Hakki Na 1
🌸🌸🌸🌸🌸
*HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸
By
_jiddah S Mapi_
*Chapter 1*
~Gani nan fitowa haneefa kiyi hakuri please charger nake dubawa"
wacce aka kira da haneefa tana tsaye tana duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta, tayi kyau sosai cikin leshi blue wanda akayi ɗinkin half bubu, kyakkyawa ce ajin karshe fara ce sol gata doguwa batada kiɓa kuma batada rama, irin cif ɗin nan ce, ɗaurin kanta yayi kyau ta zuba gashinta d yake da tsayi da tsantsi ta baya, takalmin kafanta flat ne baki da jaka shima baki a hannunta, da alama sauri take domin ta zubawa kofan babban falon ido tana ɗan tsaki kaɗan, hannu tasa ta dafe kanta kana tace "dan Allah Noor ki fito kinsan idan munyi latti Abba will punish us"
da ɗan gudu ta fito tana sa charger cikin karamin jakan dake rataye a kafaɗarta, wata kyakkyawar budurwa ce wacce taji kyau har ta gaji dashi, farace doguwa ba kiɓa ba rama tasa bakin abaya me tsagu a gaba, fararen kafafunta idan abaya yayi gefe sai su bayyana, tana wani irin shining jikinta kamar madara, bayan tasa charger a jaka ta ɗau ribbon dake hannunta ta kama gashinta wanda ya sauka har gadon bayanta yana taɓo ɗuwawunta, kamewa tayi kana ta ɗau siririn mayafin tayi rolling a kanta, bakin glsss ta ciro tasa a idonta ya rufe mata rabin fuskan, hakan ya kara fitowa da asalin kyaunta, takalmin kafanta me tsini ne baki, cingum ta jefa a baki tana fitar da kamshi na musamman, saida ta ganta a waje kana ta fara taku cikin iyawa da yanga da yauƙi har ta iso wajen haneefa wacce take kallonta tana murmushi, tana isowa ta rungumeta kana ta lumshe ido cikin sanyin murya da zaƙin murya tace "am sorry sis Ina ɓata miki time a duk lokacin da zamu fita am so sorry please"
a hankali haneefa ta shafa bayanta kana ta janyeta daga jikinta tace "oya let's go munyi latti"
jerawa sukayi suna tafiya a tare a cikin maƙeƙen gidan, gidane na alfarma tsararre kuma kerarre gefe guda masu gadi ne da masu kula da harkokin gidan, compound suka nufa da sauri wani guard yazo ya buɗe musu marfin mota, motan baki ne kirin da jikin harda glass ɗin tinted ne, jikin motar kamar kwai gashi yana sheƙi, haneefa ce ta fara shiga kana Noor ta mika mata jakanta sannan itama ta shiga ta zauna a gefen haneefa, driver ne yazo ya shiga, gaishesu yayi haneefa ce ta amsa Noor ta maida hankali kan wayarta tana latsawa ko kallonshi bata yi ba, getman ne ya buɗe musu maƙeƙen get ɗin kana driver yaja motan suka fita, haneefa ta kalli Noor kana tasa hannu ta karɓe wayan dake hannunta, yamutsa fuska tayi kana ta shagwaɓe fuska kamar zatayi kuka tace "haba hanee ki bani mana ina da chat da classmate tawa ce"
sawa a jaka haneefa tayi kana tace "da alama baki ma tsorata da lattin da mukayi ba, kin manta halin Abba ne? wallahi idan muka rasa wannan takaddan ba zamu fita outside ba muna nan nigeria har wani sati"
murmushi tayi kana ta gyara glass É—in dake idonta tace "kada ki damu ko Abba be samar mana wannan takaddan ba, inada wanda zai bamu, ke meyasa kin fiye tsoro ne?"
