abunda ya Faru Ranar har Yaya Nazifi ya kwaceta.
Subai tace"Wai ni Nazifin ya suka kare da wannan yar Jinkan matar nashi..? Tanan tana aikin nata a Abujan kenan..? Mariya tace"Eh gaskiya tana Abujan..kwanaki naji inna Abu tazo suna mganar da Mama kan cewa Tana Abuja sai dai in Yaya Nazifin ya samu Lokaci yaje mata Weekend.."
Zanniratu tace"Tabdijam...wannan wani irin Aure ne anyi ba'ayi ba kenam.."Subai tace"Ke Duk Abunda ya Faru shi yajama kansa...Auran jari yayi sai kuma yaga karshensa.."Mariya tace"Haka ake ta Fadi ma a anguwa..mudai shuru muke aminin ya Abdullahi ne karka Tofa mgana takai mai Shima irin ya Abdullahi ne akwai son Girma.."Gabadayansu suka Sheke Da Dariyan Nishadi da ka gansu kaga yan"uwa Da suke tsananin Son Junansu Jaririyar na Hannun Subai Shi kuma Saleem na Hannun Mariya sun kule Cikin Bedroom Falo kuma Kanwar mijinta ne sai wata yar Dattijuwa da uwar mijinta ta Turo mata ta zauna mata na sati Tunda aiki aka mata.
Bangaren Hafsah kuwa Har Abdullahi ya Dawo ya Isketa batayi Girki ba kuma ko wanka bata sake ba Tun kayan Shirin Zuwa kaduna barka ne ajikinta.
Bayan Sallar Isha"i ya Dawo koda ya Shigo Amir yayi barci sai Amira ta Rugo tana mai oyoyo ya Tarbeta ya Dauketa yana Tambayanta Amir tace yayi barci Sun kariso Tsakiyar Falon inda Hafsah ke zaune tana latsa wayarta Amira tace"Abba ina jin yunwa..".
Kai Tsaye Abdullahi ya kalli Hafsah Cikin mamaki yana Fadin"Baki yi girki bane..? Amira ke kukan yunwa fa kina jinta ."Batare da ta Dago ba tace"Ban girka ba.."Galala yayi yana kallonta kafin yace"Saboda mene..?kai Tsaye Hafsah tace"Bakomai kawai Ra"ayi.."Shi yama manta Abunda ya Faru da safe Cikin kulawa yace"Baki lafiya ne..?
Kai ta girgizamai kafin tace"lafiyata kalau..."Jin haka yasa ya gane Rainin Wayau ne kawai, kawai sai ya kada kai ya Sauke Amira yana Fadin"Kinga Mamata bari na fita na siyo miki abinci ban Riko muku komai ba na manta.."Sauketa yayi Lokaci Daya yana Barin Falon tana jinsa yakara Fita Da mashin din nasa batare daya ma kara kallon Barayin Datake ba.
*Shakira...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Janafty*❤️
*Dedicated To:My Habibaty💞Aisha Idris Abdullahi..*!
*Godiya Tare da Jinjina mai Hade da Fatan alheri zuwa gareku Dimbim Masoyana na Nesa Dana kusa,Hakika naga Salon Soyayyarku ga wannan D'an karamin Labarin nawa mai Taken MASIFAFFAN MIJIN HAFSATU...❤️,Ina godiya Sosai ga Sharhinku da kuma Kayattacen Sakonninku Na Soyayyah da kauna zuwa gareni Nagode Sosai Allah ya saka da alheri Godiya Gareku Masoyana na Wattpad da kuma WhatsApp,Allahu ya bar Zumunci Janaftyshakira nayi musu Son Kauna Mara iyaka...*
*012*
"Tana nan Zaune har ya Dawo Dauke da Ledoji Guda Biyu,Koda ya Dawo Amira tayi barci Tashinta yayi ya bata Ledan mai Dauke da gasshiyar kaza,sai Take away din Jalop din Shinfaka sai Fura.
Sai da yaba Amira taci ta Koshi kana yaci Sauran ya Tada ita yakaita Tailet tayi Fitsari ta wanke Hannunta da Bakinta Da kanshi yakaita Dakinsu ita da Amir Daya Rigata yin Barci Hafsah na Zaune yazo ya wuceta ko kallo Bata ishesa ba itama Haka Bata kara Bi ta kansa ba sai ma ta Kishingide kamar mai Barci Saboda Bacin Ran Abunda ya mata Haka kurum Taji bazata iya Controling Din Fushinta akan karfin Ikon da Abdullahi ke nuna mata Lokaci Bayan Lokaci ba.
Sai wajen 12am na Dare kana ta mike ta Tattara Lodojin da suka barsu nan Tsakar Dakin ko Kazar basu Cinye ba da Shinkafar,Ta kwashe komai ta Kai Kicthen ta saka Cikin Fridge din Kana Ta Rufe Kitchen ta Dawo Daki ta kashe Wutar waje ta kashe na Falon Lokaci Daya ta Kulle kofar Falon Dakinsu Amira ta Shiga ta gyaramusu kwanciya Hade da yi musu addu"a,kana ta Fito ta Shiga Bedroom dinsu ta iske Tuni Abdullahi ya Dade da yin Barcinsa mamaki ya kamata wato Ita ke kidanta Tana Rawanta bai ma Damu ba kyafci tayi ta Shiga Taiolet Tayi wanka Lokaci Daya ta Dauro alwala tazo Tayi Shafa"i da wuturi Ta Dauki Filo ta Jefa kasa ta kwanta Bayan Ta Dauki Blanket ta Rufu Dashi.
Da asuba da Abdullahi ya tashi yaga Hafsah a kasan Cafet Tana Barci Mirmishin Takaichi yayi acikin Ransa kuma yana Fadin zan koya miki Hankali Hafsah ko Kallonta baiyi ba ya Shiga Toilet yayi wanka Tare da Dauro alwala yazo ya saka Jallabiya ya tsallake Hafsah zuwa masallaci sai bayan ya Fita ne Hafsah tatashi itama ta Shiga tayi wanka tazo ta Tada salla,Ganin har wasu masallatan sun Tada sallah.
Bai Dawo masallaci da wuri ba Sai da Haske ya bayyana koda ya Dawo Tagama komai hatta su Amira sun Shirya Jiransa kadai suke shima Sama sama ya Shirya ya kwashesu zuwa makaranta Dagachan ya wuce wajen aiki,Haka Zamansu ya kasance Hafsah ita ta Dauko Tsiyan sai Abdullahi ya nuna mata yafi ta sanin kan Tsiya Shima kawai ya Fita Batunta yayi Banza da ita bai ma Nuna yasan me take ma Fushi ba.
Dole kanwar naki Hafsah ta watsar da Tsiyan nata ganin Uban gayyar dai bazai Kalleta ba Ballatama ya bata Hakuri Ranar data Fara gaisheshi da safe kafin ya amsa sai da ya murmusa Lokaci Daya yana Fadin"Lafiya lau Hausi...Kin gama Gaban dani..? Shagwabe mai kawai tayi Lokaci Daya da Hararansa Batace komai ba Shima kawai sai ya Biyemata Kamar Babu Abunda ya Faru,Ganin yasa Hafsah ta Sakankace cewa Abdullahi zai barta Zuwa Suna.
Ana Gobe Suna Subai"a ta Kirata awaya Tana gayama ta Gobe ne zasu Tafi sunan Saboda Mama tace su Tsaya su Tafinma da Anty Zanniratun Sako Zuwa Gobe,Tace mata Su Hadu gidan mama Gobe da Misalin karfe 8am na safe Nan Sukayi sallama,nan take Hafsah ta Kira Ammi tana Fadamata itama kuma Tace zata Turo Direba da sako ya kawomata ta kaima Zanniratun In ta samu Lokaci ko Bayan suna Hafsah zata Rakata Taje ta mata barka.
Zuwa Yammah Ammi ta aiko Da sakon Atamfofi Guda Biyu masu kyau da Tsada sai Babban pampers mai Guda 50,Da Rigan yarinya mai kyau itama Hafsah tayi ta Jin Dadi,tace ta Huta Siyan wani abu sai tace ita Da Ammi kuma Daman ta sani Harda natan Ammi ta Hado sanin ba wata sana"a takeyi ba Duk da Babu Abunda ta nema ta rasa Abdullahi ya Tare mata gaba da baya Sai dai Abunda Ba"a Rasa ba.
Abdullahi na Dawowa ta kwaso kayan Tana nunamai Ya amsa ya gani yayi Godiya nan yake gayamata ya bama Mama 15k ta hada ta siyan ma Zanniran wani Abu sai a aikamata Dashi,Danashi dana Hafsah nan tayimai Godiya Bata gayamai Zuwa Zencen Sunan gobe ba sai da zasu kwanta kana ta gayamai bai ce mata komai ba yace Allah ya kaimu Sai da safe Bayan ta gama Shiryawa Ranar ma bashi ya Kai su Amira makaranta ba Mai mashin dinsu ya kaisu Yana kallon Hafsah tana ta Shiryawa sai da Tagama Shirya kayanta Cikin Karamin akwatinta na Kayanta kala Daya da Hijabi wanda zata Sauya na gobe sai sakon Ammi.
Abdullahi ma Shirin Fitan yake Domin ya gayamata Za"a Fara Ginin Gidanshi na Gra,Domin har an kawo Siminti da Bulo,da kasa Tun Shekaran jiya zai Fara Biyawa Yayi mgana da ma"aikatan kafin ya wuce wajen aiki,Subai"atu sai kira take tana Fadin Hafsah tayi Sauri Gata Gidan Mama.
Sai da ya Bari ta saka Hijabi kana ya kalleta yana Fadin"Wai ina zaki ne naga kina saka Hijabi..?Cikin Dariya Hafsah tace"Kaima da wata mgana..Yau ne fa Sunan Zannira baka ga Subai ma Sai Kirana take ba Suna Gidan Mama suna Jirana."Kai Tsaye yace mata"Au kin gama Fushin Dani ne..? Yafada yana kallonta kai Tsaye jin haka yasa Jikinta yayi sanyi tayi galala tana kallonsa yana Saka Takalminsa Sawu Ciki yake Fadin"Babu inda zaki...Tunda har ni nan zan Hanaki Abunda iko na ne ammh ki Nuna min ban yi Daidai ba ki Dauki gabadani na kwanaki Kidaina Dafa abinci kina ma ya"yanmu Horo da yunwa Saboda Ni na Haifesu ko..?
Yafada Lokaci Daya yana mikewa Ido ya sakarmata ganin Har Hawayen Idanuwanta sun Fara Zubowa Cikin Bacin Rai ya Cigaba da Fadin"Kyaleki nayi naga iya Gudun Ruwanki...naga inda karshen Tsiyanki zai kai ashe Babu inda zai kai...Na bari ne dama sai kin gama naki ni kuma na Fara nawa..Suna ne Bazaki ba..Sai na gani Tsakanin Hafsah da Abdullahi wanene ke Auran wani.."Yana gama Fadin Haka ya kwashi Jakarsa da Key din Mashin sa ya Fice yana Fadin"Yau ma ki Dauki Gaban dani..Karki Dafa komai ki bar yaran da yunwa kinji ko.."
Daga haka ya fice ya barta nan Taaye tana Tsiyayan Hawaye,Tana Jinsa ya Fito da mashinsa ya Fice Bata san sadda wani kukan bakinciki ya Turniketa ba,Ta Fada kan gado kawai ta sakeshi wiwi kamar karamar yarinya wani Bakinciki da Takaichi na cin Ranta da Zuciyarta Tana Cikin kukan ne Taji karar wayarta Ta Dago kanta Shabe Shabe da Hawaye ta Jawo Jakarta Inda tasaka Wayarta ta Bude ta Dauko sai taga Ammi ne ke Kiranta da Sauri Ta Daga Kiran Lokaci Daya Ammi na Fadin"Hafsah kun tafi ne..?
Jin Haka yasa wani kukan ya kara Zuwarma Hafsah kawai sai ta sakarma Ammi kuka Cikin Firgici da tashin Hankali Ammi ke Fadin"Innalillahi...Hafsah meya faru..? Ina Abdullahin..?ko wani Abu ne ya Faru daku..?
Duk atare Ammi ta Jero mata wadanan Tambayoyi,Ammh Hafsah ta kasa mgana Saboda kuka Cikin Tsawa Ammi tace"Dallah kiyi mgana lafiya kike ma mutane kuka..?
Jin haka yasa Hafsah tace"Ammi..Ya hanani zuwa Sunan ne..."Tafada Cikin Shesshekan kuka Wani Karamin Tsaki Ammi Taja Lokaci Daya tana Fadin"To Shine kuma Abun kuka..? Nifa har kin saka gabana ya Fadi Allah yasa Daddynku yana Barci kila da kin saka Jininsa ya Hau in yaji wannan Shirmen naki.."Cikin kuka Hafsah ta kara Fadin"Ammi Ranar fa Haka ya hanani zuwa barka yauma har na Shirya yace bazani ba.."Ammi tace"Sai me.
? Sai me in ya Hanaki..? Inace ba kanwarsa bace da suke Uba Daya..? Yafi ki son kije wajen yar"uwansa kuma yahanaki sai kiyi Hakuri ki zauna Ranar daya Lamunce miki sai KiTafi Hafsah.."Cikin Takaichi Hafsah tace"Ammi Su Subai na chan gidan Mama suna Jirana kuma kowa zai je Ammi sai ni kadai sai ya Hanani.."
Ammi tace"Tsiyana Dake sakarci Maman Hamzana,Suna yafi Mijinki ne..? Kuma na Tabbata wani Laifin kikemai Shiyasa ya Hanaki Zuwa Sunar ko...?
Shuru Hafsah tayi taki mgana Jin Haka yasa Ammi tace"Hmm ni na sani..Meyasa Hafsah wani Lokacin kin cika Wauta ne..! Karfa ki manta ke matar aure ce wacce ke karkashin mijinta akullum ina gaya miki Aljannarki Tana karkashin Kafar mijinki ne,sai ya Daga Zaki Shiga,kuma Aure Bautar Allah ne,Kuma Shi Aure dan Hakuri ne kinga in kikace bazaki yi Hakuri ba Wlh zaki Sha Wahala ne kawai Hafsah.."
Tura baki Hafsah tayi kafin tace"Toh ni Ammi me nake mai..Iya Biyayyah Wlh ina yi da Hakurin da kikace.."Ammi tace"Toh in kinayi me ye na kuka Saboda yace bazaki suna ba..? In kina yi sai kiyi Hakuri ki Share Hawaye dama ai Aure ya gaji Haka.."Cikin Marairaicewa Hafsah tace"To Don Allah Ammi ki Kirashi ki Rokeshi Da Allah da Annabi ya barni naje.."Ammi ta Rike Baki Tana Fadin"Ni Jikar Hadiza..? Rufamin asiri Abdullahi na ganina da kima Ina Ruwana da Shiga Hurumin da ba nawa ba..? Yanzu bamu da iko akanki Hausi Kin bar karkashin ikonmu Tun Ranar da igiya uku ta Hau kanki kikabar Karkashinmu Zuwa karkashin Mijinki,Saboda haka yafimu iko Dake.."Bakin Hafsah kamar ya Fado Tace,"Kai Ammi yanzu dai baki Kiransa ko..?
Ammi tace"A"a wlh karya da Ciwo..Na kirasa nace mai me..? Haka kurum Jama kai Raini da lalacewa sai na Kirashi nayi mai mgana kan Abunda yake da iko akansa..?ko Babanki yaji labari sai ya batamin rai bakisan kwanciyar Hankalinsa da nawa Ba Yana da Nasaba da Kowaccenku tana zaune lafiya Gidan Mijinta ba kuma Dukkanku kun yi sa"an Mazaje na gari ya"yan albarka Da Dangin Mijin na gari nan Shekaran jiya Abdullahi yazo yana gayama Babanki Ya siya Fili a Gra har zai Fara Gini Dukkanmu muka sakamai albarka kinsan anyi..?
Ta karishe Fada da Sigan Tambaya Hafsah tace"Bansani ba Ammi..'Ammi tace"Toh Ina laifinsa...kiyi maza ki Share hawayenki ki kirasu kice su tafi Baxaki samu zuwa ba In Ya dawo kin Lallabasa in ya barki bayan suna sai Ki rakani muje mu mata wuni mu Dawo.."Hafsah tace"Shikenan Ammi nagode..Ki gaida Daddy in ya tashi..Anty Hadiza Shuru bata Haihu ba..?
Ammi na Dariya tace"Sai ki kirata kice mata taki Haihuwa..inaga Cikinta da Sauransa bai wuce wata Takwas bafa Girman ciki ne da ita irin na Walid ne..'"Hafsah tace"Na kosa ta Haihu naje Kano na Rabu da Zuwa Kano Ammi Tun sanda Anty Hadiza ta Dawo Daga Saudiya.."Ammi tace"Toh shine me..? baku na waya da juna ba..?
Hafsah tace"Eh Ammi.."Ammi tace"Toh banga Abun Damuwa ba..Kowa ya zauna agidan Auransa yaci gaba da Bautar Aure.."Baki kawai Hafsah ta Tura Ammi Kuma ta Fara Fadin"Umm.Auta..Autan Zinariya Autan Hamza kuma Maman Hamza..Kuma kanwar Hadiza Ko Hausi.."Jin Kirarin Ammi yasa Hafsah ta manta bacin Ranta ta Shiga Dariya Ammi bata kashe wayarta ba sai da ta tabbatar da Hafsah ta saki Ranta.
Suna gama Waya da Ammi Hafsah taci karo da Kiran Subai"atu wajen Guda Biyar Lokacin tana waya,Da sauri ta Kirata Tana Daga Kiran Subai tace"Wai Gimbiya matar Ya Abdullahi ko kin Fasa zuwa ne..? Kefa muke ta Jira Har yanzu baki kariso ba..?
Cikin sanyin Murya Hafsah tace"Ku tafi kawai Subai...Bazan samu zuwa ba..'Cikin mamaki Subai tace"Bangane mu tafi ba kawai..? Ko Ya Abdullahin ya hanaki ne..?
Hafsah tace"Eh yace bazani ba..Ku tafi kawai in kunje ku gaisheta,Kuyi Hakuri da bata muku Lokacin danayi Kuma Don Allah in zaku iya ku Biyo ku karbi sakon Ammi ku kaima Zanniran.."Subai tayi karamin Tsaki kafin tace"Bansan Meyasa Ya Abdullahi ke haka ba sam..."Hafsah dai Shuru tayi batayi mgana ba Subai tace"Shikenan in da yuyuwa zamu Biyo..Baya dai kyautawa.."Tana jin Mama na Tambayan me yafaru Subai na Fadamata yadda Hafsah ta Fadamata bata tsaya Jin me Mama ke Cewa ba ta kashe wayarta kawai.
Tana nan Zaune Har su Subai"a suka kariso basu wani Tsaya ba Ta basu sakon Ammi da 3k cikin kudinta Data ke dashi tace su kaima Zanniran,Har waje ta karasu Ita da Direban Mahmud ne,sai Jidda,Da inna Abu sai Inna Talatu wata kanwar Mama ce,Tana Daga musu Hannu suka kule ma ganinta kana ta koma Cikin Gida ta Shiga Falonta kenan Wayarta ta sake neman agaji,Tana Dubawa taga Umman Sadiq ce ta Daga suka gaisa Kana Umman Sadiq ke Tambayan Hafsah ya Suna..?
Hafsah tace"Bata je ba tana gida..? Cikin mamaki Umman Sadiq ke fadin"Kina gida?toh saboda mene baki je sunan ba..? Ko ba yau bane Sunan Zanniratun..?
Hafsah tace"Yau ne Umman..Har na Shirya sai yace bai yarda naje ba..Su Subai"atun ma sun wuce yanzu.."Umman Sadiq bata Jira cewar Hafsah ba kawai ta yanke Kiran ta Kira Abdullahi Lokacin yana Office yana Tsaka da aiki yaga Kiran Umman Sadiq bayan ya Daga sun gaisa kai Tsaye tace'"Meyasa kake Tauye Yarinyarnan ne Abdullahi..?
Jin Tambayar nata yayi ta mishi bambarakwai cikin mamaki yace"Wata yarinya kuma Umma..? Cikin Takaichi tace"Kaniyarka nace..Kaji ko..? Nace kaci Gidanku Abdullahi.."Jin Haka yasa ya natsu yana Sosa kansa Cikin Lallashi yace"Umma kiyi Hakuri Don Allah bangane inda mganarki ta Dosa bane.."Umman Sadiq tace"Miye Dalilinka na Hana Hafsah zuwa Wajen sunan Zannira Kowa ya tafi sai ita kadai..?
Jin haka yasa ya gane bakin Zarensa Ransa ya baci wato Kararsa Hafsah takai kenan lalle Cikin Saukar da kai yace"Umma ki kyaleta Hafsah ta Fara Rainani ne.."Umman Sadiq tace"Toh kai waye da baza"a Raina ka ba..! ? Ka Fita daga idona na Rufe Abdullahi banda mugunta ka Hanata zuwa suna sunan ma na yar"uwanka kowa ya tafi sai ita kadai.."Kansa na kasa yace"kiyi Hakuri Umma.."Bata Damu ba tace"Bawai mganar Hakuri bane kayi maza ka Kirata awaya ka bata Izinin tafiya yanzu kafin yan Tafiyan su mata Nisa kaji ma na gayamaka..'Ransa amatukar bace yace"Naji Umma Shikenan zan yi yadda kikace.."kyafci tayi Lokaci Daya tana yanke Kiran wayar yabi da kallo yana Sauke Numfashi acikin Ransa kuma ayyana Yadda Hafsah ta fara ganin gadon barcin harda zai Hanata zuwa waje ta Kira Umma takai kararsa
Ita kuwa Hafsah batasan aikin da Umman Sadiq tayi ba Tana Zaune tana latse latsen wayarta Sai ga Kiran Abdullahi sai da gabanta ya Fadi da sauri ta Daga ko Sallamanta bai amasa mata ba, yace mata"Kin kyauta Tunda bakin ki ya iya kai karana..Sai ki Shirya ki tafi Allah ya Kiyaye Hanya Hafsahtu.."Jin haka yasa tayi kalan Tsausayi kafin tace"Wh Allah ban kai karanka wajen kowa ba..Umma ce.."Wannan damuwarki ce ban ce kimin wani Dadin baki ba ki Shirya ki Tafi kawai Malama.."
Yafada yana Shirin yanke Kiransa da Sauri tace"Toh don Allah na kwana sai gobe na Biyosu mu dawo.."cikin kulufuwa yace"Bama kwana Daya ba in zaki iya bari ma sai ta yaye Yarinyar Duk Dayane awajen Abdullahi..Tunda kin nuna ni ban isa dake ba Hafsah ai babu kuma Abunda zan kara cewa Duk Abunda kika yanke Daidai ne.."Shuru tayi batare Datayi mgana ba Shima bai Jira cewarta ya Datse kiran Tsalle ta Buga Tana Murna nan da nan ta Kira Subai tace Suna ina ne..? Tace yanzu suka wuce Danmagaji, Nan Hafsah tace su Jirata gatanan zuwa Cikin mamaki Subai tace"Ya barki ne..? Hafsah tace"Eh Umma ta kirasa ku jirani yanzu zan hau adaidai nazo na sameku.."Cikin Jin Dadi Subai tace"Yauwa har naji Dadi sai kinzo...Direba Don Allah samu waje ka faka.."
Dama kayanta na Shirye Hijabi Kadai ta Zura ta Dauki Jakarta da key din Gidan sai karamar Jakarta na Tafiya ta Rurrufe ko"ina Tana Kulle gidan ne sai ga Almajirinta yunusa Kudi ta bashi tace bata nan sai gobe zata Dawo,Tana Fitowa ta samu mai adaidaita tace ya Fara kaita Gidan Mama kana Allah yasa Tana da kudi wajen 5k a Hannunta Duka ta Dauko Gidan Mama ya kaita ta bata key din Gidan,ita kanta Mama taji Dadi Dataga Hafsah zataje agurguje tamata sallama ta Fice Tana Cikin adaidaita zuwa kwangila ta Kira Abdullahi kamar bazai Daga ba sai da ta kusa yankewa kana ya Daga yana Fadin"Lafiya..?
Cikin Sanyin Murya Hafsah tace"Dama zance ne Don Allah ka Kira mai mashin dinsu Amira kace in ya daukosu ya kaisu gidan Ammi Tunda gidan mama basu Mariya ita kadai ne zasu dameta ne kawai gwara suje gidan Ammi kafin gobe.."batare Daya Tankata ba kawai ya katse Kiran Batayi mamaki ba ta maida Wayarta jaka aranta kuma tace Koma Tsiyan ne in ta Dawo sai su Dora.
Cikin Lokaci kadan ta isa Danmagaji Sai gata har wajen da sukayi parking Tana zuwa ta sallami mai adaidaita Subai ta Rumgumeta tana Fadin"Har naji Dadin ganinki Qawata.."Dariya kawai Hafsah tayi Suka Shiga Mota Inna Talatu na mata barka Jidda kuwa Fadi take"Wlh Darajan Umma kikaci Anty Hafsah ammh bayan ita Da Mama ba wanda ke iya Kaucema Umarnin ya Abdullahi.."...
Hafsah na Dariya tace"Na sani...Sai na dawo zamu Dora Dashi.."Subai tace"Bakomai..Dayake ma kunfi kusa kuma kinsan Halin yan kayan ki zaki gyarota.."Mirmishi kawai Hafsah tayi acikin Ranta tana Fadin Wake sabo da Halin Abdullahi a kullum ikonsa kara yawa yake.."Daga haka suka bar mganar Suka Fada Hiransu Lokaci Daya kuma Direba nata Zuga Gudu a hanyar kaduna.
*Anitha...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*DEDICATED TO:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
_*Wannan Shafin Sadaukarwa ne gareku Gidajen da ake Zuba Sharhi Mai ma"ana Musamman Gidan Janaf Novella 1&2,Zauren Janafty,Taskar Janafty,Masifaffan Namiji Fans,Sillar Hallaci Fans Group,Aisha Alto Novels,Intelligent Fans group,Tare da Masarautar Janafty Shakira Da ma wadanda Ban Ambata ba Ina godiya Sosai ina ganin Comments dinku kuma Hakika naji Dadi kwarai Allahu ya bar zumunci Ameen ya Allah..*_
*013*
"Misalin karfe 11am da wani Abu suka isa Kaduna anguwan Sarki inda gidan Mijin Zannira yake wani katon Gida ne mai kyau da Tsari Dayake mijinta Babban Injiniya ne.
Lokacin da Zannira Taga Hafsah Tayi mamaki Cikin Farinciki ta Rumgumeta Tana Fadin"Oyoyo ga Anty Hafsah...! Tafada Cikin Murna da Farinciki Subai tace"Hmm.Allah yayi dai zata zo Sunan nan ammh ai gogan Hanata yayi.."Baki Zannira ta Rike Tana kallon Hafsah wacce ke Dariya kasa kasa Cikin mamaki tace"Eye..? Shi yaya Abdullahin ya Hanata zuwa Gidana..?
Subai tace"Kina mamaki ne..? Kadan Daga karamin aikin sa ne kema kinsani.."Kai kawai Zannira ta Ta kama tana Fadin"Oh Oh..Wannan yayan namu Sai Allah Daya Halleceshi.."
Mariya Data kariso tana musu Sannu da zuwa tace"Shikenan kuwa Anty Zannira.."Tafada Tana Dariya,Zama Sukayi saman kujerun Falon aka Fara gaggaisawa,Jidda kuma ta Shigo da Ledan kayan da suka zo Dashi na kayan Sunan da Mama ta Siya ma Zanniran da wanda mutane suka aiko dashi,sai kuma kudaden da Yaya Abdullahi ya bata ta kara mata da wasu,sai yaji da Ganyen wanka.
Gidan bawasu mutane Kannen Mijinta ne,sai matar dake mata wanka,Sai mariya sai wata makociyarta sai su da suka zo yanzu,Kunsan yan kaduna kowa yana Sha"aninsa ne Daga kai sai Danginka kawai,abinci kuma chan Gidan iyayen Mijin akayoshi Sun iso ba Dadewa sai ga matan kannenshi Dana yayyinshi da Yar'sa guda Daya Sun iso da kololin abincin da nasu kayan Suna akwati Guda.
Nan fa aka Hade ana ta gaisawa Dayake Duk an san Juna,sai da sukayi sallar azahar kana aka Zuba abinci akaci jalop din Shinkafa da Coslow,sai Alale,sai Zobo da kunun aya abinci dai sai wanda yagani Abun achanachan,Wannan Hirarranki da akai tayi,shi ya mantar da Hafsah Tunanin Tsiyar da zasu Tafka da Abdullahi in ta koma.
Wajen yammah Sai ga Kiran Ammi Ina Dagawa ta Fara min Fada Tana Fadin"Kin kyauta Hafsah Sai da dai kika Tafi Allah yasa da izini mijin naki kika Tafi.."?
Hafsah tace"Allah Ammi da izininsa waya gayamiki na Tafi..'?Ammi tace"Mai mashin dinsu Amira ne ya kawosu yace Inji Abdullahi in ya Daukoso ya kwasosu nan Bakinan kina Kaduna..'Hafsah tayi Mirmishi Tana Fadin"Eh Wlh Ammi Allah ya Dorani kansa ya barni yanzu hakama Gani gidan Zanniratu..".
Ammi tace"Shikenan Tunda Ya barki ina Zanniran.? Bani ita mu gaisa..? Da hanzari Hafsah ta mike zuwa Dakin Zanniran Dayake ita da Subai'atu suna Falo Da Mariya taci karo sai ta mika mata wayar tana Fadin"Kai ma Zannira Ammi ce.."Da sauri ta karba Ta Shiga Ciki ta mika mata Wayar tana Fadin"Ammin Anty Hafsah ce.."Ta karba Cikin Fara"a Da Farinciki suka gaisa da Ammi Tana Fadin"Naga sako Nagode Ammi Allah ya kara Budi.."Ammi tace"Bakomai Zannira..Zuwa Bayan suna Insha Allahu zaki ganni..Allah ya raya ya sunan yarinyar..?
Zannira tace"Maryam.."Ammi tace"Allah ya Raya Maryam Allah yayi mata albarka.."ta amsa da Ameen kana sukayi Sallama Ta mikama Mariya Wayar ita kuma ta Fito ta kawoma Hafsah,alokacin ma taso ta kira Abdullahi sai kuma kawai ta Fasa Sanin ko ta kirashi ba lalle bane ya Daga kiranta yadda Ransa yake bace da ita Umman Sadiq ta Kira sukayi mgana har ta bama Subai"atu suka gaisa tace ai ta Kira Zanniran ta mata barka.
Zuwa yammah suka Tashi Suna gyara gidan inda aka Bata,Har zuwa mangariba Lokacin Duka Dangin Mijin Zanniran sun Tafi,Sai kanwarsa Guda Daya,Yanka kuma Dama Raguna uku aka yanka Tun kafim su iso sai Gobe zasu Yanka su Soya,Sai bayan sun yi sallar mangriba ne suka Lura Jidda bata gidan Subai"atu ta kalli Mariya Tana Fadin"Mariya ina yarinyar nan taje..? Na bani ni Subai"atu...?
Mariya tace"Wlh bansani ba Anty Nidai Tun bayan la'asar Data karbi Wayata ban kara ganinta ba.."Kanwar mijin zannira ce tace"Naga fa ta Fita tun dazu..Lokacin ma sai Kiranta ake awaya Tana Fadin gatanan zuwa Har Tana Tambayanta Ina ne Malali Gra..? Dukkansu Salati suka saka Lokaci Daya wanda ya Fito da Zannira da Inna Talatu Daga Ciki suna Tambayan lafiya..?
Mariya ke maida musu Zencen Dafe kai Zannira tayi Tana Fadin"Na Shiga uku ni Zannira ina Jidda ta sani a kaduna Don Ubanta...? Mariya tace"Hmm kina mamaki ne Anty..? Kila sai tafiki sanin wani wajen Jidda Dakike gani wlh batajin mgana Agida Ya Abdullahi cin Ubanta yakeyi yanzu kuma Taci Darajan Mama ta Roka ya barta shine Kuma tazo ta samu Sa"a yanzu haka Ba mamaki samarinta ne taje Haduwa dasu.."
Subai tace"Ammh ko in hakane Jidda Taci amanarmu...Mama sai da tace mu saka mata ido..Domin ya Abdullahi ya hanata zuwa ita ta saka baki ya barta ammh Don Allah jibi wannan aikin..'Ta karishe Fada Ranta bace Hafsah tace"Toh ku kiran lambar mariyan mana..?
Jin haka yasa Jikin Subai na Rawa ta Dauko wayarta ta lalubo Lambar mariya ta Hau kira gashi Tana Ringing ammh ba"a Dagawa Subai tace"Shegiyar yarinyar nan bata Daga Kiran..! Sai Hafsah tace bari ta Kira ta wayarta Itama ta Kira ba"a Daga ba,Zannira ma ta kira sau Hudu Itama Bata Daga ba nan da nan Ransu ya baci Zannira tace"Bari na Kira Ya Abdullahin na gayamai Tunda na lura Jidda zakka ce acikin Gidanmu.."
Tafada Lokaci Daya ta na neman Layin Abdullahin Da Sauri Hafsah ta Rike mata Hannu Tana Fadin""'A'a karki kirasa ki gayamai Wlh Babban kuskure ne...In yaji Abunda ke Faruwa ba Jidda kadai ba hatta da Mu kanmu Wlh bazamu Tsira ba gwara mu Fara samun mafita kafin mu kira wani mu Fadamai mu Dagula komai."Zannira ta saki ajiyar rai Tana Fadin"Da kin bari na Kirashi na gayamai..Yarinyar nan Tagama Batamin rai wlh..Tana fa ganin kiranmu ammh taki Dagawa balle taji me za"a ce mata..?
Subai tace"Ta Daga..? Ai bazata Daga ba saboda tasan Dalilin kiran namu."Tafada Cikin bacin rai Inna Talatu fadi take"Gaskiya akai Cigiya gidajen Radio kar yar mutane ta bace batasan ko"ina ba.."Ba wanda ma yabi ta kanta Mariya ce dai zatayi mgana Zanniran ta Kayfta mata ido Ganin kanwar mijinta ta Zura musu Ido kuma ba Badi ta tafi da wannan Labarin gidansu kamar cin Fuska ne ga ita Zanniran Dalilin haka kowa ya bar mganar Zannira ta koma Cikin Bedroom dinta tana gwada layin Mariyan ita kuma Subai"atu da hafsah suka Shige Dakin da aka Saukesu Hafsah na kara gwada Layin Mariya ita kuma Subai tana Kiran Layin Mama
Mama na Daga Kiran Subai ta Fara Fadin"Mama kinga Abunda yarinyar nan ke son jazamana ko.? Mama tace"Meyafaru wata yarinyar..? Subai tace"Wata yarinyace banda Jidda Mama... ? Mama tace"Jidda kuma me tayi..? Tafada tana kallon Auwal Dake zaune yana cin Abinci jin ta ambaci Jidda yasa ya Dakata da Jin cin Abinci yana kallonta.
Cikin Bacin rai Subai ke maida Ma Mama yadda akayi Mama tace"Ai ni daman nasan Za"a Rina..Jidda batajin mgana kuma Bata Nadama..Ita ta sani In bata Dawo ba zuwa anjuma ki kirani ki Fadamin Yayansu na Shigowa zan Sanar dashi in ma kasheta zai yi in ya Daawo ita ta sani.."Daga Haka ta yanke Kiran na Subai Auwal Dake gefe yana Tambayanta meke faruwa ta gayamai Tsaki yaja yana Fadin"Wlh ko baku Fadamai ba sai na Fadamai in akayi wasa Yarinyar ba karamar yar iska zata zama ba.."
Mama tace"Ka bari ba kyau ka Dinga ma Dan"uwanka Fatan Banza.."Auwal yace"Yo mama karya nayi..? Indai kuna sakama Ya Abdullahi baki in yana mata Hukunci bazata bar Abunda take aikatawa ba..In ba yar iska take son zama ba Daga zuwa suna kaduna sai kima Hanya ki Fita..? Daman ai tana da samarinta a boye kece baki sani ba.."
Mama dai tayi Shuru batayi mgana ba Ranta Duk ya baci Auwal kuwa sai bambamin Fada yake Tagaji ne tace'Kafa dameni Don Allah..Fadanka ne zai sa ta Daina ko kuma Hargaginka..? Ni tashi kabani waje Tunda ba wani Taimako da zaka iya bani.."Auwal ya mike yana kakkabe Jikinsa Lokaci Daya yana Fadin"Allah baki Hakuri Mama..Ni bani bane mai Laifin karkamin Rataya.."Daga haka ya Zura Takalminsa ya Fice ya bar Mama Cikin Zullumi.
A chan Kaduna kuwa an gaji da Kiran Layin Mariya ammh Jidda bata Daga ba har bayan Isha"i bata ba Dalilinta,Karfe 9 tayi sai Tsoro ya kamasu,suka Fara Tunanin ba lafiya Ganin haka yasa Zanniran ta Kira Mijinta ta Fadamai Abunda ke Faruwa yace mata gashi ma ahanyar Gidan Yaji kanwarsa taje gida Tana Fada kanta ta Dafe Abunda take Tsaro ya Riga ya Faru,dayake Tun Jiya dashi da yaran suka koma Gidansu chan suka kwana.
Yana isowa yayi tama Zanniran Fadan meyasa bata Kirasa ta Fadamai ba Hakuri kawai ta bashi Lambar mariyan ya karba ya saka wayarsa ya Kira Har ta kusa katsewa kana Jidda Ta Daga Kiran Tana Fadin "Hello..."Jin ta Dauka yasa Zannira ta karbe wayar da Sauri Tana Fadin"Kina gidan Uban waye Jidda..?
Jidda Tayi Tsuru Tsuru Jin Muryan Anty Zannira Cikin Rawan murya tace"Ga...gani nan zuwa..An.."Bata karisa ba Zannira ta Laulayo Ashar ta sakarma Jidda ta Hada da Fadin"Kinci Ubanki..Na Rantse da Allah sai kin gane baki da wayau..wawiya kawai.."Batama karisa mganarta taji mganan Namiji yana Fadin"Baby ina zamu bi.."Daganan kuma taji an yanke Kiran Galala ta tsaya tana Bin Wayar da kallo ganin Tana Huci yasa ya dafa kafadarta yana Bata Hakuri Cikin bakinciki Tace"Fisabillahi yanzu Abunda Jidda tamana ta kyauta kenan..? Abun kunya take so tajawomana Cikin Zuru"armu..?
Lallashinta ya Shigayi da bata baki,Kafin ya Fice Daga Gidan Zuwa Cikin gari Dagachan zai wuce Gidansu Dama Tun jiya yagayamata sai baki sun Tafi zai komo,Yana Fita ta tafi Dakin da ta sauki su Subai tana gayamusu Yadda sukayi da Jidda mariya ta kada baki tace"Dama ai Tana da samarinta aboye ko agida Gidansu Rumana Take zuwa su Hadu ko kuma amakaranta.."Subai tace""Ai Shikenan ta kyauta ma kanta..In ta bata Rayuwarta ko da mu zai Shafemu nata sai yafi na kowa Domin in ta rasa Kimarta ta ya"mace kafin muyi kuka ta Rigamu yi.."Ta karishe fada Cikin Bacin Rai Hafsah ta kada kai Tana Fadin"Gaskiya bata kyauta ba sam.."Zannira ta Bude baki Zatayi mgana kenan Suka Ji Karan Hon da Bude get.
Da sauri Zannira ta Fice tana Fadin"Inaga gatanan Shegiyar..."Jin haka yasa Dukkansu suka Fito zuwa Haraban Gidan illai kuwa itace Suna Isowa tana Fitowa Daga wata Hadaddiyar bakar Camry Mota wani Saurayi Dogo Fari Shima ya Fito Daga bangaren Direba yana mata mgana Gabadayansu sai Jikinsu yayi sanyi,Ran Zannira yakara baci Ta Saki Murya tana Fadin"Jidda...!!!
Jidda ta waigo da Sauri ganinsu Dukkansu yasa Jikinta ya Farawa Dama Abunda take gudu kenan sai da tace ya ijiyeta bakin get basai ya Shigo da ita ba,ya matsa sai ya Shigo da ita ganin haka yasa ta waiga tana Fadin"Shikenan u tok on phone.."Hannu ya Daga mata yana Fadin"Alrigt bby.."Lokaci Daya yana mika mata wata Ledar Restaurant haka Tana Kallonsu Zannira ta saka Hannu ta karba kana ya Shiga motarsa yaja ya Fita Daga gidan.
Cikin Sanyin Jiki Jidda ta Fara takowa zannira bata Tsaya ta kariso ba ta Bita da Sauri Subai na Fadin"Kibi sannu kinsan Wajen aikin ki bai gama warkewa ba.."Ina ko Jinta batayi ba Tana zuwa gabanta ta Daga Hannu ta wanketa da mari kyawawa guda Biyu Subai tace"Dakyau...Kara ma Shegiya.."Tafada Lokaci Daya suka karisawa gareta Jidda kuwa Kumatunta ta Dafe Lokaci Daya tana Sakin Kuka.
Zannira tace"Ashe baki da mutunci bansani ba..!? Gidan Uban wa kika je..? Waye kuma wanchan..? Jidda Tana Hawaye ammh Taki mgana Subai ta Ja kunninta tana Fadin"Ke Abun kunya gaba kika bashi ba baya ba ko..? Wlh Wannan Abunda kikayi a kunnan ya Abdulllahi Tunda baki da mutumci..'mariya ma ta saka baki Tana Fadin"Bafa zatayi mgana ba..Taurin kai gareta ga laifi ga kuma Saurin kuka..Nan fa suka Taru da Subai da Zannira suna ta zagin Jidda ita kuma ba mgana sai kuka Mariya ta Fizge Ledan Hannunta Ta Bude tana Fadin"Wannan Abun ya kaiki bin Saurayi..?
Ta Fada tana nuna musu Abunda ke Cikin ledan,Kaza ce da Take away sai Ice cream,Zannira ta karbi Ledan Tana Fadin"Shi ya kaita mana...?Kazan nan baki Cinta ne..?ko kuwa Ice cream din baki Taba gani ba..?Ammh wlh kinji kunya kuma Na miki alkawarin da kaina zan kira ya Abdullahi na gayamai karyan iskanci kikeji.."Tafada Lokaci Daya tana watsama Jidda Ledan ta kama Hanya ta koma Cikin Gida Hafsah ne ta kama Hannun Jidda Bayan ta tattara mata Ledanta Suka Rufama su Subai baya Zuwa Cikin Gida.
Afalo Jidda ta make tana Sharan kwallah Hafsah ta kalleta tana Fadin"Meyasa baki Gudun mgana..?Yanzu Fisabillahi ina kika je..?jidda na Shesshekan kuka Take fadin"wani Saurayina ne da muka Dade tare dashi Anty Hafsah yana son zuwa Gida ammh Saboda Fadan Ya Abdullahi na Dakatar dashi,Shine Shine dana gayamai Nazo kaduna Shine yazo zai zo sai na Hanashi Shine shine.."Hafsah ta katseta da Fadin"Shine me..? Sai ke kika bishi ko...? Jidda ta Sunkuyar da kai Tana Fadin"A"a Allah ban Bishi ba Da Farko dayace nazo Malali Gra na sameshi ban je ba nace sai yazo..Shine Dayazo muka Hadu anan kofar Gidan Anty Zannira,Mun fara Hira sai yace na Shiga mota ina Shiga yaja Mota muka Shiga Cikin gari Har kuka nayi kan ya Daawo Dani gida,restaurant kadai muka je ya Dawo dani gida.."Hafsah tace'Koma menene Baki kyauta ba Jidda Mace bata Bin Namiji yanzu inda Daya Daukeki ya kaiki wani Wajen da bai dace ba ya Cutar dake me zaki ce..? Ya kamata in ma yana Sonki da gaske ne ya gabatar da kansa wajen Magabantaki yafi wannan Boye Boyen da kike yi.."Kai Jidda ta kada kafin tace"Naji Anty Hafsah Insha Allahu bazan kara ba.."Hafsah tace"Shikenan muje kibama Yayyinki Hakuri Ransu ya baci..Kuma sai Naka ne zai ga Kayi ba Daidai ba ya kwaba maka Suna Sonki ne yasa suke lura da al"amarinki.."
Hafsah ta tasa Har dakin da suka Sauka tabama Subai Hakuri Baki kawai ta tabe tana Fadin"Nifa Jidda baki Batamin rai ba..In kin gyara Rayuwarki Don kanki Jidda..Allah ya kyauta ya kuma Shiryamu gabadaya.."Zannira kuwa cewa tayi"Jidda nifa Nagama nawa..Tunda gani Gidan Mijina kuma Alhamdulillah Tundaga Yarintata har Zamanin yan matanci ban yi irin naki ba gashi kuma nayi Aure naga Riban Haka In kin gyara Rayuwarki Don kanki in kin batama kanki kimawa Jidda.."Jidda dai Ranar tasha Fada Inna Talatu ma sai da ta mata Mama kuwa ta Kira Wayar Subai aka bata ta Dinga mata Fada ta kuma ce ita ta Hana Auwal ya gayama Abdullahi Domin bai Dade da Fita ba Kuma Data sake yaji wannan Labarin Kashinta sai ya bashi Mama tace in aure take so ta gabatar da wanda Tabi din sai ayi mgana chan agidanta ta karisa makaranta Kuka Jidda ta sakama Mama sai kuma Maman ta koma Lallashi da Nasiha nan tayi mata alkawarin bazata kara ba Ammh Don Allah karta gayama Ya Abdullahi sanin Halinsa Kila ma SS3 din ma bazai barta ta karisa ba Aure zai mata dama koma waye.
Zuwa Washegari kowa ya manta mganar Tunda Jiddan ta bata Hakuri,Ranar kuma Tun safe suka Tashi da aikin Soyan nama Dama mai Daddatsa musu naman Tun safe yazo ya Daddatasa ya kuma yayyaka musu nasu kawai su Tafasa su Soya ne,Dayake Naman yana da yawa Basu gama ba sai bayan La"asar kuma Zannira tace basu Tafiya sun sai kasashi Sun Diba nasu Dana Mama,sai Gidan Inna Abu sai Kuma na Ya Auwal Dana Ya Abdullahi sauran kuma ita da Dangin Mijinta Shiyasa Abun ya kaisu har yammah basu gama ba Duk yadda suka so su koma Zaria Aranar bai yuyu ba Dole suka Bari sai Gobe.
Hafsah naji Sanda Subai ta Kira Mahmud Tana gayamaj Sai gobe zasu Dawo,ammh ita bata Kira Abdullahi ba kuma Shima bai Kirata ba,Tasani yana chan Cike da Ita bama zata Kirasa ba ya Mata Halinsa Cikin kannensa Ta bari in ta koma Gida Chan suyuta har su gama ba wanda ya sani.
Gari na waye Tun safe suka gama Komai kowacce tayi wanka Sun Hada kayansu Suna Shirin Tafiya direban Mijin Subai kadai Suke Jira Dama Shi zai zo ya maidasu mariya dai nan nan sai Sati na samu Tana da Test a makaranta,Bayan kowacce tayi wanka Suna Falo Gabadayansu Suna Hira Subai ta kalli Zannira tana Fadin"Niko Anty Zannira wani anguwa Matar Yaya Nazifi ke Zaune..?Zannira tana bama Maryam Nono tace"Yaya Nazifin Inna Abu..?
Subai tace"Eh Shi so nake nidai naje Gidan nan naga matar nashi Da"ake ta labarinta bantaba ganinta ba.."Hafsah tace"ina jin fa anguwar Rimi suke Zaune.."Subai tace"Yauwa Don Allah bamai lambarsa mu Kirasa muji suna nan ko a"a Abunka ga ma"aikaciyar gidan Talabijin.."Ta fada tana Dariya Zannira tace"Kuma kinsan Weekend kadai take yi nan Sauran Duk Wajen aikinta Abuja takeyi bama lalle bane ku sameta.."
Subai tace"wai tama taba zuwa Gidanki kuwa..? Zannira tace"Tazo Sau Daya Haihuwan Gidado Tamin barka Shi ya Nazifin yaso mu Dinga Zumunci ammh Taki baki ganta ba akwai shan kamshi da Daukan kai naje sau Daya Lokacin gaskiya suna Gidan Babanta ne nan Ndc,Tundaga Lokacin ban koma ba Wannam Haihuwan dai Basu zo ba ammh Shi ya Kirani ta waya yayimin barka.."Hafsah tace"Ai bata son Shiga Mutane Nima ko Gidana sau Biyu taje..Ni kuma Sau Daya sanda muka zo nan Nida Abban Amira da zamu Tafi muka Biya muka gaishesu.."
Subai tace"Lalle yaga Rayuwa..Don Allah me lambarsa ya bani nidai ban barin garin nan sai naje naga komai."Zannira tace"Gulma zai kai ki kenan.."?
Kai Tsaye tace"Kusan Haka.."Tafada Tana Dariya Mariya ce tayi karab tace"Bafa mai lambarsa anan inaga.."Hafsah tace"Nima wlh banda ita ammh gata Sakinar nan inada ita.."Subai tace"Yauwa Kirata kice mata kina kaduna muji ko tana Gida.."Nan da nan kuwa Hafsah ta Daga waya ta kira Sakina Sai da ta yanke bata Daga ba kira na Biyu ne ta Daga muryanta chan Ciki kamar mai Barci Hafsah tace"Hajiya sakina kin Tashi lafiya...?
Dagachan Bangaren Sakina Dake Nannade Cikin bargo tace"Lafiya kalau..Matar Abdullahi Usman.."Dama haka take Kiranta Hafsah tace"Ashe zaki gane ni..? Sakina tace"Saboda..? Ina da Layinki aie..kawai dai Abubuwa ne sai a hankali ya gida..? Ina oga da Yara..?
Hafsah tace"Duk suna lafiya suna Zaria ni gani kaduna Tun Shekaran Jiya.."Sakina tace"Kai Don Allah..? Me kika zo yi kaduna kuma..? Hafsah tace"Suna muka zo kanwar Abban Amira ta Haihuwa wacce ke nan Kaduna.."Sakina tace"Oh..Allah sarki zannira kenan Kamar naji Nazifi na mganarta ba C.s akayi mata ba..? Hafsah tace"Eh wlh...Jiya akayi suna Shine yau zamu koma nace bari na Taboki naji ko kina kaduna ko kila kin koma wajen aiki..?
Sakina tace"Ayyah Wlh ban koma ba Kingani Tun Ranar monday na saka ran komawa ammh na tashi da Fever da Ciwon kai Sai Da naje asibiti Jiya kawai sai na Dauki Excuse sai Ranar Friday in naji Sauki zan koma.."Hafsah tace"Shikenan zamu zo kafim mu tafi..Ina Ya Nazifin yana gida ko an Fita..? Sakina tace"Yana office Wlh Tun safe ya fice sai kunzo kiyima mai jego sannu in na samu Lokacin zan Shigo insha Allahu"Hafsah tace"Zataji sai mun iso.."
Daga haka suka yanke Kiran Dama Handfree ne, Hafsah ta Saka da Sauri Subai ta mike tana Fadin"Wlh sai munje ku Shirya da Habu Direba ya iso muyima Zannira sallama Dagachan sai mu wuce.."Haka ko akayi Ba Dadewa sai gashi ya iso nan sukayi mata sallama Harda kwallarta Ta basu sakon Turaman Atamfa Biyu na Mama Dana Inna Abu Inna Talatu ma ta bata nata Sai sakon Nama Da yawa Datace akai ma Mama ta Diban nata dana Ya auwal sai ta aika gidan Inna Abu na Ya Abdullahi kuma tabama Hafsah tace takai mai Sun Rabu Cikin kewa Don ma ga mariya sai Sati mai zuwa zata dawo,ammh harda ita za"aje gidan Nazifi Domin tace wlh Sai taje itama allah barshi in sun Fito sai su sauketa Boss Stop ta Hau Adaidaita ta dawo.
Daga Gidan Zannira sai anguwar Rimi Gidan Nazifi Hafsah ita ta gane Gidan Tunda suka Shigo Layin da Farko sun so su bace Ammh Daga baya sai ta gane Gidan Hon suka zuba abakin katon bakin get din megadi ya leka ya Bude musu get suka Sulala Jiki ga Bakar Motar Sakinan nan Anaconde tana Fake,Suka Firfito Daga Motan suna kallon Farfajiyar Gidan Subai sai kalle kalle take kafin tace"Shima dai Ya Nazifin da kwadayi da Buri dame wannan Gidan yafi ma wanda Ubanta ya basu duk da Banta ba zuwa ba.."
Hafsah na Dariya tace"Babu sai Abunda ba"a rasa ba.."Subai tace"Gashi yanzu ya Dawo Gidansa don Dole Domin ko yaya Guntun Gatarinka yake yafi sari ka bani.."Kafa hafsah ta Take mata Daidai Lokacin da Jidda ke Tura Kofar Falon gidan ganin haka yaasa tayi Shuru suka saka kansu Ciki Lokaci Daya da sallama.
*Janafty...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*DEDICATED TO:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
_Shafin yau Gabadayansa Sadaukarwa ne zuwa Gareki *MY BEST❤️HALIMA..* ALHERIN ALLAH YA KAI MIKI ADUK INDA KIKE AMEEN..._
*014*
"Falon babu Kowa sai karan Talabijin Daya ketayi Shi kadai...Kwata kwata Babu motsin kowa Cikin mamaki Dukkansu suke Bin Falon da kallo ganinsa kaca kaca da alama dai matar Gidan bata Dubashi ba.
Saman Center Table din Dake Tsakiyar Falon Ga Filet nan da kofuna da kuma Goran ruwa da lemo Wanda da alamu Harda wanda akayi amfani Dashi Jiya da Daddare dana yau da Safe, kila da megidan zai Fita ne,ya Taimaki kanshi.
Suna Ta Raba ido Cikin Falon,Subai Ta kalli Hafsah tana Fadin"Ke wai matar gidan kuwa tana nan..? Hafsah tace"Tana nan mana..Da bata nan da batace tana nan ba kinsan tace batajin Dadi kila Tana ciki ne.."Mariya ce Ta kara bude baki ta kwarara Sallama sai ga Sakina ta Bude wata Kofa dake yammah haka ta Fito Dagani Daga barci tatashi Domin Rigar barci ce ajikinta mai igiyoyi,Sai wata Hula Dake saman kanta Fuskarta Duk ta yamutse Alamun dai Tun barcin Jiya bata iya Tashi ba sai yanzu.
Da Mirmishi ta Tarbesu Lokaci Daya tana karisowa kusa dasu Cikin Fara"a tace"Sannun ku da zuwa..ku zauna Ashe Kun kariso...?Hafsah tace"Eh wlh..Muna Ta sallama muka ji Shuru..? Ta fada tana zama kan Daya Daga Cikin kujerun da sukayi ma Falon kwanya,Suma su Subai"atu da mariya da Jidda Hade da Inna Talatu suka nemi waje suka Zauna,Lokaci Daya suna gaisheta ta amsa Tana kallon Inna Talatu ganinta Babba yaasa ta gaisheta ita kuma ta amsa Tana Tambayanta gida da yara.
Mirmishi Sakina tayi batayi mgana ba Hafsah ce tace"Wasu yaran Inna..? Wadanan yan Boko ne yara ba yanzu ba.."Inna Talatu tace"Ikon Allah daman Haihuwan Tsarata ake sai sonda Mutum yaga dama..? Kai yaran zamani.."Tafada tana kyabe baki Dariya suka sakamata Harda Sakinan Subai ce tace"Inna baki gane ba..Ba yanzu suke Bukatar ya'yan ba sai zuwa Gaba.."Inna Talatu ta tabe baki Tana Fadin"Aikin Banza ai Duk wannan Shirme ne da Biyema ka"idan Yahudawa Annabi da kansa yace kuyi Aure ku Haiyayyafa sai nayi alfahari Daku Ranar lahira ammh ku kuma kuna ma Tsara Lokacin da zaku samu ya"yan ne Allah ya kyauta To.."suka kara sakamata Dariya saboda sanin Halin Inna Talatu na barkwanci da kuma Ban Dariya.
Sakina dai batayi mgana ba, sai Mirmishi sai chan ne,Hafsah ta kalleta tace"Kanwar Mama ce muna ce mata Inna Talatu.."Yake tayi Tana Fadin Allah sarki Kafin Hafsah ta Nuna Subai tana Fadin"Nasan baki santa ba Ita ke bima Zannira sunanta Subai"atu azaria take aure..su Mariya kuma nasan kila kin ganesu..? Sakina ta kallesu Daya bayan Daya kafin tace"Allah Sarki..Sannunku da zuwa.."Suka amsa da yauwa Subai"atu dai nata yan kalle kalle Tana Tabe baki Sakinar na Lura da ita,sai itama ta Dauke kanta ta Mike tana Fadin"Bari na kawo muku Ruwa...kunzo ban lahiya banyi komai Cikin Gidan ba.."
Hafsah tace"Ayyah bakomai da kin barsa ma munsha Ruwa saman Hanya muke.."Bata saurareta ba tawuce zuwa Kitchen suka Bita da kallo ganin yadda take wani taku ta kowani Kira na Jikinta yana amsawa Baki Subai ta Rike tana Fadin"Ji wai macen Aure..? Ji gidanta..?gaskiya Ya Nazifi kyan jiki kawai yabi da Dukiyar mahaifinta ammh banda haka wlh banga Abun so anan ba.."Hafsah ta Take mata kafa tana kyafta mata ido Mariya nata Dariya Inna Talatu dai bata saka musu baki ba Domin Itama Sakinar bata bata Sha"awa ba sam..
Ruwa da Lemo ta kawomusu da Kofuna kana ta koma ta Cikin Bedroom dinta ta Dauko wayarta tazo ta zauna ta Dora kafa daya Kan Daya tana latsawa Subai kuwa sai Binta da kallo take awulakance,ganin basu sha Ruwan ba yasa Sakinar ta kallesu Tana Fadin"Kun ki shan Ruwa..? Hafsah tace"Zamu sha..Dayake kinga Daga gidan zannira muke bamu tare da kishi.."Itace tasha Ruwan sai Inna Talatu Subai da Mariya da Jidda ba wanda yasha,Sunanan zaune sau Daya Sakinar ta Dago tana Tambayan Hafsah yasu Amira..? Tace suna Lafiya suna Gidan Ammi.
Sunyi zaman mintuna Talatin kana Subai ta kalli Hafsah tana Fadin"Muyi Harama ko..?12 ta wuce kada muyi Dare Bisa Hanya.."Tafada tana mikewa Lokaci Daya tana Gyara zaman Saleem Dake Hannunta,suma Duk sai suka mike suna Fadin"Ai kuwa Toh sakina mu zamu wuce.."Cewar Hafsah sai Lokacin Sakina ta ijiye wayarta tana Fadin"Tun yanzu..?
Hafsah tace"Muna Bisa Hanya ne..Zaria zamu koma.."Sakina tace'Ai nagode..Ku gaida gida Allah kiyaye Hanya mungode.."Subai ce tace"Toh in yaya Nazifin ya dawo sai agayamai mun zo..Allah kara lafiya.."Sakinar ta karba da Ameen Fuskarta ba Fara"a Sosai iyakarta Rakiyarsu bakin kofar Falonta ta koma Subai bata Samu Bakin mgana ba sai da suka Dauki Hanya kana ta kalli Hafsah Tana Fadin"Gaskiya matar nan ta Ya Nazifi bata da Kirki..Duk Fadin Rashin kirkinta dasu Zakiyyah ke Fadi ban yarda ba sai yau Dana ganta.."
Hafsah tayi Dariya tana Fadin"Wai ina Ruwanki da Rashin Kirkinta..? Matar nan kin Cika gulma.."Subai tace'"Allah ba Zencen gulma ba sai gaskiya Shiyasa ba"a son Dogon Buri,kinga da Lokacin da zai yi Aure yabi yadda Sunna ta koyar mai addini da Tarbiya Shi kuma sai yabi Mai kyan Diri da kuma Tarin Dukiya Shiysa Tunda yayi Aure yake ta kwarewa kamar kudin Guzuri.."Dariya ta kama Mariya da Hafsah suka kyakyalce da Dariya Jidda dai Tabe kawai Tayi Dayake ita ke gidan Gaba.
Mariya ce tace"Haka ake ta Gulma a anguwa ana Fadin Auran kudi yayi Gashi kuma ya Auro ma kansa wacce tafi karfinsa kwanaki Mama naji suna mganar da Ya Abdullahi Da suka samu matsala ya Taba marinta ta koma Gida Babanta ya Kira Baba wada yace wlh sai yamaka ya Nazifi a kotu Baba wada yace Abun bai kai nan ba,Ya Kira ya Abdullahi yace maza ya Raka Shi Ya Nazifin suje suyi ban Hakuri wanda ya jawo Ruwa ya Dakesa Shi kadai da Mutumcinsa bazai bari Nazifi ya maidashi Mutumin banza ba.."
Salati Subai ta saka ta na mamaki kafin tayi mgana Hafsah tace"kwarai kuwa Kwanaki sunje kano..Shida Abban Amira ammh kusan Halin yayanku Wlh ko Tadin bai taba yi Dani ba.."Mariya tace"Tabdijam Wake jin Zence abakin Ya Abdullahi in banda Mama..? Ko nima Ranar bai san ina Ciki bane Ina ma Mama gyaran Daki Dana Fito muka Hada ido kinga Ruwan Harara..?Dariya suka sakamata Lokaci Daya Subai tace"Da farko Haushinsa nakeji ina mai Allah kara ammh yanzu ya koma Bani Tsausayi Wlh inda ina da Diya Budurwa sai na wanketa na bashu Naga yarda Shegiya zata kare sai taje ta Rungumi aikinta Ubanta kuma sai ya maye mata Gurbin Nazifin..'
Hafsah ta Rike baki Tana Fadin"Lalle lamarin Babba ne..Ai bata baci ba ga Muhsina sai ya Jirata in ta kara Girma muyi Tuwona maina.."Duka Subai ta Daka mata abaya Tana Dariya Mariya na Tayasu Jidda kuma daman bata Cika saka musu baki ba in suna mgana Inna Talatu kuma taji sanyin A.C mota Tuni Barci ya saceta,Mariya ce ke Tayasu Da Dariya Dayake ita akwai manyance,Bus stop suka ijiye Mariya ta Hau adaidaita ta koma Bayan sunyi Sallama nan suka Barta tana neman Abun hawa.
Suna Tafe suna Hira gwanin Sha"awa Suna gabda Shigowa Zaria Subai tace"Jidda wai yaushe ne,Bikin autar Goggo Habiba ne..? Jidda tace"Wlh na manta ammh fa an kusa kamar naji Mama suna mgana da ita datazo mata Barkan Anty Zannira Tace watan Gobe ne.."Hafsah tace"Kai Abun har yazo..kamar fa Shekara aka saka ko..?
Subai tace"Eh mana nima nayi mamaki..Komai aka sakama Lokaci sai yazo lalle kice Danja zatayi Diban baki.."Hafsah tace"Aifa..Allah dai ya kaimu.."Jiddaa tace"Kafin na Madina din wannan Asabar din Diyar mijinta na Aure fa Shiyasa ma Tace ma Mama bazata samu zuwa Kaduna ba Tadai Kira Anty Zanniran ta mata barka.."Hafsah tace"Allah sarki..yakamata kuma ama Goggo kara kowani Sha"ani Da ita da ya"yanta akeyi.."
Subai tace"Sai Ya Abdullahi ya wakilataki kije Qawata.."Hafsah tace"Wa..? Rufamin Asiri ina Lallaba yan kayana yanzu ma Baku san Abunda zan Tarar ba na Tsiya.."Ta fada tana Dariya Dayake ta basu labarin yadda ya Barta ta Taho Tunda Ranar da sukazo da Daddare Umman Sadiq ta Kirata tana Tambayanta ko ya Kirata yace tatafi sai tace gatama akaduna.
Basu iso Zaria ba sai Wajen Biyu na Rana Dayake basu yi Gudu ba Gidan Mama Tawagar Sunan ta yada Zango suka bama Mama sakonta ita kuma tayi ta Hamdalan Sun dawo lafiya daya suka baro masu wanka sukace Lafiyarsu kalau suna gaisheta Dama koda suka iso Mama tayi Danwakenta da yajinta da manja nan suka baje sukaci suka Koshi suka Dora da Ruwa kana aka Zauna zaman Hira Bayan sunyi Sallar azahar.
Cikin Hiran ne Subai ke Fadin"Mama Ashe haka Matar Ya Nazifin nan take mara Mutumci..?Mama tace"Ho ke Subai"atu ina kika ganta kuma..? Nan mariya ke gayama Mama Yadda akayi Mama tayi Dariya Tana Fadin"Hoho..Subai kina nan da Halinki..Ina Ruwanki da Rashin Kirkinta Tunda Mijinta yaji kuma yagani.."Subai tace"Mama bawan Allah ya koma Abun Tsausayi.."Hafsah tace"Don Allah mu ki kyalemu da wannan mganar in baza ki iya gani ki kyale ba ki barshi.."Hararanta Subai tayi Daganan bata kara Mgana ba ammh haka Kurum take jin Haushin Sakina acikin Ranta.
Sai Da sukayi La"asar kana Kowa tayi Shirin komawa Gida kafin su Tafi sai Da Mama ta saka Suka Shiga Gidan Inna Abu ita da Subai suka kaimata Sakon Naman Sunanta da Turmin zanin Sakon Zannira ta karba tana ta Godiya ta sakamusu albarka suna gidan ma sai ga Baba ya Shigo nan Inna Abu ke gwadamai Shima yayi ta Godiya yana saka musu albarka kana suka musu Sallama suka Fito Direban Mijin Subai Shi ya Fara kai Hafsah Gida kana ya wuce da ita Dama ta karbi key hannun Mama Tunda nan Abdullahi ke Barin key din Guda Daya Dayan kuma Dama yana Hannunshi ne.
Tana Komawa Gida ta Zage ta Fara Gyaran Gidan ganin Duk yayi Kura ta Share Tsakar Gida da Kitchen ta Share ganin yadda Abdullahi ya Birkita mata shi kawai Wajen Dafa Ruwan lipton,Ruwan zafi ma cikin Kittle yake sakawa,Dakin barcinsu kuwa Taga Abu kaya duk ya watsar Sai da ta gyara haka Tailet Ya watsar da Soso nan Sabulu chan komai dai ya Batashi Bayan ta Share ko"ina ta gyara sai ta koma Zaman gyara kayan Abdullahi na Cikin Wardrope wadanda kila wajen Daukan kayan da zai sakane Duk ya Birkita goggun Ciki ga kuma Kayanta da nashi wanda aka Dawo Dasu Daga wanki da Guga nan ya Turasu waje Daya Tana Gyarawa Tana mita acikin Ranta sai Gabda da mangariba ta gama gyaran kayan kana ta Fito Zuwa Kitchen ta Duba Fridge dinta taga Tana da Sauran Nama da Nikakken kayan Miya kawai sai ta Dora Musu Jallop din Shinkafa,Acikin ranta kuma tana Addu'an Allah yasa wannan karon Abdullahi ya siya mata gas Tuni Take nacin ya siya mata yaki wai saboda yara bata da Hankali wata Rana Sanda zasu je kusa ma bata sani ba Tunda Taji haka ta Hakura damai magiya.
Ta idar da Sallar mangariba kenan ta Kira Ammi ta Shaidamata Ta dawo Ammi tace"An dawo lafiya..Su Amira dai Kila sai Friday zasu dawo..Taji Dadin kiwon Tsohon Mijina ta nace taki Tafiya.."Hafsah na Dariya tace"Kai Ammi kodai ke kikaga Sabon Miji kika makalemai kina ma Daddy jan Aji Shi kuma ya kama Sabuwar amaryansa..?
Ammi tace"Wa..? Wannan ai ba megida bane Tunda baya Cefene.."Hafsah ta saka Dariya Ammi na Tayata tana jin Hayaniyarsu Amira Hafsah tace"Ammi kina ganin ba Matsala..? Kada fa Hayaniyarsu Amira ta Saka jinin Daddy ya kara Hawa..?Ammi tace"Ko daya karki damu ai shi Hayaniyar yaran yake so Tunda yanzu duk baku kusa dashi..Baki ga yadda yake sakewa dasu ba suma Sunfi son zama Dakinsa indai yana Gidan.."Hafsah tace"Shikenan Ammi..Ki gaida Daddyn zan kirasa.."Ammi tace"Shikenan.."Daga haka suka yanke Kiran Juna Hafsah na Mirmishi Sanin Diramar Ammi da Daddy kan Son Yaran da suka Haifa ita da Anty Hadiza,Koda Ammi tace sai Ranar Friday su Amira zasu dawo bata damu ba sanin Direba ke kaisu makaranta kuma Suna da kayansu chan Gidan Ammi kamar yadda suke dashi Agidan Mama Tunda suna yawan zuwa wasu kayan adawo dasu wasu kuma abarsu chan.
Koda Abdullahi ya Dawo ya Iske Hafsah ta gama Komai Har wanka Tayi ta Saka kaya Cikin Wasu Ubansu Riga da wando yan kanti wadanda suka kamata Sosai suka Fitar mata da Surar Jiki gefe daya kuma Tama kanta Barin Turare Duk inda ta gifta sai Tashin kamshi kawai take,kanta kuma wani Karamin Vail din gyale ta Daura,koda ya Shigo Gidan yaga Hafsah ta Dawo bai yi Mamaki ba Tunda ya Biya Gidan Mama ya ga Sakon Zanniran kuma Maman ta gayamai Sun Dawo Tun dazu Subain ma da Hafsah tare suka Fita.
Koda ya Shigo Hafsah Tana Sallar Isha"i Saboda haka kawai sai ya wuce Cikin Bedroom Karamar Jakarsa ya ijiye da key din Mashin Dinsa,kana ya Shiga Toilet ya iske ta sakamai Ruwan zafi a kittlle kawai sai ya juye yayi wanka Dashi ya Fito Kenan Daga wanka yana Sanye da Bakin Wando sai karamin Towel yana Goge Jikinsa Dashi sai ga Hafsah ta Shigo kallo Daya yayi mata ya kauda kansa kawai ya karisa gaban madubi ya Dauki mai ya Fara Shafawa.
Da kallo Hafsah ta Bisa sanin Hali yasa kawai ta karisa garesa ta Rumgumesa ta Baya Lokaci Daya ta Zuro Hannuwanta saman Cikinsa wanda Dukkansu sai da Jikinsu ya amsa Cikin kissa ta kwantar da kanta saman Bayansa Sanin tayi Laifi sai ta ke kokarin amfani da Hanyar da tasan Zata sauko da Fushinsa Da wuri.
Yana Jinta ya mata Banza sai ma Kokarin Rabata da Jikinsa yake yi Jin Haka yasa ta kara makaleshi Lokaci Daya ta Shagwabe Murya tana Fadin"Abdullahina Kana ganina na Dawo Shi ko mgana ko..? Tafada Lokaci Daya tana amfani da Hannunta Duka Biyu Tana Shafa kwantattacen gashin Daya kwanta saman Kirjinsa,Wanda sanadiyar haka Tsikar Jikan Abdullahi ta Fara tashi Ganin tana neman Birkitamai lissafi yasa yayi Sauri Juyowa Lokaci Daya yana saka Hannu ya Raba Hafsah da Jikinsa Kallonsa take Cikin manyan Idanuwanta Shima sai ya sakarmata ido kawai yana kallonta ammh Fuskarsa ba Fara"a ko kadan
Ganin Haka yasa Jikin Hafsah sai yayi sanyi Duk Confident din Datazo dashi sai ta nemeshi ta Rasa,Sai kawai ta sadda kanta kasa tana wasa da Zoben Hannunta Cikin sanyin Murya tace"Sannu da zuwa ka Shigo ina Sallah.."
Yana kokarin Rabata ya wuce yake Fadin"Uhm...Na Shigo kina Sallah.."Daga haka bai kara komai ba ya Bude wardrope yana neman Jallabiyan da zai saka bata Dandara ba ta kara Binsa ta saka Hannun kenan zata Rikosa yayi saurin kaucewa yana kallonta Lokaci Daya yana Fadin.."Ina Kika ijiyemin Jallabiyoyina..? Yafada yana kallon Gefe Saboda Shigar datayi Domin wanke Laifinta ya kusa yin Tasiri a tare da shi.
Batare Da tayi mgana ba ta matsa gefensa ganin haka yasa Shima ya matsa hade da Juyamata Baya,Mamaki ya kara kama Hafsah aranta tace Abun Babba ne,Jallabiyansa ta Daukomai mai Ruwan toka tana Fadin"Gata ko na chanzo maka wata ne..?
Bai mata mgana ba illah ido Daya Zubamata lokaci Daya yana mika mata Hannunsa tagane Abunda yake Nufi ta mikamai Jallabiyan ta koma gefe tana kallonsa Bai sakata ba ya maidata ya Dauko Baka ganin haka yasa ta Girgiza kai ta Fice kawai Zuwa Kitchen ta Hado ma Abdullahi Dinner dinsa Zuwa Tsakiyar Cafet din Dake Cikin Falon.
Ta kawo mai Ruwa kenan sai gashi ya Fito yana waya Jin datayi yana ambaton Mutumina yasa ta gane da Nazifi yake mgana Yana zama kan Daya Daga Cikin kujerun Falon taji yana Fadin zataji Daga Haka sukayi sallama,Abincin ta Zubamai Cikin Filet tana Fadin"Na saka maka Coslow din ne..? Bai mata mgana ba sai ya Sauko kasa ya Tankwashe kafa Sai ta mikamai Filet din Hannunta zuwa gabansa ta Turamai Dan Vowl din Data saka Coslow din Shi kuma ya saka Cokali ya Diba ya zuba kana ya Fara Cin Abinci gefe ta koma tana kallonsa Sakamakon Ita ta Riga taci nata Tun Dazu.
Hankalinta ta maida kan Talabijin tana kallon Tashar Arewa24,Chan taji yana Fadin"Ashe kun Biya gidan Nazifi yau..? Hafsah ta waigo tana Fadin"Eh wlh..na kira sakinar tace tana gida bata koma ba batajin Dadi.."Kada kai yayi kafin yace"Yan suna..? Gashi kin Dawo na zata chan zaki zauna sai Zannira ta yaye kana sai ki Dawo.."Kai Hafsah ta Sunkuyar Lokaci Daya tana Fadin"Allah baka Hukuri.."Bata Rufe baki Ba Abdullahi ya katseta da Fadin"Shoutup...!!! Gabanta ya Fadi sai ta kara Sunkuyar dakai tana Wasa da adon kwalliyar Rigarta.
Cikin Bacin Rai Abdullahi ke Fadin"Banda kin Rainani Hafsah har ni na ce bazaki je waje ba ki kira Ummata ki kaimata karata ko..? Saboda Umma ke Auranki ko..? Ko kuma Ita Zanniran tafini Muhimmanci ne Tunda kika zabi ki Farantamata ni kuma ki Sabamin ko..? Hafsah ta Dago Tana kallonsa Cikim marairaicewa tace"Allah Abban Amira ba Haka ba..!Ba haka bane To yane Hafsah..?
Ya fada yana Tsareta da mayen Kallonsa mai kama da Tuhuma Cikin Fargaba ta maida kasa tana ajiyar Zuciya,Kada kai Abdullahi yayi yana Fadin"Kinsan meyasa na Hanaki zuwa sunan nan..? Bai bata zarafin mgana ba yacigaba da Fadin"Saboda ki gane ni keda iko dake..Kuma kina karkashina ne..Ina da ikon da zan Hanaki zuwa Sunan komawaye ba Kanwata Zannira ba koda kanwarki ce ko yayarki Ni Abdullahi ina da ikon da zan ce bazaki ba kuma ta zauna ammh saboda ki nuna min iyakata ki ka kira Umma ta Tilastani yin Abunda ban Shirya ba kin kyauta ai gashi kin je kinyi ma Zannira Suna kin Dawo kin barta Chan ita da Mijinta suna zamansu lafiya ke kuma kin Dawo kin Tarar da mijinki wanda kika Nuna ma bai isa Dake ba yayi kyau...".
Maganganunsa sun kashe Hafsah Jiki sai ta kada kai Tana Fadin"Nidai nasan ban Kira Umma na gayamata komai ba ita ta Kirani Tana Tambayanta meyasa banje suna ba sai nace mata kai ka Hanani batama Jira cewata ba ta yanke kiran kuma Harga Allah bansan cewa kai Zata Kira ba da ban barta ba ammh na amsa Laifina Don Allah kayi hakuri.."Yana jinta har tagama mganarta bai Tankamata ba,Ganin yayi mata Shuru yasa ta marairaice tana Fadin"Kaji..? Bazan kara ba Insha Allahu.."
Tafada tana sakarmai Idanuwanta kamar bazai Tanka ba sai kuma ya Dago yana kallonta ajiyar Zuciya ya saki Lokaci Daya yana Fadin"Ya wuce..Ammh kuma karki Fasa biyema mara Hankalin yarinyar nan Subai"atu ni ba irin sakaran Mijinta bane mara wayau ko"ina sai ki ganta tana saka kafa in kikace ita zaki dinga bi Wuyana zaki Sha Allah.."Dariya ta kusa kama Hafsah sai ta kanne Tayi Saurin Fadin"Insha Allahu.."
Ture Filet din gabansa yayi ya mike yana Fadin"Kwashe kayanan ya isheni..Nazifi na muku ban gajiya ya koma sakina ke Fadamai kun zo.."Ta mike tana Fadin"Eh muna amsawa..Sakon Naman sunanka nawajena Zannira tace azo maka Dashi.."Tabe baki yayi yana Shiga Bedroom dinsu yace"Ita kuma gulmanta yayi yawa ina Abunda ya Shafi Abdullahi da Naman suna ko ce mata kikayi mijinki baya Siyan miki nama Shine yasa ta aikomin dashi..?
Yafada yana Tsare Hafsah da ido,Da sauri tace"A"a wlh cewa tayi dai adiban maka kaida Auwal..Ni ba ruwana.."Mirmishi yayi kafin yace"Haka Chan naje Mama na turamin gabana nace wannan ai Shirmen mata ne Naman suna ta Hada suci agida,..."
Hafsah batayi mgana ba ta kama Bakinta Shima bai kara mgana ba ya Shige Ciki ya barta tana kwashe Kayan da yayi amfani Dashi.
*Shakira.."*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*015*
"Allah ya taimaketa wannan karon bai tsawaita Fushinsa ba Bata taba zaton Abun zai zo da Sauki kamar haka ba sai dai kuma Sha"anin na Abdullahi sai Allah Shi madaci ne ga Zaki ga Harbi.
Da safe suna Breakfast Take gayamai Sakon Ammi na Su Amira sai Friday zasu dawo Har ta bashi Labarin Diramar Ammi da Daddy kan su Amira Abdullahi yayi Mirmishi yana Fadin"Sai ki Shirya yau in na Dawo Daga Office muje mu gaishesu Daganan sai mu kaima su Amira kayansu Tunda suna Debema Daddy kewa su Zauna chan Har sai sun gaji dasu sun Dawo dasu da kansu.."Baki Hafsah Ta Bude Cike da mamaki da kuma Farinciki kafin tace"Makarantar Haddarsu fa Abban Amira..?
Yana Tura kwai bakinsa yace"Su Dinga zuwa Dagachan mana...Ko Ammi ma sai ta Tuka mota takaisu yanzu ma karki mamakin ba Direba ke kaisu Amira makaranta ba Itace da kanta.."Hafsah tace"Ammi ai babu Ruwanta...Bantaba mantawa Nida Anty Hadiza Ita ta koyamana Mota Duk da Fadan Daddy ya Dinga yi.."Kai Tsaye Abdullahi ya kalleta yana Fadin"Gashi Anty Hadiza ta Mori koyon Motan nata, ammh ke baki Mora ba har yau baki jin wani iri..?baki jin kamar kin Fita Dabam ko Hausina..? Kin Taso A Katon Gida da kuma motoci ammh kinzo kina Rayuwa a karamin Gida tare da Miji mai Rufin Asiri baida Mota ballatana katon Gida sai dai Mashin baki jin wani irin in kika shiga Cikin Danginki da yan"uwanki..?
Kur Hafsah tayi mai da ido kafin Lokaci Daya Annurin Fuskarta ta Chanza Idanuwanta suka Chanza Launi Cikin karaya da Muryan Kuka Tace"Kana Tamtama da Irin Son da nike maka ne Abban Amira..? Kai ya girgiza mata zai yi mgana ta Dakatar dashi da Fadin"Ko kuwa Irin Tarbiyan da iyayena suka bani ne ka Raina..? Kai ya gyada mata yana Fadin"Karki min mummunar Fahimta Hafsatuna...Ina Tsausayinki ne sai ina ga kamar ban miki adalci ba kamar kinfini karfina na so kaina da yawa da Nuna ina Sonki har na Aureki..".
Ranta ya baci Hawayen idanuwanta Suka zubo Cikin Wata Irin Murya Tace"Banta Tsammanin Zuciyarka zata maka irin wannan Tunanin akaina ba...Tunda na taso agidanmu agaban Ammi a kullum karatunta garemu nida Anty Hadiza Shine mu daina Dubam kanmu ko matsayinmu ko na Mahaifinmu Mu Rika Duban Na kasa Damu mu kuma sani Cewa ko yatsun Hannayenmu ba Daidai bane,Daddy ya karantar damu Gidan Uba Dabam yake da Gidan Miji Abban Amira ya kuma Sanar damu ba Lalle bane Abunda ka samu gidan Mahaifinka ka samu gidan Mijinka ba Ya horamu kam zamu iya Yin Aure mu samu Fiye da Abunda muka samu Daga garesu kuma zamu iya Aure bamu samu Kamar yadda muke samu ba sai dai ya Horemu Da kada mu Raina arzikin wani komai kankantarsa,Mu dai mu kasance masu Wadatar zuci da kuma Dogarai ga kai da kuma Tsayawa ga Allah,Sun kuma Horar damu mu Sani Takala ko mai kudi Duka Daya yayi Su..Tunda ga Ranar Dana Gabatar da kai wajen Daddy ya yi min Nasihan cewa Zabi nagari shine mafi a"ala kuma Ranar da za"a kawoni Gidanka a matsayin Matarka Daddy ya Fadamin cewa Kada na Dauka naje zaman Jin Dadi ne Zaman Aure waje ne na Bauta kuma wajen samun aljanna ce..Saboda haka sai namike tsaye kuma nayi aiki Tukuru Domin wajen samun aljannah ba"a samunsa da waasa.."Ta Dakata tana Share kwallahrta Abdullahi Dayayi Shuru yana kallon Hafsah sai Jikinsa ya mutu ya taso Daga Inda yake ya karisa gabanta ya Duka ya saka Duka Hannunwansa saman Kafadunta ya Dagota Lokaci Daya ya Saka Hannu yana Daukemata Hawayenta yana Girgiza mata kai alamun kartayi kuka.
Kukan ne ya kwace mata ta Fada Jikinsa tanayi,Hannayensa ya saka ya Rungumota Yana sakin Ajiyar zuciya itama Rumgumesa tayi kam Tana sakin Kukanta Bayanta ya Shiga Shafawa yana Fadin"Shiii..Is ok..Am Srry kinji bazan kara wannan mganar ba i promise u.."
Kara Lafewa tayi saman Kirjinsa Tana Fadin"Tunda na Aure ka Abban Amira wani abu bai taba Tsolemin ido ba..Miye Mota..? Bakomai bace a zamana dakai kana Bani Abunda Gidajen masu Hawa Motocin basu bama Matansu ba,Farincikin da kake bani da kulawar da kake bani Nida ya"yana yafi yemin duk wani kawan Duniya awajena kai mai arziki ne Domin ban Taba zuwa wani waje an Raina ni ba..Kana bani Abinci mai kyau da Gina Jiki kana Dinkamin Suturu na alfarma masu Tsada Dani da ya"yana,Kana bani Lokacinka uwa uba kana Saukemin Duka Hakokkina Kana kuma kana Darajamin iyayena da yan"uwana kamar yadda kake Mutumta naka miyefi wannan arziki..? Ni awajena Duk macen Data samu wannan Tagama samun arzikin Duniya sai dai ta jira na Lahira kuma.."Tafada lokaci Daya tana Dagowa ta saka Kwayam idanuwanta Cikin nashi Kashemai Jiki tayi yasa kawai ya kamata ya Rumgumeta Rumguma mai Tsawo kafin ya Dago ta ya Sumbaci lebenta Sumbata mai Tsawo da Muradi kafin ya Dago Habarta yana kallonta Cikin Ido Lokaci Daya yana Fadin"Alhamdulillah..ina godiya ga Allah da samunki A matsayin Matata Uwar ya"yana Hakika na yarda kuma na gamsu Fatana kimin Afuwa da mganata kinji ko...? Hafsatu zata iya ma Mijinta Abdullahi Bawan Allah afuwa..?
Yafada yana wani lumshe mata ido Jikinsa kawai ta koma ta Fada ta Dada kamkamesa Jin Haka yasa ya gane ta Hakura Shima Kara kamkameta yayi yana Shakan Kamshin Turaranta,Sun Dade ahaka kana ya Dagota yana Fadin"Hafsatuna na Makara fa...?Sakinsa tayi Tana Tura baki Dariya kawai yayi yana kallonta Bedroom dinsu suka koma ya Dauki briefcase dinsa da key din mashin dinsa Har waje ta Rakashi kana ta Rufe gidan ta koma Dakin ta Fara kwashe kayan da suka bata zuwa Kitchen.
Bayan Sallar Isha"i Suka Tafi Tudun wada sai dai su Ammi suka gansu kwatsam,Su Amira ma basu wani Damu dasu ba,Suna makale da Daddy da Ammi,su kuma suna Jin Dadi Tunda Gidan ba yara,Hafsah sai wani Shagwaba takema Daddy Ammi ta kalleta tana Fadin"Yau ni naga Abunda ya isheni ni Zinaru..? Uwa tazo ta nanikemin Miji Diyama tazo ta Hau nanikamin miji wai me kuke nufi ne..?
Abdullahi na Dariya yace"Ammi kema sai kija maigidanki gefe kiyi Banza dasu.."Ammi tace'Haka Za"ayi kuwa..Ammh Laifin megidan ne ba Cefene ni kuma na saba Mijina cefene yake min.."Dariya suka saka Hafsah tace"Kai Ammi ina Laifima..?Daddy yace"Kyale Zinaru..So take abarmata ni ita kadai..Alhalin Tunda tayi sabon megida ya watsar dani ni kuma sai na koma wajen amaryata kawai bashi kenan ba.."Dukkansu Dariya suka saka Cikin Farinciki sai wajen goma saura na Dare suka koma Gida Shima Din Daddy ne ya matsa su koma Gida Hakika Sunji Dadi Da Abdullahi yace su Amira su zauna har sai Ranar da suka ka gaji suka maidasu sun kai musu kayan sawansu dana Makarantar Haddarsu dama already kayan makatantar na gidan kafin su Tafi Hafsah Taji Abdullahi da Daddy suna mgana kan Gininsa Daya fara yace mai Har Ginin ya Fara tsawo ammh ya Tsaya sai karshen wata kudinsa Sunyi kasa Taji Dai Suna Ta Tattauna mganar bata saka musu baki ba ganin bada ita suke mganar ba.
Kwana Biyu Tsakani Abdullahi na Office ya Kirata yana Fadamata ta yanzu gaya Transfer din kudi ta account Dinsa,har na Kimanin Miliyan Daya da Rabi Daddy ya Turamai yace ya kara Ahidimar Gini,Murna ya kama Hafsah kuma har ga Allah Taji Dadi Sosai Suna gama Waya da Abdullahi ta Kira Daddy tana mai Godiya yace karta damu Abdullahi Tamkar da ya Daukesa Miliyan Daya da Rabi ba wani abu bane,Don ma bai samu yarda yake so ba 2 million yayi Niyar Bashi Hafsah tayi ta Godiya Da irin karamcin da Iyayenta suka ma Mijinta.
Abdullahi kuwa Cikin Farinciki ya Kira Nazifi Ya gayamai bayan ya Kira Daddy yamai Godiya Mamaki ya kama Nazifi Cikin mamaki yace"Kuma sai ka karba..?Abdullahi yace"eh...In ban karba ba zan maida mai dashi ne Nazifi..? Karfa ka manta bani na Rokesa ba Shi da kansa yayi Ra"ayi ina zaune na ya aiko Min Dashi kuma Hadisi ne ba"a maida Hannun kyauta Baya.."
Nazifi yace"Hmm Duk da Haka Mutumina karka Fara wannan gangancin nima da Haka na Fara kaga Daga irin wannan ana baka kana Karba Shikenan wlh baka da wani katabus nan gaba ma Gidan bazaka iya Tutiya Dashi ba Domin ko wani Abu ya Faru ita Hafsah zata iya Dukan kirji tace da kudin Mahaifinta acikin Ginin Gidanka alokacin kana da tacewa..?Abdullahi yace"Nifa banaki mganar bane Mutumina Abu Daya nakeso ka gane Surukaina Suna da Bambamci da irin Iyayen sakina Tunda na Auri Hafsah ban taba kamasu da Wani Abu na Rashin Dattako ba..Na Shaida su na kuma yaba da irin Tarbiyansu bance maka hakan Bazata Faru ba,Zata iya Faruwa mana Tunda dama mace ita yar Gori ce ko Shekara Dari kayi kana Bauta mata Rana Daya ka kuskure zata iya maka Gori ammh Abunda nake so ka gane Sakina da Hafsah suna da Bambamci kai tun Farko Daman kasiyama kanka ne abokina ni kuma Allah na gani ban Daukan ma Kaina ba Itama Hafsah ta sani Shiyasa take kiyayemin Kan wasu abubuwan.."
Nazifi yace"Ai shikenan Tunda kace haka..Zan Shigo zuwa gobe sai muje naga yanayin aikin Nima ya kamata nazo na Fara gina nawa na Gaskiya din nan.."Abdullahi yace"Gaskiya ya kamata ko Saboda in ka Tara iyali in kunxo zaria ba sai kun Sauka Gidan Baba ba kuna da gidanku..."Nazifi yayi karamin Tsaki Kafin yace"Kai Rabani kaji Mutumina ni yanzu Wlh bana ma Kaunar na Hada Zuru"a Da Sakina kwata kwata.."
Abdullahi ya Rike baki yana Fadin"Subhanallah miye zafi kuma..? Nazifi yace'Bama Abunda Baiyi zafi ba Mutumina kai kafi Kowa sanin Halin Danike Ciki..Nagaji da Hallayar sakina Nagaji da Fama da Ciwon mara kada Ciwon Rashin mace kusa Dani ya kasheni Tunda Sakina tafi karfina na yanke Shawaran Aure zan kara Insha Allahu.."
Abdullahi yace"Topha Aure kuma...? Anya baka Hada ma kanka zafi ba kuwa Abokina.."?Nazifi yace"Bawani zafi..kaji mutumina..Kadai ka bari na Shigo zamu Tattauna.."Daga haka sukayi sallama suka yanke Kiran Duk wani masoyin Abdullahi sai da yaji Labarin alherin da Mahaifin Hafsah Yayi mai Mama da Inna Abu kuwa Har Tudun wada suka je yima Daddy Godiya ya Dinga Fadan meya sukaje Kamar wasu kudi ne masu yawa Mama dai sai Godiya kawai sukeyi,Inna Abu tana ta saka albarka dasu ka koma gida tana bama Baba Wada Labari Tana Fadin kaga gidan karamci da Dattako mallam ba irin Surukan Shashashan Yaron nan ba.."
Baba wada yace"Ina zaki Hada Abu..? Ai Iyayen yarinyar nan mutanan kwarai ne Abdullahi yayi Dacen Surukan kwarai Allah dai ya saka da alheri ya bar zumunci.
Ranar Friday Nazifi ya Shigo Zaria Bayan sunje sun Duba wajen Ginin Nazifi ya kalli Abdullahi yana Fadin"Shege mutumina Gini fa yana ta Nisa.."Abdullahi yace"Kai dai bari so nake nan da Shekara mu Tare...Wanchan ya Fara mana kadan gashi ana ta Tara iyalai.."Yafada yana Sosa Sajensa Dariya Nazifi ya saka ya bashi Hannu suka Tafa suna Gefe Inda suke Tsaye Suna Bin ma"ikatan da Kallo Nazifi ya waiwaya yana Fadin"Katon Gida ne fa anan wajen Mutumina..Ammh naga kamar Flat biyu zaka yi ko..?
Abdullahi yace"Eh 2 Flat ne mana..Daya na Hausina da yara,Sai Dakin baki Daya kuma Nawa ne Megida.."Yafada yana Dariya Nazifi ya kallesa yana Fadin"Kodai...kodai Aure zaka kara ne Abokina.?
Abdullahi ya ware ido yana Fadin"Aure..? Rufamin Asiri ina Lallaba Rayuwa ni da matata da ya"yana..Ban ce maka bazan kara Aure ba Har Abada..ammh Bani da Ra"ayi kila in yana Cikim Kaddarata sai kaga na kara ammh gaskiya For now bani da wannam Ra"ayin Wannan sai kai mutumina.."Nazifi ya gyada kai yana Fadin"Hakan nda kyau....Kai in Baka da Dalilin kara Aure ni ina Dashi abaya a tsarina Mata Daya ta isheni Rayuwa ammh a yanzu dana zauna nayi Tunanin in nace zan Zauna akan Tsarina na Baya ni zan Cuci kaina gwara na Auro wacce zata kula dani ta kuma Sauken Nauyin Hakkin na Dake kanta ita kuma sakina Taje ta Cigaba da aikinta Bazan Hanata ba."Abdullahi ya gyada kai alaman gamsuwa yana Fadin"Hakane kaima ta wannan Bangaren kana da gaskiya..to ka samu yarinyar da kake so ne..?
Nazifi ya kada kai yana Fadin'"No..ni yanzu ba so nake nema yarinya mai Hankali wacce ta Fito Daga gidan Tarbiya wacce zata kula dani da Duka Hakkokina kuma in na saka mata Doka bazata iya Tsallakewa ba ballatana tayi Sa"insa dani kamar yadda sakina ke yi dani.."
Abdullahi yace"Tabbas Hakane..Ammh Duk da haka ya kamata ka Bincika ko wannan karon kuma a kaduna garin gwamma zaka lula ka samo mana wata ma"aikaciyar Gwannatin.."Yafada yana Yar Dariya Tabe Nazifi yayi yana wasa da key dim Motarsa yace"Umh..Allah ya Tsareni nayi da Farko ban ji Dadi ba..In Auran kudin ne sai dai na bawani Labarin in auran mace mai kyau ne da Dirin ciki da ilimin Duka naga Dahir Saboda haka yanzu karamar yarinya zan nema yar Sakandiri na aura in na Ga dama na barta ta Cigaba agidana in banga Dama ba kuma na Hanata gwara mu zauna Hakan zaifin kwamciyar Hankali Da Natsuwa akam Auran irin su Sakina.."
Abdullahi ya Dafa kafadan Nazifi yana Fadin"Toh mutumina ka Dudduba ko Cikin Dangi mana baza"a raasa irin wacce kake so ba.."Nazifi yace"Kai Rabani da wannan aikin...Ni ban san ma wasu yanmata Cikin Dangi ba ba tsayawa Tantancesu nake yi ba gwara na nema agari..kwanaki munyi mgana da Salisu Eng.yace min Yana da kannen mata Har guda Hudu naje na Duba Daya Daga Cikinsu in tayimin Shikenan.."
Abdullahi yace"Toh sai kaje ka Duban Din ba laifi suma gidansu suna da Tarbiya anguwansa Daya dasu Hafsatuna aie.."Nazifi yace"Eh Dama na Jira na Shigo ne mu Tattauna sai ka Rakani muje na gansu in na samu wacce tamin Fine in ban samu ba ma Duk Daya ne."Abdullahi yace"Ok toh me zai Hana bayan Na Dawo Daga Office da yammah mu Hadu a anguwa sai muje ka gansu Daganan sai rakani na Shiga Gidansu Hafsah na karama Daddy da godiya.."Nazifi yace"Bakomai Shikenan bari na karisa gida sai mun yi waya.."Daganan sukayi sallama Dama nan Nazifin yazo ya samu Abdullahin Nazifi ya Shiga motarsa ya tafi Shi kuma Abdullahi ya Tsaya suka Tattauna da Shugaban masu kwangilan ginin kana ya hau Mashin Dinsa ya wuce wajen aikin Lokacin Har pass 10 na safe.
Haka ko akayi yadda suka Tsaran haka sukayi Abdullahi sai Gabda mangariba ya taso Daga Office Direct Gidan Mama ya wuce chan ya ijiye mashin dinsa yayi alwala Suka Shiga sallar mangariba bayan sun Idar ya Fito kenan yana Laluban Wayar Nazifin sai gashi a gefensa ashe Tare sukayi Salla Shi Nazifin yana Layin Baya Daganan Gidan Baba wada Suka Shiga Tare Abdullahi ya gaida Inna Abu kana suka Fito Suka Shiga Gidan Mama sun isketa Tana Sallah Jidda na Tsakar Gida Tana wanke Innerwears Dinta,ta Dago tana gaishesu Abdullahi ya amsa Fuska ba Fara"a Nazifi kuma ya kafeta da ido Domin Duk sanda zai ga Jidda sai yaji Faduwar gaba yana kallon Abunda take wankewa sai da ya murmusa ganin yadda taji kunya tayi Saurin Suran Botikin ta Shige Kitchen tana Sunne kai da Kallo ya Bita yana jin wani irin Acikin Ransa game da Jiddan.
Basu jira Maman ta idar da Sallah ba Abdullahi yace in ta idar Ta gayamata zasu Fita da Nazifi su dawo tace Toh,Sun Fito kenam sukaci karo da Auwal a Kofar Gidan Jin Abdullahi Tare zasu Fita da Nazifi yasa ya Sadda kai yana Rokon Abdullahi ya aramai Mashin dinsa zai je ya gaida wani dan ajinsu ne baida Lafiya Mikasa Abdullahi yana Fadin"In ma Tadi zaka gashi..Sai dai ka dawo da wuri muna Dawowa zan wuce gida.."
Nazifi yace"Kyaleshi...kai Auwal in kadawo in da zakaje ka kaimai Ita gida ni kuma in mun Dawo zan ijiyeka gida ba Shikenan ba.."Abdullahi ya kada kai yana Fadin"Fine..Tunda zaka maidani Gida.."Yafada yana Zakuda kafada,Daganan suka wuce Auwal kuma ya Shige Cikin Gida yana Murna.
Gidansu Hafsah suka Fara zuwa Sun yi sa"a Dawowar Daddy kenan nan suka Duka suka gaisheshi Kana Nazifi ya Taya Abdullahi godiya Daddy yace bakomai,Su Amira kuwa suka Rugo suna ma Su Abdullahi oyoyo Amir ne ke Tambayan Momy Abdullahi yace Tana gida Ammi tazubo musu Lafiyayyan Tuwon Shinkafa wacce Taji miyan agushi da Nama da man Shanu nan suka baje sukaci sukayi nak,Tare ma da Daddy suka Fita sallar Isha'i masallacin Dake kusa da gidansu Hafsah,Basu Dawo ba Daganan suka ma Daddy sallama suka karisa Gidansu Salisu engr.
Dama Salisun ya sam da zuwansu Duk da Baya gidan yana Gidansa Nagoyi Dayake yayi Aure ammh ya Kira Mamansu Hajiya Amina ya gayama zuwansu Nazifi ita kuma ta Umurci yaran da kowacce ta Shirya kafin isowarsu Nazifin,Suna zuwa Kofar Gidan Nazifi ya Kira Salisu yace gasu sun iso,sai yace Bari azo ashiga dasu Basu wani Jima ba sai ga wani yaro yazo yayi musu Jagora zuwa Falon gidan,
Gidan Ba gidan get bane,ammh kuma Babbam Gidane daga gani Suna Rufin Asiri Duk da mahaifinsu ya Rasu,Salisu asali Abokin Nazifi ne tare sukayi Jami"a,Toh Tunda suna Tare da Abdullahi sai kuma Duka suka zama abokan juna dama Duk yawaanci abokan Nazifi Duk abokan Abdullahi ne haka Shima anashi Bangaren Tunda sun zama Daya aminaine Tun ba na yanzu ba Tun Suna yara Tasowar anguwa Daya kuma iyaye Suna Zumunci.
Sun samu Tarba mai kyau Sosai am kawo musu abinci da kayan Shaye Shaye,Zuwa Chan sai ga Hajiya Aminan da kanta ta fito sun Gaisa tana ta saka musu albarka Fitan ta ba Dadewa sai ga Jerin yanmatan Hudu kannin Salisu sun Shigo Falon kowacce Da Shiga ta alfarma...
*Shakira....*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
_*Wannan Shafin ya Tafi ne kai Tsaye Zuwa ga Hazikan marubuta Masu Nuna min Kaunarsu Afili,Hakika Bakina yayi Kadan Wajen Nuna musu Godiyata....Ina Kike MY JIKA KAUSAR AGLAN NISSA,dake HASINA AUTAR MANYA,Sai ke My Mom DEEJART,ina kike FATIMA FATNOOR,Da ke kanki Kanwata NIMCYSARAUTA,Bazan Manta Dake ba FAUZIYA S MADAKI,Da ke kanki My Habibaty AISHA IDRIS ABDULLAHI...Dukkanku ina Rokon Allah yayi Riko Da Duka Hannayenku Wajen Rubuta alheri..Alherin Allah yakai muku adukkan Inda kuke Ku sani ku Kara Sani Ni Janaftyshakira Kuna Burgeni...*_
*016*
"Duka yanmata Hudun ajere suka Shigo Kowacce na Bin Bayan yar"uwanta Cikin Shiga ta alafarma da kece Raini na musamman kowacce tana Tashin kamshi da Gayunta na musamman wanda take ji Har acikin Ranta itace zatayi nasaran samun Zankadeden Miji irin Abokin yayansu Salisu.
Barkat Itace Babbansu Itace kan Gaba Doguwar mace ce mai Fadin Fuska da Dara Daran Idanuwana Farace tas kamar atabata Jini ya Fito Tana da Dirin Jiki na Mata Daidai gwargwardo,Itace ke Bin Salisu Duk da akwai wata tsakaninsu Sadiya Allah yayi mata Rasuwa,Barkat Tana aji uku ne a Abu Samaru inda take karantar Micro Biology,Tana kuma sanye ne da Wata Ubansu Doguwar Rigar leshi wacce aka mata Dinkin A Shape ya kama ajikinta Sosai sai Daurin Maryam babangida Datayi ta yane Jikinta da wani Siririn gyale Fuskarta yana Fitar da wani Annuri wanda Daga gani kasan Haka baiwarta Take ammh kuma Daga kallonta zaka Fahimci bata da yalwar Fara"a kamar Sauran kannenta,akallah a shekaru bazata wuce Shekaru 25 aduniya ba ammh Fuskarta da yanayin Tsarin Jikinta ya Boye Duka Shekarunta.
Sai Bahiya wacce ke Bimata Itama Farace sosai sai Doguwar Fuska gareta Mai Dauke da madaidaicin Hanci da kuma Karamin Bakinta,Idanuwanta basu kai na Barkat ba,Ita nata suna da kwarmin Sosai Sudan Shige kadan itama Tana sanye Cikin Riga da Sikat na Atamfa tayi Daurin Ture ta bazo gashin Dokin datayi kari Dashi ta baya Bayan ta saka wani Mayafi baki ta yane kanta Dashi,Bahiya tana Abu ne itama aji Biyu Tana karantar Computer Science ne akallah a shekaru zatayi Shekaru 23 aduniya,ita tana da Fara"a soaai Domin Duka Fararan Hakoranta Suna Washe ne,sabanin Barkat da Ko Burbushin Fara"a bashi a saman Fuskarta.
Sai Ta ukunsu Bahijjat,Itama Farace Kamar sauran ammh bata kaisu haske ba,sai dai bata da Diri Sosai Sirintantan ya Fito Sosai,tana da kyau Ammh kuma Fuskarta Doguwa ne,haka Karan Hancinta,itama karatu take a poli tana Nd2 tana karantar SLT,ashekaru bazata wuce 20 aduniya ba sai Karamarsu Aina ita kuma Yarinya Sosai Ammh bata da Haske kamarsu Black beauty ce,Tafi kyau ma sai dai Bata da Tsawo Gajera ce Sosai,tana Shekaran Karshe a makarantar Sakandiri ta yanmata Dake basawa Ashekaru bazata wuce 18 ba in ka kalleta ma zaka Fahimci yarinyartar sosai itama taci kwalliyarta Sosai Duk dama Hajiya ce ta matsa mata sai tabi Jerin yan"uwanta ammh ita sam Bata Ma Fatan tayi Aure yanzu Shiyasa ma bata damu kanta ba kuma Tana Fatan Insha Allahu ma baza"a zabeta ba Tunda ga Na sama da ita su Anty Bahiya.
Duk acikin Mintunan da basu gaza Goma ba Nazifi da Abdullahi Suka karesu musu kallo Dama already Salisu yayi musu Bayanin Sunayensu da kuma matakin karatun kowaccensu Shiyasa suna ganinsu suka Tantance kamannin kowaccensu,Su kuwa Dukkansu zama sukayi saman Kujeran Dake Fuskanta Abdullahi da Nazifin kansu na kasa kowacce da Abunda take sakawa acikin Zuciyarta,bayan sun Hada baki wajen gaishesu Cikin Girmamawa.
Abdullahi ya waiga ya kalli Nazifi Shima ya kallesa,Kana Abdullahi ya maida kallonsa kansu yana amsa gaisuwan nasu Cikin kulawa Da Sauri Barkat ta Dago Idanuwanta sama suka Hada Ido Hudu da Abdullahi Lokaci Daya taji gabanta ya yanke ya Fadi,Shi kuwa Kansa ya dauke sama yana Fadin"Sannun ku da Fitowa yan mata.."Yafada batare Daya Shirya Fadin Hakan ba ganin Nazifin yayi Shuru yaki Cewa komai.
Jin Muryansa yasa kowaccensu ta Dago kanta tana kalloshi a kallon Farko Dukkansu sun zata Abdullahin ne, wanda zai zabi Daya acikinsu ganinsa Cikin Farar Shadda Tazarce harda Hula sabanin Nazifi da bai ma Sanya Hular ba kuma Shi Tunda ya kare musu kallo Yaji ba wacce zatayi Daidai dashi Gwarama karamarsu sai dai kuma tayi Gajarta dayawa Shiyasa kawai ya Kara Hade Ransa kawai ya maida Hankalinsa wajen latsa wayarsa.
Su kuwa kowacce sai ta Fara gyarawa Barin ma Bahiya datafi kowa Rawan kai da kafa,Cikin yanga tace"Yauwa..Baku Ko sha Ruwa ba..? Tafada tana wani karya Murya Take mata kafa Bahijjat tayi Tana Hararanta ta kasan Ido yayin da Barkat Ta Lumshe ido Cikin Sanyi Jiki da Kasala kana Ta Bude tana Bin Abdullahi da wani irin kallo Wanda ita kanta ta kasa gane kanta Duk Jin kanta da Jan ajinta Sai gashi ta saki Idanuwanta gabadaya Tana kallon Kowani Motsi na Abdullahi Tana naji aranta yau Taga Namijin Data Dade Tana nema.
Abdullahi yayi Mirmishin yake yana Satan kallon Nazifi Lokaci Daya yana dan zakudan Kafadansa ganin haka yasa Nazifi ya Dago kansa yana kallon Abdullahin wanda ya Rausayamai kai Cikin Alamun kayi mgana mana,Kallonsa Nazifi yayi kafin ya maida hankalinsa kansu Ido Cikin Ido yake kare musu Kallo Kur kai kana ganin kallon kasan na Kurullila ne Shiyasa kowaccensu ta maida kanta kasa,Sai Barkat wanda dama Chan kanta na gefe ne Hankalinta da Numfashinta yana kan Duk wani Motsin Abdullahi ne.
Cikin Gadara Nazifi yace"Masha Allah...Lalle Hajiya ta iya Haihuwa..Sai dai gashi ba wacce ta gabatar mana da kanta Tun zuwanmu..."Yafada kai Tsaye yana kallonsu Bahiya ce tayi Mirmishi ta Dago Cikin Salo Tana Fadin"Ok..Ba matsala Ni Sunana Bahiya..'Bahijjat tayi karaf tace"Haba Bahi ki bari mana Anty Barkat ta Fara mgana mana.."
Baki Bahiya ta Tura bata kara mgana ba Abun sai ya kusa saka Abdullahi Dariya sai ya kanne ya koma gefe kawai yana kallon Ikon Allah ganin Nazifin yana kokarin Raina musu wayau Cikin Ladabi Bahijat tace"Anty Barkat ki Fara mgana Don Allah.."
Ta Fada Tana kallonta Ko Dago kanta batayi ba kanta na kasa Tana wasa da Zoben Hannunta ganin Taki mgana ne yasa Nazifi ya kalli Bahijjat yana Fadin"Ku ku Fadamana Sunayenku..Tunda Taki Fadi Kila ta cire kanta ne Ba Damuwa.."yafada kai Tsaye yana kallon Barkat din aransa yana Fadin"Allah raka taki gona Duk mun sanku irinsu Sakina ne masu Jin kai sai ka kwasa ka kai Gidanka ka kwasan ma kanka Bala"i.."
Jin Haka yasa Bahiya ta Fara gabatar da kanta sai Bahijjat sai Aina,Barkat ce ta karshe kamar Batazatayi mgana ba ta Bude Baki Cikin yangar da ya zamar mata Jiki tace"Barkat..."Daga haka ta Rausaya kanta gefe kawai Nazifi yaso ma ya saki Tsaki sai dai ya Fasa Abdullahi kuwa Ruwa ya Dauko ya tsiyaya a kofi ya Tsiyaya yasha Kadan,Ya ijiye Kofin kenan Ganin Falon ya Kara Daukan Shuru,sai wayarsa Dake gaban Aljihunsa ta Dauki Kara ya Zarota da Sauri Ganin Sunan mai kiran yasa ya Dafe kansa yana kallon Nazifi Lokaci Daya yana Fadin"Nayi ma Hafsatuna Laifi ban Kirata na gayamata zan Tsaya wani waje ba..'
Nazifi ya kada kai yana Fadin"kaima baka kyauta ba..Gata ita kadai agida su Amira na wajen Ammi.."Mikewa yayi yana Fadin"Bari na Lallasheta ina Jiranka awaje.."Yafada yana kama Hanyar barin Falon Lokaci Daya yana Daga Kiran da Fadin"Hafsatun Abdullahi..."Ya fada Cikin Wata Murya mai Cike da kauna da Muradi mai Girma ba Barkat ba Hatta su Bahiya sai da suka Raka Abdullahi da ido Suna Tunanin kowaye wannan gayen ya gama Haduwa acikin Ran Bahiya kuwa tana addu"ar Allah sa ya zabeta in shine wanda ke neman Matan.
