Recent Updates

Jalal Ali Complete Hausa Novel

 


*💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫*
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by


    
         *ANNAFIE💖…✍️*
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
💫💖Jalal Ali(1)💖💫💫

Da mugun gudu tashigo cikin dan matsakaicin gidan nasu ba tare data kula Da matashin daya fito daga dakin dake cikin soron gidan nasu ba.. Cin karo sukayi tayi baya zata fadi yayi sauri riko ta ta dawo jikinsa.. Hannu ya saka yayi kasa da hijab din uniform dinta daya rufe mata fuska.. Tuni kyakkawar fuskar yarinyar ta bayyana.... Yace "imaan bn hanaki shigowa gida da gudu haka ba meya faru"... Wacce aka kira da imaan ta washe masa duka fararen hakoran ta.. Kyawun yarinyar ya kara fitowa sbd dimple din ta da suka lotsa.. Tace "yaya babu komai fa".. Tayi maganar tana kallon hanyar kofar gida.. Kallon ta yayi cike da tuhuma dan yasan halin kanwar tasa da shegen tsokana.. Kokarin sauka ta farayi daga jikin sa domin ta arce kawai.. Amma seya rike mata hannu..  Cike da tsoro imaan ke kallon sa da manyan idanun ta ... Yace "keda wane".. Ya fada yana leka kofar gidan.. Imaan kau jikinta har rawa yake sbd tsoro.. Wlh da ace wanine ya riketa bashi ba seta ganna masa cizo ta shige da dije me kanwa tazo ta sameta anan wajen... Ganin dije me kanwa ta taho a mugun fusace yasa yasa Auwal juyowa ya kalli kanwar tasa.. Yace "meya hadaki da dijeh"... Imaan da gaban ta ke mugun faduwa ta marairaice "yaya ni babu abinda nayi mata.. "Bata karasa ba dije ta bugo kofar cike da bala'i.. Ai imaan bata san lokacin da ta kaima yayanta yakushi ba.. Ta arta cikin gida a guje...... Wata tsohuwa ce ta fito rike ta buta ganin yanda imaan ta shigo da gudu yasa tsohuwar firgita tana kokarin juyawa se ta zame faduwa kasa tayi timm.. Kobi ta kanta imaan batayi ba ya.. Ganin mutanen gidan sun firfito yasa ta shige dakin tsohuwar da gudu harda saka sakata.. Tana sauke numfashi.. Se kuma ta fashe da dariya ganin yanda tsohuwar ta fadi ta saki kara gashi duk a firgice take...

Auwal yayi saurin tare dije dake kokarin afkawa cikin gidan .. Yace "dijen gala meya faru".. Dije data cika tayi fam. Tace wlh seta fadamun inda ta kaimin kanwa ta wlh seta biyata.. Dije ta fada kamar zatayi kuka sbd tana tsoran taje gida innarta ta mata shegen duka... Auwal yace "meya faru".. Dije ta fashe da kuka..  "Kawai daga suna er gala gala Na bata ajiyar kanwa ta na zagaya baya zanyi ba haya shine ta kwashe ta kullamin kasa a cikin kuma banga kanwar ba saura kadan.wlh seta biyani konayi mata dukan tsiya".. Auwal ya runtse idanu yana ganin kadan knn daga aikin imaan amma yasan tabbas kila dijen ta taba yiwa imaan din wani abu sbd yasan imaan bata barin bashi ko za'a shekara... Yace "to kiyi hakuri".. Tsalle ta daka ta rantse "wallahi bani zuwa ko ina se an biyani konayi mata dukan kawo wuka ai tasan halina ehe bn da mutunci".. Jin ihu a tsakar gidan yasa Auwal saurin zaro 200 ya bata dan yasan imaan ta kara tabo wani.. Karba dije tayi tace "kuma wlh zan kamata senaga uban da ya tsaya mata a kauyen nan"... Kobi ta kanta auwal beyi ba ya shiga gidan da sauri.. Shame shame ya iske kakar tasa da sauri ya karasa yana fara kokarin daga ta yana kallon wadan da suka yi cirko cirko. Bayan ya daga ta yace "Adda meya faru ne" Adda dake dafe baya tace "meke faruwa a wajene".. Yace "babu komai"... Adda ta kalli dakin ta dake rufe tace "wlh se Allah ya sakamun tsakani na da wnn muguwar yarinya me bakin hali ta Muhammadu.. Tana gani na fa na taho tasaka kafa ta tadiye ni tsabar mugun ta daga dazu kafin ta tafi boko na jefe ta da tsintsiya.. Dan nasan sbd shi ta yarda ni tunda ba kyale gareta ba kuma wlh yau se naci ubanta seta san wacce ta yarda... Kuma ko ta fito min daga daki KO inci uban ta mamman"... Imaan dake daki ta kyalkyale da dariya tace "ai ni babu abinda na maki bn rama ba zande rama ta fada tana cire farin hijabin nata.. Tuni dogon gashin ta wanda akayiwa kalaba ya bayyana dan babu dan kwali akanta... Zaro idanu tayi jin yayarta Abida cike da masifa tana  fadin.. "Kuma wlh nima ki fito jiranki nake yau me rabani dake se Allah dan wnn bakin naki idan bn gurzashi da kasa ba kice ba sunana Abida diyar mamman da jummala ba".. Imaan ta murguda baki duk da yanda gaban ta ke mugun faduwa.. Auwal ya kalli Abida.. "Ke kuma uban me tayi maki".. Kamar zatayi kuka tace "kwaran kwatsi yaya senaga ubanda ya tsaya mata kawai dazu na siyo kokona yarinyar na ta zubamin gishiri a ciki.. Gashi babu komai kuma yunwa nakeji hakanan nasha kuma setasan ni tayiwa haka wlh"... imaan ta murguda baki tana danewa saman gadon Adda me shegen taushi.. Auwal ya kalli Abida da keta cika taba batsewa.. Tabbas yasan imaan zata aikata fiyema da hakan amma yasan ramuwa ce tayi...yace "to sannu dan Allah idan ta fito kiyi mata koda kallon banza ne kiga yanda zanyi dak... "... "Dan ubanka ka sake ka tabamun diya kan wnn aljanar diyar sena mugun saba maka.. Kai Auwalu, Auwalu ka kiyayeni zan mugun saba maka".. Jummala da tashigo daga gidan ynx ta fara masifa tana hura hanci.. Adda ta tabe baki tace "nide a fito min ita daga daki tun kafin ta maida mun sama kasa"..... Auwal ne ya fara kiran sunan ta.. Imaan ta leko ta window.. Ganin yanda kowa ke jiranta tafito.. Tasan nan tana fitowa duk sun sami nama dan duk haushin ta sukeji tab kuma wlh bazata fito ba ehe.. Auwal yace "imaan ba magana nake maki ba"... Imaan ta leko ta window suka hada ido da Adda data mugun hade rai..".. Da sauri taja baya tanajin yau kome za'ayi mata bazata bude kofar nan ba... Auwal yace "wai ba magana nakeyi maki ba".. Tace "yaya se kawai na fito su duken".. Yace "babu me dukanki AI inanan".. A ranta tace tab idanba  bn fita sbd tasan uban kowa jiranta yakeyi anan.. Ta kalli yayarta hurera.. Ganin yanda ta saita jiranta kawai take ta fito kuma wlh bazata fita ba ita da fita se Abbanta ta ya dawo... Duk yanda akayi da imaan akan ta bude kofa kin budewa tayi.. Dan ita tasan me ta aikatawa kowa a safiyar yau kawai... . Washe baki tayi ganin Baban nata ya shigo ya Auwal ya sauke ajiyar zuciya dan dama shi besan yanda zeyi ba.. Imaan harda tsalle domin kau tasan ynx babu wanda ya isa ya daketa a gidan nan... Baba na kallon dukan su yace "lpy de ko" Adda ta fashe da kuka inafa lpyr er ka tana neman karyani tunda sauran Karina.. Wlh yau bazan yarda ba".. Baba ya karasa bakin kofar yace "imaan".... Fashewa da kuka imaan tayi.. "Kuma wlh Baba bnyi masu komai ba hurera ce fa ta zubar da ruwa Adda ta fadi amma sunce nice"... Murmushi Auwal yayi yana barin wurin.. Duka duka shekarun Imaan 11 Amma tsabar wayon ta tana wahalar da babba.. Adda ta kalli hurera... "Oohhh sbd nace bazaki shigarmin daki ba shine zata mun haka ni dama nasan babu ruwan imaan".. Murmushin jin dadi imaan tayi Baba yace "bude kofar".. Kamar zatayi kuka tace "dukana zasuyi fa".. Hurera tace "wlh ko Baba babu ruwana Allah yau sena karya yarinyar nan"... Baba na kallon hurera yace "zoki karyata din".. Fuu Hurera ta wuce dakin uwar ta tana kunkune tasan duk abin ta  inde Baba nan nan bazata iya dukan Imaan ba.. Jummala tace "malam duk abinda yarinyar nan keyi kaike hure mata kunne da wadan nan shegun malaman kaine ma gaba gaba kuma wlh senaci ubanta..." baba yace "zoki dakeni anyi din shashasha kawai".. Adda tace "kuma wlh daidai nake da duk wani shege dayace ze taba marainiyar Allah bama gidan nan ba kaf cikin garin nan... Fuu jummala ta shige dakin ta Abidama tabi bayan ta... Bude kofar Imaan tayi ta fito.. Da sauri tazo ta rungume Baba ta shi kuma ya shafa kanta..

Adda ta shigo duba dakin ta tayi taga ko tayi mata wani abu.. Ganin babu yasa ta sauke ajiyar zuciya dan tasan halin imaan...Baban yaja imaan zuwa bakin gado.. Ganin duk yanda tayi yasa yace "kinci abinci".. Girgiza masa kai tayi.. Yace "ina kudin dana baki ki sayi waina".. Ta ware hannu.. 'Kafin in tafi boko Hurera ta amshe".. Ya shafa gefen fuskar ta cike da tausayin ta.. Yasan da ace imaan irin shiru shirun yaran nan ne da se an maidata bola.. Se Allah yayota da shegen fitina.. Inde kayi mata seta rama ko agidan nan daga shi se Auwal take dagawa kafa Amma ina ko Adda bata barta ba... Wani kwanan silba Adda ta dauko cike da fura ta mikawa imaan "ungo yi kurba uku ki bani sauran".. Imaan ta washe baki ta karba ta fara shan furar cike da farin ciki.. baba ya bita da kallo cike da tausayawa.... Itama bayan sun hada idanu ta sakar masa murmushi... Tashi yayi yace "bari naje na dawo dama zuwa nayi na bada kudin abincin rana.. Nan ya bama Addan nata dana imaan snn ya fita ya nufi dakin jummala ko kallon ta beyiba ya aje mata kudin ya fita.. Dan yasan koya hada mata dana imaan bazata bata ba sede tayi ita da yaranta taci.. Ta bisa da harara kafin tayi kwafa.. "Wlh senayi maganin ku daga kai shegiyar diyar taka"...

Urs

✨✨✨

Annafie😍

Any one reading this book should knw that its not for free its just #300 pay through the Account below
2148886852 Nafisa Abdulbasir and show ur evidence via this number 07051376476.. But for now enjoy the free pages😊 thank you Annafie loves you all 🥰❤️as you keep supporting me encouraging me as I keep suburbudo maku novels masu dadi 🥰
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/H27abREXIQn8Rp0DbZBhE2*💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫*
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
         *ANNAFIE💖…✍️*
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
💫💖Jalal Ali(2)💖💫💫

Imaan seda ta shanye furar da Adda ta bata tass dan muguwar yunwa takeji.. Rabon ta da Abinci tun jiya da daddare a gidan umma da sukaci taliya tare da kuluwa... Imaan ta wani lumshe idanu sosai taji cikin ta yayi mugun cika.. Marfin kwanon ta dauko a hankali ta rufe tana satar kallon Adda dan tasan ta farka daga gyangyadin da take taga ta shanye kashinta ya bushe.. Daukar kwanon tayi a hankali zata mayar dashi wajen sa marfin ya subale ya fadi.. Imaan ta waro idanu ganin Adda ta watstsake idun ta .. Wani hade rai tayi tana kallon imaan... "Au shanyewa kikayi keda ba'ayi maki abun arziki.. Ni me kike so naci tunda kinsan matar ubanki idan ba ganin dama tayi ba ba bani Abinci zatayi ba".. Tura baki imaan tayi.. "Toh dama wane yace zeci".. Ganin Adda na niyar dauko mafici yasa imaan fita a guje... "Wlh cikin kudin ki da mamman yabani na abinci zan dauka sede kici wani abun tunda baki san me tausaya maki ba".. Imaan na fitowa tsakar gida taga jummala tana kokarin hada wuta.. Kafin imaan ta arce tayi saurin damkota... Zuciyar imaan har wani zillo take tsabar tsoro tana mugun tsoran duka dukda ba yau ta fara shansa ba amma takasa sabawa.. Ta kalli kofar dakin Adda.. Har ynx tana jiyo muryar ta tana masifa... Jummala tace "ubanwa na kama ynx".. Idanun imaan har sun fara tara kwalla... Ta bude baki zatayi magana.. Jummala ta kifa mata wani shegen mari.. Wanda yasa imaan fashewa da kuka.. Tuni Hurera ta aje tray din tallarta data fito dashi ynx.. Karasowa wajen da jummala ke dukan imaan tayi.. "Yauwa innarmu ci ubanta".. Itama batayi wata ta ba tafara dukan ta.. Banda kuka babu Abinda imaan take yanda suke dukan ta seka rantse wata babba suka samu... Adda ce ta fito .. Ganin yanda jummala ke dukan ta yasa ta saki wata ashar.. Hakan yasa suka saketa imaan da take kuka sosai ta fita gidan da gudu.. Adda tace "muguwa wlh se Allah ya sakawa marainiyar Allah".. Jummala cike da masifa tace "kina fa ganin abinda tayi mun da safe".. "Taje tayi din duk bakece kika maida ita haka ba ai gara da take ramawa inba haka ba seki kasheta.. Yarinya tun tana karama kike zalintar ta".. Jummala ta kawo dauri har goshi.. Tace "beyiwuwa yaran da na haifa basu sakamun ciwon kai ba wata ta sakamun".. Ta juya tana kallon Hurera.. "Maza Auta dauki talla kije ki dawo kafin ki dawo na gama yau abinda kike so zan maki wato dan wake maza diyar albarka" cike da farin ciki Hurera ta dauki farantin tallarta ta fice... Adda ta tabe baki.. "Bakin cikin ki de imaan bazatayi maki tallaba.. Yaran da kika haifa de suyi maki suyi ta gantali".. "Ga babban gantali nan bokon da take naga de tallar da suke karuwa ce suko fa.. Bnd iskanci da yahudan ci uban me suke a bokon..

Imaan bata tsaya ko Ina ba se gidan umma kanwar Abban nata dan gidan tane kade take samun salama idan tace gidan kawu lawal zata matarsa ba kaunar ta takeyi ba... Umma na ganin ta shigo tana kuka ta tashi daga bakin murhu da sauri... Diyar albarka waya taboki... Fashewa tayi da kuka  ta fadawa umma abinda ya faruwa... "Kan uba wato Hurera ce ta dake ki wlh bari muje nida Talatu se munci uwarta".. Da sauri umma ta kalli kuluwa dake kofar daki tace "kul karki sake bana son wnn rigimar" tura baki kuluwa tayi cike da fushi.. Umma ta dubi imaan " shiga daki ki cire uniform din kizo kici abinci tunda yau babu Islam".. A hankali imaan tace "bana jin yunwa"... Umma tace shiga daki ki canza kaya to ki kwanta.. Wucewa dakin umma tayi umma bita da kallo cike da tausayawa...."...

Umma kanwar mahaifin imaan ce wato malam muhammandu (mamman).. Su uku Adda ta haifa malam Lawal shine babba se mamman se umma mahaifinsu ya rasu tun da dadewa Adda ce kawai ta rage..kusan a tare lawal da mammam sukayi Aure.. Inno matar lawal wata irin masifaffiyar mata ce yayin mamman ya samu mata me saukin kai da kawai ci zainab kwata kwata bata da hayaniya Allah ya bata hakuri sosai dajuriya ko daya batada matsala da Adda da mijin ta da yan uwan mijin ta akasin inno da kowa ya santa a garin.. Ita dama zainab dama ba asalin er garin ba can wani kauye ya aureta hanyar zaria... acan yawon sa na kiwo ya aurota.. Matsala daya zainab ta fara samu da adda shine ta rashin haihuwa.. Dan duk cikin yaran Adda taga jika amma a wajen kowa amma bnd zainab nan ta fara ganin sauyi har aka fara goran ta mata inno ce ganin yanda ynx ta fara samun shiga wajen adda yasa ta zuga ta akan yakamata mammam ya kara aure aikam zancen ya shiga kunne Adda tuni ta matsawa mammam akan seya kara aure.. Zainab ma cewa tayi ya kara.. Wnn shine dalilin auro jummala.. Jummala kawar inno ce can suke wayon tallarsu dama.. Masifaffun mata ne babu abinda suka sani se neman kudi.. Ko shekara jummala batayi ba ta haifi santalelan danta me kama da uban sa Auwal. Sunansa.. Nan fara zainab ta fara fuskantar kalubale iri iri.. Gashi ita bata da kowa wajen umma kade take samun sauki se mijin ta dan jummala fitinanniyar mata haka haka zasu zo su taru ita da inno suci mata mutunci Adda kuwa bata cewa komai bata da wajen wanda zata kaiwa kukan ta.. Bata da kowa se yayanta mutum daya wanda shima ynx baya kasar sbd ya fita karatu shida matar sa daya aura...haka taketa hakuri.. Bayan auwal tazo tayi.. Nana snn Abida.. Duk yaran halin uwar su suka dauko idan ka cire auwal.. Suma kansu rashin mutunci suke mata bama su kade ba har yaran inno idan ka cire Abbakar.. Yaran umma ne kade ke girma mata sune ke rage mata kadaici... Samun cikin Hurera ne yayanta Umar ya dawo daga kasar waje a ganin halin da take ciki yaso ya dauke ta su koma da ita kaduna inda yake dazama ynx kasancewar ya zama cikakken likita Amma taki.. Shima har ynx be samu haihuwar ba bama ya haihuwa shi infact.. Kin yarda tayi domin kau tana son mijinta shima yana sonta.. Har yayi fushi ya tafi.. Sede yakanzo ya dubata lokaci lokaci

. jummala na gab da haihuwar Hurera zainab ta samu ciki.. Zokuga farin ciki wajen Adda da mamman.. Adda kamar ba ita ke hantarar Zainab ba.. Kulawa ta musamman take bata.. Haushi kamar ya kashe jummala ganin koda ta haifi Hurera ba ba ta ita ake ba.. Kowa hankalinsa yana kan zainab gashi ynx ba gida daya suke zaune da inno ba.. Jummala ta shiga ta fita akan cikin zainab amma ina Allah yace se yazo duniya... Cikin na cika wata tara zainab ta haifi kyakkyar diyar ta me kama da both iyayen nata bayan nakuda me tsayi.. Tana haihuwar ta kallon ta kawai tayi ta shafa kanta tare dayi mata addu'a snn tace ga garin ku nan... Mutuwar zainab ta girgiza mutane dayawa amma su jummala da inno ko ajikinsu.. Dr Umar har kuka yayi sbd rashin kanwar tasa.. Yaso ya amshi diyar tata ya bawa matar sa ta rike kasancewar basu taba haihuwa ba amma ina Abba yace sam.. Baze iya rabuwa da jinin zainab ba ya yarje masa duk lokacin dayake so haka ma Adda ta cije.. Dole ya hakura ya barmasu er'su.. Nan aka maida mata sunan mahaifiyar ta wato zainab se ake ce mata imaan.. Wajen umma ta taso dukda tana kawo ta wajen mahaifin ta anan jumalla ke samun damar cin zalin yarinyar sbd ta tsaneta fiye da yanda ta tsani uwarta ganin yanda Adda da Abba duka dauki son duniya suka daura mata. Ana yayeta Abba ya dauko diyar sa ya maido ta gida.. Sbd yanaso ta saba da yan uwanta.. Sede me.. Kaf cikin yaran sa idan ka cire auwal babu me kaunar imaan.. Tun tana shekara biyu tasan mene maraici tasha wahala iya wahala jummala batada imani ko kadan daga ita har yaran ta.. Dukan da imaan tasha wajen nana da Abida ba'a magana.. Shiyasa tun tana 7yrs itama ta taso da shegen rashin ji dukda ba wani karfi ne da ita ba amma ta iya mugunta iri iri gashi tasan duk wani meyi mata.. Imaan ko daya bata barin bashi.. Kowaye yayi mata seta rama bata ragawa kowa.. Bama a gidan su ba kaf cikin kauyen.. Ita kanta jummala idan tayi mata laifi tsoran ramuwar ta takeyi dan wlh seta rama KO daya bata biyo halin mamanta ba dan ita bata san menene hakuri ba kaf cikin yaran jummala babu me zuwa makaranta se talla dan tace ita ba zasuyi boko ba acewarta yahudanci me kuma islamiyar ma ba zuwa suke ba.. Itako kota daura was imaan talla setayi danasani ranar.. Makaranta kau tanason makaranta duk da garin bawani damuwa da karatun yara mata akayi ba.. Idan ma mace tayi nisa shine tayi junior dan kaf cikin garin ma daga js3 ta tsaya sede ko maza idan zasu cigaba suna zuwa makarantun dake kewaye da kauyen su.. Suma yawanci dangin me gari me suke zuwa.. Amma ko namiji dayayi js3 ze fantama harkan gona kiwo ko wani karamin kasuwancin.. Ita de imaan tun wani me bautar kasa da aka taba kawo masu taji yace ana zuwa har jami'a kuma idan ka gama zaka fara aiki ta zama irin su likita lauya da sauran su taji tana son zama lauya dan ita ta tsani taga an shiga hakkin mutun shiyasa ita bata da hakuri ko kadan ga duk wanda zeci zalin ta.. Koda ta fadawa abban ta sede yayi dariya kawai... Dan yasan da wuya shima zeso haka amma yasan abin maganane kawai.. Shekarunta 12 ynx shigar ta js1 knn yasan nan da shekara biyu zata gama js3 se kuma maganar aure.. Itakam sosai take dagewa wajen karatu.. Tana daga cikim daliban da ake alfahari dasu duk da ba wani karatu bane me inganci.. Itakam imaan bata son tayi aure so take ta zama lauwa.. Garin sbd yanda ake aure dawuri yasa baka samun yarinya sama da shekara goma shatakwass da yarinya ta shiga shekara sha hudu inde ta fara al'ada se kaga an fara shirin yi mata aure.. Kananun yara se kaga suna da samari ko ita imaan din masu sonta yawa ne dasu sbd tsabar kyaun yarinyar.. Amma shiriritar ta baya bari ta kula su.. Barta de da jan fada da fitina ko yayi mata seta rama.. Kawayen ta biyu Hauwa kuluwa ta gidan umma da kuma Talatu kowa ya sansu a kauyen basa jin magana kuma basa dagawa kowa.. Sede su duka sunada samari sabanin ita dukda sun dan girme ta.. Amma ita kawai karatu takeso.. Dukuwa da masu sonta dayawa mutum daya takejima kunya data gansa shine Abbakar dan gidan kawu lawal yaron inno idan ya ganta yana tsokanar ta da matata.. Sede ta rufe fuska kawai...

Wnn knn..

✨✨

Bayan imaan ta ciro kayan ta dake nan gidan umma ta saka ta cire uniform din ta saka a kayan datti dan duk kayan ta umma ce ke wankewa ko daya bata iya wanki ba.. Gadon umma ta haye tana sauke ajiyar zuciya.. Tana tunanin abinda zatayiwa jummala da Hurera wanda ze saka ta huce a haka bacci ya dauke ta.....

Urs

✨✨✨

Annafie😍

Any one reading this book should knw that its not for free its just #300 pay through the Account below
2148886852 Nafisa Abdulbasir and show ur evidence via this number 07051376476.. But for now enjoy the free pages😊 thank you Annafie loves you all 🥰❤️as you keep supporting me encouraging me as I keep suburbudo maku novels masu dadi 🥰
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/H27abREXIQn8Rp0DbZBhE*💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫*
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
         *ANNAFIE💖…✍️*
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
💫💖Jalal Ali(3)💖💫💫.

Bayan umma ta gama abinci ta zubama su kuluwa ta da take ta fushi ita a dole an hanata zuwa taje taci uban Hurera.. daki umma ta shiga taga imaan dake bacci tana sauke ajiyar zuciya.. Murmushi kawai tayi tana kallon ta cike da tausayi.. Kwata kwata  yarinya bata san dumin uwa ba ..tasan daba dan itaba wahalar da yarinyar nan zatasha ba karama bace dukkuwa da ba kyale gareta ba dan ko daya bayo halin mahaifiyar tata ba... Se gab da magrib sann ta tasheta.. Bayan tayi sallah suka fice ita dasu kuluwa.. Gidan su talatu sukaje.. Talatu nada girman jiki duk ta fisu girma ko fada suka taro dama itace me karfi... Can dandali sukaje dan sun san acan zasu iske hurera da.. Aikam can suka sameta.. Ta juya baya da dan tray dinta.. Su imaan suka lafe yayinda talatu taje ta cakumo kwalarta.. Hurera na ganin ta gaban ta yayi wata irin muguwar faduwa.. Nan ta fara tunanin abinda tayiwa imaan wanda bata rama ba.. Tuni ta tuno dukan da suka mata dazu.. Tana shirin yin ihu Talatu ta rufe mata baki.. Ta jata zuwa inda su imaan suka lafe.. Fitowa sukayi kamar wasu yan daba dan dama idan suna tare da talatu rashin jinsu har wani yawa yakeyi.. Talatu ta saka hurera a hammata yayinda su imaan suka dunga dukan ta har seda tayi kuka snn suka kyaleta suka ruga suna dariya.. Nan suka bazama neman wadan da suka masu laifi talatu na matse masu su a hammata suna duka.. Suna niyar kwashewa wata larai gyadar ta sukaji ance kuluwa, imaan, talatu.. Da sauri suka juya suna kallon yaya Abbakar a tsorace.. Kallon su yake dan yasan tunda sukazo wajen nan mutane dayawa sunji a jikinsu.. Yace "kafin na rufe idona na bude kunbar wajen nan". Ai tuni suka saka kafa.. Nan duk wadan da suka gansu kuma sun san suna da case dasu suka suka fito daga wajen boyen su.. Gidan umma suka wuce Bayan sunyi sallahr isha'i sukaci abinci.. Imaan tayiwa umma sallama ta shiga gida.. A kofar gidan su taga Abida tana zance ta saurayin ta iliya dukan su babu wanda be harareta ba.. Itakam ko kallon su batayi ba ta kafka gidan.. Daidai jummala ta sauke dan waken ta ta sakashi a ruwan sanyi.. Daki da shiga domin hado kwanoni... Ganin haka yasa imaan zuwa ta dauki botikin danwaken ta fito dashi da sauri Abida na kallon ta.. Can inda almajirai ke tururuwa taje ta mika masu aikam suka hau kai.. Ta baro masu harda botikin ta taho ranta fess.. Wnn karon Abida bata nan.Baban ta ta gani yasa ta jira sukaje tare.. Carko carko suka gansu jummala se zazzaga masifa take bayan abida ta gaya mata taga fitar imaan da botikin danwaken.. Abinka dame jin yunwa duk jiran ta suke ta shigo.. Yaya Auwal de na gefe murmushi kawai yayi dukda yanajin yunwa amma yasan tunda imaan ta fita da dan waken nan sede suyi kwanan yunwa.. Rike hannun Baban ta tayi ganin yanda suna shigowa jummala ta taso da sauri.. "Wlh yau duk inda kika kaimana abinci sekin fito dashi shegiya Mayya".. Baba ya daga mata hannu "wlh karki sake zagar min diyar".. "Aidama duk abinda take kaike daure mata kugu wlh seta fito min da dan wakena wlh ko tunda ba ita zamu kwada muci ba".. Abba yace "an daure kugun idan kinaso ta dena kema ki dena abinda kikeyi mata" daga haka yaja hannun ta zuwa dakin sa.. Jummala ta fashe da kuka hakama su Hurera.. Jummala tace "wlh bazan yarda ba ai zaka fita ka barmu da ita".. Kala becewa jummala ba dan yasan sune suka tsokanota kuma ramuwa tayi.. Imaan kau taji dadin dawowar sa tasan da be dawo ba da kila  yau setayi laushi sbd dukan da zata sha... Jummala bala'i kawai take yanda kasan dan waken ze dawo su hurera se kuka kam suke.. Tuni imaan tayi bacci a dakin Baba.. Be yarda ya kaita dakin su da suke kwana ba ya kaita dakin Adda dan yasan inde ze kaita dakin su to su Abida sun samu nama ne barin ma yanda sukejin yunwar nan..... Haka rayuwar imaan take acikin gidan su kwata kwata bata da wani yanci idan sun samu dama su kamata su daka itama idan ta samu dama ta rama.. Sosai take shan wahala a gidan masifar jummala kade bala'i ce bare ajega yaranta har tsoran komawa gida take idan Abban ta baya nan duk masifar adda bata isa ta hana jummala tayi mata abinda zatayi ba ita kanta imaan tasan tana rashin uwa shiyasa wani lokaci idan tana ita kade ta zauna tasha kukanta setaji inama ace itama tanada inna kamar su Hurera duk da umma na kulawa da ita amma tana son mamanta duk da bata taba ganin ta ba. Tana hanyar ta na dawowa daga makaranta.. Bayan sunyi sallama dasu talatu ta hadu da Abbakar.. Rufe fuska tayi yace "matar yan junior class".. Murmushi tayi tace "yaya ina wuni".. Yayi murmushi.. Cike da kaunar yarinyar dajin dadin yanda takejin kunyar sa.. Shide Allah ya daura masa tsananin sonta kuma insha Allah data girma ze aure ta dukda inno tana gargadin sa akanta amma shide tun tana yarinyar ta yake sonta.. Labari sukai tayi har seda suka zo kusa da gidan su ya bata naira dari.. Tura baki tayi yace "sefa kin karba nasan kila ma bakici abinci ba".. Karba tayi dan yunwa kam takeji sbd jiya kafin Baba ya fita ya bata kudi amma ta tashi ta neme su bata gani ba tasan de Hurera ce kuma bataje gidan umma yau ba hakama Adda tsoran haduwa take da ita sbd laifin da tayi mata jiya.. Karba tayi snn ta karaso gidan.. Kanwar abbakar din sa'ar Nana ce ta Gani itama tayi aure seda gaban ta ya fadi dan tana mugun tsoran haduwa da Nana da kuma wnn ummi din.. Ummi data gama ganin sanda Abbakar ya bata kudin ta mika mata hannu "bani".. Imaan ta hade rai tana noke kafada.. Wani mari ta kai mata a fuska. Wanda yasa imaan fashewa da kuka tare da mika mata kudin babu shiri.. Ummi ta damki hannun ta suka shiga cikin gidan ummi na masifa wlh kika sake na kara ganin ki da yayanmu senaci kutumar ubanki... Duk suna tsakar gidan Nana na zaune da tsohon cikin ta yanxun nan jummala ta gama bata labarin Abinda imaan ta mata da safe.. Ta shiga wanka imaan ta zare zanin ta aje gefe gashi gidan babu kowa Su hurera duk sun tafi talla.. Seda ta kusa hour da gama wanka tana tsoran fitowa wani ya shigo Allah ya kawo Adda itama seda ta gama ci mata mutunci snn ta dauko mata zanin da sauran Abubuwan da take masu. Nana ta cika tayi fam.. Aikam tana ganin sun shigo tare da ummi ta tashi kwanon data gamacin zogale ta dauka ta nufi imaan ta kwada mata a kai.. Imaan ta sake fashewa ta wani irin kuka tana dafe kanta.. Nana ta sake sakar mata wani marin.. Wanda seda kukanta ya dauke kafin ta zube kasa taci gaba da wani kuka wanda ya cika gidan Nana da ummi suka hau dukanta tana kuka babu wanda ya hanasu.. Adda kanta bata gidan bare tazo....suna can suna dukanta har basu kula da shigowar Baba daya dawo daga masallaci ba tare da wani mutumi dake bayan sa.. A tare suka saki salati suna karasowa cikin gidan se lokacin su Nana suka kula dasu.. Duk tsayawa sukayi suna kallon Baba cike da tsoro da mutanen dake bayan su masu shigar yan gayu cewar Hurera da bata gane su wanene ba.. Su jummala kau tuni suka gane wane Dr umar ne tare da matar sa duk da ynx sun kara kyau alamar kudi sun zauna hakan be hana ta kasa ganesu ba dukda tsawon shekarun da suka dauka basu gansu ba.. Da sauri matar Dr ta karaso inda imaan take dake kuka sosai.. Daga ta tayi cike da tausayinta se kuma kawai ta rungume ta tanajin kamar ta fashe da kuka Allah ya daura mata mugun son yara se gashi Allah be bata ba.. Shiyasa ko daya bata so taga ana wahalar da yaro musamman imaan da take marainiya.. Shikam Dr shiru yayi yana kallon diyar er' uwar tasa tilo yanda ake dukan ta se kace ba mutum ba.. Baba ya mari Nana cike dajin haushi da daci.. Kafin ya nuna mata hanyar fita "daga yau karna kara ganin ki a gidan fucemun.. Ficewa Nana tayi a zuciye ummi tabi bayan ta... Jummala ta shiga daki ta dauko masu tabarma tana dan yake cike da borin kunya.. Duk zama sukayi yayin da hajiya fati ke duka fuskar imaan da duk shatin duka ta fito tanaji kamar tayi mata kuka.. Dr de idon sa na kan imaan yana kallon ta.. Shi kansa Baba kasa hada ido yayi da Dr jummala ta kawo masu ruwa cike da borin kunya tace "sannu ku da hanya ga ruwa".. Dr ya dauke kansa daga na imaan ya maida kan baba da kansa ke kasa yace "malam mamman inaso zan tafi da zainab kaduna zata koma wajena da zama tunda kai ka kasa riketa a matsayin ta na mahaifin ta".. Ya fada cike da bacin rai yanajin wnn karon duk turjiyar Baba wlh seya tafi da imaan.. Baba ya dago da sauri yana kallon   fuskar sa bega alamar wasa ba snn ya dauki duban sa ya maida ga imaan dake jikin hajiya fati tana sauke ajiyar zuciya.. Hajiya fati tace "dan Allah ka bamu ita nayi alkhawarin zan rike maka ita Amana kuma bazamu rabaka da ita har abada ba.. Zamu bata ilimi da anyi hutu kuma zata rika zuwa inda kake.. Dr de bece komai ba.. Jin ance makaranta yasa imaan cikin muryarta data sha kuka tace "Baba zanje makaranta inyi karatu Baba bana son wnn gidan su inna kullum se sun dukeni dan sunga ni mamana bata nan baba kai kade nake so da Adda da yaya su duk bana son su.. Fashewa da kuka hajiya fati tayi tana rugume imaan kowa a wajen seda yaji tausayin ta.. Jummala kam tabe baki tayi.. Ko daya bata damuba sbd tasan baba baze taba basu ita ba.. Kafin wani yayi magana Adda ta shigo da sauri tana fadin "wanene ya yazo da jibgegiyar mota ta masu kudi ya aje a kofar.." Shiru tayi ganin Dr.. Da sauri ta karaso.. Dr dakta kaine ka koma haka lallai yan birni.. Na dauka tun wancan lokaci zaka sake dawowa da maganar daukar diyar nan dan wlh gara ka tafi da ita kafin jummala da yaran ta su kashe ta.. Dr.. Yayi kasa da kai "ina wuni Adda".. "Lpy lau ta fada idon ta na sauka kan imaan ware hannu tayi.. Ka gani ko wlh yau kila shirin kasheta sukayi".. Numfasawa Baba yayi snn yace "na amince ka tafi da ita Amma da sharadin zaka rinka kawota tana gashe dani... Kowa yaji dadin wnn furucin na Baba idan ka cire jummala da Abida.. Hatta Hurera dadi taji dan gwara imaan din ta tafi kota huta... Hajiya fati ta saki murmush tana kara rungume imaan.. Dr yace "inshaallahu bazan rabaka da er'ka ba.. Jummala tana son tayi magana amma tsoro ya hanata.. Baba ya aika Hurera ta kira masa umma snn ta wuce ta kirawo kawu lawal".. Fita tayi da sauri cike da jin dadi.. Gidan umma ta fara zuwa ta fada mata cike da murna tace "za'a tafi da imaan birni wani me mota ne yazo...tuni Dr ya fado mata a rai ta shiga daki domin daukar hijabin ta.. Kuluwa ma dataji komai tuni na ture kwanon abincin ta tayi gidan su imaan... Yanda hurera ta fadawa umma haka taje ta fada a gidan kawu lawal.. Su inno suka tashi da mmki ganin zaman ba nayi bane yasa suka sabi hijabin su....

Jummala de kasa hakuri tayi ta fashe da kuka dan Allah karku rabani da ita wlh sharrin shedan ne zan kula da ita dan Allah kuyi hakuri...".. Adda se harararta take tana tabe baki .. Baba de bece komai ba amma yasan zeyi kewar diyar tasa yana sonta fiye da duk wani mahaluki dake cikin duniyar nan yasan amma ya zeyi idan ya barta akacigaba da dukan ta beyi mata adalci ba.. Inno ce tace.. "Yakamata kuyi hakuri karku dauke ta tunda har jummala tace zata riketa kuyi hakuri mama" inno ta fada cike da daci.. Wani kallo kawu lawal yayi mata.. Ita kanta umma jikin ta yayi sanyi tanason imaan har ranta kuma tasan zatayi kewar ta kuluwa se tura baki takeyi itafa bata so kawarta ta tafi ta barta amma tana so taje birni ta dawo ta basu labari.. Su Abida kam bakin ciki kamar me.. Haka sunaji suna gani aka saka imaan a mota hajiya fati ta zauna gidan baya rungume da ita .. Dr yaja motar suka tafi... Dayawa  wasu sunji dadin tafiyar ta irin yara da ta addaba wasu kuma suke ganin gangancin baba na barin diyar sa tafiya birni kawai aje can a lalata masa tarbiyyarta.. Jummala kau bakin ciki kamar me.. Duk na ba son imaan take ta zauna tare dasu ba bataso duk wani cigaba ya sami imaan...

Imaan kau suna daukar hanya hajiya fati ta bata cake, se nama da drink tace taci sosai imaan taci sbd yunwar da takeji.. Seda taci ta koshi snn ta bingire da bacci.. Hajiya fati ta janyo ta ta rungume tana shafa gashin gaban kanta tanajin son yarinyar har cikin ranta tana kuma farin cikin ta samu diya itama.. Bacci sosai imaan tayi dan seda suna gab da shiga kaduna ta farka.. Imaan ta rinka bin garin da kallo tunda take bata taba barin kauyen su ba shiyasa ganin yanda motoci ke wucewa ga titi da manyan gine gine yasa ta washe baki tana kallo.. Hajiya fati se kallon ta take tana murmushi hakama Dr dake kallon ta ta mirror.. Ana kiran magrib suka iso cikin unguwar su da take shiru babu wata hayani ga manyan gidaje ta ko ina.. A daidai wani gate Dr yayi hon megadi ya bude suka shiga cikin gidan.. Imaan ta ringa ware idanu tana kallon wajen dan ita bama tasan inane wnn ba amma ya birgeta.. Hajiya ta bude kofa tana kallon imaan tace "fito".. Fitowa imaan tayi.. Tana kallon gidan "this ur new home my daughter welcome dear".. Kadan imaan ta tsinta cikin turancin dan haka se tayi murmush kawai.. Dr ma ya fito yana kallon ta tare da murmushi....

Urs

✨✨✨

Annafie😍

Any one reading this book should knw that its not for free its just #300 pay through the Account below
2148886852 Nafisa Abdulbasir and show ur evidence via this number 07051376476.. But for now enjoy the free pages😊 thank you Annafie loves you all 🥰❤️as you keep supporting me encouraging me as I keep suburbudo maku novels masu dadi 🥰
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/H27abREXIQn8Rp0DbZBhE2*💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫*
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
         *ANNAFIE💖…✍️*
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
💫💖Jalal Ali(4)💖💫💫.

Hannun ta hajiya ta kama suka nufi entrance din gidan imaan se kalle kalle take yau gata a irin gidan yan film..

Da suka shiga cikin parlon imaan har tsoro seda taji dan kar ace gidan yankakkai aka kawo ta.. Ganin yanda tayi yasa hajiya fadin "nan gidan ku ne kinji daughter".. Imaan tasan daughter na nufin diya hakan yasa taji dadi.. Tunda ta taso umma ce kade ki kiranta da diyar ta ita bata san mene ne dadin uwa ba.. Hajiya ta shafa kanta tace "daga yau ki kirani da mommy nice mamanki kinji".. Imaan ta gyada kai cike da jin dadi.. Dr ya haye stair.. Mommy ma ta kama hannun ta suka hau dakin mommy suka shiga.. Mommy ta shiga tayi alwala snn ta zubawa imaan ruwan alwala tace ta shiga tayi.. Shiga tayi seda ta gama kalle bathroom din snn ta dauki ruwan ta fara alwala.. Koda ta fito mommy sallah takeyi dan haka itama sallahr tayi.. Basu tashi ba se ishai snn mommy ta shiga toilet ta hada mata ruwan Wanka tace ta shiga tayi.. Ruwan wankan da ta gani dashi kade tayi amfani bata yarda ta taba komai ba sbd tsoro takeji.. Kafin ta fito mommy ta dauko mata wata T-shirt dinta ta da wani wando dan karamin wando.. Mommy ta dube ta tace  kin gama ina kasa bari nayi mana warming din abinda zamu ci kinji.. Imaan ta gyada kai.. Bayan ta shafa cream din da aka ajemata ta saka T-shirt din da tazo mata gwuiwa snn ta saka wandon bataga hijabin ta ba dan haka ta dauki hular da mommy ta aje mata ta fita.. A parlor ta iske dr zaune yana kallo bata ga mommy ba.. Ya ware mata hannu commom my daughter come to ur father.. Cike da jin dadin yanda ya kirata ta karasa kusa dashi ya zaunar da ita a side dinsa cike da so da tausayin yarinyar ya shafa gefen fuskar ta har ynx shatin marukan basu dauke ba.. Mommy ta fito daga kitchen rike da tray me dauke da gasashshiyar kaza se lafiyayyar jellof rice  se tea wanda yaji kayan hadi.. Dr ya kama hannun imaan suka sauka kasan carpet.. Duk da imaan bata jin wani yunwa seda ta washe baki ganin abincin yan gayu.. Ga kuma kaza.. Tuni fuskar su mommy ta bayyana farin ciki...imaan ta saki jiki taci abinci sbd yayi mata mugun dadi gashi dama ita batada wani boye boye.. Seda suka gama dr yace.. "Imaan kinson nan gidan".. Ta gyada masa kai da sauri.. Yace "toga mommy ki nan ni kuma abbanki kinga daga yau kin dawo nan gida kome kikeso feel free mune iyayen ki kinji" imaan ta gyada kai cike da jin dadi.. Tace "Abba kace zanje makaranta".. Duk murmushi sukayi Abba yace "sure zakije boading ta kwana dan kiyi karatu sosai".. Imaan ta washe baki tana kallon mommy se kuma can tace "to kace kuma na dawo nan kuma kace zan rika kwana a makaranta".. Mommy tayi murmushi tace "ai da anyi hutu zaki dawo wajen mommyn ki kinji".. Imaan ta gyada kai.. Nan suka maida hankali suna kallo.. Tuni imaan tayi bacci a jikin mommy.. Mommy ta dauke ta ta kaita dakin dake kusa da nata ta kwantar da ita. Tayi mata addua tare da shafa kanta ta fito.. Parlo ta dawo wajen Abba ya kalleta yace "mommyn imaan".. Cike da farin ciki mommy tace "wlh ina sonta har raina". Abba yayi murmurshi yace "inshaallah ta zama taki me rabaki da ita se mutuwa ko aure".... Mommy tace "Allah ya saka da alkhairi Dr ka gamamin komai kuma inshaallah zan tsaya tsayin daka wajen inganta rayuwar imaan"...

Washe gari bayan sun gama breakfast imaan da tunda take bata taba ka break me dadin wnn ba har wani natsuwa taji.. Dama ita bata cika wani karin safe ba sau daya take cin abinci a rana idan kuma ta samu tayi sau biyu.. Bayan sun gama mommy ta ska ta tayi wanka bayan ta nuna mata yanda ake amfani da komai na toilet din... Bayan imaan ta gama shiryawa cikin kayan ta da tazo dasu mommy ta shigo cikin shirin ta na gayu sosai kama hannun ta tayi suka fita.. Motar mommy suka shiga mommy taja motar suka fita daga gate din.. Imaan da bata taba ganin mace ta duka mota ba tace.. "Mommy dama mata na tuka mota".. Dariya mommy tayi tace "kina so ki iya".. Imaan ta gyada "to ki bari sekin girma kinji" imaan ta gyada kai cike da jin dadi.. Mommy taita janta da fira imaan da shegen surutu tuni ta sake.. Seyiwa mommy tambayoyi take.. Ita kuma ta bata amsa.. Hakan yasa imaan ke fahimtar wasu abubuwan.. Wani babban boutique sukaje.... Siyayya sosai mommy ta rinka yi mata na kaya babu abinda bata siya mata ba na kayan sawa.. Imaan bnd murna babu abinda takeyi.. Bayan mommy ta biya an saka masu a mota snn suka wuce super market inda mommy ta siya mata man mayamaye na shafawa da turaruka daidai shekarun ta. Snn ta siya mata kayan ciyeciye.. Imaan dadi kamar me ta damke hannun mommy tana tayi mata surutu mommy na biye ta..daga nan mommy saloon ta wuce da ita ta saka aka kwance kitson kanta aka wanke mata dogon gashinta me cika snn akayi mata kalaba me kyau.. Kukan da imaan tayi da ana kitson ba'a magana  dan ta tsani a taba mata kai.. Aikam tayi kyau sosai.. Amma taki yarda a tufke wai zafi dole aka sakar mata kanta.. Haka suka dawo gidan mommy ta zauna da kanta ta shirya mata kayanta ta aje mata komai inda ya kamata da dakin nata da mommy tace nata ne.. Mommy ta nuna mata komai yanda ya dace snn tasaka tayo wanka ta shirya cikin daya daga cikin kayan da mommy ta siyo mata.. Mommy masha Allah kawai ta furta tana kallon yanda kyau imaan ya sake fitowa.. Tayi mugun kyau cikin riga da wandon baby pink color se yarintar ta ta sake fitowa.. Abba na dawowa imaan taje tana basa lvrin kayan da mommy ta siyo mata.. Ganin yanda yarinyar ta sake tana farin ciki shiyasa shima yaji hankalin sa ya kara kwanciya.. Yaja chick dinta "yarinya er' mommy and next upper Monday zaki tafi sch.. But before then gobe lesson teacher zezo seya fara koya maki karatu na 1week kafin ki tafi... " sosai imaan taji dadi ta fada jikin Abba cike da murna se kuma ta tashi ta haye stairs domin taje ta kara ganin dakin ta dayayi mugun yi mata kyau.. Ya kalli mommy yace "Allah yayi maki Albarka".. Tayi murmurshi tayi tace "wace sch ka samomata".. Abba yace "nan malali FGC kaduna".. Mommy ta gyada kai.. "Good yayi kasan dama I preferred federal schools din nan sbd su komai nasu da tsari gashi babu wasa".. Yace "sure hakane wnn"... Washe gari sabon lesson teacher din imaan ya fara zuwa yakuma fara koyar da ita.. Imaan ta natsu sosai sbd tanason karatu shi kansa duk da yaga akwai gyararraki a karatun nata ya fahinmci tana da kwalkwal wa. Kasancewar ba bahaushe bane yasa imaan abin keyi mata wahala sbd da turanci yake mata bayani.. But bayan ya tafi suka zauna ita da mommy ta kara fayyace mata komai.. Hakan yasa mommy dagewa wajen ganin ta koya mata turanci domin shi speaking abu ne da zaka iya kare kanka a ko ina.... Mommy denayi mata hausa tayi haka ma Abba. Da farko imaan find it very hard but yanda suke mata yanda zata gane yasa ta fara ganin saukin abun tuni har itama ta fara kokarin maida masu.. Sbd sharpness din brain din tata tuni komai ya fara zauna mata akai...

Satin Imaan daya amma idan kaga yanda ta koma baka taba cewa daga kauye ta fito.. Wato hutu natsuwa da samun abinci me kyauma wani abu ne daban... Ta kara wani kyau hasken skin dinta ya kara fitowa kyauwunta ya wani bayyana sosai.. Harta maganar ta ta sauya har ta fara sabawa da turanci dan babu maganar hausa ynx kam ita da hausa se a cikin zuciyar ta amma bade a baki ba.. Dan su Abba ma sun hanata.. Imaan tayi missn abubuwa da yawa kamar rashin jin da suke wanda anan babu dan uwanyi da kuma babanta su jummala kai ko daya batayi kewar su ba.. Ranar suka kara zuwa kasuwa aka sakeyi mata siyayya.. Kunsan yanayin federal sch ko Maggie ba'a yarda kaje dashi ba duk de wani abu daya shafi girki. Sede irin su madara cornflakes golden morn su chocolate drinks biscuit da sauran kayan makulashe domin acan ana bada abinci lafiyayye kuma no Bullying  snn kuma akwai dokoki da tsaruka lafiyayyu duk wata federal sch haka take. Ko wace state akwai kamar biyu ko uku wasu boy and girls wasu kuma girls only.. Maganar karatu kam ba'a magana tunda federal government akace....

Ranar saturday mommy ta gama hada mata dukkan kayan ta a cikin boxes din nata komai ammata na er' gata imaan dake zaune saman kujera cikin wata ash doguwan rigar data karayi mata kyau se hade rai take.. Mommy tace "what". Tura baki imaan tayi kamar zatayi kuka tace "mommy bana son zuwa I want to stay with you" murmurshi mommy tayi "bnd abinki shi dama ai haka dan boading yake da kinje zaki manta damu ki kama harkan gabanki".. Imaan ta tura baki.. Kawai har bata so gobe sunday tayi dan Abba yace sunday zata tafi.. Washe gari jikin ta duk a sanyaye ta tashi mommy na kula da ita amma ta share ta Abba ne ma me dan janta da fira.. Suna gama lunch imaan ta shirya cikin house wears dinta.. Ta fito tym din har an kai kayanta mota.. A parlo ta iske su abba nan sukayi mata fada sosai akan tayi karatu sosai bnd abokan bnza.. Fashewa da kuka imaan tayi.. A dan zaman da tayi dasu ta saba dasu sosai sbd yanda suke janta a jiki tana jinsu kamar iyayen ta... Abba ya kama hannun ta sukayi gaba Mommy already ta fita dan bata so imaan taga kukan ta.. Mommy ce tayi driving dinsu har sch.. Aka mata checking snn Abba ya hada ta da guardian ya basa kudin ta akan duk abinda take so taje ta tabayeta snn ya hadata da seniors ss2 da kuma ss3.. Ganin yarinya me kyau yasa duk suka amsheta da hannu bibbiyu.. Itade imaan se kuka take.. Mommy ta rungume ta tana lallashin ta before Abba ya Kama hannun ta su fita....

Er ss3 din ta tafi da ita dakin ta kowa ya ganta se yace ina kika samo wnn yarinya me kyau haka.. Aike tayi ta saka a kira mata wasu yara.. Yaran na zuwa cike da surutu suka gaisar da senior din tasu tace "ku ynx de ga frnd na samar maku class dinku daya dan haka duk inda zakuje ku tafi tare amma wlh idan kuka koya mata rashin ji sena saba maku... Duk dariya sukayi mu mun isa amma aunt ina kika samo wnn fne gal haka.. Tace "bn sani ba".. Duk da turanci suke magana kasancewar sch din ba'a hausa or any languages excluding English and French sune ba vanacular ba.. Imaan tanajin su duk da tasan wasu abubuwan dole suyi mata wahala.. Daya daga cikin su tace "ynx de ki bamu ita muje room dinmu lets show her to our mates mun samu new comer wnn ita zatana yi mana Queen a hostel din nan".. Aunt tace yusrah kimun shiru.. Maryam gata nan kuje amma bnd mugunta nasan halin ku.. Maryam tace "haba babu case.. Suka kama hannun ta sukaje.. Daga ganin yaran kasan yaran manya ne.. A hanya suka mata introducing kansu.. Anan taji ma duk a abuja suke karatu kawai suke ana.. Room dinsu sukaje sukayi introducing dinta ga sauran yan mates dinsu nan kowa ya shiga yi mata welcome.. Taji dadin yanda suka tare... Nan su yusrah sukaje suka kwaso kayanta.. Bayan sun shirya mata komai a inda house captain ta bata.. Suka shiga nuna mata komai da kuma tsarin sch din wanda already duk ta sani.. Har books din da zasuje class dasu gobe seda suka nuna mata.. Ta kula suna da surutu amma kuma suna da maida hankali.. Shine ma dalilin dayasa aunt ta hada ta dasu.. Da sukaje je dining cin abinci da daddare ne ta hadu da mazan class din su kowa se welcome yake mata.. Wani da yusrah ta gama introducing masu yace "and ynx mu zama mu biyar ya kalli imaan yace am farouq and he's muneer ya nuna na gefen sa "kinga mu hudu ne a group din mu ni muneer yusrah da maryam.. Muna rashin ji but muna karatu sosai fa so zaki shigo cikin mu kema ko kina so ko bakyaso we're all frnds tun muna primary muke a abuja" murmurshi kawai imaan tayi domin ba karya kawai sun birgeta domin ko yanda suke speaking ma abun kallo ne kuma daka gansu kaga yaran manyan mutane..

Tun imaan bata sakin jikinta dasu yusrah har ta saki domin ko ta kula su babu ruwansu kusan irn halin su daya suma basajin magana amma suna karatu sosai tuni imaan ta ware ta shige cikin su kuma duk abinda bata sani ba sunanuna mata kuma tana ganewa.. Sosai suke natsuwa su nuna mata duk abinda bata gane ba se gashi cikin lokaci kankani kanta ya ware ta dauki abubuwa dayawa a game dasu yusrah da maryam harma dasu farouq da kuma wajen aunt dinta sch din ta hada mutane daga wajaje daban daban na cikin kasar. Tuni bakin imaan ya saba da speaking ta kuma kara koyon maganar rashin ji kau sede abinda yayi gaba though wnn shi cike da natsuwa da wayewa suke abinsu.. Duk visiting su Abba na zuwan mata basu bari tayi rashin komai ba.. Itama ta dage tana karatu sosai sbd kyan ta shiyasa take da farin jini kowa yana sonta bare ma tana tare dasu maryam.. Baka taba cewa imaan ce tada fito daga kauye.. Sbd yand ta maida hankali shiyasa ko a exam bata sha wahala ba.. Kuma ta fito da result me kyau suka amshi number juna ita dasu maryam dan su rinka gaisawa.. Koda akayi hutun bata koma kauye ba se abba ya sakata a islam dama tayi nisa seta jona daga inda ta tsaya wanda datazo hutu zata rinka zuwa. Koda suka koma sch second term imaan bata wani sha wahala ba dan ynx itama har zata iya zaunar da wani ta nuna masa abinda be gane ba.. Hutun second term ma bataje gida ba.. Idan kaga imaan sak irin yaran yan gayun nan wanda ke mugun jin dadi.. Su mommy sunaji da ita sosai suna bata kulawa kuma alhamdullh komai nata ya canza ta kara kyau.. Koda suka gama js1 imaan na cikin daliba masu kokari.. Itakam taji dadin haduwa dasu farouq domin kau a set dinsu suna daga cikin dalibai mafi hazaka itama ynx ta shiga daga cikin su ana damawa da ita....

Urs

✨✨✨

Annafie😍

Any one reading this book should knw that its not for free its just #300 pay through the Account below
2148886852 Nafisa Abdulbasir and show ur evidence via this number 07051376476.. But for now enjoy the free pages😊 thank you Annafie loves you all 🥰❤️as you keep supporting me encouraging me as I keep suburbudo maku novels masu dadi 🥰
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/H27abREXIQn8Rp0DbZBhE2*💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫*
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
         *ANNAFIE💖…✍️*
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
💫💖Jalal Ali(5)💖💫💫.

Mommy ta kalli imaan dake zaune saman daning rike da wayar ta suna waya dasu yusrah compress call suke se labarin sch suke cike da nishadi da yarinta.. Ynx imaan suka duka bata wuce 13 yrs ba har tayi shekara daya amma kamar anan aka haifeta komai nata ya canza sosai su mommy suke nuna mata so da duk wani kulawa na dan gata itama shiyasa take masu shagwaba son ranta tanajinsu kamar iyayenta.. Duk da tayi kewar su Baba bata yiwa abba maganar zuwa kauyeba.. Dukkuwa da tana so taje dan harsu jummala tayi kewar su.. Bayan sunyi sallama mommy tace "zaki natsu kici abinci ko senayi maki dure.. Kwanan na naga duk kin rame se uban tsawo da kikeyi".  Kamar zatayi kuka tace "mommy bafa rashin cin abin ci bane da kike tamun dure . ance wai ynx tsayi zanyi.. Ta fada tana washe baki".. Mumushi kawai mommy tayi.. Wnn hutun ma haka ta koma bata je kauye ba.. Seda ta dawo hutun js2 second term snn Abba yace ta shirya suje.. Sosai imaan taji dadi.. Har ta kosa taje taga su kuluwa wlh da talatu.. Kaya kala daya Abba yace ta dauka sbd katsina zasuje shida mommy kuma tafiyar ta kwana dayace dan haka zasu ajeta ta kwana daya idan zasu dawo se su dauke ta.. Ko daya bayaso taje ta dade sbd ya tsorata da abinda su Nana sukayi mata.. Murna sosai imaan tayi.. Cikin kayan ta ta dauka ta zabar wa su kuluwa da talatu snn da hurera.. Su abba de se binta da murmurshi..

imaan ta cewa su mommy tayi bazayi bacci ba har su sauka amma ina tuni bacci ya dauke ta.. suna isowa garin yara suka fara bin motar har seda suka kawo kofar gida Abba yace wa mommy tashi diyar taki.. Mommy tace "my daughter".. Imaan ta bude fararen idanun ta masu cike da bacci ta kalli mommy se kuma ta wartsake da sauri tana kallon garin su da babu wata canzawa da yayi.. Bude motar tayi ta fita da sauri hango yaya auwal da tayi.. Fadawa jikinsa tayi cike da murna.. Da farko yaya Auwal be gane ta ba amma jin muryar ta data kara taushi ya gane ta.. "Imaan kece haka".. Tayi murmushin daya kara fito da kyanta.. Hurera da tazo fitowa rike da tray din tallar ta ta tsaya tana kallon imaan .. Imaan ta karasa da sauri bata damu da yanda take ba ta rungume ta.. Hurera kam wani Abu ne ya tsaya mata a wuya fara ture imaan tayi.. "Malama lafiya wai ji wani munafurci".. Tabe baki imaan tayi kafin tace "ke ta shafa ni ynx banda tym dinki".. Ta nufi cikin gidan.. Adda na kofar dakin ta haka ma Abida da jummala duk suna. Zaune tsakar gidan.. Dukkan su babu wanda ya gane imaan sede binta suke da kallo ganin wata farar yarinya medan tsayi tana shigowa.. Da gudu imaan takarasa wajen Adda.. "Adda oyoyo".. Duk mikewa sukayi lokaci daya kuma suka gane ta.. Imaan ta rungume Adda.. Adda kam kallon ta take.. Se kuma can ta washe baki "imaan wai kece haka kamar baturiya".. Imaan tayi murmurshi.. Jummala kam tuni taji hankalin ta ya tashi Adda tace "kai Allah me iko ynx imaan kece haka? Ashe dama muna da irin larabawa bamu sani ba".. Imaan ta washe baki.. Babane ya shigo tare da Abba se mommy dake rike da er karamar bag din imaan wacce ta sanya kayan ta kala daya sena bacci.. Se kuma jakar data zubo masu tsaraba.. Jummala ta dauko tabarma da sauri imaan kam ta tafi wajen baban ta cike da murna dan tayi kewar sa shima yayi kewar ta kuma har ransa yaji dadin yanda yaga ta canza.. Zuciyar jummala na tafarfasa ta kawo masu ruwa bayan sun gaisa.. Abida kam haushi kamar me ko kallon imaan batayi ba kamar yanda itama batabi ta kanta ba.. Hurera kam daki ta shige tana kuka itama wlh setaje birni...

Suna nan zaune sega su talatu da kuluwa da gudun su jin ance imaan tazo.. Suna shigo imaan taje ta rungume su se ihu suke suna murnar ganin ta... Adda ta tabe baki.. Kafin tace.. "Dubi dan Allah yara duk baki sunzo sun mamutse ta.. Dan Allah yaushe yaran nan zasuyi hankali.. Har fa girgan dangi sun fara.. Ita imaan dince ma gatanan ko farawa batayi ba babu abinda ta kara se uban tsayi se kuma fari bau.."..  Tura baki imaan tayi tana hararar Adda suma su kuluwa haka.... Abba basu wane dade ba suka fara shirin tafiya sbd a hanya suke.. Abba yana kallon imaan yace "we will be going dear take care".. Ta gyada masa kai.. Mommy ta shafa kanta . "take care my daughter i will miss you".. "I will miss more mommy".. Murmurshi mommy tayi.. Jummala ta tabe baki.. Adda kam washe baki tayi tace "nide inaga imaan ta dawo baturiya to komai ta canza malam".. Har mota ta raka su abba ita da su kuluwa bayan sun tafi snn ta shigo.. Adda ta kama hannun ta muje akwai fura a daki na dama maki.. Cike dajin dadi tace "to Adda".. Adda ta rike haba.. "Oh ni wai imaan ce haka se naita ganin kamar mafarki".. Imaan bata ce komai ba.. Duban su kuluwa Adda tayi.. "To sufa wadan nan bakaken mutanen nide bakiran su nayi ba" kamar imaan zatayi kuka tace "kai Adda".. tabe baki Adda tayi "keni bansan kilibibi irin na yan birni in zaki gane wadan nan ba kalarki bane ki gane".. Tare sukasha furar dasu kuluwa suna ta bata lvrn abinda ya faru da bata nan itama ta basu lvrn makaranta.. Anan ne takejin wai an saka bikin Abida data lissaba setaga tym din bikim suna hutun jsce dan haka zatazo.. Ta firfito masu da tsarabar su.. Ta basu suka karba cike da murna sukaje suka kaima su jummala nasu ko kala basu ce mata ba bare ngd.. Dan wani irin bakin ciki jummala takeji ganin yanda imaan din ta koma.. Dan ita da ta dauka idan taje er aiki zasu mayar da ita.. Wlh ta tsani duk wani cigaba da yarinyar nan zata samu yanda ta tsaneta ko uwarta bata tsana haka ba...

Tare dasu kuluwa sukaje gidan umma.. Sosai umma tayi farin cikin yanda ta koma dama tanajin lvrn sunzo ta saka aka siyo mata kifi tayi mata taliya suka zauna sukaci.. Ita kanta tasan tayi missing su kuluwa da daddare da sukace tazo su fita se cewa tayi aa dan batajin zata iya wnn yawon.. Yaya abbakar har gidan yazo.. Har ynx imaan najin kunyar sa dan haka ta kasa sakewa dashi tare dashi suka koma gida shi yarakata.. A lokacin tasamu damar fira da baban ta da kuma yaya Auwal.. Daga nan kuma ta tafi dakin Adda domin kwana acan sbd bama zata iya zuwa dakin su ba ynx dan yanda taga jummala da yaranta suna cika suna batsewa tasan zasu iya mata duka.. Itakam bawai tabar rashin ji bane.. Aa duka ne jikin ta baze iya dauka ba sbd ta kwana biyu bata sha ba.. Kafin tayi bacci seda sukayi lbr da Adda .. Adda tace "wnn matar uban nata bakin ciki yayi mata katutuwa kina ganin tunda kika zo batada walwala se bakin ciki ya kashe ta lokacin da kika samo miji acan" dariya kawai imaan tayi..."..

Washe gari da safe sega inno tana kallon imaan seda hankalin ta ya tashi.. Sama sama ta amsa gaisuwar imaan dake brush ta shige dakin jummala... Nana ma ta samu lbrn zuwan ta tanaso tazo ta ganta amma tsoran Baba take..

Su Abba ba dawowa suka biyo suka dauke ta.. Ta baro cike da kewar su duk da yan uwan nata mafi kusa babu wanda ya kulata..

Hutu na karewa suka koma sch ta cigaba da maida hakali sosai wajen karatu.. A ynx imaan tana daga cikin student masu kokari dan ynx ko competition za'ayi harda ita a ciki.  Inde babu ita akwai daya daga cikin su frnds din nata.. Dama kunsa yanda federal sch suke suna hada competition tsakanin duk wasu sch dake cikin Nigeria.. Imaan taga gurare daban daban kuma ta kara fahimtar abubuwa. .  a haka har sukayi hutun jsce.. Wnn hutun data samu ya kara mata kusanci dasu mommy sosai.. Dan duk inda mommy zataje tare suke zuwa.. Ynz kam alamun girma sun fara bayyana a gareta ta zamo mace shafe dinta sun fara fitowa ga skin dinta ta kara wani kyau da daukar ido ta zama wata er gayu ga wani irin kyau da natsuwa a tare da ita jikin ta se murjewa yake karayi.. Kamar yanda tace zataje bikin Abida taje Abba ya hada ta da driver ya kaita.. Yanda imaan ta zama abin kallo ba'a magana duk wasu wadan da suka san suna sonta a da ynx sun san tafi karfin su.. Kamar yanda tayi tsammani bata wani samu tarba me kyau daga wajen yan uwanta ba.. But ita ynx a ganin ta yakama wnn abun duk su dena tunda ita ynx taga ba kalar rayuwar da ake knn ba sede abinda bata sani ba tsanar da suka mata ynx tafi ta da dan ynx harda hassada..har gobe yaran inno da jummala bazasu taba sonta ba.. Yanda sukaki kulata se abin yayi mata ciwo sbd ynx ta fara sanin ciwon kanta. Sunnuna mata ita bare ce abun yayi mata ciwo amma seta danne.. Yaya Abbakar kau ynx ya rigada yasan imaan tafi karfin sa dan haka yaga ya dace ya nemi wata.. Shide ko zata cigaba da karatu ta tsaya a iya secondary baya so taje jamia sbd yana jin lvrin yan matan jamia dake birni.. Bikin nan ko daya beyiwa imaan dadi ba sbd taga total wariya daga yan uwanta shiyasa Abba na zuwa daurin aure daze tafi ta bisa . se taji gaba daya garin ya fita a ranta barin ma da kowa cikin yan uwa keyi mata maganar aure.. A wajen su Abba ita karamar yarinya ce sosai amma meyasa nan suke mata haka ita ynx karatune ma gaban ta. 

Tun daga lokacin imaan bata sake zuwa ba.. Tana ss2 first term akayi bikin su kulawa ita da ya Abbakar amma bata samu zuwa ba sbd tana sch duk da taso tazo.. Seda akayi yi hutu kam snn ya hada ta da driver ya kawota su koma tare Dan ba kwana zatayi.. Ba har gidan kulawa taje.. Kuluwa tayi murna sosai dan ta dade bata ganta ba..kuluwa tana kallon imaan da tayi wani kyau gashi ta zama wata cikakkiyar budurwa dan dukda bata da kiba jikinta a murje yake snn komai cip hips dinta da boobs komai ya ciko a tym din 17yrs zata cika amma seka rantse tayi 19 duk da kallo daya zakayiwa kyakkawar fuskar ta ka gane shekarunta.. Kuluwa tace "kawata amma de aure zaki kusa ko".. Imaan ta girgiza kai.. Dan ita ynx ma planing din da suke su rubuta exam a ss2 din nan su shiga university.. Jin haka yasa kuluwa fadin "kai kinga kawata ance matan jamia bnd iskanci babu abinda suke".. Imaan ta girgiza kai.. "Inde har ka kama kanka babu abinda ze same ka kede kawai kiyimun addua.. Nan suka zauna suna ta lvri imaan na kara bata lvrn yanda sch take.. Ta bata tsarabar ta da abinda ta kawo mata snn taje gidan talatu nan ma de lvrn ne kuma duk sun natsu kamar ba marasa jin magana ba....

Se wajen karfi biyar snn suka fito zasu tafi.. Adda ta rako ta.. Duk da jummala bata kulata ba taje tayi mata sallama .. Wata harara jummala tayi mata kafin taja tsaki tace "dallah bace mun anan kinje kina ta rayuwar karunwanci zaki zo kina dage mana kai ko an fada maki bamu san abinda kike ba" kalmar tayiwa imaan nauyi kuma tayi mata zafi dan haka bata san sanda tace "karuwanci ya kare a kanki er hassada kawai".. Daga haka ta fice Adda dama tayi gaba.. Cike da bakin ciki tace zakiga karuwanci atoh.... Imaan ji tayi duk haushin garin takeji dama Abba baso suke tazo ba itace ta matsa.... Ta koma gida da kwana biyu lokacin ana gobe zata koma sch suna zaune suna breakfast Abba yace "kun yanke sch din da kuke shirin zuwa ne".. Ta girgiza kai tace "no Abba but inshaallah idan mun koma sch zamu yanke".. Ya gyada mata kai.. "My daughter my barrister don't worried kinji duk sch din da kuka yanke ki fada mun inshaallah Zan samo maki admission just feel free".. "Thank you Abba na".. Murmurshi mommy tayi cike da jin dadi..

Koda suka koma wnn term din sun cigaba da shawara akan makarantar daya kamata su tafi se kuma akaci sa'a duk ra'ayinsu daya duk low suke son karanta.. Zaune suke a field duk su duka biyar din duk cikin kayan sport.. Suna dan ball suna wasa duk de cike da shiririta.. Can dai muneer ya aje ball din snn yace "guys you knw what?" Duk kallon sa sukayi.. Yace "about the sch".. Farouq yace "munajin ka".. Muneer yaci gaba "a kwai wata sch da mukayi magana da Dad dina.. Sch din private ne but akwai karatu sosai karatu suke sosai fa sbd just 3yrs ne zaka samu bsc certificate but for low student se ka karo karatu na 1yr idan kana so zaka iya jonawa tare da sch din but a abroad ne can Canada tunda dama makarantar a canada yake nan ta cikin Abuja branch ne kawai.. Kuma da karatu sosai kunga idan muka tafi sch din cikin 4yrs mun hada law din mu but ya kuka gani".. Maryam tace "sure nasan sch din akwai karatu sosai kuma makarantar nada kyau though naga basu da hostels but a kwai apartments a waje student suna kamawa kuma duk kusa da sch ne.. Farouq yace.. "To mu yanke ta kawai lets talk to our parent about the sch".. Hakan kau akayi.. Imaan ta dauka abba baze Amince ba sbd taga baya son zuwa Abuja seda babban dalili amma se taji ya amince.. Duka kowa ma ya amince cikin iyayen nasu dan duk sun san juna dasu Abba sbd suna haduwa wajen visiting...

Kamar wasa suka fara karatun exams har suka fara yau gashi har sun gama.. Kasan cewar sun san sch daya zasu tafi shiyasa basu wani damu ba sosai. Sede fatan suci exams....

Kamar yanda suke addua exam ta fito kuma duka sunci.. Ana fara raba admission Abba ya kawo mata nata da Dad din su muneer ya samo masu gaba dayan su.. Tayi murna sosai ta rungume Abba tana murna.. Ya mika snn ta koma ta rungume mommy Abba ya mika mata wani kwali yace "ur phone".. Imaan ta zaro idanu with so much excitement se kuma ta rungume mommy tana murna.. Mommy tace "ynx de wayata zata huta".. Imaan ta rufe fuska.. Abba ya bata sim.. Wayace me tsada sosai irn wacce ake yayi Kasancewar ta iya waya se kawai tayi setting komai taci gaba da amfani da abarta.. Su yusrah suna ta tsokanar ta wai mutuniyar an faso wayar mommy ta huta...

Imaan bata taba zuwa Abuja idan ba daga sch ba se wnn karon shima sede idan wata sch zasuje kuma iya karsu sch din snn su koma.. Yau taga garin sosai kuma kuma tayi kyau.. Har set dinsu sun fara zuwa an fara lectures sune dai se ynx suke clearance makarantar ta hadu sosao daka gani kasan yaran manya manya ne a sch din dan harda ma wasu yan kasashen daban daban.. Bayan sun gama da sch sukazo suka kama apartment su muneer kowa daban daban ya kama su kuma suka kama daya su uku.. Apartment din yanada kyau sosai komai na more rayuwa akwai sa snn suka shiga kasuwa sukayi siyayya daidai da cokali seda suka tabbar sun siyesa.. A gidan su yusrah ta kwana washe gari suka idasa suyayyar ta koma kaduna tare da driver.. daga nan ta fara shirye shiryen tafiya ana saura kwana biyu tafiya suka shirya su duka zuwa kauye.. Wnn karon ma kamar koda yaushe zuwa akai tayiu kallon ta..se aka fara tsegumi wai yarinya takai shekara 18 amma babu aure anje an kaita birni to zaman me take har ynx maganganu de iri iri marasa dadin ji... ".. Bayan Abba ya gama zaiyane waya Baba komai akan makaranta da zata fara ya sauke numfashi yace "duk yanda ka yanke akanta daidai ne babu abinda zance da kai se godiya.. Zainab erka ce na baka ita halak malak".. Adda tayi saurin cewa "mamman bnfa gane ba.. Wnn wane irin karatu har ynx ba'a gama ba macece fa.. Shekara shatakwass kana ganin Hurera ana ta magana batayi aure ba shekara sha tara snn itama wnn so kake ka jawo maganganu".. Baba yace "ai kalar tasu al'adar knn" tabe baki Adda tayi "bokon me ana zaune kalau.."..

Jummala data fito daga daki tace "nima haka na gani Adda"wani kallo Baba yayi mata hakan yasa tayi shiru ita de imaan kanta na kasa.. A haka suka taho bayan taje tayiwa umma bn kwana.. Haka nan Abba yaji.. Baya so dan ynx imaan ta sake zuwa sbd yawan maganganun da sukeyi....

Ranar da zata tafi sch Abba da mommy fada suka rinkayi mata sosai na nasiha suna nuna mata ta tsare mutuncin ta snn kuma karta canza daga halinta wanda yasan ta dashi... Shida mommy suka kaita har makarantar har dakin ta imaan se kuka take.. Already dama su maryam tun dazu ka iso....

Urs

✨✨✨

Annafie😍

Any one reading this book should knw that its not for free its just #300 pay through the Account below
2148886852 Nafisa Abdulbasir and show ur evidence via this number 07051376476.. But for now enjoy the free pages😊 thank you Annafie loves you all 🥰❤️as you keep supporting me encouraging me as I keep suburbudo maku novels masu dadi 🥰
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/H27abREXIQn8Rp0DbZBhE2*💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫*
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
         *ANNAFIE💖…✍️*
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
💫💖Jalal Ali(6)💖💫💫.

Kamar yanda suka tsara cewa karatu zasuyi sosai haka suka dage da karatu sun maida hankali sosai.. Kamar yanda kukasan yanda rayuwar university take mutane masu halaye daban daban zaka gani kuma kowa kalar rayuwar dayaga dama ita zeyi sede idan ka tsare mutuncin ka.. Su imaan sun fuskanci wadan nan kalubalen barin ma wnn data hada yaran manya manyan masu kudi.. Su imaan abinda sukeyi kawai ya kaisu wato karatu sede dan rashin jin da suka sabayi.. Kuma ynx kansu ya kara waye wa. Amma duk da haka basu manta da abinda ya kaisu ba.. A haka har suka kammala hundred level.. Sun zama wasu big girls ynx yan gayu irin classic ladies din nan gasu kyawawa.. Idan kaga yanda imaan ta zama bakayi mata kallo daya ka dauke kai ta zama wata irin cikakkiyar mace wacce duk wani namiji meji da kansa yake da buri bata da wata kiba amma ba siririya bace domin tana da wata irin sura me jan hankali.. Kuma akace farar mace alkyabar mata.. Tanada wani irin haske me saka natsuwa ga duk me kallon ta ga kuma kyan fuska imaan wata irin kyakkyawace kamar wacce ta hada iri da larabawa ga uwa uba gayu ta iya daukar wanka.. Ko fita tayi a sch dayuwa ne ba'a biyo ta ba.. Dama imaan babu jin magana ta iya latsa gayu gashi Idan mutum na sonta seya like mata kamar chewing gum itakam ta iya gara samari..tanada wani abu da ko kallon namiji tayi se yaji jikin sa ya mutu amma ko dame kake yawo bazata taba sake maka ba dukan su haka suke.. Wani lokacin farouq yakance.. "Madam a rinka dagi mana" sede kawai suyi dariya kuma karatu suke sosai.. Dan koda result dinsu ya fito sunada saka mako me kyau.. Ita kanta Mommy wani lokacin idan ta kalle ta se tace masha Allah seta kara gode wa Allah dayasa ta rabota daga kauye da ynx kila anyi mata aure.. Ita ma ynx ko maganar can akai mata se taji bata son zuwa.. Gaba daya ji tayi ta tsani garin ynx.. Ko a hutun nan da Abba ya mata maganar zuwa cewa tayi aa.. A hakade ta cinye hutun ta ta koma 200 level...

✨✨✨✨

10:46am.. Haka agogon dake jikin bangon parlon ya nuna.... Magidancin mutumin dake zaune a saman dining din da aka kayata da kayan more rayuwa ya sauke idonsa daga kan agogon.. Kyakkyawan mutum ne wanda yadan manyan ta Amma tsabar hutu da jin dadi yasa baka gane hakan.. ALH ALII ABBAS knn babban dan kasuwa kuma me kula da duk wani shige da fice na kasuwanci a kaf cikin Nigeria.. Mutum ne wanda yake da manya manyan company's cikin da wajen kasan nn snn yanada tarin dukiya wanda ni kaina bazan iya kayyadeta ba.. Sannanen mutum ne wanda an sansa sosai kuma gwamnati tana damawa dasu.. Ya sauke idanun sa akan matar dake zaune a dinging din suna fuskantar juna tana sanye cikin wasu kaya na alfarma se daukar idanu take alamar hutu ya zauna.. Kara kallon Agogon yayi snn ya kalleta.. Cikin muryar sa me cike da dattaku yace "JALAL fa ya fito".. Dan murmurshi tayi tace "aa gsky inaji har ynx be tashi ba... Mikewa Alh Ali yayi yana dan murmurshi kinga bari kiga naje ta tasosa dan nasan halinsa.. Tashi yayi zuwa cikin parlor wanda yaji kayan more rayuwa snn ya nufi wata kofa wacce ta sada shi da wani part daban.. Shima wnn parlor ne wanda aka zuba dukiya dukda be kai wancan girma ba amma an kayatasa wanda da ka gani kasan meshi dan gata ne.. A gyara yake tsaf very silent ga haske bnd kamshi babu abinda ke tashi.. Stair ta nufa ya fara hawa.. Ya tsaya a corridor me dauke da dakuna uku... Dakin da yake tunanin dannasa na ciki ya murda kofar dakin a bude yake ya tura ya shiga.. Dumdin dakin baka ganin komai se Ac da aka kure dakin ya dauki  wani irin sanyi ga kuma daddan kamshin turare me kwantar da hankali ya bude ko ina.. Da sauri ya nemo switch din dakin ya kunna lokaci daya dakin ya dauki haske.. Bedroom ne aka kawata shi sosai ta yanda ze birge duk wani me kallon sa.. Alh Ali ya gama bin dakin da kallo kafin ya sauke idonsa a akan bed din dan nasa.. Murmurshi yayi ganin yanda dan nasa ya kudundune a  cikin white duvet din me shegen taushi ko fuskar sa baka gani se bakin gashin kansa daya leko .. Dady ya karasa ya zauna gefen gadon kafin a hankali yace "son".. Jin shiru be ko motsa ba yasa yayi kasa da duvet din yana kallon kyakkawar fuskar dan na hannu yasa cikin gashin kansa yana shafawa zuwa dan siririn sajen sa daya kwanta lufluf ya wani nannade tsabar yanda yakeda santsi da taushi..ko motsi beyi ba idanun sa a lumshe gashin idon sa ya wani kwanta... ganin ko motsawa beyi ba yasa Alh Ali karayin kasa da duvet din... "Hey sleepy son".. Dan yamutsa fuska yayi ya ciji pink lips dinsa da suka kara ma fuskarsa wani irin kyau.. Kasancewar sanyin AC daya shigesa.. Alh Ali ya rage AC din snn ya juya ga dan nasa yana shafa gefen fuskar sa.. "JALAL".. Dan bude idanun sa yayi ganin haske seya rufe da sauri se kuma ya sake budewa a hankali.. Tar ya bude fararen idanun nasa akan mahaifinnasa.. Cikin cool muryar sa me cike da bacci yace "Dad".. "Yes my son, my sleeping son still on the bed".. Jalal ya juya idon sa ya kalli Agogon dake dakin 11:02am.. Yagani snn ya kalli Dad din nasa yace "buh is still morning Dad".. Dad ya daki shoulder dinsa "common boy namiji baya zama a gado so wake up don't be lazy.. Kasan you're going to rule a whole company not even company company's cos is tym to take over all ur company's I've done mine saura naka"... Dan yamutsa fuska yayi.. "No dad ba ynz ba ni banaso".. Ya fada kamar zeyi kuka... Dad yace "thank you god for blassing me with dis lazy son da babu abinda ya sani se rashin ji but I love you, I love you my only son my happiness".. Murmurshi jalal yayi.. "Love you more daddy".. Dad yace "good ynx de mamanka ta hada maka breakfast a kawo maka nan ko zakaje parlor ne".. Dan yamutsa fuska yayi yana dan hade rai.. "No Dad I will go to granny's place".. Dan shiru daddy yayi se kuma yace "ohk son.. Am going now idan ka gama shiryawa ka kirani I will send drivers su tafi da kai".. Gyada kai jalal yayi.. Peck yayi masa a goshi yana mikewa rabi da kwatan duk wasu kadarorinsa da sunan dansa ya bude sa.. Shiyasa ynx yake son yi masa handing over na wasu company's din domin ya natsu ya zama busy ya rage yawan rashin jin da yake da kuma damuwa.. Dan lumshe idanu Jalal yayi bayan fitar Dad dinsa kafin a hankali ya cire duvet din ya sakko da kafar sa saman lallausan carpet din dake gefen gadon ya kafin ya mike tsaya.. A hankali ya nufi  bathroom dinsa.. Seda ya dauki 20mts kafin ya fito sanye cikin wata milk bathrobe data haska golden skin dinsa.. Wajen cottens din widow yaje ya bude daidai lokacin da motocin Daddy ke fita.. Ya dan lumshe idanu yana cizar lips dinsa na kasa kafin a hankali ya dawo gaban mirrorn sa da yake cike da tsadaddun creams da turaruka.. Wani cream ya dauka ya farawa shafawa skin dinsa me daukar ido a hankali kamar me gudun ji mata ciwo.. Gaba daya a kashe fin rabin hour daga shafan sa zuwa shiryawan sa.. Yayi wani irin kyau cikin bakin hadin me taushi rigar ko gwuiwar sa bata za ba wani irin dinki aka masa me shegen kyau kuma kasan cewar sa fari dukda ba wani sosai ba se kayan suka kara haskasa.. Be saka hula ba se gashin kansa dayasha gyara.. Wayar sa ya dauka se car key kade ya fito.. A hankali yake sauka daga stairs din kamar wani mace.. Hararar kofar da zata sadashi da main part din yayi.. Baya son bi kokada kuma daddy ne yasa a rufe tasa ynx dole seta nan ze rika bi.... Kansa kasa ya fita.. Duk da be daga kai ba yasan akwai mutane a dakin. Suko kamshin sa ya riga ya gama cika masu hanci tun kafin ma ya fito.. "Morning son".. Matar dazu ta fada.. Ko kallon ta beyi ba bare ta saka ran ze amsa da sauri budurwar da bazata wuce 24 ba tace "yaya ina kwana".. Itama be kalleta ba ya nufi kofar fita.. Yarinyar ta kalli matar tace "Mama meyasa yaya Jalal yake haka".. "ware hannu matar tayi "Zulfa kin fa san halin yaron nan ba mutuncin kowa yake gani ba kaf cikin gidan nan kuma babu wanda ya isa yayi magana".. Shiru Zulfa tayi batace komai ba.. Tanajin kamar ta bisa amma tana tsoran wulakancin da zeyi mata.. Babban compound de me dauke da manyan duplex har hudu wanda ko wane babu na banza a zuba dukiya sosai duk da wanda ya fito yafi girma.. Wata er hanya yabi me zagaye da flower yanda flowers din suka zagaye se ya bada wani kyau sosai ko rana bazata dakeka ba.. A hankali ya yake tafiya har ya karasa part din kakar dasa da suke cewa granny....

Tana zaune a parlor ta hamkice idan ka ganta baka cewa ta haifi kamar Dad.. Gefen ta kuma wata budurwa ce da bazata wuce 22 ba tana ganin sa tatashi da sauri ta nufesa ya rungume "morning yayana".. Cin dinta yaja "morning lil sumy".. Karasawa yayi jikin kakar tasa ya rungume ta "morning granny".. "Morning jika hope de kaci abinci".. Ya shafa cikinsa "nop kuma yunwa nake ji".. Dariya granny tayi "ja'iri dole zaka langwabe mun tunda yunwa ce ta koroka idan rashin mutunci ne seka rufe ido".. Yayi murmurshi yana dage gira.. Anan da da nan granny ta saka aka cika masa gaba da breakfast seda yaci ya koshi snn ya kwanta saman ciyar granny.. Wayar sa ce tayi riging ganin Daddy yasa yadan marairaice.. "Hello Dadd"..  "My son wai baka gama ba the meeting is starting immediately after zuhur prayer..".. Jalal na cizar lips dinsa yace "I will be coming my self just send the location dad".. Nan daddy ya fada masa inda za'ayi meeting din.. Sukayi sallama seda ya kara yan mintuna snn ta tashi ya fito duk mutanen daya hadu dasu se sun gaisar dashi amma ko daga kai baya yi.. Wajen da aka tanada domin motocinsa kade ya nufa.. Motoci ne na gani na fada wanda duk daya idan za'a fadi kudinsa seka rike baki.. Wajen wata mota ya nufa wacce a jikin numbern motan an rubuta DEEN8 ya shiga.. Da gudu yaja motar ya babu shiri gate man ya wangale masa gate.. Ya hau titin unguwar tasu da mahaukacin gudu kamar ya samu babban titi..

Ana kiran sallahr azahar ya isa inda dad ya tura masa daya daga cikin mayan company's din da Daddy ya gidanawa dan nasa na sarrafa Auduga wanda sunan JALAL ALI ABBAS nema sunan da ake Kiran company din Jalal alwala yayi ya shiga akayi jam'i dashi.. Bayan sun fito jalal ya gaisa da Dadd din nasa da kuma kanin sa Alh isa Abbas da kuma sauran manya manyan mutane.. Ba tare da bata lokaci ba suka shiga meeting din.. Inda Daddy ya damka masa wnn company din da kuma wasu a hanun dan nasa kuma shi ze cigaba da kula dasu.. Wanda dayawa sunga gangancin daddy nayin haka sbd as yanda kowa yasan jalal bayajin magana be kamata yayi haka ba but shi kade yasan dalilinsa nayin haka ba.... Se la'asar snn suka fito bayan sunyi sallah jalal kuma ya sake zama tare da nashi workers din.. Inda yace masu su cigaba da tafiya da komai kamar da baya so a samu matsala if not zasu sha mamaki.. Kuma he will not resume work for now se sun gansa.. Biyar da wani abu ya dawo gida wnn karon ma su mama na parlor bebi ta kansu ba ya nufi part dinsa fess yake domin yana fita ake zuwa a gyara.. Bed room dinsa ya shiga ya fada saman gadon sa yanajin yanda kansa kemugun sara masa.. Seda aka kira magrib snn ya tashi yayi Alwala ya ya tafi masallaci.. be dawo ba seda akayi ishai part din granny ya tsaya yaci abinci snn ya dawo bathroom ya shiga yayi wanka ya fito ya shirya cikin wasu simple kaya da sukayi mugun masa kyau.  Wayar sa ya dauka ya kunna data da sauri ya danna vedio call ma wata number da aka rubuta mamy.. Ganin ta dauka ya sauke ajiyar zuciya yana kallon fuskar kyakkyawar mata.. Yace "mamy " tace "my son how are you doing".. Dan lumshe idanu yayi "fne mamy ina Mummy na".. Mamy ta amsa da "tana nan lpy kaji" dan langwabar da kai yayi "I want to see her" girgiza masa kai tayi "no son" dan bata so yashiga damuwa ko kadan kuma ganin mahaifiyar tasa ze sakasa damuwa.. A hanakali yace "pls mamy" ya fada cikim sanyi.. a hankali ta gyada kai ta maida back camera.. Gaban jalal har faduwa yake hoping that zega wani cangi a tare da mahaifiyar tasa... Watace gwance akan wani gadon asibiti jikin ta duk na'urori da suke taikama mata.. Runtse idanun sa da suka kada sukayi jawur yayi kullum bashi da wani buri daya wuce Allah ya tashi kafadun mahaifiyar tasa da tunda yayi wayo haka yasanta ta.. Da sauri yayi ending call din yana sauke ajiyar zuciya.. Snn ya dauki car key dinsa ya fita da sauri.. Mama dake zaune a parlor ganin ya fito ze fita tayi saurin fadin "my son don't go out pls is nyt already" kallon ta yayi da jajayen idanun sa yace "mind ur business and take up ur eyes on me".. Yayi gaba se kuma ya dawo.. Yace "am not ur son don't ever call me ur son again go and find another son but not me..".. Daga haka ya fice motar sa ya nufa wacce ya fita dazu.. Seda ya bude ya shiga snn ya dauki wayar sa yy dialing wata number.. Bayan an dauka yace "labib where are you guys".. Shiru yayi kafin yace "send me the location... Babu jimawa labib ya tura masa daga nan ya rufe motar.. Da mugun gudu yaja motar yabar gidan.. Tara saura ya isa wajen.. Da yakeda haske bau kamar da dare ba ga manya manyan motoci parke a wajen.. Fita yayi daga motar yana tafiya a hankali y nufi entrance din wajen.. Kai a hankali yashiga wajen da kai kana ganin sa kasan babu karamin mutum se wane da dan wane.. Gurin beyi kama da na mutanen kirki ba dukda wajen cin abinci ne da wasanni kamar su snooker da sauransu. Maza ne ga mata birjin cikin wasu irin shiga gurin yayi wani silent se yan kananun maganganu ga kuma wata cool music dake tashi ka kamshin flowers dana abinci ko ina... Yana shiga kallo ya koma kansa nan mata dayawa suka shiga gyara yanayunsu suna kallon sa kamar mayu.. Be kalli kowa ba ya nufi inda ya hango frnds din nasa suna snooker Labib da Ak.. Karasawa wajen su yayi labeeb ya basa side Hug “ welcome deen”...Ak ya mika masa hannu suka kashe tare da fadin "wai kaga yanda kallo ya koma kanka.. Man kana dauka wlh ga bebs very classic many are here because of you amma kai kaki ganewa".. Dan tabe baki yayi yana samun kujera ya zauna.. Labib yace "wlh Deen bazaka gane wnn harkar ta  mata akwai dadi.. Yanda mata suka haukace a kanka wlh komai zasu iya maka do you knw that bebs nawa suka tambaye mu kai daga sun ganmu anan kawai".. Tabe baki yayi yana.. Tambayar sa akayi abinda za'a kawo masa.. Ba tare daya kalleta ba yace "wine".. Babu jimawa aka kawo masa wine din da akayi rapping dinta da kansa ya budeta irin cool one din nan ce me tsada bame irin bugawwar nan ba.. Tsiyayawa yy a cup kafin ya kai bakinsa yayi sipping a hankali.. Tare da lumshe idanun sa....

Urs

✨✨✨

Annafie😍

....

Any one reading this book should knw that its not for free its just #300 pay through the Account below
2148886852 Nafisa Abdulbasir and show ur evidence via this number 07051376476.. But for now enjoy the free pages😊 thank you Annafie loves you all 🥰❤️as you keep supporting me encouraging me as I keep suburbudo maku novels masu dadi 🥰
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/H27abREXIQn8Rp0DbZBhE2*💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫*
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
         *ANNAFIE💖…✍️*
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
💫💖Jalal Ali(7)💖💫💫.

A hankali yake sipping wine dinsa yana kallon su labib dake snooker kafin ya daga cup din ya shanye snn ya zuba wata ya shanye ya kara zubawa ya shanye se lokacin hankalinsa ya kwanta.. Ya jingina da kujerar tare da lumshe idanun sa..labib ya dawo kusa dashi ya dafa shoulder dinsa yayi yace "Deen".. Jalal ya bude lumsassurn idanun sa ya kalli labib.. Labib yace "what's up kana da damuwa sosai wine bazata mantar da kai damuwa ba share ur problem with someone.. You knw a problem share is a problem solve".. Jalal ya maida idon sa ya lumshe Ak ya dawo kusa dashi ya zauna yace "mata suna saka kwanciyar but kai baka hulda da mata just wine but ko yaya ne ka fara dating ka ga matan wajen nan ko wacce burin ta kace kana sonta".. Tabe baki jalal yayi kafin yace "girls? Do you say girls?".. Kallon su yayi gaba daya snn yace girls can't solve my problems I will never date any girl infact mata basa gabana".. Labib yayi murmurshi irin ka yi missn din nan.. "Man mata duniya ne wlh you will not understand wlh ko dating kayi zakaji dadi".. Jalal ya tabe baki.. "I have nothing to do with girls I don't think I will love any girl".. Ak yayi dariya.. "Bazakayi aure ba knn". Jalal ya juya fararen idanun sa da suka canza launi ya kalli Ak.. "Sure I wil not".. Labib ya yamutsa fuska kafi yace "look Deen kalli girls din nan I assure you duk wacce kace kanaso cikin su will not think twice zata amince Jalal dubi matan da suke binka fa".. Jalal ya juya idanun sa yana kallon mata kafin ya dauke idonsa ganin yanda suke kallon sa kamar mayu daukar shisha yayi ya fara sha kafin a hankali yace "I will rather die than to love or marry any of these girls".. labib yace "nifa wani lokaci tsoro kk bani lfyr ka lau kuwa" wata harara Jalal yayi masa.. Labib yayi dariya "lyk serious yanda mata ke binka but bakada wani feels nasu" Jalal na hararar sa yace "feelings a jikin wadan nan din komai nasu a bnza cheep gals like them".. Ak yace "you mean kana da feelings knn".. Jalal daya gaji da magana yace "bnga abin feelings a jikin wadan nan ba..".. "Wait kai babu wata kalar macen da kk so ne" Ak ya tambaya... Dan lumshe ido Jalal yayi ya bude kafin yace "Akwai".. Da sauri suka ce wow wace kalar mace kk so.. Shiru Jalal yayi kamar bazeyi magana ba... Se kuma yace "My mum is so simple tana da sanyi kuma tanada hakuri.. Shiyasa suka cuceta.." Ya kallesu.. Yace "I dont want a girl lyk her.. I love a girl that is so stubborn but not selfish.. I love an educated girl both boko and islam wacce tasan mutuncin ta not a girl that is so open, open to all mens not a girl that is so frendly to mens not a cheap girl.. An appreciate girl not a girl that comes from wealthy home na tsani gadara.. And I love a girl that will love me not because of something I have.. A girl that's not after my money a girl that will love me for real.. A girl with pure heart".. Shiru yayi se kuma ya dago. yana dan cizar lips dinsa. Labib yace "tab aikam wnn zamanin babu ita".. "Kaima kasan babu ita gsky".. Jalal yace "kawai wnn a tsarin wacce nake ganin zan iya so ne.. But ku aje maganar mata babu su a tsari na".. Duk kallon sa kawai suke su wani tym din har mmki yake basu.. Seda jalal ya shaneye duka wine din da aka kawo masa snn ya tashi.. A hankali yana dan lumshe idanu dayawan matan wajen suka bisa da kallo suna hadiye miyau shiko ko kallo basu ishesa su labib suna bayan sa tare da wasu beb.. Yana karasawa wajen motar sa ya juyo ya kalli su labib hannu kawai ya daga masu kafin dan yanda suka taho tareda matan nan sun mugun bata masa rai.. hakan yasa ya fisgi motar sa ba tare da yabi ta kansu ba.. Yana driving yana tunanin dad dinsa yasan ynx yana can hankalinsa a tashe.. Cusa hannun sa yayi cikin gashin kansa yanajin ransa  na kara baci yasan Dad dinsa baze ji dadi ba.. Yana cizon lips dinsa yace "am srry daddy.. I can't change the way you want dad.. Am a spoiled child bad boy but is not my fault Dad"... Wata irin hon ya sakar wa gateman dayasa ya bude babu shiri.. Ya shigo da mugun gudu yana gama parking ya kalli Agogo 12 harda minti shida.. "Budewa yayi ya fita ya nufi part dinsu.. Dad ya gani tsaye bakin kofar tausayin dad din nasa ne ya kamashi.. Daddy ya karaso da sauri.. "Jalal bakajin magana ko, baka son farin cikina ko"... Rungume dad din yayi.. "Srry daddy srry pls ur happiness is mine  but daddy I can't change, I can't Dad.. I knw you are worried because god have blessed you with a bad boy lyk me.. Dad am a bad boy dad I just hate my lyf I hate it cos am making you sad" daddy ya rugume sa you're not bad you're my son and I love you".. "I love you too dad".. Shiga ciki sukayi.. Mama na tsaye hankali tashe tace "Jalal my son".. A fusace ya juya yace "keep shout don't ever call me ur son I hate you yes I hate you".. Girgiza mata kai daddy yayi.. Seda ya kai jalal har saman gadon sa snn ya fito.. Toilet jalal ya nufa wanka yayi ya fito daure da towel idanun sa sunyi jajur turare kawai ya fesa ya sauya kaya ya kwanta se bacci.....

Bari na dan baku labarin Jalal kadan nan gaba zakuji sauran labarin though nasan ba lallai ku fahimce ni ynx ba amma nasan nan Gaba zaku fahimce ni... JALAL ALI ABBAS shine sunan sa wanda yawanci ana kiran sa da DEEN.. Matashin saurayi dan shekarar 29.duk da kananun shekarunsa yayi suna sosai wanda ba cikin Abuja kade ba kusan duka jahohin dake cikin Nigeria bawai ansan sa a fuska ba amma a suna.. Wanda Duniya takewa kallon BAD BOY  a very bad boy dan wasu kan kirasa da baddest dukuwa da basu taba ganin sa ba kowane yasan fuskar sa ba amma ansan sunan sa motocinsa da kuma wasu abubuwan da suka dangance sa mutane na masa kallon mutumin da ya fito da munanen halayen sa ba tare daya damu ba wanda suka danganta hakan kila sbd kudin mahaifinsa ne yasa yake abinda yaga dama.. Tunda kowa yasan Alh Ali yasan ya tara dukiyar sa ba kasuwanci ba kuma ba governati ba dan ko siyasa kake idan ka kama Alh Ali to zaka samu biyan bukata baya siyasa amma yanada say me karfi acikin kasar nan.. Wnn ne yasa ake ganin duk Abinda Jalal yake sbd mahaifinsa tsayayye ne shiyasa yake komai son ransa ba tare daya damu da Abinda za'ace ba. Yanda kowa yasan Jalal shine a drunker.. Duk wata harka ta shaye shaye da neman mata Jalal na cikin ta kuma be damu duniya ta sani ba yanada wani irin bad record a idon mutane.. Sbd yanda ake yada maganganunsa a duniya.. Kuma be taba fitowa yace komai ba ba'a kamasa ba kuma ba'a nuna ya dena ba yanda ake yada bad record din Jalal a idon duniya abin ba'a magana dan wasu har tarihin sa tun yana karami sun sani.. Cewa har kisan kai ya tabayi tun yana dan shekara 12.. Na dan uwansa SAIFUDDEEN wanda yake a matsayin twin brother dinsa har prison an kai sa daga baya kuma bayan shekara daya aka fito dashi.. Kuma yana fitowa ya fara shaye shaye.. Tun yana 14yrs yasan giya wanda babu wanda yayi yunkurin kama sa sbd ana ganin mahaifinsa nada kudi daga karshe ma da aka ga magana tayi yawa se aka dauke sa daga kasar zuwa America wanda seda ya shekara goma sha biyu acan.. Dawowar sa tasa ya hadu da wasu gurbatattun yaran masu kudi irin sa suka fara sheke aya ta shaye shaye da neman mata... Wanda aka ce har gidan giya da sauran su duk ya bude amma babu wanda ya isa ya hana yayi komai.. Abinda yake kara bama mutane mamaki shine yanda ya fito da munanen halinsa a fili sunan sa yayi fice sosai duk da basu san sa fuskar sa ba sede idan sukayi la'akari da yanayim kudin mahaifin nasa se suga harda sangarta babu inda zaka tambaya kaji wai ga halin Jalal me kyau.. Kamar yanda kuma babu inda zaka tambaya kaji halin Mahaifin sa Alh Ali mara kyau kowa yasan mutum ne me taimakom talakawa da jin kai.. Amma kuma ga yanayin dansa.. Se kuma wasu su dauka kila irin mugun son dayake wa dan nasa yasa baya iya hana sa duk abinda yakeyi.. Wnn shine kallon da akewa JALALUDDEEN.. Jalal duka yasan da wnn shedar da akayi a kansa kuma be daba fitowa yace beyi ba  duk da yasan ko rabin abinda ake fada bayayi he knows he's a sinner a bad boy but not as bad as they think duk sanda yaga wani lbri akansa sede yayi murmushi yace am not bad but I' will soon be bad.. Komai nasa a fili yake kamar yanda be taba cewa komai akan munanam halin sa da sukayi fice ba.. A zahirin gsky abu daya yasan yanayi wato drinking yes he's a drunker  but apart from that babu wani laifi dayake wanda ake fada bawai yayi shiru bane sbd abin baya masa ciwo aa yana masa but kawai yafiso duk yanda ka dauke sa haka yake.. Sometimes se yaji duniyar gaba daya ta ishesa seyaji mene ma amfanin sa a duniyar but sometimes se ya gane cewa Allah ya barsa ne to take revenge and surely inshaallah Abinda yake fadawa kansa..

Alh Abbas mutum ne me tarin dukiya a wancan lokacin yana da mata biyu haka ma yara biyu Ali dakuma Isa.. Isa na dan shekara 12 mahaifiyar sa ta rasu se mahaifiyar Ali granny ita tacigaba da rike kamar danta ali nada shekara 22 da biyu isa nada 20 mahaifinsu ya rasu yabar masu tarin dukiya.. Yan uwan babansa sukace a raba masu.. Aka raba aka mikawa kowa tasa sukacigaba da karatu da kasuwanci.. Wanda dukiyar su ta kara haba ka.. Tafiya batayi nisa ba isa ya hadu da yan damfara suka wawushe masa dukiyar sa ko sile basu barsa da ita ba.. Ya girgiza sosai dan har ciwo ya kwanta hakan yasa Ali janyo dan uwan nasa a kan tasa dukiyar ta data habaka.. Kansu hade yake sosai.. Allah yasa sakawa dukiyar Ali hannu dan yanda arzikinsa ya haba ka dan yana daga cikin mutanen da ake cewa yaro da kudi.. Tun yana karamin sa ya mallaki dukiya iya dukiya.. Atika ce matar sa ta farko... Tana sonsa yana son ta sede tunda ya aure ta be haihu da ita ba Alh Ali mutum ne me tsananin son haihuwa.. Amma dole ya hakura sbd zaman lpy suke da matar sa kuma yaga ita ma ta damu. kuma ko daya beda niyar kara wata matar amma yana haduwa da fareeda da Allah yasa saka masa sonta yasa ya yanke shawarar karo aure .. Wnn ne ya haddasa husuma tsakanin sa da atika hakika yana son atika kuma yana son fareeda.. Amma irin halayen da Atika ta rinka nuna masa yasa ya rinka mmkin anya itace.. Dan seda ta hanasa zaman lpy....auren sa da fareeda yakara birkita duk wani zaman lpy na gidan dan atika seda ta hana fareeda zaman lpy shi kansa Alh Ali ko baccin kirki bayayi fareeda tana da hakuri dan haka tana jure duk wani Abu da Atika take mata.. Ganin abin bashi da niyar karewa yasa ya saki Atika suka rabu.. Yasha fada wajen granny amma sede ya bata hakuri.. Tafiyar Atika ta wata daya Fareeda ta samu ciki.. Farin ciki wajen family din nan ba'a magana wata tara ta haifu boys dinta yan biyu masu masifar kama da juna.. Wadan dan sune saifuddeen da kuma JALALUDDEEN..Alh Ali yana son yaransa kamar me dan gata yake nuna masu sosai sum taso cikin gata sosai barin yanda arizikin mahaifin su ke kara habaka yana kara fice.. Alh Ali nada makiya wanda besan yana dasu ba kunsan me kudi.. Hankalin. Atika ya tashi sosai ganin fareeda daga zuwan ta haihu.. Ganin irn son da Ali yakewa yaran yasa da matar sa yasa ta cire ran Alh Ali ze sake bi takanta Hakan yasa tayi aure bisaga matsawar ganginta.. Tana aure ko shekara ba'ayi ba ta haihu diyar ta mace lokacin su jalal nada shekara biyar.. Batayi wani farin ciki ba sbd tana ganin wata taje gidan Ali ta haifi yara maza ba ita ba ynx ta mallake komai na gidan. Zulfa ko shekara batayi ba Mahaifin ta ya rasu.. Bayan shekara biyu da rasuwar sa granny tace ya maido da Atika beyi gardamaba ya maida ta ta dawo tare da diyarta twins lokacin shekarar su 7.kuma basu da kanne suna ganin gata sosai dan ba karamin so mahaifin su yake masu zaman lpy ne ya wanzu tsakanin Atika da fareeda babu wani fada duk da atika na bakin cikin itace matar sa ta farko bata haihu dashi ba. Idan ta tuna cewa bata da komai cikin tarin dukiyar sa se hankalin ta ya tashi.. suna zaman lpy har na tsawon shekara biyu kafin komai yazo ya canza.. Daga Alh Ali har Atika suka canzawa fareeda da yaran ta.. Fareeda shine lokaci me wuya ta ta taba experiencing dan ya fita har kanta daga ita har yaran ta zulfa ta koma itace ersa atika matar sa su jalal ko sunje wajen sa kyarar su yakeyi suka ko ma tsoransa gashi suna bala'in son mahafin su.. Fareeda nada hakuri hakan yasa bata taba fadawa kowa ba daga karshe ma seya dauke atika da diyar ta suka bar kasar.. Duk da abin ya dami fareeda bata taba nunawa kowa ba gashi su jalal basu da magana se ina dad.. Sede ta basu hakuri tace ze dawo.... Ana haka wata rana sun dawo daga sch suka iske Mahaifiyar su kwance bakin ta se kumfa yake suna da dan wayo lokacin shekarun su goma da gudu suka fita suka fadawa me gadi.. Ganin ta haka hankalin sa ya tashi ya kira driver suka dauke da zuwa asibiti.. Snn aka sanar da mamy kanwar mummy (fareeda).. Bayan yan Awanni likita ya fito ya sanar dasu cewa fareeda was poison.. Me kashe duk wani jijiyoyin jiki komai nata ya dena aiki hankalin su mamy ya tashi da granny gashi daddy yabar kasar ko samunsa ma ba'ayi.. Granny ce ta biya komai akai kai mummy China  inda acan din ma babu wani Abu da za'a iya mata domin kau poison din kirkirarrene da maganin sa yake inde ko ba wnn maganin ba to babu lafiyar ta sede zasu rinka yi mata juyen jini duk wata snn zasu bata duk wata kula both internal and external sbd karda skin dinta ko wani abu nata ya samu matsala har zuwa lokacin da zasu samu maganin poison din.. Hankalin mamy ya tashi.. Haka suka rinka kashe makudan kudade wata tafiya da granny tayi itama shknn bata sake waiwayar su ba.. Mamy ce ke ta dawai niya duk wasu kadarorinta suta rinka saidawa wnn tsakanin su jalal sunga rayuwa ba'a magana su kansu seda suka zama abin tausayi.. Ganin halin da suka shiga yasa mamy sakawa a maidasu Nigeria.. Wnn dan tsakanin sunga rayuwa babu uwa babu uba gashi de duk suna raye amma babu abinda zasu iya yi... Suna da kudi suna da komai amma abinci seda yayi masu wahalar ci dan babu me bi ta kansu babu wanda yake tasu.. Daga karshe su suka fara neman abinda zasuci ta karfin su duka duka shekarun su goma sha biyu a lokacin.. Kwatsam ana haka aka kashe saif har gida wanda aka daura alhakin kisa akan jalal.. Alh isa ne yasa aka rufe sa a matsayin wanda yy kisa.. Seda yayi shekara daya snn aka ciro sa dad dinsa wanda yayi shekaru be gani ba yazo ya ciro sa.. Jalal yaro ne me wasa me dariya amma ynx ya dawo baya ko daya ko magana bayayi damuwa tayi masa yawa da tashin hankali ga tunanin dan uwansa gakuma na mahaifiyar sa ga mahaifin sa ya fito dashi amma babu ruwansa dashi.. Jalal ya koma shike nemo abinda zeci da kansa  bashi da burin daya wuce sanin who's behind all this cos yasan tabbas wanine ke masa haka but who.. Har Mahaifin sa yasan baya masa yawa duk da ynx Mama na jawo sa jikinta amma ya kasa dena damuwa ita da kanta ta fara basa giya tace masa maganin damuwa ce tun bayajin dadin ta har yazama addicted to it wanda idan be shaba bayajin dadi.. Lokaci daya kuma daddy ya dauke sa zuwa America.. Inda zuwan sa America ya canza masa rayuwa dad ya dawo yana son sa kamar da yana basa kulawa ya sakasa a makaranta sede ko daya be taba tambayar sa ina mahaifiyar sa ba.. A hankali a hankalo rayuwar Jalal ta fara sauyawa.. Komai ya fara canzawa ya fara komawa bad boy kamar yanda kowa ke kallon sa Dad dinsa ya dawo yana sonsa sosai amma dukda haka be sauya ba.. Yana da tarin damuwa sosai har ya rasa yanda zeyi yana zuwa duba mahaifiyar sa lokaci zuwa lokaci Amma baya iya zama sbd zuciyarsa zata iya bugawa.... Wnn knn

Nasan duk baku fahimceni ba amma karku damu da sannu zaku fahimce komai... but one thing about Jalal’s lyf. Is sadness

Urs

✨✨✨

Annafie😍

.......

Any one reading this book should knw that its not for free its just #300 pay through the Account below
2148886852 Nafisa Abdulbasir and show ur evidence via this number 07051376476.. But for now enjoy the free pages😊 thank you Annafie loves you all 🥰❤️as you keep supporting me encouraging me as I keep suburbudo maku novels masu dadi 🥰
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/H27abREXIQn8Rp0DbZBhE2*💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫*
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
         *ANNAFIE💖…✍️*
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
💫💖Jalal Ali(8)💖💫💫.

Karfe tara da wani abu Jalal ya tashi daga bacci kafin 10 yayi wanka ya shirya cikin wasu kananun kaya masu taushi da sukayi matukar yi masa kyau... Kallon kansa yayi a mirror.. Duk tym din daya kalli kansa seya tuno da Saif.. Da yananan da da shima irin kamannin sa knn da ynx kila tare zasu shirya cikin kaya irin nasa .. Lumshe idanu yayi yana kokarin hadiye bacin ransa.. Fita yayi parlor babu kowa sede a gyare yake.. Haka ake zuwa a gyara masa duk inda ya bata da yar bar wajen.. Be taba rufe ko ina nasa ba be aje wani privacy shide haka komai nasa yake open duk abinda kaga dama kayi masa me kyau ko mara kyau.. Ficewa yayi daga parlorn zuwa main parlor.. Duk suna dinning kamshin turaren sa yasa duk suka juyo suka kallesa.. Nufowa yayi inda suke yana taku a hankali.. Zulfa ta kura masa idanu tanajin kamar taje tayi hugging dinsa...

Peck yayi wa daddy snn yaja kujera kusa dashi kafin cikin muryar sa me taushi yace "morning Dad".. "Morning my son how was ur night" "Alhmdllh".. Shiru yayi ba tare daya kalli mama data zuba masa idanu ba.. Zulfa tace "morning yaya" bnza yayi da ita ko kallon ta beyi ba bare tasaka ran ze amsa.. Tace "me za'a zuba maka".. Wata harara ya zuba mata kafin yace "leave".. Kallon sa ta tsaya yi ya kara hade rai yace "I said leave"... A hankali ta juya tabar wajen... Kallon mama Atika yayi fuska daure kafin yace "excuse us pls".. Dan murmushin yake tayi kafin ta mike tace "yaro dan baba".. Bnza yayi da ita.. Daddy de bece komai ba.  Duk wani abu da zesa ran dan nasa ya bace baya sonsa. Yana mugun son dansa na amutu.. Kallon Daddy yayi tare da sakin murmushi "I love you Dad".. Daddy ya shafa sumar dan nasa yace "my son kaki barin rashin ji ko".. Ya kalli dad yace "zan dena Dad".. Shiru kawai daddy yayi shide ynx yasan idan ba lallaba dan nasa yayi ba baze dena abinda yake ba.. Idan ma yace fada ze masa baze dena ba.. Cos ynx jalal yakai level din da kome za'a masa baze dena abinda yake ba kuma openly kome zakayi kayi but baxe dena ba sede lallashin... Daddy yace breakfast fa.. Dan yamutsa fuska yayi yace "no dad I will eat in granny's place".. Gyada kai daddy yayi.. Tashi Jalal yayi.. "Bye Dad see yah".. Dad ya daga masa hannu.. Gidan ya bari gaba daya.. Be dawo ba se bayan azahar part din granny ya sauka can yaci Abinci snn ya dawo part dinsa bayan yayi wanka ya dawo parlo ya zauna yana daukar remote dauka ya kunna TV dan yasan ynx kila wasu labarai sun fita.. Aikam hasashen sa gsky ne domin kau labarai ne ake akan inda yaje jiya wai wasu samari sunyi raping wata an kamasu sunce shine ya sakasu kuma yaje wajen.. Snn anyi magana dashi ya amsa cewa eh shine ya fadi kuma shine a page dinsa na twitter mutane suna ta Allah wade da halin sa wai mene abin alfahari da mummunan hali irin nasa.. Kashe wa yayi tare da tabe baki.. Kallon wayar sa dake ringing yayi kin dauka yayi snn ya tashi sama ya koma yayo alwala ya fito mama na parlorn tare da wasu members din fam din news din suke kallo suma ko kallon su beyi ba ya fice zuwa masallaci.. Jerowa sukayi da Mahmoud yaron Alh isa yayan sumayya.. Shima kusan duk sa'anni ne.. Mahmoud yace "kaga news din yau ko" jalal ya gyada kai.. Cike da damuwa Mahmoud yace "but yakamata kayi wani abu wnn abun ya tsaya I know you're not as bad as yanda suke fada".. Murmushi Jalal yayi yace "what if nine din fa. Kawai ka dauka nine".. Kallon sa Mahmoud yayi cike da tausayawa Jalal ya dafa shoulder dinsa snn ya wuce zuwa part dinsa a parlor ya zauna ya dauko wayar sa dailing wata number Ana dauka yace "salim akan maganar company di nan na Dad kuje kusa share".. Katse wayar yayi ya sake dialing wata number bayan an dauka yace "Bature.. Get their pics address dinsu and yarinyar ma ku bin ciko min ko wacece harda iyayen ta"... Abinda ya fada knn snn ya katse wayar yana runtse idanu..

Bayan sallah ishai yana zaune rike da wayar sa yana son kiran Mamy amma yna tsoro.. Can de ya daure ya kira.. Tana tace.. "Jalal you're very stupid you're very very stupid.. Me kk Tunanin kana yi.. Ynx har gani kake birgewa ne a rinka fadin munanen halaye akanka.. Kuma kayi shiru harma wani amsawa kk yi".. Shiru yayi yanajin yanda take fada. Tasan bashi bane amma batasan cewa be amsa ba bema san wanda ya amsa ba.. A hankali yace "am srry mamy".. Fashewa tayi da kuka se kuma tace "jalal pls ya isa haka ka fito ka nunawa duniya ko kai wanene pls bana son wnn abun".. Se kuma ta fara yi masa nasiha.. Runtse idanu yayi bayan sun gama waya da mamy yanajin yanda ransa ke baci.. Wayar sa ya dauka tare da keys din mota ya fita ya dauke daya daga cikin motocinsa ya fice...

