Recent Updates

Hakki na 8


 ðŸŒ¸ðŸŒ¸ðŸŒ¸ðŸŒ¸ðŸŒ¸

    *HAƘƘI NA*

🌸🌸🌸🌸🌸



 By

_jiddah S Mapi_



*Chapter 8*



              ~hannu tasa tana É—agoshi ya cije baki ya daure ya mike, idonta ya cika da hawaye tasa hannu tana share mishi jikinshi daya É—an É“aci da Æ™ura, jin hawaye ya É—iga a kafanshi ya É—ago fuskanta yana kallonta, kuka ta fashe dashi lips nata yana rawa, kallon yadda take kuka yayi, duk wani yanayi kyau yake mata, a hankali yasa hannu yana share mata hawayen, ganin tana kara sauko da wasu yace "shiiii ki daina kuka shikenan"

cikin kuka tace "kayi hakuri"

"ba komai bakiji ciwo ba?"

girgiza kai tayi, yace "yawwa to ki daina kuka"

a hankali tace "kaji ciwo ko?"

girgiza mata kai yayi "bayana ne kawai ya É—an bugu"

"sannu"

janshi da hira tayi tana bashi hakuri, yace "ba komai" har ta rakashi ya hau mashin nashi tana É—aga mishi hannu har ya tafi, komawa ciki tayi ta samu megadi tace "motan waye wanda ya fita yanzu?"

"a ciki aka kawo amarya"

jijjiga kai tayi kana ta koma ciki, neman noor ta fara taga bata nan, yah faruk kawai ta gani suna zaune da abokanshi suna hira, elham ma ta zama busy tana hira da mijinta, gefe ta samu ta zauna tayi tagumi, waye yayi musu wannan abin? tuna lokacin data faɗa kanshi tayi, a hankali ta runtse ido tana kallonshi yana cije leɓe, "koma wanene yayi wannan abin ya kara kusantani ne dashi"

da sauri ta bigi bakinta, tunawa da rashin kyaun abin a addini, noor ce ta shigo fuska ba yabo ba fallasa hannunta rike da katon flask tana tafiya kamar zata tashi sama, a cike take ba abinda take gani idan ta rufe ido kamar haneefa da wannan me raken, ji take kamar ta É—aura hannu aka ta tsala ihu, murmushin jin daÉ—i haneefa tayi ganin noor ta shigo, buÉ—e flask É—in tayi ta fara rarraba snacks É—in akan.duk wani plate data gani empty, yah faruk ya lura da yanayinta sharewa yayi watakila Æ´an rashin kunyan nata ne suka motso, saida ta gama rabawa ta bawa wata flask É—in ta kai mota, zama tayi a gefe tana kallon mutanen wajen, da akwai abinsha wanda zai bugar da ita ya cireta daga wannan tunanin da ba abinda zai hanata sha, haneefa ta taso a hankali ta karaso inda take, dafata tayi tace "ina kikaje?"

ba tareda ta juyo ba tace "naje É—auko sako"

"okay"

tashi tayi a wurin har aka gama dinner kusan karfe 11 kafin suka fito da yan faruk, ya rike hannayensu su duka, mota sukaje noor ce a gaba yanzu, ita kuma haneefa a baya, ta kwanta ta fara jin bacci, kallon noor yayi wacce take cika tana batsewa, hannu yasa akan goran dake gefenshi ya mika mata, karɓa tayi ta buɗe ta ɗaura a bakinta, fita sukayi daga wurin, ta shanye ruwan tass kana ta rike goran a hannunta ta murza da karfi, saida ta lanƙwasa kafin ta rike da karfi tana kallon titi, wannan yaron zata koya mishi hankali, ko hanyan da haneefa tabi ba zai kara yadda yabi ba.


yah faruk yasa hannu ya karɓe goran ya sauke glass ya wurgar, hannu yasa ya buɗe wani bowl ya ciro chocolate babba ya mika mata, karɓa tayi ta ɓare ta cinye duka kana ta yasar da ledan, murmushi yayi kana ya mika mata tissue ta karɓa ta goge bakinta da hannunta, ganin har yanzu bata runtsa ba ya ciro wayanshi ya shiga game ya mika mata, karɓa tayi ta fara game ɗin, saide tanata faɗuwa dan tunaninta baya nan, itafa idan ranta ya ɓaci sai tasha syrup take sauka, amma duk abinda za'ai mata ba zaisa ta sauko ba.


karɓan wayan yayi ya kashe kana yace "noory?"

