Hakki na 12
🌸🌸🌸🌸🌸
*HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸
By
_jiddah S Mapi_
*Chapter 12*
*ki biyani haƙƙi na ki karanta haƙƙi na ba tareda haƙƙin kowa a kanki ba, mun kusa gama free pages, masu son biya zaku iya biya kai tsaye ta account nawa 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, turo katin shaidan biya 08144818849, naira 300 ne, insha Allah zan saki a group ɗin da zaki rinƙa samu kullum ba tareda tsallaken page ba*
~Ta sameta a ɗaki ta kwanta rub da ciki tanajin ranta kamar wuta, a hankali ta tura kofan ta shigo, towel karami ta ɗauka first ta fara tsane gashinta wanda ya jiƙe da ruwa, cire kayan jikinta tayi kana tasa riga da wando buɗaɗɗe, kallon noor tayi tana cigaba da tsane gashin tace "a koda yaushe idan kika shiga tsakaninmu sai Allah kara kusantani dashi, meyasa ba zakisa a ranki wannan haɗin Allah bane, kuma babu wanda ya isa yaja da ikonshi?"
kwafa tayi tana kallonta ta cikin madubi ko motsawa batayi ba, ta san ba bacci take ba, tace "you have to respect him sabida zai zama mijin yayarki, and shi É—in abokin yayanmu ne, noor kada negative behavior É—inki ya haifar mana da matsala watarana, you know I love you but your love can't stop me from loving my love"
"you can't love him sama dani"
kallonta tayi tana daga kwancen tayi maganan, murmushin takaici tayi kana tace "there's different between love and love, akwai so na jini wanda ɗan uwa yake yiwa ɗan uwa, akwai kuma so me shauƙi wanda masoyi yake yiwa masoyi, Yah faruk is my brother zan iya hugging nashi ko sau ɗari ne a rana ɗaya banji komai ba, shima haka, but Anwar is my love da nayi hugging nashi zanji shauƙi, zanji kamar na shiga jikinshi ko zuciyanshi na huta, noor ki gane mana, ki gane irin soyayyan da Allah ya ɗauramin na anwar, nima da zan iya cireshi a raina dana cire ko dan na zauna lafiya dake, but i can't, ko wani rana jinshi nake yana kara shiga raina, a duk lokacin daya kalleni ji nake kamar kada ya daina kallona, noor inason Anwar please ki dawo normal ki daina nuna mishi halin da babu kyau"
"ba komai zan daina"
murmushin jin daÉ—i tayi "that's my sis I love you"
murya ƙasa tace "love you too"
washe gari Abba yace suje da faruk ya nuna mishi komai na company, yayi godiya yace "Abba ina neman alfarma"
Abba yace "ina jinka me kake so?"
"zan koma wajen inna ta saboda ita kaÉ—ai take zaune"
giÉ—a kai Abba yayi "ba komai ka gama aikinka ai amma ka bari sai gobe ko yau kakeson tafi?"
"a,a zan bari sai gobe"
"amma zaka rinƙa zuwa kana dubamu ai ko?"
"eh Abba"
tareda ya faruk suka tafi company aka nuna mishi komai ya kuma fahimta dama business ya karanta hakan bai bashi wahalan ganewa ba, office nashi me kyau aka bashi makulli ya kalla tareda godewa Allah wanda ya kawoshi wannan matsayin ba tareda yasha wani baƙar wahala ba, duk da yasha wahala a rayuwa to gashi Allah ya dubeshi.
tun a ranan ya fara aiki kuma Alhmdllh ya gane komai, koda zai koma gida Abba ya turo driver a É—aukeshi baiji daÉ—i ba domin yafiso ya tafi da mashin nashi wanda ya saba da hawanshi, koda ya koma gida Abba yace ya aikin?
godiya yayi yacewa Abba bayason driver yana zuwa ɗaukanshi zai tafi da kanshi, ganin yafi sakewa da tuƙa mashin Abba ya amince da kudirinshi, koda dare sukasha waya da haneefa kaman gari ba zai waye ba, har bacci ya fara ɗaukanta yace "haneefa?"
kin amsa mishi tayi ya kuma cewa "haneefa"
muryanshi kasa, ganin bata amsa ba ya kalli wayan yayi murmushi da may be tayi bacci ne, yace "saida safe"
a hankali tace "uhummm"
"bakiyi bacci ba?"
murya a shagwaɓe tace "um um sai kayi bacci zanyi nima"
"meyasa?"