.....,

Zaune take gaban mirror tana daure da towel tun dazu ta gama shafa man amma ta kasa tashi ta saka kaya.. Ta dubi yusrah dake shiryawa alamar wacce zata fita tace "aifa tunda farkon semester ne dole aita tsula tsiya" yusrah ta gama yafa veil dinta tace "kinga laifi na".. Murmushi imaan tayi kafin ta mike tace "kinga bari na tashi nayi isha'i".. Yusrah ta fice tana daga masu hannu.. Bayan imaan ta idar da sallah ta kalli maryam dake da danna waya tace "ke yau babu wanda ze zo wajen ki ne".. Maryam tace "se 9".. Dan marairaicewa imaan tayi kafin tace "pls kizo muje sharp sharp mu siyo choculates din nan mu dawo kuma kinga ice cream dinsu da dadi".. Hararan ta maryam tayi "am going no where nace maki by 9 zan fita".. Dan murguda baki imaan tayi kafin tace "karki je ni nasan da su farouq ko muneer suna nan da ko kallonki ma zanyi su zasu kaini" maryam na dariya tace "ko ynx ma bata baci ba gaki da samari kawai kira zakiyi a kaiki".. Imaan ta murguda dan bakin ta kafin tace "ke rabani da wadan nan yan wahalar" mikewa tayi ta isa gaban mirror ta warware dogon gashin ta ta fara tajewa tana yamutsa fuska sbd zafi.. Kallon ta maryam tayi snn tace "wnn kan naki yana bukatar gyara goben idan zamu fita shopping se mu biya saloon".. Imaan na hararar ta mirror tace "ce maki nayi ina so a gyara mun" dariya maryam tayi "ai wlh baki isa ba ga gashi har gashi amma baki iya gyara sa".. Bnx imaan tayi da ita dan ta tsani a taba mata kai.. Tana gama gyara sa.. Ta fara shiryawa cikin wani doguwar rigar black Abaya er simple ce bata da wata kwalliya sosai amma tayi mata kyau sosai ta yafa veil din se abayar ta kara haskata kasancewar ta fara fuskar ta fayau babu wata kwalliya amma tayi kyau sosai.. Wata er bag ta dauka pink me teddy ta goyo ce tace "bari na dauki wnn ta ciko ta dam kuma babu wanda ze shamun chocolate ehe".. Goya abarta tayi tazo wajen takalman su wani pink ta dauka shima me taushi dan har wani gashi gashi ne a jikin sa.. Maryam ta bita da kallo dan imaan first class ce a wajen kyau gashi de bata kwalliya amma idan tayi dan simple dressing dinta se kaji kamar ka saceta. Imaan tace "hey madaam why the look".. Tabe baki maryam tayi tana dauke kai... imaan tace "am going" "pray before leaving" cewar maryam.. Fita imaan tayi a hankali kanta a kasa Arean cike yake da manya manyan motoci kasancewar gidanjen student dake wajen ga kuma manya manyan entries..

Imaan ta fito kanta kasa duk duks da yanda take jin idanun mutane a kanta.  Da sauri ta karasa bakin titi..tama manta bata fito da wayar ta ba bare ta kira uba.. Bata dade da tsayawa ba wata dankareriyar mota ta parker gabanta. Imaan ta dauke kai wani saurayi ne ya zuge glass kallo daya imaan tayi masa da dauke kai. "Hey cute where to?".. Kin kallon sa tayi.. Yace "no response".. Ba tare da ta kalle sa ba tace "am not alone pls".. Tana fadin haka ta fara tafiya a kafa.. Yawanci wajen duk manyan mutanene so bama ka wani samun taxi musamman da daddare da samari ke zuwa.. Tana cikin tafiya wata motar ta kara tsayawa sauri ta kara ita idan ita kade ce ta tsani shiga motar wani barin ma saurayi har gara magidanta wani tym din dan kan sanari yafi rawa.  Ganin fa bazata samu abun hawa ba gashi dare nayi yasa ta yanke shawarar ta samu wani kawai ya kaita amma suna zuwa tayi wayo ta bace masa.. Dan murmushi tayi kafin ta tsaya babu jimawa kuwa wata motar ta tsaya gabanta.. Mutumin ya zuge glass din kato ne sosai daga ganin sa magidanci ne ganin katon mutumin da uban muni yasa imaan fadin "wai"... Dariya nason kufce mata ganin wnn katon mutumin daya tare ta amma seta gimtse tana dan hade ranta yace "yammata ina zuwa" ya fada cike da duniyanci.. Wani kallo tayi masa kafin ta dauke kai tace "that's not ur business".. Dan murmushi yayi yace "da kin fada babu damuwa idan nayi maki rakiya".. Tana hade rai ta fada masa inda zataje. Dan murmushi yayi yace "ba damuwa kiashigo na rage maki hanya".. Hoping that zata shigo.. Dan kyakkyawar yarinyar ta mugun tafiya dashi shi ji yake ma da zata amince ze iya auren ta sede idan taki nan gaba kawai seya afka bariki da ita dan kallo daya zaka mata kasan zatayi dadi.. Ko kallon da kake wani kwanciyar hankali kk ji inaga wani abu yadan shiga tsakanin ku.. Zagayawa tayi ta bude ta shiga ya sakan mata murmushi.. Ita ma murmushin ta saki sbd dariyar dake cinta.. Sakin jiki tayi suna dan hira dan kar ya zargi wani abu sede data fakaici idon sa seda sakar masa da harara a haka har suka karasa kayataccen gurin parking yayi cikin jerin motocin dake wajen.. Suka fito yana fadin "komai na wacen nan yana da dadi sede akwai wani idan kina so sena kaiki nasan zaki ji dadin komai nasu".. Imaan tace "to idan mun fito daga nan se muje can". Cike da jin dadi yace duk yanda kikace ranki ya dade... Murmushi tayi suka nufi entrance din..

Zaune Jalal yake ko Abinda yasa a kawo masa ma be sha ba gaba daya ransa a dagule yake shi idan ta mutane ne baya taba damuwa amma mamy da daddy sune damuwar sa.. Dan daga idanun sa yayi yana kallon yanda samari da yan mata keta zuwa.. Dan guntun tsaki yaja yana mmkin yanda mata suke zubda mutunci su sbd kudi da wani abin duniya.. Idon sa ne ya sauka akan imaan da mutumin nan da suka shigo ynx yana magana tana murmushi.. Yaja guntun tsaki ganin kyakkyawar yarinya kamar wnn tana zubda mutuncin ta kuma tsabar son abinda duniya ta rasa wanda zatabi se wnn katon mummunan mutumin dayayi sa'ab ubanta shifa shiyasa mata ke basa haushi se yaga ga yarinya kyakkyawar gske amma ba mutunci.. Kamar blink of eyes yaga mutumin na dauke kai ta sakar masa harara tana murguda baki.. Kawai samun kansa yayi da kallon ta.. har suka zo suka zauna wata kujera dake kusa dasu yana tambayar ta abinda zata siya.. Hankali kwance ta zayyano masa kome take so harma da wanda bata zo da niyyar siya ba duk ta fara masa.. Ya tashi yaje ze amso.. Imaan ta bisa da harara kafin tace "wahalal le".. Jalal beji Abinda tace ba amma he saw yanda sound din yy escaping daga bakin ta koma ya fahimci me tace.. Dan lumshe idanun sa yana kallon ta da mmki dan har mutumin dan yaje ya dawo bata bar hararar bayan sa ba amma yana karasowa da niki niki din kayan ta saki kayataccen murmushi.. Underneath his breath yace "ya salam see this girl.. Dan zama wancan yayi tace "thank you.. Yace suke nan kike bukata".. Ta gyada kai" yace "are you sure feel free ki fada mun".. Kamar bazata ce komai ba se kuma tace "muci pizza mana".. Cike da jin dadin wnn yarinyar wayayya ce ya tashi ya koma can. Jalal duk yanajin abinda suke fada.. Imaan ta bisa da harara kafin tayi saurin kwashe duk kayan daya kawo ta dauki bag dinta cikin sanda.. Kafin tayi sauri ta fice bat da bace daga cikin wajen.. Duk da yanda ransa yake A bace besan sanda yayi murmushi ba.. Kawai jira yake yaga mutumin ya dawo.. Aikam segashi ya taho ma'aikaciyar wajen na biye dashi rike da kwalin pizza.. Tun kafin ya karaso yanayin fuskar sa ya fara sauyawa ganin bata nan kuma ta kwashe komai alamar tafiya tayi.. Be san sanda yace "what".. Dariya ta kusa kufcewa Jalal ganin yanda mutumin yayi.. Harda cire hula kafin ya fice da sauri... Jalal tashi yayi shima kawai yana so yaga yanda zasu kare m. Shi ba mutun bane me shiga irin wanda nan but yau yanda aka fara komai a idon sa yanaso a kare... Imaan na fita kuwa dama boyewa tayi batayi gangancin taran abin hawa ba tafiso seta ga motar sa tabar wajen kafin ta fito tasan nayi.. A kan idon ta ya fito yana da kalle kalle.. Kafin yace "jar uba ni yarinyar nan zata latsa ta mayar Bnx" kan Jalal a kasa ya wuce mutumin ya tafi wajen motar sa ya shiga but yana kallon mutumin ta cikin mota .. Mutumin ya gama dube duben sa ya shiga mota raia bace.. Yabar wajen.. Seda imaan taga ya tafi snn ta fito daga inda ta buya tana tura dan bakin ta harda murgudawa snn ta karasa titi da sauri ta tari taxi ta shiga.. Jalal da duk yana kallon ta ya saki murmushi kafin yace "smart girl".. Tada motar sa yayi ya nufi gida karfe goma ya iso gida.. Dan murmushi yayi yanajin dadi yau besha giya ba yasan yau his dad will be happy...

Imaan na shan yoghurt din me dadi sosai tana dariya su Maryam na taya ta suma duk da kayan ciye ciyen sun baje sunaci imaan na basu lvri suna dariya.. Yusrah tace "wato shi yaga yasamu hot baby an fada masa irin wacce ya saba gani ce" imaan tace "bade shi dan iska bane besan zainabu ya dauko ba".. Maryam tace "wani zubin duk muguntar mu tsoran ta imaan nake" yusrah tace "wlh ai tayi masa da sauki ma" "ynx de yakamata gobe kuzo muje shopping duk abinda bamu dashi mu siyo mu huta" cewar maryam.. Yusrah tace "kinga ma ina so naje saloon se farouq ya kaimu nasan yana available".. Shiru imaan tayi itafa bata son zuwa saloon har ga Allah.. Maryam na kallon ta tace "sefa kinje ko baki so.... Muje ku kushiga saloon ne se muyi shopping din tare da farouq....

Washe gari bayan sun dawo daga lectures karfe biyu yusrah ta dafa masu Abinda zasu ci... Wajen 4 suka gama shiryawa suka fito inda farouq na jiran su suka shiga ya jasu suka tafi.. Suna ta lbari a hanya kuma duk akan sch dinsu ne.. Wajen saloon din is opposite to shopping mall din dan haka suka fara ajesu snn suka dawo suka shiga mall din.. Imaan harda yan hawaye yusrah se dariya take mata.. Bayan an gama wa yusrah suka fito.... Su uku ne cikin motar Ak ke driving while Labib na gaba yana ta uban surutu se Jalal a baya yana dan danna system dinsa dukkansu kayan sport ne a jikin su... Labib ne yace "woww God  of mercy".. Labib ya fada ya kallon su imaan da zasu tsallaka titi.. Slow Ak ya farayi da mota "oh my godness see girls.. Ive naver seen a beutiful girls lyk them".. Ba tare da Jalal ya dago ba yace "guys this is not tym for girls.. Lets go pls".. Ak yace "oh no i can't.. deen.. Whats an awesome" ya fada yana tsaida mota daidai saitin su imaan.. Jalal ya dago kai ze sake magana idon sa ya sauka akan imaan da take sanye cikin wata nevy blue din doguwar riga ta yafa veil din rigar.. Kasancewar ta fara yasa take son kaya masu duhu se suke kara haska skin dinta.. Tuni ya gane ta hakan yasa ya fasa maganar da zeyi kuma ko kallon motar da ta tsaya kusa dasu basuyi ba.. Yusrah tace "aifa maza babu hakuri".. Ak da labib dukayi kasa da glass dinsu.. Sallama Labib dake saitin su yayi masu.. Hakan yasa suka amsa ba tare da sun kallesa ba "uhm mufa bamu muka kar zomon ba rataya aka babu" Ak ya fada yana kallon imaan data mugun hade rai.. Kallon su yusrah tayi dan ita bata hade rai ba se kuma ta kalli imaan.. Dariya tayi dan kuwa tasan sbd saloon din nan ne yasa imaan keta hade rai.. Ta kalli su labib da kallo daya zaka masu kasan yan hutu ne tace "srry don't mind her kukan saloon take".. Waro idanu sukayi.. Labib ya fashe da dariya. Hakan yasa imaan ta kallesa kamar zatayi kuka tace "kaikuma ya isheka just take yr tym".. Ta fada tana kumbura baki.. Labib ya rike bakin sa yace "srry but is so surprising as ur age.. You still cry for saloon"... Imaan ta dauke kai tana murguda baki.. Jalal da ya fara enjoying conservation din nasu yace "rashin kunya" but underneath his breathe.. Ak yace "sisters where to".. Yusrah tace "school".. Yace "wow student ne knn wane school"... Imaan data gama kuluwa tace "oh god kun aike mu ne pls let us".. Labib yace "wnn kawar taki de masifafface kiriss take jira ta kai mana duka kamar mune masu saloon din".. Yusrah da dama ta biyesu ne danta kular da imaan tace "ta gidan gaba ma kuwa".. Ak yace "ga rashin kunya".. Ta kalli Ak ta manyan idanun da ta sakar masa harara.. Jalal ya gyara zama yana kara kallon su.. Kawai ji yake dama su cigaba da tsokanar ta yaga karshen rashin kunya.. Labeeb yace "alryt kafin ta huce fushin ta a kanmu pls help us with ur digit".. Da sauri imaan tace "bamu da waya".. Jalal ya ciji lips dinsa.. Ak yace "we said dan Allah".. Yusrah ta bada  numbern ta snn ta fada masa sunan sch dinsu..imaan bnd harara babu abinda take masu daga su din har yusrah.. Jalal a ransa yace "harara miss".. Dan tunda ya fara ganin ta bata minti daya bata saki harara ba.. Labeeb yace "tnx see kun ganmu ya kalli imaan masifa girl see yah" dariya yusrah tayi yayinda da imaan ta murguda baki.. Ak yace "pls what's her name".. Yusrah tace "imaan".. Imaan duk suka maimaita harda jalal.. Imaan tace "kuma karna sake naga mutane a sch din mu" labeeb yace "kuma se munzo.".. Ta dauke kai sallama sukayiwa yusrah snn suka wuce yusrah tace "wow" tana bin motar da kallo lokaci daya kuma idon ta ya sauka akan numbern motar DEEN4.. Zaro idanu tayi kafin tace "what?".. Imaan tace "menene".. Yusrah tace "deen deen deen fa?" Yusrah tayim maganar bakin ta na rawa Cike da comfusion imaan tace "who's he?".... Batare da yusrah tace komai ba ta kama hannun imaan dama already su maryam sun gama shopping an saka komai a mota suma suna ciki su kawai suke jira.. Yusarah ta bude motar suka shiga...

Urs

✨✨✨

Annafie😍

....

Any one reading this book should knw that its not for free its just #300 pay through the Account below
2148886852 Nafisa Abdulbasir and show ur evidence via this number 07051376476.. But for now enjoy the free pages😊 thank you Annafie loves you all 🥰❤️as you keep supporting me encouraging me as I keep suburbudo maku novels masu dadi 🥰
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/H27abREXIQn8Rp0DbZBhE2*💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫*
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
         *ANNAFIE💖…✍️*
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
💫💖Jalal Ali(9)💖💫💫. 

Tun kafin farouq ya gama reverse yusrah tace "ynx muka hadu da wasu guys suka tare mu har sun karbi numbern mu da address din mu the guys are very hot but you knw what"... Duk suka girgiza kai.. Yusrah tace "bayan sun tafi a bayan motar sa Deen naga an rubuta".. Maryam tace "what deen fa kukace mun shiga uku".. Imaan tace "wai menene wane Deen din".. Yusrah tace "dan de baki kallon news amma bama a abuja ba da tuni kin san wane Deen".. Maryam tace "in kinji ana baddest, bad boy da baya tsoran kowa da kuma kome za'a masa to Shine Deen duk wanda kika sani yasan sunan deen..he's a very bad boy from a very wealthy family".. Imaan da shegen tsoro tace "mun bani".. Farouq yace "Deen baze tsaya a  a titi haka daku ba".. Maryam tace "amma kasan babu wanda yake amfani da numbern sa ko".. Farouq yace "definitely but I don't think harda Deen a cikin su.. May be brothers or frnds but not deen".. Duk shiru sukayi se hankalin su yadan kwanta jin bashi bane...

Gab da magrib suka tashi daga ball din sanda jalal ya iso daga gida ana kiran magrib dan haka yana parking ya wuce masallaci.. Bayan ya dawo daga masallaci ya wuce part dinsa wanka yayi snn ya fito parlor tun kafin ya sakko daga stairs ya hango zulfa dake zaune tana kallo a parlon sa.. Kamshin sa ne ya cika mata hanci yasa ta juyo da sauri tana kallon sa yayi kyau sosai cikin golden jallabiyar.. Ta mike tana dan murmushi.. Zaunawa yayi yana canza channel tace "good evening brother" dan kallon ta yayi.. Bata da laifi amma wani irin haushin ta yake ji sbd sanda babansu ya watsar dasu su da mahaifiyar su  itace ta koma diyar sa basu ba .. Zulfa kyakkyawar yarinya ce.. Allah ya dasa mata wani irin mugun son jalal har bata son yanda zatayi ba mama tayi fadan har ta gaji amma ta kasa cire sa a ranta tanada samari sosai amma bata ga kamar jalal ba.. Zulfa kamar zatayi kuka tace "yaya dan Allah" wani kallo ya mata kafin yace "find ur way out".. Marairacewa tayi cike da kissa zata sake magana yace "don't let me repeat my self zulfa get out".. Ya fada fuska kamar hadari.. Babu shiri  ta fita ya bita da harara.. Imaan ce ta fado masa a rai besan sanda ya saki murmushi ba gaba daya ganin daya mata daga jiya zuwa yau duk ta gama daure masa kai.. Dan kansa ya dafe.. "Ops jalal ina ruwanka da ita"...” Imaan” sunan ta ya fado masa a rai yana hango fuskar ta tana harara.. Dan tabe baki yayi kafin ya tashi "he just wish ya kara ganin ta ko sau daya ne.. Part din granny ya tafi.. Zulfa,sumayya da sauran wasu yan family din .. Gaisar dashi sukayi ya amsa ciki ciki yana zama kusa da granny ta shafa kansa snn tace "a zuba masa abinci".. Cike da natsuwa ya fara cin abincin kamar wanda ya tuna wani Abu ya dago ya kalli sumayya suka hada idanu yace "wane sch ma kike?".

Fada masa tayi.. Dan lumshe idanu yayi.. Domin ko nan ne makarantar da su yusrah sukace suke .. Anan yayi sallahr ishai ya dade tare da granny dan da Mahmoud m yazo hira suka dan taba.. See 10 snn ya koma part dinsa.. Daddy na nan dan haka ya zauna sukayi kallo tare.. Dadi yaji dadin ganin yanda dan nasa jiya daya yau be fita ba kuma be sha giya ba.. Sun dade da dad kafin su tashi kowa ya tafi ya kwanta...

..

Ranar gaba daya labarin Deen suka rika bama imaan ita kam duk ta tsorata dashi but farouq ya basu tabbacin ba shi bane amma kuma idan duk abokanen shedanancin su ne fa.. Dan tabe baki tayi inde suna takamar su mugaye ne ita ma ta iya ehe... Da wnn tunanin tayi bacci..

Washe gari se 11 suke da lectures dan haka suka sha baccin su se 10 suka tashi da sukayi break fast suka shirya su farouq suka zo daukar su a motar muneer suka wuce..

Bayan sun fito first lectures dinsu suna tare su uku suna dan duba wani karatu su farouq sunje su dawo.. Wayar yusrah ta fara ringing number ta gani.. Ta dauka hade da sallama labib yace "Yusrah how you". Ta amsa ta "fne." "Kina free ne".  Tace "who".. Labib yana dan murmushi yace "ina kawarki me kukan saloon" waro idanu yusrah tayi tana kallon maryam da imaan se kuma tace "tana nan".. Yace "ohk then tell her that zamuzo yau after isha'i". Yusrah da jikin ta ke rawa tace "ohk zan fada mata se kuma ta katse wayar.. Ta kalli imaan ta fada masu yanda sukayi da da labeeb.. Tabe baki imaan tayi tace "ai se kuje ni babu inda zani besides karatu ma zanyi".. Maryam tace "kike ta masifa nasan duk tsoro kike ji".. Imaan ta hade rai "su sunma isa sumin abinda Allah bemun ba wlh a shirye nake dasu.. Se 5 snn suka dawo.. Duk da sunajin bacci haka suka kiyi sukayi girki snn suka dan zauna suna hutawa ne danna waya nayi mejin waka nayi.. Se magrib snn suka tashi sukayi sallah imaan tayi wanka ta dauki sch bag din ta tafi karatu su maryam nace mata tsoro takeji ta share su.... Suma wanka sukayi suka shirya suka bar gidan dan basa ma so su samesu a gida...

Ranar yau jalal wuni yayi danna system dinsa da wuri ya tashi ko break beyi ba tea kade yasha yana duba wasu abubuwa seda akayi a azahar ya tashi yayi sallah a daki.. Snn ya dauki waya ta kira mamy vedio call bayan sun gama gaisawa ya bukaci ganin mum dinsa inda ta nuna masa ita likitoci na a kanta suna aikin su.. Jalal ya ciji libs dinsa yanajin wani zafi a ransa.. Sometimes zeji ya tsani rayuwar sa but yana so yasan wadan da suka aikata hakan wa mum dinsa.. He have to catche them a cut them into pieces.. Ya sauke ajiyar zuciya kafin yace "am not bad but I will soon be.. I will be very dangerous just continue"... Ya fada yana cizar libs dinsa.. Kwanta wa yayi saman gadon sa tuni bacci ya dauke sa wanda be tashi ba se bayan la'asar.. Alwala yayi yay sallah kafin yayi kiran sumayya ta kawo masa wani Abu me sauki domin yaci sbd yanda yaji kansa na mugun sara masa ... Ya dauko system dinsa yacigaba da wasu ayyuka yana cikin yi sumayya ta shigo.. Ganin yanda yake aiki yasa ta aje masa ta fita.. Wayar sa ya dauka yayi kira.. "Hello bature those people get me all their information immediately am talking of yaran da sukayi raping din and yariyar da akayi raping inason komai da komai harda iyayen su".. Katse wayar yayi.. Kafin yaje ya bude abincin da aka akawo masa.. Kadan ta diba yaci snn ya cigaba da abinda yake seda akayi sallah ya tashi zuwa masallaci wanda seda akayk ishai ya fito.. Wanka yayi ya shirya snn ya dauki wayar sa ya kira labeeb.. Yana dagawa yace "kuna ina".. Labeeb yace "anya yau tafiyar mu daya dan wajen bebs din nan najiya zamuje.. Dan tabe baki Jalal yayi kafin yace "ku biyo tanan and pick me up am so lonely".. Ya fada tare da aje wayar... Ko 10mins ba'ayi na suka kirasa.. Be dauka ba ya dauki wayar tare da ficewa.. A gaban gate dinsu sukayi parking suna cikin motar labeeb.. Jalal ya bude back seat ya shiga.. Ak yace "so surprising yau kaine zaka bimu a yawon mu na mata".. Jalal ya tabe baki "I will wait in the car ku kuma kuje kuyi harkokin ku".. Labeeb yace "ai ba wani harka kawai I just want to see them again yanayin imaan din nan is just melting me and yusrah na sane take tsokanar ta so I just want to see them again".. Jalal ya tabe baki yana danna wayar sa kafin yace "wnn mara kunyan kude cigaba da biyesu a haka kananun yara zasu rainaku".. Ak yace "iyayen son girma".. Jalal de be kara magana ba har suka isa inda Arean su labeeb ya dauko waya ya kira yusrah.. Jalal yai ta kallon yanda wajen ya cika da motoci a ransa yace "wato ita de harka inde ta shedananci ce tafi samun kasuwa dayawan iyaye basu san abinda yaran su suke ba wasu su tsare kansu wasu kuma sede addua".. Labeeb ya kalli Ak "wai suna dinnercas nan gashi can muje".. Wajen suka tafi. Aka bude masu gate suka shiga da motar su .. Shima kansa wajen cike yake da manyan motoci an kayata wajen haske ta ko ina ga flowers masu daukar hankali se fararen kujeru kashi kashi a love guarding.. Se babban restaurant dinsu dake wajen.. Kiran yusrah yayi ya fada mata sun iso.. Hakan yasa su maryam suka taso ita da yusrah waya kare a kunnen yusrah suna masu kwantacen motar su har suka gane.. Suka karaso su Labeeb suka fita.. Da wayo da wayo suka kalli numbern motan ganin ba Deen bane yasa suka suka sauke a jiyar zuciya.. Ak yace "student sannu ku ku ai dadin ku kawai kukeji".. Yusrah tace "wane dadi kawai munzo dinner ne".. Labeeb yace "bnga imaan ba".. Taje karatu "cewar yusrah".. "I can see duk itace mara kunya cikin ku tunda ga wnn frnd din taki nan tunda tazo ko kallon bnza bata mana ba bare harara".. Murmushi maryam tayi kafin tace "imaan masifa".. Duk dariya sukayi kafin subar gurin su karasa inda Su yusrah suka baro dinner ce lafiyayya.. Labeeb yace "wow zamuci dadi but ai want to see mara kunyan kawar nan taku".. Maryam tace "taje karatu amma idan ta gama zata biyo ta nan" Ak yace "i love the way she stares ta iya harara over".. Duk dariya sukayi.. Kasancewar su Labeeb nada barkwanci shiyasa tuni suka sake dasu har sunajin dadin wnn moments din da suke spending tare sede basu minti biyu basu ce imaan ba... Jalal na cikin mota watching them and wondering where the smart girl me shegen harara called imaan is.. Dan tabe baki yayi kafin yace ni ina ruwana ya cigaba da danna waya dukda yanda kansa ke masa ciwo sbd beci wani abun kirki ba... Kamar ance ya daga kai yaganta ta taho sanye cikin dogon hijiab maroon ta goya wata white teddy sch bag hannun ta rike da jotter da pen.. A natse take tafiya kasancewar wajen bau yake yasa yake ganin fuskar ta da babu ko digon kwalliya se natural beauty dinta tayi wani fresh kananun lips dinta sun kara wani haske.. A hankali take tafiya waya kare da kunnen ta tana waya da su maryam da suke mata kwatancen inda suke kin fada mata suna tare da su Ak sukayi dan kartaki zuwa. Tana zuwa daidai satin motar su ta tsaya tana kallon su yusrah dake tare dasu Labeeb.. Wani hade rai tayi tana hararar su duk da basu ganta ba se kuma ta murguda baki ta juya.. Jalal dake kallon ta seya juya ya kalli su Labeeb ganin basu ganta ba yasa ya maido da kansa inda take.. Se kuma be ganta ba kalle kalle ya rinkayi amma be ganta ta dan tabe baki yayi kafin ya bude motar ya fita .. Restaurant din wajen ya nufa kansa kasa... Yana shiga da ita ya fara hangowa kanta ya fara sauke idon sa.. Tana zaune ta daura jotter dinta atable din tare da wayar ta tana dan dubawa se kuma tayi dan rubutu a jotter din dauke kansa yayi daga kallon ta ya nufi wani bunch din dake kusa da nata ya zauna..yana  zama aka kawo masa menu din yayi selecting abinda yake so snn ya dauki wayar sa yana dannawa but lokaci lokaci yakan saci kallon ta tana wajen wani guy yazo ya zauna hakan yasa ta dago da sauri ta kallesa.. Hade rai tayi tan tsuke dan bakin ta gayen zeyi magana tayi saurin fadin.. "Hey this place is taken can you excuse me".. Gayen yace "sure but can you help me with ur contact".. A takaice tace masa "no" ze saki magana tace "wlh miji na yazo ya ganka anan se kayi dana sanin yimun magana" da sauri yace "srry na tafi".. Imaan ta bisa da harara kafin tace "wasu de kamar bunsuraye haka suke insha wnn uban hijab din amma kazo kana mun magana" ta fada tare da murguda baki.. Jalal besan sanda murmushi ya subuce masa ba a ransa yana fadin wnn wace irin yarinya ce.. Kullum yana ganin ta da deference characters.. Gada de yarinya karama dan yasan wnn ko 20 bata kai ba.. Kamar daga sama yaji tace "pls can you help me with your phone I want to browse something nawa netwrk din tsayawa yake".. Dan cizar lips dinsa yayi ganin yanda ta wani marairace kamar ba ita ta gama masifa ba ynx.. Ba tare da yace da ita komai na ya mika mata wayar sa ta washe baki tare da fadin tnx... Bece da ita kala ba sede ya lumshe idanu ita kuma ta juya ta cigaba da abinda take... Lokaci lokaci yake satar kallon ta... Abinda yayi order aka kawo masa kafin yayi wani yunkuri yaga imaan ta juyo tana kallon ma'aikacin tace.. "Hey mr I first this guy but ka fara kawo masa are you salecting".. Ma'aikacin ya kalli imaan yace "srry ma'am what you order isn't ready".. Imaan ta tsuke dan bakin ta tana hade rai.. "What I was sitting for over 10mins and you're telling me what I ordered isn't ready bakusan darajan costomers ba" imaan dake mugun jin yunwa ta fada.. Jalal was just staring at her yana kallon yanda ta hade rai tana zuba ma ma'aikacin masifa wanda idan ze mata lafiyayyan duka babu tantama seta suma.. ma'akacin yace "we're srry ma'am".. Imaan ta kalli abinda jalal yayi order kafin tace "give me that and bring another for him"... Ta fada batare da ta yarda ta kalli jalal ba.. Jalal da idon sa yake a lumshe amma yana kallon ta kasan idanu a ransa yace "what a stubborn girl".. Ma'akacin ya mika mata ganin idanun jalal a lumshe snn ya tafi da sauri domin kawo masa wani tabi bayan sa da harara snn ta fara cin snacks din a natse tana lumshe idanu..ma'aikacin ya kawo wa jalal wani yana basa hakuri kai kawai jalal ya gyada masa.. Kafin a hankali ya fara cin nasa.. wayar imaan ce tayi kara ta saka wayar a hand free amma bawai da kara sosai ba yanda de zata iya ji ta cigaba da abinda take da wayar Jalal.. Yusrah tace "ke wai baki zuwa".. Imaan tace "ke wai basu tafi ba".. Jalal ya dago ido yana kallon ta .. Yusrah tace "Allah ke suke jira".. Imaan tace "ban zuwa kawai idan kinga alamun yan iskane kusan yanda zakuyi ku gudu snn kuyimun text din kalar motar da suka zo da ita. Kawai naje sace tayoyin kalar yanda nayi ma wnn gayen". Jalal be san sanda ya zaro idanu ba ji za'a sace tayoyin motar su.. Beji abinda yusrah tace ba se yaji imaan tace "ohk ganinan to..."tashi  tayi tana hada kayan ta snn ya juyo rike da wayar Jalal batare data kallesa ba tace "ur phone thank you".. Batare da yace komai ba ya nuna mata ta aje.. Ajewa tayi tana mmki wnn gayen da babu ruwansa da kule kule.. Shikam binta yayi da kallo harta je ta biya kudi ta fice.. Sauke ajiyar zuciya yayi kafin yace "who's she?"... Bashi da me bashi amsa hakan yasa shima ya tashi yaje ya biya kudin ya fice.. Wajen su Labeeb yaga ta nufa.. Shi kuma wuce mota yana kallon ta har ta karasa inda  suke....

Labeeb na ganin ta yace "oh pretty kinga dama knn kinzo".. Ta dan murguda baki snn tace "karatu fa nayi".. Ak yace kinga rabu dashi ynx de ya kukan "saloon".. Imaan bata san sanda ta saki mumushi ba.. Labeeb ya waro idanu.. "Do you have this perfect smile thought harara da murguda baki kawai kika iya".. Imaan ta tura baki tana zaunawa gefen maryam.. Tsokanar ta sukai tayi har seda ta sake dasu anan sukaji surutu.. Har suna mmki.. Sanin tare da jalal suke yasa suka fara shirin tafiya dam sunmayi mmkin wnn tsawon lokacin da suka dauka be kira waya ba...

Tunda suka taho idon sa na kan imaan dake ta sakin murmushi.... Sukayi sallama snn su Labeeb suka shiga mota yayi wa motar key snn ya juyo yana kallon Jalal yace "Deen kace kana nan".. Ya hararesu.. "Kuna can kun tsaya cikin kananun yara".. Ak yace "man you will not understand those girls are so nice and lovely been with".. Labeeb yace "and that imaan oh I love all of her she's just unique"..jalal besan sanda ya saki tsaki ba.. Labeeb ya fashe da dariya kafin yace "deen da zakabi tawa just kuyi dating da imaan din nan zaman ku ze bada chitta".. Jalal ya ya mutsa fuska yace "wnn mara kunyan".. Duk juyowa sukayi suka kallesa "kai taya kasan bata da kunya" cewar AK.. Cike da basarwa jalal yace "i can see yanda karamar yarinya ke hararan ku but you're busy opening teeth for her ku kunga fara ko".. Ya fada a ransa kuma fadu yake da ta sace maku tayar mota ai zagu gane she's unique.. Dariya sukayi Ak yace Deen namu.. God show me ranar da deen ze fara son wata mace".. Bece dasu komai ba.. Labeeb yace "ina mukayi ne".." Take me home" cewar jalal.. Babu musu suka kaisa gida.. Be iske kowa a parlor ba ya wuce part dinsa.. Kwantawa yayi saman gadon yana kallon sama.. Imaan ce kawai ke fado masa with her different characters.. Abinda ya fahimta da ita de she's very smart, stubborn, confidance and bata tolerating... Lumshe idanu yayi... Kawai abubuwan da tayi yau sun tsaya masa a rai.... He just wish ya kara ganin ta may be ya karasanin wasu halayen nata...

Urs

✨✨✨

Annafie😍

......

Any one reading this book should knw that its not for free its just #300 pay through the Account below
2148886852 Nafisa Abdulbasir UBA BANK and show ur evidence via this number 07051376476.. But for now enjoy the free pages😊 thank you Annafie loves you all 🥰❤️as you keep supporting me encouraging me as I keep suburbudo maku novels masu dadi 🥰
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/H27abREXIQn8Rp0DbZBhE2*💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫*
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
         *ANNAFIE💖…✍️*
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
💫💖Jalal Ali(10)💖💫💫.

Kasancewar yau Friday yasa lectures dinsu da wuri ne shiyasa tun kafin 8 su farouq sukazo daukar su a mota bnd lvrin su Labeeb babu abinda suke bama su farouq telling them they're so nice.. Ga tsaraban chocolates da suka kawo masu masu uban yawa wai bakin imaan ze so chocolate kamar me...  12 suka taso suka dawo gida.. Imaan ta zauna tayi masu hadden girki kasancewar yau Friday suna samun visitors sosai.. Snn sukayi wanka suka shirya zuwa masallaci... Bayan sun dawo maryam ta kalli imaan tace "yau fa nasan kina da baki" imaan ta tabe baki tace "karatu zanyi barin ma Arean nan zanyi".. Yusrah tace "kije ina.. Gyara kwanciya imaan tayi tana kara lumshe idanu.. Arann park zanje the place is so silent... Yusrah tace "uhm mude jeki koyo seki koya mana..".. Imaan de batace komai ba dan bacci takeji... Da la'asar ta tashi daga baccin da sauri ta shiga toilet tayi wanka ta fito daure da towel.. Su maryam na parlor suna cin Abinci.. Shafa tayi snn ta saka hijab tayi sallah.. Jin ana ina matan gidan nan yasa ta dage labule ta fito wata murjace itama nan makofciyar suce .. Maryam tace "ai kune manya ga iskanci ga kwakwalwa wata kawata na kawo ku koyawa wnn combine course din na Mr John wai monday ze masu test kinsan ba mutunci ne dashi ba shine take neman me koya mata".. Yusrah tace "tab ai wlh kinga tunda na dawo bn natsu ba sede zuwa gobe zan duba cikin mu ma imaan ce kawai zance ta iya nasan jiya shi ta duba".. Murja tace "yauwa kawass dama inason tutorial dinki nasan zata gane".. Murmushi imaan tayi tace "babu damuwa nima ynx karatun zanyi but am leaving this area Arann park zanje". Ta fada tana kallon kyakkyawar beb din da murja ta shigo da ita taci gayu.. Murja tace "babu damuwa se kuje can ai tanada mota mude kam karatun mu se exam tazo".  Duk dariya sukayi.. Murja ta dubi beb din tace "sumayya ga imaan nan amma fa batajin magana ta tsokano maku fada babu ruwana dan wlh ina tsoran Allah ina tsoran muguntar imaan"... duk dariya sukayi yayin da imaan ta ballawa murja harara snn ta dubi sumayya tace "kinga waccen munafuka ce".. Dariya murja tayi sosai tace.. "Sumayya isa Abbas inde imaan ce gata nan na barki da ita zata nuna maki halinta".. Itade sumayya murmushi kawai take tanajin su.. Imaan taje ta bude fridge ta dauko mata ruwa da lemo masu sanyi.. Sumayya tayi godiya.. Shiga cikin imaan tayi kasancewar yau Friday yasa ta saka doguwar rigar tamfa.. Da tayi mugun yi mata kyau tayi simple daurin dankwali snn ta dauki mayafi bayan ta feshe dukkan jikin ta da turare snn ta dauki sch bag ta cikata da kayan ciye ciye bayan tadauki kayan karatun.. Ta fito parlor ta iske sumayya da su maryam suka mata tayin abinci taki ci..sede lemu tasha.. Yusrah tace "kinga taki cin Abinci".. Imaan tace "ku barta na daukar mana kayan ciye ciye" kasancewar ita bata wani fiya cin abu idan zatayi karatu ba sede daga baya yunwan ta kamata.. Murmushi imaan tayi tace "muje".. A motar sumayya sukaje Arann park wajen ya kayatu sosai kuma babu yawan mutane kuma wajen shiru.. Suka samu wata cement chair wacce zataci mutum biyu suka zauna tare da fito da kayan karatun su imaan ta fara nuna mata duk inda bata gane ba.. Da yake imaan surutu ne da ita yasa da an fara se su fara wani surutun da gulmar duk wanda ya shigo be masu ba.. Itama sumayya da yake sakin jiki ne da ita se ta biye mata suna ta dariya suna nishadi.. Kasancewar da wasa da dariya suke yasa sumayya fahimtar duk abinda take nuna mata kuma tuni ta sake da ita sunayi suna ciye ciye.. Sosai sumayya taji imaan ta birgeta  gata de tasan a girme zata iya bata 3yrs amma ta iya mu'amula da mutane snn ga kokari dan yanda take nuna mata tana ganewa tasan ba karamin kaine da ita ba.. Snn yarinyar tayi mugun yi mata kyau dan a hankali a hankali take satar kallon ta.. Lakaci daya taji ta mugun shiga ranta..

Se da aka kira sallahr magrib snn suka tashi sukaje sallahr bayan sun idar imaan ta kalleta tace dare baze maki ba.. Sumayya tace "when are you leaving" imaan tace "am leaving by 9 my frnd farouq will come and pick me up".. Sumayya tace "good bari na tafi gida gobe zanzo se mucigaba.. Wlh naji dadin tutorial dinki".. Duk da imaan bata wani karatu a weekend seta amsa mata da ohk.. Zuwa sukayi sumayya ta dauki kayan karatun ta.. Imaan tabar nata sukaje ta rakata har mota"...

Waya kare a kunnen sa yana magana a hankali kamar wanda baya so ajisa ya zauna a wata kujera batare daya kula da kayan imaan dake kai ba.. Seda ya gama snn ya kula da kayan karatun da kuma sch bag din data bari a bude gasu chocolates nan da biscuit se su apples.. Ga handouts dinta nan da kuma hardcover inda take jotting itama a bude se pain a sama.. Idanun sa ne ya sauka akan sunan ta Zainab Muhammad.... Kamar ance ya daga kai ya ganta ta taho kanta a kasa shigar atampar tayi mata kyau sosai .. Kawar da kansa yayi tunma kafin ta gansa a ransa ya furta "again an ya yarinyar nan ba aljana bace sbd yau kwana hudu knn kullum seya ganta".. Ganin mutum zaune a kujerar ta yasa ta danyi slow tana kallon sideview din nasa a ranta tace "wow whats a handsome".. Ta fada duk da bata ga fuskar sa ba.. Juyowa Jalal yayi suka hada idanu.. Ta kusa daburcewa amma seta dake tana hade rai.. Jalal ya dauke idon sa a kanta underneath his breathe yace "masifa".. Imaan ta karaso.. Tayi sallama fuska daure.. Shima ba tare daya kalleta ba ya amsa ciki ciki.. Ganin yanda yayi matan yasa tace "excuse me pls this my space".. Rasa amsar daze bata yayi shi kuma baze tashi ba karma ta rainasa dan ya kula wnn tuni zata raina mutane.. Hakan yasa yayi bnz da ita.. Kuluwa imaan tayi ganin yanda yayi bnza da ita tace "malam am talking to you this my space kuma karatu nake".. Ta fada cike da masifa.. dan cizar lips dinsa yayi kafin ya daga ido ya kalleta.. "Can you stop shouting".. Ya salam imaan ta fada a ranta.. Ita de taga ba shouting take ba amma tsabar ranin hankali zece tana shouting.. A zahiri kam harara ta zabga masa tace "ohk stand up and get urs".. Wani kallo yayi mata kafin yace "an rubuta sunan ki a jiki ne".. Imaan tayi folding hannayen ta tace "ina ruwanka all I knw is ka tashi you can get another wnn nawa cos ga kayana nan".. Ta fadi maganar tana murguda baki he saw yanda dan karamin bakin ta ke motsi cike da masifa.. Dan gyara zama yayi yana kara balancing a kujera kafin yace "alryt meyasa ke bazaki canza wata ba you can parked ur things and get another".. Kai.  ta fada a ranta tunda take babu gayen daya taba latsata kamar yau ko dan yaga yana da kyau ne shiyasa yake wani jin kasan to ita ba kalar matan nan bace.. Imaan ta fada a ranta dan ko daya bata gane shine wanda ta ari waya wajensa ba jiya... Imaan tace "am parking to no where cos I first you".. Ta fada cike da rashin kunya.. Shi har mmki take bashi wnn wace irin yarinya ce da bata tsoran kowa.. Ganin yayi bnza da ita yasa tace "malam you're westing my tym karatu nake fa".. Dan kallon ta yayi se kuma ya kalli hard cover din ta.. Dauka yayi yana kallon hand writing dinta masu kyau snn ya kalleta yace "I didn't stop you".. Ganin wnn dan rainin wayo ne yasa kawai ta juya ta bar wajen ba tare da ta dauki komai ba".. Dan tabe baki yayi kafin ya cigaba da bin hard cover din yana duba rubutun da tayi da jotting din.. Can wata kujera taje ta zauna tana kallon sa tana hararan sa hoping that zezo ya bata hakuri.. Ya ganta amma ya share.. Wanda suka gama wayane ya karaso Jalal ya daga kai yana kallon matashin da zasuyi tsara bayan ya gaisar da jalal ya amsa snn Jalal ya fito da wasu passport ya mikawa matashin snn yace "Ameer wnn ranar da saif ze rasu na gansa a gidan mu a part dinmu ma but after the incident bn kara ganin sa ba inaso ka binciko mun shi.. And you didn't bring any information akan wnn poison din"..Ameer yayi dan murmushi "we're still Woking on it" Jalal ya gyada kai snn sukayi sallama daAmeer .. Mikewa Jalal yayi da kamar ya aje mata hard cover din se kuma ya fasa ta tafi dashi.. Imaan na kallon sa har ya fita sakin baki tayi ganin ya tafin mata da jotter wanda sukayi amfani dashi ynx ita da sumayya... Tasowa tayi tana kara hade fuska kafin ta dauki waya ta kira farouq yazo ya tafi da ita.. Ta dauki handout tana dan karantawa ranta duk babu dadi.. Sede tayi tsaki tace "baka san halina bane".. Farouq na zuwa ya kirata ta kwashe kayanta ta fita .. Yana ganin yanda take kumbure kumbure yace "yau kuma waya tabo zainabu Abu".. Ta cije libs dinta kafin tace "wlh ze san ni yayiwa haka Allah de ya kara hada mu".. Dariya farouq yayi.. Tofa wane me gangancin ne.. Nan imaan ta kwashe komai ta fada masa.. Ta karashe da fadin duk da ba wani abu sosai zanyi da jotter din nan ba nasan wata rana zata mun amfani and babban abinda yafi bn haushi shine yanda ya gama latsani ni akwai ma wanda ya taba mun Abinda yamun.. Ai kawai he should pray lets not meet for the second tym dan wlh seya gane kurinsa.. Dariya kawai farouq yake yana tunanin wane wnn.. A haka har suka iso...

..

Yana gama parking ya wuce part din kanin daddyn nasa daya kirasa tun yana hanya.. A parlorn sa ya iske su tare da Abokin Dad dinsa Alh barau.. Kansa kasa ya shiga ya gaisar dasu suka amsa snn Alh barau yace "yajikin fareedan".. Jalal ya amsa da Alhmdllh yanajin ransa babu dadi cike da tausayin mum dinsa.. Alh isa yace "to Allah ya bata lpy" Jalal ya amsa da Ameen.. Alh barau yace "toya yanayin jikin nata ana samun cigaba kuwa".. Shiru jalal yayi yanajin wani daci a cikin ransa.. Alh isa yace "my son kayi hakuri kaji nasan kai jarumine mum dinka zata samu lpy ynx maganan poison din nan har ynx ba'a samu maganin ba... Kome doctors din sukace.. "Da kyar jalal yace "har ynx de Abba".. Alh isa yace "srry son inshaallah zamuga yanda za'ayi keep on praying" gyada kai yayi kafin yayi masu sallama ya fita.. Tun bayan da akayi poisoning mum dinsa babu wanda ya kara bi takansu se lokacin da dad dinsa ya fito dashi daga kurkuku lokacin da dad dinsa ya dena kyarar sa ya janyo sa jikinsa se lokacin suma suka dawo da kula sa be sani ba ko abinda akawa mahaifin nasa ne ya shafesu har suka dawo kula dashi sbd koda dad ya dawo yana son Jalal kaman hauka har yau be kara bi ta kan mummy ba ko tambayar ta be tabayi ba hakama granny.  Alh isa ne da Alh barau Sukacigaba  da biyan duk wasu bills da ake bukata game da lafiyar mummy har yau kuma kuma koda yaushe suna tambayar sa idan ana samun cigaba .. idan kuma akwai wani taimako da zasi iyayi shiyasa sunadaya daga cikin wadan da yake ganin girman su.. Amma idan ka cire su to shi kowa ma ya matsa masa lamba....

Har ya shiga parlor ya tunada hard cover din nan yaje ya dauko sa.. Ya taho yana dan kallon sa gamshin ta kamar me a jikin littafin..

Ranar weekend imaan baccin ta tasha yayin da su yusrah suka fita karatu dan ita dama weekend hutun ta take sha se yamma sumayya tazo.. Sukayi karatu imaan ta fada mata yanda akayi da jotter ta karashe da fadin Allah besan halina ba but zamu hade.. Ita de sumayya dariya kawai take dan ta kula imaan din nan bataji.. Gab da magrib suka gama komai suka shiga kitchen tare sukayi girki snn suka yi sallah tym din su maryam suka dawo.. Tare duk sukaci abincin da sumayya data sake dasu.. Snn suka rakata har mota ta tafi..

Duk yanda imaan ke adduar Allah ya hadata da gayen nan basu hadu ba domin kau har kusan 2weeks ynx kam semester tayi nisa dukan su sun maida hankali a wajen karatun su.. Sumayya ma duk abinda bata iya ba takanzo su koya mata yanda suke rayuwa se abin yake birgeta komai nasu cikin barkwanci duk wani abu daze sakasu dariya shi sukeyi.. Wani irn mutunci sukeyi sosai da imaan dan inde har lectures dinsu beyi yamma ba sosai takanzo su wuni tare... Ranar imaan na tare da wani saurayinta daya matsa mata se sun fita suna cin wani kayataccen eatery daya amsa sunan sa na manyan mutane kamar ance ta kalli window taga Jalal ya fito a wata mota ware idanu tayi tana kallon sa da kyau ganin shine tsabar yanda take so ta gansa jikin ta har wani rawa yake.. Tama rasa abinda ya kamata tayi.. Saurayin nayi mata magana amma bata wani responding dama ba abinci take ci ba waya kawai take dannawa se kuma dan kalli TVn dake wajen..

Jalal na shiga da ita ya fara hada ido a wajen.. A ransa kuma yace "to its has been a while".. Hararansa tayi ya dauke kai.. Imaan ta dauki wayar ta text tayiwa farouq tare da kalar motar da jalal yazo da ita.. Ta aje wayar lokaci lokaci takan kalli Jalal ta kalli window taga ko farouq yazo sbd tasan babu nisa daga inda yake ynx. Hada idanu sukayi da Jalal ta balla masa a harara tana kara daure fuska.. Jalal ya dauke kansa yana kokarin hana kansa murmushi dan yasan mugun haushinsa take ji.. Ajiyar zuciya ta sauke ganin farouq ta window... Kusan minti biyar kafin farouq ya dago ya mata alamar aiki yayi.. Wani numfashi ta sauke tana kallon jalal da kansa ke kasa.. Dagowa yayi suka hada idanu ya dage mata gira daya alamar yade?... Gwalo tayi masa tana wani murmushi.. Jalal ya tabe baki kafin ya ya tashi sbd wani uzuri daya taso masa.. Itama da yake sun gama suka mike.. Jalal na isa wajen motar sa suka fito ba tare daya kallesu ba ya bude motar ya shiga dama ba tasa bace ta Mahmoud ce da suka fito tare shi ya sauka wani waje shi kuma yayo nan.. Yayi mata key zeyi reverse yaji motar na wani cikewa.. Budewa yayi ya fita daidai lokacin da imaan zata shiga mota tayi masa gwalo tana ware masa manyan idanun ta cike da jin dadi ta shige motar suka bar wajen.. Jalal ya bita da wani kallo alamar lafiya kafin idanun sa ya sauka akan tayoyin motar da duk suke a sace.. Daya duba seyaga duka an sacesu".. Jalal ya ware idanu cike da mamaki kafin yace "this is serious"... Dan dafe kai yayi "oh this girl.. What's a stubborn girl".. And cizar lip yayi kafin yace "and lastly de an sace min taya".. Shi har mmkinta yake.. "Idan zatayi abu ita babu ruwanta kawai duk abinda yazo kanta yi take".. Waya ya dauka ya tura message kafin ya koma cikin motar ya zauna.. Cikin seconds wani yazo da motar sa.. Karbar key din yayi snn ya shig motar ya bar wajen shi kuma wancan dayazo da me saka taya suka fara sakawa...

Imaan kau zuciyar ta fess ta koma gida.. Suna zaune a parlor sede ta fashe da dariya hango fuskar jalal kawai take tasan ko kafin a saka masa wasu tayoyin ya wahala su yusrah sa tambayar ta suke amma taki fadan abinda ya faru.. Seda farouq yazo ya fada masu.. Suka dunga kyalkyala dariya....

Jalal yasan ganin imaan baze masa wahala ba amma de ynx bata ita yake ba tukun ta lafiyar mom dinsa yake dan kasar ma yake so ya bari sbd yanaso likitoci suyi masa bayani akan kan wani cigaba da suke ganin za'a samu...

Itama imaan har ta manta dashi ta maida hankali akan exams dinta da suke gab da farawa su labeeb kan kawo masu ziyara lokaci lokaci snn kusancin su da sumayya ya kara yawa.. A haka har suka fara exams dinsu ta first semester 200l.. Sun maida hankali sosai sunci serious kosu farouq a gidan suke wuni sbd idan sun gama karatu suna danyi discussion.. Sometimes wasu kanyi joining dinsu.. Ita kanta sumayya duk da ba course dinsu daya ba duk combine courses dinsu tana joining dinsu... A haka har suka gama aka basu hutu.. Ranar da suka gama ranar Abba ya turo a dauki imaan.. Itama cike take da kewar su .. Mommy ba karamin delicious ta hada mata ba tsabar murna har a baki take bata.. Imaan kam idan tana gaban mommy jin ta take kamar wata er 10yrs har zuciyar ta matawa take ba itace ta haifeta batake ba itace ta haifeta ba.. Baba na yawan fadu mata arai tana mugun kewar sa Amma har cikin ranta taji ta tsani garin ta tsani zuwan shi.. Koda Abba yace ta shirya a kaita tace bata zuwa.. A haka de ta cinye hutun ta ta koma sch....

Kamar yanda suka saba dama farkon samester ba shagalin su suke sha.. Ranar suna zaune sumayya ta shigo.. Rungume juna sukayi.. Maryam tace ke se yau ake ganin ki tana murmushi.. Tace "wlh.. Snn ta bude jakar ta ta fito da invitations masu mugun kyau guda biyar ta basu "gashi bikin yayata akeyi next 2weeks dan haka zuwa dole".. Dariya sukayi.. Student da zuwa biki".. Hararar su tayi.. "Ai wlh baku isaba se kunzo tunda de semester batayi nisa ba.. And ko wane event se kunzo ba wasu dayawa bane kamu se dinner snn yinin biki shknn".. Yusrah yan inada biki tuni tace "kwantas kamar kin ganmu ne mu biyar din nan cas se munzo".. Nan sukace mata zasu zo taji dadi sosai dama ita ba wasu kawaye ne da ita ba....

Urs

Annafie😍

Any one reading this book should knw that its not for free its just #300 pay through the Account below
2148886852 Nafisa Abdulbasir UBA BANK and show ur evidence via this number 07051376476.. But for now enjoy the free pages😊 thank you Annafie loves you all 🥰❤️as you keep supporting me encouraging me as I keep suburbudo maku novels masu dadi 🥰
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/H27abREXIQn8Rp0DbZBhE2💫💖Jalal Ali(11)💖💫💫. 

- [ ] Imaan ta dubi wayar ta dake ringing for the fourth time.. Imaan ta marairace kamar zatayi kuka tana daure da towel.. Sumayya tanaji ta dauka tace "haba dan Allah tun dazu kunki zuwa harfa an fara tafiya".. Imaan tace gamu nan fa har mun fito" pls kuyi sauri... Katse wayar tayi yusrah ta bi imaan da harara "tun dazu neman kayan sawa kade kina bata mana lokaci".. Murguda baki imaan tayi kafin ta dauko wani tsaddiyar atampa anyi masa wani lafiyayyen dinki na doguwar riga.. Sakawa tayi simple daurin dankwali ta saka ear rings masu kyau fuskan ta as usuwal no make up amma tayi kyau atamfar tayi mugun haskata snn libs dinta Kamar ta shafa pink lipstick.. Mayafin ta saka bayan ta dauki bag dinta da sabuwar wayar ta da Abba ya canza mata.. Maryam tace "pretty girl I love you".. Murmushi imaan tayi tana dage gira.. Suka jera suka fita da ka gansu kasan babu raini kuma idan kaga fuskar su babu kwalliyar haukan nan suka shigar motar muneer.. Farouq ya juyo yace "I got the prettiest frnds shiyasa kuke cin uban gayu".. Duk dariya sukayi maryam ta basu address din suka tafi... Irin unguwan manya manyan masu kudin nan ne wanda da wuya ma kaga mutum sede kaga manyan motoci imaan ta rinka bin unguwar da kallo tunda take bata taba ganin irn wnn unguwar ba sometimes ta kan godewa Allah ta kuma godewa Abba da mommy da sukayi sanadiyar canzawar rayuwar ta ynx kila tanacan anyi mata aure tana wahala wata kila ma harda yara kuluwa ce ta fado mata a rai.. Murmushi tayi tanajin wani irin kewar ta.. Sukayi parking a waje cikin jerin manyan motocin.. Imaan ta kira sumayya tace suna waje.. Babu jimawa seka sumayya dake kusa.. Ta karaso cikin kaya na alfarma ga kwalliya an mata tayi wani kyau.. Rumgume su tayi daya bayan daya tana murnar ganin su.. Ta kama hannun imaan "lets go inside kuci abinci se mu wuce..." Tare su ka tafi su muneer zasu tsaya tace se sun shigo... Imaan da kyar ta iya kame kanta bata tsaya kallon gidan ba dan tunda take bata taba ganin gida me kyau ba kalar wnn su kansu su yusrah sun san me gidan nan ya tara.. Part dinsu suka nufa..mutane sun fara ragewa sbd duk an fara tafiya wajen kamun.. Sumayya ta ajesu a wani parlor tuni tuni aka cika masu gaba da abinci kala kala .Sumayya seda taje ta taso da mom dinta ta kawota wajen su imaan suka gaisa..mom tace "yaude naga su imaan maryam da kuma yusrah kullum se an bani lvrin ku ya karatu".. Suka amsa da Alhmdllh.. Sumayya duk wani makusancin ta seta nuna masu su imaan kuma a tare su hannu bibiyu.. Hakan yasa su imaan sukaji dadi ganin yanda kowa ke marhabun dasu... Bayan sun gama suka fito zuwa wajen kamun sumayya tace bafa zasu tafi a yanda suka zo ba dole ta hada su farouq da wasu matan guda biyu.. Tace ga yan mata na maku.. Dariya sukayi.. Tuni hada su yusrah da wasu cousins dinsu da sukace ta samo masu budurwa.. Ya rage daga ita se imaan kawai duk wanda ya mata maganan imaan tace bata bayarwa imaan de su murmushi take.. Sumayya ta kama hannun ta kinga muje ciki tare zamu wuce bari naga ko zulfa ta shirya tazo mu wuce... Part din dayafi ko wane girma da haduwa suka nufa.. Suna tafiya suna dariya.. A daidai kofar entrance din Jalal ya fito waya kare a kunnen sa.. Gaban imaan ya wani mugun faduwa dan ita ta fara ganin sa cikin wani tsadadden yadi cream color yayi wani masifan kyau kansa babu hula se gashin sa dayasha gyara yanada magana yana dan cije lips dinsa bema kula dasu ba.. Sede daga idon dazeyi ya sauke idon sa a akanta har ya dauke kai se kuma yayi saurin maidowa gareta domin tabbatar da ita din ce.. "Yes she's the one" ya fada a ransa.. Katse wayar yayi kafin underneath his breathe yace "oh dis gal".. Imaan kau hantar cikin ta seda ta kusa kadawa.. Kafin a ranta tace "dama anan gidan yake".. Sumayya tace "yaya Jalal zakaje ko pls kada kace bazaka ba"... Dan yatsina fuska yayi yace "to me zanyi".. Sumayya ta marairace tace "pls mana" Yace ke ya baki tafi ba.. Tace "zulfa nake jira".. Hade rai yayi "bazan je ba".. Ta langwabar da kai "pls".. Yace "alryt kizo se muje tare but not with that gal zulfa or whatever ever".. Cike da jin dadi tace "to yaya bari nazo muje.. Gyada mata kai yayi kafin ya kalli imaan da duk ta gama tsorata wani kallo yayi mata irn na ke kuma fa ?daga ina..? Imaan ta dauke idon ta da sauri... Shiga ciki sukayi nan babu kowa se uban kamshi dake tashi imaan ta jinjina kai tana mmkin irin dukiyar dake nan ciki ynx nan wnn data sace wa tayar motar nan ne gidan su nop dole yayi jinkai wnn dukiya kamar baxa'a mutu ba and kuma gata a gidan.. Suka shiga part din su zulfa tana tare da wata kawar ta se make up da ake mata.. Sumy tace "wai har ynx baki shirya ba to wlh tafiya zanyi.. Zulfa ta harareta to ki tafi mana dan ma ina da kawar tafiya bare kimun wulakanci... Dariya sumayya tayi zulfa ta kalli imaan tace "wow sumy ina kika samo wnn kyakkyawar" sumy ta murguda baki tana fadin ina ruwanki.. Duk dariya akayi ta kama hannun imaan suka fito tana fadin mun tafi se kun taho... Suka fito Sumayya tace "ina fada mata da yaya Jalal zamuje wlh se an aje kwalliyar nan ta biyo mu".. Imaan tace "wai brothern ki ne" sumy ta gyada kai.. "Eh dad dinsa wan Abban mu ne".. Shiru imaan tayi har suka fito..motar sa na nan parke yana jiran su ya leko da kansa suna gaisawa da wani.. Idon imaan ya sauka akan numbern motan DEEN9.. imaan seda kanta yadan juya.. A ranta ta kara fadar deen shine..deen kokuma motar deen din ce.. Sunan sa dataji an fada ya fado mata.. Jalal.. JALALUDDEEN.. Wani miyau me daci ta hadiye tana addu'ar Allah yasa bashi bane.... Jalal duk yana kallon ta ta mirror yaga yanda jikin ta yayi sanyi.. Besan sanda yayi murmushi ba a ransa yana fadin dama yarinyar nan nada tsoro.. Zuge glass dinsa yayi kafin yace "zaki sani"... Sumy ta bude ma imaan ta shiga kafin ta bude gaba ta shiga.. Kamshi da sanyin dake cikin motar yasa ta wani lumshe idanu.. Jalal ta tada motar suka bar gidan snn ya kalli sumy yace "a ina ne".. Dariya sumy tayi tace "kai yaya wajen ma baka sani ba".. Dan tabe baki yayi.. Sumy ta fada masa kafin tace "yaya ga kawata imaan sch dinmu daya she's so brilliant duk abinda bn gane ba ita ke koya mun".. Dan kallon imaan da duk take a tsorace yayi ta mirror kafin yace "oh I see sannunta to".. Ya fada yanawa imaan wani kallo da duk yasa taji kamar ta fashe da kuka.. Kawai tuna ranar da tasa farouq ya sace masa taya take yanda taitayi masa gwalo snn babban tashin hankalin ta karda ace shine Deen din nan the baddest din da ake fada  .. Sumy tace "imaan ga yayana Jalal ko kice yaya Deen".  Imaan ji tayi kamar ta daga hannu ta fashe da kuka finally de wanda tayiwa laifi ya kamata ta and kuma ba kowa bane se Deen the bad boy din da ake fada.. Ta kyar ta iya hada magana tace "ina wuni" wani kallo yayi mata wanda yasa ta dauke kanta da sauri tana sauke ajiyar zuciya.. Sumy kam sanin halinsa yasa bata wani damu da yanda yaki amsawa imaan din ba sede bata san yanda imaan din zata dauka ba.. Sumy ce kade ke magana dukan su babu wani me bata amsar kirki.. Imaan kam tun kallon da ya mata bata kara yarda sun hada ido ba duk ma ta kosa su isa Kamshin sa duk yabi ya cika mata hanci.. Jalal ya kalli wayoyin dake saman cinyar sumy hannu yasa ya dauki wayar imaan yace "sis yaushe kika canza waya"... Sumy tace "yayi maka kyau ko wayar imaan ce".. Dan tabe baki yayi kafin ya kalli imaan ta mirror hada ido sukayi dan itama daidai ta dago jin ya amshi wayar ta suka hada ido wani kallo yayi mata.. Bata san sanda ta murguda masa baki ba.. A ransa yace "uhmm mai hali".. Rike wayar yayi yana dubawa kasancewar babu password snn yana driving da hannu daya a haka har suka isa kallon yawan motocin dake wajen yayi snn ya kalli sumy "ynx wajen nan dake cike da mutane kikeso naje anya zan iya shiga".. Sumy ta marairace "bari naje na duba mana waje wanda bazaka takura ba idan na samu I will call you seku shigo" ya gyada mata kai.. Ta ta kalli imaan "bari naje".. Kafin imaan tayi wani yunkuri ta bude motar ta fita.. Kallon sa tayi ganin ba ita yake kallo ba hankalinsa na kan wayar ta kamar tace ya bata se kuma ta fasa.. Tazo zata bude kofa yace "ina zaki".. Yanda yayi maganar ba tare daya kalleta ba yasa ta balla masa harara ya dago manyan idanunsa ya kalleta dauke kai tayi tana kokarin budewa taji motar a rufe.. Juyowa tayi tana marairaice wa "pls open the car".. Tabe baki yayi.. Kafin yace "do you think you're smart?".. Kin basa amsa tayi ta kallesa kamar zatayi kuka.. A ransa yace "so she's a fear lady" tunda yake ganinta be taba sanin tanada tsoro ba ganin da yayi mata yau ya gano matsoraciya ce kawai... tace "pls am srry kaga de ramawa nayi nima 1-1 kawai" ta fada cike da tsoro but gathering more courage... Dan kallon ta yayi se kuma yace "nop ni babu abinda na maki but yau zanyi this is ur phone kinga cikin sauki zan rama".. Marairaicewa imaan tayi idanun ta har sun fara tara kwalla.. Wayar sa ce tayi ringing ganin sumy yasa ya dauka.. Tace "yaya kaga gashi na samu".. "Ohk gamu nan". Y fada yana katse wayar yaji sanda imaan ta sauke ajiyar zuciya ya kalleta.. Dan tura baki tayi tana dauke kai.. Ya saka wayan ta aljihu snn ya bude motar itama ta bude ta fito.. Daidai lokacin da su zulfa suke fitowa daga mota knn.. Cak ta tsaya tana kallon su lokaci daya taji wani irin kishi.. Ita kanta imaan taga irin kallon da take mata irin me kama dana kishi.. Jalal ma ya gani seya saki wani murmushi yana kara matsowa kusa da imaan.. Yana kallon zulfa.. And imaan saw that smile sbd tym din daya matso kusa da ita.. Bata an kara ba se jin soft hands dinsa tayi cikin nata wani irin abu taji tundaga hannun nata dake cikin nasa har cikin kanta.. Shi kansa Jalal seda ya lumshe idanu sbd yanda yaji hannun ta da wani irin taushi kamar auduga be tabajin hannu mai laushi irin nata ba....Dakewa kawai yayi yana kallon zulfa data kasa boye kishin ta.. Kofar imaan da bata rufe fa ya tura imaan ciki itakam kamar wata mutum mutumi ta shige shima ya shiga tare da rufe kofar.. Se a lokacin hankalin ta ya dawo tayi sauri zare hannun ta tana daure fuska "stop touching me".. Dan tabe baki yayi kafin ya maida hankalin sa ga zulfa data koma mota ta zauna.. Ranta a matukar dagule tana tunanin abinda suke cikin mota.. Seda sukayi kusan minti biyar snn ya bude motar ya fita itama fita tayi tana wani hade rai.  Zulfa na cikin mota tana kallon su tafiya a hankali imaan keyi duk jikin ta a sanyaye tama rasa da wane zataji.. Tuntube tayi ta tafi luuuu zata fadi yayi saurin tare ta ta fado jikinsa runtse ido tayi tare da rike rigar sa gam tana sauke numfashi se kuma ta fara bude idanun ta a hankali har ta bude a kan fuskar sa.. Dan hade rai tayi tana tura baki se kuma tace "to sakeni".. Wani kallo yayi mata ganin karfin hali irin na yarinyar nan ko ynx idan ze saketa faduwa zatayi amma shirin yi masa masifa take.. Ganin yanda ta wani hade rai yasa ya saketa.. Aikam ta cakumosa jin zata fadi babu shiri ya rungume ta jin zata rinjaye sa su fadi kasa tare . within blink of eyes se sede kawai sukaji sun Rungume juna very tight yanajin yanda kirjin ta ke bugawa and yanda ta makalkalesa yasa yaji yarr wani abu me kama da kasala kasancewar be taba hugging wata mace ba..ga jikinta wani irin taushi da dumi wanda yasa kasa sakin ta besan sanda ya lumshe idanu ba cikin ransa ya furta ya salam.. Ita kanta imaan kasa motsi tayi domin kau yaune karo na farko da namiji ya taba rugume ta jikinta har wani irin yammm yake mata dumi da kamshin jikinsa ya cika ta bugun zuciyar ta ya kara wani gudu.. Zulfa is just watching them ganin yanda suka rungume juna har kusan minti 2 sunki sake wani irin bakin ciki da kishi yasa yasa ta bude motar ta fita tabar wajen tunda take yaune karo na farko data taba ganin Jalal da wata who's she?.. Ganin wucewar zulfa yasa Jalal ya dawo cikin hayyacinsa.. Ya sassauta rungumewar da yayiwa imaan snn a hankali yace "malama sakarni mana".. Imaan tayi saurin sakin sa cike da kunya amma seta hade rai tana tura baki se kuma tace "to ni nace ka rikeni ne".. Banza Jalal yayi da ita yana Tunanin anya akwai abinda zesaka bakin yarinyar nan mutuwa... A haka suka shika ciki zuwa inda sumy ta samar masu.. Yanda aka kawata wajen da ka gani kasan babu kushe sanda suka shigo anata gudanar da komai.. Kaf cikin kawayen nata babu wanda bata gani ba duk da su basu ganta ba.. Seda imaan ta saita kanta kafin sumy ta gane wane abu.. Tunda suka zauna bata yarda ta kallesa ba kamar yanda shima be kalleta ba wayar sa kawai yake dannawa.. Wayar ta kuma na aljihun sa .. Can de jin kansa na ciwo ya tashi ya dubi sumy "I will be going call me idan kun gama so that I wll take you back".. Sumy tace to yaya... Be kalli imaan ba bare ta saka ran ze bata wayar ta itama bata kallesa ba.. Tafiyar sa ce ma yasa ta dan sake har taje wajen su yusrah anan samari suka mata chaa sumy ce me cewa an bada ita.  Sede duk inda imaan tayi idon. Zulfa na kanta.. Imaan sede ta tabe baki a ranta tace kila budurwarsa ce... Se kuma tace "ni ina ruwana dakinsan meke tsakanin mu da baki ji haushi na ba cewar imaan ta fada a ranta... Kamu yayi dadi duk da imaan ba cikin dadin rai tayi sa ba amma su yusrah kam abu yayi masu.. Komai kamar yan uwa ga wadan. Da sumy ta hada su suna tare tuni har soyayya ta kulle..ana gamawa sumy ta kira Jalal. Bayan ya iso ya kirasu suka fita tare lokacin har an fara tafiya su yusrah duk sun wuce... Suka shiga motar imaan ta balla masa harara tana tunanin ubanme yake nufi da rike mata yawa.. Jalal na kallon ta ya nuna kamar ma be ganta ba.. Suna shigowa cikin unguwar su kiran maryam ya shigo wayar sumy.. Bayan ta dauka.. Maryam tace.. "Kinga tare zaku dawo da imaan ko ina ta kiranta a kashe mun wuce yusrah ma inajin sun isa sede zuwa gobe".. Sumy tace "ohk za'a maido da ita".. Daidai nan Jalal yayi parking a kofar gida jin ana kiran sallahr isha'i.. Sumy tace "yaya zaka sake fita ne".. Yce "zaku sake fita ne".. "Nop imaan zaka mayar dn Allah sch dinmu"... Yace "kuje kuyi sallah kafin na fito se tazo mu wuce".. Cike da jin dadi sumy tace "tnx bro".. Bude motar sukayi suka fita..

Imaan tayi magrib da isha'i sumy ta kawo mata abinci kadan taci.  Sbd hankalin da kaf yana kan Jalal tana tsoran binsa amma bata so sumy ta gane wani abu.. Shima kar yaga kamar wani tsoransa take.. Kiran sumy yayi yace "ta fito".. Sumy ta kama hannun ta suka karasa wajen motar yana ciki ta bude gaba ta sakata snn tayi mata bye bye tare da fadin karki manta da gobe fa kizo da shirin kwana plspls kinga dinner ne.. Imaan ta gyada kai.. Jalal yaja motar suka bar wajen... Kusan tafiyar minti biyar sukayi babu me cema wani kala.. Se can ta dan kallesa tabe baki tayi kafin ta dauke kanta  daga garesa snn ta fada masa inda ze kaita.. Shiru bece da ita kala ba har ta cire rai setaji yace "am not taking you home".. Gaban imaan yayi wata irin faduwa amma seta dake ba tare da nuna masa taji tsoro ba tace  "where are you taking me to".. Jinjina courage din ta kawai yake domin yaga tsoro karara a idon ta amma ta wani dake.. Dan kallon ta yayi.. Tayi saurin dauke kanta tana kara daure fuska.. Ya maida hankalin sa ga driving snn yace "you're going to pay what you did".. "Pay" ta fada ba tare da tasan maganar ta kubuce mata ba.. Sede ji tayi yace "sure gobe bazaki kara yiwa wani rashin kunya ba and later ki sace masa tayar mota".. Wlh yanda imaan ta tsorata da wnn gayen ba'a magana gaba daya a mugun tsorace take idan ta tuna kuma shine Deen se hankalin ta ya kara tashi amma dukda haka ta wani daure fuska Tana hana kukan da take ji zubowa dan tasan irin wadan nan mutanen idan sukaga kanajin tsoran su sunfi maka iskan ci... Ba tare da ta kallesa ba tace "but you did it first why did you sited on my seat at the fisrt place.. And took my book away".. Yanda take magana kade yasan she's about to cry.. He just wish yaga tana kuka so irin wadan nan matan marasa jin magana dama can cry oh wow shikam yau seyaga kukan ta ko ze barta.. Cos he can see yanda take hana kukan zubowa.. Se wani kara daure fuska take.. Ya tabe baki "cigaba da mun rashin kunya I will sure you why".. Cike da masifa tace "anyi din wlh if you try doing nonsense seka raina kanka and better take me home or drop me here".. Taso ta basa dariya amma ya dake.. A ransa yace kura ga tsoro ga ban tsoro .. A fili ko yace "so bakin ki baze mutu ba ko".. "Eh din baze mutu ba do what ever you think you can do" ta fada tana balla masa harara da idanun ta da suka fara tara hawaye amma tsabar masifa amma taki tayi shiru... parking yayi snn ya kwantar da kujerar sa yana kallon ta.. Shi tunda yake for his entire life babu macen da ta taba koda hararar sa ma balle har ajega gaya masa magana but wnn karamar yarinyar that is not even up to 20yrs tana hararan sa... Camly yace "don't do that again".. Kamar ya kara ingiza ta yayi.. Ta kara balla masa harara tan murguda baki... Bata an kara ba se ji tayi ya wani irin Fizgota ta fado jikinsa.. Tana kokarin tashi ya saka duka hannayensa sa ya zagaye ta ta kwanta a jikinsa sosai.. Hannu yasa ya dalli bakin ta.. ta kasa dago hannun ta ta taba lips dinta kawai seta kwantar da kanta a kirjinsa ta fashe da kuka dan wlh zafi taji.. Jalal najin yanda zuciyar ta ke mugun bugawa tana kuka.. Dan kara zagaye ta yayi da hannayensa se yaji duk beji dadi ba da take kukan ya lumshe idanu yanajin hawayenta na sauka a kirjinsa sa.. He wanted to say srry amma baze iya ba sbd yasan zata kara rainasa ne... Ita kanta yanda take kuka a kirjinsa sa se taji kamar is the best place to cry.. Ga jikinsa da wani irin dumi.. Dago jaw dinta yayi yana kallon fuskar ta data jike da hawaye ta lumshe idanun ta dogayen eyelashes dinta sun wani jike duk se yaji ta basa tausayi.. Ya dubi pink lips dinta da sukayi wani irin pink shima lumshe idanun sa yayi kafin a hankali ya daura lips dinsa a nata.. Ya bata wani light kiss for 5 secs.. Cak numfashin imaan ya tsaya jikin ta nayi mata wani irin rawa yanda ta zauna a jikinsa ya zagaye ta da duka hannayensa ga warm lips dinsa daya dora a nata yasa taji gaba daya hankalin ta ya wani irin tashi tunda take hakan be taba faruwa da ita ba.. Bugun zuciyar ta ya kara karuwa takula wnn tantirin dan iskane Dan haka gwara ta natsu su rabu lpy... Ta bude idanun ta cikin nasa.. Batasan tym din da tace "dan Allah kayi hakuri wlh bazan kara ba".. Taso ta basa dariya amma ya dake yana sake daure fuska yace "idan kika kara sena koya maki hankali".. Gyada kai tayi.. Ya taimaka mata ta sauka daga jikinsa ta koma kujerar ta.. Shi kansa duk ta sakar masa da wata irin kasala.. Besan meyasa ba daya taba ta seyaji wani irin daban barin ma ynz da ya bata wnn light kiss din duk seyaji bashi da kuzari kamar kar ya cire.. Bawai be taba taba mace ba.. Amma nata is different.. Dan satar kallon ta yayi kafin ya gyara seat dinsa ya cigaba da driving ta gefen idanu yake kallon ta yanda ta natsu.. Betaba ganin ta haka ba so this is her weakness ya fada a ransa... Imaan kau shiru kawai tayi dan su rabu lpy but she's just boiling from inside kawai tunanin abinda zatayi masa domin ta rama kawai take.. She will not let him go free. No.. Tana ta wnn tunanin se kawai taji an tsaya dagowa tayi taga yayi parking dede apartment dinsu.  Imaan ta bude mota seda ta tabbatar da kafafun ta sun sauka tace "kuma Allah ya isa.. And don't think I will let you go just lyk that atoh dan imaan bata barin bashi ta karashe maganar tare da jan wani tsaki ta fice tare dayi masa banging din kofar da karfi... Binta yayi da kallo ta cikin motar har ta shige ciki.. Murmushi yayi yace "stubborn girl".. Ya fada yana shafa lips dinsa se kuma yace "now I knw ur weakness".. Ya fada yana fito da wayar ta a aljihun sa.. Yace "she must come for this...

Urs

✨✨✨

Annafie😍2*💫💫💖JALAL ALII💖💫💫*



Written by



           *ANNAFIE💖.. ✍️*

     (Smll but mighty😉)



Writer of

*LOVE CYCLE❤️*

*SABODA DUNIYA🌃*

*ADAAN💕*

*JALAL ALI🤩*



Bismillahir rahmanir raheem

💫💖Jalal Ali(12)💖💫💫.

Kai a kasa imaan tashiga parlorn su maryam na zaune suna kallo.. Yusrah tace "waike ya muna ta kiran ki wayar ki baya shiga"... Se ynx ma imaan ta tuna bata amshi wayar ta ba.. Amma dukda haka bata dago kanta ba sbd bata so su gane tayi kuka tasan hankalin su tashi zeyi.. Tana zuwa bedroom dinsu ta cire kayan jikinta ta daura towel ta shige bathroom.. Tana wanka amma tunanin abinda zatawa Jalal take sede tana tsoran abinda zeje ya dawo dan takula shima A ne.. A haka de ta fito hankalin ta na kan wayar ta tasan kila mommy ta kirata.. Bari zatayi se gobe ta kirasu ta tambayi zuwa dinner idan an barta ta kwana idan kuma ba'a barta ba shknn... shiryawa tayi cikin sleeping wears ta shiga parlor har lokacin su yusrah na nan kallo suke bata kallesu ba ta wuce kitchen tea ta hada ta fito duk suka bita da kallo.. Zaunawa tayi snn tace "kuna ganin za'a barmu mu kwana kuwa.. Duk da sumy tace dinner baze dare ba but bana so dare yayi mana a waje".. Maryam tace "idan yayi dare mu kwana kawai".. Gyada kai imaan tayi.. "What take you har wnn lokacin baki dawo ba".. Ta gefen ido imaan ta kalleta se kuma tace "brothern sumy ne daze kawo ni be zo da wuri ba wayata ma can gidan na mantota".. Wani kallo maryam tayi mata imaan ma ta juya ta kalle ta dan kar su zargi wani abu.. Ajiyar zuciya duk suka sauke yusrah tace "brothern ta kode kode".. Murmushi kawai imaan tayi tana tuna Abinda ya faru tsakanin ta da Jalal yau.. Nan suka fara lvrin samarin su....

Washe gari imaan ta kira mommy a wayar yusrah bayan sun gaisa ta fada mata wayar ta a kashe take tana chargy ta tambayeta dinner.. Mommy tace "imaan sbd baki taba tambayana wani biki ba shiyasa ma na barki wnn kuma sbd duk nan cikin garin su maryam suke.. So inde har kunyi dare ku kwana bana son tafiyar daren nan kuma kima kama kanki".. Murmushi imaan tayi.. "Inshaallah mom za'a kiyaye thankyou mommy na I love you".. Mommy tayi dariya.. "Mayaudariya I love you too".. Daga haka sukayi sallama suna dawowa daga sallahr juma'a bayan imaan tayi girki ta kwanta tasha bacci tunda ita bawai wayane da ita ba bare ta latsa... Dinnern karfe 8 ne yake farawa yauma kamar jiya seda imaan ta hargitsa kaya kafin maryam ta dauko mata wata tsaddiyar atampa ko taba sata batayi ba kasancewar tasan imaan ta tsani less atampar ma dan de kawai biki ne.. As usual no make up amma tayi wani kyau sbd yanda atampar ta haska ta ga dinki ya wani kara fito da ita daurin dankwalin nan tayi na zara buhari ya zauna das a kanta dama tayi parking din gashin ta.. Idan ka ganta kamar ka sace... Already sumy ta turo masu address din event center din.. Tare dasu muneer suka tafi.. Koda sukaje an fara gudanar da komai gwanin ban sha'awa.. Sumy ta tare su cike da murna.. Tuni samarin su yusrah suka zo suka makale masu..imaan ta samu wata kujera can on the edge ta zauna sbd batason takura ko kadan.. Duk ma wanda yazo ze zauna setace masa is taken ta wani sha kunu tana danna wayar farouq dake hannun ta idan ka ganta ma dole ta birgeta ka.. Lokaci lokaci takan taga kai ta kalli yanda ake gudanar da komai ga abinci iri iri a gaban ta ko daya bataci  ba ... Kamar ance ta daga kai.. Suka hada idanu da Jalal cikin wani dakakken yadi se laeeb suna dan magana.. Dauke kai tayi gabanta na wata irin faduwa.. Ganin sa tare da Labeeb.. Dan kara daga kai tayi   wnn karon tare da Labeeb suka hada ido shi kuma baya nan.. Sauke ajiyar zuciya tayi ganin Labeeb ya nufo inda take.. "Wai dama kece".. Murmushi tayi tana dan hararar sa "aa kaine". Yayi dariya yana zaunawa "lyk serious da kyar na ganeki kinyi wani irin kyau".. Dariya tayi.. Kamar tace mene hadin sa da Deen din nan amma seta fasa tayi shiru kawai sukai ta lvri.. Har tym yaja basu sani ba sede sukaji an tashi.. Wajen 11 saura.. Maryam ta kirata ta wayar farouq "imaan mun wuce gidan su sumy ga kayan mu nan ma" tace "ohk gani nan"..ta fada tana katse wayar.. Sumy ta karaso wajen ta kalli labeeb tace "yaya labeeb ko kai zaka tafi damu wlh motana amarya tace na barmata ta kara".. Labeeb ya mike "ohk kumuje"... Fara tafiya sukayi sumy tace "so yaya Labeeb ina kasan imaan".. Kallon imaan yayi yana Murmushi dauke kai imaan tayi tana murmushi... Ya kalli sumy yace "imaan very stubborn girl me kukan saloon.." Imaan ta balla masa harara.. Tsokanar ta sukai tayi har suka isa gida.. Suma lokacin su maryam duk sun isa amma basu shiga ba suna tare da samarin nasu.. Duk tare suka shiga harda wasu kawayen sumyn da suke yan sch daya.. Dakin sumy dana yayar ta ta duk nan ta sauke kawayen nata su maryam dama ba wuyar sabo ne dasu ba tun jiya duk sun saba hakan yasa suka shige cikin su ana ta lvri.. Sumy ta kama hannun imaan suka fita kinga wnn dakin ba isar mu zeyi ba.. Muje akwai wani room ko mu uku ne sumu kwana.. ".. Fita sukayi tare da imaan dan tafe kai sumy tayi.. Snn tace "kinga na manta akwai maganin Amarya tace na karbo na manta rakani pls... Tare suka fito da imaan din.. Tunda taga part din da suka nufa gaban ta ya rinka faduwa.. Inaa gsky tsoran zuwa take no bazataje ba.. Suna zuwa gab.imaan tace "kinga jeki dawo bari nadan amsa call".. Sumy bata kawo komai ba ta shiga yayin da imaan ta matsa daga wajen dan bataso ko daya su hadu duk da tanason ta amshi wayar ta.. Sede abinda bata sani inda ta dawo ynx dede kofar sa ta tsaya domin daddy yasa an bude masa sbd biki.. Ko minti biyu batayi da tsayuwa ba ya bude kofar.. Tun bata daga kai ba ta gane shine sbd scane dinsa.. Gaban ta yayi wani mugun faduwa amma bata dago ba duk da taji alamar kallon ta yake shiko mmkin kome take tsaye anan yake .. Dan murmushi yayi kafin cikin cool voice dinsa yace "me kikeyi a wajen part dina".. Dagowa tayi ta zabga masa harara dan bata da lokacinsa.. Murmushi yy shi ba mutum bane wanda magana ta dama but he enjoy having conservation with her kodan wnn yarintar tata oho.. Yace "malama magana nake me kike bukata da har kikazo part dina".. Wani kallo ta juyo tayi masa kafin tace "me zan bukata idan ma ina da bukata na rasa wajen wanda zani sekai".. Dan taku yayi zuwa kusa da ita kafin yace "really".. Dan tafiya ta farayi dan ko daya bata son kusancin ta dashi.. Sede batafi two step ba idon ta ya sauka akan zulfa data tsaya tana kallon su da alama part din jalal din zata.. Tsayawa imaan tayi domin kau duk da tana nesa da ita taga wani irin kallo da take mata.. And jalal saw that hakan yasa ya karaso kusa da ita sosai imaan bata daga kai ta kallesa dukda tanajin sa kusada ita sosai.. Idanun sa akan zulfa yasaka hannun sa cikin na imaan a hankali.. Dan runtse idanu imaan tayi domin kau har ga Allah bataso wnn bawan Allahn na tabata ba dan tasara me takeji ide har ya taba ta.. She kansa kusan hakan ne wani ko hannun ta ya taba ya rasa abinda yake ji.. She ba wani taba mata yake ba besides shi ya tsani harka da mata but he don't know why he enjoy touching her he just want hug her again and kiss her kamar jiya he just want to feel more akan abinda yaji ranar nan... Imaan ta fizge hannun ta da sauri.. hakan yasa tayi baya zata fadi sbd da karfi ta fizge irin a masifar nan yayi saurin taro ta da hannu sa na dama ita kuma tayi saurin zagayo da hannunta a shoulder dinsa yanda sukayi din seyayi kamar yayi huging dinta ta side ne domin hannun sa na zagaye a cikin ta.. Zulfa ji tayi kamar ta kurma ihu watching them a haka.. Jalal yadan saci kallon ta snn ya maido da duban sa akan imaan dauke kanta tayi tana kokarin zamewa amma yaki bata damar hakan hannu yasa ya juyo da fuskar ta ya matso da ita dede tasa yana kallon indanun ta imaan ta lumshe nata idanun gaban ta na wani mugun faduwa.. Jalal ya dunga bin fuskar da kallo da tunda yake ganin ta be taba ganin ta da make up ba.. Dubansa yakai kan lips dinta da suke pink sosai he just want to kiss them again and feel her warm more a hankali yace "where are you going.” Shiru imaan tayi yace “she’s my girlfriend tana sona more than ur expectations and zata iyayin komai akaina".. Imaan de babban burinta ya sake ta ko daya bata so yana riketa barin ma ta riketa very tight a ynx se taji jikin ta har wani rawa yake"... dan kallon zulfa yayi da har idanun ta sun fara hawaye ganin wata a jikin jalal.. Dauke kansa yayi ya maida akan imaan har lokacin idon ta a lumshe a hankali yace "look at me".. Kokarin bude idon ta tayi amma ta kasa murya can kasa yace “look at me.. Imaan taki kallon sa murmushi yayi kafin a hankali ya daura lips dinsa a nata yana lumshe duka idanun sa.. Imaan ji tayi kamar zata fadi jin warm lips dinsa masu taushi a nata ta kankamesa juyoda ita yayi tare da hugging dinta ya zagaye ta da duka  hannayensa har tym din yana rike da lips dinta giving her a kiss fiye ma dana jiya wanda shi kansa besan ya iya ba tuni zulfa tabar wajen.. Jalal yaga tafiyar ta amma duk da haka ya kasa sakin imaan he don't knw why but he enjoy the moment.. Ita kanta imaan bazata iya fassara yanayin ta ba cos yanda jalal yayi hugging dinta da yanda dumin jikinsa ke ratsa ta is something else.. Jin tsuyuwar batayi masa yasa ya dauketa zuwa wata kujera me kamar ta lilo dake gefen part dinsa an kawata wajen da flowers zaunawa yayi tana jikinsa and har lokacin be saketa yanda yake kissing dinta very slowly cike da kwarewa yasa imaan kasa fahimtar abinda ke faruwa sunyi 5mins kafin hankalin ta ya dawo jikinta.. Batasan sanda ta fara hawaye ba karanto inalillahi a zuciyar ta kawai tunanin how it happens take dama irin haka na faruwa before you knw it sekaga anzo anyi abin kunya daga baya kuma azo ana danasani from the both side kowa zega kamar baze faruba amma shedan se da Addua da kuma kiyayewa..imaan ta rigada ta gane cewa namiji daban ne he can deceive you in different ways duk dubarar ka namiji yafita he's more smarter than you..tunanin da yazo ran imaan shine kawai ta fita harkan wnn mutumin duk wani abu da zatayi tasan yafi karfin ta kawai kafin yazo ya zubda mata da mutuncin ta... Hawayen da yaji tanayi ne ya maido dashi a hankalin sa.. Jinginar da bayan sa yayi sama yana sauke ajiyar zuciya yayin da ya kara rungume ta a jikin sa kusan minti biyu tana kokarin sauka kara janyo ta yayi jikinsa ta fashe masa da kuka. "Dan Allah kayi hakuri wlh I promise bazan kara maka rashin kunya ba I promise" taso ta basa dariya amma ya dake beyi ba rabata yy da jikin sa ta zauna gefensa ya kamo hannun ta ya saka mata wayar ta still be sakin hannun ba yace "share hawayen"... Sharewa tayi da sauri ya dan yi murmushi amma be bari ta gani ba ya idasa share mata hawayen yana fadin "kin yarda bazaki kara mun rashin kunya ba?".. Gyada kai tayi da sauri a ranta tana fadin bama se in zaka kara ganina ba" dan ji take daga nan wajen gate ta nufa bazata kwana gida daya da wnn dan iskan ba.. Hancin ta yaja kafin yace "good girl".. Mikewa imaan tayi ta nufi hanyar fita.daga part din.. Koda ta fita babban compound na gidan har ynx akwai mutane sbd yanayin biki.. Gate ta nufa direct koda ba fita akwai wasu motocin duk a waje wasu suna fira har ynx kusan 12 saura wuce su tayi kanta a kasa tana tafiya cikin katuwar unguwar da ko ina haske ne.. Haka de ta rinka tafiya tasan kome take sha a unguwar nan de bazata samu taxi ba. Setaje babban titi amma ta qwammace taje can duk Nisan data kwana a gidan nan tare da wnn dan iskan. Ko tunanin wani abu ze iya faruwa da ita a wnn daren batayi burinta kawai ta tafi... Kanta a kasa har tayiwa gidan nisa tanata tunane tunane. Sede kawai taji tsayuwar mota ta saitin ta taji tsoro sosai ganin dankareriyar mota.. Jalal yayi kasa da glass din yana kallon ta itama dauke kai tayi tana tunanin dalilin dayasa ya biyo ta.. Har lokacin idonsa na kanta yace "what bring you out da daren nan".. Kamar tayi bnza dashi se kuma tace "gida zanta tafi".. "Gida? Kin duba tym kuwa" Jalal ya fada da mmki.. Tace "eh amma tafiya zanyi".. Da mmki yake kallon ta ya jingina da seat kafin Camly yace "enter let me drop you home"... Imaan ta girgiza kai da sauri dan wlh mugun tsoransa take ba'a taba samun wanda ya mata abinda ya mata ba.. Kuma tayi ganganci ta har take tunanin zata iya ramawa mutumin da aka kira da baddest duk da batasan laifukansa ba yaci ace ta shiga taitayinta akansa tunda har aka kirasa da baddest.. Yace "kina tunanin zaki samu abin hawa da daren nan enter the car my friend".. Dan kallonsa tayi kafin tace "thank you  I will trake har na samu abin hawa.. Jalal ya lumshe ido yanajin babu dadi be taba ganin ta cikin sanyi irin wnn ba gashi cikin daren nan tace zata tafi.. Yasan duk shine sila dan haka baze iya barin ta tafi ita kade ba sbd besan me ze sameta ba.. Har ta fara tafiya ya kara zuwa saitin ta yana hade fuska yace "na zama tsaran wasanki ko get into the car now before nashigar dake da kaina".. Camly yake maganar but babu wasa a tare dashi.. Dan kallon sa imaan tayi se kuma kamar bazatayi kuka ba tace "promise me you won't touch me".. Jiyayi kamar ya fashe da dariya kullum halayen ta daban daban yake gani.. Batare daya bata amsa ba yace "get in".... A sanyaye ta bude motar ta shiga ta rufe . ... Seda suka bar unguwar yace "meyasa baki so na tabaki".. Ya fada yana tuna moment dinsu na dazu.. Ta gefen ido ta kallesa kafin tace "hakanan".. Yace "there must be a reason so tell me".. Ya fada hankalin sa na wajen driving.. Tace "ai babu kyau".. Ware idanun sa yayi yana kallon ta kafin yace "oh really?".. Shiru imaan tayi batare data kallesa ba.. Yace "rashin ji da rashin kunya akwai kyau knn".  Dan tura baki tayi "to ba nace na dena yi maka ba"... Ya dage gira daya kafin yace "sauran fa".. Ta juya ta kallesa alamar suwa.. Ya fahimceta dan dan haka yace "wadan da kikewa rashin ji".. Kamar ta murguda baki amma tayi saurin tunawa setace "ai kai nace na dena yiwa".. dan tabe baki yayi yana maida hankalin sa ga driving.. Imaan ta kalli side view dinsa.  A ranta tace he's just handsome.. Dan duk wandanda ta gani a gidan su sumy yafisu kyau kaf.. But why is he bad kodan yaga yana da kyau kuma yanada kudi domin ta kula babansa yafi na sumy kudi... Muryar sa taji yace "duk tym din da nake ganin ki rashin ji kikeyi".. Ta juya ta kallesa tace "a yaushe ka taba gani na".. Yayi murmushi yace "ranar da kukaje siyayya tare da wani sugar daddy saurayinki bayan ya gama siyayya kika masa wayo kika gudu kika barsa..  I was sitting beside you".. Ta juya ta kallesa da sauri.. Se kuma ta rufe fuska tana dariya Jalal yaji dadi yasan de at least zata rage jin haushin sa.. shida he don't care ko zakaji haushinsa ko zakaji munanen halayensa baze damu ba.. But ita kawai bayaso ta tafi tanajin haushin sa tace "tun last semester amma baka manta ba".. Yace "sure and the next day muka tareku kun fito daga saloon".. Ta kallesa da sauri.. Se kuma tace "banda kai su labeeb ne".. Ya dan tabe baki "I was sitting at the back you guys baku ganni ba".. Imaan ta saki wani murmushi yace "you're just frowning face sbd an maki saloon".. Imaan murmushi kawai take tana tuna Abinda ya faru.. Ynx duk hararar nan da take yana kallon ta  .. Yacigaba. "ranar da su labeeb sukazo tare mukazo.. I was inside the car naga sanda kikazo kika tafi and later on I met you in the restaurant.. You borrowed my phone".. Tun kafin yakarasa tace "wai dama kaine".. Ya dauke kansa "eh mana ga Aron waya na bayar amma kuma an kawo min abu kika amshe sede a kawo min wani babu ko kunya".. Imaan ta kyalkyale da dariya tana tuna Abinda tayi a tym din.. Yace "Agabana ake maganar za'a sace mana taya idan su Labeeb sukayi misbehaving segashi ba'a sacewa su labeeb ba ni an sace mun".. Imaan ta kasa daga kai ta kallesa kawai kunyar sa take ji.. Yace "you're so stubborn where are you from".. Dan murguda baki tayi kafin tace "ina ruwanka".. Dan murmushi yayi kafin a ransa yace "me hali baya canzawa"...

Suna karasowa gaban apartment dinsu kamar jira take ta bude da sauri ta shige gida tare da rufe gate din.. Jalal yayi murmushi tare da yin reverse ya wuce...

Imaan ta shiga ta kunna wayar ta.. Tun kafin ma ta zauna.. Wayar na kawowa kira ya shigo.. Yusrah.. Dauka tayi.. Ta kara a kunne hankali tashe yusrah tace "imaan wai kina ina sumy ta dawo tace ta dauka nan kika dawo kuma baki nan".. Imaan ta cire mayafin ta kafin tace "ina gida".. "Gida kuma yaushe kika tafi kuma kedawa da daren nan".. "Ni kade". Cewar imaan.. Maryam ce ta karbi wayar "to me akayi maki zaki tafi kuma ke kade ce a gidan fa taya zaki tafi ke kade".. "Wlh kaina saramun yake pls kibama sumy hakuri wlh babu Abinda akamun".. Tsaki maryam taja tace "amma baki kyau ta ba kuma ke kade zaki kwana gidan kome".. Imaan tace "eh su saudat duk sunanan ga hayaniyar su nan"... Kashe wayar maryam tayi cike da takaici.. Wanka imaan ta shiga seda ta shirya cikin kayan bacci ta hada tea snn tayiwa sumy magana ta what's app.. Hakuri ta bata snn ta fada mata Jalal ne ya maido ta amma karta fadawa su su maryam.. Tuni sumy ta huce with much surprise take fadin "wai yayan nawa kode kode".. Imaan tace "nop babu komai"...

Jalal na komawa part dinsa a parlor ya iske zulfa se kaiwa take tana komawa idanun ta sunyi jawur alamar kuka tayi.. Nunawa yayi kamar be ganta ba ya nufi stairs.. Tace "yaya Jalal".. Tsayawa yayi ba tare daya juyoba... Sanin baze juyoba ya sakata fadin... "Yaya ita waccen yarinyar dame ta fini da har ka zabeta fiye dani bayan kasan cewa Ina sonka"..  Juyowa yayi yana kallon ta.. Zulfa ta share hawayen ta.. "Yaya look at me me tafini dashi kyau, siffa kome wlh duk abinda kk so zan baka nide burina kawai ka soni".. Yana mata wani kallo yace "get out and kar na kara ganin ki a part dina". Fashewa tayi da kuka.. "Wlh sekasoni me zakayi da waccen karamar yarinyar me kk so wajenta wanda ni bazan baka ba kuma kasancewar inasonka".. Wani kallo kawai yake mata.. Juyawa zulfa tayi ta fita tana kuka sosai .. Jalal yace "stupid girl".. Ya haye sama zuwa bedroom dinsa.. Wanka yy ya shirya cikin kayan baccin sa snn yabi lpyr gadon sa.. Imaan ta fado masa a rai ya tuna dan conservation din da suka samu tare daze maidata gida.. Murmushi kawai yy yana lumshe idanu...

Urs

✨✨✨

Annafie😍

......💫💖Jalal Ali(13)💖💫💫

Har mama ta fara bacci zulfa ta shiga tana kuka sosai.. Mama ta tashi a firgice ganin zulfa na kuka yasa ta kamota.. "My daughter what's wrong".. Cikin kuka zulfa ta zayyane mata komai.. Ta kara da fadin "meyasa baya sona mama wlh ina sonsa".. shiru mama tayi.. Kafin tace "da gske kingan sa da wata a gidan nan".. Zulfa ta gyada kai. Mama ta dubi zulfa snn tace "go and shower snn ki kwanta I will think about it ai gobe daddy ze dawo".. Zulfa ta tashi tana share hawayen ta snn ta fita.. Mama ta tashi tanaji kamar tayi tsalle.. Atleast ynx Jalal yafara kawo mata cikin gida tasan dad dinsa idan yana daukar komai da yake ji bazeyi tolerating wnn ba and daga nan kuma ze dauki mummunan mataki.. Murmushi kawai tayi tana jinjina kai...

Washe gari karfe 8 su yusrah saka dawo gida imaan ko tashi batayi ba daga bacci batayi ba dan hankalin su ya kasa kwanciya duk da sumy tace su zauna sunyi chat da ita lpy amma sukaki zama.. Ganin tana bacci peacefully yasa hankalinsu ya kwanta basu tashe ta ba suka fara kokarin hada breakfast.. Sede bude ido tayi taga sun gama komai tace "kai daga ina".. Suka harare ta ba'a sani ba taya kike tunanin hankalin mu ze bayan bama tare dake ko so kike muci amanar mommy"... Murmushi imaan tayi cike daso da kaunar su.. Tare sukayi breakfast din  snn suka kama wata hidimar dan suda gidan biki de se an daura aure duk da imaan tace bata zuwa.. Duk mmki suke abinda yasa tace bata zuwa duk yanda suke da sumy.. Farouq da suka shigo suma yace "kode kin ma wani halin naki ne bakyaso ku hadu". Dariya kawai tayi amma batace komai ba tana tuno moment dinsu da Jalal har ynx idan ta tuna setaji kamar har ynx lips dinsa na a nata...

Shikam Jalal yau bacci yayi sosai har ma ya manta da wani daurin aure yau daddy ya dawo daga dubai amma har lokacin Jalal be tashi ba kamar de wanda ya shawu kuma bema sha ba.. Daddy ne ya shigo da kansa ya tashesa ganin yana bacci.. Jalal ya ware idanu se kuma ya rungume dad din nasa cike da farin ciki.. Wanda shi kade yake gani a ynx yaji farin ciki.. Duk da baya masa maganar mum dinsa yana sonsa sosai sbd yasan bayin kansa bane... Dad ya shafa kansa "my love how are you" "fne daddy ya hanya" "Alhamdllh get dress my frnd ko ka manta yau daurin aure".. Jalal ya sosa kai "no dad bn manta ba".. "Alryt tym na kurewa ga kayanan na siyo maka masu kyau I knw you'll love it".. "Sure dad".. Jalal ya fada yana kallon kayan da daddy ya aje masa.. " daddy yace "be fast nima ynx zan fito semu fita tare ko".. Jalal ya gyada kansa.. Dad na fita ya shiga bathroom.. 30mins ya dauka wajen shiri  gaba daya.. Ya fito cikin wata lafiyayyar farar shadda anyi mata wani aiki me mugun jan hankali yasa hula data zauna a saman kansa tsaf yayi wani bala in kyau kamar ka sace se wani uban kamshi yake yanda kasan shine angon bambamcin sa kawai shi besaka malum malum ba.. A nan main parlor ya samu Mahaifin nasa tare da kaninsa Da kuma sauran abokanen sa suma manyan mutane ne sosai.. Kusan shiga iri daya sukayi da Dad dinsa dande shi Dad din yasaka babbar riga.. Dad na ganin sa ya ware masa hannuwa.. "Come to me my little son" yazo daddy ya rungume sa kowa se murmushi yake na wasu yakai ciki na wasu iyakar sa labba.. Domin Daddy be damu da duk wasu munanen halayen dan nasa ba shide kawai yana sonsa kuma bayajin kunyar nunasa a ko'ina hakan yasa wasu ke ganin duk abinda Jalal din keyi harda sangarta.. Dad ya kama hannun sa suka fita mota daya suka shiga shida dadd din nasa idan ka gansu gwanin ban sha'awa kuma duk wanda yaga jalal yasan dan gata ne.. Mama ta tasaki labule tare da juyowa tana kallon kanwar tata.. Tace "har ynx ina iya bakin kokarina sede me son da mahaifin nasa yake masa yasa kome zeyi baya tsawata masa ke idan wnn yaron ze dauki hannu ya zabga mun mari a gaban sa wlh baze tsawatar masa ba semade ya lallabasa..duk wani so yana nunamin but there is clear deference between me and his son".. Hajiya jamila tace "tab to wnn wane irin kauna yake wa yaron nan".. Mama ta hadiye wani yawu kafin tace "kawai a jinin sa take. Inde kanaso ku shirya to duniya ka nuna kanason wnn dan nasa ko wadan da ke tare dashi din ai duk munafikansa ne amma in kinga yanda suke nuna son Jalal kamar me ai duk mun san su.. Lokacin da uban ya manta dasu waye ya taimaka masu ba haka sukai ta gararanba amma ynx kinga kowa nunawa yake yafi sonsa".. Hajiya jamila. ta sauke numfashi "to ynx mene abun yi".. Mama tayi wani murmushi tace "zan san abunyi dadi nama yaron banza ne ba wani wayo ne dashi ba kome zakayi sede kaji tsoran ubansa amma idan dan tashine baka da wani dar babu abinda ya sani sede yayi bacci yaje yawon iskancin sa ya shawo giyar sa yayi tatul ya dawo gida ya sake kwanciya washe gari ya tashi yana yan muzurai sakare kawai".. Duk dariya sukayi suna kara aibantasa dan kawai zuciyar su tayi sanyi...

Seda aka daura aure snn su yusrah sukazo ba tare da imaan ba daidai lokacin da motar sageer zata fita jalal ke driving sageer kuma yana daga front seat yana hada wasu takardu.. Hada idanu sukayi dasu Maryam tsaf ya kallesu ko zega imaan amma be ganta ba dauke kansa yayi yana zuge glass din sama su yusrah suka bar ganin sa a ransa yana fadin kome ya hanata zuwa.. Wata zuciyar tace kila fushi take.. Dan tabe baki yayi irin ita de ta sani yaja motar suka bar wajen da mugun gudu duk ma wanda ke kan hanyar sede ya basu hanya...

Yusrah ta sauke wata ajiyar zuciya snn ta dubi maryam.. "Tabdi wanan gayen hot ne kinga mutum kar yan littafi".. Maryam tace "tayani gani and daga gani very classic ji wani kallo daya yayi mana ya dauke kai yana wani zuje glass".. Yusrah ta kama hannun ta kinga muje naga sumy se naji ina ta suka samo wnn.... Maryam na dariya tace muje.. Sumy na dakin ta itama taci kwalliya kamar Amaryar tana ganin su tazo ta rungume su cike da murna tana shirin tamyar imaan sukace "ke wani hot muka gani a ina kuka samo sa".. Sumy ta yamutsa fuska "ana biki mutane dayawa taya zan gane wanda kuke nufi".. Yusrah tace "no wnn dan gidan nan be da alama sbd motar sa daga nan ta fito.. Wlh ya mugun haduwa gashi very classic oh wow".. Wani murmushi sumy ta saki domin ta gane wanda suke nufi tace "yaya Jalal ne dan nasan babu wanda ze ruda ku haka kamar shi".. Maryam tace "bn taba ganin sa ba amma".. "Yaya Jalal ne fa ynx dinma sa'a kikaci amma imaan ta sansa dan shine ya kaimu kamu... Wait wai tana ina".. Maryam tace "mura take mun baro ta tana ta bacci" tayi mata karya dan bataso taji daban.. Sumy tace "Allah sarki Allah ya bata lpy bacin kince bacci take dase naje naga yanayin jikin nata".. "No karki damu ai da sauki" cewar yusrah"...

can wata unguwa su jalal sukaje tare da sageer. Nuna masa wani gida sageer yayi snn yace "kaga a nan gidan a nan iyayen sa suke wancan kuma suna zaune tare da matar sa yana da yara biyu amma ynx baya nan yana bayelsa  yakan dawo every 2to 3 months".. Jalal ya kalli gidaje snn yace "inaso a sakamun duk wani ido a gidajen nam shi kuma ku barsa sa zuwa lokacin daze dawo ba sauri muke ba a sannu zanji dalilin daya kaisa gidan mu kafin rasuwar saif.. Sageer ya gyada kai snn yace "bnji kace komai ba akan batun wanda sukace kayi attempting kashewa ba". Batare da Jalal ya kallesa ba yace "inasane I knw bature has already done with that".. Sageer yace "bro you have to wake up fa".. Jalal ya kalli sageer se kuma yasaki murmushi kafin yace "tym is coming barsu su rinka mun kallon sakare se till the day I point them out one by one they will pay for all what they did for now damuwa itace mum dina".. Ya karashe yana cizar lips dinsa yasan mum dinsa itace raunin sa dan haka samun lpyr ta kamar ance ya tashi ne daga bacci ne. Sageer yayi murmushi amma a kasan ransa yana tausayawa dan uwan nasa"...

.. Su yusrah ma ranar da wuri suka dawo sbd ana zuwa daukar amarya suka taho bayan sumy ta cikasu da kayayyakin biki wanda har suke ganin yayi yawa..

Imaan kam tana gida babu inda taje tana kan waya.. To kunsan wani lokacin inde bakasan kan zancen abu ba babu ruwanka dashi bama ka sannin yana existing ko abu ka gani inde bakasan shi ba ba kowane ki maida hankali bare ma kasan wani abu na faruwa.. To haka ta kasance da imaan tunda take bata taba haduwa da wani abu daya danganci Deen ba koma ta gani to bata maida hankali akai.. Amma yau tana shiga twitter taga lvri akan Deen shiga tayi tana bibiyar tweet din.. Nan taga latest na week din.. Nan gaban ta yayi mugun faduwa.. Ta shiga sosai to knw more about him.. Anan taci karo da bad halayensa.. Imaan ta runtse idanu cike da tsoro.. Ynx me irin wnn halin ta tsokano. Wnn ai yafi karfin baddest.. A rappist kuma a drunker ai babban me laifi ne wanda yakamata a kiyaye".   Hankalin imaan ya tashi sosai ta rinka addu'a Allah yasa ko a hanya kar su kara haduwa bare ko magana ta kara hadasu.. A haka su maryam suka dawo suka sameta bata yarda sun gane halin da take ciki ba ta shige cikin su suka rinka duba kayan biki .. Suna dan lvr harda labarin jalal suka bata tunma kafin su fadi sunan sa ta gane jalal suke nufi dan yanda suke fadar kyansa da kuma dagin kan ta gane shine.. A ranta tace "da zaku gane shine Deen zaku dawo hankalin ku amma de ita bama zata nuna masa ko magana sunyi ba".. Sumy tace "ai shine ya kaiku kamu".. Imaan tace "oh wai shi bn wani gansa ba ni".. Kallon ta sukayi.. Ta ware manyan idanun ta da gske fa bebi ta kaina ba nima bnbi ta kansa ba"...... Tun daga ranar imaan bata sake haduwa da shi ba har ma mantawa take ta taba ganin wani waishi jalal.. Karatun ta kawai takeyi sbd ynx semester tayi zurfi gashi dama kowa yasan karatun law yasan akwai karatu. Dan haka karatu suke sosai barin ma daga wnn semestern bazasu dawo ba SIWESS. dinsu zasuyi se kuma exams snn su dawo suyi final semester.. A haka har suka fara exams sunci wani mugun serious gashi mutane har wani like masu ake sbd suyi koyo dan kowa yasan su kaf kokari ne dasu na fita gasu de marasa jin magana amma suna daga cikin masukokari goma da za'a lissafo"...

****

A hankali jalal ya karasa cikin office din mutumin Wanda yake kamar uncle din mum din nasa shima ya taka rawa sosai a rayuwar sa.. Kansa kasa ya gaisar dashi mutumin ya amsa snn ya nunawa Jalal wajen zama.. Zaunawa Jalal yayi.. Dr Ameen ya dago ya kallesa kafin yace "jalal I have been waiting ka fada mun yanda kukayi da likitocin nan amma shiru shiyasa nayi kiranka".. Kan Jalal a kasa yace "babu wani cigaba da aka samu uncle sunce har ynx sun kasa tantance asalin poison din bare su hada mata maganin ta kawai de ynx suna taimaka mata da relievers ne".. Shiru uncle yayi.. Kafin yace "jalal why not muyi trying maganin mu na nan".. Uncle yayi shiru yana sauraren Jalal danjin mezece dan wnn shine karo na uku yana masa wnn maganar amma yaki Amincewa.. Jalal yace "babu damuwa uncle yanda kace".. Cike da jin dadi yace "good za'a iya mata ai acan ba seta dawo nan ba nasan abinda kk gudu knn inshaallah zata samu lpy".. Jalal ya gyada kai dan har ynx be cire hope da samun lafiyar mum din tasa ba duk da tsawon shekarun data dauka a kwance.. "Uncle Ameen yace zan bincika bn samo ina gudun karkaki amincewa ne kamar wancan karon amma inshaallah da  ansamu zan nemeka".. Jalal yace "ngd uncle Allah ya saka da Alkhairi".. Uncle yayi murmushi cike da tausayin Jalal sallama yayi masa snn ya fice... Daidai ze hau lifter suka kusa cin karo da imaan data tazo zata sauka.. Da sauri ta ja baya tana kallon sa gaban ta na faduwa amma ta dake.. Shima kallon ta yayi ya dade be ganta se yaga harta rame koda yake yaji su Ak na labarin exams suke.. Imaan kau a mugun gajiye take dan fitowar ta daga exam knn tazo submitting abu.. Ganin kallon da yake mata yasata fadin "good Afternoon".. Jalal yayi wani murmushi kafin yace "pass".. Gaba tayi ya bita har suka sauka daga lifter.. Snn yace "its has been a while ko kin dena rashinji"... Dan murmushi tayi amma batace komai ba shima shiru yayi har seda suka fita compound din sch din yace "let me drop you".. Imaan tayi shiru itafa ynx a garin nan idan da wanda take tsoro to yabiyo bayan jalal din nan.. Dan kallon sa tayi kafin tace "hope de ba wani abu zakamun ba".. Ya dan lumshe idanu sa kafin yace "I won't touch you I promise".. Itama murmushi tayi kafin ta bude motar ta shiga .. Seda suka fara tafiya tace "dama kana shigowa sch din mu".. Dan kallon ta yayi kafin ya maida hankalin sa ga driving snn yace "sure akwai wani uncle dina anan".. Shiru imaan tayi yace "how is ur exams" "Alhmdllh.gobe nake gamawa"... Ya gyada kai kafin yace "Allah ya taimaka daga nan se gidako".. Ta gyada kai tana sakin murmushi dan m jalal ya kalle ta inde tana murmushi.. Wani kyau yake mata shide kawai zece itace mace ta farko dayake tsayawa suyi having conservation cos komai nata is different.. Yace "where are you from" ta gefen ido ta hararesa.. Amma batace komai ba he saw her dan haka yace "sena tsokane idon nan idan kina hararata".. Imaan ta saki murmushi tace "to ina ruwanka"... Ya girgiza kai kafin yace "stubborn.".. Ta dauke kai kamar bazata ce komai ba se kuma tace "nice stubborn din".. "Yeah you're very stubborn".. Tace "not as stubborn as you". Ya kalleta kafin yace "really" gyada masa kai tayi ya dage kafada.. Daidai nan suka iso. Imaan ta kallesa kafin tace "thank you" yace "till when".. Ta langwabar da kai kafin tace "I don't knw beside kilama ba zaka kara gani na ba"... Ya tabe baki in don't care yace "good a gaida gida".. Budewa tayi ta fita yana kallon ta har ta shige gida . Snn ya juya motar zuwa gida..

Washe gari suka gama exams dama tuni kayanta a shirye suke tun kafin ta dawo daga sch har driver ya iso dan haka wanka kawai tayi aka zuba bags dinta a mota sukayi bankwana dasu yusrah har sumy seda tazo sukayi bnkwana kasancewar se exam zata dawo karo na farko knn da zasu dade basu hadu dasu maryam ba har kuka seda tayi yanda kasan an rabu knn.. Mota tashiga tana daga masu hannu har tabar ganin su.. Wajen 6 ta kusa sanda suka isa gida.. Da gudu imaan ta fito ta rungume mommy ita kanta mommy duk sanda zata dawo cikin wani farin ciki take tsintar kanta dan imaan akwai dadi zama idan ta tafi mugun kewar ta take.. Lafiyayyen abinci mommy ta hada sbd dawowar ta ta.. Daddy kam outing ya shirya masu duk da yanda imaan ta gaji haka suka fita da dare se 11 suka dawo sun kaita wajen ciye ciye sosai..

Satin ta daya ta fara zuwa court nan imaan taga yanda ake gudanar da Abubuwa duk da tasan su a rubuce kuma suna practicing a class amma wnn daban ne tunda zahiri ne.. Cikin sati uku imaan ta kara samun experience sosai kuma tana maida hankali tuni ta koyi .. dubaru da kuma fasihohi dan dama kanta akwai dauka barin ma da take da abun zuciya dan har zuciyar ta nata mugun son zama lauya.. Sukan ziyarci garuruwa sosai kuma tana kara fahimtar matsalolin dake faruwa da kuma yanda zaka gane gskyr zance komai tana daukewa a kanta.. Ynx haka ma daga zaria suke suna dawowa signing kawai taje yi snn ta fito domin samun abin hawa duk da babu nisa daga court din zuwa gidan su amma takan hau napep ta kawota har gida.. Daidai junction din daze shigar da ita layin gidan Su tace ya aje ta sbd gidan dake farkon layin da take son shiga duba wata makwafciyar su da batada lafiya dan tasan ta wuce ynx ba lallai ta shiga tunda bawani fitowa take ba dan idan suna tare da mommy kafin kace wani Abu sekaga tym yayi... Tunda napep din ta tsaya a kan idonsa har lokacin data fito ta basa kudin sa.. Ta juyo.. Jalal ya wani waro idanu.. Cike da mmki.. Kafin yace "I gueses so er kaduna ce".. Bude motar yayi ganin har ta wuce koma kula da motar sa dake parke a wajen batayi ba.. Yace "hey stubborn".. Cak imaan ta tsaya domin ta kara gasgata abinda kunnen ta ya jiye mata.. Hakan yasa ta juya domin tabbatarwa.  Aikam shine tsaye more handsome than ever.. Imaan tace "you me kk anan".. Ta fada tana kalle kalle.. Ya ware hannuwa kafin yace "you refuse to tell me inda kike so I find it my self anyway I just came to see you".. Wani miyau imaan ta hadiye tana masa wani kallo kafin ta kara kallon cikin unguwar tasu da bakowa but tasan a ynx Abba na iya dawowa.. Tace "pls me kk anan". Ta dage gira "am I not welcome".. Imaan ta furzar da iska kafin tace "ni nace kazo ne". "Ni kuma nazo". Cewar jalal yana kallon duk yanda hankalinta ya tashi.. Dan ita har ga Allah tsoran wnn bawan Allahn take.. Yace "I was just kidding you nazo ganin wani client din Daddy ne shine motana ya samu matsala And bansan kowa a kaduna ba tun dazu ina cikin mota I was just planing kila naje idan da akwai available flight kawai na tafi.. Ajiyar zuciya imaan ta sauke kafin tace "oh ni kuma bnsan wani m.. "Maganar ta ta makale ganin motar Abba.. Juyawa Jalal yayi shima yana kallon motar kafin ya juyo yace "ur Dad?" Ta gyada kai.. Kafin yace wani Abu motar Abba ta karaso wajen.. Tsayawa Abba yayi kafin ya zuje glass.. Imaan da duk taji babu dadi tace "Abba sannu da zuwa".. Abba ya amsa Hankalin sa na kan jalal... Jalal ma kai kasa yace "Abba barka da zuwa".. Cike da nazarin sa yace "barka meke faruwa anan".. Jalal yace "Dama motane ne ya samu matsala and bn san kowa a kaduna ba so I just met her zata wuce she's a frnd to my sister in sch".. Abba yace "kaima a Abuja kk". Jalal ta gyada kai kansa kasa haka kawai yaji Abba ya mugun yi masa kwarjini.. "What's ur name" cewar Abba.. "Jalal".. Cike da nazarinsa Abba yace "Ali Abbas".. Jalal ya dago da sauri ya kallesa kafin ya gyada kai yace "eh nine" ita kanta imaan gaban ta seda ya fadi sbd tasan kila yasan munanan halayen Jalal din ne.. Abba ya kalle imaan snn yace "you both enter the car lets go home snn ya dubi jala rufe motar muje gida za'a kira me gyara nan akwai rana".. Jikin Jalal a sanyaye yy locking motar haka kawai yaji baya iya yiwa Abba gardama.. Imaan kam gaba daya tsoro ya cikata.. Ta bude baya ta shiga Jalal ya shiga gaba.. Abba yaka ja motar zuwa gida...