"na'am"

"meya faru?"

ji tayi kamar ta sanar mishi abinda ke faruwa sai kuma tace "ba komai"

kallonta yayi sannan ya maida hankali kan titi yace "waya taɓaki?"

kuka ta fashe dashi, ya san akwai abinda yake damunta, hannu yasa ya janyota jikinshi yana cigaba da tuƙi yace "it's okay"

bubbuga bayanta yake kaÉ—an kaÉ—an har itama tayi bacci kamar yadda haneefa ma tayi, a hankali ya juya ya kalli haneefa kana ya kalli noor É—in, bayan Abba da momy babu wanda yakeso a duniya kamar noor da haneefa, Allah yaci gaba da kare mishi kannenshi ameen, har suka isa gida aka buÉ—e musu get suka shiga, a compound yayi parking kana ya juyo yana taping haneefa "ke haneefa tashi"

tashi tayi tana murza ido yace "munzo gida"

buÉ—e motan tayi ta fita ba tareda ta É—au jakanta ba dan yanzu 11:30 ana neman karfe sha biyu, "noory noory? tashi"

mika tayi kamar zata tashi sai kuma taci gaba da baccinta, tsaki yaja shiyasa baiso tayi bacci ai saika É—auke ta, kallon haneefa yayi wacce take tafiya tana gyangyaÉ—i yace "ga wayanta rike"

karɓan wayan tayi ya ɗaga noor suka tafi ciki, Abba yana tsaye sai kallon agogo yake, ganin sun shigo ya sauke ajiyan zuciya "tare kuke?"

jijjiga kai yayi "eh Abba"

"meyasa kuka jira dare?"

"wallahi Abba basu gama da wuri bane"

yana magana da noor a hannunshi, "kaita ka kwantar kazo munada magana"

"okay Abba"

wucewa yayi da ita ya kaita har É—aki, kwantar da ita yayi akan gado itama haneefa ta kwanta, rufasu yayi da blanket ya kashe wutan É—akin kana ya fita tareda janyo musu kofan ya wuce kasa domin yin magana da Abba.


a zaune ya sameshi yana rike da wani takadda, zama yayi a ƙasa gefenshi yace "gani Abba"

kwafa Abba yayi kana yace "Umar inaso ne muyi magana mai muhimmanci ka bani hankalinka"

"to Abba ina jinka"


"kaga wannan takaddan? takadda ne na sirri, sirrin duniyoyi da manyan kuÉ—aÉ—e wanda zai isheka daga kanka har jikoki babu talauci, inaso in mallaka maka wannan takaddan domin kana da kanne mata koda na faÉ—i na mutu banaso na barku da talauci, saide akwai sharaÉ—i dayawa akan takaddan domin ba karamin gwagwarmaya nayi ba domin na samu, kuma sai Allah yasa na samu, abin dubawa anan shine inada abokan gaba wanda suke tare dani na san ba sona suke tsakani da Allah ba, kuma idonsu akanka, ba zaka gane ba saboda har yanzu kai yaro ne"

shiru yayi, sai kuma ya ɗaura da "ina neman wanda zan aminta dashi nayi mishi gwaji har sau uku idan ya cinye gwajin shi zan danƙawa wannan takaddan, idan na mutu saika karɓa kasa hannu daga nan kubar kasar nan kaida mamanka da kuma kannenka"

zuciyan Faruk ya fara bugawa da sauri da sauri, "Abba meyasa kake wannan maganan? ba zaka mutu ka barmu ba"


"mutuwa dole ne faruk saboda haka inaso ka tayani neman aminctaccen mutum wanda zan iya bawa wannan takaddan"

jijjiga kai yayi jikinshi a sanyaye yace "to Abba, amma dan Allah ka daina wannan maganan"

murmushi Abba yayi kana yace "to na daina, tashi kaje ka kwanta"

tashi yayi tareda cewa "good night Abba"

