Intisaar Book 1 Complete
INTISAAR BOOK ONE
.
Khaleesat haidar.
A gajiye ta shigo gidan hade da kullo gate, ta
nufi sashin su ba tare da ta kula da mutanen
dake tsakar gidan ba, bare ta gaishesu,
"lallai
yarinya nan kin rika... Ta juyo da sauri tare
dadawowa da baya tace "kuyi hakuri ban kulabane
wallahi, ina yinin ku?" wata farar mata mai
matsakaicin jiki tana linke kayan shanya tayi
tsaki hade dace "ai bamu ba, wataran mahakaxaki mance da uwarki, munafukar Allahkawai,
bace mana da gani, ta tsunkuyar da kai takasa
wucewa, don ita har ga Allah hankalinta nebayawajen amma tasan baxata iya fidda kantaba.
Dan haka kawai sai ta kara maimaita "kuyihakuri"
kawai. Tabe baki ta xaunen tayi tare da mikewa tace "banxa Agola kawai, tayi sashinta tashigetare da banko kofa, itama farar hakan tayimata
hade da cemata shegiya tayi nata sashin.
Jikintaa mace ta karasa palon nasu, momynta dake
kwance tana karatun Adduo'i, ta dubeta bata ce
komai ba ta kau da kanta, ta nemi guri taxauna
tare dacewa " ina yini momy, momy ta mikexaune tana dubanta tace me ya faru
Intisaar? Ta
kirkiro murmushi tace bakomai momy, batasakecemata komai ba, sai ca tayi "ya mai jikin?"
tacejiki da sauki sosai, hajiyarsu tace kila gobema asallamesu daga Asibitin, momy tace "to Allah
yasauwake, kiyi sallah ga abincin ki can arufe,"
tace to sannan tashiga bathroom tayi alwala
tafito, tana idar da sallan ta jawo abincintata fara ci, "momy ina ihsaan,? Momy tace taje
kitso
tare da mikewa tashiga bedroom dinta,
Intisaar
na gama cin abincin ta fita da kwanukan ta
dawo, ta watsa ruwa, sannan tace wa
momy ta
tafi wajen Innah. A hanya suka hadu daZainab,
Zainab ta dubeta tace "har kin dawo dagadubiyan?" eh na dawo daxun nan, ban madade dashigo wa gidan ba, tana magana ne tana
tafiya,
Xainab ta dan kwala mata kira hade dacewa
"wajen innah xaki ne?" eh can xani me yafaru?
Ok kice ta bani dambu na, dan daxu kursumtace
min ta siyo mata dayawa, intisaar tace tokixomuje mana, "aa Hajiya ta aikeni ne " toshikenan
idan ban manta ba xan karbo maki, xainab taharareta da wasa tace "xaki gane kuranki nekuwa
idan kika manta" intisaar bata ce komai ba, ta
wuce tana dariya. Cikin gidan innar tasutake,
dan babban gida ne na gaske. Tana isasashin
innar ta ganta xaune a bakin kofar falonta, tanakulla magunguna, intisaar ta hade rai tace"wai
innah bakya gajiya da daure daurenmagungunada kunce kuncensu ne, innah ta hade raiitama
tace "to dan gidanku ba duk dan saboda kunakeyiba" intisaar ta gyara xamanta tace "to ina
dambuna da xainab innah? Da sauri ta juyotanaduban intisaar din tace "oh ni Rahmatu
nashigauku, to yanxu uban wa yace maku na siyadambu,?" intisaar ta tabe baki tace "cinye
kayanki innah, sannan ta mike ta shigepalon tayikwanciyarta." daga waje taji innah na cewa
"inatakwarata?" ta yi shiru kamar baxata amsa ba,
Saikuma tace "tana wajen kitso," to meyasabakikawota nayi mata ba.? "Ke har wani kitsokika
iya innah.?" innah bata sake cewa komai bahartagama abinda takeyi ta shigo parlon. Sunjimasuna hira da inna, har aka kira maghrib ta yi
salla,
sannan ta diba abincin da fadila ta kawowainnahtaci. Ba ita ta bar sashin innah ba sai wajen
karfe goma saura, bayan ta dibar wa xainabdambunta itama ta debi nata, tayi mata saidasafe ta kama hanyar sashinsu, duk da tsakargidan da haske sosai dan ko ina kwan fitila
ne.
amma gabanta faduwa yake yi sosai,da sauri ta karaso gida ta bude kofa ta shige tare dakullewa, momy ta dubeta tace " ke da waye
haka,?
Tayi dariya tace bakowa, momy tace to yayi.
Washegari bayan sun karya ita da kanwarta
Ihsaan suka je goudan Abba, yana xaune aparlonsa yana sauraren labarai suka shiga,
kursum na xaune a kasa ta hade rai, daalamarabu take jira. Ya amsa masu yana murmushi, ya
dauki ihsaan yace "mamata yau kin tashi da wurikenan, sannan ya dubi intisaar yace ke kikayimata
kitso ko inna? Tayi dariya tace a’a saloonakayimata," to yayi kyau, ya dubi kursum yace"yauwa
ina jinki, Tace dama Abba gyaran gashi xanje asaloon, yace nawa ne? Dubu biyu ne Abba,
yaxaro ya bata, sannan ya dubi intisaar yaxaro
dubu biyun ya mika mata yace "ke ma kigyaragashin naki, sai kuje tare," tayi murmushihade
da godiya, kursum ta dubeta cikin tashin hnklidatakaici, sannan ta mike tace ngd Abba, ta
fice.
Intissar ta da da yi masa gdya sannan takamahannun kanwarta suka bar parlon. A hanyasukahadu da Hajiya tsaye suna jiranta, gabnta yyi
mugun faduwa, ta daure ta karaso bakintanarawa tace "ina kwana hajiya.... Ido ta xaromata
tace "ban kwana ba dan ubanki, da sauriIntissarta mika mata dubu biyun dake hannunta, takarbe
kuwa, sannan tace "bnxa kawai, sukayigaba daita dasu kursum, kursum tayi mata gwalotare da
fashewa da dariya, ita dai bata ce komai bata
kama hannun kanwanta suka yi sashinsu.
Ihsaantace, "amma anty ai ke Abba ya ba wa kudinkika
basu?" intisaar tayi mata murmushi tace ai nasu ne dama, sannan ta ja ta suka shigepalor.
Momy na shara ta karbe ta karasa sannan
ta gyara gidan, ta kwaso kayanta tana guga.
Ihsaan na jikin momy suna kallo, tace
"momy,daddy yace kitso na yyi kyau wai, momy tayimurmushi tace "sosai ma kuwa" intisaartace
"nima ae irin shi xanyi," to ba kin ba sumomynanty Xainab kudin ba, momy ta dube intisartace
"wani kudin?" nima bn san mata ba. Ihsaan tace Abba ne ya bata two thousand yace tayikitso
shine momynsu khadija ta karbe, momy tamikeba tare da tace komai ba ta dauki hijab tace"idan kin gama gugan ki dauki kudi ki siyogolden
morn tun daxu ihsaan take so kuma bbu, ni
xanje
na gaida innah, ihsaan ta mike tace momynimaxan biki, eh dama tare xamu ae daukohijabin ki,
suka fice tare. Intisaar ta cigaba da guganta. xainab ta shigo, ta dubeta tace inadambuna, saida ta ja mata rai sannan ta dauko ta bata
tanadariya, xainab tace amma ke kka dibar minko?
Eh nima ga nawa can, xainab tace shiyasanaganshi dan kadan, intisaar dai bata ce matakomai ba ta karasa guganta ta kashe dutsengugan ta kai kayan daki, ta dawo ta dubixainab
tace yau baxa kiyi kwalliyan friday bne?
Tace "uhum bari ma ki ga, aikena pa hajiya tayi.
Tayi hanyar fita, intisaar tace ina xaki,?
Supermarket!
Tace ba tare da ta kalleta ba, tace jirani nimaxan siyo golden morn yanxu, ta daukokudin da
hijab suka fita ta rufe kofa, xainab tacemomytana wajen innah ne, yea tana can, sukakamahanyar supermarket. Da kafa suka taka dan
bawani nisa sosai, sai da intisaar ta rakatagidansukawarta dake Area din ta karbo litattafaisannan
suka kama hanyar gida. Umma suka gani atsakar gidan ita da 'yar ta Rahmatu tanamatatsifa, intisaar ta gaida ta, bata ko kalla indatake
ba bare ta amsa, ta dubi xainab tace ke danubanki ba aikenki hajiya tayi ba kika biwannangantalalliyar ku ka je gantali koh? Xainab tayatsine fuska ta danyi tsaki ba tare da tace matakomai ba ta nufa sashinsu, intisaar taisashinsuita ma da saurinta.
... Tana shiga parlonsu ta tar da ummanta
tana shiri xata fita, tace "momy ina xaki?"
momyba tare da ta kalleta ba tace "inda kikaaikeni"
sai da ta gama shirinta tsaf sannan tacexasu je
dubiya da innah... Wayan intisaar yyi kara tadauka tana cewa "kar dai har kun dawosamira?"
daga can bangaren samira tace nace makiaetare xamu, ni ga ma ni a gate dinku kiyimaxa kishirya, tace mata "Allah karki ba kankiwahala ni
bbu inda xani, ta kashe wayan. Momy tadubeta
tace ina xaku, "wai dole tare xamu gidanMaryam
kuma nace masu baxa ni ba, momy tace"waimaryam da akayi bikinta?" eh ita... Aa bakikyauta ba intisaar ayi bikinta ki ki xuwakumayanxun ma kuje gidanta kice ba xaki ba, ki
dauredai ki shirya kuje, amman karki dde, ni natafi. innah tana jirana, ki tabbatar kin kulle minkofa,
tace"to momy Allah ya kiyaye, a bakin kofatahadu dasu samiran suka gaisa sannan tawuce.
Ba dan ranta ya so ba ta shirya suka bargidan,
suna ta mata tsiyan bbu wanda xai xo
bukinta,
ita dai murmushi kawai take yi dan bata dalkcnsu, karfe sha biyu suka iso gidanmaryam,
tayi murnar ganinsu sosai, amma sai tahade waintisaar rai, da kyar intisaar ta shawo kanta, tana
dariya, dan tasan bata kyauta mata ba tundabata je bikinta ba. Ta cikasu da kayen ciyeciyeda soft drinks, lkcn sllh nayi suka yi gaba
dayansu, sannan ta kawo masu abinci sunacisuna hira. Daga bisanni intisaar ta basuuxurintana cewar xata wuce gida dan momy batanan,
maryam ta fahimce ta dan hka tayi matagdyanxuwan da tayi, intisaar ta hada ta da dubu biyu
ta amsa da kyar sannan ta bar su samira agidanta wuce. A dai-dai gun da xata hau motaummi
ta kirata, ta dauka tana cewa ummi ansallameku
ne, ummi tace "eh yanxu ma xamu wucegida, cama nake xaki xo intisaar, intisaar tayimurmushi
tace "to bari na taho ina hanya dan munjegidan
maryam." tana isa hsptl ta gaida nurses dindakereception ta haye sama taje ward din daummin
take, cak ta tsaya a stairs din gabanta na
faduwa, kamr warce aka hankado ta juya dasauri ta fara sauka, da sauri ya bita har sukasauka kasa ya maxa ya shige gabanta yace"meye kika gudu 'yan mata, nayi laifi ne,
fuskartaa daure tace a'a ta juya ta haye sama, jin ya
biyota ne ya sa ta tsaya, ya karaso yace "yakika tsaya kuma, bata ce komai ba tayi hanyarward
din kawarta yana biye da ita. Xaune tagaummi
tana duba Novel, ta karaso, shima ya shigodakin,
gefen ummi ta xauna tana ce mata ya jikin,
taceda sauki ya su mummy? Ta daga kanta dasauri tace doctor dama ka shigo, yyi murmushi
yace
"yea, kin warware sosai yanxu ko? Tace "eh
nagode Dr. Yace no probs wannan kawarkice, tadubi intisaar tace eh, yace hmm.., what's her
name? Ta dubi intisaar da tayi kmr ma batasansuna yi ba tace "Intisaar sunanta" waww..
To menayi maki intisaar tun jiya kke guduna, itadaibata ce komai ba sai wayanta da take
dannawa,
yyi murmushin karfin hali yace o.k , am srrytoidan ina damunki, tace "o.k" sannan ta dubi
ummi tace momy pa, ummi tace "sunje kirantaxi
ita da su falmata yanxu xamu wuce dama." Shikam juyawa yyi ya bar dakin, intisaar ta danja
tsaki, ita dai ummi bata ce komai ba. Karfeukusuka bar hsptl din, bayan ummi taje tayi maDrfaruuq godiya dan yana da kirki sosai, takuma
maida masa Novels dinsa da ya bata takekarantawa, sannan ya nemi alfarman tabashinmbr intisaar bbu musu ta bashi yyi mata
gdya.
Har bakin taxin ya rako su, momy ta sakemasagdya sannan ta shiga motar, suka kamahanyargida.
Yau wajen sati uku kenan, kullum sai Dr,faruuq ya kirata, wani lkcn ta dauka, wanilkcn taki dauka dan ko ta dauka bashi da watamgnar
da ya wuce ta amince masa, ita kuma yanxukam ba abinda ke gabanta ba kenan.
Ummi ba mata adalci ba da a bashi nmbrta, kuma taje har
gidan nasu ta nuna mata bata ji ddin hknba.
Suna xaune da momy suna kallo da daddareyakirata, ta mike ta shige daki da sauri danbatasan ta jawo hnkln momyn tata, ta daga, taji
Yace"intisaar, tace ina jinka, murya can kasa yacemata " bni da lfya yau, sosai ki mani addu'akinji,
tace "xan mka Allah ya sauwake, yacenagode.
sai da safe, tace tam. Tana fita hanyar ktchen tayi taje ta wanke kwanukan da aka ci abinciagidan dan momynta ce tayi girki, ko da takomapalonsu ihsaan tayi bacci. momy kuwa,Abba yakirasu da su hajiya yana masumagana, tana
kwantar da kanwarta tayi wanka ta kwantaitama.
Washegari bayan sun dawo daga
makaranta, taje tayo wa momynta cefanesukashigo gidan tare da xainab, ita ma an aiketa,kayanta da ta shanya taga fadila tanakwashewa
tana xuba su a kasa, xainab tace "meye hkafadila, fadilar tace mele. Intisaar tace"meyasa
baxaki kira ihsaan ta kai mun ciki ba fadila,"fadilar tace "sbda baki isa ba," intisaar tace"shikenan nagode," kursum ta fito da sauri
tace"kar ma ki gode mana mahaukaciya kawai,
intisaar tace "nagode" sannan ta kwashekayannata xata wuce ciki, fadila ta banke ta,cukumota
xainab tayi tana cewa ke wacce irin dabbacefadila, wllh sai kin gya min me intisaar tatsaremaku a gidan na, kokuwa suka farayi, sai gauwarsu ta fito da gudunta, me ye hka?? Meya
faru, kursum da sauri tace "wancan dabbarce tahada su fada, bata bi ta kansu ba ta cafkointisaar ta dinga xuba mata duka, tana kukatace"
wllh momy ni banyi mata komae ba, ummabata
saurareta ba ta dinga jibgar ta kamranaikota
tana cewa "kaji min matsiyaciya, dan
uwarki, nandin gidan ubanki ne da xaki hada manayara fada
munafuka, tuni xainab ta cika fadila tana"waiumma me tayi maki ne, dan me baxa kitambayi
munafukar yarki abinda tayi ba to.... Tanamagana ne tana kuka, sai ga hajiya ta fitodasauri ta cafke xainab tana cewa , danubankiintisaar kanwar uwarki ce ko ubanki, kukaxainabtake yi kawai, uwar ta watsa mata mari tajefarda ita sannan ta koma kan intisaar, daga itaharumma sukayi mata tatas, da kyar ta samusukabarta ta shige palonsu tana kuka sosai,momynta
na xaune tana yanka alaiyahu. Xubewa kasatayitana kuka sosai, ihsaan ta xauna kusa da itatana
share mata hawaye, momy bata ce komai ba, ta
karbi cefanen ta wuce kitchen, tayi kukasosaihar barci ya dauketa. Da magrib momy tatasheta tayi sllh, ta bata abincin kowa ta kai
masa sashinsa, hajiya ta fara kaiwa, xainabnabakin famfo tana alwala ta karaso da sauritakarba tana cewa kiyi hkuri intisaar Allah xaisakamaki, tayi murmushi bata ce komai ba tawuce. Ta dauki na umma ta kai mata, yusuf ta ganibakin kofa ta mika masa ya amsa sannan tadauki na inna ta kai mata. Tana xaune kandarduma, ta gaisheta, ta dubeta da kyautace
"wa ya saki kuka intisaar,?" ta sunkuyar dakanta
tace "ciki na ne ke mani ciwo, da sauri innatamike ta shige ciki ta dauko magani ta jika tabata tasha, batayi musu ba ta karba ta sha,
innata xauna tana ta mita wai cikinta na ciwobaxa
ta xo ta karba magani ba tana san ta kashekanta, da kyar ta samu ta barta ta wucesashinsu. Tasan dan inna bata nan neshiyasa
sukayi mata hkn, dan da tana nan bbuwanda xaimata hka. Ko da tashiga parlonsu, momy takaiwa Abba abinci a sashinsa, ta dan ci abincitayiwanka sannan ta kwanta. Tana xaune tana
sama ihsaan rani, momy kuwa na daki tajianyisallama, da sauri ta jawo hijab dinta ta sadanyar shimi kadaine jikinta da xani, sannan taamsasllmn tana mikewa, daga wajen yashigoyana
murmushi yace ihsaan lalli ake yi, tace eh"unclesannu da xuwa," ya dubi intisaar yaceyauwa
kanwas ya momy pa, sai ga ta ta fito taceHaisam yaushe a garin, yyi murmushi yadurkusaya gaisheta, yace "da safe naxo momy,amma bn
dde da shigowa gida ba." ayya to ya hanya,? YaceAlhmdllh, ita kuwa intisaar ta mike ta kawomasaruwa ya amsa ya sha yana gdya, suna hiradamomy sai ga kursum, ta shigo ba ko sallama babu.
Tace
"yaya umma na kiranka, yace baki iya
Gaisuwabne, ta yi tsaki tace ina yini ta fice, ya bita dakallo ya kasa cewa komai, ya mike yyi yakeyace"momy da daddare xan xo muyi hira, tace toHaisam Allah ya kaimu, ya dubi intisaar yace"kanwata naga sai kyau kika karawa meyesirrin,
Tayi dariya tace "kai yaya bnda sharri, yyidariya
yace, "da daddare kije wajen inna mushahira,tace "to yaya Allah ya kaimu, sannan ya fice
dasauri dan ya riske Kursum amma har tashigegida. Yana shiga uwar tashi ta farabalbalesa damasifa, ita bata san shige shige da gantali, dagaxuwansa ko hutawa bai yi ba har yaje yawo,yyidariya yace "yau naga ikon Allah, bnda ikonxuwawajen matar ubana, A'a uwar ubanka, bamatarubanka ba, wllh ka fita harkana haisam.
Mikewa yyi yace "to Allah ya kyauta sannanyyi sashinsa yana waige-waigen inda xai gaRahma amma bai ganta ba. Da daddaresukahadu da yaya Haisam a sashin inna, sunyi Hirasosai tun suna yi da inna har ta bingire awajentana barci, Intissar ta dinga dariya, yace "tokarki
tasheta mana kanwa," tace to na daina yaya. Yace to yanxu samarinki nawa,?
Tayi dariyasosai sannan tace "ko daya yaya," yace "kinmaidani wawa ko?" tace "lah, hava yayanawllh
a'a," yace to gya min gskya, tace "Allah yayabana kulasu, yace "to ki daina hka, wataranAbbaxai ce ki fito da miji, idan kuma baki da, xai
iyahadaki da wanda ransa yaso, dan hka, kidai-daita da mutum daya, kuma bance wai ki tarasamari ba, tayi dariya tace "to yayana," a hkaya
rakota har sashinsu yyi mata sai da safe.
Ta fitodaga wanka kenan wayanta yyi kara, sai dayakatse aka sake bugowa sannan ta dauka,
"intisaar," taji ya kirata, ta amsa ba tare datakula ba, yace "ya gida"? Tace lau, yyimurmushi
yace to yyi kyau, dama na kira ne na gaidaki,bye..
Ba shiri ta samu kanta da ce masa yajiki?Yyi jim, sannan yace "to da sauki, ammadaxunnan aka cire min drip, tace "to Allah yasauwake,
yace ameen ngd, sannan yyi mata sallama yakatse wayan. Washegari da ta dawo dagamkrntasai ga mis cals dinsa, ta dauka tana kallonwayan, samun kanta tayi da send din nmbr,ba
tare da ta shirya ba, ya dauka, suka gaisa,sannan da sauri ta fara kame-kame, "emmdama
mis cals dinka na gani," yace hmm, yea nakiraki
daxun, "ok naje mkranta ne," sai tayi da tasanin
kiransa ma, ta dai dake dai tace "ya jikin,"yaceAlhmdllh, daxun ma naje karban treatment,tayishiru, can dai tace "to mene ya sameka?"yace
hmm... Owwh bari na kiraki, na manta wllh,
........
Yana katse kiran nata ya kirata, "yi hkuriIntissaar, i 4got, tace o.k, sannan yace"idona keciwo," 4 d past 4 dayz yanxu,spec dina ya
Bugeni a idon, Ayya, Allah ya sauwake.. Ameen
ngd.
A hankali taji ya kira sunan ta, ta amsa tana
saurarensa, "ki bani ixini naxo gidankumana, dasauri tace "a'a karka damu, kaga bye.. Yanxu
inaaiki ne, sai anjima, ta kashe wayan. Taxaunatayi jim tana tunanin abinda ya Haisam ya
gyamata jiya, ihsaan ce ta shigo tace "Anty, innatace na kiraki, tace "to, tare da mikewa tadaukihijab, sai kuma ta tuna bata cire uniform ba,
tacire, sannan taje kiran da innah ke mata.Rahma da khadija suna wankin uniform dinsu abakinfamfo, suna ganinta sai suka tare hanyarwucewa, ta dan yi jim a wajen, sannan tace
"kugafara xan wuce, Rahmatu tace "idan anki
pa?"khadija ta kara dacewa "ko gidan ku ne
nan?" itadai bata ce komai ba sai kallonsu da ta tsaya
yi,kumfar wankin Rahmatu ta debo da yawa
ta
yarfa mata a fuska, ihsaan ce ta xo da gudutana
cewa me "me tayi maku?" khadija ta tura taharsai da ta fadi, intisaar ta kalleta cike datakaicitace "ita kuma me tayi maki khadija"?
Ihsaan
kuwa tuni ta mike tana kuka ta cire talkaminkafarta tana dukanta dashi, daukartakhadija tayia fusace ta tsoma ta cikin guttern dakewajen,
intisaar bata san lkcn da ta fixgo khadija batadinga dukanta har ta jefata cikin kwatan
itama,da gudu rahmatu na kuka da ihu taje ta kirahajiya da umma, dan suna kusa da gate axaune. Da gudu kuwa suka karaso wajen, hajiya tafara ciro 'yar tata daga ciki kwata tana salatitare da cewa "mai xan gani hka?" ummahkuwata cafko intisaar din da ta juya da gudu xatabarwajen, dukan fitar hnkli ta dinga yi mata dadukakarfinta, hajiya ma ta xo ta sa hannu, kukaihsaan ta dinga yi tana kwalawamommynsu kira,sai ko gata ta fito, ta kallesu bata ce komaiba,ta juya ta wuce abinta, su fadila da kursumduksun fito, hka aka dinga hayaniya, dukansunaxagin intisaar, "wllh sai naga bayan ku da
uwarkua wannan gidan, shegu munafukai kawai,tunda Kuka shigo gidan nan muke.... Muryar inna
dasuka ji na ya katse su, sai ummah dake tataunan cingam, "me xan gani hka Aisha?"
cewarinna knan tana duban Hajiya baki bude,ummahtace cin halin ko in kula, gata nan kitambayetamana, hajiya ta maxa tace "kashe min 'ya
xatayida har xata danneta tana duka?" innah tadubiintisaar dake ta faman rusa kuka ita daihsaan,
tace "nashiga uku ni Rahmatu, yanxu me'yar nantayi maku da har xa kuyi mata taron dangi?
