Recent Updates

Hakki Na 6

 


🌸🌸🌸🌸🌸

    *HAƘƘI NA*

🌸🌸🌸🌸🌸



 By

_jiddah S Mapi_



*Chapter 6*



              ~da asuba haneefa ce ta fara tashi, miÆ™a tayi tana salati bayan ta kunna wutan É—akin, idonta ne ya sauka akan kayan dake kasa rigan noor da wando dasu jaka, kallon noor tayi wacce take bacci sosai gashinta ya kwance ya barbazu akan pillow, gabanta ne ya faÉ—i ta fara tunanin ina taje da wannan kayan? sauka tayi daga gadon ta kwashe kayan ta kai washing machine, takalmin ta maida a ma'ajiyan takalma, alwala taje tayi kana tazo ta tada salla, saida ta idar ta fara tashin noor tareda kiran sunanta "noor tashi kiyi salla"

turo karamin bakinta tayi sannan ta buÉ—e ido É—aya ta kalleta, komawa tayi ta kara jan duvet É—in baccinta taci gaba dayi, haneefa ta kara tashinta cikin bacci tace "am off banayi"

shiru tayi "to kodai date nata ya canja?"

girgiza kai kawai tayi sannan ta juya ta fita daga É—akin, kitchen taje ta fara taya mai girki aiki, saida suka haÉ—a breakfask sannan taje É—akin Momy ta gaisheta, Momy tace "noor kam tana aikin nata na bacci ko?"

"eh momy bacci take"

"tayi salla ne?"

"a,a tana off"

"okay"

tashi Momy tayi suka sauko tareda haneefan, yau weekend kowa yana gida harda Abba dasu ya faruk, Abba ne ya fito daga É—akinshi hannunshi rike da jaka yasa haneefa ta kira mishi driver ya bashi sako zuwa bank, zama yayi akan kujeran dining yana tambaya ina noor?

haneefa tace "bacci take"

faruk ya fito daga ɗaki yana kallon makullin dake hannunshi, gani yayi kamar gefen key holder ɗin ya karye, waje ya fita zuwa wajen compound ya duba motanshi, waro ido yayi ganin yadda gaban glass ya fashe ga taya yayi faci komai na motan ya ɓaci, da karfi ya kira me gadi, yana zuwa ya durkusa, "waya fita da motata?"

me gadi ya kalli motan, sai yanzu yaga abinda ya faru, hannu yasa ya dafe kirji kana yace "yallaɓai wallahi ban sani ba"

"baka sani ba? kamar yaya? waye a bakin get?"

"wallahi bansan wanda ya fita da motan ba, ni dai na san jiya da wuri nayi bacci amma banga kowa ya fita da mota ba"

yana magana jikinshi yana rawa, ran faruk ya ɓaci sosai, da karfi ya fara kiran duk ma'aikatan gidan, suka taru a gabanshi yana tsaye yana karkaɗa makullin, kana ganinshi kasan ranshi ya ɓaci, yana son motan sosai har cikin ranshi, sannan Abba bai daɗe da siya mishi ba, 2weeks kacal motan yayi, tambayansu ya fara waya taɓa mishi mota? kowa yace bai sani ba, girgiza kai yayi "kuje shikenan"

komawa ciki yayi ranshi yana tafasa ya fara kwalawa Noor da haneefa kira.

tana zaune akan sallaya sai yanzu taga dama ta tashi tayi salla, jin ya faruk yana kwala mata kira taji kamar ta tsula fitsari a wando, a take idonta ya fara raina fata, ta san yau ta kaÉ—e har ganyenta.


jin kiran yaki tsayawa Momy da take zuba abinci wa Abba ta kalleshi tace "meya faru kake kiransu haka?"

