Hakki Na 4
🌸🌸🌸🌸
*HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸
By
_jiddah S Mapi_
*Chapter 4*
~Ɓangaren me rake, ranshi ya ɓaci da marin da tayi mishi, saide yaji sanyi lokacin da ƴar uwarta ta rama mishi, idanunshi masu kalan madara ya lumshe a hankali yana cigaba da tura kus-kus na raken, baida magana shiru-shiru ne shi, koda a wurin sana'anshi bai fiye surutu ba, da yaje sun gaisa da makotanshi sai yaci gaba da abinda yake gabanshi, yauma haka ya kasance bayan ya isa wajen wani dakali da yake zama ya kwashe raken ya jera akan table dake gabanshi, hannu ya ɗagawa mutanen dake gefenshi masu saida gyaɗa da masu saida karas, suma akan table suke akewa, gaisuwa ya aika musu suka amsa, ruwa ya ɗiba ya yayyafawa raken sannan ya zauna a gefe ya ɗau wayanshi dake ringing, a hankali yake motsa jajayen lips nashi wanda suka karawa fuskanshi kyau da armashi, gashi da kwarjini, a hankali da rashin surutu yace "hello inna ta"
ta ɗayan ɓangaren muryan tsohuwa ce tace "Anwar ya hanya?"
"lafiya kalau inna ya gidan?"
"lafiya kalau ka kula da kanka banda bin abokan banza"
lumshe ido yayi ya saba da wannan nasihan inna yanzu fa ya fita daga gida ta gama yimishi wannan faɗan yanzu kuma ta kirashi tana kara mishi faɗan, jin yayi shiru tace "kana kina ko baka jina?"
giɗa kai yayi kamar tana ganinshi, tace "na san kai ka giɗa yaushe zaka daina miskilanci ne anwar? har wani kana yiwa, ka buɗe baki kamin magana"
tashi yayi ya mika rake ya karɓi kuɗin yasa a aljihu kana ya koma ya zauna yana jinta, saida ta gama surutun kamar yadda yake faɗa kana yace "inna idan kin gama zan kashe wayan"
"kenan ka gaji da jin surutu na ko? nice aku kuma nice kala uwar zance, na dameka shine..."
katse wayan yayi kana yasa a silent ya maida cikin aljihu, baison damuwa da surutu ga inna idan ta fara bata gajiya, maida hankalinshi yayi akan sana'anshi.
Anwar kyakkyawan matashi me neman na kanshi, yaro ne wanda ya taso cikin talauci tare yake da kakarshi wacce yake kiranta da inna, tunda ya tashi ita ya gani a matsayin uwar rokonshi iyayenshi sun mutu hakan yasa ya rike kakarshi duk wani damuwa nashi wa ita yake gayawa, baya ɓoye mata komai, suna zaune a wani gida ɗan karami wanda yake da ɗaki biyu, ɗaya nata ɗaya nashi, yana saida rake kuma Allah yana rufa mishi asiri yana samu har ya ciyar da inna da kanshi a sana'an saida rake, tsakanin gidansu da inda yake saida rake basuda nisa, tsakaninsu kwalta ne ba wani nisa sosai, yayi karatu saide yanayin kasan namu yasa bai samu aiki ba, ya karanci harkan kasuwanci amma har yanzu shiru ba aiki hakan yasa ya hakura yaci gaba da sana'anshi na saida rake yana addu'a Allah ya buɗa mishi, yana da abokai biyu Nasir da Jameel, sun shaƙu sosai Nasir mahaifinshi yana da kuɗi kuma yana taimaka musu, shi kuma jameel shima ɗan talaka ne kamar Anwar ɗin.