Harda gore gore ina ji?" nan fa inna ta dingarusamasu kuka har da durkushewa a wajen,dagahajiyan har umma suka tabe baki, hajiya
tace "toinna da yafi da ne?" sunan momyn intisaarinnata shiga kwalawa tana cewa "zainabu,
zainabu,da sauri ta fito tana cewa "na'am inna?"inna tasharbe majina tace "ke wai wace irin sha-sha sha
ce, ynxu kina ciki ana neman kashe makiya'ya kin ki fitowa? To Allah ya isa ban yafe ba, wllhtllhsai naci uban mutum yau, ta fadi tana kallonhajiya da 'ya yansu gaba daya, Zainab ce takaraso da sauri dan dama bata gidan, tanacewa
"inna me ya faru,?" inna ta ciro wayarta dasauri
ta mikawa xainab tace "maxa ki lallubo min number Abubakar, jikinta na rawa ta saka nmbrAbbansu
ta mikawa inna, inna ta karbe da sauri tace"Abubakar maxa ka dawo gida yanxunnan,.. A'a
idan kaxo ka gani, ta mikawa xainab wayantace"kashe min kayana, sannan ta kamo hannunintisaar din ta wuce sashinta da ita, ihsaan
nabiye dasu. Tab! Hka hajiya tace cikin tashinhnkli, yanxu hadasu tayi da Alhaji sbdawannanAgolan, lallai akwai sake, nan xainab tabarsu atsaye ta wuce, momy kuwa tuni dama takomasashinta, ummah ta dinga gyada kai tanacewa
"yau munga ikon Allah agola ta fi masu gida,nansuka dinga tsakar wa momy habaici damaganganu marasu dadi, ita dai bata tanka ba
tana daki abinta, Haisam ya shigo yanadubansu,
mamaki ya bayyana a fuskarsa yace "momymeyafaru, hajiya tace "agola ce tafi ya'yanmasu
gida, yau munga ikon Allah, tsaki yyi ya barwajen kawai, ya samu xainab tana kwashekayanta, ta gya masa abinda ya faru, saikawaiyyi sashin inna, tana xaune sai rusa kukatake
tana Allah wadai da matan Abubakar, danko itabasu ganin girmanta, kuma yau tasu ta kare
agidan nan, intisaar na xaune ta xubawa TVido,
dan ita bata ga abin kuka a nan ba da innaxatadinga yi, ihsaan kuwa na lullubeda towelalamar
wanka tayi, haisam yyi sallama ya shigo,batajiraya xauna ba ta dinga jero masa abinda ya
faru,sai ka rantse kace tana wajen, hkuri ya
dingabata, amma kmr yana xugata, dan hka sai yajuya ya dubi intisaar yace "ki yi hkuri
intisaaridan Abba ya dawo xasuyi bayani, da sauri
innatace sake kira min Bukar din, ko abinda yke
yiyafi kiran nawa ne, a lkcn Abba ya shigo
gidandamotarsa, haisam yace to gashi can ma yadawo,
tashi tayi da sauri taje ta samesa, haisam yagirgixa kai ya mike ya dauki ihsaan yace"srrykinji ko bby, yau nasan ai Abba sai yyi masubulala tunda suka tabo mamarsa, dariya
kawaiihsaan tayi, sai ga Abba da inna sun shigo,
haisam ya mike ya bar parlon bayan yagaidaabban nasa, intisaar a xata tashi inna tace"dawoki xauna, sannan inna ta fara jawabinta
tanamatsar kwalla, ya ma rasa mai xai ce, kawaisaiya mike, yace "ina xuwa baba, ya fice, sashin
hajiya ya nufa direct, ya dinga kwada matakira,
Aisha, Aisha, tace na'am Alhaji sannan ta fitodasauri tana cewa lfya kke kwada min kirahka,
yace "maxa ki bar gidan nan ki tafi gidanku,danban aure macen da xata sa mahaifiyatakuka ba,bai jira cewarta ba, yyi sashin Shafa, watoumma,ita ma ya gya mata hkn sannan yace dukwandaya dawo ya samu bai tafi ba to a bakinaurensa,ya juya ya koma wajen inna, hka ya dingabatahkuri sannan ya tabbatar mata da duk suntafigida, nan inna ta samu natsuwa dan itakadaitasan irin wlkcn da matan nasa suke mata,dakuma yanda suka sa xainabu da yaranta agaba,
sai da ya tabbatar ta hkura sannan ya daukiihsaan yyi hanyar sashin su intisaar din,intisaar
ta mike taje tayi wanka a bayin inna, ko datafitosina xaune da haisam tana tayi masa mita,intisaar tace inna wllh kin cika mita, inna
tace"nayi din, sannan taci gaba daga inda tatsaya,"
da kyar haisam ya samu ya lallabata ya barmatadakin, Abba kuwa ya kira su kursum dakhadijagaba dayansu yyi masu ta tas, sannan yasasukneel down a tsakar gidan, ya tabbatarmahaifiyarsa ta sakko sannan ya komaoffice,
Su Aisha da Shafa kuwa tuni suka bar gidandansunsan Alhaji baya magana biyu.
Washegarin ranar suna xaune ita da xainab
Dr faruuq ya kirata, taki daga wa har sabiyu xainab tayi mata mgna sannan ta daga,
Sukagaisa, tayi masa ya jiki, yace "jiki da saukiintisaar, ya su momy?" tace "lau suke" ohk..Inakofar gidanku... A dan firgice tace "me?"yace
"eh".. Kaga bna san hka malam ka rabu danidanAllah, ta katse wayan da sauri. Xainab taceb"waye?" intisaar tayi tsaki tace "oho nimaina nasani, wai wani gashi a kofar gidanmu saikace nagayyato sa, wllh xan bata ma ummi rai ne, ni
Tadaina min shisshigi," xainab ta mike hadeda tabebaki ta dauki hijab, intisaar tace "ina xaki?"ba
tace komai ba har sai da ta isa bakin kofasannan tace "am cummin" sannan ta fice. KofarKofargida ta nufa, bakin gate ta tsaya tana waige-waigen inda xata hango bakon intisaar din,hardai ta hangosa jikin wani flower yana tsayeyanadanna wayarsa, ya daga kai yana kallonta....Nan
ta gane shine bakon, dan da alama waniyakejira, tace "kai ne faruuq wai?" ya dubeta dakyauyace eh nine, tace "bisimillah wai ka shigo,"yace"to ngd sosai," tare da binta har cikin gidannasu,
tayi masa iso har sashin inna. Tana xaunetasaTV a gaba wai tana kallo, xainab tayisallamahtashiga tana cewa "inna kinyi bako," innatace"waye?" xainab ta xauna gefenta tana yardariyatace "saurayin intisaar ne, wai kunyar kawomaki
shi take yi," da fara'a sosai inna ta tarbesa,tabude fridge ta kawo masa ruwa da lemotana samasa albarka, hkn yyi ma faruuq ddi sosai
yadinga gdya, nan dai inna ta dinga jan sa dahiratana basa lbrin Intisaar, xainab kam saidariyatake yi, ta mike da sauri ta barsu tayisashinsuintisaar, intisaar tana xaune tayi shiru,alamar
tana cikin damuwa, xainab tace mata "meyafaru?" tace "wllh xainab ni bna sanwalakantawannan mutumin amma yasani gaba...
Xainabtace "to kuma meye abin damuwa bayan kinkoresa?" intisaar ta tabe baki tace bbu!
Xainabtace gskya kam, inna dai tace na kiraki tanajiranki, xainab na kai wa nan ta fice ta barmata
parlon. Jikinta a sanyayye ta dauki hijab tayisashin inna, tayi sallamah, inna ta amsa dakarfinta har abin ya ba intisaar dariya, koyaufarin cikin me inna take yi hka? Duk da
takalminda ta gani bakin kofar inna bata kawokomai a kaba, dan a tunaninta ya Haisam na ciki ne,
tanashiga palon tace "ya Haisam ka min promise
ndfail ko? Cak ta tsaya ganin faruuq xaune aparlon, kanta ya dinga mata wani irin juyi takasafahimtar komai, ya dago kai yana dubantakawaiba tare da yyi mgna ba, dakin inna ta shigedasauri, inna tace "yo kunyar me xaki ji kuma?Saikawai ta fashe da dariya" intisaar taji wani
irintakaici ya lullubeta, yanxu xainab ta kyautamataknan?
Sa ta tayi taje wajensa bare har tashigodashi gidansu kuma ma wajen innarta,
Sallamanya haisam da taji ne ya sanya ta kararudewa,inna kuwa sai xuba take ta wa faruuq,
shima yabiyeta suna ta yi, inna ta amsa wa haisamsllmaya shigo, tana wangale baki tace "haisamwannan saurayin intisaar ne yaxo gaisheni,haisam ya kallesa da mamaki suka gaisa dafara'arsa, sannan yace "to ina intisaar dininna?"
inna tayi dariya tace "wai ita kunya tun daxuta shige daki," haisam ya kirata ta fito gabantana
faduwa ta nemi gefen inna ta durkusa tanagaishesa, ya amsa yana daria yace "wayewannan?" ta kalli faruuq tace "nima ban san
shiba " dariya haisam yyi yana kallon inna, shi
kuwafaruuq yyi murmushi ya dukar da kansakawai,
hka Haisam ya ci gabada xolayarta amma itahnkalinta na waje daban, tunani kala kala yakasu a ranta, da daga kai ta dan saci kallonfaruuq din suka hada ido ta kauda kanta da
sauri,hka suka ci gaba da hira gaba dayansu
ammabnda ita da ta kurawa plasma ido. Wayan
haisamda yyi ringin ne yasa inna ta dakatar dasurutunta tana tambayansa waye, salanta
knan,da taji wayarka yyi ring xata tambayekawaye dasaurinta, yace mata mijinki ne, sannan yadaga,bai jima yana mgna ba sukayi sallamah yakashewayan. Inna tace Aliyu ne ko wa? Yace "eh
shine" inna ta girgixa kai tace "oh yaronnan baida kirki, halinku ba daya ba da nashi, bai dakirkiko kadan, bai yo halin Bukar ba, halinsa saknauwarsa... Haisam ya maxa ya katse ta yace
"toxabiya, ni xanje GRA ne ynxu sai na dawo"tace
to... Amma me Aliyun yace mka yanxu,?
Yausheyace xai dawo,? yana ina ne yace mka? Kode
yana hanya ne? Cike da kufula Haisam yacekaini inna ban sani ba, ca yyi na gaida innaRahmatu kawai, sannan ya mike sukayixchange
din nmbr da faruuq, yyi masu sallama yafice,
intisaar ta mike da sauri tace "inna bari narakasa gate ina xuwa"inna tace to kiyi maxamaxa ki dawo, tace to. Sannan tabi bayanhaisam da sauri.
Haisam ya dubeta yace "saurayin naki yahadu intisaar, ta ce "bna so yayana, ni ba ninakawosa gidan nan ba, yyi dariya yace "bndakarya dai kanwata" nan ta marairaice masa
Tayimasa bayanin yanda suka hadu da faruuq Harxuwa yau da ya xo, yyi dariya sosai sannanyace
"to amma kanwata naga ai bai da aibukumayanada hankali, ki dan basa dama mana."ita daibata ce komai ba har suka iso gate sannan
Yadubeta da kyau yace "kar fa ki ki komawakanwata, kinsan dai walakanci bai da kyau,kibasa dama ku saba, tace "to yaya baxangudu baxan koma" yauwa kanwata gud of you.
Nan sukayi sallama ya wuce ita kuma ta koma
Sashininna. Suna hira har ynxu, ta nemi gefe taxauna,tana jinsu kawai sai dai tayi murmushi. Sai
Wajenkarfe shidda yyi sallama da inna, ya batakudimai yawa, ta karba tana godya, hkn yyimugunbata wa intisaar rai, kamr warce ke jiramaimakon tace ya barshi, har bakin kofainna tarakosu sannan ta koma ciki tana masa Allahyakiyaye hanya. Suna tafe ne bbu wanda yacekomai, can dai ya dubeta yace "ngdintisaar,"bani ce da gdya ba, ta fadi ba tare da takallesaba. Yace to waye? Bata kallesa ba tace
xainab,yyi murmushi yace gskya ne, bbu wanda yasake
mgna a cikinsu har suka isa gate sannan yadubeta ita ma ta kallesa, sai ya sakar matamurmushi , ta sunkuyar da kai da sauri,bata
sanlkcn da itama tayi murmushin ba. Yyi ajiyar
xuciya yace "to kira min xainab din muyisallama," aa dare yyi ka bari sai wani lkcin,
yaceba nan gidan take bane?" eh nan takeamma
ynxu ta shiga gidansu. Yace gskya ne. Tointisaar i am vry grateful, ngd sosai, tagyadamasa kai kawai sannan ya juya ya fice, ta bisa
da kallo, ya juya suka hada ido kunya yakamatatayi saurin rufe gate din sannan tayisashinsu.
Gabanta yyi mugun faduwa ganin su
Kursum labe ta windo suna kallonsu, da sauri tayisashinsu tabude kofa ta shige. Ko da tashiga ta tarar
Momybata ciki, tayi hanyar kitchen, ta ganta daxainab Suna raba abinci, taimaka masu tayi sukagama
A tare, ita ta kai ma inna nata, xainab kuwa takaima su kursum nasu, intisaar bata ce daxainab
komai ba, itama xainab din haka.su hajiya kamyau kwanansu uku basa gidan, xainab batadamuba, hka ma haisam ko a jikinsa, su kursum
dai nehankalinsu a tashe, momyn intisaar tayikkrinshawo kan Alhajin amma hkn bai yiwu ba,innakam ko a gyalenta, dan gidan ma sai yyi
mataddi. A kwana a tashi intisaar suka shaku dafaruuq sosai, fiye da tunaninta, faruuqmutum ne
mai kirki da fara'a, duk gidansu an sanshidanduk jumm'ah sai yaxo gaida inna sannan yashigaya gaida momy. Su fadila da su kursum kambakin ciki kmr xai kashesu, gashi yau wajensatiuku knan Alhaji yaki barin iyayensu su Dawo.
Intisaar ta samu kwanciyar hnkli sosai agidandan bbu mai takura mata ynxu, yawanciIdanfaruuq yaxo gidan tare suke xaunawa har
Daxainab suyi ta hira, a wajen ummanta kuwabatada hiran da ya wuce na faruuq, hka ma awajen
inna. Abba kadai ne bai san dashi ba a gida,amma har su Hajiya da umma da basa gidan
'yayansu su kirasu sun fesa masu. Yau ma kmr kullum faruuq yaxo gidansu da yake Friday ce,
wajen karfe shidda ta rakosa xai wuce sukaiskefadila da khadija a kusa da gate a tsaye, dukdasun gansu amma basu yi kkrin matsawa
dagagate din ba, faruuq dai bai ce komai ba dantundayake shigowa gidan basu taba bude baki
sungaishesa ba, shima bai taba masu maganabadukda ba ma ganesu yke yi ba, bayan ga xainab.
Dakyar intisaar ta iya cewa ku gafara dan Allah,ganin sun kusa minti uku a tsaye kuma sun Kibarin hanyar, ke din a su wa?
Khadija ta jefomata tambayr, tayi shiru bata ce komai ba,khadija ta kara da cewa "nan gidan ubanmu
Nedan hka ba ki isa kixo ki mana iko dashi ba"saiki bari idan kin samo ubanki sai kiyi iko dagidansa idan ma yana da" fadila ta fadi awalakance tana girgixa kafa, kuka ta sakar
Masua wajen, faruuq kam kansa ya daure, ya ma
Rasame xai ce, khadija ta dubesa "bawan Allahkanabani tausayi wllh, ga ka kyakkyawa maiasali,
amma ka rasa warce xaka bige da nema saiwarce har yau ba a san ko yar gidan uban
wayebace, sai yar tsintuwar innarmu, da sauriintisaarta juya da gudu ta bar wajen, ya bita dakallo,
bakinsa yyi masa nauyin kiran sunan natama,
fadila taci gaba tana kallonsa, "ita ba yarkowabace, sannan ta samu wajen fakewa agidanmuita da uwarta sai su dinga mana isa, yauwatadaya da sati biyu knan da suka sa Alhaji yakoreiyayenmu a gidan nan sbda ita da uwarta,kadijatayi tsaki tace "ai basu ga komai ba matukunna,sai suma sun bar gidan nan kmr yanda sukasaaka kore uwata." fadila tace "nima hka,"
sannan
suka bar wajen gate din suka shige cikingidaxuciyarsu pal da murna. Sai da faruuq yyikusanminti biyar a wajen a tsaye, sannan ya bargidanjikinsa a sanyayye..
Momy ta dube Intisaar dake ta famankuka tun da tashigo a karo na farko tayimatamgna "me ya faru?" ta girgixa kai tana gogehawaye, cikin kuka tace "momy wai ni kigya minranda xan ga abbana, na gaji da gorin daakemani," hawaye ya ciko idon mahaifiyar tata. Tayi kokarin gogewa da sauri tace "me kuma yafaru?"
cikin kuka me tsuma xuciya intisaar ta koromataduk abinda ya faru, momy ta goge hawayenidonta tace "kiyi hkuri intisaar, watarana sai
lbri,
na sha gya maki" sannan ta mike tana cewa"saikiyi ma faruuq din bayanin komai, sannan tashiga dakinta." bayan faruwan hkn da
wajenkwana uku faruuq bai ce mata komai ba,iyakadai ya kirata suyi hira sosai. Ranar watalarabayake ce mata yana so su hadu gobe da
daddarea kofar gidansu, bata yi masa musu ba taceAllahya kai mu, amma gabanta na faduwa dan
tasanbaya xuwa gidansu sai ranar juma'ah.
Washegarin ranar alhamis ta gyawa
Ummantayanda suka yi dashi, tace "shikenan, ammakarkiboye masa komai intisaar," tace "to momy."
sannan ta wuce sashin inna ta taya ta hira.
Koda wasa bata gayawa inna abinda su fadilasukayi mata ba, ta barshi a xuciyarta kawai.
Da yammacin ranar wajen karfe bakwai damintigoma faruuq ya iso gidan nasu, ta nemiixini gunmomynta ta fita da cewar ba ddewa xatayiba. KarKar Abba ya sameta a waje.
Yana xauna kanwani dakali, ta karaso wajensa, ya tare ta damurmushi, tun kan ta karaso wajen
Kamshinturarensa mai ddi ya doki hancinta, takallesahade da sunkuyar da kai, ya mike yana matasannu da xuwa. A hankali ta gaishesa, ya
Amsayana cewa "ya momy da inna?" tace sunalfya.
Sannan ya xauna ya nuna mata gefensa, ta Dan yi jim, kmr mai naxari sannan ta xauna. ShiruShirubbu
wanda yace komai, can dai ya katse shirunyace
"i luv yhu my Intisaar," ta rufe fuskartakawaibata ce komai ba, ya kalli fingers dinta yace
"ringdin waye wannan?" tace na xainab ne, yace
Ok, ita ta baki? Uhm ko kana so ne? "yace aa da Dainaki ne" tayi murmushi kawai. 'intisaar' taji
Yakirata a hankli, tace "na'am" a sanyaye. Lbrinrayuwarki nke so ki bni yau, kinga am vrybusybut na ajiye komai aside, dan naji tarihinintisaardita. Ta kirkiro murmushi kawai bata ce komai ba. Bismillah if u re ready, tace "uhm to ta
Inaxan fara?" yace "ko ta ina ma Intisaar," nan da nan taji hawaye ya ciko idonta sannan tafara batare da bata lokaciba.
Ni sunana Fateemah Umar faruuq,
Ya xuba mata ido yana kallonta, can dai yasakarmata murmushi ya gyada mata kai alamartacigaba, ta cigaba ba tare da ta kallesa ba, ninataso ne a Zoo road nan kano da mahaifiyata,tana yi ma wata aiki lkcn ina da shekarahudu,
momy tace min a nan gidan ta haifeni in datakeyin aiki, dan ta fara aiki da sati biyu ne tahaifeni. Inna ita ce warce ummata ke yi maaiki,da farko dai ni na taso a tunanin inna ce tahaifeni, amma ita da bakinta ta kan ceminnadaina damunta ga mamata can, a hankli dainagano wacece mahaifiyar tawa, inna mutumcemai kirki sosai, ko sau daya bata tabawalakantamu ba, ta dauki ummata kmr ita ta haifeta,nikuma ta daukeni jikarta. A kwana a tashi
inna tasani a sch, lkcn har na isa primary 5,watarana asch aka ce mana kowa yaxo da babansaxa'ayimeetin, ni ban kawo komai a ka ba dannasanummata xata xo min, amma muna shiga ajisaiwata classmate dita maimuna tace min"intisaarke kina da Abba ma kuwa? Bamu sanbabanki ba,mu babanmu xai xo gobe. Tun da nake bantabakawo mahaifi a rai ba sai rannan, sai naji ba ddi ganin yanda kowa ke dokin babansa xai xo,nakagu mu tashi naje gida a gya min inda
babanayake, dan ba'a taba min mgnarsa ba, ina isagida Kuwa da tambayar da na tari mamata knantanawanke wanke, naga tashin hnkli ya bayyana a fuskarta sosai, inna ta fito da sauri tanacewa,waye ya aiko ki? Nace gobe akace mu kawobabanmu a makaranta, inna ta ja ni tashigardanidakinta tace "ki kwantar da hankalinki yarlele ta,gobe uwarki xata je, nan na fashe mata dakukanace ni dai babana ne xai je ba mamata ba.
Innata hassala tace "to dan ubanki xauna ki ji,babanki bamu san inda yake ba,mahaifiyarki natsince ta a titi ne ranar na dawo daga gidanaminiyata, tana da cikinki lkcn, a sume mukakaita asibiti mu da bayin Allahn dake wajen,
bayan kwana biyu ta farfado, cikin bayinAllahnda muka kawota asibiti ni da wata baiwarAllahkadai muka rage, dan sauran duk sun tsere
dawashegarin ranar. Ana sallamota na kawotagidana. Ita kuwa talatu, sunan matar knandamuke ta sintiri da ita a asibiti, a haife dai nahaifeta, na nuna mata xan kula da
mahaifiyarkixainab, dan itama ta damu kwarai da gaske,
tokinji dalilin ganin ki nan gidan da kikayi, inna
tacigaba tana kallona, bayan satinta daya nagatawarware sosai, nake tambayrta ita wacece.
Nanmomy tabawa inna tarihinta, tace daga
Misrataxo nan Nigeria, mijinta ne ya barta wajenwatatara knan bata san in da yake ba, sbda Bakincikin hkn ne ya sanya ta kasa gano yandaakayita baro Egypt, kawai ta ganta a nan Nigeria,
sannan tace ma inna tana da kishiya kuma ataresuke, to bayan sati daya inna tace ummatatahaifeni a nan gidan nata, danta tasa yayankamin rago aka sa min fateemah, Sauran
bayanandai ne duk na manta. Da yake lkcn ba wani
wayogareni sosai sosai ba ban wani nunadamuwanada yawa ba, washegarin ranar inna ta kiradantamuka je meetn din mkrantar tare. Inna tamanaabinda ko na jininmu baxai mana ba, innatatausayawa mahaifiyata sosai, duk da dailkcn dukwannan abun da take ba da san ran dannatabne, dan baya san yanda inna ta makalemanadaga ganinmu ba wai saninmu tayi bakuma tayrda damu, amma ta nuna masa bai isa yahanata abinda tayi niya ba. Lkcn ina da 3 yrs
inna ta tilasta ma danta yyi mana visa mukajeegypt nemo mahaifina, har da ita. Da kyarummata ta iya gane gidan abban nawa,amma koda suka je, sai suka ga wai stepmum dita tasaida gidan, hka muka sake dawowaNigeria.
hankalin momyna a tashe, inna ta dingakwantar mata da hankali tana cewa wataranaabbana xaixo gareta, wannan ba komai bne illa aikinasiri damuguwar abokiyar xaman tata tayi kawai.