"night son"

tafiya yayi Abba yayi tagumi a inda yake ya faÉ—a tunani, bai san time É—in da momy tazo ba saiji yayi tasa hannu ta cire hannunshi da yayi tagumin, zama tayi a gefenshi tana lumshe ido alama daga bacci ta tashi, murmushi yayi mata tace "what are you thinking?"

girgiza kai yayi "nothing"

kallonshi tayi na tsawon lokaci ta san akwai tunanin da yake, tasa hannu ta shafa gefen fuskanshi tace "muje ka kwanta dare yayi"

ba musu ya tashi yabi bayanta, É—akinshi suka shiga yayi alwala yayi sallan nafila kafin yazo ya kwanta, momy ta lura akwai abinda yake damunshi, hannu tasa tana shafa kanshi, ya lumshe ido yace "good night"

giɗa mishi kai kawai tayi, batason ganinshi cikin damuwa, har yayi bacci idonta biyu, kallon takaddan daya ɓoye a pocket nashi tayi, a hankali tasa hannu ta cire, kamar zata karanta sai kuma ta tuna may be sirrinshi ne, hakan yasa ta aje mishi ta saman gadon, mikewa tayi ta fita zuwa ɗakinsu noor, bata gansu ba tunda suka fita yau, kunna ligt tayi taga suna bacci sosai da alama sun gaji, da mamaki tace "da kayan nan me nauyin suke bacci?"

karasowa tayi ciki kana ta buÉ—e wardrobe ta ciro kayan baccinsu masu laushi da tsants, noor ta fara É—agawa ta zuge zip É—in jikinta, da alama tafi haneefa takuruwa domin kayanta yafi kamata, saida ta cire tasa mata na baccin, nan taji ta sauke ajiyan zuciya ta kara gyara kwanciya, canjawa haneefa tayi itama ta samu ta fara baccin cikin jin daÉ—i, kayan data cire musu ta kwashe ta fita dashi, a washing room a aje, fitowa tayi ta kalli É—akin faruk, tafiya tayi ta koma É—akin abba ta kwanta a gefenshi nan take bacci ya É—auketa.


Anwar yana tafiya yaje gidansu jameel, yadda ya tarar da jikin Abban gaba É—aya ba daÉ—i, jikinshi ne yayi sanyi ganin yadda jameel da kannenshi suka zagaye Abba sukayi tagumi, umma tana ganinshi ta bashi kujera ya zauna yana cewa "ya me jiki?"

fuskanta kalan tausayi tace "to gashi nan dai Anwar yadda muke fama dashi" sai kuma ta fashe da kuka, "ki daina kuka umma zaiyi lafiya insha Allah"

"ta yaya zaiyi lafiya anwar? dubi yadda ya koma, babu kuɗin zuwa asibiti, jameel ya nema har ya gaji bai samu ba, gashi yarannan ƴammatan suna da buƙatan kulawa"

jikinshi yayi matuƙar sanyi, baison ganin babba yana kuka, kai idonshi yayi zuwa jameel wanda ya sunnar da kai yana sharan hawaye, ji yayi ba zai iya cigaba da zama anan ba, a hankali ya tashi shima yana share hawaye yace "zan wuce"

zuciyanshi ba daÉ—i ya koma gida, inna tana cikin gida a zaune tana tsinan zogale taga ya shigo jiki a mace, kallon idonshi tayi taga alaman yayi kuka, bata mishi magana ba har ya shigar da mashin É—in ya aje a inda ya saba ajewa, zuwa wurinta yayi ya zauna hannu yasa ya sauke parantin dake kan cinyarta, a hankali ya É—aura kanshi a kafarta, ido ya lumshe a hankali hawaye ya fara wanke mishi fuska, shiru tayi tana kallonshi tasa hannu a fuskanshi tana share mishi hawayen, cikin muryan kuka wanda yake nuna tsantsan damuwa da yake ciki, yace "inna meyasa? babu kuÉ—in kai abban jameel asibiti ina zan samu na taimaki abokina? jameel yana cikin damuwa yana cikin tashin hankali, ba zan iya zama in zuba ido ina ganinshi haka ba, inna ta yaya zan taimaka mishi?"

