Recent Updates

Hakki na 9

 


🌸🌸🌸🌸🌸

    *HAƘƘI NA*

🌸🌸🌸🌸🌸



 By

_jiddah S Mapi_



*Chapter 9*



*Mun kusa gama free pages*



              ~Anwar yana farin ciki ya isa gida, raken daya dawo dashi ya rabarwa yara domin baisan inda zai zauna ya cigaba da siyarwa ba, inna tana ganinshi ya shigo da kus-kus ya aje, fuskanshi da alaman damuwa ga kuma farin ciki a gefe É—aya, kallonta yayi yazo ya zauna a gabanta ya karÉ“i abin gyaran farcen da take aiki dashi, ya kamo yatsanta ya fara yanke mata farcen, kallonshi tayi taga yana murmushi, sai itama taji daÉ—i har cikin ranta, tace "meyake saka murmushi?"

"inna insha Allah zan samu kuÉ—in aikin Abban jameel"

"aina zaka samu?"

"gidan wani mutum ne zanje nayi bayin flower na rinƙa kula da shuƙe-shuƙen gidan"

jikinta yayi sanyi ta kalleshi na tsawon sakonni kana tace "kana ganin zaka iya aiki a karkashin wani?"

"inna ni waye da bazan iya ba? ai ko bazan iya ba zan koya saboda munada buƙatan kuɗin"

"to nidai addu'ata Allah ya tsareka a duk inda kake"

"Ameen inna"

bayan ya gama yanke mata farcen ya haÉ—a mata ruwan wanka ta shiga banÉ—aki shikuma ya shiga É—akinshi, murna da farin ciki yakeji koba komai zai daina ganin jameel nashi yana kuka.


washe gari da asuba Jameel yayi musu sallama a firgice, anwar da yake rike da brush ya É—ago yana kallonshi cikin firgici, tsoronshi kada ace abba ya mutu, da sauri ya saki brush É—in yaje wajen jameel yace "meya faru?"

jameel yace "Abba zai mutu"

baisan lokacin daya suri jallabiya ya É—aura akan gajeren wandon dake jikinshi ba, a tare suka fita anwar ya tada mashin, yana jin inna tana cewa su tsaya zata bisu baibi ta kanta ba, direct gidansu sukaje anwar yana shiga yace "kira taxi"

wacce take tsaye da alama kanwar jameel ce ta fita da gudu ta kira taxi, É—aga Abba sukayi suka sashi a motan, nan suka shiga tafi da umma da anwar da jameel, city hospital suka nufa emergency aka karÉ“esu, bayan sun shigar sashi É—akin anwar da jameel sun gagara zama sai safa da marwa suke, kusan 1hour doctor ya fito ya musu alama dasu sameshi, har rige-rige suke wajen bin bayan doctor, bayan sun shiga ya basu wuri suka zauna yace "wannan yana cikin tsananin ciwo, ruwa ne ya taru a kirjinshi dole sai munyi aiki.kamar yadda muka gaya muku a baya, kuma kuÉ—in  aiki miliyan uku ne, kamar yadda kuka sani, ba zamu taÉ“a shi ba sai kun kawo rabin kuÉ—in wato miliyan É—aya da dubu É—ari biyar"

kwafa jameel yayi kanshi ya dafe yana jin maganan kamar saukan aradu, anwar yace "ba komai ku fara aikin zamu kokarta"

jameel ya É—ago jajayen idanunshi yace "zamu kokarta ta yaya? aina zamu samu miliyan uku? kawai mu É—auke shi mu koma gida na cire rai da rayuwarshi, muje kawai"

hannunshi anwar ya riko suka fita waje, yana sharan hawaye yace "ka samu umma ka kwantar mata da hankali zan nemo"

hannunshi ya rike "kada kasa kanka a wani hali saboda rashin lafiyan mahaifina"

cire hannunshi yayi kana yace "saina dawo"

tafiya yayi ya hau mashin nashi, unguwan da Abba ya mishi kwantance can yaje, tun a hanya ya fara ganin rantsatsun gidajen da suke layin, a bakin wani kofa yayi musu sallama kana yayi tambaya suka nuna mishi har gidan Abba, godiya yayi ya wuce har bakin maƙeƙen get ɗin ya tsaya yana karewa gidan kallo, sai a time ɗin ya tuna bai ɗauko takaddan da Abba ya bashi ba saboda ruɗewa, gashi ya koma gida sunyi nisa, gwada sa'a yayi yaje wajen masu gadi wanda suke tsaye sun tsare kofan suna kallon duk masu shige da fice na layin, gaishesu yayi suka amsa cikin ɗaure fuska, a hankali yace "Alhaji yana nan?"

