Recent Updates

Hakki Na 5

 


🌸🌸🌸🌸🌸

    *HAƘƘI NA*

🌸🌸🌸🌸🌸



 By

_jiddah S Mapi_



*Chapter 5*



*Zaku iya fara payment domin ba zamuyi free pages da yawa ba, ₦300 ne via 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ur evidence of payment via 08144818849, masu kati zaku iya tura mtn credit ta wannan Latin 08144818849*



              ~Haneefa cikin jin daɗi tayi bacci ranan, noor kuma sai taping fuskanta take tanason gane bacci take ko idanunta biyu, wannan wani irin zubar da class haneefa tayi? meyasa zata kira shi? na shiga uku, duvet ɗin ta yaye daga kanta ta leƙa fuskan haneefa, gani tayi tana bacci hankali kwance murmushi akan fuskanta, kallon wayan tayi dama tasan password, cirewa tayi ta kalli numbern da tayi waya dashi last, danna block tayi kana ta ajiye wayan ta koma ta kwanta.


Anwar bayan sun gama waya ya kurawa wayan ido yana kallon numbern data kirashi dashi, taɓe baki yayi kana ya aje wayan a gefe baiyi zaton zata kirashi ba, rufe idonshi yayi a hankali bacci ya fara ɗaukanshi, wayan ya kumaji yana ruri, yatsina fuska yayi, idonshi da suka lumshe ya buɗe sannan ya ɗaga yaga sunan Jameel yana yawo a gaban wayan, received ya danna ya kara a kunne.

"saina fara bacci kake kirana me kuma ya faru?"

"kai tashi albishir nazo maka dashi"

tashi yayi daga kwancen da yake ya zauna tareda janyo Pillow ya ɗaura kan kafanshi yace "albishir na me?"

"companyn AY ventures sun fara ɗiban ma'aikata gobe da safe suke bukatan takaddu zasuyi screening"

jijjiga kai yayi "mashs Allah gobe zamuje Allah yasa muna da sa'a, kasan banida burin da ya wuce naga na samu aiki ina kula da inna, koma wani irin aiki ne zanyi"

"na sani ka kwana da niyya gobe saimu je mu jarraba Allah yasa wannan karon ba zamu rasa ba"

"Ameen"

sallama sukayi ya kashe wayan ya kwanta, haƙiƙa yana son aiki idan ya samu ba karamin farin ciki zaiji ba, ya nemi aiki da dama Allah bai bashi ba, kullum yana addu'a Allah ya zaɓa mishi aiki mafi alkhairi.


washe gari bayan ya idar da sallan asuba yana zaune akan sallaya yana azkhar kamar yadda ya saba, jallabiya ne a jikinshi ruwan kasa, saida gari yayi haske sannan ya mike ya ninke sallayan, jallabiyan ya cire sannan ya ɗaura towel babba a ƙugunshi, toilet nashi madaidaici wanda yake cikin ɗakin ya shiga, pompo ne a ciki ya kunna ya tara ruwa a roba kana yayi wanka tareda kara ɗaura towel ɗin ya fito, mai ya shafa ya buɗe akwatin dake gefe ya ciro wani yadi coffee color wanda yake a goge, sawa yayi kayan ya karɓeshi sosai, sajenshi ya taje tareda gashin kanshi wanda yake a kwance kamar na balarabe, agogo ya ɗaura kana ya fito daga ɗakin hannunshi rike da takalmin da zaisa, ɗakin inna yaje yayi sallama, shiga yayi ya sameta tana zaune akan tabarma tana lazimi, saida ya jira ta gama ta juyo tana kallonshi

"Anwar Ina zuwa da sassafe haka?"

gaisheta yayi ta amsa tana kara tambayanshi ina zashi?

tashi yayi ya buɗe drower dake kusa da ita ya ciro wasu takaddu yace "wani company zanje suna neman ma'aikata"

shiru tayi batace komai ba, tasan koda yaje ba dole ya samu ba, lamarin kasan sai kana da uwa a gindin murhu zaka samu aiki, koda ka samu saide su danne su baiwa yaransu, kallonta yayi kana ya cigaba da gyara takaddun yana sawa a envelope, yasan tunanin da take, saida ya gana yace "inna ta? kada kisa komai a ranki Allah yana tare damu, kiyimin addu'a kawai"

