Recent Updates

Hakki na 11

 


🌸🌸🌸🌸🌸

    *HAƘƘI NA*

🌸🌸🌸🌸🌸



 By

_jiddah S Mapi_



*Chapter 11*



*Ku fara biya saura page biyu mu gama free pages, ₦300 ne 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, katin shaidan biya ta nan 08144818849*



              ~Bayan kwana biyu Abba ya kira anwar a waya yace "ina airport kazo ka É—aukeni"

bin wayan anwar yayi da kallo bayan Abba ya kashe, ga driver Amma meyasa yace ni zanje na É—aukoshi?

dama yana wajen flower wanda suka jara kyau suna kamshi yana bayinsu, haneefa ce ta bashi maganin da zaisa musu su kara kyau dan ta lura kamar ansa musu chemical É—in da zai kashesu ne, ya ajiye pipe yaje ya shirya cikin kananan kaya ya samu sani driver yace "bani makullin mota Alhaji yace naje na É—aukoshi"

bashi makullin yayi yace "Allah ya tsare"

karɓa yayi yaje compound ya shiga motan da yaga ana yawan fita da Abba a ciki, fita yayi a unguwan yana karewa ko ina kallo, da haka har ya isa babban airport, fitowa yayi daga motan yana neman Abba, can ya hangoshi hannunshi rike da babban bakin jaka, manyan kaya ne a jikinshi, da sauri ya karasa yace "sannu da dawowa Alhaji"

abba ya mika mishi hannu suka gaisa yace "ya gidan ya zaman bakunta koda shike ai yanzu ka saba ko?"

giɗa kai yayi yana karɓan jakan dake hannunshi suka karasa ya buɗe mishi kofan mota cikin girmamawa, Abba ya shiga shima ya zagaya ya shigo, sai sannu yake yiwa Abba, Abba ya saki jiki dashi yana janshi da hira har suka isa gida, sai a sannan Abba yace "aina ka koyi mota?"

"motan abokina nasir a wurinshi na koya"

"madalla gashi ka kware sosai"

fita sukayi bayan yayi parking, ya fito ya buÉ—e mishi marfin motan shikuma ya É—au katon bakin jakan ya rataya a bayanshi suka jera suna tafiya, jin sallaman Abba yasa momy É—agowa da sauri, kallonshi tayi tana zaro ido alaman ya mata surprise ta mike da É—an gudunta taje ta faÉ—a jikinshi, riketa yayi yana dariya anwar ya tsaya a baya yanajin nauyin ganinsu a haka, noor da haneefa suka shigo a tare da uniform na school a jikinsu da gudu noor taje ta rungume Abba tana dariya tace "Abba yaushe ka dawo?"

shafa kanta yayi "yanzu saukana"

haneefa kuma kallon anwar wanda ya kawar da kai daga kallonsu Momy tayi, da alama hakan sabon abune a wajenshi, ta kashe mishi ido tareda turo É—an karamin bakinta sannan tayi mishi kiss, da sauri ya É—auke kai dan baison Abba ya gansu, dariya tayi taje wajen Abba tace "Abba ka dawo? Ina tsarabata?"

"to haneefa Æ´ar son tsaraba sai anjima zan baki"

rungumeshi tayi tace "to Abba"

kallon anwar wanda yake tsaye yayi kafin ya cire makulli a aljihu ya mika mishi "gashi ajemin jakan a É—akina"

karɓa yayi ya wuce inda yasan ɗakin Abban yake, buɗewa yayi ya aje jakan kana ya fito ya maidawa Abba makullin yace "gashi na aje"

"yawwa anwar na gode ko?"

giɗa kai yayi sannan ya fita, momy ta bishi da kallo tana murmushi nutsuwan yaron ya birgeta, shiyasa takejin daɗin abotan da suke da faruk, gashi sun shaƙu kamar dama sun san juna, har faruk ya san su jameel da inna, kullum sai anwar ya bashi labarinsu.


