Recent Updates

Hakki Na 3

 


🌸🌸🌸🌸🌸

    *HAƘƘI NA*

🌸🌸🌸🌸🌸



 By

_jiddah S Mapi_



*Chapter 3*



              ~Ba magana nake ba? wa yake surutu?

shiru ƴan class sukayi kowa yana rarraba ido, noor ta zuba mishi idanunta tana kallonshi leɓenta na kasa a cikin bakinta tana tsotsa, idanunta masu kalan bacci ta lumshe kana ta kara buɗewa tana kallonshi, yasan itace hakan yasa yace "noor Aminu sadauki tashi kije kiyi kneel down a waje"

tashi tayi ta É—au jakanta da sauran milk shake É—in daya rage, cikin nutsuwa da raini take takawa har ta isa gabanshi, kallon banza tayi mishi kana ta fita daga class É—in, zama tayi a gefe tana kallon mutanen dake cikin class suna karatu.


gaban haneefa ne ya faÉ—i ganin an fitar da noor waje, tasan laifi ta yiwa malami, dafe kai tayi "Innalillahi noor me kikeso ki zama a rayuwa?"

karatu ake a aji amma hankalinta baya kan malamin, gaba É—aya ta tattara ta maida hankali kan noor, yatsa É—aya ta É—aga kana tace "excuse"

amsa mata yayi da "Yes"

tashi tayi tace zataje fitsari yace "okay"

fita tayi bata tsaya ko ina ba sai inda noor take, tana zuwa ta rankwashi kanta, juyowa tayi cikin masifa zatayi zagi, ganin haneefa tace "wash kaina unty hanee me na miki?"

tsaki taja cikin gajiya da halinta tace "noor me haka? kina ganin Æ´an uwanki suna karatu ke an fitar dake? meyasa bakya ji ne?"

"sorry"


"sorry for your self, sabida kanki kike cuta bani ba, ki nutsu ki san me kikeyi a rayuwa"

turo baki tayi har haneefa ta gama ta tafi, har aka tashi noor tana waje ganin ana fitowa itama ta mike tana kaÉ—e jikinta, minal ce tazo tace "ke noor baki da tsoro ace malami yana magana kina kallonshi up and down?"


"to ni nace yazo ya koyar damu ne? kinga bani na É—an sha kafin haneefa tazo"

komawa aji sukayi ba kowa a ciki sukaje bencin baya kana Noor ta jona pot ya fara zuƙa, saida tayi tatil har ta fara jin kanta yayi nauyi tana gani bibbiyu kana ta mike tace "na tafi" cikin muryan maye, fita tayi daga class ɗin ta bar minal aciki direct inda driver ɗinsu yake tsayuwa taje ta tsaya tana jiranshi, ita haneefa ta koma ciki tana duba noor ganin bata nan ta fito tana dubata, abin mamaki bata ganta ba sai tambayan ƴan class nasu take "Ina noor?"

kowa sai yace "ta fita ai" 

sai daga baya ta hangota zaune a gefe ta É—aura kanta a gwiwa kamar bacci take, bugunta tayi kaÉ—an kana tace "noor meya sameki?"

a hankali ta É—ago kai ta zubawa haneefa ido, da sauri ta waro ido ganin yadda idon noor ya canja yayi launin bacci da alama a buge take, dafe kirji tayi idanunta har suna cika da hawaye tace "noor? me nake gani?"

mikewa tayi kamar zata faÉ—i tana tangal-tangal, faÉ—awa tayi jikinta cikin muryan maye tace "unty haneefa kaina yayi nauyi"

daidai lokacin driver É—insu ya iso, janta haneefa ta fara har ta buÉ—e mata mota ta shigar da ita, sai É—aga hannu take tana magana, shiga itama haneefa tayi da sauri ganin mutane suna kallonsu, tana shiga ta rufe marfin motan kasancewar tinted glass ne yasa babu me ganinsu, hannu tasa ta wanketa da mari, idonta ya fara zubar da hawaye cikin kuka tace "noor ba kincemin kin daina ba? dama ba dainawa kikayi ba?"

hannu tasa a idon haneefa tana share mata hawaye É—ayan hannun kuma ta dafe kunci inda ta mareta dashi tace "ki daina kuka kaÉ—an fa nashaaa.."