"kullum cikin yimaka addu'a nake kuma Allah zai karɓa watarana"

fita yayi yana murmushi, mashin nashi me kafa biyu ya ɗauka kana ya fita ya buɗe kofa, unguwansu na talakawa ne, kana gani ka san marasa karfi ne a cikinta, a nutse yake tuka mashin ɗin, yayi tafiya me nisa kafin ya isa gidandu jameel, kiran layin jameel ɗin yayi yana ɗagawa yace "ina kofa"

jameel shima ya shirya ya yiwa ummanshi, addu'a tayi musu Allah ya bada sa'a, ya amsa da ameen.


ya sameshi ya harɗe hannu a kirji yana zaune akan mashin, leɓenshi na kasa yake ciza da karfi kaɗan yana kallon cikin unguwan, murmushi yayi kana yace "har ka fito?"

jijjiga kai kawai yayi, jameel ya hau bayan mashin ɗin, saida ya tada mashin suka fara tafiya yace "ya su umma?"

"suna lafiya meyasa baka shiga ba?"

kallon agogo yayi "banso muyi latti kusan karfe 7 fa yanzu"

"gaskiya ne, yau kam ba fita sana'a ko?"

tsaki yaja kaɗan kana yaci gaba da tuƙi kamar ba zaiyi magana ba, sai can sunyi nisa har jameel ta cire rai da magananshi yaji yace "zan fita idan mun dawo da wuri"

inda sabo ya saba da halin Anwar wani lokaci yanaji kana mishi magana zai shareka kamar baiji ba, sai idan yaga dama zai amsa, tun abin yana ɓata mishi rai yana ganin kamar girman kai ne, har ya gane ba girman kai bane haka nature ɗinshi yake, har suka isa company Jameel ne yake magana shi anwar saide yayi murmushi kawai, tun a bakin get aka duba takaddunsu sannan aka bari suka shiga, mutane ne dayawa a wurin kowa rike da takadda, jameel ya kalli Anwar shima anwar jikinshi yayi sanyi da ganin mutane da yawa da alama yauma ba sa'a suka fito.


one by one ake kira ana interview a ciki, tun suna jira har suka fara gajiya, jameel ya fara lumshe ido yanajin bacci, kallonshi Anwar yayi ya jingina da jikin bango ya fara gyangyaɗi, kallon agogon hannunshi yayi nan yaga karfe ɗaya da rabi na rana yayi, hannu yasa ya ɗan bugi jameel, buɗe ido yayi yana hamma da alama yana jin yunwa "muje muyi salla mu dawo"

shine abinda anwar ya faɗa, tashi jameel yayi suka fita, masallacin dake kusa sukaje sukayi alwala, a jam'i sukayi salla, bayan sun idar sukaje zasu shiga ciki, kofan a kulle, jameel ya kalleshi, fuskanshi kamar zaiyi kuka yace "sun rufe kofan Gee"

shiru Anwar yayi na ɗan lokaci kana ya kalli abokinshi wanda ya shiga damuwa, dafashi yayi yace "kayi knocking ko zasu buɗe"

knocking yayi kamar zai ɓalla kofan yaji shiru basu buɗe ba, kallon anwar ya kumayi idonshi fal hawaye yace "basu buɗe ba"

cije lips nashi yayi kana a hankali ya lumshe ido ya kuma buɗewa, baiji daɗi ba daga zuwa salla sai rufe kofa?

hannun jameel ya kamo yace "muje"

jameel da yaji kamar ya rasa rayuwanshi ne gaba ɗaya domin yana da buƙatan aiki, nauyin iyayenshi yana kanshi gana kannenshi mata ya zaiyi?

ya marairaice yace "mu ɗan tsaya ko zasu buɗe zuwa Anjima"

anwar ya kare mishi kallo idonshi yayi jajur alama yana jin yunwa, tausayin kanshi dana abokinshi ya kamashi, a hankali yace "ba zasu buɗe ba muje Allah yana tare damu"

jikinshi a mace suka koma kan mashin da takaddun a hannunsu, anwar yaja mashin ɗin suka tafi, a gidansu jameel suka tsaya, tunda sukayi sallama umma taga yanayinsu ta san yauma babu nasara, murmushi tayi tace "kun dawo ne?"

jameel bai yadda ya kalli umma ba don tausayi take bashi, anwar ne ya amsa da "eh umma sannu da gida ya jikin Abban?"

