Recent Updates

Hakki na 10

 


🌸🌸🌸🌸🌸

    *HAƘƘI NA*

🌸🌸🌸🌸🌸



 By

_jiddah S Mapi_



*Chapter 10*



*Littafin haƙƙi na 300 ne kacal ta account nawa 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, turo katin shaidan biya ta nan 08144818849, ta haka ne zan saki a group nawa wanda zan riƙa posting kullum*



              ~Tana gama mishi rashin mutuncin ta juya ta tafi, momy dasu Abba harda su haneefa da yah faruk suna falo da alama shawara suke, taji momy tace "shirya muje Shoprite"

kallon haneefa tayi wacce take murmushi tace "bana jin daɗi momy kuje kawai"

"to Allah ya baki lafiya jeki kwanta ki huta ko?"

giɗa kai tayi, ɗaki taje ta faɗa gado tana jin kanta yana ciwo, kamar da wasa tayi karya da rashin lafiya gashi yanzu tana jin kanta yana ciwo da gaske, haneefa ce ta turo kofa ta shigo, kallonta tayi "sannu sis"

giɗa kai kawai tayi, haneefa ta shiga toilet tayi wanka, bayan ta fito ta shirya cikin leshi blue black ɗinkin riga da skirt, ta yafa mayafi fari da farin takalmi, tayi kyau sosai, wayanta ta canja cover zuwa fari ta kalli noor tace "me zan siya miki?"

"babu"

ta janyo blanket ta rufa har kanta dan batason surutu, zuwa tayi ta yaye blanket ɗin tayi mata peck a goshi, rufe ido noor tayi har ta maida mata blanket ɗin ta juya ta tafi, tare da momy wacce tasha atamfa ɗinkin buba da mayafi babba, tayi kyau sosai, ya faruk shi zai kaisu domin Abba zaiyi tafiya, tare suka fita suna tambayan ya jikin noor, da sauki ta amsa, suka fita a tare driver ya fito musu da mota suka shiga faruk ya karɓi key, tafiya sukayi, Abba da yake ciki ya tashi yaje ya duba noor tareda yimata ya jiki? tace lafiya Abba da sauki, sallama yayi mata da niyan sai bayan kwana uku zai dawo, kamar tayi kuka haka takeji domin batason Abba yayi nesa da ita, saida ya shirya yazo ya bata kuɗi dayawa yace ta aje musu itada Haneefa na zuwa school, godiya tayi ya fita saida ta bishi a baya ta rakashi har wajen mota tana ɗaga mishi hannu, ɗaki ta koma bayan ya tafi ta kwanta tana kallon saman ɗakin.


zazzaɓi ta rinƙa ji yana damunta har ta samu tayi bacci da kyar, sai kusan karfe 3 na yamma ta tashi tana murza ido, da mamaki taga su momy basu dawo ba, waya ta ɗaga zata kira haneefa sai kuma ta aje tasan sun ratse wani wajen ne, a hankali ta sauka daga gadon tana jin jikinta weak, cire kayan jikinta tayi kana ta zaro babban towel pink ta ɗaura a kirji, ribbon ɗin dake kanta ta cire nan take gashinta suka barbazo har gadon bayanta, tanada niyan wanke kanta idan tayi wanka, shiga toilet tayi tana murza ido, a hankali ta karasa inda zata zauna domin rage cikinta da takeji ya mata nauyi sakamakon shawarma da tayita ɗurawa cikinta jiya, ta buɗe kenan zata zauna ta hango wani katon snake ya zuro kai yana kallonta, wani irin tsalle tayi ta kwala ihu "snake!!! snake!!! help please help"

shine abinda take iya furtawa gashi ta rufe kofan ta gagara buɗewa.


tsayawa yayi daga ɗaukan takaddan da Abba ya bashi sako ya ɗauka yaba isa ya kai musu a hanya, shi kaɗai Abba ya yadda dashi har yake shiga ɗakinshi, ihu yakeji daga ɗakin, ɗaukan takaddan yayi ya mikawa isa, zai fita yaji ana buga kofan ana cewa "help"

dawowa yayi yana bin inda yakejin ihun da kallo, daurewa yayi ya fara takawa izuwa ɗakin da yaji ihun yana fitowa, noor harta gaji da tsalle kamar zata sume haka take zare ido tana ihu, addu'a yayi a ranshi kafin ya murɗa handle na ɗakin ya shiga, kallon ɗakin yayi yadda yake a kimtse a gyare yasan wannan shine ɗakinsu haneefa, bubbuga kofan toilet take muryanta har ya fara dishewa tace "maciji ku taimaka"

da gudu ya karasa wajen ya fara buga kofan, ganin ba zai buɗu ba ya fara bugawa da karfin gaske, jin ana buga kofan taji ranta ya fara sanyi, muryanta yana rawa tace "please a buɗeni makulli akan gado"

da gudu yaje kan gadon ya fara duba makullin, cikin Sa'a ya samu, ya dawo ya buɗe kofan toilet ɗin kana ya shiga yana kallonta, da wani irin karfi ta rungumeshi, janye jikinshi ya fara ta ƙankameshi sosai dan ta mugun tsorata, ganin taki sakinshi yace "sakeni na duba"