"wake nemanshi?"

kallon wanda yayi tambayan yayi babu alaman wasa a tare dashi, yace "shi yace nazo"

"ina shaida?"

"na manta a gida"

da hannu suka mishi alama da ya koma, kin tafiya yayi yana rokansu su barshi ya shiga, suna cikin jayayya faruk yayi hon, buÉ—e mishi kofan akayi ya fito da motanshi, har zai wuce sai kuma ya tsaya ya sauke glass yana kallon anwar wanda yayi jugum ya tsaya ya rasa abinyi, buÉ—e motan yayi ya fito, hannu ya mika mishi suka gaisa yace "wa kake nema?"

bayani ya mishi faruk yace "kaine bakon Abba?"

kai ya jijjiga yace "eh"

"to bismilla mu shiga daga ciki dama Abba jiranka yake tin da safe sai kuma baka zoba"

murmushi kawai yayi baice komai ba har suka shiga cikin babban gidan da yake kama da aljannan duniya, bin ko ina yake da kallo har suka isa bakin babban falo, kallonshi yayi yace "bari nayi mishi magana first"

jijjiga kai yayi, faruk ya shiga ciki, Abba yana É—akinsu noor yana duba jikin haneefa wacce ake shirin É—aura mata ruwa, sallama yayi kana yace "abba bakonka is here"

kallonshi abba yayi "Are you sure?"

giÉ—a kai yayi, Abba yayi murmushi yace "okay bari a gama É—aurawa haneefa ruwan sai inje bismilla shigo dashi main palour"

"okay Abba"

fita yayi noor tana zaune a gefe tayi tagumi, da wasa da wasa haneefa tana nema ta É—aurawa kanta ciwo akan wannan me raken, saida aka É—aura mata ruwa kana Abba ya fito, time É—in Faruk ya shigo da anwar yana zaune a gefenshi suna hira, shi anwar baya magana sai eh da a,a kawai yake faÉ—a, hankalinshi akan Abban jameel da yake cikin wani hali a hospital, Abba ne ya fito yana murmushi yana kallon anwar, zama yayi akan kujera anwar ya sauka kasa ya zauna yana gaida Abba, amsawa yayi cikin sakin fuska yace "sannu anwar har na cire rai da zuwanka"

hannu yasa ya sosa kai yace "a gafarceni Alhaji"

Abba ya giÉ—a kai kana yace "ba komai"

noor ce ta fito tana kallon takaddan da aka rubuta maganin haneefa akai, wando jins blue ne a jikinta da top fari, kayan ya kamata sosai, Abba ya É—aga kai yace "noory? kawowa bakonmu ruwa da lemo"

ba tareda ta sauko ba ta juya ta koma tareda cewa "toh Abba"

ɗabi'an Abba ne idan yana falo babu me aikin da suke shigowa, taje kitchen ta ɗau plate kana ta dawo ta ɗaura ruwa da lemo ta koma ɗaki, haneefa ta samu bacci, after dress baƙi ta ɗaura a saman kayanta ta fito, ɗaukan plate ɗin tayi ta sauko kasa, time ɗin Abba ya ɗau cheque yana yiwa Anwar sign, a hankali take takawa har ta isa gabansu, Abba ya ɗago yace "yawwa noor"

jin sunan da Abba ya kira yasa anwar É—ago kai dan yaji sunan a bakin haneefa, ido huÉ—u sukayi, plate na hannunta ne ya faÉ—i kasa, ji kake tass ya fashe harda karamin glass cup da yake kai, baya tayi tana kallonshi a tsorace, meya kawoshi gidanmu?

Abba ya tsaya da sign É—in ya kalleta yace "me haka?"

durkusawa kasa tayi tana tsince glass ɗin daya fashe, "tuntuɓe nayi Abba"

"sannu"

ya kasa ɗauke idonshi akanta, nan gidansu ne kenan? zufa yaji ya fara ƙeto mishi, ta yaya zai iya aiki a gidansu?

kallon Abba yayi wanda yake miƙa mishi cheque, Ido ya zubawa cheque ɗin yanada buƙata amma ba zai iya zama anan gidan tareda wannan yarinyar ba, Abba yace "karɓa mana anwar"

a hankali yasa hannu ya karɓa, noor kuma ta juya ta koma cikin ɗakinsu, ruwan da bata kawo ba kenan, hannu tasa ta dafe goshinta wanda zufa ya fara ketowa, a fili tace "ya biyota har gida kenan?"