"da sauki anwar"

zama anwar yayi akan kujera, yabi bayan jameel wanda ya wuce ɗakinshi rai ba daɗi da takaddun a hannunshi, umma ma ta bishi da kallo, a hankali cikin son kwantar musu da hankali tace "bayan wuya sai daɗi, ka rinƙa bawa abokinka shawara ya daina sa damuwa a ranshi duk lokacin daya rasa abu"

"insha Allah umma"

abinci tasa mishi dama yana jin yunwa ya ɗau plate ɗin ya wuce ɗakin jameel dashi, kwance ya sameshi akan katifa ya ɗaura kanshi a pillow yana shesheƙan kuka, zama yayi a gefen katifan ya ajiye plate ɗin sannan ya zubawa bayanshi ido na ɗan lokaci.


numfashi ya sauke a hankali yanajin sautin kukan abokinshi har cikin ranshi, ko kaɗan baison ganin jameel cikin wani hali, baison jinshi yana kuka koda na daɗi ne balle na wuya, gyaran murya yayi, jameel bai juyo ba yaci gaba da kukanshi, hannu yasa ya janye pillown da yake kai sannan ya aje a gefe, jameel yana jin haka ya gyara kwanaciyan ta yadda ko ba pillow zaiyi kukanshi yadda yaso.


murmushin da yafi kuka ciwo Anwar yayi sannan cikin sanyi da kuma zaƙin murya da nutsuwa ya fara motsa laɓɓanshi "kana kuka dan Allah ya jarabcemu da talauci ne? ko kana kuka dan ya jarabcemu da rashin samun aiki?"

baiyi magana ba saide ya rage sautin kukan, numfashi ya sauke sannan ya ɗaura da cewa "ka sani ko wani bawa Allah yana jarabtanshi indai kai muminine ya kamata ka yadda da ƙaddara me kyau ko mara kyau,  na san kana kuka ne saboda kannenka mata da mahaifinka to amma ka sani Allah da ya yisu shi yasan yadda zaiyi dasu, idan kana kuka kana karyamin zuciya, bana samun nutsuwa ko kaɗan idan naji sautin kukanka abokina, dan Allah idan ba so kake nima nayi kuka ba ka daina"

share hawaye jameel yayi sannan ya mike daga kwancen da yake ya zauna yana kallon anwar, cikin muryan kuka yace "ba wai da sona nake kuka ba, ka duba mahaifina yana kwance ba lafiya bani da halin kaishi asibiti, ya zanyi da raina?"

"Allah zai kawo mafita dan Allah ka daina kuka"

hannu yasa ya share hawayen sannan yayi murmushi yace "na daina"

shima anwar murmushi yayi wanda yake kara mishi kyau yace "yawwa ko kaifa, sauko muci abinci"

saukowa yayi ya zauna shima ya sauka suka fara cin shinkafa da wake da mai, jameel turawa kawai yake badan yanason ci ba, ya daure ne dan ya faranta ran abokinshi kuma amininshi, anwar yana janshi da hira dan ya saki jiki ya daina shiga damuwa, bai bar gidan ba sai bayan isha, inna ta kirashi har ta gaji da kira ta hakura, ya kalli jameel wanda yake rakashi yace "yau inna saide na toshe kunne, surutu kam sai nayi ciwon kai"

dariya jameel yayi sannan yace "gaskiya inna bataso kana yin nesa da ita to idan kayi aure ya zatayi?"

taɓe baki anwar yayi "bama zanyi auren yanzu ba"

"koman nisan jifa ai zai faɗo kasa, aure ko bakayi yanzu ba zakayi gaba"

taɓe baki yayi, ya hau mashin nashi yace "ba yanzu ba dai kuma saide matan tayi hakuri dan innata ba zan iya rabuwa da ita ba"

"to Allah ya nuna min ranan da zanga kana cewa Inna zanzo ai nanda kwana biyar"

dariya yayi kana ya tada mashin ɗin yace "na tafi"

"ka gaida gida"

tafiya yayi ya tsaya a hanya ya siyawa Inna ashana da maganin sauro.