kin sakinshi tayi tana sauke ajiyan zuciya tace "no please karka tafi, zai kasheni"

runtse ido yayi jin yadda take ƙankameshi kamar zata shiga jikinshi, da kyar ya cireta daga jikinshi yaje bakin toilet ɗin yana dubawa, ganin macijin yasa yaje ya ɗau sanda yazo yana fito dashi, ta rakuɓe gefe ta kankame jikinta manyan idanunta a waje, kashe macijin yayi kana yasa akan sandan ya zai fita dashi, komawa bayanshi tayi ta rikeshi tana ihu, "ya subhanallah" ya furta a kasan makoshi jin yadda ta kuma rikeshi tama manta towel ne a jikinta wanda ya fara zamewa har saman kirjinta ya bayyana, kin sakinshi tayi har ya fitar da macijin, hannu yasa yana niyan cireta daga jikinshi yaji bata motsi, juyo da ita yayi yana kallonta, ta lumshe ido alaman ta suma, ɗagata yayi sama ya kaita ɗakin akan gado ya kwantar da ita kana yaje ya ɗibo ruwa yazo yana yayyafa mata a fuska, bata buɗe ido ba sai ajiyan zuciya data sauke me nauyin gaske, kara sa mata ruwan yayi a fuska nan ta buɗe ido tana ganinshi tasa hannu akan riganshi ta rikeshi sosai tana janyoshi jikinta a tsorace tace "ya cijeni maciji"

turo kofan haneefa tayi hannunta rike da fan ice wanda tasan noor tana matuƙar so, tayi mata surprise domin taga tana fushi da ita shiyasa ta siya mata har guda biyu a shoprite, fuska ɗauke da murmushi tace "noory have your favorite ice..."

kasa karasa maganan tayi lokacin da taga noor tana janyo anwar jikinta, roban icecream ɗin ya faɗi kasa da sauri taja da baya tana zaro ido, anwar jin karan faɗuwan abu ya kara ture noor yana kallon inda yaji karan, ganin haneefa tana kallonsu ya janye jiki da kyar ya sauka yana kallonta, nufota ya fara ta fara ja da baya tana mishi kallon tuhuma, noor ta mike taje wajen haneefa da gudu ta rungumeta tana ihu tace "snake"

hannu haneefa tasa ta zameta daga jikinta kana ta juya zata fita anwar yace "haneefa?"

bata juyo ba bakuma ta amsa ba, jikinta har rawa yake domin bataji daɗin yanayin data gansu ba, noor ta koma gado ta janyo pillow da kyar ta runtse ido bacci ya ɗauketa, juyawa yayi ya fita daga ɗakin jikinshi a sanyaye, yayi sa'a ba kowa a falo ya dudduba ko zaiga haneefa bai ganta ba, fita yayi ya wuce dakinshi, zama yayi a bakin gado ya dafe kanshi, me haneefa tayi zato? yaga rashin jin daɗi kuru-kuru a fuskanta, da ya sani da bai shiga ɗakin bama, to ai rai yaje ceto da baije ba baisan yadda noor ɗin zatayi da wannan katon macijin ba, karamin wayan da haneefa ta bashi shi yayi kara ya ɗaga yana kallon me kiran, jameel ne, "Hello"

"ga inna"

bawa inna wayan yayi suka gaisa yana tambayanta ya gida, kuka ta fashe mishi fashi ita dole sai tazo taga inda yake, da kyar ya lallasheta har tayi shiru yace gobe zai zo, ta amsa da to kana sukayi sallama, jameel yana karɓa yace "meyasa ka haɗani da inna kasan kuka baya mata wuya"

dariya jameel yayi "to ba gashi ta daina kukan ba kuma kun gaisa?"

hira sukayi yana tambayan ya jikin Abba, jameel ya amsa da sauki Abba har ya fara fita yanzu, daɗi sosai anwar yaji jin ance har Abba ya fara fita.


haneefa tana fita ta wuce ɗakin ya faruk domin ta san yana ɓangaren momy, anan ne kaɗai zata samu kaɗaici bataso taji magana daga bakin kowa har zuwa wani ɗan lokaci, tana shiga ta tura kofan ta rufe, zama tayi a kasan gado ta ɗaura akanta akan gadon tareda yin pillow da hannayenta, lumshe ido tayi, a hankali hawaye ya fara ziraro mata, idan ta rufe ido yanayin data gansu a ciki shi yake yawo a idonta, "kishi kike da noor?"

shine tambayan da tayiwa kanta, sai kuma ta kara fara sabon kuka harga Allah taji zafin ganinsu haka, saida tayi kuka taji ranta ya fara sanyi, hawaye akan fuskanta ta fara bacci a inda take ba tareda ta gyara kwanciya ba.