...

Urs

✨✨✨

Annafie

.....*💫💫💖JALAL ALII💖💫💫*



Written by



           *ANNAFIE💖.. ✍️*

     (Smll but mighty😉)



Writer of

*LOVE CYCLE❤️*

*SABODA DUNIYA🌃*

*ADAAN💕*

*JALAL ALI🤩*



Bismillahir rahmanir raheem

💫💖Jalal Ali(14)💖💫💫

Abba na gama parking a cikin parking space din duk suka bude suka fito.. Imaan de kanta kasa sum sum sum ta shige cikin gida. Jalal ya bita da kallo harta shige snn ya maido da duban sa ga Abba dake waya da bakaniken daze gyara motar bayan ya fada masa inda motar take snn ya dubi Jalal "mu shiga ciki"... Gaba Abba yayi Jalal ya bisa a baya a ransa yace "yau gani a gidan su stubborn".. Babu kowa cikin parlor se sanyin AC da kuma TV dake aiki sede babu volume.. Abba ya dubi Jalal snn yace "sit down my son".. A hankali Jalal ya zauna har cikin ransa kuma yaji dadin yanda Abba yace masa son.. Shi dama tunani yake a ina Abba ya sansa har ya gane cewa shine dandan Alh Ali..ba Abun mmki bane kasan Jalal Ali amma sanin Jalal a fuska abin mmki ne..Abba ya hau stairs babu jimawa se gashi ya ya sakko tare da mommy.. Mommy ta kallesa se kuma ta kalli Abba.. Jalal ya gaisar da ita amsawa tayi murmushi dauke a fuskar ta.. Snn ta wuce dining snn ta juyo tace "the lunch is ready my son come to dining for lunch".. Dagowa Jalal yayi ya kalle ta for the first tym.. Hakanan yaji matar ta mugun shiga ransa yaushe rabon da yace yayi ma wata kallon uwa amma hakanan se yaji yanason yaci abincin ta as her son.. Mommy ta gyada masa ya juya ya kalli Abba.. Abba ya gyada masa kai tashi jalal yayi ya nufi dining din.. Ya zauna yana dan murmushi.. mommy ta fara serving dinsa kafin tace "wai imaan fa".. Kafin ta rufe baki imaan ta fito sanye da zumbulelen hijab.. Bata yarda ta kalli Jalal ba kamar yanda shima be kalleta ba hankalin sa na kan delicious din da mommy ke serving he just can't wait to test it.. Mommy tace "get the drinks".. Imaan ta bude fridge ta fara fito da ruwa masu sanyi da kuma drink din da mommy ta hada jera a dining har ynx taki yarda ta kalli jalal she can't believe wnn mara jin maganan ne a gidan su zaune... Seat taja snn ta kalli Abba dake tsaye yana kallon su har ynx.. Dan langwabar da kai tayi tace "Abba ur sit kana ta tsayuwa".. "Good my daughter kinga mom dinki ta barni a tsaye ta jalal kawai take".. Abba ya fada yana karasowa dining din snn ya zauna.. Imaan ma ta zauna gefen sa.. Mommy ta kalleta.. "Daughter abbanki kade ko ni bazaki bani seat ba ko".. Langwabar da kai imaan tayi kafin tace "mommy yunwa".. Mommy tayi serving kowa snn ta fara ci kowa ma haka.. A hankali Jalal ke cin abincin daya mugun masa dadi he really miss his mom.. Daga ido yayi suka hada ido da imaan ta balla masa harara murmushi yayi kafin a ransa yace "I can see dole kiyi rashin ji cos you are the only child".. Abba ne yace "dama kana da sister mace knn".. Jalal ya dago ya kalli Abba da idon sa ke kan TV yace "Aa cousin sis dina ce diyar Alh isa"... "Alh isa".. Abba ya fada yana maido da dubabsa akan Jalal.. Gyada kai jalal yayi kafin yace "eh".. Abba ya kalli mommy suka hada ido snn yacigaba da cin Abincin sa.. Daga nan babu wanda ya kara magana har suka gama imaan ta kwashe plates din zuwa kitchen .. Abba ya kalli Jalal snn yace "where is ur twin bro". Jalal ya kallesa da sauri se kuma yayi kasa da kansa a hankali yace "he's late".. Shiru Abba yayi yama rasa abin fada shikam Jalal a ransa fadi yake this man knws me amma a ina.  Wata zuciyar tace kila frnd din Daddy ne... Imaan ce ta dawo daki tayi niyar komawa Abba ya kirata ta dawo yace "ki rakasa sa an gama gyara motar".. Ta gyada kai Abba ya dubi Jalal. "My son zaka iya tafiya kada kayi dare.. Any tym ka shigo kaduna you feel lyk coming kazo kaji you're free ur mommy is always around".. Jalal yace "thank you Abba thank you mom".. Mommy na murmushi tace "you're welcome my son".. Ita de imaan kallon su kawai take.. A ranta fadi take dan bakusan wanene shi bane.. Jalal yayi masu sallama imaan ta fita abinda har seda ta kusa gate snn ya karaso suka jera babu wanda yace komai har suka fita.. Se taji yace "ur parents are nice really appreciate the hospitality".. Murmushi imaan tayi ta daga kai suka hada ido.. Tura baki tayi tana dauke kai.. Yace "stubborn girl why are you not in sch".. Kamar bazatayi magana ba se kuma tace ""siwess nake".. Yace "wow Allah ya taikamaka what course".. "Law".. Ta fada ware idanu yayi kafin yace "wow I love this course".. Imaan tayi dan murmushi snn tace "and I will not depend you".. Ya kalle ta kafin yace "why".. Ta ware hannuwa alamar hakanan.. Dan tabe baki yayi yana bude motar sa yashiga snn yace "nima bn gayyaceki ba I have many professional lawyers that will depends me and sure it will be sooner or letter hope zaki zo kallo".. Tana masa wani kallo snn tace "me zakayi a courts".. "Just forget when are you resuming".. Ta dage kafada ina ruwanka.. Ya tabe baki.. "My regard to mom dan Abba tell mommy that I love her food pls idan zaki zo sch she should cook for me seki kawomin".. Noke kafada tayi snn ta juya ta tafi ya bita da kallo kafin yayiwa motar key ya kama hanya kawai wani irin dadi yakeji tunda yake babu wanda ya taba yi masa karamcin da Abba yayi masa har ransa yaji yana kaunar Abba da mommy.. Imaan ce ta fado masa yy murmushi snn yace "stubborn girl"...

Sanda jalal ya shiga daki mama da kawar ta ya wuce a parlor ko kallo basu ishesa ba bare su saka ran gaisuwa.. Haj. Huwaila tace "fitsararren banza zaka gane kurin ka sanda uban naka da kk takama dashi ze fattakeka ya wulakanta ka se muga ta fitsara.. Mama ta tabe baki.. "Kina ganin sa de babu abinda ya sani sede yasha giya yazo ya kwanta".. Haj. Huwaila ta fashe da dariya snn tace "kadan knn idan uban yaga yana niyar saka masa hawan jini ai dole ya sallamesa daganan sauran mafarautan da bamusan ko suwane ba su karasa shi"...

Bayan zuwan jalal da sati4 suka gama siwess dinsu ynx exams kawai zasu fara imaan tacigab da karatun ta a gida dan tanaso se saura sati exams zata koma..... .

Jalal ya gama parking ya fito yana kallon gidan da akayiwa wani gini irin na turawa rufe motar yayi snn ya karasa entrance din gidan.. A parlor ya iske sageer yana kallo yana ganin sa ya mike yana murmushi "hey bro welcome ka zauna".. Fuska daure Jalal yace "where is he".. Ganin babu wasa a tare dashi yasaka sageer fadin "muje yana ciki".. Jalal dake ta cije lips dinsa yana kokarin danne bacin ransa yabi bayan sageer.... Wani daki suka shiga dumdun sageer ya kunna hasken daki nan da nan haske ya kauri daki ne lafiyayye amma babu komai a cikin se de cuttens na window. Wane mutum ne a daure a rufe masa fuska da wani abu.. Da sauri jalal ya karasa ya cire abin da aka rufe masa fuska dashi da karfin tsiya tare da kifa masa wani gigitaccen mari da seda yayi wata er kara sbd a zaba.. Jalal nayi masa wani kallo kafin yace "sunana Jalal Ali Abbas.. Tasiu barde inajin shine sunan ka".. Tasiu ya gyada kai yana wani nishi kafin yace "hakane".. Jalal yace "good ina fatan kasan duka family dinka na tare dani so idan kayi misbehaving ba kai ba har su seta shafa".. Tasiu ya runtse idanun sa cike da azabar najakin da sageer yasa wasu karfafa sukayi masa.. Jalal da zuciyar sa ke tafarfasa yace "ba senayi maka wani dogon bayani ba ranar da aka kashe saif kaje gidan mu har part dinmu ka gayamun me saif yayi maku and who send you".. Girgiza kai tasiu ya fara Jalal ya kifa masa wani mari.. Dan besan meyasa ba inde akan saif ne baya iya dagawa kowa baya iya controlling kansa.. Ynx a yanda yakeji ze iya kashe mutumin nan inde be fada masa who are behind this ba".. Tasiu yace "sure munje ranar da niyar kashe ku bama saif kade ba ku dukanku sede me an rigamu hakan yasa muka gane bayan mu Akwai masu bibiyar rayuwar ku".. Jalal yakai masa wani jahilin duka.. "Su wane su and ku wane ya sakaku".. Tasiu yayi wani murmushi cike da azaba yace "for now ba abinda yakamata ka fara sani ba knn lafiyar mahaifiyar ka itace yakamata kasaka gaba I will tell you this tun kafin lokaci ya kure maka".. Shiru Jalal yayi yana kallon sa with much interest.. Dan inde akan mahaifiyar sa ne yanada rauni.. Jin yayi shiru tasiu yacigaba   kaf duniyar nan bayan wadan da sukayi poising mum dinka mutum dayane yasan kalar poison din kuma ze iya hada maganin ta cikin kankanin lokaci sede mugayen da sukayi poison dinta bazasu bari ba sunyi kokarin kashesa hakan yasa ya gudu suka nemesa suka rasa tsayin shekaru knn se jiya suka gano inda yake.. Dan haka iname fada maka ka gaggauta zuwa tun kafin su kashe sa dan inde har ya mutu mum dinka itada samun lpy sede wani ikon Allah dan shine kade yasan kalar poison din... Jalal da jikin sa ke rawa sosai idanun sa sun kara wani irin ja ya cakuli kwalar tasiu.. "Wanene shi tell me da location ko ina ne a fadin duniyar nan zanje".. Tasiu ya kasa magana sbd yanda Jalal yaci kwalar sa.. Seda sageer ya karaso ya cire hannun jalal din snn tasiu ya sauke numfashi.. Snn yace "Dr Umar a kaduna yake.. Nan ya fada masu Address din idan sun shiga kaduna..." Jalal ya fita da sauri.. Sageer get the car ryt away".. Sageer ma bin bayansa yayi amma seda yatabbatar ya rufe ko ina yayi magana da masu tsaron wajen snn ya nufi motar sa yazo saitin jalal dake kai da kawowa ya Jalal bude da sauri ya shiga.. Ya duba Agogo yasan ko kafin su isa kaduna ynx, 9 tayi.....

Gudu sageer yake sosai lokaci lokaci yakan saci kallon jalal daya lumshe idanu yana sauke kananun ajiyar zuciya bnd cizon lips dinsa babu abinda yake.. Sageer knws jalal na mugun cikin damuwa shiyasa yake mugun basa tausayi ba kowa ne ze fahimci halin da yake ciki seshi da yake tare dashi a hankali yace "inshaallahu zamu samu nasara".. Jalal ya bude idanun sa da sukayi jaa sosai ya kalli sageer cikin rauni sosai yace "bro I love my mum inaso tasamu lpy tayi rayuwa kamar kowa nima nayi farin ciki".. Sosai sageer yaji tausayin sa yasan yanda jalal yake da rauni sosai akan mum dinsa bashi da wani buri daya wuce samun lafiyar mum dinsa duk shekarun da ta dauka a kwance be taba gajiya da ita ba.. Jalal ya katsewa sageer tunani da fadin.. "I thought hajiya Atika is behind all this sheda kawai nake jira na hada akanta kafin na tunkare ta but for today na gane cewa not only hajiya Atika Akwai wasu da suke da hannu dumu dumu a cikin rayuwa ta tabbass akwai and bnsan takamaimai wace illa sukamin ba da kuma wacce suke shirin yimun ita kanta Atika ynx na fara rikicewa bnsan menene takamaimai nata laifin ba.. Ya fada yana tusa hannun sa cikin gashin kansa tare da cizar lips dinsa da karfi.. Sageer ya girgiza kai.. Shi kansa gabadaya ya kulle.. Ya dubi jalal snn yace "lets  be calm mu natsu mu gano ko suwane inshaallahu a wnn karon bazasu kara cin galaba akanmu ba".. jalal yadan lashi lips dinsa da sukayi jaa sosai har wani zugi suke masa yace "wallahi wallahi wallahi anyone who's behind  rashin lafiyar mahaifiya ta da kuma mutuwar saif seya dandana fiye da abunda suka dan dana.i.won't spare anyone I will cut them into pieces wlh sena ga bayansu" jalal ya fada cike da alwashi zuciyar sa na wani irin tafarfasa.. Gaba daya hankalin sa nakan mum dinsa he knw she's suppering kawai burin sa yaga ta samu lpy besan me tayi masu haka ba har suka sakata a cikin wnn yanayin a iya sanin sa bata da wani abokin fada kuma koma me tayi she didn't deserve this......

Tara da yan mintuna suka shigo garin kaduna kasancewar sageer yasan kaduna sosai fiye da jalal yasa ya fara bin Address din Jalal ko banda zuciyar sa dake bugawa babu abinda yake fahimta burinsa kawai su isa Address din shi kade yasan irin halin da yake ciki.. Tsabar tashin hankali bema kula da unguwar da suka shigo ba.. Har seda suka kai tsakkiyar layin ya hangi motar yan sada a kofar gidan Abba da dukan mutane yan unguwar da suka yo cirko cirko.. Yan sandan sun hanasu shiga.. Dukansu basu san sanda suka fara furta innalillahi wa'inna ilaihirra juun ba domin kau sun san an rigada an rigasu jalal kam tashin hankali biyu knn domin kau inde har yana cikin hankalinsa wnn ne gidan su imaan knn Abba shine Dr din da yasan poison din to tayaya knn how shiyasa lokaci daya ya ganesa tun ganin farko .. Jalal da gabadaya jikinsa ke wata irin rawa bude motar ya fita da sauri sageer ma ya bude yabi bayan sa.. A bakin gate din police sun so hanasu shiga sageer ya nuna masu I'd card dinsa.  Babu shiri suka basu hanya suka shiga gidan da sauri.. Da gawar me gadi suka fara cin karo yan sandan na dubata da alama kila suma zuwan su knn.. Jalal ya shiga gidan da gudu gaban sa na wata irin faduwa yanaji kamar zuciyar sa zata faso kirjinsa... Wani dan sanda yayi niyar tare sa amma ya bigesa da karfin tsiya kafin yace "Abba!!!!!!".. Da karfi ya fada har gidan yana amsawa   .. Jalal na waige waige ya kara fadin "Abba, mommy, where are you".. Yan sandan da suke kokarin gano inda mutanen gidan suke duk tsayawa sukayi kallon Jalal dake kwala kiran Abba da mommy hankali tashe.. Ga jini ko ina alamar tabbas ko ba'ayi kisa ba anyi rauni me illa.. Jalal ya juyo yana kallon dan sandan yace "tell me where is Abba, where is mommy karkuce mun sun mutu". Jalal ya fada with breaking voice.. Police yace "calm down muma ynx muka shigo bamuga kowa ba sede wnn jinin da gawar me gadi.. Tura police din yayi kafin yayi hanyar stairs da gudu yana kwala kiran Abba da mommy.. Imaan ce ta fadu masa a rai.. Cak ya tsaya kome yake tunani se kuma da karfi ya kwala kiran.. "Imaaaaaaaaaaaan!!!! Ya fada kamar ze tsaga gidan yanajin kamar kansa ze fashe.. Karasawa cikin corridor din daya hada bedrooms din nasu yayi ya kara fadin.. "Imaaaan!!!" Where are you... "My son am here".. Yaji muryar Abba dakyar yana magana hakan yasa Jalal juyawa da sauri inda yake jiyo muryar Abba.. Shame shame ya kansa kwance cikin jini.. A bakin kofar dakin imaan.. Jalal ya karasa kusa dashi cike da tashin hankali yace "Abba oh my god ya Allah.. Hasbinallahu wani'imal wakeel.. Police come over pls lets take him to the hospital".. Abba dake cikin Azaba sosai ya rike hannun jalal da karfi yana kokarin fizgo magana yace "no son.. I wish I can help but bazasu barni ba mom tayi escaping nasan basu samu damar ganin ta ba tasan kalar poison din inde har ta samu dama she zata taimakeka nasan bazu kashe ta ba tasan maganin poison din.".. Abba ya cije baki yana dafe inda aka caka masa wuka dayan hannun kuma ya rike Jalal gam.. Jalal yace "pls lets go to the hospital".. Abba ya girgiza kai.. Kafin yace "and for imaan".. Da sauri jalal yace "where is imaan".. Abba yace "ku kiramin makocina Alh Aminu da kuma Alh shamsu".. Yan sandan dake tsaye duka wani ya sauka da sauri.. Babu jimawa se ga mutanen da Abba ya bukata sun zo.. Abba ya kalli Jalal snn yace "imaan Amanace a gareni tanacikin dakin ta na  boye ta a toilet ku balla kofar ku fito da ita.. Inaso na baka amanar ta.." Ya rike hannun jalal sosai.. Snn yace "zan baka Auren zainab inaso a daurashi ynx base anjima ba ka tafi da ita ka kula da ita amanace a gareni nasan watarana mom dinta zata dawo kuma zata taimakeka".. Shiru jalal yayi yana kallon Abba duk da tsabar tashin hankalin da yake ciki ya fahimci maganar Abba dallah dallah.. Abba ya rike hannun sa "pls son zasu kashe mun ita ne".. Gyada kai Jalal yayi a hankali kafin ya daga ido ya kalli sageer... Shima gyada masa kai yayi..anan Abba ya fadawa Alh Aminu dalilin kiran.. Babu bata lokaci.. Alh Aminu ya zama wakilin imaan Alh shamsu ya zama na jalal.. Sageer ya bada sadaki 50k dake aljihun sa aka daura auren Jalal da imaan.. Abba ya sauke ajiyar zuciya yana danne ciwon sa da har ynx jini ke zuba.. lokaci daya kuma ya lumshe idanun sa.. Girgiza jalal ya farayi hankali tashe amma baya motsi.. Da sauri yakai kunnensa saitin zuciyar sa.. Fos some second ya dago "sageer zuciyar sa tana bugawa fa do something pls".. Da sauri sageer yace "police get him out ynx lets go to the hospital".. Anan police suka dauki Abba jalal ze bisu sageer ya rike hannun sa "no bro lets go ina muga halin da imaan ke ciki".. Da sauri jalal ya juya dakin da Abba yace nata ne ya shiga sageer da wasu police suka rufa masa baya.. Direct toilet suka nufa.. Suna turawa sukaga imaan zube a sume.. "Babu alamar jini ko ciwo a tare da ita kanta da yake a bude gashin kan ya barbaje.. Gaba daya ko ganin barayin batayi ba amma tsabar tashin hankali jin lokacin da suka harbi Abba da caka masa wuka yasa ta sume.. Jalal ya duka ta inda take yana girgiza ta.. "Imaan, imaan" amma ina shiru ko motsi batayi.. Hankali tashe jalal ya dauketa "Sageer lets go to the hospital we need to save their lives".. Yana rike da ita har ya sakko ya fita police din suka rufa masa baya motar su ya shigar da ita ya daura kanta  a cinyar sa yana girgiza ta amma ina ko motsi batayi.. Sageer ya shiga mazaunin driver yaja motar sukabi bayan motar da aka tafi da Abba..

.. Done...so how's it😉 was it sweet😍 ya kuke gani idan imaan ta tashi taga jalal a matsayin mijin ta the baddest da duniya ta gama sanin munanen halayensa..? and shi jalal din ze karbe ta a matsayin matar sa? If no yaya zeyi da Amanar Abba? If yes shin wane irn zama zasuyi.. Shin mene hadin Abba da mum din jalal shin Abban zema rayu koko..mutuwa zeyi..  Ina mommy take..? Meme shirin Hajiya Atika akan jalal..? Shin bayan suwane keda hannu a cikin rayuwar jalal? Meyasa yayi shiru akan duk abinda ake fada akansa be taba nunawa duniya hakan karya bane.? . Ya labarin Baba, jummala da duk kauyen su imaan.?  Wadan dukkan wnn amsoshin suna cikin littafin JALAL ALII biya 300 ta wnn acc. 2148886852 UBA Nafisa Abdulbasir domin ki karanta hankali kwance babu hakki na akanki I asure you bazan baku kunya ba zakuji dadinsa fiye da sauran littattafai na na baya.. Anan na kawo karshen free page...

Urs

✨✨✨

Annafie😍

.......*💫💫💖JALAL ALII💖💫💫*



Written by



           *ANNAFIE💖.. ✍️*

     (Smll but mighty😉)



Writer of

*LOVE CYCLE❤️*

*SABODA DUNIYA🌃*

*ADAAN💕*

*JALAL ALI🤩*



Bismillahir rahmanir raheem

💫💖Jalal Ali(15)💖💫💫

Har kusan karfe 12 na dare su jalal na hospital din har ynx babu wani bayani daga likitocin dukkan su emergency aka kaisu jalal na zaune yayi folding duka hanneyensa a kirjin sa idanun sa a lumshe shi kade yasan a yanayin da yake ciki lokaci lokaci yakan bude idanun sa ya sukayi wani irin jaa ya kalli sageer dake ta kai da kawowa tare da police din.. ganin doctor din ya fito yasa su sageer suka nufesa.. Tashi jalal yayi ya karasa inda yaga sun shiga.. Jalal ya tura kofar office din dr din.. Sageer da inspecter din naciki duk juyowa sukayi suka kalle sa.. Seat yaja ya zauna likitan ya maida duban sa ga sageer. "Gsky daba dan kun kawosa Asibiti da wuri ba da ze iya rasa ransa ko ynx haka yana cikin mawuyacin hali and idan ba'ayi gaggawar ceton lpyr sa ba ze iya rasa ransa".. Sageer ya jinjina kai kafin yace "ya kk ganin za'ayi knn".. Likita yace "eh to idan da hali yakamata a fitar dashi ko kuma wani babban absiti domin akwai aikin da za'ayi masa".. Duk maida attention dinsa sukayi garesa jin alamar Abba ze iya samun lpy musamman ma jalal.. Likitan yacigaba "sun harbe sa a kafadar sa ko nace kirji sede be karasa cikin kirjin ba.. Mun samu damar cire bullet din sede akwai wani jini daya taru wanda dole se anyi aiki an fitar da jinin sbd kar ya taba zuciyar sa.. Idan an dace bayan aikin ze iya samun lpy amma a hankali a hankali.. Snn a cikin sa ma an soka masa wuka ta shafi hunhunsa shiyasa yake ta zubar da jini so akwai aikin da da'a masa yasamu lpy sede babu tabbas sbd sauki yana wajen Allah idan kuma aka dace ze samu lpy sede ze dauki lokaci....".. Lumshe idanu jalal yayi tabbas babban burin sa shine abba ya samu lpy yasan shine babban hope dinsa a ynx dan besan inda ze gano mommy ba. Ynx duk wani fatan sa yanaga Abba.. Ze kashe konawa ne snn ze jira har tsawon lokacin da Abba ze samu lpy domin itama mummy ta tashi tayi rayuwa kamar kowa.. Idanun sa a lumshe yace "how about the girl"... Dan murmushi likita yayi kafin yace "wnn mun samu mun shawo kanta though har ynx tana cikin tashin hankali sbd tsoratar da tayi amma munyi mata Allurar bacci dan zuciyar ta tasamu natsuwa zuwa asuba zata iya farkawa so zamu sake yi mata wata.. Sbd yanda ta tsorata komai ze iya faruwa da zuciyar tata amma idan ta samu isashshen bacci.. Zata iya farkawa lpy" dan cizar lips dinsa yayi kafin ya kalli sageer snn ya fice... Sageer ya kalli likitan snn yace "zamu tafi dashi zuwa asbah se kayi duk abinda ya kamata game da abubuwan da za'ayi masa.. Gyada kai yayi tare da fadin "inshaallahu".. Tashi su sageer sukayi suka fita..

Dakin da aka kwantar da ita jalal ya nufa.. Tura kofar yayi a hankali yanda bazatayi kara ba ya shiga... Tana kwance saman gadon marasa lafiyan.. Jalal ya karasa kusa da ida idon sa a kan fuskar ta da tayi fayau idanun ta a lumshe.. Kallon taka kawai yake cike da tausayin ta all the tsiwar nan da masifar nan babu ita.. Tunawa yayi ynx akwai aure a tsakanin su.. Gabansa yaji ya wani irin fadi.. Ba kowa yake tunawa ba se dad dinsa yasan Dad dinsa yana mugun sonsa but he will not tolerate this.. Koma baze taba bari dad dinsa yasan dukkan shirin sa ba.. So he have to do something... Maida idanun sa yayi ya lumshe.. Yanajin sanda aka turo kofar amma be bude idanun sa ba sbd yasan wane... Sageer ya karaso idon sa akan imaan dake bacci.. Maida dubansa yayi akan jalal da har lokacin idonsa ke lumshe.. Cike da tausayin sa yace "inshallahu everything will be ohk da izinin Allah se Allah ya toni asirin duk wani mai hannu.  “ Jalal ya bude idanun sa da har lokacin suke jawur ya kalli sageer.. Cije lips dinsa yayi kafin yace "me nayi masu me mummy na da brother na suka nasu?.. Sun hana mummy na tayi rayuwa kamar kowa, sun kashe dan uwana sun rabani dashi, nima basu barni ba shin memukayi masu".. Shiru sageer yayi yana kallon sa cike da tausayi daga yanda yake magana kade kasan akwai tausayi.. Jalal yacigaba "wlh idan na kama duk wanda keda hannu acikin lamurana seya dandana kudar da.. Sena bambance masa tsakanin aya da tsakuwa.. Saboda mugun ta irin tasu har tana shafar wadan da basuji ba basu gani ba".. Yayi maganar yana kallon imaan.. Sageer ya dafa shoulder dinsa.." Inshallahu ko suwane za'ayi walkiya kuma zamu gansu".. Jalal ya gyada kansa har lokacin idon sa na kan imaan..... Su jalal haka suka ga wnn daren ko runtsawa basuyi ba.. duk yanda sageer yayi da jalal akan ya dan kwanta amma yaki domin baze iya ba dan ayau yasan koda zesha giya baze iya bacci ba.. Har ya kosa ya koma Abuja domin yaga tasiu yasan dole yanada masaniya akan wadan da sukayi poison mum dinsa....

Sanda suke dawo daga sallahr asuba imaan ta farka.. Kukan ta da sukaji ne yasa suka karasa ward din nata da sauri .. Imaan saman gadon ta takure a waje daya tana da makalkale jikinta bnd sunan Abba dana mommy babu wadan da take kira.. Duk wanda ya ganta a lokacin seta basa tausayi.. Dr yazo wata allurar ya sake yi mata a hankali jikin ta ya fara saki har wani baccin ya sake dauke ta.. Ya juyo yana kallon su Jalal snn yace "zuwa lokacin da zata farka nasan lokacin zata dawo cikin hayyacin ta so ko ynx za'a iya sallamar ta".. Jalal yace "zaku iya sallamar mu".. Likitan ya gyada kai snn ya fice sageer yabi bayan sa... Sageer ya bukaci a basa abba zuwa Asibitin su na sirri domin basa wani taimako kuma police din sun Amince Kasancewar sa jami'in sirri.. Snn shi kansa likitan sanin can dinma babban Asibiti ne yasa ya amince tuni ya basu sallama.. Duk yanda sageer yayi da Jalal akan yaci wani abu kin ci yayi hakanan ya hakura.. Jalal da kansa ya dauko imaan da bata da nauyi ko kadan yasaka a mota snn ya koma seat din me zaman banza ya zauna sageer yaja mota suka bar hospital din dama already an tafi da Abba cikin motar Asibitin... Tunda suka taho babu wanda yace da wani kala jalal de ya jingina da kujera ya lumshe idanun sa lokaci lokaci yakan daga kai ya kalli imaan dake bacci ta mirror...

8 da wani Abu suka shigo cikin garin Abuja ... Sageer ya kalli Jalal snn yace "ina mukayi ko gida mukayi".. Wani kallo jalal yayi masa kafin yace "muje gidan dana siya last month".. Murmushi kawai sageer yayi snn ya dauki hangar gidan.. Kafin su isa gidan har 9 ta kusa.. Unguwar shiru snn ga manya manyan gidaje.. Domin ko daga gani irin ta hutuwar nan ce baron yanda aka kawata unguwar.. Jalal da kansa ya sauka ya bude gate bayan ya dauki key a motar sageer.. Sageer ya shiga da motar jalal ya rufe gate din.. Jalal yayi parking a parking space din da zeci mota uku.. gIdan bashi da wani girma amma daga gani irin na hutawar nan ne an kawata shi sosai.. Ko jiya jalal yazo gida kullum yana da wanda ke gyarasa tunda ya siyesa.. Domin yakan dan zo ya hutu tym to tym.. Babu wanda yasan ya sayi gidan nan se sageer...

Jalal ya bude back seat ya dauko imaan dake bacci har lokacin.. A kafada ya sakata snn ya nufi main entrance din gidan.. Be tsaya a parlorn that is very clean ba ya wuce da ita saman stairs.. Rooms biyu ne a corridor din kawai. Ya bude wani ya shiga.. Saman lallausar gadon ya kwantar da ita.. Tare da gyara mata kwanciya.. Yanda wuyanta baze ciwo ba.. Gani yayi an kunna wutar gidan yasan sageer ne dan haka ya kashe mata hasken dakin ya fita zuwa dayan room din dake kallon wanda take ciki.. Shima a gyare yake tsab ga kamshi ta ko ina yana son kamshi sosai domin yana sakashi natsuwa.. Kayan jikinsa ya fara cirewa snn ya nufi toilet..Wanka yayi ya fito daure da towel se karami yana goge gashin kansa.. Cikin kankanin lokaci ya shirya cikin wasu kanun kaya ya fito... kallo daya yayiwa dakin da imaan take ciki ya nufi down stairs.. Tun kafin ya karaso ya hangi sageer dake zaune daga shi singlet da boxer yana kokarin hada tea da kayan tea din dake saman center table.. Dauke kai Jalal yayi ya nufii dispenser yana fadin "malam lafiya zaka zauna mana gida a haka bayan kasan bamu kade bane".. Sageer daya fara shan tea dinsa ya ware hannuwa "kasan de baka aje kaya a room din down stairs ba.. So ni kuma bana fara hawar maku sama ba.. Tunda ynx akwai iyali".. Ya karasa maganar cike da tsokana.. Ta gefen ido Jalal ya kalle sa bede ce komai ba ruwan zafi ya diba a cup snn ya dawo inda sageer yake ya fara kokarin hada tea din.. Seda ya gama ya fara sha snn sageer yace "malam gama ka dauko mun kayan sakawa"... Wani kallo Jalal yayi masa kafin yace "bakasan hanyar dakin bane".. Waro idanu sageer yayi kafin yace "ni awa matar gida na sama me ze kaini".. Tabe baki Jalal yayi yacigaba da shan tea dinsa.... Seda ya gama sha snn ya mike yaje wasu kayan ya daukowa sageer snn ya dawo rike dasu.. Tunda ya taho sageer ke kallon sa yna murmushi.. Jalal ya hade rai kafin yace "what?"... Sageer ya ware hannuwa yana murmushi.. "Just looking at the latest ango"... Hararar sa Jalal yayi yana mika masa kayan snn ya zauna ya daura kafa daya kan daya.. Sageer ya saka kayan snn "har zuwa wane lokaci zaka cigaba da boyewa Daddy da mamy"..Jalal ya kallesa kamar baze yi magana ba se kuma yace "baze sani ba".. Wani kallo sageer yayi masa kafin yace "how taya zakayi aure kace babu wanda ze Sani"... Jalal ya dage kafada snn yace "sure zata zauna anan har zuwa tym din da Abba ze samu lpy na maida masa diyar su".. Kallon sa kawai sageer yake kafin yace "why".. "Ita kanta idan taga nine mijin ta bazata taba yarda ba.".. Sageer yace "really".. Kallon sa Jalal yayi kafin yace "sure.. Taya zata yarda da bad boy as mijin ta besides ni kaina shigowar ta rayuwa ta ze iya dakatar da wasu abubuwan".. Murmushi kawai sageer yayi snn yace "ohk.. Zanje Asibitin ynx idan yaso kome ake ciki akan Aikin Abba I will let you knw".. Gyada kai kawai jalal yayi.. Har sageer yakai kofa ya juyo.. "Wnn motar dake parke akwai key dinta a tare da kai ne?".. Jalal ya gyada kai.. "Sure yana cikin bedroom Dina".. Ficewa sageer yayi.. Jalal kuma ya ciro wayar sa a aljihu yana dan dannawa bayan ya kwanta saman kujerar bacci yake ji sosai Amma bayaso ta farka . can de ya aje wayar wayar tare da lumshe idanun sa lokaci daya bacci ya dauke sa... Kasancewar kujerar nada dan fadi tukuma da taushi sosai yasa baccin nasa yayi tsawo.. Dan yafi 2hours yana baccin kafin ya tashi bin parlorn yayi da kallo kafin ya tashi ya nufi stairs.. Dakin da take ya shiga.. har lokacin bata tashi ba.. Maida kofar yayi ya fito dakin sa ya koma ya dauki car key dinsa ya fito da sassarfa ya ke sauka daga stairs din yasan at anytym tana iya farkawa Kuma yasan zata bukaci Abinci.. Motar dake parke a parking space din ya nufa tunda ya sayi gidan ya saye ta babu wata alamar da zaka gane cewa shine a ciki. Dama duk wani wanda yasan sa yasan cewa baya fita a motar da ba'ayiwa number da sunan sa ba so wnn ma wani taku ne ta yanda duk wata fita da zeyi ta sirri babu wanda ze kawo ma ransa shine...wani eatry yaje yana daga cikin mota yayi waya babu jimawa ma'aikacin wajen ya fito rike da bag din take away guda biyu se energy drink.. Bude back seat yayi ya saka.. Already jalal yayi masu transfer din kudin dan haka yana sakawa ya kama gaban sa.. Har Jalal zeyi reverse kome ya tuna seya kashe motar tare da fita wani boutique ya nufa yana tafiya slowly kansa a kasa kamar wani mace har shiga cikin boutique.. Yan matan dake zaune wajen suka dago suna kallon.. Cike da yanga wata tace "hello sir you need something?".. Kallo daya yayi mata kafin yace "get me 4 Abayas sleeping wears da duk wani abu da mace zata bukata in 3 dys".. Tace "harda su creams".. Dago manyan idanun sa yayi ya kalleta snn yace "I said all".. Kujera ta basa "have a seat bani 5mins".. Jalal zauna tare da crossing legs ya fito da wayar sa yana dannawa batare da ya kara kallon ko wacce cikin su ba.. Suko sunga hot guy se wani yauki suke😂.. Ciki minti biyar ta dawo rike da da basket ya dago yana kallon ta.. Snn yace "hope you didn't forget with hijab ".. Dan ware idanu tayi kafin tace "nop". ya maida hankalin sa ga wayar sa snn yace "ki saka biyu".. Juyowa tayi ta dauko hijabs biyu ta saka snn tace "wnn kilan girlfriend dinka ce ko.. Ta fada cike dason tajasa da fira.. Batare daya kalleta ba ya kalli dayar dake calculating kayan "the bills".. fada masa tayi tare fadin cash ko transfer?.. Board din da account number dinsu yake ya kalla snn yace "I will do transfer".. Babu bata lokaci yayi transfer din kudin tare da fadin "done".. Ficewa yayi aka biyosa da kayan aka saka a back seat snn yaja motar.. Duka kayan ya dauka bayan yayi parking a parlor ya aje kayan ya haura sama.. Kofar dakin ta ya tura wanda jin an turo kofa yasa imaan dago idanun ta da suka jike da hawaye sun kuma kumbura sbd tunda ya fita ta farka take kuka taga ganta a waje daban so ta dauka barayin ne suka kawo ta nan.. Tana ganin Jalal ta mike da sauri.. Kafin ta nunasa da yatsa.. Cikin muryar ta data gama shagewa tace "you.. You". Kallon ta Jalal ya tsayayi ganin yanda tayi wani iri gashin kanta duka barbaje.. "Dama kaine? "Where is my Abba mom.. Tell me".. Ta fada wasu hawayen na taru a idanu.. She's just hoping Abban ta be mutu sbd taji sanda yayi kara bayan an harba gun taji yan maganar da sukayi wanda ta gane cewa basuga mommy ba but where is she.. .. Jalal yadan ciji lips dinsa kafin yace "relax".. Da karfi tace "bazanyi ba.. Tell me me Abbana yayi maka is that why you follow me to our house".. Fashewa da kuka tayi kafin ta dago ta kara kallon sa "where is my Abba"... Kallon ta kawai jalal yake yama rasa abinda zece mata ga kansa wani irin ciwo yake masa.. Da kyar ya iya fadin "ur Abba is".. "Dead ko".. Ta katse sa da sauri.. Snn tace "meyasa ka kawoni nan.. I knw you're a bad boy but me mukayi maka.. My Abba is innocent amma kun kashe mun shi..".. Ta dago ta kallesa "take me to my Abba cos I hate you.. Yes I hate you.. Idan har nima baka kashe ni ba zan kashe ka wlh mugu, kawai".. Bude kofar jalal yayi ya fita.. Tunda yake duk yanda duniya tasan munanen halayensa babu wanda ya taba kallonsa gaba da gaba yace masa.. Bad boy ko mugu.. But yau gashi karamar yarinya cike da confidance ta kallesa ta zage sa without any fear.. Parlor yana runtse idanun sa.. Yau ya sake ganin wani halin nata wanda besan dashi ba but yasan ba laifin ta bane.. Yasan a ynx tanajin makamancin Abinda yakeji ne.. Kayan ya dauka duk ya nufi stairs har lokacin tana nan bnd kuka babu Abinda takeyi aje duka kayan yayi snn yace "kici wani abu and ga kayanan if you want to change".. Daga haka ya fice ya barta yanda take... Dakinsa ya shiga yayi wanka babu jimawa ya gama shiryawa cikin wasu kananun kayan yayi sallah snn ya fito ko dakin ta be kalla ba ya sauka.. Seda ya tabbatar ya rufe kofar snn ya nufi motar sa.. 30mis ya kaisa gidan da tasiu yake ciki.. Hannu kawai yake dagawa masu tsaron wajen ba tare daya kallesu ba.. Har ya shiga room din da aka rufe tasiu...

Tasiu ya dako idanun da da sukayi jawuur ya kalli Jalal.. Tun jiya da suka tafi babu wanda ya kara dukansa amma duk a jigace yake ga yunwa dan duk yau ba'a basa abinci ba.. Jalal ya zauna akan kujerar da ke facing tasiu.. Ya daga idanun sa da har ynx suke jaa ya kalli tasiu fuska daure.. Amma camly yace "taya kasan dukkan bayanan poising din nan"... Ganin yanda jalal ya tsare sa da idanun sa yasa yace "ina dawowa kasar nan suka turamun text cewa suna so zamuyi aiki tare dasu.. Nace na Amince suka turamun location din inda zamu hadu.. Bayan na tsaya inda sukace suka aiko driver da mota yazo ya dauke.. Bansan inane suka kaini ba domin ina shiga aka rufen fuska.. Har muka isa..duk da ido na a rufe yake yake naji alamar suna dayawa naji tsoro sosai but babu yanda zanyi sunce inde har bnyi aiki dasu ba se sun kashe ni.. Domin sune suka kashe saif.. Kokuma su tona mun asiri sunce nine na kashe saif suna da sheda me karfi da zasu nunawa duniya cewa nine na kashe saif".. Jalal ya yayi biting lips har yau fuskar wanda ya she saif tana nan tar cikin kansa.. .. Tasiu ya cigaba.. "Basu samu damar fada mun aikin da zamuyi ba.. Suka samu kiran gaggawa.. Anan naji kome akan poison din nan anan sukace zasu neme ni suka a rufemun fuska suka maido ni motata.. Wanda a wannan lokacin ne mutanen ka suka samu damar kamani.. Wlh bnyi karya ba wayata na tare daku inde har kuka duba zakuga duka sakonnin da suka turamun da numbers daban daban"... JALAL ya runtse idanu yanajin yanda zuciyar sa ke tafarfasa.. Inde har labarin tasiu gsky ne to wadan da suka kashe saif suke da saka hannu wajen poison din mum dinsa.. But suwane.?.. Ya bude idanun sa ya kalli tasiu yace "wa kk wa aiki, kai wane yasa ka kashe mu".. "Marigayi Alh falalu waddu.". Wani irin mikewa Jalal yayi kafin yace "what??" Tasiu ya gyada kai.. Tabbas shine ya sakani kuma ya biyani... Jalal da duk yaji hankalin sa ya tashi ya gyara agogon hannun sa daya gama nadar maganar snn ya fice daga dakin.. Motar sa ya shiga ya jata da wani irin sauri yabar wajen. Yana driving amma gaba daya hankalin sa a tashe yake.. Alh falalu waddu shine ze aiko a kashe sa.. Abokin Dadd dinsa ne kamar de Alh Barau... Mutumin is good to him.. Ya rasu  4yrs back.sanadiyar hadarin mota.. Tunda jalal ya fito daga prison shima yake tare dashi kamar de Alh barau.. Amma basa shiri da Alh barau wanda besan dalilin fadan nasu ba.. But taya ze aiko a kashe su.. Me sukayi masa.. Bashi da me basa wnn ansar..a da yana tunanin basa shiri da Alh barau ne sbd kodan dukansu makusantan dadd ne may be kishi ne.. But ynx ya fara tunanin wani Abu. Kodai yanada wani hali na dabab da Alh barau baya so kokuma akwai wata can tsakanin su... jalal ya tusa hannun sa daya cikin gashin kansa tare da fursar da iska.. He just can't believe abinda aka fada masa akan Alh falalu.. So me yayi masa har haka.. Ahaka har ya isa gida.. Duk da yanaso yaga ko imaan taci Abinci amma baya so yaje ta kara masa wani nauyin.. A parlor ya zauna kiran sageer yayi a waya.. Ba tare dayace komai ba ya aje wayar... Ko minti biyu ba'ayi ba sageer ya shigo da Sallama.. Ganin yanayin dan uwannasa yasa ya karaso da sauri yana kallon jalal.. Ko dagowa jalal beyi ba duk da yaji shigowar sageer.. Zama sageer yy kafin yace "tell me bro".. Batare da jalal ya kallesa ba yace "Alh Falalu waddu".. Sosai gaban sageer ya fadi amma ya daure yace "ya rasu ai.. But what about him".. Jalal ya juyo ya kallesa da idanun sa da sukayi jaa sosai.. Snn yace "shine yasaka tasiu kashe mu".. Jingina da kujera sageer yayi yanaji kansa na Juyawa snn ya kalli jalal yace "idan shi Alh falalu be samu damar kashe ku ba knn akwai wadan su daban knn wadan da sune suka samu nasarar wajen kashe saif".. Jalal ya gyada kai.. Kafin yace "and same people da sukayi poisoning mum".. Sageer na kallon sa yace "how do you knw".. Nana Jalal ya fada masa yanda sukayi da tasiu.. Snn ya kara da fadin.. "Ynx After Atika Abokanan Dad ma zasu shiga suspect dinmu".. Sageer ya jinjina kai snn yace "and ynx family din Alh falalu waddu dole mu nemo su nasan zamu samu wani abu.."..

Urs

✨✨✨

Annafie😍

.......*💫💫💖JALAL ALII💖💫💫*



Written by



           *ANNAFIE💖.. ✍️*

     (Smll but mighty😉)



Writer of

*LOVE CYCLE❤️*

*SABODA DUNIYA🌃*

*ADAAN💕*

*JALAL ALI🤩*



Bismillahir rahmanir raheem

💫💖Jalal Ali(16)💖💫💫

Mikewa sageer yayi Jalal ya dubesa "ina zakaje".. "Zanje muyi magana dasu salim domin duk wani ma'akaci su lura da komai nasa babba da karami snn bature ya fara mana aiki akan familyn Alh falalu da  kuma duk wadan da yayi hulda dasu... Kara shigewa cikin kujerar yayi batare da yace komai ba sema lumshe idanu da yayi.. Hakan yasa sageer ya nufi kofa.. Har ya kama handle din ya juyo yana kallon Jalal da idanun sa ke a lumshe.. Sosai  yaji ya basa tausayi.. A hankali yace "pls bro don't drink".. Jalal ya bude idanun sa da suke jawur ya kalli sageer.. Girgiza masa kai sageer yayi kafin yace "pls bro.. Kasani komai yayi farko zeyi karshe. Snn duk lamuran ka ka mikawa Allah. Kasani drinking can't solve any problem but Allah is always with you".. Gyada masa kai kawai Jalal yayi yana jin wani daci a ransa for now babu wani Abinda yake bukata sama da giya amma ze daure for the sake of his brother... Maida idonsa yayi ya lumshe bayan sageer ya fita.. Yafi 30mns kafin ya tashi ya hau stairs.. Dakin da imaan ke ciki ya shiga.. Har tym din tana a yanda ya barta kuma kanajin sautin fitar kukan ta duk da imaam taji shigowar amma bata dago ba.. Sbdwa ynx babu wanda ta tsana kamar sa.. Ta tsani ganin fuskar sa domin tana ganinsa as wanda ya kashe mata Abban ta da mommy.. Kallon Abincin da ya aje mata yayi snn ya kalleta.. Yasan tabbas tana cikin tashin hankali.. A hankali yace "duk wnn kukan da kike can't change anything so gara ki tashi kici Abinci kafin wani ciwon ya sameki".. Kamar jira take ta dago kanta duk da yanda gashin kanta ya zubo ya rufe fuskar ta be hanasa ganin yanda idon ta ya kumbura yayi jawur ba sbd kukan da tasha.. Tana kallon sa cike da tsanar sa tace "how can it change bayan ka rigada ka kashemun iyayena .. Wlh se Allah ya sakamun mugu kawai Azzalumi".. Runtse idanu Jalal yayi yanajin yanda kalamanta ke dukan zuciyar sa. Juyawa yayi domin bayason wadan nan kalaman da take jifar sa dashi ba.. Bayau ya sabajin an Kira sa da haka ba amma nata yafi masa zafi. Kodan ita ido da ido take fada masa oho.. Wani wawan tsaki imaan taja tana hararar sa.. Cak jalal da har ya kama handle ya ya tsaya.. Juyowa yayi a mugun fusace ya shaki wuyan imaan ya hade ta da bango.. Cikin muryar sa dake nuna tsananin bacin rai yace "did you just hissed".. Duk da yanda ya shake imaan hakan besa taji tsoro ba dan zuciyar ta a mugun dake take ji take itama gara ya kashe ta tace.. "Yes tsaki nayi maka nima ka kashe ni.. Ka kashe ni kamar yanda ka kashe mun iyaye Allah ya isa tsakanina da kai".. Se kuma ta fashe da kuka sosai.. Jalal ya cije lips dinsa da karfi kamar ze fasasu zuciyar sa na wani irin tafarfasa.. Sakin imaan yayi ta zube a wajen tana kuka sosai.. Har cikin ransa yanajin kukan nata ya tusa hannun sa cikin gashin kansa.. Kafin a hankali ya nufi kofa.. Muryan ta yaji cike da rauni wnn karan cikin kuka tace "Dan Allah me mukayi maka idan har dan na sace maka taya kamana haka to nima ka kashe ni amma babu laifin Abba na laifi na ne".. Tsayawa Jalal yayi kafin a hankali ya juyo yana kallon ta ta kifa kanta tana kuka sosai wanda daga ji kasan she's in pain.. Ta basa tausayi sosai.. Dan lumshe idanu yayi kafin yace "Abban ki be mutu ba".. Da sauri imaan ta dago tana kallon sa kafin tace "dan Allah? Da gske kk yana ina.. Pls take me to him"... Jalal ya bude ido yana kallon ta snn yace "yana hospital".. Imaan ta hade duka hannayen ta snn tace "dan Allah ka kaini wajen sa I want to see him na rokeka".. Yanda take maganan kamar ba itace take kiransa da azzalumi ba.. Matsowa yayi kusa da ita ya zauna bakin gado snn yace "kina so na kaiki ki gansa".. Ta gyada masa kai da sauri.. Yace "se kinyi wanka kinci Abinci".. Ya fada yana nuna mata kayan da suke anan.. Da sauri tace zanyi.. Gyada kai yayi kafin ya tashi yabar dakin. Dakinsa ya koma bathroom ya shiga yayi wanka snn ya fita ya shirya cikin wasu kananun kaya.. Sallah yayi snn ya dauko system dinsa yana dan daddan nawa idanun sa sun washe ba kamar dazu ba idan ka gansa ynx ma bazakace yana cikin damuwa ba.. Yadan jima yana dannawa kafin ya rufe.. Kasa ya sauka ya hada tea yana sha.. Daga kansa yayi jin foot steps din.. Imaan ce sanye cikin daya daga cikin hijabin daya siyo mata ya kai mata har kasa sosai yayi mata kyau duk da idanun ta a kumbure suke .. Snn kanta yayi wani him sbd ko taje kanta batayi ba tayi parking dinsa.. Dauke kansa yayi yanaji ji har ta karaso snn.. A sanyaye tace "na shirya".. Dan kallon ta yayi kafin yace "have you eaten". Dan langwabar ta kai tayi idanun ta sunyi rau rau kamar zatayi kuka tace "I can't eat".. Dauke kansa yayi daga duban ta kafin ya fara hada wani tea din seda ya gama ya nuna mata kujera snn yace "sit".. Babu musu ta zauna ya mika mata cup din tea din tare da fadin "shanye".. Kamar zatayi kuka ta girgiza masa kai.. Yanda tayi din idan ka ganta seta baka tausayi.. Daure fuska yy yace "take".. Karba imaan tayi a hankali babu gardama snn ta kai tea din bakin ta seda ta shanye tass snn ta aje cup din.. Mikewa yayi tare da mika mata hannun sa.. Imaan ta kalli hannun kamar bazata saka ba sbd bata so yana taba ta amma snn babu wani karfi a jikin ta yasa a hankali ta saka hannun ta cikin nasa.. Ya taimaka mata ta mike snn suka nufi mota shida kansa ya bude mata ta shiga snn ya yaje ya bude gate ya dawo ya shiga ya tayar da motar suka fita.. Seda ya fita ya rufe gate din snn ya shiga motar suka cigaba da tafiya.. Imaan de idanun ta a lumshe suke da tunani iri iri.. Inde har Abba na hospital knn wnn ne ya kaisa and that means bashine ya yi kokarin kashe sa ba tunda har ya kawosa Asibiti.. She's wrong knn but taya duk suke tare da shi ynx daga ita har abban ta.. Bata da me bata amsa tayi shiru tana kallon gari amma gaba daya hankalin ta baya jikin ta.. Tade gane ba cikin kaduna suke ba suna cikin Abuja wanda bata san taya suka zo ba.. Lokaci lokaci Jalal ke kallon ta har suka isa Asibitin wanda kana gani kasan babban asibiti ne.. Ga police ta ina a wajen da ake parking jalal yayi parking amma be fita ba kusan minti biyar sega sageer hakan yasa jalal ya bude motar ya fita.. Imaan na kallon sa taga kamar su da jalal tym din da suke tsaye.. Bata fito ba har seda jalal yazo ya bude mata tare da mika masa hannun sa.. Saka nata tayi ya taikamata ta fito.. Sageer dake kallon ta yace "madaam ya jiki".. A hankali tace "da sauki".. Jalal yace muje ko.. Sageer yayi gaba suna binsa a baya.. Imaan ta rike hannun Jalal sosai gaban ta na faduwa.. Yanda take ganin police sosai a Asibitin nan tasan na manyan mutane ne sbd yanda taga an saka tsaro.... Kasancewar sageer ya riga ya fadawa Dr zuwan su jalal yasa suka wuce inda aka kwantar da Abba direct.. Nan ma police ne masu yawa suke zagaye dakin imaan ji tayi zuciyar ta tayi mata wani nauyi sbd ko yanda taga police haka tasan Jalal bashi da hannu akan abinda ya sami Abban ta.. Maganganun data fada masa suka rinka dawo mata..... Babu damar su shiga dakin domin ba'a shiga sageer kade aka yarda ya shiga se likitoci.. Barin ma ynx da suke kan aiki.. Projectile da ake nunama duk wani me alhakin ganin sa akayi setting gaban imaan bnd faduwa babu abinda yake ta rike hannun Jalal sosai shi kansa yanajin yanda ta rike masa hannu.. Kunnawa akayi.. Tuni image din Abba ya bayyana yana kwance kamar babu rai a jikin sa likitoci sun dukufa kansa domin ana tsakkiyar aiki ne though se gobe ma zasu shiga babbar theater din... Sosai imaan hankalin ta ya tashi ta rike hannun jalal gam tana rufe bakin ta da dayan hannun sbd hana kanta kuka.. Ynx wnn Abban ta ne a kwance haka.. Su wane suka masa haka.. Meyayi masu.. All she knws is tasan Abba bashida abokan fada mutun ne me hakuri but duk da haka seda aka kaima rayuwar sa hari.. Fashewa tayi da mugun kuka tare da juyawa da fada jikin Jalal ta kankamesa.. Jalal ya zagaye ta da duka hannayensa yanajin yanda take kuka.. Ta basa tausayi sosai yasan idan tayi kukan zata samu relief tunda tasan cewa Abban ta nada rai shi kansa yasan da zeyi kukan zeji dadi.. Sageer kansa seda ya tausaya mata.... Hakan yasa ya kashe Jalal kuma ya dagota ya share mata hawayen da sukaki tsayawa snn ta ya kama hannun ta suka nufi fita.. Sageer na biye dasu seda suka shiga mota duka snn sageer ya leko ta windown Jalal snn yace "latest ango ka lallashe ta kaji lyk hug tight let all her tears fall on ur chest".. Wani kallo Jalal yayi masa sageer ya kashe masa idanu.. Snn yace "senazo kawo maku foodstuffs".. Tayar da motar Jalal yayi batare da ya kara kallon  sageer ba.. Suka bar hospital din seda ya biya wani eatry ya siya masu Abinci snn ya wuce gida.. Wnn karon ita da kanta ta bude motar ta fita.. Da gudu ta shiga parlon ta zube a saman kujera tana kuka sosai.. Koda jalal ya shigo be hanata ba sede ya zauna yana kallon ta.. Be taba ganin tana kuka kamar haka ba se yaji duk ta basa tausayi seda tayi kuka me isar ta snn ta koma sauke ajiyar zuciya.. Jin tayi shiru yasa.. Jalal ya sauke Ajiyar zuciya shima kafin yace "just pray for him Adduar ki yake bukata.. For now bazamu iya cewa komai ba akan yanayin jikin sa but we're hoping that gobe idan anyi aiki za'a samu nasara ba".. Imaan ta gyada masa kai.. Ya gyara zaman sa kafin yace "take ur food and eat".. Babu musu imaan ta dauka daya cikin take away din ta bude tana kallon lafiyayyar jallof rice din.. Diba tayi kamar me tsoran Abincin ta kai bakin ta.. Ko daya beyi mata dadi ba.. Dan haka ta aje.. Ba tare daya kalleta ba fuska daure yace "cinyesa".. Dauka imaan tayi jiki a sanyaye ta fara cin abincin seda ta kusa cinyewa snn ta aje.. Ruwan data gani ta dauka tasha tana sauke ajiyar zuciya koba komai jikin ta ya rage rawar da yake mata sbd rabon ta da abinci tun jiya.. Mikewa tayi ta kalli Jalal da baya kallon ta snn a hankali tace "thank you".. Snn ta nufi sama.. Shima tashi yayi jin ana kiran magrib ya shiga bathroom din kasa yayi alwala snn ya fito ya tafi masallaci... Koda ya dawo a parlor ya zauna yana dan danna wayar sa.. Jin an turo kofa yasa ya daga kai ya kalli sageer dake shigowa tare da wani niki niki da kaya.. Sageer ya nuna ma wancan kitchen tare da fadin "you arrange them in the store.".. Snn ya dawo ya zauna kusa da Jalal da ya dauke kansa.. Yace "latest Ango. Ina amarya".. Jalal ya hararesa kafin yace "yaushe rabon da a dake ka".. Dariya sageer yayi kafin yace "kira mamy ka tambaye ta".. Jalal ya danyi murmushi yana kallon wanda ke shiga da fita da kayan Abincin snn yace "wai kai waya saka ka.. Ka saka anata kawomin wasu uban kaya a gida".. Sageer ya ware hannuwa snn yace "Gudummuwa ta na kawo".. Jalal ya tabe baki. Sageer ya gyara zama kafin yace "call her I want to ask her".. Jalal ya aje wayar sa kafin ya tashi ya nufi stair.. Tana zaune kan prayer mat tunda ta idar da sallah bata tashi ba.. Jin a bude kofa yasa ta juyo ta kallesa.. Har ynx idon ta akwai sauran hawaye.. Kallo daya yayi mata snn yace "meet me in the down stairs"... Daga haka ya juya ya fita.. Ko minti uku beyi da zama ba ta sakko cikin dogon hijab dinta kanta a kasa kujerar dake pacing tasu ta zauna snn ta kalli sageer tace "ina wuni".. Ya danyi murmushi "lpy qlw how are you feeling". A hankali tace "fne".. Sageer ya gyada kai snn yace "I want to ask you questions feel free and tell me duk Abinda ya faru and how it happened".. Imaan ta gyada kanta.. Hawaye na taruwa a idon ta..tace "it was yesterday around 8 muna dinner duk a parlor se mukaji ihun me gadi saying banan bane Dr Umar baya nan.. Jin haka yasa Abba ya tashi ta window ya lega.. Bayan ya leka seya dawo da sauri hankali tashe ya kalli yace I should go to my room na shiga toilet na rufe.. Hakan yasa na tafi.. Ina ganin sanda ya kama hannun mommy sukayi dakinsa yana mata magana.. Bansan me yake fada mata ba but kamar cewa yake tabar gidan I think akwai abinda ya bata a dakin sa... Na shiga daki nayi kamar yanda yace.. Akan kunne nan naji sun shigo parlorn hankali na ya tashi sosai.. Inajin muryar su sanda suke dukan sa yana ihu.. I was crying ina tunanin me yayi masu.. Se kawai naji kamar suna kafar daki na.. Suna cewa zasu kashe sa inde be fada masu inda mommy take ba.. Shi kuma yace.. "Baze fada ba.. Kuma bayan shi mommy tasan komai game da poison dan haka koda sun kashe sa Abanza dan mommy seta tona asirinsu..... Imaan ta fashe da suka anan naji sun harbe sa daganan kuma suka caka masa wuka.. Bn kara sanin meke faruwa ba se dana tashi na ganni a nan".. Sageer ya gyada kai tare da gyara agogon hannun sa snn yace "kin tabajin wanda suka samu matsala dashi.." Imaan ta girgiza kai.. Sageer yace "be taba yi maki maganar poison ko wani abu ba".. Anan ma imaan ta girgiza ka.. Sageer yace "tnx madaam.. Inshaallahu Abbanki ze samu lpy you can go".. Imaan ta gyada kai kafin tace "thank you".. "You're welcome".. Cewar sageer.. Imaan ta tashi tana satar kallon jalal dake danna wayar sa... Wani nauyin sa takeji.. Duk da be fada mata ba a ynx ta fahimci cewa bashi da hannu akan abinda ya samu Abban ta sema taimakon ta da yayi.. Idan ta tuna zagin da tayi masa setaji zuciyar ta tayi mata nauyi.. Sageer ya dauke kansa daga imaan bayan ta shige ya maida kan jalal snn yace "how long Zaka cigaba da boye ta".. Ba tare da jalal ya kalle sa ba yace "da Abban ta ya samu lpy zan bata takardarta". .. Sageer ya jingina da kujera.. Yana wani murmushi snn yace "uhmmm but she's so young and beutiful why won't you accept her kuyi zaman aure".. Jalal ya dago ya kalli sageer  kafin ya tabe baki snn yace "ni bn gani ba and ni bazan zauna da ita ba".. Sageer na murmushi yace "idan ka baka so ni kabani because she's so beutiful and innocent".. Wani kallo jalal yayi masa kafin yace "wnn mara kunyar".. Sageer yaso yayi dariya ganin yanda jalal ya wani yamutsa fuska yace "oh really ashe bata da kunya how do you knw".. Jalal ya dauke kansa yaki bama sageer amsa.. Sageer ya dage kafada yana fadin "anyway i just lyk the girl" jalal ya juyo  Ya kalle sa. Sageer ya ware idanu yace "yes just imaging kids from her wow so so cute".. ganin kallon da jalal yayi masa yasa yace "her phone.. I knew she will need it".. Ya fada yana ajewa jalal waya.. "So ango da Amarya i will be going so enjoy ur amarci". Sageer ya rage muryar sa.. Yace "karda kanka ya kulle mallam don't Let dis beutiful girl go just lyk that... Enjoy ur Amarci and make love.. Cos girls are joy giver".. Pillow jalal ya dauka ya jefi sageer dashi.. Kaucewa sageer yayi yana dariya snn yace.. "Na ware.. Ga me gadi nan na samo maku".. Har seda sageer ya fice snn jalal ya saki murmushi.. Wato sageer is just defference a rayuwan shi.. Shida mamy sun zame masa wani bango na dogaro.. Shiyasa mamy da danta sun gama masa komai.. Wayar imaan ya dauka snn ya haye sama.. Dakin da take ya tura.. Tana zaune gefen gado ta rufe fuskar ta da tafin hannun ta tana kuka.. Jalal ya kalli fingers dinta da suke farare kal lafin a hankali ya aje mata wayar ta yace "ur phone".. Snn ya nufi kofa.. Ji yayi tace "Am srry".. Dan tsayawa yayi se kuma ya juyo suka hada idanu.. Ta sauke nata kasa har ynx tana hawaye.. Yace "for?".. Imaan ta dago ta kallesa  se kuma tayi kasa da kanta snn a hankali tace "for all the sort of words i said against you.. But i was wrong kaine ka taimake ni bawai cutata kayi ba".. Jalal kallon ta kawai yake.. Tayi mugun basa tausayi.. Takowa yayi ya zauna a kan bedside drower snn yace "don't mention inshaallahu gobe za'ayi masa aiki inde an dace Abba ze samu lpy a sannu a sannu just pray for him samun lpyr sa ze saka mu gano wadan da suke da hannu a wnn lamari".. Imaan ta gyada kai.. Jalal yadan cije lips dinsa kafin a hankali yace "lets talk".. Imaan ta dago ta kallesa suka hada ido se kuma ta sauke nata kasa. Jalal ya dan lumshe idanun sa ya bude snn yace "nasamu damar magana da Abba before mu kawo sa Asibiti".. Imaan ta kallesa da sauri.. Tana bukatar jin Abinda ze fada.. Jalal ya dauke kansa a kanta yadan furzar da iska kafin yace "A jiya Abba ya bani Auren ki tare da dukkan Amanar ki and some of ur nabours suka daura auren.  So for now you are my wife".. Kamar daga sama imaan taji zanjen.. Bata san sanda ta mike da sauri ba dan jikin ta har wani irin rawa yake tace "Aure kuma da ni".. Jalal ya lumshe idanun sa ganin yanayin reaction dinta a hankali yace "sure".. Yarfe hannuwa imaan ta shigayi a ranta tana karanto innalillahi.. Lallai Abba besan wane jalal ba.. Anya kuwa.. Yasan wanda ya aura wa diyar sa.. Ynx nan ita matar aure ce.. Kuma ba kowa bane angon se this .this Jalal. The bad boy.. Batasan sanda ta fashe da wani kuka ba.. Duk da idanun sa a lumshe suke amma duk abinda take yana kallo....

Urs

✨✨✨

Annafie😍

..........

*💫💫💖JALAL ALII💖💫💫*



Written by



           *ANNAFIE💖.. ✍️*

     (Smll but mighty😉)



Writer of

*LOVE CYCLE❤️*

*SABODA DUNIYA🌃*

*ADAAN💕*

*JALAL ALI🤩*



Bismillahir rahmanir raheem

💫💖Jalal Ali(17)💖💫💫

"What are you saying i don't understand"... Imaan ta fada cikin wata murya me kice da kuka... Jalal ya bude idanun sa ya kalleta ganin yanda take kuka.. Kasa cemata komai yayi ... Imaan da ta kasa gasgata abinda kunnen ta ya jiye mata tace "pls tell me that this is not true pls".. Jalal ya cije lips dinsa ko daga yanda take yasan she will naver accept dan haka shima dole ya sake ta.. Mikewa yayi kafin yace "pray for ur dad gobe za'a masa aiki".. Daga haka ya fice.. Zubewa a wajen imaan tayi tana kuka sosai.. "Aure fa, Aure fa ba abin wasa bane and ynx tayi Aure.. This is serious".... Imaan ta dade tana kuka kafin ta tashi ta shiga toilet alwala tayi tazo ta fara nafila.. Tunda tasan kukan bashida amfani dole tayi ma Abban ta Addua ko ya samu lpy.. Shima wnn tasan yanda zatayi dashi.. Ta dade tana nafilfili kafin bacci ya dauke ta......

Ana kiran sallahn asuba Jalal da ko 2hours beyi da kwanciya ba ya bude idanun sa.. Tashi yayi cike da gajiya da kalasa idanun sa sunyi masa nauyi.. Dan lumshe idanu yayi kafin a hankali ya tashi toilet ya shiga yayo alwala snn ya tashi ya fito.. Kofar dakin ta ta tura ya ganta kwance a kasa tiles binta yayi da kallo yasan ko ba'a fada masa ba.. Bata jin dadin baccin.. Knocking kofar yayi.. Kamar abinda imaan take jira knn ta tashi da sauri.. Jalal ya dauke kansa daga kanta snn tace "tym for subhi".. Daga haka ya juya ya fice zuwa masallaci.. Da kyar imaan ta iya tashi ta shiga toilet tayi alwala.. Koda ta idar da sallah se taji bata iya kwanciya baccin yau za'ayiwa Abba aiki.. Hankalin ta baze taba kwanciya ba se taji ance an samu nasara.. Duk adduar da tasani na neman dacewa ita imaan take.. Tanaji sanda Jalal ya dawo ya bude dakin sa ya shiga.. Idan ta tunawa cewa ita matar sa ce se hankalin ta ya tashi.. Taya zata zama matar wanda bata tabajin halinsa me kyau ba ko so daya.. Taya zata zama matar this baddest da duniya ta gama sanin sa as bad guy.. Imaan ta kifa kanta kawai ta fara kuka.. Dole ya sake ta taje ta auri wani mijin da she's sure idan Abba zeji halayen sa shima cewa zeyi ya saketa.. Haka ta kifa kai tana rera kuka a hankali.. Kayan jikinta tun na jiya ne amma kokadan bata damuba.. Har bata san iya tym din data dauka ba.. Dan har jalal ya shigo dakin bata sani ba kamshin turarensa ne daya daki hancin ta yasa ta dago da sauri ta kallesa yana tsaye bakin kofa  .. One thing da imaan ta sani game da dis guy call Jalal or what ever is that yana da kyau he's very very handsome fiye da tunanin ku.. Wanda one look as duk da yana namiji bazaka masa ka dauke kai.. Gashi ko wane irin kaya ya saka suna dacewa dashi.. Imaan tayi kasa da kanta but duk wann kyaun nasa da take gani da ta tuna halayensa se taji baya birgeta.. Camly yace "are you still crying".. Shiru imaan tayi.. Jalal ya karaso ya shigo cikin dakin tare da aje wani babban leda a bedside drawer yace "ur breakfast.. Make sure kinci before na dawo.. I will be going to the hospital".. Daga haka ya juya.. A hankali imaan kamar ba ita ba tace "I want to go with you pls".. Jalal da yayi backing dinta his 2 hands in his pocket ba tare daya juyo ba yace "nop just stay and pray for him".. Daga haka ya fice.. Imaan ta share hawayen ta tana kokarin danne kukan ta.. She just wish tagama karatu ta zama barrister dase inda karfin ta ya kare wajen nemo duk wadan da sukayi ma Abban ta haka.. Dakin ta fara gyarawa tana kokarin hana kanta kuka seda ta gama tsaf snn ta shiga bathroom tayi wanka.  Ta chanza kayanta da duk suka isheta snn takwanta saman gado bayan ta saka wayar ta chargy dan ko daya bata jin yunwa...gaba daya duk wani iri take ji duk da tasan mommy barayin basu ganta ba but hankalinta tashe yake she want to see her tasan halin da take ciki abd her Abba tana so ya samu lpy she want the back kamar da su koma rayuwa tare.. Ta dade tana tunane tunane kafin bacci ya dauke ta...

.........

Hajiya Atika ce zaune a wani kayataccen parlor na gidan idanun ta akan Tv gaban ta kau cike yake da fruit babu kalar da babu.. Daka ganta kasan tana cikin farin ciki.. Jin anyi knocking yasa ta kalli kofar snn tace yess come in... Hajiya Huwaila ce ta shigo tare da wata da zasuyi sa'anni da ita.. Mekewa mama tayi zuwa wajen kawayen nata tana huging dinsu.. Dayar kawar tasu me suna haj maimuna tace "wai abin dan mijin naki har ya kai haka keko ya kikayi wnn saken". Mama ta kalle ta snn ta kalli haj huwaila tace "ya shigo ne".  Haj huwaila ta girgiza kai kafin tace "wai da karasowa zatayi da mota har cikin wnn out gate din batasan Dan gold kade keda daman shigo da motar sa nan ba". Haj maimuna ta tabe baki.. "You mean all dis hadadden parking space din dake nan babu wanda ya isa ya aje masa mota".. Mama tace "kinaso ki ganta wajen yan gwangwan knn".. Haj. Maimuna tace "tab gsky kinyi sake ina tare da miji tun kafin a auri uwarka snn..  kazo ka nunamin iyaka".. Tabe baki mama tayi.. Kafin tace.. "Kunga don't spoil my mood ku zauna me kukeso a kawo maki... Duk zama suka yi.. Mama ta saka a cikamasu gaba da kaya motsa baki .. Haj. Huwaila tace.. "Kinga gist us"... Mama tana gyara zama snn tace "yau kwana biyu Jalal be kwana gida ba and that's what his dad hate no matter how inde yana gari dole ya kwana gida.. And if his Dad findout cewa Jalal baya kwana gida he'll definitely deel with him dan idan be fasa ba zasu samu matsala". "Good why not ki fada masa cewa baya kwana gida".. Cewar hajiya Huwaila.. Wani kallo mama tayi mata kafin tace "see you ya fara tunanin ina shiga tsakanin sa da dansa.. Ina so shi ya gane da kansa..and idan ze gane inaso ya kamasa dumu dumu da mace kinsan that what his dad hate ko abinda ake fada akan sa dan be taba gani bane".. Duk shiru sukayi sunajinta.. Tacigaba.. "But idan ya gani na tabbata seya mugun saba masa.. And for nan jalal yakai matakin da fada sede ya tunzura sa so daganan idan duka suka samu matsala".. Wani murmushi mama tayi snn tace "I will not tell but zaku gani.. For now nasan wayon da nayi na hada sa da kakarsa ynx haka jiran dawowar sa take"... Wata jinjina sukayi mata.. Ita kanta jin kanta take sama sbd tasan ba karamar mugunta ta shiryawa jalal ba... Haj. Maimuna tace "to baki ganin shi jalal din ze gane ki".. Mama ta wani tabe baki "wnn babu abinda ya sani se giya the only thing da nasan yanayi is baya tolerating a bisa a baya.. Yes he observe idan ana bibiyar sa.. Sede muna bibiyarsa but not that much karda ya gane.. Amma after that kome nasa is open.. He's so careless ko dakin sa ynx idan kinga dama zaki iya shiga ki masa wani mugun abun but his Dad is so observant da kome na jalal cikin gidan nan". Duk numfashi suka sauke suna kokarin hada maganganun da ta gama fada masu...

Se wajen 4 snn aka gama aikin kuma shima da hope din za'a samu nasara sede ba cikin gaggawa ba but he's happy tunda ana da hope din samun lpyr sa duk wani result dama se next week zasu sani but for now likitoci na ganin babu wata matsala sabanin wacce sukayi aiki akanta yau kuma suna ganin za'a samu nasara....kusan 30mins yayi yana driving kafin ya iso gida da. Dan bin gidan yayi da kallo snn ya fito part din granny ya nufa.. As usual a parlor ya sameta se yan aikin su.. Tana ganin sa ta wani hade rai.. Lura da hakan da jalal yayi ne yasa ya nufi dining direct yana bude warmers din wajen snn yace "good evening granny"... Kara hade rai tayi tana ganin yanda ya basar da ita.. Tasan waye Jalal inde har ba Dad dinsa bane duk yanda zaka nuna kana fushi dashi nunawa zeyi kamar be sani ba... Shiru tayi ganin ya zuba lafiyayyar moi moi din yana ci sbd tasan tana iya fara masa fada ynx ya fasa cin Abinci which is tasa shknn kila shida abincin yau sede kawai yaje ya banki giyar sa..... A natse Jalal kecin Abincin.. Yana tunanin imaan thinking that ko taci Abinci?.. Seda yaci ya koshi yasha zobon me sanyi snn  ya dauko wayar sa yana dannawa.. Muryar granny yaji tace "Jalal when will you change lyk baka ganin duk abinda Dad dinka yake ko baka gudun bacin ransa ko".. Jalal ya juyo ya kalli granny yana dan murmushi kafin yace "granny me nayi"... Cike da fada tace "ask ur self.. Kana gani er bewar Allah duk ya tashi hankalin ta gaba da kwana biyu bata ganka ba wato saboda kaga Aliyun baya nan ko"... Sanin hajiya Atika take nufi yasa jalal hade rai.. Snn ya dauki wayar sa da keys dinsa batare daya kara ce mata komai ba.. Ransa ya mugun baci.. Yasan all abinda granny take gani is.. Atika ta damu dashi batasan cewa she's the evil ba.. Daidai balconyn dake part dinsu ya hadu da Atika ta rako kawayen nata  dukkan su ganin sa seda gaban su ya fadi.. Ko kallon su beyi ba ya shige dan kallon fuskar Atika kade tana sakawa yaji kamar ze rufe ta da duka shiyasa lokaci dayawa idan suna tare da dad yake cewa tayi excusing dinsu...

Wanka yayi ya shirya tare da daukar wata system dinsa ya fito wnn karon babu kowa a parlorn dan haka ya wuce motar sa.. Seda ya zauna snn ya dauki wayar sa number sumayya ya lalubo. Ya tura mata text snn ya aje wayar yana lumshe idanu.. Kusan 10mins sega sumy rike da wani big basket ciki a kwai warmers na abinci masu kyau dan duk abinda aka dafa a part din granny yace ta debo masa.. Gaba daya hankalin sa na kan imaan daya bari a gida yake ... Sumy ta bude back seat ta saka kafin tace "yaya kana ina 2dys".. Dan kallon ta yayi.. Kafin yace "nayi busy but soon zan dawo".. Gyada masa kai tayi ta rufe motar tana masa waving har ya fice....

Yana gama parking din ya fito rike da system da wayar sa snn ya bude back seat ya dauki basket din ya shiga cikin gidan.. Parlon na nan yanda ya barshi babu ma alamar ta sakko down stairs  basket din ya aje saman center table snn ya nufi stairs.. Kamar ya shiga dakin sa se kuma ya bude nata dakin... Tsab dakin yake bata ciki but ga kamshin sabulun wanka nan da kuma karar ruwa a toilet.. Har ze fita idanun sa ya sauka akan breakfast din da ya aje mata da babu alamar an taba.. Jalal ya shigo dakin a ransa yana tunanin me yayinyar nan take nufi karde ace har ynx ko breakfast batayi ba  ynx har karfe biyar.. Ya aje system din hannun sa da wayarsa yana dubawa ganin da gsken bata taba ba.. Jin an bude kofar toilet yasa ya juya.. Yana kallon imaan data fito daga bathroom daga ita se karamin towel purple wanda ya kara haska skin farar skin dinta.. Kanta me uban yawa da tsayi ko parking din kirki batayi masa ba.. Jalal yabi fararen cinyoyinta da kallo.. Imaan ko lura da jalal batayi ba ta nufi mirror dan bata wani jima da tashi daga baccin ba ko yunwa bata ji.. Kuma data tashi baccin taji rabin damuwar ta ta tafi.. Kamshin turarensa ne ya fara dukar mata hancin yasa ta juyo direction dinsa da sauri.. Ido hudu sukayi da Jalal da ya tsaya yana kallon ta wanda shi kansa be san yana kallon nata ba.. Ya saba ganin mata halfnake a America amma be taba tsayawa ya kalla ba.. Ihu imaan tayi tare da juya baya tana shigewa jikin bango. Da sauri Jalal ya dauke kansa yace "meet me down stairs now"... Daga haka ya fice.. Imaan taji abinda yace dan haka ta murguda baki tana hararan kofa "kawai se katon mutum ya shigo maka".. Ta fada tana daukar cream dinta.. Ta fara shafawa se kuma ta marairaice kamar zatayi kuka tace "kuma Allah ya isa ganina da yayi".. Haka ta shafa man tanaji kamar tayi kuka sbd yanda ya ganta da towel.. Cikin kayan daya sayo mata jiya ta samu wata simple black abaya ta saka.. Tayi mata kyau sosai sbd har wani haske imaan ta kara this days duk da her face is swallown tayi kyau.. Hijab dinta ta dauka ta zumbula snn ta fita ta hade rai... Kallo daya yayi mata ya dauke kansa.. He can see yanda ta hade fuskaa ransa yace "I knw she's will never change".. Zaunawa tayi saman kujerar snn tace "gani".. Jalal ya juyo ya kalleta kafin yace "baki iya gaisuwa ba ko". Imaan tayi kasa ta kanta.. Kafin a hankali tace "ina wuni" dauke kai yayi.. Snn yace "me ya hanaki yin breakfast".. Kin kallon sa tayi.. Jalal ya juyo ya kalleta snn yace "so kike Allah ya kamani naci Amanar Abba ko".. Imaan ta dago ta kallesa da sauri ya dage mata shoulders dinsa.. A hankali tace "ya jikin Abba".  Yanda tayi magana kamar wata yarinya er shekara Biyar.. Jalal ya kasa dauke idon sa akanta.. Yanayin ta kade zaka kalla kasan yarinyar nan shagwababba ce shiyasa dole ta damu da lafiyar mahaifinta.. Kasa imaan tayi da kanta.. Jalal ya maida kansa ha TV snn yace "success inshaallahu".. Imaan ta dago ta kallesa da sauri duk da bata nunaba amma kallo daya zaka mata kasan cewa farin ciki ya ziyarci zuciyar ta.. Tace "da gske".. Wani kallo Jalal yayi mata.. Snn yace "eat food".. Ya fada yana nuna mata basket din.. Babu musu imaan ta matso ta fara bude warmer din.. Fried rice din ta diba a plate snn ta zuba zoban da har ynx da sanyin sa ita kanta bata san tanajin yunwa ba seda taga Abincin nan.. Ganin Jalal ba ita yake kallo ba yasa ta zuba pepper chicken din a saman shinkafar dayawa  snn ta rufe ta mike zata tafi stairs taji yace.. "Come back". Dan daga ganin yanda ta zuba abincin yasan yunwa takeji.. He don't knw why but kawai yana so yaga taci a gaban sa.. Imaan ta dawo duk da gaban ta na dan faduwa tace "gani".. Ba tare daya kalleta ba yace "eat in my present".. Imaan da harara ta biye mata jiki ta dan hararesa batayi zaton yana kallon ta ba se ji tayi yace "wa kike harara".. Waro idanu tayi.. Se kuma tace "ni bada kai nake ba".. "Sit down and eat"... Ya fada a takaice.. Zaunawa imaan tayi ta fara cin abincin a natse. Ganin idonsa ba a kanta yake ba yasa ta saki jiki taci abincin dayayi mata dadi sosai.. Seda ta gama snn ta dauki plate din ta nufi hanyar da take tunanin nan ne kitchen.. Jitayi yace "dawo".. Dawowa tayi kamar wata me tsoransa ya nuna mata basket din ba tare da yace komai ba.. "Imaan ta kallesa ta kalli basket din.. Snn a hankali tazo ta dauka a ranta tanajin kamar tace bata dauka.. Ganin yanda yake mata Abu cike da isa.. Seda ta shiga kitchen din snn ta murguda baki tana hararan kofa.. Snn tace "a haka zan aure ka kana mun wnn isar"... Bin kitchen din tayi da kallo ganin yanda ya hadu an cika sa da kaya kamar ana rayuwa gidan"..plate din data bata ta wanke snn ta kife ta fito.. Har lokacin yana zaune yanda ta barsa.. bata yarda ta kallesa ba ta nufi stairs.. Har ta kai rabi snn ta juyo tana kallon sa dawowa tayi.. Ta tsaya bakin stairs tana kallon sa.. Bakin ta na motsi maganar ta kasa fitowa.. Jalal ta yaji sanda ta dawo ya juyo ya kalleta.. Ganin yanda bakinta ke motsi yasa yace "say it".. Imaan taki yarda ta kallesa.. Tace "akan maganar auren da kace".. Jalal ya gyara zama yana kallon ta snn yace "what about it". Ta dago manyan idanunta ta kallesa snn tace "amma zaka sakeni ko".. Yanda tayi taso ta basa dariya.. Amma ya dake yace "why".. Imaan ta ware hannu snn tace "ai ba sona kk ba".. Kura mata idanu jalal yayi yana ganin yanda yarintar ta ke kara fitowa snn yace "ke kina sona ne?".. Ta girgiza kai da sauri snn tace "nop.. Kaga seka saki ni ko".. Dan cizon lips dinsa yayi kadan snn yace "idan na sakeki seki auri wanda kikeso knn".. Ta gyada masa kai.. Yace "but ai akwai abinda mata da miji suke kuma nidake bamuyi ba".. Hade rai imaan tayi gaban ta na faduwa snn tace "me".. Jalal ya tabe baki kafin yace "I will show you".. Ya fada cos he just want to scare her.. Imaan ta ware idanu tace "me wai ai bamu son juna no need to show me anything".. Tayi maganan a tsorace.. Jalal daya fara enjoying conservation din yace "but meyasa kika yarda nayi kissing dinki a gidan mu".. Imaan da dauke kai tana tuna moment din yace "kinga acan ma kin yarda da babu aure na a kanki bare ynx da akwai aure na".. Imaan da gaban ta ke mugun faduwa ta juya ta sauri ta kofa rufe kofar harda saka key.. "I will show you".. Muryar sa ta dawo mata.. To me yake nufi.. Yana nufi wani abu ze shiga tsakanin su ne.. Oh no wlh bazata yarda ta zauna da mutum irin wnn ba....

Jalal kau murmushi yayi bayan ta haye a hankali yace.. "A fear lady always trying to look strong"... Hakanan ya fada dan kawai yaga reaction dinta.. Now ya gane cewa tana da tsoro kawai masifa ce bata barin ta ta nuna.. Wayar sa ya fara lallubawa domin ya kira salim.. Jin bata aljihun sa yasa ya tuna a dakin imaan ya barta tare da system dinsa.. Mikewa yayi ya nufi stairs.. Ya murda dakin ze shiga yaji ta saka key.. Knocking ya farayi.. Imaan da har ta cire hijab ta janyo wayar ta ta dago tana kallon kofar a tsorace tasan shine.. Maganganun da sukayi ynx yasa duk tsoransa take..knocking ya karayi.. Yasa ta mike tsaye tana tura baki tace "who".. Bude baki jalal yayi cike da mmki snn ya kara yin knocking sbd yasan tasan shine.. Imaan ta tura baki tace "who's there".. Cije lips jalal yayi yace "open this door".. Imaan kamar zatayi kuka tace "do you want anything".. "Did you knw I can open this door".. Jalal ya fada a dan fusace.. Idanun imaan suka cika da hawaye tace "pls stay away from me ni ba matarka bace".. Yace "oh really? Ohk let me get the door open then you can tell me ke ba matata bace".. Yanda gaban imaan ke faduwa kamar me har hawaye sun fara zubowa cikin muryar ta me kamar ta kuka tace "I don't love you.. Just stay away from me".. Shiru jalal yayi.. Kafin can camly yace "imaan".. Sosai gaban ta ya fadi yaune karo na farko da taji ya kira sunan ta.. "Will you get that door open".. Muryar sa ta katse ta.. "I can't" ta fada tana kokarin danne kukanta shiru jalal yayi.. Kusan minti biyu taji yace "I want to take my phone".. Juyawa tayi da sauri tana kallon wayar sa da system.. Se kuma ta juyo ta kalli kofar tace "promise me you won't touch me".. Wani murmushi Jalal yayi kafin yace "alryt open and hand it over to me".. Dan tura baki tayi snn ta nufi kofa gaban ta na faduwa sosai ta bude..tana budewa Jalal ya fizgota ta fado jikin sa yasaka duka hannayen sa ya zagaye ta...

Urs

✨✨✨

Annafie😍
*💫💫💖JALAL ALII💖💫💫*



Written by



           *ANNAFIE💖.. ✍️*

     (Smll but mighty😉)



Writer of

*LOVE CYCLE❤️*

*SABODA DUNIYA🌃*

*ADAAN💕*

*JALAL ALI🤩*



Bismillahir rahmanir raheem

💫💖Jalal Ali(18)💖💫💫

Imaan ta bude baki zatayi ihu yayi saurin rufe mata baki da hannun sa snn yace "is this what you're afraid for".. Ture hannun sa tayi snn tace leave me alone".. Jalal ya tabe baki kafin yace "if not".. Yanajin yanda heart dinta ke beating yasan a mugun tsorace taje amma ynx ta wani dake tana kara tsuke dan karamin lips dinta cike da masifa.. Jin tayi shiru ya saka ya saketa ya shiga cikin dakin wayar ya dauka da system dinsa snn ba tare daya kalle ta ba yace "this the last tym da zaki kara rufe kofa".. Imaan dake hawaye tace "but promise me bazakamun komai ba".. Ficewa yayi a dakin yana fadin "I don't understand what you're talking about bari na dawo sekimun bayani"... Daga haka ya fice.. Daki imaan ta dawo tare da zubewa saman gado ta fashe da kuka.. "Ai wlh bazan zauna da kai ba atoh"..... Dakin sa ya shiga ya kira salim basu wani jima suna magana ba   ya shiga yayi Alwala dan an fara kiran magrib.. Ko dakin ta be kalla ba ya nufi masallaci.. Be dawo ba seda akayi isha'i .. Dakin ta ya tura shiga.. Tana kokarin cire hijab ya shigo hakan yasa ta fasa ta juyo tana kallon sa da sauri... Tabe baki yayi snn ya zauna saman kujerar dake dakin yana kallon yanda take kokarin hade fuskar ta yace "kin zama malama ne".. Dauke kai tayi.. Ita kodaya bata taba kawo ma ranta cewa zatayi kwana da wnn mutumin ba a rayuwar ta kamar wasa ya shigo rayuwar ta.. Katse mata tunani yayi da fadin "let's talk".. Kallon sa tayi sede bata yarda ta kalli idanun sa ba ta sauke idanun ta akan well shaped lips dinsa da suke wasu irin pink.. Yace "kina so na sake ki".. Gyada kai tayi da sauri.. Wani kallo yayi mata kafin yace "don't answer me with motion.. If not I will cancel this deal".. Tace "eh".. Ganin yanda ta gyara yanayin fuskar ta ta komar wata innocent yasa yace "Abbanki Amanar ki ya bani. Cewa I should take care of you idan baya raye but for now tunda yanada rai zan sakeki".. Wani murmushi imaan tayi wanda bata shirya ba.. Yace "for now zan barki har zuwa tym din da Abba ze samu lpy I will make sure I take all the responsibility of you har zuwa time din da Abba ze samu lpy sbd amana ce na dauka.. Agreed?". Da sauri tace "yes.." A ranta tana fadin dama yana da mutunci har yasan Amana.. Ya katse ta da fadin.. "but this should be secret no body should knw dis har zuwa lokacin da zan baki takardarki idan Abba ya samu lpy.. And kinsan bincike ake dole hakan ya zama sirri".. A sanyaye tace "inshallahu but zan koma sch zamu fara exams next week"... Jalal ya dan juya idanun sa yana dan cizar libs din sa snn yace "ohk I will see on that but ki fara karatu a gida first ga kitchen you can cook duk abinda kike bukata hope kin iya girki". Hararansa imaan tayi wanda bama ta san tayi ba tace "kai to me ka dauken".. Yanda tayi maganan very friendly yasa jalal dauke kansa snn ya mike "ohk see yah if you need something let me knw".. Gyada masa kai tayi snn ya fice.. Imaan ta sauke ajiyar zuciya ko ba komai ta samu relief.. Tunda take dashi be taba yi mata maganar hankali ba kamar yau.. Bata cire hijab din ba ta fita sbd taji dakinsa ya shiga.. Kitchen ta shiga tabi abincin dazu a plate bayan ta zuba nama dayawa snn ta fito zuwa dakin ta....

Tundaga ranar ko magana bata kara hadu su ba yo inama take ganin sa zade taji shigowar sa taji fitar sa.. Kuma duk intayi girki seta zuba masa nasa duk da be taba ci ba.. Itaba bama ta ganin yanacin abinci sede taga ya zauna a parlor yana danne danne a system se ko waya daga nan kuma seya fita.. A haka har tayi 4dys a gidan kuma tana karatu sosai snn ta natsu tanayi ma Abban ta Addua akan Allah ya basa lpy snn ya dawo da mommy lpy..

Fitowa imaan tayi daga kitchen rike da bocket din kayanta data wanke ta shanya dan kayan ta ynx saura kala daya cikin kayan daya siyo mata.. A parlor ta iskesa zaune yana danna system din sa kamshin sa duk ya cika parlorn.. Dauke kai tayi ko kallon sa batayi ba kamar yanda shima be kalle ta ta nufi stairs tana zuwa ta shiga bathroom wanka tayi ta fitk tana dan cije lips sbd cikin ta dake danyi mata ciwo tasan kila period dinta ne gashi kuma bata da pad.. Tabe dan lips dinta tayi kamar zatayi kuka gaba daya zaman gidan ya ishe ta babu wani dadi.. Shiryawa tayi cikin ash abayan da tayi mata kyau sosai.. Ta yafa mayafin Abayar snn ta fito gaban ta nadan faduwa take sauka daga stair idon ta akansa.. Tana kallon side view dinsa yanda gashin kansa zuwa sajen sa daya wani kwanta a fuskar da.. Wnn gashin ba karamin kyau yakewa fuskar sa ba gashi baki sidik kai daga gani kasan ba karamin gyara yake samu ba.   har tym din yana nan yanda ta barsa.. Yanaji har ta karaso ta zauna saman hannu kujera tana kallon sa.. Ko daya be dago ba.. Imaan ta tabe baki kafin tace "ina so na fita".. Ko kallon ta beyi ba bare ya bata amsa ya cigaba da abinda yake  .. Imaan ta dan murguda baki dan ita wlh ta tsani wulakanci.. Katse mata tunani yayi da fadin "zuwa ina" still be kalle ta ba.. Imaan ta dauke kai snn tace "shopping".. Be kalle taba yace "me zaki siyo".. Tura baki imaan tayi tana dauke kai.. Jalal ya dago idanun sa ya zuba a kanta.. Ta juyo suka hada ido  marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace "pls".. Jalal ya jingina da kujera still looking at her snn a hankali yace "am asking you".. Imaan kalle sa kamar zatayi kuka tana tura dan bakin ta.. Taya zata fara fada masa pad zata siyo.. Jalal ya lumshe idanun sa duk da take masifaffiya duk behaviors dinta irin na shagwabbu ne ga kuma yarinta.. A hankali yace "may be abinda zaki siya is not that important".. Imaan ta bisa da kallo ganin idanun sa a lumshe idanun yake maganar .. Snn so calm.. Tunda suke bata taba ji yayi magana da karfi ba kullum so calm ga muryansa da taushi kamar wani mace idan yana magana har wani nishi yake fitarwa a hankali kamar wanda yake a gajiya.. Jin tayi shiru yasa a bude idon sa.. Suka hada ido.. Imaan ta marairai kafin tace "pls bazan dade ba I promise".. Hannu ya tusa cikin tulin gashin kansa wanda yafi yawa a tsakkiya ya wani murmurde tsabar yanda yake da santsi kamar na wani mace "asking for the last tym me zaki siyo" ya tambaye ta.. Kamar imaan zatayi kuka tace "ummm pa.. pad.. Sanitary pad".. Cike da kunya ta fada tare dayin kasa da kanta.. Kamar daga sama taji yace "are you on ur period".. Ta girgiza kai tace "nop but soon may be today ko gobe".. Tayi maganar ba tare data kallesa ba.. Rufe system din yayi snn ya dauke ta yayi up stairs batare da yace komai ba.. Imaan ta bi bayan sa da harara kafin ta murguda baki tanajin kamar tayi kuka sbd fada masan ta tayi pad take so... Babu jimawa se gasa ya sakko rike da wayar sa da key din mota wuce ta yayi ya nufi kofa snn yace "lets go".. Mikewa imaan tayi tana tura baki tabi bayan sa.. 

koda suka shiga motar babu wanda yace da wani kala.. Se danna wayar ta take da har yau taki yarda ta cire a flyt mood.. A wani babban wajen saloon jalal yayi parking imaan ta dago tana kallon wajen snn ta juyo ta kallesa.. Batare da yace da ita komai ba ya miko mata ATM din sa yace " take 2432.. Shine pin din suyi maki harda kitso I will wait".. Wani kallo imaan tayi masa kafin ta hade rai.  Dan wlh ta tsani a taba kan ta barin ma ynx daya kusa sati ko tajesa batayi tasan kila seta kusa fitsari idan aka taba sa..tace "ni ce maka saloon zanyi".. Dan kallon ta yayi ganin yanda ta hade rai, yace "bana son musu fa".. Kamar zatayi kuka tace "kaina fa beyi komai ba Allah da zafi".. Camly yace "fita".. Bude motar imaan tayi ta fita a fusace ta rufe kofar da karfi snn ta tafi tana share hawayen ta.. Jalal ya bita da kallo yana murmushi kafin underneath his breathe yace "stubborn gal".. Su kansu masu saloon din seda suka fahimci dole akayiwa imaan tazo saloon din dan se wani hade rai take.. Koda aka fara mata seta sakar masu kuka dan wlh zafi takeji bana wasa ba ta tsani a taba mata kai.. Yan wajen suka ta mata dariya ana lallaba ta.. Meyi mata tace "don't mind them beautiful gal like you tana kuka.. No stop pls this long hair idan baki gyarawa ze zube.. Ita de imaan batace kala ba seda aka gama ace ayi mata kitso kalaba kuma ba kananu ba...dan ita kalaba ce kade kitson ta.. Zata iya cewa kitson da akayi mata da wayon ta be kai 10....

Madaidaita kalaba akayi mata masu kyau tayi mata kyau sosai.. Hawaye kau kamar an bude famfo.. ta mika masu ATM din suka dauki kudin su tayi masu sallama.... Tunda ta fito jalal yake kallon ta kanta a kasa baya ganin fuskan ta.. He just want to see yanayin ta a ynx yasan her mood is not good.. Dan murmushi yayi daya tuna ranar da suka gansu ita da yusrah sun fito daga saloon..... Imaan ta bude motar ta shiga ba tare data kallesa ba ta mika masa ATM dinsa.. Hakan yasa ya gane tayi kuka.. Daukar ATM din yayi kafin yace "do you just cry".. Kamar jira take ta fashe da kuka tana kallon sa tace "that's what you want ai".. Ware idanu yayi yanama motar key snn yace "ni kuma" tace "yes kuma ynx kaina ba ciwo yake ba".. Jalal na dan murmushi yace "oh so you're crying.. Me kukan saloon me kuka kitso.. Dis girl you're so lazy".. Kallon sa tayi snn tace "shi kitson babu zafi".. Yadan tabe baki cike da tsokana yace "I don't think so".. Tana hararan sa tace "just try ka basu kanka suyi maka".. Dan kallon ta yayi snn yace "sede idan zaki mun".. Ya fada yana taba gashin kansa.. kifa kai imaan tayi ta fara kuka snn tace "wlh da zafi".. Dan kallon ta yayi a ransa yace shagwaba.. Yace "ohk srry baki nunan kitson ba".. Make kafada tayi tace "bayan kaine kasaka dole nayi".. Murmushi yayi bece komai ba har seda suka isa wani super market.. Yayi parking snn yace "naga kitson".. Ta noke kafada..  dan langwabar da kai yayi kafin a hankali yace "pls".. Kasa tayi da mayafin abayar snn ta duka ta kanta.. Jalal yabi dogayen calabar da kallo kitson yayi mata kyau.. Dauke kansa yayi snn ya tabe baki yace "ni bnga abin kuka anan ba".. Kallon sa tayi da sauri.. Ya dage kafada snn ya bude motar yana fadin "lets go.'. Daga haka ya fice.. Balla masa harara imaan tayi kafin ta gyara mayafin ta ta fita.. Bin bayan sa tayi suka shiga super market din.. Kujera ya samu ya zauna snn yace "je ki dauki duk abinda kike so".. Wucewa tayi wajen da pads suke ta nufa ta dauki guda 4 snn ta dawo.. Kallon ta yayi . snn yace "mene wnn".. Hade rai tayi kafin tace "shi zan siya".. Wani kallo yayi mata kafin ya tashi.. Inda ake aje cart ya nufa ya turo babba snn yazo wajen ta yace "follow me..".. Bin bayan sa tayi tana tura baki.. Wajen irin su inners yaje yace "oya dauka mu wuce jor".. Ta girgiza masa kai da sauri "ni basu nazo siye ba"... Wani kallo yayi mata kafin camly yace "we're not hear for jokes".. Kamar zatayi kuka tace "to ka tafi sena dauka".. Dauke kai yayi daga kallon ta ba tare da yace da ita komai ba.. Imaan ta karasa wajen hadaddun bras din.. Da sukayi mata kyau sosai.. Dozin biyu ta dauka ba tare da ta yarda ta kallesa ba ta zuba cikin cart din.. Haka ma panties ta debi dayawa dan tasan tana da bukata.. Duk yana kallon ta amma ya nuna kamar ba ita yake kallo ba.. Imaan ta dauka harda sleeping wears duk wani abu da tasan zata bukata.... Seda ta gama tace "done".. Batare daya kalleta ba ya tura cart din wajen creams da perfumes yaje batare da yace bata komai ba ya cigaba da danna wayar sa.. Hakan yasa imaan ta duba creams shower gel da sabulun wankan da take amfani dasu snn ta dibi body sprays da perfume masu yawa ko hoda daya bata dauka ba.. Tace na gama.. Dan kallon ta yayi ganin babu ko powder a cikin be taba ganin ta da make up ba but yanaso yaga ya zatayi looking idan tayi.. Hakan yasa yace "baki dauka ba". Ya fada yana nuna mata kayan make up.. Hararan sa tayi tace "kaga ina make up ne".. Yace ki dauka nace". Make kafa tayi tana murguda baki "to wai me zanyi da s... Bata karasa ba taji ya fizgota ta fado jikin sa.. Kara ta saki a mugun tsorace.. Yana mata wani kallo yace "repeat that again".. Kamar zatayi kuka tace "menayi".. A ransa yace matsoraciya se shegen tsiwa.. "Excuse".. Sukaji an fada.. Wani kamilin mutum ne sanye cikin suit zeyi sa'an Abba.. Duk kallon sa sukayi har tym din tana a jikin jalal.. Mutumin yace "what's happening here".. Murmushi jalal yayi kafin yace "nothing sir".. Ya fada ya sakin imaan tare da kamo hannun ta ya rike cikin nasa.. Mutumin na murmushi cike da natsuwa yace "couples I guess".. Jalal yace "sure sir".. Gyada kai mutumin yayi snn yace "what a beautiful couples".. Murmushi jalal ya kakalo snn yace "tnx".. Har mutumin ya juya se kuma ya juyo yana kallon su yace "ur name".. "Jalal".. Noding yayi kafin yace "continue making love son bye".  Wucewa mutumin yayi.. Duk suka bisa da kallo kafin imaan ta fizge hannun ta a nasa tana tura baki.. Tabe baki yayi snn ya debe wasu daga cikin kayan make up din ya saka snn ya dube ta.. "What do you need for sch".. Dan kallon sa tayi jin yace sch ta dan sakin ranta tace "nothing se naje muke shopping and ina da kudi a account dina".. Yana kallon ta snn yace "clothes".. Ta ware hannu kafin tace "ina da kaya a sch fa"... Tabe baki yayi snn yaje wajen biyan kudi ya basu ATM suka cire.. Kwashe kayan zuwa mota...

A boutique din ranar nan yayi parkig snn ya bude motar ya fita ganin bata fito ba yasa ya dawo ta side dinta ya bude yace "sena fito dake ne".. Fito wa tayi ya rufe motar snn yayi gaba ta bisa a baya.. Yana shiga matan dake wajen suka dago suka kallesa dan tsab sun gane sa.. Ware idanu wata tayi.  "Wow sir are yo.." Shiru tayi ganin imaan tazo ta karasa kusa dashi fuskan ta a dan shagwabe.. Kallon ta sukayi snn suka kallesa dayar tace "ur girlfriend?" Ba tare daya bata amsa yace "asist her pls zata zabi kaya".. Da sauri tace "ohk sir .. She's ur wife I guess".. A takaice yace "sure".. Kallon sa imaan tayi shima ya juyo yana kallon ta snn yace "go with her".. Sosai sukayiwa yan matan kyau.. Kama hannun imaan yarinyar tayi snn tace "lets go".. Binta imaan tayi.. Suna tafiya matar tace "wow you guys  suit each other just look at you and ur husband so beautiful oh wow".. Murmushi imaan tayi kawai ita bata ga wani dacewa da sukayi da wnn jalal din ba.. Hasali ma basa wani good tym.  Kuma duk da takeji anacewa tana da kyau bata jin takai jalal.. Snn taya za'a rinka cewa ta dace da wnn me munanen halayen .. Tasan dan basusan wanene shi bane shiyasa kowa ke fadar haka".. Wasu abayas masu kyau ta zabar wa imaan da ita kanta sun birgeta seda ta dauki 24 snn ta fara daukar mata English wears sleeping wears da sauran su seda suka cika babban cart din snn suka taho.. ATM Kawai ya mika suka cire kudin aka saka masu kayan a mota.. Wani mall jalal ya shiga chocolate ya siyo masu uban yawa se ices cream.. Mikawa imaan yayi.. Washe baki tayi ta karba.. A rayuwan ta tana bala'in son kayan zaki tace "thank you".. Kallon ta yayi snn yace "maganin kukan kitso ne".. Tura baki tayi tana murmushi.. Yace "when is ur exams".. "Saura 3dys".. Ya gyada kai snn yace "you're going back tomorrow so if you need anything let me knw".. Girgiza masa kai tayi domin kau ita babu wani abu dazata bukata.. Basu kara magana ba har suka isa gida.. Ta bude zata fita ya juyo ya kalleta snn yace "you make sure baki barmin komai a mota ba park all to ur room and arrange them".. Daga haka ya fice.. Binsa tayi da harara ynx ita kade zata kwashe kayan nan.. Aikam bazata dauka ba.. Ita ma bude motar tayi ta fito ta bisa.. A parlor ta iske sa.. Yana ganin ta empty tazo zata wuce yace "kila baki son komawa sch ko".. Cak ta tsaya tana kallon sa ba itama yake kallo ba remote yake dannawa changing channels.. tura baki tayi kafin ta juya ta fice.. Ya bi ta da kallo tare da sakin murmushi wato yarinyar nan fitinan na ce knn da bazata dauko ba.. Wani murmushin ya kara saki idan tana abu kamar wata jaruma amma matsoraciya ce masifa ce kawai... Yana zaune ta rinka shiga da kayan ko kallo bata ishesa ba.. Ita kam ta cika tayi fam.. Tana gama kwashe ana kiran sallah ta shiga zatayi alwala taga period dinta yazo haka yasa tayi wanka ta fito bayan ta shirya ta fara gyara kayan a dakin komai ta sakashi inda ya dace wadan da take bukata ta sakasu a jaka kara dakuma chocolate dinta.. Ta dibi wanda zata sha ynx ta saka sauran dan dasu zata tafi. Bata kara ganin jalal ta hartayi bacci.. Shikam yana down stairs waya suke tun dazo da sageer seda suka dade snn ya kashe ko ina ya nufi stairs.. Dakin ta ya bude.. Kudundune ya ganta cikin blanket.. Tabe baki yayi tare da kashe wutar dakin snn ya nufi nasa dakin...

Wajen karfe 4 da rabi jalal yayi parking a bakin Apartment dinsu imaan ganin gidan a bude yasa ta gane sun dawo dan har yau wayar ta bata kunna ta ba tasan sun nema har sun gaji.. Jalal ya mika mata ATM din snn yace "you knw the pin ki basu suje shopping you are not allowed to go out inba sch".. Kallon sa tayi da sauri snn tace "bn gane ba".. Kallon ta yayi da kyau ya dage gira daya snn yace "sure ko an fada maki matan aure nafita any how ne".. Dauke kai imaan tayi cike da takaici bata son yanace mata matar aure nan.. Camly yace "say ur mind".. Juyowa tayi ta kallesa tana ware manyan idanun ta snn tace "kaji nace wani abu ne" tabe baki yayi snn yace "just try going out ki gani I will slaughter you and thosee tsamayen gayun da suke daukanki a mota kar ki kara don't go anywhere  without my permission".. Kallon sa tayi kamar zatayi kuka snn tace "to kai ina ruwanka".. Ya tabe baki tare da karbar wayar ta yana fadin "just try and see".. Numbernsa ya saka a wayar ta yayi saving tare da fadin call me if you need anything.. Karban wayar tayi ta fice bayan ta bude back seat ta dauki jakanta.....

Urs

✨✨✨

Annafie😍

........
...............

*💫💫💖JALAL ALII💖💫💫*



Written by



           *ANNAFIE💖.. ✍️*

     (Smll but mighty😉)



Writer of

*LOVE CYCLE❤️*

*SABODA DUNIYA🌃*

*ADAAN💕*

*JALAL ALI🤩*



Bismillahir rahmanir raheem

💫💖Jalal Ali(19)💖💫💫

Da sallama ta shiga gidan ta nufi nasu entrance din.. Tana shiga parlor sukaci karo dasu maryam ta suka taho jin muryar ta.. Wani irin rungume ta sukayi cike da murna ita kanta cike da murna ta rungume su.. Sakin ta yusrah tayi tana hararan ta .. "Your phones are switch off why".  Imaan na kokarin boye damuwar ta tace "wayar mommy ya bata nawa kuma gashi na kashe ta".. Wani kallo maryam tayi mata kafin tace "kin san halin da muka shiga kuwa.. Kiris ya rage ki ganmu a kd dan har munyi maganar dasu farouq ... Cike da sonsu tace "eyyer buddies qlw muke fa".. Ta fada tana yaye mayafin Abayar ta snn ta zauna tace "what did you guys cook yunwa nakeji".. Tayi maganan kamar zatayi kuka.. Yusrah tace gaki ga kitchen nan.. Tashi tayi ta shiga kitchen din ta zubo jellof din cuscus din dayaji hanta snn ta zauna tana cikin ci su farouq suka shigo.. Ware idanu sukayi ganin ta kafin suce "ke amma se Allah ya tambaye ki dama lpyanki qlw kika saka hankalin mu ya tashi".. Dariya tayi tana kallon farouq snn tace "I just want see whether you guys cares alot se gashin bn ganku a kd ba".. Muneer ya harareta snn yace ba'a zuwa.. Dariya tayi taci gaba da cin abincin ta... Farouq yace "babu tayi".. Kitchen ta nuna masa dan da Dane zata iya cewa yazo suci amma ynx ganin tana da aure se kawai taji bazata iya ba ...

Washe gari su maryam suka fita shopping imaan kin yarda tayi ta bisu a cewar ta wai batayi karatu ba.. Hakanan kawai taji bata son fita ba tare da nasa permission din ba.. Tunda tana da ilimi kuma a addinan ce tasan duk wacce ta saba umarnin mijin ta  tana da zunubi so duk da sakin ta zeyi she have to obey him...

Sosai imaan ke kokarin danne damuwar ta ko daya bata yarda ta nuna masu halin da take ciki ba dukda sunga ynx komai nata ya canza but se suka dauka duk exams ce duk da sunga abin yayi yawa domin ko karatu shan ice cream da sauran su imaan bata fita.. Ga wani irin saurin kuka... Imaan kau ita kade tasan me takeji tunanin mommy ynx yafi damunta akan na Abba tunda shi tasan inda yake kuma tana saka ran ze samu lpy amma mommy faa ko daya bata san inda take ba hakan na mugun damunta   shiyasa kullum cikin yi ma abba da mommy Addua take.. Kuma ta dage sosai wajen karatu.. Numbern jalal na nan a wayar ta yau sati daya knn babu wanda ya kira wani a cikin su duk da sometimes tana son fita but she rather die than to call him ya raina mata hankali.. Suna haduwa da summayya idan sun fito exams dan ynx kowa wuyar gani yake sbd exams..... Yau de imaan gaba daya ta gaji son fita take sbd she's very lonely gobe basu da exams jibi ma haka su yusrah duk sun fice saura ita kade.. Tura baki tayi ta tashi ta shiga bathroom wanka tayi ta fito daure da towel gaban mirror ta tsaya tana shafa dan gsky ita yau fita zatayi ice cream take son sha da kuma shawarma snn tanaso tadanyi fresh up ita bata wani irin saba da zama hakanan ba sbd ko tana gida suna yawan fita outing tare da Abba da kuma mummy.. Dan haka ita fita zatayi.. Shiryawa tayi cikin wata maroon Abaya da tayi wani mugun mata kyau wayar ta ta dauka gaban ta nadan faduwa.. Hakanan taji bazata fita ba she have to call him sbd yanada hakki akanta.. Dialing numbern sa tayi ta saka a kunne gaban ta nadan faduwa.. Tanaji wayar tana ringing amma be daga ba har ta katse.. Tsaki tayi cike da haushi ta cillar da wayar.. Ringing wayar ta fara hakan yasa imaan ta wani zabura tana kallon wayar gabanta na faduwa ganin shine.. Ganin zata tsinke yasa ta dauki wayar da sauri tana kaiwa kunne.. Shiru bece mata komai ba imaan ta sauke ajiyar zuciya kafin tace "ina wuni". Be amsata ba har ynx... Jin shiru yasa ta kalli wayar ganin he's still on yasa ta mayar da wayar tana murguda baki. Muryar sa cike da taushi kamar yanda ya saba magana yace "why are you calling me"..imaan ta tura baki cike da  jin haushin sa snn tace "inaso na fita ne".. "Me zakiyi".. Ta langwabar da kai kamar tana gabansa tace "am craving for ice cream".. "You are not allowed to go out".. Kamar zatayi kuka tace "pls am so lonely wlh ni kade ce pls don't say no bazan dadeba"... Dan lumshe idanu yayi yanajin yanda take magana kamar wata baby er 10yrs.. A hankali yace "kina jina".. Da sauri tace "eh".. Jalal ya lumshe idanu snn yace "don't you dare go out idan ma kin fita zan sani kuma zakiga abinda zanyi".. Dit taji ya kashe wayar.. Wurgar da wayar imaan tayi cike da jin haushi tana dana sanin Kiran sa dan ta tsani wnn isar tasa.. Ta cire veil din abayar ta yar cike da jin haushi idanun ta sun cika da kwalla amma tana hana kanta kuka.. Kwafa tayi kafin tace "wlh se kasan ni kakema haka dan kaga ina kyaleka ko".. Fashewa tayi da kuka tana zubewa saman gado.. Ta kusa 1hour a haka dan har bacci ya fara fizgar ta taji wayar ta ya fara ringing firgit ta farka ganin shine yasa tayi tsaki ta wullar da wayar.. Se kuma kome ta tuna oho ta dauko wayar da sauri tayi picking kafin ta tsinke.. "Come outside" shine kawai abinda ya fada ya kashe wayar.. Imaan tabi wayar ta harara cike da jin haushin ta wlh tunda take babu meyimata yanda yaga dama ta kyalesa kamar wnn... Veil din ta yafa tana kallon fuskar ta a mirror yanda tayi wani kyau sbd dan baccin data fara.. Ta dauki wayar ta snn ta zura silifas masu taushi da sukayi ma er kafar ta wani irin kyau snn ta fice.. Motoci dayawa ta gani a wajen  hakan yasa ta dauki. Waya ta kirasa yana dauka tace "am out".. Yace "bye ur left I will flash you".. Ya fada yana kunna hasken motar sa snn ya kashe.. Wani hadden mad jeeb ne black wanda daka gani kasan kudin ta bana wasa bane dan tafi karfin me karamin kudi.. Imaan ta dade tana kallon motar kafin ta tura baki ta dauke kanta tace "ni bn gani ba".. "Don't weste my tym".. Daga haka ya katse wayar murguda baki tayi tana hararan motan kafin ta fara tafiya a hankali toward the car. duk Abinda take yana kallon ta dan akan idon sa ta fito.. Imaan ta bude motar a hankali gabanta na faduwa.. Wani kamshi da sanyi ne suka daketa lokaci guda shiga motar tayi Tana dan lumshe idanu kafin ta bude ta daura a kansa.. He looks handsome than ever yayi wani bala'in kyau cikin black yadin me shegen taushi Kasancewar sa fari se ya kara haskasa.. Ya saka wani bakin glass baka ganin idanun sa se pink lips dinsa da suka kara wani kyau  da haske kamar kayi kissing wlh tulin gashin kansa yasha gyara ya wani mummurde se kyalli yake.. Juyowa yayi ya kalleta tayi saurin dauke kanta daga nasa ganin yanda maroon abayar tayi mata wani irin kyau yasa yace "da wane ze fitar dake".. Batare data kallesa ba tace "taxi".. Jalal yayi wa motar key snn yace "ko kuma tsamayen samarinki ba".. Cike da jin haushin sa ta juyo ta kallesa tana ware idanu snn tace "ai ba laifi bane dan na fita da saurayi na isa ne"... Wani kallo yayi mata ta cikin glass din kafin yace "seki bari se babu aure na a kanki"... Murguda baki tayi snn tace "ni stop calling me matar aure atoh".. Tabe baki yayi bede ce komai ba daga nan kowa yayi shiru babu me cewa komai. Har suka isa wane babban waje na ice cream chocolate da kuma snacks.. Ita kanta imaan gurin yayi mata kyau daga gani se dan wane da wane ke zuwa wajen.. Ganin yanda take ta kallon gurin yasa yace "bakauya kawai".. Juyowa tayi da sauri ta kallesa se kuma ta murguda masa baki a ransa yace "wnn da karfi gareta Allah kade yasan mutanen da zata rika jibga sbd tsabar masifar ta".. Nikan nace dukda bata dashi tana saka su talatu da kuluwa su jibgar mata😂... A zahiri kuma yace salan mu fita kimun kauyanci..imaan ta bude motar ta fita tana tura baki..