"no sai kinyi kafin nayi dai"
"a,a nikam ba zan iya bacci ba idan banji sautin numfashinka a kunnena ba"
lumshe ido yayi haneefa tana sashi cikin wani hali shiyasa yake gujewa yin waya da ita musamman da dare, ganin yayi shiru tace "to kayi"
muryan da take magana dashi shi yafi komai É—aga mishi hankali, ji yayi kamar ya kashi wayan sai kuma yace "kiyi bacci na fara jin bacci kinsan gobe zakije makaranta ko?"
kamar zatayi kuka tace "to kamin yadda zanyi nayi baccin dan na kasa yi"
ya rasa me zai mata a hankali yace "rufe idonki"
rufe ido tayi, kasa yayi da murya a hankali ya fara furta mata kalman "i love You"
da haka har yaji ta fara numfashi a hankali, murmushi yayi tayi bacci, har zai kashe wayan sai kuma yace bari ya bari tayi nisa, noor jin tayi bacci ta ɗago kai tana kallon wayan da yake haske, sunanshi ta gani ɓaro ɓaro an rubuta Anwar Darling da alaman love a gaban sunan, hannu ta ɗaga zata maka wayan da kasa taji an riko hannunta, haneefa ce cikin bacci tace "ka kara cewa i love you"
a hankali ta kara wayan a kunnenta, ji tayi yace "i love you so much, kiyi bacci karki makara gobe, ba naji muryanki kamar kinyi bacci ba?"
giÉ—a kai tayi domin noor tasa wayan a speaker, girgiza kai tayi "ina sonka"
"ina sonki, ina sonki, ina sonki"
da haka har ta koma baccin"
jin tayi shiru yace "good night"
bin wayan Noor tayi da kallo bayan ya kashe, aje wayan tayi tasa hannu akan pillow ta danne a fuskanta nan ta tsala wani irin ihu kaman ta haukace, da kyar tayi bacci ranan ji take kaman taje É—akinshi tasa mishi pillow har sai ya mutu kafin ta fito.
washe gari, ya yiwa Abba sallama domin faruk yace zasuje shima yau yaga inna, momy ma ya mata sallama kamar bata so ba ta amsa, noor ce ta sauko hannunta rike da jaka, hijabinta a hannu, yau canvas tasa fari wanda ko igiyan bata É—aure ba, tun daga sama take kallonshi har ta sauko, yayi kyau sosai musamman da yasa kananan kaya hannunshi cikin aljihu, da alama jiran faruk yake, gaishe dasu Abba tayi kana ta zauna tana kallonshi kallo irin na tsana da rashin so, zuba abincin tayi ta lafta barkono tanaci, idonta yayi jajur tana ci tana kallonshi, É—auke kai yayi domin ya fara tsorata da lamarin yarinyar, Abba yace "tunda sun fito ku zauna kawai muyi breakfask saiku ajesu kafin ku wuce"
kamar zai musa Abba yace "a,a banson musu"
zama sukayi Abba yace haneefa sa musu abinci, murmushi tayi ta matso da plate nata ta zuba mishi kaÉ—an akan wanda ta rage kana ta tura mishi gabanshi, haneefa ta sauko da gudu tana kiran "noor noor"
ganin suna zaune a wajen cin abinci tace "na zata kin tafi kin barni"
"ba zan taɓa tafiya na barki ba, saide idan naga waje me kyau inda yafi nan zakije"
babu wanda ya fahimci maganan a cikinsu, É—auka abincin yayi ya fara ci, ita kuma ta zuba ruwan tea me zafi ta kara barkono akai kafin ta fara sha, kowa ya zauna yanacin abinci Anwar sai zufa yake harshenshi kamar zai fita haka yakeji, wani irin azaban zafi yakeji amma ya daure yana turawa, Abba ya kalleshi yace "ya dai? a baka ruwa?"
da sauri haneefa ta tura mishi cup na shayin tace "ga tea"
"Abba yace yasha Tea"
kurɓan tea yayi nan idonshi ya sauya kala, hannu yasa akan roban ruwa ya fara sha, ba sauki, kallonshi noor take ta kasan idonta har sanda yace "Alhmdllh na koshi"
tashi yayi yabar wajen, haneefa ma tace "na koshi"
noor ta mike zatabi bayanta faruk yace "je ɗakina ki ɗaukomin jaka na na manta "juyawa tayi ta koma ɗakinshi, sani driver ne ya nuna mishi motan da zasu fita dashi, shiga yayi ya zauna a gidan gaba wajen driver ya haɗa kanshi da jikin sitiyarin motan, fuskanshi yayi jajur kaman yayi ihu haka yakeji, ruwan gora ya ɗaga yana sha saida ya shanye ya lanƙwasa goran ya jefar, har yanzu kaman wutan dalma aka naɗa mishi akan harshen, buɗe marfin motan tayi sannan ta shiga cikin nutsuwa ta zauna a baya, ganin bai ɗago kanshi ba tace "ina kwana?"
jin muryanta ne ya É—ago yana kallonta, ganin gaba É—aya ya fita daga hayyacinshi tace "subhanallah meya sameka?"
baya iya jure wahala ya marairaice yace "harshena bakina zafi"
da sauri ta buÉ—e motan ta fito zuwa gefenshi ta zauna, "meya samu bakin naka?"