yah faruk ya shigo ɗakin domin canja kaya zuwa na shan iska, haneefa ya gani fuska ɗauke da busashen hawaye tana bacci, bai taɓa ganinta cikin wannan yanayin ba, a hankali ya karaso wajenta yasa hannu yana dafe goshinta ya zaci zazzaɓi ne, sai kuma yaji ba zafi, kallonta ya kumayi yaga ta taƙure waje ɗaya tana bacci da alama batasan lokacin da baccin ya saceta ba, hannu yasa ya ɗagata ya kwantar da ita akan gadon, meya sameta? tambayan da yake yiwa kanshi kenan, a duniya ba abinda ya tsana kamar yaga kannenshi cikin damuwa, musamman haneefa wacce takesa hakuri da kawaici, canja kaya yayi kana ya fita daga ɗakin yaje ɗakinsu dan duba noor, may be faɗa sukayi, yana shiga yaga noor tana bacci, fita yayi yaje ɗakin anwar domin yin hira, anwar yana kwance yana tuna abinda ya faru yaji sallaman faruk, amsawa yayi tareda tashi ya zauna, shigowa faruk yayi ya zauna yana kallonshi yace "ya dai? kamar ba lafiya"

girgiza kai yayi "lafiya kalau, ina ka shiga yau?"

"munje shoprite dasu momy kuma kasan mata da ratse ratse saida na kaita gidan frends nata, murmushi anwar yayi "shiyasa naji gidan shiru ai"

hira suka fara kamar dama sun san juna, yadda kasan abokai wanda suka jima suna abota haka suke hira harma da faɗan sirrin juna domin Faruk ya yadda da anwar sosai, shima anwar ya fara sabawa da faruk kuma yaji daɗin rashin nuna ƙyama da yayi mishi, ko kaɗan baya nuna bambanci tsakaninsu na cewar shi ɗan masu kuɗi ne, hakan yasa ya saki jiki dashi sosai.


haneefa tayi bacci sosai kafin ta tashi tanajin kiraye kirayen sallan mangrib, sauka tayi daga gadon tsje tayi alwala tazo ta gyara mayafin dake jikinta ta shimfiɗa sallaya ta tada salla, bayan ta idar tayi addu'a kana ta ninke sallayan ta fito daga ɗakin, bata shiga ɗakinsu ba kawai ta wuce dining ta zauna tayi tagumi tana kallon manyan warmers ɗin dake kan table ɗin, mami ce ta fara fitowa "haneefa yau kece a wurin dinner da wuri haka?"

giɗa kai tayi, mami ta zauna a gefenta, faruk wanda sukaje salla tareda anwar yayi inviting nashi zuwa dinner, dama yanason ganin haneefa hakan yasa ya amince da wuri, sallama yayi ya sanarwa momy shida anwar zasu shigo, momy tayi murmushi tace "ba damuwa shima ai ɗa ne ya shigo suci abinci tare, haneefa tana jinsu bata ko ɗago kai ba ta fara serving kanta, abinci mara nauyi tasa kana ta fara ci tana sauri ta gama kafin su shigo, cikin rashin sa'a taji muryanshi yana sallama, idonta akan plate na abincinta bata amsa ba kuma bata ɗago ba, "welcome anwar"

durkusawa yayi ya gaida momy, tayi mishi nuni da wajen zama tace "have a seat"

tashi yayi ya zauna cikin nutsuwa, gefen haneefa ne kujera ɗaya ne tsakaninsu, yana satan kallonta yaga ko kallonshi batayi, noor wacce ta gama rungume pillow tana jin daɗi a ranta ta mike daga kan gadon ta kwance towel ɗin tasa wani riga dogo ya kama jikinta sosai, still black color ne dan tana matukar son color black musamman na kaya dan ba karamin karɓanta yake ba, hannun rigan ne kawai a buɗe da faɗi sosai, amma jikin fited ne ya fito da shape nata sosai, hulan net tasa a kanta kana ta fito tana kallon wayanta, ganin mangrib ya wuce ta shafa cikinta, jin ba komai a ciki ta turo baki ta fara tafiya zuwa dining, ƙamshin turarenta yasa momy ɗagowa ganin noor ce ta sakar mata murmushi tace "noory ya jikin?"

"da sauki"

ta amsa tana kallon anwar wanda ya zubawa haneefa ido da alama akwai magana a bakinshi amma haneefa taki sakin fuska, murmushi tayi sannan ta karasa ta zauna a kujeran da yake tsakaninsu, fararen kafafunta ta aje a saitin nashi ta ɗau plate tana zuba jallof na taliya wanda yake kamshi sosai, kallon ya faruk tayi tace "good evening ya faruk"

"how are you feeling now?"

"much better"

kallon anwar tayi, a duk lokacin data kalleshi sai taji kamar ta shaƙeshi ya mutu, abinda ya bata mamaki shine yadda yazo ya zauna cikinsu harma wai zaici abinci, wama ya bashi wannan daman?

murmushin rainin hankali tayi mishi kana tace "ina wuni malam anwar"

yasan da gangan tayi mishi wannan gaisuwan, ɗauke kai yayi yana zuba ruwa a cup, tunda yazo ya gagara cin komai sai ruwa da yake ɗurawa cikinshi, yace "lafiya"

kallon haneefa tayi wacce take jujjuya cokali cikin abinci ta kasa yin koda loma ɗaya ne, tace "unty haneefa good evening"

"evening how you?"