hannu tasa a gashin kanshi wanda yake da tsantsi da laushi na asalin bafulatani, tana shafawa, lumshe ido yayi hawaye yana cigaba da kwaranya, inna ta rasa me zata gaya mishi, ta rasa wani shawara zata bashi, gashi basu da wani abinda zasu É—aga me nauyi su siyar, shafa kanshi take kawai har bacci ya É—aukeshi a wurin, kallon fuskanshi me É—auke da bisashen hawaye tayi, rayuwan Anwar yana bata tausayi, hawayene ya fara sauka daga idonta, da kyar ta daure ta tsayar da kukanta, saida yayi bacci sosai tana zaune a wajen yana juyi a jikinta har aka fara kiran sallan mangrib, tashi yayi a hankali yana murza idonshi, yayi mamakin baccin daya É—aukeshi me nauyi, murmushi inna tayi mishi kana tace "je kayi salla"

tashi yayi yaje yayi alwala kana ya fita yaje masallaci, bayan ya idar da salla ya rinƙa addu'a Allah ya kawo musu mafita shida jameel, komawa gida yayi ya samu inna ta haɗa mishi abinci, zama yayi yaci, kana ya kalli karamar wayar dake hannunshi, ganin haneefa bata kirashi ba sai yaji duk ba daɗi, tuna moment nasu na ɗazu yayi, ji yayi yanayin jikinshi yana sauyawa lokacin daya tuna yadda take cusa kanta a wuyanshi, lumshe ido yayi tareda tura lips nashi na kasa cikin bakinshi, inna ta kalleshi tana mamakin yadda ya sauya lokaci guda, "lafiya?"

idanunshi har sun fara sauya kala yace "lafiya saida safe"

tashi yayi ya koma ɗakinshi ya kwanta janyo pillow, ya kasa manta moment nasu na ɗazu, da ya rufe ido sai yaji fuskanta a wuyanshi, bai taɓa tsintan kanshi a irin wannan yanayin ba sai yau, ji yayi kamar ya kirata, a hankali ya ɗago wayan ganin ya kasa bacci, haneefa shi yayi saving number ɗinta, danna call yayi, har ya tsinke bata ɗaga ba, ya kara kira shiru bata ɗaga ba, aje wayan yayi ya runtse ido yana addu'a, da haka har bacci ya ɗaukeshi.


washe gari yana tashi ya fita ya cire sim nashi daga wayan ya kai kasuwa, bayan ya siyar yazo gidansu jameel ya bawa umma kuÉ—in koba komai zai É—an rage mata wani abun, bai samu jameel a gida ba hakan yasa ya tafi da wuri, yana isa gida ya fara shirya kayan rakenshi, inna tace "baka karya ba"

"barshi inna sai anjima"

zubawa tayi a flask ta mika mishi, karɓa yayi ya ɗaura akan kus-kus na raken yace "na gode"

fita yayi daga gidan ya wuce wurin aikinshi, saide abin mamaki yana zuwa yaga ba kowa a wajen, gashi an share tas kamar mutane basu taɓa zama ba, gabanshi ne ya yanke ya faɗi, ƙarasawa yayi yana kallon wurin, ganin babu kowa ya juya ya kalli gefe, table ɗin da yake ɗaura rake yaga an wurgar a gefe an kakkarya, da mamaki ya kalli mutumin dake gefe yace "bawan Allah meya samu wurin nan?"

mutumin shima ya saba da wurin yace "wata ce ta siya wurin"

"to meyasa suka watsar mana da kaya?"

