Recent Updates

Kamar Da Wasa Complete Hausa Novel

 


Hafsat Rano: © _*HASKE WRITERS ASSO.*_



*KAMAR DA WASA....!*   




  _*NA*_


_*UMMI A'ISHA*_






_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI._




   *1*






   "Masu sauraro kamar kullum anan shirin namu zai dasa aya ayau kun dai ji mun tattauna akan wata babbar matsala wato ta yadda zakaga saurayi da budurwa sun kwashe shekaru suna gudanar da soyayya amma abin haushi arabu batare da anyi aureba shin laifin waye? Mazan ko matan? kafin inyi sallama daku ina mai janyo hankalin masoya da arike amana, gaskiya da kuma kulawa sannan aguji karya da yaudara domin hakan ba abune mai kyau ba sannan daya daga cikinsu yana raunata soyayya kuma ya illatata, anan zanyi sallama daku sai Allah yakaimu sati nagaba inda zaku jini acikin wani sabon shirin naku mai farin jini wato *Sakon na masoya ne...* kamar kullum nice taku mai gabatar da shirin wato *BILKISU LUKMAN ALIYU* Nabarku lafiya...."




 Ahankali yake zare earpiece din dake kunnenshi sakamakon jin wakar _Sulken so...._ ta maye gurbin zazzakar muryarta, cikeda takaici ya kifa kansa asaman keken dinkin da yake zaune akai yana dinka wata kyakkyawar doguwar riga ta mata, tunani yake aransa yanzufa shikenan bazai sake jin muryarta ba sai wani satin indai ba shirye shiryenta na baya wadanda yayi recording zaiji ba domin hatta wannan wanda ta gabatar ayau ma yayi recording dinshi yana nan ajiye cikin wayarshi. Babu zato babu tsammani yaji wani abu saman sumarshi mai kamada almakashi, hannu yasa domin yakamo abin amma yaji anjanye ahankali yabude lumsassun idanuwanshi yatashi zaune, kamar yadda yayi zato husna yagani tsaye sai faman yi masa murmushi take, maimakon ya mayar mata da martanin murmushin da take yimasa sai ya daure fuska kamar ta kawo masa sakon mutuwa.




 Bata damuba tabawa kanta masauki da wata kujerar roba wadda ke ajiye agaban keken dinkinshi, bata damu da yanda sauran abokan aikinshi  wadanda ke zaune akan kekunansu suna gudanar da ayyukansu yanda zasu dauketa ba domin idan da sabo tasaba, zama tayi ta tallafe kumatunta da hannuwanta tana kallonshi kamar yadda yayi sai dai shi sam ba ita yake kallo ba domin yafada duniyar tunani.




"Prince..., Prince....ina dinkin yarinyar nan?"




Sai lokacin yadawo hayyacinsa sakamakon maganar tj abokin aikinsa da ta daki dodon kunnuwansa, gefenshi ya duba ya ciro wasu kaya acikin leda ya mika masa,




"Wai meke damunka fahad?"




Kallonta yayi adage sannan cikin rashin kulawa yace,




"Mekika gani fa?"




"To ai naganka ne kamar wani marar lafiya" tayi maganar cikin kalar tausayi,




"Lafiya ta lau..." Yabata amsa yana kokarin mikewa tsaye, wata leda ta mika masa tana langwabe kai,




"Please my prince ga uniform dina ka dinka min kaji"




Batare da ya kalleta ba ya karba ya jefa cikin wani kwali dake girke gefen kekensa,wani food flask dan madaidaici mai kyau ta sake mika masa,




"Ga abinci na kawo maka"




Karba yayi ya dora saman keken dinkinsa sannan ahankali kamar wanda tayiwa dole ya furta,




"Thank u"




Jingina tayi tana kallonshi shi kuma yana kallon wayarshi, babu abinda kake ji sai karar keken dinki wanda sauran abokan aikinshi keta faman aiki. Scissors din da ke ajiye kan kekenshi ta dauka ahankali ta kai kan tararriyar sumarshi,




"Inyi maka aski?"




Sake daure fuskarshi yayi yakai hannu ya doke almakashin,




"Kibari bana so, nafada miki bana son wasan banza"




Murmushi tayi tana sunkuyar da kanta,




"To kayi hakuri"




Baice mata komai ba yatashi da niyyar fita nan itama ta mike tana kallonshi ganin haka yasa shi yafasa fitar yawuce can wani lungu kusa da wata drawer ya kwanta, duk da tana son su fita tare amma haka tayi hakuri tawuce tatafi ba don taso ba.




  Yajima kwance awurin yana jin sauran yan shagon sunata gulmarsa shida husna amma bai tanka ba har saida lokacin sallar la'asar yayi sannan yatashi,alwala yayi ya shiga masallaci duk da yana son ganin salim abokinshi amma sai yashare yashiga salla wanda acan din yahadu da salim din.




 Yana fitowa daga salla keke napep yatare yanufi gida, atsakar gida ya iske mahaifiyarshi tana wanki koda yakarasa kusa da ita kamar yadda yazata kananan kayanshi take wanke masa.




"Ayiyah wankinne dai?"




Murmushi tayi tajuyo ta kalleshi,




"To ai ba komai nakeyi ba shiyasa nace gara inwanwanke maka sauran kayan ma na hadasu zuwa gobe zan bayar akai awanko maka"




"Godiya nake Ayiyah tah, Allah dai yabar min ke"




"Amin autana, maza kaje ga abincinka can a falo na tanadar maka"




Yunkurawa yayi ya mike daga tsugunnen da yake hakan yayi daidai da fitowar mamu,




"D'an nema kadawo ashe?"




"Hajiya mamu wallahi nadawo, kina daga ciki kenan?"




"Andai ji kunya, gandamemen saurayi dakai amma baka iya wanki ba"




Kafin yayi magana ayiyah tayi caraf ta cafke zancen ta hanyar bawa mamuh amsa,




"Tunda yana da masu yimasa ai ko ya iya bashida amfani"




Wata shewa mamu ta saka tana karasowa inda suke,




"To nidai naga yanda za ayi duk ranar da akayi masa aure"




"Yakuwa za ayi? Matarsa ce zata rinka yimasa"




"Idan ta iya ko?"




"Sai ta koya" inji ayiyah, jan yar karamar kujerar tsugunno mamu tayi ta zauna kusa da ayiyan, shi dai bazai iya cigaba da kallon wannan dramar tasu ba shiyasa yawuce dakin ayiyah fuskarshi shimfide da murmushi domin idan da sabo yasaba ganinsu ahaka kusan tun tasowarsa ahaka yake ganinsu bai taba jinsu suna fada ba kai idan baka saniba baka taba cewa kishiyoyine dan ko yanzun ma da suka gama wannan rahar hira ya jiyosu suna yi kuma da alama wankin mamuh take taya ayiyah. Zama yayi saman daddumar dake shimfide cikin falon yasoma bude kwanukan dake jere reras awurin wanda yasan shi aka tanadarwa domin kullum haka ayiyah keyi masa kamar wani mai gida, funkaso da miyar taushe yagani sai shinkafa da wake da manja da salad sannan ga zubo nan mai sanyi da kankara aciki cikin wani madaidaicin jug, hannun riga ya nade yasoma zuba shinkafa da waken domin kusan abubuwan nan na soye soye irinsu waina, sinasir, funkaso duk ba damunshi sukayi ba dan haka yazage yaci shinkafa da wakensa yayi dam yasha sanyayyen zobonshi daga haka ya mike ya fito,su ayiyah har sun kammala wankin sun fada wani aikin kuma sunayi suna hira shiyasa ma ko ganin fitowarshi basuyi ba, dakinsu ya nufa wanda yake cikin soron dake hanyar kofar gida yabude yashiga daga shi sai yayanshi Abba adakin amma yanzu abban baya nan yana can jami'ar Maiduguri wato unimaid yana karantar computer science dan haka sai shi kadai adakin yanzu, kayan jikinshi yarage yabar gajeren wando kadai bayan ya Kara kofar dakin, kan dundumemiyar katifar dake malale adakin yahau ya kwanta bai kai ga rufe idanuwansa ba yajiyo alamun karar shigar sako cikin wayarshi, akasalance ya mika hannu yadauko wayarshi kirar Galaxy S10,BILKISU shine password din kan wayar tashi nan yabude yasoma duba text din duk da baiyi saving number dinba yagane husna ce domin har ya haddace number dinta saboda yanda take damunsa arana sai ta kirashi akalla sau biyar ko fiyeda haka banda text massages kai idan takira ma taji shiru abune mai sauki yaganta ashagonsu ta biyo sawunshi yarasa gane kan wannan yarinyar gashi ta tsani ta ganshi da wata mace suna ko maganane alhalin kuma shi aikinsa na matane tunda dinkin mata shine sana'arshi. Sakon yabude yasoma karantawa kamar haka... _"Ya fahad yakake, ina fata lafiya kake, abincin yayi dadi?"_ murmushi yayi ya ajiye wayar bayan yasata a silent domin shi sai yanzu ma yatuna da wani abincin da ta kawo masa dazu saboda can yabaroshi ashago bararrajewa yayi saman katifarshi domin yin bacci duk da yasan ayiyah ta hanashi wannan dabi'ar ta baccin yamma amma babu yanda zaiyi ne sakamakon yagaji dayawa gashi ya jima bai samu isasshen bacci ba kullum yana kan keke yana dinki.


***


   Murmushi tasaki ahankali wanda yayi sanadiyyar bayyanar fararen hakoranta sannan ya bayyanar da kyawawan beautiful point dinta wadanda ke kara kawata kyakkyawar fuskar da Allah yayi mata. Wayar dake makale a kunnenta take jujjuyawa cikeda annashuwa,




"Yes half soul, yanzu dai kabari sai nakoma gidan kawai sai naturo maka...."




Dan Jim tayi tana sauraron abinda yake fada bata kai ga bashi amsaba tamike daga kujerar datake zaune wacce ke rukunin kyawawan kujerun dake zagane cikin zungureren office din wanda ke dauke da kayan alatun more rayuwa banda na'urar sanyaya daki wacce ta cika dakin da sanyi wanda bazai cutar da jikin dan adam ba, jakarta ta dauka wadda take ajiye bisa dogon teburin da ke tsakanin rukunun jerarrun kujerun masu fuskantar juna, hakan yayi daidai da shigowar khulsum kawarta,




"Noorul kalb ga khulsum ta shigo zamu tafi ni ina ganin kawai kabari sai naje gida din kawai sai muyi waya ko?" Batare da khulsum tajiyo amsar da yabata ba taga tayi murmushi sannan ta amsa da,




"Zataji half soul, me too"




Daga haka ta katse wayar tana kallon khulsum,




"Wai har kin kammala voicing din?"




"Tun yaushe, ina can inata jiranki amma najiki shiru ashe kina nan kina soyewa"




Murmushi tayi ta saba jakar hannunta suka doshi kofa domin fita daga office din,




"Nima fa yanzun nan nagama fassara labaran kasuwancin nan kin san yanada wahala shine kuma hamood yakirani,namanta ma yace yana gaisheki"




"Ina amsawa, am yawwa kafin namanta wai ke mekike shirya mana ne abikin nan?"




Juyawa tayi ta kalli khulsum sannan ta harareta,




"Me zan shirya muku kuwa, ko nice amaryar da zakiyi min wannan tambayar? Ban son wulakanci"




Murmushi khulsum tayi ta dafa kafadarta,




"Bakece amarya ba amma ai kece babbar yaya kuma uwar biki kinga kuwa yazama dole kiyi wani abu"




Lumshe idanuwanta tayi sannan ta budesu bayan yanayin fuskarta ya sauya cikin sakannin da basu gaza biyu zuwa ukuba,




"Ni yanzu duk ba wannan ba wallahi abunda ke damuna guda dayane zuwan Grandma dinmu iyallo, yanzu tana zuwa zatabi ta uzzurawa mutum ta daga masa hankali, tun lokacin bikin mamaa take damuna gashi yanzu bikin Hindu da meenah yazo, ni wallahi ji nake kamar inbar gidan sai angama bikin nadawo"




Murmushi khulsum tayi bayan taja ta tsaya kamar yadda taga tayi,




"Labour kema fa da laifinki gaskiya, why not bazaki baiwa hamood dinki damar yafito kuyi aureba tunda kuna son juna? Haba dan Allah, shekara da shekaru kuna abu daya sai kace wasu wannan..., ai yakamata yanzu ace yabaro kasar Chinan nan yadawo kunyi aure inyaso sai ku koma tare idan bai gaji da zaman canba"




Saida ta sake bata fuska sannan ta kalli khulsum,




"Zanyi miki rashin mutunci idan kika kara kirana da labour dinnan, nafada miki bana so"




"Atoh kiyi min mana wayasa lokacin da kina secondary school din da aka baki labour prefect din kika karba? Ai da sai kice bakya so abaiwa wata"




Dariya tayi ta dauke kanta daga kallon khulsum,




"Kin san me kawata? Hamood shima burinsa yanzu kawai yaga yadawo Nigeria munyi aure, kuma nanda 3 months fa zai dawo, sai dai shi yafi son yayi komai na aurensa dakanshi, baya son uncle dinsa yayi masa acewarsa lokaci yayi da yakamata uncle barewa yahuta tunda tun yana dan 7 years yake yimasa wahala sannan dukkan karatunshi da wanda yayi a Nigeria da wanda yayi a outside duk shine yake sponsoring shiyasa yace sai yadawo yasamu aiki tayadda zai iya yiwa kanshi aure sannan zai kai maganar gaban uncle dinshi"




Dan karamin tsaki khulsum taja,




"To kuma sai me dan yafadawa uncle dinshi yanzu? Minister nefa, ai yanada kudin da zaiyiwa samari goma irinsa aure"




"Hakane khulsum amma kigane wani abu guda daya, abunfa da kunya kuma da nauyi ace tun kana dan karami mutum ke dawainiya dakai sannan ka girma nanma kace komai shi zaiyi maka alhalin bashi ya haifeka ba kawai zumunci ne"




"Ehh to hakane kuma da wannan dan wannan, to Allah dai yadawo dashi lafiya musha biki"




"Amin, yanzu dai tunda magrib takusa ni ina ganin mubari zuwa gobe sai mu shiga central market mu siyo kayan da zamu saka abikin dan gaskiya basaka ankon nan nasu zamuyi ba tunda nasune suda friends dinsu"




"To shikenan babu damuwa Allah yakaimu, Allah kuma yasa mutashi da wuri daga aikin nan"




"Amin,Kuma wallahi commitment dina yawa gareshi goben nan dan har dinki nake son kaiwa ga sauran siyayyar yaran nan da ban karasa ba ta kayan kitchen dinsu"




"Babu komai dai kawai Allah yanuna mana goben komai mai saukine"




"Amin ya Allah"




Daidai lokacin suka tare wani mai keke napep suka shiga domin tafiya gida.






*_Ummi Shatu_*    

[11/28, 08:14] Hafsat Rano: © _*HASKE WRITERS ASSO*_       _(Home of expert & perfect writers)_



*KAMAR DA WASA...!*  






   *_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*





   *2*






    ***Har suka kusa zuwa gida magana daya suketa yi shine maganar zuwan kakarsu iyallo,




"Mai gado Allah kina bani dariya yau dinnan" khulsum tafada tana tuntsurewa da dariya,




Harararta Bilkisu tayi daidai lokacin da suka isa kofar gidansu bilkisun yayinda gidansu khulsum ke can wata unguwa daban gaba da ta su Bilkisu,




"Banida lokacinki sai anjima saura kuma gobe karki fito da wuri"




Daga haka tafice daga keke napep din tabar khulsum na yimata dariya, ji tayi kamar kada ta shiga gidan sakamakon ganin motar ya mudan da tayi, sam ita ta tsani takura da naci amma babu yadda ta iya dole tashiga tana tafiya sadaf sadaf, atsakar gida ta hangoshi zaune kan farar kujerar roba yadora daya kan daya yayinda ammah ke cikin kitchen suna yar hira dashi,




"Sannu da aiki ammah..."




Daga haka tanemi wucewa dakinta, maganar amma ce ta dakatar da ita,




"Ke mai gado, bakiga yayanki bane zaki wuce baku ko gaisa ba?"




Juyowa tayi tadawo da baya, fuskarta babu fara'a,




"Yaya mudan ina wuni? Anzo lafiya? Yasu iyallo?"




Ta hada gaisuwar gaba daya lokaci guda, murmushi yayi ya amsa mata yana yi mata wani kallo mai cikeda sha'awa,




"Lafiya lau mai gadon zinare, ya aikinku?"




Tana tafiya take amsa masa da "lafiya"




"Manyan yan jarida kenan, ku da anganku anga labarai"




Bata amsa masa ba ta soma cuku cukun zaro key din dakinta daga cikin handbag dinta adaidai lokacin taji sallamar Hindu da minah har da mamaa wacce ke rikeda hannun yarta hudah yar kimanin shekara daya da rabi, yarinyar na hango Bilkisu ta kwace daga hannun mamaa tatafi da gudu wurin Bilkisu, dakatawa tayi daga bude kofar da takeyi ta dauketa fuskarta dauke da fara'a,




"Hudah na oyoyo daga ina haka?"




Kafin hudah tayi gwarancinta su mamaa suka karaso,




"Adda maigado yau baki taso da wuriba" inji mama,




"Wallahi fa mamaa aikinne sai ahankali, daga ina kuke?"




"Bakin kasuwa mukaje suka kai nadin gwaggwaro"




Murmushi tayi tawuce dakinta tana cewa,




"Amaren kamshi kenan"




Akan gadonta ta ajiye hudah ta kunna mata cartoon awayarta ta bata sannan ta zage ta fada wanka, tana wankanne meenah ta shigo sadaf sadaf ta dora mata wata farar takarda akan sallayarta tafice.




Bayan tafito doguwar riga kawai ta saka marar nauyi ta dauki hijabinta domin tanata jiyo kiraye kirayen salla daga masallatai daban daban, hudah kuwa tana zaune tana kallon cartoon dinta sai dariya takeyi,




Kan sallaya tahau har zata fara sallar idonta yakai kan farar takardar da meenah ta ajiye dauka tayi ta warware ta tafara karantawa,




_Adda labour yaya mama ce tace wai baza abamu komai bane na hadin amare? Wai kibada kudi zata siyo mana kaza ta dafa mana_




Murmushi tayi ta yaga takardar ta watsa ta cikin dustbin, dama kusan duk lokacin da zasu tambayeta abu indai na kunya ne sai dai su rubuta mata sai su ajiye mata wurin da zata gani ko su tura mata text, ko pad zasu tambayeta sai dai su rubuta mata shiyasa kafin lokacin ma yayi take siyo musu ko tabasu kudin su siya domin tana mutukar kaunar kannen nata saboda suma suna sonta sannan suna bata girmanta tsakaninsu babu reni hatta mamaa da tayi aure harda baby bata yimata reni bare rashin kunya, sallar magrib tayi bayan ta idar ta kara da nafila, tana kokarin shafa addu'a mamaa ta shigo,




"Yarinyar momy kallo takeyi awayar momy?" 




Mamaan tafada lokacin da take zama agefen gadon Bilkisu,




"Ai kin jita shiru, nawane zai isheku dafa kazar?"




"Adda labour yafi dubu biyu zuwa uku?"




"To shikenan zan baki kafin ki tafi, shekaran jiya fa har naturawa wannan matar da tayi miki hadin kayayyakin nan lokacin bikinki kudi suma tayi musu kuma nasan itama harda kazar zata dafo musu"




"To shikenan ai iya natan ya isa tunda yama fi kyau nifa na bikina har na haifi hudah yana jikina..."




Harararta Bilkisu tayi,




"Ban son fitsara"




"Yi hakuri Adda maigado subutar baki ce" daga haka ta shige bathroom domin yin alwala.




Daukar hudah tayi ta fita domin yunwa take ji, atsakar gida ta iskesu saman katuwar tabarma wata na sallah wata kuma ta idar rashin ganin ya mudan yasata zargar kila ko yatafi, zaunar da hudah tayi tashiga kitchen, faten doya da wake shi akayi da rana yanzu kuma da daddare tuwon shinkafa ne miyar zogale, tuwon ta zuba ta dauko tadawo wurin hudah ta soma bata itama tana ci da haka har amma tafito ta samesu. Zama tayi kusa da ita tana tsokanar hudah,




"Acici kinzo zaki cinye min abinci nida mijina, to maza kiyi kibar min gidana...." Ta karashe maganar tana jan kunnenta daya, rike kunnen da taja hudah tayi tana guduwa jikin bilkisu, janyeta tayi tana kallon amma,




"Zo baby na rabu da amma kinji, maza ci tuwo idan baki koshi bama inkaro miki"




"Badai tuwo na ba tunda ba ita ta tuka minba"




Kowa na wurin saida yayi dariya saboda jin abinda tace, mamaa ma fitowar tayi tana dariya nan tasamu gefen tabarma ta zauna,




"Yawwa mai gado wai nikam meyasa kikeda taurin kaine? Meyasa duk ranar da dan uwanki mudassir yazo bakya sakar masa fuska ku gaisa? Iya gaisawar ce fa kadai daga ita shikenan babu wani abu, dan Allah ki gyara"




"To ammah insha Allah" daga haka taci gaba da cin tuwonta tana sauraren zantukan da su mamaa keyi wanda baya rasa nasaba da shirye shiryen bikin su Hindu lokaci lokaci ta kan dan saka baki harta kammala cin tuwon tatashi taje tana wanke musu hannu itada hudah daga nan dakinta tawuce tabaje akan gado bayan ta dauko yar madaidaiciyar laptop dinta, tana ji yara suna go slow din shigowa dan kiran hindu da meenah wanda ko ba afada ba tasan angwayen ne masu kiran. Aikinta taji gaba dayi na rubuta takardar neman hutu har na tsawon sati biyu wato (casual leave) saboda bikin su meenah domin tana bukatar isasshen lokaci so take idan biki yarage saura kwana uku saita nema kamar dai yadda tayi abikin mamaa. Har misalin karfe 9 saura idonta na kan laptop din tana wani aikin daban, shigowar mamaa ce ta katseta ta tashi zaune tana gyara hudah wacce ke makale ajikinta tana bacci,




"Adda maigado faruk yazo zamuje mu tafi, ko inbar miki hudah ta kwana?"




"Ke wai ban hanaki fadar sunan mijinki kai tsaye ba, tunda ga yarku ai gara kirinka sakayawa da abban hudah wallahi idan kuma baki gyaraba wata rana sai kinji sunan nan abakin yarki"




"Wallahi Adda bana fada agida anan ne dai nake fadar sunanshi"




"Nidai na fada miki ai, dauketa kutafi da ita kinga gobe zan fita aiki kuma idan nafita bazata yarda da kowaba sai kuka zata ishi mutane dashi da dai weekend ne sai kibarta"




Daukar hudah mamaa tayi suka fita bayan bilkisu tasaka hijabinta, atsakar gida suka samu ammah da Faruk mijin mamaa suna gaisawa. Yana ganin bilkisu ya soma dariya yana cewa,




"Barka da fitowa babbar yaya, anwuni lafiya"




"Lafiya lau faruk ya mutanen gida, ya aiki"




"Lafiya lau anty mai gado"




Dunguma sukayi gaba dayansu suka fita banda amma,suna fita tun daga compound din gidan kamshin turaren su hindu ya budadesu suda angwayensu kowacce suna tsaye agefe itada angonta suna hira,




Dukkaninsu saida suka matso suka gaisa da bilkisu kafin takoma gida, tana shiga daki ta iske miss called din hamood zama tayi gefen gadonta tana kokarin bin kiran yasake kiranta nan ta daga bayan ta lumshe idonta tana saurarensa, kamar koda yaushe sun shafe lokuta masu yawa suna hira har saida bacci yaci karfinta sannan sukayi sallama.




Washe gari da sassafe ta shirya tafita domin tana da zuwa dauko rahoto kamar yadda tasaba, ko khulsum bata nemaba ta kwashi kayan aikinta itada driver suka tafi,bayan ta dawo daga daukar rahoton taje tayi voicing saida ta kammala komai sannan tasoma neman kawar tata, news room taje acan ta iske khulsum tana fassara labaran da za agabatar da misalin karfe daya nan tazauna tajirata harta gama daga nan sukaje suka dauki permission suka nufi babbar kasuwa.




 Ko acikin keke napep bilkisu sunata waya itada hamood har saida suka shiga kasuwar sannan sukayi sallama tafito daga napep din tana yiwa khulsum kallon ta ina yadace mufara? Shagon sayar da kayan kitchen suka fara zuwa domin tanada sauran siyayya da yawa wadanda bata karasa ba, sun bata lokaci sosai awurin domin yau so take tagama da wannan bangaren awuce wurin. Sai da suka kammala siyan duk wani abu wanda ke rubuce jikin list din da tayi awata takarda sannan ta biya kudin suka shiga can tsakiyar kasuwar domin dubo kayan da amare zasu saka na fitar biki da wanda ita kanta zata saka itada kawarta khulsum.




***




 Kamar koda yaushe yauma yatashi cikeda zumudin sake jin muryarta domin ayaune take gabatar da shirinta mai farin jini wanda yake sanyaya zukatan masoya da duk wani mai sauraron shirin,




Yana daga kwance saman dingimemiyar katifarsa ya dauki agogon hannunshi silver colour kirar kamfanin LX,karfe 11 saura yan mintuna, cikinsa yashafa sannan ya mike yana gyara gajeren wandon dake jikinsa, farar t shirt dinsa mai dogon hannu yaja ya mike yafita yanufi cikin gida yana mai saka rigar, baiyi mamakin jin gidan shiruba domin yasan su maryam sun tafi makaranta haka shima baba yafita kasuwa, sai dai ko motsin ayiyah da mamuh baiji ba, dakin ayiyah yadaga labule ya shiga, ga kayan karin kumallonsa nan ajiye agefe dan haka ya zauna ya lankwashe kafafu yajawo kwanikan, dan karamin food flask ne dauke da gurasa wacce tasha kuli kuli yaji sosai da man gyada hadida tumatur da albasa da koren tattasai sai zuba kamshi take sannan ga koko nan a dan madaidaicin kwanon sha na silver sai kosai shima awani kwanon na daban, bisimillah yayi ya soma karyawa yana tsice danyar albasar dake cikin gurasar domin shi baya cin danyar albasa da danyar tafarnuwa, yana daf da kammalawa yajiyo maganar mamuh wadda tafito daga bandaki tana rikeda bokiti da kwandon wanka,




"Wannan ja'irin yasamu yafito ne? Bacci sai kace mai baccin mutuwa"




Murmushi yayi yashafa kansa,




"Ina kwana mamuh, ina ayiyan ne?"




Saida ta amsa gaisuwarshi sannan tabashi amsa da,




"Taje nan makota gidan mai dan wake jajjabin yaronta murtala wanda aka sacewa babur shekaran jiya"




Mikewa yayi yana cewa,




"Allah yarufa asiri"




Daga haka daki yakoma yashiga wanka bayan yafito ya shirya cikin kananan kaya brown din riga da blue din wando, saida yagyara sumar kanshi sannan yafita yanata zabga kamshin turaren Amirul oud, cikin gida yafara shiga yayi musu sallama sannan yawuce shago.




***




   Sosai bilkisu takashe kudi wurin siyawa amare kayan da zasu saka banda nata da na mama da ta siya material mai kyau light blue da manyan atamfofi guda biyu sannan ga ankon da zasuyi ita da khulsum na wani golden din leshi, tunanin wurinda yadace su kai dinki suka farayi domin bata son takai kayan gida batare da andinka ba, khulsum ce  tace ta taba ganin shagon wasu teloli daga waje can a albarka plaza nan suka ciccibi kayan suka fita,babu wani nisa sosai amma agajiye suke jinsu lis, suna shiga plaza din suka wuce sama ahawa na uku suka ga shagon wanda ke dauke da zanen dinkunan mata kala kala ajiki anruba _Golden scissors and fashion design_ a mutukar gajiye suka kutsa kai ciki bakin khulsum yana dauke da sallama



*_Ummi Shatu_*    


[11/28, 08:14] Hafsat Rano: © *HASKE WRITERS ASSO* _(Home of expert & perfect writers)_




*KAMAR DA WASA....!*   




 

   _*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*







    *3*








     ***Nazifi ne ya amsa musu sallamar yayinda sauran kowannensu yana duke yana aikinshi,




Khulsum ciki tawuce ta zauna kan kujerar roba dake kusa da keken nazifi yayinda ita kuma bilkisu tazauna daga bakin kofa kusa da keken fahad wanda kansa yake asunkuye yana hada wata skirt ta atamfa, kamshin da yajine tun lokacin da ta zauna ya janyo hankalinsa har ya daga ido ya kalleta domin wannan shine karo nafarko da ya taba jin wani turare wanda ya sanyawa zuciyasa wani al'amari, ganinta yayi tana latsa wayarta yar karama kirar baby Nokia, ahaka yake dinkin sannan kuma yana aikin kallonta wanda kusan ita bata ma san yanayiba jimm kadan wayar tata tayi kara nan tatashi tafita yabita da kallo,shigarta ita tafi komai jan ra'ayinsa agameda ita domin gaba daya jikinta a lullube yake babu abinda zaka iya gani sai tafin hannunta da fuskarta dan ko kafarta asakaye take, bata wani jimaba ta dawo ta zauna tana sauraron su khulsum wadanda ke maganar dunkunan da suka kawo,




"Kawata ya za ayi? Daga nan gida zamu wuce ne ko zamu koma office?" Khulsum tafada tana kokarin ciro kayan da suka kawo daga cikin leda,




Saida ta dan ja numfashi sannan ta kalli khulsum din,




"Gaskiya muyi tafiyarmu gida..., yanzu haka da kikaga nafita director programs ne ya kirani wai naje nayi program dina shine nace masa bana nan kawai amaimaita na baya"




Tunda tafara magana ya dakata daga dinkin da yakeyi yana kallonta kasa kasa, muryarta ce ke kai kawo acikin kunnuwansa tabbas ko shakka babu itace macen da yajima yana burin gani, itace wacce muryarta ke sanyaya cikin kunnuwansa dan tsananin sanyinta sannan take sashi nishadi cikin kowanne irin yanayi ya tsinci kansa.




 "Yanzu waye zaiyi mana wannan dinkin na amaren acikinku?" Khulsum ta bukata,




"Gaskiya sai dai ko prince domin kamar yafi iya dinkasu" Nazifi yabata amsa,




"Ina shi prince din?" Khulsum tasake tambaya,




"Gashi can " yanuna fahad da hannunsa, daga bilkisu har khulsum juyawa sukayi gareshi suna kallonsa hakan yasashi dauke manyan idanuwanshi daga kallon da yake yi mata kamar wani tsohon maye,




"Dan Allah zamu samu dinki?" Bilkisu ta tambayeshi tana kallonshi, lumshe idanuwanshi yayi sannan yabude cikeda kasala,




"Kala nawane?"




"Ko iya na amaren ne ma kala biyu sai kayi mana"




Girgiza kanshi yayi yana juya skirt din hannunshi,




"Zanyi harda nakin ma"




"Nikuma fa?" Inji khulsum,




"A'a ke banda naki"




"Ai kuwa baka isaba wallahi, mu kawo dinkin tare ita kayi mata ni ka ki yimin?"




Murmushi yayi batare da yadaga kansa ya kalli kowaba,




"Kawo kayan nagani" yace da Bilkisu, mikewa tayi bayan ta dora wayarta akan kekenshi taje ta dauko ledar kayan ta soma fito masa dasu tana yi masa bayani, shagala yayi da sauraron muryarta harta gama, tasowa khulsum itama tayi tazo ta ajiye masa nata bai ki ba duk ya hada ya karba yana tambayar measurements dinsu, khulsum Bilkisu tafara gwadawa da tape din da yabasu sannan itama khulsum tafara gwadata sai dai tun kafin khulsum ta fada masa yake rubutawa wuri dayane aka samu sabani Boob's dinta ya rubuta 34 khulsum tace masa 38,jinjina kansa yayi ahankali ya furta,




"Manyan mata"




Saida komai ya kammala sannan Bilkisu ta tambayeshi kudin dinki, na amaren cewa yayi subada 10k sai na khulsum 6k sai na mamaa ita kuma 4k,handbag dinta ta dauka tana kokarin ciro kudin,




"Nikuma nawa fa?"




"Ke sai bayan nagama dinkawa"




"To shikenan ga wannan din"




Kudin ya karba yana ciro wayarshi daga aljihu sakamakon karar da yaji tanayi ganin husnah ce ke kiranshi yasashi saka wayar a silent ya ajiyeta gefe, sallama su khulsum sukayi masa suka fita nan yayi tagumi yabisu da kallo su nazifi binshi da kallo kawai sukeyi domin su dai asanin da suka yimasa baya karbar dinki kai tsaye haka musamman irin wannan na gaggawa. Yajima ahaka kafin ya hakura yasoma tattara kayan yana sakawa cikin leda kamar amafarki yaga wayarta kan kekensa bayan ya dauke atamfar dake wurin, jujjuya wayar ahannunshi yayi kafin ya bude yasaka number dinshi ya kira, goge number tashi yayi bayan yakira wayarshi ya ajiye wayar agefenshi. Bilkisu kam saida sukayi nisa da kasuwa sannan ta farga cewar ta manto wayarta ashagon dinki cikeda takaici ta sanarwa da mai keke napep din yajuya suka koma. Koda sukaje gaban plaza din ita kadai ce tafita domin zuwa karbo wayar tabar khulsum acikin keke napep din,




Tunda ya hangota tana tahowa ya kafeta da idanuwansa domin dama gaba daya hankalinsa awurin yake, cike da nutsuwa take takawa sannu sannu wadda kallo daya zaka yi mata ka fahimci cewar hayaniya bata rabeta ba sannan ba magananniya bace domin yanayinta kadai ya isa ya gamsar dakai hakan.




Yana nan zaune tayi sallama tashigo, shine ya amsa mata sallamar domin su nazifi basu ma kula da shigowarta ba dalilin hankalinsu yana can ga kallon kwallon da sukeyi a yar karamar television dinsu dake can saman wata kanta,




"Sorry kamar nabar wayata a nan ko?" Tafada tana dube dube,




"Ehh gashi, nayi niyyar inbiku inkai miki ma but har kun rigada kun tafi"




Hannu ta mika ta karba tana fadin,




"Babu komai nagode"




Hannun nata yabi da kallo wanda yatsunta sukasha dark maroon din lalle wanda yayi mutukar kawata hannun,




"Karki damu, Allah yakiyaye hanya"




"Amin, nagode"




Daga haka tajuya tafice daga cikin shagon, kamar dazu yanzunma binta yayi da kallo kamar zai cinyeta har yadaina hangota sai lokacin hankalinsa yakoma jikinsa domin gaba daya lokacin da tana nan baya tareda shi. Murmushi yayi yajingina da jikin bango yana bin number dinta da kallo wacce ta kasance special number, sumar kanshi yashafa yana murmushi,




"Wato komai nata special ne kenan kamar yadda itama take special...."




Haka yaci gaba da zama yana kallon number dinta har husna tashigo ta iskeshi ahaka, zama tayi akujerar dake gaban kekenshi,




"Ya fahad murmushin me kakeyi?"




Duk da yana son ya daure mata fuska kamar yadda yasaba yau yagaza yin hakan yasan hakan baya rasa nasaba da farin cikin da yake ciki, lumshe idanuwansa yayi yana sake tuno fuskarta mai dauke da beautiful points wadanda ke kara mata kyau,




"Ya fahad ina dinkin nawa?"




"Na saidashi"




Murmushi tayi dadi yana ratsata, yau wacce rana fahad ya sakar mata fuska harda tsokanarta,




"Idan kasiyar ai nasan zaka siya min wanine shiyasa"




Tallafe kumatunshi yayi da tafin hannunshi na hagu yana kallonsa, hannu takai zata warci wayarshi yayi saurin kaucewa yana harararta,




"Wai bana hanaki tabani ba?? Meyasa bakya jin magana ne?"




Marairaicewa tayi tana kallonshi,




"Am very sorry my heart beat"




Baice komai ba yasoma laluben kayanta acikin tulin himilin kayan dake gefenshi, aranshi yana tunanin halayyar husna ta son tabashi shiyasa baya sakar mata fuska sosai saboda indai zatazo wurinshi to sai tayi yunkurin taba masa hannu ko wani abu mai kamada haka, ciro mata kayanta yayi ya ajiye mata agabanta sannan yatashi ya hado mata kan kwanukanta wadanda take kawo masa abinci duk da bawai ci yakeba dan su nazifine ke cinyewa, saida tagama janshi da magana da wasa sannan ta kwashi kayanta ta tafi, tashi yayi yafita salla ana idarwa yadawo yazo yasoma yanka kayansu Bilkisu.




***




  Agajiye lilis takoma gida kamar koda yaushe yauma gidan acike yake da makota da kawayensu meenah amare domin anata shirye shirye,kanta yau har wani ciwo yakeyi sakamakon uban yawon da suka sha a kasuwa itada khulsum ga yunwa da take ji,




Sama sama take amsa kowa ta bude dakinta ta shiga itada hudah wacce ke makale da ita, tana zama Hindu tashigo rikeda lemon roba mai sanyi da ruwa,




"Yawwa yar albarka kamar kuwa kin san kishi nake ji sosai, gaskiya yau mun kwashi rana"




"Sannu anty mai gado, ai duk wanda yaganki yasan kin wahala"




"Kedai bari Hindu" tafada tana balle murfin robar lemun"




"Inkawo miki abincin?"




"Kawo min Dan sai nafara ci sannan zanyi salla" tabata amsa tana kokarin bawa hudah lemon abaki, fita Hindu tayi ita kuma taci gaba da karbar lemon tana bawa hudah.




Shinkafa da wake da ganye Hindu ta kawo mata da manja da yaji nan ta sauko taci sannan tashiga ta watsa ruwa tafito tayi salla, nan inda tayi sallar suka baje itada hudah suka hau bacci.




***




 Fahad bai bar shago ba sai bayan sallar magrib domin saida yagama yanka kayansu Bilkisu kaf sannan yanufi gida duk da irin tarin yunwa da gajiyar dake baibaye dashi, lokacin da yaje gida bai shiga cikiba dakinsu yafara shiga yayi wanka sannan yashiga cikin gidan, dukkansu suna falon mamu suna kallon wasan kwaikwayo na aku mai labari wanda ake gabatarwa agidan television din ART, daga bakin kofa yatsaya yagaidasu sannan yawuce dakin ayiyah duk da yanajiyo tsokanar da mamuh keyi masa bai kula ba domin yunwa yakeji dan rabonshi da abinci tun safe.




Abincin dare yazuba yaci wato tuwon biskin masara miyar taushe yana ci yana santi har yagama yafito bai koma inda su ayiyah sukeba yafice ya nufi dakinsa, farar jallabiya yasaka yafita sallar isha'i domin daf ake da ashiga. Koda aka idar yadawo kwanciya yayi da niyyar runtsawa amma sam yakasa yin baccin sai juyi da yafara yi, fuskarta kawai yake gani wacce ke dauke da murmushi tana yimasa magana,bashida zabi illa na yabi shawarar zuciyarsa ko zai samu sassauci.








*_Ummi A'isha_*    



11/28, 08:14] Hafsat Rano: © *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_



*KAMAR DA WASA...!*??




  _*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*




   *4*




       ***Kasa nutsuwa yayi sakamakon dukan luguden da zuciyarsa keyi tamkar zata faso kirjinsa tafito waje dan tsananin zafin sonta, ahankali cikin sanyin jiki yatashi ya dauko wayarshi wacce ke ajiye tana charge saboda akwai wutar nepa agari,


Komawa yayi ya kwanta ya lalubo contact dinta, _soul mate_ shine sunan da yasaka mata nan yakurawa number tata ido kamar wanda ke son haddaceta har zuwa tsawon wani lokaci, yanke shawarar tura mata da sakon karta kwana zuciyarsa tayi nan ya rubuta mata ya tura mata cikeda shaukin kaunarta har saida yaga sakon ya tafi sannan yaji ya dan samu nutsuwa, ajiye wayar yayi akusa dashi kamar wadda ake jira nan tasoma tsuwwa amma bai kulaba domin jikinsa yabashi husnah ce wadda ba komai zata fada masaba illah ta kara masa damuwa dan haka yashare yaci gaba da tunanin abar kaunarsa.


***


  Jikinta sanye da yar guntuwar karamar riga kalar ruwan madara wacce take marar nauyi da kauri tana tattara wani report da zata gabatar acikin laptop dinta taji shigowar sako, duk da bata dubaba saida tayi murmushi domin tasan bazai wuce hamood dintaba wanda ko mintuna biyar kwarara basuyi da gama wayaba, saida ta shanye sanyayyen lemon dake gabanta sannan ta janyo wayar bayan ta rufe laptop din. Kwanciya tayi tabude sakon, abin mamaki yabata saboda ganin wata number wadda bata hamood ba, cikin mamaki ta soma karantawa kamar haka,   _Salam yake kyakkyawa,hakika kinyiwa zuciyata wani tarko mai wuyar Ketarewa, ganinki sau daya tal yana barazanar kawar da tunanina daga gangar jikina, wallahi ban taba ganin wata halitta wacce tayi daidai da ra'ayina kamarki ba, kece mace tafarko da nafara so tun kafin nayi ido biyu da ita, dan Allah karki ki k'i amsar soyayyata domin idan baki amintaba zan iya rasa rayuwata akan sonki, wallahi ina mutukar sonki, ina sonki bilkisu._


Dora wayar tayi akan kirjinta gabanta yana faduwa sannu sannu, aranta tana tunanin to shikuma wannan waye shi? A ina yataba ganinta da har yaji yana sonta? Bata da amsa dan haka tayi watsi da tunanin batare da tabarshi yayi tasiri acikin zuciyarta ba. Addu'ar bacci tayi ta shafa tayi kwanciyarta bayan takashe wayarta, amma me koda gari yawaye tana kunna wayarta sakonshi ne yafara shigowa cikin wayarta inda yake yimata barka da safiya da wasu kalaman soyayya masu sanyaya zuciyar masoya, dan guntun tsaki taja ta ajiye wayar gefe ta kwanta batare da tabi takan mai turo sakon ba.


  Aranar ko aiki bataje ba domin sunata soye soye da dafe dafe kasancewar ranar za akawo lefen meenah, itace akan komai gashi gidan ba laifi yayi albarka domin yan uwa na kusa da makota duk anshigo domin karbar kayan, sai misalin karfe uku na yamma aka kawo kayan nan aka shiga tarbar baki da abubuwan da aka tanadar musu basu bar gidanba sai bayan da sukayi sallar la'asar sannan suka tafi nan kuma makota aketa shigowa ganin kaya wadanda suka kasance akwatuna hudu manya sai dan karamin kit na biyar kalar ruwan kasa ita kuma Hindu sai nanda kwana biyu za akawo nata. Ita dai bilkisu yau tunda tatashi kanta adaure yake domin maiyi mata sakon nan ba dainawa yayi ba sau hudu kenan yau yana turo mata sakonni masu dauke da kalaman so da kauna tun tana sharewa har ta zauna tana son sanin waye.


***


   Fahad yau tunda yafita shago baiyi aikin kowaba sai nasu bilkisu nata yawuni yana hadawa domin dinki na musamman yayi mata wanda babu irinshi ashagon kuma koda yagama hadawa bai barshi ashagon ba bare har aratayeshi a hangar wurin da suke rataye kayan da suka dinka, shi kansa ya yaba da dinkin da yayi mata shiyasa yake jin zuciyarshi wasai, Abu daya kawai yanzu yake bukata shine yaji muryarta amma yasan hakan ba mai yuyuwa bane. Wata numbershi wadda bai cika amfani da itaba yasa numberta yakirata amma harta tsinke ba adaga ba sai da yasake kira sannan yaji ta dauka cikin sanyayyiyar muryarta wadda kamar tana bacci, sallama tayi amma sai yasamu kansa da kasa amsa mata domin wani irin faduwa gabanshi yasoma yi wanda bai san daliliba,


Sau uku tana fadin "hello.... Hello....., hello"


Jin bai amsaba takatse wayarta, wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke sai lokacin yaji yasamu kwarin gwiwar yin abinda yake gabansa, tashi yayi ya tattara inasa inasa ya nufi gida lokacin misalin karfe biyar da wurin mintuna ishirin, yana zuwa gida kayan ball dinsa yasaka yafita batare da yashiga koda cikin gidanba acan yasamu ya ragewa kansa damuwa domin sai karfe 6 da wani abu yadawo. Wanka yayi yasha turare kamar wanda zaije zance yafita masallaci can yayi zamansa shida saleem har saida sukayi sallar isha'i sannan suka fito, wani sabon zaman suka sake dasawa akan dakalin simintin dake kofar gidansu saleem wanda wurin yake fuskar mutane ga hasken farin wata wanda ya hadu da hasken lantarkin dake kafe atsakiyar layin wanda ya ratsa ta cikin unguwar tun daga farkon layi har zuwa babban titi can gefe daya kuma yarane dankam masu soya awara nayi wasu kuma gyada suke saidawa da dafaffen kwai da sauransu.


  Daga kansa sama yayi yana kallon taurari wadanda suka karawa sararin samaniya ado da kawa, cikin sanyin murya yafurta,


"Abokina am in love....."


Juyawa saleem yayi ya kalleshi yana murmushi sannan ga alamun mamaki nan bayyane akan fuskarshi,


"Yaushe? Kuma wacece?"


Lumshe idanuwa fahad yayi yana jin wata sabuwar soyayyarta tana shigarshi,


"Wata classic beb ce, kuma wallahi najima dauke da sonta"


"Kodai husnah ce?"


Harararsa fahad yayi kasancewar akwai yalwataccen haske yasanya saleem ganin hararar hakan yasashi yin murmushi sannan yadafa kafadarshi,


"Bani labarinta abokinah..."


Saida yayi murmushin da shi kadai yasan dalilin yinsa sannan yafara fada masa,


"Nafara sonta ne tun ban gantaba, tun ranar da nafara jin muryarta a radio tana gabatar da wani shiri naji tashiga raina, kullum da ita nake kwana nake tashi, cikin ikon Allah sai gata jiya a shagonmu ta kawo min dinkunanta..... Amma bana jin zata soni"  Yakare maganar yana cizar lips dinsa cikeda damuwa,


"Saboda me kake ganin bazata soka ba? Kanada wani mummunan haline wanda ban saniba?" Saleem yafada yana fuskantarshi,


"Sam bahaka bane, saleem ta girmeni fa, jikina yana bani bazata yi accepting dinaba saboda zatace nayi mata yaro dayawa may be ma zata ji kunyar nunani awurin friends dinta da relatives dinta"


Dariya saleem yayi yana dafashi,


"To kai da waye ya aikeka son wacce ba sa'arka ba?"


"Saleem kenan, shi so ba ruwansa da cancanta,shekaru ko duba matsayi, kawai yakan shigane aduk sa'ilin da yaso koda kuwa ba ashiryawa hakanba, saleem wallahi dagaske ina sonta, ni girmemin din da tayi ba damuwa bace zan iya rayuwa da ita mutukar zata yarda ta aureni"


Shiru saleem yayi yana kallonsa, ganin yanda yanayin idonshi ya sauya zuwa ja yasashi gasgata aminin nashi,


"Abokina ka kwantar da hankalinka, ina kyautata zaton koma wacece zata soka itama domin baka da makusa kuma bakada wani hali ko dabi'a wadda bata kirkiba, kana da zuciyar neman na kanka sannan kana da kyakkyawar mu'amula da kowa, kayi addu'a abokina insha Allah zaka dace"


Kalaman saleem sune suka sanyayar mishi da zuciya sannan yasashi jin nutsuwa ta saukar masa, cigaba da kwantar masa da hankali saleem yayi har saida yaji acikin ransa zai samu bilkisu, cikeda farin ciki suka rabu da saleem yana tsokanarsa,


"To kai ka isa aurenne?"


Girarshi guda daya ya dage masa yana kallonsa cikeda mamaki,


"Nine ban isa aureba? Kabari abani matar a lokacin zaka fahimci na isa ko ban isaba"


Daga haka yamike yakama hanyar gida yana jin saleem har lokacin yana tsokanarsa amma bai tsayaba.....


© _*HASKE WRITERS ASSO.*_ _(Home of expert & perfect writers)_




*KAMAR DA WASA.....!*  








        ***Hannayensa gaba daya ya aza cikin aljihun wandon bakin jeans din dake jikinsa, jar rigace ajikinsa mai rubutu kamar haka, _All the best_,yana tafe yana kallon dukkan jama'ar da kowa hada hadarsa yakeyi, wayarshi ya zaro daga cikin aljihun wandonshi domin duba ko waye ke kiransa sunan Nazifi yagani abokin aikinshi domin shagonsu daya, yana dagawa yaji yace,




"Prince ga wasu sun kawo dinki wai nanda next week suke so"




"Gaskiya bazasu samuba dunkuna sunyi min yawa"




"Hakane but amma naga ka karbi na wasu jiya ai"




"Ehh hakane amma ai kadai fi kowa sanin yawan dinkunan dake zaman jirana ko"




"Babu damuwa bari nakira hamza naji"




Katse wayar fahad yayi aransa yana cewa "yadai fi domin ita wadda kaga jiyan na karbi nata daban take bazan iya bari wani yayi mata ba shiyasa"




Ahaka yakarasa gida direct cikin gidan yawuce domin cin tuwo baba yahango kofar dakin mamuh yana magana dasu maryam wanda baya iya jiyo mai yake fada,durkusawa yayi kasa yagaida shi sannan yawuce dakin ayiyah yana dallawa Mariya harara saboda laifin da tayi masa da sassafe tun kafin tatafi makaranta, zaune ya iske ayiyah tana damawa baba fura acikin kwanon sha na silver da ludai ga sukari agefe cikin wani kofi madaidaici, zama yayi gefenta yana fadin,




"Ayiyah kamar kuwa kin san yunwa nake ji"




"To ai ga tuwon tsari nan miyar kubewa da mamanku tayi sai ka saka kaci idan kaci sai kasha fura"




"Ai kibar tuwon nan kawai ayiyah iya furar kadai zansha"




Kafin tayi magana baba yayi sallama yashigo, matsawa fahad yayi yabashi wuri ya zauna kan lallausar dardumar dake shimfide awurin,




"Muhammadu wai yaushe dan uwanka zai bullo ne?"




Murmushi fahad yayi domin yagane Abba yayansa baba yake nufi, gyara zamansa yayi yana daukar cup din furar da ayiyah ta zuba masa,




"Dazu munyi video call dashi baba yace insha Allah cikin karshen satin nan zaizo gida"




"To Allah yakawo shi lafiya muna zuba ido, ai saika yanke masa wadancan barun naka ko ko kaji ayi masa sauka"




Murmushi yayi bayan yazare cup din dake bakinsa ya hadiye furar da ya kurba.




"A'a baba,zan dai siyo masa akasuwa sai ayiya ta dafe masa su amma wadancan na kiwone bana ci ba"




Ayiyah tana mikawa baba furar da ta dama masa ta daga kai ta kalli fahad,




"Ni ban taba ganin irin wannan kiwon ba sai awurinka ayita kiwata abubuwa amma baza aciba..."




"A'a ai kedai babu ruwanki, barni dashi" Inji baba,




Murmushi fahad yayi yakarasa shanye furar da yake sha,




"Baba ayi min hakuri dai har sai sun kara yawa"




"Ni ai bance komaiba muhammadu, Allah yasa albarka"




"Amin babanmu"




Daga haka yatashi yafita,sai da ya leka dakin mamuh ya rarrankwashi mariya sannan yafito yana kunkunin idan tasake zuwa sassafe ta buga masa kofa yana bacci sai ya lakada mata duka. Dakinsa yawace ya rage kayan jikinsa sannan ya kwanta yana nazarin rayuwa, ganin tunanin nasa yana neman yin zurfi yasashi katseshi ta hanyar daukar wayarsa ya fada yanar gizo yana duba labaran abubuwan dake faruwa aduniya.




Har karfe goma saura yana haka zuwa can yatuna da bai turawa rabin ransa good night massage ba dan haka yayi hanzarin tura mata yana lumshe idanu kamar tana kallonshi.






***




 Abangaren bilkisu ganin takasa gano wanda yake turo mata da massages dinnan sai tunaninta yabata cewar ya mudan ne cousin dinta wanda sam jininta bai hadu da nasa ba, wani tsaki taja bayan tagama karanta massage din da yashigo yanzu wanda take sa ran nashine, duk ji tayi kunci ya rufeta har saida takira hamood sukayi hira sannan taji damuwa da bacin ran dake tattare da ita sun kau.




 Washe gari bayan tataso daga aiki kamar ta biya ta shagon su fahad sai dai tafasa saboda tasan su ammah na can gida suna jiranta saboda gobe za akawo lefen Hindu shiyasa suketa shirye shirye domin bata son lokaci yakure ba ashirya komai ba kuma tasan baza ayi komaiba agidan har sai anjira zuwanta.




***




 Shi kuwa fahad yau tunda yafito shago suke tare da husna duk da ba wai yana son zaman nata bane domin kallo daya zaka yimasa ka fahimci haka sakamakon fuskarsa dake hade babu alamun fara'a ita kuwa husna duk inda yayi sai binsa take da kallon so cikeda burgewa domin sosai yau yayi mata kyau,




Yana dinka kayansu Hindu sai labari take bashi na garinsu shi dai kawai jinta yake amma bawai yana son labarin bane.




Yan shagon nasu kuwa kowa sai kallonsu yake yana yiwa fahad dariya kasa kasa,ganin bata da niyyar tafiya shi kuma ta takura masa yasashi fitowa fili yace taje ta tafi da yamma saita dawo, ai tana tafiya babu jimawa yagama abinda zaiyi yabar shagon, shagon su saleem yaje acan suka sha hirarsu wadda kusan rabi ta Bilkisu ce da take can bata san yana yiba. Saida sukayi sallar la'asar sannan suka nufi gida, koda yaje gida abinci kadai yaci daga nan ya kwanta baccin nasa na sabo nan yayishi har na tsawon rabin awa, karfe biyar da wani abu yafarka yayi wanka yafita filin ball duk da yau baya sha'awar buga kwallon amma yana son ya zauna ya kalli masu bugawar, ear piece yasaka acikin kunnenshi yafita yana sauraron wakar fall in love, kamshin oad kawai yake zubawa da haka ya isa filin kwallon yakama katanga yahau ya zauna yabi sahun wadanda ke zaune suna kallo, wayarshi ya ciro yayi dialing number din Bilkisu domin amatse yake da jin muryarta lokacin da ya kirata tana tsakiyar hayaniyar jama'a domin yan kawo lefen basu tafiba suna dai niyyar tafiya matsawa gefe tayi tai sallama cikin muryarta mai mutukar zaki wadda ta saukar masa da kasala mai nauyi cikin sanyin murya ya amsa bayan ya lumshe matsakaitan idanuwanshi sannan yabude su akan masu buga kwallo,




"Mai gado i really loves u...."




Jin abinda yace yabata mamaki duk da bata fahimci wayeba amma tagane itace number din da aketa damunta da turo mata massages dinnan, yanzu kam tagama yarda cewar ba yaya mudan bane wani ne daban wanda bata saniba.




"Uhmmm.kefa? Kina sona?"




Jin abinda yace ta dan nisa kadan sannan tace,




"Yanzu ina cikin wani uzurine amma idan anjima zan kiraka"




Kitt ta katse wayar takoma taci gaba da abubuwan dake gabanta yayinda shikuma tabarshi da faduwar gaba domin bugawa kirjinsa yashiga yi da sauri da sauri......










*_Ummi Shatu_*    



© _*HASKE WRITERS ASSO*_



*KAMAR DA WASA.....!*  







     _*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*





     *6*








       ***Bilkisu bata samu kanta ba sai dare bayan sallar isha domin har karfe 9 saura na dare mutane basu bar shigowa kallon kayan ba, sai tara da wani abu ta samu tayi wanka tayi shirin bacci domin a mutukar gajiye take jinta yau tsabar busy din da ta shiga sau daya kawai sukayi waya da hamood, yanzunma bata jin zata iya kiranshi shiyasa kawai ta kwanta taja bargo. Tafara bacci sama sama taji karar wayarta,idonta cikeda bacci ta kara wayar a kunnenta,




"Love..... Bacci kikeyi?"




Jin muryar da bata saniba yasata katse wayar tareda kasheta gaba daya domin bacci take so tayi. Wurin sau biyar fahad yana gwada kiranta sai yaji akashe daga karshe dole sai hakura yayi shima ya kwanta din yana tunata acikin ransa.




 Washe gari misalin karfe 10 nasafe ta sauka agaban shagonsu ita kadai domin ta baro khulsum a office tana fassara labaran turanci zuwa hausa itama kawai bikin nan da ya karato ne m d yake daga mata kafa, anutse take takawa babu hayaniya ta nufi shagon su fahad, yana daga waje kofar shagon gaban wani tebur yana yanka uniform din husna da ta kawo masa wuyansa rataye da tape na aunawa, sallamarta ce tafara shiga cikin kunnuwansa yayi saurin waiwayawa ganinta yasashi fadada murmushinsa yana sake bude kofofin hancinsa domin shakar kamshinta dakyau,




"Shiga ciki mana hajiya"




Murmushi tayi tanufi cikin shagon tana cewa,




"To nagode, Allah dai yasa ka cika alkawari"




P cap dinshi ya maida baya yabi bayanta yana murmushi,




"Ah haba hajiya ai ni bana magana biyu"




Kanta tabawa mazauni agaban kekenshi tana kallon cikin shagon wanda babu kowa aciki yau da alama sauran yan shagon sunyi nisan zango.




"Am nace nawane ma ragowar cikon kudin dinkin gaba daya?"




"Dubu biyar banda naki"




Tana kokarin bude jakarta batare da ta kalleshi ba tace,




"Ban gane banda nawa ba, ni baka dinka nawa kayan bane ko yaya?"




Zama yayi a mazauninsa yana wani murmushi mai kayatarwa,




"Na dinka miki, kawai dai ni ka'idata ce haka"




Dan dakatawa tayi daga binciken cikin jakarta da takeyi ta dago ta kalleshi cikin rashin sa,a idanuwanshi suka sarke cikin nata domin shima lokacin tsaka yake da kallonta, ahankali ta janye nata idanuwan ta maida kan jakarta tana cewa,




"Haka ka'idarka take kamar yaya?"




Tallafe kumatunshi yayi da hannunshi guda daya,




"Akaron farko nakan yiwa customer dina ragi ko indinka masa kyauta saboda ina son yakara dawowa so idan yadawo sai infara yimasa na kudi..."




Murmushi tayi tana jijjiga kai alamar gamsuwa murmushin da yakusa sumar da fahad azaune, kasa koda motsi yayi sai uba uban kallon da yake faman binta dashi har ta ciro kudin ta mika masa, karba yayi yana lumshe idanuwana sakamakon kamshinta da ya kusantoshi mutuka.




Sam ita bilkisu bata san abinda yakeyi ba dayake ma lokacin wayarta tana karar neman agaji alamar ana kiranta, ciro wayar tayi ta daga domin amma ce, tana dauka taji muryar meenah na cewa,




"Adda labour ba amma bace nice, dan Allah ko zaki taho mana da kayan kamshi?"




Agogon hannunta ta kalla na silver wanda yayi mata das,




"Meenah kufa matsala gareku,sakonku baya karewa, bari zan dubo"




Bata jira abinda meenan zata ceba takatse wayar ta cilla cikin jaka sai lokacin fahad ya dauke idonshi daga kanta,




"Am muga dinkunan...."




Fito dasu yashiga yi daya bayan daya, nan bilkisu tasoma santinsu tana yabawa dasu domin ba karamin tsaruwa sukayi ba koda tazo kan nata ai sai ta raina nasu  mamaa domin har na amaren bafin nata kyau yayiba gashi dinkin yafitar da shape mai kyau,




"Kai amma fa dinkin sunyi kyau gaskiya nasamu tailor insha Allah daga yanzu kai zan rinka baiwa dinkuna na"




"To hajiya Allah yakawoki"




Daga haka yadauko babbar leda yafara ninke kayan yana zubawa aciki tana tayishi sai yabon dinkin take, daf da zasu gama zuba dinkin cikin leda ya dubeta ta kasan ido,




"Hajiya ba zaki gayyaceni bikin ba kuma?"




Murmushi bilkisu tayi,




"To ai sai dai ingayyaceka daurin aure"




"Ai ban san angwayenba"




"To zan gayyaceka dinner"




Sai da ya dan bude idanuwanshi sosai sannan ya marairaice murya,




"To ai idan nazo baza abarni inshiga ba tunda babu wanda yasanni"




Murmushi ta kumayi ta mika hannu zata dauki ledar kayan amma sai ya hanata yaci gaba da rikewa,




"Karka damu kowa zai shiga tunda bamu raba gate pass ba"




"To shikenan zanzo insha Allah hajiya.... Kodan inga yanda kayan nan zasuyi miki domin zanso ingansu ajikinki"




Ya karashe maganar ciki ciki ta yadda bazata jiba, ai kuwa bata ji dinba tadai ji abinda yafada dafarko amma daga karshe bata jiba, tana kokarin daukar kayan ya hanata ya daukar mata yana fadin,




"A'a hajiya bari na rakaki dashi"




"Ok nagode amma ina son shiga kasuwa ne akwai abinda zan siya"




"Karki damu babu komai muje"




"To nagode"




Handbag dinta ta dauka suka fito yana biye da ita, suna fitowa hamza na zuwa dan haka fahad bai rufe shagonba yawuce yabi bayanta, har cikin kasuwar ya rakata ta kammala siyan kayan kamshin sannan suka fito bakin titi inda zata hau napep, shine yatsaya domin tare mata amma duk wanda yatare sai yaga da namiji aciki sai yace suje da haka har yatare kusan guda uku ana hudunne yaga namiji daya mace daya, cemata yayi ta zagaya ta saitin macen saita zauna, hakan kuwa tayi ya kinkimi kayanta ya mika mata tana yimasa godiya, baice mata komaiba sai murmushin da yake aika mata dashi can akasan ranshi kuma yana cewa,




"Zanyi missing dinki"




Yana tsaye har saida yaga sun kule sannan yakoma shago, yana shiga da kamshinta yasoma yin arangama nan ya lumshe idanuwanshi aranshi yafurta,




"Kamshinki yafi na kowacce mace"




Zama kawai yayi saman benci yakasa cigaba da aikin da yafara, sai hamza yake tayawa hira wanda ke kan kekenshi yana dinka wani leshi, ahaka yar nacin nasa husna tazo ta sameshi, shifa yarinyar nan har mamaki take bashi kamar ba daliba ba yawonta yayi yawa yakan kasa gane lokacin da take shiga class, yana mata dinkin yana daddaure fuska ita kuwa ko ajikinta dan sai zuba take kamar kanyar da bata da zaki.




 ***




 Haka al'amura suka cigaba da tafiya, abangaren su bilkisu dai kowa kagani acikin hidima yake domin biki yazo gaba daya gidansu angyarashi ansake masa sabon fenti sannan kayan falon amma suma ansakesu tun daga kan kujeru har tv da labulaye da sauransu, ada carpert ne malale afalon amma yanzu tiles akasa mai tsada sai katuwar plasma tv da aka manna abango ga kujeru kirar royal chairs nan falon ammi ya dawo tamkar na yarinya duk da tanata rokon Abba akan yabar gyaran haka yaji da kayan dakin yara domin aurar da yanmata biyu lokaci daya ba wasa ba amma yace itama so yake yadawo da ita amarya ai kuwa hakance tafaru domin gidan ba karamin kyau yayiba dan hatta dakin bilkisu Abba yagyare mata shi ansake mata labulaye sabbi sannan ansaka mata tv yar madaidaiciya abangon dake kallon gadonta sannan gefe ga dan fridge dinta ga uban fenti da dakin yasha nan daki yafito yayi fes dashi. Ana saura kwana biyu biki dakyar bilkisu tasamu ta tafi saloon da kunshi itada kawarta khulsum ba ita tadawo gidaba sai karfe biyar saura tana shiga dakinta tajiyo sallamar mutanen garko wato su iyallo, kasancewar daga ita sai daurin kirji yasa bata fitoba domin tana jiyo maganar ya mudan da alama shine yakawo su. Kai tsaye iyallo dakin bilkisu tashiga lokacin ita kuma tana toilet, ganin irin gyaran da dakin yasha yasata rike haba tana tafa hannaye tana zuba salati,




"Ah lallai wannan shine zama daram wato babu ma ranar tashi, irin wannan daki haka kamar agidan miji? Tab... To Allah yasawwaka, iye... Lallai.... Duniya sabuwa"




Juyawa tayi tabar dakin tafita ta nufi cikin gidan wato falon amma wadda ke can tana gaggaisawa da baki domin iyallo ba ita kadai tazo ba su wurin takwas sukazo ciki harda yayarta inna maigado takwarar bilkisu da kuma yayanta guda biyu wato kannen Abba gwaggo uwa da yafendo sai "yayansu,nan tazauna tana tabe taben baki da harare harare, sama sama ta amsa gaisuwar amma nan da nan aka cikasu da ruwa, lemo da abinci tunda dama ansan da zuwansu, shi dai ya mudan bai wani jimaba yakoma yabarsu anan. Bilkisu sarai taji abinda iyallo take fada lokacin da tashigo dakinta, tana wanka tana zancen zuci,




"Su iyallo trouble maker ansauka, haka kuma za ayita fama har sai ranar da kika bar gidan nan, Allah yarabamu lafiya"




Da zancen zuci tagama wankan tafito, ta shirya agaggauce tana saka kaya su Hindu na shigowa shiyasa koda tafito tare suka rankaya falon amma........








*_Ummi Shatu_*    


© _*HASKE WRITERS ASSO.*_



*KAMAR DA WASA....!*  









    _*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*




        *7*








        ***Su maama sai yaba kunshin nata sukeyi yayinda ita kuma take yaba kwarewar mai gyaran jikinsu domin kwana uku kacal da fara yimusu har ta sauya musu kamanni, Hindu da maama sarakan rashin kunya ganin takalmansu iyallo tuni suka tura dan kwali gaban goshi duk da hararar da bilkisu keyi musu haka suka dauke kai, itace tafara shiga cikin falon uwar harara iyallo ta tarbeta da ita tana tabe baki sabanin inna mai gado da ta washe hakora tana yimata lale tamkar zata goya bilkisu dan murna da tsantsar kaunar da take yimata, suna tsaka da gaisawa su maama suka shigo, maganar iyallo ita ta katse kowa daga gaishe gaishen da akeyi,




"Ke samodara daga ina kika tafi kika bar yar labibiyar yarinya dan tsabar rashin hankali?"




Dauke kai maama tayi saboda tasan da ita take bata amsa mata ba ta nufi inna maigado domin duk sunfi sakewa da ita,




"Yanzu ke kuma dan Allah bakiji kunyaba? Kiduba ki gani duk kannenki sunyi aure sun barki, gaku nan ku hudun duk kanku daya" Iyallo tafada tana hararar bilkisu, ai rufe bakin iyallo keda wuya Hindu ta dora,




"Kuji iyallon nan da takura, to dan munyi aure mun barta sai me? Kuma ma naga ba wuce shekarun auren tayiba..."




"Ke kika kulata ma, wai wani nan munyi kai daya da ita to ai halittar tatace mai kyau shiyasa har ba a iya banbance itace babba cikinmu....kum...." 




Tsawar da ammah ta daka musune yasa maama yin shiru bata karasa fadar abinda tayi niyya ba nan amma tashiga yimusu fada ta inda take shiga bata nan take fitaba, ita kuwa iyallo cewa take,




"Rabu dasu kibarsu su zageni kamar yadda suka saba, fitsararru dama me suka iya inbanda rashin kunya da rashin arziki? To wallahi bari uban naku yazo..."




Inna maigado ce tasoma tausarta tana bata hakuri ita dasu yafendo, su Hindu kuwa ko ajikinsu asalima tashi sukayi suka bar wurin suka wuce dakinsu.




***


 Tunda su iyallo suka zo kowa yashiga takura acikin gidannan gata da fadan tsiya ga sa ido gashi bata iya gani tayi shiru komai tagani sai tayi magna,abinda inna maigado bata iyaba kenan shiyasa kullum cikin yimata fada take wannan dalilinne yasa su bilkisu basa son zuwa garko wurin iyallo saboda fadanta da masifa su maama ne kadai daidai da ita domin basa bar mata.




Haka dai aka cigaba da lallabawa, gida ya cika dam da yan uwan Abba da amma domin itama ana igobe sa lalle yan uwanta suka zo daga dawakin tofa, mota uku suka ciko da yayyenta da kannenta da sauran 'yayan yan uwa, bilkisu kam yanzu tazama ba zama domin har tafi amaren zama busy, ko hamood dinta sai yar hi hi sukeyi, haka shima fahad yanzu bai fiya samunta ba duk da hakan yana sakashi cikin damuwa amma yazaiyi dolensa ya hakura.




Ranar alhamis aka fara gudanar da biki domin ranar ne sakun lalle anan unguwarsu gidan aminin babansu mai sabulu anan akayi kamun kamar yadda al'ada ta tanadar,amare sunsha kyau mutuka cikin shigar da sukayi ta ruwan bula, itama bilkisu itada mama wani leshi suka saka dan ubansu sai walwali suke, an cashe mutuka sannan anwarwasa haka aka tashi kowa cike da farin ciki, agajiye likis bilkisu takoma gida bayan sallar magriba ga dakinta ma cike yake da baki dole sai dakin Abba taje tayi shirin bacci dayake har lokacin shi bai shigoba, ko takan wayoyinta bata biba taje ta kwanta adakinsu meenah domin ta huta.




Washe gari aka daura aure kuma ranar ne zasu gabatar da dinner party dinsu a al-mukarram event center,tun safe amare basu samu zama ba hakama bilkisu bayan an idar da sallar juma'a a babban masallacin dake cikin unguwar tasu ta hotoro aka daura auren, auren Hindu da angonta Mus'ab aka fara daurawa kasancewar itace babba akan sadaki naira dubu talatin sannan aka daura na meenah da angonta Isma'il itama akan naira dubu talatin,gidansu kancame yake da hada hadar jama'a koda akazo yin albishir din daura auren iyallo yada magana tai tayi da habaice habaice duk inda bilkisu tawuce kuwa ko amma ko su Hindu sai ta rakasu da harara su kam basu san tanayiba domin sabgar gabansu sukeyi, maama cema da hudah tayi kashi taje tana cire mata pampers iyallo tazo zata isheta da fadan akan me zatazo gaban rijiya tana yiwa mutane kazanta, ita kuwa maama ta gurmuda mata baki tana farfara ido rankwashi iyallo takai mata tana fadin,




"Fitsararriya yau dinma fitsarar zakiyi min abainan nasi?"




Maama bata kulataba ta sabi yarta tayi falon amma wadda ke can itada danginta da abokan arziki sukuwa su iyallo tasu tawagar ta yan garko suna sitting room.




K'arfe takwas da rabi aka fara tafiya wurin dinner,amare da angwaye ba karamin kyau suka sha ba haka itama bilkisu ta hade cikin material din da fahad ya dinka mata tayi masifar kyau tasha head golden dama yau babu maganar mayafi daga ita har kawarta khulsum basu samu zama ba domin sune masu tsara komai.




 Cikeda doki fahad yasha wankansa cikin blue din tissue sabo fil da hularsa samfurin minister wacce ta saku da asalin dinkin hannu yayi kyau har yagaji, turaren Amirul oad yayi amfani dashi ya gauraya da turaren black xxs nan fa yafito tsaf dashi saurayi kalar birni, bakin takalmi sau ciki yasaka yadauki agogo yafita lokacin karfe takwas daidai na dare, sai da yashiga cikin gida yayiwa su ayiyah sallama mamuh sai tsokanarsa take tana cewa yagaida budurwar tasa, su Mariya kam saida ya cafki Maryam ya zuba mata rankwashi sannan yafita domin sashi sukayi agaba da dariya da kus kus, yayansa Abba yana zaune akofar gida yafito, shi dinma kallonsa yayi cikeda tsokana yace,




"K'anina yau hira aka nufa ne?"




Dariya yayi yawuce yana fadin,




"Wallahi wani biki zanje"




"To adawo lafiya"




Saida ya amsa sannan yawuce, koda ya isa almukarram event center tuni har wurin ya dinke da jama'a sai kawo mutane akeyi a motoci yayinda wasu sukazo a keke napep wasu kuma da kafarsu ma suka shigo cikin wurin, abangaren fahad shima yabi sahun wadanda suka shigo da kafarsu domin tafe yake hannunshi daya cikin aljihun wandonshi dayan kuma yana latsa wayarshi ta hannu, duk wanda ya kalleshi kallo daya baya iya gamsar dashi har sai yakara na biyu.




 Yana isa gaban hall din yayi tozali da yanmatan amare sunsha anko kowacce naji da kanta, ido yashiga ciccilawa yana son yaga ta ina zai hango tauraruwar tasa amma bai samu damar ganinta ba har aka gama shigewa cikin hall din nan shima yamaida wayarshi aljihu ya shiga, kusa da wasu samari su uku yaje ya zauna dama  mazaunin mutum hudune domin kujerun guda hudune, gefensu kuma wasu matane suma zaune su hudu, bai kai minti biyu da zamaba ya hango bilkisu tana rikeda hannun khulsum da wasu abubuwa a hannunsu wanda bazai iya gane ko menene ba, ji yayi yana dana sanin yimata wannan dinkin domin jikinta babu ko mayafi amma fa tasha kyau har tagaji kayan sunyi mata dadas ajikinta dukkan shape dinta yafito masha Allah, goshinsa yadafe ya sunkuyar da kai sakamakon sara masan da yaji kan nasa yayi, hankalinsa bai kara tashi ba sai da ya hangota kan step taje wurin amaren suna yin kus wadda babu wanda zai fahimci me suke cewa domin wurin sautin kidane yake tashi ahankali cikin wakar Umar m Sharif ta ranar kuke jira....!, yayi nadamar yimata dinkin nan domin gani yake kamar kowa na wurin ita yake kallo, sai da kowa ya nutsu sannan aka fara gudanar da shirye shiryen da aka tsara, taro da addu'a aka fara budewa sannan aka gayyaci babbar yaya wato bilkisu domin tabada tarihin amarya amma guda daya daga ciki, abunku da yar jarida wacce tasaba nan tazo ta zayyano tarihin Hindu daga karshe tajuya tana kallon isma'il angonta,




"Ango amaryarka tana da kiriniya sosai ada musamman wurin zane domin gaba daya bangon dakinsu da jikin wardrobe dinsu zanen tsintsaye ne da ciyayi, muna addu'ar Allah yasa bazata Zane muku bangon dakunanku da zanen tattabaru ba...."




Kowa na wurin saida ya dara nan ta sauka tabada abin maganar aka kira maama itama tabada tarihin auta minah. Duk inda tayi idanun fahad na kanta ji yake kamar yatashi yaje ya kareta mutane su daina kallonta amma babu damar hakan, lokacin da aka fara raba abinci da abin sha hirar matan dake zaune kusa dasu taja hankalinsa,




"Yanzu dai Yahanazu tagama auren yaranta saura maigado kuma babbar banza ko kunya bataji duk takai kannenta daki ita tana zaune agida..."




"Bakiga harda sake gyaran dakiba domin a tabbatar mana da ba ranar aure"




"Ai uwar tata ke daure mata kugu, idan taki fito da miji basai su hadata da duk wanda suka so ba..." Daya matar tafadi cikin takaici, idonshi ne yakai kan bilkisu wacce ke tsaka da hidimarta khulsum ta miko mata wayarta nan ta Karba ta nufi kofar baya, zip din rigarta ta baya ya dan sauka har hannun farar bra din jikinta ta dan leko amma saika lura dakyau zaka gani, cikin azama, kirjinsa yana fat fat yabi bayanta tana tsaye tana waya gadon bayanta duk awaje, cikeda kishi karara yatsaya abayanta ya kareta, jin tsayuwarshi yasata juyowa ta kelleshi bayan ta maida wayar kunnenta......








*_Ummi Shatu_*    


© _HASKE WRITERS ASSO._



*KAMAR DA WASA....!*  







   *_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*





     *8*




  *Mai fitarmin da book kiji tsoron Allah haka kuma wadanda ake turowa kuji tsoron Allah kudaina karanta min mutukar ba siya kikayi ba saboda kamar da wasa wannan karon na kudine,idan kina so ki biya ki karanta.*






     ***Sai da idanuwansu suka sarke da juna sannan tajanye nata ahankali bayan ta juya masa baya, bayan nata yake bi da kallo kasa kasa, jin takun tafiya abayansu alamun wani na zuwa yasashi saurin kai hannu kan zip din yayi sama dashi hakan yayi daidai da karasowar khulsum wurin, saurin matsawa baya yayi yayinda ita kuma Bilkisu tajuyo atsorace amma ganin khulsum tsaye bayanta tana waya yasata sauke ajiyar zuciya domin tagane itace taja zip dinta ko kadan bata kawo cewar fahad ne ba, ita kuwa khulsum bata ma san abinda ke faruwa ba kawai dai ta iskesu tsaye ne, yayinda gogan ke tsaye yayi mata kurr da ido hannayensa sanye duka cikin aljihun wandonsa.




  Kusan tsawon mintuna biyar ta dauka tana wayar daga bisani sukayi sallama da hamood dinta takatse wayar tajuyo tana kallon fahad dan tuni khulsum tabar wurin,




Langabe kai yayi yana kallonta tamkar wani yaro,




"Kazo ashe?..."




"Uhm hajjaju nazo tun dazu"




Murmushi tayi tana duba wayar dake hannunta,




"Zaka jira atashi ai ko?"




Girgiza kai yayi har lokacin kansa langabe yake,




"Idan nayi dare sosai zaneni za ayi agida...!"




Ita abinma dariya yabata yanda yake yi mata wani shagwaba sai kace hudah,




"To yanzu ya za ayi?"




"Muje ciki amma nanda 10 minutes zan tafi"




"Ok babu damuwa muje..."




Sai da ya dan rausayar da kai sannan yawuce tabishi abaya, kai idan kaga yanda suka basar sai abin yabaka sha'awah tamkar wasu saurayi da budurwa,duk da hill din dake kafarta akafadarshi tsayinta ya tsaya ahaka suka kai tsakiyar hall din wanda tuni ya kancame kasancewar amaren sun fito suna takawa mc kuwa sai kiran sunan Bilkisu yake yana cewa yana son ganin babbar yaya wato adda bilkisu yayar amare.




 Bilkisu ai jaka ta balle tashiga cikin kannen nata tana yimusu ruwan sabbin nairori suma suna yimata, su hudu gwanin sha,awa domin harda maama kamar abin hadin baki kuma sai hudah da mina suka soma kuka harda maama, ita kanta ji tayi kwalla tana taho mata shiri tabar cikin filin ta nufi hanyar fita, daga inda yake zaune yana ganin duk abinda ke faruwa abisa dukkan alamu akwai shakuwa mai girman gaske tsakaninta da kannen nata, tashi yayi yabi bayanta, kamar yadda yazata kafin ya cimmata har ta ida ficewa. Abakin kofar hall din yaganta kan baranda ta jingina da bango,




"Haba hajjaju da girmanki..."




Juyowa tayi suka hada ido idanuwanta har sun danyi ja,murmushin karfin hali tayi,




"Badai har zaka tafiba?"




"Ehh gaskiya wucewa zanyi kar gida su rufe min kofa"




Wannan yaron yanada abin dariya ta ayyana hakan acikin zuciyarta bayan ta sake murmusawa,




"To shikenan nagode, yanzu muje gaban waccan motar inbaka naka hasafin..."




Dan kada idanuwanshi yayi,




"Nidai gaskiya kibarshi, yanzu sai kowa yasan nazo biki? Bana son daukar kaya..."




Murmushi tayi tajuyo sosai tana kallonsa,




"To shikenan Allah ya kiyaye hanya nagode"




"Ba rakiya?"




Wani murmushin tayi har saida hakoranta suka bayyana tasauka tana nuna masa hanya alamar suje, jerawa sukayi har kusa da gate nan tajuya takoma ciki amma me tana zuwa gaban hall din taji yace,




"Saida safe atashi lafiya"




Juyowa tayi cikeda mamakin sake biyota din da yayi amma kafin tayi magana har yajuya yatafi, ciki takoma inda aka cigaba da hidima ba atashi daga wannan dinner ba sai karfe goma sha daya saura ahakanma dan abbansu ya iyo waya yace lallai lallai atashi haka ne nan aka rufe taro da addu'a aka tashi kowa yanufi gida. Fahad kuwa koda yakoma gida raba dare yayi yana sakawa da kuncewa kawai tunanin bilkisu ne ke azalzalar ruhinsa, harga Allah yakamu da mugun sonta to amma bashida tabbacin ko akwai wanda ta tsayar amatsayin mijin aure, yajima yana juyi har dai daga karshe yaji muryar yaya Abba yana cewa,




"Yau meke neman hana dan kanina bacci??"




"SO" yafada acikin zuciyarsa amma azahiri sai yajuya ya kalleshi ta cikin hasken kwan lantarkin da basu kasheba,




"Babu abinda zai hanani bacci kawai dai nagajine..."




"To idan kahuta sai ka kashe mana wutar muyi bacci ko?"




Murmushi fahad yayi bayan yatashi zaune,




"Gaskiya nifa bazan iya bacci aduhu ba harga Allah.."




"To nikuma bazan iya bacci da haskeba, Allah yakawo mu kuma..."




Dariya fahad yayi yana jan pillow dinshi,




"Kuma ahakan kasan har kaguwa nake kazo weekend saboda mu cigaba da fada akan rufe kofar toilet da budewa duk da dai kana hanani bacci..."




Dariya shima yaya Abba yayi yagyara kwanciyarsa yana fuskantar fahad din,




"The same thing da yake faruwa dani kenan duk time din da nakoma school wallahi wani lokacin har dariya drama dinmu kebani abokaina suyita tambayata idan sunga ina dariya ni kadai daga karshe dai nasanar dasu kai natuno kullum sai munyi fada saboda ni bana son haske kai kuma baka son duhu sannan ni bana iya kwana har gari yawaye ban shiga toilet yakai sau uku ba gashi kaikuma k'ara kadance ke tada kai daga bacci gashi kofar k'ara take dashi..."




Dariya fahad yayi yana kokarin kwanciya,




"To ai idan baka nan alla alla nake kadawo kaci gaba da bude kofar"




Dariya sukayi gaba daya nan suka cigaba da hirarsu kamar abokai dama ko tsaye abban bawani fin fahad yayiba haka suka taso tare kamar twins, wannan hirarce ta daukewa fahad hankali dan kafin su farga har 12 da rabi takusa, tashi Abba yayi yanufi toilet nan fahad yasa pillow yatoshe kunnenshi lokacin da yaji kofar tafara kara kiiiiyyyyyyyy, Abba na fitowa yakashe wutar dakin duk da haka saida fahad yakunna light awayarshi sannan ya iya bacci.



***

 Su Bilkisu yau zasu gama biki domin kuwa yau za a mika amare gidansu, tun safe Bilkisu take tattara musu sauran kayayyakinsu da ba akai ba kafin kace me gida yacika da yan kai amare ita kam Bilkisu batayi niyyar zuwaba amma khulsum ta matsa sai sunje domin saurayinta zaizo yakaisu, ana yin sallar isha'i akayi haramar kaisu saida aka gama zagawa dasu wurin iyaye sukayi musu fada sannan aka tafi kaisu gidajensu. Hudah aka fara rakawa unguwar jan bulo sannan aka raka Mina sharada, duk inda sukaje Bilkisu bata shiga domin tasan gidajen asalima kayan ciki sune suka jera. Misalin karfe goma suka dawo daga rakiyar amaren, yanzu kam yan biki saura kadan domin dama yau duk wasu suka tattafi sai najiki irinsu iyallo da yan uwan amma harda mahaifiyarta hajjo, ba karamin dadi tajiba ganin dakinta fayau babu kowa nan ta dauko hudah bayan tayi mata wanka itama tayi tabi lafiyar gado domin maama na can wurinsu amma acan zata kwana. Wani lafiyayyen bacci tayi domin tunda ta kwanta bata motsa ba saida 6 nasafe tayi nan tatashi tayi salla tasake komawa har 9 sama sama tajiyo muryar hajjo kakarta tana fadin,




"Ohh maigado ai sai asaceki dake da katifar da kike kai batare da kin saniba, kowa yatashi banda ke"




"Ai dole tayi bacci hajjo wallahi tagaji dayawa tasha zirga zirga" Inji maama wadanda suka shirya tsaf domin zuwa gidan amare suda su iyallo, sai bayan sun tafi da dadewa sannan bilkisu tatashi ganin babu hudah akusa da ita ya tabbatar mata da tabi tsohuwarta, wanka tayi ta caba kwalliya tasha gown ta atamfa dark blue, wurin ammah ta nufa wacce ke can dakinta ita da baki yan Allah sanya alkhairi, gaisawa dasu kawai sukayi tafito tawuce kitchen koko da kosai ne akayi na karin kumallo sai dankali da kwai wanda aka soyawa abba, dankali da kwan ta diba ta zauna tayi nak sannan tafito sai lokacin wayoyinta suka fado mata dan rabonta dasu tun ranar dinner da daddare, daki takoma ta daukosu gaba daya ta kunna su nan sakonni suka yita shigowa rututu kusan 10 amma aciki guda biyu na hamood ne wanda ke sanar da ita zai dawo Nigeria jiya idan yazo zai kirata dan Allah tazama mai rike masa alkawari domin itace matar aurenshi, dariya tayi tana jin farin ciki yana ratsata, sauran massages din kuwa duk na fahad ne wanda bata da masaniyar cewa shine, daga karshe ajiye wayoyin tayi ta dauko laptop dinta tayi downloading din wani Indian series mai suna Rangarasiya ita kam Allah yadora mata kaunar Indian film tana tsaka da kallo khulsum tayi sallama,




"Au ke baki tafi gidan amaren ba?"




Murmushi tayi,




"Me zanje inyi musu kuma"




"Ai shikenan, bani ruwa insha"




Kawar da laptop din tayi daga gabanta ta mike ta dauko mata ruwan ta miko mata,




"Ya labarin mutumin ne?"




"Yataho ai may be ma yanzu ma yasauka"




"Ahh lallai abun yazo amarya"




Shiru bilkisu tayi saboda tasan kawai neman magana ne irin na khulsum.




  Dasu iyallo sukaje gidajen amaren kowacce aciki babu wacce batayi cikiyar bilkisu ba amma babu ita sai maama itace ma ke cemusu kila da yamma bilkisun zataje musu nan ta gyaggyara musu abubuwan da yadace sannan suka tarkato suka dawo iyallo dai sai sakawa danta albarka take kan irin rawar daya taka wurin zubawa yayansa kayan daki nagani na fada. Har suka dawo gida bilkisu natare da khulsum suna kallo saida rana tafara yi sannan tatafi domin tanada karanta labaran rana.




 Da yamma dukkan baki suka tafi amma banda iyallo ita kam tana nan Allah kadai yasan ranar tafiyarta, haduwa sukayi maama da bilkisu suka gyare gidan tsaf yadawo yanda yake da, suna kammalawa Abba na dawowa daga garko dama duk karshen wata yake zuwa ya duba garin nasa a matsayinsa na hakimin garin manya manyan kaji da zabbi aka shigo dasu sai kwan zabbi cikin bokitin roba dama duk ranar da yaje haka yake dawowa da kaya niki niki domin jama'ar kauye akwai kara banda su yalo, gwaiba da sauransu, nan dai su bilkisu suka shiga aiki baji ba gani ita dai iyallo tana zaune tsakar gida kan tabarma ta kishingida tana ganin mai shiga da mai fita domin mutane sunata zuwama amma Allah yasanya alkhairi. Sai dare maama ta tattara tatafi bayan mijinta yazo daukarta, bilkisu rufe kofarta tayi tai kwanciyarta nan taga text din minah da na Hindu kamar hadin baki duk suna yimata korafin rashin zuwanta murmushi kawai tayi ta ajiye wayar tafada kogin tunani.




  Washe gari bata tashi dawuri ba sanin acikin hutu take ba aiki zata fita ba, koda tafito tuni har anhada abin karyawa kowa yaci sai nata kadai dauka tayi takoma dakinta taci tana kammalawa kiran abba yashigo wayarta cikeda ladabi ta daga nan yace taje yana kiranta, hijab ta dauka tafita jikinta na bata lallai akwai abinda ke faruwa bare iyallo trouble maker tana nan.....








*_Ummi Shatu_*    


© _HASKE WRITERS ASSO._



*KAMAR DA WASA...!*  







    *_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*




   *Dan girman Allah na rokeku kudaina fitar min da book, ku kuma wadanda aka turowa kuji tsoron Allah idan baki siyaba karki karanta.*





      *9*






       ***Falon tsit sai fadan iyallo dake tashi duk tabi ta cikashi da hayagaga,




"Haba yarinya tadade da kawowa misali amma kun zuba mata ido sai dai garin Allah idan yawaye tayi wanka ta saba jaka tatafi wani wai aikin gwamnati, to wallahi ya isa haka sam bazan lamunta ba kannenta duk gasu can adaki amma ita tana gida, wannan ai ba dabara bace karatunnan tayi ta dada tayi ta dada wai shin karshen biro da takarda zata gani? To wallahi wata biyu kacal na bata ta fito da miji idan ba hakaba ga dan uwanta nan mudan ai tushensu daya sai a aura mata shi...."




Zama bilkisu tayi tana sauraron fadan iyallo har saida tayi shiru sannan Abba yayi magana yabata hakuri yace insha Allah za ayi yadda tace, ita kam amma shiru tayi batace komai ba har akayi aka gama. Juyawa Abba yayi ga bilkisu yace,




"Uwata kinji abinda hajiya tafada lallai lallai kifito da miji cikin wata biyu ayi miki aure"




Daga kai tayi yayinda iyallo ta bude murya,




"Yawwa gaya mata da kyau, wannan yawon karatu ya isa haka"




Sallamarta abba yayi tatashi tatafi takoma dakinta ta zauna, sam bata sa abin aranta ba domin karma ya dameta taci gaba da harkarta. Kwana biyu da faruwar hakan iyallo ta tattara takoma garko kuma aranar maama tazo nan bilkisu take bata labarin abinda yafaru,




"Iyallo jaraba, ai wallahi adda labour da kin wanketa tas kafin tatafi"




"Ke maama kar nakara jin haka, ba mahaifiyar babanku bace? Itama fa tana da iko daku infada muku gaskiya, kedai mai gado kawai kiyi abinda tace ki fidda miji kiyi auren nan kihuta muma mu huta da maganganunsu"




Bilkisu dai batace komai ba domin har yau bata samu hamood ba shima kuma bai kirata ba, sai yanzu hankalinta yasoma tashi ganin ankusa wata daya domin har hutunta yakare takoma aiki, agefe daya kuma iyallo kullum cikin bugowa abba waya take tana kara jaddada masa maganar auren mudan da bilkisu, ita kuwa bilkisu ji take akan ta auri ya mudan gara ta auri koma waye.




 Wasa wasa lokaci sai tafiya yake amma shiru babu labarin hamood duk ta inda take tunanin zata sameshi tarasa domin daga Facebook dinshi har Twitter da instagram duk shiru, yanzu kam tashiga mutukar damuwa gashi wanda ke damunta batare da tasan ko wayeba bai fasaba kullum yake kiranta kuma yaturo mata text ganin wankin hula na shirin kaita dare yasata nemarwa kanta mafita. Daren ranar kwana tayi batayi bacciba tanata sakawa da kwancewa daga karshe shawarar khulsum ta fado mata inda take cemata,




"Ni kawai ina ganin ki baiwa bawan Allahn nan dama wallahi yafito ya bayyana miki kansa idan yayi miki kawai ki aureshi ki manta da wani hamood tunda har yanzu babu wani labari game dashi...."




Lumshe idanuwanta tayi bayan ta dafe kanta dake sara mata, tabbas yazama dole ta dauki shawarar khulsum mutukar tana son hakanta ya cimma ruwa,wayarta ta jawo ta duba agogo karfe 2 da yan mintuna na dare, text ta soma rubutawa wannan guy din da har yau bata san ko wayeba, bayan yanuna mata yatafi ne ta kashe wayar gaba daya tana jiran zuwa gobe sai ayita takare.




***


 Ga fahad kuwa abun ba sauki domin har gobe bilkisu ce zabinsa duk da yasan tayi masa nisa kokuma tafi karfinshi amma dayake ita zuciya babu ruwanta da duk wadannan abubuwan haka ta nace da soyayyarta, kullum aikin kenan tura mata love massages gashi tun bayan bikin kannenta bai sake ganinta ba dan program dinma da takeyi yanzu shiru sai wata bakuwar murya ce keyi gaba daya yarasa gane abinda ke faruwa. Bayan yadawo daga sallar asubah kamar yadda yasaba yazauna saman katifa yajawo wayarshi da niyyar yakirata ya tadata tayi salla yana kunna wayar yaga massage dinta jikinshi na rawa yabude domin wannan shine karo nafarko da ta taba turo masa sakon karta kwana, da sauri da sauri yafara karanta sakon nata kamar haka;




_Amincin Allah ya tabbata agareka, dan Allah idan har bazaka damuba ina son ganinka gobe agidanmu akwai muhimmiyar maganar da nake so mu tattauna, nagode._




Ajiyar zuciya yasauke yana jin tsoro yana shigarsa, tambayar zuciyarsa yafara yi to yanzu idan taganshi tace baiyi mata ba kokuma tace kar yasake kulata fa? Yajima zaune cikin rashin sanin abinyi daga karshe yabarwa Allah ya kwanta ya tura mata da reply,




_Sarauniyar mata ina fata kin tashi cikin aminci da koshin lafiya, insha Allah yau zan amsa kiranki batare da jinkiri ba amma inaso kibani time da kanki kuma kibani address din saboda ban san gidan nakuba, masoyinki ahar kullum....!_




Daga haka yatura mata ya ajiye wayar yana addu'ar samun nasara acikin wannan al'amari. 




 Lokacin da taga text din nashi murmushi tayi tana yabawa iya kalamansa acikin zuciyarta, babu bata lokaci tatura masa address din da time din da zaizo, koba komai tana jinta da dan dama dama yau sabanin kwanakin baya da taketa fama da kunci da bacin rai, hatta amma yau ta fuskanci walwala atattare da ita amma batace da ita komai ba.




 K'arfe uku na yamma kiranshi yashigo wayarta lokacin tana shiryawa bayan tafito daga wanka, tana dauka yace mata gashi yazo nan tace tana zuwa, karasa shiryawa tayi tafita ta zira flat din takalmi,fararen kujeru guda biyu na roba ta daukar musu tafita zuwa gaban part din Abba wanda ke makotaka da gate ta ajiye ta zauna, waya tayi masa tace yashigo, har yashigo bata dago ta kalleshi ba hankalinta na kan wayarta tana turawa da khulsum text sai dai kamshinsa da ya ziyarceta.




Da sallama ya isa wurinta ta amsa batare da ta dago ba, zama yayi yana yimata kallon kurulla, ashe ita din yar babbar koface bai saniba sai yau domin mahaifinta yarike mukamai daban daban domin yanzu haka shine commissioner na ruwa ajihar sannan kuma mai baiwa governor shawara ta musamman akan harkar ciyar da makarantun kasa da secondary,




Dagowa tayi ta kalleshi idonta yashiga cikin nashi nan mamaki ya cika ta domin ganin wanda ke gabanta,




Murmushi tayi,




"Sannunka da zuwa musa..."




Murmushin shima yayi,




"Yawwa barkanki dai hajjaju amma muhammadu nake ba musa ba"




"Ayya sorry namanta ne, ya aiki?"




"Alhamdulillah"




"Allah yataimaka"




"Amin"




Shiru sukayi dukkaninsu, kafin daga bisani ta danja numfashi tace,




"Dama kaine wanda ke kirana sannan yake turo min wannan massages din?"




Babu fargaba ko tsoro ya daga mata kai,




"Eh nine..."