"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un me zan gayawa abba? me zan gayawa Abba idan ya tambayeni meya sameki?"

lumshe ido tayi kana ta jingina kanta da seat tace "kice mishi kaÉ—an nasha"


kuka ta fashe dashi sosai, driver da yake tuƙi ya juyo yace "hajiya ki daina kuka"

lips nata ta ciza da karfi tace "ta yaya zan daina kuka? ka duba halin da kanwata takesa kanta a ciki"

"Hajiya addu'a zakiyi mata"


"malam babu abinda ya saka cikin maganan mu, ka cire tsamin bakinka daga maganar daya shafeni, gargaÉ—i nake maka"

noor tayi magana kamar zata mareshi, tsit yayi dan yasan zata iya marinshi, da haka har suka isa gida, a hankali haneefa ta rike hannunta ta fitar da ita daga motan, saida ta leka falo taga ba kowa kafin ta janyo hannunta da sauri ta wuce da ita zuwa room nasu, kwantar da ita tayi akan gado kana ta janyo bargo ta rufata, bacci me nauyi ya ɗauketa, zama tayi a gefe ta riko hannunta tana kallonta idonta yana zubda hawaye, ba abinda muka rasa a rayuwa meyasa noor take haka? duk wani gata Abba ya basu, kuɗi ilimi kyau Allah ya basu saide noor tana nema ta ɓata kyaunta da shaye shaye da kuma raina mutane.


kallon fuskarta tayi "ya Allah kada kasa Abba ya gane noor tana shaye-shaye idan ya gane tabbas zai ɗau mummunan mataki akanta, Bama ita kaɗai ba harda ni domin zaice na sani na ɓoye"

sakin hannunta tayi ta gyara mata blanket kana ta tashi ta fita tana goge hawayen fuskanta, saida ta gyara fuskan kafin taje É—akin Momy, tura kofan tayi jikinta a mace tana kakalo murmushi, Momy na ganinta tace "kun dawo?"

kai ta giÉ—a tace "mun dawo momy sannu da gida"

ƙarasawa tayi bayan ta tura kofan, kallon yanayinta momy tayi "kina lafiya? ina ita noor ɗin?"

"tana bacci kanta ke ciwo shine tasha magani"


"okay Allah kawo sauki"

"ameen momy"

abinci ta buÉ—e ta zuba, spoon tasa zataci amma taji sam bata sha'awan abincin, tunanin halinda noor take ciki shi yake hanata sukuni, sai juya spoon É—in take a cikin abincin, momy ta gyara zama tana kallonta tace "haneefa? na lura akwai damuwa a tare dake shin meke faruwa?"


girgiza kai tayi cikin sanyinta tace "ba komai momy"

"nifa na haifeku idan baku faÉ—amin damuwanku ba ma wa zaku faÉ—a?"


"momy ba komai wallahi kawai na gaji ne"

"sorry kici abinci saiki kwanta ko?"

jijjiga kai tayi.


noor baccinta take cikin nutsuwa batason abinda zai katse mata bacci ko kaɗan, cikin bacci ta janyo pillow ta rungume, bata farka ba sai kusan karfe biyar na yamma, har momy ta fara tsorata domin bini bini tana zuwa ta leƙata, tashi tayi tana miƙa tareda salati, murza idonta tayi tana tuna abinda ya faru, tsaki ta ɗanja kaɗan kana ta cire uniform na jikinta ta ɗaura towel a kirji, ribbon ɗin kanta ta cire ta baza gashin zuwa gadon bayanta, turo kofa akayi bata juyo ba taci gaba da gyaran gashinta, haneefa ce hannunta rike da plate na abinci, fuskarnan babu fara'a ta ajiye plate ɗin bata kalleta ba tace "ur good is ready"