kanta ta É—an buga da hannunta "me ya gayawa Abba? karfa zancen auren haneefa yayi mishi"

kwafa tayi kana tace "da ko sai inda karfina ya kare wajen raba auren nasu"

kasa tsayuwa tayi saida ta zaune a gefen haneefa wacce take É—aure da drip a hannu tana bacci, hannu tasa ta shafa kanta sannan a hankali tace "ba zan bari rayuwarki ta lalace ba"


karɓa anwar yayi jikinshi a mace, abba yace "noor bata dawo da ruwan ba bari na ɗauko maka"

girgiza kai yayi "a,a Alhaji ba komai yanzu zan wuce"

kin yadda Abba yayi saida ya ɗauko mishi ruwa ya bashi, karɓa yayi yana godiya ya fita da niyyan gobe zai zo ya fara aiki"

yana fita ya hau mashin nashi, ba dan halinda Abban jameel yake ciki ba, wallahi da ba zai karɓi kuɗin nan ba, wannan yarinyar ya san ba sonshi take ba, kanshi a kulle har ya isa bank ya cire kuɗin kana ya wuce asibiti, yana zuwa ya tarar da jameel da umma suna zaune sunyi jugum-jugum, murmushi yayi musu yace "an samu"

da wani irin mamaki jameel yace "me aka samu?"

"kuÉ—in"

yayi magana yana tafiya zuwa office na likita, jameel da mamaki yabi bayanshi suka shiga ciki, bawa likita yayi miliyan uku ne kuɗin aikin cif, bayan ya karɓa ya fita domin fara shirye-shiryen aiki, jameel ya kasa ɗauke idonshi akan anwar, tambayane fal a ranshi, anwar yaki yadda ya mishi tambaya sai kaucewa yake, cikin sa'a aka yiwa Abba aiki, kuma akayi nasara, murna a wurin jameel ba'a magana, kuka ya fashe dashi ya rungumi anwar yana mishi godiya, sai a time ɗin nasir yazo, domin baiji da wuri ba, sun shiga a tare suka duba Abba, yadda yake bacci kasan ya rabu da wani ciwo a tare dashi, hamdala anwar yayi, saide tunanin kalubalen da zai fuskanta yake, sai dare ya yiwa jameel sallama da niyan zai dawo gobe da safe, tare da nas suka fito, ya hau mashin ya koma gida, inna tana ganinshi tace "ya jikin Abban jameel ɗin?"

"da sauki inna, an mishi aiki"

waro ido tayi "aina aka samu kuÉ—in aikin?"

bai bata amsa ba ya wuce ɗakinshi, faɗawa yayi kan gado ya runtse ido, tunanin yadda zaiyi da wannan yarinyar yake, yasan zai fuskanci wulakanci a wurinta, to amma ya zaiyi? dole yayi aikin domin ya karɓi kuɗi.


haneefa ce ta fara motsa hannunta, noor da take gefe tasa hannu ta cire drip É—in dake É—aure a hannunta, buÉ—e ido ta fara a hankali tana kallon noor, "sannu ya jikin?"

"da sauki"

"ina anwar?"

da mamaki ta kalleta, "waye kuma anwar?"

juya ido tayi tana karewa É—akin kallo, a hankali tace "nayi mafarki yazo gidannan"

wani irin tsaki noor taja "ba wanda yazo nan gidan, zafi zazzaɓi ke saki surutu"

kamo hannun noor tayi tayi kasa da murya, idonta fal da hawaye tace "inason gaya miki wani abu"

zare hannunta tayi tace "tashi kiyi wanka Abba yace kiyi wanka idan kin tashi, saboda temperature É—inki zaiyi high"

a hankali tasa kafanta kasa, sannan ta dafa jikin gadon, toilet ta shiga tana cije baki, binta da ido noor tayi "wai tayi mafarki? kuma da gaske? wani irin so take yiwa wannan kazamin?"

tana wanka tana tunaninshi har ta gama ta fito, kaya marar nauyi tasa sannan ta shafa mai, da taimakon noor ta sauko kasa, Momy tayi mata ya jiki kana ta bata abinci, ci kawai take ba dan yana mata daÉ—i ba,  da haka har ta gama noor tana binta da kallo, momy.tace "me kike sawa a ranki haneefa? naga 2days kin rame"

lumshe ido tayi kana ta buÉ—esu ta kalli momy, cikin sanyin murya tace "momy ni..."

