Hakki na 13
🌸🌸🌸🌸🌸
*HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸
By
_jiddah S Mapi_
*Chapter 13*
*Last free pages daga wannan mun gama free pages*
~ji kake tass, karan fashewan kwalban turaren, a tsorace ta shigo É—akin ta kalli sani driver tace "wa aka sace?"
a tsorace yace "amarya"
hannu ta É—aga zata kai mishi mari Abba ya rike hannun, kofa ya sannan cikin dauriya yace "mutane suna nan dayawa kada kiyi kowa yasan abinda yake faruwa, mu kwantar da hankali akwai manyan baki wanda suke nan, calm down musan yadda za'ayi"
jikinta har É“ari yake cikin tsoro tace "karsu illatamin yarinya"
hannu yasa a bakinta ya rufe, "ba abinda zasuyi mata"
waya ya É—aga ya kira layin noor, kira biyu ta É—aga yace "sameni a É—akina"
tashi tayi daga zaunen da take tasa hijabi akan makeup É—in da yake kwance a fuskanta, É—akin Abba taje ganinsu cikin tashin hankali sai taji ba daÉ—i, to amma tana yin haka ne domin gyara rayuwan haneefa na gaba, durkusawa tayi "Abba gani"
share zufa yayi kana yace "inaso kimin wani alfarma"
jijiga kai tayi, yace "kisa kaya irin na amare kije wajen lunching a matsayin haneefa"
a tsorace ta É—ago tace "matsayin haneefa kuma Abba..."
hannu ya É—aga mata "banason ta bambayoyi kiyi abinda nace kawai"
tashi tayi ta fita, tasan dai itace tace a ɗauke haneefa amma bata taɓa zaton su Abba zasuce tasa kayan amarya taje wajen lunching ba, a zatonta zasu haɗu ne duka su fara neman inda haneefa take, da haka dai har tasa kayan da haneefan ta cire wanda ya matukar yimata kyau, momy ce ta shigo da farin mayafi irin wanda amare suke sawa a kansu su rufe fuska, takalmi dogo fari itama momy tasa mata, ta fesa mata turare, hannunta ta riko suka fito tare, fuska a rufe babu me ganinta, abba yasa a canja mota aka yiwa wani daban ado, da kanshi ya buɗe mata marfin motan ta shiga,
anwar sai kiran numbern haneefa yake baya tafiya, ya fara gajiya domin sun kusa 1hour basu zo ba, gashi baida number É—in noor, koda yana dashi ma ba zai kirata ba, jameel ya lura da yana cikin damuwa ya matso yace "yi hakuri zasu so ai, kasan shirin amare"
"jameel mutane da suna jiranmu acan"
karan tsayuwar mota sukaji, jameel yace "to gasu nan"
saida su inna dasu kannen jameel suka shiga mota, kafin ya fito ya shiga motan da amarya take, gabanta ne ya faɗi jin ƙamshin turarenshi ya buga mata hanci, cikin nutsuwa ya zauna, duk motocin suka jeru a layi suka fara tafiya, saida suka ɗau hanya, kirjinta sai bugawa yake, kallon lallenta yayi yaga sai murza hannu take ga kanta a rufe, hannu yasa ya riko hannunta baiyi magana ba sai murza ƴan yatsunta yake, jikin noor ne ya fara rawa ji take kaman ta janye hannu, amma tana tsoron kada ya gane, kallon karamin yatsanta yayi, jan lalle da bakin yayi mishi kyau sosai, a hankali ya kai yatsan cikin bakinshi, ba zato taji ya fara tsotsan karamin yatsanta, runtse ido tayi kaman tayi ihu ta daure tana zazzare ido a cikin mayafin, saida ya tsotsa sosai kafin ya cire, matso da bakinshi yayi saitin kunnenta yace "kinyi kyau, lallenki yayi kyau"
giɗa kai tayi, yace "yau ba shagwaɓa ne? ko kunyata kike ji?"