Tundaga lkcn inna ta dauki ummata kmr yar ta,
Ta nemo wata yar aikin daban dan yanxu waimunxama yan gida.sai abinda baxa a rasa bakaidaimomy ke mata, inna da ta tashi sani amkrnatsai ta sani a mkrntar kudi, Abba na biya,ummata
gani tayi kmr inna ta daurawa dan natanauyinmune, dan shima yana da nasa iyalin, dan lkcnmatansa biyu da ya'ya shidda, dan hkamomytace wa inna ta barta dan Allah ta nemiwanidan aikin da xata dinga yi, inna ta nunabacinranta sosai, tace momy kar ta sake matahka,
bbu ruwanta da lamarinta da na danta dantsakaninsu ne, sau dayawa duk bayan satibiyusai jikokin inna sun xo gidanta, ba karamintsanata sukayi ba baya ga xainab dake sonasosai, kuma dama sa'a ta ce, na sha hantarawajensu da na iyayensu, basa sona damomyna,sun tsanemu, bn san ko dan muna cin arxikinsu bne, Abban nasu kuwa tun yana dauremana da,har ya sake mana sbda yanda yagamahaifiyarsake sanmu sosai. Ya maida ni kmr yarsa,
komaiyyi ma yayansa sai yyi min nima. Tun asalidama yaya haisam yana ji dani sosai, ya daukeni kmrkanwarsa kuma yana girmama mahaifiyata.
Inada shekara 12 lkcn ina jss2 inna ta hadaaurenmahaifiyata da danta, wato AbbansuHaisam.
Ba karamin tashin hnkli momyna tashigaba dan babana bai sake ta ba ai, inna tadingamata jaraban wai ynxu kusan shekara 13 knan tana jiran wanda kila yanxu ya mace, kumama aia musulince ta halatta tayi aure tunda yadderabon da ta gansa ko sanin inda yake. Hkananinna tasa Alhaji Abubakar ya aure ummata,
Shibai nuna abin ya damesa ba, dan dukabindamahaifiyarsa take so shi yke yi. A hka ni damomyna muka koma gidansu dake shagariqtres,
wato wannan gidan na yanxu... Uhum tadanyishiru sannan taci gaba ganin yanda faruuqkekallonta a raunane, tun daga ranar har yauni daummata bamu samu farinciki ba gidan nan,saiwajen Abba da inna, sai kuma xainab dastepbrother dinta Haisam, sun tsane mu,basason mu, sun takura mana, kumahar yau
basutaba shiri da ummata ba, ita kuma tundatakebasu taba mata abu ta tanka masu ba,shiyasahar gobe Abba ke alfahari da ita kuma yanaji daita, momyna tana da hkuri sosai, da kau dakaiakan abu. Ihsaan kadai momyna ta haifa anangidan, bayan nan bata sake haihuwa ba,
Yanxu ihsaan shekaranta kusan 6 knan. Sbda irinyandasuka samu gaba ne ya sanya inna ta sa abba
Yagyara mata sashinta na nan gidan ta dawo,dandama can yayi-yayi da ita ta dawo nan daxamadan ya kula da ita da kyau amma taki dan bagirmamata matan nasa ke yi ba. Hkn yakarawamomyna tsana a wajensu hajiya, dan innatafififfitata a kansu, kuma tafi son ni da ihsaanakanya'yansu, a makaranta daya muka gama secsch
da xainab, fadila da kursum, khadija darahmakuwa suna ss2 ne ynxu hka.
Hajiya Aisha itace
matar Alhaji ta farko, ya'yanta uku, yayaAliyu,xainab da khadija, ita kuma umma shafaya'yanta
hudu, yaya haisam, fadila,kursum da rahma,saijikanta yusuf dan fadila ta taba aure ammasunrabu da mijin. Faruuq yyi ajiyar xuciya yace
"toshi yaya Aliyun yana ina?" ta dan xaro ido tace
"nima ban sani ba wllh," amma baya gidanynxuhka, ok xainab ce kanwartasa knan, eh...tacekanta a sunkuye, to meye na kuka intisaar,
Wllhnaji na kara sonki ne ma, ya ciro
handkercief yagoge mata fuskarta. "i luv you my intisaar,"
tagyada kai kawai ta kasa cewa komai, ki baniixinina turo gidanku plss, ta danyi jim, sannantace tosai nayi shawara da innata, yace o.k gobemaxan xo ai wajen innar, da kyar ya bartatashigaciki dan duk ya birkice mata ta amince masakarta ya dashi, shi din mai sonta ne da gskya,harbakin gate ya rakota ta shiga sannan yawuce,
Taji ranta yyi fari sosai, taji ta kara sonfaruuq…….
Washegarin ranar da magrib faruuq ya bargidansu, sun dde suna hira da inna dagabisannitace idan tayi shawara da danta xatagayamasalkcn da xai turo, har gate ta rakosa, yaya haisamya shigo suka gaisa da faruuq, ya danxolayeta Sannan ya wuce, faruuq ya dubeta yace
"yanaaiki ne haisam,?" tayi dariya tace kaibarrister nehka pa da ka gansa, a Abuja yake aiki kila
hu2yaxo nake ga, yace " to shi da Aliyun wayebabba?" ta danyi jim sannan tace "ya Aliyunemana" o.k shi kuma Aliyun wani aikin yakeyi?
Ko bai fara ba? Tace "wllh nima bn sani ba,"ya
dubeta da tuhuma yace "baku interact dashine?"
tayi murmushi tace aa ni bamu san junasosaiba,
o.k... Duk xamanki gidan nan baya nan ne?
Tadan xaro ido tace "a'a yana nan mana,"
Faruuqyyi murmushi yace "ko bae sake maki bne?"
Tadanyi shiru sannan tace uhm, dan ita batamasan ana tuna mata ya Aliyu ko kadan, duk takagu ya rabu da ita da xancen Aliyu, shi kammurmushi yyi yace "to shknan intisaar, nixan tafi,ya ciro kudi mai yawa ya bata," tace hava na
Mene yaya, yace yau juma'ah shi yasa, tace a'a nagode,ka barshi kawai, ya bata rai yace "tundamukedake na taba baki abu intisaar? Wllh nasanabinda nakeyi, ki karba nace, da kyar takarbatayi masa gdya sosai, sannan tayi sashinsudasaurinta. Xaune take a kasan parlon Abbayanaduba jarida, can dai ya dubeta yace "me ya
Faruintisaar ya akayi ne?" a hankli ta faramaganamuryarta na rawa, Abba dan Allah danannabikayi hkuri ka bar su Hajiya da umma sudawo,Abba ya katse ta da sauri yace "to ai ni bnida tacewa a nan, sai abinda kakarku tace, dan itakeda iko dani, kinga kuwa bni da laifi a nan."
Tayishiru, sannan ta mike tace "to Abba shknan"ta Fice ta bar palon. Yyi murmushi dan yasanuwarta ce ta turo ta, dan ya nuna mata kartasake masa mgnarsu Aisha kwanaki uku da
Sukawuce tana basa hkuri. Intisaar na fita sashininnata nufa, ko da tayi mata mgna ma bata rai
Tayisosai, tace "maxa fice ki bni waje ka finraina yabaci, idan ma uwarki ce ta turo ki kije kicematanace tashiga hankalinta, idan ba naci ba mamutanen da ba sonta suke ba ta wani damukanta a kansu" intisaar ta fice mata dagapalonnata a fusace dan ita bata san me inna take
Nufiba, to don me baxa su ci darajar ya'yansuba maa barsu su dawo gidan. Ita kam tausayinxainabdasu kursum take yi sosai, shi kam haisam
ko ajikinsa dan ko xancen ma baya so. Tana tafetana waya da faruuq, ynxu kam shakuwarsuyawuce misali, dan inna kadai yake jira tayi maabba magana dan shi a shirye yake, kuma yace xai dauke mata nauyin kara2n ta gaba daya,dariya tayi sosai tace "kai ya faruuq wajeninnapa xani ba wani gun ba, yace "ohk ai nayi xaton fita xakiyi ne shiyasa nace hkan," a hka takarasosashin inna tana ce masa "yayana ko sllh mapabn yi ba" yace "hva de kanwata gashi harwajenkarfe takwas, to kiyi alwala a bakin tap, nanwajen kafin ki shiga mana," tace "dama hknxanyi yayana, bn gama abinda nkeyi bnedaxunshiyasa lkcn sllhn ya wuceni" ko da ta isabakintap din ma sai ta tarar ana alwala, tace "kgayaya haisam ma na alwala a wajen," yahaisam,yayana yana gaisheka wai, hka nan suka ci
gabada hira da faruuq tana jiran haisam itamatayialwalan sai ta shiga ciki, "hmm to shknankanwata yi alwalarki anjima mayi magana,"faruuq ya fadi yana kkrin kashe wayan, tacea’a
ai ya haisam bai gama ba, dariya faruuq yyiyace
"baki gajiya da jin muryata ko bbynah?"
kunya yakamata tace "lalle ma yayana to bye" oh srry
myintisaar wasa nke maki, a dai-dai lkcn maialwalan ya dago, sukayi ido hudu da yaAliyu,wani irin muguwar faduwar gaba yaxomata,bakinta ya fara karkarwa ta ma rasa nemomgnar da xatayi masa, kallo daya yyi matayadauke kai ya shige parlon inna.
Faruuq kamyakira sunanta yafi sau biyar, duk da wayanna karea kunnanta amma ta kasa cewa komai, haryagaji dan kansa ya kashe. Kasa koda motsitayidaga gun da take, ta dai dake a hnkli ta juyaxata koma sashinsu taji inna ta kwado mata
kira,
da sauri ta dawo amma ta kasa amsawa, tajiinna nacewa "Aliyu ba muryar intisaar nake
jidaxu a waje ba?" shi dai baice mata komaiba illadardumar da ya dauko ya shimfida, a'a
baxakamasallaci bne, yace eh... Ya tada sallansakawai.
Sai da inna ta leko tayi ma intisaar mgnasannantayi alwala tashigo palon, gabanta namugun
Faduwa.
Sai yanxu kika ga daman xuwan knan,
intisaar ta dube innar tace "aiki nke yi ne" tokeda faruqu kke waya ko wa? Tayi shiru batace Komai ba sai hararan innar da takeyi, innatatabe baki taci gaba da dama furar da takeyi,
Aliyu ya idar ya mike, inna ta dubi intisaartace "ba ki ga yayan naki bne ba ke," ta dubesa dasauri tace "ina yini yaya," lfya kadai yace ba
Tareda ya kula ba ya nemi guri ya xauna, inna ta Nunamata dardumar da ya mike daga kai tace
"kijekiyi sllh ga shimfida can, ta mike take ta tadasallah tana dan satan kallon Aliyun. Har taidar.
inna bata daina mitan da takewa Aliyu ba narashin son xuwa gida ba, don ynxu ma badanubanshi ya kirasa ba, ba xuwa xai yi ba, shi
kamhankalinsa na wajen news din da yke kallogabadaya, hka tayi ta surutu intisaar na kallonsukmrtayi dariya, inna tace "iyye!! Gamahaukaciya namagana ko? Shi kam bai ma san tana yi ba,
innatace "ba mgna nke mka ba Aliyu," ganin baisantana yi ba yasa ta daka masa tsawa ya dawodaga kallon a dan firgice, "wai meye ne hkainnarahma?" ya tambayeta a fusace, ta mike takashe TVn, kan ta juyo shima har ya mikexai fita, ta juya tana dubansa tace "ynxu Aliyu ni ka maida mahaukaciya," to hva inna news pankekallo kke takurani hka, ta tura kofarta ta
rufe,tana cewa "sai ka tambayi haisam yandaakayi anews din" yyi murmushi ya xauna yace toinajinki tsohuwa, ta koma ta xauna ta dinga
masabnasiha ya daina abubuwan da yake yi, yagirgixa
kai yace "to menake yi inna?" kusan kullumsaiBukar ya kawo min kwamplan a kanka,dariya yyisosai yace "to ayi hkuri Hajiya" ta hade raitaceka tsaya ka saurareni ni dai," nan tacigabadabatunta, shi kam wayarsa ya fito da ya na tadanne danne. Ganin wannan nasihar ba maikarewa bane yasa intisaar ta mike tace"inna niguga xanyi, xan tafi," ehh dama tsifa xakiyi
minkuma xainab da kursum sun min daxu,gobe dasafe dai ki xo, tace "to inna, amma baki bnifurarba," inna ta dubi furar dake gaban Aliyun
tace"ga na Aliyu bai sha ba ki dauka kije dashi"intisaar ta dago kai ta dubi Aliyun ta gakallonta yake yi, suna hada ido yyi murmushin da takasa gne ko na mene, amma dai tasan bna arxikibne ,
ya kalli inna a fusace yace "to sai nace makibaxan sha bane" inna ta tabe baki tace "je ki
kidauko kofi ki diba," kai dai ban san waniirinmutum bne, har yau baxaka canxa halinkaba ko,
wae ma dan meyasa baxakayi koyi daHaisam bane, nan kuma ta fara sabon fadan, intisaardai tadeba wanda xata deba tace "to inna sai da
safeni na wuce" Allah ya kaimu. Inna ta fadi batareda ta kalleta ba. Ta dan saci kallon Aliyun dayamike tsaye yana duban inna kawae kmr yamareta, intisaar ta bude kofar ta fice, ya juyashima ya fice, inna tana baxaka sha furarbnekuma, bai ce komai ba ya fice abinsa.
Intisaar natafe tana waige-waige, can ta hangosa daganisashima ya fito ta xuba a guje, taji taci karo damutum, ta daga kai a tsorace sukayi idohudu daHaisam, yana kallonta yace lfya? Tana mai danumfashi tace tsoro nke ji ne, Aliyu yakaraso,
haisam ya dubesa ya dubeta, yace "ina yinibro,"ya amsa hanklinsa baya wajen, sannan ya
dubiintisaar yace "wllh wllh ki ka sake ganinakkakwasa a guje kmr kinga uwarki to sai naciubanki,na maki dukan fitar hankali, kanta a kasa
tace "nisauri nke yi ne shiyasa nke gudu," bai bi takantaba yyi gaba abinsa yana cewa "ko ma uban
mekke yi ni dai na gya maki" haisam ya dubetayace
"ki daina gudu idan kin gansa, shima aiyasan koyyi hauka ne baxai taba ki ba," bata cekomai batayi ma Haisam sai da safe sannan tayihanyar
sashinsu. Tana isa ta tarda rahmatu daxainab aparlonsu, ba abin mamaki bne don tagarahmatua sashinsu don duk fitsararta ita da kursumsunashigowa khadija da fadila dai ne basashigowa,
wajen karfe tara da rabi ta rakasu sashinsu,
xainab na mata dariya tace " kinga babankidaxua wajen inna," tayi murmushi kawai dansbdayanda take mugun tsoran Aliyu suke cemasababanta, don ko momy da Abba batabtsoransubhka, ita kam duk duniya bbu wanda taketsorokmr Aliyu, baxata taba iya mantawa da Aliyuba arayuwarta..
Inteesar Tana xaune a balcony tana ferewa momydankali, momy na wanke-wanke a bakintap, tadubi momyn tata tace "momy yaushe yaAliyu yadawo?" momy ta juya ta watsa mata harara
Tace
"ya xa'ayi na sani ni kuwa, kinga yaxo
Gaishenihar ynxu, bare nasan ya dawo ko kumayausheya dawo?" intisaar bata sake cewa komai ba
Tacigaba da abinda take yi. Xainab ce ta karasodasauri, tayi ma momy sannu da aiki sannan tadubi intisaar tace "inna tace na kiraki" takammala abinda take yi da sauri, sannan tanemiixini wajen momynta, tace "to amma kiyimaxa kidawo xaki min abu ne" to! kadai tace sukawuce.
A hanya take tambayar xainab me xata yiwainnar, xainab tace "aikenmu xatayi wai" abakinkofar inna suka tarda ya Aliyu tsaye, yana taxuba, xainab tace "kai yaya har ynxu bakaragewannan surutun naka ba sai ma....." da sauriyajuya yana kokarin cafkota yaga tare suke daintisaar, nan da nan ya hade rai, ya lekaparloninna yace "inna ni na tafi," tace aa har mungama hirar mai gidana,? Bai ce komai ba yabarwajen, xainab tace kai! Yaya kaga yandakayiwani irin fresh kayi kyau? Tab! Inna ce tafito dasaurinta tana cewa "Aliyu xo dan Allah." har
Yyinisa ya juyo tare da cewa ya akayi? Xo danAllahnace. Yace "aa ni baxan iya dawo wa ba."sannan yyi gaba abinsa, inna tayi tsaki tacegantalalle kawae, dama hanya nke son yaragemaku wllh, intisaar tace "aa bama so inna,
Da mayaya Haisam ne." dole ta basu kudin motardaaiken da xasu kai wa kawarta hajiya maimuna. Sun isa gidan suka bata sakon, tayi ta samasualbarka sannan ta basu dari biyar su haumota,
Jikarta murja ta rakosu har inda xasu haumota,sannan ta koma. Xainab ta dubi intisaar tace
"kk muyi save din kudin mu, mu taka kawaitunda bawani nisa, da kyar ta lallaba intisaar sukafaratrekkin don da kin yrda tayi. A dai-dai wanikatonpharmacy faruuq ya fito rike da leda ahannunsa,xainab ce ta fara hangosa, tace "lah..Intisaarkinga faruuq," da sauri intisaar ta juya suka
Hadaido, ya sakar mata murmushi ya karaso dasauriyace "daga ina hka?" suka gaya masa dagaindasuke, bayan sun gaisa ya bukaci da ya rage Masuhanya, bbu musu suka shiga, yyi drop dinsuakofar gidansu, suka fito suka yi masa gdya
sannan ya kashe wa intisaar ido, ya ja motaryawuce hade da cewa sai munyi waya, kugaidamin da inna." Aliyu suka ci karo da a gateyanatsaya, cak suka tsaya ganinsa a wajen,xainabtayi karfin halin cewa "yaya me kke yi anan?" yaxura wayarsa cikin aljihu sannan ya ddubet dakyau yace "motar uban waye kika shiga?" tahade rai tace "saurayin intisaar," ya bude
bakiyana kallonta, ganin yanda tayi mgnar kotsorobbu,kika ce me? Ya sake tambayarta, tamaimaita ranta a hade, mari ya watsa matamairai da lfya, tuni intisaar ta fara karkarwa,xainabkuwa ta fashe da kuka, ya fixgota , ta turasadakarfinta, ta xuba a guje sai bangaren suintisaar,bin ta yyi da saurinsa, intisaar kuwa naganin hkatayi wajen inna da gudu gabanta nafaduwa.
Parlonsu intisaar xainab ta afka, ya bita harcikiyana cewa "dan ubanki yaushe na farawasadake xainab," tayi bayan momy da gudu
Tanahakitare da goge hawayen fuskrta tana kumahararansa, momy ta dubeta tace "me ya faruxainab," ta fashe da kuka tana cewa " marina yyimomy banyi masa komai ba, kuma Allah yaisaban yafe masa ba," dan uwarki xo ki fita, yadakamata tsawa a fusace, xainab ta wasa mashiharara tace "anki din, kuma ka sake mamutanekofar su ka bar wajen, tunda a gidanku ba akoyamka kayi respect ba, bare har kayi gaisuwa."
Tuniidonsa yyi jajir yana kallonta kamr wanixaki.
Momy ta dubi xainab tace "shiga daki
xainab," tashige da sauri, ita kuma taci gaba da abindatakeyi," da kyar ya iya sake kofar parlon yaja dabaya kmr ya hadiyi xuciya, tsaye yaga sukhadija,kursum, da rahmatu suna kallon abinda yafaru,
wani irin wawan kallo yyi masu da yasasukakwasa a guje suna dariya. Kmr ance ya juya
tagefensa ya ga intisaar a tsaye, duk a birkicetake,
yana juyowa sukayi ido hudu, ta budo kofaratsorace xata shige parlonsu ya cafkota, kuka
tasaka tana cewa "nashiga uku yaya, wllh kayihkuri bni bace ba..... Bai ko kulata ba ya cire
takalmin dake kafarsa ya dinga xuba matadakarfinsa kmr an aikosa, kuka takeyi tana
kiranmomynta, yace "don uwarki an gya maki inada lkcnki ne bare na lamarinki,to ba a mota ba,ko ajirgi ne akayi park dinki a kofar gidan nanbburuwana, na dai ce maki ni ba dodonki bne,idankka sake ganina kika gudu sai na babbalaki
jakarbnxa kawai mahaukaciya, ya turata cike datsanayana huci, haisam ne ya iso wajen da sauri
yanacewa "hava Aliyu, me tayi mka hka xakabiyotahar kofar daki kana dukanta, Aliyun yahararesayace to sai ka rama mata
..
Haisam ya tambayesu me kuka yi masa,xainab ta fito tana goge hawayenta tace"inna ceta aikemu, shine don yaga Faruuq ya ajiyemusai yake xagina har da duka," ta dubi
Intisaartace "kema meyasa bakiyi wajen inna bakika xonan," ta goge hawayen idonta tace bata nanne, adai-dai lkcn inna ta bullo, ta karaso dasaurintatana dubansu tace "me ya faru, hatsarikukayi,ne? Nan da nan ta rude masu, haisam yyidariya,xainab kuwa ta kwashe duk abinda ya faru
Tasanar da inna, nan inna ta dinga bala'i tanamasifa tayi dakin Aliyun tana cewa Allah ya isar masu. Haisam ya dubi don intisaar ta rigatashiga ciki yace "momy bata nan ne?"
Xainabtace tana ciki, ya girgixa kai yace ammaAliyubashi da kunya ko kadan. Ya shiga sukagaisa da
momy, sannan ya basu hkuriya bar sashinnasu.
Suna xaune su uku suna hadawa yaya
Haisamkayansa don anjima xai komai Abuja, xainabtalinke wa, intisaar na gyarasu cikin jaka,rahma dakursum na kwance da yake a dakinsa suke,sunakallo
Xainab ta dubi intisaar tace "jiya faruuqsaewajen karfe goma ya bar wajen inna,"
intisaar
tace "hva" ba tare da ta kula ba,xainab taceehmana, ai can na kwana, kursum ta dubixainabdin tace kai xainab tara da rabi fa naga yabargidan nan. Xainab ta dubeta a fusace tace"jakabki ji abinda nace bne?" ca nayi har wajenkarfegoma, bnce karfe goma ba, ita dai intisaarhankalinta na wajen abinda takeyi bata cemasukomai ba. Ya haisam ya shigo yace idan sungama su rufe masa dakin, xai je wajenummarsayyi mata sallama, kursum tace "ayya yayaxanbika don Allah, abba baya bari muje wllh" yadubeta yace to xo muje, nan rahma ma tacexatabisa, yace duk su xo su tafi, ya tambayi
xainabko tana da sako dan xai je wajen hajiyarsuma,tace aa kawai dae ya gaisheta. Nan yakwashekanninnasa sukayi gidanmahaifiyarsu donyasansunyi kewarta sosai barin Rahma autar ta.
Bayansun tafi ne intisaar take tambayr xainab inakhadija, tace mata sun fita tare da ya Aliyu,batasake cewa komai ba don tasan yana ji dakanwarnan tasa khadija duk cikin kanninsa saekumarahma da kursum. Jiya maganar aurenkufaruuqyyi da inna pa.. Intisaar dai bata ce matakomaiba ita kuma taci gaba da maganarta " tace
Yabata sati biyu don akwae wani shawara dasukeyida Abba ne," intisaar tace "uhmm" ta cigaba dabinda takeyi kawae. Basu bar dakin ba saiwajen karfe biyar na yamma, sannan sukakullomasa kofar sukayi sashin inna, hirar daxainabtayi mata, shi innar ma tayi mata, ta kara dacewa "ynxu dai nace masa ya dawo bayansatibiyu kafin lkcn mun gama shawarar dababanku"
ita kam intisaar binta tayi da uhm kawai. Suna cin abinci da daddare khadija ta shigo, innatacesae ynxu? Tace eh, ta nemi kujera takwanta,
inna tace " to ina Aliyun?" tace oho! Kamr yaknan oho? To ni da kafa na dawo don ban Sakeganinsa ba, xainab ta fashe da dariya tace
"Allahya kara," intisaar dai jinsu kawae take yi, tamiketace inna ni sae da safe don barci nke ji.