numfashi ta sauke kana ta ɗau ruwan gora ta buɗe, kurɓa tayi ta rike a hannu sannan tace "noor ba zaki gane bane, inason fita a wannan satin banaso auren elham yazo ba tareda na fita waje ba, kinsan elham zatace nice best friend kuma wallahi ba zan iya ba saboda maza zasuyi yawa a wurin, kinsan fa wanda take aura ɗan babban gidane zai zama da abokai da yawa ni kuma banson cikin maza"
"haneefa kenan bama cikin maza ba har matan ma ba so kike ba, gara ki warware dan kinga Mami batason wannan halin naki na noƙe noƙe"
murmushi kawai tayi, tsayawa driver yayi kana ya juyo jikinshi yana rawa yace "hajiya mun iso"
haneefa cikin sakin fuska tace "tom mun gode"
buÉ—e marfin motan yayi ya fita, haneefa fitowa tayi ita kuma Noor tana zaune saida ya zagaya ya buÉ—e mata kafin tasa kyakkyawar kafarta ta fito, tana shan kamshi har suka jera suna tafiya, babban hall ne me kyau da alama taro akeyi a wajen, a bakin Get na shiga suka tsaya haneefa ta nuna mishi wani ticket kana suka shiga, hannun noor ta riko ganin mutane cike a wajen ana jawabi, kallonta noor tayi "zaki fara ko? sai kace yau kika fara shiga taro"
"dan Allah kada ki saki hannuna noor mutane sunyi yawa"
kafarta har harɗewa yake gani take kamar ita kowa yake kallo, noor kuma saima gyara taku da tayi tana tafiya tana kallon mutane ɗaɗɗaya ta cikin bakin glass ɗin data manna a fuskarta, da haka har suka isa wani kujeru wanda aka tanada domin baƙi, gyarawa haneefa kujeran tayi saida ta zauna kafin itama ta zauna a gefenta, hannu ta mika mata ta marairaice tareda shagwaɓe fuska tace "unty haneefa ki bani wayata to"
"a,a bazan bayar ba saimun koma gida"
turo baki tayi "dan Allah fa"
bata wayan tayi "ki kashe kisa a jaka dan kinsan nan abu me amfani za'ayi ko?"
girgiza kai tayi kana tayi reply na message ta kashe wayan tasa a jaka, hankali suka maida akan mutumin da yake jawabi, babban mutum ne me kamala da harshen turanci yake magana, mutanen wajen suma manyan mutane ne da yaran manya, kana ganin taron kasan taro ne na masu kuɗi da mukami, suna daga zaune aka kawo musu drinks da snacks haneefa ce ta karɓa ita noor bata ko kallo server ɗin ba, ajiyewa tayi a gabansu kana tace "ga ruwa da snacks"
girgiza kai tayi "I have water in my bag"
da mamaki haneefa tace "kin É—au ruwa all the way from gida kinzo har nan dashi?"
giÉ—a kai tayi.
haneefa ta saba da halin kanwar tata, haka take bata cin abinda ya fito daga hannun mutane koda kuwa ruwa ne sai tace hannunsu da kazanta, tanada kyankyami gata da kallon banza, halin Noor sai haneefa ce take iyawa.
da haka har aka gama taron aka tashi, tare suka mike suka nufi wani office, knocking sukayi aka amsa sannan suka shiga, wani mutum ne zaune akan kujera madaidaici yana juyawa yana kallonsu, noor ta zauna akan kujera ya harareta, É—auke kai tayi tana kallon haneefa wacce take tsaye tana jiran ya bata order kafin ta zauna, cikin haÉ—a fuska yace "waya baki ikon zama?"
kallonshi tayi da manyan idanunta sannan ta watsar, da hannu yayi mata alama da ta tashi, cikin masifa ta mike kana ta bashi takadda Æ´ar karama, kallon takaddan yayi sannan yace "ba zanyi sign ba raini da rashin ganin girman mutane yayi miki sign"
maida takaddan tayi cikin jaka kana tace "har duniya ta naÉ—e kada kayi, idan kai zakamin sign in shiga aljanna dan Allah kada kayi ka bari in shiga wuta"
shima cikin masifa ya tashi zai mareta haneefa tace "dan Allah kayi hakuri, dan Allah kada kayi haka we are sorry"
kallonta noor tayi kafin tace "you're sorry dai unty haneefa"
juyawa tayi tabar office ɗin bayan ta maida glass nata ta fita tareda turo kofan da karfi kamar zata ɓalla, waro ido haneefa tayi kana ganinta kasan a tsorace take, kallonta yayi bayan ya koma ya zauna, ranshi a ɓace yace "wacece wannan?"