jijiga kai tayi, yasa hannu zai É—aga mayafin a tsorace tasa hannu ta rike hannunshi, murmushi yayi "yau kin zama me tsoro fuskanki kawai zan gani kaÉ—an, nayi missing naki sosai"
kin magana tayi, ji take kaman ta tsala ihu, wai yau itace da wannan me raken suna zaune waje É—aya? dolene ta koya mishi hankali ta nuna mishi asalin bambancin dake tsakaninshi da haneefa, banza talaka mara galihu, ace motocin biki ma saina gidansu zai taho a ciki, kato dashi baida ko mota guda"
sun kusa isa hall É—in taji yasa hannu ya janyota jikinshi, a kunne ya raÉ—a mata "ko kimin magana ko nayi kissing naki"
hannu tasa ta fara tureshi, yaki sakinta har driver yayi parking, matsowa yayi kusa da ita sosai har tana jiyo sautin numfashinshi, hannunta ya kamo wanda take tureshi dashi, saida ta daina motsi tsaban rikon da yayi mata, kasa da murya yayi a kunnenta ya raÉ—a "yanzu fa ke matata ce, ba budurwa ta ba, muyi kiss, na jima inason hakan amma na É“oye saboda haramci, yanzu an É—aura mana aure please ki bari inyi"
fizge kanta ta fara jin kalaman da yake mata, wani irin tashin hankali ta shiga kamar tayi magana ya gane bada haneefa yake tare ba, kara matsowa yayi "inyi?"
girgiza kai tayi kana ta fashe da kuka, jin sautin kuka yasa hannu a bayanta yana taping kaÉ—an, "sorry shikenan na fasa, banda kuka"
sauke ajiyan zuciya tayi ya riko hannunta suka fito tare, a hankali suke takawa ana musu liki, hannunshi a cikin nata tana ji yana murzawa har suka isa inda aka tanada domin zaman ango da amarya, a tare suka zauna, su Abba da manyan bakinshi aka fara gudanar da shagalin biki, hankalin momy baya kanta kamar yadda Abba ma dauriya kawai yakeyi, Allah Allah yake a gama kira commissioner ya sanar mishi abinda yake faruwa, yanzu baison tada hankalin jama'a ne, kiran ango akayi da amarya su shigo fili, bayan sun shiga noor taso tayi rawa sai kuma ta tuna haneefa bata iya rawa sosai ba, matsowa yayi ya rike ƙugunta a hankali yace "ba kince zakimin rawa ba ranan aurenmu?"
girgiza kai tayi, yace "to meyasa bakiyi?"
kai ta kuma girgizawa tana janye hannunshi daga waist nata, matsowa yayi kusa da ita sosai yace "ba zan sakeki ba sai kinyi rawa"
mutane suka fara tafi, jameel yazo yana watsa musu kuÉ—i, abin ya birge mutane, mc yace su koma su zauna, komawa sukayi abba yana kallon mami, faruk ne ya shigo hankali a tashe, Abba ya mishi alama "an ganta?"
kamar zaiyi kuka ya girgiza kai, tashin hankali su Abba suke ciki babu wanda yake da nutsuwa cikin su uku harda sani driver, haka dai suka daure ake gudanar da lunching, saida aka kusan tashi aka fara raba abinci da drinks masu tsada, bayan kowa yaci ya koshi za'a tashi mc ya É—au mic yace yana da muhimmiyar sanarwa, ai kuwa kowa ya bada hankalinshi, ya fara jawabi kamar haka.
"wannan gift ne musamman wa amarya, an turo ance a buÉ—e kowa ya gani domin nunawa amarya farin ciki, jama'a ku tafawa wanda ya turo wannan sakon"
tafi akayi sosai kafin mc yace "ku shigo dashi"
babban akwati ne akayi rapping da Jjan flower, sannan aka zuba wasu ado masu kyau a jiki, noor ta karewa akwatin kallo, momy suna zaune a gefe itada Abba, yah faruk sai waya yake kira har yanzu shiru, anwar yace "kin san da zaman sakon ne?"
girgiza kai tayi, ya maida hankali kan akwatin wanda aka aje a tsakiyan fili, mc ya kalli amarya yace "amarya kin yadda mu buÉ—e gift naki a bainan nasi?"