"momy tambayansu zanyi"

"okay"


hijabin dake jikinta har kasa purple ne daga sama an É—aure da igiya baki, tafiya ta fara jikinta yana rawa, zuba mata ido yayi yadda take taka stair kamar zata faÉ—i, kanta a kasa har ta karaso gabanshi ta durkusa, haneefa ma tazo ta durkusa, yana daga tsaye yace "waya shiga motata jiya?"

shiru ba wanda ya amsa, tsawa ya daka musu "i said who use my car?"

jikin noor ya fara ɓari tayi rau rau da idanu, bakinta yana rawa tace "n.."

haneefa tace "nice"

kallonta noor tayi da mamaki yadda ta amsa itace tayi wannan laifin, faruk ya kalleta sosai yace "are you sure?"

girgiza kai tayi "eh jiya ne aka kirani a waya ƙawata tayi accident itada driver ɗinsu kuma dare yayi shiyasa na shiga kawai naje wajen"

yana huci yace "ina taje?"

"tayi tafiya ne shine dare ya kamata"

"wace kawar taki?"

"Elham"

wayanshi ya ciro daga aljihu yace "bani number É—in gidansu"

numbern Elham ɗin ta bashi ya karɓa sannan ya kalleta, looking serious yace "idan na kira naji saɓanin abinda kika gayamin kinsan me zai biyo baya"

jijjiga kai tayi, ya danna call, kira É—aya Elham ta É—aga tace "ya faruk good morning"

"morning ya jikin naki?"

a hankali tace "da sauki"

"bakiji ciwo ba kam?"

"eh kafata ce ta É—an gurje amma haneefa tazo sun kaini hospital a daren an wanke"

"okay Allah ya Kara sauki"

"ameen na gode sosai ya faruk"

katse wayan yayi, "daga yau idan abu ya faru kada ki kara kuskuren tafiya ke kaÉ—ai, bakya tsoron hanya ne?"

"am sorry"

Abba yana jinsu har ya gama faÉ—an suka dawo wajen cin abinci"


noor sai sunnar da kai take, tana satan kallon haneefa, ita kuma haneefa ta É—auke kai tana cin abinci bata yadda ko sau É—aya ta kalli noor É—in ba, saida ta gama ta mike tace "alhmdllh momy bari naje ciki"

binta noor tayi da kallo har ta shige cikin É—aki, Momy ta kallo noor ta kuma kalli yadda take kallon haneefa, ta san da abu a kasa.


haneefa na shiga ɗaki ta ɗau waya tayi dialing numbern Anwar, kira kusan uku kafin ya ɗaga, muryanshi kamar na kullum cikin zaƙi da iya magana yace "hello"

ji tayi kirjinta ya buga batasan me zatace mishi ba yau, jin shirun yayi yawa yace "haneefa"

lumshe ido tayi, a duk lokacin daya kira sunanta sai wani shauƙi ya ɗibeta, sai taji kamar a bakinshi sunan yafi daɗi, a hankali tace "ina kwana?"

"kin tashi lafiya?"

jijjiga kai tayi kamar yana ganinta, sannan tace "lafiya kalau"

"okay meya faru?"

shiru tayi, saida taga shirun yayi yawa shima yayi shiru tace "ina son rake"

murmushi yayi "okay anjima zan fita ai yanzu ina gida"

"to aina kake da zama yanzu?"

"a inda nake zama kullum"

"okay tom zanzo insha Allah sanda biyar nake so a yayyanka duka"


"to ba damuwa"

"da karfe nawa zaka fito?"

shiru yayi kana daga bisani yace "saina gama wankewa innata kaya"

murmushi tayi "zai kai nawa?"

"zai kai karfe 11"

katse wayan yayi tabi wayan da kallo, ita ta kirashi ita ya kamata ta kashe ba shiba, taɓe baki tayi kana ta kwanta tana kallon slin na ɗakin, haka kawai take samun nutsuwa idan tayi magana dashi, dama yau ranta a dagule akan lamarin noor sai gashi ta samu nutsuwa da shauƙi a lokacin da taji muryanshi, a hankali ta lumshe ido tana kallon hotonshi wanda ya kasa gushewa a idanunta.

turo kofan tayi, shigowa tayi kana ta tura kofan ta rufe, jingina tayi da jikin kofa tana kallon haneefa wacce take murmushi ido a lumshe, haƙika ta matukar tsorata da ɓaciwan motan ya faruk, haneefa ta ceceta, a hankali tace "ina kikaje jiya da daddare?"

tambayan da haneefa tayi mata kenan.