jikinta yana rawa tace "kanwata ce noor"
jijjiga kai yayi kana yace "itace noor Aminu sadauki?"
jijjiga kai tayi idanunta cike da tsoro, hannu ya mika mata, a hankali tasa hannu ta ciro takaddan ta mika mishi, sign yayi mata kana ya bata, bakinta yana rawa tace "sir na noor fa..."
hannu ya É—aga mata "ba zan sa hannu ba"
durkusawa tayi kasa zata fara rokanshi yace "ba sai kin gaji ba tashi kije ba zansa ba"
jiki a mace ta mike tayi godiya, a hankali ta ɗau jakanta ta rataya a gefe, murɗa handle na kofan tayi ta fita, time ɗin har Noor ta fita daga hall ɗin, nemanta ta fara bata ganta ba, saida ta gaji taje wajen motarsu, driver ya buɗe mata tana shiga taga noor zaune ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya tana glass ɗin ta maida kan gashinta wanda ta janye siririn mayafin zuwa wuyanta, pot na shisha ta ta jona a cikin motan tana zuƙa tana huci ranta a matuƙar ɓace, waro ido haneefa tayi kana tasa hannu ta karɓe pot ɗin ta buɗe motan ta fita ta jefar can nesa, dawowa tayi cikin masifa ta fara magana "Noor are you mad? kanki ya taɓu ne? shisha kike sha noor zan gayawa Abba kina shaye shaye idan baki kiyayeni ba, noor me kikeso ki maida rayuwanki ne? ina hanaki shan shisha amma bakya hanuwa? Kinada hankali kuwa?"
takaddan ta ciro ta nuna mata kana tace "kiga wannan mutumin ya samin hannu ke kuma yaki saboda me? saboda rashin kunya da kikayi mishi"
jingina kanta tayi da jikin seat na motan ta fesar da numfashi me zafi kana tace "ke kanwata ce ina sonki sosai, ba zan iya ganin kina ɓata rayuwarki inyi shiru ba, ki duba yadda Abba yake kokari akanmu amma ke kina ɓata rayuwarki"
takaddan ta yaga, zaro ido noor tayi wacce tayi shiru kanta kasa tunda haneefa ta fara magana ko numfashin kirki batayi ba
"meyasa kika yaga?"
knocking na motan tayi sannan ta sauke glass ta yiwa driver alama yazo su tafi, a hankali tace "saboda ba zan iya tafiya na barki ba"
ji tayi noor ta rungumeta, jikinta yayi sanyi
"ina sonki unty haneefa"
shigowa driver yayi kana yaja motan suka tafi, shiru sukayi a motan kowa da tunanin da yake.
hon yayi a kofan gida getman ya buÉ—e musu, cusa hancin motan yayi zuwa ciki, bayan yayi parking motan cikin motocin da suke babban compound É—in, ya fito ya buÉ—ewa noor, haneefa kam ta buÉ—e ta fito, a tare suka jera suna tafiya har suka isa babban falon dake kasa, falon ma abin kallo ne, wasu manyan kujeru masu kyau farare da chinese carpet me laushin gaske ne a shimfiÉ—e cikin falon, noor tayi jifa da jakanta kana ta cire mayafin ta yasar a kasa, abayan jikinta ta cire ya rage daga ita sai wani wando jins blue da kuma top pink, kwanciya tayi akan dogon kujeran ta É—au remote na ac ta kara kana ta lumshe ido tayi kamar tana bacci, haneefa ta kwashe kayan data zubar ta fara takawa har ta isa matattakalar upstair, É—an tsayawa tayi tace "noor ba zakije kiga mami ba first?"