Faruk ma yazo suka gaisa da Abba yayi mishi ya hanya yana wani sunnar da kai, Abba yace "meya faru naga sai sunnar da kai kake?"

shiru yayi, kana yace "ba komai Abba"

momy ta kalli Abba sannan tace "jeka faruk"

tashi yayi ya tafi ta kalli Abba tace "me yasa yake wani jin kunya?"

murmushin gefen baki Abba yayi "ba komai wani voice kawai ya turamin shine yake jin kunya"

"muji voice É—in"

"keda wa?"

marairaicewa tayi "nida kai mana"

hancinta yaja yace "ni ai naji kuma na goge"

ta san baiso taji ne kawai, sharewa tayi domin bata takura mishi akan komai.


haneefa tana murna domin tunda abba ya dawo ta san zai tsaida maganan aurenta da anwar, noor ta kula da haka, ta kudiri aniyan saiya bar gidan kafin haneefa ta É—ago maganan aure tsakaninsu, itafa ko jikokinta ba zasu auri talaka ba balle yayarta wacce suke ciki É—aya.


cikin dare Abba ya gyarawa jakan wajen zama domin kuÉ—i ne na mutane da gwala-gwalai a cike da jakan haka yasa yake bawa jakan tsaro sosai, ko momy batasan abinda yake ciki ba, har suka kwanta bacci Momy a gefenshi yana kallon jakan, can cikin dare ya tashi zaisha ruwa bai kula da inda jakan yake ba saida yasha ruwa sosai kana ya koma zai kwanta, baya ya koma yana shirin faÉ—uwa ganin babu jakan a inda ya aje, numfashi ya fara yi da karfi yana kiran sunan momy "sadiya!! sadiya?"

a hankali ta buÉ—e ido tace "meya faru?"

"ina jakata?"

tashi tayi ta murza ido tana kallonshi "jaka kuma?"

girgiza kai kawai yayi domin ya rasa bakin magana, da sauri ta sauko daga kan gadon ta rikeshi ganin yana dafe kirjinshi, cikin tashin hankali ta taimaka mishi ya kwanta kan gado yana so yayi magana ya kasa, dudduba É—akin ta fara babu jaka, hankalinta ya tashi, gashi Abba ya fara numfashi sama-sama, buÉ—e kofan É—akin tayi tana kiran "faruk?"

yah faruk dake bacci yaji sautin muryan momy tana kwala mishi kira, da sauri ya kalli agogo yaga karfe 2, baisan lokacin daya sauko ya fita ba, ganinta a rikice yaje ya riketa yana tambayan meya faru?

da kyar tace "Abbanku yana numfashi sama-sama"

har suna rige-rige wajen shiga É—akin, Abba ya gani kwance akan gado yaje da gudu yana É—agoshi yace "abba what happen to you?"

girgiza kai Abba yayi da kyar ya furta kalman "jakata"

"ina jakan naka?"

"ban gani ba umar"

dubawa faruk ya fara baiga komai ba, tare da momy sukayi niyan fita Abba yace "kada ku É—aga hankalin kowa da daren nan kuma kada abar kowa ya fita har zuwa safiya, faruk kaje ka tsaya a kofa kada kayi bacci"

jijiga kai yayi ya fita da sauri yana duba cikin gidan, baiga komai ba, zama yayi a mazaunin me gadi yana kallon ko ina na cikin gidan, momy kuma ta bawa Abba tablet nahsi yasha ya kwanta, tagumi tayi "Allah ka rufa mana asiri dukiyan mutane ba namu ba"

ta san dana Abba ne ba zai damu har haka ba.


ido biyu suka kwana babu wanda ya runtsa cikinsu uku, da Abba da faruk da kuma Momy duk ido a kumbure alaman basuyi bacci ba, saida aka idar da sallan asuba kana Abba ya daure ya zura jallabiya ruwan kasa ya fito yace akira duk Æ´an gidan, faruk ne yaje ya fara kiran kowa, noor da haneefa sai time É—in suke salla ya leka yace "idan kun idar Abba na jiranku yana kasa"

saida haneefa taji gabanta ya faɗi, itama noor tasan kiran Abba da asuba ba lafiya ba, kowa ya hallara a falo, noor da haneefa suka fito a tare noor sanye da riga da skirt sai haneefa me dogon hijabi har kasa, a hankali suka karasa suka zauna a gefen kafan momy, Abba cikin sanyi ya kalli duk waɗanda suke wajen kana ya mike ya goya hannu a baya yana bin kowa da kallo, harta faruk saida jikinshi ya bashi irin kallon da Abba yakebin kowa dashi, su mama salma jikinta har yana rawa dan bata taɓa ganin Alhaji cikin wannan yanayin ba, gyaran murya yayi kana yace "a cikinku waya ɗauki jakata?"