wucewa mutumin yayi yace "gaskiya ba zan iya sanar maka ba domin batada mutunci"

yana tsaye a wurin tazo ta gabanshi zata wuce, tayi masifan kyau cikin dogon riga baƙi wanda ya fitar da shape ɗinta, bakin glass ta manna a fuakanta, a hankali ta ɗaga glass ɗin ta tsaya tana facing nashi tace "ku watsar da komai na wurin banason datti, kuma gobe za'a fara aiki"

kallonta yayi itace wacce ta mareshi ranan, ba zai manta fuskanta ba, ta ɗaga glass ɗin sama tace "masu aiki anan sun ɓatashi da datti, gashi nan komai a ɓace, wannan ai kazanta ne, ka duba duk dattin rake ne ya ɓata wurin"

É—auke kanshi yayi yasa hannu zaija kus-kus nashi tace "ku É—aga table É—in can ku kai bola yayi kazanta dayawa"

kallon table É—in data nuna yayi, table nashi ne, yana gani wasu manyan guards suka É—aga table É—in ta gabanshi suka wuce dashi suka wurga can gefe da nisa"

barin wurin yayi tana kallonshi har kanshi ya ɓace, murmushi tayi dan ganin ya koma ta inda ya fito, mota ta shiga ta tada kana ta bar wurin, dama abinda yasa ta zuba maƙudan kuɗaɗe ta siya kenan, yau da safe tasa aka nema mata numbern me wurin, ta kirashi tace ya saida mata wajen yace a,a, ninka mishi kuɗi tayi domin so take ta wulakanta wannan bakauyen me raken, zuciyanta fes lokacin data isa gida, tana parking ta fito tana murza makullin mota tana tafiya cikin fara'a har saida masu aikin gidansu suka fara mamaki, koba komai ta raba wannan kazamin da haneefa.


tana shiga É—aki taga haneefa tsaye a gaban mirror tana kiran waya baya tafiya, gaba É—aya fuskanta yayi wani irin, ji tayi an rungumeta ta baya, kallon noor tayi ta cikin madubi taga murna a fuskanta, a hankali tace "meya faru?"

da karfi ta kuma riketa tace "unty haneefa yau haka kawai nakejin farin ciki"

"akan me?"

"kede ki bari kawai"

sakinta tayi ta ciro chocolate daga jakanta ta ɓare ta kai bakin haneefa, ɗauke kai tayi, noor tana dariya ta cusa mata a baki, shan dole tayi kana ta kuma danna call taji layin a kashe, murmushi noor tayi "na rabaki dashi ba faɗa ba zagi"

wucewa tayi dakin momy ta É—au laptop tana kallon wani film.


haneefa ganin layinshi baya shiga ta shiga tashin hankali sosai, kiran elham ne ya shigo mata tana É—agawa tace "amarya bajya laifi"

"yanzu ma laifin nayi dan zamu wuce saudi ban gaya miki ba"

"haba dai? yanzu kuna ina?"

"muna jirgi zamu tashi nanda 5mins"

"gaskiya elham banji daÉ—i ba,meyasa baki gayamin ba nazo da wuri muyi sallama?"

"tuba nake, kwana uku kawai zamuyi mu dawo"

"okay safe journey, aci amarci lafiya Ina zayd É—in?"

"gashi nan yana gaisheki"


"my regards"

kashe wayan tayi sannan tayi wani tunani, da sauri ta juya ta buÉ—e sef ta ciro riga da skirt orange color, É—inkin yayi kyau, tasa ta yafa mayafi orange kana ta É—au waya ta fito, É—akin momy taje tace "momy ki ban motanki naje duba elham suna airport zasu wuce saudi"

"oh yaushe akayi bikin har zasu tafi?"

dariya kawai tayi, Momy ta bata makulli ta karɓa zata fita noor tace "inzo muje?"

girgiza kai tayi "no yanzu zan dawo"

murmushi tayi dan tasan inda zataje, fita tayi ta shiga motan ta fita daga unguwan tana sauri taje ta ganshi, tun daga nesa taga an share wurin ba kowa sai masu aiki, gabanta ne ya faÉ—i, tayi parking a hankali ta fito tana tambaya meya samu wurin?

wani ne yace an siye"

kallon gefe ta fara ko zata ganshi, cikin rashin sa'a ko alamanshi babu, wasu daga gefe taje tana tambayan ko sunsan gidansu? cewa sukayi basu saniba, abinda haneefa bata sani ba shine noor ta bawa kowa kuÉ—i a wurin tace kada suyi wa duk wacce tazo tambayan gidansu anwar bayanin inda gidan yake.