"yajiiiii"
yayi magana kaman zaiyi kuka, murmushi tayi yanzu yaji yake yiwa wannan rakin?"
ruwa ta mika mishi daga jakanta ya ture tareda kifa kanshi daga inda ya É—ago, ta kalleshi sosai yadda yake zufa kasan yana cikin damuwa, maida ruwan tayi cikin jaka kana ta matso tace "É—ago dai"
É—agowa yayi tasa hannu ta É—ago fuskanshi, jijiyan kanshi duk sun tashi,
"let me see the tongue"
ba musu ya fito da tongue nashi, a hankali ta fara hura mishi iskan bakinta, shiru yayi ya fara jin sauki, ci gaba tayi da hura mishi har na tsawon wasu lokuta, baya ya farayi tana binshi har ya manne da jikin seat ɗin, ido ya lumshe yana jin wani sassanyan iska yana bi har ƙwaƙwalwan kashi, saida taga ya fara kamar zaiyi bacci kafin ta fara janyewa, buɗe marfin motan faruk yayi, da sauri ya maida ya rufe ganin kanwarshi tana hurawa anwar iskan bakinta, anwar kuma ganin zata matsa yasa hannu yace "har yanzu da zafi"
hannu tasa ta ɗan bugeshi a kirji kana ta matsa ta zauna, ruwan goran ta mika mishi ya karɓa yasha, nan fa yaji kamar bai taɓa cin barkono ba a rayuwanshi, a hankali yace "thank you"
tana gyara zaman jakan tace "dama kasan bakacin yaji meyasa kaci?"
"tsautsayi"
sai a time É—in faruk yayi knocking, buÉ—ewa yayi ya shiga gidan baya ya zauna yana danne danne a wayanshi, noor ta fito da jakan a hannunta ta zauna a gefen ya faruk, Anwar ne yaja motan duk sukayi shiru, noor tayi mamakin yadda ya daina jin zugi lokaci guda, sai kallonshi take tana son ganin yadda ya canja, abin mamaki garau yake "to kodai shiÉ—in aljanine? kai ko aljani yaci wannan abincin da shayin sai yaji a jikinshi balle mutum É—an adam"
wannan tunanin har suka isa kofan school nasu, sallama tayi mishi, noor ta yiwa ya faruk,ya fito ya dawo gaba ya zauna, irin wannan karamci da suke nuna mishi yasa baya É—aukan mataki akan abinda noor take mishi, faruk ya aje wayan bayan sun hau hanya yace "baka shiri da yaji ne?"
girgiza kai yayi "banson yaji yana galabaitar dani"
"to meyasa kaci?"
"ai bansan akwai yaji ba"
"so kake dai haneefa ta hura maka Iskan bakinta a naka"
da mamaki yace "yaushe ka shigo?"
dariya kawai yayi, "É—azu"
"gaskiya faruk bakada mutunci"
tsaki yaja sukaci gaba da tafiya, har suka isa gidan inna, daÉ—i yaji a ranshi, saide yasan yau masifa saiya sa audiga a kunne ya toshe kafin zai iya bacci, bayan sunyi parking a kofa anwar yayi mishi iso, kai tsaye suka shiga gidan, jin sallamanshi ta fito tana lekawa, ganin shine tace "ya maka kyau ai ya maka kyau anwar, kasa kafa ka tafi ka barni kaje can wani wuri kana rayuwa?"
ƙarasawa yayi wajenta hannunshi a kunne alaman afuwa, yace "na tuba Inna ta"
hannu tasa ta rankwashi kanshi saida yayi kara tace "waye wannan?"
faruk ya durkusa har kasa yace "ina kwana inna"
amsawa tayi tace "tashi mu shiga ciki, sabon aboki kayi?"
girgiza kai yayi"ba aboki bane É—an uban gidana ne, a gidansu ai nake zaune"
"Allah sarki mu shiga ciki bawan Allah ya sunanshi?"
"faruk"
"umaru mu shiga daga ciki ko"
ganin yadda take nan nan dashi yasan tana son Anwar sosai, shiga ciki sukayi ta kawo musu fura da nono wanda ta aje a bakin randa me sanyi, anwar yace "nayi kewanshi"
nan ya fara sha, ganin faruk baisha ba yace "sha mana"
ada yana cewa nono da fura kazanta ne, yau daya É—ana na inna har saida ya fara lushe kwano, tace "ma karo maka ne?"
girgiza kai yayi "a,ana koshi inna"
godiya tayi mishi har suka bige da hira sai kusan sha biyu yace zai wuce, anwar ya rakashi har bakin kofa, can daga nesa ya hango jameel, da murmushi a fuskanshi ya karaso ya bashi hannu suka gaisa, ya rungumeshi yace "nayi kewanka ina ka shiga?"
"nima nayi kewanka ya jikin Abba?"
"Abba ya warke yanzu yana fita aiki"
"masha Allah"
kallonsu faruk yake cike da jin daÉ—i, haka abota yake ka taimaki abokinka ka cireshi cikin damuwa, wannan abota nasu ya mishi kyau, hannu suka sa da jameel yace "ga faruk É—an uban gidanane"
faruk yace "kuma abokinshi"
jameel yace "sannunka"
tare suka rakashi har wajen mota ya shiga suna É—aga.mishi hannu, saida ya tafi anwar yace "gaba É—aya ka rame ko meyasa?"
"rashin ganinka ne"
"matsa anan may be soyayya ka faÉ—a"
dariya yayi, yace "ina nas?"