Barkat kuwa Tuni Zuciyarta ta Fara Zafi Jin Crush dinta yana Kiran wata da Hafsatunsa Lumshe ido Tayi tana maimaita Sunan Abdullahi acikin Ranta Lokaci Daya ta saki Mirmishi,ita kadai Duk Nazifi na kula Da ita Tabe baki yayi kafin yayi mgana yaga Dukkansu sun mike Bahijjat Da Bahiya suka tsaya mai sallama Barkat kuwa Da Aina Gaba suka wuce suka Fice Daga Falon Nazifi yace ma su Bahiya suma Hajiya Amina mgana zasu wuce,Sun Fita ba Dadewa sai gata ta Shigo nan Nazifi yayi mata Sallama Ya bata 10k Taki karba sai da ya nuna bai ji Dadi ba Itama sai Fada take basu Ci wani abu ba,da zai mike tace ina Abokin nashi yace yana waje tace toh su gaida gida Sun gode kwarai.
Har Nazifi ya Fice Daga Falon Tana Zaune Aranta tana Fatan Ya ga wanda Tayi mai,Domin Tasan Nazifin Sosai tare suke zuwa da Salisu Abdullahi ne ma bata wayeshi, ba Cikin Gida ta koma Bahiya ta Fara Taranta da"Hajiya waya zaba?ya gaya miki.? Hararanta Hajiya tayi kafin tace"Bansani ba mai Shigen Rawan kafa..Wazai zabeki da wannan Azarbabin naki.."
Bahijjat tace"Haka taje tana yi Hajiya Ta bari ma Anty Barkat tayi mgana taki.."Hajiya ta kada kai Tana Fadi "Daman na sani..Ke kam Bahi Allah ya Shiryaki."Tura baki take yi tatashi ta Shige Dakinsu Nan Hajiya ta nuna musu kudin Da Nazifin ya bata Cikin Yarinyata Aina tace"hajiya waye Ya Nazifin aciki wai..?
Hajiya Amina tace"Mai Sky Blue din Shadda ne..".
Dukkansu Da mamaki sukabi Mahaifiyar nasu da kallo Cikin Mamaki Bahijjat tace"What Hajiya.?na zata mai Farar Shadda ne.."Hajiya tace"A"a bashi bane..Bansanshi ba ammh Shima Salisu yace Dukka Abokansa ne Shi Aminin Nazifin ne inaga Rakosa yayi.."Barkat ta Dago Kanta akaro na Farko Tun Bayan Shigowar Hajiya Falon Cikin Kasala tace"Abokinsa..? Tafada Cikin karya wuya da Mamaki Hajiya ta kalleta tana Fadin"Eh haka Salisun yace min..Ammh me neman matan Shi Nazifin ne."
Bahijjat tace"Tabdi..Allah Hajiya na Zata Dayan ne..Shi Nazifin ya Cika Nuna kamar ma ba wacce tayi mai acikinmu Dayan kuma yafi Shi Nuna aji da suwas na manyan yara..."Hararanta Hajiya Tayi Tana Fadin"Kema sakarya ce...Tafi kibama Mutane waje,Duk Halinku Daya da Bahiya Din."Dariya tayi ta wuce Tana Fadin"Nifa Daman Bai min Ba Dama Dayan ne gwara gwara yafi kallon Mutumici Allah sa ma ba wacce tamai acikinmu..."Da Harara Hajiya ta Rakata Har ta Shige Dakinsu Barkat kuwa Jikinta neyayi sanyi Jin Abdullahi ma Rako yayi ganin Yanayinta yasa Hajiya tace"Barkat lafiyanki kuwa..? Dago Dara Daran idanuwanta tayi tana Fadin"Bakomai Hajiya.."Daga haka kawai ta mike tana Rangaji Zuwa Dakinsu kamar mara Lafiya Duk da Hajiya ta santa da Wani Irim Iko da sanyi kan komai sai da tayi mamakin Chanzawarta Kai kawai ta kada Ta Tashi da kudin Hannunta zuwa Cikin Bedroom dinta.
Abagaren su Abdullahi kuwa Basu cema Juna komai ba sai da suka Dauki Hanya kana Abdullahi ya kalli Nazifi yana Fadin"To ya Mutumina..? An dace..? Baki Nazifi ya Tabe yana Fadin"Ba"a dace ba...Kasan Allah Duk kwanwan Ja ce,In na kwasa wni Bala"in zan kara kaima kaina kawai.."Abdullahi yace"Meyasa..? kuma naga Dukkansu ba laifi Abokina.."Nazifi yace"Ban ce suna da Laifi ba Im nace zan kushesu bam ma kaina adalci ba kawai dai Abunda na Fahimta auran mace mai Ilimi Sosai wacce ta Fara girma matsala ne gwara ka auri karamar yarinya yar Sakandiri wacce zaka koyamata komai da kanka Wacce na Tabbata bazata Taba gardama ko Sa"insa da kai ba.."Abdullahi yayi Dariya yace"kuma fa Hakane kaima kayi Dabara toh ga karamarsu Mana.."
Nazifi ya Tabe baki Yana Fadin"Ita gaskiyan matsalanta bata da tsawo kuma kasanni ni Bana son Gajeran mace.."Abdullahi yace"kai..kenan ba wacce tayi maka kenan ko..? Nazifi yace"Kusan haka gaskiya.."Abdullahi ya Kada kai yana Fadin"Nifa na zata babbarsu zaka Zaba naga tafi su Aji da Kama kai.."Nazifi ya juyo yana kallonsa Lokaci Daya yace"Wa kenan..? Abdullahi ya Tabe baki yana Fadin"Wata ke ma da Suna Baraka ko wa..?
Nazifi ya Sheke da Dariya yana Fadin"Au Wai barkat ko..? Abdullahi yace"Oho ina jin Haka Sunan yake..Ita.."Nazifi yace"Allah ya Sauwake ai ni Irinsu basu Burgeni masu Shigen Girnman kai da Nuna isa Duk irinsu Sakina ne, sai ka kwasam ma kanka Ka kwashi Bala"i Ni Wlh sam Bata Burgeni ba.."Abdullahi yace"Allah ya kyauta yanzu me zaka ce ma Salisun..? Kasan fa Ba Dadi Kace mai Duk Cikinsu ba wacce tayi maka..?
Nazifi yace"Bayani zan koramai..Dama bance mai Dole wata Zatamin ba..Shima ya sani Cewa nayi zan Duba in naga wacce tamin Shikenan.."Abdullahi yace"Shikenan ammh kaki min ne..Da ko karamar kun Daidaita Gajartan ta bawani abu bane Tunda ai sakina tana Tsawo Shikenan ka Hada Both Side."Ya karishe Fada yana Dariya Nazifi ya Bankamai Harara yana Fadin"Kaima Ai Hafsah na da Tsawo In ni batamim a,kai sai ka Taimaka kaima ka Hada Duka Bangaren Mr Shawara man.."Abdullahi yace"Ikon Allah miye yayi zafi shi fa Wuta Ba Mallam..Nazifi Wada? Ni kaji nace maka ina Son Auran yara kanana ne..? Wannan ra"ayinka ne Ni ba nawa ba.."Nazifi yace"Toh sai kowa ya bar Ra"ayinsa Fakat.."
Abdullahi yace"Miye Zafi..? Shikenan Chapter close daman Salisun nake ji Gaskiyan mgana zai Ji ba Dadi.."Ko kallonsa Nazifi bai karayi ba,ballatana ya kara mai Mgana har yayi parking kofar Gidansa Abdullahi ya Bude Murfin Mota ya Fice Lokaci Daya ya Rankwafo yana Fadin"Toh mutumina sai yaushe kenan..?
Nazifi yace"Sai gobe kenan ko..? Any way muyi mgana ta waya Goben zan koma Kaduna Sakina Tamin waya zata Dawo Goben.."Abdullahi yace"Ah ba Haduwa kenan Amarya zata Dawo wajen Tsohon gauron angonta Hajj Nazifi.."Kafin ma Abdullahi ya matsa Nazifi ya Tada Motan kadan ya Rage ya kadashi yayi baya yana Dariya afili ya Furta"Ji bakinciki zai ma Hausina Asara Tunda Shi Sakina bata damu dashi ba.."Yana Tsaye a wajen har Motar Nazifi ta bace ma ganinsa,kana ya zo Zai Shiga Gida Jin Kofar gidan a kulle yasa ya Ciro dan makullin Dake Hannunsa ya Bude ya Shiga.
Hafsah har ta Fara Barci saman Kujaran Falon,Shi ya Tadata tana ganinsa Ta Mike ta Fada Jikinsa Tana sakarmai kukan Shagwaba tana Fadin"Ina ka Shiga ne Tundazu ina ta Jiranka Har Auwal yazo ya kawo ma Mashin Dinka ya tafi baka dawo ba.."?Yana Buga Bayanta Cikin Lallami yace"Am So Srry Hausina..Laifina ne da zamu Fita da Nazifi ban Kiraki na Fadamiki ba ammh ai na Fada miki da kika Kirani ko..? Tana kara Shigewa Jikinsa tace"Toh kuma Shine kace gakanan zuwa kaki dawowa da wuri ni kadai agida ina Jin Tsoro.."
Abdullahi ya Tarairayota yana Fadin"Oh my god...Am so sorry Hafsatuna Bazan kara ba kinji ko..? Yafada Lokaci Daya yana Yawo da Hannunsa abayanta Cikin Rada tace mai ga abinci yace mata Ammi ta cika musu Ciki Jin haka yasa ta washe baki Shikuma ya Shiga gayamata Diramar Ammi dasu Amira Hafsah na Dariya ammh bai gayamata inda suka je da Nazifi ba yadai ce mata sun Biya wani waje ne,Bata damu da Tambayarsa ba sanin ko zata mutu bazai gayamata ba sanin Halinsa na Zurfin Ciki da Rike sirri koda banashi bane balle na Amininsa Nazifi.
Washegari kuma Su Abdullahi suka Tafi Danja Daurin Auran Diyar Mijin Goggo Habiba amotar Nazifi dashi da Abdullahin da Nazifin da Mama sai Inna Abu da Baba wada sai Auwal sukaje sukayi samu Daurin Auren, wajen uku na Rana suka kamo Hanya suka Dawo Suna Dawowa Nazifi ya wuce Kaduna Bayan ya Kira Salisun ya mai Bayanin ba wacce tayimai Salisu bai nuna damuwarsa ba ammh acikin Ransa baiji Dadi ba sam Haka ya Kira Hajiya Amina ya gayamata Cewa Nazifin yace ba wacce tayi mai Hajiya ita kanta Bataji Dadi ba ammh sai ta nuna Allah yasa Hakan ya zama alheri,Da su Bahiya sukaji labari basu ji Dadi ba Musamman Bahiya,Bahijjat kuma ko ajikinta Ballatana ma Aina Da bata damu ba Barkat kuwa Bata bari kowa ya gane yanayinta ba ammh a zahirin gaskiya Jiya ta kwana da mafarkin Abdullahi wanda ya Shiga Cikin Zuciyarta Lokaci Daya batare data sani ba.
*******
Bayan Sati Biyu Tsakani Sai ga Waya Daga kano Cewa Anty Hadiza ta Haihu yan Biyu Duka Maza,ammh C.s akayi mata tana asibitin Murtala Aminu specialist Hop,Dake kano,Ammi ta Kira Hafsah Tana Fadamata Ihun Murna Hafsah ta saki Cikin Farinciki Dadi kamar ya kasheta Abdullahi na Office sai ga Kiran Hafsah tana gayamai Haihuwan Shima yayi murna Sosai Cikin Zolaya yace"Hafsatuna nima ko yau na Bada Himma na baki ajiya kwan Haihuwa guda Biyu ne..? Ina son Twice Sosai fa..".
Kunya ya kamata ta saki Dariya Tana Fadin"Allah ya bamu Masu albarka Yace Amin..Cikin Shagwaba tace"Abban Amira gobe zan Tafi ko..? Tunda ma su Amira na wajen su Ammi haryanzu.."Cikin mamaki Abdullahi yace"Ina zaki gobe..? Cikin Sauri Hafsah tace"Kano mana Abban Amira Kaga fa C.s akama Anty Hadizan yau Ammi tace Zata Tura Inna Asibi tatafi Chan wajenta Ni kuma ba sai gobe na tafi ba.."
Cikin Mamaki yace"Ki dawo yaushe kenan..? Hafsah tace"Wai da Bayan suna kaga nesa ne kada ayi Tafiya Rarrabe.."Baki kawai Abdullahi ya Rike yana Fadin"Hakane..Sannu Uwar Suna ko nace na Sha"ani..Allah kaimu.."Daga haka kawai ya yanke Kiran Ita kuma Hafsah jin Haka yasa ta Shiga Murna nan da nan Ta Hau Shirin kayanta bayan ta gama ta Kira Subai ta Fadamata itama tayi murna Tace insha Allahu zata je suna Nan Hafsah ke gayamata gobe zata tafi sai bayan suna zata dawo Subai ta rike baki Tana Fadin"Ke don Allah shi ya Abdullahin ya barki..?
Hafsah tace'Nima nayi mamaki kila Don suna Shiri da Anty Hadizan ne..'Subai tace"Sai dai haka..Allah sarki Allah ya bata Yayanta nawa yanzu..? Hafsah tace"Uku ne,da wadanan Yan Biyu making 5 kenan..."Subai tace'Masha Allah Allah ya rayasu"Daganan suka yanke Kiran Daga ita Mama ta Kira ta gayamawa Mama tace Ammi ta kirata yanzu Umman Sadiq ta kira itama tace Ammi ta Kirata yanzu ta gayamata,Tace insha Allahu zata yi kokari tazo Zaria Allah barshi sai ta karisa kanon.
Duk wanda ya kamata yaji Haihuwan yaji Hafsah kuwa har Daddy ta Kira tana mai Barka,Ya Dinga Tsokananta yana Fadin Yana Jiranta wata Shekara Duk kunya sai ya kamata,Abdullahi ma Daya dawo ya Kira Daddy da Ammi yayi musu barka Harda Anty Hadizan wacce har ta Farfado Tun da Rana Tunda tun Cikin Daran Jiya ne akayi aikin,Inna Asibi har ta isa Tun safe,Abdullahi yana jin Hafsah na Fadama Anty Hadizan gobe tana Kan Hanya Har Anty Hadizan tana Cemata sai suzo tare da Matar Baba Mustapha Hajiya gaje Domin yanzu suka gama waya tace suna tafe gobe Marwan zai kawota Babban Danta.
Har jinta yayi tana Fadin sai ta Bisu suzo Tare,Abdullahi bai nuna mata komai ba adaran Ranar Haka suka Raya wannan Daran cikin Farinciki da Soyayyah Tun Safe,kuma Hafsah tatashi da Gyaran Gida tayi Breakfast da wuri Ta Shirya tayi wanka Babban akwatinta ta Cika da kaya Tun safe ta Kira Mama gaje ta gayamata zata Bisu tace tayi kokari ta Biyo su Tafi tare,Abdullahi bai ce mata komai ba sai da ya Shirya zai tafi Office kana Hafsah tace"Abban Amira baka ce min komai ba.."?
Yana Daura Tek tie dinsa yace"kamar name..? Cikin mamaki tace"Baka ce min komai kan Tafiyata kano yau ba kuma baka bani kudi a hannuna ba Haka zan tafi..?.
Kai tsaya yace"Haka zaki Tafi mana Tunda ke kika Tsara Tafiyar naki.."Tsuru Hafsah tayi mai da ido cikin Rawan Murya tace"Ban...ga..ne mganar ka...ba Abban Amira.."?
Bai bama Mganarta muhimmanci ba yace"Ni nace ki Shirya ki tafi kano kije ki tare sai bayan Suna..? Ke kika Tsarama ma kanki Tafiyar bazan hanaki ba Saboda yar"uwanki ce ta Jini in na Hanaki bazaki ji Dadi ba ammh in ni zan Tsara miki Tafiya sai nace ki bari sai ana gobe suna ki tafi In akayi suna ki Dawo yau kuma sai kibisu kije ki Dubata ki Biyosu ki Dawo duk wanda kika zaba bazan Hanaki ba."
Hafsah taji ta Raina kanta Cikin Wani Irin murya tace"Ammh ai Kaasan Anty Hadiza bata da wata Kanwa sai ni ko..? Bai kamata na Tafi ba tun yau..?
Yana Daukan key din Mashin dinsa da jakar Brief case dinsa yace"Wa kika ji yace bai kamata ba.? Ya kamata mana Sosai.."
Hafsah takada kai kafin tace"Toh kagani..."Yana yar dariya yace"Shikenan Allah ya kaiku lafiya kima Mai jego barka.."Daga haka yasaka kai zai Fice Cikim mamaki tace"Abban Amira.."
Cak ya tsaya Lokaci Daya ya waigo yana Fadin"Uhmm..Menene..?
Kanta na kasa tace"Baka bani komai ba...Kasan kuma bana yi Tafiya bani da kudi a Hannuna ba.."
Kai Tsaye Abdullahi yace"Bani da kudi yanzu a Hannuna...Tunda ke kika Shirya tafiyanki na zata kina da kudinki ne Shiyasa kikaga ban hanaki ba."Yafada yana Kafeta da idanuwansa Dago kanta tayi Cikin Rau rau tace"Abban Amira waya bani kudin.? Kai tsaye yace"Ina zan sani..Nifa nazata kina da kudi ne Tunda kika Shirya tafiya yau.."..
Idanuwanta suna kawo kwallah tace"Yanzu dai bazaka bani ba kake Nufi ko Abban Amira..?
Kai Tsaye yace"Gaskiyan mgana ayanzu dai bani dashi..Shiyasa nace ki bari Zuwa ana gobe suna Lokacin na samu albashina sai na baki Ishashen kudi ammh yanzu kam ko sisi bazan baki ba keda kika Shirya tafiyan Dama baki Tanadi kudin da zaki rike bane..? Yafada Cikin nuna mamaki yana yar dariya hawaye ya kawo idanuwan Hafsah tayi maza ta Share Lokaci Daya ta kada kai tana Fadin"Bakomai nagode..Bakomai yajamin ba sai Rashin sana"a
Dariya ta kaama Abdullahi sai ya kanne yana Fadin"Allah Madam..? To ko zaki Jira in kin Kafa sana"ar taki kin samu Riba sai ki Tattara ki tafi... ? Ya fada yana mata Dariyan mugunta Takaichi ya kama Hafsah ta kadai kawai ta juya zuwa Ciki Tana Fadin"Zan tafi..Insha Allahu Tunda dai ka amince bazan Rasa yadda zan yi ba..
Shima kai Tsayen yace"Shikenan Allah kiyaye Hanya ni ba bakon zafi bane na amince ki Tafi..Ammh kuma ban yarje miki kije kina Roko ko baran kudi ba Tunda ban ce ki Tafi Dole ba Fitinarki ce atoh.."Daga haka kawai ya saka kai ya fice yana mamakin Taurin kai da Rashin Hankalin Hafsah na wani Lokacin..
*Janafty.....*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*017*
"Da kallon Mamaki Ta Bishi Lokaci Daya tana Dauke Kwallar Idanuwanta kada kai tayi ta koma Cikin Bedroom dinta ta Dauko Hijabinta ta saka Hade da Takalmi sai Karamar Jakarta Data Dauka da wayarta,Key din Gidan ta Dauko da Akwatinta Inda ta saka Kayanta bata da ko Sisi sai Naira Dubu Daya ita kawai ta Dauka ta Tura Cikin Jaka tana jin wani karfin gwiwan Tafiya da kuma Takchin Abunda Abdullahi yayi mata yau.
Fitowa Falo tayi Bayan ta kashe Wutar Cikin Dakin.
Sai da ta kashe komai na Wuta kana Ta kulle Dakin nata Tana Cikin Kulle kitchen sai ga Yunusa almajiranta yazo sallamansa kawai Tayi saboda Tayi Duka ayyukanta,Tana da wata Naira Dari,ta mikamai tace bazata dawo yanzu ba sai bayan Sati Daya,amsa yayi yayi Godiya Kusan Tare suka Fita ta Kulle Gidan Yunusa ya Daukan mata akwatin Zuwa Bakin Titi ta samu Adaidaita zuwa Gidan Ammi.
Tana Cikin adaidaitan ne ta Kira Wayar Mama Bayan sun gaisa take gayama Mama tafiyarta Kano Ita kanta Mama tayimamaki Sosai ammh bata Furta ba ta mata Fatan Kaiwa lafiya da kuma alkawarin suna nan zuwa Ita da Inna Abu gobe ko Jibi,Ahaka suka yanke Kiran Hafsah sai da Ammi ta ganta da akwati Riki Riki Nan ta Shiga Fadan wani Rashin Hankali ne Jiya Daga yin Haihuwa,yau kuma zata bar Mijinta taje chan ta Tare,Tura baki Hafsah ta kama yi sai Hawaye Dama ga Takaichin Abdullahi ga ita kuma na Ammi.
Cikin Tura baki da Hawaye Hafsah ke Fadin"Shifa ya barni Ammi.."Ammi tace"Ke kika matsamai wlh..Haba Hafsah baki da Hankali wlh Tsiyata Dake Wauta..Jiya fa akayi Haihuwan nan,Kuma Hadizar bata gida Tana asibiti fa,kuma Asibi tana chan Tun Jiya banda Rashin Hankali basai ki bari zuwa Jibi ko Gata sai ki Tafi ba.."Kuka Wurjan kawai Hafsah ta saka Alhaji Hamza ya Fito Daga Dakinsa yana Fadin"Zinaru kin Cika Fada wani Lokaci ba tace shi Abdullahin ya yarjemata ba..?
Ammi ta waiga Tana kallonsa Lokaci Daya tana Fadin"Ammh Daddy Kasan dai matsamai Tayi ko..? Jiya ne fa Hadizan ta Haihu...? Yanzu kwana nawa zatayi a kano kafin ta Dawo.. ? Cewa zatayi sai bayan suna zata dawo fa.?Hafsah tatashi da Gudu ta karisa Jikinsa ta Rumgumesa tana Kuka Riketa yayi yana Dafa Kanta alamun Lallashi.
Kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon ya Zaunar da ita,Shima ya Zauna yana Fadin"Sai me..? Ina Ruwanki ba mijinta bane ya barta..? Don Allah ki Dinga Saussauta ma Ranki Shi kanshi ya sani Itace kanwarta Duk Duniya guda Daya domin ya Barta Taje na wasu kwanaki ai ba Laifi bane Don taje..? Inda bata Kamata ba kinsan bazata je ba ...."Ammi ta Kada kai Tana Fadin"Ai Shikenan...Allah ya bada sa"a Dama baka san Laifin yarinyar nan sam.."
Daddy yace"Ba haka bane Zinaru..Mijinta ya barta baki da ikon Hanata..Gashi a banza kin sakamin Mamana kuka.."Yafada yana Share mata Hawaye Saboda Takaichi Ciki Ammi ta Shige tana Korafi Hafsah ta Kalli Daddy tana Gaisheshi ya amsa Yana Shafa kanta Cikin Farinciki Hira suka Fara sama Sama sai ga Sallaman Hajiya gaje da Marwan nan Ammi ta Fito suka gaisa tayi musu Barka basu wani Jima ba, suka Tashi,Ammi ta bama Hajiya gaje sakon Kayan wanka da maganin Jego tace ta kaima Hadiza ita kuma Hafsah 10k Daddy ya bata kamar yasan bata da kudi Ta karba Cikin Godiya acikin Ranta Tana Fadin Babu Uba Tamkar Mahaifinta.
Wajen Azahar suka isa Cikin Asibitin Murtala Aminu Specialist Hop,kano,Sun iske Anty Hadizan ma Taji Sauki Sosai Anty Asibi ke zaune da ita da Kishiyar Uwar Mijinta sai bayan zuwansu ne ma Tatafi Gida ta Dawo,Nan suka wuni a asibitin sai bayan La"asar Su Hajiya gaje suka koma Suka Bar Hafsah anan wanda Hadizan Taji Dadin ganinta Domin Duk Duniya Tana Bala'in ji da kanwarta Hafsah.
Sai Dare kana Mijin Anty Hadizan yazo ya Dauki Hafsah zuwa Gida,Gidan Hadiza aljannar Duniya kenan wajen Tsaruwa da Haduwa,Ita ta kwana da Yara Duk da Suna da mai Kula dasu harda mai Girki da Safe wanka kawai tayi ta Dauki Abun karyawan su wanda dama Tuni an Hada,sai da Taci kana Direba ya Dauketa Zuwa Asibiti,Dayake yaran sun Tafi Makaranta Tun safe.
Hafsah chan take wuni Asibitin,Da Rana kuma Asibi ta koma Gida ta Huta Da Daddare kuma Hafsah ta koma Gida ita kuma Tazo ta kwana da Hadizan,Kwananta Hudu a Asibitin aka sallameta ta koma Gida Har kuma Tsawon wannan kwanakin Hafsah ko Sau Daya bata Kira Abdullahi ba Shima bai Kirata ba,Saboda ta Dau Fushi Dashi Sosai,Shima sai ya Kyaleta kawai Yana ganin taso ta bata ma kanta ne rai ne kawai.
Washegari Sai ga su Mama da Inna Abu,sun zo wuni sukayi sai Bayan La'asar suka Tafi Bayan Mama tayo mata Yaji Inna Abu kuma tazo mata da Kubewa da Kuka,Sai Zogale Bushasshiya,Sai Sakon Abdullahi Turamen Atamfa Biyu da Rigunan yara Biyu sai Sabulan wanka da klin wanda Kudin ya bama Mama ita kuma tayi Siyayyah ta kawoma Hadizan Anty Hadiza nata Godiya Matuka da alherinsu Da zasu Tafi ta Hadasu da Direba Tace ya kaisu har Zaria.
Hafsah tasha Mamakin ganin Sakon Abdullahi,wato Shima Fushi yake da ita kenan, Kuma da gasken yake Baiyi Niyyar bata komai ba Aranar sai Ranar da yayi Niyya kenan Tana jin Anty Hadizan na Fadama Mijinta Sakon Mijin Hafsah ne,bata nuna mata ba Tana Tunanin kila ta san da Sakon alhalin ita bata san komai ba kuma bata Fadama kowa Abunda ya Faru Tsakaninsu ba sai kawai tayi Fuska Ta Nuna ma Anty Hadizan tasan komai saboda karta gane akwai matsala Ita Hadizan ma Bata da Lura ne ammh yaci ace ta Fahimci ko Waya basu yi.
Ana Gobe suna Iyalin Gidan Baba Mustapha ne,suka zo Ranar suna kuma sai ga Subai"atu da Jidda,Mariya kuma bata samu Zuwa ba sun Fara pratical a Asibiti,sai Umman Saddiq Datazo kwananta Daya a zaria suka Wuto Tare,Kwana sukayi sai washegari suka Koma,Anyi suna Lafiya an tashi lafiya an ci an sha mai kyau Raguna Uku aka yanka da katon Sa Yara sunci Sunan Abdulwaseen da Abdulaseem,Hakika Dangin Mijin Hafsah sun ma Hafsah kara Sosai sunzo kuma sun aiko da Abun arziiki,Umman Sadiq da Turamanta Biyu harda kudi 5k Shiyasa da zasu tafi,Itama ta Hada musu komai na Suna,Ta aika ma Mama Turmin zani da Inna Abu sai Umman Sadiq wacce Ta karba Dakyar,Ita kuma Hafsah sai bayan Suna da kwana Biyu ta Dawo chan ta bar Inna Asibi Sai Anty Hadiza tayi Sati Biyu kana Zata Dawo.
Koda La"asar tayi Tana Cikin Gidanta,Agajiye ta Dawo Shiyasa bata Fara ma wani aiki ba,Ammi ta Kira tace mata ta Dawo daman Ammi ke ta matsa mata ya kamata ta Dawo Gidan Mijinta,Dayake Abdullahi jiya yaje Shida Nazifi suka mata Barka ita da Daddy sun Dade sai da sukaci abinci kana suka musu sallama suka tafi,Bata iya Tsinana komai ba sai Bayan da Ta iddar da sallar Mangariba Kana ta Shiga Kitchen ta Sulala Taliya Dama Tazo da miya Daga kano,Tana gamawa ta Shiga wanka Bayan ta Fito ta saka Wasu Riga da sikat yan kanti ta yane kanta da Vail din gyale,Tana gama Shiryawa Ana Kiran Sallar Isha"i sai kawai ta Shinfida sallaya ta Tada salla Tana idarwa Ta Dauko wayarta ta Fito Falo ta Zauna ta Kira Auwal tace In ya tashi Daga Shago ya biyo ta Gidanta zata bashi sako yace mata yau ma bai je shago ba Yana Hanya ne zai Dawo daga makaranta ya tsaya yin wani abu ne yasa yakai Dare.
Kafin Auwal yazo tatashi ta Zuba Abincin Cikin wasu kololinta masu kyau Umman Sadiq ta sama Abinci Tunda tana nan bata Tafi ba tana Jiran Bikin Autan Goggo Habiba da za"ayi nan da kwana goma,Dayake batazo da yara ba,Ko Zahra gida ta barta saboda makaranta,tazo da Nama da yawa Shima ta Diban ma Umman Sadiq din da Mama sai Atamfofi Guda Biyu Cikin wanda Anty Hadiza ta bata Bayan kuma Dinkunan da tayi musu Na Fitar suna Kala uku Dataso ta hada harda wanda Zata karama Umman Sadiq sai kuma Tabari sai Umman tazo ta bata.
Ba Dadewa sai ga Auwal yazo nan yaci abincin Shima Suna Hira sai wajen goma Saura yamata Sallama ta bashi Sakon Turaman kuma tace ya bama Mariya Daya Jidda Daya,Sauran kuma tace yakaima Mama,Ta hadamai da 1k tace yayi kudin Mota ya Rike Sauran Dayake ko Kudin da Daddy ya bata bata taba baGashi kuma Anty Hadizan ta kara mata 10k da zata Dawo.
Auwal yana Zuwa Gidan Mama yaga Ya Abdullahi achan ganinsa da kaya Niki Niki yasa Mama ke Tambayansa Daga Ina yace Daga Gidan Ya Abdullahi,nan ya mikama Mama da Umman Sadiq sakon Anty Hafsah,sai Sakon su Mariya Tsalle suka kama da Murna,Ya Abdullahi na gefe yayi kamar bai ji su ba,Mama ta karba Tana gani tana ta Godiya Umman Sadiq ma Tana ta Tayasu Godiya Mama ta Bude baki tace"Kai Wlh Hafsah da iyayenta Mutanen kwarai ne...Kinga da zamu Taho Abunda ta bamu Nama Dayawa kuma gawani Hafsah ta karo mana Bayan Danyen da Ammi ta aiko mana Jiya.."
Umman Sadiq tace"Ba shakka wlh..Haba ai Hajiya Zinaru kam sai Fatan gamawa da Duniya Lafiya Macece da tasan Dattako da Mutumtata da kuma Zumunci"Mama tace"Sosai...Na Dora Turamanta ba adadi acikin Gidanan.."Nan suka yi ta yaba kyawawan Halin Hafsah dana iyayenta Jidda da dai da Mariya sai Murna suke Abdullahi kuwa na gefe kanzil bai ce ba sai da yagama Danne dannen wayarsa kana ya mike yayi musu sallama ya wuce gida Su Amira dai na gidan Ammi wajen sati Hudu kenan Suna ta shan na gidan Ammi.
Sha Daya saura Ya Shigo Gidan Tana zaune afalo tana kallon Tashar Bw,Dayake akwai Wuta Lokaci,Tana kallon maimaicin Seris Flims din da suke Haskawa Mai Suna Ameelatus Sirriya,tana son Shiri Sosai take kallonsa Bai cin ma an wuceta Lokacin datafi kano bata samu kallo Sosai ba,Tana jinsa ya saka Mashin Dinsa Cikin Dakin nan ya Rufe ya yi sallama Lokaci Daya yana Sawo kansa Falo Hannunsa Rike da key din gidan dana Mashin sai kafadansa Sagale da Briecafe dinsa.
Ciki Ciki Hafsah ta amsa Sallaman nashi Shima kai Tsayen ya kalleta,Ido Cikin Ido yace"Yan Suna andawo lafiya..? Ya fada yana Sabule sawu Cikin Takalmin Dake kafarsa Cikin wani yanga Hafsah tace"Lafiya lau Alhamdulillah.."Lokaci Daya ta wani maida Hankalinta kan Kallon Datake yi Dariya ta kamashi Sai da ya Murmusa bai kara mata mgana ba ya Taka ya Shige Ciki Hafsah ta Bishi da Harara kafin ta kwafa acikin Ranta ta Riga ta Guduri Niyyar yan kudadenta Sana"a zata Fara dashi Insha Allahu bazata kara Juran Gorin Abdullahi ba.
Sha Biyu Saura ta gama kallonta ta kashe komai ta koma Ciki ta iske har ya Fito wanka yana sanye da Dogon wando,Jikinsa ba Riga yana aiki Bisa System dinsa,
Tana Shigowa ya Dago ya kalleta itama ta kalleshi sau Daya ta Tura Kofar Tailet ta Shige kai kawai ya Girgiza Lamarin Hafsah ya koma Bashi Dariya ma Miye Abun Fushi ke da akabama zabi kika zaba sai kuma ki Dawo kina Fushin Rashin Dalili,Killer Smile yayi acikin Ransa ya Furta nasan Abunda kike so Shiyasa kike wannan Rigiman.
Yana Zaunen ta Fito wanka Daure da Towel ta isa gaban madubi ta shafa Lotion ta Fesa Tuare Humra ta gabansa tazo ta wuce ta isa ga wardrope ta Bude ta Daukowata karamar Rigar Barcinta mai Hannun Vest ta Yaye Towel din Jikinta ta Zura Abdullhi Dake satar kallonta Ta wutsiyar ido sai da yaji Numfashinsa ya Dauke ko akarin Banza Hafsah bata yarda ya ganta Haka naked indai ba a acikin Duhu ba ammh yau saboda Tana jin Tsiya agabaansa ta Sabule Towel din ta saka Rigar Barcin da marabanta da Tsirara kadan ne gashi ko pant da Bra bata saka ba Kowani Motsi tayi mazauntanta sai sun Juya ga Nonuwanta sun tsaya kyam suna Kallonsa suna sawa yana jin wani iri acikin Jikinsa.
Tana lura da irin kallonta Daya ke Binta Dashi Tun yana Kokarin Kauce ma kallonta har ya Daina Aiki Bisa System dinsa,ya koma yana kallonta ganin Haka yasa ta Dinga mai Barin Duwawunka nata Daga Wajen wardrope zuwa Bakin madubi kuma Babu Abunda zata Dauka sai dai tayi ta Tabe Tabe Lokaci Daya tana sakarmai Bayan Hade da Karkada mai da kyau saboda yagani Tana mai kwalele,Shikuma sai ya kasa jurewa ganin Reaction dinsa Har ta kumbura tayi Fam kamar ta Fasa wandon ta Fito da Hanzari ya mike ya Ture System dinsa Zuwa saman Side Drower din gadon ya mike da Hanzari Tana gabam madubi taga Tasowarsa sai tayi Sauri zata bar Dakin ammh sai ya nuna mata Zafin Nama kafin tayi wani yunkuri sai gata a hannunsa Sun Tsaya Suna kallon Juna.
Lumshe idanuwanta tayi Tana kokarin kwace kanta Cak ya Dagata yana Fadin"Wannan kwalelen da ake min Madam ya isa Haka...ataimaka abani Hakkina wajen kwana goma An barni ni kadai ba wani mai Debemin kewa Yakamata atsausayamim Madam.."Yafada yana Direta saman makeken gadonsu Tana Shirin Tashi yayi Saurin Danneta Lokaci Daya yana sakar mata Nauyinsa Kansa ya saka cikin Wuyanta yana Shakar kamshinta Nishi Ta Fara saki Saboda nauyin daya sakar mata Riko Bayansa tayi tana Kokarin Turesa,jin haka yasa ya Damke Duka Hannuwanta Ya Hada Ya tsuke cikim Nashi ya Kwantar da Hannayenta Suna kallon Cikin Idanuwan Juna Cikin wani yanayi da Fizgar Hankali Abdullahi yace"Nasan Dama wannan Fushin naki na Rashin Jin Dumin Abdullahin ki ne ko..? Toh gani yau har sai kin gaji Dani Till Down zanyi sai na samo ma Amir kani ko kanwa awannan Daran Insha Allahu.."
Tana kokarin mgana yayi Saurin Tushe Bakinta Danashi yana mata wani irin Tsotsa na musamman Tun tana Ture ture Harshensa Har ta Hakura ta sakarmai Bakin yayi ta Tsotsa Ganin Itama bazata Jure wannan Salon ba yasa itama ta Shiga Kissing Dinsa ba kama hannun yaro ganin haka yasa ya sakin mata Hannayen,lokaci Daya yakai ma Kirjinta wawaso ita kuma sai ta Saka Hannunta kan Kirjinsa tana wasa da Nipples Dinsa.
Cikin Lokaci kalilan suka Rikata Junansu da wasanninsu Nishinsu kadai ke tashi Lokacin da Abdullahi ya Shiga Hafsah sai da Tayi wani kara mai Hade da wani Irin kuka Shima din gurnani yaja Jinsa Cikin Duniyar Hausinsa Daya saba Shiga yana kwalfar Ruwan Dadi itama kara manne kanta Dashi tayi tana jin wani Irin gardin Dadi na Dibanta Jin yadda gwarzon nata ke pipun Dinta Cikin kwarewa dajarumta gashi ya Cikata Fam fam ta ko'ina Shiyasa Dadin yayi mata yawa Tana ji kamar zata Haukace.
Kamar yadda Abdullahi ya Fada Till Down sukayi Round 4 sai da Abdullahi yaga Ta Jigata kana ya Saurara mata,tare sukayi wankan Tsarki suka Dawo suka kwanta Suna Ramuwar Barci washegari sai da Abdullahi ya makara zuwa Office,Domin da safen ma sai da ya kara yace wai Duk yana Famshe kwanakinsa ne Duk Kumburin Hafsah da Fushinta nemansa tayi ta rasa Domin wanda Take Fushin Domin Shi bai san Tanayi ba wannan karon bai biyemata sun yi zaman Doya da manjan ba ya nuna mata Cewa wanda ya Riga ka kwana Dole ya Riga ka tashi.
Taso ma ya barta Taje gidan Mama ta gaida Umman Sadiq yace ta bari ya dawo da yammah sai ya kaita toh daya dawon basu samu sun Fita ba yana nanike da ita yana Kwasan Dadi in tace ya kyaleta tagaji sai ya marairaice mata yace kwana nawa bata gida,in yace haka bata iya mai gaddama sai ta sakarmai Jikin yana ta Bidirinsa sai washegari ya barta taje gidan Mama ta Wuni,sai dare ya Daukota suka koma Gida.
******
Bikin Autan Goggo Habiba ya taso wannan karon Abdullahi bai wata mgana ba Tun ana Jibi Biki suka Tafi,Da Subai"atu,Da Umman Sadiq,sai Mariya da Jidda,wanda Dakyar Abdullahi ya barsu sai da Goggo Habiban ta Kirashi tamai mgana,Harda kannen Nazifi Suka tafi,Zannira sai da tazo,Duk da bata gama wanka ba ana gobe biki sai gata,Ranar Biki kuma Sai ga Ammi tazo ita da Hajiya gaje da Inna Abu Mama dai na Gidan an barta da yara su Muhsina da Su Amira da ya"yan Zannira,Dukkansu sun sha ankon Less yan Zaria wanda Subai"atu da Hafsah suka Fito dashi Kuma Leshin yayi musu kyau kalan Blue da Pick,Su kuma yan chan Danja ankon Atamfa sukayi.
Abdullahi da Nazifi da Baba wada sai Auwal suka zo Daurin Auran Wanda aka Daura 1:00pm na Rana,Su Abdullahi basu samu Shiga Cikin Gidan ba sai da Mutanen yan Daurin Aure suka Ragu kama suka Shiga Gidan suka Gaishe da goggo Habiba suka mata Allah sanya alheri,Basu ga su Hafsah ba Su Ammi Kadai suka gani da Inna Abu sai Umman Sadiq Agidan su Zannira kuma dasu Hafsah suna Gidan da Madina ke zama da yanmata.
Daki Guda aka ware ma su Abdullahi sukaci abinci suka Sha Ruwa,Auwal dama Tuni yabi abokansa Ya"yan Mijin Goggo Habiba sun Shiga gari,Sai da sukayi Sallar La"sar kana sukama Goggo Habiba sallama zasu Tafi Ammi kuwa Tun wajen uku suka koma ita da Hajiya gaje,Da farko Abdullahi yaso su wuce ne Auwal ne ya Tsaidasu akace yana Gidan da Madinan ke zama sai Nazifi yace bari su Biya su Daukesa Dagachan sai su wuce.
Wajen ba Nisa da Gidan Goggo Habiban,Baya ne kadan suna Shan kwana sai ga Gidan Tundaga Nesa Nazifi da Abdullahi Dake gaban Mota suka Hango Jidda Tsaye akofar Gidan wanda yara ke ta wasa,ga kuma yan Mata nan nata Shige da Fice da Samari,Jidda na Tsaye da wani Saurayi ajikin wata Bakar Mota 306 Abdullahi Tundaga nesan yaji Ransa ya baci Zuciyarsa ta Fara zafi yana Tunanin wani irin mari zai bama Jidda matukar suka karisa kofar gidan.
*Anitha..*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
_Wannan Sadaukarwan Ta *MUSAMMAN NE* kamar yadda Duka Shafin na yau ya kasance Shima na *MUSAMMAN NE* Tabbas Ita Kanta Din ta *MUSAMMANCE..* The person Of *KHADIJAT SALISU YUSUF....UMMINA..❤️🤩😘🔐* Ina Rokon Allah ya iya miki Abunda kika gaza Uwa Tagari,Allah kuma yayi Riko Da Duka Hannayenki,Allah ya Cigaba Da Dafa miki Duniya da Lahira Ya kasance Dake aDukkan Inda kika Sanya kafa...ALHERIN ALLAH YA KAI MIKI ADUK INDA KIKE AMEEN..._
*018*
""kusa dasu Nazifi yayi parking Din motar tun kafin ya gama Daidaita parking Abdullahi ya Bude Murfin Mota ya Fice da Sauri yana Huci Fuskar nan ba Annuri ya Hade Giran Sama Data kasa.
Baba wada ne ya Lura da yanayinshi Cikin Sauri yace"Kai Nazifi Rike Yaro chan Abdullahi kar yace zai Dagi yarinyar nan a Bainar Jama"a kasan Halinshi da Saurin Fusata maza ka Dakatar dashi.."Da sauri Nazifi ya Bude Murfin Motan ya Fice yana Fadin"Tom Baba..."
Jidda Bata ma lura da Tsayuwar Mota ba ballatana ta Lura da Abdullahi Dayake Tahowa,Sai da Nazifi ya Fito Daga Motan ne,idanuwanta suka Nuna mata Shi Ido ta zaro,Bata gama Zarosu ba ta Diresu kan Abdullahi Dake gabanta yana Jifanta da wani kallon Zaki gane Kuranki Gabadaya sai Taji Zufa na ketomata Daurin Da mariya tayi mata na Zahra Buhari Dakr kanta yana neman kwancewa Saboda Tsoro idanuwanta Duka Sun Firfito waje saboda Tsoro.
Saurayin kuwa Abun sai ya bashi mamakin ganin yadda Jidda tayi Lokaci Daya ganin Abdullahi Cikin Duniyanci yace'Beb wannan fa..? Wani kaukkauran Miyau Jidda ta Hadiye kafin tace"Ya...ya..yaya ne.."Tafada a Rarrabe ganin kawai ya Fara Tattara Hannun Rigan Shaddarsa Sai Cikinta ya bada wani kara ta waiga Taga yara sun Fara Taruwa abunga ga kauye Cikin Fusata Abdullahi ke kallonta yana Fadin"Wato Daman ke ba Hidimar Biki ta kawo ki ba ko..? Kiran Samari ne da Tadi ya Kawoki Tunda chan na Hanaki Shine kika zo nan kika Bude Gari ko..? U are stupit in Dakikiyar kwakwakwarki bata Fadamiki zan zo garin ba kuma zan iya ganinki ba..'
Yafada Lokaci Daya yana Jifanta da wani Mummunar kallo Kafin ya kara Daka mata Tsawa yana Fadin"Waye wannan..? Wani d'an iska ne kika gayyato Har garin da ba naku ba..? Ya Fada Cikin Tsawa da Hargowa wanda yayi Sanadiyar Zubowar Hawayen Jidda Ta matsa baya Jikinta na Rawa Saurayin kuwa Sai ma Abun ya bashi mamaki Abunga ga Yan karya Kaduna gyara Tsayuwa yayi yana Fadin"Ah Beb ki Fadamai mana..Ki fadamai ni Boyfriend dinki ne mene don kuna Biki nazo na ganki naji Dadi"
Yafada kai Tsaye yana kallon Abdullahi wanda wani Takaichi ya kara kumeshi kamar ya Tsinke yaron da Mari sama da kasa ya kalli yaron sai da Yaji Haushin kansa,Aransa kuwa yana Tunanin yaron bai wuce sa'an Jiddan ba,Yaran dai masu kudi ne,Masu girman Jiki,Karamin Tsaki yaja yana jin gwara ya make Jidda agabansa sai ya gane Yana da iko da ita,Cikin zafin nama yakai mata Hannu Kawai sai Nazifi daya kariso ya Rikemai Hannun yana Fadin'A"a mutumina karka fara Fa..kyaleta ba Mutumcinka bane ka Daketa acikim mutane."
Yafada yana Nuna mai Jama"ar da suka Taru awajen suna kallon Abunda ke Faruwa da idanuwansa,Sauke Hannunsa Abdullahi yayi yana Fadin"Nazifi ka bari na karairaya wannan Shegiyar yarinyar mara Jin mgana.."
Kai Nazifi ya girgiza kafin ma yayi Mgana Jidda tayi Zumbur da Gudunta ta koma Bayansa ta Lafeshi ta Dora Duka Hannuwanta saman kafadunsa Tana Fadin"Ya Nazifii....!!! Ta fada Cikin kuka ammh sai da yaji Sunan har tsakar kansa,Tudun Nonuwanta da suka Daki Bayansa sai da kansa ya amsa Tsikar Jikinsa ya tashi,ido ya Lumshe kafin ya Bude Waiwaiya yayi yana kallon Jiddan wacce ke Sharban Hawaye,kwalliyarta Duk ta Baci da Hawaye Cikin kasala yace"Ke kuma Dallah Shoutup kin damemu da kukan ki na Banza."
Yafada Cikin Fada ammh Muryansa Cikin sanyi da Kasala Baki Jidda ta kama tana zaro Ido Nazifi ya maida kallonsa kan Abdullahi yana Fadin"Bance karka Hukunta taba ammh ka bari mu koma Gida ni da kaina ma sai na Zaneta Tunda tamim alkwarin bazata kara ba sai gashi kuma ta kara plz Cool ur mine kaji mutumina.."Yafada yana Dafa kadansa kai kawai Abdullahi ya Kada bayan ya gama Hararan Jidda dashi kanshi Saurayin Daya koma gefe yana kallon Ikon Allah acikin Ranshi kuwa yana mamakin yadda wasu ke son Takurama wasu kawai Don Suna gaba dasu juz ya kyale yarinya taji Dadin rayuwarta ya Hanata Shi Uban wa yasan me ya aikata yana kamarta.
Tsaki yayi ya koma gefe ya Ciro wayarsa yana Laluban layin Zannira Shi kuwa Nazifi Saurayin ya kallah Cikin Lokaci kalilan yayi Nazarinsa Hannu ya bashi sukayi musabaha kafin Nazifi yace"Yaro miye Sunanka..? Yana Shafa Dandazon Sumar kansa yace"Sunana Anas ammh Friends dina suna Kirana Starboy."Baki Nazifi ya Tabe kafin yace"Anas ko nace Starboy am sorry to Say ammh bana so na kara ganinka da wannan yarinya kana jina..?
Ya karkace kai yana Fadin"Saboda mene..?beb kinjisa wai kar na kulaki kina sona ina sonki waht else..? Nazifi yace"Eh haka nace Duk da bansan komai a kanka na san a yadda kake iyayenka basu yarda kayi Aure ba so kaga kuwa bai kamata kana bata mata Lokaci ba infact ma mun Hanata tsayawa da kowani Namiji sai ta gama Candy" Fuska ya yamutsa yana kallon Jidda yace"Tabdijam.Dama beb aure zaki yi yanzu..?Nifa i tot sai nan da Shekaru goma Lokacin na Dawo daga South africa na gama Masters dina na samu aiki...?
Ya karishe Fada yana ma Jidda wani kallo wacce ba bakin mgana Sai dai ta sadda kanta kasa Kafada ya Daga yana Fadin"Olrty Is ok...Ni daman ba nike Sonta ba ita ke Bibiyana ko nam dim ma Daka ganni ita ta gyyatoni ba Domin haka ba bana zuwa irin wannan Local wajen She Know aie..Ka Fadama yayanta yabi a Hankali yana Takurama yarinya ya barta taji Dadi ta More ko Beby..?Yafada yana wani Dariya kafin ya fara Tafiya yana Fadin"Bye Beb...I hv to go Tunda ga Abunda Yayyinki suka ce..So Ni badagani bane Buh ko yaushe kika kirani am Here for u ok..? Yafada yana waigowa Lokaci Daya yana kashe mata ido Daya Motarsa ya Bude yayi mata key yata da yafigeta da gudu ya bar wajen har yana Badama Nazifi kuran Jar kasa Dake wajen Abdullahi na gefe yana ganin komai Acikin Ranshi kuwa zafi yake ji Kamar yatashi ya kama Jidda yayi ta Duka sai ta Suma.
Kakkarfa ajiyar Zuciya Nazifi ya saki kafin ya waigo ga Jidda wacce kunya suka mata ga Tsoro Baya Taja tana wani Fiki Fiki da ido kallonta yake yi Tundaga sama Har kasa,Aransa kuma yana ayyana yadda Leshin da dinkin suka amshi Jikinta Sosai,Ido ya lumshe kafin ya Bude yana Fadin"Aure kike so ne Jidda..? A bazata taji mganar sai tayi Sauri ta Dago Tana kallonsa Cikin narkakkun idanuwanta tace"Ah.."a..."Tafada Muryanta na Rawa,Kai ya kada kafin yace"In ba Haka ba Toh me yasa kike gayyato samarin Banza..? Wanman dai ba dan gidan mutumci bane Daga ganinsa in Aure kike so ki Fadamin zan Fadama yayanki da kin gama Candy ya samu wani ya Hadaki Dashi kije Chan ki karata Tunda baki jim mgana.."Yafada yana Sakarmata Idanuwansa.
Hawaye suka Zubomata ta Share tana Fadin"Ni bana son Aure yanzu Ya Nazifi.'Tafada Cikin kuka sai ta bashi Dariya Cikin Mamaki yace"Kuma kike son Samari..? Har kina gayyatosu Biki..? Kwalkwal tayi da ido Tana Goge kwallarta ganin haka yasa kawai ya kada kai yana Fadin"Shiga Ciki...Bari nayi ma Abdullahin mgana.."Daga haka ya Juya ya nufi Abdullahi ita kuma ta Shige Ciki da Sauri tana Goge kwallarta Ranta ya Sosu ganin yadda Yara harda manya suka Tsaya suna kallonta.
Nazifi na karisawa kusa da Abdullahi ya Jisa yana waya yana Fadin"Zannira dake da Subai"atu ku Fito gani kofar gidan da kuke Tare da Amarya ina Jiranku.."Yafada Cikin Bacin Rai Dagachan Bangaren Zannira tace"Lafiya kuwa Ya Abdullahi.? Tsaki yajamata yana Fadin"Dillah malama ku Fito in zaku Fito kuna Batamin Lokaci muna kan Hanya ne.."Daga haka ya yanke Kiran Zannira tabi wayar da kallo Sororo Tana Fadin"Topha.."
Dama duk suna Daki Dayane dasu Subai da Hafsah da manyan Ya"yan Goggon Habiba ita kuma Madina amarya tana Dayan Dakin Ita da kawayenta Chan Jidda ta wuce dataShigo saboda bataso Su Anty Zannira su Fahimci tayi kuka har su Fara Tambayanta Dalili,har Suma su gano Abunda ya Faru suma tasha nasu Fadan da Hargowa ai kuwa bata Tsira ba tana Shiga sai da Mariya ta mata mganar Taga kamar tayi kuka sai ta mata karyan wani karo ne ya Fadamata a ido mariya harda mata Sannu
Subai"atu ta kalli Zannira tana Fadin"Yadai Madam...?Zannira ta mike tana Fadin"Ina na sani..Yanzu dai Ya Abdullahi ya Kirani Cikin Fada yace mu fito yana Kofar gida yana son ganinmu Ni dake.."Ido Subai ta Zaro Tana Fadin"Har da ni kuma?Me kuma nayi ni Subai"atu na Shiga uku..? Dariya tabama yan Dakin Hafsah tace"Kidai ki tashi ki bita kuje kuji ko lafiya Kada ku batamai Lokaci ku kara laifi.."
Zannira ta Yafa mayafinta ita kuma Subai ta mike tana Fadin"Wai yana kofar gidan goggo ne ko nan kofar gidan.
? Zannira tace"Cewa yayi yana Kofar gidan da muke tare da Amarya mu mufito yana Jiranmu Dana ma tsaya Mgana cemin yayi Dallah in zamu fito mu mu fito karmu Batamai Lokaci yana kan Hanyane"Subai ta kara Tsorata Cikin Zaro Ido tace"Don Allah..Mun bani.."
Tafada tana mikama Hafsah Saleem Lokaci Daya tana Fadin"Bai ce da Hafsah ba..?Zannira Taja tsaki ta Fice Daga Dakin Tana Fadin"Nayi gaba sai kin fito..Inda da ita ai wayarta zai Kira Tunda Matarsace yafi ki saninta bar ganinta kawarki.."Dariya ta kama Hafsah Daga cikin Ya"yan goggo Habiba,Jamila ta kada baki tace"Kwarai Tunda tana bashi Abunda Ba macen Duniyan dake bashi Bayam ita.."Tare gabadaya Dakin suka saka Dariya Harda subai'atu wanda Fargaba ya hanata tofa wani abu ta zari mayafinta tabi bayan Zannira da Sauri.
Azaure ta ganta sai suka Jera tare Har Waje suna Fita suka gansu su uku Harda Auwal,koda suka karisa Bambamin Fada ake mai Cikin Ladabi da Biyayyah yace"Kayi Hakuri ya Abdullahi ban zata zamu koma da wuri bane.."Wata uwar Harara Abdullahi ya makamai yana Fadin"Tunda mu irinka ne marasa aikinyi ko..? Daga zuwa Daurin aure sai mu shantake ko..? Daka san wannan bakin yawon naka zaka zo kayi da ka Biyo Taka Hanyar"..Ya karishe fada yana sakim karamin Tsaki Shidai Auwal kansa na kasa yana Bada Hakuri,Subai'atu jin fadan da ake ma Auwal yasa Fargabanta ya karu Nazifi ne yace"Toh miye wai aciki ba gashi ya Dawo ba sai mu wuce in kuma nan zai kwana sai mu barsa mu tafi ai duk gida ne.."
Abdullahi ya kalli Nazifi yana Fadin"Wa..? Wlh bazai kwana garin nan ba Kajima na Rantse.."Nazifi yace"Ikon Allah To saboda mene..? Naga gobe ba School balle kace saboda makaranta.."Kai Tsaye Abdullahi yace'Saboda banga uwar da zai Zauna yayi ba in ya kwana banda Garari,kai baka gani ba Tunda muka zo ana gama Daura aure ya zare Jiki ya Shiga gari yawo,haka zai yi ma in mun barsa saboda haka ya wuce mu koma gida Mama ita kadai ce agida sai Yara kawai da wadanan Sakarkarun yaran suka kaimata aiki kamar Itace tace suyi ta Haihuwa ba Tsari."
Dariya ta kama Nazifi sai da ya Dara,Subai'atu da Zannira kuwa Juna suka Kallah suna Mganata ta Ido Auwal kuwa zare Jiki yayi ya Yi wajen Mota inda Baba wada ke Ciki Ashe Tundazu yana daga zaune sai barcinsa yake Cikin,Mota ya Bude gidan Baya ya Shige yana sauke Ajiyar rai na Allah daya ceceshi da Fadan ya Abdullahi Nazifi kuwa yana Dariya yace"'kaji ka da wani mgana kaima har da ya"yanka matarka ta zubema Maman ko..?
Abdullahi yace"Duka nawan nawa ne Abokina..? Biyu fa Daga Amira sai Amir,kuma yaushe rabonsu da gidan mama sai da suka kwashi wata Daya gidan Ammi kafin su dawo,kuma ni namace tazo dasu itace ta matsama wai zata kaisu gidan Mama ga abokan wasansu su Muhsina ko Mahsana ne na manta."Yafada yana Hararan Subai"atu da Zannira kafin ya Cigaba da Fadin"Ga masu ya"yan nan.Daya nada Biyu Daya kuma wajen Hudu ba dole Mama Taki samun Hutu ba in banza ne Renon ya"yan su kai ma Uwayen mazajensu mana.."Nazifi yace"Allah sarki Raine yakai fa Mutumina..Ita kanta Maman Dadi take ji in ga ya'yan naku sun Cika gida.."
Abdullahi ya karkace kai yana Fadin"Ba wani nan...Badai a son Barinmun Uwata ta Huta kawai Shine Mgana.."Yafada yana Danna wayarsa Zannira ta kalli Subai"atu kafin suka Hada baki wajen gaishesu,Nazifi ya amsa Cikin Sakin Fuska lokaci Daya yana Tambayasu ya Hidima,da Allah sanya alheri,Abdullahi kuwa ko Dago kai baiyi ba Zannira ce tace"Ya Abdullahi gamu..Kace mu Fito Nida Subai kana jiranmu awaje.."
Cikim Iko yace"Eh ai na ganku.Sai da kuka gama Raina ma kanku Hankali kana zaku zo..? Yafada yana jefa musu wani kallo Subai ta yanko Rantsuwa tana Fadin"Yi hakuri Ya Abdullahi na tsaya bama Saleem Nono ne.."Kai kawai ya kada yana Fadin"Ko ma Saleema ne..wannan ke ya Shafa Na kiraku ne dama na Tambayeku menene amfanin Girmanku.? Dama baku da wani amfani bansani ba..? In yau bani awaje baku iya zama madadina amatsayinku na manya..?
Yafada yana sakarmusu ido,Cikin mamaki Zannira tace"Ikon Allah Duk me ya kawo wannan kuma Mijin Hafsatu..."Tafada Cikin Zolaya Harara ya makamata yana Fadin"Allah zan make ki naga alaman yarinyar nan kin Rainani Sa"anki ne ni..? Yafada yana nuna Kansa kai ta girgiza Tana Fadin"Wane ni da zama Sa"an Abdullahi Mijin Hafsah uba ga Amira da Amir Babban Yaya ga Zannira da Subai,Uba ga Mariya da Auwal harda Jidda wazai ce kai sa"ansa ne sai da ya Raina kansa.."Ta karishe fada tana Dariya,Ba Nazifi da Subai ba Hatta Abdullahi sai ya Murmusa yana Dariya ya kai mata Duka ta kauce Gimtse Fuska yayi yana Fadin"Yarinya kin gama Raina ni zanyi mganinki..Ammh kafin nam ina so ku Fadamin Tun ranar da kukazo samari nawa yarinyar nan Jidda ta gayyato nan garin..?
Zannira da Subai suka kalli Juna kafin Subai tace"Samari kuma Yaya..? ai Jidda bata gayyato kowa ba.."Abdullahi yace"wanda ta gayyato fa yau...yanzu nan ma muka gansu nan kofar gidan suna Zence.'Ido suka kwalalo atare kafin Zannira tace"A nan kofar gidan..? Wlh bamu sani ba Ya Abdullahi..".
Yace" Daman ina zaku sani Tunda kun zama manyan banza kusan Halinta Shiyasa na Hanata zuwa kuka matsa sai tazo meyasa Tunda kusanta data samu waje shikenam bazaku saka mata ido,Ku kabarta tana Abunda taga Dama...?"Subai tace"Wlh kajima mun Rantse Yaya bamu sani Su damam nan suka kwana wajen Amarya ita da Mariya da sauran kawaye mu kuma Gidan dake kusa da gidan Goggo muka kwana Sai dazu ne kafin Daurin muka zo,kuma muna fa tare da ita Sai dai Lokacin da akema Amarya Hoto ne Naga banganta ba, sai kila Lokacin ne ta samu sa"a ta Fice.."
Zannira ta kada baki tace"kai jidda bansan me take so ta zama bane yarinyar nan.."Abdullahi yace"iskanci mana..Kinga Dan iskan yaron ma Data gayyato..? Ni saboda Haushi Tunda Nazifi ya hanani Dukanta na koma Gefe..."Subai tace"Allah ya kyauta..ammh Abun nata sai gaba yake.."Abdullahi yace"Ku kyaleta tayi na karshe..In kun dawo Daga bikin zamu Tattauna Aura zanma shegiya taje chan ta karata.."Nazifi ya kalli Abdullahi yana Fadin"Aure..? zannira tace"Ina Bayanka Wlh..Auran take so in ba haka ba ba zata Dinga gayyatan kananan yara maza da sunan samarinta ba.."
Subai tace"aifa mganinta kenan Batajin mgana Ita ko Duba yanayin mariya bata yi..? Abdullahi yace"Ba irinsu Daya ba...Mariya bata da rawan kai ita kuwa Jidda kanta na Rawa da Iskanci..Ku kylenni da ita zan yi mganinta dama Mama ke Saka baki ina kyaleta ammah dis time around komai yazo karshe..Ku koma Cikin gida ku saka mata ido kawai Shine aikinku.."Zannira tace"Shikenan insha Allahu..Tasan Abunda tayi ba wamda ya kara ganinta kuma Tana cikin gidan ko.?
Nazifi yace"Eh tana ciki.Ni nace ta Shiga Ciki."Kwafa Subai tayi Abdullahi ya saka wayarsa Cikin aljihu yana Fadin"Mutumina mu wuce mun bar Baba yana Jiranmu..'Nazifi yace"Ok muje..."Zannira tace"Sai anjuma Allah kai ku lafiya.."Abdullahi yace Ameen Subai tama Zannira Rada a kunni Abdullahi na gani yace"Ke Subai kin bani da munafunci.."Dariya tayi tana Rufe baki,Zannira tace"Wai cewa tayi zaka tafi baka ga Hafsah ba..? Tayi kyau sosai Allah..."
Harara ya watsa musu yana wucewa yace"kilama Na riga ku gani kuna Haukan gulamku.."Yafada yana wani mirmishi Dariya Nazifi ya saka yana Fadin"Allah mutumina kodai ta Turo maka ta waya ne..? Abdullahi yace"Bansani ba Ina Ruwan mutum..? Kai in Sakina ta turo maka wani abu ina Tambayanka ne..?
Nazifi yace"Daga tambaya..? Yafada yana Dariya karamin Tsaki Yaja ya wuce ya barshi da su Zannira suna mai Dariya,Sallama suka karayi ya wuce agaban idonsu suka Shiga Mota suka wuce suna Daga musu Hannu,Kana suka koma Cikin Gida,Basu fadama kowa Abunda ya Faru sai aka bige da Hiran Hafsah yake son gani har Subai na Zolayanta da ashe ta Turama Abdullahi gayunta tace"Me za"a fasa..? Shifa ya siya kayan Dole kafin kowa ya gani shi ya fara gani.."Dariya suka kwashe mata Dashi.
Jidda basu kara ganinta ba sai da suka koma gidan Goggo Habiba lokacin da za"a tafi da amarya Subai ce ta jawota Dakin da suke suka mata Fada sosai Zannira harda dungurinta,kuka kawai Jidda keyi kuma suka ce Mariya ta sakamata ido in sunje gidan Amarya Tunda Malumfashi Za"a kai Amaryan yanzu nan,su kuma bazasu ba sai gobe,Nan Hafsah taji Kiran da Abdullahi yayi musu Harda da ita sukama Jiddan Fada,Bata da ta cewa Gashi kuma harda Inna Abu a yan kai Amarya da,Umman sadiq Zannira tace ga Jidda nan su saka mata ido haka suka Tafi Malunfashi Jidda nata bata rai.
Da daddare Hafsah ta Turama Abdullahi Hotunanta ta Chart,Ya gani ya Turo mata Sticker mai Love,Tare da Fadin"Wow....Das is my Wife..U look so good and Adorable...😍😍,Ammh i Miss u come back soon Wifey..!Sai ya Turamata Sticker kuka😥😥Ita kuma sai ta Turamai."Tanque MIJIN HAFSATU..HAFSATU ma tayi Kewar ABDULLAHINTA...!
*Shakira...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
_Ina Kike Y'a guda Tamkar da Dubu....Diyar kwarai irin albarka Wato *RAHMA UMMU FAREESA..* Ladingota,Taho wannan Shafin na yau gabadaya mallakin kine Dota..Ke Ta Dambance awajen Janafty Ina Rokon Allah Ya Cigaba da Dafa miki acikin Rayuwarki Har Abada..Son kauna wanda baya karewa D'iyata..._
*019*
'"Cigaba da Charting sukayi Abdullahi na gayamata yadda yayi kewarta,Ita kuma tana Biye mai Tana mai Tabara da sangarta Ganin ta kunnoshi Da yawa yasa ta kashe Datan kawai ta sauka tana Sauke Numfashi.
Subai"atu Dake gefenta ta waigo Tana Kallonta Bayan itama Tagama Waya da Mahmud dinta Dayake suna katifa Daya ne a kasa matar gidan ta Shimfida musu,Makotan su Goggo Habiba ne,Ita kuma Zannira tana Bisa gado Ita da yarinyarta sai Jamila Diyar goggo Habiba da wasu baki Suna Dakin Uwargidan Dayake gidan Uwargida da Amarya ne,sakamakon Chan gidan Goggon Baki sunyi yawa Ba wajen kwana yasa Goggo tace Jamilarta Ta kaisu gidan Alhaji Isa din su kwana makotansu ne ana zaman Mutumci da karrama Juna.
Ganin Kallon Datake mata ne yasa Hafsah tace"Kallon fa..? Nanawa ne..? Subai tace"Ke zan Tambaya naga kingama Chart da Yayanmu kina ta Sauke Numfashi kodai kodai..?Cikin Sauri Hafsah tace"Kodai me..? Subai na Dariya tace"Kodai ana Bukatar Yayan Namu ne..? Wani Duka Hafsah ta Dakama Subai tana Fadin"Kefa yar iska ce. ? Mugun saka idonki yayi yawa kina waya da naki mijin ammh hankalin na wajena ko..? Sai na Fada masa Allah."
Subai na Dariya Tana Fadin"Yo yau naga ikon Allah Ina Laifina gani nayi kuna gama Mgana kin Hau Nurfafashi Dole na maganta.."Tafada tana kashema Hafsah ido Daya,Kafin Hafsah ta Bude Baki tayi mgana Wayarta ta Shiga kara Da Sauri Subai ta Saka Hannu ta Dauki Wayar ganin An Saka *HUBBY*❤️ yasa Tagane Abdullahi ne,Mirmishi ya kwace mata da Dariya tace Tana Kallon Hafsah.."Lalle Su ya Abdullahi manja...Ahe Hubby ne kuma.."Tsaki Hafsah tayi ta Fizge wayar Tana Fadin"Bai kai a kirasa da Hubbyn bane.? Ko me kika maidashi Yar rainin Hankali.."Ta karishe fada Tana Hararanta Dariya ta kama Subai tanayi Har tana kara kwanciya kan Katifar ita kuma Hafsah sai ta Juya mata baya ta Daga Kiran Kafin tayi mgana Taji Abdullahinta ya Saki kakkarfan Ajiyan zuciya Cikin Rudewa tace"Abban Amira me ya Faru..?
Shagwabemata yayi yana Fadin"Umh.Uhm bake bace..! Itama Cikin Tabaran tace mai"Ni kuma.?me nayi..? Ta fada tana wani karya wuya Kamar wata karamar yarinya,Baki kawai Subai ta saki Tana kallonta,Dagachan Bangaran Abdullahi yace"Ina ta Kiranki baki Daga ba...Zuciyata har ta Fara Zafi Hafsatuna.."Karya wuya Hafsah ta sake yi kafin tace"Afuwan Megidana..na dan Fita ne Shiyasa.."Cikin Kaguwa Abdullahi yace"Ina kika je kuma da wannan Daran..? Da sauri Tace"Ba fita nayi ba..Tsakar gida na Fita naje nayo Fitsari Kafin mu kwanta.."Ajiyar Zuciya ya Sauke yana Fadin"Kina ina ne..? Gidan goggo..?
Hafsah tace"A"a muna makotansu inda muka kwana Jiya..Chan ba wajen kwana Don ma yau an ragu wasu sun Bi amarya.."Abdullahi yace"Eh yanzu Muka gama waya da Umma take Fadamin ita da Inna Abu sun raka Amarya Malumfashi.."Hafsah tace"ai kam mu sai gobe zamu je mu ga Daki in Allah ya kaimu.."Yace Allah ya kaimu Plz Hafsatuna ki Dawo Goben Allah gidan yayi min Girma Ina jin kewarki Sosai.."
Hafsah tace"Insha Allahu ko bamu Dawo gobe ba Jibi Tun Safe muna Tafe.."Ba haka yaso ba Dayake Goggo Habiba ne sai yace"Ok Allah ya kaimu ina Yaran nan ne..? Subai da Zannira..?
Hafsah tace"Ga Subai nan Zannira kuma Tana Ciki mu muna Falo ne.."Baki ya Tabe yana Fadin"Sai da safe...Ki kularmin da kanki kinji ko..? Hafsah tace"Insha Allah..kaima haka.."Dagahaka suka yanke Kiran Sai ji kawai Hafsah tayi Subai ta Fado mata tana Fadin"Ke daman Haka ya Abdullahi ya iya Rage murya yana Shagwaba..? Ashe dai ba Masifa kadai ya iya ba.."
Hafsah tace"Allah zan gayamai kina mishi Labe in yana Waya da Matarsa.."Da Sauri Subai tace"Rufamin Asiri Don Allah..Kada ki kara jamin wani Fadan Bayan wanda dazu nasha.."Dariya ta kama Hafsah itama Subai din Tana Tayata Kwanciya suka gyara Lokaci Daya Suna Cigaba da Hira Cikin Hiran ne Hafsah ke tambayan Subai Labarin yayar Mijinta nan take Fadamata Tunda Ummi tazo ta bata Hakuri kuma tace zata jama Uwanin kunni Shikenan Daga Lokacin ko Haduwa sukayi Sai dai Harara Daga nesa Hafsah ta gyada kai tana Fadin hakan yafi Gwara kowa ya zauna iya matsayinsa,Suna Cikin Hirar ne Barci ya kama Hafsah ganin haka yasa Itama Subai din tayi addu"ar Barci ta kwanta.
Washegari Tun wajen 10am na Safe su Hafsah da Zannira da Subai sai Jamila da wasu Jama"ar suka Tafi malumfashi,Wajen azahar suka isa Dama anyi Danki wasu kaya ne suka Tafi dashi na kitchen sai akwatunan amarya da Sauran Kayan amfani Sun iske Su Umman Sadiq sunyi wanka suna ma Ta Shirin dawowa ne,Nan suka Hadu suka kara gyaran gidan Amarya Bayan sun gama Manyan su Umman Sadiq da Wasu Daga Cikin Dangin Babanta suka mikata gidan Surukanta Dayake ba Nisa da Gidan Da yaron ya gina chan suka Barta Daganan Tashar Mota suka kara samu zuwa Danja,sai Dare suka iso Goggo Habiba sai Hamdala take tana kuma Fatan Yadda komai ya gamu Lafiya yasa Baki su koma Gida Lafiya.
Washegari Tun 11pm na safe yan Zaria suka taso wajen 1saura na Rana suka iso Gidan Mama suka yada Zango Daman nan ne Daba,Yara suna ma iyayensu oyoyo,Sun Sauka ba Dadewa Zannira Auwal ya Rakata Tasha tayi Tashan Golf zuwa Kaduna taso ta bari sai gobe ammh Mijinta ya Hana Dole ta koma aranar,subai da Hafsah ne suka kai Dare,Inna Abu kuma Suna Sauka ta karisa Gida.
Da daddare Bayan Abdullahi ya Taso Daga wajen aiki ya Biyo,akuma Lokacin ne yace Mama ya yanke Hukunci aure zai yi ma Jidda sai Lokacin ya gayamata Abunda ya Faru Ranar da sukaje Daurin Aure,Jin Haka yasa Mama ta goyi Bayansa Umman Sadiq ne kadai tace A"a kada ayi gaggawa abari ta ida karatunta,jidda na Jin haka ta Fara kuka tana bama Abdullahi Hakuri sai da aka kai Ruwa Rana da Taimakon Umman Sadiq ya yarda zai barta ta Zana WEAC DA NECO dinta wanda sun kusa Farawa ammh da Sharadin in ya kara ganinta da wani Saurayi batare da Wa'adin Daya Dibarmata ya Cika ba wlh ko Shawaran su Mama bazai Nema ba sai dai taji Ya bada ita Sadaka ga koma waye kuwa Jin haka yasa ta Tsorata sanin Halinsa kaifi Daya ne, in yayi mgana baya Chanzata kuma in yace Eh toh eh din ne Har Abada.
Subai ta Fara Tafiya Gida Mijinta yazo ya Dauketa ita da yara Hafsah kuwa sai wajen 11pm na Dare Abdullahi ya kwasheta ita da yara zuwa Gida,Duk da Ranar ta gaji gata gajiyan tafiya gata Zirga zirga ammh Abdullahi bai Daga mata kafa ba sai da ya nuna mata yadda yayi kewarta kamar yadda yake Fadi,Washegari kuma Goggo Habiba ta kira kowa tamai Bangajiyan Biki tace kuma Tana nan zuwa Tamusu Bangajiya Dama kuma sun zo da Sakon Su Cincin dasu Dubalim wanda tace abama Mama ta Rabama wanda ya dace.
******
*After 3 Month..*
"Zuwa Lokacin Dai haka Abubuwa sukayi ta Gudana Da Dadi ba Dadi,Bangaran Hafsah da Abdullahi kuwa komai yana Tafiya Daidai Kusan dai yanayin na Abdullahi Watarana Dadi Watarana kuma Madaci Dayake Hafsah Ta Riga ta gama Saninsa Bata Biyemai ta Riga ta san Halin mijinta Baya son Raini yana son abashi Girmansa Shiyasa ta zama mai Biyayyah da Sadda kai,komai Cikin Taka TsanTsan take bata kaunar Taga tayi Abunda zai batamai Rai Ballatana Har wani Fada ko karafinsa ya Shiga Tsakaninsu.
Bangaran Sakina kuwa da Nazifi Babu Chanji sai Abunda ma yayi Gaban Nazifi ya Riga ya gama Fita Sha"anin Sakina ya ijiyeta a onesite,Ya kama Harkan gabansa ,Mganar neman Auransa kuwa Tunda sukeje Gidan Salisu Engr,bai kara komawa wani waje ba,Bawai ya hakura Da karin Auren bane a'a yana so sai zuwa gaba in yaga wacce zata iya Rikesa Ba kamar sakina Datayi ma Rayuwarsa Rikon Sakainar kashi ba,Yana son in zai kara Aure yayi Shi Don Allah da kuma yarda sunnar Manzo ta tanadar Baya son ya kara Tafka irin kuskuran Daya Tafka a Baya.
Ganin Ginin Abdullahi nata Nisa yasa Shima Nazifin ya Fara Gina Filinsa na Gaskiya tare da Taimakon Shawaran Abdullahi Data Baba wada,Sai kuma sukayi Tunanin gwara su koma Masters dinsu,kafin abubuwa su sake yi musu yawa Abdullahi dama Tun Tuni ya Turama Office dinsu Takardan yana so ya karo karatu kuma An Riga anyi approving din Requesting nashi shi bai maida kai ba,ammh mganar Nazifi yasa ya maida kai kan Karatun Dukkansu atare suka yanke Shawaran zasuyi,Tunda Dama Shi karatun Masters ba kamar Digiri bane ba koda yaushe kake Shiga makaranta ba,Wani Lokacin ma sai kayi Sati baka Shiga ba, Tunda Daman ga ayyukansu da kuma iyalansu,Abdullahi ABU Zaria ya nema Shi kuma Nazifi sai ya nemi Kasu Kaduna State University kuma Cikin ikon Allah Dukkansu suka samu kowa kuma abangaran Daya karanta kafin kace me har sun kamallah Registration sun Fara Karatu.
Cikin wannan Lokacin ne Jidda tayi Candy dinta Sai jiran Sakamako,Yanzu Zuwa gidan Mama sama sama ne Abdullahi baya samun Wani Lokacin kansa gana office ga na makaranta Shiyasa Wani Lokacin sai ya kwana Biyu bai je gidan Mama ba in ma zai je a gurguje yake zuwa ya Fito Shi kanshi Nazifin Sai yayi Sati Biyu Zuwa Hudu bai Shigo Zaria ba,wani Lokacin sai yazo Duba gininsa,ko kuma yazo gaida su Baba wada,Dukkansu yanzu basu samun Lokacin kansu Ballatana na iyalansu gwara ma Abdullahi yana Bama Hafsah da Iyalansa Kulawa daidai gwargwado,Nazifi kuwa Bai Damu ba Sakina na Abuja sai tayi Sati uku bata Lekosa ba Shima bai damu ba yana ta karatunsa ya maida kansa Busy,In Sakinar bata zo ba,baya Damuwa kamar baya Ita kanta ta sani Domin ko Masters din Daya Dora bai Gayamata ba sai da tazo Tagani tayi mamaki Sosai ganin yanzu Nazifi ya Daina Damuwa da Lamarinta kamar baya Shi kuma ya maida kansa Busy ne saboda samun Saukin wasu abubuwan kuma ya samu Yanzu bai Cika Son Damuwa da wata Sakina ba Azumi yake Litini da alhamis,in tazo ta bashi ya karbi Hakkinsa in bata bashi ba baya Matsama kansa wajen nema,Ganin haka yasa Sakinar ta Fara Shiga Taitayinta ta kan dawo Bayan Sati Biyu ta kwana uku Zuwa Hudu kafin ta koma Ammh Duk da Haka Bata Dada Nazifi da kasa Da zuwanta da Rashin Zuwanta Duk Daya yake Daukansu saboda bata da kunya Har da Complain ta Faramai da Zargin Cewa ko ya Fara neman mata ne Ranar yayi Dariya kamar zai kwanta a kasa Abun ya Bashi mamaki bai iya ce mata Komai ba kawai ya Fita batunsa aransa kuma ya Jinjina Rashin kunyar Sakina yaTabbatar ma kansa Duk Iskancin Datakeyi Shine ya sakarmata Shiyasa ammh Daya Fahimci Fita Batunta Shine Matsala sai ya nuna mata Shi yama Fi son tayi Rayuwar Yancinta Domin Cikar Burinta ba Damuwa Tun Sakina na Mamakin Nazifi har ta Daina Har Bincike ta saka akayi mata ko yana Bin mata ne..? Ko kuma Aure zai kara ammh bata sameshi da Ko Daya ba sai tayi Tunanin Kila Shima ya Fara gane Abunda Ta Dade tana nuna mai ne.
****
Ana Cikin Hakane Sai ga Mahaifiyar Jidda ta Diro Nageria wato Hajiya Sa'adatu wacce ake Kira Hajiya Sa"a,Hajiya sa"a Irin matan nan masu son Abun Duniya da Budewar ido suna Rabuwa da Mahaifinsu Abdullahi ba yadda iyayanta basu yi ba da Kartaje Saudiya neman kudi ta Zauna Tayi auranta taki,dama kuma Mahaifinsu ya Rasu Sai mahaifiyarsu ne kadai ga kanwarta Lariya dama su Biyu Ta Haifa.
Wata kawarta ta mata Hanya tatafi Chan Saudiya wajen Shekara ashirin kenan Tun Bayan Data yaye Jidda,Tunda kuma tatafi bata Dawo ba Har Mahaifiyarsu ta rasu ammh Sa"a bata Zo ba,Har Akayi bikin Lariya bata zo ba,sai da ta Shekara wajen Biyar achan kana aka Fara Jin labarinta ayadda tace Zuwanta da Shekara Uku tayi Aure ta auri wani Balaraban data Fara mai aiki agidansa Matarsa ta rasu,Daga baya kuma sai ta Rika aiko da sakon kudi da kuma kaya ga Lariya tana Saidawa Dama asalinsu yan Zaria ne a anguwar Samarun zariya,Dayake kuma Basu da wasu Dangin Duk sun kare sauran kannem Mahaifiyarsu ne kuma sun Fita batunta Tunda sukace karta je Saudiya takaranci Taje suka Fita Sha"aninta,Sai Gidan Babansu wanda Duk sun kare sai wani kanin babansa kadai ya Rage Baba isuhu sai ya"ya da jikoki, Lariyace ke kare mata tana Fadin Aure tayi achan ammh ba wanda ya yarda da Ita.
Bayan Shekara da Tafiyarsu Kawarta da suka Tafi Tare ta Dawo da Tarin Dukiya ita take Fadama Lariya irin kudin da Hajiya sa"a tayi da kuma Riban Datake samu wajen sana"arta Ita kanta Lariyar ta samu Abun Duniya Sosai na Dogayen Rigunan da Sa"ar take aiko mata Dashi Tana Saidawa kafin kace ma Sa"a ta maida kanwarta mai kudi,ana kuma Cikim Hakane Allah yayi ma Mijin Lariyar Rasuwa kuma bata Taba Haihuwa ba kawai sai ta koma tana zaman kanta Bayan an bata Gidan data gada na zaman Takaba,ta koma Chan tana Cigaba da sana"o'inta Kuma suna mgana da Sa"arta ta waya ita ta bata Shawaran ta Fara Fita Dubai tana Saro kaya kada kudaden su Darkane a hannunta da wannan Shawaran tayi amfani Lariya ta Fara zuwa Dubai saro kaya kafin wani Lokaci sunan Lariya mai kayan Dubai ya Fara Shahara,shekara Biyu Tsakani ta Biya kudin Hajji taje Saudiya achan suka Hadu da yar"uwanta Hajiya Sa"a bata iya ganeta ba saboda yadda ta Sauya ta Chanza kuma Tabbas Tana cikin Daula Rayuwa Domin Tana auran wani Mai kudi ne Balarabe ammh Baya som Haihuwa kuma sai da sukayi da Sharadi Kafim auransu suka je aka Juyama Sa"a mahaifa ita kuma saboda Tarin Dukiya ta yarda ta Aureshi baDomim komai ba Saboda tana so Ta gina da kanta kafin ta rabu dashi ta koma Nageria ta Dauko yarta su Zauna tare.
Komai Hajiya sa"a ta samu to Na Jidda ne,Kowani sako zatayi ma Lariya akwai sakom Jidda,ita kuma Lariya bata mika Sakon ga Jidda saboda tataba zuwa gidan Sau Daya da kayan Sakon da Hajiya sa'a kema Jiddan Ammh da Mama ta karbi kayan da ta sake komawa sai ta maida mata da kayan tace Yayansu yace baza ta karba ba Abun ya bata mamaki ammh sai bata Fadama Sa"ar ba bata so Hankalinta ya Tashi,Sai ta Cigaba da ijiye komai awajenta Tana Jiran sai Hajiya sa'ar ta dawo sai ta Fadamata komai acikin Hakane har Ita Lariyan ta Gina katon gida ta tare to da zata taren sai tazo ta Roki mama Ta bar Jidda taje shine data kwana bayan ta Dawo Abdullahi ya Fara fada Sosai saboda Gaskiya ana Rade raden wai Hajiya sa"a karuwanci take a Saudiya tana Turoma Kanwarta kudin Tana kasuwanci bama haka ba Tarbiyan mace bata mace bace sai Tsayayyan Namiji ballatana Jidda Datake da Bala"in Rawan kai da Fi"ili.
Ashe itama Hajiya sa"a tana aiko da Kudi ana Tamfatsa mata, wani katom Gida a chika gari,ta Hannun Hajiya Lariya,Domin tana Shiryan Shiryan Dawowa ne,cikin Lokaci kadan Dayake da kudi Ginin gida ya kamallah aka saka komai na alatun Rayuwa achan Saudiya Hajiya sa"a tana so ta Tsinke Auranta da wannan Balaraben kuma sai abu ya gagara suka Fara Hayaniya Domin yace shi bazai sake ta ba,tayi tayi ammh kuma yaki Dole Dawowarta Nageria ya samu Tsaiko sai da ta Shekara 20cir kafin ta Sako kafarta acikin kasarta ta Haihu Shima Dalilin Rasuwar Mijin nata,bata baro kasar ba sai da aka Raba Dukiyarsa aka bata nata sauran kuma yan"uwansa da ya"yansa suka Raba Ita dai Saudiya ta mata komai na Rayuwa Shiyasa data Dawo Nageria bata ci Kaichio ba sai ma Cigaba tana Tunanin Data zauna acikinta Allah kadai yasan ya Rayuwarta zai kare a wulakance.
Tana Dirowa Hajiya lariya taje ta Daukota Direct gidanta suka Wuce already dama Hajiya lariya ta samo megadin dake gadin gidan Bayan kwama Biyu kuma da Dawowar Hajiya sa"a,Ta sa Hajiya Lariya ta samo mata yan aiki Guda Uku Biyu yan Matasa Daya Tsohuwa sai da tayi Sati Daya da Dirowa kana ta Shigo samaru Cikin Sabuwar Motarta Kiran Jeep,wacce Tun Tana Saudiya ta Turoma Lariya kudi ta Siya mata,Lokacin data isa Babbam Gidansu,kafin afara wata mgana ta Dinga musu barin kudi Sai kika ji bakin kowa Tsit,Baba Isuhu ne Duk da Haka sai da ya maganta,yayi mata Fada Sosai ta kuma Rantse da Allah Aure tayi ba zaman karuwanci ba, Gidansu Mamansu kuwa duk irin Cin mutumcin da suka Tanadar mata ta Rufe bakinsu da kudi Matansu kuma ta basu Tsaran kayayyanki Bayan kwana Biyu kuma ta Dawo ta saka aka Buge garun gidan aka sauya na zamani ta kuma ta Bisu da kudi Domin su ja jari sai kaji baki Shuru sune mai ke Yada ai Sa"a aure Tayi achan Saudiya kuma Daman tazo musu da Hotunan Auranta da mijinta sun gani kuma sun yarda cewa auran tayi Duk da dai mutanan anguwan suna ta gulman yawon iskanci Taje bata damu ba yanzu kawai Burinta bai wuce ta Dauko yarta Jidda ba wacce Rabonta da ita Tun Sadda ta yayeta.
Lokacin Datama Hajiya Lariya mganar kan tana so su Shirya su Shiga Cikin Zaria Wajem marikiyar Jidda tana so ta karbota Aranar ne ta gayamata komai ta kuma nuna mata Uban kayan Data ke aikoma Jidda da bata kaimata ba, sai dai ta ijiyesu,Hajiya sa'a Haushi ya kamata Tana chan Tana Tunanin Rayuwar yarta ta inganta ammh Shine za"a gayamata mganar Banza Ko Dawowarta Rabin Tsarabanta na Jidda ne Har Mota ta bada Odar a kawo mata so take ta Inganta Rayuwarta Sosai yadda Zata ji Dadin Rayuwa Ba kamar ita data sha Wahala ba.
Cikin Bacin Rai Hajiya Sa'a ta kalli Lariya tana Fadin"Wani irin Shanshanci ne wannan Lariya.? Shine kika Boyemin wannan Abun mai matukar muhimmanci..?Kin fa san cewa Komai da nakeyi Duk Dukiyar dana Tara saboda Jidda ce na Dawo ina so na inganta Rayuwarta amatsayina na mahaifiyarta Tunda Tun dana Haifeta bayan na yayeta bata kara Jin Dumin Uwa basai dai na ganta a Hoto wanda kike Turamin,sai yanzu ammh kuma kika Boyemin wannan Abun mai girma..?
Hajiya Lariya Ta rausayar dakai Tana Fadin"Kiyi Hakuri Yaya Abunda yasa ban Fada miki ba Tun Lokacin bana so a Hankalinki ya tashi ne.."Wani Wawan Tsaki Hajiya sa"a ta Saki kafin tace"Ita Karimar ce tafada miki cewa Bazasu karbi komai ba..? Ko ta manta ni Sa"a ni na Haifi Hauwa"u da Cikina..?Tafiyata Saudiya ba Dadewa naji Labarin mutuwar Alhaji Usman wake Daukan nauyin yata..? Nasan Tana chan tana Shan wahala ya zama Dole yau ba sai gobe ba naje na Dauko yata ta Dawo Hannuna Har Abada.."
Hajiya lariya tace"Ba ita bace taki karba Cewa tayi yayansu yace Jidda bazata karbi komai Daga wajenki ba Domin bata Bukatarsa.."Hajiya sa"a tace"Yayansu kuma.? Waye kuma yayansu..?
Hajiya Lariya tace"Oho ina na sanshi Banta ba ganinsa ba ammh ai na gayamiki na zan tare a sabon Gidana naje da kaina na Roki karimar sanna ta bari Jidda Ta Biyoni Dare yayi mata sai ta kwana baki ga yadda ta kirata tana mata Fadan ta Dawo gida yayansu na Fada ba, Danaga Jiddan ta Rude ne yasa na Tambayeta wanene sai take Fadamin wai ko yayansu wama..? yauwa Abdullahi tacemim kamar Shine Babba inaga shi ke Dauke dasu gabadaya Domin Jiddan na gayamiki makaranta mai kyau take kuma bata Cikin Wahala gaskiya.."
Hajiya Sa"a ta koma Ta zauna Dabas Tana Dafe kai kafin tace"Inaga Yaron Matarshi ta Farko ce daman naji labarin Yana da Babban yaro namiji Shima ba"a gidan taHaifeshi ba Shiyasa ban sanshi ba..."Hajiya lariya tace"Nima dai ban taba ganinsa ba
Hajiya Sa"a tace"Ki Shirya muje Gidan...Ko da Karfin Dukiya data Sharia sai yata ta Dawo Hannuna ina so na Jiyar da ita Dadin da ban Jiyar da ita ba A baya ba..."
Daga haka Tatashi tana wani Taku Mazaunanta na Juyawa Ta Shige Cikin kayattacen Bedroom dinta Hajiya Lariya ta Bita Da kallon Tsausayin ganin Ta Cikin bacin Rai.
*Shakira..*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*020*
"A Ranar su Hajiya Sa"a basu samu Tafiya ba sakamakon Tana Cikin bacin Ran Rashin gayamata Abunda ke Faruwa da lariya batayi ba Shiyasa ko Waya Datace Zata Turo kudi a siyama Jiddan lariyan ta Hana,ta kawo mata Excuse din cewa Ta bari sai ta Dawo har yanzu Jidda Yarinya ce ko waya sau Biyu suka Taba Mgana da ita Lokacin da tazo Tariyan Sabon Gidan Ita Lariyan Abunda yasa bata maida Hankali ba Saboda Tana chan tana kokarin Tattara Dukiyarta waje Daya ta Dawo gida Shiyasa bata maida kai akan Lamarin ba ballatana Har ta Fahimci akwai mtsala.
Sai washegari Ranar Talata Tun wajen karfe 11am na Safe Hajiya Sa"a Ta Biya ta gidan Lariya ta Dauketa acikin bakar Jeep dinta Saboda bazata iya gane gidan ba gaskiya Rabonta da cikin gari Tun Ranar da Usman Direba ya saketa Rabonta da kafarta ta Taka Babban Dodo to tana Yaye Jidda Bayan an maidota ta Bi kawarta suka Tafi Saudiya.
Da suka Shigo anguwar Hajiya Sa"a Taga Chanje Chanje dadama Na Gidajen zamani da kuma Cigaban Rayuwa Tace ma Lariya in ita kadai ce bata iya gane ko"ina,Bata gama mamaki ba sai da Lariya ta nuna mata gidan Tabishi da kallo acikin Ranta tana Fadin am samu Chanji Domin Abdullahi ya gyara gidansu Sosai bama samfarin Ginin Baya bane wannan na zamani ne.
Siririn Gilashin Fuskarta ta zare Tana Bin gidan da kallo Ta Madubin Motarta Cikin mamaki Tace"Lariya gida nan ya Sauyamin Sosai in ni kadai nazo ban iya ganewa.."
Hajiya Lariya tace"Eh gaskiya kam Yaya ai Shekarun fa da yawa ba gidan ba Duka anguwanma an samu Sauyin Yanayi Ballatana ma Gidan gaskiya ko bayan Rasuwar megidan bai Lalace ba Yayannasu ya tsaya akan gidan Sosai.."Kai kawai Sa"a ta kada kafin ta Daidaita parking a kofar Gidansu Abdullahi.
Firfitowa sukayi Lokaci Daya Hajiya sa"a na gyara zaman mayafin kanta Tana sanye ne da wani leshi mai ubansu kyau da Tsada ta Saka mayafi har kanta sai wani takalmi mai Tudu Hannayenta suna sanye da zabban Zinare harda Wuyanta da Awarwaro,Fuskarta kuma tana Sanye da wani medicated Glass dan karami na karin karfin gani ko na gayu ne bansani ba,Sai karamar jakarta mai kama da pos dake rike hannunta wanda wayarta ke Ciki sai key din Motarta makale a Yatsanta na Hagu.
Area din take bi da kallo,ba yalwar Mutane saboda Safe ne ma"aikata Duk sun Tafi aiki Yara na makaranta magidanta kuma sun Fita neman Abun bama iyalai Hajiya sa"a Ba fara bace ammh Tana da kyau daidai misali yar kimanin Shekara 46 aduniya ce kallo Daya zaka mata ka Fahimci ta goge a Duniyanci da kuma Bariki idanuwanta suna Bude ne sosai Daga ganinta tayi Shige Shige Sosai Domin Hancinta yana Dauke da Huji ne,sai bakinta dake Jere da Hakoran Makka Har guda Biyu,ita kanta Hajiya Lariyan Shigar alfarma tayi Sosai in ka gansu zaka Fahinci Yaya da kanwa ne saboda suna Tsantsan kama da juna.
*****
Mama na Cikin Daki Tun da tagama Sallar Walha ta Zauna tana addu'o'inta bata Tashi ba,gidan ba kowa Daga ita sai Jidda sai Auwal dake dakinsa yana Barcin asara Mama tayi Tashin Duniyan nan ya tashi ya Tafi Shago Tunda yau bazashi Makaranta ba ammh yaki Fitowa ko Karyawa bai yi ba Sai kawai ta Fita batunshi Mariya kuma Ta tafi asibiti Tun safe in aka Turata.
Jidda na Tsakar gida tana Wanke wanke yan kwanukan da suka Bata ne da kayan karin safe,Taji sallama kamar Daga saama Da Farko bataji ba sai da Hajiya Lariya ta Daga murya ta kara Maimaita Sallaman,kana Jidda taji ta Dago da kanta Daga saman yar Kujeran Tsakar gidan Data ke kai sai kawai taga taci karo da Lariya Baki ta Bude harda Hanci Tana Bin ta da kallo Cikin kayattacen Mirmishi Hajiya Lariya tace"Jidda..."
Da Sauri Jidda ta mike Tana Fadin"La.! Anty Lariya kice...? Tafada Cikin murna tana Rufe bakinta kafin ta Zura da gudu ta Fada Jikinta Tana murnan ganinta Hajiya Sa"a Dake bayan Lariya Hawaye suka Cika kwarmim Idanuwanta,na ganin Tilon yarta wacce Rabon ta da ita Tun Tana da Shekara Biyu da wani Abu aduniya,Jidda Dake Rumgume da Lariya idanuwanta suka kai kan Hajiya Sa"a Dake baya Tana Binsu da kallon Sha'awa,Da Sauri Jidda ta Saki Hajiya Lariya Ta matsa Gaba Tana kallon Hajiya Sa"a Cikin Bugawar Zuciya,Idanuwanta kamar zasu Fado kasa,Kamar Mommy ta take gani,wacce bata taba ganinta ba sai dai a hoto Lariya ce Taga yadda suke kallon Juna Dukkansu yasa Ta Rike ma Jidda Hannu ta Jata har gaban Hajiya Sa"a Ta Dauki Hannuwansu ta Hada waje Daya Tana Fadin"Jidda kin gane ta..?
Bakin Jidda ya kasa Mgana kawai sai Hawaye sharr Hajiya Sa"a ta kasa Hakuri kawai sai ta jawo Jidda ta Rumgumeta tana Fadin"Kinga ne ni Hauwa"u..?nice Mahaifiyarki Nice Ummanki.."Tafada Cikin wani matsanancin kuka itama Jiddan Rumgumeta tayi Lokaci Daya ta Fashe da kuka Cikin Shakakiyar murya take Fadin"Mommy...!!!!
Mama Dake Daki Taji kamar Mgana Sama sama da kuka ko Hijabin Jikinta Bata Cire ba ta Fito Tsarkar gidan Tana Kiran Jidda sai kuma tayi Turus ganin Jidda Rumgume Jikin wata mata Dukkansu suna kuka Cikin mamaki tatako gabansu Tana Fadin"Subnallahi Jidda lafiya..? Wacece wannan.?
Hajiya Lariyace ta Waigo Suka Hada Ido Cikim Mamaki Mama tace"A"a Hajiya lariya ce.."?Lariya tayi Mirmishi Tana Fadin"Eh mune karima."Tafada tana kallon Jidda da Hajiya Sa"a wanda suka saki juna Lokaci Daya suka Bi Juna da kallo Cikin Shauki da Soyayyar Uwa da yarta Mama Ta bisu da kallo Cikin mamaki kafin ta samu Zarafin mgana Hajiya lariya tace"Karima kin gane wacece wannan kuwa..?
Mama tabi Hajiya Sa"a da kallon Mamaki wacce ta kara Rumgume jidda kamar ta maidata Ciki saboda So da kauna Cikin Girgiza kai tace"Ban gane ba gaskiya."Ta fada tana kara Kallon Hajiya Sa"an Tana so ta Tuna inda ta san Fuskarta ammh sam ta kasa Tunawa Hajiya Sa"a ne da kanta ta Dago Jidda Daga Jikinta Ta kalli Mama Tana Fadin"Karima baki ganeni bako..? Sa"adatu ce Sa"a mahaifiyar Hauwa"u."
Ido Mama ta zaro kafin tace"Sa"a.?kice haka.? Ikon Allah Ba Shakka sai yanzu na ganeki ina ta kallonki Araina ina cewa kamar Sa"a kamar ba ita ba.."Hajiya Sa"a tayi Mirmishi Tana Fadin"Nice karima..Ai Shekarun da yawa ne.."
Mama tace"Duk da haka dai kin Chanza Sa"a kin kara kiba kamar bake ba Wlh ku Shigo Ciki kwa Tsaya Daga waje ke Jidda Shigo Dasu Ciki mana Tsiyana Dake wauta wani zubin.."Tafada tana Wucewa Daki da Sauri Hajiya Sa"a Tayi Mirmishi Lokaci Daya Tana Riko Hannun Jidda wacce Bakinta yaki Rufuwa saboda Murna,gefedaya kuma Hawaye Duk ya gama wanke mata Fuska.
Dakin suka Shiga suka samu waje suka zauna kan Daya Daga Cikim kujerun Falon,Jidda na nanike da Hajiya Sa"a kamar zata koma Cikinta sai kallonta take tana jin wani Farinciki acikin Ranta na yau gata ga mahaifiyarta wacce ta Haifeta,Mama kuma kitchen ta koma ta Dauko,musu Ruwa da Lemo,ta sako Cikin wani Babban Faranti ta Hado da kofuna ta kawo musu kana ta zauna suka kara gaisuwa.
Mama tace"Ikon Allah Sa"a yaushe agari..? Tun lokacin akace kin Tafi Saudiya..? Hajiya Sa"a tace"Eh Wlh Last week na dawo..Abubuwa ne sukamin yawa yasa ban samu zuwa ba sai yanzu.."Mama tace"Ikon Allah Ai kinsha na Saudiya wajen Shekaru ashirin fa.."Mama tace"Gaskiya kam.Bayan Tafiyata naji Labarin Rasuwar Mahaifin su Hauwa"u ya karin hakuri karima.?
Mama tace"Umh kedai bari..Hakuri da godiya kafin Rasuwarsa har gidanku yaje nemanki akace kin Tafi Saudiya..'Hajiya Sa"a tace""Eh wlh Haka Lariya take Fadamin..Allah ya jikansa da Rahma ya yara..? Yaran daya bari su nawa ne ma..?
Mama tace"Ameen Ameen..Su Shida ne,gasunan duk sun Girma.."Hajiya Sa"a tace"Allah sarki...Allah ya baki ladan Rikonsu kema..'Mama tace"Ameen bakomai..Kusha Ruwa mana Lariya.."Hajiya Lariya tamurmusa taDauki kofi ta Tsiyaya Ruwa tasha Kadan ta ijiye Mama kuwa sai kallon Hajiya Sa'a take Cikin mamaki da ganin yadda ta chanza Daga gani kudin sungama zauna mata Cikin sakin Fuska Mama tace"Kin dawo gabadaya ne ko zaki koma chan Sa"a..? Kamar naji an ce Kin yi aure achan ne ko Lariya kema kika Fadamin kuwa..'"
Hajiya Lariya Tace"Eh Tayi aure achan mijin ya rasu ne..Shine ta Dawo gida gabadaya."Mama Tace"Ayyah Allah Sarki..Allah yaJikansa da gafara kin dawo kenan gabadaya..? Da yaranki kika Dawo ko suna chan wajen Dangin Ubansu.."?
Hajiya Sa"a tayi Dariya Tana Fadin"A"a ai ban haihu ba..."Zaro ido Mama Tayi Tana Fadin"Baki Haihu ba.? Kai Sa"a kodai kin Tsaida Haihuwan ne..?
Hajiya Sa"a Tace"a"a ...kawai Allah ne bai kawo ba."Tafada tana Dariya Mama tace"Hakane kuma..Komai dama na Allah ne kice sai jidda kadai ta Fari kuma Auta Dama ga Jidda da son Jiki yau dai an ga Mama an manta Dani.."Tafada tana kallon Jidda,Wacce tayi Dariya ta Sinne jikin Hajiya Sa"a Lariya ce tace"Haba dai...Aiko Taga Mama ke uwartace Har Abada.."Hajiya Sa"a Ta karbe da Fadin"Sosai ma wanda zai Rike maka yaronka Tun yana karami ai Abun ka godemai ne,..Angode Sosai Allah ya saka da alheri.."Mama tace"Ameen bakomai wlh..Ai ni nawa kawai kula dasu ne duk wani Dawainiyarsu yayansu ke yi Ci da shansu makarantarsu,Tarbiyansu da kuma kula da komai namu Wlh Shine Tunda yaronan ya kawo karfi yake Wahala Damu,Sai dai kawai muyi Fatan Allah ya Biyashi ga Tamu laluran gata Iyalansa ammh bai Taba gazawa ba."
Hajiya Sa"a tace"Allah Sarki..Allah ya Biyashi bangane yayan nasu ba Shine Babban su ko..? Mama tace"Eh bazaki ganesa ba gasakiya Domin sai bayan Barinki gidan ne Marigayi ya karbo sa Yaron wajen Hajara ce ta gusai matarsa ta Farko.."Hajiya Sa"a tace"Oh Allah Sarki...Na ji labarinta kuwa.."Mama tace"Wlh kuwa Shine komai namu Shiyasa Lokacin da Lariya ta kawoma Jidda Sako Tace in jiki Taga na maido mata Wlh shi ya Hana Akarba Shiyasa nasan kuma ta gayamiki ko..?
Hajiya Sa"a zatayi mgana kenan Auwal ya Bude labulen dakin ya Shigo yana mutsuke ido Dukkansu suka Dago suna kallonsa Mama takallesa Tana Fadin"Akwana a hantse sai dan Hutu.Sai yanzu aka tashi kenan Alhaji Auwal.?
Dariya ta kama Auwal ya Sosa Kansa yana Fadin"Kai Mama..? Banfa wani Dade ina barcin ba..kuma Yaushe ma nake samun Lokacin barcin in ba yau ba.."Mama ta Harareshi Tana Fadin"Kana fa samu..Baka ga baki bane..,? Mahaifiyar Jidda ce da kanwarta.."
Sai Lokacin ya Dago yana kallonsu Cikin mamaki gaishesu yayi suka amsa suna kallonsa Jidda ya kallah yana wani Tabe baki kafin yace"ji ta kamar wata karamar yarinya sai wani Shagwaba take."Baki ta Tura tana Kallon Mama tace"Mama kinganshi ko..?
Mama tace"Rabu dashi Babban Banza ne,Dole kiyi Shagwaba gaki auta gaki kuma mai uwaye Har Biyu.."Hajiya lariya tayi Dariya Tana Fadin"Ai kuwa ita yar gata ce gaba da gaba.."Auwal ya kada kai yana Fadin"Yar gata ko Shagwabbabiya duk Mama ta bata yarinyar nan da son Jiki...Ni Malama ki Fito ki bani Abun kari.."
Mama tace"A"a tana gaisawa da Mamarta yau sai dai kayi ma kanka kaji Abunda ake maka kana ma mutane fada.."Baki ya Bude zai yi mgana Mama tace"Ka wuce kaje yana kitchen ka Dauka.."Bai da yarda zai yi ya Fice yana kunkuni Jidda kuma sai Dariya take tana Fadin"Mama kin Gano ya Auwal ko..? Baya son aiki Wlh.."Tafada tana Dariya Mama na tayata,Tana Fadin'"kyalesa Yau yaji Abunda ake ji.."
Hajiya Sa"a sai kallon Jidda Take Cikin Sha"awa,Da kauna mai Tsanani kafin Mama tace"Ina jinki Sa"a sha"anin Auwal da jidda kullum Cikin sakani mgana suke Don ma mariya tana Asibiti.' Hajiya Sa"a tace'"Allah sarki Dama haka ne...Shine yayan nasu..?
Mama tace"A"a Auwal na Hudu ne,Abdullahi shine Babbansu sai zannira sai Subai"atu sai shi Auwal din sai mariya sai Jidda ta karshe,Subaitu da Zannira sunyi Aure..",Hajiya lariya tace"Masha Allah ya rayasu..
"Suka amsa da Ameen kafin Hajiya Sa"a ta gyara zama Tana Fadin'"Wlh karima Tun ina Saudiya Lariya bata Fadamin komai ba, sai dana dawo tamin Bayani gaskiya banji Dadi ba ai ni Mahaifiyar Jidda ce ba wata bare ba bai kamata ko bani ba in wani Daga Cikin Dangina ya kawo wani Abu da cewa abama Jidda ni aganina ba Laifi bane..?
Mama tace"Hakane..Ammh ba laifina bane..Abdullahi yana da wani irin Hali ,wanda sai shi da mu da muka sanshi bazai taba karban komai Daga gareki ba Saboda yana ganin kamar Uba yake gareta shi zai iya mata komai Hakkinsa ne.."Hajiya Sa"a tace"Banki taki ba karima ammh sai ace ni mahaifiyarta bazaan bama yata abu ba..? Meye amfanin kudina in har yana Tunanin Shekarun baya ne bana Kasar ina Saudiya,kuma mahaifinta shi ya karbeta ya kawota wajenki domin ki Riketa Ina ganin Domin na aikoma Hauwa"u wani Abu Daga wajena bai kamata ya zama laifi ba.."
Mama tace"Toh nidai kam Bansam me zan ce miki ba..Sai dai kiyi Hakuri ki bari sai kun Hadu Dashi Abdullahin in kikamai Bayani kila ya yarda da Zencenki.."Hajiya Sa"a tace"Bakomai dama ina son ganinsa Ina Son Jidda zata koma Hannuna....Tunda yanzu na Dawo Ina zaune a Chika gari nayi gida ba kowa tare dani sai yan aiki Tunda lariya tacemin Jiddan tayi Candy zan dauketa Ta koma Hannuna na saka ta makaranta Domin ina so tayi karatu mai Zurfi Insha Allahu.."
Mama ta Rike baki Tana Fadin"Topha Babban mgana..Wlh bani da ikon Baki Jidda Sa"a...Mgana ta na wajen yayansu Tunda Shine kamar Uba garesu sa da ki Dawo ko gobe Allah barshi sai na Kirashi a waya na Fadamai zuwanki.."Hajiya Sa"a tace"Ba zan iya ganinsa yanzu bane..?
Mama tace"Gaskiya baya ma gida yanzu Yana zuwa wajen aiki..Kuma ma ba nan anguwan yake zaune ba yana zaune dashi da matarsa anan Tukur tukur ne,kuma ko nayi mai waya bazai zo yanzu ba sai zuwa Dare in ya tashi Daga wajen aiki.."Hajiya Lariya tace"Toh yaya in hakane Sai ki tafi da Jiddan ta miki Koda sati ne in kin Dawo da ita sai kuyi magana Kafin Lokacin ai nasan Zai ji Sakonki.."
Hajiya tace"Shikenan is ok..Karima zan tafi da jidda tamim koda Sati ne ke kuma sai ki Fara mai mgana kafin nazo na ganshi mu Tattauna.."Mama tayi Shuru kafin tace"Duk da haka akwai mtsala..Baya barinsu Fita ko'ina ko Wani waje ne ya kama sai sun Tafi sai na kirashi na gayamai yanzu kuma ina jin Tsoron ki Tafi da ita yazo gidan bata nan.."
Hajiya Sa"a tace"Topha yanzu ya za"ayi kenan? Gaskiya ina son Tafiya da Jidda..."Mama tace"Nima baxan hanaki Tafiya da ita ba..Saboda ke mahaifiyartace kina da iko akanta..Ammh dai bari nazo.."Tafada Lokaci Daya tana tashi ta Fita Dakin Auwal ta leka ta iskeshi yana karyawa Cikin Sauri Mama tace"Auwal lekamin gidan Inna Abu kagani ko Babanku wada na gida kace Don Allah ya leko..'Auwal ya Dago yana Fadin"Lafiya kuwa Mama..?
Mama tace"Mahaifiyar Jidda ce ke son Tafiya da Jidda kuma kaga Abdullahi bayanan gwara In Babanku Wada yazo sunyi mgana tatafi da ita koda Yayanku yazo bazai yi Fada ba.."Mikewa Auwal yayi yana Fadin"Wai gabadaya zata tafi da ita..? Mama tace"Eh Haka takeso yanzu dai kafin nan zataje ta mata koda Sati ne..".
Auwal yace"Kata"i yaya Abdullahi bazai bari ba Mama karma ki Fara mai wannan mganar.."
Mama tace"Dama..Wa ya aike ni nace Tasameshi da kanta maza lekamin kagani."Da tom ya amsa ya Saka Rigarsa ya Fice Daga gidan kana Mama ta koma Dakin Tana Fadin"Kudan yi hakuri na aika a kira abokin Babansu in yazo kukayi mgana in Yayansu yazo koda kin Tafi da ita bazai yi Fada ba..."Hajiya Sa"a tace"Allah Sarki Wada mijin Abu yana nan Daman..?
Mama tace"Yanan nan Wlh...Ashe kin sanshi ko..? Hajiya Sa"a tace"Eh mana Tare dashi akayi neman Aurena mana ko zamana nan ai Tare na sansu..."Mama tace"anyi haka kuwa...ai kuwa yana nan Wlh shine matsayin Ubansu bayan Abdullahi.."Hajiya Sa"a tace"Allah sarki..Ya rike zumuncin..Ina Habiba kuwa..?
Mama tace"Habiba Tana Danja kwanaki ma ta aurar da autanta madina.."Hajiya Sa"a tace'Kai...Shekaru sun ja Allah ya sanya alheri.."Suka amsa da Ameen Daidai Lokacin sukaji sallaman Baba wada Mama ta amsa Daga Dakin ta Fito tana bashi izinin Shigowa Bayan ya Shigo sun gaisa tamai Bayani Cikim mamaki yace"Sa"a da kanta ikon Allah..? Ta dawo daga Saudiyar ne.?