Murmushi tayi ta maida kanta gefe,




"Haba Muhammad to ai ni ba sa'ar aurenka bace.."




"Ko menene dalili?"




"Saboda nayi maka girma ai,inada kanne twins kamarka el'ameen da elmustapha suna Sudan suna karatu"




"A'a mutukar kin amince zaki aureni toni wallahi bakiyi min wani girma ba"




Murmushi tasake yi tana kallon Rabi mai aikin amma wadda aka kawo mata kwana biyu da suka gabata domin tayata aikace aikace, ruwan roba da lemon kwali tazo ta ajiye agaban fahad sannan tatafi hakan yabaiwa bilkisu damar cigaba da fadin abinda ke ranta,




"Muhammad wallahi ni ba mate din aurenka bace, saboda ko ahaifi na girmeka sosai, ai zakaji kunyar nuna ni agidanku da wurin abokanka amatsayin mata"




"Mutukar kin amince wallahi ni babu maganar kunya, kece dai kawai zakiji kunyar nuna ni amatsayin mijinki saboda nayi miki kankanta"




Fuskarta babu yabo babu fallasa ta kalleshi babu alamun wasa tace,




"Kasan me nake so dakai? Daga yanzun nan kar ka kuskura ka kuma zuwarmun da magana makamanciyar wannan, ada banma yi niyyar sauraronka ba amma dole tasaka na saurareka sakamakon mutuncin da kayi min abaya"




Shiru yayi yana faman aikin goge screen din wayarshi da handkerchief din dake hannunshi sai zuwa can yanisa ya kalleta kadan ta kuwa sha kunu kamar bata taba dariya ba,




"Shikenan tunda haka kikace amma ni anawa rashin hankalin idan akazo kan batu na aure wasu muhimman abubuwa ake dubawa bawai maganar ka girmi mutum ko shi ya girmeka ba dan haka nidai har gobe ina nan akan bakana dan wallahi ina sonki..."




"Naji kana sona amma ni nagama fada maka ra'ayina idan kaji fine idanma bakaji ba duk daya, sai anjima"




Daga haka tamike ta wuce cikin gida cikeda takaici wannan wacce irin lalacewa ce ace yaro karami wai yazo mata da maganar aure babu ko kunya bare tsoro lallai zamani mai yayi, dakinta tashiga ta watsar da komai dake hannunta ta kwanta kan gado idonta akan tv, gaba daya ranta abace yake meyasa hamood yayi mata haka? Duk da zuciyarta na bata yakinin tayuyu akwai gagurumin abin da yafaru dashi wanda ita bata saniba....








*_Ummi Shatu_*    


© *HASKE WRITERS ASSO.*



*KAMAR DA WASA...!*  





   *_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*






  *10*






   *Dan Allah idan baki siyaba karki karanta....*





      ***Ji take kamar tafashe da kuka ko zata samu saukin damuwar dake addabarta,




"Lallai yaron nan yama raina min wayo wallahi..."




Haka tayita fada tana yin kwafa daga karshe kasa jurewa tayi har saida ta kira khulsum, khulsum na dagawa bilkisu tafara jaraba kamar khulsum din nada masaniyar abinda ke faruwa,




"Gaskiya tailor nan baida kunya wallahi saina saita masa zama"




"Wanne tailor kuma? Inji khulsum,




"Wanda yayi mana dinkunan bikinsu Hindu mana"




"Me yayi miki wai?"




"Zuwa yayi har gida wai sona yake da aure dama kuma yadade yana turo min text harda kirana awaya duk ban san shi bane dan banza,yaron da baifi su el'mustapha ba"




Khulsum najin haka me zatayi idan ba dariyaba nan tashiga kyakyatawa ita kuma bilkisu na masifa daga karshe dai kashe wayarta tayi sai lokacin taga ashe tun tuni tanada ajiyayyen sako da yashigo, cikin hanzari ta budeshi dan tana zaton ko hamood ne amma abin takaici fahad ne,




_Gimbiya kiyi hakuri na bata miki rai wanda bana farin ciki da hakan, kiyi min afuwa kuma ki gafarce ni akan abinda nayi, ni nayi zaton aure ana ginashi ne bisa yarda da amana da kuma gaskiya da kaunar juna baya ga wannan basai an hada da wani abu can waishi fin shekaru ba, ki taimaka min kiyi nazari da tunani akan maganata sannan ki sanyata a mizani na adalci kafin ki yanke hukunci, nabarki lafiya...._




Tsaki tayi ahankali marar sauti itafa yaron nan yafara takura mata kuma gaskiya, bata yi yunkurin tura masa reply ba ta shareshi taci gaba da hadiyar bacin ranta.




 ***


Dama fahad yasan za ayi haka yasan sai bilkisu ta raina girmansa gashi kuwa hakance tafaru amma hakan ko kadan bai karyar masa da gwiwa ba, yajima zaune a inda tatafi tabarshi yana faman zaman jiran gawon shanu daga karshe yatashi yatafi batare da yasha koda ruwan da Rabi ta ajiye masa ba. Bai sanar da kowa abinda yafaru ba domin hatta salim bai fadawa ba ubangijinsa kadai ya fadawa wanda yake da tabbacin yafishi sanin komai kuma shine zaiyi masa magani sai da yakoma gida sannan yatura mata da text daga nan yaci gaba da harkarsa shima ya shareta duk da yana son yaji daga gareta ga yar naci husna da ta sakoshi agaba kwana biyu kullum ashagon take wuni wai lallai sai ta koyi dinki awurinsa, ko ya shareta bata zuciya bare tatafi haka yake hakura suke hira.






 Yau Satinta uku da komawa aiki bayan hutunta da ta cinye wanda ta dauka bayan tadawo daga aiki da yamma ammah ke yimata maganar data dan razana ta wai iyallo tace tana nan zuwa acikin satin nan gara tazo da kanta ayi maganar mudan da ita agama, kadan ta iya cin abincin da ta zubo dambun zogale da wainar shinkafa, daki ta koma ta zauna, yanzu kam yazama dole ta nemo fahad ko dan su shirya deal inyaso daga baya sai su warware, wayarta ta dauka ta tura masa text,daga nan ta wurgar da wayar saman gado tawuce bathroom.




Yana shago yana hutawa bayan yagama wasu dinkunan biki husna ta kawo masa tuwon semo miyar shuwaka amma dayake ba cin girkinta yakeba ko dandanawa baiyi ba sai su hamza ne keta kwasa yana kwance gefe yana kallonsu, wayar yazaro daga aljihunsa yaduba saboda jin sako yashigo shi duk atunaninsa ma kudinsa aka turo masa na dinkunan da yayi saboda yabawa mutanen account number dinshi amma sai yaga sako daga bilkisu tana cewa,




_Salam, yakake, kazo anjima ina son ganinka._




Murmushi yayi yamike yana tattara komatsansa domin amsa kiran gimbiya.




Saida yakoma gida yayi wanka yashirya tsaf sannan yanufi gidansu bilkisu yau kam daga waje ya tsaya ya kirata, ta kwashe kimanin mintuna goma kafin ta fito ta leko bakin gate din,yana tsaye ya jingina kafarsa da bango yana danna wayarshi,




"Bismilllah..." Tafada atakaice, bin bayanta yayi suka shiga cikin gidan inda ta tanadar musu fararen kujerun roba guda biyu. Zama sukayi ta daga kai ta kalleshi, sanye yake da blue din shadda mai kyau harda hula wacce ta saku da blue din zare amma hakan bai hana sumar kanshi bayyana ba,




Shine yakatse shirun ta hanyar cewa,




"Ina yini hajjaju?"




"Lafiya lau, kasan meyasa na kiraka?




"A'a" yafada yana girgiza kai,




"Kace kana sona zaka aureni ko?"




"Uhmm" yabata amsa,




"To nima zan aureka amma bisa wasu sharruda, kaga nafarko akwai wanda mukayi alkawarin aure dashi wanda mu duka muna son junanmu amma aka samu wata yar tangarda bama jin juna nikuma kakata ta matsawa babana akan lallai sai nayi aure acikin watanni uku kacal idan ba hakaba ta aura min wani cousin dina wanda nikuma bazan iya zaman aure dashiba,that's why nake neman taimakonka..."




"Taimakona kamar yaya?" Ya bukata yana kallonta,




"Yawwa, so nake muyi aure kamar gaske daga baya idan hamood yadawo sai mu rabu naje na auri saurayina wanda nakeso"




Murmushi yayi wanda ya bayyanar da hakoransa,




"To wannan auren namu menene sunanshi?"




"Auren taimako domin taimako na zakiyi mutukar da gasken kana kaunata"




Murmushin yasake yi,




"Gashi nikuma ban shirya aure kwana kusa ba"




"Karka damu zan baka dukkan abubuwan da za ayi amfani dashi, ni dakaina zan hada lefe inbaka akawo da komai da komai"




"Sai kace acikin shirin film ko littafin hausa? Gaskiya bazan iya wannan auren ba, da dai aure zamuyi halattacce kamar na kowa shine sai indage inyi iya bakin kokarina inga nasamo abinda zan aureki cikin watannin da kika fada amma wannan auren gaskiya ba daniba..."




Daga haka yamike yana kallon agogo,




"Ni zan wuce, nabarki lafiya"




Ya fita daga gate din gidan bata iya cemasa komai ba saboda tsananin mamaki ashe haka yake da baki da iya zance bata saniba? Ganin zaman babu amfanin da zai tsinana mata yasata tashi tashiga cikin gida, wurin ammah tawuce ta zauna anan ammah ke tambayarta waye yazo nan ta sanar da ita sabon saurayi tayi kuma dagaske yake yashirya aure, fatan alkhairi ammah tayi domin ita zabin bilkisu shine nata.




 Koda ta shiga daki kasa zaune tayi ta kasa tsaye bata son damarta tawuce, ya kamata tayi amfani da wannan yaron wurin cikawa hamood burinsa,




Wayarta tajawo ta shiga kiransa, tana daf da tsinkewa yadaga,




"Hello, sorry hajjaju wanka na shigane"




"Babu komai dama na kiraka ne infada maka na amince ayi yadda kakeso din, ya kakeso ayi?"




Wata sanyayyar ajiyar zuciya ya ajiye sannan yayi magana cikin taushin murya,




"So nake muyi aure irin wanda kowa yake, sannan bana bukatar ko sisinki kibarni inyi komai kamar yadda kowanne ango keyi..."




"Na amince..." Tabashi amsa,




"Yawwa ko kefa to shikenan insha Allah babu matsala zan fara shiri daga yau dinnan, Allah yawuce mana gaba"




"Amin"




Daga haka sukayi sallama, kowannensu zama yayi yana tunanin abinda zai tunkara, ita dai bilkisu dawowar hamood take hararowa bayan tayi wannan auren na wucin gadi yayinda shikuma fahad anasa bangaren yanda zaije ya tunkari su Ayiyah da maganar aure yake tunani.....








*_Ummi Shatu_*    


© _*HASKE WRITERS ASSO.*_



*KAMAR DA WASA...!*  



   _*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*




   *11*



   *Littafin kamar da wasa na kudine dan Allah idan har kinada bukata to kibiya kudi kisiya sai ki karanta.*



       ***Da tunanin ta yadda zai jewa su ayiyah da maganar aurenshi yashirya, bakin jeans yasaka da jar t shirt mai dogon hannu kamar koda yaushe saida yasha turarenshi wadanda suka zauna ajikin kayanshi sannan yafito daga dakinnsu yana taje sumar kanshi da karamin cumb wanda keys dinshi ke makale jiki. Tsayawa cak yayi yana tunanin ina yadace yanufa ahalin yanzu,


Waje yayi domin baida bukatar shiga cikin gidan yanzu, zama yayi kan dakali yana cigaba da taje gashinsa daga karshe yasaka cumb din cikin aljihu yazaro wayarsa ya leka instagram daga nan yashiga facebook, sakon husna yagani hakan yasashi jan dan karamin tsaki,


"Wannan yarinyar ko mayya sai haka..."


Chaten yaci gaba dayi har magrib yana zaune awannan wurin yana ganin masu wucewa daga can cikin gida yashiga yayi alwala yafito yawuce masallaci bayan an idar da salla yanufi gidan yaya Asabe babbar yayarsu wadda ke aure acan ladanai, tana tsakar gida itada yaranta guda biyar wasu nayin homework wasu kuma na game a wayarta ita kuma tana marking din test din yara domin malamar makarantace awata private school dake unguwar, ganinsa yasata ajiye abinda takeyi tana yimasa sannu da zuwa yaran kuma nayi masa oyoyo,


Kan babbar tabarmar da suke kai yahau ya zauna yana rikeda humaira wacce itace karama dan ko tafiya bata faraba,


"Autan ayiyah daga ina haka?"


"Anty wallahi yau takanas nazo miki dan wallahi akwai magana"


Dariya tayi takalli  'yarta mai sunan ayiyah yar kimanin shekaru 9 tace,


"Ilham jeki ki kawowa uncle fahad ruwa da lemo mai sanyi kinji sai kizo ki zubo masa abinci idan kin kawo"


Saida taga tashin ilham sannan ta maida hankalinta gareshi,


"Meyake faruwa?"


"Anty aure nasamo amma ban fada agidaba tukunna"


Dariya ita abinma yabata saboda jin abinda yace domin ai fahad yarone, nawama yake da har zaiyi maganar aure yanzu?


"Fahad aure kuma? Wai dagaske kake koda wasa?"


"Dagaske nake Allah"


Kafin takara magana ilham takaraso dauke da aiken da tayi mata nan ta karba ta mika masa gabanshi ta ajiye sannan ta kalleshi,


"Amma fahad aure yanzu anya baka ballowa kanka ruwa ba? Haba fahad inama laifin kakoma karatunka yar degree dinnan da kowa keyi kaima kaje kayi inyaso idan kagama sai kayi maganar Auren amma yanzu dududu nawa kake? Ai ko Abba bana jin zai jajibo aure yanzu bare kai, shiyasa tun jimawa nake cemaka kakoma karatu amma kaki...."


Murmushi yayi bayan ya kwankwadi lemon dake hannunshi,


"Anty inada burin komawa karatu amma gaskiya ba yanzuba..."


"Sai yaushe? Saika Tarawa kanka nauyi yayi maka yawa? Ai tun yanzu yadace kakoma da baka da nauyin kowa amma haka kawai kaki karatu?"


"Anty asabe nidai kawai kiyi min fatan alkhairi"


"To shikenan Allah ya tabbatar da alkhairi, ga abinci nan kaci"


Yajima agidan dan acanma yayi sallar isha'i sannan yatafi gida, akofar gida yaja burki yanemi wuri ya zauna yakira bilkisu,


Fitowarta kenan daga wanka tadauki wayar tana kokarin zama agefen gadonta,


"Ya akayi?" Shine abinda tace lokacin data daga wayar,


"Babu komai, ina wuni?"


Ajiyar zuciya tasauke aranta tana jin tafiyarsu zatazo daidai dashi domin da alama sai yanda tayi dashi,


"Lafiya lau dama nima ina son kiranka, gobe idan Allah yakaimu inaso kazo domin zaka gaisa da ammah sannan zakazo kagaida Abba ma"


"Babu matsala Allah yakaimu amma da kamar yaushe zanzo?"


"Koda yaushe kazo ma babu matsala koda yamma koda daddare"


"Tom zanzo da daddaren dan gaskiya kunyar zuwa da yamma nake"


Murmushi tayi amma bata bari yajiba tace,


"Shikenan Allah yakaimu"


"Amin kiyi bacci cikin aminci da farin ciki,saida safe"


"Allah yakaimu"


Daga haka takashe wayar ta ajiye gefe, koda tagama shirin bacci sai kuma tunani ya addabi ruhinta wato kamar da wasa karamar magana na shirin tabbata dakyar tasamu ta fidda tunanin aranta tayi bacci. Shima fahad da tunanin abin ya kwana aransa shi yanzu babban abinda ke fadar masa da gaba tayadda iyayenshi zasu amince yayi auren nan alhalin ga Abba nan agabanshi wanda shi yadade ma da budurwar amma har yau ba afara maganar aureba. Washe gari bilkisu bataje aikiba domin bata da aiki,tana dakin ammah tana gyarawa bayan tagama wanke toilet taji sallamar maama atsakar gida,


"Yar halak" tafada azuciyarta, babu jimawa sai gasu sun shigo itada huda wadda ke gudu dan tazo wurin bilkisu,


"Sannu Adda, kawo intayaki"


Sakar mata mooper din tayi ta dauki hudah dake rungume da ita,


"Ina kwana Adda labour?"


"Lafiya lau Maman hudah, wallahi yanzu nake tunaninki nake cewa to ko inje gidanki tunda ba fita aiki zanyi ba?"


"Wallahi nima daku na tashi shiyasa muna tashi nacewa abban hudah tare zamu fito idan zaije office yasauke mu"


"Ai kuwa kin kyauta, nasan daga nan har dare kuna nan kamar yadda aka saba"


Dariya maama tayi tace,


"Abinda kema kin sani adda labour"


Kinkimar hudah bilkisu tayi suka koma falo wurin ammah nan maama tafito ta samesu.


 Da daddare misalin karfe 8 fahad yayi mata waya cewar yakaraso dama lokacin tana daki tanata faman caba ado kamar gaske, maama dai na kwance tana lallaba hudah tana kallonta, mayafi tadauka tafita tana zuba kamshi dama tun yamma ta fadawa ammah fahad zaizo gaishesu,


Kamar koda yaushe yana tsaye hannunsa daya cikin aljihu yana sanye da farar shadda sabuwa fil tasha bakin aiki wannan dalilinne yasashi sanya bakar hula da bakin takalmi,


"Yaron akwai daukar wanka babu laifi matsalarshi daya yayi yaro dayawa" tafada cikin zuciyarta,


"Barka da fitowa, ina yini?"


Yace da ita yana kallonta,


"Lafiya lau, muje ko?"


Jerawa sukayi zuwa cikin gidan, wurin ammah suka fara zuwa tana zaune afalo lullube cikin mayafi, akunyace yacire sau cikin kafarsa yashiga falon daga shi sai bakar safa akafar tashi, zama yayi kanshi akasa yana gaidata, itama ammahn kanta akasa ta amsa bata ko daga kaiba bare ta kalleshi, hakan da sukai sai yabawa maama da bilkisu dariya nan kowa yayi tasa aboye, duk jinsa yayi yatakura shiyasa ko ruwa yakasa sha daga karshe yamike yafita bayan ya ajiyewa ammah kudi, bin bayansa bilkisu tayi domin takaishi wurin Abba.


Afalon Abba sukaja birki ya kalleta fuskarsa cikeda annuri,


"Ban daiyi rashin kunya ba ai ko?"


"Da kayi me?"


"Dana zo mana"


"Uhmm zancen kakeso"


Murmushi yayi baice komaiba har Abba yashigo daga can wata kofa wadda da alama itace hanyar bedroom dinshi,mikewa tsaye fahad yayi Abba na zuwa ya durkusa kasa da niyyar gaisheshi amma sai Abban ya ruko kafadarshi yana bubbuga bayanshi ahaka suka gaisa, sannan Abba yajashi kan kujera mai zaman mutum uku, abin gwanin burgewa Abba sai janshi yakeyi da hira yana yimasa tambayoyi dangane da tushensu cikin barkwanci da dabara irinta manya daga karshe Abba yace yana son ganin mahaifinsa, duk da yaji dadin ganin Abba da hirar da sukeyi amma yakasa sakin jiki duk atakure yake jinsa dan haka cikeda girmamawa da alkunya yayiwa Abba sallama yafito dama bilkisu tuni ta dade da zamewa tafice, koda yafito tsaye ya sameta tana yin waya da kanwarta mina ganinsa yasata yiwa Mina sallama ta juyo tana kallonsa,


"Ya kukayi?"


"Cewa yayi inturo mahaifina zai gana dashi"


Ajiyar zuciya ta sauke batace komai ba tayi masa alama da hannu suje ta rakashi, shi dinma baice komai ba yawuce tana biye dashi a second gate sukayi kicibus dasu Hindu itada mai gidanta wanda yazo daukarta ganin su bilkisu sun fito yasata komawa domin yiwa Abba sallama dama su take jira sufito. Gaisawa sukayi da mijinta da fahad daga nan suka wuce waje,


"Yanzu menene next abu da kake ganin zamuyi?"


"Bari dai infara yiwa babanmu maganar tukunna inyaso sai sauran su biyo baya..."


Sallama yayi mata yahau roba roba din da yazo dashi na salim yatafi, ciki takoma ta iske Hindu na jiranta nan tafara yimata santin haduwar da fahad yayi tana cewa,


"Su iyallo masu fatan tsiya to zasuga mijinki yawuce tunaninsu"


Ita dai bilkisu dariya tayi daga nan sukayi sallama tashige gida sukuma suka tafi.


 Adaren ranar bayan fahad yakoma gida yasamu baba da maganar a turakarshi, dafarko shi kansa kunya abin yabashi shiyasa yarasa ta inda zai fara sanar da baba, kawai sai yaji kunyar yacewa baba aure yakeso yaje ya nema masa dakyar dai yadaure yace,


"Baba dama.....dama akwai wata..... da nake zuwa wurinta..... to yau naje ingaida mahaifinta...... shine.....shine.... yace wai yana son ganinka...."


Shiru baba yayi ya zuba masa ido hakan yasashi kara yin kasa da kansa, mamuh kuwa dake tsaye bakin kofa wacce shigowarta kenan kuma da alama taji komai tafa hannu tafara yi tana rafka salati.....





*_Ummi Shatu_*    



© *HASKE WRITERS ASSO*

_(Home of expert & perfect writers)_



*KAMAR DA WASA....!*  




    *_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*




        *12*



 *Kamar da wasa na siyarwa ne yar uwa idan kinada bukata kisiya saiki karanta.*



     ***Ji yayi jikinsa yayi mutukar sanyi hakan yasashi yarda aransa cewar iyayen nashi ba lallai su amince da batun nasaba,


"Yanzu kai fahad har kafara maganar aure? Ahh lallai zamani yazo...." Inji mamuh, kasa yasake yi da kansa, dariyar baba yajiyo daga bisani yaji yana fadin,


"Ai ba auren akace za adaura ba kawai dai mahaifin yarinyar ne ke son ganawa dani, menene na saurin karaya kodai baki shirya aurar da d'an nakiba?"


Dariya itama tayi takarasa shigowa cikin dakin ta nemi wuri ta zauna,


"Bahaka bane baban asabe ko gobe akace mu fito muna iya fitowa tunda yarona ba zaman banza yakeba yana da sana'arsa"


"Gashi babarsa tana adashi..." Baba yafada cikin raha,


"Ni yaushe rabona da adashi baban fahad?"


Jin su baba sun mayar da abun raha yasashi zare jikinsa zai fice har yakai bakin kofa yaji baba yace masa,


"Gobe idan Allah yakaimu zanje sai ka sanar musu"


Daga kai kawai yayi yana shafa sumar kanshi batare da yace komai ba, ganin sun cigaba da maganar su yasashi karasa ficewa dasauri.


Bayan fitarshi baba yadubi mamuh cikin nutsuwa,


"Abinda nakeso daku idan har dagaske auren aka bashi to mu mara masa baya yayi tunda har yafurta, yin hakan yafi fiyeda mu bada gudun mawa wurin lalata tarbiyarsa da ruguza rayuwarsa, saboda yaran zamanin nan da kike ganinsu sai dai abarsu kawai shiyasa komai kankantar yaro ko yarinya idan suka nuna aure sukeso kawai yimusu ka huta domin idanfa baka yimusu ba to watan hanyar zasu bi ta daban,... Ai mu da muke fita waje mune muke kallon abubuwan dake faruwa Rahmatu"


Gyada kai mamuh tayi cikeda gamsuwa tace,


"Hakane Baban asabe ubangiji Allah ya shirya mana zuri'a da sauran al'ummar musulmi"


Daga nan sun jima suna tattauna maganar atsakaninsu.


Abangaren fahad kuwa ko zama baiyi adakin ayiyah ba yadauki abincin shi dake rufe yafice, dakinsu yabude yashiga sai lokacin yaji nutsuwa tazo masa domin da alama su baba bazasu hanashi wannan auren ba zama yayi bayan yarage kayan jikinsa ya zamana daga shi sai vest da gajeren wando, abincin yabude yafara ci nan kuma hankalinsa yakoma kan lissafin abubuwan da zaiyi tofa account dinshi yaduba yaga nawa yake dashi daga nan lissafe lissafe yatashi wanda ya daukeshi tsawon lokaci daga karshe abincin ma barinshi yayi. Sai da yasamu nutsuwa bayan yayi wanka sannan yakira bilkisu wacce tuni harta kwanta amma ba bacci takeyi ba,


"Kaje gida lafiya?"


Shagwabe fuska yayi kamar tana kallonshi,


"Ni wallahi bazan amsa ba tunda ai baki kirani kin tambayeni ba...."


"To ai sai kayi min uzuri dai ko"


"Nayi miki ranki yadade, dama mai gidane yace zaizo gidanku gobe wurin Abba"


"To Allah yakaimu, amma da yaushe zaizo?"


"Da safe naji yace,sai ki sanar dasu"


"Babu matsala Allah yakaimu"


"To saida safe? Ko zamuyi hira?" Yafada dan jan magana,


"A'a saida safen dai" tabashi amsa tana yatsina fuska,


"To kihuta lafiya baby...."


"Thanks" tafada cikeda bacin ran kiranta da baby da yayi,


Daga haka takatse wayar juyi tayi ta gyara kwanciyarta aranta tana cewa,


"Wannan shine Abu kamar da wasa yana shirin zama babba,hamood meyasa kayi min haka? Amma babu komai tunda ban san abinda ke faruwa ba sai dai nayiwa kaina alkawarin zama injiraka har lokacin da Allah zai sake hadani dakai..."


Sake muskutawa tayi cikeda damuwa,


"Lallai yaron nan ni yake kira da baby? Tab ai kuwa dolene ma na yanka masa serious warning wallahi...."


Da bacin rai tayi bacci wanda bata san ko na menene ba amma tafi alakantashi da rashin sanin takamaimai halin da hamood ke ciki da kuma kiranta da baby da fahad yayi.


 Koda gari yawaye bayan tafito suna karyawa da ammah take sanar da ita batun zuwan babansu fahad wurin Abba, ai ammah farin cikine ya mamayeta harta kasa boyeshi saida ya fito fili bilkisu tagani,


Shiru tayi aranta tana jin tausayin ammah domin azahirin gaskiya bata jin zata iya zaman aure da wannan karamin yaron kawai dai aure ne na wucin gadi za ayishi da zarar abin sonta yadawo zata koma gareshi domin shine yadace da ita ba fahad ba.


 A bangaren fahad kuwa tunda ya kwanta bayan yayi sallar asubah bai tashiba har 9 saida ayiyah tazo ta buga masa kofa tace baba na kiranshi sannan yataso da hanzarinsa yana kokarin zura doguwar rigar jallabiyarsa wadda yacire bayan ya idar da salla. Lokacin da yashiga dakin baba yasameshi yana karin kumallo da kakkauran koko da kosai nan ya durkusa yagaidashi baba ya amsa cikin fara'a kana yace,


"Nayiwa babanka Alhaji Nuhu magana mahaifin salim yanzu haka yashirya ni yake jira zamuje gidansu yarinyar, a ina gidan yake?"


Sunkuyar dakai fahad yayi sannan yasanar dashi, dayake sanannen mutum ne mahaifinsu bilkisun shiyasa baba bai wani wahala wurin gano inda gidan yakeba daga karshe yace fahad din yatashi yatafi. Yana kwance adaki yajiyo fitar baba hakan yasashi jin faduwar gaba babu kakkautawa dakyar yasamu yaji yakoma daidai amma baccin da bai komaba kenan hakane ma yasashi fadawa toilet yayi wanka yafito yashirya sannan yasaka kananan kaya yanufi cikin gida, yana shiga su mamuh na waje suna gyaran waken suya wanda zasuyi awara dashi da rana, ji yayi kamar yakoma dan kunya gashi yau sai yaji duk ya tsargu dasu saboda yanda daga ayiyah har mamuhn suka zubo masa ido gefe daya ga mariya tsugunne arakabe,


"Yaya fahad tattabarunka sunyi sabuwar kinkisa Allah leka kagani"


Dama mafaka yake nema dan haka yanufi dakin barun batare da yakarasa wurinsu ba yana cewa Mariya,


"Haba? Ashe zan baki biyu tunda kece kika fara yimin albishir" 


Zuwa yayi ya lelleka nan yahangosu sun doshi goma koma fiye da haka, ma'ajiyar abincinsu yanufa yaje ya ciko musu kwano da hatsi yazo ya watsa musu sannan yakoma wurinsu ayiyah yana hararar Mariya,


"Ke meyasa bakije makaranta ba? Kema gardamar karatu zakiyi ko?"


Kafin Mariya tayi magana ayiyah ta amsa,


"Ka ganta nan da zazzabi tatashi da asibiti ma zan rakata babanku yace inbari anjima inkaita wurin murja nurse makotanmu ta dubata tunda can asibitinma idan anje layine kuma ba lallaima aga likitan ba watakil nurse din za agani"


"To Allah ya sawwake, ina kwananku?" Yafada bayan ya durkusa,


"Lafiya lau ango" inji mamuh, ai baice komaiba yamike yana murmushi yafada dakin ayiyah domin karyawa yanaji mamuh nacewa ayiyah,


"Sai mufara asusu tunda danmu ya lakato aure" 


Dariya ayiyah tayi sannan tace,


"Atoh bikin auta guda ai dole anuna bajinta"


Agurguje ya karya yafito yabar gidan yanufi shago saboda yanada ragowar dinkunan da bai karasa ba kuma yaga har masu dinkin sun turo masa kudin dazu da asubah. Acike yasamu shagon kowa yafito harda yan karbar dinki da masu zuwa zaman hira shagon, hamza ya iske asaman kekenshi dan haka yanemi wuri yazauna yana jiran yagama yabashi wuri,


"Yau mutuniyarka zuwanta biyu nemanka ta dubaka taga ko ka fito amma shiru"


Duk da Tj bai fadi sunaba amma yasan husna yake nufi,


"Yar naci kenan, ni garama da ka tuna min bari inyanka atamfar can tata kafin inhau keke"


Atamfar yadauka da almakashi da sauran abunda zai bukata yafita domin yankawa.


Kamar yadda baba yafada shida mahaifin salim sukaje gidansu bilkisu a motar yayansu salim din baffa wanda shine yakaisu, lokacin da sukaje bilkisu tafita wurin aiki sun samu kyakkyawar tarba awurin Abba wanda ya karbesu hannu bibbiyu cikeda girmamawa da mutuntawa, kasancewa abune na manya masu ganin mutuncin juna anan aka kulla magana inda Abba yace yabaiwa fahad bilkisu sannan shi baya son wadannan bidi'o'in masu hana aure yayi karko dan haka nanda watanni biyu sai adaura musu aure yafi ayita dogon zancen nan suna sake shakuwa da juna daga karshe kuma ba asan me zai faruba, duk da baba yana ganin kamar hakan bamai yuyuwa bane duba da su ba karfine dasu kamar gidansu bilkisun ba amma haka yakarbi maganar Abba hannu bibbiyu aranshi yana cewa idan da yuyuwar su daga lokacin bikin sa sake dawowa su nemi alfarma, cikeda mutunta juna sukayi masa sallama suka fito inda yayi musu rakiya har gaban motarsu,wannan fa shi ake kira da babu zato babu tsammani daga zuwa tambaya ansaka ranar aure alhalin shi angon bai tanadi komai ba na biki.




*_Ummi Shatu_*    


© *HASKE WRITERS ASSO.*




*KAMAR DA WASA....!*  



   _*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*



  *13*




       ***Daga fahad har bilkisu babu wanda yakeda masaniyar abinda yake faruwa, shi fahad baima koma gidaba sai bayan sallar la'asar wannan dinma yunwa ce ta addabeshi shiyasa yana zuwa gidan ta kan abinci ya fara saida yaji ya koshi sannan yawuce dakinsu yayi wanka daga ayiyah har mamuh babu wanda yayi masa maganar kowa acikinsu kama bakinsa yayi yai shiru, bayan yagama shiryawa yafito yana kokarin rufe daki baba yashigo, kayan hannunsa yakarba sannan yashiga cikin gida baba yana biye dashi, bai san wa zai kaiwa kayanba kasancewar bai san wacce keda girki ba domin su al'adar gidan nan baka gane wacece ke girki saboda komai tare sukeyi wannan dalilinne yasashi ajiye kayan a kofar dakin baba yajuya yana kallon maryam da mariya wadanda ke ta faman kallonsa suna yar dariya kasa kasa,


"Ke Mariya kin warke zaki fara munafurci ko? Bari nazo nakama yarinya sai nayi ball da..."


"Ya akayi kuma? Dawa za ayi kwallo?" Baba yafada bayan yashigo,


"Ahh babu komai baba" fahad ya amsa yana shafa kai,


"To zo ina son ganinka..."


Bin bayan Baba yayi cikin turakarsa, sai da yajira Baban yazauna sannan shima yazauna bayan ya dora habarsa kan gwiwarsa,


"Muhammadu tofa karamar magana tazama babba, naje wurin mahaifin yarinyar nan kamar yadda ya bukata kuma mun tattauna dashi, ya yabeka iya yabo haka kuma ya kaunaceka domin duk mutumin da yaso hada zuri'a dakai to mai kaunarka ne, kuma naji dadi domin gidan da kaje gidane na mutunci da karamci saboda bana tunanin duk nahiyar nan bama cikin kano ba babu wanda bai san mahaifin yarinyar nanba..."


Shigowarsu ayiyah da mamuh ne ya katsewa baba maganar da yakeyi sukayi masa sannu da zuwa sannan suka nemi wuri suka zauna suna saurarensa,


"Yanzu dai zancen da nake maka fahad mutumin nan yabaka yarsa yace baya bukatar komai daga gareka domin har yama sanya ranar aurenku watanni uku, duk da nasan kanada sana'ar yi amma sai nake ganin kamar zaka shiga wani hali saboda aure abune mai wahalar gaske musamman ma a wannan lokacin..."


Shiru fahad yayi yana jin abun kamar amafarki wai shine zai auri bilkisu matar da yake mutukar kauna, maganar babace tadawo dashi cikin hayyacinshi,


"Yanzu menene abinyi? Kaga dai nafarko bakada muhalli domin baka gama ginin da kakeyi ba, na biyu rikon gida dole sai anshirya duk da nasan Allah shine da kowa amma mu ta bangarenmu zamu taimaka maka da abinda zamu iya sannan zan tattaro yayunka ma duk in sanar dasu"


"Baba nida tunanin da nayi ko insaida dayan filina dake digar maharba sai inkarasa ginin?"


"A'a kabar filinka bari dai zamuga abinda za ayi, tashi kaje, zamu shawarta da iyayenka"


Tunda yafito sai yarasa me zaiyi yasan dai yau yana cikeda wani farin ciki wanda bai taba jin irinsa ba, tafe yake ahankali domin zuwa yasanarwa da salim saboda magana awaya bazata yuyu ba, idonshi ne yakai kan yaran dake tsugunne gaban wata yarinya wacce ke soya awara agefen titi, wurin yakarasa yazaro dari biyar ya mikawa yarinyar,


"Ki rabawa yaran nan sadakar ta dari biyar..."


Daga haka yawuce yanajin yaran sunata murna da yimasa godiya. A shagonsu salim ya sameshi yana kwance shi kadai bayan wasu mata sun gama siyayya sun tafi. Shiga yayi ya zauna agefenshi yana fadin,


"Washh..."


Kallonsa salim yayi, "yadai abokina?"


"Katashi kaji wani labari, ansa min ranar aure yau?"


Ai kuwa tun kafin yarufe bakinsa salim yatashin yana kallonsa,


"Dawa?"


"Da hajjaju mai gado"


Dariya sunan yabaiwa salim shiyasa saida ya dan dara sannan yace,


"Lallai mutumin nan kadage sai kayiwa Abba overtaking..."


Dariya fahad yayi,


"To ya za ayi lokaci nane kawai yazo"


Dariya salim yayi,


"Allah yasanya albarka tareda alkhairinsa, ya kuma zakayi da maganar husna?"


Canja fuska fahad yayi,


"Ya kuwa zanyi, ko na taba cemaka ina sonta ne?"


Jijjiga kai salim yayi,


"Tab akwai rikici, Allah dai ya kiyaye"


"Babu wani rikici malam"


Har dare suna tare da salim, saida salim yarufe shago sannan suka tafi gida gaba daya.


Tunda bilkisu tabar gida bata dawoba sai yamma tana dakinta bayan tafito daga wanka taji wayarta na kara, su elmustapha ne dan haka ta daga tana tsaki tasan maganar dai bata wuce ta kudi,


"Elmustapha ya akai?"


Daga can tajiyo muryar el'ameen yana cewa,


"Adda labour amarya, nine shi yashiga school"


"Amarya kuma?"


Dariya taji yayi mata sannan yace,


"To Allah yasanya alkhairi mudai aturo mana picx din babban yaya"


Daga haka yakatse wayar, ita dai kanta daurewa yayi jin abinda el'ameen yace, to meyake nufi, da haka ta kammala shiryawa ta sanya yar doguwar riga marar nauyi mai hannun shimi kalar ruwan hoda sannan tasa hijab tafita, farar shinkafa da miya tasa Rabi ta zuba mata tashiga dakin ammah wacce ke kwance tana kallon shirin dadin kowa,


"Ke, yaushe kika shigo kuwa"


Zama tayi saman rug dake gaban gadon ammah tana kallon tv din itama,


"Ammah na dan jimafa ai na leko kina bayi"


"Ehh ruwa na dan watsa saboda naji garin adaure yake"


"Gaskiya ana sheka zafi"


Har suka gama hirarsu tatashi tafita ammah bata yimata maganar ansaka ranar bikinta ba har saida Abba yadawo da daddare sannan yakirata yake fada mata, rasa wanne yanayi ta tsinci kanta tayi farin ciki ko bakin ciki? Share fahad din tayi bata nemeshi ba haka shima bai kirata ba. Har akayi kwana biyu basu magantu ba ita gaba daya haushinsa takeji kamar ba itace ta kawoshi ba shikuma barinta yayi ta sarara gashi hidindimu sun fara yimasa yawa saboda tun washe garin ranar da aka sanya ranar auren nan baba yakira yayun fahad din kamar yadda yafada suka tattauna dangane da yadda za ayi akan maganar bikin fahad, shi dai baba yace zai karasa gina masa gidanshi wanda yafara hakama yayunshi maza guda biyu wadanda ke zaune a gombe da zamfara sunce zasu bada kyakkyawar gudun mawa lokacin da baba ke sanar dasu awaya sauran yan uwansa mata kuma sukace zasu taimaka masa wurin yin lefe. Yanzu kam fahad ansamu nayi domin can wurin aikin yake wuni duk da dama ginin yadan deboshi da fadi shiyasa dole sai baba yasaka masa hannu. Kasancewar yau ba ayi aikinba yasashi zama agida domin hutawa, yana kwance adakinshi duk jikinsa ciwo yake kamar shine yake aikin ginin, alamun shigowar text yagani duk tunaninshi husna ce amma da yabude sai yaga sabanin haka domin bilkisu ce taturo masa da,


_Salam idan kasamu time kazo zaku gaisa da kakarmu._


"Tofa.. Wata sabuwa nifa kunyar gaishe gaishen nan nakeji amma ya na iya? Ai idan naki zuwama sai na fuskanci hukunci"


Shi kadai yaketa maganganunshi daga karshe ya yanke shawarar kiran salim domin yarakashi da daddare. A lifan din salim suka tafi bayan sallar isha, kayan marmari suka tsaya suka fara siya mata sannan suka karasa gidan, awaje suka jira har bilkisu ta fito fuskarta dai babu yabo babu fallasa, kasancewar yasan hali shine yafara gaisheta ta amsa sannan suka gaisa da salim wanda take kallonshi ta gefen ido aranta tana jin damuwar wai wadannan zata nuna ranar bikinta amatsayin abokan ango,


"Muje ko" daga haka tawuce gaba suna binta abaya har ciki, iyallo jaraba ana zaune dakin baki ana sharbar tuwon shinkafa miyar taushe wanda tasa aka yimata ga tv ana kallo jin baki zasu shigo yasata yin lullubi ta rufe tuwon,


Cikin barkwanci da tsokana irinta kakanni ta taresu,


"Barka da zuwa angona, ina fata dai nima ka tanadi nawa dakin dan kafarka kafata"


Murmushi fahad yayi yayi shiru bai amsa ba sai salim ne yace,


"Dama ai dakunan mata biyu yayi harda naki wanda yamafi nata kyau"


Ai kuwa nan ta cafke tana cewa bata yarda ba shikuma salim yabiyeta sunata yi, daga fahad har bilkisu basa cewa komai shiru kawai sukayi sai dai murmushi sunfi minti talatin wurin iyallo daga karshe suka ajiye mata tsarabar da suka kawo mata harda na cin goro fahad ya ajiye suka fita, godiya da albarka sun shata wurin iyallo daga nan suka gaida ammah suka fita domin shi Abba yau baya nan, a compound din gidan suka tsaya yayinda salim yafita yabasu wuri, kallonshi tayi yasha coffee din yadin kufta da hula da takalmi sau ciki sannan ta dauke kai, ita kam hijabi ne ajikinta har kasa, shiru sukayi dukkaninsu na dan wani lokaci. 


"Mai gadon zinare ya ake ciki? Kinji dai yanda su Abba suka yimana wai aure nanda 2 months nikuma gani mai karamin karfe"


"To ai basai ka takura kanka ba kawai kayi abinda ya sawwaka.... Tunda aurene na wucin gadi" takarasa maganar acikin zuciyarta,


"To Allah yasa  bazaki rainaba"


"Babu matsala kayi dai dai karfinka"


"To shikenan, sai gani nagaba,nabarki lafiya, I luv u!!"


Bata amsa masaba yajuya yatafi yana daga mata hannu.



*_Ummi Shatu_*    

© *HASKE WRITERS ASSO.*




*KAMAR DA WASA....!*  



  *_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*




  *14*




*Littafin kamar Dawasa na siyarwa ne,yar uwa idan kinada bukata ki siya saiki karanta, ku kuma masu fitar min da book dan Allah ku hakura haka tunda ai kunyi na zumunci.*



      ***Wasa wasa lamari sai kara girmama yake domin biki yanata matsowa, a bangaren fahad komai yana tafiya daidai domin hatta lefenshi yakusa kammala danma yana baiwa su yaya asabe matsala saboda komai idan suka siyo suka saka idan baiyi masaba sai ya canja idan anyi magana yace shi matarshi babbar yarinya ce yar gayu ba karamar yarinya bace, tun abin yana yimusu ciwo musamman Anty Fauzy mai zuciyar tsiya amma da ta fahimci inda ya dosa saita daina damuwa daga karshe ma duk abinda zasu siya sai sunyi snapping dinshi sun tura masa ta whatsapp yagani, baba kuwa duk atamfofin da aka zuba cikin lefen shine yabada domin cewa fahad yayi yaje shagonsa yadubo duk atamfofin da suka yimasa dama sana'ar baba kenan shago gareshi a kwari na atamfofi zalla kala kala, duk da kayan sauran kadan su gama haduwa har yau bai siyo akwatuna ba saboda yace da kanshi zai siyo kuma da kudinsa, kowa agidan lamarin auren nan na fahad dariya yake bashi har baba ganin abin suke yi tamkar wasa wai fahad ne zaiyi aure, shi dai yanzu ta ginin gidanshi yake domin burinshi kawai yanzu yaga gidan ya kammala.


Bilkisu kam ta cika famm haka kawai lamarin auren nan ke bata haushi gashi kullum saita gwada number hamood amma shiru kamar koda yaushe bata shiga, yau kam amare duk sunzo gida harda maama dama hudah na gidan wurin bilkisu tun ranar da ta raka iyallo gidajensu hudah ta dankafe mata dole sai tare suka taho,


"Adda muma fa mun kwadaitu da son muga big Broz domin anty maama tace yahadu karshe ga class..." Inji meenah,


"Ehh wlhi meenah anty maama cemin tayi wai duk yafi mazajenmu kyau.... Gaskiya Adda labour kina bada kala..." Hindu tafada tana dariya,


"Yara kudai kubari zaku ganshi, wallahi big guy ne har wani suna fa ake fada masa amma ba zakuji abakina ba...."


Ai maama tana rufe baki bilkisu tatashi tabar musu wurin ta shige kitchen domin idan tazauna suka cigaba da haka tana iya make wata aciki.


Yammacin yau yammacine da jama'ar cikin garin kano da kewaye ke mararinsa domin yazo da sauyin weather, sabanin zafi da ake fama dashi kwana biyu yau garin a lullube yake da ni'imar ubangiji sansayyar iska ce ke kadawa ko ina ga sararin samaniya yayi luf luf gwanin sha'awa tamkar hadari domin da alamarsa kadan kadan, kowanne mahaluki yau yanayin yayi masa dadi ciki kuwa hadda fahad wanda fitowarsa kenan zuwa shagonsu bayan yataso daga wurin aikin gina gidansa da akeyi sai yanzu yasan lallai magidanta na kokari domin shi duk da ana taimaka masa agida amma yanzu haka account dinshi duk ya kusan yasheshi sai dan abinda ba arasa ba, yana tsaye yana yanka kayan wasu dalibai wadanda zasuyi bikin gamawa wato anko, yana yi yana cewa aransa,


"Danma dai Allah baya hana bawansa hanyar samu amma da ba haka ba sunana sorry..."


Maganar su hamza da yajiyo daga cikin shago itace ta dakatar dashi daga zancen zucin da yakeyi,


"Kayan Prince.... Kayan prince"


Ko bai waiwaya ba yasan husnah suke nufin ta taho, shi sunan nan takaici yake bashi wallahi yarasa yanda zaiyi da husnah, kamar yanda ya tsammata abayanshi ta tsaya tana murmushi murmushi dariya dariya,


"My prince... Sannu da aiki"


Aciki ciki ya amsa kamar koda yaushe,


"Yauwa"


Kallonshi tayi daga sama har kasa,p cap ce akanshi dark blue agaban p cap din anrubuta harrafin p da bakin rubutu,sai bakar t shirt mai dogon hannu wadda aka rubuta prince agaban rigar  sannan ga bakin trouser yasaka da bakin takalmi na kamfanin Nike,


"Yau kayi kyau my Prince.."


"Nagode"


"Gobe me zaka ci in dafo maka?"


"Ai kawai ma kibarshi saboda ba lallai infito shago ba"


"Haba ya fahad... Meyasa?"


"Ina zuwa wani wurine, yanzu ma fita zanyi....ina so inje inga half soul"


Yakarashe maganar acikin ranshi, duk da yace fita zaiyi amma dan naci bata tafiba har saida yagama yanka kayan nan ya kullesu yakai cikin shago yana gaba tana biye dashi har shagon su salim, key din Babur dinshi yakarbo domin dagaske bilkisu yake son gani yanzu da yamnacin nan,


"Inhau muje ka saukeni a school"


Girgiza kai yayi,


"Bana daukar mata a machine sai dai inbaki kudin napep"


Zumbura baki tayi tatafi batare da tace masa komai ba ita ala dole tayi fushi shi kam murmushi yayi yabuga babur din yabashi wuta yaje ya wuceta a kofar plaza. Bilkisu tana zaune hindu tana kitse mata kanta wanda yafi sati uku atsefe mai gadi yashigo kiranta danma kitson manya ne baifi saura biyu agama ba,mamakine ya isheta jin wai ana sallama da ita bata san fahad bane domin lokacin da yazo yanata kiran wayarta amma shiru kasancewar tabar wayar adaki, agaggauce Hindu ta karasa mata ta shiga daki domin dauko mayafi, dukansu mikewa sukayi wai zasuje su gano yayansu, ita dai batace musu komai ba ta kama hannun hudah,


Har tafita bai sakko daga kan Babur dinba yana kai yana duba wayarsa yana dariyar tsokanar da yayanshi Abba keyi masa, ita tafara fitowa fuska ba yabo babu fallasa su meenah na biye da ita,


"Yaya fahad sannu da zuwa"


Sai lokacin yasan fitowarsu Babur din yaja zuwa kusa dasu yana kallon gimbiyar tashi da ta wani dauke kai tana shakar iskar dake kadawa,


"Uhmm son girma kamar gyambo" yafada aranshi afili kuma yace,


"Yau amare ne agidan... Yakuke"


"Lafiya lau ya fahad, ai yanzu amarci sai ku kaida adda labour" inji meenah,


"Wai hakama zakuce?"


"Ehh mana ya fahad gashi kuma wallahi kun dace da juna" inji hindu,


"Shine ai, abin nasu kamar shiri ita baka shi fari...." Meenah tafada tana dariya,


"Gaskiya dai wannan hadin yayi daidai..."  Inji mama,


Tana jin duk uban surutun da suke zubawa amma batace musu uffan ba har sukayi suka gama ita abinda yakara kular da itama yayan da taji suna cemasa, gashi sunzo sun wani saki baki sai zuba suke kamar kanyar da bata da zaki. Sun jima awurinshi sannan suka shiga cikin gida amma banda hudah wacce ke makale da ita, saida yaga shigarsu gida sannan ya daga ido ya kalleta yana mikawa hudah hannu babu musu kuwa ta taho wurinshi ya dauketa yadora gaban Babur dinshi,


"Ina yini adda..."


Duk da bataso yin dariya ba amma saida tayi saboda yanayin yanda yayi maganar,


"Lafiya lau... Ya kake?"


"Alhamdulillah, ya mutanen gida?"


"Kowa lafiya"


Shiru sukayi yakoma yiwa hudah wasa wacce keta danna horn din jikin Babur din nashi, ji yake inama ace yarshi ce shida bilkisu wai... Da Allah ne kadai yasan irin farin cikin da zai tsinci kansa aciki,


"Lafiya kuwa naganka babu ko waya?"


Kallonta yayi sai kuma ya girgiza kansa yana murmushi,


"Mutum bazai zo yaga matarshi ba saida wani abu?"


Duk da maganar ta ratsata amma saita dake ta sake kallonshi aranta tana cewa, "yaron nan naga yana nema ya zake dayawa fa"


"Uhmm? Ni kawai ji nayi ina son inganki saboda nakwana biyu bamuyi tozali da fuskokin juna ba... That's all"


"To nagode, yanzu dai ai gashi kaganni, inada dan uzuri agida wanda nakeyi sai kuma kafito dani"


"Nifa ko baki koreni ba dama tafiya zanyi amma kafin sannan, zan nemi alfarma"


"Allah yasa zan iya"


"Dan Allah pics dinki nakeso ki turo min, sannan ki daure kifara kulani online murinka chat"


"Pics kuma? Me zakayi da pics dina?"


Murmushi yasake yi yasauke hudah kasa sannan yazaro dubu daya ya danka mata a hannunta,


"Nidai kawai ki taimaka kibani babu ruwanki da abunda zanyi dashi... Shikenan nabarki lafiya, kizama cikin aminci da kwanciyar hankali"


Babur dinshi yabuga yayi gaba yayinda ita kuma tabishi da kallo,


"Jishi kamar wani babba sai zaro magana da iya shiryata"


Daukar hudah tayi tashiga cikin gida, kamar yadda ta tsammata su Hindu anbaje anata zuzuta haduwar da fahad yayi da kuma yaba hankalinsa ita dai batace uffan ba tawuce daki ta ajiye mayafinta tasake fitowa tana zama khulsum na shigowa, har lokacin su maama hirar fahad suke,


"A'a kaga amare"


Dariya sukayi gaba dayansu, meenah tace,


"Anty khulsum ai yanzu kune amare gashi nan sai budada kamshi kuke" takare maganar da yiwa khulsum alama da ido,


Saida Ammah tabar wurin bayan sun gaisa sannan ta maida hankalinta Kansu meenah,


"Wai me kukeso kuce minne? Wacece amaryar? Ni ko wa?"


Dariya mama tayi,


"Kar dai kice kema baki saniba?"


"Wai me kuke magana akaine? Menene ban saniba?"


"Maganar auren adda labour mana, anfa samata rana nanda 2 months bikinta ai ni nazaci ma anko kikazo fitarwa" 


Gimtse fuska khulsum tayi ta kalli bilkisu,


"Lallai kawata, abin har yakai haka? Kullum muna tare dake amma shine kika kasa sanar dani maganar bikinki? Nagode"


Daga haka tamike zata tafi, janta daki bilkisu tasoma kokarin yi amma tana turjewa daga karshe dai saida su maama suka saka baki sannan tayarda suka shiga dakin,


"Kawata kiyi hakuri dan wallahi ni auren nan ganinshi nakeyi kamar da wasa..." Nan takwashe komai ta fada mata amma ta boye mata kudurin dake cikin zuciyarta


Dariya khulsum tayi tace,


"Nidama tunda naji yace wai ke zaiyiwa dinki ni bazai yimin ba nasan akwai wata akasa"


Kai mata duka bilkisu tayi tana cewa "bana son sharri malama"


"Allah dagaske guy din yana mutuwar sonki"


Sun dade tareda khulsum suna tsattsara abubuwa da dama domin hatta anko atake anan khulsum ta fitar dashi tace pink din net da blue din head yayinda ita kuma amarya zata saka blue din kaya da pink din head su Hindu murna suka shiga yi suna cewa wallahi yayi sosai ayi hakan ita dai jinsu takeyi bata tankawa domin tunaninta gaba daya yana ga hamood.


Shi dai ango shirinsa yake ba kama hannun yaro domin gidanshi har anyi roofing anyi wearing da komai yanzu fenti da saka kofofi dasu tiles yarage kudine ma ya yanke masa shiyasa aikin yatsaya. Kwana biyu atsakani ya dan kwanta zazzabi saboda baya samun zama yanzu ga dinkuna duk sunyi masa yawa danma yabaiwa hamza wasu yarage masa, har yayi dan zazzabinshi yagama bilkisu bata saniba domin ba waya sukeyi ba shine ma yake kiranta ita kuwa ba kiranshi takeyi ba saida dalili, ranar da yaji dan dama dama bayan sallar magrib yashirya yaje wurinta, yau kam a guest room aka saukeshi ba a compound ba kamar yadda aka saba domin yazo kenan abba kuma yadawo shine yabada umarnin akaishi guest room dinshi, har lokacin kanshi bai gama daina yimasa ciwo ba ga jikinsa babu wani karfi sosai, yana nan zaune Rabi ta kawo masa ruwa da juice da wani dan madaidaicin food flask, bai taba komaiba har gimbiyar tashigo tana sanye da milk colour din doguwar riga da mayafinta wannan fitinannen kamshin nata yana biye da ita, ayanda ya lura tana kaunar dogayen riguna sosai domin tafi sakasu fiyeda riga da skirt ko zani, har ya amsa sallamarta tanemi wuri ta zauna akujerar dake kallon tashi idonshi na kanta,


Yasan muddin idan bashine ya gaisheta ba to sai dai idan bazasu gaisa dinba shiyasa yakatse shirun da gaisheta, ta amsa kuwa fuskarta babu yabo babu fallasa,


Shagwabe murya yayi ya langabar da kai yana kallonta,


"Bawan Allahnnan har yayi zazzabinshi yagama baki saniba bare kiyi masa sannu.... Dama haka akeyi?"


"Ayya to aini ban saniba, baka fada minba"


"To ai baki nemeni ba, har yanzu ban gama warkewa ba, tabani kiji..."


Murmushi tayi ta dauke kai,


"Kai yarone, kuruciya na damunka wallahi akan me zan tabaka?"


Murmushin shima yayi,


"Au hakane yarintar? Shikenan"


"Kasan me? Maganar biki a ina zaka zauna ne?"


"A ina zamu zauna dai, can ne transformer uku sabuwar unguwar nan amma gidan bawani babba bane dai"


"Ba matsala indai dakunan sunkai biyu zuwa uku"


Gyara zamansa yayi yana kallonta,


"Daki dayane kwal..."


"Daki daya fa?"


"Ehh mana"


"Hmm lallai, to kai a ina zaka rinka kwana"


Dariya tambayar tabashi da kunya lokaci guda shiyasa ma baice komai ba, itama share maganar tayi kamar yadda yashare amma aranta cewa take,


"Ai kuwa yaro garama tun wuri kanemi wurin kwana amma banda inda nake"


Ganin lokacin sallar ishah yayi yasashi yi mata sallama domin tafiya, abubuwan da takawo masa baici ba tayi masa packaging dinsu tabishi dasu, bai musaba yakarba yatafi, yana zuwa gida dakinsu kawai yabude yasaka kayan aciki yayi alwala yawuce masallaci, bayan an idar tare da baba suka shigo gidan baba na tambayarshi abubuwan da yanzu ginin nashi ke bukata, kamar koda yaushe nan suka baje atsakar gida suka sha hirarsu har 9 nadare sannan yashiga daki bayan yarufe kofar gida. Wanka yafara yi sannan ya dauki sakon da bilkisu tabiyoshi dashi, farfesun kayan cikine yasha kayan kamshi da lemon kankana mai dankaren sanyi sai ruwa, duk da yasan zaiyi wuya ace itace ta girka amma yana fatan hakan shiyasa ma yazage ya cinye tas, saida ya dan zazzage cikinsa sannan ya kwanta, wayarshi yadauka yakunna recording din da yayi na programs dinta nan muryarta radau ta bayyana, haka yarinka bi daya bayan daya yana saurara.....





*_Ummi Shatu_*    


© *HASKE WRITERS ASSO.*



*KAMAR DA WASA...!*  




   *_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*



        *15*


*Kamar da wasa na siyarwa ne duk mai ra'ayin karantawa ta biya saita karanta, masu fitar min da book kuma kusani Allah yana ji kuma yana gani sannan yana jiran kowa a madakata*



        ****Akwana atashi alamari sai kara matsowa yake bilkisu ji take kamar tayi hauka domin har yau bata samu hamood ba amma tasawa ranta ko ranar dauren aure ne hamood yadawo mata tilas tafasa auren fahad ya aureshi, duk wasu shirye shirye tuni anfara su domin fita kunyar jama'a musamman ma bakin da za agayyata, su Hindu kuwa kusan kullum suna hanyar gidan abin nema yasamu, amaryar dai kawai tana binsu ne amma har cikin zuciyarta bata son wannan auren kawai dan dai ta gujewa jarabar iyallo da auren ya mudan ne.


Ango fahad kam abangarensa komai yana tafiya daidai yanzu hakama adaren jiya salim ya rakashi yaje kasuwa suka siyo akwatunan da za azuba lefen aciki, saida yaduba mai tsada ajin farko wanda baza araina ba sannan yabiya kudin danma yasamu ragi kasancewar shagon baffa ne yayan salim,akwatuna guda biyar yasiyo har dan kit na shida kalarshi pink mai haske sosai sai walwali da kyalli yake, dakin mamuh yakai domin acan ake tara kayan wanda kusan yanzu komai yagama haduwa sai dan abinda ba arasa ba, kowa saida ya yaba da wadannan akwatunan domin sunyi mutukar kyau, shifa yanzu wani girma yake jin yazo masa saboda zaiyi aure. Daren ranar baiyi bacci da wuriba sai wurin 2 nadare, washe gari bai fita shagoba sai yamma dan har saida yayanshi Abba yadawo ya iske shi agida,yana dakin yana baje akatifa amma ba bacci yakeyi ba idonshi biyu,


"Kaga ango... Saura wata nawane?"


"Saura yan satittika fa, saura sati nawa zakace ba wata nawa ba?"


Dariya Abba yayi yanemi wuri ya zauna bayan ya cire rigar jikinshi,


"To Allah yanuna mana ashe abin yazo"


"Yazo gaskiya domin saura kiris"


Dariya Abba yayi saboda shi gaba daya kallon abin yake kamar a mafarki wai fahad ne zaiyi aure. Da yamma yana shago yayiwa bilkisu text ya sanar da ita za akawo lefe nanda kwana biyu domin ayiyah tace yakamata akai kayan haka nan tunda yan uwa da abokan arziki sun gama gani, dawo mishi da reply tayi tace Allah yakaimu, wani text din yasake tura mata wai wanne colour din fenti zai yiwa gidan nanma tadawo da reply tace light purple. Bayan faruwar haka da kwana biyu aka shirya kai lefe tun ana igobe za akawo lefen iyallo aka sauka itada yafendo domin akarbi komai dasu, yan uwan ammah kuwa sai ranar da za akawo lefen sukazo da safe, anyi hidima iya hidima sannan annuna bajinta domin anyiwa baki tanadi na musamman, mamuh da anty Fauziyya da Anty asabe ne suka kawo lefen sai maman su salim da matan yayun su fahad guda biyu juwairiyya da kubra,


Acan gidansu bilkisu kuwa gida cike yake da mata ita kam tana daki ita da khulsum bayan sun dawo daga aiki, su maama kuwa ba zama ana can ana raping din soye soyen da za abaiwa baki tun safe suke aiki itada su Hindu ammah bata saka musu ko hannu ba sai dai tazo taga me ake ta komawarta daki wurin baki. Misalin karfe biyar na yamma baki suka karaso hajiya iyallo da guda da shewa ta taresu nan aka soma shiga da akwatina falon ammah inda yan karbar kayan suke, sosai lamarin ya kayatar domin kowa sun girmama kowa, gwaggo badiya kanwar ammah me bimata itace takawo tukwicin dubu talatin ta basu,basu bar gidanba sai jikin magriba dauke da garar arziki nan kowa ya raja'a wurin kallon kayan banda su meenah dake can dakin bilkisu suna tasu shaftar ita kuma Hindu na kwance tunda suka gama wadannan soye soyen kanta ke juyawa,


"Amarya kodai da bayani ne?" Inji khulsum, dariya maama tayi tace,


"Ai ba ita kadai ba har dayar itama dazu tagama amanta yanzune ta warware..."


Caraf meenah tayi tace,

"Kai Anty mama kiji tsoron Allah.... Maine fa yahau min kai" 


Ita dai bilkisu na zaune tana jinsu tana bin kowa da ido bata uhm bare um um, tasan da ace hamood ne yakawo mata lefe yau ai da farin cikin da zata tsinci kanta aciki Allah kadai yasani amma bata fitar da ran hakanba agaba tunda idan da rai to da rabo.


Sai dare suka samu zarafin kallon kayan bayan mutane sun baje domin hatta yan uwan ammah adaren suka tafi yanzu sai su iyallo, bilkisu na saman kujera sukuma su khulsum suna gaban akwatunan suna kallon kayan daya bayan daya, saida suka gama tsaf sannan ta raka khulsum tatafi da tadawo dakinta tawuce bata koma wurinsu maama ba domin ita kadai tasan abinda take ji.


Ango dai abangarenshi yagama komai duk da har wata yar rama yayi kadan saboda stress danma yanada mataimaka, ko shago yanzu ba sosai yake zuwa ba, shiyasa lokacin da salim yakai musu labarin wai fahad zaiyi aure abin yabasu mamaki duk sai suka fara zargin to ko husnah zai aura amma sai salim yace musu a'a wannan watace daban basu ma santa ba. Saida biki yarage saura sati daya yana shago yana dinka farar shaddar da zai saka ranar daurin aure saiga husna, daga cefane take tabiyo ta shagon dama arana takan zo shagon nan sau biyu ko sau uku,


Su biyune ashagon daga shi sai kanin hamza dake koyon dinki, sauri yake yagama yatafi gida domin ayiyah na nemansa,


Zama husna tayi gefenshi dayake akan benci yake,


"Prince... Yakake"


"Lafiya husna, ya karatu?"


Kayan dayake dinkawa ta kalla sai kuma ta kalli bakar ledar dake gefen keken da tarin invitation card aciki, babu bata lokaci takai hannu ta dauko kafin ya fauce har ta matsa tana karantawa tiryan tiryan, idanuwanta ne suka cika da kwalla ganin sunanshi baro baro ajiki domin harda saka Prince in bracket, ai cefanen da tashigo dashi shagon nan tatafi tabarshi tana kuka fahad yanata kiranta amma taki ta ko waiwayo, duk kuma yau sai yaji tausayinta ya kamashi ganin akanshi take wannan kukan, duk da yana saurin yaje gida amma hakura yayi yakira Salim dan ya rakashi school of nursing wurin husnah, kayanta da tabari yadaukar mata yatafi mata dashi, yakirata yafi sau biyar amma bata dauka ba tana kwance tanata kuka yan dakinsu kawayenta sai rarrashinta sukeyi amma taki yin shiru fiyeda mintuna talatin kenan take kukan nan, ganin taki daga wayarshi sai yatura mata text akan tayi hakuri tazo yana son ganinta, wannan shine karo nafarko da yazo wurinta har cikin makarantarsu amma ita kullum sai taje wurinshi kaf kawayenta babu wanda bai san prince ba yan dakinsu kuwa da sunanshi suke kiranta saboda kowanne bango dake jikin dakin sunanshi ne rubuce da marker, idanuwanta sunyi jajur tafito tazo wurinshi suna tsaye shida salim amma shi yana kan roba roba din Salim da alama shine ya tukosu yakawosu,


Wani sabon hawayene yazubo mata lokacin da sukayi ido hudu dashi,


"Husnah menene abin kukane? Meye zaki tada hankalinki?"


Harara ta watsa masa batare da tayi magana ba, murmushi Salim yayi yasa baki cikin sigar lallashi yace,


"Kiyi hakuri husnah, kedai prince kikeso to ko yayi aure karki duba aurensa kawai kidubi soyayyar da kike yimasa saboda rayuwa tsarice daga ubangiji tayuyu ke ata biyu zakizo, wannan ba matsala bace, ki kwantar da hankalinki dan Allah..."


Kalaman Salim sunyi nasarar dan rage mata radadin da takejin zuciyarta nayi amma har lokacin taki koda kallon fahad, har Salim yagama tsarata tasauko bata kalli fahad ba, da zai bata ledar ta wacce ta baro ashago bata kalleshi ba ta karba, tura babur din yayi yamatsa kusa da ita kamar zai takata ai kuwa babu shiri takai masa duka duk da idan tayi masa irin wannan hade fuska yake yau murmushi yayi yace,


"To ki dan kalleni mana husnah tah..."


Ai kuwa kalmar tayi mata dadi shiyasa babu bata lokaci ta dan warware harda su kyalkyala dariya ganin haka yadauki Salim suka tafi, shidai yasan baya son husnah amma yau yana tausaya mata domin tanuna masa iyakar soyayya tun ranar da tafara zuwa shagonsu taganshi tafara sonshi duk da fada yafi yawa cikin mu'amular tasu saboda ita bata kunyar tabashi agaban kowaye ko yanzu kafin su baro wurinta saida ta dafashi ta hanyar dora hannunta kan nashi,


"Gaskiya akwai matsala fa, dan wallahi yarinyar nan dagaske take sonka"


"To ya zatayi sai dai tayi hakuri tunda nidai aure zanyi"


"Sai ka kara da ita"


Dariya fahad yayi,


"So kake bilkisu ta korene daga gidan kenan"


"Kaida gidanka taya zata koreka"


"Allah saita koreni ai gida yazama nata, ko kuma daga daki kasa akoroni falo"


Dariya sukayi gaba daya, har gida salim yakaishi sannan yatafi shikuma yashiga wurinsu ayiyah domin jin ba'asin kiran da ake yimasa, gyadar yatarar da mamuh na tacewa akwando ta dahu ligif kanfata yayi a cup yawuce falon ayiyah yana ci,


"Ayiyah wannan gyadar badai dadiba ta dahu wallahi"


"To santi kake kenan, yawwa dama maganar sati dayan da amarya zatayi ananne shine nace ai gara kafara tuntubarta tun yanzu dan tasani ko"


Dan jimm yayi, tabbas yasan kam haka al'adarsu ayiyah take yayinsu ma duk da sukayi aure saida matansu sukayi kwanaki bakwai bakwai agidan,


"Idan kuma kana ganin wani za atura babba to sai atura yaje yasanar dasu..."



"A'a ayiyah bari zanje anjima infada mata"


"Yawwa ka kokarta dama shine kiran da nake yimaka"


Saida ya cinye gyadar nan tsaf sannan yatashi yafita, yaci sa'a salim na gida dan haka Babur dinsa yaje yakarba yanufi gidansu bilkisu duk da baida tabbacin ko tana nan, dawowarsu kenan daga kasuwa sun siyo furnitures tana kokarin rage kayan jikinta yakirata yace yana waje, ita wallahi bataso wannan zuwan nashi ba haka dai ta daure ta zura doguwar riga da hijabi tafita....



*_Ummi Shatu_*    


© *HASKE WRITERS ASSO.*



*KAMAR DA WASA...!*  



  _*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*



 

  *16*



*Littafin kamar da wasa na kudi ne yar uwa idan kinada bukata kibiya ki karanta.*



     ***Ba dan tanasoba haka ta fito ta sameshi yana compound din gidan tsaye jikin wata bishiya,


"Baby..."


Batare da ta kalleshi tace,


"Yakake?"


"Lafiya lau ranki yadade, ya mutanen gida?"


Atakaice ta amsa da,


"Lafiya"


"Am dama namanta ne ban fada miki wani abuba shine yanzu nazo sanar dake, mu a family dinmu idan anyi aure sai ankai amarya gidansu ango acan za aware mata daki har sai tayi tsawon kwanki bakwai ko wani abu mai kamada haka..."


"Wannan al'adar wanne garine kenan?" Ta tambaya batare data kalleshi ba,


"Fulanin kura..."


"So yanzu dai kana nufin gidanku za akaini acan zan zauna har na tsawon 1 week?"


"Ba lallai yakai hakaba dama kawai al'adace amma yana yuyuwa ma bazaifi 3 days ba ko 2"


Jijjiga kai tayi ta jingina jikin bishiyar flower tana kallon gefe,


"Babu damuwa..., ya maganar dinkuna ne wai? Naji shiru kuma tun ranar fa nayi maka maganar"


"Bani intafi dasu adaren nan zan yanka, abubuwane suka yimin yawa wallahi baby ko bakiga har nayi baki ba na fada...?"


"Bafa na son sunan nan nafada maka, so kadaina"


Murmushi yayi shi wlhi drama din da zasuyi da bilkisu kawai yake hangowa,


"Am sorry bazan sakeba amma seriously na dan rame fa"


"To ya za ayi ai situation ne"


Daga haka tawuce ciki ta dauko masa kayan da zai dinka mata takoma wurinsa,yana tsaye a inda tabarshi yana yin waya ganin tana jiranshi yakatse wayar yamaida hankalinsa gareta,


"Gashi duk riga da skirt zaka yimin..."


"Banda doguwar riga?"


"To Kaduba dai kagani idan akwai wanda zaiyi kyau da doguwar rigar sai kayi min"


"Shikenan to, kigaida su ammah"


"Zasuji"


Fita yayi yatafi ita kuma takoma ciki wurin khulsum wacce ke jiranta tayi wanka su fita gidan da za ayi mata gyaran jiki saboda yau za afara.


Cikin kwana biyu yagama dinkunan bilkisu kala takwas ne shadda guda biyu leshi guda biyu sai material da atamfa suma duk kala bibbiyu amma abinda yabashi mamaki duk cikin kayan babu na cikin lefenshi wanda yasaka amma bai kawo komai aranshi ba tunda watakila wannan din agidansu aka yimata, bai samu damar Kai mata kayan da kansa ba sai salim ne yakai saboda shi ranar yana can gidanshi ana saka masa tile da sauran abubuwan da ba akarasa ba, washe gari aka karasa komai na gidan akayi fenti gida yafito rangadau dama unguwar shiru take babu gidaje da yawa ma domin sabuwar unguwace bata fara yawaba, agajiye yakoma gida bayan sallar ishah wanka kawai yayi ya kwanta ko abinci bai nema ba babu bata lokaci baccin gajiya yace muje zuwa, koda Abba yashigo yaganshi baje yana bacci dariya yayi yace,


"Dole kayi bacci ango, irin wannan commitment Haka?"


Dasafe garau yatashi sakamakon baccin da yasha sosai adaren jiya, miss called din bilkisu yagani har guda uku hakan yabashi tabbacin akwai dalili shiyasa yayi gaggawar calling dinta back,


"Fahad dakuna nawane agidan, kofofi nawane sannan windows nawane? Muna wurin masu dinka cuttens ne"


"To hajjaju bari naturo miki gaba daya pics din gidan ki ganshi"


"Yawwa dan Allah hanzarta"


Katse wayar tayi nan yashiga whatsapp yatura mata aranshi yana cewa,


"Akwai rikici nasani"


Bai kara jin duriyarta ba sai text tamishi akan yabasu keys din gidan saboda masu zuwa jeren kaya gobe nanma aiken yayi mata aka kai musu, sai ana igobe kamu ta kirashi tana yimishi maganar itafa baza suje wata dinner ba walima kadai zatayi da friends dinta dan haka shima ya hada reception da friends dinshi kawai ya isa, tayi hakane saboda kunyar yaje dinner mutane su ganshi take,bai musa ba yace to.


Tana zaune tayi uban tagumi bayan mai kunshi tagama yarfa mata jan lalle da baki, khulsum tashigo agajiye itama daga kunshin take, zama tayi kusa da bilkisu wacce ke kallon masu shigowa da masu fita tayi tagumi,


"Wallahi fahad dinnan yayi yaro da yawa, Allah mai yadda yaso..."


Dariya khulsum tayi,


"Baiwar Allah ki rungumi kaddara kiyi hakuri, haka Allah yashirya ko jinjirine dai shine mijinki uban yayanki..."


"Tab.... Allah ya kiyaye, nifa wallahi baki ma san wani abuba, kunyar nunashi nake a matsayin mijina"


"Sai kiyi kuma malama, wai inasu maama?"


"Suna can gidanshi karasa jere"


"Gidanki dai, kyace wani gidanshi"


"Kinga malama ni idan kina tashi kitashi mutafi kitson nan idan kuma baki zuwa ki sanar dani"


"Ahh kinga karki fada min bak'a, shirya muje amma wallahi da retouching kikayi zaifi kitson nan, kinga kanki yanzu fa kullum sai yaji ruwa"


"Kanki akeji, ni tashi mutafi dan bamuda lokaci"


Hijabinta tasaka har kasa suka tafi bayan tayiwa ammah sallama iyallo sai jaraba take wai yakamata ta daina fita hakanan amma tunda tazo gidannan bataga ta yini agida batare da ta fita ba, batace komai ba tabi khulsum suka tafi,


"Shagon ma da babu wani nisa nan bayane fa amma shine iyallo sai tayiwa mutane ihu aka, kai Allah yakyauta"


"Ai keda iyallon nan taku kuna sani nishadi wallahi, gaskiya i have been missing my grandma"


Dariya bilkisu tayi,


"Uhm ai iyallo bata haduba sam wallahi, hajjaye kakarmu ta wurin uwa tafi kirki"


"Kya hadu da Abba wallahi"


"Bawani nahadu da abba ai gaskiyace"


Har sukaje shagon hirar iyallo suke yi. Kitso hadadde aka yarfawa bilkisu dan har la'asar lis suna shagon ita kuma khulsum akayi mata retouching, tun suna hanya taga su meenah nata kiranta, koda tashigo gida suma suna gidan ana yimusu kunshi har angama musu yanzu hindu ake yiwa itama ankusa gamawa,


"Wai wai wai... Gaskiya yakamata yaya fahad yaga wannan kitson da lallen" inji Hindu bayan bilkisu tacire hijab din kanta,


"To ke gaggawar me kike ko kin mantane nanda jibi suna jone ana..." Maama tafada cikin shakiyanci, tun kafin tarufe bakinta bilkisu takai mata duka ta gudu,


"Allah adda labour idan ya fahad yaga kunshin nan da kitson nan zaucewa kawaine bazai yiba"  meenah itama ta karbi zancen,


"Wai dama haka kuke bakuda kunya?" Khulsum tafada tana rike haba,


"A'a wallahi Anty khulsum ai kin san Adda labour kakarmu ce fa dole mu rinka janta" inji meenah,


"Adda mai gado ki fada masa angama komai yatura wadanda zasu jire gidan saboda anjima suma su yafendon zasu taho"


Bata tanka ba takarasa shiga cikin daki wanda yanzu kayan ciki suka zama sai saura domin duk su maama sun shirge mata kayanta sunyi mata gaba dashi sai wanda zata nema kawai aka bari, zama tayi gefen gadonta tana kallon tv domin wani Indian film ake haskawa atashar MBC Bollywood mai suna a gentleman, wayar fahad takira ringing biyu yadauka,


"Ranki yadade..."


"Am yawwa kaga angama jeren nanne shine zan fada maka katura wasu sai su kwana agidan"


"Angama ranki yadade"


Katse wayar tayi tamike tafita waje wurinsu khulsum. Kamar yadda yafada da daddare su salim da Abba ya tura domin su kwana agidan,lokacin da zasu tafi jan salim yayi yace masa,


"Allah karku kwanta mana agado kasan dai babu kyau..."


Dariya salim yayi yakai masa duka,


"Allah ko fitsararre? To ai ya Abba yadace ka fadawa tunda shine babba amma baniba"


"Shi ai nasan bazaiyi hakaba sai kai...."


"To kuwa kwana bisa gadonku daram..."


"Wallahi karka kuskura..."


"Sai kayi kuma...."


Daga haka yayi gaba abinshi, fahad kam neman wuri yayi ya zauna nan kofar gida domin cikin gidan cike yake da mata yan uwa da abokan arziki, saida yakira bilkisu yasanar da ita yatura wadanda zasu yi gadin gidan sannan hankalinta ya kwanta.


 Washe gari da shirye shirye aka tashi kasancewar ranar za ayi kamu, kuma anan compound din gidan za ayi kamun domin ita bata da ra'ayin zuwa hall, kowa kagani acikin hidima yake fuskarsa dauke da farin ciki ba ma kamar ya mahaifiyarta ammah wacce ke jin kamar ancire mata k'aya, yanzu kam tasan zasu huta da wadannan maganganun da habaice habaicen da ake yimusu acikin dangi, mutane sukan manta da cewa Allah shine gwani wurin iya tsara komai na rayuwar bayinsa kuma duk yanda ya tsara to hakance zata faru ko anaso ko ba aso, ko anshirya ko ba ashirya ba. Su meenah dai ana can wurin masu decoration ana nuna musu muhallin da yadace asaka kowacce kwalliya domin gudun kuskure, amarya fa? Ana can daki tareda bakinta wadanda suka zazzo daga sassa daban daban na jihar Kano musamman ma wadanda sukayi secondary school tare da wadanda sukayi Jami'a shiyasa itama yau tasamu nasarar warewa ta cika da farin ciki saboda ganin wadanda tajima bata ganiba amma da har masifa tayiwa khulsum lokacin da ta turawa class mates dinsu invitation card ta group chat dinsu dake Facebook da whatsapp tana cemusu ga labour prefect dinsu fa zatayi aure dan haka su daura damarar zuwa shan shagali, ai kuwa sunyi mata kara domin kusan duk wadanda ke zaune acikin kano sunzo,anyi bushasha babu laifi domin chicken pepe da lafiyayyar fried rice aka dafo aka kawowa friends din nasu wanda wannan yana daya daga cikin gudunmawar khulsum banda kayan sanyaya makoshi cikin manya manyan kuloli, ba karamin kyau amarya tayiba tun kafin tayi shirin zuwa wurin kamu, karfe uku tayi wanka da ruwan lalle da turare, tana yin sallar la'asar kuma mai kwalliya tafara aikinta, wanda suka dauki tsawon lokaci sunayi,


"Masha Allah...masha Allah"  shine abinda kowa ke fadi lokacin da amarya tafito domin ba karamin kyau tayi ba, tayi kyau na bugawa ajarida, komai na jikinta golden colour ne kama tun daga material din jikinta wanda akayi kyakkyawar doguwar riga irinta amare zuwa head din dake nade akanta da takalminta,pose da komai da amarya ke sakawa har sarka da dan kunne, kidanta daban aka saka mata lokacin da ta karasa wurin khulsum na rike da hannunta, fuskarta abude take amma da akwai wani net me kyau akanta, kujerar da aka tanada musamman dominta taje ta zauna babu bata lokaci aka fara gudanar da abinda yadace daidai lokacin dangin ango suka karaso nan aka tarbesu aka basu wurin zama suka zazzauna. Babu karya kamun yayi kyau domin babu tarkacen shirme aciki kawai dan abinda ba arasa ba aka gudanar daga nan su iyallo suka zo suka sakawa amarya lalle lokacin magriba takusa, dangin ango basu tafiba saida aka gama komai, suka daddauki pics da amarya da danginta sannan suka tafi bayan anware musu manyan jakunkunan da aka rarraba awurin. Ango kuwa yana can gidansu salim adakinsu amma yana ganin duk abinda yake faruwa awurin kamun domin yatura mutane biyu daya zaiyi video coverage dayan kuma zai rinka turo masa ta whatsapp, hakance kuwa tafaru domin komai kamar akan idonsa akeyi....



*_Ummi Shatu_*    


© *HASKE WRITERS ASSO.*



*KAMAR DA WASA....!*  



  _*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*




  *17*



*Kamar da wasa na saidawa ne yar uwa idan kinada bukata kisiya sai ki karanta.*


       ***Ba karamin kyau tayi masa ba, yau sai yaga tafi koyaushe kyau kamar zaka saceta ka gudu ko kuma ko dan bai taba ganinta cikin kwalliya kamar haka bane shiyasa yau yaga kamar canjata akayi? Kunshin dake hannunta yaketa zooming yana kallo sannan yakoma kan fuskarta itama yarinka zooming dinta yana gani,dariyar shakiyanci yayi lokacin da ya kurawa kirjinta ido bayan yayi zooming,


"Aita boye abu ayita boye abu to yau dai gashi ina kallo..."


 Saida yagama ganin komai sannan yatashi yafita sallar magrib bayan ya kullewa salim dakinshi, daga can gidansu yawuce alla alla yake yi gobe tayi adaura aurensu da bilkisu shiyasa a wannan daren baccinshi rabi da rabine yayinda ita kuma amaryar ma gaba daya daren ranar kasa bacci tayi kwata kwata bare gashi bata salla balle tatashi tayi sallar nafila ko tarage damuwa shiyasa abun yayi mata yawa, juyi kawai tai tayi danma da alama agidan ba ita kadaici bata yi baccin ba domin tana jiyo kannen ammah sunata shan hira da yan garko awannan tsohon daren, sai daf da asubah tasamu bacci ya dauketa,wurin 6 da wani abu tatashi tayi wanka tashirya cikin daya daga cikin dinkin da fahad yayi mata,yake kawai takeyi amma zuciyarta cike take da damuwa da bacin rai, gashi ta kasa cin komai sai ruwan lipton kadai da tasha. Fahad kuwa tun asussubah yatashi dama bacci sama sama yayi shi, karfe tara zasu tafi garin garko inda acanne za adaura auren, kamar bilkisu shima kasa cin komai yayi dakyar ayiyah ta tirsasashi yasha ruwan koko daga nan wanka yayi, tun yana cikin toilet din yasoma jiyo hayaniyar mutane yan zuwa daurin aure domin kofar gidansu ne m point din, yana fitowa babu bata lokaci yazuba sabuwar farar shaddarsa harda babbar riga yasha turare, kai wannan ango yasha kyau gaskiya domin ba karamin fitowa yayiba fess, koda yafito kansa har wani sara masa yayi saboda al'ummar da yagani, abokanshi ne, yan shagonsu, abokan yayyenshi, yan uwa da yan unguwa ga uban tarin motoci jere reras, salim ne yakama hannunshi sukaje har gaban motar da zai shiga suka shiga nan kowa yashiga dama su baba sunyi gaba nan suma suka dauki hanya, haka kawai garin yayiwa fahad kyau bama shi kadai ba kusan kowa da wannan shine zuwansa nafarko garin ya burgeshi, babban masallacin garin acanne za adaura auren bayan an idar da sallar juma'a,


Bilkisu tana can gabanta sai faduwa yake wanda bata san dalili ba sai dai tana danganta hakan da wannan auren da za adaura mata shi yau gashi kuma ayau din za akaita gidansu fahad domin yau ammah ke gudanar da yininta shiyasa su maama sun kammala kintsa mata kayanta gaba daya hatta wanda zata tafi dasu gidansu fahad an shirya mata cikin daya daga akwatinta na lefe. Ana idar da sallar juma'a aka daura auren fahad da bilkisu akan sadaki naira dubu talatin,bayan an gama daurin auren sun daddauki hotuna suka dawo, direct gidansu bilkisu suka wuce lokacin tasake wanka tashirya cikin leshi  riga da skirt,tun kafin tafito su meenah suka rigata sukaje sunata hotuna da ango da abokansa,ita kam adole tafita itada khulsum bayan angama yimata kwalliya,


Kasa kasa take kallonshi tana son taga koda gaskene yayi kyau din kamar yadda taji su hindu nata zuzutawa, babu laifi kam yafito sosai,shima anasa bangaren tunda ya hangota hankalinsa yayi kaura daga gareshi yakoma kanta saboda ta hadu iya haduwa shiyasa har dana sanin kwaso abokansa suzo ganinta yayi, wani kishine ke lullube zuciyarsa sama sama duk abinda yakeyi idonshi na kanta, saida suka gama yin hotuna da mutane sannan yamatso wurinta nan fa kowa yarude da daukarsu awaya, ita haushima abin yake bata, 


"Barka da yau Hajjaju...,ya fama da jama'a?"


"Alhamdulillah"


Shine abinda tafada kawai suka cigaba da hotuna, ana gamawa bilkisu takoma gida, angwaye dai daga can wurin walima suka wuce wadda zasu gabatar afilin makaranta. Bayan su Abba sun dawo kiran bilkisu yayi domin abata sadakinta sannan yakara yimata Nasiha shida waliyyinta, duk saida tabi ta bata kwalliyar fuskarta da hawaye da kuka shiyasa tun daga lokacin ba akara samun kanta ba har dare lokacin da za arakata domin fada ne na iyaye daga wannan yagama sai wannan yazo yayi nasa, ya mudan shima harda zuwa yayi mata nasihar azauna lafiya sannan yabawa maama dubu goma yace abata Allah yasanya alkhairi, tun bayan magriba su khulsum ke binta tatashi tashirya amma taki tashi saida aka fadowa ammah ai iyallo naji tazo tahau fada babu shiri tatashi tashiga bathroom tayi wanka tafito, abinci kam rabonta dashi tun jiya da rana, kayan da zata saka sai faman jikeshi da turare su meenah keyi kamshin har hawa mata kai taji yanayi, hatta pant din da zata saka gani tayi maama na shafeshi da almiski, tabe baki tayi tazauna gefen gado ta bude drewar din gadonta ta dauko pad ta warce pant din a hannun maama azuciyarta tana cewa,


"Yara kwayi kwa gama"


Bra din da zata saka ma itama saida suka tsuma ta da turare daga nan kuma suka dawo kanta itama zasu shafeta da madarar turare, tana ki tana komai saida suka shafa mata sannan tasaka kayanta tanemi wuri ta zauna duk da tanaji ana cewa tafito amma taki koda motsi saida su hajjaye suka zo suka fito da ita, saida aka kaita wurin ammah da abba tayi musu sallama sannan aka fita da ita inda motoci ke jira, kawarta khulsum ce agaba sai su iyallo da suka sakata atsakiya ba awuce dasu ko inaba sai gidansu fahad inda dangi sukayi dafifi suna jiran zuwansu, dakin ayiyah aka kaita tana lullube cikin babban mayafi, saida aka gama yan gaishe gaishe da taya juna murna sannan aka damka amanarta a hannun su ayiyah daga nan yan kawo amarya suka tafi bayan su maama sun shigo mata da akwatinta.


Duk dauriyarta saida tayi hawaye lokacin da taga kowa yatafi anbarta acikin mutanen da bata saniba,mutane sai zuwa ganinta akeyi amma babu Wanda yasamu nasarar ganin fuskarta saboda a lullube take. Har wurin karfe goma saura mutane basu daina shigowa ba sai gajiya su anty Fauziyya sukayi sukace arakata masaukinta ta kwanta ta huta, yaya asabe ce takama hannunta suka fita tarakata dakin dake soro wato dakinsu fahad  su maryama kuma suka biyosu da akwatin kayanta da food flasks din abinci guda biyu, zame mayafin kanta tayi bayan sun gaggama ficewa tafara bin dakin da kallo, babu wani tarkace dayawa aciki sannan dakin baida girma caan dan madaidaicine mai dauke da babbar katifa anshifideta da sabod bed sheet sai akwati babba guda daya amma dakin fes yake yasha sabon fenti da jan carpet malale aciki ga kofar toilet nan komai dai neat, bata ko taba Food flasks din da aka kawoba taci gaba da zamanta shiru har goma da wani abu sai lokacin taji gidan ya danyi shiru alamar mutane sun ragu, sha daya saura yan mintuna taji alamun bude kofa gyara mayafinta tayi ta lullube jikinta,fahad ne yashigo rikeda leda,yana sanye da danyen boyel kalar ruwan siminti kanshi babu hula, sallamar da yayi kawai ta amsa daga nan ta guntse bakinta, agefen katifar ya zauna yana zaro wayarshi daga aljihu,


"Hajjaju yagajiya?"


"Alhamdulillah"


Bai kara magana ba yamaida hankalinsa kan wayar hannunshi, ita dai tana zaune ta jingina da pillow sai karkada kafa take kamar wata sarauniya, sunfi minti biyar ahaka babu wanda yasake cewa uffan sai karar fanka da ta cika dakin, ledar da yashigo da ita yamika mata gabanta ya ajiye,


"Ki ci abinci gashi nan..."


Batayi magana ba ta dauke kai,


"Kinji...."


"Naji..."


Tabaya ya kwanta rigingine yana kallon sama yana danna wayarshi zuwa can yadago ya kalleta,


"Bazaki ci abincin ba ne? To kitashi kiyi wanka ki kwanta"


Shiru tayi batayi magana ba yayinda shikuma yatashi zaune ya buda ledar dake ajiye agabanta yadauko malt guda daya ya balle ya dan sha sannan ya ajiye, Flaks din da ke ajiye ya bubbude, sakwara ce da miyar ganye tasha kaji gashi ta soyu, dama yunwa yakeji dan shima rabonshi da abinci tun yaushe mikewa yayi yashiga bathroom ya daurayo hannunshi yadawo yaja abincin gabanshi yafara ci tana zaune tana kallonshi dama guda ukuce sakwarar babu bata lokaci yatashi da guda biyu, kallonshi tayi adage,


"Malam jimana...."


Dagowa yayi ya kalleta,


"Ai abincin nawane ba naka ba so zaifi kyau idan kabar min kayana haka"


Tsame hannunshi yayi daga cikin miyar yamayar da murfin ya rurrufe sannan yajanyo ledar gabanta yabude, gasasshiyar kaza ce mai romo sai kayan sanyaya makoshi malt guda biyu da fresh milk zindimemiyar roba, kazar yabude yasoma yaga yana ci yana korawa da malt,


Harararshi tayi ta janyo flask din gabanshi tana turo baki budewa tayi itama tafara ci tana kallonshi yanata cin kazarshi,


"Gaskiya wannan yaron akwai mugun ci....tab"


Sai da yaci rabin kazar sannan yamike yashiga bathroom, wanka yazarce dayi shiyasa yajima aciki, tana cin abincin tana sake jinjina kuruciyarsa to inbanda kuruciya menene na zama yacinye kazar da ita yasiyowa? 


Itama da kazar ta dora bayan ta cinye sakwarar amma bata ci da yawaba domin cinya kadai taci da dan abinda ba arasa ba saboda tarihi ko nan gaba zata tuna da taci kazar aurenta. Tana kammalawa yana fitowa daga wankan da kayanshi ajikinshi gaban akwatin kayanshi yatsaya yabude yaciro riga da wando roba kamar sport wear yakoma bathroom din yasaka sannan yafito tana zaune inda take yazo ya kwanta saitin kafafunta bayan yaja pillow daya, babu jimawa yayi baccinshi,saida taga yayi bacci sannan ta mike tashiga bathroom ita a ka'idarta idan tana period indai zatayi fitsari to saita canja pad, shiyasa saida ta dauki pad acikin handbag dinta sannan tashiga toilet, jikinta kawai tagyara amma batayi wanka ba ta canja pad tafito, akwatin kayanta tabude wai kozata samu kayan da zata saka tayi bacci dasu amma abin haushi duk night wears din bazata iya sakawa ba domin duk marassa nauyine kuma asha shagarai tasan da biyu su meenah suka yimata haka gashi ita bata iya kwana da kaya ajikinta ba, daga karshe dai sai hakura tayi tamaida akwatin tarufe, juyawa tayi ta kalleshi yawani baje yana baccinsa cikin kwanciyar hankali ga sanyin fanka yana fifitashi, bra din jikinta ta cire tabar kayan dake jikinta taje gefen katifar ta zauna ta kishingida, wayarta taciro ta duba misalin karfe daya nadare agogon wayar ya nuna mata, kashe wayar tayi tai addu'a ta shafa sannan tamaida kanta kan pillow dayake itama amutukar gajiye take bata wani jimaba bacci yace muje zuwa......




*_Ummi Shatu_*    


© *HASKE WRITERS ASSO*



*KAMAR DA WASA...!*  



  *_NA_*


 _*UMMI A'ISHA*_




  *18*




    ***Tunda fahad yakwanta bacci bai ko juya ba sai da asubah, tashi yayi yaje yayi alwala yafito yafita masallaci tareda baba suka shigo gidan lokacin harsu mamuh sun fito suna kokarin hada wuta, dakin yakoma bayan sun gaggaisa dasu,har lokacin bilkisu na kwance ta tukunkune acikin mayafi tanata sharar bacci, tashinta yafara yi tatashi tayi salla amma taki tashi dole sai kyaleta yayi ya janyo wayarshi wadda ke jikin sucket tana charge yasoma matsata. Sai karfe shida saura sannan ta farka, akwatinta ta janyo ta bude taciro soson wanka da sabulu sai brush da toothpaste tajiyo ta kalleshi yayi saurin dauke idonshi yamayar kan wayarshi,


"Malam dan bani wuri zanyi wanka..."


Kamar bazai tashiba zuwa can dai yamike da wayarshi ahannu yayi waje, saida ta tabbatar da ficewar yayi sannan ta kwashi duk abubuwan da zata bukata tashiga bathroom, harta fito tashirya tsaf tasaka wata pink din shadda riga da skirt bai shigoba, turarukanta na alfarma da sanyaya zuciya ta dauka ta shafe jikinta dashi sannan taciro mayafi ta zauna mayan ta maida akwatinta mazauninshi, handbag dinta ta bude ta ciro chingum ta saka abakinta ta dauko wayarta ta kunna. Bata dade da kunnawa ba kiran maama yashigo suka gaisa daga nan su Hindu suma suka kakkarba suka gaggaisa, bayan sun gama wayar dasu meenah saiga kiran khulsum,


"Amarya bakya laifi... Amarya kinsha kamshi"


Murmushi bilkisu tayi,


"Zan ramane wallahi, Allah yakaimu lokacin"


"Au danma na kiraki naji ya kika kwana?"


Kafin tabata amsa fahad yashigo direct bathroom yawuce tabishi da kallo,


"Ni lafiya lau natashi malama"


"Shikenan haka akeso ya angon namu?"


"Lallai kam, yana nan lafiya"


"To agaidashi ace sako injini nace ya kular min da kawata"


"Wannan sakon yafi karfina sai dai idan kun hadu ki fada masa da bakinki"


Khulsum nata tsokanarta tana ramawa daga karshe dai sukayi sallama takashe wayar, haka kawai sai kuma tunanin gida yafado mata nan taji kamar tafashe da kuka, Allah sarki rayuwa yanzu idan banda aure me zai rabata da gidansu, dakinta ne yafado mata arai da gadon da take kwanciya da komai nata dake cikin dakin, kiran da yashigo wayar tatane yakatse mata tunanin da takeyi, goggo maigado ce kanwar mahaifiyar Abba wacce aka yimata takwara da bilkisu, dauka tayi cikeda farin ciki domin goggo bilki halinta daban yake tafi iyallo kula da faran faran,


Har yafito daga wankan waya takeyi, tagaisa da wancan ta gaisa da wancan, kayanshi ya dauka yakoma toilet zuwa can yafito yana rataye kayan da ya cire saman kofar toilet din, cumb yadauka yagyara sumarsa sannan yajuya yana kallonta lokacin da yake kokarin shafa turaren amirul hub, ido suka hada ta wani janye nata cikeda sigar harara yana jinta lokacin da tagama wayar,


Zama yazo yayi gefen katifar domin saka sabuwar bakar safar dake hannunshi,


"Hajjaju kin tashi lafiya?"