"nas ai ya wuce school yayita kiran numbern ka baya tafiya"
"Allah ya bashi sa'a yasa yaje a sa'a"
"Ameen"
shiga ciki sukayi nan suka haÉ—u da inna suka fara hiran yaushe gamo, cikin hiran anwar yake basu labarin irin kula da Abba ya bashi, duk suka yiwa Abba fatan alkhairi, sai can anwar ya rakashi yana bashi labarin haneefa, daga jin yadda yake labarin zaka san yana sonta har cikin ranshi, jameel yace "gaskiya ka haÉ—u da wacce take sonka kuma naga kaima kana sonta har cikin ranka"
"amma fa jameel ina tsoron aurenta tayimin nisa ba kaÉ—an ba, bagaka gidansu ba da inda suke rayuwa"
"Allah baya duba haka kawai kayi addu'a Allah ya sanya Alkhairi tsakaninku"
"ameen jameel"
tafiya jameel yayi shi kuma ya koma gida, samun inna yayi yaci gaba da bata labari harda yadda Abba ya bashi matsayin manager, tayi hamdala tace zai kaita ta yiwa Abba godiya, yace zaizo ai da kanshi domin kuyi magana"
"magana kuma? maganan menene?"
"sai yazo zakiji inna"
ganin kamar baison maganan sosai yasa ta kawar da zancen suka fara hira.
bayan 3days da komawanshi gida ya fara zuwa aiki akan mashin nashi, yana kula da inna sosai, yau bayan ya dawo yaga kiran Abba, cikin girmamawa ya É—aga suka gaisa Abba yace anjima zasuzo su gaida inna kuma suyi maganan auren, a hankali yace "to Abba sai kunzo"
bayan Abba ya kashe ya samu zama da inna ya gaya mata duk yadda sukayi saide ya ɓoye mata abinda noor tayi mishi, ma'ana farkon haɗuwansu, ya ɗaura da "inna ina tsoron aure a gidan masu kuɗi nafison ƴar talakawa kamarni, banaso na musawa Abba shiyasa na amince ba tareda gardama ba"
"karka damu anwar ai aure nufine na Allah, idan Allah yaso saiya watsar da auren idan kuma matarka ce sai kaga ka aureta komai talaucinka"
shiru yayi yana shafa sajenshi kana ya ciza baki yace "to amma inna kuÉ—in auren ma kaÉ—ai aikine ina zan samu?"
"Allah zai baka, ba gashi ya baka manager ba a company? to ai Allah yana gani idan kayi aiki tukuru ba dare ba rana ba zamba cikin aminci sai kaga komai yazo maka da sauki, addu'a zaka dage dashi tashin sallan dare, sai kaga komai yayi sauki"
jijjiga kai yayi "to inna Allah ya bamu sa'a"
da dare Abba ya sanarwa momy cewar zasuce gidansu anwar, cikin rashin fahimta momy tace "ai dangin miji su suke zuwa neman aure ba wai baban mata ba"
"to ai nine danginshi sanin kanki na bashi da kowa sai innarshi, da yana dashi nasan da zai turosu"
"haba Alhaji wani irin auren wulakanci kakeso ka yiwa haneefa? dan kawai tana sonshi sai ya zama batada gata?"
hannu ya É—aga mata "so ba kawai bane, kuma banaso ki hurewa yarinya kunne, ita tace ta ganshi tanaso saboda haka ni duk abinda takeso shi nakeso"
fita yayi dama ya shirya cikin manyan kaya kuma yayi magana da abokanshi biyu zasu tafi tare.
tun a hanya Alhaji Umar yace "Aminu ina kuma zaka kai Æ´arka?"
"inda tace tanaso"
"haba mana kai kuma dubi unguwa duk bola, har yanzu kuma sai shiga lungu muke bamu iso ba? kayi bincike kuwa akan gidansu yaron?"
"kwarai nayi bincike shiyasa ma na É—au haneefa zan bashi"
"amma ta amince? ba dai auren dole kake mata ba?"
"itace ma ta zaɓeshi matsayin mijin aure"
kallon juna kawai sukayi har suka isa kofan gidansu anwar, kiranshi yayi a waya ya fito, yana ganinsu ya durkusa kasa yana gaishesu, su Alhaji umar sai binshi suke da ido suna mamakin meyasa Alhaji aminu zai bashi auren Æ´arshi? yayi musu iso, inna ta shimfiÉ—a musu babban tabarma suka zauna aka gaggaisa, Abba ne ya mika mata bukatanshi, ta kuwa amsa tareda fashewa da kuka, tace "mun gode Alhaji amma fa anwar bashida kowa saini, shi É—in maraya ne, anya zamu iya haÉ—a alaka da ku?"
"ba komai ai maraya É—an kowa ne, kuma shi anwar mutumin kirki ne shiyasa na bashi haneefa"
"mun gode Alhaji"
da zasu tafi suka aje kuɗaɗe, taki karɓa saida suka tafi suka bar mata kuɗin a wajen, anwar ya kaisu har wajen mota kana yayi godiya, ya dawo ya kuma tarar da inna tana kuka, saida ya samu zama ya lallasheta kafin tayi shiru, tausayin rayuwarshi takeyi.