Mama Tace"Eh Tana ma Ciki ka Shiga ku gaisa.."Daga haka Mama tamai Jagora Zuwa Cikin Dakin yana Shiga Hajiya sa"a ta shaidashi Shima Cikin mamaki yake kallanta Lokacin Data ke gaisheshi Ya Rike baki yana Fadin"Sa"a...Kice haka..? Lalle Rayuwa Shekaru nawa rabona da ganinki Tun barinki gidan abokina.."Hajiya sa"a tace"Wlh kuwa Ina Abu..? Ya kwana da yawa ya Rayuwa..? Da yara..?
Baba wada yace"Alhamdulillah..Naji Sakon ki wajen karima Agaskiyan mgana Ki bar mganar Daukan Jidda ta koma Hannunki Tukunnah Sa"a zan yarje miki ki Tafi da ita ku zauna da juna,Tunda tsakanin Uwa da ya bamai Rabasu ammh zencen ta koma wajenki da zama Dindin bamai yuyu bane Tunda dai har Tana da yaya wanda ke Rike da ita ga karima amatsayin Mahaifiya take gareta taya zaki zo Rana Tsaka kuma kice zaki Dauketa ta koma wajenki..?kinga hakam zai yuyu..?
Hajiya Sa"a tace"Ammh ai sai ayi la"akari da cewa Ta Dade bata Hannuna in abaya bana Kasar ai yanzu na Dawo Nidai amin alfarman Jiddan ta zauna wajena Don Allah bazan Rabata da nan gidan ba Domin har Abada karima mamarta ce.'
Baba wada yace'"Toh ai wannan mganar nima ba tawa bace..Ta Abdullahi ne Domin Shine wakilan mahaifinsu ko.? Saboda haka alfarma Daya zan miki na yarjemiki ki Tafi da ita ta miki kwana Biyu in Abdullahin yazo zan mai mgana,mganar kuma ki maida Jidda Hannunki ki barta agefe wannan kuma wata mganace na Dabam.."Hajiya lariya zatayi mgana Hajiya Sa"a ta Hanata,Tayi karaf tace"Shikenan zan Tafi da ita...ammh mganar Daukan ta koma wajena Gabadaya ban barta ba in na sake Dawowa zan yi mgana Dashi Yayan nasu na Tabbata zai Fahimce ni.."
Baba wada yace"Ba komai..Sai kin Dawo din sai kuyi mgana Dashi din kiji mai zai ce..ke Hauwa"u ki Shirya kibi mahaifiyarki in Abdullahi yazo zan mai bayani.."
Jin haka yasa Murna ta kama Jidda ta mike tana murna ta Shiga Cikin Dakinsu Domin ta Hado kayanta Mama ta Bita da kallo Tana Dariya Jidda karamin akwatinta ta Ciko da kaya ta Dauko Hijabinta ta Fito Mama ta Rike baki Tana Fadin"Oho ni Jidda ko kewata ma bazaki yi ba sai Murna kike zaki bi Mama.."
Jidda taji kunya ta Fada Jikin Mama Tana Fadin"Allah Mama zan yi kewarki..Da Ya Auwal da Anty Mariya.."Mama ta Rike ta Tana Fadin"Nima zan yi kewarki Autata...Sai kin Dawo ko..? Kai jidda ta Daga mata tana Mirmishi Baba wada mikewa yayi,yayi musu sallama ya Fice Daga Gidan Suma su Hajiya Sa"a mikewa sukayi suka ma Mama Sallama Jidda ana Rawan jiki,Hajiya Lariya ta Dauki akwatin Jiddan suka Fita Har waje Mama ta Rakasu,Auwal yana Kofar gida,yaga Fitowarsu mamaki yaCikashi ganin yadda Jidda ke Rawan Jiki da murna Bayan Motan Hajiya sa"a ta Bude mata ta Shiga da kanta kayanta kuma aka saka abayan Booth Auwal sai kallan Hajiya Sa"a kawai yake yana ganin ta a wata yar Duniya yana Tunanin in Jidda ta koma Hannunta ai sai Allah sai ma Daya kalli Hajiya Sa"an ya gano Inda Jidda ta gado Rawan kai da Rashin Jin mgana.
Da zasu tafi Jidda har tana ma Auwal gwalo kai kawai ya kauda aransa yana Fadin"Zaki ma ki Dawo ne Domin na Tabbata in Yaya Abdullahi ya barki kin Dade Sati Daya ne.."Yana kofar gidan Har suka bace ma ganinsa ya koma Cikin gida yana ma Mama korafin Barin Jidda Tatafi Da Mama Tagaji tace ya kyaleta Taya zata Hana Uwa tafiya da yarta koshi Abdullahi bai isa ya Hanata ba ballatana ita.
Baba wada kuma yana komawa gida ya Labartama Inna Abu Abunda ke Faruwa baki ta Rike tana Fadin"Sa"a dai sa"a ta Dawo kasar kenan..?
Baba wada yace"Kwarai in kika ganta ma bazaki ganeta ba..Ta yi kiba ta zama Hajiya Sa"a ta Chanza tayi kudi Sosai baki ga katuwar Motar da tazo dashi ba.."Inna Abu tace"Ance wai aure tayi achan wasu kuma sunce batayi ba.."Baba Wada yace"Koma dai me tayi Abu babu Ruwanki in Tayi Auren ne ma achan Allah na gani kuma ya Shaida in ma batayi ba ita ta sani..Nidai nayi amfani da girmana na bata izinin Tafiya da Hauwa"un ta mata koda kwana Biyu ne Koma dai menene Mahaifiyartace ita ta Haifeta ba kuma wanda ya isa ya Shiga Tsakanin y'a da uwa..".
Inna Abu tace"Yo ni me nace Mallam..?Baba wada yace"Eh kafin kice din ne na Tareki..In bazaka fadi alheri ba kayi Shuru da bakinka yafi.."Yafada Lokaci Daya yana Shuran Takalmansa ya Fice Daga gidan ya bar Inna Abu tana Mita ita kadai.
_Assalamu Alaikum Janafty Feeking Fans,How all are u Doing...? Gani nazo muku da wani albishir Mai Dadin ji Da Dadin Sauraro Ina Masoyana na Nesa dana kusa to Nesa tazo kusa ,Ina Tafe ne da wani Albishir na Sabon Littafina da zai Fara Zuwar muku Ranar Friday 05/03/2021...Mai Suna *RA"AYI NE KO BURI...?*....Da Farko nayi Tunanin sai Bayan Sallah zan Sakeshi Lokacin na kamallah *MASIFAFFAN NAMIJI..* Sai dai kuma kana naka Allah na nashi ne,Allah bai yarda ba wani Dalili yasa Dole zan Sakeshi yanzu Da yardan Allah,Da farko naso na Dakatar da Rubuta Masifaffan Namiji ne Sai Zuwa Bayan Sallah Bayan na Gama wannan da zan Fara,Ammh sai nayi Tunanin Masoyana Masoyan Duka Labaraina ban kyauta muku ba Hakan ya sani Dole Zan Cigaba da Rubutu muku Labarin *MASIFAFFAN MIJIN HAFSATU...* gefe Daya kuma Ina Rubuta *RA'AYI NE KO BURI..?* Wanda kun Gwada kun gani Siyan nagari mai Da kudi Gida,Na baje muku kolina wajen Rubutu muku Labarina mai Taken *UWAR MIJINA..* Labarin Mu"azzaman da Zahirah....!Haka kuma nayi Muku Nisa Cikin Dauko muku Labarina na *ALIYU GADANGA..* Labarin Captain Aliyu Abdulnaseer Tambari Buzu da His one and Only princesss Azeema Lawal Bature,Haka kuma Ban gaji ba na sake Zuwarmuku da wani kayattacen Labarin *MALIKA MALIK..* Labarin Dsp Saleem Khabir Kumo da yar amanarsa Malika Abdulmalik Dankasuwa,Duk da Haka ban gaza ba na sake Zama na kawo muku Labarin *ZAMAN GIDANMU..!* Inda Controller Abdallah Mahmud Abdallah azare da Amaryansa Asma"au ladam Sharif suka Nishadantar daku,Shi din ma ban gaza ba nasake zuwar muku da Wani Kayatattacen Labarin *NANNY...*! Inda Alhaji Tahir Mansur Danbatta Da Yar kwailarsa Mufeeda Danbatta suka Bajema na kolinsu,Sai kuma ga wani Shima Labarin *MR BELLO..!* Ya sanya mutane Dadama wani Shauki Ganin irin Salon Soyayyar Mr Bello Muhammand Jikamshi da Yar Rigimarsa Aneesa Bukar Bulama,Kada na manta da Labarin *SILAR HALLACI..!* Labarin Samiha Da Ahmed Sama"ila Jega,suma Ba Daga Baya ba,ga wani Salon kuma na *ABDULLAHIN HAFSATU..* duka wadanan Salon Labaran kun karanta kuma kun Gane inda mganar tawa ta Dosa,Toh a wannan karon ma ina so ku Hadu wajen Nuna min kauna ta Hanyar Siyan Sabon Littafina na *RA'AYI NE KO BURI..?* Akan Farashi mai Sauki ₦200 ga Masu Bukatar su Fara payment zasu iya Tura Kudin karatunsu da wannan Asusun bankin 0552179550..JAMILA UMAR GTB,sai a Turo Shaidar Biya ta wannan Layin 09069067488,in kuma Katin Waya ne sai a turo hoton katin kai Tsaye ta wannan Layin 09027767783....Kai Tsaye Mutum zai Tsinci kansa a gidan Kudi insha Allahu...Allah ya Taimakemu gabadaya Sai kunzo Masoyana..._
*Shakira..*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*Intelligent Writer"s asso..*
*021*
"Abdullahi bai san Halin da ake Ciki ba Domin Ranar Daya taso Daga wajen aiki bai Biya gidan Mama ba saboda gajiya,Shago kadai ya biya ya Duba abubuwan da suka kare,Chan ma ya bar Auwal ammh bai gayamin komai ba Shi ko Auwal Tsoro yake kada Ya Fadamai Allura ta Tono garma Shi kanshi ba lalle ya Fita ba.
Baba Wada bai samu Kiran Abdullahi ba sai Washegari da Safe,Lokacin ma yana Shirin Tafiya Office ne,Tsaye yake yana Gyara Zaman Tek tie dinsa a Wuya Hafsah na Falo Tana Gogemai Takalmi,Taji karan Wayarsa Dake Saman Fridge a Falo,Amira Dake tsaye goye da SchBag Dinta,Sun Riga sun gama Shiryawa,Ita tace ta Dauki Wayar Abbanta ta mikamai da gudu ta Dauka ta kaimai ganin Baba wada ke kira yasa ya Dauki Jakar Briefcase dinsa ya Fito Falo Daidai Lokacin Daya Daga Kiran.
Gaisawa suka Fara yi kafin Baba wada ya koramai jawabin Abunda ya Faru,Har ya gama Abdullahi bai iya katseshi ba Yana Zaune ne Saman kujera Hafsah na Sakamai Safa ta gama Tana Kokarin Zuramai Takalminsa Sawu Ciki Taji ya Ture Hannunta da kafarsa ya mike yana Fadin"Ammh Baba meyasa kuka bari Tatafi da Jidda..? Zaman kanta fa take na Fada Mama,kuma ta sani na Fada mata Taya mace zata iya Rike mace..? Tana da wannan ikon ne Baba..?
Baba wada yace"A"a Abdullahi Bafa ka ga ikon Hanata zama da yar"ta Mahaifiyar tace fa Wacce ta Haifeta Ta Dauki Cikin Wata Tara tayi Wahalan nakudanta ta Haifeta bayan haka ta Wahala da ita wajen Renonta da Shayar da ita Domin kaddara ta Rabasu yau kuma bayan tsawon wani Lokaci Ta Zo tana son kebewa da yarta sai mu Hanata Abdullahi..? Kaga hakam zai yuyu..? Ba adalci bane Bamu isa mu Raba Uwa da yar"ta ba ka barta yadda tatafi da ita tace zata Dawo da ita to ka zura ido ka gani in ta Dawo da ita tataso da mganar maida Hauwa"u Hannunta wannan kuma Nima ban goyi baya ba Gaskiya Tunda ga ka ga Karima bai Dace ace yau kuma Rana Tsaka Sa"a tace zata maida Rikon Hauwa"u Hannunta ba.."
Shuru Abdullahi yayi yana Kokawa Da Numfashinsa Saboda Bacin Rai,Cikin Wani Irin Takaichi yace"Ammh Baba.."A"a kar kace komai Kayi yarda nace Ka kyaleta ta zauna da Mahaifiyarta na wani Lokaci ba ita da kanta tace zata maidota kuma kuyi mgana ba..? Ka bata Lokaci Abdullahi.."
Kai ya Rausaya kafin yace"Shikenan Baba..Tunda kace Haka Ammh Wlh Bazan Taba yarda Jidda ta koma Hannunta ba.."Baba yace"Nima ban Amince da wannan ba,Kadai mata laminin ta zauna da yarta na wani Lokaci.."Ajiyar Zuciya Abdullahi ya Sauke Cikin Bacin rai yace"Shikenan Baba.."Ransa dai bai so ba Cikin Mirmishin Manya Baba wada yace"Yauwa...Nagode Abdullahi Allah yayi muku albarka.."
Ya amsa da Ameen Daganan suka yanke Kiran komawa yayi saman kujeran ya zauna,kamar wani mara Lafiya,Hafsah Dake tsaye gefe Ta kallesa tana Fadin"Lafiya Abban Amira..? Dago Jajayen Idanuwansa yayi yana kallonta na wani Lokaci kafin kawai ya mike yana Fadin"Bani Takalmin..'Da sauri Hafsah Ta Dauka ta mikamai bai ma Jira ta sakamai ba ya Duka ya Zura abunshi,Ya Dauki karamar Jakarsa ya Fice Ko Tsayawa karyawa bai yi ba Amir da Amira suka Bi bayansa Cike da mamaki Hafsah ta bishi da kallo kafin Ta Rufamai baya ta iske ya Fito da Mashin dinsa Tsakar Gida Cikin kulawa tace"Abban Amira tafiya zaka yi baka karya ba...?
Fuskarsa ba Annuri yace"In naje Office zan samu Wani Abu naci yanzu na makara.."Baki ta Bude zatayi Mgana Ya Dakatar da ita da Fadin"Bafa nason gaddama..Tunda nace miki bazan ci ba Baki iya kyaleni..? Yafada Cikin Hasala lokaci Daya yana Sakarmata Idanuwansa,Kai ta Lamgwabe tana kallonsa Cikin wani yanayi bata ma samu Zarafim mgana ba ya Tura Mashin Dinsa zuwa waje Su Amira suka maramai baya suna Ma Hafsah bye bye Jikinta gabadaya yayi sanyi Ta rasa me Aka Fadama Abdullahi a waya ne ya Tadamai Hankali,Tana tsakar Gidan taji Tashin mashin dinsa da wucewarsa,Kai ta kada kawai ta koma Ciki ta Fara Tattara Kofunan da su Amira Suka Bata Domin ita kanta sai taji bata Sha"awar Cin komai ganin Abdullahi cikin wani yanayi tana Fatan Allah yasa koma menene kada ya Tsawaita da Tsawo har ya wuce Tunaninta.
*******
Haka yaje Office ya wuni Sukuku kamar Mara lafiya gabadaya Ransa yana bace ne Ba Domin Baba wada bane da kansa ya saka baki Jidda tabi Mahaifiyarta ba da Wlh sai ya taka har Gidan yaga Uban daya tsaya mata ammh Dalilin Baba wada zai yi Shuru sai dai yana Jiranta tazo da mganar Daukam Jidda Allah sai ta gane bata wayau Domin bazai Taba yarda ya maida mata Rikon Jidda ba in Abu Yafaru watarana Dashi za'a Fara kuka mutanan gari dana anguwa su Fara gulman ya gaza ne yasa Mahaifiyar Jiddan ta Dauketa.
Saboda Bacin rai bayan ya Tashi Daga Office ko gidan Mama bai Biya ba yau gida ya wuce Haka suka kwana da Hafsah Cikin wannan yanayin Dayake ta Riga ta san Halin kayanta sai taja jikinta gefe kawai sanin Halinsa yanzu wannan Rabin Bacin ran da Fushinsa zai saukeshi a kanta,Bataji labarin Halin da ake Ciki ba sai da Mariya ta biyo Gidan Bayan tataso Daga Asibiti take gayamata Abunda ke Faruwa Ita nema take gayamata yau da Safe Abdullahi ya Biya ta Gidan bayan ya kaisu Amira makaranta Yayi ta Fada kan bai Ji Dadin Hukuncin da Baba Wada da Mama suka yanke ba in da yana nan Wlh ko kofar gida Jidda bazata Fita ba Mama sai Hakuri take bashi Sai a sannan Hafsah ta Gane Dalilin Bacin ran mijinta wanda yaki ya gayamata komai koda Taji labari bata yarda tamai mganar ganin kansa ya Dau zafi ga Karatu ga ayyukan Office ga ta iyalai Data iyaye,Shiyasa Taja bakinta ta Tsukeshi kada ya Sauke Fushin Jidda akanta.
Ranar Jumma"a Gidan Mama ta Wuni Ita da yara Subai"atu ma tazo nan Mama ke kara gaya musu yarda akayi Subai ta kada baki Tace"Wlh ina Bayan Ya Abdullahi Taya za"a ce bata san Ya yarinya tayi Fadi tashin girma ba kawai sai yau Rana tsaka tazo tace zata Dauketa ta koma wajenta..? Wannan ma ai ba mganar da zata yuyu bane ai Jiya mun Dade muna mgana da Anty Zannira awaya da Auwal yazo gidana Tacemin ta kira ya Abdullahi tace karma ya Fara yarda Ta Dauki Jidda in kuma Hakan ta Faru sai Allah ance ta gina Katon Gida da Katuwar mota zaman kanta take Ta Dauki Jidda ai kuma sai Abunda muka ji muka gani.."Mama tace"To daman mana..Daga ita har kanwarta Lariya basu da aure..Ita lariyan Dama Tunda Mijinta ya rasu bata kara ba Ance ita Sa,"an Tun Tana Saudiya take mata aiken kaya su take saidawa har ta Fara tsayawa da kafarta Daga Sa"ar Har lariya kowacce tana Zaune agidanta ne.."
Subai"a Tace"kin ji ko Mama..? Ni wlh ko Bata itan ta kwana Biyun Zuciyata bata kwanta ba.."Hafsah ta kada baki tace"Gaskiya kam..Ammh ai ba laifi bane Domin ta Dauketa taje tamata kwana Biyu mganar dai ta Dauketa gabadaya ta koma wajenta Shine Abunda bazai sabu ba.."Subai tace"Auwal yace Wlh datana da Wani Tsayayyen Saurayi kawai ya Abdullahi ya Aurar da ita Shikenan Gardama ta kare.."
Mama tace"Wlh nima Kamar ya Shiga Raina haka nace..Toh Babu sai Tarkacen Yara kanana Daga ita Har kawar nata Rumana Sai Tarin yara wadanda ba auransu zasu yi ba banda su Lalatasu.."Nan suka cigaba da Hira kan zence Dukkansu sai Dare suka Tafi Abdullahi yazo ya Dauki Hafsah bayan ya Dawo Daga Makaranta ita kuma Subai Mashin ta Hau ta koma Gida nan Hafsah ta barsu Amira gobe Suna da Hadda.
Hafsah bata ma Abdullahi mgana ba sai da sukayi Shirin kwanciya Tana Tsaye gaban madubi tana Daura igiyan Rigar barcinta Yayin da Abdullahi ke kwance kan Gado yana latse latsen wayarsa Hafsah ta kallesa ta Cikim madubi kafin tace"Abban Amira Ina so na maka wata mgana ammh bansani ba ko zaka karbi zencen.."
Bai Dago ba yace"Wata mgana ce.? Cikin Kulawa tace"Wata yar Shawara ce kadan..ammh karkace nayi maka Shisshigi kan Abunda ya Shafeka.."Dagowa yayi ya kafeta da ido Cikin mamaki kafin Cikin Dakewa yace"Hafsatu... "ta waigo Cikin Dari Dari Tana Fadin"Na"am..
"kai Tsaye yace Mata"Zo nan...'Yafada A muryansa Babu alamun wasa sam.
Jikin Hafsah sai yayi sanyi ta marairace Murya Tana Fadin"Me nayi Abban Amira...? Ido ya sakarmata Lokaci Daya yana ijiye wayar Hannunsa gefensa yana Fadin"Nace ki zo nan ko..? Ya fada yana Tattara Naman goshinsa Cikin Dar dar ta Fara taku zuwa garesa kowani Taku Daya in Tayi sai Zuciyarta ta Raunana Shi kuma kowani Takun ta Daya sai yaji wani iri acikin Ransa balle yadda Hasken Farin watan Dayake Hudowa ta Window din Bedroom din suna Hasketa gabadaya Sai yaji Zuciyarsa da gangar Jikinsa na Tsalle Lokaci Daya.
Tana Zuwa Gabansa ta tsaya tana Kifkifta ido,hannu kawai ya saka ya Jawota ta Fado kan Cinyarsa Ido ta zaro Tana kallonsa Shi kuma ya Hade Ransa Tamau yana Binta da wani Sanssayar kallo Cikin Sha"awa da kauna Kanta ta Dukar Bazata iya Jurema kallonsa ba Hannunsa Daya yasa ya Dago Habarta Suka Hada Ido Cikin Sanyin murya ammh mai Cike da bacin rai yace"Shekararmu nawa da Aure Hafsah..? Kai tsaye ya jefamata Tambayan Cikin narkewan kallonsa Tace"Shekara bakwai Cikin na Takwas.."Kai ya Rausaya kafin yace"Duk a iya tsawon Wannan Shekarun da muke zaune a karkashin Inuwa Daya Hafsah ashe baki yarda dani ba..? Kina min wani kallo Dabam wanda ni ban sani ba..?.
Nan da nan Taji Hankalinta ya Tashi Cikin muryan kamar zatayi Kuka tace"Abban Amira....!!!Shiiii...Ya Dora mata yatsa a saman Bakinta Lokaci Daya yana kallonta Idanuwa ya Lumshe kafin ya Bude a kanta yana Fadin"Karki cemin komai...In ba baki yarda dani ba taya Domin kin bani Shawara kan wani Abu Daya Shafeni ya Shafeki Kuma kice kar naga kin min Shisshigi..? Na taba miki iyaka akomai nawa Hafsatu..?
Ya karishe Fada Cikin nuna Mganarta batamai Dadi ba,Sai yanzu ta gano laifinta Idanuwanta suka kawo kwallah kawai sai ta Sulale kan Kirjinsa ta Kamkamesa Shima Bayanta ya Zagaye da Hannayensa suna Jin Bugawaer Numfashin Juna kafin ya Cigaba da Fadin"ai ni na Dauka ni dake mun zama Daya..Abunda ya Shafeni ya Shafeki kema Abunda ya Shafeki ya Shafeni Domin zaki bani Shawara kan wani abu sam bai Dace ki kawo kalmar Shisshigi Hafsatu Bazan Boye miki ba Raina ya Baci Da mgaanarki.."
Yafada yana Sakin Huci Kara Kamkamesa Tayi alamun ban hakuri kafin Tace"Ba Haka nake Nufi ba Abban Amira..Ammh Tunda baka ji Dadi ba am Sorry Baran kara ba Insha Allahu.."Kanta ya Sumbata yana Fadin"Bakomai ya wuce..Inda nake kara Som Matata Hafsatu Bayan Mahaifiyata Hajara tafi kowa sanina da Fahimtata.."Taji Dadin zencensa kawai sai ta murmusa ta kara gyara kwanciya saman Kirjinsa Tana Fadin"I Love u Abban Amira..."
Tudun Hips dinta ya Shafo Cikin wani Shauki yana Fadin"Me too...Ummin Amira..."Yafada yana kara kwantar da kansa saman kanta yana jin wani natauwa da Farinciki yana Shigarsa,Sun Dade ahaka kafin ya Dago yana Fadin"Umh..ina jinki Wata Shawara ce Matata zata Bani..? Kam kasuwancina ne ko kan karatuna..? Ko kuma Tunatarwa kan Zamantakewarmu ko kuma Ta iyayenmu da Makotanmu..?
Hafsah nadaga kwancen Tace"Kan Zamantakewarmu da kannenmu ne Abban Amira..Mganar Jidda ce nake so nayi maka Duk da baka Fadamin ba.."Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin Yace"Bagashi da ban gayamiki ba kin ji Labari..? Hafsah ta Dago Daga Jikinsa Tana Fadin"Ammh ai ba Daga bakin ka ba ko..?
Kai Tsaye yace Mata "Eh Ammh Ko baki ji Daga Bakina kinji Daga bakin makusantana..Ya kamata ki Fahimci Lokacin da Abu ya gama Batamin Rai ban cika son ina Tattauna mganar da wani ba nafi son Abarni ni kadai nacigaba da Nazarin Bacin raina ni kadai U know me Hafsah..Ban cika som ina Raba miki Fushin da ba naki ba zan iya zuwa na kawo miki wannan mganar kila ki Fadi Mganar da batayi Daidai da Ra"ayina ba kinga kuwa zamu samu Matsala har takai mu ga Abunda Zuciya bazata Dauka ba Shiyasa Tun Farko ban miki ma mganar ba sam Bana so Fushina ya Shafeki ne.."Yafada yana kallon kwayar idanuwanta Ido ta kada kafin tace"Hakane...Ammh ni banga Abun Damuwa ba Abban Amira Tunda dai tace Sati Daya zatayi mata zata Dawo da ita ba Tafiyar kenan ba.."
Annurin Fuskarsa ne ta Dauke na wani Lokaci kafin yace"Haka kike gani..Banga laifinki ba Domin baki da Tunani irin nawa,,baki san Abunda hakan Zai Haifar ba.."Hafsah tace"Duk da haka ni Damuwar da kasa aranka ce ta Hanaka komai bana so Abban Amira.."Cikin wani irim kallo yace Mata"Me damuwar ta Hanani..? Uhm..?
Cikin Kallon Juna ido Cikin ido tace"Ta hanaka kula matarka mana.."Ta fada Cikin Shagwaba da Tabara sai ta bashi Dariya Har sai da ya Murmusa kumatunta yaja yana Fadin"Kaji matar nan kawai kice kina Bukatar mijin ki ba wai ki Tsaya kina kwanana ba.."Kan kirjinsa ta Sunne kanta tana Fadin"Ai gaskiya ne..Tunda mganar nan Tataso baka kulani kuma kasan nayi kewarka ko.?
Tafada tana yawo da Hannunta saman Kirjinsa Bankare mata yayi Lokaci Daya yana sakin Siririyar kara kan yace"Nima nayi kewarki Fiye da yadda kike kewata Hafsatu kawai dai kinsan In Zuciyata bata da natsuwa gangar Jiki bai da ikon Aiwatar da wani abu koda kuwa Gangar Jikin yana Tsanain Bukatar Abun."Yafada yana fara yawo da Hannunsa a Gadon Bayanta Cikin wani Salo Ta Dago da kanta Tana kallonsa kafin tace"To yanzu gangar Jikin tana so..?kuma zuciya ta Hana ko..? Kunnanta ya kaima Cizo yana Fadin"kinganki ko..? Ko Zuciyar bata so Dole tayi Hakura yau na Morema Kayana ko..? Dariya tayi Ta kara makalkaleshi Shima Dariyan yake kafin Lokaci Daya ya Dagota su Hade bakin Juna.
Wannan Daran Sun Shayar da juna Zumar Soyayyar Washegari koda ya Tashi kamar bashi ba da Annurinsa ya tashi bai je aiki ba Sakamakon yau asabar sai Wajen 11am na Safe ya Shiga Cikin makaranta,bai dawo ba sai Dare Daya Dawo Daga makaranta Gidan Ammi ya Biya ga gaidasu kana ya Bi ta Gra inda gininsa ke Ta Tafiya,Koda ya Dawo Hafsah Taji Dadin ganinsa,Ya Rage nuna Damuwarsa ko afuskarsa nan kuwa kawai yayi kokarin nuna mata komai ya wuce nan ammh acikin Ransa Jira kawai yake Ranar Talata tayi yaga Shin Hajiya Sa"a zata dawo da Jidda kamar yadda tayi alkawari..? In bata Dawo da ita ba Ya Rantse da Allah in ta saka wasa sai yayi karar ta akotu.
******
A bangaran Jidda kuwa Tana chan Cikin Jin Dadin Rayuwa Aranar da suka Tafi kai Tsaye Chika gari suka wuce katon Gidan Hajiya Sa"a Suna zuwa Ta kaita Daki na musamman daaka kawatashi Domin ita komai na kayan alatun Rayuwa kama Daga na Amfani zuwa na sakawa an Tanadarma Jidda murna kamar ta kasheta Hajiya Sa"a da kanta ta Shiga ta Hadama Jidda Ruwan wanka Ta Taimaka mata ta Cire kayan Jikinta ta Shiga wanka Ji take kamar ta lasheta Saboda so da kauna.
Bayan ta Fito wanka Ta iske Hajiya Sa"a ta Fito mata da wasu Ubansu Riga da Sikat na yan kanti masu kyau da Tsada,Jidda ta Dinga Dagawa Tana Murna Domin agida Ya Abdullahi baya Barinsu saka Riga da wando koda Sikat yan kanti yanzu zaiFara Fada gashi ita kuma Tana son Daman Harkan gayu da wayewa Dama ne kawai bata samu ba,Ta saka kayan kenan Sai Ga Hajiya Sa"a Ta Shigo Dayake Sun Ijiye Anty Lariya agidanta kafin su Wuto nan.
Hajiya Sa"a da kanta Taja Jidda gaban Madubi ta gyara mata Fuska Taga kanta yayi Datti tace gobe zasu Fita ta gyara kanta da Jikinta,Falo ta jata kan Dinning ta Iske an Cika Teburin da kayan Ciye Ciye da ShayeShaye da Abinci kala lala,Hajiya Sa"a da kanta ta Bama Jidda abinci abaki Tana ci Tana kallonta kamar ta lasheta,sai da suka gama cin abincin kana ta jata zuwa Daya Daga Cikin kujerun Falon,suka Zauna kana ta Kira yan aikinta ta gabatar musu da Jidda a matsayin yarta kwara Daya da Allah ya bata Duk suka gaishe da Jidda Cikin Girmamawa,Daganan ta Jata ta zagaya da ita ko"ina na Cikin Gidan Tana nuna mata Jidda sai Bin ko"ina Take da kallo Tana Tunanin yanzu wannan Gidan na Mahaifiyarta ce Lalle Allah Abun Godiya.
Ranar kwana sukayi Hira Tsakanin Hajiya Sa"a Da Jidda,Daki Daya suka kwana sai asuba suka kwanta Sai da Hajiya Sa"a tabama Jidda Labarin Auranta da Mahaifinta da Haihuwarta zuwa komawarta Saudiya da Auran datayi Duka kuma ta karyata Rade Raden da akeyi na cewa karuwanci Takeyi achan Saudiya ba Aure tayi ba Ta Daukoma Jidda albulm din Hotunansu da Tsohon Mijinta na Chan Saudiya,Jidda tayi ta kallon Hotunan Mamanta a Saudiya Tana Jin wani Farinciki Itama Labarin Komai na Rayuwarta ta Bata da irin Takuran ya Abdullahi a garesu Tana Rumgume Jikin Hajiya Sa"a take bata Labarin irin Rikon da Mama tayi musu Kamar ita ta Haifesu bata Taba Nuna musu bambamci ba ko kadan,Hajiya Sa"a Tana ta Sauraranta acikin Ranta kuma Tana Tunanin yadda zata karbi yarta ta Dawo wajenta Har Abada.
Sai da jidda ta kwana Biyu a gidan basu Fita konan da Chan ba,Har ta Fara Chanzawa ta samu Mayuka masu kyau da Hutu bata komai sai Ci ta kwanta abincin ma abaki Hajiya Sa"a ke bata so take ta sangartta,Ranar data kwana uku suka Fita Gidan Su Mahaifiyarsu ta kaita suka ganta sai mamakin Girmanta suke nan suka wuni sai Dare suka koma Gida Dayan Washegarin kuma Suka Tafi Babban Gidansu Babansu,Shima nan din sai Mamakin Girman Jidda Suke yi ganin ta zama Budurwaa bakin Jidda Yaki Rufuwa ganin ashe itama yar Dangi ce,Tafi jin Dadin Rayuwarta Wajen Mamarta Saboda ta samu Saken Rayuwa Sosai ta saka kayan data keso ta kuma ci Abunda take so Ra"ayinta Shine Ra"ayin Hajiya Sa"a tayi alkawarin bata Dukkan wani kulawa da jin Dadin Rayuwa wanda bata ba ta abaya ba.
Basu kai Dare ba suka Biya Gidan Hajiya Lariya chan suka kai Dare,washegari kuma Ta kaita gyaran kai da gyaran jiki aka mata Gyaran Kafa da kuma na gashi nan da nan sai ga Jidda ta Fito tayi Ras da ita kana suka Shiga kasuwa tayi mata Siyayya kamar za"a Bude shago komai na Bukatar mace na mata ta Siya mata,Daganan kuma suka wuce Gidan Hajiya Lariya Suka Dunguma Gabadaya zuwa Shagon wani mai dinki ya gwada Jidda kana Suka koma Gidan Hajiya Lariyan Tare,da zasu tafi ta Dauko mayafai masu kyau da tsada wajen Kala goma ta Bama Jidda,tace asha kwalliya lafiya kamar Jidda zata Sume saboda Dadi Dama tana Bala"in son saka gyale,Gashi kuma Burinta ya Cika ta Rumgume Anty Lariyan tana ta mata Godiya.
Ana gobe Satin Dayan da Hajiya sa"a tayi alkawarin Komawa da Jidda aka kawo Sabbin Dinkunanta na atamfofinta da lesuna Masu kyau da Tsada da material kaya wajen kala ashirin,sai Takalma da jakunkuna da Anty Lariya tazo Dashi,Da farko Hajiya sa"a ta nuna batason Rabuwa da jidda zata Riketa a hannunta komai zai Faru ya Faru lariya ce ta nuna mata kar tayi hakan Saboda in Tayi haka batayi Daidai ba ta bari su maidata Daga baya sai suyi mgana.
Da wannan mganar yasa Hajiya Sa"a Ta Fasa Gudurinta ammh bata maida Jidda ba sai da ta kwana Goma awajenta kana ta Maidota gida da kaya Niki Niki kamar za"a bude wani karamin Boutique,Tare kuma da Siyan mata Wata Faskekiyar waya Samsumg Jidda Tana ji kamar tayi ta Flaying a sama saboda Murna,Motarta kuma ance bata iso ba sai sati na sama Da yammah ne suka kawota Lokacin Mama bata nam Tana gidam Inna Abu Mariya ce kadai agidan itama Daga asibiti ta Dawo ko Unform dinta bata Cire ba Taji sallaman almajirai suna ta Shigowa da kaya bata gama mamaki ba Sai gasu sun Shigo Tana kallon Hajiya sa"a tun kafin Taga Jidda ta gane mahaifiyarta ce saboda kamarsu Da taga Jidda sai da saki baki ganinta Cikin Shigar wata Doguwar riga baka tayi Rolling da mayafinsa sai wata karamar jaka da bakin Takalmi,sai Wayarta Dake Hannunta tana ganin Mariyan tayi Tsalle ta Rumgumeta tana murnan ganinta itama Mariyan ta Rumgumeta tana murnan ganinta Ko Daki Hajiya Sa"a da Lariya basu Shiga ba jin Mama bata nan,Sallama sukayi da Jidda Hajiya Sa"a tace Zata Dawo Ranar Lahadi saboda ta samu Abdullahi agida,jidda har da kuka da zasu tafi sai da Hajiya Sa"an ta Rumgumeta tana lallashinta da mata Alkawarin Zata Dawo Ranar lahadi ta Dauketa.
suna Fita ba Dadewa sai ga Mama Jidda ta makalkaleta tana Murna Ta jasu Daki Tana nuna musu kayan da Hajiya tayi musu,sai wata leda ta Databama Mama Daya,sai karama kuma ta bama Mariya tace inji Hajiya Sa"a Da mariya ta Bude nata Doguwar riga sai Less guda Daya da Takalmi sai Saitin Turare na Olive,Mama kuma atamfofi ne Guda Biyu sai leshi daya da Takami sai Turaran miski Dana Jiki,Mama ta karba tana ta Godiya ammh mamaki ya kamasu ganin Uban kayan da Jidda ta Dawo dasu Haka ta Dinga cema Mariya ta kara wani abun in tana so Mama ta Hana tace abari sai Yayansu yazo ya gani nan da nan Jidda ta bata rai sanin Halinsa,Ranar kwana sukayi ita da mariya Suna latsa wayar Jidda Cikin Sha"awa da Burgewa.
_Ga Masu Bukatar Fara Biyan kudin Karatu akan Littafin RA"AYI NE KO BURI...? zasu Biya kudi akan ₦200 kachal Ta wannan Asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo da Shaidar Biya ta wannan Layin 09069067488...in kuma Katin Waya ne sai a dauki Hoton katin a turo ta wannan layin 09027767783...Sai kunzo..._
*Anitha...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*Intelligent Writer"s asso....*
*O22*
"Abdullahi baisan Hajiya Sa"a ta Dawo da Jidda ba sai da Safe Daya je kai su Amira Makarantar Hadda Jiya Dare yayi kuma mai mashin dinsu Mashin dinsa ya samu Mtsala bai samu zuwa ya Daukesu ba,Bayan ya kaisu sai ya Biya Gidan Mama nan ne ya iske Jidda Mama kuma ta Tattaro duka kayan Harda da wanda Hajiya Sa"an tayi musu aike ita da Mariya da wayar data Siyama Jiddan ita kanta.
Tsab ya gama kallon Komai Wayar na Hannun Mama bai karbeta ba yadai kallah ya kada kai,yace ma Mama Ta maida ma Jidda kayanta su kuma Sun gode Ba Mama kadai ba Hatta Jidda sai da Taji mamaki Domin Tana Daki Tana Kukan Rabuwarta da Wayarta sanin Ya Abdullahi bazai barta da wayar ba sai gashi kuma ya basu mamaki gefe kawai ya koma yana latsa wayarsa Gefe Daya na Zuciyarsa kuma yana ta Nazarin wasu abubuwan.
Ya Dade gidan Mama sai da yasha Koko da kosai kana Ya tafi,bayan Mama ta zubamai Kosan tace ya kaima Hafsah sanin Tana son kosai Sosai,yana Hanyar komawa Gida Nazifi ya kirashi awaya yace yana gobe yana Hanya zai Shigo,Yana so yaje ya Duba Gininsa ya kara ma Shugaban ma"aikatan kudi,Shima Abdullahi yace Dama Zai je Shima wajen nashi ginin Duk da nashi yayi nisa har an kai Linter kuma anyi Rufin sama Dana Ciki.
Koda ya koma Hafsah ta gama Komanta tayi wanka Shima wankan yayi a gurguje yayi Breakfast ya Tafi Makaranta Yana da karatu Karfe 11am,Hafsah sai Murna take Taga Kosai Shi taci da Buredi tasha Ruwa,Abdullahi bai Dawo Gidan ba sai Dare,Shago ya Biya atudun wada Shiyasa yakai Dare,Washegari kuma Tun karfe 9am na Safe Sai ga Nazifi Agidan Abdullahi ma Dukansu suka karya ya Jirashi yayi wanka ya Shirya ya bar Mashin Dinsa Nazifin ya Daukesa a Motarsa suka Fita.
Wajen Ginin Nazifi suka Fara Biyawa Shima ginin yayi Tsawo Sun Dade a wajen Sosai Kafin su Tafi Chan Gra,Nazifi yayi mamakin ganin yadda Ginin Abdullahi yake Tafiya da Sauri Haka yanayin Tsarin ginin ya Burgeshi Flat uku ne aka Hadashi Cikin Bangare Daya aka Fitar da Babban Falo,Daga hannun Dama Akwai Koridon da zai sadaka da Wani Dan madaidaicin Falo,sai 2bedroom da Kitchen,Hakama Daga Hannun Hagu Shima sai Haka Tsarinsa yake sai Daga Yammah ma Shima sai dai Shi karamin Falo ne sai Bedroom guda Daya da Kitchen nan ne na Megidan kenan.
Nazifi ya kalli Abdullahi yana Fadin'"Anya mutumina kodai da Sabuwar amarya zaka tare ne..? Hararansa Abdullahi yayi kafin yace"Dillah ni kyaleni nagaji da maka Bayani in Kara aure na Cikin kaddara na zan kara ammh ni ayanzu bani da wannan Ra"ayin Domin Babu Abunda Hausina ta rage ni Dashi Ballatana naji ina Sha"awar Kara aure.."Nazifi ya murmusa Lokaci Daya yana Fadim"Ni ina da Ra"ayi..Insha Allahu sai na kara Aure wannan karon Tsakani ga Allah zan nemi aure na bazan yi irin na Farkon wajen neman Cikar Burina da Auran jari ba."
Abdullahi yace"Yo daman ai Duk wanda ya Hau motar kwadayi...! Nazifi na Dariya ya karisa mai da Fadin"Karshensa Tashar Wulakanci..Kuma nagani Domin Ta kaini ni harda Tashar ma Nadama da Danasani..'Dariya ta kama Abdullahi sai Da ya Duke,Nazifin na Tayashi Cikin Nishadi,Sun Dade awajen kafin su baro wajen Suna Hanyar Zuwa Cikin gari sai ga Kiran Mama Lokacin misalin Daya Saura ne na Rana yana Daga kiran Bayan sun Gaisa tace mai ga Hajiya Sa"a ta iso Tana son ganinshi Yace gashi nan zuwa
Bayan sun gama Wayar Abdullahi ya saki Numfashi yana Shafa Kanshi Nazifi na Driving ya Dago yana kallonsa Cikin Kulawa yace"Lafiya kuwa Mutumina..? Abdullahi ya yamutsa Fuska yana Fadin"Ina fa Lafiya..! Mahaifiyar Jidda ce ta ke son wai na bata Jidda ta koma Wajenta da zama Tunda ni ko Mama mun gaza.."Cikin Mamaki Nazifi yace'Mahaifiyarta wacce ta Haifeta..?
Abdullahi yace"Eh mana..."Nazifi yace"Toh ba kwanaki mun Taba mgana dakai kace min ita da Mahaifiyar Auwal Tun Tuni basa garin ba,sai naji kamar kace min Tana Saudiya Tun Bayan da aka anso Jidda ko..?" Kai Abdullahi ya gyada yana Fadin"Eh Mun taba mganar dakai..Wai ta Dawo ne Shine take son karban yarta ta koma Hannunta.."Nazifi yace"Ji wata mganar Banza..wannan ma ai Rainin Wayau ne.."
Abdullahi yace"Kaima ka gani..Kwanaki tazo ta Dauketa taje wajenta ta mata kwanaki Shine yanzu take son Daukanta gabadaya alhalin ba gidansu take zaune ba Gida ta gina Tana zaman kanta.."Nazifi yace"Koda ma Tana gidansu ne Cikar kamalar Yarinya ai gidan Ubanta ne, ga Mama araye kaga Har sai Ta Dauki Jidda ta koma Hannunta..? Haba wannan ai bai kamata ba sam.."
Abdullahi yace"Hmm barni da Ita zan mata Bayanin da su Baba suka kasa mata.."Nan ya koramai Bayanin Abunda ya Faru Ranar da tazo Tafiya da jidda kai Nazifi ya kada kafin yace"Na yarda wani Lokacin Mata Tunaninsu kalilan ne wlh.."Abdullahi yace"Ah sosai ma kai sai yau ka sani.."Daidai Lokacin da suka kawo kofar gidansu Abdullahi gaban Jeep din Motar Hajiya Sa"a suka Faka tasu sai da suka Firfito kana Abdullahi ya kalli Motar yana Fadin"Ina jin ma wannan Motarta ce.."
Da kallo Nazifi yabi Motar kafin yace"Ah Lalle,Da gaske kam Tatara Abun Duniya.."Abdullahi yace"Na banza ne ni awurina..kai mutumina mu karisa masallaci muyi sallah gashi chan ana kira.."Da haka suka wuce masallaci Suna Hira alwala suka Dora suka Shiga masallacin sukayi Salla kana suka Fito anan suka Hadu da Baba wada Abdullahi ya gayamai Zuwan Hajiya Sa'a Baba Wada yace Mama ta aika gida an gayamai Dukkansu Daga masallacin suka Dunguma zuwa Cikin Gidan Mama
Da sallamarsu da Jidda suka Fara Cin karo a tsakar gida Ita da Mariya Suna zaune kan Tabarma Suna ta Faman Latsa wayar Jiddan,Dukkansu suna Sanye ne da Dogayen Riguna Dinkin Rariya iri Daya wanda Subai ta taba Dinka musu ne,Suna jin sallamansu Sukayi Saurin Boye wayar kansu na kasa suna gaishesu,Ko kallonsu Abdullahi bai yi ba ya Dauke kai Nazifi ma kallo Daya yayi ma Jidda yaji gabansa ya Fadi Wani Lokacin Abun na bashi mamaki yadda indai yaga Jidda sai Zuciyarsa ta amsa Baba wada ne ya tsaya suka gaisa yana ta Zolayansu.
Dakin Mama Abdullahi yayi Sallama Inda yaga Takalma yana Tunanin Hajiya Sa'ar tana Ciki Daga Ciki Mama ta amsa ya Tura kai ya Shiga Nazifi ya Biyo Bayanshi Da Baba wada,Kusa da Mama Abdullahi ya Zauna Nazifi kuma ya samu Chan gefe Ya zauna kan Kujera mai zaman mutum Biyu,Mama kuma ta mike ta Bama Baba wada wajen da tatashi ta mishi sannu da Zuwa ya amsa yana Tambayanta ya yara.
Hajiya Sa"a Ta Fara gaida Baba wada Lokaci Daya Tana kallon Abdullahi,wanda ya Dauke kanshi sama yana wani Daukan Kai Kawai Ranta ya bata Shine Abdullahi Domin Tabbas kwarjinsa ya Daketa ashe ma yaro ne karami ba wani Babba ba yarda Take Tunani Mama ce ta Kalli Hajiya Sa"a da Lariya tana Fadin"Ga su sun kariso..Ga yayan nasu Jidda Abdullahi wannan abokinsa ne Dan wajen Mallam Wada ne.."Ta fada tananuna kowa Kai Hajiya Sa"a ta gyada tana Fadin"Masha Sannunku..Abdullahi ina gajiya..? Nazo kwanaki baka nan nasan karima ta Fadamaka zuwana da Abunda ke Tafe dani.."
Abdullahi ya Dago kanshi yana Fadin"Basu Fadamin komai ba..Sun dai sanar dani kinzo kin Tafi da Jidda zata miki kwana Biyu.."Da mamaki kowa yake kallonsa Shi kuma ya Hade Ransa Baba wada yayi Mirmishinsu na Manya yana Fadin"Kega Sa"a Bamu gayamai komai ba..Mun bari ne keda kanki ki sanar dashi sai ku Fahimci Juna.."
Hajiya Sa"a ta gyara zaman mayafin dake Jikinta Tana Fadin"No problem Daman kan Mganar Hauwa"u ne, kwarai da gaske da nazo naga Hauwa"u na yaba sosai da irin Rikon da naga anyi mata kuma naji Dadi Sosai,sai dai kuma ina Son Don Allah a matsayinka na Yayan Hauwa"u wanda ke matsayin Uba gareta kai da Mallam Wada kumin lamani na Karbi Jidda ta Dawo Hannuna Saboda Chan Saudiya Danayi Aure har Mijina ya Rasu bam Haihu ba Jidda ita kadai ce yata anan Duniya Na Dawo Nageria da zama na Dindin ina Bukatar zaman Hauwa"u awajena Kodon Shekarun da muka kwasa bama Tare Saboda wasu Dalilan da Allah ya Tsara.."
Falon yayi Shuru Abdullahi kadai ake Saurara wanda yayi kasake kawai yana kallon Kasan Cafet din Dake Dakin Mama Mirmishi ne ya kwace mai kafin yace"Acikin mganarki ya kamata ki Gane amsarki aciki kafin ki Dora wata mgana sai da kikace a matsayina na yayan Hauwa"u kuma Uba gareta Nida Baba wada kinga kenan Jidda tana da gatan da Ko kotu kike je ba wanda zai baki Rikon Jidda ta koma Hannunki..."ya fada kai Tsaye yana kallonta ido Cikin Ido Hajiya Sa"a tayi tsai Tana kallonsa Lariya kuwa acikin Ranta Fadi take dama Daga ganinsa zai yi Taaurin ido...
Baba wada dai yayi Shuru bai ce komai ba Saboda ba"a kawo gabar da zai yi mgana ba,Nazifi kuma ya maida Hankalinsa kan Wayarsa ammh kuma gabadaya Hankalinsa na kan su,Hajiya Sa"a ta muskuta Tana Fadin"Ai nasan kuna Raye..Kuma zaku iya Rike Jidda Fiye da yarda zan Riketa Sai dai kuma kuyi Duba da Duk Tsawon Shekaruna nan bana Tare da ya"ta baku Tsausayina a matsayina na Uwa wacce take Bukatar yarta a kusa da ita ba....?"
Kai Tsaye Abdullahi yace"Ana Tsausayinki mana..Kice baki Tsausayama kanki ba Hajiya to be Frank kin san kina son zama da y'arki ki ka Tsalleketa koda Tana gidan Mahaifinta ki Lula wata uwa Duniya ki ka manta da ita ?.Kawai sai yanzu Farat Daya kizo kice zaki karbeta Don Allah ke kina ganin ya Dace..?na Dauka ko baki Jidda nayi kunya bazai barki ki karbeta bawai ina miki Gori bane No ina gayamiki gaskiya ne Ban gaza ba Mama ma bata gaza ba tana iya bakin Kokarinta kuma koda Mahaifinmu ya Mutu ya barmata Amanarmu Duka Tana Hannunta ne Ta Rainemu har muka kai iyanzu kina ganin ba Rashin adalci bane kizo Daga Sama kawai kice zaki karbi yarki..? Baki Tsausayama wata Uwar da ita Bata taba Haihuwa ba kuma ta Sadaukar da Lokacinta da kuruciyarta wajen inganta yaran da bama ita ta Haifa ba..? Itama Shin ba abar Tsausayi bane..?
Yafada yana kafe Hajiya Sa"a Da ido wanda mganganunasa suka Shigesu Baba wada kai kawai yake Gyadawa alamun gamsuwa Mama kuwa na gefe tana Sharan kwallah acikin Ranta tana Godema Allah daya bata D"a kamar Abdullahi Duk da ba ita ta Haifeshi ba.
Falon ya Dauki Shuru Lariya ce tayi mgana wannan karon Da cewa"Ammh ai Itama Yayar sai ku Duba Rauninta..Taya zataji alokacin ga Sakin miji daga baya kuma akazo aka Rabata da yarta alokacin bata da wani Abun da zata iya yi akai zuwanta kuma Saudiya wannan Nufin Allah ne dama Allah ya nufi zataje chan kuma Har tayi Aure.."Mirmishin Abdullahi ya saki kafin yace"To waya ce ba Nufin Allah bane.."Komai da kika gani nufin Allah ne,Saboda haka Itama Jidda zamanta agidan Ubanta Daya mutu ya bari wani Nufi ne na Allah Mganar gaskiya ba zan tsaya kuna Fada ina Fada ba saboda mu ba Sa"anin Juna bane..Kunsan Allah..? Bazan iya baki Jidda ta koma Wajen ki da zama ba Sai dai zan miki alfarma ta karshe duk bayan kowani Wata zata Dinga zuwa ta miki kwana Biyu Ke mahaifiyarta ce ban isa ,na Raba tsakaninku ba,kuma nayi miki alkawarin duk Abunda kika Siya mata a matsayinki na uwa gareta bazan Hanata amfani Dashi ba,ko waya da kika Siyamata na barta dashi Domin Dama Abunda yasa kika ga ban Siyamata ba abaya saboda bata yi candy ba ammh Tunda yanzu tayi Shikenan bazan Hanata karban komai Daga gareki ba Nagama Mganta ko ya kagani Baba..?
Baba wada yace"Hakan Shine Daidai Abdullahi..Abunda yasa Tun Farko ban saka baki ba kenan Sanin wannan Bukatun na Sa"a bamai yuyu bane gaskiya in akayi hakan Ba"ayi ma Karima Adalci ba."Abdullahi ya mike yana Fadin"Nima shi nagani..Duniya sai ta zagemu..Mganar gaskiya kenan Ba zan maida Rikon Jidda ahannunki ba ba Saboda komai ba Sai saboda ke macece mai Rauni kema baki wuce wani ya baki Tarbiya ba kinga kuwa ke bazaki iya bama Jidda Tarbiyan Data kamata ba.."
Daga haka ko Wucewar Hajiya sa"a bai Jira ba ya kalli Nazifi yana Fadin"Muje mutumina.."Daga haka ya Fice Nazifi ya Maramai baya,Hajiya Sa"a da Hajiya Lariya suka Bisu da kallon Mamaki Baki Bude,suna Fita suka ga Jidda ta Rabe Jikin Mariya Tana Sharan kwallah wani kallon Banza Abdullahi ya Wurgamata Dole ta Shiga Taitayinta wani Dogon Tsaki yaja kawai ya Zura Takalminsa ya Fice Nazifi ya maramai Baya.
.
Acikin Dakin Mama kuwa Baba wada ne yace"Kinji dai Hukunci Da ya yanke..Kuma ina Bayansa Hajiya sai kiyi Hakuri yarki dai bamai Rabaku ammh ki barta gidan Ubanta ki Rika zuwa ganinta Lokaci bayan Lokaci itama zata Rika zuwa tana ganinki bashikenan ba.." Hajiya Sa"a ta Dukar da kai Tana jin Wani Daci acikin Ranta bata samu bakin mgana ba Lariya ta Bude zatayi mgana Baba wada ya Dakatar da ita da Fadin"Kinga ya isa..Wani Cece kuce duk ba namu bane..Mu ba yara bane kuma na Tabbata munsan Abunda ya Dace damu..'Daga haka kawai Shima ya mike yanama Mama Sallama ya Fice,Mama ta Sunkuyar da kanta Kawai batayi mgana ba Hajiya Sa"a ta saki ajiyar Zuciya ta mike Tana Fadin"Tashi mu Tafi Lariya..."
Lariya ta mike Tana saba Jakarta Mama ma ta mike tana Fadin"Kiyi Hakuri Hajiya Sa"a..."Da Hannu ta Dakatar da ita Tana Fadin"Ba sai kin ban Hakuri ba Karima ba Laifin ki bane..ammh ina so ku sani ni Sa"a ni na Haifi Jidda da Cikina Bayan na Sha wahalan Dakon Cikinta na Wata Tara na Sha wahalan Naguda na Haifeta kuma na Shayar da ita Daga jikina na Tabbata koni ban nemeta ba ita Zata nemeni Saboda haka bawanda ya isa ya Rabani Da ya"ta..Muje Lariya.."
Daga Haka Ta ja Hannun Lariya suka Fito Daga Dakin ganin Su haka yasa Su Jidda suka mike daman suna Jin Abunda ke Faruwa kuka Jidda ta saka Ta Rike Hajiya Sa"a wacce Taji kamar itama ta Fashe da kukan kanta ta Shafa Tana Fadin"Stop crying my Dota..Ba wanda ya isa ya Raba wannan kaunar da Allah Ya dasa Tsakanin uwa da ya...Ki zauna anan dim Insha Allahu zan Rika zuwa ina ganinki Lokaci Bayan Lokaci."Tafada tana Share mata Hawaye Zuru Jidda ta mata ido Kafin kuma ta saki Mirmishi Rumgume juna sukayi Lariya Da mama da Mariya suna kallonsu Cikin Sha"awa.
Kudi ta Dunbuzo Daga Cikin Jakarta bata ko san nawa bane ta Mikama Jiddan Tana Fadin"Zamu mgana ta waya kinji ko..? Da kai Jidda ta amsa Tana Fadin"Nagode Mommy.."Mirmishi ta mata ta Shafa kumatunta Tana Fadin"U are wlcm y Darling Dota.."Hannunsu Rike da juna Har Zaure kana suka Rabu ta Daga musu hannu kana ta koma Cikin Gidan Duka Kudin ta Damkama Mama,Mama taki karba tace ta ijiye kudinta sai ta Bama Mariya tace ta ijiye mata.
Achan waje kuwa Abdullahi da Nazifi suna tsaye wajen Motar Nazifin sai gasu sun Fito Kallo kallon sukama Juna Abdullahi ya Dauke kansa Gefe kamar bai gansu ba kai Hajiya Sa"a Ta kada ta Bude Motarta ta Shiga Bangaran Direba lariya ta Shiga Bangaran mai zaman banza suka Tada Motarsu sukayi Reversr suka Dau Hanya sai da suka kule kana Nazifi yace"Allah ya kyauta..ammh matar nan ta Cika karfin Hali
Ajiyar zuciya Abdullahi ya Sauke yana Fadin"Kabari kawai harga Allah Zuciyata bata kwanta ba..Ni ban isa na Raba uwa da ya ba..Ko yayane suna Tare wani abun ma ba sani zan yi ba ina Tsorin Jidda ta samu sake sai Allah Wlh Nazifi ina Cikin Damuwa inda ace yau ina da wanda zan iya bama Jidda ya Aura wanda na yarda da nagartansa ko Bashi zan iya ci Wlh nan da wata Biyu na aurar da ita Hankalina zai Fi kwanciya.."
Yafada yana Bayyana yadda Abun ya Damesa asaman Fuskarsa,Nazifi yayi Shuru yana kallonsa Kafin yace"Gani...Zaka bani Auran Jidda...?
Da Sauri Abdullahi ya kalleshi kafin yace"Dillah mu daina wannan wasan Dakai.."Nazifi yayi Dariya kafin yace"Am not Joking abokina indai zaka bani Auran Jidda ni kuma na maka alkawarin Auranta nan da Wata Biyu na killaceta agidana ni kadai.."da wani rin Sauri Abdullahi ya Rikeshi yana Fadin"Are u Serious Mutumina..?"
Nazifi yace"Wlh Tallahi..Am Serious...Kaji ma na Rantse..."Rumgumesa kawai Abdullahi yayi yana mai Bayyana Farincikinsa afili Shima Nazifin Rumgumesa yayi kafin Lokaci Daya su saki Juna Abdullahi ya kalleshi Cikin Fara"a yana Fadin"Zan fi Farinciki in ka sanar dani ba wai saboda na Furta haka bane zaka auri jidda zan Fi Jin Dadin in ka Furta kana Son Jidda So na Aure..!!!
Mirmishi Nazifi ya Sake kafin ya Riko Duka Hannayen Abdullahi yana Fadin"Haba Mutumina Ni din ne baka sani ba..? In Abu bai min bani da Kwana kwana Direct nake Fadama kowa ma waye koya muke Dashi..Kaji ma na Rantse Maka har ga Allah ina Jin Jidda acikin Raina ba Tun yanzu ba Abokina..."
Abdullahi ya kalli Nazifi yana Fadin"Alhamdulillah naji Dadi kwarai...Ba Domin komai sai Domin Na yarda Dakai abokina kuma na Tabbata zaka auri Jidda ka Riketa Kamar yadda ni zan Riketa na kula da ita.."Nazifi yace"Insha Allahu Mutumina...Karma abari ya Huce muje ni dakai yanzu mu ma Baba mgana ayi komai cikin Lokaci Dama Mata nake nema kuma na Riga na samu agidanmu ma.."
Dariyar Jin Dadi Abdullahi yayi yana Fadin"Hakane..ammh Wani Hanzari ba gudu In Salisu engr.yaji Labarin kanwata zaka aura anya bazai ji Haushi ba..? Yace Kaki kannesa kuma ni na baka kanwata..?Nazifi ya Dafa kafadan Abdullahi yana Fadin"Come on Mutumina...Salisu bai da wannan Halin sam..Ko kwanaki ma naje gidan na gaida Hajyarsu,tayi Rashin Lafiya har ta kwanta asibiti naje gidan na gaisheta Duka yaran na gansu ammh kamar Karamar da Babbar ban gansu ba suna Makaranta karka damu kanka Dani da kai mun zama Daya salisu bazai taba wani Tunani akan hakan ba infact ma ni nace ina so ba Turamin kayi ba.."
Abdullahi yayi Mirmishi kafin yace"Allah yasa..."Daga haka suka Dunguma zuwa gidansu Nazifin akofar gidan suka iske Baba wada suna mgana da wani makocinshi gefe suka koma sai da suka gama kana yazo ya samesu kan Dakalin kofar gidan suka Zauna su uku kafin Nazifi ya Fara korama Baba wada jawabi Abdullahi ya karisa kafin su gama Bakin Baba Wada yaki Rufuwa,Cikin Farinciki yace"Masha Allah..Alhamdulillah kai gaskiya naji Dadin wannan Labarin naku..Kai...Abu yayi Dadi dama na Dade ina son wannan Zumuncin Dake tsakanin Gidan Abokina marigayi Usman Direba da nawa gidan ya kara Haduwa ta Hanyar Autarayyah Allah bai yi ba sai wannan karon Hakika naji Dadin wannan mganar Sosai.."Yake Fada yana Bayyana Farincikinsa Haka suma Sun Dade suna tsara yadda komai zai kasance Nazifi yace baisan a dauke Lokaci mai Tsawo Sai aka bar mganar kan Abdullahi Yace Sadaki kadai Yake Bukata wajen Nazifi Tuwona maina ne Abun,Sun Dade suna mganar kafin Daganan Abdullahin sukayi sallama da Nazifin da Baba Wada yayinda suka Shiga Cikin Gida Shi kuma baima koma Gidan Mama ba Mashin Din Haya ya hau zuwa gida Zuciyarsa Fes.
Bangaran Baba Wada Da Nazifi kuwa suna Shiga Cikin Gida Baba wada ya Labartama Inna Abu Halin da ake Ciki,Guda ta Rangada tayi Juyi kafin tace"Ahayye...Abu namu mganin akwabemu..Ni uwar amarya kuma uwar ango ka Biyasheni Nazifi Wlh sai yanzu zan Tabbatar da zakayi aure ina gayamaka Har mai asharalle zan kira ya bugamana kidaa da waka Ni da Karima.."Karamin Tsaki Baba wada yaja yana Fadin"A"a bamai Asharalle ba ki kira Mai amada ne..Kullum bakya girma Abu baisan me kikeson ki zama ba.."
Yana Fada ya Bude labule ya Shige Cikin Dakin ya bar Nazifi da Inna Abu tana ta sakamai albarka Shi kuma yana Dariya yana Jin wani Farinciki yana Tsirgamai Har Cikin Ransa na Wannan Auran wanda bai ma san Sadda bakinsa ya Furta zai auri Jidda kuma Baya jin Nadamar haka sai Farinciki.
Nan yayi La"asar yaci abinci kana yayi sallama da iyayensa ya Dau Hanyar Kaduna Zuciyarsa na wani irin Fari yana jin wani Farincikin da baisan Daga ina yake Fitowa ba..."
*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Sai kunzo...*
*Shakira...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*Intelligent writer' asso...*
*023*
"Haka Abdullahi yajema Hafsah Cikin Wannan Farincikin Wanda ya kasa Boyuwa Daga saman Fuskarsa,Tayi ta mamaki ganin Wannan Fara"a kamar me,Data Tambayeshi sai yace mata Bakomai koma miye zata ji Daga Baya.
Su Amira kuwa Auwal ya Dawo Dasu Bayan ya Dawo Daga Shago,Shi Abdullahi yama Manta Dasu ya Taho Shi kuma yana Dawowa Shago Mama tace ya Daukesu Amira ya kaisu Gida,ya Dade sai Wajen goma yayi musu sallama ya koma Gida Bayan yayi Dinner dinsa anan Suna ta Hira da Hafsah Abdullahi ko yana Ciki ya kwanta gajiya ta Saka Barci ya Daukesa da wuri.
Washegari Inna Abu ta kasa Zama sai da ta Shiga gidan Mama ta Fara Zegunta mata Hakika Mama tayi murna ammh acikin Ranta Tana Tunanin Jidda ne,ganin ai babu Soyayyah Tsakanin Nazifin da Jidda Tayaya wannan Halin zai yuyu,Koda yake Abdullahi ne in yace Eh din ne baya iya Sauyashi Duk Rigimar Jidda sai dai tayi Hakuri kawai.
Da Mama Taji Labari sai tayi Gum da Bakinta Tunda Abdullahin bai gayamata ba,Sai da ya taso Daga aiki,kana ya Biyo ya Kira Mama Cikin Dakin Auwal ya Gayamata komai Mama tayi Shuru kafin tace"Naji Dadin wannan mganar Domin Nazifi mutumin kirki ne,Ammh kana ganin Shi Nazifin zai so Jidda Har suyi zaman Aure..?
Abdullahi yace"Karki Damu da wannan Mama Abokina ya Tabbatarmin da Cewa Yana son Jidda Tsakani ga Allah kuma so na Aure.."Mama tace"Toh ita Jiddan Fa..? Zata so shi kuwa..? Kaga fa har yanzu Jidda Yarinya ce.."Abdullahi yace"Haba Mama Kina Wani mganar yarinya A yarinyar take Abunda ko Babban Albarka Ban damu Da tana son Shi ko Bata Sonshi ba nidai Hakkina na matsayin Babban Wa gareta Shine na Nema mata Gidan zama na Har Abada,ita ta isa tace bata son Nazifi ne..?dame tafishi...? Wlh shi ba ajinta bane sai dai kawai al"amarin Aure Ya gaji haka.."
Mama ta Rausayar Dakai Tana Fadin"Shikenan...Allah ya Sanya alheri ya Shige mana Gaba.."Yace"Ameen Na riga na Barma Baba wada wuka Da nama kan mganar Saboda haka zan Kira Zannira da Subai suzo gida muyi mgana inaso ayi komai Cikin Lokaci ne Mama.."Mama tace"Ya kamata..ammh Ya za"ayi zaka karbi Lambar Hajiya Sa"a ne ka Sanar da ita ko yaya..?
Cikin Mamaki yace"Wata Hajiya Sa"an..?Mama tace"Mahaifiyar Jidda mana.."Karamin Tsaki yaja kafin yace"Ni ba wacce zan Kira Mama..Yarta ta gayamata ko ke..! Jidda kuma gobe Ki Turomin ita Gidana Ta kwana zan sanar da ita Zuwa asabar ko Lahadi kuma Nazifi zai Shigo su gana in Allah ya kaimu.."Mama tace"Hakan ya kamata Allah ya nuna mana..ya kuma Sanya alheri.."ya amsa da Ameen da haka ya mata Sallama ya Fice Daga gidan..
Daga Mariya Har Jidda ba wacce ta kawo Tunanin komai acikin Ranta,Zannira da Subai"atu sum Ji mamaki kiran da Abdullahi yayi musu da kanshi yace in sun samu Dama Cikin Satinan su Shigo yana son mgana dasu sai Zannira Tace sai Dai Ranar sati Saboda karatun yara Shima Abdullahin yace Hakan yayi Saboda Office Ranar duk da yana da Karatu a Abu in ya Dawo sai Su Hadu gidan Mama.
Kowacce ta kira yar"uwanta Tana Fadamata Kiran ya Abdullahi suna Hasashen Allah sa Lafiya,Koda suka Kira Mama kin Fada musu tayi tace Bata sani ba,Mama bata samu Tura Jidda ba sai Ranar Laraba da yammah Tace ta Shirya Tatafi gidan Abdullahi ta kwana da safe sai ta Dawo Tun da Taji haka sai tasha Jinin Jikinta Tana Tsaye a tsakar gida Tana Ninke kayan Mama Data wanke mata a kan igiya,Mariya kuma tana gefe kan Tarbama ta baje littafai Tana karatu,Mama kuma na Daga kofar Kitchen tana Tsinkan allaiyahu Zata saka Cikin Miyar Taushan da zatayi.
Jin Abunda Mama tace ne yasa Daga Jidda Har mariya suka Dakata da Abunda suke suka Dago suka kallonta Gabadayansu Cikin Mamaki Jidda tace"Mama gidan ya Abdullahi kuma..? Har na kwana..? Lafiya..?
Mama tace"Lafiya lau..yayanku yace na Tura mishi ke.."Jidda ta kwalalo ido Tana Fadin"Ni kuma Mama..?me nayi..? Mama Tace"Ni bai ce min wani laifi kikamai ba,Abunda na sani Shine yace ki Shirya kije ki kwana chan gobe da Safe sai ki Dawo.."Mariya tayi karaf tace"Kin Shiga uku Jidda..Ki Fara maimaita Lahaula walakuwwatu Tun yanzu.."Dakuwa Mama ta Sakar mata Tana Fadin""kaniyarki..Hala mala"ikan Mutuwa ne.."? Mariya na Dariya tace"Ko ba mala"ikan mutuwa bane Mama kiran ya Abdullahi ai ba alheri bane.."Mama ta Rike Tana Fadin"Haka kikace ko Mariya..? Tabbas kuwa zan gayamai.."
Jin Haka yasa Hankalin Mariya ya tashi ta Fara ma Mama magiyan ta Taimaka mata Karta Fadama Ya Abdullahi ita kuma Tana kara Tsoratata da sai ta Fada Jidda kuwa Fuskarta sam ba Walwala gabanta kuwa sai Fadi yake gaskiyan mariya ne Kiran ya Abdullahi Wlh D'aidai ku ne na alheri kai bayama kiran mutun sai in wani Abu babba ya taso,gashi Mommy ta mata waya Tana nan Zuwa Cikin Sanyin Gwiwa ta kalli mama Tana Fadin"Mama gashi kuma Mommy ta Kira ni tace zata zo...ko zan Bari sai da Safe ne..?
Mama Tace"A"a da safe baya gida yana Wajen aiki..Yanzu ya kamata Kije ba Dadewa zai Dawo Daga wajen aiki..Hajiya Sa"a kuma sai ki Kirata ki gayamata Uzurin daya Taso.."Ba haka Ran Jidda yaso ba Jiki ba Dadi ta Shige Daki Dauke da kayan Mama Mariya ta Bita da Dariya Itama Jin Mama tace wasa take bazata Fadamai ba kana ta Saki Ranta.
Bayan Sallar mangariba Jidda tatafi Mariya ta Rakata ta Hau Mashin sai dai Hafsah ta ganta kamar Daga sama su Amira suka makalkaleta Suna Murnan ganinta Cikin mamaki Hafsah ta Fito Daga Cikin Bedroom dinta idar da sallanta kenan Taji ihun su Amira ganin Jidda yasa ta Bude Baki Tana Fadin"Jidda kece Tafe yanzu da mangariban nan..?
Jidda na zama kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon Tana Fadin"Eh Wlh Anty Hafsah ina Wuni yasu Amira..? Ta Fada Tana Daga Amir wanda ke Tsalle kan Jikinta Gefenta Hafsah ta zauna Tana Fadin"Lafiya lau yasu Mama..? Ina mariya da su Auwal..?
Jidda tace"Duk suna Lafiya..Mama tace agaidaki.."Hafsah tace'Ina amsawa..Lafiya kuwa naganki da Dadaddaran nan Jidda..? Jidda tace"Lafiya lau....ai Yaya Abdullahi yace nazo gida na Sameshi yana Nemana.."Cike da Mamaki Hafsah tace"Ok..gashi bai Dawo Daga wajen aiki ba gaskiya.."Jidda tace"Eh yace ne na Jirashi.."Hafsah tace"Au Toh..ammh Tafiya ba yau ba sai dai gobe domin ai Dare yayi.."Kai Jidda ta Sunkuyar Tana Fadin"Eh Haka yace sai gobe zan koma.."
Cikin Dariya Hafsah tace"Dakyau mijin Hafsatu gashi yau ya kawomin ke.."Itama Jiddan Dariyan Tayi Daidai Lokacin da wayarta Dake Hannunta Ta Dauki Kara Tana Dubawa Taga Mommy ne sai ta Dauka Tana Fadin"Hello Mommy..."
Jin Haka yasa Hafsah mikewa Ta Fita zuwa Kitchen,ta Duba miyarta in ta karisa ta Sauke,Tuwon Semo tayi da Miyar kubewa Danya wacce Taji Kifi Ta Gama Tuwon Tun dazu ta Nannadeshi Cikin leda Kubewar ne bata karisa ba,Koda taje har ta karisa ta Sauke ta samu karamar Kula ta Zubama Mai gayyah mai aiki Nashi,sai kuma ta samu Filet ta Zuboma Su Amira Nasu Saboda ya Huce,Jidda kuma bata sa mata ba, ta bari ta saka da kanta Tunda Gidan ba bakonta bane ita kuma Batama jin Tana Sha"awar Cin wani abu Haka kurum Cikinta Duk ya Tushe..
Dakin Ta Dawo Har Jidda Ta gama wayar dama kafin ta Fito Gida ta Kirata da Niyyar ta Fadamata Fitarta sai bata Daga ba Shine yanzu tabiyo bayan Kiran Nan take Sanar da ita Tana Gidan Ya Abdullahi nan zata kwana sai gobe Itama Hajiya sa"a sai tace mata Tana ma Kaduna kuma ba yau zata dawo ba,kuma ba gobe indai ta Dawo zata Shigo ,Da haka suka Yanke kiran.
Hafsah tace ma Jidda In zataci Tuwo Ta Shiga kitchen Ta Duba Zazzabi take ji yana neman kamata Kayan abincin Abdullahi ma Dakyar ta iya Jeramai Bisa Cafet nan Gefe Jidda ma ta kama mata,kan kujera ta koma ta Nade Tana kallon Jidda na cin Tuwon Ita Dasu Amira suna Damunta da mgana itama tana Biye musu Duk da bata da Hayaniya tafi mariya son yara.
Kiran Sallar Isha"i ya Tashi Hafsat taShiga Bedroom ta Kabbarta sallah Dama tana da alwala ita kuma Jidda suna gama Cin abinci ta kwashe komai takai kitchen Ta share Saman Cafet din ta Goge inda su Amira suka Bata da Miya Tajasu zuwa waje sukayi alwala anan Falo Ta Shimfida musu Sallaya sukayi Sallar sun Idar kenan sukaji alamun Bude Kofa da Shigowar mashin da gudu su Amira suka Fita Suna Murnan oyoyo Abba Su suka Tarbesa,ledojin hannunsa ya mika ma Amira Karamar Jakarsa kuma Amira ta karba Shi kuma sai ya karisa shiga d mashin Dinsa ma"ajiyarta.
Yana Dauke da Amir a kafadansa Amira kuma yana Rike da Hannunta ya yo sallama ya Shigo Dakin Jidda Dake ninke sallayar da sukayi Salla dashi,Lokaci Daya Tana amsa Sallaman nasa Kallonta yayi kafin yayi magana Tayi Saurin Cewa"Sannu da zuwa ya Abdullahi.."
Yana zama Kan Daya Daga Cikin kujerun Falon yake amsa mata,Fuskarsa ba walwala Cikin waige waige yace"Ina Hafsah din..? Kan jidda na kasa Tace"Tana Ciki..Bata jin Dadi ne inaga Domin tace min tana jin zazzabi.."Cikin Damuwa ya mike Lokaci Daya yana Sauke Amir Dake kan Jikinsa yana Fadin"Subhanallah...Tun yaushe..?
Jidda tace"Bansani ba Wlh..Nima ban jima da zuwa ba..."Kai ya kada yana Fadin"ok..Tafi dasu Amira ki karbi ledojin Hannunsu kayan Lambu ne sai kaza ki Dibar muku Sauran ki saka Cikin Fridge din Tunda Hafsah bata jin Dadi.."Kai ta gyada kafin tace"Kai bazaka ci ba..? Da sauri yace"No am ok...Amira kuje wajen Anty Jidda ko..? Yafada yana Tura Mata su da gudu suka nufeta da ledojin ta karba ta jasu zuwa Kitchen Shi kuma ya Shiga Cikin Bedroom din nan ya iske Hafsah kwance Inda Tayi sallah ta Dunkule Cikin Hijabinta a saman Kanta ya Duka yana Kiran Sunanta Cikin Galabaitan zazzabi Ta Dago Tana kallonsa Cikin Tsausayinta yace"Hafsah baki da lafiya Shine baki Kirani kin Fadamin ba..?
Kokarin mikewa take yayi Saurin Rikota da Jikinsa ta jingina Goshinta ya Shafa yaji Zafi Rau,Saurin Dauke Hannunsa yayi Lokaci Daya yana Fadin"Kai kinji Zafin Jikinki..? Tashi maza muje asibiti Fever kike yi Sosai kila maleria ce.."Ya fada yana Shirin mikar da ita Hannunsa ta Riko Cikin Sanyin murya tace"A"a yanzu ka Dawo kana Bukatar Hutawa..karka damu Zazzabi ne kawai Bani panadol nasha nasan zai Fada Insha Allahu.."Tafada tana Kallonsa Bata Rai yayi yana Fadin"Wannan wata irin mgana ce..? Lafiyarki batafin mun komai ba Hafsah taya zan barki Cikin wannan Halin.."Kan Cinyarsa ta Maida kanta tana Fadin"Ba wani Ciwo bane Sosai..Don Allah kadaina Damuwa.."Sai Tsausayinta ya kamashi ya kamata ya Rumgume kawai yana Sauke Numfashi,Da ita ajikinsa ya mike ya maida ta kan Gado Drower din gadon ya Bude ya Dauko panadol ya ballamata Guda Biyu,Har zai mikamata sai kuma ya kalleta yana Fadin"Kinci wani abu..?
Kai ta girgiza Tana Fadin"A"a bana jin Cin komai bakina bayamin Dadi.."Maganin ya ijiye kawai ya Fice Jidda na kitchen din Ya Shigo Filet yace ta samu ta Debomai kayan marmarin,Da sauri ta Samu Filet din ta Zubamai ya karba da Ruwa ya koma Ciki Dakyar da lallashi Hafsah taci kadan tasha mgani kana ya kwantar da ita ya kunna mata Fanka,Ganin ta Fara zufa yasa ya Cire mata Hijabin jikinta ya barta Daga ita sai Doguwar Rigar Dake Jikinta ya Dade Tsaye kanta Sai da yaga ta samu Barci kana ya Shiga yayi wanka ya Sauya kaya zuwa Jallabiya koda ya Fito Falo Har Su Amira Sunyi Barci Umartan Jidda yayi da ta kaisu wajem kwanciyarsu tazo yana son mgana da ita cikin Fargaba ta kwashe su zuwa wajen kwanciyarsu ta Dawo yana Saman kujera ya koma kasa ya zauna yace ta Jawomai kulan Abincinsa da Hanzari ta mike ta Kaimai komai gabansa ya Bubbude Tuwon kuwa yaci Da yawa yana ci ammah Rabin Hankalinsa na Wajen Hafsah yafi kowa sanin Halinta in tana Ciwo haka take bata san Ta nuna mai wani Abu na Damunta saboda kar ya Shiga Damuwa sai Ciwon ya kaita kasa kana take yarda yakai ta asibiti,Ammh yanzu bazai Kyaleta ba Zuwa gobe in yaga Zazzabin bai Sauka ba zai Dauketa suje asibiti adubata abata magunguna.
Jidda kuwa na gefe Rakube har ya gama cin abinci kala bai ce mata ba Tashi yayi yana Fadin"Ke Dauke wadanan kwanukan ki maida kitchen Ki Dawo.."Da Hanzari ta mike tayi kamar yadda yace Shi kuma Bedroom din ya koma ya Shiga Tailet ya wanko Hannunsa yazo ya kara Duba Hafsah ganin kamar Zazzabin ya sauka ne yasa ya Rage mata Gudun Fankan ya Rufa mata Blanket Daidai Kafarta Zuwa saman Cikinta kana ya kashe mata Wutar Dakin ya Fito.
Inda Jidda Tatashi nan ya Isketa Zama yayi kan kujeran Dake Fuskartata Lokaci Daya ya Kiran Sunanta.."Hauwa"u..."! cikin mamaki Ta dago Tana kallonsa Lokaci Daya tana Fadin"Na"am Cikin mamaki Sanin ba kasafai ya Cika Kiran Sunanta ba,Zama ya gyara yana Cigaba da Fadin"Nasan baki san Dalilin Daya sa Nace Mama ta Turo min ke ba ko..? Da kai ta amsashi bai bata Zarafin mgana ba ya Cigaba da Fadin"Very good..Ba wani Dalili bane mai karfi..Ko nace ba laifi kikayi ba Na ce ta turomin ke ne Saboda bana samun Lokacin kaina In na taso Daga wajen aiki wani Lokacin bana samun Tsaya agida a nan kuma zam samu Lokacin da zan miki Bayani Sosai yadda zaki Fahimta Dama ba wani abu bane..Mganar Auranki ce Tataso.."
Dam! Gabanta ya Fadi da Sauri ta Dago Tana Kallonsa Cikin kwalalo Ido waje tace"Mganar Aure kuma Ya Abdullahi..? Wlh Allah na Daina kula kowa Kama Tambayi Mama ko Anty Mariya kaji.."Tafada idanuwanta suna Cika da kwallah kallonta yayi kai Tsaye kafin yace"Wayace Dama kina kula wani..? Ki Saurareni Dakyau...abokina Nazifi yamin mganar yana Sonki kuma so na Aure ni kuma na bashi har ma yayi ma Baba wada mgana Bana son mganar ta Dau Lokaci na Farko ke yarinya ce Wacce kika kasance amana gareni Babban Burina da Fatana ki samu miji na gari Dake da mariya kamar yadda Sauran yan'uwanku Suka samu...Ba Domin Nazifi yana abokina Zan yabeshi ba A"a sai Domin ya Chanchanta kuma ya Dace Da Duk yarinyar daya Nuna yana so abashi saboda bashi da wani makusa atare Dashi,kana Abu na gaba zai kula Dake kamar yadda ni zan kula Dake saboda Haka na Riga na Furtamai na bashi ke,Ranar Lahadi zai zo ku ga Juna kuyi mgana mganar karatunki kuma karki Damu zaki cigaba adakinki in dan Har Shi Nazifin ya Amince miki.."Tun sadda ya Fara mgana Jidda ke Tsiyayan Hawayen Tsausayin kanta Sadda ya Furta Sunan Nazifi sai da kirjinta ya Shiga Bugwa Taya ya ma za"a ce Zata Auri Ya Nazifi wanda take gani kamar ya Abdullahi Alhalin ga mariya wacce ke gabanta ba"a ce ita ba sai ita Karamarta da ita za"a aura mata Abokin yayanta kuma ma bama Saurayi ba mai Mata,gashi Tana da Burin yin karatu mai zurfi Burin Mamarta ne wacce tace zata nema mata ko Base University Abuja ko Maryam Abacha,gashi Lokaci Daya wannan mafarkin nata na Neman Rushewa Tuna,hakan Datayi yasa ta kara Volume din kukanta Baki Abdullahi ya saki yana Kallonta kafin yace"Ke lafiya kika Tasani kina min wannan kukan..?ko na Dake ki ne..?
Kai ta girgiza Cikin kuka Take Fadin"Ni bana son Shi Yaya Kuma nayi karama da Aure..Ga Anty mariya nan."Ransa ya baci yakai mata Dakuwa yana Fadin"kinga naki nan da baki Sonshi..? Dama wayace ki Soshi..? finshi kikayi..? Me kike dashi da Naazifi zai ce yana Sonki..? Baki da komai Wlh Domin yafi karfinki nesa ba kusa ba..Balle ki Bude baki ki gayama Mutane mganar banza kuma ai yafi ki sanin mariyan kuma yace ke Saboda Haka mgana Babu fashi ki zama Cikin Shiri xai zo ku gana Kuma Wlh in naji wani Rashin Mutumci ya Fito Daga barayinki kinsan Allah Dakaki zanyi Da sai kin gane Ni ba sa"an wasanki bane Tashi ki bani waje sakarya kawai mara wayau.."Jidda da kuka ya gama Cinta ta mike tana Rangajin kuka ta Fada Dakin su Amira kan Katifarsu ta Fada Lokaci Daya Ta saki Volume din kukanta Kamar wata Karamar yarinya.
Hafsah dake Tsaye kofar Bedroom dinsu Tana Cikin Barci Taji kukan Jidda da Sauri ta Farka ta Sauko Daga kan gadon ta Fito Falo Daidai Lokacin da Jidda ke Shigewa Dakinsu Amira Da mamaki ta kariso Kujeran da Abdullahi yake ta Zauna tana Fadin"Wai lafiya Abban Amira.? Meya faru naga Jidda na kuka..?
Kallonta yayi Lokaci Daya yana Taba Goshinta Jin Sanyi kalau yasa yayi ajiyar zuciya yana Fadin"Zazzabin ya sauka ko Hausina..?
Kai ta gyada mai tana Tsareshi Da manyan Idanuwanta Cikin Sanyin Murya tace"Meya faru..? Kansa ya Lamgwabar kan kafadarta Yana Fadin"Bafa wani abu bane...Iskanci ne kawai da samun waje wai kuka take saboda Nazifi yace yana Sonta ni kuma na Bashi,daga cewa Ranar lahadi zai zo suyi mgana Shine ta sakamin kuka Hardacemin bata isa Aure ba ga Mariya nan ba.? Ido Hafsah ta waro Tana Fadin"Wani Nazifin..?
Abdullahi ya Dago yana Fadin"Wanda kika sani Mijin Sakina.."Baki Hafsah ta Rike tana Fadin"Wai da gaske kake yace yana son Jidda.."? Mikewa Abdullahi yayi yana Fadin"Mun taba irin wannan wasan dake..? Har Baba wada ma yagamawa kuma ya nuna Murnan sa Sosai Yace baya bukatar jan Lokaci so ku Shirya nan da wata uku Insha Allah komai zai kamallah indai na isa da Jidda To na Bama Nazifi ita Amatsayin mata har Abada.."
Kai Hafsah ta Jinjina tana Fadin'Ikon Allah...Matar mutum kabarinsa..Allah ya sanya alheri..ya sakina taji..? Ko bai yagamata ba.? Hannu ya mikamata ta mikomai ya kamata tatashi yana Fadin"Kai mata abarku da gulma ni kuwa ina Ruwana..Ban sani ba ban kuma Tambayeshi ba kuma bai gayamin ba"Dariya ya kama Hafsah,Sai da ta Dara shima Abdullahim mirmishin yake Cikin Bedroom din ya maidata ya kwantar kana ya Fito waje ya kulle Kitchen ya dawo ya Kulle Kofar Falon ya Shiga Dakinsu Amira Har yanzu kuka Jidda Take Abun ma sai ya bashi Dariya Da mamaki yace"Lalle aiki ya sameki Cigaba da kuka...lalle kuwa in akan wannan mganar ne kukanki bazai kare ba.."Daga haka ya kashe musu Wutar Dakin ya Fito ya kashe na Falo ya koma Cikin Daki ya iske Hafsah ta Shiga tayi wanka ta Fito Shi ya taimaka mata ta Saka kayan Barci ya Dauketa Cak suka Dira kan gado tana Cikin Jikinsa Ya kamkameta suke ta Fira yana gayamata irin Farincikin Dayaji Lokacin da Nazifin ya nuna yana son Jidda Hafsah kuma tana bashi Wasu Shawarwarin yadda komai zai tafi Daidai.
*****
Washegari Koda Jidda tatashi Idanuwanta sun kumbura saboda kuka Hafsah kuma Taji Sauki Sosai kamar ba ita ba,Abdullahi kuwa ko ta kan Jidda bai bi yau din da wuri ya Fita su Amira ma mai mashin dinsu ya kira yazo ya kaisu Bayan Tafiyarsu ne Hafsah ta Zaunar da Jidda ta Dinga mata Fada tana nuna mata Riban yin Biyayyah ga na gaba Dakai ba laifi Jidda taji mganarta har ma ta Daina kukan Datake Misalin 12 tama Hafsah Sallama Tatafi bayan ta bata kudin Abun Hawa.
Haka ta komama Mama tana Kuka Mama na Lallashinta,Mariya da Auwal sai Ranar sukaji labari Auwal kuwa mamaki ya kamashi ganin Jidda na kukan bata son ya Nazifi Cikin Dage gira ya kalleta yana Fadin"Dillah mama ji wannan yarinya..? Don ma kin samu kinci Darajan ya Abdullahi ammh Me ya Nazifi zai ci Dake..? Kyan banza da ilimi matarsa bata Fiki ba Don ma kin samu zai Taimaka miki har wani Cewa kike baki sonsa..? A kyaleki sai ki kawo wanda ya Fishi Tunda kin zama wawiya.."Jin haka yasa ta kara saka kuka Sai Da mama ta tsawatar ma Auwal din kana Mariya kuwa Baki ta Rike tana Fadin"Lallema yarinyar nan..Kin samu Dami a akala har kina wani iskanci..? Wlh dama nice ke Danace nafi kowacce mace sa'ar samun Miji na nuna Sa"a yarda Maza ke tsada a wannan zamanin"
Wannan mganar tasa Jidda tace ma Mariya ta Bar mata taje ta Aureshi Mganar har ta kaisu ga Sa"in sa sai da mama ta Shiga mganar Jidda saboda kuka da Damuwa wayartama kasheta tayi Gabadaya Hajiya Sa"a tayi kiran Duniyan taji a kashe,gashi tana kaduna wajen kokarin Bude Shagunanta ,balle tazo gidan Taji lafiya ammh takira Lariya tace tazo Tagani ko Jiddan Tana lafiya.
*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*
*Shakira...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*024*
"Washegari ta kama Ranar Jumma'a ne Tun Safe sai ga Hajiya Lariya ta Dira Gidan Mama Lokacin Jidda na Cikin Dakinsu tana Kukanta data Farashi Tunda mganar Auranta da Nazifi ya Bullo Mama tayi Lallashin Duniyan nan taki Shuru da kukan Sai ta kyaleta, Mariya ma Tunda Sukayi wannan Tsiyar haka suka kwana ko Mgana basu yi ma juna ba, Ballatana Auwal Da Dama basu Shiri kamar Itace Sakonsa koda mariya basu Cika Fadan da suke da Jidda ba kodon Mariya ita bata da Rawan kai ne kamar Jidda...?
Tun Safe ko Tsakar gida bata Fito Ba Dama Tana Fashin Sallah,Mariya kuma Tun wajen 7am na Safe ta Fita Zuwa Asibiti Auwal kuma sai da 8am ta Buga kana ya Fita yana ma ta Sauri Suna da Test a makaranta Mama ce kadai acikin Gidan Duk da kukan Jiddan ya Dameta ammh bata da yarda Zatayi ko da Safen nan da sukayi mgana da Abdullahi ta Waya ya kara Jadaddamata mgana ba Fashi So in ma zata Daina kuka gwara ta Daina.
Bayan sun gaisa da Mama Hajiya lariya Ta Tambayi Jidda Mama Ta nuna mata Dakinsu tace ta Shiga Tana Ciki tana Tashi ta Shiga Jidda na ganinta tatashi ta Fada Jikinta ta saki kukanta Cikin Tashin Hankali Hajiya Lariya ta Riketa Tana Tambayanta lafiya..? Sai da suka zauna gefen gadonsu Ita Da mariya kana Cikin kuka Take labarta mata Abunda ke Faruwa Ido Hajiya lariya ta zaro Tana Fadin"Aure wani irin aure kuma..?
Jidda na Matsan Hawaye tace"Haka yace...Kuma wai ko zan yi kuka Jini Sai anyi..Ni fa bana Sonshi karatu nake so nayi Anty Lariya...."Kai Hajiya Lariya ta girgiza kafin tace"Ko ba karatu zaki yi ba wannan ai ba adalci bane Duka Duka nawa kike da za"a Hadaki da Wani Namiji namijin ma mai mata..? Yaushe zaki iya Zama da Kishiya kina yarinyarki Dake..?Toh ita karimar me tace..?
Jidda tace"Me kuwa..?Me Mama ta Isa tace in Ya Abdullahi ya yanke Hukunci ko Baba Wada Baya iya ketare mganarsa.."Mikewa Hajiya Lariya tayi Tana Fadin"Toh wlh bai isa ba wannan karon Mu zamu ketare..Wato Saboda Yaji Yaya tace zata karbeki ya Hana Shine ya Bullo da wannan mganar ko..?Wannan ai Rashin Adalci ne Taya zasu yanke wannan mganar mai muhimmanci batare da Tuntubar Ita yayan ba..? Gaskiya karima Ta bani mamaki.."
Da Sauri Jidda Ta mike Tana Fadin"A"a Anty bafa laifin Mama Bane..Yaya Abdullahi keda ikon Zartan da kowani Hukunci na Mama Bi ne kawai.."ko Sauraranta Hajiya Lariya batayi ba Ta Fice Daga Dakin Jidda Ta Rufa mata Baya Mama na Tsarkar Gida Taji Hajiya lariya a saman kanta Tana Fadin"Yanzu ke karima kinga Abunda kuka yanke yayi Daidai..?in ma Kuna Son ku nuna kunfimu iko da Jidda ne sai kuyi Adalci wajen Tuntubar ita mahaifiyar yarinyar ko bakomai Taci Darajan ta Tsugunna ta Haifeta...".
Mama Taji Hankalinta ya Tashi Daman Abunda Take Gudu kenan,Tasan karshenta ita za"a Dora ma Laifin komai Bataso Daga Bakin Jidda zasu Fara Jin mganar ba Taso ne Daga bakin Baba wada ko na Abdullahin Dama Tunda Taga zuwanta Tasan komai ya Lalace.
Cikin Sanyin Murya tace"Haba lariya taya zaki ce haka..? Kinga auran yazo ne ba"a gaya muku ba..? Dama ina da Niyyar kiran Ita Sa"an da kaina in gayamata komai sai gaki.."Wani Harara Hajiya Lariya ta mata kafin tace"Bawani Kina da Niyyar kiranta Haba karima in Jidda yarki ce zaki yarda Ya yanke mata wannan Hukuncin..? Wato Saboda ba yarki bace Shiysa baki da Tacewa ko..?
Idanuwan Mama suka kawo kwallah Cikin Rauni tace"Yanzu Lariya Dama kina Daukata a ba wacce ta Haifi Jidda ba..? Tafada kamar tayi Kuka Hajya Lariya Tataso mata Tana Fadin"Eh haka nace Domin na Tabbata in ke kika Haifi Jidda da Cikin ki Wlh bazaki yarda a batamata Rayuwa ba karamar yarinya da ita ku Rasa wanda zaku aura mata sai abokin yayanta kuma ma mai mata.."Ran Mama ya baci Kamar zatayi mgana sai ta Fasa Jidda Ranta bai mata Dadi ba ta kalli Mama kamar zatayi kuka Tana Fadin"Don Allah Mama kiyi Hakuri.."Ko kallonta Mama batayi ba Ta wuce Daki Tana Share kwallah.
Jidda Ta kalli Hajiya Lariya Tana Fadin"Haba Anty taya zaki ce ma Mama Haka..? Na taba Fadamuku Tun zama na da mama tataba nuna min wani Abun da zai saka naji ba ita ta Haifeni ba..? Wlh ya Abdullahi bani kadai ba,Dukkanmu yana nuna iko akanmu...hatta dasu Anty Zannira Dake gidajen Auransu.."Ko Sauraranta Hajiya Lariya batayi ba Ta Dauko Wayarta Dake Cikin Jaka tana Luluban layin Hajiya Sa"a Lokaci Daya Tana Fadin'"baki da wayau ne Jidda Shiyasa bazaki gane komai ba..Muda muka san zafinki Wlh bazamu bari hakan ta Faru ba Haka kurum a kashe miki Rayuwarki kina yarinyar ki Dake .."Ta Fada lokaci Daya tana Wucewa Fuu Cikin Fushi ta Fita ta bar Gidan Sai Duk Jidda bata ji Dadi ba Data koma Daki sai ta iske Mama na kuka Rumgumeta tayi Tana Fadin"Mama Don Allah ki Daina kuka..Har Abada kema kamar uwa kike gareni.."
Mama ta Share Hawayenta Tana kallon Jidda tace"Allah na gani..Tunda Mahaifinku ya karbo ku ya Damkamin ku Banta jin bani na Haifeku ba na Rike ku tsakani na ga Allah ina Jin kamar Dukkanku ni na Haifeku..ammh kalli Abunda Lariya tazo Tami...bakomai akwai Allah.."Ta Fada Tana kara goge kwallar Idanuwanta Itama Jidda sai kwallah da kuka Sai Mama ta Buge da Lallashinta Har sai da Taga ta saki Ranta kana.
Bangaran Hajiya lariya tana Fita ta Shiga Motarta ta bar anguwan Tun a Hanya tayi ta kiran Hajiya Sa"a bata samu ba sai da ta kai Gida kana ta sameta,Batayi kasa a gwiwa ba ta labarta mata Komai Hajiya Sa"a na Zaune ne sai Gata Tsaye Cikin wani yanayi Take Fadin'Lalle nema...Aikuwa wannan karon kowaye ya Tsaya mai karya yake ba wanda ya isa yayi ma y'ata aure yanzu Karatu zatayi.."
Hajiya Lariya ta karbe da cewa"Kema kya gani Yaya..Abunda yafi bani mamaki Karima ta kasa wani mgana sai cewa take ba Daga ita bane Laifin yayansu ne..'Hajiya Sa"a tace"Koma na waye su suka sani..Wannan karon ba wanda ya isa ya Hanani nuna ma Duniya Mahaifiyar jidda ce ni..Ina Tafe yau in nagama Abunda nake yi in kuma Ban gama ba sai Gobe...Zan zo ayi wacce za"ayi Lariya...Daga haka ta yanke Kiran Hajiya lariya na Fadin"Ina Bayanki Yaya.."
*****
Tsakanin Jidda da Mama ba wanda ya iya bada labarin zuwan Hajiya lariya da Abunda ya wa Kwana,Shuru sukayi da bakinsu,Ranar Bayan Abdullahi ya Taso Daga makaranta ya Shigo Gidan ammh bai Dade ba ya Fita Zuwa Wajen Baba wada suka Tattauna kan mganar Auran da Farko Abdullahi yace Sadakin Nazifi kadai yake Bukata Baba wada kuma yace Shine Waliyin Amarya Saboda haka Dole komai ma al"ada sai Nazifi ya Cikasa,da kansa ma ya Kirashi Sunyi mgana har ya Turo da kudin Goro da Dabino da Tabarma sauran kayan kuma Hade da Sadaki yace in zai Shigo Ranar lahadi in zai Shigo zai Zo Dashi Ba yadda Abdullahi ya iya Dole ya amince ammh yace ajirashi Zuwa gobe zai yi mgana da kannensa kuma yana so yaje Chan Danja ya sanar ma Goggo Habiba,saboda ko bakomai Kamar Uba take garesu Tunda ba wani wanda zasu nuna yau nasu na Bangaran Mahaifinsu Duk Allah ya karbi Rayuwankansu Ko Bata Shiga Cikin Sha"anin magabata ba Mijinta yana Shiga Tunda Shima kamar Uba suka Daukesa,Da haka suka Rabu da Baban Wada,kan sai Ranar lahadin in Nazifin yazo.
Washegari ta kama Asabar din Farkon mako Tun wajen Karfe 10am na Safe Mijin Zannira ya kawota Ita kadai yaran kuma chan ta barsu gidan iyayen mijin,Daga ita sai Maryam wacce suke Kira Ihsan,Har Ciki ya shigo ya gaida Mama kana ya wuce Samaru dama Daurin aure wani abokinsa akeyi Duk dashi ma yasa ya Dauko Zanniran suka Taho Tare,Da motar Haya zata Shiga,Tana zuwa ba Dadewa ta kira Subai tace mata gata ta kariso itama Bata Dauki Lokaci ba sai Gata,Mama Taji Dadi sai ina zata saka Dasu take,Gidan Daman babu Kowa sai Su Amira Suna makarantar Hadda Duk da bama Gidan suka kwana ba,sai dai Daga Haddar ne zasu Dawo ta Gidan Maman, Auwal ya Fita Shago Tun Safe Mariya kuma Tatafi Asibiti jidda ce kadai kuma Tun Safe tana kwance Bata Tashi ba.
Zannira ita ta kira Abdullahi tagayamai isowarsu yace su Jirashi Yana Cikin Makaranta Ammh yanzu in yagama Abunda zai yi zai kariso,Mama taso ta Fara kyankyasa musu Da suka Tambayi me ya Faru Jidda ke kwance Tataso kuma tana wani Tura baki,Sai mama tace Babu komai Bata jin Dadi ne Allah ya Sauwake kawai suka mata Suka Shiga Hiransu Cikin Hiran ne Ma Subai ke Fadin Daga gidan Mama Wajen Hafsah zata ta karisa wunin Ta Dubata Domin Jiya suna waya tace mata Bata Jin Dadi Jin Haka yasa Zanniran tace kafin Baban waled ya Dawo sai ta Bita Suje su Duba Hafsah din Har Mama tace bata sani ba Itama Jidda ke Fadamata Ammh Tace Da Sauki Abakin Abdullahi dai basu Ji ba.
Sai Wajen 12pm na Rana Abdullahi ya Shigo Gidan,Lokacin ma Sauri yake Zashi Danja Saboda haka Bayanin a gurguje yayi musu sai sukaji mganar kamar almara Subai Tayi murna Harda Rangada Guda,hararanta Abdullahi yayi yana Fadin"Ke miye haka..? Ke meyasa baki da Girma ne sai na Jikinki..??"Tana Dariya Tace"Murna Nake yaya..Abu namu mganin akwabemu Dama kwanaki Lokacin Haihuwar Anty Zannira da muka je gidan Wlh naji Ya bani Tsausayi har ina ce ma Hafsah da ina da yarinya Data isa Aure dana bashi Ashe Allah ya amsa Ban bashi yata ba zan Bashi kanwata kai Masha Allah Allah ya sanya alheri.."Gabadayansu suka amsa da Ameen Ameen Sauran Bayanan Mama yace Ta Fada musu,Shi zai wuce Danja Gidan Goggo Habiba Fatan Dawowa Lafiya sukayi mai ya Fito Tsakar Gidan nan Mama ke Tambayansa Ashe Hafsah bata ji Dadi ba ...?
Yana Duba agogon Fatan Dake Hannunsa yana Fadin"Eh Wlh Mama kinsan Halin Surukarki Sai a Hankali da Zazzabi take kwana Duk Dare da Zarar yammah tayi Shikenan in kuma gari ya waye sai Ki ganta kamar ba ita ba Kuma taki yarda muje asibiti sai dai ta Dinga Shan panadol."
Mama tace"Asha..Aikuwa gwara kuje asibiti adubata agani yafi ayi ta Shan mgani agida.."Yana Ficewa yake Fadin"Haka nake so ...Zuwa Ranar Monday kafin na Tafi aiki zan kaita mugani.."Fatan Allah ya sauwake Mama tayi Shi kuma ya amsa da Ameen ya Fice yana cema Mama sai ya Dawo tace adawo lafiya Su Zannira kuma na Ciki suna kara Tattaunawa Subai uwar Rawan Jiki,Kuwa harda Fadin anko kala Uku zasuyi kuma ya Abdullahi sai yayi Hakuri Domin zasu sha Bidi"a fa,Mama dai sai Dariya Take Jidda kuma na Jinsu taki mgana sai wani cin mgani Take Ganin Haka yasa Subai ta Fara Zolayanta da Amarya kawai sai ta saka musu kuka Cike da mamaki suke kallonta,tashi tayi ta Shige Cikin Dakinsu tana kuka Nan Mama ke Fada musu kukan Datake yi wai bataso ita karatu zatayi.
Subai ta saki wani wawan Tsaki Tana Fadin"Kar Allah yasa ta so mana Mama...Ke acikin abokan ya Abdullahi akwai wani Sa"anki ne..? Kindai ga Matarsa in auran kyau ne ko na ilimi bazaki Nuna mai ba gwara ma ki Saka Ranki Cikin salama mganar aure Babu Fashi Ehe.."Jin haka yasa Jidda ta kara Volume din kukanta Ita Abunda ke karamata Takaichi Shine Kowa ya tashi mgana sai yace wai Nazifi yafi karfinta toh Dama ita tace tana sone balle adameta da mgana,Ba wanda ya kara Bi ta kanta sukayi ta Hiransu Daga gani Abun yayi musu Dadi kwarai..
Wajen La"asar suka Tafi Gidan Hafsah suka isketa kwance ammh Dai taji Sauki Sun dan Juma suna ta Tattauna mganar Jidda sai da Mijin Zannira ya kira waya yace gashi gidan Mama kana suka Mata sallama suka Tafi,Daganan Subai bata koma Gidan Mama ba gida ta wuce Zannira ce ta Koma gidan Mama sukayi sallama Mama tace Su Shiga gidan Baba wada ta gaishesu Haka akayi ita da Mijinta suka Shiga Sun yi Sa'a Baba wadan na nan suka gaisheshi zannira ta Hada ta yi musu Allah Sanya alheri Bakin Inna Abu yaki Rufuwa 5k mijin Zannira ya bama Baba wada ya karba yana ta Godiya Gabda Mangariba suka Dauki Hanyar Kaduna,Mariya ana kiran Sallar mangariba ta Shigo Gidan Dayake Daga Asibitin bayan an tashi gidan wata kawarta ta wuce Sanin Halin Ya Abdullahi in ba da irin Haka ba Baka samun Zuwa ko"ina.
Tana Shigowa Mama tace yanzu Zannira suka Fita,Ta ciji yatsa Sosai Taso su Hadu,sai da sukayi Salla kana Mama ke Bata labarin Abunda ya Faru,Mariya tayi ta Ma Jidda Dariya afili ta Furtamata tana Tayata murnan Samun gwarzon miji irin Ya Nazifi Shi kuwa Auwal Daya Dawo Ana maida mgana ma Haushi Duk ya isheshi Ko mganar ma Bayaso yace a kyaleta mana ta kawo wanda yafi Ya Nazifin Tunda ita bata da Mutumci.
Bangaran Abdullahi kuwa ya isa Gidan Goggo Habiba ta Dinga ina Zata Sakashi Fura ta saka asiyomai ta Damamai,Da Zogala da kuli ta kwadantamai yaci yasha Furan ya Hada da kwadab zogalan ita ya Fara korama Bayanin Halin da ake Ciki Tayi Murna Sosai Domin Nazifi Mutum ne nagari,Tunda duk yawancin Zuwan Abdullahi Tare da Nazifin suke zuwa Gaskiya bashi da laifi,Goggo Habiba da kanta ta aika aka Kira megidan nata Alhaji mamuda,yazo sukayi mgana da Abdullahi Shima ya saka albarka yace Insha Allahu gobe zai zo ya samu Mallam wadan sai su Tattauna,Sai wajen karfe 5pm na yammah ya Baro Garin Saboda Bayaso yayi Dare Bisa Hanya gashi Saman Mashin ne.
****
*LAHADI..*
Lahadi karshen Sati kenan Abdullahi na kwance yana Barcin gajiya Misalin karfe 9am na Safe sai ga wayar Nazifi nan yake Gayamai Gashi Bisa Hanya zai Fara Zuwa Gida ne in sun gama Mgana dasu Baba zai karisa gidan Mama su gana da Jiddan.
Abdullahi yace"Ok..Mutumina sai ka iso Nima ina kwance ne ammh yanzu zan Tashi nayi wanka sai na Fito.."Daganan sukayi Sallama da sai sun Hadu.
Tashi yayi Ya Lalubo lambar Mama ya Kirata Bugu Daya ana Biyu ta Dauka suka gaisa Bayan ya Tambayeta ya Kiriniyar su Amira tace suna makaranta sai Itama ta Tambayeshi ya jikin Hafsah yace tana ma waje tana aiki Taji Sauki tace Allah kara lafiya ya gaisheta Daganan ya Ssnar da ita Zuwan Nazifi Saboda haka ta bama Jidda waya zai yi mgana da ita.
Ba Musu Mama ta Mikama Mariyar wayar tana Fadin"Mariya mikama Jidda waya Yayanku ne ke son zai yi mgana da ita.."Da Sauri Mariya Dake latsa wayarta ta ijiye Ta Karbi ta Mama ta Shiga Dakinsu Jidda na kwance kamar mai Barci nan kuwa ba Barci take ba,Mariya ta Daka mata Duka Tana Fadin"Sai ki tashi Ya Abdullahi zai yi mgana Dake ta waya.."
Dama Tana jinsu Tundaga Falo Cikin Tura baki ta mike tana Fadin"Shine kuma sai kin Dake ni..? Wayar mariya ta sakar mata kan Jikinta Tana Fadin"Bani Dukanki..? Kaji yar rainin Wayau..gashi dai yana dai jinki.."Daga haka ta Fice Daga Dakin ta barta Cikin Mutuwar Jiki ta Daga Wayar ta kara kunni Lokaci Daya tana Sallama,Ko Sallamarta bai amsa yace"Ke Jidda kina jina ko..?
Tace"Eh ina ji.."Cikin Kakkausan Murya yace"Ki Shirya yanzu Nazifi zai kariso...Ki gyara Dakin Auwal ki Saukeshi achan kinji ko..? Cikin Hadiye Miyau mai Zafi tace"Tom yaya.."Shuru tayi Shi kuma yace"Kun karbo Nama yau..? Tace bata sani ba Ajiyar zuciya yayi yana Fadin"Kaima Mama wayar na mata mgana .."Mikewa tayi Cikin Kasala ta Fita Zuwa Falo Mamar bata nan tana Tsakar Fita tayi ta mika mata Wayar tana Fadin"Gashi zai miki mgana.
"
Tana Bata wayar ta Juya ta koma Daki Mama ta kara akunni Tana Fadin"Abdullahi Mgana kake..? Da sauri yace"Eh Mama..ki saka Auwal ya karbo muku Nama mai Dan yawa ko mariya sai ta kama mata Tayi abinci haka,Duk da ba lalle bane yaci ammh akaron Farko dai ta karramashi,In da kudi a Hannunki ki Bata ta Siyo Ruwa da lemo in nazo sai na maida Miki Mama.."Kai Mama ta gyada Tana Fadin"Shikenan.."
Daga Haka suka yanke Kiran,Nan Mama ta Shiga Daki Tana gayama Mariya,Abunda Abdullahi yace Mariya ta kama Baki Tana Fadin"Au shine Dalilin Da naga Bakinta ya kusa kaiwa kofar Kibo .?Mama tace"Shine.."Tafada tana Dariya Suna Cikin haka sai ga Auwal ya Shigo Mama ta gayamai Sakon ya Abdullahi yace bari yayi wanka sai da yayi Wanka kana ya Fita Bayan ya karbi 1k hannun Mama ya Siyo Maltina guda Biyu sai Fanta Guda Daya da Ruwan gora sai Naman daya karbo Dayake suna da komai na kayan abinci yana Dawowa ya Fita Bayan ya barma Mariya makullin Dakinsa.
Mariya Bata bi ta kan Jidda ba Tatashi ta Fara gyara Dakin Auwal din ta Share Tsaf,tayi Mopping dinshi,Ta saka Turaran Wuta ta Rufo kana ta koma Barayin Girki,Jalop din Shinkafa ta Dora,Dama suna da Kabeji da Caras,sai Green Beans,Risho ta kunna ta Dora tafashen Naman gas kuma ta Dora Shinkafa su Abdullahi ya Siya musu ganin Gidan ba yara sai dai in sunzo.