"Alhamdulillah..."


"Ya bakunta?"


"Lafiya"


Murmushi yayi ya kalleta,


"Bari naje nakarbo miki breakfast anjima sai na rakaki kishiga cikin gidan ku gaisa dasu"


Jijjiga kai kawai tayi amma bata yi magana ba hakan yabashi damar mikewa yafita, yana shiga cikin gidan masu tsokanarshi suka fara suna fadin,


"Ga ango ga ango..."


Su Mariya kuwa rugowa sukayi suka rirrike hannunshi,


"Ya fahad muje mugaida Anty yanzu?"


"A'a Mariya ba yanzu ba, yanzu hutawa take zan kai mata abinci taci idan tagama zata shigo ku ganta"


Dakin ayiyah ya furmutsa yashiga duk da dakin tafare yake da baki amma haka ya tsattsallakesu ya isa gareta, cikeda farin ciki ta amsa gaisuwarsa sannan tace yaje yasamu yaya asabe yakarbi abincin karin kumallon bilkisu, fita yayi bai tsaya jin dan bikin da abokan wasa keyi masa ba wadanda ke cikin dakin, wurinsu anty fauzy yaje suna zazzaune kofar kitchen suna dama kunun farar shinkafa can gefe daya kuma masu suyar fanke nayi ga kosai shima anata sakawa,


"Ah kaga shalelen ayiyah ango..."


Dariya yayi yaduka agabansu yana cewa,


"Kai yaya asabe bari kiran angon nan dan Allah"


"To ya kwanan amarya?"


"Tana nan lafiya, yanzu ma abincin ta nazo karba"


"Dakyau ango mijin amarya..."


Mikewa yayi tsaye yana kallon anty Fauzy wacce rufe bakinta kenan,


"Anty fauziyya kema haka zakice? Shikenan bani abincin natafi"


"Za abaka ai daina gaggauta, da alama gaba daya hankalinka na can..." Anty juwairiyya dake cikin kitchen itada anty kubra tafada tana dariya, shi sam baima gansu ba wallahi sai yanzu ashe suna ciki suna hadawa amarya breakfast,


"Ohh God....,ashe yan sa ido ana ciki..."


"Mudai ga abincin amaryarka sai ka sakar mana Mara muyi fitsari" Anty kubra tafada lokacin da take fiffito masa da abincin, kayan sunyi masa yawa dole sai su mariya yakira suka tayashi dauka domin bazai yuyu yadauka shi kadai ba, har cikin dakin suka kai masa abin mamaki sai yaga bilkisu ta sake dasu sosai harda cemusu su zauna suci abincin tare, harara ya zabga musu babu shiri suka fice simi simi, tabe baki tayi tagyara kishingidar da tayi, shi wallahi wannan mulkin nata dariya yake bashi, abubuwan da aka girka yafara dubawa, chips ne aka yimasa wani hadi na musamman da dan salad sai farfesun kayan cikin saniya sai bread da ruwan zafi,


"Ranki yadade ga abincin... Bismillah"


"Ok..."


A flate daya ya zuba musu komai yasa fork yafara ci, wayarshi ce ta katse masa hanzari, husnah ce bai san lokacin da ya girgiza kai ba yace,


"Allah sarki husnah bakiyi fushi ba?"


"A'a prince banyiba, angama biki lafiya? Allah sanya alkhairi yabada zaman lafiya agaida min da ita"


Jin abinda husna tace sai tausayinta yasake kamashi bai san da biyu ta kirashi ba dan saida kawayenta suka tirsasata sukace tayi masa kirsa irinta mata ta nuna bata dauki auren da yayi da zafiba karta nuna masa komai amma da zarar burinta yacika ta nuna musu tafisu iya wulakanci, wannan dalilinne yasata dannar zuciyarta ta kirashi amma fa can kasan ranta kishine fal dankare da tsanar bilkisu wadda bata ma san da ita ba,


"Amin husnah nagode sosai..."


"Babu komai Prince ai kafi haka agareni"


Ita dai bilkisu kallonshi ta tsaya tanayi yayinda shikuma keta yiwa husna godiya, cin abincin shi yaci gaba dayi zuwa can wayarshi tasake yin kara ya dauka yana dariya bayan yasaka a hands free,


"Kai gwauro ya akayi...?" Yafada yana dariyar shakiyanci, daga can bangaren salim yace,


"Malam wallahi yau kasan wanda zaiyi maka gadin gidanka nidai nagaji tahowa zanyi"


"Karka damu yau masu gidanne zasu kwana aciki, insha Allah yau anan zamu kwana kai kuma kaje ka karata da tsohuwar katifarka..."


"Ohh hakama zakace? To babu komai ai akwai gaba..."


"Wasa nake abokina... Yanzu kadan bada jimawa ba za akawo muku breakfast kaida babban yaya, dan Allah amika min gaisuwa" 


Kit yakashe wayar yana yiwa salim dariyar shakiyanci, ita kallonshi ma kawai ta tsaya tana yi tana mamakin yanda yake da bakin tsiya,


"Hajjaju ya akayi ne? Nace kizo kici abinci kin ki ban saniba ko kina jin nauyina ne, amma ai ko za ayi fulako bai cancanta ayiwa mijiba domin shi sirrinka ne...."


Wani kallo tayi masa wanda ita kadai tasan ma'anarsa,


"Miji...? Miji kuma?"


Tsayawa yayi da cin abincin da yakeyi ya kalleta,


"Ina da wani sunanne da wuce wannan awurinki? Duniya da sauran jama'ar cikinta sun gama shaidawa ni fahad mijinki ne asalima harda sadaki na baki naira dubu talatin lakadan ba ajalan ba right....?"


"To ko in dawo maka da abinka?"


Girgiza kanshi yayi ya langabe kai yaci gaba da cin abincinshi,


"A'a, ni ai ban baki dan kisake dawo min dashi ba ranki yadade..."


Shiru tayi taci gaba da danne dannen wayar da takeyi tun dazu, zuwa can yasake kallonta yace,


"Kefa nake jira ki karya mu fita, dagaske yau zamu bar gidan nan mukoma namu..."


Tsam ta tsaya da abinda takeyi itama takai kallonta gareshi,


"To yanzu idan nashiga ciki me zanyi? Kasan dai ni ba sanin al'adarku nayi ba..."


"Karki damu zaki sani sannu ahankali"


"Dan rainin wayo...." Tafada acikin ranta sannan ta ajiye wayar hannunta ta janye flate din gabanshi zuwa gabanta ta dauki fork tasoma ci, kallonta yatsaya yi kafin ya nisa,


"Ranki yadade ai ba koshi nayiba..."


"Duk abincin da kaci daga daren jiya zuwa yanzu?"


"To ai na kwana biyu rabona da abinci fa"


Kafada ta daga,baiyi kasa agwiwa ba yasake mayar da nasa cokalin cikin flate din yaci gaba da ci atakaice dai shi yaci fiyeda rabin abincin, yarigata tashi dan haka yasake kintsawa sosai yasha hula sai kamshi yake, abokanshi sai kiranshi sukeyi awaya ana tayashi murna da fatan alkhairi, hannayensa duka biyu ya zuba cikin aljihun rigarshi yana zagaye dakin yana jiranta tagama, saida tagama jan ajinta da shan kamshinta sannan ta mike bayan tasake gyara fuskarta sosai,turare tasake fesawa jikinta sannan ta dauki babban mayafi  tayafa tarufe fuskarta, dariya yafarayi ahankali wayarta kawai ta dauka amma yace mata,


"Da dai kin dauki handbag din naki da zaifi..."


Batare da tace komai ba ta dauka tafita, rufe dakin yayi sannan suka nufi cikin gidan ai tana jiyo hayaniyar mutane tayi azamar sake lullube fuskarta saura kadan tayi karo da itacen da aka girke domin dafa sanwa, hannunta yayi saurin rikowa dama tun adaren jiya yake da wannan burin sakamakon tafiya da hankalinshi da kunshinta yayi, babu damar yin musu domin bata ganin gabanta sosai kanta akasa yake sannan mayafin mai duhune sosai, har dakin ayiyah ya shigar da ita ya zaunar da ita nan fa aka shiga zuba guda ana shewa, shidai ficewa yayi yabar dakin duk kuma sai taji wani iri wato wurima da wanda kasani dadi gareshi amma idan akace baka san kowaba to baka iya sakewa, tana jiyoshi atsakar gida suna yarawa da kakanninsa wato abokan wasanshi yana cemusu,


"Ni duk kunyi min tsufa, ga matata can duk tafiku kyau kuje ku ganta gyalenta kadai ya isa ya siyeku gaba daya...."


Daga haka yagudu bata sake juyo maganarshi ba, duk kuma sai tashiga kadaici danma anata zuwa gaisheta kamar wata sarauniya, tana zaune shiru shiru sa'arta daya Maryam da Mariya na kewaye da ita nan tayi masa text massage tana daga tukunkune cikin mayafi,


_Wai kana inane?_


Babu jimawa saiga reply yadawo mata dashi,


_Ina zuwa nan bada jimawa ba._


Zaman shiru taci gaba dayi sai dai idan ankirata awaya ta daga amma tana jiyo hirar mutane awaje group group. Wurin sha daya da wani abu tafara jiyo guda sosai da karfi aifa nan mata aka kifa kwarya ana kida mai dadi wasu kuma na rera wakar aure,


Wasa wasa gudar nan har cikin dakin da take ta cikin mayafin ta samu nasarar hangoshi sanye da babbar riga da hula, har inda take yatako yazo ya dagata, tsakar gida suka fita inda ake yin wannan kidan, daya bayan daya ake zuwa ana zuba musu kudi shi sai asaka masa acikin aljihunshi ita kuma cikin jakarta, sunfi minti talatin tsaye ana zuwa zuba musu kudin nan ita har tagama kosawa da wannan tsaiwar danma jingine take jikinsa amma babu wanda zai gane, saida kaf dangi na uwa da na uba suka gama zuba musu kudin sannan aka maida ita daki, shi kam ficewa yayi bata kara jin alamunshi ba har azahar lokacin ne kuma aka maida ita dakinshi dake can soro wai tayi salla taci abinci, kamar kuwa sun san tana da bukatar komawa dakin domin amatse take da ta canja pad din jikinta dan ita atabar pad tadade ajikinta to tayi awa uku,neat tasamu dakin anshare angyarashi an fitar da kwanukan abincin daren jiya ankunna turaren wuta na tsinke.


Bayan su anty juwairiyya da suka rakota sun fita wanka tashiga tayishi sauri sauri tafito dan kar wani yashigo ai kuwa tana fitowa tana kokarin manna pad jikin pant dinta yashigo, danma lullube take da mayafi, bai kalleta ba yawuce gaban akwatinshi sannan ya janyo kayanshi dake rataye jikin kofa yasaka cikin akwatin, kasa saka pant din tayi agabanshi sai bathroom tawuce tasaka sannan tafito lokacin yana rufe akwatin,


"Ranki yadade kiyi sauri ki shirya yanzu za akawo miki abinci...."


Bai karasa rufe bakinsa ba yaji knocking abakin kofa, tashi yayi daga gaban akwatin,


"Inajin ma gashi nan ankawo... Bari mugani"


Kofar yabude yafita ai kuwa su mariyane dauke da kwanukan abinci, karbowa yayi yashigo dashi lokacin tana saka bangles, ajiye mata yayi yajuya ya dauko wasu kayanshi dake kan drewar din dakin,


"To hajjaju nabarki lafiya, sai mun hadu a sabon gida..."


Zama tayi tana kallonshi,


"Ban ganeba, wai kana nufin ni kadai zan zauna adakin nan shiru har lokacin da za araka ni gidanka?"


Murmushi yayi,


"Ehh mana, kodai kinfi son nazauna mu zauna tare? Kibari zan turo miki su Mariya suzo su tayaki zama"


Daga haka yadauki kayanshi har katuwar akwatin yafice, bai jima da fita ba sai gasu mariya sunzo ai kuwa tasha hira domin yaran sunada surutu shiyasa taji dadin zama dasu inbanda labarin gidan da na makaranta ba abinda suke bata. Har la'asar tana tare da yaran amma mutane na dan shigowa musamman baki masu tafiya suna yimata sallama da fatan alkhairi shiyasa zuwa karfe biyar na yamma gidan tsit sai mutane kadan na kusa amma bakin nesa kam duk sun tafi, bayan sallar magrib su anty Fauzy suka zo suka shigar da ita cikin gida lokacin ma baba yadawo har turakarsa suka kaita ta gaidashi sannan aka maida ita dakin ayiyah, ayiyah kam sai nan nan take da suruka matar auta guda komai tagani ta tura mata gabanta da haka har motar daukarta tazo, anty Fauzy da anty Kubra ne zasu rakata, daki daki aka bi da ita tayiwa kowa sallama sannan aka fita da ita bayan anfitar da kayanta,Baffa ne yayan salim a motarshi shi yadaukesu yakaisu wanda tafiyar bata da wani tazara sosai can, koda sukaje su basu wani jimaba suka yimata sallama suka fita, hamdala tayi acikin zuciyarta ta bude fuskarta tana bin dakinta da kallo wanda yasha kayan alatu domin gadonta kadai abin kallone gashi dakin babu laifi da girmanshi saboda ya cinye komai dan iya mirror dinta kadai duniyane wurin da ya lashe ba dan kadan bane cire mayafin tayi ta fita falo wanda shima ba laifi ga dining area taciki ga kitchen nan ga store cikeda kayan abinci domin komai biyar biyar abba yayi mata kama tun daga kan shinkafa, taliya, macaroni, indomie, crate din kwai,semovita manja, man gyada komai biyar,


Ba karya gidan fahad yayi domin yarone mai zuciya shi dai barshi da kwalisa da iyayi amma yanada zuciyar neman na kanshi duk da baiyi karatu mai zurfi ba domin iyakacinshi diploma kawai sai sana'ar dinki da yasaka agaba kuma yayi sa'a sana'ar ta karbeshi, iyakar gata tasan iyayenta sun nuna mata domin komai mai kyau da tsada aka yimata ita kanta gidan ya burgeta dan dagwas dashi shi ba kato can ba kuma shi ba karami can ba abinta dai dai misali, tsakar gidan dan madaidaicine yasha interlocks harda flowers shuke sai pop shikenan sai kofar falo ma'ana dai safe content ne komai aciki, abu dayane yabata takaici bedroom guda daya zasuyi shearing tunda ga dayannan ba agama ba asalima data buda ko fulasta ba ayiba sai uban tarkacen kayan aikin gidan da aka zuba aciki aka rufe, alhalin gado guda biyu abba yasai mata kamar sauran yan uwanta gashi karshenta sai dai komawa akayi dashi gida......



*kamar da wasa na kudine idan har kin san baki biyaba dan girman Allah karki karanta.*




*_Ummi Shatu_*    


© *HASKE WRITERS ASSO*



*KAMAR DA WASA...!*  



  _*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*



  *19*




  Cikin bedroom dinta takoma ta zage tashiga toilet tayi wanka tafito ta zauna tayi shirin bacci cikin wani night wear milk colour riga da wando,wandon iyakarshi cinya sai rigar da bata wuce cinyaba itama, handbag dinta ta janyo ta debo wayoyinta gaba daya ta kashe sannan ta rufe jakar da kamar ta zauna zaman kirga kudaden dake ciki wadanda aka zuzzuba mata tabari sai zuwa gobe ta kirga domin bacci kawai take ji, kashe wutar dakin tayi tai kwanciyarta bayan ta lulluba domin bata iya kwanciya da kaya ba ajikinta tasan babu mamaki cikin dare idan zafi ya dameta ta fige rigar ma gaba daya. Misalin karfe 10 saura fahad yashigo gidan tareda tawagar abokanshi wadanda suka iyo masa rakiya, key dinshi yadauko yabude gidan yashiga yana jin wani farin ciki na ratsashi, har falo suka shiga danma baiyi garajen kaisu dakiba kamar yasani yace kawai su tafi yasan yanzu tayi bacci amma sukace karyane kawai dai yana yimusu kora da haline, bedroom yawuce yana shiga ya kunna fitila awayarshi ya haska ya kunna wuta, bude ido daya tayi ta kalleshi jikinta lullube da duvet hular kanta ta cire saboda santsi,kitson ya zubawa ido kamar yasamu tv


"Yadai....?" Ta fada tana yamutsa fuska domin ba kadanba sosai tafara jin dadin baccin da ya katse mata ta hanyar kunna wuta itafa duk dadin barci da nisan da yayi matsawar zaka kunna wuta to sai ta tashi,


"Ah babu komai..."


Daga haka yakashe wutar yafita,


"Ai nafada muku dama tayi bacci, yanzu gashinan haka kawai kunsa na tashi baiwar Allah..."


"Dakyau mijin yar gata... Wato ma idan tana bacci ba atashinta" inji hamza na shagonsu, shi dai alla alla yake su tafi domin shima yana son ya kwanta ya huta, ai kuwa sun wahalar dashi kafin su tafi daga karshe daya bayan daya yarinka turasu sannan yamaida kofar gidan yarufe yadawo ciki itama kofar falon yarufe yashiga dakin, wannan karon bai kunna wuta ba kawai da fitilar wayarshi yayi amfani yashiga bathroom bayan yadauki kayan baccinshi, wanka yayi,yana cikin wankan yalura da pad din data jefar cikin dustbin duk da haka bai hakuraba saida ya dauki dustbin din yayi masa kallon kurulla daga karshe dai yagane menene, baki yatabe yasaka rigar baccinshi armless da wandonta duk jajaye, yana rike da kayan da yacire, drewar yabude ya watsa kayan sannan yafita falo dan bazai iya bacciba sai yaci wani abu, balangun da yazo dashi yabude kulli daya yaci yakoshi sannan yasha yoghurt guda daya sauran yasa cikin fridge, dakin yakoma yaje kan gadon yana shirin kwanciya yaji tace,


"Malam yadai?"


"Kamar ya? Kwanciya zanyi mana"


"Bana skwatin, ban iya kwana mutum biyu agado daya ba..."


Da mamaki yake kallonta duk da ba ganinta yakeba tunda dakin akwai duhu,


"Amma dai ai kema kin san gadon nan yayi miki girma ke kadai...."


"Dagaske fa nakeyi, dan naga kamar kai kadauki abin dawasa..., ga spare mattress nan kadauka sannan kaduba cikin drewar akwai sabbin bedsheets da blankets idan kana da bukata...and lastly ka kashe wannan hasken domin bana bacci da haske akaina" Daga haka tamaida kanta ta gyara kwanciyarta, fasa kwanciyar yayi ya nufi drewar yabude yadauki duk abinda zai bukata yana kunkuni, pillow yazo yadauka guda daya yayi hanyar falo yana cigaba da kunkuninsa,


"Amma bar miki dakin gaba daya kije ki cinye..... Nima bana bacci aduhu.....haka kawai dan takura zaki wanice ke kadai zaki kwanta akan gado...."


Katifar yadawo yadauka yaje yayi shimfidarshi afalo sannan yasake dawowa dakin, wannan karon wuta ya kunna dan neman magana,


"Me kuma yafaru?" 


Tafada tana bude ido dakyar dan bacci,


"Sucket nake nema zan saka charge"


"Acan inda zaka kwanta din babune? Pls malam kashe min wuta bacci zanyi..."


"Ehhh ai dai kin tashi...."


Yafada cikin kunkuni yanda bazata jiba, wutar yakashe yafita yana ja mata kofa dama babu wani charge da zai saka kawai son yatasheta ne yasashi kunna wuta, akusada doguwar kujera ya shimfida katifar tasa ya kwanta yadora kafarsa daya akan kujerar yakunna data awannan daren yashiga instagram daga can yafita yakoma Facebook, bashi ya hakura ba sai wurin daya da rabi a lokacin yaji bacci yaci karfinshi, ajiye wayar yayi bayan yakashe yayi addu'a babu jimawa sai bacci. Daf da asubah yatashi saboda fitsarin da ya takurashi kusan ma shine yatasheshi, bedroom yashiga mutuniyar tasa tana tukunkune sanyin asubah da na fanka na kadata duk ta takure wuri daya, fankar yarage mata sannan yashiga bathroom din yayi abinda zaiyi yafito yakoma falo yayi kwanciyarshi bai kara motsawa ba sai karfe bakwai saura, yana bude ido yakalli agogo gani yayi sun zabga makara gashi ko salla baiyi ba, bedroom din yanufa kansa tsaye yakama handle yabude tana zaune kan gadon ta ziro kafafunta kasa tana daure kitsonta da tacire ribom din cikin dare batare da ta saniba dan hatta rigarma sai yanzu ta mayar, babu zato taganshi yashigo cikin azama ta yayibi duvet tarufe jikinta tana kallonshi,


"Meye haka? Ya zaka shigo min daki batare da taking excuse ba....."


"Yi hakuri..." Daga haka yawuce zai shiga bathroom,kunkunin nasa yasoma yi shi kadai,


"Haka kawai kin saka mutane sun makara sallar asubah dan kawai kin san ke bayi zakiyi ba....."


"Magana kakeyi ne?"


"A'a..." Daga haka yafada toilet yayi alwala yafito bayan yayi brush, tana sanye da hijab har kasa da towel daure ajikinta tana gyara kan gadon, dan tabe baki yayi ya dauki rug din salla ya shimfida yatada salla, ita kuwa saida tagyare kan gadon tsaf sannan tawuce toilet domin yin wanka da kallo yabita sannan yamaida kallonshi saman gadon cikin kunkuni yace,


"Gashi dai mun dawo daya dake da kika kwana wajen kwanan mutum biyar da ni da na kwana awurin kwanan mutum biyu..."


Yana kan abin sallar azaune har tafito, handbag dinta ta dauka tanufi drewar tana cemasa,


"Dan bani wuri zan shirya..."


Mikewa yayi baice komai ba yanade prayer rug din ya ajiye saman bedside drewar yafita azuciyarshi yana cewa,


"Oho dai tunda nasan me za ayi har ake wani korata..."


Kwanciyarshi yayi saman doguwar kujera bai san lokacin da wani baccin yasake daukeshi ba. Ita kuwa bayan ta shirya wani material ta saka peach tasa sarka da dan kunne golden sannan tasaka abun hannu da agogonta na gold wanda ammah ta siyo mata last year da taje umarah, turarenta na garari na fitina tabi ta bazawa jikinta sannan tafito domin yanzune zata yiwa gidan kallon tsaf kasancewar safiya tayi dan harma rana tafito, fahad tagani kwance yana bacci nan kuma ga shimfidarsa ta daren jiya, tattara komai tayi ta dauke mattress din takai daki tazo ta kwashe sauran suma takai daki sannan tasake fitowa, ta kofar kitchen ta fita baya ta dudduba gidan wanda yake dan cicif sannan tadawo ciki sai lokacin ta lura da buhun Irish potatoes dake jingine acikin kitchen din, dayake anrigada anhada mata cylinder din gas dinta tukwane kawai tafara lalubowa dama cooker gas dinta babu ruwanta da neman ashana wurin kunnashi nan ta kunna ta dora ruwan zafi.


Dankali ta fere wanda zai ishesu su biyu ta soya bayan ta juye ruwan zafin acikin tea flask, da kwai ta hada tayi masa kyakkyawar suya yabada kala mai kyau dama bata da matsalar kayan kamshi da kayan dandano komai gashi nan a ajiye sai dai kawai ta dauka, hatta dakakken yaji gashi nan cikin karamin plastic haka su kuka,daddawa, kubewa etc duk su maama saida suka harhada mata aka dako sannan aka kawo mata, fridge din dake cikin kitchen din taduba kamar tasan yayi ajiya nan taga balangu da yoghurt da kayan marmari danginsu tufa, kankana da ayaba, balangun taciro tasaka acikin oven ta dumama bayan takara masa kayan hadi, saida ta kammala hada abin karyawarta tsaf sannan ta dauko ta kawosu kan dinning mai dauke da kujeru kwaya hudu,kayan tea dinma da alama babu dan haka tafasa shan ruwan zafin taci iya balangunta da chips din data soya. Tana daf da gamawa taga andawo da wuta mikewa tayi tanufi daki domin jona wayarta a charge da alama shima fahad yatashi domin bata ganshi awurin da tabarshi yana bacciba,akan gadonta taganshi yana cigaba da baccinshi,


"Wannan ko yasha wani abune? Bacci yaki karewa? Uhmm" 


Ita kadai take maganarta tana kokarin saka wayarta a charge, handbag dinta ta dauko ta zazzage kudin data samu tafara shiryasu domin wasu yan dari darine sabbi fil wasu yan dari bibbiyu wasu kuma yan dari biyar biyar harda yan hamsin hamsin ma, hakura tayi da shiryawar tasake gwamutsasu ta maida cikin handbag din taje ta ajiye tafita falo, daga can tayi waje, flowers din da aka shuka sunyi masifar kyau ga kuma wasu kananan shukoki nan da suka dan fara fitowa kamar bishiya duk da dai bata gane menene ba,abakin slave din pop din kofar falon nasu ta zauna,


Gajiya tayi da zaman wajen tasake diba takoma cikin falon ta zauna, tana nan zaune yafito sanye da blue din shadda yana balle links din hannun rigar,


"Hajjaju barka da safiya?"


"Yawwa, katashi lafiya?"


"Lafiya lau, ya kwanan kadaici?"


Banza tayi dashi tamaida hankalinta kan agogon dake manne jikin bangon falon wanda yake tafkeken gaske mai dauke da hoton abbansu ajiki,


"Babu kayan tea ko? Bari naje nasiyo yanzu"


"Babu amma ai ga breakfast can na hada"


"Haba ranki yadade daga zuwa sai girki?  Shikenan godiya nake"


Bai jira cewarta ba yayi dinning area din yazauna yaci abincin yayi dam dan babu abinda yarage yana gamawa yayi mata sallama yafice, wani takaicine kuma yafara ziyartarta shi yayi ficewarsa yanzu hakama gidansu yatafi amma ita gashi nan yabarta agida ita kadai gashi kuma tamanta ta tambayeshi taji ko anhada mata kayan kallonta, daki ta koma ta zare wayarta daga sucket ta kunna data ta fada yanar gizo wai ko zata rage zaman kadaici......



 *Book dina na kudine dan Allah idan har baki biyaba karki karanta.*




*_Ummi Shatu_*    


© *HASKE WRITERS ASSO*



*KAMAR DA WASA...!*  



  _*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*



  *20*



    ***Fahad lokacin da yafita saida yafara zuwa gidansu yagaida su ayiyah yayi musu ban gajiyar biki sannan yawuce kasuwa duk abinda suke bukata na amfanin gida saida yasiyo daga karshe ya iyo cefanenshi na abincin rana ya hado kayan tea sannan yanufi gida, lokacin har bilkisu tagaji da chaten dinma ta kashe data tana kwance tarasa abinda yake yimata dadi, kitchen yakai kayan gaba daya ya ajiye mata sannan yanufi bedroom, akwance yaganta kamar marar lafiya tayi shiru,


"Hajjaju yadai?"


"Yawwa dan Allah wai ba ahada kayan kallon can bane?"


"Anhada mana.... Zo kigani"


Tashi tayi tabishi zuwa falo nan yajona komai saiga tashar mbc Bollywood takawo darr, ajiyar zuciya tasauke harta dan ji dadi ai kalloma ba karamin rage kadaici yakeba, yana debewa mutum kewa sosai sai yau tayarda,


"Ga kaya can a kitchen ni Zan fita.."


"Ina zaka fita? Ni kadai zan zauna agidan? Wallahi a'a kaima neman wuri zakayi mu zauna tare..."


Kujerar dake makotaka da tata yaje ya zauna, yana zama wayarshi na yin kara, cirota yayi yaduba nan yayi dariya ya daga,


"Allah yabar babban yaya, har ka tafi ne?"


Bata jin me ake cewa amma dai taji yace,


"Ehh to shikenan sai kazo"


Saida yakatse wayar sannan yajuya ya kalleta,


"Ya Abba ne wai zai koma school amma zai fara biyowa tanan kugaisa tukunna"


"To babu damuwa Allah yakawoshi lafiya"


Tashi tayi zuwa kitchen tana ware kayan da yakawo wanda zata barsu a kitchen din tabarsu anan wanda zata kai toilet ta kwasa takai sannan kayan tea din kuma takai dining area ta zuba cikin wani glass da aka tanada musammsn domin ajiya,


Saboda taji zaiyi bako shiyasa ta dora girkin da wuri sannan takoma falo ta iskeshi yana kallon spider man atashar mbc max, tana zama sukaji knocking, shine yaje yabude, khulsum ce kawarta bata hanya yayi yana cewa,


"Barka da zuwa hajiya khulsum"


"Yawwa haji fahad, ya kwanan amarya?"


Saida suka shigo cikin falon sannan ya amsa da,


"Gata nan muna bata hakuri, bai zauna ba yawuce bedroom yabar musu falon"


Kallon khulsum bilkisu tayi,


"Kekuma sai yanzu kika gadamar zuwa?"


"Kai labour yanzun bakiyi maraba da ganina ba?"


"Oho miki, ya gajiyarki?"


"Ahh gajiya ai tana tare dake hajiya, ni ai tajima da bin lafiyar jikina"


"Nima haka..."


"Gaskiyane amarsu, me kike tafasawa ne haka?"


"Wallahi girki ma na dora gashi can wai zanyi jalop din shinkafa..."


"To muje mana mu karasa, ah tashi muje"


Tare suka shiga kitchen din khulsum ta tayata suka hada komai, kayan marmarin da yakawo jiya sukayi blending dinshi suka hada banana milk shake suka saka a fridge basu kai ga sauke abincin ba Abba yazo fahad yafita yashigo dashi, kamarsu daya da fahad kuma kusan kansu ma daya dayake shima fahad din dogo ne, a falon suma suka zauna amma bilkisu tun kafin su shigo tasako hijab dinta har kasa wanda hakan ba karamin dadi yayiwa fahad ba. A mutunce suka gaisa sai lokacin takara raina girman fahad saboda koshi abban tagirmeshi kai dakyar ma idan maama kanwarta bazata fishi ba, mikewa Abba yayi zai tafi saboda yana son ya isa Maiduguri da wuri amma suka hanashi tafiya wai sai yatsaya yaci girkin amarya, dan dole yatsaya su bilkisu sukaje suka shirya table sannan tazo tace musu,


"Bismillah..."


"To godiya nake amarya" inji ya Abba,


"Ah babu komai..." Tafada tana murmushi,


"Ni gaskiya...ni gaskiya ban ganeba, ni meyasa ba agataleni" fahad yafada yana bata fuska kamar zaiyi kuka,


"Kai ai yanzu kagirma" Abba yafada cikin sigar tsokana,


"Allah ban yarda ba"


Daga bilkisu har Abba dariya sukayi ita dai tafiya tayi tabarsu saboda taga dramar tasu ba mai karewa bace kuma da alama sun saba, cikin bedroom suka shige itada khulsum suka basu waje suma suka kai nasu can, suna cin abincin khulsum na sake yimata tsiya har suka gama daidai lokacin shima fahad ya leko yace sun gama Abba zai tafi, hijab tasaka tafita sukayi sallama takoma wurin khulsum, shima fahad ta can yawuce bayan yaraka Abba, majalissar shayinsu yatafi wacce suke zama idan sun taso daga shago amma shi bawani ma cika zama yayiba sosai domin daga shago sai filin ball. Acan gidan amarya kuwa bayan fahad sun fita tareda abba babu jimawa su yaya asabe suka zo itada Anty Fauziyya fuska asake bilkisu ta karbesu takawo musu abinci da lemon da suka hada kuma babu laifi ta saki jiki da su kamar yadda suma suka sake da ita, suna nan tare sunata kallo suna hira har maman hudah tazo wato maama takawowa bilkisu kayan tarbar baki wanda yahadar da cincin, cake, alkaki sai nakiya da dubulan an dan samu tsaiko ne matar da aka bawa tayi bata gamaba sai jiya da daddare ta aiko dashi amma da tuni anjima da kawo mata,


"Ina daughter dina naganki ke daya??"


Dariya maama tayi ta zauna kan kujera suna gaisawa da su Anty Fauzy,


"Daughter ki yau tana wurin kakarta can nabarta,ya fahad baya nanne?"


"Ehh yafita" bilkisu tabata amsa tana harararta kasa masa saboda haushi suke bata idan taji sunce mishi yayan nan wallahi, ganin tasake samun yar tayin hira su anty fauzy suka yimata sallama suka tafi, ledoji ta cika musu da kayan zakin da maama takawo mata ta rakasu har kofar gida anan suke sanar da itama gidajensu zasu wuce basai sun koma gidan ayiyah ba saboda dama sun rigada sunyi sallama, wurinsu khulsum takoma bayan taga tafiyarsu nan hira ta barke bare yanzu sai su kadai har magrib suna gidan ta hanasu tafiya tace sai fahad yadawo. Bayan sallar magrib kuwa babu jimawa sai gashi yadawo yana rikeda CD flate din bikinsu da yakarbo, maama yaya sama yaya kasa ta ringa kiranshi dashi dama suna shiri sosai musamman ma dayake tana kamada bilkisu fari kawai tafi bilkisu duk dinsu ma sun fita haske saboda ammah suka biyo ita kadaici ta dauko kalar abba tayi baki amma bakin shima bawani can dayawa ba sai dai baza asata alayin farare ba, ganin yadawo suka yimusu sallama suka fita ai harda fahad arakasu kofar gida bayan sunga tafiyarsu suka koma ciki lokacin babu wuta saida fitilar wayarshi yayi amfani ya haska musu suka shiga ciki, tana shiga taga wayarta dake kan kujera tana kara tana dauka taga su elmustspha ne,kamar yadda tazata saida tagaji da surutunsu dakyar sukayi sallama ta kashe wayar tana kallon fahad wanda ke jiranta ta kammala wayar,


"Yadai?"


"Akwai abinci ne?"


"Da akwai guntu, kacinye ma kawai"


"To kekuma fa?"


"Karka damu zansha tea ya isheni"


"Shikenan..."


Dining yanufa ita kuma ta kishingida jikin kujerar tana dora rayuwar duniya a ma'auni na zahiri ba badini ba. Har ya gama cin abincin yadawo cikin falon bata bar tunani ba saida yazauna ya murza yatsunshi guda biyu asaitin fuskarta sannan ta dawo hayyacinta ta kalleshi,


"Ranki yadade lafiya kuwa?"


Ajiyar zuciya ta sauke,


"Lafiya lau kawai dai nagajine wallahi"


"To kije kici abinci mana ki kwanta ki huta"


"Gaskiya kam haka yakamata inyi bari natashi"


Tea taje ta hada tadawo falon ta zauna tasha zafi kuwa yace muje zuwa daki tashiga domin wanka zatayi ta kwanta tana cire kaya yadanno kai bayan yaturo kofa, tukwicin harara yasamu shiyasa cikin azama yafada toilet yayi alwala yafito bai yadda ya kalli wurin da takeba yafice daga dakin bayan yadauki abin salla,


"Haka kawai wai mutum da halal dinshi amma ayita nuna masa fin karfi da iko..." Haka yaketa fada cikin kunkuni lokacin da yafita falo, abin sallar ya shimfida yatada kabbarar sallar ishah. Dan neman fada bai shiga dakinba saida ya daidaici ta kwanta domin yaga yadaina ganin haske sai duhu alamun takashe fitilar data kunna, tashi yayi ya dauki abin sallarshi yanufi cikin dakin yasan bata son haske gashi tun yana salla aka dawo da wuta amma ita bata saniba,yana shiga ya lalubi makunna ya kunna nan wani fitinannen haske ya gauraye dakin, dan karamin tsaki taja tayi saurin rufe jikinta,


"Wai dan Allah menene haka? Shigo min dakin da kayi cikin wannan lokacin bai isheka ba har sai ka kunna min haske..."


"Yi hakuri dama nazaci ko baki san andawo da nepa bane..."


"To da aka dawo da ita me zanyi mata? Ko nace maka ina bukatane?"


"Ni na san abinda zakiyi da itane madam.... Nidai kawai na fada mikine"


Banza tayi masa ta juya baya tayi kwanciyarta,


"Malam idan kagama nidai ka rage min hasken nan ya takura min..."


"Nima ai kin takura min..." Yafada cikin kunkuni, bata bi takanshi ba ta mayar da idonta tarufe, saida yagama jula jularshi sannan yakashe yashiga wanka, acan yashirya yafito yana ta kukkumbura baki kamar tana ganinshi, acikin duhun ya kwashi kayan shimfidarshi yayi falo yaje ya shimfida a position din jiya sannan yakoma ya dauki pillow irin daukar nan na ehh ina cikin fushi dan kawai fincikar shi yayi yai gaba,


"Ahh malam menene haka? Karka yaga min pillow mana..."


Yaji tace yana daf da isa bakin kofa,


"Sai anyaga din"  sai dai shi tashi maganar yadda bazata jiyoba yayi, bude kofa yayi yafita yaje ya kwanta,


"Haka kawai dan kinga kin fini shine zakiyita takura min.... Allah sai nima na rama wata rana tom"


Shi kadai yake maganarshi har yagaji yahakura yayi shiru, yauma kamar jiya raba dare yayi yana chaten daga bisani yasauka yayi addu'ar bacci.....



*Book dinnan na saidawa ne yar uwa idan kinada bukata ki siya saiki karanta.*




*_Ummi Shatu_*    


©  *HASKE WRITERS ASSO.*



*KAMAR DA WASA....!*    



   *_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*




    *21*




      ***Yau anyi sa'a bai tashi da daddare ba saida asubah lokacin har anshiga masallaci, alwala yashiga yayi yafito anan cikin bedroom din yayi salla sai bayan da ya idar sannan yakoma makwancinsa yasake dora wani sabon baccin dan har bilkisu tatashi tayi wanka tashirya yana bacci saida ta shiga kitchen sannan yatashi, da kanshi ya nade shimfidar da ya kwana yashigar cikin dakin ya ajiye komai a muhallinsa sannan yashiga wanka ganin shi kadai ne adakin yasashi fitowa daga shi sai dan karamin wandonshi iya cinya dan baima kai rabin cinyar ba, lokacin ita kuma tana kitchen tana girki sai ta tuna jiya maama tace mata da dasu Hindu zasuzo amma sunce zasu mata yau ita kuma ta manto almiskinta da wani turarenta Arabian night a handbag din meenah wannan dalilin ne yasata cewar bari ta dauko wayarta takira meenah ta tuna mata kar akuma manto mata su yau ma. Tana fitowa falo taga baya nan alamar yatashi kenan, bedroom din tashiga itama kanta tsaye, tana shiga yana fitowa cikin sauri yayi baya zai koma bathroom din ita kuma fita tayi daga dakin takoma falo ta tsaya ita bata wuce kitchen dinba haka kuma bata koma dakin ba saida ta daidaici yagama kintsawa sannan ta bude ta shiga, yana gaban mirror yana taje sumarshi da cumb yasa bakin jeans da bakar t shirt mai gajeren hannu, ta cikin mirror din suka hada ido yaturo baki yana kallonta,


"Gaskiya daga yanzu idan zaki shigo kema ki rinka taking excuse.... Haka kawai kinzo kin wani kalleni"


Ita maganar tashi ma dariya tabata, wucewa tayi ta dauki duka phones dinta saida tazo saitinshi sannan ta tsaya,


"Kai excuse din kake nema kafin kashigo min daki? Kafara tukunna sai nima infara"


Tura mata baki yayi yana shagwabe fuska,


Ta cikin mudubin yake binta da kallo tana jujjuya masa baya lokacin data doshi kofa domin fita kasancewar dinkin jikinta riga da skirt ne wanda ya dinka mata lokacin bikin kannenta, karasa fesa turarenshi yayi ya ajiye gaban mirror dinta sannan yafita, afalo ya tarar da ita tana yin waya da meenah tana tuna mata sakonta dake cikin jakarta domin tana sa ran gobe zata fara salla, zama yayi yana jiran tagama, kitchen tawuce taje ta kwashe dankalin da take soyawa ta soya kwai sannan ta debo zuwa kan dining, bai jira anyi masa tayiba yataso yazo ya zauna,


"Sannu da aiki, ina kwana?"


"Yawwa katashi lafiya"


Ta amsa masa tana zuba nata dankalin acikin flate tana gamawa ta tura masa sauran gabanshi,


"Lafiya lau hajjaju.." Yafada yana lankwasa yan yatsunshi suna yin kas kas,


"Wai kai meyasa baka iya ninke kayaba idan kacire? Sai kawai ka rinka watsa min su cikin drewar any how?"


Dakatawa yayi da hada tea din da yakeyi ya kalleta yana shafa sumarshi,


"Ranki yadade wai dan Allah meyasa banida wahalar laifi ne awurinki....? Allah yabaki hakuri zan gyara"


"Ba maganar bakada wahalar laifi bane, ai gaskiya ce"


"To shikenan dai tunda ai nabaki hakuri"


Daga shi har ita babu wanda yasake magana cin abincinsu kawai suka sa agaba, itace tafara tashi nan yabita da kallo dama tun dazu jikinta yake bata irin kallon kurullar da yake yimata sannan tasha kamashi yana satar kallon kirjinta lokacin da suna cin abinci shiyasa tawuce bedroom tasako hijab har gwiwa tazo taci gaba da hidimominta, baki yatabe yatashi bayan yagama da komai na wurin,


"In kinyi hakuri ma ni gidan zan fice inbar miki yanzun nan..."


Yafada acikin zuciyarshi, tana tsaye tana shara da standing broom duk da falon babu wani datti, kusa da ita yazo yatsaya,


"Ranki yadade ni zan fita neman kudi, dinkuna ne kecan suna jirana sunfi kala ashirin gara naje na dan rage..."


"Allah yabada sa'a, amma cefane fa wazan bawa ya siyo min?"


"Bari idan naje shago zan aiko yaro ya kawo miki"


"Shikenan"


Fita yayi yaji shiru batace komai ba sai yakara dawowa,


"Yadai?"


"Uhmm ai banji kinyi min addu'a bane"


"Adawo lafiya, Allah yabada sa,a"


"Amin hajjaju, wallahi har naji dadi, i luv u irin wujiga wujiga dinnan"


Ita dariya ma yabata kawai ta girgiza kai taci gaba da shararta, saida tagama komai nata sannan tayi baki wasu mata guda biyu wadanda makotanta ne amma da dan tazara tsakaninsu sai dai duk kana iya hango gidajensu daga kofar gidanta, sosai ta karbesu da fara'a da kuma sakin fuska da zasu tafi ta dibar musu kayan zaki cikin leda tarakasu kofar gida sannan tadawo ta zauna tama rasa me zatayi gashi laptop dinta na wurinsu meenah duk yau zasu kawo mata da tana nan da ta dan rage zaman nan haka dan dole dai sai kallo ta kunna. 


Fahad gidansu yafara zuwa ya iske su maryam nata shiri wai gidansa zasu tafi bai hanasu ba dan yaga jininsu yahadu da na bilkisu, bayan sun gaggaisa dasu ayiyah yatafi shago ai yana shiga aka fara tsokanarsa,


"Ga ango ga ango"


Dariya yayi yarinka binsu daya bayan daya suna gaisawa, kayan da ya yanyanka yaciro zai fara hadawa,


Bai jima da zuwaba saiga husnah jikinta ma farin uniform ne da alama daga lecture tafito ashe ko jiyama saida tazo dubashi taga bai fito ba,


Zama tayi agabanshi ta kura masa ido lokacin da yake dinki wani kyau na musamman taga yayi shiyasa kishi ya turnuketa nan da nan,


"Husnah ya makaranta...?"


Badan tasoba tasaki ranta gudun karya gane amma shi tuni yakaranci yanayin da take ciki domin dama yasan bakin kishinta akansa,cikeda son yasake kular da ita yace,


"Baki tambayi matata ba"


Tabe baki tayi ta dauke kai, yana kokarin juya rigar da yake dinkawa tarike rigar tana kallonshi,


"Prince katsaya mana mugama hirar sai ka cigaba da dinkin"


"To husnah ai yanzu ma hirar mukeyi"


Turo baki tafara yi daga karshe ma dai tashi tayi tafice daga shagon ita adole tayi fushi, habibu kanin hamza dake koyon dinki ashagon ya aika yabashi kudin cefane yace yayi yakai masa gidanshi ai kuwa nan su hamza suka cigaba da tsokanarshi. Acan bangaren bilkisu kuwa yau bata da matsalar kadaici domin bayan su mariya sunzo babu dadewa su Hindu suma sukazo kuma yinar mata zasuyi cur, lokacin da aka kawo cefanen da fahad ya aiko ma meenah ce takarba ta dora musu girki, yau yanayin da bilkisu take jinta na farin ciki yafi gaban kwatantawa danma maama bata nan da abin sai yafi haka, ayanda ta fahimta daga meenah har Hindu duk ciki garesu nan dadi yasake kamata domin tana bala'in son kannen nan nata kamar yadda suma ke sonta, dama tabawa meenah tace ta dafa duk abinda takeso nan meenah tace shinkafa da miya zatayi ai kuwa Hindu tace bazai yuyuba taliya da miya za adafa saboda ita tunda tasamu ciki ta daina cin shinkafa ita kuma meenah tace itama bata cin taliya yanzu sai shinkafa kadai, dariya abin yabawa bilkisu tace to duk su kwantar da hankalinsu sai adafa shinkafa da taliya kowanne daban mai son shinkafa yaci mai son taliya shima yaci ita kam gaba daya zataci shinkafar da taliyar dahaka dai tasamu nasarar raba wannan fadan. Sai la'asar fahad yadawo gidan domin yana son zuwa filin ball, yana zuwa su mariya na shirin tafiya yadauko dari biyu zai basu su hau napep bilkisu ta hana tashiga bedroom dinta ta dauko dari hudu tabasu tace kowa yadauki dari bibbiyu sannan ga naira dari su biya napep din, yana shiga falo yaga su meenah,


"Ya fahad sannu da zuwa..."


Shifa idan suna cewa yayan nan jin kansa yakeyi asama yana huruwa,


"Gaskiya munyi fushi sai yau zaku zo mana, maman hudah tun jiya tazo"


Dariya Hindu tayi,


"Ayi mana afuwa ya fahad insha Allah sai kunma gaji da ganinmu agidan nan"


"A'a bazamu gaji dakuba, koda kuwa zaku zo kullum"


Ahaka bilkisu tashigo ta samesu abincinsa ta dauka ta kai masa daki tafito tana cemasa,


"Ga abincin ka can kashiga kaci"


"Nagode hajjaju"


Tashi yayi yawuce ciki, shinkafa da taliya da salad yagani, dama yunwa yake ji shiyasa babu bata lokaci yazuba yafara ci saida yakoshi sannan yashiga wanka agurguje domin yaga kamar yakusa makara, kayan ball dinsa yasaka dark blue yadauki combos dinshi a hannu yafita, sallama sukayi dasu Hindu dan yasan dakyar idan zai dawo yasamesu, sai bayan da yatafi sannan bilkisu ta dauko jakar kudinta tabawa su meenah su kirga mata tanata basu labarin abubuwan da suka kasance lokacin da tana gidansu fahad gaskiya abin ya kayatar dasu bama ita kadaiba dan abinda suka lissafa kudin da aka tara mata dubu talatin da bakwai da dari biyar har dari biyar din da ta baiwa su mariya dazu dubu talatin da takwas kenan, dubu biyar biyar tabasu harda na maama tace itama akai mata.


Daf da lokacin sallar magrib suka tafi ji tayi kamar ta rikesu ta hanasu tafiya amma babu damar hakan domin mijin meenah ne yazo daukarsu zasu bi su ajiye Hindu, ciki takoma tarasa me zatayi saboda babu wani sauran aikin da yarage ma agidan domin su Hindu sunyi mata komai kafin su tafi sai dai dan girkin dare da zata yiwa fahad wannan kuwa indomie ma zata dafa masa, dadinta ma daya da wuta shine tasamu damar fara kallon sabon series din da Bollywood ke nunawa mai suna zahba walam ya'ood, tana tsaka da kallon fahad yadawo, wanka yafara wucewa yayi sannan yazo yayi sallar magrib daga nan bai kuma fitaba sai salim da yayi masa waya wai zaizo yagaida anty amarya kafin ishah kuwa sai gashi shiyasa tare ta dafa musu indomie din da dafaffen kwai,kan dining takai musu lokacin suna kallon ball atashar sport +,daki tawuce da yar guntuwar tata indomie din acikin flate taje ta zauna taci koda tagama ma anan tayi zamanta ta bude laptop dinta tashiga YouTube domin yin kallo, sai wurin 9 sannan salim yatafi, duk da haka bata koma falon ba taci gaba da zamanta adaki daga karshe tayi shirin bacci ta kwanta bata san lokacin da fahad yazo yayi nasa shirinba dan yau bai kunna fitila ba.


Haka suka cigaba da zama idan zai shigo daki wai dole sai yayi knocking tabashi izini shima idan yana ciki idan zata shigo sai tayi knocking yabata izini ahaka har sukayi 2 weeks kuma lokacin ne zata fara fita aiki duk da cewa acikin sati biyun nan rana daidai ce da baza suyi baki ba su ayiyah ma itada mamuh sunzo sunga daki sunyi fatan alkhairi, ranar friday maama tazo dama ranar bilkisu bata fitaba amma shi fahad yana shagonsu yan shagon nasu su tj sun hura masa wutar wai dole sai yau sunje gidanshi sunci girkin amarya, daga karshe dai text massage yayi mata yace,


_Princess dan Allah ki taimaka kiyi girkin mutum biyar wallahi yan shagonmu sun dameni wai sai sunzo.... Pls hajjaju._


Lokacin da taga sakon bata yimasa reply ba amma tafadawa maama abinda yaturo ai kuwa maama tazage ta tayata suka shirya shiryayyen girki duk da cewa unguwar ba asaida abubuwa amma saida bilkisu tafita da kanta ta samo almajiri ta aikeshi can bakin titi yaje ya iyo mata siyayyar duk abinda takeso bayan yakawo mata tace anjima can yazo yakarbi abinci,


Bayan sun gama girkin wanka tashiga tayi tasha doguwar riga ta atamfa ta danyi kwalliya sama sama, tana kitchen tana zuba musu abincin itada maama wacce ke daki tana salla suka shigo, fuskarta asake ta karbesu ta kalli fahad dake wani jin kansa asama shi ga mai gida murmushi tayi,


"Sannu da zuwa, table is ready"


"Thank you sweet heart"


Basu hau dinning dinba domin yayi musu kadan sai anan tsakiyar falon suka baje ba karamin dadi fahad yajiba domin girkine na fita kunya su bilkisu sukayi shi white rice and vegetables stew ga hadadden salad yasha dafaffen kwai abin dai ba acewa komai sannan ga drinks agefe mai dan Karen sanyi kowa saida abin ya burgeshi, tafiya tayi wurin maama tabasu wuri bayan sun gama ya leko cikin dakin suka gaisa da maama yakara gaba bashi yadawo ba sai magriba saboda yau babu zuwa filin ball ita tarasa me yake ji a ball dinnan da kullum sai yaje ranar juma'a ne kawai baya zuwa. Ranar litinin tafara fita aiki sai dai wannan karon karfe uku take tashi sabanin da, zamansu da fahad normal babu wata matsala tayanda take so yake bida ita kullum kuma afalo yake kwana aikin gida kuwa wannan almajirin data samu shine yake yimata shara da mopping idan da aike ta bashi amma fa har yau fahad bai san dashi ba saboda lokacin da almajirin zaizo baya nan wani lokacin kuma kafin yatashi daga bacci dasafe zaizo yayi aikinsa yatafi amma banda falon sai tace wannan yabarshi zatayi yau dai da Allah yayi za ahadu fahad na gidan baije ko inaba dama weekend ne yana da dinkuna ashago amma baya jin zai fita yanzu sai yamma yana kwance afalo daga shi sai three quarter iya gwiwa da riga armless yana kallo sai yaji anbude gida anshigo harda sallama tashi yayi yafita jin muryar namiji yana fita yaga saurayi zaiyishi atsaye hakama ahaife kilama yafishi ahaifen,


"Lafiya? Ya akayi?"


"Ehh nazo aikine.. Nine meyiwa hajiya aiki"


"Aiki? Aikin me?"


"Shara nake yimata da iyo cefane"


"To daga yau karka kara zuwa na sallameka, karka yarda ka kara dawowa"


Saida yaga tafiyar almajirin sannan yarufe gidan yasa sakata yashiga ciki, yau kam babu maganar neman izini kawai yafada mata daki tana kan gado da bra ajikinta da skirt tana kwalliya da alama daga wanka tafito,


"Menene ma'anar wannan abun da kikayi maigado? Ya zaki kawo min almajiri gidana batare da sanina ba..."


Tuni ta dauki hijabinta tasaka tana kallonshi,


"Almajirin ne wani abu? Yaron da na girmeshi"


"Ke kike ganinshi yaro amma ni awurina ba yaro bane, ya zaki dauko wanda ko atsaye yana daidai dani, ai sai akasa banbance dani dashi wanene mai gidan, wannan ma ai tsaf zaiyi min duka"


"To yanzu me kakeso ayi wai?"


"Ai narigada na sallameshi..."


Har yajuya zai tafi tariko rigarshi,


"Da ka koreshi din to yanzu wa zan rinka aika?"


"Ni ki aikeni mana, ai gara ni kisani aikin kuma kiyita aikena da ki kawo min wancan gardin ki ajiye min agida wanda ko adake tsaf zaiyi min duka yanda nake dan kadan dinnan dani..."


Sakinshi tayi yafita yanata yi da bakinshi wanda kusan rabi kishine acikin maganganun nashi. Aranar da yamma suka shirya sukaje gidan Anty Fauziyya suka gaisheta acan sukayi sallar magrib sannan suka dawo gida da zummar gobe ma zasu jewa yaya asabe da su anty kubra. Yau da zaiyi wanka da daddare rasa kayan baccin da zai saka yayi saboda shi baya maimaita kaya idan yasaka guda daya sai anwanke yake sakawa gashi tunda yazo gidan sakawa kawai yake yana tarawa ba awankewa dama ayiyah ce keyi masa wankin inner wears dinshi manyan kayan kuma wanki yake kaiwa to yanzu babu ayiyah, tsayawa yayi agaban drewar din bayan yarike kugunshi da hannunshi guda daya......



*Dan Allah idan har kin san baki siyaba to karki karanta.*




*_Ummi Shatu_*    



© *HASKE WRITERS ASSO.*



*KAMAR DA WASA...!*  



   _*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*




   *22*



     ***Shagwabe fuska yayi ya juya ya kalli bilkisu wacce ke sanye da hijab ajikinta amma aciki sleeping dress ne riga da wando iya gwiwa,hankalinta gaba daya yana kan system din da take dannawa,


"Wai yau wanne kayan zan saka...?"


Dagowa tayi ta kalleshi sannan ta maida kanta kan laptop dinta,


"Da nice nake fada maka wanda zaka saka?"


Shiru yayi mata zuwa can yayi kwafa,


"To wallahi yau karki fito bayan na kwanta dan babu mamaki tsirara zan kwana..."


Tabe baki tayi,


"Kayi duk yadda kaso..."


Jallabiya ya dauka daga cikin kayansa yanufi bathroom yanata kukkumburo baki,


"Wai haka kawai mutum yanada mata amma komai shi zai yiwa kansa..."


"Magana kake yine?"


Yaji tafada yana kokarin shiga toilet din,


"Ni ba dake nake ba"


Tana nan zaune tana aikinta yafito sanye da jallabiya kalar ruwan kasa har lokacin bai daina kumbura ba, kayan shimfidarshi ya diba ya fita zuwa falo bai sake komawa cikin dakin ba sai asubah daga nan bacci yakoma bayan yayi sallar asubah bai tashiba sai karfe 9, wanka yayi yasa three quarter da t shirt ya tattaro kayan baccinshi da kananan kayanshi yakai tsakar gida, duk sai wani cika yake yana batsewa tana ankare dashi, yajima tsaye kan kayan yana kallonsu kafin yaje ya dauko bucket da sabulun wanki yazo gaban fanfo ya debi ruwa yafara wanke kayan yanayi yana yarfe hannu kamar wanda ake yankar naman hannunshi,


"Hajjaju yanzu idan wani yazo ya iskeni ina wanki bazaki ji kunya ba?"


Karasa ajiye kayan wanke wankenta tayi tana kallonshi,


"Au wai kai da nufinka ni zanyi maka wankin?"


Langabe kai yayi yasake bata fuska,


"To ai mata masu neman aljanna har wanki suke yiwa mazajensu"


Dariya ita abun yabata ma amma ta dake ta wucewarta daki, dakyar ya samu ya wanke kayan Amma fa ji yake kamar yayi wani gagarumin aiki gashi ko breakfast baiyi ba, falo yaje ya fada saman doguwar kujera yanata ajjiye numfashi. Saida yahuta sosai sannan yatashi ya yi breakfast lokacin karfe goma da kusan rabi, yana gamawa yasake kwanciya, wurin 12 na rana yakwaso kayan mashi yazauna domin gogesu, yana yi yana jin wakar breaker awayarshi,


"Gaskiya ni ba dan gata bane..., inyi wanki da kaina kuma gugar ma arasa mai taimako na..."


Tana jinsa bata tanka masa ba zuwa can yafara bin wakar,


"Idan zaki kije dani.... Idan nai fushi ki rarrasheni....!"


Nan dinma dai bata tanka ba har yayi yagama, ganin rana tayi express girki tayi musu bayan yaci abincin rana ya tattaro kayan sawarshi masu datti yace itama ta tattaro nata wanki zai kai musu, bayan yatafi itama ta wanke nata inner wears din masu datti, rasa inda zata shanya kayan tayi domin bata son fahad yagani shiyasa ko pant ta wanke boyeshi take inda bazai ganiba wani lokacin ma sai yafita take shanyawa kafin yadawo yabushe ta dauke kayanta amma bata taba wanke bra ba sai yau, babu yanda ta iya dole akan igiyar da ya daura ta baya ta shanya kayan. Kafin yadawo tayi wanka tashirya tana jiran yazo su tafi ziyarar da yace zasuje gidan yaya asabe da su anty kubra domin itama tana son fitar bata son zaman kadaicin nan musamman ma idan baya nan. Bai jima awurin kai wankin ba yadawo,wanka kawai shima yayi yasaka wani yadi mai laushi kalar ruwan toka amma bai saka hulaba yasha turare suka fita, drop din napep suka dauka yakaisu duk inda zasu je dama anty Kubra da anty juwairiyya makota ne domin katangarsu ma daya anty asabe ce dai awata unguwa ta daban, daga karshe gidansu yakaita wurinsu ayiyah ai kuwa ranar taga soyayya domin ayiyah kamar zata goyata dan kauna. Fita yayi yabarta tareda su ayiya yatafi majalissar su ta shan shayi wadda ke kusa da filin kwallonsu dama sunyi waya da salim yasanar dashi yana can.


Acan gida kuwa itama bilkisu tasake da su ayiyah sosai duk aikin da taga zasuyi sai ta karbe tayishi ahaka harsu Mariya suka dawo daga islamiyya suka sameta,Rungumeta sukayi suna tsalle dan tsananin murnar ganinta, itama murnar takeyi domin tana kaunar yaran duk da ba yan biyu bane amma kamarsu daya sannan a shekaru ma tsiran babu yawa, tana nan tareda su sunata bata labarin makarantarsu sai zuba mata surutu suke yi ita kuma tana cin tuwon da mamuh ta zubo mata tuwon biski miyar taushe wacce taji tantakwashi da man shanu ai kuwa taji dadin tuwon nan domin tazage ta ci babu fulako, tana daf da gama cin tuwon fahad yashigo ai su mariya na jin maganarshi atsakar gida kowacce takama bakinta, dariya abin yabawa bilkisu saboda daga jin motsinshi yara har sun daina kwarafniya,


"Meyasa kuka daina yimin hirar ne mariya?"


"Anty ya fahad ya hanamu surutu, duka yake yi sosai yafi ya Abba duka..." Inji Maryam,


"Ga dukanshi zafi..."


Dariya tayi saboda jin abinda mariya tace itama, sake nutsuwa sukayi lokacin da yashigo cikin falon, nan suka fara rige rigen gaisheshi,


"Mariya karbo min abinci awurin ayiyah..."


Tun kafin yarufe bakinshi ta tashi tafita, kallon Maryam yayi ya harareta,


"Ke kuma ina dan kwalinki? Bana hanaku zama babu dan kwali ba?"


Itama tashi tayi dasauri tashige daki domin dauko dan kwalin, sai lokacin ya maida kallonshi kan bilkisu,


"Nikuma akan me za ayi min nawa fadan?"


Dariya yayi ya zauna kusa da ita yana lumshe idanuwa sakamakon kamshinta da ya shaka wato matar nan karshe ce awurin kamshi yarasa wanne turare take shafawa take wannan kamshin shiyasa wani lokacin har kishin fitarta wurin aiki yake saboda baya son wani yaji kamshin nan sai shi kadai,


"Ni na isa hajjaju? Ai ke bakya laifi"


Dan murmushi kawai tayi batace komai ba har maryam ta kawo masa tuwon shima yafara ci ita kuma bilkisu ta dauke kwanikan da tagama ci zata fitar dashi,


"Ke mariya ita zata fitar da kwanikan...?"


Dasauri suka karbeta tana cewa ma subarshi amma suka ki, hannunta taje ta wanke sannan ta dawo tazauna,


"Gaskiya kana takurawa yaran nan"


"Basa jin magana ne..."


"Wallahi bawani rashin ji da sukeyi"


"Bazanyi musu dake ba"


Saida shima yagama cin tuwon sannan suka yiwa su ayiyah sallama suka tafi lokacin har baba yadawo daga kasuwa, yanzun ma kamar dazu a keke napep suka koma gida sun ko yi sa,a akwai wuta dayake side din ana samun wuta sosai, bedroom tawuce shi kuwa afalo yaja birki yacire rigar jikinshi yabar dogon wandonshi da singileti fara yana kallon kwallo, ita kam wanka tayi ta dauki laptop dinta tana kallo daga ita sai towel duk da yanzu tana dan taka tsantsan amma takasa sabawa da zama cikin hijab domin ita agida babu mai shigar mata daki shiyasa take cin karenta babu babbaka dan sai ta kwana da towel ko under wear dama da daddare daga pant har bra babu ruwanta dasu sai idan tana period ne take kwana da pant, bata san kirinkin da yakai fahad baya ba sai ganinshi tayi yafado mata daki dauke da braziers dinta data wanke dazu,


"Ji mana malam, wai meye hakane? Dan Allah karinka knocking before ka shigo"


"Yi hakuri, mantawa nayi"


Tana gyara hijab din datake kokarin sakawa tace,


"Waya saka dauko min shaya?"


Wartar kayan tayi cikeda jin haushi, shi kam yana dariya yawuce drewar domin itace bata saniba amma yafi minti biyar yana kallon braziers din duk saida yayi musu kallon kurulla sannan yakawo mata.


Kayan baccinshi ya dauka yawuce toilet har lokacin harararshi takeyi, sai da taga shigarshi sannan ta tashi taje ta boye kayan acan drewar dinta,dawowa tayi ta zauna taci gaba da aikinta har yafito daga wankan sanye da gajeren wando da riga armless duk farare sol masu santsi, kallonta yatsaya yi yana shafar keya,


"Hajjaju nace yau dinma a falon zan kwana...?"


"A'a akaina zaka kwana..." Tayi masa gatse dama bata gama hucewa daga fushin dauko mata braziers dinta da yayiba, dan tabe baki yayi yai gaba yana kunkuni,


"Da za ayi hakan aini so zanyi..."


Kayan shimfidarshi ya dauka yakara gaba domin yau bacci yake ji, tsabar takaici ko wutar yau bai kashe mata ba yaje yayi kwanciyarsa, itama bata kara bi ta kansa ba saida ta kammala aikinta sannan tafito zataje kitchen lokacin misalin karfe 12 saura nadare, awani baje ta ganshi ya harde hannuwa yadora kafa daya kan daya, murmushi tayi tace aranta,


"Lallai kuwa Prince... Irin wannan zuba mulki haka, baccin ma sai anyi masa sarauta"


Fridge tawuce ta dauko ruwa mai sanyi sannan tadawo takashe masa wutar falon tashige daki abinta. Da safe tanata kici kicin hada abin karyawa saboda tana so tafita office dawuri shi kuwa yanata baccinsa saman katifarsa domin tunda sukayi sallar asubah yasake komawa bacci, har tagama hada breakfast tayi wanka bai tashiba, bayan tagama shiryawa ne tazo tana karyawa yatashi, daga kwancen da yake ya daga ido yana kallonta, leshi ne ajikinta c green colour dinkin riga da skirt, batayi wata doguwar kwalliya ba amma fa akwai kamshi kamar anyi barin turare maida idonsa yayi ya lumshe yana turo baki shi bawai aikin da take fitane damuwarsa ba, damuwarshi shine yanzu duk namijin da ta gifta ta kusa dashi shima dole sai yaji irin wannan kamshin da yake jin tanayi? Kai impossible,


"Allah bazai yuyuba..." Yafada afili tare da tashi zaune,


"Hajjaju har kin shirya ne? Ina kwana?"


Daga kan dining tajuyo ta kalleshi,


"Lafiya lau"


Murmushi yayi domin dama yasan gaisuwar bata wuce haka,


Bathroom yayi sauri yaje yayi brush yadawo ya isketa saman dining din amman takusa kammalawa, kujera yaja ya zauna wacce ke kallon tata,lumshe ido yayi,


"Hajjaju wannan kamshin fa.... Gaskiya...... Hmmm.....gaskiya"


Mikewa tayi tawuce abinta tana cewa,


"Kaga ni malam sauri nake aiki ne dani da sanyin safiyar nan"


"Adawo lafiya, Allah yatsare min ke hajjaju na"


Murmushi kadai tayi tawuce daki ta nado laffaya dinta bayan ta saka safar kafa baka ta dauko komai da take bukata tazo tawuceshi tafita, duk sai yaji gidan kuma babu dadi da baiyi niyyar fitaba amma dole tasa yayi wanka yazo yashirya ganin bata nan da komanta yayi amfani har turare nata yafesa, tsayawa yayi yana kallon turaren,


"Arabian night...uhmm su hajjaju manya"


Duka saida yashafa daga body spray din har performed spray sannan yadauko kayansa yasaka yafita shago. Wurin karfe biyu saura yana shago yagama yiwa wasu yan mata dinki husna na zaune gaban kekenshi sai ga kiran bilkisu yashigo wayarshi, zuba masa ido husna tayi lokacin da yadauki wayar,


"Ranki yadade ya akayi?"


"Kaga dama cewa nayi zan biya ta gidanmu da daddare sai na taho"


"A'a hajjaju ki bari ranar juma'a ko cikin weekend sai kije"


"Shikenan..."


"Adawo lafiya"


Katse wayar tayi tana kwafa wato danma yasamu ta tambayeshi shine harda wani hanawa, bata je dinba ta koma gida ta dan huta sannan ta tada shirin dafa alala domin yau shi take kwadayi, shi kuwa fahad ba karamin fasuwa kansa yayiba bilkisu ta kirashi tana neman izini yanzu sake jin kansa yake yi amatsayin boss, bai lura da fushin da husna keyiba tunda ta fahimci matarsa ce ta kira. La'asar sakaliya yakoma gida bilkisu na falo tana bacci dan kwanciya tayi kuma bacci yayi gaba da ita riga ce ajikinta body hug da yar skirt marar nauyi amma tasa karamin hijab, bai tasheta ba yawuce yazubo abinci alala yagani yasha kwai da vegetables sai kamshi yake guda hudu yazubo yazauna yatashi dasu sannan yashiga wanka agurguje yafito yasa kayan ball dinsa lokacin bilkisu tatashi karar wayarta ne yatadata meenah ce ta kirata,


Kallonsa tayi daga sama har kasa,


"Kai da islamiyya ma kashiga wallahi tafi maka wannan zuwa filin kwallon"


Murmushi yayi yazauna yana saka safa da combos dinshi,


"Hajjaju kenan, tunda kince inshiga to zan shiga din"


Bata kara cewa komai ba shima haka har yagama yatashi yafita. 


Haka zaman nasu yaci gaba da kasancewa,watansu daya da aure taje gida tawuni cur har dare lokacin ana sa ran ganin watan Ramadan nanda kwanaki uku zuwa hudu ammah kuwa mahaifiyarta har yau bata taka taje gidan ba, duk wata siyayya da suke bukata fahad ya kokarta ya iyota dama ba wasu kaya masu yawa bane domin sunada kayan abinci enough kawai dai sai dan abinda ba arasa ba, ranar da aka tashi da azumi ranar bilkisu tatashi da period asanyaye take komai sakamakon ciwon da mararta ke danyi mata kadan, ruwan zafi ta dafa tasha lipton ko zataji dan dama dama shi dai gogan yana kwance abinsa yanata bacci shiyasa bata yarda ta dafa komai ba tabari har saida yatashi yayi wanka yafita duk yayi wani kalar tausayi kamar yauce ranar farko da yafara azumin, saida ta tabbatar yafita sannan tatashi ta dora indomie, ta juye indomie din tana soya kwai sai gashi yadawo yamanta key din drewar shagonsu wadda suke ajiye kayan mutane aciki idan ankawo musu dinki,


Jin kamshi ya cika gidan yasashi binta kitchen din bayan ya dauki key din,


"Ranki yadade ke bakya azuminne ko kema yar ganin watance?"


Banza tayi dashi taci gaba da abinda takeyi amma harga Allah bataso yasan bata azumi ba,


"Ko dai.....!"


Juyowa tayi ta antaya masa harara hakan tasa yayi shiru,


"Allah yabaki hakuri mantawa nayi ashe suhur zakiyi, ayi suhur lafiya"


Bai jira tajiyo ba yagudu yabar gidan yana dariya, shi dai yasha jin malamai suna cewa mata masu al'ada basa azumi wato itama hajjaju yau hakan take kenan, tunda yabar gidan bai dawoba sai da aka kusa shan ruwa, a kitchen ya jiyota tana aiki shikam yau duk yayi laushi ga uban dinkunan da ya yanyanka shiyasa can ma yabarosu sai bayan ansha ruwa zai koma yafara hadawa. Yajima akwance ga kayan da yazo dasu amma yakasa tashi yakai mata ita kuma bata san yadawo ba, saida ta dora kosai kafin man yayi zafi tafito daukar wayarta zata kirashi tace yataho mata da mayonnaise taganshi kwance, yau kam an zuba rana ga zafi shiyasa azumin ke wahalar da mutane, kamar zatayi dariya amma ta danne ta wuce tana yimasa sannu, bayan tadawo ta dauki ledar da yashigo da ita tawuce kitchen wanda fruits ne  aciki yasiyo, dakyar ya iya tashi yayi wanka lokacin yaji karfin jikinsa, yana gaban mirror zaune yaji wayarshi na kara, ganin salim ne yasashi dauka bayan yayi tagumin dole,


"Abokina gani nan zanzo asha ruwa dani fa..."


"Sai kazo to"


Daga haka yakatse wayar duk atunaninshi da wasa salim yake bayan yagama shiryawa yasa three quarter da t shirt yafito falo yasake kwanciya babu jimawa yaji ana knocking akasalance yaje yabude salim din kuwa yagani dagaske, cikin murmushi ya mika masa hannu sukayi musabaha yashigo dashi har falo,bedroom yashiga yadauko hijab din bilkisu yabita kitchen, ya dora mata saman kafadarta, juyowa tayi ta kalleshi yau baya magana saboda azumi na dukanshi,


"Salim ne yazo"  abinda ya iya fada kenan yajuya yafita, saida tagama komai sannan aka kira salla, fruit salad ne bata jima da gamawa ba lokacin kayan ta tattaro gaba daya ta kawo musu falo har lokacin gogan akwance yake yakasa tashi shiyasa salim ya kalleta yana dariya bayan sun gaisa yace,


"Hajjaju wannan fa yau sai kinzo kin dagashi dan yakasa tashi"


Dariya tayi takoma kitchen takawo sauran kayan ta ajiye musu sannan ta kalli fahad wanda ke kwance rub da ciki,


"Tashi kasha ruwan mana...."


Hannu yamika mata saboda ganin idon salim bata kiba takama nashi yatashi zaune azuciyarsa yana cewa,


"Wannan badan ansha ruwaba ai sunan azumina karyayye irin wannan laushi haka"


Kunu ta zuba masa ta mika masa sannan tace,


"Karka sha abu mai sanyi yanzu sai an dan jima, kafara shan mai zafi tukunna"


Kai yadaga mata shi dai salim tuni yahada tea dinsa yana sha da kosai, juyawa tayi tawuce daki tabasu wuri tana zuwa tashiga wanka. Su fahad kuwa bayan ciki ya dan dauka fanfon waje sukaje sukayi alwala sannan sukazo sukayi salla bayan sun idar suka dora da ciye ciyensu sai lokacin bakin fahad yabude sunata hira da salim, bilkisu na fitowa sanye da hijab har kasa tanata zuba kamshi fahad ya kalleta ya dage girarshi guda daya cikeda tsokana yace,


"Hajjaju sannu da shan ruwa, ansha ruwa lafiya?"


Ita dashi sun san meyake nufi amma shi salim bai saniba shiyasa shima yayi mata sannu da shan ruwan, iya na salim din kawai ta amsa tawuce kitchen tazubo dankali da kosai tafito,


"Ranki yadade sannu da shan ruwa fa naketa yimiki amma kin shareni laifin me nayi?"


"Yawwa sannu"


Murmushi yayi ya saci kallonta ta zabga masa harara, tana jinsu sai surutu sukeyi kasancewar sun koshi, suna gamawa suka mike zasu fita, kaya fahad yaje yasauya sannan suka fice yana sake tsokanarta,


"Hajjaju yau mun kai daya ko?"


"Goma aka kai" Tafada cikin gatse,


Dariya yayi yaja hannun salim suka fita, itama wurinda suka ci abincin ta zauna ta kintsa sannan ta kwashe kayan takai kitchen tawuce daki,takardar hutunta take son turawa ta mail domin daga gobe ko jibi take son farawa.....



*Dan Allah idan har baki biya kudin littafin nanba karki karanta hakkin wasu domin na siyarwa ne.*




*_Ummi Shatu_*    


© *HASKE WRITERS ASSO*



*KAMAR DA WASA....!*  



  *_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*




      *23*




     ***Bai samu yadawo gidanba sai wurin karfe 10 bilkisu duk tsoro ya isheta domin bata taba zama agidan ita kadai da daddare ba,tana daki tarufe da key yashigo kwankwasa mata kofa yayi dakyar ta tashi ta bude dan tsoro tana ganin shine ta harareshi,cikin alamun atsorace take tafurta,


"Ina kaje kakai dare haka?" 


"Ranki yadade daga shago nake wallahi, bayan mun fita daga nan salla mukaje mukayi daga can kuma shine naje gida nayiwa su ayiyah barka da shan ruwa shine nawuce shago"


Bashi hanya tayi yawuce ciki tana cewa


"To gaskiya kar ka kara kaiwa haka awaje"


"To ranki yadade"


Falo yasake fitowa yawuce kitchen yazubo abinci yaci sannan yayi shirin bacci, da asuba itace ta tasheshi ya tashi yayi suhur, kallonta yayi tana kwance kan gado tana shirin yin wani baccin bayan yayi brush yafito,


"Nima anya gobe zanyi azumin nan kuwa? To naga wadanda suka fini ma basayi"


Tana jinsa tayi biris dashi daga karshe yafice yaje yayi suhur din saida yayi sallar asubah sannan ya kwanta. Washe gari tafara hutunta kamar yadda ta nema, kullum tare suke shan ruwa da salim ranar da akayi azumi na biyar sukaje gidansu fahad suka yimusu sannu da shan ruwa bayan Bilkisu ta siya musu kayan tea, shi kuwa fahad kayan marmari yasiya musu suka kai musu washe gari kuma suka je gidansu Bilkisu can dinma kayan marmarin fahad yasiya cikin manyan ledoji suka kai ita surukuntar fahad da ammah dariya take bata domin basa sakewa da juna, har karfe 9 nadare suna gidan wurin goma suka dawo gida. Bilkisu sai da tasha azumi bakwai ana takwas ta dauka danma ranar ansamu ni'ima agari dan har ruwa aka sheka shiyasa bata wani jishi ba sosai, bayan ansha ruwa fahad ya fara halin nasa na tsokana, har bedroom yabita yabar salim afalo,


"Hajjaju yau wasu takwas suka kaifa wasu kuma bakwai wasu shida ke kuma first ramadan yau"


Harararshi tayi ta gyara zamanta,


"Kafita daga idona..."


Ficewa yayi daga dakin gaba daya yana dariya, akwana atashi haka azumin yafara tafiya domin har anfara lissafin salla, duk kannenta babu wadda batazo ba ita da mijinta sunyi mata barka da shan ruwa ba, azumi yaraba tsakiya abba ya aiko musu da kaya kaca kaca kayan tea ne, kayan abinci da sauransu ba ita kadaiba harsu mamaa kowa ya aika masa dashi. Tunda salla ta taho fahad yazama busy domin aiki yayi musu yawa dama duk karshen azumi ashago suke kwana su kwana suna aiki amma wannan karon saboda bilkisu yahakura sai dai yataho da kayan gida yayita yankawa da safe idan yafita sai ya dinka, ana saura kwana biyar salla yake tambayarta wai ita bazata yi dinkin salla ba ehh tace masa kawai, har ana igobe salla bai samu kansa ba cefane ma sai yaro yatura yace yaje tafada masa duk abinda take bukata sai yazo yabashi kudin yaje yasiyo yakai mata, zamansa agidan yanzu kalilan ne, dawowarta daga kunshi kenan itada khulsum dan aiken yazo list tayi tabashi na abubuwan da take bukata domin shinkafa ma ita zata dafa ranar sallar ba tuwoba. Fahad bai dawo gidanba sai 11 nadare domin acanma yasha ruwa yau, ido biyu yasamu bilkisu batayi bacciba domin itama duk vegetables din da zata bukata ta zauna ta gyara gamawarta kenan yashigo amutukar gajiye,atamfa yar ubansu ya dinko mata dark pink mai zanen agogo ajiki, karba tayi tana kallon dinkin da yayi mata riga da skirt fitted, daga atamfar har dinkin sunyi mata kyau,


"Thank you..." Tafada cikin nuna alamun jin dadi, bai amsaba ya kalleta,


"Duk wannan kwalliyar ni aka yiwa?"


Yafada cikeda tsokana,


"Kai kasani..."


Dariya yayi yawuce bathroom domin watsa ruwa. Bayan yafito ya dauki shirgin shimfidarsa yafita,


"Ni wai ko tausayina ma ba ayi kullum akoroni falo hmmm"


 Washe gari akayi salla, tun da aka sauko taketa samun baki,fahad ya hade cikin dark blue din shadda harda hula yayi kyau sosai, saida yaci abincin sallar da tayi sannan yafita, su mariyane sukayi mata rabon abinci, aranar da yamma sukaje gidansu fahad din ita dashi barka da salla da gidan yayyenshi washe gari kuma sukaje gidansu Bilkisu, bayan salla da kwana biyu kuma suka tafi garko gaida hajiya iyallo.


Bayan salla da kwana biyar saiga fahad da sabon roba roba dama tun safe taga yafice ranar bai zauna yayi baccin safen nanba,tana tsakar gida tana karatun littafin hausa yashigo gidan da babur din,dakatawa tayi da abinda takeyi ta tsaya tana kallonsa daga shi sai three quarter da bakar t shirt,sam bata san cewar ahaka yafita ba sai yanzu,


"Wannan roba robar fa...?"


"Ranki yadade nawane,dan kudina da na samu da sallar nan ne duk na tattare naje nasiyo machine dinnan"


"Allah yasanya alkhairi, kuma shine kafita har wata uwar duniya ahaka?"


Kallon jikinsa yayi bayan yakafe Babur din,


"Meya faru da bazan fita ahaka ba?"


Girgiza kai tayi taci gaba da abinda takeyi,


"Yadai kamata idan angirma asan angirma..."


Murmushi yayi yana shafa sumar kanshi,


"Hakane, bari nayi wanka naje nayi aski sumata tafara yawa..."


Bata tanka masaba yawuce ciki, saida tagama abinda takeyi sannan tatashi tana kallon babur din nashi, farine tass sabo fill sai kyalli yake yi abayan machine din wurin daura lamba andaura wani kyakkyawan abu mai kamada madubi wanda ajiki aka rubuta _prince_ adan karkace, girgiza kai tayi azuciyarta tana cewa,


"Wannan yaron kana fama da kuruciya.."


Falo tashiga baya ciki da alama yashiga wankan da yace zaiyi, bedroom tawuce domin ajiye nail cutter din da tagama amfani da ita, maganarshi tajiyo daga cikin bathroom,


"Hajjaju dan Allah kifita zan fito.... Wallahi babu kaya ajikina"


"Ni nasa kashiga wankan ahaka?"


Bakin kofar ya matso sosai,


"Gaskiya kifita, kemafa boye min kikeyi ba dole nima inboye jikina ba"


Bata kara bi takansa ba ta ficewarta dama ba zama tazo yiba saida ya tabbatar tafita sannan yafito daga shi sai towel, agurguje yashirya wai dan kar tashigo ta sameshi ahaka, kananan kaya yasaka sannan yafita falo, abincin shi da yafita baici ba ya dauko yaci sannan yafice, su ayiyah yaje yakaiwa Babur din suka gani da sauran yan uwa dake kusa ranar ko filin ball baijeba dan bashi yadawo gidanba sai bayan sallar ishah kasancewar babu wuta agari yasa bilkisu bata samu zarafin ganin askin kanshi ba da yayi, yana dining yana cin tuwon da tayi na semo miyar busasshiyar kubewa wacce taji busasshen kifi tashiga daki abinta tayi shirin bacci. Kudurtawa yayi aransa cewa nan bada jimawa ba zai kawo canji awannan zaman nasu, gaskiya yazama dole suyi rayuwa irin wacce kowanne miji da matarsa keyi, kamar kullum shimfidarsa yayi afalo ya kwanta bacci, washe gari tatashi da farin ciki domin su maama sunce mata zasu zo su wunar mata duk da itama ayau bata tashi da wuriba makara tayi, saida tafara yin wanka sannan ta fito domin shiga kitchen, yana kwance saman doguwar kujera husnah nata damunshi da kira ganin tayi masa miss called har guda uku yasashi dagawa a na hudun hakan yayi daidai da fitowar bilkisu bata ko kalleshi ba tawuce kitchen abinta, saida yagama wayar da yakeyi sannan yashiga wanka batare da ya debe shimfidarshi ba, yana gaban mirror yana taje sumarshi bilkisu tashigo binshi tayi da kallo musamman ma sumar kanshi domin wani irin aski ne akayi masa duk an saisaye gefe da gefe amma tsakiyar ba ako taba ba,


"Hajjaju na ina kwana?"


Saida tasake kallon kanshi sannan ta amsa da,


"Lafiya lau, yanzu dama wannan shine askin da kake cewa zakayi? Gaskiya yakamata kasan kagirma wallahi"


Wani dan malalacin murmushi yayi ya kalleta ta cikin mirror din yana cigaba da taje kanshi,


"Wai hajjaju sai kiyita cewa nagirma bayan har yanzu ban girmaba tunda babu wani abu da ya canja.... Ina dai saka ran zan girman very soon wallahi kuma no marcy"


"Ni ba dogon bayani na tambayeka ba, waccan shimfidar da ka kwana akai wa kabarwa ya dauke maka?"


"Matata mana..."


Kallonshi tayi sosai sannan tajuya tafita batace dashi komai ba, koda yagama yafito yanata tutturo baki ya harhada kayan ya kwashe yakai ciki sannan yasake fitowa lokacin tagama hada komai na karyawa saida yayi breakfast sannan yamike yana kallonta,


"Ranki yadade mu mun tafi shago zamu karasa dinka kayan da basu samu shiga da salla ba"


"Allah yabada sa'a"


"Amin godiya nake"


 Gidan tagyara bayan fitarsa tana gamawa takoma kitchen tahada wanke wanke tafara bayan tagama tashiga bedroom tana gyarawa taji sallamar su maama nan gida ya rude da farin cikin ganin junansu da sukayi su ukune sukazo har huda ta hudu bajewa sukayi afalo suna shagali.


 A lissafin bilkisu yau zata koma aiki shiyasa tatashi da wuri tayi komai nata na aikin gida sannan tayi shirin fita nan fahad yace zai kaita a machine dinsa dama bata taba hawaba ba wai dan tasoba tayarda, tana gama shiryawa shima yafito da three quarter da body hug,


"Kasan me? Nifa bazaka kaini ahaka ba gaskiya, meyasa kake hakane?"


"Gaskiya hajjaju kina yawa..."


Ciki yasake komawa yasako jallabiya ruwan kasa yadawo yadauketa suka tafi yau kam jinsa yake acikin wani yanayi wanda bai taba tsintar kansa ba, kusancinsu da bilkisu ya haifar mata da wani lamari mai girman gaske kun san yanda lifan yake wurin zaman baida wani girma, abakin gate din office dinsu ya ajiyeta bai bari taga idonshi ba yayi wani kasa da ido, saida yaga shigarta ciki sannan yajuya yatafi. Da tatashi ma shi yaje ya daukota yasamu khulsum nata yimata tsiya itama tana ramawa, koda ya kawota gida baiko shigaba yakoma shago. Da daddare kuwa har tafara bacci taji shigowarsa dakin yana kokarin yin shimfida agaban gadonta, kallonshi tayi bayan tasa hijab tatashi zaune,


"Ji mana malam, me zakayi?"


"Bacci, yau anan zan kwana"


"Saboda wanne dalili?"


"Wallahi yau tsoron kwana ni daya nakeyi, dan Allah karki koreni"


Komawa tayi takwanta tana cewa,


"Tun da lokacin da kake kwana afalon bakaji tsoronba sai yanzu?"


"To ai ban taba tsorata ba sai yau shiyasa"


Juya masa baya tayi taja bargo tarufe gaba daya jikinta tana cewa,


"Nidai idan kagama ka kashe min wuta pls"


Duk da baya son duhu amma babu yadda ya iya haka yakashe wutar tunda yanaso ya kwana adakin atunaninsa tahakanne kadai zai sa yakara samun kusanci da ita. Washe gari tana son taje kitso ta can kuma zata biya ta gidansu khulsum domin ta dubata saboda taga text dinta cewar bata da lafiya yau, shine yakaita duk inda zataje bayan tagama yakoma daukota, kallonshi tayi sama da kasa yana sanye da koriyar t shirt mai gajeren hannu da hoton tsintsaye ajiki anrubuta angry birds, sai bakin wando mai kyau amma dan tsiya an yanke gwiwar an wani tsagashi shiyasa ga gwiwarsa nan awaje ga wani dan banzan askin da ya sarkaba yanzu irin wadanda yan kwallo keyi ko musicians awani saisaye gefe da gefe amma kuma tsakiyar atara uban suma, ita duk ma ashigar tasa wannan askinne yafi yimata takaici,shi dai kallon tsaf yake yimata ta cikin bakin glass din dake fuskarsa kasancewarshi mai hasken fata glass din ba karamin kyau yayi masa ba dama yanzu baya raboda saka glass tunda yasai babur saboda iska da kwarukan dake fadawa mutum ido idan yana tuki,


Yanda take kare masa kallo haka shima yake kare mata kallon batare da ta saniba,


"Wai kai dan Allah sai yaushe zaka girma ne? Kullum kai kenan cikin shiga marar kan gado"


"To hajjaju wai yau kuma meye laifin shigar tawa?"


"Oho..."


Daga haka ta tattare skirt dinta ta hau machine din, juyawa yayi ya kalli kafarta duk kwaurinta awaje yau bata saka safa ba,


"Ranki yadade ki sake jan skirt din naki kirufe kafarki"


"Muje kawai ko naja ba rufewa zaiyi ba tunda ba zani bane"


Saida ya tura baki sannan yafigi machine din yaringa bin lungu wai dan kar yabi ta cikin gari mutane su ganta.


***

 Ahalin yanzu basuda wani matsala a zamansu sai dai fa har gobe zamane suke yinsa irin na yaya da kani bawai mata da miji ba domin har yau dagashi har ita basu san menene aurenba suna dai zaune ne kawai tsawon watanni biyar da aurensu, tun ranar da yace mata yana jin tsoron kwana shi kadai yadawo kwana cikin dakin amma yana kasa ita kuma hakimar na kan gado,yau tunda asuba taga kiran maama tana dagawa taji tace mata ankai meenah asibiti ana zaton ko haihuwace, nan tayi maza tashiga kitchen domin hada abincin da zata tafi musu dashi asibiti dama shiyasa yanzu bata kashe wayarta da daddare saboda tana tunanin za anemeta saboda daga meenah har Hindu cikinsu yatsufa, fahad yana kwance yanata baccinsa bai san meyake gudana ba saida tagama komai tayi wanka sannan ta tasheshi lokacin karfe 6 nasafe, da kayan dake jikinsa ya dauki key zai fita ta dakatar dashi,


"Ba dai ahaka zaka fita ba ko?"


Fasa fitar yayi yaje yacire armless din rigar dake jikinsa yasaka jallabiya harda hula sannan yafita, suna tafe yana ta kunkuni,


"Wai sai anyi abu ace wani kagirma bayan har yanzu ayaronka kake tunda babu abinda ya canja... Hmmmm zan girman dai akwai lokaci"


Ita dai da yake hankalinta ma baya wurin bata san meyake yiba, wani private hospital ne mai suna al shaddad hospital aka kai meenah acan suka iske maama da mahaifiyar mijin meenah saida suka gaisa da fahad ya tambayi ya mai jiki sannan yatafi gida yaje yaci gaba da baccinsa, wani hukunci na ubangiji itama hindu babu jimawa aka kawota amma ita tana zuwa baifi da mintuna ashirin ba ta haifi yarta katuwa mace nan duk hankali yasake tashi ganin meenah shiru har lokacin tana can dai tanata fama, ammah kuwa da kokari har wannan lokaci bata zo asibitinba tana can gida dai tana tayasu da addu'a sannan tahada komai da ake bukata da abinci tabawa rabi mai aikinta da driver sunkai, su bilkisu kam babu wanda yabi takan abincin da aka kawo domin lokacin ana tunanin yiwa meenah aiki aciro yaron dan har anbaiwa mijinta takarda yasa hannu ba akai ga biyan kudin aikinba Allah ya takaita ta haifo yaronta namiji shima tubarkalla da girmansa.


Sai lokacin kowa yasamu nutsuwa, bayan an kaisu dakin hutu fahad yazo lokacin magriba takusa jariran dai ana ganinsu gasu nan gwanin sha'awa amma iyayen na can ana yimusu karin ruwa sunata baccin gajiya har cikin dakin da jariran suke bilkisu takai fahad ta fara dauko masa macen ta mika masa ya karba yana murmushi, kallon jaririyar yake tayi yakasa bada ita,


"Bazaka dauki dayan bane?" Yaji bilkisu tafada sai lokacin yabata ita yadauki namijin yana mai cigaba da kallon yarinyar, shi dai yana son ahaifa masa yar budurwa ko dan bashida kanwa mace ne oho, bata jaririn yayi yafita yana yimusu Allah yaraya, sai wurin 10 nadare yadawo yadauki bilkisu, washe gari aka sallami masu haihuwar suka tattara sai gidan ammah, dakin bilkisu nada aka sakasu, tunda akayi haihuwar nan bilkisu can take wuni,ana igobe suna suka sha lalle da kitso har masu jegon duk su hudun, da tayi niyyar kwana sai washe garin suna zata koma gidanta amma fahad ya uzzura mata nan Ammah tace tatafi inyaso tadawo da sassafe,


Tanata fushi taje suka tafi shi dai sai santin kunshinta yakeyi da yagani batare da yafito fili ya nuna mata ba har sukaje gida, kasa kasa yake kallonta yana hadiyar yawu, zama tayi bakin gado ta cire mayafinta da dan kwalin kanta hakan yasake saka fahad acikin wani hali, zama yayi agefenta,


"Hajjaju... Dan Allah nidai yau dinnan..."


Kallonshi tayi dama har lokacin bata huceba,


Dan matsawa kusa da ita yasake yi taja baya tana fadin,


"Menene haka??"


"Gaskiya yau yakamata.... Abani.... A..b..a..ni... Ha...kki..na"


Ita saboda yadda ya rarraba maganar ma sai takasa ganewa, nan ta kalleshi yawani matso jikinta sosai yana shafa sumarshi alamun kunya,


"Kace me? Me kace?"


"Cewa nayi yakamata yau abani.... Hakki... Na"


"A ina hakkin naka yake?"


"Ni na nasan a inda yake idan har kin bani dama kuma kin yarje min"


Wata uwar harara ta dalla masa ta mike zata bar wurin da azamarshi yariko hannunta shima yamike tsaye, daga idonta tayi ta kalleshi dayake yafita tsawo kafin tace wani abu jin hannunshi tayi akan waist dinta yamaida ita ta zauna bisa cinyarsa, kokarin yi masa masifa tayi amma ya hanata yin hakan ta hanyar hade bakinsu wuri guda, kokawar kwacewa tafara yi amma takasa saboda yanayin karfin ba daya bane, yana kokarin rabata da rigar jikinta taci nasarar kwatar kanta har ya balle bra din dake jikinta. Hannunta ya riko a masifance take kallonshi da fushi akan fuskarta,


"Dan Allah mai gado yau daya dai ki amince min..."


"Kasan Allah duk ranar da kasake yunkurin tabani ko tam..."


Idanuwanshi dake lumshe yabude ya kalleta,


"Me kike nufine wai? Amma dai ai kin san Shari'a ta bani damar yi ko da karfine ko?"


"Ok fyade kenan zakayi min, right?"


Girgiza kai yayi yamaida idonshi yarufe,


"Ni bazan taba yimiki fyade ba, da yardarki da amincewarki zan kusanceki...."


"Lallai yaron nan bakada kunya..."


"Banida kunya...? To bari infito amarar kunyar tunda har anyi min tambarinta"


Ja daya yayi mata sai gata kusa dashi bakin da ya kirashi da marar kunya yayi magani tareda ragewa kansa zafi bayan yayi fatali da sutturarta, sosai fa yau fahad ya jagwalgwalata daga karshe yabarta ba dan wai yakushi da dukan da takeyi yana shigarshi ba kawai dai ya kyaleta ne,rigarta ta jawo tasaka tana faman cika tana batsewa.


Daga haka ta mike tawuce bathroom cikeda fushi, juyi yayi ya baje sosai akan gadon yana maida numfashi ahankali.....



*Idan har kika karanta alhalin baki biyaba keda Allah domin yana ji kuma yana gani.*




*_Ummi Shatu_*    


© *HASKE WRITERS ASSO.*




*KAMAR DA WASA....!*  



   _*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*




     *24*




     ***Har tafito daga bathroom din bayan tayi wanka bai motsa daga inda yakeba, kayan baccinta ta dauka ta koma bathroom din tasaka sannan tafito fuskarta ahade babu fara'a,


"Malam dan tashi zan kwanta"


Batare da ya bude idonshi ba yace,


"Ki kwanta mana amma ni bazan iya tashiba yanzu jikina babu karfi saboda akwai abinda yashirya yi kekuma kin katse shi"


Batare da ta tanka masa ba dan taga abin nasa harda rainin wayo aciki tawuce can karshen gadon tayi kwanciyarta bata ko cire hijab din jikinta ba,


"Wallahi akwai matsala ajikinki billy, yanzu ke dan tabakin nan danayi bakiji komai ba? Dan Allah kibari ko dan romance mu sake yi...."