bayan Abba ya dawo ya aika a kira mishi noor da haneefa, suka sameshi a falo, noor tasa dogon hijabi har kasa domin rigan jikinta bai wuce gwiwa ba, bayan sun zauna abba yayi gyaran murya yace "nayi magana da inna wato kakar anwar, munyi magana akan auren haneefa da anwar, to abinda nakeso ku sani shine ba canja magana daga baya, ina nufin naje nayi magana ba wanda zai canja magana daga baya, haneefa banda canja magana dan kinsan bana magana biyu"
jijjiga kai tayi, yace "Allah muku albarka, auren zamu yanka ba nisa, idan yaso zaki gama school naki acan"
murmushi ya kasa tafiya daga fuskan haneefa, noor kuma tunda ta sauke kai kasa take sauraran Abba har ya gama bata É—ago ba saida yace "kuje na sallameku"
a hankali ta mike ta wuce É—akinsu, haneefa kuma momy taja hannunta suka shiga É—akinta, zaunar da ita tayi a bakin sofa ta riko hannunta ta girgiza ta sosai kafin tace "kina cikin hayyacinki kuwa? kina lafiya haneefa?"
giÉ—a kai tayi kana ta marairaice tace "momy ina sonshi har cikin raina dan Allah ki bari na aureshi"
sakinta momy tayi tana dafe kai, ji take kamar ta naÉ—a mata É—an banzan duka ko zata samu sauki a ranta
"momy in tafi?"
rasa abinda zata faɗa mata yasa ta girgiza kai, a hankali ta tashi ta fita, momy tabi bayanta da ido kamar wata doluwa, bayan ta fita ta dafe kanta da jikin gadon ta rasa me zata yiwa haneefa ta dawo hayyacinta, haka dai ta hakura ta fara addu'a Allah ya zaɓi abinda yafi alkhairi.
haneefa ta shiga É—aki cikin murna ta É—au waya zata kirashi, kiranshi ne ya shigo ta É—aga tareda zama akan gado tace "hello"
amsawa yayi suka fara waya tana nuna mishi matukar farin cikin data shiga lokacin da abba yace yaje gidansu, shima ya nuna mata farin cikin da yaji, haka dai sukaci gaba da hira tana zuba mishi shagwaɓa, ji yake kamar ace an riga an ɗaura musu aure, wannan shawgwaɓan da take mishi yayi mishi yawa da kyar yake daurewa yana biye mata, domin abu kaɗan yana iya kunnashi idan yana tare da ita, wani lokacin sai ya haɗa da lipton da lemon tsami yake iya bacci, gashi ta kasa ganewa haka yanayinta yake ta riga ta saba, duk wayan da zasuyi baya mata zancen noor saide ita kam kafin ya kashe sai tayi zancen noor yafi sau ishrin, da alama tanason noor har cikin ranta,
noor na kwance a gefe ta cire hijabin tana karanta takadda, bini-bini tana kallon haneefa har suka gama wayan ta kashe, aje takaddan tayi kana taja bargo ta fara bacci.
jameel ya matukar taya anwar murna, har saida sukazo da abba da umma sukayi mishi Barka da samun aiki, ya yiwa Abba ya jikin, inna tayi farin cikin ganin abba ya samu lafiya.
_one month later_
zancen auren haneefa Aminu sadauki da anwar ya baza ko ina na cikin garin kano, duk wani lungu da saƙo zancen auren kawai ake, domin mahaifinta ba karamin mutum bane, abokanshi suna manyan mutane ne, daga kan invitation card zakasan wannan auren ƴar gidan manya ne, Abba da kanshi yaje gidansu inna yace zai siya musu wani gida inna tace a,a ya bari basaso, ganin kamar batason barin gidan ne yace to zai turo masu gyara su gyara, ta yadda da hakan, a cikin week ɗin ya turo masu gyara aka fara rushe gidan, gyara me kyau akayi inda ya maida gidan gidan masu rufin asiri, kuɗi ya turawa anwar a account nashi domin shirye-shiryen auren.
haneefa ba kanta gyara kawai takeyi ita da kanta, kama daga gyaran jiki kawarta elham itace ta haɗata da me gyaran, momy ma ta barwa Allah sai ido kawai, harda maganin sanyi take bata, waya da anwar ba dare ba rana, ko wajen aiki yake tana kiranshi, ya ɗaga tayi ta mishi shawagaɓa, yauma haka bayan ta tashi daga school suka aje noor a gida ita kuma ta wuce waje gyara, bayan an gama ta kalli kanta, tayi kyau sosai jikinta kamar na larabawa har wani glowing take, gashin kanta kuma yasha gyara sosai sai sheƙi yake, ga wani kiɓa da tayi kamar wacce bata shan komai sai madara, tambayanshi tayi "yaushe zakazo?"
"anjima zanzo nida jameel"
"tom shikenan sai kunzo"
bayan ta koma gida ta shiga toilet tayi wanka, koda ta fito noor kallonta take yadda tayi kyau tayi ɓul-bul, sai sheƙi take kamar yaune auren, wani bakin ciki ne ya tokare mata kirji tunawa da wanda zata aura, kaya tasa kana tayi salla, bata yiwa noor magana ba dan koda tayi mata bata maida mata amsa me kyau, shiyasa itama bata kulata sosai.
mama salma tasa ayi musu girki, ta haɗa musu abinci me kyau tareda juice wanda ita da kanta ta haɗa, bayan sallan isha ya kira haneefa yace sunzo, tasha bakin abaya ta yafa mayafinshi akanta, lipbalm fari tasa akan ɗan karamin lips nata, agogo ta ɗaura me kyau, kana ta fesa turare me ƙamshin gaske, kallon kanta tayi a madubi, kamar ta lashe kanta sai murmushi take, wayanta ta ɗaga fita, a bakin kofa suka haɗu da noor, da kallo ta bita har ta sauka akan stair, sai kuma ta share ta shiga ciki, koda ta isa kofan falon da suke saida ta leƙa, ido huɗu sukayi dashi, yana zaune akan sofa yasha riga baƙi da farin wando, bakin rigan ya fito da farantaka da kyau na fatarshi, hannu yasa ya shafa sajenshi alaman na kamaki kina leƙe, shagwaɓe fuska tayi kafin tayi sallama tana dukar da kai, jameel yace "amaryarmu kin fito?"