"club"

tashi tayi daga kwancen da take, takawa ta fara tana kallon noor da mamaki har ta isa gabanta, hannu tasa ta ɗauketa da mari, kafin ta ɗago ta kara kai mata wani marin ta ɗayan ɓangaren, cikin zafin abinda ta faɗa tace "noor me kike nema ki zama? club kinada hankali?"

kanta kasa bata É—ago ba hawaye ya fara bin fuskanta yana sauka kan kafar haneefa.


jikinta ne yayi sanyi ko kaÉ—an batason ganin kanwarta tana kuka, a hankali tasa hannu ta É—ago fuskanta ta fara share mata hawayen, saida ta gama ta janyota jiki tana bubbuga bayanta kaÉ—an, ganin kuka ya kwace mata tace "it's okay ki daina kuka"

shiru tayi dama tasan idan tayi kuka zata karya mata zuciya shiyasa batayi wani rashin kunya ba ta fashe mata da kuka, ta san haneefa da tausayi da saurin yafiya shiyasa tayi haka, saida taji tayi shiru sannan ta zameta daga jikinta tace "idan kinaso ki kasheni da bakin ciki to kici gaba da wannan abinda kikeyi"

tana faÉ—an haka ta juya zata tafi, hannunta ta rike tace "kiyi hakuri ba zan sake ba"

"kanki kike yiwa, kece zaki haifi yara ana nunasu ana cewa mamansu tana shaye-shaye kuma tana zuwa club"

"ba zan kara ba"

shiru kawai tayi ta kalli agogo taga karfe tara da rabi, library ta tafi domin yin karatu kafin time ɗin tafiyanta yayi, har ji take kamar 11 ba zaiyi ba taje inda yake ta ganshi, idanunta suna mararin ganinshi, tana burin sake sanyashi a cikin idonta, takaddan take me home ta ɗauka ta fara karantawa domin rage mata lokaci, Abba ya ƙawata musu library yasa musu takaddu na turanci.


noor waya ta ɗaga bayan ta cire hijabin dake jikinta, riga baƙi da skirt pitch ne a jikinta, ta gyara hulan kanta sannan ta janyo teddy ta rike a cinyanta ta buɗe data ta shiga watsapp, group nasu ta shiga tana ganin conversation na mutanen ciki, saida ta gama karantawa ta hango minal tana recoding voice, tayi niyan sauka ganin minal yasa ta tsaya saida ta turo voice ɗin kana ta buɗe tanaji, dariya tayi itama ta danna voice ta fara recoding, mutanen dake group ɗin suka fara cewa "ga noor ga noor"

bata magana a group saida wanda ta saba, wani ko ana mata magana bata kulasu kuma sun bata admin, tana tura voice É—in suka fara mata reply, ganin na'eem yayi magana tace "birthday boy"

ya gajiya yayi mata sukaci gaba da hira group É—in yana daÉ—i idan noor tana online, duk da ba magana take ba amma idan tana chatting da frends nata har zuciyanta takeyi suna hirane kamar Æ´an uwanta.