Inna batason abinda zai taɓa mata anwar ko fita yayi ta rinƙa kiranshi kenan a waya tana tambayar ya yake ya kaza ya kaza, har sai ya gaji ya kashe wayan, idan ya dawo tayi ta masifa har tayi shiru ta sauko suci gaba da hira kamar ba abinda ya faru, Anwar yanada kwarjini da cikan haiba, baya son raini ko kaɗan bai damu da harkan mutane ba, baya shiga harkan mata, akwai ƴammata dayawa wanda suke sonshi saide shi basa gabanshi burinshi yayi sana'a ya ciyar da kakarshi ya rufawa kanshi asiri.
zuwa ake ana siya raken mutane dayawa hakan yasa yana jin daɗi domin duk lokacin da ya fito yana samun masu siya dayawa, wani ma saiya kira an kara kawo mishi dami kafin ya tashi, yana cikin gyara wanda ya kankare motan Nasir ya tsaya a gefe, kallonshi yayi kana yaci gaba da aikinshi, sauke glass yayi ya leƙo yace "inason rake"
ko kallonshi Anwar baiyi ba saboda yasan halinshi tsokana ya kawoshi, dariya nasir yayi yace "nace a bani rake ko baka son customer ne?"
cigaba yayi da gyaranshi, buɗe marfin motan nasir yayi kana ya fito, shina yana da kyau masha Allah gashi chocolate color yanada haske amma ba fari bane, rufe motan yayi ya karasa wajen anwar hayewa kan table ɗin yayi ya ɗauki rake ɗaya wanda yake a fere a gyare ya fara sha, yana sha yana kallon Anwar saida ya shanye kana yace "My gee nazo ne muyi magana"
aje wuƙan hannunshi yayi kana ya janyo kujera ya zauna yana kallonshi yace "ina jinka Nas meya faru?"
gyara zama nasir yayi looking serious yace "Abba ne yazomin da wani zance wanda banji daɗinshi ba sam"
"zancen me?"
yayi magana yana kallon nas, kwafa yayi kafin yace "wai karatu zan tafi a outside kuma wallahi banaso, banson tafiya na barku kaida jameel, kaninshi ne yace zai kaini school a germany"
murmushi wanda yake karawa fuskarshi kyau yayi, saide bai fiye yin murmushin ba, kullum fuska ba yabo ba fallasa, idan yayi kuma ba karamin kyau yake karawa fuskan ba, cikin murna da taya nasir farin ciki yace "wannan ai albishir zakamin nas, abin farin ciki ne karatu fa zakaje ka kara wanda zai gyara future ɗinka may be ma harda namu"
"my gee banson tafiya na barku wallahi zan cewa Abba bana so"
"dan Allah kada kace haka, so kake muyita zama dukanmu ba cigaba? kaga idan ka tafi kayi karatu zamu samu cigaba a rayuwa domin ci gabanka ai namu ne"
yana magana yana jin daɗi saide kasan zuciyarshi baison yaji kalman nas zaiyi nesa dashi, amma ai wannan abin murna ne, shiru nas yayi ya zubawa Anwar ido yasan kawai ya amsa ne dan yanason cigabanshi amma badan yanason tafiyan nashi bane.
Noor bacci take tsakani da Allah duk malamin daya shigo saide ya gama lesson nashi ya fita batama san inda take ba, wata malama itace take ɗaukan social studies, itace ta karshe a lesson bayan ta shigo tasa a bata attendance, kiran suna ta fara duk wanda ya amsa sai tayi marking da biro blue, class ɗin yayi shiru domin kowa yanaso yaji sunanshi, Noor Aminu sadauki, shiru kakeji bata amsa ba, an kira sunan ya kai sau uku noor tana bacci, malaman tace "ina Noor?", Aneesa da take zaune a gefe tana rarraba ido ta fara bugun Noor a hankali tana kiran sunanta, da karfi malaman tace "ina noor? naga tazo school"
Anee jikinta yana rawa tace "gata nan tana bacci"
cikin tsawa ta kira sunanta "noor Aminu?"
noor kamar a mafarki taji ana kiran sunanta, gyara kwanciya tayi kana ta janyo teddy bag nata taci gaba da baccin, tashi malama tayi taje inda take kwance da karfi ta bubbuga bencin tana kiran sunanta, a hankali ta tashi tana murza ido haɗe da turo karamin bakinta tana kallon malaman bibbiyu.
