Recent Updates

Harihin Namiji 4

 


*BASTARD BI*TCH*

(Harijin Namiji)

2023


Hassana Bamalli

Oum Aphnan✍🏾


               4️⃣

Ali & Hajiya Huwaila


Lumshe ido tayi ta warce ƙafarta a hankali sakin hannu da baki yayi yabi bayanta galala da kallo cikin madarar shauƙi ga abubuwa da kwasha kwasha ,Hajiya ta tara kayan ruwa . So masha Allah.

Saida takai bakin ƙofa sannan ta waigo ta kallesa ,cikin wani irin fizgar rai ta kashe masa ido guda gamida ɗaga masa giran saman idon da ta kashe masa . 

Motsi Adams apple din maƙoshinsa yayi daga sama zuwa ƙasa alamun ya hadiye wani abu mai nauyin gaske .washe baki yayi yina mirza hannuwansa duk biyun “Eh yaseen an yaƙeni” ya fada cikin gungunai 


Cike da gadara da Muryar taƙama tace “Na dauke ka inason in gwada ƙunjin ka...sooo...” katseta yayi cikin rashin fahimta 


“Hajiya meye ƙunji” 

“zan gwada nauyin injinka in yayi zaka zame mun permanent driver ɗina ,Amma kafin nan kaje wajen Sarkin gida ya baka dokokin zama a cikin gidan nan” 


Zibewa yayi a ƙasa yina kwararo mata godiya irin na dabbobi ƴan tasha.


Yanayinsa sosai yake daɗa fizgar zuciyarta tanajin kamar ta ɗana...anya ba zan ɗana lafiyayyen fresh cucumber 🥒ɗin nan ba?

_Yes cucumber nace😅think wisely_


Tana sa ƙafarta a bakin ƙofar baby dufailat ta kirata a waya 

“Hello sweet ”  cikin shagwaɓaɓɓiyar murya tace “Momy gani a airport ba'a zo ɗauka na ba” 


“Oh so sorry sweett  ,gamunan a hanya” 


Ali yanda Hajiya Huwaila ta furta kalmar sweet din ya daɗa jefa tunaninsa a banzan tunani ,don haka bai san sanda ya kai halshensa saman bakinsa ba yadan lashe 


Kafesa da ido tayi “Yane?”


Sosa ƙeya yayi duk ya daburce irin na marasu gaskiya 


“Eh wato..wato Hajiya dama cewa zanyi gaskiya alajin gidan nan ya more da ya samu cankwadeɗiyar budurwa irinki” 


Hangame baki Hajiya Huwaila tayi cikin mamaki mata ƴar shekara 40 ana kiranta budurwa 


“Ali budurwa fa kace?”


Sosai yaji dadin yanda ta fara sakin jiki dashi ga dukkan alamu dai haƙarsa zai cinma ruwa 


“Eh where is Hajiya ina ƴan matan yanzu like samu selfie haka..Hajiya tafiya kasa ƙasa chamber agwagwa al'amura na ƙasa night....hmmm su kuwa ki gansu sun tafi sululu ba shape Kamar taɓarya sai haske smells! Maisa ciwon kai .ƙwaila ta samu caro_white.....amma fa ke jibeki Hajiya kalar madara kalar Naira haba gaskiya ki gode ma Allah hajiyata” 


Kanta gingiringim yayi jin an yabeta ance tafi ƴan matan.

“To ko kaima zaka zama Alhajin ne ɗan tselan_uwa” 


Ta jefesa da magana mai halshen damo,in ya gane ya huta...in Bai ganeba aje a gatse ta masa.

Abunka da mai neighbor ƙiris ,aikuwa yayi caraf 


“Hajiya dakuwa nayi camama yanzu ai abun ba zaran yadawa bane ,nidai a bani dama in gwada ƙarfin injina yaseen na iya tuƙi”


Waro Ido Hajiya tayi , kai dama Yaron two application letters yazo dashi kenan? Na neman aikin tuƙin mota da tua kan ɗakin gidan😝


“Zan baka dama kana ya dawowa gobe da misalin sha dayan safe Alhaji baya nan ,sai mu gani” 


***

Yaseer

Delay ya sauka a Nigeria yake barcin salary ba mahaluƙin da yasan dawowarsa bare ƴan matansa su fara masa sintiri.

Saida ya kwana ya yini sannan ya fito falon sa daga shi sai gajeren wando da red T_Shirt,yina fitowa falo ya riski House girl dinsa ta takarƙare sai gugan kayan wutan falon take da basu yi wani ƙuran kirki ba 


Wani yanutsatsen kallo ya bita dashi ,a ransa yace gaskiya wannan halittar mummuna ce arziƙinta ass😉 da saidai a kai bola ya daɗa cafe ass* dinta da Ido yina admiring alokaci guda kuma yina jin tsanarta ,what is that alaji?😎 Are you going into dementia?😆


Tsawa ya daka mata haka nan yaji yinason ya tijarata

“Keeee!”

Pauly dabatas da zuwansa ba wani zabura tayi tana gyara wuyar rigarta 


“Sabahul khair ya sheikh” ta masa gaisuwa irin na larabawa 


Wani harara ya kwarara mata “Yes sheikhhhh...mata Sheikh. You stupid brat, ƙazamar ina ne ke?, gaba-daya kin cikamun falo da wari da ƙarni meye haka?


A daburce tace “Sir turaruka masu dadin ƙamshi da room freshener na saka ma ɗakin kuma har kujeru da labulai na saka mawa bansan kamshinsu bazai maka ba...” 


Kwatseta yayi cikin bullying 

“Dalla gafara can....ina magana kina yi ke doluwar ina ce? 