Ita mamaki ma fahad ke bata yanzu wato yasan komai kenan dama can ido yazuba mata bai nuna ba amma yana sane da komai, kunya taji tarufeta dan haka tayi gaggawar juya masa baya,


"Kinji..." Yasake yimata magana yana kallon bayanta,


Ganin bazata kulashi ba yayi shiru ya hakura ai ko wanka bai tashi yayiba daga nan inda yake kwance yacire rigarshi da wandonshi ya wurgar yazauna da iya singileti da gajeren wando, dayake yau itama adan tsorace take dashi bata matsa akan sai ankashe wuta ba ahaka suka kwana da haske, shi dai fahad kasancewar abun yana ranshi har mafarkinta yayi da asubah da yatashi kunkuni yayita yi shi kadai,


"Kaida hakkinka amma anhanaka anbarka da yin mafarki idan kayi magana kuma ace kayi rashin kunya..., ni bada yin abuba nida wanka da asubar nan....."


Tana jinsa tayi kamar bata jiba da tajiyo alamun wanka yakeyi bayan yashiga bathroom ficewa tayi tabar dakin tashiga kitchen tana mamakin wannan al'amari wato shi a wannan shekarun nasa har yasan yanda zaiyi da mace lallai, abu mai sauki tahada masa takai dining sannan taje daki zata shiga wanka yana baje saman gado jikinsa sanye da jeans da t shirt da wayarshi ahannu yana chaten da husna yar nacin tasa domin yau kusan kwana uku kenan tanata turo masa sako amma bai budeba sai yau kuma cikin rashin sa,a ashe tana online,


Tana harararshi tashiga wanka harda saka key, bayan tafito sanye da hijab ta kalleshi,


"Malam dan fita zan shirya"


"To ranki yadade"


Yana fita tasawa kofar key tashirya ta dauki duk abinda zata bukata tafita ta sameshi akan kujera yana kwance,


"Bari naje gida sai zuwa dare zan dawo, kayi zamanka basai ka kaini ba zan hau napep"


"To shikenan Allah yatsare"


Fita tayi aranta tana mitar dalilin dayasa bata siyi motaba ma tun wuri, shi fahad murna ma yayi da bashi zai kaita ba domin yasan idan ya dauketa sake famo masa tabon abinda ke damunsa zatayi, haka yawuni agida ranar jikinsa duk babu kwari sai la'asar yafita yaje gidansu acan yaci abinci sannan yatafi dama yasamu su ayiyah suma suna shirin tafiya gidan sunan. Su bilkisu kam yau kansu yasai kayuwa domin suna yayi suna, yara sunci sunan ammah da abba macen yahanazu zasu kirata da Minal namijin kuma lukman zasu kirashi da sultan, gida ya cika dam da dangi da abokan arziki su iyallo da baki baya shiru cewa bilkisu tayi yanzu kuma saura ita itama nanda yan watanni suna so suzo suna, batace komai ba taci gaba da harkarta dama ammah tatura akirata tazo surukanta sunzo iyayen fahad nan taje taji dasu.


Har bayan suna da kwana biyu kullum sai taje gida amma a napep domin shi fahad bai kara daukarta a babur dinsa ba acewarsa saiya warke. Bayan sati uku da sunansu meenah zasu koma gidajen mazajensu ranar bilkisu taje gidan zasuyi sallama da masu jego dama tun yamma hadari yake haduwa amma taki tafiya saida duk suka tafi suka barta bayan sallar isha fahad yazo ya dauketa, ai tun ahanya yayyafi yafara jikasu kafin suje gida sunyi jalaf da ruwa ga hanyar babu haske ga uban gudun da fahad ke shekawa ganin idan tayi wasa tana iya fadowa yasata kankameshi, bayan sunje gida inbanda sanyi babu abinda suke ji daga shi har ita,kayan bacci tasaka yau babu maganar wanka ta kwanta, shigowa dakin shima yayi yana digar da ruwa ya kwashi kayan da zai saka yaje falo ya canja yaje yakwanta kusa da ita, tashi tayi kafin tayi magana ya rigata,


"Ki taimaka min wallahi yau sanyi nakeji kuma duvet dinnan naki yafi wancan blanket din nawa dumi... Zazzabi ma nake ji fa"


"Malam wallahi bazai yuyuba...."


Yabude baki zai sake magana kenan sukaji wata tsawa mai mutukar karfi dan hatta dakin da suke ciki saida ya girgiza, bata san lokacin da kankameshi ba shima haka, jikinta gaba daya rawa yake ga ruwa da ake kwararawa kamar da bakin kwarya, ahaka suka yi bacci suna kwakume da juna har asuba, shine yafara farkawa har lokacin ruwa akeyi, kallonta yayi tana bacci cikin kwanciyar hankali rungume akirjinsa tayi matashin kai da kirjin nasa,


"Su hajjaju iyayen son girma amma kuma ana tsoron tsawa...."


Pillow yajawo zai kwantar da ita akai domin ya fahimci tana fashin salla duk da boye masan da take tayi domin idan bata salla bata son yasani idan asubah tayi saita tashi taje tayi alwala sai tazo ta zauna kamar irin ta idar da salla dinnan tana tasbihi bayan kuma tun lokacin da ya fara kwana adakin ya fuskanta saboda duk lokacin da zata tashi sai yafarka domin abu kadanne ke farkar dashi abacci,


Bude idonta tayi wanda ke cike da bacci kamar jaririya ya kwantar da ita ya mike, ga mamakinta sai taji tana bala'in jin sanyi bayan yatashi babu jimawa ciwon kai yasata agaba, sam fahad bai san abinda yake faruwa ba har saida rana tayi duk da har lokacin anata yayyafi yashigo dakin da niyyar yin alwala tayi masa magana,


"Dan Allah ko zaka samo min maganin ciwon kai"


Matsawa yayi kusada ita ya dafa goshinta,


"Da zazzabi?"


"A'a iya ciwon kanne"


"Sannu, Allah ya sawwake bari naje na samo miki"


Sai bayan da yatafi sannan ta janyo wayarta ta kunna ta tura masa text domin pad dinta yakare abinda ya hanata ma wanka kenan tun dazu,


Yana gidansu wurinsu ayiyah zai karba mata abinci text din nata yashigo yana dubawa yaga tace,


_Dan Allah ka dan taho min da pad._


Murmushi yayi aransa yana cewa,


"Wato baza dai afada min baki da bakiba wai kunya akeji hajjaju kenan"


Saida yajira aka karasa abincin rana sannan aka zuba ma bilkisu cikin food flask, maryam yadauka zasu tafi da ita domin ta ragewa bilkisu aiki tunda yau suna gida ruwa ya hanasu zuwa makaranta, ta wani chemist suka fara biyawa yashiga domin siyo mata maganin ciwon kan kuma cikin sa'a yaga harda pad dinma gashi nan ana saidawa kala kala, guda biyu ya siyo mata yakarbo mata maganin suka wuce shida maryam. Har yakoma tana kwance rikeda kanta wanda ke azalzalarta, afalo yabar maryam yashiga cikin bedroom din ya taimaka mata ta tashi zaune,


"Kiyi wanka sai kici abinci kisha maganin ko?"


Kai ta daga masa tana jiran yafita daga dakin sannan sai tatashi domin tana kyautata zaton tayi staining, tun kafin ta koreshi ya fahimta dan haka yamike yafice bayan ya ajiye mata maganin da pad din agefenta, lallabawa tayi ta tashi cikin sa'a taga staining din bai taba bedsheet dinba iya kayan jikinta ne, wanka tashiga tayi da ruwa mai dumi wanda ke cikin babbab tea flask dinta, har lokacin kanta bai sarara mata ba, body spray kadai ta fesa ta saka kaya riga da wando na Pakistan, ta lallaba tafita falo, yana kwance a kujera maryam na mopping din falon ganinta yasa bilkisu fadada murmushinta,


"Maryam daga zuwa kuma sai aiki"


"Ehh anty, ina wuni? Yajiki?"


Zama tayi akujerar nesa da fahad tana amsawa, da kanshi yatashi yaje ya dauko mata abinci da flate yakawo mata, saida tafara hada tea tasha sannan tabude abincin, dashishi ne yaji kayan hadi da albasa ga mai nashe nashe ai kuwa taji dadin ganin dashishin nan domin taci da yawa dama yau bata ci komai ba, kwanciya tayi bayan tasha magani bacci yayi gaba da ita sai lokacin fahad yasamu yafita yabar maryam atare da ita, koda yaje shagonma hankalinsa na gida domin bini bini sai yakirata yaji yajikin nata har magrib tayi bayan yayi salla ya koma gida yadauki maryam ya maida ita gida daga can ayiyah tabashi tuwo yatafiwa da bilkisu. Tsawon kwana biyu ta dauka tana fama da ciwon kan kafin tasamu sauki tafara fita aiki amma da ko aikinma bata zuwa, khulsum har gida tazo ta dubata haka ma maama masu jegone kadai basu zoba tahanasu tace taji sauki basai sunzo ba kowa yadauka laulayin ciki tafara basu san bahaka bane. Shi dai fahad yanata iya kokarinsa na ganin sun zama abu daya amma taki amincewa shikuma baya son yanuna mata karfinsa shiyasa yake kyaleta, yauma kamar kullum saida sukayi rikici daga karshe ya sauka kasa yayi shimfidarshi ya kwanta wai yayi fushi,can cikin dare tafara jin nishinsa yana murkususu kamar bazata kulashiba amma sai taje inda yake ganinsa tayi duk ya jigata sai gumi yake baccin da basu komaba kenan domin abin ya tsananta zuwa asuba yasamu ya lafa masa, bayan gari yafara haske yatashi ya dingisa yayi alwala yayi salla yana dafe da gefen mararsa na hagu, akwance agida yawuni ranar gashi yakasa cin abinci sai ruwan tea kadai yake sha bilkisu tayi tayi akan yaje asibiti yaki daren ranar halin da yashiga har yafi najiya babu shiri ta dauki wayarsa ta dangwala dan yatsanshi tashiga neman contact ya abba takira lokacin karfe 12 nadare yana tsaka da bacci yadauka,


"Kanina ya akayi?"


Cikin tashin hankali bilkisu tayi magana, dama abban yazo gari yana nan cikeda tashin hankali shima yasako kaya yafito ko cikin gida bai shigaba saboda kowa na gidan yayi bacci. Bilkisu na can tanata fama dashi domin kuka yake ta yimata wiwi yana rike mararsa ahaka Abba yazo gidan yasoma kwankwasawa da azamarta taje ta bude shida salim ne sukazo a motar ya baffa ai basu jira komaiba ahaka suka daukeshi sukayi kama kama, itama dogon hijabi kawai tasaka ta daura zani tabisu,asibiti mafi kusa suka je  wani dan karami na kudi, wajen karfe dayan dare Dr yafito yace aiki za ayiwa fahad  domin k'arine a mararsa kuma yagirma dole sai ancire nanda zuwa safe za ayi masa aikin matsawar sun biya kudin aikin amma ahalin yanzu aunyi masa allurar da zata sakashi bacci dan yasamu saukin ciwon,azaune su bilkisu suka kwana da ita da Abba da salim, zuwa asuba Abba yasanar da gida abinda yake faruwa kafin gari yagama wayewa su baba duk sunzo dasu ayiyah har su yaya asabe sun zo nan aka biya duk wani kudi da ake bukata,wurin karfe 9 nasafe ake sa ran yimasa aikin shiyasa kowa ya zauna yana zaman jiran tsammani,kafin lokacin da za ayi masa aikin anty kubra da anty juwairiyya suka zo dauke da abincin da suka shiryo amma dayake hankali ba akwance yakeba babu wanda yakula balle har yaci.


Karfe tara da wurin rabi aka shiga da fahad theater ayiyah sai addu'a akeyi itada mamuh abin tausayi, tunda aka shiga dashi basu suka fitoba sai sha biyu na rana kallo daya zakayi masa kagane amutukar wahale yake sannan yajigata,sai faman baccin wahala yake, wani daki aka kaishi gado biyune adakin amma daya gadon babu kowa akai, wuni yayi yana bacci bai farfado ba sai la'asar sai lokacin hankalin kowa ya dan kwanta yanyameshi akayi kowa nayi masa sannu bilkisu dai daga dan baya ta tsaya saida kowa yagama sannan tamatsa itama bayan taga fitarsu mamuh yarage saura abba da salim kadai, duk wanda yayi masa sannu sai dai yadaga masa kai amma baya iya amsawa, koda bilkisu ta matsa idanuwanshi yazuba mata wadanda suka sake girma sakamakon dan fadawar da yayi,


"Sannu... Yajikin.... Allah yabaka lafiya"


Kai yadaga mata sannan ahankali yakamo hannunta cikin nashi yana mai yimata alamar da ta zauna agefenshi, batayi musuba ta zauna tana kallonshi, lumshe idanuwanshi yayi har lokacin yana rike da hannunta, sunata zaune ahaka har anty Fauziyya tashigo ta kirata wai tazo inji ayiyah, tashi tayi tafita bayan yasaki hannun nata, koda taje ayiyah matsa mata tayi tasata agaba dole sai taci abinci domin wuni guda bata ci abincin kirki ba, daurewa tayi taci abincin tuwon shinkafa miyar wake bayan tagama ci tayi alwala tayi salla sannan takoma cikin dakin tare dasu Mariya wadanda suka biyo anty fauziyya suka taho tare.


"Sannu ya fahad....." Inji su mariya kai yadaga musu sannan yamaida kallonsa ga bilkisu hannu ya mika mata amma sai taki kamawa saboda ganinsu mariya awurin gaban gadon taje ta zauna amma sai ya dan dungureta koda ta kalleshi sai taga yana yimata alama da ta zauna asaitin kanshi matsawa tayi ta zauna tana zama yamaida kansa kan cinyarta yana ciccije lebe sakamakon amsawar da wurin da akayi masa dinki yayi hannunta ya damke cikin nasa yana rumtse idanuwa duk sai yabata tausayi domin tasan abinda zaisa kaga namiji na kuka to bafa karami bane abin ahaka suka kasance har wani baccin ya dan daukeshi kowa ya leko yaga ayanda suke baya shigowa saiya koma shiyasa duk nauyi da kunyar duniya tataru ta dabaibaye bilkisu musamman ma da taga su ayiyah sun leko amma sai suka koma har magrib yana kan cinyarta saida ya farka sannan abba yataimaka mata ya kwantar dashi saman pillow, salla taje tayi daga can tazauna wurinsu ayiyah har karfe 9 nadare suna asibitin da su ayiyah zasu tafine lokacin da mijin anty fauziyya yazo daukarsu sukace bilkisu ma tatafi gida sai su mariya subita su tayata kwana shikuma fahad abba yakwana awurinsa, turo baki fahad yayi ya bata rai yana kallon mamuh wadda itace ke tsara hakan, kallonshi ya mayar kan bilkisu ganin ta mike daga kujerar da take kai azaune acikin zuciyarshi yanata masifa,


"Ga matata ga komai maimakon abarta mu kwana tare shine kawai za awani ce ya Abba ya zauna ya kwana awurina, ni wallahi mamuh baki kyauta minba..."


Haka yaketa fada acikin ransa amma afili babu bakin magana domin tamkar andinke masa bakin baya iya magana gashi duk jikinsa kamar ba nashiba musamman ma daga mararsa zuwa babban yatsunshi na kafa,


Jin kowa nayi masa sallama suna tafiya yayi saurin yiwa salim alama da ya kira bilkisu,


"Hajjaju oga fa yana magana"


Murmushi tayi ta koma da baya tana cewa,


"Lallai salim kaima din hajjajun zakace"


Tana zuwa yayi mata alama da ta sunkuyo taji, duk atunaninta magana zaiyi mata akunne amma tana mika fuskarta saitin tashi taji yabata hot kiss a kumatunta mikewa tayi tana harararsa shima harararta yayi murmushi ne ya subuce mata batare da ta shirya ba, hannunta ya riko yana yimata alama da wai shima tayi kissing din kumatunshi,


"Dan Allah kaga ni sakar min hannu gasu can ni kadai suke jira kar kasa azargi ko wani abu mukey...."


Murmushin karfin hali taga yayi kafin yagirgiza Mata kai alamun bazai sakar mata hannun ba, hannunshi tayiwa kiss tana kokarin fita abba yashigo ganinsu ahaka yasashi saurin komawa da baya, hararar fahad tayi,


"Kagani ko...."


Bata saurareshi ba tafice daga dakin, binta da kallo yayi yana yimata dariya acikin zuciyarshi, dama ita kadai ake jira tana zuwa suka tafi,itada maryam da mariya aka sauke agidanta tana shiga wanka tafara yi sannan tayi sallar ishah domin batayi ba a asibitin acikin wannan daren takira maama da ammah duk ta sanar dasu rashin lafiyar fahad da asibitin dayake kwance ahalin yanzu sannan takira khulsum wacce har tafara bacci itama tasanar da ita, dayake jiya batayi isasshen bacciba shiyasa yau tunda ta kwanta bata tashiba sai da asubah duk da hakama ta makara sallah domin har masallatai sun jima da idarwa......



*Littafin kamar da wasa na siyarwa ne yar uwa idan har kinada bukata ki siya ki karanta domin yana dauke da dunbin darrusa na rayuwar da muke ciki yau, ka karanta halak dinka yafiye maka alkhairi akan karanta hakkin wani.*




*_Ummi Shatu_*    



© *HASKE WRITERS ASSO.*



*KAMAR DA WASA...!*  




   _*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*




    *25*



      ***Kitchen tashiga bayan ta idar da salla sukuma su mariya suna kokarin gyara mata gidan, saida ta shirya lafiyayyen abincinta tazuba a flask wanda zata kai asibiti sannan ta zubawa su mariya suka ci daga nan tabasu kudin napep saboda sai sun koma gida sannan zasu shirya su tafi makaranta danma dai sunyi wanka agidanta da sunje gida uniform kawai zasu saka, bedroom tashiga bayan ta sallami su maryam sun tafi, tana kokarin daura towel idonta yakai kan wayar fahad dake ajiye saman bedside drewar tana karar neman agaji, koda taje gaban wayar sunan husnah tagani ajiki nan wayar takatse wani kiran yasake shigowa, ko kadan bataji tana sha'awar daga wayarba har tayi tagama sai lokacin ta dauka ta jona masa a charge kasancewar akwai wuta. Wanka tashiga tayi tafito ta kintsa adan hanzarce sannan tayi breakfast kafin ta hada komai wanda zata tafi dashi tarufe gidan tatafi, shatar napep ta dauka yakaita har asibitin lokacin karfe bakwai da wurin rabi,iya ya abba ne kadai awurin da alama babu wanda yazo tunda yanzu garin yawaye, saida suka gaisa ta tambayi yamai jiki sannan tashiga ciki, idonshi akan kofa shiyasa tana shigowa idanuwansu sukayi arangama da juna, murmushi taga ya sakar mata kasalalle yana kwance rigingine kanshi tallafe bisa hannunshi na dama,


Har gaban gadon takarasa zata zauna, hannu yamika mata yakamo nata, zama tayi tana kokarin ajiye handbag dinta bayan ta dire kayan da tazo dashi. Kallonta yake tamkar yau yafara ganinta domin ba karamin haduwa yau dinnan tayiba, leshi ne ajikinta dark pink anyi mata gown tasha lafaya itama pink duk ta lullube jikinta, juyawa tayi ta kalleshi,


"Sannu yajikin?"


Daga mata kai yayi yana matsa mata yatsunta bata kai ga sake yin wata maganar ba Abba yashigo dauke da brush da toothpaste,


"Gaskiya mijinki jinyarsa akwai takurawa.... Ni yanzu ma gida zanje anjima zan dawo"


Murmushi bilkisu tayi ta dan karkatar da kai tana kallon fahad wanda idanuwanshi ke lumshe,


"Meya faru yayanmu?"


"Shifa idan yana ciwo nafarko bazaiyi bacciba sannan na biyu bazai ci abincin ba na uku bazai sha magani ba sannan komai sai anyi masa kamar wani jariri, yanzu gashi yanace sai ankawo masa brush kuma bari kigani ko yayi brush din bafa cin komai zaiyi ba kuma Dr yace zai dan iya cin abinci kadan kadan bawai dayawa ba"


"Sannu da kokari, Allah yabada lada....,ayi mana afuwa amma"


Bude idanuwa fahad yayi ya kalleta yana jin wani irin sabon sonta yana shigarshi,


"Yanzu dai gashi sai kusan yanda zakuyi kiyi masa brush din"


"A'a babban yaya ai sai ka taimaka min"


Da taimakonshi suka samu yayi brush din sannan ta zubawa abba abinci yafita waje yaci, Dr ne yashigo shida wasu nurse maza guda biyu yaduba jikin fahad sannan yafita yabar nurse din domin su gogewa fahad wurin da aka yankashi, ai ana saka audugar da aka tsoma cikin ruwan spirit ya runtse idanuwansa tareda sake damke hannun bilkisu tun nurse din Suna tsokanarsa sun zaci shagwaba ce har kowa ya fahimci dagaske yake domin kuka yasaka musu saida aka gama suka fita Abba yashigo tsayawa yayi yana kallon fahad wanda har lokacin bai daina kukanba,


"Kai wai menene amfanin kukan ne? Dallah malam tashi kaci abinci saboda ni tafiya zanyi"


Ko motsi baiyi ba bare asaka ran zai yarda yaci abincin, shi dama idan lafiyarsa kalau yana son abinci sosai amma idan bashida lafiya to shida abinci sai ahankali, gyara zama bilkisu tayi tafara lallashinshi,


Gefen lifayarta tasaka tafara goge masa fuskarshi, kanshi tashiga shafawa sannan ahankali ta sunkuya daidai kunnenshi tafara yimasa rada,


"Kaifa yanzu ba yaro bane kagirma, kayi hakuri.... Yi shiru katashi kaci abinci, dan kadan zan baka dama kai na dafowa..."


Ahankali ahankali yasoma rage kukan nashi har yadaina gaba daya sai ajiyar zuciya da yake ajiyewa, mikewa tayi da niyyar yiwa ya abba magana amma sai taga wayam wato yafice yabasu wuri kenan, tea ta hada masa mai kauri bai kai rabin cup ba ta taimaka masa ya dan tashi yanata cije lips, yana hawaye yana shan tea din wai ahakanma dan itace amma da wanine da sai ansha fama dashi kafin yasha, wainar kwai guda daya da dankali guda biyar ta sake bashi yana ci yana yamutsa fuska yana gamawa ta mayar dashi ya kwanta, wayarshi ta ciro ajakarta tabashi yakarba ya ajiye agefen pillow din da yake kai, su ayiyah ne suka shigo harda baba lifayarta taja tarufe fuskarta kadan tasauka kasa ta gaidasu bayan sun gaisa tafice waje ta zauna bisa bencin dake kofar dakin anan ammah ta sameta itada Rabi mai aikinta, tare suka shiga ammah ta dubashi sannan tafito itada rabi suka bar ammah acan wurunsu ayiyah. Sunata hirarsu da Rabi har khulsum tazo itama tashiga ta dubashi tafito tatafi saboda wurin aiki zata tafi. Wurin misalin karfe 10 saiga maama dasu meenah abban hudah yakawo su anan suka shantake kamar ba dubiya suka zo ba domin anan ammah tatafi tabarsu,kowaccensu rikeda yarta har su anty fauziyya sukazo suma dauke da girke girken da suka iyo, shikuwa marar lafiyar yana daki kwance shida salim suna hira amma dayake jiya baiyi baccin kirki ba da daddare yanzun sai hamma yake danyi.


Bayan anyi sallar azahar suna gama cin abinci salim yaleko yakira bilkisu tashi tayi batare da ta bude warmer din da rabi takawo ba yanzu, dakin tashiga fahad na baje sai faman lumshe idanuwa yake, hannu yamika mata yajata gefenshi,


"Zo ki tayani baccin rana luv"


Ita abinma maimakon yabata haushi kunya yabata saboda ga abokinshi zaune kan gadon marassa lafiyar dake makotaka da na fahad amma babu patient akai, maganarsa tasake juyowa ahankali domin tunda aka kawoshi asibitin ma sai yanzu ne sukaji yayi magana amma da ko me yarike maganar oho,


"Zo muyi baccin rana hajjaju"


Dan satar kallon wurinda salim yake tayi amma sai taga shi hankalinsa ma ba awurinsu yakeba domin yana ga kan wayar fahad dake hannunsa, jin kunyar gwasaleshi tayi agaban abokinshi domin tasan babu wanda yasan irin zaman da sukeyi kusan kowa yazaci zaman aure sukeyi na hakika, tana can duniyar tunani ya hardota da hannunshi zuwa kan kafadarshi bai tsaya ananba yashiga shafar bayanta kamar wata jaririya, lumshe idanuwa tayi tai shiru kamar mai yin baccin da gaske shi dai mutumin abu biyune suka taru suka hadar masa lokaci guda ga ciwo ga kuma wani abu dake sauka asassan jikinsa gaba daya wanda yafi kamada kasala kasala, gajiya gajiya, ji yayi bazai iya jure wannan kamshin nata dake barazanar tarwatsa tunaninsa ba, bakinshi yakai kan goshinta yabata kiss mai sanyi sannan ya soma kokarin lulluba da lifayar jikinta anan ne kuma taso bashi matsala amma sai ya shagwabe fuska,


"Allah sanyi nakeji fa..."


"To akawo maka bargo?"


Girgiza kai yayi harda makale kafada,


"Ni naki nakeso, dan wannan mayafin naki zai isheni.."


Yar kokawa sukayi kafin ta farga yashige cikin lifayar tata ya kwakuma akirjinta amma fa duk abinnan dake faruwa bai motsa kafafunsa ba iyakacin hannayensa da kanshi ne yake motsawa, salim dake zaune yana jin duk abinda ke faruwa tunda ya kallesu sau daya bai sake iya kallonsu ba sai bayama yajuya musu domin sunyi mutukar bashi kunya. Mintuna kadan taji jikinsa ya dan saki alamar yayi bacci da dabara da komai tasamu ta zare jikinta ta tashi tafita bayan ta gyara masa kwanciyarshi yadda bazai takuraba, tana komawa wurinsu maama sai kuma duk ta tsargu da kus kus din da sukeyi musamman ma da ta kama Hindu na gulmarta da ido itada meenah,


"Adda labour ya mai jiki?" Inji maama, banza tayi da ita ta karbi Minal dake hannun hindu ta rike tana lakutar kumatun yarinyar,


Duk dan bikin da suke tayi tana jinsu bata tanka ba daga karshe ta jawo warmer din da ammah ta aiko musu da ita tabude domin bata san ko wanne irin kalar abinci bane, farfesun koda ne cikin warmer din sai tashin kamshi yake wannan dalilin ne yasata niyyar baiwa fahad yaci domin naman ya dahu ligif zai iya ci,


"Maman hudah zuba muku kuci ni ba ci zanyiba sai dai shi ku bar masa"


Jin irin dariyar da sukayi yasata tashi gaba daya tabar musu wurin kafadarta dauke da Minal, kamar da wasa take bin hanyar da tagani wacce zata kaika sassa daban daban dake cikin asibitin, aranta sai yaba tsari da haduwar asibitin take yi wani daki tawuce wanda shine na karshe ajerin dakunan dake bangaren, ahankali yamaida kofar yarufe yafito yana rikeda mukullin motarsa yana dan sosa kunnenshi na dama dashi, wani kamshine ya mamaye wurin, daf da zata sha wata kwana wacce zata kaika pharmacy wayarta ta subuce ta fadi kasan tiles din dake shimfide awurin kadan yarage yataka wayar tata saboda irin garawar da wayar tayi ita kadai amma sai Allah ya takaita, sunkuyawa yayi yadauko wayar yamika mata daidai lokacin da ta jiyo hannunta daya ta mika masa domin dayan tarike Minal dashi, tun daga kafarshi tasoma kallonshi, farin takalmine akafar tashi yana sanye da shadda ruwan kasa da hula sai farin glass dake idonshi, kamar hadin baki idanuwansu suka sarke cikin na juna, wata faduwar gabace mai girma ta saukar mata wacce tayi sanadiyyar sakin Minal dake hannunta sai shine yayi azamar tare minal din ya rungume yana yiwa bilkisu wani irin kallo mai dauke da alamomin tambayoyi daban daban, cikin rawar jiki da rawar baki ta furta,


"Hamood...."


Shi dinma cikeda rawar baki yace,


"Bilkisu.... Kece ko kuwa mafarki nake?



*Book dinnan na kudine idan kina bukata kibiya saiki karanta.*




*_Ummi Shatu_*    


© *HASKE WRITERS ASSO.*




*KAMAR DA WASA.....!*  



*_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*




     *26&27*



      ***Daga ita harshi kasa sake furta koda kalma daya sukayi sai kallon juna da suketa faman yi kamar yaune suka soma ganin juna,


"Bilkisu kin sakani acikin mutukar damuwa, Allah yasa ba aure kikayi har kika haihu ba..."


"Haba hamood har yaushe zanyi aure inhaihu batare da saninka ba, najiraka najiraka har nagaji, na nemeka duk inda nasan zan iya samunka amma nagaza daga karshe dole tasa na fidda wani mijin nayi au..."


Arazane ya kalleta har yana cin tuntuben matsawa kusa da ita,


"Wai kina nufin kinyi aure? Wannan shine abinda bazan taba iya jurewa ba bilkisu, rashinki agareni babbar matsala ce wadda bata da magani... Bazan taba iya jurewa ba"


"Hamood nikaina wannan auren nayi shine kawai arashinka amma tunda...."


"Bilkisu karki cemin komai, yazama dole ki dawo gareni muje mu shimfida daddadar rayuwar da muka jima muna tsarawa kanmu, yazama dole mu cika burinmu da alkawarin da muka jima muna yiwa juna..... Dole ki kashe aurenki kidawo gareni domin kece farin cikina..."


Duk da ba acikin nutsuwarta takeba domin jikinta inbanda rawa babu abinda yakeyi amma hakan bai hanata murmusawa ba,


"Hamood wallahi kaine burina, kaine mijin da nadade ina yiwa kaina mafarkin samu dan haka yanzu lokaci yayi, kai dai kawai kabani dan lokaci kankani zanyi handling komai...."


"Bilkisu sai nake ganin kamar idan kika tafi yanzu bazan sake ganinki ba..."


"Karka damu hamood ka kwantar da hankalinka ni takace kai nawane kamar yadda muka dade muna yiwa juna fata, bani Minal intafi saboda kar wani acikin sisters dina yazo yaganmu"


"To ai sai kibani number dinki saboda ta wannan hanyar ne kadai zan rinka sanin halin da kike ciki..."


Batayi musuba ta rubuta masa awayarshi tabashi takarbi Minal, yana tafe yana waiwayenta itama haka har suka bacewa juna tana shawo kwana sukayi kicibus da meenah wacce tataho nemanta domin zasu tafi gida abban minal yazo daukarsu,


"Adda maigado ina kika shigane mukayita dubaki shiru gashi wayarki taki shiga?"


Murmushin dole ta kakalo takalli meenah,


"Wayarce tafadi wlhi inajin sim din yagoce..."


Jerawa sukayi suka tafi meenah sai hira take yimata amma ina hankalinta ita gaba daya ba awurin yakeba, sam yanzu bata cikin nutsuwarta, ganin hamood yatada mata tsohuwar soyayyar da ta jima tanayi masa domin yanzu ji take zata iya yin komai dan ta kashe kaddararren auren nan na fahad taje ta auri hamood dinta,


Sama sama suka gaisa da baban minal sukayi sallama da kannen nata suka tafi suna tafiya tanemi wuri ita kadai ta zauna tana tunanin menene abinyi? Anty fauzy ce tataho wurinta tana murmushi,


"Hajjaju to ga mijinki can yatashi yana ta yiwa mutane daru akan shan magani sai kije kibashi..."


Mikewa tayi zuciyarta tana suya domin sam fahad bai dace da itaba hamood shine wanda yadace yazama mijinta domin irin mai shekarunsa takeso 35 a matsayinta na yar shekara 30 ba wai fahad ba dan 25,zuciyarta babu dadi tashiga dakin da yake duk yabi ya ruda mutane, ganinta yasa su ayiyah fita aka barsu su biyu sai salim na cikon uku, zama tayi gefen gadon ta dauki maganin ta mika masa baiyi musuba yakarba yana babbata fuska.


Tamkar zaiyi kuka haka yake taune maganin yana korawa da ruwa har ya shanye su tass komawa yayi yamaida kansa bisa pillow ya kwantar yana hararar salim wanda ke zaune yana kallonsu,


"Baby zansha sweet bakina daci...."


Batace masa komai ba amma yaga amsar maganarshi acikin idanuwanta,sake bata rai tayi tajanyo handbag dinta ta bude ta ciro yar karamar milk chocolate tabashi. Tunda magrib takawo jiki tace zata tafi gida babbata rai fahad yashiga yi domin shi idan ta son ranshi za abi abar bilkisu ta kwana dashi ba ya Abba ba,yauma kamar jiya dasu mariya aka hadata dan su bita su tayata kwana duk da ita bata so hakanba domin tana son sakewa tayi waya da hamood sosai adaren yau,


Sam yau batayi garajen hada daki dasu maryam ba domin a falo tayi shimfidarta sukuma tabarsu acikin bedroom, zama tayi ta harde kafafuwanta kan katifar da fahad yake kwana, tana sanye da rigar bacci fara tas mai santsi iya gwiwa sai bakar hula akanta, daman jiran kiranshi takeyi shiyasa kiran na shigowa tayi murmushi ta dauka tana kwantar da murya saboda dare ne,


"My sweetheart yakike? Yanzu dan Allah menene abinyi? Ni nafi son kiyi gaggawar dawowa gareni"


Murmushin jin dadi tayi,


"Karka damu hamood ka kwantar da hankalinka very soon zan zama mallakinka"


"Are u sure?"


"Am 100% sure hamood...."


Dariya sukayi atare lokaci guda, sun jima sun bata lokaci sosai suna shan hira domin har wurin karfe 1 nadare suka kai yana sanar da ita abubuwan da suka faffaru saida bacci ya takurawa bilkisu sannan sukayi sallama. 


Washe gari da safe bayan ta sallami su mariya sun tafi sake kwanciyarta tayi har saida hamood yakirata sannan tatashi, bayan sun gama waya tashiga wanka tashirya sannan tatafi asibiti amma yau bataje da wuriba kamar jiya shi dai fahad yana kwance ya kosa yaga zuwanta, dauke da basket din abinci ta shiga dakin tasha yaluwar Arabian gown mai manyan stones ajiki tayane kanta da wani mayafi mai kauri milk colour, tunda suka gaisa da ya Abba bata sake furta komai ba, fahad sai kallonta yake taki kulashi wannan dalilinne yasashi niyyar jan magana, shagwabe fuska yayi,


"Baby inata kiranki ban sameki ba, dama zan fada mikine ki taho min da kayana gashi yanzu sai na ya abba nasa saboda dazu ya gyara min jikina..."


Jijjiga kai tayi tana kallon wayarta,


"May be network problem ne"


"To kibani abinci inci saboda zan sha magani"


Dariya Abba yayi yana tattara kayansa zai fita,


"Yaro yasamu sauyin yanayi wato yanzu da kanka ma kake cewa abaka magani kasha ah lallai angaida bilkisu..."


Murmushin yake tayi tatashi ta zuba masa potatoes plan din da ta iyo sannan ta hada masa tea dan kadan, yauma kamar jiya da taimakonta yaci abincin sannan yasha magani, haka tawuni acikin wani hali, hali na rashin walwala domin ita bata ki a sallami fahad ayauba su koma gida inyaso ayita takare, yauma magrib nayi ta tafi gida itada su maryam, lokacin bacci nayi suka sha hirarsu da hamood.


Gaba daya fahad yakasa gane kanta a yan kwanakin nan ada tana sakar masa fuska suyi wasa da dariya wani lokacin har tsokanarta yakeyi amma yanzu tadaina sai shan kunu da daure fuska, ita kuma anata bangaren kawai so take yawarke a sallameshi suje gida ayi wacce za ayi domin hamood yace baya son bikinsu ya dauki dogon lokaci yafiso ayishi kwana kusa, kullum sai sunyi waya dashi fiyeda sau uku wani lokacin ne ma idan tana cikin mutane bata yarda ta dauka. Yau kam tun kafin taje asibitin husna taje duba fahad itada kawayenta domin kullum idan taje shagonsu bata samunshi sai ace baizo ba daga karshe dai su hamza suka fada mata fahad baida lafiya, wahala sosai tayi masa kamar ba student ba domin harda girki da fruits ta siya ta kai masa, suna tafiya bilkisu na zuwa shiyasa basu haduba tadai ga kayan dubiya amma bata san waye yakawo ba.


Satin fahad biyu a asibiti aka sallameshi domin jiki yayi kyau kuma babu laifi ya murmure sosai kamar ba majinyaci ba, tunda suka koma gida ya fuskanci akwai matsala domin bilkisu ta kafa ta tsare, duk da dai batace masa komai ba amma daure fuskar da take tayi ya isa yasanar dashi akwai matsala shi dai baice mata komai ba har dare, yana zaune gaban dressing mirror bayan yafito daga wanka da kayan bacci ajikinshi riga armless da wando iya cinya tashigo dakin, zama tayi gefen gado tana kallonshi so take tayi masa maganar amma bata san ta inda yadace tafara ba dole sai hakura tayi domin ta sake dan bashi lokaci. Bayan kwana biyu tadawo daga aiki yana kwance falo tawuce bedroom yau dai ta daura aniyar sanar dashi inyaso komai ta fanjama fanjam domin hamood ya matsa da son ganin fitowarta, fitowa tasake yi daga cikin bedroom tazo ta zauna tana fuskantarsa,


"Fahad.... Dan Allah inaso zamuyi magana..."


Kai yadaga mata bayan ya tattaro gaba daya hankalinsa gareta,


"So nake ka sawwake min..."


Kallonta yayi cikin rashin fahimta,


"Kamar ya fa...?"


"Ina nufin so nake ka sakeni...."


Tashi zaune yayi babu shiri yana kallonta,


"In sakeki? Laifin me kikayi min da zan sakeki? Anya kuwa kin san abinda kike fada?"


"Nasan abinda nake fada mana, auren ne bana bukatarsa yanzu shiyasa nace ka sawwake min"


Murmushi taga yayi sannan yamike yana mika,


"Allah ya kyauta, ni wallahi da zaki taimaka ma da kin hau kaina kinyi birgima sosai ko zan samu gajiyar dake jikin nan nawa marar dalili ta baje amma nasan bayi zakiyi ba, bari kawai natafi filin ball naje na basar acan...."


Daga haka yawuce bedroom yayi shirin ball yafito yana sanye da kayan ball ajikinsa jajaye na club din Barcelona harda safa hannunsa rikeda wayarshi da bakaken combos dinshi, wani kulli ne taji ya tokare makoshinta wato ma mahaukaciya ya dauketa ko yaya da har zai tashi yabarta without saying anything, babu bata lokaci ta mike taje gabanshi,


"Malam ji mana... Bakaji abinda nace maka bane?"


Juyowa yayi ya kafeta da ido bayan ya ajiye takalmanshi akasa,


"To mekikeso nace miki baby? Banida abinda zance shiyasa kikaji nayi shiru"


"Fahad wallahi tun muna shaida juna ka sakeni domin bazan iya zaman aure dakai ba, kalleka fa ka kalleni ai kaima kasan ni ba mate din aurenka bace dan haka kawai ka sakeni tun kafin duniya ta jimu..."


"To wai dan Allah laifin me kikayi min da zakice sai na sakeki, ko kuma ni laifin me nayi miki?"


"Babu abinda kayi min kawai bana bukatar auren ne ahalin yanzu"


"Hmmm bilkisu kenan karfa kiga kin girmeni kirinka yimin kallon sakarai ko marar wayo, ashe kecema mijin mutukar zan rinka aiki da umarninki...."


Sunkuyawa yayi zai dauki takalmanshi ta kamo rigarshi yadago yana kallonta,


"Wallahi fahad sai ka sakeni, akan me zaka dage sai kayi rayuwar aure dani..."


"A'a dan Allah basai kin yimin sharri ba,yaushe nataba nemanki? Na taba cewa sai na kusanceki?"


"Ni ba wannan maganar nake yimaka ba, maganar saki nake yimaka, ka sakeni kawai...."


Murmushi yayi sannan yadauki takalminsa yana kallonta,


"Zan tafi....me zan samu? Kiss ko hugging?"


Wani takaicine taji ya lullubeta ga bakin ciki da yake taso mata a makoshinta,


"Wai kai wasa ka dauki maganar nan ne?"


Wani sakaran kallo yayi mata sannan ya maida kallonsa ga wayarshi wadda ke vibrating alamar kira yashigo,


"To idan ba wasa ba menene? Ai wannan maganganun naki basuda maraba da wasan kwaikwayo hajjaju.... Ni natafi sai na dawo"


Tsabar bakin ciki rasa abinda zatai tayi,kasa koda kwakkwaran motsi tayi tana ji tana kallonsa yasaka kai yafice daga cikin falon yana amsa wayar da akayi masa, 


"Hello anty fauziyya..."


"Auta yajikin naka?" Tafada daga daya bangaren,


"Anty nasamu sauki ni yanzu hakama filin ball zanje"


"Kai, kar kaje fa kajawa kanka matsala"


"Ahh babu komai Anty wallahi ras nake jina"


Kasa motsawa tayi daga wurin taci gaba da tsaiwa kamar wadda aka dasa har saida kafafuwanta suka fara nuna alamar gajiyawa da tsaiwar da take nan tazame ta zauna kamar abin shiri sai kuma kuka ya balle mata tashiga rusashi kamar wata yarinyar goye domin harta manta rabonta da kuka irin wannan.


Abangaren fahad kuwa sosai abinda yafaru tsakaninsa da bilkisu ya tsaya masa arai,ko kadan hakan baiyi masa dadiba amma haka dai yadaure ya yakice damuwar yashiga sha'aninsa duk da dai abun yana fado masa arai lokaci zuwa lokaci. Saida yabuga ball sosai sannan yafita yaje yanemi wuri ya zauna dan yahuta, shifa yanzu matsalar ma idan yakoma gida bai san ayanayin da zaije ya iske bilkisu ba wannan abu yanzu shine babbar damuwarsa.


Tunda bilkisu tayi wannan zaman yan borin tana rusa kuka bata dainaba saida kiran hamood yashigo cikin wayarta da rarrafe taje ta dauko wayar tadaga muryarta har ta dishe dan tsabar kuka,


"Sweetheart yasakeki...?"


Cikin dasasshiyar muryarta ta amsa amsa,


"Wallahi hamood yaki ya sakeni, nayi nayi amma abin ya faskara..."


"Don't tell me this sweetheart, you should insist akan dole sai ya sakeki, ki matsa masa sosai,bana son ki kara koda 1 week agidansa...."


Daga kai tayi tamkar yana kallonta,


"Yanzu baya nan yafita amma da zarar yadawo zan dora daga inda natsaya..."


"Yawwa one love..."


Kit takashe wayar tana jin sabon kuka yana taho mata,ahaka fahad yadawo ya isketa zaune dirsham kan rug tana hawaye,


"Hajjaju..... Wai dan Allah menene matsalar ne? Meke faruwa?"


Yace da ita yana kokarin tsugunnawa agabanta, jajayen idanuwanta wadanda suka kankance ta dago tana zabga masa harara,


"Fahad wallahi idan har baka rabu daniba sai kayi nadama tareda da nasani mai tarin yawa...."


"Ni wallahi bana son inji irin wadannan kalmomin suna fitowa daga bakinki"


Hayayyako masa tayi da masifa da tashin hankali tuni yatashi yawuce bedroom domin har anfara kiran sallar magrib, wanka yayi yafito yashirya yasaka jeans da jallabiya milk colour yafita bayan yasha turare tana zaune inda yabarta tana ta kuka,


"Ni narasa maganin abinda kukan nan zaiyi miki bilkisu.... Dan girman Allah ki barwa Allah lamarinsa ki sanyawa zuciyarki ruwan sanyi..."


Mikewa tayi tana hawaye tana tunkararsa,


"Wallahi fahad ko duniya zata tashi bazan cigaba da zama da kai ba domin ba kaine farin cikina ba, farin cikina yana wurin waninka dan haka yazama tilas ka sawwake min..."


Bai jira takaraso ba yafice da sauri yabar gidan, masallaci yatafi daga can yawuce wurinsu salim wato majalissarsu ta shan shayi, ita kuwa bilkisu tana nan zaune dakyar tatashi tayi salla bayan tayi salla hamood yasake kiranta yana kara jaddada mata maganar neman sakinta awurin fahad.


Gaba daya fahad bashida nutsuwa domin wasa wasa damuwar da bilkisu ke ciki tafara tasiri akansa saboda yau kimanin kwana biyar kenan suna cikin rashin kwanciyar hankali tun ranar da aka sallamoshi daga asibiti rabonshi da cikakkiyar nutsuwa domin bilkisu tasashi agaba da masifa da tijara tun abin baya damunsa har yafara damunsa,


Dama tunda haka tafara faruwa tadaina kwana acikin daki sai falo yanzu sai shine ke kwanciya aciki sannan tadaina girki kwata kwata sai dai tahada tea tasha shiyasa kwana biyar kacal duk tafita hayyacinta fahad yayi lallashin yayi ban bakin amma abin yaci tura. Yau ma kamar kullum yana daki yana shiryawa zai fita yajiyota tana yin waya afalo,saurarawa yayi dakyau nan yaji abinda take fada,


"Hamood ka kara hakuri wallahi ina iya bakin kokarina ganin ya sakeni but he refused... I don't even know what to do..."


Bai bari yakarasa jin wayar tasuba yaje yakarasa shiryawarshi yana niyyar fita tashigo ta watsar da wayoyin kan gado bayan ta watsa masa harara tawuce cikin bathroom, killer smile ya danyi aranshi yace,


"Daidai kenan"


Karamar wayarta yadauka yafita yabar babbar domin yasan tafi amfani da karamar, lifan dinshi yagoge da duster sannan yahau yafita.Saida yayi nisa da unguwar sannan yatsaya yayi packing agefen titi receiving calls dinta yafara bi yana dubawa har yagano abinda yake son yagano babu bata lokaci yayi dialing number hamood, a kasalance yaji yadauki wayar,


"Sweetheart ya sakeki ne?" Abinda kunnuwan fahad suka jiye masa kenan nan yayi kwafa yafara balbalawa hamood masifa kamar zai yashe hanjin cikinsa ya yar,


"Ban saketa ba kai meya hana ka saketan dakiki?, kai wanne irin garane marar tunani da nutsuwa? Dan tsabar jakanta shine zaka rinka kiran matata kana hure mata kunne wai sai takashe aurenta kunyi aure...... To wallahi bari kaji infada maka wani abu...."


Katseshi hamood yayi cikin bala'i,


"Shut up..... Karka kawo min raini anan domin ni ba sa'anka bane, bilkisu kuma dolenka ka rabu da ita na aureta saboda ita ba matar karamin yaro bace irinka....."


"To ai karamin yaron yayi abinda Kai babban banza ka kasa yi, kawai kazo kana yaudarar matar mutum dan tsabar jahilci da dakikanci,da kasan kana son nata meyasa baka tsaya ka aureta ba sai yanzu da tayi aure zaka dawo kana bibiyarta.... To wallahi am warning u daga yau karka kuskura ka kara kirar min matata idan kuma ka ki ji bazaka ki ganiba..."


"Uban me zakayi idan ansake kiran matar taka? Me kake dashi? Waya san dakai a kasar nan, matsiyaci kawai irinka malam...."


"Zaka san koni waye duk ranar da ka sake gangancin kiranta, banza dan akuya kawai...." 


Katse wayar yayi sannan ya kasheta gaba daya ya jefa acikin aljihunsa yabuga Babur dinshi yayi gaba, gidansu yaje amma sam bai nunawa su ayiyah yana tareda matsala ba mamuh sai tsokanarsa takeyi wai yayan barunsa yau su zasu yanke suyi farfesu suci a matsayin abincin rana, shi dai sai dariya yake yajima agidan kafin yatafi da niyyar zuwa kasuwa wurin baba domin bai iskeshi agida ba yasamu yafita kasuwa acan ya shantake wurinsu baba wanda gaba daya shagunan dake layin duk na dattijai ne kamar baba shiyasa suke zamansu zama na mutunci ga yar majalissarsu nan gaban shagunansu karkashin wata bishiyar darbejiya, gefe fahad yakoma yayi zamansa yana sauraren hirar su baba irin tasu ta manya, rabonshi da yazo shagon baba yayi zama irin wannan har yamanta amma yau acan yayi sallar azahar ma nan aka kawowa su baba damammiyar fura cikin katuwar kwarya tasha sugar da gasasshen nama, cups aka fito dasu daga wani shago kowa yana diba sosai abin ya kayatar da fahad wato zama irin na iyayenmu da kakanni abin burgewa ne domin kowa yasan yanda zai zauna da kowa.


Abangaren bilkisu kuwa neman duniya tayiwa wayarta amma tarasa sai babbar amma sama ko kasa tarasa karamar, babu inda batayi checking ba agidan amma bata ganiba daga karshe dai tagane cewa fahad ne yadauka nan ta sake hawa ta cika tayi famm tana jiran dawowarsa amma shiru har hamood yakirata a daya layin nata dake kan babbar wayar yana fada mata irin zagin da fahad yayi masa hakan yasake tunzurata,shi kuwa fahad sai yamma yabar wurinsu baba yanufi shagonsu bayan magriba yakoma gida taso masa bilkisu tayi tamkar zata dokeshi,


"Bani wayata fahad, waye yace ka daukar min waya? Wai menene amfanin zama da mutumin da shi baya son zama dakai? Wacce riba zaka samu?"


Zama yayi saman kujera yana kallonta duk tabi ta hargitse,


"Bilkisu yakamata ki nutsu ki gane mai sonki da gaskiya, wallahi mutumin can yaudararki yakeyi, kiyi hakuri ki karbeni a matsayin miji nikuma nayi miki alkawari bazan baki kunya ba amma wallahi shi ba sonki yakeba dagaske nine nan masoyinki na gaskiya..."


"Ni ba dogon jawabi na tambayeka ba cewa nayi kawai ka sakeni babu ruwanka da rayuwar da zan shiga, babu ruwanka da yana sona ko sabanin haka sannan kabani wayata...."


"Anhanaki wayar kizo ki kwata ai kinada karfi......"


Yafada yana mikewa tsaye babu shiri taja da baya tana kallonsa, nunata yayi da dan yatsa,


"Bari infada miki fa kibar ganin ina kyaleki bafa tsoronki nakeyi ba kawai ina rabuwa dake ne saboda ina respecting dinki ko kina tunanin idan karamar yarinya nake aure age mate dina ko wadda na girma the same way zanyi treating dinta kamar yadda zanyi treating naki? amma wallahi idan kika kaini bango zaki fahimci bakida wayo zaki gane shayi ruwane, tunda kika zo gidan nan abinda kika gadama shi kikeyi ban taba takura miki ba to nima baki isa kin takura min ba, saki ne kuma baza ayiba idan kina iyawa ki saki kanki mana, haba kin takura min dayawa alhalin nikuma bahaka nake yimiki ba daidai da hakkina wannan ba taba bani akayi ba saboda Kin rainani amma ban taba takura miki akan hakanba bayan kuma inada karfin da zan kwata da karfin tsiya..."


Zaro idanuwa tayi tana hawaye cikeda masifa da jin haushinsa tace,


"Dama abinda ke ranka kenan so kake kayi min fyade to kazo kayi idan baka da imani..."


"Zaki gane banida imani sai ranar da na daureki nayi kaca kaca dake nayi round biyar akanki ranar ne zaki san banida imanin...."


Daga haka yawuce cikin bedroom yabarta anan tana sharbar kuka amma hankalinta yayi mugun tashi da jin kalamansa na karshe gaskiya idan fahad yayi mata haka ya cuceta idan ya rabata da martabarta bazata taba yafe masa ba kai wallahi muddin yanemi aikata mata abinda yafada saita raunata shi, zama tayi awurin taci gaba da risgar kuka har tsawon wani lokaci. Shikuwa fahad lokacin da yashiga daki dariya ma dramar su tabashi wato bilkisun nan shegen tsorone da ita sai son girman tsiya domin ya hango tsoronshi karara acikin idanuwanta da dukkan fuskarta gaba daya. Wanka yashiga yayi yafito yunwa na ciciyarshi domin bai wani ci isasshen abinci ba, daga shi sai gajeren wando da farar vest yafita yana janye singiletin zuwa saman kirjinsa sai shasshafa cikinsa yake yi,tana zaune inda yabarta bai ko kalleta ba yawuce dining kamar yadda ya tsammata batayi girki ba sai dafaffen shayin na'a na'a cikin tea flask wanda yanzu shi tamayar abincinta, babu yadda ya iya shi dinma tea din yasha ya dauki slice bread yashafa butter ajiki yaci yana tasowa ta mike tsaye duk da atsorace take dashi amma haka tayi karfin halin yimasa magana,


"Kabani wayata tun muna shaida juna...."


Banza yayi da ita yanufi bedroom,


"Wallahi ko kanaso ko baka so sai ka...."


Juyowa yayi yadawo da baya tana ganin haka ta dora hannu akai tafasa ihu saboda duk atunaninta abinda yafada dazu zai aikata, tsayawa yayi gabanta ya zuba mata ido,nan taja baya cikin sauri,


"Daina gudu karki damu yanzu babu abinda zanyi miki amma duk ranar da nahau kanki wallahi sai kin gane bakida wayo ai nafada miki sai nayi round 5, idan banda rashin tunani irin naki ya za ayi kinada aure ki zauna kina sauraron tatsoniyar wani jahili awaje? Me hakan yake nufi? To wallahi this is the last warning babu ke babu shi, ban son dakikanci da shashanci..."


Idonta fall hawaye muryarta adashe ta kalleshi,


"Fahad ni kake fadawa haka? Ni kake addressing da dakikiya jahila shashasha?"


Sauke idanuwansa kasa yayi sannan cikin sanyin murya yafurta,


"Am very sorry...."


Daga haka yajuya yashiga daki ya kwanta amma baya jin zai iya bacci adaren yau kamar yadda itama bilkisu baccin ya gagareta, inbanda sakawa da kwancewa babu abinda yakeyi har dare ya tsala. Kwana biyu haka nafaruwa har lokacin bai bata wayarta ba kuma bai sanarwa da kowa ba wani lokacin sai yaji kamar yafadawa koda wani daga cikin yayunshi ne amma sai wata zuciyar ta haneshi, gaba daya bilkisu ta hana kanta sukuni danma tana dan shakkarsa yanzu bata son yayi abinda yayita ikirarin zaiyi akanta, yau da safe yana daki kwance yamike yafito falo kwance ya sameta wayarta ya mika mata,


"Bilkisu ga wayarki.... Shi masoyi akoda yaushe yana kokarin ganin yayi abinda masoyinsa zai kasance cikin farin ciki koda kuwa shi din zai dawwama acikin bakin ciki, kamar yadda kika nema kije na sakeki saki daya...."


Cikeda farin ciki ta mike,batace komaiba tawuce bedroom taje tafara hada kayanta, duk abinda zata nema tazuba cikin babban akwati nan ta janyoshi tafito tana rikeda handbag dinta da akwatin,


"Ga akwatinan lefenka can harda sadakinka duk yana ciki..."


"Nabar miki saboda banyi miki dan nakwace ba..."


Bata sake cewa komai ba tasaka kai tafice daga cikin falon, wasu hawaye ne masu dumi suka zubo daga idanuwansa......



*Yar uwa littafinnan na siyarwa ne idan kina so ki biya saiki karanta*



*_Ummi Shatu_*    


© *HASKE WRITERS ASSO.*



*KAMAR DA WASA....!*  



   _*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*




    *28*



     ***Runtse idanuwansa yayi yana jin wani irin kunci acikin zuciyarsa, hawaye yayita yi awurin har saida yaji kansa yasoma sara masa sannan yasamu yatashi yana share fuskarsa da handkerchief din dake cikin aljihunsa, wayarsa kawai ya dauka sai keys dinshi yafita daga gidan dan baya jin zai iya sake awa daya acikin gidan tunda wacce yake zaune saboda ita bata nan, Babur dinshi yabuga yabar gidan bayan ya rufe ko ina, kai tsaye gidansu salim ya wuce yabude dakin salim din yashiga ya kwanta yana jin kansa na cigaba da sassara masa saboda kukan da yayi domin rabon da yayi kuka irin wannan har ya manta. Yana kwance yarasa meke yimasa dadi har salim yashigo ganin idanuwansa arufe yasashi zaton fahad din kila bacci yakeyi wannan dalilinne yasashi ficewa batare da yayi masa magana ba.


Har wurin 12 na rana fahad na kwance dakin salim saida yaji dan dama dama sannan yatashi yatafi gidansu, bai shiga cikin gidanba yabude dakinsu nada shida Abba yashiga yasake kwanciya babu wanda yasan yashigo gidan domin ko babur dinshi bai ajiye wurinda za aganiba, sai lokacin yasamu damar yin kukan bakin ciki nan yarinka yi kamar karamin yaro babu jimawa yafara jin zazzabi zazzabi ajikinsa amma dai yadaure bai tashiba har azahar tayi, anan daki yayi sallah dama wayarshi akashe take saboda bama yason wani ya kirashi, salim ne yabiyoshi gidan bayan yakoma dakinsa yaga baya nan sannan har gidansa yaje amma gidan akulle ga kuma wayarshi akashe. Yana kwance duk jikinsa nayi masa ciwo salim yashigo ganinsa kwance alamun ba kalauba yasa salim fara tambayarsa amma fur fahad yaki magana sai ko ido da yake bin salim dashi,ganin yaki magana yasa salim shiga cikin gida wurinsu ayiyah domin karbo musu abinci, ayiyah na tsame alalan da ta dafa cikin cooler ita kuma mamuh na dama kunun gyada suna aikinsu suna hirarsu, koda salim yafada musu abinci yazo karbar musu shida fahad wanda ke dakin abba basu kawo komai ba suka zuba musu yakoma wurin fahad, dakyar da fada da komai fahad yatashi suka ci alalan domin kwaya daya ma yaci sai dan kunun da ya kurba yakoma ya kwanta,juyin duniya salim yayi akan fahad yasanar dashi abinda ke damunsa amma yaki daga karshe salim yatashi yafita. Tunda salim yatafi fahad ke kwance ya rufe kofar dakin shiyasa babu wanda zai tsammaci cewar da akwai mutum aciki,ahaka yakwana yawuni har dare yayi sai dai idan lokacin sallah yayi yatashi yayi yakoma ya kwanta,har dare atakaice dai acikin wannan halin fahad ya kwana agidan babu Wanda yasani har saida safiya tayi lokacin da baba zai fita yazo saitin kofar dakin yajiyo fahad yana yin tari cikin mawuyacin hali, buga kofar baba yashiga yi wanda har karar bugun ta janyo hankalinsu ayiyah suka fito domin ganin meke faruwa, cikin mawuyacin hali yataso yazo ya bude kofar yana jin kamar zai fadi saboda rashin karfin da jikinsa ke fama dashi,wuri yasamu yazauna ya jingina da bango yana kallon su baba dake kokarin shigowa cikin dakin,


"Muhammadu... Ya akayi? Tun yaushe ka shigo cikin dakin nan?" Baba yafara tambayarsa cikin mamaki,


"Tun jiya ne baba..."


"Ikon Allah, to ya zakazo kashiga daki karufe kanka kai daya, ina matar taka?" Mamuh tafada cikeda mamaki,


"Na saketa...."


Ai gaba dayansu jin maganar tasa sukayi tamkar saukar aradu acikin kunnuwansu.


"Saki.....?"


Su ayiyah suka fada cikin razani har bakinsu na haduwa wurin tambayarsa,


"Muhammadu meyasa kayi haka? Meyasa ka yanke hukunci da kanka batare da ka tuntubemu ba?" Baba yafada cikin kwantar da murya,


"Baba kuyi hakuri dan Allah....."


Dukansu samun wuri sukayi suka zauna cikeda jimami, sunfi mintuna goma ahaka babu wanda ya iya yin magana zuwa can baba yaja gwauron numfashi cikeda damuwa yace,


"Fahad meyasa ka saki yarinyar nan yar mutunci yar gidan mutunci? Laifin me tayi maka haka...?"


Kasancewar dan jiri na daukarshi yasashi zamewa ya kwanta idanuwanshi taf da hawaye,


"Baba ni bata yimin laifin komai ba..... Kawai..... Kawai dai.... Kawai bazan cigaba da zama da ita bane...."


"Me? Fahad acikin hankalinka kake kuwa? Wannan wanne irin shashanci ne? Ina kataba ganin anyi haka? Kowa da yake zaune da abokin zamansa ba hakuri yakeyi ba?" Mamuh tafada cikin fada,


"A'ah yimasa ahankali.... Ai ba tatashi zamu biyaba, ni yanzu haka ta gidansu yarinyar zanbi inbaiwa mahaifinta hakuri sannan innemi bikonta adawo da ita dakinta tun abu baiyi nisa ba.... Saki nawa kayi mata?" Baba yakarashe maganar yana kallon fahad wanda idanuwanshi ke rufe,


"Baba babu aure atsakaninmu fa yanzu saboda saki.... Saki ukun...."


Ai tun kafin yarufe bakinsa su ayiyah suka rufeshi da fada ta inda suke shiga ba tanan suke fitaba shi baba sai shiru ma yayi yana saurarensu daga karshe ayiyah tatashi tafita cikin fushi, saida itama mamuh tafita sannan baba yadora da nasa fadan amma shi nasa cike yakeda nasiha, sun jima baba yana yimasa fada sannan yatashi yafita bayan yasanar dashi cewa gobe zaije gidansu bilkisu su gana da mahaifinta, agaba baba yasashi suka shiga cikin gida har dakin ayiyah yakaishi sannan yafita shikuma fahad ya kwanta nan saman daddumar dake shimfide a falon, sam ayiyah bata saurareshi ba bare ta kulashi sai can wurin azahar sannan tashigo wurinsa dauke da kwanon kunu wanda ta dama masa domin ta fahimci baici komai ba kuma yana tare da yunwa domin gashi nan duk yafige ya fita kamanninsa, yako ji dadin kunun nan domin da zafinsa haka ya zauna yasha da yawa sannan yakoma ya kwanta yana jin irin sarawar da kansa keyi masa.


A bangaren bilkisu kuwa tana fita daga gidan fahad sai kuma hawaye suka fara gudana daga idanuwanta, dama mata haka suke wani lokacin sune zasu nemi sakin da Kansu amma ana sakinsu kuma sai sufara kuka karasa dalilinsu, napep ta tare tahau tana kuka har sukaje kofar gidansu, da yake safiya ce Abba yana gida ko fita baiyi ba, ammah tana kitchen itada Rabi mai aikinta suna hadawa Abba abincin karyawa.


Fuskarta sharkaf hawaye tashiga cikin gidan shiyasa kallo daya ammah tayi mata tagane cewa ba kalau ba musamman ma da taganta da sanyin safiya irin wannan, barin abinda takeyi tayi suka shiga cikin falonta har lokacin bilkisu kuka take wanda ita kanta bata san dalili ba,


"Mai gado duk yanda akayi ba lafiya ba saboda idan lafiyace takawo ki bazaki taba zuwa da safiya irin hakana sannan bazaki shigo kina kuka ba...."


Hawayen fuskarta ta goge yayinda wasu ke kara zubowa,


"Ammah ya sakeni......"


Salati ammah tashiga yi tana karawa cikeda tashin hankali,


"Saki mai gado? Saki fa kikace? Meya hadaku? Wani abun kikayi masa?"


Girgiza kanta tayi tana hawaye,


"Babu abinda nayi masa..."


"To Allah yarufa asiri... Zauna nan zan kawo miki abin karyawa"


Tashi ammah tayi takoma kitchen suka karasa hada kayan karin kumallo ta dauki na bilkisu takai mata sannan ta dauki na abba tanufi wurinsa cikeda karfin hali take gudanar da komai, cikin farin ciki da annashuwa suka karya tareda Abba saida suka kammala sannan tayi kokarin sanar masa,


"Ga mai gado can fa tazo dazun nan babu jimawa...."


Shiru abba yayi yana kallonta,


"Lafiya kuwa?"


"Ba najin lafiya ce takawo ta gaskiya"


"Kira min ita naji"


Tashi ammah tayi takwashe kayan da suka gama amfani dasu tafita, yanda tabar bilkisu haka takoma ta sameta tana zaune sai faman goge hawaye take,


"Zo abbanku yana kiranki...."


Wata mummunar faduwar gabace ta ziyarceta, tunda aka fara rigimar sakin nan bataji ko darr ba sai yanzu saboda bata tanadi amsar da zata baiwa abba ba, gabanta na faduwa har suka shiga falon Abba,


"Uwata lafiya? Meke faruwa?"


Zama tayi gaban Abba,


"Abba sakina yayi..."


"Saki.... To laifin me kikayi masa?"


"Babu abinda nayi masa"


"Babu abinda kikayi masa?" Inji ammah, daga kai bilkisu tayi alamun ehh,



"To shikenan zan kira mahaifinsa dashi kansa yaron suzo aji mai yafaru saboda shi aure gyarashi akeyi akoda yaushe saboda yafi rabuwar tunda ba asan abinda Allah ya boyeba..."


"Abba saki ukune fa...."


"What...? Yana shaye shaye ne?"


"A'a baya shan komai"


"Amma har saki uku? Yanzu abinda yaron nan zaiyi mana kenan ina yimasa kallon mai hankali? Shikenan tashi kije, Allah yazaba miki abinda yafi zama alkhairi arayuwarki.... Kiyi hakuri kinji uwatah, wannan jarrabawa ce babu komai insha Allah zaki samu wanda yafishi"


Tashi tayi tafita har lokacin bata daina kukaba yayinda shikuma Abba da ammah ke can sunata jajanta abin gaba dayansu zukatansu babu dadi.Tana nan zaune falon ammah ta kifa kanta jikin kujera ammah tashigo cikeda damuwa ta zauna sannan daga bisani ta daga kai ta kalleta,


"Mai gado wannan kukan da damuwar babu abinda zai tsinana miki sai ko ma yakara miki damuwa dan haka ki tattara komai ki mikawa Allah lamarinsa sannan kibaiwa zuciyarki hakuri amma wannan kukan ba mafita bace.... Ga abinci nan dauki kici..."


Batayi musuba ta share hawayenta taja abincin da Ammah takawo mata soyayyiyar agada da kwai sai farfesun hanta da ruwan zafi, kadan ta dan tsakura tahada tea tasha ta mayar ta rufe kwanukan, kafin wani lokaci har ammah tasa angyara mata tsohon dakinta nada wanda yanzu yake arufe babu kowa aciki domin mai aikinta ba kwana takeba da safe take zuwa tatafi da daddare, komai da take bukata akwaishi acikin dakin gashi Rabi ta shirya mata kayanta cikin drewar, bata yarda sunyi waya da hamood ba domin suna tare da ammah duk tsawon yinin ranar sai dai wani lokacin idan tayi shiru sai tarinka tambayar kanta anya kuwa tayiwa fahad adalci? Anya kuwa tayi abinda yadace? Haka take ta yawaita yiwa kanta wadannan tambayoyin amma daga karshe tayi fatali dasu tana ji aranta abinda ta aikata daidai ne domin ita hamood takeso ba fahad ba. Tun aranar dukkan yan uwanta suka samu labarin abinda yafaru marar dadi wai auren bilkisu da fahad ya mutu, duk waya suka bugo mata suna tayata jaje da jimami kafin suzo gidan gobe, duk da yinin ranar tayishi sukuku ne amma da daddare tasamu kuzari domin sunyi waya da hamood ta zayyane masa dukkan abinda yafaru yayinda shikuma yace da zarar ta kammala iddah zai fito sai maganar aure.


  Fahad haka yawuni kwance yana ciwon kai sai daf da magrib yasamu yayi wanka bayan ayiyah ta dafa masa ruwan zafi gashi throughout baici komai ba sai ruwan kunu da yaketa sha sama sama, gaba daya yayunshi fada suka rinka yayyafawa lokacin da labarin abinda yafaru yaje musu shi dai yaki magana domin shi kadai yasan abinda yake ji. Yana fitowa daga wanka yadauki t shirt acikin kayan abba yasaka da wando yayi salla ya kwanta har saida baba yashigo sannan yaga ayiyah tashigo rikeda maganin ciwon kai da balangu wanda baba yakawo, agaba tasaka shi har saida yaci naman yasha magani sannan tafita tabarshi babu jimawa bacci ya daukeshi ko sallar ishah bai samu damar yi ba. Washe gari ma da ciwon kan yawayi gari ga rashin iya cin abinci dake damunsa aranar da salim yazo yasan komai na daga abinda yafaru amma fahad bai sanar dashi gaskiyar abinda yafaru ba kawai dai yafada masa cewa sun rabu da bilkisu rabuwa ta har abada. Atakaice dai saida fahad yayi kwana uku akwance ganin haka yasa su ayiyah matsanta masa akan yaje koda chemist ne idan bazaije asibiti ba, wanka yayi ya shirya cikin kayanshi wanda salim yaje ya debo masa jiya, riga kalar ruwan toka mai botira sai wando rouser baki, ahaka ya daure yafita zuwa chemist din daga can kuma yawuce shago iya tj da customers dinsa guda biyu wadanda ke jiran yagama yimusu dinkinsu yabasu kadai yasamu acikin shagon, zama yayi kan keken hamza bayan sunyi musabaha da tj, yana nan zaune yana hango mutane daketa kaiwa da kawowa awaje ya hango husnah wacce tafito yin cefane direct shagon tashigo ko cefanen bata kai ga yiba, fuskarta da alamun damuwa ta karaso gabansa ta zauna,


"Haba ya fahad.... Ina kashiga kwana biyu dan Allah? Gaskiya ka sani acikin damuwa wallahi...."


Tagumi ya rafka yana kallonta,


"Husna banida lafiya ne...."


"Ayyah my prince sorry.... Tun yaushe? Meke damunka? Kaje asibiti?" Tajero masa wadannan tambayoyin cikin damuwa,


"Yanzu ma haka daga chemist nake nabiyo ta nan...kinga magungunan da nakarbo nan....."


"Ayya sannu... Muji... Da zazzabi?"


Tafada cikin sanyin murya tana kai hannu goshinsa zuwa wuyansa, baiyi yunkurin hanata ba har tagama tattabashi domin jikinsa akwai alamun fever kawai dai bai gama sauka ajikinsa bane,


"Sorry bari naje kasa nasamo allura nayi maka saboda bana so zazzabin yarufeka...."


Baiyi magana ba sai kai da yadaga mata kawai nan tayi maza ta sauka kasan plaza din tashiga wani pharmacy tayi amfani da kudin hannunta tasiyo alluran da take bukata guda uku takoma wurin fahad lokacin tj yafita masallaci sallar azahar customers dinsa kuma sun tafi, zama tayi gabansa tana hada allurar sai faman girgiza kai takeyi alamun tausayawa,


"Ya fahad kayita zama da ciwo ajikinka tun tuni baka nemi magani ba...."


Hannunshi daya ta kama ta yimasa allurar a damtsensa sannan takara yimasa wata daga bisani takoma daya hannun tayi masa guda daya.Jiri yaji yafara daukarsa nan yayi gaggawar riketa gudun kada ya fadi ai kuwa ta riku a hannun maza domin ji tayi kamar zai ballata, saida tajira allurar ta dan fara sakinsa sannan ta fita takira mai napep yazo har gaban plaza din ya tsaya, cikin shagon takoma ta kamo fahad suka fito dai dai lokacin da tj yadawo daga masallaci shine ya rike fahad din yataimaka masa yakaishi cikin napep, tare da husnah suka tafi gidansu yayinda shikuma tj yakoma shago, har gida husnah ta rakashi amma bata shiga cikiba daga waje ta tsaya bayan taga shigarshi gida itama tajuya tatafi.


Sosai bilkisu ta ware ta sake bata saka damuwar komai aranta ba dan kamarma harsu maama sun fita damuwa amma ita ko ajikinta saboda sunata shirya yanda al'amuransu zasu kasance itada hamood sannan kullum sai yabita office sunsha hirarsu ta soyayya shiyasa basuda matsalar komai, bayan sati biyu da faruwar lamarin suka shirya zuwa kwaso kayanta agidan fahad itada su maama dama shi fahad rabonsa da gidan tun ranar da bilkisu tasa kafa tabar gidan dan hatta kayan sawarshi ma da sauran kayan bukatunsa na yau da kullum sai salim ne yaje ya debo masa shiyasa ranar da zasu kwashe kayanma sai salim dinne yaje yabude musu gidan tunda gidansu fahad din suna da masaniyar za azo adebi kayan saboda baba har gidansu bilkisu yaje suka tattauna da Abba akan maganar tareda baiwa juna hakuri akan abinda yafaru, wuni su bilkisu sukayi suna aikin tattare kayan zuwa karfe uku na yamma sun kwashe komai babu abinda suka bari sai akwatunan lefen fahad kamar yadda ta sanar dashi tun farko, salim bai bar kayanba ya kwashesu zuwa gidan anty fauziyya can yabarsu sannan yakoma wurin fahad wanda ke kwance ciwon kirji da ciwon kai na addabarshi,


"Salim ta kwashe komai nata ko? Dama nasani..."


Kallonsa salim yayi cikin tausayawa,


"Wai abokina ya akayi hakan tafaru? Meyasa ka saketa? Yanzu baku saniba ko kilama tanada juna biyu kuma katashi ka saketa...."


Girgiza kai fahad yayi,


"Bata da wani ciki saboda babu...."


Sai kuma yayi shiru bai karasa ba,


"To ai laifinka ne, danme zaka zuba mata ido kazauna kana kallonta? Da ace kayi abinda yadace da tuni yanzu wallahi kuna tare tunda ko bata zauna dan kaiba dole ta zauna dan cikin jikinta...."


"Salim mubar wannan maganar kar zuciyata tafashe..."


"Allah ya sawwake yabaka lafiya, amma yakamata kayi gaggawar cireta aranka kamar yadda itama tayi..."


Shiru fahad yayi masa domin shi kadai yasan abinda yakeji, haka yayita murkususu har zuwa dare danma tare da salim din yanzu suke kwana, karfe 9 nadare a asibiti tayi musu saboda tsananin da jikin fahad yayi wani zazzafan zazzabine ya mamayeshi inbanda karkarwa babu abinda jikinsa keyi ga ciwon kirji dake barazanar tarwatsa mata hakarkari wannan dalilinne yasa su baba kaishi asibiti shida salim, babu bata lokaci aka bashi gado nan aka shiga kara masa ruwa babu ji bare gani saboda jikinsa yagama galabaita sosai.......



*Idan har kin san baki biya ba kiyiwa kanki adalci nima kiyi min karki karanta.*




*_Ummi Shatu_*    


© *HASKE WRITERS ASSO.*

_(Home of expert & perfect writers)_




*KAMAR DA WASA...!*  




  _*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*




  *29*




      ***Tunda aka kai fahad asibiti yake cikin mawuyacin hali gaba daya bai san a inda yakeba bare yasan wanda ke kansa, babban likitan da yake dubashi sai faman fada yake tayiwa su baba yana cewa ya za ayi abar karamin yaro kamar fahad yakamu da ciwon hawan jini wanda ke barazanar taba kwakwalwarsa da lafiyar jikinsa? Domin acewar likitan Allah ne kadai ya takaita abun aka kawoshi asibiti dawuri amma da ace ba akawoshi tun wuriba to irin wannan ne kesawa mutum yana tsaka da tafiya ya yanke jiki yafadi shikenan yahadu da babbar lalura dan haka yazama dole asan yanda za ayi yanisanta kansa da damuwa da yawan tunani domin jininsa yayi masifar hawa hawan da ba aso dan haka yanzu dole akan magani zasu dorashi domin lalurar ta rigada ta kamashi. Daga ayiyah har mamuh kuka suke yi jin wai dan karamin dansu yahadu da cutar zamani ta hawan jini tunda ko su da suke tsoffi basu gamu da irin wannan ciwonba lallai wannan jarraba ce daga Allah, kullum a asibitin suke wuni suna kula da fahad, salim da ya Abba wanda yazo gida saboda dan break din da suka samu na good friday Easter monday, suke kwana awurin fahad sannan suna kula dashi, husnah ma kusan kullum sai tazo asibitin ta dubashi wani lokacin ma har girki take iyo masa, shi dai fahad tunda yafara bude ido dishi dishi yake kallon kowa baya ganin mutane clearly sai ahankali sannan ganinsa yasoma washewa har yadawo daidai acewar Dr Allah ne yarufa asiri abun bai shafi ganinsa ba, tunda yafara gane mutane bai furta koda kalma daya ba har yaji dan sauki, karin ruwannan da aketa yimasa har yagaji dashi gashi duk jikinsa ciwo yake yimasa saboda alluran da aka huhhuda jikinsa dasu, satinsa biyu a asibiti aka sallameshi bayan andorashi akan magani sannan duk karshen wata zai rinka zuwa yana ganin likita, da yamma aka sallamesu suka tattara suka koma gida. Wanka yashiga yasamu yayi yafito Abba da salim na zaune saman katifa salim na karanta labaran da BBC suka saki akan Facebook,yarfe hannu fahad yayi domin har lokacin hannunsa na dama akwai cannular ajiki wadda har hannun ya dan kumbura kadan musamman ma wurin da aka saka cannular din, zama yayi gefen katifar yana duba kayan da zai saka yana ji aransa dole yabar garin kano domin yayi masa zafi bazai taba iya cigaba da zama agarinba,


"Yazama dole ma inbar garin nan wallahi....."



Dagowa Abba yayi ya kalleshi sannan yagyara kishingidar da yayi agefen katifar,


"Kamar ya?"


"Ya Abba wallahi bazan iya cigaba da zaman garin nan ba.... Gaba daya garin yafita akaina"


"To ina zaka tafi?" Salim ya bukara yana kokarin tashi zaune,


"Salim karatu zan koma...., kuma ba arewa ba, kudu zan tafi idanma son samune inbar kasar gaba daya ko Niger ne intafi"


"Fahad kenan sai hakuri fa rayuwar nan, kayi hakuri kadauki abinda yafaru dakai a matsayin jarrabawa...."


Jin abinda yaya Abba yafada yasashi yin murmushin dole shi kansa ajikinsa yana jin irin ramar da yayi duk yadawo wani shafal shafal dan har yakasa da akiba, bai sake magana ba yadauki bakar round neck t shirt mai gajeren hannu yasaka sannan yasa blue din wando yamike yana laluben turarensa yana jin zuciyarsa na suya,


"Bilkisu wallahi kin yiwa zuciyata tabon da bazai taba gogewa ba har abada......" Yafada acikin zuciyarsa yana kokarin feshe jikinsa da turare, yana gamawa yanufi kofa zai fita domin so yake ya dan fita ya zagaya ko zai ji karfin jikinsa saboda yanzu kam baida wani karfi na azo agani,maganar salim ta dakatar dashi daga yunkurin fitar da yayi niyya,


"Lover boy ga husnah fa na magana a whatsapp....."


Komawa yayi da baya yakarbi wayar yana duba sakon nata kamar haka,


_My prince ya jikin? Kasamu kayi wankan kaci abinci....? Dan Allah karka zauna da yunwa_


Murmushin karfin hali yayi yana kallon salim da ido salim yayi masa alamar tambaya, daga girarsa guda daya yayi ya tsuke baki har lokacin fuskarsa dauke da murmushi, dariya salim yayi,


"Abokina kenan.....,husnah fa kullum idan taje dubaka sai tayi kuka"


Kafin fahad yayi magana Abba yatashi yafita yabar musu dakin gaba daya dan suji dadin tattaunawa dakyau, su dinma basu wani jima acikin dakinba suka fita, da kafa suka dan bi lungunsu fahad har zuwa bakin titi domin fahad ya ware kafarsa sai magrib sannan suka koma gida. Cikin kwana biyu jikinsa ya dan warware yaji dama dama amma kuma har lokacin raunin dake cikin zuciyarsa bai warkeba kawai yana daurewa ne sannan yaji dadin cewa baba saki uku yayiwa bilkisu domin da yace saki dayane yasan dole atursasasu sake  zama da juna koda kuwa bata so shikuma bazai so hakanba.


***


A bangaren bilkisu kuwa tana kammala idda abba yace hamood dinta yafito saboda kowa agidan yasan hamood hatta iyallo mutanen garko tasan da zaman hamood domin har gida yaje ya gaisheta yakai mata sha tara ta arziki, khulsum itama ba abarta abayaba wurin yiwa hamood campaign saboda tasan asalin soyayyarsu tun farko duk da bataso rabuwar bilkisu da fahad ba kuma hakan bawai yayi mata dadi bane to amma babu yadda za ayi tunda bilkisu tace saki ukune shima kuma fahad din kamar hadin baki saki uku yace yayi mata. Cikin kankanin lokaci hamood yatura uncle dinsa yaje wurin Abba nan zancen aure ya kullu domin shi Abba baya son zaman zawarcin nan shiyasa yakeso shima ayi bikin da gaggawa, shima senator barewa baija lokacin da tsawo ba yace nanda wata daya sai asha biki sannan kar akai bilkisu da ko cokali yadauki nauyin komai saboda gaba daya 'yayansa ne, aifa nan bilkisu aka shiga shirye shirye da gyare gyaren jiki kowa na gidan cikin farin ciki yake saboda bilkisu baza tayi dogon zawarci ba su elmustapha ne kadai da suka zo hutu basu ji dadin aurannan da zatayi ba domin haka kawai sukaji jininsu bai hadu da na hamood dinnan ba, biki saura sati biyu aka kawo lefe akwatuna goma masu tsada da kyau komai naciki na dunbin kudine nan shirye shirye suka sake zafi babu kama hannun yaro domin hamood yace har dinner zasuyi domin wajibine suyi kara'i. Cikin kankanin lokaci aka kammala komai bilkisu ansha gyara iya gyara duk wani gyara na amare tasha shi sannan tasha tukudi kamar babu gobe domin iyallo ce tazo dashi galan galan tun ana saura sati daya biki dama burinta taga bilkisu tayi sure bawai tasake zama agida ba shiyasa farkon mutuwar auren tazo tayita zuba masifar da kowa na gidan saida yayi la'asar kuma tace lallai lallai bilkisu tafitar da miji tana gama idda aure zatayi wannan dalilinne yasa lokacin da aka gabatar mata da hamood tarinka taka rawar murna.  Ranar juma'a aka daura aure ranar asabar akayi yinin biki kuma aranar za akai amarya dakinta sannan za aje dinner, daga amarya har ango farin cikinsu bazai misaltu ba da misalin karfe 8 aka tafi wurin dinner sannan daga can za awuce akai amarya, amarya da ango sunsha dark purple din kaya sunyi kyau mutuka kuma sun burge, har karfe 10 ana wurin dinner din daga can aka raka amarya sannan kowa yasan inda dare yayi masa, gidan amarya yasha kyau a unguwar sabuwar G R A, babban gidane mai dauke da upstairs kasa falo da kitchen da dining area da bedroom guda daya sai sama mai dauke da corridor da kuma bedrooms guda biyu, gaba daya yanda aka tsara gidan yaburge bilkisu, bata wani jima ita dayaba hamood yashigo dauke da kaji da kayan motsa baki, zama yayi kusa da ita yana murmushi,


"Sweetheart yau dai burinmu ya cika, muna yiwa Allah godiya..."


Murmushin itama tayi batare da tace komai ba, kamar yadda addini ya tanadar saida sukayi salla raka,a biyu sannan suka zauna zaman ciyar da juna abinda yashigo musu dashi sunayi suna yan wasanni irin na masoyan da zuka jima acikin tafkin kauna suna linkaya, dakinsa yakoma domin yin shirin bacci kafin yadawo tuni itama tashirya cikin nata kayan baccin masu daukar hankali, tana kwance lamo yashigo sanye da riga da wando dark blue yazo ya kwanta abayanta tareda dora kansa bisa nata, ahankali yake yimata tafiyar tsutsa agashin kanta wanda yasha gyara dan gaske, sun dan fara nisa kadan cikin kogin so suka fara jiyo bugun kofa mai sa firgici wanda ke nuni da ba lafiyaba domin Wanda ke yin bugun tamkar zai balle kofar haka yake yi, cikin bacin rai tare da jan tsaki hamood yatashi yamaida rigarsa yafita dan ganin ko waye itama batayi kasa agwiwa ba tabi bayanshi bayan ta mayar da kayanta, tana zuwa falon kasa yana bude kofa, wata farar matashiyace tashigo taci daurin dankwali irin na yan duniya gaba daya zubinta ma irin na yan bariki ne, wani kallon baki isaba tasoma watsawa bilkisu daga sama zuwa kasa sannan tamaida dubanta ga hamood,


"Meye haka? Me zan gani ni wasila? Dama munyi haka dakaine?..."


"Yi hakuri wise bakya ganin yanzu dare ne?"


"Ina ruwana da wani dare? Malam bafa haka mukayi dakai ba.... Wato kai ga ango ko jikinka sai rawa yake zakasha angonci, to ayi angoncin nagani..... Wuce mutafi...."


Matsawa sosai bilkisu tayi tana karewa matar da hamood yakira da wasila kallo wacce ahaife bazata girmeta ba,juyawa yayi ga bilkisu cikin sanyin murya yace,


"Bilkisu yi hakuri bari naje nadawo, karki damu zuwa safe zan dawo...."


Wani kallo bilkisu tayi masa sannan tamaida kallonta ga wise wacce ke tsaye tana karkada kafa ta taro dan kwalinta gaban goshi alamun no respect,


"Haba hamood ina zakaje awannan daren? Ita wannan din wacece? Menene matsayinta agareka? Meye hadinka da ita da har zatazo ta fitar dakai daga cikin gidanka a wannan daren....?"


Bai samu damar amsa mata tarin tambayoyin da ta jero masa ba sai kwaya daya inda yafurta,


"Matata ce....."


Kafin bilkisu tayi magana wise ta rigata,


"Kana bata min lokaci fa..."


Bai sake bi takan bilkisu ba yawuce gaba wise na biye dashi kamar wani danta, akan idon bilkisu suka shiga motar wise suka bar gidan, kallonta ta maida kan agogo karfe 1 saura nadare......


 

 *Dan Allah idan har kin san baki siyaba karki karanta min littafi domin na siyarwa ne.*



*_Ummi Shatu_*    



© *HASKE WRITERS ASSO.*



*KAMAR DA WASA....!.*  




  *_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*




     *30*




     ****Zama bilkisu tazame tayi awurin tana dafe kanta da hannunta guda daya wanda yasha kunshi radau,


"Wannan wacce irin masiface? Adaren amarcina za azo atafi min da miji abarni ni kadai....."


Agogo tasake kalla nan ta kura masa ido kamar tana son gano amsar tambayarta awurinne domin ko kiftawa batayi, tsabar bakin cikima ko tsoro nemarsa tayi ta rasa dadinta daya dai gidan akwai mai gadi, ganin zaman da take babu abinda zai amfana mata yasata tashi dakyar kanta yayi mata masifar nauyi taja kafarta wadda ta tari jini saboda tsabar zama atakure tawuce cikin bedroom, tana kwanciya idanuwanta suka kai kan wayoyin hamood guda biyu dake kashe ajiye kan bedside drewar sai agogonshi na azurfa wani abu taji yataho ya soke mata zuciyarta sai kuka kamar anbude bakin fanfo, har asubah takai tana hawaye domin tarasa gane da wacce kalma zata kira wannan abinda yafaru shin da wulakanci zata kirashi ko kuma da tozarci?.


Har asuba bata samu ta runtsa ba saida tayi salla ne bacci ya kwasheta nan kan rug din da tayi sallar, bacci tayi mai cikeda mafarkai daban daban wanda takasa tunawa bayan ta tashi, wanka tayi ta shirya duk zuciyarta akuntace domin tana cikin matsananciyar damuwa, sake kwanciya tayi domin bata san me zatayi ba kwata kwata ahaka har rana tafara yi nan yunwa tasoma damunta, fita tayi zuwa falon dake kasa,abubuwan da hamood yashigo dasu adaren jiya su ta dan kakkarima taci tsabar bakin ciki ko wayarta bata kunna ba domin bata bukatar kowa ya kirata. Karfe sha biyu da wani abu su iyallo sukazo itada dasu Hindu sun rakota zatayi ma bilkisu sallama saboda ayau zata koma garko, su elmustapha ne suka kawosu shiyasa bilkisu ta dan samu ta warware daga kuncin da take ciki domin ko ba komai ganin yan gidansu yasata farin ciki,


"To shikuma mamuda yake ko hamidan yana ina?"


Iyallo tajefeta da tambaya tana tsaka da kwankwadar lemon kankana mai sanyi, saida kowa yayi dariya jin sunan da iyallo ta kakabawa hamood,


"Yanzun nan yafita iyallo dan bamu san zakuzo bane ma da babu inda zaije sai ya jiraku...."


"Allah sarki ai babu komai, nidai abinda zan fada miki shine kinga dai ke yanzu ba yarinya bace, dan haka ke zaki yiwa kanki fada basai kin jira wani yayi miki ba, kiyi hakuri ki zamanki adakinki kamar sauran yan uwanki..... Allah yakawo kazantar daki, mai gado kema Allah yabaki magaji, Allah yabaki yara masu albarka kisamu na aike....." Ajiye lemon hannunta tayi tahau matsar ido nan maama ta dunguri meenah suka hada kai suna kuskus,


"Hajiya iyallo to kuma menene abin kuka?... Kufa matsalata daku bakwa rabo da koke koke...." Inji emustapha,


"Ai sabgar mata akwai ban haushi malam.... Komai abin kukane... Suyita yiwa mutane kuka akan abinda bai kai yakawo ba" El'ameen yakarbe zancen,


"Kai naci gidanku.....kai mai sunan malam jakar ubaka..."


Dariya el'ameen yayi yamike yana gyara earpiece din dake kunnensa,


"Oho dai idanma kin zagi ubana ai danki kika zaga...."


Salati iyallo tafara yi tana fadan wai ita ba danta ta zaga ba domin danta dan albarkane yakaita hajji yakaita umarah sannan yagina mata gida mai kyau dan haka babu abinda zatace dashi sai Allah yayi albarka, duk da bilkisu natare da damuwa amma caftar su iyallo da jikokinta tasata nishadi ba kadan ba, kayan zakin da suka kawo mata cikin bokitai suka shigar mata kitchen sannan suka tafi ai kuwa ji tayi kamar ta dora hannu aka tafasa ihu. Har kofar gida ta rakasu saida taga tafiyarsu sannan takoma ciki, kwanciya ta sake yi saida aka kira sallar azahar sannan tatashi, tana cikin yin sallar taji zuwan wasu bakin shiyasa ta hanzarta ta idar tafito, yan gidansu hamood ne da matar uncle dinsa da yaran gidan guda biyar sudinma sallama suka zo yimata saboda zasu koma birnin tarayya ayau, basu wani jima ba shiyasa ko snacks din da takawo musu basu ciba sai packaging dinshi tayi musu suka tafi dashi. Ahaka takarasa wuninta cikin rashin walwala da bacin rai har dare babu hamood babu labarinsa gashi yabar wayoyinsa duk agida bare ta tuntubeshi taji a ina yake. Daren yauma sai bacci barawo amma tajima batayi bacciba tanata sakawa da kuncewa, washe gari ma hakance ta kasance hamood shiru har kirjin azahar dai dai lokacin khulsum tazo tanata tsokanar bilkisu ita dai bata da tacewa saboda damuwar dake cikin ranta tafi gaban kwatantawa,


"Wai ina angonne inyi masa tsiya, shikenan sai ya boye min kawata ko awaya inkasa samunta?"


Murmushin yake na dole bilkisu tayi tace,


"Ai kuwa yafice tun sassafe saboda yanada uzuri kin san kamfanin saida motocin uncle dinsa shike kula dashi to shine aka kirashi...."


"Ahhh cewa zakiyi yatafi yasamo muku kudi dai labour..."


Dariyar da ta tsaya a iya fatar baki kadai tayi,da taimakon khulsum suka dan girka abinci bayan tabawa mai gadi yaje ya iyo mata cefane, har yamma khulsum na gidan tana bata labarin saurayinta wanda take son aure, ita dai bilkisu kawai tana zaune ne amma gaba daya tunaninta na ga hamood kacokan tana ta son sanin inda yatafi, daf da magriba khulsum tatafi nan kuma taci gaba da zaman kadaici da damuwa.


Wasa wasa saida hamood yayi kwanaki hudu sannan sai gashi da ranar Allah yashigo yasha farar shadda kal sabuwa fil da hula harda dan farin glashinsa na ido dayake shima kyakkyawane babu laifi domin black beauty ne ga hanci, mikewa bilkisu tayi cikeda fushi ta juya masa baya alamun tana cikin bacin rai, kamota yayi yadora akan cinyarsa,


"Hamood ashe haka amana da soyayya suka ce?"



"Sweetheart.... Kiyi hakuri.... Tun farko ban sanar dake cewa inada mata ba wallahi babu yanda zanyi ne.... Hadin iyaye ne shiyasa kawai ban fito na fada miki ba...."


"Ni hamood ba wannan ne damuwata ba, damuwata shine yaza ayi adaren amarcinmu wata mata tazo ta tisaka agaba tatafi dakai kuma wai kabita baka dawoba saida ka shafe kwanaki hudu..... Saboda Allah kun yimin adalci?"


"Kiyi hakuri sweetheart...ai ban sanar da ita bane shiyasa amma nayiwa tufkar hanci hakan bazata kara faruwa ba...."


Duk da haka nunawa tayi bata hakura ba nan yasoma lallashinta wanda daga karshe lallashin yasoma canja salo domin gaba daya ya canja akalarsa izuwa wani fannin daban, bedroom din dake cikin falon suka yiwa shigar bazata domin farantawa junansu, al'amari yafara nisa amma kuma sai me kwata kwata hamood ji yayi baida kuzarin da zai iya aiwatar da wani abu awannan lokaci domin gaba daya halittarsa bata koda motsi tamkar lagwanin da yayi shekara acikin kalanzir yayi laushi haka yazama nanfa wani tashin hankali da damuwa da bacin rai suka dirar musu daga bilkisu harshi domin kowa anasa hasashen laifin dan uwansa yake gani kokuma matsalar kowa gani yake daga daya bangaren ne banasa ba.......




*Kamar da wasa na siyarwa ne, me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*



*_Ummi Shatu_*    


© *HASKE WRITERS ASSO.*




*KAMAR DA WASA....!*  




    _*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*




    *31*




      ****Cikin fushi da bacin rai hamood yafice daga cikin dakin yakoma falo daga shi sai gajeren wando, sam batayi yunkurin binsa ba saboda ita dinma cike take da bacin rai, kusan mintuna ishirin ta debe ahaka kafin tatashi saboda jin anata kiraye kirayen sallar la'asar, lokacin da tafito falon abinda idanuwanta suka gane mata yayi masifar razanata, hamood zaune yadora daya akan daya idanuwansa jajur hannunsa rikeda tabar sigari yana busawa shiyasa gaba daya falon ya turnuke da warin sigarin,


Gabansa taje gabanta sai faduwa yake zuciyarta na bugawa,


"Hamood.... Meye haka kakeyi? Subhanallahi dama kana shan sigari.....?"


"Idan raina yabaci ba.... Ai dole nasha sigari mai gado... Irin wannan zafi da kika hada min ai yazama confirm in dan wartsake...."


