Gudu da Waiwaye Complete Billyn Abdul Novel
*_Typing📲_*
*_🏃🏻♂️GUDU DA WAIWAYE.....!!_*
_(Shi ya kawo mugun zato)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_ƊAN DANO_*🤤🤤😋😋
*(1)*
MALAM Rabi'u Shema, cikakken bakatsine jinin rumawan asali da ALLAH ya azurta da wani sirrin ƙyau mai fita da kwarjini.
Ya fitone da ga yankin karamar hukumar Dutsamma dake jihar katsina, a wani ƙauye da ake kira Shema, danginsa uwa da uba duk sun fitone daga wannan yanki.
Sanadin ƙaddarar neman na kaine ta dalilin kasuwanci ya tsinci kansa a garin kano, shi kaɗai ya fara zuwa kafin daga baya ya kawo matarsa mai suna iya ladi.
Ƴaƴansu huɗu a duniya, maza uku mace ɗaya.
A yanzu haka da shekaru suka shuɗa gidan Malam Rabi'u ya zama family house mai ɓangarori huɗu.
Ginine irin na mutanen da, shiyyasa ya kasance gida babba da har ƴaƴansa Uku duk suka sami gurbin zama da iyalansu a cikinsa.
A yanzu haka dai ALLAH ya azurtashi da jikoki daga tsatson waɗannan ƴaƴa huɗu da zasu iya kaiwa kusan ashirin da huɗu, harda ƴaƴan ƴarsa mace Marwa dake aure acan garin Dutsamma kuma guda biyu.
Duka ƴaƴan malam Rabi'u ALLAH baisa sunyi karatun boko ba har suka kai minzalin hankali, amma sunada ilimin addini gwargwadon iko.
Babban ciki mai suna Hamza shine ya fara auren matarsa ta farko Ruƙayya, wadda ya koma gida ya auro ɗiyar zumu, wato ɗiyar gwaggonsa ƙanwar mahaifinsa.
Ruƙayya ta tare a kano tare da mijinta Hamza annan cikin gidansu, ya gina ɗakuna biyune da bayi ya katange wajen, Ruƙayya tana samun soyayyarsa data iyayensa mai tsafta harma da ƙannensa.
Sai da Ruƙayya ta shekara uku a gidan sannan ta samu ciki, bayan ya kai haihuwa ta haife ɗiyarta mace wadda taci suna maryam.
Haihuwar Maryam da watanni biyu Muktar yazo da batun sake aure.
Hankalin Ruƙayya ya tashi ƙololuwa, hakama iyayensa suka nuna sam basu yardaba.
Yashiga damuwa sosai, saboda yanason Suwaiba, kuma harma sunyi alƙawarin aure, da farko yaso ya haƙuran amma sai ya kasa, yaje can gida Shema ya sanar ma mahaifin Ruƙayya halin da ake ciki.
Mahaifin Ruƙayya yazo kano, inda ya wanke Ruƙayya da faɗa tas, sannan ya koma nasiha a gareta, hakama iyayen Hamza ya samesu ya nuna musu suyi haƙuri su barsa tunda yanaso, da yaje gefe yana aikata abun banza gara ya auro yarinyar zaifi kwanciyar hankali.
Badan su iya ladi sun soba suka amince akai auren Suwaiba da Hamza.
Suwaiba dai asalin iyayenta ƴan dawanau ne, amma yanzu suna nan zaune a cikin garin kano, bata da damuwa sam, dan tunda ta tare gidan Hamza batajin daɗin kowa sai shi, iyayensa da ƴan uwansa basa sonta, ƙiri-ƙiri suke nuna mata fifiko akan Ruƙayya.
Danne zuciyarta tayi tamkar bata gani, takuma kwantar da hankalinta tana musu biyayya su duka, wannan halayyar tatace ta saka suka fara sassauta mata, har itama Ruƙayyar kanta.
Koda yaushe zakiga Maryam maƙale da Suwaiba, dan tanada son yaran tsiya, tun Ruƙayya na ƙwacewa bisa zugar matar Yusha'u harta hakura ganin Suwaiba bata taɓa cutar da Maryam ɗinba, lokacin ma da Ruƙayya zata yaye maryam sai Suwaiba ta amsheta ta yayeta, tundaga wannan lokacin kuma zaman Maryam ya koma hannun Suwaiba.
Kawaicin ɗan fari yasa Rukayya ta ƙyale mata.
Cikin hikimar ALLAH kuma sai Suwaiba da Ruƙayya suka fara laulayin ciki a tare, Rukayya na biyu, Suwaiba na farko, tare sukaita laulayinsu har ALLAH ya saukesu lafiya, sai dai Ruƙayyace ta fara haihuwar ɗiyarta mace, taci sunan Rahama, bayan kamar sati biyu dayin suna sai itama Suwaiba ta haihu, amma ita namijine.
Itama ranar suna yaronta yaci suna AHMAD, Suwaiba mutum ce mai azabar kawaici, sai yazam har akan Ahmad halayyarta na nan, dan sam yitake kamar ba ɗantaba, dukda kuwa tana ƙaunarsa sosai, wani lokacin tana zaune zaita kuka amma tai biris dashi, har sai Ruƙayya ta shigo ta ɗaukesa tana mata faɗa, ko bashi nono sai Ruƙayyan ta tsaya a kanta wani lokacin.
Wannan kawaicin da takeyi mai tsanani a kansa yasaka Ruƙayya maida hankalin kula dashi da Rahama, sai suka taso tamkar wasu tagwaye, idan ka ganshi hannun Suwaiba to nono zaisha.
Maryam kam ta zama ƴar ɗakin Suwaiba, itace tamkar uwarta, itama Ruƙayya tana kawaici akanta, dan bata faɗar koda sunanta kamar yanda itama Suwaiba bata faɗar sunan Ahmad.
Ahaka yaran suka fara wayo har zuwa yaye, sai zaman Ahmad ya koma wajen Ruƙayya gaba ɗaya, kamar yanda Maryam take hannun Suwaiba.
A wannan karon sai Ruƙayya ta fara samun ciki kafin Suwaiba, sai da cikinta yakai kusan wata bakwai sannan Suwaiba itama ta fara laulayi, a wannan haihuwarma dai Ruƙayya mace ta haifa, wadda taci suna Sakina.
Su Ahmad sunyi murna sosai an haifa musu ƙanwa, sai nan nan suke da ita dukdama bawani wayone dasuba lokacin.
Bayan haihuwar Sakina da kusan wata taƙwas itama Suwaiba ta haife ƴarta mace, itama taci suna Raheenat.
Ƴaƴa zun fara cika gidan malam Muktar, dan haka sunayen iyayensu ya fara ɓuya, Ruƙayya ta koma Ayyah, Suwaiba kuma Gwaggo.
Tun daga kan Sakina Ayyah (Ruƙayya) bata sake haihuwaba, sai Gwaggo (Suwaiba) ce ta cigaba da haihuwa, tayi Mudanseer, Abubakar, Fa'iza, Sadiya, sai auta Zainab.
Daganan ne haihuwar ta tsaya itama, yaransu sun taso kansu a haɗe, inba sanar maka akaiba baka taɓa sanin ƴaƴan wance da wance, tare suka haɗu wajen gina ƴaƴansu a tarbiyya, sun gina gidansu bisa ƙyaƙykyawan tsari mai birgewa duk da sheɗancin kishin sauri da suke fuskanta lokuta da dama.
Sai ƙanin Hamza mai suna Yusha'u, shima dai matarsa ɗaya da ƴaƴa biyu, shima a cikin gidan ya gina nashi ɗakin matarsa ke zaune, shima sai ya ja katanga iya sashensa kamar yanda Hamza yayi, ya auri matarsa mai suna Ɗausiyya (Gaje) kusan tare da auren yayansa hamza na biyu, hakanne ya saka Gaje ɗaukar kishin duniya ta aza akan Suwaiba tamkar mijinsh ɗaya, dan komai na auren Suwaiba yafi nata.
Taso saka ruɗani a zaman Suwaiba da Ruƙayya, su haɗe kai su ware Suwaiba a gidan, amma sai UBANGIJI ya hana hakan, babu irin munafircin da batai musu, sai yazam ko saɓanin ya shigo tsakaninsu baya wani daɗewa suke fahimtar juna.
Lokacin da riƙon Maryam ya dawo hannun Suwaiba ba ƙaramin baƙin ciki Gaje ta shigaba, taita zuga Ruƙayya akan ta amshe Maryam, amma sai ALLAH bai ƙaddara hakanba.
Abinda kuma yazo ya sake haɗa ƙiyayyarsu Haihuwar namiji da Suwaiba tayi, wato Ahmad, dan kusan tare itama Gaje ta haihu dasu, sai dai itama mace ta samu kamar Ruƙayya, wadda taci suna Binta.
Nanma Gaje ta so ta cusama Ruƙayya ƙiyayyar Ahmad sai hakan bai faruba, dan kuwa Ahmad ma sai ya dawo hannun Ruƙayyan gaba ɗaya.
Tunda Gaje ta fuskanci bazatai galabar ɓata zaman Ruƙayya da Suwaiba ba sai ta koma kishi dasu gaba ɗaya, kullum burinta ta yaya zata ƙuntata musu kota haɗasu faɗa.
Sukam watsar da lamarinta sukayi tankar basusan da zamanta a gidanba.
Ahaka zaman nasu yaci gaba da tafiya har Ilyasu ɗa na uku wajen su malam Rabi'u yayo nasa auren shima.
Ilyasu ya auro matarsa mai suna Sailuba, tunda Sailuba ta tare a gidan sai Gaje ta shiga jan ra'ayinta da cusa mata tsanar su Ruƙayya (Ayyah) a zuciya, a hankali itama abun ya fara tasiri a ranta, sun ware kansu su biyu, bakajin cikinsu sam a gidan, sannu a hankali sai suka fara jan ra'ayin mazansu ma.
Daga nan ne fa zumincin iyalan malam Rabi'u yaso fara tangal-tangal.
Hankalinsa ya tashi lokacin da ya fahimci daga inda matsalar ke neman fitowa, dan haka ya tara ƴaƴansa duka huɗu har Marwanatu autarsu da itama tai aure acan dutsamma.
Ta inda ya shiga ba tanan yake fitaba wajen banbamesu da masifa akan sheɗancin matansu dake nan lalata zumincinsu.
Jikinsu kuma duk sai yayi sanyi, dan tabbas sun fahimci kuskurensu sosai, haƙuri sukaita bama iyayen nasu.
Iya Ladi tace ita sam bazata haƙura ba sai Yusha'u da Ilyasu sun ƙara aure, danta fahimci matsalar daga wajen matansu take.
A take Ilyasu ya amince zai ƙara auren, amma Yusha'u sai ya bada haƙuri akan shifa baida ra'ayin sake mata bayan matarsa Gaje.
Iya Ladi tace aikuwa bai isaba, ƙara aure ya zamar masa tilas, tadai bashi lokaci yaje ya nema wadda taimar daga lokacin har tsawon shekara uku.
Kwanaki kaɗan dayin wannan Zama, zancen ƙara auren Ilyasu ya taso, zai auri wata yarinya anan ƙasan layinsu mai suna Zubaida.
Bayan Ilyasu ya ƙara aure a nanma sai Gaje taita tunzura Sailuba, sam zaman lafiya yaƙi tsakanin matan Ilyasu saboda munafurcin Gaje.
Haka rayuwar ta cigaba da tafiya a wannan family, a cikin gida ɗaya har kawo yanzu da duk sun mallaki hankulansu, ƴaƴansu duk sunyi girma, yayinda tsufa ya kama Malam Rabi'u sosai, hakama iya ladi, dukda dai ita Alhmdllh jikinta da ƙwari tunda komai tana iyayima kanta.
Hamza talakane mai ƙoƙarin neman na yau da gobe, yanada wadatar zuci da bai amince ya zauna roƙoba, duk wahalar sana'a yana ƙokarin ganin yayi ya samawa iyalansa abinci, da abinda zai kula da iliminsu, dan ya tashi zuciyarsa nason ƴaƴansa suyi karatun boko, amma ga sauran ƴan uwansa sam ba haka baneba, sun tsani ilimin boko, a ganinsu watsa tarbiyyar yarane kawai, inda yana da kyau da iyayensu suma sun sakasu ai..
Hamza yasha zaunar dasu ya fahimtar dasu banbancin zamanin yanzu da nasu daya shuɗe, sai dai sam sunƙi fahimtarsa, hakanne ya sakashi ƙyalesu kawai.
Shi ƴaƴansa Suna zuwa makarantar boko ta gwamnati tamkar sauran yara, sannan da yamma suje islamiyya, da dare suje allo.
Rayuwa ta shuɗa inda malam Hamza (Baba) ya fara aurar da ƴaƴansa, Maryam ita aka fara kaiwa ɗakin miji, sai Rahama da suka tashi sa'anni da Ahmad, daga nan sai Raheenatu.
Shima Yusha'u ya aurar da Binta, wanda bayan bikin da kwanaki kaɗan yace zai kara aure.
Tashin hankali kenan, da ga mama Gaje, wadda tai tsalle ta dire akan bai isaba, ita tafi ƙarfin zama da kishiya wlhy.
Rigima tayi rigima har takai Yusha'u ya saki Gaje da cikinta ɗan wata bakwai.
Wannan shine sanadin barin Gaje gidan, shikuma yayo aurensa.
Daga nanne suka sami zaman lafiya, kowa ya koma mutunta ɗan uwansa a gidan.
Amaryar Yusha'u ta sinkuto masa ɗiya mace bayan shekara ɗaya, wadda taci suna Umm-Rumana.
Ƴaƴan Baba Hamza mata daya aurar Dukansu iyakarsu sakandire aji uku yake musu auren, dan haka Ahmad ne ya fara wuce aji uku na sakandire a gidansu.
Ahmad ƙyaƙyƙyawan yaro mai cikar halittar asalin rumawan katsinawa, komai nasa mahaifinsane, yanada ƙwazo a makaranta ga rashin hayaniya, dan sam da wahala kaji ance ga abokin faɗansa, inhar kaga yayi faɗa to ankaisa maƙurane, dan yanada zafin zuciya idan aka kaishi ƙarshe, sannan idan yay fushi da abu Ayyah ce kawai ke iya lankwasashi cikin sauƙi.
Dan Ahmad ɗan gatan Ayyah ne sosai, duk abinda kaga Ahmad ya nema ya rasa sai dai idan Ayyah bata da ƙarfin siyensa, shima kuma saitayi ƙokarin saya masa makamancinsa, harya fara zama saurayi komai nashi yana ɗakinta, tsakaninsa da mahaifiyarsa kuwa gaisuwace kawai, dan kallonsa ma bata iyayi saboda kunyar ɗan fari.
Ya daɗe baisan ba Ayyah ce ta haifesa ba, da yasani kuman ma bai damuba, abinda kawai ke bashi mamaki kawaicin mahaifiyarsu, dan sam bata sakewa dashi, tun abun bai damunsa harya ɗan fara damunsa, amma daya ƙara hankali sai ya fuskanci ba sonshi bane batayi kawai al'adace irinta hausawa, tunda itama Ayyah ai bata kula yayarsu Maryam, komai sai gwaggo.
Tun Ahmad na sakandire aji ɗaya suka haɗu da Samina, an tashi makaranta sun nufo gida shi da su maryam sai suka iske yara na damben faɗa a wani lungu.
Maryam tayi ƙoƙarin rabasu amma ta gaza, hakan yasa Ahmad ɗaukar ƴar bulala ya tsutstsula musu a ɗuwawu, dole suka rabu kowa na shafa wajen yana kuka.
Yarinya ɗaya a cikinsu sai ta maido faɗan akan Ahmad daya dokesu, tsayawa yay kawai yana kallonta da mamaki, dan alokacin shekarun nata bazasu gaza bakwai ba, inma sun wuce sai dai ƴan wattani.
Kuka take kashirɓan akan saita rama dukan da yay musu, ta kama ƙasan rigarsa ta riƙe tana kai masa duka da ɗan hannunta.
Shi dariyama ta bashi, dan haka ya tsaya yana kallonta yanayi, ganin da gaske take sai Rahama ta kamata ta janye tana dungure mata kai, nanko yarinya takuma daddagewa ta fasa musu kuka harda zagi.
Sunyi mamakin rashin kunyarta, suka wuce suka barta tana cigaba da zaginsu.
Washe gari sun taho makaranta suka gamu da yarinyar jiya da ko sunanta basu saniba, tana ƙyalla ido taga Ahmad saita samu dutse ta jefa masa, aiko sai akan goshinsa, kafin kace kwabo sai jini.
Dole aka kaisa ƙyamiz daga nan makaranta, yarinyar kuwa ta tsere gida basu sake ganintaba.
Bayan kwana huɗu Ahmad ya samu sauƙi ya koma zuwa makaranta, a randa ya koma yakuma yin gamo da yarinyar nan a hanya ana faɗa da ita.
Tsayawa kawai yay yana kallonta, ya kula batajin magana sam, tana ganinsa ta kwasa da gudu zata tsere, amma saiya cafkota, kuka ta saka masa da magiyar yayi haƙuri.
Shiko ya zare mata idanu yana faɗin, saiya rama zubar masa da jini da tayi.
Sosai take kuka tana tsalle da bashi haƙuri, shiko ya tsaya kawai yana kallonta.
Ganin bazata nutsuba yasashi fadin, “Kinga nutsu na fasa ramawar”.
Tsayawa tai tana share hawayenta, tace, “Da gaske ka haƙura?”.
Kansa ya ɗaga mata alamar eh.
Hakan ne yasa ta nutsu, sai kuma takai hannu tana taɓa masa ciwonsa inda aka saka bandejin, dukta marairaice alamar jin tausayinsa.
Hannun nata ya janye yana murmushi, yace, “Kinga ai ya warke, yaya sunanki?”.
“Samina” ta faɗa har yanzu hankalinta nakan goshin nasa data fasa.
“Suna mai daɗi” ya faɗa yana miƙewa riƙe da hannunta, cikin makaranta suka karasa yana tambayarta ajinsu, sashen ƴan firamari ya kaita, saida ya kaita har cikin aji, ya ɗauki naira ɗaya ta ƙwandala ya bata a cikin kuɗin taransa naira uku da Ayyah ta bashi.
Tun daga wannan ranar sai yazam kullum Samina saita zo wajen Ahmad, tun su Rahama na mangareta har suka bari, dan shaƙuwace ta fara shiga tsakaninsu a hankali, harma takai ga Ahmad yasan gidansu Samina, dan anguwarsu ɗaya, sai dai ba layinsu ɗayaba, tsakanin makarantar su Ahmad da gidansu Samina babu nisa, shiko Ahmad gidansu da akwai ɗan nisa da makarantar.
Haka suka kasance a tare, idan Samina ta taho makaranta bata shiga sai ta jira Ahmad yazo, dayake makarantar firamare din kusa take da sakandire ɗin, shikuma shine zai kama hannunta ya rakata har ajinsu yakuma cire ƙwandala ya bata a kuɗinsa na tara.
Shaƙuwar dake tsakaninsuce tasa har Ahmad yasan gidansu Samina, wadda ashe bai saniba ƴar uwarsace ta jini.
Dan kuwa Samina ɗiyar Mama Gaje ce tsohuwar matar Yusha'u ƙanin Hamza daya saki da ciki.
Ashe bayan fitowarta ta haifi Samina sai tai aure a can garin Bauci, kuma da Samina ta tafi sannan tana jinjira, haihuwarta biyu acan zaman yaƙi daɗi ta kashe auren ta dawo kano da Samina, dan wancan mijin ya kwace ƴaƴansa.
Tunda kowa ya fahimci hakan a gidan sai ya fara jan Samina jikinsa, yayinda Ahmad yaytama Kawunsa Yusha'u naci akan ya dawo da mama gaje mahaifiyar Samina gidan dan ALLAH.
Da taimakon Ahmad daya kama kafa dasu Iya Ladi Mama Gaje ta sake dawowa gidansu, inda Samina da Ahmad suka kasance ƙarƙashin inuwa ɗaya.
A wannan karon Mama gaje da shirinta ta dawo gidansu Ahmad, dan kuwa sai da ta gama mallake zuciyar kowa musamman Malam Rabi'u da Iya Ladi.
Dawowarta kuma gidan ya sake ɗaukar sabon salon zama, sai dai kowa na dannewa da kawaici saboda yanzu akwai ƴaƴa a tsakani.
Da taimakon Ahmad dukan yaran gidansu suka samu shiga makaranta a yanzu, musamman ganin ita Samina tanayi tunda ba'a gidan ta tashiba.
A haka har Samina itama ta shigo sakandire ɗin dayake maza da matane a haɗe, hakan ya saka shaƙuwarsu ta sake ƙarfi mai ban mamaki, tana aji ɗaya yana aji biyar, amma ko yaushe suna tare, hakan yasaka abokansa suka fara kiransa da suna Sharukhan baban soyayya😂............✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan kafin a fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_Typing📲_*
*_🏃🏻♂️GUDU DA WAIWAYE.....!!_*
_(Shi ya kawo mugun zato)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*(2)*
.............Yakanyi dariya kawai, dan a sannan ba soyayyar bace a tsakaninsu, duk da dai ta musu kamu basu saniba.
Tun ana yaya da kawa har abin ya fara rikiɗa yana zama soyayya, soyayyarma mai ƙarfi da shaƙuwa, kowa ya san da hakan a cikin iyayensu kuma duk da iyayen Ahmad mata basuso hakaba saboda mugun halin Mama Gaje.
To Amma ya zasuyi da hukuncin UBANGIJI? Dole suka ɗauke idanunsu suka koma musu addu'a da fatan ALLAH yasa kar Samina tayo gadon halin Uwarta.
Bayan Ahmad ya kammala sakandire saiya fara bin mahaifinsa kasuwa wajen sana'arsa ta saida yadikan maza da huluna, amma sai baban yace da hakan ai gara ya koya koda sana'ar ɗinkice ko wani abun.
Ahmad ya aminta da hakan ɗari bisa ɗari, dan haka yashiga wani shagon koyan ɗinki anan bayan layinsu kusa da makarantar su samina.
kusancin da suka samune ya kara sake ƙullesu sosai, dan kullum daga gida Ahmad da Samina tare suke tahowa, saiya rakata makaranta zai dawo shago wajen aikinsa.
Sannan da an tasosu daga makaranta komi yake a shago sai ya ajiye ya rakata har gida, wataranma sake biyoshi shagon ta keyi, data shiga gida babu daɗewa zata fito wajensa su koma tare..
Ƴan shagon kan musu dariya, musamman da suke ganin sunyi ƙanana, badai za'ace za'ai musu aure a wannan shekarunba.
Lokacin da Baba ya fahimci wannan shashancin nasu sai yaytai ma Ahmad ɗin faɗa, yakuma ce karya sake ganin Samina ta bishi shago bayan ta dawo makaranta.
Yaji faɗan baba ya dakatar da Samina, amma dukda hakan wataran saita ɗan zagaya a ɓoye taje, musamman ranar weekend da babu karatu.
Shekararsa ɗaya a shagon aka yayesa, zuwa lokacin kuma ya kware a aikinsa sosai dan ya nuna ƙwazo matuƙa.
Ayyah ta fasa ɗan asusunta da takeyi da ribar kayan sana'arta ta siya masa keken ɗinki, yayi murna sosai, hakama yan uwansa sunyi farin ciki, wani ɗakin dake cikin gidan aka fasama kofa ta baya aka saka masa keken ɗinkin, sai yazama shike ɗinkama baba yadika ana kaiwa kasuwa a siyar ɗinkakku, sai kuma masu kawowa da yakemawa, harma na mata yana dan jagulawa dukda bai wani ƙwareba saboda dinkin maza ya koya.