Ina nufin ke! ,You You in person gaba-daya ɗoyi kike ,gaskiya bakida aji warin naki ma irin na ƙazaman maza kikeyi ....No I can't”


Ɗage hannunta tayi sama tana shinshinan hammatanta idonta shake da ƙwalla itabatas warin da takeyi ba


Journal din hannunsa ya wurgo mata a fuska “Fita must be fired bazan iya zama da ƙazama ba"


Ruɗewa tayi ta zube a ƙasa ta phase ihu “Sir wallahi nayi wanka karka koreni"


Nuna mata ƙofa yayi “Dalla fita”


“Sir karka koreni wallahi nayi wanka ,Ni uwace inada yara da suke jirana da albashin da kake bani..”


“Ohhoooo shi yasa kullum kike jinki so dull and idiot bazaa taba ganinki attractive or romantic shaaa...to ni ɗan gayune and bazan yes zama da dusa irinki ba” 


Hawaye ne ya gangaro mata a ido 

“Shikenan sir zan ringa gayu nayi alkawari” 


“Kya ɗauki wannan matakin a gaba ba a gidana ba....out!” yes daka mata wani wawan tsawa yina ƙoƙarin kai mata hauri da kafa .


A guje tayi merer ƙofa jikinta na swamp saidai ta kasa tafiya duk dahargagin da yike mata ,ba abinda take tunani illa yaranta wazai cigaba da ɗaukan nauyin su ? Wannan ya sata cafewa a bakin kofa tana cigaba da magiya taki tafiya.


Haushine ya ishesa ya shiga dakinsa da sauri .

Aikuwa chamber mara zuciya ta dawo ta dauki towel jasata cigaba da goge electronics din kenan sai gashi da belt din wandonsa ya kuwa ce zo muje.


Da gudu ta fice tana kururuwa .maida ƙofa yayi bam! Ya rufe , ya yarda belt din hannunsa yina haki 


Waya ya dauko ya kira Agency din su anty faty



Hajiya Rakiya ,kallon Saratu tayi,bayan ta gamajin duk bukatunsu nason yin aikin aikatau


“one kike ko?” jinjina mata kai sarah tayi 

“Saratu ,aikatau ba na yara masu ƴanci irinki bane,ana kawo mana yarane daga kauye wanda basu yi makaranta ba sai mu kaisu inda za'a taimake su da abinci da sutura a haka suna aika ma iyayensu da albashinsu a samu na siya masu kayan daki in sun tashi aure amma ke jibeki fa,kyakkyawa dake ƴar birni ga iliminki mashaAllah....kiyi haƙuri kije gida nayi maki Alkawarin samun maki aiki ko casual ne a waterboard ” 


Saratu haushin kanta da kanta taji ,wannan kyau nata yina cutar da ita ,cikin hawaye tayi maza ta je ƙasa ta watsa gwuiwoyinta a ƙasa


“Hajiya banason aikin waterboard din aikatau din nikeso ,nidai kawai ki clothi”


Lallabata ta soma yi amma ina Saratu na sake tuburewa cikin hawaye ,ta gama yanke tsammanin akwai ma'aikatan da zasu dauke ta aiki.


Hajiya Rakiya shiru tayi tana tunanin dubarar da Zataayiwa Saratu itakuwa Saratu sai magiya takeyi duk muryarta ya cika office ɗin.


Wayar Hajiya Rakiya ne yayi ƙara da sauri takai dubanta kan screen ɗin.

Sir Yaseer ta gani sunansa na yawo a screen ɗin .da sauri ta daga ma Saratu hannu 


“Shishhhhh🤫” kana tace “Hello Barka na da samunku sir” 


Jifanta da massivea yayi “madam na soma salaryya da incompetent maids da agencyn ku suke turo mun” 


A rude tace “Sir wancan matan da na turo ai tana da natsuwa kuma...” katseta yayi 


“Kuma ƙazama ba”


“Eweeeh😱 sir an kawo wannan kace mata mummuna mai siffan gorilla tana baka tsoro da dare ,ka koreta....an kawo wata kace budurwar ka bata sonta...an kawo wata kace mayya ce ta fiya kallo ...an kawo Wannan Kace ƙazama"


A hassale Yaseer yace “Madam kinada competent candidate ko babu..? In Babu please leave my ears to rest.” yes ƙare maganarsa yina aniyar kashe wayarsa.


 idonta sauka yayi akan Saratu ,da sauri tace “Akwai sir ,wannan nasan dolezatayi maka” 


Chili tray yayi “Indai tana wanka fine” ƙirittt ya kashe wayarsa.


Wani wawiyar ajiyar zuciya Hajiya Rakiya ta saki ta tsaida kallon ta kan Saratu 


“Saratu akwai aiki yanzun nan, amma fa campurmin irin tijararrun larabawan nan ne ,wallahi kwanakin baya ɓaras yakarya mana wata mai aiki wai ta fiye muni ya dauka aljana ne ya ganta a duhun magriba ,ya kai mata nushi a hannu yakaryata kinsan ƴan ƙwallo da mugun tirenin....hmmm yinada matsala ga tara ƴan mata kinsan larabawa da jaraba”


“Hajiya indai zai bani albashina in nayi masa aiki to zan kiyaye dokokinsa” 


Jinjina kai tayi cikin tausaya mata “Shikenan Allah yaba mai rabo sa'a”




Nurse ɗinku ce dai😍

Oum Aphnan





Kar a manta littafin kuɗine regular 300# vip 500# special 1k 

Zaki iya biya ta katin Mtn ma wannan number 09065990265 

Ko ta nan bank din

7782217014, Mohammed Hassana ,Fcmb bank.

No comments