Gaba daya ita rasa ma abinda zatace tayi saboda mamaki da takaici shiyasa kawai tawuce sama tashiga dakinta tayi wanka tazo tayi salla tana idarwa ta sauko amma wayam babu hamood wato har yasake komawa inda yafito batare da yayi mata sallama ba ko? Ta ayyana hakan acikin ranta, sosai taji hakan yayi mata ciwo, kitchen tawuce ta debo snacks tazo ta zauna taci. Zaman kadaici tayi har dare yayi tanata zuba idon hamood shiru gashi bai dauki wayoyinshi ba kai asalima tunda yashigo gidan bai leka ko cikin bedroom ba iyakscinsa bedroom din da ke kasa, har lokacin bacci yayi taje ta kwanta hamood bai shigo cikin gidanba ita kanta gaba daya takasa bacci daren wannan rana sai misalin karfe 12 nadare hamood yashigo cikin gidan cikin yanayin da yakara tsorata bilkisu game dashi domin acikin maye yashigo har dakinta yafado yana hada hanya yana layi,


Cikin zazzare ido tamike zaune tana kallonsa bakinta yana rawa,


"Hamood.... Innalillahi.... Wai dama kana shaye shaye ne? Haba hamood meyasa zakayi min haka? Wannan wacce irin rayuwace?...."


Cikin maye ya nunata da dan yatsa,


"Babu ruwanki da rayuwata..... Ko kabarinmu daya? Bana son takurawa...."


Mikewa tsaye tayi cikeda damuwa da bacin rai,


"Ai ko ba kabarinmu daya ba yazama dole infada maka gaskiya amatsayina na abokiyar zamanka, yau kwata kwata kwananmu hudu zuwa biyar da aure amma gashi nan munanan dabi'unka sun fara bayyana... Seriously am highly disappointed....."


Ai kafin tarufe bakinta ya dauketa da wani gigitaccen mari, dafe kuncinta tayi cikeda mamaki baki abude tana kallonsa,nan ya nunata da dan yatsa,



"Idan kika kara zagina sai na ballaki....."


Bai kara magana ba yafada saman gadonta yakwanta rub da ciki, ko takalmin kafarsa bai cireba, gaba daya tayi mutuwar tsaye ita kam ganin irin marin da hamood ya zabga mata she can't believe wai yau itace acikin wannan rayuwar itada hamood, tajima tsaye kamar wadda aka kafa kafin tanemi wuri ta zauna tana kallonsa yanata sharar baccinsa cikin maye,


"Ohhh Allah.... Ya Allah kayi min maganin wannan masifa...."


Dakyar da sudin goshi tasamu bacci ya dauketa saboda tajima bata samu bacci ba kai rabonta da bacci isasshe kuma mai dadi tun kafin bikinta. Asubar fari ta tashi tayi salla tsakanin mata da miji sai Allah hakan yasa tasoma tashin hamood akan yatashi yayi salla amma fafur yaki tashi daga karshe ma da ta matsa masa afusace yabude ido yadago ya daka mata tsawa,


"Malama wai sallar nan ubanki zan yiwa? Karki sake ki kara tashina..."


Jin abinda yace yayi mutukar razanata, wai ita hamood ke fadawa haka? Rabuwa dashi tayi saboda taga kamar har lokacin mayen bai gama sakinsa ba, anan ita kam taci gaba da zama har gari yagama wayewa, wanka tayi tashirya ta sauka kasa ta shiga kitchen duk ranta adagule zuciyarta a cunkushe wato dama ance zauna da mutum kaga halinsa wato shi hamood wadannan ne nasa halayen kenan? Ahaka ta kammala hada breakfast dinta tanata zancen zuci bayan ta kammala takai kan dining takoma sama lokacin karfe goma tawuce, sai lokacin hamood yatashi bai ko kalleta ba yashiga bathroom babu jimawa yafito yawuce dakinsa domin shiryawa bin bayansa tayi agabanta yashirya yasake fitowa tana ganinsa baiyi salla ba nan abun yasake daure mata kai, kai tsaye dining yaje tana biye dashi yaja kujera ya zauna itama haka,


Chips yasoma ci da spoon yana kunna wayarsa wadda bilkisu bata san da itaba sai yau,


"Hamood ina kwana....?" Takatse shirun nasu,


"Lafiya lau sweetheart...."


Shiru dukkaninsu sukayi sai zuwa can ta saki ajiyar zuciya dama ita ba abincin take ciba kawai tana jujjuyashi ne,


"Hamood meyasa dan girman Allah ka dauki dabi'ar da ban sanka da itaba ka yabawa kanka....? Hamood dama kana shaye shaye ne? Jiyafa da daddare har marina kayi sannan da asuba ka zagi ubana, gashi yau ko sallar asubah banga kayi ba...."


Saida ya ja wasu seconds sannan yadago ya kalleta,


"Kiyi hakuri sweetheart wallahi duk wadannan abubuwan ban san lokacin da nayisu ba, amma hakan bazai sake faruwa ba, jiyane kin bata min rai dayawa wallahi, duk yanda akayi tsohon mijinki dinnan banzan yaron nan baiso aurenmu dakeba shiyasa yayi min asirin da zan kasa kusantarki..."


Ajiyar zuciya taja ta sauke tana kallonsa,


"Bana tunanin fahad zai aikata abinda kake fada nidai ashawarata kaje asibiti sannan ka binciki wannan matar taka...."


"Matata bata aikata komai ba bilkisu ni nafi danganta matsalar dake tunda ita ko yaushe naje gareta lafiya lau nake gabatar da al'amurana kinga kuwa idan hakane matsalar daga gareki ce..."


Shiru tayi saboda ta fuskanci hamood bazai taba ganewa ba tunda bai san kaidin mataba, har ya kammala babu wanda yasake cewa komai mikewa tsaye yayi,


"Ni nafita.... Zanje office"


Bai jira cewarta ba yafice, tagumi ta rafka bayan tasauke ajiyar zuciya, ranar ma bai dawo gidanba sai 12 amma ba acikin mayeba.



Haka dai aka cigaba da zaman doya da manja domin ta fuskanci salla kwata kwata bata dameshi ba gashi da saurin fushi abu kadan zai hau yafara zagin mutun ko zagin iyayenshi, satinta biyu agidan ranar da yamma daf da magriba sai gashi rikeda babbar trolley wasila na biye dashi tasha attach da wani siririn mayafi, tana zaune afalo suka shigo dama gama girkinta kenan tayi tuwon semo miyar agushi wacce taji busasshen kifi, ganinshi tareda wasila abin yayi mutukar Sosa ranta shiyasa ta dauke kanta. Cikeda rashin damuwa suka karaso ciki hannunsu sarke cikin na juna, wani kallon banza wise kebinta dashi amma ita bata saniba saboda bata ko kalleta ba, gabanta hamood yakarasa yana kallonta,


"Sweetheart dan Allah wasila zata dan zauna damu na tsawon wani lokaci....."


Dagawo tayi ta kalleshi kallo mai kunshe da ma'anoni daban daban batare da ta tanka masa ba tawuce tanufi sama, ajiye trolley din yayi yabi bayanta,


Tana zaune kan stool din dake gaban dressing mirror tayi tagumi tacika tayi famm, tsugunnawa yayi agabanta,


"Haba sweetheart bai kamata fa kiyi hakaba, menene abin damuwa anan? Wasila fa bazata wuce 2 weeks ba zata tafi...."


Harararsa tayi sannan ta kawar da kai gefe,


"To meya hana tazauna anata gidan da zata biyoka nan?"


"Dan Allah kiyi hakuri gidan nata ake dan gyara mata kin san kuma mata da neman fitina musamman wadanda aka yiwa kishiya kiris suke jira suce kayi musu laifi...."


Dakyar dai yasamu ya lallasheta ta sauko,


"To tashi muje kasa..."


"Kaje ina zuwa, sallah zanyi"


Tashi yayi yafita ita kuma tashiga toilet tayi alwala tazo tayi salla tasake gyara fuskarta sannan tasauka kasa, wani karin bakin cikin ta tarar domin hamood ne da wasila kan dining sun gama cin abincin da tasha wahala ta girka kuma ita girkinta batayi da wise ba iya daidai cikinta da na hamood tayi tunda bata san da zuwan wise dinba, fuskarta adaure ta bubbude flasks din nan taga wayam sai ko gutsattsari nanfa tasake hasala ta kalli hamood yayinda ita kuma wise ke kallonta up and down,


"Hamood meye haka dan Allah? Waye yasa ku cinye min abinci?"


"Ayya sweetheart ai nazaci kinci naki wannan nawane shiyasa muka ci...."


"Koda nakane ai kamata yayi kujirani nasauko bawai kawai ku saka agaba ku cinye ba"


"To dai aikin gama yagama just kawai kisake shiga kitchen and find something sharp sharp sai kici ko indomie ne...,bari ni naje nayi salla"


Daga haka yamike yafita ita kuma wise tatashi tawuce bedroom din kasa, kallon wurin da suka ci abincin tayi duk sunyi kaca kaca dashi da miya kamar kajine suka ci kokuma masu bulallen baki, cikeda bacin rai tagyara wurin taje kitchen ta dafa tea taci da snacks takoma daki. Tunda wise tadawo gidan sai abubuwa suka sake kazanta domin ko abinci taci anan zata bar flate din bazata daukeba sai dai bilkisu ta dauke sannan baza tayi girki ba sai wanda bilkisu tadafa zata ci da bilkisu tasamu hamood tayi masa complain sai cewa yayi ita wise bata iya girkiba dan ko shiga kitchen wahala yake mata tayi hakuri har sai ranar da wise din takoya, maganar matsalarsu kuma da ta tuntubeshi akan suje asibiti sai cewa yayi shifa lafiyarsa kalau dan haka babu asibitin da zaije saboda awurinta ne kadai yake fuskantar wannan matsalar amma awurin wise rass yake, ita dai adaddafe tazauna da wise har na tsawon sati biyu kowa harkarsa yakeyi ba ruwan kowa da kowa aikin gidanta kuwa ita keyin kayanta amma wise ko cokali bata dauke mata wani lokacin ma idan tagama cin abinci haka zata yi ball da kwanon komai tsadarsa shiyasa daga ranar da tazo gidan zuwa yanzu ta fasa kwanuka da dishes babu adadi ita dai bilkisu bata taba yimata magana ba saboda badashi tazo ba kayan hamood ne kawai dai ansiyane da sunanta. Satin wasila biyu da yan kwanaki bilkisu tasamu hamood akan maganar tafiyar wise, karkatar da hular kansa yayi ya kalleta,


'Gaskiya kiyi hakuri dan ko zata tafi ba yanzuba saboda amfaninta yafi naki yawa agareni domin awajenta nake samun nutsuwa..."


Daga haka yasa kai yafita dama lokacin ficewa zaiyi, wannan maganar ba karamin ciwo tayi mata ba dan har kuka tasata daga karshe ta rarrashi zuciyarta aranar da yamma sukayi waya dasu elmustapha suke fada mata saura kwana biyu su koma Sudan shiyasa ta daura aniyar zuwa gida gobe domin suyi sallama,tun adaren ranar ta sanarwa hamood shiyasa washe gari tayi asubancin zuwa gida domin 9 acan tayi mata koba komai zata samu sassaucin zaman kuncin da take ciki, kowa nagidan yazaci laulayi ne yamaida ita yanda take ayanzu ita kuma bata sanarwa da kowa ba, acan duk su hindu suka sameta shiyasa tasake cikinsu sunata cafta sai daf da magrib takoma gida tana shiga bedroom dinta tayi turus saboda gaba daya aburkice yake akwatunan lefenta babu ko daya sannan laptop dinta dake kan bedside drewar itama wayam gashi da alama komai nata mai daraja dake cikin dakin anyi gaba dashi......





*littafin Kamar da wasa na siyar© *HASKE WRITERS ASSO.*




*KAMAR DA WASA....!*  




   _*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*




    *32*



*Littafin kamar da wasa na saidawa ne   me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*




    ***A mutukar razane tafita daga dakinta ta nufi na hamood shi dai bata ga wata alama dake nuna cewar anshigar masa dakinba sai dai bata da tabbas, sake fitowa tayi tanufi wurin mai gadi hankalinta atashe nan ta fara tambayarsa suwaye da waye suka shigo gidan amma yace mata babu kowa yau kwata kwata ma basuyi baki ba wasila ma tun safe itama tabar gidan har yanzu kuma bata dawoba haka shima hamood,


Cike da damuwa takoma cikin gida ta nemi wuri ta zauna afalo tana jimami duk kuwa da kiraye kirayen sallar da ta jiyo anayi a masallatai daban daban, to kenan barawon ko kuma barayin ta katangar baya suka shigo? Ta tambayi zuciyarta asirrance, bata samu ta motsa daga inda take zauneba su hamood suka shigo shida wise kamar kullum hannunsu sakale cikin na juna, mikewa tsaye tayi,


"Hamood yau gidan nan babu lafiya... Barayine suka shigo, gaba daya sun kwashe min kayana na lefe da laptop dina harda agogona na gold...."


"What....?" Yafurta da karfi, ai tun kafin tasake magana yanufi upstair da sauri gudu gudu, yana zuwa yashiga bedroom dinshi mintuna kadan yasauko hankalinsa amutukar tashe,


"Kai... To ai nima harda dakina suka shiga, kudin wata mota da na siyar shekaran jiya nazo dashi gidan nan sun dauke.... 7 hundred thousands cash..... Ohh my God"


Wani wulakantaccen kallo wise ta watsa musu su duka biyun kafin ta yi gyaran murya,


"Hmmmm haba dear... Wai kai baka gano game dinba har yanzu? Tab..."


Kallon wise yayi idanuwanshi sun fara yin jaa,


"Me kike nufi?"


"To ai wannan abune abayyane kuma afili... Kawai dai matarka sun hada baki da barayi sun shigo gidanka sun yasheka idan bahaka ba tayaya akan san kashigo da kudi? Sannan tayaya zasu iya haurowa gidannan har su shigo batare da anyi guiding dinsu ba.....?"


Zaro ido bilkisu tayi cikeda tashin hankali sakamakon jin sharrin da wise ke neman kulla mata, shi dai hamood bai sauraresu ba yayi waje da sauri,


"Ke mahaukaciyar inace? Me mijina yayi min da zan hada kai da wasu har in cutar dashi?" Bilkisu tafada tana huci,


"Karyar banza, mijina mijina... Mijinki a ina? Mijin da bai damu dakeba.... Sannan ni kika kira da mahaukaciya ko? To bari innuna miki ni din cikakkiyar mahaukaciya ce...."


Kafin Bilkisu tayi wani yunkuri sai jin abu tayi agoshinta tauuuu take hankalinta ya bar jikinta na wucin gadi, jin duka kawai tayi tako ina, ita ba ma'abociyar fada bace domin rabonta da dambe harta manta,ko lokacin da tana yarinya batayi rayuwar fada ba bare yanzu shiyasa wise tasamu galaba akanta kafin hamood yashigo tayi mata laga laga duk ta kumbura mata fuska ga goshinta dake tsiyayar da jini sakamakon kwada mata flate din silver da tayi awurin, dakyar hamood ya iya banbare Bilkisu daga hannun wise wacce keta faman gwarata abango duk ta yayyaga mata kayan dake jikinta, cikin bedroom dinta ya turata ya rufe sannan yazo ya kama Bilkisu yashigar da ita dakinta dake sama, suna shiga tafashe da wani irin kuka mai cin rai gamida ban tausayi.



****


 Sosai jikin fahad yayi kyau kuma ya samu sauki sai dai har gobe akan magani yake kullum sai yasha wasu kwayoyin magani kanana guda uku, yana kwance shi kadai acikin daki domin ya abba yakoma makaranta wayarshi na hannunshi ya tsurawa pic din Bilkisu ido wanda aka yimata ranar bikinsu,


"Wai dagaske Bilkisu kin barni...? Dagaske shikenan narabu dake? Dan Allah Bilkisu kidawo gareni,ki tasheni daga wannan mummunan mafarkin da nakeyi.... Dan Allah ki tasheni kice mafarkine ba gaskiya ba, Bilkisu kice min duk abubuwan da suka faru acikin mafarki ne, wallahi ina sonki.... Ina sonki Bilkisu....."


Salim dake tsaye akansa kawai ido yazuba masa yana kallonsa aransa yana tambayar kansa wannan wacce irin jarrabawa ce abokinsa ke fama da ita? Wai har yanzu yakasa daina son Bilkisu, ohh Allah....,


Fauce wayar dake hannun fahad yayi sai lokacin fahad din yayi firgigit alamun dawowa daga duniyar tunani, kan screen din wayar salim ya kalla hoton Bilkisu ne rangadadau gashi nan tasha mutukar kyau girgiza kai salim yayi yazauna kusa da fahad wanda ke goge hawayen idonshi cikin dabara gudun kada salim din yagani sai dai kashh ya makaro domin salim din yajima da ganin hawayen da yake zubarwa tun lokacin da yashigo cikin dakin,


"Kasan Allah? Zaka kashe kanka abanza akan wata aba banza wai ita soyayya.... Ya zaka zauna kayita kukan zuci da na fili akan so? Wallahi idan baka daina wannan tunanin ba kadai ji abinda Dr yafada maka ko jiya da na rakaka yace idan har baka bar damuwa da tunane tunane ba wannan hawan jinin naka zai janyo maka ciwon zuciya...."


Sake goge hawayen yayi da bayan hannunshi yakawar da kanshi gefe batare da ya kalli salim ba ya runtse idanuwansa,


"Salim wallahi nayi kokarin yin hakan amma nagaza, nakasa cireta araina, nakasa daina tunaninta, nakasa daina ganinta acikin mafarkina, nakasa salim, nakasa, nakasa daina sonta..... Meyasa Bilkisu zatayi min haka?"


"Kai ai banza ne wallahi, anfada maka haka ake so? Anfada maka haka ake soyayya kamar za amutu idan aka rabu? Wallahi ka maida hankalinka, matar da tajima da mantawa ma dakai shine zaka zauna kana westing din time dinka abanza kana tunaninta..."


Tashi zaune fahad yayi yana fuskantar salim,


"Malam karka sake ka zage ni ko ka zagar min mata..."


Dariya salim yayi wacce tasake kular da fahad,


"Lallai kuwa, kasan wani abu? Ai dai pics dinta kake zama kullum kasaka agaba kana kallo ko? To insha Allah daga yau zaka daina, kai wai mekakeson jawowa kanka ne? Ciwon zuciya ko tabin hankali? Anya wannan bilkisun ba asiri tayi maka ba kuwa? Wallahi karaba kanka da soyayya..."


Daga haka yamike zai fita daga dakin,


"Dallah malam ban wayata..." 


Juyawa salim yayi ya kalleshi,


"An hanaka, ai wallahi ko zan baka wayar nan sai nagoge hotunan Bilkisu gaba daya...."


Tun kafin yakarasa fahad yadaka tsalle yabishi amma ina bai iya cimmasa ba domin aguje yabar gidan har kofar gida fahad yabishi ganin bazai iya kamashi ba yasa ya hakura yatsaya yarike waist yana haki gashi baya son fita cikin unguwa ahaka domin daga shi sai gajeren wando da t shirt, cikin gida yakoma yashiga daki yayi wanka yashirya sai faman fushi yake, aransa yana cewa idan har salim yagoge masa hotunan Bilkisu to zasu samu babbar matsala, yana shiryawa yana tunani, adaki yayi sallar la'asar sannan yashiga cikin gida wurinsu ayiyah, mariya na shirin tafiya islamiyya yayinda maryam tuni har ta dade acan, dundu ya zuba mata yana fadin,


"Uwar nauyi kullum kece karshen tafiya makaranta kiga maryam tajima da tafiya amma ke sai kinyi makarar da kika saba..."


"Ya fahad Allah hadda na tsaya yi idan naje ban iyaba dukana za ayi.."


"Wai zaki wuce kitafi ko sai nayi ball dake..."


Dasauri tawuce tabar gidan bayan tasaka takalminta, falon mamuh ya leka tana kwance tana jin shirin wasan kwaikwayo mai suna madubi hoton kowa wanda ake gabatarwa atashar freedom radio,


"Mamuh dan Allah me zan samu? Allah yunwa nakeji"


Dagowa tayi ta kalleshi,


"Au ai nazaci baka janye yajin aikin cin abincin da kakeyi ba, shiyasa yau ban raba dakai ba tunda naga ko anbaka baci kakeyi ba..."


Dariya yayi yasaki labulen bayan yakarasa shiga cikin dakin,


"Nidai dan Allah abani wani abu inci kar kuma ulcer ta kamani"


Mikewa zaune tayi tana rage karar sautin radion ta,


"Ai dole abaka abinci dan auta, gaka kuma shagwababbe.... Ohh su fahad ankasa daina baci..."


Shidai yana jinta baice komai ba har ta miko masa kwanon abincin, dan waken fulawa ne subil subil dashi kanana kanana nan tamiko masa robar yaji da ta mai da maggi, dama yau ayiyah bata nan tana can kura tatafi biki kuma sai gobe zata dawo,


"Wai mamuh dan Allah meke rage damuwa ne? Menene maganinta?"


Saida tagyara zamanta takashe radion da take sauraro gaba daya sannan ta amsa masa,


"Fahad hakuri da addu'a sune suke jagorancin maganin kowacce damuwa, duk abinda yasamu bawa mutukar zaiyi hakuri kuma zaiyi addu'a to da yardar Allah zakaga ubangiji ya yaye masa damuwarsa... Kowa na duniya da kagani yanada damuwarsa daban wacce ke damunsa sai dai kawai fadane bazai yiba amma idan da ace wani zai fito yafada maka damuwarsa sai kaga kai taka damuwar bata kai kazauna kana damuwa ba... Hakuri da addu'a sune mafita acikin rayuwa"


Rufe kwanon dan waken yayi yana gyada kai alamun gamsuwa, kallonsa tayi tana harararsa,


"Meke nan kayi? Wai kana nufin har kaci?"


Ashagwabe yadaga kai yana bata fuska saboda yasan halin mamuh yanzu sai tace sai yacinye shikuma yanzu kwata kwata baya iya cin abinci sosai domin ba dadinsa yake jiba,


"Wallahi sai ka cinye abincin nan fahad... Shiyasa dama ban bayar ankai maka dakiba dan ba lallai kaciba kokuma kaci kwaya biyar kabaiwa almajirai sauran kazo kayi karyar kaine ka cinye..."


Tamkar zaiyi kuka yanata yamutsa fuska yasake jan kwanon gabansa yana ci, mamuh sai kara yimasa Nasiha take cikin hikima kan muhimmancin hakuri da kuma yarda da kaddara, kamar yadda tace saida ya cinye dan waken nan tass sannan yatashi cikinsa acunkushe dan tsabar koshi, ai fasa hawa babur dinsa yayi sai akasa yafita, shagonsu yaje fuskarsa babu yabo babu fallasa dama yanzu haka yakoma bai cika walwala ba, yana saman tebur din da suke yanka dinkuna tj yana yanka wani swiss material shikuma fahad yana guiding dinshi yanda yadace yayi yankan salim yazo, sallamarsa kadai fahad ya amsa daga nan yadauke kai dariya salim yayi yadafa kafadarsa,


"Abokina ga wayarka..."


"Ai da ka rike gaba daya kaga saika kasheni da hujja..."


Dariya maganar tabawa salim ya kalleshi,


"Ga dai mai neman kasheka can shiyasa nagoge hotunanta dan nafuskanci wallahi sonta na iya zama ajalinka idan har kayi wasa..."


"To idan tazama ajalin nawa sai me? Ina ruwanka?"


"Da ruwana mana tunda mu zata jawa asara kullum baka da aiki sai dai kasa hotonta agaba kullum kayita kallo kana hawaye... Allah prince kashiga hankalinka karage son nan da kake yimata saboda ina tsoron kar ciwon nan naka yasake tsananta..."


Banza fahad yayi dashi yawarci wayarsa yasoma duba folder din da hotunan Bilkisu suke amma duk empty wato salim dagaske yake yagoge din kenan? Goshi yadafe yana jin bacin ransa yana karuwa, duk maganganun da salim keyi masa baya tankawa dan yadau fushi sosai dashi daga karshe ma bar masa wurin yayi yasauka kasa yashiga masallaci yayi kwanciyarsa sai da lokacin salla yayi sannan yafita yayi alwala, bayan an idar da salla yafito salim na bayansa yamika masa hannu suyi musabaha amma yaki, shi salim ma dariya fahad kebashi wallahi, sanin idan yaje gida tunanine zai addabi ruhinsa yasashi tunanin inda yadace yaje kamar yaje wurin husnah sai kuma yatuna ashe sufa yan school of nursing  6 nayi ake rufe musu gate bashiga ba fita, majalissin marigayi sheikh ja'afar yaje inda wasu dalibansa guda biyu ke gabatar da darasi kowacce rana daga bayan sallar magrib zuwa lokacin sallar ishah sosai hakan yadebe masa kewa bayan an idar da salla yatashi zuciyarsa wasai sai dan abinda ba arasa ba, salim sai kiran wayarsa yakeyi amma yaki dagawa daga karshe kuma kiran husnah yashigo itama bai dauka ba har saida kiran yakatse sannan ya kirata, a dakalin dake kofar gidansu yazauna sunata waya da husnah basu taba doguwar waya irin ta yauba har wurin karfe 9,baya son shiga gida yanzu domin yasan muddin sukayi ido hudu da mamuh sai tasashi yaci tuwon dare shikuma akoshe cikinsa yake, yana kokarin tashi yaya Auwal yafito daga cikin gidan wato babban yayansu mijin anty fauziyya,


"Lahh.... Yaya yaushe kashigo gari?"


"Ba tun dazu naketa jiranka agida baka shigo ba... Wai yanzu me kake shiryawa ne?"


"Yaya karatu fa zan koma"


"A ina?"


"Wai da maryam abacha nakeson tafiya ko Ogun state ance akwai wata private university acan..."


"Kai dalla rufewa mutane baki, kaje kayi applying a federal university Kaduna kacike D E saboda karka makara, kaga kusa da gidane kacike duk course din da ranka keso...,sai da safe"


"To shikenan yaya agaida su anty"


Daga haka sukayi sallama yawuce shikuma yaci gaba da zama awurin yana jin baida mafitar da tawuce abinda yaya auwal din yafada yazama dole yabar garin kano koda zuwa kadunan ne.......




*_Ummi Shatu_*    wane me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*


*_Ummi Shatu_*    


© *HASKE WRITERS ASSO.*



*KAMAR DA WASA...!.*  




  _*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*





*Littafin kamar da wasa na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*




   *33*




     ***Cigaba yayi da zama awurin bai shiga gidaba har saida yaji sauro ya takura masa da cizo sannan yatashi yashiga ciki, bai shiga wajensu mamuh ba yashige dakinsu kawai yayi shirin bacci ga mamakinsa sai yau yaji baccin ya kauracewa idanuwansa domin aduk dare yasaba yasa hoton bilkisu yayi ta kallo har sai bacci ya daukeshi amma yau gashi babu salim yagoge masa komai,


Juyi yayi cikeda takaici sannan yaja wani guntun tsaki, haka yayita juye juye yana faman zuba tsaki har wurin karfe 12 ganin baccin yaki zuwa yasashi kiran ya abba bugu uku zuwa hudu kuwa yaji yadauka,


"Kanina bakayi bacciba? Ina fata dai ba damuwace ta hanaka bacci ba?"


Sai da yajuya daga kwancen da yake zuwa rigingine sannan yayi murmushi mai dan sauti,


"Ya Abba wallahi al'amarinne sai ahankali yau fari gobe tsumma...."


"Fahad hakuri zakayi fa, kayi kokari karage damuwa kaga condition din da kake ciki ayanzu haka...."


"Insh Allah, yanzuma kasa bacci nayi shine nace bari natabo abokin kwanana inji ya yake ciki...." Yakarashe maganar cikeda tsokana hakan yabawa Abba dariya,


"Ni test guda biyu gareni gobe shiyasa nazauna ina dan taba boko....."


"Allah yabada sa'a, yi bokonka nima bacci zanyi.... Saida safe"


"Shikenan amma pls karka yawaita tunani.."


"Insha Allah babban yaya..."


Daga haka sukayi sallama yajefa wayar karkashin pillow ya lumshe idanuwansa, yasan har yamutu bazai daina son bilkisu ba domin sonta acikin jinin jikinsa yake mutukar za arabashi da sonta to sai dai arabashi da numfashinsa wannan dalilinne yasashi yin mafarkinta awannan daren irin mafarkin da bai taba yiba wai ga mutane nan cike dam akofar gidansu bilkisun koda yaje sai yahango bilkisu tsugunne a tsakiyar mutanen ta hada kanta da gwiwa ba aganin fuskarta agabanshi wani yazo ya kama hannunta yatafi da ita alhalin fahad yanata kiranta fuskarsa sharkaf da hawaye amma bata ko waiwayo ba, shiyasa lokacin da yafarka da asubah jikinsa jike sharkaf da gumi duk kuma asanyaye, haka yatashi babu kuzari yashiga toilet, bayan yafito yana kokarin saka jallabiyarsa yaji baba na buga masa kofa, fita yayi suka fita masallacin tare, sai da yadawo daki yakwanta bayan yadawo daga masallaci sannan mafarkin da yayi yasoma dawowa cikin kwakwalwarsa,


"Meke faruwa da bilkisu.... ?"  Shine tambayar da yake ta yiwa zuciyarsa, kasa komawa bacci yayi haka yazauna  shiru yanata sakar zuci zuwa can yajawo wayarshi yasoma bincikar ajiyayyun muryoyin da ya adana nata amma su dinma wayam babu ko daya kwafa yayi da dukkan karfinsa yana jin haushin salim na sake turnikeshi,


"Wato har voice din nata ma duk yahada yagoge? Sai nayi maka wulakanci salim.... "


Daga haka yakunna radion wayarshi ko zai dan debe kewa yarage kadaicin da yake ciki, har ya dan fara bacci sama sama yaji kamar amafarki acikin radion ana cewa,


_"Zamu yi amfani da wannan damar wurin taya abokiyar aikinmu wato Bilkisu Lukman Aliyu murnar daurin aurenta tareda zankadeden angonta wato ma'arufi sha guda Hamood Ahmad barewa, muna addu'ar Allah yabasu zaman lafiya yakawo kazantar daki....!"_



Shiru yayi yana saurare har aka kammala sanarwar wasu zafafan hawayene suka ziyarci fuskarsa yana sake maida hankalinsa kan wakar nazifi asnanic wacce ke tashi,


_Na barki ya zan da raina.... Ban kwana...,sai watara na cewar bakina...., ban kwana...., amma kamarki ni ban mancewa.....,ban kwana, ko dare ko ko da rana, sai wata rana nasake fada ban kwana sai wata rana rabin jikina... Ni dake ayau muyi ban kwana sai wata rana rabuwa ba mutuwaba yar uwa rabin raina ban so muyo rabuwa.....!._


Kashewa radion yayi nan yadaga wayar da niyyar bugata da bango amma kuma ko me yatuna oho sai yafasa ya cillata gefenshi,hawayen takaici yaci gaba da zubarwa har na tsawon wani lokaci.


Yana nan kwance jikinsa babu kuzari yaji wayarshi tana vibrating kamar bazai dauka ba sai kuma yajawo yadauka yana goge hawayen idonshi,


"Yan mata...." Yafada muryarshi asanyaye, jin abinda yace yasa husnah murmusawa,


"Ya fahad ina kwana...?"


"Morning dear, how was ur night?"


"Fine sweet heart, dama nakiraka ingaidaka ne...."


"Nagode, me kikeyi yanzu?"


"Na shirya ne zan fita lecture amma ba zama zanyi ba saboda ina son zan shiga kasuwa insiyo lace zan kawo ka dinka min,ranar friday zanje Kaduna..."


"Bari nayi wanka zanzo inrakaki.... Idan kin fito daga lecture din just call me"


Daga haka yatashi ya shiga wanka domin yanzu ya kudurtawa ransa mantawa da bilkisu tunda har itama tamance dashi to babu amfanin yazauna yana damuwa akan wanda bai damu dashiba,da yardar Allah wannan zai kasance karo na karshe da zai zubar da hawaye akan soyayyarta. Wanka yayi yashirya yasha turare sannan yashiga cikin gida yanata kokarin danne damuwarsa sunata raharsu da mamuh ya karya da wainar shinkafa miyar taushe da ruwan zafi yana gamawa yatashi yafice, cikin plaza yaje ya ajiye babur dinsa sannan yataka da kafa zuwa school of nursing domin daga nan din zuwa can baida wani nisa yana hanya husnah ta kirashi tana sanar dashi gata nan fitowa,


Yana zuwa daf da gate din makarantar ya hangota sanye cikin uniform dinta fari tass da dan farin hijabinta marar girma sosai sai bakin toms akafarta da side bag dinta itama baka, jingina yayi da jikin bangon gate din yana kallonta tana tahowa gareshi tana magana awaya, tana zuwa ta tsaya gabanshi suna kallon juna kowannensu fuskarshi dauke da murmushi ahaka tagama wayar tana kallonsa sanye cikin kananan kaya jar t shirt da bakin wando da bakar p cap sai jan sau ciki akafarsa da jan agogo yana sakale da earpiece acikin kunnenshi, sosai yau dinnan yatafi da ita over duk da idanuwanshi sun danyi luhu luhu, can kasan makoshinta tafurta,


"Prince kayi kyau sosai..."


Saida ya lumshe idanuwansa sannan yabudesu akanta,


"Kin fini yin kyau ai..., muje ko"


Tare suka jera akafa suka nufi plaza har shagon da zata siyi leshin saida tazabi wanda yayi mata aka fada mata kudinshi tana niyyar ciro kudin fahad ya biya, shagon sayar da kayan dinki suka shiga yasai duk abinda zai bukata wurin dinka mata leshin, suna daf da shagonsu salim ya kalleta,


"Bakya bukatar kayan kwalliya.....?"



"Inada kayan kwalliya prince..."


"Turare fa? Ko kina dasu muje akara wasu"


Shagon su salim suka shiga nan fahad yayi tamkar ma bai san salim dinba saboda wani irin dauke kai yayi yana zaro wasu turaruka yana dorawa saman teburin dake gaban salim din,


"Nawa wadannan turarukan?"


Dariya salim yayi,


"Koma nawane ai kaima kasan dole inrage muku tunda budurwarmu za asiyawa..."


Harararsa fahad yayi yana motsa baki kamar mai son cewa wani abu amma baiyi magana ba,


"Husnah kiyiwa saurayinki fada yabar gaba dani, daga kawai nayi masa fadan gaskiya shikenan yake fushi dani...."


"Ayya ya fahad kayi hakuri ku shirya..."


Kallonta yayi nan suka hada ido tayi saurin janye nata domin ba kowacce macece zata iya jure kallon kwayar idanuwanshi ba domin akwai wani sirri na musamman aciki duk da idanuwan nashi farare ne tass,


"Babu ruwanki husnah kirabu dashi ai yasan laifin da yayi min babba ne...."


"Tom shikenan nidai nazama yar kallo tunda kunfi kusa da juna..."


Dariya salim yayi yana saka musu kayan acikin Leda,


"Abokina ashe yau soyayya ce tatashi shiyasa naganka cikin farin ciki...."


"Oho maka dan sa ido kawai..."


Da wasa da dariya suka rabu suka haura sama shagon su fahad, atake ya yanka leshin yana kallonta,


"Me Zan dinka miki? Riga da skirt ko da zani?"


"A'a kayi min da skirt"


Murmushi yayi ya dan harareta,


"Da zani zanyi miki zaifi yimiki kyau..."


Matsawa tayi kusa dashi inda yake kokarin karasa yankan kayan,


"Ya fahad banfa iya daura zaniba...."


"Ohhh husnah case... Zan rinka daura miki to"


Kafadarshi ta dan buga tana turo baki, tare sukayi yankan suka koma ciki duk inda yayi tana biye dashi kamar jela yan shagon sai dan kus kus sukeyi duk da dama sun saba ganinta wurin fahad dan indai kaganta ashagon to wurinsa tazo, har azahar suna tare lokacin sallah nayi duk suka fice sallah sai ita kadai bayan an idar fahad ne kadai yashigo amma duk sauran sun wuce sabgoginsu yana zama ta matsa tana karkade masa sumarsa,


"Ya fahad wani abune fari akanka..."


Hannunshi yasa ya kade wurin sannan yaci gaba da dinkin tanata yimasa hira zuwa can ta nisa tana niyyar yin magana yayi saurin janye hannunshi wanda allura taso datsewa,


Hannun tayi saurin kamawa tana shafa masa wurin daga ido yayi ya kalleta,


"Husnah meyasa bakya jin magana ne? Na hanaki tabanin nan amma kinki yarda nanfa ba bayelsa bane..."


"Haba ya fahad kuma dan na tabaka menene? Ai is nothing,normal..."


Saida yataka keken taku biyu sannan yadakata ya kalleta,


"Kina son wata rana nayi disvirgin dinki acikin shagon nan ko? Idan bakya so to kidaina tabani amma idan kika cigaba da tabani komai na iya faruwa dan zan iya baki baby batare da andaura mana aureba, kiyi hakuri har muyi aure sai ki tabani son ranki... Harma sai ankai level din da zakiji na isheki baki son tabanin...."


Ai tana jin abinda yafada tayi saurin rufe fuskarta ta hanyar kifa kanta kan keken da yake dinki, murmushi yayi yana cizon lips dinshi yasan dama dole taji kunya amma shi iyakar gaskiyarshi yafada mata domin idan ba haka yayi mataba to zasu cigaba da taba juna daga karshe har lamarin yayi kokarin kazanta,


"To ki daga kanki inkarasa hada miki intafi gida yunwa nakeji..." Yafada yana murmushi,


"Bari naje nakawo maka abinci...."


Kafin yayi magana tatashi tafice cikeda kunya dan har lokacin bata yarda ta bude idanunta ba, tana fita kuma saiga salim shi yaci gaba da tayashi hira har yan shagon suka dawo kafin 3 yagama dinka mata hadaddiyar skirt da riga yana kokarin mikewa sai gata tashigo itada kawarta hafsa tasha kwalliya cikin doguwar riga ta atamfa da dan mayafi, ahankali yafurta,


"Kinyi kyau princess......"


Murmushin jin dadi tayi ta ajiye masa abincin tana furta,


"Thank you"


Basu wani bata lokaci ba takarba tatafi yau dai yayi niyyar cin girkinta shiyasa yakira salim awaya yazo suci tare, jalop din macaroni da dankali yaji sadden sai kamshi yake tare sukaci shi dai fahad tsakura kawai yake saboda baya zagewa yaci abinci yanzu. Sosai al'amarinsa da husnah aka samu cigaba domin yana sakar mata fuska yanzu sabanin da ammafa har gobe bai taba jin sonta yana yawo acikin jininsa ba kawai dai yana biye mata ne kuma yanajin shakuwa mai karfi tsakaninsu.Duk da baya son karatu kusa da gida yacike D.E kamar yadda Yaya auwal yace yanzu kawai zaman jiran admission yakeyi.


***


 Bilkisu kam ranar da sukayi fada da wise tayi kuka kamar me dakyar hamood yashawo kanta ta canja kaya yakaita chemist aka yimata plasta awurin aka manne da audiga da bandeji, suna dawowa kuma yakalleta yana fadin,


"Shawarar da zan baki babu ruwanki da shiga sabgar wise domin ita dambe awajenta ba komai bane sannan tafi karfinki saboda harda maza dambe take...."


Cikin masifa da jin haushi bilkisu ta kalleshi,


"To yanzu me kake nufi? Nufinka kenan wannan ciwon da taji min taci bulus bazaka tsawatar mata ba?"


"Kinga bilkisu dan Allah kibarni naji da bakin cikin satar da akayi min, nidai nafada miki babu ruwanki da ita idan kuma bahaka ba to jiki magayi...."


Tsabar bakin ciki kasa cewa komai tayi har yafita daga dakin, tagumi ta rafka tama rasa wanne irin tunani yadace tayi. Tun daga wannan rana takoma rayuwar daki domin bata fitowa sai idan wani abu zatayi shiyasa zaman gaba daya ya dameta kuma ya gundireta wannan dalilinne yasata yanke shawarar tunkarar hamood da maganar komawarta aiki ko tasamu tarage kadaicin da take ciki tunda ko babu komai fitar zaiyi keeping dinta busy, aranar da daddare bayan yashigo ta sameshi da maganar wani kallo yayi mata irin na yan iska sannan yaci gaba da abinda yakeyi yana cewa,


"Mai gado kenan, wai ke wacce irin macece? Atunaninki zan amince dake har inbarki kifita aiki bayan alhalin nasan har yanzu wannan karamin yaron ba daina sonki yayiba? Ai sai kuhada kai kurinka ha'intata..."


Cikin bacin rai ta kalleshi bakinta har rawa yake yi,


"Hamood kallon da kake yimin kenan? Wannan itace sakayyar da zaka yimin? Idan har Zan iya hada baki da fahad inci amanarka to meya hana inzauna tare dashi tun farko?"


"Look mai gado dan Allah karki nemi yimin hayaniya yanzu saboda agajiye nake i have to rest so pls walk out....."


Bakinta abude da mutukar mamaki tajuya tafice zuwa dakinta rasa wanne irin fassara zata yiwa wadannan kalaman na hamood tayi, wato dai yanaso yace mata bai yarda da itaba? Kasa bacci tayi a wannan daren shiyasa tunda sassafe takira abbanta awaya ta sanar masa nan yace zai kira hamood din tabashi number dinsa, wurin 9 yashiga dakinta yace tatashi zasuje gidansu abbanta na nemansu duk wannan maganar yana yinta ne cikin daurewar fuska, haka suka je gidan babu wanda ke cewa ko uffan Abba yana zaune falonsa yagama karyawa amutukar ladabce hamood yagaida Abba da Ammah kowannensu ya amsa fuska asake sannan Abba yayiwa hamood maganar da yakirashi dominta wato na komawar bilkisu aiki,


"Hamood mai gado ta kirani tace tana son zata koma aiki amma da tayi maka maganar kanuna kamar baka aminceba domin ma tamkar har yanzu baka gama yarda da itaba hakane....?"


Sosa keya yasoma cikeda ladabin karya yace,


"Abba wallahi bahaka nake nufiba, nidai kawai banida ra'ayin matata tayi aikine nafiso tazama full hause wife"


"To shikenan ke mai gado kinji abinda yace, tunda baya bukata kiyi hakuri...

Kibari anjima zan turo miki kudi a account dinki sannan duk sanda kike da wata matsala ki sanar dani..."


"Shikenan Abba, nagode madalla"


Tafada tana share hawayenta, anan hamood yatafi yabarta zata wuni bayan yatafi su amma Nasiha suka yiyyi mata har tasaki ranta, tun kafin tabar gidan taga abba yatura mata dubu dari biyar cikin account dinta, bayan sallar magrib tana niyyar tafiya saiga Abba yadawo shida ya mudan wanda yakawoshi gida daga garko domin yau can abban yaje kuma cikin rashin sa'a motar da suka tafi da ita tasamu matsala ganin zata tafi Abba yace ya mudan yakaita gida, baya tashiga suka tafi lokacin da sukaje kofar gate din gidan anan ta sauka suna yin sallama da ya mudan hamood yadanno motarsa shida wise hakimce agaba kamar kullum tayi daurinta na ture kaga tsiya.........




*_Ummi Shatu_*    


*Wannan littafin na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*




    34 ***Tana shirin barin wurin hamood yakaraso shida wasila wani mugun kallo ya watsa musu ita da ya mudan sannan ya danna hancin motarsa zuwa cikin gida, bata kara ko mintuna ukuba tashiga itama tabar ya mudan zaune yana jimami tambayar zuciyarsa yake tayi,


"Wai dama wannan shine mijin da bilkisu ta aura?"


Yayiwa kansa tambayar nan tafi sau dari kawai tunani yake shin yafadawa bilkisu gaskiya ko kuma karya fada saboda ko babu komai ai yar uwarsa ce daga karshe dai yabi shawarar zuciyarsa na kawai yaja bakinsa yayi shiru domin gudun abinda zaije yazo jan motarsa yayi yabar wurin yanufi gida.


Bilkisu adarare tashiga cikin gidan saboda iya kallon da hamood kadai yayi musu ya isa sanar mata cewa there is something wrong, tana shiga falo suna tsaye shida wise juyowa gaba daya yayi yana harararta,


"Daga ina kike? Maigado bafa zan lamunci yawon ta zubar ba acikin gidan nan..."


Ita tsabar takaici ma sakin baki tayi tana kallonsa, har saida yadiga aya sannan tayi magana,


"Lallai hamood, ya mudan nefa dan uwana abba yasa yakawo ni tunda kai bakaje ka daukoni ba..."


"Ni bawanki ne da zanje na daukoki ko kuwa ni driver dinkine? Kishiga hankalinki kin gane ko..... Aikin banza kawai Malam haka kawai najawa kaina masifa naje na jajibo yar matsiyata...."


Zaro ido bilkisu tayi tana kallonsa,


"Hamood ni kake kira da yar mutsiyata? Wallahi karyar mutum yakira iyayena da wannan sunan, yayan matsiyatan dai suna inda suke..."


Daga haka tawuce sama tana shiga daki tazauna tana ta surutu ita daya cikin masifa,


"Haba wannan wacce irin rayuwace wai? Mutum kullum idan banda cin mutunci da jaraba bashida zance.... Ni wallahi zaman gidanka yafita akaina gaba daya nagaji da igiyar aurenka haba...."


Tun daga ranar tsakaninta da hamood babu daddadar magana abu kadan sai zagi ita dai ji take ankusa zuwa gabar da dole zata bar gidansa domin gudun kada cutar hawan jini ta kamata saboda kullum cikin bacin rai take da damuwa idan yau basu debota da hamood ba to sai sun haura da wise shiyasa duk tabi ta lalace ta fige, tana cikin wannan halin bikin khulsum yazo bilkisu nason taje ayi komai da ita kamar yadda khulsum din tayi mata amma fafur hamood ya hana sai bikin dai yabarta ranar da za afara bikin tun sassafe tabar gidan domin dama jinta take kamar akan kaya, gidan hamood ya zame mata tamkar kurkuku, duk ankon da aka fitar ta turawa khulsum kudi ansiya mata dama ko takan hamood bata bi ba domin wani wulakanci yake ji kwana biyun nan, zuwanta gidan bikin cikin mutane yasata mancewa da damuwarta domin ga kawayensu nan yan makarantarsu da abokan aikinsu, kwana uku aka dauka ana yin bikin sai da aka kai amarya gidanta sannan bilkisu tasamu zama. Lokacin da ta koma gida babu kowa agidan daga hamood har wise din asalima ita daya ta kwana agidan, washe gari ma haka kai saida tayi kwana uku ita daya ce kwal cikin gidan tana rayuwarta takira hamood yace mata yana abuja amma yau ko gobe zai shigo so take yadawo ayi wacce za ayi domin yakamata su nemi magani saboda tagaji da wannan zaman na cuta domin akwai cutarwa acikinsa. Tana zaune falo tana kallon tashar zee world mai gadi yayi mata knocking, hijab tasa ta leka cemata yayi sunyi bako wai hamood ne ya aiko shi, fita compound din gidan tayi, kamar a mafarki taga dr Abrar wato tsohun saurayin khulsum kawarta domin kamarma shi zai auri khulsum din Allah ne dai baiyiba kawai,


"Ahhhh likita... Yau kai nake gani?"


Murmushi yayi yafito daga cikin motarsa,


"Hajiya Bilkisu yan jarida..., ya aikinku? Ina kawarki ashe tayi aure ta kini ko?"


Dariya bilkisu tayi,


"Likita ba kinka tayi ba kawai dai Allah ne baiyi zaku zama ma'aurata ba..."


"Adai yimin dadin baki irin na yan jarida..."


"Ba dadin baki bane gaskiya ce kawai Dr..."


"Wai dama kece wacce hamood yace inkawowa sakon nan?"


"Ehh nice..."


Tafada cikin murmushi,


"Ok to amma meyasa ban taba ganinki a asibitinba? Ai akwai tarurruka da ake shirya muku domin wayar muku dakai da kuma shawarwari da ake baku na musamman domin kula da lafiyarku... Idan har zakubi ka'ida to ko mai lafiya bazai fiku walwala da tsawon kwana ba...."


"A'a likita wai meke faruwa ne? Wanne ciwo kenan?"


Gyara tsayuwarsa yayi, cikin murmushi yace,


"Karki damu bilkisu u know am a Dr,wai dan nasanki ko kin sanni isn't something bad duba da yanayin aikinmu am always confidential soo feel free, wallahi da asibiti ma kikazo bazan taba nunawa cewar nasanki ba that's the rule.... Mu a ka'idar aikinmu koda ace kasan mutum when he comes to u with such case zaka nuna kamar ma baka taba ganinsa ba sai ranar unless shine yayi maka magana i hope u understand?"


Goge fuskarta tayi da gumin dake tsattsafowa tasake kallon Dr abrar dakyau,


"Likita dan Allah fada min in a simple way da zan fahimta saboda ni duk wadannan maganganun naka babu wanda na fahimta am confuse...."


"Bilkisu kenan.... Wai bake hamood yacewa zai aiko akawo muku magani ba? Last 3 days yaje hospital wurina karbar drugs dinsu wanda yakesha saboda lalurar da yake dauke da ita but unfortunately ranar babu maganin ba akawo ba kuma yace min tafiya zaiyi amma idan ankawo intaimaka inkawo masa gida zan samu matarsa sai nabata saboda itama tanada bukata u know he's my childhood friend...."


"Nidai to... Amma wallahi har yanzu ban ganeba da dai wasila na nanne may be ita yake nufi not me..."


"Wasila....?, wasila kuma? Har yanzu suna tare da wasila?"


"Likita kasanta ne...?"


"Ehhh ai itace ta jona masa HIV din... Can wurin yawon barikinsu suka hadu, dama suna tare?"


"Kana nufin ba matarsa bace?"


"Mata? Mata kuma? Tayaya wasila tazama matarsa? Sai dai ko farkarsa...."


Ai tun kafin ya karasa bilkisu take jin jiri yana daukarta abu biyune suka taru suka dagula mata lissafi awannan lokacin nafarko jin wai hamood yanada HIV na biyu kuma jin wai wasila karuwarsa ce, sama sama take jin bayanin likita amma tunda jimawa tadaina fuskantar komai maganin tasa hannu ta karba daga nan tawuce ciki jiri yana cigaba da daukarta ko sallamar da yake yimata bataji.



***


Cikin nasara admission dinsu fahad yafito kuma yasamu inda suka bashi BSC laboratory level 200 saboda result dinshi na diploma yayi masifar kyau dan da distinction yafita kuma SLT ya karanta shiyasa, shi anasa zabin ma pharmacy yaso subashi yadora amma suka bashi laboratory dole babu yadda ya iya hakan zai daure ya karanci lab din,babu bata lokaci yashirya yaje ya karbo admission letter dinshi, har makaranta ya kaiwa husnah tagani tayi congratulating dinshi, suna tare yaya Baffa yayan salim yayi masa waya wai yazo ya sameshi agida, sallama yayiwa husnah yahau Babur dinshi yatafi yana zuwa yaya baffa ke sanar dashi wai wasu turawa ne zasu karbi hayar gidansa idan har zai basu zasuyi aiki na shekara daya agarinne kuma a wannan area din suke son gidan, baba fahad yakira awaya ya sanar masa babu bata lokaci baba ya amince shima fahad baida zabin da yawuce ya amince din, cikin kwanaki biyu aka gama komai aka bawa turawa gida suka hau gyarashi,kudi mai yawan gaske suka biya aka sakawa fahad cikin account dinsa. Da wadannan kudin yadiba yaje yayi registration ya kama hayar dakin da zai zauna anan opposite din makarantar wanda ya kasance private hostel na manyan yara shi dinma a babban yaron yafito bayan yagama registration yakoma gida zaije yashiryo yadawo saboda nanda yan kwanaki za afara lectures.





*_Ummi Shatu_*    


*Wannan littafin na siyarwa ne,me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*



   35***Babu bata lokaci fahad ya kammala shirye shiryensa na tafiya makaranta domin shi aburinsa idan yatafi bazai dawo gidaba sai semester ta kare, duk abubuwan da zai bukata ya tanadi kudinsu domin acewarsa baya so ya debi kaya daga nan kano har zuwa kaduna wai za arainashi yafi son sai yaje can sannan yasiyi komai, anan gida dai ayiyah da mamuh sunyi masa jar miya cikin plastic da dakakken jan yaji mai daukeda tafarnuwa wai dan adan saukaka masa yayinda su anty Fauziyya suka yimasa snacks. Ana igobe zai tafi yaje gidajen yan uwansa duk yayi musu sallama shida salim bayan sallar ishah suka dawo gida bai samu ganin husnah ba a wannan dare domin ka'idar makarantarsu karfe 6 ake rufewa, shiyasa yabari sai washe gari da safe zaije ganinta before yawuce.


Lamo yayi kwance bisa katifarsa yana sake sake acikin ransa wato gaba daya rayuwar nanma jarrabawace acikinta da gaibu saboda duk yadda kakai ga shiryawa kanka rayuwa baka taba sanin abinda zai faru gobe komai iya hasashenka shidai koda wasa bai taba kawowa zai yi soyayyar aure da husnah ba asalima kallon mai dan tabin hankali yake yimata ada amma yanzu duk da bajin sonta yakeyi acikin ransa ba tana da wani muhimmanci agareshi, bilkisu dai insha Allah yamanta da ita koda kuwa hakan zaisa ya dawwama acikin bakin ciki da damuwa. Washe gari kamar yadda ya tsara bayan yagama shiryawa cikin kananan kaya bakin jeans da t shirt din polo yellow, hatta takalmin da yasaka na kamfanin polo ne da p cap, gidansu salim yaje yayiwa mamansu sallama sannan suka wuce wurin husnah tare, kasancewar weekend ne bata da class shiyasa da personal tafito tasha yellow din atamfa mai zanen kwarya, tana karasowa salim yafara tsokanarsu,


"Kaga amarya da ango.... Wato tsabar ma zuciyoyinku anko suke da juna shine harda saka kaya kala daya...."


Murmushi fahad yayi itama haka amma batace komai ba sai fahad ne ya mayar masa da martani,


"Kasan aduk lokacin da masoya suka shaku da juna to komai nasu rikidewa yake yakoma iri daya shiyasa sai ka gansu tamkar wasu yan biyu... Ni bakaga har wani kama mukeyi da ita ba.... Ko husnah ta? Ai kamarmu daya ko?"


Dariya tayi tarufe fuska tana fadin,


"A'a ya fahad wallahi kafini kyau..."


Dariya yayi yana kallon wani wuri,


"To ai kinfini haske Asma'u kuma ma dai kamar tamu daya..."


"Kana dai kawai tsokana tane fa..." Tafada cikin shagwaba,


"To kuma meye abun turo min bakin? Ko kina son inbaki goodbye kiss ne...."


Dariya tayi ta juya masa baya,


"Nidai bana so..."


"Nima bance kina so ba kawai tambayace yan matanah...."


Shidai salim ashe yajima da sulalewa yabasu wuri yana can zaune gaban wata bishiya mai dauke da benci a karkashinta,


"Ya fahad dan Allah idan katafi karka manta dani.... Karka maye gurbina da wata... Wallahi idan kayi min haka zan iya rasa raina..."


Saida ya matsa kusa da ita sannan yafara yimata magana kasa kasa cikin alamun rarrashi da tarairaya,


"Haba husnah ai ko amafarki bazan taba mantawa dake ba.... Kina da wani babban bangare acikin zuciyata, kisa aranki akoda yaushe kina cikin zuciyata kuma insha Allah bazan taba zama sanadiyyar rasa rayuwarki ba domin zan baki kulawa zan sadaukar miki da lokutana aduk lokacin da kika bukaci hakan.... Amma kin san me? Karfa nima ina tafiya kiyi min kishiya...."


Murmushi tayi kwalla tana ciko idanuwanta,


"Ya fahad only u, kasa wannan aranka nice dai nake tsoron yanmatan Jami'a kar inje ina nan wata ta kwace min kai...."


"Husnah no need to worry about that....saboda ni wallahi tsoron mata nakeyi yanzu.... Karki dauka da wasafa... Seriously tsoron mata nake ayanzu dai...."


Kallonta yayi yanda take hawaye dagaske tana gogewa,


"To menene wai na kukanne?? Idan bakya son natafi shikenan sai infasa karatun husnah indai hakan zai saki farin ciki..."


Girgiza kai tayi tana share hawaye,


"A'a ya fahad kaje, Allah yabasa sa'a.... Sai munyi waya"


Daga haka tajuya tatafi yasan wani kukan takeyi wanda bata son yagani duk kuma sai yaji wani irin tausayinta yana shigarshi, shida yazo suyi sallama amma gashi tatafi da kuka ko sallamar ma bata bari sunyi ba.


"Allah sarki husnah Allah yabani ikon faranta miki...."


"Amin" salim ya amsa wanda karasowarsa wurin kenan, dafa kafadar fahad yayi yahau bayan Babur din yana cewa,


"Rabuwar masoya tana zafi gashi ku baku sababa....." 


"Dallah can... Meye hakan"


"Ahh waka ce mana nake yimuku... Allah sarki husnah..."


Buga Babur din fahad yayi suka fita sai da suka bar kofar makarantar sannan yace da salim,


"Salim wallahi husnah tausayi take bani... Ina tsoron kar zuciyarta tashiga wani hali saboda soyayyata kamar yadda tawa zuciyar ta tsinci kanta sakamakon halin da bilk....."


Sai kuma yayi shiru domin baya son tunata baya kaunar tunawa da ko sunan bilkisu arayuwarsa domin abinda yafaru tsakaninsu shine abu mafi muni da ya taba faruwa dashi wanda baya jin zai iya mantawa,


"To ai indai zaka danne zuciyarka kanuna mata soyayya ka riketa da gaskiya bazata taba shiga halin da kake tsoron shigarta ba...."


"Zan kokarta insha Allah i will try my best to makes her happy,lovely and even special... I will for eva care for her"


Dariya salim yayi,


"Ai nasan zaka iya... Lover boy"


Da hirar husnah a bakunansu sukaje gidansu fahad yayi sallama dasu ayiyah har baba ma yana nan yana jiran tafiyarsa bai fitaba sai lokacin yake jin kamar zaiyi kuka, su maryam kam kukan suke tayi kamar anyi musu mutuwa shiyasa shima saida yaji kwalla na shirin zubo masa da koke koke dai yadau kayanshi yatafi shida salim wanda zaiyi masa rakiya har inda zai hau motar Kaduna.



Bayan sallar azahar yashiga kaduna, dakinsa wanda yakama yaje ya shirya kayansa yaci snacks ya kwanta domin hutawa duk da yana son shiga kasuwa yasiyo abubuwan da yake bukata na amfainin yau da kullum da kayan abinci. Zuwa dare ya kammala komai yagyare dakinsa tsaf ya siyo duk abubuwan da yake bukata, kwanciya yayi kan katuwar katifarsa ya bararraje ya kira gida saida suka gaisa da kowa na gidan sannan yakira ya abba shima suka dan taba hira sannan yakira husnah daga karshe ita kam hira suka sha sosai domin har 10 da wani abun domin shagwabar da yasaba yaketa zuba mata,


"Ko inje infadawa baba adaura mana aure akawoki nan mu zauna.... Ni kin san bana son harkar yunwa gashi bana son yin girki da kaina...."


"Ka rinka zuwa captaria kana ci mana..."


"Yanmatanah abincin saidawa farin maggi suke sakawa nikuma bana so idan naci sai nayi amai...." Yakarashe maganar cikin shagwaba, dariya husnah tayi,


"Ya fahad kaifa dadina dakai shagwaba...."


"Kin manta ni dan auta ne? Komai ayiyah tasamu ni take baiwa fa...."


"Su Mariya fa? Basune auta ba?"


"Ke wadannan fa "yayana ne, yaran sister nane..." 


"Badai 'yayanka ba,'yayan Anty dai.... Kai ai tukunnah..."


Dariya yayi ya lumshe idanuwanshi,


"To me kike ci na baka na zuba..., nima din kwana nawane muna yin aure zaki haifo yan biyu kafin shekara ta zagayo...."


"Wai wai... Lallai ya fahad, yauwa dama inaso in tambayeka wai dan Allah...."


Jin tayi shiru yasashi bude idanuwansa,


"Menene? Go on ina jinki..."


"Wai meya rabaku da matarka"


"Husnah dan Allah kar muyi wannan maganar saboda ciwona zai iya tashi kinga nasamu kwana biyun nan yasauka...."


"Shikenan ya fahad insha Allah bazan sake yimaka magana kwatankwacin irin wannan ba,Allah yakara maka lafiya..."


"Thank you husnah"


Sun jima suna hira daga bisani sukayi sallama kowa zuciyarsa fari tass saboda dadadan kalaman da suka fadawa juna.


Washe gari yafara fita lectures tun aranar yayi friends guda uku dama su ukune tun level one suke tare haidar da Bashir sai mukhtar shi dai fahad baya son hada kai da kowa a makarantar nan kamar yadda su ayiyah sukayi masa fada akan ya tsaya yayi abinda yakaishi sannan banda kula abokai barkatai domin hakan babu fa'ida acikinsa amma saboda yanda suka manne masa dole saida ya kulasu dukda yana jin tsoro domin yaga kamarsu yaran manyane shikuwa ba dan kowan kowa bane sai dai sam ko kadan su basu nuna masa hakanba domin aranar ma dakinsa suka bishi bayan sun fito daga lecture harda kokawa akan guntun snacks din dake cikin jarida a nannade wanda yarage shiyasa shima ba adauki wani lokaci mai tsawoba yasaki jikinsa dasu saboda yaga basuda wani mummunan hali basa shaye shaye basa iskanci basa komai shi dama dan shaye shaye ya tsana bazai taba iya abota dashiba.Kullum suna tare su hudunnan kamar wasu yan hudu shi mukhtar gidansu a abuja yake sukuma su bashir duk yan cikin Kaduna ne, duk lokacin da suka fito daga lecture sai dai su zauna suyita bacci adakin fahad ko kuma wani lokacin suyita buga games a wayoyinsu ko game din kati shiyasa fahad yafara  kokarin nemarwa kansa mafita domin baya son zaman nan na asara shiyasa ya yanke shawarar fara zuwa shagon dinkin da yagani tsallaken gidan da yake zaune su mukhtar nata tsokanarshi suna cewa yana babban yaro amma shine zai je yana dinki? Shi dai cewa yayi ehh babu komai ai Sana'a ce saboda yasan basuda masaniyar irin kudin da yake samu ta hanyar dinkin nan shiyasa kwana biyu da baiyiba duk jinsa yake sai shankali hatta kafarshi kumbura takeyi ita kadai tana sabewa.


***


Tunda bilkisu tazauna acikin falonta bayan tafiyar Dr abrar takasa samun nutsuwa gaba daya jinta take kamar acikin mafarki, takasa zaune takasa tsaye sai kaiwa da komowa takeyi burinta kawai taga dawowar hamood cikin gidan ta zazzage masa abinda ke cikinta,


"Wannan ai cin amanane da mugunta, ni hamood zai yiwa wannan butulcin...? Ohh my God.... What a heartless..... Wannan wacce irin mugunta ce..."


Wasu hawayene ke kwaranya daga cikin idanuwanta mikewa tayi tawuce bedroom dinta tasoma hada kayanta gashi abin haushi akwatunanta ansace balle tazuba kayan aciki duk da hamood yayi mata dadin bakin wai zai siya mata wasu, haka dai taci gaba da zama amma babu hamood babu labarinsa tana ta kiran wayarshi kuma akashe har dare bai dawo gidanba sai wise ce tadawo gidan da misalin karfe 10 nadare ko kallonta bilkisu batayi ba amma itama yau kallo daya zaka yimata kagane ashirye take da ko wanne irin bala'i wanda mutum keji dashi, babu wanda ya tankawa wani wise tawuce bedroom dinta wanda ke falon kasa sam hakan bai damu bilkisu ba ayau domin yanzu ita ba ta wasila takeba ta hamood takeyi so take yazo gidan ta kare masa tanadi amma abin takaici da bacin rai bai dawo gidanba har 12 nadare har lokacin bilkisu bata runtsa ba tana jiran taga ta inda hamood zai bullo anan falon ta kwana har asubah dama tunda tazauna bata tashi sai dai idan salla zatayi.


Safiyar ranar da misalin karfe goma tana zaune tana zaman jiran tsammani domin bata son tatafi gida tasake dawowa tafiso tatafi gaba daya da takardar sakinta ko wani abu mai kamada haka, ga kayanta nan agefe wadanda ta shirya domin tafiya dasu, akan idonta wise tafito tashiga kitchen ta dafo indomie tazo takoma daki, har takosa da zaman tana shirin tafiya inyaso sayita su kare awaya taji dirin shigowar motarsa, mikewa tsaye tayi ta rike kugu tayi tsayuwar ashirye nake da duk abinda mutum yazo dashi tana jijjiga kamar ansaka mata wayar wuta masiface rubuce kan fuskarta ahaka hamood yabude kofa yashigo ya isketa.....




*_Ummi Shatu_*    


36***Tunda hamood yashigo ta dauke kai tamayar dashi gefe daya ganin haka yasashi shima hade rai yadaure fuska kamar bai taba dariya ba,


"Macuci.... Azzalumi..... Mugu to Allah ya toni asirinka....yanzu dama hamood kasan kana dauke da kwayar cutar HIV amma shine ka aureni ahaka har kake burin hada shimfida dani?"


Wani mugun kallo ya watsa mata sannan yazare farin tabaran dake sanye cikin idonsa, zama yayi kan kujera ya dora daya kan daya yana watsa mata kallon dake kara tafarfasa ranta,


"To sai me dan na aureki ina dauke da HIV? Bake kika manne min kika like min akan dole sai na aureki ba? Karfa ki manta har aurenki kika kashe dan kawai in aureki in zauna dake...."


"Ya isa haka malam.... Ai duk wadannan abhbuwan dakake ikararin cewar na aikata na aikatane acikin rashin sani... Kuma ina nadamar hakan ahalin yanzu, wallahi hamood kaci amanata kuma ka zalunceni wanda bazan taba yafe maka ba har abada.... Sannan ka gaggauta sallamata domin gidan ubana zan tafi insha Allah nagama zama dakai...."


Wata shakiyiyar dariya yasaki irin wacce ke dauke da mugunta tsantsa aciki sannan yayi mata kallon uku ahu,


"U are such an idiot mai gado, sai yanzu nasan bakida tunani sam.... Hmmmm to idan ke shashasha ce ni mai hankaline... Bazan taba sakinki ba koda kuwa za amaimaita yakin duniya akaro na uku.... And lastly abinda zan fada miki shine u should mind ur tongue kisan irin maganar da zaki rinka fada min idan bahaka ba jikinki zai rinka gaya miki....."


Yana kokarin mikewa taje tasha gabansa cikeda masifa da tashin hankali,


"Wallahi hamood koda baka sakeni ta dadin rai ba to yazama wajibi ka sakeni ta dolen dole koda kuwa agaban kotu ne domin nagama zama da macuci,mayaudari, mashayi kuma mazinaci... Ko kana tsammanin har yanzu ban san irin kazamar rayuwar da kuke yi kaida waccan karuwar ba? To Allah yagama tonar asirinku dan haka kasakeni kuma kabani kudina naira dubu dari biyar wanda abbana yabani kai kuma ka lallabani ka kwace....."


Tafa hannaye wasila tashiga yi wacce fitowarta kenan daga cikin daki,


"My dear yanzu kana tsaye kanajin abinda wannan mahaukaciyar take fada maka amma shine bazaka dauki mataki ba?"


Tun kafin wise tarufe baki hamood ya dauke bilkisu da wani gigitaccen mari wanda yayi barazanar makantar da ita, zafin marin yasa bilkisu sake daga murya tana furta,


"Allah ya isana macuci azzalumi kuma wlhi sai ka bani kudina sannan dolenka ka sakeni...."


"Banza yar gidan matsiyata ni zaki yiwa sharrin na karbar miki kudinki? Uban me uban naki yake dashi da har zan karba? Saki kuma bazan yiba ko kin zaci nima irin wannan sakaran yaronne da zan sakeki aduk lokacin da kikaso? Koda zan sake ki yazama dole inmore sadakina dan haka sai kishirya daukar kwayar cutar HIV...."


Tun kafin yakarasa bilkisu ta dadimeshi tana kuka,


"Ni ba yar matsiyata bace sai dai idan kaine dan matsiyata kuma wallahi daga yau nagama zama dakai...."


Wani marin yasake bata sannan yashiga dukanta babu ji ba gani har saida takai kasa lokacin ne yafara ball da ita yana nausa mata kafa aciki, kuka bilkisu takeyi tana ihun neman dauki ganin yana kokarin kasheta yasa wise zuwa tana kokarin hanashi amma yahaukace kwata kwata bayaji bare gani,


"Nashiga uku hamood ka kusa kasheta... Kar kayi kisan kai kaga yanda takeyi fa... Kabarta haka"


Shine abinda wise keta fada amma hamood yaki saurararta ganin haka yasata sulalewa daga gidan tagudu tun kafin hamood yakashe bilkisu azo tafiya dashi ahada harda ita.


Bilkisu kam tajima da fita daga cikin hayyacinta sakamakon na jakin da hamood ya lakada mata abu na karshe da zata iya tunawa shine taji hamood ya gwarata da kujera ta fadi akan hannunta na hagu wanda take awurin wani azababben zafi ya ziyarceta, cikin azababben ciwon kai take bude idanuwanta ahankali wadanda suka kumbura suntum sakamakon uban bugun da suka sha,


Ammah ce da meenah zaune acikin dakin wanda ko ba afada mata ba tasan asibitine domin ga alamu nan sun nuna hakan, ga ruwa nan ana kara mata a hannunta na dama sannan hannun hagun ta kuma an daddaureshi dasu bandeji alamun dori,


Wasu hawayen nadama ne suka zubo daga cikin idanuwanta, ganin ta dan motsa yasa ammah da meenah azamar tasowa dukkaninsu Wanda har bakinsu na haduwa wurin yimata sannu,


"Sannu mai gado..." Inji ammah,


Kai ta dan daga cikin azabar ciwo ta rinka binsu ammah daya bayan daya da kallo kamar yau tafara ganinsu. Bata iya cewa komai ba sai ciccije baki da takeyi sakamakon ciwon da dukkanin jikinta keyi mata musamman ma hannunta na hagu,


"Sannu adda labour.... Allah yatashi kafadunki"


Dagawa meenah kai tayi tana cije baki hawaye na kwaranya daga cikin idanuwanta ahaka su maama suka shigo itada Hindu,maama na dauke da sultan ita kuma Hindu tana goye da meenal abayanta sai hudah wadda hannunta ke rike da nata, cikin zuciyarta take wani irin kuka mai tsuma rai saboda ganinsu mama da 'yayayensu yasake fama mata raunin da take fama dashi, su gasu da yaransu agidan mazajensu cikin walwala da kwanciyar hankali amma ita tanata shiga cikin runtsin rayuwa,


"Allah ka gafarta min... Allah natuba... Astagfirullah..." Shine abinda taketa fada cikin zuciyarta, jinta take ta tsani hamood ta tsani duk wani namiji mai irin halinsa ahalin yanzu,


"Allah ya isa..." Shine abinda lebanta suka furta amma babu wanda yaji, cikin tausayawa da jimami maama da hindu suka karaso gaban gadon su dinma kamar zasuyi kuka,


"Sannu Adda.... Sannu... Sai Allah yasaka miki insha Allah" inji mamaa,


"Kuma inbanda zurfin ciki irin na Adda labour bata fa taba fadar irin zaman da sukeyi ba bare tafadi cewar yana dukanta..." Hindu tafada tana kokarin zama agefen gadon,


"Ni dama tun jimawa wallahi na fuskanci akwai matsala kugafa irin ramar da tayi har iyallo ke cewa ciki ne..." Meenah itama dake tsaye kusa da amma ta tofa nata,


"Ai Dr yace babu wani ciki yanzu... Yace bata da komai, gara ma da Allah bai bata ba domin hada zuri'a da irinsu wannan hamood din hatsarine... Allah yabata masu albarka nan gaba" maama tafada tana kokarin mayar da kwallar da take kokarin cikowa idanunta, ammah dai har akayi aka gama bata tofa tata ba suna nan zaune sunata yimata sannu har Abba yazo yadubata yatafi hakama mazajensu duk sunzo sun dubata, khulsum amarya itama daren ranar sai gata, kowa yaga bilkisu sai yaji tausayinta sakamakon kumburar da fuskarta tayi tsabar duka. Lokacin da dare yayi meenah ce tace zata kwana da ita amma ammah tace a'a kowa yatafi gidansa inyaso Rabi mai aikinta sai tazauna su kwana tare hakan kuwa akayi, ita dai bilkisu kasa baccinma tayi sakamakon suyar da zuciyarta keyi motsi kadan zata furta,


"Allah ya isa..." Acikin zuciyarta kokuma afili. Saida tayi kwana uku agadon asibiti sannan tafara tashi har ta zauna kuma an danyi sa'a kumburin fuskar tata ya dan ragu, har ranar babu wanda yayi mata maganar hamood may be suna son abar asibitinne tukunna sai asanar mata abinda yafaru, aranar tana zaune maama na kusa da ita agefen gadon tana bare mata ayaba tana ci sai ga hajiya iyallo ita da yakumbo mai gado, tunda iyallo tashiga dakin take tsinewa hamood,


"Ni dama wallahi wannan yaron ban yarda dashiba... Yaro sai kace dan dambe wani murgujeje dashi... Wallahi tsohon mijinki shine miji mai gado... Yaro mai kunya ko gaisheka yakeyi idanuwansa akasa bazai taba yarda ya hada ido dakaiba amma shi wannan idonsa atsakar ka yake sai yasaka idonsa cikin naka sannan zaiyi maka magana....Allah yasawwake,Allah ya kwashe masa albarka macuci"


Tun abun na bawa su maama haushi har yadawo yana sakasu dariya, iyallo nata faman hamuki ya mudan yashigo wanda dama shine yakawo su,yana yiwa bilkisu yajiki iyallo tahau cewa,


"Ai shikenan yanzu sai acika min burina ayi hadin nan.. Ni dama tun farko mudansiru naso abawa aka ki..."


"Dan Allah iyallo mu ki kyalemu muji da abinda muke ji..." Maama tafada tana hararar gefe,


"To fitsararriya dadinta ma dai bake naceba balle kiyimin rashin arziki... Fitsararriya kawai.."


Shi dai ya mudan ficewa yayi daga dakin da alama shima baiji dadin maganar iyallo ba ko meye dalili? Bilkisu kuwa jin iyallo ta ambaci fahad har tana yabonsa yasata dulmiya kogin tunani.....



*Wannan littafin na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*




*_Ummi Shatu_*    


*Wannan littafin na siyarwane me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*



      _BILKISU_


  37 ***Har iyallo ta karici bambaminta tagama bilkisu batace uffan ba kusanma gaba daya yanzu tadaina fahimtar abinda suke cewa domin tadade da yin nisa acikin kogin tunani tabbas maganar iyallo gaskiya ce fahad yarone mai kunya kuma nagartaccen namiji domin ita kanta ta shaida hakan duk da har yanzu bata jin zata iya zaman aure dashi domin yayi mata kankanta shekarunta sunfi nasa, to tayaya zatayi rayuwar aure dashi? Tayaya zai rabeta amatsayin matarsa? Haba ai da kunya,jikinta yanzu yafara bata cewar wannan abunda yafaru da ita harda hakkin fahad kila Allah ne yayi masa sakayyar cutarwar da tayi masa itada hamood shiyasa ya hanasu jin dadi da farin ciki a lokacin zaman aurensu, ita kanta sai yanzu take ganin wautarta da rashin wayon da ta aikata gaskiya hamood ya shammaceta ya cutar da ita, wasu hawaye masu zafi taci gaba da zubarwa ganin haka yasa iyallo sake dagewa wurin tsinewa hamood ita kuwa bilkisu ita kadai tasan dalilin kukanta gashi kukan zuci takeyi marar sauti sai dai kawai aga hawaye na zuba alhali likita yace irin wannan kukan yafi illa dan haka ta nisanceshi amma ita kanta tasan bazata taba iya hana wadannan hawayen zubaba domin direct suke tahowa daga can cikin zuciyarta. 


"Adda labour dan Allah kiyi hakuri kidaina kukan nan haka.... Maganin me kukan zaiyi ne?" Mama tafada cikin rakwarkwabewar fuska,


"Mamaa yazama dole inyi kuka... Barni in koka ko zuciyata zatayi sanyi...."


"Kidai yi hakuri kuma ki daure dan Allah...."


"Maama..... Bazan.... Baz....."


Ai bata kai ga karasawa ba kirjinta ya sarke idanuwanta suka kakkafe, wata gigitacciyar kara maama tasaka yayinda su iyallo kuma suka hau zuba salati, karar da maama tafasa itace ta janyo hankalin ya mudan yashigo cikin dakin cikin tashin hankali ganin abinda ke faruwa yasa shi fita da sauri zuwa office din likita, maama na rike da ita tana gunjin kuka likita yashigo yafitar dasu ta hanyar basu umarnin su fice daga dakin, yajima akanta sannan yafita har lokacin jikin maama bai daina rawaba da nasu iyallo domin su duk atunaninsu mutuwa bilkisu tayi amma sai likita yace musu bahaka bane su kwantar da hankalinsu da ranta kuma insha Allah zata samu lafiya, ita dai bilkisu na can bata san abinda ke faruwa ba domin tadade da rabuwa da hankalinta, lokacin da su ammah sukazo ma baccinta take tasha sai ruwa da ake kara mata, tsaki meenah taja tasamu wuri ta zauna kusa da Hindu bayan tadawo daga leken bilkisu ta window din dakin da take ciki,


"Wai dan Allah sai yaushe za abar baiwar Allahn nan tahuta ne? Haba jama'a Karin ruwa yaki karewa...."


"To ya za ayi Ameenah... Allah dai yabata lafiya..." Inji ammah, zama sukayi jugum jugum har sai da likita yakira ammah nan suka rankaya gaba daya suka tafi, dan takaitaccen bayani yayi musu dangane da matsalar da bilkisu tasamu amma yace yanzu sun samu nasarar shawo kan matsalar sai dai yanada kyau ta guji tunani da shiga bacin rai domin maganar gaskiya zuciyarta na daf da bugawa saboda damuwa, duk cikinsu babu wanda bai kokaba sai Ammah kadai itace ke basu hakuri, zuwa dare bilkisu ta farfado hakan ya dan kwantar musu da hankali musamman ma da sukaga duk wuraren da yataru jini ajikinta ya barbaje, babu laifi taji sauki sosai sannan ta samu lafiya matsalar kawai dorin hannunta ba akunce ba likita yace sai nan da sati biyu haka suka yita faman kaiwa da komowa har zuwa lokacin da aka kunce dorin aka sallamesu, duk bilkisu tabi tasake kekashewa kamar wadda tayi shekara akwance. Lokacin da suka koma gida ba karamin mamaki tashiga ba domin ganin kayanta gaba daya nasawa andebosu da duk wani abu wanda yake mallakinta ne, ita dai har ta kwana ta yini tasake kwana babu wanda yayi mata maganar hamood ko wata magana mai kama da haka, shi kansa abba baiyi mata maganar ba iyakaci idan taje ta gaisheshi suka gaisa shikenan amma bai yimata maganar hamood ba haka itama ammah duk da suna zama suna yin hira, sai akwana na biyarne maama tasake dawowa gidan domin dubata itada hudah harda farfesun kaji da dambunshi wanda ta iyowa bilkisu, cikeda sha'awa bilkisu ke kallonta domin har cikinta ya dan fara turowa duk da dai tanada girman ciki amma kowa yaganta yaga mai juna biyu, saida suka sha hira afalon ammah ganin lokacin salla yayi yasa bilkisu tafiya dakinta tayi wanka tazura doguwar riga tayi salla tana idarwa maama tashigo tana rikeda hannun hudah, kwantar da ita tayi kan gadon bilkisu sannan ta yunkura zata tashi nan bilkisu tayi hanzarin dakatar da ita,


"Yawwa maama wai dan Allah waye yakaini asibiti ne? Sannan hamood kuwa yayi sakin?"


Komawa maama tayi ta zauna tana kallon bilkisu,


"Adda labour wallahi ranar hudah muka kai asibiti nida abbanta, gaba daya sai najini ba anutse ba sannan hankalina duk yatafi gareki shine fa nace masa mubiya inganki dakyar ma yayarda wai yana gudun makara a office, ina shiga na iskeki cikin wannan halin hamood yanata kwallo dake.... Abban hudah ne ya daukeki yakai cikin mota bayan nakiraki shine muka wuce dake asibiti, sai bayan da akayi admitting dinki sannan nakira su ammah..."


Jijjiga kai bilkisu tayi cikin damuwa sannan ahankali tace,


"To ya maganar sakin? Ya sakeni?"


Kai maama ta daga mata cikeda damuwa,


"Ya sakeki bayan sun debota da Abba domin Abba waya yayiwa uncle dinsa yasanar dashi komai nan uncle din nasa ke cewa shi dama bashida wani hadi dashi inbanda almajiranta da yazo yi har Allah yahadasu yake wanke wanke agidansa dahaka yazama tamkar dan gida.... Ke intakaice miki zance ma shi kansa hamood din saida Abba yasa aka nemoshi sukayi babu dadi dan cewa yayi shi bazai sakeki ba har sai anbiyashi komai nasa tun daga kayan lefe har sadaki... Sai da Abba yabiyashi sannan ya sakeki saki biyu..."


Tagumi bilkisu ta rafka tana jin kirjinta nayi mata suya,


"Lallai hamood yacika marar mutunci.... Nimafa akwai kudina a hannunshi wanda Abba yabani yace wai in ranta masa wani mutum yasiyarwa da mota to kuma yanzu yadawo masa da ita shine zai cika yabashi kudinsa saboda already kudin hannunshi ya tura za a kawo musu sabbin cars...."


"Babu komai adda maigado kawai kiyi addu'a insha Allah bazaki tagayyara ba kuma sai Allah yasaka miki... Ni wallahi idanma son samune tsohon mijinki yadawo kusake dinkewa.... Allah sarki ya fahad bawan Allah komai nasa na mutunci...."


Shiru bilkisu tayi tana saurarenta har saida taji tayi shiru sannan tasauke nannauyar ajiyar zuciya tana kallonta,


"Maama kenan...."


"Wallahi dagaske adda labour fahad shine yafi dacewa dake saboda yanada yakana da alkunya..."


Rasa abin cewa tayi daga karshe taja bakinta tayi shiru tana jin maama sai faman kwarzanta fahad take tayi. 


Sam abinda maama ta fada baiyi tasiri acikin zuciyarta ba sai dai yatsaya mata arai fiyeda tunanin mai tunani domin daren ranar kawai tunanin rayuwar da tayi agidansa tayita yi tana tuna dabi'unsa da kuma halayensa wadanda ko makiyinsa bazai kushe ba, tarasa a wanne aji yadace tasaka wannan al'amari, shin yanzu idan fahad yadawo zata iya aminta dashi? Wannan shine tambayar da tayiwa zuciyarta amma sai ta girgiza kanta,


"Dan mutunci kam bani da ja yanada mutunci da hankali amma zamana tareda shi a matsayin miji da mata.... Hmmm" sai kuma tayi shiru takasa karasawa, karshenta dai wannan dare sai bacci barawo shine yasamu nasarar saceta lokacin da take tsaka da tunani tana tambayar kanta wai meye dalilin da yasa kowa ke yimata fatan fahad yadawo gareta?.




_FAHAD_



Tuni fahad yafara zuwa shagon oga Abdul, lokacin da yafara zuwa Abdul din bai wani daukeshi serious ba domin bai zaci cewa ya iya dinki ba sai da yaje wurin sau uku sannan yace yazo yazauna ga keke nan yafara, wata atamfa yabashi da measurement da komai yace ya dinka, ai tunda fahad ya dinka atamfar nan sai Abdul yasoma bashi wani girma na musamman domin koshi fahad yafishi kwarewa afannin dinki expert ne awannan fannin tun daga ranar kasuwar fahad ta bude babu bata lokaci sunanshi ya yadu acikin makarantarsu domin duk wata budurwa mai ji da kanta ta fahad take bawa dinki, bama yan makarantar ba hatta daga cikin garin abuja ana kawo masa dinki, wasu bawai dinkinne damuwarsu ba a'a kawai so suke su kulla alaka dashi sosai oga Abdul yayi farin ciki da zuwan fahad shagon domin zuwansa yakawo masa alkhairi masu dinbin yawa ga fahad babu mugunta aduk lokacin da zaiyi yankan sabon style zaiyi agaban sauran yan shagon ya koya musu gobe ma wani zai sake kirkira. Sosai yamayar da kanshi mr busy domin har majalissin dare yake zuwa inda magidanta ke daukar karatu shima yadauka dan wayo kam yayiwa su mukhtar wayo,kullum yanada abinyi baya zaman banza shiyasa baida matsalar komai ahalin yanzu kudi suna shigo masa ko ta ina dan idan yayiwa yayan manya dinki sai an nunka masa kudin dinkin nasa sannan abashi koda kuwa yafadi abinda za abashin, husnanshi kuwa kullum suna tare awaya domin tunda yazo kaduna baije kano ba, kullum idan zaiyi girki sai yakirata ta koya masa yauma daga lecture yafito awahale domin tea kadai yasha da safe kuma sai 2 yadawo dakinshi wani tea din yasake sha saida yaji dan dama dama sannan yakira husnah domin ta koya masa yadda zai dafa dan wake dariya yajiyota tanayi tareda fadin,


"Ya fahad dan wake kuma? Tabdijam lallai yau dan wake zaisha jifa..."


Jin dariyar da takeyi yasashi sakin murmushi,


"Kinga idan bazaki koya min ba ni kawai ki fada min kin barni yunwa nata faman damuna..."


"Am sorry sweet prince..... Yanzu fara jika kanwa saboda da ita zaka kwaba fulawa din..."


Yamutse fuska yayi kamar tana kallonshi,


"Gaskiya husnah dan waken nan ba yau ba, bari kawai indafa indomie tunda naji shi nasa hadin yawa gareshi"


Kafin tabashi amsa aka bude kofa, bashir ne yashigo mukhtar na biye dashi,


"Malam tashi muje gidansu bash.... Wallahi kuma ko baka so sai kaje..."


Batare da yayiwa husnah sallama ba yakashe wayar yatashi zaune yana kanne ido daya saboda yunwa,


"Wallahi yunwa nakeji mukhtar kubari muci indomie mana..."


"Dallah kazo muje, akwai abinci acan fa..." 


Baiyi musu ba yakama hannun mukhtar din yamike suka fita, lokacin da sukaje gidansu bashir kanwar bashir din mai suna suwaiba itace keta hidima dasu amma kuma sai kallon fahad take tayi kamar zata cinyeshi shiyasa duk ya takura, suna kokarin barin gidan babansu bashir yadawo Alh Usman mai fitila shahararren attajirin dan kasuwa,afalonsa duk yatara su yana yimusu fada da Nasiha kan su zauna suyi karatu banda wasa sannan su nemi sana'ar yi komai kankantarta ai nan su bash sukayi  farat sukace fahad sana'ar dinki yakeyi hakan ba karamin burge Alhaji Usman yayiba nan yarinka saka masa albarka yana cewa yataimaka ya koyawa abokanshi ma domin ko karatun mutum yagama ba lallai yasamu aikin yi akan lokaci ba daga karshe yabaiwa fahad kyautar wani hadadden yadi na maza irin mai tsadar nan sky blue da turaren oud wanda shima kudinsa akalla zai kai dubu ishirin, bayan sun fito suwaiba ta biyosu tana ta yiwa fahad kwarkwasa da shagwaba shi dai baya iya cewa komai. Tun daga wannan rana suwaiba ta manne masa domin har number dinshi tasamo take damunsa shikuma harga Allah yanzu tsoron mata yake kuma ma banda haka ga husnah agefe, harsu mukhtar saida sukayi masa maganarta amma yace shi baya soyayya dakyar yasamu ya yageta daga jikinsa, ba ita kadai ba duk macen dayaga take takenta na sonshi take fita harkarta yakeyi. A daddafe dai yagama semester dinnan yakoma gida dauke da dunbin nasarori sau biyu kacal yaje ganin gida a wannan semester din.




*_Ummi Shatu_*    


*Wannan littafin na siyarwane me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*




BAYAN SHEKARA D'AYA



   38***Yau garin kano antashi da muku mukun sanyi da tarin hazo wanda ya lullube ko ina shiyasa duk inda ka duba mutane tsilla tsilla kake gani kowa yana yin al'amuransa cikin rashin sakin jiki da takurewa saboda sanyi, a titina kuwa duk motocin dake wucewa da sauran ababan hawa kowa ya kunna fitila saboda nagabansa ko mai tunkaroshi yahangoshi tun daga nesa, fahad yabi sahun mutanen da sanyin yau ke takurawa, dawowarsa kenan daga asibitin koyarwa na malam aminu kano wato (Aminu kano teaching hospital) inda yake gabatar da practical dinsa tun sati uku da suka gabata yafara zuwa, yana dawowa yasa maryam ta dafa masa ruwan zafi yadaure yayi wanka yafito duk sai kakkarwar sanyi yakeyi, agogon wayarshi ya kalla nan yaga karfe biyar da rabi,


"Ohh Allah... Ji yanda lokaci yaja amma kai sai kazaci ba afi karfe uku bama...."


A gaggauce ya shirya cikin riga mai dogon hannu baka sannan yasake dora wata t shirt din mai gajeren hannu ita kuma ja yasaka bakin jeans, sannan yadora rigar sanyi akan rigunan da yasaka wadda takusa kai masa zuwa gwiwarsa, bakar hula yasaka kirar sakar inji ta kamfanin Nike domin ga sunan nan rangadadau agaban hular, har kunnuwansa yarufe da hular sannan yasaka bakar safa mai kauri akafarsa, dan guntun turarenshi da yayi saura shi yadauka yakarar dashi ajikinsa sannan yawuce gaban katifarsa yajawo system dinshi wacce ke kunne muryar sheikh abdurrahman sudais natashi cikin suratul kahfi, kashewa yayi ya ajiyeta kan pillow dinshi sannan yadauki wallet dinshi da bakin glass yafita, cikin gida yashiga gaba daya suma su ayiyah suna falon mamuh suna shan dumi cikin wani katon kasko wanda suka zuba garwashi aciki, su maryama na zagaye da kaskon suna jin wuta,


"Wai... Gaskiya dakin nan akwai dumi... Mamuh yau anan zan kwana..."


"Kai meyasa baka raboda sakarcine? To kazo ka kwana din ai sai mu kaika inda ranka ko taska muce ga gandamemen saurayi nan amma har gobe bai daina kwana dakin babarshi ba..." Mamuh tabashi amsa tana gyara lullubin dake kanta,


"Ayiyah kina ji fa... Kice wani abu"


"Kyaleta autana, yau wannan kaskon wutar adakinka zai kwana"


"A'a ai sai dai ku nemo naku ko kibada naki..."


Dariya sukayi gaba daya yamike daga tsugunnen dayake gaban kaskon wutar kusada su Mariya har yana dungure mata kai cikin fada yace,


"Ke dalla kirinka kula gashi nan zaki jefa gefen hijabinki cikin wuta... Karki jawa mutane gobara....."


Mikewa tsaye yayi ya kalli iyayen nashi,


"Sweet mamuh zan tafi store.."


Sake juyawa yayi ga ayiyah,


"Loving momy naje store..."


"Kai dai kasani ja'iri, adawo lafiya..." Inji mamuh, ita kuwa ayiyah dariya tayi tace,


"Allah yabada sa'a autanah.."


Saka kai yayi yafita yana jin su Mariya na hada baki wurin cewa,


"Ya fahad kasiyo mana chocolate..."


Yana kokarin fita kawai yakoma dakinsu mask yadauko domin yazama dole yatoshe kofofin hancinsa saboda hazo dan yasan muddin yafita ahaka akwai matsala domin bayan wani bangare na zuciyarsa da ya tabu sakamakon matsanancin hawan jinin dake damunsa harda wata lalurar mai kamada asthma amma kuma ance ba ita bace. Roba roba dinshi yahau yafita daga layin kafin yakarasa gidansu salim yazaro wayarshi daga aljihunshi yasoma kiran salim din, yana dagawa yace,


"Kai gwauro.... Dan Allah zo ka rakani store insai turare mana..."


Ai salim najin haka yasake tukunkunewa cikin bargo,


"Wallahi babu inda zan iya fita a wannan sanyin, kabari gobe da safe ko yamma sai muje mana,


"Tab kasan kuwa yanda na matsu da turaren nan? Ni bazan iya rayuwa babu turare ba malam..."


"To sai kadawo, nidai babu inda zanje..."


Katse wayar fahad yayi yajefe cikin aljihunsa yaci gaba da tukinsa sakamakon yahau babban titi danma daga hancinsa har idonshi duk a rufe suke. Ihsan store yashiga cikin sa'a yasamu dukka turarukan da yake amfani dasu wadanda suka kasance ba masu matsanancin karfiba saboda shi yanzu al'amuransa sai ahankali,suma su ayiyah saida yadauka musu sabulun wanka sinki biyu domin duk wanda zai siya musu abu agidan to guda biyu yake siya, daga karshe yadaukawa su Maryam gidan chocolate yanufi wurinda ake biyan kudi, yana shawo kwana yayi kicibus da maama rikeda jaririn yaronta ahannunta, sam ita bata ganeshi ba domin fuskarshi arufe take,


"Hajiya maama...."


Taso ta dauki muryar amma saita kasa gane ko tawaye, ganin bata ganeshi ba yasashi cire glass din fuskarshi da mask din da yarufe hancinsa, cikeda mamaki maama taware idanuwanta tace,


"Ya fahad idonka kenan.... Yaushe akasa?"


Dariya yayi yamika hannu yakarbi awwab dake hannunta wanda tuni har yafara wayo,


"Wallahi hajiya maama ina nan, ina babynki hudah yanzu tagirma ko?"


Dariya maama tayi,


"Tagirma tana can gida wurin adda labour..."


Jin ta ambaci labour yasashi dan runtse idonshi,


"Allah sarki... Tana lafiya ko? Yanzu nasan ta haihu ma may be...koda yake bari nayi shiru kar mijinta yasa akamani"


"A'a wai baku taba haduwa ba? Ai tana gida, yanzu batada aure..."


"Ya salam.... Sun rabu da mijinne ko kuma rasuwa yayi?"


"Wallahi rabuwa sukayi, ai kwata kwata aurenta bai wuce 3 months ba suka rabu...."


"Ikon Allah... Allah yarufa asiri,wallahi ban saniba nima da yake yanzu nakoma Kaduna da zama can nake karatu, practical yanzuma nazo yi wallahi..."


"To Allah yataimaka amma dai yakamata kaida adda labour ku tuna baya, yanada kyau akoma gidan jiya"


Dariya fahad yayi ya rausayar da kai yana kallon fuskar awwab ganinshi yake kamar bilkisu ce ta haifeshi dan tsananin kamarsu kasancewar kamarta daya da maama,


"Ai yayar takice miskila ce maama... Tanada wuyar sha'ani...."


Dariya itama mamaa din tayi sannan tace,


"To ai zaku daidaita tunda kai kanada saurin fahimta da saukin kai..."


"Haka dai kikace, Allah yazabi abinda yafi alkhairi..."


Bata kai ga amsawa ba abban hudah yakaraso domin har yagaji da jiranta acikin mota,


"Haba nidai nasan tsayawa gaisawa da wata ko wani kikayi saboda naji shirun yayi yawa..." Yafada yana mikawa fahad hannu domin yin musabaha,


"Ehh wallahi mijin adda labour nagani shine natsaya muke gaisawa..." Tafada tana dariya, murmushi fahad yayi,


"Ahh kice yayanmu ne, babban yaya yakake?"