A hankali hannunsa ya fara faɗawa akan dinkin matan ma, kafin kace mi komai ya zama Alhmdllh, harma yana taimakawa gidansu da abinda ALLAH ya hore masa, gefe kuma yanama Samina hidima sosai dasu ta karatu da buƙatun yau da kullum.
Ganin yasamu madogara kuma yana samu Alhmdllh sai yay aniyar komawa karatu.
Kowa ya bashi goyon baya, dan haka ya shiga kokarin neman gurbi a jami'ar b.u.k.
Ya samu shiga jami'ar B.U.K, dayake takardunsa sunyi ƙyau sosai, kuma a lokacin tsadar rayuwa batakai hakaba sosai.
Komawarsa makaranta yasakashi sake zama busy, ko ɗinkima sai yayi da gaske yake samu yaɗanyi, ga kuma aikin yana samu, ganin zai iya korar customers ta wannan hanyar sai ya fara koyama ƙaninsa Mudanseer shima, aiko Alhmdllh Mudanseer ma sai ya maida hankalinsa sosai, sai ya zam yana taimakawa Ahmad ɗin da wasu ayyukan.
Tunda Ahmad ya shiga rayuwar Samina ya fara canjata sai baba Yusha'u kejin daɗi sosai, dan abubuwa da yawa sai Samina tabar biyema mahaifiyarta, dan a hannunta ta tashi, lokacin da mama Gaje ta dawo gidansu Ahmad sai tarbiyyar Samina ya banbanta dana sauran yaran gidan.
Daɗin hakan da Baba Yusha'u ya jine ya sashi zaunar da ƴan uwansa duka a gaban iyayensu su iya ladi, aka kuma kira masa Ahmad da Samina, a gaban kowa ya kuma sake damƙa ma Ahmad amanar kula da Samina, tare da alƙawarin aura masa ita a duk lokacin da suka kai munzalin girma, ya kumace ko bayan babu ransa bai yarda wannan alƙawarin ya tashiba.
Murmushi kawai Ahmad yayi kansa a ƙasa saboda kunya.
Yayinda sauran ƴan uwa da tsoffi su malam Rabi'u wannan abu yay musu daɗi, dankuwa koba komai zumincin ƴaƴansu zai ƙara danƙo da ƙarfi.
Albarka kowa ya sakama abin, tare da addu'ar kaiwa lokacin da rai.
Tun daga wannan lokacinne kuma Samina bata kula kowanne namiji, kowa yasan an mata miji Ahmad, hatta da danginsu na Shema kowa yasan hakan.
Mama Gaje dai batace hakan bai mataba, bakuma taji a ranta zuwa nan gaba idan Samina ta sami wanda yafi Ahmad zata hanata barin Ahmad ɗinba, idan kuma Ahmad yayi arziƙi dama ta dawo hannunta, dan kuwa sai yanda tayi dasu Ayyah akansa.
Tunda Ahmad ya gama secondary ya koya ɗinki yana kama ƴan kuɗaɗe sai nauyin Samina ya kusan koma kansa, shine duk wani bukatunta na makaranta, shine dinkinta da bukatun yau da kullum na ɗiya mace, hatta dasu kayan ciki na mata bai gazaba wajen bata kudin saye.
Wannan hidima da yake da ita sai ta ƙara saka mata girmansa da ƙaunarsa a zuciyarta, bata da hira sai ta Ahmad, duk wani namiji a idonta mace ne, Ahmad ɗintane kawai take kallo da gashin arziƙi, shine kuma kawai nagartaccen namiji a idonta.
Bayan samina ta gama secondary lokacin Ahmad na shekararsa ta ƙarshe a jami'a sai yake bata shawarar komawa karatu.
Lokacin suna zaune a ƙofar gidansune a shagon ɗinkinsa suna hira, dama mafi yawan lokuta anan suke hirar tasu.
Kallonsa tayi da ɗan murmushi ta dukar da kanta ƙasa saboda kunyarsa, cikin muryarta mai cike da yanga tace, “Haba Hubby, kamar ka manta yanda al'amuran suke a gidannan namu, idan nace zan cigaba da karatu yanzu a ina baba zai samu kuɗin ɗaukar nauyina?, kullum ana haɗa na masara da ƙyar a ina za'a samo na karatu kuma?, sannan a ziri'ar mu kaf babu macen data taɓa gama secondary sai nifa, shima da taimakonka, saiko ƙannenmu uku mata da ayanzu suma zasu kammala, iyayenmu ma bazasu amince naje jami'a ba nima nasani”.
Murmushi Ahmad dake kallonta da tausayawa yayi, ya sauke ajiyar zuciya har lokacin idonsa a kanta, a hankali yace, “Samie na ai komai na ALLAH ne, indai kina da ra'ayin karatun baki da matsala, dan ba baba zamu dorama wannan nauyinba, nine zan ɗauki nauyin matata da kaina, kinga insha ALLAHU idan ubangiji ya shige mana gaba sanda zaki kammala ƙila koda karamin aikine na samu, sai maganar aurenmu ko, kodama baki gamaba inhar aka samu ɗan abin rufin asiri sai mu rufama kanmu asiri a wankemu a miƙamu daga ciki kowama ya huta”.
Maganarsa ta ƙarshe ce ta sakata jan hijjab ɗinta ta rufe fuskarta saboda kunya tana ƴar dariya.
Shima dariyar yayi mai sauti yana shafa kansa, yace, “Sorry bazan sake bama matata kunyaba, ammafa randa aka kaimin ita zan cire kunyarnan dukanta insha ALLAHU”.
Babu shiri Samina ta tashi ta gudu zuwa gida, duk kiran da Ahmad yake mata akan ta dawo su karasa magana kasawa tayi, dole ya haƙura ya ƙyaleta.
Daya shiga gidan suka haɗuma da sauri ta kauda fuska taƙi kallonsa, lokacin suna a tsakar gida itada su Rumana suna shafa kurkur a fuska.
Murmushi kawai yay yana ɗauke kansa, dan baya wasa da yaran gidan, idan ka cire Samina babu mai yawan ganin haƙoransa a cikinsu.
Duk sannu sukai masa, ya amsa kamar yanda ya saba, sai da yazo gab da shiga sashensu ne suka haɗa ido da Samina data saci kallonsa.
Ido ɗaya ya kashe mata yana murmushi, tai saurin ɗauke kai tana murguɗa masa baki.
Shigewa yay yana maijin nishaɗi da ƙarin kaunarta a ransa.
Da daddare Samina take sanarma mahaifiyarta yanda sukayi da Ahmad.
Mama Gaje da daɗi ya lulluɓe ta washe baki tana rungume Samina.
“Yo Samina wannan kuwa abin amincewane da guduma, damacefa tazo mana, ai wannan yaro bamusan abinda zamuce masaba a rayuwa, ALLAH dai ya saka masa da alkairi, yakuma kaimu lokacin aurenku, dan kuwa Suwaiba ta haifama Ruƙayya, niko Ruƙayya ta rainar mini”.
Duk da Samina bata fahimci zaurencen mahaifiyarta na ƙarshen maganarba Babu kunya ta amsa da amin, dan tana tsananin son Ahmad da har takai batajin kunyar yin duk wani abun daya shafesa a gaban kowa, iyayensu maza kawai take iya ɗagama ƙafa akan Ahmad.
Hatta kakanninsu Iya ladi da baba Rabi'u bata jin kunyarsu akan Ahmad.
Sai washe gari Ahmad ya samu saƙo a rubuce daga wajen Samina akan amsar cigaba da karatunta.
Yaji daɗin hakan sosai, a ranar kuma ya samu su baba da batun su duka harma da kakanninsu.
Da farko dai tsoho mai ran ƙarfe malam Rabi'u har yace a'a, danshi kam baiga dabara ba a wajen nan sam.
Amma sai Ahmad yayta lallashinsa da nuna masa ra'ayinsa akan matarsa tai karatu mai zurfi, tunda yanzu suna da dama saita fara kafin shi yaɗan samu madogarar da za'ai hidimar aurensu, in yaso ita saita ƙarasa karatun a gidansa.
Fatan alkairi yay musu, tunda ya fahimci Ahmad nason lamarin, bai kamata a katse masa hanzariba matsayinsa na babba namiji a gidan.
Kwana biyu dayin zancen Ahmad ya amshi takardunta ya tafi dasu makaranta.
Tun daga ranar Ahmad yashiga faɗi tashi wajen ganin ya samawa Samina gurbin karatu, kasancewarsa mai ƙokari a makarantar yasashi kusanci da mafi yawan malaman cikinta, ta hanyarsu ya samawa Samina gurbin karatu.
Lokacin da labarin hakan yazo mata tayi farin ciki harma ta rasa ina zata saka kanta dan daɗi.
Hakama iyayensu kowa yaji daɗi, babu kuma wanda ya nuna rashin dacewar hakan, dan a ganinsu Ahmad ɗin yanada ra'ayin matarsa tasamu karatu mai zurfi shiyyasa ya maida Saminar makaranta.
Sauran ƴan uwantama ƴammatan gidan sun tayata murna da wannan cigaba, koba komai suma zasu saka ran cigaban tunda aka fara daga kanta.
Nauyin karatun Samina daya dawo kan Ahmad sai ya sa abubuwa suka sake masa yawa, dan kuɗin shigarsa basu kai nauyin ɗukar hidimar da yakeyiba, gashi dai-dai da kuɗin mota wannan sai Samina tazo wajensa take amsa. Ga nauyin karatun Mudanseer ma shine yake bada mafi yawan ƙarfinsa, dukda mahaifansu na taimakawa tanan ɓan garen.
Kuma a gefen hidimar gidama baya zuba ido baneba, yanayin ƙoƙarinsa wajen taimakon mahaifinsu.
Wannan abubuwan da sukaimasa yawane ya sakashi fara tunanin faɗaɗa neman kuɗin nasa, akuyarsa da ya saya Ayyah na kula da ita yace zai saida ya zuba kayan ɗinki na saidawa, saboda akuyar ta haifi yara biyu sai Ayyah ta amince masa aka saida, da kuɗin akuyar yaɗan sayo kayan su zare da wasu ƙananun abubuwa irinsu allura, almakashi, zips da sauransu ya zuba a shagon, teloli dake cikin gida da masuma shagunan dake kusa sai sukanzo sukan saya anan, kamar wasa sai ALLAH ya sakama abin albarka ake ciniki, idan duk suna makaranta sukan ɗan ɗebo kayan sayarwar a ajiye cikin gida, duk wanda yazo saya sai yayi sallama a bashi.
Ahmad bai tsaya ananba kawai, har komawa yay idan ya taso makaranta ya sari lemuka ya ɗora a kansa yana zuwa bakin titi saboda motoci masu wucewa, wani lokacin kuma biredi, ko kayan fruits haka.
Da waɗannan sana'oi da wahalhalu Ahmad ya cigaba da kula da karatunsu shi da Mudanseer da samina, sauran ƙannensa ma yakan basu gudunmawa, hakama yayunsa dake gidan aure sukan taimaka masu da abinda ALLAH ya hore musu.
Ahmad ya kammala degree ɗinsa ya samu yay bautar ƙasa, daga nan kumane ya dawo zaman gida sosai, dan babu dai maganar aiki.
Yaci gaba da sana'oinsa na ɗinki da saida kayan ɗinki, zuwa yanzu kuma hannunsa ya faɗa sosai ya ƙware, ɗinkuna yake na zamani masu birgewa, duk wasu samari ƴan kwalisa da ƴammata zaka samu ɗinkinsu ya fitone daga shagon Ahmad, wanda aka fi sani da Ahmad sharukhan, idan ɗinki yaɗan kwanta saiya koma sana'arsa ta sai da lemo da ruwa, kokuma kayan fruits.
Yanzu dai haka takai Ahmad yana hayar keke napep ne, yay ɗinkinsa da yamma ko dare, da safe zuwa la'asar yana neman taro da kwabo da adaidaitarsa a gari.
Matsala ta farko data fara shigowa tsakanin Samina da Ahmad shine, bayan barinsa makaranta Samina tayi sabbin ƙawaye, sanda yana nan koda yaushe suna tare, sai dai lokacin karatune zaka samesu ba tareba, duk wanda ma yake mu'amula dasu yasan suɗin masoyan junane.
Samina tun tana secondary takanyi karatun novels ɗin hausa, rayuwar jin daɗi da dukiya da akeyi a novels na ƙayatar da ita, har wani lokacinma takanyi addu'ar ALLAH ya buɗama Ahmad ɗinta shima yay arziƙi ya gina musu ƙaton gida, ya narka musu kayan alatu da jin daɗi, su ringa hawa motoci na alfarma ita dashi.
A wancan lokacin burin nata bai taɓa kaita ta nemi canjin Ahmad da masu irin suffar jaruman littafiba, shiɗin dai takema addu'ar ya samu su mora.
Takai koda Samina ta karanta littafi sam bata wani damuwa da ɗaukar darussan rayuwa ko ilimin da littafin yazo dashi, ita kawai soyayya da kayan ƙawane ke ɗaukar hankalinta da ƙara faɗaɗa burinta, tama kai inhar buk bana masu ƙazamin arziƙi bane ƴan gayu batason karantawa, data fara karatun taji ana faɗin jarumin littafi nashan wahalar neman nakansa sai buk ya fitar mata akai ta ajiyeshi, tafi son taji ana suffanta ƙyawun jaruman littafi tare da dukiyar da tunani bazai iya musaltawa ba, to takanji kamar tai tsalle ta ganta a buk ɗin saboda shauƙi.
Haɗuwarta dasu Nafy ne ya fara nuna mata hanyar samun cikar wannan burin nata, tun tanajin haushin kushe mata Ahmad da sukeyi akan talaucinsa har zuciyarta ta fara rawa da aminta da maganarsu.
Dan kuwa dai sunyi nasarar fara tsundumata shafe-shafen mayukan bilicin, dukda kuwa tanada haskenta gwargwadon iko, sannan Samina ƙyaƙyƙyawace babu laifi.
Ƙananun burikan Samina sun fara faɗaɗa, dan yanzu kowane biki saita san yanda ta ƙwalkwali Ahmad kuɗin ankonsa. Ada bata kula kowane saurayi sai Ahmad, amma zuwa yanzu kam ai samari babu iyaka take kulawa, dataga kazo da ƴar kalar manyan mutane babu wani jan aji take miƙa kanta.
Tun Ahmad na zuba mata idanu akan ƙananun sabbin ɗabi'unta harya kasa haƙuri ya tuhumeta akan bilicin data fara, ya tabbatar masa shi bama ya ra'ayin farar mace, yafisonta da kalar fatarta choco color, alokaci haƙuri tabasa, ta shirya masa ƙaryar ba bilicin baneba, kayan gyaran jikine irin namu na gida take amfani dashi.
Cayay kosu ɗinne tabar amfani dasu sai sunyi aure ya yarda da ingancinsu.
Ta amsa masa da to, amma tana bama su Nafy labari sai suka zugata akan ai ba aurenta yakeba, taci gaba da abinta, gashinan harta fara zama big girl shine zata wani biye masa, inharfa bazata cire tsoron Ahmad a rantaba to bazata taɓa wayewaba ta zama cikakkiyar ƴar jami'a balle shima ta maidoshi kan hanya su shinfiɗa ƙyaƙyƙyawan rayuwa irinta jaruman littafi🤦🏻♀.............✍🏻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_Typing📲_*
*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*(3)*
...........Da waɗannan shawarwarin dukkan ginin Ahmad ya fara rushewa ga tarbiyyar Samina, ta fara biyema ruɗin su Nafy, idonta ya fara buɗewa da rayuwa ta manyan yara masu aji, duk wani dandalin wayewa suna wajen matsayin manyan baƙi masu lokaci, wannan damar samarin jami'a ƴan ƙwalisa da lectures suka samu wajen shiga jikin su Samina, sai ga ƴaƴan manya masu abin magana a aljihu sun fara kutso kai cikin rayuwarsu.
Tunanin Samina ya fara bata cewar lallai Ahmad bazai zama dai-dai da burinta na rayuwar Jaruman novels ba, saboda har lokacin dai ana nan jiya iyau, buga-bugar sana'a ce dai kawai a samu na yau na gobe sai an fita nemansa, suturar kirki wannan ta shiga taro Ahmad bashi da ita, gaba ɗaya kayan nasa duk yadin (Tashi sama sallau) ne, idan ƙananun kaya ka gansa dasu ma dai na gwanjone ba sabbi ba, ƙyawune kawai Ahmad ɗin zai iya mata burga dashi.
A samarinta kuma na yanzuma akwai waɗanda zasu iya linkashi ƙyawun, ga kuɗi na gaske suna mata wasa dasu, wanda suka fara lulluɓe zuciyarta dana mahaifiyarta wajen mance alkairin Ahmad a garesu.
Duk tsiyar da Samina ke aikatawa mama gaje ta sani sarai, kwaɗayin abinda Samina ke kawo musu na ciye-ciye ne ya lulluɓe idanunta ruf.
Idan cikin samarin Samina wani yace zaizo bata kawoshi gidansu, sai dai ta kaisa can gidan kakanninta da suka haifi mama gaje.
Hakan yasa Ahmad baisan mi Samina ke aikatawa ba, dan bai taɓa kawoma ransa zata kula wani saurayi bayan shiba, musamman da yasan akwai alƙawarin aure a kansu da ƙaunar juna mai ƙarfin gaske.
_________________________
A yanzu haka Saminar na gidan kakarsu, taima Ahmad ƙarya Inna mari bata da lafiya dan kawai tasamu taje wani bikin ƙawarta da za'ayi.
Sai dai tsoron kar wani yakai masa gulma yasata kiransa a waya ta sanar masa cewar zataje wajen kamun bikin ƙawarta.
Bai musa mataba ya barta, amma yace ta jirasa yazo da mashin ɗin Sufyan zai kaita.
Hakan ba ƙaramin haushi ya bataba, amma yaya ta iya dashi.
Shiri take da sauri-sauri gudun kar Ahmad yazo ya sameta a gidan...... Dan tafison su tafi tare dasu Nafy, kiran da taji Iya kishiyar kakarta Inna mari na ƙwala mata daga waje yasa gabanta faɗuwa, tasan dai yanzu haka Ahmad ne yazo.
“Samina!, Samina!!, Wai Samina baƙya jinane kokuwa lalatar takice ta motsa ne?”.
Ta sake jiyo muryar iya daga tsakar gida.
Cikin cuno baki ta fito daga ɗakin dake can cikin wani lungu tana gyara ɗaurin ɗankwalinta ture kaga tsiya tana kumbura fuska.
“Kai Iya, irin wannan kira haka saikace na mafarauta, ɗan kwalifa nake ɗaurawa saboda su Nafy zasuzo yanzu mu wuce, mi kuma zan miki?”.
Baki iya dake tsaye bakin murhu tana ƙokarin hura wuta ta riƙe, “Samina anya wannan rayuwar ta dace dake kuwa? Baƙya ganin kinason wuce gona da iri? Yanzu nan kodan yaron nan Ahmad ai ƙyaɗan sassauta wani abun, wlhy kibar biyema lalatattun yarancan su Nafisa karsu kaiki su baro”.
Baki Samina ta ɗan taɓe tana gyara zaman gyalen kafaɗarta, “Iya nifa wlhy banajin daɗin irin maganganun nan naki, ni mi nakeyi mara ƙyau a rayuwata dan ALLAH?”.
“Ba nace kina wani abu mara ƙyau bane ba Samina, Inason dai ki tsaya matsayinki kodan Yaronnan da ya gama wahalar duniya a kanki, karsuje su hure miki kunne akan ɗabi'u mara amfani”.
“A'a Atine, anface ka fadi alkairi ko kai shiru, dan Ahmadu yaymata wahala sai akace bazata mori ƙuruciyarta ba? Naga ba aure aka ɗaura musu ba alƙawarin auren ne kawai ko?”.
Wata dattijuwar tsohuwa mace dake fitowa daga bandaki ta faɗa tana ƙokarin ajiye butar hannunta.
Su duka kallonta sukayi.
Iya tace, “Amma dai Mari ai kowa yasan dama ALLAH shine yake yanda yaso ga mutum, amma kinsan ta yaro ƙyau take bata ƙarko, tunda har da alƙawarin auren, wataranama ɗaurawa za'ayi kamar yanda muke fata
“Uhm Atine, mubar wannan batunma dan ALLAH, dan yanzu ba lokacin yinsa bane, ni dai abinda nasani kawai shine bazamuyima yarinya auren doleba, idan tace Ahmad takeso zamu bata, idanko ta kawo waninsa shima zamu bata”.
“Hakane Mari”.
Iya ta faɗa tana ɗauke kanta daga garesu ta koma ƙoƙarin hura wutar data fara.
Daga Samina har inna Mari kakarta harar Iya dake duke sukayi.
Samina ta maida kallonta ga kakar tata tana murmushi, “inna mari bara naje karsu Nafy suyita jirana, kinsan za'a fara kamun ƙarfe uku na yammane”.
“To Samina ALLAH ya tsare, a dai dunga kula saboda ƴan saka ido, kana rayuwarka baka damu da kowaba saikiga anata ƙokarin taɗo ƙafarka da harshe, bayan ko MANZON ALLAH ma yace mu kiyayi harsunanmu”.
“Humm Inna ai mutanen duniya ba'a iya musu, sunfi son kullum su ganka jiya iyau, kuma idan arziƙin kayi sune zasu fara zakalkalewar kai nasune”.
“Maganarki na kan hanya wlhy ƴar albarka, kedai jeki karki makara”.
“Okey my sweet kakus bye”.
“Duk da ban iya turancinba Samina, nima bye”.
Ficewa Samina tayi tana dariyar zancen kakar tata.
Itama inna mari ta shige ɗakinta tana ƙyalkyata dariyar sake ƙular da kishiyarta iya Atine.
Murmushi kawai Iya tayi, tasan duk ita akema habaicin, ta girgiza kanta tana nemawa abokiyar zaman nata da jikarta shiriyar ALLAH, tare da fatan ganewa kafin guri ya ƙure musu.
Kamar an saita Samina na fitowa daga ƙozajjen soron gidan kakanninta da Ahmad ta fara cin karo zaune bisa ɗan dandamalin dakalin dake ƙofar gidan maƙwafcinsu.
Ta tsaya tsam tana ƙarema kwalliyarsa kallo, tabbas Ahmad ƙyaƙykyawane, shiyyasa duk rashin tsadar kaya sukan zauna masa a ƙyaƙyƙyawar surarsa suyi ɗas.
Ba wani kayane mai tsada a jikinsaba, hularsa ƙube da ita kaɗai ta iya saninsa dashi ta ƙarshen gayunsa ya saka, ta zauna ɗas akansa, inda daga bayan ƙeyarsa kwantacciyar sumarsa ta jinin fulanin rumawan asalin katsinawa ta bayyana, sai yadi mai ƙarancin kuɗi mai kama dana ƴan makaranta kalar ruwan shanshan bale, takalmansa ƴan saƙe suma masu ƙarancin kuɗi, sai agogon fatar da itace ta saya masashi naira ɗari huɗu ɗaure a hannunsa da zoben azurfa a yatsansa, kayan sun ɗauki guga, dan haka suka kwanta luff tare da ɓoyewar tsufan da suka fara a idon mai kallonsa, ƙamshin turarensa yake mai ƙarancin kuɗi, amma akwai daɗi ga hancin mai shaƙa.
Ganinta ya sakashi miƙewa yana ƙawata nutsatstsiyar fuskarsa da murmushi na musamman.
“Barka da fitowa tauraruwar mata ma'abociyar haske da walwali”.
