Recent Updates

Harihin Namiji 5

 UGC


*BASTARD BITCH*

(Harijin Namiji)

2023


Hassana Bamalli

Oum Aphnan✍🏾


               5️⃣

Saratu Amsan takardan dake ƙunshe da

adreshin gidan Yaseer din tayi ,tana fita daga Agency din ta tsaida mai ɗan sahu ,bata tsaya ko'ina ba sai unguwar masu kuɗi😂GRA. 

Batayi wani dogon gabatar da kanta a wajen masu gadi ba suka barta ta shiga saboda sun ga sanda ogansu ke firing ɗin mai aikinsa dole zai bukaci wata,hanyar shiga Asalin falon gidan suka nuna ma Saratu ta wuce ƙirjinta na lugude saboda gaba-daya gidan ma tsoro yake bata,tunda uwarta ta haife ta bata taɓa shigowa layinba ,bare tsararren gida irin na Yaseer .


Yaseer kam cigaba da mayata da sababi yayi yana kaiwa da dawowa tsakanin falo da bedroom ya rasa wanda zai fanshe hushinsa a kansa ,wani mugun tsaki yaja


“Mtsewwww” ya koma kan kujerar dake gefen TV jaraf ya zauna ya dauko remote ya fara saita tashan TV din ,saidai duk inda ya kamo NO SIGNAL kenan dai bazasuyi ba .


Kamar mai magana da mutum haka ya dauki hargowa


“A’ah wani iskanci kenan wannan? Kuma ba signal?This is ridiculous...No reasoning !Non sense...no..no...no...” Inda inda ya kamayi ,ya rasa kalar Zagin da zaiyi.

Haka yana jaraban yina nuna TV din da remote yana daddanawa da ƙarfi irin da bala’in nan sai ya dannu dole .


Saratu daga waje bugun kofar ta soma yi “Bam! Bam! Bam!” tsaki yaja ya koma ya jingina da kujera yina numfarfashi amma yaki cewa a shigo .

Ba zato yaji ƙuuuu! An wangale ƙofar an burmo ciki kamar wacce aka jeho ta.


Duk da yina cikin tsiya ne amma saida ya ɗan firgita ,wani zabura yayi ya gyara zamansa


Ita kuwa Saratu a fujajan ta shigo kamar wacce aka ingizota ,tana shigowa tayi karo dashi ya kafe ƙofa da ido ,cikin numfarfashi ta isa gabansa  .Batayi wata wata ba ta soma da gaishesa


“Ina yini sir ,I was sent by....” katseta yayi da sauri 

“Me kikeyi anan?"

Cikin haki tace “Eh dama an turo Ni ne daga..” a ƙufule ya daɗa kwatseta yina huro hanci .


“Nace me kikeyi anan”

Gwuiwoyinta ne suka ɗan yi sanyi ,a hankali tayi sauki da muryarta “Eh dama an turo Ni ne daga ma'ai...”


“Dallah rufe mun massai (Toilet squat) ɗin bakinki,Ban tambayeki wa ya turoki ba ,cewa nayi me kikeyi anan?” 


Dararas! 

Gabanta ya yanke ya fadi

Hada gira tayi cikin rashin fahimta,A tsorace kamar zata rushe da kuka ta kada baki tace

“Sirrr...”


Zunbur yayi ya mike yina gyara ƙugun gajeren wandon jeans dinsa dake sassaɓowa kadan .Ai tsit tayi bakinta na rawa jira kawai take taji an rufe ta da duka,ilai kuwa yace


“Zan maki duka! Yanzu zan tattaka ki ,Na iya lallasa mace sosai da sosai zan maki bijibiji a nan wajen ,Ni nake magana kina yi?” 


Ja da baya ta soma yi saboda gani take a kowani daƙiƙa tana iya jin hannunsa a jikinta,Hakan ya sashi dakatawa yina haki,ƙirjinsa na sama da ƙasa ,kana ya ɗaura da masifar cikin numfarfashi


“..Kin kwankwasa ƙofa kamar mahaukaciya,baki jira izinina ba You banged the door (kin bugo ƙofar) ,ke gidahumar ina ce?”