"am good"

tashi tayi ta rungumi momy cikin shawagaɓa tace "momy me kika kawomin daga shoprite?"

"ice cream muka kawo miki ba haneefa ta kai miki ba?"

girgiza kai tayi "a,a ni nata kawomin komai ba"

kallon haneefa mami tayi "where is the ice cream?"

sai a time ɗin ta buɗe baki tayi magana "momy yana ɗaki naje tana bacci that's why na aje a saman drower am sorry yayi melting"

jijiga kai momy tayi, noor ta koma ta zauna akan kujeran data tashi, kafanta ta kai wajen na anwar ta takashi da karfi har saida ya runtse ido da karfi dan wani irin zafi yaji ga tiles ɗin sanyi sosai, janye ƙafan tayi ya ɗago ya kalleta tayi mishi murmushi ta kalli haneefa wacce take kallon plate nashi tace "sis baki cin komai ko dai abincin ne bai miki ba?"

girgiza kai tayi "yamin"

"let me get you juice and some slice of cakes"

jijiga kai tayi "don't worry am not hungry na koshi sosai"

"okay"

ta faɗa tana gyara zama, yah faruk Kam sai cin abincinshi yake, anwar ganin ta kawo kafa zata kuma takashi yasa kafanshi da sauri ya ɗaura akan farin kafanta da yake kan tiles ɗin yana sheƙi, kallonshi tayi shima ya kalleta, hannu yasa ya shafa kwantaccen sajenshi wanda yake karawa fuskanshi kyau da kwarjini, idanunshi da suke a lumshe ya zuba mata su, manyan idanunta dara-dara masu kalan madara ta zuba mishi itama tana kallonshi, murmushin gefen baki yayi dan shima ya ɗan sake mata nauyin kafanshi kaɗan, janye kafanta ta fara ya danne yana so ya koya mata hankali kada taga yana mata shiru dayawa, ta cika har tana neman fashewa sai huci take tana son ta janye kafanta, spoon ɗin dake hannunta ta sake kasa, haneefa ta kalleta ganin zata durkusa ta ɗauka haneefa ta ɗaga mata hannu, a hankali tasa kanta kasan table ɗin zata ɗau spoon ɗin, idanunta suka sauka akan na anwar wanda yake shafa kafan noor, ita kuma tana janyewa, jikinta ne ya fara rawa, kasa ɗaukan cokalin tayi, ta kuma kasa janye idonta akansu, ji tayi gabanta ya faɗi har wani jiri-jiri ta faraji, da kyar ta haɗiyi wani yawu me ɗaci tasa hannu ta ɗau spoon ɗin ta ɗago kanta, idonta har ya sauya kala, kallonshi tayi baima san tana kallonshi ba idonshi akan noor yana mata murmushin gefen baki wanda ko ita bata taɓa ganin yayi mata hakan ba, kallon noor tayi wacce take haɗe rai tana huci, aje cokalin tayi a fusace ta tashi da gudu ta bar wajen, tana hawan stair ta fara sharan hawaye da bayan hannunta, ɗaki ta shiga ta zauna a inda icecream ya zuɓe ɗazu har tana jin gum na sugar a wajen, kuka ta fashe dashi tana jin wani irin kishi yana tokare mata kirji.


noor ta bita da ido tana murmushi a ranta, koba komai ta samu hanyan da zata rabasu tunda haneefa taga shine yasa kafa akan nata ba ita tasa a nashi ba, kuma taga alama haneefa nada kishi sosai hakan zai kara taimaka mata wajen aikinta, da mamaki yabi bayanta da kallo, ya rasa me yake damunta, faruk ma yabita da kallo kamar yadda momy ma take kallonta, noor ta mike tabi bayanta, kallon bayan noor yayi kamar da gayya take tafiya domin duk jikinta yana motsi, runtse ido yayi yana furta "astagfurullah"

tura kofan tayi jin ana tura kofa haneefa tayi sauri ta share hawayen dake fuskanta ta tashi daga zaunen da take, noor ta kalleta da kyau tace "kuka kike unty haneefa?"

girgiza kai tayi tana kakalo murmushi tace "a,a noory me kika gani?"

"naga idonki yayi ja"

kanta ta girgiza tace "kaina ke ɗan ciwo na shigo nasha magani ne"

"sorry let me get you paracetamol okay?"

giɗa kai tayi "thanks noory"

paracetamol ta ɓallo mata da ruwan gora ta kawo mata, a hankali ta karɓa ta shanye domin tana da buƙatanshi, saida ta shanye noor tace "kwanta ki huta"

kwanciya tayi akan gadon taja duvet ta rufata dashi, ta juya zata tafi taji ta rike mata hannu, jikinta ne yayi sanyi ta kasa juyowa, tasan bata kyautawa haneefa, koba komai haneefa tana da nutsuwa da rashin magana gata da hakuri, to amma idan ba haka tayi ba tana ganin haneefa zata faɗa babban rami a gabanta, ba zataso haneefa ta auri talaka wanda baida feature ba, a yadda take sonta ta gommace ita ta auri talaka duk da yadda take kyamansu akan haneefa, saboda batada matsala tana da yanayin shiru-shiru, murya ƙasa tace "ki juyo"

juyowa tayi taki yadda su haɗa ido, tace "kalleni mana ko akwai abinda kikamin wanda bakyaso na gane?"