Samina ta kallesa a wani yatsine tana cuna baki gaba, ba tare data amsa masa kalmomin yabonsa ba ta maida murtani da faɗin, “Kai yaya, dama zakazo ɗin amma kaki kirana ka sanarmin kuma? Gashi nacema su Nafy su jirani a gidansu saimu tafi tare”.
Murmushi yaɗanyi duk da yanda tai masan ya bashi mamaki, “Yi haƙuri Samie na, banzo danna hanaki ƙyautata zaman tareba, nazone dama na kaiki basai kinsha wahalar jiran abin hawaba”.
Yanzu kam sosai ta juyi ta kallesa, cikin waro masa manyan idanunta tace, “Ka kaini kuma yah Ahmad? Da wane motan?”.
Huci yaɗan fidda mai ɗaci, dan ta fara ƙokarin janyo fusatarsa da wannan salon rainin wayon data ɗakko, amma kasancewarsa sonta na ɗawainiya dashi saiya sauke numfashi da ƙokarin hadiye dukkan fusatar tasa ya saki murmushi a karo na babu adadi.
“Banda abunki Samina ina naga mota, wannanma mashin ɗin Sufiyanu ne na aro danna sauƙaƙa miki wahala”.
“Tofa, to ALLAH yay mana maganinta ita wahalar, karka damu na hutar dakai, kaje kawai zamu tafine dasu Nafyn tunda kaga na musu alƙawarin binsu dan ALLAH”.
Wani irin bugawa yaji zuciyarsa tayi, sam baya ƙaunar alakar Samina da su Nafyn gidan ɗan-majillisa, amma ya kula yanzu dukkan hankalinta yana ga mu'amulantarsu. Ganin zata tafi yay saurin tsaidata ta hanyar faɗin,
“Okey to babu damuwa tunda kin samu abokan tafiya, ga wannan kozaki buƙaci wani abu a wajen”.
Har tayi niyyar wucewarta saita dawo baya jin ya ambaci kuɗi, babu kunya tazo ta amshe kuɗin dayake miƙomata canzazzu ƴan hamsin-hamsin rabin bandir ɗaya.
Godiya tai masa cikin ladabi, ta tura kuɗin a jakarta tare da sakar masa murmushi duk dan dai hankalinsa ya kwanta da barinta ta wuce ita kaɗai.
Ta ɗaga masa yatsun hannunta guda biyu alamar bye cike da wani salo.
Da kallo kawai ya iya binta tamkar wani soko, ya sauke ƙaramar ajiyar zuciya yana nufar roba-roba mashin ɗin dayazo dashi kalar jaa, hawa kawai yay ya zauna yana kallonta harta ɓacema ganinsa, yanda take tafiyarta cikin yauƙi da yanga sai sonta ya kuma nunkuwa a ransa, yanason Samina so irin mai tsanani ɗinnan, dankuwa dashi ya girma a zuciya tun baima gama sanin ma'anar SO ɗinba.
Ya ɗauki kusan mintuna talatin a wajen kafin ya hau mashin ɗin yabar anguwar da tunanin ina ya dace ace yaje, dan shidai a yanzu ya koma majalisar abokansa dariya zasuyi masa, yanda ya fito yana ɓare-ɓaren jiki zaije yakai Samina, sai gashi Samina ta watsa masa ƙasa a ido, bayan kuma dama kullum abokansa na nuna masa yanzu Samina ta canja, ta fara fin ƙarfinsa amma sam yaƙi fahimtarsu balle ya yarda da batunsu.
Yawo yaytayi a gari, sai da ya fahimci man ciki yayi ƙasa kafin ya koma gida.
Ya iske abokansa na hada-hadar shiga sallar magriba a massallaci, dan haka shima yay haramar yin alwala domin samun jam'i.
Bayan an idar duk suka fito ɗai-ɗai zuwa majalisarsu da suka kafa a ƙofar gidan su Yakubu abokinsu, saboda baranda dake wajen, shikuma yakubu yanada shagon littatafan hausane da yake bada rancin da saidawa.
Hannu suka shiga bama juna suna gaisuwa, Ahmad ya miƙama Sufyanu key ɗin mashin ɗin yana faɗin, “Broth nagode, ALLAH ya bada ladan zuminci”.
Amin suka faɗa a tare, yayinda Sufiyanu dake amsar key ɗin ke faɗin Sharukhan ɗinmu nazata fa sai dare zamu ganka ALLAH, Amma kunyi saurin dawowa kaida gimbiyar taka”.
Murmushin yaƙe Ahmad yayi kawai, ya kishingiɗa kusa da Musa yana bama Sufiyanu amsa da, “Ai ba yaune ainahin bikinba fa, kamu sukayi yau shiyyasa, sai jibinema ɗaurin auren, kasan mata da shegen son bidi'a, shiyyasa a kullum ake ƙara nisanta talaka da samun aure cikin sauƙi”.
Cikin damuwa Rabilu yace, “Maganarka gaskiyane wlhy Ahmad, ba gamunanba, acikinmu nan wanene bai isa aurenba, kuma duk munada ƴammata amma babu kuɗin yin auren, to wai muma fa kenan dakeda sana'oi munkuma ɗanyi karatun, inaga waɗanda basuda sana'ar babu karatun kumafa”.
Salisu daya zabga tagumi ya wani marairaice fuska yana harɗe kafafunsa dake lilo a ƙasan benci, “Abokai wlhy bidi'oin biki suna taka rawar gani wajen ɗora mata a burin auren mai hannu da shuni, tana kuma jefa rayuwarsu a garari harma da ƙara yawaitar fyaɗe, yanzu irina masu ƙarfin sha'awa idan baka danne zuciyarkaba ai tuni zaka afkama ƴar wani ka jefa kanka a halaka da ƴan uwanka a damuwa ko”.
Lumshe idanu Ahmad yayi a hankali, dan maganar Salisu ta sosa masa inda ke masa ƙaikayi, yace “Uhumm” kawai ba tare da ya ƙara komaiba.
Hakane ya saka Sufiyanu da Yakubu dake kusa dashi kallonsa.
“Sharukhan yaya dai?”.
Ameenu da tun ɗazun baice komaiba ya faɗa yana kallon Ahmad ɗin shima.
Buɗe ido Ahmad yay da suka canja launi zuwa jaa, yay murmushi kawai yana girgiza kansa.
Hakanne yasaka su cigaba da hirarsu akan matsalolin aure da burikan da mazan da ƴammata ke dorawa saboda son gasa da masu kuɗi keyi lokacin bikinsu.
Sallar isha'ice ta tadasu a majalissar, dukansu suka dunguma zuwa massalaci, akabar waɗanda zasu sake alwala irinsu Ahmad.
Bayan sun idar da salla zama sukai islamiyyar da suka tsarama kansu kamar yadda suka saba a kowanne dare, malam Sulaiman ne malaminsu, wato limamin massalacin, bayan ƙarin karatu yay musu nasiha kamar yanda ya saba.
Ƙarfe tara da rabi dai-dai suka fito, kowa daga nan gida ya shiga domin cin abinci.
Tsakanin gidansu Ahmad da majalissarsu gida biyar ne, hakan yasakashi takawa a hankali suna tafiya shida Salisu da shima gidansu ke maƙwaftaka da nasu Ahmad, suna isowa kowa ya shige.
Gidansu Ahmad gidane na talakawa irin masu ƙaramin ƙarfinnan sosai kamar yanda kukaji tun a farkon labarin, ginine irin na zamanin daya shuɗe, duk da dai yana mulmule da suminti har jikin bango, amma kallo ɗaya zakaima gidan ka fahimci ingantaccen ginin daya samune yasaka sumintin daɗewa bai zabtareba, saika shiga soro biyu kafin ka iso ainahin tsakar gidansu, amma a shiga farkon gidan zakaci karo da turken awakine da mahaifansu mata ke kiwo, sai kejin kaji daga gefe wanda baida nisa sosai da ƙofar banɗakinsu.
A shiga farkon gidan ɗakunan kakanninsu da aka zagaye da katanga zaka fara iskewa, sai sashen Baba Iliyasu daga bangon gabas, sai sashen Baba Yusha'u mahaifin Samina daga can Bangon arewa, suna kallon sashin kakanninsu, sai sashen iyayen Ahmad a bangon yamma suna kallon sashensu baba Iliyasu.
Tsakar gida zaka fara tararwa, sannan kabi siririyar hanyar da zata sadaka da ainahin sashen da matan Baba Hamza mahaifin su Ahmad suke.
Ya shafa kan tunkiyar daketa ɓara kuka saboda rashin ganin ɗanta kusa da ita, “K dan ALLAH ki rage ihunan, tunkiyarnan sam baki da hankali akan ƴaƴa, inama ya shiga shima uban ɓarnar” Ahmad ya ƙare maganar yana leƙa ƙasan kejin kajinsu kozai gano ɗan jaririn ragon tunkiyar.
Can kuwa ya hangoshi kwance, dan haka yasa hannu ya zaƙulosa ya kai gabanta ya ajiye kafin ya shige ainahin cikin gidan da sallama.
Mahaifiyarsa da ƴar kunya ke tsakaninsu saboda shine na fari a gabanta ya fara cin karo tana ɗibar ruwa a tulun dake ƙasan barandar ɗakunansu cikin kofin silba.
Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta tamkar batama gansaba, sai ƙannensa dake zaune a tabarma da fitila a gabansu sun baza littatafaine suka amsa masa, sai kuma Ayyah matar babansu ta farko dake riƙe dashi a ɗakinta data amsa itama daga cikin ɗakinta.
Ya gaida Gwaggo data gama zuba ruwan harta ɗora a tiren data shirya abincin babansu tana shirin ɗauka zuwa ɗakinsa, sau ɗaya ta amsa ta ɗauki tiren tai gaba abinta, yaɗan bita da kallo yana kauda kansa a lokaci ɗaya.....
Ayyah dake fitowa ta katsesa da faɗin, “Ɗan albarka ka dawo?”.
Murmushi yay mata yana ƙarasawa gabanta da cewa, “Eh Ayyah na, ina yini?”.
“Lafiya lau ɗan albarka, kaga tashi ga abincinka nan yau miyarka nasaka akai dole a gidannan, maza kaci karya huce, ga manshanu nan dana soya maka ɗazun”.
Cikin faɗaɗa fara'arsa ya miƙe yana faɗin, “ALLAH ya saka da alkairi Ayyah na, ya jiƙan malam ya ƙara muku nisan kwana da lafiya”.
Amin ta faɗa ita da ƙannensa.
Baba dake daga can ɗakinsa duk suna jinsu shi da gwaggo, ba yaune suka fara ganin hakanba, dan soyayyar Ayyah da Ahmad ALLAH ne kawai yasan iyakarta, amma ba mutumba, inhar ba faɗa maka akaiba bazaka taɓa ɗauka ba itace ta haifesaba.
Saman tabarmar da ƙanwarsa Sadiya ta shinfiɗa masa ya zauna, tuwone na jar masara dayaji dahuwa ta ma'iya, sai miyar tafasa da akayita da gyaɗa sai ƙamshi takeyi, ya buɗe kwanon langa ɗan ƙarami da manshanun ke a ciki ya zuba, tare da barbaɗa yajin daddawa da shikuma ke a robar cingam.
Laumar farko daya kai ya lumshe idanu saboda daɗin da miyar tayi, Zainab dake ajiye masa ruwa tai ƴar dariya ciki-ciki, “Yah Ahmad kaji miyar ta haɗu ko?”.
Idanunsa ya buɗe ya ɗaga mata kai kawai batare da yace komaiba.
Ayyah dake ƙoƙarin kunna redio ɗinta tai saurin faɗin, “To akku, ki tashi masa akai yaci abincinsa cikin salama”.
Baki Zainab ta kumbura tana barin wajen, hakan yay dai-dai da shigowar Mudanseer ƙanin Ahmad ɗin.
Sallama yay suka amsa, ya ajiye ledar hannunsa gaban Ayyah yana cewa, “Ayyah gashi nan inji Yaya Maryama, tace gobe insha ALLAHU zama tazo gidan”.
“Karma tazo” Ayyah ta faɗa rai a jagule.
Ɗago ido Ahmad yay ya kalli Ayyahn, kafin ya maida kan Mudanseer dake ƙoƙarin zama kusa dashi.
“Miya faru kuma da Yaya Maryaman?”.
“Yaya abinda kasani kullumne dai, faɗa suka sakeyi da kishiyarta shikuma jakin ya daki yaya maryama ɗin, amma sai batazo ta faɗaba tai shiru, sai ɗazunne Inna Haule tazo da zancen gidannan”.
Shiru Ahmad yay kamar bazai tankaba, ya tsame hannunsa daga abincin da yakeci yana ture kwanon silbar gefe, miƙewa yake shirin yi Ayyah tace,
“Ɗan albarka dama ka zauna kaci abincinka, itafa ta zaɓama kanta wannan rayuwar, mizaisa ku zauna kuna ɓata ranku a banza, maza koma ka zauna ka karasa ci”.
Komawa yay ya zauna, danba tarbiyyarsu bace jayayya da maganar manyansu, Mudanseer ya ɗauki ruwan dake gaban Ahmad yasha tare da wanke hannunsa, cikin kwantar da murya yace, “Yah Ahmad babu tayine? Bayan ga ƙamshin manshanu inaji ya cikan hanci ɗan gatan Ayyah”.
Hararsa Ahmad yayi, amma baice komaiba, hakanne ya saka Mudanseer ɗin yin murmushi ya saka hannu suka cigaba dacin tuwon, wanda a yanzu Sam Ahmad baya wani ci sosai saboda damuwar halin da ƴar uwarsa take ciki................✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_Typing📲_*
*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*(4)*
.............Har suka kammala babu wanda ya sake magana, Ayyah natajin redionta, su Zainab kuma na Assignment ɗin makaranta.
Ahmad ne ya fara tashi, bayan ya wanke hannu ya shiga ɗakin Ayyah, kusan mintuna biyar sai gashi ya fito hannunsa ɗauke da ƙananun kaya, dukda ya zama saurayi har yanzu kayansa na ɗakin, dukda kuwa sunada nasu ɗakin a ƙofar gida, takalman daya fita dasu ya ziro hannu ya ɗauka ya maidasu cikin ɗakin, sannan ya saka silifas ɗinsa dake gefe a wanke.
Ficewa yay daga gidan batare daya cewa kowa uffanba.
Ayyah taɗan rage sautin redio ɗinta tana kallon Mudanseer dake kwashe kayan da sukaci abincin.
“Mudan banso kayi maganar yarinyarnan gaban ɗan albarka ba, yanzun nan saiya saka abun a ransa kasandai halinsa”.
“Wlhy nima Ayyah sai bayan na faɗa na gane nayi kuskure, dan sai sauke ajiyar zuciya yake”.
Ayyah tai shiru cikin damuwa.
Ahmad kuwa yana fita ɗakinsu dake a soro na farkon fita daga gidan ya shiga, ya canja kayansa kafin ya ciro wayarsa da screen ɗin yay rugu-rugu saboda azabar lalacewa yashiga neman Number Samina, harta yanke ba'a ɗagaba, ya sake kira a karo na biyu nanma babu amsa.
Bai gajiyaba ya cigaba da kira, sai da yay mata kira na takwas ne ta ɗaga kamar a fusace.
Sautin kiɗan daya jiyo yana tashine yasakashi saurin faɗin, “Wai Samina kina nufin har yanzu baku koma gida bane?”.
Guntun tsaki ta saki yanda bazai jiba, daga can tana murguɗa baki da harar wayar, “Ai yanzu zamu tafi” ta faɗa a cinkin sanyin murya dan tsabar munafunci.
Kansa ya dafe yana gyara zama akan yololuwar katifar barcinsu, “Haba Samina, kinsan kuwa ƙarfe nawa yanzu? A matsayinki na mace ace kina waje har kusan sha ɗayan dare? Kina nufin da anan gidan kike zakikai wannan lokacin baki dawo bane? Koma shiyyasa kika tafi can ɗin danki samu lasisin yin yanda kikeso?!!”. Ya ƙare maganar a tsawace.
Sosai ta firgita, jikinta na ɓari cikin in ina ta shiga fadin, “To yaya amma kuma ni ba wani abu nakeyi mara ƙyau ba fa, Nifa wlhy wannan bin ƙoƙwanton da abokanka suka koya maka bana sonshi, ni dai subar haɗani dakai gaskiya, ahaka kake tunanin zamuyi aure babu yarda a tsakaninmu?”.
Leɓensa na ƙasa yaɗan ciza yana cewa, “K banason iskancifa, ni kike faɗama wannan banzar maganar...?”
Batama bari ya rufe bakinsaba ta katse wayar ta koma cikin rawa.
Innalillahi kawai ya shiga ambatawa da ɗunbin mamakin Samina, anya kuwa itace ma ta ɗaga masa wayar nan? To amma ai muryartace, kansa ya dafe cikin tsagwaron mamaki da damuwa.
Har Mudanseer ya shigo Ahmad bai saniba, Mudanseer dake tsaye kansa ya sake maimaita kiran sunansa a karo na uku,
“Yah Ahmad!!”
Aɗan firgice ya buɗe idanunsa dake a rine da duhu, tashi yay zaune sosai yana sauke tagwayen ajiyar zuciya, “Mudanseer yaushe ka shigone?”.
Zama Mudan yay kusa dashi cikin damuwa, “Yah Ahmad tunfa ɗazun na shigo, inata maka magana amma baka ko motsaba, halan zancen Yaya Maryam kasaka a ranka, kokuma yauma gimbiyar taka tayi wani tutsun?”.
Guntun murmushi Ahmad yay yana kallon ƙanin nasa, yaɗan taɓe baki yana ɗage kafaɗu, cikin ƙoƙarin kauda maganar Samina yace, “Mudanseer, dolene halin da yaya Maryam ke ciki ya dameni, bansan miyasa ta kafe akan wannan rayuwarba, inajin takaicin yanda a kullum mijinta ke mata dukan kayan wanki amma bazata faɗaba, shin wai ita wane irin sone har haka a tsakaninsu da bazata rabu dashi ba”.
“To ni wlhy Yah Ahmad nama kasa fahimtar wannan al'amarin nasu, kaga kuwa yanda yaji mata wani mugun ciwo a hannunta”.
Babu shiri Ahmad ya miƙe tsaye yana faɗin, “Ciwo kuma? Amma ta zauna bataje asibitiba?”.
“Wlhy batajeba in gaya maka, sai da naje na tasata gaba ƙyamis ɗin Shamsu, dama kuɗin ɗinkine ɗazun Farida ta kawo ina jira ka dawo na baka sai Ayyah taimin aike wajen yaya Maryam ɗin na iske halin da take ciki”.
Cikin tsagwaron takaici Ahmad ya jingina da bango yana lumshe idanu zuciyarsa na masa wani irin zafi, tsawon mintuna uku suna a haka kafin ya fice daga ɗakin yabar Mudanseer shima da nasa tunanin.
Shagon da suke ɗinki ya buɗe ya shiga, ta kowanne fanni ya rasa abinda ke masa daɗi, da ɗan hasken screen ɗin wayarsa yay amfani wajen haskawa ya nemo fitilar da suke kunnawa a shagon idan babu wuta, da yake suna cajinta da hasken rana ne, tayi ƙau da haske saboda ranar da aka zuba yau.
Ya sagalata jikin ƙusar da suke ajiyewa ya zauna a kujerar da tazama tasa, dan babu mai hawa wannan keken sai shi.
Ɓacin ran da yake cikine yasashi duƙufa kan aikin wasu kaya daya yanka tun jiya da hantsi, ɗinkin yake amma sam zuciyarsa bata wajen, tana can a tunanin Samina, ganinfa bazai iya daurewa ba saiya ja tsaki yana take keken ya tsaya da aiki, wayarsa ya ɗauka ya sake kiranta, ƙin ɗagawa tayi harta tsinke, ya ajiye wayar a wani yanayi.
Kamar zai haƙura sai kuma ya dai sake kira, tana gab da tsinkewa ta ɗaga.
Kafin yayi magana tace, “Na koma gida, harma na kwanta barci Hubby na, dan ALLAH kayi haƙuri ɗazun wayarce ta mutu ashe babu cajine”.
Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke murmushi na neman kuɓce masa, Murya a sanyaye yace, “To sannu da zuwa”.
“Uhumm” ta faɗa daga can.
Shiru sukayi su duka, jin hakanne yasa Ahmad cewa “Kiyi barcinki sai da safe, nima ɗinki nake ɗan ragewa”.
Kamar bazata amsa ba, sai kuma tace, “Ɗinki a daren nan Yah Ahmad?”.
Murmushi yayi mai sauti saboda jin daɗin nuna kulawarta gareshi wadda ta daɗe batai hakanba, yace, “To Samie na ya na iya, na kwance ai baiga gariba”.
“Hakane Yah Ahmad, amma dai kaje ka kwanta kaima, sai da safe”.
“Nagode My Samie” yay maganar a hankali tamkar mai raɗa.
Itako daga can baki taɗan taɓe tana ajiye wayar da maida hankalinta ga Ma'aruff sabon saurayin da tayi yau a hotel ɗin da sukaje wajen kamun ƙawarsu, shine ya kawota har gida a mota, koda suka iso sai suka zauna hira bata fitaba duk da kuwa dare yaja, dan kusan sha biyu ma.
Kallonta Ma'aruff yay yana ɗan ɓata fuska, “Shi kuma wanene wannan?”.
Ta ɗago manyan idanunta ta kalleshi da wani fari, “Karya dameka, yayana ne”.
“Yayankine amma kika nuna damuwarki a kansa harda kashe masa murya?”.
“Wannan duk farfaganda ce dan a rabu lafiya”.
Shiru yay baice komaiba, ganin hakan yasa ta ɗakko masa wata hirar.
Da yake shima ɗan duniyane sai ya basar da zancen suka ɗora hirarsu.
______________★★★★___________
Ahmad kam kalaman Samina ne suka ɗan sanyaya ransa, ya jingina da bango yana lumshe idanu, shi kansa baisan iya adadin son da yakema Samina ba, bashi da burin daya wuce a yanzu ya mallaketa matsayin matarsa ta aure.
Yayi zurfi a tunani ya tsinkayo muryar Baba na faɗin, “Amadu! Kai Amadu shin barci kakeyine a shagon wai?”.
“A'a baba”. Ahmad ya faɗa da sauri yana miƙewa tsaye.
A ƙofar shagon yaga baba tsaye, “Sannu baba, wani abu kake buƙata?”.
“A'a babu komai, na fitone zan rufe gida saina leƙa ɗakinku naga Mudan ne kawai a kwance, shiyyasa nai tunanin ko kana nan, nakumaji ba ɗinkin kakeba ashe?”.
Shafa kansa yay yana faɗin, “Eh wlhy baba, ɗinkin dai na fara sai kuma allura ta karye na tsaya sakawa, ashe babu mai ƙyau a shagon ma sai mun nemota da safe”.
“To ALLAH ya kaimu, ka rufe kaje ka kwanta hakanan, kanaji jiya sai da ɓarayi suka shiga gidan Alhaji mamman”.
“Wlhy kuwa baba, haka nima nakeji ɗazun da safe, ALLAH ya rufa mana asiri to”.
“Amin ya rabbi” baba ya faɗa yana juyawa gida.
Komawa cikin shagon Ahmad yay ya kashe fitilar sannan yazo ya rufe shagon ya koma cikin gida bayan ya rufe gidan.
Uzirinsa ya shiga bayi yayi, yay alwalar barci daya sabarma kansa kafin ya nufi ɗakinsu.