Seda suka fita suka jera snn imaan tace "zan saka samari na su kawoni tunda ynx kanunamin kaga next zuwa ba zanyi kauyanci ba." Dan kallon ta yayi kafin yace "idan na sakeki knn".. Ta dage kafada "aa kafin ka saken m".. Jalal yayi murmushi kafin yace "just try it da rabon za'ayi kisan kai knn".. Yanda suka jero suna dan magana se ka daura wata firar soyayya suke.. Sunyi wani bala'in kyau bana wasa ba .. Suna shiga wajen aka wani  rinka kallon su musamman ma yan mata wajen da suka kafe jalal da idanu.. kana ganin su kaga yaran manya.. Tsayawa imaan tayi jalal kuma ya tafi domin masu ordern Abinda zasu siya.. Ganin yanda ake ta kallom jalal yasa ran imaan baci.. Barin ma wata kyakkyawar beb data kafe sa da idanu tun dazu dan ta kula yarinyar ma bata gane cewa bashi kade yazo ba sbd yanda take.. Kallon sa.. Gani tayi tana kokarin mikewa.. Hakan yasa imaan ta juya ga jalal da sauri ko kula da wani dan tudu dake gabanta batayi ba burin ta takarasa ga jalal.. Sede kawai ji tayi ta bige da kafar ta snn ta fadi kasa tare da bige guiwan ta.. Zafin da taji yasa ta fara yarfe hannu bataso tayi kuka .. Juyowa jalal yayi da sauri yayo kanta.. Yana kama hannun ta ta fashe da kukan da take rike tare da fadawa jikinsa.. Runtse idanu Jalal yayi sbd unexpected ta fada jikin.. He don't no why but her touch is difference inde ta taba sa se yaji wani iri.. Rungume ta yayi yana dan buga bayanta ita kuma tana kuka dan sosai ta bige a kafar ta da gwiwan ta.. Kallon ma'aikatan wajen yayi ganin mutane idon su yana kansu yasa yace "am going to my car kumin take away I will be waiting in my car"... Ya fada yana daukar imaan data makalalkalesa sosai tana kuka.... Suka fice duk aka bisu da kallo cike da birgewa.. Back seat ya bude suka shiga.. Dan bubbuga bayan ta yake a hankali yana fadin sorry.. Cikin kuka tace "my leg wayyo kafana zafi".. Dago ta yayi ya fara share mata hawayen kafin yace "muga kafan".. Kallon sa tayi se kuma tayi saurin sauka daga jikin sa tana noke kafada.. Wani kallo yayi mata kafin ya tabe baki yace "to da meyasa kika fado jikina"".. Tura baki tayi kafin tace nina sani ne.. Ya tabe baki kafin ya bude ya fita ganin ma'aikacin wajen ya taho da manyan ledojin da aka zuba abinda ya siya.. Anan back seat aka zuba kayan ya koma driver seat yana kallon ta ta mirror yace "da akwai kuma Inda kike bukatar zuwa ne".. Girgiza kai tayi kafin tace "take me home"har tym din hawaye take... Bece komai ba yayiwa motar key suka dauki hanyar sch har yazo gaban Apartment dinsu imaan hawaye take.. Yanayin parking ya bude motar ya fita back seat ya bude ya shiga camly yace "is the leg paining you" ta gyada masa kai. Yace "to muje ayi maki kamu" da sauri ta girgiza kai dan batason kamu tace "zafin ba sosai ba ai".. Ganin yanda ta tsorata yasa yace "bn yarda ba"... Da sauri ta dago kafan tare da daga rigar ta tana nuna masa tace "ka gani fa".. Jalal yabi kafar ta ta dake fara sal gwanin bn sha'awa da kallo.. Dan lumshe idanu yayi just wanting to touch the leg yace "I want check ko ba se anyi kamu ba".. Tace "duba ka gani ba se anyi ba".. "A haka zan duba".. Jalal ya fada yana kallon ta.. Tace "tayaya".. Saman cinyar sa ya nuna mata yace "a nan".. Ba tare data kawo komai ba ta dauki kafar ta kyar ta daura a cinyar sa.. Wani lumshe idanun jalal yayi yanajin yanayinsa na sauyawa.. Yabi kafar da kallo har zuwa gwiwan ta duk a bude.. A hankali yace "ina ne".. Ta nuna masa kafar da kuma gwiwan ta.... Hannun sa ya dauka a hankali ya daura akan kafar ta.. Ita kanta se taji wani irin jin hannun sa me taushi akan kafar ta.. Jalal kam ba'a magana jin yanda skin din ta keda wani irn taushi.. Dan murza kafar yayi tayi er kara snn yace "nan ne?" Ta gyada masa kai.. Murza mata ya shiga yi feeling her soft skin imaan kau zafi bata san lokacin da ta daura hannun ta akan nasa ba.. Daurewa kawai jalal yayi yana matsa kafar amma gaba daya ta sakar masa da wata kasala.. Seda ya tabbatar kafar bazatayi tsami ba snn ya saki yaxo wajen gwiwan imaan bata san sanda ta shige jikinsa ba tare da sakalo hannu ta wuyan sa cike da tsoro tace "pls kar kayi mun da zafi dan Allah my knee is paining me".. Cikin muryar jalal data fara shakewa yace "I won't".. Daura hannun sa dake dan rawa yayi saman gwiwan ta.. Imaan tasaka dayan hannun ta ta zagaye sa.. Ya salaam jalal ya furta yana kallon gwiwar dan gurjewa tayi.. Bakin sa yakai saitin gwiwar yana dan hura mata iskar bakin Snn yana dan murza mata a hankali.. Imaan ji tayi tsigan jikinta ya wani tashi yanda yake hura mata iskan bakin sa da yanda soft hand dinsa ke dan danna gurin ya sakar mata wani kasala wani dumi taji jikin ta nayi.. Bata san sanda ta daura kanta a shoulder dinsa ba tanaji kamar kar ya dena.. Yanda ta kwanta a jikinsa yasa duk yaji wani irin he feels kamar janyo ta ya rungume ta sosai a jikin sa ko yaji saukin abinda yake ji ynx kawai ranar da yayi kissing dinta a gidan su yake tunowa.. Allah ma ya sani he enjoyed that moment.. He want to do more but baze bari haka ta kasance ba ya fiso su rabu lpy ba tare da wata matsala ba.. Kallon ta yayi yana tattaro natsuwar sa snn yace "idan kinje ki shafa rub ze dena".. Gyada masa kai tayi a sanyaye.. Yace "oya tashi a jikina".. Yay maganar a zuciyar sa yana fadin Allah yasa kar ta tashi.. Tura baki tayi kafin ta tashi a hankali.. Bude motar yayi ya koma mazaunin driver snn yace "you kan go make sure you park all this.. Sbd naki ne".. Shiru imaan tayi tana dan wasa da fingers din ta kafin tace "pls when are you taking me to wajen Abba I want to see him".. Banza yayi da ita be ce mata komai ba.. Hakan yasa a sanyaye ta bude kofar tare da kwashe duka manyan ledojin ta rufe motar zata tafi yayi kasa da glass dinsa yana kallon ta snn yace "ki shirya by 4".. Kallon sa tayi tare da sakin murmushi kafin tace "thank you".. Dauke kansa yayi tare dayiwa motar key yabar wajen dai dai tym din da yusrah tazo wucewa duk da bata ga fuskar jalal ba taga side view dinsa.  Da sauri tace "oh my god imaan ina kika samo wancan handsome din duk da bnga face dinsa ba but his side view is damn cute oh wow and see his mad ride".. Wani kallo imaan tayi mata kafin tace "kinga ni tayani kwasar kayan nan na gurde kafa ta".. Yusrah ta tayata suka shigar dasu zuwa ciki.. Imaan rub ta dauka ta shafawa ciwon ta kamar yanda yace.. Yayin ta su yusrah suka shiga fito da manyan robobin ice cream da yoghurts.. Kala kala masu uban waya.  Dayan ledan kuma snacks ne lafiyayyu masu yawa suma dayar kuma chocolate ne.. Dadi wajen su yusrah kamar me dan wlh idan zasu tasa wadan nan kayan sui taci se sun kusa sati basu kare ba.. Se tambayar ta suke ina da samoshi tayi banza dasu tana shan ice cream din dayayi mata mugun dadi...,

A parlor ya iske dad din nasa tare da kanin sa Alh., isa suna dan fira da alama dinner ma tare sukayi.. Sosai suke birgesa.. Shiyasa he wish ace saif na nan da komai tare zasu rinka yi babu abinda zasu raba.. Kokarin danne dacin da yake ji yayi ya gaisar dasu suka amsa cike da farin ciki.. Alh isa yace "my son ka dawo".. Gyada kai yayi.. Dad yayi murmushi sosai yake jin dadin yanda Alh isa yake kula da jalal ya dauke sa kamar dansa.. Shi dama duk wanda zeso jalal to yana sonsa.. Yace "son have you eaten".. Gyada kai jalal yayi duk kuwa da babu abinda yaci.. "Dan tun yan kwanakin da yayi ba'a gida ba granny take fushi dashi.. Shima ya tattarata ya watsar dan yasan zigata akayi shiyasa ko part dinta ya dena zuwa.. Shi nan ba ta ita yake ba ta kansa yake as far as dad dinsa baya fushi dashi to kowa ma yayi he don't fucking care as yanda jalal yake ko a family dinsu babu wanda ya isa ya tare sa da sunan fada . who are you self?.. Shiyasa yaji dadi tym din da imaan ta koma sch dad bayanan".. Sallama yayiwa dad snn ya nufi part din sa..

Kayansa ya cire ya shiga toilet wanka yayi ya fito ya shirya cikin pajamas snn ya dauko wayar sa domin ya kira mamy ganin bata online yasa ya aje snn ya bude fridge dinsa.. Wasu tsaddun wines ne cike.. Binsu yayi da kallon tare da sakin murmushin takaici idanun sa suna sauya kala kafin yace "good job".. Rufe fridge din yayi tare da kure AC kamar yanda ya saba.. Ya kashe wutar dakin tare da kudundunewa cikin duvet  yana sakin ajiyar zuciya a haka har bacci ya kwashe sa...

Urs

✨✨✨

Annafie😍*💫💫💖JALAL ALII💖💫💫*



Written by



           *ANNAFIE💖.. ✍️*

     (Smll but mighty😉)



Writer of

*LOVE CYCLE❤️*

*SABODA DUNIYA🌃*

*ADAAN💕*

*JALAL ALI🤩*



Bismillahir rahmanir raheem

💫💖Jalal Ali(20)💖💫💫

7:45am wayar hajiya atika tafara ringing ganin haj. Huwaila ce yasa ta fasa fitan da zatayi ta koma saman gado  ta zauna snn ta dauki wayar.. "Huwaila lafiya kike Kira na da safiyar nan da ina dakin miji na fa".. Daga can haj. Huwaila tace "ke dole ce tasakani kiranki kinsan kuwa Tasiu ya dawo tun sati biyu da suka wuce amma babu shi babu labarin sa iyalansa ma sunce basu gansa ba".. Ya mutsa fuska mama tayi kafin tace "waye kuma Tasiu".. Wani tsaki huwaila taja snn tace "dillah wanda mukabama contract din kashe saif da jalal".. Tabe baki mama tayi snn tace "to ni ina ruwana tunda be sanni ba Alh falalu wasu kade ya sani baya duniya kuma kinga ni am out of this".. "Just think of if ace wasu ne ke bin diddiginsa kuma idan Falalu wasu ya rasu ai Manga yanada rai snn inde aka gane manga to kema asirinki ya tono".. Faduwa gaban mama tayi snn tace "to wane ze gane wa ye kuma ze bibiye mu".. "Baki ganin Jalal ne" cewar huwaila wani tsaki mama tayi kafin tace "karki batan rai mana wnn babu abinda ya iya amma ina zargin kila wadan da suka rigamu kashe sa ne".. Ajiyar zuciya huwaila ta sauke snn tace "Allah yasa ba wata kulalliyar bace.. Ynx de duk inda manga yake ki saka ido akansa".. "Karki damu da sannu zamu tafi da komai har mu gama yi masa illa " cewar mama tana dariya   sallama sukayi mama tayi jigum tana tunanin rashin ganin Tasiu da ba'ayi ba...

Wajen karfe hudu da rabi jalal ya kira imaan tana dauka yace "am waiting"... Babu jimawa sega imaan ta fito sanye cikin dogon hijabi daya mugun yi mata kyau tunda ta taho yake kallon ta kamar wata balarabiya zataje masallaci".... She look so innocent dan gaba daya jikin ta a sanyaye yake ko dan zata gano Abba ne oho".. Bude motar tayi ta shiga tanajin yanda kamshin sa da sanyin AC suka hadu.. "Ina wuni".. Tace masa.. Be ko kalleta ba yayiwa motar key seda suka fara tafiya snn yace "when are you finishing ur exams".. Ba tare data kallesa ba tace "saura 5dys".. Shiru Jalal yayi yana tunanin karyar da zeyiwa dad dinsa domin baxe bar er mutane ta rinka kwana ita kade ba... Babu wanda ya sake magana a cikin su har suka iso Asibitin.. Sosai gaban imaan yake faduwa kawai taoron yanda zata tarar da Abba ta take shima ya kula da hakan amma bece da ita komai ba.. Suna zaune har Sageer ya karaso snn duk suka fito.. Sageer na kallon ta yace Amarya Amarya.. Murmushi imaan ta kakalo ta daga kai suka hada ido.. Kowa ya dauke kansa snn ta gaisar da sageer.. Ya amsa yana fadin ya studies tace Alhamdllh... Ba tare da bata lokaci ba suka nufi dakin da Abba yake wanda yake cike da mugun tsaro Gaban imaan faduwa yake kawai kamar wancan lokacin yauma a projectile aka haska mata shi kamar tana gaban.sa. Sosai jikin imaan ya fara rawa tana kallon Abban nata yanda duk aka daure kafadar sa da kuma cikin sa duk da bandeji snn kansa ma.. Rufe bakin ta tayi tana kokarin hana kanta kuka jalal ne ya kama hannun ta ta kallesa tayi saurin runtse hannun ta.. Kawai she just wish ta gama karatu wlh da seta nemo wadan da sukayi ma Abban ta wnn abin sbd tasan bashi da hakinsu amma ji yanda suka maida shi kafa daya duniya kafa daya lahira.. Kuka ta fashe dashi hakan yasa jalal ya kama hanun ta suka fita mota ya mayar da ita suka shiga back seat yayinda Sageer ya shiga driver seat.. imaan ta kifa kanta a cinya tana kuka sosai.. Sageer ne yace "inshaallah ze samu lpy but I want to ask you some questions ". Shiru imaan tayi amma bata dago ba.. Hakan yasa sageer yaci gaba "an samu nasara a wajen aikin da akayi wa Abba sede sauki yana daga wajen Allah snn ki gode ma Allah cewa be mutu ba sbd komin daran dadewa ze tashi kuma asirin wanda suka masa haka ze tuno so ki kwantar da hankalin ki tunda Allah yasa yana da rabon numfashi a gaba".. Gyada kai imaan tayi.. Sageer yace "ai want ask of ur relatives though bazamu fada masu cewa yana rayeba sbd yanayin aiki but yakamata mu san inda suke.. A hankali imaan ta dago kanta ta share hawaye snn tace "bansan family din mommy ba dan ba a nan suke ba.. Abba kuma bashi da kowa mamana ce kade er uwarsa and she's late".. Duk kallon ta sukayi cike da mmki.. Imaan ta fashe ta kuka tana fadin.. "Abba ba shine Mahaifina ba Amma yamun Abinda ko babana bemun ba ya mayar dani mutum snn ya inganta rayuwa ta.. Mommy ta zame mun kamar uwa ta kula da maraicina na uwa dana rasa.. A can kauyen mu suka dauko ni suka sakani a makaranta suka rike ni kamar er da suka haifa.". Bakin jalal har rawa yake wajen fadin you mean ba sune iyayen ki ba". Ta gyada kai tana kuka sosai. "Basu bane.. Tun ina karama suka dauko ni suka rabani da wahalar da nake sha..ranar da aka haifeni ranar mamana ta rasu.. Na taso cikin rashin dadin uwa bani da me sona se babana da umma.. But there love are not strong enough tunda basu iya protecting dina ga makiyana amma nasan da mamana tana da rai duk wata wahala bazan sha ba.. Ashe wahala na me karewa ce shiyasa Abba ya raboni da kauye ya dawo dani gidan sa ba kallon wan mamana kade nake masa ba kallon uba nake masa sann mommy uwa.. Ina sonsu fiye da tunanin kowa sbd sune silar farin cikine da duk wani jin dadi na bn san me abba na yayi masu ba, sukayi kokarin kashe sa wlh my Abba's heart is pure.. His heart is pure.. Ta fada tare da fashewa da kuka.. A hankalk jalal ya janyo ta jikinsa yana bubbuga bayan ta wlh tayi mugun basa tausayi.. Just imagine mutum tunda ya taso besan mamansa ba.. Tunda ya taso wahala take sbd rashin uwa sedaga baya komai ya sauya koshi nan ynx ya yakeji bare ita da bata santa ba.bata taba shan nonon uwa ba. Ynx dama all this while imaan marainiya ce.. Harga Allah yaji wani mugun tausayin ta da kuma kaunar Abba sbd yayi abinda ba kowa ze iya ba and mommy give her the best motherly love duk da basu hada komai ba ... Abinda she be samu ba knn.. Mamy ce kade zata iya masa haka ita kuma jinyar mummy  take.. har suka iso imaan bata bar kuka ba.. Jalal ya dago ta yana kallon ta kafin yace "imaan".. Kallon sa tayi yace "stop crying Abba ze samu lpy kuma Asirin ko suwane ze tono just pray for him and ga sageer nan he will stand by Abba dan ganin an kama masu laifi".. Gyada kai imaan tayi hakanan taji hankalin ta yana kwanciya su Jalal sun wani birgeta".. Babu wanda ya kara magana har suka iso.. Bude motar imaan tayi zata fita se kuma ta juyo ta kalli Jalal suka hada ido tayi kasa da kanta kafin tace "thank you".. Dan lumshe idanun sa yayi snn da bude dakan ta.. Imaan ta fice... Sageer na kallon ta har ta shige snn ya kalli Jalal ta mirror yace "man anya ba son beb dinnan kake ba".. Wani kallo jalal yayi masa snn tace "wnn mara kunyan kawai ta bani tausayine amma babu komai"Wani kallo sageer yayi masa kafin yace "tell that to birds but not me I can see you have feeling for this girl".. Wani guntun tsaki jalal yayi kafin yace "and zan nuna maka ba haka bane ranar dana rabu da ita".. Sageer ya tabe baki snn yace "kana rabuwa da ita zan aure ta atoh cos I will not let this beautiful girl go off just lyk that either me or you".. Cike haushi jalal yace "none of us".. Dariya sageer yayi sosai yana driving snn yace "man haushin fa na menene.. ".. Banza jalal yayi dashi shiru sageer yayi snn yace "babu wani bayani da zamu samu daga bangaren Abba inde har baya farfado ba kokuma. Ansamu mommy".. Ba tare da jalal ya dago ba yace "let's just concentrate on Alh falulu's family da kuma wadan da suke aiki dashi.. Su salim ba suna dubamin a companies din Dad nima zan koma work soon".. Sageer ya kalle sa snn yace work kuma karfa a dauka kazama serious" murmushi Jalal yayi snn yace "nop kawai dole ne zanyi basaja domin na rinka kwana tare da wnn girl din bazan barta gida ita kade ba".. Gyada kai sageer yayi yana dan murmushi snn yace "kode na samo maka film din soyayya".. Batare da jalal ya kawo komai ba yace "kaima kasan I only watch horror film, zumbi da sauran su ranar ma na siyo wasu bande samu tym din kallo ba".. Dariya sageer yayi ganin be fahimce sa ba snn yace "dallah am talking of ynx da baka da aure ynx kam you need romantic movies ko".. Banxa jalal yayi dashi dan ya kula sageer tsiya yakeji.....

Tundaga ranar basu kara koda waya ba imaan ta cigaba exams dinta sosai take maida hankali dan tasan Abba zeji dadi idan ya tashi ya ganta da result me kyau... Ranar data gama text kawai jalal yayi mata na cewa yana waje.. Da mmki imaan take kallon wayar ta ta taya yasan tym din datake gama exams.. Dama already kayan ta a shirye suke wadan da tasan zata bukata dan bata tafiya kaya sede idan zata dawo ta karo.. Har mota su yusrah suka rakota jalal duk na kallon su be sauke glass ba bare su gansa.. Tana shiga ya tayar da motar suka bar wajen.. Gaisar dashi tayi ya amsa ciki ciki ta tabe baki.. Wani eatry ya tsaya zeyi masu take away imaan tace "idan naje zan dafa da kaina".. Kallon ta yayi snn yace "nima kina nufin jagwalgwalon ki zanci".. Ta ware idanu "waya fada maka I can cook fa even Abba said am a chef".. Tabe baki yayi kafin yace "tell that to the birds" daga haka ya bude motar ya fita.. Ta bisa da harara tare da tabe baki.. Take away yayi masu snn ya dawo just abinci kade ya siyo sbd yasan akwai drinks da fruit a gida.. Babu wanda ya kara magana har suka iso gida.. Budewa tayi ta fita ta barsa da ledar take away.. Binta yayi da kallo har ta shige... Bin parlorn imaan tayi da kallo yanda yake a gyare tsaf ko se kamshi yake.. Sama ta wuce ta bude dakin ta ta shiga.. Shima a gyare ta gansa.. Ta bude wardrobe dinta itama cike date da kaya bayan kayan da suka siyo an kara wajen uku.. Dakin ba kamar waccan karon ba domin kau ynx duk wani abu da zata bukata akwai sa a wadace.. Tabe baki tayi kafin tace "sekace wacce tazo zama a gidan".. Wata zuciyar tace "waye ze zauna da bad boy".. But yana da mutunci wata zuciyar ta fada.. Dan murmushi tayi data tuna yanda ya tsaya mata wajen abbanta and he's doing his very best just ya rike amanar da abba ya basa.. Attleast zata zauna lpy dashi kuma su rabu lpy.. Da wnn tunanin  ta fito domin da zasu taho tayi wanka.. Yana parlor ta wuce kitchen ta shiga ganin shima yanda aka kara cikasa damkam babu Abinda babu.. Ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin me zata dafa masu.. Lafiyayyar rice and stew ta dafa with chicken snn tayi cucumber juice.. Jalal na parlor yana dan danna wayar sa yaitajin kamshi.. Lokaci lokaci yake kallon kitchen din.. Fitowa imaan tayi tana kallon sa snn tace "na zubo maka". Hararan ta yayi snn yace "nayi maki kama damecin jagwalgwalo".. Murguda baki tayi snn tace "nayi maka kama da me dafa jagwalgwalo".. Wani kallo yayi mata hakan yasa ta shige kitchen da sauri.. Babu dadewa se gata da tray din abincin ta kawo gaban sa ta aje.. Ko kallon ta jalal beyi ba ta koma kitchen ta fito da nata Abincin har ta fara hawa stairs yace "come and take dis ur food bazan ci wasan yara ba".  Batare data juyo ba tace "take it ur self".. Daga haka ta kasara da sauri.. Jalal yabita da kallo..shi rashin kunyar ta har mmki take basa dan ya kula tsoro ne da ita.. Ko sumy bata isa ta fada masa haka ba bare wann yasa sumy ta girme ta da kusan 2yrs shikam ze bata 9yrs.. Kallon abincin daya cikasa da kamshi yayi kafin ya dauki spoon yayi testing .. Wani dadi yaji besan sanda ya lumshe idanu ba.. kara ci tayi yana tabe baki kafin yace "so she can cook".. Dan murmushi yayi kafin yace "I knw is mommy".. Yayi maganar yana tuna abincin dayaci a gidan su.. Seda Jalal yaji cikin sa ya cika snn ya tashi.. Barin gidan yayi gabadaya.. Ta window imaan taga fitar sa.. Hakan yasa ta fito dan dama tsoran fitowa take  bin abincin tayi da kallo ganin ya kusa cinye ba.. Ta murguda baki snn tace "dan rainin wayo dole ka tafi tunda ka cinye Abinci".. Kwashe plates din tayi taje kitchen ta wanke.. Snn ta dawo parlor cartoon ta kunna tana kallo.. Bata tashi ba seda akayi magrib.. Bayan isha'i kam ta dawo tacigaba da kallon ta..

Jalal kau gida ya wuce.. A parlor ya iske dad dinsa tare da mama da kuma Atika duka suna kallo cike da nishadi.. Wani bakin ciki jalal yayi ganin su a tare.. Shine yaron dad dinsa amma wasu daban sune family din dad dinsa.. While shi an kashe masa dan uwa snn ga mum dinsa can kwance rai hannun Allah... Ji yayi zuciyar sa na tafarfasa. "Son".. Muryar dady ta katse sa.. Daga kai yayi ya kalli Dadd da jajayen idanun sa sometimes seyaji haushin Dadd dinsa sbd yanda ko maganar mum dinsa be tabayi masa ba se kanin sa wanda shine yake tsaye akan ciwon ta.. "Come to me my son". Dad ya fada yana ware masa hannayensa.. Dauke kai Jalal yayi snn ya fice.. Yanaji dad na kwala masa kira amma inaa motar sa ya nufa da mugun gudu yabar gidan.. Seda yayiwa gida nisa sosai snn yayi parking tare da kifa kansa a sitiyari "I hate her yes I hate her".. Ajiyar zuciya yashiga saukewa kafin ya dauko wayar sa he need to see his mum itace family dinsa shima.. Vedio call ya kira mummy tana dauka ganin yanayinsa tace "Jalal my son what wrong with you".. "Mamy I want to see mumm pls mamy don't say no".. Sosai yabama mamy tausayi.. Hakan yasa ta nuna masa mum da take kwance kamar kullum.. Runtse idanu yayi tare da kashe wayar. Ya daki sitiyari idanun sa sunyi jawuur zuciyar sa na tafarfasa "I will cut you all. Into piece you will regret coming to JALAL ALII'S life billah anyone among you will be my flesh I won't free anyone, I will kill them with my own hands yea am a bad boy yes Jalal is a bad boy".. Tayar da motar yayi zuwa inda yasan ze samu su Labeeb....

Tun tana saka ran dawowar sa har ta dena dan har 11 tayi.. Tsoro ya mugun cikata.. Bade yana nufin ita kade zata rika kwana gidan nan ba.. Tashi tayi a sanyaye ta koma daki wanka tayi ta shirya ta kwanta amma bacci yaki zuwa gani take kamar wasu zasu shigo.. Wajen 12 taji karar bude gate hakan yasa ta tashi da sauri window ta leka ta sauke ajiyar zuciya ganin shine ya shigo da jahilin gudu. Yana gama parking ya bude ya fito hanun sa rike da wine da akayi rapping.. Tuni imaan ta gane mene.. Snn kallo daya tayi masa ta gane a bige yake... Ta saki labulen ta sauri snn ta dawo bakin gado ta zauna gaban ta na faduwa.. Idanun ta suka tara kwalla.. "Why is he choosen to be bad he looks calm but why is he this bad".. Ada tana wasu wasi da halayen sa sbd yanda ya taimaki Abba amma ynx ta yarda.. He came back home drunk taya zatayi rayuwa da mashayi.. Dafe kai imaan tayi tare da fashewa kuka.. Tanaji yaxo ya shiga dakin sa.. Kuka imaan tayi sosai tanajin wani iri.. Ta dade kafin bacci ya dauke ta....

Urs

✨✨✨

Annafie😍..... *💫💫💖JALAL ALII💖💫💫*



Written by



           *ANNAFIE💖.. ✍️*

     (Smll but mighty😉)



Writer of

*LOVE CYCLE❤️*

*SABODA DUNIYA🌃*

*ADAAN💕*

*JALAL ALI🤩*



Bismillahir rahmanir raheem

💫💖Jalal Ali(21)💖💫💫

Ana kiran sallahr asuba yazo yana mata knocking seda yaji alamun ta tashi snn ya wuce sbd an fara sallah.. Imaan tabi kofar da  harara kafin taja wani tsaki.. Kawai wani mugun haushi yake ba ta kara jana wani tsaki "harda wani tashi na sallahr asuba kamar ba wanda ya dawo a bige ba".. Toilet ta shiga tayi alwala snn tazo ta kabbara sallah.. Tana idarwa ta fara azkar taji sanda ya dawo ya shiga dakin sa.. Tacigab da adduoin ta seda ta gama tsaf tazo zata tashi taji kamar karatun Quran.. Mikewa tayi taje saitin kofa.. Aikam karatu ne cikin kira'a me dadi kuma ba kowa bane jalal ne.. Imaan ta dawo bakin gado ta zauna kiri'ar sa dadi and he can  recite it so perfect.. Inde har mutum yana iya tunawa da ubangijin sa ya karanta Quran yayi sallah kan lokaci to meyasa ze saka ya saba masa. And yanada mutunci.. Wata zuciyar ta fada.. Dafe kai imaan tayi tarasa tunanin da zatayi kwantawa tayi saman gado duk setaji haushin sa da takeji ya tafi.. Da wnn tunanin bacci ya dauke ta... Bata farka ba se tym din da taji ya bude kofar ta cikin bacci ta gansa sanye da jallabiya se kuma taga ya fita.. Karar bude gate taji hakan yasa ta dauka ko ya fita.. Juyawa tayi taci gaba da baccin ta se 11 ta farka shima wata yunwa ce ta tashe ta .. Har ta nufi bathroom kome ta tuna oho.. Cottens ta daga tana kallon motocin dake parking space motoci biyu ta gani sabanin jiya daya dawo uku ne.. Hakan yasa ta gane ya fita.. Da sauri ta nufi kofar fita wine din nan takeso ta dauko dan wlh bazata yarda ya rinka sha mata giya cikin gida ba... Bata damu da shigar dake jikin ta ta nufi dakin sa.. Turawa tayi a hankali tana dan lekawa ganin babu kowa yasa ta shiga dakin da sauri.. Bin dakin tayi da kallo ganin yanda yake a gyare da kamshin sa ta ko'ina dan lumshe idanu tayi... Sauke idanun ta tayi akan wani dan karamin fridge dake gefen bed dinsa.. Karasawa tayi da sauri ta bude.. Fruit ne kade se kwalbar wine din.. Da sauri ta ciro ta tana kallon ta gaban ta na faduwa.. Har zata tafi tace bari ta kara dubawa.. Sama ta bude wajen freezer din.. Ware idanu imaan tayi tana kallon wasu manya manya chocolates, chocolate , ice cream da sauran su.. Miyanta tsinkewa yayi bata san sanda ta zauna ba ta fara fito dasu ba Zama ta gyara ta fara bude wafa din tanaci wani dadi imaan taji wanda seda ta lumshe idanu.. Ita dama Allah yayita da son zaki..... Da sauri imaan ta juya jin an bude bathroom.. Jalal ne ya fito sanye da wata bathrobe se karamin towel yana goge gashin kansa tuni kamshin sabulinsa ya cika dakin.. Mirror ya nufa dan ko kula ma da ita beyi ba.. Samun kanta tayi da bin jikinsa da kallo sbd yanda golden skin dinsa ke wani daukar idanu kai daka gani kasan bakaramin hutu take samu ba kuma lafiyayya ce snn ko ba'a fada ba kasan ana kashe mata kudi bama na wasa ba.har wasu kanunun gashi ne suka wani kwanta.. Ita kanta karya take tace skin dinsa bazatayi taushi ba.. Jalal da be lura da ita ba yana kallon mirror yaga mutun zaune ta bayan sa ta kura'a masa idanu.. Juyawa yayi da sauri domin tabbatar wa kansa cewa itace.. Aikam itace ganin yanda take kallon sa yasa yace "ke me kike mun a daki".. Ware idanu imaan tayi kafin ta fara kame kame.. Yace "do you just look at me naked?".. Da sauri ta girgiza kai gaban ta na faduwa snn tace "yanxu nazo".. "And why are you here". Yayi magana yana folding hands dinsa.. Girgiza kai tayi tana zare idanu snn tace "ai ynx zan tafi.. Dama dama".. Se kuma tayi shiru.. Yace "good nide kika kalla babu kaya ko to nima bazan yarda ba sena Rama".. Yayi maganar yana ganin yanda tayi looking so sexy dan wandon jikin ta iyakar sa rabin cinyar ta pink se wata riga light blue din riga ta tayi mugun yi mata kyau kayan sun kamata sun fito da duka shafe dinta barin ba Ass da boobs dinta.. Gashin kanta tayi parking dinsa.. Sbd ba'a gyare yake ba yasa duk yawani kwanta mata se tayi looking kamar wata er baby tayi mugun kyau hasken ta ya kara fitowa.. Jalal don't knw why but wasu naughty things yake tunanin aransa dayana kallon ta ta.. Girgiza kai imaan take tana kokarin mikewa snn tace "pls nayi hakuri".. Dan biting lips dinsa yayi data mike ji kawai yake kamar ta motso kusa dashi.. Shi kansa yasan wlh no doubt a yanda take din nan he will hug her and have the fun of his lyf".. A hankali yace "come here".. Hoping that zata zo he don't knw why but he has different feelings akanta.. Bayau ya fara ganin mata half nake amma wlh be taba jin abinda yake ji akan imaan ba game dasu..ba  Da wayo imaan ta wawushi chocolate din nan dayawa ta saita kofa kafa me naci bn baki ba sede jalal yaganta a fit ta fice.. Murmushi yayi yanajin kamar ya bita dan wlh ganin ta haka ta mugun tayar masa da hankali... "Hey jalal no girls".. Wata zuciyar ta fada masa.. wata tace "she's ur  halal just enjoy atleast have funs not sex just romance".. Dan murmushi yayi yanajin anya hakan ya dace.. Se kuma ya dage kafada "da. Ai babu aure na akanta and ai kiss her and I enjoy let me enjoy more niba dutse bane am matashi at the age of 29 why can't I enjoy my samartaka.. And she's my halal".. Dan lumahe idanu yayi moment din da yayi kissing dinta kawai yake fado masa Allah yasani he enjoyed that moment bana wasa ba.. How he feels her daya rungume ta.. Oh the feelings is just inexpressible.. Dan lumshe idanu yayi yana biting lips dinsa ganin yanda yake ta dirty thinking akan yarinyar da yake so su rabu lpy.. Dole yabar gidan nan dan wlh yasan ze iya afka mata a halin da yake ciki dan ita kade yake jin haka akan ta kuma idan yana ganin ta hankalin sa baze taba kwanciya ba.. Da wnn tunanin ya gama shirin sa yabar gidan.. Sede imaan taga fitar sa snn ta fito tq hada breakfast...

Direct gida jalal ya wuce.. Yauma kamar jiya duk suna parlor sede yau babu zulfa kila yasan ta fita work ne.. Kallo daya Jalal yayi masu ya wuce dakin sa.. A parlor ya zauna yanajin ransa na wani baci.. Turo kofar parlorn akayi.. Yasan ba kowa bane se Dad dan haka ko daga kai beyi ba.. Dad ya zauna kusa da dan nasa cike da kaunar sa.. Hannun sa dad ya kamo yana murzawa a nasa snn yace "Jalal".. Ko kallon sa Jalal beyi ba.. Dad yacigaba "I don't knw why but may be am not worth to ur best".. Dan kallon sa Jalal yayi da confusion. Dad ya gyada kai.. "Yes son.. Before my jalal is not lyk this but now you're always sad, not happy, may be am not worth of knowing ur problems".. Jalal ya girgiza kai "no dad".. Dan murmushi dad din nasa yayi yanajin babu dadi snn yace "look son.. Ur happiness is mine.. You're my number one happiness, I love seeying you happy but why are you always sad, am ur father duk abinda kakeyi is paining me but you're my son and I love you yes and I do everything because of you.. Son pls tell me what will make you happy?  I promise you inde kudi na siya zan siya.. Idan karfi na siya I will use you all my strength  just to get you out of the sad lyf, tell me kana son aure ne? Pls son ka fadamun.. Kallon mahaifin nasa kawai yake cike da tausayawa Allah ya sani yanason dad dinsa sosai.. Dan wlh da baya son sa da da tuni ya watsar dashi sbd yanda ya watsar dasu dukda yasan bayin kansa bane.. For now yasan he's dad can't get him out from the sad lyf.. Samun lpyr mum dinsa itace farin cikin sa.. For now his dad will not understand se ranar daya kama wadan da suke da hannu dumu dumu a cikin rayuwar sa.. Yasan duk abubuwan da ake fadin yanayi na munanen halayensa is affecting his Dad he is just trying to be strong. Dad ya kama hanun sa yanajin mugun tausayin Jalal snn yace "pls son pls".. Jalal ya dago idanun sa da sukayi mugun jaa yana kallon dad rungume sa yayi yanajin kamar ya fashe da kuka dan zuciyar wani zafi take masa yasan indan ba ya sha wine ba yau baze taba samun natsuwa ba.. A hankali yace "be strong dad I will change inshaallahu I will change as you always dreamt me to be am srry dad  I love you dad".. Rungume sa dad yayi yanajin tausayin sa da kaunar sa sosai.. A hankali yace "my son muje kayi break fast ur mom has.." "No pls dad I will not eat her food and she's not my mom".. Kallon sa kawai Dad yake ya rasa gane dalilin daya baya sonta while ita kuma bata da magana seta jalal.. Ze zage ta ze kore ta ya kyare ta  amma bazata taba cewa komai ba sema de tace "yaro ne".. Dad yace "pls son ita fa maman ka ce and she love you".. Mikewa jalal yayi yana daukar key din motar sa ya fice mama na ganin sa ta taso "Jalal my son are you ohk".."get out of side get out".. Ya daka mata tsawa.. Se kuma ya nunata da yatsa "the last warning don't ever call me ur son am not ur son I hate you yes I hate you". Daga haka ya fice daga parlon ta bisa da kallo snn ta juyo a sanyaye ta kalli dad da shima ya fito "srry kinji soon ze dena inshaallahu" murmushi tayi kafin tace "babu komai ai da na kowa ne". Dad ya nufi part dinsa.. Seda taga ya shige snn ta tabe baki.. "Ko uwarka na rigata shigowa gidan nan bare kai. Wlh you did not hate me but soon se ranar dana rabaka da uban naka zaka gane kurinka lokacin da zaka fara garari motar hawa ma ta gagare ka bnza mashayi kawai.. Babu abinda ya sani se shan giya"....

..

Ganin har dare yayi be dawo ba yasa ta dauka yau ma kila a bigen ze dawo.. Hawayen ta ta share snn ta nufi dakin ta "shknn ita kuma da mashayi zata cigaba da rayuwa" wanka tayi ta shirya cikin kayan bacci snn ta kwanta.. Sede me kasa yin baccin tayi kawai tafiso taga shigowar sa dan Allah tsoro take ji bata so ta kwana ita kade.. Har 2 jalal be dawo ba.. Tsoro ya cika imaan ko daya ta kasa yin baccin.. Gani take kamar wasu zasu shigo sbd baya nan.. Can angle din bango taje ta lafe tare da fashewa da kuka.. Tana ganin ynx ita kade zata kwana a wnn katon gidan.. Se wajen 3;30 snn bacci ya kwashe ta...

Ana fara kiran sallahr asuba ta farka.. Jikinta se ciwo yake mata sbd a kasa ta kwana alwala tayo tayi sallah snn ta dawo ta kwanta sbd baccin dake idon ta.. Tuni bacci yayi awon gaba da ita.. Se gab da azahar ta farka..sbd yunwar da takeji ko wanka batayi ba tayi brush ta sakko kasa.. Seda ta hada tea tasha kafin ta dafa masu light abu.. Diba tayi ta tafi dashi daki.. Seda taci snn tayi wanka ta fito tayi sallah.. Ta idar tana tunanin dalilin kin dawowar tasa.. Tunanin kiran sa tayi dan wlh tsoro takeji ya barta tana kwana ita kade a gidan nan.. Shiryawa tayi cikin wata atampa Riga da skirt kayan sunyi mugun yi mata kyau.. Daga sch ta dawo dasu dan cikin kayan daya siya mata daga abaya se English wears.. Tana cikin taje kai taji an bude gate ga hon.. Hakan yasa ta duba da sauri ganin motar sa ce yasa ta sauke ajiyar zuciya.. Taciga da shirin ta.. Tayi dauri ture kaga tsiya tulin gashin ta ya bullo ta kasa.. Yanda tayi kyau kamar ka sace kayan sun fito da ainahin surar jikin ta.. Tanajin lokacin daya shiga dakin sa be dade ba yafito.. Plate din da taci Abinci dazu ta dauka ta fito.. Zaune ta gansa a parlor ya dukufa yana danna system dinsa yayi wani kyau cikin long sleeve shirt din jin kamshin ta ya wani cika parlon yanajin ta amma be daga kai ya kalleta ba .. Seda ta sakko stairs din tace "ina wuni".. Be dago ba yace "lyf".. Tabe baki tayi wuce kitchen.. Samun kanta tayi da zuba masa Abinci sbd taga ranar yaci.. Gaban sa ta kawo ta aje.. Dagowa yayi zace "waya sakaki" Idon sa ya sauka akan ta suka hada idanu.. Dan langwabar da kai tayi tana marairaicewa snn tace "abinci na kawo ma. Sbd tuna yanda ya kamata a dakinsa jiya kar yace zeyi mata wani abu.. "Yanda tayi din seda jalal yace ya salam sbd yanda ta turo dan pink libs dinta.. Samun kansa yayi da gyada mata kai kawai.. Baya tayi sbd yanda kamshin sa ya cikata.. Ta nufi stairs.. Kallon jalal ya bita dashi yanda kayan sukayi mugun yi mata ya fito da duk wani surar jikinta.. Bata da wata kiba skin dinta ce a murje se kuma surar jiki da Allah yaba amma jikinta dan karami ba wani babba ba... Biting lips dinsa yayi yana kallon ta har ta shige snn ya tura hannun sa cikim gashin kansa ya jingina da kujera yana lumshe idanu.. Tafiyar ta ya fara ji tana sakkowa ya ki bude idanun sa dan baya so ya kara kallon ta.. Parlon ta shigo ta zauna saman hannun kujera kamar zatayi kuka snn tace "wai meyasa jiya baka kwana nan gidan  ba tsoro nake ji ni sosai".. Bude idanun sa yayi yana kallon fuskar ta ganin kamar zatayi kuka yasa yace "tsoro kikeji".. Ta gyada masa kai.. Shi kuma ya langwabar da kai snn yace "ni kuma ai nan ba gidan mu bane".. Kamar zatayi kuka tace "inajin tsoro".. Kallon ta yayi kafin yace "come here".. Kallon sa tayi ya gyada mata kai a hankali hoping that zatazo.. Tashi imaan tayi a hankali ta karaso inda yake ta tsaya tace "gani".. Hannu yasa ya fizgota ta fado jikinsa sosai imaan ta tsorata ta fara kokarin mikewa shi kuma ya gyara mata zata sosai a saman cinyarsa ta zauna da kyau sann ya zagaye ta da duka hannayensa yanajin kamshinta me dadi yana shiga hancin sa.. Duk yanda imaan ke kokarin tashi kasawa tayi tuntana tana mutsu mutsu dinta har tayi lakwas ta cikin jikin sa gabanta na faduwa cike da tsoro tace "pls am srry".. Ya zuba mata farfaren idanun sa yana kallon fuskar ta snn yace "srry for what".. "Nide ka sakeni" ta fada tana turo baki.. Jalal yabi yan pink lips din nata da yanajin yau nothing kan stop him from kissing these cute lips da suke mugun tsole masa ido. He want to kiss them to his satisfaction and enjoy.. "Idan naki fa".. Ya fada yana kara rungume ta a jikinsa feeling yanda jikin ta ke rawa kasa magana imaan tayi tanajin yanda ya rungume ta a jikinsa har tana jin bugun zuciyar sa.. Jalal ya maida kansa ga system yacigaba da dannawa lagwass imaan a jikinsa tanajin wani irin kasala gaba daya kamshin sa da dumin jikinsa sunsa duk jikinta ya mutu kamar kar ya sauke ta haka take ji kamar is the best place to sleep takeji.. Jin tayi shiru yasa ta juyo yana kallon ta yanda tayi din kade ya nuna masa she's feeling what he feel for her.. Dago da kanta yayi yana kallon ta dayan hannun sa yasa yaja dan kwalin ta baya yana kallon gashin gaban kanta yanda ya kwanta yayi mata wani kyau dayan hannun sa yakai ya fara shafa gashin  zuwa gefen fuskar ta.. Wani lumshe idanu imaan tayi tanajin yanda soft hands dinsa ke yawo a fuskar ta.. A hankali yace "kina jin tsoron kwana ke kadai?.." "Uhm" ta fada bata son ta kalle sa.. Ya matso da fuskar sa daidai tata snn yace "look at me".. Maido da idon ta yi tana kallon kyakkawar fuskar sa duk da abinda takeji kasa dauke idon ta tayi daga kallonsa.. Ya hada goshin sa , hancinsa da nata.. Snn yace "kina so na rinka kwana gida".. "Uhm" ta fada har lokacin idanun ta a nasa.. Lumshe idanu yayi kafin ya daura lips dinsa a anata ya fara kissing dinta.. Lumshe idanu imaan tayi because a yanda take ji ynx she need the kiss.. Sosai ya kara rungume ta yana kissing dinta fiye dana ranar nan dan yau shan bakin ta yake sosai.. Ita kanta  she enjoys it wani yamm jikin ta yake mata  tanajin kamar sucigaba da zama a haka.. Kwance ribom din ta yayi ya tusa hannu cikin tulin gashin ta yana shafawa wata ajiyar zuciya ta sauke tanajin yanda soft hand dinsa ke wayo cikin kanta zuwa wuyan ta.. Sun dauki lokaci ahaka kafin taji hannun sa akan zip din rigar ta.. Zare bakinta tayi daga nasa da saure tare da shigewa jikin sa tasaka duka hannunwan ta ta kankamesa tana boye fuskarta a kirjin sa kafin cikin muryar ta data fara disashewa tace "no, no pls".. Yanda tayi masa din seda jalal yaji kamar ya zauce shima zagaye ta yayi da hannayen sa a cikin jikin sa yana runstse idanu.. Yanda suka kankame junan su kamar wasu masu kewan juna da suka dade basu ga juna..ba   Tana jin yanda zuciyar sa ke biting shima haka.. Sun dade a haka. Kafin jalal yaje saitin kunnen ta a hankali kamar wani ze jisu yace "baki so na gani".. Bnxa tayi dashi.. Jalal na jin yanda duka chest din ta da nasa suka hadu.. Kamar wani karamin yaro yace "in gani".. Noke kafada tayi tana kara shigewa jikinsa.. "Why".. Kin basa amsa tayi. Tanajin yanda zuciyar sa ke wani irin bugawa.. Ze kara magana aka fara knocking kofar.. Wani zabura imaan tayi ta sauka a jikin sa ko second daya bata kara ba ta nufi stairs da mugun gudu jalal ya bita da kallo da idanun sa da suka sauya kala har ta shige.. Lumshe idanu yayi kafin ya kalli door din da ake ta danna door bell yasan ba kowa bane.. Sageer ne.. Tashi yayi a hankali yana jin jikin sa a mugun mace .... Bude kofar yayu batare daya bari sun hada ido da sageer ba ya koma wajen zaman sa.. Shigo wa sageer yayi yana fadin "kasan ynx gidan na masu aure ba zaka shigo kai tsaye ba".. Zaunawa yayi yana kallon jalal da idanunsa ke a lumshe.. "Bro are you ohk".. Be yarda ya kalli sageer ba ta yace "muyi abinda ke gaban mu pls".. Dariya sageer ya fashe da ita.. Kafin yace "don't tell me har ka fara shan amarci".. Jalal ya bude lumsassun idanun sa yayiwa sageer wani kallo snn yace "what are you talking about".. Sageer zeyi magan idanun sa suka sauka akan dankwalin atamfar imaan ta ribom dinta a saman kujera.. Wani  irin waro idanu yayi snn ya kalli jalal suka hada ido. Jinjina yayi masa da hannu kafin yace "latest ango".
I’m srry for yesterday’ 😩 wlh kwana biyu matsalan wuta muke samu. Ni kuma ga wayana zukau pls kumin uzuri kunji 🥺...

Urs

✨✨✨

Annafie😍

........*💫💫💖JALAL ALII💖💫💫*



Written by



           *ANNAFIE💖.. ✍️*

     (Smll but mighty😉)



Writer of

*LOVE CYCLE❤️*

*SABODA DUNIYA🌃*

*ADAAN💕*

*JALAL ALI🤩*



Bismillahir rahmanir raheem

💫💖Jalal Ali(22)💖💫💫

Jalal ya dauke kai dan babu abinda zece sbd sageeer has already caught him right handed.. Sageer ya fashe da dariya.. "Oh ni Jalal is that you... Don't tell me kana nan kana making love with the beautiful young lady da kk claiming bata da kunya.. Banxa jalal yayi dashi.. Sageer ya zauna tare da janyo abincin da imaan ta kawo sageer ya fara ci.. Lumshe idanu yayi kafin yace "wow gsky dole nazo nayi aure oh my god matar ka ta iya girki Jalal".. "Malam kazo muyi abinda ke gaban mu".. Jalal ya fada yana wani daure fuska.. "Ai babu wani daure fuska malam ka gama enjoying da matar ka shine ni zaka daure mun.. Let enjoy the food kafin nima nayi auren".. Sageer ya fada yana cin Abincin.  Murmushi jalal yayi yaude yasan ya bani.... Sageer ya kashe masa idanu kafin yace "tell me what just happen".. Jalal ya dage kafada.. "I just have some feelings for her.. I don't why but akan ta kade nakeji".. "That means you love her".. Wani kallo jalal yayiwa sageer da yayi maganar snn yace "take that out of ur mind Abba na samun sauki zan maida masa diyar sa.. And daga yau ko kallon ta bazan karayi ba".. Wani murmushi sageer yayi kafin yace "uhmm".. Jalal ya hararesa kafin ya maida kansa yacigaba da danna system dinsa.. Seda sageer yaci ya koshi snn yace "kasan Manga?" Jalal ya dago tare da zuba masa idanun sa... Sageer daya gane me yake nufi yace "yayi MD aka company din dad wanda ya fara mallaka maka".. "What about him" cewar Jalal.. Sageer yace "good a zahirin gsky manga da Alh falalu ba wasu makusanta bane amma a badini kulle suke dan abisa binciken danayi suna da wata boyayyar alaka wacce babu wanda yasan da ita".. Jalal ya cije lips dinsa snn yace "that means nemo inda manga yake shine ze saka musan shirin Alh falalu akanmu dakuma dukkan dalilinsa da kuma wadan da suke tare".. Sageer ya gyada kai "exactly, sede yafi shekara uku baya Nigeria daga shi har iyalansa".. Jalal ya lumshe idanun sa yanajin zuciyar sa na tafarfasa meyasa wadan da baya tsammani suke shigowa lamarin nan.. Bude idanun sa yayi ya kalli sageer snn yace "inaso a gano ko wace kasa ya tafi".. Sageer ya mike snn yace "we have to meet su bature domin ba maganar waya bace already ma nace su jirani a gida na.. So ina jiranka a mota aje ayi sallama da amarya but kar a dade pls".. Daga haka ya fice.. Jalal ya bisa da kallo yana murmushi yasan halin iskancin sageer nesa ba kusa ba.. Tashi yayi tare da daukar wayar sa yabi bayan sageer... Seda sageer ya biya wani eatry ya siyawa jalal abinda zeci kuma ya tsare sa yaci snn suka nufi inda zasuje...

Jalal be dawo ba seda akayi sallahr isha'i a masallacin  unguwar su ya tsaya yayi ta snn ya karaso gida.. Imaan dake parlor tana kallon cartoon ta sauke ajiyar zuciya jin shigowar sa dan tsoro duk ya cikata dama tana ganin kila yau na  baze kwana nan ba...

Tana zaune har ya shigo imaan tayi kasa da kanta taki yarda ta kallesa sa.. Shima kallo daya yayi mata ya dauke kai ya haye sama.. Imaan tabi bayan sa da harara.. Bai wani jima ba ya sakko.. Parlorn ya dawo ya zauna.. Imaan bata kallesa ba ta maida hankali akan cartoon din da alama yanayi mata dadi sosai....

Remote din ya dauka tare da chaza channels.. Da sauri imaan ta juyo ta kallesa kamar zatayi kuka.. Nunawa yayi kamar be ganta ba yacigaba da chanje chanjen channels.. A hankali imaan tace "kuma ba cartoon nake kallo ba".. Dan juyowa yayi ya kalleta.. Yanda tayi din taso ta basa dariya.. He love this her character ta tsoro kokuma shagwaba... Yace "nima kallo zanyi".. "To ka bari nagama tunda na rigaka ynx zasu gama".... Shima langwabar da kai yayi kamar yanda tayi snn yace "to nima ki bari nagama kinga ynx zasu fara".. Ya fada yana tsayawa akan wata channel da alama har sun fara film din.. Daure fuska imaan tayi kafin ta maida kanta ga kallon.. Shima shiru yayi be sake cewa komai ba ya maida kansa akan film din.. Yanda aka fara film din is so interesting dan imaan natsuwa tayi tana kallo .. Kafin ta fara ganin.. Yanayin film din ya fara sauyawa zuwa alamar tsoro.. Duk dan yanda ta fara jin tsoro kasa denawa tayi.. Jalal kau hankalin sa kwance and ganin yanda ta natsu yasa ya dauka kila itama tanason horror film. Imaan bata tsorata ba seda aka fara nuno horros din.. Wani ihu ta kwada wanda seda ta firgita jalal.. Tasowa tayi da sauri ta dawo kusa dashi ta zauna tana kallon horros din marasa kyan gani.. Itafa ta tsani kalar films din nan.. Yanda suke tahowa kamar zasu fasa plasma din yasa ta wani kara tsorata da sauri jalal ya riko ta.. "Ke relax this just movie".. Makalkale hannun sa tayi kafin tace "am afraid".. Jalal ya zauna tare da zaunar da ita gefen sa.. "Oya relax babu abinda zasu maki ohk?".. Gyada masa kai tayi a hankali still tana kallo.. Shima yacigaba da kallon.. Matsowa tayi jikin sa sosai ta daura kanta a shoulder dinsa.. Jalal ya kalle ta snn yace "just close ur eyes if you don't want to see".. Gyada masa kai tayi amma taki rufe idon.. Murmushi kawai yayi.. A ransa yace "a fear lady"... Sosai imaan ta kankamesa tama hanasa yayi kallon cikin natsuwa kuma itama taki dena kallon yace taje ta kwanta taki.. Haka ya hakura de har aka gama kallon.. Ya kalleta yanda ta kankamesa yace "oya go to ur room".. A hankali tace "to ka rakani".. Wlh yanda tayi zuru zuru din nan ta mugun basa dariya.. Dama wnn boss lady din nada tsoro haka.. "Let's go".. Yana fadin haka yayi gaba da sauri ta bisa tare da kamo hannun sa.. Jalal ya runtse idanu inda tasan yanda yakeji idan ta tabasa data dena.. Ko kallon nan da kyar yayisa sbd yanda ta makalkale har ynx yanaji soft skin dinta makale dashi...

Suna zuwa ya bude dakin oya "enter".. Shiga imaan tayi da sauri ya rufe mata dakin tare da sauke ajiyar zuciya ya nufi dakin sa.. Imaan tabi dakin ta da kallo gani take kamar horros din zasu faso bango.. Bath room ta shiga tayi wanka shima ko dadewa batayi ba ta fito.. Tayi shafar ta snn ta fesa turare.. Sbd tsoran da takeji wata er riga kawai ta dauko ta saka snn ta haye gadon ta da sauri ta rufa da duvet har kanta ta kudundune tayi lamo tana jiran ta horros din zasu billo mata. Jikin ta har wani kyarma yake sbd tsoro.. A haka bacci ya dauke ta.. Wanda ko 30mis batayi ba ta farka a mugun tsorace.. Bin dakin tayi da kallo tana zufa.. Gani take kamar zasu faso bango suzo.. Dan motsi taji a bayan gadon ta hakan yasa ta tashi a mugun firgice ta nufi kofa ta bude ta fita. Kafar jalal ta bude ta afka cikin dakin.. Ganin dakin babu haske ko daya ga wani kamshi da uban sanyin AC yada kure yasa ta fashe da kuka "yaya jalal where are you.. I saw those horros in my room where are you pls".. Jin shiru yasa ta kara fashewa ta kuka tana nufar cikin dakin.. "Where are you yaya jalal pls come am afraid".. Dif kukanta ya tsaya jin tayi karo da abu ta mugun tsorata dan a zatonta horrs din ne.. Fashewa da kuka tayi da mugun karfi.. "Yaya jalal pls come they are coming toward me wayyo Abba na".. Da sauri jalal da sukayi karo ya kamo hanun ta "ke don't shout its me".. Wani irin rungume sa tayi..ta kankamesa.. "Am afraid I can't sleep alone".. "Shhhh" ya toshe mata maki don't cry its nyt"..  Gyada kai tayi tana sauke ajiyar zuciya.. Yanda ta rungume sa duk da akwai pajamas a jikin sa yasan ba wasu kayan kirki bane.. Kunna hasken dakin yayi.  Tuni haske ya gauraye ko ina.... Yana dan cije lips dinsa yace "sakeni"..... Sakin sa tayi.. Ya matsa daga kusa da ita ya zauna saman sofa yana sauke ajiyar zuciya tare da zuba mata lumsassun idanun sa daga ganinta kasan a mugun tsorace take.. Idanun ta sun wani jike da hawaye lips dinta sunyi wani irin pink she looks damn cute and very young gashin gaban kanta sun wani kwanta.. Bin jikin ta yayi da kallo yanda er light purpls din rigar tayi mugun yi mata kyau ta haska farar fatar ta gabadaya fararen cinyoyin da duk a waje.. Dan lumshe idanun sa yayi he just want to feel her soft skin.. Besan wani irin taushin skin ne da ita ba har ynx he feel her tana kankame dashi.. Dan koda suka rabu wanka yayi ya kwanta amma ya kasa bacci moment dinsu na dazu kawai yake tunawa.. Da kyar ya iya bude baki yace "why are you here". Imaan ta share hawaye snn tace "am afraid".. Camly yace "go back yo ur room".. "Tsoro nake ji wlh".. A dan tsawace yace "I said go back to ur room".. Fashewa tayi da kuka ta nufi kofa.. Jalal ya lumshe idanu kafin yace "come here" dawowa tayi da sauri har tana cin karo da kafar sa . hakan yasa ta fado jikin sa.. Seda jalal yace "ouch".. Ta kalle sa da baby face dinta "am srry. Dont send me out pls wlh tsoro nake ji"... See kuma ta fashe da kuka.. A hankali yace "to ni zan koma dakin ki".. Da sauri tace "I can't sleep alone".. Ya dan lumshe idanu "ohk zaki kwana dani" ta gyada kai.. Ya nuna mata gadonsa.. "Go and sleep".. Tashi tayi ta nufi gadon se kuma ta juyo ta kallesa.."are you sure you're not leaving me".. Gyada mata kai yayi.. Hakan yasa ta hau gadon wanda keda shegen  taushi.. Ta rufa da duvet dinsa kamshinsa me dadi duk ya cikata.. Lumshe idanu tayi.. Dan wlh gani take kamar tafiya zeyi ya barta.. Jalal kau kallon gadon kawai yake.. Shi kade yasan naughty thoughts din dake faruwa a zuciyar sa.. Wlh gaba daya yau ta taso mata da wata muguwar sha'awa.. He is just having crazy feelings for her ko ynx data fado kansa shi kade yasan yanda yaji.. He just feel lyk grabbing her nake and have fun.. "She's ur wife".. Wata zuciyar ta fada.. Besan lokacin da ya fara cire button din rigar sa ba.. Mikewa yayi ya kashe switch din snn ya nufi gadon bude duvet din yayi ya shiga.. Imaan seda ta sauke ajiyar zuciya sbd ta dauka fita zeyi.. Baya ya juya mata yana dan cije lips dinsa.. Se kuma ya juyo yana pacing dinta ta duhun duk da baya ganin ta.. A hankali yace "imaan".. "Uhmm" ta amsa masa.. Ya lumshe idanu snn yace "are you afraid?".. "Uhm".. Ta fada cike da tsoro Allah ya sani she hate horror films.. Jalal ya lumshe idanu kafin yace "ohk come to me".. Kamar jira take ta fara matsawa kusa dashi.. Ya kamo hannun ta tare da sakata a jikin sa ya rungume ta... Duk ajiyar zuciya suka sauke.. Yanajin yanda take boye fuskar ta a kirjin sa.. Ita kam imaam kamshin sa yayi mata dadi ga nake skin dinsa shegen taushi.... Hannu jalal yasa ya kunna bedside lamb din.. Ya bita da kallo ta cikin dan hasken.. He can't believe wai yau shine kwance da mace haka rungume da ita and having feelings for her.... Murya can kasa yace "meyasa kikeji tsoro".. "I don't lyk horrors" ta basa amsa. A hankali ya kai hannun sa saman gaban gashin kanta yana dan shafawa snn yace "don't be afraid am with you ohk".... Gyada masa kai tayi tanajin dadin yanda yake shafa mata gashin.. Dan har wani lumshe idanu take.. Ya kara rungume ta sosai tare da kawo fuskar ta daidai tasa.. Yana kallon cute face dinta tacikin dim light din snn yace "da dadi idan ina shafamaki Gashi".. Gyada masa kai tayi.. Hannun ta ya kamo yana dan murzawa snn yace "nima ki shafa mun".. Ya fada yana daura hannun ta a gashin kansa.. Wani irin taushi taji gashin nada shi hakan yasa ta fara shafa masa.. Har zuwa sajen sa dan wani dadin shafawa takeji suman sa kamar na jarirai.. Shikam jin hannun ta me taushi a kansa yasa ya kara rungume ta sosai.. Tare da saka hannun sa cikin rigar ta da sauri imaan ta tsaya daga shafa kansa tana kallon sa a tsorace.. Maida hannun ta yayi kafin yace continue babu abinda zan maki fa.. Gyada kai tayi tacigaba.. Maida hannun sa yayi cikin rigar ya daura saman flat tummy dinta yana shafawa.. Seda numfashin imaan ya dauke.. Hannun sa wani irin taushi kamar kar ya dena shafa cikin ta haka yakeji.. Shikam jalal ba'a magana.. Ji yake kamar yaje ya fara shafa boobs dinta amma baya so ta masa gardama kamar dazu.. Hade fuskar ta yayi da tasa yana kallon lips dinta.. Itama kallon sa take she just can't wait yayi kissing dinta.. Wlh yanda yake shafa kanta da tummy din ta da kuma sumar sa da take shafawa yasa taji she even want the kiss.. Kawai ji tayi ya daura lips dinsa a nata.. And gently ya fara kissing.. Imaan bata san sanda ta fara mayar masa da martani.. And jalal yaji wani mugun dadi.. Seda sukayi kissing juna for over 10mins seda ya tabbatar duka jikinta ya mutu snn ya cire lips dinsa daga nata yana kallon idanun ta a hankalin yace "imaan" "uhm".. Ta amsa cike da kasala.. Yace "can we enjoy this night".. Shiru imaan tayi..ya kamo hannun ta snn yace "pls imaan lets enjoy this nyt just fun.. Only romance I promise".. Shiru imaan tayi still.. Cikin wata irin murya yace "imaan pls you know you are my wife.. Is not haram.. And you will enjoy it just once imaan only once agreed".. Gyada masa kai kawai tayi.. Jikin jalal har rawa yake ya dauki hannun sa da shafa tummy dinta ya daura akan boobs dinta masu shegen taushi.. Har wata ajiyar zuciya ya sauke numfashin sa na sama sama.. Gently ya fara wasa dasu cike da kwarewa.. Snn a hankali yace "da dadi nacigaba".. Gyada masa kai tayi.. Ya matso da lips dinsa daidai nata in a whisper yace oya kiss me lets have fun and enjoy this nyt.. Kamar jiratake ta daura lips dinta a nata shi kuma ya shig kissing tana mayarr masa.. Ko daya bama tasan tanayi ba because his touches goes. Direct to her brain.. She can't express yanayin da take ciki but she enjoyed it.. Jalal kau dama kamar wanda ya dade yana nema.. Ya rasa wane irin magnet take dashi dan she always turn him on .. Ynx kam dayasame ta yana screaming se yaje kamar he's enjoying the happiest moment of his lyf.. Jin rigar jikin ta na takura masa yasa a hankali cikin dubara ya cire mata ita.. Cos he want it skin to skin.. Imaan kau she's gone to new world har bama tasan meke faruwa ba.. Romance sukayi sosai and they both enjoy it dan duk hankalin su ya gushe.. Seda jalal ya fara neman kofar sa snn imaan ta dawo cikin hayayyacin ta sbd masifar zafin da taji.. Nan ta fara ture sa tana tuna masa alkhawarin daya dauka na just romance .. Amma ina jalal is already gone baya cikin hayyacinsa he just want her he want to go in and feel more fun.. Jin ta a rufe fam yana taso ya shiga ya kasa yasa yaji kamar yayi kuka.. Yanaji tana kuka ta rokon sa amma ina baxe iya jurewa ba.. Be taba tsintar kansa a halin dayake ciki ba.. Karshe de seda ya shiga da karfin tsiya.. Wanda imaan taji azaba kamar zata mutu.. Jalal kam ko daya baya jin ta he's just enjoying the sex.. Wanda be taba sanin haka yake ba.. Be taba sanin haka dadin sex yake dan seda ya manta wace duniya yake... Yau ya yarda da maganar su Labeeb da suka ce girls are joy givers.. Duk da yau ya fara sanin mace amma ya tabbatar cewa imaan is just different.. Dan koda yayi first round kasa hakura yayi.. Wasa wasa seda yayi four round beyi considering  cewa sabuwa ya budeta ba dan seda ya sameta to his satisfaction snn dan duk da yanda yake jin kukan ta kasa hakura yayi.. Se gab da asuba snn ya kyale ta.. Ya janyo ta jikinsa ya rungume ta kakam yana jin wani irin tausayin ta..dan tun tana kuka anajinta har muryar ta disashe... Lokaci daya wani wahallen bacci ya dauke su..

7:30am jalal ya farka.. Binta yayi da kallo ta cikin dan hasken hawaye duk sun bushe a idon ta.. Ji yayi ta basa mugun tausayi.. A hankali ya fara kokarin zare ta daga jikin sa domin yayi sallah.. Ta fashe masa da wani irn kuka tana kara kanname masa.. Bubbuga bayan ta ya farayi kafin a hankali yace "Imaaan".. Jin murya sa yasa ta bude idanun ta da sauri.. Hade idanu sukayi.. Hannun ta tasa da dan sauran karfin ta tafara ture sa.. "Leave me.. And stop touching me Allah ya isa mugu kawai".. Dan sakin ta jalal yayi yana zuba mata idanun sa kamar wani me tsoranta ganin yanda take kuka yasa yace "am srry".. "Don't srry me mugu kawai Allah ya isa wlh bazan yafe ba kuma seka zo ka sakeni na koma kauyen mu".. Dan lumshe idanu jalal yayi kafin ya tashi a hankali ya shiga bathroom wanka yake amma tunane tunane yake he can't believe yau shine yayi having sex.. So dama haka yake da dadi idan su Labeeb suna fada seyaga kamar dadin be kai haka ba amma ya wuce tunanin sa Ashe.. But he thought mata ma sunaso.. Why is she crying.. Maganan labeeb ce ta fado masa na cewa "duk macen da bata san namiji ba dama setasha wahala sbd wanda suka fara having affairs she ze fara bude ta.. Shi kansa be dauka kofar rufe take ruf ba se ynx dan da kyar ya shigi imaan.. That means imaan don't no mens knn.. He don't knw why but samun kansa yayi cikin matsanaicin farin ciki.. A haka yayi wankan harda na tsarki ya fito.. Har lokacin tana cikin blanket din tana kuka.. Kallo daya yayi mata. Ya nufi sallayar sa.. Seda yayi sallah snn ya juyo ya kalleta.. Tashi yayi ya nufe ta.. Tanaji ya hawo gadon ta dago tana kuka sosai "malam don't come to me don't touch me again kayi iya yinka shima Bazan yafe maka ba kuma wlh seka sakeni  na tafi wajen babana mugu kawai" kuka take sosai ko ciwon dayaji mata bekai wanda takeji a zuciyar ta ba she can't believe wnn mugun ne yayi disvirgin dinta.  Taya zata fahimtar da mutane.. Babu wanda fa yasan da auren nan seshi da sageer what if idan Abba ya mutu taya zatayiwa mutane explaining what if idan yazo yace ba matar sa bace bayan ya gama da ita.. Tunda ko yan uwansa da iyayen sa basu san ya aure ta ta.. Snn taya zatacigaba da zama tare dashi yana having affairs da ita daga karshe kuma ya rabu da ita.. Snn taya zata zauna da mutumin da me munanen halayen irin sa wanda ya zabi ya nunawa duniya munanen halayensa akan halayensa na alkhairi.. Yanda take kukan is so touching.. Koshi kansa Jalal be damu da kiransa azzalumi da take ba sema wani tausayin ta da yake ji.. Hakan yasa ya fita da sauri tare da daukar wayar sa dan yanda yaga jini jikin sa yasan yaji mata ciwo he need to do something kafin wani abu ya sami er mutane dan yanda take kukan nan ta mugun rudasa.. Dakin ta ya koma ya zauna tare dialing numbern sageer....

Urs

✨✨✨

Annafie😍*💫💫💖JALAL ALII💖💫💫*



Written by



           *ANNAFIE💖.. ✍️*

     (Smll but mighty😉)



Writer of

*LOVE CYCLE❤️*

*SABODA DUNIYA🌃*

*ADAAN💕*

*JALAL ALI🤩*



Bismillahir rahmanir raheem

💫💖Jalal Ali(23)💖💫💫

Bugu uku sageer ya dauka cikin muryar bacci yace "kai wnn da ina da iyali Allah senayi shari'a da kai dan ka shiga hakki na wnn kira da safe haka".. Dan cije lips dinsa jalal yayi kafin yace "hey bro I need ur help".. Dan shiru sageer yyi jin kamar dan uwan nasa cikin damuwa . "are ohk jalal?".  "Yess but the girl".. Jalal ya fada kamar baya son fadin abinda ke faruwa ... "What about her".  Sageer ya fada cike da damuwa... Jalal da kamar anyi masa dole yace "I deflowered the girl"... Shiru sageer yayi kafin yace "kamar bnji ba de".. Tsaki jalal yaja kafin yace "malam kada ka bata mun rai mana"... Fashewa da dariya sageer yayi snn yace  "yo wane irin bacin rai kuma ka gama angwancewa ina wani bacin rai". Dan murmushi jalal yayi dan gsky sageer ya fada kawai yasan he's happy. Sageer yace "wait tell me how it happens is unbelievable ace jalal har kasan mace wai how jiya jiyan nan ka gama fadamun ko taba ta bazaka karayi ba.. But?"... Fashewa da dariya sageer yayi.. Jalal yayi kasa da murya.. "Pls bro help me wlh naji mata ciwo fa.. And the worst of all se zagi na take". "Wait kana nufin haka kabar er mutane". That's why I called  you kaikuma kana tayimun shirme.. "Ka saka ta tayi wanka I will send a nurse to check on her"..cewar sageer..  Ohk tnx.. Daga haka ya katse wayar dan yasan halin sageer... Tashi yayi ya nufi dakin duk da yanda gaban sa ke faduwa amma ya daure ya shiga.

Gani yayi ta kifa kanta a pillow tana kuka.. Sosai yaji tausayin ta ya kamashi.. A hankali ya karasa kusa da ita.. Kamar jira take ta dago "don't dare you tough me".. "Wait imaan". "Dan Allah kayimun shiru banaso"ta fada tana toshe duka kunnuwan ta.. "You have no words to deceive cos you have already done the worst..kai mugune wlh yes mugune Kawai malam just take me back home wajen babana idan Abba ya samu lpy seya warware auren da ya hada.. Wlh I regret living in the same roof with you..I never thought zalincin ka yakai haka Ka rigada ka cuceni kuma Allah ze sakamun mugu kawai".. Kallon ta kawai jalal yake dan her words are so touching he regrets abinda yayi.. He wish ace ze iya tariyar baya.. Daya goge komai.. .. Duk zaginsa da ake baya damun sa kamar yanda take masa yau.... Kawar da komai yayi ya fara kokarin tashin ta.. Taso tayi gardama amma jin wani masifaffen zafi daga kasan ta ga gabobin jikin ta dake ciwo yasa ta makalkalesa tare da fashewa da kuka.. Sosai JALAL yaji tausayin ta danshi kansa yasan beyi mata da sauki ba.. Cikin bathtube ya shigar da ita bayan ya hada mata ruwa me dan zafi.. Ficewa yayi ya barta domin tayi wanka dan karma ta fara zagin sa.. Yabi bedsheets din daya baci da kallo ganin duk jini.. Dan dafe kansa yayi kafin yace "why jalal why"..... Yaye bedsheet din yayi ya sauya wani snn ya dauki wancan yakai lundary ya saka a washing machine..

Har ya dawo bata fito ba.  Saman kujera ya zauna yana jiran fitowar ta  .. Ko 5mins beyi da zama ba ta fito cikin bethrobe dinsa ta dayi mugun yi mata kyau.. Kallo daya tayi masa ta dauke kai dan wani mugun haushin sa take ji ... Allah a yanda takeji zata iya wankesa da Mari.. Ganin ya nufuta tayi saurin fashewa da kuka cike da haushin sa tace "wlh ka sake tabani bn yafe ba.. And you are taking me back home cos I can't live in the same roof with you . I will not repeat that mistake.. Kade riga ka cuceni kuma se Allah ya saka"..     "Imaaaaaaaa! "... Y katse ta da wata tsawar da seda ta kasa tsayuwa sbd yanda ta tsorata dama gashi jikin babu kwari.. Dan haka tayi luu zata fadi yayi saurin taro ta   ta fado jikin sa.. ya zuba mata jajeyen idanun sa sbd yanda kalamanta ke dukan zuciyarsa  ..  Yana mata wani kallo yace "is it haram dan na kusanceki".. Kasa magana tayi  .. Ya daka mata tsawa "answer me jor".. Ta girgiza masa kai cike da tsoro. Yace "seems lyk kinason kari shiyasa kika fadamun this words that's are not even enough to stop me from having you again and again".. Ta girgiza da sauri ... Yace "sbd na kyale ki tunda kikazo gidan nan shiyasa kike samun daman fadan abubawan dake ranki" kasa magana tayi sbd yanda gaban ta ke mugun faduwa .."da nayi niyar kyale ki but for what you did this morning zan kara and I will see what you can do". Idanun imaan cike da hawaye tace "kayi hakuri baxan kara ba". Wani kallo yayi mata kafin ya zauna da ita saman bed dinsa ya fice daga dakin.. Ita kuma ta kifa kai tacigaba da kuka.. Tasan babu yanda zatayi but jalal ya riga ya gama da ita.. Ya cuceta ya rabata da mutuncin ta kuma ya rigada ya rage mata duk wani daraja  .. Da ace ma wani mutumin kirki ne da sauki da seta fara planing zama dashi amma taya zata zauna da mutum me hali irin jalal.. How.. Tasan ko bata rabu dashi ba seya rabu da ita daya gama samun abinda yake so.. Sosai take kukan tausayin kanta  ... Har Jalal ya shigo rike da cup din tea bata sani ba.. Sosai ta basa tausayi amma dole ya dake dan idan ba haka ba rainasa zatayi ..  Fuska daure ya mika mata cup din da sauri ta karba   kai tsaye yace "shanye duka". Gyada kai tayi da sauri ta fara sha a hankali.. Ya bita da kallo kafin ya nufi kofa jin Ana knocking kofar main entrance... Imaan tabi kofar da harara bayan fitar s snn taci gaba da shan tea din..

Nurse ce tsaye bayan jalal ya bude kofar.. Dan rissinawa tayi "morning sir .. Mr sageer send me to check on a patient". Ba tare dayace komai ba ya bata ha ya ta shigo.. Seda ya rufe kofar snn yace "upstairs the first room by ur right".. Gyada kai tayi ta nufi upstairs ta jinjina aji da kyau kalar na gayen nan.  Ficewa jalal yayi daga gidan gaba daya . sanda nurse din taje har imaan ta shanye tea din tacigaba da wani kukan  .. Jin an bude kofar yasa ta dago da sauri.. Nurse din tayi murmushi kafin tace "hi beautiful".. Ajiyar zuciya imaan t sauke... Tana kallon nurse din.. Murmushi nurse din tayi tana karasawa kusa da imaan snn ta dafa shoulder dinta.. "Hard luck dear dama ko wace mace setayi experiencing haka now tell me da ina ke maki ciwo".. Share hawayen ta imaan tayi bade tace komai ba.. Hakan yasa nurse din ta shiga toilet bayan ta dauki wasu abubuwa daga aid box dinta snn ta shiga bathroom ruwa ta hada mata da me zafi tare da magunguna.. Snn ta fito taimakawa imaan sunka shiga.. Imaan na shiga cikin ruwan fashewa da kuka tayi sbd yanda takejin azaba "srry dear zaki dena ji kinji".. Kai imaan ta gyada mata dan ta fara jin dadin ruwan... Seda tayi mata haka sau uku snn suka fito.. Sosai imaan ta rage jin zafin da take ji.. Sede kanta dake mata wani irin ciwo.. Allura nurse din ta hada tayi mata tym din Jalal ya shigo... Ganin yanda take yamutsa fuska da ana allurar yaso yayi dariya amma ya dake take away din daya kawo mata ya aje a bedside drawer snn ya kalli imaan "how are you feeling".. A hankali tace "fne". Taba forehead din nata yayi jin zafi yasa ya kalli nurse din... "Jikin ta kamar da zazzabi".. Gyada kai tayi "sure amma da anyi allura ze sauka". Be kara cewa komai ba ya fice a daki.. Kallon imaan nurse din tayi snn tace "you got a handsome man ur husband is damn cute" ita de imaan shiru tayi.. "Lyk serious and daga gani ze iya soyayya kuma ze kula da mace see pure love a Idanun sa wlh ki rike mijin ki" ita de imaan shiru kawai tayi dan da tasan wanene jalal da batayi wann Maganar ba.  Rubuta mata magunguna nurse din tayi snn ta mika mata.. "Ya siyo maki wnn wnn and you make sure kina shiga ruwan zafi kamar yanda na nuna maki dazu". Gyada kai kawai imaan tayi dan wani irin bacci take ji.. Nurse din ta maida komai a aid box dinta snn tace "am going see yah." Lumshe idanu kawai imaan tayi tare da daga mata hannu.. A parlor ta iske jalal kallo daya yayi mata ya dauke kansa tare da fadin "how is she".. "She's fne ga drugs da za'a siya mata". Karba yayi.. Duk da yasan sageer yayi crediting dinta amma ya saka hannu a aljihu ya ciro kudi masu. Yawa ya mika mata..ta girgiza kai "mr sageer has already pay me".. "You add with this".. Karba tayi bayan tayi godiya shi kuma ya karbi drugs din da tayi prescribing yana dubawa.. Seda ya gama snn ya nufi stairs yana tunanin plan din da zejewa daddy dashi.. Har imaan tayi bacci daya shiga.. Taba jikin ta yayi har tym din da zafi.. Yaja mata duvet ya rufe ta yana kallon ta dan murmushi yayi ganin yanda take baccin looking so innocent kamar bazata taba iya masifa ba.. Sauya kayan jikin sa yayi tare da daukar key din mota.. Ko minti uku be kara ba ya fice a gidan.. Seda ya fara tsayawa airport yayi booking flightna lagos just for his plan to go smooth as he knws his dad schedule na yau babu wani isashshen tym.. Gida ya wuce.. As usual mama na parlor sema ynx suke breakfast.. Ko kallonta beyi ba ya wuce part din dad dinsa .. Mama ta bisa da wani kallo tana murmushi ciki ciki sbd tana ganin plan dinta is going smooth.. A parlor ya iske dad dinsa se kaiwa da komawa yake.. Jalal na shigowa ya kallesa ransa a bace "jalal where are you from".. Shiru kawai Jalal yayi yana kallon yanda dad dinsa yayi looking so disturb sbd be kwana gida ba. "Am asking you where are you from ka fada mun".  "Am srry dad"... "Will you shout off my frnd.. You knw I will not take this nonsense of rashin kwana gida yes I told you this now tell me where are you from". Zaunawa jalal yayi yana dan lumshe idanun sa ko daya baya son bacin ran dad din sa sbd shi kade garesa.. Yasan dad dinsa ze iya jure komai da ykeyi but not for rashin kwana" dad yabi Dan nasa da kallo kome ake fadin dansa nayi be taba cewa komai ba sbd his son is his weekness bawai abin baya masa ciwo ba amma babu yanda zeyi cos jalal's lyf is sad he need love.. So yasan duk tym din daya fara rashin kwana gida abin ze zama worst gara duk abinda zeji ana fada yazamana dansa a gida ya kwana at least ze samu sauki da ace a waje ze kwana.. Yasan a ynx baze iya hana dansa komai ba but he will give him love tunda ta hakane yake masa biyayya shiyasa no matter how baze bari ya fara kwana a waje ba tunda yaki tsayawa y kula da companies dinsa so gara yasan fitar sa da shigar sa.. Jalal ya bude idanun sa jin dad dinsa yayi shiru.. Yasan the worst abinda ze bata ran dad dinsa shine yaki kwana gida... Ganin daddy ya tsaya kallon sa yasa yace "kayi hakuri Daddy". Zaunawa daddy yayi kusa dashi.." "Tell me ina ka kwana".. Dan furzar da iska yayi snn yace "dad ina gida na I was processing gobe zan tafi lagos zan koma ai".. Kallon dan nasa dad yayi "snn yace are you for real son". Jalal ya danyi murmushi "sure Dad you can call to confirm yau ma zan tafi".. Jalal ya fada dan yasan ko dad ya kira su salim ne and yasan baza'a samu matsala ba he can't live er mutane a gida ita kade so yasan idan ba haka yayiwa dad ba baze taba yarda ya kwana wani waje idan ba gida ba..   Wani farin cikine ya bayyana a fuskar dad yanajin dannasa ya fara shiryuwa but he will call to confirm.. Yace "you mean yau zaka tafi". "Yes dad gobe zanyi rusuming office Inshaallah".. "Good my son I love you".. "I love you too dad".. "Kayi breakfast". Jalal ya girgiza kai.. Sosai yaji tausayin dan nasa waya ya dauka ya kira granny a kawo masu breakfast sanin Jalal baze tabacin na mama ba   he don't knw why wnn tsanar dayayi mata bayan ita kuma tana Sonsa sede babu yanda zeyi son dan nasa ya rufe masa idanu..

Anan aka kawo breakfast din sukayi tare sukayi fira har tym din tafiyar dad office yayi... Sukayi sallama shima yaje yayi wanka....

Koda jalal ya koma gidan be samu imaan dakin sa ba kuma ta dauke take away din daya kawomata.. Dakin ta ya nufa rike da wani take away din.  Koda yaje bata dakin yade ji karar ruwa a bathroom ya sauke idonsa akan abincin data cinye tass.. Dan murmushi yayi ya aje na hannun sa snn ya fice.. Koda ta fito taga wani take away din seta murguda baki.. "Dama ba dole ka kawo ba tunda kasan dole naji yunwa.. A haka ta gama shirin ta tanaji ranta duk a bace. ... Seda ta gama tsaf snn ta sake kwanciya wani sabon baccin.. Jalal kam na kasa aikin sa kawai yake a system lokaci lokaci yakan kalli sama.. Yana dawowa sallahr la'asar ya kira dad dinsa ya fada masa cewa jirginsu se tashi sbd seda ya daidaici tym din da jirgin ze tashi ya kira in case koze tambaya.. Addua sosai dad yayi masa snn sukayi sallama.. Koda ya shigo gidan dakin imaan ya wuce to check on her.. Bacci ya sameta tanayi.. Ya taba jikin ta jin zazzabin ya sauka yasa ya fara tashinta domin tayi Sallah.. Tana ganin shine ta tashi zaune da sauri har batasan tym din da bakin ta yace "don't touch me".. Yanda tayi din kade ya gane a tsorace take dashi.. Yana kallon ta da kyau yace idan na taba ki me zakiyi".. Kamar zatayi kuka tace "bnd lpy fa".. Ya dage gira "really.. To idan kinji sauki fa.. Fashewa tayi da kuka but since day before yesterday you promised babu abinda ze shiga tsakanin mu".. Hana kansa dariya yayi yace "mene ya shiga tsakanin mu".. Fashewa tayi da kuka sosai hakan yasa ya mike da sauri.. Tashi kije kiyi sallah kar ki koma bacci kuma yamma tayi".. Gyada kai tayi tana sauke ajiyar zuciya.... Seda ya fita sannan ta tashi tayi Sallah har tym din jikin ta ciwo yake mata tana so ta sake kwanciya bacci amma taki.. Sede ta dauki Quran ta fara karantawa ta dade tanayi snn ta farayiwa abbanta addua akan Allah ya basa lpy yazo sukoma gida tabar gidan wnn mugun.. Seda ta gama snn ta dauki wayar ta suka fara chat dasu maryam.. Tayi mugun missing dinsu har ta kosa su koma sch se tambayar ta mommy suke.. Wnn ne ya saka ta kuka tayi sosai kuma.. Sometimes mommy tafi tsaya mata rai akan abba but idan ta tuna abba ne yace ta tafi karta dawo ynx setaji sanyi.. A haka har akayi magarib.. Tana cikin Sallah isha'i ya kawo mata dinner ya fice.. Tana gamawa kuwa ko kallon abincin batayi ba ta kwanta duk da yanda take jin tsoro haka ta kudundune da kwanta da bazata Kara gigin zuwa dakin sa ba... A haka bacci ya dauke ta...

Koda tayi Sallahn asbah wani baccin ta koma.  Bata tashi ba se 10 wani yunwa ne ya tashe ta.. Bathroom ta shiga tayi wanka yaukau taji kwarin jikin ta kawai ranta ne a bace idan ta tuna cewa ta tashi matsayin budurwa.. Mijin tane yayi deflowering dinta amma mijin wucin gadi a bad boy da kowa ke tsoro.. Wnn abun ne ya tsaya mata a rai.. Seda ta gama shiryawa tsab snn ta fito.. A parlor ta gansa zaune yana danna wayar sa kallo daya tayi masa ta dauke kai kamar yanda shima tun daga kallo daya be karayi mata ba.. Ta shiga kitchen tace "Allah ya isa mugu".. Breakfast ta fara hadawa iya cikin ta seda ta gama tsab snn ta zuba ta fito.. Ko kallon sa batayi ba kamar yanda shima be kalletaba seda ta wuce ya dago yana kallon ta har ta shige.. Jingina yayi da kujera yana lumshe idanu.. "He just can't believe yayi having affairs da ita". Ya cije lips dinsa yana tuno ranar daya fara ganin ta ranar ganin farko ya dauka er iska ce.. Se kuma ta koma smart gal , stubborn gal   da suka labeeb suka tare su ranar data fara yi masa magana ya ara mata waya tace kuma zata sace masu taya.. Ranar da suka fara fada har ya tafi da jotter dinta., ranar da ta sace masa tire, ranar da suka hadu a bikin bikin gidan.. Hannunta daya fara rikewa their first kiss, kiss na biyu.. And ynx kamar a mafarki ta zama matar sa   and the best of all yau sunyi having affairs shine ya maidata mace.. He wish ace ya kara but baze taba bari zuciyar sa ta yaudaresa ba.. He knws baze karya ba yana da much feelings akan ta dan kamar tanada wani magnet da yake mugun jan sa gareta but baze kara yarda wani abu ya kara shiga tsakanin su ba ze daure no matter how har Abbanta ya samu lpy ya sawake mata

Urs

✨✨✨

Annafie😍😍*💫💫💖JALAL ALII💖💫💫*



Written by



           *ANNAFIE💖.. ✍️*

     (Smll but mighty😉)



Writer of

*LOVE CYCLE❤️*

*SABODA DUNIYA🌃*

*ADAAN💕*

*JALAL ALI🤩*



Bismillahir rahmanir raheem

NOT EDITED

💫💖Jalal Ali(24)💖💫💫

Kamar yanda jalal ya dauki alkhawarin koda wasa baze kara yin wani abu daze wani kuskure wanda se kusantasu ba.. Hakan ta kasance dan ko kallo bata ma ishesa ba kamar yanda itama ko daga kai batayi ta kallesa magana ma bata hadasu yes suna haduwa kamar a parlor ko zataje kitchen amma ko daya babu mece wa wani ci kanka kowa gida daya suke rayuwa amma kowa harkan gabansa yake.. Sosai imaan taji dadin yanda ya rabu da ita hakan yasa ta fara tunanin kila mistakes ne amma idan ta tuna ya rabata da mutuncin ta se ranta ya baci wani zubin ma seta zauna tasha kuka.. Duk a rayuwar su tana kula dashi baya wasa da sallah snn duk wani abu daya jibanci addini Jalal yanayi sede he drink yes jalal is a drunker cos yasha dawowa gida a buge hakan yasa ta yarda ta duka munanen halayensa da ake yadawa a social media she wonder meyasa mutum irin wnn wanda ko wasa da sallah bayayi yake da kalar wnn halayen and be taba denying ba kamar yanda take gani a social media ma amsawa yake eh yayi kuma ayi shiru ba'a cewa komai sbd kudin babansa she want see dis his father da ko kadan baya damuwa da hali irin na dannasa and yes ta kara tabbatarwa babansa na daure masa kugu tunda gashi ko gida baya kwana tare suke kwana ma babu abinda yayi.. The worst lalacewar da ai harda rashin kwana gida.. She can't believe itace ke rayuwa da me irin halayen nan but one thing data fahimta is kamar yana  cikin damuwa tunda idan yana gida kullum cikin danna system yake kokuma ya kwanta ya lumshe idanu kamar me bacci kallo ma be cikayi ba.. Sometimes setaji kamar ta tambayesa amma babu fuska.. Itama bazatayi attempting ba sbd bama taso su fara cigaba da magana har a samu wata matsalar.. Besides shirin ta na makaranta ma take dama Abba ya biya kudin semestern nan tasan tana da kudi a account din da zasu isheta  har a gama semestern nan sede bata san wane ze biya mata wanda zataje canada ta karashe 1yr dinta ba inde har abba be samu lpy ba but she's hoping yasamu lpy soon she really miss him da kuma mommy gidan nan jinta take duk a takure take shiyasa ta kosa ta koma sch wlh...

Jalal kam duk wani zancen imaan ya ajesa gefe aikin gabansa kawai yake musamman ta hanyar da ze kama manga cikin sauki daya shigo kasar bangaren Abba ma yana iya kokarinsa na ganin ya samu lpy haka sageer ma yana basa goyon ba dari bisa dari...

Duk tunanin daddy jalal yana Lagos shiyasa koda yaushe cikin waya suke ya fada masa ya aiki.. Bayan kira en can ya tambaye su game da JALAL sunce yanacan kuma yana aiki sosai.. Daddy sosai yake farin ciki.. Mama ko daya bata yarda cewa JALAL na lagos ba tasan yana cikin garin abuja duk da bata san takamaimai a ina ba.. Amma tasan yana ciki.. Duk tunanin ta plan dinta ne ya fara aiki.. Shiyasa kwana biyu cikin farin ciki take lokaci kawai take jira ta gano inda yake ta tona masa asiri wanda se uban nasa ya tsanesa...

Imaan ce ta ce saukowa daga stairs amma idon ta nakan JALAL dake kwance saman kujera ya lumshe idanu wanda ta tabbatar ba bacci yake ba.. Kuma tunda ya dawo sallahr azahar yake nan gashi har la'asar ta kusa.. Dauke kantan tayi ta wuce kitchen domin dafa abinda zata sakawa cikin ta.. Cikin kankanin lokaci ta dafa abu me sauki snn tazubo a plate ta fito still yana wajen har imaan ta wucesa se kuma ta dawo.. A hankali tace "are you okey".. Ko bude idonsa beyi ba bare ta saka ran amsa.. Sanin idon sa biyu yasa tace "Yaya Jalal".. Dan bude idon sa yayi ya yakalle ta tare da gade gira alamar "what?".. "Baka da lpy ne" ta fada gabanta ba faduwa ganin irin kallon da yake mata.. Maida idanun sa yayi ya rufe ba tare dayace komai ba.. That's what make imaan regrets talking to him ta murguda baki ta juya zata tafi yace "come back".. Cak ta tsaya gabanta na faduwa.. Kafin ta juyo tana duban sa...  Jalal ya tashi zaune ba tare daya kalle ta ba yace "wa kikewa murgude".. Kamar zatayi kuka tace "nifa bada kai nake ba".. Ya dago kansa ya kalleta ganin kamar zatayi kuka yasa yace "yaushe zaki koma sch".. Dan ajiyar zuciya ta sauke kafin tace "jibi".. Gyara zaman sa yayi kafin ya dauki remote ya fara canza channels yace "kiyi Sallah mu fita".. Kallon sa tayi ganin ba ita yake kallo ba tace "ohk".. Snn ta tashi ya bita da kallo har ta bace ma ganin sa.. Hakanan imaan taji dadin wnn fitar da zasuyi seda tayi wanka snn tayo alwala.. Tsab ta gaba shirin ta cikin daya daga cikin dogayen rigunan daya siya mata.. Ko kwalliya batayi ba amma tayi kyau sosai sbd yanda natural beuty dinta ya fito... Koda ta fito parlor baya nan dan haka ta zauna zaman jiran sa... Tafi minti biyar kafin ta fara jiyo kamshin turaren sa dan daga kai tayi tana kallon sa.. Manyan kayane jikin sa amma be saka hula ba.. Ta kula baya son saka hula kodan yaga sumar sa nada kyau oho kuma kyau yake sosai.. "Kallon fa" muryar sa ta katse mata tunani dauke kai tana tura baki.. Ko kallon ta beyi ba ya wuce.. Itama bayan sa tabi tana tura baki.. Wani mota ne daban suka shiga sabanin wanda ta sani.. Tarasa shikam motoci nawa garesa kuma tunda suka zo bata yayi amfani da mota me sunan Deen ba... Babu wanda yace da wani komai har seda suka iso wajen wani babban wajen saloon snn ta dago kamar zatayi kuka tace "nifa kaina beyi komai ba" dan mugun tsoro takeji a taba mata rabon data gyara sa har ta manta.. Kula da yanda ta tsoratan ne yasa yace "karki bari na rigaki fita".. Tuni hawaye sun cika idon imaan ta rasa mene hadin sa da gashin ta.. Gashi bata ga fuskar yi masa rashin kunya ba a kwana biyun nan wani tsoran sa takeji bana wasa.. Budewa tayi ta fita daidai lokacin da JALAL ya zagayo..Kamar bega hawayen idon ta ba yace muje.. Haka ta bisa tanajin kamar ta ruga ta shige mota.. Wajen ya kayatu sosai.. Akwai layi dan haka seya bukaci akaita VIP. Mutum daya ce a wajen kallo daya imaan tayi wa wacce za'ayiwa ta gane ta.. Itace tasoyiwa JALAL magana har imaan ta fadi a ranar..shikam JAlal bema gane taba duk da yanda take kallonsa.. Yayi wa wacce zatayi saloon din magana "zaki dauki tym ne before ki gama mata"... Kafin me saloon din tayi magana wacce tace "you shouldn't mind a fara yi maku kawai.." Kallo daya yayi mata snn yace "ohk tnx" snn ya juya ga imaan dake ta wani hade rai yace "madam kije aiyi maki".. Zuwa tayi ta zauna ba tare data kalli waccan ba.. Sbd wnn beb din dake wajen yasa imaan ko kuka batayi ba dukkuwa da irin zafin da take ji.. Amma daga gani kasan dauriya take.. Jalal was even wondering ko ya akai haka.. Yayin da waccan beb din ke kallon JALAL kamar ta hadiyesa.. Imaan kau lokaci lokaci take sakar wa waccan harara.. Har aka gama imaan batayi ko digon hawaye ba.. Ganin an gama batayi kuka ba yasa yace "har an gama" hakan yasa beb din maido da kanta ga imaan.. Masha Allah ta fada duk da tasan tana da kyau imaan ta fita ga gashi.. Tasan inde JALAL na tare da imaan he will not even look at.her. sbd bata son jalal ya tafi bata san sanda tace "ayi mata kitso mana".. Wani kallo imaan tayi mata sede kafin tayi magana Jalal yace "eh ayi mata" to dama zuciyar imaan a kusa take kiris take jira dama.. Se kawai ta fashe masu kuka.... Dan cije lips jalal yayi dan dama yana mamkin dauriyar.. Beb din tace "oh god srry ki bari ayi maki ko ibra ne mana" noke kafada tayi tana hararrar ta.jalal ya kalli me saloon din yace "do it for her".. Sosai imaan ke hawaye ita baza'ayi mata ba.. Seda me saloon din tace.. "Sir you have to do something cos I don't think zata natsu ta bari ayi me kyau".. Jalal ya taso daga kujerar da yake ya dawo kusa da ita ya zauna yana kallon ta.. Yace "babu zafi ki bari ayi".. Gyada kai tyi still tana hawaye.. Har aka gama tsaga batayi motsi ba.. Sede ana farawa ta fashe da kuka.. A hankali Jalal ya kamo hanun ta cikin nasa yana dan murzawa "srry bazakiji zafi ba".. Gyada kai tayi tana sauke ajiyar zuciya.. Haka akai tayin kitson yana murza mata hannu.. Sosai suka birge me saloon din yayin da  beb din ke zaune tana kallon su she just wish ace itace can take kuka ana mata kitso while jalal na gefe yana murza mata hannu... Ibra akayi mata masu kyau brush din ya wani kwanta sosai kitson ya mata kyau duk da shukkune amma kitson har gadon bayan ta.. Atm dinsa ya bata ta ciri iya kudin ta.. Snn yazo kama ya hannun imaan data maida veil dinta.. Har zasu tafi se ya juyo yana kallon beb din yace "thank you".. Murmushi tayi ta kalli imaan.. "Cry cry lady till we meet next tym am jiddah" murmushi kawai imaan ta kakalo  amma bata ce komai  ba.. Daga haka suka fita.. Seda suka shiga mota snn tace "Allah ba'a kara mun kitso".. Kallon ta yayi snn yace "kila de koma zamuyi su kwance suyi maki sabo".. Fashewa imaan tayi da kuka "ni ai bada kai nake ba".. Murmushi yayi snn ya fara driving.. Wajen siyen su chocolates sukaje sbd yanayin ta yasa ya shiga shi kade chocolates ya siya masu yawa ya kawo motan snn ya shigo.. Seda suka fara tafiya snn yace.. Zanyi maki transfer a account din wancan ATM dake hannun ki kome zaki bukata kibama su yusrah su siyo  .. Ba tare data kallesa ba tace "nima ai zan iya siya da kaina".. Ba tare daya kalleta ba yace "don't try that yes don't try that".. Shiru tayi batace komai ba.. Har suka isa gida.. Shine ya shigo mata dq ledan chocolates din masu uban yawa har daki.....

Washe gari ta shirya duk abinda zata bukata ko haduwa ma basuyi ba taje ji shigar sa da fitar sa...

Ranar da zata koma tana parlor tana breakfast ya fito sanye da jallabiya kallo daya kawai tayi masa kamar yanda shima be kalleta ba ya bude system dinsa yana dan dannawa  sun dan jima a haka kafin ya dago dede idama ta dago suka hada ido ya dauke kansa zuwa ga system din kafin yace "ke baki iya gaisuwa ba ko".. Tura baki tayi tana dan kukunai.. Dagowa yayi ya kalleta.. Ware idanu tayi kafin ma yayi magana tace "nifa bnce komai ba" "zo" ya fada yana kallon ta.. Tashi tayi a hankali ita ynx wani shakkar sa take ji kodan tsare idan da yake oho.. "Gani tace "bayan ta karasa kusa dashi" kallon kanta dake bude yayi yace "shi wnn kan ba'a rufesa".. "Zafi nake ji".. Ta fada a hankali yace "saura kije sch din ki rinka barin kai bude".. Shiru tayi batace komai ba.. Ya maida hankalin sa ga system snn yace by what tym zaki tafi".. "4".. Girgiza kai yayi kawai kafin yace "ohk you can go".. Juyawa tayi har zata haye sama tace "na zubo maka breakfast?"..jalal ya tabe baki  "yau kuma ci kayanki".. Itama tabe bakin tayi ta haye sama....

Wajen 4:30 suka baro gidan seda ya biya da ita wajen me nama ya siyamata meyawa both tsire da kilishi da balango snn suka wuce makarantar.. Hakanan imaan taji wnn karon har son komawa sch take dan gidan can jinsa take kamar prison.. A daidai bakin gate dinsu yayi parking  imaan ta fara kokarin budewa tafita dan tasan su yusrah sun dawo.. Ji tayi ya riko hannun ta ta juyo ta kallesa da sauri.. Shiga kallon ta yake tayi kasa da idon ta.. "Let me remind you this koda ki manta.." Ya fada still yana kallon ta.. Imaan taki dagowa ta kallesa... Yace "yes just be careful.. Yeah i 've to tell you this sbd akwai igiyoyina akan ki kome kikeso su maryam su siya maki or you called me idan ma baki sanar dani ba I will knw am I clear".. Gyada masa kai kawai tayi.. Sakin ta yayi ta fita.. Ta bude back seat ta fito da kayanta almajiri ta saka ya shigar mata dasu ko bi takan Jalal bata sakeyi ba ta shige ciki.. Seda ta shiga snn JALAL yayi reverse ya koma gida...

Yanda su imaan suka rungume juna ita dasu yusrah kasan sunyi missing juna.. Baby jimawa su faruq ma suka dawo.. Duk da suna chat amma kamar wadan da suka shekara basu ga juna ba.. Tuni kowa ya fito da tsarabar sa sukaci naci suka bar na bari... A ranar sun so fita yawon shirmen su da suka saba na farkon dawowa amma sbd yanda imaan ta nace bata zuwa dole su duka suka hakura.. Faruq yace may be bataso samarin ta susan ta dawo karda su farayi mana layi a kofar gida.. Ita de kam murmushi kawai tayi... Washe gari koda zasuje siyayayya kin binsu tayi har hakan yaso basu mamki.. Se masifa suke mata amma tayi biris dasu.. Yusrah tace "ke bamu son iskanci taya zaki nade a kan gado mune ma zamu fita maki siyayyar".. Imaan ta tabe baki "sede fa kuyi tunda nace maku kaina na ciwo ai seku barni kuma kuna ganin ga sanyi bayan kunsan yanda nake da saurin mura".. Maryam na hararar ta tace "yo ke murar ki har wani se kin fita kede kawai ki fadi dalilin rashin zuwan ki".. Banza kawai tayi dasu.. Haka suka gama balbalin bala'in su suka tafi.. Tayi murmushi kawai tayi kwanciyar ta...

Kasancewar wnn semestern ta karshece yasa basuyi wani shirme ba sosai suka maida hankali suna karatu duk da suna da sauran shekara daya da zasuyi finally amma karatun duk anan yake can duk practice ne da sauran su... Su yusrah sunyi mamkin canzawar imaan bawai tazama miskila bane aa.. Kodaya bata fita daga sch se gida duk fitar da zasuyi bata taba bin su sede suyi masifar su barta sun kasa gane dalilin sauyawar ta tunda suka dawo imaan bata fita ba.. Samarin ta sede suzo su gama zaman su a kofar gida amma amma bata fita idan sunyi magana se tace sanyi..

Ranar imaan na kudundune cikin bargo ranar ko sch bata je ba sbd murar da take tana cikin game a wayar ta maryam ta shigo.. Daidai tayi wata atishawa knn maryam tace "uhm duk kumewa a dakin dakike sede da murar ta biyo ki Allah wulakanci da kike wnn karon yayi yawa sede mutane suzo wajenki amma ki wulakanta su".  Tabe baki imaan tayi kafin tace "Akwai wanda na kira ne" maryam tace "kinga nide ba wnn ba.. Akwai birthday din latifa yau dan Allah karkice baki zuwa".. Imaan zatayi magana maryam ta kama hannun ta, "kinga de yanda muke da latifa.. Kuma ba wani gayya zatayi ba sabon wajen ba'a dade da budesa ba babu hayaniya se yaran manya ke zuwa wajen kuma wajen very silent nida ita mukaje duba wajen kuma babu maza ko a matan ma imu imu ne mu 12 ne se ita 13..".. Imaan sosai take so ta fita tayi missing dan yawon nan at least just for today let her just enjoy.. Dan langwabar da kai tayi tace "amma kinga mura nake ko".. Maryam tace "akwai tea wlh idan kinsha zaki ji saukin murar nan".. Imaan ta gyada kai "ohk zani".. Rungume ta maryam tayi "yauwa love wlh I really miss fita da se ki shirya da anyi isha'i.. Gyada kai imaan tayi tana murmushi kawai she can't wait yau ta fita.. To an kwana biyu.. Yusrah ce ta shigo tana hararar imaan "ai shiyasa na turo maki maryam dan kin san ni ba iya lallabaki zanyi ba sede muyi baran baran".. Murguda baki imaan tayi ta koma tacigaba da game dinta... Tsaf imaan ta gama shirin ta tayi wani mugun kyau Allah idan ka ganta kamar ka sace seda ta gama tsab snn ta zauna gaban ta nadan faduwa gani take kamar jalal ze san ta fita.. Se kuma ta tabe baki to sema ma idan ya sani ai ba auren azo a gani bane atleast let her enjoy just for today da tana da niyar kiran sa amma ta fasa.. Tissue dinta ta dauka da wayar ta ta fito parlor su maryam suna zaune tare da wasu kawayen su.. Rungumeta su yusrah tayi.. "Wow my beautiful angel Allah baki ga yanda nake missing fita outing dake ba".. Murmushi kawai imaan tayi.. Motar faruq suka amsa maryam tayi driving dinsu zuwa can..

Wajen ya hadu babu karya ga wajen yanayin tsarin wajen kansa abin birjewa ne ya tsirarrun mutane ne kawai a wajen  wasu zaka ga budurwa da saurayi wasu mata wasu maza babu ruwan wani da wani classic bebs and guys ne kawai a wajen ga wata cool music dake tashi a wajen..

Inda zasuyi birthday din an tsarashi sosai kawai harkar cima za'ayi da hotuna se a yanka cake a danyi nishadi a tafi.. Ita kanta imaan seda taji dadin fitowar ta dan wajen kade abin kallo ne.. Koda aka fara imaan seda ta bukaci tea me citta sbd murar da take ko muryar  ta ka kaji zaka gane... Sosai hankali mutane yayo kansa sbd yanda tsarin nasu ya kayatar gasu duk mata.... Imaan najin idanu wasu guys a kanta amma ta wani faske.. Ana gama yanka cake yusrah ta tabo imaan tana mata rada "kefa tawan bade kasuwa ba kinga yanda wasu hot can suka zura maki na mujiya".. Murmushi kawai imaan tayi ta dauke kai... Ko 1mins ba'ayi ba kunnen ta ya fara jiyo mata karar wani bike ita kanta karar wani irin taushi ne da ita wanda da kaji kasan ba kananun kudi zasu siye sa ba.. A hankali wata daga cikin su ta furta wow.. Hakan yaja dukkan hankalinsu kan JALAL  daya wuce ta gaban su cikin wani ubansu dressing daya dace da bike yanda sumar kansa tasha gyara ba'a magana ya toshe idanun sa da wani black spec baka ganin idanun sa se wel shape lips dinsa da sukayi wani pink.. Ba su kade ba kowa a wajen seda kallo ya koma kansa.. Tuni su yusrah suka gane sa da sauri ta tabo maryam.. "Ke yayan sumy oh dis guy is very hot very handsome".. Imaan kam daskarewa tayi Allah ji take kamar a leda take zaune tama kasa dauke idon ta daga kansa.. Se ynx ta fara regretting fitowarta.. Duk yanda zuciyar ta ke kokarin daurewa kasawa tayi... Akan idon ta ya sauka daga bike din ya fara tafiya.. Duk takun takarminsa daya har zuciyar ta takeji.. Dan tafiya yake daidai da bugun zuciyar ta.. Tana kallonsa har yaje ya zauna.. Ko dagowa beyi ba idon sa akan wayar sa.. Tanajin yanda su maryam da sauran keta maganar sa amma t kasa cewa kala.. Har aka kawo masa abinda yayi order imaan kallonsa tke.. Yakai kusan 5mins kafin ya dauki stick meat yakai bakin sa.. Yayi yaci kadan snn ya dago ya zuba duka idanun sa dake cikin glass din akan imaan yana dan tauna naman a hankali.. Yanda baka ganin idanun sa da yanda yke taunar naman da yanda lips dinsa ke motsawa seya kara masa wani kyau.. Imaan ji tayi kamar zata fadi a kujerar datake ganin yanda yake kallon ta ko dar babu idanun sa duk da acikin glass ne direct akanta suke....

Urs

✨✨✨

Annafie😍😍*💫💫💖JALAL ALII💖💫💫*



Written by



           *ANNAFIE💖.. ✍️*

     (Smll but mighty😉)



Writer of

*LOVE CYCLE❤️*

*SABODA DUNIYA🌃*

*ADAAN💕*

*JALAL ALI🤩*



Bismillahir rahmanir raheem

💫💖Jalal Ali(26)💖💫💫

Da kyar imaan ta shiga ba tare data gama shirya abinda zata fada masu ba... Maryam kade ta iske a parlor tana ganin ta ta wani mike "imaan" murmushi ta kakalo kafin tace wani abu yusrah ta fito daga kitchen itama kallon imaan din ta. Tsaya yi.. Maryam tace "ina kikaje duk kin tashi hankalin mu numbern ki bata shiga haka ma mommy".. Kafin imaan tayi magana yusrah tace "da ido na naga kin shiga wata mota snn na kiraki baki picking ba at the end ma you switch off ur phone".  Sosai gaban imaan ya fadi dan karyar ta ta riga  ta gama karewa tunda yusrah ta ganta... Ita kanta maryam da mmki take kallon yusrah dan bata fada mata haka ba.. Ganin yanda duk suke kallon ta yasa ta zauna tanajin wani kuka.. Yusrahh tace "imaan nasan halin ki ba tun yau ba and I don't want to think different akanki sede imaan I have to ask ina. Kikaje for almost 4dys.. At least koma ina ne yakamata ki fada mana ko hankalin mu ya kwanta..... Maryam da tun dazu ta kasa magana ta dawo kusa da imaan ta zauna tace "imaan dan Allah kina ina tsawon kwanakin nan".. Fashewa imaan tayi da kuka kamata yayi su yusrah su san wnn zancen sbd ynx sunfi karfin frnds a wajen ta.. Yusrah ta dawo kusa da ita ta rungumeta ba tun yau ba ta fahimci kawartata na cikin damuwa ba.. Maryam ma kukan ta fara "dan Allah imaan ki fada mana wani abu ya farune".. Share hawayen tayi. Ta fara basu lvrin tun daga ranar da suka hadu a gidan su jalal.. Bata fadi kiss din daya shiga tsakanin su snn ta boye masu cewa shine Jalal Ali dan bata san yanda zasu dauki abun ba.. Babu abinda ta boye masu har yanda aurensu ya kasance rashin lpyr Abba rayuwar su da JALAL har first nyt dinsu duk ta fada haduwar da sukayi a wajen birthday dalilin dayasa yaita kallonta rashin fitar da take har de zuwa yau.. Sosai sukayi kuka kuma sun tausayawa imaan.. Maryam tace "but meyasa baki fada mana ba ai da munyi masa addua" yusrah ta share hawayen ta snn tace "Inshaallah zamu rinka yi masu addua kuma ko suwane se asirin su ze tuno mun riga mun zama yan uwa abinda ya shafeki ya shafe mu pls karki kara boye mana komai shima Allah ya saka masa da alkhairi.." Sosai suka shiga kwantar mana da hankali har seda ta dan sake suka zubo abinci sukaci.. Seda suka gama yusrah tace "so the cute guy".. Tayi maganar tana kallon imaan.. Dariya maryam tayi.. "Ashe ranar gulmar mijin wata muke bamu sani ba".  Ware hannuwa imaan tayi "ai da abba ya samu lpy za'a raba auren".. Wani kallo suka mata.. Maryam tace "baki da hankali taya zaki samu miji kalar wnn ki rinka wasa dashi.. Dama da. Iri su kika dace".. Yusrah tace "dallah rabu da ita zama ynx kika fara bayan ya riga yasha romo ai zama daram wlh na samu miji kalar wnn ina makale da abuna sch din ma day zanyi".. Duk dariya suka yusrah ta kamo hannun ta "ke wlh koda wasa karki sake dashi ga kudi ga kyau snn ya kula da ke da kuma Abba to me kuma kikeso kina tunanin zaki samu kamar sane ".. Maryam ta yi buda "ai dole muzo mu sake gyaran amarya tab.. Irin wnn kanayin sake ake kwace makasu.. Wow.. Shiyasa indan muna yabonsa imaan take bris damu ashe ita harta mallakesa amma ta maida mu banzaye can you imagine se ynx na kula jiya kallon love kawai yake mata yazo yayi garding kayar sa dan kaf gurin ita kade ya kalla oh wow". Ita de imaan murmushi kawai kawai take tasan da zasu san wane JALAL din nan da duk maganar nan basuyinta.. Yusrah ta tabo "so ya weekend din".. Ta fada tana wani kashe idanu.. Dauke kai imaan tayi ta tashi ta shige ta barsu da mmkk cike da ciki .. Da daddare bayan sun gama karatu.. Maryam tace "hope de kin kirasa kinji ya jikinsa".. . tabe baki imaan tayi "keni fa ba wani shiri muke ba".. "Baki da hankali wlh to baki isaba kinga duk jin kansa da kike fada da wanda muma muka sheda seya sauke you're even deceiving ur self da kike fadin ze sakeki taya ze samu mace kamar ki ya saki.. Sede idyan ke kika bata komai".. Ita de kallon su kawai take tasan da sun san wane JALAL duk wnn maganar ma bazata tashi ba...

Hakanan imaan taji kamar ta kirasa amma wata zuciyar seta gargade ta.. Haka de tayi baccin ta ba tare data kira ba... Washe gashi wajen 11 suka fito daga test din suka dawo gida wanka kaya kawai ta sauya ta kwanta su yusrah kuma suka fita..tana kwance JALAL ya fado mata  a ranta tace "ko ya jikinsa".. "Ki kira mana".. Wayar ta ta dauka tanajin ta kira ko karta kira can kawai tayi dialing.. Amma harta gama ringing ba'a dauka ba.. Tura baki tayi zata fara kukune kira ya shigo.. Ta hadiye maganr ta gabanta nadan faduwa.. Seda ta kusa katsewa snn ta dauka.. "Hello".. Daga can cikin muryar sa me cike da mura yace "uhm what?..".  Tura baki imaan tayi kafin tace "ya jiki"... Jalal ya gyara kwanciyar sa mura duk ta hanasa sakewa snn yace "se ynx".. Dan langwabar takai tayi kamar yana kallon ta tace "I'm srry".. Ya lumshe idanu "ya test din".. "Alhmdllh kayi breakfast".. "Nop bnyi ba".. Da damuwa tace "why".. "Zanyi ynx amma". Se kuma yayi shiru tace "Amma mene"... "How I wish zan samu that pepper soup and tea".. "I can prepare it for you but how can you get it".. "I can drive my self to ur place".. "Are you sure".. "Yeah".. Ya bata amsa tace "by what tym. Zaka zo". "After isha'i Inshaallah"... "To me zakaci ynx"... Ya tabe baki. "I will fne something light".. "Alright sekazo" "bye".. Daga haka sukayi sallama.. Su maryam ta kira tace "su siyo nama da yawa da kuma duk abinda tasan zata bukata....

Su maryam suka taya ta tayi masa lafiyayyen farfesu da kuma white rice and stew da kuma tea me yaji..... Wajen karfe takwas da rabi ya tura mata message "ina waje".. Tura baki imaan tayi tana kallon su yusrah da suka zubo mata idanu dama tun dazu suke tsokanar ta tuni suka fashe is ta dariya.. Ta dauki hijab dinta tare da basket din ta fita.. Kanta kasa ta fita a gate tana tafiya kamar tasan inda yayi parking.. Message ne ya shigo wayar ta tana dubawa tata shine "ke kuma ina zuwa".. Dan murmushi tayi a hankali ta dago hasken motar taga ya kunna hakan yasa ta nufi can a hankali.. Front seat ta bude ta shiga.. Yana zaune a driver seat da wata katuwar rigar sanyin tayi mugun yi masa kyau seda imaan ta lumshe idanu sbd wani kamshi dake tashi a motar.. Dan kallon sa tayi ganin yanda yake ta struggling da numfashi.. Tace "sannu"..kallon ta yayi kafin yace "ai kin kyauta".. Ta ware idanu "me na yi".. "Still yana kallon ta yace "wane ya gogamun murar?" Murmushi imaan tayi snn tace "bnd sheri". Ya dage gira daya snn sauke idon sa akan basket din "nan fa duk menene". Ta dage kafada "idan kaje zaka gani".. "Uhm idan munje de".. Daga hka yayi wa motar key suka fara tafiya.. A tsorace imaan tace "ina zaka kaini".. Kallon ta yayi kafin ya maida hankalin sa ga driving.. "Kinsan satar mutane nake".. Dauke kai imaan tayi tana dan kukune "naga de wnn kaide ka dauko ni daga inda nake".. "Uhm se kuma naga nine da dauko kafafunki na kawo cikin motar ko".. Murguda baki imaan tayi bade tace komai ba.. Dan kallon ta yayi snn yace "do it again.. Murgudawa imaan tayi cike da masifa.. Murmushi Jalal yayi da yayi mugun yi masa kyau snn yace "I can see kin manta what happened the first tym da nace ki dena murgude".. Kallon sa tayi tana tuna yaushe ne yace ta dena... Tuni ta tuno ranar da sumayya tace ya mayar da ita gida.. Dauke kai imaan tayi batace komai ba.. Maida hankalin sa yayi ga driving.. Snn yace "ko kin manta na tuna maki".. "Nide bn saka ka ba". "Cute smile dinsa yayi daga nan be kara magana ba... Kallon inda suke parking imaan tayi budewa yayi ya fita snn zagayo ta inda take   ya bude.. "Come out".. Babu musu imaan ta sauko shi kuma ya dauki basket din yana gaba tana binsa a a baya.. Har suka karasa can wani carpet da aka kawata shi da kendir wajen gaba daya very dim bama ka gane mutane idan ba kusa ka matso ba.. Ga kuma dumi... Ganin JALAL ya zauna itama seta zauna.... "Inajin yunwa sosai fa I haven't eat".. Waro idanu tayi.. "Why".. Ta dage kafada "babu abinda kemun dadi se wnn and ni kuma bn iya ba".. "Do you mind coming to my place zan rinka yi maka".. Ta fada ba tare data shiryawa maganar ba.... Fara ci yayi snn yace "you shouldn't mind gobe  da safe zan koma gida ai.. Granny zatayi mun.. ".. Murmushi imaan tayi snn tace "what of ur mum".. Kallon ta Jalal yayi se kuma yaci gaba da cin naman.. Itama bata sake magana ba amma hakanan jikin ta yayi sanyi.. Dagowa yayi ya kalleta ganin yanayin ta yace "me zakici?".. Ta girgiza kai kawai.. "Ko shawarma da samosa baki so" gyada kai tayi.. Ya tabe baki "to se ankawo".. Murguda baki tayi.. Ba tare da bata lokaci ba JALAL yayi order.. Wanda cikin 30mins aka kawo katuwar leda lokacin har ya gama.. Ya kalleta.. "Snacks da chocolates kawai ne naki ice cream nasu yusrahhh ne karkisha ki kwaso wata murar ki goga mana".. Dauke kai imaan tayi bayan ta saka komai cikin basket....