itama noor bata kalleta ba, tana kallon gashinta ta madubi tace "okay"

zama haneefa tayi a bakin gado tana kallonta da alama batama damu da abinda tayi ba, tana gama gyara gashin tasa slippers zata shiga toilet haneefa tace "dakata"

cak ta tsaya hannunta akan handle na kofa, ba tareda ta juyo ba, haneefa tace "idan kika kara shan abu wallahi saina gayawa Abba, kibar ganin ina ɓoye mishi halayenki zan faɗa mishi komai, domin ba zaiyu ida yazo ya sani nima ya bani laifi ba"

tana jinta har ta kai aya, kana ta tura kofan ta shiga, ran haneefa ya ɓaci kenan batama ji abinda ta faɗa mata ba?.


tana shiga ta kwance towel ɗin ya rage babu komai a jikinta, bathtub ta shiga ta kunna ruwan ɗumi dana sanyi duka suna zuba a kanta, lumshe ido tayi sannan tayi lamo a cikin bathtub tana jin daɗin ruwan, maganan haneefa yake mata yawo aka, wai zan gayawa Abba, kenan ta daina sonta? lumshe manyan idanunta tayi a hankali kuma ta buɗe ta cije ɗan karamin jan lips nata kana ta ɗau sabulu me ƙamshi ta fara gogawa a jikin softwhite skin nata, a ƙalla ta kai awa ɗaya a toilet sannan ta kashe shower ta fito tana maida gashinta wanda yake a jiƙe baya, babban towel pink ta ɗaura kana ta janyo karami ta ɗaura a kanta, fitowa tayi daga toilet ɗin tana danna hannunta aka domin son goge ruwan da yake kanta, ganin haneefa bata nan ta kalli abincin data kawo mata, taliya ne jallof gefe kuma kunun madara, stool ta janyo ta zauna a gaban mirror ta jona drayer ta fara busar da kanta, saida ya bushe ta ɗau man gashi ta shafa kana ta taje tayi parking, mayukanta masu kamshi ta shafa sannan ta mike taje ta ɗau wani riga pink dogo silk tasa, rigan ya mata kyau ta fito kamar ƴar India, zama tayi a gefen gado tasha kunun madaran kana taci taliyan kaɗan, mikewa tayi bayan ta kunna wayanta sannan ta fito tana tana tafiya cikin nutsuwa da yanga, da ihu tace "salamatu?"

mama salma dake zaune tana cin abinci taji muryan noor tana kiranta saida gabanta ya faɗi, loman abincin ya kasa wucewa maƙogaronta saida ta tufar, jiki na rawa ta shiga ciki tana amsawa, waya a kunnenta tana magana ta ɗan matsar da wayan gefe tace "jeki fitar da plate na ɗakina"

da sauri tace "to noor"

gefe ta kumayi da wayan kana tace "wai meyasa kike kirana da noor haka gatsau? baki iya daraja mutum bane ko bakisan darajan masu kuÉ—i bane?"

kanta kasa tace "kiyi hakuri hajiya"

tsaki taja sannan ta wuce tana cigaba da waya, É—akin Momy taje, haneefa ce acan tana zaune tana game, kashe wayan tayi a hankali taje ta bayanta ta rungumeta, lumshe ido tayi sannan tace "am sorry sis ki yafemin ba zan kara ba"

shiru haneefa tayi mata, saida ta maimaita am sorry kusan sau uku kafin tace "kimin alkawari ba zaki kara shan abu ba"

sakinta tayi kana ta zagayo ta zauna a hannun kujeran da take, kallonta tayi tace "nayi"


"sha? me akesha?"

cewar Faruk wanda ya shigo yanzu, jikin noor ya fara rawa a tsorace tace "juice ne ya faruk nace banson me citta ba zan kara sha ba"

kallonta yayi yana so ya gano gaskiya, maida kallon yayi zuwa kan haneefa yace "me akesha?"

itama a É—an tsorace tace "ginger juice"


jijjiga kai yayi kana ya juya ya fita, dafe kirji noor tayi tace "ya Allah na gode daka ceceni"

"ki daina idan kinaso Allah yaci gaba da cetonki"

jijjiga kai kawai tayi.