Mudanseer na ɓararraje a katifarsu yana jan nasharin barci, Ahmad ya shinfiɗa abin salla a gefe yana girgiza kai, salla ya tayar yay sha'i da wutiri, bayan ya kammala yay addu'oinsa ya cire rigar jikinsa dan sam baison kwanciya da kaya takura masa sukeyi.
Da ga shi sai boxer ya kwanta, bayan ya tura Mudanseer gefe da ƙyar saboda shima dai ƙatonne masha ALLAH.
Bargonsa yasa ya rufe jikinsa ruf har saman kai, dan komai zafi saiya lulluɓa yake iya kwanciya, sannan komai sanyi saiya cire kaya yake iya barci.
★★★★★★★★
Iya na zaune tsakar gida ta zabga uban tagumi tana jiran taga ta inane Samina zata ɓullo.
Inna mari kuwa babu ruwanta, tuni ta shige ɗaki tai kwanciyarta tana shaƙar barci.
Sai wajen sha biyu da kwata sabon saurayin Samina yay haramar tafiya, ya kalleta ido cikin ido yana wani narkesu a cikin nata.
Hakanne yasaka tsigar jikinta tashi, tai saurin janyewa ƙirjinta na wani irin bugawa, tabbas batajin magana, amma har yanzu rawar kanta bai taɓa sawa ta yarda wani namiji ya taɓa aikata mata wani abu mara ƙyauba koda runguma kuwa, duk da kuwa tana jin sha'awa sosai irin wadda kowacce mace mai lafiya kanji a lokacin da takai shekarunta.
“Babie zan tafi, amma babu abinda zan samu”. Yay maganar cikin raɗa kuma a saitin kunnenta.
Matse jikinta tayi kaɗan, muryarta naɗan rawa tace, “Yallaɓai kamar mi kenan?”.
Wani mugun murmushi ya saki yana sake matso da kansa jikin wuyanta, sai da ya busa mata iska a wuyan kafin ya kai hanci yana shinshinar ƙamshin turarenta, cikin raɗa-raɗa ya sake faɗin, “Komai ma na samu inaso babie”.
Yanda gashin jikinta ke miƙewane yasata ɓalle murfin motar ta fice ba tare data shiryama hakanba, ya bita kallo da idanunsa da suka fara rinewa yana murmushi, “Babie akwai wayo, shikenan na gode ga wannan kiyi amfani dashi wajen kwalliyar gobe”.
Kamar bazata amsaba sai kuma ta ƙyalla ido taga yawan kuɗin, wani irin taji a ranta, tai azamar miƙa masa hannu tana faɗin, “Nagode sosai, amma kamar sunyi yawa ka rage”.
Wata siririyar dariya yayi mai sauti yana dukan sitiyari kaɗan, ya maido kallonsa gareta har sannan da sauran dariyar a fuskarsa, “Babie nawanema waɗanan kuɗin da har kike tunanin sunmiki yawa? Ai ƙyauta bata yawa, yanzunma dan babu kuɗine a jikina shiyyasa, kinga shiga gida sai da safe”.
Kanta kawai ta iya ɗaga masa, ta wuce sim-sim kamar wata munafuka.
Sai da yaga ta shige sannan ya tada motar yabar wajen yana dariya abinsa.
Da sauri Iya ta miƙe tana kallon Samina data shigo kamar a tsorace, tai kanta tana faɗin, “Samina kinada hankali kuwa? Tafiya biki shine har sulisin dare?”.
Ƙaramar ajiyar zuciya Samina tayi, taɗan marairaice yanda iya zataji tausayinta,
“Iya wlhy mota muka rasa tun ɗazun, da ƙyarma muka samu wannan ta kawo mu”.
iya batace da ita komaiba, itama sai ta raɓa ta gefenta ta wuce zuwa ɗakin iyar ganin Inna Mari harta rufe ɗakinta ma ita.
Dan gidan nasu ɗaki biyune kacal sai runfar girki, ɗakin inna mari sai ɗakin iya Atine.
Iya dai bata yarda da maganar Samina ba, amma sanin bata da wani ƙarfin iko a gidan sai batace komaiba, ta ɗauki butarta ta zagaya ban ɗaki, koda ta fito ta shiga ɗakinta sai taga Samina na ƙoƙarin cusa abu cikin tsummo karanta na wanki data ƙule da safe zata aikama ƴarta dake aure ta wanke mata, saboda ita bata iyawa.
Nanma kallo ɗaya tai mata ta ɗauke kanta, ta haye gadon ƙarfenta rakuminka ɗaka tai kwanciyarta.
Samina kaɗai taita shigi da fici a tsakar gidan, sai da ta kammala shirin barcinta kafin ta kwanta kusa da iya a kan gado, babu abinda ke mata yawo arai sai haɗuwar sabon saurayinta.
Ya haɗu iyakar haɗuwar da zuciyarta ke tabbatar matama yafi mijin novels, da alama kuma sunada kuɗi kamar yanda kullum take mafarkinta akan mijin aurenta, ga ƙyaƙyƙyawar nasaba da itama take masa hasashe. Shin dama marubuta da gaske suke akwai mazan novels a zahiri kenan? A tunaninta koda akwaisu bazasu so ƴaƴan talakawa ba kamar yanda na littafi keyin soyayya da ƴanyan talakawa irinta, sai gashi a dare ɗaya tayi gamo da Ma'aruff. Ta lumshe ido a hankali, wani irin daɗi na kamata, yau gata zata mallaki mijin novel.....
“Yah Ahmad fa?”
Wata zuciya ta ambata mata acan ƙasan ranta, da ƙarfi ta rintse ido tana sama da ƙasa da numfashinta, dan wani irin faduwar gaba taji a ranta, tabbas tanason Ahmad, tanada tabbacin kuma yafi dukkan maza matsayi a ranta, sai dai bashida kwalitis ɗin da take buƙata ga namiji, tabbas tanason namiji ƙyaƙyƙyawa, Ahmad ƙyaƙyƙyawa ne, tanason namiji mai suffa mazan gaske, Ahmad yanadashi, tanason namiji ɗan gayu, Ahmad ba ɗan gayu bane, tanason namiji mai dukiya, Ahmad baya da dukiya, tanason namiji mai nasabar sanannan gida, iyayen Ahmad talakawane babu wanda ya sansu sai danginsu da iya jama'ar layinsu, tana so!, Tana so, tana so da yawa, sai dai Ahmad baida su, bai dasu da yawa.
Yaya zatayi kenan tunda a yanzu tasamu mai dukkan nagartar da ita take buƙata? Zatabar Ahmad ɗinne ta samu *CIKAR BURINTA?* kokuwa zata bar cikar burinta ta anshi *BUƘATAR ZUCIYARTA?......*
“K Samina wai mike damunkine haka?”
Firgigit ta dawo hankalinta, ta juya kwanciyarta tana faɗin, “Babu komaifa Iya, kawai ina lissafine na jarabawar dake tunkaromu kwanan nan, saboda Yah Ahmad yace na dage da karatu”.
“To ai bakiji maganar tashiba, tunda kinyi watsi da ita kin koma bin gidajen bikin da ba tsarankiba, Samina karki ruɗar da kanki, karki bari ƙarya ta lulluɓe ganinki, karki yarda da wasiwasin zuciya, kar dauɗar duniya ta toshe jinki da tunaninki, inba hakaba wlhy zakiyi *GUDU DA WAIWAYE...* ƙarshe kuma zai kawo miki *mugun zato ne* ga duk masu ƙoƙarin ɗora tunaninki akan *keken ɓera*”.
Shirun da Samina taji Iya tayine ya sakata gane ta gama, maganganun Iya sunyi tasiri sosai a ranta, sai dai sheɗaniyar zuciyarta na mata kutse cikin tunanin dake nuni da (A'a), baki ta ciza da ƙarfi kamar zata huda laɓɓanta, gaskiya tana buƙatar dogon tunani akan wannan al'amarin, idanma son samune harda shawara.
Da wannan tunanin ta ingije abun a ranta ta samu barci ya saceta mai cike da mafarkin Ma'aruff.😳🤫
*Washe gari*
Asubar fari Ahmad ya farka tamkar yanda ya saba, da addu'ar tashi barci ya buɗe idanu, ya miƙe zaune yana janye bargonsa tare da yin miƙa mai ɗauke da hamma, sai da yaɗanyi minti biyu a zaunen kafin ya miƙe da ƙyar, fitowa yay daga ɗakin nasu zuwa soro daga shi sai boxer ɗin, ɗan jujjuya jikinsa yay yanda ko ina zai motsa kusan na mintuna biyar, kafin ya koma ɗakin ya ɗauki jallabiyarsa ya saka ya ɗau buta zuwa cikin gida.
Babu wanda ya fito harya shiga bayi ya fito, ya zauna saman ɗan dutsin dake tsakar gidan kusa da kwatanniyar ruwan agwaginsa ya fara alwala.
Ayyah ce ta buɗe ɗakinta ta fito, ya kalleta yana kuskure baki, isowarta kusa dashi yay daidai da zubda ruwan bakinsa,
“Ayyah na kin fito?”
Yay maganar cikin yanayin muryar wanda ya tashi a barci, yana kai ruwa a hancinsa zai shaƙa.
“Eh ɗan albarka, ka tashi lafiya dai ko?”.
Sai da ya face ruwan daya shaƙa ya amsa da “Alhmdllh”.
Bayi ta shige ba tare data sake cewa komaiba, shima ya cigaba da alwalarsa.
Yana kammalawa zai miƙe Ayyah ta fito daga bayi, sai ga Gwaggo ma ta fito daga lungun ɗakin baba.
Itama barka da fitowa yay mata yana nufar hanyar soro.
Kamar yanda ta saba haka ta amsa cikin halin ko in kula.
Ahmad ya yarfama Mudanseer dake jan nashari ruwa a fuska, kamar kullum ya farka a fusace yana ƙun ƙunin faɗin,
“Kai yah Ahmad, kai yah Ahmad, ni ALLAH ka dainamin abunnan, sai kace wani ɗan riƙo kullum kaita tadani da ruwa?”.
“Kai dai ka sani uban ƴan mita, dilla tashi kai alwala mu wuce masjid, saura ka tsaya shegen kashinka na ƙa'ida harmu makara kamar jiya”.
Cikin tuttura baki Mudanseer ya ɗauki buta ya fita yana layin barci kamar zai faɗi.
Ahmad ya girgiza kansa kawai, sallar raka'atainul fijir ya tada kafin Mudan yagama kalularsa su wuce...........✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*(5)*
............A ɓangaren Samina kuwa sai da Iya tayi da gaske ta tashi sallar asuba, rashin kwanciyar wuri da batayiba yaja mata nauyin jiki, tana gama sallah ta koma ta kwanta a gado.
Iya kam fita tayi kamar yanda ta saba, duk da tsufanta haka tai gohon haɗa wutar kokon saidawa da takeyi da safe, saida ta ɗora holoƙon tukunyar da takeyi ta zuba ruwa sannan ta ɗau tsintsiya ta fara share tsakar gidan, kafin gari ya gama haske ko ina yayi ƙal har soro, tasa ruwa ta wanke bayinsu, dukda kasancewarta tsohuwa ta tsani ƙazanta.
Sai da taga gidan ya mata yanda takeso sannan ta haɗa wanke-wanke ta fara, a haka tukunyar kokonta ya tafasa, ajiye wanke-wanken tayi taje ta sheƙa kokon a botikin fenti guda uku kamar yanda ta saba, ta kimtsa gindin murhun tana maida dumamen tuwonsu, saita koma wajen wanke-wanken ta ƙarasa da sauri.
Waken ƙosai data ajiye ta ɗakko a ɗaki, har lokacin Samina na baje a gado tana barci, hakama Inna Mari na ɗaki duk kiciniyar aikin da Iya keyi tana jiyo ta amma tai zamanta, Sa'idu autan inna mari, ƙanin mama gaje kuwa yana ɗakin soro kwance shima ko sallar asuba bana tunanin yamaje yayi.
Iya ta surfa wakenta ta gyarashi tsaf cikin hanzarin da ALLAH ya bata, ta ɗauka a kanta ta fita markaɗe makwaftansu.
Sammakonta ya saka itace farko kullum, yauma dai ita ta fara buga gidan Rabi mai markaɗe. Mijinta yazo ya buɗe, kafin ya koma ciki ya tado rabin.
Kamar jama'a jira suke, sai gasu sunata shigowa markaɗe, sai da aka fara markaɗa na iya ta dakko ta dawo gida abinta.
Koda ta shigo babu wanda ya fito, bata damuba ta sauke tukunyar tuwon ta sata gefe inda zafin wuta zai dinga kai mata ta aza kasko a murhun tare da zuba man gyada ta yanka albasa a ciki.
Zaman buga ƙullun tayi, wanda yay jajir saboda kayan miyar da yaji, gishiri kawai ta saka masa tai masa bugu mai ƙyau, zuwa lokacin manta yayi zafi yanda take buƙata.
Duk abinda zata buƙata ta kawoshi kusa da ita sannan ta zauna suya.
A hankali mutane suka fara sallamar sayen koko da ƙosai, dan Iya gwanace akan tsafta da iya sarrafa ƙosai harma da kokon, hakan yasa kullum customers basa yanke mata, hardaga layukan bayansu da gabansu duk zuwa ake sayen kayan sana'arta, shiyyasa kafin wani dogon lokaci zakiga komai ya ƙare.
Sai da hayaniyar ƴan sayen koko da ƙosai ta cika gidan sannan inna Mari ta fito daga ɗakinta, babu kunya taje ta ɗeba koko da ƙosan ta koma gefe tanaci tana kallon yanda masu saye suka yanyane iya har tana neman ruɗewa.
Maimakon taje ta taimaka mata saita kauda ido tana taɓe baki.
A haka Sa'idu ya shigo gidan, buta ya ɗauka ya shiga banɗaki, zuwa can sai gashi ya fito, shima dai koko yaje ya ɗiba da ƙosai ba tare da ya gaida kowa a cikinsu ba ya koma ɗakinsa.
Har dai akaci cinikin nan aka tsire Samina tana barcinta.
Bata fitoba kuma sai da iya na wanke kwanikan data ɓata.
Bata ko kalletaba ta fice cikin hijjab, kusan awa guda sai gata ta dawo ɗauke da leda baƙa.
Iya na zaune tanacin tuwo Samina ta zari kwano da kofi a wanke-wanken da Iya tayi ta shige ɗaki.
Ajiyar zuciya kawai Iya tayi tana janye idanunta ta maida kan tuwonta dake mata dadi fiye da kilishin dayay sati biyu a tsume😢😞😋.
________________________________
Sai da gari ya ɗanyi haske Ahmad da Mudan suka shigo cikin gidan, dan tuni baba shi ya dawo tare da sauran ƴan uwansa, tsoho baba Rabi'u kuwa baya iya fita saboda ƙafa.
Ɗakin baban suka shiga, suka gaidashi cikin girmamawa, kamar yanda ya saba ya jaddada musu nasihar jin tsoron ALLAH a duk halin da suka tsinci kansu, tare da riƙe gaskiya a zamantakewarsu da kowa a rayuwa, su nemi gumin halak komai wahalarsa da ƙankantarsa, su saka a ransu albarkarsa na wajen UBANGIJI ba wayonsu ba, duk sauƙin Haramun su gujeta dan ita halaka ce, karsu zama masu biyayya wa jagorancin miyagun abokai akan harkokin banza, ko bayan babu ransa su riƙe zumincin juna danshi tsanine mai kai bawa zuwa aljanna, idan mutuwa ta riskesa a wannan yinin karsuyi masa kuka, karkuma ai masa zaman makoki, ya yafema kowa, su roƙa masa gafara wajen kowa, baya bin kowa bashi ba'a binsa.
Wannan itace nasihar da yake musu akowacce safiya, wadda tun suna ƙanana sunma gama haddaceta a ƙwalwarsu saboda yawan bita da suke samu daga mahaifinsu abin alfaharinsu.
Jiki a sanyaye suka miƙe suka fito daga ɗakin, ɗakin Ayyah suka shiga, tana zaune saman abin salla tana jan cazbaha.
Ƙasa suka tsugunna itama suka gaidata cikin girmamawa, fuskarta ɗauke da murmushi ta amsa musu, kafin ta turo musu kwanon dabino tana faɗan, “Mudan gashi, nadai san Ɗan albarka yau azumi yakeyi”.
Murmushi Ahmad yay yana ɗaga mata kansa, Mudan yaja kwano ya ciri dabino bakwai yana ƙaramar dariya da tsokanar Ahmad, “To mudai bamayi Ayyah, kuma ci mukayi abunmu, amma tunda ɗaki ɗaya muke kwana da Yah Ahmad nasan za'a rinƙa dibamin ladan ganin ido a azuminsa”.
Dariya Ayyah takeyi, Ahmad kam dake miƙewa ya shureshi da ƙafa yana hararsa, akwatin ƙarfe na lefen auren Ayyah🤣 da kayansa ke ciki ya nufa, “Ayyah kibar biyema wannan shashashan wlhy, dan mudan bazai taɓa hankaliba inaga”.
“Tab lallaima Yah Ahmad ɗinnan, duk hankalinan da nake dashi baiyi makaba ashe? To zakasha mamaki kuwa, Ayyah samun albarka kinji naje na ɗebo ruwa yau inada wajen zuwa da safen nan”.
Ayyah dake haɗiye dariyar da take musu tace, “ALLAH yay muku albarka Mudanseer, ya shirya manaku ku zama jaruman musulinci da MANZON rahama zai alfahari da haihuwarku, ALLAH ya baku rufin asiri mai albarka da amfani ya tsareku da dukkan wani sharri da abun ƙi”.
“Amin Ayyahnmu, maman ɗan albarkanta”.
Mudan ya faɗa yana miƙewa, Ahmad dai da yasan neman magana mudan keyi sai bai ko kalleshi ba harya fice.
Ayyah ta juyo tana kallonsa da murmushi, “Ɗan albarka mi zakayi da safen nan?”.
Kansa ya langaɓe cikin ƴar shagwaɓa yace, “Babu komai Ayyah na, akwai abinda zan mikine?”.
“Eh to ba wani dai mai yawa bane, sonake kaje ka sanarma kawunku lurwanu matsalar da ake ciki game da ƴar uwarku, dan babanku yariga ya rantse babu ruwansa, ya kuma hana a sanarma ƴan uwansa, nima dai banason suma sani ɗin, saboda gutsiri tsomar iyayenku mata na gidannan. tun jiya Gwaggo keson fita tasamu ta sanarma Kawun naku Babanku ya hanata fita, saboda yasan ina zataje......”
Kayan hannunsa da yakeson ya ɗan goge ya ajiye saman akwatin bayan ya rufe, ya gyara zamansa sosai a ƙasa cikin sake tsuke fuska yace, “Ayyah, wannan karon banason kowa ya shiga wannan maganar, har kawunma ki barsa, ni da kaina zzan kawo ƙarshen matsalar Yaya Maryam, dan wanan mijin nata *KAREN BANA* ne, *ZOMON BANA* yake buƙatar yayi maganinsa, ku zuba mana idanu kawai......”
Shiru kawai tai tana kallonsa dajin ƙarin ƙaunarsa, muryarta naɗan rawa tace, “A'a ɗan albarka, karka jefa kanka cikin matsala, wannan maganar babbace, banason zuciya ta lulluɓe ganinka harka aikata abinda zaisa muyi nadama mu duka, kasan dai halin babanku”.
Murmushin takaici Ahmad ya ɗanyi, ya matso kusa da Ayyah sosai, “Karki damu Ayyah, insha ALLAHU ba mummunan abu zan aikataba, ta ƙyaƙyƙyawan hanya zan gyara komai da izinin UBANGIJI”.
“To shikenan ɗan albarka, ALLAH ya albarkaci rayuwarka, ya tsare gabanka da bayanka, ALLAH ya cika maka burukanka na alkairi ya kuma share hawayenka a duk lokacin da zasu kwaranyo koda babu ranmune”.
Cikin sukar zuciya ya amsa da amin.
Bai sake cewa Uffanba ya ɗauki kayansa a hannu ya fita.
Ɗakin Gwaggo ya shiga, ciki-ciki ta amsa masa sallamarsa, bai damuwa ya durƙusa har ƙasa ya gaidata.
Ta amsa masa tamkar yanda ta saba cikin nuna rashin kulawa.
Shiru yay zaune a wajen, shi bai tashiba bai kuma motsaba, gashi ba hira sukeyiba, tama maida hankalinta wajen bama zu Fa'iza umarnin ruwan kamu da zata ɗora.
A haka Abubakar ya shigo ya samesu, shima dai masha ALLAH ya fara zama saurayi, Gwaggo ya gaida kafin ya gaida Ahmad.
Amsawa Ahmad yay yana miƙa masa kayan hannunsa, “Abu amshi kayanan ka goge mani, zanje wani waje na dawo, ka tabbatar sun gogu daƙyau, karkamin iya shegen da kaima Mudan shekaran jiya a kaya kajini ko?”.
“To Yah Ahmad, amma sai dai dutsin yana wajen Yaya Salisu, dan jiya daya amsa ina shago bai dawo dashiba, gashi babu gawayima ya ƙare”.
“Kaje ka amso dutsin, bara naga inada wata naira ɗari anan, saika sayo gawayi na hamsin, hamsin ɗin kayi kudin tara da shi”. Yana maganarne yana laluben aljihunsa.
Gwaggo da tun ɗazun tana saurarenau bata tankaba ta katseshi da faɗin, “Kabar kuɗinka, kai Abu kaje ga gawayi can lungun ɗakin Yaya na kashe jiya kayi masa gugar dashi, dama saboda ku aka fara tarashi kwa rage cacar kuɗin sayen tunda iccen yana bada rushi sosai”.
Murmushi Ahmad yayi har haƙoransa suka bayyana, a hankali yace, “Mun gode Gwaggonmu”.
Shiru tayi bata amsa masaba, shima sai ya miƙe sim-sim cike da kunya yay mata sallama ya fice.
Abu ya danne dariyarsa da ƙyar, danshi Gwaggon tasu da Yayansu dariya suke bashi a kullum, sai kace wasu surukai.
Gwaggo da tasan shakiyancinsa ne ya motsa ta ɗakko mafici tana kai masa duka, da gudu ya fito a ɗakin yana dariya.
Ahmad yana gaban kejin kajinsu tsugunne Sadiya tazo zata fice riƙe da kwanon langa babba, tai masa sannu tana ƙoƙarin wucesa.
Kiranta yayi, hakanne ya sakata tsayawa tana juyowa gareshi, “Na'am Yaya nazone?”.
“A'a karki zo” yay maganar cikin gatse yana zaro ɗan tsakonsa sabon ƙyankyasa daya mutu daga kejin.
“Yi haƙuri Yaya”.
Baice mata komaiba sai da ya miƙe, “Mi zaki sayo muku?”.
“Yaya ƙosai Baba yace, na ɗari da hamsin”.
Bai bata amsar maganartaba ya lalubo ɗarin aljihunsa ya miƙa mata, “Amshi wannan kije Mudan na fanfo ki amshi ɗari a hannunsa saiki sayo, shi kuma baban ki maida masa kuɗinsa”.
“To Yah Ahmad mun gode, ALLAH ya kara buɗi na alkairi mai albarka”.
“Amin” ya amsa akan laɓansa, ya ɗauke kansa daga sadiya yana ƙwalama Zainab autarsu kira.
Babu ɓata lokaci ta iso hannunta riƙe da tsintsiyar da take sharar tsakar sashensu.
“Idan kinzo shararnan ki sharo cikin kejin nan, wannan ɗan tsakon a wullasa masai karna dawo na iskesa anan wajen, sanan a wanke kwatanniyar agwagi a zuba musu sabon ruwa”.