girgiza mata kai kawai tayi idonta a lumshe, tuna rainin wayon da wannan mutumin yayi mata kawai take, ji take kamar ta koma office É—in tayi mishi rashin mutunci, juyawa tayi ta kwanta rub da ciki tana ji ranta yana tafasa, ji tayi an murÉ—a handle na kofan, runtse ido tayi so take ace bacci take, ta zaci Abba ne, muryan ya faruk ta tsinto, kirjinta yana dukan tara tara ta runtse ido ta rungume É—an karamin trust pillow da yake gefenta, kallonta yayi kana yace "ke ban hanaki kwanciya akan cikinki ba?"
yi tayi kamar bata jishi ba, yasan ba bacci take ba
"okay karki tashi ina zuwa"
tashi tayi da sauri tana murza ido, ganinshi a tsaye tace "ya faruk?"
so take wai ta nuna bacci take, harara ya ɓalla mata, shima yana kama dasu fari sol handsome guy da alama shine babba akansu, tashi tayi ta bar wurin ta haura sama, ɗakin mami ta faɗa babu ko sallama ta haura gado taja blanket, tsayawa mami tayi tana kallonta, daga toilet take bataji sallama ba sai ganin yarinya kawai tayi akan gado, mami kyakkyawar mace ce tana nan fara sol tana da kiɓa gata da son ado.
"noor what's rong with you?"
girgiza kai tayi "nothing mami am just tired"
kallon haneefa tayi wacce take gyara farcenta tace "meya sameta?"
"ba komai mami wai ta gaji ne"
"Are you sure?"
jijjiga kai tayi.
"anyi muku sign?"
girgiza kai haneefa tayi "mami munje baya nan"
"okay gobe zaku koma?"
tayi magana tana shimfiÉ—a sallaya, girgiza kai haneefa tayi "no shikenan za jira auren elham kawai mami"
"that's good"
hijabi tasa kana ta tada salla, noor tana cikin blanket tana jinsu, dama ita ba son tafiyan take ba, tafison su jira auren unty Elham ɗin dan tasan akwai casu, ita duk inda zataje a cashe ayi shagali ta haɗu da yaran manya masu kuɗi irin babanta to tana so, shiyasa ma duk frends nata babu talaka, layin da talaka yabi ma idan da dama ba binshi zatayi ba, noor tana da girman kai yadda bakwa zato, bata kula talaka batason abinda zai haɗa ta da talakawa gani take kamar hakan kazanta ne, ta samu kuma iyayenta suna kyautata musu, duk abinda suke so itada Haneefa a wurin Alhaji Aminu sadauki yana yimusu, gashi itace auta hakan yasa ta shagwaɓe dayawa, gata da raini bata ganin darajan kowa saina haneefa da mami da ya faruk da Abba, bayan waɗannan babu wanda noor take ganinshi da gashi, tana karatu a kasar morocco watarana ta mari malaminsu hakan yasa aka koreta a school ɗin ta dawo nigeria itama haneefa tace ba zata iya zama acan ita kaɗai ba hakan yasa itama ta dawo, Abba ya sasu a wani school anan secondary suke ita haneefa tana ajin karshe ita kuma Noor tana ajin kusa da karshe.
Alhaji Aminu sadauki shine mahaifinsu shi É—an asalin garin Adamawa ne bafulani na asali, aiki ya kawoshi garin kano anan suka haÉ—u da matarshi wacce take Æ´ar babban gidane mahaifinta me kuÉ—i ne anan kano, shima Alhaji Aminu É—an babban gidane mahaifinshi me kuÉ—i ne sosai, hakan yasa shima ya zama me kuÉ—i yana harkan saida gold da zinare, sun haifi É—ansu na fari me suna Umar faruk, bayan haihuwan faruk sun jima basu kara samun rabo ba, har sun cire rai sai Allah ya kara bata wani cikin ta haifi Æ´a mace itace Haneefa, itama saida sukayi kusan 3years kafin Allah ya kara basu wani cikin wanda daga kanta har yau kimanin shekara goma sha takwas basu kara samun haihuwa ba, itace Noor, haneefa yarinya ce me hakuri da sanin ya kamata, batada matsala ko kaÉ—an gata da sanin ya kamata, tun suna yara tanada hakuri sosai.