karfe goma da rabi haneefa ta shigo ɗakin tana murmushi tana kallon agogo, toilet ta shiga tayi wanka ta fito ta ciro wani lotion me kamshi wanda ta haɗa da kulacca, shafawa tayi noor tana kallonta tana chat har ta shafa powder da lipbalm, mascara ta shafa a gashin idonta wanda ya kara mishi tsayi sosai, tayi kyau matuƙa, kitson kanta ƙanana ta kame da ribbon sannan taje bakin wardrobe ta ciro wani abaya pitch color tasa, gel ta shafa a gaban gashinta ya kwanta lub, ta yafa mayafin abayan ta rufe gashinta sai gel ɗin data shafa ake gani ta gaban goshinta, takalmi flat tasa kana ta fara feshe jikinta da turaruka masu kamshi, saida ta gama ta kalli kanta a madubi "madalla ga ubangijin da yayi wannan halitta"

shine abinda ta faÉ—a a ranta, jaka kalan abayan ta É—auka, side bag ne yayi kyau shima da adon baby a jiki, wayanta ta É—aga tana kallon time, 10:50, murmushi tayi tana lumshe ido tareda cije lip na kasa, idan bata ganshi yau ba bazata iya bacci ba.


"Unty haneefa zan biki"

noor tayi magana tana sauka daga gado tareda kashe data, kallonta tayi tace "a,a ki bari gidansu elham zanje karɓan anko na, yanzu zan dawo"

mamaki ne ya kamata, haneefa bata taɓa hanata binta unguwa ba, duk inda zataje tareda noor take zuwa, yau kawai tace ba zata bita ba?

"to koda ba zaki jima ba zan biki"

"a,a noor"

ta faɗa tana fita daga ɗakin, jikin noor ne yayi sanyi dan bata taɓa yimata haka ba, meyasa zata hanata binta? ko dai har yanzu fushi take dani?.


Anwar wanki yake a cikin gida yana wanke kayan inna, ita kuma inna tana gefe tana girki tana bashi labari, tsohuwa ce me kamala gata duk da ta tsufa jikinta me kyau ne, idan ka ganta bazaka zata tana cikin babu a rayuwanta ba, tsaf tsaf take gata da tsafta, jin ya mata shiru yana cigaba da wanki ta kalleshi tace "wai kai anwar meyasa kake haka ne? kai wani irin miskili ne? ina magana kana jina zaka min shiru?"

kallonta yayi da lumsashun idanunshi yace "inna ina jinki ai"

"kana jina kenan nice kala uwar zance ko?"

girgiza kai yayi, tayi karamin tsaki kawai itama tayi shiru, ta san yafi son haka, yafiso a zauna shiru ba magana, ɓangaren anwar kuwa tunanin halinda Abban jameel yake ciki na rashin lafiya, musamman idan ya tuna yadda jameel yake kuka hakan yana kara karya mishi zuciya, da haka ya gama wankin ya ɗibi ruwan zafi daga cikin tukunya ya zuba a bahon wanka, shiga ciki yayi dashi, duk abinda yakeyi cikin nutsuwa yake abinshi, yana shiga ya kunna pompo ya haɗa ruwan ya zama da ɗumi, kana yayi wanka, fitowa yayi da towel a waist sannan ya shafa mai yasa kananan kaya, turare ya fesa, ya fito ya nufi inda yake aje kus-kus nashi, inna tace "ba zaka jira abinci ba?"

girgiza kai yayi "idan kin gama zanzo na É—auka anjima"

"zan kai maka da kaina"

jijjiga kai yayi ba tareda yayi magana ba ya buÉ—e kofa zai fitar da kus-kus É—in, cikin masifa tace "bama zakace ka gode ba kenan?"

a hankali yace "na gode"

tagumi tayi tana tausayawa matar da zata auri anwar, ta tabbata sai bakin cikin rashin magananshi ya kasheta, wannan miskili haka?.


yana fita ya fara tafiya cikin nutsuwa yama manta sunyi magana da haneefa cewar 11 zata zo, tafiyanshi yake cikin nutsuwa har ya isa bakin titi, haneefa wacce take zaune cikin mota tana kallon wurin bini-bini take kallon agogon dake É—aure a hannunta, yace mata 11 kuma har 12 bai fito ba? ta fara gajiya har ta cire rai zai fito, driver yana zaune yana kallonta, ganin tana cikin damuwa yace "hajiya lafiya?"