tari noor ta fara tana mika hannu zata É—au cup na ruwa, da sauri mami ta mika mata tace "sorry"

shan ruwan tayi, har yanzu bata daina tari ba, saida mami ta riketa tana bubbuga bayanta, haneefa ganin tari yaki tsayawa ta mike ta shiga kitchen, basa rabuwa da citta da kananfari, ta ɗibo a cup ta kawowa noor, karɓa tayi ta sha, sai sannu suke mata, da haka ta hana haneefa magana a wurin, momy ma bata kara tambayan haneefa ba.


washe gari, da sassafe yaje asibiti ya duba Abba kana yayi musu sallama ya fita, already ya gayawa inna ba zai samu dawowa ba domin aiki ya samu a gidan wani, gidan bai ɓata mishi ba domin yazo jiya kuma yasa hankali a hanya, yana isa ya basu takaddan da Abba ya bashi, buɗe mishi get sukayi ya shiga da mashin nashi yayi parking a bakin kofa kana ya wuce ciki, sallama yayi Abba ne a falo ya amsa tareda mishi iso, kanshi kasa ya shiga ya durkusa ya gaida Abba, cikin sakin fuska da fara'a Abba ya amsa tareda cewa "kazo?"

"eh Alhaji"

takaddan da yake ɗauke da shuƙokin fulawa Abba ya mika mishi, kana ya fara mishi bayanin yadda zai kula da duk wani flower da abinda ya shafi garden, yasa hankali sosai ya gane, Abba yace "ɗakinka a dab bakin kofa gefen ɗakin masu gadi"

jijjiga kai yayi, Abba yace "daga yau zaka fara aiki"

giÉ—a kai yayi.


sunje karɓawa haneefa allura domin doctor yana da patience, driver be ya jasu, haneefa da hijabi dogo army color a jikinta, jikin ya ɗanyi sauki, noor kuma abaya light purple tasa da ɗan karamin mayafinshi, hannunta rike da waya tana pressing, buɗe musu get akayi zasu shiga suka hango mashin a dab inda zasu wuce, saida driver ya koma baya, ya fito ya buɗe musu marfin motan yace "hajiya ku fito kafin a yiwa wanda ya aje mashin ɗin magana ya ɗauke"

ran noor ya ɓaci sosai ta fito tana kallon mashin ɗin, shiga ciki sukayi ta kwalawa me gadi kira, ya amsa jiki na rawa, tace "wani bakauyen ne ya aje mashin anan?"

"hajiya wani bako ne"

"banda dakikanci baiga compound bane zai zo ya yiwa mutane parking na ruɓaɓɓen mashin anan?"

shiru yayi kanshi kasa, taja wani dogon tsaki kana tace "kafin nan da minti biyar inga an fitarmin da wannan mashin É—in a gidannan"

"to hajiya"

haneefa sai kallonta take yadda ta rufe ido tana surfa masifa, hannunta ta rike tace "ki rage masifa"

tafiya suka fara har suka shiga ciki, Abba suka fara gani yace "noor kira duk masu aikin gidannan"

ba tareda ta shigo ba ta koma baya, kiransu tayi sukazo a tare, haneefa ma ta jirasu saida suka iso kana suka shiga a tare, baya haneefa taja ganin anwar zaune a gefen kafan Abba, wani irin murmushi ne ya suɓuce mata da sauri ta fara matsowa tana kallonshi, ɗauke kai yayi kaman bai taɓa ganinta ba a rayuwarshi, ganin haka yasa itama ta dakata tana kallonshi, noor ta zuba mishi ido kallon yadda ya ɗauke kai bai yiwa haneefa magana ba, Abba yace "yawwa wannan shine sabon ma'aikacina, shi zai rinƙa bayin flower kuma ya kula da garden da fatan zaku haɗa kai ku zauna lafiya"

a tare sukace "eh Alhaji"

murmushi Abba yayi ya kalli anwar yace "ga masu aikin gidannan ka gabatar da kanka wasu"