Tana tafe a hnkli cikin sassarfa kmr mara gskyatajikamshin turaren Aliyu, gabanta yyi mugunfaduwa, tasan duk yanda akayi yana nan
wajajen,nan da nan ta fara neman wajen da xatabuya,har wani rawa jikinta yke yi sbda tsoro, jikinwataflower dake wajajen ta labe xuciyarta nabugawa,
yana ko karaso wa dae-dae wajen sai yatsaya
kmr mai tunani, ganin hka ya sa ta fasa ihudona tunaninta ya ganta ne, ba karamin firgitayyi bada karar da tayi, ya koma baya da sauri yanasallati, da sauri ta fito daga flowern ta nakokaringudu, yyi hanxarin cafkota, ta kara fasa
masawani ihun, muryar Abba sukaji, yana cewa"fateemah me yafaru?" ba shiri ya cikata
tare dadurkushewa yana kallon kafarta yace
"subhanallaimae kika taka?" Abba yakaraso da sauri
wajen,me kka taka fateema, me ya faru, ta ma rasa
mexata ce, amma har ynxu jikinta bari yake,Aliyun
yyi maxa yace "ina jin abu ta taka naxowucewane naji tana ihu," tambayar Abba ya sake
jefomata muryarta na karkarwa tace "Abbanima bnsan meye ba" Abba ya ciro da torch yana
haskakafar, Aliyu ya karba yana duba mata kafaryace"sannu, amma ai ba komai a kafar, yana
makiciwo ne," tace aa da sauri, Abba yace "toAllahya kiyaye dai, me ya hanaki kwana wajeninna,?
Tace bakomai, yace "to Aliyu dan rakatacikingida," yace to Abba, tashiga gaba yana biyedaita a baya, Abba kuma yyi nasa parlon.
Tana gaba yana biye da ita a baya, yanadan waige-waige yana duban kofan palonabbannasa, har dai yaga ya kashe wutan parlonalamarxai shiga bedroom dinsa knan, ya ji ddinhknsosai, ya juya da hanxari xai shige gabantaamma yaga wajen wayam bbu kowa, itakam
abba na shigewa palonsa tayi ta kanta dantasan sauran bayanin, cikin rashin sa'a ta tarda momy ta kulle kofa, a rude ta shiga jijjiga
kofartana kwalawa momyn nata kira, momyn tatamaa tsorace ta iso xata bude kofar tana cewa"lfya,
menene,?" amma tuni ya karaso wajen, taxabgaihu tana "wayyo momy ki....." bugun da yakaiwabakinta ne ya hanata karasawa, a dai-dainan Momy ta bude kofar, hkn kuma bai hanasariketakmr wata 'yar shi yana duka ba, momy tajuya takoma ciki ba tare da tace komai ba, "donAllahyaya kayi hkuri wani abu ne ke bina shi yasanayi ihu," dukanta ya dinga yi ba sassaucihar daidaga karshe yyi wani irin juyi da ita yawurgar,sannan ya bar wajen yana huci kmr xaki,kuka tadinga yi tana kiran ummanta, can dae ganinmomy ba fitowa xatayi ba yasa ta mike da
kyarta shiga palon nasu. Ita dai har tayi barcimomybata ce mata komai ba, sai ma ca mata datayixata kara mata idan bata rufe mata baki ba,
doletasa ta hadiye kukan nata har bacci yyi gabadaita. Da safe ita da kanwarta suka gamabreakfst,ta kwashi kwanukan xata je ta wankemomy tagatana dingishi, "xo nan intisaar", ta dawotanakallon momyn tace na'am, me ya samikafarki,
"yaya Aliyu ne ya buge min kafar" to yyikyau, Jeki. Haushi ya cikata sosai amma bata cekomaiba ta gama wanke-wanken ta ja kanwarta
Sukayisashin Abba su gaidashi. Inna na palon nasa A xaune rahma na kusa da ita a xaune, a taresukashiga parlon da xainab da ita ma taxo gaida
Abba, abba ya dubi intisaar da ta nemi guritaxauna yace "ya naga kina dingishi,?" innatace"me ya samu kafar," tace "bugewa nayi"garinyaya? Inna ta tambaya tana kallonta, abbayace"ko dae jiya kin ji ciwo ne?" eh kadai tacesannanta fara gaida abba, ya amsa, xainab ma tagaidashi, ya dubi intisaar yace "to bari Aliyu
Yaxo ya duba maki kafan ko?" bata ce komaiba,
sai TV da ta kurawa ido. Anjima xaku jegidannafisa ku taya ta gyare-gyare ta dawo jiyadadaddare, Nafisa kanwarsa ce, kuma autawajeninna, shekaransu goma knan aiki ya kai
mijintagermany, xainab taji ddisosai, intisaarkuwa batawani santa sosai ba, xainab tace "to abba
wa xaikai mu ne, bamu san gidan ba ai, abba yace
"ehAliyu xai kai ku dama ai," a dai-dai lkcn Aliyuyashigo palon da sallamarsa , yana sanye da
Fararshirt da bakar wando, kamshin turarensa yagauraye ko ina, ya nemi gefe ya tsugunna yagaida inna, ta amsa tana cewa sai ina? Baikulata ba ya gaida abbansa ya amsa yana
Cewaka tashi lfya? Bai ce komai ba ya maidawayarsaaljihu ya xauna. Xainab ta dubesa tace "inakwana yaya?" yace "lfya lau" intisaar ma tagaishesa ya amsa da lfya! Abba yace "yauwaxaka kaisu jan bulo gidan Nafisa ina fatan
Kasanta dawo, ya hade rai bai ce komai ba, xainabtace"ki tashi muje mu shirya intisaar," abba yace
"kugyawa fadila ma, har da ita xaku." suka ce to, sannan suka mike xasu bar palon. YauwaAliyuka dubawa fatimah kafarta dingishi take yiwaijiya bugewa tayi, ya dago da sauri yana
Kallonkafartata, ita kam da sauri tace "lah Abba
wllh bawani ciwo yke min ba ya ma daina." inna
tacemunafuka a hkn ya daina maki ciwon? Batatanka mata ba ta fice da sauri xainab ta bibayanta. Fadila xainab taje ta sanarwaabindaAbba yace, ta kama hanya abinta ta wuce.
Dakyar xainab ta lallaba intisaar ta shirya donkukata dinga mata wai bbu inda xata Aliyu kashe Taxai yi a hanya, tun xainab na dariya har ta
daina,tace "wllh bai isa yyi maki komai ba..
Ba don ta yarda da maganar Xainab ba tagama shirinta, don tasan kila ma ya damketaxainab din ba tsayawa xatayi ba. Su ka yiwamomy sallama, ta hada su da ihsaan suje, a
Canbangaren inna suka sami Aliyun, inna tace"maxaka kai su Aliyu, bai ce komai ba ya mike yaficesuna biye dashi a baya, intisaar duk a
Tsoracetake, kofar gida suka yi gaba daya, xainab
dai saikallon ikon Allah takeyi, suna fita ya cirodububiyu ya mikawa xainab yace "gashi ku haubike,ni ina da waje mai important da xa ni," bani
wayarki na sa maki nmbr Nafisan idan kinjecanki kirata..... Ta mika masa yasa mata nmbrsannan ya mika mata wayanta, yyi wajen motarsa dake parke a gurin, ya bude knan ihsaan tace "uncle amma kai dady yace ka kai mu,"yajuya yana kallonta sannan yace "xo nan,"
intisaarta ruko ta da sauri dan xuwa xatayi, waniirinkallo yyi mata ba shiri ta sake kanwartata, tatafi
kuwa da saurinta, "me kika ce?" ta sakemaimaitawa tana kallonsa, rankwashi ya kaimata a ka har sau uku, ta fashe da kuka,
yace"na taba wasa dake ne?" nan da nanhawaye yaciko idon intisaar, xainab ma ta hade raiammabata ce komai ba.... Daga ta yyi sama ya sako
gaban motar sannan ya kulle motar ya ja tasukayi gaba, intisaar ta xaro ido tace "ya tafi daitaxainab," xainab tace "mu tafi kawae ae xai
dawoda ita," ba don ran intisaar ya so ba xainabta jata suka yi busstop, don duk hankalinta na
wajenkanwarta, kuma taso taje ta sanar da momyamma xainab ta hanata, wae ai ba gudu xai
yi daita ba. Anty nafisa tayi farin cikin ganinsusosai barin yanda taga sun xa ma yan mata gabadaya. 'ya'yanta biyar suma duk sun girma,
Antynafisa tana da kirki sosai, aiki suka je taya taamma bata bari sunyi komai ba sai hirar dasukadinga yi, basu bar gidan ba sai wajen karfetakwas mijinta ya mai dasu gida, ta cika sudatsaraba sosai, sannan tace ita ma xata xogobe.
Amma abinda ya daure masu kai bai wucerashinganin fadila a gidan ba amma basu cekomai basuka ja bakinsu sukayi shiru. Ko da suka
Koma gida Aliyu bai dawo ba, hnklinta ya tashisosai, ta
gyawa momynta da ihsaan ya fita tun dasafe,momy bata ce komai ba tana ta harkargabanta,
ganin hka ne yasa tayi sashin inna ta gyamataita da xainab, inna tace "duk inda suka jexasudawo, meye abun damuwa, ba kanwarsa
bace,"
ita dae hnklinta bai kwanta ba. Xainab tabajewainna tsarabar da nafisa ta basu, tana ta saalbarka. Karfe tara da minti hudu Aliyu ya
shigopalon, yana rungume da ita tayi bacci...
Inakukaje hka Aliyu, yace "in da kka aikeni," batasakecewa komai ba, ya kwantar da ita sannanyace"sae da safe" ya fice. Da sauri intisaar ta
Miketaje kusa da ita da durkusa tana tada ta,
Innatace "ya haka tana barci xaki tashe ta, je kishinfide ta a daki" ta dauketa tashiga daki
Takwantar, sannan ta fara duddubata don ita
Batayarda da Aliyu ba kilama cutar ta yaje yayi, sai Da inna ta kirata sannan ta dawo parlon, inna
Tace"Aliyun ya shiga ya gaida nafisa,?" duka suka yiwuri-wuri suna kallon inna, intisaar ta maxa
taceeh," to meyasa fadila baku dawo tare ba?
Tun takwas ta dawo ita, xainab tace "ohonmata," nandae inna ta dinga yi masu surutu, harintisaar ta
mike tace "inna ni dae sai da safe bacci na keji,"
kamar warce ta tuna abu kuma tayi saurincewa
"au na manta a nan xan kwana, sannan tashigedakin inna," sae da tayi wanka tayi shirin
Baccifaruuq ya kirata, sun jima sosai suna waya daga bisani sukayi sallama ta kwanta.
.
.... Yau wajen watan su Hajiya uku basagidan, bbu yanda momyn intisaar bata yi daAlhaji ba amma yaki hucewa, inna kuwaidan kana son ganin bacin ranta kayi matamaganansu, ko kayi nuni da cewar tayihkuri tabar Abba ya dawo dasu, nan da nan xaku Batada ita. Yau Aliyu ya cika sati hudu da dawo
wa,har ya gaji da yi ma Abbansu magiyan yabaruwarsa ta dawo gidan, Anty nafisa ma taxo
tayima inna magana da ta fuskanci abinda akeciki,amma tace lallai sai sunyi shekara daya agidaniyayensu, abun yana damun Aliyu sosai,xainab ma harta fara damuwa, ita kuwa fadila daman satan hanya take yi taje wajen mahaifiyar ta suyi ta sake sake da kwance kwance.
Yaukam abin ya ishe Aliyu yaje suyi tata kare da inna,tana xaune gaban akwatin talabijin waetanakallo, intisaar tana daki lkcn tana kwance,
Aliyuya nemi gefe ya xauna yace "inna wajen kinaxo,"
tace "to sannu da xuwa" ya danyi tsaki yace “nifa inna na gaji da rashin uwata a wannangidan, ke waye ya raba ki da danki da harxakirabamu da uwarmu sbda wani dalilinbanxa, toni de na gaji wllh, idan xaki kira danki kiyimasamagana ya maido min da hajiya ta gidannan to,idan kuma ba hka ba wllh na bar gidan nansaekun sake ganina, ta juya tana kallonsa tace"kwantar da hankalinka, uwartaka tacidarajarintisaar xan sa a maido ta, amma ba donhka bawllh sai na nuna masu ni na haife Abubakar,
yace
"darajar wa?" inna tace "intisaar," dondaxun nantaxo ta sani gaba tana kuka, kuma don hkaxansa a maido Aisha da shafa, wani irin bakin
Cikida takaici ya mamayesa, ita intisaar dinwaceceda har xa aci darajar ta, lalle inna, ya dubetayace " intisaar din banxa, ai sae daimahaifiyatataci darajarmu ba ta wata intisaar ba,wayanintisaar dake palon ya fara kara, inna takwalomata kira taxo ta dauki wayarta kuma wayeyakirata," ba karamin tashin hnkli Aliyu yashiga bada ya gano intisaar na dakin, a sanyaye tafito tadauki wayartata ta koma ciki, ya mike a fusace yana duban inna, "wllh idan kika sake
Takuramauwata a gidan nan hajiya Rahmatu sai na......
Kamin duka ko? Inna ta karasa masa, danbnxanyaro fitsararre, mai halin bnxa kawae, yajuyayana dubanta yace ni? Tace a'a uwarkaAisha, yyihuci yace shknan mu xuba dake, ya juya yaficea fusace, a gaban wannan jakar inna kexaginsa,tab lallae, inna ta fashe da dariya tana "donubanka ya ka wuce, ka tsaya mana muga ni Dakai waye tatattce, bai tanka mata ba yyigaba,
Yaron bnxa kawae, kai Allah dae ya shimaHaisam Albarka yaro mai kirki, mai hankalidabiyayya, intisaar ta fito tace "hva inna donAllah
ki dena biye yaya Aliyu, inna tace "mantadashi dai dai nke dashi dan uwarsa, kuma bariuban
nasa ya dawo, kece shaidata kinga daiyanda yaxaxxageni, intisaar ta xaro ido a tsoracetace "A'a wallahi ni ba shai'dar ki...
Tana kwance a palon momyn ta suna kallon tashar Kidscov ita da ihsaan, momy kuma tana bedroom kursum tashigo, "intisaar ana kiranki," ta dubeta da sauri tace "wa?"
Kursum tace "inna" ta mike da sauri kmr dama jira take tace "momy inna tana kirana," momy tace "sai kin
dawo" kursum tace "ina kwana," lfya lau, momy ta amsa daga ciki sannan suka fice, a hanya
intisaar ke tambayarta ko aiki inna xata sa ta, kursum tace "oho tana dai palon abba," su
ka shiga da sallamarsu palon, inna na xaune kan carpet xainab na kusa da ita, Abba na xaune
yana kallon Aliyu dake durkushe a gefensa kamar me neman gafara, fuskar nan tasa a hade, nan
da nan taji gabanta ya fadi, ta daure ta nemi gefen xainab ta xauna, ta gaidasu.... "ehe , ki
gayawa babanku abinda Aliyu yyi min jiya, don ya karyatani ynxu," inna ta fadi tana kallon
intisaar ranta a hade. Abba yace "intisaar ki gaya min me ya faru jiya, me Aliyu yyi ma Inna?
Intisaar tuni ta firfito da idanuwa a tsorace tace "ni?" inna tace "kwarai kuwa ke kadai ce
shai'data a nan don ya karyatani," Ni Hajiya ki daina cewa na karya taki don.... Abba ne ya katse shi da
tsawa "wllh ka sake bude bakin ka a nan Ali xan watsa maka mari," Abba ya dubi intisaar yace "ina
jin ki fateema," ita kam tuni ta fara rawan dari, ta juya ta sace kallon Aliyun, ta ga kallonta
yake yi, idon nan nasa yyi jajur. Ta girgixa kai muryarta na rawa tace "wllh Abba ni ban
san komai......" inna ta daka mata tsawa tace "to ke din ma karyatani xaki yi, bayan nace kina
wajen kuma kece shai'data,?" aa inna, ta fadi tana kokarin maida kwallar da ta taru a idonta, xan fadi
gaskiya. Ta juya ta kara sacen kallon Aliyu, har yanxu kallonta yake yi, ta ma rasa wani irin
kallo yake mata, can dai tace "Abba dama yaxo ya same inna ne akan maganar dawowarsu
Hajiya,
shine sae inna ta fara masa masifa......" fashewar dariyar xainab ne ya katse ta,
Abba yace "meye haka,? get out" da sauri xainab ta mike ta fice tana dariya. Inna kam tuni ta
Bude baki tana kallon intisaar, Abba yace "ina jin ki fateema" ta dan gyara xama tana kallon
Aliyun sannan taci gaba " shine sai bai ce mata komai ba, tana ta fada har......" murmushin da taga
Abba yayi ne yasa tayi shiru. Sai a lokacin inna Ta saka salati tana tape hannu baki a bude,
Abba ya dube intisaar yace "je ki fateema" ta mike da sauri ta bar falon ba tare da ta kalle kowa ba.
Da sauri ta shige palonsu, momy dake xaune ta dubeta tace "lafiya?" ta kirkiro murmushi tace
Ba komai. To ranar dai Intisaar ko nan da kofa bata fita ba, tana palo a xaune har da yamma,
Xainab ta shigo tana ta tuntsirar dariya, ita dai bata Ko kalleta ba ma, ta dae gama dariyar ta ta fita.
Wajen karfe biyar taji muryar inna da alamar sashinsu xata yo, da sauri ta figi hijabinta ta
fice, momy tana ina xaki amma tuni ta fice, ta canxa hanya don ma kar su hade da innar,
Ta sashinsu xainab ta bullo, xainab tace "daga ina haka? Ina xaki" ko kallonta ma bata yi ba tayi
gaba abinta, dariya xainab tayi tace "yau yarinya ta watsa ma innar ta kasa a ido," hanyar gate
intisaar tayi har wani xaxxabi ma take ji, xaune taga Aliyun a kusa da gate yana waya......
.. Yana ganin ta kuwa ya mike, ta tsorata sosai ta juya xata gudu, yayi hanxarin fixgo ta,
Ta saki kuka tace "na shiga uku me nayi....." tura ta da yayi ne ya sanya ta hadiye sauran
Maganar tata, "Allah ya taimake ki yau da sai nayi gunduwa gunduwa da ke" ita kam babu baki
Sai gyada masa kai kawai takeyi, tashi a gaba kar nayi ball dake, da sauri ta fice daga gate din
Ba tare da tasan inda xata ba. Gidan wata kawar xainab dake nan layin ta shiga, farida tayi
mamakin ganinta don tasan baxuwa gidansu intisaar take ba, nan dai ta tsaya har tayi
maghrib sannan ta kama hanyar gida, yanxu tsoranta daya gamuwar ta da momynta don
tasan inna ta gya mata. Tana isa gate tayi jigum a bakin gate din ta kasa shiga, can dae sai
ta fara leke-leken cikin gidan, taji an kirata, da sauri ta juya a dan firgice suka yi ido hudu da
faruuq,
"lah.. Ya faruuq yaushe kaxo?" yace "hmm” leken
me kike yi a cikin?"
no xainab nake jirane, mu shiga ciki," tayi saurin shigewa gidan, ya bita a
baya yana murmushi, yasan ba gaskiya ta fadi ba.
Ta juya ta dubesa tace kaje can wajen inna gani nan xuwa dama momy ce ta aikeni," to bari
Na fara gaida momyn mana," da sauri tace "a’a kadai je gun inna idan xaka tafi sae ku gaisa,"
yace ok
sannan yayi sashin inna.
Tana isa kofan parlonsu sae da tayi kusan minti biyar sannan ta shiga,
momy da ihsaan na cin abinci, ta nemi gefe ta rakube, momy ta harareta bata ce komai ba.
A haka suka gama cin abinsu. momy taje tama ihsaan wanka, ita dae tana nan a bakin kofa
A xaune. Xainab ta shigo da sallama tace "ke yar walakanci ce pa yarinyar nan, shine xaki bar
bawan Allah tun daxu yana jiranki," ta mike da sauri tace "bari nayi wanka na manta ne,"
sannan ta shige bathroom tana satan kallon momy dake shafawa kanwar tata powder. Ta saka
kayan barcinta sannan ta dora dogon hijab har kasa ta fito, ta dubi momy tace "ina xuwa momy,"
ko kallonta ma bata yi ba ta fice a sanyaye, ko me inna ta tsara mata oho. Tana isa sashin inna
ta nemi gefe ta tsaya sannan ta fara kiransa, bugu daya ya dauka tace "ka fito ya faruuq ina
nan waje," yace "baxaki shigo....." da sauri ta katse sa ta hanyar cewa "aa ka dai fito ina jiranka
sannan ta kashe wayan" ya dubi inna yace "inna ni xan tafi sai wni lkcn," aa to ina intisaar
dinm baxa ta xo bane, yace "aa tana nan waje tana jirana.
Yana fitowa ya kalleta yayi murmushi yace "sae yanxu?" bata ce komai ba sae gyada
Masa kai da tayi, sae da ya fara shiga suka gaisa da momy sannan ta rakosa gate, ya dubeta yayi
Yar dariya yace "me ya hadaki da innar taki baki San shiga wajenta?" tayi yake tace "aiki xata
sani ne shi yasa" yyi dariya yana kallonta yace "ke dae fadi gaskiya kanwata," ta kauda kai bata ce
komai ba sae hmm. To bara na wuce kar Abbanki yaxo ya same mu a nan ko?" da sauri tace
"wa?"
ya kashe mata ido yace "Aliyu mana" tace
"uhum kaga sai da safe ya faruuq yau ba hira kake san min ba" yayi dariya yace "dama ae wuce wa
Xanyi bayan kinsan kin wa inna laifi xaki turani can" bata ce komai ba sai murmushin da tayi, ya
Ciro kudi mai yawa yace taba ihsaan, don yasan ita ba karba xata yi ba, shima din da kyar ta
Karba, suka yi sallamah ya wuce, sannan tayi
sashinsu.
Tun faruwar abin suke wasar 'yar buya da inna, yau dae kam har dakinsu inna taxo ta
sameta, tayi mata tatas, ita dariya ma abun ya bata, can dae ganin ba kyaleta inna xatayi ba tace "to
naga dae inna ba sharri nayi......" dundun da inna ta kai mata ne yasa ta fashe da dariya, tace
"kai ni inna ki kyaleni, haka kawae ban ji ba ban gani ba ya Aliyu ya min duka," da kyar inna ta kalleta
Ta bar sashin nasu, momy dae bata ce masu komai ba, sai gashi da daddare wae xata wajen
inna, momy tace "amma baki da kunya wallahi" tayi dariya tace "to momy ae dae inna ta ce."