"Unty hanee?"

"Na'am"


"kullum idan na kwanta sai nayi mafarkin aurenki, bana mafarki saina aurenki, wai muna shagali mijinki kyakkyawa É—an governor ko minista ne ban sani ba, amma É—an babban gidane, wai duk garin kano labarin aurenki kawai ake, biki ake na gani na faÉ—a"


murmushi tayi "to noor hakan ai yin Allah ne, Allah ya zaɓa mana abinda yafi alkhairi"

"Ameen"



*Washe gari*


sunyi shiri tsaf domin zuwa school noor tasan yau uncle na maths ne a class dama ta tsaneshi iya tsana, hakan yasa ta ɗau teddy bag nata wanda abba ya siya mata a morocco brown ne da hoton katon baby a jiki, kwalaben kayan maye ta ɗura a ciki kana ta ɗau waya tayi dialing number da tayi saving da besty Aneesa, tana ɗagawa murya ƙasa ƙasa tace "kanwar minista? ki tabbatar yau kinzo da kayan caji saboda uncle maths ne a class"


"na sani shiyasa na cika jakata dashi, yau ko yaya minista ba zaisan abinda na É—iba ba balle getman na school, ke akwai fa party gobe da dare a meera club"


"karki gayamin besty"

"wallahi kuwa around 9 za'a fara"


noor da taji tafiyan mutum tace "ke saimun haÉ—u a school"

rataya jakan tayi sannan ta fito tasa canvas irin na maza fari, tayi kyau sosai, sauka tayi kasa ta gaida Abba da ya faruk, kin cin abinci tayi domin tasan abinda zatasha idan taje school, ba yadda Abba baiyi da ita ba tace akwai cake a jakanta, saida haneefa ta gama suka fita, kamar yadda suka saba haka driver ya jasu suka kama hanya, yau akwai goslow hakan yasa suka tsaya suna jiran motoci su tafi, noor ta matsu sosai ta samu ta samu su tafi ji take kamar ba zasu isa school ba, da kyar suka samu motoci suka ragu a hankali yaja motan suka wuce goslow, ajiyan zuciya ta sauke ganin sun wuce, cikin rashin sa'a motarsu ta kusa buge wani wanda yake kokarin tsallakawa da rake a cikin kus-kus, salati haneefa ta fara shima driver ya fara salati yana addu'a, noor kuma tasa hannu a kirji ta dafe tana zaro ido ganin saura kaÉ—an su bigeshi, garin yin kwana ya É—an bugi kafarshi da kyar ya samu ya taka birki, ajiyan zuciya me karfi ta sauke, haneefa kuma har idonta ya cika da hawaye tayi hamdala, driver ya buÉ—e marfin mota domin dubawa ko mutumin yaji ciwo, mutane har sun fara taruwa a wurin suna duba mutumin da aka É—an bige mishi kafa, noor a fusace ta buÉ—e motan ta fito hannunta rike da jakanta, cikin masifa ta ratsa mutanen da suke wajen taje inda yake yana É—ibe raken da suka zube kasa.


Driver yace "bakaji ciwo ba?"

É—agowa yayi zaiyi magana yaji saukan mari a fuska, da mamaki ya juyo yana kallonta tana huci ta kuma zabga mishi wani marin, hannu yasa ya dafe kunci yana kallonta da mamaki, su suka bigeshi kuma itace zata mareshi?

haneefa dake cikin mota ta zaro ido ganin abinda noor tayi, da sauri ta buÉ—e kofan motar ta fito, batasan lokacin data isa inda suke ba, ganin kyakkyawan matashi wanda zai kai shekara 30, fari sol dogo dashi ga saje yana dafe da kunci ta juyo ta kalli noor

"meyasa kika mareshi?"