Nazifi kuwa Koda 10am tayi tamai agidansu,Booth dinsa Shake da kwalayen Minti da Cingam,Yara suka Dinga kwasa suna Shiga Dashi Cikin gidan Baba waada,Auwal na kofar gidansu Ya Hangi Zuwa Nazifin wanda yaci wani Danyan Shadda Mai kalan Sararin samaniya Dinkin zamani ya saka wata Hula zanna Bukar kafarsa sanye da wani Takalmin sawu Ciki na Fata,Haka Tsiyayan Hannunsa Dauke da Agogon Fata na Kamfanin Rado iya Haduwa ya Hadu Domin in kamai kallo Daya sai ka kara Auwal har Kofar gidan Baba wada yazo suka gaisa kana ya wuce Shago.
Nazifi ya Shiga Sun gaisa da Baba wada da Inna Abu kana ya Fito da Kudi Dubu dari da Hamsin yace Dubu Dari Sadakin Jidda Dubu Hamsin kudin nagani ina so da kuma Gaisuwan iyaye Baba wada ya karba yana ta Sakamai albarka,Saboda zumudi ko Tsayawa karyawa bai yi agida ba Koda yake ina yaga Abun karyawan har ya hutu yar mulkin tana kwance,Dama Jiya ta Dawo Daga Abuja Ta kwanta sai barci take nan Da yayi mgana sai tace Barcin gajiya ne Shiyasa ma Tuni ya Fita Batunta,tana kwance yazo yace mata zashi Zaria adawo lafiyan ma Ciki Ciki ta Furtamai bai Damu ba Ya Fice Domin yana ji acikin Ransa komai ya kusa zama Tarihi.
Dumaman Tuwon Masara Miyar kukan da Inna Abu tayi yaci yasha Ruwa,Kana ya Kira Abdullahi yace gashi nan ya iso Abdullahi yace shima gashi nan zuwa Domin Yanzu suka gama Mgana da mijin Goggi Habiba ya kariso yana gidan mama,Da haka suka yanke Kiran Minti Talatin Yayi yawa sai ga Abdullahi ya iso Shida Alhaji mamuda sai da ya Shiga Gidan Mama suka gaisa ya iske Har Mariya ta kusa gama Girki Jidda kuma na Ciki kwance Aikuwa mariya tana gayamai ya Shiga ya Fattakota Dole ta Fito ta Shiga wanka tana Sharan kwallah Mama kuwa na Tsakar gida tana Bude sakon da Goggo Habiba ta aiko mata dashi ita da Inna Abu sako ne irin na kauye irinsu kuka,kubewa,Garin alabo,Zogala da Sauransu.
Atsakar gidan Baba wada suka yada zango Bayan Inna Abu ta Shimfida musu Babbar Tabarma,bayan gaishe gaishe sai kuma mganar Hadin Aure ya Biyo baya,Baba wada yace Shine Waliyin Amarya sai dai in Alhaji mamuda ya zama waliyin ango,ana ta Dariya Alhaji mamuda yace"Yaji Bakomai ai daman Abdullahi da Nazifi sune ya"yansa.."Nan Baba wada ya gabatar da Sakon da Nazifi yazo Dashi da kudin daya bashi da kuma Su Tabarmu da goro,Shi kuma Alhaji mamudan ya maidama Baba wada amatsayin suna neman yardasu agame da Auran Jidda da Nazifi Baba wada yace an basu nan aka sanya Lokaci nan da wata uku masu Zuwa abun yayi ma kowa Farinciki da Burgewa,Baba wada kamar bakinsa ya yage saboda Farinciki Basu bar gidan ba sai da suka ci Danwaken da Inna Abu tayi musu Lokacin ana Kiran Sallah suka Dunguma zuwa Masallaci Bayan sun Fito Abdullahi ya kalli Nazifi yana Fadin"To kai Mutumina sai munyi waya kenan zan karisa Gra wajen masu ginin nan na gani na kwana Biyu ban je ba..
Nazifi yana Shafa Kansa yace"Ok..Ammh ba Rakiya abokina..'?Hararan wasa Abdullahi yayi mai yana Fadin"A"a kai ai dan gida ne...kuma zaka Neman Yakin aure ne Adawo lafiya.."Ba yadda Nazifi bai yi kan Abdullahi ya Rakashi ammh yaki,Nan ya bar Alhaji mamuda wajen Baba wada Kofar gida suna Hira sai anjuma zai wuce 5k Abdullahi ya bashi yace yayi na Mota ya Hau mashin Dinsa Zuwa Gra.
Nazifi kuwa Kunya kuma Duk sai ta kamashi gashi kofar gidan ammh ya kasa Shiga,Sai da yaga ba Sarki sai Allah kana yayi Kundubala yashiga Cikin Gidan nasu Abdullahi Lokaci Daya yana Sallama Cikin Muryansa mai Amo da Sauti..
*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*
*Anitha...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*025*
"Lokacin Da yayi Sallama babu Kowa a Tsakar gidan Dukkansu Suna Cikin Daki,Shiyasa basu Ji ba,Jin ba"a amsa ba yasa ya kara Wata Sallamar Daidai lokacin da mariya ta Fito Daga Dakin Mama sai Tajiyo Sallama ta amsa Lokaci Daya tana Bada izinin Shigowa Duk da Dama Ranta ya bata Yaya Nazifin ne.
Cikin Takun natsuwa irin na masu Ilimi ya Shigo Gidan,Mariya na ganinshi ta gaisheshi Cike da girmamawa Cikin Fara"a kadan ya amsa yana Tambayanta karatu tace Alhamdulillah,kai tsaye ya kalleta Yana Fadin"Mama na Ciki..?
Kafin ma Mariyan ta bashi Amsa Mama Dake Cikin Tace"Eh ina Ciki Nazifi naji Shigowarka Lokacin Ina Sallah ne Shigo Daga Ciki mana ka Tsaya anan kamar bako.."Ta Fada Tana Daga Cikin Daki Jin Haka yasa ya Sabule Takalmi sawu Cikinsa yayi Sallama Mama ta amsa ya Shiga Nesa da ita ya Durkusa yana Gaisheta ta amsa Tana Fadin"Haba Dai Nazifi karmuyi Haka Dakai mana..? Don Allah ka Tashi ka koma Bisa kujera Don Allah.."
Jin ta Saka Roko da Allah yasa ya Tashi ya Dofana Kan kujeran ammh kansa na kasa haka kurun yake ji wata kunyar mama Wacce bai Taba ji ba,Tambayansa Iyali Mama tayi yace suna Lafiya Daganan kuma sai Falon ya Dau Shuru Mariya Mama ta kwalama Kira ta amsa sai gashi ta Shigo Kallonta Tayi Tana Fadin"Kai shi Dakin Auwal Mariya kizo ki kimai Ruwa da Abunsha Tunda ita yar mulki Tana Ciki kuma Taji Shigowarsa ammh bata Fito ba.."
Da To Mariya,Mama ta kalli Nazifi Tana Fadin"Nazifi kuje Dakin Auwal kafin Jiddan tazo..Sai fa kayi Hakuri da Halinta kasan ta yarinya ce akwai kuruciya akanta Da kuma Rawar kai kamar Uba kake gareta in tayi wani abu ba Daidai kai mai sakata a Hanya ne har zuwa ta gane Watarana.."Kansa na Kasa ya Murmusa yana Fadin"Insha Allahu Mama..Nagode Allah saka da alheri ya Jikan magabata Ameen.."
Mama tace"Ameen..Bakomai Daga kai da Jidda da Abdullahi Duka Dayane awajena...Tun da naji Abun alherinan nake Murna Allah yasa ace gwara da akayi Allah sa kuma muna da Rabon ganin Lokacin.."Kunya Duk sai ta kamasa ya Sunkuyar da kansa yana amsawa mama da Ameen kafin ya mike ya mata Sallama ya Fito Tsakar gidan ya Saka Takalminsa ya wuce Dakin Auwal Tunda ai gidan ba bakonsa bane.
Ya Iske Mariya aciki Tana ta Jeramai kololin abinci,Saman Karamar katifar Auwal ya yada Zango Lokaci Daya yana Bin karamin Dakin da kallo Duk da ba wasu kaya Daga katifa sai Kayansa sai Cafet sai Littafan karatu da akwatin kayansa Dakin Dai Tsaf dashi Sai kamshi Turare yake Tashi,Mariya ya kallah yana Fadin"Sannu da aiki Mariya..yau ba Zuwa asibitin ne..?
Tana Shirin Fita tace"Laa..Ba komai Ya Nazifi..Eh yau bazani ba sai gobe.."Kai ya gyada yana Fadin"Olrigt Allah ya kaimu..."Yafada Lokaci Daya yana Fito Da wayarsa Daga aljihu,Mariya kuma ta Fice ta barshi Tana Shiga Dakin Mama ta isketa tana ta Fama da Jidda kan ta Fita Taje ta samu Nazifin ammh Taki ta tsaya sai wani Bata rai Take,Duk da Daman wajen kwalliyama Tsiya suka Tafka da mariya ita kuma ta nace sai ta mata kwalliyar ta sakata ta Shirya Cikin wani Ubansu Leshi mai kyau da yarari da Tsada Cikin Wanda Hajiya Sa"a tayi Mata ne,Dinkin Riga da Sikat ne kayan sun kamata sun Fitar mata da Duka Suran Jikinta Kanta kuma wani Irin Dauri ne mai kyau Mariya tayi mata,ta mata Feshin Turare.
Wani Takalmi mai Tsini Mariya ta Dauko mata tace ta saka Sai Mayafi Yana da girma ammh ba Sosai ba sai dai kuma Shara Shara ne ana iya ganin Komai na Kayan Jikinta,Ganin haka yasa Mariya ta karisa ga Jiddan Ta Riko Duka Hannayenta Tana Fadin"Haba yar kanwata..Miye haka kinga yadda kikayi kyau Shine xaki bata kwalliyanki..! Ko bakomai ki Je kinga dai abokin Ya Abdullahi ne kuma bazai Taba Jin Dadi ba in aka wulakantashi Plz kije ku gaisa sai ki Dawo.."Tafada Cikin karya Wuya Kallonta Jidda Tayi Tana Tura baki kafin tace"Naji zan je..Ammh muna gaisawa zan dawo Abuna.."
Mariya na Danne Dariyanta Tace"Eh naji..Da kun gama gaisawa ki Fito abunki ammh Don Allah ki Zubamai abinci kinji ko Jidda..? Kai ta gyada Cikin Cinmgani kafin tace,"Shikenan..Ammh Da ban yi Niyya ba.."Mariya tace"Yauwa..Nagode ko kefa..Muje na Rakaki har Kofar Dakin ma..."Daga haka ta Rike Hannunta Suka Fice Daga Falon Mama tarakasu da kallo Tana Mirmishi acikin Ranta Kuma Tana Fatan Allah ya Tabbatar da wannan Abun..Da sai Tafi kowa Jin Dadi.
Har kofar dakin Auwal Mariya ta Rakata kana ta Saki Hannunta Tana Fadin"Oya..Sai kin Fito ko..?Kai Jidda ta Daga mata,Mariya ta Juya Tatafi Tana kashe mata Ido Daya,Bayan Tafiyar Mariya sai Jidda ta kasa Shiga Domin Tana Jin Muryan Nazifi yana mgana ta Waya Gyara ma Tsayuwarta Tayi Tana Tunanin yadda za"ayi ta Shiga Ba zato ba tsammani Taga kawai an yaye labulen Dakin Dago Idanuwanta tayi Karaf suka Hada 4eyes dashi yana Tsaye yana kare mata kallo Tunda Ga sama Har kasa kafin ya Dire kallonsa nashi kan Fuskarta Cikin wani Yanayi na Bugun Zuciya wanda baisan Dalili ba.
Ita kanta Jiddan Zuciyarta ne ke Bugawa Fat..!Fat..! Kamar wacce Tayi Gudun Tsere,Ga Jikinta ya Fara rawa Domin idanuwan Nazifi akanta suna sakata taji kamar Tana Jin sanyi kanta ta maida kasa ta Fara waasa da adon gyalenta Taki Cemai komai Shi kuma sai kawai Daya gama Morema kallonta ya Kada kai yana Fadin"Ki koma Tunda bazaki Shigo ba..Bazan matsama miki ba Jidda sam.."Yafada Lokaci Daya yana Sakin Labulen Dakin ya koma Ciki ya barta nan Tsaye.
Sai kuma Taji bata kyauta ba ko bakomai Ya Nazifi bai Chanchanci wannan Tozarcin Daga gareta ba, Sai kawai tayi Kudunbala Ta yaye Laluben ta Shiga da Siririyar sallamarta Yana zaune gefen katifa ya Tankwashe kafafunsa yana ta Danne Danne acikin Wayarsa ya amsa mata Sallaman batare Daya Dago ma ya kalleta ba,Ganin haka sai ta Duka ta Cire Takalminta Cikin Sanda ta kariso Cikin Dakin Nesa Dashi ta Zauna Kanta na kasa Tana Fadin"Ina yini Ya Nazifi..!!"
Kamar bai jita ba yayi mata sai kuma Taji bata ji Dadi ba Idanuwanta suka Ciko da kwallah ta Tura baki ita kadai Ta kauda kai bata kara mgana ba, Shi ma kuma yana nunamata yana gaba da ita sai yayi kamar Babu Mutum mai arai awajen Cigaba kawai yayi da Taba wayarsa,da Farko taso Tatashi Tayi Ficewarta ne sai wata Zuciya tace Kin Tanadi amsan da zaki bama ya Abdullahi in ya Ritsaki..?
Tuna Haka yasa Ta kauda wannan Tunanin Fushinta ya Sauka Ta Dago Gefen idonta Tana Satar kallonsa Tagama Hankalinsa na kan wayarsa bai ma Kallon Barayinta,Waro ido Tayi kai Tsaye Tana karemai kallo Acikim Ranta tace"He is Cute,and Simple ba kamar ya Abdullahi ba."Ta fada Lokaci Daya Tana sakin Mirmishi.
"Kingama kallon nawa..? Me kuma ya baki Dariya atare dani.? Kawai Taji ya jefomata Tambaya kai Tsaye Idanuwanta suka Fito waje Cikin mamakin Dama yana kallonta ne,Sai ta daburbuce ta Sunne kai Tana Tunanin amsan da zata Bashi ba abun tace karya bane ya riga kamata ganin Tayi Shuru yasa ya Dago yana kallonta kai Tsaye yace"Umh..Dake fa nake mgana Hauwa"u.."
Yafada Cikin Muryan kamar ta Bawa da Uban gidansa,Jin haka yasa tace"..Ni...Ni ba kai nake ma Dariya ba.."Kai tsaye yake kallonta yace"Bani kike ma Dariya ba wa kike mawa..? Naga Dagani sai ke acikin Dakin nan ko.? Uhm...Zo ki zauna nan Sai ki Fadamin Abunda ya baki Dariya ajikina.."Ya Fada yana nuna Mata gefensa..
Ido ta Zaro Tana kallonsa Shi kuma sai ya Hade Rai yana Fadin'Eh...Ki zo nan nace.."Ya Fada irin so Commondely haka Marairaicemai Tayi Tana Fadin"Don Allah kayi Hakuri ya Nazifi...Nifa ba kai nake ma Dariya ba.."
Tafada tana wani karya wuya wanda Ita kanta Batama san Tayi ba Wani iri yaji Kawai Shima sai ya Biye mata ya karya Wuya yana Fadin"Naki na Hakura sai kinzo nan ki zaunan kin gayamin Abunda kike ma Dariya..?ko kinga kaina da Furfura ne Shine kike Dariya za"a Hadaki da Tsoho ko..?.
Yafada Cikin Sigar Zolaya Jin haka yasa ta Bude baki Tana Fadin"Laaa..Kai ne Tsoho..? Kai ya Gyada mata yana Fadin"Eh mana..Naga kamar nayi miki Tsufa Shiyasa kike min Dariya ."Baki ta kama Kafin tace"Nifa ba kai nake ma Dariya ba Kuma injiwa yace kai Tsoho ne..?
Kai Tsaye yace mata'"Inji Amaryata Jidda mana.."Yafada yana Kafeta da ito Kunya ya kamata ta Sadda kai Tana Mirmishi Gefensa ya Nuna yana Fadin"Nace ki Dawo nan ko..? Ko ni kike son na ijiye Girman na Biyoki..?Da sauri ta girgiza kai Mirmishi yayi yana Fadin"Ahto..Tunda naga kamar haka kike so..
Cikin kunya tace"Ni fa bance ba.."Tafada Lokaci Tana zama Nesa Dashi,Kallonta yayi kai tsaye Shima yana gyara zama Yana Fuskanta yace"Uhm ina jinki Fadamin me kike ma Dariya..'? Kanta na kasa tace"Allah ni ba kai nake ma Dariya ba.."Rausayar Dakai yayi yana Fadin"Toh naji bani kike ma Dariya ba..? Dariyar tame cece..? kamar bazatayi mgana ba Sai chan kuma tace"Kawai nace ne U are so Simple ba kamar ya Abdullahi ba.."
Dariya ta kamasa sai da ya Dara kafin yace"Who tell u ina da Sauki akan Abdullahi..? Baki Tunanin sai Hali yazo Daya ake abota.."?Dagowa tayi tana kallonsa karaf suka Hado Ido Kallon Juna sukayi na wani Lokaci kafin Jidda Ta Dauke kanta,Shi kuma sai da ya kara Moran ma kallonta kana yace"Umh kinyi Shuru.."Kai tsaye tace"Haka kurum..Nake ganin kuna da Bambamci.."Mirmishi ya saki Lokaci Daya yana ijiye wayarsa a gefenta kana yace"Hmm..Ana ki ganin kenan.Eh bazan ce miki bamu da bambamci ba yes muna Dashi..Wasu Hallayar tamu Tasha Bambam kamar wani Lokacin Yayanku yafini Zuciya da Saurin Fushi.."Yafada yana kallonta Kai ta gyada batace komai ba kafin kai tsaye yacigaba da Fadin"Jidda as u know bari mu tafi kai Tsaye Nasan dai zuwa yanzu kinsan Abunda ke Tsakanina Dake ko..?
Haka kurum Taji ta Natsu tana Sauraransa ganin haka yasa ya Cigaba da Fadin"To Da farko dai Kisanni kinsan Gidanmu da iyayena da kannina Sunana Kamar yadda kika Nazifi Wada nibamai kudi bane ammh ina da Rufin Asiri Ina aiki a hukumar nepa Dake kaduna Da Albashina wanda Bazan Raina ba kana kuma Ina Da matar Aure Daya,haihuwarce Allah bai kawo ba Ina da gidana a kaduna sai kuma wani Danake ginawa anan zaria,Kana kuma ayanzu haka na koma Kasu ina so na Hada Masters dina,Kinji kadan Daga Cikin Wanene Nazifi Wada..".
Kanta Na kasa tace"Allah ya taimaka.."Yace Ameen kana ya Zarce da Fadin"Kinsan meyasa nake miki wannan bayanin..? Bai bata Zarafin mgana ba yacigaba da Fadin"Saboda muna Kokarin zama karkashin Ihuwa Daya Jidda amatsayin mata da Miji..Kinga ya kamata all Ni kisanni nima na san komai naki Saboda muna Fatan zama ne tsakaninmu na Muddin Rai Duk da bansani ba ko kin karbeni na zama abokin Rayuwarki ko nayi miki Tsufa ko kuma saboda ina da da Mata ba ki sona.."!
Baki ta Bude Kafin ta Rufe Tana Fadin"Ni ban ce haka bafa.."Mirmshi yayi yarintar ta na Burgeshi yace"Naji baki ce ba..Ammh ki Dago kanki ki kalleni shin zaki iya maneji dani a matsayin Mijinki? Shin zaki yarda Na zama abokin Sirrinki na Har Abada..?Zaki yarda ki ZAMA mace mafi Daraja da kima acikin Idanuwana.."!
Yafada yana kafeta da mayen kallonsa Duk sai Jikinta yayi sanyi Tana jin wani yanayi atare da ita,Kanta ta Sunkuyar tana ji har acikin Ranta Ya Nazifi bai da makusa,Ita din wacece da zataje bai mata ba amatsayin miji?,Kafin Shigowarta Dakin Bata taba Zaton Haka ba sai gashi bayan Shigowarta komai ya Chanza Ji take in yana mgana kamar Muryansa tana Tsulamata Bulala agadon bayanta ganin Tayi Shuru yasa ya Sauke ajiyar zuciya yana Fadin"Baki karbeni ba ko jidda..?
Yafada kamar zai yi kuka da Sauri ta Dago Tana Fadin"A..a...Na amince ammh.."Da sauri ya tari Numfashinta yana Fadin"Ammh me Jidda..?look ki Fadamin Duk Abunda ke Ranki Ni dake mun zama Daya In ma baki sani ba bari na gayamiki Tuni Waliyanki Sun bani ke Har sadakinki na Biya so ina nace ina da iko Dake kamar banyi karya ba ko..?
Ido Ta zaro ta kallonsa Mirmishi yayi yana Fadin"Yes..Duk da nasan baki sani ba..Ammh Dalilin Shigowata garin yau Dalili biyu ne na Farko gabatar da saka Ranarmu na Biyu na ganki na kuma Baki Hakkinki Agame da Zabin mijin da kike so.."Jikinta ya kara yin sanyi An Biya Sadakinta... ? Toh Tunda an Biya ai bata da ta cewa Ganin Tayi Shuru ne yasa yace"Uhm ina jinki..? Ko kunyana ake ji..?
Rufe Fuskarta Tayi da Tafukan Hannayenta tana Fadin"Eh..Ka bari na gayamaka ta waya.."Wayarsa ya Tura mata yana Fadin"To sakamin Lambarki in na koma gida sai na Kira ki muyi mgana Duk da Zuwa Sati mai zuwa gaskiya wata wayar zan kawo miki.."Cike Da mamaki tace"Saboda mene..?
Wuya ya karya yana Fadin"Cos Jidda is Belong to me..Only me.."Yadda ya Fadi mganar ne sai da Taji Tsigan Jikinta ya Tashi Ta Shagwabe Fuska tana Fadin"Mommy fa ta Siyamin wayar..Shine zaka ce zaka kwace.."Ta fada Tana Tura baki,Shima Bakin ya Rike yana Fadin"Au bansani ba...Kinga am Sorry..Bazan karba ba sai kawai na Sauya miki Layi hakan yayi..?
Hararansa Tayi Tana Tura Dariyan Nishadi yayi yana Fadin"Kaina Bisa wuya nidai a sakamin Lambar..Sai abani Ruwa nasha Madam duk da sai da na Roka.."Kunya ya kamata ta Sadda kai kawai kasa tana yarDariya Shi kuma yana kallonta Wayar ta Dauka Taga da Password ta gayamai kai Tsaye ya gayamata ta Bude ta sakamai lambar Data bashi sai yaki karba yace mata"Kiyi Saving mana."Kallonsa Tayi tana Fadin"Kai..ni kuma..?Wani Suna zan saka maka.."
Sai da ya lulubi kwanyan idanuwanta kana yace"Habibty...."Wani iri Taji kai Tsaye ta narkar da Idanuwansa Cikin Nashi Shima kawai sai ya wani Lumshe ido kamar zai kwanto mata sai yayi baya da kanshi Hannunta na Rawa tayi Saving bayan ta saka Suna ta mikamai wayarsa ya karba yana Binta da wani mayen kallo Abinci ta Fara zubamai kana ta Zubamai Ruwa da Kunun ayan Ta Dago Tana Fadin"Don Allah Ya Nazifi kayi Hakuri.."
Yana Kishingide yace"Hakurin me... ? Abincin Ta nuna mai tana wani Shagwabe Fuska Mirmishi yayi kafin yace"Karki damu Madam..Watarana ma ke da kanki zaki Cinyar dani ko..? Sunne kai Tayi Tana Dariya Saukowa yayi kasa ya tankwashe kafa ya Fara Cin Abinci Jefe yana Jefama Jidda Tambaya tana Bashi amsa kafin kace me suna Hira Sai gashi ya Tada Filet din Abinci Jidda ya kallah yana Fadin"Kai..Duk ni na Cinye wai..?
Dariya ta kama Jidda ta Saki Jiki Tanayi Shima yana Tayata,Tashi yayi ya koma Bisa katifar yasata matsar da kayan abinci,Kana yace ta Dawo ta zauna Tun Jidda na nokewa har Daga karshe ta saki Da Nazifi yana ta bata labarai Na makaranta da yadda Rayuwar makaranta yake da kuma na ma"aikatansu,Sai ga Jidda ta Zage suna ta Shan Hira Cikin Love,Basu ankara ba sukaji Kiran Sallar La"asar Nazifi ya saki Baki yana Duba agogon Fatan Dake hannunsa kafin yace"Baby La"sarfa nake gani.."Kai ta kauda Tana Mirmishi mikewa yayi a kasalance yana Fadin"Bari naje nayi sallah nazo na tafi..Naga alaman in na Biye miki yau kwanan zaria zan yi ko..?
Mikewa tayi Tana gyara gyalanta Tana Fadin"Nifa ba Ruwana.."Nazifi yace"Naji ba Ruwanki..Ni da Ruwana.."Yafada yana kallonta Tare suka Fito Yace Taje Cikin Gida ta Zubomai Ruwa abuta Haka taje Ta ga Mariya atsakar gida tana ganinta ta Shiga Mata Dariya Ita kuma Jidda tayi mata Banza,Ta dibi Ruwan ta kai mai nan kofar dakin Auwal din yayi alwalan tana Tsaye kana ya mika mata,ta koma Ciki Shi kuma ya wuce masallaci.
Koda ta koma Duk Dariyan Mariya Bata kulata ba Mama ce tace"Autana Ya tafi ne yayan naki.?Tana Tura baki tace"A"a sai ya Dawo Sallah.."Daga haka ta Shige Daki kana ta Fito itama alwalan tayi tazo tayi sallah Sai ga Su Jidda harda kara Shafa Hoda ana gyaran Fuska Mariya ta Shigo ta ganta sai tayi kamar bata ganta ba,Tana gyara zaman mayafinta taji karan wayarta Data barta nan kan gado tana Daukowa Taga Bakuwar lambace ta gane Shine tana Dagawa yace ta Fito yana Jiranta.
Data koma sallama kawai sukayi Ya Bata 10k,kana ya bata 2k ta kaima Mariya da Farko taki amsa sai da ya kalleta yana Fadin"Miye haka..? In Abdullahi yayi miki kyauta Haka kike mai..?
Jin haka yasa tasa Hannu Bibbiyu ta karba tana mai godiya Tasata yayi ta Rakashi yama Mama sallama ya bata 5k ta karba tanata sakamai albarka Jidda ma Ta ba Mariya nata itama tana Godiya Sallama sukayi da Mama ya Fito Har Kofar Dakin Auwal Jidda Ta rakashi kana yace ta koma Daganan in ya isa gida zai Kirata sai ga Jidda kamar zatayi Kuka da zai Tafi,Ta Dade tsaye nan bayan Tafiyarshi kafin ta koma Cikin Gida.
Yana Fita gida ya koma ya ma Su Baba wada Sallama ya basu Abunda zai basu ya wuce Wajen Biyar ya Dauki Hanyar Kaduna Zuciyarsa Cike da Farincikin samun Hadin kan Jidda.
Baba wada ne ya Shigo Da Daddare yama Mama Bayanin komai da kuma sanya Lokacin Auran Mama tayi ta saka albarka Koda Baba wada ya Kira Jidda ya gayamata bataji wani iri ba,Tunda Shi Nazifin ya gayamata bata dai Nuna ba,Baba wada yaFita ba Dadewa sai ga Kiran Nazifin Sai ga Su Jidda an haye gado ana kashe Murya mariya dai na gefe Tana ganin Abun mamaki da Auwal ya Dawo Falon Mama suka Dawo mariya na Radamai Abun mamakin Data gani yana cin Abinci yana Fadin"Hegiya jidda...Taga Salon manya.. Wanda ba irin na yara ba..Magulmaciya.."
Yafada yana Dariya,sai da Mama ta taka musu burki kana Suka yi Shuru ita ko uwar gayyar ma Bata sani ba Tana Cikin Daki Suna waya sai mai Shagwaba take yana Biye ma Tabaran Shagwabanta da kuma Yarintar,Dama yana komawa wanka kawai yayi ,sai sallah ya koma ya kwanta abinci kuma Tun Abincin dayaci azaria Cikinsa ya Cika koda ya Dawo wai Sakina Indomie ta Dafa don ta Raina ma kanta wayau Barinmata yayi ko Kallo ma bata ishesa ba Tunda ya Shige Cikin Dakinsa bata kara ganinsa ba Shiyasa ya samu dama Yana Biyema Kwailar Amaryansa Yana sata sakin jiki Dashi kuma ba laifi ta Fara sakin Jikin Dashi...
*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*
*Janaftyshakira...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*026*
""Adaran Hira Tsakanin Nazifi da Jidda Tayi Tsawo sosai,Sai Biyema Tabaran Jidda yake da Shagwabarta saboda yana so ta saki Jiki Dashi Sosai Kuma ta Fara Sakin,Sai gashi Dukkansu Suna Jin Dadin Hirar.
Cikin Hirar ne Nazifi ke Tambayata wata mgana ne tace zata gayamai Ta waya..? Cikin Sangarta tasakomai mganar Cigaban karatunta,Domin har Ga Allah taji Acikin Ranta zata iya Auran Ya Nazifi mtsalanta Daya Shine karya Hanata Cigaba da karatunta Shine Tashin Hankalinta,Shi kuma yace mata ta bari sai anyi Auran in yaga Yadda Take bashi kulawa Sosai kuma Ta Dauki alkawarin komai bazai Sauya ba nadaga kulawar Datake bashi,Toh Zatayi Ilimi har sai da kanta Tace tagaji Jin haka yasa ta Dauki Murna Sosai Tana mai Godiya Basusan iya Lokacin da suka Dauka Suna waya ba Har mariya Datake Duba littafanta Ta Gaji Ta kwanta ta bar jidda sai Araund karfe 2pm na Dare sukayi Sallama kowa ya kwanta Ransa Cike da wani Annuri wanda ke Fitowa Daga kasan Ransu.
Washegari Kuwa Tun Wajen karfe 10am na safe sai ga Hajiya Lariya da Hajiya Sa"a ransu a matukar bace Alokacin gidan Babu Kowa Auwal ya Tafi makaranta mariya kuma Tatafi asibiti Mama ce kadai atsakar Gida Jidda Tana Falon Mama Tana Goge kayanta Suka Shigo ko karba Sannu da zuwan da Mama ke musu basu yi ba,Hajiya Sa"a ta Fara gaggayama Mama mgana Son Ranta Tana Fadin Don ba Ita Ta Haifi Jidda ba Shiyasa zata yarda akashe mata Rayuwa Tana yi Hajiya Lariya na Tayata,Jidda naji ta Fito da Sauri ganin Mama na kuka itama sai taFara kukan Tana Rokon su Hajiya sa"an kan suyi Shuru ammh ko Sauraranta ba wacce Tayi...
Iya Kokari Mama Tayi wajen Fahimtar Dasu,Ammh suka ki Fahimta Daga karshema Hajiya Sa"a tace Tazo Tafiya da yarta ne Babu kuma wanda ya isa yayi mata Aure,Tana ji Tana gani Hajiya Lariya taShiga Cikin Dakinsu Jidda ta Hado mata kayanta ta Fito Da Farko Jidda Taso Tayi Tirjiya ganin mama na Sharan kwallah ammh kuma Sai Mama tace ta Bisu ba komai Jidda naji nagani Hajiya Sa"a da Hajiya Lariya suka Tasata Har Cikin Mota sai Chika gari.
Suna Fita Mama ta koma Cikin Daki Taci kukanta Ta Share Hawayenta kana ta Dauki Waya ta Kira Abdullahi yana Office ta gayamai Abunda ya Faru Ransa matuka ya baci Cikin Fushi yace"Don Allah Ki Daina Bata Ranki abanza Mama..Nafi karfin na Tsaya ina Sa"insa da Wannan matar...Karki Damu Yadda ta Dauki Jidda da Hannunta Haka zata Dawo da ita kuma Mganar Auran jidda da Nazifi Wlh bazai Taba Tashi ba sai dai in Dayansu yau ya Fadi ya Mutu kafin Lokacin.."Mama ta Share Hawayenta Tana Fadin"Shikenan ammh baka ji irin manganganun Datake Fada bane..Tana ganin kamar wai don Jidda ba yata bace Shiyasa na yarda Za"ayi mata Aure.."
Mirmishin Takaichi Abdullahi yayi yana Fadin'Eh Ba ke kika Haifeta ba..Ammh kin mata Abunda ita Datake uwarta bata Mata ba ta, ita da ta Tsallake tatafi wayon Gantalinta shine yanzu Take da wani Bakin mgana..?karki Damu Mama...Kinfita iko da Jidda kuma da izinin Lahi sai kin Aurar da ita kuma Jidda yata ke gareki har gaban Abada.."Da wadanan kalaman na Abdullahi yasa Hankalin Mama ya kwanta Sukayi Sallama.
Sun gama waya ba Dadewa Sai ga Sallaman Baba wada Dashi da yara,da kwalayan minti da Biscuit,Sai goro Nan Mama ta tarbesu Cikin Fara"a Bayan sun gama gaisuwa ne ya gabatar mata kayan Saka Ranar Jidda sai kuma Sadakin Mama batayi mgana ba Ta Kira Abdullahi Ta gayamai sai yace Tabama Baba wadan Waya Dashi Sukayi mgana yace Baba wada ya Rike Sadakin a Hannunsa Tukunnah,Kwalayen Mintin kuma Da Biscuit din Yace abarma Mama Hakki ne Dama su Gani kuma su Raba ma wanda ya kamata yaji kuma ya sani.
Bai wani Jima ba ya mata Sallama ya Tafi Abdullahi shi da kanshi ya Kira Zannira yace in ta samu Dama gobe tazo Gida kan mganar Jidda,Tace insha Allahu zata zo ko bata kwana ba Haka ya Kira Subai ma ya gayamata,Goggo Habiba ma Sunyi mgana tana ta Saka albarka Itama ya Bukaci ganinta Gobe in ta samu Dama tace Insha Allahu Tana tafe,Umman Sadiq kuma Mama da kanta ta kirata ta gayamata,Tayi ta Murna tana Saka albarka Tana yabon kwakwayan Halayyar Nazifin Abunda kuma yasa Abdullahi bai Kira Ita Umman ba ya bari ne sai Su Mama sun Raba kayan Sa Ranar daman yana sa Ran zuwa gusai Weekend dinan Sai ya wuce mata Dashi yayi mata Bayanin komai.
*******
Da Abdullahi ya koma Gida Da Daddare yayi ma Hafsah Bayanin komai itama Tayi Fatan alheri da Safe kuma da zai Fita yace in Tagama Abunda take ta Shirya Taje Gidan Maman,Saboda Maman tace ya kamata Hafsah din Tazo Tunda Duka anzama Daya.
Lokacin Dayake gayamata Tana Tsaye Kofar Dakin tane Shi kuma yana Tsakar gida yana Duba Mashin Dinsa Dataki Tashi,Ya Dago kansa yana cema Hafsah.."Kinga fa inaga yau sai dai na Bar mashin din nan gida ta samu mtsala..Zan kira Auwal in ya Dawo makaranta Yazo ya Dauka yakai min wajen Bakanikan nan na kofarDoka.."..
Hafsah na Tsaye tace"Ayyah ba Jiya Lafiya lau ka Dawo da ita ba.."Kai Tsaye yacemata'Halin karfe Nasara kenan bashi da Tabbas.."Yafada Lokaci Daya yana Sakarmata Idanuwansa Lokaci Daya ya gano Ramar Datayi Shi bai sani ba Dayake baya samun Zama In ya Fita aiki Tun safe sai Dare ya Dawo a gajiye barci wani lokacin Har asabar kuma yana Shiga makaranta Lahadi ce Kadai Ranar Hutunsa Daya kamata ya Zauna agida kuma Baya zaman Saboda Hidimomi Da yawa.
Cikin Bacin Rai ya kara kafeta da Ido Yana Fadin"Hafsah..Wai meke Damunki ne..?kinga yadda kika Rame kuwa kin Lalace Don Allah miye haka... ? Zazzabin Daren ne har yanzu bai sauka ba ko yaya..?
Yafada Yana kallonta Cikin Bacin Rai,kai Hafsah ta Saukar Cikin Sanyin Jiki,Bataso ta Tadama Abdullahi Hankali ammh ita kanta taasan Bata da Lafiya Wuni Take kwance kasala Ciwon kai da Zazzabin Dare ammh bata bari ya sani ba,Gashi bata iya wani cin Abinci Shiyasa Duk Ta Rame ganin Taki mgana yasa kawai ya Kada kai yana Fadin"Dole gobe muje asibiti adubamin ke..Wlh ban yarda Dake ba baki da lafiya ammh baki san gayamin Duba Don Allah yadda kika Rame sai kwarmin ido..? Yafada yana Sakin karamin Tsaki Lokaci Daya yana Tura Mashinsa dinsa gefe key din ya mikamata yana Fadin"Auwal zai zo ya karba...In yazo ki Bashi 3k Cikin kudin Dake Hannunki.."
Da To ta karba Shi kuma ya Rataya Jakarsa ya Fice tana mai Fatan adawo lafiya Har ya Fice Tana Tsaye nan kofar Dakin,Kasala ce ta Lullubeta a kasalance Ta Juya ta koma Ciki,Kan gado ta koma ta kwanta komai batayi Tunanin kaudawa Don ma Allah ya Taimaketa su Amira Suna gidan Ammi Jiya Datazo suka Saka kukan sai Sun Bita tace abata kayan makarantansu Tatafi Dasu,Ita Kanta Ammin sai da Tambayeta ko Bata lafiya ne..? Tace lafiyanta lau ammh ai duk wanda yasan Hafsah in ya ganta sai ya gane tayi Rama Sosai.
Sai dataga 12pm na Rana ta wuce kana Dakyar ta iya Rarrafawa Tayi wanka ko Shara batayi ba Dama Safe Tea kadai Abdullahi ita batama Shan ba Fatan tsaki Taji Tana Bukata kawai,Ammi ta Kira tace Don Allah ayi mata Tana Gidan Mama a aiko mata Dashi Tunda Ammi Taji Haka aranta tace Arina wannan Ramar naki Hafsah Toh Allah ya Raba lafiya kulle Gidan Tayi ta samu mai adaidaita yakai ta Gidan Mama Koda Ta isa Har Sun kariso Zannira da Subai" sai Goggo Habiba nan aka Shiga gaisawa suma Suna ta mganar Ramarta ammh sai tace bakomai.
Sai da sukayi sallar azahar kana Mama ta gabarar musu da kayan saka Ranar,Su zannira suna ta saka albarka Subai kuma Harda Guda Daman Tun zuwansu suna Tambayan Jidda mama ta gayamasu yarda akayi da kuma Abunda Abdullahi yace Suma basu Damu ba sukace Susan karya Take bazata iya Ja da ya Abdullahi ba,Raba komai sukayi su Diban ma Mama da Danginta sai nasu,Na goggo Habiba sai na Umman Sadiq,sai na Ammi Sauran kuma na makota ne,Sai na Hajiya Sa'a da ita kanta Jiddan Wanda Baba wada yabata Umarnin a Cire musu.
Direban Ammi Daya kawoma Hafsah Fate akabama Sakon Ammi ya kaimata Sakon na Zuwa Hannunta sai Kiranta Tana ta Fatan alheri da saka albarka,La"asar nayi goggo Habiba ta koma Bayan Ta Shiga Gidan Inna Abu sungaisa Zannira kuma sai gobe zata tafi,Subai ma Da Wuri tatafi Saboda yau mahmud din yake Dawowa Daga wata Tafiya Da yayi,Hafsah kuma tana kwance Tun Bayan Data idar da sallar la"aar ta kasa Tashi Tatafi gida tanan nan Har Auwal Ya Shogo bayan ya Huta yaci abinci ya karbi key din gidan Dana Mashin ya Tafi yaje ya Dauki Mashin din yakaita gyara Chan ya barta sai zuwa gobe da yammah za"a gama gyaran.
Abdullahi kuma Sai da ya Tashi Daga Office yabiyo Gidan Mama ya iske Hafsah kwance Mama ta Fara mai Fadan meyasa basu je asibiti ba Yana Latsa wayarsa yace"Mama kinsan Halin Hafsah kuwa daTaurin kai..? Wlh ta Rainani Har sai nawa zan mata magiya tayarda muje asibiti a gwadata aduba Aga meke damunta ammh bani da wannan kimar idanunta sai Abunda Taga Dama Shi zatayi ."Ya karishe Fada Cikin Bacin Rai Zannira ce ke bashi baki Tana ma Hafsah Fadan kamar wata karamar yarinya sai ta Rika zama da Ciwo Bata dai ce komai ba,Dakyar ta Rarrafa tayi sallar Isha"i Aka zubamata Tuwo ta Faraci ko Loma Biyar batayi ba Zuciyarta ta Fara Tashi sai amai nan ta Fita Waje tana Sheka shi Abdullahin na Tsaye gefenta Duk Hankalinsa ya Tashi ya kalli Mariya yana Fadin"Ke bani Ruwa.."Da Hanzari ta Diba takaimai ya kamata ya wanke mata Bakin yajata zuwa Dakin Mama tama kasa zama sai Kwanciya kawai Tayi ajikinsa hawaye na Bin gefen Idanuwanta Hankalin Abdullahi dasu Mama ya Tashi Mariya na Waje tana Share Inda Hafsah tayi aman Zannira ce tace Yakamata Atafi asibiti agani.
Mai Adaidaita Abdullahi ya saka Auwal ya samo musu Dashi da Mama Suka Tafi Asibitin ko Acikin Napen ma Kan Cinyar Abdullahi take ta lamgwabewa kamar wacce bata da Jini,Abdullahi Fada kawai yake yana Fadin"kinga Abunda nake gudu ko Mama..?Yanzu don Allah miye amfanin wannan..? Bayan ku iyayena ina da wacce ta Fiyemin ita ne..? Itace komai nawa..Ciwonki nawa ne Hafsah Domin sai da Bazakarki da lafiyarki nake iya Rawa Nima ammh kalli yadda kika maida ki..?Don Allah jibi fa Mama..?
Yake Fada kamar yayi kuka Asibitin Dan Fulani Dake kan Fage suka kaita Suna zuwa aka karbeta aka bata gado bayan an Dibi Jininta da Sauraran Gwaje Gwaje,Drip aka sakamata da Alluran Barci Tunda Jikinta ba kwari in kaga Abdullahi kamar Shine bai da Lafiya Rana Daya Duk ya Fada kamar bashi ba,Ko Abinci bai iya sakama Cikinsa ba Tun karin Safe,Zannira yakira ya Fadama an basu gado,sai gasu Ita da Auwal sun zo Asibitin Har zuwa Lokacin kuma Hafsah bata Tashi ba Suna aaibitin sai Wajen Sha Biyu Saura Suka Tafi Tare da Abdullahin ya wuce gida su kuma suka wuce gidan Mama Gida ya kwana Shi kadai Tun safe ya Kira Ammi ya gayamata Halin da ake Ciki,Shi kuma Wanka kawai yayi ya Hado mata kaya Dazata sauya sai Abun bukata irin kayan Tea da Sauransu Fulas din Ruwan zafi kuma Daga Gidan Mama an zo Dashi koda yaje asibitin ya iske Ammi da Daddy da Inna Abu sunzo,Ga kayan karyawa nan Daga gidan Mama sai Wanda su Ammi suka zo Dashi,gaisuwa sukayi Sukamai yamai Jiki Lokacin Hafsah na barci Bata tashi ba, Bai Jima ba ya wuce Wajen aiiki Daganan Tunda yayi kokarin ganin likita akace ya Hau ra sama Shi kuma yana Sauri ya makara yaasa bai Tssya ba yace sai ya Dawo.
Zuwa yammah asibitin ta Cika da Mutane Dayake suna Vip ne sai aka samu Wadatar waje,Saboda Ciwon Hafsah yasa Zannira bata koma Aranar ba,sai Washegari Subai ma Tazo,Akuma Ranar ne Likita yabama Abdullahi Takardan sakamakon gwajin Hafsah inda yamai albishir din Tana da Ciki har na Tsawon wata uku Sai Murna da Farimciki Abdullahi ba kunya yazo yana Fadama su Ammi da Mama suma sukayi ta Allah ya Raba lafiya Ammi tace Daman ita ta Zargi haka Tun Farko ganin kamar irin Ramar datayi Lokacin Cikin Amira.
Sai dai Hafsah ta Shafe kwana Hudu a asibiti kana aka Sallameta ta koma Gida,Saboda yanayin karfin Jikinta sai Ammi ta bata yar aikinta Guda Daya Harira tazo Tana kula da ita,Su Amira kuma Suna wajenta,Kwana Biyu da Sallamota sai ga Umman Sadiq tazo ta Dubata kwananta Daya ta Juya Bayan Mama ta bata kayan saka Ranar Jidda Tayi ta Fatan alheri.
Sai da Hafsah ta kwashe Wajen sati Biyu kafin ta gyagice ammh fa Har yanzu Jikin ba karfi bata iya wani aiki mai karfi wannan Dalilin ne yasa Abdullahi ya kara Rokon Ammi Data bar musu Harira ko Wata Biyu Tayi Zuwa Lokacin da Cikin Hafsah zai yi kwari Ammi ta amince,Sosai Hafsah ta samu Hutu da Jin Dadi ga Abdullahi na kula da ita yana ji kamar kan wannan Cikin ne zai Taba Haihuwa Hatta da Nazifi yazo Dubata Dayazo ne ma Tana Daga Cikin Daki Taji Nazifin nabama Abdullahin Labarin suna Waya da Jidda Sosai Domin ma yace mata zai je Chan Gidan mamar nata kuma bata musa ba Duk da Tanuna Tsoron Ita Hajiya Sa"an Abdullahi yayi Tsaki yana Fadin"Karka Taka kaje ko"ina..Na bari ne Hankalina ya kwanta ne..Kwananan Jidda zata Dawo ko Taki ko taso.."
Da haka Suka Cigaba da Tattaunawa mganar kafin su Fita Tare Abdullahin bai Dawo gidan ba Sai Dare.
******
Bangaran Jidda kuwa Ta Shiga Takura Sosai Domin Hajiya Sa"a tayi Tsaye so take Ta Hana wannan Auran Jarabawarta ta Fito kuma Duka taci sakamako mai kyau,Hajiya Sa"a taji Dadin hakan sai ta Siya mata Jamb tace Zata Rubuta in taci Zata wuce Jami"ar Abuja ne.
Lokacin Datake Fadamata Haka baki Ta Tura Tana Fadin"Mommy yafa ce zai barni na Cigaba da karatuna Har sai nagaji Don kaina.."Jin Haka yasa Hajiya Sa"a Ta aika mata da Dakuwa Tana Fadin"Au har ya Hure miki kunnin da zaki Rika Ja"in Ja da mganata Hauwa'u..? Toh bai isa ba..Ba yanzu Zaki Aure ba sai kin kamallah Digree dinki Lokacin Saurayi Dan Gidan Manya zai Fito miki Wanda ya Dace Dake da kuma Ra"ayina kiyi auranki ammh a yanzu bazan yarda ki Auri wannan Yaron ba,Bai da ko Sisi,ga Hidimar kansa Data Matarsa da wanne zai ji da Hidimarki ko Da tashi Ko Data matarsa ko Data iyayensa... ? Ina Duba miki Wuyar rayuwa ce Jidda ammh naga baki ganewa Yafara Hure miki kunni da Dadin Bakinsu irin na Yaudarrarun Samarin zamani..."Ita Dai Jidda bata kara Mgana ba sai Tura baki Take Domin a Hakikanin gaskiya Nazifi ya Fara Tasiri acikin Zuciyarta Har yanzu in baikirata ba Ya shiga Busy inya Kirata Da Daddare ta Dinga mai Fushi kenan ya manta da ita,Shikuma ya Biye mata yayi ta bata Hakuri Zuwa Lokacin kuma bai sanar ma Sakina ba yaushema suka samu Zama koda wani Lokaci Tana Abuja In ta Dawomai Weekend kuma yanzu ba Irin Baya ne yana Shiga Cikin makaranta har Ranar asabar Lahadi kuma Itace yake samun Lokaci zuwa inda ya kamata Dukkansu kowa ya maida kanshi Busy in ka gansu bazaka Taba cewa Miji da mata bane Saboda ba wani Fahimtar Juna atsakaninsu.
Achan Zaria kuwa kowa yaji Nazifi zai kara Aure kuma Jidda zai Aura sai ya Jimai Murna Sosai kannensa Haka sukayita murna Suna Fadin yanzu ne Yaya Nazifi zai yi Aure Domin Auran Sakina basu Daukesa aure ba.
Sai da Jidda ta Cika Sati Biyu agidan Hajiya Sa"a kana Abdullahi ya Kirata awaya da Farko kamar bazata Dauka ba sai kuma ta Dauka Sai kuma taji Sabanin Tunaninta ba Fada ba Zagi sai ma Lallabi yace ta Dawo Gida Hakanan tana so tacemai Mommy tace bazata koma ba ammh yaki Bata Damar haka yace Gobe Ta Dawo Gida yana Jiranta kartabari yazo da kanshi ya Dauketa tasu bazatayi kyau ba Jin Haka yasa Hankalin Jidda ya Tashi ta samu Hajiya Sa"ar da mganar sai ta Rufeta da Fada tace in ya matsu yazo Tana Jiransa Sai Jidda ta Rude sanin Halin Ya Abdullahi sai ta Kira Wayar Nazifi Tana kuka Tana gayamai Shi kuma sai ya kara Firgitata yace gwara ta koma Tasan Halin yayansu Duka ba mai Wahala bane awajensa Gwara tayi yarda zatayi ta koma Haka ko akayi ta sakama Hajiya Sa"a kuka da Birgima Dole sai ta Maida ta gida Tun Tana ganin Abun wasa ne,taga dai da gaske take Ranar ta wuni kuka bata kuma ci Abinci ba Hajiya Sa"a ta Kira Lariya ta gayamata Sai gata tazo..Ganin Irin kukan da Jidda keyi yasa ta Kalli Hajiya Sa"a Tana Fadin"Kinga yaya gwara mu Tattara yarinyar nan mu Maidata..Kar Ciwon yunwa da kuka su mata illah kinga wa gari ya waya..?
Hajiya Sa"a tace"Nifa Wannan Auran ne bana so Lariya kin sani.."Lariya tace"Mu maidata..Sai mu koramai Bayani wannan karon babu Daga kafa.."Ba yadda Hajiya Sa"a zatayi Tabi Shawaran Lariya suka Tattara Jidda suka maida ta Gidan Mama Suka kuma Zauna Suna Jiran Zuwan Abdullahi Tunda Hajiya Sa"an da kanta ta Karbi Layinshi ta kirashi yace yana Hanya zai Dawo Daga wajen aiki Gashi nan zuwa.
Sai Bayan Sallar mangariba Ya Shigo Gidan,Sama sama Suka gaisa dasu Hajiya Sa"a,Ko Zama bai yi ya karkace kai yana Fadin"Gani naji kin kirani ina Fata lafiya..? Domin ina kan Hanya ne,agida ina da mara lafiya ku Hanzarta Fadin Abunda ya kawoku ko..?
Hajiya Sa"a Ranta ya baci ta kallesa Tana Fadin"Ba wata mgana bace mai Tsawo kan mganar Auran yata ce da kuka yanke...Toh ni ban yarda ba Kuma ban amince ba Jidda karatu zatayi Domin har na Fara Nemar mata makarantan Data Dace da ita.."
Tafada Tana Masa wani kallo Mirmishi ya saki kafin yace"Kin makara Hajiya bakin alkalami ya Riga ya Bushe...Mama baki Basu Mintin saka Rana bane nan da Wata uku za"ayi Dama ko baki zo ba Mama zataje ta kai miki ta kuma Miki Bayani ko bakomai mun Fita Ladan Haihuwar da kika mata..'Hajiya Sa"a ta mike a Fusace Tana Fadin"Kambu a sakama yata Rana bani da labari..? Wlh baka isa ba in kuma kukace sai anyi Wlh zan makaka a kotu.."
Kafada ya Zakuda yana Fadin"Fine..Dama chan muka je Dayafi wannan kananan mgangaun da kike...Ni bani da Lokacinki Bawai Domin bansan irin Amsan da zan gayamiki bane sai don Ni ba Haka Tarbiyata take ba ko ya Babba yake ina bashi Girmansa ba Domin haka ba Wlh ke kanki baki isa ki Tsaya agabana kina Fadamin haka ba..kuma ki Bude kunnenki kiji dakyau Auran Jidda Nazifi ba Fashi in kinga ya tashi,Toh Dayansu ne yamutu..Gwara ki Shafa ma kanki lafiya..".
Cikin Harzuka tace"Au haka kace..? Kai ya gyada kafin yace"Eh haka nace...Mama ki basu Sakon zan karisa gida sai da Safe.."Daga haka ko waiwaye ya Fice da Auwal yaci karo a tsakar gidan wanda Ransa yayi masa Fari na Irin amsan daAbdullahi ya basu Mama akabari da basu Hakuri Mintin ma da Biskit din Ko kallonshi basu yi ba Hajiya sa"a ta warci Hannun Lariya suka Fice Jidda da mariya na Ciki Jidda sai kuka take Mariya na Bata baki ammh acikin Ranta Tana Jinjina ma karfin Halin Hajiya Sa'a.
*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*
*Shakira...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*026*
""Adaran Hira Tsakanin Nazifi da Jidda Tayi Tsawo sosai,Sai Biyema Tabaran Jidda yake da Shagwabarta saboda yana so ta saki Jiki Dashi Sosai Kuma ta Fara Sakin,Sai gashi Dukkansu Suna Jin Dadin Hirar.
Cikin Hirar ne Nazifi ke Tambayata wata mgana ne tace zata gayamai Ta waya..? Cikin Sangarta tasakomai mganar Cigaban karatunta,Domin har Ga Allah taji Acikin Ranta zata iya Auran Ya Nazifi mtsalanta Daya Shine karya Hanata Cigaba da karatunta Shine Tashin Hankalinta,Shi kuma yace mata ta bari sai anyi Auran in yaga Yadda Take bashi kulawa Sosai kuma Ta Dauki alkawarin komai bazai Sauya ba nadaga kulawar Datake bashi,Toh Zatayi Ilimi har sai da kanta Tace tagaji Jin haka yasa ta Dauki Murna Sosai Tana mai Godiya Basusan iya Lokacin da suka Dauka Suna waya ba Har mariya Datake Duba littafanta Ta Gaji Ta kwanta ta bar jidda sai Araund karfe 2pm na Dare sukayi Sallama kowa ya kwanta Ransa Cike da wani Annuri wanda ke Fitowa Daga kasan Ransu.
Washegari Kuwa Tun Wajen karfe 10am na safe sai ga Hajiya Lariya da Hajiya Sa"a ransu a matukar bace Alokacin gidan Babu Kowa Auwal ya Tafi makaranta mariya kuma Tatafi asibiti Mama ce kadai atsakar Gida Jidda Tana Falon Mama Tana Goge kayanta Suka Shigo ko karba Sannu da zuwan da Mama ke musu basu yi ba,Hajiya Sa"a ta Fara gaggayama Mama mgana Son Ranta Tana Fadin Don ba Ita Ta Haifi Jidda ba Shiyasa zata yarda akashe mata Rayuwa Tana yi Hajiya Lariya na Tayata,Jidda naji ta Fito da Sauri ganin Mama na kuka itama sai taFara kukan Tana Rokon su Hajiya sa"an kan suyi Shuru ammh ko Sauraranta ba wacce Tayi...
Iya Kokari Mama Tayi wajen Fahimtar Dasu,Ammh suka ki Fahimta Daga karshema Hajiya Sa"a tace Tazo Tafiya da yarta ne Babu kuma wanda ya isa yayi mata Aure,Tana ji Tana gani Hajiya Lariya taShiga Cikin Dakinsu Jidda ta Hado mata kayanta ta Fito Da Farko Jidda Taso Tayi Tirjiya ganin mama na Sharan kwallah ammh kuma Sai Mama tace ta Bisu ba komai Jidda naji nagani Hajiya Sa"a da Hajiya Lariya suka Tasata Har Cikin Mota sai Chika gari.
Suna Fita Mama ta koma Cikin Daki Taci kukanta Ta Share Hawayenta kana ta Dauki Waya ta Kira Abdullahi yana Office ta gayamai Abunda ya Faru Ransa matuka ya baci Cikin Fushi yace"Don Allah Ki Daina Bata Ranki abanza Mama..Nafi karfin na Tsaya ina Sa"insa da Wannan matar...Karki Damu Yadda ta Dauki Jidda da Hannunta Haka zata Dawo da ita kuma Mganar Auran jidda da Nazifi Wlh bazai Taba Tashi ba sai dai in Dayansu yau ya Fadi ya Mutu kafin Lokacin.."Mama ta Share Hawayenta Tana Fadin"Shikenan ammh baka ji irin manganganun Datake Fada bane..Tana ganin kamar wai don Jidda ba yata bace Shiyasa na yarda Za"ayi mata Aure.."
Mirmishin Takaichi Abdullahi yayi yana Fadin'Eh Ba ke kika Haifeta ba..Ammh kin mata Abunda ita Datake uwarta bata Mata ba ta, ita da ta Tsallake tatafi wayon Gantalinta shine yanzu Take da wani Bakin mgana..?karki Damu Mama...Kinfita iko da Jidda kuma da izinin Lahi sai kin Aurar da ita kuma Jidda yata ke gareki har gaban Abada.."Da wadanan kalaman na Abdullahi yasa Hankalin Mama ya kwanta Sukayi Sallama.
Sun gama waya ba Dadewa Sai ga Sallaman Baba wada Dashi da yara,da kwalayan minti da Biscuit,Sai goro Nan Mama ta tarbesu Cikin Fara"a Bayan sun gama gaisuwa ne ya gabatar mata kayan Saka Ranar Jidda sai kuma Sadakin Mama batayi mgana ba Ta Kira Abdullahi Ta gayamai sai yace Tabama Baba wadan Waya Dashi Sukayi mgana yace Baba wada ya Rike Sadakin a Hannunsa Tukunnah,Kwalayen Mintin kuma Da Biscuit din Yace abarma Mama Hakki ne Dama su Gani kuma su Raba ma wanda ya kamata yaji kuma ya sani.
Bai wani Jima ba ya mata Sallama ya Tafi Abdullahi shi da kanshi ya Kira Zannira yace in ta samu Dama gobe tazo Gida kan mganar Jidda,Tace insha Allahu zata zo ko bata kwana ba Haka ya Kira Subai ma ya gayamata,Goggo Habiba ma Sunyi mgana tana ta Saka albarka Itama ya Bukaci ganinta Gobe in ta samu Dama tace Insha Allahu Tana tafe,Umman Sadiq kuma Mama da kanta ta kirata ta gayamata,Tayi ta Murna tana Saka albarka Tana yabon kwakwayan Halayyar Nazifin Abunda kuma yasa Abdullahi bai Kira Ita Umman ba ya bari ne sai Su Mama sun Raba kayan Sa Ranar daman yana sa Ran zuwa gusai Weekend dinan Sai ya wuce mata Dashi yayi mata Bayanin komai.
*******
Da Abdullahi ya koma Gida Da Daddare yayi ma Hafsah Bayanin komai itama Tayi Fatan alheri da Safe kuma da zai Fita yace in Tagama Abunda take ta Shirya Taje Gidan Maman,Saboda Maman tace ya kamata Hafsah din Tazo Tunda Duka anzama Daya.
Lokacin Dayake gayamata Tana Tsaye Kofar Dakin tane Shi kuma yana Tsakar gida yana Duba Mashin Dinsa Dataki Tashi,Ya Dago kansa yana cema Hafsah.."Kinga fa inaga yau sai dai na Bar mashin din nan gida ta samu mtsala..Zan kira Auwal in ya Dawo makaranta Yazo ya Dauka yakai min wajen Bakanikan nan na kofarDoka.."..
Hafsah na Tsaye tace"Ayyah ba Jiya Lafiya lau ka Dawo da ita ba.."Kai Tsaye yacemata'Halin karfe Nasara kenan bashi da Tabbas.."Yafada Lokaci Daya yana Sakarmata Idanuwansa Lokaci Daya ya gano Ramar Datayi Shi bai sani ba Dayake baya samun Zama In ya Fita aiki Tun safe sai Dare ya Dawo a gajiye barci wani lokacin Har asabar kuma yana Shiga makaranta Lahadi ce Kadai Ranar Hutunsa Daya kamata ya Zauna agida kuma Baya zaman Saboda Hidimomi Da yawa.
Cikin Bacin Rai ya kara kafeta da Ido Yana Fadin"Hafsah..Wai meke Damunki ne..?kinga yadda kika Rame kuwa kin Lalace Don Allah miye haka... ? Zazzabin Daren ne har yanzu bai sauka ba ko yaya..?
Yafada Yana kallonta Cikin Bacin Rai,kai Hafsah ta Saukar Cikin Sanyin Jiki,Bataso ta Tadama Abdullahi Hankali ammh ita kanta taasan Bata da Lafiya Wuni Take kwance kasala Ciwon kai da Zazzabin Dare ammh bata bari ya sani ba,Gashi bata iya wani cin Abinci Shiyasa Duk Ta Rame ganin Taki mgana yasa kawai ya Kada kai yana Fadin"Dole gobe muje asibiti adubamin ke..Wlh ban yarda Dake ba baki da lafiya ammh baki san gayamin Duba Don Allah yadda kika Rame sai kwarmin ido..? Yafada yana Sakin karamin Tsaki Lokaci Daya yana Tura Mashinsa dinsa gefe key din ya mikamata yana Fadin"Auwal zai zo ya karba...In yazo ki Bashi 3k Cikin kudin Dake Hannunki.."
Da To ta karba Shi kuma ya Rataya Jakarsa ya Fice tana mai Fatan adawo lafiya Har ya Fice Tana Tsaye nan kofar Dakin,Kasala ce ta Lullubeta a kasalance Ta Juya ta koma Ciki,Kan gado ta koma ta kwanta komai batayi Tunanin kaudawa Don ma Allah ya Taimaketa su Amira Suna gidan Ammi Jiya Datazo suka Saka kukan sai Sun Bita tace abata kayan makarantansu Tatafi Dasu,Ita Kanta Ammin sai da Tambayeta ko Bata lafiya ne..? Tace lafiyanta lau ammh ai duk wanda yasan Hafsah in ya ganta sai ya gane tayi Rama Sosai.
Sai dataga 12pm na Rana ta wuce kana Dakyar ta iya Rarrafawa Tayi wanka ko Shara batayi ba Dama Safe Tea kadai Abdullahi ita batama Shan ba Fatan tsaki Taji Tana Bukata kawai,Ammi ta Kira tace Don Allah ayi mata Tana Gidan Mama a aiko mata Dashi Tunda Ammi Taji Haka aranta tace Arina wannan Ramar naki Hafsah Toh Allah ya Raba lafiya kulle Gidan Tayi ta samu mai adaidaita yakai ta Gidan Mama Koda Ta isa Har Sun kariso Zannira da Subai" sai Goggo Habiba nan aka Shiga gaisawa suma Suna ta mganar Ramarta ammh sai tace bakomai.
Sai da sukayi sallar azahar kana Mama ta gabarar musu da kayan saka Ranar,Su zannira suna ta saka albarka Subai kuma Harda Guda Daman Tun zuwansu suna Tambayan Jidda mama ta gayamasu yarda akayi da kuma Abunda Abdullahi yace Suma basu Damu ba sukace Susan karya Take bazata iya Ja da ya Abdullahi ba,Raba komai sukayi su Diban ma Mama da Danginta sai nasu,Na goggo Habiba sai na Umman Sadiq,sai na Ammi Sauran kuma na makota ne,Sai na Hajiya Sa'a da ita kanta Jiddan Wanda Baba wada yabata Umarnin a Cire musu.
Direban Ammi Daya kawoma Hafsah Fate akabama Sakon Ammi ya kaimata Sakon na Zuwa Hannunta sai Kiranta Tana ta Fatan alheri da saka albarka,La"asar nayi goggo Habiba ta koma Bayan Ta Shiga Gidan Inna Abu sungaisa Zannira kuma sai gobe zata tafi,Subai ma Da Wuri tatafi Saboda yau mahmud din yake Dawowa Daga wata Tafiya Da yayi,Hafsah kuma tana kwance Tun Bayan Data idar da sallar la"aar ta kasa Tashi Tatafi gida tanan nan Har Auwal Ya Shogo bayan ya Huta yaci abinci ya karbi key din gidan Dana Mashin ya Tafi yaje ya Dauki Mashin din yakaita gyara Chan ya barta sai zuwa gobe da yammah za"a gama gyaran.
Abdullahi kuma Sai da ya Tashi Daga Office yabiyo Gidan Mama ya iske Hafsah kwance Mama ta Fara mai Fadan meyasa basu je asibiti ba Yana Latsa wayarsa yace"Mama kinsan Halin Hafsah kuwa daTaurin kai..? Wlh ta Rainani Har sai nawa zan mata magiya tayarda muje asibiti a gwadata aduba Aga meke damunta ammh bani da wannan kimar idanunta sai Abunda Taga Dama Shi zatayi ."Ya karishe Fada Cikin Bacin Rai Zannira ce ke bashi baki Tana ma Hafsah Fadan kamar wata karamar yarinya sai ta Rika zama da Ciwo Bata dai ce komai ba,Dakyar ta Rarrafa tayi sallar Isha"i Aka zubamata Tuwo ta Faraci ko Loma Biyar batayi ba Zuciyarta ta Fara Tashi sai amai nan ta Fita Waje tana Sheka shi Abdullahin na Tsaye gefenta Duk Hankalinsa ya Tashi ya kalli Mariya yana Fadin"Ke bani Ruwa.."Da Hanzari ta Diba takaimai ya kamata ya wanke mata Bakin yajata zuwa Dakin Mama tama kasa zama sai Kwanciya kawai Tayi ajikinsa hawaye na Bin gefen Idanuwanta Hankalin Abdullahi dasu Mama ya Tashi Mariya na Waje tana Share Inda Hafsah tayi aman Zannira ce tace Yakamata Atafi asibiti agani.
Mai Adaidaita Abdullahi ya saka Auwal ya samo musu Dashi da Mama Suka Tafi Asibitin ko Acikin Napen ma Kan Cinyar Abdullahi take ta lamgwabewa kamar wacce bata da Jini,Abdullahi Fada kawai yake yana Fadin"kinga Abunda nake gudu ko Mama..?Yanzu don Allah miye amfanin wannan..? Bayan ku iyayena ina da wacce ta Fiyemin ita ne..? Itace komai nawa..Ciwonki nawa ne Hafsah Domin sai da Bazakarki da lafiyarki nake iya Rawa Nima ammh kalli yadda kika maida ki..?Don Allah jibi fa Mama..?
Yake Fada kamar yayi kuka Asibitin Dan Fulani Dake kan Fage suka kaita Suna zuwa aka karbeta aka bata gado bayan an Dibi Jininta da Sauraran Gwaje Gwaje,Drip aka sakamata da Alluran Barci Tunda Jikinta ba kwari in kaga Abdullahi kamar Shine bai da Lafiya Rana Daya Duk ya Fada kamar bashi ba,Ko Abinci bai iya sakama Cikinsa ba Tun karin Safe,Zannira yakira ya Fadama an basu gado,sai gasu Ita da Auwal sun zo Asibitin Har zuwa Lokacin kuma Hafsah bata Tashi ba Suna aaibitin sai Wajen Sha Biyu Saura Suka Tafi Tare da Abdullahin ya wuce gida su kuma suka wuce gidan Mama Gida ya kwana Shi kadai Tun safe ya Kira Ammi ya gayamata Halin da ake Ciki,Shi kuma Wanka kawai yayi ya Hado mata kaya Dazata sauya sai Abun bukata irin kayan Tea da Sauransu Fulas din Ruwan zafi kuma Daga Gidan Mama an zo Dashi koda yaje asibitin ya iske Ammi da Daddy da Inna Abu sunzo,Ga kayan karyawa nan Daga gidan Mama sai Wanda su Ammi suka zo Dashi,gaisuwa sukayi Sukamai yamai Jiki Lokacin Hafsah na barci Bata tashi ba, Bai Jima ba ya wuce Wajen aiiki Daganan Tunda yayi kokarin ganin likita akace ya Hau ra sama Shi kuma yana Sauri ya makara yaasa bai Tssya ba yace sai ya Dawo.
Zuwa yammah asibitin ta Cika da Mutane Dayake suna Vip ne sai aka samu Wadatar waje,Saboda Ciwon Hafsah yasa Zannira bata koma Aranar ba,sai Washegari Subai ma Tazo,Akuma Ranar ne Likita yabama Abdullahi Takardan sakamakon gwajin Hafsah inda yamai albishir din Tana da Ciki har na Tsawon wata uku Sai Murna da Farimciki Abdullahi ba kunya yazo yana Fadama su Ammi da Mama suma sukayi ta Allah ya Raba lafiya Ammi tace Daman ita ta Zargi haka Tun Farko ganin kamar irin Ramar datayi Lokacin Cikin Amira.
Sai dai Hafsah ta Shafe kwana Hudu a asibiti kana aka Sallameta ta koma Gida,Saboda yanayin karfin Jikinta sai Ammi ta bata yar aikinta Guda Daya Harira tazo Tana kula da ita,Su Amira kuma Suna wajenta,Kwana Biyu da Sallamota sai ga Umman Sadiq tazo ta Dubata kwananta Daya ta Juya Bayan Mama ta bata kayan saka Ranar Jidda Tayi ta Fatan alheri.
Sai da Hafsah ta kwashe Wajen sati Biyu kafin ta gyagice ammh fa Har yanzu Jikin ba karfi bata iya wani aiki mai karfi wannan Dalilin ne yasa Abdullahi ya kara Rokon Ammi Data bar musu Harira ko Wata Biyu Tayi Zuwa Lokacin da Cikin Hafsah zai yi kwari Ammi ta amince,Sosai Hafsah ta samu Hutu da Jin Dadi ga Abdullahi na kula da ita yana ji kamar kan wannan Cikin ne zai Taba Haihuwa Hatta da Nazifi yazo Dubata Dayazo ne ma Tana Daga Cikin Daki Taji Nazifin nabama Abdullahin Labarin suna Waya da Jidda Sosai Domin ma yace mata zai je Chan Gidan mamar nata kuma bata musa ba Duk da Tanuna Tsoron Ita Hajiya Sa"an Abdullahi yayi Tsaki yana Fadin"Karka Taka kaje ko"ina..Na bari ne Hankalina ya kwanta ne..Kwananan Jidda zata Dawo ko Taki ko taso.."
Da haka Suka Cigaba da Tattaunawa mganar kafin su Fita Tare Abdullahin bai Dawo gidan ba Sai Dare.
******
Bangaran Jidda kuwa Ta Shiga Takura Sosai Domin Hajiya Sa"a tayi Tsaye so take Ta Hana wannan Auran Jarabawarta ta Fito kuma Duka taci sakamako mai kyau,Hajiya Sa"a taji Dadin hakan sai ta Siya mata Jamb tace Zata Rubuta in taci Zata wuce Jami"ar Abuja ne.
Lokacin Datake Fadamata Haka baki Ta Tura Tana Fadin"Mommy yafa ce zai barni na Cigaba da karatuna Har sai nagaji Don kaina.."Jin Haka yasa Hajiya Sa"a Ta aika mata da Dakuwa Tana Fadin"Au har ya Hure miki kunnin da zaki Rika Ja"in Ja da mganata Hauwa'u..? Toh bai isa ba..Ba yanzu Zaki Aure ba sai kin kamallah Digree dinki Lokacin Saurayi Dan Gidan Manya zai Fito miki Wanda ya Dace Dake da kuma Ra"ayina kiyi auranki ammh a yanzu bazan yarda ki Auri wannan Yaron ba,Bai da ko Sisi,ga Hidimar kansa Data Matarsa da wanne zai ji da Hidimarki ko Da tashi Ko Data matarsa ko Data iyayensa... ? Ina Duba miki Wuyar rayuwa ce Jidda ammh naga baki ganewa Yafara Hure miki kunni da Dadin Bakinsu irin na Yaudarrarun Samarin zamani..."Ita Dai Jidda bata kara Mgana ba sai Tura baki Take Domin a Hakikanin gaskiya Nazifi ya Fara Tasiri acikin Zuciyarta Har yanzu in baikirata ba Ya shiga Busy inya Kirata Da Daddare ta Dinga mai Fushi kenan ya manta da ita,Shikuma ya Biye mata yayi ta bata Hakuri Zuwa Lokacin kuma bai sanar ma Sakina ba yaushema suka samu Zama koda wani Lokaci Tana Abuja In ta Dawomai Weekend kuma yanzu ba Irin Baya ne yana Shiga Cikin makaranta har Ranar asabar Lahadi kuma Itace yake samun Lokaci zuwa inda ya kamata Dukkansu kowa ya maida kanshi Busy in ka gansu bazaka Taba cewa Miji da mata bane Saboda ba wani Fahimtar Juna atsakaninsu.
Achan Zaria kuwa kowa yaji Nazifi zai kara Aure kuma Jidda zai Aura sai ya Jimai Murna Sosai kannensa Haka sukayita murna Suna Fadin yanzu ne Yaya Nazifi zai yi Aure Domin Auran Sakina basu Daukesa aure ba.
Sai da Jidda ta Cika Sati Biyu agidan Hajiya Sa"a kana Abdullahi ya Kirata awaya da Farko kamar bazata Dauka ba sai kuma ta Dauka Sai kuma taji Sabanin Tunaninta ba Fada ba Zagi sai ma Lallabi yace ta Dawo Gida Hakanan tana so tacemai Mommy tace bazata koma ba ammh yaki Bata Damar haka yace Gobe Ta Dawo Gida yana Jiranta kartabari yazo da kanshi ya Dauketa tasu bazatayi kyau ba Jin Haka yasa Hankalin Jidda ya Tashi ta samu Hajiya Sa"ar da mganar sai ta Rufeta da Fada tace in ya matsu yazo Tana Jiransa Sai Jidda ta Rude sanin Halin Ya Abdullahi sai ta Kira Wayar Nazifi Tana kuka Tana gayamai Shi kuma sai ya kara Firgitata yace gwara ta koma Tasan Halin yayansu Duka ba mai Wahala bane awajensa Gwara tayi yarda zatayi ta koma Haka ko akayi ta sakama Hajiya Sa"a kuka da Birgima Dole sai ta Maida ta gida Tun Tana ganin Abun wasa ne,taga dai da gaske take Ranar ta wuni kuka bata kuma ci Abinci ba Hajiya Sa"a ta Kira Lariya ta gayamata Sai gata tazo..Ganin Irin kukan da Jidda keyi yasa ta Kalli Hajiya Sa"a Tana Fadin"Kinga yaya gwara mu Tattara yarinyar nan mu Maidata..Kar Ciwon yunwa da kuka su mata illah kinga wa gari ya waya..?
Hajiya Sa"a tace"Nifa Wannan Auran ne bana so Lariya kin sani.."Lariya tace"Mu maidata..Sai mu koramai Bayani wannan karon babu Daga kafa.."Ba yadda Hajiya Sa"a zatayi Tabi Shawaran Lariya suka Tattara Jidda suka maida ta Gidan Mama Suka kuma Zauna Suna Jiran Zuwan Abdullahi Tunda Hajiya Sa"an da kanta ta Karbi Layinshi ta kirashi yace yana Hanya zai Dawo Daga wajen aiki Gashi nan zuwa.
Sai Bayan Sallar mangariba Ya Shigo Gidan,Sama sama Suka gaisa dasu Hajiya Sa"a,Ko Zama bai yi ya karkace kai yana Fadin"Gani naji kin kirani ina Fata lafiya..? Domin ina kan Hanya ne,agida ina da mara lafiya ku Hanzarta Fadin Abunda ya kawoku ko..?
Hajiya Sa"a Ranta ya baci ta kallesa Tana Fadin"Ba wata mgana bace mai Tsawo kan mganar Auran yata ce da kuka yanke...Toh ni ban yarda ba Kuma ban amince ba Jidda karatu zatayi Domin har na Fara Nemar mata makarantan Data Dace da ita.."
Tafada Tana Masa wani kallo Mirmishi ya saki kafin yace"Kin makara Hajiya bakin alkalami ya Riga ya Bushe...Mama baki Basu Mintin saka Rana bane nan da Wata uku za"ayi Dama ko baki zo ba Mama zataje ta kai miki ta kuma Miki Bayani ko bakomai mun Fita Ladan Haihuwar da kika mata..'Hajiya Sa"a ta mike a Fusace Tana Fadin"Kambu a sakama yata Rana bani da labari..? Wlh baka isa ba in kuma kukace sai anyi Wlh zan makaka a kotu.."
Kafada ya Zakuda yana Fadin"Fine..Dama chan muka je Dayafi wannan kananan mgangaun da kike...Ni bani da Lokacinki Bawai Domin bansan irin Amsan da zan gayamiki bane sai don Ni ba Haka Tarbiyata take ba ko ya Babba yake ina bashi Girmansa ba Domin haka ba Wlh ke kanki baki isa ki Tsaya agabana kina Fadamin haka ba..kuma ki Bude kunnenki kiji dakyau Auran Jidda Nazifi ba Fashi in kinga ya tashi,Toh Dayansu ne yamutu..Gwara ki Shafa ma kanki lafiya..".
Cikin Harzuka tace"Au haka kace..? Kai ya gyada kafin yace"Eh haka nace...Mama ki basu Sakon zan karisa gida sai da Safe.."Daga haka ko waiwaye ya Fice da Auwal yaci karo a tsakar gidan wanda Ransa yayi masa Fari na Irin amsan daAbdullahi ya basu Mama akabari da basu Hakuri Mintin ma da Biskit din Ko kallonshi basu yi ba Hajiya sa"a ta warci Hannun Lariya suka Fice Jidda da mariya na Ciki Jidda sai kuka take Mariya na Bata baki ammh acikin Ranta Tana Jinjina ma karfin Halin Hajiya Sa'a.
*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*
*Shakira...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
_Gabadaya Shafin na yau Sadaukarwa ne gareki Bestyna *SA'ADATU ALKALI D/TSAFE..*❤️Ina Rokon Allah yayi Riko Da Duka Hannayenki Halinki na gari ya Biki..Alherin Allah yakai miki Har gadon Barcinki.._
*027*
"Tunda Mama Taji mganar Kai Abdullahi kara da Hajiya Sa'a tayi ikirari sai Hankalinta ya Tashi ammh bata Nuna ba sanin Halin Abdullahi na kafiya da Dakiya Tasan bazai Fasa ba kuma Bazai yarda anemi Sulhu ba sai dai in Hajiya Sa"an ne da kanta Ta nemi Sulhu.
Shiyasa Tun Safe batare da ta gayama Kowa komai ba ta Fita ta bar Gidan Auwal da jidda nata Tambayanta inda zata tace Ba Dadewa zatayi ba yanzu zata Dawo Tana Fita Bata zarce ko"ina ba sai gidan Baba Wada ta sameshi acikin Dakinsa,Inna Abu Ta Shiga tagayamai Zuwa Mama ita tamata iso Har Cikin Dakinsa Bayan sun gaisa ne Mama taKoramai Jawabin komai Ta Karishe da Fadin"Don Allah ina so ka Shiga Mganar nan Mallam..Kasan Halin Abdullahi bashi da Taushi Kuma Ra"ayi ne Dashi Gwara ka Shiga maganar kafin Hajiya Sa"a ta aikata Abunda tace kuma abubuwa suzo basu yi Dadi ba.."
Baba Wada yace"Ashha..Abu dai Baiyi Dadi ba...Ai ba"a Haka yanzu da baki gayamin ba Shi Abdullahin shuru zai yi kenan..?karki damu Insha Allahu hakama Bazata Faru ba ai shi Aure wani Abu ne na Ubangiji kuma Sulhu alheri Insha Allahu Tunda kin nemu Da na Shiga Mganar zan Shiga.."Mama Taji Dadi tayi ta godiya sai Bayan Tafiyarta ne Baba wada ke korama Inna Abu Abunda ke Faruwa baki ta Rike Tana Fadin"Oh ni Abu yau naga Abunda yafi zare tsayi..?Kajimin karfin Hali Barawo da Sallama wato Ita Tayi kudi bari ta Nuna ma Mutane karfin arziiki..Toh in ta Fasa kai Abdullahi kara Kotu Ta Raina Ubanta kuma Auren Hauwa"u da Nazifi ba Fashi da yardan Allah.."Kallonta kawai Baba wada yake yi yana Kada kanshi Afili ya Furta.."Mata..!Mata..! Sai a barku kawai.."
Kai Tsaye Baba wada ya Kira Abdullahi a waya yace in ya tashi Daga wajen aiki ya Biyo yana son Ganinsa Haka kuwa akayi yana Tashi kafin ya Karisa gida, ya Biyo Tare suka Shiga Sallar mangariba sai da suka Fito kana Baba wada yamai mganar da Mama Tayimai Kai Tsaye Abdullahi yace"Eh Baba..Ku barta ta kainin Kotun ina Jiranta Wlh.."
Baba wada yace"A"a baza"ayi haka ba Abdullahi in Rai ya baci Toh Hankali ke Nemoshi..Bazamu Biyemata ba ita mace ce mai Rauni kuma Zuciyarta bata da wani Dogon Nazari In ma mgana zamu yi ai ba da ita zamuyi ba..Tana da Wakilai da waliyyai akwai Iyayenta maza na Bangaran Uba dana Uwa Saboda haka na yanke Shawaran zan kira Nazifin da kaina namai Bayani Ko Ranar asabar ko Lahadi dukkamu zami Taci Chan samaru gidan Uban ita Sa"an Mu samu Koda wani Babba wanda ya isa da ita mu koramai Jawabi na Tabbata Shi zai Fahimcemu harma kaga an samu Masalaha.."Kamar Abdullahi zai yi Gaddama sai kuma ya Duba Matsayin Baba Wada awajensu Shiyasa ya amince da Shawaran Baban wadan suka rabu kan Sai ya Kira Nazifin sunyi mgana.
Nazifi kuwa Dama Jidda ta gayamai komai Domin ajiyan yayi ta Kiran wayarta bata Dauka ba sai zuwa Chan ta Kirashi Cikin Damuwa Tana kuma kuka sai yake Tambayanta lafiya ita kuma ta Gayamai Shima bai wani Damu ba sai ma yakama Dariya Har Jiddan taji Haushi sai kuma ya koma yana Lallashinta da Bata baki,koda yaji bai Kira Abdullahi ba Domin ya Tabbatar wannan ba wata mtsala bace awajenta kuma Mganar zata kaishi kara wannan Shirmen banza ne kawai shiyasa ya Share Mganar ko Abdullahin bai kira ba Sai kuma gashi Baba wada ya Kirashi yana mai Bayani Jin haka yasa Bai nunamai yaji mganar ba suka Rabu da Baba wada kan Ranar asabar zai Shigo Saboda in ya Shiga makaranta bazai Dade ba Baba wada yace Shikenan Bari suyi mgana da Abdullahi.
Koda Baba wada ya Kira Abdullahi yamai bayanin yadda sukayi da Nazifi bai Ce komai ba yace Allah ya kaimu Duk da Ranar Shima zai Shiga Cikin makaranta Ammh bazama zai yi ba,Nan suka Rabu kan sai Ranar asabar din.
Ranar asabar kuma Tun 7am Na safe Nazifi ya Shiga Cikin makaranta,Yabar sakina agida Jiya tazomai Weekend ammh ya Fita ne ma Tana barcinta Shi kuma bai Damu da ita ba Domin yanzu kowa ta kanshi yake,Bukata indai ba Sakina ta Nuna Tana Bukatarsa ba bai Cika Zafafama kansa ba azumi ne yana Kokarin yi kuma sanin bazai samu abu ba Toh sai ya Dangantashi Da baya so kawai ya Shiga Harkokinsa Dayake kuma Baya samun zama daya dawo gida Sai barci sai kuma gobe yanzu kuma jidda ta Shigo Rayuwarsa Su Raba Dare suna waya Hankalinsa kwance In yana officema suyi waya kuma Alhamdulillah Tana Debemai kewa Sosai Shiyasa yau din ma Daya Fice bai bi takanta ba Tunda ya Leka Dakinta yaga Tana barci kamar wacce tayi aiki. aikin Datayi Dayane aikinsa kuma ita ta nuna She is ready shiyasa kowa ya Sauke nauyin kowa yana ma Tunanin kila shi ya Dawo da ita ko kuma Domin Taga ya Daina Nuna Damuwa da ita ne kamar Baya Ohon mata,acikin Ranshi yasama ko Mganar Auransa Ya taso bai da Matsala Domin sai ka Damu da mijinka kake Jin Labarin zai yi Aure ka Nuna Damuwarka Toh Sakina dai Baya gabanta Ballatana ma ta Damu Shiyasa yake taHarkokinsa ko ajikinsa bai yi Tunanin ya Tattauna komai da ita ba sai Abun yazo kusa.
Koda ya Shigo Zarian Har Abdullahi ya Shiga Makaranta ya Fito nan gidan Baba wada suka Hadu,ko Gidan Mama Abdullahin bai Shiga ba Daman ba Da mashin Dinsa yazo ba Tana gida Ta Haya ya hau yaje makaranta ya Dawo Nazifi na zuwa Gida kawai ya Shiga suka gaisa daasu Inna Abu ya Fito suka wuce Baba wada ke ta Nuna Hanyar Tunda bai manta ba,da zasu zo neman Auran Sa'an Shida marigayi Usaman Direba suka zo,Duk da kuma an kara gine gine,Gidan yaso ya bace Masa sai kuma ya gane sai gasu Kofar gidan Mahaifin Hajiya Sa"a anihin Babban Gidansu.
Yaro suka aika sukace don Allah a musu sallama da wani Babba ba Jimawa sai ga wani Yaro matashi kamar sa"anin su Abdullahin ya Fito bayan sun gaisa sai Baba wada ke kara Tambayanshi nan ne gidansu Sa"adatu,wacce taje makka..? Yace eh nan ne gidan sai Baba wada yace Toh don Allah yana so yayi musu sallama da wani Babba Cikin iyayen ita Sa"an sai Matashin yace gaskiya Duka sun Rasu sai wani kanin Babanta Guda Daya Baba isuhu Shine mahaifinsa ammh Shi baya Fita sai dai su Shiga Saboda yana Fama da Ciwon kafa Jin haka yasa Baba wada yace yaje yayi musu iso Suna son ganinsa ne Ba Gaddama ya koma Ciki bai Dade ba yazo yayi musu Jagora zuwa Cikin Gidan har Dakin da Baba isuhu ke kwance yana Jinya.
Suna Shiga Dakin Baba wada ya ganeshi Saboda yana Daga Cikin wadanda suka basu auran Sa"an,Bayan sun gaisa sun mai ya Jiki sai ya nuna Bai ganesu ba Baba Wada ne ya gyara zama yayi mai Bayani Sosai yarda zai gane Kai ya Fara gyadawa yana Fadin"Masha Allah..Anyi haka kuwa..Kwanaki ai har nan din Sa"ar ta kawomana yar wajen nata mai ma Sunanta ma..?
Baba wada yace"Hauwa"u suna Kiranta Jidda.."Yace" kwarai an yi haka kuwa Sannunku da zuwa.."Baba wada ya amsa da yauwa kafim Matashin nan ya Dawo da Ruwa da lemo,Basu bi ta kanshi ba Baba wada ya Fara kora Jawabin Abunda ke Tafe dasu Sai da ya gama kana Ya kara da Cewa"Shiyasa mu ka yanke Shawaran gwara muzo Gidan Iyayenta domin mu samu Babba wanda zai Shiga mganar Kasan mgana da mata sai a Hankali Tunda an kasa Fahimtar Juna.."Baba isuhu yayi Shuru kafin ya Gyada kai yana Fadin"Topha..Haka akayi..?gaskiya Sa"a bata kyautaba kuma Tayi Rashin Hankali Kuma mu nan bata gayamana ba Koda yake sai Tayi sati bamu ganta ba Daga ita Har Kanwarta lariya Suna Chan Sunyi Gidajensu suna zaune sai sun lekomu kana ammh Duk da Haka zan Shiga mganar Tunda har yau matsayin Uba nake garesu bari Mugani.."Yafada yana kwalama ma Matashin Daya kawosu Kira mai Suna Musa Sai gashi ya shigo kallonsa yayi yana Fadin"Kana da Lambar Sa"adatu..?
Kallon Babansa yayi yana Fadin"Yaya Sa"a Ta Chika..? Yace mai eh sai yace yana da itaDa sauri yace"Yauwa maza ka Kiramin Ita kabani na mata mgana ba.."Ba musu ya Kirata Dayake Tana da lambarsa har gidanta yana zuwa tana mai alheri Tana ganin kiran ta yanke ta Kirashi Shi kuma Bayan sun gaisa Yace Baba isuhu ke son mgana da Ita sai ya mikamai Bayan Sun gaisa Baba isuhu yace in Tana gida Ta kariso yanzu yana son ganinta bata kawo komai Tace gatanan zuwa.
Cigaba da Tattaunawa akayi Tsakanin Baba Wada da Baba isuhu,Har ya nuna mai Nazifi a matsayin Mijin da Jidda Zata aura yayi ta saka albarka ko Minti Talatin ba"ayi ba sai ga Hajiya Sa"a tayi matukar mamaki Data ga su Baba wada,Sai kallon Abdullahi Take yi Shi kuma sai ya kauda kai Zama tayi suka gaisa da Baba isuhu kana ta waiga suka gaisa da Baba wada kafin Baba isuhu ya Fara yi mata Fada da Nasiha mai Ratsa jiki ya Dade yana Nutsar da ita Kafin ya Dora da Fadin"Sa"adatu Taya zaki Hana araya Sunar ma"aikaci..?ke ba abun Farincikin bane Yarki ta samu Miji kamar wannan ba..? Yara nawa ke neman Dakin kan nasu basu samu ba ammh ke kin samu kina wasa da Damarki haba Sa"a Don Allah kibari kinji ko..? Ke yanzu Uwace ba yarinya bace bai kamata kina Irin wannan Abun ba Don Allah ki Janye wannan mganar ta zuwa kotu haka sam bai Dace ba ai kun zama Daya yanzu keda Kika bar kasar nan baki Dade da Dawowa ba bq Abun ki Godema Allah bane Masha Allah yarinyarki tataso Cikin gata kamar Tana gabanki toh menene Abun damuwa..? Ai Abun Farinciki ne ace yau sa"a kina Raye kin kai yarki Dakin Auranta kin saka mata albarka."
Kanta na kasa ta Dago sai da ta karema Nazifi kallo Dakyau kana ta muskuta Tana Fadin"Baba nifa bana ki bane..Mganar karatun Jidda ne ina da Burin Tayi karatu gaskiya.."Baba wada yayi mirmishi yana Fadin"Toh wa kika ji yace bazata Cigaba da karatunta ba..? Na tabbata Nazifi zai iya biyama Jidda ne ko nawa ne tayi karatu Saboda haka baki da wannan mtsalam.."Kai Tsaye Sa"a tace"sai yayi alkawari bana so sai na amince kuma Daga Baya mganata ta Sauya.."
Dariya ta kama Baba wada ya murmusa Baba isuhu yace"To Shikenan kai kayi mata alkawarin zaka bar Yarinyarta ta Cigaba da karatunta Tunda Bukatarta kenan.."Nazifi ya kalli Abdullahi shi kuma ya Dagamai kai Sai ya Sunkuyar dakai yana Fadim"Insha Allahu..Indon wannan ne tuni mun gama mgana da Jiddan da Tuntuni ma Tagayamin mtsalan da bamu kawo yanzu ba.."
Baba isuhu yace"kinji ko..? Don Allah sa"a datu adinga Hakuri kinji ko..?ina Fatan shikenan ba wata mgana.."Kai ta gyada Tana Fadin"Insha Allahu Baba nagode.."Yaji Dadi ya Dinga saka mata albarka,Kudi ta Debo a jakarta ta zube gabanshi ta Fice suma Kudin suka bashi kafin su mai Sallama Yayi ta godiya yana saka musu albarka,kana suka mai sallama suka Fito a Tsakar gidan suka Hadu da Hajiya Sa"a Nazifi ne ya tsaya ga gaisheta da Umarnin Baba Wada ko bakomai Surukarsa ce ta Chanchanchi Darajawa Dakyar ta amsa sai Hararan Bayan Abdullahi take wanda ma Bai san Tanayi ba.
Nan dai gidan suka Barta suka koma Daga nan Gida suka maida Baba wada kana Daganan suka koma Gidan Abdullahi sukaci Abinci Wanda Harira ta taimaka Hafsah tayi Daganan Nazifi ya kara Dubata masha Allah tayi kyau taki kiba kamar ba ita ba Daganan kuma suka Wuce Wajen ginin Nazifi chan sukayi sallar Azahar,ginin Shima yayi nisa Sosai ammh Nazifi yace kafin bikin in bai gama ba Haya zai kamama Jidda Shima Abdullahi Sunje Gra,Shima kadan ya Rage gida bai kamallah ba, An gama komai SauraFenti da kuma intelock din tsakar gida da kuma Kayan wuta,Ammh acikim Ranshi yana Tunanin kila komai ya Tsaya kenam sai kuma Bayan Bikin Jidda Tunda Hidimarta ce ke gabansa Allah Barshi bayan anyi sai ya maida Hankali ko loan zai iya ci a Wajen aikinsa Ya karisa komai kafin Hafsah ta Haihu Allah barshi a rika Cireewa a albashinsa.
Sai 2pm na Rana suka Rabu da Abdlullahi a gidan Mama ya barsa ya koma gida Shi kuma ya Shiga Dakin Auwal jidda tazo ta sameshi sukayi Hira Duk dai kan mganar tsare tsaren Biki ne La"asar nayi yayi mata sallama Ya wuce bayan ya zo mata da leda guda na Shopping din kayan kwalliya jidda sai wani yanga ake Mariya da Auwal na mata Dariyan Da tace bataso Mama ce ke Shiga Cikin mganar tace akyalemata autanta Da Daddare sai ga Baba wada yazo Shi ya kora ma Mama yadda komai ya Gudana yace ta kwantar da Hankalinta komai ya wuce taji Dadi Har ranta Tana ta mai godiya.
*******
Tafe Tafe kwana Nesa Wuni yana karewa muna Shiga kwana,kwana yana karewa muna Shiga Satittika,Satittika yana kwarewa muna Shiga Shekara da Haka muke Cinye Sauran kwanakinmu a Duniya Bamu sani ba Allah ka Bamu Dacewa Ameen.
Gashi yau Bikin Jidda Sauran Sati Hudu Cif ta kowani Bangare Shirye Shirye keta Gudana Ta Bangaran Abdullahi Kuwa Kudi ya Bada Mama da Ita kanta Jiddan da Subai"atu suka je Jaji suka Zabo mata Kujeru da gado da Katifa masu kyau da Tsada, masu kyau Ita kuma Zannira tayi mata Gadon karfe da kuma kayan Kallo sai Subai"atu datayi mata Fridge,da Labulai sai Center Cafet,Hajiya Sa"a kuma Taga ba Sarki sai Allah ta saki Tunda dai Auran nan na yarta ce ba na wani ba Tuni ta watsar da komai ta shigo Cikin gida anayin komai da ita,shi kanshi Nazifin yanzu a gidanta ya zama Dan gida Tunda Tun bayan Faruwar haka indai yazo Zai Dauki jidda Ta rakashi Suje ya gaisheta Tun Tana wani basarwa Har tazo taDaina Hakama Hajiya Lariya itama yaje gidanta wajen Sau Biyu Sun gaisa ita ta sakama Jiddan ta Rakashi Family Hause din Mamarsu ya gaisheshi Suka ganshi Harda Babban gidansu na na Barayin Inda su Nazifin suka Taba zuwa Wani Lokacin ma in ya Shigo Garin a Chikan yake samunta in taje ma Sa"ar Weekend,Yanzu kuma Tsakanin Jidda da Nazifi wata irin Soyayyace mai karfi da Shakuwa ta Shiga Tsakaninsu in ka gansu sai kace Damam chan Masoya ne Nazifi dan Rayuwa ne yasan kan Mace Sosai kawai waje ne bai samu ba sau yanzu matukar so da kulawa yake nuna ma Jidda itama Haka sai dai Tana Kokarin Bashi Girmansa a matsayinsa na abokin yayanta gefe Daya,kuma Suna Shan Soyewarsu.
Goggo Habiba 50k ta kawo Gudummuwa Da nata dana Ya"yanta Domin Bata da bakin Godema Ya"yan yayan nata Kowani Sha"ani da Jiikinsu da aljihunsu ake musammanma Yaya Abdullahi sai Ammi ma 50k Hafsah ta kawo Mama taji Dadi Harda Hawayen Dadi,Sai Umman Sadiq itama ba"a barta a Baya ba 30k ta aiko ma Abdullahi tace Gatata Gudummuwar nan Mama ma yan"uwanta sun Hadamata Dubu 50k Dashi a kahada akaje kano akayi ma Jidda Siyayyar kayan Kitchen da Duk Abun ya kamata Tunda Flat House ne mai Dan Girma Nazifin ya kama anan Famwaki Tunda ginin dai bai gamu ba nan za"a yima Jidda Jerenta in sun gama Cin amarsun zai mai data kaduna,Daman Dubaran Hakan in ya tashi komawa Sabon gidansa basai an Wahala ba Tunda wanchan gidan Sakina Ta Cikashi da kayanta sai ya barmata Sai ya yanke Hukunci na Zaria gidan Jidda ne,In sunzo basu da mtsala wajen Sauka Chan kaduna kuma ko Dakinsa Zasu zauna Suyi Rayuwarsu Cikin Soyayyah da kaunar Juna.
Hajiya Sa"a Tazo Ta Tambayi Mama Abunda Ba"a siya ba Mama tace komai an Siya sai Abunda ba"a rasa ba Wannan Dalilin yasa Mama ta mata Bayanin komai kawai sai takoma Gida sukayi mgana da Lariya sukaje suka Siya katifa da Fridge Babba mai Biyu sai Gas na Zaune mai Shidda,sai Labulai da kuma Zannuwan gado,Dama tana da wasu Datazo mata dashi Daga Chan Saudiya,sai wasu Expansive kololi masu kyau da Tsada Data kara mata,sai Home Theater,Sauran Abubuwa dai masu Tsada ta Siya dasu Dinning Kuma Bayan sun yo Siyayyah Direct Gidan Mama ta wuto Dashi Mama nata Godiya Sosai Abdullahi ma Dayazo ya gani bai ce komai Ba Duk da yanzu ba irib da Bane suna gaisawa sama sama da Hajiya sa"an.
Bangaran Amarya da kawayenta Kuwa Rumana ne sai wasu Wadanda suka gama Makaranta Tare,sai Mariya 50k suka nema ya basu na Walima da Shagalin Biki,Kayan akwati kuwa Wata matar abokinsa ta Hada komai akwatuna Bakwai,Shake da kaya sai Wanda yagani Da kanshi ya kwaso ya kai gidansu Su Inna Abu suka gani,Sai da Biki ya Rage Saura kwana Goma kana Aka Hadu aka kai kayan Yan"uwan Inna Abu da makota sai kannensa Suka kawo kayan Gidan Mama acikin masu karban kayan Harda Hajiya lariya Sa"a dai Tana gida Masha Allah kaya Sunyi kyau Sosai Dayake Abun Gidane haka aka gama ganin kaya ana saka albarka Sunci Sunsha Harda Tukwaici aka basu suka Ki karba sai da Zannira ta matsa kana suka karba Dayake Tazo Ranar da za"a kawo kayan Dasu Hafsah wacce Cikinta dan Wata Shida gayinan ya Fito yayi Girma kamar CikinFari.
Baba wada ne ya Kira Nazifi yana Tambayanshi yako gayama Matarsa Sakina yace "A'a ammh Cikin Satinan zai gayamata.."Fada Baba wada ya Fara mai yana Fadamai bai kamata ba Tana da Hakki ya gayamata zai kara aure yace Insha Allahu zai gayamata Dama yayi Niyyar sai ya samu wasu Kudi a Hannunsa ne ya Damkamata Na siyayyarta in ta karba Shikenan in bata karba ta Rasa Da Haka suka Rabu da Baba wada Wanda shi Daman ya Riga ya Bari sai in tazo Weekend din wannan Satin Tunda Rabonta da kaduna wajen Sati uku kenan Toh a ina zai ganta..? Shiyasa bai Fadamata ba har yanzu...!
******
*Kaddara ta sake Hadasu...*
Yau Ta kama Jumma"a wacce tayi Daidai da Saura kwana Takwas Bikin Jidda da Nazifi da misalin karfe 6:30pm na yammah a Kofar main get na ABU SAMARU,yan makaranta ne Birjit suna Tsaye wasu kuma Suna Tafiya ne,Ayayinda wasu kuma ake ta zuwa Daukansu,Kowa dai kagani yana ta Haraman komawa gida ganin Ga Mangariba ta kawo Jiki kuma Dare ya Fara Shiga.
Tana Tsaye a bakin Titin Duk inda Hankalinta yake yakai kololuwar Tashi ganin Duhu yayi bata samu Bus ba,Koda tazo duk sun Cika,agogon Fatan Dake Hannunta ta kaima Duba Lokaci Daya ta saki karamin Tsaki acikin Ranta tana jin Takaichin Rashin samun accomadation da batayi ba,dayake ta Shiga aji Hudu da ta samu mai zai jamata wannan Jiran,Yanzu ita Tunaninta ma Daya koda ta samu Abun Hawa Lokacin da zata bata kafin ta kai gida Shine Abun Tunaninta,Sake sakin Wani Tsakin Tayi tana gyara zaman gyalen Abayar Dake Jikinta.
Doguwar mace,wacce ke sanye da wata bakar abaya da gyalensa tayi Rolling,sai Kafarta sanye da wani bakin Takalmi mai tudu Katadarta Rataye da wata bakar Jaka sai Hannayenta Dauke da wasu manyan littafai na karatu Fuskarta sanye da wani Farin gilas na gayu,Daga ganin Fuskarta Tana Cikin Damuwa Duk da bata son Hawa mashin Sai ta yanke Shawaran Bari kawai ta Hau mashim Din Tunda bata da mafita Hannu ta sanya tana Tsaida Masu mashinan ammh su kansu sunki Tsayawa.
Fitowar Abdullahi kenan Daga Cikim makaranta Shima ya tsaya yin wani Abu ne yasa yakai yammah haka,Ya fito kenan yana Kan Mashin dinsa kamar wasa ya Hangota tana Tsaye kamar tana Tsaidashi har ya wuce Sai kuma yayi wani Tunani kawai ya Juyo yana Tunanin mace ce kuma ga Dare ya Kawo Jiki Tana Bukatar Taimako Shi kanshi bai Taba Daukan wata mace a mashin dinsa ba in ba Hafsatu ba ammh sai gashi yau ya tsaya gaban Wata mace yana Tambayanta inda zata Abunda bai san ya akayi hakan ta Faru ba.
*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*
*Anitha...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*028*
"ko a mafarki Taji wannan Muryan bazata Taba mantawa da ita ba Muryan Datake kwana Da ita Tatashi da ita cikin Ranta,Muryan da ko Mutuwa tayi ta Dawo Bazata taba mantawa da ita ba..
Idanuwanta Dake Cikin glass ta Zaro Tana kallon Abdullahi Shima ganin irin kallon Data kemai ne yasa ya Zura mata ido yana Binta da kallon mamaki Gefe Daya kuma na Zuciyarsa na so ya Tuna inda ya san Fuskarnan Tunda wajen akwai Wadatar Filitu masu Haske sun Haske Fuskarta Sosai.
Ya Bude baki yana Shirin yayi mgana Wata Budurwa Dake karisowa kusa dasu Ta kira Sunanta.."BARKAT SHEHU...'"Tafada Tana Dafa kafadarta Lokaci Daya Da Mamaki Abdullahi ya kara Bude Manyan Idanuwansa yana kallonta sai da aka Kira Sunanta ya Tuna inda ya santa Gidansu Salisu Karya wuya yayi yana kallonta yadda ta Juya tana mgana da wacce ta Kira Sunanta.
"Barkat kin samu Leap ne..? Zaman Littafan Hannunta Barkat tagyara tana Fadin"A"a abokin Yayana ne zai Ragemin Hanya..Dare yayi gashi Ban samu Bus ba.."Yana jinta Sai da ya kara kallonta Cikin mamaki acikin Ransa kuma yana Fadin komai nata bai Sauya ba,Sallama sukayi da yarinyar kana ta kariso kusa Dashi Tana kallonsa Ido Cikin Ido Tace"Tudun Wada zani.."
Ta fada Cikin yanganta da kuma Jin kai,Shima kai tsayen ya kalleta yana Fadin"Ok...Allah ya sa zaki iya Hawa mashi..Kinsan Abunka ga Talaka da ita muke Lallabawa..."Kai Tsaye yana kallon Gefenta Saboda bayason kallon kwayan idanuwanta yana jin Wani iri acikin Ranshi.
Kai ta Rausayar Tana Fadin"Waye Ubana da zanje Bana Hawa mashin..? Muje Allah ya kaimu lafiya..'Jin haka yasa ya karkata mata Mashin Din yadda Zataji Dadin Hawa Rigarta ta Tattaare ta kasa,Dama kuma Barkat bata iya Hawa Mashin ba sam,Ta Yunkurawa ta Hau sai Littafan Hannunta suka Subuce suka Fadi kasa,Tsayawa tayi Tana kallonsa Cikin Wata Shagwababbiyar Fuskar da bata san Tana Dashi ba Saurin kauda kai yayi yana Fadin"Kamar kaya yayi miki yawa ko..?kwaso na Rike miki Anan gaba.."Da sauri ta Duka ta Tattaro ta mikamai ya karba Tana kallonsa Tace'Nagode..."
Duk yadda yayi mata Wajen Hawa sai da ta kusa Faduwa Yayi Saurin Riko Kafadanta,ita kuma sai ta Cakume Bayansa Dukkansu Sun ji Sanda bakon yanayin ya Ziyarcesu mussmman ma Barkat wacce Taji Abun har Cikin Kokon Ranta Saurin matsawa gaba yayi Saboda Bayason Kusancinsu Shima Tsausayi ne ya kaishi Daukan Wata mace a saman Mashin Dinsa ammh bai sababa.
Sai da Ta Daidaita zama kana suka Fara Tafiya ga Iska yana ta kadawa Sai Barkat ta kamkame Jikinta tana Kallon Bayan Abdullahi Cikin Wani yanayi na Shauki da muradi mai Girma acikin Zuciyarta kuma kara godema Allah take daya Hadata da Sanyin Idanuwanta wanda yasa Bata ganin kowani Namiji da gashi sai shi Tun Ranar Data ga Abdullahi bata kara Sukuni ba Tun Tana Daukan Abun Wasa Har ta Fahimci da gaske ne,,Tasha ta Kwanta tayi ta kuka ko kuma ta kaima Allah kukanta Cikin Dare kan Allah yaye mata Abunda Take ji game da Abdullahi ammh Abu yaci Tura,Sai ma karuwa yake Kwanakin nan duk ta Rame ta lalace Ga karatu ga Tunanin Abdullahi Yan"uwanta da Mahaifiyarta suka Shiga Damuwa Sosai sanin Halin Barkat,wacce Bata iya Bayyana Abunda ke Damunta Bata da Hayaniya Sosai Hajiya Amina Tayi Tambayan Duniyan nan Ammh Barkat ta kasa cemata komai Harta ya"yansu Salisu sai da ya Tsareta da Tambaya shima Taki gayamai sai yayi mata Nasiha ya kyaleta,Taji saukin Abun kwana Biyu,saboda Tana addu"a sosai ammh bawai Soyayyar Abdullahi ta Fita Daga Ranta ba sai gashi Alokacin Da tagama Fidda ran Kara ganinsa Allah ya Hadasu Lalle Allah Abun Godiya ne.
Kamar Daga sama Taji muryansa.."Meyasa kike kai Dare a cikin makaranta alhalin Kina mace..? Cikin Sanyin muryanta tace"6pm na tashi lacture,kafin na Fito Daga Cikin makaranta Duhu ya Shiga nayi kokarin na samu Mota Bansamu ba.."Abdullahi ya kada kai yana Fadin"Gaskiya akwai Hadari a matsayinki na mace ki Rika kaiwa Dare a irin wannan yanayin.."Kara Saussauta Murya tayi Tana Fadin"Insha Allahu..Yau din ne ma Dama in Dare yayi min Wajen Bahi nake zuwa na kwana Tunda ni ban samu accomondation ba.."
Bai kara mgana ba ya Cigaba da Tukinsa Kimanin Minti Talatin sai gasu Har Kofar gidansu,Barkat din Ta Sauka ya mika mata Littafanta ta karba Tana kallonsa kafin tace"Nagode Kwarai..Allah ya saka da alheri.."Bai mata mgana ba sai ga Salisu engr.ya Fito Daga Gidan ganin Abdullahi yasa ya saki Baki yana Kallonsa kafin ya Kariso yana Fadin'"Wa nake gani kamar Abdullahi Usman..?
Abdullahi yace"Nine Alhaji Salisu..'Yafada yana yar Dariya karisowa yayi sai suka kusa Cin karo da Barkat Cikin Mamaki yace"Ke kuma Daga ina..? Kafin Tayi mgana Abdullahi ya Rigata da Fadin'"Daga makaranta....Ni na kawota na ganta bakin makaranta ga Dare.."Salisu yace"Ayyah...Mungode.."Daga haka ya bashi Hannu,suka kara gaisawa Yana mai murnan Auran Jidda da Nazifi sai da Abdullahi yaji kunya ammh Shi Salisun bai Nuna komai ba Domin a yanzu hakama Shigarsa Gida zencen suke da Hajiya Amina tace matar Mutum kabarinsa,Nazifin da kanshi ya Kirashi ya gayamai Bayan ya Turamai katin Bikin..
Bayan Sun gama gaisawa sai Salisu yace Abdullahi ya bashi Lambarsa bai Dashi Barkat Dake labe Daga kofar gidansu Taji kamar an sakata acikin aljannah Domin Tasha Satar wayar yayan nasu Domin ta Duba Lambar Abdullahin,Sai dai tayi Rashin sa"a ta Dauki na wanda bashi ne ba,Yana karantoma Salisu itama Dagachan tana Daukewa,Murna Ta Cika mata Ciki Sosai Jin Sunyi sallama Abdullahi yaja Mashin Dinsa yaTafi Shi kuma Salisu ya Tunkaro gida,Jin haka yasa ta Zura da Gudu zuwa Cikin Gida.
Hajiya Amina da Bahijjat dake Falo Suka Dago Suna kallonta a Razane Hajiya Amina tace"Ke Barkat lafiyanki kuwa..?meya faru.?Baki Barkat ta kama Tana Fadin"Hajiya magen gidansu Maimun ne ta Biyo ni.."Tsaki kawai Hajiya Aminar Taja ta kauda kanta gefe ita kuma Bahijjat Dama Assigement Take sai ta maida kanta ta Cigaba da Abunda Take ganin haka yasa Sum Sum Barkat ta Karisa Dakinsu Tana zuwa ta Fada kan Gado Tana Fadin"Finale..yau dai na samu Burin Raina...Insha Allahu Burina zai Cika..."Ta ke Fada Cikin wani Tsantsan Farinciki Tana Rumgume Duka Hannayenta a kirji adanuwanta a kulle tana Tuna Abdullahi da komai nashi.