A hanya suka hadu da xainab, ta bude baki tace yau kuma wajen inna xa a? Har an manta... Duka ta kai
mata ta bar wajen da sauri, xainab ta bita ita ma tana cewa "tab ae wllh sae na rama" da
sauri ta bude kofar palon ta afka ciki tana dariya,
Inna tace "lafiya ke da wa?" ta juya da sauri xatayi magana sae kuma tayi shiru ganin Aliyu
xaune a parlon yana cin abinci... Xainab ta shigo ta da'da mata duka ita ma sannan tace "na rama"
intisaar dae bata ko kalleta ba sae kame-kamen da ta fara yi, inna tace "ku dae ban san randa
xaku girma ba," Aliyu ya mike yayi tsaki ya dube
xainab yace "get out kar na fasa maki kai," ta harare sa
tace "saboda kan nawa......" da gudu ta fice ganin ya yo kanta, ae intisaar na ganin haka ita ma
ta fice a guje, inna tace "kai wallahi mugu ne yaro nan" kofar ya rufe ya dawo yaci gaba da cin
abincinsa yana kallo. Suna xaune a palon inna,
xainab na daddanna mata kafa, intisaar kuwa kallo takeyi sae kursum dake kwance ita ma
tana kallon, inna tace "wannan yaron yace xae xo da bakuwa yau ko me xamu girka mata?"
xainab ta yatsine fuska tace wai Aliyu? Inna tace "eh," ta tabe baki tace abinda muka dafa a gidan
xamu bata mana. Khadija dake dakin inna tace "kamar ya abinda muka dafa xamu bata? Ita bakuwar
xa a ba wa dafa duka?" xainab tace "shi kuma dafa dukan ba abinci bane ba koh?" khadija tayi
tsaki tace oho. Kar ki min rashin kunya wallahi don xan fasa maki baki, xainab ta fadi tana kokarin
mikewa, inna ta fixgota tace rabu da ita.
kursum je ki ki kira min Zainabu, da gunguninta ta fice wae ita ta gaji. Ba a jima ba momy ta
iso, inna tace "zainabu shinkafa da miya xaki girka min, wae Aliyu xai xo da bakuwa, wannan
gantalallun 'ya yan sai yawo suke da hankalina.
Ta ce "to inna sannan ta fita." xainab tace "inna budurwarshi ce?" inna tace kya barni
budurwa,"
kursum tace yau akwae buduri kenan. Nan inna aka tashi aka fara gyare gyare su xainab na
tayi mata dariya kuma suka ki taya ta, intisaar kadai ce ta kama mata aikin don wae bayan
la'asar xasu iso. Momy ta gama girki ta kira xainab taxo ta dauka ta kawo sashin inna. Karfe hudu
da rabi ya shigo parlon da sallama, yana sanye da kananan kaya yayi kyau sosai, inna ta amsa
da fara'arta tana cewa "ina yarinya," yace tare muke, sannan ya dubi su xainab yace "ku kuma
uban me kuke yi a nan, da sauri intisaar ta shige dakin inna, xainab ma ta bita kursum kadae ce
taki tashi, har yarinyar tayi sallama da siriyar murya, inna ta amsa da karfinta tana wangale baki,
yarinyar ta shigo palon.
... Tana shigowa palon ya nuna mata kujera ta xauna, kursum dake kwance dama tuni ta
mike tana karewa yarinyar kallo, doguwa ce kyakkyawa fara amma da ganinta kasan ta
hada da mai, tana sanye da atamfar Holland an mata shegen riga da skirt dinkin ya dameta sosae,
sannan ta sakale wani dan guntun mayafi kalar atamfar tata yellow a wuya, make up kuwa
har da na hauka don har da su blusher, sae
wani yatsine fuska take, inna dama tuni bakinta a bude yake... Kursum ta dan sa kafa ta bugi
inna alamar ta rufe bakin, ba shiri kuwa ta rufe hade da cewa "ikon Allah! Ina yini? Yarinyar ta
kalle innar tace "sannu baba" tana taunar cingam hade
da karewa parlon kallo, inna tace "yauwa pa" Aliyun kuwa tuni yayi hanyar fridge xae
dauko mata lemo da ruwa. Inna dae ta dage sae kallonta take daga sama xuwa kasa, can sae
ta fashe da dariya, kursum ta rufe fuskarta cikin kujera dan ita ma kar tayi, don shi ke cinta,
daga yarinyar har Aliyu juyawa sukayi suna kallon inna, inna dae ta kasa daena dariya, Aliyu yace "wae
meye haka ne Hajiya?" tayi kokarin shanye dariyar tace "wallahi wani abu na tuna ne" sae kuma
ta kwalo wa xainab kira, "xainab ku xo gu gaisa da Antyn taku mana" xainab dama kamar jira
take tafito da sauri don tuntuni take son lekowa amma tana tsoran kar Aliyu ya ganta, intisaar ma ta
fito don tana san ganin budurwar tashi, gefe suka nema suka xauna, xainab ta kalle yarinyar
sannan ta kalle intisaar da ta sunkuyar da kai
saboda dariyar dake cinta, ita kanta xainab daurewa take amma da tuni ta fashe da ita.
Inna ta sake kwashewa da dariya tana kallonsu xainab din, tace "ku kawo ma antyn taku abinci
“No”a barshi kawae naci a gidanmu kafin na fito," Aliyu sae kallon inna yake cike da takaici.
Inna ta kara dacewa "to ai bamu ma san sunanki ba" sunanta safeeyna, Aliyu ya taya ta fadi. "ayya
amma wannan telan naki bai maki adalci ba, atamfa har atamfa amma ya tashi yayi maki
dinki kamar 'yar babyn roba, ae wannan riga taki ko ihsaan jikin ta baxae shigeta ba, amma
wannan anyi dan banxan tela," inna ta fadi tsakaninta da
Allah babu ko dar. Xainab bata san sanda dariyar da take ta hadiyewa ya kubce mata ba, ta
Xube jikin intisaar tana dariya kyal kyal kyal,
intisaar ta daure iya daurewa amma ta kasa rike nata dariyan, nan ita ma ta fashe ta har da
xubewa kasa, kursum ma yi take har da bingirowa daga kan kujera, inna ta bude baki tana kallonsu
da mamaki can ita ma dae ta fashe da dariyar suka taru suka dinga yi, "ni wallahi ca nake xabiya
ce ma ta shigo don hasken yayi yawa, tsoro ma ne ya kamani...." inna ta sake jefo masu. Xainab
har da hawayenta don dariya, intisaar cikin hijab din xainab tashige ta dinga yi kamar wasu
sababbin kamu. Aliyu kam kasa cewa komae yayi sae kallonsu da yake yi daya bayan daya.
Safeenah kam iya kan kulewa tayi shi, ta mike tsam tana kallon Aliyun a nutse tace "Haidar help me
out of dis forsaken house plss" inna tace "lah har xata wuce?, ko me take cewa?" tuni safennar ta
fice daga palon innar da takalminta me kamar tsani,
inna ta tafe hannu tace "ohh yanxu idan ta fadi da tsautsayi ba karyewa xatayi ba da wannan
tsanin dake kafarta" ya mike da sauri duk a rikice yake ya fice ya bita yana kiran sunanta, inna ta bude
baki tace "ikon Allah ko sallamah babu ni Rahmatu" sae kuma ta mike da sauri tayi
bakin kofa tana cewa "Aliyu kakai ta, ta gaida xainabu tana ciki" amma tuni har sun ma isa gate. Ta
dawo tana cewa "inda ranka xaka sha kallo" ta kallesu xainab da har yanxu dariya suke kamar
mahaukata, ta hade rai tace "kai ni fa bana son iskanci dariyar meye haka?" kursum ta mike
tace "na tafi wajen momy ni kam kun ga tafiyata, don yau idan ya Aliyu......" shigowar khadija ce ta sa
tayin shiru, don dama taje wanke gashi, ta dubesu idonnan na ta a xare, tace "kai!! me
kuka yi wa yaya Aliyu? Naji yace wallahi sai ya sumar da mutum daya a gidan nan " tana fadin haka,
kursum ta bar falon a guje xa ta sashinsu intisaar, nan da nan hawaye ya fara sintiri a idon
intisaar, cikin kuka tace"xainab wallahi ke ce kika....." wani axababben ihu can ciki ciki
suka ji kursum ta saki... Sallati inna ta saki ta fice a
guje tana cewa shikenan ya kashe ta!!
Intisaar ta daura hannu biyu aka tace wayyoo nashiga uku na lalace, xainab tuni ta firfito da ido cike da
tsoro tace "mun shiga uku!!!"
Aliyu ya kauda kanshi ba tare da yace
mata komai ba, sai da Abba ya bari tayi mai
isarta tayi shiru sannan ya nisa yana duban
Aliyun da kyau yace "ka gya min meye
Matsalar ka a gidan nan, me ke damunka?" kansa kawae
ya sunkuyar ba tare da yace komai ba, "why is it alwayz you in this house? Don me ba a kawo
min karar haisam sae taka? Look.. Wallahi ka sake taba min wani a gidan nan sae nayi mugun saba
maka,
mutumin banxa kawae, tunda ka dawo gidan nan hankalina bae kwanta ba" ya dago kai da
kyar
yana duban Abban nasa yace "to Abba ka
gyawa inna ta fita harkata ta daina min...." shut up!
Abba ya katse sa a fusace, " dama duk cikin 'ya yana kai ne baka da manner, amma xanyi maganinka" Abba ya mike ya shige
Bedroom sakamakon kiransa da akayi a waya, sae a sannan Aliyun ya dago ya fara kallonsu daya
bayan daya a palon, ya mike yana duban innar dake kallonsa yace "ba wata tsiya bace idan
na bar maku gidan, amma sae kun sake gani na "
sannan ya juya xae fice, inna ta mike da sauri tana cewa "to Bukar sae kafito gashi nan ya
hada kaya xae bar gidan wae" ido Aliyu ya xaro yana kallonta, ya koma inda yake da sauri, Abba
ya fito yana kallonsa yace "to tashi ka wuce" bae ce komai ba sae tiles din palon da ya xubawa
ido,
Nan Abba ya dinga masa fada kamar xae ari baki, inna na ta xuga sa, har dae daga karshe
Abba yace ya fice masa a palo, ya mike ransa a bace kamar ya hadiyi xuciya ya bar palon.
Da Yammar ranan intisaar da xainab suna tsakar gida tare da inna dake yi ma ihsaan tsifa take tambayar su
Ko sun ga Aliyu tun daxu don tun bayar barinsa palon abba basu sake ganinsa ba khadija
ma ta kai masa abinci daxu da rana ta gama bubbuga kofarta ta dawo bae bude ba, xaenab tace
"kila tafiyar yayi," inna ta dan marairaice fuska tace "Allah dae yasa ba tafiya yayi ba...."
Budewar gate din da akayi ne ya sanya su duka suka maida hankalinsu wajen, Aliyun ne ya shigo, yayi
Sashinsa ba tare da ya kalle su ba, sae ga Hajiya ma tashigo rike da jaka, umma na biye da ita a
baya,
sannan khadija ma tashigo da wani jakar a hannunta, da gudu xainab taje ta rungume
uwartata, kursum ma dake kusa da wani flower a xaune taje da gudu ta rungume ummarta
harda kuka, nan da nan inna ta hade rai kamar bata taba dariya ba, intisaar ma ta mike da sauri ta
karbi kayan dake hannun hajiyar tana masu sannu da xuwa, har kasa suka durkusa suka gaida
inna, ta amsa masu can ciki-ciki ba tare da ta kallesu ba, momyn intisaar ma ta fito tayi masu sannu
da xuwa da fara'arta, sannan duka sukayi sashinsu, tsakar gidan ya rage daga inna sae intisaar
da ihsaan, inna ta tabe baki tace "shegu munafukai,
wallahi ni banyi farin ciki da xuwansu ba tsinannuna mutane." intisaar cike da jin haushi tace "ni
bana son wannan abinda kike yi inna wallahi,"
sannan ta bar mata wajen ta koma sashinsu.
.. Tun ranar da Hajiya da umma suka dawo gidan suka shiga taitayinsu, don ba karamin
tashin hankali suka shiga ba kwanakin baya don a nasu tunanin Alhaji ya sake su ne basu sani
ba.
Kullum da sassafe suke xuwa gaida inna. Abinda basa yi da, har wani shiri suka tsiri yi da
Momy duk da na munafurci ne. Yau kam intisaar na xaune gaban inna tana mata hira, inna tace
"yauwa wannan yaron faruuq yaxo ya sameni jiya da daddare wae yana so ke da xainab kuje
Gaida mahaifiyarsa," intisaar ta firfito da ido tace
"kai; inna sae kika ce masa me?" eh nace ranar juma'a ya xo ya kai ku, gobe kenan." intisaar ta hade
Rai tace a’a ni babu inda xanje inna, ke kinga hakan ya dace? Saboda gantali kawae sae na kwashi jiki
Naje gidansu" nan da nan inna ta hade rai tace "to idan yaxo goben karki bisa" intisaar ta mike
Ta fice daga palon tana cewa "ni kam babu inda xanje." tana komawa sashinsu ta fadi ma
momynta, momy tace "A'a ko da ma xaki je gidan nasu ba yanxu ba sae lokacin da ya dace," da
yamman ranar faruuq din ya kirata, da kamar baxata dauka ba sae kuma ta dauka don taji
haushinsa sosae, anata tunanin it’s not decent yace xae kai ta gidansu bayan ba ayi
maganar komai ba tukun.
Bayan sun gaisa yake ce mata
inna tayi mata magana, tace "eh amma babu
inda xani" yayi murmushi yace "to shikenan kanwata." nan dae ya dinga mata hira har yace mata
xae je masallaci don lokacin sallah ya kusa.
Da daddare xainab ta shigo palonso intisaar din tace "ke wae inna tace gobe faruuq xai kai mu wajen
momynsa" intisaar tace "eh amma babu inda xani"
xainab tace saboda me? Ke kinga hakan ya dace?
Intisaar ta tambayeta tana jiran amsa"
Xainab tace "to meye a ciki don munje gaida mamarsa?
Ni dae banga rashin dacewar hakan ba wallahi" intisaar ta mike tace "ke kya iya xuwa, amma ni
baxan je ba." sannan ta shige daki, xainab ta tabe baki ta yi gaba abinta. Washegarin ranar juma'a
inna ta xo sashinsu wajen karfe sha daya, tana kwance tana kallo, momy kuwa na bedroom, inna
tashigo palon tana cewa "ke wai wace irin yarinya ce xaki bar bawan Allah tun daxu yana jiranki,
wannan wani irin wulkanci ne, na aiko a kiraki yafi sau hamsin sae kice min kina xuwa?" intisaar
tabe baki tace "ko ma de sauna nawa ne ni dae
ki rabu dani inna babu inda xani pa" au uwar taki ta hura maki kunne kice min baxaki ba kenan?"
da sauri momy ta fito tace "maxa ki shirya kuje, ni ban hanata ba inna" dolenta ta shirya cikin
atamfa java red colour an mata dinki riga da skirt dama gata fara sosae sae ya amsheta, ta danyi
kwalliya tayi kyau sosai sannan ta dauki hijab dinta har kasa, ta fito palo tace "momy na
tafi" momy tace "ki kama kanki, kuma ku tafi da ihsaan, sannan ki turo min xainab" ae da ita
xamu momy, momy tace "eh nasani," tana fita tayi sashin su xainab, ta hadu da khadija a
bakin kofa tana dauraye cup, tayi mata wani irin kallon
banxa sannan tace "amma de kinyi batan hanya ne ko?" tayi jim sannan tace momyna ke kiran
xainab. Aliyu ne ya fito yana dubanta yace
"get out" cikin tsawa, xainab ta fito da sauri ita ma ta
shirya cikin wani material ja, tace gani nan xuwa intisaar. Gidan uban wa xaki? Aliyu ya
tambaya yana kallon xainab din, "inna ce xata aike mu gidan kawarta wae," bae sake cewa komai
ba ya shige ciki kawae, hajiyarsu kuwa tana sashin umma suna tseguminsu da suka saba. A
tare suka je sashin inna da xainab din bayan taje kiran da momy ke mata, ita dinma ta ja mata
kunne ne akan su kula da kansu, ashe faruuq din
ma bae xo ba inna duk tabi ta axalxalesu.
Sha daya da rabi ya shigo gidan, suka gaisa sannan,
inna tace, "amma dei da wuri xaka maido su ko?" yace in'sha Allah inna. Ita dae intisaaar
hade rai ko kallonsa ma bata yi ba. Har bakin kofa ta rakosu sannan ta koma. Sae da suka
hau kan kwalta sannan ya fara hira da xainab, ita dae jinsu kawae takeyi sae wayanta da take ta
daddannawa.
Tafiyar kusan minti talatin sukayi sannan suka iso gidan nasu, yayi horn aka
Bude gate ya shiga yayi park, sannan ya bude masu kofa suka fito, da ganin gidan kasan lallai
mahaifinsa mai kudi ne sosai. Kanwarsa ya kira ta fito,da ganinta baxata wuce su ba, tayi
masu sannu da xuwa tashiga dasu ciki da fara'arta Har palon mahaifiyarsu tayi masu iso,
sannan ta nuna masu kujera su xauna ta cika su da drinks da kayan ciye ciye, ba a dau lokaci ba
mahaifiyar tasu ta shigo palon, suka sauka har kasa suka gaisheta ta amsa da fara'arta
tanai masu sannu da xuwa sannan tace suyi xamansu a kan kujerar, xainab tace nan ma yayi momy,
"a’a don Allah kuyi xamanku nan ba bakon waje bane," da kyar dai xainab ta xauna kan
Kujerar amma intisaar taki xama, hakan yasa momyn
Ta gano ita ce fateemar. Nan dae ta tambayesu ya mutanan gidan suka amsa mata da duk
Suna lafiya. Ba a jima ba faruuq ya shigo yace xae wuce masallaci tayi masa Allah ya kiyaye hanya
sannan ya wuce yana kallon intisaar amma bata bari sun hada ido ba, sae da suka fara yin
sallah, sannan aka cika su da abinci kusan kala hudu,
Ita dae intisaar ta kasa sakin jikinta ga kunyar momyn da take ji, ganin hakan yasa momyn ta
basu waje tashiga ciki, a tare da kanwarsa ummi suka ci abinci, yarinyar na da kirki sosai,
suka dinga hira kamar da can sun san juna. Karfe biyu faruuq ya shigo gidan ummi ta kai masa
abincinsa dakinsa sannan ta dawo suka ci gaba da hirarsu akan makaranta da sukeyi, sae da
faruuq ya dawo parlon sannan momy ma ta fito, nan dae aka dinga hira amma ban da intisaar da
sae dae tayi murmushi, karfe uku da rabi yace xae maidasu gida saboda traffic, momy tashiga ciki ta
hado masu tsaraba mai yawa tun daga kan atamfa har xuwa sabulai da omo da
jeweries na fashion masu kyau, da after dresses, ummi ma tashiga ta hado masu nata tsarabar na
kayan make-up da turarruka kala-kala, intisaar tace "mun shiga uku xainab, don Allah kice ma
faruuq yace su rage sunyi yawa wllh. Xainab tayi banxa da ita ta dinga godiya kawae, har kusa da
motar suka rakosu sannan ya ja motar suka bar gidan.
Ganin yayi park a wani supermarket ne ya sanya intisaar tace masa "me xamuyi a nan, yace
wannan ba matsalarki bace. Sannan ya shiga ciki, wani tsarabar ya kara hado masu, sannan
ya siya ma inna malt carton daya, da peak milks holland, aka xo aka xuba kayan cikin booth
sannan suka bar wajen. Ana gama sallar la'asar suka iso gida, ya fiffito masu da tsarabar
tasu xainab ta bude baki tana kallonsa tace "me yasa xaka daurawa kanka nauyi haka ya faruuq,"
yace ni dae ku shiga dasu ciki xanje masallaci nayi sallah yanxu, sae na dawo. Kursum ce ta taya su
suka dinga jidar kayan suna sashin inna dasu, shima dan gulma tayi hakan amma ba don
saboda da Allah ba, Aliyu suka tarar xaune a palon, inna ta mike cike da doki tace "kar dae har kun
dawo?" intisaar tayi mata alamar tayi shiru saboda Aliyu dake xaune, haka ma xainab da ta daura
hannunta a baki alamar inna tayi shiru, inna tace "ayyo
haka ne pa." Aliyu yace "ina suka je da?" da sauri inna tace "gidan hajiya Maimuna na aikesu." to
wannan kayan meye haka? Cikin in ina inna
tace
"eh eh.. au ita ce ta bada a kawo min mana" nan ya shiga bubbuda ledojin yana kallon kayan baki
bude inna tayi maxa tace "maxa kuje can guriin xainabu gani nan xuwa" da sauri kuwa
suka juya suka bar wajen, sannan inna ta dinga kwasar kayan tana shiga dasu dakinta Aliyu na
binta da kallo "Allahu akbar.. Yanxu har da maltina aka kawo min?? Lah har da madara ni rahma,
amma mutanan nan anyi mutanan kirki."Aliyu ya bude baki yana kallonta sae kace warce bata taba
shan madara ba ko malt, ita da duk wata abba ke jido mata su dayawa, amma ko sati biyu
ba sayi take shanyewa da yara. "kai Allah ya shima wannan yaron Albarka" Aliyu ya dubeta yace
"wani yaro?" au na manta ne Allah ya shima maimuna Albarka xance, ko da yake ma duk
Daya ne, don dan ta da ya dawo daga waje ne yayo min tsarabar. Aliyu ya tabe baki ya jawo
Abincin gabansa xai fara ci akayi sallama faruuq ya shigo palon bayan inna ta amsa da karfinta,
Mikewa tayi ta rasa inda xata sa shi sae ca take "sannu da xuwa dan Albarka," ya nemi guri ya
xauna ya gaidata ta masa cike da jin dadi, sannan ya ba
Aliyu hannu sukayi musabaha, da dan fara'arsa Aliyun ya karba don bai san sa ba. Inna ta
Mike ta bude fridge ta jido masa lemo kusan kala hudu da ruwa roba uku, ta dire masa a gabansa
Tana tambayensa ya hanya, sannan ta shige ciki ta fito da cin-cin da alkaki bakin nan nata yaki
rufuwa. Godiya ya dinga yi mata, don yana jin dadin yanda inna ke nan nan dashi, ko xaka ci
abinci ne, bari na kawo maka cokali kuci tare da Aliyu, wannan shine Aliyu jikana da nake baka labari,
dariya ma abin ya ba Aliyun, ta dauko cokalin ta saka masa tace suci tare. Aliyun bai yi musu
ba ya sauko yana cewa ki dae yi a hankali karki fadi da wannan barin jikin da kike yi. Bata ko
tanka masa ba tace "wannan shine faruuq saurayin intisaar ae nasan baka san shi ba, Haisam ne
ya san sa," dago kai Aliyu yayi yana kallonsa, nan da nan dan fara'ar dake fuskarsa ya bace, inna
tace to kuci abincin mana kar ya huce, ajiye cokalin hannunsa yayi fuskar nan tasa a yatsine yace "ya
dae ci, amma ni wannan ba isar mu xai yi ba," faruuq ya dago yana kallonsa, ya gane
nufinsa,don hka sae yayi murmushi yace to ni bari naci tunda bako ne ni, da sauri inna tace eh
hakan ma yayi sae ya hakura ayi na dare. Hade rai Aliyu yayi yana kallon inna yace
"kamar ya na jira na dare? Ban gane nufinki ba?"
Inna ta mike ta tabe baki hade dacewa "maida wukar dan nan" sannan ta shige daki sae ga ta ta
Fito da garin rogo da suga ta xube masa a gabansa tace "ka debo ruwa a pampo ka jika kasha don
ruwan kenan na kwaso wa faruuq.