jiki a mace ta koma mota har tana jin kanta yana ciwo, bayan ta rufe marfin motan ta jingina da jikin seat tana kara trying number É—inshi switch off, wasu hawaye taji sun fara zirya a idonta, dama batada wuyan kuka, haka kawai taji ta rabu dashi kenan, jan motan tayi ta koma gida, a compound tayi parking ta fito tana tafiya a hankali, kana ganinta ka san tana cikin damuwa, abba ne ya riketa yace "lafiyanki?"

firgigit ta dawo hayyacinta ashe ta kusa buge Abba ne, kakalo murmushi tayi tace "lafiya kau Abba"

kallonta yayi na Æ´an seconds kana yace "ki gayan gaskiya meya sameki?"

kanta kasa domin ɓoye hawayen dake shirin zubo mata tace "ba komai Abba naje airport ne su elham sun tafi"

"kina son elham É—in nan, to ba zakuyi waya ba idan sunyi landing"

kai ta giÉ—a a ranta tace "ina sonshi Abba"

shafa kanta yayi "ki shiga ki huta kinji?"

giÉ—a kai ta kumayi kana ta wuce ciki, É—akin momy taje ta aje mata key, sannan ta juya ta fita, bin bayanta noor tayi da kallo har ta rufe kofan, saide jikinta yayi sanyi ganin yanayin haneefan, basarwa tayi "damuwan na lokaci kaÉ—an ne, gyara miki feature É—inki nake, ba zan iya ganinki cikin rayuwan talauci da kaskanci ba"

cigaba tayi da kallonta hankali kwance.


haneefa faɗawa tayi kan gado tana kara kiran numbern, har yanzu shiru, buga wayan tayi da jikin katifa, a hankali ta jawo Pillow ta ɗaura kanta, wani ɗan marayan kuka ne ya suɓuce mata, tasa pillow tana toshe bakinta dan bataso kowa ya jiyota.


anwar yana tafiya yaji kanshi yana sarawa, anan ne kaÉ—ai yake samun ciniki sosai, ya zauna a wurare da dama bai samun ciniki hakan yasa ya nemi me wajen da kyar ya samu suka barshi ya zauna, yana cikin rufawa kanshi asiri kuma ace yau wannan yarinyar ta siye wajen? Ina zaije? yana cikin tafiya yaga wani mutum tsaye a gefe ya dafe kai da alama yana cikin damuwa sosai, kamar zai wuce sai kuma ya tsaya yana ganin yadda yake buga jikin motan, aje abin raken yayi kana ya karasa wajenshi yayi sallama, É—ago kai mutumin yayi yace "wa alaika salam"

"lafiya ka tsaya cikin rana kamar akwai damuwa, zan iya taimaka maka?"

kallonshi yayi yace "wallahi matsala aka samu motan taki tafiya na kai rabin awa anan babu wanda yazo taimaka min"

murmushi yayi yana gyara hannun riganshi yace "inane ya ɓaci?"

a ciki ne, buÉ—e mishi marfin motan yayi ya shiga, shima ya shiga, jakan dake gefe baki ya É—aga ya buÉ—e, da sauri anwar ya kalleshi daloline a cike da jakan sai gefe guda kuma kuÉ—in nigeria"

maida zip É—in yayi ya rufe ya kalleshi yace "ga abinda ya hanani zuwa siyan abin gyaran, idan na bari ina tsoron kada Amin sata, Amma tunda kazo bari naje na siyo, ka kulamin da jakan sosai dan Allah"

girgiza kai yayi "kawo naje na siyo kawai yallaɓai"

girgiza kai yayi "baka yadda dani bane?"

shiru yayi, mutumin ya buÉ—e marfin motan ya fita ba tareda ya rufe ba, anwar dake zaune a wurin idonshi akan jakan yana kallon kuÉ—i tsirara, nesa dashi mutumin yayi saida ya jima bai dawo ba, har anwar ya fara gajiya ya fito yana lekawa ko zai ganshi, abin mamaki har yanzu bai dawo ba, kusan 1hour kafin ya hangoshi yana zuwa, ajiyan zuciya ya sauke dama har ya fara tsorata, yana murmushi ya karaso yace "sannu na barka kai kaÉ—ai"

murmushi anwar yayi kana yace "ina abin gyaran ba komai"

mika mishi super glue yayi ya karɓa ya shiga ciki, manna inda ya ɗan ɓantare yayi kana yace "shikenan"

kallonshi mutumin yayi kana yace "ya sunanka?"