É—ago kai yayi sukayi ido huÉ—u da noor wacce take aika mishi mugun kallo, a hankali da rashin magana sosai yace "sunana anwar, ni ba kowa bane kuma ba É—an kowa ba, ina neman halal É—ina ne hakan yasa nazo gidannan da niyan yin aiki tukuru"

tafi sukayi mishi hadda haneefa wacce ta kasa daina murmushi, noor ta kalleta ta kalli anwar wanda ya ɗauke kai, cikin ɓacin rai ta juya ta a bar wajen, ɗaki ta shiga ta rufe kofan da karfi, "ta san yabi bayan haneefa ne, kuma wallahi saita koya mishi hankali, abinda yace yazo gidansu shi zaisa ya bar gidan, cikin zafi ta fara watsi da kayan jikinta wanda ta tuɓe, sanadinshi haneefa ta rasa mijin aure ɗan babban gida, taso ta rabasu shine zaisa kafa ya biyota har gida?"

ji tayi an buÉ—e kofan, da gudu haneefa tazo ta rungumeta, ji tayi kamar zuciyanta zaiyi bindiga, cikin murna haneefa tace "anwar yazo har inda nake noor"

janyeta tayi daga jikinta tace "ban gane me yake tsakaninki da shiba"

sakin noor tayi ta zauna bakin gado tana murmushi me cike da shauƙi da tsananin soyayyan da take mishi, hannu tasa ta rungume jikinta kana tace "i love him"

a mugun firgice noor ta kalleta, da sauri ta karasa inda take ta durkusa kasa tareda dafata tace "kinyi hauka ne?"

jijjiga kai tayi "kwarai nayi hauka akan soyayyarshi, ki kirani mahaukaciya ba zan damu ba, abinda na sani shine kawai ina sonshi, kuma zanso ya aureni muyi zama irin na mata da miji"

ta kasa ɗauke manyan idanunta akan yayar tata wacce take ganin tsananin soyayya akan fuskanta da gangar jikinta, zufa taji yana ƙeto mata a hankali tasa hannu ta share, har yanzu tana kallon haneefa wacce take murmushi tana lumshe ido, hannu ta dunƙule kana ta buga gefen gadon saida yayi kara, da sauri haneefa ta kalleta tana kallon hannunta wanda ya fashe ya fara jini, kamo hannun tayi tace "ke me haka?"

idonta har ya sauya kala tace "ki sakarmin hannu, ina nema miki inda zakije ki huta kina tura kanki cikin wahala? ko dai asiri ya miki?"

hannu tasa ta toshe mata baki, itama fuskanta ba yabo ba fallasa tace "anwar ba haka yake ba, kada ki kuskura ki kara alakantashi da wannan mummunan É—abi'an"

kallonta take idanu a ware tana mamakin yadda ta sauya lokaci É—aya, tashi tayi ta juya mata baya kana tace "kenan ba zaki iya jure kanwarki tana zagin anwar ba?"

itama haneefa ta mike ta juya mata baya tace "gaskiya ba zan jure ba"

kirjin noor ya fara dukan uku-uku, a hankali tace "kina nufin kinfi sonshi fiye da kanwarki wacce kuka fito ciki É—aya?"

girgiza kai tayi ba tareda ta juyo ba, tace "wannan ne kuma ban sani ba gaskiya"

juyowa tayi tana kallonta, hannu tasa ta dafa kafaÉ—anta tace "haneefa kin yadda kiyi raunataccen soyayya mara galihu, ki auri wanda baida komai sa talauci? kisa rayuwan yaranki wanda zaki haifa cikin talauci?"

jijjiga kai tayi "na yadda"

idon noor ya cika da hawaye a hankali tabar wurin ta faɗa toilet, rufewa tayi harda makulli, ta jingina da jikin kofan ta fara sulalewa kasa, hannu ta ɗaura a saman bakinta tanajin wani kuka me karfi yana shirin ɓalle mata, a hankali ta fara raira kuka, bata taɓa tsanan wani mahaluki kamar yadda ta tsani anwar ba, shine mutum na farko daya fara shiga tsakaninta da haneefa, kuka ta fara tana tuna kalman haneefa na cewar batasan wa tafi so tsakanin ita da anwar ba, kenan tana haɗa soyayyan da take mata da wani katon talaka?"

kuka ta fashe dashi me cin rai.


haneefa bataji daÉ—in kalaman da tayi mata ba, saide ita har zuciyanta haka yake, bata faÉ—i abinda baya zuciyanta ba, komai data faÉ—a daga kasan zuciyarta yake, tanajin sautin kukan noor a banÉ—aki ta juya ta fita daga É—akin, ba zata iya barin anwar ba Allah ya sani, tana mishi son da ko momy batajin zata iya hanata zama dashi.