Takaici ya hana Aliyu cewa komai sae bin inna da yake yi da kallo har ta koma ta xauna tana ci gaba da
hirarta da faruuq, shi kanshi faruuq din abin ya basa dariya sosae don har sae da ya dan
dara,
can sae Aliyu ya turawa faruuq din garin yace "shi da ya kwaso yunwa har haka ya shigo sae ya hada ya sha, ni kam am okay" ya fadi a walakance yana duban faruuq din da har
yanxu murmushi na fuskarsa, sallamar Haisam ne ya sanya inna bata tanka masa ba, inna ta
amsa da murnarta tana cewa "yawwa yaron kirki sannu da xuwa shigo ka taya ni godewa faruuq abin
arxikin da yayi min" haisam ya shigo suka gaisa da faruuq da fara'a sannan ya gaida inna da
bakinta yaki rufuwa, yace kinga inna bari naci abinci tukun yunwa nake ji, idan yaso in nagama
sae na taya ki murnar, faruuq ya dubi haisam yace "bismillah kaxo muci wannan don ni ba
wani yunwa nake ji ba," nan da Haisam ya xauna suka fara cin abinci da faruuq din suna hira inna
na tsoma masu baki, haisam ya dubi Aliyu da ya kura wa TV ido yace "ya dae bross lafiyanka?,
kardai yau ma baka je clinic din ba" Aliyu ya watsa masa harara yace a fusace "spare me malam bana
son sa ido plss" daga haisam din har faruuq suka kwashe da dariya inna na tayasu har da
kwanciyarta, Aliyun ya kulu matuka amma bai sake cewa komai ba illa gnash din hakora
da yayi fuskar nan tasa a tamke. Har dae suka gama cin abinsu sannan inna tace idan basu koshi ba
ga gari su jika, faruuq yace a’a ya koshi haka ma, Haisam Nan inna ta fara jawabinta tana
washale hakora " kaga haisam daxu su intisaar suka je gaida mamar faruuq suka yi masu sha tara
ta arxiki, bari na kwaso maka ka gani, gaskiya gidan mutunci ne wannan gida" nan inna ta dinga
jido ma haisam kaya yana ta yabawa da kara taya innar tasa godiya. Ido Aliyu ya xuba mata yana
kallonta cike da mamaki, daxunan tace masa kawarta ta bada a kawo mata yanxu kuma
tace daga gidansu faruuq, dama gidansu faruuq din sukaje? "kaga har kwalin maltina fa haisam,
kai ni dae banda bakin gode maka faruuq, Allah dae yayi maka albarka ya dada budi," ta fadi tana
kallon Aliyu baki har kunne, taga yana mata wani kallon rainin wayo yana girgixa kafa, ta juyo
tana kallonsa da kyau tace "meye kake kallona haka,?
Ka taba kawo koda gwangwanin madara daya ka kawo min gidan nan ne bare maltina? Kuma
Don yanxu na samu me min sae ka dinga min bakin ciki? To ahir dinka, Allah ya fika, har gwanda
haisam duk sati yana yo min tsaraba amma ban da kai don bakin rowa irin taka," ta juyo
tana murmushi taci gaba da shi ma Faruuq da haisam albarka. Ya mike tsam yana kallonta bacin
rai karara a fuskarsa yace "ai ke ba uwata bace da xan dauka gwangwanin madara na kawo
maki,
Idan ma kyautar nake son yi ae uwata na nan da ranta, don haka baki isa nayi maki kyauta ba
Hajiya, wa inda suka ga xasu iya sae su maki.
Aikin banxa kawae aikin hofi, mutum ya tsufa bae san ya tsufa ba" yana kaiwa nan ya fice
Ba tare da ya jira cewarta ba, sashin hajiyarsu ya
nufa, yana shiga ciki rae bace ya fara
Magana "mumy kina gidan nan xaki bar 'yar ki ta fita
raka wata banxa can gidan saurayi? Hajiya ta mike da sauri tana cewa wa kenan? Kursum
daka palon tace "xainab mana daxu ta raka intisaar gidan saurayinta suka dawo da kaya niki-
niki wallahi," hajiya ta xabga salati tana tafe hannu tace "wallahi ca tayi min inna rahmatu ce xata
aiketa gidan kawarta...." bae kara sauraran mahaifiyar tasa ba ya dubi kursum cikin tsawa yace
"ina xainab din?" a dan tsorace tace "tana can Palonsu intissaar can inna tace suje ae" maxa jeki ki
kiramin ita, ta dan marairaice fuska don ita mugun tsoransa takeyi tace "yaya ko naje
ba xuwa xatayi ba da dae kaje da kanka" bae kara bin ta kanta ba yayi sashinsu intisaar din rai
bace yana kwadawa kanwartasa kira, yana isowa wajen sae ya daina kiran nata don yasan
xata iya gudu idan taji muryarsa, daga dan nisa ya hango ihsaan bakin tap tana dauraye cup
din da tasha corn-flakes, tana ganin sa ko ta ruga ciki a guje tace "momy kinga ga uncle nan xuwa,"
intisaar ta xaro ido tace ya Aliyu? Ihsaan ta gyada kanta, nan suka shige bedroom din
momy a guje don tsiyace kadae ke kawo Aliyu
sashinsu, yana isa bakin kofar ya bude yana karewa palon kallo, momy na xaune dama ita ma a palon,
ya kalle ihsaan yace "xo nan," ta isa gareshi tana kallonsa, yace "me kika gudo kika cewa,
kuma idan baki gaya min gaskiya ba xan xaneki yanxu a nan" nan ta marairaice fuska xatayi kuka
tace "nace ma Anty xainab da Antyna kana xuwa"
shine sae sukayi me? Ya tambayeta yana kallonta, "shine sae suka gudu suka shiga
daki," rankwashi ya kai mata har sau uku yace "ki
ka sake gani na kika je announcement sae na cire maki wannan katon idon naki, wawiya
kawai fice min a gaba. Ta ruga da gudu ta fada jikin momynta da ta tsurawa TV ido tun daxu,
tana kuku Ya juya xae bar wajen kenan don yasan ba fitowa xasu yi ba ya ci karo da hajiyarsu
itama ta karaso wajen a fusace, Aliyun yace "me kuma kika xo yi nan Hajiya?" bata bi ta kansa ba ta
dinga kwada ma xainab kira tana cewa
"wallahi ki fito daga gidan nan kar na ci ubanki
Munafukar yarinya," ganin momyn intisaar din a xaune
A palo ne yasa ta ja ta tsaya, Aliyu yayi dan tsaki yayi gaba abinsa, don baya son uwarsa tana
masifa ko neman magana a gidan, ita kuma aikinta kenan. "Zainabu! Ki gya min dalilin sa 'yata
bin watsatsiyar yarki gidan saurayi don a bata ta?"
hajiya ta fadi fuskarta a tamke, ko kallo bata ishe momy ba da ke ta aikin kallonta tana
rungume da 'yar ta, hakan ya kara hassala hajiya don tana matukar bakin cikin sharesu da
momyn ke yi a gidan, kenan ma mahaukata kawae ta maidasu don ba dai amata abu ta tanka a
gidan ba, cikin daga murya hajiya tace "wae ba da ke nake ba ko kurama ce ke?" nan ma de
momy ko kallonta bata yi ba, hava nan hajiya ta dinga
gaya mata maganganu marasa dadi masu kuntata xuciya duk don momy ta kulata amma bata
ci nassara ba don momy murmushi ma kawae take yi. Hayaniyar hajiyar ne ya fargar da umma
ta karaso sashin da saurinta tana cewa "lafiya hajiya me ya faru, rashin kunya ta maki ko me?"
ina fa,, yawon iskancin da da ta sa 'yar ta take yi, shi xasu koyawa xainab dita, tunda gashi yau
har shiryata tayi suje gidan saurayin 'yar tata. Umma
ta xabga salati tana jujjuya kai tace "wallahi kursum taxo ta sameni wae xainab ta bi intisaar
gidan saurayi ya cika su da kaya duk na tsamman shirmanta ne shiyasa ban tanka mata ba"
hajiya tace "Allah ya isa tsakanina dasu," umma tace "to yanxu ina shegiyar xainab din take" bata jira
amsa ba ta afka palonsu intisaar din ta tsaya
gaban momy tana cewa "ki fito mana da 'yar mu kar mu aki abinda baki xata ba gidan nan yau,"
tana magana ne tana nuna momy da dan yatsa, momy tayi murmushi mai sauti, ta kama hannun ihsaan
suka shige bedroom ta kulla kofar. Galala umma ta bita da kallo, hajiya ma ta shigo palon
tace "idan ba tsoro ba dan uban mutum meyasa bae tsaya ba" nan suka dinga xaxxaga mata
rashin mutumci kwando-kwando suna xage-xage, gori kam ta sha shi kala-kala, abinda ya fi bata
masu rai bae wuce yanda ta barsu su kadae suna ta haukansu ba, don a da can idan suna mata
tayi shiru har dadi sukeji a nasu tunanin tana tsoransu ne,.
Ido Aliyu ya xuba masu yana kallonsu, yayi murmushin da xa a iya kiransa da na mugunta
sannan ya hade rai yana kallon xainab din yace "ina kuka je jiya?" ta yarfe hannu hawaye na
sintiri a fuskarta tace "don Allah kuyi hakuri..."
wani irin tsawa ya daka mata yace "it seems kina wasa dani ko?" cikin kuka tace "aa yaya"
gud! Gaya min inda kuka je jiya. Ta juya tana kallon intisaar dake kuka wiwi sannan ta kalle
abban nasu da ya Aliyun tace "gidansu faruuq muka je
gaida mahaifiyarsa" abba yace "waye faruuq din?" saurayin intisaar ne," ta fadi, kanta a
sunkuye.
Cike da mamaki abba ya tsaya kallonsu,
Aliyun yace "amma ina kika ce mun xaku jiya?" "aa
Inna ta...." wani irin tsawa ya daka mata yace "rufe min baki kar na taka ki" yayi hakan ne don baya
Son Abba yasan da ixinin inna suka je, kawae so yake
ya lallasa su barin intisaar. Xainab na ganin hakan tasan yau kam sun banu, nan Aliyu ya dinga
tsarawa abba yanda suka yi jiyan da irin karyar da sukayi mashi, xainab ta san inna ce kadai
gatansu yanxu don abba yayi fushi matuka, da dubara tashiga yi ma kursum tex da wayan
dake hannunta kan cewa ta kira masu inna suna palon abba xa ayi masu duka, duk a rude take,
ganin yanda Aliyu ke tayi wa abba tsari yana dada bata masa rai. Ba a jima ba, kursum ta maido
mata reply, ta bude da sauri hannunta na karkarwa taga me tace, "NO" abinda ta gani knan
boldly
wato baxata turo innar ba. Ta kara sautin kukanta tana kallon intisaar da ta kife kanta
ita ma tana yi, tun ba yau ba tasan kursum muguwa
ce. To wa xata kara yi ma tex yanxu? Don kursum ce kadae hope dinsu, ita ma tace no. Yaya
haisam ta tuna, don haka da hanxari ta shiga yi masa tex duk da baya gidan, ya taimaka ya
kira masu inna taxo. Kafin tayi sendin Aliyu ya
ganta
ya fixge wayar da sauri yana cewa "you re
vry
stupid, wat do yhu fink yhu re doin?" abba
ya
karba wayan ya ajiye gefensu yana kallonsu.
Haisam yyi dariya sosai da yaga tex din, don
sbda tsabagen masifa Aliyun yyi sendin bai
sani
ba. Ai kam yana kiran innar ya gya mata ta
taho
da gudunta tana salati. Tun daga bakin kofa
ta
dinga kwada wa abba kira, hkn ba karamin
bta
wa Aliyu rai yyi ba, don yyi niyar yyi masu
laga-
laga ne, sai yaji kmr ya hankadata ta koma,
nan
ta sake masu kuka tana cewa "ynxu Bukar
don
na tura yaran nan su gaida uwar yaron nan
me
kirki shine nayi laifi?" Abba ya girgixa kai
yace
"dama ke kika ce su je?" ta goge hawayen
dake
idonta tace "eh mana," basu gaya min ke
kka ce
suje ba ne." ya kallesu yace "ku tashi ku tafi."
yyi
hkn ne don baya son uwartashi ta daga
masa
hnkli. Aliyu ya dan bugi kafarsa a kasa yace
"shit" inna ta dubi hajiya da umma dake
xaune a
palon kmr su hadiye xuciya don takaici tace
"to
munafukai ae sae a tashi a bashi waje kuma
ko,"
tayi tsaki ta wuce tana surutanta, don ana ta
tunanin su suka gya masa, duk da su din
suka
gya masa.
.
Suna fita Abba ya girgixa kai cikin damuwa
yace "ni bn san me ke damun inna ba, tana
tsufa
ne hnklinta na komawa na yaro," hajiya ta
mike
ta tabe baki hade dace wa "kawae de ta
kare
matarka ne, amma ka dae yi bincike da
kyau."
tana kai wa nan ta fice, umma ma ta bita a
baya
tana cewa "mu dae Allah ya rufama 'ya yan
mu
asiri kar a sa su a hnyar da bae dace ba, don
wannan lamarin akwae abun dubawa a
ciki"
momy de bata ce komai ba, amma tasan da
ita
suke, ta mike itama xata bar palon Abba ya
kirata ta dawo, Aliyu ma ya tashi ya bar
masu
palon cike da jin haushin inna, ko waye yaje
ya
gya mata ma oho. Suna tsakar gida a tsaye
ita
da xainab suna ta dariyan abinda ya faru
jiya da
safe, hajiya da umma sun je barka, inna tana
can
sashinta, su biyun kadae ne a tsakar gida,
shirun
da intisaar tayi ne fuskarta ya bayyana
alaman
tsoro ya sa xainab ta dakata daga surutun
da
take yi tace "me ya faru," tana waige-waige,
da
sauri intisaar ta fixgota da gudu suka je
bayan
wani flower suka buya, xainab na maida
numfashi a tsorace tace "wae menene?" ita
din
ma numfashin take mayar wa tace "ya
Aliyu."
xainab tace "a ina kika..." tsit tayi ganin
Aliyun ya
doso ta inda suke, cikin kasaita yake tafiyar
tasa,
yana sanye da t'shirt fara kal, da 3quatre
shima
fari tas, intisaar ta bi shi da kallo da
idanuwanta
kmr xasuyi magana, farar kujerar roba ya
dauka
ya ajiye ta opposite inda suke ya xauna.
Basu da
wata fargaba don sun tabbatar idan ba
kusa da
flowern ya xo ya tsaya ba baxae gansu ba,
ya
ciro wayrsa daga Aljihu yana dubawa, suka
ga yyi
murmushi mai kyau har sae da dimple dinsa
ya
nuna, ya lumshe manyan idanunsa ya sake
budesu, ko me ya gani oho. Ashe dae ya
Aliyu na
murmushi, tambayr da intisaar tayi ma knta
knan
a xuciyarta, nan dae ta tsaya ta kare masa
kallo
sosai, don ita kullum kallon tsoro take masa
a
gidan. A xuciyarta tace "ashe dae yana da
kyau
har hka," ta tsura ma sajensa da ya kwanta
luf-
luf a fuskarsa ido, daga sama xuwa kasa ta
dinga kallonsa ko kifta ido bata yi, ashe dae
shi
din kyakkyawa ne sosai, amma duk da hka
faruuq dinta ya fisa kyau tasani, xainab ta
xungureta tace "ke wannan kallon fa?" a
tsorace
intisaar din tace "da'alla dubi yanda kika
bani
tsoro."xainab tace "to naga kina neman
cinye min
yaya da ido, intisaar ta tabe baki tace "ni
kallon
mamaki nkeyi masa" to wae taya ma akayi
kika
san yana xuwa? Xainab ta tambaya tana
kallonta, kamshin turarensa, intisaar ta bata
amsa ba tare da ta kalleta ba. takun da suka
ji
yasa suka kara labewa sosai, momy ce taxo
ta
wuce, bai ce mata ba, bata cemasa ba har ta
wuce sa, da alama sashin inna xata, sae da
ta
wuce shi sannan ya bita da kallo har ta kure
masa, yyi murmushin da intisaar ta gaxa
gane ko
na menene, sannan ya cigaba da danna
wayarsa,
xainab tace "yau mun shiga uku hka xamu
ta
tsayawa ni kam na gaji wllh" intisaar bata
tanka
mata ba ta dan kara satan kallon Aliyun,
taga
kara hakikincewa yyi ma kan kujerar. Ihsaan
ce
taxo wuce wa tana kuka, kila ta tashi bata
ga
momynta ba da yayarta, don bacci take yi,
xata
wucesa ya fixgo ta yace "cum hia, wa ya
dokeki?"
bata ce komai ba sae kallonsa da takeyi, ya
daura ta kan kafarsa yana cewa "idan kika
sake
kuka xan maki allura" ba shiri tayi shiru ya
dago
wayrsa yana ta nunamata ko pix ne ko
meye ma
oho dae, su dae hka suka dinga lekosu har
daga
karshe suka ga ya sauke ta ya mata mgna a
hnkli ta ruga sashinsa da guda, ba ajima ba
ta
dawo rike da chocolate, suka ji yace mata
"run..
Momy tana wajen inna je ki sameta," da
gudu
kuwa tayi sashin innar. Idan ba don intisaar
da
ta dinga rike xainab ba da tuni ta mike ta
bar
wajen, ita kam tsoran abinda xai yi masu ne
yasa ta dinga rike xainab kar ta tona masu
asiri.
don sun gaji sosai gashi aliyu yaki barin
wajen
har sunyi kusan awa biyu a durkushe,
momy da
ihsaan ma tuni suka xo suka wuce. Ba su
suka
bar bayan flowern ba sae da aka kira la'asar
Aliyu ya wuce massallaci. Tana xaune gefen
inna
da ta dage tana ta kirgan kudi 'yan dubu
daddai,
da ta kirga sai ta mikowa intisaar ta duba
ko dai
dai ne, intisaar kam ta xuba mata ido don
bata
san inda ta samu kudin ba, har dae daga
karshe
suka gama kirgan kudaden inna ta dubi
intisaar
din bakinta a wangale tace "nawa knan
gaba
daya?" intisaar tace "dubu dari biyu da
hamsin,
ina kika samo su inna?" ba tare da inna ta
kalleta
ba tana kkrin hada kudaden waje daya tace
"fili
na na saida." intisaar ta xaro ido hade da
bude
baki tana kallon inna. Sallamar haisam ya
sanyata rufe bakinta, inna ta amsa mashi ba
tare
da ta lura da halin da intisaar ta shiga ba ya
shigo, suka gaisa yace "kina sha'aninki inna,
ina
kika samo kudi hka?" ya tambayeta yana
karewa
palon kallo, a xuciyarshi yana cewa kar dae
wani
abun inna ta kuma saidawa, don saranta
knan, in
dae bata da kudi to bata ki koh plaxman
palonta
ta saida ba, hkn kuma na bata wa abba rai
sosai
ba kadan ba, don duk abinda yke mata bata
gani
sae ta saida wani abun palonta ko daki,
"wllh fili
na na saida haisam" haisam yace "mene?"
Ba tare da inna ta kallesa ba tace "nace
mka fili na na saida. Ko bka ji ne" ya nemi
kujera
ya xauna yana kallonta cike da mamaki yace
"wani filin inna?" don dai shi yasan a ynxu
hka
inna bata da fili, idan ba dae wanda ake
mata
gini taje ta saida ba, "wannan din da
babanku ya
siya min" ta fadi tana mikawa intisaar
kudaden
ta kai mata daki. Haisam ya yo waje da ido
"yace wani filin abba ya baki?" inna ta hade
rai
tace "na jan bulo mana" haisam ya saki
salati
yana kallon innar, inna tace "kai ni don Allah
ku
rabu dani, ina da bukatar kudi kuma baxan
saida
kaddarana ba?" haisam yace "ya salam!
Ynxu
inna abba ca yyi maki filin naki ne? Daga ya
baki
takardu ki ajiye masa sae ki je ki saida fili?
Wai
ma nawa kika saida filin?" "ni dubu dari
biyu da
hamsin aka siya," inna ta fadi a marairaice.
Haisam ya mike da sauri yana kallonta ya ma
kasa cewa komai," filin abban kika saida
masa
dubu dari biyu da hamsin? Kin san nawa ya
sayi
filin inna, haisam ya girgixa kai yana kallon
innar
cike da takaici, ita kam sai wuri-wuri take
da ido.
Aliyu yyi sallama ya shigo yana cewa "har
kin
dawo daga yawon inna?" ya kalli haisam da
yanayinsa ya sauya xuwa bacin rai yace "me
ya
faru guy?" Aliyu filin abba taje ta saida dubu
dari
biyu da hamsin wae" haisam ya fadi cike da
jin
haushi, Aliyu ya xaro ido yace "wat?" filin da
yke
cewa xai fara gini cikinsa nxt yr?" dariya
Aliyu ya
dinga yi har da dafa bango, intisaar kam ido
ta
xuba masu tana kallonsu ita ma tasan inna
bata
kyauta ba, tuni inna aka fara hawaye, irin
dariyar
da Aliyu yake yi ne ya kara kullar da haisam,
to
meye abun dariya a nan, ta rangada wa
abbansu
asara, don ko shi bai sayi filin hka ba, cikin
karkarwar murya inna tace "to ni ina nasan
filinsa
ne, da naga bai sake min mgna ba ai nayi
xaton
ya bani ne, kuma Aliyu ba kai ka bani
shawarar
ba to?" Aliyu ya xaro ido yace "wa? Aa karki
sake
saka ni cikin wannan case din Hajiya" inna
tace
wllh kai ka sani, kana ji ko haisam, jiya ya
shigo
da daddare nake ce mashi bnda kudi kuma
ga
bikin jikar aminiyata ya taso bari bukar ya
dawo
na tambayeshi kudi, sae Aliyu yace min ae
Bukar
bai da kudi ynxu hka sae dae idan xan saida
kujeruna ne na biya bukatata, to naga dae
taya
xa ayi na saida kujerun palona, palo ya
xamo
wayam, kuma kwanakin baya ma da na
saida
fridge dina ma ae sae da bukar yyi min
masifa,
to yana fita a jiyan sae na tuna ai akwae
takardun filin da bukar ya bani......" Aliyu ya
daka
mata tsawa yana cewa "ke inna rahmatu
wllh kar
ki saka ni cikin wannan case din na gya
maki,
idan dae mutum ba hauka ya fara ba ta ya
xai
kin kima kujerunsa ya saida don an bashi
shawarar, ni dama wasa nke maki, kuma
magana
ce na gya maki." tuni inna aka fara kuka
wiwi,
Aliyu ya fice yana dariya, Haisam kam kasa
cewa
komai yyi, tun ba yau ba yasan Aliyu mugu
ne,
idan ba hka ba taya xa a saida kaddarar
mahaifinsa mai muhimmanci yayi ta dariya.
Ya
juya ya fice kawae ba tare da yace da inna
komai
ba, to waye ma yyi mata jagora taje tayi
wannan
aika aikan, Aliyu na fita yaje ya sami
hajiyarsa
yana ta dariya ya bata lbrin abinda inna tayi,
ta
hade rai tace "to meye abun dariya a nan
Aliyu,
gadonku fa ta walakanta kke dariya hka?"
ya
mike yana kallon umman tashi yace "ni
banyi
depend a gado ba mum, Allah ya hore min
don
hka, 4 ol i care," ya fice yana ci gaba da
dariyarsa don yasan drama xa ayi a gidan
yau
idan abba ya dawo. Abba ne tsaye kan inna
yana
faman bambamin fada kmr xae maketa,
inna ba
baki sae idanuwa, "kinsan nawa na sayi filin
ne
xakiyi min hka inna, daga baki ajiya sae ya
xama
naki, ina aka taba yin hka? Bbu shawara
bbu
komai xaki je ki walakanta min abun da
akalla
xan iya saida shi miliyan daya da rabi."
hajiya da
umma dake palon ji sukayi kmr su shide
don
murna, Aliyu ya kasa hadiye dariyar dake
cinsa
ya fasheta, abba ya juyo kansa ya dinga
masifa
kmr xai maresa, ba shiri ya kame kansa, don
ran
abba yyi mugun baci ranar. Ganin ba sarki
sae
Allah yasa inna ta fashe masu da kuka tana
cewa "tunda yusufa ya rasu dama nake
shan
wahala a duniyar nan, daga kai har 'ya
yanka
bakwa tsinanani da komai, ni ke yi ma kaina
duk
bukata, Abba ya bude baki yana kallonta ya
ma
kasa cewa komai, shi din ne baya mata
komai?