da mamaki kowa ya kalleshi, jin sunyi shiru ya daka musu tsawa wanda yasa anwar É—agowa ya kalli haneefa, itama da gani tana cikin tashin hankali.

kowa ya fara magana a tsorace "bani bane"

zagayasu yake yace "duk wanda ya É—auka ya gayamin cikin rufin asiri kafin nayi bincike"

shiru duka sukayi, dafe kai yayi yace "okay muje ayi checking ɗaki-ɗaki, Amma ku sani duk wanda na kama jakan nan a ɗakinshi zanyi maganinshi daga kaina ba zai kara kaunan taɓa kayan wani ba"

jijjiga kai sukayi, da hannu ya musu alama su tashi, tashi sukayi zasu fita yace "a fara da ciki"

É—akinsu noor da haneefa aka fara dubawa, saida akayi É—aÉ—É—aya da komai kana yace "muje"

fita sukayi a tare kowa da gaskiyanshi, É—akin momy akaje aka watsar da komai nan ma babu, nan akaje É—akin faruk kana sukaje na abba, duk babu ciki, sauka sukayi zuwa cikin gida, tun daga É—akin megadi harna driver danasu mama salma aka duba babu, anwar yana gaba baijin daÉ—in É“atan jakan ba, Abba ya juya zai koma ciki yace "Abba saura É—akina"

"na yadda da kai anwar fiye da yadda na yadda na iyalaina"

kanshi kasa yace "na gode Abba amma da an duba dai"

momy tace "muje mugani dai saboda gudun zargi"

a tare suka shiga ɗakin aka fara dubawa babu komai, ajiyan zuciya ya sauke har zasu fita noor ta kalli katifan taga ya ɗan ɗago, dawowa ɗakin tayi ta ɗaga gadon nan saiga jaka kwance a kasan katifa a buɗe gold da kuɗaɗe a shimfiɗe ciki, zaro ido momy tayi tareda faruk, haneefa kuma hannu tasa a baki ta toshe tana kallon anwar, zufa ya fara ƙeto mishi ganin yadda kowa yake binshi da kallo, kasa ƙasa sauran masu aikin suka fara gulma a wajen, kallon tuhuma Abba yayi mishi kana yace "Anwar me zan gani?"

girgiza kai kawai yayi, baida bakin magana manyan idanunshi gaba É—aya a waje alaman ya tsorata sosai, abba yace "meyasa kayi haka?"

noor sai girgiza kai take tace "ashe muna tareda É“arawo bamu sani ba"

bai É—ago ba balle ta samu ya kalleta, haneefa ta karaso gabanshi ya sunkuyar da kai, tace "ka buÉ—e baki ka gaya musu kai ba É“arawo bane, ba kai kayi sata ba, na san halinka nasan ba zakayi haka ba"

ganin yayi shiru ta manta dasu Abba a wajen, matsowa tayi sosai tasa hannu ta ɗago haɓanshi, ganin ya kasa ɗaga ido ya kalleta tasa hannu bibbiyu ta rike fuskanshi ta matso da nata cikin kasa da murya tace "kayi magana my Anwar"

a firgice momy ta É—ago tace "ke haneefa baki da hankali ne? stay away from him...."

Abba ne ya É—aga mata hannu, tayi shiru yace "haneefa me nake gani? me nake ji? matsa a wurin"

kin matsawa tayi tace "Abba bashi yayi satan ba wallahi na san ba zai iya ba"

"ta yaya akayi kika san ba zai iya ba?"