"ke bacci kike mana a class? bacci kikazo yi ko karatu?"
cikin muryan maye tace "duka biyu"
da mamaki kowa ya zaro ido hadda masu sa hannu a baki tsaban mamaki, zata koma ta kwanta unty taja hijabinta ta ɗagata tareda kai mata mari a fuska.
dafe kunci tayi tareda buɗe baki, ganin ta ɗaga hannu zata kara mata marin ta rike hannunta cikin muryan maye tace "wallahi kika sake kika kara marina saina nuna miki asalin kalana"
hannunta malaman ta rike ta fara janta zuwa waje ita noor sai turjewa take ganin waje malaman takeso ta kaita ta tureta da karfi saida ta faɗi kasa, komawa tayi cikin class ta zauna, tashi malama tayi ta kaɗe jikinta kana ta fita ta kira sajent yazo da bulala, nuna mishi noor tayi tace "inaso kayi mata duka bulala ishirin masu zafi zaka bata har sai ta dawo hayyacinta"
naɗe hannun riga yayi ya ɗau bulala zai fara dukanta, ring aka buga alaman an tashi, kowa ya fito daga class unty ta hana ƴan class nata fitowa sai an gama dukan noor, haneefa da takeji kamar ba za'a tashi ba ta ɗau jakanta da sauri ta nufi kofan class nasu noor, waro ido tayi ganin sajent yana dukan noor ba tausayi, batasan lokacin data shiga cikin class ɗin ba, taje ta fara karɓa mata dukan, rungume noor tayi bulalan ya fara shiga jikinta, unty tace "haneefa ki tashi ki fita"
murya na rawa tace "ba zan iya gani ana dukan kanwata ba Malama kiyi hakuri kice ya barta"
"kinsan me tayi?"
"dan Allah kiyi hakuri"
noor sai hannu take ɗagawa tana cewa "ki barta ta kasheni ai Abba ba zai barsu ba saiya ɗauresu"
jin muryanta ya tabbatarwa haneefa tana cikin maye, gabanta ne yayi mugun faɗuwa, da sauri ta mike taje gaban malaman ta durkusa kasa ta rike kafanta tace "na haɗaki da Allah kice ya barta"
ganin yadda ta rike kafanta yasa malaman tace "barta sajent"
barinta yayi tace "ban yafe muku ba"
Malama ta tashi kowa, fita akayi ya rage daga haneefa sai unty da noor, anee cikin sanɗa ta fita tana dukar da kai bataso a gane ita ta bata.
malama tace "ki jawa noor kunne bata ɗau rayuwa me kyau ba"
jijiga kai tayi "zan faɗa wa abbanmu insha Allah"
"sannan zamu koreta a school namu domin bama son ta koyawa wasu yaran shaye-shaye"
"dan Allah Malama kiyi hakuri i promise you wannan shine last time da zata kara shan abu i promise"
"okay tunda kin roka na sanki ke mutuniyar kirki ce haneefa na bata last chance, Idan ta kuma she will the school forever"
jijjiga kai tayi "thank you unty"
fita tayi ta barsu, haneefa ta durkusa a gaban benci inda noor ta ɗaura kanta tasa hannu a gefen fuskanta ta shafa hawaye ya fara sauko mata tace "noor?? Noor?? Noor? why?"
hannu tasa zata goge mata hawayen da sauri ta ɗauke kai tace "ki barni naga kinfi so kiga ina kuka, meyasa kikeyin haka do you want to kill me?"
girgiza kai tayi idonta yana lumshewa.
"Then why?"
girgiza kai ta kuma yi, a hankali ta mike ta mika mata hannu, tashi tayi tana rike da ita har suka fita waje, motansu ta hango da alama driver ya jima da jiransu, jikinta a mace ta riketa har suka isa bakin motan, jakanta dana noor ɗin duk yana tare da ita ta rataya, tayi mamaki da bai fito ya buɗe musu marfin motan ba, buɗewa tayi ta taimakawa noor ta shiga ta zauna kana ta ajiye jakan itama ta shiga ciki ta zauna, rufe marfin motan tayi, hannu tasa tana gyarawa noor wuyan hijabinta taji muryan ya faruk yace "meya sameta?"
wani irin bugawa taji kirjinta yayi, a firgice ta ɗago tana kallon mazaunin driver, cikinta ne ya ɗaure taji kamar zatayi fitsari a wando ta kalleshi hankalinshi akan waya yana duba sako, saida ya gana dubawa ya maida wayan cikin aljihu sannan ya juyo, yayi kyau cikin kananan kaya riga orange color da wando black, suna kama sosai da kannenshi saide sun fishi haske, shima fari ne amma bai kaisu ba, gashin kanshi a kwance lub kamar balarabe.