Dariya abin yabawa fahad jin mijin mamaa na kiransa da wai Yaya bayan kuma yagirme masa ahaife sosai, karbar pampers din dake hannunta fahad yayi bayan yamikawa abban huda awwab, dama pampers kadai tazo siyawa awwab irin babban nan, wurin biyan kudi fahad yaje yahada yabiya har da nasu duk da sunata cewa yabarshi, har zai tafi maama ta dakatar dashi ta karbi number dinshi domin ita dai haka kawai take kaunar fahad shiyasa ba ason ranta aurensu ya mutuba dan dai kawai kaddara tashiga cikine.Lokacin da yakoma gida magrib tayi shiyasa saida yatsaya yayi salla sannan yashiga cikin gida yakaiwa su ayiyah abunda yasiyo musu, sunata saka masa albarka yadauko abincinsa shida Abba yafito domin abban ma yana gari tun watanni biyu da suka wuce yagama service yanzu haka yana zuwa bureau of statistics acan yake dan taba kwadago,


Yana zama gefen katifa kamar da tunanin bilkisu yazauna domin gaba daya hirar da sukayi da maama ce tafara dawowa cikin tunaninsa, sama sama yaci abincin yana daf da kammalawa yaji anfara kiran sallar isha kasancewar yanayi yasauya yanzu da wuri ake yinta, tashi yayi yafita masallaci bayan yadawo ya cire rigar sanyin dake jikinsa ya kwanta da sauran rigunan ajikinsa da safa akafarsa bargo yaja ya lulluba sannan yajawo laptop dinshi yakunna, gaba daya tunanin bilkisu ne ke neman addabar ruhinsa duk da yanata kokarin ganin hakan bai kasanceba. Duk abinda yasan idan yayi zai dauke masa hankali kar yakai ga tuna bilkisu yayi amma abin yafaskara, laptop din ya ajiye agefensa ya kunna wa'azin marigayi sheikh Albani Zaria yana saurara wanda yarage volume din sosai, daga kanshi yayi ya kalli sama kawai yana dulmiya cikin kogin tunani, ji yake kamar zai sake fadawa tafkin kaunarta akaro na biyu duk da bazai so hakanba, yasan kawai yana yaudarar kansa ne wurin kokarin hana zuciyarsa tunaninta domin abinda zuciyar take so ne, kamanninta bazasu taba gushewa daga cikin zuciyarshi ba, to tayaya ma zuciyarshi zata manta da ita alhalin silar sonta ne ya illatata har tasamu rauni daga wani bangare na jikinta, jin anturo kofa za ashigo yasashi maida hankalinsa ga kofar, yaya abba ne yashigo yana rataye da jakar laptop dinshi yana sanye cikin farin yadi,


"Amma gaskiya yau kayi over time... Duk cikin aikinne haka?" Yafada cikin sanyin murya sannan kuma ayanda yayi maganar ahankali yayita irin yadda yakeyi duk lokacin da ciwonshi yatashi hakan yasa Abba karasowa cikin faduwar gaba,


"Na dan biya ta gidan Anty asabe ne wai zan yimata register din wani abu nasu na malaman makaranta.... Wai amma lafiya kuwa?"


Murmushi fahad yayi yana gyara kwanciyarshi zuwa barin dama tayadda zai fuskanci Abba dakyau,


"Lafiya lau nake meka gani?"


"Naji maganarka ne ahankali... Amma kasha maganinka kuwa?"


"Nasha dazun nan, ka kwantar da hankalinka fa lafiya lau nake Allah"


Sai lokacin Abba yajishi yadan samu sukuni, ajiye jakarshi yayi yakalli fahad,


"Wannan sandararren abincin fa...?"


"Nakane mana..."


"Tab, ni ai yanzu ruwan zafi zansha, bari nashiga cikin gida nasa su Mariya su dafa min..."


"Su Maryam na aikatuwa hannun samarin gidannan... Idan kowa yayi aure dai sa huta suma" inji fahad,


Daukar flask din abincin abba yayi yanufi hanyar fita yana cewa,


"Ni ai ko nayi aure da daya acikinsu zan tafi..."


"Katafi da ita tazama yar aikinku ko? Ai ayiyah bazata baka ba dama dai nine..."


Baiji abinda Abba yake fada ba sakamakon karar da wayarshi tasoma yi, ganin husnah yasashi jin gabanshi yayi faduwar da har saida yasa hannu ya dafe kirjinsa,cikin sanyin murya yadauki wayar itama najin muryarshi haka yasata jin hankalinta yatashi nan tashiga tambayar ko ciwonshi ke neman tashi amma yace mata a'a saida taji sunjima suna hira baiyi wani abuba sannan hankalinta ya kwanta. Tunda suka gama waya da husnah yake cikin duniyar tunani, idanuwanshi alumshe ga wa'azi nayi cikin system dinshi amma azahirin gaskiya ba wa'azin ma yake saurara ba ahaka abba yadawo dakin yayi shirin bacci yadauki laptop din yakashe masa sannan ya kwanta saboda duk azatonshi bacci fahad din keyi bai san tunani yake tayiba tunanin bilkisu wadda yasan har gaban abada bazai taba iya raba zuciyarshi da sonta ba duk da har gobe yana jin zafin abinda tayi masa amma baya danganta hakan da laifinta ko laifinshi yabarshi amatsayin rubutacciyar kaddara wacce shida ita basu isa guje mata ba.



*_Ummi Shatu_*    


BAZATA



*Littafinnan na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*



40***Sam daren ranar fahad bai samu runtsawa ba ko kadan yana ta sake sake cikin zuciyarsa ya kwance ya saka har dare yayi nisa duk da gargadin likita yana yawan fado masa zuciyarsa inda likitan ke cewa yaguji yawaita tunani haka kuma ya rinka samun isasshen bacci arana fiyeda na awa shida. Ganin dai bashida mafita sannan kuma baida guntuwar dabara yasashi fawwalawa Allah dukkan lamuransa dakyar yasamu bacci ya daukeshi wanda sanadiyyar hakan saida ya makara wurin tashi sallar asubah, sau uku Yaya Abba na tashinsa amma yana sake jan bargo balle ga uban sanyin da ake zurarawa sai bayan da aka fito daga masallaci Abba yasake tashinsa, tashi yayi yana babbata fuska kamar zaiyi kuka yanufi toilet saboda kwata kwata baya son taba ruwan sanyi a wannan lokacin sai dai hakan yazama dole. Har gari yawaye rana tafito bai tashi daga baccin da ya koma ba sama sama yake jin sallamar da Abba keyi masa bayan yashirya tsaf domin tafiya aiki, shikam sake gyara kwanciyarshi yayi yaja bargo ya lulluba amma ko minti biyu baiyi ba karar wayarshi ya tasheshi, dan guntun tsaki yaja sannan ya lalubo wayar wadda ke can karkashin pillown Abba,


"Abokina ya akayi?" Shine abinda yace bayan ya daga wayar,


"Kafita ne?" Salim yafada daga daya bangaren,


"A'a ina gida akwance...."


"To bari nazo nakarbi key din babur dinka dan Allah..."


"Sai kazo, idan kashigo ka dubashi can gaban katifa dan Allah basai ka tasheni ba...."


Daga haka yakashe wayar yasake gyara kwanciyarsa cikin sa'a bacci yafara fisgarsa amma lokacin da salim yashigo dakin saida yatashi duk da salim din bai tasheshi ba, bude kansa yayi ya leko yana lumshe idanuwa,


"A'a kaida kace kar atasheka kuma menene haka?"


Maida kansa yayi ya kwantar yana cewa,


"Dallah malam ni ka rabu dani bayan kaine ka tadani..."


Dariya salim yayi yafice daga dakin yana cemasa,


"Ka jirani inje indawo inyaso sai mu hau saman dakyau"


Koda salim yafita kasa komawa baccin yayi ganin lokaci na tafiya yasashi tashi yajanyo babbar rigar sanyinshi yasaka yafita dukkan hannayensa suna cikin rigar, cikin gida yashiga yadebo ruwan zafi yazo yayi wanka, yafito kenan yana shiryawa salim yadawo, kananan kaya yasaka yadora rigar sanyi yar madaidaiciya mai dogon hannu, zama yayi gefen katifa yana shafa mai, ahankali yace da salim,


"Abokina jiya nasamu labarin matata...."


"Wacce mata? Husnah?"


Harararshi fahad yayi sannan yayi murmushi duk a lokaci guda,


"Yaushe husnah tazama matata? Ai ba adaura mana aureba tukunna, maganar hajjaju Bilkisu nake yimaka.."


Tsaki salim yaja cikin jin haushi yace,


"Wai dan Allah meyasa kai baka da zuciya ne? Yanzu kai ko Bilkisu da kanta tadawo gareka taroki alfarmar ka mayar da ita gidanka yadace ka yarda da hakan? Bare kuma ba itace ta nemi hakanba, wai ana so dole ne? Tunda bata sonka kayi hakuri ka rungumi mai sonka amma bawai wadda bai damu dakai ba.... Harga Allah nidai am not happy da wannan madness din naka...."


Daga ido fahad yayi yana kallonsa saboda har lokacin salim din yana tsaye,


"Shikenan....." Fahad yafada yana cigaba da shafa mai akafarshi yana gamawa yajanyo safa yasaka yasan duk yadda zai kai ga yiwa salim bayani bazai taba ganewa ba saboda shi kadai yasan abinda yakeji, tabbas yasan Bilkisu bata sonshi to amma ai shi yana sonta kuma bashi ya dorawa kansa ba da shi yadorawa kansa da tuni yajima da cire sonta daga zuciyarshi ko dan yahuta.


"Ka zauna mana, bari nakarbo mana abinci muyi breakfast sai mufita gaba daya...."


Zama salim yayi yana harararshi har lokacin haushin kalaman fahad din yakeji, babu jimawa fahad yakawo musu gurasa da miya da dafaffen shayi mai kayan kamshi, ganin har suna kokarin gama cin abincin amma salim bai saki fuska ba yasa fahad langabar da kai,


"Haba abokina kayi hakuri mana ai na hakura kamar yadda kace inyi..."


"Yadai fi maka, amma matar da taso kasheka shine yanzu kake son sake tarayya da ita"


"To ai magana tawuce, nace maka na hakura"


Lab coat dinshi ya dauka da sauran abubuwan da yake bukata suka fita tareda salim, saida yafara zuwa jami'ar bayero yaga husnah sannan yawuce asibiti domin yanzu acan take karatu tana karantar Bsc nursing, shi kansa yasan abinda ya fadawa salim ba gaskiya bane domin bazai taba iya daina son Bilkisu ba shi yanzu fargabarsa ma guda daya ce kar wani yasake zuwa ya rabashi da ita ta hanyar aureta, gaba daya yinin ranar nan haka yayishi sukuku su kansu sauran daliban wadanda aka turosu tare saida suka fuskanci akwai matsala domin kamar marar lafiya haka yazama, su bash ma da suka kirashi video call saida sukayi korafin rashin kuzarinsa domin su ba kano aka turosu ba suna can Zaria, har yagama abinda zaiyi yatafi gida bashida wadataccen kuzari tun daga wannan lokaci yake jin ciwon kai sama sama. Kwana uku da haduwarshi da maama a super market takirashi suka gaisa duk da yaso share maganar Bilkisu amma yakasa saida ya tambayeta nan suka dan taba hira sukayi sallama, saving din number yayi ya ajiye wayar, yasan zaiyi wahala salim ya fahimceshi amma zaiyi iya iyawarsa wajen ganin ya fahimtar dashi, tashi yayi ya shirya yafita bai zame ko inaba sai shagonsu salim lokacin salim din na kofar shagon shida wani mai gyaran generator ganin fahad yasashi yin murmushi, ciki fahad yashiga yana dudduba turarukan dake jere reras,


"Malam me kake nema? Kasan dai babu irin turarenka anan domin kai babbar harka kakeyi mukuma na yaku bayi muke saidawa..."


Dariya fahad yayi yazauna kan kujera yana bashi hannu, musabaha sukayi fahad na cewa,


"Zaka fara sharrin nakane da ka saba? Nifa magana nazo muyi akan Bilkisu..."


Tsaki salim yaja sannan cikin fada yace,


"Wai dan Allah kai maye ne?"


Lips fahad yalashe yana murmushi,


"Mayen sonta ba, pls salim be serious... Wallahi Bilkisu bata taba yimin wani abu na cutarwa ba aduk tsawon zamanmu kawai abu daya tayi min wanda wannan ma kaddara ce da sharrin shaidan amma kai kanka shaidane munyi zaman lafiya da ita tunda kaima kana zuwa gidan kuma idanuwanka suna gane maka..... Wallahi salim ina sonta narasa ya zanyi...."


Ajiyar zuciya salim ya sauke sannan ya kalleshi,


"Nifa har yanzu banji kafadi abinda yarabaku ba nikuma shi nake son sani...."


"Salim wannan kuma ai sirrine, amma karka dora laifin akanta ka dorashi akaina... Sannan mubarshi azuwan kaddara"


"Shikenan Allah ya zabi abinda yafi alkhairi"


"Yawwa abokina, amin, dan Allah kazama cikin shiri domin wannan karon dakai za ayi yakin sannan katayani da addu'a.... Bari nahaura sama"


"Ashirye nake ai" salim yafada yana dariya, fita fahad yayi yahaura sama yana murmushi,


"Salim kenan...." Yafada acikin zuciyarshi lokacin da yake kokarin shiga cikin shagonsu. Tsawon sati biyu yadauka yana ririta maganar aranshi amma yarasa ta yadda zai iya fadawa su ayiyah ko baba, shidai yasan yayi addu'a a tsawon sati biyun nan sosai kuma har yau baiji canjiba gameda soyayyar Bilkisu sai dai abinda ke yawan fadar masa da gaba shine watanni biyu kenan da su baba suka kai musu kudin aure shida ya Abba, shi fahad gidan kanin Baban husnah dake Kaduna aka kai masa shikuma ya Abba Nusaiba kanwar salim, duk da haka baya jin zai iya hakura da auren Bilkisu koda kuwa mata uku yakaiwa kudin aure mutukar yanada gurbin da zai sakata, kullum da maganar yake kwana yana tashi amma idan yaje cikin gida sai yakasa sanar dasu amma yau ya kuduri aniyar fada ko yasamu yaji sauki acikin ranshi, mamuh yasamu tsakar gida tana daka fura ita kuma ayiya na dafa kindirmo, zama yayi kan kujerar mamuh yar tsugunno,


"Ayiyah dan Allah wani taimako nake son kuyi min.."


Dukkaninsu dakatawa sukayi daga abinda sukeyi suna sauraronsa, dakyar yasamu karfin yin magana,


"So nake ku sanarwa da baba yaje gidansu Bilkisu tsohuwar matata ta ya tambayar min izinin aurenta... Wai tunda jimawa suka rabu da tsohon mijinta nikuma wallahi har yanzu.... Ina.... Sonta..." Kai idan kaji yadda yakarasa maganar sai yabaka dariya amma su ayiyah basuyiba domin sun dake, nan kowa taci gaba da abinda takeyi babu wacce ta tanka masa har yakaraci zamansa yatashi yafita bai kara yimusu maganar ba suma basuce masa komai ba haka shima baba baice masa uffan ba shiyasa yafara tunanin kila su ayiyah basu sanar masa ba, tun yana daurewa har yasamu baba dakansa yayi kokarin yimasa maganar amma sai baba ya katseshi ta hanyar cemasa iyayensa mata sun yimasa maganar, nan mamaki ya ishi fahad, jin wai ashe baba yasani amma yayi shiru, shi dinma shirun yaci gaba dayi yana addu'a.


Bayan sati daya da faruwar lamarin ranar asabar yana kwance dasafe yana bacci kasancewar babu aiki Abba yashigo yana tashinsa, yana bude ido abba yace masa,


"Baba yace katashi kashirya zamu rakashi anguwa anjima..."


Duk haushi yaji ya kamashi haka kawai yana baccinsa mai dadi Abba yakatse masa saida yagama nuku nuku da kunbiya kunbiyarshi sannan yatashi yayi wanka ganin irin shigar da Abba yayi harda babbar riga yasashi shima kwaikwayon shigar abban ko ba komai babbar rigar zatayi masa maganin sanyi, kasancewar sanyine basubar gidaba sai bayan azahar su shidane acikin motar da baban salim da baba sai salim din da fahad gaban motar kuma ya baffane ke driving ya abba na zaune gefenshi,shi dai fahad nata son ya tambayi inda zasuje amma babu dama domin da ya tambayi salim cikin rada ma cewa yayi shima wallahi bai saniba, tafiya sukayi mai nisa shidai sai yaga kamar yasan garin amma kuma gaskiya yakasa tunowa sosai yadda yakamata. Karfe uku da wani abu suka karasa babbar fada wacce ke girke tsakiyar garin sai lokacin fahad yatuna garin ashe garko ne garinsu Bilkisu domin aurensu nafarko anan aka daurashi,


"To amma me mukazo yi nan kuma? Ko rasuwa akayi musu?"


Wannan tambayar ita yake ta yiwa kansa har suka shiga ciki inda jama'a ta dan taru amma kuma mutanen basuda wani yawa sosai, daga can baya suka zauna shida salim sukuma su baba suka wuce can gaba, tsawon mintuna goma aka dauka ana gaishe gaishe kafin daga bisani aka fara daurin aure, sudai su fahad basa jiyo abinda ake fada bayan kamar mintuna biyar aka gama daura aurenshi da Bilkisu batareda yasaniba akan sadaki naira dubu talatin aka daura auren wanda baba shine yabada sadakin, kiransu ya Abba yazo yayi nan suka karasa gaban manya shidai yaga anata nunashi amma bai san daliliba saida suka fito bayan sun gama gaishe da manyan sannan yake tambayar Abba dalilin nunashin da aka yitayi aciki,


"Ango ake tambaya shine aka nunaka saboda wasu sun zaci wai nine..."


"Ango kuma? Wai auren wa mukazo ne?"


"Aurenka da Bilkisu mana...,congratulations lil bro...."


Jin abinda yace yana dafa kafadarsa yadaure masa kai shida salim, saida sukayi sallar la'asar aka fito musu da abinci sannan sukayi haramar tafiya, goro da alawa da dabino aka kawo musu fal aka saka abayan mota,suna kokarin shiga cikin mota su baba suka karaso fuskarsu dauke da fara'a hannunsa cikin na abbansu Bilkisu suna sake yin doguwar musabaha......



*_Ummi Shatu_*    


*FARIN GANI*


*Wannan littafin na siyarwane me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*




41***Shi dai fahad har suka bar cikin garin garko sukayi tafiya mai nisa bai bar mamakin abinda ke faruwa ba jinsa yake kamar acikin mafarki gaba daya lamarin yadaure masa kai, yana so yayi tambaya amma yana jin kunyar kar su baba suga rashin kunyarsa, shiru yayi kawai ya lumshe idanuwansa yana sauraron hirar su baba wadda mafi yawanta akan irin halin dattako da karamcin abbansu Bilkisu ne, godewa Allah yake tayi acikin zuciyarsa domin yasan shine yayi masa wannan gatan yasake aura masa Bilkisu akaro na biyu. Daf da lokacin sallar magriba suka shiga cikin garin kano, murnarsa bazata taba kwatantuwa ba a wannan lokaci, ko cikin gida bai shiga ba yawuce dakinsu yabar ya Abba da salim da aikin shigar da kayan daurin aure cikin gida, wanka yafara yi da ruwan sanyi domin yanzu ko sanyinma sai yaji yadaina ji shifa yanzu jinsa yakeyi tamkar anzare masa wata doguwar kaya daga cikin jininsa, yana fitowa yatarar har Abba yafita masallaci haka shima salim baya nan may be ko yatafi gida kokuma yaje salla, agurguje shima yashirya dan gudun kada yarasa jam'i.


Bayan an idar da salla tareda salim suka koma dakinsu domin yana son dauko wayarshi wadda yabari acan bayan yayi wanka,


"Abokina wai tayaya duk wadannan abubuwan suka faru cikin sauki haka....?" Salim yafada yana dafe da kafadar fahad wanda yasha kananun kaya,


"Wallahi salim nima ban saniba... Gaskiya su baba sun shammaceni saboda ban taba zaton zasu aminceba duba da yadda sukayi biris da maganar bayan na sanar dasu..."


Dariya salim yayi,


"Ashe babban shiri suke yimaka..."


"Kabari kawai abokina... Babu abinda zamuce da iyayenmu sai dai muce Allah yakara musu nisan kwana sannan yayi musu sakayya da gidan aljannah... Aljannar ma jannatul firdaus..."


"Amin amin... Tofa yanzu kai kakusa zama mai mata biyu tunda ga husnanka agefe tana jira"


"Ai yanzu ma wurinta nakeso ka rakani...."


"Wa? Ni? Tab ai wallahi babu ni awannan tafiyar... So kake tayi fushi dani saboda narakaka ka fada mata kayi mata kishiya, last time ma dani mukaje, gaskiya bazanje ba, saboda wallahi sai tayi tsammanin ko ni ke zugaka..."


"Zuga kuma? Kajika da wani zance kuma, shikenan tunda bazaka jeba, ni bari naje"


"Allah yakiyaye hanya... Bani aron laptop dinka, wanna surprise u....."


"Kasan inda take ai kaje ka dauka..."


Turare yakara feshe jikinsa dashi sannan yadauki rigar sanyi yadauki wayarshi yafita yana duba wayar tashi cikeda mamaki ganin miss calls har guda biyar yana dubawa yaga maama ce cikeda fara'a yayi calling dinta back bugu uku yaji ta daga tana dariya,


"Ango ko duk kacaniyar fama da jama'arce haka?"


"A'a Maman hudah, naje salla ne wallahi, sai kuma kikaji abu ko?"


Dariya tayi cikin farin ciki tace,


"Wallahi fa, Allah yasanya alkhairi yabada zaman lafiya..."


"Amin maama, nagode sosai"


Sai da ta dan kara tsokanarshi sannan sukayi sallama ya ajiye wayar kawai tunanin da yake tayi shine ko har yanzu Bilkisu tana nan ayanda take kokuma ta canja?


"Hmmm may be tayi kiba ko kuma ta rame... Kila tayi haske ko kuma fatarta na nan kamar da..."  Yafada yana tuki murmushi kwance kan fuskarshi, yau jinsa yake kamar yana yawo akan iska saboda farin ciki, saida yakusa isa gidansu husnah sannan yakirata awaya yace mata gashi nan zuwa shiyasa kafin yaje har tagama shiryawa taci kwalliya tana ta zuba kamshi cikin doguwar riga ta material, inda suka saba zama suyi hira idan yazo yauma acan suka zauna kan daddumar data shimfida musu, yanata janta da wasa yana fara'a irin wacce tajima bata ga yayiba sai abun yabata mamaki har tagagara yin shiru,


"Ya fahad wannan fara'ar fa? Gist me pls..."


Murmushi yayi ya gyara zamanshi yana wasa da agogon dake daure a hannunshi, gaba daya bai san ta yaya zai sanar da itaba amma yazama dole yafada mata saboda baya son yafara munafurtatta tun daga yanzu,


"Yanmata na kin san me? Ur aunt is back...."


Daga idanuwanta tayi ta kalleshi fara'ar dake kwance kan fuskarta tana gushewa,


"Which aunt? Banfa ganeba..."


"I mean matata...." 


Shiru yaji tayi batace komai ba zuwa can kawai tamike tana karkade jikinta,


"Allah yasanya alkhairi yakuma baku zaman lafiya...."


Da sauri shima yamike ya rikota,


"Haba husnah... Dan Allah kar kiyi fushi... Kiyi hakuri kinji, ki tsaya ki saurareni..."


Idanuwanta dake kokarin kadawa izuwa launin ja ta zuba masa,


"Ni kaji nace kayi min laifine? Dama nasan itace aranka, ita kakeso kake kauna to kuma menene sabo aciki wanda ban saniba? Ni dama ba sona kakeyi ba ita kakeso nikuma nake yin son maso wani..."


Hannuwanta dake cikin duka nashi yarike gam yasake matsewa,


"Husnah wallahi Allah kema ina sonki... Meyasa zakice ita nakeso? Wannan auren fa nikaina wallahi ban san dashiba sai dazun nan... Haba yanmata na"


Wata harara ta watsa masa acikin duhun da suke sannan cikin fada tace,


"Sakar min hannu, kaje kayita zama da matar taka.... Nidai kasani nafasa aurenka saboda bazan taba zama tareda itaba....."


Gaba daya hannuwan nata yayiwa ja daya sai gata kan jikinshi rungumeta yayi sosai ajikinsa wai zaiyi rarrashi amma taki bashi damar hakan daga karshe daga shi har ita basu san menene ya gifta ba kawai dai sunji sun shagala da tsotsar bakin juna abinda bai taba faruwa ba tsakaninsu asalima idan itace ta nemi taba koda hannunsa ne fada yake yimata. Kifa kanta tayi saman kirjinsa tana kuka ahankali,


"Kiyi hakuri husnah.. Bana son wannan kukan naki... Kuma kisani bafa fin son bilkisu nayi ba akanki... Kema u are always in my mind... Yanzu duk yadda zan kwatanta miki u won't understand but am assuring u idan mukayi aure gonnah show u how much u mean to me..."


Haka yayita rarrashinta da kalamai masu dadi amma taki saurararsa daga karshe ta fincike tayi cikin gida tana sharar hawaye, daddumar da suka zauna ma sai shine ya nade yamika ciki, haka yatafi babu kuzari atare dashi domin wani irin tausayinta yake ji amma kuma da zarar yatuna da cewa shine sanadin kukanta sai yaji wani iri, tun yana hanya yaketa kiranta amma taki daga wayar. Ahanya yayi salla sannan yawuce gida, yunwa yakeji sai dai yana kunyar shiga gidan musamman da su anty asabe suka kirashi suna tayashi murna harda kiransa da ango, cikin sa'a yana shiga dakinsu ya iske abba yana cin tuwon biski miyar kubewa, zama yayi suka karasa tare sai ga salim yashigo,


"Karbi system dunka..., ya kukayi da mutuniyar?"


"Tayi fushi inata kiranta taki dauka..."


"Saika rarrasheta..."


"Dolena ai... Zan gwada"


Ficewa salim yayi dama Abba yadade awaje shikam, ga mamakin fahad yana duba system dinshi yaga hoton Bilkisu kan screen din yafito radau ashe duk hotunan da salim yagoge awayarshi da jimawa ya ajiye masa sune, wani farin cikine ya sake lullubeshi nan yarinka bin hotunan daya bayan daya yana shafawa.



_BILKISU_



 Dawowarta kenan daga islamiyyar da take zuwa kowacce asabar da lahdi, tana fitowa daga wanka ammah taleko tace tazo inji Abba dama yau yadawo daga garko tun jiya canma ya kwana,agaggauce tasaka doguwar riga ta dauki hijabi tafita tanufi sashen Abba, suna zaune shida Ammah tana sake shirya masa kayansa wadanda zai tafi umarah dasu yauda daddare,


"Mai gado... Karbi wannan"


Hannu tasa takarbi kudin da abba yamika mata,


"Sadakinki ne gashi nan... Jiya aka daura miki aure insha Allah nanda sati uku zuwa Hudu zaki tare agidan mijinki, kiyi hakuri kiyiwa mijinki biyayya sannan ki zauna lafiya dashi..."


"To Abba..."


"Allah yayi miki albarka... Tashi kije"


Tashi tayi kanta na sara mata yana yimata wani irin juyawa ahaka tafita daga falon tana fita Abba yadubi ammah yace,


"Mahaifin tsohon mijinta ne yazo min da maganar neman aurenta shine kawai nace yafito adaura aure takoma gidan mijinta domin da sabon gini gwara yabe..., zaman nan nata dama yana damuna wallahi shiyasa tunda Allah yakawo ai gara ayi"


"To Allah yabasu zaman lafiya yasa mutuwa ka raba" inji ammah,


"Amin, kinga ko babu komai itama iyallo yanzu zata samu zama wuri daya wannan sintirin zata hakura dashi"


"Hakane".


Tunda Bilkisu tashiga dakinta take kuka ita dai tasan bata bakin ciki da zabin Abba amma harga Allah bataso wannan aurenba, wannan wanne irin aurene za adaura ba afadawa kowa ba sannan ba abarta ta ko ga mijinba? Tunda aurenta yamutu da hamood take addu'a babu dare babu rana akan Allah yafito mata da miji nakirki mai kaunarta saboda Allah amma shiru kakeji har yau babu wanda yazo yayi sallama da ita akan yana son zai aureta, ya mudan ma lokacin da iyallo tayi masa tayin aurenta ki yayi kiri kiri yace bazai auri bazawara ba saboda yanada budurwarsa gashi yanzu har matarsa ta haihu shiyasa iyallo kullum cikin zuwa gidan take tana fada da masifar Bilkisu taki aure bayan zaman da tasha da yanzuma gashi tasake dawowa, iyallo bata yin wata daya batazo gidan nan ta tayarwa da kowa hankali ba, wannan zuwan da tayi kuwa na karshe cewa tayi Alh Ilya zata aurawa Bilkisu dama ai idan akabi salsala dan uwanta ne, kuka Bilkisu keyi sosai domin duk tunaninta alh ilya dinne aka aura mata domin irin alhajin kauyen nanne matansa uku da 'yaya rututu kai idan kaga tukunyar da ake girki da ita agidansa sai ka kalleta ka kara, gashi kuma ba acikin garko ma yakeba acan wani kauyen kayau yake shiyasa abin yake tsoratata. Saida tayi kukanta ta godewa Allah sannan tayi shiru amma fa bata da walwala, daren ranar Abba yatafi umarah ita kam da ciwon kai ta kwana washe gari ko aiki bataje ba tana daki akunshe daga karshe takira maama tana kuka tana fada mata wai Abba yadaura mata aure da alhajin kauye gashi har yau bata ga mijinba, hakuri maama tabata sannan tayi mata kalamai masu kwantar da hankali tace insha Allah auren nan zataga fa'idarsa da alkhairinsa, da ta tambayi maama ko tasan waye mijin nata maama cewa tayi bata sanshi ba haka sukayi sallama taci gaba da zama cikin fargaba gashi sam ammah taki bari ma suyi maganar dole tahakura ta zubawa sarautar Allah ido.


Bayan kwana biyar da daura auren fahad yashirya yaje gidan wai gaida su ammah dakuma yimusu godiya tun tuni yake bin salim akan ya rakashi amma yanata kawo uzururruka shiyasa yau yashirya yayi tafiyarsa shi kadai, iya ammahn ce kadai ita tayi masa lale tasa Rabi takawo masa kayan motsa baki amma baisha koda ruwaba, shi kunya ammah kunya dan dakyar ma suka gaisa daga karshe ammah tashige bedroom zuwa can takira Rabi tace ta rakashi dakin Bilkisu.


Kasancewar Rabi tasan ba a shigarwa Bilkisu daki daga waje ta tsaya ta nuna masa dakin yashiga bayan yacire takalminsa, tana kwance kan gado tayi ruf da ciki tana shan iska domin dakin cike yakeda sanyin air condition, sannan ga kamshinta nan wanda yasani tun usuli yacika dakin, kalba ce akanta kan babu dan kwali sai yar doguwar riga iya gwiwa light pink mai karamin hannu, ganinta yayi tayi masa yar karama acikin idanuwansa domin babu abinda takara saima yarinta da ta kara kai idan basani kayiba zakace yar 22 years ce saboda rashin girma......




*_Ummi Shatu_*    


42***Tamkar wanda yasamu tv haka ya tisata agaba yana kallonta yafi mintina goma tsaye kanta yana kallonta irin kallon kurulla kamar wanda keson gano canjin da jikinta yasamu a kwanankin da basa tare,


Gefenta yasamu ya zauna yana cigaba da kallonta ahaka wayarshi ta dan fara kara cikin azama ya matseta ya danne karar sannan ahankali yamaida ita silent kafin ya maida kallonshi kanta, juyi tayi daga rub da cikin da take zuwa rigingine tana mikar da tasata bankaro kirji tareda sakin hamma a lokaci daya amma har time din cikin bacci take domin rabonta da bacci mai yawa tun ana igobe Abba zai sanar da ita maganar aurenta.


Sake cika yaga tayi a idanuwanshi ta chest dinta wanda ko bra babu, dan hararar wurin yayi yana jin kishi na taso masa sakamakon tunawar da yayi cewar ta taba aurar wani fa bayan shi, shikuma gashi da jarabar kishi musamman ma akanta, idonshi yamayar kan cinyarta da ta dan bayyana kadan sakamakon kwayewar da rigar tayi lokacin da take yin juyi, luwai luwai jikinta yake haka yarinka binta daga kasa har zuwa sama sannan yadauko daga sama izuwa kasa, kan kwaurinta ya tsayar da idonshi yana cije baki sam baima taba kula da singalalinta ba sai yau, anan ya tsaida kallonshi yana ta son tunowa da abinda yataba karantawa a facebook dangane da cikar kwauri sai zuwa can yatuna wani post ne da jimawa yakaranta wai ta kwauri ake gane sweetness din mace, idan sha rabanta acike yake to babu karya tayi, ga mamakinsa sai yayi hanzarin maida kallonsa kan hips dinta domin yana daya daga cikin abubuwan da aka fada acikin post din dan ranar da ya karanta ma shi kunya ya rinka ji shi kadai haka kawai wani friend dinshi tagging dinshi akan post din, yana cikin nazarin hips din nata zuwa samanta yaji wayarta ta kaure da kara ahankali tamika hannu ta daukota idanuwanta arufe ta daga wayar ta kara acikin kunne,


"Kawata nace yanaji shirune.... Nashirya fa tun dazu..."


Cikin bacci taji abinda khulsum tafada wallahi ita sam tamanta ma ashe sun shirya tafiya asibiti dubo Christy abokiyar aikinsu wadda aka yiwa cs kwana biyu da suka wuce amma babyn babu rai shine sukace zasuje dubata yau domin suna zaman mutunci da ita.


"Yi hakuri Maman Khalifa wallahi bacci ne ya daukeni... Bani 10 minutes ina nan zuwa..."


Har lokacin bata san da mutum acikin dakinba duk da tunda tafarka take jin wani kamshi ya cika dakin, tunda tafara waya yaja baya sosai yamatsa daga kusa da ita sabanin da,


Tashi zaune tayi Allah yasota atishawa ta fito mata amma da niyyarta ta kwaye rigar jikinta tashiga toilet, kamar ance ta kalli bayanta taga mutum ba karamar razana tayiba saida tayi ta maza sannan ta iya controlling kanta amma acikin zuciyarta addu'a ta kamayi ba kakkautawa jikinta har rawa yakeyi saboda tsoro, fuskarshi ta kalla tabbas fahad ne to amma meya kawoshi dakinta? Wannan itace tambayar da tafi kai kawo cikin kwakwalwarta,


"Malam lafiya?" Tafada cikin dakewa, ai ga mamakinta sai taga ko kallonta baiyiba hankalinsa na kan wayarshi dake hannunshi fuskarshi kuma daure kamar an aiko masa da sakon mutuwa, kasake tayi tana kallonsa sosai taga yacika mata idanuwa domin a yar shekara dayan zuwa da rabi da bata ganshiba yasake zama cikakken namiji duk da ba kiba yayiba amma ya dan murmure kuma har yanzu za asashi sahun sirara, gashi dan tsaurin ido har gemu taga ya tsayar na rashin kunya irin yanda samarin yanzu keyi idan suna tashen balaga, har takaraci kallonsa tagama bai daga ido ya kalleta ba, shaddace ajikinsa mai kwabo kwabo milk colour harda hula amma yacire hular tana ajiye kan cinyarsa fuskarsa tayi haske sosai da duk jikinshi gaba daya ma amma kowa yaga fuskar yasan he's still young, sosai abin yabata haushi da tayi masa magana ya shareta,


"Malam dakai nakefa? Meya kawoka dakina? Yakamata kashigo min daki any how?"


Sai lokacin ya daga ido ya kalleta amma baiyi magana ba dolenta tajanye idanuwanta daga gareshi saboda kwarjinin da yayi mata. Cikin fushi taja hijabinta tafita, dakin Ammah taje tana tambayarta me fahad keyi adakinta nan ammah tace shida dakin matarsa sai aje ana tambayar me yakaishi?


Sake komawa dakin nata tayi jiki babu kwari wato shi aka sake aura mata akaro na biyu ashe ashe zamansu bai kareba Allah kadai yasan ranar karewarsa, ita dai tasan bazata yiwa Allah butulciba amma gaskiya bahaka taso ba, ba da fahad take son gudanar da kayan kunyar nanba, bata son yaga girmanta har yakai ga rainata dama gashi yanzu tafara ganin salon rainin nashi tunda ko gaisheta baiyi ba bare tasa ran zata bashi umarni yabi kamar zamansu na baya, afusace tashige cikin bathroom bayan taja towel dinta dake kan kofa, tana wanka tana tunani yanzufa yaron nan dan baida kunya sai yace zai ziyarceta a shimfida ko? 


"Subhanallahi... Allah ya sawwake... Ashe kuwa zan mutu da budurcina..." Tafada acikin zuciyarta. Shi dai yana zaune yana sauraron karar ruwan da take wanka dashi acikin bathroom, yasan jira take yagaisheta kamar yadda yakeyi ada amma abinda bata saniba shine yanzu ba da bace idan har tunaninta shine zai gaisheta to zasu shekara basu gaisa ba sannan yanzu itace ma zata rinka gaisheshi ko tana so ko bata so dolenta dan bazai dauki raini ba, jinsa yake yi yanzu a matsayin babba gaba da ita,


Yanata murmushi shi kadai sakamakon abinda yagano a facebook dama post din da akayi magana akan cikakkiyar mace dinnan ta yadda ake gane alamominta yatafi nema wanda yakai kusan shekara da karantawa amma dayake Facebook baya goge abu komai jimawar da yayi sai gashi yasameshi bayan dogon bincike, duk macen dake da kananun ido to jarababbiya ce awurin shimfida,sannan wadda dan yatsanta na kafa nakusa da babba yafi babban tsawo to tanada bukata sosai, mai hips sosai tanada nisa, haka mai manyan mazaunai, sannan mai manyan chest itama tanada yawan bukata,mai dan mitsitsin baki to halittarta ma ta ya mace hakan take, yana tsaka da sake karantawa ta bude kofa tafito daga cikin bathroom din fuskarta babu fara'a shima gimtse tasa fuskar yayi yana sake karanta post din wanda wannan shine karo kusan na biyar da yake ta tisawa yana sake maimaitawa, shi bai damu da yaga wadannan abubuwan da ya karanta atare da husnah ba amma akan Bilkisu kam sai yagane komai.


Tana cika tana batsewa ta nemi wuri ta zauna bayan ta dauki man shafawa ita duk abinda yafi bata mata rai shine rashin gaishetan da baiyiba sannan tana yimasa magana yayi wani banza da ita dan tsabar rainin wayo acikin hijab taketa nuku nukun shafe jikinta da mai saboda yanzu yanayi ya sauya duk da jiya da yau zafi akeyi amma idan kayi wanka baka shafa maiba sai kayi fururu saboda lokacin sanyine, ta gefen ido yake satar kallonta,yatsun kafarta yaketa satar kallo ai kuwa yaga nakusa da babban yafi babban tsayi, daidai lokacin ta mike ta isa gaban wardrobe dinta ta juya mishi baya tana neman kayan da zata saka,kallonta yake tayi ta baya ya kafe hips dinta da ido,


"I will find it out...." Yafada acikin zuciyarshi yana dariyar mugunta,


"Uwar son girma, ashe har yanzu halin nan yana nan ba asauyaba na son girma...  Very soon Zamu banbance nidake waye babba...." Yasake fada cikin ranshi, doguwar riga ta ciro ta atamfa tanata yin kunkuni,


"Kawai zaka wani shigo min daki kasani agaba... Ban son takura..."


Daga haka tawuce bathroom tana cigaba da kunkuninta, duk abinda take fada yana jinta saboda shi jinsa akusa yake komai kankantar motsi sai yajishi shiyasa suke yawan fada da abba yayanshi domin idan yana bacci ko tari abba yayi sai yaji, jine dashi sosai kamar maciji ko kana dan nesa dashi kayi gulmarshi sai yaji sai dai kawai yarabu dakai yayi kamar baiji ba. Mintuna kadan sai gata tafito rikeda hijabinta a hannu, akofar bathroom din ta tsaya ta shanya towel dinta sannan takaraso cikin dakin daidai lokacin da wayarta tafara kara cikin sauri ta dauka tana cewa,


"Gani nanfa... Fito kofar gidanki zanzo da mai napep inyaso kawai sai mu wuce..." 


Daga haka ta ajiye wayar tawuce gaban mirrior ta bulbula turare halinsu daya dashi wurin son kamshi kwata kwata bata gajiya da siyan turare ko tanada kwalba ishirin a ajiye kan mirror dinta, maroon din mayafi taciro kasancewar atamfar jikinta akwai ratsin maroon ajiki ta dauki hand bag milk ta dauki wayarta sannan tanufi wurin shoe rack tadauko flat din takalminta tasaka tayi hanyar kofa, sai da takusa zuwa kofar cikin isa da kasaita taji yace,


"Ina zakije?...."


Bata ko kulashiba tayi niyyar fita nan taji yasake maimaita ina zakije?


Kanta tsaye tabude kofar zata fita amma kawai sai ji tayi ya danko waist dinta yadawo da ita baya, sam bataji lokacin da yataso ba bare taji tafiyarsa, mayar da kofar yayi ya rufe, yanda ta sha kunu haka shima yasha kunu, kawar da kanta tayi gefe daya tana huci yayinda shikuma yake kallonta ko kiftawa baya yi,


"Wai meye haka? Wannan wanne irin wulakanci n...."


Bata kai ga karasawa ba taji ya fincikota wanda har saida kirjinsu suka manne wuri daya, numfashinsu ke haduwa kowa yana shakar na kowa, ido ta daga dakyar ta kalleshi shima yana kallonta,


"Wa kika tambaya da zaki fita?....... Ehye?.... Tambayarki nake.... Nace wa kika tambaya?" Yakarasa magana cikin tsawa,


Yana kallon yadda idanuwanta ke kadawa tamkar zata fashe da kuka, cikin bakin ciki da rawar murya tace,


"Ba asaniba..... Dallah ni ka sakeni...."


Sake matseta yayi har lokacin yana rikeda damtsenta daya tana manne kirjinshi,


"Ni kike cewa baki saniba?.... Idan kikayi wasa wallahi daga yau bazaki sake ko taka daidai da kofar gidaba.... Zakiyita zama cikin gidan nan babu fita har sai ranar da na gadamar daukarki na kaiki duk inda nakeso...."


Sake matsota yayi cikin huci yace,


"Sannan kisan irin maganar da zaki rinka fada min idan bahaka ba sai kinyi nadama...."



Fincikarta yayi wanda har kayan hannunta suna zubewa yaje ya jefata kan gado nan ta zabura ta mike wanda hakan yaso bashi dariya amma yadake,


Tsayawa tayi ta rike kugu tana haki tamkar dambe zasuyi,


Matsawo yafara yi ahankali yana cewa,


"Ko dambe zakiyi dani ne? Nace dambe kika tashi yi dani....?"


Kafin tabashi amsa wakar ali jita tafara tashi daga cikin wayarshi,  _"Rana da wata suna da haske gimbiyata sai ke soyayyarmu har abada...ko rana da wata sun daina haske gimbiyata sai ke soyayyarmu har abada..... I love u baby.....Sarauniya baby...."_


Komawa yayi da baya yadauki wayar domin yasan husnah ce saboda ita kadai yasawa wannan tune din,


Zama yayi kan bedside drewar dinta yadauki wayar,


"Sweet ma'u ya akayi.... Ko har yanzu fushin akeyi dani?" Yafada yana murmushi kasancewar tun lokacin da yafada mata anmayar da aurensu da Bilkisu bata daukar wayarshi sai yau da ta kirashi,


"Ya fahad Allah kai dinne kana bani headache dayawa...."


Hands free yasaka wayar tayadda Bilkisu zataji komai wacce har lokacin ke tsaye tana rikeda waist dinta,


"Am very sorry one love... Ki yafewa Prince dinki idan bahaka ba ciwon zuciyata yatashi dama kuma kin san ata sanadiyar sonki ya kamani...."


Ajiyar zuciya husnah ta sauke sannan cikin sanyin murya tafurta,


"No ya fahad dan Allah kabari bana son inrasaka.... Na hakura, bazan sake bata maka rai ba.... Ranar ma ban san meya sameni ba har nayi fushi dakai... Am so sorry..."


"Kishi...." Yafada yana murmushi yana satar kallon Bilkisu wacce tacika tayi famm sai huci takeyi kamar bijimin sa,


"U are right.... Ni nasan inada kishi akanka bana son nayi shearing dinka da kowa amma babu yadda zanyi i will accept koma meye...."


"That's why am loving u.... I love u yanmatanah..."


Ai Bilkisu bata jira tagama jin wadannan mugayen kalmomin nashiba ta shige cikin bathroom ta bugo kofar da karfi garammm wadda hatta husnah dake kan waya saida taji, har suka gama waya da husnah Bilkisu bata fitoba, hularshi yadauka yasaka yasan acike take dashi na ya hanata fita unguwa gashi kuma yazo yana waya da wata agabanta duk da baida tabbacin ko tana kishi ko sabanin haka amma yadauki alwashin gano hakan, itace bata saniba duk maganganun da yake fadawa husnah ita yake fadawa indirectly amma yasan bazata ganeba, gaban bathroom din yaje yatsaya yakara kunnensa amma baiji motsin komai ba yasan ba komai takeyi ba,


"Kin dai ji abinda nafada miki ko? Karki sake inji labarin kin fita... Sannan ki kira ita kawar taki kifada mata nahana wannan fitar..."


Cikin jin haushi da masifa yaji tace,


"Sai anfitan... Kayi abinda zakayi... Kuma baza akiratan afada mata dinba kai ka kirata mana da kanka... Aikin ban..."


"Idan kika kuskura kika karasa ko...idan ba tsoro ba kibude kofar mana....", kwafa yayi da karfi sannan yace,


"Ni ai bana kiran matan mutane iya inda Allah ya tsayar dani na tsaya... Gobe aiki kadai nayarda kifita baya ga nan duk inda kikaje keda Allah..."


Bai jira abinda zatace ba yawuce yafita yana jin wayarta nata ringing duk da bai dubaba yasan abokiyar tafiyar tatace taji shiru shine kila take kira, duk da bai fada directly ba tagane da hamood yake da yace wai shi baya kiran matan mutane, jin yafita yasa wasu hawayen bakin ciki zubo mata, wai ita fahad kanin kanin bayanta ke yiwa haka wannan wacce irin kaddara ce? Wai meyasa zaman nan yasake kulluwa?....





*Littafin nan na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*




*_Ummi Shatu_*    


JIYA IYAU...



*Wannan littafin na kudine me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*




43***Tafi mintuna goma cikin bathroom din bata ko motsa ba kawai hawayen bakin ciki da takaicine ke fita daga idanuwanta ba abinda yafi tsaya mata arai irin iko da isar da yake neman fara nuna mata, danme zai sakata agaba yana yi mata tsawa? Bude kofar bathroom din tayi tafito ko zama bata yiba ta nufi falon ammah wacce ke zaune suna gaisawa da Abba amma kafin Bilkisu takarasa har sunyi sallama kasancewar su lokacin salla yayi acan,


Zama tayi idanuwanta duk sun sauya cikin bacin rai tafara magana,


"Ammah gaskiya yakamata kijawa fahad kunne..... Naga abin nasa yana nema yayi yawa, ni bana son nuna isa da gadara...."


"Wani abu yayi miki?" Ammah ta bukata bayan ta zuba mata ido tana sauraronta,


"Ammah waifa har nagama shiryawa zamu fita nida khulsum dubiyar abokiyar aikinmu shine zai wani ce wai baza niba...."


Murmushi ammah tayi kafin tace,


"To ni mai gado menene nawa? Shine dama yakeda ikon yabarki ko ya hanaki kuma tunda ya hana ba shikenan ba?"


Wasu zafafan hawaye taji sun zubo mata sakamakon abinda taji ammah tafada, wato shikenan haka za abarshi azuba masa ido yayita yin abinda ya gadama?


"Amma ammah haka za abarshi....?"


"Mai gado to me kikeso nayi akai? Shine yakeda iko dake bani ba... Akan ya hanaki fita unguwar shine zaki zauna kina kuka? Allah ya kyauta to"


Tashi ammah tayi tafita zuwa kitchen domin ganin wacce wainar Rabi mai aikinta take toyawa ganin haka yasa Bilkisu tashi tafita zuwa dakinta. Tana shiga taji wani abu yatsaya mata arai musamman da ta shaki kamshin turarenshi wanda yatafi yabar mata adakin, karar wayarta ne ya katse mata tunani nan ta daga cikin sanyin murya,


"Haba labour irin wannan jira haka? Kin barni tsaye fiyeda 30 minutes.... Nidai tuni nakoma cikin gida gashi inata kiranki baki daga ba hope u are doing good?"


Ajiyar zuciya Bilkisu tasauke cikin sanyin murya mai kunshe da zafin rai tace,


"Am very sorry kawata,kin san me? Hanani zuwa yayi dan rainin wayon nan har saida yabari nagama shiryawa ina kokarin fitowa yace bazan jeba...."


"Wai wa kike magana ne?" Khulsum ta bukata,


"Fahad fa...."


Dariya khulsum tayi sannan cikin kara tace,


"What? Wowwww.....fahad again? Wonderful... Tofah, kice love kuka zauna yi shiyasa nayita kira kika ki dagawa..."


Cikin fushi Bilkisu tace,


"Malama bana son wulakanci... Abinda yafi love a'a kin manta sex...."


Dariya khulsum tayi cikin tsokana tace,


"Ai shi dinma bazance a'a ba may be kunyi tunda mata da mijinta ai komai na iya faruwa...."


"God forbid...." Daga haka takatse wayar cike da takaicin khulsum, yanzu tasan ba khulsum kadai ba kusan kowa haka zai rinka kallonta fanko ana yimata kallon tayi tarayya da kanin kaninta, kwanciya tayi cikeda bacin rai sai kuma wayar da yakeyi yi tafado mata,


"To wai aure yayi ko kuma budurwarsa ce?" Shine tambayar da tayiwa kanta bata samu amsarta ba tasoma kukan bakin cikin da ya kunsa mata, saida tasha kukanta ta more sannan taji zuciyarta tayi sanyi kadan kawai sai taji bata son sake ganin koda mai kamarsa ne, gaba daya wani irin haushinsa takeji, da haushinsa ta kwana ranar washe gari kuwa bayan tadawo daga aiki harda kulle kofarta gudun kar yashigo mata kamar jiya amma kuma sai taji shiru baima zo ba.


FAHAD


Tunda yabar gidansu Bilkisu yake jin nishadi atare da shi bawai bata mata ran da yayine yafi burgeshi ba a'a yadda yafara sata tayi laushi tun ba aje ko inaba shi yafi bashi dariya, sannan bawai yahanata fita bane dan ya kuntata mata sai dai kawai yana son ya nuna mata tsakaninsu shine jagora kuma shine shugaba koda kuwa shekarunta sun ninka nashi sau dari, dole awannan zaman nasu sai ya gyara mata zama kuma ya nuna mata karfin power din da yake da ita.


Da niyyarshi yaje gidansu husnah amma sam taki yarda yasan kunyarshi takeji sakamakon abinda yafaru tsakaninsu rannan shima kansa kunyar yakeji but babu yanda ya iya saboda mai faruwa ta rigada tafaru. Daren ranar yana kwance kan katifarsu ya tasa kanshi da pillow yadora laptop dinshi kan cikinshi yana kallon wani Nigerian film kawai sai yaga film din yayi kama da irin rayuwarsu shida Bilkisu saboda shima guy din cikin film din matar ta girmeshi amma yadda take tarairayarshi abin gwanin burgewa, lumshe ido yayi yana tunanin to ko sai yaushe shi zai samu irin wannan tarairayar wurin hajjajun tashi, murmushi yayi kafin yace,


"Mai gado rigima..."


"Kai kuma kaida waye kake magana?" Abba yace dashi wanda shigowarshi kenan cikin dakin,


"Ya Abba kallo nake yi, kasan wani lokacin idan mutum yana kallo ko yana karanta novel kamar me aljanu yake zama saboda zakaji yana magana shi kadai...."


"Gaskiya kam... Allah yabada sa'a"


Har yagama kallon baibar tuna bilkisu ba hakama lokacin da yazo yin bacci murmushi yarinka yi shi daya. Washe gari bai samu zuwa gidansu ba saboda sunsha aiki sosai a lab shi kansa bai samu tasowa ba sai 6 shiyasa kawai yayi zamansa agida yahuta dan ko salim basu haduba ranar,yana so yakira Bilkisu amma bayason tasamu dama dayawa akanshi shiyasa ya shareta yakira husnah suka raba dare suna hira, washe gari kam da wuri yadawo gida domin lokacin da yadawo ma 3 batayiba, shago yawuce bayan yayi wanka domin akwai wasu dinkuna da aka aiko masa daga abuja tun shekaran jiya wata yar makarantarsu shiyasa can yaje yafara yankawa saboda cikin week dinnan takeso, karfe biyar daidai yabar dinkunan yafita yauma yana son yaje yaga dramar da zasuyi shida mutuniyar tasa, duk da kananun kayane ajikinsa haka yatafi gidan surukai, yana zuwa su ammah na fita itada driver da Rabi mai aikinta shi da yazaci ma Bilkisu ce sai yaga ba ita bace,


Dama yana jin kunyar zuwa ahaka ammah taganshi da kananun kaya maroon din riga mai rubutun yes ajiki har sau uku sai bakin wando da p cap, koda wasa Bilkisu bata zaci zaizo ba da bazatayi saken barin kofarta bude ba, yauma baccin takeyi kamar mai shan wani abu domin sun daura itada baccin yamma yanzu tunda ba nadare takeyi sosaiba zama yayi gefen gadon dan mugunta maimakon ya kyaleta amma sai yafara neman hanyar da zai tadata. Tv yakalla da alama da kallo takeyi before baccin ya dauketa volume yakara Wanda tajishi har tsakar kanta babu shiri ta bude idanuwa tana laluben remote,


Ganinshi zaune yasata hade rai sosai kamar yadda shima yayi,


Hijabi ta yayima ta saka tana harare harare, baki yatabe cikin ranshi yace,


"Nadai gani..."


Daga shi har ita babu wadda yayi magana suna zaune shiru shidai hankalinsa nakan tv ita kuma ta dauke kai gefe daya cikeda jin haushinsa,diff nepa suka dauke wuta zamansa yagyara akan gadon sosai ya jingina bayan yadauki kafafuwansa gaba daya ya azasu bisa gadon, wayarshi yaciro yakira mukhtar saboda dazu lokacin da yafito daga shago yaga miss called dinshi yasan lokacin da yabar wayar a charge ne yakirashi,


"Ango howfar?" Mukhtar yafada yana dariya, dariya shima fahad yayi sannan yace,


"Kajika wannan ai tsohon zance ne abinda ba yau aka daura auren ba bakuma jiyaba..."


Bilkisu na jin yafadi haka tamike daga kan gadon ta sauka saboda tasan duk yadda akayi maganarta akeyi matsalar auren yaro kenan komai zai iya kwashewa wanda yashafi sirrinsa da iyalinsa yafadawa friends dinshi ta ayyana hakan cikin ranta, bathroom tashiga babu jimawa tafito fuskarta jike da ruwa alamun wanketa tayi lokacin yagama wayar yana dai cigaba da latse latse awayar,


"Karka kara shigo min daki ahaka, sannan karka kuma gigin tashina idan ina yin bacci...." Tafada cikin muryar dake nuna fushi karara bai tanka mata ba taji yana kiran waya domin a speaker yasaka, laptop dinta ta dauka ta matsa can kan prayer rug dinta ta zauna,


"Yanmatanah ya azumin?" Taji yafada cikin karya harshe,


"Babu wahala ya fahad... Ankusa ansha ruwa ma ai"


"To me zan kawo miki?"


"Kanka...." Tafada muryarta ahankali,


"Ko baki fada ba ai dama ni nakine ke kadai...."


"A'a ya fahad badai ni kadai ba bayan kayi min kishiya da tsohuwar matarka bayan kuma...." Saurin cire wayar daga hands free yayi sakamakon jin husnah na neman yimishi baran barama, duk abinda yakeyi Bilkisu najinsu shiyasa bata san lokacin da ta mike afusace ba taje gabansa ta tsaya tana huci,


"Tashi kafice min daga daki....I said get out from my room...." Katse wayar yayi sannan ya kalleta fuskarshi atamke,


"Daina yimin tsawa aka.... Ban son hayaniya"


"Anyi din... Katashi kafitar min adaki kuma karka sake dawowa..."


Yi yayi kamar baijita ba, hakan yasake kular da ita,


"Fahad katashi kabar cikin dakin nan nace..., akanme zakazo kana kawo min nonsense anan...."


Tun kafin takarasa yatashi yahadata da bango ya matse,


"Wa kike yiwa shouting aka? Ni sa'anki ne?"


Wata uwar harara ta dalla masa kafin ta tureshi tana cewa,


"Kai waye da baza ayi maka shouting akai ba? Ubana ne kai? Zaka wani zo min har cikin daki ina baccina katada ni sannan kazauna kana damuna, bazanyi tolerating wannan ba...."


Tsayawa yayi yana kallonta har saida tagama sannan yace,


"Ki gama fadin duk abinda ke ranki amma idan kika bari na kamaki ko...."


"Idan katashi dukana bayan ka kamanin ka dakeni da ice ko da dorina mai baki dubu..."


"Ni ai ba mahaukaci bane ko jahili da zan zauna ina dukan mata... Koda yake su wasu shashashan matan ai sunfi son mijin da zai dakesu...."


Haushin da ya rufeta yafi na dazu shiyasa tasake tunzura ta hayayyako masa cikin zafin rai da kunar zuciya tace,


"Ai maganar ciki ba magana bace idan har ba tsoro akejiba afito fili afada amma bawai ayita magana atukunkune ba... Idan anso masu dukan ai sun cancanta asosu dinne..."


Baki yatabe sannan yace,


"To ai dadin abin dai su babu wata soyayya da za anuna musu sai ta duka, akamasu a lakada musu duka idan dare yayi kuma arabesu amma da rana babu marabarsu da jakuna while wasu matan suna can ana riritasu ba ason ko kuda yasauka akansu...."


"Kafita min adaki nagaji da wannan hayaniyar taka..."


"Baza afita dinba..."


"Saboda kai...."


Bata karasa ba taji ya shako ta, idanuwansa cikin nata yake kusanta fuskarshi kan tata tayadda kusancin nasu har yai yawa, lumshe idanuwa tayi tana jiran jin bakinsa kan nata dan taga kamar hakance manufarshi amma sai taji sabanin haka dal taji ya dalle mata baki yana cewa,


"Wannan bakin naki na rashin kunya nakusa nayi maganinsa....sai na kasheshi murus tayadda bazai kara fada min bakar magana ba...." Ita kanta saida taji tsikar jikinta tana tashi saboda yadda yayi maganar, su da suke fada amma voice dinshi tayi sanyi takoma cool sosai sannan tasauya tana fita a rarrabe sabanin dazu kodan kusancin dake tsakaninsu ne oho,kasa bude idanuwanta tayi sai dai tana ta kokarin kwace kanta daga rikon da yayi mata saboda hatta bugun da zuciyarshi keyi tana jinshi kamar yadda shima yake jin nata kasancewar manne suke da chest din juna wani karin takaicin ma shine babu fa komai ajikinta sai iya yar doguwar rigar da ta zira sai hijabi....




*_Ummi Shatu_*    


*Littafina na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*




44****Dariya ma shi taso bashi saboda yadda ta runtse idanuwa tana jiran taji abinda zai biyo baya, afirgice ta bude idanuwanta tana kallonshi saboda jin yadda ya take mata babban dan yatsan kafarta, muryarta na sarkewa tana rawa tafara hankadeshi tana cewa,


"Meye haka... ? Dallah ni sakeni..."


Sake damketa yayi yana kokarin saita kanshi, rikon da yayi mata ba karamin riko bane domin da irinta guda biyar zasu hadu ba lallai su iya kwatarta ba,


"Kin san me? Ina raga miki nefa saboda wani dalili wanda nabarwa kaina sani amma wallahi idan kikayi wasa...."


"Kadaina raga min din, kayi duk abinda zakayi....."


Tafada cikin jin haushin abinda yayi mata, juyi daya yayi ya canja musu position ita takoma jikin bango,


"Karki damu kiyi tayi min rashin kunya akwai ranar fanshewa, duk ranar da natashi hukuntaki kisa aranki ranar sai kinyi kuka da idanuwanki...."


"Dan Allah idan katashi yin hukuncin ka kasheni har lahira...."


Murmushin mugunta yayi wanda itama dakanta saida ta fahimci hakan domin da alama bai kai har zuci ba duba da yadda ya cure baki,


"Bazan kasheki ba amma zaki wahala over..... Sai kin gane ke karamar yarinyace ranar..."


"Kaine karamin yaro bani ba....."


Wata matsa yasake yimata hakan yasata kokarin tureshi tana ta huci saboda bacin rai,


Saida yabari tayi nisa wurin kokarin tureshi ta gama sakar jiki ya murde hijabin ya yar, nan sabon fada yatashi domin da iya karfinta take kokarin dauko hijabin daga kasa shikuma yasa kafa ya take, durkushewa tayi awurin tahada kai da gwiwa bayan tasaka kukan zuci,


"Matsoraciya kawai..... " yafada yana murmushi, daga haka yafice yabarta sai faman kuka take kukan bakin cikin rainatan da fahad yayi domin yanzu tagane yagama rainata tsaf sam baya ganin girmanta gashi duk maganar da tazo bakinshi sai yafada mata sai kace wata mate dinshi,


"Ni Bilkisu naga takaina.... Wannan wacce irin rayuwa ce..."


Haka taketa fada cikin kuka har tsawon wani lokaci, saida tagama kukanta ta share sannan tashiga wanka tafito duk sai faman kumbure kumbure takeyi ita kadai ahaka su ammah suka dawo suka sameta duk bata da cikakkiyar walwala sai cika take tana batsewa ita dai ammah idone nata batace uffan ba.


Washe gari awurin aiki khulsum tabi ta dameta akan takira fahad ta tambayeshi idan yabarta sai su wuce duba Christy basai sun koma gidaba saboda idan suka bari aka sallameta har tadawo aiki ba karamar kunya zasu jiba, agaba khulsum tasata da naci dole ta tashi tafita waje itafa bama ta da no dinshi dan rainin hankali, maama takira tana dagawa tace,


"Maama kinada number din wannan dan rainin wayon ko?"


Dariya maama tayi tana cewa,


"Adda labour amarya...."


"Maama ban son rashin kunya ina tambayarki kina yimin wasa..."


"Wai number waye kike tambaya?"


"Ban saniba ai kin san wanda nake nufi munafuka, kituro min yanzu"


Daga haka ta katse wayar takoma wurin khulsum, babu jimawa taji text yashigo sake tashi tayi tafita har khulsum na tsokanarta tana cewa,


"Ohh su labour yau lobayya ce ta motsa koda yake ai amarya kike..."


Bata kulaba tafice takira number fahad tanata ringing amma ba adaga ba harta katse, sake Kira tayi anan kuma sai aka daga amma ga mamakinta sai taji anyi shiru, ahankali kamar bata so tayi magana,


"Hello... Idan natashi daga aiki zanje dubiya...." 


Kafin takarasa taji wata zazzakar murya tayi magana,


"Sorry mai wayar baya nan idan yadawo zan sanar dashi...." Batare da jiran amsar da zata bayarba kawai taji ankashe wayar, wani kululun bakin cikine ya tokare mata kirjinta kawai sai taji tana dana sanin kiran da tayi masa, shine dan walakanci zai barwa mace wayarsa? To ko wannan din itace wannan yarinyar da suke yin waya da ita? Kai ba ita bace, ita can ai tasan muryarta, ita dai tasan mutane da yawa suna yaba baiwar muryar da Allah yayi mata but gaskiya ta wannan har tafi tata zaki da taushi da kuma sanyi domin kana jin muryarta kasan irin matan nanne da suka yi nutso cikin kogin daula jin dadi da hutu ya ratsa ko ina ajikinsu su akewa kirari da hurul aini na duniya,


Tsaki taketa ja tana kwafa tarasa ina zata saka ranta taji dadi amma fa abisa dukkan alamu ita wannan dinma babbace domin kamar zata girmeta, shiru tayi tana tunani, itafa takanas mutane suke wanko kafa suzo gidan radio ganinta saboda kawai dadin muryarta da sukeji to amma muryar wannan ko ita mace saida tajita har cikin kwakwalwarta, to wacece ita? Meye hadinta da fahad?


Kafin tasake yiwa kanta wata tambayar da batada amsarta khulsum tafito rikeda hand bag dinta,


"Labour yadai?"


"Nothing, na kirashi ne ban sameshi ba shine nake jira ko zai kira..."


"Ok to kafin kugama bari naje nayi voicing din report din can... Ke kinyi nakine?"


Girgiza kai tayi cikin sanyin murya da na jiki gaba daya tace,


"A'a ni koma fassarar banyiba tukunna... Jeki kiyi nakin kawai...."


Daga haka takoma cikin office ta zauna tasoma juyawa kan kujerar da take kai. 


FAHAD



Sosai Bilkisu taso rikita masa lissafi yau saboda kusancin da sukayi har yayi yawa jinta ajikinshi tana half naked yasaukar masa da wata irin kasala da sha'awarta mai karfin gaske amma koda yatuna ta auri wani kafin shi ahalin yanzu sai duk yaji bacin rai da bakin ciki sun rufeshi wadanda sune sukayi sanadiyyar gushe sha'awar data taso masa shiyasa ma yabar wurinta babu shiri yanufi gida, dakyar da sauraron karatun kur'ani yasamu yaji daidai. Washe gari dayaje asibiti sunada tarin ayyuka masu wahalar gaske wadanda zasuyi shiyasa dole sai mutum ya nutsu sannan yayi taka tsan tsan wurin fitar da result din, office din Dr murja yashiga yakai wayarshi da laptop domin suna yin good time da ita tana mutukar ji dashi duk cikin daliban da aka turo babu kamarshi awurinta shiyasa sauran students din ke zargin wai sonshi takeyi gashi ahaife ma zata girmi Bilkisu matarshi,  system dinshi yasaka a charge ita kuma wayar yabata ajiya yafita shiyasa lokacin da bilkisu takira bata sameshi ba Dr murja ta daga, bai samu kanshi ba sai around 3 duk agajiye yake yashiga office din Dr murja yakarbi wayarshi da laptop domin tafiya gida, har zai tafi yaji tace,


"Soul mate takiraka..."


"Ok tom zan kirata"


"Wacece ita?" Tafada bayan tazuba masa gaba daya idanuwanta wadanda take juyasu cikin salo na daukar hankali shi wallahi kunya ma yakeji idan tana yimasa wannan farin,


"Anty wife dinace fa..."


Yafada yana shafar kai, juya idanuwa tayi ta shagwabe fuska,


"Ashe kanada aure shine ban taba saniba?"


"Wallahi inada aure....."


"To amma tana kula dakai? Zo kafada min mana handsome..."


Dariya yayi cikeda kunya yafice daga cikin office din, tun yana cikin asibitin yake faman kiran wayar Bilkisu amma bata dauka ba kuma tana zaune tana fassara labarai amma taki dauka tana kallon wayar har tayi tagama bata daga ba ita tarasa dalilinta na jin mugun haushinsa yau fiyeda kullum. Wannan dubiyar dai bataje ba sai khulsum ce tatafi ita kuma tawuce gida tana zuwa gida taci abinci tayi sallar la'asar takira Abba ta gaidashi sannan tawuce toilet, wanka tayi tafito tashirya cikin kayan shan iska riga armless zuwa gwiwa da wandonta duk light purple, ta dauko system dinta ta fita zuwa dakin ammah da wayarta ahannu tana zama wayar tasoma ruri sam batayi niyyar dagawa ba saboda tasan ko waye amma sanin ammah na iya yin magana yasata dauka,


"Ke wato shine zanyita kiranki amma dan rainin wayo ki k'i dagawa ko?"


Jin abinda yace yasata tashi sim sim tafita daga dakin amma zuwa nata,


"Ba dake nake magana ba...?" Yafada cikin tsawa,


"Kaga malam ya isheka ni kar kayi min ihu aka, borin kunya kakeyi ba komai ba kuma wallahi sai kafadi wacece matar da ta daga wayarka lokacin da nakira idan bahakaba har kunnensu abba maganar nan dan bazan iya zama da mai kula mata awajeba...."


"An kula matan kiyi duk abinda zakiyi.... Meye naki aciki dan nakula mata? Kabarinmu dayane dake? Ban son shisshigi..."


"Wallahi duk wadannan maganganun akunnen abba, mayaudari kawai...."


Daga haka takashe wayar gaba daya komawar da batayi dakin amma ba kenan, tun daga ranar rigima takice taki cinyewa har tsawon makonni biyu suka dauka suna wannan fadan ta waya domin bai samu zuwa gidan ba ita ta damu akan lallai sai yafada mata alakarsu da matar da ta daga wayarta lokacin data kirashi acewarta tana gudun sake facing irin abinda hamood yayi mata yadauko karuwa ya ajiye mata azuwan matarshi ce ita tunaninta kenan amma sam bata taba zargin kanta da yin kishinsa ba, shikuma hakan da take ta fada ne yake bata masa rai shiyasa yau yashirya zuwa gidan domin ayita takare.


Sai bayan da yayi sallar magrib sannan yaje gidan, kamar koda yaushe iya amma yasamu falonta tana kallo kasancewar mai aikinta tatafi, tashi yayi yafita cikeda kunya zuwa dakin Bilkisu wacce ke zaune kan abin salla, yi tayi kamar bata ganshi ba taci gaba da tasbihinta,


Agefen gadonta ya zauna harda kwanciya tana ganinsa bata tanka masa ba text yake turawa shiyasa shima baiyi magana ba bayan mintuna biyu da tafiyar text din saiga kiran husnah dama ita yaturawa yana yimata barka da shan ruwa kasancewar yau alhamis,


"Husnah ta....kinsha ruwa lafiya..."


Kamar acikin mafarki Bilkisu taji tace,


"Ya fahad bayan azumin karyewa yayi bayan sallar la'asar saida nagama shan wahalat...."


Bai karasa jiba yaji bilkisu taja tsaki da karfi tamike tana nannade prayer rug dinta,


"Malam idan kagama karufe min kofar bayan kafita", ganin dagaske fitar zatayi tabar masa dakin yasashi ajiye wayar yamike dasauri yasha gabanta,


"Wai me kike nufine? Karfi da yaji nema kikeyi ki goga min kashin kaji ko bakin fenti...."


"Allah ko?"


Matsarta yayi yana kallonta fuskarta gaba daya babu annuri,


"Wai ke mai kike nufi? Dan kawai kinji mace ta dauki wayata? Waima ina ruwanki ne, budurwata ce wadda zan aura sunanta Dr murja medical Dr ce a asibitinmu she's 35 years old, ita kuma wannan husnah ce itama budurwata ce nurse ce yanzu haka tana yin bsc nursing dinta a BUK she's 22 years old nanda yan watanni zan aureta,sai me kuma kike son ji....?"


Ita kanta a lokacin nan tasan bata cikin nutsuwarta bata san dalili ba, cikin fushi da bacin rai tace,


"To kasan kana da duk wadannan meye naka na damuwa da lallai saika aureni? Ai da sai kaje kazauna dasu..."


Murmushin rainin hankali yayi mata yana jan dan gemunshi na rashin kunya,


"Waye yadamu saiya aureki? Ni? Lallai... .."


Afirgice ta kalleshi cikeda mamaki, idanuwansu ne suka sarke da juna cikin fada tace,


"To ai ba adole.... Kana iya sawwake min kowa sai yahuta tunda bakaine ka damu da aurenba"


"Hmmm Bilkisu kenan....!"


Haushine da mamaki suka sake kamata har ta daga kai ta kalleshi akaro na biyu, har lokacin yana wasa da gemunsa,


"Da kike cewa in sawwake miki da nine na aureki? Ai bani na aureki ba ina zaman zamana aka ce an aura min ke, tunda bakida ra'ayi kamar yadda nima banida interest akai kina iya zuwa kisamu wadanda suka daura kisasu su warwareshi....." Yakarasa maganar yana daga kafada,


"Ni kake fadawa haka?"


"Yes ai gaskiya nafada miki ni ban nemi aurenki ba sadaka aka aura min saboda ance wannan tsohon dan duniyar yaudararki yayi daga karshe ya sakeki..."


Kwallace taciko mata ido takai hannu zata dakeshi yarike yana yimata murmushi mai kona zuciya,


"Fahad sakeni... Ka sakeni.....ko ana aure dole ne?"


"Oho ni nasani ne? Nima ai dolen aka yimin tunda inada wadanda nakeso aka tashi aka bani matar sadaka"


Wannan Kalmar ba karamin kona mata rai tayiba dan har saida tanemi sliver abakinta tarasa saboda dimuwa wai ita yakirada matar sadaka, shikuwa gegewa yayi ta gefenta yadauki wayarshi yafice nan ta durkushe tasoma kuka, tunda tazo duniya bata taba jin bacin rai irin nayau ba, tamkar zata mutu haka takeji, kwana tayi tana kuka wannan dalilinne yasa dasafe ta tashi da matsanancin zazzabi da ciwon kai sai kakkarwar sanyi take yi ga wani irin lafiyayyen ciwon kai asibiti ammah tasata agaba suka tafi suna zuwa akace jininta ne yayi kasa bama hawaba kasa yayi nan aka bata gado sai rawar jiki takeyi idabuwanta faful da hawaye duk sun kumbura.....




*_Ummi Shatu_*    


*me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*




45***Taimakon gaggawa aka fara neman bata domin inbanda kadawa babu abinda jikinta keyi kamar wacce ke tsakiyar kankara, bayan kamar wasu mintuna wadanda bazasu gaza 30 ba nurses din suka zo wurin ammah suna yimata bayanin yakamata fa suje su samo jini saboda su basuda shi anan, duk da ammah bataso ta sanarwa su Hindu to amma babu yadda za a yi dole sai sun sani, wannan gayawa wannan da haka duk zancen ya yadu a junansu babu bata lokaci duk suka yiwa asibitin tsinke,text maama ta turawa fahad amma kasancewar yana cikin lab yana aiki bai ganiba.


Tun abinda yafaru jiya tsakaninsa da Bilkisu da zarar yatuna sai yayi murmushi ita daukar kanta takeyi watta babba bayan shikuma awurinshi mararbarta da jaririya kadanne gaba daya yagama rainata sanine bata gama yiba, dayake yau juma'a manyan kaya yasaka saboda ta can zai wuce masallaci, duk da cewar karshen makone hakan bai hanasu samun ayyuka da yawa ba shiyasa bashi yasamu kansa ba saida lokacin sallar juma'a yayi. Har saida yafito daga salla sannan yaga text din maama tana sanar dashi Bilkisu babu lafiya sannan ana bukatar jini, harda kwatanccen asibitin da take kwance, batare da yakoma asibiti ba yawuce inda maama tafada masa an kwantar da Bilkisu, wani dan karamin asibitin kudine dake nan unguwar tasu sai dai da dan tazara tsakaninsu da gidansu, a reception yaga meenah wacce taje kiran wata nurse wadda zata auna jinin mijinta aga ko zaiyi daidai da na Bilkisu,


"Ya fahad sannu da zuwa..."


"Yawwa meenah, ya mai jikin?"


"Dasauki tana ciki muje"


Tare suka karasa wurinsu ammah wadanda ke tsaye akofar dakin da Bilkisu take harda mijin meenah ganin fahad yasa amma gyara lullubinta suna gaisawa kuma tawuce tabar wurin, shi dinma hakan yafi sakewa shiyasa yasamu damar cemusu abar jinin mijin meenah shi sai adebi nasa dan baya ko tantama nashi zaiyi mata saboda shi jininsa irin wanda zai iya bawa kowa ne, tare suka tafi lab da nurse akayi komai da yakamata aka debi jininsa leda daya da rabi bai samu tashi ba awannan lokacin ya dan kwanta sai bayan kamar mintuna ishirin sannan yatashi yana dai dan jin jikinsa babu karfi but babu wani jiri ko hajijiya, wurinsu Hindu yakoma dama sunata zuwa suna lekashi suna komawa, suna zaune su uku daga Hindu sai maama sai meenah ammah tatafi gida da yan jikokinta haka shima mijin meenah yatafi, sannu suke tayi masa yana amsawa shi idanma banda yar yunwar da yakeji ai da zai dan jima a asibitin,


"Tafarka ne?" Ya tambaya yana kallon kofar dakin da Bilkisu ke ciki,


"Ehh amma yanzun dai gaskiya bacci takeyi...amma ai zaka iya shiga"


Juyawa yayi yashiga, tana kwance tayi fayau da ita ana kara mata jinin wanda har guda dayan yakusa karewa, jingina yayi ajikin bango ya harde hannuwanshi akirjinshi yana kallonta, hijabi ne ajikinta saboda sanyi sai doguwar riga ta atamfa, fuskarta ya kalla yaga ta wani bata fuska kamar irin idonta biyun nan ba bacci takeyiba, murmushi yasaki mai kayatarwa sannan ahankali yafurta,


"Hajjaju ana fada da jinina kenan......"


Ahankali yakarasa gaban gadon duk fuskarta akode amma idanuwanta luhu luhu akumbure ga bakinta ya bushe sosai irin yadda yake yi dinnan idan mutum yana cikin halin jinya,


"Am very sorry soul mate... Nasaki kuka ko? Am sorry kiyafe min...."


Kamar tana jinsa yaga tasake bata rai harda dan turo baki,


"Are we fighting?" Yafada yana murmushi, bakin da ta dan turo yakai nashi kai ya tsotsa sannan yadago yana murmushi,


"Ai nace miki am sorry.... Stop fighting with my blood Mana baby.... I said am very sorry about what i did... Pls forgive me kinji.... Ki yafewa dan kaninki...!"


Goshinta yayiwa light kiss sannan yasake yiwa lips dinta wadanda ada suke abushe amma tun lokacin da ya tsotsesu suka dawo kamar anshafa musu lipstick, sakin hannunta yayi wanda da yakama yana murzawa cikin nashi saboda tsabar taushinsa,


"Tunda kin ki hakura am going, anjima zan dawo kinji...."


A kumatu yasake bata wani kiss din sannan yatashi yana kallonta murmushi yasake yi saboda yadda taketa hade rai tana motsa baki kamar mai yin fada alhali kuma bacci ma takeyi yasan abinda ke zuciyarta ne taketa amayoshi lokacin baccinta. Da baya da baya yake tafiya yana murmushi har lokacin idanuwanshi na kan fuskarta, saida yazo daf da bakin kofa sannan yayiwa tafin  hannunshi kiss ya hura mata, ganin yana kokarin juyowa yasa su maama dake leke ta glass din kofa saurin guduwa kowaccensu kunshe da bakinta dan kar yaji, bude kofar yayi yafita yana kallon su maama wadanda ke tsaye cirko cirko kamar marassa gaskiya,


"Maman hudah lafiya dai ko?"


"Lafiya lau ya fahad, mun dan fita ne dawowarmu kenan..."


Dan bata fuska yayi sannan yace,


"Ku da kuke da patient ina kuma zakuje dan Allah?"


"Ahhh ya fahad bafa nisa mukayi ba..." Inji Hindu,


"Nidai dan Allah ga amanata nan zanje gida idan huta anjima zan dawo, pls and pls ku kular min da ita... Idan tana bukatar wani abu akirani.. " yakarashe maganar yana kallon maama wacce ke dariya,


"Insha Allah zamu kula da ita kamar kana wurin..." Inji meenah,


"Yawaa nagode, bari naje..."


Juyawa yayi yatafi suna sake yimasa sannu, shi sai yanzu yafara jin dan ciwon kai kadan kadan da dan jiri jiri yasan bawai dan andebi jinin bane may be saboda ciwon dake tare dashi ne, tunda yabar wurin su meenah ke gulmar abinda suka gani,


"Ya fahad dinnan kamar wani salihi ashe shima number 1 ne..." Hindu tafada tana dariya,


"Ai kibari kawai adda labour fa tahuta amma takasa ganewa.." Mamaa tabata amsa,


"Gentle dashi wallahi..." Inji meenah, hirar dai suka bata lokaci sunayi kasan idan kaga mai son wanda ya shafeka kaima sonshi kakeyi watakila dalilin kenan da yasa suke kaunar fahad.


Daurewa yayi yakai kanshi gida duk da jirin da yakeji, yana shiga yawuce ciki baiko kalli dakinsu ba dake soro,


Falon ayiyah yashiga yawuceta zaune gaban murhu tana karasa daka kuli kulin da zata yiwa baba kwadon zogale wanda idan yadawo daga masallaci zai ci, ita kuma mamuh tafita zuwa gidansu salim,


Anan tsakar falon ya kwanta yayi pillow da damtsen hannunshi, ahaka yaji motsin shigowarsu mariya daga makaranta,


"Sai yanzu kuke dawowa daga makaranta ko? Kun tsaya wasa ahanya ko?"


"Allah ya fahad sai yanzu muka samu napep..." Maryam tafada tana cire sandal din dake kafarta,


"Bari natashi nakamaku zama ku fadi gaskiya..."


Sun fara rantse rantse kenan ayiyah tashigo dauke da kwanukan zogalen da ta dafa,


"Kai da naga kamarma bakada lafiya amma shine zakazo kafada yara da fada ko fahad?"


Murmushi yayi sannan yatashi zaune,


"Ayiyah lafiyata kalau fa kawai dai jinina aka dan diba..."


"Jini? Meya faru?" Ayiyah tafada tana mikewa tsaye daga durkushen da tayi tana ajiye kwanuka,


"Babu komaifa... Bata da lafiya ne wai kuma ana bukatar jini shine aka debi nawa"


Yana fadar haka ayiyah tagane Bilkisu yake nufi,


"To Allah ya sawwake yabata lafiya.... A asibiti take kenan?"


"Ehhhh, ayiyah taimaka kibani zogalen nima inci..."


"Allah ya sawwake, gashi ai dama babanku na dafawa..."


Hado mishi tayi cikin plate harda su tumatur da sauran kayan lambu, zama yayi sosai yaci sannan yakoma ya kwanta babu jimawa bacci yayi gaba dashi bai farkaba sai daf da la'asar, yafito tsakar gida domin yin alwala,zama yayi yasa maryam takawo masa ruwan alwala, yana yin alwalar mamuh tazo tana tambayarsa awanne asibitin su Bilkisu suke domin suna son suje dubata yanzu fada mata yayi yakoma falon ayiyah, yana salla yaji tafiyarsu suna yimasa sallama shi kadai aka bari agidan domin harda su maryama aka tafi. Bayan ya idar da salla yasake kwanciya sai lokacin yamika hannu yadauko wayarshi yana dubawa text din husnah na barka da friday yagani sai kuma miss called dinta da nasu bashir, daya bayan daya yarinka bin miss called din yana kira bayan yagama yatashi ya yafita kofar gida yazauna yana jiran dawowarsu ayiyah.


Yafi mintuna talatin zaune awurin sannan suka dawo, maryam na rikeda babban warmer mai kyau,


"Maryam me kika samomin?" Yafada yana kokarin tashi tsaye,


"Surukarka ce tabayar akawo maka wai kaci ka maida jinin jikinka...."


Jin abinda mamuh tafada yasashi yin dariya saboda yazaci wasan da tasaba yimasa yauma tayi, binsu yayi suka shiga cikin gida,ga mamakinsa kuwa sai yaga ashe dagaske ne domin agabansa maryam ta ajiye warmer din tana cewa,


"Ya fahad wai gashi..."


Budewa yayi nan kamshi ya bugeshi mai dadi, farfesun hanta ne cikin warmer din yaji kayan kamshi sai kamshi ne ketashi,


Kallonsu mamuh yayi sannan yakalli maryam yace,


"To kuma ni zaki kawowa ki ajiyewa? Mika musu..."


Dauka tayi takai gabansu mamuh ta ajiye, cikin plate mamuh ta zuba masa ta mika masa,


"Wallahi mamuh wannan yayi yawa... Rage"


"Ba ragewar da za ayi, kaida kabada jini har leda daya da rabi ai dole kaci abubuwan da zasu kara maka jini dannan...."


"Mamuh dazufa da bakya nan wallahi naci zogale dayawa..."


"Saifa ka cinye fahad, dauki maza ina kallonka..."


Dauka yayi yafara ci ita kuma taci gaba da raba nasu, yana ci yana hadawa da ruwa har ya cinye saboda ita hanta akwai cikawa mutum ciki shiyasa yajishi yakoshi over, tashi yayi yafita bayan ya gama yakoma dakinsu, salim yaturawa text yana sanar dashi anjima zai rakashi su dubo Bilkisu, wanka yashiga domin yanzu ya danji karfin jikinsa.


Bayan sallar magrib suka tafi asibitin su uku saboda harda ya abba,dukkaninsu sunsha dogayen kaya, babu kowa adakin sai iya Bilkisu da meenah suna zaune kan gadon Bilkisu na shan tea har lokacin tana sanye da hijabinta, jin sallamarsu yasata sake kasa da kanta bata ko dagoba saboda bata son ganin sun hada ido da fahad saboda tasan yanzu bata da wata martaba a idonsa tunda ashe sadaka aka aura masa ita tasan ba kowane yakitsa wannan abunba sai iyallo saboda dama itace ke cewa zata aurar da ita sadaka, yanzu gashi anja mata reni da wulakanci a idon yaro,


Tana ji su Abba na tambayar yamai jiki suna yimata sannu dakyar ta iya amsawa sakamakon kukan da ke kokarin taho mata, lokacin da taji meenah na gaisawa itada fahad sai taji kamar da biyu yake yin gaisuwar nan ta shareshi bata ko dago ba daga karshe su Abba suka fita suna yimata fatan samun sauki haka itama meenah sai ta tashi tafita yarage su biyu kadai cikin dakin,


"Sannu... Yajikin? Ke daga fada miki gaskiya shine zaki kwanta ciwo...?"


Jin abinda yace yasata dagowa ta zuba masa harara saboda ta tsani ke dinnan kafin ta dauke idonta yarama,


"Ni ai ka kira da matar sadaka ko?"


"To da matar meye? Sadaka aka bani kuma nakarba..."


"Wallahi karya kake yi..."


Nuna kanshi yayi da yatsa,


"Ni kike cewa ina yimiki karya?"


"Ehh din...."


Kafin yayi magana meenah tashigo rikeda waya nan ta mikawa Bilkisu tana cemata,


"Adda labour gashi su elmustapha ne..."


Karba tayi suka fara gaisawa dasu elameen suna yimata ya jiki, bata saurari fahad ba wanda ahankali yace,


"Yarinya kuma sai kin biyani jinina da na baki dan ba kyauta nabayar ba..."


Shima bai sake bi ta kanta ba yayi waje abinshi yabarta da kunar zuciya domin maganganunshi sosai yanzu suke bata mata rai,wayar nan kawai tanayi ne bawai dan tana fuskantar abinda take cewa ba......



*_Ummi Shatu_*    



*Littafina na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*




46****Daren ranar ma haka ta kwana batayi bacciba saboda tsabar bacin rai da damuwa da zarar ta tuno maganganun da ya yayyaba mata sai taji kwalla ta ciko idonta. Washe gari dasafe aka sallameta suka koma gida, suna zuwa tasamu tashiga wanka tafito domin shiryawa kamar tasaka hannu aka tayi ihu haka takeji idan har tatuno da maganganun fahad, ahaka ta daure tashirya tana cikeda damuwa tana gamawa Hindu takawo mata abin karyawa nan ta zauna tasoma dan kurbar ruwan zafi bawai dan tanaso ba amma sauran kayan karyawar ko tabasu batayi ba ahaka Hindu tadawo ta sameta tana rikeda sultan a hannunta,


"Adda mai gado yabaki ci abincin ba? Saifa kin dan daure..."


Jin abinda Hindu tace yasata dagowa ta kalleta da kodaddun idanuwanta wadanda ko kwalli babu,


"Hindu banida apatite abakina wallahi, sam bana jin dadin komai..."


"Duk da haka ki dan daure mana, sannan dan Allah ki gyara fuskarki kisaka koda powder ne da kwalli... Amma ya fahad yazo yaganki ahakan nan ai akwai matsala..."


Harara ta watsawa hindu sannan tamaida kallonta kan sultan wanda ke miko mata hannu yana yimata gwaranci, mika hannu tayi zata karbeshi amma Hindu taki sakinshi tana cewa,


"Kai bari kar kaje ka karasa mana addarmu kaga dazun nan tadawo daga gadon asibiti..."


Murmushi Bilkisu tayi ta karbeshi sakamakon kukan da yafara yi, ita kuma haka Allah ya dorawa yaran kannenta kaunarta duk sun shaku dasu babu wanda yake yimata kiywa,


"Dan Allah adda labour ki daure kici abincin nan kar yayi sanyi sannan ki gyara fuskarki saboda tsaro..."


"Ke hindu idanma fa akan fahad kiketa wannan damun nawa bazan yiba..."


"A'a wallahi Adda labour ni basaboda shi bane kawai dai ai kinga idan kika saka kwallin fuskarki zatafi fitowa amma yanzu Allah baki ganki ba duk kin canja kin sake fadawa..."


Bata sake yin magana ba ta jawo abincin gabanta ta bude tafara ci tanayi tana bawa sultan, saida tagama tsaf ta zauna gaban mirror tana shafa powder sai tajiyo sallamar khulsum, tana jiyosu sunayi itada hindu atsakar gida hindu nacewa bazasu amshi uzurinta ba tunda bataje asibiti ba saida suka dawo gida. Anan gaban mirrior din khulsum tashigo ta sameta tana zizira kwalli,


"Labour patient har an warke anfara coda ado za atari oga?"


Harararta Bilkisu tayi ta taso daga gaban mirror din tadawo gefen gado kusa da khulsum,


"Zaki fara ko? Allah yakawo ki ai kuma..."


"Ah to ai gaskiya ce anwarke mana me kuma yayi saura banda akoma bakin daga..."


"Sai kiyi kuma..."


"Yawwa wai ke yaushe zaki tare ne? Allah kinga labour ki tare tun kafin abinnan ya bayyana dan wallahi ni harga Allah ban yarda da wannan ciwo ciwon nakiba.... Laulayi kika fara ko?"


"Wai ke meyasa ba a abun arziki dake ne? Ni dan Allah kinga karki bata min rai..."


"To yi hakuri, sorry kinga jiya banzo asibiti na dubaki ba ko? Wallahi khalifa ne nima baida lafiya... Amma yaji sauki yau"


"Babu komai ai da kinyi zamanki ma kin kula dashi"


"Ai yaji sauki yana can tare da babanshi"


"Allah yakara masa lafiya..."


"Amin... Yawwa wai mutuniyar kin kuwa taba gwada hadin nan dana turo miki rannan?"


Dariya Bilkisu tayi saboda ita wallahi ma sai yanzu tatuna da sakon da khulsum din ta turo mata,


"Madam kedai kije kiyi tayi amma ni wallahi bazan yiba..."


Kallonta khulsum tayi cikin jin haushi,


"Allah yashiryeki labour maza dai ki tsaya kallon ruwa kwado yayi miki kafa wallahi idan baki kama mijinki a hannunba... Hmmm zaki ganene"


"Toh Anty..."


Dariya khulsum tayi sannan tayi kasa da murya tace,


"Wai dan Allah laulayinne da gaske?"


"Ban saniba..."


Kafin khulsum tasake magana suka jiyo sallamar fahad atsakar gida amma ahankali kamar wani marar gaskiya, mikewa khulsum tayi tana cewa,


"Bari na kwashi yanmatan kafafuwana inbarku kusha morning show dinku, ga wata gumba idan kinaso sharp sharp ce wallahi...."


"Banaso akai gaba..."


"Kedai kika sani wallahi, ni sai anjima"


Mikewa tayi ta kwanta bayan fitar khulsum tana jiyo lokacin da khulsum din suke gaisawa da fahad atsakar gida mintuna kadan tsakani taji shigowarsa ta hanyar bude kofa da yayi bata ko motsa ba ayadda take bare ta dago ta kalleshi, daga dan nesa yatsaya yana kallonta, riga da skirt na leshi tasaka wanda aka yiwa simple style yayi dass ajikinta, dakin gaba dayanshi sanyayyen kamshine ke tashi cikinsa,


"Yajiki......?" Yafada yana murmushin da bazata ganeba,


"Da sauki"  ta amsa kamar bataso domin badan shi din mai jin magana ce komai kankantarta ba da bazai jiba,


"Dama nazo dubaki ne, hope kinji dadin jinina dake jikinki?"


Juyowa tayi afusace ta harareshi,


"Dadinta ma dai banice nanemi da kabani jinin ba, badanma lokacin da aka saka min bana cikin hayyacina ba da me zanyi da jininka.... Wa yasani ma ko guntun sikila ne..."


Murmushi yayi yana kallonta yasan dai maganar dayace wannan matar sadakar da yakirata dashi ne yaketa sosa mata zuciya har take neman hanyar mayar masa da martani,


"Kiyi hakuri bani na kar zomon ba rataya aka bani, kuma ratayar ma ban karba ba......"


"Idanma ka karba idanma baka karba ba ruwanka, sannan da kake cewa sadaka aka aura maka ni ai yanzu ma kanada damar da zakace kafasa... Tunda ba adole"


"Akan me zance nafasa? Ai narigada na karba"


"Duk da ka karba ai kasan hanya mafi sauki wacce tadace da zakabi ka mayar da sadakar...."


Tabe baki yayi yasamu kan bedside drewar yazauna yadora kafa daya akan daya,


"Ni yanzu ba wannan ne yakawo ni ba inada abin yi dubiyace ta kawo ni..."


Wani kallo tayi masa yana sanye da kananan kaya amma yadora lab coat asama kafarshi rufe cikin bakar safa, takula akwai shi da saka safa akafa sai kace wani marar lafiya,


"Yanda kake da abinyi haka nima nake dashi, nidai kawai ka datse igiyar auren nan kowa ya huta..."


"Ban ganeba.... Wai kina nufin ni fahad na sakeki? Idan hakan kikeso zan yimiki amma abisa sharadi guda daya..."


Mikewa yayi daga kan bedside drewar yaje yatsaya mata aka dukkan hannahensa yasaka su cikin aljihu,


"Kifara sanar dasu Abba irin zaman da mukayi dake dafarko da irin gangancin da kika sakani nayi harna sakeki lokacin da wannan shedanin tsohon dan duniyar yake tsaka da hure miki kunne, sannan sai kisake fada musu abinda ke faruwa ayanzu idan har kikayi haka to wallahi zan yimiki yadda kike so...."


Sosai kalamansa suka bata haushi ta lura yanzu baida magana saita hamood magana daya sai ya jefo hamood aciki, takasa gane tsakanin shi da hamood waye yafi wani tsanar dan uwansa saboda shima hamood din lokacin da tana gidansa baida magana sai ta ya kira fahad da karamin yaron nan marar kunya, shi kuma fahad yanzu magana kadan zaice tsohon dan duniya,tana can duniyar tunani har fahad yawuce yabar mata dakin yayi tafiyarshi kawai sai bude ido tayi taga baya nan,


Tagumi ta rafka tana tunani, ai ko giyar wake takesha bazata taba gigin aikata wannan abun da fahad yafada ba, ai idan ta kuskura abba yaji cewar itace ta kashe aurenta karo nafarko dan ta auri hamood wallahi kashinta yabushe,


"Ai yanzu bakida mafita banda wacce tawuce kiyi hakuri ki zubawa sarautar Allah ido...." Zuciyarta tafada mata, shiru tayi kawai tana tunani, yanzu ita shikenan haka zatayi rayuwarta da yaro karami wanda baya ganin girmanta? Tunfa daga yanzu ya rainata to inaga wani abu ya hadasu ai sunanta sorry kawai, tsaki taja takoma ta kwanta tana istigfari acikin zuciyarta.