tsaki taja kaÉ—an fuskanta kamar zatayi kuka tace "ba komai muje kawai"

haka kawai yakejin yarinyar a cikin ranshi, tana da sauki sosai batada girman kai kamar ba Æ´ar masu kuÉ—i ba, yadda take bashi daraja kaman ba driver ba, yace "to hajiya"

har ya tada motan zasu tafi ta hangoshi yana tsallaka titi, wani irin murmushi ne ya suɓuce mata wanda bata san daga ina ya fito ba, kallon driver tayi tace "tsaya"

tsayawa yayi ta zubawa Anwar da yake tsallakawa yana duba titi ido, saida ya iso ya fara jera raken akan table, bai kula da motan da yake gefenshi ba, ya gama shiryawa ya zuba musu ruwa, gaisawa yayi da sauran makotanshi, zama yayi a inda ya saba zama, hannu tasa ta buÉ—e marfin motan, a hankali ta fito da kafafuwanta wanda sukasha bakin takalmi suna shining, murmushi akan fuskanta ta fito tana kallonshi, takawa ta fara har ta isa inda yake, kanshi kasa yana game a Æ´ar karamar wayanshi, cikin sanyin murya tace "barka da warhaka"

É—ago kai yayi ya kalleta, murmushi me sanyi tayi mishi, shima ya maida mata murmushi wanda yasa zuciyar haneefa bugawa da sauri da sauri, tana daga tsaye tace "zan iya zama"

kallon gefenshi yayi kana ya matsa sosai yace "bismilla"

zama tayi tace "ya inna?"

daÉ—i yaji har ranshi, ba abinda yake faranta mishi rai kaman yaji ance ya inna, "tana lafiya"

jijjiga kai tayi, ta kasa É—auke idonta akanshi, ganin tana kallonshi ya kawar da kai gefe, ta zubawa kanshi ido wanda yake É—auke da lallausan gashi, cikin sanyi da mutuwan jiki tace "ina rake na?"

sai a time É—in ya tuna sunyi magana, hannu yasa ya shafa sajenshi kana ya kalleta yace "sorry hajiya na manta"

tashi yayi ya fara kankare rake, tana kallonshi har ya gama ya yayyanka yasa mata a leda, mika mata yayi tace "na gode"

hannu tasa a cikin jaka ta ciro wasu bandir-bandir na dubu É—aya ta mika mishi, hannu yasa ya karba ya kirga É—ari biyar biyar uku ya cire, ya mika mata sauran canjin, kallonshi tayi tace "a,a na bar maka"

girgiza kai yayi ya aje mata akan cinya sannan ya zauna a gefe yace "a,a kuÉ—ina 1,500 ne"

da mamaki tace "ka maida hannun kyauta baya kenan?"

girgiza kai yayi "ba haka bane iya kuɗina nake karɓa"

ganin zatayi magana ya tashi yaci gaba da aikinshi bai kara biyowa ta kanta ba, shiru tayi jikinta yayi sanyi, tasa hannu ta É—au kuÉ—in tasa a jaka, a hankali ta mike tana rike ledan dake hannunta tace "to na tafi"

"Allah tsare"

ya faÉ—a ba tareda ya kalleta ba, tafiya take cikin nutsuwa har ta isa bakin motan, kara kallonshi tayi taga yana cigaba da aiki ne, shiga motan tayi ta zauna a gefen driver bayan ta aje ledan, tace "gashi"

kallon ledan yayi yana washe haƙora yace "hajiya wannan duka namu?"

"kaida wa?"