fuska ba yabo ba fallasa yace "meya sameta nace?"
kasa magana tayi dan suna mugun tsoronshi, sunan noor ya kira babu alaman dariya a tare dashi yace "noory?"
amsawa tayi kamar me bacci "na'aaam"
da mamaki ya juyo ya kalleta, hannu yasa ya buɗe gidan gaba yace "waye drivernku? noory ta dawo gaba kuma meya samu muryanta baccin me take yanzu?"
shiru haneefa tayi idonta fal da hawaye bakinta har yana rawa ta rasa me zata fara gaya mishi, kada tayi karya ya gane, dan tasan tabbas saiya kakkaryata.
noor ta buɗe motan ya fara sakinta saide har yanzu bata dawo hayyacinta ba, zama tayi a gefenshi, haneefa sai addu'a take Allah ya rufa musu asiri, kallonta yayi yaga tana ɗauke kai bataso su haɗa ido, cikin ɗaure fuska yace "ke? juyo ko kalleni"
a hankali ta juyo ta zuba mishi idonta wanda suka sauya kala tana kokarin maidasu normal, yace "meya sameki?"
ɗauke idon tayi da sauri kana tace "bacci"
baiyi magana ba yaja motan suka fara tafiya, duk yadda taso ta daure kada tayi bacci ko tayi wani abinda zai gane ta gagara, jingina kanta tayi da jikin seat ɗin kana tasa hannu ta cire karamin hijabin dake jikinta wanda ya jiƙe da zufa, bacci ta fara, ya juyo ya kalleta so yake ya gane wani abu a tare da ita, saide bai taɓa kawo hakan akan kanwarshi ba, gani yake kamar tana kama da masu shaye-shaye, da sauri ya kawar da tunanin dan yasan halinta tanada raini da rashin ganin girman mutane amma bata shaye-shaye ko bin maza.
cikin baccin da yaci karfinta ta sulale daga kan seat ɗin ta ɗaura kanta a cinyarshi hannu tasa ta rikeshi cikin baccin sannan ta sauke ajiyan zuciya.
kallonta yayi yaga yadda ta rikeshi, tsaki ya ɗanja kaɗan jin zuciyarshi yaki aminta da noor yau, warin magani ya fara ji daga jikinta saide ƙamshin turarenta yana nema ya hana warin maganin bayyana, a hankali ya matso da hancinshi zuwa bakinta ya shinshina, haneefa ji tayi zufa yana wanke mata fuska, kar dai ya faruk ya gane wani abin?
wari yaji kamar na syrup, gabanshi ne ya faɗi kirjinshi ya bada sautin dib dib, kallonta ya kumayi tana bacci sosai ta rikeshi, hannu yasa yayi taping bayanta yace "noor?"
cikin bacci ta buɗe baki tace "na'aam"
tabbas syrup ne, da sauri ya juya ya kalli haneefa, tattaro nutsuwa tayi tana murmushi kamar ba komai.
"me tasha?"
danne ranta tayi tace "mura takeji har kanta yana ciwo, to nice health prefect shine naje medicine room na ɗauko mata syrup na bata ta shanye"
ajiyan zuciya ya sauke me karfi jin abinda haneefa ta faɗa, bai juyo ba yace "duka ta shanye?"
jijjiga kai tayi "eh duka kwalba ɗaya"
"Amma ke daƙiƙiya ce wani malamin ne ya baki health prefect? bakisan kan komai ba zasu baki health, kin taɓa ganin inda aka shanye magani kwalba ɗaya a time ɗaya?"
girgiza kai tayi "naga batada lafiya ne sosai yake damunta"
"dalla rufemin baki gaki kamar me wayo noor ma ta fiki wayo, bakisan bugar da ita zaiyi bane? yanzu kiga baccin da take ai maganin ne yake sata, You have to be very careful"
"tom"
ta faɗa cike da tsoro da kuma murnan bai gano abinda ya faru ba, har suka isa gida yana mata faɗa akan ta rinƙa kula da magani kafin ta bawa mutane wanda rabin faɗan zagi ne, buɗe musu kofa akayi ya wuce compound yayi parking, haneefa ta buɗe ta fita tareda ɗaukan jakansu ta rataya, kallon noor yayi wacce ta kara gyara kwanciya a cinyarshi tana cigaba da bacci.