Tun daga ranar har takarasa warwarewa takoma aiki fahad bai sake zuwa gidanba ita anata bangaren hakanma yafi mata kwanciyar hankali saboda baizo inda takeba bare yafada mata bakar maganar da zata hanata bacci kamar yadda yasaba, kokari ma take tayi tasamu ta yakice matsalarshi daga zuciyarta. Shi dinma yayi hakanne domin yabarta ta sarara kuma ta huta sannan shima aiki yasakoshi gaba koda yaushe cikin aiki suke mutum baida lokacin kansa,


Ana saura kwana uku abbanta zai dawo daga tafiyar da yayi masu hayar gidan fahad suka tashi wato wadannan turawan da suka karbi gidanshi dama already sun gyara gidan sai dan gyare gyaren da baza arasa ba. Ranar laraba da daddare Abba yasauka wanda da tunima yajima da dawowa dan dai kawai yabiya ta wurinsu elmustapha ne yagansu, dawowarsa da kwana biyu fahad yarako babansu domin yiwa Abba sannu da zuwa dama awurin maama yake jin komai yanzunma itace tasanar dashi dawowar Abba,


Tunda fahad yagaida Abba yakoma gefe ya zauna yana saurarensu suna tattaunawa cikin fahimtar juna da mutuntawa, ahaka ammah tazo ta samesu suka gaisa ta fita, babu jimawa saiga Bilkisu itama tasha dogon hijabi har kasa,durkusawa tayi ta gaida baba sannan tamike zata fita, hada ido sukayi da fahad ta harareshi wannan karon bai ramaba amaimakon hakama sai yayi murmushi kawai, bayan fitarta ya maida hankalinsa kan maganar da su Abba sukeyi inda abban yake cewa tunda yadawo ai sai ayi maganar tarewar Bilkisu agidanta, dan haka idan har babu matsala nanda sati biyu sai ta tare agidanta nan baba yace babu kuma anyi abu akan gaba saboda dama mutanen da suke zaune agidan fahad din sun fita dan haka ko gobe ake son tariyar babu damuwa, anan dai aka bar zancen azuwan nanda sati biyu zata tare saboda abata dama ta gabatar da dan shirye shiryenta da take son gudanarwa.


Fahad sun bar gidansu Bilkisu cikeda karramawa ga uban kayan tsaraba da Abba yabawa baba, washe gari fahad yasoma gyara gidansa gashi a lissafinsa bazaifi sati daya da tariyar ba zai koma makaranta, haka dai yake ta kaiwa da kawowa danma yayunshi na taimaka masa. 


Bilkisu kuwa tun lokacin da abba yasanar da ita maganar tariyar nan take cikin kunci, kullum cikin fushi take hatta khulsum saida ta fahimta har saida ta tambayeta meke faruwa nan ta sanar da ita wai tarewa zatayi nanda yan kwanaki dariya khulsum tayi tace,


"To ai ke gata ma akayi miki wannan uban sanyin dake tunkaro duk wani mai rai ai zakifi more amarcinki tunda gaki ga mijinki.... Danma kun kwafsa kin yarda yayi miki ciki tun kafin ku tare..."


Harararta Bilkisu tayi sannan atunzure tace,


"Dallah ni tashi muje news ko intafi inbarki, ke kika san wani ciki ni ban sanshi ba"


Daga haka tafigi handbag dinta tayi gaba tanata masifa aranta ita daya.


Cikin kwanaki kadan aka gama gyarawa fahad gidansa wannan karon kam komai gaban kansa yakeyi babu maganar tambayar ra'ayin Bilkisu kamar wancan, duk abinda yayi masa shi yakeyi yanzu, babu karya gida yafito yayi das dashi kowa yagani yasan gidan amarya ne, kwana biyu atsakani su maama sukazo da motar kaya aka soma shirya mata kayanta aciki komai sabone fil aledarshi, yana shirin baro cikin asibiti maama tayi masa waya tana tambayarsa wai duka bedrooms din guda biyu nasune?


Dariya ma shi abin yabashi shiyasa bayan sun gama yarawa da maama yakira Bilkisu wadda rabonshi da ita tun sati biyu da suka wuce, har wayar ta tsinke bata daga ba wannan dalilinne yasashi tura mata text massage.


Tun tana cikin bathroom tana wanka take jiyo karar wayarta amma bata fitoba saida tagama tana zuwa taga miss called da massage guda daya massage din tabude bayan ta duba miss called din,


_Ki fadawa kannenki su zaba miki daki guda daya, dayan kuma subarshi empty saboda na matata ne...._


Ganin abinda ya rubuto mata yasata zama agefen gadon tana huci azuciyarta tana tambayar kanta wai ita zai hada da matarshi agida daya? Ai kuwa sam wannan abune wanda bazai taba yuyuwa ba....




*_Ummi Shatu_*    



*Littafina na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*



47**** Kamar a mafarki sai taji abun na damunta, akan me zaice zai hadata da wata agida daya? Ai wallahi bazata taba sabuwa ba idan har yadamu da dole sai yayi auren to sai dai ya nemawa matar tasa wani gidan amma ba wannan ba, cikeda masifa ta jawo wayarta wadda ta cillar kan gado saboda takaici, maama takira amma har ta katse bata dagaba dan haka ta kira meenah wannan dinma saida tayiwa meenah kira biyu sannan Hindu ta daga,


"Meenah kar ku wani bar empty bedroom duka ku saka min kayana ako ina dama ai gado biyu ne ko? So kuyi min jerena ako wanne daki...." 


Bata ma jira taji maganar Hindu ba ta katse wayar saboda ita duk atunaninta meenah ce, dukansu dariya abun yabasu lokacin da Hindu ke kora musu labarin fadan da taji Bilkisu nayi,


Ita kam cikin fada da masifa take yin komai tana shiryawa sai babatu takeyi ita kadai,


"Can da iyawarku kaida matar taka...., nidai abinda nasani shine bazai taba yuyuwa ka hadani da karamar yarinya ba salon tazo ta rainani...., kuje can ku karata ka kaita duk inda zaka kaita wannan damuwarku ce ba tawa ba..."


Ahaka ta gama shiryawa tasaka blue din material fitted gown tana daura dan kwali tajiyo karar wayarta, zuwa tayi ta dauka tana ganin fahad ne tayi tsaki ta sake jefa wayar saman gado tafita daga dakin ma gaba daya zuwa dakin ammah wacce ke zaune tana waya da Rabi mai aikinta tana sake karanta mata abubuwan da zata sake hado mata daga kasuwa, zama tayi tana sauraron ammah har tagama wayar ta sauketa daga kunnenta,


"Ammah kunyi waya ne dasu maama?"


Kallonta ammah tayi tana danna wayarta,


"Meya faru?, munyi waya dasu dazu nace musu subar gado daya su saka miki daya saboda wai yace daya dakin idan matarsa tazo anan zata zauna..."


Bata rai Bilkisu tayi kamar karamar yarinya tasoma magana cikin damuwa,


"Kuma shikenan ammah dan matarsa zata zauna aciki ni sai afasa saka min gado biyuna? Ni wallahi yanemi wani gidan yakaita can..."


Girgiza kai ammah tayi tana kallonta,


"Wai dan Allah sai yaushe zaki girmane mai gado? Mijin naki nawa yake da har zakice yayi gida biyu? Shida ba aiki yakeyi ba shine zakice yanemi wani gidan? Kinga.... Tam, maza dai kibari wannan maganar taje kunnen abbanku.... Zakiyi masa bayani nidai babu ruwana..... Karki bari nasake jin wannan maganar kinji dai nafada miki..."


Jin abinda ammah tace yasata sake jin bacin rai ya rufeta yanzu shikenan babu mai goyon bayanta? Haka zata zauna gida daya da karamar yarinya amatsayin kishiyarta? Tun daga lokacin take ta fushi, fushi takeyi da kowa,komai su maama sukace tayi sai tace baza tayiba, kunshi, kitso, gyaran kai duk taki yi bare asa ran zatayi gyaran jiki. Ana saura kwana uku ta tare hajiya iyallo tazo amma wannan karon ita kadai tazo ko yafindo mai gado basu taho tareba wai tana can tana kula da jikokinta wadanda aka yiwa shayi har su shida, ko kadan Bilkisu bata so zuwan iyallo ba wannan karon kamar waccan saboda yanzu abubuwan da iyallon takawo ita ba amfani zatayi dasu ba, kuma haka kawai sai inzauna inta dirkar kayan gyaran jiki saboda wannan yaron? Haka take ta tambayar kanta, tsumi ne hadadde irin na mutanen kauye sai tukudi da gumba amma fafur taki sha sai su maama ne suka rabe atsakaninsu. Lokacin da khulsum tazo kuwa saida suka yi fada da Bilkisu saboda takawo mata hadin kankana da kwakwa sannan kuma tace mata yakamata suje ayi mata kitso da kunshi amma tayi biris, tabe baki khulsum tayi tace,


"Duk dai wannan zille zillen da kikeyi bashi zai hana mu mikaki gidanshi ba jibi ehe... Kuma dole abashi hakkinsa ta dadin rai idan anki kuma ya kwata ta karfin tsiya....."


Shiru Bilkisu tayi bata kulata ba taci gaba da abinda takeyi, nan tasake jiyo maganar khulsum tana cewa,


"Badanma ina tausayawa mutum ba kar dan karamin cikin dake jikinsa ya zubeba ai wallahi da sai na zuga fahad yayiwa mutum lisss..."


"Wai ke kika yimin cikin? Ni kidaina jamin jaraba malama..."


Bilkisu tafada cikin fushi, dariya khulsum tayi taci gaba da tsokanarta, duk yadda sukaso ta gyara kanta da jikinta ki tayi ita kuwa dama ammah bata kulaba tunda tasan rashin yin kitso da lallen bashi zai hana ta tare dinba. Shima fahad bai sake nemanta ba tun lokacin da ya kirata taki dagawa, yasan fushi takeyi saboda yace tare zasu zauna da husnah shi kanshi idan son samune zaifi son ace kowa da wajenta to amma ai baida karfin rike gida biyu shiyasa lokacin da yasamu ayiyah da maganar tace a'a karma yafara saboda bazai iyaba, itama husnan yasanar da ita tare zasu zauna da Bilkisu saboda gara tasani tun yanzu domin so yake Bilkisu tana tarewa yatura asaka musu rana da ita domin shi ya Abba yake jira shima yagama shirinsa tsaf kawai sa ranane yarage. Ranar da su maama suka yi jere agidan ya kwana adakin Bilkisu kuma akan gadonta, kawai tunani yayita yi acikin ransa yana sake jinjina girman ubangiji saboda gashi cikin iyawarsa da hikimarsa yasake dawo masa da Bilkisu akaro na biyu,


"Hmmmm ko yanzu wanne irin zama kuma zamuyi oho... M" haka yaketa maimaitawa acikin ranshi. Ranar laraba da daddare aka raka Bilkisu gidanta tun amota iyallo take zuba ruwan fada tana cewa wannan amarya akwai shashasha shine ko dan sunkuben lallen nan bata kunsa ba bare tayi kitso? Ita dai Bilkisu najinta batayi ko da tariba har suka karasa gidan inda su anty kubra dasu anty asabe ke zaune suna zaman jiransu, babu Wanda yakara koda mintuna goma acikin gidan duk tafiya sukayi lokaci guda kamar ana korarsu,yaye mayafinta tayi bayan tafiyarsu tana kallon dakinta wannan karon komai blue ne amma furnitures dinta farine tass kirar royal, bata bukatar sake fita koda falo saboda bacci take son tayi tahuta amma kuma bata son wannan dan rainin wayon yazo ya isketa tana bacci saboda jikinta na bata komai na iya faruwa.


Sai dai abinda bata saniba shine fahad yashirya zamansu yanda zai kasance, sam bazasu yi zama irin nada ba yanzu yanaji aranshi lokacin shine yazo shima, awanccan zaman Bilkisu tayi yadda takeso to yanzu shima shine zaiyi yadda yakeso shiyasa lokacin da yadawo ma bai ko shiga dakinta ba yawuce daya dakin wanda kayansa naciki dama wanka yayi yashirya cikin kayan bacci masu taushi yayi kwanciyarsa babu jimawa bacci yayi gaba dashi,Bilkisu nata jiran shigowarsa shiru shiru har tagaji da saurare tayi bacci ba ita tatashi ba sai asubah, tana kan gadon tana niyyar saukowa taji yana yimata knocking,


"Kitashi lokacin salla yayi..."


Daga haka taji shiru alamar yabar wurin, sake kwanciyarta tayi bayan tayi salla ba ita tasake tashiba sai 10 saura wannan dinma karar wayarta ne yatada ta,tsaki tayi sakamakon ganin khulsum ce me kiran nata,


"Labour har yanzu ba awartsake bane?  Ko dai sai nazo ne?"


"Uwar me zakizo kiyi min? Wallahi khulsum zan ramane..."


"Shikenan sai nazo din to"


Katse wayar tayi tana hamma saboda yunwa da kuma sauran bacci baccin dake kanta, wanka tashiga tayi tafito ta shirya tsaf cikin doguwar riga ta atamfa coffee colour sai dison yellow yellow ajiki, batayi kwalliya ba dan kawai powder tashafa sai kwalli ta fita falo, dama kayan abinci tasan babu matsala domin wannan karonma kamar waccan abba ya ajiye musu komai cikin store, afalo taganshi kwance daga shi sai three quarter da yar t shirt, yana kwance kan three sitter yana lallatsa waya, kanta ta dauke kamar bata ganshiba shima haka domin yasan awannan shegen son girman nata bazata yimasa magana ba saboda jira take ya gaidata tukun, harda wani dan bata rai yayi sai kace shine babba koda yake shima yanzun jin kansa yake a babba tunda shi yake aurenta ba itace take aurenshi ba dan haka yazama tilas tayi respecting dinshi a matsayinshi na mijinta, maganar hakkinshi kuwa dama shi yanzu ba ta wannan yakeyi ba saboda aduk lokacin da yatuna cewar ta auri wani yayi tarayya da ita sai yaji baya sha'awar abun, gaba daya abun yafice masa akai saboda yatsani hamood dinnan tsana mai tsanani. Kitchen tawuce domin taga kayan tea akan table,tana neman cattle tajiyo buga gida, duk haushi yabi yakamata sakamakon rashin gaishetan da fahad baiyiba,


Fitowa tayi daga kitchen din dan ganin suwaye, daidai lokacin da su mariya suka shigo dauke da kuloli akansu fahad yana biye dasu, nunata yayi yana cewa,


"Maza ku kai mata gata can"


Nufarta sukayi suna fara'a babu shiri itama tasaki fuskarta tana yimusu murmushi gamida karbar kayan dake kansu, maryam tariko kular wainar shinkafa ita kuma maryama tariko kular miyar agushi, anty Fauziyya ce tashiryo musu wannan wainar ta musamman domin ta hutar da amarya girkin safe, fahad baiko kalleta ba yawuce dayan bedroom din wanda ke gefen nata amma akwai dan tazara kadan,


Tare ta hada musu tea din dasu Maryam suka karya, ba karamin dadi taji wainar nan tayi mata ba wannan dalilinne ma yasata zagewa taci wainar sosai tana korawa da ruwan tea, daga nan falo suka tarkata suka koma ta kunna musu kallo har lokacin fahad bai fitoba ko breakfast dinma shi bai fito yayiba har 12 saura. Misalin karfe daya saura mintuna biyar ya Abba yakawo musu abincin rana, su maryama ne suka shigo da abincin amma shi ko shigowa baiyiba yadai ce agaidata, yanzunma tare suka ci abincin ranan shinkafa da miya da salad, bayan sun gama tawuce dakinta domin lokacin salla yayi, wanka tayi tai alwala tafito tashirya tana ta mitar shine babu wanda yazo mata yau wato har khulsum dinma da take cewa zatazo shine itama tayi zamanta ko leke, da abin sallarta tafita ahannu da hijabinta wurinsu maryama, tunda tashiga falon kamshi yacika kofofin hancinta wanda ko ba afada mata ba tasan na dan mulkinne saboda da alama yau da mulki yatashi da nuna isa,


"Anty ya fahad yanzu yafita yace lallai lallai muna yin salla mutafi gida saboda zamuje islamiyyar yamma..."


"Ba yau alhamis ba, har yau kunayin islamiyyar ne?" Tafada tana kokarin shimfida rug din sallar,


"Ehh munayi ranar juma'a ne kawai ba azuwa yanzu..." Maryama tabata amsa,


"Ok, fahad din yaci abincine?" Tayi tambayar da ita kanta bata san daliliba,


"A'a baiciba" suka hada baki wurin amsawa,


Sallarta ta tayar batare da ta kara magana ba, bayan ta idar tatashi tawuce daki tana ninke hijabinta tabarsu maryama afalo suma suna yin sallar, rasa abinda zata bawa yaran tayi daga karshe ta dauko wata atamfarta wadda matar abokin abba ta aiko mata da kyautarta lokacin da tana gida amma bata dinkaba,saida ta wahala kafin tanemo ledar da zata saka musu aciki, da atamfar da dari biyar tabasu sukayi mata sallama suka tafi, wayarta ta dauka tana latsawa amma kuma can kasan ranta tunani takeyi, wato wannan yaron dan rainin wayo ya karo wulakanci shine harda wani ficewa baiko fada mataba? Ohh sai yanzu tagano dalilin dayasa jiya baiko shiga dakinta ba, wato irin zaman da ya zaba musu kenan ahalin yanzu? To azuba agani zataga tsakaninsu wanda zai sauko yabi daya........



*_Ummi Shatu_*    

*Littafina na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*




48***Kawai tana zaune ne amma bawai dan tana jin dadin zaman ba, tunani ne fal ranta wanda mafi yawa na wulakancin fahad ne atoh wulakanci mana ita aganinta ai wannan wulakancine wato ahaka yake son yakawo wata gidan ya ajiye alhali ita baya girmamata?


"Wanne girma zai baki tunda yace ke matar sadaka ce...." Zuciyarta tabata amsa a sirrance,


Tabbas ko tantama batayi wannan shine dalilin da yasa yanzu baya rawar kafa akanta tunda ita matar sadaka ce ba matar so ba, kamar zatayi kuka takeji sauki daya tasamu shine su elmustapha sun kirata awaya sun shafe dogon lokaci suna hira cikin barkwanci. Tana nan zaune har daf da magriba lokacin ne fahad yadawo yana rikeda bakar leda wadda yasiyo fruits aciki dayake yau yana azumi itama husnah tanayi kawai bayaso yasawa husnah zargi ko mummunan tunani akan Bilkisu shiyasa baije wurinta sunsha ruwa tareba kamar yadda suka saba, yasan muddin yaje yasha ruwa awurinta yau to zata raina Bilkisu ko kuma taki ganinta da kima shikuma bazai so hakanba.


D'an bata rai tayi lokacin da yashigo cikin falon ganin haka yasa shima ya dan tsare gida kadan yawuce can saman dining yana sanye da shadda kalar ruwan shanshanbale, amma babu hula akanshi, ganin bai kulata ba yasata mikewa cikeda takaici tawuce bedroom dinta nan yabi bayanta da kallo yana girgiza kai,


"Hajjaju kenan.... Kina wahalar da zuciyata fa.... Kina azabtar dani" yafada acikin zuciyarsa, saida yasha ruwan tea da fruits sannan yaje yayi salla, tsintar kansa yayi da yin addu'ar Allah yasaka sonshi azuciyar Bilkisu kamar yadda shima yake sonta. Tunda tashiga daki tsabar takaici bata sake fitowa ba kawai mamakin fahad takeyi, to meyake nufi? Wannan tambayar tayiwa kanta tafi sau goma amma bata da amsarta, fahad kam har yasha ruwansa yagama yafita sallar ishah baiga Bilkisu tasake fitowa ba, shima ana idar da salla yadawo gida, daki yawuce ya dan kishingida yana kallo a laptop dinshi gefe daya kuma yana dan taba chat da friends, shi kadai yaketa dariya sakamakon hirar da sukeyi da su mukhty, sun sakashi agaba sai tsokanarshi suke suna cewa sai yafada musu yadda al'amarin ya kasance dariya kawai yaketa tura musu da gwalo yaki yayi magana shine bash yake cewa kai ku rabu dashi ai dama mijin hajiya ne kila ta gwabeshi akan yayi shiru kar yafada mana,wannan maganarce tabashi dariya wai mijin hajiya,har lokacin bacci yayi Bilkisu ta kwanta bata kara ganin keyarshi ba yauma haka tayita raba ido ko zai shigo amma shiru. Washe gari ita da kanta ta hada breakfast mai sauki tana falo tana karyawa yafito yanata shan kamshi kamar bai iya dariya ba,


Wuceta yayi zuwa kan table yazauna shima yafara karyawa abunda yasake kona ranta kenan yasata mikewa takoma bedroom tabar masa falon gaba daya, tana zaune gefen gado da system akan cinyarta saboda nanda kwana biyu zata koma aiki dama sati daya aka bata kawai taji yana knocking abakin kofa,


"Yes..." Yafada atakaice, bude kofar yayi ya dan leko kansa ciki batare da yashigo ba yace,


"Ki duba store koda akwai abunda babu wanda kike bukata saiki rubuta fita zanyi...."


Batare da ta kalleshi ba tace,


"Kayan miya zaka siyo kadai...."


Baice komai ba yakoma yaja mata kofar, wanka yaje yayi yafita bai wani jimaba yakawo kayan miyar yasake komawa kai tsaye gidan anty asabe yawuce ta can suka tafi kasuwa tare da ita, kayan lefen husnah suka hado sannan suka sabunto lefen Bilkisu nada suka sassauyo kayan ciki da akwatunan saboda kafin yakoma makaranta za akai lefen husnah sannan za ayanke rana, wuni cur sukayi akasuwa shida anty dan sai yamma liss suka koma gida duk da tana ta cewa yazauna yaci abinci yace a'a girkin amarya zaije yaci,


"Babu ko kara ko fahad?" Ta fada tana dariya, baiyi magana ba yasaka sau cikinsa yanufi gida.


Kamar yadda jiya bata san fitarsa ba haka yauma batare da ta saniba yayi tafiyarsa shiyasa abun ya tsaye mata arai, tana kitchen tana girkin abincin rana khulsum tazo dauke da danta khalifa,tare suka karasa wuni da yamma tatafi, khulsum na tafiya bayan takoma ciki tayi wanka tana shiryawa fahad yadawo, yunwa yakeji sosai sannan gashi yagaji lilis, rigar shaddar dake jikinsa yacire ya zamana daga shi sai yar farar singileti da dogon wando, zama yayi kan table yafara bude abincin dake wurin, jallop din shinkafa ne sai hadin vegetables salad mai dauke da dafaffen kwai aciki. Yana tsaka da cin abincin yajiyo karar wayarshi amma bai iya tashiba saboda yana jin dadin abincin sosai ba kadan ba, yayi missing girkinta da ita kanta gaba daya, saida ya koshi dam sannan yataso yana rikeda tissue yana goge bakinsa, dai dai lokacin itama tafito daga cikin daki, kallon juna sukayi tazo tawuce shi tanufi dining area ta bude fridge ta dauko banana milk shake ta zuba acikin glass cup tazo tawuce daki, ganin abinda ta debo yasashi shima komawa dining area din yazuba cikin cup ya shanye yana lumshe ido saboda gardi da dadi gashi yadau sanyi ba karya, rigarshi da ya cire yaje ya dauka tareda wayarshi yashiga daki, zama yayi saman katifa yana kokarin kiran husnah saboda itace ta kirashi dazu, tana dagawa yace,


"Am sorry my love.... Dazu kin kirani time din ina tare da antynki ne ina cin girkinta mai dadi...."


Duk da taji haushin maganarsa amma saita waske tanuna kamar bataji zafin hakan ba tace,


"Babu komai my prince dama zan fitane zamuje kasuwa nida Fa'iza...."


"Adawo lafiya my love.... Allah yatsare"


Daga haka sukayi sallama yakatse wayar dama tun lokacin da suka jone da husnah ko ba ya gari idan zata fita saita tambayeshi shiyasa har sun dade da sabawa da wannan tsarin sam basa kallonsa asabon abu. Irin zaman da su Bilkisu suka faro shi suka cigaba da yi na ba ruwan kowa da kowa, gaisuwa kuwa tab rabon da taji fahad ya gaisheta har ta manta gashi yanzu wani sabon salon wulakanci da ya koya shine sai yarinka kiranta da Bilkisu, idan zaiyi mata magana sai dai yakira sunanta, yauma da zai fada mata sakon su ayiyah tana daki tana ware kayan sawarta tana karasa shiryawa cikin drewar, zama yayi gefen gadonta yace,


"Am Bilkisu ayiyah tabani sako.... Tace wai gobe za akai lefen ya Abba gidansu salim idan kinada lokaci kije akai dake...."


"Naji...." Tafada atakaice saboda tasoma kosawa da wannan rashin kirkin nashi akan me zai rinka kiran sunanta kai tsaye? Duk da bawai yau yafara ba amma yau kamar hakan yafi kona mata rai. Washe gari da yamma bayan tadawo daga aiki ta shirya tatafi gidansu fahad sai kaffa kaffa ayiyah takeyi da ita, dama tasan bata da matsalar uwar miji dan ayiyah na mutukar sonta hakama sauran yan uwan mijinta kawai dai abinda ta lura shine matar ya sunusi wato anty juwairiyya bata faran faran da ita tun wancan lokacin har yanzu dan tun aurensu nafarko taketa kukkushe Bilkisu tana cewa ai fahad tsohuwar yayarshi ya auro dan wannan a haihuwar kajima ai ta haifeshi, ko yauma da ta shigo gidan kowa yanata murna da lale marhabun da ita amma banda Anty juwairiyya shiyasa itama takama class dinta daga gaisuwa bata kara cewa komai ba,tarba ta girmamawa aka yimusu agidansu salim akwatuna shida masu kyau suka kaiwa nusaiba bayan an karbi kayan da babu jimawa suka koma gidansu fahad lokacin magriba tayi, Bilkisu tafito tsakar gida tana alwala sai ga fahad yashigo daga masallaci yake anty juwairiyya na ganinshi tafara cewa,


"Kaga sabon ango....kaima nanda wani satin zamuje Kaduna mukai maka naka...."


Baiyi magana ba sai murmushi kawai duka hannayenshi na cikin aljihun rigar farar shaddar da take jikinsa,gun Bilkisu yakarasa ya tsaya kusa da ita tana alwala,


"Zaki tafi yanzune injiraki ko sai anjima sai indawo in daukeki?"


Jin abinda yace ba karamin dadi yayiwa Bilkisu ba saboda tasan dai ko babu komai anty juwairiyya zata gane fahad na yinta kuma tanada wani matsayi na musamman agareshi,rausayar da kai tayi ta kalleshi sannan tace,


"Da sallah nake son nayi... Ko sauri kakeyi?"


"A'a kiyi mana... Kiyi sai mutafi"


"Yawwa nagode" tafada tana kokarin shiga falon ayiyah inda anty juwairiyya ke tsaye tana kallonsu sai jan fahad take da maganar bikinsa shida husnah amma yaki biye mata suyi saboda shi yanada wani abu guda daya akan Bilkisu, idan daga shi sai itane baya raga mata ahalin yanzu amma idan agaban mutane ne ko wani to yana nuna har gobe yana sonta yana martabata, shiyasa abun bai cika damun Bilkisu ba saboda sai idan iya shi da itane yake nuna shine oga dole ta girmamashi. Har ta idar da salla bai bar kofar falonba yana tsaye da wayarshi a hannu yana dannawa, lokacin da take yiwa ayiyah sallama tana jiyo anty juwairiyya nace masa,


"Ko da amaryar ake soyewa ne dan kanina...."


"Kai anty nifa gaskiya kin saka min ido da yawa..." Yafada yana dariya, sosai Bilkisu taji dadin amsar da yabata, fitowa tayi rikeda irin kayan snacks din da aka basu agidansu salim wanda anty asabe ta zubo mata, karba yayi daga hannunta yawuce gaba tana biye dashi abaya har waje, su ya Abba na zaune akofar gida shida salim sai taji duk kunya ta kamata musamman ma lokacin da zata hau bayan babur din nashi dole saida ta dafa kafadunshi duka guda biyun, har sukaje gida babu wanda yace da wani ci kanka sai dai idan sun dan shiga kwari ko gargada yaji ta rikeshi da haka suka je gida. Cikin yan kwanakin aka kammala komai na zuwa kd domin kai lefenshi komai iri daya yayi ma husnah da Bilkisu bai banbanta ba ita Bilkisu ma bata san wacce wainar ake toyawa ba, ita dai kawai abinda tasani shine bazata taba daukar raini ba nashi ko na matarshi, ranar da aka tafi kai lefen ma bai fada mata ba saboda har gobe irin zaman da ya zabar musu sukeyi, ita anata ganin ai ba ita yadace ta rinka shan kanshi ba ko kuma ta nemi shiri dashi, shiyasa gaba dayansu ba wani dadin zaman sukeji ba saboda kowa baya sakarwa kowa, har aka kai lefen aka saka rana wata biyu babu wanda ya gaya mata batama saniba gaba daya, shi kam fahad shirin komawarsa makaranta yasaka gaba yana kammalawa ya tafi bayan yabar mata duk abinda yasan zata bukata. Wani lokacin Mariya ko maryama ayiyah ke turo mata su tayata kwana amma ba kullum ba, tunda yatafi kuma bai kirata ba sai bayan kwana hudu da tafiyarsa nan dinma iyakarta gaisuwace daga nan ya tambayeta ko da akwai abinda take bukata tace babu shikenan yace mata sai anjima, hakace take faruwa har yayi sati uku da tafiya a lokacin ne yazo gida  weekend, tun ranar Thursday yazo yana son komawa Monday ko Tuesday,lissafin bikinsu kuwa saura sati hudu babu yan kwanaki, a wannan zuwan da yayi yai niyyar fadawa Bilkisu maganar aurenshi da husnah, ranar ya fada mata da safe tana karyawa zata tafi aiki saboda Monday ce shikuma yana kwance kan three sitter yana kallo, a laptop dinshi,


"Bilkisu aure zanyi fa...., yau saura sati uku da kwana biyu..."


Saida ta dan ja numfashi sannan cikin halin ko inkula tace,


"Allah yabada sa'a... Ko akwai wani abu da zanyi baya ga haka?"


Girgiza kai yayi yana murmushin takaici bai san sai yaushe Allah zai karbi addu'arshi yasa Bilkisu ta soshi kamar yadda yake sonta ba, ita kuwa tsabar takaici da bacin rai ko gama cin abincin ba tayiba tabarshi ta tashi ta dauki wayarta da handbag dinta tafita dama tun dazu mai napep din dake kaita aiki yazo. Fahad kwanciyarsa yaci gaba dayi har saida husnah ta kirashi tace yataimaka yazo ya dinka mata atamfarta domin da ita take son tatafi gida jibi, jibi zata gama exams dinta kuma idan tatafi bazata dawoba sai bayan bikinsu saboda hutun session ne, tashi yayi duk jikinsa babu karfi yayi wanka yashirya cikin kananan kaya, bakar riga da milk colour din trouser, zama yayi ya karya sannan yafita yasamu husnah a shagonsu salim tana jiransa, tsokanarsu salim yafara yi yana waka yana cewa ga amarya ga ango, tare suka haura saman shagonsu fahad inda zaiyi mata dinkin.


Bilkisu kam tana can office tarasa me yake yimata dadi, ita dai tasan ba kishine ke dawainiya da itaba kawai dai bata son yarinya karama tazo ta nemi rainata shiyasa bataji tana farin ciki da auren da fahad zaiyi ba, duk zuciyarta babu dadi take gudanar da ayyukan dake gabanta, lokacin da taje yin voicing din news kuwa kasawa tayi saboda sai tafara tiryan tiryan sai ta tsaya tana inda inda kamar yaune tafara koyon aikin daga karshe dai sai hakura tayi ta mayarwa head of news din tace kanta ke ciwo bazata iyaba, haka ta tarkata nata inata tafito domin tafiya gida dama yau khulsum bata zo ba, abin bakin ciki saida taje gida taga ashe yau bata fito da keys dinta ba wato mantaso tayi aciki da safe bata dauko ba koda yake da safenma acikin kunar zuci take saboda maganar da fahad yafada mata na aurenshi ko ina ruwanta da zaizo yasata agaba yana wani cemata aurenshi yakusa? Tsaki tayi ta tsayar da mai napep dinta dama Allah ya taimaketa bai tafiba, wayar fahad taketa kira amma bai dagaba har sau uku, tasan duk yadda akayi baya tare da wayar saboda bai fiya kin daukar wayaba matsawar yana kusa, yanzu bata da zabin da yawuce tabishi plaza shagon dinkinsu ta karbo nashi mukullan, hakan tayi tashiga napep tatafi plaza dinsu, lokacin shikuma yana zaune shida husna dasu tj yana yiwa husnah dinkinta su tj kuma sai hirar siyasa sukeyi shidai dariya yakeyi kawai saboda ganin yanda suka hakikance suke tada jijiyar wuya saida cikin kowa yafara kugi saboda yunwa kowa yadare yatafi neman abinci yarage saura su biyu ashagon, ahaka Bilkisu tashigo ta samesu, da mamaki fahad ya dago yana kallonta ranta abace fuskarta adaure amma shi sai ya fadada tashi da murmushi saboda husnah dake zaune,


"Hajjaju yadai? Lafiya kuwa?"


"Inata kiranka baka daukaba...., keys dina ashe ban fita dasu ba... Bani na wajenka"


"Kashhhh, bari salim yadawo, dazu wallahi yazo ya karba yaje siyo fetur ne a Babur dina kuma duk keys din tare suke... Sorry fa..."


"To ya zanyi da mai napep dake jirana?"


"Ba matsala bari na sallameshi sai na mayar dake gida nima nakusa tashi,have a sit" yafada yana nuna mata wurin zama kan wani benchi dake ajiye shi kadai babu komai akai, tashi yayi da kanshi ya sauka kasa domin sallamar mai napep din, daga ita har husnah babu wadda yayi tari ita husnah ma wayar hannunta take latsawa yayinda Bilkisu ke bin shagon da kallo har ta dire kallonta kan husnah wacce ke sanye cikin riga da skirt na leshi c green taci daurin zahra buhari hakan yabawa kitson dake kanta damar lekowa ga dan siririn mayafinta kalar kayanta kan kafadarta barima guda ukune jere akunnenta kallo daya zaka yimata ka fahimci yar jami'a ce dan tsantsar wayewar da take tare da ita sam bata san cewa itace budurwar fahad ba amma ita husnah tuni tagane Bilkisu itace matar fahad hakan yasata dan kallonta ta gefen ido tabbas black beauty ce kuma ita dinma babu raini tun daga dressing dinta pink din materia ne ajikinta mai tsada shiyasa komai nata pink tayi amfani dashi ciki kuwa harda hill din takalmin kafarta saboda ita ba ma'abociyar saka flat bace.....




*_Ummi Shatu_*    


*Littafina na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*




49***Har yadawo babu wanda yayi magana acikinsu yana zuwa yazauna a mazauninsa da yatashi dazu,


"Hajjaju nabar wayar a silent ne ashe ban saniba..." Yafada yana murmushi,


"Babu damuwa..." Ta amsa hankalinta na kan wayarta dake hannunta, karfe uku saura agogon silver din dake daure a hannunta yanuna duk tagaji kawai alla alla takeyi taganta agida tasha tea ta kwanta ta huta, tsitt shagon yayi baka jin maganar kowa sai karar keken da fahad yake dinki dashi, kowa yanada dalilinsa na yin shiru, husnah da fahad dalilinsu daya ne saboda ganin Bilkisu zaune awurin shiyasa suka kasa sakewa suyi hira ita kuma Bilkisu hayaniyarce bata so domin har wani dan ciwo ciwo kanta keyi,wayarta take dannawa tana chaten da khulsum tana tambayarta abinda yahanta zuwa aiki yau,


Ninke kayan da yagama hadawa yayi ya mikawa husnah nan takarba can kasan makoshinta ta furta,


"Thank u my prince..." Kan labbanta kawai ya kalla yayi murmushi, mikewa yayi yana yin mika saboda zaman da yasha, yana kokarin daura agogon hannunshi wanda yacire yaji husnah ta fauce,


"Dama ai nafada maka sai nasace agogon nan wallahi yafi dacewa dani..."


Kallon agogon yayi ya kalli husnah shi ba wai tsadar kudin agogonne damuwarsa ba a'a yanda yake son agogonne saboda kwata kwata wannan shine sawarshi na uku a Kaduna yasiyo shi kuma unisex ne maza da mata kowa zai iya sakawa, 7 thousands ya siyeshi amma tun ranar da husnah taganshi ahannunshi tace sai yabata shikuma yahanata yace zai saka mata irinshi a lefe amma da yake kansa yadau caji gaba daya ma yamanta da sunyi magana makamanciyar wannan lokacin da ake hada lefen. 


"Hmm ya fahad sai munyi waya dai kawai..." Tafada ahankali saboda kar Bilkisu tajita,hannunshi ya mika mata,


"Bani agogona before kitafi... Bani pls"


Makale kafada tayi tajuya zata tafi nan yayi gaggawar riko rigarta ta baya babu shiri ta tsaya, duk abunnan da sukeyi Bilkisu bata san sunayiba domin abinda yake gabanta takeyi wato chaten, saida tajiyo motsin fara kokawarsu sannan ta daga kanta ta kallesu abin yayi mutukar bata mamaki saboda ita kallon salihi mutumin kirki take yiwa fahad amma yanzu sai ganinshi tayi dumu dumu yana kokawa da mace har yana hadata da jikinshi, to meye hakan? Har wajen baranda suka fita suna kokawa yana kokarin kwace agogonshi amma husnah ta hanashi wannan dalilinne yasashi turata jikin bango ya matseta yana neman kwacewa,


Ganin kamar sunma manta da ita yasata tashi ta dauki jakarta fuuu tafito, abayan kofa tagansu suna manne da juna har lokacin basu daina kokawar ba, wani dogon tsaki taja sannan tawuce, dukansu tsayawa sukayi suna kallonta tana kokarin kaiwa karshen steps din benen, sakar masa agogon husnah tayi yajuya yabi bayan Bilkisu bai ko koma cikin shagonba bare ya rufeshi cikin ikon Allah sukayi kicibus da nazifi zai koma shagon, yana sauka kuma yaganta tsaye itada salim suna gaisawa alama yayiwa salim da ido nan ya wulla masa keys din dake hannunshi ya cafe yaje ya dauko babur din yatsaya agabanta ,dauke kai tayi sannan ya karkata mata tahau, duk husnah na kallonsu daga can inda take tsaye asama, har saida taga sun tafi sannan ta sauka itama tatafi. Bilkisu kam wani irin bakin ciki takeji wanda batasan dalili ba, ganin da tayiwa su fahad manne da juna yaki ya bace daga cikin idanuwanta da zuciyarta gaba daya, ji take kamar ta shakeshi tayita dukansa ko zata huce, har sukaje gida bataji bacin ranta ya ragu ba,


"Kenan Allah kadai yasan abinda sukeyi idan su biyune kadai...." Tafada acikin zuciyarta saboda yanzuma sukayi haka agabanta inaga su biyune kacal ashagon, tsaki taja tasake ja akaro nabiyu tana kokarin rage kayan jikinta, falo tafita ta hado tea tazauna tana sha sai faman jan tsaki takeyi saboda bacin rai,


Duk tsakin da take ja fahad na jinta amma bai yi maganaba kuma yasan dashi take,


"Ita ta dazun da kaketa hada jiki da ita, ita kuma wacece?"


Yaji tafada cikin murya mai dauke da fushi,


"Husnah ce fa matar da zan aura, har sadakina yana gidansu..."


Banza tayi dashi saboda ita ba wannan ta tambayeshi ba, wani tsakin takuma ja sai yanzu tagane dalilin yarinyar na kin yimata magana dan ko sallamarta bata amsaba tana ankare da ita,


"Mtswwww wato kishi kenan zatayi dani? Ni ai ba sa'ar kishinta bace..." Tafada cikin fushi sannan ta dangwarar da cup din hannunta ta mike tawuce cikin daki taje ta kwanta saboda taji ciwon kanta yafara tsananta. Har yaci weekend dinshi yakoma bata dawo daidai ba koda yaushe cikin fushi take,shidai tunda yasamu yakoma school bai waiwayo gidaba sai after 2 weeks. Ranar da yadawo da daddare yaje gidan anty asabe ya debo lefen Bilkisu yakawo mata, tana kwance adaki tana aiki acikin system dinta, zama yayi agefen gadon yana kallonta itama kallonshi takeyi tun lokacin da yafara shigowa da kayan har lokacin da ya kammala yazauna dan nesa da ita kadan,


"Bilkisu ga wannan.... Kayanki ne"


Kallonshi tayi ta kalli kayan,


"Kayan menene? Kayan fadar kishiya ne ko me?"


"A'a ba kayan fadar kishiya bane, kayan lefenki ne, ai kinga lokacin da mukayi aure banyi miki ba..."


"Ehh hakane..." Tafada tana jin zuciyarta na wani irin tafarfasa, itafa gaba daya haka kawai take jin haushin auren da zaiyi batare da wani daliliba,ganin bazatace komai ba yasashi tashi yafita, harga Allah da yace mata kayan fadar kishiyane babu abinda zai sata karba amma tunda yace mata lefantane shikenan, tashi tayi da kanta ta jera akwatunan gefen wardrobe dinta. 


Tunda biki ya karato fahad yazama busy Bilkisu kawai kallonshi take tana jin mugun haushinsa musamman ma ranar da yazo mata da maganar wai ta gyara kayanta na falo tasasu a side daya saboda itama husnah tasamu wurin saka nata duk inda yabi da harara take rakashi, babu abinda ya shalleta da aurenshi sha'anin gabanta kawai takeyi da fita aikinta acan take rage tunani da damuwa wadda bata san musabbabinta ba, duk cikin yan uwanta da gidansu babu wanda ta fadawa saboda aganinta wannan ai be abinda zata zauna tana fada bane, ko khulsum saida tafara ganota sannan ta sanar da ita wai fahad ne zaiyi aure,


"Yanzu ke mijinki zaiyi aure amma kike zaune ahaka? Shine bazaki tashi ki gyara kanki ba..."


"Khulsum nifa banida lokacin su wallahi, basune agabana ba suje can su karata..."


Cikeda jin haushi khulsum ta kalleta tana harararta,


"Maza dai kibari kiyi saken da zaki dade kina cizon yatsa bare gashi kince karamar yarinya zai auro..., wallahi ina tausaya miki mutukar baki zage dantse ba kina ji kina gani zata kwaceshi...."


"Ni dama ban rikeshi ba ai, taje ta kwadashi ta cinye..."


"Hmmmmm labour kenan, kina son guy dinnan fa kawai kin kasa ganewa ne saboda zafin kishin dake damunki da shegen son girman tsiya....."


"Ni kar kiyi min sharri malama...., kinga tafiyata sai gobe"


Bata jira cewar khulsum ba ta yi tafiyarta,tana zuwa gida ta tarar anfitar da kayanta duka waje an fente gidan da sabon fenti 2 colours wanda zai shiga da kowanne kalar furnitures, duk sai kuma takara jin babu dadi damma dai falon yanada girma sosai haka bedrooms dinma sannan ba lallai wanda ke daya dakin yajiyo motsin wanda ke cikin dayan ba wannan shine saukinta iya falo da kitchen da store kawai zasuyi shearing, da damuwa makale saman fuskarta tayi wanka tashirya sannan ta dora girki, dan wake tayi tana tsamewa daga cikin tukunya fahad yashigo,sanye yake da kananan kaya yaje ya amso kayansa wadanda zaisa ranar daurin aure da ranar dinner, kitchen din yabita dan ganin me takeyi ganin dan wakene yasashi zubawa acikin flate yawuce bedroom dinta yazauna yaci acan, har yaci yagama yafita maganarsu batafi guda uku ba, shiyasa lokuta da dama yakance Bilkisu miskila ce koda acikin ranshi ne domin tanada wani murdadden hali mai wuyar fahimta cikin sauki. Tunda aka fara hidimar bikin nan ta tsame kanta daga sabgar kowa su maama ma da sukace mata zasuje bikin hanasu tayi tace indai saboda ita zasuje to suyi zamansu, daren ranar abba yakirata yayiyyi mata nasiha sannan yace me take bukata yanzu na gyaran daki ko falo ko na kayan kitchen tace babu komai saboda itama gaba daya kayanta sabbine fil babu abinda take bukata kuma kitchen dinta cike yake da kayan amfani duk da haka saida Abba yasaka mata kudi cikin account dinta. Tun ana saura kwana biyu masu jeren husnah suzo fahad yacewa Bilkisu ta matsar da kayanta na kitchen tasaka a side daya hakama na falo amma duk tayi mirsisi da yayi magana kuma tafara yimasa masifa bai kulataba saboda ya fuskanci kwana biyun nan fada takeji shi kuma yanzu ba wannan ne agabanshi ma in fact ma bayaso husnah tazo ta iakesu cikin wannan halin, bayan yafita daga gidan maama yakira yafada mata abinda ke faruwa yace da Bilkisu ta gyara kayanta ta mayar side daya amma taki, washe gari saiga maama shiyasa ranar ko aiki Bilkisu bata jeba sake kuluwa tayi lokacin da taji dalilin zuwan maama wai dan kawai ta tayata gyara kayanta abarwa husnah space shikenan tahau fada kamar dama jira take ita dai maama bata kula ba itace ta zage ta gyara kitchen din ta sakawa Bilkisu nata abangaren dama ta barwa husna daya ban garen, falo ma haka tayi ta jerawa Bilkisu kujerunta suna kallon dakinta ta raba falon biyu,har dare suna tare da maama saida ta gama komai sannan tatafi, ita dai Bilkisu sai kunkuni take tana cewa fahad zai san ita yakai kara wurin kanwarta.


Washe gari yan jere sukazo ita dai tayi tafiyarta office shiyasa kafin ma tadawo har sun gama sun tafi ranta ne yabaci saboda ganin yanda falon ya matse babu space sosai, kayan husnah dukka milk colour ne tun daga kujeru har su cuttens da sauransu, dakinta kawai tawuce kai tsaye taje ta zauna tanata zancen zuci cikin bacin rai,


"Haka kawai za awani zo atakura min....mtswwww"


Sam bata son fita falo saboda bata kaunar ganin kayan husnah, bakin cikin ganin wadannan kayan shine yahanata bacci adaren yau, shi kuwa gogan tana jinsa sai kaiwa da kawowa yakeyi shi alalle ango, rashin baccin da bata yiba shine ya haifar mata da matsanancin ciwon kai da safe dan dashi ma ta tashi, jin tace bata da lafiya yasa fahad kawo mata magani amma taki sha saboda haushinsa takeji bata san daliliba gashi tsabar wulakanci tunda yafita daga gidan bai dawo ba har yamma,tambayar kanta tashiga yi kenan nuna mata yake son yi bai damu da lafiyarta ba? Ko kuwa so yake yanuna mata wulakancinsu na maza alokacin da giyar aure ke dibar su? Da wannan takaicin ta wuni zuwa yamma tasamu ta tashi tayi wanka ta shirya, kitchen tashiga dan samarwa cikinta abinda zata saka masa tana yi tana mita saboda ada gaba daya kitchen dinnan natane sai inda takeso zata ajiye abu amma yanzu aikin banza anwani zo an kakaba kayan wata aciki, indomie ta dafa ta soya kwai guda biyu takoma falo tana hararar kayan husnah tasamu wuri tazauna, saida tagama cin abincinta tayi salla sai ga khulsum, tsayawa khulsum tayi tana karewa falon kallo hannunta kan habarta,


"Tirkashi...hajji fahad dai yadage sai yayi mana kishiya.... Har anzo anzuba jere?"


Ita dai bilkisu tana jinta batace komai ba ita kuwa khulsum saida taje ta leka ko ina har bedroom da kitchen duk saida ta duba sannan tazo ta nemi wuri ta zauna tana bawa Bilkisu shawarwari, bayan tafiyar khulsum kawai jin hawaye tayi wadanda bata san dalilin zubowarsu ba, gaba daya tayi sanyi kalau tayi sukuku da ita, shi kuwa uban gayyar taga kamar adokance yake da wannan auren saboda ko zama baya samu yanzu idan yafita tun safe baya dawowa sai dare ita dai tasan wannan bai dameta ba amma kawai bata cikin walwala da farin ciki,yan gidansu kuwa da sukace mata zasuzo tayata zama kin yarda tayi amma duk da haka saida suka zo, ana igobe daurin aure har gida su ayiyah sukazo suka yi mata nasiha akan tayi hakuri sannan kuma azauna lafiya idan husnah tazo ta riketa kamar kanwarta, ita dama tasan su ayiyah na sonta bata da case dasu. Washe gari takama ranar daurin auren husnah da fahad sai Abba da nusaiba kanwarsu salim amma shi fahad nashi auren a Kaduna za adauroshi gidan da ake rikon husnah, Bilkisu na can dakinta tana aikin da babu gaira babu dalili dan kawai ta debewa kanta kewa tarage damuwar dake ranta wacce bata san ko ta mecece ba fahad yashigo cikin shirinsa tsaf na tafiya daurin aure, farar shadda mai tsada yasaka sai jar hula da farin takalmi wato dai kwankwasiyya atakaice sai zuba kamshi yakeyi,


"Ranki yadade ni nafito, sai Allah yadawo dani... Insha Allah tare da amarya zamu taho..."


Banza tayi dashi saboda aganinta wannan ma ai rainin wayo ne wato saima yanzu zai sakaya sunanta da yake maganar aurenshi zai fada mata,


"Mai gado bakiji ni bane....?" Yafada yana tsuke fuska,


"Idan najika me zanyi maka? Ko daukarka zanyi akaina inkaika har wurin daurin auren?" Tafada cikin masifa,


"A'a nidai yau ba ranar fada bace ranar farin cikina ce ranar da bazan manta da ita ba, ki nemi abokin fadanki amma ba Muhammad fahad ba...."


Daga haka yajuya yafita hakanne yasake kular da ita har taji kwalla tafara zubo mata, wurin karfe 10:30 khulsum tazo lokacin tagama kukanta amma idanuwanta jajur suke,


"Labour kuka kikayi ko? Haba ke kuwa sai kace karamar yarinya?" Khulsum tafada tana kallonta,


"Hmm khulsum ba zaki gane bane yaron nan ya iya bakar magana kamar rainon gwauro..." Tafada acikin ranta amma afili sai tacewa khulsum,


"Nifa babu kukan da nayi uwar son jin tsurku.... Zaki fara sa idon naki da kika saba..."


"Allah ya shiryeki kawata, kina wahalar da zuciyarki wallahi.... Tab inama nice fahad"


"Da kece me zakiyi?" Bilkisu ta tambayeta tana harararta,


"Da Allah kadai yasani...."


"Kya dai ji dashi"


"Allah dai yabar kawata uwar gida agidan fahad wallahi ko amarya tazo kece star...." Khulsum ta fada tana rangada guda, tun Bilkisu bata biyeta har ta biye mata suka yita yarawa zuwa can saiga meenah da maama amma banda Hindu wai bata jin dadi kuma da yake cikinta ya tsufa haihuwa ko yau ko gobe, sune suka raya mata gidan har tasamu damar manta damuwarta. Har dare suna gidan dan acewarsu sai ankawo amarya akan idonsu hakan kuwa akayi bayan sallar magrib sai ga yan kawo amarya damma sun tsaya agidansu fahad anyi budar kai amma tun yamma suka iso, duk da su maama suna taya Bilkisu kishi amma hakan bai hanasu tarbar yan kawo amarya da fara'a ba, ita dai Bilkisu tana daki ita da meenah, tana ji yan kawo amaryar wasu daga cikinsu na cewa su dai baza suje dinner ba sun gaji, tabe baki tayi tabi lafiyar gado ta kwanta, fahad kuwa tun safe lokacin da yayi mata sallama yafita bata kara sakashi cikin idanuwanta ba, shikam yana can gidansu dakinsu na da shida ya abba tun bayan dawowarsu daga Kaduna yake cikin ruguntsumi bai samu kansa ba yanzu ma haka shirin tafiya dinner suke yi shida abokansa dan hatta su mukhtar duk sun zazzo suna dakin salim ansaukesu acan. 


Bilkisu na kwance tana jin hayaniyar dake tashi ta yan kawo amarya ga kawayen amarya sai ihu da shewa sukeyi bata samu taji gariba har saida suka tafi dinner dinnan nan su khulsum suma sukayi mata sallama suka tafi da sauran yan uwan su fahad, bayan kowa yatafi amma tana jiyo yar hayaniya adakin husna ta shiga wanka tayi shirin bacci ta kwanta duk da tasan yaudarar kanta kawai takeyi dan ba yi zatayi awannan lokacin ba, 12 saura aka dawo daga dinner din nan sabuwar hayaniya ta tashi hakan yasake kona mata rai bayan kamar mintuna talatin taji karar tashin motoci zuwa can kuma taji tsitt alamun kowa ya tafi, ita dai tana kwance daga inda take bata ko motsa ba, 12 da wani abu taji motsin shigowar fahad, kai tsaye dakinta yafara shiga yana rike da leda a hannunshi na dama hannunshi na hagun kuma yana rike da wayarshi da babbar rigarshi, kai daga gani kasan a mutukar gajiye yake domin hakan ya bayyana akan fuskarshi karara, langabe kai yayi yana kallonta cikin shagwaba yace,


"Shine ko nemana ma ba ayi?...."


Wata harara ta dalla masa amma sai yayi murmushi, ya karasa gaban gadonta ya ajiye mata ledar, kallonshi tayi afakaice yana sanye da dark purple din shadda dinkin half jamfa da hula babbar rigar kuma na rike hannunshi,


"Ga kayan kwalam da makulashenki..."


"Bana so ka kaiwa amaryarka......"


"Karki damu tare na siyo muku nata yana falo, yanzu zanje na kai mata...."


Bata tanka ba ta dauke kanta taja duvet ta dan jiyo kadan ta kalleshi,


"Zanyi bacci dan kashe min hasken idan zaka fita..."


Murmushi yayi maimakon yafita saima ya zauna kan stool din dake gaban mirror,


"Basai fa kin koreni ba zan tafi, bari na dan huta..."


Bata kulashiba taja duvet ta rufe har kanta tana sauraron ajiyar zuciyar da yake saukewa ahankali zuwa can kamar bayan mintuna 15 taji yatashi yakashe mata wutar yafita, tofah kamar amafarki sai taji kuka ya subuce mata wanda bata san musabbabinsa ba,ni kaina Ummi A'isha so nake naji dalilin kukan Bilkisu........




_jiya yar dakina asked me wai sis ummy wacce irin kamace da yan Jami'a? I laugh over and over and over again then nace mata, yan gayu masu class kuma wayayyu saboda seriously duk wadda tayi jami'a zaki sameta komai nata is different tun daga mu'amalarta da mutane and so on, hatta a dressing dinta ma wallahi zaki fuskanci mai class ce babu baragada da yawan hayaniya shiyasa kukaji na siffanta husnah da haka, da nace kana ganinta zaka gane yar Jami'a ce what i mean is da zarar ka ganta kaga mace mai class kuma abar burgewa, and da nace tayi hudar kunne guda uku bawai fa ina nufin hakan baida kyau ba a'a kawai inaso innuna irin ta kure kwalliya da gayu mai yawa so dan Allah kar ayi min mummunar fahimta wallahi duk abinda nafada da kyakkyawar niyya nafada, tnx for ur love and support._




*_Ummi Shatu_*    


*Littafina na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*


50***Kuka take yi harda shessheka gaba daya ta jike pillow din da take kai, ga wani matsanancin ciwon kai wanda yafara damunta har tsawon karfe daya da kusan rabi takai tana wannan kukan, 

Dai dai wannan lokaci shi kuma fahad na can tare da husna, lokacin da yashiga kishingide ya isketa ta dan fara bacci, tashinta yayi ta hanyar kama yan kafarta wadanda sukasha jan lalle da baki yana jansu ahankali, bude ido tayi tana kallonshi cikeda gajiya da tarin bacci,


"Ya fahad... Sai yanzu kadawo?"


"Wai har kin fara bacci asma'u? Oya tashi kici abinci sai ki kwanta..."


Yafada yana janyo hannunta, kafada ta noke tamaida kanta ta kwantar saman pillow,


"Ni bana jin yunwa, kaci kayanka..."


Murmushi yayi ya matsa jikinta, ahankali yace,


"Ko kema kina jin tsorone?"


"Name?" Tafada tana bata rai,


"Kar kici min kazata kuma nace sai kin biyani......!"


Daga shi har ita dariya ce ta subuce musu ta harareshi sannan ta gyara kwanciyarta izuwa rigingine,


"U kid yourself sweetheart.... Good news da zan baka yanzu shine am off, soo allow me to sleep pls....."


Murmushi yayi yana shafar lallen hannunta,


"To kinga dadinma zagewa kici kaza kenan tunda ba biyana zakiyi ba, wake up pls"


Girgiza kai tayi tana lumshe idanuwanta,


"Na koshi wallahi, sai da safe zanci...."


"Ok, sleep tight my love, good night...."


Bata amsaba ta gyara kwanciyarta ta hanyar juyawa daya bangaren, shikam yunwa yakeji sosai saboda yau da yunwa yawuni throughout shiyasa ya zauna yaci rabin kaza yasha madara, tashi yayi yashiga bathroom yayi wanka yafito ita dai husnah ko kayan jikinta dakyar ta iya canjawa saboda tsabar bacci da gajiya,shiryawa yayi cikin kayan baccinsa maroon colour masu santsi sannan yatashi yafita, dakin Bilkisu yanufa saboda haka kawai yake jin zuciyarshi bata nutsu da yanayin da Bilkisu ke cikiba shiyasa yasake niyyar komawa dakinta yaganta,


Kamar amafarki taji bude kofa babu shiri ta hadiye kukanta ta toshe bakinta da hannunta guda daya, fitila ya kunna sannan cikin sassarfa yakarasa gaban gadon da take lullube ta wani tukunkune wuri daya,


"Billy....." Taji yafada cikin son jan magana amma sai tayi shiru kamar mai bacci,


"Billy tashi kiji.....kinji"


Nan dinma shiru tayi masa tana shasshekar kuka azuciyarta,


"Wai kina nufin kema kinyi bacci? Ok shikenan good night.....have a nice sweet dream"


Daga haka yajuya yaje ya kashe mata wutar yafita bayan yarufe mata kofa. Yana fita ta cigaba da shasshekar kukanta,kusan daren gaba daya bata samu runtsawa ba har saida asubah takawo jiki lokacinne bacci yasamu nasarar yin gaba da ita, su fahad kuwa tunda yabar dakin Bilkisu yana zuwa ya kwanta kusa da husnah babu jimawa yabi sahunta wurin yin bacci saboda tsabar gajiyar dake tattare dashi sallar asubah makara yayi dan sai wurin 6 sannan ya tashi, yana yin salla yasake kwanciya daidai lokacin ita kuma husnah ta tashi, wanka tayi ta caba ado ta sake kwanciya gefen fahad tana kallonsa yana ta sharar bacci hannunsa kan cikinsa, hamdala ta shiga yi ga ubangijin rahma dan ko yanzu ta mutu tasan Allah ya cika mata burinta, kasancewar jiya da yunwa ta kwana yasata jin cikinta yafara kiran ciroma babu shiri ta tashi tajanyo ledar da fahad yazo da ita adaren jiya, kaji guda biyune aciki amma yaci rabin guda daya sai fresh milk kwali biyu, fresh milk din tafara sha sannan taci rabin kazar da ya ajiye, rasa abinda zatayi tayi gashi takasa komawa bacci kuma lokacin karfe bakwai da wasu mintuna wadanda bazasu gaza biyar ba, tana nan kwance tana kallonsa har shima yafarka hada ido sukayi tayi masa gwalo, hannu ya mika mata amma sai ta gagara kama nashi saboda yau jinta take awani takure duk da ba yau tafara kama hannunshi ba amma dai na yau ya banbanta da na kullum, jikinsa ya matso da ita yana tsokanarta da idanuwanshi,


"Kin ci abinci?" Ya tambayeta ahankali, daga kai tayi sannan tace "ehh"


"Husnah kenan wai duk kinyi laushi why? Dan Allah kidaina tsorona,bari ma ki gani wanka zanyi infita..." Daga haka yatashi yawuce toilet kafin yafito ta dan gyaggyara dakin duk da babu wani datti da yayi sai dai dan abinda ba arasaba. Falo ta dan leka tana sa ran ko zata ga matar gidan amma shiru babu motsin kowa, kafin takoma daki fahad yashirya saima da ta daidaci cewar ya shirya sannan tashiga dakin, yana tsaye gaban mirror dinta yana karya hularshi da zai saka,


"Ya fahad ina kwana?" Tafada tana murmushi sannan tana kallonsa,


"Lafiya lau husnatah, ya bakunta?"


Dariya tayi tazauna agefen gadon tana kallonsa ta cikin mirror shima kallonta yayi yasakar mata murmushi sannan yajiyo,


"Bari induba hajjaju ko ta tashi..." Kai ta daga masa hakan yabashi damar wucewa yafita, dakin Bilkisu yabude yashiga da sallama akan labbansa, tana zaune gefen gado tana shafa mai da alama daga wanka tafito sai dai fuskarta duk a dan kumbure,


"Ashe kin tashi? Yakike?", dan tsuke fuskarta tayi saboda tasan rainin wayon nashi yazo yimata inbanda haka menene nashi na wani cemata yatake, jin bata tanka masa ba kuma taki kallonshi yasashi dan matsawa gab da ita,


"Billy yakika tashi...?"


Sam kin yarda ta kalleshi tayi saboda bata son yaga yanayin da idanuwanta ke ciki, har yagama neman maganarshi yafita bata tanka ba kuma bata kalleshi ba, wurin husnah yakoma yayi mata sallama yafita. Fitarshi babu jimawa su Anty Fauziyya sukazo da sauran yan uwan husnah wadanda suka kwana agidansu fahad, food flask din da aka zubowa kowa breakfast dinshi daban, anty asabe ce tashiga wurin Bilkisu takai mata nata, basu dade agidanba suka tafi sai lokacin da zasu tafi sannan Bilkisu tafito ta rakasu bakin kofa sannan takoma ciki tayi kwanciyarta, haka tawuni adaki a kwance dolece kawai take tadata ango kuwa bashi yadawo gidanba sai dare saboda anata baki yan uwa da abokan arziki duk wanda yaje gidan ya Abba to gidan fahad zai zarto shiyasa husnah yau tasha baki har ta godewa Allah amma fa Sam bata ga bilkisu ba hakan yasa mata tunani aranta na anya kuwa ko lafiya?.


Lokacin da yadawo dakin Bilkisu yashiga har lokacin tana kwance bakinta akekashe alamun bata ci komaiba, zama yayi saman bedside drewar yana kallonta,


"Kinci abinci ne?" Wani kallo tajuya tayi masa sannan takawar da kanta duk sai yaga tayi masa wani iri kamar marar lafiya,


"Dan Allah kici abinci rabin raina..." Yafada yana dariya shiru tayi masa, tashi yayi yafita yana fita taja dan siririn tsaki tagyara kwanciyarta, shi kam yana can suna zuba love da husnah dan yana kwance dare dare akan kafafunta tana bashi labarin irin bakin da tasha yau, daga nan bai sake fitaba sai dai idan salla zaije, ana yin sallar ishah kuwa yarufe gida yashiga gida yana tunanin ya kamata ya hada husnah da Bilkisu inyaso ko gaisawace suyi, yana shiga dakin husnah yaga tasha wata kwalliyar kamar bata kwanciya bacci ba, saida suka gama hira suka ci abinci yayi shirin bacci sannan yashiga dakin Bilkisu, itama tuni tayi shirin baccin tana zaune tsakiyar gadonta tana cin abincin da aka kawo musu daga gidansu fahad,


"Billy husnah zata zo ta gaisheki..." 


"Ina ciwo ne?" Ta tambaya batare da ta kalleshi ba,


"A'a" yabata amsa,


"To bana bukata, ko zamana takeyi agidan?


"Allah yabaki hakuri, inzo muci abincin?"


Nan kuma bata tankaba saboda taga nema yake ya maidata wata bi ta nan, yana fita ta tashi tamayar da kofarta ta kulle, daren yau dai babu laifi ta dan samu damar yin bacci da wuri saboda jiya batayi ba yayinda ango da amarya ke can suna debewa junansu kewa danma dai har yanzu amaryar bata samu tsarki ba amma duk da haka an aikata abinda ba arasa ba, fahad baiyi bacci da wuriba yanata tunani wato dan adam yana nashi ne Allah na nasa, shi ko acikin mafarki bai taba zaton cewa zaiyi tarayya da wata mace koma bayan Bilkisu ba ashe husnah matarsa ce bai saniba sai yanzu. Washe garima haka Bilkisu tawuni curr adaki abinci kuma daga gidansu fahad ake kawowa, gaba daya zaman gidan ya isheta ya gundireta yakuma gama fita akanta, saida husnah tayi kwana uku gidan sannan suka hadu, ita Bilkisu tafito ita kuma husnah na zaune falo da waya a hannunta tana yin game, sama sama suka gaisa Bilkisu tawuce kitchen tayi abinda zatayi tafito, daren ranar fahad ya sameta da maganar girki domin yakamata husnah tafara girkinta adaina kawo musu daga gidansu fahad acewarta shine yake tambayar Bilkisu ya abin zai kasance,


"Ni zan dafawa matarka abincin da zata ci? Tabdijam to wallahi bazai yuyu ba, kowa yayi girkinsa final.... "


Shifa yagama lura da Bilkisu yanzu akusa take abu kadan ke bata mata rai tayita surfa masifa, baice komai ba yabar maganar sai da yakai 12 adakinta suna zaman kurame sannan yatashi yakoma dakin husnah,washe gari tunda sassafe Bilkisu ta tashi ta shirya saboda ankirata awaya wai Hindu ta haihu ansamu mace amma suna asibiti saboda yarinyar ba lafiya ansakata cikin kwalba, ganin shiru ango bai fitoba yasata kiranshi awaya amma wayar akashe, tsaki taja ta dauki handbag dinta tafita falo daidai lokacin shikuma yafito daga dakin husnah,


"Ya naganki haka? Lafiya?"


Batare da ta kalleshi ba tace,


"Asibiti zanje Hindu ce ta haihu"


"Masha Allah, Allah yaraya.... Zan kaiki ne?"


"A'a kayi zamanka zan hau napep" tafada ciki ciki saboda harga Allah haushin fahad takeji irin karshen nan,


Adawo lafiya yayi mata bata kulaba tafice bayan ta rufe dakinta,husnah dake tsaye bakin kofa duk abinda yafaru tana ji, komawa dakin husnah yayi nan suka bude babin soyayya wato ansamu dama tunda Bilkisu bata nan shine yau ake baja kolin soyayya. Tunda Bilkisu tabar gidan bata dawo ba sai dare saboda a asibitin suka wuni gaba dayansu,lokacin da tashigo gidan suna falo zaune suna kallo yayi pillow da cinyar husnah amma ganin Bilkisu sai yatashi zaune suna yimata sannu da zuwa ciki ciki ta amsa daga haka tawuce bedroom nan yatashi yabita ciki, bata kalleshi ba ta shiga rage kayan jikinta tana amsa masa tambayar da yake yimata wai ya tabaro masu jiki? Toilet tawuce taje tayi wanka tazo ta kwanta kasancewar tayi zirga zirga yau babu bata lokaci bacci ya dauketa bata ma san lokacin da fahad yazo yimata saida safe ba. Tun daga ranar bata wuni agida acan asibiti take wuni tun safe idan tatafi sai dare,ranar da kwanakin da zaiyi adakin husnah suka kare zai koma dakin bilkisu yaga ikon Allah kasancewar yajima adakin husnah bai fito ba lokacin da yashiga dakin Bilkisu wata uwar harara tarinka zuga masa shi dai baice komai ba katifa ma ya shinfida akasa bai nemi hawa gadonba duk da yasan idan yayi niyya bata isa hanashi ba, bedsheet yaciro sabo daga cikin kayanta nan ta harareshi,


"Malam ajiye min kayana.... Ita matar taka bata baka nataba?"


Ajiye mata yayi yafita zuwa dakin husnah mintuna kadan sai gashi yadawo dauke da Sabon bedsheet harda bargo hakanne yasake kular da ita shiyasa bacci sai sama sama tayi abinda bata saniba shine shi har lokacin ma babu abinda yashiga tsakaninsa da husnah saboda tun ranar da aka kawota acikin period take kuma irin matannan ne masu yawan kwanaki gashi dadin dadawa baya son mai afkuwa ta afku Bilkisu tana nan yafi son sai bata nan sai ya sha angoncinsa hankali kwance, wannan dalilinne yasa lokacin da tace masa agidan Hindu zata kwana ana igobe suna bai hanaba saboda daren ranar ango yake,Bilkisu kam ana can gidan mai jego anata shirye shiryen suna tama manta da rayuwar wata aba wai ita husnah amma abinda yake daure mata kai shine tana yawaita tunanin fahad haka kawai sai taji  yafado mata arai. Kamar yadda ya tsara adaren ranar yasamu kasancewa da husna, duk da ta nuna jarumta da daurewa amma hakan bai hanata jigatuwa shiyasa kwana tayi tana yimasa raki abangarensa shikam ya godewa Allah sannan yasake bawa husnah wani gurbi mai girma acikin zuciyarsa saboda yasameta cikskkiyar budurwa wacce kowanne da namiji ke fatan samu. Da safe suna kwance tayi pillow da kirjinsa sai faman rarrashinta yaketa yi yana lallabata yaji kiran Bilkisu yasan maganar dinkice wadda yayi mata wannan dinma da fada da masifa tayarda zaiyi mata amma da wai shagon wasu zata kai ayi mata tareda su maama shikuma yace bai san maganarba idan bazata bari ya dinka mata ba sai dai ta hakura da dinkin gaba daya, ganin yakafe yasata bashi atamfa guda daya daga cikin lefenta shine ya dinka, daga wayar yayi idanuwanshi alumshe,


"Bilkisu... Ya akayi?"


Tun daga yanayin da taji yayi magana tagane akwai abinda suke yi, tsaki taja acikin zuciyarta tana cewa "kwa karaci iskancinku dama ai ba yau aka faraba"


"Ranki yadade ke nake sauraro....."


"Baka yimin dinkin bane?"


"Nayi mana, inkawo miki?"


"Idan baka kawo minba to da waye zai kawo?"


"Yi hakuri bari inkawo miki yanzu" yafada cikin sanyin murya sakamakon jin husna tana tsokanoshi, katse wayar Bilkisu tayi tana tsaki, kallon husnah fahad yayi sannan yashafa kanta,


"Bari naje na kaiwa antynki dinkinta da nayi mata..."


Makale kafada tayi,


"Ni kadai kuma zaka bari?"


Mikewa tsaye yayi yana cewa,


"To ko zaki rakani mu tafi tare?"


Daga masa kai tayi tana bata fuska,


"Sorry yanzu zan dawo.....ai bazaki iya fitaba... Keda naga kina tafiya irin ta yan kaciya..." Yafada cikin sigar tsokana, turo masa baki tayi tahau tirje tirjen kafafu akan gadon, kayan jikinsa yasauya daga na shan iska zuwa jeans da t shirt ta polo yadauki p cap yaje gabanta yayi mata kiss sannan yafita, tashi tayi tabi bayansa har zuwa tsakar gida yadauki machine dinsa yafita, saida taga tafiyarsa sannan takoma gida. Lokacin da yaje kofar gidan Hindu Bilkisu nacan suna aikin abincin suna sunata kukkulla alale da dafe dafen abinci,daga ita sai t shirt da bakar skirt ta fita ta yafa mayafi, yana zaune saman roba roba dinsa yabasar, daga nesa lokacin da take fitowa yake kallonta duk sai yaga tadawo masa wata yar yarinya da ita tayi karama, koda ta karaso kasa kallonta yayi saboda gani yake kamar zata fahimci abinda yafaru acikin idanuwanshi, kasa yarinka yi da idanuwanshi har yabata sakon yatafi bai yarda sun hada idoba,sai bayan da yatafi ma sannan yatuna bai tambayi Bilkisu sunan jaririyar ba, nan yakirata awaya amma har tayi tagama bata daukaba yasan tana can tana cikin aiki sai dai fa sosai yau dinnan tayi masa kyau kawai bai furta mata bane, lokacin da yakoma gida cigaba sukayi daga inda suka tsaya shida husnah sunsha amarcinsu sosai kafin Bilkisu tadawo dan sai washe gari tadawo bayan sun gama komai na soye soye da gyare gyaren gida, tunda ta dawo kuma sai fahad ya daukewa husnah diff sam baya yarda suyi wani abu na wasa ko raha afalo sai dai idan acikin dakine, haka suketa rabon kwana kowa kwana biyu girki kuma kowa nasa yakeyi sam basu ma cika haduwa ba saboda kafin husnah tatashi dasafe Bilkisu tabar gidan ta tafi aiki idan kuma tadawo husnah bata fitowa tana daki a kunshe indai kaganta tafito to tare da fahad ne. Haka kwanaki suka cigaba da tafiya dan yanzu wasa wasa su husnah zasu kai sati shida da aure, dan fahad har yakoma makaranta amma satinsa daya yadawo gida weekend, ranar asabar da hantsi saiga nusaiba matar ya Abba yakawota dama bata taba zuwa gidanba,Bilkisu na falo tasha riga da wando masu taushi blue colour tana aiki a system dinta gefe daya kuma tana sauraren malam Aminu daurawa cikin shirinsa na tambaya mabudin ilmi, ranar fahad zai bar dakin husnah yakoma nata amma baya nan tun safe yafita shago saboda yataho da dinkuna sosai daga kd, tarba sosai Bilkisu tayiwa nusaiba har husnah tafito suna dan taba hira ita dai bilkisu jine nata saboda bata fiya hayaniya ba ita saima ka zauna da ita awa guda baifi tayi magana sau ukuba zuwa hudu sai dai dasu Hindu da khulsum kawarta tana sakewa sosai tayi hira dasu,wanka ta tashi taje tayi tashirya cikin doguwar gown ta atamfa tafito,tambayar nusaiba tayi me zata dafa mata tace komai ma, kitchen tashiga ta dora girki doya da vegetables sos bayan tagama ta zubo mata takawo mata, zance ta iskesu sunayi wanda ya dangancin kishi sai taji husnah daga ganinta tana cewa,


"Ai kuwa wallahi idan baka rike mijiba wata ce zata shigo ta rikeshi dakyau... Wasu matan akwai sakaci dan watama hatta abin shinfidar miji bata san ta adana ta alkinta ba sai dai idan yanada wata matar tabashi..."


"Ai mata sha'aninmu sai hakuri kishi yayi mana yawa..." Inji nusaiba, ita Bilkisu sarai tasan da ita husnah take sai dai bata da ajin da zata zauna tayi kace nace da ita, ita da wanda ya ajiyeta zatayi, akule tawuni har nusaiba tatafi amma bata tankawa husnah ba, la'asar liss fahad yadawo bata kulashi ba yayi shirinsa yafita ball, da daddare tana shirin bacci sai gashi yashigo tashi tayi tsaye cikin masifa tace,


"Malam bana bukatar wannan bargon da wannan bedsheet din acikin room dina ka fitar min dashi and you better warn your stupid wife wallahi idan tasake attempting yimin bakar magana ko gugar zana sai ranta yabaci saboda ni ba sa'arta bace..."


Tunda yaji haka yasan akwai abinda yafaru ko kuma husnah tafada mata wani abu, fita yayi yamayar dasu blanket din dakin husnah lokacin ma ita tajima da yin bacci, sake komawa yayi dakin Bilkisu yatarar tafito masa da bedsheet da blanket. Zama yayi saman katifar da scissors a hannunshi wanda zai yanka wasu dinkuna,


"Me husnah tayi miki?" Ya tambayeta yana auna atamfar da yaware,


"Meya hana ita baka tambayeta ba?" Tabashi amsa tana kokarin kwanciya,


"Tayi baccine ai..."


"To sai ka bari sai ranar da tatashi saika tambayeta..."


"Allah yabaki hakuri dai zanyi mata magana insha Allah"


Bata cemasa komaiba tayi kwanciyarta tabarshi yana aikin yanka dunkuna, washe gari saida yayiwa husna fada sosai akan koma me tayiwa Bilkisu to kar ta kara aikita irinsa saboda ba mate dinta bace, sannan yace tabata hakuri badan tasoba tabi umarninsa sukaje tabawa Bilkisu hakuri tun daga ranar zamansu yaki dadi saboda husnah gani take kamar fahad yafi son Bilkisu kai kamarma tsoranta yakeyi saboda duk dadin da sukeyi daga Bilkisu tashigo zai daina yauma suna falo suna soyayyarsu yanata goyata amma bilkisu na dawowa daga aiki yadaina da tayi magana sai cewa yayi bata ganin antynta ta dawo ai idan sukayi agabanta gani zatayi kamar sun cimata fuska wannan abu shine yakona mata rai har takasa jurewa saboda ko rikeshi tayi idan Bilkisu na wurin sai ya bata rai ita kuma bayan tadade da fara zargin kamar zamansu akwai wani abu saboda taga duk ranar kwanan Bilkisu da dinkunan da zaiyi yake tafiya dakinta acan zai raba dare yana yankawa amma ita ranar kwananta baya yin abu makamancin wannan. Ita kanta Bilkisu fa kawai tana zaune ne agidan bawai dan tana jin dadin zamanba musamman ma yanzu da taga husnah na neman hanyar da zata rainata tayi mata rashin kunya amma bata shiga shirginta, ranar da fahad zai dawo weekend wato ranar juma'a ranar ne yakama ranar sunan anty Fauziyya yayarsu wacce ta haifi yaronta namiji, su husnah tun safe aka shirya aka tafi sune yan aiki ita kam Bilkisu saida tadawo daga aiki sannan tashirya tatafi dama already tasiyo kayan barkarta. Lokacin da taje su husnah suna dakin mai jego an babbaje itada mutuniyar tata anty juwairiyya wacce ke kara hura mata kai tana zugata tana cewa sai yanzu fahad yayi aure ya auri daidai dashi amma da yawani tashi ya debo yayarsa, ai ko governor yazama itace first lady saboda itace yarinya wacce zasu tsufa tare, zama tayi gefen mai jego wacce keta lale marhabun da ita tare dasu anty asabe da nusaiba matar abba, tana rikeda jaririn anata cika mata gaba da kayan sanyi da abinci,batafi mintuna 20 da zuwaba taji husna na cewa,


"Ni alalen nan ce takasa isata anty juwaira..."


"Amarya ai ke wannan kwadayin mai daliline... Kinada cikakkiyar lafiya"


"Kai anty juwaira nifa ranar girkina ya fahad kwana yake yana yankan dinkuna..."


"Saboda tsabar rashin amfaninki..."


Dukansu da suke cikin dakin dariya sukayi banda Bilkisu wacce tasan da biyu husnah tafadi haka, wato habaici takeyi mata kenan, wai meyasa ita kishiya bata raina abin gori ne? Ta tambayi kanta gaba daya ji tayi gidan sunan ya isheta shiyasa ta yi musu sallama tayi tafiyarta gida, wannan karon bazata fadawa fahad ba amma wallahi takusa nunawa husnah true colour dinta, sai ta nuna mata ita ba sa'arta bace bawai ashekaru kawaiba har awurin mijin ai har gobe tana rikeda tutar soyayyar fahad duk da yayi watsi da ita bawai yana nufin yadaina sonta bane tunda duk lokacin da ranta yabaci agidan nakowa ma sai yabaci. Akule yadawo ya sameta ciki ciki sukayi magana yasake fita, bayan sallar ishah sai gasu tare husnah ya daukota daga gidan sunan dama adakinta yake ranar, bayan kwana biyu yakoma dakin Bilkisu dama akule take dashi saboda gorin da husnah tayi mata na wai kwana yake yi yana yankan dinki adakinta saboda batada amfani, ganin yashigo da atamfa a hannunshi yasata tashi zaune fuskarta adaure,


"Malam yaufa baza kayi min wannan yankan adakina ba... Idan yankan zakayi katafi falo Allah yabamu alkhairi"


Kallonta yayi da mamaki,


"Atamfa guda dayace fa..."


"Ita dinfa, wallahi bazaka yankata adakin nanba, sai dai kakoma can inda kafito kaje kayanka, ko acan din haka kakeyi? Wato saini da aka rainawa wayo ko? To wallahi bazai yuyuba..."


Shi gaba daya yanzu yakasa gane kan Bilkisu kullum awuya take jira kawai take ya tabata suyi rikici duk ta tada masa da hankali shikuma baya son tanka mata saboda husnah yasan tana iya ji ai kuwa kamar yasani dan husnah na labe tana saurarensu,


"Allah yabaki hakuri bari na ajiye"


"A ina? Wallahi kaji narantse atamfar nan bazata kwana cikin dakin nanba mayarta can inda ka dauko...."


Juyawa yayi yafita, husnah najin alamun fitowarshi taruga zuwa dakinta ta kwanta, yana shiga ya jefa atamfar kan akwatunanta yajuya yafita. Zaman dai duk babu dadi gaba daya Bilkisu tasake ramewa duk ta kare atsaye ita wallahi da ace abbanta zai yarda haya zata kama tabar wannan gidan amma tasan ko tafada su Ammah bazasu yarda ba ga yanzu wani sabon iskanci da husnah ta tsira duk ranar girkinta sai ta rinka boye fahad ko Bilkisu nason ganinshi indai yana bacci bazata tasoshi ba sai tace wai dan tsabar rashin tausayi baza abar mutum yahuta ba yaje shago yadawo, shiyasa duk abun yafita ran Bilkisu ko zaman falo bata cika yiba dama kallo ke zaunar da ita da taga abin da rainin hankali sai tasa aka siyo mata babbar plasma sabuwa da receiver da komai aka kafa mata acikin bedroom dinta bayan ta falonta amma fa kallo daya zaka yimata kagane takasa da akiba. Sauki daya yanzu suka samu dukansu basa zama agida saboda husnah takoma makaranta ammafa kusan kullum sai sunzo da kawayenta su Fa'iza suna yadarwa Bilkisu magana sai dai bata fiya jinsuba saboda idan acikin bedroom take zaka isketa ta kunna tv shiyasa bata fiya jiyo hayaniyar da take gudana afalo ba kuma abinda ta lura duk ranar da fahad ke gari husnah bata wannan iskancin bata kawo kowa amma idan baya nan to kullum tare da friends dinta suke zuwa har magrib suna tare, yau ita Bilkisu tana gida bata fita aikiba saboda ciwon mara take yi kamar me kusan tun lokacin da ta fara period bata taba ciwon Mara mai azabar wannan ba shiyasa ko fita batayi ba, saida taji ya lafa mata sannan ta shiga kitchen zata dafa ruwan zafi tana sanye da doguwar riga marar nauyi da hula baka, tana kitchen su husnah suka shigo su uku tana ji husnah na cemusu wai su shiga kitchen su dafa musu abinda suke so, ganin Bilkisu na ciki sai suka fara rashin mutuncin nasu, 


"Kawata ya babynmu? Meyake so ne?" Inji fa'iza,


"Ai wai dama kawarmu har mun samu karuwa?" Inji Ruky,


"Tun wanne zamani? Ai ni ba juya bace wallahi kuma sannan matar so ce shiyasa cikin kankanin lokaci aka dirka min ciki, yanzu inajin yayi 2 months da yan kwanaki...."


"Ai wasu ba juya bane kawai duniyancine ke hanasu haihuwa..." Ruky tafada tana dariya, Bilkisu na jinsu tana kokarin juye ruwan zafinta,


"Ehh mana ai dama wasu ba wucema shekarun haihuwar sukayiba kawai tsabar iskancin da suka shuka ne awaje suka yita shan pills suna abortion da haka suka kashe mahaifar...." Husnah tafada tana dariya harda shewa, kashe gas dinta tayi ta dauki tea flask dinta tafita, aganinta rashin class da rashin tunanine zai sata tanka musu saboda yaran da basufi meenah ba karamar kanwarta akanme zata tsaya tayi kace nace dasu? Tana shiga daki tazauna tarasa abinda keyi mata dadi kawai sai tafara kuka kukanne yasaukar mata da zazzabi mai zafi dama gashi bata jin dadin jikinta agaskiya tagaji da wannan rainin wayon dan haka barin gidan fahad zatayi inyaso yazauna da husnan, text ta tura masa cewar ita gida zata tafi, tunda yaga text dinta yasan ba lafiyaba duk da shima din tsakaninsu akwai rashin jituwa amma ai lafiya suka rabu yasan may be itada husnah ne, tun kafin tafada masa abinda yafaru yaji ransa yabaci, aranar yabaro kaduna yadawo gida bayan sallar magrib sai gashi, kowacce na dakinta,dakin Bilkisu yashiga ya sameta zaune tsaf cikin shirinta dama shi take jira tasan yana hanyar zuwa,idanuwanta kadai yakalla yasan tasha kuka,


"Bilkisu meya faru?"


"Kasan me? Nagaji da zama da matarka, kawai ni ka sawwake min inbar mata gidan, ni sa'arta ce da zata rinka kawo kawayenta suna haduwa su zageni? Ni nataba yimata haka? Yarinyar nan yau harda suce waini juyace,kuma wai....." Wani kukan tasake fashewa dashi cikin sauri yazauna kusa da ita ya kwantar da ita kan kirjinsa akaro nafarko,


"Am sorry.... Stop shading your tears... Fada min abinda yafaru wai me?"


Kasa magana tayi sai sautin kukanta dake tashi cikin dakin har lokacin tana rungume ajikinsa yana shafar gadon bayanta, saida yabatar tagama kukan ta dan tsagaita sannan yayi magana,


"Me tace miki bayan haka?"


"Cewa fa sukayi wai saida nagama yawon iskancina nasha pills da abortion sannan na aureka shiyasa wai har yanzu ban haihuba..."


 Ji yayi ranshi yabaci sosai kwata kwata bai taba zaton husnah zatayi masa hakaba, sakinta taji yayi ahankali sannan yamike yafita......




Yau banyi editing ba kuyi hakuri da spelling mistakes


*_Ummi Shatu_*    



*Littafina na kudine me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*




51***Amutukar fusace yashiga dakin husnah, ransa idan yayi dubu to ya baci yau, tana kwance rub da ciki da waya a hannunta tana rubuta assignment, figota yayi ya finciko ta, atsorace tabishi yana rike da ita yana janta har dakin Bilkisu wacce ke zaune har lokacin bata daina kukaba, jin tahowarsu tareda husnah yasata saurin hadiye kukanta ta goge fuskarta, banko kofar fahad yayi yatura husnah yana huci,


"Husnah.... Maimaita abinda kuka fada mata keda kawayenki...."


Zaro ido husnah tayi kafin ta dora hannu aka,


"Nashiga uku ni asma'u...

Anty me mukace miki? Nida wa? Ni yau ma da babu inda naje shine zakiyi min karya ki hada min sharri....." Tun kafin ta rufe bakinta taji wani wawan mari wanda ko tantama batayi fahad ne ya dauketa dashi dan ransa yakai makura wurin baci gaba daya idanuwansa sun juye daga farare zuwa jajaye,


"Waye yake yimiki karyar? Sa'arkice ita? Kifada min abinda yafaru ko inyi ball dake....."


"Ni wallahi karya take yimin... Karya ne.... Bance mata komai ba amma dan tsabar munafurci shine zata hadani dakai saboda tana bakin cikin muna zama lafiya... Wallahi karya tak...."


"Idan kika kara cewa karya take yimiki wallahi sai na fasa miki baki... Dama bakida mutunci ban saniba? Matar tawa zaki saka agaba kirinka zagi? Sa'arki ce? Ni kin taba ganin na zageta? Zaki fada min abinda yafaru ko sai nayi wasan kura dake?...... Ki fada min inda kika ganta tana zubar da ciki ko tana shan pills kamar yadda kuka ce....."


Ganin yayi kan husnah gadan gadan yasa Bilkisu saurin mikewa ta tashi tasha gabanshi, kokarin tureta yayi yana cewa,


"Asma'u baza kiyi min bayanin abinda kukayi ba sai na hau ruwan cikinki?.... Bari na kamaki"


Rikeshi gamm Bilkisu tayi ta kalleshi da idanuwanta wadanda ke jajur, sannan ta kalli husnah,


"Zo ki fice.... Fitar min adaki..."


Sim sim husnah tawuce tana harare harare, duk fahad yana kallonta lallai yarinyar nan munafuka ce wato saima ta nuna ita sam batayi hakaba sharri akayi mata shifa yatsani zama da mutum munafiki wanda baya kaunar zaman lafiya, har husnah tafice Bilkisu na rike dashi, hannuwanshi duka biyu ta kama tasaka cikin nata,


"Kai kuma ai bahaka akeyi ba.... Meyasa zaka kawota gabana har karinka marinta kana neman dukanta akaina....., bazata ji dadiba, gara ka tambayeta kaida ita idanma fadan ne sai kayi mata daga kai sai ita amma idan ka kawota gabana kayi mata fada ai tamkar kayi mata cin fuska ne......"


Kallonta yayi da idanuwanshi wadanda ke cikeda bacin rai shi yasan ba abanza yake kaunar Bilkisu ba, tanada sanyin hali da farar zuciya sam bata da mummunan nufi akan kowa,


"Kiyi hakuri kinji....insha Allah zanyi maganin abun..."


"Na hakura amma gaskiya gida zan tafi.... Gidannan yayi mana kadan mu biyu, matarka bata san ganina haushina takeji, nima kuma haushinta nakeji kaga zama wuri daya bazai yuyu ba... Ni kawai duk ranar da kasamu damar canja min gida sai indawo amma yanzu gida zan tafi...."


Murmushi yayi yajata bakin gado ta zauna shikuma ya tsugunna agabanta yana kallonta,


"Kawai sai kitafi gida kije kice musu kin kasa kishi da yar karamar kanwarki akanta kika dawo gida?"


"Ni ba akanta bane, fitinace bana so.... Kana jin fa abinda suka fada min wai ni yar iskace...."


"Kibar maganar nan pls.... Nidai ai nine na aureki ko? To ban zargeki da hakaba dan haka duk wanda ma zaice kinyi haka kar abin ya dameki tunda ni mijinki ban zargi haka daga gareki ba.......ni nasan atsaftace kike soo don't worry about that...."


Shiru tayi batace komai ba har lokacin idonta bai bar fitar da kwalla ba saboda ba ataba jifanta da wata muguwar magana makamanciyar wannan ba,


"Ina zuwa...." Ganin yamike yasata rikoshi,


"Fahad karfa kace zaka daki yar mutane.... Babu kyau duka...."


"Ni ba dukanta zanyi ba, ina zuwa..."


Dakin husnah yakoma wacce itama sai yanzun takoma bayan tagama jin duk abubuwan da suka fada shida Bilkisu, zama yayi agefen gadonta ita kuma tana tsaye atakure duk atsorace take dashi dan bata taba sanin cewa yanada zuciya har hakaba,


"Husnah abinda kikayi kin kyauta kenan? Meyasa zaki fada mata haka? Kin san zunubin dake cikin wannan maganar kuwa? Ko court fa takaiki za a iya yimiki bulala saboda kazafi kika yimata......."


"Dama ai ita kafi so shiyasa kullum abayanta kake, baka son laifinta...."


"Husnah ba maganar ita nafi so bane... Maganace ta gaskiya.... Bilkisu ba sa'arki bace bai kamata kizo ki rinka fada mata magana irin hakaba..."


"Gaskiya ya fahad wallahi kaima tagama dakai inbanda haka ya daga fada maka magana zaka hau kai ka zauna batare da kayi bincike ba? Ni kasan abinda ta fada min?"


Mikewa yayi cikin fushi,


"Karya kikeyi babu abinda ta fada miki.... Kin san wani abu husnah? Wallahi zan yi mugun bata miki rai akan wannan maganar, matsawar kina son mu shirya to yazama wajibi ki iya bakinki bana son rashin kunya kuma bazan taba lamunta ki raina min mataba saboda ai ko bata girmeki ahaifeba ta rigaki zuwa gidan nan anan kika tarar da ita, ita bata takura miki ta hanaki kwanciyar hankali ba sai kece zaki takura mata? Da lokacin da zan auroki ta tada fitina tanuna bata yarda ba kina tunanin zan aureki ne?, wallahi tun wuri ki shiga hankalinki......"


"Amma dai ya fahad ai....."


"Will you shut up ko sai na bigeki.... Ban san bakida kunyaba ai sai yau... Mun kusa fara fada dake asma'u"


Mikewa yayi cikeda fushi sai kuma taga yakoma ya zauna hannunshi kan kirjinshi, babu shiri yazame ya kwanta kan gadon kafafuwanshi akasa hannunshi dafe da chest dinshi, lumshe idanuwa yayi yana jin bugun zuciyarshi yana fita ahankali ba normal ba, tsugunnawa husna tayi gabanshi ta dafa shi,


"Sannu ya fahad.... Dan Allah kayi hakuri.... Yau kasha maganinka?"


Kai ya daga mata hakan yasata sake matsawa kusa dashi,


"Ka kara wani pls..."


"Nabarshi a kaduna..."


"A'a akwai wani anan... In dauko maka?"


"Kar yazama over dose husnah kinga dazu nasha wani..."


"No bazai zamaba, dan Allah kasha magani"


Tashi tayi ta dauko masa harda ruwa yasha yasake kwanciya babu jimawa bacci yayi gaba dashi, ita wallahi tana son fahad har cikin ranta amma ta tsani bilkisun nan bata kaunarta ko kadan gashi shikuma taga kamar yafi sonta. Bilkisu na dakinta bata sanma abinda ke faruwa ba tadai ga shiru bai dawoba, tunani tayi abinda fahad fa yafada gaskiyane idan taje gida me zata cewa su ammah? Tunda ita dai bada fahad sukayi fada ba tasan su abba bazasu barta ta zauna ba ai jarabar iyallo ma kadai ta isheta tunda kullum tana hanyar zuwa gidan dan bata cikakken sati biyu bata zoba, tashi tayi ta maida kayanta ta ajiye ta hada tea din da tun rana tayi niyyar sha amma yaran nan suka bata mata budget, yau kwata kwata babu abinda tasaka acikinta tun safe, zama tayi tasha tea din sannan tashiga wanka. Abangaren fahad kam yana can yanata bacci dan ko sallar ishah baiyiba har yanzu yanata bacci har 11 sannan yatashi husnah na zaune kasa ta kifa kanta saman gado itama anan baccin yayi gaba da ita, tashi yayi duk jikinsa babu kwari,tashin husnah yayi tana tashi ta tsaya tana kallonsa,


"Tashi ki hau kan gado ki kwanta..."


Tashi tayi tahau kan gadon shikuma yamike saboda baiyi sallar ishah ba gashi ma yunwa yakeji,


"Kinyi sallah?"


Daga masa kai tayi hakan yasashi fita daga cikin dakin yana zaro wayarshi daga aljihunsa, dakin Bilkisu yashiga ga mamakinsa idonta biyu tadai yi shirin bacci da laptop kusa da ita tana rikeda cup din tea,kunnenta ta makala earpiece tana sauraron kundin tarihi na Malam Aminu Ibrahim daurawa, daga kai tayi ta kalleshi dama dogoyen kayane jikinsa riga da wando na wa gambari kalar ruwan toka,zama yayi gefenta ya zare earpiece din guda daya yasa a kunnenshi,


"Me kikeji?.... Kekuma kina son wannan malamin naga alama...."


"Yana fadar abubuwa masu amfanine sosai shiyasa...."


"Hakane.... Bacci fa nayi sai yanzu natashi saboda dazun nan bana jin dadine"


"Sorry..."


"Gashi yunwa nakeji.... Kinada abinci?"


"Ni banyi girkiba.... Zakasha tea?"


"Sai insha din ya na iya...."


Tashi tayi tasauka daga kan gadon tatafi zuwa wurin wani dan karamin show glass wanda kayan tea dinta ke ciki tun lokacin da suka hada kitchen da falo da husna ta kwashe kayan tea dinta tadawo dasu cikin daki,shikam fahad tunda tace masa yau batayi girkiba yasan abin yazo domin har yaganeta idan tana period wuni zatayi shan tea, tea ta hado masa lafiyayye harda bread ta kawo masa yana zaune yana kallonta, rigar baccinta bamai nauyi bace kuma ba mai shara shara bace iyakarta gwiwarta da hular bacci akanta, karbar tea din yayi yace,


"Thanks..." 