Gnin ta dage sae rera msu kuka take ne
yasa ya
shiga bata hkri, tce "hka kawae baxan
kyautatawa
aminiyata ba jikarta xatayi aure, kuma
nasan idan
na tambayeka ba bani xakayi ba," Abba ya
girgixa kai yana mamakin uwartashi, duk
juma'ah
sae ya bata dubu goma bayan abubuwan
da yake
siyo mata duk karshen wata sannan ya
damka
mata dubu ashirin ko tana da bukatar kudi,
amma yanxu kiri-kiri tace bbu mai taimaka
mata
a duniyar nan sae Allahnta, komai ita take
ma
kanta. Abba yace "to shknan inna, Allah yasa
hkn
shine mafi alkhairi, kudaden sun isheki de
ko? Ta
dan fara kame kame tana goge kwalla tace
"ni
idan san samune akara min dubu hamsin,
ko
kuma dari ma." takaici yasa abba gyada kae
kawae, ya dubi Aliyu yace anjima ka ciro
mata
dubu hamsin Ali, xan bka, "tab! Ai ni abba
accnt
dina ko dubu goma bai kai ba ina ga ma."
... Inna ta galla masa harara tace "Allah ya
dauwamar dasu a hka," Haisam yace
"anjima xan
ciro na kawa maki inna." nan ta dinga sa
masa
albarka, abba yyi mata sallama ya fice daga
palon nata cike da jin haushin hali irin nata,
Aliyu
ya bi bayansa yana cewa "wannan ai sata
kiri-kiri
ne kawae, daga an baki ajiye sae ki
maidashi
naki" bai jira me xata ce ba ya fice da sauri
yana
dariya. Haisam na fitowa daga palon innar
umma
ta aika a kira mata shi yaje, nan kuwa ta
balbalesa da masifa tana cewa" kai dinnan
soko
ne wllh, Aliyu ya fika wayo nesa ba kusa ba,
kana tunanin idan ka dauki kudin naka har
dubu
hamsin ka bata Alhaji bka xai yi ne? Kai dae
bn
san wani irin yaro bne Allah ya bani, don
meyasa
baxakayi koyi da Aliyu ba, duk ka bi ka tare
gurinta sae kce ta asirce, wllh idan baka yi
gaggawan sauya wannan mugun halin
naka ba
sae na saba mka" haisam ya girgixa kai cike
da
takaicin hali irin na uwartasa yace "Allah ya
kyauta! Sannan yafice a fusace. Shi kam
Aliyu
hajiya yaba masa ta dinga yi tana sa masa
albrka, shi dae bai tanka mata ba. Da
yammacin
ranar Haisam ya kaita gidan aminiyartata
bayan
ta shiga kasuwa tayi kaca-kaca da kudin, a
dole
ita wae sae ta kyautatawa kawartata tunda
bikin
jikarta ce. Su hajiya kam sun ji ddin xuwan
inna
gidan bikin don kwana biyar tace xata yi, ko
ba
komai xasu dan samu sarari a gidan su
sheka
tsiyarsu yanda suke so. Intisaar na daki
wajajen
karfe goma na safe tana duba wani Novel
na
turawa taji hayaniyarsu hajiya a tsakar
gidan, ba
shiri ta fito ta tarda su hajiya sun saka
momynta
a gaba sae maganganu suke gya mata fadila
na
taya su, "idan banda rainin wayo tun asubar
fari
take ta facakala da ruwa sae kace ita daya
ce a
gidan, ynxu idan ruwan ya dauke mu da
wanne
xamuyi ayyukan mu, mun xo muna mata
mgna
kuma ta maida mu mahaukata, to dae mai
daure
maki kugu a gidan bata nan, idan kikayi
wasa...."
xainab ce ta karaso wajen da sauri ita ma
tana
cewa hva hajiya meye yyi xafi hka da
sassafe xa
ku sa momy a gaba kuna..." kyakkyawan
mari
hajiya ta watsa ma xainab din tana cewa
"wuce
ki bni waje munafuka kawai, dama tun ba
yau ba
kike nuna ni ba komai bace a wajenki, idan
bnda
hka taya xa a maida ni mahaukaciya baki xo
kin
tsaya min ba xaki gya min mgnar bnxa, baki
ga
yanda fadila take yi bne don ubanki,"
intisaar ta
kalle momynta da ta tsaya tana kallonsu
kawae
bata ce komai ba, umma ta hankade xainab
tana
cewa bace mana da gani mara xuciya
kawae
warce bata san ciwan kanta ba. Girgixa kai
momy tayi kawae taci gaba da wankin da
take yi
a bakin famfon, hajiya ta fixge bokitin a
fusace ta
xubar da ruwa da kayan dake ciki sannan
tasa
kafa tayi ball da sauran bokitan tana cewa
"don
babanki baxa kiyi wankin nan ba yau wllh,
mu ma
muna da bukatar ruwa" umma ta kashe
famfon
tana kwadawa rahma kira ta kawo mata
kwado
su kulle. Intisaar ta goge hawayen idonta ta
dubi
momynta da ta tsaya kallonsu kawae ba tare
da
tace uffan ba, tace "momy ki bari anjima xan
je
waje na debo makii ruwan wankin, xo mu
tafi" ta
fara jan hannun momyntata su bar wajen,
momy
kam kasa barin wajen tayi, ta xubawa fadila
dake ta faman xaxxaga mata xagi tana
cewa
"mutum ya xame mana annoba a gida,
kuma idan
ana magna ya dinga yi kmr kurma don
tsoro,
wllh hajiya ni kawae da kun bari watarana
na
lallasa ta na nuna mata....." ji kke tass! Momy
ta
xuba mata tagwayen mari masu rai da lfya,
hava
wa! Nan fadila ta gigice ta fasa ihu don
batayi
xaton marin ba, cike da mamaki hajiya da
umma
suka dinga salati suna cewa ita fadilar kika
mara? Hajiya ta fixgo fadilar tace "xage ki
rama
fadila, wllh sae kin rama," umma kam tuni
aka
shige gida da gudu anje shirin dambe, don
tace
wllh sae ta rama ma 'yar ta. Fadila ta dage
xata
mari momyn, intisaar ta fixgota da karfi
tana
cewa "ke yar karamar 'yar iska, ni xakiyi
facing
ba momyna ba," nan intisaar ta dage ta
dinga
xuba mata mari tana tana cakume da
kwalar
rigarta. Nan fa gida ya hautsine, umma ta
fito da
gudunta bayan ta canxa kaya, tayo kan
momy da
gudu tana cewa "ae yau sae dae ni ko ke?"
tam
nan fa momy ta xage ta kai umma kasa suka
dinga cin dambe. Su rahma da kursum suka
hadu suka dinga dukan intisaar din da taki
sakin
fadila har ynxu bayan ta kaita kasa ta haye
kan
ruwan cikinta tana jibgarta iya karfinta.
Hajiya na
ganin an kai umma kasa ana ta nakada, ta
fice
waje da gudu tana kiran jama'ah su xo su
ga
xainabu xata kashe Shafa. Xainab na shiga
daki
da kukanta dama abba ta kira amma yaki
xuwa,
ya Haisam ya tafi kaduna tun jiya, don hka
kawae sae ta kira Aliyu tana kuka ta gya
masa,
sannan ta fito taga irin damben da ake ci,
kuka
ta dinga yi sosae ta ma rasa abinda xata yi
ga
muryar Hajiyrsu can a wje tana aibanta
momy,
mata suka dinga tururuwa cikin gidan duk
da wsu
gulma ya shigo dasu, ihsan ma kuka ta
dinga yi
a kusa da xainb tana cewa "Anty kice
momyna ta
bari." da kyar matan suka kwace umma a
hannunm
momy, sannan aka raba su intisaar shi ma
da
kyar don intisaar komawa tayi kmr
mahaukaciya
duk tayi ma fadila kaca-kaca hka ma kursum
dake..
Xainab ta karasa kusa da intisaar da
hanxarinta
bayan an rabasu, ta fara janta ixuwa
palonsu,
fadila kam ihu ta dinga yi tana fixge fixge
daga
rikon da akayi mata wae a barta sae ta
kashe
intisaar yau, momy ta ja bokitin ta ta tara a
famfon tana cewa "kuma wanki yanxu na
fara,
bnga uban da ya isa ya hanani ba, kuna
tunanin
shirun da nake maku tsoro ne, wllh duk
wanda
yace baxae kame girmansa ba a cikin ku xai
ko
sha mamaki." rirrike hajiya aka shiga yi wae
sae
tayi ma momy duka, hka ma umma ko
kunya
bbu. Wata yar dattijuwa da tashigo gidan ta
dube
momy tace "to ke 'yar nan tunda gaba suke
dake
ki bari anjima kiyi wankin mana, ina ce
sunce aiki
suke son suyi da ruwan su ma" momy tace
"ki
bari kawae baaba wllh munafukan mutane
ne,
idan bnda hka famfofin gidan nan sun kai
biyar
pa, kuma ko wanne na da nasa pampon a
bangarensa, nan bangarena ne amma sbda
neman mgna suka kwaso jiki suka xo wae
baxanyi wanki ba, kuma wllh baaba tank
din
gidan nan babba ne, ko xan kai washegari
ina
wanki bbu abinda xae ragu a ruwan amma
dayake jirana sukeyi shi yasa nayi laifi, toh
bari
kuji, wllh tllh daga yau duk shegen da yace
xae
sake takani a gidan nan sae ya sha
mamaki."
hajiya tace "mu kke gyawa magana hka
xainabu,
dama ashe kina mgna hka amma don
munafurci
idan kinga Alhaji sae ki dinga yi kmr na
kirki?
Don Allah ku sakeni na gwada mata hnkli."
momy
tace "ku kyaleta don Allah" umma ta dinga
dura
mata ashar ta uwa ta uba tana daga inda
take,
don bata sake gigin matsowa kusa da ita
ba, a
dai-dai lkcn Aliyu ya shigo gidan, ya girgixa
kai
cike da takaici ya jingina gefen gate din
rungume
da hannuwansa yana kallonsu, muryar
momy yaji
tana cewa "don Allah don Annabi ku kyaleta
ta
dokeni, wllh tllh Aisha sae kinyi da kin sanin
sani
na, don laga-laga xan maki kuma ba lallai ne
mijin ki ma ya gne ki ba. A fusace Aliyun ya
karaso cikin tsakar gidan yana kallonsu
daya
bayan daya, basu ma san yashigo ba, ya
dubi
fadila da bata da maraba da hauka gashin
nan
yyibuya-buya, daga ita sae leggings, intisaar
ta
dube fadilar dake xaginta ta uwa ta uba
tana
kiranta da 'yar tsintuwar innarsu, tace " duk
da
hkn dae ban xage ina karuwanci ba, na fita
tun
asuba na dawo karfe takwas din dare."
fadila ta
kara rudewa ta shiga galla wa masu rikonta
cixo
wae sae sun saketa ta mata duka, sae kace
ba
ita aka kwata da kyar daga hannun intisaar
din
ba ynxu, Aliyu ya karaso wajen ya sa kafa ya
kwashe fadilar ta xube kasa sannan yashiga
ball
da ita yana cewa "yau xaku ci ubanku gaba
daya,
go down on ur kneels, i said go down on ur
kneels." ya fadi cikin tsawa sannan yyi kan
intisaar din da tuni ta juya a guje xata bar
wajen
ita ma ya cafkota ya watsa mata mari
lafiyayye,
momy ta karaso inda yke da sauri tana
cewa
"kai! Kai! Wllh kar ka kuskura ka taba min
'ya,
cika ta, ta fixge hannunsa daga rikon da yyi
wa
intisaar din, cikin tsawa tace mata shiga ciki,
ta
ja ihsaan ma suka bar wajen" binta yyi da
kallon
mamaki, ya juya kan su hajiya dake ta cacan
baki amma an rasa wanda xae tunkareta
yace
"wllh hajiya kina bni mamaki, ynxu meye
amfanin
irin wannan abun, don me baxa ku kama
girmanku ba, dube yanda yar cikin ku tasa
ku
gaba tana gaggaya maku maganganu, sae
faman
kumfar baki kuke," kai Aliyu kasan me ya
faru
ne? Kasan irin abinda tayi ma umma?"hajiya
ta
fadi tana xaxxaro ido, yyi tsaki yace koma
me
tayi maku kuka siyar wa kanku. Ya dube su
kursum da har ynxu suka ki yin shiru ya
daka
masu tsawa yana cewa "bna son naga ko
wani
dabba a tsakar gidan nan ryt now, get out"
da
sauri duka suka watse suka yi sashinsu,
shima
yyi nasa bangaren ya bar umma da hajiya a
wajen..
Gaba daya mutan gidan sun hallara a
falon Abba washegari da safe, Momy na
xaune
kan 1seater fuskar ta a daure ta xuba ma
plasman ake manne jikin bango ido, intisaar
na
gefenta a kasa a xaune, hajiya da umma na
xaune a 2seater suma rai a hade, sauran
'yan
matan ma gaba daya sun nemi gu sun
xauna a
palon, ihsaan kadae ce ke gefen abbanta a
xaune, Aliyu ya shigo da sallamarsa a dalilin
kiran da abba ya aika ayi masa, ya nemi gefe
shima ya xauna. Abba yyi ajiyar xuciya ya
dubi
intisaar yace "fateemah ki gya min abinda
ya faru
a gidan nan jiya bayan na fita" nan intisaar
ta
koro masa duka abinda ya faru a jiyan, ya
jinjina
kai yace "ikon Allah" hajiya ta yi saurin cewa
"kaji
munafuka amma ai baki gya masa irin
fitsarar da
uwartaki ta dinga mana ba" abba ya daka
mata
tsawa ransa a bace yace "ki shiga
hankalinki." ta
ja bakinta tayi shiru tana hararar sa. Abba
yyi
shiru sannan ya nisa ransa a bace yace
"xainab
ban san ki da irin wannan halin ba, amma
gskya
jiya kin ban mamaki, a tunanina ko da ace
abinda yafi xagi shafa ta maki bata cacanci
ki
rama ba bare har ki hau ta da dambe ba,
kinga
kina da laifi a nan tunda dae shafa ba
sa'arki
bace, don me baxaki jirani na dawo ba ko ki
kirani a waya? Har xagi dubi tsabagen idon
Aisha
baki ji kunyar 'ya yanta ba kice mata
karuwa.?"
tsam momy ta mike tayi masa wani irin kallo
tayi hanyar fita daga palon ba tare da ta ce
komai ba, kiranta abba ya shiga yi amma ko
waiwayowa bata yi ba har ta fice daga
palon.
Hajiya tayi murmushin takaici tace "ka gani
wa
idon ka ko? Wllh jiya na dde ina naxarin
anya
kuwa xainabu ce wannan, rirrike ta fa aka
dinga
yi xata min duka bayan an rabata da umma.
Umma ta tabe baki tace "uhum ae ni naga
abun
mamaki jiya, yarinyar da mutum sae ya
rantse ya
dada rantse wa yace ko kuda baxata iya
kashewa ba, amma ashe duk wannan shiru
shirun
da take yi don taga inna na nan ne, jiya ta
nuna
mana ko ita wacece." Aliyu kam tunda ya
shigo
falon yake ta daddanna wayrsa bae ko daga
kai
ba. Abba ya dube su intisaar din gaba daya
yace
"daga yau na sake jin abu makamancin hka
ya
faru a gidan nan wllh tllh sae na karya
mutum,
kuma bna son naji wata magana ya fita
daga nan
har yaje kunnan inna, idan na kama mutum
da
karya wannan dokan sai na saba mashi
kwarai
da gaske, ku tashi ku ban waje shashashan
bnxa
kawai" duka suka mike suka bar palon,
intisaar
kam jikinta yyi sanyi sosae. Hajiya tace tana
nuna intisaar "har da 'yar mitsitsiyar 'yar
nan, ta
dubi tsabagen ido na tace min mayya" sae
kuma
ta fashe da kuka tana girgixa kai tace amma
bbu
komai ai tun farko idan muka ce mka ga
abinda
xainabu tayi bka yarda ynxu kam ai ka gani
da
idonka, Aliyu ya mike yana kallon abban
nasa
yace "kayi hkuri abba," sannan ya fice. Nan
hajiya da umma suka dinga aibanta momy,
hajiya
sae matse kwalla take, abba kam tv ya xuba
ma
ido bai tanka masu ba, umma tace "har ca
tayi
wae fadila ba 'yar ka bace karuwan....."
tsawa
abbaya daka masu ya mike yana cewa "ku
fitar
min a palo don Allah, sannan ya shige
bedroom."
hajiya ta bude baki hka ma umma, hajiya
tace
"da yake ran matan so, kuma yar gwal ya
bace
dole duk ka fice hayyacinka ae. " nan da
suka
gaba babatunsu su mike suka fice daga
palon
kowa da takaicinsa.
Intisaar na xaune kan darduma bayan ta
idar da sllhr isha'i, Abba yyi sallama ya shigo
palonnasu, ta ce "sannu da xuwa abba, ina
yini"
yace "lfya lau fatima ina momyn taku?" tace
"tana cikin daki" bai ce komai ba ya shiga
dakin
da sllma, ba kasafai Abba ke shigowa
bangaren
matan nasa ba sai da babban dalili, ta mike
ta
kwashe kwanukan da suka ci abinci ta fita
dasu
ta wanke don momynta ce tayi girki, sae da
tashiga kicin ta kwaso sauran kwanukan
wanke-
wanken mutan gidan sannan taje bakin
famfo
tana wankesu don tana tsoran wankesu a
kicin
kar 'yan gidan su rutsa ta, tun da safe dama
momy bata barta ta fito ba, ita tayi duka
ayyukanta sae xainab da ta fake idon
hajiyarsu
ta dan kama mata. Tana gama wanke
kwanukan
ta kwashesu tayi kicin din don ta ajiye ko
wanne
a maxauninsa, Aliyu ta gani tsaye yana hada
coffee, ta juya da sauri xata bar wajen taji
yace
"one more step, yhu are in trouble."
mutuwar
tsaye tayi a wajen xuciyarta na dukan uku-
uku,
yau ta shiga uka dukanta xai yi tasani " ya
karaso inda take ya xagayo ya tsaya
gabanta
yana mata wani irin kallon, tuni kwalla ya
taru a
idonta, yyi murmushin mugunta yace
"yaushe
kuka fara samun liver a gidan nan daga ke
har
uwarki," amsar ki kadae xata ceceki yau a
nan,
idan ba hka ba wllh tllh sae na fasa kanki a
nan
wajen, save my tym ki bani amsata, am ol
ears.
Ya fadi da tsawa " kuka ta fara yi tace "ni
dae
don Allah don annabi kayi hkuri ka....."
muryar
Abba suka ji yana cewa "wat's goin on in
there?"
ya fadi da xolaya, Aliyun ya kirkiro
murmushi ya
fara kame-kame, No Abba.. Kawae taimaka
mata
nke ne... Sae kuma ya karbi kwanukan dake
hannunta ya fara kkrin ajiye su inda suke,
Abba
yace "uhum ok yyi kyau hkn, idan ka gama
kaxo
ka sameni, we hve an issue 2 discuss"
Aliyun
yace "yes sir" batare da ya kallesa ba sannan
abba ya bar wajen, da gudu intisaar ta juya
ta
bar wajen bayan Abba yyi gaba, wae
juyawar da
xai yi sai ganin wajen yyi wayam ba kowa,
ya
cije lebe cike da takaici sannan ya ajiye
kwanukan hannunsa ya juya ya bar kicin
din
yana tunanin irin abinda xae mata idan ya
kamata. Bayan kwana biyu komai ya dawo
nml a
gidan, da momy ta dauki xafi sosae amma
abba
na xuwa ya bata hkuri sae ta ajiye fushin da
tayi
da tace masa komai ae ya wuce, ya ji ddin
hkn
sosae don idan ba wannan karan ba ma bai
taba
ganin bacin ranta ba kuma ya gano ita ke
da
gskya bayan yyi bincike sosae a kan lamarin,
su
hajiya kuwa ya je yyi masu kashedi mai
girma
akan su fita harkar matarshi, idan xaman
gidan
da suka je sukayi na kusan wata hudu bai
ishesu
ba to xasu koma ne, hkn yasa suka kame
kansu
don sun san shi sarai. Ranar laraba inna ta
dawo
gidan da mota shake da kaya, har gida aka
kawota aka ajiye, su intisaar da xainab suka
dinga shigowa da kaya kowa na murnar
dawowan ta, ita kuwa baki har kunne ta
dinga
fadin irin yanda aka dinga karramata a
gidan
bikin don inna akwae son girma, bakin
kofarta su
hajiya suka tsaya sukayi mata sannu da
xuwa
sama-sama suka yi gaba. Ta ja dogon tsaki
tace
"munafukan bnxa kawae da alamar ma
basu yi
farin ciki da dawowa na ba." intisaar dake
ta
faman bubbude kayan da suka shishshigo
da
bata tanka wa inna ba. Momy ma taxo tayi
mata
sannu daxu suka danyi hira sannan ta
wuce,
falon ya rage daga ita sae jikokinta tana ta
faman kullawa kowa tsarabarsa a leda.
Intisaar
ta kai nasu gida, hka ma xainab da kursum.
Fadila ta shigo gaida inna, inna ta saka
sallati
tana kallon fadilar tace "hatsarin mota kika
yi
fadila?" ta tambaya ganin yanda bakin fadila
ya
kumbura da fuskarta, xainab dake cikin
bedroom
tana gyara ma inna daki, ta toshe bakinta
ganin
dariya na neman subce mata. Fadila ta
harari
innar tace "hatsarin jirgi nayi ba ta mota
ba." ta
juya ta fice fuuuu. Inna ta kwashe da dariya
tana
cewa "ikon Allah," xainab na gamawa ta fito
tana
dariya tace "inna ki min alkawari idan na
gya
maki maganar nan xaki barshi a cikin ki"
inna
tace "hva Abu, sae kace wata yarinya sae
naje
ina cewa ga abinda xainab tace min."
xainab tace
"yauwa inna." nan xainab ta xauna ta
xayyane
wa inna abinda ya faru kwana hudu da
suka
wuce a gidan." bata kai karshe ba inna ta
mike
tana cewa " kut! Ae yau sae sun gya min ko
pampopin gidan nan na ubansu ne, sae sun
gya
min me xainabu ta tsare masu a gidan nan"
xainab ta mike a rude tana cewa "nashiga
uku
inna don Allah ki rufamin asiri abba yace kar
wanda ya gya maki, ballani xai yi wllh" shi
bukar
din yace kar a gya min? to xai dawo ya
sameni
shima," inna ta fadi a fusace ta fice daga
palon."
da gudu xainab tayi sashinsu ta shige
bathroom
ba tare da ta bari hajiya ta ganta ba jikinta
na
bari. Inna ta karaso tsakar gidan cikin daga
murya tane cewa "ina munafukan gidan...
To don
ubanku ku fito ku gya min ko ubanku ne ya
dasa
ma da'na famfofi a gidan, ku fito ku gya min
ko
nairan ku nawa ne a ciki na biya ku. Sbda
me
xaku sa min 'ya a gaba a cikin gidan nan,
uban
me ta tsare maku? Ku fito ku gya min me
xainabu ta tsare maku nace matsiyata "
cikin
daga murya inna ke ta xuba masu rashin
mutumci.
Momy ta dube intisaar fuskarta daure tace
"don ubanki sai da kika je kka gyawa inna
wannan mgnar bayan abinda....." intisaar ta
xaro
ido a tsorace tace "wllh momy ban gya ma
inna
komai ba, tana bani tsarabar mu ae ban
sake
komawa ba ma." abin ya daure wa momy
kai, to
waye ya gya ma inna wannan mgnar? Hajiya
kuwa kasa xaune tayi sae kaiwa take tana
komowa a palonta, ynxu xainabu sae da
taje ta
gya ma tsohuwar nan wannan mgnar. Hka
ma
umma dake ta lekar innar ta taga da 'ya
yanta,
tsinuwa kam sun sha shi ba adadi . Ganin
inna
taki barin tsakar gidan ne tana ta masifa
yasa
momy ta fito ta dinga bata hkuri ta koma
sashinta, amma kememe inna taki ta dinga
xunduma masu ashar tana cewa ae yau sai
tasa
sun bar gidan nan, momy tayi sumsum ta
koma
sashinta ganin ba sauraranta inna xatayi ba.