"Abba na zauna dashi tun kafin yazo gidannan wlh ba zai iya ba"

duk mutanen wajen sai rarraba ido suke, kowa yana mamakin abinda yake faruwa, har yanzu taki cire hannunta daga fuskanshi, sani driver yace "a gafarceni Alhaji amma dolene zanyi magana, anwar ba zai iya sata ba, inada tabbacin bashi yayi ba"

wani kallo noor tayi mishi wanda yasa ya dukar da kai, Abba yace "aina kika sanshi?"

"a wajen saida rakenshi"

shiru yayi kana yayi gyaran murya yace "faruk É—auki jakan ka buÉ—e mugani"

faruk da jikinshi yayi sanyi ya ɗauki jakan ya buɗe, Abba ya kalli komai yaga ba abinda aka taɓa, kallon anwar yayi wanda har yanzu baiyi magana ba yace "na sallameka daga gidannan kaje ka nemi wani aikin"

jikinsu ya mutu, noor ce kaÉ—ai take murmushi kamar tayi tsalle haka takeji, haneefa kuma ta fara sharan hawaye tana kallonshi, giÉ—a kai yayi sai a lokacin yayi magana yace "na gode Alhaji, taimakon da kayimin kaÉ—ai ya isa nayi maka godiya, ko dan ganin mahaifin jameel yana tafiya da kanshi ba sai an rikeshi ba"

durkusawa yayi ya rike ƙafan Abba yace "na gode Allah ya saka da Alkhairi"

faruk yana tsaye hannunshi har rawa yake baiso haka ya faru da anwar ba gashi baida hujjan kareshi domin a ɗakinshi akaga jakan, fitowa Abba yayi daga ɗakin tareda mutanen wajen, a waje suka tsaya suna jiran ya tattara komai ya fito, noor ta kasa ɓoye murmushi akan face nata, haneefa kuma ta rike Momy tana kuka, Abba yana kallonta baiyi magana ba, anwar ya samu babban jaka ya zuba kayanshi a ciki yasa duk wani abu na buƙata aciki, dama rigan jikinshi me kyau ne domin yadi ne wanda yasha ɗinki me kyau, jakan yasa a bayanshi kana ya fito yasa takalmi, hannu ya ɗaga musu yana murmushi alaman ya tafi, cikin nutsuwa yake tafiya noor ta ɗaga hannu sama ba tareda ta bari kowa ya ganta ba tace "Allah na gode ma, Allah na gode ma ka rabamu da talauci da safiyan nan"

haneefa ta juya baya har ya isa bakin get, zai buÉ—e kofa Abba yace "anwar?"

tsayawa yayi ba tareda ya juyo ba, a hankali Abba yace "zo mana"

juyowa yayi yazo har inda yake yace "gani"

shafa kanshi yayi kana yasa hannu ya É—agoshi sannan ya rungumeshi, hawaye yaji yanabin idanunshi, sai yau yakejin É—umin uba a jikinshi, bai taÉ“a samun runguma daga uba ba sai yau, ko Abba bai yafe mishi ba yaji daÉ—i a haka, bayanshi Abba ya bubbuga a hankali saida sukayi 5mins a haka sannan yayi niyan zameshi daga jikinshi, rike abba yayi sosai yaki sakinshi, jikin Abba ne yayi sanyi jin yadda ya rikeshi, noor kaman zata faÉ—i saida ta rike ya faruk, me haka? 

da kyar Abba ya samu ya sakeshi, ya zuba mishi ido yace "wani ubane zai yadda É—anshi ya bar gidanshi ba tareda ya aikata wani laifi ba?"

gaba É—aya wajen sukayi shiru, yasa hannu a karo na biyu ya shafa kan anwar yace "na san ko allura ba zaka iya É—auka ba balle waÉ—annan makudan kuÉ—in, sannan ai kaine ka aje jakan da kanka a É—aki ta yaya zaka É—auka? kuma idan ka É—auka meyasa zaka zauna? ai guduwa zakayi, nayi maka gwaji kusan sau uku ban sameka da wani laifi ba, saboda haka na baka manager na companyn kera gwala-gwalai nawa"