Cikin gajiya da masifarsa ta buɗe baki tana son kare kanta “Kayi hakuri sir ,dama ina.. ”


“Kin rufe mun ruɓaɓɓen bakinki a nan wajen ko kuwa?” sa hannu tayi akan bakinta🫢alamar tayi shiru.

Wani muguwar tsaki yaja 


“Ɗan fita ki bani waje...” juyawa tayi quietly ba tare da tace komai ba ta nufi ƙofar zata fice 


“In kin ga dama kina iya kwankwasa kofar ki jira a baki izini sannan ki shigo”

A sanyaye tace “To”  ta juya ta fita 


Jefar da remote din hannunsa yayi akan gefen kujerar da yake .

“Ba tarbiyya☹️” ya fada yina relaxing akan kujera .

Ai kafin ya idasa kwantar da bayansa a allon kujeran , yaji bugun ƙofa kamar saukan aradu


“Gwan gwan gwan” kafe kofar dake girgiɗi kamar zai ɓanɓaro daga jikin bango yayi da ido yana hura hanci,kamar mahaukacin zaki .


Habawa haka Saratu ta Cigaba da bugu . Bugu take iyakan ƙarfinta“Gwan gwan gwan” wage Baki yayi da karfi yace “Shigooooo” Cikin sallamawa yanzu ba kofarsa yake jiba  ya tankacin kunnensa dake ƙoƙarin fashewa,ya firgita matuka da yanda take bugun kofar,Amma still taki daina buga kofar cigaba da bugawa tayi “Gwannnnn gwannn gwannnnn!” 


Da iyakan karfinsa ya sake cewa“Shigo naceeeee”


Hankado ƙofar tayi da sauri ta jeho jikinta falon tana nishi.


Yaseer da yake a furgice kallonta yayi 

“Ke dakata ...dakata ,dama ke ƴar baƙin cikine ko? So kike ki karya mun ƙofa? Fadamun shine dubaranki ko...don Allah don Annabi je ki jingine mun kofar in ganshi a ɓalle kinji ko?”


Saratu zare ido ta ringayi uwa mayyah.


“A’ah ,Allah ya baka haƙuri na ɗauka bakaji bane” 


“Ga kurma kuma ai dole bazanji ba .

Na lura ke muguwa ce ,so kike ki karya mun ƙofa ” 

Cabe fuska tayi cikin gundura da masifarsa “Sorry sir😌” 


Kai yatsarsa yayi kan togaciyar frame ɗin glasses dake saman karan hancinsa wanda ya raba tsakani da tsakanin madubin  👓 idonsa 

Ya ɗan cogale wajen da yatsarsa ,yina daidaita zaman tabarau din a fuskar sa ,cikin gadara yace “Zauna!!” 


Yana faɗin haka ya maida ƙafarsa ɗaya ya harɗe akan ɗaya .

Godiya tayi,gami da  ɗosana ɗuwawunta akan kujeran


“Now when cleaning my home ,you have to be very careful ,if you break anything you pay for it”

(Saurara! Idan kina goge mun gida dole kiyi da lura idan kika ɓata ko menene wlh sai kin biyashi” 


Jinjina kai tayi“To”


Kafeta da ido yayi na sakwanni biyu kafin yace “Good!”(yayi kyau) 


Ya mike yina ƙara gyara zaman kwaɓaɓɓen wandonsa dake saukowa daga ƙugu.


“Hold on ,I'll be back shortly ”(Ke dakace Ni ina dawowa ba jimawa) 


Ya fice daga falon ya haure saman gidan .bin bayansa da kallo tayi kyakkyawan Balarabe ,ma'abocin amon murya dake nuna lallai ya saba da shan tean su na larabawa da yake hana dakushewar murya ,ingarma sosai ,ma'abocin cikar zati da manyan damatsa ,kyakyawa Ajin farko ma'abocin kwantaccen gashin gira ,gazar gazar ɗin gashin ido cunkushe akan dara daran idanuwarsa da suka kasance jajaye irin na jarababbun Mazan nan wanda in suka damƙi mace hmmumm sorry!