Seda ya gama parking a kofar gidan su snn ya juyo ya kalleta "kema haka ake zuwa a parker da motoci anzo wajen ki zance ko".. Ta tabe baki "to bn isa bane".. Ya dauke kai "har ma kinyi yawa ai na sheda".. Batace komai ba ta bude zata fita yace "imaan".. Jin yanda ya kirata ta juyo suka hada ido.. Taso yin kasa da nata amma ta kasa sbd yanda ya tsare ta da idanun yace.. "Promise me bazaki sha ice cream ba".. "I promise" ta fada bama tasan ta fada ba.. "Murmushin sa me kyau yayi kafin a hankali yace "ohk bye".. Fita imaan tayi da sauri bayan ta dauki ledar....

Tana shigowa su maryam suka wani rungumeta "oyoyo" tana hararsu tace "munafinci".. Maryam tace "babu komai mude bamu leda".. Tuni suka fara budewa.. Ita kanta se ynx taga abubuwan dake ciki.. Tanaji tana ganin ice cream din sun bata sha'awa amma taki sha hakanan kawai taji bazatasha ba..... Seda tazo kwanciya conservation din daya shiga tsakanin su.. ya dawo mata Hakanan taji wnn zuwan da tayi gidan dan zaman da sukayi har zuwa yau ya cire 80% ba haushin sa datake ji.. Cos ita de kanta sheda ce halinsa me kyaune ta ko ina.. But meyasa yake aikata munanen halaye kuma yke nunawa duniya and there must be reason behind his drinking habit..

Washe gari after isha'i tana kwance sbd yanda ta gaji yau tun safe suka fita se 5 suka dawo su maryam duk suna parlor ita kam ta dawo daki dan ta kwanta tayi bacci amma ta kasa kawai tunawa take da jiya kamar ynx suna tare da JALAL.. Tunani take yakamata ta kirasa taji ya jikin sa amma wata zuciyar na hanata.. Tuna consercation dinsu na jiya ne yasa take so ta kirasa dan bata dauka yana surutu sosai haka ba.. Har ta dauko wayar zata kirasa se kuma ta aje tana tura baki karma ya rainani.... Ajewa tayi tana so ta kwanta.. Har ta lumshe idanu kawai taji kira ya shigo wayar ta.. Janyowa tayi ta duba.. Waro idanu tayi dan ko daya bata dauka ze kirata ba.. Da kyar ta iya tattaro courage tayi picking.. Ta kara a kunne ba tare da tace komai ba... Shiru ne yabiyo baya na yan secs.. Kafin yace "uhm I can see ke baki kiran mutane ko"..Ware idanu imaan tayi "dagajin wnn muryar taka kaji sauki".. "Yes naji sauki amma kin bani wahala".. Imaan ta tura baki "ni kuma".. Yace "eh ke kika goganmun ai".. Murmushi imaan tayi wanda har seda jalal yaji sound dinsa.. Jalal yadan cije lips dinsa kadan snn yace "dariya ma kike ko sena fadawa matar da zan aura".. Shiru imaan tayi kafin tace "wacce zaka aura kuma".. "Sure".. "Kana ina"...yace "gidanku"..imaan ta tabe "to sannu masu gida".. Ware idanu JALAL yayi "kode kema nan zan maido ki". "Zamu zauna gida daya da matar da zaka aura knn".. Da confusion yace "wacece". Tabe baki imaan tayi snn tace "kafini sanin wace ita".. Tuni zulfa ta fadowa jalal ya wani waro idanu "ashe baki manta ta ba".. Tace "uhm".."to meyasa". Hade rai tayi tace "oho".. Dan lumshe idanu yayi snn yace "cos you remember the first touch and the kiss ryt"... Waro idanu imaan tayi.. Tama rasa abin fada... Tura baki tayi ta kashe wayar.. Gabanta na faduwa.. Tana tuno yanda yayi huggnng dinta a ya bata lafiyayyen kiss"...  Se kawai duk wani moment daya taba kissing dinta ya rinka fado mana..taba lips dinta tayi se takejin kamar ynx yake kissing dinta... Test ne ya shigo wayar ta ta duba da sauri shine ta gani yace "why did you hang the call daga maganar gsky".. Kamar ba zatayi reply ba se kuma ta fara masa typing "ni maganar iskanci ce bana so"... Ko minti biyu ba'ayi ba ya turo mata.. "Iskanci kuma ai an riga anyi sede kari"... Wani waro idanu tayi se kuma ta fara tura masa "seda ka nemi wacce kk so kuma zaka aura din kuyi dama ynx gaku a kusa"..... Da minti uku ya tura mata "sede kedin tunda kece matata".. Murguda baki imaan tayi ta wullar da wayar wato ni ka gama dani ita kuma ka auro ta sabuwa dalleliya ko... Sosai taji ranta ya baci "Allah ya isa kuma budurci na".. Ta fada kamar zatayi kuka a haka bacci ya kwashe ta....

Tundaga ranar imaan bata wani sake samun isashshen lokaci ba sbd test da suke tayi ga kuma exams da zasu fara. Sosai suka dage suna karatu sbd wnn final year ce.. Tanaji suna ta maganar karo nasu karatun na 1yrs acan canada amma ita batasan ya zate ba.. Tasan de kila ita da tafiya se Abba ya lpy... Tunga ranar ko waya basu karayi da jalal ba  ana gobe zasu fara exams ta shigo taga su maryam suna kallon labarai akan Jalal Ali wata ta fito tana kuka tana magana cewa ita marainiya ce bata da kowa ita bata san shine Jalal ba ta roke sa ya taimaka mata ya dauketa a matsayin ze taimaka mata ya bata gida da komai kuma lokaci lokaci yakan duba ta har yace ze aure ta.. Sosai ta kamu da sonsa amma daga karshe yasa mata kayan maye a lemu yayi amfani da ita still ya bata hakuri akan cewa ze aure ta yacigaba da amfani da ita kuma ya saba mata da kayen maye daga karshe ma se ya barta bayan ya gama lalata rayuwar ta.. Seda daga baya ta gane shine Jalal ali.. Ynx ta kawo kukanta akan a dauki mataki a biya mata hakkin ta.. Snn aka kawo view din mutane.  Wasu suna fadin ai sede tayi hakuri nata ma me sauki ne wasu kuma suna fadin fada bata baki dan Jalal ya riga yafi karfin hukuma wasu kuma suna Allah wadai da hali irin nasa dama gwamnatin gabaki daya...

Maryam tace "nide anya hukuma bata tsoran JALAL din nan.. Laifi yake kai tsaye batare da an taba daukar mataki ba.." Yusrah tace "kina gani babansa shine me kula da duk wani shige da fice na kasuwanci a kasar nan taya za'a kamasa a dakilewa mutum hanyar samun sa.. Irin mutanen nen sede kabi yanda suke so idan ba hakaba komin dukiyar ka suna da hanyar dakile ta a lokaci daya..  Maryam ta girgiza kai.. To Allah ya kawo karshen su ai basufi karfin Allah ba... Tashi imaan tayi ta shiga daki.. Karo na farko da taji ta kasa gasgata wnn lbri.. Bata da wni hujjar hakan amma a dan zaman da tayi da jalal beyi kama da mutumin da ze yaudari mace ba.. Idan ma zina yakeso yayi da ita she's quite alryt a take ze fada mata idan zatayi tayi idan batayi ya nemi wacce ta fita kuma irin kudin da su Jalal suke dashi zasu iya sakashi su neme mata da suka fita ma...

Washe gari suka fara exams sun dage sosai koda yaushe zaka gansu karatu suke duk wani abu daze kawo musu wargi cikin karatun su sun ajesa.. Wnn sumayya ma tayi joining dinsu wajen karatu.. Ranar sun fito daga exams duk sun gaji su uku ita da maryam da yusrah suna cikin sch zasu koma gida.. Suna tafiya suna lvrin exams da tayi masu dadi.. Wata muta ta wuce su.. Dawowa tayi ta tsaya saitin su amma ko kallon ta basuyi ba suna niyar wucewa jalal ya sauke glass din din motar.. Da mmki imaan take kallon sa yayin da su maryam sukayi mutuwar tsaye sbd wani balain kyau da yayi tunda suke basu taba ganin sa kusa kusa ba.. Yaukam gasu gashi har ma yana kallonsu.. "Assalamu Alaikuum".. Jalal yayi masu Sallama suka amsa.. Ya kalli imaan snn yace "madaam ai kun shigo mu wuce ko".. Yanda yayi maganar tare da tsare da idanu yasa babu musu tacewa su maryam muje ".. Zagayawa sukayi suka shiga ita kuma ta shiga gaba a tare maryam da yusrah suka ce "ina wuni"..a hankali yace "ya kuke ya exams".. Suka amsa da lpy qlw.. A hankali imaan tace "ina wuni".. Kallon ta yayi snn ya maida hankalin sa ga driving yace "yusrah da maryan kusan me".. A tare sukace aa.. Yace "kawar ku bata da kiraki". Kafin ma suyi magana ta daure fuska "me nayi maka".. Dariya su yusrah sukayi yace "kunga tsarguwa da kai ko".. Dauke kai imaan tayi batace komai ba har suka iso kofar gida.. Su yusrah suka masa godiya suka fita kallonsa tayi tace "tnx".. Zata bude ta fita ya kamo hannun ta yace "dawo madaam rakani zakiyi".. "A hakadin kana gani duk na gaji ko wanka bnyi ba" ta fada kamar zatayi kuma.. Kwaikwayon muryar ta yayi "to mene idan kin fita a hakan".. Tura baki imaan tayi.. "Malam sakemun hannu". Kallon hannun su dake hade yayi ganin yanda yayi kyau snn ya kalleta yace "uhm uhm".. Kamar zatayi. Kuka tace "Allah kaga ko wanka bnyi ba".. Batare daya saki hannun ba ya fara driving muje gida se kiyi wankan... Bata kara magana ba tayi shiru tanajin yanda yake wasa da yatsun hannun ta hannunsa so soft kamar karya dena.. Parking yayi wani eatry ya kalleta "me zakici".. A takaice tace masa "rice".. Budewa yayi ya fita babu jimawa se gashi da take away ya aje a seat dinta suka cigaba da tafiya.. Har suka isa gida babu wanda ya sake magana...
Bana samun wani comment you guys kuna karanta littafina but no comments no support nothing nothing se na dade bnyi post ba a rinka biyo ni private ana mun magana kamar wani ke rubutamun kuma kuna karantawa amma baku ecouraging dina seems like novel din babu dadi ko? Don’t wrry wlh idan na tafi hutu se kun ganni and I mean it

urs

✨✨✨

Annafie😍😍*💫💫💖JALAL ALII💖💫💫*



Written by



           *ANNAFIE💖.. ✍️*

     (Smll but mighty😉)



Writer of

*LOVE CYCLE❤️*

*SABODA DUNIYA🌃*

*ADAAN💕*

*JALAL ALI🤩*



Bismillahir rahmanir raheem

💫💖Jalal Ali(28)💖💫💫
Har suka isa gida babu wanda ya sake magana. Imaan se ajiyar zuciya take saukewa Allah ya sani yau she miss her abba and mommy tayi mugun kewan su tanaji kamar kamar rayuwan su na baya ya dawo lokacin da suke tare da mommyn ta suke kula da ita kamar mahaifan ta ko daya basu taba nuna kyamar ta ba. Ita kanta tanaji kamar mommy ce mahaifiyar ta. Dan satar kallon jalal dake driving tayi hakanan taji wani kimar sa a idon ta atleast she’s happy sbd yazo. Har suka isa gd babu wanda yayi magana. Bude motar imaan tayi ta fita ya bita da kallo har ta shige.  Snn ya kwashe gift din a ransa yana fadin stubborn girl but very intelligent”. 
Tana daki ya shigo da gift din ya zube mata su akan gado snn ya fice imaan ta bisa da kallo kafin ta fara rage kayan jikin ta zuwa shigar wanka. Bata wani dade ba ta fito ta fara shirya wa gaba daya tana jinta wani very weak   Babu wanda take missing kamar mommy kawai tanaso tasan inda take. Already dama tayo alwarta sallah ta tayar tayi nafila domin nunawa Allah godiyar ta da kuma samun lpyr abba snn ya dawo mata da mommy cikin koshin lpy.   Cire hijab din tayi ta zauna gefan gado tana dan tunane tunane tana tuanin yanda rayuwa gaba daya ta juya mata wai yau itace take shirin zama barrister abun kamar a mafarki. Shin dama da gske har zata iya kawowa haka. Seta tuna yanda take rayuwa da lokacin batasan ciwon kanta ba wanda bata da hakuri ko kadan koda kuwa dukan mutuwa za ayi mata. Duk da tana tsoran duka amma tasan bata barin bashi. Ko ynxn ma bata barin bashin amma tasan ciwon kanta. Ta kalli jikin ta. Tasan da tashin kauye tayi da bata kai haka ba bama zata kama kafar kalar wnn rayuwar ba.  Amma ynx dubeta very beautiful, educated and classy tasan zata iya jerawa da yaran masu kudi bama sa O inta ba. Abba da mommy sun bata jin dadin rayuwa wanda a ko ina zata nuna cewa ita er gata ce. Wasu hawaye taji sun zubo mata wlh ta dauki alwashin ko ba ynx ba seta dauki fansar abinda akayiwa Abbanta. Mikewa tayi zuwa dakin jalal hoping that ze yarda suje taga Abban ta. Dan tana kewar sa.   Shaf ma tama manta da wani knocking kawai ta tura kofar ta shiga. Daidai fitowar jalal daga wanka knn dagashi se boxers.  Still imaan tayi tana kallonsa tama rasa abinda zatayi shima din kallon ta yake dan beyi expecting dinta ba. Dan tunda sukayi having affairs tsoron shiga dakin take.   Jalal ya tsare ta da idanu ganin yanda duk ta birkice.  Tana kokarin neman abun fada. Ya  Dage gira daya yayi snn yace “mace da shiga dakin matashin namiji babu knocking”  da sauri tace “ I’m srry wlh bnsan bnsan “. Se kuma ta juya masa baya tanajin kamar ta nutse  sbd kunya.  Wani murmushi jalal yayi snn yace “umm ke fadi gskyr abinda ya kawoki madaam”. Da sauri imaan ta fice a dakin.  Daga inda jalal yake yana jiyo karar rufe kofar ta. Wani murmushi yayi ya rasa wane irin tsoro yarinyar nan take dashi da kuma karfin hali dan idan baka zauna da itaba you will naver agreed that tana da tsoro haka ba   . Seda ya gama shirinsa tsab  snn ya fito dakin ta ya nufa. Sede yana murdawa ya jisa a rufe knocking yayi mata alamar ta bude amma taki dole ya kyaleta yana mmki so dama tanada kunya ko dan abinda ya fada ne yasa taji kunya. Dan murmushi yayi kafin yabar gidan ma gaba daya. Imaan kau ina bama taso ta gansa gaba daya kunyar maganganun sa take. Se bayan ishai snn ya dawo ya taho mata da kayan ciye ciye cos yasan ba lallai taci abinci ba. Sede babu yanda beyi ba amma ta ki budewa dole ya kai komai kitchen snn ya zauna parlor yayi yan danne dannen sa  snn shima yazo ya kwanta.   Yunwar data addabe tace tasa ta bude kofar ta wajen 10am ta fito     Ko a tym din jalal na parlors yana shan coffee da wayarsa a kunne da alama making call yake. Dauke kai tayi ta nufi kitchen. Egg kawai tayi frying ta hada tea kauri ta fito. Bata ko kallesa ba ta nufi dining sbd bread din data gani.  Anan ta zauna ta fara breakfast dinta dan har tym din waya jalal yake.  Duk da tanajin idonsa a kanta amma tayi biris dashi.
Seda ya gama wayar snn ya nufo inda take. Imaan bata motsa ba duk da tanajinsa ya nufo dining din. A bayan ta ya tsaya  tare da dafa kujerar yana kallon ta. Dauriya kawai imaan tayi jinsa kusa da ita sosai. “Ke baki iya gaida miji ba ko”.   Tura baki imaan tayi snn tace “ni bn ganka ba ai”.   “Umm amma jiya ai kin ganni ko”. Kamar zatayi kuka tace “yaushe na ganka ni”   Dan rankwafo da fuskar sa yayi dede tata kafin yace “ na tuna maki ne” da sauri imaan tace “ni fa Allah ba da gangan na shiga ba I just went to ask idan zaka kaini wajen Abba🥺“  dan tabe baki yayi kafin yace “mijin wata de kika kalla and sena fada mata kuma”.  Hade rai imaan tayi “to mene zan kalla”  wani murmushi yayi snn ya dawo side dinta ya zauna kujerar kusa da ita snn yace “na fada maki abinda zaki kalla”  fashewa  da kuka imaan tayi duk da kukan ba har xuci ba tace “Allah ni ba da gangan na shiga ba” tayi maganar tana mikewa dukkuwa da bata koshi ba.  Saurin kamo hannun ta yayi “common dawo kiyi breakfast” babu musu ta dawo ta zauna tana tura baki tana cigaba daci.  Kallonsa tayi snn ta kalli hannun sa ta tura baki ”nide ka saken hannu Malam”. Ta fada tana fisgewa. Dan murmushi yayi kafin yace “dadin abunma matan da zan aura tana da hannun” imaan ta murguda baki “ se kaje ka kama nata ai”    Idanu kawai ya zuba mata yana son gano expression dinta amma ta dauke ta cigaba da break fast dinta seda ta gama tass snn ta tashi dan kallonsa tayi suka hada idanu yayi saurin ware idanun yace “no breakfast for me” hararansa tayi snn tace “tought tazo ta baka ne”.  Idanun sa kawai ya zuba mata dan yama rasa me zece mata tura baki tayi ta wuce kitchen kawai zatayi masa ne badon halin sa ba.  Hakanan taji tana son hada masa lafiyayyen breakfast tadan dauki lokaci kafin ta gama ta gyara a kitchen din ta jera komai ta fito dashi    Koda ta fito baya parlon. Wayar ta dauka ta tura masa message “ the breakfasts is ready”. Babu jimawa ya turo mata “I naver thoughts zakiyi anyway ina bedroom dina”    .  Dan shiru imaan tayi  snn tana tunanin taje ko kartaje. Tura baki tayi ta dauka ta nufi stairs”    Bakin kofa ta tsaya tayi knocking. Daga can yace “yes come in”   Turawa tayi a hankali kanta kasa ta shiga  kallo daya yayi mata daga danna system din da yake bayan ta aje a table din dake gaban gadon sa yace “tnx”.  Fitowa imaan tayi tana tunanin waishi wnn wane aiki yake ne kullum danne danne a system. Daki ta koma ta kwanta tare da dauko wayar ta tana dan danne danne. Chat sukeyi dasu maryam suna tayi mata tsiya      

Wajen 4 ta gama hada lunch yanxu dashi tayi shiyasa ta jera a dining da nufin data gama ta debi nata ta tafi daki. Tana cikin jerawa   Ya  fito bata juya ta kallesa ba tacigaba da abinda take.  Kujera yaja ya zauna yana Kallon ta kafin a hankali yace “this is mommy’s training I knw”  tura baki tayi kafin ta fara masa serving ta gama itama tayi nata.   A natse jalal ya fara cin abincin wanda yayi masa dadi sosai. Dan dago ido yayi ya kalli imaan data marairaice taki cin abincin ta zuba masa idanu.  dage gira daya yayi  kafin yace “what”   Imaan ta kara wani marairaicewa tana kallonsa kamar zatayi kuka tace “dan Allah ka kaini wajen Abbana inaso nagansa pls.   Cigaba da cin Abincinsa yayi  batare da yace komai ba. Dan bayajin ze kaita wajen Abba a ynx cos a wancan aikin da akayi akwai wani ciwo da basu lura ba seda aka sake amma ana saka ran dacewa.  Muryar imaan yaji tace “kaji dan Allah na shirya”.  Girgiza mata kai yayi batare da ya dago ya kalle ta ba.  Jiki a sanyaye imaan ta mike tabar dining din. Jalal ya bita da kallo har ta haye sama da sauri. Maida kansa yayi yacigaba da cin abincin. Imaan kau tana zuwa daki ta fada kan gado ta fara kuka. She’s missing her Abba she’s so worried kawai tana boye damuwar ta ne. Amma tana son ganin sa.  Ta dauki kusan 30 mins kafin ta goge hawayen ta ta sauka daga gadon tazo zata bude kofa knn jalal ya turo. Zuba mata ido yayi yana kallon ta kafin a hankali yace “imaan” juyawa tayi da sauri zata koma ciki ya riko hannun ta. Tsayawa tayi tayi batare data juyo ba.   A hankali jalal ya saka dayan hannun sa ya juyo da ita suna fuskantar juna … kasa imaan tayi da kanta tana kokarin hana kanta kuka. Jalal ya saka hannunsa ya tallafo habarta yana kallon ta dukda taki yarda ta kallesa. Camly yace “you cried” girgiza masa kai tayi batare da ta yarda  sun hada ido ba. .….…”bazasu bari a shiga ba sbd jamian tsaro suna aikin su” idanun ta na tara ruwa snn tace “idan yaji sauki zaka kaini” tayi maganar cikin sanyi. Murmushi ne ya subucewa jalal sbd yanda tayi din kai kace baxata ta iya wani abun ba. “ umm zan kaiki” dan tura baki tayi ganin yana murmushi snn tace “ya isheka”.  Ware idanu yayi kafin yace “me kuma nayi”  cire hannun sa tayi a fuskar ta dan bata son wnn kusancin nasu. Tana kokarin kwace hannun ta ya hana ta. Ta kallesa kamar zatayi kuka “ nide ka sakeni” ya nuke kafada   Yanda yayi din seda imaan taji wani iri. Daurewa kawai tayi tace “amma de kasan babu kyau taba mace ko”. Jalal ya dage gira daya “really Ohk, let’s go out”. Ya fada sbd yanaso ta saki jikin ta. Shiru imaan tayi tana kallon sa bade tace komai ba. Sakin hannun ta yayi. Ya nufi wardrobe dinta ya ciro mata wani well iron hijab yazo har gabanta ya warware ya saka mata. Har kasa hijab din kuma hular ta zauna mata dass tayi wani irin kyau.   Shi kansa zuba mata idanu yayi    Ganin haka yasa imaan tsuke baki “to wai ina zamuje”. A ransa yace “dis shagwaba gal”. Amma a zahiri hannun ta ya kamo yace “let go my frnd”.  Babu musu imaan ta bisa yana rike da hannun ta har suka fita. Shida kansa ya bude mata mota ta shiga snn ya zagaya ya shigo ita de se mmki de se mmki take.  “Is he dis frndly?” Kawai haduwan su na farko take tunawa ynx kuma wai mijin ta ne though bawai miji na har abada ba amma wani tym din idan ta tuna rayuwar ta setaga ta sauya da abubuwa dayawa.  Kawai rayuwar ta ta kauye take tunawa ko ya suke ynx. Tanason taje taga baban ta Adda da kuma sauran yan uwanta “ kas kas yayi mata da hannun sa dede idon ta hakan ya katse mata tunani ta kallesa. Driving dinsa yake batare da ya kalleta ba yace “what are you thinking let share it together”  noke kafada tayi tace “um um”. Jalal ya dan kalleta kafin ya maida hankalinsa ga tuki “waike waya koya maki shagwaba mommy ko abba”   Imaan ta ware duka idanun ta “ni kuma yaushe nayi shagwaba”.   “Kullum”ya  fada   Ware hannuwa imaan tayi “nide babu wani shagwaba ko haka budurwanka take maka”   Kallon ta yayi kafin yace “sede idan zaki koya mata” ta dauke kallonta daga nasa tace “aa idan kunyi aure zatana yimaka ai”. “Really to nima shiyasa kuke mun”. Imaan ta kallesa da sauri “nidin  aini bn iya ba but may be nima idan nayi auren na koya”. Murmushi jalal yayi kafin yace “nima seki rinka yimun ai” ta dan hade rai “saboda me” “saboda nima mijin ki ne”  dasauri tace “aa”. Ya dauke idon sa daga kanta “kinmanta knn ko na tuna maki” kamar imaan zatayi kuka tace “nide bnma iya ba kuma ba seka tunamun ba” murmushi yayi “shagwaba si ur nature ko da yaushe cikin yi kike”.   Imaan ta daure fuska “to ni ynx daure fuskana zan rikayi”.     Jalal be kara magana ba ya maida hankalin sa ga driving.  A wajen wani eatry yayi parking. Snn ya kalleta .…”lets go”  Duka budewa sukayi suka fito    Suka shiga …… Kallon ta Jalal yayi yace “me zaki ci cos baki yi lunch ba”    “Fada masa tayi. Yasa aka kawo mata ….:. Seda taci ta koshi snn suka fito suna shiga mota yace “adress din gidan su maryam ko yusrah”.  Ware idanu tayi cike da farin ciki “are you for reel”. Ya kalleta “ ko mu koma gida”.    Da sauri ta girgiza kai tare da fada  masa.  Ba tare daya kalleta ba yace “meyasa baki son mu koma gida”. Kamar zatayi kuka tace “ni kade”. Shima kwaikwayonta yayi “to bagani ba”.   Dan murmushi imaan tayi bade tace komai ba... “so yau itace this handsome guy rich kid dashi yake mata magana cikin salama the bad boy kaf Abuja da kewaye”.   Babu wanda ya kara magana har sukaje gidansu yusrah. Ta bude da sauri ta fita ko sallama batayi masa ba. Ta zagaya ta nufi gate din ya zuge glass din “no bye ko”. Ware idanu tayi se kuma ta daga hannu tayi masa waving”.     Shima yayi mata same thing snn ya wuce. Itama ta shiga tanajin ranta fess.   Rumgume juna sukayi ita da yursah dan murna. Se kuma yusrah ta saketa. Tana kallon ta “uhm su matar aure manya sega tafiya babu sallama”. Rufe fuska tayi. Ke you won’t understand wlh.  Rufemun baki. Cewar yusrah. Imaan tace kinga muje na gaisar da Ammi se muje gidan su maryam “. Bayan sun gaisa. Suka wuce gidan su maryam kasancewar babu nisa a kasa suka tafi bnd tsokanar imaan babu abinda yusrah take.   Da sukaje gidan su maryam ma dasawa sukayi tun tana shiru har ta biye su.   Wajen gab da magrib Maryam  ta shiga Twitter ta tsinci tweet din wani yana Allah wade da halin JALAL ALI. idan bnd lalasewa mene abinda prouding da munanen halaye. Da tabi tweet din setaga abubuwan da aka saba fada ne  “wai jiya Jalal Ali ya bude wani gidan jiya. Inda jiya da daddare  ya fara aiki. Kuma kwana akayi ana shaye shaye da zinace zinace    Munanen abubuwan da akayi har sun bace. Kuma Jalal ya hallicci wajen dan Akwai motar sa ma a wajen.”  Wasu mutane sun fito sunyi magana akan hakan ba dacewa bane. Inda yau shima da safe ya fito yace.  Babu wanda ya isa ya hanani abinda nayi niyya kudi nane banawani ba rayuwa ta ce bata wani ba snn babu wanda ya isa ya hanani jin dadi ga kuma duk wani meso the door is open”. Labari ya fara bude ko ina inda dayawa suke Allah wade da wnn hali nasa wasu kuma suce ai daurin gindin ubansa ne tirr da irin wnn dukiyar maganganu de iri iri.    Tunda maryam ta fara karantowa jikin imaan ke rawa inda take jin batu akan wanda take tare dashi kuma mijin ta. Sede har ga Allah zuciyar ta bata yarda cewa ya aikata ba sbd jiya after ishai jalal na gida. Dan idon ta biyu tym din da yake mata knocking. Dis definitely something serious that she have kwn. Sede abinda ke daure mata kai meyasa ya amsa. Meyasa zece yayi kode da gske yayi? Kai wlh beyi ba. Kotayi rantsuwa bazatayi kaffara ba Jalal beyi ba sede idan akwai wani abu a kasa. 
Kasa saka baki imaan tayi a maganar su yusrah dan bata san me zatace ba. Su kansu da suka kula da yana yinta se cewa sukayi “um ai wnn kadan knn kikaji wnn Jalal din ya kai kololuwar bad ke idan akwai abinda yafi bad to jalal ya kai. Murmushi imaan ta kakalo kafin tace “to Allah ya shirye sa. Daga nan ta nemi su canja wata fira. Itama duk a sanyaye sukeyinta....   bayan ishai jalal ya kirata ta fada masa address din su maryam.    Befi 30mins ba ya kirata yace ya karaso. Su maryam suka rakata har mota. Suka gaisa da Jalal duk cikin sakin fuska snn imaan ta shiga suka wuce. 
Tun ganin yanayinta duk a sanyaye ya gane ta samu lbrn knn. Hakanan kawai se yaji babu dadi. Tunda yake idan bayan mamy da daddy babu wanda yake damuwa da yada zantukansa da ake. Sede hakanan yaji bayaso imaan ta sani baya so ta rinka masa kallon bad boy he feel lyk ya fada mata gsky kawai. Amma ina baxe iya ba koshi besan ta ina ze fara ba yafi so kawai gsky tayi halin ta. Yasan mamy nacan jira take ya hau online ta masa fadan meyasa ya amsa. Abinda bata sani ba shine shima kansa neman me amsawar yake. Amma ya rufe ko wace kofa. But with tym komai ze warware. Da wnn tunanin suka iso gida
  Wanka imaan  ta shiga bayan ta shigo daki. Seda ta gama shirinta tsab cikin kayan baccin da suka rufe jikin ta duka snn ta fito. A parlor ta iske jalal ya dukufa aiki a system dinsa.   Shima ya sauya shigar sa zuwa ta bacci.   A hankali ta karasa cikin parlon duk da Jalal yaji shigowarta be dago ba.   Imaan ji tayi ta kasa maganar data kawota. Se kawai ta tsinci kanta da fadin “what do you want for dinner”. Jalal ya dago ya kalleta cos he wasn’t expect dis   Maida dubansa yayi a system snn yace “just coffee”.   Zuwa tayi ta hado masa ta kawo. Ba tare da ya kalleta ba yace tnx. Sama imaan ta koma dan ji tayi duk tsoran masa magana takeyi.   Sede mene koda taje ta kwanta kasa bacci tayi. Kawai abun ne ya daure mata kai meyasa yake haka shn da gske ne koko. Kuma mene dalilinsa na amsawa.Ta dade kafin ta yanke shawarar itafa seta tambaye sa.   Kara tashi tayi ta fito a karo na biyu.   Sede tana nufar parlon tun kafin ta sauka ta hango jalal ya dunkule hannu ya bige glass table din dake gabansa wanda she’s sure inda ace bame kyau bane da tuni ya da gargaje  Ya dafe kansa gashin kan ya wani barbaje idanun sa sunyi jawuur. Sosai imaan ta tsorata. Labewa tayi daga gefen stairs din. Ganin ya taho. Har ya wuce ya shiga dakinsa be kula da ita ba. Sosai hankalin imaan ya tashi gabanta ya shiga faduwa. Dan hakanan taji hankalinta be kwanta da shigar tasa ba. 

Urs
✨✨✨
Annafie😍💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
              ANNAFIE💖…✍️
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
💫💫💖Jalal Alii(29)💖💫💫
Gaban ta na faduwa ta nufi kofar dakin nasa ta kanga kunne ko zataji wani abu....jin shiru yasa ta tura kofar a hankali inda idon ta ya sauka akan jalal dayayi zaune saman gadon da kwalbar giya yana barewa. Dago manyan idanun sa da sukayi jawur yayi ya zuba mata daka gani kasan his addicted   Duk da ya ganta amma bayajin ze iya fasa shan wnn giyar sbd shi kade yasan yanda yake ji a ransa. Ita kade zesha ya samu salama. Dan haka ya maida kansa ya cigaba da barewa   Imaan kam kallonsa kawai take hawaye na zuba a idon ta . Shin wnn wace kalar rayuwa ce gaba daya se taji ranta yana baci taya mutum ze maida giya maganin matsalar sa musulmi dashi kuma wanda yasan Addini. Bata ankara ba ba se gani tayi yana kokarin daga kwalbar. Cikin azama da wani irin courage ta karasa garesa ta fisge kwalbar. Wanda cikin wani irin sauri jalal ya kalleta da jajayen idanunsa “Give it to me” girgiza masa kai tayi hawaye na taruwa a idon ta “no dis can’t change anything sema zunubi da zaka samu” wani irin tsawa ya daka mata tare da mikewa kamar ze kaimata duka “I said give it to me stop wasting my my tym joh” Fashewa da kuka imaan tayi cike da tsoran yanayin sa amma ta dake tace “beat me yes beat but I will not give this to you. Jalal i can’t watch you drinking alcohol while we’re living to gether you can harm me in anyway or the order”. Cusa duka hanneyensa yayi cikin gashin kansa tare da kifa kansa saman gadon idanun sa sunyi wani irin jawuur “imaan will not understand he didn’t choose to be druker but babu yanda zeyi he’s already addicted , ya fara shanta at very tender age tana debe masa kewa a duk lokacin da yake cikin damuwa.   Bathroom imaan ta shiga ta tuttule duka wine din snn ta dawo. Ta zuba masa idanu. Sosai ya bata tausayi ganin tundaga inda take har sound din numfashin sa tana jiyowa.  Sede batasan mene jin dadi a rayuwar giya ba da ace be sabawa kansa ba da duk haka bata faru ba. A hankali tace “Jalal”   Juyowa yayi da sauri ya zuba mata jajayen idanun sa. Da kyar ya iya fadin “go pls”. A hankali imaan ta karasa kusa dashi ta duka tana kallon sa kamar yanda shima yake kallon ta. Idanun ta na zubar da hawaye tace “Allah can solve all ur problems but don’t drink it’s haram” gyada mata kai kawai yayi. Har ta juya zata tafi ya kamo hannun ta. Juyowa tayi ta kallesa se kuma ta zauna gefen sa. Dan tayi tunanin wani abun ze ce mata. Kawai se gani tayi ya rungumeta tsam a jikin sa yana sauke ajiyar zuciya.  Ita kanta batayi kokarin hanasa ba sbd  tarasa me zatayi to stop him dan tana iya tafiya bata sani ba ko akwai wata wine din.  Wayar sa data gani ta dauka ganin babu security ta shiga ta sanya karatun Qurani  sun dade a haka kafin tafara jin nufashin sa yana sauka a hankali. Tabi kyakkyawar fuskar sa ta kallo taga bacci ya dauke sa.  Sosai taji ya bata tausayi ta tabbata jalal na cikin damuwa sede meyasa ya dauki shan giya amatsayin maganin damuwar sa.  Ace mutum har mutum kamar jalal kyakkawan namiji me jini a jika ga kamala da kudi amma yana shaye shaye. Ita de kam ta dauki alkhawarin inde suna tare she won’t watch him drinking. A haka har bacci ya dauke ta bata sani ba.   …,… Har makara sukayi sallahr asuba jalal ne ya fara bude idanun sa ya zuba a kanta dan murmushi ya saki a ransa yace “oh dis stubborn wife even ur sleeping face is so breathtaking” yabi pink lips dinta da kallo a hankali yace “these lips”. Dan lumshe idanu yayi yanaji kamar yayi kissing but yasan yanayi zata tashi. Shi kansa yasan he miss them. Lips dinta suna daga cikin abubuwan da suke mugun daga masa hankali. Though dukan ta ma yasan so dayawa tana tayar masa da duk wata shaawa but her lips is the best. Idan tana magana ko shagwaba duk da yasan nature dinta ne se yaji kawai kamar ya kamata ya bata best romance of her lyf shiyasa sau dayawa yake dan janta da fira dukkuwa dashi ba ma abocin magana bane. But having conservation da ita yana mugun saka sa emotions.…, a hakanli ya fara kokarin zare jikinsa dan kar ya tashe ta.   Sede yana motsawa ta bude idanun ta masu cike da bacci. Dauke kansa yayi daga kallon ta kafin a hankali yace “thank you”. Daga haka ya nufi toilet. Imaan ta bisa da kallo  har ya shige snn itama tashi ya koma daki. Tanayin sallahr asuba ta koma ta cigaba da baccin ta.  .... koda ta tashi wajen karfe shadaya Jalal baya gidan . Wanka tayi ta gyara ko ina na gidan tsab snn ta leka dakinsa ganin a gyara yasa ta dawo ta shiga kitchen ta fara Girki lafiyayye ta diba nata ta zuba sauran a flask  ta gyara kitchen din ta fito a parlor ta zauna taci nata tana kallo tana chat din ta har ta gama taje ta wanke plate din ta wuce sama ta kwanta tacigaba da wani baccin.
Tana idar da sallahr ishai ta shiga wanka har ta fito ta gama shirin ta bataji dawowar jalal ba. Hakanan gaban ta ya fara faduwa karde ace jiya ta hanasa sha yau yaje waje yasha ya koshi kila ma har ya kasa dawowa gida wata simple doguwar riga ta saka ta fito parlor ta zauna ta kunna kallo ita tsoron ta daya kar yaje can ya bugu kuma ya barta da kwana ita daya a wnn katon gida da har yau bata gama sanin ko ina na cikin sa ba.  Idon ta na kan tv amma hankalin ta na wani wajen jin an bude kofa yasa ta mike da sauri dan bata kawo na ranta shine ba sbd ko daya bataji tsayuwar motar sa ba. Ganin shine yasa ta sauke ajiyar zuciya.   ..jalal ya ware idanu yana kallon ta “madaam are you ohk” kamar zatayi kuka tace “thought bazaka dawo ba”. Jalal yace “uhm da bazan dawo ba gasky”. Imaan ta kara sauke ajiyar zuciya kafin tace “sbd mene”    Yace “sbd kona zauna babu abinda zaki mun sunan kuma inada aure”. Imaan da bata fahimcesa ba tace “ akwai abinci a kitchen” bece da ita komai ba ya wuce  dakin sa. Imaan kam zaunawa tayi taci gaba da kallon ta sbd taji dadi bawai giyar ya fita ya sha ba.  Tayi kusan 30mins a wajen kafin taji kamshin turaren sa daga kai tayi tana kallonsa yayi wani kyau cikin  kayan baccin masu taushi ya kara wani fresh. A ranta tace “ummm handsome”.  “Madaam kallon fa”  waskewa tayi tare da fadin “na zubo maka Abinci” seda ya zauna saman kujera kafin ya dube ta ya gyada mata kai tashi tayi ta nufi kitchen babu jimawa ta zubo masa ta kawo. Ganin spoon daya yace “kefa” ta girgiza kai “ni tea zan sha” daga haka ta wuce kitchen ya bita da kallo 1 cup of tea ta hado ta dawo parlo ta zauna kafin ta fara sha yace “ki daukomun system dina a daki”. Kallon sa tayi ganin ba ita yake kallo ba yasa ta hararesa snn ta tashi ta wuce. Tana tafiya ya dauki tea dinta ya fara sha a hankali.  
Tun kafin ta karaso ta hade rai ganin ga nasa beci ba kuma yana sha tea dinta. Aje system din tayi kamar zatayi kuka tace “amma de kasan ba naka bane ko”  ya dage gira  yana kallon ta kafin yace “wa kika harara”  murguda baki tayi kafin tace “nide ka bani ai na dauko maka system din ko”.  Mika mata cup din yayi “karbi kayanki” a hankali imaan ta karasa ta karba. Zata taho batare da ta kula ba ta taka kafan sa yi tayi kamar zata fadi sede bata fadin ba amma ta sharara masa duka tea din me zafi a fatar hannun sa.  Runtse idanu jalal yayi yace “ouch” dan da zafi shi kansa sbd zafin tea din a hankali yake sipping. Sosai imaan taji tsora ta matsa gefe.   “Am srry pl” jalal ya cije lips din sa yana hararanta “so kike ki ragemun farashi ko salan idan nayi aure matana taga tabo a jikina ko”.  Tsuke fuska imaan tayitare da kama kugu tana kallonsa “oh kai just tabo ne ma knn. Ni nace mene ni me kakeso nace. Nida already ka riga kayi disvirgin dina  se nayi aure mijina yaji ni open”. Wani irin ware idanu jalal yayi yana kallon imaan kafin ya dage gira yana kallon ta “really?” Dauke kai tayi tare da murguda baki a hankali yace “come here” noke kafada tayi. Hannu yasa ze fisgota tayi kokarin zillewa sede kuma ta zame da tea din daya zuba. Tayi luuuu zata fadi jalal yayi azamar jawota suka fada kan kujera gabadayan su suka kwanta yana kasa tana sama tana kokarin sauka ya zagayeta da duka hannayensa. Marairaicewa tayi tana kallon sa “dan Allah kayi hakuri”   Idonsa a kanta yace “repeat what you said”. Kamar zatayi kuka  “nifa bada kai nake ba”  juyar da ita yayi ta dawo gefen sa shima ya juya suna fuskantar juna. Sbd kujera ce yasa suka hade sosai har numfashin su na sauka saman na juna. Ya zuba mata idanun sa itama kanta kallonsa take a tsorace. Murya kamar me wisphering yace “idan mun rabu mijin jinki ze jiki open ko?”   Ta girgiza kai da sauri. Dan lumshe ido yayi ya sake budewa a kanta a hankali yace “I will have you to my satisfaction kafin ki bar gidan nan. Zanyi disvirging dinki da hujja. Then idan kinje ki fada masa jalal test you before him.” Hawaye suka taru a idon imaan ta fara girgiza masa zatayi magana ya daura hannun sa a lips dinta “shhhhhhh let’s both enjoy it together ko kinaso nayi da karfi”. Imaan ta girgiza kai da sauri. Jalal ya lumshe idanun sa cikin wata kalar murya yace “let’s start”.    Ya fada yana kara hada ta da jikin sa sosai tare da sakin wani ajiyar Zuciya. Idanun sa ya lumshe har ynx yace. “I miss this worm body and the soft skin”   Kasa magana imaan tayi sbd yanda jikinta ke rawa gaba daya wani weakness take ji. Tunda da su yusrah suka fara mata en dirke dirken nan ko kusa da ita yazo setaji sauyi bare ynx da yayi hugging dinta.   A hankali taji ya fara shafa bayanta tundaga bumbum zuwa wuyan ta. Yanda yake mata din kamar wata jaririya. Imaan har wani lumshe idanu take sbd dadi tuni jikin ta ya fara mutuwa tanajin kamar kar ya dena. A hankali jalal ya cire hular kanta ya warware gashin da yake tupke.  Snn yayi kasa da zip din   Rigar ta imaan duk ma bata sani ba sede taji yana kasa da rigar ne ta rike hannun sa. Be hanata ba ya taimaka mata ta tashi zaune ya maida ita saman cinyar sa tare da yi mata wajen zama a jikin sa. Imaan ta girgiza masa kai “pls karka cire mun riga” ….  Bece da ita komai ba yakai hannun sa kan bottom din rigar sa a hankali ya fara bottuning  har ya cire rigar sa ya wurgar snn ya fara kokarin cire tata. Tana so tace ya bari amma she can’t wani irin abu kawai takeji game dashi na daban.   Kasa yayi da rigar hakan yasa imaan saurin boyewa a jikin sa dukkuwa da akwai bra. A yanda imaan ta shiga jikin sa seda yace “ouch”. Feeling imaan’s skin nake is something else. Skin dinta nada wani irin taushi na daban jikin sa har wani rawa ya fara sbd tsabar yanda yake da feelings a kanta.    Kasa yin komai yayi sbd gaba daya yanda jikinsa yayi weak sede kawai ya saka duka hannuwansa ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya.  Imaan kau ba a magana dan jikin ta har wani dumi yake dauka she can se jalal can give the best hug ever. Tanaji kamar suyi ta zama a haka. A hankali jalal yakai bakin sa saitin kunnen ta cikin wispher voice yace “ur skin is so soft I love it” kafin ya fara bata kisses a kunne. Imaan bata taba sanin shaawa na mugun existing a jikin ta ba se yau dan wani irin abu taji tun daga kanta har zu kafafunta batasa sanda itama ta rungumesa ba. Hakan kam yayi wa jalal dadi a hankali yayi kasa da ita ya kwantar da ita saman kujerar shi kuma ya koma sama ta cikin dubara ya idasa cire rigar ta ta kasa ta rage daga ita se pant da bra yabi boobs dinta dake cikin bra da kallo ko first night dinsu be tsaya ya kallesu haka ba. A hankali yakai lips dinsa ya fara kissing dinsu ta cikin bra din yanda yake kissing dinsu dede da wani dan sound kadan bakaramin yima imaan dadi yake ba. A hankali ya fara tahowa zuwa wuyan ta snn yazo lips dinta. Imaan batayi kokarin hanasa kissing lips dinta ba cos she’s waiting for it. She can say jalal got the perfect kiss kuma tunbayau ba ta sheda. Tun kiss dinsu na farko she enjoyed it ....seda jalal ya tabbatar jikin ta ka gama mutuwa snn ya dauketa ya rumgumeta a jikinsa sosai snn ya nufi stair da ita. Itakam ta lafe domin kau jikinta ya gama daukar sakonninsa. Dakinsa ya shiga da ita ya kwantar da ita a saman gadon sa. Snn ya yazo ya kashe duka hasken dakin tare da kunna Ac snn ya koma saman gadon yaja masu blanket ya rufa masu tare da janyo ta jikin sa. Har tym idan idonta a rufe. Murya can kasa yace “imaaaan” “ummm” ta fada ba tare data bude idanun ta ba. Yace “I don’t knw why but I have much feelings on you”. Ita de imaan bata ce komai ba. Hannansa yakai ya fara balle huk din bra dinta kafin yace “ I want to have you today,tomorrow and every day of our togetherness”. Imaan de kam babu baka se kunne dan har maganganun sa ma mugun shigan ta suke wani irin feeling takeji from no where.”  I hankali jalal ya fara bata wani perfect romance wanda seda ta kusa gigicewa sbd dadi. He played with every part of her body and she loves the way he did. Ita kanta ta basa gudunmuwa sosai. Dan bata tashi dawowa hankalin ta ba seda akazo me wuyar sex knn. Nan fa zani ya canxa dan wlh na yauma da zafi I mean mugun zafi. Sede inaa jalal ya shiga wata duniya ta daban. Dan jiyayi ta kara wani dadi. Dadin da baze iya fassarawa ba duk kukan da take jalal bema san tanayi ba. Shi kansa kukan dadi yake. Tun first night dinsu na farko ya gane dadin sex and today ma he can say yau ya kara tabbatar wa. Seda jalal yayi having dinta tu his satisfaction snn ya kyale ta. Ya janyo ta jikin sa ya rungume. Yanajin wani irin farin ciki na daban imaan kau tun kukan na fita har ya dena fita. Tuni bacci ya dauke ta tayi tana sauke ajiyar zuciya. Shima baccin ne ya daukesa me cike da farin ciki.  Ni ma ANNAFIE nace seda safen ku.
Yauma seda suka makara sallah dan se 8 Jalal ya farka. A hankali ya zare jikinsa daga nata ya shiga bathroom yayi wanka yayo alwala snn  snn ya dawo ya shirya ya kabbara sallah. Seda ya idar ya gama addua snn ya tashi ya dawo saman gadon ya janye bargon yana kallon fuskarta. A hankali yace “wifey” ya fada tare da jan hancin ta. Imaan ta bude idanun ta masu cike da bacci ta kalli Jalal  shi kuma ya dage mata gira. Ture hannunsa tayi daga saman fuskar ta tana kokarin jan blanket din ta rufe jikin ta...   murmushi yayi tare da kawobakin sa dede kunnen ta yace “madaam gani kuma na nawa. Sede anjima kadan”. Fashewa imaan tayi da kuka. “Bana so zafi nakeji”. In a lower tune voice yace “I will not do it hard daga yau babu zafi”. Kara karfin kukan ta tayi “That’s what you said yesterday but I feel the pain and steel feeling it”.  Jalal ya ware idanu “ really mu gani to idan da ciwo sena kyaleki”.  Rike blanket din tayi gam   Yayi dariyar dabe shirya ba “why are hidden my frnd naga komai fa”.  Noke kafada imaan tayi. Yace “ohk muje kiyi Wanka”. “ to ka kawomin towel mana” tashi yayi ya dauko mata towel dinsa ya mika mata. Karba tayi ta saka snn ta yayi blanket din kanta a kasa ta fara kokarin sauka. Sede ta kasa jin wani zafi ta kasan ta. Komawa tayi ta zauna tana sauke numfashi. Jalal ya matso tare da mika mata hannun sa  babu musu ta saka nata a ciki. Ya taimaka mata ta mike. Da taimakon sa suka shiga bathroom din. Sede duk yanda yaso ta bari yai mata wanka ki tayi dole ya fito ya barta.   Tsab imaan tayi wankan ta da ruwan zafi tamkar wancan lokacin. Seda ta gama snn ta fito bayan tayi alwala already har ya gyara dakin ya dauko mata wata rigar da hijab babu musu ta karba ta saka tayi sallah. Tana idarwa ta koma saman gadonsa ta rufa tuni wani bacci ya dauketa. Shima dawowa yayi ya kwanta a gefen ta wani bacci shima ya kwashe sa. 
Se wajen 11 ya farka ya dubeta har tym din bacci take peacefully. Key din motar sa ya dauka yafice a gidan gabadaya domin nemo masu breakfast.    Be jimaba ya dawo tsab ya jera komai a dining he fne it defficult sbd be saba ba. But he tried. Bashi da matsala da tea sbd yasan akwai ruwan zafi a flasks.... yana cikin jerawa ya ganta ta sauka a stair a hankali yanda take tafiya kade zaka gane ta gurzu.  Kugu ya kama yana kallon ta da dan murmushi. Suna hada idon ta fashe da kuka. Da sauri Jalal ya karasa kusa da ita. “Menene kuma”. “ ba kaine kemun dariya ba”. Ya ware idanu “ni kuma” hade rai tayi kafin tace “inajin yunwa”.  Dining ya nuna mata breakfast is ready”.   Ya fada yana mika mata hannun sa. Kin kamawa tayi tacigaba da tafiyar ta da kyar. Sede kawai ji tayi ya dauke ta yanda kasan jaririya. Tsuke fuskar tayi tana kallon sa ya gade gira. “Tell me is this my work I mean ur step”. Boye fuskar ta tayi a jikin sa cike da kunya. Shima murmushi yayi suka karasa dining din. Shida kansa yayi serving dinta  ya bata. Babu musu ta fara ci dan wata irin yunwa takeji. Shikam bama ci yake ba ya zura mata idanu. Kawai he’s just happy dadin imaan ya wuce misali. Kallon sa imaan tayi kafin ta murguda baki tayi “malam stop looking at me”.  Murmushin gefen baki yayi “I’m thinking of something sweet to night”. Da sauri imaan ta fara girgiza kai kamar zatayi kuka. Shima girgiza kan ya fara yi kafin yace “kawai muje ayi maki kitso”.  Noke kafada tayi dan tasan me yake nufi. Yau kam kodame yake yawo bazata yarda yayi mata wani abun ba. Bazata yarda ya maida ta abincinsa ba kuma daga karshe yazo ya rabu da ita.  Na yau ma kawai ji tayi bazata iya kallonsa ta zagesa ba kamar wancan karon. Hakanan taga wani girman sa take gani kodon ynx sun dan saba oho ga wata irin kunyar sa da takeji shikam ta kula ko a jikin sa.    Seda taci ta koshi snn ta tashi. Ko kallonsa batayi ba. Ta fara tafiya a hankali.  Muryar sa taji yace “anjima you won’t feel this pain” kallon sa tayi da sauri. Kamar zatayi kuka tace “thats what you said yesterday ai”.  Murmushi yayi kafin ya taso ya kama hannun ta su fara hawa stairs din a hankali yanda bazataji zafi fa yace. ... “Bazakiji ba I promise” noke kafada tayi tace “to wai kai bakajin zafin ne”. Dariyar dabe shirya ba ta subuce masa. Itama murmushi tayi dan se ynx tayi reallizing abinda ta fada.  Hannun sa ya zagayo ta shoulder dinta nata kuma ya maidashi bayansa snn yace “ki bari anjima zan fada maki” noke kafada tayi.  Suna isa bakin kofar ta ta tsaya. Tace “ya isa haka tafi dakin ka.  Babu musu ya sake ta. Ya shige tare da rufe kofar.    Tana tunanin anya ya dace sucigaba da zama da jalal kuwa. Tura baki tayi ta shige bathroom dinta wanka tayo tayi alwala ta shirya tayi Sallahr snn ta kwanta .....

Urs
ANNAFIE😍💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
              ANNAFIE💖…✍️
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
💫💫💖Jalal Alii(30)💖💫💫
Koda yamma shida kansa ya kawo mata lunch. Nan ma kin bari tayi ya shigo sede tazo bakin kofa ta karba ta rufe kofar ta ta koma taci ta koshi  bata jima ba taji ya kara yi mata knocking.  “Wife I’m going out”. Tura baki tayi kafin tace “a dawo lpy”.  Dan jingina da kofar jalal yayi kafin murya can kasa yace “haka akewa miji ko goodbye” Yanda yayi maganar seda imaan taji wani iri. Dan kasa furta komai ma tayi . In a lower tune voice yace “imaaan this not the ryt way to say goodbye for ur husband”. Da kyar imaan tace “nide seka dawo”.    Jalal ya kara jingina da kofar snn yace “and what do you have for me idan na dawo din”。  kamar imaan zatayi kuka tace “um um”. Murmushi yayi snn yace “olryt then bye”.  Daga haka ya fice da dan sassarfa ya fice sbd jiran sa da akeyi...jin shiru yasa imaan ta tashi cottens ta zuge. Tana kallon parking space din ko zata gansa. Babu jimawa kam segasa ya taho. Sanye cikin kananun kaya da suka mugun karbar jikinsa. Sosai yayi mata kyau bazatayi karya ba tunda take bata taba ganin namijin da komai nasa ke birgeta ba se jalal bawai bata taba ganin namiji me kyau bane Amma na jalal is different komai nasa unique ne. Har seda taga ya shiga mota yabar gidan snn ta dawo   Tana tunanin ina zeje.  Wani zuciyar tace “kila wajen budurwar sa zeje”。 tura baki tayi tana fadin “budurwar ma ai nafita kyau”.   Karar message ne shigo wayar ta. Hakan yasa ta duba da sauri ganin Jalal ne “har kin gama kallon nawa”. Ware idanu tayi kafin ta hade rai ta tura masa “ni na kalleka naji mene yaushe ma na kalle ka”.   Babu jimawa wani message din ya sake shigowa “zance zanje. Nayi kyau ko nazo nasake”. Kumbura baki imaan tayi kamar zatayi kuka ta tura masa “wani kyau babu wani kyau da kayi”.  “Ohk tohm bari na dawo seki shirya ni yanda yanda zanyi kyau ko”. Murguda baki imaan tayi “malam don’t trying coming kaje ita ta shirya ka mana”. “Ai kece mata na ke zaki shiryani ko but anyway anjima zamu hadu”. Aje wayar tayi tana hararanta.  Kafin ta kwanta. Tanajin ranta na baci wato zeje wajen wata wacce yake so ita kuma ya dawo ya biya bukata da ita lallai ma “.  

Se bayan ishai jalal ya dawo be samu kowa a parlor ba sede tv dake aiki alamar ta zauna a parlon bayan tafiyar sa. Gama sauran youghurt nan da cake. Dakin sa ya wuce yayi wanka. Ya dauki system dinsa dan aiki yayi kadan snn ya tashi ya nufi dakin ta. 
Imaan dake tsaye gaban wardrobe daure da towel dan fitowar ta wanka knn ta gama shiri zata dauki kayan bacci. Taji an shigo. Da sauri ta juya dan kafin ka ta gansa kamshin sa yayi mata iso.... juya baya tayi da sauri bayan su hada ido kamar zatayi kuka tace “taya zaka shigomin daki babu sallama”. A hankali jalal ya taka zuwa inda take idon sa akan fararen cinyoyinta. Kafin ya rugomota ta baya  ya daura Kansa saman shoulder dinta. Murya can kasa yace “dake da gidan nan da duk wani abu dake cikin sa mallakina ne”. Muryar ta nadan rawa tace “to sakeni na shirya”. Unexpected taji ya bata wani warm kiss a wuyanta. Ta runtse ido da sauri yace “na fada maki daga ynx tare zamu rinka kwana”. “To ka saken na saka kaya.    Sakin ta yayi ya karasa kusa da wardrobe din. Wata er fingin riga ya dauko mata ya mika mata girgiza kai tayi “nide ba ita…” bata ankara ba se ji tayi ya fisge towel din jikin ta. Aikam babu shiri ta fada jikin sa ta kankame sa jalal ya wani runtse idanu “ouch ke”。”to nide ka bani towel dina” ta fada tana boye fuskanta a kirjinsa. Lumshe idanu yayi kafin yaje dede kunnen ta ya rada mata “soon zaki dena kunyar nan yarinya”  tana noke noke ya saka mata rigar snn ya dauke ta ya nufi dakin sa da ita.   Yana dire ta saman gado ta fashe masa da kuka.  Shima hawowa samon gadon yayi ya janyo ta jikinsa.  A hankali yace “what”. “Wlh da zafi nide bana so”.  Murmushin gefen baki yayi “bazaki ji zafi ba fa”. Kara fashewa tayi da kuka.  Ya kwantar da kanta a chest dinsa “oya sleep babu abinda zanyi maki”. Shiru imaan tayi ta lafe tana sauke ajiyar zuciya.  Wayar sa ya dauko yana dannawa da hannu daya while dayan kuma yana murza wuyan ta a hankali.  Ita kam tayi lakwas.  Sosai taji dadin kwanciya kamar dama wajen is main for her she can say is the best place to sleep  a haka har wani bacci me dadi ya dauketa.    Jalal ya bita da kallo bayan yaji ta fara sauke numfashi a hankali.  Lips dinta ya kai dede nata yayi kissing.  Imaan is the full definition of beuty. Komai nata is so attractive. Besan iya feelings din yarinyar nan da yakeji ba he can say tunda yake betabajin wata yarinya na birgesa ba kamar imaan komai nata yana birgesa he can say all kara rungume ta yayi yanajin wani abu daban a game da ita betaba sha awar kwana da wata ba kamar ta ya rasa wani kalan magnet ne jikin yarinyar nan da yake attracting dinsa.  Aha haka shima baccin ya kwashe sa.
Koda sukayi sallahr asuba wni baccin suka koma...10:30. Imaan ta bude idon ta akan fuskar jalal dake bacci   Binsa tayi da kallo a tsanake tana kallon yanda gashin kansa da sajen sa suka kwanta luf luf a kyakkawar fuskar sa gashin idon sa abin kallone ne. Bare azo ga well shapes lips dinsa. Wadan da suke wasu dark pink. A ranta tace “umm they can give the perfect kiss 💋”. “You feel lyk kissing me ryt?”  Wani irin waro idanu imaan tayi se kuma ta boye fuskar ta cike da kunya. Dagota yayi ta dawo samansa suna akwancen ya dago fuskar ta suna kallon juna “oya kiss me “。girgiza kai imaan tayi da sauri. Dan langwabe kai yayi “plssss”. Numfashi imaan t sauke kafin ta saka hannuwan ta ta tallabo fuskar sa tana kallonsa kafin ta lumshe idanu a hankali ta fara matsawa da lips dinta zuwa nasa shima nasan idon ya lumshe. Har wata ajiyar zuciya ya sauke jin soft lips dinta a nasa cikin 3secs ta cire batare da ya bude idon sa ba yace “again”. Babu musu ta kara masa wani kamar wancan ya kara cewa “Again”  ta sakeyi masa kamar wancan. Bude idon sa yayi kafin ya juyata ta koma kasa shikuma sama “bari na nuna maki yanda akeyi”. Be jira cewar ta ba ya fara bata wasu lafiyayyun kisses da suka so zautata. Tuni wasan ya fara chanza salo. And yau imaan bataji zafi ba sema dadi ta basa 💯 coopuration. Bata taba sani sex lyf da dadi ba se yau she enjoyed it to the fullest. Se wajen azahar snn suka natsu  . Ya rungumeta suna sauke ajiyar zuciya. Sun dade ahaka kafin yazo dede kunne ta yace “so how’s the breakfast”.  Boye fuskanta tayi a kirjin sa. Yace “ynx ke zaki bada amsar tambayar da kikayimun jiya”  shiru tayi batace komai ba. Yace “you asked me kai bakajin zafi ne hope ynx kinji ni abinda nake ji”   Hannu tasaka ta rufe bakin sa. Yayi murmushi kafin ya dauke ta su shiga bathroom. Duk yanda imaan take zillewa kin barinta jalal yayi seda sukayi wankan tare. Sukayo alwala ya nado abarsa a towel. Suka fito. Guduwa imaan tayi tayi sallah ta shirya snn ta fita zuwa kitchen. Abinci me rai da lpy tayi masu ka tana gab da gamawa jalal ya shigo kitchen din bama ta kula dashi ba ya seda ta juyo zata kai wasu flasks din dining ya gansa tsaye. Sosai ta tsorata. Dan har ta fara baya ganin shine yasa ta balla masa harara “kaiko” ya ware hannuwan sa. “Matsoraciya”. Tura baki tayi tare da mika masa flask din hannun ta “kaimun dining”。babu musu ya karba yakai. Ya dawo ta kara masa.  Daga karshe shi ya jera komai. Ita kuma ta gyara kitchen. Ta fito ta zauna. Shima kusa da ita ya zauna. Ta kallesa kamar zatayi kuka “to wane zeyi serving” tashi yayi ya zuba na mutum daya. Ganin kansa kade ya zubamawa yasa ta murguda baki ta tashi zatayi serving ya rike hannun ta “zauna tare zamuci”. Kamar tayi masa musu se kuma ta zauna. Still be saki hannun ta ba ya fara bata Abincin. Shima yana cin nasa. Har suka kusa cinyewa a haka wayar sa ce tayi ringing. Ganin bature yasa ya dauka da sauri.  Ko gaisawa basuyi ba taga ya mike “what are you sure manga na hannun ku”.     “Ohk ganin nan aha zamuyi waya da sageer. Zeji mun da sauran familynsa snn ku tabbar inda kuka kaisa babu wanda yaga fuskar ku har shi. Okey bani 30mins na iso”.  Kallon imaan yayi “am going out wife ki natsu kici abinci”. Daga haka ya nufi stairs. Imaan ta bisa da kallo. “Waye manga me zasuyi masa? Karde ace harda garkuwa da mutane suke.  Kai knw baze yiwuba sageer boyayyen jami’in tsaro ne tabbas akwai wasu abubuwa masu Mahimmacin wanda mutane basu sani ba game da jalal but menene she’s sure he’s a bad boy dan ko drinking habit dinsa ma alama ce amma jalal nada kyawawan halaye wanda ita da ta dan sansa zata fadi haka.  Tashi tayi jiki a sanyaye tabi bayan sa. Shiryawa yake yana sauya shigar sa zuwa wani lafiyayyen yadi dayayi mugun yi masa kyau. Karasawa tayi saman kujera ta zauna tana kallonsa. “Ina zakaje ne”. A hankali ya karasa so inda take ya mika mata links dinsa da agogo. Karba tayi ya mika mata hannun sa ta gane me yake nufi dan haka ta mike ta saka masa links din da agogon snn ta saka a dayan ma. Turare ya dauko ze fesa ta karba ta fesa masa a hankali snn tace “baka fadamun inda zakaje ba” ta fada tana aje turaren bayan ta gama fesa masa   Janyo ta jikinsa yayi ya rungume tare da kissing dinta a cin din ta “tnx wife sena dawo”. “A dawo lpy ta fada masa”. Ya sakar mata murmushi tare da jan dan hancin ta... snn ya fice. A sanyaye imaan ta bisa da kallo har ya fice cikin sassarfa. Komawa tayi ta zauna tana sauke ajiyar zuciya. Definitely akwai abubuwa da jalal yake boyewa dayawa. Wanda haka kawai taji tanason ta sani. Abunku da masu karatun bincike. Tabbas akwai wani boyayyen lamari tare dashi. Yes he’s bad but munanen halayen yake nunawa kuma tabbas akwai dalili that make him choose to be bad. Kamar drinking habit dinsa bawai he’s addicted kawai ba. Akwai dalilinsa nashan giya.  And maganar sa kuma da ake yadawa tabbas akwai karya ba zatace duka ba but shi meyasa yake amsa harda karyar. Akwai abubuwa dayawa daya kamata ta sani wanda seta shiga jikinsa sosai snn zata sani. Sede bazata yarda sucigaba da rayuwar aure dashi ba sbd akarshe rabuwa zasuyi.... dakin sa ta gyara kafin ta sauka kasa nan ma ta gyara ko ina. 
Har wajen 9 jalal be dawo ba. Sosai imaan ta shiga damuwa  dan har ta fara tunanin ko lafiya. Bataji karar shigowar motar sa ba se gani tayi ya bude kofa ya shigo. Ta mike da sauri tana kallon sa. Kallo daya kuma ta masa ta gane yanayin sa a little bit angry snn his eyes are red. Ware mata hannunsa yayi tare da kakalo murmushi “commom wife”. Babu musu ta tafi ta fada jikin sa ya rungume ta. Tare da kissing dinta a goshi. Sakin sa tayi tana kallonsa domin kokarin gano yanayinsa. Amma seya dauke kansa ya wuce sama. Dakin sa ya shiga ya rage kayan jikin sa ya shiga wanka. Bayan ya fito ya shirya cikin kayan bacci snn ya zauna gefen gado.  Wlh yau da ba don imaan ba babu abinda ze hanasa shan wine kwalba biyu. Tusa hannun sa yayi cikin gashin kansa. Shin suwane ke shiga rayuwar sa ne me yayi masu. Meyasa bazasu fito gaba da gaba su gwabza ba suke bi masa ta karkashin kasa. Duk da tunanin sa yanakan Hajiya Atika. Daga baya kuma ya fara zargin manga da Alh falalu waddu da kuma Hajiya Atika sune matsalar sa amma ynx ya gane su bama komai bane. Alh falalu waddu,manga,Hajiya Atika,Tasiu duk tafiyar su daya suna da nasu laifin sbd sunyi attempting kashe masa dan uwa. Sede basuyi nasara ba kuma a bayanan tasiu ya gane wadan da suka samu nasarar kashe seif sune suke keda hannu a gubar mum dinsa. To suwane wadan nan me suke so meyayi masu ne ya tabbata suma a jikin sa suke. Yanason sanin Abubuwa dayawa game da masu shigar masa rayuwa masu yada maganganun banza akansa da Kuma masu amsawa. Lallai yakamata ya tashi tsaye.   Imaan ta dade tana kallon sa bema san tashigo ba har ta karasa gefen sa ta zauna jalal be sani ba.  Seda ta dafa sa ahankali. Snn ya dago ya kalleta da sauri idanun sa are so reddish numfashin sa kansa me zafi ne. A hankali ya kwantar da kansa saman cinyar ta tare da zagayo da hannun sa ta weist dinta.   Sosai imaan taji ya bata tausayi hakanan taji duk haushin sa da take ji ya koma tausayi hannun ta ta tusa cikin gashin kansa tana dan shafawa. Lumshe idanu yayi yanajin dadin yanda take masa “I knw you won’t let me drink so what next”. Ya fada idanun sa a lumshe. Sosai taji ya kara bata tausayi wato ya dena sbd yaji maganar ta. Tace “lets receite Quran” wayar sa ya mika masa. Babu musu ta karba ta bude ta kunna suratul bakara suka rinka bi a hankali sunyi nisa sosai kafin ta fara jin saukar numshin sa tare da ajiyar zuciya.  Gyara masa kwanciya tayi itama ta kwanta tare da shigewa jikinsa aikam ya rungumeta sosai tuni bacci ya daukesa
Washe gari suka tashi da wani labarin yanda de aka saba masa kamar koda yaushe.  Be nuna mata komai ba ya zauna sukayi breakfast tare though babu wanda ke magana a cikin su. Ya shirya yabar gidan. Wajen 4 ya dawo ynx ma somehow dai but not lyk yesterday. Ko daki ma be shiga ba ya zauna a parlo yana kallon tv. Imaan ce tazo tare da cup din tea ta mika masa. Kallon ta yayi se kuma ya karba tare da fadin tnx “。imaan ta zauna gefen sa tare da shigewa jikin sa ta daura kanta a shoulder dinsa. Dan lumshe idanu yayi a ransa ya furta “girls” hakanan yaji damuwar sa na da raguwa zagayo da hannun sa yayi ta bayan ta yacigaba da shan tea din seda ya shanye tass snn imaan ta kai hannun ta dede bottom din rigar sa ta fara cirewa. Jalal ya ware idanu yana kallon ta. Ta tura baki “wanka” murmushin dabe shirya ba yayi tare da saka dayan hannun sa ya rungumota ta dawo gaba daya jikinsa snn yace “amma ke zakiyimun ko” ta ware duka manyan idanun ta “ni kuma” ya hade goshin sa da nata in a wispher voice yace “um ke and you will massage me after that”. Be jira cewar ta ba ya dauke suka haye sama be direta ko ina ba se cikin bathroom din. Imaan ta idasa cire masa rigar zata juya ya janyota ya kunna masu shower. Dole imaan ta hakura akayi wankan bayan sun gama ya nadota a towel suka fito. Tare suka shirya. Kafin tayi masa massage kamar yanda yace. Har wani bacci yake ji sbd tsabar taushin hannun ta hakanan yaji duk wata damuwar sa ta tafi kansa ya dena ciwo da dane sede yasha giya ya koshi. Ganin ya fara bacci yasa imaan tashi zata tafi se ji tayi ya janyowa jikinsa ya rungume. Tare sukayi baccin …....
A daren ranar gaba daya cikin nishadi sukayi ta ko daya ranar imaan bata yarda ta bar jalal cikin bakin ciki ba a cewarta hakan da zatayi shine ze manta da giya. Kuma taci nasara. Dan ko daya be kawo giya a ransa ba.  Amma duk yanda yaso yayi having affairs da ita ki tayi. Dole ya hakura ya kyale ta. 
Washe gari tana kitchen tana hada breakfast Jalal ya shigo. Kallonsa tayi sn tace “ina kwana”  ya noke kafada ta ware duka idanun ta “menayi” “kinmun rowar kanki ma na”  juya masa baya tayi tacigaba da abinda take. A hankali ya karasa ya rungumota ta baya dan runtse idanu tayi. Ya kai bakinsa kunnen ta yace “ynx de nasan babu zafi besides we will all enjoy it”. Tura baki kawai tayi a hankali yace “mijin ki baze jiki open ba kullum a rufe kike wife dadin ki baze bari ya gane cewa kinsan namiji ba you’re very sweet and tidy”. Sosai imaan ta runtse idanun ta sbd yanda maganganunsa ke shiga kanta. A hankali ya fara kissing dinta a kunne kafin ya juyo da ita ya rungumeta ya fara bata kisses. Tuni ta biyesa.  Ganin sun fara nisa daga dan karamin romance zasu fara babba yasa tace “abu akan gas”  “muryar sa na rawa yace ki kashe mu tafi daki pls”  girgiza kai tayi tare da kamo hannun sa ta maidashi parlon ta rufo kitchen din ta maida kayan ta snn tacigaba da abinda take.    Seda ta gama tsab snn ta fito. Ko abincin tsakura kawai jalal yake se binta yake da idanu tasan me yake nufi amma tayi biris dashi dan bazata iya cigaba da biyesa ba. 

Da yamma jalal na zaune a parlo yana kallo imaan tazo ta zauna saman cinyar sa tare da zagayo da hannun ta ta wuyan sa.  Jalal ya zuba mata lumsassun idanun sa kafin yace “jan fada ko”. Da tura baki “ni fita zamuyi inaso na siyo creams and perfume irin naka amma”. “Muyi using nawa mana to”. “Eh amma muje mu karo inaso na fita ko kila akwai abinda zan siya”. Key dinsa ya dauka “lets go”. Kiss tayi masa a sajen sa kafin tace tnx husband”. Daga haka ta tashi ta wuce sama ya bita da kallo. Abaya ta sanyo me kyau ta veil dinta tayi kyau sosai yarintar ta tasake fitowa   . Kallon ta kawai jalal yake harta karaso kusa dashi. Yayi gaba ta bisa har suka karasa mota. Suka bude suka shiga.   Sun dan fara tafiya Jalal ya kamo hannun ta yana murzawa a hankali cikin nasa. Murya can kasa yace “wife idan mun dawo fa”. Tura baki tayi tareda noke kafada  shiru Jalal yayi be kara magana ba. Amma be sake hannun ta ba yadan murzawa while drinving da one hand. Wani babban super maket sukashigo. Daga gani na manya ne da kusan komai nasu abroad ne hatta ma’aikatan ....  kayan gurin sunyi matuka kayatar da imaan. A hankali ta kamo hannun sa tace “ka tayani zaba”  murmushi yayi kafin yace “inners”. Tura baki tayi “kaine zaka zabar mun inners”. Murya can kasa yace “her size din bra dinki nasani”. Imaan ta waro idanu yace “sure ynx ma zan daukar maki komai and a dakina zan aje yanda base kin rinka fita ba”. Rufe fuskan ta tayi da tafin hannun ta tana murmushi wato ta kula jalal ya iya naughty talks. Hannun ta ya kamo suka karasa wajen inners din. Shi da kansa yake dauka kamar yanda yace haka tanaji tana gani yaita lodar kaya seda suka gama da inner snn sukaje wajen su abayas ya kara mata wasu snn creams da perfumes tana turawa shi kuma yana daukar mata abinda tace da wanda ma batace ba. Ji sukayi ance “hello” duk juyawa sukayi suna kallon ta. Sarai sun gane ta jidda ce. Wacce suka hadu a saloon ranar imaan ta hade rai dan wani irn haushin ta takeji. Ita kuma ta sakar masu murmushi “kwana dayawa”. Imaan ta kakalo murmushi. Tace “ykk” jidda tace “lpy qlw”. Daga haka imaan ta dauke kai tayi gaba dan bata so magaana tacigaba da hadasu. Jalal zebi bayanta knn tace “handsome do you mind sharing contact with me”. Girgiza mata kai yayi “am not with my card”.   Jakar ta ta bude cike da wayewa ta ciro nata na mika masa “here is mine I’m Jiddah” da jalal baxe karba ba idon sa hango masa imaan ta wani mirror data labe tana kallon su.   Hakan yasa ya karba.  Imaan da zuciyar ta ke tafarfasa ta taho afusace ta fisge card din ta ketasa ta watsawa jiddahr snn tace “stay away from him,yes i said stay away from my husband” daga haka ta kamo hannun jalal ta turo basket din suka taho.

Urs
✨✨✨
ANNAFIE😍😍💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
              ANNAFIE💖…✍️
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
💫💫💖Jalal Alii(31)💖💫💫
Ficewa imaan tayi tabar jalal wajen biyan kudi. Jalal can’t help it but smile. Unbelievable is imaan jealous at him. Yayi murmushi bayan ankwashe kayan zuwa mota.   Bude motar yayi ya shiga. Imaan na zaune ta kurawa window idanu. Bacin ranta shine har ma amsar numbern wata yake ita Kuma gata a gida sede yazo ya biya bukatar sa ta ita to wlh bazeyiyu ba sede ya dauki daya ko ita ko yanmatansa and so call budurwarsa da yake fada. Shima Jalal daure fuskar yayi yana kallon ta bayan sun fara tafiya yace “I can see kina so ki hanani yin kasuwa. Ynx for godsake beb kamar waccan ta bani numbern ta after all the sort of words har da yagawa”   Juyowa imaan tayi tana kallonsa cike da takaici. Kamar tayi magana se kuma ta dauke kanta tana kokarin hana kanta kuka. ...a hankali yake satar kallon ta yana dan murmushi har suka isa gd. Bude motar tayi zata fita yace “wife” juyowa tayi ta kallesa “am not ur wife je ka kawo yanmatan naka or ur so called girlfriend su zauna da kai” se kuma ta fashe da kuka ta fice motar da sauri. Ta ruga ta shige ciki. Bude motar jalal yayi yana kiran sunan ta amma inaa.    Koda ta shiga cikin kitchen kawai ta fada ta kifa kanta tana kukan da ko ita kanta batasan dalili ba....  sound din kukan ta dayaji a kitchen yasa ya nufi can direct. Bakin kofa ya tsaya watching her tana kuka kamar me. Har hakan yaso basa mmki.  Is this love or what.   Camly yace “imaan”. Banza imaan tayi dashi bata dago ba.  “Anyi maki wani abu ne?”  Dago idanun ta tayi tana kallon sa “ are yau asking me Jalal tambayana na kake ohk good am leaving ai ba dole sena zauna da kai ba ka sake ni sudin suzo su zauna tare da kai”. Ta fada tare da juya masa baya.  Wani murmushi yayi kafin a hankali ya karasa ta bayan ta ya rungumota. Murya can kasa yace “is this love cos jealousy is a sign of love...that means you love me?”  Ware idanu imaan tayi se kuma ta ture sa ta juyo tana kallon sa tace “this is neigther jealous nor love. I just can’t take it. Nice matar ka ryt. Tunda har nima bana kula kowa dole kaima ka kyale kowa idan mun rabu seka kula who so ever you want”. Zuba mata idanu jalal yayi tace she’s not jealous but abinda takeyi is just out of jealousy. Ganin murmushi ma yake mata yasa kawai ta juya zata fita. Bin bayan ta yayi a hankali ya dauketa. Ya daurata saman cabinet shikuma ta shiga ta tsakkiyar kafafunun ta ya hada ta da jikin sa tare da zagaye waist dinta. Yace “now tell me kike so ayi mrs Jalal”. Tura baki tayi tana kokarin ture sa. Ya kara shigewa jikinta tare da kai fuskar sa dede kunnen ta.  Yace “kinaso duk na dena kula su”. Gyada masa kai tayi. Yace “ohk tell me you love me”. “Ni nace ina sonka n” bata karasa ba kawai ya hade bakin su. Lumshe idanu imaan tayi kafin ta zagayo da hannun ta ta wuyan sa dayar kuma tana shafa sumar sa. Snn kuma ta fara mayar masa da martani.   Wasan su ya dau dadi dan yau kowa na bada hadin kai. Daukar ta jalal Yayi suka wuce dakin sa. Acan aka idasa komai. Nikam nace ummm😐😐
  Seda akayi magrib snn suka lafa. Da za a kwanta ma aka daura daga inda aka tsaya. ...
Tundaga nan wani shakuwa ya shiga tsakanin su koda yaushe suna makale kome yake so imaan nayi masa kamar yanda itama ta gane Jalal is just frndly. Kullum cikin tsokanar ta yake wai sonsa ta fara.
  A hankali imaan ta fara bude idon ta tana kallon side din ganin babu jalal zaune ta tashi tana mmki yana ina. Seta tuna tana bacci taji yana fadin bari yaje ya dawo.  Kallon takardun da system din daya bari a gadon tayi tun safe yake aikin nan and she’s sure kiran da akayi masa ne ya tashe sa. Da addua ta tashi a bakin ta snn ta fara kokarin gyara dakin. Tattare masa komai tayi ta aje masa a inda yake ajewa. Wata envelope ce ta fado. Hotunan dake ciki duk suka zubo binsu tayi da kallo kafin ta duka zata maida hotunan ciki  idonta ya sauka akan wadan da ke ciki hoton. Yara ne yan biyu yan shekara biyar tare da mamansu. Se kuma wani su biyu. Se kuma wanda suna jarirai.  Se kuma wanda suke harda babansu duka hotunan cike da nishadi suke duk da hotunan da ne. Mamakine ya cika imaan dan wnn hutunan ba kowa bne se jalal. Bazata iya gane jalal din a ciki  ba sede tabbas shine a jikin hoton dukkuwa da yana karami ne. Knn dama Jalal yan biyu ne ta dauki wanda suke su Hudu Jalal na kama da iyayen sa duka biyun snn babu abinda ya raba tsakanin sa da twin bro din nasa . Where is he” sometimes tanajin ta damu da rashin ganin iyayensa duk da watarana takanji yana waya da mamy amma baya ending lpy dan seya shiga tsananin damuwa wanda har yake shan giya dukda yanxu baya sha ynx kuma kanta ya gama daurewa shin ina dayan twin dinsa meyasa yake shiga damuwa a duk tym din da suke waya da mamy ita kanta duk ya gama daurewa. Wait yama suke da zulfa da har take zaune a gidan su kuma a part dinsu. Tabbas maman jalal da baban sa basa tare tunda inde zeyi maganar babansa koda wasa bayasaka mamansa. Tanacikin wnn tunanin har jalal yazo ta bayan ta bata sani ba. Sede ji tayi ya rungumota ta baya yana murmushi idon sa akan picture din  murmushi ta kakalo snn tace “dama ku twins ne”. Yace “sure nunani anan ciki”. Kallon cute boys din kawai take tana kokarin gano sa ta nuna saif snn tace “gaka”. Ya girgiza kai tare da jan cin dinta “yarinya bata san mijin ta ba”   Kallon jalal tayi snn ta kalli hoton tace “you so much look alike”. Yace “sure”. Tace “where is he”.  Mikewa kafin yace “he’s dead” daga haka ya shige bathroom. Binsa tayi da kallo se taji wani tausayin sa ta rinka kallon hoton barin wanda sukayi su biyu. Lallai mutuwa daban ce sunzo tare amma daya ya mutu yabar daya. Amma a yanayin da yayi maganar duk setaji daban maida hotunan tayi tacigaba da gyaran dakin. Bayan ya fito ta taikama masa ya shirya. Taje ta hada masu breakfast snn tayi wanka shida kansa ya taimaka mata ta shirya snn suka fito breakfast.  Suna cikin yi tace “baka fadamun sunan sa ba”   Kallon ta yayi kafin yace “saifuddeen  Ali Abbas ni kuma Jalaluddeen Ali Abbas” duk da yasa tasani amma ya fada mata complete sunan”. Jiki a sanyaye tace “ Allah ya jikansa” ya amsa da Ameen. Ita de imaan gaba daya kanta ya daure. She want to knw more about dis jalal.... dayamma tana zaune a parlo tunani yayi mata yawa. Ta dauki wayar ta social media ta shiga tayi searching ABOUT JALAL ALI’s twin bro.      And ta fara ganin labarai kala kala  THE BADEST BOY WHO COMMITTED A CRIME AT THE AGE OF 12.  HE KILLEDS HIS TWIN BRO SAIFDDEEN.   wani kuma JALAL THE BAD BOY WHO KILLED HIS TWIN BRO...

Imaan ji tayi kanta na wani irin juyawa yanzu har wnn dinsa ya kai haka dan uwansa na jini kashe wayar tayi. Domin da ta shiga da niyar sanin kome game dashi amma ynx bazata iya ba wnn kade ma ya isheta. Kisa ya kashe dan uwansa wanda sukazo duniya. Shin wajen wa zataji wnn zancen shin gsky ne ko karya ne idan kuma karya ne taya mahaifin sa zebar wnn koda yabar komai. Wata zuciyar tace kila shiyasa basa shiri da mamyn sa ko. Dafe kai imaan tayi Dole ta natsu dole tasan dawa take rayuwa. Shin shi meyasa baya daukar mataki.   Sumy ce ta fado mata arai.  Yakamata ta sami sumy dan suyi magana. Da wnn tunanin tabar komai a ranta

Koda ya dawo imaan bata fada masa komai ba. Ba kuma ta nuna masa ba. Ta sake dashi. Suna parlor ta fara bacci a jikinsa. Ya dauke ta ya kaita daki kafin ya dawo ya kira mamy. Jin ya ambaci mamy yasa imaan ta koma daga biyo bayan sa ta tayi. Tana tsoron kar ya ganta. Tana son sanin abinda suke tattaunawa da mamyn nasa. Komawa tayi ta kwanta sede ta kasa bacci zuciyar ta fada mata taje taji me suke cewa. Haka de ta hakura. Jin ya shigo yasa ta lumshe idanun ta kamar me bacci. Ji tayi ya kunna karatun alqurani a wayar sa snn ya janyota jikin sa ya rungume.  Imaan najin yanda yake sauke ajiya zuciya tasan halin da yake ciki kamar de koda yaushe idan sukayi waya.  
Washe gari kuma suka tashi da wani sabon labari akan Jalal din. Ita kanta ta kula da jalal yau duk wani sukuku yake dauriya kawai yake Breakfast ma tea kade yasha ya koma parlo idanun sa a lumshe. Ynx abin yafi damunsa wlh sbd wadan da yake suspecting basu bane to suwane knn .suwane ke shiga rayuwar sa. Kansa har wani irin ciwo yake ji yake kamar ze tsage yayi iya tunanin da zeyi na ya gano amma ya kasa. Imaan ce ta zauna kusa dashi tare da kamo hannun sa tana murzawa. Ya bude idonsa akanta ita kanta seda ta tsorata. A hankali tace “what’s wrong with you”. Zuba mata idanun sa yayi. Ze iya cewa ita din ta daban ce. Tunda yake a rayuwar sa babu wanda idan yana cikin damuwa zeso ya kasance dashi yayi kokarin kawar masa da damuwar sa se imaan. Ze iya cewa ita din da daban ce dan dayawa idan yana tare da ita damuwar sa tana tafiya baze ce duka ba amma 50% na tafiya sbd ita ya dena shan giya.  Muryar ta ya karaji tace “ka kaima Allah kukan ka”.  A hankali ya dauki kansa ya maida saman cinyar ta   “Ta tura hannu cikin sumar sa tana dan shafawa. A hankali yace “imaan”.   “Naam”. Shiru yayi bece kumai ba har ta cire ran zeyi magana se taji yace “bansan me nayi masu ba har suke shiga rayuwa ta” “ kabar su da Allah ai basu fi karfin sa ba”. Yace “mene laifin mahaifiya ta me tayi masu”. Wnn maganar daya fada yasa bata san sanda tace “wani Abu ya samu mamyn ne”. Bude idanun sa yayi ya zuba a kanta. Kafin yace “mamy ba itace mahaifiyata ba. Mamy mahaifiyar sageer ce mamy kanwar mamana ce”  imaan ta kanta ya gama daurewa ta zuba masa idanu knn ba maman sa bace to wace mamansa me akayi mata kamar yasan me take tunani ya dauko wayar sa. Ya nuna wani vedio ya nemo tare da mika mata “wnn itace mahaifiyata”. Amsa imaan tayi da sauri tayi playing mum ce kwance kamar koda yaushe likitoci sun rufu akanta ...imaan ji tayi jikin ta ya fara rawa. Zuciyar ta tana tsitstsinkewa. Jalal yace “19yrs knn tana haka she was poisoned.and har ynx ba asamu magani ba”. Imanna ta rufe bakin ta da hannunta tana kokarin hana kanta kuka amma tuni hawaye sun balle mata. Tashi jalal yayi daga jikin ta ya janyota jikinsa ya rungume kankamesa imaan tayi tare da fashewa da kuka sosai.  Lumshe idanu jalal yayi yana ji shima dama ze iya kukan.   Yace “kamar yanda kikasan mahaifina yana da ariziki sosai shine me kula da duk wani shiga da fice na kasuwan ci a kasar nan. Su biyu ne baban su ya haifa. Yana da step brother wanda shine Abban su sumy duka granny nace ta rike su. Ba mum dina bace ta farko wajen dad. Hajiya Atika itace ta farko mamar zulfa knn dan bayan auren mum da dad suka rabu.  Akan mu dad dinmu ya fara haihuwa. Bamu san wani abu waishi ki ba soyayya muka sani. Nida saif ko bacci zamuyi hannu mu a rike yake muna samun duk wata kulawa wajen dad da mum. Tsabar shakuwar mu da saif ko rashin lpy tare muke. Is hardly kiga ranmu a bace. Sbd mu farin ciki muka sani. Granny ce tasaka dad ya dawo da hajiya atika bayan rasuwar Abban zulfa.  Koda ta dawo gidan muna zaman lpy tana son mu muna son zulfa. Lokaci guda Dad ya dauke mana kafa. Idan munje wajen sa seyayi mana tsawa haka ma mum babu hali taje inda yake. Ko dakin mu ya dena zuwa. We love our dad duk da mum tace mu dena zuwa amma se munje be taba dukan mu ba sede tsawa.  Lokaci daya kuma suka zo suka bar Nigeria shida Hajiya Atika da zulfa... koda yaushe muna tambayar mum yaushe ze dawo seta ce mana soon. We alway caught mum crying setace mana idon ta ke ciwo.  Wani rana ranar da bazan taba mantawa ba fresh memory har ynx nake ganin sa” runtse idanu jalal yayi  yanajin zafin abun. Wasu hawaye na zubo masa but be damu daya gogeba yacigaba “ranar muka iske mum dina tana aman jini the last day danaji muryan mum dina the last day dana ga idon mum dina a bude we ran and call granny sukazo aka dauki mum dina zuwa asibiti mum  nida saif ware craying cos we love our mum. Mamy ce tazo taita lallashin mu ashe wai anyi poison mum dinmu. And su kansu basu san gubar ba. Granny da mamy suka saka aka fitar da mum har damu. Can ma abu daya. Guban ba a san makarin ta ba dama sun san wace irin guba ce da sauki amma basu san kalar ta ba amma suna bincike gubar inde tana jiki bazaka iya gane ta ba se Idan a tsurar ta take. Binciken da har yau ba a gano ba    Koda granny ta dawo ma shiru tunda ta taho daddynmu shiru. Ganin yanda koda yaushe muke kuka yasa mamy tasaka aka maido damu nigeria sbd tasan granny na nan sede mene tunda muka dawo granny ta saka a maido damu part din mu. Mamy nacan na kula da mum bata san cewa nan babu me kula damu ba. Imaan bamu iya komai ba an kawo part mu kade babu kowa. Dagani se saif kullum muna makale da juna. Abinci sede mu bude fridge muci. Tun muna cin drink da biskit muka koma cin danyar indomie. Cikin wata uku muka cinye komai da kika sani bamu iya girki ba bare mu dafa. Tym din duk mun kare mun lalace munyi baki sbd babu abinci da wankan kirki kaf cikin gidan mu babu me kula damu. Part dinmu mune muke sharewa ganin ba da datti ake barin sa ba duk da bamu iya komai ba. Babu me taimaka mana. Ko part din granny mukaje babu me budewa bare sauran yan gidan. Imaan muda muka saba da dariya mukazo muka denayi. Kuma hankalin mu na kan mum dinmu. Kinsan cewa abincin seda ya gagaremu. Karshe cikin gari muka rinka zuwa muna aikin karfi su yarfa mana abinci akwano muci da wnn hannun nawa nayi shara nayi wanke wanke nayi wanki nayi har kwadago. Alokacin mahaifina baxaki gammu kice mahaifina na daga cikin masu arziki a kasar nan ba wulakanci ko babu wanda bamusha ba anjefemu an takure mu. Haka zamu hakura duk dan sbd mu samu abinda zamu ci. Yara damu muka fara neman Sana’a duk dan mu samu abinda zamu ci mun saida har ruwa munbi motar sauke block Kamar bamu da gata. Tym din kawai burin mu mu samu kudi sosai muma sbd munsan kudin mamy zasu iya karewa tunda baban su sageer ya rasu a wajen kakar su suke. Kinga muka saida ruwa a tasha mubi motar bulo mu samo kudi mu siye abinci muci mu aje wasu. Muka dena kula kowa a gidan mu.ranar mun dawo daga bin motar bulo mukaga wani a part dinmu. Tasiu knn duk kallonsa mukayi yace mana shi masu kwasar shara ne aka daukesa aiki a gidan nan wai ze kwashe shara.  Mukace ya barshi mu babu anan. Muka wuce sama muna wasan mu na yara nida saif dan tym din iya junan mu kade muke raha. Nace ya shiga wnka bari na kirga mana iya kudin da muka tara idan sun kusa isa mu bada a turawa mamy”.    Saif ya shiga wanka ni kuma na kirga kudi. Mun tara dayawa dan duk aikin da mukeyi abincin kade muke siya shima a maneji. Ina mugun son seif dan a tym din shi kade ne farin cikina kamar yanda shima nine nasa  tare muka taso muke koma tare bamu san rabuwa ba.   Bayan ya fito daga wankan nima na shiga.” Jalal ya cije lips dinsa da karfi zuciyar sa na wani irin tafarfasa yace “ina cikin wanka I hered saifs voice sama sama ana dan bige bige. Se kuma naji yayi wani kara tare da kwala kiran sunana da mugun karfi.” Rigata kawai na zura na fito “ anan naga mugun tashin hankali fuskar mutumin da komin wata kalar tsufa zeyi a duniya baxan manta ba naga ya cakama saif wuka   Mutuwan tsaye nayi a tym din while saif yana mun alama dana gudu. Bansan tym din dana ruga da gudu ba na cakumi mutumin daya juyo yana kokarin kashe ne ba. Yanda na rike masa wuya seda seda fatar sa ta cikin farcina na  saboda yanda na shakesa cike da cike zuciya dukkuwa da yafi karfina wukar daya cakawa saif ya ciro ze cakamun na samu damar kwacewa na yanki fuskar sa dashi tabon da nasan baze taba gogewa ba. Hakan yasa ya sakeni ya nufi kofa da gudu nabisa amma ya rigani fita zan fita saif ya kirani. Hakan yasa na ruga wajen dan uwana dake cikin azaba yana kiran sunana. Na rasa me zanyi masa kawai na tashi da niyar na kira mutane but saif hold my hand very tight and said. Jalal am going pls take care of our mum. I love you I love mum pls take care of her no matter how dan Allah karka kaji da ita she’s our mum I love you”. A kan idona dan uwana wanda muka zo duniya tare yabar duniya na rugume sa ina kuka sosai saying kar yatafi ya barni but he’s gone sun kashe mun shi. Last words dinsa sunamin yawo ina ganin jinin dan uwana a kasa nasan azaba ya riga ya gama shanta tun kafin na fito wanka. A tym din last decision dina shine na dauki wukar na kashe kaina. Hakan yasa na dauko wukar dede na dauka knn sega su Abba isa da kuma wasu yan gidan wai sunji wanin mu na ihu gani na da wuka da kuma gawar saif yasa suka rinka kallona na fashe da kuka ina kallon Abba isa.  Kafin nace komai ya daka mun wata tsawa. Snn yazo ya dauke ni da mari. Ya karamun wani. Yana tambayana wane fada mukayi da saif har na kashe sa. I was trying to tell him amma yaki saurarena. Hada ni da securities snn ya kira police.  Basu barni naga sallahr dan uwana ba basu barni naga rufe sa suka tafi dani.  Har dan karamin hauka nayi I even try beating the police sbd yanda nakeji a raina.  Na kasa yarda seif ya tafi ya barni. Shknn ya tafi Duk da a tym din bn isa dauri ba aka wuce dani gidan yari dukda can din a rufe nake.  Tun ina haukan su barni har na hakura na zauna.  Ban tabajin na tsani dad da matar sa ba se ranar. Da ace be tafi ya barmu ba da ba ayi poison mum dinmu ba da bamu sha wahala. Da ba a kashemun twin brother na. Naji na tsani kowa last word din saif na dawo mun. Yace na kula da mum karna gaji da ita yace yana son mum nima yana sona amma be fadi dad ba hakan yasa na gane yana fushi dashi. Seif yabar duniya yana fushi da dad. Seif ya tafi ya barni saboda sakacin Dad.babban damuwa na shine idan mum dina ta tashi taga seif ya rasu ya zataji.  Lokacin zuciyana ta gama bushewa naji bana son kowa na tsani kowa kuma inaji cewa zaman kaina nake inaji cewa Allah ya barni da rai sbd mamana. Mum dina itace rauni na. Kamar yanda fansar jinin dau uwana shine babban abinda na saka gaba bayan lafiya mum dina. Labari ya gama bude duniya cewa Yaron Ali Abbas ya kashe dan uwansa. Wnn labari ya zagaya inda baki tunani.  Seda nayi shekara daya kwatsam sega Dad dina yazo fito dani. Nida shi babu wanda yayiwa wani magana dan a tym din shine number one wanda na tsana a duniya. Bn tsani Abba isa ba sbd inaganin yayi ne bisaga rashin sani sbd yana ganin abinda nayi wa dan uwana ba haka bane.  Tunda muka dawo gida hajiya Atika ta jani a jiki kulawa sosai tana bani. I was thinking Dad ze tambaye ni mum da dan uwana amma shiru duk da ya cironi babu ruwansa dani nima a tym din ko ganin sa bana sonyi yanayina ya sauya bana magana bana dariya magana ma bana so. Ganin yanda nake shiga cikin damuwa yasa Atika ta fara bani wine and unknowngly nake sha ganin idan nasha ina samun saukin ciwon da nakeji a zuciyata yasa koda yaushe ta bani nake sha idan ma bata bani ba nida kaina zance ta bani wasa wasa har na saba bnsan cewa illace ga lafiyata ba. Se watarana na kamata tana waya wai yau dad yayi mata fada kaca kaca akan dansa sbd yace ze maidani makaranta tace aa ya fara mata fada wanda da baya yi. Nan na labe naji komai. Tana cewa dama boka ya fada mata duk lokacin da yayi idon biyu da yaran sa ko matar sa asiri ze karye. Suma sauran baze taba tunawa dasu ba se ya gansu   Snn anan nakeji wai ai koma me zeyi ta riga tamin dafin da har in mutu baza ataba ganin mutuncina ba saboda ta koyamin shan giya snn mum dina da seif shi dasu har abada.   Aikin da ta dade tana shiryawa baze rushe ba. Anan na gane cewa itace silar da tasaka dad dinmu ya barmu anan na gane kilama ita ta kashe seif rashin lafiyar mum dina da kuma rayuwata da take fadin ta lalata. Bansan tym din dana shiga na shageta ba. Ina ta tambayar ta me memuka mata ta shiga tsakanin mu da Dad. Tana kokarin tureni amma ta kasa dan shakewar ba zata nayi mata.  A haka dad yazo ya sameni

Urs
✨✨✨
Annafie😍💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
              ANNAFIE💖…✍️
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
💫💫💖Jalal Alii(32)💖💫💫
Da kyar dad ya iya banbare ni a jikin ta kalman I hate you kade take fita bakina. Nace sena kashe ta Dad ne ya kama ni muka wuce dakin sa.  A ranar dad ya gamamun processing komai na makaranta secondary gidan da zan zauna da komai da zan bukata a Americans. Washe gari shida kansa ya kaini ya nuna mun komai snn ya dawo dani gidan da zan zauna kome na more rayuwa Dad ya bani. Har lokacin kuma bana masa magana. Daze tafi ko daga ido bnyi na kallesa ba hakan yasa ya juyo yana kallona yace “am srry son. Bansan me zance maka ba but kayi hakuri wlh ina sonka I dont knw what came over me amma kayi hakuri pls kayi karatu kome kakeso a duniyar nan zanyi maka” tym din ya bani tausayi saboda nasan bayin kansa bane. But I wonder meyasa baya tambayar mum da seif. Sena tuna nima seda ya ganni ya tuna dani. Wnn yasa na yafe masa.  Na fara sch a America kuma ina maida hankali sosai. Anan na saci kafa naje china anan na gano mahaifiyata. Ina sonta kuma a duk lokacin dana ganta sena tuna da Kalaman seif a ranar na gane cewa komai na mamy ya kare. Ta sayar da komai nata akan maganin mum dina. Kudin asibitin ma harda bashi sbd koda yaushe suna bata kulawa ta musanman ta yanda babu wani abu na jikin ta daze samu matsala. Ina da wasu agogon gold da Dad ya bani suna bayar snn nayi ciko dan  huge money din da akebin mu seda suka sayi gold din. Koda na koma bnd kudi kuma bn kira dad ba da wnn hanun nawa nake akin karfi na nemi abinda zanci kafin ya turomun. Yana turomun kuma nake turawa mamy ni kuma duk abinda zanci da karfi na nake nema. Wnn hannun da kike gani shi kansa yaga rayuwa Maganar drinking habit dina kam se tayi gaba. Tym din da dad yayi visiting dina ya sameni da kwalaben wine Kuma bani da kudi yayimun fada sosai wai banama karatun shaye shaye nake anan nake kashe kudina. Na tashi na kallesa ido cikin ido nace ya kyaleni a yanda nake rayuwata ce. Beyiyuwa besan yanda akai nayi surviving ba kuma yazo yana fada wai bnyi dede ba idan ze iya zama dani a haka ya zauna idan baya iyawa ya barni.ai ba rayuwar sa bace.  A ranar dad yayi kuka sosai ganin dansa ne a cikin wnn rayuwar yaro daya tilo daze iya nunawa duniya cewa nasa ne. Ya bani tausayi a tym din amma na dake. A ranar na gane cewa yana mugun sona sbd kukan dayasha ya bani hakuri sosai snn yace mun ni dansa ne baze yarda ni ba kuma nasani cewa sbd sauyin halina baxe barni ba ze zauna dani a kowane hali snn ze yi kokarin ganin nayi farin ciki. Ranar duk wata soyayyar dad dina ta dawo sede inaji a raina farin cikina ya tafi tunda na rasa dan uwana. Kila se idan mum ta dawo rayuwa kamar kowa ..daga lokacin dad ke kawomun ziyara akai akai amma hakan be hana komai daga rayuwata ba. Kuma daya turomun kudi zan aikama mamy. Wlh idan kika ganni ina aikin karfi bazaki taba cewa ubana yana daga cikin masu fada aji ba. Architecture shine course din dana karanta. Tun ina 100level na fara samun kudin da course din. Na iya zane fiye da tunanin me tunani. A tym din ne na fara zama jalal na tashi daga maraya. Na dena aikin karfi sede kudina suyi mun Dad besan Ina samun kudi ba dan bebar turomun ba na koma daukar dawainiyar mum dina da mamy da komai da suke bukata. Kafin na gama nasamu kudi fiye da tunanin me tunani idan kika ganni bazaki taba cewa nine wanda nasha wahalar nan ba shan wine kuma se abinda yayi baga am already addicted. Ina gamawa company’s sukayi mun caaa ba America kade ba har dubai. Babu wanda nace zanyiwa aiki sbd ina so na dawo nigeria na dauki fansa. Ina son sanin me mukayi mata nasan bani da hujjar kamata sede zan dawo na nemi wanda ya kashe seif shine abinda zanyi. Maganar mum kam bn taba given up ba.  Bna aiki a kowane company sede ynx haka a dubai inadaga cikin manyan manyan masu zane.kinsan babu kasar da takai dubai kawata kasar su Suna biya na huge amount of money din da ko dad dina yaji seya firgita. Haka ma kasar America da kuma wasu manyan companies na duniya babu wanda yasan da wnn se mamy da kuma sageer. Na nemi a boye ne sbd inaso sucigaba damun kalon sakarai wanda giya ta lalata kuma me takama da kudin ubansa da kuma soyayyar da yake mun ba tare da sun san cewa nidin young billionaire ne ma ba wanda babu kasar da bazan iya cewa ni me kudi bane. A cikin manyan companies din Nigeria inada shears har kuwa dana Dad dina. Bazan ce nafi Dad kudi ba Sbd bnsan iya dukiyar sa ba Amma nasan zan iya gwabzawa dashi a ko inane ma. Mum na samun kulawa ta musamman sbd kudin da nake bama asibitin ya wuce misali. Dad be dena bani kudi ba kuma bn dena amsa ba ko result dina bn nuna masa ba ballema yasan nayi abin kirki ko bnyi ba shide burin sa na zauna tare dashi inde kudi ne zemun duk abinda nake so. Dad dina ya bani tausayi sosai sbd anan na gane ze iya komai a kaina na gane cewa ya dauki son duniya ya dauramun. Inason dad sosai nima dan shi kade nakejin zan iya dagamawa kaf cikin nigeria har kuwa yan uwansa. Ranar da zan dawo irin tarban da ya shirya ma daban ce. Dan comboi akamun da motoci 20 duka nawa a baya an rubuta DEEN da kuma number ga security ta ko ina. Ranar na shigo nigeria da burika kala kala babu sauki a zuciyata dan bn dawo da niyar girma ma kowa ba se mahaifina. Ni kaina naji dadin abinda Dad ya shirya mun.   Muna cikin tafiya kafin na shiga mota wani daga cikin mutanen baba na naji yace “ji wanda yayi kisan kai ne akema wnn tarbar kisan kam ma na dan uwansa” ya fadi maganar ne dan naji he tought irin masu hakurin nan ne dazan kyalesa kodan saboda yana tare da dad kuma ya girme ni. Juyowa nayi ta kallesa babu alamar wasa a fuskata. Bnyi wata wata ba na dauke sa da maruka har hudu tsit akayi ana kallona shi kansa kallona yake snn ya kalli dad din yaji hukuncin da ze dauka. Kafin dad yayi magana nace “kode wnn kar ya sake yabi comboi din nan kuma ni da koma” dad yasan ba karamun aikina bane dan haka yace da wnn kar yabimu ze tura masa mota daga baya. Wnn yabama mutane dayawa mmki na wane irin so dad kemun. Tun kafin na karasa ga mota aka bude mun cike da ladabi. Na shiga. Wnn abun da nayi a airport kafin na karasa ya bude ko ina ana fadin “duk da nayi kisan kai amma dad yake nunawa duniya soyayyar sa gare ni.   Har na wulakanta wani nasa amma ya kasa komai.
Koda muka koma gida duk wanda ya shigo da niyar gaisheni sede na daga masa hannu babu wanda na gaisar apart from dad dina. Atika kam na zuwa na dakatar da ita.  Nayi mata tsawa nace tabar wajen. Kowa ya tsorata da dani dan babu wata fuska da mutum zemun kallon banza.   Dad ya mallakamin gidaje dayawa kuma nayi farin ciki. A ranar wani security da yayi delay wajen buden gate yabar gidan da dare kuma a ranar dad yasa wani. Kowa ya tsorata da sabon wukancin dana shigo dashi.   Har nayi kwana uku bnje na gaisar da kowa ba sede aje azo a gaisar dani. Atika ta mugun shan jinin jikinta sbd ta gane jalal din ynx bana da bane. Bama ita kade ba kowa a gidan shakkata yake. Hatta family dina babu wanda nake sakarwa fuska. Da kyar daddy na yayi convincing dina na fara zuwa wajen granny se kuma daga baya naji duk bn kyauta ba sbd suma kila duk rufe masu baki akayi su manta dani a hankali a hankali na fara sabawa dasu da kuma yan uwana sede kaf cikin su kowa na shakkar shiga trabt dina. ..anan ne abba isa yake tambayana game da mum shida Alh barau naji dadi bn nuna masu nike biye ba sukace zasu taimaka mun. Bn nuna masu komai ba. Dan haka sukaci gaba da bada tasu gudmmuwar naji dadi sosai hakan yasa suda iyalansu sukeda girma a idona.   Maganar giya kuma bn dena sha ba ina nan ina zuwa inda ake sha. Sede mene abinda ta bnsan ya akai ba wai sega police sunzo gida wai zasu kamani nayi committing wai crime an shigo da drugs  Kuma nine na shigo dasu dad yace su bada sheda babu. Bayan kwana biyu akazo wai anyi case din raping iyayen yarinya da yarinya suka zo wai nine yarinyar ma tace dad yace sheda sukace babu wnn dalilin yasa iyayen ta suka fusata wai an nuna masu karfin iko kafin kice mene labari ya bide ko ina. Inda duk suka zuciya suka fito wai tunda bza a dauki mataki ba su rinka yada kome ake idan an nuna masu karfin iko da kudi ai baza a nuna masu baki ba.  Bn taba commiting crime ko daya da ake fada ba. Babu wanda yasan haka se sageer da kuma wasu mutane na irin su saleem da kuma bature. Ko dad be sani ba. Yanda ake fadin laifukana a social media abin seya fara daure mun kai harda kuma me amsamin wanda nayi iya bincikena na kasa. Nasan abin yana damun dad Amma babu yanda zeyi sbd yana son. Abu daya kawai ya fada mun shine bazeyi tolerating rashin kwana gida ba. Wnn yasa nake kiyayewa sbd ina son dad dina kuma banaso na rasa shi a karo na biyu. Dalilinsu nayimun abinda sukemun ne shine bansani ba. Hakan ya kara karfi wajen drinking habit dina sbd abin na damu na am just trying to be ohk but am not. Lokaci daya kasar nan aka faramun kallon bad boy me aikata munanen ayyuka kuma na amsa sbd babana ya dauremun gindi. Ni kuma se nayi tunanin zama banza irin abin be dameni ba nabar komai nawa a sake dan naga dan a dauka harkar giyana kawai na sani bn damu da komai ba. Bana aikin komai se kudin dad dina. Nasan dayawa suna tausayawa rayuwata cewa idan babu dad ya zanyi. Dad ya damu da drinking habit dina sosai dan shine kade wanda ya sheda inayi kuma nake nunawa kowa. Ni kaina inason na dena sha kodan dad amma na kasa atika bata bar sakamun wine a fridge ba har ynx kuma bn dena sha ba sbd ina bukatar ta. Na riga na saba. Babu wani komai nawa da nakewasa security komai na barsa sakaka sbd subar wani slide mistake tunda sunamun kallon wawa. Sede ina bincike ta karkashin kasa musamman munanen halayena da ake yadawa inada hanyar kamasu amma so nake naga karshen su yanda zasu kama kansu da kansu kinsa ance idan baka iya kama barawo ba shi seya kama ka shiyasa na barsu. Bangaren su mom kuma wadan da nake zargi ma basu bane ba. Ya kalli imaan da idanun sa da sukayi jawuur yace “am not bad but I will soon be bad” amma wlh duk wanda ke shiga gona ta seya dandani azaba me tsanani. Masu batamun suna kuma we shall see. Sosai imaan take kuka shin wann wace irin rayuwa ce jalal yake ciki lallai yayi facing rayuwa kuma yana kan facing.   Janyota jikinsa yayi ya rugume ta thanks imaan thanks for changing my lyf from a drunker. Hakan shine babbar gudunmuwar da har dad dina be bani ba. Inason na bari sbd dashi amma na kasa but ta silar ki na dena.  Dagowa imaan tayi tana share hawayen ta tare da kamo hannun sa “inshallah zan taimaka maka with all i can do dan ganin bayan makiyan ka hakika sun bata maka suna Amma inshaallah nan gaba kadan sune masu kuka. Mum kuma zata samu lpy ta izinin Allah”.   Sosai jalal ya janyo ya rungume ta hakanan yaji ya samu saukin abinda yakeji a Zuciyar sa  dama ance a problem shear is a problem solve.  Sun dade a haka kafin tace. “ muje kayi breakfast”. Babu musu ya kama hannun ta suka tafi dining ta zuba masa langwabar kai yayi tare da nuna mata cinyar sa. “Nide ni dawo nan ki zauna” a hankali ta tashi ta zauna ya zagaye dan tummy dinta snn yace “oya feed me”.  Babu musu ta shiga basa abincin a baki seda yaci ya koshi snn yaje dede kunnen ta ya rada mata “wife jiya bnyi ba fa”. Lumshe idanu tayi. Dan hakanan wani tausayin sa take ji kawai tana so ta saka sa farin ciki. Dole ta yarda. Bayan kome ya lafa suna toilet cikin bathtube. Sun dade ciki bamusuda niyar gama yanka. Se cuda ta yake itama haka. Tace “to ynx dad ya akai ya barka kazo nan”. Jalal lumshe idanu kafin yace “Dad be sani ba na fada masa ina lagos. Hakan yasa ya fara tunanin na shiryu. If he find it cewa bana lagos zeyi fushi dani. Cos naga bacin ransa ranar da bn kwana gida ba. Ya janyo ta jikinsa tare da daura kanta a chest dinsa snn yacigaba “naga bacin ransa sosai. Ina son dad dina shine kade gareni banason bacin ransa dan haka nake kiyayewa. Maganar munanen halaye na kuma bawai be yarda ba. Ya yarda sbd drinking habit dina sheda ne. Sede bawai ko wane ba wani ze dauka cewa frnds dina ne zasuyi wanda a ganin sa nine na daure masu gindi shiyasa yajamun warnings kome zanyi bnda rashin kwana gida dan baze dauka ba. Cikin kwanakin labaren da ake yadawa nasa ze dauka cewa abokainane. Bamashi kade ba yan gidan mu gabadaya. Sede amsawar da nakeyi itace suka rasa dalili sunsha tambaya na meyasa nake amsawa. Sede Kawai nace masu idan nine fa  babu wanda na bama fuskar daze cemun meyasa nakeyi suma a ganin su na riga na zama bad. Shi kansa dad tsoron fadan yakemun kar nace zan tafi. Sede Abinda baze dauka ba shine rashin kwana gida kuma ina kiyayewa. Dan banason bacin ransa.   Sosai imaan takejin tausayin sa da mamakin meyasa ake shiga rayuwar sa haka sede bata raba dayan biyu. Dan dukiyar baban sa akeyi tabbas tunda inde har dansa ya lalace to bashi da wani magaji kuma idan har ana nunawa duniya cewa dansa lalatacce ne to hakan ze rinka affecting dinsa watarana har ya yanke jiki ya fadi. Snn shima jalal din kashesa zasuyi. Kamar yanda atika take da shirin yi. Suma masu shiga rayuwar jalal din karshe kashe sa suke da shirin yi. Suna abinda suke ne dan su jefi tsuntsu biyu da dutse daya. Su kashe uba su kashe da. Dan tabbas abinda sukeyi ba sunayi ne dan ya rayuba. Tanaji a jikinta dan dad sukeyi. Kuma ko suwane sun san da plan din atika. A yanda ta fahimta shine ita atika tana harin rayuwar jalal ne kamar yanda tayi a baya akan tasiu aka rigata.ita da falalu waddu. Kuma har ynx cikin cikin harin ta take yanda zata samu damar mallakar dukiyar babansa ita da erta.. imaan ce ta shigo rike da cup din tea ta mikawa jalal dake ta faman danna system   Ya karba tare da fadin “ tnx wife” ... ta zauna gefe kafin tace “shi wnn rubutun da kakeyi kullum na menene wai”. Dagowa yayi ya kalleta. Kafin yace “ina ajewa mum ne. Taga irin rayuwar da danta yayi bayan kwanciyarta rashin lafiya” jikin imaan ne yayi sanyi. Tasan bazata iya ma kamanta yanda jalal yakeji a zuciyar sa ba but she knws he’s in pain. His heart is sad. Kawai wasu sbd jin dadinsu sun maida masa rayuwa haka duk da gatan da yake dashi. Gsky she have to do something dan ta taimaki rayuwar sa. Tanaso ko bayan rabuwar su ne ace tabama jalal gudunmuwa. Tasan duk ranar da mum ta samu lafiya taji labarin danta setayi kuka sosai taji tausayin danta fiye da kanta. Gsky jalal mutum ne me hakuri da tawakkali da wani ne da ynx ya manta da mum dinsa ya kama hanyar gabansa. A ynx yanda labarin Jalal ya bude duniya babu wanda zece ba haka bane se randa Allah ya bayyana gsky. Tanaji ji ajikinta allah ya hadata da jalal ne dan ta bada gudunmuwar taimakon sa shiyasa har sukayi aure kuma har ya fada mata haka bayan ko mahaifinsa be sani ba. Kuma inshaallahu ko bayan rabuwar su zata taimaka masa.  Muryar sa taji yace “kinsan har da auren da mukayi dake duk na rubuta”. Imaan tace “nida zamu rabu dama baka rubuta ba”. Dagowa yayi yana kallon ta. Snn yace “tun ranar dana fara ganin ki seda na rubuta. Cos ranar bnsha giya ba sbd draman da kuka buga da wnn gayen I knw she will enjoy it cewa danta besha giya ba “ murmushi imaan tayi. Snn tace “to shknn amma de shiknn kasaka ko” ture system din yayi ya janyo ta jikinsa snn yace “nop ganin da nayi maki na biyu ma bansha ba. Ke all those 4dys dana ganki bnsha ba. Sbd ina ganin ki da deferent characters so tunaninsu na hanani drinking. And you remember our first kiss duk na bata lvri”. Ware idanu imaan tayi. Tace “why kana so ko mun rabu naitajin kunya ko “ yaja hancin ta “see you kunyar me bayan babu abinda bamu aikata ba. Idan ma tace meyasa nayi zance. Kawai I have feelings for the girls idan ina tare da ita bana iya controlling kaina beside komai ma na rayuwar mu na fada mata ko mun rabu my mum will knw you”. Boye fuskan ta tayi a jikin sa tana rokonsa dan Allah yaje ya goge amma yaki. Dole ta hakura.  Yanda sukacigaba da rayuwar su yanda kasancewa basu san cewa rabuwa zasuyi ba. Kamar de yanda suka tsara komai imaan tana masa duk wani abu de ze saka sa farin ciki shi takeyi. Shi kansa jalal ya rasa tayaya ya shaku da ita fiye da kowa. Idan yana tare da ita yana cikin farin ciki koda yaushe. Duk wata kalar yarintar ta babu wacce baya biye ta. Sede yasan duk da yarintar ta tana da hankali   Barin yanda ta nusar dashi Addini dan tasaka sun dage seyiwa mum adduar samun lpy suke. Snn kuma tace ya kamata a sayawa mata asibiti daga china zuwa saudia. Kuma kar wanda ya bari ya sani bayan sageer. Yaso yace aa sageer yace ayi haka. Dole ya hakura ya fara processing dan long process ne. Kuma tace ya jaraba maganin addini kila yafi na turawa. Sossi yaji dadin yanda ta damu da mum din tasa.   
Yau imaan tunda asuba ta kasa komawa bacci se juye juye take tana kallon jalal dake baccin sa hankali kwance. Can ta tura baki ta fara tashi sa. Bude idanun sa masu cike da bacci yayi. Ganin yanda ta tura baki yasa yace “what’s wrong wife” “nide ka tashi muje exercise”. Ware idanu yayi “exercise kuma ynx” ta gyada masa kai “kuma ba a gidan nan ba”. “Wife bacci nake ji why not in the evening”. Kukan shagwaba ta fara yi masa dole ya tashi ohk muje tashi ki shirya”. Ya noke kafa tayi kamar zatayi kuka tace “nide kaine zaka shirya ni”. Babu yanda jalal ya iya dole ya fara shirya ta inde imaan ce yasaba kadan daga aikin ta knn. Sunyi kyau sosai cikin kayan sport din.   Yana cikin driving tace “yaushe zaka koyamun mota” murmushi yayi kafin yace “yaushe kike so”. “Yauda evening” yace “an gama uwar gida sarautar mata”. Imaan ta murguda baki.  
Kayataccen wajen motsa jikine sukaje. Tunda zasu shiga tace ya siya mata popcorn be musa ba ya siya. Suka shiga. Da sukaje se cewa tayi yayi she will watch him ita bazata iya ba. Ya kama kugu yana kallonta “kefa kikace zakiyi”. Kamar zatayi kuka tace “nide kai nakeso kayi”. Dole ya fara exercise din a ransa yana fadin yau kuma rigimar imaan ta safe ce knn. Haka kam akayi yanayi tana cin popcorn dinta shima kansa se yaji dadin abun shi yana exercise watching her eating popcorn happily se yaji abun ya birgesa  a haka har ya gama babu abinda tayi. Tace masa yazo suyi judging. Babu musu yaka kama hanun ta suka shiga dan filin judging din suna zagaye sunayi suna lvri imaan nayi masa shirme yana biyeta. Seda rana ta fito snn yace su koma.  Ta shige jikinsa suna tafiya a hankali har zuwa mota. Tunda suka taho akan idon Zulfa da tayi kusan mutuwar tsaye tana kallon sa. “dama jalal na cikin garin nan yaushe ya dawo. Wai mene tsakanin sa da yarinyar nan yaushe jalal ya santa ne yaushe ya fara kula mata da yake biyewa yarinyar nan suna wnn iskancin   Har motar su tabar wajen bata bar kallonsu ba  jin an dafa ta tabaya ne yasa ta juya da sauri. Tana kallon kyakkyawar budurwar Jiddah tayi murmushi tace “uhmm kema suna birgeki ko”. Kabar da hannun ta zulfa tayi cike da masifa snn tace “Dallah rufemun baki Allah ya kyauta su birgeni wlh bazasu taba ba inde har da waccan shegiyar yarinyar ce”. Wani irin murmushi jiddah tayi kafin tace “koda ita bata birgeki nasan shi yana birgeki cos in all indications sonsa kike kamar yanda nakesonsa  shiyasa kike kishi da matar sa” “what matar sa fa kikace. Ai yaya jalal bashi da wata mata sama dani sbd shidin gidan mu daya ni er uwar sa ce kuma nice zan aure sa”.  Cike da confusion jiddah tace “you mean waccan ba matar sa bace”. Zulfa ta girgiza kai. “ yaya jalal bashi da aure domin kau gidan mu daya dashi bama ya garin nan yana lagos mamakin ganin sa nake anan”. Wani irin murmushi jiddah tayi kafin tace “aikam yana garin nan dan ina yawan ganin sa sede idan ku yashuka. Thought ma matar sa ce cos they’re together all the tym” Zulfa da zuciyar ta ketafar fasa tace “ba matar sa bace yaya jalal baya kula mata”. Jiddah tayi murmushi “karuwar sa ce knn” kasa magana zulfa tayi zuciyar ta na tafarfasa ta rasa me waccan take basa da ita baze zo ta basa ba. Wlh inde jalal ne she’s ready to give him everything. Kuma tunda ya zabi waccan akanta to a yau sede duka rayuka su baci dan seta tona masa asiri seta fadawa dad cewa babu inda yaje yana cikin Abuja tare da da wata suna karuwanci yau sede ayi baran baran tasan dad baze dauki wnn ba. Sbd a duniya shine kade sharadin daya kafa masa.  Jiddah tace “idan kuma baki yarda ba har gidansu nasani sbd akwai abinda yarinyar ta tabamin nace nikam sena san inda suke dan a da nayi alkhawarin sena rabata da mijin nata. Amma tunda ynx na gano bama mijin ta bane fine babu wani shamaki ynx. Da sauri zulfa tace “pls kaini gidan” ware hannu jiddah tayi kafin tace “let go”. Motar jiddah suka shiga. Inda zulfa keta sake sake a cikin ranta. 
Boooom🥰😻. Bari mu bada hutu 😻 zamuje hutun sallah daga yau. Aje ayi kitso ayi kunshi ayi aikin sallah 😂 nima zanje inyiwa mijina. Kowa ya kawomun naman sallah 😂. Inshaallah Allah zuwa bayan sallah taurarun naku jalal da imaan zasu dawo. Ya kuke ganin za a kare. Shin kuna ganin cewa zaman imaan da jalal ze cigaba da dorewa koko kucigaba da bin Annafie.😍 small but mighty 😉 kunsan bata littafin banza dan haka mu hade daku bayan sallah 🥰 thank you
07051376476 what’s app number