Abdullahi kuwa koda ya koma Gida Hafsah na Tambayansa taga yayi Dare sai yace mata ya tsaya wani Abu ne,alwala yayi yayi sallar mangariba da Isha"i ba Dadewa sai ga Auwal ya kawomai sakon katin Bikin Daya sa aka Bugamai guda 100 wanda zai Rabama Mutame,Guda 50 ya Cire yabama Auwal Sauran yace ya Dauka Sauran kuma ya kai ma Mama Ya Dade agidan sai Wajen Goma ya Tafi Gidan Mama.
********
Tun Jiya Nazifi ya Kira Sakina awaya yana Tambayanta yaushe zata Shigo..? Abun ya bata mamaki sanin yanzu Nazifi ya Daina Damuwa da Zuwanta da Rashin Zuwanta,Sai tacemai sai Gobe asabar zata Shigo yanzu hakama Tana kano ne,Mamaki ya Cikashi Domin Shi dai bata gayamai ba bai Nuna mata komai ba yace Allah ya kaimu.
Washegari sai Wajen 1pm na Rana Sakina ta iso Abun da ya kara Bata mamaki ganin Nazifi ya Sauya Funitures din Falon Da komai da komai mamaki ya Cikata Sosai sai dai kuma koda ta Shigo Nazifi baya gidan Zuciyarta kuma ta kasa Natsuwa a acikin Zuciyarta kai Tsaye ta Daga waya ta Kirashi tace Gata Ta Shigo ammh baya gida yace mata yaje wani Waje ne ammh gashinan zuwa.
Shuru Shuru ba Nazifi ba Dalilinsa Zuciyarta ta kasa Natsuwa ta Sake Kiranshi sai bai Daga ba,Sai bayan Isha"i kana Nazifi ya Shigo Gidan,Ya iske Sakina Afalo Tana aiki Bisa System Dinta Tana ganinshi Ta Mike ganinsa da Ledoji,Kan Center table din Falon ya ijiye yana kallonta kafin yayi mgana Ta Rigashi da Fadin"Wai ina ka Shige ne..?
Sai da ya zauna Kujeran Dake kusa da ita kana yace"Wani Uzuri ne ya Tsaidani..An dawo lafiya..?"Komawa tayi ta zauna Tana amsawa Lokaci Daya kuma Tana kallonsa Shi kuma sai ya basar da ita ya waiga yana Fadin"Baki Dafa komai bane..?Kai Tsaye tace"Me zan iya Dafawa..? A gajiye na Shigo gidan.."Bai yi mamaki ba yace"Eh kwarai aikin Mijinki Shine na gajiya ammh aikin gwannati bana gajiya bane Tunda gashi nan Shi na Shigo na samu kina yi.."
Bata Kalleshi ba tace"Wani aiki zan Turama Manaja Tun Shekaran Jiya yake Jirana ..kuma kasan yanayin aikina bai kamata kana yawan korafi ba.."Baki kawai ya Tabe yana Fadin"Wazan ma korafi..?ko nayi Ba"a karbansa Shiyasa ma na kama kaina..Allah bada sa"a ma"aikaciyar Jarida Hajiya Sakina Badamasi.."Cikin mamaki Ta kallesa sai ya Fara mata Dariya Dauke kai Tayi Tana bin Falon da Kallo Take Fadin"Naga Gida yasha gyara...Hala wasu kudade ka samu..?"
Kishingida Yayi Jikin Kujera yana Fadin"A"a me kika gani..? Abunka ga Talaka Bawan Allah Na Sauyasu ne ganin Tunzuwanki basu samu Chanji ba...."Yafada Lokaci Daya yana Fito da wayarsa yana Dannawa kai ta Jinjina tana Fadin"Saura na Dakunan barcinmu.."Kansa na Bisa wayarsa yace"Naki ne ya Rage..Nima nawa na Sauya komai.."Ido tasakarmai Tana Fadin"Au...Nifa..?Kai Tsaye yace"Ni ai banyi kudin da zan Sauya miki kayan Daki ba Sakina ko Kin manta Lokacin da kika Fadamin haka..? Ya fada yana Tsareta da ido bata samu Zarafin bashi amsa ba yace"Duba wayarki na Tura miki Sako.."Jin Haka yasa ta Jawota daga Gefenta ta Duba Dagowa tayi Tana kallonsa kafin tace"Naga kudu Har Dubu Dari da Hamsin na Miye ne..?
Kai Tsaye yana kallonta Ido Cikin Ido yace"Kudi ne ki kara Siyayyah..Aura zan kara Ranar Sati mai zuwa sanin ku Manya ne bakomai yake Burgeku ba ban Siya miki komai ba nace gwara na baki kudi..Ga wannan.."Ya Fada yana Mikamata katinan Daya Zaro Daga aljihunsa Bata karba ba illah Ido Data Zuramai Tana Binsa da kallo kamar Mutum Mutum Kan Cinyarta ya ijiye mata yana Cigaba da Fadin"Autarsu Abokina Abdullahi Zan aura Hauwa"u jidda..Zamu Fara zama azaria kafin Hutun Dana Dauka ya kare in ya kare zan Dawo da ita Kaduna....Kinga kenan baki dawata matsala yanzu..Na Zabi hakane saboda na baki yancin Samun Damar kula da aikin ki Da kyau..Ni kuma na Samu wacce zata kula Dani daDuka Hakokina da Martabana Daga yau Zaki iya zama a Abuja Har Abada Sakina Ban damu ba Ranar da kika samu Lokaci sai ki Lekomu a hakan ma Wlh mun gode.."Yafada yana yar Dariya.
Ganin yadda ta kafeshi da manyan idanuwanta ne baki Bude ta kasa mgana yasa kawai ya Mike yana maida Wayarsa aljihu Leda Daya ya Dauka Cikin Ledojin yana Fadin"Ga shin nan ki Dauka kici karki Dinga aiki ba Abinci acikin ki Hakan Illah ne ga Lafiyanki ni kuma Bana son Abunda zai Tabamin Lafiyan Uwargidata Ran gida.."Yafada yana Cije baki Gaba yaci zai Shiga Dakinsa kamar mai aljanu haka Sakina tayi Wurgi da System din gabanta Ta Hada da Katinan Auran Tayi Fatali Dasu Cikin Zafin nama ya waigo yana kallonta ganin yadda Take Huci Tana kallonsa Mamaki ya Kamashi ya Bude baki yana Fadin"Lafiyarki kuwa..?
Cikin Wani Gadara da Takama tatako Zuwa gabansa Tana Fadin.."Ni kake kallon Tsabar idona kana Fadamin zaka kara Aure Nazifi Wada..? Tafada tana Nuna kanta Cikin wani irin Bacin rai Abun ma sai ya Bashi Dariya,Har sai ya Murmusa gyara Tsayuwa yayi yana Fadin"Kamar ya..?Toh ke wacece da baza"a gayamiki ba..? Da kiji Daga Bakin wani fa..? Au gwara kij Daga Bakina.."
Ya Fada yana kallonta Kankance Ido Tayi Tana Fadin"Ni sakina Badamasi nice yau kake cewa zakama Kishiya Nazifi..?kishiyarma Da wata karamar yarinya kuchaka kazama Wacce bata..."Saurin Dakatar da ita yayi Lokaci Daya yana Daga mata Hannu Cikin bacin rai ya Fara mgana"Don Allah ya isa haka Sakina me ta miki da zaki Rika kiranta da wadanan Sunayenan..? Ina Ruwanki da ita..? Ai ban Dauka zaki Nuna kin Damu ba Don zan kara aure ba Sakina na Dauka Bayan Dukiyar iyayenki Da aiki babu wani Abu mai muhimmanci acikin Rayuwarki..Na zabi nayi Aurena ne na samu kwanciyar Hankali ke kuma ki Zauna da aikin Gwamnati na Har Abada Wlh bazan kara Korafi ba..ya kamata kisan mganar da zaki Dinga Fada malama.."Yafada yana kokarin Juyawa Cikin Wani Hargagin kuka Sakina taci kwalan Nazifi Tana Fadin"Wlh baka isa ka wulakantani ba kamar ni zakace zakama kishiya..? Kishiyar ma da wata yar isk..."Bai bari ta kai karshen Mganarta ba ya Yarda Ledan Hannunsa ya saka Hannu ya Finciki Wuyansa Lokaci Daya yana Ture Sakina Baya tatafi ta Fadi Saman Cafet tana gunjin kuka Ransa yayi bala"in baci Cikin kakkausan Murya ya Nunata yana Fadin"Ke yar gidan Uban waye da baza"ayi miki Kishiya ba..? Sakina wadanda suka fiiki komai da komai ma an musu Kishiya kuma sun Zauna Dole Ballatana ke..Kin yi karya ki Hanani Abunda Allah ya Riga ya Hallatamin Kuma Wlh in Bakin ki ya kara Budewa kika zagi Jidda ko kuma kika Kara Rikemin Wuyan Riga wanchan karom mari kikasha wannam karon kuwa sai na barki kwance saboda Duka Abaya nayi Hakurin duk wani iskancinki keda iyayenki Saboda nasan Laifina ne ammh banda yanzu da wata ta Riga ta Nuna Nima ina da Darajata kamar ko wani Da Namiji..'Yafada yana sakin mata Huci kamar wani mahaukaci ganin haka sai ta Firgita ta Shanye mganarta Ledan kazansa yaDauka ya Shige Dakinsa Lokaci Daya da Banko Kofa Cike da Bori Sakina ta Mike ta isa Jikin Kofan Tana Bugawa tana kuka ta Hadawa da Zagezage Harda Abdullahi take ta zagi Yana Ciki yana Jinta ammh sai yayi kunan Uwar Shegu da ita gefe Daya kuma yana Tunanin dama Har yanzu sakina na sonsa..?
Bai san iya Adadin Lokacin Data Dauka awajen ba Shidai bayan ya gama cin gazansa ya Kora da Ruwa yayi Shirin Barci ya kwanta ya Toshe kunne da Ear phone suna waya da Jidda suna mgana kan jeren da za"aje yimata Gobe yabama Banza ajiyarta Har ya gama wayarsa ya kwanta yayi barci Daganan bai kara Jinta ba.
Ita kanta Sakinar bata san iya adadin Lokacin Data Dauka akofar dakin Nazifi ba gajiya tayi taja Jikinta zuwa Dakinta ta Fada kan gado ta kara sakin wani marayan kuka,Abun na Zuwar mata Daga karkashin Zuciyarta ne,Tana Tunanin har ita Nazifi zai ma wannan Wulakancin wai kishiya..? Ita kaf cikin kawayenta ba macen da aka tabama Kishiya sai ita kuma Dukkansu ma"aikatan gwannati ne yanzu in wannan labarin ya Fita Abun kunya ne awajenta Babban ma Abun Takaichi yadda Abun yayi mata ZAFI har ga Allah tana son Nazifi kuma Bata kaunar wata mace ta Kusance shi,Uwa uba kuma ya Rasa wazai aura sai wata kazamar yarinya kanwar abokinsa Take nan Tsanar Abdullahi ya kamata duk ko a Baya Duk acikin Abokan Nazifin Tafi kowa ganin Girmansa ammh Dalilin haka sai Taga bakinsa Tana Tunanin Shi ya Hada Nazifin da Jidda Tunda a iya saninta Nazifinta bai da Ra"ayin Tara mace Fiye da Daya.
Kwana Tayi kuka Dama Tana Hutun sallah,Tun asuban Fari ta Shirya kanta da karamin akwatinta acikin Zuciyarta Tana Tunanin Abunda zata yanke Shine Daidai Tunda ta Kira Abbanta ta gayamai komai kuma ya bata izinin Tahowa gida Allah barshi Sai ya zaba ko Ita ko Amaryansa Hajiya na gefensa Tana Fadin Tsiyan Dan Talaka kenan Bai iya samun Waje ba ammh banda Haka har Shi Nazifi ya isa yama Sakina Kishiya,Wajen Misalin 6am na safe yana Zaune kan Darduma yana azkar Yaji Tashin Motatanta Domin yau bai je masallaci ba ya makara,agida yayita ko Gizau bai yi ba ballatana yayi kokarin Tashi ya Bita acikin Ransa kuma yana ma Jin Dadin haka Dama da Rashin Ta da ita din Duk Dayane awajensa.
Bai Fita ko Kofar gida ba yana Gida Kazan da Siyo mata Jiya ko Tabata batayi ba yaji Dadin haka ya Gyara zama yaci Abinsa Lokaci Daya kuma yana kallon Talabijin Cikin Nishadi,yana ganin Kiran Alhaji Badamasi yaki Dauka sai da ta katse kana ya Kirashi Abun mamaki ko gaisuwansa bai amasa ba ya Rufeshi da Fada kamar yayi wani laifi wai don me zai kara Aure..? Abun sai ya bashi mamaki bai Tankaba sai da yace Toh sakina Ta Dawo gida sai ya Zaba ko Ita ko Amaryansa.
Wannan karon bai iya Shuru ba,Sai ya Tanka yace"Ammh Abba meya kawo wannan mganar..? Aure fa Sunnar ma"aiki ne,kuma kasani Da Biyu ma yace mu Fara Bantaba Jin inda akace namiji ya zauna da mace kwara Daya Tal ba..Sai dai in Hakan Ra"ayinaa ne..Kuma Lokacin da zan Auri sakina Bamuyi daku Cewa bazan kara Aure ba Ballatana wata mgana ta Fito Mganar Na zaba ko Ita ko Jidda Wannan kuma Ra"ayinta ne Lokacin da mukayi Aure ban mata Dole ba ita Taji ta gani yanzuma Da kafarta ta saka Kafa ta barni so in Taga Dama ta Dawo in bata ga Dama ba ta Zauna bandamu ba Domin har gs Allah ni bance tatafi ba..mganar gaskiya kenan.."
Jin Haka yasa Alhaji badamasi ya saki Baki kawai yana Sauraran Nazifi bashi kadai ba Harda Hajiya da Sakina Dake gaban iyayenta Wayar a speaker yasa Nazifi bai Jira Wani mgnaba ya yanke Kiran,ko ajikinsa sakina kuwa Dataji kalaman Nazifi sai Ranta ya kara Baci Ta mike Zuwa Dakinta Tana Jin wani Kuka yana Taho mata Daga kasan Ranta Duka iyayenta suka Bita da Kallon Tsausayinta...
*******
Yau lahadi Tun Safe Yan Jere suka Tafi,Zannira Wacce Tun Jiya ta Sauka ita da Tawagarta,Sai Subai"atu da Hafsah sai Inna Talatu,Da Hajiya Lariya da Goggo Habiba wacce Itama Tun Ranar Jumma'a take gidan Mama Umman Sadiq ne sai gobe zata iso Ita da gayyarta.
Tun Wajen 10am na safe suna Famwaki Kuma ba laifi karamin Flat mai kyau Nazifin ya kama Sosai gidan yayi kyau 2 bedroom sai Kichen aciki da Tiolet awaje kuma akwai Rijiya da Bohol,sai Tailet din Waje da Filin Tsakar gida kafin yammah sun gama Gyara ko"ina Dama Tun Jiya kayan Suka iso,Gida yayi kyau Masha Allah,Kalan gidan Ash And Black,Abun sai wanda ya gani Kowa yayi Bajintarsa Sosai Sai Dare suka koma Gidan Mama Duk da basu da yunwa Daga gidan Inna Abu aka kawo musu abinci,Sun gama komai kayan gara ne,kadai ya Rage Shima Abdullahi yace asaurareshi Zuwa Gobe Duk Dama Goggo Habiba tazo da Buhun Masara Biyu,Dana Dawa sai Buhun Danyan Shinfika Shiyasa Abun yazo da Sauki.
Amarya Jidda Tana Chika gari gidan Mamarta Hajiya Sa"a ita da Mariya da Rumana kawarta Tun Ranar jumma"a suka Tafi,Ana Chan Hajiya Sa"a ta Gayyato Wata Hajiya Laila a saudiya suka Hadu Tana gyaran Amare Sosai Take gyarata Gefe Daya kuma tana Tsumata da kayan Mata Washegari kuma Ta aika da Sakon Turaran Wutan Dana Daki Dana Jiki,sai Glass din Da kuma Kayan Gara komai Buhu,Da kwalayen su Taliya da macaroni da Indomie,Koda Abdullahi yazo ya gani bai yi Mgana ba,Dayake yanzu suna da Fahimtar juna da Hajiya Sa"a din Taga uwar bari Har Waya suna yi,Yanzu din ma sai da ta Kirashi Ta gayamai yayi mata godiya kayan Abincin Daya kawo kuma Sai yace Mama suyi amfani Dashi a gida.
Sai Ranar alhamis Jidda ta Dawo Gidan Mama Hajiya Sa"a agidanta Zatayi Taronta ita da Danginta,Gidan Mama ya Riga ya Cika da Baki Umman Sadiq tazo ita da Zahra ta zama Budurwa Ta kai Shekara 10,Harda Abokiyar zamanta tazo,Sai Su Ammi itama tana Zuwa Takai Dare sai ta koma Gida Hafsah kuma Abdullahi ya Hanata kwana Komai Dare gida take komawa,Harira kuma ta koma gidan Ammi ganin Jikin na Hafsah da Sauki tana iya yin aikinta da kanta.
Ranar Jumma"a Nazifi ya Tattaro ya iso Bayan ya Dauki Hutun Sati uku Daga wajen aikinsa na Amarci Makaranta kuma Ba lalle bane ya Shiga Tunda sai wani Abu ya Taso,Da yammah kuma Su Jidda sukayi Walima Wanda Subai"atu da Zannira suka Hada,Akofar gidansu Abdullahi akayi Walimar aka saka Kanufi da Kujeru aka gayyato Malama Safiya muhammed Ba"are tazo Tayi wa"azi ga ma"aurata,An Raba kofuna da Kananan Qur"ani sai Carbi da Dabino Wanda Auwal ya Dauki Nauyi,Zuwa Dare baki Sun Cika gidajen Biyu,ya"yan Goggo Habiba su Jamila sun Diro Anty Hadiza ma Tazo,Gidan Inna Abu ma ya Cika da Dangin Su na uwa Dana Uba sai Hidimar Biki ake ganin haka yasa ya Tattara sukabar anguwan Shida Abdullahi zuwa gidansa Tunda Hafsah Tun Jiya tayimai Yaji ko Ganinta bai yi ba Da ita dasu Amira balle yace ta koma gida Suna gidan Mama sai Bayan Biki.
Achan ne Nazifi ke bama Abdullahi Labarin Abunda ya Faru Tsakaninsa da Sakina Abdullahi yayi ta mamaki ammh kuma sai ya Shanye mamakinsa sanin Halin mata yafi haka,Ya dai Bama Nazifi Shawaran karya saketa Ya kyaleta in ta gaji zata Dawo,da kafarta Nan suka kwana Dayake Duk yawancin Tarin Abokan nasu Daya ne,Duk da kowa yayi gayyarsa Both Nazifin da Abdullahin.
*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*
*Shakira...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*029*
*YININ BIKI...*!
"Yau ta kama Asabar ne wanda yayi Daidai da Ranar Daurin Auran Jidda da Angonta Nazifi Tuni Kowani bangaren gidajen ya kaure da Sha"ani Tare da Shagalin Biki ba Gidan Mama ba,ba gidan Inna Abu ba,kuma Ta ko"ina Area su ta Dinke da Jama"a Tunda dama Duk anguwa Daya ne sai Taron Mutane yayi yawa Sosai.
Bangaran ango kuwa Tun Wajen 9am na Safe suka Baro Gidan Abdullahi Cikin Shigar Shadda mai Ruwan Sararin samaniya Riga da wando Duka Harda Babban Riga,Kala Daya sukayi Hatta Takalmi da agogo Wanda Shi Abdullahin ya Dinka musu Shi kuma Nazifi sai ya Siya musu Hula zanna Bukar mai kyau da Tsari.
Shagalinku Hotel suka Nufa Inda Sauran abokan Nazifin suka Sauka Abokan aikinsa Wadanda Suka zo Daga Kaduna sai Wadanda sukayi karatu Tare,chan suka Bata Lokaci sai Gabda Daurin Auran kana Motocinsu suka Shigo Cikin Gari,Dama a masallacin kusa da Gidan Baba Wada za"a Daura Auran da Misalin Sha Daya na Safe Koda suka isa Waje ya Dinke da Jama"a ba Tsaka Tsinke Dakyarsuka samu Hanyar Shiga Cikim Masallacin.
Karfe 11:10am na safe Shaidu suka Shaida Daurin Auran Hauwa"u Usman Direba Jidda da angonta Nazifi Wada kan Sadaki mafi Daraja kuma lakadan ba ajalan ba,Ayayinda Baba wada ya zama Wakilin Amarya Shi kuma Mijin Goggo Habiba Ya zama Wakilin ango Daurin Auran Daya samu Dimbin Hallatan Mutane Daga Waje Waje dadama Ciki akwai abokan aikin Abdullahi da abokan karatunsa Haka bangaran ango ma akwai abokan aikinsa Daga kaduna da Wasu Daganan Zaria,da abokan Auwal da Tsofaffin abokan Baba wada Dama na Mahaifinsu.,sai kuma Dangin Hajiya Sa"a na Uwa Dana Uba Duk sun mata kara Sunzo kwarai da gaske Taro fa Yayi Taro Abun sai wanda ya gani da idanuwansa Harda Salisu yazo Daurin Auran kuma Dashi Bayan Daurin Auran suka yada zango a Usmaniya Restaurant Dake kongo Zaria akayi Reception.
Bangaran Amarya kuwa agidansu Rumana kawarta suke zama,Dayake abinci aiki suka kai akayi musu Ba wanda ya Wahala Hatta Drinks Nazifi ya kawo musu Tun Safe mai kwalliya tazo ta gwangwajesu,sai wanda ya gani Amarya Jidda tayi kyau Har Gaji da kyau,Da Safe Shadda ta saka Wacce Duka Gidajen Biyun Sukayi ankonta Da gidan Mama da gidan inna Abu Sukayi ankonta kowa ka gani Dashi,Daga Cikin Gida kuwa Su Hafsah da su Subai"atu ke kai da kawo Abinci anan aka Dafa Tuwon Shinkafa,da Shinkafa da Wake,Sai zobo da Ruwa Suma Din Biki yayi Biki Tuni Kowa yaci wankansa yana ta Warwarsawa su Hafsah makotansu Mama sukaje sukayi wanka Suka Shirya Daman Kayansu da komai da komai yana gidan Bayan sunyi Wanka Sunyi kwalliya suka Dinga Daukan Hotuna Su da ya"yan Goggo Habiba su Jamila kowacce ta yarda ya"ya suna chan Gidan Mama suna Shan Biki,Subai"atu dai bata da yarda zatayi Saleem na Tare da ita Taso Ta makalama mahmud da yazo Daurin Aure Shi kuma ya gudu yaki karbanshi,Zanniratu kuma Tana Wani Daki Tare da Dangin Mijinta da suka zo mata Biki Subai"atu kanwar mijinta ne Tana Tare da kawayen Amarya.
,Su Ummi kuma sunzo har sun Tafi.
Ita kuma Hajiya Sa"a da Tawagarta Suna gidanta chan Take nata Taron sai zuwa yammah yan chan zasu Taho akai amarya dasu.
Nazifi Suna wajen Reception ya Ciro Wayarsa yaTurama Sakina Sakon... *Alhamdulillah...An daura Aure..Yau na Tabbata Miji ga Hauwa"u...Fatan Allah ya bamu zaman lafiya.......*Ya Turamata da gayyah ya nuna mata ya zabi Jidda Fiye da ita aikuwa Tana gani Sakina ta Fara kuka Tana Fadin manganganu Tunda Ta Dawo Gida bata da kwanciyar Hankali ko wajen aikinta Bata koma ba Tun Tana Tunanin ganin Nazifi har ta Daina Ta Shiga Damuwa Sosai kullum sai kuka Bata taba Tunanin haka take son Mijinta ba sai wannan gabar Kawarta Rukky Ita Hajiya ta Kirata tazo Tana Bata baki Bayan ta karanta Sakon Nazifi Sakina na kuka Tana Zagin Nazifi da Abdullahin da Ita kanta Jiddan Rukky ta Bude Baki Tana Fadin"Wai ina ce ba wannan abokin nashi da kuke Mutumci da matarsa bane Nazifin ya auri kanwarsa..?
Sakina na kuka tace"Eh Shine...Hafsah ba.."Rukky tace"Kinji ko..? Wlh itama da Hadin Bakinta In banda Munafunci ai babu yarda za"ayi Ace Mijinki zai auri kanwar Mijinki bata sani ba in gaskiya ne ta Kiraki ta Fadamiki mana.."Cak kuka Sakina ya Dauke idanuwanta Jajir take kallon Rukky kafin kawai ta Zabura kan Dressing mirror ta lalubo wayarta Jikinta na Rawa ta lalubo Lambar Hafsah ta Kirata.
Hafsah na chan ana Hotuna da ita Taji wayarta Dake Cikin aljihun Rigar Shaddarta ta Dauki Ringing Dama Doguwar Riga Tayi mai aljihu saboda Cikinta Daya Fito,Sosai ya sakata kiba yanzu Duk yawancin kayanta sun mata kadan,Tana Daukowa ta Duba taga Sakinar Nazifi sai da Gabanta ya Fadi ammh kaucema Hayaniya sai tamatsa Gefe ta Daga Kiran,Abun ya bata mamaki Dataji Sakina na kuka tana mata mgana kan cewa Har da ita aka Taru akaci amanarta Wajen Tusama mijinta kanwar Mijinta Data rasa Mijin Aure,mganganu dai gasunan masu alama da Cin mutumci da Zagi Duk kawaicin Hafsah Sai da Ranta ya baci Jin Tana Neman Zagar mata miji sai kawai ta yanke Kiran Ta juyo ta Dawo sai ga Subai"atu Cikin mamakin gani Chanjin Fuskar Hafsah take tambayanta Abunda ya Faru ita kuma ta gayamata wata uwar ashar Ta lailayo ta Lafta kafin Tace"Kata'i lalle nema Matarnan ta Cika yar iska yo ke kuma sai kika ce mata me..?
Hafsah tace"Me zan ce mata..?biye mata zanyi muyi ta Hayaniya..?kashe wayata nayi.."
Subai"atu ta Ciji yatsa kafin tace"Nayi Takaichin Lokacin Data Kira wayar bani na Daga ba wlh da sai ta Raina kanta..Dama tana son Mijin nata don Durun ubanta Take wulakantashi..? Ta kwantar da Hankalinta mun ma kanwarmu karatun komai Wlh sai ta Bata mamaki Shegiya kota ma Abujan ne ko Kadunan ita ta sani..."
Hafsah tace"Ohon mata..Ammah ai maganganunta ba ilimi sam..Ina ma ji Wata a kusa da ita na Tayata Allah kyauta asan Kishiya akwai zafi ammh sai ka samar ma kanka Natsuwa.."Subai"atu Tayi Tsaki Tana Fadin"Kar ma ta samar kanta...Ubanta zataji Wlh..Gata ga aikin Abuja nan Miye nata na Damuwa bashi ta Rike ba da Sai ya Rika bata Abunda Namijin Duniya Ke bama mace Shegiyar ashe Tasan Kan Abun Wlh naso kaduna Jidda zata Fara zama mije mu Baje Iskanci Da sai ta kusa Mutuwa saboda bakinciki.."Hafsah tace"Kai..Sai kuma ba chan bane..Kidai ki kama girmanki Yaya
kike ba kawar amarya ba.."
Subai tayi Shewa kafin Tace"Tudu Biyu nake Takawa gani Yar amarya kuma Wlh Ta wani Bangaran kawar Amarya ce.."Dariya Hafsah Tayi Tana Fadin"Shegiya..Allah ya Shiryaki."Ta wuce Subai tabi bayanta Tana Fadin"Ameen Harda mai Ciki ma.."Hafsah na Jinta tamata banza ganin haka yasa Ta Bita tana Tsokanarta Ga Hotunanta sunyi kyau ko ta Turama Yaya Abdullahi ne ko kallonta Hafsah batayi ba sanin Shakiyancin Subai yafi gaban haka.
Sai Wajen La"asar kana Abdullahi da Nazifi suka gama Sallaman mutanensu,Daganan Cikin garin Suka Dawo Suka Shiga Gidan Inna Abu,su ka gaishesu ,kannen Nazifi sai Tsiya sukaima nan ya tsaya sukayi Hotuna suna Fitowa suka Hadu da Auwal nan ya Dake sai sun Tsaya Sunyi Hoto Domin mai Hoto Guda ya Dauko nan ma Sun Bata Lokaci,Kana suka Shiga Gidan Mama suka kai gaisuwan iyaye,Duk da gidan yana Cike ne,Mama kuwa Sai Shiga take tana Fita Abdullahi yayi mata kala Hudu yace itama ta Shiga ta Fita Uwar amarya sai Nuna Nazifin ake,ana ga ango chan Mutane natama Abdullahi Allah sanya alheri,basu wani jima ba Saboda mata Sunyi yawa Suka Fito Daga Gidan,Daga nan Kofar gidan Baba Wada suka koma Inda Daga gefe suka saka Babbar Tabarma suna Zaune Shida Mijin Goggo Habiba nan suka zauna suka kara gaggaisawa Shi kuma Nazifi sai ya zame Jikinsa dashi da wani abokinsa suka Tafi Gidan da Jidda ke Zama,Suna zuwa sai ga Auwal ya Shiga Har Ciki ya Fito da Jidda ga mai Hoto ya Shiga Daukansu Da su Mariya da Sauran kawayen Amarya,sai Gabda mangariba suka baro Wajen suna zuwa sukayi alwala Suka Shiga sallah bayan sun Fito ne Suka Fara kokarin Daukan Amarya Tunda Tawagar Hajiya Sa"a sun iso tundazu Gidan Mama.
Zannira ce ta Kira Wayar yaya Abdullahi ya Dauka sukayi mgana akan Abasu Mota zasu kai Jidda chan wajen Hajiya sa"a ta mata Nasiha suyi sallama Tunda su nan kowa yayi nashi,Harta shi Abdullahin yayi mata nashi Nasihan sai yace su Dakata Sauran abokansu na Anguwa su iso da Motocin su gama dai Kimtsa ta da komai da sunzo aka Fito da ita zasu kaita gidan Inna Abu Wajen Baba wada in yagama Mata Nasihan sai su wuce Dukkansu Chan Shika garin in sun Dawo Daganan sai Dakin Auranta basai sun Daawo ba,Da haka suka Kashe wayar,Bayan sungama Mgana ne ya ja Nazifi Gefe suka Tattauna yace hakan Daya Tsara yayi,yanzu Duka Motocin zasu iso.
Yana Kokarin Maida wayarsa aljihu ne yaga Alamar Sakon akan wayarsa sai ya Dakata ya Bude kamar yadda ya Zata ne Itace Domin Tun Ranar daya Rage mata Hanya koda yaushe sai Turomasa Sakon MorningMassges,da kuma na Good nite,sai na Jummat"mubarak kuma kowani Lokaci Zata saka Sunanta a kasa,Yana ta mamakin ina ta samu Lambarsa Lokacin kansa yayi Zafi da wannan Sha"anin Shiyasa bai Taba bin takai ba yana ganin Sakom nata bai Taba dai maida mata Reply ba,yau kamar kullum ga Abunda Ta Rubuto.
_I wish you a Hearty Congratulation on This occasion...may Ur Life always Shower you with such Happy and Succeessful Moment...Allah ya Sanya alheri...ya kuma Basu zaman lafiya Ameen....BARKAT SHEHU..._
Mirmishi yayi Yau dai na Farko ya Maida mata da Reply din Ameen Nagode Barkat.."Barkat bata Taba tsammanin Abdullahi zai maido mata amsa ba,sai kawai ta ga Sakonsa Tsalle ta Buga adaki Ta Fada kan Littafanta na makaranta Wanda ta Dauko Tana karatu Saboda sun Kusa Fara test ne a makaranta,Rungume wayarta tayi Tana jin wani Farinciki na Ratsata Bahiya ce ta Shigo Dakin Jiya Ta Dawo Weekend ganin Barkat Cikin wannan Halin yasa ta Rike baki Tana kallonta kafin tace"Anty Barkat lafiya kuwa..?Hajiya tace lafiyarki kike Ihu ke kadai..?
Sai Lokacin Ta Dawo Cikin Hayyacinta Ta Bude Lumsassun Idanuwanta akan Bahiya kafin ta yunkura Ta mike ko kallon Bahiya batayi ba ta Dauki Wayarta Ta Tura kofar Tailet ta Shiga ta Rufo Kofar Batare da tabama Bahiya amsa tambayanta ba ganin haka yasa ta Tabe baki ta Fice Sanin ko Zata Shekara Tsaye Barkat bazata bata amsan Tambayanta Datayi mata ba...Barkat kuwa Kofar Tailet ta Jingina Dashi Tana ta Murnanta Lokaci Daya tana Fadin"Alhamdulillah.."Dama Abakin Hajiya taji Zencen Auran kanwarsa Da Nazifin Lokacin da ya Salisu yazo da safe yana Fadamata Daurin Auran na 11 na safe ne,shiyasa ta Turamai sakon Allah sanya alheri.
Su Goggo Habiba da Umman Sadiq da Inna Talatu sai Ammi suka kai Jidda Nasiha wajen Baba wada,Yayi mata Nasiha Sosai Shida Mijin Goggo Habiba,Daganan gidan Mama suka maidata tayi mata Sallama suka Rumgume juna suna ta Kuka Dakyar aka Bambare Jidda tana kuka aka Fita da ita Lokacin Sauran abokan sun iso da Motocin,Abdullahi shi ya amshi key din Motar Nazifi yace zai Dauki Jidda da kansa ya kaita Dakin Auranta Saboda haka Motar aka Sakata Daga ita sai Ammi sai Umman Sadiq da Goggo Habiba Dangin Hajiya sa"a Dama da Motocinsu suka zo Sauran Motocin kuma Kawayen Amarya su Rumana su Mariya suka Shisshiga Subai"atu kuwa da Hafsah Motar wani Ishaq suka Shiga Dayake Duk yan anguwa ne Zannira kuma Wata mota ta samu ita Dasu Jamila,Motoci a kallah sun kai goma Dayake anyi Abun da Tsari ne,ba Tururuwa kowa ya samu Harda kannen Nazifi Sun samu Shiga.
Gidan Hajiya Sa"a suka Fara Zuwa Abdullahi kadai ya Shiga da Mota,sai Danginta da Shigo da Tasu,Ciki yau ne karo na Farko Daya Taba zuwa Gidan,yana Cikin mota yace Su Goggo Su Fita da ita Don Allah Minti goma su Fito Haka kuwa akayi Basu wani Jima ba yan Nasiha ne da Sallama Dama kuma ta mata,suka Fito da ita,Abdullahin ma Tana kiran Umman Sadiq ta waya yana cewa su Fito
Tafiya zuwa gidan Amarya Tawagar ta kara yawa Tunda Har dasu Lariya Suna Zuwa kofar gidan Jidda ana Kiran Sallar Isha"i,Abdullahi da kanshi ya Rike Hannun Jidda har kan gadon Auranta,ya zaunar da ita ya Dafa kanta yayi mata addu"an Zaman lafiya Daganan ya Fice Su Ammi kadai ya Jira su da ya Dauko ya maidasu da kanshi Chan yaga su Hafsah da Subai"atu sun Fito Daga Mota Abunda Ya bashi mamaki ganin Hafsah Da gyale Ransa ya Baci Kamar ya Fito ya mata mgana sai kuma ya faasa Domin Rabonsa da ganinta Tun Shekaranjiya Banda ta Rainasa ta san Bayason mayafi Shine ta saka ga Cikinta ya Fito,ko kafin ma ya Fito sun Shige Gidan kawai sai yayi kwafa yace Zasu gamu,Su Umman sadiq ganin Dakunan kawai sukayi suka saka albarka suka Fito Abdullahi ya maidasu Daganan Ammi ya Dauka ya maidata gida Anty Hadiza Tun dazu tatafi Saboda Su Abdulwaseen suna ta Rigima bai Shiga ba ya Juya Ammi nata mai godiya.
Yana komawa yaga gida wayam Ba wasu Mutane Duk an Tafi Gidan Amarya ya Shiga Cikin Gida yasa aka Kira masa Mama Yake Tambayanta Gidan Amarya wanchan Zugan zasu kwana..? Mama tace Eh aiko Abdullahi yace ba wacce zata kwana Wayar Zannira yakira yace su Tattaro kaf dinsu su Dawo gida in ba Haka ba Ransu ya baci Zannira ta Fara mgana kan kawayen Jidda zasu kwana yace ba wacce zata kwana Tunda ba Farillah bane Ango zai kwana Dakin Amarya Saboda Haka Wlh ko su Tarkato su Dawo ku kuma in yazo Dukkansu bazasu ji da Dadi ba,Mama dai batayimgana ba ganin Tunda yace ba wanda zai kwana da gaske yake sai Fada yake yana Kiran su zannira Manyan banza ko kunya Sunje Gidan kanwarsu zasu kwana,Zannira ta kara kiran Abdullahi tana Fadamai Duka Motoci Sun Tafi yace su Tako akafarsu Tsautsayin Dayaasa suka Shiga Ciki Suka zauna Har suka kai Dare ya Dawo Dasu.
Sanin Halinsa yasa Zannira na Fada kowa ya Fara Shiri Dama iyaye Tuni suka kama kansu suna ganin gida suka Shige Motoci aka koma Dasu Daganan ne ba Motar Data Dawo,Da Jidda taji labari sai kuma ta kama kuka, Subai"atu takalleta tana Fadin"Hakuri fa zakiyi...Laifin Yaya Abdullahi ne Shi a komai sai ya Nuna iko..Don ina laifi Don yabarmu mun kwana na yau kadai mun Rakashe kawai kawai yacewai kowa ya koma gida.."Ta fada irin Abun bai mata Dadi ba Mariya tace"Hmmmm...Aini Abun ya bani mamaki Wlh.."
Rumana tace"Gaskiya Yayan nan naku ya kwafsamana toh ke Qawata kin Shirya kwana da angon ne..?kawai sai Jidda ta saka Kuka Zannira tace"Kima yi Hakuri Da wannan kukan..Domin kinsan bamai Tsallake Umarnin yaya Abdullahi kinsan yazo gidan nan yaci mana ba karamin aikinsa bane.."Hafsah na gefe tana Dariya Subai kuma sai Tura baki Take Jidda dai taga da gaske suke Tafiyan zasu yi ta Kara Volume din kukanta Tana Rike Mariya,Mariya ta Fizge Hannunta itama kamar ta koka tana Fadin"Sakeni Jidda kinfi kowa sanin Halin Yaya Abdullahi Wlh nima ba Ragamin zai yi ba.."Dole Jidda Tana ji tana Dukkansu Harda kannen Nazifin Suna ta Dariya Kawayenta ma kaf Zannira ta Taro suka fito Suka bar Jidda na kuka Zannira tace tataso ta Rufe gida kafin ango Ya kariso Dakyar ta taso ta Rufe Gidan Tana kuka.
Sun Dade awaje Zuga Guda ba Abun Hawa Dole suka Fara Bin Hanya,ko Masu Napep babu ballatana wasu su Rage,Hafsah ga Ciki ga Tafiya Dukkansu Sun gaji Subai"atu tace Hafsah ta Kira Abdullahi yazo ya Taimakesu Tace bari ta gwada Data Kirashi sai da Tagama Bayaninta kana yayi Tsaki yace Waya kaisu..? Gidan Amarya ai na yara ne da suka je suna ganin waje sai su Fito a Dawo dasu ammh suka Share kafa,ai yanzu sai su Dandana Tafiyar kasa.." Daga haka ya kashe waryarsa,Dole Kowaace ta Wasa kafarta Sauran kawayen Jidda suka samu Mashin Sukayi Gida Rumana ne da Mariya da kanwar Mijin Subai Ke ta Shan Tafiya basu iso gida ba sai Goma Saura Suka iske Abdullahin da Nazifin a kofar gida,Saboda Haushi ba wacce ta kallesu kowa ta maida kanta gefe Hafsah kuwa Dakyar ta kawo Bayanta da kafarta sai Ciwo Suke Dariya ta kama Abdullahi Dayake akwai Wuta Haske ya Gauraye wajen Haka ya ga Fuskar ko wacce ba Fara"a Auwal ma na Zaune da Abokansa Sai da yayi Dariya afili ya Furta ya Abdullahi yayi Tsiya.
Suna Shigewa ya kalli Nazifi yana Fadin"Ango Sai ka Tafi gidanka Sai Allah ya kaimu gobe..Nima gida zan karisa nayi wanka na kwanta na gaji.."Hannu Nazifi ya bashi sukayi musabaha kafin Suyi Sallama bai Tafi da Motarsa ba Makullin Mashin din Abdullahi ya Karba wacce ke Hannun Auwal,ya Tafi da ita Motar kuma ya barma Abdullahi Shima bai Tafi da itaba Nan kofar Gidan Baba wada ya bar Motan ya Hau Mashin Din Haya zuwa Gida.
Shi kuma Nazifi kofar Doka ya Tafi ya Siya kayan Sanyi da kuma Kaji Guda Uku,Sai ya Dawo Gida ya Dauki karamar Jakar kayansa Dayazo Dashi Daga kaduna Sauran Sabbin Dinkinsa suna wajen Tela sai Gobe zai kamallah Misalin Karfe 11:pm da wani Abu na Dare ya Shiga Gidan Daman yana da Makullin gidan a Hannunsa Budewa kawai yayi ya Shiga da Mashin ya Faka kana yazo ya Rufe Gidan ya Taka ya Tura Kofar Falon ya Shiga da Sallama Jin Shuru yasa Direct yayi Cikin Bedroom din Jidda Dake a tsorace Manne Abayan Kofar Bedroom dinta Tajiyo Shigowarsa Lekowa tayi ganin Shine yasa yajita kawai ta Fadkmai Bisa Jikinsa Kadan ya Rage Dagashi har ledojin basu yi kasa ba ya Zame ledojin a kasa ya saka Duka Hannuwansa ya Riketa ajikinsa yana Fadin"Kinga..Bar wannan Tsoron am Here for u..kinji ko..!"
Yafada yana Shafa Bayanta Zuwa Kugunta alaman Lallashi.
*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*
*Shakira...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*030*
"Shagwabe mai Tayi Tana Fadin"Ka Barni sai Tsoro nake ji Gashi ni kadai agida..."Tafada Cikin Tabara da sangarta Shiko Nazifi Tunda yajita acikin Jikinsa Komai nashi ya Chanza yanzu din ma Dakyar ya iya Lalubo amsa da zai bata da cewa"Am so Sorry My Jidda bada gangan bane...Kinji ko..?
Ya Fada Yana Shafa Bayanta Cikin Wani Salo Saurin Sakinsa Tayi jin yadda yake Shafata kallonsa Tayi Ido Cikin ido kafin Tace"Kai ne ka sa Ya Abdullahi ya Korarmu su Anty Mariya da kawayena ko..? Tana Fada sai ga Hawaye Tuni Nazifi ya Rude yaga Amarya na kuka ya Rikota Zuwa Jikinsa yana Fadin"A"a Wlh bani bane...Bansan ma sanda ya aikataba..."
Tana Tura baki tace"Toh meyasa da ka sani baka Hanashi ba....Kuma Bakace su Dawo ba..?"Mganar sai da ta kusa Sakashi Dariya sai ya kanne yana Fadin"Nayi iya yina yaki ya Fahimceni kinsan Halin yayan naku kaifi Daya ne...In ya karkace ko Hafsah bata iya maidashi Daidai Ballatana ni..."Yafada yana Dagota Lokaci Daya yana Share mata Hawaye.
Ganin yadda Tayi da Fuska yasa yaJata gefen gado yana Fadin"Meye na Fushin..? Keda zaki yima Farinciki gaki ga Angonki.."Wata Uwar Harara Ta makamai Data Sanyashi Dariyan Dole mikewa yayi ya Cire Babban Rigan jikinsa Saurin Kauda kai Tayi Tana Share kwallarta Rigar saman ya Cire ya Rage Dagashi sai Vest da Dogon Wando,Kallonta yayi yana so yayi Dariya sai ya Fasa Cikin alamun Lallashi yace mata"My Jidda tashi muje muyi wanka.."
Jin Haka tayi Saurin Haurawa Chan Tsakiyar Gadon Tana Fadin"Ni nayi wanka na..."ta Fada Tana Tura baki bai Damu ba ya Kada kai yana Fadin"Orly ni bari nayi.."Daga haka ya Shige Tailet bai wani Jima ba ya Fito Ruwa na Diga ajikinsa,ita kuwa Har ta Fara gyangadi Daga Zaune bai Tasheta ba sai da ya Sauya kaya Zuwa Jallabiya yaje Kitchen ya Dauko Filet da Kofuna yazo ya Saka musu kaza Guda Daya Kofunan kuma ya Zuba musu Madaran,kana ya Haura saman gadon yana Tashinta Dakyar ta iya Tashi Barci yaci Idonta Gajiyar Biki ne,Mayafinta ya Zare mata ya zaunar da ita kan Cinyarsa yayi Kokari Taci kazan Taki Ci Dakyar ta yarda taci kadan ya Bata Madaran tasha shima kadan Sai Lallabata yake ita kuma tana ta Shagwaba tana Tura baki bayan Sungama ta sake Komawa kan Gado ta kwanta Shima ya kwashe komai yamaida Kitchen.
Dakyar ya iya Lallabanta ya Rakata Bayi tayi Brush Ta Yi alwala Shima yayi suka Fito ya Shimfida musu sallah Jidda sai Cewa take tana jin Barci Shidai yana ta aukin Lallashinta,Harsuka Idar Da sallar yayi musu addu'o'i Duk da bai Tswaita ba,Suna Idarwa ta Haye gado kallonta kawai yayi Akwatin da"a kazo mata dashi ya Duba ya Dauko mata Rigar barci Shima an sha Daga kafin tatashi tasaka Shidai nashi lallashi ne da Ban baki Da farko yaso ya kyaleta ne ganin ta gaji ammh kuma sai yaji bazai iya ba Harta Fara Barci Tajishi kusa da ita TunJidda na Dauka Abun Sharan Fage ne haryazo ya Fara wuce Tunaninta Da Farko a irin Salon wasan daya Tafi da ita ta saki Jiki Tana Jin Dadi ammh kuma da Gangara tatafi sai ta Fara kuka tana Neman Taimako ammh ina Lokacin gogon naka bai ma Jinta yana Kokarin Shiga wata Duniya ta Dabam Duk da Yajita a matse ne tsam ammh bai iya Saurara mata ba Haka ya Dinga Tura kai Tun yana Waje waje har yazo ya Shige Ciki gabadaya ya Cigaba da aiki ba kama Hannun yaro.
Ba karamin Jarumtar Yarinyar yagani ba Sosai Duk da Tasha kuka da Koke koke Yaga Kokarinta kwarai Sai ya Tuna Lokacin Daran Farkonsu da Sakina Irin yadda ta Dinga kuka kamar wacce ya yanka tana mai Allah ya isa wai ya yagata Lokacin ma ai ita ba yarinya bace,Ammh kalli Jidda yarinyace karama ai ta iya Daurinyan Daukansa Duk da yana na Farko nan ko baisan karatunsu Subai bane da Hafsah na karta nuna gazawarta Ta nuna Jarumtarta Yana karama Mace a Daraja Sosai a idon mijinta.
Adaran ya Taimakamata Dama yaga Ruwan zafi a Flaks Dashi Yayi mata amfani Yadai Sha Shagwaba ne da Tura baki har ya Godema Allah Bayan ya gama gasata yayi mata wanka ya Nadota Cikin Towel ya kawota kam gado Shima ya koma ya Samu Tsarki ya Fito koda ya Fito Har ta koma Barci,shima Wandonsa Gajere ya Zura ya koma Kusa da ita ya kwanta yana Sauke Numfashi Lokaci Daya yana Jawota Jikinsa ita kuma sai ta kara lafewa Lumshe ido yayi kamar mai barci ya Tuna irin Kiran da Sakon Cin Mutumci da Zagin Da Sakina ta Dinga aiko mai Jiya Shiyasa ma ya kashe Duka wayoyinsa ya bama Banza ajiyarta Abunda kuma yake kara Bashi mamaki Dama wai yana daWani Daraja a idon Sakina ne..? Bai taba Tunanin don Yayi Aure zata iya Daga Hankalinta haka ba,Shi kuma yayi alkawarin Barinta Da aikinta ne ya Daina mata Korafi sai asamu zaman Lafiya.
Har Zuwa Washegari da Shagwaban Jidda tatashi Shidai Nazifi sai aikin Lallashi yake yana Saka mata albarka Tunda shi ya Kira Ruwan yana gidan bai iya Fita ba sai Bayan La"asar da su Zannira suka zo da su Hafsah kawo mata Sauran akwatunanta da wasu kayan sai kayan Su Cincin da Sauransu sai Lokacin ya samu Fita,Kowa yaga Jidda sai ya Fahimci dai Taji maza Domin abun ba Sauki Sai wani Sunne kai Take tana wani Sanyin jiki ba wanda ya Nuna mata wani abu sai dai sun kara bata Wasu Shawarwarin da zasu Taimaka mata Sosai kan zamanta kewarta.
Sai Dare suka bar gidan chan suka bar Mariya da Rumana su kuma da su Goggo Habiba zasu Tafi suka Bisu Subai"a tace kada a kuma irin na Jiya,suma su Mariya basu Dade ba suka Tafi Su Hajiya Lariya suka bi suka Rage musu Hanya sukabar Jidda ita kadai Tana yan kananan kuka Nazifi kuma Suna tare da Abdullahi Ana idar da Sallar mangriba suka Rabu Abdullahi ya Shiga Gidan Mama Shi kuma ya Wuce gidansa wajen yar Shagwabansa ai kuwa koda yaje ya sameta Tana ta kukan an barta ita kadai Sai da ya zauna yana ta aikin Lallashi yau dai Babu Abunda yayi mata Suna Jinya ne ammh ya Nannadeta Cikin Jikinsa Sunyi Barcinsu Cike da Soyayayyah da kauna.
Ranar Monday kuma yan biki duk sunWatse Domin Tun Safe Zannira ta koma Kaduna ita da yaranta Mijinta ya Turo Direba ya Dauketa Goggo Habiba ma Ta koma Dama ya"yanta Tun Jiya suka Tafi Jamila ce kadai ta Tsaya zasu koma Tare,Su Inna Talatu ma Duk sun koma Umman Sadiq ne kadai ta Tsaya sai Zuwa Laraba ammh Tuni abokiyar zamanta ta koma jiya ita da Zahra,Gidan ya Rage sai su Hausi da Subai"atu Sun Share kafa sun Zauna wai sai Gobe zasu koma Su suka Taya aka Gyara gidan aka Kankanta inda ya kamata Dayan Dakin Suka koma Suka Dasa Hira Suna Shewa Hafsah da Ciki Gaba Subai kuma Tana karkace sai Zuba Take Suna Dariya.
Abdullahi Shi Duk azatonsa Hafsah ta koma Gida Ranar yaje aiki,Daya Dawo ya Biyo ta gidan Mama da Su Amira da Su Muhsina ya Fara cin karo Daganan ya gane basu koma Gida ba mamaki ya kamashi yana Bayyana Rashin Hankalin Yaranan subai da hafsah bai Shiga gidan ba sai Bayan Sallar mangariba bayan ya Fito Daga masallaci Nazifi dai ko ganinsa Ranar ba wanda yayi yana Gida Duka Salollinsa acikin Gida yake yi Toh ina ma Zashi Jidda bazata barshi ba Duk inda ya saka kafa zata saka Tana Nannade dashi kamar wani zai kwace mata Abun fa nama Nazifi Dadi Domin Shidai bai samu haka ba sai Shima Abun ya zamarmai kamar Farkon Farinsa.
Yana Shiga Gidan Direct Dakin Mama ya Shiga kuma ya wuce su Hafsah a Dayan Dakin Suna Sallah Su Amira na Biye dashi Da su Muhsina Suna mai oyoyo yana Rike da Hannayensu ya Shiga Dakin Mama Ya samu Daya Daga Cikin kujerun Falon ya zauna da Mama suka Fara gaisawa suna ma Juna Barka da Watsewa Taro Lafiya Umman Sadiq na sallah ne Shiyasa ya kalli Mama yana Fadin"Mama naga gidan Shuru Ba kowa ne..?
Mama tace"Umh kadai bari yanzu Hajara ke fadin Mutane Rahma ne...Jiya da Shekaran jiya Gidnan Cike ammh yanzu Babu kowa...kowa ya watse.."Abdullahi yace"Daman haka ne Mama..Dazu ma Goggo Ta Kirani tace a Shaida muku Ta isa gida lafiya.."Mama tace"Alhamdullillahi Barkanmu..
angode Allah ya bar zumunci.."
Abdullahi ya amsa da Ameen kafin ya waiga yana Fadin"Mama ina Mariya..? Banganta ba..? Mama tace"Ta fita yanzu..Taje Raka wata abokiyar karatunta Da bata samu zuwa mata biki ba sai yau yanzu Taje rakata.."Kada kai yayi yana Fadin"Shine Daga Rako har yanzu...? Bata da Hankali ne bata ganin Duhun mangariba ta kawo ne..?
Mama tace"Nima nace karta Tsaya fa..."kyafci yayi kawai ya Kada kai Wayarsa ya Fito Dashi yana Dannawa su Amira kuma nata Mugun waasa Mama na Faman Bari Bari Dagowa Abdullahi yayi ya Daga musu Tsawa Duk sai Suka Natsu kallon Mama yayi yana Fadin"Mama ina iyayen yaran nan suke ne..?
Mama Tace"Suna Dakin Farko..Ka wucesu ma."Karamin Tsaki Yaja yana Fadin"Wato Su Shaffafu da mai kowa ya koma Gidansa Su Uban me ya zaunar dasu..?Mama tayi Dariya tace"Naji Suna Fadin sai gobe zasu koma...Duk su suka gyara gidan nan Wlh ni Hafsah ma Nake ji ga Ciki kada Bayanta ya kage.."Mikewa yayi yana Saka Wayarsa a Gaban aljihunsa Lokaci Daya yana Fadin"A"a Mama Kowacce tazo ta wuce ta koma Gidan Mijinta an gama Biki Dai kowa ya watse Suma su Tafi Gidajensu an gode Allah ya bar Zumunci.."Mama dai Batayi mgana ba sai Dariya take Umman Sadiq kuma na Sallah ba Halin Tayi mgana.
Ficewa Yayi Daga Dakin yana Fita Suka ci karo da Mariya Baya Taja tana Sosa kai,kallonta yayi Daga sama Har kasa ita kuma sai Gabanta ke Fadi Domin gyale ne ajikinta Saurin rankwafa tayi Tana gaisheshi bai amsa ba ya Jefa mata Tambayar"Ke Daga ina kike..? Cikin Sarkewar murya tace"Naje Raka wata Qawata ce..."Harara ya Zabgamata yana Fadin"Hala gidansu kika kaita ne...?
Ta Bude Baki Zatayi mgana kenan ya Dakatar da ita yana Fadin"Wuce ki bani Waje....Kar in kara ganin kin Fita Da Mangriba kuma in na Sake ganinki da wannan mayafin sai kin Raina kanki.."Da gudu Mariya ta Shige Dakin Mama ya Bita da Karamin Tsaki kafin ya Daga Labulan Dakin da su Hafsah suke Daidai Lokacin Nepa suka maido Wuta Haske ya Gauraye Dakin,Hafsah na Zaune a kasa Ta Mike kafafunta Saboda ta Dan kumbura Saboda Zirga Zirga,Subai kuma tana kan karamar katifar Dake Dakin Tana bama Saleem Nono ganin Lekowar Abdullahi yasa Dole Subai Tayi Shuru da Labarin Datake bata ta maida alaqan gaisuwanta ga Abdullahi.
Bai amsa ba kai tsaye yace"Ku kuma Shafaffu da mai..Zaman me kuma kuke yi..? Subai tace"Mun idar da sallah ne muna Zantawa ya Abdullahi ko Hafsah Tazo kana Kiranta ne.? Harara ya zabgamata kafin yace"Baki da kunya ko..?Sunne kai tayi tana Rike Dariyarta Hafsah ma sai da ta Dara,Karamin Tsaki yaja kafin yace"Ke mai ba ma D'a Nono da ke Mai Ciki da kika wani yi Rashe Rashe gidan Mutane kowacce Tatashi ta Shirya ta kwashi ya"yanta ta koma Gidan Mijinta Banga zaman me kukeyi ba Bayan Tun Jiya aka gama Biki.."
Marairaice Fuska Subai Tayi Tana Fadim"Kai ya Abdullahi Yanzu kuma....? Bamu gama Shirya kayanmu ba da Munbari sai Gobe ne sai mu Watse.."Karisa Shigowa Dakin Yayi yana Fadin"Kinsan Allah yau din zaku watse...Bamai kara kwana agidanan nan...Ke Ki tashi yanzu mu Wuce gida ke kuma Bari na Fita nama Auwal mgana ya samo Miki mai adaidata ki kwashe ya"yanki ki koma gidan mijinki Bana son Rashin Hankali.."Zatayi mgana ya Dakatar da ita Cikin Bacin Rai yana Fadin"Wai ina Wasa Dake ne Subai"atu..? Kinfi kowa Sanina bana son Gaddama..Wlh Tunda na Rantse kowacce sai ta tafi..Gwara tun Wuri ku Shirya.."Daga haka ya Fice yana ta Fada Dole kanwar naki Kowacce ta mike Hafsah Dataji Tagaji hakanan ta Mike ta Fara Hada kayanta Subai sai Gunguni take tana Fadin"Kayi Aure ma Ya Abdullahi bazai bar iko akan ka Nifa Mijina sai Gobe yace na koma gida.."Hafsah na Dariya tace"Ba Dole zaki iya kwanciyarki sai Gobe.."Harara Subai ta sakarmata Hafsah kuma na Mata Dariya.
Subai Tace Mama ko Umman Sadiq su Rokeshi ya barsu su kwana Zuwa Gobe Umman Sadiq Data idar da Sallah Tace"A"a bazamu saka baki..Ba yafimu gaskiya..Gwara,ku koma Gidajen mazajenku Tunda dai an gama baki Babu amfanin zaman Allah ya bar zumunci.."Jin haka yasa kowacce ta Shirya Subai"a ta Fara Tafiya Auwal ya Abdullahi yama mgana ya Samo mai adaidaita suka Shiga ita da yaran da kayanta Auwal din ya Rakata Zuwa Gida Suna Tafiya Shima Abdullahi ya kwashesu Zuwa Gida Kayansu ne yace su bari sai Gobe Auwal zai kaimata Gida.
Koda Hafsah ta koma Sai Ciwon Baya da Ciwon Kugu babu Abunda ta iya Tsinanawa sai kwanciya Abdullahi sai Fada yake yana Shanshancin Banza kawai kinsan Halin da kike Ciki ba sai ki Zauna agida ba ammh sai Ki biyema Subai tana janki Waje waje kuna zuwa kamar wasu Sakarkaru ai gashinan ya gama Fadansa bata Tankaba,Shi yayi ma Yaran Shinfida ya kwantar dasu ita kuma ya sa Ruwan zafi ya mata Wanka ya gasa mata Jiki yazo ya Shafa mata man zafi ya Hada mata da Tausa Su Hafsah sai Barci Sai Lokacin Shima ya samu ya Shiga wanka yazo ya Sauya kayan Barci ya kwanta Shi kanshi yana Bukatar Tausan Domin a matuka agajiye yake Sosai.
*******
*Bayan Sati Biyu....*
Kimamin Sati Biyu da yin Bikin jidda da Nazifi Zuwa yanzu Sun Riga da sum zama Jini da Hanta amarci ne sukaci kamar ba Gobe In kuka ga Salon da Jidda ke ma Nazifi sai Kun Rike baki Dama gata da Rawan kai da karambani To yayi mata amfani Domin Tana gwadama Angonta kuma yana Yabawa Dakyar ya bata Hutun kwana uku Daganan kuma Tunda ya koma ba Daga kafa Zuwa yanzu in ka gansu sai kayi mamaki sunyi kiba sun kara Haske Daga gani Suna Cikin kwanciyar Hankali Sosai da kuma Jin Dadi.
Tundaga Ranar Lahadin Da su Hafsah sukaje ba wanda ya kara Komawa sai da ta Cika Sati Dayane Ranar Hajiya lariya taje ganinta Tare da kaimata wasu Turarankan Jiki dana Tsuggune kuma Taji Dadin ganin Jiddan taSaki Jikinta kamar ba ita ba Haka ta koma ma da Hajiya Sa"a Labari mai Dadi sai itama Hankalinta ya kwanta Mariya da Rumana ma sun koma Sai Ranar da Tacika kwana Takwaas ta matsamai sai yakawota gidan Mama Suka gaisa tayi ta Murna aikuwa da Abdullahi yaji labari yayita Fada yace karya kara kawota sai tazo Sallama in zasu koma Kaduna haka kuwa akayi Gobe Lahadi yake Saka Ran Su koma Kaduna Domin ya gama Cinye Hutunsa zai koma Bakin aiki.
Ranar asabar ya Dauketa a Mota suka Fara Zuwa Hajiya Lariya suka Mata Sallama Taji Dadi Tayi ta saka musu albarka sun Dade kafin su mata sallama Ta bama Jidda Kyautan Su Gumba da kuma Hadin kwakumentin Mata Da yawa Bayan ta mata Nasiha da kuma wasu Shawarwarim zamantakewa Daganan gidan Hajiya Sa"a suka yada zango Daman ta san da Zuwansu anyi musu Girke girke sai wanda ya gani,Hajiya sa"a sai wani Sunne kai Take ita mai Suruki Taji Dadin ganin yadda Jidda ta samu Jin Dadin Rayuwa kuma Hakika sai yanzu Zuciyarta ta samu Natsuwa Ita ta Rikesu sai gabda mangariba suka Fito Daga Gidan Bayan tayi musu Nasiha kuma ta saka musu albarka Gefe Daya kuma ta Jadaddama Nazifi karya manta da Cigaban karatun Jidda yace mata Da sun koma Abunda zai Fara Neman mata kenan Tunda Jarabawarta Duka sunyi kyau.
Ana mangariba suka Shigo Gidan Inna Abu Tana ta maraba dasu,Nan yabarta yayi alwala ya Fita Zuwa masallaci,bayan an idar suka Shigo da Baba wada nan ma Basu Jima ba sallama ne da yan Nasihohi suka Biyo Baya Daganan sai Gidan Mama nan din ma Ko Minti Talatin Basu yi ba suka musu Sallama Jidda Har da kuka ta Rumgume Mama da Mariya Auwal na gefe nayi musu Dariya Daga gidan Mama gidan Subai"a sukaje sai dai ta gansu kwatsam Itama Sallaman suka mata Subai taja Jidda Ciki ta kara mata wasu Shawaran kuma ta Tabbatar mata tanayin yadda suka Koyarda ita Subai Taji Dadi ta kara Nuna mata karta wani Damu ko da Sun koma Kaduna Sakina ta Dawo karta Fasa Abunda ta saba tace Insha Allahu.
Gidan Abdullahi ne karshe Suna Shiga Gidan ana ta Kiraye Kirayen Sallar Isha"i Abdullahi baya Gida bai Dawo Daga Wajen aiki ba Kila ya Tsaya a Shago ne,Nan Nazifi ya barta ya Fita masallacin Layinsu Hafsah yayi sallah Isha"i Sun so Tafiya Hafsah tace su bari Abdullahi ya Dawo sai Tara Saura ya Shigo Gidan Daya gansu Fada ya kama yi Sun yi Dare sama sama Sukayi sallama ya kara Ja ma Jidda kunne sosai kana sukayi musu Sallama Suka Tafi Har Waje Hafsah da Abdullahi sukayi musu Rakiya suna Daga musu Hannu.
Da suka koma Gida Kayansu Suka Shirya kawai..Shi Daman bai da wasu kaya Jidda ce..Kayan sawa kawai yace ta Dauka Komai na Bukata akwai akwatunanta Biyu ta Cika da kaya Sai Daya na kayan Kwalliya Da kayan amfaninta Sun gaji Wanka kawai Sukayi Suka Kwanta Washegari Tun karfe 6am da wani Abu na Safe suka Dauki Hanya bayan sun Biya Sun bar ma Mama key din Gidan Daya kawai suka Tafi Dashi Koda wani Abu zai Taso.
Sun isa Wajen Misalin Goma na Safe,Jidda Tana ta mamakin Girman Gidan,Domin Taga ya kara mata Girma akan zuwan da suka Taba yi,Dakinsa ya Sauketa,Daga ganin gidan Sakina bata Lekosa ba Tun Bayan Tafiyarsa Zagewa yayi ya Taya Jidda suka Taftace ko"ina kana ya Sake Wanka ya Dau key din Mota ya Fice Da cewa zai Je wajen aiki Dagachan zai Biya ya yomusu Takeaway Kada tayi Girki ta amsa mai Da Tom ammh Ranta ba Dadi zai barta ita kadai agidan Tunda Daga Dukkan Alamu Sakinar Bata garin.
*******
Zaune yake a Office ya Tsurama waje Daya ido yana Tunani Hausawa Sunce ka gaida mai Gaisheka,Kimanin Wajen Wata Daya kenan kullum sai Barkat tayi mai Sakon Fatan alheri na Safe Dabam na Rana Dabam Tun Baya maida kai Hardai ya Fara maida mata Reply din Godiya Koda ba Kullum ba Lokaci Bayan Lokaci.
Acikin Ranshi Bai kawo komai ba...Hankalinsa ba"a kwance yake ba Shiyasa bai Fahimci kwana Biyu bai ga Sakonta ba,Domin Tun Bayan Hidimar Bikinan Dayayi Kudadensa Duka Suka kare Shagoma ba kaya Ga Bankinsa ba wani kudi Sosai 30k ne ya bari aciki na Siyan kayan Abinci Tunda Wata tayi Nisa ga Hidimar gininsa Dama Shi ya Tsaya Cak An gama komai Interlock din Farfijiyan gidan ne ba"a saka ba sai Fenti da kuma kayan Furnitures Domin Komai Sabo yake so ya Zuba Gashi bashi da kudi ga Haihuwan Hafsah bai Tanadi komai ba Ko Biyar bai bata na Ajiyar Haihuwa ba,Gabadaya Baya Cikin Natsuwarsa,kuma Shi ba Mutum bane mai Neman Bashi ba Gwarama ya Nemi loan a wajen aikinasu Allah barshi Duk Wata sai a Dinga Cirewa Cikin albashinsa Daya je nema awaje sai an gama jin Sirrinka Daga karshe ace Babu Cikin Tunanin Mafitan ne ta Fadomai arai Wayarsa ya zaro ya Shiga Wajen ma"ajiyar sako yana Duba Sakonta na Karshe wajen kwana Biyu kenan Tun Sakon Datayimai Da Daddare Sakonta bai kara Shigowa ba.
Sai ya Fara Tunanin anya Lafiya..? Bata Taba Tsallake Rana ba Tun Bayan Data Fara Turamai Sakon gaisuwa Sai wannan karon Tuni wata Zuciyar tace mishi ba Lafiya Tabbas Da Farko yaso ya Kira Layin nata Duk da bai Ma Adanata acikin Wayarsa ba Domin Abun bai Dadashi Da kasa ba Duk da Yafara Tunanin inda yarinyar ta Dosa a kanshi ammh Baya Tunanin zai bata Fuska basar da wannan Batun yayi ya Cigaba da aikinsa ammh sai me Zuciyarsa ta kasa Natsuwa yana ji kamar bai kyauta ba ko Bakomai ka Damu da wanda ya Damu dakai.
Tuna Haka yaasa ya Dauko Lambar Nata Daga ma"ajiyar Sakonninsa ya Kirata Tayi Ringing Harta Gama ba"a Daga ba Saiya kara Kira nan ma Ba"a Daga ba Tabe baki kawai yayi ya Shareta Daganan ya Tatattara Zencenta ya watsar Ya Cigaba da aikinsa Ya ma manta da ya Kira sai Da yana gabda Tashi Daga Office yaji wayarsa na Ringing Ya Dauko ya Duba baima Gane lambarba Domin ba Lamban wayarta ya Rike ba ya Daga Kiran da Sallama.
Dagachan Bangaran Bahiya Dake Haraban Asibitin Muslim Specialist Hospital Danmagaji ta amsa Sallaman Nashi Cikin mamaki Domin Ita ta zata Ko yar"ajinsu Anty Barkat din ne Duk da Taga Wani @ haka ta Sanya ma Lambar,Lokacin Daya Kira Wayar tana Jaka ita kuma Taje Siyo magani a pharmacy,Koda ta Dawo kuma Bata samu Duba wayar ba Baki Suna ta Zuwa kuma Suna Tare da Hajiya ne Yanzu ma ta Fito Rakasu ne sun Koma Gida ita da Bahijjat,Hajiya bazata Dawo ba Bahijjat ce zata Dawo kawo mu Abinci Tunda Tun Shekaran Jiya aka kawo Barkat din Ulcer dinta ayatashi kamar baza ta Rayu ba,suka kwasota zuwa Asibiti.
Cikin Mamaki Bahiya tace"An wuni lafiya..? Abdullahi ya amsa Shima Cikin mamaki bai Samu Zarafin mgana ba Bahiya tace"Amh..Mai Wayar Anty Barkat bata da lafiya Tun Shekaranjiya muna Asibitin musulmi an bata gado.."
Abdullahi yace"Subhanallahi...Meya sameta..? Bahiya tace"Wlh Ulcer dinta ce tatashin mata..Ammh da Sauki.."Abdullahi yace"Ayyah....Allah ya bata lafiya.."Ta amsa da Ameen da Haka Tayi mai sallama ta kashe Wayar,Abdullahi yayi Jim yana wani Tunanin kafin ya kada Kai Karamar Jakarsa ya Dauka da Key din Mashinsa ya Fice yana Tunanin in ya koma gida yayi Wanka kila yaje asibitin ya Dubata.
*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*
Y
*Shakira...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*031*
"Bai Shigo Gida ba sai da ya Tsaya Masallacin kan Hanya yayi Sallar mangariba kana ya kariso Gidan,abinci kawai yaci Sama sama yayi Wanka Hafsah Tana Falo Tana Tattara Kololin Da Sukaci abinci Su Amira kuma nata Waasa ita da Amir.
Kwashe komai Tayi takai Kitchen,Ta Rufe Kitchen din kana ta Dawo Daki Bedroom dinsu ta Wuce kai Tsaye Abunda ya bata mamaki ganin Abdullahi Tsaye yana Saka Links din Hannayen Rigan Yadin Dake jikinsa mai Ruwan Golden Cikin mamaki Tace"Abban Amira Fita zaka sake yi..?
Fuskarsa ba Walwala yace"Eh..! mamaki ya Kamata ganin indai Ya Shigo gida bai Cika Fita ba ko wani Waje zashi kafin ya Shigo Gida yake zuwa uzurinsa in kuma ya Shigo Da Wuya ya sake Fita sai kuma Gobe,Kallonsa ta karayi Ganin ya isa Gaban Madubi yana Yin Cubbing din kansa Kafin ya Dauki Hulansa Kalan kayansa Ya Saka yana Duba kansa a madubi.
Kasa Hakuri Tayi ta Sake Tambayanshi"Ina Zaka Abban Amira..? Naga Dare yayi kuma baka Fita in ka Riga ka Shigo Gida.."Dagowa yayi yana kallonta Cikin Mamakin yadda ta Damu da Fitarsa bai Saki Fuska ba Yace"Eh ta kama ne...Zanje asibiti ne Duba Mara lafiya.."Daga Haka kawai ya Wuceta Zuwa Falo Ta kada kai Tabiyo bayansa Key din Mashinsa ya Dauka yana Ma su Amira Tsawa kan su Daina Mugun Wasa,Dole suka Natsu kallon Hafsah yayi yana Fadin"Sai na Dawo.."Jikinta a Sanyaye Tace adawo lafiya Tana kallonsa ya Fice Kamshin Turaransa kuma ya Samu Wajen zama afalon.
Kasan Cafet ta koma Ta Zauna ta Mike Kafa,Ammh acikin Ranta Haka kurum Take ji ba Dadi Wani Tunani naso ya Shiga Ranta Game da Fitar da Abdullahi Sai Tayi Saurin Kauda Wannan Tunanin ta Kira Amira tace ta Dauko Sch Bag dinta ita da Amir Suzo in an Basu Homework suyi Da Gudu kuwa suka Shiga Dakinsu Amir na Fadin Shi zai Dauko Jakarsa da kansa da Kallo Hafsah ta Bisu Domin Daga Fuskarta Bata da Walwala.
Awajen Kofar kibo ya Tsaya ya Siya ayaba da Lemo,sai Kankana da kuma Maltina Guda Goma,ya Hada Dashi,kana ya Wuce yana Zuwa Cikin Asibitin ya Faka Mashin Dinsa kana ya Kira Wayar Barkat din sai Bahiya ta Dauka yace mata gashi yazo wani Daki suke tace suna Wajen Female ward a Aminity 2 Kashe Wayarsa kawai yayi ya Dauki Ledansa Dake Gaban Mashin ya Wuce Dayake Asibitin ba Bakonsa Bane yasan Dakunan.
Cikin Lokaci Sai gashi a Kofar Dakin Turawa yayi ya Shiga Da Sallama da Salisu suka Fara Hada Ido Sai Barkat wacce ta ke Zaune a Jingina Bayanta da Filo Bahijjat na Bata Faten Wake a baki Tana Karba da Dakyar Dukkansu yana Shigowa Suka Bishi da Kallo Baki Salisu ya Bude yana kallonshi Cikin Mamaki Barkat kuwa Dake Zaune sai da ta kara Bude idanuwanta Ta Kara Tabbartama kanta Shine ba gizo bane,Bahiya da Bahijjat kuwa kallo Suka Bi Juna Dashi Domin a karon Farko Sun Fara Tunanin ina suka san wannan Fuskar.
Gefen Gadon Abdullahi ya Karisa ya ijiye Ledan Hannunsa Kafin ya Bama Salisu Hannu suka gaisa Tare da Tambayan Juna ya iyalai,Salisu Duk da yayi mamaki Bai Tambaye Abdullahi ba,Shi kuma bai ce komai ba ya Dai Juya Bangaran Barkat wacce ta Sakarmai Ido tana kallonsa Cikin Sanyin Murya yace"Sannu ya Jikin naki..?cikin Muryan Ciwo tace'Naji Sauki..."Kada kai yayi yana Fadin"Allah kara afuwa.."Ta amsa da Ameen nagode a Hankali Tana gyara zaman Doguwar Rigar Dake Jikinta.
Salisu yace"Abdullahi Rabona Dakai Tun Ranar Daurin Auran Nazifi Fa haduwa tayi wahala ango kuma an koma Kaduna ko..? Abdullahi yace"Wlh fa..Sun koma Kaduna tun Satin chan Hala kunyi waya ne..? Salisu Dake Tsaye yace"Eh Munyi mgana Dashi yace min ya koma Bakin aikinsa..'"Abdullahi yace"Haka Hutunsa ya kare.."Salisu yace"Masha Allah..Allah Basu zaman lafiya.."Abdullahi yace"Ameen yasu Hajiya..? Salisu yace"Lafiya lau...Dazu ta bar Asibitin nima yanzu na Shigo Ina Shirin Wucewa ne ma sai kaga..Ke Bahi bashi Kujera mana kina Zaune.."
Bahiya Tayi Saurin Mikewa Tana Turama Abdullahi kujeran kai ya Girgiza yana Fadin"No..Nagode Nima ba zama zanyi ba Wucewa zanyi Dare yayi...Allah kara afuwa.."Dukkansu suka amsa da Ameen,bahijjat da Bahiya kuwa a kalaman Yayansu Salisu suka Tuna inda suka san Abdullahi Suna Ta mamaki Me ya Hadashi kuma da Anty Barkat Basu da amsa wannan Tambayan Abdullahi yayi musu Sallama zai Tafi Salisu yace su Fita Tare Yace Bahijjat ta Shirya ya ijiyeta Gida Tunda Bahi kadai ke kwana da Barkat din Godiya sukayima Abdullahi yace ba Bakomai Barkat Dake zaune tana Jin Tama Warke Gabadaya ya kallah yana Fadin"Sai anjuma..Allah kara afuwa sai munyi waya.."Kai ta gyada mai Tana Fadin"Nagode Ameen ya Allah...!
Daga Haka suka Fice Harta Bahiya Datatafi Rakiya Suna Baya Suna Gulma da Bahijjat,Barkat kuwa suna Fita ta Sulale ta Fada kan gado Tana ma Allah Godiya,Farinciki kamar ya Kasheta Wayarta Dake kan Dirowan Gadon ta Rarrafa ta Dauka ta Shiga Ma"ajiyan Text ta Turama Abdullahi.
_Tanque so much...For u Care...Barkat Relli Appricent..._ lokacin Daya ji Shigowar Sakon Suna Sallama ne da Salisu Shiyasa bai Duba ba,Salisu da Bahijjat suka Shiga Motar Salisu Ita kuma Bahiya ta koma Shi kuma sai ya Tada Mashin Dinsa ya Bar asibitin kusan Tare suka Fita da Salisu.
Ganin Tara ta wuce yasa yayi Gudu Bisa Mashin din ya Isa Gida Koda ya koma Tuni Su Amira Sunyi Barci Hafsah ma ta Bingire saman Kujera Shi ya Kashe Wutar Dakunan Dana waje ya gyara ma su Amira kwanciya Ita kuma Hafsah ya Dauketa Zuwa Ciki Sai Lokacin ta Farka ya Direta Saman gado tace"Abban Amira sai yanzu ka Shigo..?
Kai Tsaye yace mata"Eh..Na Shigo Kin kwanta kinbar kofa Bude."Hamma Tayi kafin tace"Wlh ina Jiran Dawowarka ne Barci ya kwasheni."Yana CireRigan Jikinsa yace"Aifa..Naga alama ai Tunda kika samu wannan Cikin kika zama Raguwa.."Baki ta Tura tana kunkuni Sai ta bashi Dariya ya Murmusa yana Fadin"Eh karya nayi..?ki Rantse da Allah ba ki zama Raguwa ba..? Banda barci babu Abunda kike iya Tsinana ma kanki Ballatana ma ni na Saka Ran za'a ji Tsausayina.."jin haka yasa taJuya Baya Tana Fadin"Sai da Safe.."Dariya ta kamashi yayi yana Fadin"Zaki sani ne Yarinya zan kamaki.."
Kayansa Ya Cire ya Sauya Dana Barci Wutar Dakin ya Kashe kana yazo Gefen Hafsah ya kwanta ya ja musu Bargo Ya Jawota Jikinsa ya Rumgume yana Sakin Ajiyar Zuciya tana Jinsa sai ta Kara lambo Shi kuma yasan Batayi Barci ba yasa ya Zura Hannu yana Shafa Cikinta Da Sauri ta make Hannunshi Dariya yayi yana Fadin"Au baki barci ba..? Da sauri tace"Allah nayi barci bakai ka Tadani ba.."Tafada a Shagwabe tana Tura baki Hancin nata ya lakuce Lokaci Daya yana Kara Rumgumeta Cikin Jikinsa.
Washegari kuma Sai da yaje office kana ya Bude Sakon Barkat Mirmishi kawai yayi sai ya Kirata wannan karon ita ta Dauka ya Tambayeta Jiki tace taji Sauki Kilama an juma su koma Gida yaji Dadin Haka yayi mata Fatan Sanun lafiya Kafin ya yanke Kiranshi yana Shirin Tashi Office yaga Sakonta na anyi Dirsharge Dinsu bai Kirata ba sai ya Tura mata Sako da Cewa"Alhamdulillah...May Allah grant u Shifa Ameen..."
Bai Kirata ba Sai da aka kwana Biyu da Sallamanta kana ya Kirata Yana Tambayanta ya Jikinta tace mai ta samu Sauki Sosai yanzu hakama tana Shirin Komawa Cikin makaranta Saboda Suna da Test Ranar Monday Har ma yana Tambayanta ta samu Wajen zama ne tace A"a Hostel zata je Wajen Bahiya Suyi Sukwatin,Fatan alheri yayi mata Kafin Suyi Sallama da Juna Barkat Tana jin Cewa acikin Ranta Lokaci kadan Kawai ya Rage Burinta ya Cika akan Abdullahi.
Su Bahiya suka Gayama Hajiya Labarin Zuwan Abdullahi Asibiti da kuma Kiran da yake mata itama Tayi mamaki Sosai,Hakama Salisu Dayazo ta Tambayeshi ko yasan Wani Abu Dake Tsakanin Abokinsa da Barkat din yace Wlh bai sani ba Shima Yadda Ya ganshi A asibitin ya bashi mamaki matuka Tunda bai mai mganar ba Shima bai Mishi ba Hajiya Tace Allah sa muji Alheri Domin Tana Hasashen Wani Abu Allah ya Tabbatar mata,su Bahiya da Bahijjat kuwa gajiya sukayi da Tambayan,Barkat meke Tsakaninta da Abdullahi ammh Wlh ko kallo basu Isheta ba Basu Damu ba sanin Halinta na kyaluwa da Banzatar da Mutane Haka Har Ranar lahadi Tayi Ita da bahijjat suka Tattaro Suka Koma Cikin Makaranta Dama Ciwon Barkat din ya Dawo da Bahiya Din Bahijjat Kadai Suka Bari Agida Aina ma Tana Makaranta ammh Ta kusa Dawowa Domin Exams Zasu Fara ayi Hutu Su Dawo Gida.
Abdullahi bai kara Neman Barkat awaya ba itama Bata Kiranshi Sai dai kowani Safe da Yammah Da Sakonta yake cin karo,Har ya Riga ya saba da Sokonninta in bai gani ba har Damuwa yake,Domin acikin Sakon nata Dauke da kalamai na Nuna Damuwa Sosai da Mutum da kuma addu"o'in Fatan alheri da nasara da kuma Cigaban Rayuwa Uwa uba kuma da Tambayan Lafiyan iyalansa Tun Baya maida kai har ya zama Shina ya kan Tura mata na Happy Jumma"ar ko Gud Morning Duk a zuwan kulawa yabawa ne.
Ranar Friday ya Shiga Cikin Makaranta sai ya Kirata tace Tana Cafterian,Sai yace Kawai Ta Jirashi Gashi nan zuwa ba Jimawa sai gashi Barkat Tayi mamaki Sosai kan yadda Abubuwa Suketa zuwa mata da Sauki nan suka zauna Suka gaisa ta sa aka kawo mishi Drinka da Snacks,Yana ta mata Tsiyan sai yaci Tunda yar makaranta Tana da kudi,Ita kuma sai mirmishi Take Cikin Jin Dadi da jin kai,Sun Dan Jima atare awajen Suna Hira Farkon mganace kan Harkan karatun kafin sun gangara kuma Kan Harkan Rayuwa Shi ya Daukesu Wajen awa Daya suna Hira Ya Fahimci Barkat Tana da Ilimi Sosai da kuma wayon Sanin zamantakewar Rayuwa Sosai Ganin yammah tayi yaasa yayi mata Sallama da zai Tashi ya Biya Duka kudin Abunda suka ci Barkat din Ta bata rai akan ita zata Biya ya Hanata Dole ta Hakura Tare Suka Jero tare Har Zuwa Wajen Daya Faka Mashin Dinsa nan sukayi Sallama kan sai Sunyi yawa Ya Hau Mashin Dinsa ya Tafi Tun yana Hanya yaji Shigowar Sako Sai da ya isa gida ya Duba ya ga Sakon Godiya ne Masu Cike da kalaman Jan Hankalin Da Namiji Daga Barkat Abun yayi Mishi Dadi Sai da Shima yamaida mata da Sakon Godiya Shima Tare da kalaman Jinjina Gareta Daga karshe yayi mata Fatan Samun Nasara a Test din da Suke Rubutawa,Lokacin yana Falo ne Zaune kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon Hafsah kuma na Zaune,a kasa ta Mike kafa Su Amira kuma na gefe suna Wasa Mgana ma Take mai kan Zata Fara Zuwa awo ammh Gabadaya Hankalinsa Baya Tare da ita Ganin haka yasa ta Tago Tana kallonsa Sai Taga yana Mirmishi Shi kadai mamaki ya Cikata Tayi Galala Tana Binshi Da kallon Mamaki Domin Abunda Bata sani ba Barkat din ne Tayi ma Abdullahin Tayin ko zasu koma Whatsop ne Yace mata Why not Dama yana Online sai gashi Tamai Mgana Korafi ta Faramai na Yadda Ta Girmamashi a matsayinshi na Bakonta ammh Shi kuma Sai ya Biya kudin Komai Shi kuma sai ya na mata Wasa yace Watarana Zai zo Su Fita Tare Sai ya karar da Duka Kudin Kashewarta na makaranta Tun Hafsah na kallon Abdullahi Tana mamaki Hardai ta Daina Tana Kallonsa ya Tashi ya Shige Ciki Bayan yace mata Ta kai Su Amira Ciki Da ido ta Bishi Acikin Zuciyarta Tana mamakin me ya Dauke ma Abdullahi Hankali Wanda yasa ko Mganarta bai Saurara ba..? Bata da wannan amsan Dole ta Kira Amira tace ta kama Hannun Amira Suje suyi Fitsari Tazo su kwanta Domin Tunda ta Zauna Taji Bayanta ya kage Bata iya Tashi.
*******
Bangaransu Jidda kuwa Sai da Suka kwashe Kimanin Sati Biyu Suna Cin Amarsun kana Sakina ta Diro Gidan,wanda babu Wanda yasan da Zuwanta Ko Chan Gidansu Basu sani ba Domin Hajiya da Alhaji Badamasi yace bazata koma ba sai Nazifi ya Tako ya zo da Kafarsa ya Bata Hakuri Toh ina Zata Jira Tunda Nazifi ya Shukata kamar Dussa ta kirashi Har sau Shurun Masaki ammh bai Daga Kiranta ba kuma ta Turamai Sako Shima bai Taba maida kai Ba ganin Haka yasa ta Shirya ta koma Abuja bakin aikinta Duka Duka kwana Shida tayi Ta Dauki Excuse na Bata Jin Dadi Daga Abujan Direct Kadunan ta wuce.
Ai kuwa Tun Ranar Data Diro garin Da Mugun gani taci karo,Domin Nazifi da Jidda ta iske a Tsakar Falo Yana mata yan Goye Goye Kuma Dukkansu ba wasu kayan Kirki ajikinsu Sai Wani Wasan Banza Suke Abun ya Soki Zuciyarta ganin Yadda Nazifi yayi kiba Sosai ya Murje kamar ba shi ba Ita Kanta Jidda ta Sauya Aure da Jin Dadin Rayuwa Sun Sauyata ta zama wata Babbar mace kugunta da Kirjinta sun kara Cika Sosai.
Su basu ma san da Shigowarta ba Sai Jin Katon Tsakin Dataja musu a Tsakar kansu sukaji Gabadayansu suka waigo Ganin Sakina Sai da gaban Jidda ya Fadi Tana Goye Bayan Nazifi ganin bai Sauketa ba itama sai ta kara Lafewa,Kallon Sakina yayi Yana Fadin"A"a uwargida Sarautar mata..Kece Tafe ba Sanarwa.."?Yafada Lokaci Daya yana Sauke Jidda yana Fadin"Babyna Sauka muje muma Antynki Oyoyo..."
Sauka Jidda Tayi tana Murza ido Cikin Shagwaba Take Fadin"Ni ban yarda ba yaya sau Goma fa kace zakamin Doki Dokin.."Kanta ya Shafa yana Fadin"Ehmana..Dole nayi miki Babyna,...Kinga Antynki Ta Dawo Bari mu gaisheta sai muzo in yi miki Doki Dokin ko..?jin haka yasa Tawashe baki tana makaleshi Sakina Dake kallonsu Taji Wani Bakinciki Na Taso mata Daga kasan Ranta bata Jira Sun kariso ba Taja karamin akwatinta ta Shige Dakinta Tana Kokarin maida Hawayen Idanuwanta kada su gani Taji kunya,Tana Shiga ta Banko Kofa Harda saka key Ta Sulale nam kasa Lokaci Daya tana Fashewa da wani kuka Dake Fitowa Daga Kasan Ranta.
Da kallo Suka Bita Nazifi ya Tabe baki irin mai Damu ba Jidda ce tace"Yaya naga ta Shiga Ciki bata Tsaya mun gaisa ba.."Nazifi ya rikota yana Fadin"Karki Damu Bbyna..Zaku gaisa anjuma Yanzu muje Kitchen na Tayaki Girki in mun gama Muje muyi wanka ina so zan Fita ne.."Da to ta amsa kafin Su Rankaya Tare zuwa Kitchen Domin indai yana Gidan Tare suke komai Abunsu Gwanin ban Sha"awa,in ka gansu sai sun Baka Sha"awa Sosai Jidda Take Fitoma da Nazifi Salo Salon da Yayyinta su Subai"atu suka Koyar da ita,Dawowarsu kaduna Zannira tazo Itama Taje mata Hakama Hajiya Sa"a da Hajiya lariya Sunzo mata Hakika Hajiya Sa"a tafi kowa Farincikin Ganin yadda yarta ta koma gwanin Ban Sha"awa nan suka wuni sai yammah Suka Tafi,Nazifi da Jidda sukayi ta ina suka saka Dasu Hajiya Sa"a taji Duka Hankalinta ya kwanta Tana ta Jin Dadi da alfaharin yarta ta samun Gidan Zama nagari Tare da Jajirtatten Miji mai Kokarin Sauke Nauyin Dake kanshi,Su Mama kuwa kullum sai ta Kirata sunyi mgna ita da Inna Abu Mariya ma Haka Tagama nacin Mariyan Tazo Taki Zuwa Tana Tsoron ya Abdullahi Domin Tana da Tabbacin indai yaji labari bazai Barta ba.
Tare sukayi Girkin suka Gama Doya Jidda ta Dafa da Miyar Soup na Kifin Saidin,Tare suka Jera komai Bisa Dinning,ganin ana Ta Kiran Sallar mangariba yasa Nazifi ya bar Jidda na gyara Kitchen din Shi kuma ya koma Daki ya Shiga wanka ya Shirya yazo ya iske Jidda afalo yace mata zai Fita masallaci Dagachan zai Biya wani Waje Ta Faramai Shagwaban kar yaje ya zauna ya Rumgumeta yana mata alkawarin bazai Dade ba Har Kofar Falon ta Rakashin kafin suyi Sallama tana mai Addu"an Dawowa lafiya tana Juyowa Taci karo Da Sakina Data Fito Daga Cikin Dakin Ta Tana wani Taku Daya Bayan Daya tayi wanka ta sauya kaya ammh kallo Daya zakayi mata ka Fahinci Tasha kuka Domin ga Fuskarta nan ta Kumbura da idanuwanta.
Kallon Jidda take Ido Cikin Ido Irin na Wulakancin nan,ita kuma Jidda sai ta Dauke kai Tana gaisheta Bata amsa mata ba sai ma Tsaki Data saki Ta koma ta zauna kan Daya Daga Cikin Kujeun Falon Lokaci Daya Tana Daukan Remot din Tibin Dake Falon Jidda bata Damu ba ta Wuce Cikin Bedroom dinta itama tana Juya mazaunanta, da kallon Mamaki Sakina ta Bita Tana Tunanin Dan Hakin daka Raina Daman Shi ke Tsole maka ido.
Nazifi Sai Wajen 9pm ya Dawo Gidan Lokacin Jidda tasha Wanka an kashe Dauri itama Tazo Falo ta Zauna Tana Jiran Dawowarsa yana Shigowa tatashi da Gudu ta Daneshi tana mai Sannu da zuwa Shima Rumgumetan yayi yana jin Wani Farinciki acikin Ransa sai da suka kariso Falon kana ya lura da Sakina Cikin Mamaki yace"A"a uwargida Sarautar mata..an Fito..?Kallon Tara Saura tayi musu kafin ta Dauke kai Bai Damu ba Jidda taja Hannunsa Zuwa Saman Dinning Daya ma Sakina Mganan tazo Suji Abinci Ko Kallonsu batayi ba basu Damu ba Sukaje suka cinyarda juna Sakina na Zaune ne ammh Rabin Hankalinta na kansu Duk yadda taso Ta kauda kanta Ta kasa ganin Karuwan cin yarinya karama Kiri Kiri,Shi kuma yana Zaune yana Biye mata,Taji kamar Bakinciki ya kasheta.
Bayan sun kamallah Cin Abincin suka Dawo Falon nan ne Nazifi yace yana son mgana Dasu Dukkansu Nasiha ce kawai yayi musu sai kuma mganar Raba kwana,ya Saka cewa in Sakina ta Dawo zai koma Wajenta Har tatafi Tunda dai ita bamai zama bane sai tayi Sati Uku bata zo Gida ba,In kuma Batanan sai ya koma Wajen jidda,Ya bama Sakina Daman tace wani Abu taki cewa komai sai ma Tsaki Data saki Ta Tashi Ta Shige Ciki Da kallo Dukkansu suka Bita Jidda kuwa Duk ta Damu na yadda yau zasu Raba makwanci ita da yayan nata,Ammh Daya Lura da Haka sai ya Fara Kokarin kwantar mata da Hankali Sai da ya Rakata Har daki tayi wanka ya Tayata ta saka Kayan Barci ya kwantar da ita Shima ya Bita suka kwanta Suna makale Da Juna Yana mata Hira Sama sama Har Barci ya kwasheta kana ya Zare Jikinsa ya gyara mata kwanciya ya Rage mata Wutar Dakin ya Lallaba ya Fice Zuwa Dakin Sakina.
Koda yaje Dakin Sakina ya Iske ta kwance kamar mai Barci nan kuwa ba Barci Take ji ba kuka Take yi jin Motsinsa yasa tayi Lamo kamar mai Barci Tailet ya Shiga ko Ta kanta bai bi ba,Wanka yayi Ya Fito ya Saka kayan Barci ya Koma Gefenta chan Nesa ya kwanta ya juya mata Baya Jin Haka yasa Kukanta ya karu Na Bakinciki ganin Nazifi ya Juya mata Baya Shi ko Daman Ba Tun yau ba ya Daina neman wani abun Wajen sakina sai Dai in da Son Ranta.
Gajiya tayi da kukan ta Rarrafa ta isa Gareshi Ta Rumgumeshi Tana kuka yana jinta yasan Bukatartace ta kawota sai ya Shareta ganin bazata iya Jurewa ba yasa ta Faramai Salo Salo Wanda ya kasa Jurewa ya Juyo Gareta Shima ya Fara maida mata martanin Wasanninta Awannan Daran dai Sun Mori Juna Sosai Domin yayi mamakin Hadin kan da Sakina ta bashi Wanda Shi Rabon da ta bashi Irinshi Har ya manta.
********
*Bayan Wata Daya...*
Acikin Wata Dayan Daya Gabata zaku matukar mamaki in nace muku Soyayyah mai karfi Ta Shiga Tsakanin Abdullahi Da Barkat,wanda Daman ita Barkat din ita ta Fara Jan Tsanin Da Abdullahi ya Hau kai,Batare Daya sani ba ya jishi ya Fada Tarkon Soyayyar Barkat Cikin kankanin Lokaci ba Domin komai ba sai Domin Ta iya Salon kulawa da Namiji Da kuma Salon yadda Namiji zai Fada Tarkon Sonta Batare Daya sani ba.
Da Farko Abun nasu ya Fara da Kamar wasa ne sai kuma Abun ya zama na gaskiya Suna Chart kuma Suna Waya kuma suna Sharing Din mgana ta Text massages,In Abdullahi ya Shiga Makaranta Zai Nemata Suje Cafteria ko Libary su sha Hira sai Yammah Suke Rabuwa wani Lokacin ma sai Dare zai Taho Ta bashi Su Chaculate da Minti Tace ya kawo ma su Amira,In ya kawo musu Baya Cewa Inji Wance Ita kuma Hafsah Duk a Tunaninta Shi ke Siyowa ammh kuma ta Fuskanci Wasu Chanje Chanje Daga Abdullahi kamar na yawan Rike waya a ahannunsa Duk da Baya Waya da Barkat din sai ya Fita ammh Suna Chart ko Massages in yana Gida kana Yanzu Sai ya Kule kansa acikin Daki yana ta latsan Waya wani Lokacin Abincinsa baya ci sai Chan Dare Hafsah dai Har ta kare ta tambayeshi yace Bakomai Sai kawai ta kyaleshi ammh kuma idanuwanta na kanshi Domin Tafi kowa sanin Waye Abdullahi.
Abdullahi Abun yazomai a Bazata ne a Baya bashi da Niyyar kara Aure Domin yana ganin yana da Hidomomi,Sai dai Shigowar Barkat Rayuwarshi komai ya Sauya yaji yana da Sha"awar kara Aure nan kusa Duka Burinsa na Hafsah ta Haihu a Sabon Gida ya Rushe shi ya Fara tunanin in Barkat Zata amince Dashi zai gyara Dakin Dake kusa da na Hafsah ya ijiyeta kafin Komai ya kankama Zuwa Bayan Haihuwar Hafsah din yagama Komai sai su koma Gabadaya.
Hafsah Ta Fara zuwa Awo asibitin Tudun Wada awon Cikinta wanda ke Cikin Wata na bakwai yayinda Gefe Guda kuma Soyayyah Tana kara nuna Tsakanin Abdullahi da Barkat,Babu Wanda Abdullahi ya gayamawa sai Nazifi wanda Shima ya Bashi Shawaran Shi yana ganin bai kamata yayi Aure a irin wannan yanayin ba ammh Sai ya Nuna mai ba komai Zai Tuntubi Barkat din yaji in zata amince ta Fara zama awannan Gidan da Suke Ciki,in ta amince zai Ggyara Dakin dake kusa dana Hafsah ta Fara zama kafin ya kamallah Ginin Gidansa.
In zai yi Wayar Dare da Barkat din Falo yake Dawowa Saboda Hafsah yanzu Saurin Barci Gareta nan da nan Data kwanta sai Barci ya kwasheta,Yau ma Din Haka din ne ta kasance Tun 9pm ta kwanta Su Amira ma Abdullahi ya Kaisu Dakinsu ya kwantar Dasu,ya Dade a falo Suna Charting da Barkat din sai ya Nuna mata yana son zai yi mgana da ita ammh Awaya zai Kirata Tace Shikenan.
Sai da ya Duba Ya ga Barcin Hafsah yayi Nisa, kana ya koma Falon ya kira Barkat din Bayan ta Dauka Sun Gaisa Tatambayi Hafsah Dasu Amira,shi kuma yana Tambayanta karatunta tace Alhamdulillah,Tunda Tana makaranta bata koma agida ba Har Bahiya ma Taje gida Weekend ita bataje ba Saboda Basu gama Test dinsu ba,Dayake ana Saka musu Interval sosai.
Gyara Kwanciya Abdullahi yayi yana Kiran Sunan Barkat Jin sa Cikin Serious Tone yasa itama ta Natsu Cikin Sanyin murya yake Cemata"Barkat kinsan dai ni bamai karfi bane.Kinsan inda nake aiki..Kuma kinsan Ina da Mata da ya"ya Biyu sai kuma Cikin na uku..Bayan Haka ina da Nauyin Iyayena Data kannina Bayan Ta iyalaina Da kaina..Kuma kinga ni ba yaro bane da zan Tsaya ina ta Yaudaranki Hakika kinmin kuma ina Son ki zama abokiyar Rayuwata in kin amince zaki iya Zama Dani acikin Gidana da muke Lallabawa Dani da matata da ya"yana Zuwa gaba in komai ya Daidaita na kamallah Gidana sai mu koma..In kin amimce ni kuma nayi Miki alkawarin nan da Wata Daya zan Killaceki agidana a matsayinki na Matata..!
Zuciyoyi Biyu ne Suka Buga alokaci Daya Zuciyar Barkat ta Buga da Farinciki mara Misaltuwa zuciyar Hafsah kuma Dake Tsaye Kofar Bedroom dinsu ta Buga ne da Fargaba da mamaki Hade da wani Kishi Daya Taso mata Daga kasan Ranta Bakinta ta Dafe kada Kukan Daya Taso mata ya Fito,Tana jinsa yana Fadin"Alhamdulillah.....Zan gabatar da mganarmu gobe Wajen Aminin Mahaifina Dake Matsayin Uba garemu...Yadda mukayi Dashi zan sanar Dake..."
Baya Taja da Sauri Saboda kada Yaji Motsinta Da Sauri ta Tura Kofar Tailet ta Shiga tana maida Numfashi,Kasa Tsayuwa tayi jin kamar Dan Cikinta na Juyawa,Kasa ta Sulale Hawaye suna kwarayomata Lokaci Daya Tana jin wani zafi acikin Ranta Fitsari ne ya Tada ita ta Farka Sai taga Bata ga Abdullahi ba Abun ya bata mamaki Ta sauko Daga kan Gadon zata Falo sai ta Fara Jin mgana Sama sama Shine yasa ta Labe Daga Kofar Bedroom Daidai Lokacin Dayake ma Barkat wannan Bayanin zufa ya ketoma Hafsah kasan Bayin Ta Sulale Fitsarin Data ke kokarin Rikewa ya kwace mata nan kasa ta Sakeshi Lokaci Daya tana Fashewa da kuka Jin Motsin kamar Shigowar Abdullahi Cikin Dakin yasa ta Dafe Bakinta kar ya ajiyota ammh acikin Ranta maimaita kalmar Aure kawai atake Lokaci Daya da mamakin yadda Abdullahi ya iya Boyemata wannan Bakon al"amarin....!
*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*
*Janafty...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*032*
"Cikin Tafiya a hankali ya Shigo Cikin Bedroom din,Sadaf Sadaf Saboda kada Hafsah ta Farka kan gadon ya kwanta Lokaci Daya yana Laluban gefen da Hafsah ke kwance yajita Wayam sai ya mike Zaune yayi amfani da Hasken Wayarsa ya Haske Gadon yaga Bai ganta ba sai ya Fara Waige Waige kafin ya mike Tsaye Wutar Dakin ya kunna ya Haske ya Gauraye Motsin Dayaji a Tiolet yasa ya saki ajiyar Zuciya sai yanzu Zuciyarsa ta bashi Tana Bayi ne.
Gefe Daya kuma na Ransa na Wani Tunani kodai Hafsah Tajishi yana waya ne..? Anya kuwa..? Duk sai ya Tsargu Jin Shuru bata Fito ba yasa ya karisa Kofar Toilet din yana Kiran Sunanta Jin Motsinsa da Kiran Sunanta Dayake yi yasa tayi Kokarin Dafa Bangon Bayin ta Mike Tayi Saurin kwabe Rigar Barcin Jikinta ta jefa Cikin kwandon kayan wankinsu Dake Cikin makewayin,Ta yi Sauri ta Zari Towel Dake Rataye saman Wata igiyan Dake Daure Daga sama acikin makewayin.
Taba Kofar yayi yana Fadin"Wai Hafsah me kike Cikin Toilet da wannan Daran..? Kina lafiya kuwa..? Dakyar ta iya Bude baki tayi Gyaran Murya Lokaci Daya Hawaye na kara kwaranyomata Jin Datayi yana Kokarin Bude kofar yasa ta Kamfaci Ruwa a wani karamin Kofi Daga Cikin Bambin Dake Bayin ta Watsa ma Fuskarta Saboda Kada Abdullahi ya gane tayi kuka..
Bude kofar Tailet Din yayi ya Shigo Lokaci Daya yana Bin Hafsah da wani kallo na kamar bai yarda da ita ba ita kuwa sai Tayi Tsuru Tsuru Da sadda kai kasa Saboda kada ya Fahimci Wani Abun Shi kuma mamakin ganinta Da Towel ne ya kamashi Cikin mamaki yace"Ya naganki Haka kuma..? Wai lafiyarki kuwa..? Ko baki lafiya ne muje Asibiti..?
Da Sauri Hafsah ta Girgiza kai Tana"A"a Lafiyata Kalau...Fitsari ya Tadani sai kuma naji Zafi Shine nace bari nayi wanka kila naji Dadin Barci.."Tafada tana Kauda kanta ganin irin kallon Dayake mata.
Cikin Tsareta da ido yace"A'a...Taya zaki yi wanka Awannan Lokacin..? Pass 12 fa kuma kinga bake kadai bane Hafsah Ko zaki bar wankan nan ne Na Samu Ruwa da Karamin Zani na Dinga Shafa miki Ajiki Kila kya samu Barci.."kai ta Girgiza Tana Fadin"Don Allah ka barni nayi zan fi samun natsuwa..Kaga kuma Bayin Daki ne fa.."Tafada Lokaci Daya tana Jan Botiki ta Fara Zuba Ruwa da kallo ya Bita wani Tunani na Shiga Ransa kafin ya kada kai ya Fice Lokaci Daya yana jawo mata Kofar makewayin.
Da kallo Ta Rakashi mai Cike da kunci kafin kukan Datake Rikewa ya Fito ta Sakeshi Gabadaya ammh Tanayi tana saka Hannu kada Abdullahi ya jiyota,Dakyar ta iya Wanka wanda Watsama Jikinta Ruwa kawai Tayi,sai kuma Tsarkin Fitsarin Data bata Jikinta Dashi,Alwala ta Dauro Domin Ta Tabbata Barci bazai Taba Daukan ta ba gwara ta kai kukanta ga Allah kila ya yaye mata Damuwa...!
Tana Fitowa Ta iskeshi kan gado yana Jiran Fitowarta Kai Tsaye ya kalleta yana Fadin"Kin Fito..? Yake tamai Lokaci Daya tana gyadamai kai,Wardrope dinta ta Nufa ta Bude ta Dauko Wata Doguwar Riga ta saka da Hijabi Ta Dauki Darduma ta Shimfida Cikin mamaki yake Binta da kallo ganin zata kabarta Sallah yasa ya Katseta Lokaci Daya yana Fadin"Me zaki yi kuma..? Badai sallah ba..?
Kai Tsaye tace"Eh salla zanyi.."Cikin mamaki yace"Sallah..? Baki sallar Isha"i bane kafin ki kwanta..? Hafsah tace'"Nayi..Na kasa Barci ne Shine nace bari kawai nayi alwala nayi Sallah koda Raka"a Shida ne.."Abdullahi dai kallon Hafsah kawai yake kamar Wata Bakuwa ganin Tana mgana Bata son kallonsa.
Cikin Tsuramata ido yake Fadin"Yanzu fa Farkon Dare ne Hafsah...Ga Jikin ki yayi Nauyi ke baki Tsausayin kanki ne..? Allah ma ya sani Saboda haka bar zencen Sallar nan maza kizo ki kwanta..'Yafada yana nuni da bata Umarni,Kai ta Sadda tana Fadin"Bari to nayi Shafa"i da wuturi Domin banyi ba barci ya kwasheni.."Tafada Batare Data Saurareshi ba ta kabarta Sallah Da kallon mamaki kawai ya Bita acikin Ranshi yana Tunanin kodai Hafsah taji Wayarsa da Barkat ne..? Ammh in Taji ai bai ga alama ba sai dai yana Tunanin kodai bata da lafiya ne..?
Yana nan zaune yana kallonta tayi Idar da Salla Raka"a uku ta Zauna Lokaci da mike kafarta kanta na kasa tana kokarin son maida Hawayenta kada Abdullahi ya gani,shi kuwa yana ta lura da ita da Duk wani motsinta Yana kallonta ta Daga Hannu Tana addu"a Hawaye sun Fito Daga Cikin Idanuwanta Saukowa yayi Daga kan gadon ya Tsaya agabanta yana Fadin"Hafsah..Lafiyanki kuwa..? Kina addu"a kina kuka..?
Jin Haka yasa tayi Saurin Dago kanta Lokaci Daya tana Dangwalo Hawaye tana Fadin"Kuka kuma..? A"a Digon Ruwa ne inaga Abban Amira.."Jinta kawai yayi yana Binta da kallo ganin yadda take kokari wajen Tashi yasa ya saka Hannu ya Dagata cak zuwa kan gado ya kwantar da ita ya Lullubamata Bargo bayan ya Ciremata Hijabin Jikinta Kallonsa Tayi kafin ta kakaro Mirmishi tana Fadin"Nagode.."Mirmishi yayi mata kafin ya Kashe Wutar Dakin ya koma ya kwanta Abayanta ya Zuro Hannuwansa ya Zagayeta Tsakanin Cikinta ajiyar Zuciya ta Sauke Lokaci Daya da wasu Siraran Hawaye suka Zubomata Kalaman Abdullahi nayi mata lugude acikin Ranta kasa Motsi Tayi Saboda kada ya Fahinci Halin Dayake Ciki Bata son ya Fahimci ta san komai Tunda dai bai yi Niyyar sanar da ita ba Duk da ko Tana matsayin matarsa...Ta Dade Batayi Barci ba Tana Tunanin Halayyar Da Namiji Shi kuwa Tana jin Saukar Numfashinsa akan Dokin Wuyanta alamun Barci ya kwasheshi ita kuwa sai gabanin Asuba kana Barci ya iya kwasanta Barci mai Cike da Rudani Da Damuwa.
******
Washegari ma Tana kallonsa Tun Safe yana ta Shiri Su Amira ma Kiran mai mashin Dinsu yayi yace yazo ya kaisu Shi yana Sauri Tun 7am ya Fita ko karyawa bai yi ba yace mata Suna da Meeting a office kallonsa kawai take bata yarda Dashi ba Haka kurum acikin Ranta taji Cewa Wajen Baba wada zashi Kan Mganar Dataji yanayi Jiya,Hawayenta Ta Share kawai ta koma ta lafe kan gado Bayan Mai Mashin Dinsu Amira yazo ya Tafi Dasu kwance kawai take Ammh gabadaya tana jin kanta kamar ba ita ba in ta Tuna wai Abdullahi zai kara Aure.
Illai kuwa Abdullahi na Fita Gidan Baba wada ya nufa ya Fara zuwarmai da mganar,Shi kanshi Baba Wada yayi mamaki Karin Auran na Abdullahi sai dai kuma bai isa yace Don me zai kara Aure Tunda Allah ya Hallartamai Baba wada yace ba Damuwa in Ya tsara komai sai ya kira Mijin Goggo Habiba Su tafi gidansu Barkat din neman Auran Abdullahi yace ya bashi nan da kwana Biyu zai kirashi a waya su Karishe,Da haka suka Rabu da Baba wadan ya Karisa Gidan Mama itama ya zauna ya gayamata yana son ya kara Aure ba Mama kadai Dake zaune ba Hatta da Mariya Dake Cikin Dakinsu Tana Shirin zuwa asibiti,sai da ta Razana Mama ta maimaita Kalmar Auren Da Abdullahi yace zai kara yafi a kirga Cikin nuna ma Abdullahi kamar yayi gaggawa ya bari zuwa Bayan Hafsah ta Haihu ammh sai Abdullahi ya nuna mata Babu komai Ba matsala,Jin haka yasa Mama taja bakinta tayi Shuru kafin ya Tafi sai yace Ma Mama ta Rufe mganar kar kowa yaji Saboda Bayaso mganar takai kunnin Hafsah Don bai gayamata ba Ya bari sai komai ya kamkama uwa uba kuma Cikin Dake Jikinta Baya so Hankalinta ya Tashi.