girgiza kai tayi "what do you mean unty haneefa?"

murmushin gefen baki tayi kana tace "you know i love Anwar ko?"

kin bata amsa tayi, ta kalleta na tsawon seconds sannan ta kuma cewa "please go and feed him naga baici abincin ba, like yana cikin damuwa kuma ke kaɗaice wacce zan iya yadda ta raɓeshi saboda ke ɗin kanwata ce na jini, nasan ba zaki cutar dani ba"

janye hannunta tayi "kiyi bacci bani da time ɗin bashi abinci kamar wani yaro"

"yaro ne a wajena noor, ganinshi nake kamar baby I will feed him idan ke bazakiyi ba"

tashi tayi zata sauka noor tasa hannu ta maidata tace "koma i will"

komawa tayi tana cije baki, ta rufata da blanket ɗin ta juya a fusace ta bar ɗakin, meyasa duk abinda tayi baya tasiri a tsakaninsu?

haneefa tana kallonta har ta fita, lumshe ido tayi.


noor tana fita ta turo kofan da karfi "wato nayi feeding nashi ko? okay I will feed him the most dangerous food in the world"

tafiya take har ta isa inda suke zaune, godiya ya yiwa momy bai wani ci abincin sosai ba momy tace "anwar ai bakaci komai ba"

girgiza kai yayi "na koshi na gode"

fita yayi daga ɗakin yana kallon faruk wanda yake ɗura abinci, murmushi yayi "acici"

dariya yayi yace "niba kamar kai bane ga abinci naki ci"

fita yayi ya koma ɗakinshi ya zauna a bakin gado, ɗago wayan yana kiran layin haneefa, kusan sau uku kafin ta ɗaga murya ƙasa tace "Hello"

ajiyan zuciya ya sauke kana a hankali yace "meyasa bakya min magana?"

lumshe ido tayi tana jin sautin muryanshi har cikin zuciyarta, cikin sanyin murya yayi kasa sosai ta yadda ita kaɗai zata jishi yace "kinaso zuciyata ta buga ne? kinsa na saba dake na shaƙu dake shine kike neman ki gujeni?"

jin tayi shiru yace "haneefa?"

"umm"

"me nayi miki?"

"kana sona?"

shiru yayi domin baida amsa shidai yasan yana jinta a ranshi kuma bayason ranta ya ɓaci ko ta ɗauke mishi wuta taki mishi magana sai yaji kamar zuciyarshi zai fashe, a hankali ta kara furta "kana sona?"

giɗa kai yayi kamar tana kallonshi, murmushi tayi dan tasan abinda zaiyi kenan, murya can kasa tace "ka faɗamin da bakinka ba wai ka giɗa kai ba, kamar yadda zan faɗa maka, i love You anwar ina sonka sosai anwar"

kyakkyawan idanunshi masu ɗauke da zara-zaran eyalashes kamar na mace ya lumshe a hankali ya kuma buɗewa, bai taɓajin kalman daya daki zuciyanshi kamar wannan kalman da haneefa ta furta mishi yanzu ba, tace "kana sona?"

muryanshi da yake rikita mata lissafi ya motsa baki a hankali yace "ina sonki"

ji tayi kamar ta tashi tayi tsalle akan gadon, sai kuma tace "kace i love you haneefa da karfi"

murmushin gefen baki yayi kana yace "i love you...."

jin yayi tsit ta zubawa wayan ido, noor ce ta zauna gefenshi tana mishi murmushin da yasan idan tayi to akwai abinda take shiryawa, hannunta rike da plate na abinci da spoon akai, a hankali bakinshi ya furta "noor"

da karfi kirjin haneefa ya buga, kara kallon wayan tayi jin sunan daya kira, "noor kuma?"

idonta har yanzu a waje tana kallon wayan a mugun tsorace, noor gyara zama tayi kamar zata haɗa jikinta da nashi, ta ɗau spoon ta ɗibi shinkafa da waken dake kan plate ɗin ta kai bakinshi, ido ya zuba mata wayan a kunnenshi tace "have it, haneefa ce tace nazo nayi feeding naka, so feel free and eat"

haneefa ta mike daga kwancen da take tana jin abinda kanwar tata take faɗa, matsowa tayi kusa dashi tace "pleassss kaciiiiii"

kallonta yayi ya kuma kalli abincin da takai saitin karamin bakinshi, haka kawai yaji bai yadda da wannan abincin ba, ganin tana kara matsoshi ya buɗe baki a hankali tasa mishi, taunawa ya fara yana addu'a a ranshi har ya haɗiye, kara ɗibowa tayi ta kai bakinshi ya karɓa yana ci, hankalinshi ba'a kwance ba domin ta tsareshi ta matso har jikinta yana taɓa nashi, shinkafa ɗaya ya tsaya gefen bakinshi, yasa hannu zai cire tasa lallausan hannunta ta rike nashi, kallonta yayi ta kashe mishi ido ɗaya tareda shagwaɓe fuska tace "no amanarka aka bani"