É—ago ido yayi ya kalli Abba, murmushi yayi mishi "yeah kai mutum ne me hankali da nutsuwa"

kallon haneefa yayi wacce take dariya tana share hawaye yace "wani ubane ba zai so É—anshi nutsatse ya auri Æ´arshi ba?"

haneefa ta kalli Abba hawaye yana bin fuskanta, ya É—aga mata hannu, yaga soyayyan anwar a fuskanta, ta matso yasa hannu ya janyota jikinshi ya shafa kanta yace "kina sonshi?"

giÉ—a kai tayi, yasa hannu ya rungume anwar ta É—ayan É“arin yace "kana sonta?"

kai ya giÉ—a hawaye sun bin kuncinshi, wani farin ciki ne ya mamaye Abba yace, "kun shirya auren juna?"

shiru sukayi yasan kunya sukeji, yace "ba komai zaka kaini wajen innarka muyi magana"

jijjiga kai yayi, haneefa ta É—ago tana cije baki ta kalleshi, É—auke kai yayi dan baison Abba ya gansu, mama salma tayi guÉ—a tana murna tace "Allah ya saka maka da alkhairi Alhaji kayi abinda duk uba ya dace yayi"

momy ta kasa magana ganin abin take kamar almara, sai bin kowa take da kallo, ya faruk yana murmushi yace "congratulations Anwar"

Abba yace "kowa ya watse kuma zanyi bincike akan duk wani wanda yake da sa hannu a wannan satan"

noor ce farkon tafiya kamar zata tashi sama, bata tsaya ko ina ba sai É—aki, drower ta buÉ—e ta ciro jakan school nata, wasu kwalabe ta ciro ta buÉ—e ta fara kwankwaÉ—a babu kakkauta, saida ta shanye duka ta watsar da jakan da kwalaben a gefe, kwanciya tayi a kasa kan tiles ta fara jujjuya ido, "aure? aure fa?"

da haka har bacci ya É—auketa cike da maye.


momy tana ganin Abba ya sake hannun haneefa ta riketa ta janyota suka fara tafiya, kallon momy tayi tace "momy my hand"

bata kalleta ba taci gaba da janta, tirjewa haneefa take tana cewa "momy please"

saida ta kaita É—aki ta wurgata kafin ta rufe kofan ta juyo tana kallonta, kanta kasa, momy tace "É—ago ki kalleni?"

a hankali ta É—ago ta kalleta kana ta maida kanta kasa, cikin É“acin rai ta fara magana "kin sanshi ne? kinsan daga ina ya fito? kinsan danginshi? ko dan ya nuna muku shi na Allah ne saiya zama shiÉ—in baida matsala? keda nake gani kinada wayo ashe noor ma ta fiki sanin ya kamata, ina ke ina me bayin flower na gidan babanki? kuma ma me saida rake? haba haneefa"

kuka ta fashe dashi saida momy ta gama tace "momy i love him, wallahi jinshi nake har cikin raina, ki taimaka ki goyamin baya na aureshi kada na mutu dan Allah"

"kin haukace ne?"

matsowa tayi wajenta ta durkusa kasa tasa hannu a kafanta ta rike tana kuka tace "momy na san kinsan zafin so, kinsan miye soyayya, momy nasan kinason Abba ganin yadda kike nuna mishi soyayya a idon kowa, nima inason anwar ki barni kada kice ba zan aureshi ba dan Allah momy"

hannu tasa ta É—ago ta, share mata hawayen tayi kana ta janyota jikinta tace "it's okay my dear ki nutsu kiyi tinani sosai, idan ya kwanta miki a rai kina ganin zaki iya rayuwa cikin babu, keda Æ´aÆ´an da zaki haifa, ba komai saiki aureshi, amma kiyi tinani me kyau akwai future kisan me kikeyi kinji my dear?"

"to momy na gode"

zaunar da ita tayi a bakin gado kafin ta juya ta fita, wayanta ta É—aga ta kira layin wata kawarta, cikin tashin hankali tace "haneefa ta tonamin asiri wai ke saida rake takeso rukayya"

"baki mata maganan Ahmad bane?"