Bayan Fitarsa Mariya Ta Fito Daga Dakinsu Tana Fadin"Mama Aure naji ya Abdullahi na mganar zai kara ko..? Mama ta kada kai tana Fadin"Hmm Haka yace Nima Abun ya bani mamaki Aure haka Cikin gaggawa..Ni Wlh ban taba kawoma yayanku Aure yanzu ba.."Mariya tace"Tabdijam...Lallenema Toh Mama a ina zai Sakata..? Bai fa gama Gininshi ba Bikin Jidda ya Tsaida komai ga Anty Hafsah da Tsohon Ciki Mama Gaskiya Ya Abdullahi yayi gaggawa.."Tafada Cikin Jin Haushi kamar za"ayi ma kishiya.
Mama tace"Nima shi nagani...Naga Yadda yake Mganar kamar yana son Auran kusa ne ko wata yarinya ce kuma Oho Donni ko Da zence banji Labarin yana neman Aure ba.."Mariya dai ta Rike baki kawai Tana Jajantama Lamarin Haka Auwal ya Shigo ya Samesu yana Tambayan lafiya Mariya ta Koramai Jawabi ido ya Zaro yana Fadin"Aure..? Kan bala"i ita Wacce yarinyace zata kawo kanta..Nifa ina ganin mai iya zama da ya Abdullahi Bayan Anty Hafsah da Wahala Wlh..".
Mama tace"Atoh..Tazo dai ta gani..In Zasu Daidaita in batayi Hakurin Hafsah ba ko"ina bazasu jeba za"a fara jin kansu.."Nan ne dai suka Hadu Suna Ta Tattauna mganar, Karyawa sukayi Mariya ta Fice Zuwa asibiti Auwal ma wanka ya Shiga Domin yana da Class karfe 9am na Safe suka bar Mama Tana Janjanta Abun Cikin Ranta na Tsausayin Abdullahi Daya Jajibo ma kansa Aure
Abdullahi kuwa Sai da yaje Office ya Kira Nazifi yamai Bayanin komai Nazifi ya Cika da Mamakin Jin har yanzu Abdullahi bai bar mganar nan ba Cikin Rashin son yarda Nazifi yace"Kai mutumina anya Abun bai yi kusa ba..Kaga da baka gama gininka ba..Ga Hafsah nada Nauyi Duk kai kadai fa..! Ni ina ganin da kabar mganar kara Auran nan zuwa gaba.."Abdullahi yace"Karka Damu Duk na mata Bayani ta Fahimta..Ta yarda zata Zauna agidana Zan gyara Dakin Da nake ijiye Mashin Dina kafin Zuwa gaba na karisa gina na..Nidai yanzu ka Kira Salisu kai mai Bayanin komai.."Nazifi yayi ajiyar rai kafin yace"Shikenan bari na Taboshi naji.."suka rabu akan yadda sukayi zai Kira Abdullahi ya gayamai.
Nazifi ya kira Salisu Engr.Bayan sun gaisa Nazifi ya koramai Jawabin Komai Salisu bai yi mamaki ba sai ma Farinciki Daya Cikasa Dama Tun ganin Da yayi ma Abdullahi a asibiti yazo Duba Barkat yake ta addu"a aransa Allah ya Tabbatar da Zarginsa Domin Har ga Allah Zai mata Sha"awar samun Nagartattacen Miji irin Abdullahi,Sun Rabu da Nazifi kan anjuma da yammah zai je Gidansu ya samu Hajiya Da mganar ,daganan zai samu Wan Babansu yayi mai mgana Wanda Daman Bayan Rasuwar Mahaifinsu Shi ne ya zama kamar komai nashi.
Salisu ya samu Hajiya Amina Dayaje Gidan Da Daddare ya labarta mata komai nan take Shaidamai Bahiya tazo da labarin Abdullahin na zuwa Wajen Barkat a makaranta,Tayi Murna Sosai tace yaje gidan Wan Baban nasu yamai bayani bai samu ba Sai Washegari yaje yamai Bayani Shi kuma yace Abdullahi ya Turo magabantan Ammh zai Kira Barkat din yaji ta Bakinta kuma ya Kirata wanda taji Abdullahi ya kara Shiga Ranta ganin yadda ya Fada mata kuma ya aiwatar ba kunya tace ta amince Shi kuma yace yana Jiran Wakilan Abdullahi.
Salisu Nazifi ya kira ta waya ya gayamai Shi kuma yace zai kira Abdullahi Suyi mgana,Bama Kiransa yayi ba Washegarin Ranar yazo Zarian ya kawo Jidda ta Rubuta Jamb suka Hadu da Abdullahin yamai bayanin komai jin Haka yasa Abdullahi baiyi Wasa ba suka Tafi Kasuwa Dashi da Nazifi suka Siyo Goro da kwakayan Biskit da Minti da Tabarma dasu Dabino ya Rakashi Atm ya Ciro Kudi 150k Dama Kudin Albashinsa ne ya Ijiyesu ne zai ba Hafsah tayi Siyayyah Suna,toh ganin maganar tataso sai ya Kwaso kawai yana Tunanin Daukan Loan awajen aikinsa yayi Hidimar Biki da gyaran inda Amarya zata zauna Gefe Daya kuma ya Sallami Hafsah kartazo ta Haihu bai Siyan mata komai ba.
Daya ma Nazifi wannan mganar kamar yace wani Abu sai kuma ya Fasa yana Tunanin kodai Asiri Shegiyar Barkat din nan tama Abdullahi ne,Daya Birkice akanta Aransa kuma yana Ji ba Lalle su Shirya da Abdullahi ba Domin Abdullahi bazai iya zama da macen Datake da jin kai da isa kamar Barkat ba.
Gidan Mama suka Fara kai kayan Tagani ta saka albarka Lokacin Jidda na gidan Bayan ta Dawo Daga Jamb din Tabiyo gidan Mama Labarin Auran Abdullahin Har ya Shiga kunnanta Daganan Gidan Baba wada suka Kai mai ya gani ya saka albarka Abdullahi ya Damkamai kudin Hannunshi Duka yace Duk Abunda suka Nemi So yake suyi zuwa Daya ayi komai agama..Shi ya Kira Mijin Goggo Habiba yamai Bayani kuma yace zai Shigo Garin Ranar da Baba wada ya Tsara zasu neman mai Auran ita kanta Goggo Habiba Tayi ta Fada Dataji labari Tana Fadin Abdullahi bai kamata yayi Aure a irin wannan Lokacin ba..
Abdullahi ya Dakatar dasu Baba wada yace gobe Shida Nazifi zasu Tafi Gusai Sai ya gayama Umman Sadiq tukunnah in ya Dawo sai su Tafi kuma Duk abunda ake Ciki Barkat na sane Domin Abdullahi na gayamata,Nazifi nan suka kwana agidansu Shida da Jidda Washegari kuma Tun Safe suka Dau Hanyar Gusai Hafsah Kuma Tuni ta Fawallama Allah komai ko afuska bata Bari Abdullahi ya Fahimci tasan Wani Abu kan karin Auransa ba Ko Zuwansa Gusai bai gayamata ba cemata yayi kaduna zashi Shida Nazifi bata kawo komai aranta ba tamusu Fatan Dawowa lafiya.
Sun Isa Gusai Lafiya da Misalin 11am na Safe Umman Sadiq tayi mamakin Zuwansu kwatsam Haka sai dai bata Nuna ba sai da suka Huta suka sha Ruwa kana Abdullahi ya Sadda kai yana karanta ma Umman Sadiq mganar karin Auransa a karkace Take kallonsa kafin tace"Aure fa kace Zaka kara Abdullahi..? Anya kana da Hankali kuwa..?
Shuru kawai yayi kansa na kasa Nazifi ma Dai baiyi mgana Ba Cikin Fada Umman Sadiq ta Cigaba Da Fadin"Ina Daukan ka mai Hankali Ashe kai Sakarai ne bansani ba kai in banda Rashin Hankali yau ko kyautar Mata aka baka sai ka amsa..? Ka manta Halin Dake ciki ne..? Ina zaka sakata awannan karamin Gidan da kuke Ciki..? Bama kokarinka na ka gama gini gidanka ka Tare kai da matarka ta Haihu achan ba kokarin kara Aure kake kai Abunka ko..? Toh ban amince ba ba kuma zan lamunta da wannan Auran ba yarinya da Tsohon Ciki kasa Hawan jini ya kamata ba.."..
Tafada Tana kokarin Tashi Da Sauri Abdullahi yace"A"a Umma karkiyi Saurin yanke Hukunci..Ita yarinyar ai Tasan ni bamai Wani kudi bane sai Rufin Asiri kuma nayi mata Bayanin komai ta Fahimci..Zata Fara zama dakin Dake kusa da Hafsah kafin na Karisa gini na mu koma Gidanmu Umma mganar Hafsah kuma Da amincewarta Umma zanyi wannan Auran.."Ya Fada suna Hada ido da Nazifi wanda yayi Kur yana kallon Abdullahi yadda ya Shararama Umma karya alhalin Suna Hanya ya tabbatarmai da bai gayama Hafsah komai ba Tukunnah.
Umman Saddiq tayi Shuru tana kallonsa kafin ta kalli Nazifi Tana Fadin"Gayamin gaskiya Nazifi Shin da sanin Hafsah kan wannan Auran.? Nazifi ya Sadda kai yana Jin kunya yin karya gefe Daya kuma yana jin Idanuwan Abdullahi masu Cike da Tsammani a kansa Cikin karfi Hali yace"Eh Umma..Inda bata amince ba kema kinsa Abokina bazai Taba rikoto Aure ba ayanzu.."Yafada yana Takama Abdullahi yatsu Cikin Takaichin karyan Dayasa yayi ma Umma Shi kuwa Abdullahi ajiyar Zuciya Ya Sauke jin Nazifi bai Tona mai aasiri ba.
Umman Sadiq tayi Shuru kafin ta kada kai Tana Fadin"Naji..Wata yarinya ce wai ma zaka Aura..? Nazifi ne yace"Yar Tudun Wada ce...A makaratar ABU samaru suka Hadu kanwar abokinmu ne Salisu Umma.."Umman Sadiq tace"Kenan itama Digirin Take yi..? Nazifi yace"Eh Umma ammh Tana Shekaran karshe ne ta kusa Gamawa"Umman Sadiq ta Tabe baki Tana Fadin"Naji...Sai dai bazan amince da mganarku ba sai na Kira Hafsah Dakaina na Tambayeta Domin Haka kurum naji Ban yarda Daku ba.."
Daga Abdullahi Har Nazifi sai da Gabansu ya Fadi suka kalli Juna..Umman Sadiq na Lura dasu Tatashi ta Shiga ciki ta Dauko Wayarta Tazo ta Kira Hafsah kuma ta saka wayar a Spekear kowani karan Shigan Wayar da Zuciyar Abdullahi yake Bugawa
Hafsah kuwa Lokacin da Kiran Umman Sadiq ya Shigo Tana kwance ne kan Doguwar kujerar Falonta ta kasa komai Tun Bayan Fitan Abdullahi Wayarma an Ci sa'a tana kusa da ita ta jawota ganin Umma ke kira yasa ta yunkura ta Mike Lokaci Daya tana Daga Kiran da sallama Umma ta amsa Hafsah ta gaisheta ita kuma ta amsa Tana Tambayanta Jikinta da kuma yata tace Jiki da Sauki kuma yara na makaranta.
Umma ta gyara zama Tana Fadin"Hafsah..Tambayarki Zanyi kuma ina so ki Fadamin gaskiya.."Hafsah tace"Insha Allahu Umma.."Ta gefen ido ta kalli Abdullahi Da Nazifi wadanda suka Sadda kai kasa Sun gama Sadakarwa yau sun gama Jin kunya da Girmansu suna karya.
Umman Sadiq tace"Wata mgana Mijinki Abdullahi Suka zo min Da ita Dashi da abokinsa Nazifi gasu Zaune agabana.."Gaban Hafsah ya Fadi acikin Ranta tace Shikena mgana ta Tabbata ammh Cikin yake da nuna bata san komai ba tace"Mganar me fa Umma..? Umma tace"yazo min da Zencen yana so ya kara Aure..kuma cikin gaggawa nan da Wata Daya ko Biyu Toh na Nuna Ban amince ba Saboda ke sai kuma ya Tabbatarmin da Saninki zai kara Auran kuma da yardanki Shin Hakane..?
Hafsah Taji mamaki ya kamata Wani Abu na Zuwa Daga karkashin Ranta tayi Shuru kawai Tana Jin Ruwan Hawaye na Taruwa acikin Idanuwanta Jin Shurunta yasa Umma ta kalli Abdullahi Cikin bacin Rai tana bamkamai Harara Cikin mamaki Sukaji Hafsah na Fadin"Eh Umma gaskiya ya Fada miki..Sai da ya gayamin na kuma amince Daman Don Allah karki Hanasa Tunda dai yana so Umma kuma Daman bazai Zauna Dani ni kadai ba Yana Da Damar da zai karo uku ma ba Daya ba Umma Tunda Allah ya bashi Dama.."Hafsah ta Karishe Fada Hawaye na Wanke mata Fuska ba Umma Sadiq kadai ba Hatta su Abdullahi jikinsu yayi Sanyi barin ma Abdullahi Daya ji Wata kunyar Hafsah ya kamashi Da kuma Wani karin Tsausayinta da Sonta.
Umman Sadiq tace"Shikenan Tunda kince Haka Daman gani nayi Hidima zatamai yawa.."Hafsah Tayi Mirmishin Dayafi kuka Ciwo tace"Bakomai Umma..Allah zai Rufa Asiri.."Umma tace"Shikenan Allah Shigemana gaba ke kuma Allah ya baki Juriya ki kwantar da Hankali kinga bake kadai bace..Allah ya Saukeki lafiya..Hafsah na Kokarin Sakin kukanta Take Fadin"Ameen Umma nagode...agaida su Zahra.."Ganin kukan nata na neman kwacewa yasa ta yanke Wayar da Sauri sai kuma Dukkansu Sunji alamun a kalaman Hafsah na karshe kuka take.
Ajiye wayar Umma tayi ta mike ko kara kallonsu batayi ba ta Fita Daga Dakin Tana Fita Nazifi ya Numfasa yana Fadin"Na Dade ina baka Shawara kan yadda zaka Tafiyar da gidanka ammh wannan karon ina Bayan Hafsah..wlh samun mata irinta sai ka Tona kuma ka Rubuta Wlh Wannan Barkat Din Daka kema Rawan Jiki bazata taba maka Hakuri da Biyayyah Hafsah gareka ba ballatana ta iya da Halinka na Saurin Fushi da Korafi ba.m."Wani kallo Abdullahi ya Sakarmai kawai kafin ya Dauke kai Shima Nazifin kai ya Dauke kawai yana kunkuni wai Abdullahi ya sakashi karya yana jinsa yayi mishi Banza.
Abinci Umman Sadiq ta kawo musu Sukaci suka Koshi kana suka Fita Sukaje sukayi Sallah bayan Sun Dawo suka gaisa da Mijin Umman Da abokiyar zamanta ko Su Zahra basu Jira Sun Dawo Daga makaranta ba Sukayi musu Sallama suka Dau Hanya Bayan sun Zube musu Tsaraban su Minti da Biskit,Umma kuma ta Bada Zuma mai kyau tace akaima Hafsah Garin alkama da Garin Konu kuma tace akaima Mama suka karba suna Godiya.
Koda suka Dawo Nazifi ya kawo Abdullahi gida bai Shiga ba.Ya wuce Abunsa Domin in garin Allah ya waye gobe yake son su koma Kaduna Abdullahi kuwa da kunya ya Shiga Gidan sai dai me Hafsah ta tarbeshi Sosai ta kokarta Tayi Girki Tayi Wanka taci kwalliya Ganinta Haka sai ya kaasa mgana Daya bata Tsaraban Umma Haka take Murna tana Tambayanshi ya suka Baro Su Umman Shidai kawai yake yake mata Duk Abun kuma sai ya Dameshi sai alokacin yake ganin Rashin kyautawarsa bai iya ce mata komai ba Har Washegari da Safe kalma Daya ya gayamata Lokacin Data Rakosu Shi da su Amira zai kai su makaranta Dagachan ya wuce Wajen aiki.
Ya kalleta yana Karban Karamar Jakarsa Dake Hannunta yace"Don Allah Hafsatuna kiyi Hakuri kinji..? Banso haka ba bani da wani ZABI NE don Allah ki yafemin kar Allah ya kamani Da Fushinki.."Mirmiahi Dayafi kuka Ciwo ta Sakarmai kafin tace"Waya gayamaka kayi laifin a wajen Hafsah..? Karka Damu...Ko ka gayamin ko baka gayamin ban isa in ja da Hukuncin Allah ba Abban Amira.."Kallonta yayi gani Hawaye sun Cikamata ido kai Tsaye yace"Ban gaya miki bane Saboda Bana so Hankalinki ya Tashi..Ga kuma Ciki Tare Dake ina Tsoron ki Shiga wani Hali.."
Dariya kawai Hafsah tayi kafin tace"Haba dai..Kamar ban yarda da Allah da kaddara ba..Kuma wacece ni da zan Hanaka Kara Abunda Allah ya Hallatarmaka..?Ban isa ba..Ina Fatan Allah ya kaimu Lokacin ya kuma Sanya alheri.."Tana Gama Fadar haka ta juya ta koma Daki Tana Share Hawayen Idanuwanta da kallon Tsausayi Abdullahi ya Bita yana Jin Hafsah ta gama Samun wani Wawakeken Fili acikin Zuciyarsa Jiki a Sanyaye ya Gungura mashin Din zuwa Waje ya Tada ya Hau,Amira ta Hau baya Amira kuma ya sakashi gaba suka Dau Hanya.
Kwana Biyu Tsakani Su Baba wada da Mijin goggo Habiba da Nazifi sukaje gidan Wan Babansu Salisu Dake Sabon gari chan suka iske Salisu Dayake yasan da Zuwansu sun Samu Tarba Sosai Sunci sunsha kafin su gabatar da Abunda ya kawosu ganin sunce suna Shiryeni basu son Jeka ka Dawo yasa nan da nan aka Fadi Sadaki da Dukiyar Aure baba wada ya zaro ya Bada Duka 150k Sdaki da Dukiyar Aure suka kama sun Gabatar da kayan sa Ranarsu suka kuma Bukaci Saka Ranar kar ya Dau Lokaci kamar yadda Abdullahi yace toh anyi dai komai Cikin Girma an saka Ranar Kwana 50 cif masu zuwa da Wannan albishir din suka koma ma Abdullahi Duk da bai so Haka ba bai da yarda zai yi Hakanan ya Hakura Shi ya ma Kira Barkat din ya gayamata sai ta mai na yan Duniya zuwan bata sani ba Nan kuwa Daganan Sabon garin Salisu gida ya wuce ya gayama Hajiya Amina komai ya kuma kai mata Sadakin a Hannunta Shine Bahiya da Bahijjat suka Kirata suna Ihun Murna Suka gayamata Bahiya tana Makaranta ammh Tunda Taji Labari ta Gudo ta bar Barkat din achan tace gida zata koma ta kwana.
Bangaren Su Zannira da Subai"atu kuwa Abakin Mariya sukaji labari Subai Zannira kuma Bakin Jidda Data je Gidanta Take gayamata Sunyi mamaki kwarai ainin Barin ma Subai washegari sai gata Gidan Mama Tana Tambayaa Mama tace kwarai an saka Rana Daganan Subai bata Tsaya ba sai gidan Hafsah ta Isketa Sai karfin Hali Domin Duk Ta Rame ganin Subai sai Rauninta ya Bayyana ta Fada Jikinta tana kuka Subai tana lallashinta Sai da tayi ya isheta kana tayi Shuru.
Subai ta kalleta tana Fadin"Kinga yadda kika Rame kuwa... ?;badai mganar Auran ya Abdullahi ne zai saka Kije ki kashe kanki ba..Kinga yadda kafafuwanki suka kumbura kuwa.."?Hafsah ta Kada kai Tana fadin"Haba ko Daya..Kawai Tausa ne kadai na yau da basu samu ba..Ammh gobezan je awo zan musu Complain naji..Mganar Auran Abdullahi kuma bai gabana Subai'atu Abu Dayane agaba na Sauka Lafiya.."
Subai tace"In bai gabanki..Meyasa naga kin Rame kuma nazo kin ganni kin kama kuka.."Hafsah tace"Kukam Dacin Rai ne Subai...Abu Daya ne ya batamin Rai game da wannan Auran Subai ko da bani da wani matsayi wajen Abban Amira bai kamata na Fara ji wannan mganar Daga bakinsa ba..? Kana kuma bai kyautamana ba Da bai bari ya kamallah Gidanshi ba kuma bai bari na Sauka lafiya ba ammh yaja jibo Aure."Tafada Hawaye na Kawo mata.
Hannunta Subai ta Rike kawai Tana lallashinta Domin bata da ta cewa nan ta Dade sai yammah ta koma Gida kowa yaji labarin Auran Abdullahi sai yayi mamaki ya kuma Kira Hafsah yace kar ta Tada Hankalinta Su Ammi kuwa da kanshi yaje ya gayamusu sai ganin Kiran Ammi Tayi Hafsah tana Gayamata kar ta Tada Hankalinta Sai kawai ta sakama Ammin kuka ita tayi ta lallashinta da ban baki da Nasiha Musamman Daddy yace taje yana son ganinta Abdullahin yakai ta Shima yayi mata Nasiha Sosai wanda yasa Taji Zuciyarta ya yi sanyi ...
Ita ko Anty Hadiza Dataji Fada ta kamayi da Abdullahin tana Fadama Ammi ya cika zalama ina yaga karfin Rike mata Biyu,ga gininsa bai gamaba ya Dauko Aure Ammi ta Takamata Burki ta kuma Haneta da kiran Hafsah ta Raunana mata Rai Fadan Ammi yasa Data Kira Hafsah batayi Korafin baa ammh tace karta Damu Duk Abunda Take Bukata ta Kirata ta gayamata Fatanta karta Damu ta Cigaba da addu"an Allah ya Sauketa lafiya.
*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*
*Janafty...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
_Domin ku Masoyana na Nesa dana kusa..Hakika Daga Jiya Zuwa yau naga Salon Kaunarku da Soyayyarku Zuwa gareni Dalilin Wannan Littafin..Nagani kuma na Shaida Nagode kwarai Allah bar zumunci Masoyana masu Bina ta Wattpad kuma ina Ganin Sharhinku kuma ina Yabawa Sosai Nagode Allah ya bar Zumunci Ameen Ga Tukwaicin Wannan Page din zuwa Gareku Da Fatan zaku Taya *ABDULLAHI* Da *BARKAT* Happy Marriage Life..._
*033*
"Kamar yadda Abdullahi ya gayama Nazifi Zai Dauki Loan ma'ana Bashi a wajen aikinsa Allah barshi sai adinga Cirewa Da kadan da kadan Cikin albashinsa har ya gama Biya Toh yayi hakan ammh bayan Nazifi ko Hafsah bai yarda yayi Zencen da ita ba azuwan sai dai kawai Taga ya Bata kudi a Hannunta Tayi Siyayyah kayan Haihuwa Dashi Sauran kuma yayi Gyaran Dakin da Barkat zata Zauna Da Akwatuna da kuma na Hidiman Biki kafin kuma Aga Abunda Allah zai yi.
Sai dai Abunda bai sani ba Tuni Hafsah Taga Takardan Bashin bata Dai mai mgana bane kuma Bata Nuna mai Ta gani ba Tunda bai mata mganar ba Sai kawai ta Kyaleshi ammh batayi wani mamaki ba Sanin Daman Dole sai Abban Amira ya kare da Cin Bashi Abunda batamai Sha"awa Toh ammh Tunda zai Dauko yar Mutane ai zama bai ganshi ba.
Bayan Saka Ranar Abdullahi Sun Hadu da Barkat ammh acikin Makaranta yaje ya sameta Suka Sha Hiransu Tun Wajen La"asar yaje Domin Daga Wajen aiki ya Dauki Exvuse ya koma Gida yayi Wanka ya Sauya kaya ya Hau Mashin Yatafi Chan Barkat ta Rikeshi da kalamanta na kwantar da kai da Nuna ma Namiji kamar Sarki yake Tun Abdullahi na Duba agogo har ya Daina ya Share kafa ya Biye Barkat Tana ta mai Hira Cikin kwarewa da kuma Salon Sace Zuciyar Da Namiji Dama ita Barkat Irin Matanan ne masu Wayau ga ta da iya Kalamai da iya Sarrafa Harshe Wajen yadda zata Dawo Da Namiji Gabadaya Hankalinsa akanta Toh da Irin Haka ta Jawo Hankalin Abdullahi Gareta Har ya Fada Tarkon Sonta bai sani kuma Ita Haka Salonta yake in Har kayi Zama da ita na wani lokacin Koda bata Sonka Zakaji Duk Duniya ta maka kunci Indai ba Barkat ka mallaka Gabadaya ta zama Matarka ba Sau Taru maza SunSha Wahala a kanta matuka ammh bata Basu Fuska sai akan Abdullahi Da Tundaman Chan Tace Shi take Jira Domin ya Gama Cika Duka Sharadinta na Irin Namijin Datake Buri.
Da irin Salon Soyayyarta da Shagwabarta Tana wani Kiransa My Man,shi kuma ya Biye mata ya Share kafa Har Wajen 11:20pm na Dare kana ya Farga Shima Kiran Hafsah ne ya Shigo Wayarsa Sai Lokacin Hankalinsa ya koma Gida ya mike yana Cema Barkat din zai Tafi nan ma Kukan Shagwaba ta Fara wai bataso ya Tafi Wani bata lokacin ya kara Wajen Lallashinta kafin ta yarda ya Dauketa a Mashin Dinsa Zuwa Kofar Hostel dinsu kana sukayi Sallama ya Fito Daga Cikin makaranta Gudu ya sakarma Mashin Din Ganin Dare yayi Sosai Abunda bai tabayi ba.
Koda ya iso Gida 12pm na Buga Na Dare,Mashin Dinsa yakai Dakin Dayake ijiye Kafin ya Shigo Falon Hafsah ya gani Zaune ga Tsohon Ciki Tana Jiran Dawowarsa Tana ganin Shigowarsa Ta Mike Dakyar tana Fadin"Na Tsorata Abban Amira ina ka Tsaya ne..?naga baka Taba kaiwa Pass 10 awaje ba ammh yau har 12 na Dare kana Waje gashi ina ta Kiran layinka yaki Tafiya sanda kuma na Sameka Baka Daga Ba Hankalina ya Tashi yanzu Haka Auwal nake Shirin kira naji ko kana Gidan Mama ne.."
Ta karishe Fada Cikin Tashin Hankali kamar tayi kuka ajiyar zuciya ya Sauke yana jin bai kyautaba akallah dai ya gayama Hafsah ga inda zashi,Gabanta ya Karisa ya Riko Hannunta yana Fadin"Afuwan Matar Abdullahi..Laifina ne kafin na Fita ban gayamiki inda zani ba Sam...Cikin Abu Samaru na Shiga Wajen Barkat Muna ta Hira Wlh bansan Lokaci ya Tafi haka ba.."Tunda Taji ya ambaci Barkat tayi Saurin Zare Hannunta Wani Abu na Sukan Ranta Tace"Ka Tadamin Hankali..ammh Ko ina kaje..Abban Amira Sai ka Tuna ka barni ni kadai agida ga Halin Danake Ciki Dagani sai yara.."Tafada Tana Kallonsa Ido Cikin Ido kansa ya Shafa yana Fadin"Naji Ban kyauta ba Kiyi Hakuri Don Allah..Haka bazata Sake Faruwa ba.. !
Kada kai kawai tayi tana Fadin "Ya wuce ga Abincinka fa..? Tafada Tana kallonsa Fuska yadan yamutsa kafin yace"Wlh na Koshi Hafsatuna sai dai da Safe.."Kallonsa Tayi a kaikace kafin kawai ta kada kai ta Shige Cikin Bedroom Bayanta yabi yana Tambayanta Su Amira tace Sun Dade da yinBarci Sun gaji Da Jiran Dawowarsa Bai Tanka ba ya Sabule Rigar Jikinsa ya Tura Kofar Tailet ya Shiga Hafsah ta Bishi Da kallo Lokaci Daya Tana Kada kai Ta koma ta kwanta Tana kokarin maida Hawayen da Suka Cikamata kwarmin Ido.
Washegari kuma kafin ya Fita aiki ya Bata Kudi 50k yace Tayi Siyayyah kayan Haihuwa da komai da komai Harda kayan da zatayi Fitar suna Tayi Hakuri ba Haka yaso ba Da Farko Taso taki karba ne Ganin Anty Hadizan ma ta aiko mata da Sakon Kayan Jarirai Kala kala Sabbi da overroll Kala kala suma kadan ma Zata Kara,Kuma Daddy ya sakamata 50k cikin Bankinta Duk Domin kar ta Tada Hankalinta bata gayama Abdullahin ba ganin bai da Lokacinta yanzu yana Shirye Shiryen Dauko Sabuwar Amarya,In ya Fita Tun Safe Sai yammah yake Dawowa inya Dawo Bai da Lokacin kowa sai Chart da Barkat,ko kuma ka ganshi Dai da waya yana ta latswa Shiyasa ta kama kanta Fatanta Allah ya Sauwaketa lafiya.
Godiya Tamai ta amshi Kudin Ta Ijiye,sai da yaje gidan Mama Sukayi Mgana kana ya Kira Zannira yamata mganar Hada akwatuna Saffa Saffa Guda Biyar zai Tura mata Dubu Dari biyu Da Hamsin Tace sai Dari Uku da hamsin Harda na Hafsah yace Shikenan kafin ya bar Gidan Mama sai da suka gama Mgana yace mata Ma"aikata Zasu Fara gyaran Dakin Dayake ijiye mashin Dinsa Zai saka a Fasa Wani Waje ta Baya ayi mata Tailet a Dakin Tunda Dakin Ciki da Falo ne kuma masu Girma Kicthen kuma Suyi Maneji Ita da Hafsah kafin Su koma Sabon Gidansu Mama tace Hakan yayi tayi mai Fatan alheri.
Ana Gobe ma"aikatan zasu zo Abdullahi ya gayama Hafsah,ya kuma Gayamata Zasu yi Sharing kichen da Barkat Din Kafin su koma Sabon Gida aranta Tace Daman ban Mamaye Kitchen din ba,Yawancin kayan Kitchen Dina Suna Dakina Cikin kwali ban Fito Dashi ba,Afili kuma tace Allah kawo su Lafiya Washegari suka zo Dama Ranar ta kama Lahadi ne,Yana Gida Dama ita bata saka kaya adakin Shine Daman kan Saka Mashin Dinsa da Sauran Abubuwan da ba"a Raasa ba,ya kwashe Silin Suka Farayi,Dama Dagashi ne sai Floor sai Filista sa Fenti Sai kuma Bayin Dayace Za"a Fitar ammh Taga an Siyo Kwalayen Tayes su Zai saka mata afalo kila Daga ciki kuma ayi Siminti.
Aranar Da yammah Tana Jinsa Suna Mgana da Barkat din Tana gayamai ta Dawo Gida Sun Gama Test,Inaga tace mai yazo yace bazai Yuyuba Yana wani Uzuri ne Ammh Daga baya kuma sai Taga ya Shiga yayi Wanka ya Shirya Cikin Dakakkiyar Shadda Fara yaci Hula ya Fesa Turare Tana Falo yazo ya Sameta Yana gayamata Zai je Gidansu Barkat ya Gaida Mamarta Tunda Mganar ta Bullo bai leka Gidan Ba,Ta Gefen ido Ta kallesa Acikin Ranta kuma Tana ta maimaita Suna Allah ganin Shedan na Shiga Zuciyarta yana Saka mata Wani Irin Kishin Abdullahi.
Jiki na Rawa ya Fita Chan Yaje ya iske Barkat tayimai kwalliya da Girke Girke kala yaci yasha kana Tamai Jagora Har Falonsu na Cikin Gida ya gaida Hajiya Amina Tayi ta saka albarka Tana Fadin Abun Allah kenan Gashi Nazifin Dayazo Neman Auran Allah bai yi ba Shi da yayi Rakon Dashi Allah yace,3k ya bata ta karba Tana Godiya,ya iske Duka yaran Hatta Aina ta Dawo Daga makaranta kuma Sunzo Sun gaisa Dukkansu Yana Gidan ma sai ga Salisu nanma suka gaisa Duka suka Dan Taba Hira yana Tambayan yanzu Nazifi ya Daina Shigowa Garin Abdullahi yace gaskiya Sai da wani kwakwaran Dalili Salisu yace Amarya ta iya Rike angonta Shida Abdullahi dariya kawai yayi bai ce komai ba nan Salisu ya barshi ya Shiga Cikin Gida bai Dade ba ya Fito Sukayi Sallama ya Tafi,Abdullahi bai Dade ba Karfe 9am Yayi musu Sallama suka Rabu da Barkat kan Gobe zai zo Ta kaishi Sabon Garin Gidan Wan Babansu ya gaisheshi Har Kofar gida Ta Rakashi Da Leda Shake dasu Sweet tace yakai ma Su Amira sai Turare Datace ya kaima Antynta Hafsah Abdullahi Sai Godiya yake Hakika yaji Dadin kyautar Bangirma Irin na Barkat.
Koda ya Dawo Har Auwal ya Maido Su Amira Gida Ya kuma Baje musu Tsarabansu yana Fadin Sabuwar Antynsu da zasuyi kwananan ne ta kawo musu Suka Karba suna Ihu Suna Tsalle Hafsah na gefe Tana kallon Ikon Allah itama ta waigo ya mikamata nata Turaran ta karba Tayi godiya Ko a Fuska bata nuna mai Wani Abu ba,Shi kuma abangaransa Baya Fahimtar Komai.
Siyayyah kayan Haihuwa kuma Anty Hadiza ta Turama kudin Tace ta Siyamata Harda Turaman Atamfa da less,adinka mata Daga Chan ta aiko mata Dashi Abdullahi ma ta bama kudin ya Turama Anty Hadizan sai Lokacin Take gayamai Kudin da Daddy ya bata ya saka albarka kuma ko Afuska bai Nuna Wani Abu Itama sai ta Share kawai ta ijiye kudin Dama akwai Abubuwan Datake son Siya Bayan Allah ya Sauketa Lafiya.
*****
*Bayan Wata Daya..*
Alokacin da Bikin Abdullahi da Barkat ya Rage Saura Kwana Goma Sha Hudu kenan ma"ana Sati Biyu yau asabaar akuma yau Din ne za"aje kai kayan Auran Abdullahi Zuwa Gidansu Barkat din.
Azuwa wannan Lokacin Tuni Abdullahi ya kamallah Gyaran Gidan Dakin Barkat an kamallah komai an Fitar da Bayi da komai anyi Fenti ya sauya mata Kofa Bedroom din ma Ya sanya mata Kofa gidan Gabadaya ya Sake mai Sabon Fenti mai Tsada,,Kicthen ma Ya kara Gyarashi an Saka musu Sabon Cabinet,Kayan Hafsah gefe ta mai Dashi Ta barma Barkat kusan Rabi da kwatan Kitchen din Har ma Abdullahi yayi mgana tace kar ya Damu Su da ba zama zasuyi ba,Lokaci Kadan zasu koma Sabon Gidansu yadai kyaleta ne kawai Saboda Baya son matsa mata ganin Halin Data ke Ciki na Cikinta ya Shiga Wata Tara ma"ana Watan Haihuwansa kenan Duk Ta Kumbura ta zama a lallaba.
Iyayen Barkat din da kanwarta Bahiya sunzo sun Duba Dakin nata Ranar Hafsah ma tana Ciki batama Son da Zuwansu ba Sai da suka kariso kana Abdullahi ya Kirata ya gayamata Dakinta ta Fara Saukesu ta kawo musu Ruwa suna ma cewa ta barshi Ganin Halin Data ke Ciki,Taki basu Jima Sukace sunzo Duba Daki ne Ta Shiga Ciki Ta Dauko Musu makulli Ta mika musu Suka Fita Basu Wani Jima ba Suka Leko suka mata Sallama Tare da Bata makulli ta amsa Tana musu Fatan Zuwa Gida Lafiya Domin batayi Girki ba kwance Take Tana Fama da kanta.
Bangaran Ita Barkat din kuwa da Hafsah basu Taba ganin Juna ba Sai dai ita Barkat din Tataba ganin Hafsah a hoto a wayar Abdullahi ammh ita Hafsah ko kusa wannan bai Dameta ba,Su Amira kuwa ai sun zama yan Gidan Anty Domin yasha kai su Wajenta su mata Wuni Ranar da basu da makaranta,sai yammah yake zuwa ya Dawo Dasu da Tsaraba Niki Niki Suzo Suyita Murna Suna Labarin Anty ta basu kaza Anty tace musu kaza Mommy Anty BARKAT na gaisheki Sai dai kawai tayi yake toh me Zatace..? Gefe kawai ta koma ta zama yar kallo,Dama Barkat din Shiryen Shiryen Fara Jarabawa Suke Bayan Bikin da kwana Goma Zasu Fara Jarabawar first Semester.
Koda aka kawo kayan Akwatunan Gidan Mama Zannira ta Saukesu Biyar na Barkat guda Daya kuma na Hafsah ne,Sai da Abdullahi yazo ya gani kana yace Mama su Shirya wadanda zasu je su kai kayan na Hafsah kuma ya Dauka yakai mata ta Karba Tayi Godiya yace mata ta Shirya yakai ta Gidan Mama Taga kayan Barkat Din sai ta Nuna mai Bata iya Zuwa Batajin Dadin Lallabata yake Shiyasa ya kyaleta da kuma Hankalinsa yanzu yana kan Auransa kawai.
Mama ta Kira Ammi da kanta ta Fadamata Ammi kuma ta mata alkawarin zata zo a kai kayan da Ita Umman Sadiq tace sai Biki Zata zo Subai ma da Zannira ta Kirata cewa tayi Wlh baza taje ba Tana Taya Kawarta Hafsah kishi Da Abdullahi yaji labari Wani Dogon Tsaki yaja yace Su kyaleta Dama Baya gayyartata,Hatta da Nazifi wannan karon Baya goyon Bayan Abdullahi kan Wannan Auran Koda yaushe sukayi Waya sai yayi mai Complain din komai nashi ya Tsaya Saboda wannan Auran Shi bakomai ya Rasa ba Wajen Matarsa Hafsah ba,Gashi yanzu Ginin nashi ya Tsaya Shagon ma yanzu ba wasu kaya Duk Sun kare ba kudin Sarowa ga Hidiman yau da kullum albashin ma ba wani mai yawa bane Tunda Duk Wata Suna Cire Bashinsu 10%,In Nazifi yama Abdullahi wannan mganar basu Rabuwa Lafiya sai Abdullahi ya Fara Fada Shi kuma ya Fita Batunshi Domin Shi yanzu ya samu kwanciyar Hankali Sosai Jidda Taci Jamb Dinta yana ta ma kokarin Sama mata addmission a Kasu ne ta samu Gurbin karatu,Bangaran Sakina kuwa Tana ganin kwarewar Ruwan Bulla agidan Nazifi Alhaji Badamasi yayi Fada Sosai Lokacin da Sakina ta gayamai ta koma Gidan Mijinta Hajiyarsu Kuwa Takaichi kamar ya kasheta ammh Sakina Ta Nuna tana son Mijinta bazata iya Rabuwa Dashi ba,Dole suka saka mata ido Abaya sai Tayi Sati Uku bata zo kaduna ba ammh Ganin kamar Jidda Tafi ta Morewa sai ta koma tanayin kwana Goma Zuwa Sha Biyu Tana Dawowa Domin Tana Chan ne ammh Gabadaya Hankalinta na kan Nazifin Da Jidda na ganin yadda Jidda ta mallake Nazifin Karamar yarinya da ita ta iya Makirci da Yadda zata maida Namiji ya Dawo karkashinta.
Ranar da za"a kai kayan Abdullahi Har da Hajiya Sa"a tazo Mama ta Kirata Domin Tun Bayan Auran Jidda komai ya Daidaita Suna Mutumci yanzu Sosai,Ammi ma tazo sai Inna Abu da Zannira sai Mariya Data yi Rantsuwan sai Taje su kenan suka Tafi sai Inna Talatu,Amota Biyu Sukayi kayan Amotar Hajiya Sa"a aka saka Ta Dauki su Inna Talatu da Inna Abu da Mariya ita kuma Zannira suka Shiga Motar Ammi Suka Tafi Sai da suka je Gidan kana Ammi ma Taga ai Tasan Gidan Marigayi Alhaji Shehu basu da Nisa Sosai tama san Hajiya Amina Domin sun yi zaman Zuwa Islamiya ajinsu Daya Tun Lokacin Su Hafsah Suna yara.
Am musu Tarba na Girma da karammawa Matan wan Babansu Barkat din Da Makota suka karbi kayan Suna ta saka albarka Ruwa kawai suka Sha Sauran kayan Toye Toyen a Mota aka saka musu Ammi Sun gaisa da Hajiya Amina Sosai Shine har take Tambayanta Dama Abdullahi Dan'uwansu ne Dariya kawai Ammi Tayi Inna Abu ce tace ai Mahaifiyar Matarsace kamar Uwa Take garesa Kowa yayi mamaki Sosai nan kuma suka kara Tabbatar da an zama Daya Mariya kuwa sai kwakwa take Taga Amarya bata ganta ba taga Dai Bahiya da Bahijjat,Aina tana Sch,Barkat kuma Bata Gidan Tana Makota Saboda kunya Duk Da Karatun ma Jarabawarta Take tayi Ganin Lokaci Nata karatowa
Da zasu Tafi 10k suka basu Tukwaici Da Farko sunki Karba Sai da Suka ga basu Ji Dadi ba kana suka Karba Sun Koma Gidan Mama Suna Tadin Kirkin Gidansu Barkat din,Zannira dai sai Washegari zata koma Inna Abu kuma da inna Talatu ana Dawowa suka Nufi Gida su aka bama ma 10k din Ammi da Hajiya Sa"a sunfi karfin kudin sukace bazasu karba ba itama Hajiya Sa"a ta Jima nan Gidan Mama Suna Hira da Ammi Nan ma Tayi mangariba kana ta koma Gida Ammi kuwa tana nan Har Dare har sai da Abdullahi yazo ya isketa Bayan sungaisa yayi ta mata Godiya tace bakomai da Zata tafi sai Gobe Abdullahi yazo Gida ya Sameta yace mata Insha Allahu.
Sai bayan da yan kawo kaya suka Tafi ne Barkat ta Dawo Gidan Bata ga kayan ba sai Chan Dare bayan Kowa ya watse sai isu isu Hakika kayan Sunyi Daidai Ruwa Daidai Kurji,Bayan tagama ganin kayan Ta Turama Abdullahi Sakon Godiya da Jinjina yaji Dadi Sosai acikin Ranshi yana Tunanin in ya samu kudi zai karama Barkat din kaya Har ga Allah Daya na Cikin Wadata sosai sai ta samu Abunda ma yafi Haka.
Shiryen Shiryen Biki Duka ya kamkama Ammh yafi Yawa ta Bangaran Gidansu Barkat din,Domin Hafsah dai Ta kanta Take yi Tana Jiran Haihuwa ne yau ko Gobe Gidan Mama kuwa Subai ce Daman bai Son Bidi"a abiki To wannan karan Tana Taya kawarta Kishi ko Gidan Maman batazo ba Da Zannira tayi mganar Fitar da anko Subai tace Wlh bazasu yi wani anko ba Mariyama tace Wlh bawani ankon da zasuyi Dole ta bar Mganar,Sai dai Tana Kiran Hafsah awaya suna mgana Sosai tana kara kwantar mata da Hankali Tazo Gidan Hafsah Taga kayan da Abdullahi yayi mata ta Dauki Wasu ta kai mata Dinki sauran Ta bar mata Kudin Hannunta kuma tace ta adana In Ta Hauhj Lokacin zasu koma Sabon Gidansu sai ta kara Wani Abun Hafsah tayi na"am da Shawaran Subai Sosai Domin Ita Din kawace ta Amana agareta.
Ana Saura Sati Daya Bikin Dangin Barkat Suka zo suka mata Jeren kayanta Masha Allah itama Taji kaya Sosai,sai wanda ya gani,Sun Jera komai yadda ya kamata Kitchen din ma sun Sun Jerama Barkat din Abunda ya Samu Domin Kicthen din yayi musu kadan gaskiya,Basu Damu ba Sanin Daman Barkat din ta Fada musu zamansu anan na wani Lokaci ne da zarar ya kamallah Gininsa zasu koma Sabon Gidansu a Gra Shiyasa ma Sauran kayan Barkat din Duk ba"a zo Dashi ba Fridge kadai aka Zo mata dashi Sauran gas dinta da Sauran kayan amfani agida aka barsu sai Zasu koma Chan Gida sai tayi mgana akai mata kayanta chan cikin Sakewa Ranar da suka zo Dankin ma Hafsah Bata nan Tatafi awo Subai ce da Mariya Ya Kira suka zo Agidan Mama akayi musu Abincin Dama yayi musu Bayanin Hafsah bata nan Tatafi awo ammh haka Suka Dinga Surutun wai kishi ne yasa Ta bar Gidan Hafsah kuwa Daga Asibiti Gida ta wuce taje ta kwanta Sai Da Ammi ta matsa mata ne ta koma Gida Lokacin yan Jeren ma sun Tafi Subai ma ta koma Gida Mariya ta iske agidan da yara sai da ta Dawo da Abdullahi ya Shigo Gidan ya maidata Gida ita ko Dakin ma bata kallah ba Tunda ma Sun kulle Abunsu sun Tafi da makullinsu Abdullahi Dai na da wani Ammh bata Damu dama tace zata ga Dakin ba Shima bai Damu Daya ce mata komai ba ammh yaso ya mata Masifan kan gidan Ammin Data Biya ammh ganin ta Hade Rai yasa Dole yayi Shuru da bakinsa.
Ammi da Daddy 100k suka bama Abdullahi suka ce ya Kara ba yawa yaji kamar ya saka kuka Yaji kunya Sosai,Kuma ya kara Tabbatarma kansa Iyayen Hafsah Dabam ne,Mutane ne masu Dattako da Sanin ya kamata Yazo Gida yana Gayama Hafsah yace Tatayashi Godiya Wajensu Daddy Ta Kira ta musu Godiya Daddy yayi Ta lallashinta Ta Tabbatarmai da bata tada Hankalinta ba,Haka yaje ya sanar ma Dasu Mama,Mama ma ta Kira Ammi Tana ta Godiya Har Umman Sadiq sai da Ya gayamawa itama ta Kira Ammi Tana mata Godiya acikin Ranta Tana Tunanin Abdullahi ya bata kunya na yarda iyayen yarinyar nan suka Daukesa ammh Sai da yayi Sanadiyar Damuwar yar"su.
Da su yayi amfani ya Siya kayan Abincin da za"ayi Hidima Na Gidan Mama da gidanshi 30k kuma ya bama Barkat na Walima da Hidimar Biki,Sauran kuma ya bama Auwal ya Dan Saro kaya Haka,kada Shagon ya Durkishe ba kayaTunda katinan Biki da kayan da zai Saka Nazifi yaji da Barayin,Umman Sadiq ana Saura kwana Biyar Biki ta iso Goggo Habiba kuma Ana Saura kwana Hudu Tazo ta Buhun Masara Dana gero Harda na Shinkafa da Sauran su kuka da kayan kauye irin su kayan Miya da Sauransu Umman Sadiq kuma Shinkafa kawai tazo Dashi da kudi Ta Damkama Abdullahi Zannira kuma ita Tace zataji da Sauran Cefenan Gida da Abubuwan da za"a Bukata Subai kuwa bama wanda ya ganta agidan Mama tana Gidan Hafsah.
Sai ana Gobe Bikin Jidda ta iso,Sakina kuma Dataji labari Dadi Taji Domin Tunda akayi mata Kishiya toh ayi ma Uban kowa ma ta kuma yi alkawarin sai ta Kira Hafsah tayi mata Murna Taga ya zataji, Zannira ma aranar tazo Saboda Uwar Mijinta ba lafiya ammh Taji Sauki Shiyasa tayi Tsaiko Ya"yan Goggo Habiba su Jamila ma Duk sun iso,ammh Suna zuwa Gidan Hafsah suka yada Zango Har da Madina Tazo Daga malunfashi da kannen Nazifi Duka Suna Gidan Hafsah Dasu Mariya,Zannira ce kadai agidan Mama Tana Taimakawa da wasu abubuwan Tunda Itama Maman zatayi Taron nata.
Gidan Abdullahi kuma Su Subai ne sai Anty Hadiza da tazo,Ita da yan Biyunta,sai Jidda dasu Jamila da Mariya Suke ta Bidirinsu Domin Su Debema Hafsah kewa kuma Ba laifi sun Debemata kwarai Domin sai da Bikin yazo Gabda kana Taji Damuwarta ta karu Nazifi Tare da Jidda suka zo Suna Chan Tare da Abdullahi agidanshi Tunda nan din ya Cika,Su Amira da su Muhseena suna Tsakar Gida suna ta Wasa bawani Taro ne Hafsah Zatayi ba isu isu ne sai makota kuma da ba"a rasa ba.
*****
Ranar asabar Daya ga Watan Goma Shekara ta Dubu Biyu da Ashirin da Misalin karfe 11am na Safe Duban Mutane suka Shaida Daurin Auran Barkat Shehu da angonta Abdullahi Usman Direba akan Sadaki mafi Dataja lakadan ba ajalan ba,Daurin Auran da"aka Daurashi a Sabon Gari Gidan Wan Babansu kenan
Daurin Auran Daya masu Hallatar manyan Mutane kama Daga abokan karatun Abdullahi Abokan aikinsa da kuma abokansu Tun na yara Shida Nazifi,Ga Jama"ar Salisu Data Baba wada mijin Goggo Habiba ma yana Wajen Daddy ma yaje Daurin Auran Auwal da Tawagan Abokansa Mijin Zannira Da Mijin Subai ma sun Hallaci Daurin Auran Hatta da yan Gidansu Hajiya Sa"a Suma sun Je Daurin Auran Gaskiya Ya samu Jama"a sosai Wanda zai iya Misalantashi dana Farkonsa,Bakin Abdullahi baya Rufuwa Saboda Farincikina,Dashi Da Nazifi Suna Sanye ne da kaya iri Daya Farar Shadda Riga da wando Har da Babbam Riga Wacce Taji aiki da Hular zanna Bukar akansu Abunda sai Wanda yagani., ana Gama Daura Aura ya Fito da Wayarsa ya Turama Barkat Sako da Cewa
_Alhamdulillah Now u are Officcialy Mrs Abdullahi Usman Direba..Allah ya bamu zaman lafiya.._
Barkat na Cikin kawayenta da yan"uwanta agidan da suke zama Ba ita ta Bude Sakon ba wata kawartace Nusi abokiyar karatunta Ta Bude Sakon ta karanta afili nan da nan suka saka mata Ihu da Cewa,itama sai Hawayen Farinciki Tana Hamdala aranta da yau Allah ya Cikamata Burinta ta zama Matar Abdullahi Barkat tasha Kwalliya Sosai Tayi kyau ainun Sunyi anko na Less mai kyau Sunsha kyau Su Bahiya Suna ta Rawan Jiki abu nasu mganin a kwabesu Aina dai Ita kadai ce Tayi Missing Tana makaranta kuma Babu Halin Tataho Tana Chan Tana Cizan yatsa.
Su Abdullahi kuma Daga Wajen Daurin Aure Shagalinku sukaje sukayi Reception Wanda Nazifi da wasu abokansu suka Dauki Nauyinsa kuma na kowa da kowa ne Harda iyaye irinsu Baba Wada dasu Daddy, Suma Sunje sunci sun Sha kuma Suna Addu"an Allah yabama Ma"aurata zaman lafiya Daganan dai iyayan suka kama kansu Abokan ango da ango kuma suka Nufi Gidan iyayen amarya suka Shiga Har Ciki Suka gaisa ana ta Nuna Ango kowa kagani yana Son Barka ne Daganan Gidan dasu Barkat ke zama Suka Nufa chan aka je akayi ta Hotuna kala Abokan ango na ta ma Abdullahi Shakiyanci Suna Fadin ya More Duka Matansa ya Hada yara kanana yana Morewarsa Baya mgana Sai dai Mirmishi kadai Domin yau da Barkat ta Tabbata matarsa yana jinsa kamar yana yawo a gajimare ne sai Wajen 3pm da wani Abu suka Baro Wajen Bayan su Nazifi sun Jadaddama Kawayen Amarya cewa karfe 5pm na yammah zasu zo Daukan Amarya Daganan Gidan Mama suka Nufa,Chan suka Iske su Ammi dasu Goggo Habiba Su Hajiya Sa"a da Hajiya lariya dasu Inna Abu Suma sunci kwalliyarsu Gidan Cike da mutane makota da yan"uwan Har Cikin Gidan suka Shiga Abdullahi Daya Ga baiga Zannira ba ya Tambayeta Mama tace Dazu Tatafi Gidansa Sai Lokacin ya Tuna yau tun Bayan Wayar da Sukayi da Hafsah bai kara Kiranta ba Sabewa yayi zuwa Waje ya barsu Nazifi na gaisawa da su Umman Sadiq ya Fita ya Kebe kanshi ya lalubo lambar Hafsah ya Kirata ammh Har Tagama Ringing bata Daga ba Kira Wajen Hudu yayi mata Bata Daga ba Sai Ranshi ya baci ya maida akalan Kiran nashi ga Zannira Bayan ta Daga sun gaisa tana mai Murnan an Daura aure lafiya Ya katseta da Tambayan Hafsah tace bari ta Duba mata Suna Ciki ita da su Subai koda Ta Shiga ta isketa tana Sallah ne sai ta gayamai batare Dayace komai ba ya Datse Kiran yana Sauke ajiyar Zuciya.
Bangaran Hafsah kuwa Wacce Taci Kwalliyarta Cikin Wata Super mai Tsada Cikin Wanda Ammi ta Dinko mata ne na Fitar Biki Shiyasa ko kayan Abdullahi na Fadar Kishiya bata Bi ba Tunda ta samu kaya Hatta Anty Hadiza tayo musu anko Atamfa da Leshi kala Biyu,Dinkin Doguwar Riga tayi Saboda Cikinta Su Amira kuwa Yan kanti Abdullahin ya Siya musu bama Shi suka Saka ba Shaddan da Subai ta Dinka musu Hardasu Muhusina suka Sanya,Tun Bayan Da Gari ya waye Hafsah gadai Ta nan ne su Mariya da su Jidda Manyan mata suna Waje suna Girki Suna Hiran Yawancin Hiran Sakina ne Jidda na Bada labari Subai na Dariya jin wai Sakina na Fadan wai Nazifi ya Daina kula da al"amarinta Hafsah na Ciki Tana jinsu Domin acikin Kirjinta Wani Nauyi Take ji Subai ne Data Shigo ta Fahimci Halin Data ke Ciki ta Dinga Lallashinta ta matsa mata ta Shiga tayi Wanka ta mata kwalliya da Safe Wani Less ta saka ammai Dinkin Buba suka zo Suna ta Daukanta hotuna Domin dai su Debemata Kewa Anty Hadiza kuwa kallon kanwarta kawai take Tsausayinta na kama Su suka Taimaka Wajen Rage mata Damuwa ammh Lokacin Da Ta tabbatar da an Daura Aure Sai da Tayi kuka Kishi ya Taso mata Tailet ta Shige tayi mai isarta kana ta Fito ba wanda yace mata meyasa tayi kuka Domim Kuka ai Dole ne,Su dai sun gama abinci sun kwashe a kololi kowacce Taci wanka sun koma gefe makota dai sun Shisshigo Allah Sanya alheri.
Lokacin da Abdullahi ke Kiran Wayar Hafsah Tana Hannunta kuma Tana gani Taki Dagawa Kuka ya kawo mata Wato sai yanzu ma ya Tuna da ita Tailet ta Shige Tasha kukanta kana Ta Dauro alwala ta Fito ta Tada Sallar la"asar ganin Lokaci yayi,kuma Data idar Zannira ta gayamata sai tace wayar bata Hannunta bata gani ba,Sai kawai ta Share Zencen.
Hudu da Rabi Abdullahi ya Kira Zannira yace Yanzu su Nazifi zasu Dauko Amarya,Tace Shikenan Shi ya Kira Mama ya gayamata yace Gidanta za"a Fara kawota Daganan sai su kaita Chan nan ma ta sanar ma su Ammi Suka Tashi suka Fara Shirin Tarban Amarya Tun Hudu da Rabin Su Nazifi da Sauran abokan suka Tafi Chan Tudun Wada Daukan Amarya,Bata ma Gidan Tana Sabon gari Gidan Wan Babanta Sai da suka Jirasu suka Dawo da ita Daga Nasiha,Barkat din an Mata Nadi Cikin Lifaya ne,Sai kuka take ba"a wani Dau Lokaci ba Tunda dama an yi mata Nasihan da za"a mata Yayansu Salisu da kanshi ya sata Cikin Motar Nazifi kanwar Hajiya Amina ta Shiga da matar Wan Babansu Guda Daya Sauran Motocin kuma kawaye da su Bahiya da Sauran yan"uwa suka Shiga aka Tafi.
Sun Samu Tarba wajen Su Ammi da su Hajiya Sa"a agidan Mama,Maman suka Damkama Amanarta kuma ta amsa ta saka albarka anyi Barkwanci Sosai da Nishadi kafin Daganan kuma su Ammi da Su Inna Abu Dasu Umman Sadiq dasu Hajiya suka Kara Rakiyan Amarya zuwa Tukur Tukur Gidan Abdullahi Chan Dinma Su Anty Hadiza ne da Zannira manya suka Tarbesu,Dakin Hafsah suka Kaita Da Farko Suka Mika ta ga gareta a matsayinta na Babba ta kuma ce ta karba yan Nasihohi ne suka Biyo Baya Kafin Su Ammi da su Inna Abu suyi musu Jagora zuwa Dakin Barkat din,su Zannira suka Gabatarmusu da kololin Abinci da Abunsha na Tarba Iyayen dai basu Wani Jima ba Suka Fito aka maidasu Gida yanmatan ne da Su Bahiya suka Rage Suma su Ammi Tuni Suka Wuce Gidan Mama Aka bar Su Subai wacce ma ko Kofar Dakin Hafsah bata Fito ba Tana Cikin Bedroom Dinta tana Lallashinta Tana ta kuka Tun Lokacin da taji Gudan kawo amarya Komai nata ya Tsaya su Zanniran ma Falon Hafsah suka Dawo Suna Hira suna jin Su Bahiya da kawayen Barkat din Suna ta Shewa sai Wajen 8am na Dare suka Ji Tafiyarsu Domin dai Abdullahi ba"a kwanan mai agida Su zannira ma Gidan Mama suka Koma ita da Jamila Dasu Jidda da mariya Anty Hadiza ma Binsu tayi Dagachan zatabi Ammi su koma Gida Subai kadai aka Bari tace sai Gobe zata koma Ganin bazata iya Barin Hafsah Cikin Wannan Halin ba.
Bangaran Abdullahi kuwa sai da suka gama Sallaman bakinsu Duka Sukayi Sallama da Nazifi Daga Gidan Mama ya Dauki jidda Zuwa Gidansu,Su Ammi sun Wuce Gida Hajiya sa"a ma Sun Tafi Umman Sadiq ne kadai dasu Goggo Suka Rage sai su Zannira anan yake jin wai Subai na Gidansa Chan zata kwana bai ma Bi ta kanta ba Domin bata ita yake ba,Kofar Doka ya Wuce Daganan ya Siyo kayan Tarban Amarya Mashin Din Haya ya Hau Zuwa Gida Mashin Dinsa yana Wajen Auwal Tun Fara Hidimar Bikin.
Subai da Hafsah suna Falo Sukaji Bude Kofar Abdullahi da Rufe Gidan Dayayi da makulli Zuwa Shigowarsa Gidan,Hafsah na jin Haka ta Daga kai ta kalli agogo 11:30pm na Dare,tashi Tayi Tsam ta Shige Ciki Tana Danne wani Abu Dake tasowa Daga kasan Ranta,Subai ta Bita da kallon Tsausayi ga Tsohon Ciki ga kuma
Kishiya ai Abun yayi mata yawa Gaskiya.
Dakin Hafsah yana kulle ne Abdullahi Daya Tura yaji ta a kulle ya kwankwaa Subai tataso ta Budemai Dama su Biyu Da Hafsah ne zaune suna Hira yara Tuni Sun Dade da yin Barci Subai ta musu Shimfida ta kaisu Daki Sun kwanta Budemai kofar tayi ya Shigo yana kallonta kafin yayi mgana tamai Sannu da zuwa Cikin Dakiya ya amsa yana Gyara zaman ledan Hannunsa Lokaci Daya yana Takawa Tsakiyar Falon Cikin Kalle kalle yace"Ina Yaran nan ne..?
Subai tace"Sun yi barci Tun Dazu.."Kai ya kada kafin yace"Ita Hafsah fa..? Subai Tace"Ta Shiga Ciki Inaga ta kwanta ne..."Bai kara mgana ba yana gyara zaman Babban Rigan Dake Jikinsa ya Shiga Cikin Bedroom Subai ta Bishi da kallo Kafin ta tabe baki ta Shige Dakin Yaran aranta Tana Fadin"Namiji munafuki..!
*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*
*Janafty...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
_Wannan shafin Zai Tafi ne kai Tsaye zuwa ga Tauraruwata Cikin Taurari Wato Sisinah *AISHA ALTO..* Hakika ke din ta Dabamce Kin Gama Sangartani kin gama Gatantani,Na yarda Labarin Masifaffan Namiji nawa ne, kuma Ni nake Rubutashi Da Hannuna ammh kuma Ina so kowa ya sani kuma ya Shaida Ba Domin ita ba da bazai Taba kai muku Inda kuke ba har ku karanta Ta Dauki Nauyin Yimin posting aduk Lokacin dana Gama Typing,Tace Sisinah ki kwanta ki Huta zan Miki posting baki Da Damuwa,Hakika Kirkinta gareni Ya wuce mai karatu ya kwatatanta bani da bakin da zan mata Godiya ko na Biyata ga alherinta gareni Sai dai Na Cigaba da Rokon Allah a Duk inda Take ya Tsareta ya Jibanci lamarinta Allah ya bata Miji nagari mai sonta mai kaunarta In Ta Tara Zuru"a Allah ya Tsare mata su,Allah ya bata aljannah Firdausi Allah ya Shayar da ita Ruwansa na *ALKHAUSAR*..! Alherin Allah da Fadadarsa tare da Rahamarsa ya Cigaba da Bibiyarta har Karshen Numfashinta Zuciyata Tana Girmama Alherinta gareni Ina kuma Fata Da Rokon Duk wanda ya karanta Page din nan Zai Cike Tagging Dinsa da *AMEEN* Da Capital Letter..._
*034*
"Hafsah na Ciki Tana Jinsu Duk Mganar da sukayi da Subai Tana Jinsa yana Tambayanta da amsan da Subai ta bashi Dama Tana Zaune Gefen gado ne, da Katon Cikinta agaba kwata kwata bata da karfin gwiwan kallon Abdullahi cikin kayan Angwanci Kuma wai da sunan zai mata Sallama zuwa Dakin Amarya Zuciyarta bazata Dauka ba,Tana Jin Tahowarsa zuwa Cikin Bedroom din Tayi Zumbur ta kwanta ta lumshe ido kamar mai Barci nan kuwa Zuciyarta ne da Kirjinta ke wani Lugude wanda wannan Abun Shi ake Kira Kishi kumallon Mata.
Yana Shigowa Cikin Bedroom Din da Sallama ya Hangeta kwance Tunda Akwai Wutar Nepa Lokacin,Mamaki ya kamashi Ganinta kwance acikin yanayi na kamar bata Shirya kwanciyar ba Har gabanta ya karisa yana kallonta,Dukawa yayi a Gabanta yana Kiran Sunanta Cikin Rada Rada Ammh Hafsah Taki Ko Motsi Kura mata Ido Yayi sai ya Fahimci gashin Idanuwanta na Motsi Sai lokacin ya Fahimci ba Barci take ba kawai Shine bata san gani ko kuma Haduwa Dashi,Dama ko na Kiran Waya Jikinsa ya bashi Tana ganin Kiran Nashi Ra"ayin Dauka ne batayi ba kuma Tsakani ga Allah Ranshi ya baci kawai ya Danne ne ganin Halin da ake Ciki yanzu yana Mgana sai ta Fassarashi ta wata Hanyar,Na Biyu kuma Tana da Lalura Ko bakomai Tana Bukatar a Daga mata kafa Ta samu Allah ya Sauketa lafiya.
Mikewa yayi Lokaci Daya yana Sakin Ajiyar Zuciya Zaman Babban Rigansa ya gyara Lokaci Daya ya Saka Hannunsa Guda Daya ya gyara mata zaman kanta Saman Filo da bata kwanta Daidai ba Yaja Blanket Dake Gefenta ya Rufe mata kafarta,Kana ya Shafi Fuskarta yana Fadin"Wai Hafsatun Abdullahi Da kanta Take gudun ganin Mijinta Abdullahi..? Ina Fatan Kiyi Barci Cikin kwanciyar Hankali mai Cike da mafarkina Matata.."!
Sanda ya Fadi haka sai da Bakinta ya Tura Hawaye suka kara Cika mata Ido Wato Tayi mafarkinsa Gata yar iska Shi yana chan yana Holewa da amaryansa,juyawa yayi ya kama Hanyar Fita kafin ya Fita sai da ya Rage mata Gudun Fanka kana ya Fice Daga Bedroom din Idanuwanta ta Ware tana Bin Bayansa da kallo kafin Hawayen Datake ta Dannewa su Zubo Wani kuka Taji yana Kokarin Fitowa Daga kasan Ranta yasa ta Danne Bakinta Jin Har yanzu bata ji Ficewarsa Daga Dakin nata ba.
Yana Fitowa Falo ya Shiga kwalama Subai Kira Waya Take da Mahmud ta yanke da Sauri ta Fito Tana Saka Dankwalin kanta,Dayar ledan Dake Hannunsa ya mika mata yana Fadin"Ki Diba kici in kina Bukata Sauran kuma ki sakama Hafsah da yara a Fridge Zuwa gobe kar ya Lalace.."Subai bata ja wata mgana tace toh Ta karba Ya juya yana Cema ta sai da Safe tace Allah tashesu lafiya sai da ya Fice kana ta Bude ledan kaji ne guda Biyu sai Madaran Hollandian masu Sanyi manyan guda Biyu baki Tatabe kawai batare da Tayi mgana Ba Fita Tayi Waje Lokaci Daya tana kai Duba zuwa ga Dakin Barkat din Taji Abdullahi Bayan ya Shiga yana saka ma Kofar key,Baki ta Rike aranta tana Fadin Shagali,Kafin ta wuce Kitchen ledan gabadaya ta Saka Cikin Fridge,Ta Rufe tana kara Bin Kitchen din da Kallo Tana Tabe baki ganin yadda yan"uwan Barkat sukayi Ta salo Wajen Danka kayan Kitchen din kamar sun Samu wani Falo..
Fitowa tayi ta Rufeshi bata saka makulli ba Domin ya bace ba"a ganshi ba yara sun Dauka Sunyi Wani Wuri Dashi Dakin Hafsah ta koma Lokaci Daya ta Rufeshi da makulli Bedroom din ta Shiga Tana Kiran Sunan Hafsah Wacce Taji Kiran Daga sama Tayi Zumbur ta mike Daga kukan Data Zauna Dirshan saman Gado Tanayi Galala Subai tayi Tana kallonta Kafin ta samu Zarafin mgana kawai Hafsah Tayi Saurin Wuceta Ta Bude Kofar Tailet ta Shige Tana Fito da kukanta Sarari ko ta samu Saukin Abunda Take Ji acikin Zuciyarta Kofar Bayin Ta Sulale ta Jingina da Kofa Kawai ta Saki baki Tana kuka kuka mai Tsuma Zuciyar Dukkan wani mai Sauraro Subai Dake Cikin Bedroom din ta iya jiyota kai kawai ta Girgiza kafin ta Karisa Kofar Tiolet din Tana Fadin"Bazan Hanaki Kuka ba Hafsah.Domin Abun kuka ne ya sameki..Hakika naga Kokarinki kina ma da karfin Hali..Sai dai ki Tuna da Abu Daya yayinda ki ke Zaune Cikin Bayi kina wannan kukan Da Daddare gaki da Tsohon Ciki Toh ki Fa Tuna Shi Ya Abdullahi yana Dakin Amaryansa kuma na Tabbata kinsan ba kuka zai kwana yi ba ko..? Ya kamata ki ma kanki Fada kiyi Kukan nan Kadan ki Share Hawayenki kodomin Tsira da lafiyarki.."Subai ta Fada Lokaci Daya Tana barin Wajen Kara Rushewa da kuka Hafsah tayi Alokacin bazata iya Contolling din kanta ba sai tayi kukan Da Tadade Tana Rikeshi acikin Zuciyarta.
Gadon Subai ta gyara musu,Akwatinta da Tazo Dashi ta Bude ta Sauya kaya zuwa Rigar Barci ta koma ta kwanta,Tun tana Saka Ran Fitowar Hafsah Shuru sai ta Tsorata Tana kokarin Saukowa Daga kan Gadon ne sai ga Hafsah ta Fito Tana Goge Ruwan Fuskanta Daure Take da Towel,Wanka tayi bayan Tagama kukan ajiyar Zuciya Subai ta Sauke kafin tace"Thank god..Na zata kin Suma ne a bayi saboda ya Abdullahi wanda ke chan da Amaryansa Suna Soyewa.."Wani kallo Hafsah tayi mata batayi mgana ba Subai bata kara bi ta kanta ba ta koma ta kwanta Tana Fadin"Ni bake nake ji ba..Abun ke Cikin ki nake ji Hafsah Don Allah ki Tsausayama kanki da wannan Damuwar kada Wata Cuta ta kamaki na Tabbata ko mai kawo mana Dauki kafin mu samu ansha Wuya Domin na Tabbatta Mijinki yadda yake wannan angwancewan yau ko Mama bata isa ta Fito Dashi Daga Dakin Chan ba.."Tafada Cikin Jin Haushin Hafsah din Lokaci Daya Tana Juya mata Baya.
Bayanta Hafsah tabi da kallo Tana Dauke Hawayen Idanuwanta acikin Ranta kuma tana Fadin na Daina Damuwa da kuka Insha Allahu Subai,Rigar Barcinta Doguwa ta Sanya Dama Tayo alwala ta Shinfida sallaya ta Saka Hijabi ta zauna Dakyar Domin bayanta ya kage bata iya Sallah a tsaye Raka"a Hudu tayi,ta Hada da addu"an samun Sassauci kana ta nade Abun Sallan tazo ta kwanta ganin Har Subai Tayi Barci Tana Shirin Tashi ta kashe Wutar Dakin Nepa ma Suka Dauke Wuta sai kawai ta Bude Labulen window Saboda iska ya Shigo Taji garin da Dan Zafi zafi,Kwanciya kawai Tayi ba Domin Tana Jin Barci ba Domin Data Runtse ido Sai ta Hangi Abdullahi Cikin wani yanayin da ita kadai ce Tasan yana Shiga sai Tayi Sauri ta Bude tana Kiran Sunan Allah Mirgina mirgina kawai Take ba Domin Tana jin Dadin kwanciyar ba.
****
Bangaran Abdullahi kuwa da makullin Hannunsa ya Bude Dakin Barkat ya Shiga,Ya kuma maida kofar ya kulle Falon yabi da kallo yadda komai yayi kyau Neat Falon kalan Pick and Ash,Kamshin Turaran Wuta sai Tashi yake,Masha Allah kawai yace acikin Ransa ya Taka da Takalminsa Zuwa Cikin Bedroom din Barkat.
Tana Zaune Bisa gadonta Jikinta Nannade da Lifaya kanta ma ta Shigar dashi Ciki,Daga Kofar Bedroom din ya Tsaya yana kare mata kallo Ita kuma tana Jin Motsin Dama Bude kofarsa da Rufewarsa Tana Jin Takun Shigowarsa ta Jikin Mayafinta Take karemai kallo acikin Ranta tana Jin kamar ta zarce Sauran mata.
Sai da ya gama More ma kallonta kana ya kariso Tsakiyar Dakin,Ledan Hannunsa ya ijiye kan gado kana ya Duka ya Cire Takalmin kafarsa ya Haye gadon Har Zuwa Inda Barkat ke zaune ya Zauna agefenta Har kafadunsu na Gogan na Juna,Dukkansu sai da sukaji Wani yanayi Domin Tunda suke ko Hannunta Abdullahi bai Tana yarda ya Taba ba ya bari sai ta zama Halilinsa Tukunnah.
Ajiyar Zuciya ya Sauke yana Shakan kamshin Dake tashi a Dakin da kuma Wanda ke Tashi Daga Jikin Barkat,Rankwafowa yayi Zuwa Jikinta yana Fadin"Amarya kin sha kamshi...! Yafada Cikin Wani Salo noke kafada tayi batayi mgana ba,Yar Dariya yayi yana Fadin"Nifa in ma Siyan baki kike jira nayi gwara ki ma Bude kimin mgana na Riga na gama Siyan bakinki Tuni Tunda na Mika Sadaki aka Daura mana Aure"Yafada yana leken Fuskanta kokarin nokewa take ya Riketa yana yar Dariya da kansa yasa Hannu ya Cire mata Lifayan daga kanta Zuwa Wuyanta Lokaci Daya yana Fadin"Masha Allah.."
Kurama Juna Ido Sukayi na wani Lokaci kafin Abdullahi ya Lumshe ido yana Fadin"Bari na kara..Alhamdulillahi ya Allah.."Mirmishi ta sakarmai Lokaci Daya tana karya wuya itama Tace"Alhamdulillah..Allah ne Abun godiya.."Kallon Sha"awa yake Binta da ita ita kuma Duk sai Jikinta ya Saki Ta yunkura ta gyara zama kawai ya kwanto mata Bisa Kafadanta yana Fadin"Amarya Bakya laifi ko kin kashe Dan masu Gida..Finale ga ki a Gidana amatsayin matata sai kume me ya Rage..?
War ta mai ido kafin tace"My Man...!Saurin Dagowa yayi yana Fadin"Sai Shagali ko..? Yafada yana Dariya kunya ya kamata ta Suke kai tana yar Dariya Shima Dariyan yake Tashi yayi Daga kan Kafadanta ya Sauka Daga kan gadon Ledan kazan ya Dauka ya Tura gabanta yana Fadin"Bari na Fara Ciyar da Amaryata Kamar yadda Annabin Rahma Salallahu alaihi wasallan ya koyar damu Daga nan koma menene sai ya Biyo baya.."Yafada yana Kokarin Cire Babban Rigan Dake Jikinsa da kallon kasa kasa Take Binshi Har ya sake Hayowa kan Gadon yaja ledan ya Bude ya Cire Madaran Hollandian din guda Biyu ya Bude Kazan a Babbar Takardan yana Fadin"Sai fa kinyi Hakuri Amarya..Na Riga na kulle ko"ina kuma bana Tunanin akwai Filet nan Ciki ko..?
Girgiza kai Tayi Kafin tace"Anya..? kamar Duka Suna Kitchen.."Kai ya jinjina kafin yace"Mu barsa...Ni zan cinyar dake da kaina Amaryata.."Shagwabewa tayi zatayi mgana Daidai ta Bude baki ya yako naman ya Saka mata abaki Wani Zaro ido Tayi Tana kallonsa Shi kuma sai ya Sakamata Dariya Cikin Wani Salo ta Harareshi Tana Tauna Naman Lokaci Daya tana Fadin"my man Sai fa na Rama..naki wayon nan naka.."Yana Kara Sakamata Cikin baki yana Fadin"Ina son irin Wannan Ramuwar Baby.."Yafada yana Kashe mata ido Daya Hannu ta saka ta yago Wani katon Naman ta Nufi Bakinshi dashi Kansa ya kauda gefe Yana Fadin"Kai kai..Baby wannan yama bakina yawa fa..?
Yafada kamar wani karamin yaro bata Saurareshi ba Ta Kama Hannunshi Shima ya Riketa ta Turamai Cikin baki,Bakin nashi ya Cika ya kalleta yana bata Rai Dariya ta kama Barkat itama ta sakamai Dariya ganin haka Shima yace sai ya Rama suka Shiga wasan Tusama Juna nama Cikin Baki Cikin Nishadi da Soyayyah sai gashi sun kusa Cinye nama Daman Kowanne na Jin Yunwa kadan suka Rage Abdullahi ya Dunkule Cikin leda ya Iijiyeta nan Saman Side drower din gadon,Madaran Hollandian ya Dauko musu Guda Daya ya Bude ya Kurbi ya Nufi Bakin Barkat Dashi Marairaicewa Tayi ammh Duk da Haka sai da ya Juyemata Shi Cikin bakinta sai da yayi mata Haka Sau uku kana Shima yace sai Ta Rama ma kura Aniyarta bata da yadda zatayi Dole tamai yadda yayi mata Daganan ne kuma Abdullahi ya Zarce da kissing Din Bakin Barkat kamar ya samu Sweet tuni itama Taji Ta Sauya Layi ta sakamar Jiki yana Sarrafa Bakinta Lokaci Daya kuma yana Sarrafa gangar Jikinta..
Sun Dau wani Lokacin kafin ya Saketa ya koma Gefe yana maida Numfashi kunya ya kamata ta Maida kanta ta Rufe da Filo Saukowa yayi Daga kan gadon yana Cire Rigan Jikinsa Lokaci Daya Yana Fadin"Kash..Nayi mantuwa ban Dauko ko Jallabiyata Daga Dakin Hafsah ba..Ballatana kayan Barci.."Yafada yana Ijiye Rigarsa saman Gado Hanyar Tailet ya Nufa yana Fadin"Bari nayi Wanka Baby..in na Fito sai kiyi ko Zaki zo muyi Tare ne .?
Dagowa Tayi Ta ballamai Harara Mirmishi yayi ya Shige Cikin Tailet,yana Shiga Barkat ta Mike tana Sakin Mirmishi Gadon ta kallah yadda suka yamutsashi mikewa Tayi ta kakkabe ta sake gyarawa kana ta Dauki Ragowan Lemon Hollandian da Sauran kazan ta kai Falo ta Saka Cikin Fridge dinta na Falo Dama Biyu akayi mata Daya na Kitchen Daya na Falo,Ta Dawo Bedroom din kenan sai gashi ya Fito Da Gajeren Wandonsa sai karamin Towel bisa kansa yana Tsane Ruwan kansa Tana ganinshi ahaka ta Juya Tana kokarin Rufe Jikinta da Lafayanta Dariya ta bashi ya kalleta yana Fadin"Ki shiga kiyi wanka ki Sauwake ma kanki wannan Abun..Infact ma da kin Tambayeni da baki saka Wata Lafaya ba Am Not interesting of it Bata Burgeni sam.."Ya Fada yana Jifanta da wani kallo Da Sauri Ta Juya Wardrope dinta Ta Bude ta Ciro Rigar Barcin da Bahi ta Ciro mata kafin su Tafi wacce akama Barin Turare Har tana Tuntube Wajen Shiga Tailet Dariya ta kamashi ya Daga Murya yana Fadin"Bi sannu dai..Ki kuma Dauro alwala kafin ki Fito.."Tana jinsa tayi masa Banza ammh afili Sai ta Murmusa kawai.
Wankan nata bai jima ba ta Fito Bayan ta Dauro alwala ta kuma Saka Rigar Barcin nata mai kalan ja Wacce marabanta da Tsirara kadan ne,Sai ta kuma Nado lafayan nata Saboda Yadda Suran Jikinta ya Bayyana Cikin Rigar Barci Yana Tsaye ya Shinfida Sallaya ya Saka Wandonsa da Rigansa Tana Fitowa ya Bita da kallo kamar ya saka Dariya sai dai kuma ya kanne Cikin Dakiya da bada Umarni yace mata"Ki Dauki hijabinki Sallah zamuyi..? Allah sa kin Dauro dai alwala..?
Kanta na kasa ta Dagamai kai Baki kawai ya Tabe ya Dauke kai ganin baya Kallonta yasa ta Raba ta Gefenshi ta Bude Wardrope ta Dauko Hijabinta ta Saka kana ta Cire lifayan ta maida Cikin Wardrope dinta Tazo ya Jasu Sallar Wacce sukayi Raka"a Hudu kana ya Cika da Sauran Addu"o'in zaman lafiya bayan ya Dafa kanta ya mata addu'an Suna Idarwa ita ta Fara Tashi ta koma kan Gado ta kwanta wai tana Jin Barci bai ce mata komai ba sai yama ya Tashi ya Kashe Wutar Dakin,ya cire Rigansa ya Saka Cikin Wardrope wandon ma Cire ya bar kanshi Dagashi sai Gajeren Wando Barkat na Hangenshi ta Dan Hasken Dakin Gabanta kawai ke faduwa ta Tuna Shakiyancin da kawayenta ke ta mata Dazu wai yau Abdullahi zai yi Hawan Daushe harda na Bariki ma akanta kuma Dai Taga alaman haka.
Sai da ya kashe wayarsa ya ijiyeta nan saman Dressing mirror kana ya Fesa Turare Spry na Jiki kana ya Hayo gadon,da Sauri Barkat ta matsa Shima ya matso har suka kai karshen gado ya Kureta Cikin Tsoro Take Fadin"My Man y...! Shiii...yace mata yana kallonta ta Cikin Duhun Dakin Tsit tayi Tana jinTana gani ya Jawota Jikinsa ya Rumgume Lokaci Daya yana Cire mata Hijabin Datayi Sallah Dashi Lokaci Daya yana Fadin"Kema dai kinsan bazan iya kyaleki ba..Kina Wani kira na My Man..Ammh kina kokarin Hanani zama My Man din na gaske.."
Yafada yana yawo da Hannunshi a Gadon bayanta,Tsoro ya kama Barkat ta Fara Rawan Jiki Dago kanta yayi yana Fadin"Are u Ready...? Bata samu zarafin mgana ba sai Daga kai da Zuma da Farinciki ya Hade Bakinsu Waje Daya Yana Kissing Dinta Hannu Daya ya Tallabi kanta Hannu Daya kuma yana karakaina Bisa Jikinta,up Side dowan yayi mata sai gata a kasansa Shi kuma yana samanta Rigar Barcin mai Budewar gaba ce yana Saka Hannu ta Bude ta Bayyana mai Komai Tudun Nonowan Barkat sun kara Saka Abdullahi ya Fita Daga Hayyacinshi,ya Shiga murzashi Lokaci Daya Cikin Wani Shauki Ita kanta Barkat din Sakarmai Jiki Tayi tana Bankaromai Kirji,bata kara Fita Daga Hayyacinta ba sai ya kafa baki yana Shan Daya yana wasa Da Daya ai sai ta Rude ta Rike kanshi Tana wani Sakin Numfashi sama sama kamar mai Asthama.
Tuni Barkat ta saki Jiki ta zata iya Abun kenan Bata ankara ba Taji Abdullahi yayi Kasa da pant Dinta kafin tayi wani yunkuri ya Bude mata kafafu ita dai Daganan bazata Dora komai bayan Addu"an saduwa da iyali Dataji yana karantowa sai kuma Dunfarun wani Abu zuwa gabanta mai kama da icce ko wani Abu dai mai karfi Ihu take so ta saki Shi kuma sai yayi Saurin Dade baki,Ya tura na kofar ba hanya ya Dawo baya ya Sake yunkura nan ba Hanya kawai sai ya Dadaddage ya koma da Baya ya Sawo kai da karfi sai gashi ya Shige Dukkansu wani Numfashi Suka saki Kamar Wasu Wanda Shooking ya Shigesu Cikin Wani yanayin Fitan Hayyaci Abdullahi ke Driving Din Barkat Domin dai ya Riga ya Shiga Wata Duniya ta Dabam..
Shafewar Mintuna Talatin kafin ya Daga mata kafa,Tana ta kuka ya Jawota jikinsa yana Ta lallashi da sakamata albarka a Daran ya Taimaka mata ta gyara kanta ta Gasa kanta Allah ya Taimake su an Dawo da Wuta sukayi amfani da Kittle dinta suka saka Ruwan Zafi,Shi yayi mata wanka ya maidota Daki Zanin gadon kuma ya Cire ya wanke a bayin Cikin Daran Duk da batayi wani Jini Sosai bai Damu ba sanin Mata kala kala ne ammh ai Shi Shaida ne yau din ya Cika MAN din da Barkat din ke Kiransa Shima wanka yayi bayan yayi wankan ya Tsarki ya Dawo Dakin,Wandom kayansa ya maida ya koma ya kwanta bayan ya Jawota Jikinsa Cikin Farimciki da Annushuwa barci Dukkansu ya kwashesu mai Cike da Kaunar Junansu da kuma Farincikin Mallakan Junansu har Abada.
*****
*Washegari...*
Tun Safe Subai tatashi da aiki Daga Sallar Asuba bata koma ba ta Share Dakunan Hafsah,ta Saka Ruwa a kittle tayi ma yara wanka ta Shiryasu Hana Hafsah komai Tayi Bayan Ta Surkamata Ruwan Wanka Tace taje Tayi tace ta kwanta ta Huta kafin Rana ta Fito Domin Tana lura da ita Jiya Sai gabanin Asuba Barci ya Dauketa,Komawa Hafsah tayi ta kwanta Subai ta kada yaran Zuwa Falo ta kunna Musu Mbc3 suna kallon Cartoon Ita kuma ta Fita Tsakar gidan Kitchen Tashiga Domin Samar da Breakfast ko Ba Domin su ba Domin Amarya da angon Dake gidan..
Dankalin Turawa ta Fara Ferawa Sai Taji Buga Gida ta Saki Abunda Take yi Taje ta Bude sai ga Yunusa ne almajiri gaisheta yayi ta amsa kana ya Shigo Sharan Tsakar gidan ya Fara kana yaje ya Zubar da Bola yazo ya Zuba Ruwa ya wanke Tsakar Gidan Saboda ayyukin dayasha Jiya kana Ya Cika Bambinan Ruwan Dake nan Waje wanke wanke kuma Tun Jiya kafin su Jidda suka Tafi suka wanke komai Suka aadana Sauran ayyukan kuma makota suka Karisa kafin su Tafi.
Dankali Ta Soya mai Dan yawa kana ta Soya kwai Sai ta Dafa Ruwan Tea,Awani Food Flaks ta Sakama Barkat da ya Abdullahi Ruwan zafin ma ta Sake musu Cikin karamin FlaksDin Ruwan Zafin Hafsah nan kitchen din ta Bar musu komai ganin basu ma Tashi ba nasu Ta Dibar musu ta Zubama Yunusu nashi Ta Sallameshi kana ta Dauki nasu Zuwa Dakin Yaran ta Fara Hadama su Tea din da Zuba musu Dankali da kwai din sai kazan Jiya Ta Sakama kowa Tsokar naman a gabansa da Ruwa nasu kuma ta Dauka Ta Shiga Ciki ta Iske Hafsah Tatashi Har ta Shirya Cikin Riga da zani na Atamfa Cikin Wanda Abdullahi yayimata ne,Tayi kyau Sai dai Tayi Rama kuma Idanuwanta Sun Kumbura kamar yadda Kafafuwanta suka Haye Sukayi Sumtum.
Tare da Subai suka karya Kiri kiri Hafsah taki Cin kazan nan sai da Subai taci ita Madaran Hollandian din kadai tace ta Dauko mata Shi tasha,Falo suka koma Bayan Subai Ta Tattara komai da suka Bata Zuwa Kitchen ta Dawo Daki Ruwan Wanka ta Juye ta Shiga Tayi ganin Har Goma Saura yau take som komawa Gidanta.
Itama Das ta Shirya Cikin Doguwar Rigar Shadda Wacce Taji aiki,Tazo nan Falo suka Hadu da yara suna Kallo Lokaci Daya suna Hira da Hafsah Wacce ke zaune Dirshan a kasa ta Mike kafa Saboda kumburin Kafarta ya Saki.
Bangaran Amarya da ango kuwa Dakyar suka iya tashi suka gabatar da Sallar asuba Ranar Abdullahi bai iya zuwa masallaci ba Bayan sun idar da sallah suka kara manne Juna suka koma Barci Basu suka Tashi ba sai Pass 9 shima Wayar barkat ce Ta tadasu,Bahiya ce ta Kirata tana Shaida mata suna nan zuwa zasu kawo mata Sauran kayanta anjuma Jin Haka yasa Abdullahi ya Sunkuci Barkat din zuwa Bandaki Duk Nokewarta Tare sukayi Wanka Tun Tana Jin kunyar Har ta Saki Jikinta Bayan Sun Fito ya shafa mata mai shima ya shafa sai ya tuna baida kayan Saawa a Dakin Barkat kayansa na Jiya ya maida yana kallon Barkat Dake gaban madubi Tana Daura Dankwali Bayan ta Saka Wani Less Dinta Dinkin Riga da Sikat Cikin Shawa'awa yake kallonta kafin ya karya Wuya yana Fadin"Baby na Bari naje na gaida Hafsah da kwana naga ya kwanan yara Daganan zan Debe kayana Tunda bani da ko Jallabiya a Dakin ki.."
Bata Waigo ba tace"Ya kamata My man.."Tafada tana wani Rangwada bai iya Wucewa ba sai da ya karisa ya Rumgumota yana Kissing Din Wuyanta Nokewa tayi tana mai Shagwaba ganin kamar yana so ya Zarce ne yasa ta marairaice Tana Fadin'"Ban fa warke ba Wajen yana min zafi Har yanzu..'Shima a marairaican yace"Ah bakin Shiga Ruwan Zafi ba Baby Man dinta..?
Hararansa Tayi Lokaci Daya Tana Turesa Daga Jikinsa Mirmishi yayi yana Fadin"Zan kamaki ne..Bari naje.."Ta Rakashi da Fadin'Sai ka dawo My man.."Waigowa yayi ya Huramata Kiss tayi Salon karba Tana Dariya nan ya Fice ya barta Tana kallonsa Wani Farinciki na Dibanta yana Fita ta Fara gyaran Besdroom din Duk Da Tana Jin Zafi Daga kasanta ammh ta Daure.
Yadda yaga Tsakar gidan ko"ina Fes Sai Abun ya bashi Sha"awa ya sani Ko abaya Hafsah bamai kazanta ba Da sallama ya Tura kanshi Dakin Hafsah yaran na ganinshi Suka Taso suka Dabaibayeshi Amir da Mahsin Dake kanana ya Dauka Muhsina kuma da Amira ya Riko Hannayensu kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon ya zauna yana amsa gaisuwan Subai Hafsah kuwa kanta na Gefe ta gaisheshi Cikin Sanyin Murya ya amsa yana Tambayanta ya karfin Jikinta tace Da Sauki,Daganan Shuru ya Biyo baya Ganin haka yasa Subai tatashi ta basu Waje zuwa Dayan Dakin Hafsah ma Gefe ta maida kanta taki kallon Barayinsa yana lura da ita kai kawai ya Girgiza batare Da yayi mgana ba,Ya Dade yana Biyema yaran kafin ya Turasu Daki Wajen Anty Subai"a Mikewa yayi Lokaci Daya yana kallon Kumburin kafar Hafsah Cikin kulawa ya Duka yana Taba Kofar Lokaci Daya yana Fadin"Meya Faru ne..?naga kafarki ta Kumbura ne..?
Saurin Janyen kafarta Tayi Batare data ma kallonse ba Ballatana ya saka Ran zatamai mgana sai ma Kokarin Tashi Da take ganin Tana ta Dafe Dafen kujera yasa ya Mike tsaye ya saka Hannu ya Dagata Tsaye kallon kallonsu sukama Juna na Wani Lokacin kafin ta Kauda kai Tana Cije baki Lokaci Daya Tana Fadin"Nagode.."Tafada tana kokarin Rabawa ta gefenshi Bake Hanyar yayi Lokaci Daya yana kallonta kanta kawai ta Daga Sama batare da ta bari sun kara Hada ido ba kada kwallar Idanuwanta su Zubo,Sunfi Minto Goma ahaka ganin ta Fara gajiya ne yasa ta samu Bakin kujera ta Zauna tana Dafe baya Lokaci Daya tana Cije baki Ajiyar Zuciya ya saki Yana Fadin'"Don Allah karki Saka Damuwa aranki Hafsatuna kinga bake kadai bane..? Kada damuwarki Tama Abunda ke Cikin ki illah..".
Akarkace ta kalleshi kafin tace"Damuwar me Abban Amira..? Wai saboda kayi Aure..?hmm ina ce baga ka nan agabana ba babu Inda ya Ragu Daga Jikinka ba.? Allah na Tuba me zai saka na Damu ai ba kaina Farau Kishiya ba kuma ba kaina gamau ba.."Ta Fada tana kokarin maida kwallar Data kawo mata Mirmishi kawai yayi kafin ya kada kai yana Fadin"Naji Dadin haka..Bari na Shiga na Sauya kaya..Sannan zan Dibi Wasu kayana na kai Dakin Barkat ko Jallabiya bani Dashi achan."Tak Hafsah batacr mai ba ganin taki ta Tankashi ne yasa ya Shiga ya Bude Wardrope ya Dibi kayan Nashi Da Duk Abunda zai Bukata Ya Fito Tana nan inda ya Barta ganinsa da kaya A hannu yasa ta kalleshi Lokaci Daya ta kauda kanta Shima Kallon nata yayi yana Fadin"Ina Abun karyawa..? Ko kuma baku karyan bane..?
Kamar Bakinta na Ciwo tace'"Mun karya mana..Kayi ma Subai mgana ita ta Samar mana Abunda muka karya awannan Halin Nima neman Taimako nake.."Ta Fada tana Gintse Fuska Bai yi Gaddama ba illah ya Daga kafa zai Wuce yana Fadin"Allah baki Hakuri.."Daga haka ya wuce sai da yakai kayan ya Dawo kana ya kwalama Subai Kira ta Fito yace ina Abun karyawansu tace yana Kitchen yace ta kwasa ta kai musu Dakin Barkat din Bata da yadda Zatayi Ammh acikin Ranta bata So ba Shi kuma ya Kwashi yaran zuwa Dakin,Dama su Amira ba Bakinta bane su Muhsin bata sani ba Shi yayi mata Bayani Dayake tana son yara ta Shiga Ciki ta Dauko musu Sweet Duk Ta Raba musu Falo Suka Dawo Gabadayansu Har da ita suka bar Abdullahi acikina yana Shiryawa Sauran kayan nashi Barkat ta karba ta Jeramai Cikin Wardrope dinta yana Ciki yaji Shigowar Subai sama sama suka gaisa ta Ijiye musu Farantin kayan karyawan nasu Tayi ma su Amira Tsawa tace su Wuce su barsu su karya Tana ta Rabu Dasu Ammh Subai taki Ta Tarasu suka Fice yana Ciki yana Jinta sai da yayi yar Dariya aransa yana Jinjina ma mata wai nan Taya Kawarta Hafsah Kishi take Lalle iska na Wahalar da mai kayan kara.
Tare suka karya agurguje Tunda Nazifi sai Kiranshi yake,Zasu Fita Wajen 12:30pm na Rana ya Fito Daga Dakin Barkat bayan ya gama Shanye Duka Janbakin da aka sakamai ya kuma bata Kwalliyar ta da nashi,wanda sai da ya Sauya kaya Dakin Hafsah ya Shiya ya manta bai Dauki agogonansa ba ya saka yayimata Sallama ya Fita Nazifi na Waje yana Jiransa shi ya Daukesa suka Fita Tare yana ta Tsokanar sa da ango kasha kamshi shi kuma yana ta Dariya.
Tunda ya Fita Barkat ta Maida kofarta ta Rufe,Sai Wajen 2pm da wani Abu ta Bude shima Subai ne ta kwankwasa mata ta mika mata kulan Abinci Babba wanda ta Girka ta karba ta Shiga Dashi ta maida kofarta ta Rufe,Misalin 3 da wani Abu sai gasu Jidda,da Mariya dasu Jamila dasu madina Anty Zannira kuma Tare da Anty Hadiza suka zo Sunzo ba Dadewa sai ga Dangin Su Barkat din sun zo Da kannenta da kawayenta da wasu Daga Cikin iyayenta,nan fa kika ji Shewa na Tashi Hafsah dai suna Dakinsu basu Fito ba Da Mariya ne ma ta Fita Wanke Hannu Bahijjat ta Fito da Kulan Abinci da Filet Filet da kayan da sukayi amfani suka karya Suna Wankewa ita da Bahiya,Sun gaisa da mariya sama sama ta Dawo Daki Tana Basu Labari.
Sai Wajen yammah suka gama Abunda ya kawosu,Da zasu Tafi suka kawo Hafsah kula Saiti Daya da su Cincin da Dublan Sauran kuma suka Dauka suka ce Gidan Mama zasu Tafi Dagachan zasu Wuce gida Suma su Jidda ba su Zauna ba kafin mangariba Duk Suka Tafi Har subai Domin Ita Daganan ma Gidan Mijinta ta Wuce Anty Hadiza da Jidda Duk Gobe zasu koma,Zannira ce sai Talata ita da Umman Sadiq Goggo Habiba ma sunce gobe zata koma ammh Tace kafin Tatafi zata Shigo gidan...
Koda Bayan mangariba tayi Gidan Yayi Tsit Barkat na Ciki Ta Kulle Kofarta Hafsah ma ta Sakayo Daga ita sai su Amira suma Sun Natsu ganin Abokan wasan nasu suma Sun Tafi Tun 9pm sukayi Barci Ganin Amira ta Fara gyangyadi yasa tace ta kama Amir ta kaishi yayi Fitsari tazo ta kwanta Domin in sukayi Barci bata iya Daukan su Saboda itama Tayi Nauyi.
Ita kadai ce Zaune afalo Tana Kallon Tashar Arewa24 suna Haska wani Sabon Film Kallon kawai Take ba Domin Tana Fahimta ba Tana Jin karan Dirin Mota Ranta ya bata Nazifi ne ya kawo Abdullahi Domin Dazu Jidda tace Nazifi ya gayamata gidansu Barkat zasu gaisuwan Surukai kila Daganan suka yada Zango Gidan Mama Daga Dakinta tana jin Tashin muryoyinsu shida Nazifin sun Dauki Lokaci mai Dan Tsawo suna mgana kafin suyi Sallama ya Tada Motarshi ya Wuce Shi kuma Abdullahi ya saka makulli ya Bude gidan ya Shigo Yana Duba Wayarsa karfe 10pm Daidai Dole Barkat ta Dinga Kiranshi tana mai kukan ya barta ita kadai ashe Dare yayi Sosai..
*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*
*Janafty...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*Plz Take Note masu Turomin kudi Suna Fadin kudin karatun Littafin Masifaffan Namiji ne,Ya kamata ku kara sani kuma ku gane Masifaffan Namiji bana kudi bane Free Novel ne,Ra"ayi ne Buri..? Na kudi kan Farashi mai Sauki ₦200 Vip ₦500,So ku Hanzarta Payment Free page sun kusa barinku Shima ina mai Tabbatar muku Zaku ji Dadinsa Fiye da Masifaffan Namiji ma,Domin neman karin Bayani Juz Contact Me ta wannan Layin 09069067488..Ina Maraba da Masoyana aduk inda suke...*
*035*
"Dakin Hafsah ya Fara Shiga,Da sallama abakinsa ya sawo kansa Dakin Hafsah na Zaune Tayi Rashe Rashe a kasa ta kurama Tibi Ido ammh ba Domin Tana Fahimta ba.
Dagowa tayi ta amsa Sallamansa Lokaci Daya Tana kallonsa Karisowa yayi nan kusa da ita ya Zauna akasa Sannu da zuwa tamai ya amsa yana Fadin"Yauwa..ya Karfin jikin nakin..? Tace "Da sauki Alhamdulillah..."Tafada Tana yamutsa Fuska Dakin yabi da kallo kafin yace"Naji Gidan Tsint..Ina yaran nan suke ne..? Kai Tsaye tace"Sun Dade da yin Barci.."
Kada kai yayi kafin yace"Ina kawarki..? Tatafi ne itama..? Da mamaki Ta kallesa kafin Tace"Kawata kuma..? Yace"Eh Subai mana Babbar kawarki ce ai ko... ? Yafada yana yar Dariya Daure Fuska Hafsah tayi kafin tace"Eh mana ai tama wuce kawa a wajena Subai Matsayin yar"uwata nake kallonta.."Kai ya gyada yana Fadin"Tabbas naga alama Tunda Har tana Tayaki Kishi an Miki Kishiya Tana gaba dani Mama tace ko Gida bata Jeba Duk Saboda an yi miki Abokiyar Zama na Shaida wannan Kaunar.."Yafada yana Wani Mirmishi Hafsah ta saki baki kawai Tana kallonsa bata samu Zarafin mgana ba yace"Wannan kayan fa..? yafada yana Nuna Kulan da kayan su Cincin Din Da Dangin su Barkat suka Kawo mata kai ta kauda gefe kafin tace,"Yan"Uwan amaryanka suka kawo kafin su Tafi.."
Abdullahi yace"Ok..Naga ma sun kai Gidan Mama,Harda na Goggo Habiba da Umman Sadiq da mama Harda Turamen Zannuwa suka Hada musu.."Hafsah tace"Allah Sarki angode Allah ya Bar Zumunci.."Ya amsa da Ameen yana Taba kafarta Lokaci Daya yana Fadin"Kumburin nan yana Damuna fa..? Last awonki me suka ce miki..? In ban manta Lissafin ba kina Watan Haihuwanki ne ko..?
Tana kallon Cikin kwayan Idanuwansa tace"Eh...Basu ce komai ba Sunce zai Sauka Ahankali."Bai kara mgana ba illah matsamata Kafar da ya Fara matsa mata yana Fadin"Rashin Matsa ta din da ba"ayi ne ammh ai da yanzu ta sauka.."Mirmishin Dayafi kuka Ciwo Hafsah tayi kafin tace"Wa nake Dashi da zai matsamin kafar..?bani dashi Abban Amira.."! Tafada idanuwanta na cika da kwallah Kallonta yayi ido Cikin ido Kafin ya Dakata da Abunda yake Itama Shi Take kallo Saurin Danne Abun Yaji aransa yayi kafin ya Riko Hannunata yana Fadin"Meyasa kike Fadin wannan mganar..? Wakike dashi fa kika ce..? Ni ba wani Abu bane awajenki Hafsatu..?
Sabule Hannunta tayi kafin Tace"Ba haka nake nufi ba...Nufina ina na ganka ballatana Har kamin Tausan..? Kaida Tunda aka Fara wannan Hidiman baka da lokacinka kanka ma Ballatana na ya"yanka yanzu ma na san Amaryanka na Chan na Jiranka.."Rufe bakinta Keda Wuya Wayarsa ta Dauki kara ya Dakata ya Ciro ta a aljihu ya Duba Ajiyar Zuciya ya Sauke ganin Barkat ne Kallonsa Hafsah Tayi kafin tace"Ita ce ko..? Karka Damu Tashi kaje Allah tashemu lafiya..'
Tafada tana Kokarin Tashi Da Sauri ya mike ya Taimaka mata Ta mike Tsaye tana Cije baki Shi kuma yana ta mata Sannu,Kamata yayi Ya kaita Har kan Gado ya kwantar da ita Godiya tamai kawai ta koma ta kwanta Tana Sauke Numfashi,Kallonta yayi yana Fadin"Kinci Abinci kuwa..?ko basuyi Girki bane kafin su Tafi..?
Hafsah tace"Sunyi mana Subai ta Dafa Da Rana Akwai Sauransa Shiyasa ba"ayi wani Girki ba.."Kai kawai ya gyada yana Fadin"Shikenan mu kwana lafiya..in kinji Jikinki ba Dadi Juz Call me kinji ko..? Da kai ta gyadamai alamun To,Dukawa yayi ya Sumbaci goshinta kafin ya Fice bayan ya kashe mata Wutar Dakin,Falo ya koma ya Tattara kayan su Cincin din da kular ya kai Dakinsu Amira suma ya Dubasu yayi musu addu"an barci ya Rage musu Fankan Dakin kafin ya Fito Sai da ya kashe Wutar Falon kofar kuma ya Turota ya Rufe kawai Tunda Hafsah ta Riga ta kwanta.
Dakin Barkat ya Shiga ya isketa tayi Fushi Harda kuka yana Shiga Bedroom din tataso ta Rumgumeshi Tana mai kukan Shagwaba wai ya tafi ya barta Riketa yayi Yana Shafa bayanta zuwa kugunta alamun Lallashi,Dagowa tayi Tana Fadin"Shine ka tafi ka barni ni kadai ko .? Alhalin ma naji Shigowarka Nayi ta Jiranka ban ga Shigowarka nan ba.."
Hannunta yaja zuwa kan gado,Suka zauna Kumatunta ya Tallaba yana Share mata Hawaye, Cikin Sigar lallashi yake Fadin"Am so Sorry Amaryata,Kinsan na Fita Nazifi na Jirana Munje gidanku mun gaida Surukai Daganan kuma muka Biya wani Waje,kafin Mu Dawo Gidan Mama kinga Goggo Tana nan bata Tafi ba sai gobe,Umma ma Tana nan fa,Kuma Nazifi gobe zai koma kaduna mgana na Tsaya mukayi mai muhimmanci Domin ba lalle bane goben kafin ya Tafi mu Hadu,Mganar kuma na Shigo Gida Tun dazu Bai kamata ki Damu ba, kinsan Halin Hafsah take Ciki Tsohon Ciki Gareta yanzu ke kinga nayi adalci na Shigo Gidan ban leka Dakin ta na ganta ba..? Kina ganin in kece Zakiji Dadi..?
Yafada yana kafeta da ido Saurin Maida kanta tayi Saman Kirjinsa Tana Fadin"Ni ba Haka nake nufi ba..Kawai na Damu ne kabarni ni kadai gasu Bahiya Tun Dazu,Suka Tafi suka barni ni kadai..'Rumgumeta yayi yana Fadin"Kiyi Hakuri gobe muna Tare...Ba inda zani na Dauki Hutu Sati Daya zamuyu sai kin gaji Dani.."Kara kamkameshi Tayi Tana Fadin bazata Ta taba gajiya Dashi ba Sun Dade suna gayama Juna kalaman Soyayyah,Kafin ya Tambayeta taci Abinci tace taci Wanda aka kawomata Ruwan Wanka yace ta Hadamai zai yi wanka tatashi ta Hadamai ya Shiga wanka Bayan ya Fito ya saka Jallabiya Dare yayi komawa kawai sukayi suka kwanta Suna kamkame da juna Hira Suke Cikin Shauki da Soyayyah,Bai mata komai ba Sanin Tana da Rauni ammh Ta bashi Hadin kai yayi yadda yake so da Jikinta Itama ta Nuna mai Kokarinta Wajen maidamai martani kafin su Nade Cikin Jikin Juna Barci mai Dadi Ya kwashesu suna kamkame da juna.
******
Washegari Tun Safe Hafsah tatashi Hakanan Tayi ma su Amira Wanka tayi musu Shirin Zuwa makaranta,Ta Fita Zuwa Kitchen ta Dafa musu Ruwan zafi,Ta Soya musu Buredi Mai kwai Dashi Suka karya Dakin Barkat din ma yana Rufe ko Motsin Abdullahi bata ji ba ganin yara na neman makara yasa Ta Kira Auwal a waya tace yazo yakai su Amira makaranta yace gashinan zuwa ba Dadewa sai gashi yazo Shi ya Daukesu Zuwa makaranta.
Dakyar ta Daddafa Ta Gyara Dakunanta Lokacin yunusa yazo yayi mata wanke wanke da Sharan Tsakar gida ya Zubar da Bola ya Zuba mata Ruwa,Tabashi Abun karyawansa ya Tafi Nasu Abdullahi kuma ta Zuba musu Cikin Wata karamar kula Ruwan zafi kuma Ta saka musu Cikin karamin Falas Ita Ragowar Shinkafan Jiya ta Dumama ta koma Daki Taci ta koshi tasha Ruwa,waya ta Dauka ta Kira Subai sukayi mgana tayi mata Bangajiyan Biki Daganan kuma ta Kira Ammi suka gaisa nan take Gayamata Anty Hadizan Yanzu zata koma ga Direban Mijinta nan yazo Daukanta nan aka bata ita Sukayi mgana tace kafin Tatafi Zata biyo Suyi Sallama da Hafsah Din Tace tana Jiranta kana Sukayi Sallama.
Basu Jima da gama waya ba Sai ga Anty Hadizan tazo bata jima ba Sukayi sallama Tatafi bayan Tayi ma Hafsah Nasihan Hakuri da kuma bata Shawaran in Taji Wani Ciwo ta Kira Ammi ko Mama ta Fadamata Tunda dai Uban gayyar yanzu ta Amarya yake Har ma Anty hadizan Tatafi Bai sani ba Kofar Dakin Barkat din ma arufe yake alamun basu Tashi ba ko Sun Tashi ma basu Dai Fito ba.
Abdullahi bai Fito Daga Dakin Barkat ba sai Wajen Sha Biyu Saura na rana,Ya shiga Dakin Hafsah yana ta kamshin Turare Cikin Shigar Wata Shadda mai kalan Sararin Samaniya,Hafsah na Ciki kwance Ya shigo ganinta kwance yasa Ya zauna Gefen gadon yana Fadin"Lafiya kike kwance..?
Numfashi Taja tana Fadin"Lafiya kalau..Nadai kwanta ne kawai.."Kai ya Ggyada yana Taba kafanta Cikin kulawa yake cemata"kinga Kafar ta sauka ko..? Batayi mgana ba illah ido kawai Data zuramai,Yadauki Lokaci mai Tsawo yana matsa mata kafan kafin ya Dago yana Fadin"Ina su Amira ne..? Waya kaisu makaranta kinsan Wlh sam na Manta ban kira mai mashin dinsu yazo ya kaisu ba.."
Saurin Janyen Kafarta Hafsah Tayi Ta mike Zaune Dakyar tana Gyara Daurin Zanin Dake Jikinta Bata Dade da yin wanka ba ta Saka Sabuwar Tamfanta ta Riga da Zani,Dankwalinta ya Zamo Da Sauri ya gyara mata Yana mata Sannu ta amsa tana Fadin"Dama ai ban jira kaba..Auwal na Kira yazo ya kaisu.."Kunya kuma sai ta kamashi ya Sosa kai yana Fadin"Wlh na Sha"afa..Ban kuma yi Tunanin kiran Auwal din ba sam...Kiyi Hakuri plz.."
Hafsah tace"Bakomai karka Damu..Ya kwanan Amarya..? Abdullahi yace"Lafiya lau..Ya za"ayi ne ina so na Hadaku ne muyi mgana Gabadaya yaushe kike ganin ya kamata muyi zaman..? Yafada yana Riko Hannunta Lokaci Daya yana Jinginata da Jikinsa Fuskarta ta Saki Tana Fadin"Eh to ka bari Zuwa Da yammah mana..Kaga kila yau ma za"ayi baki ko..? Yana Shafa Tulelen Cikinta da Hannunasa Guda Daya yake Fadin"Eh goggo Habiba tace zata zo Ita da Umma kafin su Tafi..bansani ba Ko yan"uwan Barkat din zasu Dawo.."Hafsah tace"Kila zasu Dawo Suma.."