"hajiya dake mana"

dariya tayi "bana shan rake"

da mamaki yace "bakya sha kuma kika siya?"

da hannu ta mishi alama dasu tafi, jan motan yayi suka É—au hanya.


noor ta ɗaga glass lokacin da sukazo gab dasu, huci take zuciyanta kamar zai fasa kirjinta ya fito fili, kallonta minal tayi ganin yadda take huci ta ɗau goran ruwa ta buɗe ta mika mata, karɓa tayi ta ɗaura goran a bakinta saida ta shanye duka sannan ta sauke goran, sai a lokacin ta samu bakinta ya buɗe tayi magana, cikin sassarfa da tashin hankali tace "me nake gani minal me zan gani? haneefa tanaso ta zubar mana da class, tana so ta zubar da darajan family ɗinmu? me ya haɗata da me rake?"

kanta ta haɗa da jikin sitiyari tana ji zufa yana ƙeto mata, ya zatayi idan freinds nata sukaga haneefa a wajen me rake? shikenan class mata ya zube?

cikin zafi tasa hannu ta buÉ—e marfin motan zata fita minal ta riko hannunta, juyowa tayi ta zubawa minal manyan idonta tace "menene?"

"calm down noor, me zakiyi mishi?"

"zan bambance mishi tsakanin me kuÉ—i da talaka"


"idan kinje kinada tabbacin shi yake kiranta? ai da idonki kikaga ita tazo, ki bari ki tabbatar da abinda kike zargi kafin ki É—au mataki"

"minal I can't wait wai har saina tabbatar, can't you see yadda take kallonshi tana murmushi? idan ban yiwa tufkar hanci ba akwai gagarumin matsala nan gaba"

"no noor calm your self down, ki kyaleshi may be daga yau ba zata sake zuwa ba, kikasan ko aika akayi mata na siyan rake?"

dawowa tayi ta zauna a mazaunin driver, ta dafe kai cikin takaici tace "nayi blocking number É—inshi fa daga wayarta kuma na goge ta yaya akayi ta samu?"

minal tace "kinga fito zan jamu kinyi weak ba zaki iya driving ba"

fitowa tayi itama minal ta fito suka canja waje, minal ce take jansu, noor sai ruwa take sha dan ta rasa abinyi, har kofan gida ta kaita sannan tace "kibi a hankali kada kiyi haneefa ta gane kinbi bayanta control your self"

"okay minal, but please this should be a secret between I and you, koda aneesa ne banaso taji wannan maganan, saboda abin kunya ne kinji?"

jijjiga kai tayi "ba wanda zaiji noory"

tana tsaye a wajen har minal ta tafi, cikin takun isa da kasaita wanda ya zame mata jiki ta fara tafiya, hannu tasa tayi knocking na kofan, shiru ba'a buɗe ba, dama da ɓacin rai ta shigo gashi ta kara tarar da wani, sai faman knocking na kofan take getman be buɗe ba, zama tayi a gefe tana girgiza kafa, ji tayi an buɗe kofan, ɗago idonta wanda yayi jajur tayi tana kallonshi, "kiyi hakuri hajiya na ɗan zaga ne"

"ka zaka É—akin ubanka"

tayi maganan kamar zata mareshi, shiru yayi domin wannan zagin ya daki zuciyanshi, koba komai ya haifi kamarta harda wanda suka girmeta, shine zata mishi wannan zagin, a zuciye tazo zata wuce taga bai bata hanya ba, cikin masifa tace "musa zan iya zabga maka mari idan baka matsamin a hanya ba"

matsa mata yayi ta wuce kamar zata tashi sama, so take kawai ta ganta a É—aki tasha syrup ko hankalinta zai kwanta, getman yana ganin ta shiga ya rufe kofan ya samu wani dake zaune a gefe da alama shima me kula da gidan ne, yace "ka rubutamin takaddan aje aikin gadin nan"

"haba malam musa, kaida nake ganinka me hakuri meyasa zakayi haka?"