"haba unty haneefa bakya ganin abinda yayi ne? tsaya mana fa yayi a titi da wasu ruɓaɓɓun rakenshi da banzan kazamin kayan jikinshi dan neman masifa so yake mu bigeshi ace masu kuɗi basuda hankali basa tuƙi a hankali..."

kafin ta karasa taji saukan mari har uku a kuncinta, da mamaki ta dafe kunci har saida jakanta ya faɗi kwalaben ciki suka fito duk suka fashe a kan kwalta, mutane sai kallonta suke suna kallon kwalaben serup, haneefa ma ta kalli kwalban ta kuna kalli noor wanda ta buɗe baki hannu dafe a kunci tana kallonta da mamaki domin tunda suke bata taɓa marinta ba, iyaka tayi mata faɗa sai gashi yau ta bata marin da yayi shocking nata.


"ni kika mara?"


"eh ko zaki rama?"

kanta kasa hawaye ya cika mata ido ta kalli kwalaben da suka fashe ta ɗago ta kalli mutanen da suke mata kallon ƴar kwaya kana ta kalli mutumin da yake tsaye yana kallon haneefa, cikin sanyin jiki da kunya wanda bata taɓa jin irinshi ba sai yau ta durkusa ta ɗau jakanta ta rataya, haneefa durkusawa tayi kasa ta fara kwashe raken daya zube kasa, shima ya durkusa ya fara kwashewa, atare suka kwashe har suka wanke ta tayashi ya jera a cikin kus-kus ɗin kana ta kalleshi tace "dan Allah kayi hakuri ka yafe mata"


murmushi yayi sannan ya kalleta da lumsashun idonshi ya motsa lips nashi a hankali yace "ba komai"

daga haka bai kara magana ba yasa hannu kan kus-kus É—in zai tafi tace "ji mana"

tsayawa yayi tasa hannu a jaka ta ciro kuÉ—i masu yawa ta mika mishi, kallonta yayi kamar ba zaiyi magana ba, sai kuma yace "ki barshi bana bukata"


"idan ka faÉ—i haka kamar baka yafewa kanwata ba kenan"

a hankali ya girgiza kai da alama bai fiye son surutu ba yace "a,a banso ne kawai ki barshi"


a hankali tace "to ka bani numberka"

kamar ba zai bayar ba yaga ta marairaice kana yaciro ƴar karamar waya ya mika mata, dubawa tayi ta ciro babban wayarta kirar Iphone 14 ta ɗau number ɗinshi kana ta kirashi tayi mishi saving na numbern ta da Haneefa, mika mishi tayi ya karɓa yaja kus-kus nashi zai tafi tace "nasa maka haneefa"

giÉ—a kai yayi kana yaci gaba da tafiya, mutanen wajen sunata kallonsu, driver ya koma jikin mota yana kallon haneefa yana sa mata albarka, noor tana cikin mota ta cika tana batsewa, kirjinta kamar zai fito fili tsabar bugawa, ido ta zubawa wannan me raken tana kallon duk abinda yake faruwa tsakaninshi da Haneefa.


bata taɓa shan mafi irin na yau ba, haneefa bata taɓa ɗaga hannu ta mareta ba sai yau, ji take kamar gefen fuskanta zai fashe tsabar zafi, ta jikin madubi ta kalli fuskanta idonta yayi jajur ga gefen fuskan ya kumbura shatin hannun haneefa ta gefe da gefen duk ya fito, dunƙule hannu tayi kana ta buga a jikin glass na motan ta buɗe ta fita tana kuka, napep ta kana kana ta faɗa mishi school nasu, haneefa tana kallonta har suka tafi, buɗe mota tayi ta shiga driver ya jata, noor a cikin mashin ɗin sai sharan hawaye take tana cizan leɓe, akan wani banza kazami me saida rake haneefa zata mareta? wannan abin yana ƙona mata rai idan ta tuna.


suna isa kofan school ta fito zata tafi yace "Hajiya kuÉ—i na"

ba tareda ta kalleshi ba tace "banda kuÉ—i"

tafiya taci gaba dayi ya fito yace "ban gane baki da kuÉ—i ba, kinsan baki da kuÉ—i kuma zaki shiganmin mashin?"

kai ta giÉ—a "na sani kuma na shiga, banda kuÉ—i saide kayi abinda zakayi ko bakaga jakata bata tare dani bane?"