Urs
✨✨✨
ANNAFIE😍😍💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
              ANNAFIE💖…✍️
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
💫💫💖Jalal Alii(33)💖💫💫
Fashewa da kuka zulfa tayi zuciyar ta na wani irin tafarfasa. Snn ta kalli jiddah tace “ngd”. Daga haka ta tari wani abun hawa ya maida ta da dauki motar ta ta wuce gida. 
Koda suka dawo. Jalal ne yayi mata wanka. Manma shida kansa yake shafa mata. Ganin yanda ya dade a shafa man yasa imaan tura baki tace “wai har ynx baga gama shafa man ba” jalal ya dan langwabar da kai snn yace “wife skin dinki ta kara wani taushi kin kara wani haske da kyau look at ur boob fa sun wani ciko Awwwn”. Yayi maganar yana dan shafawa. Kamar zatayi  kuka tace inajin yunwa fa. Ya langwabar da kai amma de after breakfast zaki bani nasha ko “ ta gyada masa. Wani doguwar riga ya dauko ya sakamata. Seda ya gama ta shirya sa snn ta kama hannun sa zuwa kitchen. Seda sukaje snn ta nemi waje ta zauna “you will prefer breakfast for us” wani zaro ido yayi. “Wife  i can’t cook idan bazaki iya ma dauko hijab dinki muje muci waje”. Ta noke ka fada. “ i want ur own”. Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace wife nifa bn iya ba I dont even knw where to start” tace “am here zan koya maka komai” Murmushi yayi yade kula yau rigima takeji “Ohk me zamu dafa”. “Kawai muyi wainan flour bame egg ba. A sakamun onion dayawa”. Tsaye yayi yana kallon ta a sanyaye “mene kuma wainan flour kawai mu soya egg or indomie. I don’t even knw where to start. Ni nasan wani wainan flour ne” noke kafa tayi snn tace zan koya maka. Babu yanda ya iya. Dole ya debo flour ya kwaba tana nuna masa ya yanka albasa dayawa kamar yanda tace idon sa duk yayi ruwa. Ta saka tissue ta share masa. Snn ya fara suya. Ko daya bata taya sa ba duk yayi wani iri har suka gama ta dauko suna dawo parlo ya hada masu tea sukasha. Kasa cin wainar flour din yayi itakam taitaci abinta. Shi gashi wata ta kone wata ta dame amma haka taci hankali kwance. Shikam tea ya hada abinsa yasha da bread yana mmkim ita meyaja mata cin wnn kuma yau din nan.   Tana gamawa ta dawo parlo ta kwanta. Shikam komawa daki yayi yay wanka ya sake shiri ya fito se kamshi yake. Yayi kyau cikin kananun kayan. Tunda ya taho imaan kallonsa take yazo ya zauna gefen ta tare da janyo ta jikin sa. Ta kwanta a chest dinsa tare da tusa hannu ta ckin rigar sa ta shige jikin sa sosai tana shakar kamshin sa. Yace “wife am going out zamu fita tareda sageer akan mayar da mum saudia. Gyada masa kai tayi. Ya shafa gefen fuskar ta kafin yace “wife are you Ohk”. Gyada masa kai tayi yace” me kikeso na taho maki dashi”. Girgiza kai tayi kafin tace “ ka dawo ka karayimun wainar flour”. Ware idanu yayi “wainar flour again “ gyada kai tayi tana daure fuska”. Murmushi yayi kafin yace “alryt wife zan maki amma ki sani today idan na kamaki ko I will spend the whole day and nyt on you”. Murmushi tayi kafin tayi kissing dinsa a gefen fuskar sa tace “bye”. Dan lumshe idanu yayi kafin yace “wife sena dawo”. Daga haka yayi mata light kiss a lips din ta snn ya tashi yana daga mata hannu. Ya rasa yanda akayi ya saba da imaan tundaga farkon haduwar su ze iya cewa itace mace ta farko daya taba sabawa da ita tunda yake. Kuma mutum ta biyu daya shakuwa da ita bayan sageer a rayuwar sa.  
Hajiya Atika ji tayi kamar tayi tsallen murna bayan zulfa ta gama fada mata komai tana kuka kamar ranta ze fita. Amma seta dake. Tana nuna rashin jin dadin ta snn tace “gsky wnn ba abin da za a boyewa dad bane dole na kirasa a waya na fada masa. Duk da yau ze dawo kasar nan amma kafin nan kije ki fadawa granny yakamata tasan halin da ake ciki wama yasani ko asiri tayi masa jalal da babu ruwansa da mace” wnn last word din na mama shine ya kara tunzura zulfa ta tafi.  Tanajin yau kila seta saka an daure yarinyar nan.  
Granny na parlon suna breakfast harma da yaran gidan yaran alhaji isa da matar sa. Yanda ta shiga tana kuka yasa duk suka mike suna tambayar ta lpy. “Cikin kuka tace jalal ne”. Granny tace jalal kuma. Ke ina kika gansa jalal da yana lagos”. Nan ta fashe da kuka tace “wlh babu wani lagos din daya tafi. Yana cikin Abuja nan ta kwashe komai ta fada masu”. Tuni suka shiga sallallami. Granny tace “zulfa bana son shashanci fa”. “Granny idan baki yarda ba kizo muje kiga inda suke wlh da gske ne”. Ggranny da ranta ya gama baci tace na hajiyar su sumy “kiramun Alh isa. Yazo muje mu gani inde kam har da gske ne Jalal ya aje karuwa to iskancin sa yakai.tunda harma da cin amanar ubansa.  Koda yake ai shi uban ne ke daure masa gindi to yazo yau sede ya zaba koni ko wnn dan da yake jawo mana magana. Amma baya iya daukar mataki. Nima ai uban nasa kade na haifa amma hakan be hana na basa tarbiya ba yau sede yazo ya zaba koni ko wnn yaron. Da baya tsoran kowa baya tsoran jamana magana.
Mama kam tuni ta kira kawarta. “ kinga kizo a kwashe ta dake dan kila yaune ranar cikar burin mu dan ina zaune zulfa tazo min da zance. Nan ta kwashe komai ta fada mata. Ta karashr da fadin kiyi sauri kizo ayi dake. Suna gama wayar tayi wani tsalle. To mashayi yaude zaka gane kurin ka semuga ta tsawa da nuna iko da uba sakarai kawai babu abinda ya sani se giya.  Mayafin ta ta dauka ta nufi part din granny.  Sanda Abba isa yazo sbd kiran da granny ta saka akayi masa. Da yaji abinda ke faruwa he was shocked shi kansa seda yaji ransa ya bace. Sede shi yaso yaje shi kade tare da zulfa. Amma granny ta dage setaje. Dole ya hakura. Hakan yasa mama ma taja su sumy da sauran yan gida da hajiya huwaila data karaso sukaje ....
Imaan ta dade wajen kwance kafin taje tana mugun son taci peanut. Tashi tayi a hankali ta nufi dakin ta da a ynx seta kwana ta tashi ma bata shiga ba. Hand back din ta dauko ta duba idan tana da cash. Ganin da kudi ciki yasa ta dauko. Ta bude wardrobe ta dauko hijab zumbulele har kasa ta saka. Me gadi zata aika yayi sauri ya kawo mata. Tana dede balcony din ta hango Abba isa ya shigo granny na bayansa. Suna magana da me gadi. Duk tana hango su. Kafin taga sun nufo cikin gidan a hankali a hankali suka fara shigowa. Gabanta ne ya fadi gani sumy zulfa da wasu yan gidan su jalal din. Juyawa tayi ta koma parlor jikin ta na rawa tana tunanin me zatayi. Tunanin kiran jalal ne ya fado mata. Hakan yasa ta nufi stairs sede ko karasawa batayi ba taji. Muryar zulfa. “Abba ka ganta ko wlh da gaske itace karuwa ya aje a gidan nan”. Cak imaan ta tsaya gaban ta na wani irin faduwa. A hankali ta juyo tana Kallon su Abba granny da sauran mutanen gidan. Idon ta tasauke akan sumy dake mata wani irin kallo a irin wai imaan ce. Ita kanta sumyn she was shock. Ynx dama imaan ce. Tabbas bazata manta ba itace silar haduwar su. Ta tuna sanda ya amshi wayar imaan din. Tasaka ya maida ta gida. And washe gari ta ce ta rakata part din su jalal bata shiga ba tace waya zatayi latter on ta dawo bata ganta ba sedaga baya kuma tace masu ta tafi gida. Da sukayi waya kuma tace jalal ne ya maida ta. Ikon god lallai mace daban ne ynx har imaan ta iya jan raayin yaya jalal koda yake namiji akan jikin mace mene baze iya ba. Amma imaan ta bata mmki granny ce tace “wacece ke“. Shiru imaan tsyi idanun ta na tara hawaye ganin irin wnn zugar da sukayo mata. Hajiyan su sumy ce tace ”ba imaan bace kawar sumy”. Zulfa tace “itace munafukar na dade ina ganin su tare har kiss naga sunyi a gidan mu”. Granny da sumy data kasa dauke idon ta akan imaan ta tace “itace Abba kawata ce”. Granny data fusata tace “sumayya meyaja maki kawance da karuwa”. Fashewa da kuka imaan tayi “wlh bahaka bane”. Wata tsawa granny tayi mata “rufemun baki idan ba karuwanci ba mene kikeyi a gidan namiji”. Girgiga kai imaan ta shiga yi. Abba isa yace “zo yarinya”. Kafin ya rufe baki granny tace babu inda zataje. Zoki bar gidan nan zulfa da sumy ku kwaso mata kayan ta. Abba zeyi magana granny tace “zan saba maka daga Alin har jalal din zasu zo su sameni yau sede Ali ya zaba koni ko dansa inde har baze iya daukar mataki akan shashashan yaron sa ba. Hajiya huwaila ce ta fizgo imaan ta kifa mata mari “bakiji ana cewa ki bar gidan nan ba hada kayanki ki tafi gidan uban ki er matsiya ta kawai yarinya karama dake kin iya karuwanci”. Fashewa da kuka imaan tayi yayin da hajiya huwaila ta watsata waje. Zulfa kuma suka shiga dakin ta suka janyo trolleys dinta suka watsat mata.  “Matsiyaciya sekin rabu dashi yau din nan” cewar zulfa. Sumy tazo tana kallon imaan. Wlh nayi danasanin sanin ki a rayuwata ashe haka halin ki yake. Girgiza kai imaan tayi tana kuka. Granny ta fito kwashe kayanki kibar gidan nan wlh na kara ganin ki sena saka an daure kaf dangin ku. Snn shima Ali nasan ya kusa isowa kasar nan. Isa jeka dauko sa ka kawosa nan yaga abinda dansa ke aikatawa.  Tashi imaan tayi ta dauki trolleys dinta guda biyu da suka watso mata. Da kuma hand back dinta dake hannun ta tun dazu. Ta fara ja. Zulfa da hajiya huwaila suna rakata da zagi suna turata. Zuwatayi zata fita gate din me gadi daya kasa komai yace kiyi hakuri. Murmushi kawai tayi ta wuce tana hawaye su zulfa na rakata. Kuka kawai imaan keyi tana tunanin ina zataje. Ya zama dole ta tafi karta hada jalal da iyayensa musamman ma mahaifinsa sbd alwashin da granny ta dauka ya bata tsoro. Sede batasan ina zataje. Bazata iya zuwa gidan su maryam ko yusrah ba dan bataso su gane cewa Jalal Ali take aure. 
Granny ta kalli Alh isa Tace daga airport ka wuto da Ali nan yaga tsiyar da dansa ke shiryawa. Yace “amma hajiya da baki koreta ba kin bari yaya yadawo ya dauki mataki”. “Zaka wuce koko nasan babu matakin daze dauka shiyasa nina fara dauka kafin ya dawo wuce ka dauko mun shi nasan ya kusa sauka ...wucewa yayi tafi. Su hajiya atika da suka gama zagaye gidan ta dawo tace “wlh duk rashin ji da jalal yake bn taba dauka ze iya tsallake maganar mahaifinsa ba sbd yanda yake masa komai da yakeso ashe babu wani lagos yana nan yana holewa mun dauka ya shiryu”. Granny de batace komai ba dan ranta ya baci ita tunanin ma idan ya kawo masu shege suyi ya dashi
Abba isa be fadawa Dad komai ba ya kawosa gidan Jalal Dad de yay ta kallon gidan kafin yace “ina ne nan ka kawo ni”. Shide bece komai ba yace “mu shiga” babu musu ya shiga. Suka gaisa dame gadi snn suka karasa ciki. Yayi mmkin ganin su granny duk gaishe sa akayi tare dayi masa sannu d zuwa. Ya amsa snn ya gaisar da granny. Amsawa tayi snn tace “ina danka” yana lagos Dad ya fada ganin yanda taci serious. Ta mike tsaye “to babu wani lagos yana garin nan Kuma anan gidan yake rayuwa shida karuwar sa yanzu nazo na koreta. Wani irin shock Dad yayi yana juya kalaman granny.  Jalal yana Abuja. Ji yayi ransa na wani irin baci. Zata sake magana yace “kuzo mu tafi gida daga haka ya fice hakan da Yayi kade sun gane cewa ransa ya matukar bace shiyasa babu wanda yasake tankawa suka fita. Wajen megadi ya tsaya. Yace “karkamun karya. Tun yaushe jalal yake gidan nan”. “Zeyi wata hudu rankaya dade”. Gyada kai. Dad yayi yace “shida mace”. Yayi kasa da kansa “eh ranka ya dade”. A takaice Dad yace idan ya dawo ka turo mun shi “ daga haka ya fice. Suma sauran duk sukabi bayansa suka shiga mota suka tafi.   Ran hajiya Atika fari sol tanaji yau burin ta ze cika.   
Taxi ta tare tana kuka sosai. Hakuri ya bata yace ina za a kaiki. Tace kaini car park”. Babu musu suka fara tafiya. Tanajin zaman su da jalal yazo karshe. Dan tasan familyn sa zasu iya masa abinda yafi haka. Tasan shima ba wani damuwa zeyi ba tunda bawai auren soyayya suke ba. Fatan ta kawai karta zama silar daze rasa Dad dinsa. Karta zama silar rabuwar su da dad dinsa   Tunda ya riga ya fada mata his Dad will not take it likely with him idan har ya gane baya lagos barin ma suji wai tare yake da karuwa kamar yanda suka kirata. Kalmar tayi mata ciwo Amma ya zatayi. Dole kuma ta tafi. Tasan de Ze kula mata da Abban ta. Ita da kanta ma zata ringa zuwa dubasa amma ynx she’s going. A haka har suka zo car park  ta dauko jakar ta ta biyasa kudin sa snn taja trolleys dinta suka fita Allah yasota ma akwai wajen 20k ajakar ta. Motar zaria taje ta shiga. Dan daga can zata samu motar kauyen su itama gidan ubanta zata tafi tunda bata da wajen zuwa. 
Jalal nayin hon megadi ya bude masa ko gate din be rufe ba ya biyo motar jalal din. Ganin ya taho hakan yasa jalal fitowa daga motar ya jira me gadi. Yana karasowa suka gaisa. Me gadin yayi kasa da kansa “dama rankayadade wasu ne suka zo suka kori madaan suka watso mata da kaya” “ what” Jalal ya fada yana kallon kallon me gadin “wane su”. Kansa kasa sosai yace “nade ji wata me suna zulfa suke ce mata tana cewa Wlh nan ne gidan snn suka shigo. Muka gaisa sukace su iyayen ka ne. Babu jimawa senaga sun fito da ita sun watso mata kaya. Tana kuka.   Se kuma ga Dad dinka dan naga kuna kama yazo ya shiga kuma yayimun tambayoyi. Daga nan yace idan kadawo kazo gida ka samesa”.  Jalal da zuciyar sa ta gama tafarfasa ya shiga cikin gidan da gudu. Tun a parlon yagane ba karamin cin mutunci sukayi mata ba dan ga wasu kayan ta nan duk a kasa. Wayar sa ya dauka ya hau kiran numbern imaan se yaji tana ringing a gida. Daukar wayar yayi yana kallo ya rasa wane tunani zeyi. Shin ina imaan ta tafi bayan sun koreta wane irin kora suka mata. Fitowa yayi da sauri yana kiran megadi idanun sa sun fara canza kala. Bayan yazo yace “su nawa ne suka zo”. Suna dayawa  gsky ina tayi ta data fito. Ya nuna hanyar da imaan tabi. Nan tabi sun tura ta. Tana kuka”  cikin tsawa jalal yace “and you stupid you just watch them. Why can’t you follow her self”. Shiry yayi. Jalal yayi tsaki kafin ya shiga motar sa yana bin hanya da ko ze ganta. Amma kome kama da ita be gani ba.” Mmkin sa ma taya akai zulfa tasan gidan nan. Bibiyarsa take knn. Aikam yau zata gane kurin ta daga ita har shegiyar uwar ta. Da gudu ya figi motar ya dauki hanyar gida. Zuciyar sa wani irin tafarfasa take. Imaan daya bari a gida lafiya lau sun kore ta. Ina suke so taje ita da babu kowa data sani. Ya zataji. Cije lips din sa yayi daya tuno me gadi yace masa suna ta turata suna jiba da kayan ta. A hankali yace “and imaan cried. My wife cried because of you zulfa. Cizar lips dinsa yayi da karfi. Shi babban tashin hankalin sa ma shine ina imaan ta tafi ina ze ganta...
A firgice gate man ya bude gate saboda wata uwar hon daya sakar masa. Da wani jahilin gudu ya shiga gidan wanda duk wadan da ya gifter seda suka fara tunanin giyar yau ta daban ce kila. 
Dad na parlon sa yana zagaye yama kasa zama he can’t believe wai shi jalal ze rainawa hankali bayan bata masa suna da yake harda bigirewa maganar sa he knws sbd ya basa soyayya ne shiyasa iskancin sa ke gaba knn.
Su Abba isa da sauran mutanen gidan suna parlo kowa da abinda yake sakawa dan basu taba ganin dad yayi fushi da dansa ba irin yau.   Tun kafin jalal ya karaso duk suka mike dan su gane shine. Dan har bakin part dinsu ya kawo motar. Ko dedeta parking beyi ba ya fito a mugun fusace. Da kuwa muryoyinsa yake kiran zulfa “Zulfaaaa zulfaaa. Duk mikewa sukayi yayin da jikin zulfa ya fara rawa. Yana shigowa ko ta kan mutanen wajen bebi ba yayi kan zulfa ya kifa mata wasu wawayen maruka da seda taga wuta wuta. Yace “how dear you I say how dear you Ina ruwanki da rayuwata” da sauri mama ta taso “no jalal kade na dukan mun yarinya saboda wata banza can idan kamun na kyale ka to bazan dauka akan dukar mun diya ba. Sbd watan can kawai”. Wani irin kallo yayi mata yana maimaita kalmar banxa a ransa snn yace “do you just called imaan banza. Wlh you will pay for this zagin da kikayi mata will not went in vein am telling you this” “ keep that ur mouth shout kafin na fasa shi” Dad dake saukowa saman step ya fada camly kallonsa Jalal yayi zuciyar sa na tafarfasa. Amma bece komai ba. Bayan dad ya ya sauko yana kallon jalal yace “after all abinda kayi mun na karya shine har da zuwa kana zagin matata kana tayar mana da jijiyoyin wuya akan wata karuwa, dan dana haifa ya aje karuwa a gida for almost four months jalal karuwa so babu inda ka tafi kana can ka aje karuwa. Jalal da ransa yayi mugun baci yace “watch ur tongue Dad. Imaan ba karuwa bace. She my wife yes imaan matata ce ta sunna” ya kalli duk yan wajen da sukayi shock dajin abinda ya fada. “Duk wanda yayi gigin kiran matata da karuwa Allah ne kade ze rabani dashi. Imaan is my wife and ”   Wani tsawa Dad ya daka masa. “Jalal kayi aure kayi aure batare da sani na ba ni mahaifin ka. You get married without my knowledge Jalal. Kana so kasakamun heartbreak ne,sbd kaga ina kyale ka kana yin komai shiyasa kake abinda kaga dama. Saboda kaga inason ka that’s why kake komai hankalin ka kwance. All abinda nake maka be isheka ba harda zuwa kayi aure ba tare da sanina ba. Jalal aure fa aure. Am trying all my very best just to make you happy amma baka gani. Bar ganin cewa kai kade gareni wlh zan iya daukar mataki akanka ina ganin bin ka a hankali shi ze saka ka shiryu amma ka maidani shashasha. Jalal aure fa aure”. “Will you shout off Daddddd” “I said shout off”   Jalal ya fada a mugun tsawace. Wanda har gashin kansa seda suka barbaje idanun sa sunyi jawuuuur sbd tsananib bacin rai.  Kowa a wajen seda yayi mmkin tsawar daya dakawa dad din dan kamar ze tsaga gidan. Abinda kuma basu taba ganin yayi ba. Jalal ya karasa gaban dad din nasa yace “I lost happiness for the past 19yrs.. you are always claiming you want me to be happy but ko sau daya baka taba kiran sunan mahaifiyata ba. Baka taba damuwa da tana ina ba wane hali take ciki ba.  Baka taba tambayana ina dan uwana na ba. But kana claiming cewa kana son farin ciki na. Do you think kudin da kake mun spending will take me out of the saddest lyf. Oh good you’re wrong dad. Cos this ur son is not just a drunk but a billionaire ur money is nothing to me all I want is my mother. Inaso ta dawo rayuwa kaman kowa. And the most pain ful shine you naver ask of her balle brother na daya dade da barin duniya. An kashe dan uwana agaban idona. Kana tunanin zan kara wani farinciki.” Ya nuna hajiya Atika “look at thet woman you think she loves me ryt? Ur so calling mata or whatever let me tell you something she’s the reason behind my drinking. Ita ta fara bani giya tun kafin na tafi America. Kuma koda yaushe tana saka mun a cikin fridge dina   Am already addicted tun ina yaro. Kullum sena sha giya .sbd my heart is alway sad. I want my mom. I mss my brother da na rasa gaban ido na. Dad sanda na gama shan wahala ina neman abinda zanci where were you ina gararamba kamar bani da kowa. Althose mutanen nan babu wanda ya taimaka min and daga baya an dawo ana mun kallon bad boy. All this so da kake nuna mun babu abinda ze canza at least just even ask of my mother. Zanji dadi but you didn’t. You see that imaan da kuke kira da karuwa she’s an angel ta canza rayuwa ta cikin kankan kanin lokaci . I feel happy when ever I’m with her the first day danayi skipping bnsha giya ba. Shine ranar dana fara ganin ta Ashe imaan will be a lyf changer to my world. Na aure ta sbd wani dalili that I don’t want you to knw. Imaan change me from a drunker to a better person. I can’t remember when last nasha giya. She spent all the tym just to see me living a happy lyf. Let me tell you this my heart can’t take this anymore. Bazan juri rasa imaan ba. She’s one in a zillion. The only girl dazan iya rayuwa da ita. Cos word can’t say how i feel for her. SHE’S A GOD’S GIFT TO MY SADDEST HEART”... ya juya yana Kallon su da jajayen idanun sa snn ya karasa gaban hajiya Atika yace “she did the wost. Ta rabamu da dad dinmu at the first place. I lost my brother and my mother was poisoned and fall sick for the past 19yrs. Kin koyawamun shaye shaye. And now kinaso ki rabani da imaan” yayi wani murmushi “Dad If anything happens to my wife I won’t spare any one either you bring my wife back or anything can happen” daga haka ya fice daga gidan ya shiga motar sa yabar gidan badaya

Bawai na dawo bane I just said bari na bada barka da sallah😻
Urs
✨✨✨
ANNAFIE😍😍💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
              ANNAFIE💖…✍️
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
💫💫💖Jalal Alii(34)💖💫💫
A hankali Dadd da idanun sa ke kofa dan har jalal ya fita be dena kallon wajen ba. Maganganun sa ne kawai ke yawa cikin kansa yama rasa ta yanda ze fassara su. Zuciyar sa na wani irin buguwa. Har ynx kwakwalwar sa cikin fayyace maganganun sa take.   Bama shi kade ba kowa a wajen maganganun yawo suke masa kowa se juya maganar sa yake. Sumy kam hawaye take tana dana sanin abinda tayiwa imaan. Granny kanta da take wajen tama kasa magana. Tunanin ta kawai ina fareeda take. Tabbas fareeda tasan bata da lafiya daganan kuma bazatace komae game da hakan ba zulfa se zufa take jin wai imaan matar jalal ce to yaushe sukayi aure. Yayinda ta kasa gasgata abinda ya fada akan maman ta.  Hajiya Atika kam tafi kowa shiga tashin hankali ita abubuwa sunyi mata yawa tama rasa yanda zata fassara komai. Har ynx Dad be ko kalleta ba. Amma idon granny da wasu yan family din kallon ta kawai suke. Yayin da dayawa suka tausaya ma Jalal lallai is in pain. Yayinda kowa ke tunanin mene dalilin Atika na koya masa shan giya. Bayan a idon kowa ta nuna tana kaunar jalal din.  Mikewa Dad yayi tare da dauke idon
Sa daga kofa. Ya maida kan Abba isa “what if something happens to him yana wnn driving din”. Sun gane jalal yake nufi. But daga jin muryar sa kasan he’s totally broken. Granny ce ta kalli kowa snn tace “kdowa ze iya tafiya” a hankali duk suka fara ficewa. Kowa jiki a sanyaye parlorn ya rage daga Dad se granny Abba isa da kuma mama. Hajiya huwaila tuni ta faki ido ta fece da taga reshe yana niyar juye wa da mujiya.  Granny ta kalli mama snn tace “zaman me kike anan”. Fashewa da kuka tayi “wlh hajiya babu ruwana wlh ni bnsan komai akan harkar shaye shaye sa ba” camly granny tace “ki tafi nace”.   Kallon Dad da har ynx be kalleta ba tayi se kuma ta nufi daki tana kuka wiwi. A hankali granny tace “Aliyu”. Kallon ta yayi da idanun sa kafin cikin rawar murya yace “ina fareeda take”. Girgiza masa kai tayi itama cike da raunin.  Tasowa yayi dawo inda take ya zauna gefen ta snn yace “mum where is fareeda am asking you”. “She was poisoned kusan shekara 20knn. But nima tundaga nan bnsan komai akai ba”. Runtse idanu Dady yayi kafin yace “ almost 20yrs fareeda nashan wahala sbd poison,almost 20yrs my son is in pain,I didn’t deserve to be a father I caused all my son’s sadness”. Ya Allah ya lumshe idanu se hawaye. Abba isa ne ya dafa Dad. “Don’t say this. You did it unknowingly”. Ya kalli Abba isa. “Me nayi mata tayimun spoiling yaro. The only child I have. Na rike mata erta. Amma ni ta lalata mun nawa. I understand why Jalal hate her yau na fahimta. Ta nuna tana son sa kamar danta but she’s spoiling him behind my back”. Kasa magana Abba isa yayi yanade dan bubbuga kafadar Dad. Cikin rauni sosai yace “why my son. Why only my son😭. They called him badboy meyayi masu. And fareeda ma me tayi masu sukayi poison dinta my innocent wife isa tana Ina”. “Tana China” gyada kai dad yayi kafin yace “anya Jalal ze yafemun kuwa pls call him for me”. Granny de kam tausayin dan nata ya rufe ta sosai. Ta rasa ya akayi idon su ya rufe suka manta da ita. Numbern jalal Abba isa yayi dialing amma baya picking kallon Dad yayi kafin yace “he’s nit picking the call”.  “I won’t forgive my self if something happens to my son. Na rasa dan uwan sa. Zuciya ta bazata iya daukar rasa jalal ba”

Tunda jalal yabar gidan be tsaya ko ina ba se gidan su yusrah ya akai aka kira ta. Da mmki ta fito na wane kuma ke kiran ta. Ta tsorata sosai ganin yana yin sa.   Bata san sanda tace “lafiya meyasa meka” jalal ya ciji lips dinsa yace “imaan fa taxo nan” girgiza kai tayi da sauri kafin tace bata zo ba gsky wani Abu ya faru ne” “I can’t find her” “kuma bata gidan su Maryam”.  “Shigo muje”. Bude motar yusrah tayi ta shiga  seda suka fara tafiya tace “wani abu ya faru da imaan din ne”. Ba tare daya kalleta ba yace “family dina sun gano munyi aure and sunje sun koreta”. Dafe kai yusrah tayi gaban ta na faduwa. Tana adduar Allah yasa tana gidan su maryam. Koda akaje bata nan hankalin su yusrah ya tashi sosai maryam tace “bataje kaduna ba kuma” jalal ya girgiza kai “gidan akwai police sunce mun bataje ba but koda zuwa anjima ne kila idan Allah yasa taje zasu kirani”.   Kiran sageer ne ya shigo wayar sa. Jalal yadan cije lips dinsa kafin ya dauka daga can sageer yace “hey bro why are you Abba isa ya kirani” dan lumshe idanu jalal yayi kafin yace “sageer I can’t fine imaan sun koreta sageer sun kori imaan nazo har wajen frnds dinta bata nan”. Cike da kwantar da hankali. Sageer yace “Common bro nasan zata dawo babu inda zataje kasan babu wanda ta sani a garin nan idan basu ba so ka dawo gida kila ma ta dawo”. “Yes I think so”. Daga haka ya kashe wayar yayiwa su maryam sallama. Ya tafi gida. A waje yayi parking tun kafin ya shiga ya tambaye me gadi imaan kota dawo. Amma yace aa. Duk da haka be yarda ba ya nufi cikin gidan tun a parlor ya fara kiran sunan ta amma shiru. Dakunan gidan ya shiga ya rinka dubawa. Amma be ganta ba ya wuce cikin gidan can baya ya dudduba amma be ganta ta.  Waje ya dawo ya bude motar sa ya shiga. Ya kifa kansa da sitiyar. “I knw you will come back dear bayan ma kince zanyi maki wainar flour”.  Haka jalal ya zauna yana ta zaman jira ko imaan zata dawo har akayi magrib shiru kiran sageer ya shigo wayar sa jalal ya dauka “tunma kafin yace komai jalal yace “sageer imaan bata dawo ba”. “Where are you” cewar sageer “ina gda”. “You wait for me gani nan zuwa but make sure kayi sallah kaji”. Kashe wayar Jalal yayi yana lumshe idanun sa zuciyar sa na wani irin buguwa. All his hope is imaan ta dawo besan wani irin kora suka mata ba amma shide ta dawo ze bata hakuri on behalf of yan uwansa.
 
A zaria imaan ta samu bus ta shiga wacca zata kaita har wajen kauyen su.  A hanya imaan taita kalle kalle tana tuna ranar data fara barin kauyen su. Wanda tun lokacin rayuwa ta canza mata lumshe idanu tayi tana tuno Abba a da da kuma ynx da besan wane ke kansa ba. Ita kanta tasan jalal yanada kirki tunma kafin tasan wane asalin Jalal din tasan ze kula mata da Abban ta kafin ta dawo. Sede ita ynx babban burin ta shine Allah yasa kar ya samu matsala da family dinsa. Koda sun sake haduwa dashi takardar saki zata amsa. Tafiyar kusan 40mins suka iso kauyen nasu.   Imaan ta sauka tana kallon mutanen dake sauka wajen da duk suka bita da ido. Ita kanta duk seta gansu wani iri taga ta fita daban a cikin su. Wani abokin Yaya Auwal me suna okasha ta gani sarai ta gane sa a wajen yake kanikanci. Karasawa kusa dashi tayi tayi sallama “kallon rashin sani yayi mata tare da amsa sallamar” a ransa yana fadin wnn baturiyar fa. Dukkuwa da hijab ta saka hakan be hana hasken ta fitowa ba idan ka ganta se kace balarabiya ta kara wani kyau na musamman. Tace “imaan ce kanwar yaya auwal”. Ware idanu yayi yana kallon ta tare da washe baki “imaan kanwar mu sarkin rigima kece kika zama wata balarabiya haka”. Murmushi kawai imaan tayi snn tace “ina so akaimun kayana gida”. Ya rike baki “ikon Allah imaan wai kece haka. Kai jamaa ance ai ynx habuja kike ji yanda kika zama dan Allah”. Murmushi kawai imaan tayi. Dan ta gaji kuma da surutun. Wani me kura ya kira aka zuba mata trolleys dinta. Shima ya aje aikin dayake ya biyo ta suka taho. “Ke de shknn dr ya dauke mana ke ya maidaki can kina ta zama baturiya. Anya ba kasashen larabawa kike zaune ba.” Murmushi kawai imaan tayi dan tama rasa me zatace. “Kai imaan wai kece de”. Har suka karaso cikin garin surutu yake mata  yayinda duk inda ta wuce binta kawai ake da kallo dan babu wanda ya gane ta. Imaan taita kallon garin nasu da ko daya be canza ba. Dan murmushi tayi a ranta tana tuno rayuwar su ta da babu inda bata zagaye a garin nan. Sede idan rashin jin su be tashi ba.  Da sallama ta shiga gidan nasu wanda tun a waje ta gane yanda ya kara lalacewa.   Wani hayaki daya buso ne yayi mata sallama. Ta runtse idanu. Ita yaushe rabonta ma da hayaki.   Jummala dake gaban murhu tana saka danwake ta mike ganin tana shigowa da kaya. Batayi magana ba imaan ta shigo. Binta jummala tayi da kallo dan bata gane ta ba. Imaan ta kara shigowa. Ta samu wani dakali ta zauna. Ta gaji sosai ga wata irin yunwa da takeji. Jummala tace “sannu bakuwa mukayi ne” da sauri okasha yace “wai baki gane ta ba imaan ce fa”..... wani irin faduwa gaban ta yayi. Tana kallon imaan da kyau   “Inna ina wuni”. Wani irin miyau jummala ta hadiye tana kallon imaan dan bata taba tsammanin ganin ta haka ba. Domin kau boko yace ta na can habuja tana karuwanci ta riga ta gama sanin namiji. Jin ance imaan hakan yasa hurera dake zawarci ta fito hoda rike a hannun ta da alama shafawa take jin ance imaan shiyasa ta fito.  Murmushi imaan tayi tana kallon er uwar tata. Dan ko babu komai shi dan uwa daban ne she missed them dan kaf duniya bata da kamar su. Hurera tace “imaan kece haka”. Hurers ta fada tana kallon imaan da komai nata ya sauya sabanin da. Duk da dama can imaan kyakkyawa ce amma ynx ta kara zama wata cikakkiya wayewa da hutu sun bayyana a jikin ta. Fatar jikin ta a wani irin murje. Wani kal kali da ita yanda kasan ka latsa jini ya fito. Duk wanda ya ganta yasan tana tare da jin dadi. Hurera ta kalli kanta. Banda baki babu abinda ta kara gashi tayi wata katuwa. Sabanin imaan da take cif cif dede shekarun ta. Jin an anbaci imaan yasa Adda fitowa da sauri. “Wace imaan din ce ake fadi Banda tamu wacce dr ya rabamu da ita da karfi da ya”. Shiru tayi ganin imaan zaune washe baki imaan tayi ganin Adda da har ynx bata sauya ba. Ware idanu imaan tayi kafin ta mike ta nufi Adda ta rungume ta “Adda na I missed you”. Washe baki Adda tayi tare da rabata da jikin ta tana kallon ta cike da farin ciki “Allahu akbar imaan wai kece haka imaan de jikata ce ta koma baturiya haka. Kai kai birnin tarayya ba karya ba wai jikalle tace haka. Kinji jikin ki wani taushi ga kamshi kamar kamfanin turare.” “Imaan ta boye fuskar ta a jikin Adda tana murna    Wani dogon tsaki jummala tayi kafin tace aikin banza. Ta juya wajen tukunyar dan waken ta. Shewa Adda tayi kafin tace “woho ande ji kunya bakin ki be kama jikata ba kin ganta ta dawo rumui fes fes. Aniyar ki ta biki. Kinbi ki bude gari cewa imaan nacan habuja tana karuwanci babu wani karatu se Allah ya nuna maki iya karki. Kin ganta fess fess wnn ko a kasashen ketare se haka. Tsabar boko kina ji hausar ma ta fara mantawa”. Tasowa jummala tayi a harzuke tace “wnn din ina wani mutunci anan ace zumbudediyar budurwa irin wnn amma babu aure ai daga ganin ta ma kinsan tasan maza wlh. Wnn hasken da jan a banza masu kasar zasu barta. Ai dole su rinka shaka mata kudi tana bin gidajen masu kudi...” “wowowo ande ji haushi Hassada kiri kiri kinga tafi yaran ki daga wacce kullum se sunyi fada da miji se wacce take zawarci se wacce Abinci ma nan take zuwa ci. Imaan kau tafi karfin tayi karuwan ci dallele zata samo a habuja wanda ze girgiza kaf dangin ku da garin nan na gaba daya dan dama can imaan ba kalar garin nan bace. Sede asirinki ya kare akanki da kuma ubansu da kika gama dashi. Nide kam da jikata munfi karfin ki. Daga haka ta dauki trolleys din imaan ta fara shiga dasu ciki. Imaan de tayi tsaye binsu kawai take da kallo. Shin dama har yanzu su bazasu canza ba ita wlh ta manta ana kalar rayuwar nan. 
Kafin kace mene gidan ya fara tara mutane. Ana zuwa ganin imaan ciki harda su Abida da duk sun yamutse. Kowa yazo yaga imaan seya kara inda kowa seya zagi jummala data gama bude gari cewa imaan karuwanci take. Imaan de na zaune kallon su kawai take. Bnd yunwa babu abinda take ji ga wani irin zafi da take ji kawai so take ta kwanta amma tasan mutane bazasu barta ba kowa yazo sede ta bisa da murmushi dan dayawa ta gane su. Sede wadan da aka haifa bayan tafiyar ta. Amma har wasu kannen ta gasu nan duk sunyi aure. Ganin Abun bana karewa bane yasa adda kamata tasakata a daki.  Ta rufe. Jummala kam bata kula kowa ba tacigaba da saka dan waken saydawar ta da hurera ke saida mata amma zuciyar ta bakin ciki kamar ya kashe ta. Jira kawai take litinin tayi kam ta kaima bokan ta ziyarar sassafe. Amma yau dole su zauna da inno duk da kuwa tasa cewa tana nan zuwa anjima.
Damar mar fura Adda ta dauko wa imaan ta bata. “Ungo sha dan wacca koni ba abinci take bani ba bare ke. Ubanki kuma ta gama dashi idan anjima yayanki ya shigo ko balango ne seya siyo maki. Jiki na rawa imaan ta fara sha furar saboda yunwar da taje ji. Kuma sosai taji dadin furar dukkuwa da ta saba shan fura masu dadi kala kala. Adda ma taji dadin yanda tasha furar. Shigowar umma ce ta saka Adda bude kofar ta tare suke da talatu da kuma kuluwa. Tashi imaan tayi ta rungumesu cike da murna. Kawayen amana knn. Bazata taba manta yarintar ta dasu ba sudin tana jin su har ranta.. kuluwa ta rike baki imaan kece haka. Kin tafi shiru shiru kamar ba zaki dawo ba”. Hararar ta imaan tayi “ni na isa na manta da garin mu school ne ya rike but Alhmdllh am done just 8months suka ragemun”. Talatu da duk ta zazzage ynx tace “imaan harta maganar ki ta canza hausar ma se ana hadawa da turanci ynx”. Dariya imaan tayi. Tare da gaida umma ta koma ta rungume ta nayi kewar ki umma na”. “Imaan ya ta kamar ba zaki dawo ba kin manta damu. Kinsan Babanki har can yaje da yaji ku shiru. Wasu gidan ku a rufe da jamiai wai kun koma habuja. Ni kade ya gaya ma haka. Ynx shi ina Dactan yake bezo ba da hajiyar. “Sosai gaban imaan ya fadi. Jikin ta yayi sanyi data tuno Abba ba can kwance bema san wanda ke kansa ba. Kanta kasa tace “suna can Abuja umma. Nima na gama ne saura na wata takwas da zan koma shknn na gama”. “Adda tace shi boko wai harda sauran wata takwas har ynx keni nagaji badan nasan a ynx kinfi karfin duk wani namiji dake kauyen nan ba da nace baki komawa seda auren ki”. Murmushi kawai imaan tayi a ranta kam fadi take aure kuma na  nawa “.
Umma ce tace “bari a aika a siyo maki lemo da ko biredi ne”. Girgiza kai imaan tayi. Snn tace “ba bread ba ni flour zamu siyo muyi wainar flour umma inaso naci”. Kuluwa tace “wlh nima tun jiya nake marmarin ta”. “To ai babu damuwa bari a kira yaro”. Imaan ta dauko jakar ta ta ciro dubu biyu “umma gashi a siya” ware idanu umma tayi aa ki bari akwai kudi a gida zan sa yaro ya kawo. Imaan ta makale  umma “noo nide babu inda zaki ki bari a siyo”. Talatu ce ta karbi kudin ta bama yaro ta fada masa abubuwan da ze siyo. Snn suka dawo suka cigaba da fira tare da Adda. Yaro na kawo flour dasu  lemuka suka fito waje suka hada gawayi aka fara tuya sunaci ana ta dan labari. Hurera dake tsakar gidan ko kallon su batayi ba da imaan ma tayi mata magana kin kulata tayi. Tabe baki imaan tayi. Snn a ranta tace “naga dubun ki dan ynx kam tasan hurera ba sa ar yinta bace. Suna cikin tuyar sega. Nana ummi da kuma Abida. Duk sunyi wani. Iri. Kallo daya sukayi wa imaan suka ja tsaki cike da hassada suka tafi dakin jummala. Kuluwa tace “aikin banza kuwai masu bakin ciki”. Da sauri nana ta juyo “ku kuma mayu ba daga ganin ta kun wani makale to babu abinda zaku samu itama matsiyaciyar ce”. Kuluwa zatayi maga umma ta hana ta “ “na hanaki wnn kinki ko” shiru kawai tayi badan taso ba. Imaan kam ko daga kai batayi ta kallesu ba. Secin wainar ta take da lemun kwalba da ta manta rabon data sha.
Dan gani take wnn shirme rashin abinyi ne da rashin sanin ciwon kai Se magrib snn yaya Abbakar suka shigo tare da Yaya Auwal. Sosai imaan tayi murnar ganin su. Suma haka suka zauna aka suna labari. Har Baba ya dawo snn suka tafi. Har dasu kuluwa. Imaan ta gaisar da baba kanta kasa. Ya amsa kafin yace “yasu dacta ya Abuja”. Imaan tace “lpy qlw”. Yace “ai naje sbd dacta ya taba kwatantamun gidan shine jamia suka cemun ai kuna Abuja “imaan ta gyada kai”. Yace “toya karatun an gama ko”. “Eh Abba an gama sede inde akwai wata takwas dazan karo a Canada 🇨🇦 can kasar turawa ce daganan zan samu aiki”. Imaan ta fada duk da bata san lokacin komawar ta ba amma tana fata Abba ya samu sauki”.  Baba ya jinjina kai yayin da Adda ta bude baki wai kasar turawa zaki tafi imaan. Kila ma acan zaki samo miji. Kila ta silar ki zan fara shiga jirgi. Daidai lokacin da jummala da inno suka shigo gidan knn. Dan tun dazu tabar gidan zuwa gidan inno suna ta sakawa da kwancewa.   Inno ta gaisa da imaan tana kokarin kare mata kallo itade imaan tunda ta gaisar da ita batace komai ba.  Wucewa gida inno tayi dakin jummala da tuni ta shige ita. Basu wani dade ba ta fito tayi masu sallama. Jummala data rakata tayiwa baba wani kallo ta wuce daki. Baba yayi kasa da kansa kafin yace “bari naje imaan seda safe”. Imaan ta bisa da kallo ganin yanda jikinsa ke rawa. Tabe baki Adda tayi. Snn tace “kadan kika gani dan ta gama tashi se abinda tace”. Jikin imaan ne yayi sanyi. Ta tada kai tana kallon hurera data shigo tana fadin “innar mu ga nama.  Mu ba matsiyata bane munfi karfin cin wainar fulawa duk birnin da take takama dashi a tsiyace ta dawo me za ayi da wata wainar fulawa kuma”. Imaan ta bita da idanu. Kafin ta tabe baki. Lallai inde mutum a duhu yake to a duhu yake. Taya ita da take zaune Abuja azo ana mata burga da wani dan nama wanda bama tajin zata iya ci a ynx   Adda ta tabe baki kafin tace “aikin knn sede a fita aje wajen samari a shigo da leda kala kala. Auren ta ya dade da mutuwa sbd abin duniya take kawo masu shiyasa bata damu ba danta daya a gidan auren ta fito. Yana nan kila se gobe ki gansa. “ tashi imaan tayi dan bacci take ji so take ta kwanta”.
Saman gadon Adda ta haye kafin tace “Adda nayi kewar gadon nan” Adda ta washe baki. Nan da bn rinka rufe daki ba datuni kin kashe mun shi ai da rashin jin ki.” Dariya imaan tayi. Tana tuna irin rashin jin data zuba. Bama gidan su kade ba kaf garin wane be santa ba. Tsabar rashin jinta. Ita kanta tasan tayi karami da babba babu wanda ta daga mawa. Sun dade suna labari kafin ta juya tana so tayi bacci. Jalal ya fado mata  dan lumshe idanu tayi tana tunanin ko yana ina. Ko ya zeji idan yazo ya iske bata nan. Tasan baze ji dadi ba amma dole ta tafi sbd bata so su kara samun matsala da danginsa. Runtse idanu tayi. Tanajin babu dadi kwana ita kade. Ta riga ta saba kwana dashi ta riga ta saba da jikin sa. Rungume pillows tayi. Bazata iya fadin abinda takeji game da jalal ba ynx but she knws she missed. Juye juye imaan ta rinkayi dan kwata kwata ta kasa bacci. Seta tuna daren su na jiya tanaso tayi bacci ya hana he spent the whole nyt akan ta.  Kuma itama da safe ta hanasa baccin   Dan lumshe idanu tayi tana tuna alkwarin da tayi masa kafin ya tafi.   Fuskar sa kawai take hangowa idan ya dawo ya iske bata nan. Duk yanda imaan taso tayi. Bacci kasawa tayi sede taita juye juye ga zafi tanaji.

Babu yanda sageer beyi ba akan jalal yazo su tafi gida Amma jalal ko kallon sa beyi ba ya kifa kansa a sitiyari. Gashin kansa duk sun wani hargitse. Sageer ya kamo hannun sa “lets go bro”. Jalal ya dago kansa ya zubawa sageer idanun sa da sukayi jawuur. Snn yace “meyasa har ynx bata dawo ba why will she left meyasa bata jira ni ba”.  Shiru Sageer yayi se can kuma yace “imaan bata da kowa a Abuja inde har bada gidan su maryam ko yusrah. Bata kd to tabbas ta tafi gidan su I mean kauyesu”.  Da sauri jalal. Yace “exactly but ina ne kauyen ya sunan kauyen.  Sageer ya ware hannu. “Kai zan tambaya”.  Girgiza kai jalal yayi bn sani ba. I think muje gidan su maryam nasan kila sun sani...dare yayi baka da contacts dinsu ne. Girgiza kai yayi. Se kuma ya dauki wayar imaan dake hannun sa. Ya bude snn yayi searching yusrah. Dialing yayi yana Adduar ta dauka .. yusrah na dauka ya tambaye ta “ tunani yusrah ta shiga kafin tace ”gsky bn sani ba nade san tabbas tace mun a kauye Abba ya dauko ta Amma bn san wane kauye bane”. Seda kan jalal ya sara. A hankali yace “ohk thank you” daga haka ya kashe ya kira Maryam ya kira. Itama  samething karshe har su farouq ya kira amma basu sani ba.  Jalal ya tusa dukka hannayen sa cikin gashin kansa. Tare da jingina da kujera zuciyar sa na wani irin buguwa. Inde har da gske imaan ta tafi tayaya ze same ta. Bayan ko sunan garin be sani ba. Ta ina ze fara neman ta.  Lumshe idanun sa yayi. Yana sauke numfashi a hankali ya mugun bama sageer tausayi   Tabbas ya dade da sanin Jalal yana son imaan tun ranar da sukaje kaduna kuwa. Sbd ita ce mace ta farko da jalal ya taba tsayawa sukayi maganar kirki. A hankali sageer yace “lets go home”. Shiru Jalal yayi bece komai ba hakan yasa sageer ya fita ya koma ta side din jalal din “fito let me drive you home”

Urs
✨✨✨
ANNAFIE😍😍💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
              ANNAFIE💖…✍️
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
💫💫💖Jalal Alii((35)💖💫💫
Da kyar Sageer yayi convincing Jalal ya biyo sa suka taho gida. Idanun Jalal a lumshe suke. Gabadaya. Ya rasa ta ina ze fara. “Taya ya zamusan sunan kauyen da take”. Jalal ya fada still idanun sa a lumshe. Kallon sa sageer yayi. Kafin yace “wajen mutum biyu”. Jalal ya bude idanun sa da sukayi wani irin jaa  ya kalli sageer amma bece komai ba. Hakan yasa sageer fadin “daga Abba se mommy” jalal ya maida idon sa ya rufe be kara cewa komai ba har suka karaso gida. Jalal be jira komai ba ya bude motar ya fita sageer ya bisa da kallo har ya shige snn shima ya bude ya fito.
Dad na parlor ya kasa tsaye ya kasa zaune. Burin sa kawai yaga sageer ya dawo masa da dansa har gida duk da sunyi waya yace “ya kwantar da hankalin s a amma ya kasa sbd yasan wane jalal.  Yana shigowa dad ya juyo ya kallesa. Ko Kallon Dad jalal beyiba. Ya wuce part dinsa. Dad ya bisa da idanu kafin ya kalli sageer daya shigo. Bin bayan jalal yayi yayinda sageer ya nemi waje ya zauna bayan ya gaisar da Abba isa da kuma Mahmoud.
Kwance Dad ya samesa saman wata lallausar kujera ya lumshe idanun sa. Sosai Dad yaji tausayinsa. Ya karasa ya zauna gefen kafafun Jalal tare da shafa gefen fuskar sa. Camly yace “my son”. Bude idanun sa yayi ya kalli daddy wanda har seda dad din  ya tsorata. Sbd yanda sukayi wani jaaa.   Hannun sa Dad ya kamo jikin sa na rawa “am srry”. Dan lumshe idanu jalal yayi kafin ya bude akan dady. Cikin raunin da Daddy be taba ganin Jalal dashi ba yace “Daddy I can’t find imaan I can’t find her ta tafi ta barni”   Sosai Daddy yaji tausayin jalal. Gsky ko wacece wnn dansa na sonta cikin kwantar da murya sosai Dad yace ”zata dawo inshaallah zan Nemo maka ita inde that will make you happy I will do it just to make you happy my son”   Jalal ya kama hannun Dad sosai “thank you Dad thank you”. Murmushi dad yayi kafin ya tashi ya shiga toilet ya hada ma dana sa ruwan wanka cos he’s ready to spend all his tym and strength saboda farin cikin dan sa.   Bayan ya fito. Ya kalli Jalal “come and take a shower my son” tashi Jalal yayi ta nufi toilet yanajin jikin sa duk babu karfi.
Parlo Dad ya koma anan ya iske su sageer. Zaunawa yayi ya dubi sageer kafin yace “who’s this imaan and ina Jalal ya samo ta and how do they even got married”. Sageer da yasan dama dole wnn tambayar ta biyo baya. Ya gyara zama dama ya shirya amsar sa tsab.  Yace “bansan tym din da suka hadu ba amma de ita yarinyar ba anan take ba a wani kauye take. Sede tana hannun wanI wan mamanta ne a kaduna. Yan fashi sun kai ma dad din hari har gidan sa. A kaduna ni kuma tym din jalal ya rakani aiki kaduna so shine muka samu labari mukaje. Ban san ya akai jalal ya san imaan ba dan da alama har babanta ya sansa. Mun iske sa cikin jini tare dan sun masa ramuka ya bama jalal Amanar imaan tare da auren ta a lokacin kafin ya bar duniya. Mamanta kuma bamu san inda take ba har ynz.”  Dad yace “ynx ina kake tunanin zamu ga yarinyar”. Sageer ya girgiza kai. Bana tunanin tana Abuja   Dad ya girgiza kai. Baka tunanin ta koma kauyen nasu” sageer ya gyada kai nima haka nake zargi sede babu wanda yasan sunan kauyen bamu san wane kauye bane”. Iska dad ya fursar yana tunanin mafita. “Kafin yace “I can see jalal ya damu da ita” “ sure hakane”. “Mucigaba da bincikawa ko Allah ze sa musan wane gari ne koda mutanen da suke tarayya dasu ne. I don’t want anything to happen to my son ina son kawo karshe damuwar sa and ya maganar fareeda”. “Inshaallah gobe zamu maida ta saudiya” gyada kai “dad yayi kafin yace “ka bashi tea yasha idan ya fito Wanka”. Tashi sageer yayi ya tafi part din jalal yayin da yabar Daddy da Abba isa suna tattaunawa. Tym din da sageer ya shiga har jalal ya fito wanka. Be tanka sa ba ya fara hada masa tea din ya mika masa. Jalal ya kalli tea din. Kafin ya dauke kai yace “gobe zanje kaduna”. Sageer yace “take this tea din ka shanye ko nayi tafiya ta”. Karba jalal yayi yasha. Seda ya shayen snn sageer yace “me zakayo a kaduna”. Zanje gidan su imaan ne and neighbors din su ko akwai wanda yasan kauyen”.  Mikewa sageer yayi. Kafin yace “ohk am going. We will go together. And don’t let this stop you from sleeping”. Binsa da kallo yayi kafin ya maida idon sa ya lumshe. Babu jimawa da fitar sageer Dad ya shigo. Ganin idanun sa a lumshe yasa ya shafa kansa tare dayi masa peck a goshi snn ya kashe masa wutar ya fita. Bude idanun sa yayi a cikin duhun. Yana ganin kamar imaan zatazo ta kwanta gefen sa tanayi masa shagwabar da ta saba.   Runtse idanu yayi. Sanin cewa bama zata zo ba. Shi kansa yasan baze iya bacci ba a yanda yake ji din nan. Besan yanda akayi  har zulfa tasan gidan sa ba. Bibiyar sa take knn   Definitely wnn shirin atika ne bana wani ba....
Dad na daki yana dan kaiwa da kawowa. Inde kam har imaan zata zama silar farin cikin dansa da silar shiryuwar sa.  Zeyi duk yanda zeyi domin ganin ta dawo gare sa. He need to see this girl da har ta dauki zuciyar Jalal haka. Shida bayawa mace second looks. And ya tabbata jalal love her dan yasan dansa baze taba yarda ya zauna da ita ba bayan baya sonta. Har kuma yayi masa karyar baya garin nan sbd ya zauna da ita. Kallon kofa yayi da sauri jin a bude an shigo. Ganin Atika ce yayi saurin dakatar da ita. Zatayi magana ya daka mata tsawa “leave my Frnd”. Har ta juya baya. Yace “you can’t spoil my soon and think I will let you go just lyk that   Duk wani me hannu a cikin rayuwar Jalal a shirye nake da tarwatsa rayuwar koma wane wlh. Jalal is my son and I will fight for his happiness. I can’t watch you spoiling my soon and making his heart sad. Zan tashi tsaye ga duk wani me shirin tarwatsa farin cikin dana. I don’t knw ur reason Amma kisani dake da duk wani me hannu a ciki zaku gane kurin ku let me finish imaan case snn na dawo kanku if you lyk kije duk inda zakije cikin kasar nan”. Fita Atika tayi da sauri tanajin irin alwashin da yake dauka. Wayar ta ta dauko domin kiran Hajiya huwaila Amma batayi picking ba. Zaunawa tayi saman gdo yau ko zulfa taki kulata tanacan daki bnd kuka babu abinda take.
Yana fita daga part din yayan nasa ya dauki wayar sa ya fara turawa alhaji barau sako. “Lets meet tomorrow it’s an urgent meeting.” 

Washe gari bayan Dad ya dawo daga masallaci dakin Jalal ya shiga dan ganin halin da yake ciki da kuma abinda ya hanasa zuwa masallaci. Zaune ya samesa saman prayer mate yana karanta. Alqurani. Girgiza kai yayi kafin ya juya ya fita. Yanayin jalal kade ya isa ya basa tausayi saboda yanda yake karatun cike da sanyi.

Ko daya imaan batayi bacci ba saboda tunanin ya Jalal zeji idan yazo ya iske bata nan. Tasan ba lallai ya wani damu ba sbd kawai yana tare da ita ne dan rike amanar Abban ta. But for her she missed him zuciyar ta ta saba dashi sosai a en kwanaki nan. Se gab da asuba ta samu damar bacci. Adda ce ta tashe ta sallah ta fita domin yin Alwala babu kowa tsakar gidan dama tasan ba wani sabon su bane yin sallah da wuri.   Tana yin Alwalarta ta. Shiga tayi sallah tare da hayewa saman gadon. Se bacci.
Wajen 8:30 Adda ta tashe ta tana masifa “ace mutum yayta kwanciya da safe ina amfani daga zuwanki birni seki koma wata ranga ranga”. Tashi imaan tayi. Tanajin kanta nayi mata wani irin ciwo kamar ze tsage. Hararan  Adda tayi kamar zatayi kuka tace “kai Adda bnd lpy fa”. Adda ta kalle ta. “To kin ta kwanciya tashi zakiyi ki karya ki shiga magani”. Imaan da har wani zazzabi takeji. Ta sakko daga saman gadon. Trolley dinta ta sauke inda Allah ya taimake ma na sch ne wanda dawo dashi. Ta fito da brush ta saka makilin  tana so tayi wanka. Amma bata da sponge snn bata da  soup. Butar Adda ta dauka ta fita tsakar gidan daya cika da hayaki. Ga mutane nata shigo inda Allah ya taimaketa ma da hijab dinta. Su jummala ana gaban murhu ana toya kosai yayin da hurera na gefe taci wata uwar kwalliya tana zubawa mutane koko da kosai da alamu de siyar wa suke. Duk dagowa sukayi suka bita da kallo kamar wasu mayu. Itama seta dauke kanta tare da samun waje gefe ta duka zatayi brush. Sede kamshin kosan gaba daya ya dame ta ji take yana hawar mata kai. Brush din ta fara yi. Sede jin kamar zatayi Amai yasa ta  fasa ta fara wanke bakin ta. Ta mike knn wani Amai ya daho mata. Babu shiri ta duka. Ta fara sharara Aman nan. Lokaci daya kallo ya dawo kanta. Har jummala dake tuyar kosai juyowa tayi tana kallon ta. Yayinda wasu suka fara ce mata sannu. Adda ce ta fito jin Aman. Karasowa tayi da sauri ta dafa. Imaan da har yanzu take amman. “Oh ni wai jikin ne de knn sannu kinji”. Wani irin washe baki jummala tayi kafin tace “Ayya an dawo da tsaraba knn”. Kowa kallon jummala yayi. Ta tabe baki tana kallosu “kallon me kuke mun bayan ga zahiri nan kuna gani. Alamun ciki sun bayyana ga yarinya”. Hatta imaan wnn karon seda ta dago ta kalleta gabanta na wani irin faduwa. Adda tayi saurin fadin “ahir dinki a kaf zuriar mu babu me cikin shege kede hassada ce kawai kuma kanki zata kare”. Mikewa jummala tayi. “Hassadar mene. Daga fadar gsky idan ba ciki ba menene”   Kallon ta kawai imaan take with shock “ciki kuma”. Kama hannun ta Adda tayi bayan ta wanke mata fuska “. “Muje jikalle bakin ciki take kinfi yaranta ta kowane fanni dama ta dade da gayama en garin nan cewa a watse zaki dawo gaki fess”. Imaan de batace komai ba suka koma dakin Adda. Koko da fanke da bread adda ta kawo mata. “Maza ki ci kisha magani”. Imaan ta rinka Kallon kokon  zuciyar ta na wani irin tashi tanajin Wani Aman na tahowa amma tana kokarin dannewa. Bread din imaan ta dauko ta gutsira a hankali ta kai baki. Ta fara taunawa. Kallon kokon tayi. Babu shiri ta dauke kai tana kokarin tashi. Sede tana yunkurawa. Ta fara kelaya Amai. Tsayawa Adda tayi tana kallon ta. Kafin tace “yau naga ta kaina daga dawowa se rashin lpy koda yake habuja fa dole ki kasa cin cimar mu. Kilan ma wainar flour da kikaci jiya ce ta bata maki ciki.” Wata mata data zo siyen kosan ce ta daga labulen tana kallon imaan da take sauke numfashi da kyar “ohni daga dawowa se cuta” “kinde gani maman dije”. Daga can jummala tace babu wata cuta. Kude tsare ta kuji ubanda yayi mata ciki. Shigowar yaya Auwal ce ta dakatar da Adda daga yin magana. Ta dube sa tace “uwar ka hassada ce zata kashe ta”. Bebi ta kansu ba. Ya kalli imaan data jingina da gado tana sauke numfashi yace “meke damun ki”. Kanta ta nuna masa idanun ta a lumshe. Ya Auwal ya taba wuyan ta jin zafi sosai yasa yace “subhanallah zazzabi ne me zafi a jikin ta. Sauro ya cije ta ne”. Wnn maganar da yayi itace ta saka jummala shiru a ranta tana fadin kode ba cikin bane. Inde ko hakane malam ya cuceta yaci mata kudi domin kau yace tana can Abuja tana karuwanci tasan namiji”. Adda kam marairaicewa tayi “ni se nake ganin ko yanayin ne be karbe ta ba”.   Yaya Auwal yace “bari naje na samo maki magani me zaki ci”. “Tea” imaan ta fada a hankali tanajin yanda kabobin jikin ta ke dandaka. Fita yaya Auwal yayi Adda ta gyara wajen yayinda kowa ke cewa jummala ta cika hassada. Dama already ta gama yade garin da imaan na habuja tana karuwanci. Duk wanda yazo wajen ta siyayya se tayi masa zancen dan ynx gidan kullum da mutane. Ta saida koko da kosai da safe da rana kuma dan wake Baba kam ta gama dashi ynx bashi da bakin magana. Ko Adda a boye yake mata magana.  Dawowar imaan fess ya tabbatar wa mutane cewa hassada ce. Haka ma ynx
Yaya Auwal ya siyo mata magani dasu madara dama already Adda ta daura ruwan zafi a mangal. Yana kawowa ta hada mata tea ta bata imaan tasha tea snn tasha magani tana gamawa shanye wa ta kwanta se bacci.

Yaya Auwal ya fita zuwa wajen innar su. Kofa ta nuna masa. Zoka fita a gidan nan dan na kula ba wajena kazo ba “girgiza mata kai yayi “haba inna imaan fa erki ce” “rufemun baki ba yata bace ba wlh. Duk da hurera ke zawarci nasan cewa akan idona ta” ganin fadan nata zeyi yawa yasa ya bata hakuri ya fita gidan gaba daya dama already yasan baba ya fita sbd ynx ba wani zaman gidan yake ba. Idan ya fita tun safe se dare. Sbd fitinar jummala
Wajen karfe 12 imaan ta tashi da wani irin zazzabi me zafi jikin ta se kyarma. Adda ta taba jikin ta jin irin zafin tace “nashiga ku. Ynx ke daga zuwa birni se kisaba bayan ga tushen ki aikam badan muna kewar ki ba da komawa zaki wlh”. Imaan de batabi ta kan Adda bata nufi waje da sauri. Tana kokarin rike aman ta. Seda tana zuwa kofar daki. Ya kwace mata anan ta duka tana amayar da tea din da tasha. Jummala,inno,ummi,Nana,Hurera duk suna tsakar gidan. Suka rinka binta da. Kallo. Adda ta fito itama tana kallon imaan din. Tsam ummi ta mike tana dan murmushi tare da karasawa wajen imaan din tace “lafiya kuwa meke damun ta”. Imaan de bata ce komai ba tana ta kokarin amai dukda cikin tababu komai. Adda tace “ina ruwanki bnsan kilibibi”. Kuluwace ta shigo gida sbd yaya Auwal ya biya ya fada mata bata da lpy shine suka taho ita da ya Abbakar. Ganin halin da take ciki yasa ta dogo imaan ta amshin ruwan da Adda ta debo ta wanke mata fuska. Ya Abbakar yana mata sannu batare daya yarda ya kalli inno ba bare yaga hararar da take aika masa. “Imaan jikin ki zafi sosai anya bazamuje asibiti ba”.   Tayi maganar tana kallon Ya Abbakar. Nana tace “Asibiti name kuma bayan kunsan abinda ke damun ta” Sosai gaban kuluuwa ya fadi ta kalli Nana murya nadan shagewa tace “meke damun ta” da sauri jummala dake son tabbatar da hasashen ta tace “kinga ummi kuje tare ni kaina naga jikin nata yayi tsanani kila bata saba bane kinsan habuja. Adda da duk ta damu tace “nide ku kaita Asibitin nan kunsa er dakta ce. Seda asibiti”.
Kuluwa ce ta shiga ta dauko mata hijab ummi ma ta mike. Kuluwa bataso da ummi zasu tafi ba sede bata ce komai ba sbd kar yaya Abbakar ya dauka wani Abu.  Wata rakwakkwababbar adede ta. Yaya Abbakar yawsamo masu. Kaf kauyen guda biyu ne. Bama koda yaushe kake samun su ba. Suka saka imaan a tsakkiya se yaya Abbakar a gaba. Suka tafi asibitin dake kauyen kusa dasu.  Akwai layi sosai. Amma kasan cewar yaya Abbakar yasan su yasa. Aka karbe su. Yan tambayoyi yayi ma imaan akan yanda take jin jikin nata. Tana fada. Masa. Jinin ta yasa a ka diba domin test. Sun dau lokaci kafin ya dawo yana murmushi. “To ai kai abokina ciki ne da ita har wata daya”. Mikewa kuluwa tayi a rude “ciki kuma a ina imaan din”. Yaya Abbakar kam kallon likitan kawai yake yama kasa magana. Yayinda ummi ta saki wani murmushi. Imaan kau lumshe idanu tayi tana karanto hasbunallahu wa nimal wakeel kuluwa zata kara magana yaya Abbakar ya dakatar da ita tare da fadin ku tashi muje”. Dole ta hakura ta juya tana kallo imaan da har lokacin idon ta yake a lumshe kamar ma bataji abinda aka fada ba...gaba ummi tayi bata tsaya kama imaan ba kamar dazu. Hakama yaya Abbakar. Kuluwa ce da idon ta suka fara tara kwalla ta kamata.   Koda suka shiga napep din babu wanda yayi magana har suka karaso cikin gari a kofar gidan umma ta saka a sauke su. Ummi ta kalleta da sauri. Tare da fadin dalili. “Wani kallo kuluwa tayi mata “ina ruwanki”. Dariya sosai tayi snn tace “Abin kunya de kam an riga an dauko”. Kuluwa batace mata komai ba. Ta kama imaan suka fita. Yaya Abbakar ma babu abinda yace suka wuce zuwa gidan su imaan   ... suna gani ummi ta shigo duk suka mike “ya tana ina ne”.  Tabe baki ummi tayi  “kunya ai bazata barsu suzo nan ma domin kau ta jawo abin kunya ciki wata daya”. Tafe hannuwa suka shiga yi suna sallami. Adda kam dif taji bakin ta ya dauke tama kasa magana...

Urs
✨✨✨
ANNAFIE😍😍💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
              ANNAFIE💖…✍️
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
  Aa
Bismillahir rahmanir raheem
💫💫💖Jalal Alii((36)💖💫💫
Inno tace “akaf dangin mu babu wanda ya taba cikin shege se ita” “to wama yasan wnn kona nawa nawa ne. Habuja fa. Aini tun kallon farko da nayiwa imaan na nasan tasan namiji”. Ummi ta kyabe baki “abin kunya dai kam anyo shi yaude munga karshen karyar Abuja da boko”. Dariya jummala tayi “wama ya sani ko shi dackan koro ta yayi idan ba haka ba meyasa wnn karon ta dawo ita kade?”
Adda de kam daki ta shiga ta zumbulo hijabin ta ta fito tana kallon su snn tace “Allah kaga yanda wadan nan bayi suke bin wanna baiwa taka ta sharri sbd hassada Allah kashiga tsakanin su da ita” daga haka ta nufi kofa. Nana tace “bari na biyo ki domin na tabbatar Hurera ma bin bayan ta tayi jikin ta har rawa yake.
Umma ta dauke kanta daga imaan ta ta zauna kasa ta jingina da gado idanun ta lumshe. Ta kalli kuluwa. Kiyi mun bayani kin tasani kina ta kuka wani abu ya samu imaan din ne. Share hawaye
kuluwa tayi “umma ...umma imaan” se kuma ta kifa kai ta fara kuka  umma da duk hankalin ta ya tashi tace kiyimun bayani kuluwa”. Kuluwa ta dago ta kalli imaan da idanun ta ke lumshe tana tuna last haduwar da sukayi take fada mata zataje makaranta. Yanda imaan tayi mata bayani bata taba dauka imaan cewa zata yarda ta siyar da mutuncin ta ba.  Tana kallon imaan tace “meyasa wayewa zata saka ki zubda mutuncin ki mene amfanin ilimin inde har haka ilimi da wayewa suke wlh bama bukatar su.” Ta kalli umma da ta kasa sanin inda zancen ya dosa tace “umma imaan tana da ciki. Umma imaan ta jawo mana abin kunya makiyan mu sun samu abin fada akan mu”. Wani irin salati umma tayi tana kallon imaan da hawaye ke fita a idon ta babu tsayawa. Umma ta shiga girgiza kai “imaan kice mun ba gsky bane. Kice mun karyane sbd ni nasan kina da tarbiyya kalle ni kicemun ba haka bane”.   Imaan de kam ko motsi bata yi babu wanda ze iya fassara yanayin da take ciki.  Umma ta zauna gaban ta tana kallon ta tace “imaan bude ido ki kalle ni” a hankali imaan ta bude idanun ta ta kalli umma    . Camly umma tace “mene gsky zance imaan ki fadamun baki da ciki. Kice mun ba gsky bane dan Allah karki mun karya”. Fashewa imaan tayi da kuka dan she don’t knw what to say bata san me zata fada masu ba bata san ta ina zata fara inde har da gske tana da ciki to cikin Jalal ne. Taya zata fahimtar dasu cewa cikin nan da ubansa taya zata fara fada masu tayi aure basu sani ba. Kuma zasu gane cewa Abba na gadon Asibiti kuma abinda ko ganin sa tasan bazasu samu damar yi ba snn rayuwar Abba kamar wani sirrine me a wajen jalal ta kula basa so asan cewa yana raye kuma fadar da zatayi hakan ze iya bama wasu makiyan damar sanin cewa Abba na raye kuma zasu cigaba da kawo masa hari kuma zasuyi wani plan din  bata san ta yanda mutane zasu dauki zancen ciwon nasa da auren nata ba duk yanda zata fada tasan gani zasuyi kamar wasan yara inde har bashi Abban yazo yayi masu bayani da kansa ba. Wlh da ace tasan tana da ciki da batayi gigin dawowa kaunyen nan ba gefe umma ta koma ta zauna hawaye na fita a idon ta “meyasa imaan meyasa. Karfa ki manta ke marainiya ce karfa ki manta iyayen ki talakawa ne. Be kamata wayewar da kika samu tasa ki manta suwane iyayen ki ba. Wai tsaya. Ina dacta taya baku dawo tare ba” sosai gaba imaan ya fadi jin umma ta sako da zancen Abba. A haka Adda dasu Nana suka iske ta a cikin gidan. Yanayin su kade ya bama Adda amsar cewa imaan ciki ne da ita. Ta shiga girgiza kai “wlh kaf dangin mu ba a taba cikin shege ba se a kanki imaan. Ynx kashe shi mamman din kukeso kuyi. To wlh cikin shege bade a zuriar mu ba. Bade kuma jika ta ba. Zaki dawo ki sameni.” Daga haka ta juya tana kuka sosai. Hurera ta shigo tana mata wani kallo...”to yan birni kuma da tsarabar da aka dawo knn lallai kam ande ji kunya daga haka ta saki bude ta fice” Nana ma tazo ta yada tata maganar ta wuce. Imaan ta bisu dakallo tana mmkin anya wadan nan jinin ta ne kuwa  shin me tayi masu suka tsane ta haka mene laifin ta. Shin dan ta rasa mahaifiya shknn se kowa ya fara kokarin ganin ci bayan ta. “Lumshe idanu tayi tana kewar Abba da mommy. Tare da tausayin mahaifin ta wanda ta kula ynx gba daya baya tare da natsuwar sa. Ta kalli umma da kuluwa da suke ta hawaye tasan kosu da suke kaunar ta bazasu fahimce ta ba.  Kife kanta tayi tana fashewa da wani irin kukan. Babu wanda take hangowa se baba wanda yafi kowa sonta a duniya. Da kuma yanda ze dauki lamarin.  

Alh barau ya zubama Alh isa ido yana sauraren abinda ze fada bayan sun gama gaisawar. Dan yasan abune mahimmi wanda yasa suka hadu a wajen kebewar tasu. Alh isa ya nisa kafin yace “jiya da na fada maka Jalal yayi aure ya kaji lamarin”. Dan jinjina kai alh barau yayi kafi yace “kasan har ynx bn fita daga shock I naver thought yana da wayon aure. Har kuma ya boye. Though ze iya boyewa sbd bacin ran Mahaifinsa. Sede abin daurewar kai shine auren sa. Aure fa  Aure fa ba abin wasa bane yaushe yayi hankalin yin aure”. Alh isa dake kallon Alh barau yace “kasan wace yake aure”. Alh barau ya girgiza kai kice da son jin zance. Dauke kai Alh isa yayi kafin yace “ita wnn yarinya daga gida Dr umar ta fito kuma a gidansa can kaduna aka daura aure. Dr umar ne ke rikon ta tun tana yarinya”. “What Dr umar yana da rai ne. Taya jalal yasan sa me daurin auren ke nufi”.  Cewar Alh Barau hankali tashe murmushi Alh isa yayi “calm down my frnd su basu san kome game da wnn ba domin kau jalal bema sansa ba. Ikon Allah ne ya kaisa gidan. Har Dr ya daura masu aure kafin yabar duniya sede nasan da wata manufa yayi”. Alh barau yace “yaya zamuyi knn snn ina yarinyar take ynx”. “Tana kauyen su  snn ynx zamu maida hankali ne kan mutum biyu. Wnn yarinyar da kuma matar Dr dan tabbas nasa da dalilin tafiyar ta. Dan haka dole mu saka idanu akansu. Neman su ya kamata mu farayi”. Alh isa yayi maganar idon sa Akan Alh barau dake ta faman gyada kai alamar ya gamsu.  

Sageer dake driving ya juya ya kalli jalal da idanun sa suke a lumshe baze iya fassara yanayin da dan uwan nasa ke ciki ba. Amma yasan yana cikin damuwa. And ba komai bane ke dawainiya dashi se soyayyar imaan. Sunje kaduna duk wasu neighbors din su imaan sun tambaya ko sunsan kauyen su amma babu wanda ya sani.  Ko ynx da kyar sageer ya samu suka dawo gida. Kuma tunda jalal ya shiga motar ya lumshe idanun sa ko uffan be ce ba har suka shigo cikin Abuja.   Murya can kasa sageer yace “take it easy bro You’ve seen a lot so dont let this into ur mind abun ze ja maka wata matsala.”  Jalal ya bude idanun sa ya kalli sageer.  Kamar zeyi magana. Se kuma ya fasa. Ya cigaba da bin gidan nasu da kallo wanda shigowar su knn. Yanajin ya tsani gidan da kowa dake cikin sa. Dan sune silar duk ma wani abu daya samesa kuma yake kan samun sa a duniyar nan.   Suna gama Parking bece da sageer komai ba ya bude ya fita   ...sageer ya bisa da kallo ganin yanda yake tafiya wani a hankali. Dan girgiza kai yayi snn ya bude ya shiga. Jalal be samu kowa a palor ba ya nufi part din sa. Bedroom dinsa ya bude ya shiga. Bathroom ya fada tare da sakarwa kansa showar ko kayan cikin sa be cire ba. Idanun sa a lumshe.yanajin kamar imaan zatazo ta cire masa. Sanin bata nan yasa ya cije libs dinsa tare da fara zare bottoms din a hankali. Yana saka wa ransa imaan ce ke cire masa kamar yanda. Ta saba. Tunawa da yayi ba ita bace yasa ya saka hannu ya yaga rigar snn ya fara wankan cikin zafi zafi dan bama yaso ya kawo ma ransa itace. Sageer daya shigo ynx ganin ya shiga wanka ya fice domin hada masa tea dan duk yau babu abinda jalal ya da a cikinsa   Yasan tun jiya ma babu wani abu a cikinsa.
Sanye yake cikin bathrobe ya fito yana dan tsane gashin kansa. Gaban mirror ya nufa. Ya zauna saman kujeran dake gaban mirror yana kallon kansa. His eyes are so redish telling exactly what his heart is going through. Lumshe idanu yake. Yana dan cizar lips dinsa a hankali. Shigowa sageer yayi da cup din tea. Ya nufi inda jalal yake ya mika masa “take bro”. Babu musu jalal ya karba har tym din idon sa a lumshe  suke.   Kamar sageer zeyi magana se kuma ta juya ze tafi har ya kai tsakkiyar dakin ya tsinkayi muryar jalal a disashe yace “may be imaan is tired of living with me” cak sageer ya tsaya. Se kuma ya juyo yana kallon jalal da har tym din idonsa a lumshe. Sageer yayi folding hannunsa yana Kallon jalal kafin yace “why did you said that bayan kana ganin an koreta an wulakanta ta and you’re still expecting her to stay”. Jalal ya ciji lips dinsa da karfi. “Yeah naji an koreta an wulankata ta but why cant her stay because of me”. Wani kallo sageer yayi masa. Kafin yace “you as who? As a husband who’s just leaving with her because of some reason wanda at any tym zaka iya rabuwa da ita or as a husband. Wanda yake zaune da ita badan yana sonta ba?”  Jalal ya bude idanun sa da sukayi jawur yana kallon sa “nace maka bana sonta ne. Nace maka zan rabu da ita ne” sageer ya ware hannu. “Fada kuma na nawa”. Jalal ya cije lips dinsa da karfi kamar jini ze fita. “Sageer koda na fada kasani I don’t mean it”. Tabe baki. Sageer yayi. “Idan ni nasani ita ai bata sani. All what she will think is. Dama ba sonta kk ba kuma ga familyn ka sunzo sun kore ta. So why will she stay what imaan did is ryt dan da kimar ta bazata zauna inda za a wulakanta ta ba gara ta tafi wajen iyayen ta. Ta zauna dasu duk yanda suke”. “Will you shout off sageer”. Jalal ya fada cikin tsawa. Dan bema san lokacin da ya mike daga kujerar da yake ba. Yana kallon sageer da jajeyen idanun sa yace “did I have to tell imaan I loved her. Wlh sageer you knw this da bana son imaan wlh I won’t stay with her. Zan iya taimakon ta ba tare da auren ta ba. But. I love her. Ina son imaan tun kafin nasan zan aure ta. She’s my choice I love her from day 1 i mean day 1 tun ranar dana fara ganin ta i felt the sign of love  I try to deny it but is real. I never thought I will love any girl apart from my mother except when I met imaan. You see that small little girl called imaan. Wlh  I love her she’s an angel. She turn every single of my sadness to happiness   Whenever ever am with her I feel calm and happiness she’s peace of mind. And that love. Sageer koda bana son imaan tun farko she deserves to be loved  sbd haduwa da imaan ya canza abu dayawa na cikin rayuwata. Just take my drinking habit. Itace silar denawa ta. Ta tsaya tsayin daka domin taga. Na dena. Look at yanda rayuwa ta ke tafiya. No one cares about me. No body knws what I’m going through. My heart is very sad. Just trying to be ohk. But rayuwa da imaan ya fara chanza mun bakin ciki zuwa farin ciki. She trys her very best to make me happy and. I’m. bare kuma ina sonta. Komai nata inaso. Se ynx dana saba da ita I’m so so addicted to shine zasu suyi kokarin rabani da ita.and ita kuma. Imaan kawai ta tafi. Without even thinking of halin da zan shiga kawai ta tafi”. Sageer kallon jalal kawai yake har ya gama zancen sa. Wanda tun yanayi cikin zafi har ya komayi cikin rauni. She dama already yasan jalal loves imaan kawai yana karyata kansa ne. A hankali ya matsa kusa da jalal daya ya juya masa baya a ynx yana sauke ajiyar zuciya ya tafe shouder dinsa. Kafin yayi magana. Jalal ya juyo ya rungumesa. Cikin rauni ya fara magana “pls bro help me. I can’t endure loosing imaan. I love her. I knw you always want my happiness. Dan Allah ku nemomin. Imaan. Bazan iya juren rashin ta ta wlh bazan iya ba. Bansan cewa sonda nake mata yakai haka ba se dana kwana na tashi bn ganta ba. Pls bro help me. Inajin rashin ta har cikin raina my heart is been severally sad but this tym around I can’t take it I feel the pain of loosing her har cikin raina” kasa magana sageer yayi dan be taba jin jalal na magana irin haka ba. Kuma be taba dauka son har ya kai haka ba. Ji yayi idanun sa sun cika da kwalla. Idan ya tuna cewa imaan tana daga cikin farin cikin jalal. Imagine ace ur lyf is sad tun farko. And latter on you find out someone wanda yake saka ka farin ciki duk wani farin cikin ka yayi relying akan sa. Daga baya kuma kazo ka rasa sa. Jin an turo kofa yasa duk suka kalli Dad daya. Shigo. Wanda already yaji komai.   A hankali Dad ya warewa jalal hannu come to me my son.  Babu musu. Jalal yaje ya rugume dad dinsa sosai. Haka shima dad ya kankame dan nasa ciki da tsanin kauna da tausayin dan nasa a hankali yace “pls son forgive me. Pls my son. Ur dad is very srry”. Gyada kai kawai jalal yayi ba tare da tace komai ba   Dad yace “I promise you duk inda imaan take sena nemo maka ita. Inde that will make you happy I will koda duka strength dina ze kare inde that will make you happy wlh I will. Ur dad is here for you. I’m here to clear all my mess. And when imaan is back. We will join hands and. Change ur saddest life. To the most happiest life. Ur mother will come back kuma zatayi rayuwa kamar kowa”. Sosai Jalal ya kankame dad yanajin wata kaunar sa. Shi kansa yasan yana kaunar dad dinsa ....
Kallon sageer Dad yayi snn yace “my son give sumayya a call tell her to prepare something light for my little se ka kawo masa cup of tea”. Babu musu sageer ya fara kokarin dialing numbern sumy yana ficewa a dakin domin zuwa ya hado masa tea. Da taimakon Dad jalal ya shirya ya saka kaya marasa nauyi snn dad ya cigaba da lallashin sa har sageer ya dawo da cup din tea. Babu musu jalal ya karba ya fara sha sageer ya zauna ya zuba ma dan uwan sa ido. A ransa yana mmkin taya imaan ta shiga zuciyar jalal haka. Yasan jalal yana da damuwa kuma yana da juriya amma meyasa ya kasa jure na imaan. Knocking akayi. Dad ya bada izinin shigowa. Sumy ce ta shigo rike da warmer. Granny ta shigo se Mahmoud a baya. Ita kanta sumy seda ta tsorata ganin yanayin dan uwan nata. Duk da har ynx ta kasa gane ya akai imaan ta auri jalal bata sani ba. Tasan jalal ya santa amma bata san taya suka kulle ba. Kuma ta kula ga dukkan Alamu dan uwanta na tsananinn son imaan. Se taji duk haushin kanta takeji. Akan yanda jiya suka rika treating imaan. Granny ce da kanta ta rika bama jalal Abincin shima be musa ba ya karba. Suna lallashin sa shide bece da kowa uppan ba. Seda granny ta tabbatar ya koshi snn ta barsa  kallon su kawai jalal yake yana ganin yanda kowa ke kokarin calming dinsa. Sosai yaji dadin kulawar su. Amma yasan kome zasu masa. Bazasu cire masa digon abinda yakeji cikin ransa ba. Imaan kade ze gani a gaban sa ya samu salama. Dan. Ji yake zuciyar sa ta masa wani empty kamar imaan ta tafi da komai na zuciyar tabar masa kwanko. A ynx babu abinda yake son gani kamar ta. Shi kansa ya dade da sanin yana sonta amma be   dauka ya kai haka ba.   Idan ya tuna korar ta akayi se yaji zuciyar sa na tafarfasa. Yanajin babu dadi dan yasan itama taji babu dadi. Amma duk da haka yanajin hakan be kai har ta tafi ta barsa ba. Sbd ya dade da sanin cewa imaan ma tana son sa    Se da akayi sallah sukayi ta tare a cikin daki da jalal har Ishai ma granny da suka koma ta aiko masu da abinci sukaci. Sageer yayi masu sallama. Snn ya tafi. Dad ma ya dade yana lallashin dannasa snn shima ya tafi.  Maida idanun sa yayi ya lumshe tare da sauke ajiyar zuciya system dinsa ya janyo ya fara danne danne. Bama mom dinsa lvri kamar yanda ya saba. Anan ne ya samu damar zayyane mata duk abinda yakeji game da imaan. Kafin ya gama his eyes are so redish. Kanshi na wani irin sara masa. Yanajin zuciyar sa so empty. Kallon gefen sa yayi. Se yake ganin kamar tana dakin ta zata zo daga baya. Cizar lips dinsa yayi sosai. Kafin ya rufe system din. Ya mike tsam. Wajen da yake aje keys dinsa ya nufa. Ya dauki key daya. Yana kallonsa kamar me nazarin wani abu se kuma yace. “Srry imaan I have to”. Yayi maganar cikin rauni. Har ya nufi kofa. Se kuma ya dawo dan baya son dad yasan da fitar sa. Wasu keys din ya dauka. Ya fice kofar side dinsa ya bude wacce direct zata kaisa waje yabi ya fita. Wajen jerin motocin sa ya nufa ya dauki daya. Ya fice da mugun gudu. Yana driving amma jikin sa har rawa yake yasan yau inde be sha wine ba baze taba samun natsuwa ba. Ya cije lips dinsa “don’t blame me wife blame ur self you just left without even my permission as ur husband kin tafi bada izini na ba zaman su kike ko nawa. Yayi maganar yana buga sitiari. Eatry din daya fara haduwa da imaan ya nufa. Yaje ya zauna a exactly seat din da ya zauna wancan karon. Looking directly to the door yana ganin kamar ba zata zo. A yanda ya zauna duk wanda ya gansa seya firgita. Ya dade idon sa akan kofa. Yana tuna first tym daya fara ganin ta first tym daya fara ganin love of his life. Tambayar sa akayi me za a kawo masa shine ya dawo dashi cikin hankalin sa. Tusa duka hannuwansa yayi cikin sumar sa yana jinjina abinda ze fada. Fuskar imaan ya gani tana girgiza masa kai kamar zatayi kuka. Runtse idanu yayi tare da cizar lips dinsa yace “wine”
Duk yanda imaan take tunanin kauyancin en garin su to ya wuce nan. Dan babu jimawa. Sega makota sun fara shigowa. Wai sunji imaan bata da lpy sunzo dubata.   Dole umma ta fito ta baro imaan a daki ita da kuluwa. Makota ne keyin sallama umma ta amsa. Tare da shinfida masu tabarma a baranda  Wata me suna. Mande tace “aa base mun zauna ba wani. Lvri mukaji a gari wai imaan da ta dawo daga habuja harda tsaraba”. Umma ta daure fuska “bn fahimci zancen ku ba”. “To hakade mukaji. Ashe maganar jummala gsky ce. Babu karya cikin abinda take fada akan yarinyar nan” wata kuma tace “to shi dactan da suka tafi tare yana ina” da sauri mande tace “Ke raba kanki da talakan da yasamu waje kika sani ko wani mugun abun tayi masa. Idan ba haka ba ai shine ke maido ta da mota amma ance a kura a kura aka dauko kayan ta” umma da idanun ta suka cika da kwalla   Tace “ku rika kyautata zato dan Allah”. Da sauri suka katse ta. “Ahhhh wane zato kuma ga mugun abu ta dauko. Kema wlh kiyi ta kanki dan wama ya sani ko wani mugun abun tayi shiyasa ta gudo. Dan inde mutum ya saba da bariki baya barinsa seda dalili” shiru umma tayi tana kallon su suka cigaba da fadin maganganu marasa dadi akan imaan. Karshe de se daki umma ta koma ta barsu nan zaune. Har tym din suna zaune jigum jigum babu wanda yace da wani. Kala. Umma ta bi imaan da kallo tana tuna yanda jiya taitacin wainar flour imaan da bata son wainar flour. Tabbas alamomin ciki duk sun bayyana ga imaan amma tayaya mene ribar imaan na zuwa ta bada kanta.  Umma ta share hawaye.   Jin wasu mutane suna kara shigowa gidan. Suna surutai yasa umma fashewa da kuka. “Ynx imaan ina amfanin wnn abin da kika jawo mana. Mene ribarki. Ku tuna kefa marainiya ce. Har wace irin wayewa ce zata saka ki manta asalin ki. Fashewa da kuka imaan tayi sosai. Tanajin zuciyar ta nayi mata nauyi. Tasan babu wanda ze fahimce ta a ynx. Amma Allah ma sheda ne. Da hankalin ta bazata taba yarda ta zubar da mutuncin ta a rariya ba

Kafin kace mene lvr ya zagaye gari cewa imaan tayi cikin shege. Jummala kam tuni taje wajen malamun ta ta caske masa kudi dan da har ta fara zargin kudin ta kawai yaci. Koda da dawo seta wuce gidan kawayen ta. Da sauran mutane tana kara aibanta imaan. Seda ta daidaici lokacin daura dan waken ta yayi snn ta wuce gida.   Aikam yau. Jummala taga costumers sbd kowa naso yaji zance. Aikam ta baje baki tacigaba da gayamasu duk abinda yazo ranta. Ita da yaran ta kam zuciyar su fess.
Tun kafin baba ya shigo gidan aka fara taresa da zancen. Wanda. Ikon Allah ne kawai ya rikesa. Dan jiyayi zuciyar sa ta wani irin bugawa. Dukda wani bangare na zuciyar sa yana gaya masa karyane. Sede ya kasa gane dalilin daya saka ya shiga razani.
A hanya yake haduwa da wasu abokanen nasa. Inda. Wani malam audu ke jajenta masa. Nan baba yake cewa shi bema sani ba.  Malam audu yace “malam mamman inaga akwai wani lamari babba wanda bamu sani ba. Dan ya kamata kayi nazari cewa meyasa wnn karon dacta be kawo sa da kanta ba. Dan naji wani lvr a gari na cewa wai wani mugun abun ta aikata shiyasa ta. Gudo. Dan haka Ina shawartar ka daka kiyaye ka boye erka dan gsky mutanen burni basu da mutunci “ sosai baba ya tsorata da lamarin kuma yayiwa malam audu godiya ya nufi gida zuciyar sa na wani irin bugawa.   Yana bukatar yaje yayi nazari. Shin imaan ersa ce tayi ciki. Er marainyar diyar sa. Yasan imaan da rawar kai. Amma bayajin imaan zata aikata wani mugun abun sede idan itama yi mata akai kuma maganar ciki ya rasa inda ze saka tunanin sa. To kode fahimtar hakan da dacta yayi shiyasa ya korota. Dole yaje ya bincika amma kam ze boye diyarsa idanma wani abun ta aikata sbd yasan tabbas ramuwa tayi sbd ita se anyi mata takeyi....

Koda Baba ya shigo gida jummala na tsakar gida ita da yaran ta. Sun siyo doya da kwai sun bage sunaci tsabar murna. Dawowar imaan kawai suke jira shigowar baba yasa duk suka natsu. Yayinda jummala ta mike ta rike kugu “yau zaka gasgata abinda na dade ina fada maka kayi biris dani sbd kaga mafi soyuwar erka tana kyau ta waye tayi fari ka banzatar da zancena. To yaude gashi ta dawo da abin kunya kuma ga dukkan zato wani mugun abun ta aikata. Snn inaso a dauko ta daga gidan can ta dawo nan dan nan ne gidan ubanta atoh”. Kafin Baba yayi wata magana adda ta fito tana kuka wiwi. “Mamman wnn yarinya taka bata da imani bata rike mutuncin ta ba. Kaf dangin mu babu wanda ya taba cikin shege. Mamman ciki fa tayo ciki fa. Gashi ta gudo tazo mana nan wama yasan ne tayi. Mu karta ja mana. Maza azo a kiramun lawal. Itama umma ku kirata ynx dukkowa yazo yau senaji wanda yayi mata cikin nan. Dan wlh bazamu yarda ba”.
Babu yanda Baba ya iya dole yayi yanda tace din shigowar yaya Auwal knn ya aikesa gidan umma akan tazo ita da imaan. Snn ya aika gidan inno a kira yayan nasa. 
Shi kansa yaya Auwal maganar ta dakesa dan har gidan sa ake zuwa ace ai kanwar sa tayi cikin shege. Sbd damuwa kasa fitowa yayi se ynx da duhu yayi. A yanayin daya iske su umma kade seda suka basa tausayi. Ya kalli imaan da duk tayi wuja wuja. Ga damuwa da yunwa suna damunta tanajin yunwa amma ta kasa cin abinci bama tasan me takeson ci ba. Abincin da umma tayi mata dole aman sa tayi. Sakon baba ya fadawa umma. Snn ya karasa kusa da imaan ya kamo hannun ta tare da fadin “imaan”. Fashewa da kuka imaan tayi tare da fadawa jikinsa tasan a wnn gabar  shine kade ze iya fahimtar ta ya tausaya mata. Shafa bayan ta yayi kafin yace “tashi muje gida”. Imaan ta girgiza masa kai “yaya I’m afraid bazan iya kallon babana ba. I don’t knw what to tell him. Im going back yaya auwal bazan iya zama garin nan ba just tell baba that I’m srry tell him to forgive me”. Shi kansa yaya Auwal yasan cewa imaan ta canza yasan cewa rayuwar ta tada da ynx ba daya ba sede yanajin akwai wani abu me karfi dan gane da wnn cikin nata. Zeyi magana yaji muryar umma a disashe “kunga ku tashi muje”. Komai imaan batace ba dan wani irin shakkar umma taji tanaji. Tana mata kallon uwane kamar de mommy. Haka imaan ta tashi jikin ta babu kwari suka tafi. Koda suka fita a hanya duk inda suka gifta sede kaji ana itace aikam daga gani da gske ne tunda se dare take fitowa. Tirrr wayewa de batayi amfani ba yaude munga karshe boko” wasu kuma se kaji suna. Mude kartaja mana Allah yasa ba wani abun ta aikata ba taja ai tashi kauyenmu kasan idan bakauye yasamu waje be iya cin arziki ba. Harda ma kwadayin ubanta ynx wa gari ya waya taje ta kwaso abin kunya. Sosai maganganun suke shiga kunnuwansu amma ya zasuyi. Kuka kawai imaan take tanajin tausayin su umma kuluwa kam dum dazu Abbakar ya aiko wai tazo. Suna shiga gidan imaan taji kafafunta sunyi mata nauyi sakamakon mutanen da ta gani su kawu lawal matar sa inno da kuma jummula ga adda da bakin ta yaki shiru. Yaya Auwal ne ya kamo hannun ta “muje imaan” “zaki shigo ko sena zo ka karerayaki Allah de ya isa abinda kika mana”. Dukushewa imaan tayi agabansu ta kasa dago kai ta kallesu. Fuskar baban ta kade take hasasowa. Kawu lawal yace “imaan ki natsu ki fadamun gskyr Abinda ya faru zanyu maki tambayoyi”. Gyada kai imaan tayi kanta cikin hijab dinta. “Na farko wane yayi maki ciki snn na biyu ina dacta”. Shiru imaan tayi dan wlh bata san me zatace masu ba. Idan tace cikin ta yana da uba to tayaya. Kuma ina Abba shine tashin hankalin ta. Inno ta tabe baki “irin wnn fa baka gane wanda yayi mata ciki sede asan nayi kawai”. Da sauri Adda tace “asan mene ai wlh gobe gobe sena samo magani an zubar da cikin nan da ba za a haife mana shege ba”. A wani irin razane imaan ta kalli Adda wanda ita kanta bama tasan tayi ba har tana girgiza kai. Kuma babu wanda ya kula se baba da yaya Auwal. Da sauri jummala tace zubar wa kuma? “ adda ta rike kugu eh makira. Dama abinda kikeso knn. Amma kisani idanma wani mugun abin kikayiwa jikata wlh bazata haife mana shege ba kuma se Allah ya saka ma marainiya kuma shege bade a gidan nan ba. Idan kinma manman na kyale ki bazaki ma imaan ba wlh. Dan kome kika mata harda dana ze cuta” Mikewa jummala tayi “kai yau naga ikon Allah wnn wane irin abin kunya ne. Yarinya tayo karuwancin ta se kuce nice ina na ganta ma. Nide babu rwana ni akayi niyar kuntata mawa gashi kuma ya dawo kanku. Kuna wahalar da kanku ne wajen tambayar waye yayi mata ciki. Allah kade yasan wanda yayi. Shawara ta shine ku boye ta dan Allah kade yasan mugun abinda ta aikata kuka ganta anan. Ehe” baba dake kallon imaan cike da nazari yace “mamana ina dacta da na bama Amanar ki”
Kamar daga sama imaan taji maganar baban ta kallonsa tayi dan tsorace kafin tayi kasa da kanta tana share hawayen da suka taru a idon ta.” Daga yau baki kara barin garin nan har se dacta ta dazo kokum nayi bincike”.  Da sauri imaan ta dago tana kallon babanta. Wane bincike zeyi to. Ita bama wann ba babban tashin hankalin ta shine dayace bata kara barin garin nan. Ba kowa ne yazo ranta ba se Jalal......

Urs
✨✨✨
Nafeesatuh😍😍💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
              ANNAFIE💖…✍️
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
  Aa
Bismillahir rahmanir raheem
💫💫💖Jalal Alii((37)💖💫💫
“Ko bakiji ba” muryar umma ta dawo da ita daga tunanin jalal da ta tafi gyada kai imaan tayi tana share hawayen ta. Umma tace “tashi mu tafi” da sauri. Adda tace “taje ina. Babu inda zataje wlh tana gidan ubanta kuma daki na. Babu inda zata” umma bata kara magana ba ta kalli yaya auwal “kasiyo mata abinci yau bataci komai ba”. Daga haka ta fice. Jummala tace “ya siyowa wa fasikar bade dana ba” kalmar ba imaan kade ta daka ba har baba wanda ya kalli jummala da sauri zeyi magana tayi masa wani kallo “to yi magana mu gani”. Shiru baba yayi. Inno tace “kaga tashi mutafi. Allah de ya kyauta abun magna kam an jawo mana”   Babu musu ya tashi suka fita  adda ta tabe baki ina ma amfanin haihuwa irin taku mata duk sun gama daku.   Ta juya ta kalli imaan “ke kuma zaki tashi ki shiga daki ko ko ai duk ke kika ja mana”. Babu musu imaan ta tashi ta shiga daki tanaji hurera na mata habaici amma tayi biris da ita tashige ta cigaba da kukanta.  Wajen me tsire yaya Auwal yaje. Ya siyo me yawa ya dawo gida dakin addan ya shiga ya iske imaan ta kudundube a kasa tana ta kuka ya karasa kusa da ita “er kanwata”. Da sauri imaan ta dago fashewa da kuka tayi tare da fadawa jikinsa ta rungume sa. Pls yaya Auwal help me I can’t stay baxan iya zama garin nan ba i knw no one will understand me yayana. Babu wanda ze fahimceni.”  Sosai auwal yaji tausayinta ya mika Mata tsiren hannunsa “zakici”. Kamshin na dukan ta karbi ledar da sauri ya taimaka mata ta bude ganin yanda jikin ta ke rawa. Aikam babu shiri ta fara ci  Zuba mata ido yayi ganin yanda take cin naman da ka gani kasan yunwa takeji. Kuma tabbas akwai ciki jikinta. Tunda har ya saka ta wnn rawar jikin wajen ci. Seda taci dayawa snn ta dago ta kalle sa. “Yaya har ga Allah bani da niyar bata maku suna wnn cikin kaddara ta ce kuma babu yanda zanyi nasan babu wanda ze fahimce ni kaf gidan nan ma bare yan garin nan”. Sosai yaji tausayin kanwar tasa. And maganarta  ta ynx yasa ya fara tunanin ko kaddara ce ta afka mata. Tuni yaji wani tausayin imaan din. Sosai. “Imaan fyade aka maki ne”. Kallon sa imaan tayi da sauri dan batayi tsammanin tambayar ba. Lokaci daya kuma Jalal ya fado mata. A rai  se taga bazata iya kamanta sa da kalmar fyade ba. Snn kuma bazata iya cewa akwai aure akanta ba. Share hawayen ta tayi. Snn tace “karka damu inshaallah soon gsky zatayi halin ta”. Murmushi yayi kafin yace “inshaallah ki kwantar da hankalin ki nasan bazaki taba yin abinda ze jawo mana zagi ba. Ki cigaba da addua seda safe kinji kanwata”. Daga. Haka ya tashi dan bayaso taga hawayen sa. Dan shi ya riga ya sakawa ransa cewa fyade akayiwa kanwar sa. A bakin kofa yaci karo da baba idanun sa sunyi jawur  yake kallon auwal. Shi kansa auwal din yaji tausayin baba matuka. Kama hannunsa yayi. Zuwa dakin sa ya zaunar dashi. Kafin yace wani abu baba yace “fyade akayi mata ko dan inaji a jikina imaan bazata ci Amana ta ba” “nima haka nake tunani baba. Sede bata gayamun haka ba” cewar yaya Auwal. Baba ya jinjina kai “inde hakane Dr be rike amanar dana basa” da sauri auwal yace “kar kace haka baba. Inaji a jikina wani abu ne ya faru. Tunda kaga har ta dawo gida ba tare dasu ba. Abinda ya kamata shine karmu kara bari tabar cikin garin nan har se munyi bincike itama da adda zata bari. Da kauyen su Adda aka tafi da ita. Dan mutanen garin nan bazasu barta ba wlh” Baba ya girgiza kai “ nima babu inda zan bari taje ...
Imaan najin cikin ta ya cika ta bingire a wajen se bacci. Sama sama taji shigowar Adda tana masifa. Ita de bata motsa ba sbd baccin da takeji.

Jalal irin shan da ake cewa mun kwana biyu bamu hadu ba yayi. Dan shi kansa baya kallon gaban sa. Gashi har wasu ya taho dasu. Yace “any day without you imaan i will take one and blame ur self not me”.    Haka ya taho se sumbatu yake. Ikon Allah ne kawai ya kawosa gida da gaba daya en gidan sun fito dan tunda daddy ya shiga yaga bayanan hankalinsa ya tashi fiye dana kullum sbd yasan a yanayin dayabar dan nasa. Yana shigowar yaga kowa a waje yayi parking a bigen sa yana layi ya fito. Sumar sa kamar anyi yaki. Lips dinsa sunyi wani irin red. Ya kalli dad dinsa. Tare da ware hannu “ Dad why are they all here they are waiting for me to come back drunk ryt?”. Dad ya girgiza masa kai “no my son they all care for you” “fuck them all no one among them have a single care for me. They all want my sad lyf. They chease my imaan out because am leaving a happy lyf with her. Tell them to all go away I hate them I them they chease my imaan. They always want to see me sad. And fne you’re happy now. Imaan is my happiness and she left me haka kukeso ai” da ido dad yayi masu sign duk su tafi. Shikuma yabi bayan jalal daya nufi side dinsa yana tangadi.   Yana zuwa ya fada saman gado ko takalmin sa be cire ba. Dad da idanun sa suka cika da kwalla ya matso kusa dashi yana cire masa takalmi yanajin da ze san inda imaan din nan take da ayau din nan ze iya kashe ko nawane dan a kawo masa ita.  “I’m srry Dad. May be nine kaddarar ka. I don’t think i will ever be happy  without imaan daddy. I go so many things but I don’t knw why my heart can’t endure loosing imaan I love her. I love her and I love her heartfully amma sun rabani ni da ita. I don’t think I have any strength to fight them. Tunda sun riga sun rabani da ita. Ramain nothing kawai suzo su kashe ni. All the strength da nake dashi imaan have taken all. I’m suffering since at my young age. They kill my twin bro. A idona ya rasu.  My mom is still suffering. And imaan ma dana fara samu farin ciki tare da ita sun rabamu. Me nayi masu haka ne.”  Dad hawaye kawai yake be sani ba. Dan dukan su har sageer ya shigo basu sani ba.   Seda yace “waya fada maka imaan ta tafi. Imaan will come back because she loves you”.   Tashi zaune jalal yayi yana kallon sageer da jajayen idanun sa “that’s what I thought but I was wrong. Da tana sona. She will not go and leave me all alone” yanda jalal yayi maganar cike da tausayi. Tashi Daddy yayi yana share hawaye dan baze iya kallon dan nasa a haka ba. Sageer ya bisa da kallo kafin ya maido da duban sa ga jalal.  “Imaan will come back to you soon” jalal ya kallesa “promise” sageer ya gyada kai “sure I promise.”  Murmushi jalal yayi kafin ya koma ya kwanta tare da lumshe idanun sa sageer naso yace ya tashi ya sauya kaya amma ganin yanayin da yake ciki yasa Yy shiru toilet ya shiga yayo alwala ya kabbara sallah raka biyu yayi tare da rokawa dan uwansa shiriya snn ya rage masa radadin son imaan dayakeji a ransa. Yasan jalal has go through alot. Na imaan ba komai bane. Amma akan ta yasan mene farin ciki. Tunda ya taso ze iya cewa imaan ce kade yasan jalal ya taba zama ya bata tym har suyi having conservation. Gefen dan uwansa ya dawo ya kwanta a ransa yanajin kamar ya kira mamy ya fada mata domin itama tasan da zancen auren.