"zan iya juran komai amma banda zagi daga bakin Æ´ar cikina, talauci ba hauka bane, kuma kuÉ—in ubanta baya gabana ina neman na rufawa kaina asiri ne"

"kayi hakuri malam musa"

kin hakura yayi saida ya rubuta mishi takaddan aje aiki, ya aika ciki aka kaiwa momy idan Abban yazo a bashi, bai musu sallama ba yabar gidan.


momy na zaune a falo taga noor ta shigo, cikin fara'a tace "noory? kin dawo? ya jikin maman minal É—in?"

"da sauki"

ta faɗa ba tareda ta juyo ba, cikin zafin rai ta wuce tana taka matattakalar stair, da ido momy ta bita tana mamakin abinda yadda take behaving, tana cikin mamaki akayi sallama, ta amsa tareda yin iso, me kula da ɓangaren baki ne ya shigo da takadda a hannu, gaida momy yayi ta amsa ya mika mata takaddan yace "gashi inji malam musa megadi"

karɓa tayi tace "okay"

buÉ—ewa tayi ta fara karantawa, "yayi resign meyasa?"

tambayan da tayiwa kanta, kallon inda noor tabi tayi, ba dai noor ce tayi mishi rashin kunya ba?

tashi tayi ta fita daga falon, har inda yake zama taje tace "ina yake?"

sun tabbatar mata da ya tafi, bataji daÉ—i ba sam, jiki a mace ta koma falon ta zauna akan kujera tana mamakin meyasa ya aje aiki a lokaci É—aya kuma ya tafi?.


tura kofan ɗakin tayi za shiga, haneefa har ta canja kaya tasa riga da wando silk, tana kwance ta rungume teddy bear, tana murmushi harda dariya na farin ciki, kana ganinta kasan tana cikin farin ciki sosai, ganin noor ta shigo ta tashi daga kwance da take, da sauri ta karasa inda noor take ta rungumeta tana juyi da ita, noor ta zuba mata ido tana kallon yadda take dariya, rabonta da ganin haneefa cikin farin ciki ta jima, sai yanzu take ganin tana dariyan da bata taɓa yin irinshi ba, ji tayi kaman an watsa mata acid a kirji, a hankali tasa hannu ta zake haneefa daga jikinta tace "murnan me kike?"

sai a time É—in ta tuna abinda takewa murna, da sauri ta dawo hayyacinta ta daina dariya da murna, tace "am Ina murnan zamuyi dinner a bikin elham"

kallonta tayi sosai "dinner ai an daÉ—e da faÉ—an za'ayi"

juyawa tayi bata kara magana ba ta zauna a gefen gado, noor ma bata kara cewa komai ba, ta cire mayafin dake jikinta, canja kaya tayi tana kallon haneefa ta cikin madubi, ranta ba daÉ—i ko kaÉ—an, haneefa kuma tana kara tunashi tana kara jin wani sabon farin ciki a ranta.


tana tafiya ya juya yana kallon motansu, har suka bar wurin sannan ya tashi ya koma inda ya bari ya zauna yana kallon kuÉ—in daya cire a cikin wanda ta bashi, sawa yayi a cikin aljihu yanzu baida buri kamar yaga ya samu kuÉ—i ya kai abban jameel asibiti anyi mishi aiki, gashi ciwo sai gaba yake yana karuwa, tagumi yayi yana tuna inda zai samu kuÉ—i har dubu É—ari biyar ya biya kuÉ—in aikin Abban, yayi nisa cikin tunani yaji anyi tafi a bayanshi, yasan nas ne a hankali ya juya ya kalleshi, zaka yayi a gefenshi ya É—au rake ya fara sha, yace "tunanin me kake harda tagumi?"