Haneefa da safe ta shirya da wuri dan zuwa school tana murmushi ita kaɗai idan ta tuna wayan da sukayi jiya itada wannan mutumin, yau ko breakfask batayi ba ta zauna akan sofa tana jiran noor ta gama su tafi, Allah Allah take suje ta ganshi a hanya, noor tana kallonta har ta gama breakfask ta rataya jaka ta nufo inda take, a hankali tace "muje"

bata jita ba tayi nisa cikin tunani, sai murmushi take tana lumshe ido, yatsu noor ta haɗa sannan ta kyafta daidai idon haneefa tace "let's go"

firgigit tayi ta kalli noor sannan tasa hannu ta ɗau jakanta tace "okay"

fita sukayi a tare noor tana kallonta har suka shiga mota, driver ya jasu suka tafi, a hanya tasa hannu ta sauke glass, abinda bata taɓa yiba kenan, da mamaki noor ta kalleta, saida suka isa inda suka kusa bugeshi ta fara lekawa tana karewa wajen kallo, bata ganshi ba, inda taga ya nufa jiya da alama shine wajen zamanshi ta fara kallo, nan take fuskanta ya canja, kallon table ɗin tayi da alama rake yake ajewa akai domin ga kasa nan da dusan raken, gaba ɗaya fuskanta ya nuna reaction na rashin jin daɗi, a hankali ta komar da kanta cikin motan ta manna kanta da jikin seat ɗin, lumshe manyan idonta tayi sannan ta ciji lips, batasan daga ina ba ta fara jin wani bakin ciki yana mamaye zuciyanta, haka kawai taji tanason ganin wani abu wanda idan bata gani ba idanunta ba zasu samu nutsuwa ba, noor so take taji meya canja haneefa haka? me take lekawa take kallo haka? meyasa ta koma shiru a lokaci ɗaya?.

hannu tasa ta dafata kana tace "sis are you okay?"

girgiza kai tayi idanunta a lumshe tace "yeah am okay"

kara kallonta tayi "but kamar akwai damuwa"

girgiza kai tayi "no"

"okay na baki ruwa?"

tsayawa driver yayi kana ya juyo yace "ruwa hajiya?"

wani irin tsawa noor ta daka mishi wanda yasa har haneefa saida ta tsorata, cikin masifa da raini tace "wa ya maka magana? dama sake mana kunne kake kaji me muke cewa?"

girgiza kai yayi "kiyi hakuri hajiya naji kamar kince ruwa ne"

hannu ta ɗaga mishi "kaji kamar nace ko kuma kasa kunne kaji nace, kaga tsiyan talaka ya fiye gulma da shiga harkan daba nashi ba, banda talauci da shishigi ina kai inasa baki a zance yaran gida?"

tana magana tana murguɗa baki kamar zata kai mishi duka, haneefa tace "baki da hankali ne? bai girmeki bane?"

ɗauke kai tayi bayan taja wani dogon tsaki, ci gaba yayi da driving har ya kaisu school, buɗe motan tayi ba tareda ta jira ya buɗe mata ba, tana fita ta turo marfin motan kamar zata ɓalla saida haneefa ta runtse ido lokacin da taji karan rufe motan, girgiza kai tayi ta bawa Driver hakuri kana ta fito tana addu'a Allah ubangiji ya shirya mata noor.

a zuciye ta shiga class tana taka kasa kamar zata maida kasa, akan desk ta zauna ta ciro pot na shisha ta fara zuƙa ba tareda ta kalli kowa a cikin class ɗin ba, saida tayi tatil sannan ta zauna akan benci, bataso idan ta yiwa mutum faɗa haneefa tasa mata baki, yarfata takeyi tana nuna kamar batada matsayin da zata yimusu faɗa, bacci tayi yauma me isanta kafin a tashi ta warware ta koma kamar ba itace tasha abu ba, lokacin da aka tashi suna cikin tafiya taga haneefa ta kuma sauke glass tana leƙe, abin mamaki yanzu ma fuskanta ba walwala ta ɗaga glass ɗin, bataji daɗin rashin ganinshi ba, noor tace "wa kike dubawa?"

kallon noor tayi kana tayi murmushi tace "bana duba kowa so nake naga ko akwai wuta ko sun ɗauke"

batayi magana ba dan tasan confirm karya ta shirga mata akwai abinda takeson gani.