“To yaya” ta amsa a ladabce.
Ficewarsa yay ba tare daya sake amsawa ba.
Majalissar abokansa yaje inda suketa bikin karya kumallo, wasu da koko wasu da shayi dai dai ƙarfinsu, sai indomie da ƙalilan ɗonsu sukeci da aka dafo daga wajen mai shayi.
Zama yay yana miƙama kowa hannu suka gaisa, duk sukai masa tayi, amma sai ya girgiza musu kai, nanfa suka hau masa ƙorafi akan hakan.
Murmushi kawai yayi, danshi babu wanda yasan yana azumin idan ka cire Ayyah, ko Gwaggo idan ba taga Ayyah nata ƙoƙarin haɗa masa abin shan ruwa ba bata cika sanin yana azuminba.
Text message ya shiga tafa ma Samina da ƴar ƙwaƙur din wayarsa, yanayi yana ɗan murmushi harya kammala ya tura mata sannan ya maida wayar aljihu yana fuskantar hirar da abokan nasa keyi mai kama da santin abincin da suke lodama cikinsu.
__________________________________
Samina na tsaka da cin indomin data sayo wajen mai shayi da tea ɗinta mai kauri ta tsinkayo shigowar saƙo a wayarta vivo ƙarama da Ahmad ya siya mata dan karta gani wajen tsaranta, jawota tai daga ƙasan filo ta buɗe saƙon.
Murmushi tayi saboda abinda saƙon ya ƙunsa, sai kuma ta taɓe baki tana ajiye wayar gefe.
Har yanzu dai zuciyarta bata sama mata matsayaba game da zaɓin da ya dace tayi, Ahmad ko Ma'aruff?, sai dai wani gefen na kawo mata kutsen wata shawara mai sakata ban tsoro akan Yah Ahmad.
A haka ta kammala cin abincinta ta fiddo kwanikan, inda su Iya suke ajiye wanke-wanke takai ta ajiye, ta nufi ɗakin kakarta inna mari dan bata labari akan abinda ya faru jiya.
Inna Mari na tsakar ɗaki zaune tana juya wani turmin zani mai ƙyau Samina ta ahiga.
Zama tai gefenta tana fadin, “Inna wannan zaninfa?”.
“Uhhm, wlhy Samina Haire ce ta aiko dashi jiya da daddare, wai sotake na cigita mata ko akwai mai saya, itama ɗanta yayo mata shine zata sayar saboda fatara ta isheta, nikuma badan karna ɗaukarma kaina rigimaba dana saya na ajiye saboda fitar sunan ƴar uwarki binta, na huta kinga”.
“Eh kin kawo shawara Inna, to ki ɗauka kawai”.
“Kijiki da wani zance auta, idan na ɗauka da shekarun tsohuwarki zan biyata?”.
Dariya Samina tayi, ta karkace gefe tana kwanto kuɗin data raba uku wanda Ma'aruff ya bata ta ɓoye sauran tazo nunama inna mari kashi ɗaya, ta ajiye gabanta.
Sosai inna mari ta firgita, cikin ƙwalalo idanu tace, “Samina! Ina kika samo waɗanan maƙudan kuɗin haka? Kar dai sata kika far......”
“Inna sata kuma? Dan ALLAH daina min baki mana, sabon saurayi nayi jiya ɗan masu kuɗi, shinema ya kawoni har gidanan, yakuma bani w aɗanan kuɗin dubu biyar dazai wuce”.
“Kai dan ALLAH jikallena da gaske?”.
“Wallahi kuwa Inna”.
“Tofa, kice arziƙin yazo Samina, lokacin cin moriyar haihuwa yayi, yanzune mijin aure dai-dai dake ya iso gareki”.
“Hummm” kawai Samina ta faɗa.
Itako inna mari ta ƙule da murna harda ringume Samina, atake ta cire dubu ɗaya taba Saminar wai ta kashe, ta ajiye dubu uku kuɗin zani, ɗaya kuma ta saƙe cikin zaninta tana faɗin “Wannan kayan kicin zamu fara saye, dan yanzu sune ƙaryar, muma dolene asamu a jerin lissafi, ballema gidan daya dace a tarama kayan kicindin ƴan gaske zakije”.
Ita dai Samina murmushin yaƙe kawai take iyayima inna mari, tanaso tace abama mamanta nata tanaji tsoron jarabar Inna mari.
Yanzu da bata ɓoye wasuba ko mama gaje inna mari bazata tunaba, amshesu zatayi duka.............✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*GW*
*(6)*
..............Ahmad na barin majalissarsu shago ya shiga, ya samu ya ida haɗa rigar wandon jiya da ya fara cikin kuzarinsa, yana shirin Fita Mudan ya shigo cikin shirin makaranta.
“Yauwa Mudan ka fito?”.
“Eh wlhy yaya, gara naje dan yau text gareni, amma zan dawo da wuri insha ALLAH”.
“Masha ALLAH, idan ka rigani dawowa to dan ALLAH kai ƙokarin haɗa kayancan nasu Jamila, banason suzo gobenma bamu kammala ba mu sake saɓa alkawari, nima zan ɗanje wani wajene, bansan kuma ko zan dawo da wuriba gaskiya”.
“To yaya babu damuwa, amma ta gama biyan kuɗinta kuwa?”.
“A'a gaskiya bata gamaba, Ƙawarta dai ta kammala, amma ka duba littafin da ake rubutawa zakaga nawa kuɗinta ya rage, karka bata kayannan saita fara danƙa maka kuɗi”.
“Angama insha ALLAHU yaya, ga sauran kuɗin jiya na wajen Faridan, dubu ɗaya da ɗari uku na taɓa na maganin Yaya Maryam”.
“Barsu a hannunka, bani dai ɗari biyu kawai a ciki, saika bama su Ayyah kudin cefane, dan na lura yau baba sai a hankali bashi da kuɗi”.
“Eh wlhy kam naji yana faɗama Gwaggo yanzu data aika yaba auta kuɗin sayo omo”.
“To ka basune?”.
“Nabata naira ɗari ta sayo ɗan babban nan ƙila yakai ko jibine”.
“Okey babu damuwa, kaje karka makara nima wanka zanje nayi na fitan, a dawo lafiya, ALLAH ya bada sa'ar text”.
“Amin yayana abun alfaharina”.
Madan ya faɗa cikin ƙarajin ƙaunar ɗan uwan nasa.
Ahmad baice komaiba ya kulle shagon ya fita zuwa cikin gida.
Sannu yayma su Ayya dake a tsakar gida suna cin ɗumamen tuwo ita da gwaggo a kwano ɗaya.
Ayyah ce kawai ta amsa masa, gwaggo kuwa ko inda yake bata kallaba.
Ruwa ya ɗiba a botikin ƙarfe yazo zai sake wucesu.
Ayyah dake binsa da kallo tace, “Ɗan albarka badai da ruwan sanyi zakai wankan ba?”.
Ruwan ya ajiye yana murmushi, “Dashi zanyi Ayyah, sauri nakene shiyyasa, kuma ai rana taɗan fara zafi babu sanyin sosaima”.
“Hakane, amma kuma mura nake tsoron kartai maka kamun kisan mummuƙe”.
Kafin ya samu bata amsa Zainab da Fa'iza suka sanya dariya saboda zancen Ayyah na ƙarshe.
Cikin harara ya kallesu, hakanne ya sakasu yin tsitt suna haɗiye dariyar da ƙyar.
Ƙwafa kawai yayi ya ɗauki ruwansa yana faɗin, “Karki damu Ayyah bara na watsa”.
Harya fito da ga wankan su Ayyah na tsakar gida zaune, shiga ɗakin Ayyah yay ya shafa mai acan, ya shirya cikin yadinsa ruwan ƙasa da Abu ya goge masa, yayi ƙyau sosai, yana tsaka da taje kansa akai sallama a ƙofar ɗakin.
Amsawa yay yana juyowa saitin ƙofar, “Wanene?”. yay maganar yana ɗage labulen.
Umm-Rumana dake tsaye cikin Uniform ɗin islamiyya ruwan madara kanta a ƙasa tace, “Yaya nice, dama Yah Sufyan ne yace na sanar maka yana jiranka”.
Sakin labulen yayi yana faɗin, “Okey, kice masa ina zuwa”.
Cikin ɗan risinawa ta amsa da “To”.
“Umm-Ruman jirani mu wuce”. ‘Fa'iza ta faɗa daga ɗakin Gwaggo tana ƙokarin jawo hijjab ɗinta da jakar makaranta’.
“Kiyi sauri to, dan mun makara wlhy, nima harmun fita dasu Salima Yah Sufyan ya maidoni”.
Fa'iza na fitowa Ahmad ma ya fito daga ɗakin Ayyah yanata ƙamshinsa mai sanyi.
Kusan a tare suka fita shi da su Fa'iza, suka wuce islamiyya shi kuma ya hau mashin suka bar anguwar shi da Sufyan da yake masa hirar su Fa'iza.
Ahmad da ke a bayan mashin ɗin ya ɗan daki kafaɗar Sufyan kaɗan,
“Kai malam ka isheni, kabar saka shirgina a cikin na yarancan kaji”.
Sufyan yay ƴar dariya yana shiga lingun da zai kaisa gidansu Inna mari yana faɗin, “Oh bakasan shirgin yara sai na Samina ko? To ai baifi shekara biyu da rabi tabama su Umm-Rumana ɗinba itama, da yakema sunada girman jiki aiba komai zata nuna musu ba”.
“Kai dai kasani alhaji”. Cewar Ahmad yana ƙoƙarin sauka a mashin ɗin.
Sufyan dake ƴar dariya shima ya sauka yana kafe mashin ɗin.
Waya Ahmad ya ciro daga Aljihu yana ƙoƙarin kiran Samina, dan wani waje zasuje yace su biyo su duba Inna mari sai su wuce.
Kusan kira huɗu bata ɗagaba, yana ƙoƙarin hangen inda zai ga yaron da zai aika a kiratane wata danƙareriyar mota data gama ƙoshi ta faka a gabansu.
Daga Ahmad har Sufyan motar sukebi da kallon mamaki, wanda ke a ciki bai fitoba kusan mintuna uku.
Ɗauke kai Ahmad yayi da ga motar ya cigaba da neman layin Samina ko zata ɗauka, dan shi abinda kawai zuciyarsa ta bashi bata kusa da wayarne....
Cikin tsagwaron gayu Samina ta fito da ga ɗakin Inna mari, sai ƙamshi take zabgawa, wanda bai saniba bazai taɓa ɗauka ta fitone da ga irin gida nasu Ahmad ba.
Tana ma inna mari da iya sallama wayarta ta shiga ƙara, tsaki taja mara sauti, dan tasan dai bai wuce Ahmad sarkin naci ba, dan duk kiran da yay mata tana zaune tana kwalliyane, amma dan iya shege taƙi ta ɗaga.
Amma Ma'aruff na kiranta yace ya iso ta fito jiki yana rawa.
Sam idanunta bai kai kansu Ahmad ba, saboda suna daga bayantane, taku take ɗai-ɗai tamkar tazo filin gasar sarauniyar ƙyau ne, ƙamshinta kuwa tuni ya buɗe hancin Ahmad da Sufyan da ke binta da kallo baki buɗe tamkar sakarkaru.
Daga cikin motar Ma'aruff dake kallonta ya miƙa hannu ya buɗe mata murfin gefensa, a gaban idonsu Ahmad ta shige motar.
Wani ƙululun baƙin ciki da ya tokare maƙoshin Ahmad ne ya wuce da ƙyar, yaso ya danne amma sai ya kasa, ya yunƙura cikin zafin nama zai je gareta Sufyan yay azamar ruƙo hannunsa yana girgiza masa kai.
Dole Ahmad ya haƙura ya zubama motar ido har tabar wajen, Sufyan dake ɗaukarsu video recording a waya ya sauke yana sauke numfashi kusan a tare.
Baicema Ahmad komaiba akan hakan, sai Mashin da ta haye abinsa ya tayar yanama Ahmad nuni da shima ya hau suje.
Har sukaje inda suke son zuwa babu wanda yay magana balle su ɗakko zancen Samina.
Sun isa wajen ƙawarsu mai suna Zaheedah, tare sukai karatu da ita, da farko catai tanason Ahmad, amma sai bai ɓoye mataba ya sanar mata yanada wadda zai aura tayi haƙuri.
Tayi fushi a lokacin, amma daga baya sai ta dawo kuma tace su zama abokai, badan Ahmad ya soba ya amince saboda matsawar Sufyan da Ameen, tun daga lokacin sai suketa zuminci, tare da taimakon juna akan karatu har ALLAH yasa suka gama.
Sun cigaba da zumincinsu, yayinda suke haɗuwa jefi-jefi dasu Ahmad ɗin, sai ko waya ita sunayi akai akai.
Tarbar mutunci suka samu daga wajen Zahidah, ta kaisu har falon baƙi dake a cikin gidansu, kafin wani dogon lokaci an cika musu gabansu da kayan ciye-ciye.
Sufyan ne kawai yaɗanci wani abu, amma banda Ahmad dake a zumi, wanda dole ya faɗa musu azumi yakeyi saboda fushi da Zaheeda tayi akan baici abin gidansuba.
Gaisuwa sukayi cikin mutunta juna, kafin su ɗora da hirar yaushe gamo, dan sun ɗan daɗe basu haɗuba.
Sun mata bayani akan abinda ya kawosu game da taimakon da zatai musu akan yaya maryam.
“Karka damu Shema, insha ALLAHU zan bada gudunmawata, domin gyaran aure aiba abin wasa baneba, amma ku yaya maganar naku auren? Musamman ma kai Shema da nasan akwai matar tamu a hannu?”.
Murmushin yaƙe kawai Ahmad yayi, amma baice komaiba, sai Sufyan ne ya bata amsa da faɗin, karki damu, soon zakiji bayani mai daɗi insha ALLAHU”.
Cikin faɗaɗa murmushi tace, “To ALLAH ya tabbatar mana, ya kuma kaimu lokacin”.
Da amin suka amsa, inda Ahmad ƙoƙarin danne ɓacin ransa kawai yakeyi a wajen.
Kusan awarsu biyu a gidan sannan sukai mata sallama suka tafi, bayan ta haɗasu da leda ta kayan shan ruwan Ahmad. Da ƙyar suka amso, dan sai da ta ɓata rai sosai sannan.
Sufyan yaso su ƙara zuwa wani waje danya ragema Ahmad ɓacin ran da ya lura yakai ƙololuwa a ciki, amma sai Ahmad ɗin yaƙi yarda, yace su wuce gida kawai.
Sufyan na kafe mashin a majisarsu Ahmad bai zaunaba, hannu kawai ya bama su Salisu dake zaune su uku kawai suka gaisa ya nufi gida abinsa.
A ɗakinsu na zaure ya yada zango, da ƙyar ya iya zame kayan jikinsa ya zauna daga shi sai best da boxer, baiyi auneba yaji jawaye masu ɗumi nabin kumatunsa.
Wai yau shine akan idonsa yarinyar da ya gama ɗorama buri ta shige motar waninsa ba shiba, bayan yaji a ransa tabbas taga kiran da yay mata a waya taƙi ɗauka.
Gaba ɗaya kansa ya kulle game da Samina, ya rasa wane kalar tunani zaiyi ko zaiji sassauci.
Bai motsa daga wajenba har aka kira sallar zuhur, ya tashi daƙyar ya fice bayan ya saka jallabiya a jikinsa.
Suna idar da salla ɗakin ya sake dawowa ya kwanta, nanma dai tunaninsa ya ɗora daga inda ya tsaya, bai sake fitaba sai da la'asar tayi, an idar da salla ya sake nufo gida, zamansa ke da wuya a bakin katifarsu Sufyan ya shigo ɗakin da sallama.
Hannu ya bashi sukai musabaha, kafin ya zauna a kusa dashi gefen katifar,
“Abokina ba tunani ko ɓacin rai akanta ya kamata ka sakama ranka ba, ɗaukar mataki da gaggawa kafin abun yay nisa shine yafi dacewa da kai, bansan miyyasa a kullum kake maida kanka ragon namiji akan Samina ba, ka riga ka sakema yarinyarne da yawa shiyyasa har take iya kawo maka waɗannan salon rainin wayon tamkar ba kanuwarka ba, ni dai yanzu da zakaji da ka shareta kawai, kaje ka samu su baba da maganar aurenku, gara ko hayar ɗaki ɗayane ka kama, tunda dai gwargwadon iko kana samun taro da kwabon da zaka iya riƙeku koda ba'a samu komai baja-baja ba, kaga saita karasa karatunta a cikin gidanka hankalinka kwance”.
Sosai shawarar Sufyan taima Ahmad daɗi, ya kuma gamsu da ita ɗari bisa ɗari, godiya yay masa akan hakan, daga nan suka ɗan ƙara tattaunawa akan maganar yaya maryam, Sufyan ya kara masa shawara game da Samina kuma.
A haka Mudanseer ya shigo ya samesu, gaidasu yayi ya ajiye kayan hannunsa ya fice zuwa cikin gida saboda azabar yunwar da yakeji.
________________________________
Bayan sallar isha'i Ahmad na zaune a ƙofar ɗakin Ayyah yana buɗa baki, sai dai rabin hankalinsa nakan wayarsa, da alama dai akwai abinda yake tsumayen gani, amma yaƙi ya shigo......
“Ɗan albarka wai bazaka ajiye wayar nan kayi buɗa baki bane?”.
Murmushi Ahmad yayi yana ajiye wayar gefensa, ya cigaba da cin alalar da Ayyan tai masa dan buɗa bakin, sai dai zuciyarsa sam babu daɗi, yau gaba ɗaya da ɓacin ran SAMINA ya yini a ransa, ya kuma tura mata massege akan ta dawo gida yau ɗinnan sai dai har zuwa yanzun bata shigoba, ya kirata kuma wayar a kashe.
Yana cin abincin yana sauraren hirar ƙannensa dake daga can gefensa a ƙofar ɗakin barcinsu, sai Ayyah da Gwaggo dake a ƙofar ɗakin gwaggon suna cin tuwo suma
Shigowar saƙo a wayar tasane ya sakashi saurin ɗaukarta har jikinsa na rawa, ko da ya buɗe saƙon sai yaga abokinsane Sufiyan yake masa “Please call me”, numfashi ya ɗan sauke a ɓoye, zuciyarsa duk a cunkushe.
A kullum canji yake sake gani da ga ɗabi'un saminar sa, baisan mike shirin shigoma duniyar jin daɗinsu ba sam? Sai a yaune ya fahimci inda matsalar take ashe.
Haka dai ya gama buɗa bakin zuciya duk babu daɗi, duk ƙaunarsa da alala sai gata yau batai masa wani daɗi ba.
Ruwa ya ɗiba ya ɗan watsama jikinsa, yazo ya shiga ɗakin Ayya ya ɗauki kayan barci ya fita zuwa ɗakinsu na zaure.
Canja kayan yay ya fice waje wajen abokansa. Acan ya iske Sufiyan, sai da ya gaisa da kowa sannan yaja hannun Sufiyan suka koma gefe.
“Sufiy ya akaine? Naga kamin Please call me ne?”.
Kaɗan Sufyan ya sauke numfashi yana cije baki, “Abokina wlhy akwai matsalane?”.
“Matsala kuma Sufiy? Akanmi to?”.
“Wannan banzar yarinyar mana Sha'awa, wai ni zataima rashin mutunci akan ɗan uwanta na legas ɗinnan yazo wajenta?”.
Cike da mamaki Ahmad yace, “Itama Sha'awar abinda ta daukarma ranta kenan? Wai miyasa zukatan ƴammatan yanzu mafi yawansu sukafi karkata akan kuɗi da mai kuɗine abokina?”.
“Wlhy kuwa Ahmad, gaskiya bazan iyaba mace ta zauna tana zubamin iskanci, ya isa hakanan, wannan karon na barta har abada...”
Da sauri Ahmad ya katseshi da faɗin, “Haba Sufyan karkace haka mana, kaimafa kasan Sha'awa na sonka, ɗazunfa kaine ka gama fahimtar dani akan Samina, ƙilama kayi kuskuren fahimtar tane........”
“Ahmad kuskuren fahimta fa kace? Sam babu wani kuskuren fahimta akan batuna, Please kai daine kake neman kasa fahimtar tawa”.
“Kaga yi haƙuri abokina, wlhy na fahimceka, yanzu kabar komai a hannuna zan sameta, idan munji dalilinta bashi da muhimmanci sai kawai ka barta, amma nikam wannan abu yana bani mamaki na ƴammatan wannan zamanin, su kawai idan kaga suna kwantarma saurayi kai da nuna tsantsar ƙauna yanada wasu wakilai masu farar fuskane (kuɗi) a banki?, mafi yawancinsu haka halinsu yake, ƙalilanne na gari masu son mutum domin ALLAH, Shin suna mantawa da cewa su waɗan nan masu kudin da rarrafe suka tashi suma?”.
“Ahmad mubar zancennan, wlhy ƙaramin ɓacin rai kawai yakeyi, ai kai bakace hakaba, domin kuwa kayi sa'a, duk waɗannan banzayen halayyar sam Samina bata dashi, son gaskiya take nuna maka bawai wata abar banza dukiya ba, ko ganin da mukai mata ɗazun sai daga baya na zauna ina nazari akai, maybe ma ba abinda muke tunani bane akanta wlhy, naga rankane ya ɓaci kawai shiyyasa na sake barinka ka huce akan maganar”.
Ahmad da zancen Sufyan yay masa daɗi yay murmushi, dan yanason yaji ana yabon Saminar sa a koda yaushe.
Cikin abokansu suka koma suka zauna, daga nan fira ta ɓarke a tsakaninsu, duk da dai Ahmad yayi gum, sai maida hankalinsa da yay wajen cigaba da neman layin Samina.
Amma har lokacin kwanciya yay kowa yay yunƙurin tafiya gidansu bai sameta ba, a wannan daren da ƴar damuwa ya kwanta, garama jiya daga baya taɗan sanyaya masa ransa..............✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*(7)*
.............A ɓangaren Samina kuwa shopping Ma'aruff ya fita da ita, sun shiga cikin shoprite inda Samina ta rikice, dan bata taɓa zuwa ba, sai dai tanajin labari wajen su Nafy, tuni kanta ya nema kwancewa, dan sai tagama kamar ba'a kano take ba.
Ma'aruff dake taku ɗai-ɗai cikin ƙasaita irinta masu ji da dukiya ya bama Samina umarnin ta zaɓi duk abinda takeso.
Sam bata cutar da kantaba, tako ware ƙwanji tana lodar kaya iya son ranta, shiko yana biye da ita yana kallo tamkar ba kuɗinsa zai biya da kayan ba.
Ta ɗauki kaya sosai sukaje wajen biya, ATM ɗinsa kawai ya miƙa ya koma gefe, aka gama cirewa aka saka musu a leda, ɗaya daga yaron shagon ya ɗauka ya bisu mota dashi.
Daga wajenma ba gida ya kaitaba, wani gidan gona sukaje, wanda take ƙyautata zaton yana da alaƙa dashi, wajen yayi ƙyau, dan an gyarashi na musamman domin hutawa.
A kujeru suka zauna, inda Ma'aruff da kansa ya fiddo musu ice-cream ɗin daya siya musu da gashashshen kaza.
Da farko dai Samina taɗan noƙe baza taciba, wai ita kunya, amma da taga zataima kanta buƙulu tuni ta fara kai lauma harma tana neman zarta Ma'aruff ɗin.
Shi abunma dariya yaso bashi, amma sai ya fuske abinsa.