Da asubah imaan ta tashi jikinta nayi mata wani irin ciwo sbd kwanciyar kasa da tayi. Kallon Adda tayi dake gefe tana sallah. Itama tashi tayi tanajin jikin ta nayi mata wata irin dandaka alamar zazzabi. Koda ta fito wajen babu kowa. Ba abin mamaki bane sbd tasan yan gidan sallah ba wani damun su tayi ba. Alwala tayi ta koma daki. Ta kabbara sallah. Har ta idar adda na saman sallaya. Wani kalan yunwa imaan keji tana so ta janyo sauran naman ta na jiya taci amma tsoron adda take. Kamar ta shiga ranta taji Adda tace “ke ynx da abinda zaki saka mana knn. Kin jawo mana abin kunya makiya sunga kofar mana dariya” shiru imaan tayi. Adda ta fashe da kuka “to wlh dan shege bade a zuria ta ba” daga haka ta tashi tana balai ta ninke abin sallahr snn ta fice daga gidan ma gaba daya. Imaan ta kwanta inda tayi sallah. Kawai tunanin wane irin rayuwa zatayi a kauyen nan take. Tunda baba yace bazata kara fita ba. Knn zaman ta ya dawo nan knn. Bata san har iya tsawon wane lokaci abba ze dauka kafin ya samu lpy ba dan tasan shine kade ze iya fitar da ita daga wnn zargin. She don’t knw of Jalal ko ze neme ta. Meyasa ma ze nemeta. Tunda dama zaman da suke na wucin gadi ne. Idan ma dan sbd amanar Abba ne to. Ba ganin ta zeyi ba har se Abban ya samu lpy and that’s the end karshen auren su yazo. Dan runtse idanu tayi. Data tuna cewa rabuwa zasuyi da jalal. Wani irin ba dadi take ji but she don’t knw why all she knws is. Ynx she’s so attached to him. Ya riga ya saba mata da kansa kwana biyu da tayi ba tare dashi ba ji take kamar a kan kaya take. She miss all of him   Taasan cewa auren su na wucin gadi ne. But she can’t dany what she’s feeling for jalal. She loves him.tasani ba tun ynx ba tana kokarin hana kanta but she can’t jalal daban ne kawai. Tasan cewa yana da wacce yake so amma bazata iya hana zuciyar ta sonsa ba.   Lumshe idanu tayi tana tunanin ko ynx yana ina. Yana jin abinda takeji kuwa. Tasan ba lallai ba tunda bawai sonta yake ba. Amma se ynx takejin dama bata taho ba. Da tasan kalar abinda zata iske anan knn dama bata taho ba. A haka har bacci ya dauke ta bama tasani ba. 
Karfe takwas da wani abu ta farka da sauri sbd wani amai daya taso mata. Babu shiri ta fita sede ko nisa batayi ba ta fara kwarara shi a tsakar gidan.  Duk binta da kallo akayi. Imaan bama tasan sunayi ba. Seda da gana amaye duk abinda taci jiya snn ta dago. Wane irin faduwa gaban ta yayi ganin tarin mutanen dake tsakar gidan. Yau har wadan da basu zuwa yima jummala siyayya sunzo dan su gane ma idon su. Abin haushi ma harda masu aure dan wasu duk gasunan da kananan yara. Ita kanta imaan zata iya recalling faces din wasu sa’anninta.  Wanda tasan ynx duk suna da yara. Irin kallon da kowa keyi mata se taji duk ta tsorata. Wata tace “ashe de kam da gske ne” “ga Zahiri mun gani. Nan nan za azo da mota ana mana yanga su ala dole yen birni sun waye. To ga wayenan sun kaiki sun baro”. Imaan ta kasa daga kai ta kalli masu magana. Ganin yanda kowa ke yaba mata magana kamar dama jira suke. Sbd yanda duk ta tsargu yasa ta tashi da nufin tafiya daki. Jummala ta daka mata wata irin tsawa “ubanki ne ze kwashe maki Aman cikin shegen da kikayi” da sauri ta dawo ta nufi drum duk ma ta rude kamar ba imaan ba. Ga wani zazzabi dake cinta. Hurera tace “ande ji kunya”. Kasa dago kai imaan tayi ta kalleta. Haka ta debo ruwa ta kwashe ta share aman tanajin yanda suke yada mata magana. Imaan se kokarin danne kukan ta take tama kasa daga ido ta kallesu. Tana gamawa. Tazo zata shiga daki taji “hurera tace “a hayye yan birni yaran yan gayu. Anje an saki jiki ansha dadi. An kuma dawo da abin kunya” tuni kowa dake gidan ya fashe da dariya. Shigewa daki imaan tayi tare da fashewa da kuka. Sosai kalamansu suke mata zafi. Wani irin danasanin dawowa garin nan take. Da ace tasan tana da ciki wlh bazata taho ba. Kuka imaan take sosai. Domin har lokacin bata dena jiyo voice dinsu suna mata ihu ba. Ji tayi ta tsani garin nan ta tsane sa domin kau cike yake da marasa ilimi.   Se wajen 10 snn taji sun lafa se kananun maganganun su jummala da takeji. Jin shigowar Adda gidan yasa imaan juyawa kamar me bacci. Cike da fada tace “zaki tashi koko ga magani na samo maki dan wlh bazan iya bude ido naga shege ba. Jin hakan yasa gaban imaan faduwa. Adda ta dauko kofi ta zuba ruwa. Kamar zatayi kuka take fadin Allah ne kade ze saka mana tsakanin mu da dacta dan ya cucemu. Bame ke ba hatta ni nunani ake. Wnn ba halinki bane sauyaki akayi. Ke kuma kikaje kika bude kafafu aka zura maki ciki. To wlh ba a gidan nan ba. Maza tashi kisha. Da kyar na samo shi wlh. Tashi nace”  a hankali imaan ta tashi ta zauna idanun ta sun wani kumbura saboda kuka. Adda ta tabe baki “baki ga komai ba” karbar cup din imaan tayi tana kallon maganin gaban ta na wani irin faduwa. Adda ta tsare ta maza sha. Imaan ta kai maganin bakin ta. Yanda Adda ta tsare ta yasa taji koma mene ze faru sede ya faru.  Lokaci daya ta saki maganin ya zube a jikin ta wani kuma saman gado” wata irin mikewa adda tayi ta daura hannu saman kai “wlh tana sane tayi” ta juyo ta kalli imaan “ke duk wahala dana sha a kasa zaki zubar mun da magani. Shege kike son haifar mana to wlh baki isa ba. Kinsan wahalar danasha”. A hankali imaan dake hawaye tace “adda kiyi hakuri” “rufemun baki Allah ya isa abinda kika mana wlh kuma kin cuci maraicin ki. Uwar ki ba haka take ba ubanki ma haka dan ma baya ruko da addua shiyasa matar sa ta shanye sa. Zaki kici ubanki inde a gidan nan ne kuma wlh baki haifar mana shege a gidan nan”.
Daukar hijab adda tayi ta fita tana bambami.   Bata dade da fita ba baba ya shigo ya kalli imaan data kasa daga ido ta kalle sa. Wani irin tausayin ta yakeji. Muryar sa a shake yace “me zakici”. Da sauri imaan ta dago ta kallesa. Se kuma ta fashe da kuka tana girgiza kai. “A hankali yace kiyi hakuri Allah ze saka maki”  imaan ta dago da sauri ta kalli mahaifin ta. Baba ya fita da sauri jin jummala tana kwala masa kira. Yana fita ta rika masa wni kallo. “Kai ynx har wani hada ido kk da waccan. Wacce ta jawo maka abin kunya. Da yake ita er so ce ai har daki kake binta. Hurera kam dayake ba kaunar ta kk ba daga auren ta ya mutu kaki yarda ma kaji dalili ka rufe bewar Allah da fada”. Shide baba bece da ita komai ba ya sa kai ya fito. Imaan duk tanajin su banda hawaye babu abinda take. Tayi mugun danasanin dawowa garin nan gashi ynx ance bazata koma ba tasan baba duk kallon fyade aka mata yake. Sosai yanda suke sheganta mata ciki abin ke mata ciwo tasan babu yanda zatayi kaddara ce ta kawota kauyen nan ta rinka bin maganin daya bare da kallo gaban ta na wani irin faduwa.  Ynx wnn duk dan a zubar mata da ciki aka samoshi. Cikin ma bana kowa ba sena jalal.  A hankali ta saka hannu tana shafa flat tummy dinta. Ynx nan jinin Jalal ne a cikin ta.  Dan lumshe idanu tayi. Tare da sakin murmushi. Ko daya bata taba dana sanin wnn cikin ba. A hankali take ta recalling moments dinsu da jalal da kuma yanda aka samu cikin. Sunyi shearing unforgettable moment da jalal. So how will Jalal feel idan ya ga tana da cikin. Wata zuciyar tace “meyasa kike tunanin zeji dadi bayan ba auren soyayya kukai ba bama lallai yaji wani dadi ba tunda rabuwa dama zakuyi besides shi yanama da yan mata” dan da nan jikin ta yayi sanyi kawai hakanan taje ta saki jiki da mutumin da bama ajin ta bane ba kuma sonta yake ba   “But you love him” wata zuciyar ta fada. Runtse idanu tayi kafin tace “sure I love him” ita kanta ma bata san cewa tana sonshi ba  bama tasan sanda ta fara but she’s sure she loves jalal. Shiyasa ma harta sake dashi.  And now sunyi nisa da juna. Bata sani ba ko he miss her too. Or he don’t even care. But ita de tasan she misses him badly. Musamman yanxu da take dauke da cikin sa. Tanajin wani irin sonsa da bama tayi tsammani ba   Duk da tasan yafi karfin ta batajin zata iya dena sonsa besides bata jin zata iya rayuwa da wani namiji bayan jalal. Ya riga da ya saba mata da kansa. And now sunyi wa juna nisa. Bata san inda zasu sake haduwa ba sbd tasan babu wanda yasan a wane kauye take. Sede idan Abba ne ya samu lpy but when. Kwana biyu da tayi babu shi tana ji kamar ta shekara. Kallon cikin ta tayi. Har yanxu se shafa sa take. Wani zuciyar yace “ga unforgettable gift nan ya baki”.  Ta goge hawayen ta koba komai. Koda sun rabu idan taga dansa zataji dadi ta rika tunawa dashi. She wish ace koma mene zata haifa yayi kama da jalal. Sbd tasan kila ko sun hadu da jalal   Kilan takardarta ze bata tunda tym din Abba ya samu lpy. Ai daga nan zata cigaba da karatun ta su fara sabuwar rayuwa ita da danta dasu Abba idan ta kammala kuma. Ta samu aiki tazo ta dauke Baba dasu umma daga rayuwar wnn kauyen me ciki da kauyanci   .....shigowar ya Auwal ce ta dawo da ita daga tunanin ta. Ganin yanda take hawaye yasa ya karaso da sauri taba jikin ta yayi jin zafi sosai yasa yace “subhanallah imaan sannu kinsha magani”.  Ta girgiza masa kai. Ya auwal ya dauko flacks din tea da kuma bread daya shigo dashi daga gida yasaka matar sa ta hada masa ne.  Tea din ya hada mata snn ya mika mata babu musu imaan tasha dan wata irin yunwa takeji. Yaya Auwal de yayta bin ta da kallo har ta shanye ta dago ta kallesa idanun ta cike da hawaye tace “nagode yaya”. Ya gyada mata kai yayi yana ganin yanda gaba daya ta sauya daga imaan din daya santa. Daga labule akayi. Sega jummala.  Wani irin kallo tayiwa yaya Auwal kafin tace “ynx har wnn abin ta fini ko. Wato ka daurewa iskanci dama. To wlh zan hanaka shigowa gidan nan inde wajen karuwar nan zaka rika zuwa wato harda kawo mata tea da biredi”.  Yaya auwal ya mike “kiyi hakuri daga haka ya fita”.     Ta kalli imaan da kanta ke kasa tace “malama fito waje kiyi aikin gida”. Kallon ta imaan tayi tanajin maganar kamar daga sama. Wai aikin gida. “Ko bakiyi ne kike kallo na” cewar jummala.  Abidace ta shigo cikin gidan tare da mijin ta. Harda buda “inaa me juna biyun take”.   Jummala tace “gata ina mata maganar aikin gida se wani kallo take mun”.  Abida ta shigo dakin “na rantse da Allah ko ki tashi kona nakada maki shegen duka”.   Hurera ma ta fito daga ita se daurin gaba bata damu da iliya mijin Abida dake wajen ba. Shigowa  dakin tayi ta kama hannun imaan ta mikar da ita tsaye snn ta kama hannun ta har wajen wanke wanke “zauna kiyi mana aiki malama. Ko munada maki shegen duka kuma wlh duk kauyen nan babu me kwatar ki ynx ba da bane Bare baba ya shigar maki. Ko adda sede tayi rakin ta ta gama amma wlh bata hanani dukan ki. Ba birni kikaje ba ko ina kikaje banza karuwar banza”. Imaan ta rinka bin hurera da kallo anya wnn er uwar tace kuwa. Dan tsanar tayi yawa Abida ta karaso kusa da ita “wai ko bakiyi ne seki fada Mana” Dukar da kai imaan tayi. Kafin ta dauki soso da omon. Tana kokarin danne kukan ta tasan ba karamin aikin su bane su zaneta. Itada ynx bata da lafiyar nan. Haka ta zauna tana wanke wanken nan kamar ba imaan din Abba ba.  Su kuma suka koma gefe suna kallon ta se yada mata magana suke.  Iliya ne yace “ke tashi zo zubomun kokon nan daki”. Babu musu imaan ta tashi. Ta dauki cup ta zuba masa kokon tana ta kokarin hana aman da takeji saboda warin kokon”. Ya kawo masa. Abida tace “ kinga nima jeki zubomun” tashi imaan tayi babu musu ta zubo masu ita ynx bata son wnn fitinar tasu. Wlh wani tsoronsu ma takeji yo ta dade bataga fitina ba irin tasu “.   Bayan ta zubo. Ta juya zata koma wajen wanke wanken Amai ya kwace mata. Dukawa tayi ta fara kwara sa duk abinda ta taci seda ta amayar dashi. Banda dariya da suke mata babu abinda suke.   Tanajin su babu yanda ta iya tana gamawa ta tashi ta debo ruwa ta fara wankewa seda ta gama snn ta koma wanke wanken me uban yawa.  Kuluwa da yaya Abbakar ne suka shigo. Ganin abunda imaan take yasa ta karasa da sauri wajen imaan “ wanke wanke kuma wane mara imanin ne ya saki “.  Jummala tace “nice nice nan nasaka ta ko da abinda zakiyi ne”. Kulawa nayi mata wani kallo tce “wlh batayi imaan tafi karfin wnn wanke wanken. Kude da kuka saba kuzo kuyi kayanku “. Iliya yace “wane kuma bata saba ba ga babban sabo nan a cikin ta”. Duk suka fashe da dariya.  Kuluwa ta kama hannun imaan “tashi muje”.  Ya Abbakar daya nemi waje ya zauna yace “hawwa ina ruwanki dama shine dalilin dayasa kika matsa muzo”.  “Yaya taba jikin ta fa kaji zafi wlh bata lpy ga kuma ciki”.  “To koma de mene ai ita tajawa kanta ni kinga babu ruwana inde har kinsan abunda ya kawoki knn tashi muje”. Kamar yanda kuluwa ta saki baki tana kallon ya Abbakar haka imaan ma. Hawayen idon ta sunki tsayawa mamaki take kamar ba yaya Abbakar din da tasani ba fashewa da kuka kuluwa tayi yayin da ya Abbakar ya tashi ya bar gidan. Su hurera kam bnd dariya babu abinda suke. Imaan kam tunda ta dukar da kanta tacigaba da wanke wanken bata kara dagowa ba.  
Kuluwa kam dukawa tayi ta cigaba da kuka. Koda Adda ta shigo basu dago ba. Wani irin zagi ta kudunduma tana fadin “wlh ba cikin shege tayi ba ko uban mene babu wanda ya isa ya kara sakamun jika aiki”. Kama hannun imaan tayi “tashi muje” duk fashewa sukayi da dariya sunabin Adda da taja imaan dake da kallo “hurera tace “karuwar jika” Adda ta fito bayan imaan ta shiga daki “ke bazawara ki mana shiru idan ma karuwancin ne wane ya kaiki Allah kade yasan gidan mutanen da kike zuwa kina bude kafa”. Hurera ta fashe da dariya “bude kafa ga wacce tayi nan kin saka a daki harda tsarabar da ta samo wajen bude kafafu”.   Tashi kuluwa tayi tabar gidan dan zata iya cigaba dajin cin mutuncin da akewa imaan ba. Bata tsaya ko ina ba se gidan su. Ko tsayawa gaida iyayen nata batayi ba tace “umma dan Allah imaan ta dawo gidan nan wlh can cin mutuncin ta ake kuma kinga can inna jummala na Sana’a kowa ze iya shiga gidan yaci mutuncin ta. Tashi baban kuluwa tayi yana gyara hular sa “babu abinda ze saka ta dawo gidan nan na wuce fada me gari na nema na nasan akan maganr ta ne kuma a matsayina na wanda ke aiki a fada be yiwuwa ace a gidana zata zauna” daga haka ya fice kuluwa ta bisa da kallo hakama umma.

Sageer da suke waya da mamy bayan ya gama tambayar su ya suka isa saudiyya tace “lpy qlw wlh ya jalal”. Kallon jalal dake zaune ya kurawa window ido yayi snn yace “mom akwai matsala and kuma laifin mu ne da bamu fada maki ba had it been mun fada maki tun farko da kila duk wnn matsalan bata faru ba” mamy dake kallon sa da kyau tace “me ya faru”. Labarin komai ya rika bata be boye mata ba tundaga kan tasiu da suka kama zuwan su kaduna auren jalal har zuwa yau.
Mamy seda ta shiga shock “sageer aure amma bazaka iya fadamun ba what’s wrong with you guys da kun fadamun da duk haka bata faru ba nan ta fara masu fada. Snn kara dayi masu nasiha.

Da sauri Atika ta dauki wayar ta ganin huwaila ke kiranta. Dama tunda abin nan ya faru huwaila bata daukar kiranta. Shiyasa komai ya cakude mata batasan ya kuma zatayi ba gashi yanxu ko zulfa bata kulata. Tana dauka tace “haba huwaila ashe dama haka kike ke ba kawar arziki bace” “aa wlh na tsorata ne amma kina ganin yaron nan yana da kudin daya fada kuwa”. Tsaki atika tayi “wlh bashi dasu. Duk wani kudi da kika sani uban ne ke basa. Nide ynx ba wnn ba kinsan cewa Alh.Ali maganar matar sa yake” “dan Allah to tayaya” atika tace “wlh abubuwa sun kulle mun bansan ya zanyi ba ga alwashi daya daukar mun” huwaila tace “ni ba wnn ba. Wai ashe manga yazo abuja wata daya knn amma ba a san inda yake anya yaron nan ba yanda da wayo ba”. Atika tayi shiru kafin tace “na fara zargin sageer Amma ba jalal ba sbd nasan wane shi wlh ko dakinsa kika shiga bema sani ba nima abinda yasa yasani sbd tunda yana yaro yasan ni ke basa giya ya tsane ni ne sbd yasan ni na raba ubansa da uwarsa

Urs
✨✨✨
Annafie😻💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
              ANNAFIE💖…✍️
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
  Aa
Bismillahir rahmanir raheem
💫💫💖Jalal Alii((38)💖💫💫
Aikam dole musan inda manga yake dan wlh asirin mu yana gab da tunowa kisaka ido sosai akan sageer ni kuma zan saka a kula mun dashi nan waje”.  Daga haka suka cigaba da tattauna yanda zasu bullowa lamarin. 
Sageer ya kalli jalal da yayi banza dashi yana shiryawa for the fourth time sageer yace “I’m talking to you bros where are you going”. Jalal ya juyo y kalli sageer da jajayen idanun sa snn yace “gidana”. Be jira cewar sageer ba yayi ficewar sa. Kusan cin karo yayi da zulfa da take kokarin shigowa. Jalal ya zuba mata idanun sa yanaji kamar ya kashe ta ya huta. Idanun ta a kumbure alamar tasha kuka tace “pls yaya kayi hakuri ka yafe mun wlh zan iya auren ka ka hadamu nida imaan din pls”. Tayi maganar cikin kuka sosai daga gani kasan tana mugun kaunar sa. Camly yace “this the last time da zaki sake comparing kanki da imaan” daga haka ya tsallake ta. Sbd a yanda yke ji yanzu bashi da wani strength din yin wani masifa. Shi kade yasan abinda yake going through a zuciyar sa abubuwa sun masa yawa. Komai sabo yake dawo masa yake sabo. Ganin sageer ya biyo bayan sa ne yasa ya kara sauri ya shiga motar sa yabar gidan da mugun gudu. A yanda yake ji a ynx he need to stay alone. Yanaso ya natsu yayi tunani. Dan cizar libs dinsa yayi yana tunanin kila abu wani yayi wa imaan ya fursar da isaka “imaan if I didn’t something wrong you  should’ve told me ba wai kawai kiyi deciding tafiya ki barni ba. Or because I didn’t say I love. Ki dawo wlh not just love I will give you ever best love of ur life I promise not to talk of any gal except you i love you and words are not enough to say how much I love you” idan kaji yanda jalal ke magana seka tausaya masa. Gefen hanya ya samu yayi parking saboda wani jiri dake dibar sa. Ya kifa kansa da sitiyar kafin a hankali cikin wani irin raunin murya yace “me nayi masu. Mene laifi na. Tun ina yaro baku barni na huta ba. Duk wani masoyana se kunga bayansa. First of all kun rabani da mahaifina. Then mahaifiyata. Ya runtse idanu “my mum is still suffering my innocent mummy. And you kill my twin bro. Kun barni ni kade before I found imaan. And now. Imaan has gone. Almost 3dys without her. Is that mean imaan has gone forever or what.   Noo then if she’s gone I will be gone. This is too much for the innocent me I will leave the world for them. They call me bad boy but god knws I’m not a bad boy. Sageer will take care of my mum but for me its over”. Daga haka ya cigaba da driving daya daga cikin gidanjen sa yaje wanda yasan sageer ba lallai ya gano sa ba. Ya dauki kwalaben wine dinsa ya shiga dasu
  Ganin mota ya shiga shima sageer ya koma Ta dauko key. Bin bayansa yayi sede ko barbashin motar sa be gani ba. Gidan da suka zauna da imaan ya fara zuwa. Be gansa ba hankalinsa ya tashi sosai nan ya fara bi dukkanin gidajen jalal da yasan ya sani amma be gansa ba.  Hankalin sageer ya tashi sosai dan har yamma be gano jalal ba. Gida ya koma dan wayar sa ma be dauko ba kamar yanda yasan jalal din ma be fita da tasa wayar ba. Duk tsaitsaye ya gansu sunyi cirko cirko a parlor dad se kaiwa da kawowa yake. Yana ganin sageer ya karasa wajen sa “sageer where is jalal ina kuka je”. Shiru sageer yayi seda dad ya kara tambayar sa snn yace “dad I can’t find him yace mun de gida zeje gidansa and na duba duk wasu gidajen da nasan zeje but baya can.   Shiru dad yayi kafin yace “follow me muje”. Har sun nufi kofa granny tace “nima zanje dan Allah” dad ya kalli Alh isa yace “ka taho tare da ita...
Dad ne ya rinka ma sageer kwatancen gidan har sukazo abba isa kuma suna bayansu da granny da sumy da itama tace seta zo dan gaba daya itama ta shiga damuwa. Dad Addua kawai yake Allah yasa jalal yana nan dan yasan jalal nasan wnn gidan. Shine ya basa shi tun yana karami kuma jalal din nason gidan. Jin gidan a bude yasa dad yaji wani relief. A daya daga cikin bedroom din gidan suka samu jalal yasha giya yayi tatul. Da sauri sageer ya karasa kusa da jalal. Dad kau mutuwar tsaye yayi. Har seda Abba isa ya kamasa snn ya sauke ajiyar zuciya yana kallon jalal dake dan fitar da numfashi sama sama ga kwalbar gida a gefen sa. Granny da sumy fashewa sukayi da kuka.   Sageer na taba jikin sa yaji wani irin zafi sageer ya kalli dad “jikinsa da zazzabi sosai”. Mikewa jalal yayi ba tare da yace komai ba ya nufi toilet. Sede kawai ji sukayi yana kwarara Amai. Da sauri duk suka kasara bakin toilet din. Sede jalal ya gama amayar da duk giyar daya tuttula snn ta fito yaki kollon kowa a cikin su. Wata giyar ya dauka ya fara barewa. Sageer ya karasa da sauri ya amshi ta “baka ga condition din da kake ciki ba kanason kashe kanka”. Jalal ya kalli sageer da jajayen idanun sa kafin camly yace “yes sageer inaso I want to die. Gara na koma wajen mahaliccina tunda basa son rayuwa ta then I have to leave. Ni da mummy mutuwar mu tafi rayuwar mu. 20yrs mummy batasan wake kanta ba ita kade tasan azabar da take sha 20yrs bani da peace of mind se yaushe zan samu farin ciki. Is better nida mummy duk mu mutu mubar masu duniyar suci abinda zasuci. Nasan babu abinda nayi masu then hakkin mu baze barsu ba mene amfanin zaman duniyar nawa. My heart is sad everyone ya sanni a badboy ba gara na mutu ba. Pls ku tafi ku barni. Sanda kuka tabbatar na mutu kuzo ku dauki gawata. And for imaan sageer duk ranar da ka hadu da ita tell her inasonta tayi hakuri bn fada mata da bakina ba but I love her”. Kuka sosai granny take wnn karon ko sageer seda yayi hawaye. Wayar sa ya dauka ya kira doctor “pls doctor it’s urgent I will send you the location”. Suna gama wayar ya tura masa masa address din.
Allurar bacci doctor ta fara yiwa jalal. Snn ya fara duba sa. Jinin sa ya hau sosai. Ruwa ya kara saka masa tare da rubuta magunguna snn ya bama sageer “se an kiyaye gsky dan at any time za a iya samu matsala gobe da safe zanzo in duba sa.
Bayan doctor ya tafi abba isa ya kalli Dad da tun dazu beyi magana ba snn yace “yakamata ka tashi muje gida mama da sumayya zasu zauna dashi snn ga sageer girgiza kai dad yayi “I can’t go and leave my only son a cikin wnn halin and inde wani abu ya samu dana then nima tawa ta kare”.   Kade na wnn maganar mana yaya”. Dad yace “ka koma gida ka sa a kawo mana duk wani abu da zamu bukata”. Dole Abba isa ya tafi    Direct gidan Alh barau ya wuce. Bayan sun gaisa a parlon Alh barau din Abba isa ya gama basa labarin komai. Dariya Alh barau yayi kafin yace “kenan burin mu na gab da cika. Dan wlh dansa ne ze kashe sa cikin sauki dan idan ba ikon Allah ba jalal na barin duniya sede ayi gawa biyu. Ai bamu san soyayya zatafi illatasa haka ba ai da ita muka fara bi” Abba isa yayi dariya. “Hakan ma yafi tunda inda soyayya ce ba lallai abin ya damu uban ba. Amma duniya tasan munanan halayen dan ka abin da ciwo. Ynx de ita waccen yarinyar zamuji da ita. Either ta mutu kokuma mu mu boyeta. Kawai de mu fara gano inda take kafin su.”  Alh barau yace “hakane amma ya batun fareeda an samu wadan da zasu mana aiki a kanta acan saudiyyar koko”. “Girgiza kai Abba isa yayi “me tsaronta ne kade yake da ikon ganin ta. Yanzu babban matsalar mu shine wnn yarinyar sbd nasan doctor umar nada babban dalilinsa na hada auren tabbas”. Wnn hake ne.cewar Alh barau “kaga dayan biyu. Either tasan wani abu game da poison din kokuma tasan cewa mune behind ciwon fareeda”. Alh isa yace “kai fareeda fa ita da rayuwar duniya har abada barta taita zama a haka kafin mu karasata. Ita taja komai ai da tun farko ta amince ai da ynx tana rayuwar ta. Yaranta duka suna nan kuma  ba zasu shiga tashin hankali ba da mijin tane kade zata rasa”. (Kuji fa se kace rayuwar a hannun su take). 

After 2mounths
Kwanaki sun shude akayi sati ynx gashi har watan cikin imaan uku. Watan ta biyu a kauyensu amma ji take kamar ta shekara biyar. Ta azabtu iya azabtuwa.Kuka kam bazata iya auna bokiti nawa ta zubar ba. Zagi dacin zatafi kam babu wanda batasha ba. Ga cikin ta me mugun wahalar wa. Gidan su seda ya zaman mata a living hell zata iya cewa bata taba rayuwa me tsananin wnn ba ga cin zarafi yan kauyen ma ko ganiya basa yi. Jummala kam Costomers dinta sun kara yawa. Badan Adda ba da seta maida imaan baiwa a gidan nan. Amma duk da haka imaan bata tsira ba aikine de se adda bata nan take sakata.  Umma ce ke aiko mata da abinci. Kuluwa da ta fara kawo mata yaya Abbakar ya hana wai ba a bariki yake samo kudin ba. Kuma ya hana kuluwa zuwa gidan wai karta koya mata halin ta su nana kam da abida kullum suna gidan wani zubim harda mazajen su.   Ynx ma haka imaan na dakin Adda tanajin zancen su suna ta yabo mata magana iri iri. Yunwa takeji so take ta fito taje ta samo abinda zataci. Tun jiya take jin yunwa duk yau bataci komai ba. Furar da adda ta bata takasa sha. Hakama taliyar da umma ta kawo duk basu take son ci ba. Hijab dinta ta dauka ta saka yayi mata kyau sosai abin mamaki ko daya imaan batayi rama ba sema wani kyau da haske data kara dukkuwa da wahalar da take sha. Cikin kudin da tazo dasu ta dauki 2k ta fito. Kanta kasa.   Hurera tace “keee karuwa ina zuwa. Nan fa babu masu kudi. Ko an kasa hakuri ne haka nan za aji da yan kauyen”.   Imaan de batace komai ba kanta a kasa ta fita “tasan da hurera zata san wanda yayi mata cikin nan da bazata taba kawo ma ranta cewa zata kalli wani namiji ba  dan murmushi imaan tayi kafin tace “jalal is beyond expectations he’s handsome and adorable kullum jin sonsa take har wuya. She loves him so bana wasa ba. She miss him bana wasa ba cikin dake jikinta kade ne yake saka ta farin ciki ta kosa ya fito duniya wani irin kaunar abunda ke ciki take. Barin ma ynx da taga ya fara fitowa. Kullum cikin shafasa take. Adda tun tana nacin seya zube harta hakura.    Tunda ta fita kowa se kallon ta yake. Wasu su yaba mata magana wasu kuma su bita dana mujiya itade bata dago ba. Wajen me saida kifi taje bata yarda ta kalli kowa na wajen ba ta mika kudin tace “a bani na duka”. Me kifi ya amsa. Yayinda yan wajen suka fashe da dariya itade imaan batace komai ba burinta kawai ya zuba mata ya bata taje taci dan ji take kamar zata mutu. Wani a wajen yace “Abbakar ya kake faskewa ne gafa kanwar ka. Dafa kaso yarinyar nan” wani tsaki Abbakar yayi yace “dallah mene haka Allah ya tsare ni da auren karuwa”. Dago ido imaan tayi suka hada ido da yaya Abbakar. “Bar kallona kafin na wanka maki Mari” me kifin yace “sede kace ba kanwar ka ba” “niba kanwa ta bace bana hada iri da kalar wadan nan dubi fa ciki ne jikin ta cikin ma ba shege wlh na tsane ta ni dama tunda akace zata fara jamia na sallama”. Me kifin ya mikawa imaan data fara hawaye kifin ta yace kiyi hakuri “. Fashewa da dariya yan wajen sukayi.  Muryar adda ce ta saka sukayi shiru. “Imaan me kike anan suke maki dariya” imaan ta rungume adda bayan ta karbi kifin ta. “adda ya Abbakar ke zagi na”. Se lokacin Adda ta kula dashi. “To wawa ita kanwar taka kake zagi a titi yanzo ko kowa ya zageta harda kai a cikin su. To shknn wlh se Allah ya saka mata”. Shine bece komai ba “muje ke kuma ai kece idan kifi kikeson ci baki jira na dawo wnn kaddararren cikin da kika ki bari a zubar idan kin haifesa zamu ga me rainon sa.   A hanya suka hadu da yaya Auwwal nan ya tambayi meke faruwa “adda ta fashe da kuka ta fada masa karya da gsky” jinjina kai kawai auwal yayi shima ya kula da yanda Abbakar yake akan imaan din. 

Babu abin tausayi kam se jalal da dad. Dan jalal gaba daya ya fita hayyacin sa kullum cikin allurar bacci ake masa da karin ruwa. Bayaci baya sha se anyi da gaske yace gara mutuwar sa da rayuwar da. Maganar giya kam sede idan be samu dama ba. Idan ka gansa kamar ba jalal ba. Gashin kansa ya kara wani yawa babu gyara. Maganar maganganun sa da ake yadawa kam shiru kake ji sageer ne tsaye kan komai baga lafiyar mummy ba baga Abba ba baga jalal ba baga neman imaan ba. Shima duk ya fita hayyacinsa. Shima dad na iya kokarin sa Amma ina. Lallai se ynx aka tabbatar da yanda dad ke son dansa dan ko aiki baya zuwa kuma ya hana kowa yazo inda yake. 
Dad ya shigo dakin da jalal yake sageer na zaune gefen sa while jalal kuma yana kwance idon sa a rufe.   Bayan dad sun gsisa da sageer dad yace “ya jikin nasa”. A hankali sageer yace “da sauki. “ dad yabi dan nasa da kallo yanajin kamar ya fashe da kuka. Dan bude idanun sa jalal yayi suka hada ido da dad din. Da sauri dad yace “my son”. Dan lumshe idanu yayi sann ya bude. Dan ynx ko magana ma bayayi sede yabiku da kallo Dad yaso a fita tashi amma jalal ya nuna ko daga gidan aka fitar dashe seya kashe kansa. Sbd bayajin ze iya barin kasar nan imaan na ciki.   “Pls son forgive me”.  A hankali tace “ I hv already done that daddy. I love you and I love mummy. I love sageer. And pls dont forget to tell imaan that i love her  I love her since from day one” wani irin tari ne ya kufce masa sega jini. Dukan su wata irin kara sukayi sukai kan jalal. Rike hannun sageer yayi tare dafe saitin zuciyar sa bakinsa duk jini yace “sageer inajin wani ciwo a zuciya ta na kasa cika wasiyar seif. May be idan mummy ta samu lpy bazata iske Kowa a cikin mu ba”. Wani irin fita dad yayi yana kokarin kiran emergency. Bayan ya gama ya dawo ya rike jalal dake ta tari yana hawaye da fadin ya yafe masa. Babu jimawa emergency suka zo daukar jalal akayi a ambulance aka tafi dashi. Dad kam kuka yake sosai. If anything happens to my son i won’t forgive my self. Sageer kansa hawaye yake. Dan yafi kowa sanin irin halin da jalal ke ciki.   Suna zuwa hospital din aka tafi dashi emergency nan da nan likitoci suka rufu akansa.    Sunyi kusan 2hrs kafin a samo kan numfashin jalal.  Doctor din na fitowa su dad suka bisa da gudu har zuwa office dinsa. Jikin dad har rawa yake yana tambayar meke damun dansa. Murmushi yayi kafin yace “da sauki damuwa ce kawai. Mun kuma shawo kan abun sede muyi fatan Allah ya basa lpy”. Ajiyar zuciya Dad ya sauke. Snn ya koma wajen jalal yana lekasa da window an saka masa naurar hancin nan. Sake kiran sageer doctor din yayi a sace dan kar dad ya sake biyosa.   Office din doctor ya nufa gabansa na faduwa.
Tunda aka shigo da jalal akan idon ta. Har zuwan sageer office din doctor. Hakan yasa tayi saurin zuwa kofar office din ta kanga kunne.
Doctor na kallon sageer yace “mene matsalar sa I mean jalal”. Sageer ya nisa kafin yace “yana saka damuwa a ransa and ynx kuma besan inda matar sa take ba. Shine ya haddasa masa wnn ciwon”. Doctor ya nisa snn yace “yana da ciwon zuciya kuma ya dade yana cinsa ynx haka yakai limit din da a kowane hali ze iya rasa ransa. Lallai inde har ba a gaggauta yi masa abinda ze saka farin ciki ba idan ya farka. A kowane hali ze iya rasa ransa”.   Wani irin tsinkewa zuciyar sageer take yana sauraren doctor har ya gama bayanin sa. Godiya sageer yayi masa da fadin za a kiyaye.
Jin za a fito yasa jiddah tayi saurin barin wajen. Sede inaa tuni sageer ya ganta hakan yasa ta ruga da gudu. Kokarin bin bayan ta yayi amma ina batayi wata wata ba ta shige motar ta. Cikin yan mintuna tayi mata key tabar wajen. Dole sageer ya hakura sbd yasan kafin ya dauko mota ta tsere masa. Sede zuciyar sa tayi masa wani irin nauyi. “Who is she”
Jiddah bata tsaya ko ina ba se a gaban katon gidan su   Tayi hon me gadi ya bude. Ko dede ta parking batayi ba ta fito da sauri. Ta nufi entrance din gidan nasu. Bata kula da wanda ke zaune dining yana cin abincin ba ta nufi stairs “hajiya jiddah wnn saurin fa”. Cewar matashin saurayin dake zaune saman dining din. Daka gani kasan yayan ta ne shima suna kama sosai. Kafin tayi magana wata mata ta fito daga kitchen daka gani kasan ita ta haife su duka. Kamar jidda zatayi kuka tace “yaya Muhammad wlh sauri nake. Ummana mommy fa”. Ta karasa tana kallon ummanta.”tana dakin ta inajin wani abu”.   Jiddah ta fara hawan stairs “umma we have to do something jalal is in critical condition.
Wani daki ta bude ta shiga.   Dede mommy tana linke sallaya knn da alama sallah ta idar. Tana ganin yanda jiddah tq shigo tace “yade meya same ki ne haka”.  Jiddah ta Zauna saman gado kamar zatayi kuka. “Mommy da matsala. Jalal tun wnn abun daya faru basa tare da imaan maganar da ake wlh ynx yana asibiti a ko wane hali ze iya rasa ransa.  Mommy I’m afraid wlh kar wajen taimakon jalal kuma yazo ya rasa ransa”. Sosai hankali mommy ya tashi to inde kam hakane yakamata ta bayyana ynx. Sede idan ba jalal da imaan ba wane ya kamata yasan tana raye wane ya kamata yasani “ kallon jiddah tayi snn tace “Yaya yana gida”. Jiddah ta girgiza kai “bnsani ba but let me check” “idan yana nan you let me knw ina son magana dashi”.   Fita jiddah tayi. Mommy ta sauke ajiyar zuciya. To ina imaan ta tafi?   Jiddah ce ta shigo. Mommy “ yana parlor “. Tashi mommy tayi tare da jiddah suka nufi kaya taccen parlon yayan nata. Kamilallen mutum ne zaune  a daya daga cikin kujerun parlorn da ka gansa kaga dan boko sosai. Mommy ta gaisar dashi ya amsa tare da fadin “mene naga duk kunyi wani iri”. Yayi maganar cike da tsokana.   Jiddah tayi murmushi ta fara basa labarin dalilin daya kawosu. Abie ya gyada kai. Kafin yace “dama can da farko kunyi kuskure. Waya fada maku cewa zasuyi wani tunanin maida jalal gida da matar sa.”  Mommy tace “kawai de naga idan imaan ta koma can gidan zata fahimci wasu abubuwan. Cos she’s very sharf bn dauka zasu koreta ba. Kuma babban matsalar shine daga jalal har Alh Ali basa nan akayi wnn aika aikan”. Abie ya gyada kai kafin yace “ gashi ynx kunja an raba masoya. Ai na fada maku tun ganin da nayi masu a super market na gano suna son junan su and ke jiddah kinfi kowa sheda haka”. Jiddah tace “sure matsalar da aka samu itace dukan su basa gida kamar yanda Mommy tace. Ynx de we have to do something.”  Mommy tace “mutum biyu ya kama ta nayi magana dasu imaan da kuma jalal. And dukan su babu wanda zamu iya Gani”. Abie yace “you have to do quick domin ceto rayuwar jalal “. Kamar Mommy zatayi kuka tace “and imaan bamu san ma inda take ba ni bnma san wane hali take ciki ba”. Abie yace “then sageer. Yakamata kuga sageer a yau din nan domin shine kade ze fito daku a duhu kusan duk halin da ake ciki”. Ya kalli jiddah. Dole ki koma asibitin nan ynx ki taho da sageer” “shiru jiddah tayi kafin tace “abie I’m afraid ya ganni fa. Baka ganin idan ya ganni ynx da matsala”. “ common my daughter bn sanki da sanyi ba. Sageer is very wise baze yi wani abu da za a samu matsala ba”.   Gyada kai jiddah tayi kafin ta tashi tabar su tare. Motar ta ta koma ta shiga. Asibitin ta sake nufa zuciyar ta cike da tausayin jalal.
Dede sageer dake kokarin bude mota ya shiga tayi parking. Sageer na ganin motan ya gane ta. Dan haka ya tsaya yayi folding hannayensa yana kallon ikon Allah. Seda jiddah ta gama kare masa kallo a cikin motar snn ta fito. Sageer ya ringa binta da kallo yana mmkin wace ita. Kafin tayi magana yace “who are you”. Kai tsaye  jiddah tace “ I’m jiddah”. “I’m not asking of just ur name”. Sageer ya fada yana mata wani kallo. Itama wani matsuyacin kallo tayi masa kafin tace “then you can follow me”. Daga haka ta juya ta shiga motar ta   Da mmki kawai yake kallon motar a ransa yana fadin ya shiga ko kar ya shiga. Definitely dole ma ya shiga sbd yasan dame take tafe. Bude motar yayi ya shiga. Yana shiga jiddah taja motar da wani mugun gudu. Kaman ya tambayi ina zasu je. Se kuma ya fasa yayi shiru. Har suka iso gidan su jiddah me gadi ya bude suka shiga babu wanda yayi magana. Seda ta kashe motar snn ta juyo ta kallesa “lets go”. Bata jira cewar sa ba kawai ta fita. Da mmki kawai sageer ke kallon ta kafin shima ya bude ya fita. Fuska daure yabi bayan ta   Suka shiga katon parlorn. Babu Kowa ynx se kamshi da sanyin AC. shide sageer mmki kawai yake dan ga dukkan alamu nan gidan su ne. “To who is she”. Direct parlorn Abie ta wuce dashi inda ynx har su umma da ya Muhammad suna ciki. Da sallama sageer ya sauka. Yana bin yan parlorn da kallo. Ganin duk be sansu ba.Har ya wuce Mommy ya maido da idonsa akanta. A ransa ya furta “Mommy” be santa ba be taba ganin ta ba. Amma yasan hoton ta a wayar imaan da kuma Abba da ya bincika. So finally mommy is back.  Haka nan yaji wani abu daya tokare masa makoshi akan jalal da kuma halin da dan uwansa ke ciki yana wucewa. Daga damuwa zuwa wani farin ciki
Manage pls
Today is my birthday 🎂 say a prayer for me pls 😻🥰🎉🎂🎊✨
Urs
✨✨✨
Annafie😘💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
              ANNAFIE💖…✍️
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
  Aa
Bismillahir rahmanir raheem
NOT EDITED

💫💫💖Jalal Alii((39)💖💫💫
Mommy ma ganin kallon da yake mata yasa ta gane ya gane ta. Lokaci daya idanun ta suka cika da kwalla. Tace “have a seat my son”. A hankali sageer ya zauna Mommy ma ta zauna. Sageer ya gaisar da yan parlon duk suka amsa   Snn ya maida idon sa akan Mommy kamar mommy zatayi kuka tace “ina dr?  Ya jikin jalal”. Sageer ya furzar da iska.”jikin Abba da sauki muna da hope din ze samu lpy soon Inshaallah ze dawo cikin hankalin sa. But jalal” se kuma yayi shiru   “Mene ya faru dashi “ cewar abie “ze iya rasa ransa a ko wane lokaci tunda imaan ta tafi komai ya rikice masa. Mun duba ta a ko ina daka sani amma bamu same ta ba so muna tunanin ta tafi kauyen su sede babu wanda yasan wane kauye ne almost to month kenan”. Abie yace “kana ganin ynx dawowar imaan ze taimaki rayuwar jalal.”  “Sure dan tunda ta tafi kome ya rikice”. abie ya nuna Mommy “tunda abin ya faru tana gidan nan kanwata ce uwar mu daya uban mu daya basa shigowa abujane sbd wani dalili na doctor wanda har ynx be fada mana ba amma de tabbas ga poison nan ya bata yace Idan Mommy ta samu lafiya bo bayan babu ransa asirin ko su wane ze tonu dan itace zata tona komai. Duk muna bibiyar rayuwar ku. Anan muka gane doctor yana raye poison na waje na sauran poison din da akayi mata amfani ne. Idan kuka kaima likitocin ta zasu yi bincike snn susan kalar maganin da zasu hada....  sageer tashi yayi ya kalli gabas yayi sujada. Kafin ya juyo yace “abba na gode Allah ya saka da alkhairi Allah ya biya ku da mafificin alkhairi. Mommy tace “but dis should be secret domin ko makiyan ko suna tare daku. Bana so wani yasan nida Doctor muna raye har se kome ya dede ta dan rayuwar mu tafi ta kowa hadari. And wacce tata take cikin babban hadari a ynx itace imaan. Dan haka sekun kular mun da yarinya. Kauyen su kuwa shine kauyen KWANAR DAN AUDI (saura naji wani yace wnn kauyen babushi a zaria nima sakawa kawai atoh dan banason kauyen da aka sani 😂 dan bakusan wahalar dana sha ba kafin nima na gano sunan kauyen”). Wani irin ajiyar zuciya sageer  saki kafin yace “finally”. Snn ya kalli abie yace “ngd gode sosai Allah ya saka da alkhairi I hve to go now”.  You can go but sageer ina son magana da kai”. Duk tashi sukayi aka bar sageer da abie.   Seda akayi magrib snn suka fito sukaje sukayi sallah snn suka dawo sageer ya kara zuwa sukayi sallama da mommy. Snn ya fito suka karayin sallama da abie da sauran yan gidan abie yace “wacce ta dauko ka seta maida ka”. Murmushi sukayi jiddah ma ta tashi ta suka fito. Bayan sun hau titi sageer yace “da farkon fa na dauka wata muguwa ce”. Jiddah tayi murmushi kafin tace “ynx ai ka sanni ko”. Sageer ya gyada kai. “But how”. Se kuma yayi shiru dan yama rasa taya zeyi tambayar. Jiddah tace “na dade ina bibiyar rayuwar jalal kaine ma bn sani ba. But jalal na san su sun sanni beside imaan ma ta tsane ni. Kasan fa”. Sageer ya ware idanu. Jiddah tace “nice na nunawa zulfa gidan su jalal”. Baki bude sageer ke kallon ta ta dage kafada tana murmushi “karki bari jalal yaji wnn magana”.   Murmushi kawai jiddah tayi kafin ta kaisa har asibitin. Tym din duk an shiga sallahr ishai. Tana ajesa ta juya shi kuma ya wuce masallaci.
Bayan sun fito sallah tare da Daddy da abba isa harma da Alh barau dayazo duba jalal din sageer yace “nasamo sunan kauyen su imaan”. Da sauri dad ya kallesa yace “are you sure a ina”. Dad ya jero masa tambayar su kansu su Abba isa hankalin su duk yana kansa sageer yace “wajen wata class mate dinsu da sukayi secondary. Maryam kawarta ta samo mana da aka cigita. Wai ta taba zuwa garin nasu. Wai gidan malam mamman. Ko gidan su imaan kace babu wanda be sani ba.”   Wani irin rungume sageer dad yayi. “I just can’t wait jalal ya farka. I will be the first to tell him”. Daddy yayi maganar so excited. Alh barau yace “masha Allah amma naji dadi”. Abba isa yayi murmushi “just can’t wait to see jalal face idan ya samu wnn abishir din”.   Cike da farin ciki suka karasa cikin asibitin. Dad ya rika leka jalal ta window yanaji kamar yaje ya tashesa ya sanar masa. Dad ko granny be fada mawa ba yafi so se jalal ta sani tukunna.
A daren ranar sageer ya gama bincike akan kauyen su imaan seda ya tabbatar ya samu information akansa da komai da komai da hanyar garin sann yayi bacci.
Wajen karfe 9 da wani abu jalal ya farka. Yana bin dakin da kallo kafin ya sauke idon sa akan sageer. Sageer dage kallon sa ya daga masa gira “morning bro”.   Jalal ya dauke idon sa. Dama already da safe doctor dayazo ya cire masa naurar dake taimaka masa wajen numfashi saura karin ruwa. Hannu jalal yasa ya cisge karin ruwan. Snn ya fara kokarin tashi. Da sauri sageer ya karaso kusa dashi ya rike sa. “Hey bansan iskanci fa”. Wani kallo jalal yayiwa sageer “with whose permission kuka kawoni nan”. Shima sageer din hararansa yayi snn yace “mu bar ka ka mutu knn”. Jalal yace “nace maka ina son ina son na sake rayuwa ne. Ku barni na mutu mana”. “Bazaka mutu ba my son Inshaallah damuwar ka ta kusa zuwa karshe”. Jalal ya daga jajayen idanun sa ya kalli Dad. Yasan dad will not understand what he’s going through   Kallon sageer yayi kafin yace “sakeni I want to ease my self”   Matsawa sageer yayi yana dan murmushi. Jalal ya tashi ya nufi toilet working slowly looking so sick. Dad yace “mun gano garin da imaan take my son”. Cak Jalal ya tsaya bede juyo ba dan ji yake kamar beji da kyau ba  dad na murmushi yace “jiya mukasan sunan garin su wajen wata kawar ta”. Jalal ya juyo yana kallon Dad. Kafin ya kalli sageer. Sageer ya dage kafada tare da ware hannu.    Kallon Dad jalal ya karayi. Snn ya kara kallon sageer “is this real”. Sageer ya balla masa harara “matar ka taje ta shige wani kauye can wai KWANAR DAN AUDI” tazo se bamu wahala take”   Mantawa jalal yayi da wani ciwon da yake. Yaje ya rungume dad tare da sauke ajiyar zuciya “Dad when why didn’t you wake me up tun jiya ku fada. Da ya tuni kila ynx naga imaan dad I miss her. I miss imaan”. Dad ya dago kansa yana shafe gefen fuskar sa. “Da jiya da yau duk daya my son”.  Jalal ya lumshe ido snn yace “thank you daddy thank you”.  Kallon sageer dad yayi kafin yace “thank ur bro he really really try is such a blessing having him as a frnd and brother he’s God’s gift to us”.   Juyawa jalal yayi yana kallon sageer Dad kuma ya juya ya fita. Dad na fita jalal ya ware idanu. “Hey bros tell me how“. Sageer na hararan sa snn yace “ko kunyar daddy baka ji kai ala dole dan soyayya oh ni. Jalal haka ka zama ita de little gal mara kunya din”.  Jalal ya shafa beards dinsa da sukayi yawa snn yace “you won’t understand bro wlh I just can’t wait to see her. I miss her”. Dariya sageer yayi snn yace “ai seka samu lpy zamu tafi besides asibiti ma basu sallame ka ba”. Wani kallo jalal yayi masa kafin yace “sun dade basu sallaman ba. Wani yace a kawoni asibiti. Look bazan iya bacci bnga imaan ba a yau din nan se ina na kace sunan kauyen”.  Dariya sageer yayi yace “KWANAR DAN AUDI”.   Wani murmushi jalal yayi kafin yace “hayin dan audi ne”. Sageer yace “babu fa inda zakaje yau atoh already na gama gani kome game da garin”.
“Abeg bro lets go home and get prefare kafin tym ya kure”. Kallon sa kawai sageer yake. Cike da mmki kamar ba jalal ba. Gsky so ba karya bane. Dad ne ya shigo tare da Abba isa. Duk kallon jalal suke suna murmushi. Abba isa yace “saurin me kk my son ai ka bari a sallame ka”. Jalal ya langwabar da kai “ abba na samu sauki fa”. Dad yace “then we are planning to go next tomorrow”. Jalal ya dago da sauri ya kalli dad. Sageer ya fashe da dariya. Girgiza kai jalal yayi “no dad I’m going today”. Dad ya kalli dan nasa. “Look at you. A haka zakaje wajen matar taka. Look at ur self. Kalli mirror fa. Face dinka ya ciki da gashi. Ka tashi daga DEEN ka dawo deeni”. Duk dariya sukayi. Dad yace “you need to Berbe all this hair I want imaan ta ganka more handsome. Kamar yanda ta sanka. Duk da na ka rame kaga zuwa gobe se kayi kome then jibi we will both go together” jalal yace “no dad jibi yayi nisa I will finish everything today then tomorrow”. Dad yace “dubi inda kk fa emergency ma”. “Dad I’m good nide gobe naji sauki I’m serious”. Dad yayi murmushi yace “ohk then as you said my son”. “I love you daddy”. Duk dariya sukayi Abba isa yace “mara kunya kawai”. Daga haka su dad suka fita zuwa wajen Doctor.   Juyawa jalal yayi ya rungume sageer snn yace “tnx bro I love you”. Se kuma ya juya yana kallon kansa a mirror. Yace “I have to punish dis gal dubi yanda ta maidani. Zataga kwanar dan audi ganin idon ta”. Dariya sageer yayi sosai snn yace “ande ji jiki”
Doctor ne ya shigo tare dasu Dad. Ganin Jalal da kwarin sa yace “good lallai ka samu lpy”. Gwada sa yayi snn yace “babu wata matsala zamuyi sallamar ku. Zan rubuta maki drugs snn seka kiyaye kaji”. Gyada kai jalal yayi snn Doctor ya fita.
Babu wanda sukasan cewa an gani kauyen se gani sukayi anyi dawo da jalal garas. Granny tasa aka kawo masa lafiyayyen abinci. Sosai jalal yaci ya koshi kowa ya gansa yasan yana cikin farin ciki. Fuska sake yaje amsawa duk wanda yazo masa ya jiki. Atika de kam dad yaje yayi warning dinta karma ta sake tazo inda suke. Zulfa ma tazo tayi masa ya jiki sede jikin ta duk a sanyaye yake Allah yasani tana kaunar jalal. Sumy kam farin ciki kamar me. Sede komai ya lafa snn sageer ya dauki jalal suka fita. Jalal sebin gari yake da kallo. Shi yaushe rabon ma daya fito ya za gaya gari. Yana can zuciyar sa a cinkushe. Ynx kam wani irin farin ciki yake ji. Sageer dake lura da yanayin sa yace “bro guess what”. Jalal na hararan sa yace “abeg tell me” sageer yayi murmushi yace “nasamu poison din nan fa”. Da wani irin mmki jalal yace “how?where? Pls no jocking”. Sageer yace “I’m serious”. Ganin yanda yayi magana cike da serious yasa jalal yace “pls tell me bro”. Jalal yayi maganr cike da rauni. Sageer yaji tausayin sa sosai. Dan haka nan ya fara basa lvri. Be boye masa ba ya gama masa komai. Fadin irin farin cikin da jalal ya shiga a tym din bata lokaci ne. Kuma ya dade be shiga kamar sa ba. So his mom now zata samu lpy abinda suka dade suna nema tun kafin yayi wayo yau sun samo. A hankali ya furta Alhmdllh fuskar mom dinsa kawai yake hangowa ta bude fararen idanun ta tana masu murmushi. A hankali yace “oh god when”. Shima ynx ze zama me mummy. Sageer ya kamo hannun “no condition is permanent just keep praying. Jalal ya gyada kai. Gaba he’s speechless. So that jiddah. Mumurshi yayi yana tuna abunda imaan tayi mata tasan da ace tasan mommy na gidan su bama zata fara ba. So now. How will imaan feel idan taga jiddah bibiyar rauyuwar ta take dan ta taimake ta.
Wani babban wajen gyaran jiki sageer ya kai jalal. Ganin kallon da jalal keyi masa yasa ya ware hannu “inaso gobe imaan ta ganka a sabon ango”. Murmushi kawai jalal yayi yana hango how he will hug imaan tomorrow give her I perfect kiss and tell her I love you. Awwwn he just can’t wait”.   Tabo sa sageer yayi yace “abeg let’s go nan da gobe babu nisa fa”. Hararan sageer jalal yayi kafin ya bude motar ya fita.
Spa aka mashi lokaci daya golden skin dinsa ta kara wani kyalli abinda da lafiyayyar fata. Kuma tasha gyara. An gyara masa kansa da sajen sa. Tuni ya dawo ainahin jalal din da kuka sani baka taba cewa yayi wani ciwo se er ramar da yayi. Amma kyawunsa ya kara fitowa. Shima sageer seda aka masa snn suka baro wajen. A boutique suka shiga suka sayi kaya suka zanza ann suka bzama yawo cikin gari. Idan kaga jalal baka cewa wani abu na damun sa   Yau da farin ciki biyu ya tashi dama a duniya bashi da wani buri daya wuce samun lpyr mum dinsa to kuma ga alamu yana gani. Sunje sun duba jikin abba Alhmdllh yaji sauki dan ance masu ba a kowane lokaci ze iya farkawa....
Koda suka dawo gida part din granny ya wuce itace taita tsokanar sa. Se dare snn ya dawo ya iske dad da Abba isa suna ta tsara yanda za ayi tafiya gobe. Shide gaisar dasu kawai yayi ya wuce dakin sa.   Alwala yayi ya fara salloli yana gara godewa Allah snn kuma da nuna farin cikin sa   Jalal be kwanta ba se 3. Kuma asubar fari ya farka. Idan ya tuna yau zeyi ido biyu da imaan se yaji wani irin farin ciki. He just can’t wait to see her ji yake kamar ya shekara biyu ba ganta ba
Jalal ya dade gaban mirror wajen shiryawa. Ita kanta sumar sa tym din daya dauka wajen gyara ba karami bane. Ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda sky blue dinkin ya mugun karbar sa. Yana cikin saka agogo imaan ta fado masa ya tuna inda tana nan itace zata saka masa. Murmushi yayi I’m coming wife.    Ya dauko hula da ta dace da kayan ya saka. Idan ka gansa banbancin sa da ango babbar riga. Yayi wani irin kyau mara musali. Jalal is just handsome and adorable kallon sa kade zakayi a tym din se kaji wani kwanciyar hankali.   Sageer ne ya shigo shima cikin nasa shirin. Yayi mugun kyau. Wani ware idanu sageer yayi yace “da kyau wlh. Se kace ango.”  Dage gira daya jalal yayi to wane idan ba angon ba.  Dariya sageer yayi sosai kafin yace “da kyau gsky ka samu lpy. Anyway kai kade ake jira “. Fitowa sukayi tun kafin jalal ya karaso kamshin turarensa yayi masu sallama duk binsa sukayi da kallo. Dan ba karamin kyau yayi ba. Zulfa ji take kamar imaan tafi kowa saa a rayuwa.  Dad yazo ya rungume sa. Snn ya juya yana kallon Abba isa,Alh barau da sauran abokanan dad guda biyu wanda duk dasu za ayi tafiyar yace. “ “Kunga ango ko” duk dariya sukayi Alh barau yace “ango an samu lpy”.  Kan de jalal a kasa yana dan murmushi.     Abba isa yace “ku tashi muje toh”. Duk waje suka nufa.  Jalal be dauka haka za ayi tafiyar ba. Domin kau wasu arnayen motoci ne Dad ya hada comboi dasu kusan guda ashirin.  Ga securities sbd yanayin tsarin tsaro na kasar nan. Jalal da sageer motar su daya map suka samu na garin wanda shine yayi guiding dinsu.  Jalal se kallon hanya yake yana tuna ranar da sukaje da sageer inda anan ne aka basa auren imaan    Tsokanar sageer de kam ya shata har ya gaji.  Seda suka zo zaria snn suka dauki hanyar garinsu imaan. Jalal kallon hanyar kawai yake. A ransa yana fadin she all cross dis pls without my permission as her husband.    Sun danyi tafiya kafin su kawo. KWANAR DAN AUDI. Jalal ya ringa kallon kauyen gabansa na faduwa ganin kauye ne sosai bana wasa ba. Ynx imaan anan ciki suke rayuwa. Tun a bakin tasha ake kallon motocin cike da mmki security din dake motar gaba ne ya bude glass yana kallon su okasha yaya Auwal da kuma ya Abbakar yace gidan me gari za a kaimu. Okasha yace “cikin garinne”. Securityn yace “bismillah kuzo ku nuna mana.  Babu musu kam okasha ya mike ya Abbakar ya riko sa “baka da hankali ne.”  murmushi securityn yayi yace “karku damu gidan me gari zamuje kuzo muje kuma”. Shiru yaya auwal yayi kafin “muje”. Kamshi da da AC seda yasa suka lumshe idanu.  Okasha na washe baki yace “kai duniya na inda suke malam ko ina me gari ya samosa”.    Sune suke nuna masu hanya zuwa gidan me gari.  Mutane se kallon motocin suke. Duk inda aka ga motocin se an tsaya. Idan sun wuce kuma a bisu a baya. Jalal kallon garin kawai yake da yanda mutane ke binsu. Hango irin high class din da imaan take dashi yayi. Gsky Abba ya cika mutum.  A gidan me gari sukayi parking.  Wanda su yaya auwal duk suka fito. Suka shiga gidan me garin cikin fada da duk hankalin su ya tashi suna tunanin wadan nan manyan motocin daga ina kode shigaban kasa ne yazo..jikin yan fadar har rawa yake suka sa a kara shin fida carpet snn suka ace su shigo. Ya Abbakar ya fito tym din mutane an taru anata kallon motocin da kuma duka securityn sun fito su jalal suna ciki sunata kallon mutanen da suka zagayesu. Bayan ya fada masu aka fadawa su dadddy.  Se lokacin aka bude masu duk suka fito. Nan fa kallo ya koma kansa. Shi kansa yaya Abbakar sakin baki yayi yana kallon su.   Dan se sukayi wasu larabawa a cikin su daka gansu kasan sune manyan kasar.   Mutane aka bisu da nan mujiya jalal duk se yaji ya wani tsargu. Ciki duk suka shiga baban kulawa dasu me gari se rawar jiki suke aka kawo masu Abba ruwa.  Alh barau ne ya gabatar masu da komai snn ya kara da fadin “musabbabin zuwan mu nan shine akan wata yarinya dake garin nan. Wato imaan ta wajen malam mamman”. Zuciyar ta Awwal tuni ta fara tsitstsin kewa shiknn abinda suke tsoro an gano inda imaan take kashin su ya bushe. Bama shi kade ba kowa a wajen. Seda ya shiga tashin hankali ynx imaan irin wadan nan mutanen ta jawo masu su ynx ya zasuyi.  Alh barau yacigaba. “But kafin nan munason ganin mahaifin nata idan babu damuwa.”  Me gari ya kalli yaya awwal. Babu damuwa ai semu saka ayi kiran sa”. Sakawa me gari yayi ayi masa kiran Baba har wajen aikinsa. Cikin minti shabiyar sega Baba tare da dan aiken sun dawo. Jalal ya rinka kallon wanda akace shine mahaifin imaan.  Lallai kam ga kama nan. Ji yake kamar ya tashi ya rungumesa ya fada masa ya iya haihuwa. Idan hankalin Baba yayi dubu to ya tashi.  Dauriya kawai yayi ya gaisar da bakin cike da girmamawa. Alh.barau yace “kaine mahaifin imaan”. Baba ya gyada kai hankali tashe. “Eh nine”. Alh barau yace “to kuyi hakuri da Abinda ya faru matsala ce ta faru cikin rashin sani karku ga bamu zo da wuri ba. Dalili ko shine bamu san inda zamu samu imaan ba. Hakika komu kanmu munyi danasanin barin ta gida domin kau. Mu kanmu tashin hankalin da muka shiga baya misaltuwa bare kuma shi mijin nata”. “Mijin ta kuma”. Duk suka hada baki wajen fada. Kowa se raba ido yake imaan nada aure kuma. Baban kuluwa yace “bn tari numfashin ka ba amma mu bamu san imaan tana da aure ba “. Alh barau yace “eh to ze iya yiwuwa. Tunda muma sedaga baya muka sani. Sbd wata matsala data faru. Dr umar ya daura auren imaan da dan mu jalal.  Yayi magana yana nuna masu jalal dake zaune. Duk kallon jalal suke cike da mmki. Shi kansa Baba kallon jalal yake da wani irin farin ciki. Finally de yau Allah ya kawo karshen damuwar ersa. Shi dama yanaji a jikinsa imaan bazata taba aikata wani mugun abu ba. Duk masu binta da sheri yau kila se sun mutu sbd bakin ciki idan sukaga wane mijin imaan kuma uban cikin sa.  Yaya awwal kallon Jalal kawai yake yana hamdala cike da farin ciki lallai kau imaan su takewa kallon wawaye shiyasa tayi shiru. Ynx kamar wnn imaan ke aure ynx wnn shine ke shiga tashin hankali sbd imaan. Finally cikin yana da uba. Baba yace “wnn shine mijin imaan”. Jalal ya dago idon sa ya zuba akan baba. Kafin way sauke cike da ladabi yace “eh nine Abba”.  Murmushi baba yayi kafin yace “lallai ka bayyana a dede”. Daddy yace “kuyi hakuri ya aure ta batare da izinin ku ba amma Inshaallah zamu fada maku dalili ynx de muna so muka imaan. Ya Abbakar baki bude kawai yake kallon jalal bama shi ba kowa daga cikin fadar kallon sa suke cike da mmki.    Yayi awwal kau ya kasa rufe baki sbd murna.   Baba yace “muje tana gida”. Daga haka suka fto zuwa gidan su imaan.  Kafin kace mene gari ya karade ko ina cewa shugaban kasa yazo. Duk wnn abun dake faruwa gidan su imaan basu sani ba. Yauma kamar kullum duk suna gidan suna tsakar gida ana ta yada maganganu. Harda mazajen su abida su iliya. Tun dazu Adda ta daurawa imaan ruwan wanka kuma yayi zafi dan ynx idan ta sakawa jikin ta ruwan sanyi har firgita take. Amma tsoron fita take ta samesu. Barin ma yau da sukayi kaca kaca jummala da adda sbd jummala ta saka imaan wanke wanke adda tace bazatayi ba.  Ynx haka adda ta fita samo mata abunda zataci ne. Daurewa kawai tayi ta fita. Bata yarda ta kalli kowa ba ta wuce gaban murhun ta zuba ruwan snn ta surka. Hurera tace “ke karuwa” banza imaan tayi da ita da sauri hurera tazo ta kifar da ruwan imaan ta bita da kallo. Hurera na hura hanci tace ko zaki rama ne nace ko zaki rama ne “. Iliya yace “ki nada mata shegen duka idan tayi gardama.” Duk suka fashe da dariya. Imaan tayi kokarin kaucewa hurera ta wani fisgota. Snn ta debo ruwan sanyi ta watsa mata “nabi ruwan zafi da gudu shi cikin shegen har wani riritasa kike”. Ruwan sanyin na sauka jikin imaan ta saki wata irin kara a firgice. 
  
Suna gama parking duk suka fito suna kallon gidan su imaan din jalal jin zuciyar sa yake wani kusa da imaan idan ya tuna tana ciki jira kawai yake ayi masu iso yaje ya kanta yana bayan kowa ya fito ya kalli su ya Abbakar yana murmushi ya basu hannu suka gaisa da suka gaisa da ya auwal yana murmushi yace “her brother I guess”. Da kyar yaya auwal ya iya gane turancin dan ba kalar wanda ya saba ji bane. Yaya auwal a gyada kai “eh nine”. Be gama rufe baki ba sukaji ihun imaan cike da razani. Da sauri jalal ya kalli dad “this’s imaan voice definitely something is wrong”. Be jira cewar su ba ya fada cikin gidan hakan yasa duk suka bi bayan sa. Dukansu babu wanda ya kula da shigowar su. Ganin imaan a jike tana ta kyarma ga kuma botikin ruwa hannun hurera da kuma dariyar da suke mata yasa lokaci daya ya fahimci meke faruwa se ynx ya tuna da cewa imaan fa marainiya ce a gidan. Cikin en seconds yayi wnn tunanin. Cike da bacin ran daya durar ma zuciyar sa a ynx yasa beyi wata wata ba ya saukema Hurera lafiyayyaun maruka har uku wanda seda duka wutar ta ta dauke tuni yan cikin gidan suka mike. Jalal yace “how dare you i said how dare you dirty pig”. Kallon jalal imaan kawai take wanda bata san daga ina ya bullo ba. Shima juyowa yayi yana kallon ta a hankali yace “imaan”. Wani irn fadawa jikinsa imaan tayi tare da tusa kanta cikin kirjin sa ta fashe da wani irin kuka. Kukan da duk wanda yaji yasan she’s in pain”. Rungume ta jalal yayi shima kafin a hankali yace “I’m srry wife I’m srry for coming late”.  20secs silent dif kakeji se kukan imaan da yake fita. Har su daddy da wasu securities din duk sun shigo bama su kade ba harda wasu mutanen garin duk an shigo ana kallon ikon Allah kowa yazo seyaga imaan rungume jikin jalal tana kuka. Jummala da tana gani aka mari erta babu halin magana. Domin kau ko cikin ta ne ya tsure babu hakin magana. Bama ita kade ba harda su abida da nana jiki ya mutu.    Kyarma imaan ta fara sosai a jikin jalal sbd ruwan sanyin daya shige ta. Jalal ya kalli dad yace “Dad she’s catching cold”. Yaya auwal yace “bata son ruwan sanyi ze iya sakata zazzabi”. A rude jalal ya kalli wani security yace “get me a jacket right away”. Babu bata lokaci wani ya fita se gashi da katon rigar sanyi. Ya mikawa jalal. Kallon yaya awwal yayi kafin yace “a ina zata canza kayan”. Dakin adda yaya awwal ya nuna mata. Hakan yasa ya jata zuwa dakin.
Adda na gidan umma labari yazo mata wai ka manyan motoci nan an turo daga habuja su tafi da imaan sun gano ta sunzo kamata. Babu shiri Adda ta kamo hanya hakan yasa umma dasu kuluwa ma suka biyo ta. A hanya Adda se banbami take. “Ita imaan din har wani mugun abu zata iya aikatawa duka nawa take subar mu da cikin shegen da suka mata mana   Bakin Adda mutuwa yayi ganin irin motocin dake kofar gidan nasu ga kuma masu bakaken kaya. Duk afkawa cikin gidan sukayi ganin yanda ya cika da mutane yasa Adda fadin. “Mugaye wlh babu wanda ze taba mun jikata babu abinda tayi ina imaan din.”  Trolley din imaan daya gani shine ya bude ya ciro wasu kayan ya mika mata jikin imaan na rawa ta fara saka kayan. Jalal ya dauko kayuwar rigar sanyin ya saka mata snn ya janyo ta jikinsa ya rungume “I’m very very srry”. Jin cikin ta ya dan turo yasa ya sake ta yana taba cikin. “What’s this imaan”. Shiru imaan tayi tana dan murmushi. Wani murmushi Jalal yayi kafin with so much excitement yace “are you pregnant”. Gyada masa kai imaan tayi tana murmushi. Wani irin rungumeta Jalal yayi kafin yace “ohh my goodness”. Daga haka kuma ya saketa. Kobi ta kan hular sa data fadi beyi ba ya fita. Gaba daya happiness tin tin. Ya rufe masa idanu bema damu da mutanen dake wajen ba yace. “Dad Daddy. I will soon be a father. Daddy imaan is pregnant”. Yayi maganar yana rungume. Dad. Duk wajen cikin yan kauyen babu wanda ya fahimci me jalal ke nufi sunde gane yana cikin farin ciki.   Adda ya bisa da kallo “ wnn baturen fa. Me yake a daki na jama’a ina jikata” kowa Kallon jalal kawai yake gashin kansa kawai abin kallo ne. Daddy ya kalli Baba shima da farin ciki yace “tana da ciki ne”.   Baba yace “eh tana da ciki wata uku”. Da sauri Adda tace “wane cikin a yaushe”. Yaya awwal yace “adda mijin imaan ne yazo imaan tanada aure ashe”. Zaro ido adda tayi tace “ina mijin”. Yaya awwal ya nuna jalal da shima yake kallon ta.   Adda taje ta taba jalal. “Wnn baturen ynx wnn ne imaan ke. Aure”. Shime jalal ya gyada kai “eh nine”. Daga hannu Adda tayi “Allaahuu Akbar. Aikam imaan tana da ciki wata uku ma. “
Nace ba idan kunji dadin page din nan I need comments thet will bust my head 🥰
Urs
✨✨✨
Annafie😍💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
              ANNAFIE💖…✍️
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
  Aa
Bismillahir rahmanir raheem
NOT EDITED

💫💫💖Jalal Alii((40)💖💫💫
Se a lokacin Hurera da ta dawo daga guguwar marin da tasha tana kallon Jalal da akace mijin imaan ne “to tayaya ta tambayi kanta”. Jummala kam cikin ta wani irin kullewa yayi tanaji kamar da zagaya bayi tsoron su jalal ya hanata kwakkwaran motsi. Iliya da matar sa tunda suka saki baki basu rufe ba. Bama su kade ba da yawan mutane kauyen suman tsaye sukayi. Adda tace “wlh tunda tazo garin nan take laulayi”. Yaya awwal yace “adda kiyi shiru mana kinga ko zama basuyi ba”.  Wani irin zagi tayiwa yaya awwal “inyi shiru fa kace. Ynx kamar wnn balaraben mutumin a sheganta masa ciki kana ganin ya cancanci a rufe masa to wlh sena fada”. Adda ta fashe da kuka tana kallon Jalal tace “wlh tunda tazo garin nan suka fahimci tanada ciki suka suka hanata sakat ko ina ta gifta me cikin shege gidan nan suke wuni safe da yamma Suna zagin ta. Kullum kuka bata da sukuni kaga algungunmar nan” tayi maganar tana nuna jummala da fitsari ya kusa kufce mawa barin ma da taga duk sun juyo suna kallon ta.   Adda ta fara kuka tana fadin. “Imaan kullum kuka shiyasa idan an tambaye ta tayi shiru ashe tasan ciki da ubansa”. Ya Abbakar yace “adda kiyi shiru mana kofa zama basuyi ba”. Cike da balai tace “algungumi waye yaga ta zama an sheganta ta masu ciki kalli kudin su fa. Uban waye ya kaika zagin ta wawa kawai kungansa shi kansa idan kunji yana zagin ta kamar ba dan uwanta ba bewar Allah sede taita kuka tayi shiru sbd taga babu wanda ze fahimce ta. Yo abinka da en kauye”.   Sageer ya kamo jalal dayaga yanayinsa ya sauya idanun sa sunyi jawuur. Da ka gansa kasan he’s boiling from inside. Murya can kasa sageer yace “bro control pls”.   Fisge hannun sa yayi kafin yace “will you shout off sageer”. “Didn’t you here what she’s saying. My wife,cikina,dan da zan haifa suke kira da shege. Imagine shege. Dad shege fa. I don’t need more explanation cos I knw imaan goes through alot. Duka mutanen kauyen nan kowa idon sa akan matana da kuma cikin ta just think of wane hali ta shiga over  2months”.   Yanda yake magana gaba daya mutanen wajen sunsha jinin jikinsu. Er hausar da yake hadawa da ita ce tasa suka fahimci cewa akan imaan da cikinsa yake magana kuma daga gani kasan bakaramin kaunar cikin yake ba. Jummala de jikin ta rawa kawai yake. Dakin Adda ya shiga be cewa imaan komai ba ya kamo hannun ta. Suka fito be kalli kowa ba ya nufi hanyar fita. Daddy yace “where are you taking her to”. Tsayawa jalal yayi ya juyo ya zuba jajayen idanun sa yana kallon daddy snn yace “I don’t think I can stay in dis village in the next 20mins with this illiterate people around dan komai ma ze iya faruwa and I need to see doctor for imaans and my unborn child health.”  Har ya juya se kuma ya juyo. Yana kallon su jummala da kyau wanda suna iya gane bacin ran da yake ciki yace “and you. You can’t hurt my innocent wife and think you will go just like that. You will all pay for what you did to her”.  Daga haka yaja imaan suka fita ya bude mota ya sakata snn ya shima ya zagaya ya shiga ya jingina da kujera ya lumshe idanu.  Adda da tabisu da kallo har suka fice ta kalli sageer da yake ta dan smiling yana kallom drama tace “kai kanajin hausa ne ka fassaramun abinda yake cewa dan na kula kamar ba wani jin hausa yake ba”. Sageer daya gama kula da yanayin su jummala yace “yace baze kara minti ashirin a garin nan ba tafiya zeyi da matarsa da duba masa lpyr ta da cikinsa. Snn yace abinda sukayiwa imaan bashi ne su dauka zasu biya”. Jummala fitsari har kufce mata ya farayi. Hurera da nana kam yanda kasan wadan da aka tsamo a cikin ruwa. Gani suke kamar a mafarki ne”. Daddy ya kalli baba yace “ina tunanin dole mutafi ynx tunda jalal ya bukaci haka kafin ma a samu matsala zamu sake dawowa Inshaallah ynx se ku hada mu da wasu mu tafi idan muka dawo zakuji dukkan bayani “. Adda tayi saurin fadin “ai babu wanda zeje wajen ta seni din ta wane gareta ida bani ba”.  Daddy ya kalli Adda yace “ai dole muje dake se a hada da wani kuje tare”. Adda tace wnn kuma sede ummanta to ai mune kawai masu kaunar ta kaf garin nan”. Daga haka ta nufi daki ta hado kayan ta tana kallon sageer tace “to kai zoka shiga dani motar karsu wadannan mutanen su hanani shiga.”  Murmushi sageer yayi snn suka fita ya bude mata motar daban ta shiga. Adda tace “kai kai. To dan Allah ina imaan ina kalar kauyen nan shiyasa ta zuba masu idanu”.     Umma ma tare suka shiga bayan taje gida ta shirya. Kuluwa har kukan farin ciki tayi tana so taga imaan amma batasan a wace mota take ba.  Su daddy sallama sukayi da baba bayan yayi masa kyautar kudade masu tsoka. Snn ya ya shiga mota. Sageer ma ya shigo motar su jalal amma wnn karon a gaba kallon su yayi ganin duk yanda sukayi ko wane ya jingina da kujera idanun jalal a lumshe while imaan kuma tana hawaye tana kallon window idon ta kan baban ta da yaya auwal .  A haka motocin suka fara tafiya motane an taru anata kallo motocin wasu seda suka bisu har suka fita garin. Suna barin gidan jummala tayi bayi dan kau cikin ta duk ya kulle. Su hurera kam daki suka shige suna gani komai kamar a mafarki. Hurera na kallon yayarta Abida tace ynx wnn shine imaan ta aura. To yaushe tayi auren.
Yaya awwal na kallon yaya Abbakar yace “kaga ikon Allah ko cikin de da ubansa.”  Shiru kawai yaya Abbakar yayi yama kasa kallon yaya auwal da matar sa kuluwa dan wani irin kunya yakeji   Nan fa gari ya dauka ashe mijin imaan mugun me kudi ne a habujar ma yace “idan ya dawo seya daure yan garin gaba daya”.
Tunda suka taho motar shiru babu wanda yayi magana. Juyowa sageer yayi yana kallon yanda sukayi din idan ka gansu seka tausaya masu daka gani kasan cike suke da kewar juna.   Wayar sa ya dauka yayi masu connecting wakar ric hassani (beautiful to me). Baby gal I love you so,I will never let you go,never see a gal like dis before,I just wanna let you knw babee. That you’re beautiful to me. Na you I wan marry.....kun gane 😂. Sageer yasa driver ya rufe masu ta bayan yanda su sageer din baza su gansu ba.  Wani murmushin da jalal be shirya ba yayi. Kafin ya kalli imaan dake kallon wani gefen ...murya can kasa yace “imaan” shiruu tayi bata juyo ba tamaki yarda ta kallesa. Dan murmushi yayi kafin ya kamo hannun ta yana dan murzawa snn ya janyo ta ya maido ta jikinsa imaan ta lumshe idanu tare da daura kanta a chest dinsa tare da sauke ajiyar zuciya. Dan murmushi jalal yayi yanajin wani farin ciki. He can’t express how happy he’s yasan imaan ta riga ta zama wani bangare na jikinsa     Ya daura kansa saman nata yana dan shafa bayanta. Ganin taki bude ido yasa yaje saitin kunnen ta yana maming wakar “I knw many guys they love youuu but I the only one for you see all the love I will give to you more than anyman can give to you yeye cos you’re beautiful to me beautiful to me”   Yanda wakar ke dan tashi da kuma yanda jalal kebin wakar se imaan taji abin na kaimata har kai. Se gani take kamar jalal yana son ta. Tasan idan tace yana son ta she’s deceiving her self amma kuma meyasa yazo. Wani zuciyar yace “kin raina Amana ne”.   Bacci ne ya kwashe ta a jikin jalal. Jin saukar numfashin ta a hankali yasa jalal ya bita da kallo. Yace “finally” kissing dinta yayi a forehead dinta kafin yace “I miss you babee”. Hannun sa ya kai dede cikin yana shafawa. “Hello mummy’s or saif namesake. Ur daddy loves you”. Ita de imaan bata san meke faruwa ba haka Jalal yaita labari da cikinsa. Dan ji yake duk duniya babu abinda yake so a yanxu sama da cikin dake jikin imaan. Yanxu ya fahimci meyasa daddy ke hakuri dashi ashe haka son da da mahaifi yake.
  Bayan laasar suka iso cikin gidan. Koda motacin suka fara parking jalal be fito ba. Se kallon imaan da take bacci kawai yake. Yo wata biyu babu bacci cikin natsuwa. Ta cikin motar yake kallon kowa. Adda ta fito se wurga idanu kawai take tana kallon gida bakin tama ya rufu ruf. Tuni su sumy aka fito dan tun dazu ta kosa taga imaan she really want to see her and apologize. Adda tayi kasa da murya tana magana kasa kasa “kinga wani gida aljannar duniya ynx imaan anan tayi rayuwa me yaja mata komawa kauye. Ita de umma shiru tayi. Sageer ne yazo ta wajen su yace “kaka kuzo muje a kaiku masauki”   To. Adda ta bisa. Suna tafiya tayi kasa da murya tacema sageer “banga jikata ba fa”. Sageer yayi murmushi yace “jikarki na tare da mijin ta”. Adda tace “ni se nake ganin kamar beson mutane to se kunshe a mota daga shi se ita”. Murmushi sageer kawai yake. Part din granny suka shiga. Nan suka samu tarba me kyau wajen granny. Aka ware masu katon daki ita da umma akace nan zasu zauna   Banda washe baki babu abinda Adda take

Jalal be fito ba seda motar ta kaisa har wajen kofar shiga part dinsa. Kallon imaan da har ynx take bacci yayi hura mata iska yayi kafin yace “wife”. Bude idanu imaan tayi akan jalal tana kallon sa se kuma ta tura baki jalal ya dage gira yace “idan kika haifa mun yaro me harara da tura baki se nayi punishing naki”. Kamar imaan zatayi kuka ta tashi daga jikin sa tana kallon gidan su jalal. Faduwa gaban ta yayi. Bade anan yake nufin zasu zauna ba. Bude motar jalal yayi ya kamo hannun ta suka fito     Bude kofar part din nasa yayi. Suka shiga imaan ta ringa Kallon parlon na Jalal da yayi mata kyau sosai daka gani kasan na dan gata ne. Stairs suka hau yana kallon dakunan dake corridor din snn ya kalle ta yace. “Wane room kike so ko room daya zamu zauna” noke kafada tayi jalal ya ka hancin ta “to baki isa ba”. Daga haka ya bude dakin sa suka shiga.    Sakin ta jalal yayi ya fada saman gado tare da ware. Mata hannayensa “common wife let me feel you”. Noke kafada imaan tayi kafin kamar zatayi kuka tace “wanka”. Jalal ya ware idanu yace “nazo nayi maki” ganin yana kokarin tashi yasa tayi saurin shigewa bedroom din. Dede kofar jalal yazo ya jingina kafin yace “do you knw I can open this door”. Imaan tace “to ba wanka zanyi ba”. Yace “then banine keyi maki ba”. Ta tura baki “to yau ni zanyi”.   Murmushi Jalal yayi kafin ya dauki waya ya kira sumy.   Sumy da rabon da ko kallon kirki yayi mata ta dauki wayar da sauri. Yace ”get her a simple dress da zata saka wajen granny” daga haka ya kashe wayar   Wani dakin ya shiga yayi wanka amma har fito imaan bata fito ba. Shiryawa yayi cikin kaya marasa nauyi snn ya kabbara sallah ya fara rama salloli.   Bayan ya idar ya tashi zuwa parlor. Summy ya gani rike da trolley se basket din Abinci. Tace “inji granny” karba yayi har ya juya tace “yaya inaso inganta” batare da ya juyo ba yace “zata shigo ai”.     Aje basket din yayi a dining snn ya wuce da trolley din sama.   Gaban mirror ya ganta daure da towel dinsa aje trolley din yayi kafin yazo ya rungume ta ta baya yana kallon ta ta cikin mirrorn “did you miss me”. Shiru imaan tayi itama tana kallon sa. Ya lumshe idanu kafin yayi kissing dinta a wuya. Murya can kasa yace “with whose permission kika bar garin nan”. Imaan ta tura baki tace “to ba budurwar kace suka koreni ba”. Ya dage gira “then ke kuma kawai se kika tafi you should have fine somewhere ki jirani but sbd baki sona am not ur Choice kawai shine kika tafi ba”. Ta tura baki “kai kana sona ne  kawai de bakason cin Amana”. Kallon ta jalal ya tsayayi. Se kuma yayi murmushi kafin yace. “Do you love me?”   Imaan tace “inajin yunwa”. Hannun sa yakai saman cikin ta yana dan shafawa snn yace “so you left with my unborn babee. Dama wainar flour din nan”. Se kuma ya ware idanu yana kallon imaan “im just happy. I will soon be a father oh my god”.  Yayi maganar yana rungume imaan sosai. Itama rungume sa tayi kafin tace “thank god you love it”. Wani irin kallon imaan yayi kafin yace “what do you mean”. Kamar imaan zatayi kuka tace “thought I’m the only one. Cos kowa baya son sa”. Jalal ya kamo hannun ta snn yace “why did you think I will not be happy”. Kamar zatayi kuka tace “cos I’m not ur choice”. Yace “ohk ke kinasona knn shiyasa kike son cikin”. Waro idanu imaan tayi tace “ba nice mamansa ba I have to love him”. Murmushi jalal Yayi. He really miss this gal wlh “then im the father i have to love my son”. Yayi maganar yana shafa cikin  yace “can’t wait to see you in the next 6months darling I love you” yayi kissing cikin wani irin dadi imaan keji so jalal yanason cikinsa”.   Taimaka mata yayi ta shirya snn ya kama hannun ta suka fita parlor shida kansa yayi feeding dinta snn yaje ya dauko mta hijab tace “ina zamuje”. Yace “zamuje ganin Doctor a dubanmun lpyr yarona”. Shida kansa ya saka mata snn suka fita.  Mota suka shiga jalal ya dauki hanyar asibiti. 
Koda sukaje Asibitin likita ya duba imaan sosai ya gano cikin ta lpyr sa qlw. Hakan yasa jalal samun kwanciyar hankali. Yayi wa doctor godiya. Doctor yace “but yana bukatar Dad dinsa. I mean babu isashshen sex”. Murmushi jalal yayi kafin yace “ohk zamu kiyaye”. Sede suka fito snn jalal yace “you see even my babee is missing me hope you hered what the Doctor said”. Murmushi imaan tayi tare da ware idanu   ...Akan hanyar su ta dawowa imaan tace “ya jikin Abba na”. “Soon Abba ze samu lpy a ko wane lokaci ze iya farkawa”.   Da murna imaan tace “Allah ya basa lpy”. Yace “ameen kin kosa  ya samu lpy mu rabu ko”. Kallon sa imaan tayi. Ji tayi gaban ta ya fadi tunda ta gano irin son da takewa jalal bata son abinda ze raba su kuma. Dakewa tayi tace “ai haka kayi alkawari”. Kallon ta jalal yayi kafin yace “imaan bayan kin tafi. Do you feel anything kamar love or let me say did you miss me. Lyk irin that deep missing”.  Shiru imaan tayi tana tunanin ta fada masa ko karta fada masa ta gane so yake ya gane ko tana son sa. Dan haka a takaice tace masa “no”. Kallon ta kawai jalal yake yama rasa me zece. Shine kade yake haukansa knn. Dauke kansa yayi yacigaba da driving. Kafin yace “then ki bari idan kika haifamun yaro na seki tafi”.   Imaan tace “dalili”. Ya kalle ta da kyau snn yace “dashi kika zo ne”  jikin imaan yayi sanyi ta dauke kanta zuwa wani wajen. Karde ace shima yana sonta. Idan ba haka ba meyasa zeji haushi dan tace bata missing dinsa.  Ganin duk yanda ya hade rai yasa taji kamar tace tana sonsa. Amma se tayi shiru tacigaba da kallon wani direction din.  
A part din granny suka sauka tare suka shiga ita da jalal din nan suka iske Adda a parlor su sumy da Mahmud duk suna nan gasu granny da umma adda an canza kaya sabbi anci ansha ta zage se labari take basu umma de sede tayi murmushi.  Tana ganin imaan ta washe baki. “. Imaan taje ta gaisar da granny snn ta gaisa dasu muhmud. Rungume ta sumy tayi tana bata hakuri. “I’m srry imaan I’m very very srry” murmushi kawai imaan tayi kafin tace babu komai. Granny tace “dawo nan ki zauna kusadani me kikeso kici”. Daga kai imaan tayi ta kalli jalal hada ido sukayi yayi saurin dauke kansa murmushi tayi kafin tacewa granny masar dazu zata kara. Tuni sumy taje ta zubo mata aka kawowa imaan ta zauna tanaci happily. Da ta daga ido se ta kama jalal yana kallon ta. Hakan ba karamin nishadi yake saka ta ba. Cos ta fahimci kamar jalal ynx yana da feelings a kanta. Kodan tana da ciki oho”. Se wajen 9 na dare suka koma part dinsu. Wanka jalal yayi ya dauko system dinsa ya fara dannawa.   Imaan ma ta shiga wankan har ta fito jalal be dago ba bare ya kalleta.   Shiryawa tayi cikin kayan bacci kafin ta hau saman gadon  ta dauke system ta fashe da kuka.  Kallon ta yayi da sauri yace “what’s wrong with you”. Ta tura baki ba kai bane. Tun dazu se wani share ni kake. “.  Ya jinginda gadon snn camly yace “ai laifin ki ne why will you say bakiyi missing dina ba. Imaan kusan 64dys amma ko daya baki missing dina ba and you’re expecting me to be happy”. Shiru imaan tayi tana sauraren sa. Kafin ta dago ta kallesa ganin idanunsa a lumshe. Yasa ta sauka gadon ta aje system din snn ta dawo ta side dinsa ta zauna a jikinsa tare da dora kanta saman chest dinsa. Ta saka hannunta tana shafa sajen sa. A hankali tace “i miss you”. Idanun sa a lumshe yace “am not forcing you to say it you’ve say it bakiyi missing dina ba”. Imaan ta shige jikinsa kamar zatayi kuka tace “I’m serious. I think of you in every minute,the two months i spent without you kamar shekara biyar ne my heart is so attached to you bansan da haka ba seda na bar nan. I miss all of you. I miss ur voice,ur smile,ur touch,the hug,kisses, i miss you all dear”. Jalal ji yake kamar a mafarki wani irin farin ciki yaji from no where so imaan loves him. Ynx a bakin imaan yake jin wnn maganar.   Still idanun sa a lumshe yace “did you love me”. Shiru imaan tayi tana kallon sa. Ganin har lokacin idon sa a lumshe yake. Kara shigewa tayi jikinsa tana kara rungume sa ta lumshe idanun ta kafin a hankali tace “yes I do i love you”. Bude idanu jalal Yayi yana kallon ta kafin yace “are you sure since when”. Yanda jalal yayi maganar with so much of excitement.   A hankali tace “I dont knw when or where. But I knw I love you I don’t mean just love but i want to spend my whole life with you i try to deny it but was wrong jalal i love you”. Kallonta kawai jalal yake yanda take maganar idanun ta a lumshe. Lips dinsa ya kai dede nata tare da lumshe idanu kafin ya hade bakinsu. Ya rungume ta sosai. Yama kasa magana sbd farin ciki. Ko daya imaan bata hanasa ba dan tayi kewar sa she missed him so badly. Sun raba dare suna raya sunna dan se gab da asuba sukayi bacci. Sunayin sallahr asuba kuma wani baccin ya kwashe su. 
Se 12 suka tashi tare sukayi wanka snn suka fita parlor already granny ta aiko masu da breakfast. Jalal da kansa yayi feeding matar sa    Suna gamawa sega su Adda da umma dasu granny. Jalal ya gaisar da adda tana washe baki tace “lafiya lau ashe duk kunajin hausa kuke mana turanci”. Murmushi jalal yayi yana kallon imaan. Adda taita yaba gidan. “Imaan kina nan me ze saka ki tuna da wani kauye dan Allah”. Adda ta dade a part din dan har laasar  tabar part din. Shima granny ce tace tazo a zagaya da ita taga gari.     Seda ya kula su adda sun bar gidan snn ya dawo. Imaan na zaune a parlor yace “imaan bring ur hijab lets go out. I want to show you something”. Tashi imaan tayi ta dauko hijab dinta. Kama hannun ta yayi suka fito. Dede itama zulfa ta fito. Daga jalal har imaan duka dauke kai sukayi. Imaan harda wani kara shigewa jikin jalal. Hakan ya saka shi murmushi.  Seda suka fita daga gidan snn imaan ta kalli jalal dake driving tace “ina zamuje”. Ya ware idanu kafin yace “zance “ shiru kawai imaan tayi bawai dan ta yarda ba.  Jalal ya rinka bin Address din da sageer ya tura masa. Har suka iso gidan su jiddah. Suna zuwa me gadi ya bude masu gate sbd yasan da zuwan su. Muhammad ne ya fito suka gaisa da jalal. Snn ya gaisar da imaan tare da fadin muje ciki “. Babu musu suka bisa. Jiddah ce kade cikin parlorn tana aiki a system. Tsayawa imaan tayi tana kallon jiddah da mmki. A ranta tana fadin me jalal yake nufi. Wato da gaske de zancen ze zo kuma shine yazo harda ita. Kodan yaga ta fada masa tana sonsa shiyasa ze bullo da hanyar wulakanta ta. Idan ba haka ba mene na zuwa da ita. Nan da nan idon ta ya cika da kwalla.  Jiddah na murmushi ta kallesu bismillah ku zauna mana”. Tuni jalal ya kula da yanayin imaan hakan yasa ya kamo hannun ta murya can kasa yace “let go”. Togewa imaan tayi ba tare da ta yarda ta kallesa ba.

Urs
✨✨✨
Annafie💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
              ANNAFIE💖…✍️
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
  Aa
Bismillahir rahmanir raheem

💫💫💖Jalal Alii((41)💖💫💫
“My daughter”. Imaan taji muryar Mommy wani irin juyawa imaan tayi direction din tana kallon Mommy dake saukowa daga stairs. Tsaye imaan tayi ta kasa gasgata abinda idon ta ke gaya mata. “Mommy”. Imaan ta fada.”yes dear”. Juyawa tayi ta kalli jalal. Ya gyada mata kai. Imaan ta matsa a hankali kusa da Mommy. Se kuma ta rungumeta tare da fashewa da kuka. “Mommy where have you beeen all dis while. Mommy Abba nacan kwance beda lpy Mommy na”. Mommy na bubbuga bayan ta tace “is ok Abba ze samu lpy kinji ki kwantar da hankalin ki.”  Mommy na kallon jalal tace “welcome my son lets go abie din na ciki”. Duk tafiya sukayi tare harda jiddah. Bayan sun gaisa Abie yayiwa jalal bayani kamar yanda yayiwa sageer ya kara da fadin “munyi magana da sageer Inshaallah gobe nida kaina zanje saudiyyar nakai poison din. Dan haka se kuce Alhmdllh snn karda mu kosa sauki se a sannu ake samun sa kunji “. Imaan har rugume mommy tayi sbd farin ciki she just can’t wait taga mum din jalal ta samu lpy asirin duk wani makiyan sa ya tonu kowa ya gane cewa jalal is not a bad boy she just can’t wait to see her husband out of the sad lyf... jalal is just watching her ya kula da yanda take farin ciki wnn kade ya nuna masa cewa imaan na sonsa and he’s happy   Now mummy zata samu lpy zata gansa har yayi aure and his unborn child...  Mommy ta kara da fadin “and jalal keep showing to people that you’re careless ko nan gidan bamu yarda ku kara zuwa ba idan munason ganin ku zamu neme ku cos mutane zasu saka ido akan ku konace makiyan ku kubar komai hannun sageer. Ko wajen Dr ku dena zuwa. Kawai do ur work a zaune and imaan. Ynx kowa yasan cewa er dr ce komai ze iya faruwa dan haka seka ska ido sosai akanta”. Gyada kai Jalal yayi snn Mommy suka tashi suka fita da imaan suka bar abie da jalal.  
Imaan kamar zatayi kuka tace “Mommy ynx bazan ringa zuwa wajen ki ba”. Mommy tayi murmushi tace “sure ki kula da kyau. Kawai ynx ki kula da mijin ki ki tabbatar duk wani natsuwa yana samu a wajen ki cos jalal yana cikin damuwa karda zafin yayi masa yawa. And cikin ki se kin kula dashi sosai. Dan daganan har zuwa lokacin da asirin makiya ze tunu koda kuwa cikin yazo duniya ne se kun saka ido. Dan yanxu sekiga an hari danku ma shi ba a haresa ba”. Gyada kai imaan tayi Mommy tace “me zakici na sa a kawo maki “ imaan tace “Mommy zanci indomie me sydine”. Tashi Mommy tayi kafin tace “bari nasaka jiddah ta kawo maki  inaso zanga jalal”. Daga haka ta fita. Shiru imaan tayi tana tunanin “kila da tun wancan karon ta yarda jalal ya karbi numbern jiddah da duk basu sha wnn wahalar ba. Hakanan se taji kunyar hada ido take da jiddar. Bayan jiddah ta gama dafa mata indomie din ta kawo mata.   Imaan tace “nagode”. Murmushi jiddah tayi kafin tace “ci kinji kar abar babee da yunwa”. Murmushi imaan tayi kafin a hankali tace “I’m srry bansn meyasa nakasa tsayawa na fahimce ki ba”. Jiddah tace “kede cinye indomie”.   Imaan ta fara jin indomie din seda taci ta koshi snn ta sha ruwa ta kalli jidda tace “thank you Allah ne kade ze biyaki”. Jiddah tace “hope ynx de bakijin haushi na”. Murmushi imaan tayi bade tace komai ba. Jiddah ta dafa shoulder dinta tace ki godewa Allah wlh jalal yana sonki kafin a samu namiji me son matar sa kamar yanda jalal yake sonki se an wahala wlh”. Imaan kallon ta kawai take dan ita tunda take jalal be taba ce mata yana sonta ba kawai de mutane ke ganin haka. Amma ita kanta tasan jalal is not her type kawai de yna kulata ne sbd he’s very caring. Ganin imaan ta shiga tunani yasa jiddah tace “ki bar ganin kamar wasa. Wlh jalal yana sonki. Da kinsan halin da jalal ya shiga bayan tafiyar ki da baki tafi ba. Seda ya koma ruwa tsulumdum wajen shan giya duk don saboda ke bayaci baya sha imaan Zuciyar jalal ta kusa bugawa. Badan Allah ya kaini asibiti ba a ranar da jalal ya rasa ransa. Da baki dawo kin samesa da rai ba tunda kika tafi komai ya tsaya masa. Amma ranar da aka fada masa inda kike ya samu lpy. Jalal truly love you wlh ni sheda ce”. Wani irin sanyi jikin imaan yayi. “So jalal loves her da ya mutu fa. Me yasa be fada mata ba why daya fada mata da meze saka ma ta tafi”. Jiddah ta kamo hannun imaan snn tace “imaan ki gode Allah da kika samu namiji kamar jalal. Dan haka kema ki sosa ki dage sosai wajen ganin kin kawar da duk wani bakin ciki da jalal ze shiga imaan kome jalal zeyi maki kiyi hakuri. Bare ma nasan baze ba. Sbd yana sonki fiye da tunanin ki. Yan mata dayawa suna sonsa amma wlh kallo basu ishesa ba amma ke kam yana neman rasa ransa saboda ke.  You’re God’s gift to jalals life. Allah ne ya kawoki dan kisakasa farin ciki. Dan haka seki dage ina rokonki karkiyi amfani da son da jalal ke maki ki kun tatawa rayuwar sa pls. He need you do ur very best domin kiga kin yaye masa duk wani bakin ciki”.  
Sosai jikin imaan yayi sanyi domin kau Mommy ma tazo ta daura mata daga inda jiddah ta tsaya. Har motar jalal suka rako ta imaan ta shiga tana dagawa mommy hannu tanaji kamar karta rabu da mommy.  Seda suka dauki hanya imaan ta kalli jalal tace “congratulations” kamo hannun ta yayi yana dan muzawa shima jikinsa duk a sanyaye always yace “I just can’t wait Mommy na tasamu lpy”.  “Nima inaso” imaan ta fada tana murmushi yace “su maryam gobe zasu zo nace su bari se jibi”. Imaan tace “why”. Yace “sbd gobe zamu koma gidan mu. So kinga idan sun zo. Zamuje ku karbo result dinku zuwa next two week zamu tafi canada can zamu zauna har ki gama karatun ki na 8months and tym din my unborn yazo duniya”. Wani irin dadi imaan taji. “So finally zata gama karatun ta” hannun sa takai bakinta tayi kissing snn tace “thank you very much husband I love you”. Kallon ta jalal yayi snn yace “no thanks dear”. 
Bayan sun koma jalal na kwance a palor yana kallon tv imaan tazo ta zauna gefen sa ta hade rai. Jalal ya tashi zaune tare da jawo ta jikinsa yace “tell me what is wrong with you babee”. Kamar imaan zatayi kuka tace “ashe bayan na tafi kacigaba da shan wine”. Shiru jalal yayi yana kallonta. Imaan saka hannunta a gefen fuskar sa tana shafawa kadan tace “why”. Jalal ya lumshe idanu ya bude kafin yace “is all ur fault babee”. Imaan tace “why kome ya same ka bazaka iya mikawa Allah ba”. Jalal ya zagayo da hannun sa ta waist dinta tare da daura kansa a shoulder dinta. “Tunda kika tafi komai ya tsayamun. Nasan da kinsan irin sonda nake maki da baki tafi ba. Kinsan cewa na dade ina sonki”. A hankali imaan ta fara shafa gashin kansa. “Na dade ina sonki bnsan tayaya zanfada maki ba ina tsoron na fada maki kuma kice baki sona nasan I will be so heart broken. The first tym I set my eyes on you imaan I felt the sign of. Love . I can’t deny it cos is real ko da yaushe idan muna tare inajin nishadi inajin farin ciki every single minute da zamuyi spending wlh dadi nakeji tun kafin na aure ki kuwa. A tunanin ki sakin ki zanyi ko”. Yayi maganar yana kallon ta. Imaan ta gyada kai tana murmushi yace ”lol we’re dying to gether I love and I love you. I want to spend the rest of my life with you imaan in fada maki gsky koda Abba ya samu lpy bazan iya rabuwa dake ba ina maki wani irin so da bnsan kalarsa ba. Banajin zan iya hada soyayyarki da ta wata mace kidin de ke kade ke nake so kuma dake kade zan rayu pls imaan koda kinaji a ranki wata rana zamu rabo pls let me beg you dan Allah ki dena ina so mu rayu na har abada I want you to be the mother of my children till eternity”. Rungumesa imaan tayi sosai tace “I will not mijina I love you and I will keep loving you till my last breath”.   Jalal yaje dede saitin kunnen ta yace “tun lokacin dana bude hanyar nan na riga na maida ke tawa you’re mine I you will forever be mine I love you zainabuuu na”. Shigewa imaan tayi jikinsa cike da farin ciki.
Washe gari imaan suka tare a gidan su imaan tayi tunanin wancan gidan da suka zaunane setaga wani daban haduwar gidan ba a magana. Kuma gashi harda uba uban lefe granny ta hada mata. Su sumy sune suka jagoranci komai   Adda taga gidan imaan se murna take umma ma ta yaba sosai. Ranar imaan taga so wajen jalal bana wasa ba. Washe gari su maryam suka zo sun dade suna maida yanda akayi a gida   Kafin jalal ya dawo suje makarantar su karbo result dinsu. Sunyi farin ciki sosai ganin yanda suka ci. Shi kansa Jalal ya yaba sosai da yanda result din nasu yayi kyau sosai.
Imaan har macewa tayi ta koma wani kauye dan kau soyayya suke sha ita da jalal snn suna mugun kula da cikin su. Idan kaga yanda suka kara kyau ba a magana. Satin da zasu tafi canada jalal ya gamayi masu duk wani processing da gidan da zasu zauna da komai. Ana sauran kwana biyu su tafi sukaje kauyen su imaan tare da umma Adda kam granny tace a bar mata ita. Itama Adda tace taga wajen zama.
Tunda suka shiga garin ake kallon motar su har suka isa gidan umma tarba suka samu me kyau wajen kuluwa. Imaan ta rungume kawar ta. Murna wajen kuluwa kam ba a magana domin kau Ynx an wanke kawar ta kowa ya gane cikin da ubansa.  Koda ya Abbakar yazo sama sama suka gaisa da imaan dan ji take kawai ya fita ranta. Bayan sun gama da gidan umma suka wuce gidansu imaan. Wanda tunda jummala taji sunzo garin ta rufe daki ita da yaranta sede suyi ta leken ta ta window. Irin kyan da imaan tayi ma kade ya isa yasa ka gane tana cikin jin dadi. Ga mijin ta a gefen ta duk inda tayi idon matar sa a kansa. Jalal ya samu ganin baba. Anan ya cirewa baba duk wani thought be boye masa komai ba ya sanar dashi halin da ake ciki. Tun daga kan yanda ya auri imaan though be fada masa ainahin labarin sa ba. Amma baba yaji a jikinsa cewa akwai wani abu kuma yaji dadin yanda jalal din ke son imaan. Yayi masu nasiha sosai tare da fatan alkhairi. Jalal ya bukaci baba shima yabar kauyen amma ya kafe dole ya hakura tare da aje masa kyautar kudade.   Imaan ta bama kuluwa kyautuka dayawa dan ko wane trolley tayi masa ita da talatu ga kuma kudi zuba masu kudade dan tasan suna da bukata. Tana nan ta aje a ranta cewa setazo ta dauke su daga garin nan. Su hurera kam ko kallon inda suke batayi ba bare su saka ran wani abu duk sun fice mata a rai sheganta mata ciki da sukayi yafi komai tsaya mata a rai. Suma ko fitowa basuyi ba sunade kallon su ta window.   Tana ta kallon tsakar gidan da ynx ko digon abu jummala bata saidawa sbd maganar mutane. Har taso turgudewa. Jalal yayi saurin rungumo ta yana kallon ta tare da dage gira daya. Yace “ki kula fa idan wani abu ya sameki da yaro na nafi kowa asara I both love you ”. Zare jikinta tayi tana gudun kar baba ya fito har mota suka rakasu su imaan suka dauki hanya.
Ranar da zasu tafi imaan duk se taitajin wani irin tunda take bata taba barin kasar nan ba. Bata taba shiga jirgi ba. Tanason taga Mommy da Abba kafin ta tafi. Amma babu yanda ta iya. One thing da bata sani ba shine Abba shima baya cikin kasar ynx haka. Har suka isa airport jikinta a sanyaye. Jalal ya kamo hannun ta murya can kasa yace “why are you like this bafa kwanar dan audi zamuje ba”. Murmushi imaan tayi tana hararar sa yace “bazan taba manta sunan garin nan ba yabani wahala. But ina sonsa cos my smile keeper was born there”. Murmushi imaan tayi tana kallon su labeeb da AK da sukazo yiwa su maryam sallama. Labeeb nayi masu wani kallo ita da jalal yace “ummm masoya sede mukaji an zama mata da miji babu notice”. Ak yace “enhen dama ai munce you guys you suit each other Amma kai aa baka son raini ashe zagayewa kayi”.   Jalal ya janyo imaan ta side dinsa yace “I love this little babee tun kafin ma ku kusanta. So karkuga  laifi na danna zagaye inda akwai abinda yafi love ko aure zan iya yiwa imaan ina sonta fiya da tunanin kowa I love her more than what can say”. A hankali imaan ta daura kanta a shoulder dinsa tanaji kamar tafi kowace mace saa. Da ace mutane sun san how nice jalal is da basuyi gigin kiransa da bad boy ba. But tym is coming Inshaallah ita da kanta zatayiwa mutane proving that jalal isn’t a bad boy. He’s the full definition of a man,handsome and a gentle
Zaune suke a parlor inda suka saba haduwa Alh barau yace “meyasa ka dakatar da su habib da aikin su and kayi shiru ka zuba masu idanu”. Abba isa na wani murmushi yace “sbd bana so a samu matsala. Banama so duniya tasan yayi wani aure. Shiyasa nasa a dakatar da duk wani labaran sa da ake yadawa” “mene hujjar hakan”. Alh barau ya tambaya “duka daya nake so nayi masa inaso na zuba masa idanu dagashi har matar tasa. Duk da ni bama najin matar dan banga alamar auren manufa ne aka hada ba. Kuma yarinya ce kara ma ashe ko saar sumy batayi ba matsala ta daya shine cikin dake jikin ta. Shine damuwa na”. Alh barau yayi saurin dadin “nima shine amma kasan cikin nan kamar kwalelan mu ne. Bn taba ganin abinda jalal ya maida hankali akai a irin cikin nan. Da kuma matar sa dan haka abin kamar da wuya “. Wani irin murmushi Abba isa yayi “bade zezo duniya ba. Allah ya kawosa. Beside ai bama da yaron zamu fara ba da shi uban yaron zamu fara dan next labarin sa da zamu fitar wlh komi kudin ubannasa baze fita ba se an kamasa. Daganan zanji da yaron. Se uban snn se waccan mara amfanin. Then finally atleast zan samu peace of mind.”  Alh barau yace “tabbas to Allah de ya kaimu” Alh barau yace Ameen.
 

After 6 months
Cikin imaan har ya cika wata tara baya bata wata matsala. Inde har zataci abinci to batada damuwa ci take kamar mene abun har tsoro ya fara bama jalal gashi taki yarda suje asibiti. Ko daya kuma cikin be hanata karatu ba dan tana maida hankali sosai. Cikin ta ya isa watan haihuwa Amma kuma babu inda bata zuwa. Adda ma tazo dan daddy yace tazo ta zauna dasu sbd at anytime imaan zata iya haihuwa. Sosai imaan taji dadin zuwan Adda itakam Adda fadi take “ynx fa sede jummala taji cewa nabar nigeria na shiga jirgi.   Sosai take basu nishadi. Jalal ma kansa ynx ya sake da ita. A dan moment din nan jalal ya samu farin cikin da be taba samu ba tunda yake a rayuwar sa. Ko sau daya ba a kara maganar munanen halayensa ba ga mum dinsa anata magani likitoci sunce sauki yana wajen Allah sucigaba da addua...

Ranar da imaan zata haihune tasha wata irin wahala wacce basuyi tunanin zata shata ba sbd yanda cikin be bata wahala ba.  Tun safe suke asibiti har wajen 2 imaan bata haihuwa. Jalal duk ya tashi hankalinsa Adda kam harda kuka.  Shi kansa jalal din ji yake dama zeyi kukan. Har se bayan laasar imaan ta samu damar haifo kyawawan yaranta mace da namiji masu kama da babansu sak. Farin ciki wajen jalal ba a magana   Ya hada imaan ita da yaranta yana ta zubo masu godiya. Kafin ya saketa ya dauki yaran yana kallo tare da hamdala cikin zuciyar sa. Imaan ta kwantar da kanta saman shoulder dinsa kafin kamar zatayi kuka tace “ni meyasa basa kama dani”. Ya dage gira daya yana kallonta. “Nidin aibana wasa bane babee”. Imaan ta kara shigewa jikinsa tana kallon cute cute yaran da komai basu mance ba a kamannin babansu. Ta kalli cute cute lips dinsu irin na jalal ne suma. Murya can kasa tace “I love them sbd suna kama da kai”. Jalal yace “that means kinfi sona akansu” imaan tayi kissing dinsa da cik dinsa kafin tace “Allah ne ya bani su amma ta silar ka. Ina balain sonsu tun kafin suzo duniya idan kuma na tuna cewa kaine mahaifinsu se naji wani farin ciki”. Jala ya shafi gefen fuskar ta kafin yace “is such a blessing having as wife  you take me out of the saddest lyf. You change me from a drunker to a better person you try all ur very best just to make me happy and now kin haifa mun beautiful kid wanda kallon su kade a ynx ya isa ya sakani farin ciki  thank you wife I love you and I love my kid”.  Macen ce ta wani tabe baki tana mutsu mutsu kafin ta fara kuka. Duk kallon ta sukayi. Jalal ya dauko ta yana kallon imaan kafin yace “little mom imaans character kalli yanda ta tabe baki kamar mom dinta”. Murmushi imaan tayi tana kallon yarinyar kafin ta kalli yaron shima da yake ta mutsu mutsu shima yana niyar tashi she can’t believe yau itace da yara”.
A ranar jalal yayi ordern kayan yara dana imaan din da komai da zasu bukata. A asibitin suka kwana kafin washe gari a sallamesu .... ranar da aka sallamesu ranar daddy yazo yaga kids din  dasu granny harda kuluwa da ko abuja bata taba zuwa ba segata a canada. Daddy ya kasa boye farin cikinsa na samun jikoki domin kau ranar da aka haifi jalal kawai yake tunawa. How happy he was. Har ya kosa fareeda ta samu lpy shikam dan ma babu wanda ake bari ya ganta idan ba mamy ba. Domin tsaro sosai aka saka mata   Amma nauyin asibitin duk shine ya dauka kuma ko so daya besan cewa an samu poison din ba. 
Duk yanda aka so jalal ya dena kwana tare da imaan fur yaki yace shi babu wani bacci daze yarda ya karayi batare da matar sa ba adda de kam tayi masifa har ta gaji. Amma kullum jalal rungume da matarsa yake kwana.
Ranar suna aka radawa yara suna. Fareeda da saifudden.  Sunane wanda akayi sa kamar biki dan kowa kaunar yaran yake a ido ma idan ka gansu se sun birgeka.
   Watan su Amnah da Amaan(saif da fareeda) biyu imaan ta kammala karatun ta danma yaran sun dan bata wahala but Alhmdllh kome ya tafi dede dan jalal is there for her.  Makarantar basu da matsala wajen sakin result dan in one month tym result ya fita.   Dan haka seda suka jira result ya fito snn suka dawo nigeria. Tym din su Amaan sunyi wayo yaran Idan ka gansu masha Allah kamanin su da dad dinsu ta kara fitowa barin ma Amaan. Kowa yaga yaran se sun birgesa gasu jawuur dasu. Result din imaan yayi kyau sosai yanxu ta zama cikakkiyar lauya. Unbelievable bata da abinda zata sakawa Abba dashi sede addua kuma zata dage iya iyawar ta domin taga tagano makiyansa. 
Satin imaan biyu da dawowa amma jalal yaki bari ta fara zuwa aiki danma yace bazatayi a karkashin gwamnati ba lauya me zaman kanta zatayi su maryam duk sun fara zuwa.duk da de basu fara shariar ba
Ranar su maryam suka kawo mata ziyara. Anan ne suke bata lbarin su labeeb da suke so su turo gidan su. Imaan tayi farin ciki sosai tayi masu fatan Alkhairi. Suna zaune amaan na hannun yusrah tana masa wasa while imaan na feeding amnah. Maryam dake kallon wayar ta tace “what. Yaushe rabon da naji wani deen kunji me yayi kuma”. Wani irin faduwa gaban imaan yayi. Tama kasa magana se kallon maryam take. Yusrah tace “ni har na gaji daji wlh se aikin yadawa amma basa iya daukar mataki akai”. Imaan de ta kasa cewa komai   Maryam tace “wlh I don’t think wnn karon ze sha kin kuwa san waya tabo”. Yusrah tace “wane”. Maryam tace “bari kiji Abinda yayi.Shekaran jiya an kama wasu da suka shigo da hard drugs a jikinsu anyi kokarin kamasu amma sun gudu. Se jiya da aka tare motar wata budurwa aka bata drugs din ta karfin tsiya snn akayi raping dinta.  Anan police suka kama wani daga ciki dan sauran sun gudu. Wanda aka kama din shine wanda ya fadi inda suka samu drug din da sukayi amfani dashi. Snn ya tona sauran yaran. Sunce sune aka kama sun shigo da drugs suka samu damar guduwa. Da aka tambayesu drugs din wane sunce na DEEN  ne. Kuma shine yace a samu jikin mace budurwa ayi testing mata snn suyi raping dinta sunji yanda test din ze bada dan drugs din yana karawa mace wani irin dadi. Inde har da gaske yana aiki to za a cigaba da shigowa da drug din. Ana sayarwa shima ya zama business. Kinga knn yawan shaye shaye da kuma zinace zinace zeyi yawa da kuma fyade dan zasu rika bama yara kanana kuma kinsan er wane sukayi raping”  yusrah da duk ta shiga tashin hankali jin irin wnn laifi da deen ke aikatawa da kuma irin balain da yake son kawo masu tace “aa” “yarinyar Alh Abba Mando ce”. Wani irin waro idanu yusrah tayi kafin tace “kutt wlh nasan mutumin nan ko kudinsa ze kare se yaga bayan DEEN abin sa yakai tunda har ya fara taba yaran manya ynx zasu tashi tsaye”. Maryam tace “to ai kodan saboda gabar dake tsakanin sa da mahaifin deen kamar yanda mukaji labari baze yarda ba tabb” murya imaan na rawa tace “wanene shi Alh Abban”. Yusrah tace “yana daya daga cikin manyan kasar nan. Kuma babban makiyin shi baban dee  din ne ance kuma basu jituwa kinga kau ai baze yarda ba”.
Wani irin yamm jikin imaan yayi. Ko sau daya batajin zata yarda da wnn wani kuka kawai taji yana taho mata dis is a set up wlh sharri ake masa wato an bullo da yanda dole Za a ga bayansa ko. Kuma kowa yarda zeyi sbd duniya tasan wayeshi. No gsky she have to wake up. Dole ta tashi tsaye akan mijin ta tym yayi da zata kawo karshen damuwar mijin ta abu ne me hadari amma dole ta shiga sbd mijin ta but now tanason taga jalal domin sanin halin da yake ciki ita kanta tasan wnn karon seya girgiza idan yaji wnn labarin

Urs
✨✨✨
Annafie💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
              ANNAFIE💖…✍️
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
  Aa
Bismillahir rahmanir raheem
NOT EDITED
💫💫💖Jalal Alii((42)💖💫💫
Ganin yanayin da imaan ta shiga yasa maryam fadin imaan “are you Ohk?”  Kallonsu imaan tayi tana kokarin danne hawayen ta tace babu komai kafin ta tashi tare da amnah a hannun ta ta nufi sama dakin ta tashiga. Rufe kofa tayi tare da fashewa da kuka. Wnn wane irin balai ne ynx tayaya jalal ma ze fita a wnn tarkon. Hard drugs abune fa daya shafi kowa. Hankalin ta ya tashi sosai jin diyar ko wane suka taba.   Wayar ta ta dauka tayi dialing numbern jalal. Har ya gama ringing ba a dauka ba. Sake kira tayi but still jalal is not picking the call. Imaan ta fashe da kuka tana sake kiransa. Har tayi masa 6 missed calls amma be daga ba. Fashewa da kuka tayi sosai ta juya kiran zuwa sageer Amma be daga ba. Tashin hankali sosai imaan ta shiga. Ta janyo amnah ta ta rungume tana kuka sosai. Su maryam ne suka shigo ganjn yanda take kuka yasa hankalin su ta tashi suka fara tambayar ta lafiya. Imaan ta kasa cewa komai sede kuka da takeyi. Yusrah ta amshi amnah ta saka ta adan gadon ta Amaan ma haka. Maryam ta rungume ta tana tambayar “lpy meyafaru” imaan ta rungume maryam tana kuka sosai tade kasa magana. Yusrah ta fara ringing ganin Ak ne yasa ta dauka “gamunan zamu zo mu dauke ku”. Yusrah tace “aa ku barshi kawai imaan kuka take tun dazu”. Yace “karki damu sunyi waya da mijin ta zezo ynx” daga haka ya kashe wayar. A sanyaye yusrah ta kalli maryam ta fada mata yanda sukayi da Ak. Imaan na kuka sosai tace “dan Allah karku tafi.”    Maryam zatayi magana wayar imaan ya fara ringing. Ganin sageer ne yasa imaan daukar wayar da sauri. Jin yanda take kuka yasa sageer fadin ki kwantar da hankalin ki nima gani nan zuwa gidan zan dauke ki muje can gida. Nanny ta shirya su Amaan I’m coming” daga haka ya katse wayar bema bata space din magana ba. Kuma shima da kaji muryar sa kasan yana cikin damuwa. 
Su Ak na zuwa suka tafi dasu yusrah. Duk da basu so tafiya ba danma sunga tafi itama za ayi da ita. But they’re just wondering me saka ta kuka haka cikin lokaci kankani.   Tsab imaan ta shirya ita da yaran tare   Babu jimawa sega sageer. Shine ya dauki Amaan ta dauki Amnah nanny dinsu kuma ta dauki  wasu abubuwan. Bayan sun shiga mota sageer na kallon yanda take kuka sosai. A sanyaye yace “kiyi hakuri Inshaallah bazasuci galaba a kanmu ba”. Da sauri imaan tace “he’s not picking my calls”. Shiru sageer yayi be kara magana ba. Domin kau be san me zece mata ba.  
Suman zaune kawai Alh Ali yayi zuciyar sa na wani irin bugawa domin kau yasan kodame yake  wnn karon yasan Jalal baze tsira ba. Domin kau an tabo inda bama kasar nigeria ba har wasu kasashen se sun saka baki. Bare kuma an hadda babban makiyin sa. Ai ko kowa ya hakura shi baze ba. A wnn karon ko daya ji yayi be yarda ba wnn set up ne amma taya ze fahimtar da duniya cewa n ba haka bane bayan tuntuni kowa yasan wane jalal. Ya kalli kanin nasa da duk shima ya shiga tashi na hankali yace “call jalal for me.”  Waya ya dauka ya fara kiran jalal amma har ta katse be dauka ba. Har sau uku amma be dauka ba   Ya kalli Daddy yace “he isn’t picking the call”. A takaice daddy yace “call sageer”. Kira daya Ya dauka “hello Abba” “sageer Ina jalal” cewar abba isa “abban bn sani ba he isn’t picking my calls”.   Daddy dake jin komai ya mike “definitely something is wrong with my son I have to see him”. Abba isa yace “calm down duk ka tashi hankalin ka”. Daddy ya kalli Abba isa cike da bacin rai da tashin hankali yace “I should calm down kace isa. I should calm down kana gani suna son kashe mun yaro na da ransa. Allah kade yasan halin da yake ciki a ynx haka. Wlh anyone who’s behind this nagano sa sena kashe sa da hannu nan”. Kafin Abba isa yayi magana Alh barau ya shigo da waya a hannunsa yana mikawa daddy yace “Alh Abba on phone he want to speak with you”. Kallon wayar kawai daddy yake zuciyar sa na wani irin bugawa. Alh barau ya saka wayan a hands free.muryar Alh Abba mande ta daki kunnuwan Daddy. Da kakkausar murya cike da bacin rai Alh Abba yace “Alh Ali Abbas bude kunnen da kyau ka saurareni. Wato abun shashashan yaron naka ya tsallake kananun masu kudi ya dawo kaina ko.”  Alh Abba yayi wani dariya me cike da ciwon er sa da aka lalata yace “wlh wlh wlh kaji na rantse. Koda zan rasa abinda na mallaka duk duniyar nan wlh se nasaka anyi danka kisan wulakanci se kaji mafificin ciwon abinda naji. Kuma nasan da gangan kayi amma kasani wnn karon yaron ka baze tsira ba koda kuwa sama da kasa zasu hade ne. Zan nuna masa shi karamin dan duniya ne tunda har yake tsoran bayyana kansa kowa ya sansa sede halayensa. Kuma kaji ynx kaga abinda ze faru” daga haka ya kashe wayar”. Wane irin buga tabir yayi cike da tashin hankali yace “I want to see my son his wife and my two grandchildren. And my mom ku muje gida ynx”. Ko saurarinsu beyi ba ya nufi hanyar fita duk suka bi bayansa. Babu shiri duk suka bi bayan sa.  
Kusan duk a tare suka isa da sageer da sageer. Compound din tsit kakeji. Sageer ya bude ya fito tare da Amaan  imaan kuma ta fito rike da Amnah tana kuka. Kabar Amnah daddy yayi kafin yace “ki kwantar da hankalin kinji”. Imaan ta gyada kai. Dad ya nufi part din Granny har tym din Amnah na hannunsa hakan yasa kowa ya bisa zuwa part din granny.   Duk carko carko ya gansu sunyi tsaye. Granny na ganin Dad tace “ni kasa fahimtar meke faruwa meke damun jalal ne”.   Shiru dad yayi yana kallon mom din tasa. Kafin ya zauna ya lumshe idanu yama kasa magana. Adda tace kuyi mun bayani meke faruwa ne. Imaan taje ta rungume ta da sauri. Daddy ya rinka kallon cute amnah dake ta mutsu mutsu a hannun sa. Snn yace “ina so cikin 1hr anemomin inda yaro na yake”   Fita abba isa yayi. Minti daya baayi da shigar sa ba sega motar jalal shigo gidan dani irin gudu. Hakan yasa duk kowa ya mike suka nufi inda jalal yake. Idanun sa sunyi wani irin mugun ja ya fito daga motar. Kowa kallon sa yake. Jalal beyiwa kowa magana ba ya nufi daddy. Karbar ersa yayi snn ya tafi wajen sageer ya karbi amaan ya shiga part din granny. Direct dakinta ya shiga ya rungume yaransa. Kowa tsayawa yayi a parlor yama kasa shiga inda yake daddy ya kalli granny da broken voice dinsa yace “something is eaten my son nasan wnn karon shi kansa ya girgiza. Fashewa da kuka granny tayi tace “nashiga uku wnn wane irin balai ne “. Imaan kanta kuka takeyi sosai. Adda ma kukan ta fara “kuyimun bayani mana meke damun shi jalal din”. Daddy ya kalli imaan dake kuka sosai yace “jeki wajen mijin ki”. Kamar jira imaaan takeyi ta nufi dakin granny da sauri. Rungume ta gansa da yaran ya rungume yana ta sauke ajiyar zuciya. Karasawa imaan tayi da hada su duka ta rungume tana kuka sosai. Jalal ya bude idanun sa da sukayi jawurr yana kallon imaan.  Kafin ya sauke yaran ya ajesu gefe ya janyo imaan sosai ya wani rungume ta a jikinsa imaan tanajin yanda zuciyar sa ke beating fast fast. Kukanta karfi ya kara sosai. Jin kukan yayi yawa yasa. Jalal ya dago jaw dinta yana kallon face dinta muryar sa a disashe yace “stop crying love”. Wani irin kuka imaan ta kara fashewa dashi   Jalal ya rungume ta sosai shima “imaan bansu su ba bansan suwane ba suke ta bibiyar rayuwar mu tun kafin nasan wane ni sun hanani sakat”. Imaan tama kasa magana ta kasa cewa komai.  Dagowa tayi da saurin jin jiniya.  Sosai ta cikan kunnuwan su hakan yasa suka gane gidan suka shigo. Muryar imaan na rawa tace “police”. Wani murmushi jalal yayi snn yace “i knw they must come wnn ba baramin crime bane. Ko wane babana wlh bazan barni ba”.   Imaan zatayi magana Amaan ya fashe da kuka sosai. Lokaci daya amnah ma ta dauka. Da sauri imaan ta karasa wajen su ta dauki imaan jalal kuma ya dauki amnah jijiga su suka farayi.  Amma yaran sunkiyin shiru.