yatsa ɗaya tasa ta cire mishi tare da shafa lips nashi saida yaji tsikan jikinshi ya tashi, da sauri ya matse kafanshi domin ji yayi kamar jikinshi ya sauya, noor bata kula ba saida ta gama bashi abincin ta ɗau juice dake cike a cup ta kai bakinshi, girgiza mata kai yayi, ta kuma matsowa sosai kamar zata shiga jikinshi tace "kasha"

"a,a banso"

bakinta ta kawo kunnenshi ta inda haneefa take sauraran komai, ta tsaya kamar an zare mata rai gata a tsaye amma bata motsi, jin noor tace yasha taji gabanta ya kuma faɗuwa tashin hankali yayi mata yawa, har sarawa taji kanta yanayi, da kyar zuciyanta ya iya furta "me zaisha?"

da wani irin murya wanda noor batasan ta iya ba tace "kashaaaa"

girgiza mata kai yayi dan ya fara tsorata, idanunta wanda suka koma kalan bacci dan shan syrup da take ta lumshe a hankali cikin wani irin voice da yasashi karɓa tace "uhum nikam saika sha"

buɗe baki yayi tasa mishi ya fara sha, sai karan shan abu kawai kakeji wayan dake hannun haneefa ya faɗi kasa, fashewa yayi ta durkusa kasa, kuka takeso tayi amma ta gagara, saida taji numfashinta ya ɗauke na wucin gadi kafin ta saki wani ɗan marayan kuka.


noor kuma ganin wuyanshi ya ɗauke ta matsa daga gefenshi kana ta tashi tabar wajen, dafe kirji yayi bai taɓa tsoro irin na yau ba, ya rasa ina juriya da kwarjininshi ya tafi, kallon wayanshi yayi ya duba yaga haneefa ta kashe, saida ya nutsu ya sake trying number ɗinta yaji a kashe, noor tana fita ta koma ɗaki tayi sallama, haneefa ta kifa kanta kawai da gadon bata yadda sun haɗa ido ba, fuska a sake tace "haneefa baccin ne harda saukowa kasa?"

giɗa kai tayi bata yadda ta ɗago ba, domin hawaye yaki tsayawa, hannu tasa tana jan zip ɗin rigan sama, cikin shagwaɓa tace "wash zip ɗin yaki janyuwa"

haneefa batasan lokacin data ɗago tana kallon noor ba, bayanta kawai take iya gani, zip ɗin riganta a buɗe, wani irin bugawa taji zuciyanta yana yi, a hankali tasa hannu ta share hawayen dake sauka kamar ruwa, tashi tayi taje tasa hannu ta juyo da ita, kallon gaban riganta tayi kamar ya ɗan fashe, murmushi ta kakalo kana tace "meya yaga miki gaban riga?"

"oh sorry wallahi na ɗan faɗi ne"

"sannu"

hannu tasa taja mata zip ɗin sama tace "kin bashi abincin?"

"eh kamar yadda kika ce"

jijjiga kai tayi, "bayan abinci fa?"

"abinci kaɗai kikace na bashi shi na bashi"

"okay Amma ba ruwa ko juice?"

girgiza kai tayi "babu may be yanada pure water a ɗakin nashi kinsan ya saba dashi"

"okay Amma juice ɗin da naji kina bashi fa?"

"mama salma ce ta haɗa"

tayi magana tana tura baki.


murmushi haneefa tayi kana tace "sannan meyasa kikaja zip naki a bakin kofa, dan nasan kece kikejan zip rabi bakya iya ja har kasa"

shiru tayi ganin haneefa ta ganota, haneefa tazo ta rike hannunta ta zaunar da ita bakin gado tace "noory? kefa kanwata ce tare muka tashi na san abinda zaki iya nasan wanda ba zaki iya ba, kina son nayi zarginki keda anwar ko? never, wannan ba halinki bane, na san kin tsaneshi to amma inaso ki sani Abba yana dawowa zan mishi maganan anwar aure nakeso muyi"

juyawa tayi zata tafi ranta ba daɗi, taji noor tace "saide idan na mutu zaki aureshi"

"ko kuma idan ni na mutu ba"

tana faɗan haka ta juya ta fita tareda tura mata kofan da karfi, tashi noor tayi ta buga jikin dressing mirror, tayi watsi da kayan dake gaban suka zube kasa masu fashewa suka farfashe, me zatayi ta kori wannan daga gidansu? meyasa haneefa take makauniyar soyayya?