"nas ina tunanin jikin Abban jameel, yanzu haka ana neman dubu É—ari biyar domin yimishi aiki, abin yana damuna, kullum jameel yana cikin kuka banson ganin abokina cikin wannan halin, gashi babu aikin yi da zamuyi har mu tara mishi wannan kuÉ—in"

yana magana idonshi yana cika da hawaye, domin anwar yanada tausayi abu kaÉ—an yana iya sashi kuka, girgiza kai nasir yayi kana yace "nima kullum ina cikin wannan tunanin to amma kasan bamuda yadda zamuyi, nima Abba baida wannan kuÉ—in amma inada plan kuma nasan zaiyi aiki"

kallonshi Anwar yayi alaman wani plan?

murmushi yayi "kuÉ—in tafiya school nawa zan bada ayi mishi aikin dashi, kaga saimu nemi dubu É—ari biyu kawai"

"kada mu ɓata maka feature idan kayi karatun nan karuwanmu ne duka"


"a,a my gee zan taimakawa Abban jameel ba zan iya karatu cikin nutsuwa ba idan na tuna halinda suke ciki"

shiru anwar yayi dan bayida tacewa, yanason su taimaka kuma baison karatun nas ya samu matsala, haka dai har ya gama siyarwa yamma yayi suka tashi tare suka tafi gidansu anwar É—in, inna tana kwance a É—aki cikinta yana ciwo, shiyasa bata kaiwa anwar abinci ba, yana sallama yaji bata amsa ba hankalinshi ya tashi, da sauri ya karasa É—akinta ya buÉ—e labule yana kiran "inna?"

a hankali tace "anwar ka dawo?"

ganin tana kwance ya karasa ciki da sauri, nas ne ya shigo mishi da sauran raken, "bakida lafiya ne?"

yayi magana a tsorace dan baison abinda zai taɓa lafiyan Inna, cikin son kwantar mishi da hankali tace "cikina ke ciwo"

a hankali ya kwantar da kanshi a cikinta ya fashe da kuka, hannu tasa tana shafa kanshi tace "kaga shiyasa banason faÉ—a maka banida lafiya yanzu saika fara kuka, alale aka kawomin daga gidan malam sa'adu naci da zafi shiyasa nake ciwon ciki"

rungumeta yayi da karfi hawaye yana zuba daga idonshi ya ciza leɓenshi wanda ya koma ja saboda yawan sha da yake, a hankali yace "inna meyasa kikaci? kinsan banida kowa sai ke, banaso na rasaki, idan na rasaki rayuwata ta lalace kenan"

shafa kanshi tayi sannan tayi murmushi tace "kada ka damu anwar ba zaka rasa ni ba, ina tare da kai a koda yaushe, tashi kaci abinci"

kin tashi yayi saida tayi da gaske kafin ya tashi, nas ya shigo yana cewa "ina wannan tsohuwar ne? yau na jita shiru"

ganinta a kwance yace "subhanallah meya sameta?"

anwar cikin sanyi yace "cikinta ke ciwo"

"sannu Allah kawo sauki, bari na siyo mata magani"

sai a lokacin ya tuna ashe ana shan magani, ya rikice da ganinta a kwance harma ya manta ana shan magani, kallon nas yayi kana ya ciro kuÉ—i a aljihu yace "gashi"

kin karɓa yayi "innarka ce kai kaɗai? ai nima tawace"

fita yayi da niyan siyo magani, abinci kaÉ—an yaci ya wanke hannu ya dawo gefenta ya zauna yayi tagumi, da yana da kuÉ—i da asibiti zai kaita ba zai tsaya wai tasha magani kawai ba, to amma ba kuÉ—in dole yayi hakuri da maganin kawai, inna kuma tana jin ciwon cikin sosai amma tana daurewa ta nuna mishi na komai saboda bataso yasa kanshi cikin damuwa, ta san idan ya ganta ba lafiya damuwa yake sawa a ranshi har ya rame, sai kuka kuma kamar karamin yaro, har nas ya kawo maganin yana zaune ya zuba mata ido yana kallonta.

nas ne ya bata maganin tasha sannan ta koma ta kwanta, shima anwar pillow ya janyo ya kwanta a gefenta, nas yace "karka sa komai a ranka zatayi lafiya"

lumshe ido kawai yayi...




*Haƙƙi na is 300 via 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, your evidence of payment via 08144818849*

No comments