girgiza kai tayi kanta a cikin mayafi, hannu yasa ya fara warware igiyan da aka ɗaure fashi wanda yake sheƙi yana walƙi sosai, saida ya kwance kana ya fara ɗaga marfin, ji yayi ya mishi nauyi, da hannu yawa faruk alaman ya tayashi ɗagawa, faruk ya karaso wajen, mutane sai ɗaga waya suke suna video, musamman kawayen haneefa, ga elham tana zaune itada mijinta suna video, da sauri faruk yayi baya ganin hannu me lalle kwance cikin akwatin, mc ma a tsorace yayi baya, Abba da yake kallonsu ya daure yaje yana tambayan "menene?"
daurewa yayi ganin hannu me lalle a kwance cikin jini, a hankali ya karasa wajen yasa hannu ya ɗago gawan da yake kwance cikin akwatin jini ya ɓata fararen kayan dake jikinta, kwantar da ita yayi a ƙasa ya juyo da fuskanta nan yaga haneefa kwance idanu a lumshe fuskanta ɗauke da murmushi kamar yadda ta saba kullum, anwar da yake zaune ya gagara tashi, noor ce ta yaye mayafin dake kanta, batasan lokacin data karasa inda suke ba, mutanen wajen kowa ya tsorata sun zuba ido suna kallon noor dake cikin kayan amare haneefa Kuma a kwance cikin jini, anyi mata yankan rago, baya noor tayi kana ta sulale kasa babu wanda yabi ta kanta hatta momy ta kasa magana sai zazzare ido take, inama ta samu tayi maganan ko zuciyarta zai buga daidai, anwar saifa jameel ya taimaka mishi ya tashi, tsallaka noor yayi wacce take kwance a kasa ba wanda yasan tanada rai ko ta daina numfashi, inna tazo tasa hannu aka tace "wacece wannan?"
Elham wacce mijinta ya fita da ita dan ta fara zaucewa ya sata a mota kafin ya dawo ciki yana kallon yadda kowa yayi shiru ba wanda ya iya yayi magana,
ya faruk ya samu waje ya zauna, abba sai bin fuskan haneefa yake da kallo, zubewa anwar yayi akan gwiwoyinshi, hannu yasa ya É—ago gawanta ya rungume, jini ya É“ata mishi babban riga wanda yake fari sol, mannata yayi a kirjinshi kana yasa hannu yana shafa kyakkyawan fuskanta wanda yake É—auke da murmushi, manna fuskanshi yayi da nata a hankali ya runtse idanunshi wanda suke É—auke da zara-zaran eyalashes, da karfi yace "haneefaaaa!!!"
ganin bata buÉ—e ido ba ya kuma tsala ihu yace "haneefaaaa dan Allah ki tashi"
kallon su Abba yayi yace "dan Allah abba ka tasar min da ita dan Allah fa, faruk ku taimaka kuce ta tashi"
faruk yayi shiru a lokacin da zasu yanka jikinshi ba zasuga jini ba, inna tace "haneefa? kenan wannan ce amaryan? ita kuma waccan wacece?"
jameel yace "kanwarta ce noor"
kayan jikinshi daga fari ya koma ja, sai kuka yake ya rungume gawan yaki saketa, ƴan jarida ne suka cika wajen, sukayi kan Abba suna aika mishi tambayan daya kusa rusa mishi ƙwaƙwalwa, "Alhaji shin da gaske ne ka yiwa ƴarka auren dole shiyasa ta gudu har ta haɗu da ƴan fashi?"
kin amsa musu yayi, suka kara jefa mishi wani tambayan "Alhaji ance haneefa batason anwar kai ka tilasta mata aurenshi saboda wani kuÉ—iri naka"
a zafafe za juyo ya kalli mc kana ya karɓi mic, cikin zafin rai da dauriya irin na maza yace "ina sanar da ɗaurin auren ƴata noor da ɗana anwar"
anwar kam hankalinshi yana kan haneefa sai kuka yake bema kula da abinda Abba yake shirin yi ba.