*karfe ɗaya na dare*


Noor ce kwance akan gado tana bacci cikin nutsuwa, haneefa kuma tana zaune a gefenta tasa rigan bacci tana rike da waya ta zubawa numbern ido ji take kamar ta kira amma ta gagara, tayi kusan 20mins a haka ganin ba zata iya kira ba ta kashe wayan kawai tasa a caji, kallon noor tayi wacce tayi nisa cikin baccin, a hankali tasa hannu ta maida mata gashin daya rufe mata fuska baya, duvet ɗin ta gyara mata tayi mata peck a kumatu sannan ta kashe wutan ɗakin tayi addu'a ta shafawa noor dan tasan batayi addu'a ba ta kwanta, itama shafawa tayi kana ta lumshe ido tanaso tayi bacci, da sauri ta buɗe idon ganin fuskanshi yana mata murmushi, wannan mutumin yaki fita a idonta koda yaushe tana ganinshi yana murmushi, taƙure kanta tayi tana son tayi bacci amma data rufe ido shi take gani, a hankali ta fara addu'a Allah yasa ɓacci ya ɗauketa, da kyar ta samu baccin ya ɗauketa.


jin saukan numfashinta a hankali yasa noor ta buɗe ido ta yaye duvet ɗin kana tasa hannu ta kunna wutan ɗakin, idonta kyar babu alaman bacci, leka fuskan haneefa tayi taga tana bacci ne da gaske, murmushi tayi kana ta sauko da santala santalan kafafunta daga kan gadon ta ɗaura akan lallausan carpet ɗin da yake shimfiɗe a ɗakin, a hankali take takawa har ta shiga toilet, cire kayan baccin tayi kana tayi wanka ta ɗaura towel ta fito, mayuka masu kamshi ta shafa sannan ta gyara gashinta ta taje ta bazashi a gadon bayanta, wuri wardrobe taje wanda yake  cike da kaya, wani wando jins blue ta ciro, sawa tayi kana ta ɗau riga milk color shara-shara da tsagu a hannun tasa, rigan ya matukan karɓeta, kallon white body ɗinta tayi yadda take glowing a cikin daren yasa ta saki murmushi, a hankali taje gaban mirror ta shafa powder da lipstick fari, hula picap tasa a kanta sannan ta ɗauko wani katon space baki tasa a idonta, takalmi baki me tsini tasa sannan ta ɗau side back black ta rataya, kallon kanta tayi kamar zataje zaɓen sarauniyar kyau, murmushi tayi kana ta kashe wutan ɗakin, cikin sanɗa ta fita dan bataso haneefa ta jita, a hankali ta murɗa handle na kofan ta fita, cikin sanɗa take tafiya har ta isa ɗakin ya faruk, lekawa tayi taga yana bacci, ta shiga a hankali taje ta samanshi inda ya aje kanshi, hawa gadon tayi ta zaro makullin motan da yake samanshi sannan ta fito tana tafiya a hankali har ta sauka kasa ta fita daga main palour, hamdala tayi ganin ba wanda ya ganta, compound taje ta duba motan taga yana nan a wanke yana sheƙi, motan kana zuwa wuri dashi ansan ka hau mota, ba karamin mota bane lafiyayye wanda ya amsa sunanshi mota, da kanta ta buɗe makeken get ɗin tana nishi da kyar, kallon inda getman yake shimfiɗe yana bacci tayi wani murmushi wanda ita kaɗai ta san dalilin yinshi, ta san yana bacci ne sanadin kwayan data zuba mishi a drink ɗazu ta bashi yasha, shiga motan tayi ta kunna sannan ta fita a gidan, saida ta fita ta dawo ta rufe gidan makullin kuma tasa a pocket na wandonta, motan ta shiga da wayarta kirar Iphone 14 a hannunta ta kira wani number bayan ta shiga tace "gani na fito ki fito bakin titi"

Anee ta amsa da "to"

tuƙi take cikin kwarewa, a bakin titi ta hango anee tayi dressing cikin dogon riga da wando itama tasa picap, murmushi tayi bayan ta buɗe ta shigo, "ina ministar kika fito a wannan time ɗin?"

"minister yana bacci"

dariya tayi "kin bashi yasha?"

"da bai sha ba zakiga na fito?"

dariya tayi kana taja motan suka tafi, sunyi tafiya me nisa kafin suka isa wani babban clube wanda aka rubuta welcome da manyan harufa wurin an kunna disco light, babban wajene me kyaun gaske, parking sukayi a ciki sannan suka fito, noor ta rufe motan tasa makullin a aljihu, shiga ciki sukayi, ana ganin noor akasa tafi, "ga ƴar gidan Alhaji Aminu sadauki, ga kuma Kanwar minista"

noor hannu kawai take ɗaga musu, waje aka basu VIP suka zauna, table na gabansu an cika da kwalabe na drinks dana shaye-shaye, noor ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya tana kallo mutanen wurin.