anwar bayan ya gama gabatar musu da kanshi Abba yasa aka nuna mishi ɗakinshi, cikin nutsuwa yake tafiya har ya isa ɗakin, ba laifi ɗaki ne me kyau komai akwai aciki, lumshe ido yayi yana tuna inna, shi yana nan zai fara kwana a ac, ita kuma tana can tana bacci cikin zafi da rashin galihu, shiga ɗakin yayi ya tarar da kayan sawa wanda Abba yasa mishi cikin wardrobe, kuma duk irin kayan da yake amfani dasu shi yasa mishi, kallon gadon da yake shimfiɗe a gyare sai ƙamshi yake fitarwa yayi, lumshe ido yayi yana tuna yadda haneefa take murmushi tana kallonshi,.da alama tayi missing nashi sosai, shima yayi missing nata amma dolene ya nuna baima santa ba domin gudun rigima, naɗe hannun riganshi yayi wanda yake longsleeve ne, wandon ma ya naɗe kasan kana ya fito daga ɗakin ya nufi inda flower suke, da taimakon sani driver ya karewa wajen kallo, nuna mishi payp na ruwa yayi, wanda zai rinƙa ja daga dem zuwa inda flower yake, jonawa yayi ya fara fesawa flower ruwa, flowers ne masu kyaun gaske kamar ka sacesu ka gudu, saida ya gama ya kula babu mashin nashi a inda ya aje, da mamaki ya kalli sani yace "ina mashin nawa?"

"Hajiya tasa a fitar waje"

"wace hajiyar?"

"noor"

shiru yayi kana ya fita ya shigo da mashin nashi ya kai can wurin parking, dawowa yayi ya zauna a gefen sani suna hira yana karewa gidan kallo, da rana aka kawo musu abinci me kyau yaci kaÉ—an kafin yayi alwala suka shiga masallacin dake kusa da gidan wanda Abba ne ya gina, sukayi salla, yana dawowa ya shiga É—aki dan baison haÉ—uwa da haneefa, ita kuma haneefa ta wuce É—akin momy tana murmushi tace "sannu momy"

da mamaki momy ta kalleta, ya akayi ta warware haka? murmushi ta yiwa momy tace "Momy sannu da aiki"

jijjiga kai tayi tana kallonta baki a sake, bata takura mata da tambaya ba sukaci gaba da hira.


noor saida tayi kuka me isanta kafin ta tashi ta wanke fuskanta, fitowa tayi daga toilet ɗin ta zauna a bakin gado ta dafe kanta, tunanin ta yadda zata ɓullowa al'amarin take, tashi tayi tasa dogon riga wanda yake a buɗe daga kasa, daga sama kuma ya kamata sosai, pink ne rigan sai tasa flat shoe pink, wayanta ta ɗauka kana ta fito tana pressing har ta sauka kasa, buɗe kofan falo tayi kana ta fita, hannunta ta goya a bayanta tana karewa flowers na gidan kallo, suna nan lub-lub a gyare sai ƙamshi sukeyi, zagayawa ta fara tana kallon duk wani lungu da saƙo, jijjiga kai tayi tana cije leɓe kana ta koma ciki, ba zaiyi tasiri a gidannan ba, sai tasa an koreshi koran kare ma kuwa.


haneefa duk yadda taso su haÉ—u da anwar bai yadda hakan ya faru ba, hasalima idan ya ganta saiya koma cikin É—aki har sai ta tafi kafin zai fito, noor tana binsu da kallo har yanzu basuyi magana da haneefa ba kowa harkan gabanshi yake yi, sai dare haneefa taje tana mishi knocking, yana zaune suna waya da jameel yaji ana knocking, a hankali ya É—aga kai yana kallon kofan, saida yaji ba'a tsaya ba yace "ina zuwa jameel"

"okay"

kashe wayan yayi kana ya mike yana tambaya "waye?"

jin anyi shiru ya buÉ—e kofan yana lekawa, ganin haneefa tsaye tana murmushi, shima yayi mata murmushin yace "sannu"

"i miss You"

shine kalman daya fito daga bakinta, lumshe ido yayi yana jin wani abu yana yawo a cikin jikinshi, cikin sanyi da rashin sanin abinda ya faÉ—a yace "nima nayi missing naki"

da hannu tayi mishi nuni daya fito, fitowa yayi ta janyo mishi plastic chair ya zauna, itama zama tayi tana facing nashi tace "ka saki jiki ba kowa sai masu gadi"

ta faɗi haka ne duba da yadda yake taƙure kanshi yana kalle kalle da alama baiso Abba ya ganshi ne tare da ita, saida tayi maganan ya ɗan saki jiki yana kallonta, "ina ka kai wayarka?"