bata tsaya ko ina ba sai garden ta zauna akan kujeran da yake wajen wanda yake da kyau sosai, jingina kanta tayi da jikin kujeran ta ɗaga kanta sama tana kallon bishiyoyin dake wajen, a hankali ta kuma lumshe ido, sam zuciyanta ya kasa zama lafiya ji take kamar ansa wuta a ciki, ya kasa zama a ɗakin so yake ya ganta ko zaiji sauki, a hankali yake tafiya har ya isa garden, daga nesa ya hangota ta lumshe ido da alama tunani take, yana tausayin yarinyar domin batada hayaniya gata da hakuri da kawaici, cikin sanɗa ya karasa har inda take, bakinshi ya kai kunnenta yace "ke!!!"

a ɗan tsorace ta ɗago tana ware ido, dariya yayi ta zuba mishi ido tana kalloshi, bata taɓa ganin wanda dariya yayi mishi kyau kamar anwar ba, gaba ɗaya saiya zame mata kamar balarabe, har yanzu ta kasa yadda yazo gidansu neman aikin bayin flower musamman yadda take ganin fatar jikinshi tana sheƙi kamar ba ɗan talakawa ba, tafi yayi ta kalleshi yace "i love you haneefa"

sai a lokacin tayi dariya domin taji daɗin kalman, janyo kujera shima Yayi ya zauna yana facing nata yace "inaso muyi magana"

zuba mishi ido tayi alaman tana jinshi, gyaran murya yayi yace "haneefa kinsan akwai banbanci tsakanina dake ko? mahaifinki yanada kuɗi ni kuma kinga daga gidan talakawa na fito, kada mu ɓatawa juna lokaci nidai nasan kinfi karfina ba zaki iya auren..."

yatsa ɗaya tasa ta rufe mishi baki, kallonta yayi yaga tana jujjuya mishi kai, a hankali ta janye tace "na sani a haka nake sonka, kuɗi, dukiya, babban gida, duk basuda anfani a zaman aure idan babu soyayya, ni so kawai  nake maka, ina jinka har cikin raina, na san kaima kana sona kada kaji tsoron kuɗin babana ka kalli son da nake maka"

shiru yayi dan shikam baijin zai iya yafison ya auri ƴar talakawa kamar shi, "kada ka damu da noor domin har yanzu yarinya ce she's just 19 bata kai 20 ba"

ganin yayi shiru ta sauko daga kan kujeran tazo gabanshi ta durkusa, hannunshi ta rike tana murzawa a hankali tace "tun ranan dana ganka na kasa gane kaina, anwar ban taɓa son wani ɗa namiji kamar yadda nake sonka ba, ban damu da inda ka fito ba, na sani kaima kana sona kada ka ɓoyemin idan baka sona ka faɗamin kawai"

jin yayi shiru ta mike tace "ba komai ba zan takura maka ba"

tafiya ta fara yace "wa zai samu yarinya me nutsuwa kamarki yace baya so? haneefa keɗin mutuniyar kirki ce, ina sonki har cikin raina, hakurinki da kawaici shi yasa naji ina sonki, to amma..."

"to amma me?"

"haneefa kinyi min nisa...."

"banyi maka komai ba sai soyayya"

ta faɗa tana dawowa, matsowa tayi da kujeran ta zauna kusa dashi tana kallonshi tace "anwar ina sonka"

daga maganan da take kasan da gaske tana sonshi, shikam so yake ya sanar mata bambancin dake tsakaninsu amma taki yadda, ganin yayi shiru ya zuba mata ido tana mishi surutu tana dariya tace "me kana kallona?"

lumshe mata ido yayi ya kuma buɗewa, tace "me hakan kenan?"

kara lumshe idon yayi yana shan leɓe kamar yadda ya saba yace "inajin bacci"

bai taɓa mata shagwaɓa ba sai yau, hakan yasa taji hakan a bakon yanayi, dukar da kai tayi kasa tace "jeka kwanta to"

"um um"

kallonshi tayi "meyasa?"

"ban gaji da kallonki ba"

kallonta kuwa yake ba ɗauke ido, nauyinshi ta faraji a hankali ta juya tace "zan tafi saida safe"

ganin ta tashi yace "karki tafi please Ina missing Inna idan kin tafi wa zai kula dani?"

"muje please"

tashi yayi suka fara tafiya a tare, har bakin kofanshi ta rakashi kana ta juya zata tafi yace "bakiji ba"

juyowa tayi ta kalleshi "i love You"

ya faɗa murya kasa-kasa, murmushi kawai tayi ta bar wajen tana jin daɗi a ranta, da faruk sukaci karo time ɗin da take tsalle a falo tana juyi, da sauri ta nutsu jin ya riketa, "ke lafiyanki?"

"sorry ya faruk"

sakinta yayi yana kallonta, tsaki yaja kaɗan kafin ya fita, ɗakin faruk yaje yayi sallama kana ya shiga, ganin yana salla ya jira saida ya idar sannan yace "rakani please"

"Ina?"

"wajen budurwata"

anwar ya kalleshi bai taɓajin faruk yayi maganan budurwa ba sai yau, maƙe kafaɗa yayi "ba inda zanje kuje ku barni a gefe ni kaɗai"

"to dama kana nufin ka zauna tare damu ne kaji sirrinmu?"


"sirri? miye sirrin naku?"