Yinada cikar ƙasumba lufluf kamar yina watsa masu taki .

Luuuu tayi da idanuwarta ta sauke akan sharaɓan ƙafarsa ta baya ,lulluɓe yake da gashi amma tsokar naman wajen ya murɗe alamun tirenin.


Sosai ta gama karancesa a abinda bai wuce second goma ba,da sauri ta sunkuyar da idon ta tana fadin Astagfurullah ,tasan tabbas kamar abinda ta aikata zunubi ne.


Bai jima ba sai gashi da wani doguwar takarda na aiyukan da ake masa a gidan duka 

Matsowa yayi gefenta ya tsaya ,tana ganin hakan itama tayi maza ta mike tsaye 


“Wannan shine duk ayyukan da nike bukatar anamun a gidana ,if you mess it you will go” cabe Baki tayi a ranta tana cewa shi alfahari yakeyi zai kori mutum 


Wangale takardan yayi ya nuna mata lamban farko da yatsa “Kece alhakin kula da underwears dina(Pant din maza ,guntayen gajerun wanduna da sauransu) ki kula da kyau a kowani rana akwai kalar wanda nike sakawa in sunyi datti zaki wankesu kowanne ki saka masa turarensa...” Duk da ta ɗan ƙunshi mamaki amma tace “To”


“Oya kama saman takardan ki kalli rubutun da kyau” cikin Sulɓin jiki takai hannu zata riƙe.


Wani harara ya banka mata kamar mace ko ɗan daudu din nan “Dont be slow"( Kiyi da jikinki mana) 


Da karsashi ta damƙi takardan tana fadin “Ok"


Rikewa yayi da karfi jin ta fizgi takardan da karfi “Ke !! Yagawa zakiyi?🤥”


Cikin murya raɗaraɗa tace a hankali “Na shiga uku” 


“Yi hakuri!” ƙwafa yayi ya cigaba da karanto mata ayyukanta har ya kare tana gyada masa kai . ,Sannan ya zame hannunsa ya nufi kan kujeran da yake tun asali 

“Ki adana takardan nan yina da matukar muhimmanci” amsa masa tayi da “To”.


Zama yayi ya cigaba da laluben tashoshin Tvn still tana tsaye .. 


A zafafe ya ɗago “Inajin zuciyata na rawa kamar kallona kike yi ,ko ke mayya ce”?.


Gyaɗa masa kai tayi da sauri “Oya get to work” a daburce tace “Me zanyi?”


“Ji shashasha! Meye kika gani farko a list? Je ki shirya mun wanduna na!” 


“To na tafi”A fujajan tabi stairs din da taga ya fito ta nan duk da batasan kan gidan ba

Tsaki yaja “Mtsewww incompetent!”



Topah itama bata cancantan ba👌🤭?







_Let's stop faffing around my guyz...kowa dai yasan na kudine ,Tom ko ki biya ko muyi tafiyar babu ke_ 

_Time is not by our side ,In kin biya *Vip* zan Ina updates sau biyu a kowace rana saboda mu gama kafin Ramadan, *Special* zan rinka maku posting sau uku Inshallah....By God grace we shall move thnk you guyz_


Yanda za'a biya kuwa 

VIP 500#

SPECIAL 1000#

REGULAR 300#


ZAKI IYA BIYA TA KATIN MTN TA WANNAN NUMBER 09065990265 KO TA NAN BANK DIN 7782217014, Mohammed Hassana Bamalli,Fcmb 

Zaki tura shaidar biyanki ta 09065990265


ƳAN NIGER KU ZAKU BIYA DA KATIN ARTEL 500F




HASSANA BAMALLI🥰

(Oum Aphnan)

No comments