saɓanin Noor, batada kunya ga raini ga rashin sanin darajan mutum, kuɗin mahaifinta yasa bata ganin darajan kowa, koda ƴan aikin gidansu bata raga musu, gata da kyankyami ko gidan mutane sukaje bata cin komai har su dawo, ko a school idan ba ubanki ya kai ya kawo wajen kuɗi ba bata kulaki, Allah ya basu kyau daga su har faruk domin sunyi gadonshi wajen iyayensu, mami ba karamar mace bace, ga Abba da yake asalin fulani shima ba karamin kyakkyawa bane.
Abba yana da kyauta da taimakon al'umma saide baya ɗaukan raini, idan yayi magana baya canjawa, yana son ƴaƴanshi fiye da komai a rayuwarshi saide soyayyan da yake musu baya hana ya ɗau mataki idan sun aikata ba daidai ba, basa fita saida driver kowacce bata rabuwa da kuɗi, noor tana tsoron Abba sosai duk da suna shiri amma tana tsoron ɓacin ranshi sosai.
Mami bayan ta idar da salla tace "ki kira elham ta tura miki ankon da zasuyi É—in ta watsapp kinga saiki siya kada kizo kina nema lokacin daya kare ko?"
waya ya É—auka tayi dialing number É—in elham, bugu É—aya ta É—aga bayan sun gaisa tace ta tura mata ankon ta watsapp, amsawa tayi da "to" kana tace "ki gaidamin little sis"
"zataji"
ajiye wayan tayi bayan ta kashe ta kalli inda Noor take "Elham na gaisheki"
murmushi ne ya suɓuce mata daga kwancen da take tace "ina amsawa, amma gaskiya Unty Elham tayi sa'an miji, Kinga pre wedding pics nata kuwa? sai yawo yake a social media ashe ɗan gidan governor ne, kai gaskiya zanso ace kema unty haneefa kin auri ɗan gidan governor ko ɗan gidan president inada tabbacin zan kara samun girma a cikin kawayena, kullum addu'a ta shine ki auri ɗan gidan minister ko president ko governor"
É—agowa tayi daga kwancen da take tayi fari da idanu kana tace "wow dako anga shagali ranan ba kaina, wallahi aurenki akwai shagali saimun girgiza garin kano, anko nida frends É—ina sai munyi sun kai kala goma, dama na gaya musu kowa ya shirya auren unty haneefa daban dana yayar kowacce"
ido haneefa ta zuba mata tunda ta fara magana har saida ta gama, bayan ta gama tana dariya har dimple nata yana lotsawa tace "kin gama?"
haÉ—e fuska Noor tayi "kamar yaya na gama? it's ur big day fa dan nayi É—auki na fara shirya mishi shine kike cewa na gama"
"to ke kiyi lissafin naki mana sai nawa ne? nifa kinga a aurena dole za'ayi walima"
yamutsa fuska Noor tayi kana tasa santala santalan kafafunta a kasa ta sauko daga kan bed É—in tace "ko me za'ayi ai de zamuyi dinner da lunching ba? then it's okay"
Mami tace "ke kam da son abin shaiÉ—anci kike, ba wani dinner da za'ayi saide muyi walima da lunching ko hanee?"
girgiza kai haneefa tayi cikin jin kunya ta rufe fuskanta tace "eh mana mami"
taɓe baki noor tayi kana ta fita daga ɗakin ta koma ɗakinsu.
*Haƙƙi na ₦300 ne via 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, or mtn credit via 08144818849, send your evidence of payment 08144818849*
No comments