Tun
a kofar gida haisam da Aliyu suka dinga jin
muryar inna kmr speaker, Aliyu ya tabe baki
ya
koma mota ya ciro apple dinsa da ya manta
a
ciki, haisam kadae ya karaso gate din ya
shiga
gidan ransa a bace, wannan wani irin
masifa ce
hka, kullum sae anji hayaniya a gidansu sae
kace
makaranta, yana shiga gidan ya ga irin
rashin
mutuncin da inna ke xubawa a gidan ya
juya ya
bar gidan kawai. Dariya Aliyu yyi ganin
yanda
Haisam ya fito daga gidan, ko kallonsa
Haisam
bai yi ba ya shige motarsa yyi gaba. Aliyu ya
shiga gidan ya dauki farar kujerar roba ya
xauna
gefen wani flower yana ta kallon inna yana
cin
apple dinsa with much interest. Tana ta
masifa
har da kukanta, "wllh kwado xan sa wa
duka
famfofn gidan, duk shegen da xae yi amfni
da
ruwa yaje waje ," tana kai wa nan ta fice
daga
gidan tana gunjin kuka. Dariya Aliyu ya
dinga yi
har da buga kafa, hajiya ta fito jin muryar
dan
nata, ta rike haba tana cewa "ka ga makirci
ko
Ali, ynxu bayan duk abinda Alhaji yace sae
da
wannan tsinanniyar matar ta gya wa
wannan
mayyar tsohuwar ko?" shi dai bai ce komai
ba
yana ta cin tufarsa. Umma ta fito ita ma tana
cewa " wannan anyi makirar mace....."
shigowar
inna ce ta sa su yin tsit. Kananan
kwadunaye
inna ta shigo da har guda biyar, su ka bita
da
kallon mamaki. " idan akwae shegen da ya
isa ya
matso kusa da famfofin da na ya gani." hka
inna
ta dinga dasa wa famfofin kwado tana mita,
sashinsu intisaar da nata kadae ne bata je
ba,
Aliyu binta yke tayi da kallo har ta gama, ta
dawo tsakar gidan ta dauki kujera ta xauna
tana
girgixa kafa. Sumsum su hajiya da umma
suka
shige gida, Aliyu ya mike yyi hanyar kicin sae
gashi ya fito da tabarya, yyi hanyar daya
daga
cikin taps din, bugu uku yyi ma kwadon ya
balle,
inna ta taso da gudu tana cewa xan ci
ubanka
wllh idan ka sake shiga gonata Aliyu....
Tsawa ya
daka mata yana cewa "to me kke nufi hajiya,
baxan wanke hannuna ba kuma ko meye?"
yyi
tsaki ya bude tap din yana wanke
hannayensa,
ranar dae hka Aliyu ya maida inna
mahaukaciya a
tsakar gidan, tana yi, yana ta kyalkyale
dariya,
hkn yasa ta dinga rusa kuka wae bukar take
jira
a tsakar gidan. Abba yyi jigum yana
sauraran
maganganun uwartasa da bae da ma'ana
kuma
bai da tushe, ya jira har ta kai aya sannan ya
mike yana kallonta rai bace "to wae baaba
meye
na tada maganar da ya wuce kwana da
kwanaki,
meyasa kike yin hka ne fisabilillahi, ynxu ca
akayi
maki xainab din bata hkura bne ko kuma su
hajiya basu amsa lafin nasu bne?" inna ta
marairaice fuska tace "to ni ina nasani, ca
nke ae
maganar tana nan ne har ynxu," Abba yyi
tsaki
yace "wannan wani irin abu ne don Allah,
ko ma
bai wuce ba ina ruwanki cikin maganar,
tsakanina
ne da iyalina," inna dae sae wuri-wuri take
da ido,
su hajiya kmr su yi shewa don murna, ya
dube
gaba daya 'ya yan nasa dake falon fuskarsa
a
tamke yace "cikin ku waye ya gya ma baaba
wannan maganar? Kuma duk wanda yyi
min krya
sae na yi mugun saba masa wllh" yasan
momy
baxata taba gyawa inna wannan mgnr ba
duk da
su hajiya sun ce masa ita ta gya wa innar
amma
bai tanka masu ba, don yasan wacece ita.
nan
xainab ta dinga cunkulin inna alamar ta rufa
mata asiri jikinta na bari, hankadata inna
tayi
tana cewa "ke don ubanki ki rabu dani sae
shisshigeni kike yi sae kace yarinya," xainab
saura kadan ta saki fitsari don ca take inna
tona
mata asiri xatayi. Aliyu ya daka ma
kanninnasa
tsawa yana cewa "ba magana ake maku ba
wawaye kawai," inna ta kalle Aliyun kmr me
naxari, can sai tace "to ni Aliyu ne ya gya
min
wannan mgnar ba kowa ba." Aliyu ya firfito
da
ido yace "ni inna," ta galla masa harara tace
"munafuki kawai, shine ya gya min bukar,
ko
karya nayi mka?" Abba ya juya yana kallon
Aliyun
ransa ya dada baci, Aliyu xai yi magana abba
ya
daka masa tsawa yana cewa "karya knan
tayi
mka," inna tace "Atoh dae, ina xaune yaxo
ya
sameni ya gya min, intisaar ae tana wajen
lkcin,
ko krya nayi intisaar?" ta tambaya tana
kallon
intisaar din.
Intisaar tayi narai-narai da ido cikin
karkarwar murya tace "don Allah don
annabi inna
ki rufa min asiri ni wllh ina gidanmu lkcn, bn
san
kun yi ba" inna tace "au hka ne kuma, daga
ni
sae shi a palon lkcn." haisam ya kalli Aliyun
da
ya ma kasa cewa komae sae kada wa da
idonsa
yyi yana kallon innar ko kifta ido baya yi, sae
dariya ta subce masa, abba ya juya yana
kallonsa a fusace, ya mike yyi saurin barin
palon
yana yar dariya, shi dae yasan inna sharri
tayi
ma Aliyu don Aliyu bai da surutu kawae dae
yasan ramuwar irin abinda Aliyu ke yi mata
a
gidan tayi ne. Ranar kuka ne kawae Aliyu
bai yi
ba, don wanki babban bargo Abba yyi masa
"tashi ka bni waje karka sa na watsa mka
mari,
abinda yaci ace kanninka ne sukayi sai
gashi wae
kai da knka kayi" Abba ya fadi cikin bacin rai
bayan yyi fadan har ya gaji, Aliyu ya mike
kmr
xaki ya fice fuu daga palon, inna ta rakasa
da
cewa "munafuki kawae." hajiya ta mike a
fusace
ita ma ta fice daga palon, sae bayan ya fita
su
kursum suka fashe da dariyar da suke
hadiyewa
tun tuni, inna ma ta taya su dn ta rama
iskancin
da ya dinga mta a tsakar gida jiya, har
xainab
sae da tayi dariyar, intisar kadae ce bata yi
ta ba
ta hade rai. Intisar na tsakar gda tana taya
xainb
tsifan kanta aka bude gate din gidan gaba
daya
suka maida hnklinsu wurin gate din su ga
wanda
xae shigo, Aliyu ne da safeenah su ka shigo
gidan, xainab tace "tab, amma wannan
yarinyar
jaka ce mara xuciya, ynxu sae da ta sake
xuwa
gidan....." da sauri intisaar ta katse ta da
cewa
"kinga ni ba ruwana ki bar xancen nan
xainab"
bangaren hajiya suka wuce bayan intisaar
da
xainab sun gaisheta tayi masu bnxa, shi ko
ya
watsa masu harara. Xainab ta fashe da
dariya a
hankali tana cewa "ina ma Allah ya kawo
inna
nan mu ci dariya wllh," intisaar tace "ki dae
ci
dariya amma bnda ni" xainab tayi dariya
tace
"shegiya matsoraciya, dubi fa kayan da tasa
yau
har gwanda na ranan nan," intisaar ta mike
tace
"kinga idan baki son tsifan nan ne na wuce
don ni
bbu ruwana wllh karki ki jaxa min" xainab
ta
fixgota tana dariya tace "to yi hkuri nayi
shiru xo
ki karasa min." suna wajen har bayan kusan
awa
biyu sannan suka fito, hajiya sae wangale
baki
take yi tana cewa "Allah yyi maki albarka
safeenah, mun gode sosai, ki gaishe min da
hajiya kice sae naxo, umma ma tafito tana
cewa
"Allah dae ya nuna mana wannan abun
arxikin"
leda kato su hajiya da umma suka cika mata
da
tsaraba khadija na rike da ledan kmr xata
shige
jikinsafeenar dake ta murmushi tana gdya,
hajiya ta hade rai ganin xainab da intisaar
tace
"don ubanki kin xo kin gaida antynki ko sae
na
taka ki a nan," ta galla wa intisaar harara
tace
"tashi ki ba mutane waje munafuka kawae."
da
sauri intisaar ta mike ta bar wajen tayi
sashinsu,
safeena tana yatsine fuska tace "wae hajiya
wacece wannan yarinyar?" hajiya ta tabe
baki
tace "agolar gidan ce" safeenah tace
"tabdijam"
umma tace to ya muka iya. Aliyu ya fito da
makullin mota don maida ta gida xai yi yace
"ta
yi maki wani abu ne dear?" ta tabe baki tace
"muje kawae" har gate hajiya da umma
suka
rakota suna sa mata albarka, hajiya tace "ki
fa
ba wa hajiya sakona," tace "xan bata hajiya"
sannan suka wuce ita da Aliyun. Umma tace
"gskya amintakan ku da hajiya mairo yyi,
tunda
har ta dauki tilon 'yar ta xata ba danki,"
hajiya
tayi murmushi tace "ae ni bbu abinda xance
da
mairo, baki ji yanda naji ba ran da ta kirani
take
gaya min irin rashin mutuncin da tsohuwar
nan
tayi ma safeenah da bama gidan, wllh naji
takaici
sosae" umma tace "to ae laifinsa ne, don me
yasan bama gidan xai daukota ya kawo ta
bayan
yasan yan hassada ne a gidan, idan kin
bibiya
ma xainabu ce ta xuga innar tayi ma
safeenar
hkan." hajiya tace "ae ba takanas ya dauko
ta ya
kawo ta gidan ba, hanya ce ta biyo dasu ta
nan
shine yace bari ta gaida kakarsa, ae tasan
bama
gidan." muryar inna da suka ji tana kwada
wa
fadila kira ne yasa suka yi tsit, kursum tace
"bata nan" inna ta rike haba tace "ohh ni
rahmatu
yarinya ta maida kanta gantalalliya kmr
akuya
anki tsawatar mata, amma ba laifin kowa
bne, na
bukar ne, ae da ya aurar da ita da duk hka
bata
faru ba." tayi gaba tana ta mitocinta. Hajiya
da
umma suka tabe baki, umma tace "randa
wannan
tsohuwar xata mutu ae sae na xuba ruwa a
kasa
nasha," hajiya tace "ae ba ke kadai ba
shafa."
Abba yace "gani inna," bayan yaje kiran da
mahaifiyar tasa ke masa. Dama bukar dubu
ashirin xaka bani nayi ma yaran Nafisa
tsaraba
don gobe xanje gidanta, Abba yace "to inna
bari
haisam yaxo ya ciro maki." tace "yanxu fa
nake
so ni dae wllh, don bn yarda da wannan
wayon
naka ba, sau dayawa hka kke min" Abba ya
jin
jina kai yace "ynxu xai kawo maki baaba."
cike da
jin haushi yyi maganar ko sati uku ba ayi ba
da
ta saida masa fili sannan ya kara mata da
dubu
hamsin amma har tana tambayar wani dubi
ashirin din. Haisam tasa ya kaita sukayi
shoppin
din, ta jida kayan kusan dubu talatin, dole
shi ya
cika sannan ya maido ta gida. Washegari ta
samu Abba wae ya samo wanda xai kaita,
haisam baya nan, don hka dole yasa a kira
masa
Aliyusukayi
Aliyu na shigo wa palon Abban nasa ya
nemi gu ya xauna ya gaida shi a ladabce
sannan
yace "gani Abba" Abba ya hade rai yace "ka
gaida
inna ne yau?" inna ta tabe baki tace "ae ni
rabon
da Aliyu ya gaida ni tun ran da na ce shi yyi
min
wannan gulman" Aliyu ya xaro ido yace "kai
inna
ki dinga jin tsoron Allah mana" inna tayi
salati
tana kallon dan nata tace "wllh Bukar tun
ranar
Aliyu ko bangarena baya xuwa, ko ya gan ni
sae
ya kauda kai." Abba ya dube Aliyun yace
"gidan
nafisa xaka kai ta anjima," da sauri inna tace
"xuwa karfe sha daya dae" Aliyu ya mike
yana
kallon Abban nasa fuskarsa a tamke yace
"gskya
Abba ina da urgent meetin da xan wuce
ynxu...."
Abba yace "ni kke gayawa hka?" ya kauda
kansa
bai ce komai ba, inna kuwa ta dage da cewa
"wllh shi xai kaini, dolensa sae ya kaini, Allah
kai
xaka kai ni Aliyu" Aliyu ya juya yana mata
wani
irin kallo kmr ya maketa don haushi. "iyye
yaro
bashi da mutumci ba shi da kunya sae kace
ba
jininka ba Bukar, wllh bae yo halinka ba,
Haisam
kadae da xainab suka yo halinka a gidan
nan"
abba yyi murmushin takaici ya kalli Aliyun
yace
"je ka kawai." Aliyu yyi maxa yace "ohk naji
xan
kai ki ki shirya" inna tace "kaci sa'a wllh"
fice wa
yyi ba tare da ya bari sun hada ido da
abbansa
ba. Tare da intisaar da xainab inna xata,
amma
hajiya na ganin hka sae ta tura xainab gidan
wata kawarta wae ta karbo mata sako, duk
don
kar ta bi innar, don tasa xainab ko ta hanata
xuwa ba ji xata yi ba shi yasa ta bullo da
hkn.
Intisaar bata san Aliyu xai kai su ba da
baxata
fara bin inna ba, wae sae da suka fito
tukunna
inna ta fara kwada wa Aliyu kira a tsakar
gidan
wae ya fito sun shirya. Intisaar ta dafe kirji
tace
inna shi xai kai mu dama, nayi xaton adai-
dai ta
sahu xamu hau ae, inna harareta tace "ka ji
shirme, gidan dan nawa da motoci xan hau
motar
haya, inna ta sake kwada wa Aliyu kira sae
gashi
ya fito fuskarsa daure yana sanye da polo
fari da
baki, da 3quatre fari kal, shi dae kam yana
san
3quatre, intisaar ta fadi a xuciyarta, inna ta
xabga salati tana tafe hannu tace "uban wa
xaka
bi a hka yaron nan?" Aliyu ya hade rai yace
"kmr
ya wa xan bi a hka?" tace "nashiga uku ni
Rahmatu nace uban wa xaka bi da wannan
dangalallen wandon?" yyi tsaki ya ce "idan
xaki ki
wuce na kai ki, don ina da gurin xuwa
hajiya,
meye ruwanki da abinda nasa" inna ta
girgixa kai
kmr xatayi kuka tana cewa "la! Wlh baxan je
da
kai a hka ba kaji min gantalallen yaro." Aliyu
ya
tabe baki yace "to Allah ya raka taki gona,
dama
ni bnyi niyar kai ki ba ae," sae ma a lkcn ya
kula
da intisaar da ta labe a gefen innar, duk
wannan
abinda akeyi su hajiya na labe a taga suna
lekowa, hajiya taji ddin yanda dan nata yyi,
inna
ta lalubo waya tana kallon intisaar tace "kira
min
bukar" da sauri intisaar tace "bn iya ba ni
xainab
ce ta iya."a fusace inna tace "amma kin ji
haushi
kuwa" nan ta dinga kwadawa fadila kira
taki
fitowa, sae tayi waje don neman wanda xae
ciro
mata nmbr dan nata, a dai-dai lkcn Abba ya
kirata, ta dauka da sauri tana cewa "Bukar
ne?"
Abba yace "nine baaba kun tafi ne" tace "ina
fa,
wandon shaidanu yasa wae xae bini dashi,
irin
wandon nan dae da ya saba sa wa a gida"
Abba
ya kashe wayan ya kira a Aliyun, kasa daga
wayan yyi ji yake kmr ya makure inna don
takaici, can dae ya daga bai ce komai ba har
Abba ya gama sannan Abban ya kashe
wayan,
idonsa yyi jajur, ya juya fuu ya shige ciki,
inna
tace "Atoh dae." bai jima ba ya fito da
dogon
wando yyi hanyar motarsa inna ta ja
intisaar
suka bishi, tana cewa "hka kawae ya janyo
mana
kallo a gari, yaro sae kace kafiri." shi dae bai
tanka mata ba har ta ja intisaar suka shige
motar, intisaar dae jikinta bari yake, don
bata
bari sun hada ido dashi ba, "to uban wa
kuka
cewa da wannan yarinyar xan kai ku?" ya
tambayi innar fuskarsa a murtuke, inna tace
"ubanka muka cewa" to bata isa ta xauna
baya
ba na ja ta don bata kae wannan matsayin
ba
tun wuri ta dawo gun da ya dace ta xauna,
gaban intisaar ya fadi ta kalli inna, to ina
xata
xauna, ita fa wannan tafiyar ba dole sae ta
koma
gida, dama don taga tare da inna ne kuma
baxai
iya yi mata komai ba don inna baxata bari
ba
shiyasa ma bata ce ta fasa ba, amma da ace
da
su xainab ne to fasawa xatayi, inna tace "to
bbu
gun da xata xauna da ya wuce nan, bai sake
cewa komai ba don baya son magana, ya ja
motar suka wuce. A hanya hka inna ta dinga
magana a hnkli a kunnen intisaar, intisaar
dae
hadiye dariyarta kawae take don bata ma
san me
inna ke cewa ba ta dage sae mutsu-mutsu
take
mata a kunne, ita a dole xata ba Aliyu
haushi,
kallonsu kawae yake ta madubi, intisaar ta
lura
da hkn sae ta shiga taitayinta, yyi tsaki
kawae ya
kara volume din wakar dake tashi a motar, a
hankli intisar ta matso kusa da inna take
nuna
mata hanyar gidansu faruuq cikin murya
kasa
kasa take magana, inna ta bude murya tana
cewa
"Allah sarki yaron Arxiki" brake Aliyu ya taka
da
karfi, inna ta saka salati a rude tana cewa
"lfya?"
ya fito da sauri ya bude bayan motar, da
gudu
inna ta fito tana cewa "fito intisaar yau mun
shiga uku me ya faru?.
A rude inna ta dinga tambayrsa me ya
sami motar bayan intisaar ta fito, bai ko
kalleta
ba ya shiga kwaso masu ledojin tsarabarsu
da
saurinsa, inna ta dada rudewa tana cewa
"purse
dita na ciki akwae kudade da yawa fito min
dashi
da sauri wllh har da daham dina a ciki, ya
ciro
purse din ya ajiye kan ledojin da yake ta dire
su a
gefen titi, inna ta kin ki me abinta da sauri
tana
lekar motar a tsorace, "to wae me ya samu
motar?" inna ta tambaya tana jan intisaar su
matsa daga kusa da motar, bai ko kalleta ba
har
sae da ya tabbatar ko tsinkesu bai bari a
cikin
motarsa ba sannan ya rufe motar, ya juyo
yana
kallonsu fuska daure yace "ku nemi motar
haya
da xae kai ku inda xaku, don baxan bata lkci
na
na bar abinda ke gabana na dauko ku a
mota ku
dinga min iskanci a cikin motar tawa ba."
Yana
kai wa nan ya shige motarsa ya ja ta ya bar
su
tsaye a wajen, inna ta xabga salata tana
girgixa
kai tace "amma wannan yaro na Bukar anyi
tantirin dan iska, ynxu xubar damu yyi a
dajin
Allahn nan ya wuce?" sae kuma ta fashe da
kuka
tana cewa "wannan masifa da me yyi kama
ni
Rahmatu" intisaar ta dinga tuntsire dariya
tana
karewa inda ya ajiyesu kallo ita dae bata ga
alamar daji ba a wajen amma inna tace daji
ne,
sannan ga motoci na ta wuce wa abinsu,
har da
mutane ma nata harkokin gabansu a wajen.
kukan da inna ta dinga rusawa ne ya fara
jawo
hanklin jama'ah wajen, intisaar tace "kai
inna don
Allah kixo muje mu hau mota mu wuce,
dube
yanda kika janyo ana ta kallonmu," cikin
kuka
wiwi inna tace "wllh baxan hau motar haya
ba
don ubanki, hka kawae dan nawa na da
motoci
sae na buge da hawa ta haya" intisaar ta
kulu
matuka ita kam da ta sani bata bi inna ba,
wannan disgrace din har ina? Taruwa
mutane
suka fara yi a kansu ana tambaya lfya? Nan
inna
ta dinga surutu ratata akan abinda jikanta
yyi
mata, intisaar ji tayi kmr ta nutse a wajen
don
kunya, da sauri tayi gaba ta barta a wajen
cike
da takaici, ita ba kudi ta fito da ba bare ta
hau
mota ta koma gida, ta juya daga nesa tana
kallon inna da mutane suka gama
kewayewa, ko
me take gya masu oho. Da kyar mutane
suka
lallaba inna ta hau adai-daita sahu, tana
gunjin
kuka ta shiga tana cewa "Allah dae ya isa
tsakanina dashi," sae kuma ta fara
kwadawa
intisaar kira tashigo su wuce, kasa xuwa
wajen
intisaar tayi sbda mutanan da suka taru a
gun,
har kusa da ita tricycle din ya tsaya sannan
inna
tace "maxa shigo intisaar, Allah xai saka
mana,"
fuskarta daure tashiga, mutanen wajen
suka bisu
dacewa " Allah ya saukeku lfya Hajiya, Allah
ya
kiyaye, ya ja da ranki" inna ta ding a
washale
baki tana gdya tare da daga masu hannu,
shi
kanshi mai tukin dariya yake yi. Sae da suka
yi
nisa sannan inna ta dube intisaar tace
"kinga
mutanen arxiki koh, har biya mana sukayi,
Allah
yyi masu albarka dae" intisaar bata ko
kalleta ba
bare ta tanka mata. Har bakin gate Napep
din ya
ajiyesu, inna ta dinga gdya ya fiffito masu
da
kayansu, intisaar ta dauki wanda xata iya ta
shiga cikin gidan inna na biye da ita a baya
tana
cewa "to ynxu bayan duk wlkcn da yyi mana
ba
gamu a gidan ba. Nafisa tayi murna da
xuwan
mhaifiyar ta ta sosai,'ya yanta duk suka xo
gaida
kakar tasu dayake ranar asabar ce suna
gida,
sae da inna taci ta sha sannan ta soma
xayyano
wa Nafisa irin abinda Aliyu yyi masu a kan
titi,
Nafisa tace "amma wllh Aliyu bai da
mutumci ko
kadan inna, kinsan kuwa tunda na dawo ko
sau
daya bai taba xuwa gaida ni ba ko yi min
sannu
daxuwa, amma haisam xuwansa biyu
knan," inna
tace "ranar da ya kawosu xainab bai shigo
ba?"
Nafisa tace "xan masa karya ne inna?" nan
inna
ta kwadawa intisaar dake dakinsu maryam
kira,
dayake maryam din sa'arsu ce da xainab,
suka
shigo tare da maryam din, inna tace "ranar
da
Aliyu ya kawoku gidan nan dama bai shigo
ba?"
intisaar tayi jim don dae ba Aliyu bane ya
kawosu
motar haya suka shiga amma da suka koma
gida
basu ce kin kai su yyi ba, da sauri tace "eh
bai
shigo ba" inna ta galla mata harara tace
"munafukan bnxa kawae amma ca kuka yi
min ya
shigo da na tambayeku," intisaar tace "uhm
ae
xainab ce bni bace" nafisa tace jeki kawae
abinki,
kika san ko yy masu gargadi akan kar su ce
bai
shigo ba, bala'i inna ta dinga yi tana cewa
"wllh
yaron nan mugun shaidani ne, amma xai ci
ubansa bari na koma gida dae" intisaar ta
fice.
The end of book one.
No comments