Jin yanda police din suka cika gidan yasa hankalin kowa ya kara tashi. Adda de bata fahimtar komai kuma babu wanda yace da ita komai. Direct part din granny sukayo dan maikatan gidan sun sanar dasu sanar dasu inda dad yake. Ko daya daddy be motsa ba har suka shigo. Kallon su Daddy yayi daga zaunen yace “da permission din wa kukan shigomin gida”.   Shugaban police din yace “we are srry sir both ur son is under arrest”. A fusace daddy ya mike yace “ku baku isa ku kamanin yaro ba laifin mene yayi kun gansa ne”. Wayar sa police din ya dauka ya kira shugaban police din na kasa gaba daya. A hands free ya saka wayar tare da fadin “sir yace his son did not commit any crime babu wanda ze iya arresting dinsa shi Alh Ali ne ya fadi haka”. Daga can bangaren yace “jalal is our suspect dan haka dole mukamasa. Kuma wnn sakon daga sama ne this tym arround dole jalal yazo hannun hukuma dole se yayi bayani da bakin sa dan haka kuyi arresting dinsa ynx nan shugaban kasa ya rigada yayi singing kuyi aikin ku”. Katse wayar police din yayi snn yace “we want to do our job sir”. Wani irin tsawa Dad ya daka masa kafin yace “babu wanda ya isa ya tozarta yarona”. Waya dad ya dauka direct ya danna kira wa shugaban kasa.   Bayan ya dauka dad ya gaishe dashi cike da girmamawa kafin ya kara da fadin “ur excellency babu wanda ya isa ya tozarta mun yaro dan nasan dana be aikata ba. Nasan Alh Abba ne da wnn aikin amma kasani ko sama da kasa zata hade bazan yarda jalal ya aikata hakan ba  a bari nayi magana da lauyoyina tukunna kafin a tafi mun da yaro. Dan wlh babu wanda ze tozarta mun daya daga baya kuma azo a gane bashi da laifi bayan an gama nunawa duniya cewa shi me laifi ne”. Daga can bangaren president yace “dole jalal yaje hannun hukuma Alh Ali I’m srry to say”. Cike da bacin rai yace “kazaman yan sanda bazasu kamamun yaro ba suje su tozarta sa. Bana son gidansa gida na ka turo Dss Ynx kuma wlh koda wasa hotan dana ya bayyana wlh sede tattalin arzin kasar nan ya rushe a shirye nake ynx dede nake na da kowane mahaluki dake shirin ganin bayan yarona”. Daga haka ya katse wayar. Kirane ya shigo waya police din “over over ku gaggauta barin gidan nan”. Ko minti daya basu kara ba suka fita daga gidan.   Sosai Alh barau da alh isa suka sha jinin jikinsu.   Adda tace “shi jalal din mene yayi”. Babu de wanda ya kula su. Fita sageer yayi. Cikin minti goma sega DSS sun shigo.    Gaisar da daddy sukayi kafin su tambayi inda jalal. Yake. Kafin wani yayi magana sega jalal ya fito rike da Amnah dake ta tsala ihu. Imaan ma na bayansa rike da amaan se kuka suke.   Daddy ya kalli jalal da shima kallon sa yake. Murmushi jalal ya sakarwa dad. Tare da fadin “I’m srry Daddy”. Daddy ya rungume dansa tare da fadin “I promise you koda komai nawa ze kare wnn karon se inda karfi na ya kare wajen wanke ka daga laifin da aka makala maka.”  Murmushi jalal yayi kafin ya kalli granny ya mika mata amnah snn ya juya yana kallon DSs din. Shugaban su yazo kusa da jalal yace “Jalal Ali Abbas you’re under arest”. Hannu ya mika masu suka saka masa. Ankwa. Kuka imaan take kamar me ta mika adda amna taje ta rugume jalal tana kuka sosai.  Murmushi yayi yana kallon ta kafin ya dauke kai. Take care of ur self and the kids. I love you

Babu yanda suka iya haka suka tsaya sunaji suna gani aka tafi da jalal. Wadan da basa kuka kadan ne. Imaan kam har shidewa numfashin ta yake. Seda granny ta saka aka kaita dakin nan imaan ta kwanta tasha kuka.
Daddy kau baa magana domin shigewa daki yayi yana ta waya. A haka har dare yayi ko gidan cikin jimami takewa domin kau kuka tayi sa harta gode Allah gasu amaan da suke ta kuka danma granny da adda sun amshi yaran. Ita dasu sede idan zasu sha Nono sumy ce ma ke tare da ita har se dare snn ta tafi.  Wajen karfe sha daya imaan ta tashi daga kwanciyar kukan da take ta shiga toilet awala ta doro tayi ta kabbara sallah. Ya dade tana mikawa Allah kukan ta kafin daga baya ta dauki wayar ta gobe dole ta koma gida gobe ta domin kau duk wani abu da take ganin zata bukata yana gida. She need to sit down and think but for now she want to knw wane jalal. Direct tweeter ta shiga ta fara duba duk wani labarai da ake fada ta dade tana dubawa kafin ta dauki user name din da ake amfani dashi a matsayin sunan jalal ana amsa duk wani laifi da kuma kuma komai ma da ake amfani dashi da sunan jalal din ne.   Snn ta shiga labarin yau da akeyi. Sosai tayi going through komai ta gashi nan harda hoton yarinyar da kuma hotunan wadan da sukayi raping din da kuma hotunan su da aka yasa time din da suka shigo da drugs din kafin su samu damar kubucewa ... ranar ko sau daya imaan batayi bacci ba.
Washe gari sega sammaci an kawowa Dad   Zuwa next week za a shiga court. Ana zargin jalal da laifuka masu yawa. Laifukan kuma sune laifin fyade,shigowa da hard drugs,safarar mata,da kuma bude wajaje ba bisa kaida ba wadan da sun haramta ma a bude.  Hankalin kowa ya tashi sosai. Ita kanta imaan bakaramin girgiza tayi ba. ..tayi kuka tayi kuka harta gode Allah wajen karfe sha daya ta shirya bayan ta gama shayar da yaran ta tabar su wajen granny part dinsu jalal ta nufa. Bata kalli kowa dake dakin ba ta wuce part din jalal ta bude ta shiga daya daga cikin keys din motar jalal din ta dauka. Dama already jalal ya koya mata mota tun a canada dan sometimes na idan zasu fita itace ke driving kuma haihuwar ta ya bata kyautan mota uku.  Fitowa tayi har yanxu bata kalli su mama ba bare su ta gaidasu ta fice. Hajiya atika ta tabe baki “zan ta yanda zaku fita wnn karon”.
Direct wajen motocin jalal ta nufa ta dauki DEEN7 tayi warming kafin taja motar ta fita a hankali maikatan gidan se kallon ta kawai suke lallai itace kade ta isa ta hau motar nan. Amma ko inda yake parking babu wanda ya isa yakai tasa motar.
Gida imaan taje. Dakin ta ta shiga ta dauko system dinta. Ta samu waje tare da daura system dinta saman cinya. Harhada komai nata tayi kafin ta tura request din zama lauyar jalal haka sageer ma ta tura masa. Kafin ta turawa su maryam a matsayin wadan da zasuyi assisting dinta. Snn ta nuna tana son ganin su a gida yanxu.    Ko minti biyar batayi da turawa ba sega kiran sageer. Dauka tayi sageer yace “where are you”. Tace “ina gida gidana”. Yace “ohk we are coming”. Kashe wayar imaan tayi kafin ta fada duniyar tunani batasan ta ina zata fara ba. But dole ta shiga kowa ba abin yarda bane gara ita tayi da kanta. Wani irin tausayin jalal kawai take. Allah kade yasan halin da yake ciki. Tayi wani murmushi kafin tace “ka kwantar da hankalin ka Inshaallah wnn karon babu wanda zeci galaba a kanka inshaallahu karshen duk wasu makiyanka yazo”.
Tare da jiddah sageer yazo. Bayan duk su gaisa an jajanta wa juna sageer yace “imaan naga sakon da kika turamun kina ganin zaki iya. Aiki ne me hadarin gaske fa”. Imaan ta gyada kai hawaye na fita a idanun ta tace “zan iya Inshaallah”. Jiddah tace “nima hankali na yafi kwanciya da ita din sbd bamu san dawa zamu yarda ba”. Sageer ya gyada kai “nima hankalina yafi kwanciya da ita din sede wnn kukan sekin dena sa you have to be strong very strong”.   Jiddah tace “hakane kam dan aikine babba a gaban ki.” Sageer yace “banajin ta zata iya she’s very smart kawai be strong”. Jiddah tace “amma kana ganin daddy ze amince kuwa”. “Bana jin Dad jalal nake ji” jiddah tace haka ne. Sun dade a wajen suna dan tattauna mahimman abubuwa. Kafin daddy ya kira. Sageer ya dauka cike da ladabi. Muryar daddy cike da damuwa suka gaisa yace “imaan ta turon da sako” sageer yace “nima haka amma ina ganin ita din yakamata “. Daddy yace “na duba abubuwan da ta turon snn tunda ta turomun nasa aka kara bincikamun komai a kanta duk da nasani komai excellent”. Sageer yace “and she’s very smart mu gwada mu Gani Ynx haka muna tare da ita”. Daddy yace ina gida kuzo ku sameni”.
A parlor suka samu dadday tare da Abba isa da kuma Alh barau. Abba isa ya kawo masa wani files kwararrun lauyoyi ne ya kawowa daddy domin tsayawa jalal a kotu. Daddy ya amsa bayan ya gama dubawa ya aje yace “bari sageer yazo”  zuwan su da imaan shine ya bama su Alh barau mmki. Bayan duk sun gaisa Daddy ya kalli su abba isa yace “itace lauyar da zata tsayawa jalal”. Abba isa yace “what imaan din risk ne fa sosai”. Sageer yace “wnn ba damuwa bane zamu bata tsaro na mussamman Inshaallah dan Inshaallah inajin zata iya”. Alh barau yace “gsky da za aji shawarata gwara a dauki daya daga wadan nan lauloyin”. Daddy yace “ita din zatayi kuma na yarda. Abu ne wanda yake bukatar natsuwa. Na kusa da kai ma seya cuce taw. Su wadan nan bamu san su wane ba gwara de ita din tay”. Alh barau ze sake magana abba isa ya masa wani kallo kafin Abba isan yace “babu matsala Allah ya taimaka ynx se muke muga jalal din”. Duk tashi sukayi imaan ta tafi cikin gida domin taga yaranta...
wajen da aka kai jalal baka cewa na me laifi ne. Domin kau komai na bukata akwai. Sede ga police ta ko ina zagaye dashi alamar me babban laifi ne aka kai. 
Duk wanda yaga jalal se yaji kamar yayi masa kuka. Idanun sa kade sun isa suyi defining halin da yake ciki. Karbar yaran sa yayi kafin su gaisa da dad. Ya dago ido ya kalli imaan. Dake tsaye har lokacin ta kasa dena kallon sa. Gefen sa ya nuna mata yace “come and sit down wife”. A hankali taje kusa dashi ta zauna. Ya kamo hannun sa cikin nata yana murzawa. Dad ya karanto masa dukkan abinda ake zargin sa dashi. Snn yace “matarka ce zata tsaya maka a kotu”. Wani irin dagowa yayi ya kalli dad snn ya kalli sageer yace “what kunsan hadarin dake tattare da shariar nan kuwa over my dead body”. Kallon imaan yayi snn yace “bada izini na ba na gaya maki”. Sageer yace “wait jalal imaan is very smart”. “I don’t care meyasa smartness din nata besa ta gank hadarin da take neman saka kanta ba bazan yarda ba”.   Duk yanda suka su suyi convincing dinsa yaki yarda har ran sageer yaso ya baci. Cike da tsawa yace “jalal ko kanaso ko bakaso se imaan tayi wnn aikin idan ba ita din ba wa kk tunanin zamu saka yaushe har ka fara trusting mutane da har kake tunanin mu dauko wani mu saka”. Ganin yanda ran sageer ya baci yasa jalal yin kasa da murya dan be saba gani ba yace “sageer hadarin zaka duba”. Sageer yace “u promise you zan saka a bama imaan tsaro na musamman Inshaallah babu abinda ze same ta”. Bada ran jalal yaso ba ya amince.”  Kafin a tafi a barsu shida imaan.  Har seda akace lokaci yayi snn suka fito. Direcf gidan ta aka wuce da ita tare da yaranta da nannyn su daddy yace adda da granny ma anan zasu zauna da ita. Cikin kankanin lokaci sageer yasa aka turo da police masu yawa domin tsaron imaan.
Ganin missed call dinsu yusrah yasa ta dauki wayar ta ta tura masu text na su sameta a gida.

Cikin 1hr kam se gasu. Sunyi mmkin ganin police kuma seda aka bincikesu tsab snn suka shiga. Dama already tasan da zuwan su. Dan ynx babu wanda yake da izinin shiga inda take seda izininta kona sageer dan sageer yace duk abinda ya sameta su kuka da kansu. A parlor suka iske imaan zaune tana jiran su. Ko zama basuyi ba yusrah tace “imaan baki da hankali kin san wane zakiyi depending kuwa. Deen fa kinsan hadarin wnn gayen kuwa. To wlh tunda kikaga an kamasa abun yafi karfin mu” maryam tace “wai tayi suka kawo maki komai. Kinsan hadarinsa kuwa” imaan na kallon su da kyau tace “wlh ko zan rasa raina senayi depending dinsa kuma halinsa ku bazaku gayamun halinsa ba dan shi wanda kuke magana akansa din ba kowa bane mijina ne kin kuwa ga se inda karfi na yakare bazan zuba ido a tozarta uban yara na ba”. Da wani irin shock sukace “what jalal ne deen. Tayaya”. Imaan tace “ta yanda kukaji na fada tun kafin na aure sa nasan wane shi ina sane na boye masu”. “Yusrah tace “kai jalal beyi kama da me mugayen hali irin deen ba he’s kind and innocent”. Imaan na kallon ta tace “abinda nakeson ma duniya proving knn”. Maryam tace “how tayaya ta zama shi”. Imaan tace “ta kazafin da ake masa mana. Ni nasan wane miji na nasan komai nasa nasan abinda ze aikata nasan kuma wanda baze yi ba ku kanku sheda ne base na fada. Dan haka ynx kun shirya jin wane jalal ko ko. Dan lokaci na kurewa.

Urs
✨✨✨
Annafie😍💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
              ANNAFIE💖…✍️
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
  Aa
Bismillahir rahmanir raheem
💫💫💖Jalal Alii((43)💖💫💫
Imaan bata boye masu komai ba akan wane jalal har video mummy dake gadon Asibiti seda ta nuna masu. Dukansu babu wanda beyi kuka ba harta imaan din tana kuka tanayi masu bayani. . Maryam tace “ko daya jalal a fuska bemayi kama da halayensa da ake nunawa ba I guess shiyasa suka ki bari duniya tasan fuskar sa dan dole se an samu wanda ze bibiyi rayuwar sa. Kuma a gano karya suke. Yusrah tace “in my own view sunyi poison mum dinsa ne sbd akwai wani abu data sani game da koma suwane snn abinda akewa jalal anayi ne da manufa dan a kuntatawa daddy yanda zeyi affecting dinsu gabadaya.”  Maryam tace “abinda nima na fahimta knn. Wadan nan ba kowa bane sena jikinsa. Kinga na farko Atika ta shigo ciki,manga ya shigo ciki,ga kuma falalu waddu shima yana ciki. Wadan da dukansu makusantan Daddy ne.”  Imaan ta gyada kai dama tasan bata da matsala akan kawayen ta they’re very sharp”. Maryam ta cigaba “duka wadan nan kuma kinga basu bane bawai an cire su gaba daya ba amma dole mu kara zargin wasu makusanta nasa”. “Suwa knn”. Yusrah ta tambaya. Imaan na kallon maryam tace “idan na fahimce ki Alh isa Abbas da kuma Alh Barau malali kike fadi”. Maryam tace “sure su nake magana”. Imaan tayi murmushi tace “sune number 1. Suspect dina I don’t knw why but tun ranar da jalal ya fadamun wane shi suke fadomun arai. Bazan tun karesu gadan gadan ba Amma zamuga abinda bincike ze bada. Domin kau inde naga ana niyar kadamu lokaci daya zan jeho su ciki bazasuyi tsammani ba kwata kwata”. Murmushi sukayi. Kafin suce “Inshaallah mijin ki ze fito” sun dade suna tattauna yanda zasu bullowa lamarin kafin su tashi su tafi. Da daddare sageer yazo. Shima nan ya kawo mata duk wani abu da yasan zata bukata. Domin kau duk wani bayanai da suka dade suna hadawa shekara da shekaru seda ya kawo mata. Ya tafi ya bata tym domin ta duba. A daren ranar abinda ta dukufa dubawa knn. Washe gari ma sunje wajen jalal. Duk da fushi yake da ita akan shariar da tace zatayi hakan be hana imaan rungume sa ba ta haye saman cinyar sa. Jalal yaki kallon ta yaita kallon yaransa da suke ta bacci yana dan shafa fuskar su imaan ta juyo da fuskar sa saitin tata ta matso da fuskar ta dede tasa tana kallon cikin idanun sa. Ajiyar zuciya jalal ya sauke tare da rungume ta snn ya hade bakin su tare da rungume ta sosai   Sunyi kusan minti biyar suna missing kissing juna dan ba karamin missing juna sukayi ba kwana biyu jinsa suke kamar wata shekara dan koda yaushe suna makale da juna   Amnah ce ta fara mutsu mutsu zatayi kuka. Jalal ya kalle yanda ta tabe baki tana shirin yin kuka. Yace “ni bn fahimci me mummy na take nufi ba tanason son ta hanani jin dadi da matata”. Jalal ya fada yana kissing imaan ta wuya. Snn yace “kishi take dani”. Yayi maganar yana shafa bayan imaaan”. Imaan ta shige jikinsa sosai. “Kyale ta kafin nasan ta wana sani”. Jalal ya daura kansa a saman tana yace “wnn wace irin lauya ce.” Imaan tayi dariya tace “lauyar mijin ta”. Jalal ya dalli bakin ta snn yace “keda kikace you will not depend me”. Imaan ta dafe bakin ta kamar zatayi kuka tace yaushe “. Ya kara rungume ta snn yace “ranar dana fara zuwa gidan ku a kd kin tuna ko”. Yayi maganar yana dage mata gira. Imaan ta boye fuskar ta a jikin sa tana murmushi jalal yace “oh yarinyar nan fa kiyimun rashin kunya iya iyawarki” dariya imaan tayi tace “zaka dawo gidan ne ai kadan ka gani”. Jalal ya langwabe ka “i need something special cute babee”. Imaan ta kamo dan gashin gemunsa tace “duk abinda ze saka farin ciki my love”. Seda imaan ta tabbatar jalal ya shiga farin ciki sosai snn na baro sa

Ana gobe za a shiga sharia umma ta kira imaan da yake duk ta siya masu waya. Bayan sun gaisa imaan tace “umma kunga har ynz ba azo an tafi daku ba ko”. Umma tace “aa imaan wani labari nakeji a gari. Kinsan hamza yaron malam babba yana aiki a kaduna gidan wani me kudi shine yazo mana da wani lvri cewa inde har wanda yazo garin nan a matsayin mahaifin mijin ki shine to tabbas yanzu haka mijinki yana a kulle wai ana zargin sa da manyan laifu ka”. Shiru imaan tayi. Kafin tace “hakane umma amma sheri ne gsky nice ma zanyi shariar gobe kinsan abinda na karanta knn dalilin da yasa kika ga ba azo an dauke ku kun dawo gidan da Jalal ya baku ba knn. Sbd dawowar ku nan din ma hadari ne na gaske amma idan komai ya lafa zanyiwa baba bayani snn ku dawo”. Umma tace “babu komai imaan Allahu ya fitar dashi. Babanki duk ya damu wallahi domin kau jummala ta bude gari da cewa kudin mijin ki ashe na haram ne wai da erta ta auri miji irin wnn gwara ta mutu a kauye cikin talauci. Murmushi me ciwo imaan tayi kafin tace “umma ku kwantar da hankalin ku. Zansa a kawo maku wayoyi da zaku ga shariar da kanku. Zaku komai yanda yake tafiya domin kau live za a nuna anjima zansa a kawo maku”. Umma tayi godiya snn tayi ma imaan addua suka kashe wayar....

“Kasan yarinyar nan dariya take bani. Shekarunta 21 amma gani take zata iya. Batasan lokacin da muka fara shiryawa abin nan ko haihuwar ta ma ba asan zaayi ba kila ma ko aure uwar ta ba ayi ba”. Murmushi Alh isa yayi yana kallon Alh barau snn yace “wane ita ai ko wane uban ta be isa ya fitar da jalal ba. Dan taga ta gama da first class shiyasa take tunanin zata iya da wnn batasan cewa lokacin da mukayi namu shirin ko makarantar su ba a bude ba. Kawai dadin da zeji ynx shine da be karbi wadan nan lauyoyin ba da wlh se sun jawo wa jalal laifin ma da beyi tunani ba”. Alh barau yace “amma baka tunanin ya fara fahimtar wani abu game da kai inda ba haka ba tayaya zeki amsar wadan can lauyoyin.” “Ko daya ya fara tsorata ne shiyasa yake ganin gara ita din  dan har shawara ya tambayan tayi nace tayi sbd nima ina gudun wnn sageer din ya kawo wani kwararren gara ita din mace ce tunanin ta karami ne. Kasan sageer din nan nafi jinsa fiye da kowa shida mahaifiyar sa da ace mun kula dasu tun farko aida ynx ba wnn zancen ake ba” cewar Alh isa
RANAR SHARIA
Duk inda inda baku tunani wnn sharia ta kai. Domin kau mutane daga gurare daban daban birni da kauye wnn sharia ta kai. Har ma da wasu kasashen. Domin kai kowa burinsa yaga an kawo karshe DEEN daya addabesu kuma yake shirin kawo masu wani balai a kasa. Dan na wasu suna cewa dan anga shi dan masu hali ne shine aka kamasa daban aka hana yam sada kamasa. Daddy kau yace duk wanda ya fito masa da yaro to wlh akwai damuwa. Dan ko wajen shariar ma baze zo ba babu wanda ya isa ya tozarta masa da yaro a bari se an kama sa dumu dumu da laifi.
Idan kunga yanda court din ta cika da jamaa se kunsha mmki kowa yana so yaji yanda zata kasance. Gashi kuma za a nunasa live. Ko a wayar ka ma zaka iya gani gidajen talabijin da gidajen radio duka zaku iya saurare. Harda kauyen su imaan duk abin ya dauka dan su jummala an tafi gidajen da suke kallo domin abama ido abinci. Su umma da baba kam a tab din da imaan ta aiko masu da ita anan zasu kalla  
Gidan su jalal kwansu da kwarkwatar su kowa yazo. Kotun ta wani irin cika cika taban mmki. Yaran imaan suna hannun Adda da granny. Se kallon family din su ake. Wasu sede su tura baki irin zaku gane kurinku kude bade masu kudi ba. Zuciyar Daddy banda bugawa babu abinda yake. Yanaji inde har akayi nasara akan su to kila shikam karshensa knn domin ko yasan akayi nasara to hukuncin kisa za a yanke wa jalal Abinda zuciyar sa kuma bazata iya dauka ba.

Imaan ba karamin kyau tayi ba cikin kayan lauyoyin ba she looks very cute and young baka taba cewa ba tayi aure. Idan ka gansu ita dasu yusrah se sun birgeka. Sunzo zasu shiga wani yace “gade mata har mata amma marasa kishin alumma marasa kishin mata yan uwansu Allah wade da masu kare mugun mutum irin jalal Inshaallah se anci galama a kanku.”  Nan mutane suka fara Allah wade. Kala su imaan basu ce ba. Abun ya daki zuciyar imaan nan ta kara jin wani kwarin guiwar yin sharia domin tanason duniya tasan kallon da sukewa jalal ba haka bane...

Bayan an shiga court kowa ya natsu ana jiran alkhali. Shigowar sa ce tasa kowa ya mike akace “courrrrrt”. Seda alkhali ya zauna snn ya buga masu suma duk suka zauna. Me karantowa ya tashi ya karanto date da snn ya kara da fadin. Alh Abba mando yana karar Jalal Ali Abbas. Akan laifu ka kamar haka. (Fyade da gurbata tarbiyyar matasa. Shigowa da mugayen kwayoyi,bude haramtattun wurare ba tare da kaida ba). Daga haka ya zauna. Alkhali yace “lauyan me kara”. Tashi yayi tsaye tare da dan rissinawa yace “ya me girma me sharia sunana Barr.Sule yaro. Nine kauyan wanda ke kara,a tare dani akwai Barr.Abu dauda”. Daga haka ya zauna.  Alkhali yace “lauyan wanda ake kara”. With full courage imaan ta tashi ya rissina tace “sunana Brr. Zainab Muhammad a tare dani akwai. Yusrah ta tashi Barr. Yusrah Abubakar   “Da kuma”. Maryam ta tashi tace “Maryan Muhammad”.   Daga haka suka zauna. Alkhali yace “shin ko lauyar wanda ake kara ya amince da zargin da ake masa”. Imaan ta tashi tace “Aa my lord kaf babu wanda na amince dashi. Domin kau akaf babu inda fuskar jalal ta bayyana wanda za ace gashi shine ya aikata nagode yane sharia”. Imaan ta zauna. Alkhali yace “ko lauyan wanda keda kara yanada magana”.   Barr. Sule yaro ya mike “eh ina da magana my lord”. Alkhali yace “kotu ta baka dama”. Brr. Sule ya mike yana kallon kotu snn yace “yame sharia a.  A takaice zan bada bayani akan jalal. Wanda kowa ya sani da Deen. Anan wajen bama sena nuna ba kowa yasan irin mugayen laifukan da yake aikatawa kowasan sa a matsayinsa na bad boy. Shi kansa yana amsa.”  Da sauri imaan tace “Objection my lord”. Alkhali ya bata dama. Imaan tace “yamata lauyan wanda ke kara yasan abinda ze fadawa kotu. Babu wata sheda da ta bayyana cewa Jalal shine ke amsa laifukan domin ko account ne na yanar gizo kowa me ze iya budewa”. Alkhali yace “ka kiyaye”. Barr. Sule yaro yace “nagode yamai sharia. Amma manya manyan hojjoji na anan sune. “Yusuf makarfi,musa lawal,da kuma Kado Ibrahim.wadan da sune aka kama sukayi raping Hanifa yarinyar ga Alh Abba mando bayan sub dirka mata kayan maye yame sharia ina son kotu da ta bayyana mana su anan”. Me karantowa ya tashi yace “Hanifa Abba mando,yusuf makarfi,musa lawal da kuma Kado Ibrahim”.  Kotu nason ganin ku anan.   Tashi hanifa dake zaune tare da iyayenta tayi. Ta shiga wajen da ake tabayar snn suma su Yusuf ana shigo dasu. Brr.sule yaje ya tambayi hanifa sunan ta. Snn yace “kinsan wadan can” yayi maganar yana nuna su yusuf”. Hawayen ya kawo idon hanifa tace “eh nasan su”. Yace “ina nufi kin taba sanin su kafin wnn incident din”. Hanifa ta girgiza kai “aa ban sansu ba”. Yace “ko zaki bamu labarin abinda ya faru”. Ranar na dawo daga makaranta ina tafiya bnsan da mutum a motana ba senaji ya sakamun nife. I was afraid sosai cikin tsawa ya rinka bani direction din da zanbi. Har muka zo wani wajen anan naga sauran biyun daganan se kuma ta fashe da kuka. “Saka bani drugs sukamun dole senasha kosu kashe ni. Duk da haka bnsha ba suka duramun.  Ina gani sukayi raping dina” daga haka ta fashe da kuka sosai. Lauyan yace “maye sharia inaso zanyiwa su yusuf wani tambayoyi... alkhali ya basa dama. Yaje wajen su yusuf yana kallon su. Tambayar su sunan su. Bayab sun fada yace “wane ne ya saku wnn aikin”. Sukace “jalal ali”. Kowa acikin su yace shine. Snn ya kalli alkhali yace “yamai sharia duk wann laifuka jalal yana aikatasu da wasu. Bayayi da ansa amma yana saka wasu domin koda kuwa an tashi sune ze bari a ciki da wadan nan hujjojin nake so kotu ta kawo mana karshen jalal da kuma irin taasar da yake aikatawa ngd”.   Alkali yayi rubutu yace “ko lauyar wanda ake kara tana da magana”. Imaan ta tashi tace “yes my lord inaso zanyi masu tambayoyi”. Alkhali yace “kotu ta bada dama”   Tashi imaan tayi tana kallon hanifa tace “Hanifa Abba mando ko”. Hanifa tace “eh”. “Imaan tace wanene kika gani a cikin motar ki cikinsu” hanifa ta nuna yusuf “shine nagani”. Imaan tace. Babu wani abu da yace maki kawai direction ya rinka baki”. Hanifa tace “eh.”  Imaan tace “kinsan wajen da suka Kaikai” “aa bansani ba”.   Imaan ta juya wajen su yusuf tace “yusuf makarfi sunan ka ko” yace “eh”. Suma sauran duk ta tambayesu sunan su. Suka amsa imaan tace “wane ya baka ka shigo da drugs”. Yace  “jalal Ali Abbas”  tace kudin ya baka koko”. Yace “aa kawai zuwa nayi na amsa” tace “good daka amso drugs din shine yace ka samu diyar Alh mando ko kwai cewa yayi ku samu budurwa”. Yace “cewa yayi ita zamu samu ya bamu adress dinta da komai”. Imaan tace “a waya kukayi magana kokuma ido da ido”. Yace “mun hadu dashi but he was wearing mask dan haka bansan fuskar sa ba”  imaan tace “ko zaka iya tuna inda kuka hadu dashi” “eh a gidan sa ne”. Tace “bani address din gidan”. Babu musu ya bata adress na daya daga cikin gidan jalal. Taje wajen tace “musa lawal ko” yace “eh.”  Kaine wanda yan sada suka kama ko “yace eh.” Tace “kaima kaga jalal din “ya girgiza kai “aa yusuf ne ya kawo mana aikin da kuma huge amount of money nida kado da ake bukata”.   Tace “good”. Kado kam sunan sa kawai ta tambaya” snn ta juyo ta kalli alkhali tace “ina neman kotu da ta daga wnn zaman zuwa nan da sati daya Inshaallah zanyi proving ma kotu cewa jalal bashi da hannu akan abinda ake zarginsa dashi”. Alkhali yace “ko lauyan wanda ke kara yana da magana “. Tashi yayi kafin yace “bayan hujjojin dana bada wanda ina tunanin suna da karfin da zasu iya kama jalal bani da wata magana”. Daga haka ya zauna. Alkhali ya juyo ya kalli jamaa snn yace. “Bayan sauraren bayanai daga bakin lauyoyi kotu ta daga wnn zama zuwa sati me zuwa. Daga haka ya buga gudumar nan. Kowa ya mike. Yayin da kowa ke tabe baki yana kallon family din daddy da kuma imaan.
Bayan sun hadu da aka fito daddy na kallon imaan yace” sannu da kokari Allah yayi maki albarka”. Imaan tayi murmushi bade tace komai ba. Hakanan daddy yaji imaan ta birgesa bawai don tayi wani abun kirki bane ba aa ta saka basira sosai a ciki.   Shi kansa sageer imaan ta birgesa domin kau abinda tayi a zama na farko din yayi domin kau ko daya bata bata fadi hujjar ta ba tade saurari hujjar su. Hakan kuma wayo ne. Jalal kansa a dakin da aka rufe sa yaji komai. Shi kade yasan abinda ya hango. Yayin da duniya kowa fadi yake. Ai bata da wani abu da zatace shiyasa ta bukaci a daga zama. Kuma Allah baze nuna mata hanyar cigaban zalinci ba. Su jummala kam fadi take “yo duk karatun lauyancin abinda zata iya knn shashasha da ita. Inshaallah se karshen su yazo a hada har da ita a kashe.
Sageer musamman yazo ya samu imaan yace “well job hakan da kikayi yayi dede”.  
A satin idan kunga yanda imaan tayi keeping kanta busy se ta baku tausayi aiki take babu dare babu rana. Dan a wnn satin ko jalal ta fisa shiga tashin hankali. Kuma ba ranar banza kullum se taje taga mijin ta da yaran sa. Jalal sede yaja hancin ta yace “wnn wace irin lauya ce”. Sede ta rungumesa tace “lauyar mijin ta”

Ranar da zaayi zama na biyu kotun ta cika fiye da tsammani domin kowa burin sa a yankewa jalal hukunci a gaban idonsa. Yayin da wasu suka kafama tv ido wasu kuma radio wasu kuma waya. Dan duk inda baku tunani ana kallon wnn shariar. Bayan anzauna an fadi shariar da ake alkhali ya bukaci lauyar wanda ake kara ta kawo hujjojin ta. Imaan ta mike tace “yamai sharia ina bukatar kotu data bani dama in kara yiwa su yusuf wasu tambayoyi.  “Kotu ta baki dama”. Imaan ta nufi su yusuf tace “yusuf da karfe nawa kukayi magana da jalal a gidan nasa snn wane date ne”. Yace “7 ga watan july  2023 wajen karfe 4:50 ina tunani”. “Imaan ta rubuta snn tace “ya sunan ka na gsky”. Shiru yayi. Imaan tace “malam yusuf makarfi ka boyewa kotu sunan ka. Sunan ka jabeer ba yusuf ba mene dalilin boyewa kotu sunan ka bayan ba sunan ka yusuf ba” yusuf yace “sunana Yusuf”. Imaan ta kalli alkhali snn tace “my lord ina neman kotu da da bani dama na shigo da malama zuwaira mahaifiya ga jabeer wanda kuka sani da Yusuf”.   “Kotu ta bada dama”. Babu jimawa aka shigo da. Malama zuwaira imaan ta tambaye ta sunan ta tace “zuwaira Abdullahi”. Imaan tace “kece mahaifiyar sa”. Tace “eh”。”aina kuke”。tace “a zaria”. “Yaushe rabonki dashi”。tace “za ayi shekara daya da rabi”. Imaan tace “ a ina yake ko ina yace maki zeje”. Tace “Lagos yace zeje neman kudi daganan kuma be dawo ba. Amma muna waya yana tura mana da kudi”. Imaan ta kalli kotu tace “wnn itace mahaifiyar jabeer wanda yayi karyar sunan sa yusuf snn ga hotunan su nan ita dashi tun lokacin yana yaro”.   Yurah ta tashi ta mika abu a enveloped.   Imaan ta dawo kan yusuf tace “malam Yusuf kuma jabeer. Mene dalilin dayasa ka boye mana sunan ka”. Yace “jalal din ne ya bukaci haka”. Tace “ka tabbata yace “eh”. Imaan tace “kace kun hadu dashi a gidan sa wajen karfe 4:50 ranar 7th july  wanda duka nan mun yarda adress din da ka bamu haka ne”. Yace “eh hakane”. Ta kalli alkhali snn tace “karya ta biyu knn domin kau a ranar jalal yana wani gidan marayu nasa wanda yake taimakawa marayu da kuma marasa karfi a ranar sun samu tattaunawa me tsayi wanda ta kaisu har magrib kuma tun hudu suka fara. Inaso kuma kotu ta bani dama dana gabatar da shedu na malam yahaya da kuma malama Hawwa da malam muntari wadan da sune jalal ya zauna dasu a  ranar”. Kotu ta bada dama   Kiran su akayi duk suka fito. A wnn karon kowa ya kalli fuskar sa sekaga alamun mmki bama yan cikin court din fa duk wani me Kallon shariar ya shiga mmki “Jalal da gidan marayu”. Harta daddy ya kasa gasgata abinda yaji. Abba isa da Alh barau kau. Kallon imaan suke da wani expression sunma kasa dauke ido a kanta.   Bayan sun zo imaan ta tambaye su sunan su snn tace “gidan marayun da kuke aiki zaku iya fada mana na wane”  “jalal Ali Abbas”. Tace “ko zaku iya fada mana abinda ya faru tsakanin ku da jalal 7 ga watan 7 kuda jalal. Malam ya yahaya yace “mun yi zaman meeting dashi jalal din wanda ya dauke mu har bayan magrib”. Ta juya ta kalli alkhali tace “kunji inda jalal yake ranar. Mutum daya baze zama biyu ba jabeer yayi mana karya ta biyu”. Ta kalli jabeer tace “ko zaka iya fada mana dalilin yin karyar taka.”  Jabeer yace “shine ya bukaci hakan bn taba ganinsa ba bamu taba haduwa dashi ba a waya muke magana dashi shine ya bukaci hakan.”  Tace “how sure are you cewa jalal din ne” yace “shine ya fadamun shine kuma ya bukaci dana boye sunana da kuma inda muka hadu shine yayimun kwatancen duk har gidansa yace nace anan muka hadu”. “Tayaya kawai za a kiraka a sakaka aiki a turo maka kudi kai kuma kayi”. “Objection my lord. Yakamata lauyar wanda ake kara ta sani cewa kowa yasan wane jalal babu inda ya taba fito da kansa duniya tasan fuskar sa. Snn ba abun mmki bane ace ya kira ya saka aiki an ayi masa tunda shi jabeer kudi yake nema kamar yanda ya fada shi jalal din shine ya sakasa. Kuma maganar yana zama gidan marayu ko yana da gidan marayu ze iya zama set up ne tunda mu ba fuskar sa muka sani ba kuma mu ba wani hoto muka gani ba daze tabbatar da sun zauna din ba nagode”. Alkhali yace “kinji abinda brr. Suke ya fada ki zaki iya bamu wani sheda”. Imaan tace “yamai sharia ina da sheda da zata bayyana cewa ba jalal bane.   Wani abu imaan ta karba hannun maryam snn tace “anan cikin akwai recoding duk wayar da sukayi.da jabeer” ta mikawa me sharia. Alkhali yasa a kunna duka wayar. Kamar yanda jabeer ya fada hakane shi wancan din shine yaka jabeer yayi duk abinda yayi. Bayan an gamaji. Kowa de se kallon imaan yake yanaso yaji dalilin ta na mika wnn recoding din. Tace “kowa yaji muryar nan yasan bata jalal bace ko daya mata kama kafa da muryar jalal ba. Ina so inyiwa mutane proving kuma ynx. “. Ta juya tana kallon alkhali da manyan idanun ta tace “inaso amun connecting da jalal daga inda yake  kulle ynx da kuma asa police su tsare sa a tabbatar cewa tabbas shine yake magana”.   Babu bata lokaci akayo Connecting da jalal daga inda yake. Ba mmki bane idan nace maku kowa tsuma yake domin jin muryar jalal. To abu ne da babu wanda ya taba sani ga kuma sunan sa yayi fice. A wnn karon idan kalli fuskar daddy granny da kuma sageer zaka suna murmushi. Imaata tace “Assalamu Alaikuum”. Cikin taushi sanyi da kuma natsuwa sukaji muryar Jalal yace “waalaikissalam”。tace “ko zaka iya gaya mana wanene kai”. Yace “sunana Jalal Ali Abbas”.   Muryar jalal seda ta karade ko ina da ake kalloo shariar imaan tace “my lord wnn murya ta jalal da kukaji da kuma wnn muryar ta recoding da kukaji ko sau daya bata kama da muryar jalal.”  “Objection my lord ba abun mmki bane jalal ya saka wani yayi waya da jabeer din tunda shi mutum ne me basira idan ba haka ba meyasa yake aikata laifuka amma be taba nuna kansa ba baku tunanin yayi ne sbd irin wnn ranar”. Alkhali yace “ki kinji abinda lauyan me kara yace tace “naji my lord amma yau zan cirewa mutane duk wani thought”.   Tace “Jalal Ali Abbas kanajin mu” yace “eh”. Tace “cikin laifukan da ake zargin ka dasu ko akwai wanda ka yarda shi”. Camly yace “ko daya”. Tace “kotu tanason ta san wanene kai”.  Shiru jalal yayi kafin ya fara magana “sunana Jalal Ali Abbas. Sunan mamana fareeda Daddy na ya auri wata matar kafin mummy na. Snn mu biyu ne aka haifa a gidan mu which is my twin bro da kowa ya sani saif.”  Nan ya fara basu labari cikin sweet voice dinsa data karade ko ina tunda aka haifesu. Tafiyar da dad dinsu yayi yabar su. Poison mum dinsu da akayi. Wahalar da sukasha da kuma kashe saif da akayi a idon sa fitowar sa prison da kuma atika data fara basa giya. Kamata dayayi tana waya. Tafiyar sa America be boye masu komai da da kuma karatun da yake. Samun aikinsa da da kuma irin kudin da yake samu mutanen sa da suke aiki a manyan companies din nigeria da kuma shears din daya zuba. Dawowar sa nigeria da kuma labarin sa na karya da ake yadawa. “. Ya karasa da fadin. “Bansan komai ba game da laifin da ake aikata bnsan menayi masu ba suke son ganin bayana laifi daya nasan inayi shine drinking habit dina kuma shima tunda nayi aure Alhmdllh na dena”. Duk wanda ke cikin court din kusan seda suka zubarwa jalal da hawaye. Bama yan cikin court din ba a ko ina da ake kallo se an tausayawa rayuwar jalal kowa yasan cewa tabbas yaga rayuwa. Imaan ta goge hawayen ta ta amshi wani CD hannun yusrah ta bada aka mikawa Alkhali tace “wnn shine vedion mummy jalal dake kwance gadon asibiti bata san inda kanta yace ba almost 20yrs knn amma ko sau daya jalal be taba kosawa da mum din tasa ba dukkuwa da halin da yake fuskanta a nigeria”. Kunna vedion akayi. Anan da nan seka mummy likitoci akanta”. Imaan tace “taya mutum me wnn ze tsaya aikata laifuka. Snn ga list din sunayen wadan da ke ma jalal aiki a company din. Duk wanda aka kirana ze sheda yana aiki kuma su masu companies din sun san suna masu aiki. Jalal ba sakare bane kamar yanda makiyansa ke tunani. Jarumin mutum ne ne wanda ya tashi ya nema da guminsa bada kudin daddyn sa ba. A ynx yanada kudi fiye da babansa.   Kowa ka gani ya shiga shock da labarin jalal kona ganin dan kudin babansa yasa yake abinda yaga dama. Daddy kau be taba sanin da wnn labarin ba. Bamashi ba harta su abba isa sun shiga shock dan kallon sakarai shashasha suke masa wanda giya kade ya sani ynx kam duk wani mejin haushin jalal ya koma tausayi. Harta su wadan da sukayi karar tasa. Yayinda suka daura laifin kan atika
Imaan tace “shedata ta gaba kuma shine manga”. A wnn karon atika da huwaila har fitsari seda suka kusa saki. Kallon manga dayayi mugun baki yayi kawai suke an fito dashi ya tsaya dashi wajen me tambaya.  Bayan imaan ta gamayi masa tambayoyi tace “ko zaka fada mana wace rawa ka taka wajen tarwatsa tayuwar jalal”. Nan yace “muna aiki ne tare da Marigayi Alh falalu da kuma Hajiya Atika matar Alh Ali Abbas. Se kawar ta hajiya huwaila Mun taka rawar gank sosai wajen raba Alh Ali da matar sa wanda mukayi asiri yaji ya tsani matar sa da yaransa inda yaji baya son su besides ya ma manta yana da mata da kuma wasu yara. Sann munyi kokarin kashe yaran amma bamu samu dama ba aka riga mu”. Imaan tace “shedata tagaba sune hajiya atika da hajiya huwaila.”  “Kotu tana son ganin hakiya atika da hajiya huwaila”. Jiki na rawa suka fito.bayan imaan ta tambaye su sunan su tace “kun yarda da abinda manga yace “ suka ce “eh”. Hajiya atika tace “amma wlh bani bace ke shiga rayuwar jalal kuma bamu bane muka kashe saif giya kade nasan ina basa”. Cike da kwarewa imaan tace “mene dalilin ki nayin hakan”. Cikin kuka tace “wlh sharrin shedan ne kuma da kuma abin duniya sbd nice matar sa ta farko nice yakamata na haihu dashi ba wani ba”. Murmushi imaan tayi kafin tace “shedata tagaba kuma shine tasiu”.
Karasawa imaan tayi wajen tasiu snn tace “kaine kaje kashe su jalal baka samu dama ba wanda su hajiya atika suka saka. Yace “nine” tace “ko zaka iya mana bayani akan wanda ya kashe saif”. Nan tasiu ya bata duk labarin daya bama jala. Wani cardboard paper ta amsa hannun maryam ta nuna masa wani zane tace “shine wnn”.    Da sauri yace “eh shine”. Imaan ta nuna mutane snn ta nunawa alkhali tace “wnn shine wanda yaje har gida ya kashe saif ba jalal ba. Jalal yasan fuskar sa shine kuma ya zana sa a matsayin sa na architec snn tasiu ma ta gansa snn baki da baki ya gaya masa shine ya kashe saif kuma shine yaje har gidan Dr umar yayi attempting kashe sa. Ynx dr umar yana asibit bamu sede idan ya farfado kuma yana hannun jamiai ne. Ta mika hoton aka bama alkhali snn tace “ ina neman koto da tasa a binciko mana wnn bawon Allah snn da kara mana sati daya domin gano wanda ke shuka tsiya da sunan jalal na gode. Daga haka ta koma ta zauna ba karamin birge mutane imaan tayi just look at how young she’s but very smart and talented”. Abba isa har imaan ta zauna be dena kallon ta ba yama rasa wane tunani zeyi but cewa dr Umar ba raye yafi komai daga masa hankali. Alkhali ya gama rubuce rubuce snn yace ”ko lauyan wanda ke kara yanada magana”. Mikawa yayi kafin yace “babu my lord”

Urs
✨✨✨
Annafie🥰💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
              ANNAFIE💖…✍️
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
NOT EDITED
💫💫💖Jalal Alii((44)💖💫💫
Alkhali yace “ bayan sauraren manya manyan hujjoji daga bakin lauyan wanda ake kara kotu ta bada damar a nemomata duk inda wanda ke jikin zanen nan yake. Wanted ana nemansa ciki da wajen kasar. Snn kotu ta bada izinin da a kama hajiya atika ,hajiya huwaila,manga,tasiu snn tacigaba da tsare su jabeer. Kotu zata dage wnn zama zuwa sati me Zuwa lauyar wanda ake kara tayi kokarin kawomana wanda yake shiga rayuwar jalal domin bata masa suna. Idan Allah ya kaimu sati me zuwa wanda muke tunanin shine zama na karshe da zamuyi.” Daga haka ya buka guduma kowa ya mike courrrrrt”.     Da sauri granny tazo ta rungume imaan “masha Allah gsky kedin ta musamman ce a rayuwar jalal kinyi abinda rabin mata bazasu iya ba ke jarumar macece Allah ya biyaki da aljanna ya raya maki zuriar ki”. Murmushi kawai imaan keyi. Adda na washe baki tace “ai imaan bata barin bashi tun tana karama yarinyar ya ce ne basira shiyasa makiyan ta suka kasa cin galaba akanta yo bata bar kowa ba harni ba dagamun take ba. Bare kuma ynx data girma tayi karatu ai se inda karfin ta ya kare akan mijin ta” Daddy na murmushin daya kasa bacewa fuskar sa yace “Tabbas kedin madubi ce shigowarki rayuwar mu alkhairi ne. Keda sageer babu abinda zance maku sede na maku fatan alkhairi kun taka rawar gani a rayuwar dana wanda koni bnyi ba Allah ne ze saka maku “. Murmushi imaan tayi tana kallon daddy tace “ngd “. Abba isa ma yazo yana kallon ta yace “well job my daughter kinyi kokari”. Murmushi imaan tayi tana kallon sa da kyau tace “tnx Abba”. Irin kallon da tayi masa seda yaji zuciyar sa ta wani tsinke”. “Alh dan Allah karka bari su tafi dani wlh sharrib shedan ne nayi alkhawarin zan rike jalal kamar dana”. Dauke kai daddy yayi yana jin babu dadi. Shin me yayi masu ne shida dansa da matar sa. Fuskar marigayi Alh Falalu kawai ke fado masa. Kana tare da makiyan ka amma baka sani ba ...
Imaan na fitowa yan jarida sukayi mata ca. Duk yanda taso kaucewa kin barin ta sukayi. Wani yace “brr.zainab kome kasancewar ki yarinya karama. Kuma wnn ce shariar ki ta farko bakiji tsoran shiga sharia me hadari irin wnn ba. Wacce take cike da sarkakiya. Dan inba ynx da kika fayyacewa duniya komai ba gsky babu ta inda za ace jalal mutumin kirki ne”. With full courage tace “tsoron me. Ai babu tsoro akan abinda ka tashi kanason yi tun kana yaro. Inde kanason cikar burin ka to dole sena jajirce ka cire duk wani tsoro”.   Wani yace “a wnn sharia har ynx ba a gama gano gsky ba kina ganin a zaman na karshe gsky zata bayyana koko”.   Imaan tace “da ikon Allah koda zan rasa raina sena gano makiyan jalal domin tabbatarwa duniya cewa shidin mutumin kirki ne “ wani yace “tabbas kuma in Allah ya yarda ko su wane se asirin su ya tonu Allah yayi maki Albarka gsky kin cika mace me hazaka wnn sharia bugu daya kin girgiza makiya muna bayan ki”. Murmushi imaan kawai keyi.   Nan fa aka fara yabon jalal. Kowa fadi yake yake suna masa kallon dole muryar wani bnza aka sa amatsayin tasa bayan muryar sa is far different from wacce aka nuna. Wasu mata suka zo gaban imaan “gsky kin burgemu kedin Abin koyi ce. Allah sarki jalal. Labarin sa ya tabani kuma duk da wnn basu barsa ba. Sun dauka sakarai ne ashe yafi su wayo. Wow he’s a billionaire kunji voice dinsa wani irin taushi da dadi. Just can’t wait nagansa nasan he most be handsome brr Zainab dan Allah we need to see this guy”. Kallon su kawai imaan tayi voice dinsa kade sunji sun rikice inaga sun gansa. Murmushi ta kakalo kafin ta kalle su da kyau tace “shi jalal din da kuke fada. Lauyar sa ai itace matar sa”. Daga haka imaan ta barsu wajen hangame da baki. Ta shige rantsetsiyar motar ta wacce jalal ya bata. Yan jarida kam da police se binta suke.   Tuni duk masu hararan su daddy suka koma dagawa motocin sa hannu.
Ranar duk gidan tvn da zaka gani zancen jalal ake da kuma lauyarsa wato imaan. Dimin ko ta birge kowa hakama jalal fadi ake ynx duk inda makiyansa suke hankalin su tashe yake.  Baku tambaye ni su jummala ba. Karshe de yan gidan koro ta sukayi inda taje kallo. Zuciyar ta kamar zata mutu sbd bakin ciki. Yayin da yan garin fadi suke ai imaan er garin su ce. Suma ynx suna da kamar imaan. Dan wasu cewa sukayi ranar da za ayi sharia se sunje sun bama idon su abinci. Bama yan kauyen ba daya sunce next sharia dasu za ayi ta domin ganin bayan makiyan jalal. Yanda suka ga imaan ta firgita makiyansa a duka daya sunsan bazata basu kunya ba a next sharia dan sun jinjina mata. A shekarunta baka taba cewa zata iya.  Nan da nan aka buga hotunan wnn aka rubuta WANTED.  Kafin kace mene hotunan sun bide ko Ina. Wasu ma fadi baa tambaya ba sunce suma zasu bada tasu gudunmuwar domin kawo wasa”.    
Imaan wanka kawai tayi ta shirya yaran ta tare da nanny suka fita zuwa part din granny inda daga can zasu wuce wajen Jalal. Ko ka gani cikin farin ciki wasu kam yake suke. Daddy just can’t wait yaga jalal dinsa.
Wani irn rungume jalal daddy yayi yace “im very proud of you my son takun ka ya birgeni kowa na maka wani kallo ashe kaidin jarumi ne. So tell me son. Billions din nan naka nawa zaka bani”. Wani murmushi jalal yayi yana kallon daddy da fuskar sa take cike da tsantsar farin ciki”. Jalal yace “I can give you all my daddy”.  Daddy ya kara rungume jalal yace “I’m very very happy today gsky matar ka abin koyi ce amfanin ilimi ayi aiki dashi”.   Jalal ya dago ya kalli imaan tayi kasa da kanta tana murmushi. Granny tace “nifa na fara kishi wnn wane irin kallo kake mata. Nice fa uwar gida”. Jalal na hararan granny yace “kinason firgitamun mata ko ni ita kade ce ita din de da kika gani ita kade ce mata na”. Adda tace “wlh yan abuja baki da kunya”. Duk dariya sukayi sumy tace “Adda dan baki nan santa ta tafi ta barsa cewa yayi seya kona kowa na gidan”. Wani dariya kowa ya fashe da ita ana kallon jalal daddy yaja cin dinsa yace “ni kaina nunawa yayi be sanni ba. Maganganu kala kala imaan kin masa wani abu ko”. Dariya suka. Jalal ya boye fuskar sa a jikin daddy granny tace “kunga kuzo muje mu barsa da matar sa nasan ynx kawaici yake mana”. Duk dariya sukayi kafin kowa ya nufi hanyar fita.imaan tazo ta kwantar dasu amaan akan gadon jalal taki yarda ta kallesa. Jalal yace “yau I will hug my babee first before them”. Juya masa baya imaan tayi tana tura baki. A hankali jalal ya taso tare da rungumeta ta baya snn yace “babee me kuma nayi”. Kamar imaan zatayi kuka tace “ka wani je ka kashe murya kowa yanajimun muryar ka me dadi wasu mata har zuwa waje na sukayi wai they love you could you imagine”.  Jalal ya sakalo da kansa ta wuyan ta yace “then se kikace masu mene”. Ta tura baki “na fada masu matar tasa itace lauyar sa ai”. Jalal ya yamutsa fuska “babee kina son kashemun kasuwa wlh. Baseki masu hanya ba ynx nan kowa ya ganki a matsayin matana ai seki firgitasu saboda kinfi ko wace mace ta ko wace hanya. Babee ki barmun haka ki barni nayi kasuwa pls”. Juyowa imaan tayi kamar zatayi kuka ta fara dukansa a kirji. Jalal ya janyota suka fada saman gado ya rungume ta a jikinsa sosai yace “wata isa ta hada kanta da imaan matar jalal ai kedin kinfi ko idan nace kowa ina nufin kowa a zuciyar jalal ke kade ce. Kece da farko kuma ta karshe. Na rufe kofa dagake.ina maki wani balain son dan ban taba yiwa wani mahaluki ba wlh imaan zan iya rasa komai na rayu amma bndake kedin kyauta ce ta mussaman I love i love you and I love you babee.”  Hade bakin su imaan tayi. Batare da tace komai ba jalal ba. Kamar jalal kau jira yake ya karbe. Sunyi kissing juna kusan 10mins daka gani sunyi missing junan su. Imaan zata zare bakin ta jalal yace “no babee pls”. Muryar sa a shage ya kara rungume ta. Then wasan ya canza salo. Duk da kaya jikin ta seda jalal yayi romancing dinta. Ganin bashi da niyar bari yasa imaan fadin “bafa a gida muke ba”. Yayi mata peck a goshi snn yace “babee wai koma kizo ki dan kwanan mun”. Imaan ta ware idanu tace “tayaya bazasu bari ba ai”. Jalal ya matsa da fuskar sa dab da tata snn yace “ke ba lauya ta bace. Tambayoyi kawai zaki mun cikin dare”. Dariya imaan tayi kafin tace “bazasu taba bari ba”. Jalal yayi wani murmushi snn yace “zaki gane kurinki idan na dawo i will eat you all the day and night just get ready.”  Imaam tace “am ready for you”. Jalal nadan shafa lips din ta yace “yarinya sekin ce ummmm babee dadiii babeee I love you.babee cigaba. Awwww babeeee zafi”. Shigewa jikinsa imaan tayi sosai    Tace “babee you’re bad”. Yace “not as bad as you ke kika lalatani ai”.  Tashi imaan tayi tana gyara kayan ta. Jalal ya tayata. Imaan ta mike camly jalal yace “babee”.   Juyowa tayi yace “thank you”.   Hararansa tayi tace “shiru”. Tashi yayi tare da kamo waist dinta ya hadata da jikinsa yana kallon ta da kyau yace “so you’re going”. “Tace “zan dawo”. Yakai hannunsa gefen fuskar ta yana shafawa snn wace “kwanan zaki zo”. Ta ware idanu. Ya marairaice “don’t you feel how eracted I am I just want to go in”. Imaan ta langwabar da kai tanajin yanda jalal ke ga bata naughty talks. Kissing dinsa tayi kafin tace “I promise you ranar da ka dawo I will make you satisfied”. Yayi dariya yace “ai ko bakiyi alkhawari ba yarinya”.
  Zame jikinta imaan tayi ta fita ya biyota da rike da twins dinsa. Yana kissing dinsu yace “soyayyar mamarku ta hanani daukar ku yau”. Sageer dashi kade ne ya jisa ya masa wani kallo yana murmushi.
Da su imaan zasu tafi jalal ji yayi kamar kar su tafi. Juyowa yayi ya rungume sageer bayan sun tafi. Sageer ya ture sa “se ynx ka ganni”. Jalal yace “you’re the best of all ko mene ya faru dani na farin ciki sanadib ka ne Allah ya Biyaka dan uwana”. Murmushi sageer yayi sun dade suna tattaunawa seda sageer ze tafi jalal yace “bro.pls ma kularmun da imaan nasan kanayi amma inaso ka bata tsaro na musamman kai kanka kasan ynx rayuwar ta tafi ta kowa hadari a ynx haka. Dan Allah sageer ka kula. Idan wani abu ya same ta bazan iya jurewa ba”. Sageer na dariya yace “wa ba dole ba. Ni ai sheda ne”. Dariya jalal yayi yace “thanks bro”. Sosai sageer yaji dadi domin kau kallo daya zakayiwa jalal kasan yana cikin farin ciki

“Kaga abinda muka raina yana shirin hanamu bacci look at how smart dis gal is. Gsky we are mistaken da mun sani tun farko muka gama da ita”. Alh isa yace “Alh barau bazaka gane tashin hankalin da nake ciki ba. Kaga kallon da yarinyar nan tamun yau kuwa. Definitely tasan wani abu game dani bakaji tace dr. Umar na raye ba tayaya wnn tunani ya bace mun gsky sageer yayi playing intelligence dina”. Alh barau yace “tun yaushe nake fada maka illar barin wnn yaron” kamar Alh isa zeyi kuka yace “wnn yaron yanada basira yanda baka tunani wani yunkuri da zamuyi a kansa shine ze sa mu kama kanmu shiyasa nace mu rabu dashi gashi wanda mukewa kallon shashashan. Shine ya maidamu shashashan”. Alh barau yace “ynx mene abunyi kasan a ko wane lokaci zasu iya kama kwage ko. Ai bama a kowane lokaci ba kwage kamar an kamasa ne. Kuma yana shiga hannu wlh mun bani dan ana kama Habib seya tona mu”. Alh isa ya core hular sa yana fifita “kasan duk inda habib yake ynx gudun tsira yake. Kuma ana kamashi dole muma a kama mu domin baze tsaya wata wata ba ze tona mu. Dan haka ynx duk inda habib yake kafin su gansa gara mu mugansa mu kashe sa. Barin sa duniyar nan shine kawai rufim asirin mu wlh Ynx gudun tsira ake bana wani abu ba”. Alh barau yace “mun shiga uku wnn wace irin yarinya ce”. Jifa yan tambayoyin da tayiwa su jabeer a zaman farko ashe karyar su take son fara nunawa. Gsky”. Alh isa kam kasa magana yayi abin duniya duk ya ishesa

A kauyen su imaan kau har zuwa gidan umma ake wai ta bada numbern imaan. Aikam tasha kira kamar ba gobe  dayawa sunce mata zasu zo shariar. Ya karshe. Imaan ta aika ta mota aka taho da baba dasu jummala umma da mijin ta kuluwa da yaya abubakar har su inno. Babban gida tasiya masu. Kowane da part dinsa kuma tsakanin wani part akwai tazara zuwa wani babu ruwan wani da wani.  Gidan imaan aka sauke su. Imaan ta fito ta rungume kuluwa. Tana murnar ganin su ta rungume umma. Snn ta gaisar da baba. Ko kallon su jummala batayi ba ta tafi ta rungumw matar yaya Awwal. Jummala kam da yaranta ze baza idanu suke suna kallon gidan imaan din kamar wata Aljannar duniya. Ga police ko ina zagaye da ita. Tun anan jikinsu yayi sanyi domin kau sun riga sunsan imaan tayi masu nisa nesa ma ba kusa ba. Tuni imaan tasa aka gabatar masu da abinci. Kuluwa tace “ynx imaan anan kike rayuwa. Gsky Allah ya dagaku sedw mu gode masa. Imaan tayu Murmushi umma tace “har ynx banga jikoki na ba fa”. Murmushi imaan tayi tasa nanny ta kawo yaran umma ta dauke su tace masha Allah gasu kau kamar ubansu. Shiru su jummala sukayi jikin su yayi sanyi domin kay sun riga sunsan imaan ta wuce da capacity din tasu. Ganin yanda taki sakar masu fuska yasa ko yaran ma basuyi gigin dauka ba. Har yaya Abbakar bata sakar masa fuska ba.   Yaya auwal kam se labari imaan din take basa. Baba ya kalli jikokinsa yace “masha Allah”.   Sun dade a gidan kafin su tashi su tafi gidan da tasiya masu. Imaan da kanta da dauki babanta a motar sa. Se yaran tq suka tafi seda ta fara zuwa dasu gidan su jalal. Anan duk suka kara gane lallai dukiyar Alh ali ba karama bace. Hannu bibiyu aka tare su dan daddy rungume baba yayi yana zuba masa godiya yace “hajjin bana tare zamuje dole mu gode wa Allah daya bamu yarinya kamar imaan. Ita din kyauta ce ga ahalina”. Sosai baba yaji dadi adda se washe baki take. Da taxo wajen su jummala kau tayi kicin kicin tace “inda nice ba sena saka an daure ku ba kunci saa imaan din tana da zuciyar musulmai. Ni bnga yan biyun jalal ba fa a kawomin tattaba kunne na naji dumin su”. Duk wani abu na more rayuwa sun gani a gidan da imaan ta basu kuma sun yaba sunyi murna abinda ko a mafarki basu taba tsammani ba.

Ana jibi zaa koma sharia aka samu damar kamo kwage wani ne ya gansa a lagos aikam tuni yayi waya yab sanda sukayi ram dashi. A ranar aka taho dashi Abuja.   Sageer ne ya kira imaan ya sanar mata. Jikin imaan har rawa yake sbd farin ciki domin kau tasan Allah ne kwai ke taimakon ta bawai iyawar ta ba shiyasa bazata taba wasa da addua ba.  
Direct aka bata damar shiga wajen sa da wasu police a tare da ita. Imaan ta kallonsa cike da tsana idan ta tuna cewa shine wanda ya kashe seif kuma wanda shine silar daya abbanta yake kwance. Tana masa wani kallon tace “ sunanka na gsky”. Kwage da yayi ligi ligi sbd dukan dayasha yace “musa kwage”. Tace “kaine ka kashe saif?”  Yace “eh nine” tace “kaine kasakawa hajiya fareeda poison” yace “aa bani bane Saif kade na kashe se dr. Umar umar dake kaduna”. Imaan tace “good mene suka maka”. Yace “duka wnn umarni ne daga Habib shi nakewa aiki kuma shike Biyana”. Imaan tayi rubutu kafin ta dago ta kallesa da kyau tace “waye habib.”  Yace “ shine wanda ke aikata duk wasu laifuka a memakon jalal duk wani abu da kikaga ance jalal yayi to Habib ne ya sakasa. Hadda Twitter account din da ake amfani dashi a matsayin Jalal habib ne. Mugun masanin computer ne”.  Imaan ta sauke ajiyar zuciya tana ganin lallai da sauran ta ina zata samu habib din nan ta ina zata fara bincikar sa lokaci yana son kure mata fa”. Tace “kasan a ina yake”. Yace “nan cikin abuja yake amma zeyi wahala ki iya kamasa “. Shiru imaan tayi. Can kuma ta kalli kwage tace “zaka bada bayani a kotu”. Daga haka ta fita. Tayiwa sageer bayanin duk yanda sukayi ya kara da fadin bn san ta ina zan fara ba ni gashi ba wata masanniyar computer ba. Jiddah dake gefen sageer tace “ bani sunan duk wasu account da ake amfani dasu da sunan jalal din”. Kallon ta imaan tayi. Muhammad yace “ta samu lambar yabo ta musamman inde akan wnn fannin ne dan haka kwararriya ce. Babu bata lokaci imaan ta bata. Jiddah ta kwashe komai. Gida ta koma ta shiga dakin computar ta ta dukufa aiki. Harta imaan ranar a gidan su jiddah ta wuni har dare amma basuyi kokarin kamosa ba. Jiddah tace mutum ne me basira. Amma nasan ta yanda zan bullo masa.  
Wasa wasa se gashi har ranar da za’a shiga shariar ba a gano wane habib ba. Sekusan dab da da zaa shiga snn Allah ya bama jiddah damar shiga shafin nasa gaba daya. Shima habib din ya fahimci ana bibiyar sa ne ya shiga domin goge duk wani details nashi. Wanda anan ne jiddah ta rigasa. Tace kuzo da sauri “imaan da sageer da suke ta kaiwa da kawowa sukazo. Lokaci daya jiddah sageer ya kwashe komai nasa snn jiddah tace “a ynx haka yana cikin garin nan kunga adress din a ko wane lokaci ze iya fita ya gudu batare daya tafi da wayar sa ba da zata mana indicating duk inda yake dan haka wadan nan hanyoyin sune wanda ze bi guda uku cikin minti sha biyar ze iya tsere mana dan haka dole a samu mutum uku wadan da ba jamiai ba su kama mana shi domin kau zuwan wani jamii ze iya basa damar buya dan haka a gaggauta kafin ya gudu.   Imaan data rikice tace “ynx ya zamuyi”. Wani tunani ne ya fado mata tuni ta dauki wayar ta tayi kiran Faruk. Yana dauka tayi masa bayani bayan sun gama tace then muna bukatar mutum daya. Kallon yayanta jiddah tayi tace “yaya muhammad ko zaka taimaka mana”. Sageer yace sure. Tuni imaan ta basa hanyar daze bi sabanin wacce taba faruk da muneer.  
Sageer yace “in the next 30mins zaa shiga sharia than haka lets go and get dress”.   Imaan ta gyada kai tanajjn zuciyar ta na tsinkewa burin ta be wuce taga a kawo habib ba.
Har tym din da zasu shiga sharia babu kiran ko daya daga cikin su faruq”. Haka de imaan ta daure ta shiga. Wnn karon court din tafi ko wane lokaci cika. Harta yan kauyen su imaan ba a barsu a baya ba ga kuma su jummala   Wnn karon ma kama ko wane lokaci live ake nunasa a ko ina daga duk inda kk zaka iya kallo
Bayan Alkhali ya shigo kowa ya mike domin girmamasa.   Bayan an karanto akan shariar da ake alkhali yace “laiyar wanda ake kara ke muke saurare”. Imaan ta tashi tana kara gyara rigar ta da tayi mata mugun kyau tace “my lord kamar yanda na fada cewa a wnn satin zan kawo shedata to Alhmdllh ynx kwage yana hannun mu. Dan haka inason ganin musa kwage anan” me karantowa ya tashi yace “a shigo da musa kwage”.   Babu jimawa aka shigo da musa kwage. Daddy ya rinka Kallon sa yanajin wata tsanar sa. Wnn idan ya tuna shine ya kashe masa saif yaji kamar ya tashi yaje shima ya caccaka masa wukar. Wani irin yake ji idan ya tuna irin Azabar da saif yasha kafin yabar duniya.  Imaan ta matsa kusa dashi tana kallonsa cike da tsana tace “ki zakayi mana bayanin wane kai da kuma hadin ka da jalal. Nan ya fara bayani kamar yanda yayi mata a baya. Da kuma wanda ya saka sa.  Bayan ya gama imaan tace “to yamai sharia wnn shine mashin saif ba jalal ba kuma kamar yanda yace  wnm habib din shine le aikata duk wasu laifuka a maikakon jalal. Zan so kotu tayi hakuri ta bamu hutu kona 2hrs ne domin zuwa da habib wanda yana hanya an taho dashi kuma Inshaallah shine shedata ta karshe shine ze fada mana dalilinsa na aikata duk wasu laifuka a matsayin jalal ali Abbas”. Alkhali yace “kotu ta dage wnn zama zuwa nan da awa biyu. Snn tana bukatar ganin JALAL ALI ABBAS a zama na gaba”.   Daga haka ya buga guduma.
Suna fitowa imaan ta kira su faruk tace “kun same shi” “eh yana hannun mu yanxu haka”. Wani murmushi imaan tayi “tace “masha Allah ku dake sa snn kuyi masa tambayoyi karkuzo dashi nan se nan da awa daya da rabi.” 
Yanajin haka ya juya da sauri ya dauki wayar sa. “Ku hada su duka ukun ynx base anjima ba”. Daga haka ya kashe wayar. Jikinsa na wani irin tsuma. 
Imaan zuwa tayi wajen yan kauyen su da tayi mamakin zuwan su suna ta gaisawa. Wayar ta ne yayi kara tagawa tayi. Tun kafin tayi magana taji ance “Brr. Zainab. Da fatan ba mijin ki bane kike karewa kade ba hope kinsan inda yaranki suke. “. Ditt taji an kashe wayar. Da sauri imaan ta karasa wajen su daddy da granny tace “Adda ina nanny take da yara.   Suna cikin tana wani room anan tana basu madara”. Sumy ta fada. Imaan tace muje room din. Ganin yanda ta tashi hankalin ta yasa duk suka mike sukabi bayan su. Harda Su Alh isa kuwa. Koda sukaje dakin babu kowa. Gade kayan yara nan da feeder dinsu.  Wani irin fashewa da kuka imaan tayi “nashiga uku sun dauke mun yara na bani”. Wani irin mutuwar tsaye kowa yayi a wajen mahmud yace “ki mana bayani”. Kafin wani yayi magana wayar imaan tayi kara. Dauka tayi da sauri. “ inde har kinason yaranki to ku gaggauta kawo habib hannun mu a kashe ko a raye inba haka ba keda yaranki har abada “.   Wani irn fashewa da kuka imaan tayi ta rungume adda tana kuka “wayyo Adda ku taimake ni yarana karsu mutu na bani”. Adda ma fashewa tayi da kuka “wnn wane irin balai ne “ jikin dad har rawa yake ya dauki waya domin kiran commissioners of police.
Tuni aka baza police to ina cikin garin. Amma har ya rage “saura minti sha biyar babu yara babu labarin su”.   Ga sageer shima basu san inda yake ba.   Imaan gabadaya ta fita hayyacin ta banda kuka babu abinda take idan ka ganta kuma seka tausaya mata ita jalal ma takeji tasan idan ya sani ze fita mugun shiga damuwa. A haka har lokacin komawa yayi.  
Tass imaan ta goge fuskarta cikin dakiya ta shigo. Alh barau da Alh isa kallon ta kawai suke da mugun mamaki.  
Suka mike bayan alkhali ya shigo. Bayan ya zauna yace “muna bukatar ganin Jalal Ali Abbas”.   A wnn karon idan kaga yanda kowa ya natsu yana son ganin wane jalal se kayi mmki. To kowa burinsa ya gansa yaga wane jalal din nan. Duk wanda yake kallon shariar daga ko ina kowa ya natsu. Yanda wajen yayi tsir yasa kowa ke iya jiyo takun takalmin sa. Wanda yake bugawa dede da zuciyar mutane musammam makiyansa. Then tuni kamshinsa ya cike ko ina ya danne na kowa. Kafin ainahin fuskar jalal da babu wanda yasanta ta bayyana. He looks more handsome than ever duk wanda ya dora idonsa akan jalal seya yaba. Nan wasu suka rinka wasu wasi. Is this the jalal. The bad boy. Ko tari bakaji. Fuskar nan tasa a mugun daure. Idonsa akan kwage. Lallai baze taba mantawa da wnn fuskar ba. Kwage ya rinka kallon jalal yaron da tun yana yaro ya masa tabon da baze taba mantawa ba. Alkhali yace “ko zaka iya fada mana wanene kai”. Jalal yace “JALAL ALI ABBAS wanda akafi sani da DEEN”. Babu wanda wnn sunan be daki kunnensa ba ba yan cikin court din ba ba kuma masu kallo a tv ba”. Wasu baki a hangame kawai suke kallon sa. Kowa yaga fuskar sa yaga jarumi. Alkhali yace “lauyar jalal mu sauraren ki”. Tashi imaan tayi ba tare da ta yarda ta kalli jalal ba dan zata ita fashewa da kuka. Shikam Kallo daya yayi mata ya fahimci akwai damuwa a tare da ita. Imaan tace “habin is her wanda shine shedata ta karshe”. Me karantowa yace “kotu nason ganin Habib”.
Tunda aka shigo da habib zuciyar su abba isa ke wani tsalle da daddy ze kallesa a lokacin zega yana suke zufa to dande shima hankalinsa nakan jikokinsa da aka sace ne.
Imaan ta karasa wajen habib bayan ta tambaye sa sunan sa  ya fada ta dauko recording wayar nan da jabeer ta kunna tace “ko zaka gaya mana muryar wane wnn”. Yace “murya tace”. Imaan tace “Twitter account din da ake amfani dasu da sunan jalal ko zaka gaya mana na wane”. Yace “nawa ne”. “Kaine ke kirkirar laifi kuma ka amsa”. Yace “nine”. Tace “duk da sunan jalal Ali Abbas” yace “eh”. Imaan ta amshi wasu takardu hannun maryam tace “wadan nan sune shedar cewa habib shine wanda yake aikata duk wani laifi da sunan jalal”. Ta mika aka bama alkhali snn ta juyo tana kallon habib tace “ ko zaka fada mana dalilinka nayi hakan”. Yace “bani da wani dalili aiki nake ana biyana. Duk abinda nake sakani ake”. Imaan tayi wani murmushi tace “suwa kakewa aiki”. Ya kalli audiences kafin ya kalli imaam yace “Alh isa Abbas da kuma Alh barau”. Wani irin mikewa Daddy yayi kafin yace “whaaaaatttt”. Bama shi kade ba harsu granny seda suka mike. Jalal kam suman tsaye yayi a lokacin. Sumy da mahmud girgiza kai kawai suke. “Wnn karyane jalal dana ne bazan taba cuta masa ba yaya ka gaya masu”. Daddy yace “Hakane kani na ne Alh barau kuma babba aminina ne “. Alkhali ya buga guduma kotu tana son ganin Alh barau da kuma Alh isa”. A wnn karon jikin kowa tsuma yake. Jalal kallon su kawai yake yana son hana zuciyat sa yarda da abinda kunnesa yaji. Imaan ta karasa gaban su. Tana so ta tambaye su amma ta kasa jurewa. Fashewa da kuka tayi tace “ina yara na where are my kids.”  Muryar Alh isa na rawa yace “wane yara kuma imaan kina hauka ne nifa uncle din jalal ne”. Cikin kuka sosai I maan tace “shout off and bring back my kids”. Da wani tashi hankali jalal yace “wife. Which kid are you talking about”. Cikin kuka tace “yaran mu jalal he kidnapp our two kids with their nanny wai inde na nuna habib se sun kashe su”. A firgice Jalal yace “whaaat my little kids nooo”. Ganin yanda wajen ya hargitse yasa alkhali buga guduma. Hakan yasa kowa yayi shiru. Ko minti daya ba ayi ma aka fara jin kukan yara. Da sauri imaan ta juya tana kallon jiddah da kuma faruk rike da yaranta. Se wasu hannun police sun kamosu. Imaan ta ruga wajen su jidda  anshi amaan dane wani irin kuka.   Alkhali yace “brr. Zainab ki dawo wajen ki”. Imaan na kuka nace my lord tge way my kids a crying is not nrml we newd to take them to the hospital”. Alkhali yace “calm down dawo ki zauna a kaisu asibiti ynx”.   Yusrah tazo ta kamo imaan ta maidota wajen ta yayin da adda da wasu maikatan kotun aka tafi dasu nanny da yaran asibiti bayan an hadasu da police.
Alkhali ya kalli wadan da suka sace yaran yace “mene dalilin sacen yaran da ku kayi” cikin tsoro sosai wani yace “wlh millions biyar biyar sukace zasu bamu amma bamu taba ba”. “Suwane”. Da sauri suka nuna su Alh isa sune ya me sharia”.   Daddy ya runtse idanu zuciyar sa na wani irin bugawa. Jalal kallon su kawai yake dan he’s total out of words. Cike da tashin hakali Alh isa yace “wallahi sharri suke mun wnn set up ne nifa jalal kamar da yake a gurina”.   *”karya kake munafuki algungumi mugun maciji azzalumi me halin dabbobi Inshaallah yau Allah ya kawo karshen duk wani zalincin ku”. Duk juyawa sukayi suna kallon wanda ke maganar. Imanna tayi saurin fadin “Abbana”. Sageer ne tsaye gefen sa wata mata me mugun kama dashi. Se Abban imaan tsaye yare da mommy dake tura wata farar mata dake zaune saman keken marasa lafiya. Matar fara sosai skin dinta wata irin murjajjiya yanda kasan bata taba sanin mene rana ba a duniya. Bakar Abayar dake jikinta ta kara haskata ta fito mata da ainahin kyanta idanun ta wasu irin farare. Bakin daddy na rawa yace “fareeeda”
Jalal kam ko ina na jikinsa rawa yake he just can’t believe what he’s seeying. Maganar bakinsa ma ta makale. Jikinsa yayi wani irin rauni idanunsa sun cika da hawaye. Da kyar ya iya jawo maganar dake bakinsa yace “Muuuuuuummmm”

Urs
✨✨✨
Annafie💫💫💫💖JALAL ALII💖💫💫💫
(You’re God’s gift to my sadheart💔)

Wretten by
    
              ANNAFIE💖…✍️
        (Smll but mighty😉)

Writer of
LOVE CYCLE ❤️
SABODA DUNIYA🌃
JALAL ALI🤩
 
Bismillahir rahmanir raheem
Am srry wlh bana samun damar editing kwanan nan sbd bnd lpy typing din ma da kyar nakeyi
💫💫💖Jalal Alii((45)💖💫💫
“Muuuuuuummm”  muryar jalal ta daki kunnen mummy mutum biyu ta sani da wnn voice din shima a muryar yara tasani her beautiful kids saif and jalal tunda ta farfado kusan 2weeks knn abinda take tambayar kanwar tata knn. Ina yaranta. Sede mamyy tace ta bari su Koma nigeria. Ta fada mata 20yrs knn tana kwance. Now tasan her little kids sun girma 30yrs ai ba wasa ba. And voice din jalal da taji ynx ya tabbatar mata da yaranta sun girma tabbas. A hankali ta juya fararen idanun ta zuwa inda ta jiyo voice din. Kurawa jalal da jikinsa ke wani irin rawa ga hawaye sun taru a idonsa ido tayi tana so ta gane wanene daga cikin yaran nata. Jalal or saif. Imaan ta kurawa matar da jalal ya kira da mum idanu kafin takalli jalal da har ynx kallon mum din tasa yake da alama ya kasa gasgata abinda idanun sa ke nuna masa   Bama imaan kade ba kowa sede ya kalli jalal kuma ya kalli mum dinsa wnn ya nuna masu cewa mum din jalal dake asibiti ce ta samu lpy. Alh isa kam a wnn karon kafar sa kasa daukar sa tayi domin ko durkushewa yayi cikin dan abinda suke dan ya riga yasan tasa tazo karshe kuma. Alh barau kau kallon su mum da Abba yake without blinking dan gaba daya kamar ya fita hayyacinsa ma.
Jalal ya fito daga inda yake ya nufi mum din tasa data kura masa idanu tana so ta gane wane cikin yaran nata. Jalal yazo ya durkusa gaban mum dinsa idanun sa cike da hawaye hannun sa se rawa yake yama rasa ina se taba a jikinta.  Mummy data gane jalal ne tace “jalal my son”.   “Mummyyy”. Se kawai ya rungume ta yana kuka mara sauti. Mummy ta lumshe idanu itama hawayen suna zubo mata. Ta tusa hannunta cikin gashin kansa tana shafawa. Bama ita kade ba dayawa a wajen seda suka zubdawa jalal da mum dinsa hawaye. Zaunawa imaan tayi tacigaba da kuka tasan ko ita da ta tashi batasan maman ta ba bazata nunawa jalal shan wahalar rayuwa ba.
Mummy ta dago da kan Jalal tana kallon sa tare da shafa dan sajen dake gefen fuskar sa tace “my little jay haka ka girma”. Tayi maganar tana murmushi. Har tym din hawaye basu tsaya a fuskar jalal ba ba ya kurawa mum dinsa idanu gani yake kamar mafarki yake. Kallon Bayan sa mum ta farayi tana kallon cikin court din. Snn ta kalli jalal tace “where is ur twin”. Wani irin sanyi jikin jalal yayi. Hakanan yaji shi baze iya fada mata mutuwar dant da bakinsa ba.   Daddy ne daya karaso yace “fareeda”. Da sauri mummy ta juya tana kallon daddy. Kamo hannunsa tayi da sauri muryar ta na rawa tace “meke faruwa ne mene kuke A court wani abu ya samu da jalal dinne ne ko saif”.   Daddy ya daura hannun sa saman nata. Jikinsa duk a sanyaye domin kau ynx ya riga yasan inda shariar ta dosa shi har bama yaso yaji karshen ta domin ko yariga san me sakamako zaya bada.  “Is ohk dear ki kwantar da hankalin ki babu abinda yaron ki yayi. Ajiyar zuciya jalal ya sauke yana kallon mum din sa daddy a tare when last”.   Buga gudumar da alkhali yayi yasa kowa ya maida hankali garesa yace “sukuma wadan nan suwane lauyar wanda ake kara ko kinsan dasu”. Imaan ta share hawayen ta tace “no my lord amma suma zasu iya mada sheda me karfi da zata iya gamsar da kotu cewa Alh Isa da Alh barau are the once behind jalal sad life tunda naga kamar suna niyar wahalar da sharia. Idan babu damuwa zan iya gabatar dasu a matsayin sheda”. “Kotu ta baki dama”     Imaan ta karasa wajen Abba tanaji kamar taje ta rungume abban nata tace “Dr umar ko zaka iya gaya mana meka sani game da rayuwar Alh barau akan jalal”. Abba yayi murmushi me ciwo yace “Ni likitane kuma ya kasance na iya hada poison sede idan mun hada muna amfani da ita jikin dabbobi manyan dabbobi. Snn mu fitar da maganin ta. Dalilin hada poison din nan kuwa shine mukan samu maganin kananin cututtuka da kuma manya kamar su corona ebola da sauransu. 20yrs da suka wuce wadan nan mutane sun zo sun sameni har inda nake anan abuja suka bukaci na nuna masu irin poison din dake hannu na I was surprise nace me zasuyi da itane. Shine suke cemun na sunaso su bude kamfanin magani ne shiyasa. Nan na dauki wata da bn dade da hadawa ba na basu nayi masu bayani akanta na kuma gaya masu tana da hadarin gaske domin ko idan mutum ma ya shata duk wani abu nasa seya dena aiki snn dole seda ita za ayi magani maganin ta yana jikin ta kome za a samu baze magani ba. Anan ne suka fito mun da kudirin su wai sunaso na basu ita zasu bani ko nawa ne. Tun a tym din na gane mugun abu sukeson aikatawa. Ni kuma nace bazan basu ba hasali ma ko wnn da suka gani ita knn bn nuna masu inada saura ba. Su kuma jin nace ita knn shine sukace “daide knn”. Nan suka bukaci zan karbi tayinsu koko. Nace ko daya. Tana hannun su suka dagata suka nunamun sukace nida ita har abada. Kuma babu abinda na isa nayi. Daga haka suka tafi suka barni.   Hankali na ya tashi sosai domin ko poison ne me hadari. Nasan a lokacin sunfi karfi na dan haka babu yanda zanyi dasu. Sede na fara bibiyar rayuwar su a boye dan hankali na ya kasa kwanciya. Cikin kwana uku wani Doctor abokina yake bani lbarin an kawo masu wata patience matar Alh Ali anyi poison dinta kuma basu gane komai ba sun turata kasar waje. A lokacin hankali na yayi matukar tashi kuma har yau abin nan dashi nake kwana nake tashi gani nake kamar nine na bata gubar. Kuma abin ya matukar dauremun kai domin ko nasan Alh isa kanin Alh Ali ne. Snn kuma Alh barau babban amininsa ne. Gsky Amama tayi karanci. Nan nacigaba da bibiyar rayuwar su alokacin nasan jalal da dan uwansa.  Wanda tausayinsu kade ya isa yasa nasan duk yanda nayi hajiya fareeda ta samu lpy.   A lokacin na fara kokarin tafiya china su Alh isa suka kamani wai sun kula ina bibiyar su. Nima da nake cike nadasu nace su tsaya su gani asirin su yana gabda tonuwa domin ko sauran poison inda da ita kuma se naji anyi hajiya fareeda magani. Anan naga tashin hankalin da suka shiga. Sede a tym din basu cemun komai ba. Amma tundaga ranar na shiga balain rayuwa kullum cikin farautar rayuwa ta ake naso barin kasar amma suka saka akayi blocking passport dina. Danaga rayuwata suke nema bilhakki shine yasa na gudu na koma kaduna. Ko abuja bana shigowa seda babban dalili. Bnsan ta ina zan fara taimakon wnn baiwar Allah ba domin kau amana tayi karanci. Har se lokacin da jalal yazo gidana tare da imaan diyata. Tun anan na yanke shawarar hadasu aure zanyi sede hakan beyiyu ba domin ko bnsan taya akai suka gano inda nake ba sukaso gidana ko dare sosai beyi ba matata tasamu damar guduwa ni kuma sunjimun raunika wanda da su jalal basu zo da wuri ba da na rasa raina. Anan ne na daura aurensa da diyata imaan wanda daganan bn kara sanin meke faruwa ba se farkawa nayi na ganni a asibiti. Sageer yamun bayanin cewa za aje akwi poison din dana bawa matata. Wanda anan na fada masa maganar password dina kuma nace ko jalal kar yasan na farka. A ranar aka gyaramun inda muka wuce saudiyya acan na hada maganin poison din aka fara mata aiki dashi wanda ya daukemu tsawon wata takwas kafin ta farfado. Wnn shine abinda na sani akan Alh isa da Alh barau. “
Fashewa da kuka mummy tayi kafin tace “ hakika Alh isa da Alh barau mugayen mutanene. Basu cancanci zama mutane nakusa ba wajen Alh Ali. Domin ko halinsu ko hanya dan Alh Ali ya rikesu da zuciya daya. Bayan Ali Ali ya tafi ya barmu dagani se yarana wanda tabbas nasan bayin kansa bane. Nashiga matukar damuwa dan kullum bani da aiki se kuka. Barin idan su jalal suna tambaya na ina dad dinsu. Wasa wasa har ya share wasu watanni be dawo ba. Wata rana ina zaune a parlor Alh isa da Alh barau suka shigo. Sunzo min da wata bukata da tayi mugun dauremun kai dan nayi mmki matuka. Sun fadamun wai Alh ya barni knn har abada nida yarana domin kau yafi son matar sa ta farko. Dan haka karnayi sanya kawai nazo muci kudi tare. Naji dakin Alh na dauki duk wasu kadarori nasa mu samu na samu. Idan ma ina tsoron karya dawo ya nemi kadarorinsa ne toh wlh sunyimun Alkawarin baze dawo ba daga can zasu gama dashi kuma wlh Alh isa wai ze aure ni kuma ya rikeni da yarana”. A lokacin idan raina yayi dubu ya baci wlh dan bn taba tunanin wnn magana daga bakin kanin miji na ba. Babu abinda yafi dagamun hankali shine wai zasu kashe mijina kuma ya aureni. Ganin yanda Alh ali ya daura sa akan komai nasa amma kokarin ganin bayansa suke. Raina ya baci sosai aikam nayi masu zagin cin mutunci na koresu nace bana son kara ganin su. Kuma su rubuta su aje alh ali ya gama taimakon maciya Amana irinsu kuma ko shekata dari ali zeyi be dawo ba inanan ina jiransa.
Bayan kwana uku da haka ina zaune ina shiryama yarana kayansu sega Alh isa. Nayi mmkin ganin sa har sama. Hankali tashe nace lpy. Ya karasa har cikin dakin yace dan Allah nayi hakuri kar na fadawa Alh Ali. A yanda ya shigomin daki se abin ya bani tsoro kuma raina ya baci nace “ai tunda ya fada ze iya kuma su sani bazan taba amincewa ba snn wane iskanci ne ya kawosa har daki na.  Se kawai naga ya fashe da dariya. Yace “ base kn kara ganin sa ba snn zaki fada masa”. Kafin nayi magana naji an rikeni ta baya tare da tsiramun wani abun kamar Allura snn suka sakeni na juya ina kallon alh barau daya tsiramun idona cike da hawaye domin kau na riga nasan sun rigada sun cutamun sede babu wanda suke fadomun a lokacin se yarana ina tunanin taya zasuyi rayuwa cikin wadan nan azzaluman domin kau su Alh isa sun gama bani mmki. Sukamin waving hannu sukace “hajiya fareeda idan kin isa ki hanamu cin dukiyar nan daga haka suka fashe da dariya suka fita. Dukewa nayi ina hawaye domin kau na farajin canji a jikina. Bn taba dauka ma zan sake rayuwa a doron duniya ba.
A hankali dad ya share hawayensa ya kalli su abba isa yace “Allah ya sani na rikeka a matsayin ka na kani na wanda muke uba daya kuma da zuciya daya. Amma karasa dame zaka sakamun se kayi kokarin tarwatsa farin ciki na na rike duka kai da yaran ka da matar ka amma ni ka kasa rikemun nawa. Me nayi maka kake neman rayuwata. Kayi poison matata ta 20yrs knn tanashan wahalar poison wanda konan yaci ace ka gane Allah ya nuna yafika. Ka saka kashe mun Yarona snn ka daura alhakin kisan akan dan uwansa. Wani irin rutse idanu mummy tayi tana karanto innalillahi domin kau ynx ta fahimci saif baya duniya. Daddy yace “ka hana yarona zaman lpy tunda ya taso besan menene farin ciki ba kowa nayi masa kallon bad boy ashe kaine babban gurbatacce wato kayi hakane dan nima kaga bayana na ko to Allah yafika. Amma dan Allah me nayi maku me mukayi maku kuka mana haka. Alh isa yace “kayi mana komai amma meyasa seka nunawa duniya cewa a karkashin ka nake ci meyasa baka barni na tsaya da kaina ba kowa se yasan kaine me kudin bani ba. You didn’t give me any space da nima zan mallaki tawa dukiyar fiyema da taka”. Tas tas tas. Kaji jalal da babu wanda ya kula da sanda ya karasa kusa dashi ya sauke masa maruka har uku snn ya jasa tare da fara bugasa da bango banda huci babu abinda jalal yake. Rungume granny sumy tayi tana ta kuka .  Da kyar police suka banbare jalal da har ya fara fitarwa da abba isa da jini. Idanun sa sunyi mugun ja jikin sa har wani irn rawa yake. Cikin daga murya yake fadin “kaine ka tara masa kudin da dole seya maka abinda kake so nawa ka basa dukiyar ka ce matsiyaci. Ba a karkashin nasa kakeci ba Allah ne kade ze rabamu da kai mugu Azzalumi you runs our happiness   Mu mum is suffering for good 20yrs just because of you. Kuma wlh kasani jinin dan uwana daya mutu sbd da kai bazan taba yafewaba. Maci amana tir da danuwa irin ka wlh”. Aka dago Abba isa dayayi jinanina da jini. Daddy yana kallon sa muryar sa a disashe yace “daka gayamun abinda kakeso knn danayi maka base ka tarwatsa farin cikin mu ba ynx ina amfani dan Allah mene ribar ka anan a ganina zaman mu tare kamar wani karfafa zumunci ne ai da kowa da kudinsa ganin kaddarar data faru da kai yasa na janyo ka jikina bnsan cewa ka maciji bane. Ynx just take jalal as an example sanda yaje ya nemi kudinsa na sani ne. Kanaji agabanka aka fadi kudinsa. Be dogara dani ba yaje ya nemi nasa” ya kalli Alh barau yace “kaikuma bazan ce komai ba Allah ze sakamun.”  Imaan ta kalli alkhali tana share hawayen ta tace “yamai sharia da wadan nan hujjoji nake so wnn kotu me albarka data gane cewa jalal bashi da laifi akan laifukan da ake zargin sa dashi nagode”. Ta koma ta zauna. Alkhali ya dago yace “bayan sauraren hujoji da bayanai wajen lauyan dake kara da kuma lauyan da ake kara kotu ta gane cewa “jalal Ali Abbas bashi da laifi ko daya cikin laifukan da ake zargin sa dashi dan haka kotu ta wankesa. Snn ta gargadi duk wani social media da zata yada wani abu na banza akansa”.. kotu ta yankewa hajiya atika da hajiya huwaila da manga da tasiu da kuma habibu daurin rai da rai da kuma horo mai tsanani. Snn kuma akwai tara da hajiya huwaila zaka bada ta miliyan 50 abisa gurbata rayuwar jalal da tayi tun yana yaro. Snn habib ma Akwai tarar miliyan 50 sbd batawa jalal suna daya rinkayi. Kotu ta yankewa jabeer da sauran yan uwansa hukuncin shekara 5 a gidan yari tare da horo me tsanani. Snn kotu ta yankewa Alh isa da Alh barau da kuma musa kwage hukuncin kisa ta hanyar rataya.... snn akwai tara da alh isa dakuma Alh barau zasu bama hanifa da miliyan hamsin hamsin. Daga haka ya buga guduma.  Nan kowa ya mike. Da sauri imaan ta karasa wajen Abba ta rungumesa tare da fashewa da kuka “Abbana”. Abba yayi murmushi yace “my daughter my barrister am very proud of you” mommy tazo tana shafa bayan ta “kukan kuma fa namene my daughter thank god Allah kade yasan ladar da kika samu”. Imaan ta dago tana kallon iyayen nata with so much love tace “thank you Abba thank you mommy kome na zama nan gaba kune sila Allah ya biyaku”. Abba ya shafa gefen fuskar ta yace “ke er mu ce idan bamuyi maki ba wa zamuyi mawa Allah ya maki Albarka yasa ki cigaba da zaluko mana azzalumai”.  Imaan na murmushi tace ameen. Baba ya kasa tashi kallon ertasa kawai yake da iyayen nata yasan tabbas Allah ne kade ze sakawa abba da Mommy bisaga yanda suka dauki diyar tasa kamar er cikin su. Zuwan baba wajen ne yasa abba ware idanu yana kallon baba cikin shiga ta alfarma kamar ba baba na kauye ba abba ya mika masa hannu suka gaisa baba yace “kome imaan ta zama a rayuwa kaine sila dacta nagode Allah ya saka da alkhairi”. Abba yace “haba imaan ai ya’ta ce”.
Tunda suka fito jalal be samu wani natsuwa ba yan jarida sunyi masa caaaa ko ina daukar kyakkyawar fuskar sa ake. Jalal ya gaji da amsa tambayoyin su burinsa kawai yaje wajen mommynsa he want to hug her and fell his mum. Da kyar ya samu yasha. Karasa wajen su ya rungume mamy cike da dubin kaunar ta “no words. Mamy i have no words to thank you Allah ne kade ze saka maki gsky kin cika er uwa abin alfahari”. Mamy ta shafa gefen fuskar sa “yaro na Allah ya maka Albarka”.   Juyawa yayi ya rungume sageeer “rabin jikina bani da kamar ka wollah”. Wani murmushi sageer Yayi yanajin wani farin ciki. Jalal ya karasa wajen mum din tasa ya durkusa yayi kissing dinta a forehead snn yace “I miss you mum I really really miss you mummy hakika uwar harama ce gashi kina dawowa duk wata damuwa ta tafi. Thank god thank you sageer thank you mamyy and thank you imaaan”. Ya dora kansa saman cinyarta. Mummy ta tusa hannun ta cikin sumar sa. Tana tuna time din da idan har tayi ma daya shima daya setayi masa. Haka zasu kwanta saman cinyarta taita shafa masu gashi. So now saif has gone. Muryar jalal taji yace “mummy kina tuna saif ko”. Mummy tace “yes my son I remember those days”. Jalal ya dago yana kallon ta. Yace “almost 18yrs knn amma har gobe inajin zafin mutuwar sa. But I thank god mutuwa tana kan kowa. And now I have the little saif. I have two beautiful kids. Saif and fareeda. With my wife imaan I thank god”. Mummy ta ware idanu cike da farin ciki tace “wow ynx har ina da jikoki who is she wacece imaan”. Jalal na wani murmushin farin ciki yace “the lauya wacce ta tsayamun a kotu she’s my wife”.   Mummy ta rinka hango kyakkyawar lauyar da taita kallo a kotu. Domin kau tun batasan wacece itaba taji tanason yarinyar kodan taga ita ke kare danta. Tun acan taji ta shiga ranta. The girl is very beautiful,young and educated. And kuma gashi surukar ta ce. Mummy tace “oh that beautiful young lady”. Jalal ya lumshe idanu cike da farin ciki yace “that young lady mummy is and angel 😇 she’s God’s gift to my saddest heart. She live with me tun tym din da kowa ya sanni da bad she change me to a better person and ynx kuma ta tsaya tsayin daka domin ganin ta nunawa duniya cewa that jalal da sukewa kallon bad boy is not bad at all.” Mummy ta shafa gefen fuskar sa tace “you love her and i love her too my son where is she”. Jalal yace “nasan ynx itama tana can tare da Abba lets go home nasan anjima zaki ganta”. Daga haka yajata zuwa mota. Har ze shiga. Ya hango sumy da mom din su sunata kuka mahmud ne ma me dan dauriyar ciki. Zuwa yayi ya kama sumy yana kallon cikin idon ta yace “lily na banaso in kara ganin kinyi kuka kinji”. Jiki na rawa tace “yaya Jalal kayi hakuri”. Share mata hawayen ta yayi yace “oya let’s go home”. Duk tashi sukayi suka nufi motocin su ya bude masu suka shiga snn ya kama motar da mum da mamy take yana kallon sageer yace “kai bazaka zo muje ba”. Sageer ya sosa kai yace “zanzo”. Tabe baki jalal yayi snn yace “ka kular mun da imaan nasan ynx tanacan wajen Abba.”  Murmushi sageer yayi. Jalal ma yayi murmushi yana tuna ranar da imaan ta farfado wane zagi ne besha ba akan Abba”  
Imaan ta fito hannun ta rike dana Abba da Mommy kamar za a kwace mata su. Su jummala kam an zama yan kallo domin kau ynx sun fahimci rayuwar imaan kwata kwata ba kalar tasu bace ta marasa ilimi se ynx rashin ilimin keyi mata ciwo ynx de ga imaan nan kaf cikin kauyen su ya fita zakka. Ita ynx Imaan kusan family nawa gareta ga bangaren su baba da familynsa wanda gabadayan su da dawo dasu abuja ga kuma su Abba. Snn ga yayan mommy abie su jiddah knn dan har ynx ma suna tare.  Sageer ya karaso suka kara gaisawa Abba yace “we are going to the hospital zamu amshi yaran daganan se mu wuce” sageer yace “ohk then muje”. Duka shiga motoci sukayi suka biya suka amshi yaran da akace iskace suka sha sosai shiyasa suke wnn kukan amma ga magani ynx haka ma bacci suke. Bayan sun fito sageer ya kalli jiddah dake shirin shiga motar imaan yace “ba a mota na kikazo court din ba”. Jiddah ta ware idanu. Tace “and dole kuma a taka zan koma”. Yadan sosa kai kafin yace “ohk I will droup you”. Kamar zatayi magana se kuma ta bude ta shiga. Hanyar gidan imaan suka dauka. Suna cikin tafiya yace “ tnx for ur contribution Allah ya biyaki”. Jiddah tace “no tnx”. Yace “can you be part of us. Part of our family”. Tace “dama am already part of the family”. Ya sosa beard dinsa kafin yace “ohk I love you am I welcome”. Murmushi jiddah tayi tama rasa me zatace masa yayi kasa da murya yace “tell me pls”. Jiddah tayi rolling eyes kafin tace “I will think about it”. Dede nan suka karaso gidan su imaan sageer yace “I will call you bye”. Budewa tayi ta fita tace “tnx”.  Daga haka yaja motar ya fita. Imaan ta ringa ma jiddah wani kallo. Jiddah ta ware idanu “madaam wnn kallon fa. Bafa a motar jalal na fito ba duba da kyau ta sageer ce”. Dariya sosai imaan tayi tana tuna yanda take kishin jalal ada. Imaan tace “da ta jalal ce da tun acan ba sena rushe glass din kin fito ba duk dariya sukayi
Wani part daban cikin part din daddy aka budewa mummy ashe ma taba ina takawa kawai de bazata juri tafiya me tsayi bane. Barin dad dinsa da mummy din tasa yayi domin su dan zauna ya koma part dinsa. Ya lumshe idanu yana tunanin imaan. Kawai yarinyar ta riga ta gama da komai na rayuwar sa ne tun ranar daya fara ganin ta ya fara ganin sauyi.  Ya tuna first maganar data fara hadasu daya zauna mata waje   Bedsides drower dinsa ya janyo sega jotter dinta daya taho da ita ranar murmushi yayi yana kallon sunan ta   Kafin yayi kissing jotter din yace “can’t wait to hug you babee.” Yayi murmushi he have to tank Abba sbd shine tushen komai.
Mutane ne ake ta shigowa yima mummy barka dawowa harda abokan daddy suma duk sun zo yo masa jaje. Da kaga dadyy kasan dauriya kawai yake domin kau he is totally broken har ynx abin ya tsaya masa a rai. Daga karshe ma sede ya koma daki ya rufe.
Se bayan ishai su imaan suka zo tare da twins dinta su Abba de sunce se gobe zasu shigo dasu baba.   Ta window jalal yaga motar imaan wani murmushi yayi kafin yace “finally dan dama tun dazu yake jiran ta”.    A parlor suka hadu dashi bama ta kula dashi ba ta nufi part din da take tunanin nan mummy ta sauka. Ta rike da Amaan nanny kuma amnah. Se kawai ji tayi an rungume ta be wani damu da nanny ba duk da tama saba gani da farko ta tsorata but jin kamshin turarensa yasa ta tura baki “kanaso ka bani tsoro ko”.  Yaje saitin kunnenta yace “part din mijin ki ya kamata ki fara zuwa”. “Ni ba wajen ka bazo ba wajen mummy nazo ai”. Ya dage gira “really aikuwa keda ganin ta se gobe ki fara bani hakki na tukkun”. Kamar imaan zatayi kuka tace “dan Allah kayi hakuri mijina” yaja hancin ta kafin ya karbi Amaan tare da kama hannun ta “ohk lets go”. Tare suka shiga kan imaan kasa. Tunda suka shiga mummy da mamy suke kallon su. Har suka karaso yace “mamy mummy here is imaan and our two little kid”. Imaan zata duka mummy tayi saurin kama hannun ta tare da girgiza mata kai “aa diyata zauna kusa dani kinji Allah yayi maki Albarka yasa ki cigaba da ganin haske a rayuwar ki”. Imaan tace Ameen ina wuni mummy ya karfin jiki”. “Da sauki ya yaran”. Suna lafiya”. Jalal ya langwabar da kai “mummy banji kince Allah ya barta ta tare da mijin ta ba”. Dariya sukayi mummy tace “to Allah ya barki tare da mijin ki ya raya zuriar ku”. Suka ce ameen da sauri jalal yace “that’s my mum”. Mamyy ta karbi yaran da suke ta juya idanu kamar sunacin abinda ake cewa tace “masha Allah” ta mika wa mummy murmushi mummy take tana kallon yaran. Kawai tuna sanda ta haifi nata twins din take”.   Wasa wasa mummy taitajan imaan ta hira tuni imaan ta sake to dama bata da wahalar sabo barin ma jalal da ko kunya bayaji koda ze fita agaban su mum din yazo yayi kissing dinta snn ya fice. Se 10 ya dawo yana kallon imaan yace “nan zamu barmasu yaran ne”. Mamy tace “tunda muna da abincin basu ko”. Dariya jalal yayi kafin yaje ya karbi yaran duka snn yacema imaan “let’s go”.
A parlor suka hadu da zulfa da abin duniya ya isheta kaf part dinsu ita kade ce gashi sumy ma tana cikin yanayi bare taje wajen ta. Tana ganin jalal ta zube tare da fashewa da kuka tace “dan Allah yaya jalal kayi hakuri Allah bani da masaniyar komai akan abinda mama keyi maka” hakanan jalal yaji wani tausayin ta yake ji dan zuciyar sa ynx ta wanke shar yakeji. Yace “kin gaisar da mummy”. Ta girgiza masa kai. Camly yace “kije ku gaisa mana”.
Jalal daya fita wanka ya kalli imaan dake feeding twins din yace “feed then kafin nima kizo kiyi feeding dina”   Murmushi kawai imaan tayi har ta gama feedin yaran ta kwantar dasu a cikin dan gadon su snn ta nufi toilet wanka tayi. Sanda ta fito ta iske jalal na dan danna system dinsa. Gaban mirror ta nufa tayi yan shafe shafen ta snn ta saka wata er rigar bacci. A hankali ta haw saman gadon tare da shigewa jikinsa jalal yayi kissing libs dinta kafin yace “mrs jalal”. Imaan tace “yes my love thought wnn rubutun ya kare”. Ya aje system din kafin ya juyo ya zakaye ta da hannayesa yana shinshina wuyanta yace “yace concluding nake mata mana kafin gobe na bata”.  Imaan ta juya ta rungume sa snn tace “so now tell me how do you miss me”. Jalal yayi rolling eyes dinsa kafin yace “I will show you”. Yakai hannun sa saman zip din rigar sa yace “ are you ready my smile keeper”. Imaan ta lumshe idanu kafin tace “sure babee am alwaye ready”.
Tsab mummy ta tari zulfa mamy ta zobo mata abinci snn ta bata daki a part dinta tace “daga ynx kin zama diyata kinji forget ur past dear
Washe gari jalal ya damkawa mummy system din yace “dis for you mummy”. Karba mummy tayi kafin tace “may god bless you my son”.  Daddy ne ya shigo yace “mene ake badawa bnd mu”. Mummy tace “nawa ne ni kade”. Daddy ya kalli jalal my son ina nawa yake. Jalal ya ware idanu yace “ daddy ai ka rigata gani labarin duk abinda ya faru nake bata sanda bata nan ynx zata ga komai”.  Daddy yace “wife I will read it for you”. Cike da farin ciki yace “lol daddy as you wish thank god nima ina da matar nan”. Daddy yayi dariya ya kalli mummy yace “yaron nan akan  matar sa seda yace se ko kowa na gidan nan ya gane kurinsa babu kunya fa”. Dariya jalal yayi kafin ya nufi kofa ya fita “nabarka kaida matar taka” su Abba sun zo sun gaisa sosai daddy Abie ma yazo da duka family dinsa hakama su baba gidan gaba daya seya cika da mutane kamar ana wani biki dan har su yusrah sunzo gasu jiddah ita kanta imaan seta zama busy dole jalal yabar gidan ya tafi part din granny. Da har ynx cikin ji mami take. Varin ma sumy dake ta kuka tun jiya har ynx taki shiru. Jalal daya shiga part din granny ita ya fara tambaya granny tace masa “tanacan tana ta kuka”.  Jalal ya shiga dakin tana ganin sa ta kara fashewa da kuka. Jalal ya kamo hannun ta yace “komi na duniya me wucewa ne ki dauki musali kamar ni. Shakaru nawa ina cikin bakin ciki amma daga jiya zuwa yau kamar bn taba ba. I want you to be strong kinji kanwata”. Sumy ta gyada kai. Yace “good oya tashi muje parlor kinji”. Tashi tayi suka fita. Dede sageer ya shigo tare da yaya Muhammad. Gaisawa sukayi sageer na kallon sumy yace “ darling sis are still crying. Murmushi tayi kafin ta gaishe dasu”. Sageer yace “common dear be strong lily let’s move on”. Sun dade dan har seda su abie suka tashi tafiya snn. Sageer ya kalli jalal yace bari naje na dawo. Jalal ya kamo hannun sageer yace “se wani kamu kafa kake da yayan ta to na gano ka”. Dariya sageer yayi kafin yace “bro am coming akwai lbr daga haka yabi bayan Muhammad”. Suna fita muhammad yace “I think I’ve found a partner” sageer ya ware idanu yace “who is she”. Ya Muhammad na shafa beard dinsa yace “the gal I mean sumayya”

After 9years
Jalal ne tsaye ta window yana kallon Yaran nasa da suke ball a dan karamin filin ball din da aka kawata tashi da grass carpet. Amaan ne rike da ball ze buga while amnah na goal keeping. Yaran wasu irin kyawawa dasu kaf kamanin jalal ya game fitowa a tare dasu gara amna ta dauko wasu abubuwa daga jikin imaan Amma Amaan kau komai nasa jalal ne. Amaan ya buga ball din yace ya fara murna whlie Amna ta kwanta zatayi kuka ita a dole bata yarda ba. Memories kawai suke dawo wa jalal domin kau amaan yana mugun tuna masa da saif. Dan amaan babu abinda ya mance na kamannin saif. Bude gate me gadi yayi motar imaan ta shiga. Jalal ya bi motar da kallon kafin ya bar windown domin zuwa tarbar matar tasa. Bawai yana barin ta aiki bane aa idan sharia ta kama wacce ya kamata ta taimaka din shine yake barin ta amma koda yaushe tana makale dashi dan ko kadan jalal bayaso yaga imaan tayi nisa dashi ko daya. Kafin ya isa har yaran sun rigasa isa sukaje suka rungume imaan ta da fito cikin shigar lauyoyi ta kara wani irin kyau. Amnah da tafi Amaan surutu tace “daddy we first you”. Jalal ya langwabar da kai yace “and now is tym for daddy abeg I want hug my wife”. Matsawa sukayi yayin da ya warewa imaan hannu ta rungume sa and yaran suma suka rungume su.
Imaan ta gama shirya cute yaran nata tana kallon yanda sukayi tace “now we will wait for daddy”. Amaan ya ware idanu “mummy I just can’t wait to see mummy daddy Abba and mommy I miss them”. Imaan ta nuna masu cartoon tace “oya am coming dearies”. Daga haka tayi kissing dinsu. Ta nufi bedroom dinsu. Nan ta iska jalal har tym din yana shan cofee din data basa kamar zatayi kuka tace “shine baka shirya ba”. Tasowa jalal yayi yana kallon lips dinta data turo yace “amnah ke ta biyo wlh kinsan yanda libs din nan ke attracting dina kuwa. Yayi maganar yana huging dinta. Imaan tace “kaga de karmuyi dare ko”. Yace “kinga su Amaan suna bukatar ganne. Look sageer da jiddah har sunyi haihuwa biyu,Su labeeb da maryam ma biyu Ak da yusrah ma biyu   ,Mahmoud da zulfa ma biyu, sumy da muhammad ma biyu, kuma duk seda aka haifi su Amaan snn akayi bikin su. Madaam we have to waje up mu haifi koda daya ne. Duk wanda imaan taso kaucewa dole ta hakura sanda suka gama shiri suka fito har su Amaan sunyi bacci.     Imaan tace “ina jiran ka a mota ka dauko yaran mu tafi.”  Daga haka ta fice murmushi jalal yayi kafin yasa karfi ya dauki yaran duka. Inda Allah ya taimakesa ma basu da nauyi. Ta madubi imaan keta kallon sa tana zaune a driver seat taita danne dariyar ta harta ya shigo dasu motar ya rufe sannan ya dawo gaba tace “well job my love”. Hararan ta jalal yayi imaan tayi ma motar key suka fara tafiya ta kamo hannun sa tace “common my babee meyasa zakayi fushi da masoyiyar ka”. Yace “for my life bazan taba ba. Komai naki farin ciki yake sani”. Imaan ta lumshe idanu kafin ta kallesa tace “burinaaa in rayu da kai har numfashin karshe”. “Kinrikita dukka tunanina” jalal ya fada yace “kinga samun wakar senafin jin dadi bi inadan ina kallon ki”.

Tunda yaran suka bude ido suka ga inda kayi parking suka Bude motar da sauri suka fita. Har rige rigen shiga suke. Mummy na rike da layla diyar sageer tayi saurin sauketa gefe dan karsu bigeta. A tare suka dale kan cinyar ta. “Mummy”. Rungume mummy tayi “my dearies”.  Jiddah tayi saurin fitowa daga daki “an iso knn ji har mun rigasa”. Sageer yace “jalal ne fa barin ma idan suna tare da imaan shirirta kala kala”. Daddy dake saukowa daga stairs rike da afra first borne din sageer yace “aini imaan da jalal yanda kasa jiya aka daura auren su”. Da sauri su Amaan sukaje suka rungume Daddy”.  “Wake gulmarmu”. Cewar jalal daya shigo rike da hannun imaan”.   Sageer yace “wanda ka raina”. Jalal yaje yayi huging mummy hakama imaan   Jalal yace “su muhaamad basu iso bane”. Jiddah tace “tare zasu zo dasu Abba da baba su zulfa ma haka”. Jalal yace “shine ake cewa mun dade daga kun rigami zuwa”. Shigowar zulfa da mahmud ne yasa babu wanda ya tankasa da sauri zulfa taje ta rungume mummy ta zaman mata uwa ynx. Ko minti goma ba ayi ba su abba suka iso. Dasu sumy. Gidan ya cika ga cute cute yaran duk inda ka waiga sune. Imaan kallon kowa kawai take cike da farin ciki lallai abba shine silar canzawar komai na rayuwar ta. Idan ta tuna irin rayuwar da ake a kauyen su a da amma ynx komai ya canza sede tace Alhmdllh. Kamar yanda take wnn tunanin haka ma jalal yayin da yake gani itace silar sauyuwar tasa rayuwar. Dagowa suka hada idanu. Ya kashe mata ido daya ita ma kashe masa tayi tana murmushi. Sageer ya dauke kansa now he’s happy dan uwansa is life living a happy life”.....................
ALHAMDULILLAH
YAUWA anan na kawo karshen littafin JALAL ALI dan Allah duk wanda na batamawa ya yafe mun snn kurakuren da mukayi Allah ya yafe mana dafan ynx kowa ya fahimci littafin Jalal Ali. Domin farko littafin dayawa sukan biyoni private suce mun gsky as jalal yana star din littafi be kamata ya zama bad ba. So ni kuma already na rigada na tsara littafina tun can shiyasa duk bnyi aiki da wadan nan shawaran ba domin da na dauka da kila littafin baze zo a yanda zaku fahimta ba.amma nasan ynx kun fahimta wanda kuma be fahimta ba yayi hakuri haka littafin yazo kuma kowa yasan dan adam na kuskure nagode

Urs
Annafie❤️🎊💖

Follow me on wattpad account @ NafeesaAguga

07051376476

07014979567

No comments