Bai yi mgana ba Sukaji Sallaman Barkat Din Daga Falon,kallon juna Sukayi Itadashi kafin ya yunkura yana Fadin"Barkat ce tazo gaisheki ne.."Yafada yana mika mata Hannu ta kama ya Taimaka mata ta mike Tsaye ya Gyara mata Dankwalinta da Daurin Zaninta ya Rikota Zuwa Falo Barkat din na Zaune kan Daya Cikin kujerun Falon Tana Sanye da Riga da Sikat na atamfa da mayafinta suna Fitowa ta mike Abdullahi ya kalleta yana mata Mirmishi ita kuma ta ballamai Hararan Wasa Duk Hafsah na kallonsu Ta kauda kai Shi ya Taimaka mata ta Zauna kan Kujera shi da Barkat din Suna Binta da Sannu Sai da Zauna kana ta kalleshi Tana Fadin"Nagode Abban Amira..."
Mirmishi yayi mata bai yi mgana ba Barkat din ta rankwafa tana gaida Hafsah din ta amsa tana Mata ya bakunta,Tace Lafiya lau nan Hafsah ke mata Godiya Taga sako Tayi Mirmishi tace bakomai an zama Daya,Kallon Abdullahi Hafsah Tayi Tana Fadin"Kun karya..? Abun karyawanku na Kitchen fa..Sai hakuri Saboda yanayina Ruwan Tea Kadai na iya Dafawa sai Soyayyah Buredi da kwai.."Mirmishi Barkat din Tayi kafin tace"Ayyah bakomai an kina ma kokari Allah ya raba lafiya.."Da Abdullahin da Hafsah suka Hada baki suka Amsa da Ameen Ameen.
Sun zauna Shuru kafin Abdullahi ya mike yana Kallon Barkat din yace"Ke tashi muje mu karya ko..? Ta mike tana Fadin Toh Waigowa yayi yana kallon Hafsah yana Fadin"Bari naje mu karya..Ya kamata asan yadda za"ayi ko mariya ta Dawo nan ta Rika kwana wajenki Saboda yanayinki Abubuwan suna miki yawa.."Hafsah tace"Da kabarta.Bakomai zan iya ai ina Motsa Jikina.."Yana Shirin Fita Daga Dakin yake Fadin'Bana som wannan gaddaman naki..Karki Kara sakamin baki Abunda ya kamata Shi zanyi.."
Jin Haka yasa bata kara mgana ba har ya Fice ta Bishi da kallo Aranta Tana mamakin yadda Abdullahi ke rawan Jiki kan Wata Mace bayan ita Lalle Rayuwa kenan Maida kanta tayi Jikin Kujera kawai ta Lumshe ido kamar mai Barci,Abdullahi da kanshi ya Shiga Kitchen ya kwaso musu Abun karyawansu suka koma Daki suka Karya,Daganam bata kara jin Duriyarsu ba,Jidda ta Kira Hafsah Tana gayamata sun Wuce taso Ta Biyo kafin su Tafi Ya Nazifi ya Hanata bata damu ba tace Bakomai Allah ya Kiyaye Hanya.
Sai Wajen 2pm na Rana Hafsah Tatashi Ta Dafa Taliya da Miyar Kifi Dama Tun Jiya Subai tayi mata Miyar,Taliyar kadai ta Dafa bata ma iya ci ba Su Amira kuma Ta Kira Auwal yace har ya Daukosu Suna Gidan Mama Zasu taho Gidan Tare dasu Goggo Habiba,Shine yasa ta Dibi Abincin taci kadan Nasu Abdullahi kuma akula ta Zuba Musu Komai Tunda suna Ciki basu kara Fitowa ba,Kofar Dakin nata ma yana kulle ne.
Ta idar da Sallar La"asar kenan Sai ga su Goggo Habiba da Umman Sadiq,Da mariya sunzo Tare da su Amiran da Inna Abu da Inna Talatu Hafsah Taji Dadin ganinsu Sosai ta saka Mariya ta Zubo musu Abinci Suka ci suka Sha Ruwa da Lemo,Inaga Hayaniyarsu Abdullahi yaji ya Fito Zuwa Dakin Hafsah suka Gaisa da su Goggo Habiban Yana Dakin sai ga Barkat din ta Shigo ta Duka Har kasa ta gaishesu Abdullahi ya nuna mata Goggo Habiba da Inna Abu yayi mata Bayaninsu Ya nuna mata Umman Sadiq yace ga mahaifiyarsa Dama Tana ganinta taga Kamarsu da Abdullahi Duk da Daman ai Tasan ba Mama bace ta Haifeshi..
Nan Su Umma suka Taramu suka mana Nasihan Hakuri da zama da juna Abdullahi kuma suka Dinga mai Nasihan yayi adalci,Sun Dan Dade sai gabda mangariba suka Yi Shirin Tafiya,Abdullahi da kanshi ya Fita ya sama musu Abun Hawa Mariya kuma yace gobe da safe zai Kira Mama ya gayamata ta Shiryo kayanta Gobe ta Dawo nan Wajen Hafsah ta Dinga kwana Saboda ta Rage mata wasu ayyukan Su Umman Sadiq suka ce Hakan yayi Domin Ayanzu Hafsah Tana Bukatar Tallafi da mataimaki.
Chan ya Tsaya yayi Sallar mangariba da Isha"i kana ya Dawo Gidan Dauke da kayan Marmari da kuma Naman Soyayye da Danye,Da kanshi yakai Kicthen ya saka a Fridge din Ya kaima Hafsah nata kana ya Shigarma da Barkat nata Sai Wajen 9 da wani Abu sai ga Abdullahin da Barkat din a dakin Hafsah suka isketa tana Tashin Amira tatashi taje tayi Fitsari Taje ta kwanta,Abdullahi ya Tada ita,ya kaita tayi Fitsarin ita da Amir din yakaisu Makwancinsu yayi musu Addu"a suka kwanta kana ya Dawo Falo Daman Daya Shigo ya gayama Hafsah yanzu Yana son zai yi mgana dasu Dukkansu.
Bayan ya Bude Taro da Sallama kana ya kora musu Jawabin Da Hafsah ya Fara Inda ya kalleta yana Fadin"Hafsah ga Barkat...Kanwatake gareki ba Kishiya ba..Na Shaidake kuma ina da Kyakyawan yakini a kanki..Bazaki bani kunya ba,Nasan ki nasan Halinki na kuma san Abunda zaki aikata da wanda bazaki aikata ba..Ki zauna da ita da Zuciya Daya kamar yadda na sani..Ki kama Girmanki kina gaba da ita,In Tayi ba Daidai ba Kina da Damar da zaki Yimata gyara akomai na Cikin Gidanan Saboda haka Don Allah Don Annabi Hafsah ki zama Wakiliyata akomai na Cikin Gidanan Domin kece ni..Nine ke Yau in na samu zaman Lafiya Daga ke ne Hafsaatu..Kinfi kowa sanina Daga Mama sai Umman Kece ta Uku Wajen sanin Abunda ya Shafeni Gabadaya Ina Fatan zaki min wannan alfarman Hafsatun Abdullahi...?
Ya karishe Fada yana kallonta Numfashi ta Sauke kafin tace"Insha Allahu..Bazaka samu Wata matsala Daga barayina ba.."Ta Fada tana gyara zamanta a kasan Cafet dinta,Cikin Jin Dadi yace"Alhamdulillah naji Dadin Haka..Barkat na Dawo gareki..Kindai san ke karama ce acikin mu.Baki Dade da Shigowa Cikinmu ba..Ni ne mijinki kuma ina Gaba Dake,Hafsah kuma wakiliyatace Itama Din kamar yaya Take gareki bawai bana Sonta bane yasa na Aureki ba,A'a ina son Matata Domin itace Rufin Asirina Itace Silan Da kika ganni Har Kikaji zaki iya zama dani a matsayin Abokin Rayuwarki..Nasanta Fiye da yadda na san kaina Barkat..Hafsah mai Hakuri ce mai ladabi ce mai Biyayyah ga Duka Umarnina..Saboda haka ki bita Sau da kafa kar naji kinyi Sa'insa da ita ko kuma ta nuna miki baki Daidai ba kiki jin mganarta,Akomai ki Rika Tunawa ke Karamace Ina Rokon da Allah da Annabi ki Yi mata Biyayyah kamar yadda na sanki dashi in Hakan ta Faru zan Fi kowa Farinciki Domin sai da Zaman lafiyanku Nawa zaman lafiyan zai Dore ina Fatan kema zaki min wannan alfarman..?
Kan Barkat din na kasa tace"Insha Allahu..Nima Daga barayina baza"a samu wani matsala ba.."Abdullahi yace'Nagode..Naji Dadin haka sai Barayin Rabon kwana..Ya za"ayi in na gama kwanakina Bakwai a Dakin Barkat Hafsatuna ya zaku Raba Abun ne..?
Hafsah tace"Sai naga mu barsa a kwana Bibbiyu ko..? Ta Fada tana kallon Barkat din Wacce ta gyada kai Tana Fadin"Eh yayi Anty Hafsah..."Abdullahi yace"Shikenan Sai mganar Girki Wacce keda Miji ita keda Girki kenan ko..? Hafsah tace"Eh hakan yayi.."Abdullahi yace"Shikenan Allah bamu zaman lafiya...Sai mganar Barkat Zata koma Makaranta nan da kwana Bakwai Saboda Zasu Fara jarabawa so nayi ma Mariya mgana zata Dawo wajenki Hafsah da zama ta Dinga Taimaka ki Allah barshi sai ta Rika Zuwa makarantar Daga nan kafin Barkat din ta gama Exams Dinta ta Dawo gida.."Hafsah tace"Allah bada sa"a..Shikenan Nagode Sosai.."
Abdullahi yace"Bana son wannan Godiyar fa..Me nayi miki..? Abunda yake Hakkina ne na Sauke fa.."Kada kai kawai Hafsah Tayi batayi mgana ba Ya mike Tsaye yana Fadin"Dare yayi bari muje mu kwanta...Gobe ina so muje Gidan Mama da gidan Baba Wada ta gaisheshi Har Gida zan kaita ta gaida Ammi da Daddy Insha Allahu..'Hafsah na Zaune tace"Allah ya kaimu Allah bada iko..Sai da Safenku.."
Mikewa Barkat din Tayi tama Hafsah Sallama ta Fita Shi kuma sai da ya Tsaya ya Taimakama ta Mike yakaita Cikin Bedroom ya Ciro mata Rigar Barcinta ya Taimakamata ta saka ya kwantar da ita,kana ya Kashe mata Wuta ya Jawo mata Kofar ya koma Dakin Barkat,Yau din dai bai iya Dagama Barkar din kafa ba Sai Da ya kara Moran Sadakinsa Dakyau Ita kuwa Barkat sai kuka take da Shagwaba shi kuma yana Biyemata yana lallashinta Da Sakamata albarka.
Washegari kuma Kamar yadda Abdullahi yace da Yammah ya Dauki Barkat din Amashin dinsa Wanda Auwal ya Dawomai da ita da Safe,Suka Fara Zuwa Gidan Mama Daganan suka Shiga Gidan Baba wada suka gaisheshi Yayi ta musu Nasiha da saka musu albarka Daganan sai gidan Ammi Chan suka ma jima Ammi da Daddy sun karbi Barkat kamar yadda Suke Karban Hafsah basu bari sun Tafi ba sai Da Ammi ta matsamai Sukayi Dinner,Kana suka yi musu Sallama suka Tafi Daddy nata saka musu albarka da kuma Nasihan zaman Hakuri Ammi Harda kayan kwalliya dasu Tararan Wuta tabama Barkat din ta karba Tana ta Godiya.
Daganan Gidansu ya kaita suka gaida Hajiya Amina,Sai Wajen 10pm na Dare suka Dawo Gidan,Har Suka Dawo kuwa Abdullahi Bama Barkat yake labarin Irin karamcin iyayen Hafsah Da Ga yadda yake bata labarin ta Fahimci yana ganin Girmansu da Darajansu uwa uba kuma Ta Lura Ba karamin Girma da kima ita kanta Hafsah Take dashi a Wajen Abdullahin ba Domin Koya Mganata ta Gifto akanta yabonta yake Tun Tana Jin bata Jin Haushi Har ta Fara Ji Ta gaji da Jin kalmar Hafsatuna kaza Hafsah na kaza ta Rasa gane wani irin Sadaukarwa Hafsah tama Abdullahi Data Riga ta kamashi kam a Hannunta.
Su Umman Sadiq da goggo Habiba Rana Daya suka Tafi Zannirace Ta koma ana gobe zasu Tafi Gidan Mama taro ya tashi kowa ya koma Gidansa Lafiya ana ta Fatan Allah ya bama su Hafsah zaman lafiya.
******
*Bayan Sati Daya..*
Acikin Satin Dayan nan Barkat da Abdullahi sun gwangwanji Amarci Sosai,Domin Daman Hausawa sunce Amarya ko Ta Buzuzuce sai Anyi Dokinta kamar Hakane ya Faru Domin Abdullahi fa yayi Rawan kafa Hafsah sai dai ta kauda kanta kawai batama Cika Fitowa Tsakar Gidan ba,Kamar yadda Abdullahi yace Mariya ta Dawo Wajen Hafsah,Nan take kwana Da safe in ta gama Ayyukan Gidan,Tayi ma su Amira wanka ta Shiryasu,suka Tafi makaranta sai ta gyara Dakunan Hafsah bayan tayi Abun karyawa in tana da Shiga makaranta ta Tafi in kuma bata Dashi ta zauna Wani Lokacin in Tana makaranta Hafsah ke Dafa Abincin Hakanan Tunda Amarya anata Amarci.
Kullum da Safe Barkat din Zata Shigo su gaisa ta Tambayeta ya yara Daganan kuma bata kara ganinta sai wani Safiyar Su Amira dai yam Dakinta ne da sun Dawo makaranta Suna Wajenta Mariya dai bata Shiga sai in Zata mika mata abinci ko kuma Abdullahi ya Kirata Barkat din Tana Girmama Hafsah Domin Anty Take kiranta ammh Kishi kam Tanayi da Hafsah domin Wani Lokacin Tana Jin Haushin yadda Abdullahi ke kula da Hafsah Sosai Tana ganin Fiye da ita Amarya ma.
Ranar da Abdullahi zai bar Dakin Barkat Har wajen 10pm na Dare yana Dakinta yana Lallashinta sai kuka take wai bazata iya kwana ita kadai ba Dalilin Haka yasa ya Umarci mariya yace Taje Dakin Barkat din ta Kwana Hafsah dai batayi mgana ba Tana ganin ikon Allah Barkat din yarinyace da za"a ce tana Jin Tsoron kwana ita kadai,batayi mgana ba Mariya dai na Tura baki Tatafi Dakin Barkat aranta kuma Tana ganin Bariki Wajen Barkat,Falo tace zata kwanta Barkat din Tace Tatashi su Shiga Ciki Tace nan din ya mata bata Damu ba Tashige Ciki ta barta nan Mariya ta Bita da Harara.
Washegari kuma Su Bahiya da Bahijjat kannen Barkat suka zo Tana ta ma Shirin Tafiya makaranta ne,Mariya Hafsah tace ta Cigaba da Girki Allah barshi In Barkat din Tagama Jarabawa ta Dawo sai ta Fara Abdullahi yaji Dadin Haka sosai ya Dinga ma Hafsah Godiya,Barkat din ma bata wani Damu ba Da Abdullahin ke Fadamata sai ma Haushin Irin Godiyar Da Abdullahin kema Hafsah din taji kamar itace Zatayi Girkin.
Ana Gobe Barkat zata koma Cikin makaranta Abdullahi ya koma Bakin aikinsa,Ita kuma Ranar tayi parking din Abunda zata Bukata Littafan karatunta Dama Suna Chan makaranta kayan sawa ne sai Sauran Abubuwa Abdullahi 10k ya bata yace ta siya Abunda Take Bukata Duk da Farko bai So Barkat din ta koma Cikin makaranta ba yaso ta Zauna Dakinta ta Rika zuwa tana Dawowa sai Barkat din ta Nuna Ta fison komawa chan din Saboda Nisa,kuma Exams Din nasu ba wani Interval a tsakani zata Wahala Shiyasa ya barta Tare da Bahiya Zasu koma Ranar Talata Din.
Ranar Talata Tun Safe Barkat din ta Shirya Bahiya ta Biyo mata Dakin Hafsah ta Shigo sukayi sallama Bayan Ta Kulle Dakinta Abdullahi baya nan ya Tafi aiki Daga Mariya sai Hafsah,mai Keken Napen da Bahiya tazo Dashi ya kwashesu Har Chan Abu Samarun Saboda suna da kaya,Nazifi bai da Labarin Barkat din zata koma Cikin makaranta sai Aranar daya Kira Abdullahi yana gayamai Jamb Din Jidda ya Fito kuma Taci, yanzu yana Ta Kokarin nema mata da addmission samun Gurbin Shiga Jami"a ne sun Tattauna kan mganar Project din su na Masters dinsu da zasu Farashi Domin suna gabda Kamalla komai Cikin mganar ne Abdullahi yace Sai Jibi kila zai Shiga Cikin makaranta Domin su gana da Supervisor dinsa Daganan kuma sai ya Biya Wajen barkat din anan ne ma Nazifi ke jin Labarin Barkat ta koma Cikin makaranta.
Cikin Mamaki Nazifi yace"ikon Allah....ammh kam bakayi ma Hafsah adalci ba...Ita ka hanata Cigaba da karatu kai kuma kaje ka Auro yar Jami"a ayadda na sanka nayi mamakin daka bari Barkat din Har ta Koma Cikin makaranta da Auranka akanta.."
Abdullahi yace"Bansan mganar Banza..Hafsah Sai da tagama na Aureta kuma nagayamata bazata Cigaba ba,Barkat kuma tana Cikin yi na Aureta ban isa na Dakatar da ita ba...Abunda yasa na Barta ta koma Cikin makaranta Saboda ta bani Hujjan Nisa da kuma Zirga zirga Shiyasa na barta kuma Sati Hudu ne zasu gama Jarabawar ta Dawo Gida Kaji Dalilina.."
Nazifi ya Tabe baki yana Fadin"Allah ya bada sa"a...Abdullahi yace Amin Daganan suka Rabu Nazifi nata mamakin Abdullahi Tsaki Yaja acikin Ransa Tuna Sakina Data Fara Dawowa Hayyacinta Domin yanzu Duk Weekend agida take yinshi ta Fahinci Jidda ta Fita Morewa kuma yanzu yaga ta Sauya Ranar girkinta zatayi Shiga mai kyau ta kuma yi Girki mai Dadi saboda Shi an daina Dafanai Indomie ta Fahimci in Tayi Sake Wlh Jidda zata sakawa Nazifi ya Korata gida yadda baya wani ganinta da Mutumci daga Ita Har iyayenta Ballema Alhaji Badamasi Ya cire Bakinsa kan Nazifi Tunda yamai Rashin Da"arnan sanda ya Kirashi Lokacin da zai kara Aure Hajiya ma Yace ta Cire bakinta Sakina na Son Mijinta ta barsu su Zauna lafiya Dole suka kama kansu Domin ko ma mgana sukayi Sakina bata Sauraransu Taga Wankin Hula zai kaita ga Dare.
*****
Kamar yadda Abdullahi sukayi da Nazifi Ranar alhamis ya Shiga Cikin makaranta suka Hadu da Supervisor dinsa,Daganan ya Biya Wajen Barkat Data ganshi Sai Shagwaba takemai da kukan wai Tayi Kewarshi chan ya lalace Wajenta Har Dare Wayarsa tana Silent ne Shiyasa akayi ta Kiransa Bai Sani ba Tun Wajen karfe 2pm na Rana Hafsah ta Fara naguda Mariya ta Kira Abdullahi bai Dagaba sai ta Kira Mama ta gayamata Mama ta Rude tace gatanan Zuwa Bayan Mama tazo ne,Taga Haihuwan Hafsah tazo Da matsala Domin ta Fara Digan Jini kadan nan da nan tace ta Sake Kiran Abdullahin nan ma bai Daga Kiran ba Mama ma ta Kirshi da Layinta bai Daga ba kawai sai ta Kira Ammi ta gayamata ita kuma tace Gatanan zuwa
Ammi da kanta Ta Tuko mota Zuwa Gidan Hafsah Tana zuwa suka Kwasheta ita da Mama zuwa Asibiti,Suka bar Mariya agida ita da yara asibitin Abu Tudun Wada suka je Tunda nan take awo Suna zuwa aka karbeta Cikin ikon Allah kuma suna Zuwa Asibitin sai kuma Digan Jinin ta tsaya sai Naguda ta taso gadan gadan suka ce azo da kayan Haihuwa Ammi ta koma Gida ta Dauko ta Dawo Mariya ita ta Kira Subai ta gayamata suna Asibitin sai gata tazo,Hafsah bata Haihuwa ba sai 5:30pm na Rana ta Sunkuto yarta Mace mai kama da Abdullahi kamar yayi Kaki bayan Hafsah ta galabaita Sosai Ammh Alhamdulillahi Tunda ta Haihu lafiya.
Sai da suka gyara Hafsah da jariiriyar kana suka Kawota Wani Daki Daga labour Room din Jaririyar suka Fito ma dasu Ammi Dashi,Hafsah kuma suka ce sun mata alluran Barci Zata Huta Zuwa Dare,kar su Shiga bata son Hayaniya,Su Mama sai Santin Jaririyar suke suna saka albarka,Auwal ma ya kira Mama ta gayamai Hafsah ta Haihu Suna Asibiti,sai gashi yazo Ammi nata Tambayan Abdullahi Mama tace an ta Kiransa bai Daga ba,Sai itama ta Kirashi bai Dauka ba Sai ta Kira Daddy tana mai Murnan Yayi Sabuwar Amarya yace Abama Mama waya Nan yake mata Barkwaci yana Fadin a kula da Ammi kar ta Fincikema Sabuwar Amaryansa kunni Saboda Kishi ana ta Dariya kafin Zuwa mangariba Labarin Haihuwan Hafsah yakai ko"ina Nazifi ma jidda ta gayamai Tun yana Wajen aiki itama Zannira jidda ta kirata ta gayamata Shima din ya Kira Abdullahin bai Daga ba.
Anan Asibitin Likita yace Hafsah zata kwana sai Zuwa da Safe zasu Sallameta Tunda lafiya kalau ta Farka Jikinta Alhamdulillah,Subai ta koma Gida tayo Girki Auwal yazo ya karba Mariya dai na Gida ita da yara Ammi Dai ta koma Gida ta bar Mama kuma Har zuwa Bayan Isha"a Ba"a samu Abdullahi awaya ba.
Shi kuma yana Chan Wajen Barkat ta Hanashi Tafiya,Abunda ma yasa yaga Kiran da akayi ta masa Lambar Mama zai bama Barkat din tace zata kirata su gaisa yana Dauko Wayar yaga Kiran Yan Gida Rututu,Hafsah,Mama,Ammi,Nazifi,Mariya,Zannira Har da Auwal Hankalinsa ya Tashi yana ta Salati Allah sa lafiya Mama ya Kira Cikin murna take gayamai Haihuwan Hafsah Yanzu kuma suna Asibitin Abu ta Tudun Wada,Abdullahi ya Rude ga Murna ga kunya sai da suka gama Waya da Mama yake Fadama Barkat Haihuwan Hafsah din Cikin Damuwa yake Fadin"Baki kyautamin Ba Barkat...Kowa ya kirani bai Jini ba..Naji kunya Har Hafsah ta gama naguda ta Haihu bani Agida..."
Hakuri ta Fara bashi bai bi ta kanta ba yace bari ya tafi tace ya gaida Hafsah tana mata Barka,ko Sauraranta baiyi ba ya Haye Mashin Dinsa ya bar Cikin makaranta yana Tunanin Wani kallo Su Mama zasu yi mai in yace yana Wajen Barkat akayi ta Kiransa bai ji ba..? Ita kanta Hafsah ya zataji Abun...? Har acikin Ransa baiji Dadin haka ba sam.
*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*
*Janafty..*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*036*
"Asibitin yawuce Direct, Mama ya Kira ta Mai kwatancen Dakin da Suke,Koda yaje har Hafsah ta tashi Daga Barci Mama ta kara mata karamin Filo a bayanta Tea ne a Hannunta tana Sha Wanda Auwal din yazo Dashi,Daga Gida Mama ta Hada mata.
Da sallama ya Shiga Room din Mata uku ne Hafsah ce ta Hudun kuma Duka Yan Haihuwa ne kowacce ga Mijinta agefe yana Rike da kyautar da Allah yayi musu Banda Hafsah Wacce Mama ce ke Rike da Jinjiran Auwal na Zaune kan Wata Farar kujera yayinda Hafsah ke kurban Tea din ahankali kamar Wacce bata son sha.
Tunda ya Shigo Hafsah ta kafeshi da ido na Dan Dakikai kafin ta kauda kai Domin Tun Bayan Data Farfado Ta Tambayeshi Mama tace,An ta kiran Wayarshi Bai Daga ba,Ranta bai baci ba ammh Taji ba Dadi Ace har Ta Haihu ammh Babu Abdullahi ba Dalilinsa,Tana ji suna gaisawa da Mama bayan ya gaida Sauran yan Dakin Auwal ma ya gaisheshi ya bashi Kujeran Dayake kai ya Zauna Lokaci Daya Mama na mika mai Jaririyar Tana Fadin"Ga Sabuwar Amarya Ammi da Inna Abu sunyi.."
Abdullahi ya karbeta Bakinsa Har kunni yana Fadin"Ah ba Shakka..Masha Allahu..Ammi da Inna Abu sunyi kishiya kuma Daga gani sai tafi Amira Fada Wajen Daddy da Baba wada fa Mama..? Ya fada yana Dariya Lokaci Daya yana kure jaririyar da ido yana kara godema Allah Mama tace"Sosai ma..Ai Dazu Ammin ta bar nan sai kishi Take nunawa.."Abdullahi yace"Allah Sarki..Naga kiranta Mama kema Naga naki kuyi Hakuri Wlh Wayar tana Silent ne,Kuma Na Shiga Cikin Makaranta na Tsaya Ganawa da Supervisor dina Shiyasa.."
Yafada yana kallon Hafsah Wacce Tayi Saurin kauda kai kamar bata ji mai yake fadi ba Saboda yana Fadin Cikin makaranta ya Shiga Ranta ya bata Wajen Barkat yaje shine ya Bige da wai Supervisor dinsa yaje gani,Mama ce ta katse Abdullahi da kallon Mamakin Dayake bin Hafsah dashi ganin yadda ta wani Hademai Rai kamar ba ita ba,Cikin Dariya Mama ke Fadin"Ai ma Haihuwar tazo da Sauki Tun kafin mangariba ta Haihu,Tuni ma labari ya gama Baza gari yanzu ba Dadewa muka gama mgana da Umman Sadiq,Subai ma bata jima da Fita ba Zannira ma ta kirani tace Mariya ta Kirata ta Fadamata Allah yasa Haihuwar tazo da Sauki Duk da Farko taso ta bada gaddama Ammh Allah ya Tsare ya kuma Sauketa lafiya.."
Abdullahi ya Jinjina kai yana Fadin"Hakane...Angodema Allah Mama.."Ya fada yana kallon Hafsah Auwal ne yace zai Tafi Mama Ta Bishi Zuwa Waje bayan yayi ma Hafsah da Abdullahi sallama Suna Fita Abdullahi ya kalli Hafsah yana Fadin"Hafsatuna Sannu da kokari..Allah yayi miki albarka Yanzu ya ya kike jin jikin naki..? Hop babu Inda ke miki Ciwo ko..?
Dan Yake tayi kafin tace"Eh..Babu..Nagode..'Cikin Jin Dadi yace"Alhamdulillah..Kinga kin karo Haifo ma Daddy da Baba Wada Sabuwar amarya ko..?Kai ta gyada mai Kafin shi kuma ya Dago yarinyar ya Sumbata Lokaci Daya kuma ya Fara mata Huduba Duk Hafsah na kallonshi sai da ya gama kana ya kalleta yana Fadin"Allah ya Raya Karima..Takwaran Mama ce.."
Kofin Hannunta ta ijiye Saman karamin Durowan Dake gefen gado Cikin kulawa tace"Allah ya Rayata.."Ya amsa da Ameen,filon bayanta ta gyara ta koma ta kwanta Dakyau barci na neman Daukanta Sama sama Taji Shigowar mama da kuma Sunanta da yarinyar taci Mama sai Murna kamar tayi kuka,Ita dai Daganan barci ya kwasheta batasan yaushe Abdullahi ya Tafi ba Shi kuwa Sai wajen Sha Biyu Saura ya bar Cikin Asibitin zuwa Gida Ya bar Mama zata kwana Zuwa Gobe.
Da Safe kafin Abdullahi ya Tafi Office Asibitin ya Fara Biyawa yama iske an basu sallama Bill din yaBiya da Sauran Magungunar da ya Siya,Mota ya samu ya Biya kudi Aka kwashesu Zuwa Gida Harda Ammi Datayi sammako ta kawo musu Abun karyawa sai da suka bar Asibitin Shima ya Hau mashin zuwa Wajen aikinsa yana Office yayi ta samun Wayar mutane,masu mai Barka Goggo Habiba ma ta Kirashi Tamai barka Haka ma Umman Sadiq,Daddy ma ya kirashi Suka Dade Suna mgana Yana ta Zolayan Abdullahi Da ya gayama Amira shifa ya Sauya Amarya Saboda Haka ta Nemi angonta Shi kuma yana Cemai Da Tsohuwar zuma ake mgani Sun gama waya dashi kenan sai ga Kiran Baba wada shimai dai Fadi yake ya Sauya Amarya Abdullahi na Dariya yana Fadin Shikenan kowa yayi ma uwata tawaye saboda yaga Sabuwar Amarya,Haka dai suka mai barka Cikin barkwanci da Fahimtar Juna Duka kannensa Zannira da Subai suma sun kirashi sun mai Barka,Nazifi ne Wayar karshe Daya amsa Shima Barkan yamai yace Jidda ta Fadamai Tun Jiya kuma ya Kirashi bai Daga ba sai yace mai yana Cikin makaranta ne Lokaci,basu wani Jima suna Waya ba suka yanke Yana gabda tashi Daga aiki Yaga Shigowar Sakon Barkat na Barka sai kuma ya Tura mata Lambar Hafsah Zata Kirata su gaisa ta kuma yi Mata barka.
Lambar ya Turama ta kawai Domin Tun Da ya barota basu yi mgana ba,Jiya Daya Dawo Gida kashe wayarsa yayi da safe kuma yana Asibiti bayan kuma yazo Office aiki Bai barsa ya kirata ba,koda ya tashi Daga aiki ya koma Gida,gida ya Cika da yan Barka Ammi Da inna Abu sai Mama,Mariya da Subai duk suna nan Dole Dakin Barkat ya Bude ya Shiga kawai,Sai bayan Isha"i suka Watse Ammah Mama ta nan sai Hafsah ta Kara Jin Sauki ita ke mata Wanka ita da Karima Wacce Su Mariya da Subai suka ce za"a dinga ma alkunya da NOOR,bayan sunji labarin Sunan Mama yarinyar taji Sun ji Dadi Sosai.
Hafsah nada kwana Uku da Haihuwa Zannira tazo tayi barka ta kayan Sunanta Atamfa da Rigan Yarinya guda Biyu,bata kwana ba ta koma tace sai Ranar Suna Nazifi ma ya kawo Jidda da Sakina Wacce ba Domin Allah tazo ba Tazo ne Taga Kishiyar Hafsah taga kuma wani irin zama Suke sai kuma Tayi Rashin Sa"a Barkat din bata nan Data Tanbayi Hafsah ina Amaryanta Subai ne Dake gefe ta bata amsa da Tana Makaranta Daganan ganin ba Fuska sai bata kara mgana ba Ita kuwa Jidda ta Shige Cikin yan"uwana ana ta Hira da Shewa Da gayyah ma Subai ke ta Kuranta Jiddan Da tayi kiba ko Dai sun samu Rabo ne..?jidda Sai sai Tayi Dariya Sanin Halin Anty Subai din ba Dama,Hafsah kuwa Allah Allah take Su sakina su Tafi kafin Subai ta ballo mata wani Ruwan.
Jidda ta kawo mata Rigunan yara masu kyaj Sai Turamen Atamfa Guda Biyu da less na Nazif ne,Sakina kuma 2k ta bata Suna Haraman Tafiya Sai ga Hajiya Sa"a da Lariya sunzo ma Hafsah barka suma da kayan arzikinsu Sakina ta Kara Raina kanta Dataga Mahaifiyar Jidda Domin taga ta kera sa"a,Lariya kuma ta santa taje kaduna sau Wajen Biyu sun Hadu,Wajen 5pm na Yammah Nazifi yazo ya kwashesu suka koma Daman bayan ya kawosu Tare suka Fita da Abdullahi Tunda Ranar lahadi ne ba aiki,nan suka bar su Hajiya sa'a sai da sukayi sallar mangariba suka Tafi.
Umman Sadiq bata zo ba tadai yi Sakon kudi,Abdullahin ta Turomawa 10k tace ya bama Hafsah din a Hannunta,Daya bata kin karba tayi sai da ya Hadata da Umman awaya kana ta yarda ta karba tana ta Godiya,Barkat ta kira Hafsah a waya tayi mata Barka ana Jibi suna sai ga Hajiya Amina da Bahijjat sunzo barka Harda Turmin atamfanta,da kudi 2k,Hafsah tayi ta musu Godiya Abdullahi baya gida ma Lokacin sai da ya Dawo Mama ke Fadamai,dama kuma Sunyi Waya da Barkat din take gayamasa Zuwansu Hajiya Aminan har acikin Ransa yaji Dadi kuma ya nuna Fuskarsa.
Ana gobe suna Anty Hadiza ta Diro Da Tawagarta Hakama Zannira,Subai ma Tazo tace sai Bayan Suna zata koma Ganin Haka sai Mama ta koma gida aranar ganin Hafsah ta warware kuma ga Su Subai suna kara kula da ita,Mama ta Koma gida ba Dadewa sai ga Goggo Habiba ta iso,Adaran Ammi ta aiko Direbanta da akwati guda na kayan Suna Dinkakku da kuma na yara Inji su ita da Daddynta Hafsah kamar tayi kwallah Saboda Farinciki Anty Hadiza ma Tazo da mata kaya sosai,Hafsah dai Taga gata Gaba da baya Harta da Goggo Habiba ba"a Barta abaya ba.
Ana gobe suna Daddare Abdullahi ya Kira Barkat yana Tambayanta yaushe Suke da Jarabawa..? Dama sunyi Wata da yammah sai tace mai sai Monday da Safe,Cikin bata Umarni yace ta Dawo Gobe da safe ta samu Suna Saboda kowa yazo sai ya Tambayeta Tunda sai Monday zasu yi wata Jarabawa ko zuwa Ranar asabar ko lahadi sai ta koma Ammh sai Barkat ta fara kawomai Wata mganar Banza wai Batayi Karatu ba In ta Dawo Gida Hayaniya bazai barta ba,Ran Abdullahi yakai kololuwar Baci ganin yadda Yake Bama Barkat Umarni ammh kuma tana Nuna mai Abunda take so Shi zatayi Tsawa ya Dakata mata Cikin Fusata yake Fadin"Ke..Ki shiga Hankalinki fa..? Ni sa"anki ne Da zan Dinga mgana kina Katseni..?
Jin Haka yasa Mamaki ya kama Barkat Sai ta karya wuya tana Fadin"Haba My Man..?Allah banyi karatu bane kuma in na Dawo Gida Hayaniya bazai barni ba kuma Infact ma Saura kwana nawa ne nagama Jarabawan gabadaya na Dawo gidan Mijina..?Ni kaina bana jin Dadin zama anan Kasani ina matukar kewarka Mijina..? Ta karishe Fada Cikin karya Murya da Shagwaba.
Yana jinta yayi mata Banza sai da Ta Kira Sunanta kana yayi gyaran Murya yana Fadin"Kinga ni duk ba wannan ba Malama ki Dawo Gida Gobe da safe..Umarni na baki ba Shawara ba.."Tana kokarin kara mgana ya katseta da Fadin"Ban Bukatar wani Korafi..Kiyi Yadda nace kawai.."Daga haka kawai ya katse Kiran nashi Ransa na masa Kuna Bangaran Barkat kuwa Sai Haushi ya kamata jin Abdullahi ya kashe mata Waya yana mata Fada saboda Tace baza tazo Ta samu Sunan Hafsah ba,Kishi ya taso mata tana Tunanin Saboda Hafsah ne yayi mata Tsawa kuma ya kashe mata Waya sai kawai ta Shareshi ta kuma Gudurta aranta bazata koma Gidan ba Sai taga yadda zai yi da ita.
Shi kuma Tunda sukayi Haka ya Shareta ammh Yana jiran yagani Shin Zata Dawo kuwa..? Ko kuma Zata yi yadda yace,in ko ta saba Umarninsa Wlh Barkat Zata sha mamakinsa,Ranar suna Tun Safe ya Fita Zuwa Wajen aiki,Ammi achan gida itama Take nata Taron,Haka ma Mama Tunda Su Goggo Habiba na nan da Su Inna Abu Su kuma su Zannira suna gidan Hafsah,Tun safe aka yanka Raguna Biyu kafin Azahar sun gama Girki da kona kowacce taci Wanka Hafsah kuwa sai Shiga Take suna Fita ita da Noor,Hafsah Tun Jiya akayi mata Kitso da Lalle tayi kyau sosai ga jegon ya karbeta tayi kiba tayi kyau Sai wanda ya ganta,Makota Suna ta Shigowa Yan"uwan Mijin Subai ma sunzo mata Suna Hajiya Sa"a da lariya sun zo ammh basu Jima ba suka wuce gidan Mama Dagachan kuma suka ce zasu Biya su yi ma Ammi Barka kana su wuce gida,Kannen Nazifi Duk sunzo Ma Hafsah kara Sosai,Sai Hotuna suke Farinciki ya Cika Zuciyar kowa yammah nayi Su Mariya suka saka M.p suka kunna Kida suna Cashewa Subai ce gaba gaba ta kuma riko Hafsah tace Dole sai tayi rawa Hakanan ta Shigo Su Zannira da Anty Hadiza suna gefe suna Dariya su Mariya kuma na Daukansu Vidion Su Amira ma dasu muhsina sunce baza"a barsu a baya ba suna ta takawa Zannira Da Taga Muhsina na Rawa tace yar'nan baki yar ba Uwarki Ba Mutuniyar kirkir ce ba,ana ta Dariya,Suna Cikin Rawan ne sai ga Bahijjat da Matar Salisu yayan Barkat sun leko Sunan Hafsah ta karbesu Hannun Bibbiyu,Bahijjat Ta gane sai ita Bahijjat din ce tamata Bayani matar yayansu,sai Bayan mangariba suka tafi.
Sai Bayan Isha"i Gidan ya Ragu ya Rage Daga Mariya sai Zannira sai Anty Hadiza da Subai Jidda bata zo ba Daman Nazifi yace bazata samu zuwa Suna ba,Auwal sai Dare ya leko Yace Daga gidan Mahaifiyarsa yake Mamarsa tazo garin Har tazo tayi ma Mama barka Shine ya Rakata gida Daganan ya Biyo ta nan, nan Subai ke Tambayansa wai Aure tayi achan Niger din..? Yace mata eh har ta Haihu Wajen uku bata dai Dade da yin Auran bane,Dayake Auwal din yana waya da Mahaifiyarsa sosai kuma tana yi mai Sako,Gidan kakaninsa ma yana zuwa Suma suna Zuwa Wajensa Lokaci Bayan lokaci.
Abdullahi bai Shigo gidan ba sai Wajen 9:30pm na Dare yana Shigowa da Mashin Dinsa Dakin Barkat ya Fara kallah ya ganshi a kulle Ransa ya kara wani baci,yaji wani Abu ya tasomai Daga kasan Ransa Har ya Daidaita zaman mashin dinsa ya Sauko Abun ya kasa sakinsa,Dakyar ya leka Dakin Hafsah suka gaisa da su Anty Hadiza,Su Subai suka gaisheshi ya amsa Yana Fama dasu Amira da su Muhsina wadanda suka Rukumkumeshi,suna mai oyoyo Haka ya kwashesu har Bedroom din Hafsah ya isketa zaune gefen gado Tana Bama Noor Nono Tana ganinshi ta sakarmai Mirmishi Tana Fadin"Abban Noor.."
Gefenta ya zauna yana Fadin"Nidai Ban yarda ba gaskiya ana ta yima Uwata Tawaye..Daddy yayi mata Baba wada ma Haka kema yanzu Abban Amira ya bace Daga bakinki Na koma Abban Noor ne.."Yafada yana wani kwabe Fuska lokaci Daya yana kallon Hafsah Wacce Dariya ta kamata Ganinsu Amira yasa ta korasu Wajen Anty Hadiza,Suna Fita ta Ciro Noor Daga Nono ta mikama Abdullahi Lokaci Daya Tana Fadin"Meke Damunka...?
Kai Tsaye te jefamai Tambayan karban Noor yayi yana Fadin"Me kika gani..? Ya suna ya Hidima..?
Kafadarsa ta Dafa tana Fadin"Lafiya lau Alhamdulillah...Allah Abban Amira wani Abu na Damuka naga Ranka abace ne..? Kallonta yayi ido Cikin ido kafin ya kada kai yana Fadin"Shiyasa nake fada bayan Mama da Umma kece mace ta uku datafi kowa sanina...Karki Damu Bawani Abu ne Gajiya ce ina yin wanka naci Abinci zan wartsake.."Mikewa Hafsah tayi tana gyara Wuyan Riganta Lokaci Daya tana Fadin"Bari na saka Subai ta Hada Maka Abinci..Dakin Barkat din zaka zauna..?
Kai ya gyada mata Lokaci Daya yana Fadin"Koma ki zauna In na Fita zan mata mgana ta Bani abinci karki damu kinfini Bukatar Hutu.."Komawa tayi ta Zauna tana Fadin"Kawota toh kaje kayi wanka kaci Abinci ka kwanta Sannu.."Mikamata Noor yayi ya mike yana Sakin Siririn Tsaki Lokaci Daya yana Fadin"Bari naje...Sai da Safe.."Hafsah tace"Allah Tashemu Lafiya..plz Abban Amira kaci Abincin ka kwanta ka Huta kaji ko..? Dukawa yayi ya Sumbaci goshinta yana Fadin"Insha Allahu Matar Abdullahi.."Itama Martanin Mirmishin ta maidamai Har ya Fice Daga Dakin,Tana jinsa yana Cema Subai ta kawomai Abinci Dakin Barkat yana Jiranta Daganan ya Fice Dakin ya Bude ya Shiga wanka ya Shiga ya gasa Jikinsa kana ya Fito ya saka Jallabiya Ya iske subai ta kawonmai Abincin,Ya zauna yaci kadan,ya ture ya koma ya kwanta akan kujera yana kokuwa da Bacin Ransa yana Tunanin ba Shakka Barkat bata sanshi ba,sanin da tayi mai ba wani mai yawa bane,domin Data sanshi bata yi kokarin Saba Umarninsa ba.
Haka ya kwana Cikin Bacin ran Barkat,Da safen ma kafin Ya tafi Office Cikin ABU din ya Shiga kuma ya Jima ammh Bai nemi Barkat din ba Daganan ya wuce Wajen aiki,ita kuma Barkat ta Damu Bayan Har Dare taga Abdullahi bai kirata ba,Taso ta kirashi sai kuma ta Fasa,Da sukayi mgana da Bahiya ta gayamata Abunda ya Faru Fada ta Hau mata ta nuna mata bata kyauta ba,mijinta ne ya isa da ita ne,Shiyasa yace ta koma Jin Bahiya ta bata Rashin gaskiya yasa sai ta Sauko,ta yanke Shawaran zata koma,ganin Yammah tayi sai ta bari sai da Safe,Bayan ta gama Abunda zatayi ta Ta Hayo Mota Ta Dawo Lokacin Data Shigo Gidan ma Kaskon karshen ake soyawa na Naman suna,Tuni sun gama komai,Gaishesu tayi suka amsa banda Subai Datake nata wani kallo Dakin Hafsah ta Fara Shiga ta Dauki Noor suka gaisa Sai ga Anty Hadiza ta Shigo nan Hafsah ke nuna mata Anty Hadizan tace yayarta ne,Barkat din ta kara gaisheta ta amsa Cikin Sakin Fuska tana kallonta tana ganin kamarsu da Hafsah din.
Ta dan Jima Dakin Hafsah din kafin ta Fito zuwa Dakinta,makulli ta saka ta Bude ta Shiga Dama Daga ita sai yar jakarta Data sako Littafan karatunsa kaya kuma bata zo da ko Daya ba sai Hijabi Tunda tana da wasu anan gida da yawa ma,Tunda ta Shiga Daki ba wanda ya karajin motsinta sai da aka gama girki mariya ta leka ta kai mata ta amsa sai kuma zuwa chan Bayan an Raba Naman Mariya ta mika mata ta karba tayi godiya an Dibar ma Abdullahi sai Hafsah da yara,sai Mama da ita da su Inna Abu,da goggo Habiba sai Ammi da Daddy sauran kuma suka Raba ma kansu sai na Mokota Zuwa La'asar sun gama komai kowacce tayi wanka sai Shirin Tafiya Zannira gidan Mama ta wuce da nasu Maman Bayan sunyi sallama da Hafsah kan gobe zata wuce,Anty Hadiza ma Gidan Ammi tayi itama Goben zata koma,Subai kuma Ta nan sai Bayan mangariba Mijinta zai zo Daukanta saboda yara,Auwal ma yazo Hafsah ta bashi nashi,ya karba yana ta Godiya Subai yabi da mijinta yazo Daukanta zasu ijiyesa agida.
Gida ya Rage Daga Mariya sai Hafsah sai su Amira Barkat na Cikin Dakinta ko motsinta Ba"a ba yau Abdullahi da Wuri ya Shigo Gidan Ana yin Sallar Isha"i Barkat na Jin Shigowarsa kuma ya yada Zango Dakin Hafsah Duk da yaga Dakin Barkat din da Hasken Wuta,Hafsah ta nuna mai komai yadda aka raba yace yayi kyau nashin ta ijiyemai anan ne yace mata Eh nan take Fadamai Barkat ta Dawo kuma an bata nata bai ce komai ba Ganin haka ita Hafsah bata kawo komai ba,Ta shiga nuna mai Kayan Sunan data samu tare da bayanin Sunan wadanda suka bata yana ta gani yana godiya da saka albarka nan Dakinta yaci Abinci,dayace zai yi wanka Hafsah ta kalleshi tace"Abban Amira kaje Dakin Barkat mana Kayi achan..? Ai yanzu ka zama nata Har sai nayi Arba"in ni da Noor mun kara Samun Lafiya.."
Hararanta yayi Lokaci Daya yana Fadin"injiwa..? Wannan Tsarin ki ne ba nawa ba Malama.."Yafada yana Tura Kofar Toillet,ya shige yayi wankansa ya Fito ya saka Jallabiya,Yazo ya Dauki Noor ya Fita zuwa Falo yana Biye ma su Amira suna wasa da Noor tana Hannunshi.
Barkat kuwa Shuru Shuru bata ga Shogowar Abdullahi ba gashi taci kwalliya tana Tashin kamshin Tun Tana saka Ran Shigowarsa har ta Fara Sarewa wayarta ta Dauka ta Kirashi bai Daga ba ta kara kira bai Daga ba Kira na uku ne ya Kashe mata kiran Gabadaya,Baki Barkat ta Bude Hawaye na Cika mata ido Kishi ya Turniketa Domin Acikin Ranta tana Tunanin Duk Fushin da Man yake akanta Saboda Hafsah ne kan kujera ta Fada tana Sakin kukan Daya taso mata Daga kasan Ranta.
Hafsah kuwa ganin ana ta Kiran Abdullahi bai Daga ba yasa ta Zargi wani Abu kai Tsaye ta kalleshi Tana Fadin"Kawo Noor Abban Amira kaje Ka kwanta ka Huta..Ke Amira maza kije kiyi Fitsari keda Amir kuje ku kwanta Wajen Anty Mariya.."Jin haka yasa suka Shige Cikin Bedroom Din har suna Rige Rige.
Abdullahi ya gane Nufunta sai dai bai Tanka mata ba ya mika mata Noor din ya mike Lokaci Daya ya Dauki Wayarsa yayi mata Sallama ta rakashi Har Kofar Daki,yana Fita ta maida kofar ta kulle ta koma Daki Afili ta Furta.."Hmmm yau Barkat ta taba yan Maza..Allah ya Kyauta kiga Masifar Abdullahi yau."
Tana Kwance kan kujera bayan ta gama Kukanta ta Share Hawayemta,taji Shigowarsa Da Sauri ta tashi Tana kallonsa Shi kuwa Ransa ya Hade Tamau kawai ya Rabata zai wuce da Sauri Tasha gabansa Lokaci Daya ta Fada Jikinsa tana sakin mai kukan Shagwaba Lokaci Daya Tana Fadin"My Man ka sakani kuka..?
Tafada tana kara lafe mai Bisa Jikinsa,Haushi ya kara kamashi Da Sauri ya saka Hannu ya bambareta Daga Jikinsa Kai Tsaye Yana kallonta itama Shi take Kallo ta wani karya wuya,gefenta ya Raba zai Shige Cikin Bedroom din tayi Saurin Riko Hannunsa Tana Fadin"Plz mana my Man Am Sorry...!
Ta Fada tana wani karya Murya,Da Sauri ya waigo Cikin Fusata yana Fadin"Sake ni Don Allah...! Yafada cikin kakkausan Murya Da sauri ta Sakeshi Tana kallonsa karamin Tsaki yaja yana Fadin"Ban da Tsabar kin Raina ma kanki wayau Ashe kinsan Abunda kika aikata Tunda kike bani Hakuri..? Ya fada yana Tsare da ido Da Sauri tace"ba haka bane My M..."
"Dakata Don Allah..."Yafada Lokaci Daya yana Dagamata Hannu Da sauri Barkat ta Kama bakinta ganin yadda yake jifanta da wani kallo lokaci Daya yana Fadin"Har ni na baki Umarni nace miki ki Dawo Gida Jiya da Safe ammh Tsabar kin Rainani baki Daukeni a matsayin Mijinki Tunda Har zance ga Abunda Zaki yi ammh Kika nuna min iyakata Tunda sai yau zaki kwaso kafafunki ki Taho Toh kin makara da kin sani baki Dawo ba Domin da Dawowarki da Rashinsa Ni awajena Duk Dayane Barkat....Sai dai ina So ki san Wani Abu Guda Daya Wlh Tallahi kinji ma na Rantse miki Ba wata ya macen da Zan Aura tana karkashina kuma na Bata Umarni taki bi,ko kuma ina mgana tana min gaddama ko kuma In bada Umarni taki bi tace Ita sai Ra"ayinta za"a bi Toh bazamu Shirya ba..Ni agidana Namiji ne kuma Jajirtattace ne,kuma mai Fada aji kuma mai iko ne kuma mai Fada ne Wajen matarsa ke bama Ke da kike matsayin matata ba Bama Hafsah Da Take matsayin matata ba Wlh ko Kannena Dake Gidan Auransu ina Saka Musu Doka kuma su Bi,kuma na basu Umarni su bi Ballatana ke da kike karkashin Ikona,Toh Baki isa ba Karatun ma da kike yi Ra"ayina ne in yau nace Kin gamashi Wlh Ko Duniya zasu Taru akaina baki isa ki Komata ba Wlh,Baki sanni ba ko..? Hmmm ki Tambayi Hafsah Zata Fadamiki kowaye ne Indai kina son zaman Lafiya ki Bini a sannu ko kuma Wlh Ranki yayi ta Baci indai Bazaki san Abunda kike yi ba.."
Ya karishe Fada yana nuna ta da yatsa Lokaci Daya yana Sakin Numfashi,Afusace ya juya ya Shige Cikin Bedroom din ya Hau gado ya kwanta yana Jin Haushinsa akan Barkat ya Ragu ita kuwa da ido ta rakashi Har ya Shige,Jikinta a sanyaye ta koma ta Zauna kowani Dakika maganganunsa suna mata amsa kuwwa Cikin kunni Afili ta Furta"Topha..!
*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*
*Shakira...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*037*
"Ta Dade zaune maganganun Abdullahi na mata amsa kuwwa acikin kunnuwanta,Mamaki ya kamata wani irin Bakin Kishin Hafsah ya mamaye mata Rai Tana Tunanin ba saboda komai Abdullahi ya gaggayamata wadanan mganganun ba sai Saboda bata zo Sunan Hafsah ba In ba Haka ba Me tayi mai da zafi da zai gayamata Haka.
Kishin Hafsah ya Tsaya mata arai Ta kasa Sukuni sai tayi yunkurin tashi ta bishi Ciki sai kuma Ta Fasa,sai da ta Sassaita kanta kana ta mike ta Bishi Cikin Bedroom din Zuciyarta Cike da Kishin Hafsah me Tsanani na ganin yadda Ta kama Zuciyar Abdullahi komai zai yi ko mgana zai yi sai ya ambaceta.
Koda ta Shiga ta iskeshi kwance yayi kwanciyar D'aida'i Bisa Gadon Idanuwansa na kallon Rufin Dakin,Yana ganin Shigowarta ya Juya baya Lokaci Daya yana gyara kwanciyarsa,Karisawa tayi Cikin Tafiyar kasaita zuwa gabansa ta Rankwafa Tana Fadin"My Man..! Tafada Tana kallonsa Ganin ya wani Lumshe ido Kamar mai Barci.
Kara Karya Murya Tayi Tana Fadin"Am Srry kayi Hakuri Bazan kara ba..Kuma a think in ban zo Sunan ba wannan karon akwai Next Time ko..? Tafada tana kallonsa Ganin yaki mgana yasa ta Dora Hannunta saman Kirjinsa Tana Shafawa,Karaf kuwa ya Bude Idanuwansa ya Sauke akanta Lokaci Daya ya Saka Dayan Hannunsa ya Dauke nata Hannun kafin ya mike Zaune batare Daya mata mgana ba Yaja Filonsa ya Tashi zai Fice Daga Bedroom din,Da Sauri Ta Mike Zata Biyoshi Tana Fadin"My Man...!
Bai bari ta karisa mgana ba ya juyo a Fusace Yana kallonta lokaci Daya yana Nunata da yatsa yana Fadin"Kinga..? Kinsan Allah..? In kina son kanki da arziki kada ki Biyoni in kuma baki ji ba Kika Sake kika Biyoni kina Damuna Wlh Tallahi zan Fita na bar Miki Dakin nan in kuma na Fita bazan Dawo ba sai dai gobe..!Yafada Cikin Kakkausan Murya ya Fadi Haka Lokaci Daya kuma yana jan wani Dogon Tsaki ya Fice Daga Bedroom din yana Fadin"Banda Iskancin Banza da Raini Miye na Damuna na kwanta ina jin Barci..? Kin gama yin Laifin da gangan kuma ki Dawo kina son Rainin min Wayau..wlh baki isa ba ba wacce zan auro Tana karkashina tace bazata bi Umarni ba.."
Galala Barkat tayi Tana Bin Abdullahi da kallo har ya Bar mata Dakin Ajiyar zuciya ta Sauke kafin ta koma Gefen gado ta Zauna tana Fadin"Jar Uba..."Kawai ta iya Fada tana mamakin yadda Abdullahi ya Rufe ido yana Nuna mata nashi Kwanjin akan kowacce mace,ammh sai ita tasakashi Mizani kan Duk Saboda Hafsah ne yake mata Haka,Tashi Tayi ta Shige Tailot tayi wanka ta Fito Tayi Shirin Barci sai Lokacin ta Leka Falo ta ga Abdullahi kwance kan Doguwar kujera yana Barci ta Dade tana Kallonsa kafin ta kada kai ta koma Ciki ta Hau gadon ta kwanta Bayan ta Rage Wutar Dakin Barci ya saceta ne da Tunanin Irin Abunda ya wakana Tsakaninta da Abdullahi.
Al"amarin Abdullahi bai kara Bata Tsoro ba sai da Asuba Tunda ya Tashi yayi wanka yayi alwala ya Fice Zuwa Masallaci bata Kara ganinshi ba,yana Dawowa Dakin Hafsah ya Shige yayi kwanciyarsa kawai Itama Hafsah taso tayi mgana ammh ganin yadda yake ta wani Fushi yasa ta kama Bakinta,Saboda bata so Ta Shiga Abunda ba Ruwanta,Balle ta san Halin yan kayanta yanzu sai ya Sauke mata Gabadaya Fushin Barkat din akanta,Dalilin Haka ne yasa Ta Tattara Ita da Noor ta koma Dakin yaran,Ta kwanta Su Amira kuma Suna Kitchen tare da Mariya tana Dafa Abun karyawa.
Tun Barkat na Jiran Dawowar Abdullahi Har ta gaji da Jiransa Tatashi tayi wanka,ta Shirya Cikin doguwar riga na Wata Shadda,Wajen karfe 8am na safe ta Fito Daga Dakinta zata gaida Hafsah a Tsakar gidan suka Hadu da mariya suka gaisa su Amira ma suka gaisheta Ta amsa Tana Tambayansu bazasu Hadda bane sukace an basu Hutu Tare dasu ta Shiga Dakin Hafsah din.
Hafsah na Cikin Bederoom dinta Tana Shirya Noor bayan tayi mata wanka Abdullahi na kwance yana ta Barci yau asabar kila ba inda Zashi ne sai anjuma,Daga Cikin Dakin Hafsah ta amsa Sallaman agurguje ta Shirya Noor din ta Fito,suka gaisa da Hafsah Din Barkat ta karbi Noor a Hannun Hafsah tana mata Wasa,Su Amira nata Hayaniya sai Hafsah tace su Natsu Kada su Tashi Abbansu na kwance yana Barci Sai alokacin Barkat ta Fahimci Inda Abdullahi ya yada Zango bayan ya Dawo Daga Sallar Asuba,Nan da nan Kishi ya Turniketa sai dai bata nuna ba tadai yi yake kawai,Jin haka yasa su Amira suka Fice zuwa Wajen Anty Mariya itama Barkat din bata Dade ba ta mikama Hafsah Noor ta Fice Zuwa Dakinta zuciyarta Cike da Kishin Hafsah Tana ganin itace Silan Rashin Jituwa Dake Tsakaninta da Abdullahi Hafsah ne Sila.
Da Mariya ta gama Breakfast ta Mikama Hafsah nata ta sakama yaran sai na Abdullahi,Sai Hafsah tace ta Dauki na Barkat ta mika mata,Sai ta Dauka Tana Shiga sai ta isketa kwance tana ta kuka Mariya Abun ya bata mamaki Bayan ta ijiye Farantin kayan karyawan ta karisa gareta Tana Fadin"Anty Barkat lafiya kuwa..?
Sai Lokacin Barkat taji Shigowar Mariyan,Da sauri ta mike tana Share Hawayenta ammh Ta makara Mariyan ta Riga ta gani,Kokarin kakalo Mirmishi Tayi Tana Fadin"La bakomai wani Abu ne ya Fadamin Cikin ido.."Kallonta Mariya tayi tana Zama gefenta aranta tana Fadin sai naji Kwal uwar Daka Kafadarta ta Dafa Tana Fadin"Haba Anty Barkat...Nifa kamar kanwa nake gareki,domin kin gayamin Damuwarki wani Abu ne..? Kar ki manta yayana fa kike Aure...?
Kallonta Barkat tayi Tana wani Tunani Acikin Ranta Da kamar Bazatayi mgana ba sai kuma ta Bude baki tana gayama Mariyan Abunda ya Faru tana gayamata tana Kuka ta karishe Tana Fadin"Daga karshe Har cewa yayi bazan koma na karishe Jarabawana ba ammh wannan bai Dameni ba nasan Zence ne kawai yake bazai iya Hanani ba.."
Kallonta Mariya Tayi kafin tayi wani Dariya na Zaki gane Kuranki Lokaci Daya ta Dakata tana Fadin"Mganar ya Abdullahin ne zencen banza..? Lalle bama kisan wanene Mijinki ba naga alama.."Barkat tace"Kamar ya..?bangane ba..?
Mariya ta gyara Zama Tana Fadin"Eh mana mamaki naji da kikace wai mganar ya Abdullahi Zence ne kawai..Shine nace baki san waye mijinki ba..Wlh In ya Fadi mgana baya Sauyata Kaifi Daya ne in yace Eh...Eh ne,in yace A"a A'a din ne Wlh Ina mai Baki Shawara ki Bashi Hakuri in Allah yasa kina da Rabo ya Sauka Daga Fushinshi ya kyaleki ki koma Kada ki bata Shekarunki a Banza,In kuma kika Zauna kina Tunanin Fade kawai yake,Toh ina mai Tabbar Miki Bazaki Taba komawa makaranta ba Ballatana ki samu Damar karisa Jarabawarki.."
Ido Barkat ta Zaro Tana Fadin"Eh..Dama Haka yake.."Mariya tace"Ya Abdullahi yafi gaban Hakama..Shi mai Iko akan Kannensa,kinga ko su Anty Zannira Umarni yake basu Subi..Ballatana mu da muke gida,Baya son gaddama yana son Abashi Girmansa yana son a Girmama mganarsa baya son Raini sam..Kinga Anty Hafsah ita zaki Tambaya zata gayamiki Wanene Ya Abdullahi Tsautsauran Ra"ayi Gareshi ba kowa zai iya zama Dashi ba sai mai Hakuri.."
Idon Barkat ya Raina Fata ta Cigaba da gyada kai kafin tace"Haka yake ma ita kanta Anty Hafsah..? Mariya tace"Kwarai ma kuwa haka ma yake ma kowa Duk wanda yake kokarin Tsallake iyakar daya ijiyeshi.."Barkat tayi Tagumi kawai Ta kasa mgana Mariya na Shirin kara mgana Taji Kiran Abdullahi Daga Dakin Hafsah ta Mike da Sauri Tana Fadin"Na bani gashi chan yana Kirana.."Daga Haka ta Fice da Sauri Barkat ta Bita da kallo Tana Ayyana Zencen mariyan acikin Ranta ashe tayi kuskure bata sani ba..? Tayi kuskuran yima Man dinta gaddama yanzu gobe in ya Hanata komawa makaranta ya zatayi..?
Ashe Kiran Da Abdullahi yake ma Mariya Noor zata Dauka tana kuka Hafsah kuma ta samu Barci Shi kuma ya Tashi zai Shiga Wanka Bayan ya Mika mata ita ya Shiga yayi wanka ya Shirya Cikin Saukakkan yadi ya Fito Falo ya karya Har Lokacin Hafsah bata tashi ba Har Noor tayi Barci Fita yayi zuwa Dakin Barkat din ya sameta kwance tana karatun Handout dinta tana Jin Shigowarsa ta Mike tana gaisheshi ya amsa Fuskarsa ba Walwala mikewa tayi Tana Fadin bari ta kawomai Ruwa yasha Dakatar da ita yayi yana Fadin"No..Ki barshi kawai nasha Ruwa..Kinsan Abunda ya Shigo Dani..?
Ta girgiza min kai Kafin ta samu Zarafin mgana ya Cigaba da Fadin"Kinga dai Hafsah ta Haihu kuma Tana Bukatar Hutu Mariya ce kadai ga yara aiki yayi mata yawa ki Taimaka mata da wani aikin..."Cikin Girmamawa tace"Ok..Insha Allahu my man.."
Kai ya gyada yajuya zai Fice tayi Saurin Riko Hannunsa Ya waigo sai ta marairaice tana Fadin"Don Allah My Man...Kayi Hakuri na Tuba bazan kara ba.."Tafada Lokaci Daya Hawaye na Cika mata ido Kallonta yayi sai ta bashi Tsausayi yasaka Hannu ya Dagota ya Dafa kafadunta yana Fadin"Is ok..Komai ya wuce karki Damu.."Yafada yana Shafa kumatunta,Fadawa Jikinsa Tayi Tana mai Godiya Rumgumeta Shima yayi,Sun Dade ahaka kafin ya saketa yana Fadin"Bari na fita...Zan leka gidan Mama muyi sallama da goggo Habiba da Zannira.."Da adawo lafiya ta Rakashi ya Fice Har sai da taji Tashin Mashin Dinsa kana ta koma Daki.
Saboda Gudun karta kara wani Laifi,yasa ta Fita sukayi Girkin Rana Tare da Mariya ta kuma Yi ma su Amiran wanka ta Share Tsakar gida,Sukayi wanke wanke ita da mariya Saboda yunusa almajiran Hafsah Babansa ya rasu ya tafi Garinsu,Abdullahi kuma Gidan Mama yaje suka yi sallama da Goggo Habiba Shi yakai ta Tasha ya sakata a Mota,Zannira kuma Mijinta yazo ya Dauketa suka Tafi Daga nan gidan Mama makaranta ya Shiga Sai gabda mangariba ya Dawo Shago ya Biya yaga Abubuwan Da suka kare bai Jima ba chan ya bar Auwal ya Nufi gida ya Iske Barkat da Mariya sun yi Tuwon Shinkafa da Miyar Agushi,Sosai yaci ya koshi Bai Jima a Dakin Hafsah yamata sallama ya koma Dakin Barkat,Chan ta kara Bashi Hakuri shi kuma yace ya Hakura Ranar dai an kwana ana Soyewa kamar baaza"a rabu ba.
Washegari Abdullahi bai Fita aiki ba,Tun Safe Barkat kemai mganar komawa makaranta ammh yaki ce mata komai sai da 1pm na Rana tayi bayan sun Gama Girki ita da mariya tayi wanka ta Shirya tace mai Zata Tafi yace ba inda zata Sai ido ya Raina Fata ta Fara kuka yayi mata Banza karshenta ma Fita yayi yabar,Gidan ya barta Tana kuka Ganin Wankin Hula zai kaita ga Dare yasa ta Shiga Dakin Hafsah Tana kuka tana Komai ta gayamata,Hafsah batayi mamaki ba Sanin Halin Abdullahi tace bari ta Jaraba ta gani ta Kirashi awaya tace yana ina ne..? Yace mata yayi Nisa,Sai ta Fara Kokarin Shigarmai da mganar Barkat tana Rokonshi kan ya bar Barkat din ta koma makaranta ta Idasa Jarabawarta.
Abdullahi yayi gyaran Murya yana Fadin"Au zuwa Tayi takai Miki karana..? Tayi abanza kinsan Allah nayi Rantsuwa bazata koma Cikin makaranta ba..Ban ce bazata Karisa Jarabawarta ba ammh mganar ta koma Cikin makaranta ne Bazata koma ba in ta Yarda sai dai ta zauna Dakin Mijinta,Ta Rika zuwa tana Dawowa Fakat na gama mganata.."Daga Haka ya yanke Kiran ko Tsayawa Sauraran Hafsah ma bai yi ba..
Barkat bata Bukatar wani karin Bayani Tunda a Speaker aka saka Taji Komai,toh ya zatayi Dole tabi yarda yace ta koma Daki Tana Kunci Bahiya ta Kirata ta gayamata bazata samu Damar Dawowa ba ga yadda Sukayi da Abdullahi Bahiya nata Bata Hakuri,sun Dade suna mgana kana suka Katse Hajiya Amina ta Kira itama tana kaimata Korafin ita Fada ta Rufe ta dashi ta kuma ce Abdullahi yayi mata Daidai Jin Haka yasa Barkat din ta Kama bakinta ganin ba wata mafita sai na Bin Umarnin Abdullahi miji ga Hafsatu angon Barkat.
Koda ya Dawo Kara Jadaddamata yayi ya kuma ce in Taki Bin Umarninsa Wlh sai dai ta Hakura da Karisa Jarabawar,Ina Barkat zata Biyema Abdullahi tayi asaran Shekarunta na Baya,Duk Girman kanta sai da isarta Abdullahi ya Damata in ma wani Iskanci take ji ya Damata ya Shanye Da Daddare ma tana ta wani Fushi da Tura baki bai Biyemata ba sai ma Zoyalanta da yafara yana Mata Cakulkuli Dole ta saki Ranta kuma ya Karbi Hakkinsa ya Mori Abunsa Son Ransa.
Washegari Tun 7am ta Fita Taje p.Z Ta Hau Motan Samaru,Domin karfe 11am suke da Paper bata ma Tsaya Jiran Abdullahin Dayace in zai Fita aiki zai kaita ba Su Amira kuma mai mashin dinsu ya kaisu Tace kawai ya bari taje ta Hau Mashin din Haya yace Wlh bata isa ba da Auransa akanta bazata Hau Bayan wani kato ba sai dai taje ta Hau Mota komai adaidaita,Dole ta Hakura ta Nemi mai adaidaitan bata samu ba yasa ta karisa P.Z ta hau Motan Samaru Har takai makaranta tana Tsaki Ita kadai,Araina nace kyayi ki gama Indai Abdullahi ne baisan kinayi ba.
*****
Kwanci Tashi ba Wuya awajen Allah gashi Har Barkat ta kamallah Jarabawarta sun samu Hutu,tana Gida Umarnin Abdullahi kuma Shi aka Cigaba da bi na zuwa arika Dawowa Har ta kamallah Jarabawarta.
Sai Lokacin suka Raba Girkinsu ita da Hafsah Tunda Hafsah nada kwana Ashirin da Haihuwa Mariya ta koma Gida,Su Amira kuma sun samu Hutun makaranta Suna Gidan Ammi Daga Hafsah sai Noor Shiyasa Abun yazo mata da Sauki.
Zama Tsakanin Barkat da Hafsah zama ne dai na zaman Lafiya Tunda basu Fada ko wani Hayaniya Barkat na Girmama Hafsah daidai Gwargwardo Tunda Abdullahi bai sakar mata ba ya Nuna mata Darajan Hafsah Sosai,ammh Ta Ciki na Ciki Domin Barkat bata iya Boye Kishinta kan Hafsah tana ganin kamar tamallake Abdullahi ne Wani Lokacin ko Abu ne ya Faru ita ke shan Wahalansa Saboda Gaddamanta da kuma Taurin kai ita kuwa Hafsah ta san Halin yan kayanta tana Bi Dashi yadda ta Fahimceshi,Shiyasa Kafin kaji kansu sai andade kuma ko Fadansa yake Shuru take mai sai ya gama dai ta Rika bashi Hakuri ba kamar Barkat ba Da komai sai tace tamai Bayani Shi kuma Abdullahi bayason Doguwar mgana Shiyasa suke yawan samun mtsala.
Ya barta Taje gida ta Wuni,Ta kuma Je gidan Mama da Inna Abu,sai gidan Subai"atu Har Gidan Goggo Habiba ya kaita Kaduna ne da Gusai yace in Hafsah tayi Arba"in zasu Tafi Gabadaya Tunda Daman Hafsah ta Neme Izinin Zuwa kuma ya lamunce mata.
*****
Bayan Hafsah Tayi Arba"in Abdullahi bai Tsara musu Tafiyar ba sai da Hafsah tayi Yawon Arba"in Dinta nan Zaria Shima Daga Gidan Mama sai Gidan Inna Abu,sai Kuma Gidan Subai"tu wanda duka arana Daya Taje gidan Mama da Inna Abu,Gidan Subai ne taje ta wuni,sai gidan Ammi Tayi Arba"in da kwana Hudu Ranar Asabar Abdullahi yayi musu Tashan Mota suka je kaduna Har Dashi Gidan Zannira suka Fara Sauka Tayi ta ina ta saka Dasu,Tunda tayi aure Sau Daya Abdullahi ya Taba Zuwa gidanta sai Yau na Biyu Hatta Mijinta Shima sai Rawan Jiki yake,nan sukayi sallar azahar sukaci Abinci kana suka yi musu sallama suka Tafi Gidan Jidda Harda Zanniran sun kuma yi Sa"a sun iske har da Sakina Dama Sun san da Zuwansu,Jidda tayi musu Girke girke Kala kala Nazifi ya Tayata Lokacin da suka zo Haka take Murna Tana tsalle kan Jikinsu Zannira sai da Abdullahin ya Dakamata Tsawa Bakin Hafsah yaki Rufuwa ganin Jidda Har Ciki ya Fito Dama kuma Dataje Gidan Subai ta kyankyasa mata Cikin na Jidda,cikin ya karbeta tayi kiba ta Sauya kamar ba Ita ba Sakina kuwa sai Dan Wuya da Kwarmim Idanuwa Dakyar ta Fito Falo suka gaisa ta koma Ciki kamar mujiya nan Zannira da Hafsah da Barkat suka Shiga Ciki Suka bar Abdullahi da Nazifi Suna Hira bayan sun gabatar musu da Abinci sunce sai Zuwa anjuma.
Da suka Shiga Ciki ne Jiddan ke Fada musu Ta samu Addmission a Kasu zata karanta Polical Science,Suka Tayata Murna Barkat dai Tana gefe ba wanda yabi ta kanta sai ma Zannira ce ke Sakota Cikin Zencen suna Gidan Har Bayan La"asar sai da suka Ci Abinci sukayi sallar la"asar kana Suka Shirin Tafiya,Zannira da Nazifi sunyi sunyi su kwana Abdullahi yace ba kwana suka zo yi ba Wlh bazasu kwana Ba Tunda sukaji ya Rantse suka ma kama Bakinsu sanin Hali,Nan suka bar Zanniran Gidan Jidda su kuma suka Dauki Hanya Daman Tashar Motar da Abdullahi yayi musu Shi zai kaisu kuma shi ya maida su Sai Dare uka iso Zaria.
Basu samu Tafiya Gusai ba sai da Sati ya Zagayo Ranar Jumma"a suka Tafi Abdullahi ya Dauki Excuse awajen aiki,Su Amira ma Ranar basu je makaranta ba,Tafiyar safe sukayi Motar Haya suka Shiga wannan karon ba Shata yayi musu ba Saboda Rashin kudi,Wajen 12pm na Rana suna Dakin Ummam Sadiq tana ta Hidima dasu su Zahra da Sadiq nata Murna sun ga Anty Hafsah da Ya Abdullahi.
Azuwansu Gusai Barkat ta kara Tabbatar ma kanta Hafsah ta mata Zarrah ko acikin Dangin Abdullahi Motsi kadan Umman Sadiq Taga Hafsah tayi sai tace lafiya Haka Abokiyar zamanta sai nan nan suke da ita da Noor,Mijinsu Umman Sadiq ma Daya Dawo Shima dai Hafsah Barkat sai dai su gaisa da ita kawai Hafsah ce yar gida,ko Wajen kwana ma ita Hafsah Dakin Umman Sadiq ta kwana Barkat kuma Dakin Abokiyar zaman Umma,Abdullahi kuma Dakin Kofar gida nasu Sadiq ya kwana Da gari ya waye kuwa bayan sun karya sunyi wanka Suka je gidan kakanin Abdullahi nan Taga yadda Suke kamar su Goya Hafsah Har Wata Abokiyar Wasan Abdullahi tana Fadin Rigima ce yasashi kara Aure ammh ita tana Ganin Duk Duniya ba macen da zai samu kamar Hafsah Abun ya batama Barkat rai Har sai da ta Nuna ta Hade Rai Hafsah nema ke kare mata,Hafsah nan gidan ta kwana Barkat kuma takaichi yasa Tabi Abdullahi ta koma Gida Wajen Umman Gwara nan din da Sauki akan chan Gidansu Umman Sadiq din da Kiri kiri wasu suka Nuna basu Ji Dadin Auran da Abdullahi ya kara ba,Ranar lahadi da zasu Tafi sun ga kara kuwa da Tsaraba,Mota guda Mijin Umman Sadiq yayi musu Shata ya Biya aka Loda musu kayansu da Tsarabansu Har gida suka Suka bar su Umman Sadiq da kewa.
Bayan sun koma Hafsah ta Raba Tsaraba ta bama Barkat tace ta aika gida,nata itama ta Kai ma su Ammi Sauran kuma ta kaima Mama da Inna Abu,sauran kuma suka ije agida,suna amfani Dashi koda suka Dawon Hafsah sukayi ta Kira Suna ma Bangaji da Tambayan Noor Datasha Iskar Mota mura ya kamata sai da suka je Asibiti ita da Abdullahi Likita ya ganta ya Rubuta mata mgani.
Bayan Dawowarsu da kwana Uku Barkat ta Shirya zata Gidansu Abdullahi ya Hanata Da ta Fara Korafi sai ya Dakatar da ita yana Fadin"Ke meyasa kin Cika kawo matsala ne .? Ya kamata ki Rika Fahimtar wani Abu..Bana son yawan Fitan Rashin Dalili me zaki je gida kuma kiyi..?me kika Rasa Fisabillahi..? Inace ba kafin mu Tafi kinje ba.. kawai sai kuma Saboda ban da Hankali sai kuma na barki ki koma ko.?Ba Haka nake ba ni ba Sakarai bane da zan bar matata ta Dinga Fita Duk inda taga Dama Ina da Tsari Kuma Tsarina nake Bi malama ki koma ki zauna ba inda Zaki.."
Baki Tahau Turawa tana Fadin"Allah nafi sati Uku Rabona da zuwa gida..Ina son ganin Hajiya da Sauran yan"uwana.."
Mamaki ya kama Abdullahi ya Rike Baki yana Fadin"lalle me kin samu Wuri..? Ke sati uku kikace Ita Hafsah tace me..? Wlh tana Fin Wata Biyu bata je gida wajensu Ammi ba kuma bata min Korafi kin fi ta son iyayenta ne..? Ina mai Tabbarmiki ko gatan banza ta Fiki ammh Bata kin Bin Umarnina inda na ijiyeta nan take tsayawa bata iya Tsallakeshi Gaskiyan Nazifi ne Bazan Taba samun Macen da Zatamin Biyayyan da Hafsatuna takemin ba abaya ban yarba ba Ammh Zuwa yanzu na gama yarda da Hakan.."
Ya Fada Lokaci Daya yana Hade Rai,Kallon Takaichi da Kishin Hafsah ta bishi Dashi kafin kawai Ta Bude baki Tana Fadin"Nidai na Shiga uku Ni barkat..? Komai Hafsah...Kai ka Kira Hafsah kannenka su Kira Hafsah Mama Hafsah Inna Abu Hafsah..! Umman Gusai Hafsah,Kowa Hafsah kowa Hafsah komai zakayi Hafsah kwatancenka Hafsah ne Shin Ita kadai ce matarka..? Ko ni bani da wani amfani a wajenka da wajen Dangina ne har Kuma Da kake min Gorin gata... ? Ni wlh na gaji Na gaji..Wannan Hafsah Tana Tsayamin a kahon Zuciyata Sunanta na Fadarmin da gaba Tana Shigemin Hanci da yawa nagaji Nagaji..!
Tafada Lokaci Daya tana Sakin Kuka Galala kawai yayi da baki yana kallonta Bai samu Zarafin mgana ba,ta kwasa Zuwa Cikin Bedroom dinta tana kuka Da kallo ya bita Har ta Shige Ciki wani Munafikin Mirmishi ya saki Lokaci Daya yana Daga Murya yana Fadin"Hafsah..! Hafsatu Matar Abdullahi bawan Allah..Wai ita kike cewa ta Tsayamiki arai..? Kin gaji da jin kowa na Kiran Hafsah ko..? Lalle kuwa Halin mutum Jarinsa,in Ko Hakane ashe zaki Mutu da bakinciki Domin Sunan Hafsah a Rayuwar Abdullahi kamar wani Zanen kaddara neda"a ka Riga aka Rubutu kinga kuwa kina da katoton aiki kenan.."Daga Haka ya saka kai ya Fice Daga Dakin nata Yana ta mamakin yadda ta iya gayamai Mgana kan Hafsah.
*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*
*Janafty Shakira..*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
*038*
"Har Abdullahi yakai Office yana Tunanin maganganun Barkat Abun ya Dauremai kai matuka kuma Kaso mafi yawa Daga Cikin kimarta sai yaji Ta Ragu ba saboda komai ba sai Saboda Ta Nuna Kishinta karara akan Hafsah har kuma Hakan ya saka mata Tsanarta acikin Ranta Batare da ta mata komai ba..Miye laifin Hafsah..? Itafa tazo ta isketa da Mijinta Suna Rayuwansu Ta Shigo Cikinsu Ashe kuwa indai Ita bata Bude baki Tace tana Shigar mata Hanci bai kamata ita Barkat din Tace Haka ba,Domin Shi yana da yakini kan Hafsah 100%Bata da Tunani ko Zuciyar Cutar da Barkat Tana Zaune da ita ne Tsakaninta da Allah.
Tagumi kawai ya Zuba Lokaci Daya yana Cigaba da Auna Abubuwa masu Girma Ta Bangaran Hafsah da Barkat,Ko kankani basu ma Daidai ba Domin Akowani Mizani in ya Auna sai yaga Hafsah Tayi ma Barkat Fintinkau Bata iya ma Tsara da ita,Ta Bangaran Hakuri,ta mata Zarra ta Bangaran Ladabi da Biyayyah Wlh zai bada Rantsuwa kan cewa Duk Matan Duniya Ba Mace mai Ladabi da Biyayyah Uwa Uba Hakuri Bayan Hafsah,Sai kuma Bangaran iya Mu"amala da kuma Yadda zata Tafiyar da zamantakewarta Yafi kowa sanin Wacece Hafsah bai Taba Jin wanda ya Fadi aibunta ba Kama Daga Danginta Zuwa Danginsa ba,Hakika Tayi Gadon Dattako da kuma kyawawan Halin Iyayenta,Ya sani Mama Tamkar uwa take gareshi Ammh Ita kanta tana Girmama Hafsah,Umman Sadiq ita ta Haifeshi ammh Tafi Girmama Bukatun Hafsah Fiye da nashi Bukatun Kuma Tana Fadamai koda yaushe sukayi mgana kan ya Rike Hafsah da gaskiya da Amana Domin In ya bari ya Rasata ko kuma Giyar Rudin Duniya ta Sameshi ya Wulakantata Toh Tabbas Watarana zai yi Nadama,Kuma zai yi Kuka da idanuwansa Domin bazai Taba sanun mace kamarta ba bai kara gasgasata mganar Umma ba sai yanzu Daya Auro Barkat yaga Bambamce Bambamce Halayyah Da yawa ta Bangaran Hafsah sai kuma yanzu yake Tunanin kodai mganar Nazifi gaskiya Bayan Hafsah ba Macen da zata iya Hakuri ta zauna Dashi..?
Gabadaya Ransa yana Jagule ne Dakyar ya iya yakice komai ya maida kai ga aikinsa ammh Kuma Gefe Daya na Zuciyarsa na karfafamai Gwiwan Takama Barkat din Burki Domin Bazai Lamunci ta Raina mai Mata ba gaskiya Indai Hafsah batace ta Tsare mata komai ba itama bata da Wannan Damar da zata Fadi Wata mgana kan Hafsah Domin akomai Da take ganin Hafsah Ta mata Fintikau Halayyanta ne suka Siya mata Duk Wannan Kimar Datake gani tana Kishi akanshi.
******
Baiwar Allah Hafsah bata son Wainar da Aka Toya da safe Tsakanin Abdullahi da Barkat ba Dama Jiya ita ta Fita Girki Barkat din ta karba,Da Safe kuma Abdullahi ya Shigo mata Sallama ya isketa tana Wanka Su Amira Kuma Daman Mai mashin Dinsu ya kira yakaisu so basu Hadu ba Balle Taga Cikin yanayin Daya Fita Noor kadai Dake kwance kan gado yayi ma Wasa ya Fice.
Har Wajen 12pm na Rana bata ji Motsin Barkat ta Fito ta Daura Girki ba sai Abun ya bata mamaki Ta sani da Wuri take Gama Girkinta,Sai Tayi Tunanin kila Girki Daya Zatayi ammh sai me Har Pass2 shuru bata ji Motsinta ba Duk da haka dai bata Fito ba,Tana Daki Ita da Noor Dataji yunwa Sai Ta Hada Tea tasha,Har Amira suka Dawo Makaranta Barkat bata Fito ba Suna Ta Tambayan Abinci sai ta Hada musu Complex suka Sha Suka kwanta kafin Lokacin Islamiya sai Lokacin ta Fito Tsakar gidan Abun mamaki Dakin Barkat din ma na Bude ammh Kwata kwata ba Motsinta sai Hafsah ta Fara Tunanin kodai Bata da lafiya ne..? Kamar zata Shiga sai kuma ta Fasa Tunda Daman bata Shiga Dakinta sai ta kama Kuma Daman yau din Barkat din bata Leko Ta mata gaisuwan Safe da Abdullahi ya kafa Dokar Haka ba, sai kawai Zuciyarta ta bata ba lafiya.
Dakinta ta koma,Itama takwanta ita da Noor sai Hudu Saura Tatashi Tayi sallah tatashi Su Amira sukayi sallah sukayi Shirin zuwa islamiya,Ta rakasu Har Kofar gida kana ta Dawo Cikin Gida,Tayi Tunanin ta Kira Abdullahi sai kuma ta Tuna yana Office yana aiki bazata so ta tayar mai da Hankali ba,sai kawai ta Share acikin Ranta kuma Tayi Wani Tunani inda Barkat din Tana so ta san Tana Cikin wani hali ko bata lafiya da Ta Kirata ta sanar da ita Tunda suna Gida Daya amfanin zaman Taren kenan ammh Tunda taki Fitowa bata Bukatar wani ya sani kenan kawai sai ta Fita Batunta ta kama Harkan gabanta
Ganin Har 5pm na yammah Tayi Shuru bata Ji Motsin Barkat ba sai kuma Zuciyarta ta kasa Natsuwa Batare da Tunanin komai ta Isa ga Kofar Dakin Barkat din Tana Doka sallama ammh kuma Shuru ba"a amsa ba,Sai kawai ta Tura labulan Dakin ta Shiga Falon ba kowa Ta kara Rangada Sallama taji ba"a amsa ba Sai Tsoro ya kamata ko Barkat din na Cikin wani Hali da Sauri Tana goye da Noor abayanta ta Tura Kofar Bedroom din ta Shiga Lokaci Daya Tana Kiran Sunan Barkat din.
Abunda ya bata mamaki yasa ta Dakata bata karisa ga Shiga Cikin Bedroom din na Barkat ba ganinta Zaune Gefen gadonta ta Kishingida da Gadonta taci Kwalliyarta Cikin Riga da wando Wadanda suka kamata kanta ba Dankwali tasaka Band ta Daure gashinta kafarta kan Daya tana Taunan Cingam gefe Daya kuma Tana ta latsa wayarta Kamar ma bata ji Hafsah ta Shigo Tana sallama ba, Tare da Kiran Sunanta ba.
Mamaki ya kara kume Hafsah ta Bita da kallo kafin tace"Ikon Allah Barkat lafiya kuwa..?kina ji ina ta sallama baki amsani ba kamar ba yar musulma ba..? Tafada tana kallon Barkat din Wacce tayi kamar bata jita ba Sai Ran Hafsah ya baci ta kada kai Tana Fadin"Allah ya baki Hakuri dana Shigo Miki Daki ..Dama Shuru naji Duk yau baki Fito ba, Sai nayi Tunanin ko lafiya Shine na Shigo na gani Saboda Hakkin zaman tare ammh Alhamdulillah Tunda kina Lafiya.."Daga Haka ta Juya Zata Fice Barkat ta Dago Tana mata wani Wulakantattacen kallo Idanuwanta sun kumbura alamun Tasha kuka Mikewa zaune Tayi Tana Fadin"Ina Jinki Kina Sallama Kawai banga Damar amsawa bane..Mganar kuma Kinjini Shuru ina Abunda ya Dameki ai ba zamanki nake ba balle Fitowata ko Rashinta ta Dameki,mganar kuma zaman tare ke kika sanshi Malama ba Wata Amana Tsakanina da Kishiya Saboda haka karki kara Shigomin Daki Daga yau Kowa Tashi kawai ta Fissheshi Malama.."Tafada tana wani Karkace kai tana Jifan Hafsah da wani kallo na, na Gama Tsanarki.
Hafsah Data Waiwayo Tana kallonta Tunda ta Fara mgana Mamaki ya Cikata ta Bude baki kawai Tana kallonta,Dakyar ta iya Rufe bakinta kafin tace"Ai Shiyasa na Fara baki Hakuri Da Farko..Mganar kuma Ba zamana kike ba Duk bai taso ba Dukkanmu muna karkashin Mutum Daya ne..Dama gani nayi ke keda Girki kuma kinki Fitowa ga yara sun Dawo makaranta Dazu suna Jin yunwa Complex na Hada musu suka Sha suka Tafi islamiya kada su Dawo kuma su sakemin kukan yunwa bana so na Shiga Hakkinki Ranar girkin ki na Shiga Kitchen ina Girkin Hakan ba Dadi Shiyasa na Shigo na gani ko Baki lafiya ne sai na Tambayi Izininki na Girka kodomin yara da kuma Abban Amira da zai Dawo Daga aiki a gajiye yana Bukatar Abinci.."
Har tagama Bayaninta Hararanta Barkat take sai da ta ida kana ta Mike tana Tafa Hannuwanta Lokaci Daya Tana Fadin"Wow..Bravo..Hajiya Hafsah...kinyi iya Tsara kalamai ba Shakka sai dai kuma kin makara bazasu Taba Tasiri a kaina ba Munafuka mai Fuska Biyu,Dama tun Shigowata Gidanan nasan Sai kin kawomin Mtsala azamana da Mijina gashi kuma kin Fara Tunda komai nayi mai baya gani sai ya ambaci Sunanki kamar don ke kadai akayi Shi Bazan Boye miki Na Tsaneki Kuma Allah ya isa Tsakanina Dake Tunda kina son Rabani da Mijina.."Tafada Idanuwanta sun kawo Kwallah baki Hafsah ta Bude tana Bin Barkat da kallo kafin tace"Ban..Bangane ba Ni..."Dillah Rufemin baki Karya nayi Ke ba Munafukar bace..? Har kina wani kokarin cewa baki gane inda na Dosa ba da anyi mgana sai ace ke mai Hakuri Hafsah mai Hakuri Hafsah me kaza..! Kan me nima ai mace ce ki barni nasamu Sakewa mana Nida Mijina Don Allah ki kyalemmu hakanan Bana kaunar ina Tare dashi naji yana Ambatan Sunanki Raina na kuna Kamar zan Mutu nake ji..Na Rokeki ki barni da Mijina Don Allah mganar Girki kuma in kin matsu ki Girki kici Keda ya"yanki kuma In kika Kuskura kika bama Mijina Wlh Allah ya isa ban yafe ba kuma sai Allah ya Kamaki da Cin Amanata Ranar Girkina.."Tafada Lokaci Daya Tana Haki Da Share Zufan Dake Digo mata Daga saman Goshinta.
Harta gama Mganarta Hafsah na Tsaye Tana kallonta Zuciyarta na kuna Idanuwanta Suka Cika da kwallah sai Tayi Saurin Dannewa ta Dago Tana Mirmishin Dayafi kuka Ciwo kafin tace'Naji Duka maganganuki..Sai dai ban isa na Sauya Miki Abunda ke Ranki game Dani ba.Ammh ina so ki sani ko ki yarda ko karki yarda Wlh Tallahi Ni Hafsah da Zuciya Daya Nake Zaune da kowa bama ke ba..Mganar kuma na barki da Mijinki Dama ni Ina Ruwana..? Inace Girki Arabe yake kuma kowa baya Shiga Hakkin kowa..?mganar abinci kuma zan Dafa kodon Ya"yana kuma nayi Miki alkawarin Insha Allahu Bazan Bama Abban Amira ba ballatana Allah ya kamani da laifin Cin Amana Daga karshe ina mai Baki Hakuri Insha Allahu haka bazata kara Faruwa ba.."Ta karishe Fada tana jin wani Daci akasan Ranta lokaci Daya ta Juya ta Fita Daga Cikin Bedroom din Barkat din ta Rakata da Dogon Tsaki Lokaci Daya Tana Fadin"Stupit kawai.."Kafin ta koma ta kwanta tana kwafa Tana jin kaso Mafi yawa Daga Cikin bacin Ranta ya Ragu Tunda ta gayama Hafsah Abunda ke Ranta ammh Duk da Haka bata Huce ba tana ji kamar ta kasheta saboda Kishi da Haushi.
Hafsah kuwa koda takai Dakinta bata gani saboda Hawayen Daya wankemata ido kan kujera ta samu ta Zauna tana Kuka,tana Tunanin yau ita Barkat ke Kira Munafuka..me tayi mata..? Bata son komai ba Tsakaninta da Mijinta ba..In Hakane toh sai tace me.? Wani irin Abu ne Abdullahi baya mata Tataba Dora laifin kan wani..? Kodon mai Kishiya bai Mutuwar Allah me yasa take Zarginta..? Ta kasa gane komai sai Tayi kukanta ya isheta kana ta Share Hawayenta Ta kuma yi kokarin Cire Abun Acikin Ranta da Tunanin kirkiro ma kanta aikin Dazatayi wanda zai Dauke mata Hankali.
Wankin Noor da Uniforms dinsu Amira ta fito dashi ta wanke,Ta Share Dakinta Ta gyara Ko"ina Tayi ma Noor wanka ta goyata Gabda mangariba su Amira suka Dawo Daga makaranta Ta umarcesu da suyi alwala suka yi Sallah Tare bayan sun gama Ta Dauko Qur"ani suma tace su Dauko ta Shiga yi musu karatu Noor na Goye abayanta tayi Barci
Sun Dade suna karatun Kafin tace su Maida Qur"anan Su Dauko Littafan Bokonsu su yi Aikin da aka basu,Suka tashi Suka Dauko Ita kuma ta Mike tana Tunanin gwara ta nemi Abunda Zata ci ita da ya"yanta Shayarwa Take tana Bukatar Abinci Sosai Wuni kawai tayi Shan Ruwan Tea,su kansu su Amira yunwa Sukeci Karamin Hijabinta ta Sanya ta Dauki karamar Fitila mai Batir Dayake Sun Dauke Wuta ta Shiga Kitchen tana Goye da Noor ta Fara Jajjaga kayan Miya kafin ta Kunna Gas Dinta Wanda Abdullahi ya gaji ya Siya mata ta Dora Jallop din Taliya.
Ta Zuba Taliyan kenan Taji an kwala Kiran Sallar Isha"i yasa ta koma Daki Tayi sallah taso ta Shinfide Noor Daga Bayanta Ganin tayi Barci Ashe barcinta bai yi Nisa ba ta Farka ta Fara kuka Dole ta zauna ta bata Nono Ta mikama Amira ita,ta koma Kitchen tana Duba Girkin nata,Ita kuma Noor an Tsigeta Daga Nono bata Koshi ba ta Fara Kuka Hafsah kuma na kokarin Sauke Taliyan ta kashe gas ta Zuba musu sai ta Shigo Gabadaya Taji Karan Mashin Din Abdullahi da Shigowarsa.
Da kukan Noor ya Fara Cin karo Tun kafin ya kafe mashin Din ya sauka ya Fara Fadin"Kukan wa nake ji haka..? Noor ce ina Hafsah din take ne kika bar yarinya nata Tsala kuka..? Ya fada yana Sauka Daga kan Mashin Din Lokaci Daya yana Saba karamar jakarsa,Hafsah Data kashe gas ta Leko Daga Kitchen Tana Fadin"Ga ni nan Abban Amira Ina Kitchen ina Kokarin sauke abinci karya Kone..Kuma ma fa yanzu nagama Bata Nono da zan Fito na bama Amira ita ta Riketa Haushin na Cireta anono bata koshi ba yasa kaji tana yanka wannan Ihun kamar wacce ake yankata.."Tafada Tana kallonsa Cikin mamaki Abdullahi yace"Abinci kuma..? Ina ita Barkat Din Da bata Girka ba ko ba ita keda girki ba yau..?
Hafsah Cikin Halin ko In kula ta Juya Zuwa Kicthen din Tana Fadin"ita keda shi mana..Bata Girka bane.."Cikin Kakkausan Murya yace"Saboda mene..? Hafsah ta Fito Dauke da kulan Abinci da Filet Filet na Zubawa Tana Fadin"Bansani ba Abban Amira.."Tafada Tana kokarin Daidaita kanta Ta gabansa ta Wuce tana mai sannu da zuwa Bayanta yabi Zuwa Cikin Daki Acikin Ranshi yana Tunanin Lalle Barkat ta Rainashi ya kuma Zama Dole ya nuna mata kalansa.
Yana Shiga Amir ya taso yana mai oyoyo,Ya daukesa Lokaci Daya ya karisa kan Daya Daga Cikin kujerun Falon ya zauna Kafin ya Sauke Amir Noor ya karba Hannun Amira yana Lallashinta Lokaci Daya yana Kallon Hafsah wacce ke kokarin Zuba ma su Amira Abinci yace"Kinga Bar Zuba abincinan zo ki karbeta ki bata Nono Tana ta kuka Fa.."Tana Zuba Abincin Tace"Rigimarta ce kawai fa Abban Amira bata da yunwa.."Cikin Daga Murya yace"Wani irin Rigima yarinya na Kuka kina Gayamin Rigima..? Kizo ki Amsheta nace bana son Gaddama Kin sani kuma.."Ya fada muryansa Tana Bayyana yadda Ya Hassala Jin haka yasa Bata kara mgana ba ta Tura ma Su Amira Filet din data Zuba Musu Taliyan Tana Fadin"Oya kuje Tiolet ku wanko Hannuwanku ga abinci kuzo kuci ku kwanta Gobe akwai School."Suka Mike Tare Amira tana Fadin"To Mommy.."kafin su wuce Zuwa Cikin Bedroom Din Abdullahi ya bisu da kallon Sha"awa gefe Daya kuma yana Jinjina Hafsah Domin Bata wasa Wajen Tarbiyansu Shiyasa koda yaushe zaka gansu Cikin Natsuwa da kalama.
Karisowa Tayi kusa dashi ta Zauna ta mika Hannu ya Bata Noor ,Shi ya zage mata Zif din Rigarta ta baya Ta Ciro Nonon ta mika ma Noor ta karba da Sauri ta Fara tsotsa lokaci Daya Tana Sauke ajiyar Zuciya Abdullahi ta kallah ya bankamata Harara yana Fadin"Ji yadda yarinya ke Sauke Numfashin Wahala ammh Ana mgana kina Fadin wai Rigimartace.."Ko mgana Hafsah batamai ba Shima bai Damu ba ya Mike Kawai ya Fice Batare Daya kara mata mgana da kallo Ta Bishi Tana wani Tunani acikinta ranta Su Amira ne suka katseta da suka Dawo Falon.
Afalo ya Iske Barkat tana Zaune tana Kallo ta Dora kafa Daya kan Daya Ta sauya Shiga Tunda yanzu Atamfa ce ajikinta Riga da zani tayi wani Daurin Dankwali na Ture kaga Tsiya,Sallamansa ma Dakyar ta amsa Tunda ya Shigo kallo Daya yayi mata ya kauda kansa Kafin ya Karisa Cikin bedroom dinta ta Rakashi da Harara.
Yana Shiga Jakarsa kadai ya ijiye ya Sabule kayan Jikinsa ya Fada Tiolet yayi wanka Ya Fito ya Shafa mai ya Fesa Turare ya saka Wata bakar Jallabiya ya Fito Falon Hannunsa Rike da wayarsa Inda ya barta nan ya isketa ammh wannam karon Wayarta na Hannunta tana Dannawa Kanta ya Tsaya Lokaci Daya yana Nazarinta kafin yayi gyaran Murya yana Fadin"Ina Abincina..? Naga har na Fito wanka baki kawomin ba..? Ko sai na Roka..?
Yafada yana mata wani kallon in kikace zaki kawomin wani Raini Zaki gane baki da wayau,Banzar iska tamai ko tama san yana kanta yana mata mgana Ran Abdullahi ya baci Cikin Mamaki yake Binta da kallo kafin ya saka hannu ya Fizge wayar Hannunta yana sakin Huci Jin am Fizge wayar yasa ta Dago a Zafafe Tana kallonshi Cikin Fushi yace"Ke Bada ke nake mgana ba..? Tambayanki nake ina Abincina..?
Kai Tsaye tace"Abinci..? Ta kada kai kafin tace"Ban Girka ba..Kuma ban ga Damar girkawa ba Sai yaya..? Ta fada Lokaci Daya Tana mikewa,Wani Sororo Abdullahi yayi yana kallonta kafin ya nuna kansa yana Fadin"Ni..Ni kike cema Baki Girka ba kuma baki ga Daman girkawa ba Barkat..? Yafada yana Nuna kansa Wani Rausayar dakai Tayi Tana Fadin"Eh kaifa..Ban girka ba nace zan maka karya ne..?Dama na bari ne sai Ranar da na koyi Hakuri da Biyayyah irin na Hafsah sai na Cigaba da girkin..!
Tafada tana wani Girgiza kai Abdullahi da Zuciyarsa ta Fara Tafarfasa yaji Ta kawo mai Wuya Yana Tunanin wani irin Raini ya auro ma kansa,Tunda yake ba Macen da tataba mai irin Wannan Salon Rainin da Barkat tamai,Tuni Idanuwansa Suka Sauya launi Jijiyoyin kansa Suka Tashi Radau Kallonta yayi ido Cikin Ido kafin yace"Kin san kuwa wa kike gayama Mgana Haka..? Nifa Mijinki ne ko kin manta ne..?
Ta Koma ta Zauna Tana Fadin"Nasani mana..Ba Abdullahi bane Mijin Hafsah ba.."Tafada tana Sakarmai ido,Wani Irin Zafi yaji Ransa na masa kamar ya Daga Hannu ya Zabga mata mari sai wata Zuciyar ta kwabeshi,ganin in ya Cigaba da Tsayuwa Wlh sai Barkat taci Ubanta kawai sai ya Wurgamata Wayarta ya kada kai ya Fice ta Rakashi da Mirmishi kafin ta Mike ta Dauki Wayarta Tana Fadin"Dama Ashe ni na bada Dama ake min Abunda aka ga Dama.."
Yana Fita Fuu sai Dakin Hafsah Tana Zaune tana Cin Abinci Noor na kan Cinyarta,su Amira sun Shiga Ciki sun kwanta, ya Fado Dakin Har sai da ta Tsorata Kusa da ita ya zauna kan kujera Yana Kallon Hafsah Wacce ta Dakata da cin Abinci Tana Fadin"Abban Amira lafiya kuwa..? Muryansa Cikin Kaushi yace"Tashi ki Sawo min Abinci.."Kawai ya iya Fada yana Sakin Huci Sama sama Galala ta Bisa da kallo Bata samu Zarafin mgana Ya Daga Murya yana Fadin"Ki tashi ki bani Abinci nace ko..?
Ya fada Cikin Fushi yana Tsareta da ido ajiyar Zuciya ta Sauke Data gano Dalilin Masifar Cikin kwantar dakai Tace"Sai dai kayi Hakuri Abban Amira na Riga nayi alkawarin Bazan baka Abincin nan ba..? Ido ya sakar mata Yana Fadin"What.? Saboda mene..?
Kai Tsaye tace"Saboda bana son Amanar Barkat ta kamani...Tunda ba Ranar girki na bane bani da Hakkin baka abinci."Bata gama mgana ya Mike a Fusace yana Fadin"Wannan ai Zencen banza ne..? Kina matata kuma a kawomin wani iskancin banza acikin Gidana Uban waye kuma yace miki haka.? Ehe nace waye yace zaki ci amanar barkat...? Tunda ita bata Girka ba Hakkinki ne ki Girka ki bama Ya"yana Nima ki Bani Tunda zama na Kike ba zaman wani ba Malama.."Ya Fada yana wani Sakin Nishi na Masifa Kai kawai ta Girgiza Tana Fadin"Kayi Hakuri Abban Amira ban Taba saba Umarninka ba ammh yau zan saba Bazan iya baka abinci ba alhalin Barkat tamin Allah ya isa bata yafemin ba matukar na Baka abinci Ranar girkinta.."
Tafada Cikin kwantar da Murya Sai Abdullahi yaji kamar Jiri na Neman kadashi Saboda kalaman Hafsah Cikin Wani Fushi mai Tsanani yace"Ita tace Haka..? Kai Hafsah ta Sunkuyar kafin ta Ture Filet din gabanta ta Mike Sai da ta Shimfidar da Noor kan kujera ta Dago Tana Fadin"Nidai ina kara baka Hakuri Abb..."Bata idasa ba Taji ya Damki Dankon Hannayenta Da karfi ya Girgizata yana Fadin"Tambayanki nake ki gayamin ita tace haka..? Yafada Cikin Tsanani Fushi sai da Hafsah ta Tsorata Domin Duk Fushin Abdullahi bata taba ganinsa Cikin wannan Fushin ba.
Cikin Rawan Murya tace"E..eh ita tace min haka.."Ido ya Runtse kafin yace"Wani Abu ya Faru bayan Bana nan ko..? Yafada yana kureta da ido Girgizamai kai Tayi Tana Fadin"Bafa Abunda ya Faru Abban Amira.."Karya kike..Wani Abu ya Faru..? Ya katseta Cikin Daka mata Tsawa kafin ya Cigaba da Fadin"Zaki Fadamin Abunda ya Faru ko kema sai Ranki ya baci..?
Yafada yana Sakarmata Jajayen Idanuwansa Numfashi ta Sauke ta karya Wuya tana Fadin"Abban Ami.."Ashe ke ba Wakiliya ta bace in bana gida..? Kice makwafina in bana Gida Hafsah Saboda Haka ki Fadamin Abunda ya Faru yanzu Ina Jiranki.."
Hafsah ta Runtse ido ta Bude Zatayi mgana kawai ya saketa yana Fadin"In baki Fadamin ba.Ban yafe miki ba Hafsah kuma bazan Taba yafe miki ba indai baki Sanar dani Abunda ya Faru ba bayan bana nan.."Yafada yana Kokarin Controlling Din Fushinsa Ido Hafsah ta Zaro Tana Fadin"Baka yafemin ba Abban Amira..?
Cikin kakkausan Murya yace"EH BAN YAFE MIKI BA HAFSAH MATUKAR BAKI SANAR DANI BA.."jin haka yasa Hafsah bata da Zabi Tiryan Tiryan ta Shiga Zayyanamai komai Har karshe ta Karishe da Fadin"Plz Abban Amira karka ce zaka yi wani Abu..Ka bari ka wuce yanzu kana Cikin Fushi ne plz.."Ko Sauraranta bai yi ba ya saka kai zai Fice ta Bishi Ta Riko Hannunsa Tana Fadin"A"a Abban Amira ina zaka..? In kayi mata wani Zarginta zai Tabbata akaina tace na Hada mata Gulma Na Shiga Tsakaninta da Mijinta Don Allah ka kyaleta Ni Tayi mawa kuma Wlh komai ya wuce..'"
Fizge Hannunsa yayi yana Haki yake Fadin"Wlh karya take Hafsah..Ita Wacece..? Ita din Banza da Wofi Ita Har ta isa ina Auranta Tana Karkashina tace zata zo Gidana ta Raina ni ta kuma Raina min mata..? Me take Takama dashi...? Wlh sai ta gane bata da wayau matukar bazata Darajani ba Kuma bazata Girmamaki kamar yadda Ni da Sauran yan"uwana muke Girmamiki ba Wlh sai dai ta bar Min Gida Bazan Dau iskanci ba Kinjima na Rantse.."Hankalin Hafsah ya Tashi ta Dafe Kirji ko kafin tayi wani yunkuri ya fice ta Bishi da Gudu Tana Fadin"A"a Abban Amira karkayi haka.."
Waigowa yayi yana Fadin"Ki koma Daki Hafsah.."Taki komawa tsawa ya Dakamata wanda Harta Barkat Dake Dakinta sai da tajita Cikin Kakkausan Murya yana Nuna mata Hanyar Dakinta yana Fadin"Ki koma Dakinki ki Zauna...Babu Abunda zaki iya yi, awannan al"amarin saboda Haka Babu Ruwanki.."Daga haka ya Barta nan tsaye ya Banga Labulan Dakin Barkat ya Shiga Cikin Fusata.
Baya Hafsah taja ta Dafe Kirji Tana Fadin"Innalillahi Wa'inna illaihirraju"un.."Domin a yanayin Abdullahi kadai ta Tabbarta da kalamsa Tsoronta kuma Tasan baza"ayi mai kyau ba kasa komawa Daki Tayi Taja ta Tsaya Cikin Zullumi.
Barkat na Tsaye Tun Bayan Jin Tsawan da Abdullahi yayi ta Mike Tana Tunanin ko lafiya..? Bata gama Tunani ba taga ya Fado gabanta kamar wani Zaki Cikin Hargowa ya Nuna ta da yatsa yana Fadin"Me kika Fadama Hafsah dazu..? Wasu irin mganganu kika Fadamata Dazu Data Shigo Dakinki ta Dubaki ko kina lafiya...?ya fada yana Huci kamar wani mayunwancin zaki.
Barkat Ta saki baki tana kallonshi kafin tayi wani Munafukin Mirmishi Tana Fadin"Ba Shakka ashe harta Gaya maka..? Oho na gane ta Zugo ka ne kazo kamin Tijara Saboda an Taba yar gwal..? toh bude kunninka Ba komai nace mata sai Munafuka mai Fuska biyu mai kuma Kokarin Raba mata da Miji..."Bam..! Abdullahi ya saka Hannu ya make mata baki yana Huci Cikin mamaki ta Dafe bakinta Tana Bin Abdullahi da kallo kafin tabi Hannunta da kallo ganin Jini yasa ta Saki Kuka Tana Fadin"Kambu kan Na Fadi gaskiya ka Fasa min baki..?
Abdullahi yace"Kadan kika gani..In kika kara Zagin Hafsah sai Na zabga miki mari Wlh Sakarya kawai mara Tunani.Karya akayi bata Fiki komai bane..? Ke Uban me kika iya..? Ina ce a zaman Aure Ginshiki Shine Hakuri ladabi da Biyayyah ga Abokin Rayuwarka ke ki Fadamin in kina Kare Guda Daya Baki iya komai ba sai Girman kai kishi mara amfani Kina Kishi da wacce tafiki Komai..na fada na kara fada Hafsah Tafiki Komai Barkat maimaikon Kiyi Kishi Da ita wajen kwaikwayom kyawawan Hallayarta sai kike kishi da ita Wajen Kokarin ki Wargazamin Zaman Gidana kina zagin Uwar ya"yana mata ta Farko matar Rufin Asiri na ko..? Toh baki isa ba Wlh Kin kuma yi karya Wlh ni Abdullahi komun son da nake ma mace bata isa tazo gidana ta kawomin wani iskanci ba Cikin biyu za"ayi Daya ko Ta Sauya Halinta mu zauna Daya ko kuma ga Hanya nan ta kama Gabanta ba Lalle ba Dole.."Ya karishe Fada yana nuna mata Hanyar Fita.
Barkat da Kuka yaci karfinta ta Dage iya karfinta ta kurman Ihu wanda ya Tsorata Hafsah ta Fada Dakin da Gudu a Tunaninta Abunda Abdullahi bai Saba bane yake yi wato Duka,Sai kuma Taga sabanin haka Tsayawa kawai Tayi Cikin Damuwa,Barkat kuwa Data ganta sai Tayi kukan kura tayi kanta Abdullahi ya Shiga Tsakani Ya Daga Hannu zai mareta Hafsah ta Tare tana Fadin"A"a karka Fara Abunda ka kyamata Abban Amira.."Fadin Haka yasa ya maida Hannunsa yana Jifan Barkat din da wani banzan kallo.