Daga haka yafara sha ita kuma ta koma saman gado taci gaba da aikinta har yagama yawuce bathroom dinta yayi alwala yafito, rug din sallarta ya dauka ya dan kalleta,


"Zo muyi sallar ishah naga kema kamar bakiyi ba...."


Tasan halin nasa zai fara shiyasa tace masa,


"Ni ai tawa tariga taka zuwa..."


"Seriously?" Yafada yana murmushi, batayi magana ba tadai jijjiga kai hakan yasashi shimfida abin sallar yayi, kafin ya idar har ta kashe system din da wayarta ta kwanta, sallama yayi mata yafita bayan ya idar saboda adakin husnah yake kasancewar wancan zuwan adakin bilkisu yabar gari. Washe gari da safe husnah agaba tasashi tana bashi hakuri amma yace shi bashi zata bawa hakuri ba Bilkisu yake so taje tabawa hakuri, tashi tayi tafita nan yayi hanzarin bin bayanta saboda gudun samun matsala, Bilkisu na gaban drewar tana fito da kayan da zata saka daga ita sai daurin kirji dayake daga wanka tafito,bude kofa husnah tayi tashiga,


"Anty kiyi hakuri akan abinda yafaru..."


Juyowa Bilkisu tayi tai mata wani kallo sannan tace,


"Pls walk out from my room... I said get out..." Daidai lokacin fahad yashigo,


"Kiyi hakuri..." Inji husnah,


"Yawuce but kifitar min adaki pls..."


Juyawa husnah tayi tafita shikuma fahad yamaida kofar yakaraso ciki, karasa fitar da kayan da zatayi tajuyo ta kalleshi,


"Kai kuma fa? Me kake bukata?"


Girgiza kai yayi, "nothing"


"Ok bani wuri inshirya to..."


Kada kai yayi yafita, shifa yagane Bilkisu son girmanta ajininta yake wallahi, afalo yazauna ya kwanta yana danna wayarshi dan yaji motsin husnah acikin kitchen tana aiki, yana nan kwance Bilkisu tafito cikin shirinta na fita aiki, yau komai nata brown tasaka, kallonta yayi cikeda sha'awa,


"Kinyi kyau..."


Jin motsin husnah a kitchen yasata cewa,


"Thank u my dear..."


"Adawo lafiya but kamar bakiyi breakfast ba..."


"Bana jin yunwa karka damu, idan naje office zan karasa gida"


"Adawo lafiya" yafada yana kara kwanciya, duk abinda sukeyi husnah na labe tana jinsu akofar kitchen, kwafa tayi da karfi amma shi fahad bai jiyoba Bilkisu ita kuma tafita, husnah ita kadai tasan abinda zata shirya musu saboda taga fahad yama rainata akan matarsa harda marinta? Wallahi saita rama ta wata hanyar. Kamar yadda ta fadawa fahad yau gidansu takarasa wuni sai da magriba takoma gida,daren ranar ma adakin husnah ya kwana washe gari kuma zai dawo dakinta, ranar da yadawo dakinta tunda safe garin kano yake daure da wani matsanancin zafi kowa kagani rike yake da abin fifita masu kankara da ruwan sanyi kuwa kasuwarsu ce tabude ranar saboda kowa abu mai sanyi yake bukata, karfe 3 tadawo daga office saboda yunwa gashi ita har gobe takasa sabawa da cin abinci a office sam bata iyawa, tuwon shinkafa ta tuka miyar busasshiyar kubewa da kifi, sannan ta tafasa magarya wannan dabi'artane tun tana gida abubuwan nan guda biyu duk lokacin da tagama period tana amfani dasu almiski da magarya saboda tasan yau zata samu tsarki, dama bata wuce kwana biyar ata dade tayi shida. Bayan magrib tasamu tsarki tana yin sallar magriba fahad yadawo daga filin kwallo wanka yayi ya dauki mattress yafita tsakar gida yayi shimfida saboda zafi, Bilkisu na daki bata fitoba tana dai jiyo yar hirar da sukeyi shida husnah tana cemasa ita karatun nan yafi wanda tayi da wahala saboda tulin sunayen magungunan da suke haddacewa sannan sai sun haddace class din da yake da group dinshi da dossage dinshi na manya da na yara, dariya taji yana yi yanace mata ai dama kowanne karatu akwai irin tashi wahalar domin shima hakan take yanzu wata wahala karatunsu ke zubawa saboda yakusa zuwa karshe, ita dai bilkisu tana jinsu ne kawai batada niyyar shiga shirginsu koda akusa dasu ma take bare tana nesa, tunani itama tafara yi da tunifa itama tazama nurse ko Dr dan har tasamu admission a school of nursing amma taki yi tace mass com takeso saboda shi take sha'awa tun tana karama.


K'arfe 9 saura taji su husna shiru da alama sun bar waje sun dawo ciki amma kuma ai yau fahad adakinta yake, bata kai ga gama tunaninta ba taji yar kara daga waje kuma da alama fahad ne ta zaci abin wasane sai tajiyoshi yana ta salati, atamanin ta sauka tafita daidai lokacin itama husnah tafito rikeda wayarta wadda ta kunna light,


"Kuyi ahankali kar ta harbeku.... Kunama ce..."


Husnah na haskawa kuwa sai ga kunama katuwa irin rikakkiyar nan baka kirin da ita, wata zabura husnah tayi saboda tsoro sai Bilkisu ce ta kashe kunamar cikin rawar jiki, fahad kam na kwance yadafe gefen kanshi inda kunamar ta harbeshi,


"Kira min ya Abba... Yazo muje asibiti"


"Wanne yazo ku tafi asibiti kawai ya siyo maka magani saboda kar abata lokaci...." Bilkisu tafada tana dangwala masa dan yatsanshi ajikin wayar, husnah ta mikawa bayan tayi dialling number din ya Abba, yana dagawa husnah tace zata turo sunayen magani yayi sauri yakawo yanzu kunama ce ta harbi fahad,


Dukansu arikice suke saboda wani irin nishi fahad yakeyi mai wahalar gaske duk yabi yahada gumi sai sannu suke yimasa amma baya iya amsawa. Lokacin da Abba yakawo maganin duk yagama jigata, cikin azama husnah ta karbi maganin dama harda allura tayi gaggawar yimasa sannan suka bashi maganin yasha, alama yayiwa Bilkisu da ta kaishi daki nan ta kamashi akan kafadarta suka shiga ciki kayan shimfidar tashi ma da yayi sai ya abbane yashigar musu dashi falo yatafi ita kuma husnah tabishi tarufe gidan. Sosai Bilkisu tayi nadamar kamo fahad bata bari ya Abba yakamashi ba saboda nauyin da taji yayi mata sosai dakyar ta iya kaishi dakinta suna zuwa bakin gado saboda layin da yaketa yi hajijiya na daukarsa akokarinta na kwantar dashi suka fada saman gadon tare yabita ya rufe, iya yinta tayi amma tagagara tureshi saboda nauyinshi har lokacin garin adaure yake sai dai akwai kamshin ruwa alamun anyi akusa da garin, jin gumin dake fita daga jikinsa tasan yana shan azaba cikin ikon Allah nefa suka kawo wuta nan sanyin iskar fanka tasoma ratsashi yadaina gumin, hannunta ta mika ta warware net din dake jikin gadonta pink colour nan hasken yaragu akansu, ita gaba daya mamaki ya rufeta saboda jin nauyin fahad gaba daya yasakar mata nauyi dakyar take numfashi. Baccine itama ya saceta ahaka, husna daketa kaiwa da kawowa tana dan labewa ko zataji motsinsu tun lokacin da suka shiga daki amma sai taji shiru har 12 takai tana zirga zirgar laben nan idan taji shiru sai taje ta kwanta da anjima sai tasake komawa daga karshe sai gajiya tayi ta kwanta tai bacci. Misalin karfe biyu nadare fahad yafarka, daidai lokacin ansau iska agarin sannan yayyafi yafara sauka amma bamai karfiba, juyawa yayi niyyar yi amma sai yajishi ajikin Bilkisu dafarko yazaci ma husnah ce amma yanayin kamshinsu da ya banbanta yasashi gane Bilkisu ce yana kwance dumu dumu akanta ta zagayeshi da hannuwanta ta rungumeshi tsantsan, yayi pillow da kirjinta, ahankali ya bude idonshi ya kalleta har lokacin kanshi yana dan ciwo kadan kadan,


"Ohh Allah inama yau akwana ana lafta ruwa...." Yafada ahankali kafin yarufe bakinsa ruwan ya dan fara karfi daidai lokacin kuma difff nepa suka dauke wuta, ahankali ya dan raba jikinsa da nata yana sinsinarta daidai lokacin ruwa yasake karfi kamar da bakin kwarya......




*_Ummi Shatu_*    


*Littafina na kudine me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*



52****Cikin bacci yaci gaba da sinsinarta saboda kamshinta is special & different da duk kamshin da yataba ji abaya, duk dauriyarsa na wai yau yabarta kasawa yayi, baima san lokacin da yarabata da rigar baccinta ba, rawar sanyi yaga tafara sakamakon ruwan da ake shekawa bargo yajanyo ya lullubesu sannan yamaida hankali wurin ruda mata jiki da soyayyarsa mai zafi, duk kyankyaminshi amma yau haka yadage yana lasar ko ina na jikinta kamar wani tsohon maye, duk yabi ya rude yarasa ma ta ina zai fara,


Bilkisu kam cikin bacci taji abinda fahad keyi mata harga Allah tazaci cikin mafarki take, sosai itama take mayar masa da martanin abinda yake yimata, tun tana yi cikin bacci har tafarka saboda lamarin ya zarce tunaninta, koda tafara fahimtar abinda ke faruwa taso tayi gardama amma sai ya hanata ta hanyar rufe mata baki ruf da nashi, cikin lokaci kankani ya fitar da ita daga hayyacinta nan yarinka juyata son ranshi, abin yayi mutukar bashi mamaki saboda yanda take rawar jiki kamar yaune tasoma shiga cikin wannan yanayin, duk wani pattern da wani password da yasan idan yasaka mata zata dau charge yasaka mata shiyasa tahau tsuma, ayau yayi alkawarin sai yashayar da ita zumar soyayyarsa sannan sai yasata acikin wata duniya wacce bata taba sanin cewar akwaita ba, hakan kuwa akayi domin Bilkisu kawai dai ayi sha'ani dan hamood mugun cutarta yayi da bai taba attempting bata farin ciki kwatankwacin hakaba saboda shi kansa kawai yasani, duk fahad yabi ya rudata tagama fita hayyacinta,rikeshi tayi kamar zata koma cikinsa lokacin da nutsuwarta zata zo, duk da shima yana cikin wani hali amma saida yayi dariya domin a yar kauye tafito ba yar birni ba awannan fagen,


"Wayaga Ambaliya...." Yafada acikin ranshi, saida yabarta tagama samun nutsuwarta sannan shima yafara kokarin nemo tashi nutsuwar, jikinta gaba daya yagama mutuwa murus babu karfi ko kadan cikin wannan halin taji abinda fahad ke neman aikatawa ita dai yau tasan tafaru takare dan bazata iya hanashi ba yariga da yayi nisa tabar damarta tun da farko saboda tamkar mayunwacin zakin da yayi kwana da kwanaki baici abinci ba haka ya zame mata, tanata kokarin tureshi amma takasa saboda jikinta amace yake, kuka tafara yi aboye saboda bata son yaji yasamu damar rainata amma inaa tun tana na boye harta fara na fili, tana kuka tana magiya amma yau fahad yazama kurma kuma makaho dan baya ji kuma baya gani kawai abinda yayi niyya yabada himma,murya bilkisu ta bude tana tsaga kuka daga baya taji shima yafara tayata, tabbas yau badan ruwan da ake kwararawa da babu abinda zai hana husnah jiyo duk abinda ke faruwa, jin kukan nasu yafara yawa yasashi rufe musu baki tahanyar hade bakinsu wuri guda zuwa wani lokaci yasake budesu suka cigaba da koke kokensu yaufa tunda yasamu dama baiyi wasa da damarsa ba saida ya tabbatar sun zama abu daya, har lokacin kuka takeyi sosai kamar me shima yana tayata, rungumeta yayi sosai har lokacin yana samanta sai sauke numfashi yakeyi kamar me, tureshi tayi cikin kuka tace,


"Ni dagani... Ka dagani..."


Shiru yayi mata har lokacin yana manne da ita bai dagata ba yanata faman ajiye numfashi, saboda yasan idan yatashi sanyin da zata ji ba kadan bane saboda gaba daya windows din dakin abude suke. Yana jinta tanata shasshekar kuka sai jan zuciya take shima haka,gaba daya yarasa ma wanne irin farin ciki zaiyi saboda ayadda yasamu Bilkisu abin yayi mugun gigita tunaninsa kwata kwata baiyi tsammanin cewar zai sameta a matsayin cikakkiyar budurwa ba amma sai gashi ya isketa fiyeda muradinsa,


Harshensa yakai saman wuyanta yana sake lasarsa ta ko ina, tureshi tayi amma ko motsi baiyiba maimakon ma yabari sai yakoma lasar saman kirjinsa,kuka tasake fashewa dashi cikin sauri ya maida bakinsa kan nata dolenta tayi shiru, duk da yariga da ya karbi abinda yajima da tsole masa ido hakan bai sa ya ya kyaleta ba sai neman fitina yake tayi yaki yarabu da ita,kuka kam ta shashi harta godewa Allah saboda ita yanzu babban tashin hankalinta tayadda zata iya kallon fahad da safe, duk sai taji kunya da haushi sun kamata. Suna nan kwance nane da juna har aka fara kiran assalatu sai lokacin ya iya tashi,


"Tashi muje kiyi wanka..." 


Shiru tayi kamar bata ji abinda yaceba, sake maimaitawa yayi amma shiru sai kuka take ta faman yi,


"Am very sorry soulmate wallahi bada niyya hakan tafaru ba.... Tsautsayi ne..."


Kukanta taci gaba dayi tana tattatare gashinta Wanda ya hargitsa mata,


"Yi hakuri ki tashi muje kiyi wanka..."


"Bazanyi ba.... Ni ka kyaleni" tafada cikin kuka,


"Allah yabaki hakuri..." Daga haka yatashi daga kan gadon har lokacin ba adaina ruwa ba windows din dakin yaje ya rurrufe bayan ya dauki wayarta dake saman mirror rufe dakin yayi rikif da cuttens sannan yadauki tea flask dinta wanda ke cikeda ruwan zafi, cikin fada tace,


"Malam ajiye min ruwana...."


"Yi hakuri zan dafa miki wani"


Shiru tayi taci gaba da shasshekar kukanta shikuma yashiga toilet, kai ashe garin dadi na nesa, ashe mata suna suka tara..... Ashe wani kaya sai dai amale, wadannan maganganun sune yaketa fada acikin ranshi, dama yasan za arina saboda bilkisu ta hada duk abubuwan da yake muradi sai gashi yau yasamu dama ya yi son ranshi,


"Allah sarki soulmate na wahalar dake, nakasa controlling kainane shiyasa" yafada cikin zuciyarshi, finally dai yau gashi Bilkisu tazama tashi da wadannan maganganun yayi wanka yafita, yana tsaye gaban wardrobe yana duba kayan da zai saka aka kawo nepa, 


Runtse idanuwa Bilkisu tayi tana hawaye gaskiya sai yau tagane fahad yadade da gama rainata, bata taba sanin shi cikakken marar kunya bane sai yau, tana ganinshi yasaka t shirt da three quarter yafita, kitchen yashiga ya dafa mata ruwan zafi cikin babban flask's sannan yakai mata daki, lokacin har ta dan fara bacci yatasheta, harara ta dalla masa sannan tamaida idanuwanta ta rufe, shi kam bai kwanta ba har saida yayi sallar asubah, ahankali ya kwanta gefenta yana facing dinta kana kallonta kasan ta wahalta, tsura mata ido yayi yana kallonta wani sonta yake ji yana sake shigarshi gaskiya Bilkisu ta cancanci yabata award duba da irin shekarunta amma ta tsaya ta kare mutuncinta, shekara talatin da doriya ai ba wasa bane gashi kuma tana fita aiki tana gwagwarmaya da maza awaje amma duk da haka ta daure,


"Gaskiya ke jaruma ce....." Yafada ahankali yana kai hannunsa kan bargonta da take lullube aciki, kamar marar gaskiya haka ya rinka yi sand'a sand'a har yashige ciki ya matsate sosai suna shakar numfashin juna, hannu yakai kan kirjinta cikin bacci taji ta buge masa hannu, murmushi yayi yaci gaba da kallonta har baccin shima yayi gaba dashi. 


Misalin karfe 7 Bilkisu tafarka bude idanuwanta tayi taga fahad ajikinta ya wani kankameta take daren jiya yafado mata, dama ai yasha fada mata wai duk ranar da yatashi kamata sai ta raina kanta kenan wannan ne dalilinsa na sakar mata karfinsa? Harararshi tayi ta daga hannunta da dan guntun karfin da yarage mata ta turashi, bude ido yayi sannan yamayar ya rufe bayan yamatsa daga jikinta, sai yanzu take nadamar kin bin umarninsa da bata tashi tayi wanka ba tun jiya domin jikinta gaba daya yayi tsami yanzu ko ina ciwo yake yimata bata jin zata ko iya sauka daga kan gadon saboda azaba, rasa ta yadda zata tashi tayi sai ta yunkura saita koma ta kwanta duk yana kallonta,


"In daukeki inkaiki....?" Taji yafada cikin rada,


"Bana so....." Tafada cikin fada,


"To shikenan" yafada yana kunshe dariyarsa, kwanciyarta taci gaba dayi saboda bata san ta yadda zata tashinba, tashi yayi yazo zai dauketa nan tafashe da kuka,


"Kuka dai kuka dai hajjaju.... Dan Allah kirage kukan nan Adda labour"


Ji tayi kamar ta kwadeshi jin ya kirata da Adda, tamkar jaririya haka taga ya dauketa yayi toilet da ita,ruwan zafinta yakoma ya dauko mata bayan ya ajiyeta,


"Ni ka fita.... Zanyi wanka"


Juyawa yayi yafita, jikinta ta samu ta gasa sosai sannan taji dama dama, wanka tayi tafita ahankali tana takawa, fahad dake tsakiyar daki tsaye yana rikeda bedsheet dinta suka hada ido ita yau kunyar duniya ta taru mata aka wai itada fahad ne jiya suka raya sunnah ko amafarki bata taba kawowa haka zata faruba. Zama tayi kan stool tana duba doguwar riga saboda tagaji da tsaiwar,fitowa yayi daga cikin toilet din yana kallonta kasa kasa gaba daya idanuwanta sunyi luhu luhu duk fuskarta ta kode kuma ta kumbura, sai tura baki takeyi tana kunkuni,


"Mugu kawai..... Azzalumi mamugunci kawai.... Kawai dan kaga kafini karfi.... Kazami... Da wani kazamin bakinshi awurin...."


Duk abinda take fada yana jinta amma bai tankaba sai na karshen,yasan dalilinta na fadin haka saboda irin baran baramar da bakin nashi yayi adaren jiya, murmushi yayi sannan yace,


"Ni bakina ba kazami bane tunda ai inda ya taba din mai tsafta ne...."


Shiru tayi masa tazaro doguwar riga mai karamin hannu,


"Bani wuri zan shirya..."


Kan gadonta yaje ya haye yana murmushi wato ita wannan tamanta jiya yagama ganin girman natane gaba daya da zata rinka korarshi? Kwanciya yayi ya dan rufa amma yana kallonta, salla tayi azaune sannan ta tashi bayan ta idar, ita tana yiwa fahad kallon karamin yaro ashe ita yamayar small girl bata saniba, kan gadon taje ta kwanta tana harararsa, kwanciya tayi aranta tana cewa,


"Yanzu dama akan wannan kayan wahalar husnah ke jin haushina? Ni wallahi taje nabar mata.......wannan wahala har ina... Allah sarki su maama ashe yaran nan haka suka sha azaba suda akayi aurensu ma shekarunsu baiyi rabin nawa ba...."


Tunani take tayi aranta har taji muryar fahad yana cewa,


"Thank u soulmate and am very sorry, it was a mistake...."


Bude idanuwanta tayi amma takasa kallonshi, kawai saita juya masa baya ta fashe da kuka,


"Meye kuma abin kuka? Am sorry, inkira husnah ta dubaki?"


Ai tana jin haka tajuyo afusace tana harararsa,


"Sai dai uwar...." Shiru tayi bata karasa ba amma yasha harara fa,bayanta yamatsa ya kankameta yana shakar kamshin da gashin kanta keyi, turewar duniya tayi masa amma takasa dolenta ahaka bacci yayi gaba dasu gaba daya, duk haushinsa takeji fitinanne kawai saboda yadda yake shafa mata kirji acikin bacci bayan kuma babu abinda tasawa kirjin nata, daga daren jiya zuwa yau ta fahimci  yana son wasa da kirjinta abu kadan sai yakai hannu, ita dai bacci rabi da rabi tayi saboda fitinarsa, wurin 10 suka tashi har lokacin ana yayyafi ruwan da aka kwana anayi bai gama daukewa ba, wanka yashiga yayi yafito yatsaya gaban mirror yana shiryawa daga shi sai dan guntun pant na maza bai kai ko rabin cinyarsa ba, tana lura dashi sai wani munafukin murmushi yakeyi kasa kasa wanda tasan da ita yake dan tuni tajima da tsarguwa,


"Tab... Ambaliya.."


Taji yafada kasa kasa yana dariya, shiru tayi kamar bata jiba saboda me zatace? Abin kunya ne tarigada tayishi tabar masa jikinta yayi yadda yaso dashi adaren jiya tasan wannan yake yiwa wannan munafukin murmushin,dan rashin kunya ahaka yarinka kaiwa da kawowa acikin dakin arabin tsirara daga karshe yadauko kayansa yasaka jar t shirt mai gajeren hannu da jeans baki,


"Wanne magani zan siyo miki tunda kince baza akira husnah ba?"


Wayarta ta dauka ta kira khulsum tunda mijinta Dr ne ita saboda harga Allah bazata iya kiransu maama ba duk da cewa akwai kyakkyawar alaka tsakaninsu to amma wannan lamarin ai dabanne, har wayar tayi ta tsinke khulsum bata dauka ba, juyowa tayi ta kalleshi jin yazauna gefenta yana kai hannunshi kan igiyar dake gaban doguwar rigarta, kallon da tayi masa yasashi dan ja baya bata kai ga sake kiraba saiga kiran khulsum yashigo, lokacin da ta dauki wayar rasa abinda zata cewa khulsum tayi bayan abaya tagama cika baki yanzu kuma kawai sai khulsum taji fahad yayi aika aika? Katse wayar taji khulsum tayi tana dariya, tunani tafara yi to meya dace tayi kodai kawai cemasa zatayi yaje chemist yasiyo mata maganin ciwon jiki? Dan wallahi jikinta inbanda ciwo babu abinda yakeyi musamman ma cinyoyinta zuwa kafarta gashi duk sunyi tsami, jin shigowar text yasata saurin dubawa shi dai yana zaune yana kallonta duk da taki yarda su hada ido, gani tayi khulsum ta turo mata text akan abinda yadace tayi da maganin da yakamata ta nema tasha dan jin saukin radadi daga karshe khulsum takare da tsokanarta tana cewa lallai daren jiya yayi musu dadi gashi dama ankwana ana ruwa,


Mika masa wayar tayi batare da ta kalleshi ba nan yakarba yayi forwarding din massage din zuwa wayarshi sannan yabata, dan murmushi taga yayi ya lashi lips dinshi na kasa,


"Kazami kawai...."


Mikewa yayi tsaye yana yin wata mika ta musamman,


"Ranki yadade bari inje indawo, dan Allah karki kara yin kuka kinji?"


Banza tayi masa ta rufe idanuwanta tasake jan bargo, bargon ya dan ja sannan yakai fuskarshi dab da tata babu zato taji ya manna mata kiss akan bakinta, dauke fuskarta tayi tamayar daya side din, murmushi yayi yajuya yafita.....




*_Ummi A'isha_*    


*Littafina na kudine me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*




53****Yana fita wani wahalallen bacci yasake yin gaba da ita yau kam tasan haka zata wuni tana baccin nan saboda daren jiya kadan tayi,


Fahad kam yana fita yaga dakin husnah wallahi gaba daya ya manta da ita sai yanzu yatunata dan ko lokacin da yake cewa Bilkisu akira husnah ta dubata bawai dan husnan na cikin ranshi bane shifa idan yana tare da Bilkisu yakan manta kowa da komai,


Bedroom din husnah yashiga har lokacin tana kwance cikin bargo da wayarta ahannu tana chaten, zama yayi gefen gado yana kallonta,


"Wai ke bakya gajiya da chaten ne? Haba asma'u ga abubuwanan masu yawa wadanda zasu amfaneki...."


"Ya fahad yanzu fa na dauki wayar ina duba group din yan class dinmu ingani ko zamuyi lecture din...."


"A wannan ruwan? Tab"


"Allah ance fa za ayi, tashima zanyi infita"


"Allah yabada sa'a, zaki kira napep ko?"


"Uhmmm, ya jikinka? Yadaina zafi ko yanayi?"


"Da sauki yadaina tun lokacin da nayi bacci.... Yanzuma fita zanyi"


"Ina zaka ya fahad? Ya anty?"


Murmushi yayi,


"Ba nisa zanyiba antynki kuma ai tana daki..... Kina son ganinta ne?"


Ajiye wayarta tayi tana mika tareda yaye bargon da take lullube,


"Wacce ni? Uhm uhm idan mun hadu dai sai mu gaisa"


Mikewa yayi yana murmushi,


"Husnah kenan.... Bari naje sai nadawo"


"Adawo lafiya...."


Lokacin da yafita gidansu yafara zuwa kasancewar yau antashi da ruwa har baba yasamu agida bai fitaba sukuma iyayenshi mata suna soya fanke da miya, acikin flask aka zuba mishi yatafi dashi, chemist din dake makotaka da gidansu salim yaje yasiyawa Bilkisu maganin sannan yakira salim yafito, arumfar chemist din suka fake suna gaisawa, salim ya kalleshi cikin tsokana yace,


"Mijin hajiya kai kuma meye yafito dakai cikin ruwan nan....?"


"Kasan me iyali, hajjaju nazo saiwa magani..."


Dariya salim yayi,


"Gaskiya kai mijin tace ne, sai yadda akayi dakai, yanzu acikin ruwan nan aka aikoka..."


"Dallah tafi can kai baka san mata da miji ba, wani abinma idan kasha giyar soyayya ka bugu to basai ance kayiba zakayi.... Ni bari nawuce nasan tana can tana jirana"


"Idan andauke ruwa to zanzo"


"Ina? A'a banda yau, yau matata hutawa zatayi basai kazo ba"


Dariya salim yayi yace,


"Kai dai kasani, mijin hajiya kawai"


Dariya fahad yayi yakarasa gaban rubber rubber dinshi yana cewa,


"Naji dai, ai nafi gwauro wanda yake kwanan shago"


"Agaishesu...." Salim yafada lokacin da yake shiga cikin gidansu. Tunda fahad yafita bilkisu take kwance tana bacci cikin bacci taji fitsari kamar zatayi me dakyar ta lallaba ta tashi ta sauka daga kan gadon, hula ta dauka tasaka akanta tafita saboda dole saita nemo ruwan zafi kitchen tashiga ta dora a karamar tukunya mintuna biyu ya tafasa tajuye ta fito tana gwame kafafu daidai lokacin husnah tafito cikin shirinta na tafiya school, tsayawa tayi tana kallon bilkisu amma bata yimata magana ba tabata hanya tawuce itama Bilkisu batace mata uffanba tunda aganinta ita husnan ce yadace tafara yimata magana amma idan ita tayi mata magana ma babu mamaki ta disgata taki amsawa shiyasa ta shareta tawuce, da kallo husnah tabita,


"Ciwon kafa take yine? Ko kuma bata da lafiya to? Nashiga uku kardai cikine da ita? Wayyo ni...."


Da sanda tabi bayan bilkisu ta kuwa ci sa'a Bilkisu bata rufe kofa ba amma tadai karota, bata hango cikin gadonta sakamakon net din da yake sauke ya lullube gadon, ita kuwa Bilkisu lokacin ma tana bandaki tana gasa cinyoyinta zuwa kafafunta da ruwan zafi saboda lokacin da taje yin fitsari kasa tsugunnawa tayi sam saboda tsabar tsamin da cinyoyinta sukayi bata san lokacin da tafara kwalla ba, husnah nata sand'a har labulen ta dage tana leken cikin dakin daidai lokacin fahad yashigo kwata kwata bata ji karar shigowar machine dinsa ba, shi kuma da yaganta tana leka dakin Bilkisu sam bai kawo komai ba aransa,ji tayi yace,


"Asma'u lafiya...?"


Firgigit tayi tajuya tana kallonsa,


"Ya fahad uhmm....uhmm dama... Dama anty ce naga kamar bata jin dadi shine na leka inyi mata sannu kuma banji motsinta ba.... Inajin bathroom tashiga..."


"Ok, kije mai napep dinfa yana waje, kije zan fada mata"


Daga kai tayi tawuce zata tafi tana kallon ledar maganin dake hannunsa da flask din abincin da yake rike dashi,


"Fanke ne idan kina so..."


"A'a bana ci...."


Daga haka tawuce tana waiwayenshi shikam bai san tanayi ba saboda dakin bilkisu yashige harda rufe kofa ganin bata kan gado yasan tana cikin bathroom yana ajiye kayan hannunshi sai gata tafito tana takawa dakyar sai cije lips takeyi,


"Sannu....." Yafada ahankali, bata amsaba sai tukwicin harara da ta bashi,


"Kaida wa naji kuna magana?" Ta tambayeshi batare da ta kalleshi ba saboda yau tunda garin Allah yawaye sau daya kacal ta yadda suka hada ido,


"Nida husnah ne wai ta leko ta gaisheki kuma taga bakya nan..."


Jijjiga kai kawai bilkisu tayi batace komai ba amma ita tasan abinda husnah tafada karya takeyi tunda tagabanta tawuce amma bata ko daga kai ta kalleta ba, yarinyar nan ta lura yar sherri ce ta ajin karshe amma ita dai bata da lokacinta,


Wuceshi tayi yabita da kallo gaskiya bilkisu akwai saurin karaya da raki dan gaba daya jikinta awani sanyaye yake gashi sai tattale kafafuwa takeyi, ta cikin rigarta yagane bata saka komai ba sai iya rigar kadai saboda ga alama nan yagani na fulaninta sunyi cirko cirko suna kallonsa, gaban gado tawuce ta zauna yabiyo bayanta shima ya zauna kusa da ita,


Matsawa zatayi ya rikota,bata yarda ta kalleshi ba tajuya masa baya sosai,


"Kinyi brush....? Ga abinci ayiyah tace akawo miki"


"Nayi..." Tafada atakaice,


"Inkawo miki abincin?"


"Uhmmm" tasake amsawa atakaice, tashi yayi yaje ya dauko mata yakawo mata gabanta sannan yafita domin kawo mata ruwa, bude fanken tayi yasha miyar taushe wacce ta wadatu da gyada da tantakwashi nan tasoma ci hankali kwance, ruwa fahad yakawo mata ya zauna gefenta yana kallonta amma mafi yawan kallon a kirjinta yake duk tana ankare dashi aranta tana cewa fahad dai ko maye ne sai haka saboda ya sakawa kirjinta ido tun ba yauba tun zamansu na farko tasha kamashi yana satar kallon kirjinta amma a lokacin idan suka hada ido sai ya basar ya sunkuyar da kai ko yafara shafa keya, atakure tagama cin fanken kwata kwata ma kwaya uku taci ta dauki maganin ta balla tasha, mike kafafunta tayi saman gado taja bargo ta rufe kafafuwan nata zata kwanta da hanzarinsa ya matsa wai zai gyara mata pillow din da zata kwanta akai, babu zato tajishi ya dadimi abunda yajima yana tsole masa ido, runtse idanuwanta tayi tama kasa magana dan har lokacin hannunshi na wurin,


"Nidai kabari dan Allah.... Kabari mana...." Tafada idanuwanta arufe tana tureshi amma takasa dan bai bari dinba, kirjinshi ta buga da hannunta sannan ta tureshi ya matsa yana dariya, rasa irin kwanciyar da zatayi tayi saboda tasan kota fara bacci sai ya taba tunda tun jiya suke wannan fadan dashi dan haka kawai sai tayi rub da ciki, dariya taji yayi ahankali yace,


"Duk salon rowar ne haka hajjaju? Ba kyau fa rub da ciki, idanma saboda ni akayi to afasa ba sake tabawa zanyi ba"


Banza tayi dashi taja bargo ta lumshe idanuwanta,


"Kai yaron nan fitinanne ne na karshe wallahi..." Tafada cikin ranta bayan ta kawar da kanta gefe daya har lokacin a rub da ciki take. Shima fanken yaci yasha ruwa sannan yakoma kusa da ita, dariya yayi sannan ahankali yace,


"Ohhh su hajjaju labour angama zagaye zagaye dai daga karshe kuma andawo min dole dai nine nabude fadar...."


Dariya yayi ya kwanta akan gadon bayanta yana rera waka ahankali,


"Ko anaso ko ba aso nine nabudeta fadar...."


Cikeda bacci ta dago kanta tana tureshi daga bayanta, tashi yayi yana kallonta,


"Lafiya kake kokarin tashina da hayaniyarka bayan kasan bacci nake?"


"Ayya labour tayaki baccin fa zanyi... Nima Allah bacci nakeji..." Yafada cikin shagwaba yana wani lullumshe mata idanuwa, mayar da kanta tayi ta kwanta amma kuma sai yaga tayi saurin sake tashi sakamakon cire belt dinshi da taga yafara yi yana kokarin cire jeans din jikinshi,


"Menene haka?" Tafada tana kokarin boye tsoronta da yake kokarin bayyana,


"Karki damu trouser din zan cire saboda damuna zaiyi, bana son bacci da abu mai nauyi"


Batayi magana ba har saida taga yacire wandon ya jefashi can gefe daya ya kwanta daf da ita sannan tasake kwanciya a rub da ciki, turata yayi yafara kokarin juyata yana cewa,


"Wai ke wacce mummunar dabi'a kike Neman ki koya ne.... Babu kyau fa"


Ganin taki juyawa yasashi tashi ya dauketa cak ya juyata takoma rigingine tana kallon sama saurin saka hannayenta tayi ta harde kirjinta kwanciya yayi yana murmushi,


"Duk dai wayon amarya......"


Shiru tayi masa kamar bata jiba sannan taki bude idonta, bai sake magana ko motsiba saida ya fahimci tafara bacci sannan ya lallaba ya cire hannayen nata yamaye gurbinsu da kanshi ya kwantar awurin ahaka yayi bacci. Gaba dayansu bacci sukeyi haikam kasancewar jiya basuyi na kirki ba har lokacin sallar azahar yayi yawuce basu farka ba domin wani ruwan ake tafkawa, saida karfe 3 tayi sannan Bilkisu tabude idanuwanta ganin yanda fahad ya kanainaye kirjinta yasata tureshi aranta tana mitar nacinshi, ya takurawa kirjinta dan jaraba baccinma akai zaiyi? Bude idonshi yayi ya kalleta nan ta kawar da nata idanuwan bata bari sun hada ido ba,


"Ya zaki katse min baccina....?"


Shiru tayi masa ta yunkura ta tashi dakyar tana cije lips dinta duk da dai ciwon ba kamar na dazuba amma dai da akwai, hannunta yakama yana kallonta idanuwanshi narai narai,


"Ciwon yake yimiki har yanzu?"


Kai ta daga masa alamun ehh, tashi tayi shima yatashi yana cewa,


"Am sorry..."


Bata amsa masa ba tayi hanyar waje yana biye da ita kitchen tanufa saboda tasake dafa ruwan zafi saboda wanda ta dafa dazu duka ta yi amfani dashi, gas ta kunna zata dora ruwa yana tsaye abayanta yana kallonta, tukunyar ya karba ya debo mata ruwa yadora mata, suna tsaye ya tafasa ta sauke sannan ta dauki tea flask din tana dan buda kafa bin bayanta yayi da kallo sannan yabi bayanta da sauri yana cewa,


"Kawo inkai miki..." Sakar masa tayi ya dan kalleta sannan yace,


"Wai wannan gwamewar duk menene musabbabinta? Ko nine?"


Banza tayi masa tawuce suna zuwa falo yasha gabanta ya tsaya yana gyara short wandon dake jikinshi,


"Yanmata Magana fa nake yimiki...."


Ji tayi kamar ta makeshi kuma tafashe da kuka daure fuska tayi takawar da kai gefe,


"In dan taba dan Allah?" Harara ta watsa masa ta gefen ido ta kewayeshi zata wuce da hannu daya yadawo da ita yana yiwa kirjinta kallon rashin kunya har lokacin yana rikeda hannunta daidai lokacin husnah tabude kofa tashigo Bilkisu bata jira karasowarta ba tawuce tashiga daki,


"Sannu da zuwa husnah..." 


Yafada ahanzarce sannan yabi bayan bilkisu zuwa cikin daki saboda ko sallar azahar basuyi ba gashi la'asar ta kusa, a kan pillow yasameta zaune saman gado abinma dariya yaso bashi amma yafuske, butar da ta fito da ita ta dauka tacika da tafasasshen ruwan zafin tawuce toilet saida ta dan jima aciki sannan tafito saboda saida ta sake gasa jikinta,


A bakin kofa taganshi tsaye yana jiranta, "kijira ni muyi tare", yafada cikin tsokana, bata jirashi ba tayi sallarta dan lokacin da yafito ma har takai raka'a ta biyu, tana idarwa tatashi ta kawo la'asar saboda lokaci yayi. Kan gado tasake komawa ta dauki pillow mai laushi ta ajiye wurin kafarta ta dora akai ta kwanta bayan ta saki net din dake jikin gadon, tasowa yayi yazo yayi knell down agaban gadon kusa da ita dan har tana jiyo numfashinsa,


"Da zaki yarda wallahi sai inyi miki wani taimako..."


Shiru tayi idanuwanta alumshe hannayenta rungume akan chest dinta,


"Yanzu ina yafi yimiki ciwo?"


Kafafuwanta ta nuna masa zuwa cinyarta batare da tayi maganaba sannan har lokacin idonta rufe suke,


"To tsaya in taimaka miki..."


Tashi yayi yaje ya tsiyayo ruwan zafi a flask yazo yazauna gefenta yazame hular kanta nan gashinta dake jike ya bazu tasa hannu ta sake maidashi baya, rigar tata ya dan ja zuwa sama nan santala santalan laps dinta suka bayyana sai shining suke, tun daga kan kafarta yake gasa mata har zuwa cinyarta babu karya kuwa taji dadi mutuka domin ciwon yaragu da kaso mai yawa, lokacin da yagama harta dan fara gyangyadi, tashi yayi yaje ya ajiye komai da yadauko sannan yadawo, shammatarta yayi kawai taji ya cakumo kirjinta tashi tayi cikeda masifa yayi saurin guduwa yana cewa, "Ai ba ayin aikin banza a kano nima na karbi ladan aikina..."


Batayi magana ba tajuya ta gyara kwanciyarta taja bargo, saida ya tabbatar da tayi bacci sannan yakoma kan gadon ya kwanta kusa da ita yana wasa da gashin kanta. Husnah kam yau acike take famm da fahad saboda bai taba yin hakaba gaba daya yau sun wani kule adaki shida Bilkisu sunki fitowa, to me suke nufi? Kitchen tashiga ta dafa farar taliya sannan tayi sos din kwai tafito duk ranta ajagule, zama tayi afalo taci abincin ta ganin har tagama bai fitoba yasata sadadawa taje ta dan labe amma tsitt kamar babu kowa acikin dakin, komawa falo tayi taci gaba da zama har magriba tayi sannan ta tashi taje tayi salla tasake fitowa lokacin suma su bilkisu sun tashi, tana kwance kan rug din salla da carbi ahannunta fahad na kusa da ita yana yimata maganar abinci, labewa husnah tayi tana saurarensu,


"Hajjaju me zakici to idan bazaki ci wannan fanken ba?"


Saida taja wasu sakwanni sannan tayi magana ahankali,


"Ni babu abinda zanci..."


"No, zakici wani abu gaskiya, zaki ci indomie?"


Daga masa kai tayi yatashi yafita, yana fita yaga husnah wacce babu zato taga yabude kofa yafito,


"Uhmmm ya fahad dama zuwa nayi in tasheku naga baku fitoba shine nace may be baku san lokacin salla yayiba....."


Fuskarsa babu yabo babu fallasa yace,


"Mun tashi, zo muje ki dafa min indomie...."


Hade rai tayi tajuya tana kunkuni,


"Tabdijam... Nice ma zan dafawa matarka abinci? Impossible wallahi bazai yuyu ba"


Jin abinda tafada yabashi mamaki,


"Husnah nikike fadawa haka ko? Wato bazan saki abu kiyi ba?"


"To ai naga bakai zaka ciba.... Matarka zaka kaiwa fa"


"To matar tawa ita kika yiwa bani kika yiwa ba? Zaki wuce muje kitchen ko sai nayi miki rashin mutunci"


Turje turje tafara yi tana buga kafa akasa ganin haka yasashi wucewa cikin kitchen din batare da yasake bi ta kanta ba, da kansa yadafa musu manyan indomie guda uku sannan yasoya kwai yajuye yanufi dakin Bilkisu tana kwance har lokacin tana tasbihi,


"Tashi kici abincin hajjaju..."


Yunkurawa tayi ta tashi ta dauki fork ta debo takai bakinta tafara taunawa kenan taji yace,


"Kanwarki ce ta dafa mik...."


Ai bai karasa ba yaga ta tsaya da taunar da takeyi ta kafeshi da ido,


"Wasa nake yimiki wallahi ni na dafa... Kin san dai ai wani time din ina girki a kd"


Jin ya rantse yasa ta cigaba da ci tana kunkuni,


"Ni kar ka kara saka wannan nonsense wife din naka cikin sha'anina..... Ban son raini..."


Murmushi kawai yayi yana kallonta gaskiya Bilkisu tana da bala'in son girma,


"Daina zagar min mata..."


Yi tayi kamar bata jishiba, fork yadauka shima suka cigaba da cin abincin tare, bayan sun gama ta hada tea tasha, shikam yana nan nane adakin kamar cingum har sukayi sallar ishah, sai bayan da yayi shirin bacci sannan yafita zuwa dakin husnah tana kwance cikin kayan bacci tana waya da Ruky tana bata labarin abinda yafaru wai har ita fahad zai ce ta dafawa wannan tsohuwar wife din tashi abinci? Ita kuwa tace bazata dafaba, zugata Ruky taci gaba dayi tana cemata wallahi karta yarda idan bahaka ba rainata zasuyi kuma bilkisu gani zatayi kamar yafi sonta, tana jin fahad ta katse wayar ta gimtse fuska, kallonta yayi shima fuskar tashi gimtse,


"Asma'u har ni zance kiyi min abu ki k'i yi ko? Dama kin rainani har haka ban saniba? Good nagode ba laifinki bane nawa ne...."


"Haba ya fahad kayi hakuri pls... Ni wallahi da kaine zakaci zan dafa maka..."


"To ke waye yace miki ita zataci...?" Wannan tambayarce ta so kada mata hanjin cikinta shiyasa takasa bashi amsa tayi shiru,


"Babu damuwa nagode, saida safe"


Juyawa yayi yafita tabi bayanshi da harara,daga shi har bilkisun haushinsu takeji. A falo fahad ya zauna ya kirasu mukhtar yana tambayarsu ya school sukace normal ne kawai yaci gaba da hutawarsa, dariya yayi sukayi sallama dashi ya wuce dakin Bilkisu bayan yaje ya rufe ko ina na gidan, kwance ya isketa cikin riga da wando na bacci masu dan kauri amma abubuwan dake tsokale masa ido gasu nan abayanne,dariya yaso yi saboda ganin ta jera pillow a tsakaninsu,


"Dan sammin kadan intaba dan Allah Bilkisu..."


Juya masa baya tayi nan tajishi yana dariya kasa kasa yana cewa,


"Yarinya jiya tasha....."


Juyawa tayi ta harare shi duk yawani bi ya hasketa da hasken dake wayarshi,


"Kafa dameni... Bacci nake ji" 


Kashe hasken taga yayi,nan tagyara kwanciyarta tana mamakin shi wai ita yake kira da yarinya lallai yaga gadon baccinta dole yakirata da haka. Duk yadda taso kar yarab'u jikinta saida ya kwakumeta cikin dare dole ahaka sukayi bacci. Washe garima haka suka wuni cur adaki saida yamma tafita tashiga kitchen ta girka tuwon semo miyar kuka, aranar yabar dakinta yakoma dakin husnah duk haushinsa husnah keji saboda ganinta ya raina mata hankali yazo sai wani bacci yaketa faman yimata. Bilkisu dai saida tayi kwana biyar bataje aiki ba har saida taji ta garau, fahad shima bai koma makaranta ba acewarsa sai wani satin har lokacin bai sake attempting na kusantar ta ba amma sai dai tana shan dakuma haka zaiyita fakarta yana taba mata kirji gata ita kuma ba gwanar saka bra ba wani lokacin ko fita zatayi bata son tasaka amma yanzu tasan fahad bazai bariba dan ko jiya da tafito zata fita aiki yana falo kallo daya yayiwa gurin yagane bata saka ba janta daki yayi sakamakon husnah na wurin,


"Baki saka bra ba why?"


Musawa tayi tana ta turo baki, hannu yakai ta rike tana harararsa,


"Kibari naji mana tunda kince kin saka...."


Tureshi tayi tawuce gaban wardrobe ta dauko tawuce bathroom fita yayi yana dariya, lokacin da taje office khulsum tsokanarta tarinka yi tana cewa amarya take gashi nan har tafara wani shining gaskiya ko ita ta fahimci hakan amma tazaci ko Shea butter din da tafara shafawa ne na cikin lefenta. Ana gobe fahad zai koma kd adakinta yake shiyasa ranar ma yayi mata wayo saida yabarta tafara bacci sannan yaje ya far mata sosai yauma yaci galaba domin saida yafara rudata ya kasheta da soyayya sannan yayi abinda yayi niyyar yi, ranar ma sunsha kuka shikuma yasha yakushi da cizo amma bai hakuraba saida yayi abinda yaso shiyasa lokacin da yabarta bata da karfi ko na sisin kwabo, bai ma yarda yayi wanka adakinba dakin husnah yagudu can yaje yayi wanka yayi alwala yafito haushi da bakin ciki kamar zasu kashe husnah ganin yazo yayi wanka anan dan ko magana ma kin yimasa tayi. Saida karfe 6 tayi sannan yakoma dakin Bilkisu tana kwance har lokacin idanuwanta sunyi fici fici saboda kuka dan jiyama sosai ta dandana kudarta fahad fa babu damane a wannan fagen domin akwai rike wuta gashi ta fahimci irin mazan nanne masu dogon zango baya samun nutsuwa cikin karamin lokaci shiyasa take shan wuya a hannunshi, sunkuyawa yayi agabanta yadafa hannayenshi akan gadon yana kallonta,bige hannayen nashi tayi nan yafado mata, kallonta yayi yana murmushin rashin kunya,


"Kina bukatar kari ne?"


Harara ta watsa masa sannan ta yunkura dakyar ta tashi aranta tana tunanin wai meyasa yake yimata wayo ne har haka? Ita ina nata wayon yake tafiyane?


Bata kara bi takanshi ba tawuce toilet yauma saida ta dage wurin gasa jikinta sannan taji dadi sai kunkuni taketa yimasa tana kiransa da mugu, shikuma ga rashin zuciya da zarar yaga wuri sai yayi tsokana aranar da yamma ya tattara yayi tafiyarsa kd kuma yace sai yajima basu ganshi ba, aranar da yatafi da daddare ita yafara kira awaya kafin husnah duk Bilkisu bata son hirar nan tashi saboda mafi yawanta baran baramace da rashin kunya aciki daga karshe cemata yayi wai dan Allah tacire kayan baccinta suyi video call, kawai mamaki fahad ke bata bata taba sanin dan air ne shi mai lasisi ba sai a yan kwanakin nan dan wata maganar ma idan yafada ita da ba itace tafada ba kunyace take hanata motsi, harda fushi yayi saboda taki yarda suyi video call bayan sunyi sallama tafita kitchen dafa Lipton da lemon grass taji husnah tafito falo tana waya da fahad wai dan Bilkisu taji saboda dama taji motsin fitowarta, dariya bilkisu ita abinma yabata wato ita husnah bata san kwantai ma tasamuba na hirar tunda saida yafara kiranta suka debe awa da awanni yana yimata magana shine ita dan ankirata yanzu harda su zuwa tura haushi? Bata kulata ba tawucewarta daki.


Tunda fahad yatafi tafara wata irin kiba ta lokaci daya ada ita yan shafal ce amma yanzu duk tabi tacike tako ina harda dan kumatu tayi acikin satikan da basufi biyu ba ga shining da fatarta keyi da wani lightening na musamman ita harga Allah ta zaci ko man da ta sauyane ya karbeta,su maama dukansu lokacin da suka hadu agida da suka ganta santin canjawar da tayi suka rinka yi hakama khulsum ita dai bata kawo komai ba. Ranar asabar tana gida babu aiki ranar khulsum taje asibitin su mijinta ta dawo tabiyo ta gidan, adaki suka kule suna ta shan chapter husnah kam halin nata data saba tayi taje ta labe musu tana jin hirar da sukeyi ta hamood tsohon mijin Bilkisu har khulsum nacewa taganshi rannan a asibitin su abban Khalifa sai Bilkisu tace may be maganin HIV yaje siya ita dai Allah ne yakareta da tuni ya yaba mata jaraba, ai husnah najin haka ta rufe baki cikeda mamaki, da gudu takoma daki takira anty juwairiyya tana fada mata abinda kunnenta yaji nan fa juwaira tarinka famfa ta tana cewa karta yarda wallahi taje gidansu fahad ta tada maganar dan duk yanda akayi iyayenshi da yayyenshi basu san da maganar ba waya sanima ko itama bilkisun tana da ita karta yarda tabar maganar nan, ai suna gama waya husnah ta shirya tsaf dama lokacin yammace ta sulale tafita tanufi gidansu fahad ita Bilkisu lokacin ma khulsum tatafi tabarta tsaye gaban mirror tana karewa kanta kallo tana so tagano kibar da su khulsum keta cewa wai tayi da kuma haske......



*_Ummi Shatu_*    

*Littafina na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*



54****Bilkisu bata san meyake faruwa ba sai sha'anin gabanta kawai take tayi tana sake kallon kanta bayan tafito daga wanka, dagaske kam ta dan sake murmurewa ba kamar da ba lokacin da tana tsaka da ramar nan kamar wata majinyaciya amma yanzu kayanta ma duk nema suke suyi mata kadan saboda matsarta sukeyi. Husnah kam lokacin da taje gidansu fahad iya ayiyah da mamuh tasamu kadai suna girkin abincin dare suna dafa tuwon biski miyar karkashi shiru tayi bata fadi abinda yakawota ba har magrib saida baba yadawo sannan tace wurinsa tazo dama karar fahad da Bilkisu takawo, tambayarta baba yayi mesuka yimata nan tafara kora jawabi,


"Baba dama ya fahad ne da matarsa..... Ni gaskiya munafurtata sukayi saboda kwata kwata ban san cewa Bilkisu nada HIV ba sai yau......"


Ai daga mamuh har ayiyah dake zaune awurin dukansu kirji suka dafe cikin razani da tashin hankali sukace,


"HIV...?" Suka fada cikin hadin baki,


"Ehh wallahi mama dama ashe tanada ita shine ta boye bata fada ba...."


"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un..... HIV kuma? To aini koda wasa mahaifinta bai sanar dani hakaba... Sannan shima fahad din baiyi min maganar ba"


"Nima baba bai fada minba dan lokacin bikinmu ma da nace yayi test sai cemin yayi wai yayi shi bashida matsalar genotype da sauran cutukan zamani dake hana aure..."


"To yanzu shi fahad din yasani? Ina nufin yasan matar tasa tanada HIV?"


"Wallahi baba yasani, da saninsa kawai boye muku yayi dan karku hanashi zama da ita, kuma kowa yasan mijinta nada shima yanada HIV din amma ahaka ya fahad yace wai sai ya zauna da ita"


Shiru dukkaninsu sukayi na wucin gadi shi baba ma gaba daya yarasa abinda zaice sai hada zufa yakeyi lallai kuwa idan hakane fahad kuruciya na yawo dashi, waye yafada masa ana irin wannan makauniyar soyayyar akashe kai?


Su mamuh kuwa har yanzu basu daina salati da sallallami ba, kallon husnah baba yayi sannan yace,


"Asma'u abinda nakeso dake kitashi kitafi gidanki kije ki zauna, shikuma zan kirashi zaizo, idan yazo zamu san matakin da zamu dauka"


Sunkuyar dakai tayi cikeda ladabin karya tace,


"To shikenan baba.... Nagode Allah yakara girma"


Sallama tayi dasu mamuh suna cemata ta tsaya tatafi da tuwon biski tace a'a bata iya ciba, cikin jimami tatafi tabarsu kowa yayi shiru suna tunanin mafita.


Bilkisu na falo sanye da doguwar riga yar kanti tana kallo husnah tashigo tawani dauke kanta bata kalli inda bilkisu takeba tawuce daki jimm kadan tafito tashiga kitchen tana cewa,


"Su tsohuwar guzuma dai ankusa abar gidan da aketa tunkaho dashi ana huhhura hanci..... Ashe ana makale da kabari salamu alaikum..."


Ita Bilkisu sam bata gane abinda husnah ke nufi ba shiyasa da taji hayaniyarta na neman damunta tatashi takoma daki ta kwanta taci gaba da kallonta, lokacin kwanciya nayi tai azamar kashe wayarta saboda bata son nacin fahad. Ranar juma'a da yamma saiga fahad yadawo mamaki abin yabawa Bilkisu saboda shi da yayita cewa sai sun nemeshi kafin su ganshi amma shine yakasa hakuri yadawo? Hamdala tarinka yiwa Allah da ba adakinta yake ba yana dakin husnah dan haka suje can su karaci fitinarsu, shi kuma lokacin da yaga Bilkisu mamakin yar kibar da yaga tayi yarinka yi sai taba mata kumatu yake wadanda suka fara luhu luhu gashi ba laifi komai na jikinta ya sake dan bunkasa,wani zumudi yafara yi na son sake kasancewa da ita kawai yana son yasamu dama ne amma ahalin yanzu babu dan ranar husnah ce shiyasa yana fita Bilkisu tatashi tarufe dakinta tayi kwanciyarta. A bangaren husnah kuwa ko da wasa bata nunawa fahad ga abinda wai taje ta shirya ba lafiya lafiya suka kwana amma da safe tun kafin yatashi daga bacci baba yakirashi awaya yace anjima kadan yana son ganinshi shida su bilkisu, tunanin duniya fahad yayishi wai ko zai samu yagano dalilin da yasa baba ke nemansu amma sai yakasa, juyawa yayi yakalli husnah yafada mata cewar ta shirya anjima zasuje gida baba na son ganinsu daga nan yamike yafita, dakin Bilkisu yashiga har lokacin ita bata tashi daga bacci ba tana tunkunkune cikin bargo, zama yayi gefenta yaja kumatunta nan tabude ido ta kalleshi,


"Kitashi ki shirya zamuje gida baba na kiranmu..."


Gabanta taji yafadi,


"Lafiya?"


"Ehh to lafiyar kenan dai...."


"Allah yasa..."


Sake jan kumatunta yayi sannan yatashi yafita, tashi itama tayi tashiga wanka.


K'arfe 8 nasafe suka gama shirunsu tsaf a niyyar fahad yasamo musu napep su tafi gaba daya amma sai husnah tace ita kawai suje a machine din fahad inyaso sai tahau napep, wannan dalilinne yasa tafiyar tasu ta bambanta kafin suje tuni husnah taje tasake tsara karya da gaskiya harda su kukanta wai fahad baya adalci yafi son Bilkisu kuma itace take bashi umarni komai sai abinda tace shi zaiyi yanzu ma adakinta yake amma maimakon yasamo musu napep su taho gaba daya sai yaki yace wai Bilkisu zai dauko ita kuma taje tahau napep, kowa dake zaune wurin abin baiyi masa dadiba nan baba yashiga bata hakuri, tana nan zaune tagama kukan munafurcinta sai gasu fahad, su mariya najin Bilkisu suka fito sukaje da gudu suka rungumeta abin yasake baiwa husnah haushi,duk da tahada karya da gaskiya tafada hakan bai hana su ayiyah yiwa Bilkisu kyakkyawar tarba ba. Saida aka gama gaisawa sannan baba yacewa fahad,


"Fahad meyasa baka adalci tsakanin matanka? Haka ake zaman aure ko mu haka kataso kaga munayi a wannan gidan?"


"Baba menayi?"


"Asma'u maimaita abinda kika zo kika fada mana....."


"Baba tsoronta yakeyi sai abinda tace masa yakeyi, kuma ma ashe tsohon mijinta yanada HIV amma ahaka ya fahad ya aureta shiyasa lokacin bukinmu da nace muje muyi test yaki zuwa yace wai yayi anan...."


Hangame baki fahad yayi cikeda mamaki ita kuwa Bilkisu har tafara halin nata na saurin kuka, 


"Bilkisu abinda tafada gaskiya ne wai tsohon mijinki nada HIV"


"Ehh gaskiyane baba..." Bilkisu tafada cikin kuka, kafin baba yayi magana fahad yace,


"Amma baba ai ita bata da ita.... Wallahi kawai tada zaune tsaye ne irin na husnah....."


"Ba tada zaune tsaye bane gaskiyane nidai kawai aje ayi test dan kaima kila kana da ita" husnah tafada tana hararar fahad,


"Ya isa, kai fahad katashi ka debesu gaba daya kuje kuyi test inyaso abinda duk sakamako yanuna ku kawo min...... Ku tashi kuje"


Sam abinda baba yafada bai yiwa husnah dadiba ita so tayi ace suna zuwa iyayen su rufesu da fada sannan suce fahad sai yarabu da ita, Bilkisu kam sai faman hawaye takeyi tana kukan zuci ahaka suka tashi suka fita, kallon bilkisu yayi cikin fada yace,


"Daina yimin kukan nan, kar na kara jinsa...."


Share hawayenta tayi tai shiru husnah na bayansu, juyawa yayi ya kalleta,


"Ke kuma tunda kin zama uwar mutane sai ki kaimu asibitin da yadace...." Tasan gatse yayi mata amma duk da haka sai ta fadawa mai napep asibitin da zai kaisu, lokacin da sukaje asibitin babu mutane dayawa dayake private ne kuma weekend ne, nan aka debi jinin kowa amma bilkisu saida fahad yariketa sannan tabari aka dauki jinin har lokacin kuka takeyi kadan kadan. Sun dan jima suna jiran result sannan aka kawo musu gaba daya suka tafi ko budawa basuyi ba,gidansu fahad suka koma suka kaiwa baba result din shi da kansa yabuda yagani sannan yadago yana kallonsu,


"To kamar yadda sakamako dai ya nuna kowannenku lafiya kalau yake.... Allah yakara rufa asiri, sannan wannan kar yakawo fitina atsakaninku kubarshi amatsayin kawar da zato"


"Baba ni so nake tafada mana a Inda taji ance bilkisu tanada HIV"


"Ai zancen duniya baya buya..." Husnah tafada tana murguda baki,


"A'a fahad, abar maganar nan haka kaji, kar Ku kara tada maganar nan...

Allah yayi muku albarka"


Nasiha sosai su baba suka yimusu sannan suka yi musu sallama suka tafi, tunda suka koma gida fahad ke rarrashin bilkisu sai dakyar yasamu ta hakura tayi shiru ta daina kuka, ita tarasa me ta tarewa husnah agidan nan da bata kaunarta ko lokacin da suke zaune lafiya agaban fahad ne take yimata magana amma idan baya wurin ko kallo bata isheta ba. Tsabar abinda husnah tayi fahad baiji dadinsa ba aranar yabar kano yakoma kaduna ko sallama baiyi mataba shi da titsiyeta yaso yayi sai tafada masa munafukin da yace mata bilkisu nada HIV amma kuma sai baba yace abar maganar. Tunda yakoma kd yadaina daukar wayarta idan tayi masa massage ma baya yimata reply daga karshe kawai sai ta shirya tabishi can kawai sai ganinta yayi da dan akwatinta dama dakinshi shi kadai ne, yanata daddaure mata fuska amma daga karshe dole ya hakura yasakar mata fuska yace ya hakura komai yawuce amma karta kara, duk zuwanta ya takura shi baya samu suyi hirar soyayya da bilkisu kamar yadda yasaba yimata ita kuma batama san husnah na wurinsa ba ita dai taga bata nan kwana biyu. Saida husnah tayi sati daya awurin fahad sannan tadawo gida tana dawowa ta hau yada habaici tana yiwa kawayenta waya tana cewa daga wurin oga take acan taje ta huta sosai abin ya taba zuciyar bilkisu aganinta ai wannan munafurcine fahad yayi shine ko yafada mata husnah na wurinshi nan itama tadau fushi dashi shiyasa lokacin da yazo weekend basu rabu da dadiba saida fada kwata kwata baisan laifinsa ba amma taki sakar masa fuska wannan karon ko yar karar da akeyi masa ake barinsa yayi katobararsa ba abarshi yayi ba bare abarshi yayi abinda ya gadama duk da tasan illar hana kai ga miji wannan karon kam hanashi kanta tayi saboda taji haushin abinda suka yimata shida husnah. Husnah kam tun lokacin da tadawo daga wurin fahad tafara amai da tofe tofen yawu sosai abin ya tayar mata da hankali saboda tana zargin cikine, ai kuwa tana yin test taga shine zancen zuci tafara yi,


"Tabdijam ina.... Wallahi bazan haihu yanzu ba intsufa ga wahalar karatu,ita matarka ma da take tsohuwa bata yarda tayi ciki ta haihu ba sai ni yar yarinya dani? Wallahi cikin nan zubar dashi za ayi tabdijam... "


Abinka da kuruciya duk sai tabi ta yadawa kawayenta wai cikine kuma ita bata so nan suka yita zugata suna cewa idan tabari ta haihu yanzu wallahi fahad daina yayinta zaiyi tunda ga matarsa nan ita taki yarda ta haihu sai gayunta take ci,


Tana komawa gida da daddare sukayi waya dashi har zasuyi sallama sai tace masa,


"Ya fahad.... Tunfa rannan naketa amai da tashin zuciya kuma da nayi test ashe cikine.... Nikuma gaskiya ba yanzu ba.... Kawai azubar...."


"Baki da hankali dama? Azubar fa kikace, husnah wai meyake damunki ne?"


"To ita anty meyasa ita baka yimata cikinba saboda ita kafi so? Nikuma nice zan wahala kenan..."


"Ohhh Allah.... Husnah ki shiga cikin hankalinki, haihuwa bata Allah bace? Ai ba yin kaina bane... Koda wasa karki kuskura ki attempting zubar da cikin nan idan kuma bakiji ba wallahi kika zubar zaki sha mamakina dan sai nadauki mummunan mataki akanki...."


Ummi Shatu_*????

Duk da wannan maganganun da yayi mata bata yarda ba azatonta wai barazana ce yayi mata shiyasa taci gaba da yi masa maganar itafa zubar da cikin nan zatayi ji yayi gaba daya auren yafita akansa daga bilkisun har asma'un fushi yake dasu saboda kowaccensu mai laifice awajensa, ita kuma husnah kishi da rashin wayo yarufe mata ido takasa ganin sudden changes din dake tattare da bilkisu itafa kawai idonta yarufe gani take bilkisu da biyu taki haihuwa saboda karta tsufa irin rashin dabarar da matan yanzu keyi wai aki haihuwa gudun kada atsufa. Ranar laraba yazo kano kuma aranar yake son komawa daga bilkisun har husnah sama sama yagaisa dasu dan ita bilkisu ma ko ganinsa bata yiba tana can wurin aiki sai awaya yakirata, ita kuma husnah tana gida, shi baida dabi'ar binciken wayar mutane amma yau yayi akan husnah saboda yana zargin kamar zugata kawayenta keyi ai kuwa zarginshi yazama gaskiya dan yaga chat dinsu da Fa'iza tana tambayarta wai cikin yazube tace a'a wannan maganin baiyi mata aikiba sai ciwon mara da yasata shine fa'iza ta tura mata sunan wani wai ta gwadashi mana yafi wancan karfi, ranar husnah ta raina kanta domin yi yayi kamar zai dafata yacinye nama danye saboda masifa daga karshe yace wallahi idan ta zubar da cikin nan abakin aurenta kuma kar su Ruky da Fa'iza su kara zuwar masa gida, da bacin rai yakoma kaduna itama bilkisu fushin take yi akan nada wai yazo ko yaje yaganta yayi tafiyarsa, washe gari da rana ya kirata wai dan Allah tayi masa taimako duk ranar da kawayen husnah sukazo ta fada masa da to ta amsa masa amma acikin zuciyarta tace babu ruwanta bazata zama munafuka ba. Bilkisu fa kiba kullum karuwa takeyi ga haske sannan fatarta har wani kyalli da sheki takeyi yanzu duk kayanta dakyar suke shigarta tun bata daukar maganar khulsum dagaske na wai cikine da ita har tafara dauka dan taji period dinta shiru gashi har pad tasiyo guda biyu ta ajiye amma kemadagas yaki zuwa gabanta ne yafara faduwa wanda sam bata San dalili ba, acikin satin fahad yazo nan dinma aranar zai koma fada sukayi kaca kaca da husnah akan cikin nan bilkisu na jinsu kamar zai doki husnah tsabar ransa yabaci bai ko yiwa bilkisu sallama ba yayi tafiyarsa abinda yasake kular da ita kenan, yana tafiya husnah ta aiwatar da kudurinta ta zubar da cikin ai kuwa tasha wuya kamar zata mutu dan azaba, ranar friday sai gashi lokacin husnah bata gama warwarewa ba daga ta'asar da tayi shiyasa yayi saurin ganewa tun kafin ya tambayeta tafara shirya masa karya wai kawai mafarki tayi wata mata mai kamada bilkisu tana dukan cikinta da tabarya tana farkawa taji tana bleeding sai kuma ciwo yasata agaba, fada fahad yashiga surfawa yana cewa kar ta yarda tasaka bilkisu cikin shirmenta ta hada kayanta tatafi gidansu shi yagaji da wannan masifar tata ai dama yafada mata karta zubar da cikin nan amma saida ta zubar. Bilkisu na daki tana jinsu amma bata fitoba saboda ba asata cikiba kar ace munafurci ne, aranar itama tayi gwaji da pt strip din da tasiyo tun kwanaki biyu da suka wuce amma tsoro yahanata yi, tun agwajin farko yanuna mata ciki baro baro, rufe baki tayi tana mamakin to meyasa takasa ganewa tun farko? Yanzu shikenan tayi abun kunya wai itace dauke da cikin fahad ajikinta to ko itama zubarwar zatayi? Masifar da yayita yiwa husnah ce tafado mata nan tsoro yashigeta to ai ko babu komai ma lokacine yayi wanda zata nunawa husnah cewa ita ba juya bace sannan babu abinda yasamu mahaifarta ras take tunda gashi tadau ciki. Duk da cewa husnah ta tafi yaki sakar mata fuska dan tun lokacin da ya bukaceta tahanashi yake fushi ita kuma yanzu tun ranar da tayi pregnancy test dinnan take jin wata matsananciyar bukatarshi kamar me amma ko cikin dakin nata bai kwanaba afalo ya kwana haka yabarta da juye juye da kwalla kun san mai ciki idan taso abu bata samuba.....






*Littafina na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*




55****Washe gari da safe tana jinsa afalo yana harkar dake gabansa ahaka ta tashi tayi wanka ta dan shirya sannan tasake kwanciya cikin net,har wurin 9 sannan yashigo cikin dakin kai tsaye bathroom yawuce yaje yayi wanka yafito tana nan dai inda yabarta kwance tana satar kallonshi, ganin bai san tanayi ba yasata maida kallon nata gaba daya kansa, koda wasa ita bata taba zaton zata tsinci kanta cikin wannan yanayin ba wai yau itace ke yiwa fahad kallo na daban lumshe idanuwanta tayi wadanda kasala ta cikasu, tana ganinshi ya kammala shiryawa yasa dogayen kaya kalar ruwan siminti yana kokarin fesa turare yaji atishawar ta, juyawa yayi ya kalleta,


"Sannu.... Ko mura kikeyi ne?"


Jijjiga kai tayi idanuwanta na taruwa da kwalla,


"Ayya sorry...., idan zan dawo zan taho miki da magani"


Batayi magana ba taci gaba da binsa da kallo ji take kamar ta janyoshi amma bazata iyaba, har yakarasa shiryawarsa ya juyo ya kalleta batayi motsi ba,


"Ni na fita... Akwai wani abune?"


Shiru tayi masa tana matse kwallarta,


"Wai meyake faruwa ne? Ke kam sai kace dan ke kadai aka halacci kuka? Haba bakida aiki sai koke koke.... Dan Allah kirage yawan kukan nan....."


Tashi zaune tayi tana kallonsa amma batayi magana ba,


"Bari naje shago.... Nadawo aljihu na babu nauyi ne duk na kashe kudadena wallahi....."


Juyawa yayi yafita jin batace komai ba yana fita ta rafka tagumi tana shafar cikinta da hannunta guda daya, tunani take yi kila abinda ke cikinta mace ce kila kuma namiji ne, ohh Allah mai iko shi kadai yasani, tashi tayi tafita ta shiga kitchen domin dafaffen kwai take son ci, bayan ta dafa tafito tana kallon dakin husnah kwana biyu duk sai take jin gidan yayi shiru da yawa da husnah bata nan yanzu da ace tana nan tasan tana nan tana aikin yar mata da magana, har zata zauna tajiyo karar wayarta, ciki takoma ta dauko wayar tafito ta daga sannan ta nemi wuri ta zauna,


"Labour wai yau baki zuwa aikine? Waye kika ajiye wanda zaiyi miki voicing din labaran rana?"


"Haba kawata dama fa ina nemanki yanzu nake shirin kiranki.... Yau bazan shigoba bana jin dadi"


"To wallahi ki zo dai ki karanta labaranki domin yau copers din da kika saba jibgawa aikinki suyi miki duk basu zo ba..... Nikuma kinga ni nayi nasafe bazai yuyu asake jin muryata a na rana ba MD zaiyi magana"


"Dan Allah kawata kiyi min wallahi ina cikin matsala ne bazan iya zuwaba dama kuma ina nemanki fa.... Ina son mu tattauna"


"Shikenan Allah yakara sauki, wasa nake yimiki zanyi miki news din, anjima idan natashi zan shigo...."


Sallama sukayi ta dan kishingida tana bare kwan da ta dafa guda uku, daga karshe wai ta dan kunna kallo ko zata debe kewa. K'arfe biyu saura khulsum ta karaso gidan lokacin bilkisu na kwance kan kujera, zama khulsum tayi tana cemata,


"Bani abinci yunwa nakeji..."


"Ai kuwa sai dai kisha tea dan ban girka komai ba, bana jin sha'awar girki wallahi"


"To shikuma fa?"


"Shima tea din yasha kadai yafita"


Dariya khulsum tayi,


"Kina shagalinki kawata, wato girkima sai kin gadama zakiyi, koda yake bake kadai bace ai..."


"Nida waye da?"


"Au ina kanwar taki?"


Yamutsa fuska bilkisu tayi sannan tace,


"Bata nanfa kwana biyu, amma may be zata dawo... Ke ni ba wannan ba dan Allah shawara nake so kibani...."


"Allah yasa zan iya labour... Meya faru?"


Dan shiru tayi na wasu sakanni sannan tace,


"Kinga wannan cikin da wata dabi'a yazo min wallahi.... Wai karfi da yaji kulawar fahad nake nema"


"Banfa ganeba.... Yimin gwari gwari"


Harararta tayi sannan tace,


"Ina nufin ina bukatar mijina, shikuma fushi yake tayi akan last time da yazo na hanashi kaina saboda munafurtata yayi.... Dan Allah tawacce hanya zan janyo ra'ayinshi batare da yagane ba...."


Khulsum najin haka me zatayi inba dariya ba, dariya tafara yi harda buga kafa akasa,cikin jin haushi bilkisu tace,


"Ya ina yimiki serious magana amma kina nema ki mayar da ita abun dariya?, dagaske fa nake yimiki..."


"Kin san me yabani dariya? Zamanku da fahad na burgeni, ke son girma shikuma Jan aji.... Labour kenan wallahi Allah ne ya kamaki, kin tuna lokacin bikinku, cewa fa kikayi ni yaron nan da yadage sai ya aurene me zai bani idan munyi auren?, wai ma tsaya idan aka ajiye masa ni ta ina zai fara?, yaron da ko gama balaga baiyi ba...."


"Dan Allah ni ya isheni, yanzu dai zaki bani shawara ko dariyar zaki cigaba da yimin? Kin dai san bani kadai bace cikina zai iya samun matsala idan har bai samu abinda yake bukata ba...."


Shiru khulsum tayi ta daina dariyar da takeyi,


"Kin san me labour? Ai ke yakamata kisan hanyar da zaki bi wurin janyo hankalinsa saboda kinga kowanne namiji akwai ta inda ake kamashi.... Wani ta girki, wani ta kwalliya, wani ta magana, wani ta kamshi ma kawai zai zo hannu... Yanda maza suke kala kala haka hanyoyin kamasu ma yake kala kala.....amma ke me mijinki yafi so?"


"Shima yana son abinci kuma gaskiya yanada son kamshi...."


Tsaki khulsum tayi sannan tace,


"Ashe ke da kin san ma abubuwan da yafiso shine bakiyi ba? To yanzu tashi zakiyi ki shirya masa lafiyayyen abinci sannan ki turare gidanki da dakinki da ke kanki da kamshi kinga yana dawowa sai kuyi evening show kawai...."


Dariya bilkisu tayi cikin murna tace,


"Yawwa mutuniyas kokefa.... Nagode bari natashi nabada himma...."


"Yakamata kam, yau dai ga ranar yaro tazo...."


Daga haka ta sabi jakarta tafita tana dariya. Bilkisu zagewa tayi ta gyara gidan tsaf ta turareshi da turaren wuta da freshener mai sanyin kamshi, shi kansa bedroom din ma yadda ta gyarashi abin kallo ne tasaka wani bedsheet pink colour da zanen heart atsakiya abin gwanin burgewa sannan ta danyi kwalliya da net din dake makale jikin gadon ta tattare shi yabada design mai kyau sannan gefe daya ga turaren wuta na stick mai masifar kamshi yana ci sai hayaki mai kamshine yake tashi ahankali. Ita kanta yau kwalliya taci cikin materia red colour dinkin gown gefe daya ta shirya lafiyayyen girkinta soyayyiyar shinkafa da salad kawai fahad take jira. Tana kwance kan doguwar kujera tana kallon wani film atashar African magic mai suna things i hate about you fahad yashigo, fuskarshi babu yabo babu fallasa ya nemi wuri ya zauna yana kallonta, matar nan fa dagaske kiba take hadawa bata wasaba,


"Sannu da zuwa...." Tafada idonta nakan tv amma fuskarta asake take sosai wanda har hakan yaso bashi mamaki, cikin basarwa yace,


"Yawwa ranki yadade...."


"Ga abinci can fa..."


"Ok sannu da kokari bari na dan watsa ruwa tukunna..."


Daga haka yamike yawuce ciki nan tabishi da kallon sha'awa tana jin kamar tabishi, tana nan zaune yafito sanye da kananan kaya dukansu bakake daga rigar har wandon hannunsa rikeda p cap, wani bala'in kyau taga yayi mata ba kadanba bata taba sanin cewa fahad kyakkyawa bane sai yau,kallonshi kawai ta zauna tana yi sai take ganin kamar ma da biyu yake yimata wannan yangar da jan class din domin sai wani yatsine yatsine yakeyi kamar mace, da yake yau acikin shaukinsa take shiyasa take ganin komai nasa yau kyau yake yimata yana burgeta. Tana zaune tanata aikin satar kallonshi yagama cin abincin yamike yana kallonta shi fa yau yakula da fara'a ta tashi amma baisan dalili ba,


"Zan fita...."


Taji yafada, ji tayi kamar ta dora hannu aka tafasa ihu dan tsabar haushi, batayi masa magana ba yasa kai zai fice har yaje bakin kofa taji yajuyo yace,


"Amm namanta..., gaskiya yau dakinki yayi kyau.... Da ke dinma kanki, style din da aka yiwa dakin is something amazing..... I like ur style hajjaju..."


Daga haka yafice daga cikin falon, tana jin alamun tafiyarshi tafara kwalla, cikeda damuwa da bacin rai takira khulsum tana fada mata, dariya khulsum tayi sannan tace,


"Ohh my God.... What a funny.... Wato darling fahad yagano mu shine bazai bada kai bori yahau da wuriba har sai yabamu wahala? To inyasan wata ai bai san wata ba.... Bari inyi miki text, insha Allah bazai tsallake wannan tarkon namu ba"


"Are you sure...?" Inji bilkisu,


"Am 100% sure dear... Kijirani yanzu"


Daga haka takatse wayar tana jiran text din khulsum babu jimawa kuwa saiga text din yashigo, murmushi bilkisu tayi tana bawa kanta tabbacin zatayi fiyeda yadda khulsum ta shirya mata.


Har karfe 9 fahad bai dawoba sai wurin 9:30 sannan taji shigowarshi, tana kwance cikin net a kunnenta yashiga wanka yafito sannan yafita falo daga shi sai short nicker wanda tabada tabbacin abinci yaje yaci, yana shigowa yaji kamar nishin bilkisu da sauri yanufi gadon, kwance yaganta shame shame tanata faman sakin wahalallen nishi cikin wata atamfarta dinkin riga da skirt gaba daya kayan sun matseta sosai, dagota yayi yana tambayarta cikin rudewa,


"Bilkisu menene? Meke faruwa...?"


Kirjinta ta nuna masa da hannunta alamun ciwo yake yimata,


"Ciwon kirji kikeyi?"


Kai ta daga masa tana sake dago kirjinta tana sakin nishi, gaba dayanta ya dauketa ya saka ajikinshi yana cewa,


"Ai dolema dama kiyi ciwon kirji... Kallifa yanda kayan nan suka matse ki...., bari acire kawai"


Runtse idanuwanta tayi tana sake sakin wani nishin kamar gaske dan sai ka rantse da Allah ciwon takeyi irin sosai dinnan, baiyi wata wata ba yazuge zip din rigar yacire sannan yazuge na skirt din shima yacire shi kamar yadda yayi expecting daga ita sai pant yarasa meyasa bilkisu bata shiri da bra kamar wacce take mintsininta, kasa kawar da kansa yayi yadai yi kasa da murya yana cewa,


"Zaki sha maganine infita insamo miki?"


Kai ta girgiza masa cikin dakiya da muryar wahalar ciwo tace,


"A'a.... Kayi massaging dina may be i will be ok...."


Babu bata lokaci yafara abinda tace amma kuma bai dade da farawar ba shi kansa yaji al'amarin yafi karfin daurewa irin tashi shiyasa kafin ya farga har yasoma shiga cikin wani yanayi, daga shi har ita yau kowa yabaje basirarsa wurin kulawa da dan uwansa da samar masa da nutsuwa, bilkisu kam kasa kallonsa tayi daga karshe ma ta tsiri baccin karya tana jinsa yana yimata magana akan tatashi tayi wanka amma tayi shiru. Yau kam tayi baccinta cikin nutsuwa domin tasamu abinda take muradi dan ko juyi batayi ba saida asubah tayi sannan fahad yatasheta, wanka tayi tai salla shikuma fahad yafita masallaci, abin mamaki lokacin da yadawo kwance ya isketa kan rug din salla tana faman haki da nishi kamar wacce tayi race, yanzunma abinda yafaru daren jiya shine yasake faruwa, shar da ita ta shirya ta shiga cikin kitchen bayan takashe kan 80,tana tsaka da soya doya fahad yafito cikin shirinsa, manyan kaya yasaka shadda ash colour amma babu hula, a kofar kitchen din yatsaya yana dan kasa da idanuwanshi, daga ita harshi kunyar juna sukeji ta lura,


"Good morning sweetheart...."


Taji yafada ahankali,


"Morning, how was your night....."


Jin abinda tace yasashi dan murmushi yana shafa keya,


"It was amazing....."


Shiru tayi tana dan murmushi batareda ta kalleshi ba,


"Yanaga kafito bayan gashi ina preparing break fast?"


Dan satar kallonta yayi suka hada ido,


"Ni ai azumi nake...."


Dariya abinda taji yafada tayi tajuya ta kalleshi,


"Dama ana daukar azumi bayan alfijir ya keto?, malam bakada azumi kawai katsaya kayi breakfast"


Murmushi yayi ya karasa shiga cikin kitchen din yatsaya abayanta yana taimaka mata, tare suka zauna sukayi breakfast din sannan yafita, tun da tasamu wannan dabarar shikenan kullum da ita take aiki babu dare babu asubah sannan babu rana sai yanzu take gasgata maganar khulsum da take cemata itafa ta godewa Allah da tasamu yaro sharaf ta aura wallahi zataji dadi domin duk lokacin da take son kasancewa dashi zai saurareta kuma bazai kosaba amma manyan mutane sai ahankali ga shekaru ga basir duk yagama dasu, yanzu kam ta yarda 100% auren yaro akwai advantage aciki kamar yadda shima auren babban akwai nasa advantage din. Koda fahad yakoma makaranta ma baya sati daya baizo gidaba saboda Bilkisu domin baya son ta bukaci wani abu shikuma baya nan, kullum yana hanyar kano wani abun mamaki har lokacin shi bai san ciki gareta ba. Ranar da yayi wani zuwa da yamma yan uwan husna sukazo suka kwashe kayanta ita bilkisu ma lokacin bata nan tana wurin aiki saida tadawo ta iske falon yayi wani fadi duk sai taji babu dadi, fahad ta kalla wanda ke aikin goge mata tiles din dake cikin falon saboda yau haka tafita bata dauke ko tsinke acikin gidanba,


"Wai bazaka dawo da husna ba kenan? Haba kai kuwa anayin fa fiyeda hakama kuma adawo ashirya.... Dan Allah kaje ka dawo da ita..."


"Bakiga laifin da tayi min bane?, to be honest with you, she highly disappointed me and ban jin zan sake zama da ita gaskiya...."


"Duk da haka u have to be patient... U have to forgive her... Remember bature yace without sins there is no forgiveness.... Dan Allah kayafe mata..."


Tsayawa kawai yayi yana kallonta, zuwa can yanisa yace,


"Ai yanzu ba laifina bane, itace lokacin da taje gida ta hada karya da kareraye ta fadawa mahaifinta shikuma yayi fushi akan wai zaluntar yarsa nakeyi dan haka tagama zaman aure dani.... Kin gani da ace time din ta fadi gaskiyar abinda yafaru may be idan aka bani hakuri bayan na huce zan iya dawo da ita amma sai taje ta harhada karya ta fada.... Gashi dai tana sona tana son zama dani har gobe amma babu hali.... Aurena da husna kawai mubarshi a matsayin kaddara"


"Allah yasa hakane yafi zama alkhairi...."


Daga haka ta mike tashiga bedroom din tausayi taji yabata saboda ganin yanda ya gyara dakin ya kintsa komai harda su turaren wuta, gaskiya fahad abokin rayuwa ne yanada halin manya komai nagidan yayi mata harda su wanke wanke, washe garin ranar yaje yasiyo babbar katifa mai round kamar gado yasaka adakin husnah ai bilkisu nagani tafara daure dauren fuska wato raba daki zaiyi da ita da zai wani kama yasiyo katifa? Wallahi bazai yuyu ba ai kuwa bai yuyunba, kwanansa biyu yakoma Kaduna bai dawoba sai ranar da ake sunan matar ya Abba wato nusaiba wacce ta haifi yaronta namiji, kasancewar exam yakeyi saida ya dan samu interval sannan yadawo gida sai ranar yasan bilkisu nada ciki saboda cikin yafito sosai ita kuma tasake kiba tubarkalla gaba daya kayanta sunki shiga dan dakyar tasamu doguwar rigar da ta shigeta, bra kuwa duk sunyi mata kadan sai wata kwaya daya itace take iya sawa itama tana dawowa zata figeta ta yar,


"Wannan rigar ai ta matseki..."


Cikin jin haushi ta kalleshi,


"To ya zanyi? Kana ganima ahakanma ita kadaice ta shiga jikina"


"Allah yabaki hakuri, fito mutafi"


"Amin", tafada cikin fada, dogon hijabi tasaka tafita suka tafi yana rakata gidan sunan yawuce kasuwa kananan atamfofi yasiyo mata guda shida yawuce shago duk ya yankasu ya dinka mata doguwar riga samfarin maternity saboda duk na cikin lefenta masu tsadane bazai yuyu abata ba. Tunda cikinta ya tsufa fahad ke cikin zulumi sai kace shine mai haihuwar kullum addu'arsa Allah yasa kafin yakoma makaranta ta haihu, cikin ikon Allah yana gida suna tsaka da bacci ta tashi da daddare saboda azabar ciwo, tashinsa tayi sai faman ciccije baki take yi tana cemasa bayanta da kwankwasonta ciwo, gaba dayama rasa abinda zaiyi yayi daga karshe yakira mamuh yafada mata lokacin karfe 2 nadare, kafin su mamuh suzo duk ta jigata sai faman rokarshi gafara takeyi wai ya yafe mata mutuwa zatayi duk ta rudashi hankalinsa yatashi,bai taba sanin haka mata ke wahala ba wurin haihuwa sai yau lallai duk dan da baibi mahaifiyarsa ba yayi asara domin wahalar haihuwa kadai abar dubawa ce. Su mamuh na zuwa suka wuce asibitin haihuwa mafi kusa amma na kudi, c s za ayi mata saboda bazata iya haihuwa da kanta ba, acikin daren aka yimata aka ciro santaleliyar jaririya mai kamada fahad sak, komai na yarinyar irin nashine ba tayiwa bilkisu karar ko farce ba, mamuh nata faman tsokanarshi amma yaki kulawa saboda shifa ta matarsa yakeyi, da yake anyi aikin cikin nasara lafiya lau bilkisu ta farfado washe gari duk yan uwa suka cika asibitin amma banda ammah ita kam har aka sallamesu ana igobe suna bata zo ba. Ranar da suka koma gida bayan angama yiwa jaririyar wanka tanata faman tsaga kuka mamuh tace Bilkisu ta dauketa tabata tasha, daya dakin tashiga wanda fahad ke ciki domin nata su maama ne cike harda khulsum da sauran yan uwan fahad, yana kwance yana dan baccin gajiya, jin kukan baby yasashi tashi yana tambayar bilkisu mai yasameta? Zama tayi gefen katifa tana kokarin shayar da babyn, ido ta runtse tana cije lips saboda zafi tarasa wannan zafin ko na menene,


"Sannu baby... Tsaya in tayata"


Banza tayi dashi ashe shikuwa da gaske yake dan shima matsawa yayi ya dan janye kafafun babyn ya dora kansa bisa cinyar Bilkisu, tarasa sai yaushe fahad zai daina fitina, tashi tayi tafita ta mayarwa da mamuh yarinyar domin za agasa mata cibiya, yana kwance adaki yana jin mamuh na yimasa dan biki tana cewa ina sabon shiga masu 'ya wanda dan za ahuda mata kunne harda kwallarshi?. Washe gari aka radawa yarinya suna Bilkisu dan fahad yace tunda yaga wahalar da bilkisu tasha wurin haifar yarinyar nan dolene yasaka mata sunanta, su meenah ne suka zaba mata sunan da za arinka kiranta dashi wai  Hanfa, washe garin ranar da akayi suna yakoma makaranta yabar bilkisu anata kwaskware kwaskware dan gyara jiki shikam yana cike da farin ciki yanzu baida aiki sai na dora hoton yarshi akomai nashi shiyasa bilkisu har tafara kishi, ada ita yake kira da baby amma yanzu tunda yasamu wannan jaririyar yamaida sunan kanta. Bayan sunyi arba'in harda wasu kwanaki yazo tunda yazo yakama yarinyar ya nanuke ajikinshi bilkisu duk haushi ya isheta daga karshe binsa dakin nashi tayi ta samesu kwance yadora hanfan akan kirjinsa, ture hanfa tayi ta maye wurin tana turo baki,


"Ai wurinane....."


Dariya yayi ya daga hanfa sama yana cewa,


"Baby kinji momynki na kishi....."


"Ni ba momy bace..."


"Oh sorry baby i mean..."


Sake rukunkumeshi tayi,


"Nima sai ka dagani..."


Kwantar da hanfa yayi ya dauki bilkisu yana dagata. Kallonta yayi yana murmushi ita kuma tana feeding din hanfa,


"Kema fa harija ce baby..."


Harararsa tayi, "kamanta..."


"Dagaske kinfini jaraba ni kawai juriya nafiki, ke kinada son abun amma bakida juriyarshi,da kanki zaki nema amma mintuna kadan zaki fara yiwa mutum raki kina kukan kin gaji...."


"Ni garama da ka tuna min, planning nak....."


Bata karasa ba taga yawani zabura kamar ta caka masa allura,


"Baby p me? Lallai sai yau nayarda kema karamar yarinya ce...., gaskiya koda wasa ban amince ba soo karma kifara"


"To sai muyi na musulunci ai..."


Kallo yakafe ta dashi zuwa can yace,


"So kike ki kasheni ne? Bazan iya wannan wahalar ba dan zan iya mutuwa, wannan ai muguntace...."


Duk ta yadda ta bullo masa sai ya bulle dan dole ta hakura, idan kagansu da yar yarsu kuwa abin gwanin ban sha'awa ammafa kowa acikinsu kishi yakeda ita, shi bazai ga ana feeding dinta yayi shiruba sai yace ai nashine ita kuma wai bazai kira daughter dinshi da baby ba sai ita, cikeda begen juna yakoma makaranta dama semester din karshe ne, ranar da yakoma da daddare yakirasu video call yana kwance adakinsa kan katifarsa sukuma suna kan gado bilkisu rungume da ita,


"Hy daughter...." Yafada yana murmushi,


"Hy Daddy...." Bilkisu ta amsa tana dariya,


"My daughter how are u?"


"Am fine Daddy...." Bilkisu tasake amsawa tana dariya, hira yaci gaba da yiwa hanfa ita kuma bilkisu na amsa masa daga karshe yabata fuska ganin bilkisu ta sauya mata maman da take bata zuwa dayan,


"Baby kuma yaza abata nawa?"


"We are sorry Daddy... Kadan zaka sammata kagafa kwarewa tayi..."


Haka suka cigaba da gudanar da rayuwarsu cikeda kaunar juna da tattalin juna, har fahad yakammala karatu lokacin da zai gama bilkisu hutu ta dauka a office tabishi kaduna cikeda jin dadi da farin ciki yarinka nunasu awurin friends dinshi da abokan arziki yana cewa ga familynshi idan badan shine yafada ba da tabbas dayawa bazasu yarda ba saboda ko da wasa baiyi kamada mai iyali ba.


BAYAN WASU SHEKARU.



Wata matashiyar mata nahango kyakkyawa wacce ke cikin kwalliya ta alfarma tsaye tana rarraba idanuwa a filin tashi da saukar jirage na Malam Aminu kano, tana sanye da jar atamfa ta yafa jan mayafi sannan komai nata ja tayi amfani dashi tana ta faman duban agogon dake daure hannunta,sake daga idonta tayi akaro na biyu nan tahangosu suna saukowa daga matattakalar jirgi, murmushi tasaki yayinda nima na waiga domin kallon wadanda take yiwa murmushin, wani kyakkyawan saurayi nagani rikeda hannun wasu yara guda hudu, biyu maza biyu mata, biyu kansu daya suma biyun kansu daya, dagudu yaran sukazo suka rungumeta suna kiran "oyoyo mommy"


Kallon matashin saurayin tayi ta dan bata fuska,


"Daddy kai wallahi tafiya dakai jidaline... Duk kunbi kun sakani doguwar tsaiwa wurin nan"


Ido ya kanne mata guda daya sannan yace,


"Wai ai duk acikin so ne..."


Da key din hannunta tayi amfani wurin bude musu motar nan yaran suka kwasa dagudu suka shige,


"Dadina dakai yarinta, har yau baka girma ba"


"Waye yaron? Kibari muje gida zan kamaki"


Dariya tayi takama kunne guda daya,


"Am sorry ya fahad"


Wata dariyar yasake yi cikeda farin ciki, hannunta yakama suka nufi cikin mota yana bata labarin dinner din da zata rakashi yau da daddare ta wani friend dinshi, sau dayawa idan yace ta rakashi party ko dinner sai tace a'a ita bataso suje tare ayi masa dariya kowa yana tafiya da yar karamar yarinya yar kasa da 25 amma shi yadebi tsohuwa duk lokacin da tafadi haka sai yayi dariya yace Shifa har yanzu yakasa ganin girman da taketa kurin tana dashi saboda kallon mitsitsiyar yarinya yake yimata her age is just a number, kuma ako ina baya kunyar nunata amatsayin matarshi duk inda zaije tare da ita yake zuwa, ko wannan umarar ma da sukaje da yara har ita yaso sutafi duk da last time iya su biyu sukaje sukasha soyayyarsu suka barwa ammah yaran,to wannan zuwan amma aiki ya hanata kasancewar tazama babbar jami'ar gwamnati mai kulada harkokin yada labarai shikuma ma'aikacine a asibitin koyarwa na mal Aminu maganar dinki kuwa tun shekarun baya yadaina domin bilkisu takafa ta tsare ita kadai yake yiwa dinki ahalin yanzu amma yanada babban shago da yabude yazuba ma'aikata sukeyi. Kowa yasan irin shakuwa da soyayyar dake tsakanin ma'auratan, lokuta da dama su maama na gulmarsu idan suka hadu suce sun rasa wannan irin kauna ta adda labour da ya fahad duk sunbi sun bata junansu da shagwaba kullum cikin yiwa juna shagwaba suke kuma duk fahad ne ya koya ma Bilkisu, ita dai Bilkisu babu abinda zata cewa fahad sai fatan alkhairi domin ya zame mata wani babban jigo acikin rayuwarta, guy din yayine tako ina yanada yakana da kunya da kawaici ga iya soyayya shiyasa baya taba gundurarta sannan yana respecting dinta takowanne bangare baya taba treating dinta kamar karamar yarinya sai ta bangaren love, itafa yanzu da zataga wacce karamin yaro da babba zasu fito neman aurenta da zata bata shawarar ta auri yaron domin sai yafi kulawa da ita, abangaren fahad shima hakane kwata kwata baya sha'awar auren karamar yarinya acewarsa wacce ta girmeka tafi kula dakai zatayi treating dinka kamar baby amma kananan yaran nan babu abinda suka ajiye sai rashin kunya, ahalin yanzu dai yaransu hudu da bilkisu hanfa da Muhammad fahad sai Mimi da Awwab, to muna addu'ar Allah yaraya su amin.


Alhamdulillah anan labarin kamar da wasa ya kammala ina addu'ar ubangiji Allah ya taramu cikin ladan nidaku yakuma yafe mana a inda nayi kuskure. Hakika ban taba sanin inada dunbin masoya har hakaba wallahi sai yanzu, tabbas kun nuna min kauna da kuma soyayya, da yawa daga cikinku wadanda suka siyi book dinnnan ban sanku ba banma taba tunanin kun san da niba, ina mutukar godiya hakika soyayyarku wallahi itace abar dubawa agareni bawai kudin da kuka siyaba domin mai sonka shi zaiso kayanka nagode Allah yabar zumunci,sai mun hadu cikin kundin haske wato gamayyar alkaluman marubutan haske gaba daya, zanzo muku da wani labari mai salo daban akan darajar malami da amfaninsa cikin alumma, sai mun hadu da yardar Allah taku ahar kullum Ummi A'isha.




*_

*_Ummi Shatu_*    





No comments