É—ago kai tayi "ina wuni?"
ya amsa mata cikin sakin fuska, nan suka fara hira, ya kalli agogo yace "ni zan wuce idan naga ka jima zan tafi, idan kuma ta barka ka fito to saimu tafi"
dariya tayi "ai kuwa ba zai fito da wuri ba, gara ka zauna anan ayi hiran da kai"
"kai ina amarya gaskiya ba zan iya jiranku ba"
anwar dai yanata kallonta, ganin sai wani kyau take karawa, ga wani sheƙi da kiɓa take kamar ya saceta ya gudu"
jameel ya mishi sallama zai wuce saida tasa yasha juice dan cewa yayi ba zaici abinci ba a koshe yake, da kyar dai yasha sukayi sallama.
ɗauke kai yayi daga kallonta da yake ya maida hankali kan babban wayan da abba yace ya siya domin sauƙin aiki, tashi tayi ta kama yatsun hannunta duka tana wasa dasu har ta iso gabanshi, ido ta zuba mishi, yaji ƙamshin turarenta amma bai ɗago ba yasan tana kusa dashi, tayi 2mins a tsaye kafin tace "malam wai bakaga nayi kyau bane?"
murmushi yayi yaki kallonta yace "kinyi kyau"
ganin ya raina mata hankali tace "to ka kalleni mana"
kin kallonta yayi "kinyi kyau mana Æ´ammata"
hannu tasa ta warce wayan kana ta zauna a gefenshi ta marairaice fuska ta turo baki kamar zatayi kuka tace "to ka kalleni mana"
hannu yasa yayi tagumi yana kallonta yace "kinyi kyau sosai, ai ko ban faÉ—a ba kinsan ke É—in kyakkyawa ce"
"nikam ban yadda ba saida na faÉ—a?"
"yi hakuri baby ta juyo nayi ta kallonki har in tafi"
kin juyowa tayi saida ya tashi daga inda yake yaje gabanta yace "sorry"
bashi wayan tayi kana ta juyo suka fara hira, abinci ta matso mishi dashi yakici, tasa akan plate É—in ta matso gabanshi tace "nima banci abinci ba"
"kici to"
"um um kai zaka bani"
ido ya waro, wannan yarinyar mantawa take basuyi auren ba, yace "kici dai idan kin gama saina tafi"
kuka ta fashe dashi harda hawaye dole saiya sauko, a hankali ya sauko ya tankwashe kafafu, yana kallonta yace "to ki daina kukan"
spoon ya É—auka ya É—ibo abincin ya kai bakinta, buÉ—e É—an karamin bakinta tayi yasa mata ta fara tauna tana share hawaye, mamakin yadda take a sakalce yake har tagama cin abincin, zai tashi ta É—iba ta kai bakinshi, ba dan yaso ba saida tasa yaci kaÉ—an kafin ta kyaleshi, kiran me aiki tayi aka fitar da plate, nan suka fara hira tace "ba yaji?"
girgiza kai yayi, dariya tayi, yace "tsokanata kike?"
"a,a" ta faÉ—a tana noke dariya, da haka har suka gama hira ya tafi, komawa É—aki tayi cike da murna.
yau saura 1week É—aurin auren haneefa da anwar, noor har batason zuwa school dan batasan da zata bawa kawayenta maza da mata ba, ta gama baki da tsara yadda auren haneefa zai kasance, sai gashi haneefa ta watsa mata kasa a ido, taji ta tsani kanta, har yau bata wani yimata magana, gashi har mutane sun fara taruwa a gidansu, wai sunzo aure, ko ta ina tabi tsaki kawai take ja, haneefa ta watsar da ita sai shirye shiryen bikinta take, IV É—inta ta kai har school ta bawa malamai da kawayenta na arziki, noor ko online bata fiye hawa ba, duk wanda yayi mata tambaya akan bikin cewa take itama batasan komai ba, Abba ne yasa momy taje har kasan egypt ta siyo kayan lefe, anwar bai so ba Abba yasa aka kai kayan gidansu, shima anwar da jameel sun zama busy domin shirye shiryen bikin kawai sukeyi.
biki saura kwana uku, gidan Alhaji Aminu ya cika da mutane, Æ´an adamawa sunzo, harda manyan bakinshi wanda ya gayyato masu yawa, duk wasu masu faÉ—a aji dake garin kano sun shirya tsaf domin wannan auren, momy ta gayyato Æ´an uwanta da abokan arziki suma sun cika É—akinta tsab suna gudanar da biki, haneefa kuma ta maida hankali akan waya koda yaushe suna tareda elham a waya tana bata shawara da yadda zata kula da kanta, kawayenta ta cire musu ankon dinner, batayi mamaki ba da taga noor bata cire anko ba, ita dai kawai tana raba wanda ta cire, light purple ne ita kuma zatasa fari.