Sun ɗan taɓa hira, inda yayta mata tambayoyi a fakaice game da kanta, itako taita basa amsa kanta tsaye.
Kusan awa biyu suna wajen, kafin yace ta tashi ya kaita wajen bikin.
Sai da suka biya ta gida ta ajiye shopping ɗin da yay mata, sannan ya kaita wajen bikin inda su Nafy sukaita ihun ganinta, bai tsayaba yaja motarsa yay gaba ya barta anan tunda bashi da alaƙa da bikin nasu.
Yauma sun raƙwashe sun ƙwalle abinsu, ansha hidima sosai, dan sosai Samina ta manta da wani Ahmad, acan aka kusa kwana wajen dinner ɗin, sai gabannin asuba suka tashi, gidan amarya aka kaisu suka karasa kwana.
Samina bata tashi ganin massege ɗin Ahmad ba sai da safe.
Dukda taji tsoro sai da ta taɓe baki, tana mamakin yanda yake bata umarni tamkar wani mijinta.
Kashe wayar tayi gaba ɗaya dan karma ya kirata, basu bar gidan amaryaba kuma sai yamma da akayi buɗar kai sannan suka wuce gida.
Koda Samina ta dawo gidansu inna mari bata zaunaba, kayanta ta haɗa waje ɗaya bayan ta ɗibar musu abin ci a cikin kayan da Ma'aruff ya saya mata, ana sallar isha'i ta baro anguwar zuwa anguwarsu..
_____________________________
Ahmad da bai samu barci sosaiba a daren jiya yau sai ya daɗe kwance bayan sun dawo sallar asuba.
Har takai Ayyah ta fara cigiyarsa saboda ya saba shigowa shi da Mudanseer da safe gaidasu, amma yau har kusan sha ɗaya babushi babu alamarsa, Mudan ne kawai ya shigo ya gaidasu da safen ma.
Ayyah ta aika Zainab auta ɗakin su Ahmad dan taga ko lafiya, dan tata jiran ko Mudan zai shigo ko Abu, amma babu wanda ya shigo a cikinsu.
Zainab tayi sallama kusan huɗu babu amsa, dan haka ta tura ƙofar cikin sanɗa ta leƙa kanta, kwance ta hango Ahmad a katifarsu ya lulluɓa da bargo har saman kansa, sai fuskarsa daya bari a buɗe kawai.
Komawa tai da baya ta sake rufe masa ƙofar, taje ta sanarma Ayyah.
Gwaggo na jinsu amma batace komaiba, sai Ayyah dataketa ƙorafi akan kodai bayajin daɗine, ganin Gwaggo taƙi saka baki yasata jan zani ta saka a kanta ta fita zuwa soron.
Koda ta shigo ɗakin kaɗan taja bargon daga saman kansa ta ɗora yatsunta a goshinsa, zafi rau kansa, hakanne yasata fahimtar bayajin daɗi kenan.
Sanyin yatsunta da yaji a kansane ya sakashi buɗe idanunsa da ƙyar.
Ganin Ayyah ce ya sashi ƙoƙarin tashi zaune, da sauri tace,
“A'a, kaga yi kwanciyarka ɗan albarka, dama baka da lafiya shine ko Mudan baizo ya sanar mana ba?”.
Cikin magana da ƙyar Ahmad yace, “Ciwon kaine kawai Ayyah, Mudan kuma baisanma bana jin daɗiba”.
“Ai ciwon kai ya wuce ace masa kawai ɗan albarka, sannu kaji, bara na saka maka ruwan wanka a wuta, saika daure ka tashi ka watsa ruwan ka karya kumalo sai kasha magani”.
Fuska ya ɓata sosai, dan bayason magani sam, sanin hakane yasa Ayyah cigaba da lallashinsa har ya yarda zai watsa ruwan.
Ayyah ta fito a farko, shikuma yana bayanta dafe da kai suka fito daga ɗakin, da Samina dake fitowa daga cikin gida sukaci karo, Ahmad yay mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa.
Sai Ayyah ce kawai ta amsawa Samina gaisuwar da take yimata.
Ayyah tace, “Ɗiyata ashe kin dawo?”.
Kan Samina a ƙasa tace, “Eh Ayyah, jiya da daddare na dawo”.
“ALLAH sarki, to yaya jikin Inna Mari ɗin?”.
Sai da Samina ta saci kallon Ahmad da ya raɓasu zai wuce tankar bai santaba sannan ta bama Ayyah amsa da “Jikinta Alhmdllh, taji sauƙi shiyyasama na taho, amma Ayyah yah Ahmad kuwa lafiya yake?”.
Cikin murmushi Ayyah tace, “ALLAH ya ƙara lafiya to, Ɗan albarka kuwa bayajin daɗi, nima yanzu nazo dubashi naga bashi da lafiya”.
Muryar Samina na rawa ta shiga jero masa addu'ar samun lafiya, Ayyah kuwa na amsawa cikin jin daɗi.
Ahmad ko koda ya wucesu jiyake tamkar ya shake wuyan Samina saboda kishin dake cin ransa, ya gaida Gwaggo dake hada-hadar ɗora girkin rana.
Amsawa tai cikin satar kallonsa, dan muryarsa ta tabbatar mata bayajin daɗi, ta ɗauke kanta tana cewa, “Baka da lafiyane?”.
Sai da ya kalleta, murya a sarƙe yace, “Kaina kemin ciwo”.
“ALLAH ya sawwake” ta faɗa tana shigewa ɗakin da suke ajiye kayan abinci.
A saman laɓɓa ya amsa yana binta da kallo, ya ɗan lumshe idanunsa yana jingina da katangar da aka zagaye sashen nasu da ita.
A haka Ayyah ta shigo ta sameshi
“A'a, tsayuwar mi kakeyi kuma anan ɗan albarka?”.
Idanunsa ya buɗe a kanta yana sauke numfashi da buso iskar bakinsa, yace, “Babu komai Ayyah ”.
“To jeka zauna na haɗa maka ruwan saika watsa”.
Umarninta yabi, yaje ya zauna a kujerarta dake ƙofar ɗaki ajiye.
Bayan ta haɗa ruwan Zainab tazo takai masa banɗaki.
______________________________
“Wai lafiya na ganki a sukuku? Bayan kuma ba haka kika fitaba”.
Samina ta ajiye ledar omon data siyoma Mama gaje tana faɗin, “Babu komai mama, Yah Ahmad ne baida lafiya”.
Shiru Mama gaje tayi bata tankaba.
Kishiyar mama gaje mahaifiyar Umm-Rumana da suke kira da Amma na daga bakin murhu tana haɗa wuta, tana jin uwar da ƴar, sai dai batayi ko tariba, saboda tun a daren jiya ta jiyo kalaman Mama gaje akan Ahmad tasan akwai matsala, dan agaban idonta Samina ta shigo da ledoji niƙi-niƙi a hannu, daga baya ta jiyo murnar da Mama gajen takeyi daga cikin ɗaki, har tana kushe ƙokarin Ahmad duk da wahalar dayay da Samina a baya, koma yake kanyi har yanzun.
Saminar ma batace komaiba ta juya ta zata fita, da sauri mama gaje tace, “Ina kuma zakije? Bayan nace ki wanke min zanin gadoncan dana jiƙa tun jiya”.
“Mama ina zuwa” Samina ta faɗa ba tare da ta saurari mamar tataba ta fice da hanzari.
Kanta tsaye sashen su Ahmad ta nufa, ta iske Gwaggo a tsakar gidan tanata aikinta na abinci, sai Sadiya dake taimaka mata da wasu ayyukan.
Gaisheta tayi, Gwaggo ta amsa da fara'a tana tambayarta yaushe ta dawo?.
Faɗa mata tayi jiya cikin jin nauyinta, Sadiya dake dariya ganin yanda Gwaggo da Samina kejin nauyin juna itama ta gaisheta.
Kafarɗarta Samina taɗan buga tana faɗin, “Baki da kunya yarinyarnan, ina Yah Ahmad yake? Koya koma ɗakinsu?”.
“A'a yana ɗakin Ayyah, sun tsareshi ita da Iya yana shan magani, kinsan maigidan naki da magani tamkar jariri yake”.
Dariya kawai Samina tayi, saboda Gwaggo dake a wajen bata iya bama Sadiya amsaba..
Samina ta leƙa ɗakinsu Sadiya, dan taga takalman Fa'iza, ciki ta shiga da sallama, Umm-Rumana da Fa'iza dake Assignment na islamiyya duk suka kalleta.
Da yake ta girmesu, kuma suna kallonta matsayin wadda yayansu zai aura sai suke bata girma sosai, gaisheta sukai, ta amsa tana ɓata fuska saboda ganin Rumana a wajen, dan mahaifiyarsu ta riga ta cusa musu ƙin kannenn nasu da suke uba ɗaya sosai.
Umm-Rumana ma saita maida hankalinta ga Assignment ɗin bata saka musu baki cikin hirarsu, dan tasan ƙaramin aikin Samina ne ta ci mata mutunci yanzun nan.
A gabanta Samina taja Fa'iza suka fita, danta rakata ɗakin Ayyah ta duba Ahmad.
Batai yunkurin binsuba, dukda tanason taje tai masa sannu itama.
Sun shiga ɗakin da sallama, Ayyah na tsaye akan Ahmad ita da Iya kakarsu suna lallaɓashi yasha magani, sai kumbura fuska yake tamkar zaiyi kuka.
Iya ta dungure masa kai tana faɗin, “Ragon kawai, ni nama taɓa ganin namiji na tsoron magani inba kai ba Amadu”.
Sake tsuke fuska yayi yana langabe kai gefe idonsa akan Ayyah dan taji tausayinsa.......
Ayyah zatai magana cikin son yin dariya su Samina sukai sallama, koda suka shigo bai kallesu ba, sai Iya ce tace, “To ai yanzu kasha tunda ga matarka nan ko”.
Bai tanka ba, sai ruwan dake hannun iya ya amsa tare da watsa sauran maganin hannunsa cikin baki ya matse ido yana tuttula ruwa a baki ya haɗiye da ƙyar.
Yana gama shanyewa kwanciyarsa yayi a gadon Ayyah na karfe yayma kowa banza.
A hakane su Samina sukai masa sannu da jiki, takuma ƙara fahimtar fushi yakeyi da itane da gaske.
Duk kuma sai taji babu daɗi, jikinta yay sanyi sosai, gwiwarta a sanyaye ta fito ta koma ɓangarensu.
_______________________________
Wasa-wasa dai sai da ciwo yaja Ahmad kusan kwana uku, dan daga ciwon kai abu sai ya koma zazzaɓi, har saida yasha ledar ruwa biyu, kullum sai Samina tazo gaishesa, amma baya kulata sam.
A yaran gidan duk wanda sukazo gaisheshi yana amsa musu koda a gabantane, amma ita sai baya kulata.
Duk da abin na mata ciwo sai ta daure ta faɗama Sufyan halin da ake ciki, Sufyan bai tsaya mata rufa-rufa ba ya sanar mata ganin da sukai mata a ƙofar gidan su Inna mari, harma ya nuna mata video din daya ɗauka dan yaga tana neman musa cewar itace.
Laƙwas jikinta yayi, nanfa ta shiga haɗo ƙarya ta shirya masa akan ita bata da alaƙa da Ma'aruff, saurayin ƙawartane Nafy, tayi kuskure amma ya bama Ahmad hakuri akan shiga motar ma'aruff ɗin da tayi.
Dole dai akan wannan magana sai da Sufyan yasaka su zama su uku ya sasantasu, Samina harda kukanta tana bama Ahmad hakuri.
Daga baya bayan masifar da taci a wajensa yace ya hakura.
Tun daga ranar komai ya sake koma musu kamar da, suka cigaba da tattali da soyayyar junansu, yayinda a ɓoye Samina take tare da Ma'aruff, idan yaso su haɗu gidansu Inna mari take zuwa su haɗu a can.
★★★★★★
Ɓangaren yaya Maryam kam babu wanda yasan miya faru, sai ga mijinta har gida yazo yana bama su Baba hakuri akan abinda yake mata, sannan itama ya bata haƙuri da neman afuwarta.
Babu irin tambayar da Ayyah bataima Ahmad ba akan ya sukayi da mijin Maryam ɗin, amma yaƙi faɗa, yace shi babu komai.
Ƙyalesa Ayyah tayi kawai badan ta yarda ba, amma ta fahimci koma minene shine ya aikatashi, kuma ko Maryam ɗinma bata san asalin miya kawo gyara a cikin lamarin auren nata daya nema hargitsewa ba a shekarunnan..
Matsaloli sun sake kunno kai tsakanin Samina da Ahmad, dan ta sake birkice masa ya rasa kanta.
Gashi yanzu abubuwa yake gani a wajenta wanda bashine ya siya mata ba, yasan kuma iyayensu basu da ƙarfin saya matan, dan har waya ta canja, tun tana ɓoye masa har komai ya fito ya ganta da wayar.
Duk iya tuhumar da yay mata kuma taƙi sanar masa gaskiya.
Abinda ke ƙara tada masa hankali kuma da ita sam yanzu batajin shakkarsa balle akai ga tsoro, ƙiri da muzu take masa rashin kunya idan yay mata faɗa akan kuskure.
Dan akan wayar nan daya gani a hannunta sosai rikici ya ɓarke a tsakaninsu har takaisu ga zuwa gaban kakanni, saboda maganar taje wajen iyayensu mata, sukuma suka gumtsawa mazan, daga nan ne kuma su iya sukaji suma, malam Rabi'u kuma ya kira Ahmad ɗin da Samina domin yaji gaskiyar maganar.
Da farko Samina ta musa, amma da taga babanta na neman dukanta a wajen saita faɗi gaskiya.
Ran kowa ya ɓaci ranar a gidan, dan haka take a wajen malam Rabi'u tsoho mai ran ƙarfe ya tsaida watan bikin Ahmad da Samina, a cewarsa ko haya gwara a kama musu su fara zama kafin ALLAH ya hore asan abinyi.
Kowa yaji daɗin yanke hukuncin da Malam yayi, dan kuwa kusa aka saka bikin, wata biyu kacal, lokacin Samina ta gama exam ɗinta, a cewar malam taje gidan mijinta ta ƙarasa karatun, tunda dama shine ya nace akan sai tayi
Wannan abu ya mugun tada hankalin mama gaje da Samina, dan zuwa yanzu dai gaba ɗaya tunaninsu ya karkatane ga Ma'aruff dake kashema Samina kuɗi tamkar baisan ciwonsu ba.
Ahmad kuwa ji yake kamar an masa rahama, dan sakayau ya jisa, shi kansa dama a buƙace yake da auren ainun, saboda muguwar sha'awar da ya fahimci yana da ita akan abokiyar halittarsa............✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*(8)*
............Sosai hankalin mama gaje da Samina yake a tashe, tunda suka baro sashen su Baba Rabi'u sai suka kasa zaune suka kasa tsaye.
Samina da ke share hawaye tace, “Wlhy mama bana sonshi yanzu, kinajifa wai ɗakin haya ɗaya za'a kama a ajiyeni kafin komai ya warware? Har sai yaushene komai ɗin zai warware a garesu baki ɗaya, tunda muka dawo rayuwar gidannan a talakawansu muka iskesu, shekara kusan goma sha takwas basuyi arziƙiba sai yanzu da za'a cuceni za'ace zaizo, wlhy nama kula danginmu ƙashin tsiyane dasu, shiyyasa duk wanda sukaga ALLAH zai ɗaukaka sai su nema dakushesa, kaf yaran gidannan da sukai aure tunda kan su yaya Maryam har zuwa su yaya Binta waccece ba'a cikin wahalar rayuwaba?, kowacce matsalolin fatara da babu sun gama isar rayuwarta, duk sun lalace sun zama wasu tsofaffi sa'anninku, babu wata mai gidan nunama sa'a a cikinsu. Mama kinga kuwa gidan Ma'aruff inda zai ajiyeni, wlhy ko za'a haɗa kaf dukiyar ahalinmu bazata sayi wannan gidanba, na rantse da ALLAH ko sama da ƙasa zata haɗe bazan zauna da Ahmad ba, inba hakaba kuwa ALLAH guduwa zanyi daga gidannan......”
“Ki gudu ina? Babu inda zakije yarinyata, dolene ko sunaso ko basaso su baki wanda kikeso, dan koni ban amince ki rayu da Ahmad ba, yaron da ko rigar sakawa ta kirki baida ita, ki kwantar da hankalinki duk nasan maganinsu, ni warkice dai-dai da ƙugun kowanne shege wlhy, iyakaci dai suce ya miki wahala ko? To su faɗi duk abinda yay miki za'a biyashi, dan sune matsiyata”.
Samina dake shashshekar kuka tace, “Yo mama dukkan wahalarma da yaymin ɗin ta nawace? Wlhy nasan ko Ma'aruff yaji saiya ninka masa ma abinda ya kashemin ɗin”.
Tsaki mai ƙarfi Mama Gaje ta ja tana yin ƙwafa, ji take a ranta koda aurenta zai sake mutuwa bazata yarda Samina ta auri Ahmad ba, dan tasan ko barin gidannan tayi akan auren Samina da Ma'aruff gaba zataci ba bayaba, tunda da dai zasu jiƙe da naira ne.
Duk surutan da Mama Gaje keyi ita da Samina a kunnen Baba Yusha'u ne dake alwala a tsakar gida, amma sai ya nuna tamkarma bai jiba, ya ajiye butar hannunsa ya fita.
Ammi ma duk a kunnenta komai ya faru, amma saitayi kamar batasan anaiba, da dai ita ba kishiyar uwa bace data basu shawara akan suyi haƙuri kar son zuciya ya kwashesu suyi GUDU DA WAIWAYE.......
A tsaitsaye Baba Yusha'u ya shiga sashen iyayensa shi da baba Iliyasu, sun ɗanyi magana suka fito a tare riƙe da malam Rabi'u zuwa massalaci, inda acan suka iske baba Hamza ma, yayi mamakin ganin Malam a massalaci yau, dan sam baya iyawa, yakai kusan wata huɗu ma ko waje bai leƙoba, dan ya tsufa sosai.
Salla aka tayar, bayan an idar mutane na niyyar fita Malam Rabi'u ya saka baba liman roƙon alfarmar su dakata.
Babu musu akaita dawowa, ciki kuwa harda Ahmad da abokansa, shima yayi mamakin ganin kakan nasu a masallaci, jira yake kawai su fito ya tambaya.
Mamaki ya sake kamashi jin liman ya ambaci cewar Malam ne yace jama'a suyi masa alfarmar tsayawa.
Abu tamkar daga sama yaji ana ɗaura aurensa da Saminar sa, mutuwar zaune yayi a wajen, duk taɓashin da abokansa sukeyi na alamar tambaya da taya murna bai iya kula kowaba, bayan an kammala ɗaurin auren jama'a suka shiga zuwa bashi hannu suna tayashi murna, hannun kawai yake iya miƙa musu yana amsawa da amin a saman laɓɓa, amma a zahirin gaskiya baya tare da duniyarsu sam.
Falalu ƙanin Samina da suke uba ɗaya, wato ɗan ɗakin su Umm-Rumana ne ya shiga gidansu da zancen ɗaurin auren.
Babu shiri Samina dake ban ɗaki tana wanka tajawo zani ba tare data ɗauraye kumfar jikinta ba ta fito kamar wata taɓaɓɓiya tana faɗin, “Kai Falalu ubanmi naji kake cewa?”.
Yaron yaɗansha jinin jikinsa, hakanne ya sakashi haɗiye murnar da yakeyi yana komawa bayan Amminsu ya ɓuya, Samina ta daka masa tsawa tana sake tambayarsa abinda ya faɗa.
A dai-dai lokaccinne Mama gaje tayo waje itama daga ɗaki, dan da salla takeyi, saboda sauri har tuntuɓe tayi, kaɗan ya ragema ta faɗi ta dai samu ta riƙe ƙarfen barandarsu.
Falalu dake a laɓe bayan Ammi da tai tsayuwar sojan badakkare yace, “Ai dai malam ne ya ɗaura miki aure da Yah Ahmad yanzu a massalac.......”
Wani ihu Samina ta kurma tana buga tsalle ta dire ƙasa, sai gata wanwar a sume zani a gefe.
Jikin Umm-Rumana na rawa taja Zanin gadon Ammi dake a kan igiyar shanya ta yafama Samina saboda tsirara take.
A lokacinne kuma iyayensu maza duk suka shigo, harma dasu Ayyah da matan Baba Iliyasu, dan casuke wani abunne ya faru da Saminar.
Ahmad ma da Mudanseer sai gasu sun shigo, nanfa kowa ya rufu akan Samina, yayinda Mama Gaje keta kuka akan bazata yardaba idan ƴarta ta mutu, tunda tace batason auren miyyasa zasuyi?.
Kalaman mama gaje sun fahimtar da kowa daga ina matsalar take, hakan yasa Gwaggo zare jikinta tabar sashen ganin an zubama Samina ruwa ta kawo numfashi.
Samina dake hawaye ta fara sakin sambatu, “Wlhy kozaku haɗa wuta ku sakani bazan zauna da Ahmad ba, nace bana sonshi, na rantse da ALLAH sai ya sakeni, inba hakaba kasheshi zanyi, wlhy saina yankashi da wuƙa idan kuka matsa saina zauna dashi, randa aka kaini a ranar zan kashesa, garama na ƙare rayuwata a prison da na zauna zaman aure dashi”.
Da sauri Baba Yusha'u ya buge bakin Samina, ya kuma kai hannu zai doketa Baba Hamza ya riƙe hannun yana girgiza masa kai.
Daga ƙarshema sai yaja hannunsa suka fice, baba Iliyasu na biye dasu.
Mudanseer da zuciya tazo masa kusa ya nuna Samina yana zagi, “Banza kawai mara tunani, to dan uwarki saiki tashi ki kashesa ga shinan, butulu kawai mai manta alkairi, kwaɗayayya mara tarbiyya, idan kika kuma zagin Yah Ahmad a wajennan wlhy kafin ki kasheshin ni saina kasheki dan uwark.......”
Jan Hannun Mudanseer Ayyah tayi tana share hawaye, “Kaga ya isa haka Mudanseer, idan ita bata da hankali kaima baka da shine? Kunga ku wuce muje” tai maganar tana jan Hannun Ahmad dake tsaye kawai yana kallon kowa kamar ya samu TV.
Koda suka koma sashensu ma zama kawai yay ya dukar da kansa ƙasa yana kallon sumintin ƙofar ɗakin iyayen nasa, yayinda Mudanseer da Abu keta zage-zage Fa'iza da Zainab na tayasu, Sadiya ko tanada sanyin hali tamkar su Ahmad, sai tayi shiru kawai tana share hawaye.
Gwaggo kuwa ai saikama rantse batasan mi ake yi a gidanba, sai aikinta take kamar komai bai dameta ba, nanko jin zuciyarta kawai take tana tsitstsinkewa kamar zata faɗo ƙasa dan damuwa.
Cikin lokaci ƙanƙani gidan ya harziƙe, dan bakin Samina bai mutuba sai da baba Iliyasu ya lakaɗa mata dukan kawo wuƙa, tai tiɓis ɗin da ko yatsa bata iya ɗagawa.
Mama gaje kuwa ta fasa kuka da kururuwar za'a kashe mata ƴa.
Kafin kace kwabo labari ya fara fitowa a anguwa, dan duk maƙwafta najin abinda ke faruwa.
________________________________
Yanda Samina ke ambaton ƙiyyar Ahmad a bakinta abun na bama kowa mamaki, duk da dai an fahimci harda ruɗin ƙyale-ƙyalen duniya ke kwasarta, amma tabbas akwai zuga dake aiki akanta, bakuma kowa bane ke zugata sai mahaifiyarta Mama gaje, saiko Inna mari kakarta da itama tai ɗare-ɗare a zancen, gefe kuma gasu Nafy sunayi ta waya da zahiri idan sunzo gidan da ƙaryar dubata.