"Anwar"

jijjiga kai yayi kana yace "miye aikinka?"

"saida rake"


"zaka iya aikin bayin flower a gidana?"

jijjiga kai yayi "zan iya"

da mamaki yace "me yasa ka amsa da wuri?"

"saboda baban abokina ba lafiya zan iya yin aiki koma na menene in kaishi asibiti, banda aikin daya saɓawa Allah"

"baban abokinka? har yanzu akwai wannan abotan"


"Inason abokina sosai banason abinda zai taɓa shi, rashin lafiyan mahaifinshi yana sa jikina yana sanyi, haka yasa na ɗau aniyan neman kuɗi domin taimaka mishi"

"nawa ne kuÉ—in aikin?"

"miliyan uku"

jijjiga kai yayi kana yace "zan kaishi asibiti na biya miliyan biyu, miliyan É—aya kuma sai naga kana kokari a aikin kafin na baka"

jijjiga kai yayi "na yadda indai za'a yiwa Abban jameel É—ina aiki ya samu sauki"


"sunana Aminu sadauki, idan kaje g.r.a kace a nuna maka gidan Aminu sadauki"

ciro takadda yayi ya rubuta wani abu ya mika mishi, gobe da karfe 11 na safe ka sameni a gidana,idan ka nunawa masu gadi wannan takaddan zasu maka iso har falona"

karɓan takaddan yayi yana jin daɗi a ranshi, Abban jameel zaije asibiti? gani yake kamar a mafarki, godiya yayi ya buɗe motan zai fita Abba yace "karka manta aikin bayin flowers zakayi"

giÉ—a kai yayi "insha Allah zanyi"

fita yayi ya tafi, Abba ya saki murmushin jin daÉ—i, wannan yaci gwaji na farko, waya ya É—aga ya kira faruk, "Hello Abba"

"mun samu wanda yaci gwajin farko, ya kabarin wancan kuÉ—in?"

faruk da yaji daÉ—i yace "gaskiya Abba sun gudu, daga bashi jaka kafin ma juya baima san menene a ciki ba harya guda dashi, kusan mutane uku"

murmushi Abba yayi "ba kowa keda amana ba a wannan zamanin sai wanda Allah ya soshi"


"hakane Abba"

kashe wayan Abba yayi, bai taÉ“a tsammanin matashi kamar wannan zaiga kuÉ—i haka ya bari ba tareda ya taÉ“a ba, buÉ—e jakan yayi ya kara kallon kuÉ—in, yadda ya bashi haka ya samu, cikin farin ciki ya koma gida, haneefa kwance akan gado kamar da wasa zazzaÉ“i ne ya kamata har hakoranta suna haÉ—uwa, suna bada sauti gat-gat, momy da noor suna gefenta momy ta É—aga waya tana kiran doctor, noor ta zubawa haneefa ido, yanzu akan wannan kazamin take tashin lafiya? Innalillahi kodai asiri yayi? 

suna zaune har doctor yazo yayi mata gwaje-gwaje, magani da allura yayi mata, daga nan ta samu bacci ya ɗauketa, noor tayi tagumi tana kallon haneefa, ko wani irin rashin lafiya zatayi ba zata bari ta kara raɓan wannan mutumin da tunda Allah ya halicceta bata taɓa tsanan wani mahaluƙi kamar shi ba, ko me kama dashi ta gani sai taji ta tsaneshi, sanadinshi yasa haneefa ta rasa ɗan former president, ba zata yadda wani daman ya kara wuceta ba...




*Haƙƙi na is 300 via 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, send your evidence of payment via 08144818849*

No comments