kawar momy ce ta kira me kunshi har gida tazo, zanawa haneefa tayi tass akan farin hannunta, harda kafa akayi mata jan lalle, koda ya bushe ta wanke kamar ka sace haneefa ka gudu, noor tazo wucewa hannunta rike da katon roba cike da ruwa zata kaiwa momy, kawar momy tace "zo Æ´ata kema ayi miki lalle"
"a,a momy ki bari kawai banson lalle"
karɓan roban ruwan matar tayi ta bawa wata, kana ta janyo hannun noor ta zaunar da ita, nanfa aka fara yaɓa mata lalle, itama harda jaa akayi mata, murmushi tayi lokacin da taga lallen yayi mugun kyau a jikinta, bayan ta wanke ta kara kallo taga yayi kyau sosai, haneefa tana kallonta tayi murmushi ganin yadda noor tayi kyau a cikin lallen.
tun daga lokacin noor ta saki jiki aka fara shirye-shiryen biki da ita, haneefa taji daɗin haka shiyasa ma take neman shawaran komai a wajenta, bata yadda tayi mata abinda zai ɓata mata rai, haka take binta sahu da kafa.
yau take ranan alhamis gobe Jumma'a za'a É—aura auren haneefa da anwar, gidansu ba wajen sa kafa, É—akinsu haneefa cike yake da kawayensu da Æ´an uwa, noor tana zaune tasha dogon riga marar nauyi hannunta rike da waya tana kallon masu lalle, haneefa ta kalleta tayi murmushi, sau uku kenan suna haÉ—a ido haneefa tana murmushi, da hannu ta mata alaman "ya dai?"
girgiza kai tayi kana ta kashe mata ido alaman ba komai, haka har dare duk inda ta kifta saita bita da kallo, har taji jikinta yana mutuwa, tashi tayi ta koma É—akin ya faruk ta zauna, daga baya ma ta kwanta acan, koda ya dawo yaga tana kwance akan gadon bai takura ta sauka ba, katifa kawai ya janyo ya shimfiÉ—a a kasa shima yayi baccinshi.
washe gari, rana bata karya saide uwar É—iya taji kunya, yau za'a É—aura aurensu anwar, inna na hango a É—aki tasa shadda tana kuka sosai, kawarta da take gefe da sauran mutane suna bata hakuri, gaba É—aya idonta yayi jajur har kanta yana ciwo, anwar yaki yadda su haÉ—a ido dan shima kuka zata sashi, yana tareda su jameel, nas ya kira video call yanata tsokanan anwar, jameel ke maraba da baki yana basu masauki, ba karamin kyau anwar ya kara ba, bayan ya kashe wayan yaga kiran haneefa,ganin yana cikin mutane dayawa yasa bai É—aga ba, text ya tura mata "wats'up baby?"
"I miss you"
tayi mishi reply, zaiyi reply yaji an dafashi, wayan yayi cikin aljihu, abokanshi wanda suka jima basu haÉ—u ba yau ya gansu.
da karfe 2 na rana yayi shiri cikin farin shadda me kyau wanda yayi mishi kyau sosai, farin hula yasa a saman tulin gashinshi wanda yake a kwance lub,yau ya fito kamar balarabe ko ina ya gifta kamshi ne ke tashi, Abba ya aika motoci akazo har gida aka É—aukesu shida abokanshi, a wajen É—aurin aure saida anwar yayi kuka, duk inda ya gifta abokan abba ne da Æ´aÆ´ansu manya suna mika mishi hannu, gaisawa yake dasu yana sharan hawaye, koda aka É—aura Abba ya janyoshi jiki yana mishi congrats, kuka ya fashe dashi Abba ya rinka lallashinshi da kyar yayi shiru.
haneefa tasha farin lifaya an É—aura mata yayi kyau sosai, sai kyallin amarci take, kawayenta na school sukazo suna hoto, sai dariya take tana É—aga musu hannu, so take ta zame suyi waya da anwar amma mutane sun hana, noor tana sanye da farin dogon riga leshi, bata É—aura É—ankwalin me kyau ba kawai ta yafa a kanta ne, sai amsa gaisuwa take badan taso ba, koda aka sanar an É—aura aure haneefa tsaban murna har kuka tayi, noor kuma taji gabanta ya faÉ—i, haka kawai ta kasa samun nutsuwa tunda taji an É—aura auren.
da kyar ta samu ta tafi É—aki ta samu kuwa ba kowa a É—akin nasu, zama tayi akan stool tana kallon kanta ta cikin madubi, kasa É—auke ido tayi daga kallon kanta da take, a hankali taji an turo kofan, haneefa ce ta shigo domin yin waya da anwar, ganin noor tana kallon kanta ta madubi yasa ta karasa ta rungumeta ta baya, wayan ta jefar akan gado ta saita fuskanta akan nata, jujjuyawa ta fara da ita tace "my little sis me kike tunani?"
kin magana tayi ta zubawa haneefan ido ta cikin madubin, hannu haneefa tasa ta share mata hawayen da suke zuba, a hankali tace "banaso naga hawaye a wannan kyakkyawan fuskar taki, kukan me zakiyi? munafa tare a gari É—aya, sannan duk lokacin da kikayi missing nawa zakizo ki ganni"
shiru tayi tace "ba kince kinfison anwar akaina ba"
daÉ—a rungumeta tayi sosai tace "ta yaya zanso Anwar akanki? Ina sonki sosai noor, kuma nayi alkawari ranan aurenki zanyi dressing irin wanda nayi yau, harda lalle harda makeup irin wanna zanyi"
shafa fuskanta tayi "You love me?"