"ina ruwana da jakanki ki biyani kuÉ—i na tun muna shaida juna"


"idan ban biya ba me zakayi? matsiyaci talaka dakai har ka samu na shiga mashin naka"

"ke wacece da zanji daÉ—i dan kin shiga mashin nawa?"


"ai da ganina kasan ba daga gidan tsiya na fito ba, kuÉ—i dai ban fito dashi ba kuma bazan bayar ba saide kayi abinda zakayi"

cikin zafin rai ya É—aga hannu zai mareta haneefa wacce suka karaso yanzu ta tsaya tana kallon abinda yake faruwa ganin zai mareta taje wajen tace "kayi hakuri malam"


"kada Allah yasa yayi hakurin"

juyawa tayi ta shiga school, haneefa ta ciro kuɗi ta bashi, karɓa yayi yace "Hajiya da kin bari na koya mata hankali ai"

girgiza kai tayi "kanwata ce kayi hakuri ka yafe mata kasan akwai yaranta"

godiya yayi kana ya ciro canji zai bata tace "no barshi kawai"

godiya yayi mata sosai kana ya shiga mashin ya tafi, itama shiga cikin school tayi, sunyi latti saida tayi picking kafin ta shiga ciki.


noor shiga class tayi ba tareda ta nemi izini ba, kowa yana cikin class Yayi shiru tazo gaban malamin ta wuce, tsayawa yayi turus yana kallonta har taje benci ta zauna a gefen Aneesa, cigaba da teaching yayi dan yasan halinta tsab, Aneesa ta kalleta tace "meya faru besty?"

idonta jawur bakinta, jajayen leɓenta yana rawa tace "bani kwalba uku"

buÉ—e jaka Aneesa tayi ta ciro kwalabe kusan uku ta mika mata, buÉ—ewa tayi ta fara kwankwaÉ—a, saida ta shanye duka sannan ta kalli Aneesa tace "akan wani banza me saida rake unty haneefa ta mareni"


Dafe kirji Aneesa tayi kana tace "mari?..."

jijjiga kai tayi, manyan idanunta wanda suka fara zama kalan bacci sun sauya sosai, dama gata da sexy eyes ya kara haÉ—uwa da shaye-shaye hakan yasa idon ya zama kamar na me bacci, kanta ta É—aura akan desk nan bacci ya É—auketa.


Haneefa ta shiga class jikinta a mace, bataso marin Noor ba, saide tana so tasan darajan É—an adam, koba komai ai wannan ya girmeta meyasa zata mareshi? gaida malamin da yake teaching tayi ya amsa yace "haneefa Aminu yau kinyi late meya faru?"

cikin sanyinta tace "wallahi mun haÉ—u da goslow ne a hanya"

"okay okay"

zama tayi a gefen kawarta elham sannan ta ciro takadda ta fara note, hankalinta yana kan Noor batama san kwaɓa takeyi a takaddan ba, saida Elham ta rike hannunta tace "ke baki ganin rubutun da kyau ne? kiga rubbish ɗin da kike writing"


kallo tayi, waro ido tayi ta dafe kai tayi tsaki kaÉ—an kafin tace "hankalina baya nan"

yaga paper tayi ta fara sabon rubutu, tunanin wannan mutumin ya tsaya mata a rai data rufe ido sai ta ganshi yana murmushi kamar ba abinda ya faru, da haka har aka gama teaching, da tunanin marin da tayiwa noor a ranta, saide tunanin wannan me raken yafi damun ranta fiye dana Kanwar tata noor.



*Hakkina is ₦300 via 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, your evidence of payment via 08144818849*

No comments