Dan dukan da baba Iliyasu yay mata ciwo sosai ya sakata, ko magana mai ƙarfi ta kasa yi.
Kuma Ahmad ɗin dai da bakinta bai gajiya da munanawane ya samo likita ya dubata, ƴan kuɗin dake aljihunsa na ɗinki da aka biyasa ya cire ya biya kudin magani dama duk abinda aka buƙata.
Tun anama Samina mazurai har iyayenta maza da Amma suka koma lallashinta dukdan ta kwantar da hankalinta ta fahimci halin da ake ciki.
Sai dai sam taƙi fahimta ɗin.
★★★★★
Tsahon kwana huɗu abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, saima neman ɗakin da zasu zauna haya akeyi.
Ahmad kuwa yaƙi cewa kowa komai, sai bushewa yake a tsaye saboda damuwa, harya fara duhun baƙi, gashi abun na neman taɓa masa aikinsa na ɗinki, dan yanzu ya daina yin komai sai tunani.
Wanka wannan sai Ayyah ta sakashi a gaba yakeyi, hakama abinci sam bayason ci sai an masa faɗa.
Yana ƙaunar Samina sosai, duk wannan haukar cin mutuncinsa da takeyi bama yajin haushinta, a ganinsa canja masa ita akai kawai, dan Saminar sa ba haka takeba da can.
Gashi duk yanda yaso su haɗu taƙi bada ƙofar hakan, duk sanda ya aika a kirata zagi ma take maido masa, idonta ya rufe gaba ɗaya, burinta kawai Ahmad yay zuciya ya saketa.
Yau data kasance duk yaran gidan na ma'auri sunzo gidan akan wannan maganar aure data bama kowa mamaki, masoya sun zama maƙiya, wanene a anguwar baisan soyayyar Samina da Ahmad ba, sai dai baƙon da bai wuce sati ɗaya ba.
Binta yayar Samina ta kalli Saminar dake kwance a saman gadon Mama Gaje tana sharɓar hawaye, ga zazzaɓi daya rufeta saboda ƙuntata kanta da takeyi a kwanakinnan.
“Humm anya Samina kina ganin kuwa kinma kanki adalci a wannan gaɓar? Anya kuwa kece Samina ƙanwata dana sani mai tsantsar ƙaunar Yah Ahmad. Mike ruɗaki hakane kike son tafka babban kuskuren da anan gaba baki da hanyar gyarashi? Miya shiga kankine? Samina kibar biyema mama wlhy, dan daga ita har Inna mari babu mai faɗa miki gaskiya akan batunnan, kwaɗayi ya rufe muku ido ku duka, kun manta UBANGIJI dake bayarwa bai manta da shi yah Ahmad ɗinba, sannan kuma aiba ALLAH ne ya sanar muku shima bazai taɓa yin arziƙinba ko? Duk gwamna da kika gani ko ɗan majalissa, ko minista, ko kwamishina, ko shugaban ƙasa, ko babban ɗan kasuwa, ko babban ma'aikacin gwamnati to shima a baya talakane, kije ki bibiyi tarihinsa kiji, talakannan da zaki aura wataran shine zaki buɗa ido ki ganshi a wancan matsayin da ayanzu ya maida ganinki duhu Samina, wlhy dana auri mai arziƙi gara na auri talaka musha wahala tare wajen tara arziƙin, koba komai zai mutuntani ya girmamani, sannan ko mata dubu yayi a bayana sai yafi nuna kulawarsa gareni fiye dasu, a wannan zamanin kuma Samina yanda maza suka lalace da wulaƙanta mace a gidan aure, wlhy kasamu mai maka soyayya irinta Yah Ahmad ka gama morewa, kwanciyar hankali a gidan aure ita mace ya kamata tayi fata a wannan zamanin ba dukiya ba, dan daga lokacin da mai dukiyar ya kaiki cikin gidansa to fa ina gaya miki komai zai canja, dan kinbar ganin farin cikinsa da lokacinsa kuma, ki zauna kiyi tunani, karki bari damarki ta wuceki, dan daga lokacin da kika kai haƙurin Yah Ahmad bango yaji ya dace ya sakeki tun a sannan zaki fara nadama har ƙarshen numfashinki wlhy.......”
“Aniyarki ta koma miki, kujimin Yaya Bintar nan da mugun baki, ai dawwama a auren Ahmad ne zaisa nayi nadama har ƙarshen numfashina, rashin auren Ma'aruff kuwa shine sakaci da damata, idanma tunani kike maganganunki zasuyi tasiri a kaina to basu shigaba, dan jinsu nake busar sarewa ma ta fisu daraja, idan kuma shine ya aikoki kije ki sanar masa ba'a daceba, nace bana sonsa a yanzu, ko dolene saina zauna dashi, ana so dolene? So kuke nima na ƙare cikin talauci da fatara a gidan miji kamar ku, a cikinku kaf babu wata mai abin nunawa a gidan miji inba talauci ba, jibeki, shekarunki gaba ɗaya basu wuce talatinba, amma saikace tsohuwar data ƙulla hamsin, a dalilinmi zan zauna na ƙare a talauci kamar ku, aini bama ƙaramin sona ubangiji yakeyi ba da ya kaini matsayin ƙara karatunnan, da haka nima za'a cutamin, a bankani ɗakinsa na ƙare rayuwata a wahale, wataranma har surfau ɗin masara da wankau sai an sameni inayi saboda fatara da rashin abincin arziƙi mai ɗan maiƙo-maiƙo”.
Binta da tai shatata da baki tana kallon ikon ALLAH daga Samina, taɓe baki, lallai ƴar uwar tata tayi nisan da sam bazataji kiraba.
“To ALLAH ya ƙyauta miki Samina, ai duk wanda yace zai iya haɗiye gatari sai a sakar masa ƙota, ALLAH yasa kar Yah Ahmad ɗin ya sakeki muga tsiya”.
Baƙin ciki sosai maganar Binta ta ƙarshe taima Samina, a masife tace, “Bakinki ya sari ɗanyen kashi, muguwa kawai azzaluma”.
Dariya Binta ta fita tanayi, inda tun fitowarta mama Gaje ke zuba mata harara tamkar idonta zai faɗo, ɗanwake take jefawa a tukunya, shiyyasa koda take jiyosu bata shiga ɗakinba.
A ɓangaren su Ahmad ma ƴan uwansa ne zagaye dashi, shawara suketa bashi akan yayi haƙuri yabar Samina tunda tace bata yinsa yanzu, da adawo ana dana sani nan gaba barin auren tun yanzu kamar shine yafi alkairi.
Murmushi mai cike da damuwa Ahmad yayi, murya a sarƙe yace, “Yaya Maryam ina sonta, nasan duk abinda take faɗa shirmene kawai, nan gaba kaɗan zata bari muyi zaman lafiya, ana kaitane zakuga wannan shirmen dukta bari, yanzunma zugata akeyi shiyyasa”.
Gaba ɗayansu zuba masa ido kawai sukayi da mamaki, sunsan ɗan uwan nasu akan Samina babu abinda zasu faɗa masa ya fahimcesu, sai kawai duk sukaja bakinsu sukai shiru.
Haka Samina taci gaba dayin bore tsawon lokacin satin nan uku da suka shuɗe, a kuma na huɗun da aka shigane tarewar nasu, dan an samu ɗakin da zasu zauna anan ƙasan layin nasu kaɗan, harma an masa fenti, yayinda iyayensu maza suka haɗa kuɗinsu kamar yanda sukeyi aduk ƴaƴansu da zasu aurar aka siyama samina kayan gadon gwargwadon ƙarfinsu.
Kasancewar bikin yazo babu shiri sai baba Rabi'u yace ƴan shema ba sai kowa yazoba, su zaɓi wasu a ciki su ɗanzo a raka Saminar ɗakinta shikenan, dan ta jama kanta baza'ai wani taron bikiba...........✍🏻
*_Bilyn Abdull ce_*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*(9)*
............Ahmad dai duk abinda akace masa da to kawai yake amsawa, abokansa ma dake jin haushinsa akan dagiyar da yayi kan Samina haka suke taimakonsa da ɗan abinda ALLAH ya hore musu, haka suka ɗan gagganɗa sukai masa ɗinkuna kala biyar na angwanci, suka kuma haɗa kuɗin fentin ɗakin da za'a saka amarya tare da yin ƴan gyare-gyaren da suka dace ayi.
Mama gaje dai taƙi bada ko cokali da sunan kayan ɗakin Samina, haka su Binta sukaje suka jera katakan gado sai katifar da aka saka, amma ko zanin gado babu.
Sai da ƴan shema sukazo sai ga inna marwa da ƴar gudunmawarta, annan ne aka sami zanin gadon da aka saka a gadon, sai ƴan kwanika da dangi suka haɗa suma akaje aka ajiye mata.
________________________________
Ayyah harda kukanta lokacin da takema Ahmad nasiha akan haƙuri da wannan aure nasu da babu fasali a cikinsa, tasan matsaloli yanzunne zasu fara tunda zasu kasance a inuwa ɗaya, ga kuma Samina har yanzu tana akan bakanta na bazata zaunaba, harma da iƙirarin saita kashe Ahmad ɗin.
Shima baba ya masa nasiha, hakama Iya da malam, kowa dai muhimmancin haƙuri yake nuna masa, dan kuwa dai tsakaninsa da Samina haƙurinne kawai zai riƙe a zauna lafiya.
Ansha danben bala'i wajen fidda Samina a gidan, dan kuwa hayaniya ce sosai ta ɓarke tsakanin dangin mama gaje da nasu Ahmad, dan ɓoye Samina sukai suka hanata fitowa, sai da Baba Yusha'u ya shiga da kansa ya taso ƙeyarta yana cewa duk su tattara su bar masa gida.
Itama Saminar data nema tirjewa ya lakaɗa mata uban duka, ko wanka batayiba aka cimimiyeta zuwa gidan da zasu zauna matsayin Amarya.
*_10:30_*
Kowa ya kalli Ahmad a wannan lokacin yasan akwai damuwa, cikin danne fargabarsa yabi umarnin Ayyah yay wanka, cikin kayan da su Sufyan suka ɗinka masa ya saka ɗaya, yasa turare kaɗan ya fito.
Iyayensa sun bisa da addu'a, yayinda zukatansu duk suke a tsorace gameda ikirarin Samina na kashe Ahmad a randa suka tare.
A waje ya iske abokansa, ya basu hannu duk sukai musabaha, sannan suka take masa baya har gidan da aka kai masa amaryarsa.
A ƙofar gida su Salisu duk suka ja birki, Sufyan ya miƙa masa ledar da suka sayo kaza yana ɗan bugun kafaɗarsa cikin tsoka.
“Ayi amarci a hankali kar da safe mu nemo kafintan gyaran gado”.
Gaba ɗayansu dariya suka sanya, amma banda Ahmad da sam zuciyarsa ba'a wajensu tameba, sun masa sallama bayan addu'a da sukayi suka juya, rufe gidan yayi ya shiga da sallama.
Bawani babba bane gidan, irin dai gidajen talakawa ne da kowa ya sani, sai dai su biyune kawai a ciki suke haya, ɗayar matar ita kaɗaice sai mijinta da yaransu biyu, saisu Ahmad ɗin yanzu da suka tare.
Ɗakinsu shine farko, dan haka kai tsaye ƙofar ya dosa, gabansa sai faɗuwa yakeyi, hakanne ya sakashi dakatawa ya karanto addu'oi neman tsarin ALLAH daga sheɗan.
Labulen ya ɗaga ya shiga ɗakin da sallama, ɗakin sai ƙamshin sabon benti yake dana katako, Samina na zaune a bakin gado ta duƙar da kanta kamar mutuniyar ƙwarai, hijjab ne jikinta ruwan hanta, shiyyasa bai fahimci a wane yanayi take ba.
Jiki a sanyaye ya ajiye ledar hannunsa, murya can ƙasa yace “Samie na”.
Shiru bata tanka masaba, ba kuma tai motsiba, hakanne ya sakashi matsawa gareta ya kai hannu zai taɓata, wata muguwar zabura tayi tana miƙewa tsaye, ta fiddo hannunta dake riƙe da sabuwar wuƙa fil da keta ƙyalli.
Hawaye na kwarara a idonta tace, “Wlhy kana taɓani saina soka maka wuƙarnan, idan kanason kanka da arziƙinka ka sakeni kawai”.
Ahmad dake kallonta ya riƙe ƙugunsa da hannayensa duka biyu, murmushin da ya daɗe baiyiba ya saki, yace, “Haba Samina, Ahmad ɗinki nefa, ki kwantar da hankalinki dan ALLAH mu fahimci juna.....”
“Fahimtar juna? Yo ai kasani babu ita a tsakaninmu a yanzu, saki kawai nake buƙata daga gareka, inba hakaba ALLAH saina kasheka yau a ɗakinnan”.
Murmushin ya sake yi yana sauke numfashi, ya rungume hannunsa ɗaya akan ƙirji yana kai ɗayan a fuskarsa ya shafo ɗan gemunsa na gayu.
“Samina bazaki samu abinda kike bukatarba kuwa, sai dai idan ki kasheni, koba komai zanbar tarihin masoyiyata ta kasheni da hannunta, kuma koba komai zakimin takaba ai ko”.
Wata dariya da ta bama Ahmad mamaki da tsoro Samina ta kece da ita, ta ajiye wuƙar hannunta tana haɗe fuska, “Oh da wannan banzan ƙwarin gwiwar taka ka dogara shiyyasa ka kafe bazaka sakeni ba? To ai shikenan, nama fasa kashekan, kaina zan kashe, kaga saika zauna da gawa ai”.
Kallonta kawai Ahmad yake duk da furicinta ya tsoratashi, amma yasan faɗa kawai take danta tsoratashi.....
Katsesa tayi da faɗin, “Ka sakeni nace malam”.
Cikin halin ko in kula Ahmad ya zauna bakin gadon yana cewa, “Idanma zaki kwantar da hankalinki ki kwantar Samina, dan nikam dai ba sakin naki zanyib......”
Warin fiya-fiya da ya shaƙoma hancinsa ya sakashi saurin juyowa yana kallonta.
A wata irin zabura da ƙwala kiran sunanta yakai hannu ya cacumota, kwalbar fiya-fiya data kafa a baki har tasha kusan kwata ya kaɓe ta faɗi ƙasa, yayinda idanun Samina suka fara juyewa, saiga bakinta ya fara kumfa.
Sosai Ahmad ya fashe da kuka yana jijjigata tamkar mace....
Waɗanda suke gidan da duk suke jiyo mahawarar Samina da Ahmad daga ɗakinsu tun daga farko ne suka fito a guje, lokacin numfashin Samina harya fara fisga.
ALLAH ya taimaka mijin matar yanada motar da yake haya, nanfa Ahmad ya ɗauki Samina bisa umarnin mutumin suka kaita mota, babu ɓata lokaci suka doshi asibiti.
Da ƙyar su Ahmad suka samu aka karɓi Samina, sai da sukai ƙarya akan a mistake tasha fiya-fiya catake maganine sannan aka amsheta.
Komai ya kwancema Ahmad, babu abinda yakeyi sai hawaye, dan sam bai kawo shirmenta zai kai girman hakaba, duk ya ɗauka farfaganda ce kawai danya mata abinda takeso.
Har washe gari kuma basu sami labarin farfaɗowarta ba daga likitoci, duk wanda ya fito suka tambayesa baya basu amsar komai.
Tunda Safe matar wanda ya kawosu asibitin taje gidan su Ahmad ta sanar da duk abinda ya faru, hankalin kowa ya tashi a gidan, musamman ma iyayen Ahmad, mama gaje kuwa kuka take tana faɗin bazata yardaba, inhar Samina ta mutu sai sunje kotu wlhy, shima Ahmad sai an kasheshi, dan shine ya kashe mata yarinya.
Har suka iso asibitin babu wani bayani ƙwakwkwara daga likitoci, Ahmad ya faɗa jikin baba Hamza yana kuka, duk yayi wujiga-wujiga, kallo ɗaya zakai masa kasan shima yana buƙatar a bashi gadon.
Sai kusan sha biyun rana labarin farfaɗowar Samina yazo musu, amma dukda haka tana a cikin mawuyacin hali da addu'a kawai take buƙata.
Hankali yaɗan kwanta, amma banda na Ahmad, daga baya ma jirine ya kwasheshi ya faɗi, sai da aka saka masa ƙarin ruwan da ya sakashi dogon barci.
Har zuwa la'asar Ahmad bai farkaba, zuwa lokacin kuma ita Samina ta farka, idan ka ganta dolene ta baka tausayi, tayi wani zuru-zuru, idanun sun sake fitowa, amma dukda wannan mawuyacin halin da take faɗi take sai Ahmad ya saketa.
Zuwa dare Ahmad ma ya farka, babu laifi jikinsa ya ɗan masa ƙarfi, tunda har shiga yay ɗakin da aka kwantar da Samina ya dubata, lokacin ta sake komawa barci, sosai tausayinta ya kamashi, ya share hawayen da ke zuba masa saman fuska yana ɗauke idonsa daga gareta, son gaskiya yakema Samina, dan haka bazai barta ta ƙuntataba insha ALLAHU.
________________________________
Bayan kwana biyu abubuwa sun ɗan lafa, jikin Samina da sauƙi, haka shima Ahmad, sai dai damuwar da ta zame masa fitar numfashi.
Babu abinda ke ƙara sukar zuciyarsa irin zuwan Ma'aruff asibitin, a gabansa Samina ke nuna kulawarta ga Ma'aruff duk da igiyar aurensa har uku suna kanta, sannan komai na asibitin ma'aruff ne ya biya, har abinci da kayan ciye-ciye shiyake kawo musu, shi ko koya sayo ɗan abu dai-dai karfinsa koma kallonsa ba'ayi, agabansama za'a ɗauka a saka a bola.
Haushin hakanne ya saka Rahma yin magana, amma sai baba hamza ya ƙwaɓeta akan tayi shiru, komi zasu gani daga mama gaje karsu sake cewa komai.
Ranar da yamma aka sallamo Samina, ma'aruff ya ɗakkosu a motarsa ya kawosu gida, Ahmad sai mashin ya hawo ya biyo bayansu.
Babu wanda yace komai akan hakan, kowa ya shiga yay mata sannu, hakama maƙwafta sunata shigowa, ƴan son ganin zahiri a ɗauka ai gaba sunta gumtsar gulma.
Ahmad dai tunda suka dawo yana ɗakinsu kwance, sai bayan sallar isha'ine ya shiga gidan, Ayyah ta samu ta titsiyeshi yasha furar data saya masa tun da rana.
Bayan ya gama sha ne yaje ɗakin baba ya amsa kiran da yay masa, sun ɗan tattauna kafin su fito zuwa sashen malam Rabi'u.
Kamar yanda Ahmad ya bukata dukkan iyayensu mata da maza sun hallara.
Ahmad na share hawaye tamkar mace ya fara magana cikin nutsuwa.
*_“Da farko dai ina godiya ga ALLAH sannan a gareku iyayena, nasan kun nuna dukkan hallacinku gareni, tareda ƙoƙarin ɗaura igiyar da zata ƙulle zumincinmu fiye da da, ina neman afuwa a gareku badan, kubani dama na aiwatar da abinda zai kawoma kowa kwanciyar hankali, ba tare da abinda muke gani dai-dai ya koma kuskureba. Son gaskiya nake miki Samina, wanda babu ta yanda idan na musalta za'a fahimceni, a tawa fahimtar ka bama abinda kakeso kowacce irin damar da yake buƙata kuma zata kawo masa kwanciyar hankali da farinciki shine soyayya ta gaskiya, na fahimci a yanzu sam hankalinki baya gareni, to bazan tursasakiba, ni Ahmad Hamza Rabi'u ku shaida daga yau, na saki matata Samina saki daya, domin sadaukar da soyayyata ta gaskiya, taje ta auri wanda takeso, ALLAH ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba”._*
Ahmad ya ƙare maganar yana share hawaye masu zafi dake gangaroma kumatunsa.
Tsit ɗakin yayi, hatta da Samina sai da taji wani iri a ranta, amma tai saurin ture tausayinsa tana sauke numfashi irin na na rabu da ƙaya ɗinnan.
Malam Rabi'u ya saki murmushi irin nasu na manya, cikin muryarsa ta tsufa yace, “Amadu ALLAH yay maka albarka, ALLAH ya tsare gabanka da bayanka, ya share hawayenka, ya sanya farinciki a rayuwarka har gaban abadan, lallai kacika namijin gaske mai soyayya dan ALLAH, inaji kuma a raina koda ba'a nan duniyaba zaka samu ƙyaƙyƙyawan sakamako”.
A tare baba Iliyasu da baba Yusha'u sukace, “Insha ALLAHU” daga nan suma suka ɗora da sanya masa albarka, baba Yusha'u yace, “Ahmad a karo na biyu inhar ka amince na baka auren Umm-Rumana, badan komai nake ƙwaɗayin wannan haɗinba sai ƙyawawan halayenka, duk uba daya mallakeka matsayin ɗa ya gama hayewa a rayuwarsa, hakama duk surukin da ya sameka matsayin suruki yaci riba, yanda naso wannan haɗin zumincin bana fatar bijirewar wadda bata ɗaukeni da muhimmanciba zaisa gwiwa ta sarewa”.
Murmushi nanma malam yayi, idonsa kafe akan Ahmad da ya kasa koda motsi, shida yake ƙudirawa a ransa safiyar gobe zai bar garin gaba ɗaya yay nesa dasu shine za'a masa wannan dabaibayin kuma?.......
Cikin katsema Ahmad tunani malam yace, “Amadu inhar wannan haɗin bai maka ba karka cutar da kanka, dan kuwa ba tilas bane a gareka, amma ni kaina nayi maka sha'awar hakan, dan Umm-Rumana yarinyar kirkice da kowane miji zaiyi fatan samu”.
Innalillahi...... Ahmad yaketa ambata a ransa, wannan magana ta masa girma, shidai a yanzu bai dace ya bijirema iyayensa ba kodan abinda Samina ta aikata, sannan koba komai itama zai maida mata murtani, kamar kuma yanda yay alƙawarin haƙura da ita auren Umm-Rumana ne kawai zai tabbatar masa da hakan tunda ubansu ɗaya...
Ayyah ce ta dafashi, hakan yasa yay saurin kallonta, da ido taimasa alamar ya amshi auren, dan haka ya maida kansa ƙasa ya duƙar yana faɗin, “Na amsa baba, ALLAH yasa haka shine mafi alkairi”.
Dandanan fuskar kowa ta washe da murmushi, banda Samina da mama gaje, dan mama gaje ma baki ta taɓe ta miƙe riƙe da hannun Samina da tai gajeren tsaƙi suka fice.
Babu wanda yabi takansu, balle a nuna an damu dasuma.
★★★★
A wannan daren kam inhar Ahmad yayi barci to sai dai ɓarawo kuwa, dan komai ya juye masa, har mamakin abun yake da tunanin koma dai mafarki yakeyine?.
Ya ayyana hakan a ransa yafi sau dubu, harma Mudanseer dake kwance gefensa ya kasa jurewa ya tashi ya fara masa nasiha da shawarwari duk da kasancewarsa yayansa, tare da haƙuri akan canjin da ALLAH yay masa akan Umm-Rumana, inhar yay haƙuri ya riƙe watarana zaiyi dariya insha ALLAHU, ya cire zancen Samina a ransa, ya fuskanci sabuwar rayuwar gida wata soyayyar, kamar yanda itama ta nuna ta manta da shi da komansa.