a wajen Abba ya bada sadaki sannan aka samu shaidu, da waliyyai aka É—aura aure, saida aka gama É—aura auren Abba yazo zai É—auki haneefa nan anwar ya fara kuka yana janta da kyar aka fita da ita, a gefe ya kwanta jameel yasa hannu shida inna suna tashinshi, bai farka ba alama ya suma, faruk ne ya É—aga noor shi kuma jameel ya É—aga anwar aka fita dasu, asibiti aka nufa dasu ita kuma haneefa aka nufi gida da gawanta, noor ce aka fara É—aura mata drip, sannan shima aka É—aura mishi, bata hayyacinta har akayi jana'izan haneefa aka fita da ita zuwa gidanta na gaskiya, momy data kalli hannun haneefa wanda yake É—auke da jan lalle saita fashe da kuka, noor tana bacci ta daÉ—e da farkawa saide idon yaki buÉ—uwa da kyar ta samu ta buÉ—e ido, akan fuskanshi idonta ya sauka, kallon hannunta tayi wanda yake É—auke da drip, murza idonta tayi tana so ta tuno abinda ya faru, a hankali tasa hannu aka tana murza goshinta, ganin haneefa tayi kwance cikin jini, zare drip É—in tayi kana ta cire mayafin dake kanta, kanta ya zama babu É—ankwali, gashin ta barbaza hannunta yana zubar da jini sakamakon drip data zare da karfi, kallonshi tayi nan ta fara tuna komai, da karfi ta dira daga kan gadon, wani karfe dake gefen gadon da yake kwance ta É—auka zata caka mishi a ciki, a hankali ya buÉ—e ido jin kamar mutum a kanshi, ganinta a jaka yasashi tashi da sauri ya rike karfen, kokarin caka mishi take shikuma yana kare kanshi, inna ce ta shigo É—akin jin karan yayi yawa, ganin noor tana kokarin cakawa anwar karfe taje da gudu ta rike hannunta, tureta tayi gefe da karfi tareda kai mata mari a fuska, dafe fuska tayi tace "kika mareni?"
"ko zaki rama ne?"
hannu ta É—aga zata rama rike hannun da karfi, kallonshi tayi jin ya rike hannunta, zamewa tayi kana ta buÉ—e kofa ba takalmi ba mayafi kamar mahaukaciya sabuwar kamu, cikin tashin hankali take gudu tana kiran "haneefa!!! haneefa"
motoci take wucewa a titi saide su matsa bata damu tayi rai ko ta mutu ba, ta rinƙa tangal-tangal akan titi, ba abinda take faɗa sai sunan haneefa, wayan dake gefen riganta ya fara ringing, cirews tayi cikin kuka tace "bance ku kasheta ba, kun kashemin yayata, wa yace ku kasheta?"
kwashewa yayi da dariya har saida ya kusan faɗuwa kasa kana yace "kina cikin tashin hankali ne? ayya am sorry my love, banso na ganki cikin tashin hankali ba, kece kika janyo, ina sonki banason abinda zai taɓamin ke shiyasa nayi akan yayarki, shin kun duba gawan da kyau? no no no baku duba ba, bari na baki satan amsa, ai fyaɗe nayi mata"
ya kuma kwashewa da dariya, tana gudu tace "me nayi maka?"
"yawwa good garl kinyi tambaya me kyau, zaki iya tuna ranan da kikaje club da dare partyn wani É—an gidan tsohon governor? me yake da suna?"
a tsorace tana gudu tana nishi tace "na'eeem"
"good garl, kin tuno sunan, to kin tuna wani wanda kika watsawa drink a Ido"
shiru tayi yana jin sautin gudunta yace "to nine, barka da shigowa gonan Jabeer, wannan lemon da kika watsamin a ido shi yayi sanadiyyan lalacewan idanuna, kinsa bana ganin na makance, saina rike sanda nake iya tafiya, duniya ta zama min baki kirin, kema yau inaso ki É—anÉ—ana bakin cikin da kika lasamin, sannan kada ki manta ke kikasa a sace yayarki saboda son zuciya, ni kuma nayi amfani da wannan babban daman na aikata abinda nakeso, yadda nake ganin baki haka nakeso kema ki gani, sannan kuma kisa a ranki nine mijinki ni zan aureki, bakisan ta kowani siffa zan fito ba, a shirye nake nayi basaja domin aure wannan kyakkyawar halittan, Allah yajikan haneefa"
wayan ya daɗe da faɗuwa a hannunta, sai gudu take tana ganin kamar ba zata iss gida taga gawan ba, anwar da yake jin jiri yace inna ta kira jameel subi bayan noor kada wani abin ya sameta, yana magana yana cije leɓe.