"so nake wai saita kammala secondary sai nayi mata zancen ga kuma banzan zancen data fito dashi har Abbansu ya yadda"

salati matan tayi "kibani shawara kaina zai fashe"

"ki nutsu kiyi addu'a Allah zai kawo mafita"

jijjiga kai momy tayi kafin ta kashen wayan, dafe kai tayi kamar zatayi kuka.


faruk ya karɓi jakan hannun anwar fuska fal fara'a ya shiga mishi dashi ɗakin, ganin ya tsaya a bakin kofa ya riko hannunshi suka shiga ciki, zama sukayi faruk yace "ashe kanada budurwa ka ɓoyemin"

"banda budurwa"

"oh I see shiyasa naga kana bin kanwata da kallon love harda lumshe ido"

shiru ya mishi dan yasan halin faruk, murmushi faruk yayi "naji daÉ—i da kaine zaka auri haneefa, dama a raina inason hakan sai gashi Allah ya haÉ—a, haneefa tanada hakuri kamar yadda kaima kake da hakuri, bakason hayaniya itama bataso, gata da sanin ya kamata kamar kai, kuma bata iya son mutum ba har cikin zuciya take sa mutum kamar zata haÉ—eshi, kada kayi amfani da wannan daman ka cutar da ita duk da nasan halinka, ka riketa amana ka sota kamar yadda naga tana sonka"

"insha Allah ba zaka sameni da kuskure ba, amma ina ganin haneefa tamin nisa, tafi karfina bamuda komai, daga ni sai innata, kuma ni nake nemowa na bata"

"idan soyayya ya shiga ba zancen kuÉ—i ko wani abin duniya, haka haneefa ta ganka tace tana so, kuma ai Abba ya baka manager ko?"

jijiga kai yayi "na gode faruk kunyi min halacci, Allah ya saka muku da alkhairi"

"Ameen anwar"


bacci tayi sosai ba wanda ya kula domin Abba ya fita shi kuma ya faruk yana tareda anwar suna hira, sai kusan mangrib ta tashi tana layi ta faɗa toilet, wurgi tayi da kayan jikinta ta kunna shower ta tsaya a karkashin tana ji ruwa yana ratsa duk ilahirin jikinta, saida ta samu ta ɗan nutsu kana ta janyo wani karamin towel na tsane gashin kai ta ɗaura a jikinta, rabin kirjinta da rabin cinyoyinta a waje, haka ta fito kanta yana tsiyayan ruwa, zama tayi akan stool ta zubawa kanta ido ta madubi, idan haneefa ta aureshi to ta buɗewa talakawa hanyan zuwa neman aure a gidannan kenan, shine abinda take gudu, turo kofan tayi bakinta ɗauke da sallama, ganinta zaune ta zubawa mirror ido ta karaso inda take a hankali tasa hannu akan gashinta da yake tsiyayan ruwa, baya ta maidasu ta zaro towel akan kofa ta fara tsane mata, saida ta gama ta ɗau drayer ta jona kana ta fara bushar mata da gashin, bayan ya bushe ta ɗau mai ta shafa mata akan gashin sannan ta taje ta kame mata waje ɗaya, lotion ta ɗauka ta shafa mata daga fuska har kafanta da hannunta, saida ta gama taje sef ta ciro wani dogon riga marar nauyi tazo gabanta, hannunta ta kamo tasa mata rigan kafin ta mikar da ita, saida rigan ya sauka kasa kafin towel ɗinma ya sauka, duk abinda takeyi noor tana kallonta ta cikin madubi, tana ganin yadda take murmushi, fuskan noor kamar bata taɓa dariya ba, ganin haka yasa haneefa zaunar da ita kan stool ɗin sannan ta rungumeta, kiss tayi mata a kumatu tana rungume da ita tace "noory ta? fuskanki a kumbure kinyi bacci sosai ko?"

bata bata amsa tana kallonta, murmushi tayi kana ta saketa tace "bari na kawo miki abinci"

fita tayi babu jimawa ta dawo da cake akan plate, tazo ta zauna akan gado tana facing nata, yankawa tayi ta kai bakinta, a hankali ta buɗe ta karɓa, saida tayi rabin cake ɗin kafin ta ɗauke kai, haneefa tasan fushin da take shiyasa take lallaɓata, ajiye plate ɗin tayi tace "come here"

zaunar da ita tayi a gefe gadon tayi murmushi tace "my noory why silent?"

kallonta kawai take, ganin batayi magana ba tace "chocolate?"

girgiza kai tayi, "okay ice cream?"

still ta kuma girgiza kai, hannu ta É—aga "what do you want?"