hannu yasa ya buɗe marfin motan kana ya ɗagata ya ɗaurata a kafaɗanshi, da kafa ya rufe marfin motan sannan ya nufi cikin gida da ita, haneefa ta riga ta shige ciki, a falo ya tadda Abba yana karanta jarida, kafafunshi akan centre table ya cire siririn farin glass ɗin dake manne a idonshi yace "ya dai? bacci tayi a school?"
"eh Abba bacci tayi bata jin daɗi"
haneefa dai ta zauna a gefen Abba tana rarraba ido, sama ya haura da ita ya shiga ɗakinsu, kallon ɗakin yayi baya shiga sai idan Momy ce tace ya kira mata su, ɗakin nasu a kimtse komai yana mazauninshi sai ƙamshi yake.
akan gado ya kwantar da ita sannan ya cire mata takalmin dake kafanta, ac ya kunna kana ya rufa kafanta da bargo ya kashe wutan ɗakin ya fita tareda rufe mata kofan.
Haneefa saida taga ya sauko ya zauna suna hira da Abba kafin taji ranta yayi sanyi, tashi tayi taje ta fara shirya musu abincin dake kan dining, momy ta fita saida suka fara cin abinci kafin ta dawo, tana murmushi ta rungumi Abba yace "kin dawo?"
jijjiga kai tayi sannan tace "ina Auta ne?"
"tana bacci"
"bacci kuma? baccin lafiya?"
"Mura ke damunta shine na bata magani"
"okay to ba damuwa Allah ya bata lafiya"
zama tayi ta fara bawa Abba abincin a baki har saida ya koshi ta kalli Faruk wanda ya haɗa rai yana kallon abincin, "lafiya?"
shagwaɓe fuska yayi kana yace "Momy nima ki bani a baki"
tsaki taja sannan ta mike tana cire mayafin jikinta wanda yake da girma kuma yana sheƙi, ta ɗau jakanta tace "ga kanwarka ta baka mana"
dariya Abba yayi shima ya mike "kunada abin dariya"
spoon ɗin ya ɗaga ya fara ci yana kwaɓe fuska, ajiyewa yayi zaisha ruwa haneefa tasa hannu ta ɗau spoon ɗin, ɗibo abincin tayi ta kai bakinshi, murmushi yayi ya buɗe baki tasa mishi.
a baki take bashi har ya koshi yace "thanks"
daɗi taji, tana son farin cikin yayanta sosai tanason ganin suna shiri suna shaƙuwa da juna, tashi yayi yana kallon agogo ya wuce room nashi.
ajiye spoon ɗin tayi a hankali ta ɗaura kanta a gefen warmer lunshe ido tayi tana tuna wannan gayen da suka kusa bugewa ɗazu, data rufe ido sai yayi mata gizo, idanunshi daya kalleta dasu tun ɗazu tana ganinsu suna yawo cikin kwayan idonta, kunnenta yana jiyo mata maganan da yayi na cewar "kada ki damu ba komai"
tunawa tayi da yadda yake da sanyi kamar baya son magana haka yake, tana cikin wannan tunanin ta tuna ta karɓi number ɗinshi, tashi tayi kamar an tsikareta, da jakanta a hannu ta shiga ɗakinsu, kunna wutan ɗakin tayi kana ta zauna a gefen gado tana kallon noor wacce take bacci.
wayan ta ciro daga jaka ta duba numbern da tayi saving da mai rake, yi tayi kamar zatayi dialing sai kuma ta bari, ji take kamar ta kirashi wani zuciyan yace ta bari sai zuwa dare time ɗin ya nutsu sai tayi mishi sannu.