"i love you noory"
faruk dake bakin kofa yaji idonshi ya cika da hawaye, a hankali yasa hannu ya share kana ya tura kofa ya shiga, murmushi yayi yace "get ready for lunching"
a hankali ta karasa gabanshi kamar zatayi kuka sai kuma ta faɗa jikinshi ta fashe da kuka, noor ma tazo ta rungumeshi tana kuka, kasa rike kukanshi yayi ya rungume kannenshi shima yana kuka, gaba ɗaya yaji jikinshi a sanyaye, da kyar ya lallaɓa ya fita daga ɗakin yana sharan hawaye, noor ta juya zata tafi taji haneefa ta riko hannunta, tsayawa tayi cak.
"noor ke nakeso ki shiryani domin zuwa lunching, kin manta idan kinyi bacci ni nake canja miki kaya?"
jijjiga kai tayi, "kimin alkawarin kin daina shaye-shaye daga yau"
"na miki alkawari"
"to ki shiryani"
buɗe wardrobe tayi ta ciro fararen kayan da suke kwance suna kamshi, haneefa ta cire rigan jikinta ta ɗaura babban towel dama tayi wanka, sa mata rigan tayi kana ta fara gyara mata makeup na fuskanta, takalmi dogo me tsini tasa mata, ta durkusa ta ɗaure mata igiyan takalmin, jaka ɗan karami me masifan kyau ta bata, sannan ta fara fesa mata turare me ƙamshi, koda ta gama ta kalleta sannan ta rungumeta, ganin zata fara kuka noor ta janye jikinta tace "kije su Abba suna jiranki kowa ya shirya nima yanzu zan shirya"
giÉ—a kai tayi kana ta juya ta fita daga É—akin, bin bayanta noor tayi da kallo.
su abba da momy suka ajeta suna mata nasiha sai kuka take har suka gama, runguman momy tayi, kana ta rungume abba, Abba yace "muma zamuje wajen lunching É—in kada ki damu kinji?"
giÉ—a kai tayi, nanfa aka fitar da ita kawayenta suna gefenta sunyi bala'in yin kyau, anwar ma yana can ana shiryashi domin zuwa lunching, Jameel yaki barinshi yayi komai shi yake shiryashi da kanshi, kannen jameel da ummanshi suma sun shirya tsaf har da inna zasuje wajen lunching.
sai karfe 3 aka turo motan É—aukan amarya, motace me kyau fari kal anyi mishi ado da flower, murmushi takeyi tana bin ko ina na cikin motan da kallo.
noor dake zaune akan stool ta kira waya tace "ku saceta, ku kaita waje me kyau, inda babu kuɗa balle soro, ku bata abinci me kyau da ruwan sha me kyau, ko sauro idan ya taɓa unty haneefa ba zan bar kowa da rai a cikinku ba, sannan banaso zafi ko sanyi yayi mata yawa, sai nan da kwana uku zan kiraku ku saketa"
amsawa akayi, har zata kashe wayan sai kuma tace "ina kara warning naku ko sauro kada ya taɓa ta"
kashe wayan tayi kana taci gaba da kwalliyanta,
haneefa tana cikin mota sun fara tafiya har sun hau hanya taga motan ya fara tsayawa, a hankali tace "ya dai? meya samu motan?"
"Hajiya ban sani ba wallahi, kuma yanzu haka gidansu ango zamuje dan ya shirya"
"to ka fita ka duba matsalan motan"
fita yayi daga motan ya fara dubawa, ji tayi an buÉ—e marfin motan da karfi an nuna mata bindiga, idanu ta zaro zatayi ihu ya nunata da bindigan yace "shiru"
jujjuya ido ta fara tana neman driver taga shima an nunashi da bindiga, da hannu suka mata alama ta fito, sata sukayi a wani bakin mota glass É—in tinted ne babu me ganinsu, da gudu suka bar wajen da ita, driver yana ganin haka ya tashi a firgice ya shiga mota ya juya zuwa gida, time É—in har mutane sun fara watsewa, a waya ya kira Abba cikin kiÉ—ima yace "sun sace amarya"
a firgice Abba yace "kamar ya? su waye?"
yana kan bayani Abba yace "shigo"
shigowa yayi yama Abba bayani, momy da take shigowa hannunta rike da kwalban turare saida ya faÉ—i kasa......
*Haƙƙi na 300 ne ta account nawa 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, turo katin shaidan biya ta nan 08144818849, zan saki a group ɗin da zan riƙa posting kullum*
No comments