Ita kuwa Baya Taja Cikin kuka Tana Fadin"Lalle kin Ciru Tuta..Tunda kika yi Sanadiyar da Aurena ko Wata uku bai Cika ba,Ammh kin Saka Mijina yana Cemin zan iya karawa gaba bai Damu ba..Zan Tafi Domin Shi ya Bukaci Haka ammh Ki sani yadda kikayi Sanadiyar Wannan rashin Jituwar da mijina kema.."Bata karisa ba Abdullahi yaja hannunta keeee.sai Kofar Dakinta ya Wurgata sai gata Waje tama kusa Fadi Nuna Mata yatsa yayi yana Fadin"Na baki Minti Goma kachal ki Kama gabanki..Gidan Abdullahi ba wajen zaman irinku bane...Kije Gida Akara baki Tarbiya Domin kwata kwata baki Dashi Sannan Abu na karshe ina kara gargadanki Kada ki kara kuskura Bakinki ya Bude ki kara aibata matata Im kuma kika ji Wlh bakya ki gani ba...Wawiya kawai Jahila wacce iliminta bai amfaneta da komai ba.."Daga Haka yaja Hannun Hafsah Datake ta Faman bashi Hakuri Suka Shige Dakinta Lokaci Daya da Bango kofa.
Da kallo Barkat ta Bisu kafin ta Sulale nan tana kuka mai Cin Rai kamar zatayi Hauka,Gefe Daya tsanar Hafsah na kara Shiga Ranta Tuna kalaman Abdullahi yasa ta Mike ta Share Hawayenta ta koma Cikin Dakinta ta Hada kayanta Cikin karamin akwati ta Dauki Wayarta da karamar Jakarta sai Littafan karatunta na makaranta Domin sun kusa komawa makaranta tafito ta Rufe Kofarta da Makulli lokaci Daya Tana Duba agogon wayarta 10:10pm na Dare ba ta kara kallon Barayin Dakin Hafsah ba ta Ja akwatinta taje ta Bude Gida ta Fice tana Tsiyayan Hawaye.
Hafsah Dake Zaune gefen gado Ta kalli Abdullahi Dake kwance ya Juya mata baya tace"Abban Amira ta Fita fa..? Don Allah kaje ka Dakatar da ita ka dawo da ita Don Allah.."
Ta Fada kamar tayi kuka,Cikin Fushi Abdullahi ya juyo Lokaci Daya da mikewa yana Fadin"Bazan Dakatar da ita ba Hafsah ammh in kin Damu da ita kije ke ki Dakatar da ita.."Yafada yana sakarmata ido Mikewa tayi Cikin Farinciki Zata Fita Taji ya kira Sunanta ta waigo Tana kallonsa Cikin kakkkausan murya yace"ammh da Sharadi..Sai dai indan kin Fita kin Dawo da ita Badai Gidana ba kema ki bita ku Tafi Gidanku Gabadaya.."Ya fada yana Kallonta Lokaci Daya yana mikewa ya Tura Kofar Tailet ya Shiga Cikin Fushi.
Ajiyar Zuciya Hafsah ta Sauke ta Dawo ta ZAUNA gefen gado kusa da Noor Tana Fadin"Ya illahi..Allah ka saussauta Wannan Zuciyar ta Abban Amira..Allah ya Daidaita tsakaninsa da Matarsa kada Auran nan ya kare kowa ya Doramin laifi.."Tafada tana Share Hawayen idanuwanta.
_Assalamu Alaikum Masoyana Na nesa Dana kusa ku dan bani aron Hankalinku anan Kadan Da Farko ban so nace wani Abu ba sai Sakonninku yayi yawa Tsakanin posting din Jiya da wanda akayi kafin shi na Farko akwai masu Korafin Abdullahi ya cika Masifa gashi Hatta iyayensa Suma Binsa suke bamai iya mai Gaddama ko..? Toh Misali Abdullahi ya Dauki Girman da wani Babban magidanci bai Dauka ba a karamin aikinsa yake Iya Rike da Gidansu da kannensa Duka ya Biya musu kudin makaranta yayi Duka laluransu Dasu da Mama,gefe Daya kuma ga tashi Laluran gata matarsa gata yayansa..? Baba wada matsayin Uba yake gareshi yana kokarin bashi Girmanshi Tunda baya Zartar da wani Abu sai dashi da kuma Shawaransa kusan meyasa Suke Girmamasa..? Yana da kwarjini kuma yana Son Girman kuma sai Allah ya bashi,Duk Abunda zai Zartan kan gaskiya ne Taya zasu Dakatar Dashi..? Duk Abunda Abdullahi yake baya kan kuskure bane Taya ya Zasu Dakatar dashi..? Su kansu suna Girmamashi Saboda matashi ne mai Zuciya da kuma Halin Dattako Ya kamata kuma masu karatu ku Tayasu Girmama Abdullahi Domin na Tabbata awannan Rayuwar da muke Ciki samun Jajirtattacen Yaya irin Abdullahi sai Antona..Sai mgana ta Biyu kan wasu Suna Fadin bai dace akomai Abdullahi ya Dinga Kiran Hafsah ba..? In bai kirata ba wazai Kira..? Kuyi adalci Barkat fa Da Shigowarta gidan Wata uku fa kenan..? Ammh saboda Rashin ta ido sai ki Fito da Tsirfan Fara nuna Tsana da kishi ga uwargidanta da kikazo kika Tarar tayi Shekaru da Shekaru da mijinta..? Wa yan"uwansa suka sani kafin ke..? Ita tace komai nashi ita ta gyarashi Har ta ganshi tace tana sonsa kuma bai ce bayason Hafsah ba karin Auransa wani Nau'i ne Daga cikim kaddaransa bashi da yarda zai yi..ko Shekara baki Rufe agida ba kina Complain kaza Taya zaki iya Hakurin da Ita Uwargidanta tayi..? Komai da sannu ake bi kema sai ki natsu ki Fahimci me Uwargidan take yi ne ta samu wannam Kimar sai kiyi kishi irin na wayewa kema ki koyi da ita Wlh with Tym kema za"a Fara yabonki Kuma Mijin zai Dinga kama Sunanki yana Tunanin yafi kowa Dacewa ammh kuma Sakarci Barkat ya Chanchanci koma miye ya Faru da ita Ballatana Miji irin Abdullahi Yana da kyau ka nuna Ma Duniya matarka tana da kima awajenka bawai saboda ka kara Aure ka Nuna ma Amarya cewa Uwargida ita da Banza Duk Daya ba.._
*Shakira...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
_Wannan Shafin naki ne *MMAN SADIQ...* Ina jin Dadin yadda kike karanta wannan Labarin da Dukkan Zuciyarki...Nagode kwarai Allahu ya bar zumunci Ameen.._
*039*
"Barkat da kafarta ta taka Har bakin Titi,Bata samu Abun hawa ba sai da tazo Wajen makarantar Albani kana ta samu mashin din Daya Dauketa Zuwa Gida Har Ya sauketa Kofar Gidansu ta sauka ta Biyashi Kudinshi Kuka take,kuka mai Cin Rai da Tsanar Hafsah acikin Ranta Domin Tagama bama kanta yakinin itace Silan Faruwar komai.
Koda ta Zo Shiga Gidansu Kofar tana Kulle alama da har sun kwanta Bugawa tahau yi ammh ba Motsin kowa ganin karta tara Mutane yasa ta Fiddo Wayarta Cikin karamar Jakarta ta Kira Bahijjat,tunda ita Tana Gida Bahijjat ta Fara Barci Wayar Barkat ta tasheta Lokacin Da Taga Kiran Ta Tsorata sai da ta Duba agogo Wajen 10pm da wani Abu na Dare Cikin Tsoro ta Daga Kiran Tunkafin ma Tayi mgana Barkat din Cikin kuka Tace tazo ta Bude mata kofar gida Lokaci Daya tana katse Kiran
Hankalin Bahijjat ya Tashi Da Farko kamar ta Fara Shiga Dakin Hajiya ta Tadota sai Taga Ba amfani Tunda batama Jira Taga mai Barkat din tazo Dashi ba ammh acikin Jikinta Tana Ji ba lafiya Sai kawai ta Zari mayafi ta Bude Kofa ta Fice Zuwa Waje ta Zare Sakatan Kofar Tana Bin Barkat da kallo Wacce ta Shigo Dauke da akwatunta Cikin mamaki da Rudani Bahijjat ta Bita da kallo Bata samu Zarafin mgana ba Barkat ta Fada Cikin Falonsu ita kuma sai tayi Saurin maida Gidan ta Kulle ta Bi Barkat din da Gudu Zuwa Falo.
Tana Shiga,sai ta iske Barkat din Jikin Hajiyarsu Tana kuka ashe Hajiya Taji Fitanta zuwa Waje sai ta Fito Taji ko lafiya kafin ma Takai ga Fitowa sai ga Barkat din ta Shigo Da Akwati Tana ja kee tana kuka ganin Hajiya yasa Rauninta ya karu ta Fada Jikinta Tana kuka Hajiyar ta Riketa tana Lallashinta Da Tambayanta Ko lafiya ammh Taki Mgana Bahijjat ta kallo Wacce ta kariso Kusa dasu Tana Fadin"Bahijjat Tare da Megidanta Take ne ko yaya..?
Bahijjat ta saki Numfashi Tana Fadin"a"a Hajiya ita kadai ce.."Cikin Tashin Hankali Hajiya Amina taja ta kan Kujera suka Zauna Lokaci Daya Tana Fadin"Bani Ruwa tasha Sai ta samu Natsuwan yima Bayanin mai ya Faru.."Da gudu Bahijjat ta Runtuma Kitchen ta Dauko Ruwa mai Sanyi ta samu Wani karamin Kofi ta Tsiyaya ta kawo ma Hajiyar ita kuma ta kafa ma Barkat din Abaki Tana Fadin"Sha Ruwa Baraka zaki samu Natsuwa.."
Batayi musu ta karba tasha Da yawa kana ta mikama Hajiya Kofin Tana Sauke wasu Tagwayen Numfashi Lokaci kuma Natsuwarta na Dawowa Jikinta Cikin Sigar Lallashi da Rudani Hajiya Amina ta kalli Barkat tana Fadin"Baraka meya Faru Dake ne..?Ina megidanki Da kika Fito Daga Dakin Mijinki da wannan Daran..? Ina Fatan Allah yasa lafiya..?
Tafada tana kallonta Jin Haka yasa Barkat ta Barke da kuka Tana Fadin"Hajiya ta shiga Tsakanina da Abdullahi..Tun Zuwana Gidan bata barni na Huta ba komai nayi ma Mijina bana Burgeshi Aduk kalamansa Sunanta ne, akomai nashi Itace kan Gaba Hajiya Shin Nima ba matarsa bace kamar yadda take matarsa ba..? Cewa fa yake Tafini iya komai tafini Biyayyah da Ladabi Hajiya ta Rabamu.."Ta karishe Fada Tana Fadawa jikin Hajiyan Tana sakin Wani Marayan kuka Daga Hajiya Amina Har Bahijjat Dake Tsaye Abun ya Dakesu Cikin Tashin Hankali Hajiya ta Dago ta Tana Fadin"Kinga Bar wannan kukan yi min bayani..? Abdullahin Sakin ki yayi..?
Tafada Cikin Zullumi Girgiza mata kai Tayi kafin ta Dora da Basu Labarin Abunda ya Faru Ta kara Harda karya da gaskiya Ta karishe da Fadin"Wlh Hajiya ita ta Hadamu..Duk Abunda ya Faru itace sila.."Shuru Hajiya Amina Tayi tana wani Nazari Bahijjat kuwa wata Ashar ta lailayoma Hafsah Tana Fadin"Lalle ma Matar nan Shegiya ce..Ahaka kamar ta Allah ashe bata da mutumci bansani ba..! Wlh ban so ki Fito Daga Gidan nan baki Nuna mata ke Haifaffiyar Tudun wada bace ita awa..? Banza a banza da ita.."
Take Fada Cikin Masifa da Fada Dagowa Hajiya Amina Tayi Tana Fadin"Ki Rufemin baki Bahijjat...Banzance komai akan wannan mganar ba Tukunnah..Ammh Tunda har kika ji Mijinki ya Furta matarsa tamai Abunda bkya mai toh Tabbas akwai inda kika Kuskure..Bahijjat kama Hannun Barakat ku Tafi Daki ki sata tayi Wanka ku kwanta mu Jira wayewar gari in Allah yaso zan Kira yayanku muyu mgana in ta kama sai a nemi Shi Abdullahi koma menene sai mu kara ji Daga bakinsa Allah ya kyauta.."Bahijjat zata kara mgana Hajiya ta Dakatar da ita da Fadin"Kar na kara jin wata mgana..Kiyi Abunda nace kawai.."Dole tayi Shuru ta kama Barkat ta Dauki akwatunta da karamar Jakarta Zuwa Dakinsu Hajiya Amina ta bisu da kallo kafin ta kada kai ta koma Dakinta acikin Ranta bata Fatan Auran Baraka ya samu Mtsala ba Saboda komai sai saboda Aure Wani Abu ne,na Rufin asiri.
Bahijjat ita ta lallashi Barkat ta Shiga tayi wanka tazo tayi Shirin kwanciya ta kwanta koda ta kwanta ba Barci take ba,Sai faman Ajiyar zuciya take Tunda ta bar kukan Tun Bahijjat na Farke tana bata baki Har itama Barci ya kwasheta ita kuwa Barkat tayi Barci ne da Tsanar Hafsah acikin Ranta.
****
Kamar yadda Hajiya Amina tace Hakan ce ta Faru da safe ta Kira Salisu a waya tace yazo Tana son ganinshi kafin ya wuce wajen aiki ya Biyo Shima Ganin Barkat agida da Abunda ya faru sai Jikinsa yayi sanyi labarin da Hajiya ta bashi sai yasa Ransa ya baci ya Kira Barkat din yana Mata Fada Cikin kuka take Fadin"Allah ya Salisu ina mai Biyayyah Daidai iyawata.."
Dakuwa yayi mata yana Fadin"Karya kike Wlh..Ke din ne bansani ba mai Shigen Girman kai da isa..Uban waye zaki je gidansa yana auranki kice zaki mai wannan isar naki Ku zauna lafiya..? Kuma Wlh Hajiya karki Ji da waj laifin yarinyarnan ne Tunda kikaji ya Bude baki yace batamai Biyayyah hakane Domin Dama Barkat kina da Gaddama Bamai saka ki bamai Hanaki ke akomai Kina Bin Ra"ayin kanki ne,kuma na Tabbata Shi kika je kina Kokarin nunawa ya Nuna miki bazai Dauka ba Shine kika Maida laifin kan matarsa Tunda ke sakaryace mara Tunani.."
Ya karishe Fada Ransa na kuna Hajiya ta kada kai Tana Fadin"Nima nayi wannan Tunanin Sanin Halinta ba Tun yau ba..Shiyasa ma ban goyi bayanta kuma Allah na Tuba indai Namiji yasan Darajansa kansa yaushe zai zauna mace ta Dinga Iko Dashi kuna yana Auranta..? Har kuma ta Dinga aibatamai mata Duk yana kallo..? Wlh yama kyauta miki da bai miki Shegen Duka ya Hada miki da Takardan saki ba.."
Tafada Cikin Bacin Rai kukan Barkat ya karu ganin ba wanda ya Fahimceta Cikim kuka Take Fadin"Allah Yaya ni..."Katseta yayi yana Fadin"Karki ce min Tak anan wajen..Hali ai zanen Dutse mun sanki Ba tun yau ba babu kuma wanda zai gwadamana Halinki..Wlh kin bani kunya na kuma Dauka Nasihan Danayi miki ta Shigeki Ashe Duk abanza nasha gayamiki wannan Girman kan naki da isarki Ki Ijiyesu agida Domin in kika je dasu gidan wani bazai Haifa miki Da mai Ido ba Kinsa ma naji kunya yanzu da wani Ido zan kalli Abdullahi..? Ta ina ma zan Fara..?
Ya fada yana Dafe kansa Ajiyar Zuciya Hajiya ta saki Tana Fadin"Hakuri zakayi..Ka kirashi Ka Bashi Hakuri su Daidaita bayan Tayi alkawarin zata gyara Halinta.."Salisu yace"Bazan iya ba Hajiya..Zan dai Kira Amininsa Nazifi muyi mgana nace mai ya sameshi su Tattauna in ya yarda sai naje na sameshi muyi mgana.."Hajiya tace"Shikenan Allah ya kyauta na gaba.."Nan ya fice Ransa bace ya bar Barkat nata kuka Hajiya ma Dakinta ta Shige Cikin Takaichin Abunda barkat din ta aikata gashi Bahijjat bata gida Tatafi makaranta.
Salisu yana Fita ya Kira Nazifi a waya sukayi mgana Nazifi yayi mamaki sosai ya kuma Rantse ma Salisu kan Abdullahi bai gayamai Abunda ke Faruwa ba,Daga karshe yayi mai alkawarin zai kirashi yanzu in ya koma Gida Domin yazo nan Cikin kasu yana kamallah ma Jidda Registration dinta,Da haka suka Rabu Nazifi kuwa Acikin Ransa yace dama ai yasam za'a Rina Ko Mata 100 Abdullahi zai kara Aura bazai iya zama dasu ba matukar basu da Hakuri da Biyayyah irin na Hafsah kuma Dukkansu Zasu Dinga Dora laifin kan Hafsah ne Tunda basu san Dawan garin ba.
Bai samu Kiran Abdullahi ba sai Zuwa Dare Don Daga Makaranta Wajen aiki ya wuce sai Dare ya Dawo,bayan ya Dawo yayi wanka yaci Abinci kana ya Fita Haraban Gidan ya Kira Abdullahi saboda bayaso Jidda ta Fahimci Abunda ke Faruwa Sakina dai Bata nan Jiya Ya kaita kano Hajiyarta ba Lafiya sai shi ya Dawo ya barta achan.
Lokacin da Kiran Nazifi ya Shigo Abdullahi na Zaune a kasan Cafet din Dakin Hafsah yana Cin Abinci Hafsah na gefenshi Dauke da Noor tana bata Nono Amir da Amira na Daga gefe suna yi aikin da aka basu a makaranta,Falon yayi Shuru kamar ba Mutane sai Motsim Cokalin da Abdullahi ke Cin Abinci,wanda Fuskarsa take Tamke ba Annuri Tun Jiya Da har garin Allah ya waye bai ma Hafsah mgana ba Data gaisheshi Sama sama ya amsa,Breakfast kuwa Haka ya Fice bai ci ba,Tana so ta karamai Mganar Barkat bata samu Fuska ba sai Taja bakinta ta Tsuke kawai bata ma zaci zai ci Abinci ba in ya dawo sai gashi bayan yayi wanka ya Sauya kaya yace ta bashi Abinci.
Yana ganin Kiran Nazifi Ransa ya bashi wani Abu bai Daga ba sai da ya gama cin Abinci Ya Ture Farantin gabansa ya Dauki Wayarsa ya Shige Ciki Hafsah ta Bishi Da kallo yana Shiga ya Kira Nazifin Bayan ya Daga sun gaisa Da Tambayan iyalai Nazifi ya karkace Baki yana Fadin"Mutumina Dazu da safe Salisu ya Kirani yake gayamin Abunda..."Wani Salisun..? Abdullahi ya katseshi.
Nazifi yace"Salisun dai daka sani Abokinmu yayan Matarka Barkat.."Cikin Basarwa yace"Umh ina jinka sai yace maka me..? Nazifi yace"Gayamin Abunda ya Faru yayi Tsakaninka da Barkat..Abundai bai yi Dadi ba ayadda ya nuna Ranshi ya baci kuma ya bata Rashin gaskiya shida Hajiyarsu yace min kunyarka yake jin in ka bashi Dama yana so ku Hadu kuyi mgana.."Numfashi Abdullahi ya Sauke kafin yace"Dama Nima ina son mu Hadu Dashi..Zan Tambayeshi Dama kanwarsa bata da Tarbiya bansani ba..?
Baki Nazifi ya Rike yana Fadin"Assha..Yada haka Mutumina..? Don Allah karkacemai Haka Shima ai ba laifinsa bane..? cikin Fusata Abdullahi yace"Toh laifin waye Nazifi..? Ace yarinya batasan Darajan Auranta ba ka fa Duba ni kaina ta Rainani ban isa in ce ga Abunda zatayi tayishi ba sai Abunda Taga Dama wai kamar ni abokina ina Fada Barkat tana Fada,kuma wai Daga karshe ta kare a zagin Hafsah... ? Matata Uwar ya"yana matar Data ke Rufamin asirina na Duniya Itace Abun zaginta Abokina... ? Me Hafsah ta mata..?ni kaima Danake mijinta Bana ce ga laifin Da Tataba min da gangan ba sai Cikin Rashin sani ammh wai har Yarinyar nan zata Bude baki tace ma Hafsatuna Munafuka.! Wlh Kalmar ta Dakeni Mutumina inda Ace Ina Daga Cikin maza masu Duka Da Tuni Barkat tana Chika Emergency Domim sai na sauya mata kammani da Duka kaji ma na Rantse.."
Yafada Cikin Tabbatar da Abunda ya Fada,Dariya ta kusa kama Nazifi ya kanne yana Fadin"Lalle kuwa bata kyauta ba..Ammh Kasani Abunda nake gayamaka abayane yau zan maimata maka..Wlh Tallahi mutumina Ko mata 100 zaka Aura matukar basu tafiyar da kai yadda Baiwar Allah nan Hafsah ke Tafiyar dakaiba, bazaku Taba Shiryawa ba..Fada ne kawai zaku yi Tayi Domin komai suka maka zaka ga ba Daidai bane,Saboda samun mace irin Hafsah sai An Tona Hakurinta Daga Allah ne,wanda Ba kowa Allah ke bamawa ba,Su kuma matan zasu ga suna iya bakin kokarinsu baka gani kullum sai kace Hafsah tafisu Don Allah ko kai ne ya zakaji in Kana Abu ba"a gani kuma ana cewa abokim Hamayarka yafi ka iya komai..? Ka auna Abunda da Mizanin Kishi... ? Don Allah za"a zauna lafiya..? Baza"a zauna ba lafiya ba Fada ce kullum zaku Dinga yi Daga karshe ku kasa Fahintar juna ku Rabu ina amfaninshi..? Sai da na Hanaka wannan Auran kaki jin mganata..? Yanzu ina amfaninshi Aure Wata uku bai ma kai ba,an fara Jin kanku..? Wlh Duk Abun bai Yi Dadi ba Mutumina sam.."
Ya Karishe Fada Cikin Damuwa,Ajiyar Zuciya Abdullahi ya saki Yana zama Gefen Gado Lokaci Daya yake Fadin"Wlh Duka mganganunka gaskiya ne Abokina..Abaya ban Fahimci haka ba sai da nayi kuma na gani..Hakika Ba mace kamar Hafsah abokina..Zan Tauye mata Hakki maimakon Tayi Fushi sai ma Tamin Godiya zan Mata masifan kan laifin da bada gangan ta aikata ba ammh Ta bani Hakuri zan Kaurace mata Bisa karamin Abu ammh Tabini tabani Hakuri zan Hukunta ta kan laifin da ba nata ba ammh Tabini tabani Hakuri Akullum Hafsah bata Fushi mai Tsawo Dani koda kuwa me zan mata..? Arayuwarta na Hana ta Cikar Burikanta Dadama Abokina ammh Bata Taba Nuna mim wani Abu na Rashin Jin Dadinta ba ita dai Abu Daya ta sani Abdullahi Mijinta ne kuma Bautar Aure take zatayi Hakuri Dashi a Duk yadda yazo mata bakomai take Fata ba sai Aljannah Hakurinta ba irin na Mutanen Duniya bane Mutumina Hakurin Hafsah na Irin Matan aljannah ne Wlh Ina Ji ajikina Tabbas Banga mace wacce zata Iya yima Mijinta Biyayyah kamar yadda Hafsah kemin ba ta Jura Zama da Masifffan Namiji ta kuma koyo Zama dani ahaka Hakika ta Chanchanci kowani yabo na kuma na Fahimci Abunda ya kamata Tuntuni na Fahimta Nagode Mutumina..Insha Allahu zan kira Salisun miyi mgana.."Abdullahi ya karishe Fada Cikin Sanyi Jiki,Shi kanshi Nazifin Jikinsa yayi sanyi Cikin Wani yanayi yace"Duka kalamanka gaskiya ne..Nima sai bayan dana Auri Jidda na Fahimci bai kamata mu Rika ma Abu Dubar duka Daya bane..Wake Daya baya bata Buhu Duka koya aka Tsince za"a samu na kwarai Ina Nadamar Shawarwari da na Rika baka kana Muzguna ma matarka ina jin kunyar kaina ayanzu na saka ka kana Hukunta matar da bai Dace ta samu komai a wajenka ba Face Soyayyah.."Mirmishi Abdullahi yayi kafin yace"Karka Damu Mutumina..Koda Shawaranka nima da nawa Halin na Saurin Fushi da Zuciya..Ammh Insha Allahi Fushina bazai kara Tashi kan Hafsatuna ba sai dai in Cikin Rashin Sani ne.."
Nazifi yace"Dakyau Mutumina naji Dadin Haka..Sai da safe sai mun kara mgana.."Daga haka suka yanke Kiran Tagumi Abdullahi ya Zabga yana Tuna Irin Abubuwan Dayasha yima Hafsah da alherinta garesa Nadama na kara Shigansa Da kuma wani Sonta da Tsausayinta,Yana nan zaune ta Shigo ta Shimfidar da Noor,bayan Ta kada su Amira sunje sun kwanta tazo Kusa Dashi ta Dafashi ya Dago Jajayen Idanuwanta yana kallonta Cikin Mamaki tace"Abban Amira lafiyanka kuwa..? Kaga yadda idanuwanka Sukayi ja kuwa..?ko Ciwo suke maka ne..?
Ta fada Cikin Tashin Hankali Girgiza mata kai yayi Lokaci Daya ya Mike tsaya ya Rike Duka Hannayenta yana Fadin"Karki Daga Hankali ba komai..Wannan Jan ido bafa komai bane acikinsu illah Tsananin Son Matata HAFSATU da Tsausayinta Uwa uba kuma Sha"awarta Nagaji da wannan Horan naki fa Rabona dake Tun Da Cikin ki ya Tsufa bayan Kin Haihu na Daga kafa kikazo kika gama wanka kikace sai kin gama wayon arba"in kin gama kuma kika Fara jamin aji da nayi mgana sai kice kin barma Amaryani Tagama Morewa kana anya kin min Adalci kuwa..? Kinbar bawan Allah Cikin wani hali.."
Yafada yana kureta da Ido Mirmishi ta saki kawai Tana kallonsa kafin tace"Eh mana...Na bar ma Amarya kai Na wani Lokaci Tunda ai ni Tsohuwar Hannuce ko..? Ya"ya na uku fa Abban Amira..?kallonta yayi ido Cikin ido kafin yace"Zaki iya yafemin Laifikan dana aikata Miki Tun Farkon Auranmu zuwa kawo yau Hafsatuna...?
Mamaki ya Cikata ta Tsuramai Ido Tana kallonsa yadda ya marairaice mata kamar zai mata kuka bata gama mamaki ba Taga yayi kasa ya Duka kan gwiwowinsa Lokaci Daya yana Rike da Hannayenta ido ta kwalalo Cikin mamaki Take Fadin"La'ila..Meye haka Abban Amira.."Ta fada tana kokarin Dagowa yaki sai ma Fadi Daya ke.."Zaki iya yafe ma Abdullahinki Duk da yasan Shi mai Tarin laifi ne gareki..?
Yafada yana sakarmata idanuwansa masu Cike da wani Sirri wanda Hafsah ne kadai ta sani,Tuni Jikinta ya Fara rawa ganin Abdullahi Durkushe agabanta kamar zai mata kuka itama Binsa tayi ta Durkushe Lokaci Daya tana Damke Hannunsa Cikin Sanyin murya tace"A"a Abban Amira bai dace ka Dukamin ba..Ni matarkace kuma ina karkashinka..Kuma aljannata tana Wajenka Abban Amira taya zan ce kamin laifi har na iya Rikeka acikin Raina..? Ko Daya Wlh bakamin komai ba koma kamin Tun Alokacin nake yafe maka Abban Amira Nine ma zan Rokeka ka yafemin Abunda na maka Abban Amira ni yafi Chanchanta na Rokeka gafara kila Ina Kuskure maka ban..."Shiiii! Bai bari ta karisa ba yasaka Dan Yatsansa ya Dakatar da ita Tsurama Juna ido Sukayi na wani Lokaci Kafin ya Bude Baki Cikin wata Murya yana Fadin"Baki Tabamin laifi ba Hafsatuna...Nine dai mai laifin a wajenki..Kuma Daga yau nayi Miki alkawarin Duk wani laifi da zakimin da gangan ko Cikin Rashin sani ni Abdullahi na yafe miki Duniya da lahira..Kuma nayi miki alkawarin Masifaffan Mijinki zai Rikide ya koma Miki Cikakken Masoyi kuma Miji na Hakika aljannah kuma Hafsah Wlh Kin Riga da kin samu Domin Tuni na Daga Miki kika Shiga ke zaki zama Jagoran Matana na gidan al"jannah Nagode Hafsatuna Nagode kwarai Allah yayi miki albarka.."Yafada yana kara Damke Hannuwanta Jikinsa kawai ta Fada tana sakin kukanta Shima ya kamata ya kamkame yana Sakin Numfashi kamar ya saki kukan Lokaci Daya yana Bubbuga bayanta alaman lallashi.
Ganin Taki Tsagaita kukan yasa ya Dagota yana Share mata Hawaye Cikin Shagwaba yake Fadin"Wannan kukan naki nasan mganinsa... " Yafada yana Lakace mata Hanci,Saurin Zillowa tayi ta koma Kirjinsa ta lafe Shi kuma ya mike ya Dagata Cak yana Fadin"Yau ko ana so ko ba"a so sai na More Abuna.."Cikin Dariyan Farinciki tace"Balle ma ana so.."
Tafada tana Zagayo da Hannayenta saman Wuyansa ta makadesa Lokaci Daya tana sakarmai Kiss Bangare mata yayi yana mata Kukan Shagwaba Ahaka suka Shiga Tiolet ya Sauketa ya samusu Ruwan sanyi Cikin Wani Babban Bawan Hafsah da takan Tara Ruwan sama,Dayake garin ana zafi ya Tube itama Hafsah ta Tube ya Dauketa ya Tura Cikin Ruwan Shima ya Shiga Dayake Babban Baho me mai Girma,Watsa watsan Ruwa suka Fara suna Dariya kafin kuma wasan ya Chanza Salo Abdullahi yakamkame Bakin Hafsah yana Tsota gefe Daya kuma yana ta Wasa da Nonuwanta da suka Cika Sakin mata Numfashi kawai yake itama Wasa take da Nipple dinsa Lokaci kuma tana wasa da reaction dinsa wanda ta saka ya Birkice mata yana neman Shigarta acikim Bahon Dakyar ta lallashe shi ya bari suka Fito Daga bayin bayan sun yi wanka Daga Tiolet din Sai kan Gado bama wanda ya nemi kaya suka kama juna Cikin Fitan Hayyaci baka jin komai sai Tashin Numfashi Kamar zasu Cinye juna bamai Saurarama Dan"uwansa kowa kokarin Nunama Dan"uwansa yake yadda yayi kewarsa.
Kusan kwana sukayi suna Abu Daya Stayels kuwa Kala kala ba Wanda basu yi ba sun Jiyar da Juna Dadi Sosai wanda baya misaltuwa sun kuma kara yardan ma juna sun Riga sun zama Hanta da Jini,Sai Wajen 3pm na Dare suka Sararama Juna Suka je sukayi wankan Tsarki Suka Dawo suka kwanta Inda Allah ya Taimakesu Noor bata tashi ba sai gabanin Asuba Ta Fara kuka Barci ya ci Idanuwan Hafsah Dole Abdullahi ya mike ya Dauketa yana Lallashi Acikin Ranshi kuma yana Gode mata Domin ta bashi Dama ya More Dakyau.
Gabadayansu sun makara Sallar Asuba,Makaranta ma su Amira Sai wajen 8am na Safe Abdullahi ya Tafi ya kaisu yabada Hakuri Daganan ya Dawo Gida yayi wanka ya karya Sukayi Sallama da Hafsah ya Fita Zuwa Cikin makaranta Domin Allah ya Taimakeshi ya kusa gama Project dinsa,Dagachan ya wuce Wajen aiki,Wajen 2pm na Rana bayan sun Fita Sallah ya Kira Salisu yace in ba Damuwa su Hadu yace Mai bakomai gashi nan zuwa ba"a Dau lokaci ba kuwa sai gashi Suka samu wani Waje sukayi mgana sosai Salisu ya bama Abdullahi Hakuri Yace mai bakomai Dayayi mai mganar Komawan Barkat Sai Abdullahi yace ta Dakata ba yanzu ba Yana son ta ZAUNA agida Tayi koda wata Biyu ko uku in ta kara Hankali sai ta koma Ammh mganar gaskiya yanzu Baya Bukatarta Duk da bazai Saketa ba Saboda baya son ya zama Namiji mai sakin Aure ammh Tabbas ta zauna agida ta kara sanin Rayuwa da kuma yadda ake ma Miji Biyayyah.
Ba yadda Salisu zai yi ya bashi Goyon Baya suka Rabu akan Haka,awaya ya Kira Hajiya ya gayamata komai da yadda suka kare mgana da Abdullahi Hajiya tace ai yayi mata Daidai gwara ta Zauna agida Sai ta kara Hankali da Barkat Taji labari bata Damu ba tana ganin Dole ya Sauko yazo ya bata Hakuri ya maidata,Ita kanta Bahiya Da tadawo Gida Taji Labari bata Ji Dadi ba kuma itama Barkat din ta Dorama laifi tare da ankaran da ita kuskuranta ammh alokacin Tayi Nisa batajin kira.
****
*Bayan Wata Biyu..*
Zuwa Lokacin Tuni Kowa yasan Labarin Barkat bata Gidan Abdullahi,Labari har gusai Umman Sadiq dataji labari tace ai Daman ta Fada Ba kowa zata iya ZAMA da Abdullahi ba sai Hafsah.
Haka kowa yake fada in yaji Labari Subai kuwa tafi kowa Murna Hafsah kuwa bata ji Dadi ba Duk da Tama Abdullahi mganar Barkat din ya Roketa da Allah da Annabi karta karamai wannan mganar,Dole ta kama bakinta Hakika Abdullahi ya Chanza kamar yadda ya Fada,Domin Yanzu Lallaba Hafsah yake kamar Tsoka daya Amiya sai Dai Abunda ba'a Rasa ba,Fushinsa kuma yanayi Lokaci Bayan Lokaci ammh yana Controlling dinshi ba kamar baya ba Bangaran Kulle kowa Babu Abunda ya Sauya in yayi Ra"ayi Taje in bai yi Ra"ayi ba yace ya Hanata Dole ta Hanu,Bata da yarda zata yi kaifi Daya ne Dama Kuma yana nan bai Sauya ba.
Bangaran Barkat kuwa Bayan Dawowarta Gida Da Sati Uku Suka koma makaranta Tattara ta Tafi Tare da Jiran Tsammanin Abdullahi zai nemeta ya bata Hakuri,Wanda bai taba Kiranta awaya ba Itama Girman kanta ya Hanata ta kirashi ta koma makaranta da kwana Goma Jiri ya Dibeta Ranar sun Fito daga Lecture ta Fadi aka kwasheta Zuwa Clinic Din makaranta gwajin Farko sai ga Ciki ya bayyana a Gareta dan Wata uku,Yayanta Salisu tace kawayenta su kira mata ta karbi Wayar tamai Bayani Shi yazo ya Tafi da ita Tare da Takardan gwajin Cikin Barkat tafi kowa Murnan da Cikin Domim tana ganin ta samu Hanyar da Abdullahi zai zo gabanta ya bata Hakuri ta koma Dakinta Ko Domin Cikib Jikinta sai dai kuma Kash Batasan waye Abdullahi ba Koda Salisu ya Kirashi ya gayamai bai zo ba Fatan samun lafiya kadai yayi mata sai kuma 20k Daya Turama Barkat din Ta Bankinta yace na Hidimar asibiti kira ko awaya bai yi ba kuma bai je ba,Da Hajiya ma Taga Samuwar cikin Sai Take Fatan komai ya Daidaita ammh kuma Ba Tabbas Domim Tunda Barkat ta Dawo gida bai Tako Kafarsa ba sai da Hafsah ta gayama Su Mama bayan yazo ya gayamata Barkat Nada Ciki tayi kokarin Nuna mai yaje Zuwansa nada Muhimmanci ammh yayi mata Rantsuwan kafarsa bazai Taka ba Tukunnah dai Har yanzu Barkat Batayi Hankali ba in Lokacin yayi zata nemeshi da kanta Wannan Dalilin yasa ta Kira Mama ta gayamata ita kuma ta gayama Inna Abu suka Tafi Gidansu Barkat din suka Dubata,Sun iske ma Taji Sauki Hajiya Aminan tace musu ma Zata koma makaranta sati mai zuwa Karatu nata wuceta,Sauran kayan Sawanta Bahijjat tazo ta Diban mata Wajen Duka Kadan Ta Rage Hafsah na Gida sun gaisa Dai sama sama Tunda Ita Bahijjat din tana Bin Bayan yar"uwantane.
Tun Barkat na saka Ran ganin Abdullahi har ta sare Tana ji Tana gani ta Tattara ta koma makaranta Lokaci Daya tana Cigaba Da Renon cikinta,Don ma Suna Tare da Bahiya tana Taimakamata Sosai Tunda Har yanzu a wajenta Take Sukwatin.
*Wa ina Masoyan nawa ne..? Nifa ban gansu ba..? Kuna ina ku Fito mana Ina yan Gidan Janafty Shakira,Janaf Novellah 1&3,Zauren Janafty,Taskar Janafty,Ina yan Gidan Masifaffan Namiji suke..? Nasan ina da Masoya na nesa Dana kusa,Ina Masoyana masu Dogon Sharhi na Wattpad Dina..? Kuna ina Har yanzu RA'AYI NE KO BURI..? BAND 1 bai cika ba Don Allah wannan ba Abun kunyarku bane..? Na tabbata wadanda suka karanta Labarin Masifaffan Mijin Hafsatu suna da yawa sunfi Dubu da Milayan fa..? Ammh kuma ace har yanzu Janafty bata cika ko Group Daya ba... ? Anya ba Kuna son amin Dariya bane...? A"a Wlh Dariya kuke so Sauran marubuta yan"uwana suyimin kuma baku san Bayan Sallah Wani Salon labarin yazo muku a barka da Sallah ko..? Indan har ba kunya kuke so ku bani ba ina son kafin nam da zuwa gobe ko Jibi Paid Group 3 su cika na RA'AYI NE KO BURI..? ammh fa in har baku son Mutane su mana Dariya ace Tarin Masoyan Janafty bama su Son Cigabanta bane kawai masu son karuwa da ita ne..! Na Tabbata akwai wadanda ko 1k na saka Buk dina zasu Siyeshi Domin ba iya Labarina Suke kauna Suna Son Cigaba na Sosai,Ina Bukatar naga zallar kauna Ta Hanyar Siyan Littafina na RA"AYI NE KO BURI..?Kan Farashi mai Sauki ₦200 Vip ₦500 ne Don Allah in kina da kudin Siyan Guda Biyu ke Siya Daya Ki siya ma wata na kusa Dake Daya Sai Allah ya baki lada in ta karanta wannan labarin kuma ta karu Dashi,Daku nake yan Gidajena na Amana,Gidan Janaf Novellah Duka ban Cire kowa ba Ku za"a Fara ma Dariya Matukar ku kabani kunya Ina Rokon Allah ya baku ikon Siya Ya kuma sa mu Dace Duniya da lahira..Ina matukar Godiya masoyana...*
*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*
*Shakira..*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
_*Hakika Naso nayi Tuya na manta da Albasa Ina neman Dauke alkalamina kan Masifaffan Namiji Batare da na Mika Godiyata Gareta ba..Ba wata Bace Face TAKWARATA MAMAN UMMI...nagode sosai da Irin Kulawarki Gareni Allahu Ya bar zumunci Ameen..*_
*040*
"Barkat dai ta koma makaranta Tare da Jiran Tsammani Domin Ita Har yanzu har kuma acikin Ranta bata Fidda rai Da Abdullahi zai nemeta yazo ya bata Hakuri yace ta koma Dakinta ba,balle kuma Data samu Ciki sai kanta ya kara Girma Tana ganin kodomin Cikin Jikinta zai nemeta su Daidaita Ba zencen Nadama acikin Al"amarinta Balle har ta Zauna Ta gane kuskuranta nan kusa Har tayi kokarin gyarawa.
Abunda bata sani ba Shine batasan Waye Abdullahi ba yafita Taurin Zuciya ya yarda Komin Son da yake ma Mace in ta Batamai ya nuna mata kwanjinsa na D'a Namiji,Tunda Barkat ta koma Gida bata nemeshi ba sai dai Yayanta Salisu ya nemeshi da wan Babansu na Sabon gari ammh ita bata kirashi ta bashi Hakuri ba ko Wata mgana Kenan Ta na nan Har yanzu kan bakanta Girman kanta da isarta bazasu barta ta Kirashi ba Tana Jiran Shi ya Kirata ya bata Hakuri ya kuma ce ta koma,Toh yana so ya Nuna mata Tayi kuakure Babba Matukar Bata gyara Halinta ta Fahimci Gaskiyaba, zata Shekara Dubu agidansu kuma bazai Saketa ba sai yaga Karshen Iskancinta da Girman kanta.
Babu wanda bai mai mgana kan Barkat ba ammh ya nuna abarta Tukunnah Baba wada ma yamai mgana sai yace mai zata Dawo ammh ba yanzu ba Haka Daddy ma Har gida yace yazo ya Sameshi,bai ma sani ba sai Daga baya Ammi ke Fadamai Daya Nemi Abdullahin ya Dawo da Barkat din Tunda Ammi ta Fadamai Hafsah tace yayi Rantsuwa bazata Dawo yanzu ba,Toh Shima uzurin daya bashi kenan kan cewa zata Dawo ammh ba yanzu ba sai Zuwa gaba in Tagaji da zaman Gidan Rayuwa ta Horata ta kuma Fahimci Gidan Mijinta Shine Rufin Asirinta.
Dole suka kyaleshi Yayi yadda yaga Dama Tunda Matarsa ne yafi kowa iko Da ita Umman Sadiq kuwa da Inna Habiba basu Topha bakinsu ba sunce Daman sanda ya Rarumo Auransa bai Yi Shawara da kowa ba Yanzu ma Yaje chan ya karata ba Ruwansu Gwara ma Mama da Inna Abu sun saka baki ammh Abdullahi yace su Cire Bakinsu acikin mganar Barkat zata Dawo Lokacin da ita ta Bukaci Hakan,kuma Har yau bai iya Bude Baki Bayan Nazifi ya Tattauna Abunda ya Faru da wani ba gani yake kamar Za"a mai Dariya Shiyasa yayi Gum da Bakinsa kawai.. Bangaran su Subai kuwa Mariya Taje gidanta ta Tsegunta mata ita kuma ta Kira Hafsah Ta Tambayeta Shine take gayamata Abunda ya Faru wani Shewa Subai ta saki Ta Daki Cinyarta Tana Fadin"Waya gayamata Barno gabas Take don Ubanta..Ai Yaya Abdullahi sai ke Hafsah ko Ni Danake kanwarsa bana iya ZAMA dashi nayi Hakurin da ke keyi Dashi..Dama na sani wannan Auran bazai je ko"ina ba Domin bazata iya ba Karya Take Yaya Abdullahi ya wuce Duk Tunanin mai Tunani akansa Wlh.."Haka tai ta Mganarta Tana Cin Dariya Hafsah na Fadin ita bata ji Dadi ba Ta Dankara mata Zagi ta kashe Wayarta ita ta Kira Zannira Dake Kaduna ta Fadamata komai itama dai Hakan tacen Domin Yaya Abdullahi ba bakonsu bane sunfi Kowa sanin macen da zata iyi zama dashi Sai ma Hakuri Over irin na Hafsah Sun Dade suna mgana kafin Zannira tayi Allah ya kyauta su Kashe Wayar.
*****
*Bayan wata uku..*
Tafe Tafe Tun Barkat na Jiran Tsammanin Kiran Abdullahi ko Wayarsa har ta Fara Sarewa Gashi Kimanin Watan Cikinta Watansa na biyar kenan yana gabda Shiga na Shidda kenan har ya Fara Fitowa tana Shirya Shiryan Fara Zuwa awo,Allah ya Taimaketa sun gama Final Exams dinsu ta Dawo Gida ammh ba Abdullahi ba Dalilinsa Tun Makota na Dauka Abun wasa har suka Fara Zunden Barkat ta Kaso Auranta ta Dawo Gida Tun ana gulman awaje har kuma aka Fara Shigowa gida ana yada ma Hajiya Amina da mgana wannan Dalilin yasa Jininta ya Hau har sai ta kwanta a Asibiti a Dalilin Barkat din Wanda Tayi ta kuka Ammh kuma ta Kasa zama ta Fahimci gaskiya har yau har gobe laifin kan Hafsah take Dorashi ba"a kanta ba Hajiya Amina tayi Kokarin Salisu ya kara Tuntubar Abdullahi kan Mganar Barkat ammh yace bazai iya ba Tunda Har yace abarta ba yanzu zata koma ba sai ta Zauna sanda yayi Ra"ayin ta koma sai ta koma in kuma zaman ya kare Daman Haka Allah ya kaddara Dole Hajiya Amina ta bar mganar ammh Acikin Ranta tana Fargaba da Addu"an Allah yasa Kada Auran ya Tsinke gabadaya.
****
Bangaran Jidda kuwa Cikinta ya Tsufa,Haihuwa ko yau ko Gobe,Gida Nazifi ya maidota wajen Mama Dama Abunda yasa bai kawota Tuntuni ba lectures Da suka Fara ne, sai da suka samu Hutu kana ya Dawo da ita Gidan Mama ta Haihu Duk da Tun Watanin Baya ya kamallah Sabon Gidansa Su Subai dasu Hafsah da Mariya suka Gyara mata sabon Gida Aka kwaso kayanta suka Jera mata su,Gida fa yayi kyau sai wanda yagani Gini ne ginin zamani mai kyau da Tsari,Sakina kuwa Dataji Labari kamar ta Mutu Domin Nazifi ya sanar da ita Gida Mallakin Jidda ne, sai dai akwai Daki Daya na Saukarta in taje Zaria,wannan Abun yayi mata Ciwo Dama Tunda Jidda ta samu Ciki Sakina ke Cikin Wani Hali ballatana yadda taga Nazifi ya Dauki Burin Duniya da wani So da kulawa akan Cikin Jidda Shi da yan"uwansa da Danginsa Rawan kafa yake da Rawan Jiki in ka ganshi sai ya baka Tsausayi bai taba Haihuwa ba wajen Shekara goma da Auransa sai wannan karon Dole kuwa ya Nuna Murnansa afili,Sakina kuwa sai Lokacin Nadaman Hana kanta Haihuwa ya Shigeta ta koma asibiti aka Bude mata bakin Mahaifa,Domin Taji itama Tana Bukatar ta samu Ciki Ta haihu Kodomin Mijinta ya Dawo kallonta da Daraja wanda ta Riga ta Zubar dashi Tun abaya,Yanzu ta Daina Biyema kallon Rayuwar wasu kawayen nata,ta koma kallon makomar Rayuwarta,Aikin gwammati kuma ya Fara fita kanta Domin bata da Natsuwa Rana tsaka taje kano Ta Dukama Alhaji Badamasi tana kukan kan ya nema mata Transfer ta koma NTA kaduna tacigaba da aikinta kusa da Mijinta tagaji da yawon Datake Tsakanin kaduna da Abuja,Mamaki ya kamashi Sai dai Lokacin Shima bai mata gaddama ba,Domin yaga Ishara yayyin Sakina Guda Biyu da kanwarta Suna Gida Auran ya Mutu Shiyasa baya Fatan ya sake wani kuskuran da Sakina Za"a sakota itama tazo ta Shiga Layi Ita kanta Hajiyar tayi Sanyi ta Fahimci Barno gabas take Cikim Wata Daya komai ya kamallah sai dai kawai Ta jema da Nazifi Takardan Tare kuma da Rokonsa ya rakata Gidan Tibin Nta Kaduna Taje tayi Report yayi mamaki Sosai sai dai bai Nuna mata ba Shi ya kaita Tayi Reporting Ta Koma aikinta Tana Zuwa Tana Dawowa, Shi kanshi Nazifin haman sai yafi mai kwanciyar Hankali Tunda bazai ce bayason matarsa ba yana Sonta Har gobe zamansu ya Daidaita Tunda ta Roki gafaransa kuma ya Hakura da Saka Bakin Jidda ko Gidan Mama da Nazifin ya Kawota Tare da Sakinar ne Suka zo Dauke da kayan Haihuwa kamar za"a Bude Shago.
Ita kuma Maman bayan kawomata ita sai ta Nuna ya kaita Wajen Mahaifiyarta ta Haihu awajenta,Saboda Hajiya sa'a Ta Nuna mata kawaici Sosai Tana Bukatar yarta kusa da Ita Nazifi bai yi Gaddama ba Suka Tafi Harda Maman chan Chika garin Suka kai Jidda sai dai kuma Hajiya Sa"a taki karbanta tace Mama uwace gareta Har Abada Ta koma wajenta ta Haihu Dole Mama ta Dawo da ita Gida,Abdullahi Dayaji labari wannam karon dai bai saka baki ba Kowa yayi mamaki Jidda ta Dawo Gida Haihuwa ya Abdullahi bai ce komai ba Shi kuwa Daman Nazifin ya nemi Shawaransa Tun kafin ya kawota Din ya Nuna mai Haihuwan Fari tana Bukatar wani Babba kusa da ita Abdullahi yace ba matsala ya kawota wajen Mama ta Haihu bayan ta Haihu in lafiya kalau ba Wata matsala ta koma Gidanta ayi Suna ta Cigaba da wankanta ko Inna Talatu zataje Ta zauna da ita.
Haka kuwa akayi Jidda kwananta Goma da zuwa Gidan Mama Allah ya Sauketa lafiya a Asibitin Chika ta Haihu kuma Alhamdulillah Daga ita Har Jaririyar nata Suna Lafiya Dayake Haihuwan Dare ne sai Washegari Hajiya sa"a taje ta kwaasosu zuwa Gida kafin kace me agidan Mama ya Cika da yan Barka su Hafsah dasu Subai suna Ji suka Taho Su Umman Sadiq dasu Goggo Habiba ta waya aka sanar dasu Inna Abu kuwa ita ta wanke Jinjiriyae tas aka Nadeta Cikim kayan sanyi masu kyau,Jidda kuma Mama tashiga da ita Bayi ta gasata Sosai Mariya na Gida Duk da ita ake Hidima Domin tagama makaranta sunyi Final Exam suna Jiran sakamako.
Nazifi bai samu zuwa ba sai Washegari da Safe,shi da Sakina suka zo ganin Ni"imar da Allah ya basu Nazifi baki yaki Rufuwa Lokacin Daya Dauki Jinjiran ya Rumgume sai da yayi Kwallar Farinciki Nan take yayi mata Huduba, da Sunan Goggo Abu Zainabu Abu mai Tagwayen suna kowa yaji sai yaji Dadin wannan Sunan Sakina ma ta Dauki Jaririyar tana santi Kamar tayi Kuka Jidda na Fadin kema Anty Sakina Allah zai kawo naki,Subai na gefe ta tabe baki acikin Ranta tace Daga baya kenan.
Suna Gidan Abdullahi yazo Gidan Shima ya Dauki Jinjiran yayi mata addu"a Nazifi yace Sunan Inna Abu taci yace Allah ya Rayata,Nan suka barsu ya Dauki Hafsah Da yara suka koma Gida,Gidan Mama Wuni yake da Mutane yan Barka,Ana gobe suna da Zannira tazo Suka Hadu da Hajiya Lariya da Ammi,da Maman da su Hafsah dasu Subai da Jamila diyar Goggo Habiba,Umman Sadiq dai bata zo ba tadai yi sako.. Da Sakina wacce tazo Tun safe za"ayi suna da ita suka Dunguma sai sabon Gida inda za"ayi suna,chan akayi Badali ana ta Hira Subai chan ta kwana Ammh Hafsah Gida ta koma Tunda Uban gayyar bai bari ba Ranar suna kuma anyi Shagali Sosai sai wanda ya gani Jidda da Zainab zeezey sunyi kyau har sun gaji da kyau Hajiya sa"a da Danginta sunyi Rawar gani Domin akwati Guda Tayima Jidda Da ita da kayan Jaririya Mama tayi nata kokarin ita dasu Subai Hakama Gidan Inna Abu suma sunyi iya nasu Kokarin Angon Karni ma yana garin Shima Sakina kuwa Kaya tayi ma Jidda da Zeezey Abun sai wanda ya gani Anata Godiya wasu sai ta koma ma Basu Tsausayi Irin Su Zannira ammh Subai cewa Tayi ko alama bata Bata Tsausayi ba Domin Duk Abunda ya Faru da ita ita Taja.
Ko Ranar sunan ma Abdullahi hana Hafsah kwana yayi,wai Zata kwaso ma Noor Mura Dole ta Koma Gida ammh ta Bar su Amira nan Tunda su Muhsina suna nan sai Washegari ta koma Sukayi Soye suka Raba zuwa yammah kowa ya Watse,Harta Mama Gida ta koma Tun Shekaran Jiya Inna Talatu ne Daman zata zauna da Jidda Sakina kuma sai Gobe zata koma Saboda aikinta,haka suna ya Tashi Lafiya Kalau sai dai Fatan Allah ya bama Jidda Lafiyar Shayar da Zainabu wacce suke ma alkunya da ZEEZEY..!
*****
Rayuwa tayi ma Barkat kunci Domin Tafara sarewa da Jiran Tsammani na zaman Jiran Abdullahi ya nemeta taji Shuru sai ta Fara Tunanin bafa zai nemeta ba,so yake kila Har sai ta Haihu Tana Gida Hankalinta ya Fara Dawowa Jikinta Data ga ma anyi mganar Auran Bahiya da Bahijjat wanda za"ayi Rana Daya,sai ta Fara Tunanin ya kamata ta nemi Mafita bata son ta Haihu agida ko Saboda Hajiya Amina Da tadata Hankalinta sosai akan zamanta gashi ta gama makaranta ba inda take Zuwa Dole Damuwa da kunci su Taru su mata yawa.
Cikinta na Da wata bakwai ta Fara zuwa awo wanda Salisun yadauki Nauyin komai,Har kuma ga yau Abdullahi bai kara mai mgana kan Barkat ba kuma bai Tako yazo ba,Duk da sun sha Haduwa sai dai kawai su gaisa Shi Abdullahi baya mai mganar Shima Kuma Salisun yana jin kunyar Tada mganar Tunda ga yadda suka Rabu Shiyasa Shima ya Zubama Sarautar Allah ido,ko Hajiya Amina Datake cewa salisun Kirashi agayamai matarsa zata Fara zuwa awo Shi ya hana yace A kyaleshi ai yana sane Barkat din na Dauke da Cikinsa in yana Ra"ayinta Har yanzu zai waiwayeta Dole Suka zubama Sarautar Allah ido ammh Shi kanshi Salisu zaman Barkat din ya Fara damunshi Tun baya Damunshi yanzu.
Tun Cikin Barkat na Wata Bakwai Har ya Shiga wata na Takwas ba wani Labari Daga Bangaran Abdullahi sai Hankalinta ya Tashi ta Tsorata Ta Fara Tunanin ko Baya sonta ne yanzu ta sakama kanta Tunani yasa Jininta ya Hau sai da taje asibiti suna ta mata Fada bai kamata tana saka Damuwa aranta ba Tana da Tsohon Ciki Toh ya zatayi Damuwa ta zama Dole Tunda Man dinta ya Juya mata Baya bai Taba Waiwayanta ba kwatakwata.
Bangaran Abdullahi kuwa yana sane da Watannin Cikin Barkat Tun sadda Salisu ya kawomai Takardan gwajin Cikin,bai manta ba,yana ta Shirrinsa Allah ya Taimkesa Watan Shekaran Jiya ya gama Biyan Bashin Dayaci awajen aiki,ya gama Biya ba Dadewa ya samu karin Girma ya koma Office mai Girma albashinsa ya karu sai kawai ya Kira Ma"aikata ya Zube musu kudi aka Cigaba da aikin gidansa Yana son kafin Wata Biyu Su Tare acikin Sabon gida zuwa yanzu kuma yaji ya gaji da zaman wannan gidan.
Batare da sanin ko Hafsah ba yaje da kanshi yakai ma Mama kudi Naira ₦30k yace taje kasuwa ita da Inna Abu suyi Ma Barkat din Siyayyah kayan Haihuwa da ita da Abunda zata Haifa Watan gobe zata Haihu Mama Tayi mamaki Har ta kada baki Tace"Kai kuwa Yayansu kayi Hakuri ka Dawo da ita Dakinta mana Tunda dai Zuru"a ta Shiga Tsakani..!
Mirmishi yayi ma Mama kafin yace"Zata Dawo Mama karki Damu..Zata Dawo Insha Allahu ammh in ta Bukaci Hakan fa.."Mama Tace"Bukata na nawa kuma Abdullahi..? Yayanta sau nawa yana Binka Har fa wan Babanta ya Kiraka ya Rokeka ta koma Gidanka kaki yarda.."Kai Tsaye yace"Sun Rokeni ta koma Mama ban karyata ba..Ammh ita fa..? Tataba Kirana awaya ta bani Hakuri..? Bata taba ba Mama kinga kenan har yanzu tana Sha"awar zaman Gidan ne.."
Mama ta Rike baki Tana Fadin"Au..Tunda ta koma bata nemeka ba..? Kai ya kada yana Fadin"Yawuce wai Mama gashi ina Fadamiki.."Mama ta kada baki Tace"Lalle...Bata da Hankali..,sai hakuri yarinta ne ke Damunta bazata taba ganewa ba ita ko Tsausayin Mahaifiyarsu Bata ji.."Abdullahi yace"Bata ji Mama Datanaji Da Tuni Ta Dawo Gidan Mijinta..Ba wani yarinta ki kyaleta Dani Take Zencen.."
Dole Mama tayi Shuru da bakinta ammh Abun ya bata mamaki sai da ta Tsegunta ma Inna Abu,itama tace ya kyale yar iska Tunda bata da Hankali Tare sukaje kasuwa sukayi Siyayyar Kaya Da yawa Bayan sun Dawo Mama ta Kira Abdullahi tace yazo ya gani yace basai ya gani gobe su Dauka su Tafi Gidansu Barkat su kai musu,Mama tace toh washegari kuma suka Shirya ita da Inna Abu sukaje gidansu Barkat dim suka kai,Wannan kayan da su Mama suka kawo Shi ya kara Dawo da Barkat Cikin Hayyacinta Mama da bata Shuru ta saka aka Kira mata Barkat din ta kalleta yadda ta Rame sai Ido da Katon Ciki Tace"Ni kuwa y'an nan da kin Ijiye wani Abu Kin bama mijinki Hakuri yazo ya Daukeki kin koma Dakinki Kin Haihu achan yanzu ke ko Tsausayin Mahaifiyarku bakyaji Kina gida da Tsohon Ciki Haka dai gaskiya Hakan bai yi ba, ya kamata ki kira Mijinki ki bashi Hakuri ku Daidaita kanku ki koma Dakinki ki Haihu.."Inna Abu ta amshe da Fadin"Toh Karima in banda ma Rashin Hankali komai miji yayi maka ko Dukanka yayi Tunda Zuru"a ta Shiga Tsakani ai kayi kokari ka gyara auran ka koma Dakinka kada kana yaronka Dakai afara kirgamaka Aura Allah na Tuba Duk da bamu san meya Hadaku ba ammh ai girman kai ga mace agidan Auranta baya kaita ko"ina sai Nadama gwara akoma aje ayi ta Hakuri yafi zaman gidan.."
Hajiya Amina ta muskuta tana Fadin"ku gayamata kila ta jiku...Gata nan Ni da yayansu ba Abunda bamu gayamata ba ammh bata Sauraremu ba,Girman kai Daman ina zai kaita bagata nan agida ba,Shi Namiji daman har ka nuna mai ka isa bai nuna maka iyakar ka ba..Wlh yamim Daidai Dayayi Banza da ita in Tagaji da zaman gidan sai ta neman ma kanta mafita na Cire Bakina akanta Abunda ta zabama Rayuwarta Shine Daidai.."Tafada Cikin Bacin Rai Hakuri su Mama suka Cigaba da Bata Sun Jima agidan kafin su Tafi,Suka bar Barkat ta koma Daki Tana ta Kuka Nadama ya Shigeta Lokacin Daya da Som komawa Gidan Mijinta,Su Mama Daganan Gidansu Barkat din Gidan Ammi suka Biya suka gaisa kana suka gayamata Daga inda suke,Ammi tayi ta Jajanta lamarin Tare da addu"an Allah ya Daidaitasu,sun Dade sai bayan mangariba suka Tafi Bayan Ammi ta rakasu da Abun arziki.
Hafsah bata san Anyi ba Domin Abdullahi bai gayamata ba sai Washegari da sukayi waya da Ammi take cemata Jiya su Mama sunzo,Sai Hafsah tace Allah sarki,Sai Ammi tace mata Daga Gidan su Barkat suka Biyo Sunje kai musu kayan Haihu Cikin mamaki Hafsah Ta ke Tunanin Kenan Cikin Barkat din ya Tsufa Lalle ba mamaki Tunda ga Noor tana Cikin Wata na Goma ne,Abun bai wani bata mamaki ba sanin Ko Zencen Barkat din Abdullahi bayason Tayi mai kuma Tunda ya Roketa kan Haka bata kara ba ta kama Kanta ammh Tana Addu"a Duk indan Tayi sallah Allah ya Daidatasu bata son Auran ya kare Saboda ita da Zuciya Daya Ta Zauna da Barkat kuma yadda bazataso Auranta da Abdullahi ya mutu ba itama bazata so Na Barkat din ya kare ba in tayi Duba Hadisin dayace mu soma Yan"uwanmu Abunda zamu soma kanmu.
Abdullahi bai gayama Hafsah ba sai da akayi kwana Biyu kana ya gayamata,Sai ta Nuna mai Bata sani ba,Tayi kokarim tace wani Abu sai yaki bata Dama yace Tadaina Damuwa in Barkat ta Damu Zata Dawo Dakin Mijinta in kuma bata gaji da zaman Gidan ba yanzu ta Fara,Dole ta kama bakinta sanin Halin Abdullahi na kaifi Daya Da kuma Tsattauran Ra"ayi wanda bai sanshi ba shiyasa yake da Bahagon zama.
Bangaran Barkat kuwa Taga fa ba Sarki sai na Allah Hatta da Bahiya Data ke goyon bayanta yanzu ta Daina Shawara suka Hadu suka suka bata kan ta Cire wani Girman kai da isarta ta Kira Abdullahi Ta bashi Hakuri su Daidaita kansu,Tunda dai ta Riga ta Fahimci Girman kai da isa bazasu Sata Cin wani Riba agidan Auranta ba,,Wajen Sati Daya suna Ta Kokarin Bata Shawara,ita kanta Barkat din an kawo Gabar da bazata iya Jurewa ba Dole ta ijiye wannan Girman kan nata da isarta ta Kira Abdullahi Lokacin Wajen 10am na safe ne yana wajen aiki Lokacin Daya ga Kiranta Dariya ta kusa kamashi sai ya kanne ya Murmusa afili ya Furta waya gaya miki Borno gabas Take yarinya..Wlh bamai iya Ja da Abdullahi sai Allah Daya Hallicesa.
Yana gani Tana ta Kira ajere ajere yayi mata Banza sai ma ya saka wayar a Silent Hankalin Barkat ya Tashi ganin bai Daga Kiranta ba Su Bahiya suka kara lallashinta kan ta Cigaba da Kira Ranar Wuni tayi Kiranshi Har ya tashi aiki Daya Duba Adadin Kiran 76 missed calls Tayi mai Kai ya Girgiza acikin Ranshi yana Fadin yanzu kika Fara Har ya koma Gida bata Hakura da Kira ba,Tun Hafsah na Shuru Hardai tamai mgana kan wake Kiranshi Baya Dagawa sai yace mata wani Dan Rainin Wayau ne taa kyaleshi ya Cigaba da Kira jin Haka yasa ta kama bakinta kuma Har Acikin Ranta bata kawo Barkat bace ballatana ta iya wani Abu akai.
Wasa Farin Girki Wajen kwana uku Barkat ta jera kullum sai Tayi ma Abdullahi Over 100 Missed calls Baya Daga Kiranta Taci kuka Sosai su kansu su Bahiya masu Tausanta sun Sare wannan karon,Bahijjat ce ta kawo Shawaran Kiran Nazifi abokinsa Sai Barkat tace bata da Lambarsa Bahiya tace ta Kira ya Salisu baazai Rasa ba Haka kuwa akayi Barka ta Kira Salisu tace ya Turamata lambar Nazifi Tunda yaji Haka aranshi yace Tagaji da zaman Gidan kenan bai Ce komai ba ya Tura mata Ta Kira Nazifi,Lokacin Da Daddare ne baya gida ya Fita masallaci Jidda ce ta Daga Kiran Dayake Watanta Biyu ta koma Kaduna Saboda sun koma makaranta Tare da Inna Talatu suka koma Saboda kula da Zeezey Tunda Sakina na Zuwa Wajen aiki Weekend ne kadai suke zama agida.
Lokacin da Jidda ta Daga Kiran bata gane Barkat bace ta Dai gayamata Yana masallaci Suka Rabu kan in ya Dawo zata gayamai Daya Dawo sai ta manta sai zuwa chan ta gayamai An kirashi kuma Koda ya Duba ganin baisan mai lambar sai ya Share gashi kuma Dare yayi,sai da safe Barkat ta kara Kiranshi Lokacin yana wajen aiki sai da tayi mai bayanin kanta kana ya ganeta Tana kuka Tana Rokonshi kan ya saka Baki Abdullahi yazo ya Dauketa ta gaji da zaman Gida Hakanan ta Kirashi yafi sau Shurun masaki bai Daga Kiranta ba,Nazifi yayi ta Lallashinta ya kuma yi mata alkawarin zai Kirashi yayi mai mgana Suna gama mgana ya Kira Abdullahi yamai mgana ya gayamai yadda Sukayi da Barkat din,Dariya Abdullahi yayi har ya ishesa Kafin yace" Shi Daman bai ce bazata koma ba Daman ya bari ne ta zauna agidan sai ta gaji ta Nemo Taimako Don kanta Tunda yanzu Ta gane kuskuranta Shikenan ammh da Sharadi sai ta Kira Hafsah ta Roki gafaranta kan Ce mata Datayi munafuka Nazifi yayi kokarin Abdullahi yabar mganar kiran Hafsah Ammh ya Rantse sai ta Kira Dole ya kira Barkat din ya gayamata yadda Sukayi da Abdullahi ba Gaddama tace Taji Zata Kirata ta bata Hakuri.
Ranar Hafsah na Kitchen Tana Girki Taga Kiran Barkat din Taji mamaki Bayan ta Daga Sun gaisa Tatambayi yara Cikin Sanyin Murya ta Fara bata Hakuri kan Abubuwan da suka Faru Dagajin muryanta Kasan Tagama yin Laushi Cikin Tsausayawa Hafsah tace mata karta Damu bakomai Ita Daman Bata Taba Rikonta Ba ta yafe mata Har gaban Abada Barkat din Ta Dinga mata godiya gwanin Ban Tsausauyi Sai da Hafsah tayi mata kwallah Tana Tsausayinta ga Ciki ga Damuwa.
Bayan ta Kira Hafsah sai ta Kira Abdullahi Tagayamai ta Kira Hafsah din,sai yaki Daga Kiran ,sai kawai ta Turamai Dogon Sakon Ban Hakuri da kuma Tabbatar mai data Kira Hafsah ta bata Hakuri Daya gani bai Damu Daya Kira ba sai da ya Dawo Gida ya Tambayi Hafsah ta Tabbatarmai Data Kirata ta bata Hakuri kana ya yarda sai da safe kana ya Tura mata Sakom ta Shirya zai zo ya Tafi da ita yau da Daddare.
Da Barkat Taga sakon Abdullahi kamar an Gafartamata Zunubinta Tana ta Murna da Farinciki Data gayama Hajiya Amina Itama sai da tace Alhamdulillah Jin Haka yasa ta Kira Salisu ta gayamai yace Ta isa Barka sai yace ta Tura su Bahiya su Gyara Dakin Barkat din Tunda ya Dade akulle Yayi kura gashinan zuwa Haka kuwa akayi Bahiya da Bahijjat suka je Gidan Dama Barkat ta basu makullin Dakin Suka gaisa da Hafsah suka ce mata sunzo gyarama Barkat Daki ne Hafsah Taji Dadi Sosai Burinta ya Cika Tunda Allah ya Daidaita komai,Sun Gyara komai sun Share Dakin sun goge sun wanke mata Toilent da Sauran kayan Kitchen dinta da sukayi Kura Dama Hafsah bata amfani da kayanta Da nata take amfani Tunda Itama Babu Abunda ta Rasa na Bangaran kayan kitchen wasu suna Daki Cikin kwali Bata Fara amfani Dasu ba Sai Sun Koma Sabon Gida.
Sai Wajen yammah suka bar Gidan Bayan sun ma Hafsah Sallama Suna Tafiya Abdullahi ya Kirata yana Gayamata Dawowar Barkat din tace Eh yanzu kannenta suka Fita sun Zo sun gyara mata Daki karamin Tsski kawai yaja ya kashe Wayar,Ita kuma Barkat koda su Bahiya suka Koma Ta Kira mai Kitso ta Rangada mata Kitso Har kunshi Tayi yayi kyau bakinta yaki Rufuwa Sai Murna Take ko kafin Bayan mangariba Barkat ta gama Shiryawa Cikin Wani Less Dinki Buba Tayi mata kyau ainun Taci kwalliyarta Sai dai Cikin yayi mata Cikas,Su Bahiya suna ta Daukanta Hoto sai ga Yayansu Salisu yazo Ya katsesu yakira Barkat Dakin Hajiya Amina suka Tasata atsakiya Suna Mata Nasiha Salisu yaja kunnanta Sosai ya kuma Gargadeta in ta kuskura ta karayin wani Rashin Hankali sai dai ta nemi wani Gidan ba dai nam ba Bazata kashe musu Uwa ba Barkat na kuka tamai alkawarin Insha Allahu Bazasu kara Kuka da ita ba,sun Ji Dadin haka Hajiya Amina nata sakamata albarka.
Abdullahi kuwa Sai da ya Tashi Daga aiki ya Dawo Gida yayi wanka ya Chanza kaya kana yaci Abinci,Bada mashin Dinsa yaje ba Keken napep ya Hau ya Tafi Gidansu barkat din wanda wannan Shine karo na Farko Daya Taka kafarsa bayan Komawar Barkat din Har Ciki ya Shiga suka gaisa da Hajiya Amina Tana ta godiya da kuma Rokon Hakuri Yace mata bakomai,Bai jima ba yace Barkat ta Fito su Tafi,su Bahiya suka Fito mata da kayanta,Sai ita ta Fito Daga Baya yana Bakin Adaidaitanta yana Kallonta Tana Tafiya da katon Cikinta su Bahiya sun rakota kare mata kallo kawai yake ganin Duk Ta Rame itama sai kallonsa Take Idanuwanta na Cika da Hawaye na kewa da Nadama mai karfi Bai Tankata ba ya Shige Adaidaitan itama ta kama ta Shiga Su Bahiya na Daga musu Hannu suka bar Kofar gidan.
Har suka kai gida Abdullahi bai Tanka ma Barkat ba Ita kuma kunyan mai mgana take ji kanta na kasa ne,Sai da suka kawo bayan ta Fito Daga Adaidaitan Shima ya Fito ya Fito mata da akwatunanta,ya Biya mai adaidaitanta ya wuce Shikuma ya saka Hannu zai Dauki akwatunanta Guda Biyu tayi Saurin Rikomai Hannu Tana Wani marairaicewa Waigowa yayi yana kallonta Cikin Muryan Tsausayi da Nadama Tace"Afuwan My Man....Plz..!
Ta Fada Lokaci Daya Tana kallonsa,Bai ce mata komai ba ganin Haka yasa ta saki Hannunsa ta kama kunnuwanta Duka Biyun Tana Fadin"Ka yafemin Don Allah...Nagane kuskurena..! Tafada hawaye suna Zubomata Da sauri ya Riko Hannayen nata yana Girgizamata kai Lokaci Daya yana Fadin"No..Is ok..Ai kin gane kinyi kuskure ko..? Kuma kin Fahimci inda kike kuskure kin Dawo da niyyar gyara ko..? Kai ta gyadamai tana Zubar kwallah Hawayenta ya Share mata yana Fadin"Karki Damu..Komai ya wuce Yanzu mu Fuskanci sabuwar Rayuwa kawai.."Saurin Rumgumesa tayi tana mai Godiya shi kuma ya Riketa yana Bubbuga Bayanta alaman Lallashi.
Shi ya Dauki Akwatunan da Hannayensa Guda Biyu,Suka Shiga gidan Tana Binshi abaya,Sai Dai Hafsah Taji sallamansu Ta Fito Daman su take jira ita da Su Amira ganin Barkat din suka Nufeta suka Rumgume suna Oyoyo Ga Anty Hafsah baki yaki Rufuwa tana Rike da Noor ta karisa ga Barkat din Tana mata sannu da zuwa ta amsa Cikin kulawa ita ta Riko Hannunta Har Dakinta,Shi kuma Abdullahi ya Bude Dakin Barkat din ya Shigar mata da kayanta kafin ya Dawo Dakin Hafsah din ya iskesu suna gaisawa da Hafsah din,Nan Barkat din Taci Abinci kana Hafsah dasu Amira suka Rakata Dakinta,Basu Dade ba ta mata sai da safe ta Taro su Amira suka Dawo Dakinta Suka Iske Abdullshi yayo wanka ya Sauya kaya zuwa Jallabiya,Bai zauna ba yama Hafsah sallama ya Tafi Dakin Barkat din Chan ma Dayaje Duk Rokon Bam Hakurin ne yace mata bakomai komai ya wuce Shi ya Taimakamata tayi wanka ta gasa Jikinta Suka kwanta Barkat din Ita ta taja Abdullahi da Salonta har ya Biyemata ammh da Farko yana jin Tsausayinta Shiyasa bai nemeta ba ammh ganin ita tana Bukata sai ya saki Jiki suka Raya wannan Daram.
Babu Wanda yasan Dawowar Barkat sai Data kwana Biyu Da Dawowa kana Mariya tazo Gidan Ta ganta ta koma ta gayama Mama,Mama ta nuna jin Dadinta sosai da Subai taji labari tace bata so Haka ba Hafsah tace Wlh ko Daya ai yanzu Tayi Hankali Zuwanta Gida yasa ta kara sanin Waye Mijinta kowama Dayaji ta Dawo sai yace kila yanzu za"a zauna Lafiya Tunda an Gogi jigidan Juna Illai kuwa Domin Barkat kamar ba ita ba Tayi bala"in Sanyi Tsakaninta da Hafsah kuwa sai dai girmamawa Kishinta kuma ta kaishi karkashin Ranta ta Boye ta sadda kai tana Bin yadda Hafsah din ke tafiyar da Abdullahi.
*ASSALAMU ALAIKUM BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA MASOYANA MASU KARATUN LITTAFIN MASIFAFFAN NAMIJI...NAJI WASU MGANGANU NA YAWO WAI NI NACE BAZAN KARISA MASIFAFFAN NAMIJI BA YA KOMA NA KUDI..? WASU HAR SUNA FADIN MAGANGANU MARASA DADI AKAN HAKA TOH BARI KUJI NA GAYA MUKU TUN KAFIN NA FARA TSARA LITTAFI ZAN FIDDA NA KUDI ZANYI SHI KO FREE KUMA IN NA FARASHI BANA SAUYAMAI ALAQA,MASIFAFFAN NAMIJI TUNDAGA FARKONSA HAR KARSHENSA FREE DAMA NAYI NIYYAR YINSA KUMA RA"AYINA BAI SAUYA BA,AM JUZ JOKKING DANACE ZAN HADESHI DA RA"AYI NE KO BURI MU HADE A PAID GROUP,AMMH WASU SUN MIN MUMMUNAR FAHIMTA SUNA TA FADAN ABUNDA YAZO MUSU ACIKIN RANSU WASU KUMA SUNA TA BULAYIN CIGIYA NE,TOH ABU DAYA ZAN CE KO 10K KU KA SAKA KUKA SIYA LITTAFIN RA'AYI NE KO BURI..? BA KU BIYANI ADADIN WAHALATA BA WLH BALLATANA WATA #200 WANDA BAZATA KARA MIN ARZIKIN DA NAKE DASHI BA MASIFAFFAN NAMIJI LABARINA NE KUMA NI NAKE RUBUTASHI BAN TABA FARA LITTAFI BAN KARISA SHI BA WANNAN MA SAI NA SAUKESHI DA YARDAN ALLAH,IN MUTUM NA RA"AYI YA SIYA PAID BUK DINA IN BAYA RA'AYI YA BARSHI BA"A DOLE NIDAI ABUNDA NA SANI NAUYIN DAKE KAINA ZAN SAUKESHI KUMA HANNUN DAYA RUBUTA MASIFAFFAN NAMIJI SHI YAKE RUBUTU RA'AYI NE KO BURI SO DUK DAYANE AWAJENA INA GODIYA MASOYANA WADANDA SUKAYI TA PAYMENT DOMIN NUNA MIN KAUNARSU WADANDA KEDA NIYAR BIYA ALLAH YA BASU IKON BIYA WADANDA BASU DA NIYYAR BIYA SUMA ALLAH YA BASU IKON KARANTA FREE DIN IN MUNYI RAYUWA BA TILAS KUMA BA DOLE SAI DAI BAN JI DADIN YADDA WASU SUKA KASA FAHIMTA TA BA..*
*Janafty...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*
*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!
~Alhamdulillah...Dukkan Godiyata Ta Tabbata ga ALLAH shugaban Halittun Duniya...Salati Tare da Rahma Gafara Aminci Su Tabbata ga Annabin Rahma Annabi Muhammad Sallalahu alaihi wasallam Shida Iyalansa da Sahabansa gabadaya..~
*041*
Tunda Barkat ta Dawo Gidan bata kara yarda Tayi zaman Dakin data saba abaya ba,Tun Safe Zata Fito Bayan ta Gyara Dakunanta,Tafito tace Tana so Ta karbi Wani aikin ta Taya Hafsah ita kuma Hafsah sai taki Bata Daman Tun Dawowarta Tace mata Sai ta Haihu ta gama Jegonta kana zata bata Girki ammh Kwanan Miji yana nan ayadda yake in ya kwana Biyu Dakin Hafsah,Sai ya koma Dakin Barkat din ya kwana Biyu,Bai saka musu baki ba sai da Hafsah Ta nemi Daya koma kwana Dakin Barkat da kwana Gabadaya Saboda Tsohon Cikinta gashi kuma Haihuwan Fari kada wani Abu ya taso ba kowa a kusa Da ita.
Lokacin da Hafsah ke Fadamai Haka yana Zaune a kasan Cafet Dinta ne ya Tankwashe kafa yana Cin Tuwon Semo miyar kubewa Bushashiya wacce Hafsah Ta Dafamai Da Daddare,Ita kuma Tana Gefensa Zaune Rike da Noor tana bata Nono Amir da Amira kuma Suna Dakin Barkat tun Dazu Chan ma Sukayi Sallar mangariba Yanzu Chan suke zama Tunda Taja yaran ajiki Sosai.
Yana kai Lomar Tuwo bakinsa yana kallon Hafsah a karkace Gefe Daya na Cikin Zuciyarta Najin Haushin Shisshigin Hafsah na Wani Lokacin..Ina Ruwanta..? Waya aiketa Shiga Hurumin da ba nata ba bai gama mamaki ba ta katseshi da Fadin"Har ma Dazu nake ma Barkat din Zencen tadai Nuna min ba komai ammh ai nima Mace ne nasan Yanayin,kaga kuma Haihuwar Fari ce Gwara asamu wani kusa da ita Tunda bamu san Wani Yanayi Haihuwan zata zo Dashi ba Gashi kuma kai ba barinta Zakayi ta koma Gidan Gaban Hajiyarsu ta Haihu ba ko Zaka barta ne..?
Ta fada Tana kallonsa Mamaki ya kara kamashi bai samu Zarafin mgana ba sai da ya Koshi da Tuwon kana ya Ture Kololin gabansa yaja Roban Wanke Hannun Dake gabansa ya Wanke Tas ya saka Tissue ya Goge Bakinsa Tsaf kana yayi Gyatsa Lokaci Daya da Hamdala yana Fadin"Alhamdulillah..."
Yafada Lokaci Daya yana Mike kafa,Kansa ya jinginar kan Hannun Kujera Lokaci Daya yana Balle Botorin Rigan Shaddan Dake Jikinsa Dama Yana Shigowa da yunwa ya Dawo Abincin ya Fara ci kafin Wanka, Hafsah Ta Karkace kai Tana Fadin"Baka ce komai ba Abban Amira..Ina ta mgana..?
Waigowa yayi yana kallonta kafin yace"Na"am kika ce me..? Ban ji bane..! Ya fada yana Zabga Hamma Galala Hafsah Tayi Tana kallonsa Kafin tace"Kai Abban Amira yanzu Duk mganganun da nagama yi baka Jini ba..? Kai ya gyada mata yana Fadin"Ban ji ba sake maimaitawa.."Baki Hafsah kawai Ta Gimtse Ta Cigaba da Noor Nono ammh ta bata Ranta Sai Abun ya bamaa Abdullahi Dariya,Ganin yadda Hafsah Tasha kunu sai ya Matso Kusa da ita yana Fadin"Meye kuma na Fushi Hafsatun Abdullahi..? Uhmm gayamin yanzu ina Sauraranki kisan Dazu Ina cin Abinci Kuma kinga ba kyau ma kana Cin Abinci kana mgana..! Yafada yana Sosa Sajensa Cikin Dariyan Dayake ta Dannewa
Jin Haka yasa ta waigo ta kalleshi Tana Koramai Jawabin Da tayi mai Tun Farko,sai da takai aya kana ya Dage mata Gira yana Fadin"Duk wannan aikin waya saka ki ko waya aike ki..? Hafsah tace"Bangane waya aike ni ba Abban Amira gani nayi Hakan ne ya Dace kada ace mun kyaleta ita kadai.."Karamin Tsaki Yaja yana Fadin"Ace mana..Waya Damu..? wanda yaga an kyaleta yazo ya Taimaketa mana..ke banda ma Tsabar Saka ma kai Wahala da kuma aikata abu ba"a saka ka ba Ni kin yi mgana Dani nace Miki Eh na yarda..? Bafa ki min mgana ba ammh Har kinje kin ma Barkat mgana,ai Tunda kinyi gaban Kanki kin kyauta ammh Nidai bada yawuna ba ban kuma amince ba..Raban kwana ne da kukayi zan Dinga kwana Bibbiyu dakin kowaccenku kamar yadda kuka Tsara Mganar kuma Wani Abu ya Faru Allah ke Tsarewa kuma ga waya Cikinmu Duk wanda ta Kira zai kai mata agaji,Bana son Mganar da bazata yuyu ba..!
Yafada yana Daure Fuska Kwabe Fuska Hafsah Tayi Tana Fadin"Haba Abban Amira...b..."Bana son Wani mgana Don Allah ina Ruwanki wai da ita..? Malama kiji da kanki kawai Mganar kuma ko zata koma Gida ne,ta Haihu ki Tambayeta indai tana son komawa Fine ni bani da Matsala...'Yafada yana Mikewa Cikin Mika Hafsah ta Bishi da kallo Ta kasa mgana kafin ta kada kai tace"Shikenan Tunda Haka kace...Ammh Ban ji Dadin yadda kamin Wannan Fahimtar ba.."
Shima kai Tsaye yace"Nima ban jin Dadin yadda kike yanke min Hukuncin batare da Sanina ba..Ki Tsaya iya matsayinki kawai malama mganar kuma Taya kwana nidai ga Abunda nace in kinga Zaki iya Taimakawa malama Hafsah sai Duk Ranar girkin ki ki Rika Tafiya Dakin Barkat kina Tayata kwana Fakat.."Da mamaki Hafsah Tace"Kai kuma fa..?
Yana Mirmishin Mugunta yace"Ina Inda ya Dace mana...Domin ba inda zani ki Tafi Dakin Wata Taya kishiya kwana Ki kwana Cikin Tsinuwan mala'iku Domin nidai bada yawuna aka Tafi ba Atoh.."Daga haka ya Shige Cikin Bedroom din yana ta Fada da kallo Hafsah ta Bishi kafin ta kadai kai ta Mike Tana Rike da Noor wacce tayi Barci Ciki ta Shiga Itama ta Shimfidar da Noor Daidai Lokacin da Abdullahi ya Leko Daga Ban Daki yana Fadin"Ina Ruwan zafin... ?ko baki saka bane naga Kittle din bakomai..!
Ko kallonsa Hafsah batayi ba Cikin Kufuluwa tace"Zan saka kenan suka Dauke Wuta...Sai dai in na Dafa maka a Gas.."Tafada tana kokarin Ficewa Daga Dakin,baki ya Rike yana Fadin"me yayi zafi..? Barshi zan yi da Ruwan sanyi ni ba bakon zafi bane..Ammh fa Dole akamin ba Daidai ba Zan Fada.."Yafada yana Komawa Cikin Toilet Din Lokaci Daya da Rufo Kofa Hafsah najinsa ta Fice tamai Banza Sanin Halinsa Tunda ya kuma Turtse Shikenan kuma.
Dakin Barkat ta Shiga ta iske Amir yayi Barci Amira ce Kadai Batayi ba Suna ta Hira da Barkat wacce Take zaune ga Katon Cikinta wanda yayi kasa alamun Haihuwa ko yau ko gobe,Sannu Hafsah Tayi mata kana ta kama Amir takai shi yayi Fitsari takai Daki ta kwanta kana ta Dawo tace Amira taje ta kwanta sai da Amiran ta Fita kana Hafsah tayi ma Barkat Zencen yadda sukayi da Abdullahi Mirmishi kawai Tayi kafin tace"Dama fa naji ki ne kawai Anty Hafsah..Bakomai kamar yadda yace ga waya In naji wani Abu zan Kira Insha Allahu.."
Hafsah dai Duk Taji kunya Ta Dade Dakin Barkat din Har wajen karfe goma kana ta mata sai da safe ta Fice zuwa Dakinta,Sai da ta kulle kofarta ta kashe Duka Wutan Dakunan ta leka Dakin Su Amira ta gyara musu kwanciya tayi musu addu"a kana ta Shiga Bedroom dinsu ta iske Abdullahi har yayi Barcinsa bai Jira ta ba Bata damu ba Tunda Itama Taji Haushin yadda ya Nuna mata iyakarta Ta Fada Tiolet tana Jin Takaichin Abun Har Cikin Ranta.
Shi kuwa Bangaran Abdullahi ya Yi ma Hafsah Hakane Domin ta Kiyayeshi,In yana kyaleta gaba Sai Ta Rika bashi ma Umarni yana Bi,wani Lokacin Wajen Tsausayinta Cutar dashi Take bata sani ba,Shiyasa ya Taka mata Burki Tun yanzu kafin abun yayi gaba kuma ya kasa Controlling din Abun.
Washegari Haka Hafsah tatashi Tana wannan Fushin Abdullahi kuwa bai bi ma ta kanta ba ya nuna mata ma bai san Tanayi ba Dole ta Tattara Fushinta ta watsar ta saki ammh Duk da Haka bata Dandara ba Ranar da Daddare bayan ya Daawo ta kara Zuwar mai da mganar Yayi ma Hajiyarsu Barkat mgana Ko Kanwarta Data Dawo Gida Aina Aba Barkat din ta zauna mata kafin ta Haihu Tunda ta Dawo Gida Ta gama Candy,Abun sai ya koma Bashi Dariya da Tsausayi da wani kaunar Hafsah Acikin Ranshi Yana Tunanin samun Mata masu irin Zuciyanta ba, sai an Tona bai mata gardama ba,Yace zuwa gobe zai je gidan yayi mgana da Hajiyan Amina Hafsah Taji Dadi Sosai Tayi tamai Godiya Shi kuma ya Fanshe da cewa Sai ta Bashi Tukwaici,hakanan ta Saki Jiki ta bashi Abunda yafi so aduk Duniya ya kwana yana Moran Abunsa.
Washegari bayan ya tashi Daga Wajen aiki ya Nufi Gidansu Barkat ya samu Hajiya Amina ya Roketa alfarman da basu aron Aina Saboda ta Rika Taimaka ma Barkat din,Hajiya Batayi Gardama ba ta amince Daman Barkat din na Ranta Bai baro Gidan ba sai da Aina ta Hada kayanta ya Daukota suka Taho Tare sai dai Barkat ta gansu kwatsam Tayi ta Murna tana ma Abdullahi Godiya yace ta Godema Hafsah Domin ita ta kawo Shawaran ya Dauko mata Aina Din Lokacin Daya Fada mata Haka taji wani iri Ammh sai ta Danne Bata nuna ba tabi Hafsah Har Daki Tayi mata Godiya ita kuma Sai ta nuna bata ji Dadin yadda Abdullahi ya Fadama Barkat din komai ba,Har sai da ta gayamai Cikin Gatse yace"Toh karya zan yi..? Ke fa kika Kawo Shawaran kuma nayi aiki da ita Banga wani Abun mgana ba Mata dai bakwa Raina Abun Tsegumi..! Jin yace Haka yasa ta kama bakinta ammh ta sani Har ga Allah ba macen da zata ji Dadin Irin Abunda Abdullahi yayi ace Mijinka bai da Tunanin Dauko wacce zata taimaka maka sai Kishiya ta Bada Shawara hakan bai Dace ba ammh Dayake Abdullahi Audu ne Dole ta kama Bakinta ita kanta Barkat bata isa ba Domin Yanzu lallabashi Take bata Fatan Abunda ya Faru da ita ya kara Faruwa akan wata ma bama ita ba.
****
Zuwan Aina da kwana Hudu Barkat ta Haihu,Wanda Haihuwar ta Rana ce,Ranar laraba Abdullahi baya Gidan yana Wajen aikinsa Hafsah ne kadai agidan sai Mariya Datazo sai Aina sai ita Barkat din Tun Safe ta Fara Jin Ciwon mara batayi mgana ba sai da Abun yayi yawa Lokacin Har ma Ta Fara ganin wani Ruwa Ruwa na Binta,Sai ta kira Aina tace ta Kira mata Hafsah ita kuma Bayan ta Kirata Tazo tagani sai ta Fahimci Haihuwa ne Ta Daga waya ta Kira Mama ta gayamata ita kuma tace Gatanan zuwa.
Ba Dadewa sai ga Mama tazo Gidan da Farko Asibiti Hafsah tace su Tafi Har ta Hada kayan Haihuwan waje Daya sai dai kuma Allah ya kawo Abun da Sauki,Mama na zuwa Taga Haihuwan tazo Har Faya ta Fashe,Cikin kankanin Lokaci Mama ta Gyara ma Barkat din Kwanciya tana ce mata tayi Nishi Minti Talatin suka Dauka Barkat ta Haifi yarta mace Jajir da ita mai kama da Uwarta ta sak,Hafsah na Gefen Mama Duk da ita akayi Gumurzun Harda yi ma Barkat din kwallah Saboda Tsausayi Don ma Allah ya kawo mata da Sauki,Mariya dake Rike da Noor da Su Amira da Aina Suna Dakin Hafsah Cikin Zullumi Sai da sukaji Kukan Jaririya kana Suka Sauke Numfashi nan da nan Hafsah ta Fita ta Saka Ruwan zafi,Gefe Daya kuma ta Fito da kayan Jinin Da Barkat ta bata Duka ta wanke ta Shanya,Mama kuma ta juye Ruwa Ta wanke Jaririya Tas Hafsah ta Shiryata Cikin kayan Sanyi masu kyau Ruwan Zamzam kadai Hafsah ta bata Wanda take bama Noor Bayan nan kuma Mama ta Shiga da Barkat Bayi ta mata wanka ta gasa mata Jiki Sosai Gefe Daya kuma Ta Ganin kokarin Barkat Da bata nuna Raki ba ga kuma Saukin Allah a haihuwan Fari ko kari Barkat batayi ba,Wankan da Mama Tayi mata ko Hajiya Amina Abunda zata mata kenan ita kanta Barkat din ta sani Zuwa yammah Sun gama Gyara komai Daki sai Tashin kamshi Maijego na kame kan Gado Ta gama Shan Tea din da Hafsah ta Hada mata ta koma ta kwanta Tana Jin Zufa na yankoma ta Jaririya kuwa Tuni ta samu Barci Taji iskan Duniya.
Su Mariya kuma Suna waje Suna Girkin ganin aiki yayi ma Hafsah yawa,Allah yasa ma ga Mama,Kafin zuwa Dare Haihuwan Barkat ta isa kunnuwam Wadanda suka Kamata Bahiya da Bahijjat koda suka zo sun iske Hafsah Cikin yanayi mai kyau Suna ta mamaki nan take gaya musu Kokarin na Hafsah ne da Mama Su Subai da Zannira da Jidda Duk Mariya ta Kirasu ta Fada musu suka ce Allah ya Raya sai sunzo Abdullahi kuwa sai dai yaDawo Gida yaji kamshin Masu Jego Cikin mamakin komai Ya Shiga Dakin Barkat din ya Dauki Jaririyar yayi mata addu"a Da Huduba nan take ya Shaida Sunanta Habiba,Ita kuma Barkat din yayi mata sannu Mama kuwa nan take ta Kira Goggo Habiba ta mata albishir din tayi takwara Cikin Farinciki Tace Sai tazo Domin wannan Zuwan na Musamman ne.
Bahijjat ce ta kwana Bahiya Gida ta koma washegari sai gasu Matar yayansu Salisu da matan Wan Babansu,Ammi ma tazo Sai Dare Tatafi Tunda Mama na nan bata koma ba,Sai Washegari ta koma Gida Bayan Inna Talatu Tazo ta karbeta,Dama Ta Dawo Tunda Nazifin ya neman ma Jidda Nanny da zata Dinga kula da Zeezey din saboda karatunta.
Dangin barkat sai Godiya Suke na irin Hidiman da Hafsah da yan"uwan Abdullahi sukeyi kam Barkat din Hajiya Amina ma Ta Kira Mama tana ta Godiya,Subai ma tazo Tayi barka Hatta Jidda ma Tazo Ita da Zeezey dinta Data Fara wayau da Sakina,Zannira kuma tace sai Suna Hajiya Sa"a ma ta Leko Gida Dai kullum acike Inma Abu kam nan take wuni sai Dare take Tafiya Umman Sadiq dai ta Kira waya tayi ma Barkat din Barka Domin Bazata samu Zuwa ba tace,Sai ana Gobe Suna Abdullahi ya kai Barkat asibiti aka Dubata ita da Habiba wacce su Mariya suka ceza"a Rika ma alkunya da AYMANA..!
An Dubasu an Tabbatar da komai lafiya mangungunan karin Jini aka Rubuta ma Barkat Din,Suka Siya acikin Asibitin kafin Su Dawo Gida sai da ya ijiyesu gida kana Ya wuce wajen aiki,Sai zuwa yammah sai ga Auwal da kayan Abinci Niki Niki na Suna da Raguna guda Biyun inji Abdullahi,zannira ma alokacin Tazo Dama Subai Tana Gidam Ita dasu ya"yan Inna Abu kannen Nazifi,sai yan"uwan Barkat din Su Matar salisu da matan wan Babansu dasu Bahiya Sai Hafsah Da makotamsu aka Hadu ana ta Sha"ani Dinkin Suna Abdullahi ya kara musu Leshi da Atamfa ita da Barkat,Ranar suna Sai ga Goggo Habiba,Tun kuma Safe aka yanka Raguna Sukayi Abinci Kowa yayi wanka aka Sha Kwalliya anyi Hotuna Harda Kidan kwarya wanda Subai ta Buga su Mariya suka Chase,sai kuma Data gayyato mai Jego da Hafsah ta kida musu Kidan Kishinmata suka Rausayawa Abun sai wanda ya gani,Abdullahi dai gidan Mama ya koma kwana Dakin Auwal Nazifi kuma ya Tasashi Da Dariya Bai zo ba yadai aikoma da maijogo da Sako Shi da matansa washegari kuma Zuwa yammh kowa ya watse bayan Sun gama Soyensu suka Raba bayan Sun Tambayi Hafsah Tsarin Rabon ta gaya musu Harda Turmin Atamfa suka bama Mama da Inna Talatu Suna Godiya Domin Kowa yayi Bajinta su Subai su Zannira kowacce Tayi Turmi da Rigan yarinya Hafsah ma Haka Goggo Habiba ma Haka Abun sai wanda ya gani,Koda Abdullahi ya Dawo Gidan Haka Barkat din ta Dinga Nuna mai tana Nuna jin Dadinta Shima yaji Dadi Sosai Inna Talatu kuma Ta na nan Sai Barkat tayi kwana Ashirin zata koma Aina Ta koma Gidan Hakan ba karamin Dadi yayi ma Hajiya Amina ba ta Kira Mama Tana ta mata Godiyan Ranar kuma da tazo yi ma Barkat din Barka Har Dakin Hafsah din ta Shiga tana ta mata Godiya,Domin Barkat din da kanta tace ta Shiga Wajen Hafsah ta mata Godiya Ta tabbata samun kishiya irin ta sai An Tona tayi mata Abunda ko yar"uwanta sai Haka Shiyasa Tayi alkawarin Danne Duka kishinta kan Hafsah ta kuma Damaran koyon Duka Kyawawan Halayanta kodomin Rabauta anan Duniya da kuma Gobe kiyama.
Cikin kwamciyar Hankali Barkat ke jegonta gefe Daya kuma Inna Talatu na kula da ita Bata Tafi ba sai da Barkat Tayi kwana ashirin da Biyar kana ta koma Gida Da Sha Tara na arziki Daga Barkat da Abdullahi Harda Hafsah din ma Ita kanta Wanda takowani bangare take Shan Yabon Hatta ita kanta Barkat din Bakinta yanzu yabon kyawawan Hallayan Hafsah yake Fadi Domin Halin mutum Jarinsa.
****
*BAYAN SHEKARU BIYAR...*
Acikin wadanan Shekaru Biyar din da suka Gabata Abubuwa Dadama sun Faru masu Dadi da akasinsu Cikin masu Dadin Sune Harda kamallah Masters din Abdullahi,da kuma Samun Lecturing Da yayi A Federal Collage of Education FCE zaria,Shekaru Uku da suka Gabata da kuma Karin wani Farincikin ya kamallah Ginin Gidansa Tuni Sun Tare Wajen Shekara Hudu kenan da wani Abu Da Komawarsu sabon Gidan Tsohon Gidansa kuma ya barma Auwal wanda Har yayi Aure da Matarsa khadija suna Kiranta Dija Suna zaune agidan yagama Nd Dinsa ya Dora Hnd dinsa har ya kamallah ya samu aiki a NBYIS,mariya kuma Tuni tayi Auranta tana Auran wani Dan kasuwa akano aka kaita,Da komawarsu Sabon Gida Ba Dadewa Abdullahi ya mallaki Motan Hawa ya barma Auwal mashin Dinsa.
Babu Abunda zai ce sai Godiya ga Allah Domin ta ko"ina ya samu Cigaban Rayuwa da Wadata a Halin yanzu ya kara zama magidanci Yayansa Kimanin su shida kenan Hafsah Bayan Noor ta kara Haihuwam mai Sunan Daddy Hamza Suna Kiransa Daddy,sai Barkat Datake da Guda Biyu,Ta Farkon mace ce mai Suna Habiba Suna Kiranta Aymana,sai Karamin Datake Shayarwa mai Suna Abubakar suna Kiranshi Abba,Gidan ya gama kamallah ta ko'ina Jidda ma ya"yanta uku Bayan Zeezey,takara Abdullahi Da kuma Abdul"aziz sai sakina nada Daya Mai Sunanta Aka maida Sakina suna Kiranta Namesake,Sai Hajiya Subai itama ya"yanta Shida yanzu Zannira kuma ta kai wajen bakwai Mama sai dai Godiyan Allah Domin Ta ko"ina Jikoki Sun Baibayeta,ga jin Dadin Rayuwa Data samu Bayan Mariya tayi Aure saboda zaman kadaici sai ta Dauko Diyar dan"uwanta Tana Rokonta kuma Abdullahi ya bata goyon Baya Sosai,Bangaran Su Inna Abu suma Abubuwa duk sun Sauya Tunda shi kanshi Nazifi ya koma Abuja da aikinsa Gabadayansa Shida iyalansa Sakina ta koma chan tana aikinta Ita da Jidda Barkat dai ta Gama Service ta karbi Resuilt Dinta ammh Aiki kam Abdullahi yace ba'a gidansa ba Dole ta Hakura Domin dai tasan Halin Abdullahi kaifi Dayane,Duk Hakurin Data Dauko ta yafama ksnta wani Lokacin gazawa take in Masifan Abdullahi ya tashi sai tace ma Hafsah Abdullahi sai ita,bata iyawa dashi itakuwa sai Tayi Dariya Domim ko Fushinsa ne ya Tashi da masifarsa Hafsah ce ke biyemai Tana Lallashi Barkat komawa take gefe tana kallo Domin bata iya Jure wannan Hallayar na Abdullahi Duk da Tana Kishin Hafsah ammh ba kamar na Baya ba yanzu Kishin Tsabta suke yi acikin Gidan,Saboda duk iya Abunta bata kama kafar Hafsah ba Hakurinta Daga Allah ne.
Bangaransu Daddy da Ammi Suma Alhamdulillah sun samu Cigaba sosai Hankalinsu kwance Tunda Duka ya"yansu suna Gidan mazajensu Cikin kwanciyar Hankali,Hakama Gidansu Barkat Hajiya Amina Hankalinta ya kwanta Duka ya"yanta sunyi Aure Hatta da Aina Tayi Aure a kaduna,bangaran Su Umman Sadiq itama dai sai godiyar Allah Domin Har Makka Mijinsu yakaita ita da Abokiyar zamanta kannen Abdullahi Duk sun girma sun zama manya samari Ga Zahra ma an zama yan Mata,Goggo Habiba ma Tana Danja Itama Ita da ya"yanta da Mijinta Tana kuma Godema Abdullahi Domin bai manta da ita ba,Hajiya sa'a Tayi Aure Tana zaune agidanta Tagaji mutane nata mganar taki Aure tana zaman kanta Lariya ma ta kara Aure Ammh ita wani Soja ta aura tabi Mijinta Chan Lagos suna zaune sai kuwa indan sunzo ganin gida.
Mariya Ta na chan kano Tsohon Ciki Gareta ita da matar Auwal Ana ma Tunanin kusan Lokaci Daya zasu Haihu sai Shiri Su Hafsah suke Domin Sun yi alkawarin sai sunje kano Tunda sanda za"a kai Amarya Hafsah ce kadai Taje Barkat bata je ba Abdullahi ya Hana yace Shi ba mahaukaci bane da Zai saki mata Biyu alokaci Daya su Tafi kano kai Amarya.
*****
Wajen kwanansu Hudu,akano Suna Dagargazan Sunan Mariya Data Haifi yarta mace,Wacce taci Sunan mahaifiyar Mariyan Suwaiba,Dakyar Abdullahi ya barsu suka Taho sai da Mama ta saka baki ya barsu suka Tafi Chan suka bar Su Amira dasu Noor agida Hafsah ma agida ta bar Daddy Tunda ta yayeshi Barkat ne tazo da Abba,kwana Biyu yace suyi suka karyamai Doka kowacce ta Kashe wayarta suka Biye ma Subai,Daga gidan mariya Gidan Anty Hadiza suka yada Zango suka mata kwana Daya kama suka Dawo Gida koda suka Dawo Abdullahi baya Gida ya Shiga Cikin makaranta Su Amira kuma Suna gidan mama Suna da key din Gidan suka Bude suka Shiga Abunsu Barkat dai Sai Tsoro Take ji ita kuwa Hafsah Taci Dubu sai ceto ko ajikinta.
Sai Dare ya Dawo Gidan bayan ya Biya Gidan Mama ya Dauko su Amira Data zama yanmata Tana Jss1 ne Amir na Primary 5,yana Zuwa yaga sum Dawo Dukkansu Suna mai Sannu da zuwa yayi musu banza ya wuce Shashenshi Barkat da Hafsah suka kalli Juna Cikin Sarewa Barkat tace"Kinga wannan Fushin Wlh bazai sauka kaina ba..Sai da nace mu Dawo kika ji..Ki Kwashi Abincinsa ki kaimai Ciki kisha Fadanki ke kadai Nidai kinga Shigata Daki sai da Safe.."Hafsah na Dariya ta Rikota Tana Fadin"Allah baki isa ba..Tare mukayi laifin nan kuma Tare za"mu sha Fada nan.."Barkat ta bata Rai Tana Fadin"Bafa Ruwana laifinki ne.."Su ka kama Ja'in ja Har sai da sukaji gyaran Muryan Abdullahi saman kansu kana suka Natsu kallonsu yayi Dukkansu yaga suna wani karya wuya kamar munafukai sai Dariya ta kusa kamashi ya kanne Cikin Kakkausan Murya yace"Wato ma Tsabar kun Raina ni Da gangan kuka Share kafa kukayi zamanku ko..? Har kuna Kashe woyoyinku saboda kar Masifaffe Abdullahi ya Kira ko..?
Atare suka kwashi Rantsuwa ya Dakatar dasu yana Fadin"Hmmm..Ku kuka sani..Allah dai na ganinku..Fadan ne da aka min Tambari yau Bazan yi ba..Kun kyauta ba gashi kun Dawo ba Na zata Chan zaku Dauwama.."Sunne kai sukayi Suna Dariya Juyawa yayi yana Fadin"Abani Abinci ina Jin yunwa in kun kungama Gulmar taku..."Da Sauri Barkat tace"Toh Yallabai.."Lokaci Daya Suna Tafawa da Hafsah karaf kuwa Abdullahi ya waigo yana kallonsu sai Suka Fara kame kame Hafsah tace"Kinga kije ki Kwantar da Abba yayi barci ni bari naje na hadamai Abincin..'Barkat ta kama Hanyar Dakinta Tana Fadin"Tom Anty...!
Mirmishi Abdullahi ya saki kafin yace"Allah ya Shiryaku.."Yafada yana Shafa kanshi Su Amira Dake gefe suka Saka Dariya Hafsah ta Makamusu Harara tana Fadin"Kuwuce Shashenku marasa kunya.."Abdullahi yace"ji karfin Hali..? Ku kuyi ku Hana yara yi..? Kai kuce da karfi Allah ya Shirya Anty daMommy .."Suka ko wage baki suna Fada kunya ta kama Hafsah Ta juya zuwa Kitchen Barkat Daman Tuni ta Shige Dakinta Tana Dariya Abdullahi ya Bisu da kallo Shima yana Dariya Lokaci Daya ya Juya zuwa Shashensa yana Fadin.
*ALHAMDULILLAH...*
*Tammat Bihamdulillah...*
*Alhmadulillah anan na kawo karshen Wannan Labarin nawa na Masifaffan Namiji Abunda na Fada Daidai Allah ya bani ladansa kuskuran Dake Ciki Allah ya yafemin...Ina godiya ga Mutane Dabam Dabam Masoyana wandanda suka yi Jimarin Bin wannan labarin nawa,Har zuwa yau da muka zo karshe Ina godiya ga Sauran groups Dina na WhatsApp Da wadanda nake Ciki da wadanda bana Ciki Nagode sosai da Salon Soyayyarku gareni Har gaban Abada bazan manta daku ba..Sai kuma Dubin gaisuwa da Godiya zuwa ga My Wattpadian pipu's Hakika nagani kuma na Yaba Tundaga Farkon fara wannan Labarin Kuke gudanar da kayattacen Sharhi kuma Sharhi mai ma"ana wanda zai Taimake ku nima ya Taimakeni Wajen kara sanin Rayuwa da Zamantakewa Nagode sosai Allah ya saka muku da alheri Allah kuma ya baku ikon Daukan Duka Darussan dake Cikin wannan Rubutun nawa Ameen ya Allah..*
_Labarin nan ba Labarin Gaskiya bane Kirkiran Labari ne Wanda na Kirkireshi da Kwalwalwata Bawai nayi Dogon Tunani bane A"a Lokaci Daya naga ya Dace nayi Wannan Rubutun Kyauta ga Yanmatan mu Da Zawaranmu da Samarinmu da Uwargida da Amarya da Megida da ango da Amarya Saboda musan yadda zamu gyara mu"amalan Gidajen mazajenmu,Na samu Wayoyi da Dama da Sakona kan wasu Suna Fadin Labarin Hafsah yayi Daidai da Labarinsu Bla bla dai Toh Abunda nake so ku gane ga wannan Labarin Abu Daya ne Aure IBADA NE,kuma Aure HAKURI ne Jigonsa Duk macen Dake Tunanin bazatayi Zaman Hakuri agidan Mijinta ba Am Sorry To say haka zata tai ta Shiga Tana Fita Domin bazata Zauna ba Soyayyah Da kuke gani Duk awaje ne Gidan Aure ya Bambamta da zaman Gidan Iyaye Duk da Shima sai an yi Hakuri...Yan mata masu Shirin Shiga Gidan Miji Sai kun yi Hakuri Ga wacce zata Shiga ita Dayan da wacce Zataje ta Tarar ku Tuna Hakuri Shine Ginshikin Inda kika Rasashi Kin Rasa Dukkan Wani Jigon Zaman Aure Kana kada ku manta IBADA kuke je yi kuma zaman Ibada zaman Hakuri ne Allah ya bamu Ikon Hakurin Allah kuma yasa Mu zama Mataye na Gari ga Mazajenmu Nan Duniya da Gobe Kiyama Ameen.._
_*Bazan Rufe Littafin nan ba Batare da na Mika sakon Godiyata ga Wasu mutane masu Muhimmanci Arayuwata Guda Biyu ba na Farko Sisinah AISHA ALTO,hakika ke din Ta Dabamce awajen Jamila ina kaunarki Har Cikin Raina Sisinah,Da Taimakonki wannan Littafin ya kamallah kin Taimaka Wajen kokarin Posting Dinshi Nagode Sosai Allah ya saka miki da Gidan Aljannah Firdausi Allah ya Jibanci Lamarinki Allah ya sa ki gama Da Duniya Lafiya Allah ya baki miji na gari Allah ya kareki Daga Dukkan Sharri Allah ya barmu Tare..Sai Uwata Ta kaina Ni Daya Ummina KHADIJA SALISU YUSUF uwata Alherin Allah yakai miki Har gadon Barcinki Kyawawan Hallayanki Abun koyi ne garemu Allah ya Biyaki da Gidan Aljannah Firdausi Allah ya Shayar Dake Ruwa Daga Cikin Ruwan na ALKAUSAR Ameen*_
*Sai Allah ya kaimu Bayan Sallah In da Rabon mu sake Haduwa Cikin Wani littafin Batin Tunda naga Shi kuka fi so Ammh fa Banyi Alkawari ba...Har yanzu ana Cigaba da payment kan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Kan Farashi mai Sauki mai Neman karin Bayani sai ya Tuntubani ta wannan Layin Insha Allahu 09069067488...*
Tanque All....And god bless u Alwys and Forever Fans❤️
*Janafty...*
*Shakira..*
*Anitha..*
*Jamilaumar*
*Intelligent Writer"s asso..*
No comments