Ajiye wayan tayi ta shiga toilet tayi wanka tareda alwala ta fito, salla ta tada bayan ta idar ta kalli noor wacce ta tashi tana miƙa, kawar da kai tayi ta haɗa rai kamar bata taɓa dariya ba a duniya, noor kallon cikin ɗakin tayi taji kanta watsau ta warke ba wani bacci da take ji, sauka tayi daga gadon tana kallon haneefa wacce ta haɗa rai ta ɗaga hannu tana addu'a, toilet ta shiga tana cigaba da miƙa, saida tayi wanka ta fito tana kallon haneefa wacce ta shirya tana ɗaure gashin kanta, mai ta ɗauka zata shafa haneefa da take gyara gashinta tace "je kiyi alwala"
aje man tayi tana tura baki tareda magana ƙasa ƙasa ta yadda ba zata ji me tace ba taje tayi alwalan ta fito, shafa mai tayi kana tasa riga mara nauyi tazo ta shimfiɗa sallaya ta tada salla, saida ta idar ta tashi ji tayi cikinta kamar anyi yasa, babu komai sai hanci da kayan ciki, yunwa kamar zata mutu, fita tayi daga ɗakin taje kasa ta buɗe flask ta ɗibi abinci, ci tayi sosai kana taje gaban frij ta ɗau yoghourt, buɗe goran tayi tana sha ta rufe frij ɗin kana ta fita tana kallon cikin gidan.
masu aiki suna aiki masu gadi suna zaune a gefe suna gadinsu, kallon flower tayi taga sunyi kyau sosai komai na gidan normal, rigan jikinta daga gaban guntu ne kafanta a waje, daga baya kuma yana jan kasa, baki ne tana son kala black domin yana fitar da haskenta sosai, ba karamin kyau bakin kala yake mata ba.
fatan jikinta yana glowing, kafanta fari sol tasa mishi bakin flat shoe, hannunta rike da goran yoghourt tana sipping a hankali, idonta ne ya kai kan wani flower wanda yayi tsayi basu yanke ba, da karfi tace "Audu !!! Audu !!!"
wanda aka kira da audu babban mutum ne tsoho dashi haka, kana ganinshi kasan rayuwace take ɗawainiya dashi, yazo gabanta ya durkusa har kasa yace "gani ƴata"
da sauri ta tofar da yoghourt ɗin da yake bakinta, ta kalleshi a tsiyace tace "ƴarka fa kace? dan Allah kayi hakuri ka janye, meyasa ina cikin arziki Allah ya rufamin asiri kazo kana neman shafamin talauci? anyways ba wannan ba meyasa baka yanke wancan flower ɗin ba?"
kallon flower yayi kana yace "ayi hakuri ban kula ba Hajiya"
"zaka kula idan aka rage maka albashi"
"dan Allah Hajiya kiyi hakuri zan yanke kuma hakan ba zai kara faruwa ba"
tsaki taja sannan ta juya ta bar wurin, bin gidan take da kallo tana zagaya ko ina, duk wani gyara data gani saita kira me kula da ɓangaren tayi mishi gargaɗi, har garden saida taje ta duba duk wani bishiya taga komai normal, sai sanyi lub lub yanayin wurin daɗi ga ƙamshin kayan itatuwa, tafiya tayi kaɗan sai gata a swimming pool ɗaga bayan riganta tayi kana ta zauna a bakin ruwan tada kafafunta ciki tana bin ko ina da kallo, lumshe ido tayi tana tuna abinda ya faru tsakaninta da haneefa da wannan matsiyacin mai raken, bata son tuna wannan mutumin shine mutum na farko daya fara shiga tsakaninta da yayarta har mari ya shiga tsakaninsu.
sai yamma ta tashi daga wajen ta koma cikin gida, momy tana zaune a falo tana waya, a hankali ta karasa ta zauna a gefen Momy ta ɗaura kafanta akan kujeran tasa kanta a cinyan Momy ta lumshe ido, hannu momy tasa a kanta tana shafa gashinta me laushi tana cigaba da waya.
Bayan ta gama tace "ya muran naki auta?"