"nida budurwata muna hugging juna before na tafi, and sometimes har kiss nake mata tongue to tungue, kuma sai kaji romantic words da zan rinƙa faɗa mata?"

girgiza kai anwar yayi "gaskiya faruk kai ɗan iska ne, meya kaika yin haka da budurwa? idan baka aureta ba fa? shikenan sai zunubin da kuka ɗibarwa kanku?"

"kaga ba wa'azi nace kamin ba idan zaka rakani ka rakani idan ba zakaba saika faɗamin"

"gaskiya ba zanje ba, ko kunya bakwa ji? hakan ba abune me kyau ba"

"oho dai kai wayasan me zakayi da budurwarka nan gaba"

"ba zance bazan taɓa ta ba, amma zan kiyaye ba wani kiss dasu hug sai muyi aure zataga love"

tsaki faruk yaja "kaika sani kar dai ka rufe kofa da wuri domin zan dawo ba zan jima ba"

"saika dawo amma a ɗan kiyaye Allah ne ya hana"

fita yayi yaja kofan, wayanshi ya ɗaga ya kira layin Abba, saida yayi nisa da ɗakin Abba kana yace "Abba wannan anwar ɗin mutumin kirki ne, zan tura maka voice ɗin ta watsapp forgive me nayi bad word kaɗan"

murmushi Abba yayi "ba komai na shaideka"

godiya yayi kafin ya kashe wayan ya buɗe data ya yiwa Abba sending ɗin voice nasu, Abba yana kasar Egypt yaje sari yana zaune a wani wajen shan iska ya shiga watsapp ya duba sakon da faruk ya tura mishi, playing yayi nan yaji muryan faruk da anwar da duk yadda sukayi, murmushi yayi jin muryan faruk harda cewa yana kissing nata tongue to tongue, a ranshi yace "Allah ya tsareka da yin haka umar"

gamsuwa yayi da tarbiyyan anwar kuma yaji son yaron sosai har cikin ranshi, sawa yayi a ranshi da zaran ya dawo Nigeria zai mishi gwaji na karshe daga wannan zai mallaka mishi takaddan da yake na sirri a hannu.


faruk fita yayi ya siyo abu masu daɗi a shago, sai kusan 10 ya dawo ya samu kofan anwar a buɗe a lokacin suka gama waya da haneefa wacce take zuba mishi shawagaɓa ji yake kamar yace ta bari domin tana birkita mishi tunani, ita kuma ta saba da hakan ya riga ya zama jikinta dole sai tayi, da kyar ya daure suka gama wayan ya aje kenan yaji muryan faruk yayi sallama, amsawa yayi, ya shigo ya aje ledan a ƙasa kana ya zauna a gefen gadon yace "kayi bacci ne?"

"A,a idona biyu"

janyo ledan yayi yace "tashi muci"

kin tashi yayi domin so yake yayi bacci, "tashi mana"

"banajin yunwa"

"dan Allah ka tashi Abba yace kada na barka da yunwa"

a hankali ya tashi yana kallon ledan da faruk ya buɗe kaza ne babba wanda ya gasu me kyau yana kamshi sosai, plate ya ɗauko musu ya ɗaura akai da wuƙa, a hankali anwar ya fara yanka kaɗan yana ci, faruk ya kai bakinshi yace "baka tambayane ya beb tawa ba"

"ya take?"

"naje batada lafiya zazzaɓi yana damunta har tana rawan sanyi"

"kai sannu amma ka kaita hospital ai ko?"

yayi magana yana ɗaga mishi gira, girgiza kai yayi "no wani hospital kuma bayan gani"

"kai doctor ne?"

"no there's hanyoyin warkar da mace idan tana rawan ɗari"

"ban gane ba"

kallonshi faruk yayi  yana magana tun daga kasan zuciyanshi, "kai baka gane komai ne?"

"nikam bana ganewa"

"to romancing nata kawai nayi taji ɗumin jikina harta warke"

kallon mamaki anwar yayi mishi kana yayi murmushi yace "hakan is not good ka bari kuyi aure"

marairaicewa faruk yayi "ba zan iya zama ban taɓa ta ba, she's so hot"

"but zaka iya ragewa ai da haka zaka iya faɗawa zina fa"

"nop ba zamuyi ba sai munyi aure, yanzu dai taɓe-taɓe kawai mukeyi and I love it"

cire hannu anwar yayi yace "yawwa na koshi na gode"

"wai kai baka cin abinci ne?"

"gashi naci"

yayi magana yana shan yaji domin yaci barkono sosai, "ya dai?"

"yajiii"

dariya yayi ya mika mishi goran ruwa mai sanyi yana kallon yadda idonshi ya sauya kala zuwa jaa, karɓa yayi yasha kana yaji sauki, saida Faruk yayi rabin kazan kafin ya mike yace "saida safe"

"Allah ya kaimu"

fita yayi ya kai sauran kazan frij sannan ya wuce ɗakinshi, anwar da kyar yayi bacci saida ya kuma shan ruwan sanyi....



*Jiddah S Mapi...✍🏻 08144818849*

No comments