"ki rabu dashi"

dariya tayi, hannunta ta É—ago ta É—aura akan kirjinta, ji tayi kirjin yana bugawa da karfi, kallon ta tayi tace "kinji yadda zuciyata take bugawa, to kowani bugun sunanshi yake bugawa noor, idan kikace na rabuda anwar to ba karamin cutar dani zakiyi ba"

a hankali ta kwanta tareda É—aura kanta akan kafarta tace "noory anwar shine abincin zuciyata daki rabani dashi gara ki kasheni, ina sonshi sosai ji nake kamar na haÉ—eshi, ba dan kiss ko romance is prohibited a musulunci ba da zanso nayi kissing na soft and warm lips nashi, I will like to kiss him and romance him badly noory"

noor ta zama kamar statu da ido kawai takebin haneefa wacce ta janyo pillow ta rungume sosai tana tana lumshe ido tareda tsotsan jajayen lips nata, bata taɓa ganinta a wannan yanayin ba tunda suka taso saida ta haɗu da wannan mayen, wanda take da tabbacin asiri yayi mata, hannu tasa ta ɗan ture kanta daga kafarta, ba tareda tayi magana ba ta tashi ta bar ɗakin, wajen abinci taje dan ba karamin yunwa takeji ba, saida ta cika cikinta da abinci tasa hannu a fuska ta fara tunanin abinyi, wannan soyayyan da haneefa take yiwa wannan me raken yafi karfin tunaninta, ɗakin momy taje domin jin ta bakinta, ta sameta tana salla, zama tayi a bakin gado ta jira momy ta idar, jiki a mace tace "momy wannan yaron asiri ya yiwa unty haneefa"

jijjiga kai momy tayi "ba asiri bane, tsantsan soyayya ne, haka nake yiwa Abbanku"

girgiza kai tayi "momy ki yadda asiri yayi mata baki ganin yana kama da mutanen da suka fito daga daji? idan ba haka ba ina relatives nashi? kadafa ya aureta ya gudu da ita daji Momy"

ran momy ya tsinke ba dai gaskiyan noor ba, É—ago kanta tayi idonta da alaman tsoro tace "mu dage da Addu'a idan ba alkhairi bane Allah ya watsar da zancen auren"

giÉ—a kai tayi kana ta fita daga É—akin, bata tsaya ko ina ba sai garden, duk sanyin da akeyi bai hana ta zauna a wajen ruwa tasa kafanta ciki ba, saida sanyin ya fara shiga jikinta ta mike ta fita daga wajen, hangoshi tayi zaune yasa rigan sanyi yayi shiru da alama tunani yake.