"mura kuma?"
ta faɗa a ranta, a fili kuma tace "da sauki"
"sannu ki kiyaye shiga ruwa da shan abu me sanyi kinji?"
jijjiga kai tayi, tasan haneefa ce tayi wannan karyan, Allah sarki ta ɓoye halin da take ciki.
da dare bayan sun gama shiri kamar yadda suka saba shirin bacci, noor tasa wayanta a caji so take tayi bacci da wuri, haneefa wacce take cikin rigan bacci silk ruwan toka ta janyo Pillow sai juye-juye take, bacci yaki zuwa mata, fuskan wannan bawan Allah sai gani take a idanunta.
kallonta noor tayi tasan haneefa da baccin wuri to meya hanata bacci yau?
sharewa tayi taja bargo tayi shiru itama tanaso bacci ya ɗauketa, haneefa ta juya tana kallon jikin bango sai tunani take ta kasa bacci, kusan minti talatin tana a haka, kallon noor tayi wacce ta juya mata baya a hankali tace "noory?"
bata amsa mata ba.
"kinyi bacci ne?"
yi tayi kamar tana bacci, a baɗini kuma ba baccin take ba, mamakin abinda ya hana haneefa bacci take, a hankali ta mike jin kamar Noor tayi bacci, wayanta ta ciro daga cajin ta buɗe, numbern ta zubawa ido, lumshe ido tayi tana so ta kira saide gabanta yana faɗuwa.
daurewa tayi ta danna call, yana shiga bai ɗaga ba, a hankali ta kuma latsa call, kusan 3miss calls kafin taga an ɗaga, kirjinta ya buga tayi shiru kamar yadda shima yayi shiru.
a hankali tace "barkanka da warhaka"
ɓangaren Anwar ya gama hira da Inna tayi bacci kafin ya fito yayi alwala yayi salla tareda nafila, gadonshi madaidaici ya kwanta akai ya kunna fanka sannan ya yi lamo akan gado yana tuna maganan nas na cewa zai tafi karatu a kasar waje.
kiran waya ne ya shigo mishi bai duba ba saida aka kusan 3miss calls kafin ya ɗaga wayan yaka dubawa, ganin sunan haneefa yana yawo yayi mamaki, shi kam harya manta da ita da abinda ya faru, da mamaki ya ɗaga kiran sai kuma yaji tayi shiru.
leɓenshi na kasa yasa cikin bakinshi yana tsotsa a hankali, wannan ya zama mishi ɗabi'a koda yaushe zaka ganshi haka yana tsotsan lips, muryanta yaji tace "barka da warhaka"
kamar ba zai amsa ba sai kuma yace "barka"
pillow ta janyo ta rungume da karfi sannan tace "ina magana da me rake?"
jijjiga kai yayi kamar tana ganinshi, daga baya yace "eh shine"
"ka ganeni?"
a hankali yace "eh"
murmushi tayi, taji daɗi da yace ya ganeta da alama yana da girman kai ko kuma wuyan sha'ani, tace "wacece?"
"haneefa"
tunda take bata taɓa jin wanda ya kira sunanta yayi mata daɗi kamar shi ba, yadda kasan shi ya raɗa mata sunan haka taji sautin sunanta daga bakinshi, batasan lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba, lumshe ido tayi kana tace "na kira ne na kara baka hakuri"
"ba komai ya wuce"
shiru tayi shima yayi shiru, murya ƙasa tace "na gode dame zanyi saving number ka?"
"ANWAR"
lumshe ido tayi "nice name, Anwar"
a hankali yace "saida safe na gode"
kafin tayi magana ya kashe wayan, janyo Pillow tayi kamar zata maida ciki tana jin daɗi from no where, kallon bayan noor tayi sannan tasa hannu ta kashe wutan ɗakin, murya ƙasa tace "Anwaaar"
waro Ido noor wacce take cikin bargo tayi, gabanta ne yayi wani irin mummunan faɗuwa, me takeji? inama ace bacci takeyi ko kuma a buge take da tafi kowa jin daɗi, ji take kamar ta tashi ta ɗaura hannu aka tayita zabga ihu cikin daren nan ko Allah zaisa ranta yayi sanyi.
"da wa haneefa take waya? wannan kazamin me raken?"
murza ido tayi tanaso ta gane bacci take ko a cikin maye take, a cikin ranta tace "Noor kinsha syrup yau shiyasa hankalinki yake rabuwa bakya gane kanki...."
*Haƙƙi na is 300 via 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ur evidence of payment via 08144818849*
No comments