"na siyar"

da mamaki tace "siyarwa? meyasa ka siyar?"

"haka kawai"

shiru tayi tana kallonshi na tsawon mintuna kana tace "meyasa baka gayamin ba?"

"na kiraki baki É—aga ba"

jijjiga kai tayi, "ina inna?"

murmushi yayi tunawa da innanshi, yana matukar jin daÉ—i idan aka mishi zancen inna, yace "tana gida"

lura da haka ne yasa haneefa take yawan kawo mishi zancen inna, janshi da hira ta fara wanda rabin hiran na labarin inna ne, ya saki jiki da ita sosai, wayanta ta É—aga ta latsa, gani tayi karfe 12 da rabi, da sauri ta zaro ido tace "12 yayi saida safe"

murmushi yayi yace "na gode"

"nima na gode"

ta faÉ—a tana tashi daga kan plastic chair É—in, hannu tasa zata É—aga ta maida inda ta É—auko da sauri yasa hannu ya janye, duka da nashi ya É—auka ya mayar inda ta É—auko, hannu ta É—aga mishi kana ta wuce ciki, babu kowa a falo da alama Abba sunyi bacci, hatta ya faruk bataji motsinshi ba, cikin sanÉ—a ta shige É—akinsu ta cire rigan dake jikinta tasa na bacci, jona wayanta tayi da caji tana kallon noor wacce ta juya mata baya tana bacci, kashe wutan É—akin tayi kana ta kwanta a gefe ta lumshe ido tana tunanin hiran da sukayi.


noor wacce idonta biyu har wani kara kirjinta yake "fat fat"

jikinta yayi zafi kamar wuta, ji take kamar ta tashi taje ta shaƙeshi ya mutu, da wannan bakin cikin har bacci ya kwasheta, itama haneefa haka har bacci yayi gaba da ita.


washe gari suka shirya school babu wanda ya yiwa juna magana, sunyi breakfask a tare amma noor ko kallon haneefa batayi, saida suka gama ta fita hannunta rike da jaka tana nufan compound, daga nesa ta hangoshi yana bayin fulawa, ya naɗe kasan wando da hannun riga cikin kwarewa yake basu ruwa yadda ya kamata, kallon pipe ɗin tayi wanda yake daga can nesa aka janyo haɗe da dem, a hankali ta koma baya tasa hannu a jaka ta ciro reza, tafiya ta fara har ta isa inda pipe ɗin yake, ba tareda ta bari ya ganta ba tasa reza ta yaga pipe na ruwan, saida taga ruwa ya fara ɓulɓula a cikin gidan kafin ta juya ta maida rezan cikin jaka, wajen motansu taje ta buɗe ta shiga ta zauna tana kallonshi, ya zubawa pipe ɗin ido yana mamakin meyasa ya tsaya haka lokaci ɗaya? bubbugawa yayi yaga har yanzu ruwa yaki zuwa, cizan leɓe yayi baiso rana yayi bai gama wannan bayin ba.

ruwa ya fara cika gidan domin ba karamin zuba yake ba ta inda noor ta yanka, tana zaune ta naÉ—e hannu a kirji tana murmushi, Abba ne yazo zai fita cikin rashin sa'a yaji kafanshi tsundum a ruwa, kallon gabanshi yayi gidan ya kusa cika da ruwa, can ya hango anwar yana duba bakin pipe, da karfi yace "anwar?"

juyowa yayi "na'am Alhaji"

"miye haka? me kakeyi haka?"

sai a lokacin ya kula da yadda gidan ya jiƙe da ruwa, da sauri ya aje pipe ya karaso wajen Abba kai kasa yace "ayi hakuri ban san ya huje bane"

girgiza kai Abba yayi "baka lura bane?"

giÉ—a kai yayi yana mamaki a cikin ranshi, haneefa ce ta fito kafanta da takalmi me tsini, kallon Abba tayi kana ta karaso tace "Abba ayi hakuri nice na taka da ban sani ba"

kallonta Abba yayi kana ya kalli takalmin kafanta yace "shiyasa ake cewa ku daina sa wannan takalmi me tsinin yanzu makaranta zakije dashi?"