haneefa tana ganin noor ta fita ta mike ta shiga toilet tayi alwala, saida ta idar da salla tasa wani material me tsantsi ta yafa mayafi kana ta juya ta fita fuskanta ɗauke da murmushi, noor tana ganinshi taje bankin dem ta ɗau wani bokiti na ruwa, saida ta cika da ruwa kafin ta fara takowa zuwa gabanshi, bai kula ba yana can yana tunanin inna yaji saukan ruwa akanshi ruwa me sanyi sosai, jagab ya jiƙe, a hankali ya ɗago yana kallon wanda ya mishi wannan aika aikan, ido huɗu sukayi da ita tana farfar da ido, tashi yayi cikin zafin rai ya ɗaga hannu zai kai mata mari yaji an rike hannun, ɗagowa yayi yana kallon wacce ta rike mishi hannu yaga haneefa ce fuskanta ɗauke da murmushi me sanyaya zuciyan masoyi, girgiza mishi kai tayi ta saukar da hannun a hankali, bokitin dake gefe wanda ruwa ya rage rabi a ciki ta ɗaga ta matso kusa dashi har tana jiyo sautin numfashinshi, ruwan ta watsa musu a tare, sanyi taji sosai shima yana jin sanyi ya daure yana kallonta, hannu tasa ta kasan rigan sanyin dake jikinshi a hankali ta zame rigan bayan ta janye zip ɗin, ruwa ya jiƙasu har ta fara rawan sanyi, tana cire mishi rigan ta faɗa jikinshi ta rikeshi da karfi, fuskanta tasa akan sajenshi wanda yake jike da ruwa ta fara goga mishi lallausan fuskanta akan sajenshi wanda yake sheƙi yana kara mishi kyau, a hankali ta kai bakinta zuwa saitin kunnenshi, murya can kasa tace "sorry"

ji yayi tsikan jikinshi ya fara tashi, baisan time ɗin da yasa hannu yana shafa fuskanta ba, noor kanta ya kusa fashewa, ji take kamar ta ɗaura hannu aka ta rabza ihu, ganin abinda sukeyi a gabanta ta runtse ido ta juya baya, tafiya ta fara tana ji kaman tayi ihu, haneefa tana ganin ta tafi ta janye jikinta daga nashi, rigan sanyin tasa ta tsane ruwan dake zuba daga jikinshi, ɗakinshi taje ta ɗauko towel tazo, lulluɓashi tayi tace "ka koma ɗaki kada sanyi ya shiga jikinka"

giɗa kai yayi yana kallonta, bai taɓa samun soyayya kamar yadda yake samu a wajen haneefa ba, bata damu da asali da kuma kuɗi ba, soyayya kawai take nuna mishi ido rufe, yana rokon Allah yasa kada ya zalinceta a rayuwarsu na nan gaba, zaiyi iya bakin kokari domin sata farin ciki, saiya nuna mata babu wata mace a zuciyarshi sai ita, haneefa zata zamo autar mata a wajenshi, hannu tasa tayi mishi tafi, kashe mishi ido ɗaya tayi kana tace "kallon fa?"

murmushi kawai yayi mata, ta juya tace "good night sai munyi waya"

har tayi nisa yace "i love you my haneefa"

murmushi tayi ta juyo ta turo bakinta irin yadda yara sukeyi, sannan ta kashe mishi ido tace "i love you too my Anwar"

blowing na kiss tayi mishi yasa hannu ya cafe tareda mannawa a kirjinshi ya lumshe ido, juyawa tayi da gudu ta bar wajen harda ɗan tsalle kamar wata karaman yarinya, har saida ta ɓace ya daina kallonta, a hankali ya juya zai koma ɗaki yaga faruk rike da waist yana kallonshi, dakewa yayi zai raɓa ta gefe ya wuce faruk ya tare ɗayan hanyan, shareshi yayi zai wuce ya kuma tare hanya.

"wai me nayi maka?"

"irin wannan soyayyan ko ni da baby bamayi"

"to Ina ruwanka?"

"ga ruwana kun zubar"

raɓashi yayi ta gefe ya wuce, faruk yana tsokananshi har ya shiga ɗaki, ba dan haneefa ba da baisan abinda zai yiwa noor ba, wallahi ji yake kaman ya gwada mata raahin hankali na lokaci ɗaya, yarinya sam batada kunya batasan ya kamata ba, ga shaye-shaye har idonta ya nuna gashi bata ganin girman mutum ko kaɗan?"

yana sa riga yana wannan tunanin, saida ya canja kaya ya kwanta yana tuna yadda ta watsa mishi ruwa babu kunya sam,

sai kuma yaji wani irin shauƙi lokacin daya tuna yadda haneefa ta rungumeshi, wannan moment ɗin ba zai taɓa a gareshi ba...



*Haƙƙi na 300 ne ta account nawa 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, saiki turo katin shaidan biya ta nan 08144818849, ki biyani haƙƙi na ki karanta haƙƙi na*

No comments