suna zaune itada anee kafin ta juya bataga anee ba, da alama ta shiga cikine, cigaba tayi da bin mutanen wajen da kallo, wani matashi ne yazo gefenta ya zauna, murmushi yayi mata ta kalleshi ta watsar, matsowa yayi kusa da ita bata matsa ba kuma bata kalleshi ba, drinks ta tsiyaya a glass cup sannan ta ɗaga zata kai baki taji ya matso dab da ita yace "beb idan kin yadda dani na dare ɗaya zan baki duk abinda kikeso a rayuwa"

juyowa tayi ta kalleshi, yace "yes and I mean it"

murmushi tayi bata mishi reply ba tayi sipping drink ɗin, ganin tayi murmushi yaji a ranshi yayi nasaran samun wannan kyakkyawar zankaɗeɗiyar budurwar, ɗaura hannunshi yayi akan nata zai rike, sassanyar drink ɗin data tsiyaya me gas sosai ta ɗaga ta watsa mishi a fuska, da sauri yasa hannu a ido yana murzawa "wayyo idona"

shine abinda ya faɗa jin wani azaban zafi a cikin idonshi, tashi tayi ta barshi a wurin yana murza ido yana ɗaga hannu da alama ba karamin zafi yakeji a idon nashi ba.


birthday ne na abokinta ɗan gidan tsohon governor, ganinta yasa yace bazai yanka cake ba sai tazo, badan taso ba tazo gefenshi ta tsaya yasa hannu zai yanka cake itama tasa hannu suka yanka tare, Na'eem abokinta ne sosai sun saba dashi har abin yana bawa budurwarshi haushi, ɗauka yayi zai sa mata a baki yaji an rike hannunshi, kallonta yayi ta ɓata rai tana hararan noor, ko kallo noor batayi mata ba, ta fara danna waya tana duba status, sa mata yayi a baki, sannan ya kai bakin noor zai sa mata ta rike hannunshi ta kai bakinshi, tafi akayi ya gutsira kaɗan ya kai bakinta ta karɓa tana murmushi, budurwarshi kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu, waka aka kunna slow music noor ce a fili itada na'eem yafi sakewa da ita fiyeda kowa na wajen, tana rawa cikin kwarewa tana jujjuyawa, liƙi ake musu kamar ba gobe kuɗi kamar takadda haka aka watsar a wajen, sai kusan 3 na dare suka tashi daga partyn, time ɗin noor tasha shisha me bugarwa, nan fa ta bugu ta fara layi, makullin ta taɓa taji yana aljuhunta, a hankali ta fara kiran sunan anee, anee kam ta daɗe da shan abu itama suka fara tafiya a tare, tana ɗan ganewa bata fita hayyacinta duka ba, motan suka shiga suka bar wajen, tafiya suke akan titi ba kowa sai mutanen da baza'a rasa ba, saida ta sauke anee a gidansu kana ta kama hanyan tafiya gida, waka ta kunna tana ji tana driving,  takusa isa gida taji tayi karo da abu, da sauri ta murza ido, motan ne ya bugu da jikin wani bishiya dake gefen titin, glass na gaban ya fashe idanu ta zaro kirjinta ya fara dukan uku-uku, parking tayi ta fito tana dubawa, kanta ya mata nauyi ba zata iya tsayawa ba, ta koma motan taci gaba da tuƙi har ta isa gida, fitowa tayi ta buɗe, shiga ciki tayi da motan kana ta dawo ta kulle gidan, ta aje motan a inda ta ɗauka, bana glass ba har tayan motan ya samu matsala da alama batayi tafiya akan hanya mai kyau ba, tana layi kaɗan ta shiga ta wuce ɗakin faruk, yana bacci sosai tayi murmushi ta hau gadon ta aje mishi makullin, kallon fuskanshi tayi Allah ya taimaketa da bai farka ba, saide gabanta yana faɗuwa akan motan data lalata, har zata fita ta dawo tayi mishi kiss a goshi sannan tace "kayi hakuri na ɓata maka mota yaya faruk"

fita tayi daga ɗakin bayan ta rufe mishi a hankali sannan ta koma ɗakinsu ta cire kayan ta watsar a wurin, dukka da jakan da takalmin da komai ta zubar a wurin, rigan baccin data cire shi tasa ta shiga tayi fitsari sannan tazo ta faɗa kan gadon wani irin bacci ya ɗauke ta sakamakon buguwa da tayi....




*Jiddah S Mapi..✍🏻*

No comments