noor da kyar ta isa gida kafafunta sai jini yake ga hannunta yana zuban jini, tana isa ta ratsa mutanen dake zaune suna kuka, bata tsaya ko ina ba sai É—akin Abba, baki ta buÉ—e zatayi sallama domin yiwa Abba bayanin abinda ya faru, da sauri ta dakata tareda yin baya da kafanta jin abinda abba yake faÉ—a, É—an lekawa tayk ta ganshi rike da alkur'ani yana tsaye yana kuka, gefe guda momy itama tana gefe sanye da dogon hijabi tana kuka, cikin kuka yace "na rantse da ubangijin daya saukar da wannan littafi me tsarki, duk wanda yake da hannu ko baki, ko wanda yasan wanda suka aikata wannan abin saina kasheshi da hannuna, nayi alkawari saina kashe wanda yasa aka sace haneefa, wallahi tallahi ba zanyi rantsuwa a banza ba, idona idon wanda ya kashe haneefa ko yake da sa hannu, koda na gyarawa masushi motane ba tareda meshi ya sani ba, saina illata shi, Allah ya isa, Allah ya isa haneefa"
tashi momy tayi ta karɓi kur'anin ta aje kana tace "ka daina wannan kukan ya isa haka, sannan kur'ani ba abin wasa bane, haneefa ta riga ta tafi muyi mata addu'a"
"zanyi addu'a amma ki barni nayi kuka dan Allah, kinsan ba zan iya daina kuka ba akan mutuwan haneefa, duk wanda yake da hannu a mutuwannan ya cuceni"
hannu tasa tana lallashinshi, "i know it's harmful but for the sake of noor and faruk be strong, kana so suga kana kuka suma su rasa nutsuwa ne?"
girgiza kai yayi "then kayi shiru, ko ni bazan taɓa yafewa duk wani mesa hannu a mutuwan haneefa ba, saida na gaya maka kada ka aurata ma wannan matsiyacin ɗan talakawa, gashi ka haɗashi da noor ba tare da kayi shawara ba, haka rayuwar ƴaƴana zai kare cikin rashin galihu? noor ba sa'ar wannan talakan bane, haneefa ma ita ta zaɓe shi, har naji na tsaneshi"
kuka ta kara fashewa dashi kana tace "a matsayina na mace uwa wacce ta durkusa ta haifa kuma tasan zafin haihuwa ba zan tauyewa ƴata haƙƙin ta ba sai wanda ta zaɓa zata aura, Allah ya isa da kisan gilla da aka yima haneefa, Allah ya tona asirinsu, kuma noor ba zata zauna da wannan talakan a matsayin miji ba, wallahi bata tsara rayuwarta haka ba"
ta karashe magana tana kuka.
Abba da yake tsaye yace "shine mijin dana zaɓa mata shi zata zauna dashi"
momy tace "wallahi ba zata zauna dashi ba, da wanne zanji? itama da wanne zataji? mutuwan Æ´ar uwarta ko auren miji mara galihu? wanda bashi da asali bashida dangi, kasan daga ina ya fito?"
"koma daga ina ya fito ai shi É—in mutum ne kamar kowa, kuma yanada nutsuwa da sanin ya kamata"
noor wacce tasa hannu akan handle na kofa jin kalaman momy dana Abba yasa ta fara ganin duhu-duhu, jiri ya fara É—ibanta hannunta dake kan handle na kofan ya fara karkarwa, baya tayi ji kake pat ta faÉ—i kasa a sume....
*Masha Allah anan na kawo karshen free pages, daga wannan idan kin kara ganin littafin haƙƙi na a waje to na sata ne, biya ₦300 kacal ki karanta har karshe, ba tareda haƙƙin kowa a kanki ba, 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, masu kati zaku turo ta nan 08144818849 Mtn, ku turo katin shaidan biya ta nan 08144818849, idan kin biya banda dogon surutu kawai kicemin ga payment na hakki na*
No comments