jijjiga kai tayi, yace "koma ki canja kalli yadda kika jiƙa mana gida, maza jeki canja"

komawa ciki tayi ya sallami anwar kana ya koma ya canja kaya ya fito, noor tana kallon duk abinda ya faru, wato haneefa ta tseratar dashi? girgiza kai tayi tana karya wuya "zamu gani for how long zaki rinƙa kareshi"

saida ta shigo kafin driver yaja suka tafi, É—auke kai tayi daga kallon haneefa tana kallon titi har suka isa school, koda suka isa bata jira ta fito kamar yadda suka saba ba buÉ—e motan tayi ta fita, kawarta Anee tazo suka haÉ—a hanya suka shiga class, binta da kallo haneefa tayi bataji daÉ—in rashin magana da noor tayi mata ba, sam batason abinda zai shiga tsakaninta da kanwarta, jikinta a mace ta shiga class ta kwantar da kanta jikin desk, batajin daÉ—in yadda Noor take behaving, saide babu yadda ta iya haka zata jure har noor É—in ta sauko da kanta.


noor kuma suna shiga class ta cewa anee ta bata shawaran yadda zata kori wannan anwar É—in a gidansu, ai kuwa ta fara bata shawara marasa kyau, giÉ—a kai kawai take tana murmushi koba komai ta samo hanyan da zata fitar dashi daga gidansu.


a haka yayi kwana biyu yana samun kulawa a wurin Abba da faruk da kuma haneefa wacce take bashi kyakkyawan kulawa, matsala É—aya yake samu shine noor wacce bata ganinshi da daraja, yauma kamar kullum yana zaune tare da sani driver suna hira, yace "anwar amma baka ganin kamar fulawowin gidannan suna bushewa?"

da sauri ya É—aga kanshi yana kallo, sai yanzu ya kula da yadda suka fara yankwanewa, da mamaki fal akan fuskanshi yace "kumafa ina basu ruwa safe da yamma kai shaida ne"

"na sani amma ka duba abu akai"

a hankali ya mike yaje wurin yana kare musu kallo, da murmushi akan fuskanta ta karaso tana kalloshi, hannunta goye a bayanta tayi matuƙar kyau a cikin riga da wando wanda rigan yake har gwiwa da wando palazo a buɗe, rigan army color ne sannan ta yafa mayafi army color, takalmin kafanta me tsayi ne, hannunta a goye da alaman murmushi na rainin hankali tace "malam anwar bakada albarka ne? ko dai talaucin naka kakeso ka shafa mana harda flowers na gidanmu"

hannunta ɗaya ta ciro tana nuna wanda yafi yanƙwanewa tace "kalli fa common flower ka kasa kula dashi to ya za'ayi kenan idan mutum aka baka daga gidannan?"

girgiza kai tayi kana ta fara zagayeshi tana kallonshi tace "unty haneefa ta rabu da kai saida ka biyota har gida da sunan neman aiki, amma kasan bambancin dake tsakanin talaka da mai kuÉ—i kuwa?"

cigaba tayi da zagayeshi tace "baka sani ba tunda baka taɓa sanin daɗin kuɗi ba, amma dan Allah ina so kayimin wata alfarma ka fita a harkan haneefa zan baka ko nawa kake so, idan kuma kaki to fa kaida ita saide soyayya koda zan rasa raina ba zan bari kuyi aure ba, saboda haka ka faɗi nawa kakeso na biyaka"


murmushi yayi domin maganganunta sun mishi zafi, sai yau ya tsinci kanshi da mayar mata martani, yana kallonta yace "bani na bita ba, itace take kirana taba bina, koda nazo gidan nan bansan nan gidanku bane, kuma bakida kuÉ—in da zaki iya siyan soyayyata"

murmushin takaici tayi, irin na gefen baki, kana tace "talaka da faɗin rai ɗin kenan, kuɗin dana rike a duniya na tabbata ko tsohuwa bata taɓa ganin irinshi ba"

hannu ya É—aga ya nunata da yatsa yace "kada ki kara sa tsohuwata a wannan maganan"

ta lura yaji zafi sosai, hakan yasa taji daÉ—i dama abinda zai sashi jin haushi shi takeso, kai ta juya tareda jujjuya ido ta matso dab dashi har suna jiyo numfashin juna tace "idan ba haka ba?"

hannu ya dunƙule yace "zanyi maganinki"

dariya ta kwashe dashi har tana tafa hannu, juyawa yayi yanar wajen, koba komai ta sashi yaji zafi sosai.




*Haƙƙi na 300 ne via 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, send your evidence of payment via 08144818849*

No comments