Yaji daɗin shawarar ƙanin nasa sosai, dan haka ya samu ƙwarin gwiwar tashi yayo alwala yazo ya fara nafilfili yana miƙama ubangiji kuka sa.
Ranar haka ya kwana kan sallaya, sai da suka dawo sallar asubahine ya samu ya kwanta ramuwar barci.
**********
Ɓangaren Samina jinta take sakayau, duk da wani gefe na zuciyarta yana suka akan maganar haɗa Umm-Rumana aure da Ahmad, sai dai kuma tana ƙokarin kauda abin a ranta baki ɗaya, musamman yanda jikinta har yanzu babu ƙarfi, ga Mama Gaje kuma nata zuga ƙoƙarinta akan abinda tayi har Ahmad ya saduda ya saketa.
Ranar dai da tsantsar farin ciki tai barci, kusan raba dare sukai tana hira ita da Ma'aruff a waya, kowa na ƙara jadadama ɗan uwansa irin ƙaunarsa da yakeyi cikin zuciya da ruhi.
Umm-Rumana kam batasan bikin da akeba a kanta, dan babu wanda ya sanar mata da komai, ko mahaifiyarta batace mata komai akan maganarba.
Amma batayi baƙin ciki akan aurar da ɗiyarta ga Ahmad ba, dan kowa yasan mutumin kirkine, bashi da wani mugun halin da za'ace abin gudu a rayuwarsa, to mizaisa tayi baƙin ciki da hakan, tunda har mahaifin Umm-Rumana da kansa yaga nagartar Ahmad yakuma ji a ransa zai masa halacci da ɗiyarta, fatan alkairine kawai nata da musu ƙyaƙyƙyawar addu'ar zaman lafiya.
___________________________
Babu wanda yay tsamanin a ranar za'a sake ɗaura auren, sai gashi kusan ƙarfe goma sha ɗaya na safe motocin ƴan shema har huɗu sun dira maza da mata, dandanan gidan ya kacame da hayaniyar ƴan bikin da sam babu shiri, hakama dangin Ammi mahaifiyar Umm-Rumana sun cika gidan, dangin gwaggo ma haka na kusa sai ɓullowa sukeyi ta ko ina, to abinka da maganar waya.
Duk wannan abu dake faruwa Ahmad bai saniba, sai da Mudanseer ya tadashi akan ya tashi lokacin salla yayi, mamaki ya kamashi lokacin daya shigo yaga gidan a cike.
Babu kuma wani ɓoye-ɓoye Ayyah ta sanar masa aurensa za'a sake ɗaurawa bayan sakkowa masallacin juma'a da Umm-Rumana.
“Ayyah da wuri haka? Nazata ai za a bari sai nan gaba ta kammala makarantarta”.
“Haba ɗan albarka, minene wani abin jinkiri anan, Rumana dai ai ta isa aure, kuma ba baƙuwarka bace balle kace kanason sanin halayenta, kaima ba baƙonta baneba, idan batun soyayya ne kuje can a gidanku zaku ƙullata, tamafi ta shirmen wajen nan daɗi da nagarta, makaranta kuma duka wata nawa ya rage, idan taje gidan naka saita karasa ai, muma munfison ayin kawai hankalinmu ya ƙwanta, dan nafison ka riga yarinyarnan yin auren, muyi addu'a kawai ALLAH yasa haka shi yafi alkairi, maza je kayi wankan ga waɗannan kayan saika saka”.
Jiki a sanyaye ya amshi farar shaddar dake a cikin leda viva yay mata godiya..........✍🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻_**ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuoeSgXuo
*(10)*
............Ƙarfe biyu da rabi na rana ɗunbin jama'a suka sake shaida ɗaurin Ahmad akaro na biyu tare da Umm-Rumana, akan sadaki naira dubu ashirin.
Kansa kawai ya duƙar ƙasa yana haɗiyar zuciya, wai shine aka ɗaurama aure a karo na biyu cikin kwana uku kacal, sannan kuma bada Saminar sa ba, wadda ya ɗauki dukkan buri ya ɗoramawa, dukkan rayuwar aurensa da kullum yake tsarawa a zuciyarsa da itane, amma yau gashi ta nuna masa data zauna dashi gara ta kashe kanta ko shi ta kasheshi.
Kenan yanzu da Rumana zaiyi rayuwar aure? Yarinyar da bai taɓa mata cikakken kallon minti biyarba duk da a gida ɗaya suka tashi, shi zaima iya rantsuwa bai taɓa maganar data kai kalma ɗari da itaba cikin lokaci ɗaya, tsakaninsa da ita a kullum gaisuwa ce, saiko aike, shima sai idan wani dalili yasa ta gitta ta gabansa ne........
Da ƙyar ya iya haɗiye abinda ta toshe makoshinsa, ya ɗago kansa saboda dafansa da akayi a kafaɗa.
Baba Iliyasu dake kansa tsaye yay masa nuni akan ya miƙe, babu musu ya tashi tsaye, kama hannunsa kawun nasa yayi har zuwa gaban jama'ar shema, nanfa Ahmad ya shiga gaishesu cike da girmamawa, saboda yasan dayawan cikinsu dukda bawani sosai ma yake zuwa Shema ɗinba.
Atare suka rankaya zuwa cikin gida, inda aka baje musu tabarmi a zaure suka zauna cin abinci, shi dai Ahmad baici komaiba, yana gefe abin duniya duk ya gallabesa, sai sauke ajiyar zuciya yake a jere a jere.
Bayan sun kammalane sukasa aka kawo musu Amarya Rumana, wadda tun a safiyar yau mahaifiyarta ta zaunar da ita cikin hikima da nasiha ta sanar mata abinda ake ciki.
Tasha kuka, amma tasan ko giyar wake tasha bazata bijirema iyayenta ba, dan ba wannan tarbiyyar mahaifiyarta tai mataba, fargabarta ɗaya tayaya Yah Ahmad zai sota? Mutumin da baya kallon kowacce mace da arziƙi inba Samina ba, ita kaɗai ke ganin fara'arsa, ita kaɗai ke iya jin doguwar maganarsa, ita kaɗai tasan sauƙinsa.
Sukam da ko wasa bayayi dasu, iyakarsu dashi su gaisheshi ya amsa, saiko idan hanya ta haɗaku ya aikeka idan da bukatar hakan, ko ɗinki zai musu baya tsayawa jin style ɗin da suke bukata ko wani ra'ayinsu.
Nasihar da mahaifiyarta da ƴan uwanta sukai mata ce ta sata sake ɗammarar sakama ranta haƙuri, koba komai zata zama sanadin dai-daita barakar dake neman shigo musu a family, sannan zasu hana fitar haƙoran maƙiya da sunan musu dariya, bakin ƴan bani na iya zai rufe ruf wajen maida yanda akayi.
Kanta a ƙasa ta rufe fuska sosai da gyalenta ruwan hanta da akaima kwalliyar ruwan madarar les a baki suka fito, tana sanyene da atanfa ruwan madara mai ƙyau, kayantane na salla da Ahmad yay musu ɗinkin ita da su Samina, kasancewar babansu ne yay musu kayan, dayake sawa biyu kawai tai musu sai kayan suke fes tamkar sabbi, sai ƙamshi take mai sanyi.
Inna marwa dake riƙe da ita tai mata izinin ta zauna, dan sun iso soro inda ƴan shema suke.
Tun shigowarsu kuma Ahmad yake binta da kallo ƙasan ido, wani iri yakeji a zuciyarsa game da wannan auren.....
Nasihar da ƴan uwan nasu ke musu ta sashi katse tunaninsa ya maida hankalinsa garesu.
An musu nasiha mai ratsa jiki, wadda duk ta kuma sanyaya jikin Ahmad, harma da ita Rumana ɗin, dan koba komai ta fahimci wannan auren nasu farin cikin mutane masu yawane, sannan kwaranyewar hawayen mutanene masu ɗunbin yawa da Samina taso sakawa kuka.
Bayan an gama musu nasiha kakanni da abokan wasa suka koma tsokanarsu, yayinda wasu acikin ƴan uwan ke karesu, dansu duka babu mai bakin ramawa, bare dama daga Ahmad ɗin har Rumana dama basu da yawan magana.
Bayan sallar la'asar ƴan shema suka juya zuwa gida, tunda bikine bana shiriba suma basuzo da shirin kwana ba, mutum huɗu kawai aka bari suma tsoffine.
Tafiyar ƴan shema tasa hayaniyar gidan raguwa, hakan yasa Ahmad shigewa ɗakinsu ya cire kaya ya ƙwanta saboda zazzaɓin da yakeji sosai, har ya fara rawar sanyi ma.
Daga cikin gida kuwa babu wanda yasan halin da ake ciki, dan sunata shirin kai amarya ɗakinta, kayan Samina da aka kaine za'a barma Rumana ɗin, tunda dama babu ko cokalin Mama gaje acan, duk dangin su Ahmad ɗinne suka tara suka kai.
Ƴan kayan da Ammin Rumana ta fara tarawa na auren Rumana ɗin aka fiddo ake ɗan wankewa, dukda bana kirki bane zasu taimaketa ko yaya dai.
Duk bikinnan da akeyi fa Samina na gidan, saboda ta nuna abinma bai dametaba komanta yinsa take kai tsaye a gadarance a gidan, hakama Mama gaje, har dariya takema Ammi akan haɗin auren Rumana da Ahmad, wai saji sa gani, nan za'a ringa ƙullar tuwo a kwano ana wucewa dashi gidan Rumana, dan sunsan dai Ahmad bashi da abinda zai riƙe Rumana.
Babu wanda ya kulata akan zancen, dan kowa kwllon wawuya yake matama yanzu, daga ita har ƴar tata.
Gefe kuma ga munafukan ɓoye irinsu Umma (Sailuba uwargidan baba Iliyasu, aminiyar Mama gaje a gidan idan baku mantaba) dan tana ɗaya daga cikin mai tunzura mama gaje da Samina akan auren Ahmad, bayan itama akwai sangamemiyar budurwa a gabanta Salima, dan sa'arsu Rumana ɗince, tarema suka tashi su uku tamkar tagwaye, Umm-Rumana, Fa'iza ƙanwar Ahmad, sai Salima ɗin.
Ayyah da bataga giccin Ahmad ba tunda aka dawo ɗaurin aurene abin ya dameta, dan haka ta aika a duba matashi ko yana ƙofar gida wajen abokansa.
Koda Abu yaje ya tambayi su Rabilu sai sukace aisu tunda aka dawo daga ɗaurin aurenma basu sake ganinsaba, sun zata yana cikin gida yana wani abun.
Babu shiri Ayyah ta fito zuwa ɗakinsu Ahmad, saita iskeshi yanata rawar ɗari a bargo, hankalinta ya tashi sosai, tasaka Abu ya kira mata Baba Hamza.
Tunda baba yaga halin da Ahmad yake ciki sai tausayinsa ya kamasa, sunata jera masa sannu shi da Ayyah, a ɓoye ba tare da kowa ya saniba Mudanseer ya kira wani mai aikin asibiti anan kusa dasu ya duba Ahmad ɗin.
Bai ɓoye musuba ya sanar musu damuwace tai masa yawa, shine harta haddasa masa zazzaɓi, dan baya samun isashshen barci ma, ga malleria kuma a gefe itama.
Magunguna ya basa, yace yaci abinci sannan yasha ya kwanta danya samu isashshen barci.
Har Ayyah ta kawo masa fura yasha da ƙyar, zata bashi maganin baba ya dakatar da ita akan ta barshi ba yanzuba, tunda likitan yace akwai na barci suɗan ɗaga ƙafa zuwa anjima, dan Malam yace yau za'a kai Rumana, to kenan bayasha magani yay barci a nanba kuma, bayan an kaita sai yasha yatafi can ya kwanta.
Dole Ayyah tabi wannan umarni na mijinta, suka bar Ahmad, sai dai ruwan ɗumi da aka kawo masa yay alwala yay sallar magriba da isha duk a ɗaki, lokacinne kuma Ayyah ta sawo Gwaggo gaba a ɓoye tazo ta duba Ahmad ɗin.
Sannu tai masa sau ɗaya ta ɗauke kanta sai kace bata damuba, nanko ranta sai suya yake da halin da yaronta ke ciki, amma kawaici ya hana agani koda a fuskartane.
Kusan ƙarfe tara aka mika Rumana da tasha kuka tamkar hawayenta zasu ƙare ɗakinta, tasha nasiha a wajen iyayenta da dangin mahaifiyarta, malam ya bata ƙyautar da ko ita batasan minene a cikiba, hakama Iya ta bata.
Duk wanda yaga yanda take kuka saita bashi tausayi.
Haka suka mikata, basu wani jimaba suka barota tana cigaba da sharɓar kukanta.
Tunda Ayyah taga ƴan kai amarya sun wuce tazo ta tada Ahmad, da ƙyar ya iya tashi ya watsa ruwan zafi da Ayyah ta ɗumama masa, Abu yakai masa bayi, bai wani jimaba ya fito, jallabiya kawai ya bukaci a basa ya saka, dan haka Mudan ya fesheta da turare sannan ya bashi.
Baice komaiba ya saka, Ayyah tai zaman lallaɓashi yasha magani, da ƙyar yasha kuwa yana tsuke fuska da yamutseta, harda yunƙurin amai saboda tsanar da yayma magani.
Suka dai samu ya haɗiye duka da kyar.
Nasiha Ayyah ta sake masa da baba, kafin Mudanseer ya rakoshi inda Sufyan ke jiransa da mashin.
Shine ya ɗaukesa ya kaisa gida, kafin suje sai rawar sanyi yake, yanata sake ƙudundune hannunsa a ƙirji, ga jiri na ɗibarsa sabida rashin ƙwarin jiki.
Dole Sufyan ya taimaka masa har cikin gida, yay sallama a ƙofar ɗakin Umm-Rumana da har lokacin take zaune tana kuka ta amsa.
Izinin shiga Sufyan ya nema, ta bashi sannan ya shiga riƙe da Ahmad cikin ɗakin.
Babu shiri ta mike tana kallonsu a firgice, dan sam batasan Yah Ahmad baida lafiya ba, da taimakon Sufyan Ahmad ya kwanta saman gadon, Sufyan ya mikama Rumana ledar maganin Ahmad da kazar da suka saya musu da lemon ɓawo sai kankana.
“Amarya kiyi hakuri, angonki ya shigo miki ba yanda kowanne ango ke shigoma amryaba, bashi da lafiyane, muna fatan zaki kula mana dashi nanda kwanaki kaɗan ya dawo mana Ahmad ɗinsa jarumi mai yawan juriya da kowa ya sani, ALLAH ya baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba, ya kara muku hakuri da fahimtar juna, ya dasa muku soyayyar juna a zukatanku mai karfi daban mamaki da kwatance ga ma'abota soyayya”..
Itadai kanta a kasa tana hawaye bata iya bashi amsaba, ya juya ya fita yana faɗin ta rufe ƙofar shi ya wuce.
★★★★★
Sama-sama Ahmad ke jin Sufyan harya fice, daga bayama barci mai ƙarfi yay awon gaba dashi.
Har lokacin Rumana na tsaye tana hawaye, sai da taji tsayuwar ta gundireta ne ta ajiye ledojin hannunta ta nufi ƙofar ta rufe addu'a ɗauke da bakinta kamar yanda mahaifiyarta ta koyar da ita.
Zama tayi kawai ta zuba masa ido tsawon lokaci, tausayinsa na sake ratsa zuciyarta.
Itama kantane ke mata azabar ciwo, dan haka ta lallaɓa taja bargon dake saman gadon ta lullubama Ahmad data lura yana rawar ɗari, tana sakawa kuwa taga yajashi har saman kansa ya sake kudundunewa da ƙyau, ajiyar zuciya ta sauke tausayinsa na sake kamata.
Tsawon lokaci tana wajen har ta farajin saukar numfashinsa ya canja alamar barcinsa yay nisa sosai.
Tasan dolene a tausayama Yah Ahmad, dan halin da yake ciki abin dubawane, akwai tashin hankali abinda ka girma dashi a zuciyarka yazama shine sanadin rusa dukkan farin cikinka a dare guda.
Sabuwar tabarmar dake a ɗakin ta dauka ta shinfiɗa ƙasan ledar da aka saka a ɗakin ta kwanta ba tareda ta saka koda zaniba, sai filo data ɗauka kawai a gado saboda bata iya kwanciya babu shi.
Gyalen jikinta ta rufa dashi dukda bashi da wani kauri sosai.
A haka taci gaba da kukanta har itama barcin yay nasarar saceta, ga kanta yana sara mata sosai da ciwo.
_______________________________
A wannan darenma Samina da Ma'aruff sunsha hirarsu ta masoya, inda mafi yawan firar duk ta karkata wajen tsara yanda shagalin bikinsu zai kasance.
Daɗi tamkar zai narkar da ita, sai wani lumshe ido take tana dafe ƙirji da washe haƙora, har yanda take buƙatar lefenta ya kasance da kalar akwatunan da takeso da kayan gidan dazai zuba mata duk sai da ya tambayeta, sai events na garari na nunawa a gidajen tv da social media shima duksun tsara abinsu.
Cikin shagwaɓa take shaida masa yafayi ta turo manyansa, dan ita yanzu dukta tsani komai na gidansu, sotake ta kara gaba tabarsa kodan ƴan bani na iya.
Daga can Ma'aruff yay murmushi yana faɗin, “Karki damu gimbiyar mata, ni kaina na kagara na jiki a jikina lafe, ina baki gangariyar soyayya da babu sirkin ruwa a cikinta, burina kawai mallakarki tunda kinki bani damar hakan tun a yanzu, kince sai munyi aure, niko nayi biyayya na haƙura har a ɗaura a kawomin ke babie”.
“Oh ni kana bani kunya, gara dai kayi haƙuri harnazo, dan saboda na faranta makane ma nai duk abinda ya dace kar wancan shashashan ya sameni, dan kaɗan daga aikinsa ya kwata cikin ƙarfi, niko kai kaɗai nake burin cikama alƙawarin kawo maka budurcina har gida”.
“Nagode ta wajena, shiyyasa nake ƙara jin sonki na ƙaruwa a raina a kowacce daƙiƙa, dolene nazo na samu su baba ayi komai da wuri, insha ALLAHU nanda karshen wata kina nan kwance a ƙirjina”.
Yanda yay maganar da wani irin salone yasaka tsigar jikin Samina tashi, ta sauke nannauyan numfashi daya sake haukatar da Ma'aruff daga can, hakan yasashi kuma manne karuwarsa dake barci a jikinsa, dan saida ya gama holewarsa ne ma ya kira Samina ɗin.
“Sai da Safe”
Samina ta faɗa a sanyaye saboda kasalar da ya sakar mata da kalamansa.
Shima da “Uhmm” kawai ya iya amsa mata ya yanke wayar yana sake maida karuwarsa a network.
Haka Samina tai barci da ɗunbin begen abokin hakittarta, dolene ma tai yadda zatai ai aurensu da Ma'aruff a nan kusa, koba komai ta samu nauyin shekaru dake gallabarta ya fita. A shekarun da suka shuɗe Ahmad kawai take iya suffantawa da wannan yanayin, amma zuwa yanzu sam ba haka bane.
Wani gefe na zuciyarta yace yanama can yana hutawa da kanwarki amaryarsa kuma Rumana.
Baki ta taɓe tana jan tsaki, sai kuma ɗayan gefen zuciyarta ke shaida mata sam Ahmad bazaiyi hakanba, dan tafi kowa sanin halinsa idan ka ɗebe iyayensa, dan ko ƴan uwansa tafisu sanin wanene Ahmad akan abinda yake so, tasan kafin Rumana ta samu gane kan Ahmad za'a yara, dan soyayyarta ta riga ta masa ƙullin yaɗon wake a gona, kafin zuciyarsa ta fara kallon Rumana matsayin mace sai anyi babban dagama...............✍🏻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_**ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*(11)*
............Kiran sallar farko Ahmad ya farka, zazzaɓin ya sauka masa, sai dai akwai ciwon kai kaɗan-kaɗan, sai nauyin jiki da yakeji.
Ƙamshin sabon fenti dana katako ne ya tuna masa da inda yake, ya janye bargon da yake a ciki a hankali yana yunƙurawa ya tashi zaune, babu haske a ɗakin, dan Rumana ta saba idan zasu kwanta sai Ammi tace su kashe fitila, shiyyasa jiya da zata kwanta bayan ta gama shan kukanta sai ta kashe ta ajiye kusa da ita, a tunaninta ai zata riga Ahmad tashi da asuba.
Ahmad ya ɗan laluba ko zaiji wayarsa a jikinsa, sai dai babu, ya tura hannunsa ƙasan filon da ya tashi nanma babu.
Iska ya huro ƙaɗan a bakinsa yana janye bargon baki ɗaya, da lalube ƙafarsa takai ga bakin gadon, ya zurasu gaba ɗaya yana ambaton ALLAH a kan laɓɓansa.
Da sauri yay ƙoƙarin janyewa saboda jin ya ɗora akan mutum, sai dai nan ɗinma sake ɗorasu yay akan jikin nata.
Zafin da Rumana taji a ƙirjinta ne ya sakata farkawa tana faɗin “wayyo ALLAH Kadija zaki kasheni, bakicewa na haska miki fitila, ji yanda kike takani a ƙirji..”
Yanda tai maganar cikin yanayin barci da sanyin murya irin ta wanda yaji zafi sai da tsigar jikin Ahmad ta tashi, bai kawo a ransa tana wajen kwance ba, duk da ma dai zai iya cewa ya manta da ita a ɗikin.
Yana ƙoƙarin janye ƙafafun nasa Rumana ta kunna fitila ɗakin ya gauraye da haske.
Ba ƙaramin faɗuwa gabanta yayi ba ganin Ahmad zaune, sam ta manta inda takema ita, tai saurin jan gyalenta ta rufe jikinta saboda da daddare takura mata rigarta tayi shine ta zuge zif ɗin ya koma ƙasa sosai.
Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke idonsa, ya sake ziro ƙafafunsa ƙasan batare da yace mata komaiba.
Itama dai ko motsi bata sakeba harya ɗauki buta ɗaya cikin guda biyu da aka zubama ruwa aka ajiye farkon ƙofar ɗakin.
Hannu yasa ya zare sakatar ɗakin da ta saka ya fice, yanda iskar asuba ke kaɗawa a hankali ce ta sakashi buɗe hanci ya zuƙa sosai sannan ya fesota ta baki yana lumshe idanu.
Rumana dai kasa motsawa tai, sai kalmomin data faɗane ke mata kaikawo a rai, takai hannu saman ƙirjinta daya taka kunya na sake kamata, dukda ba nauyi ya sakiba taji zafi, kuma tana ɗanji har yanzu kaɗan, maida zif ɗinta tayi ta miƙe jiki duk babu ƙwari, ta ɗauke filon data kwanta tare da naɗe tabarmar.
Yanda fitilar tasu taɗan hasko waje tana hangenshi yana alwala a ƙofar ɗakin, da yake gidan bawani girmane da shiba, babu wani isashshen tsakar gida sam....
Ya katse mata tunani yayinda yake ɗaga labulen ya ajiye butar, kamar zai tafi sai kuma ya dawo da baya ya shigo ɗakin.
Ta gabanta yabi zuwa gaban gadon, ya ɗaga filo yana sake duba wayarsa, ganindai babu ita saiya maida kallonsa ga Rumana dake tsaye jikin Wadrobe kanta a sunkuye tana kallonsa gefen ido.
“Sufyan bai bada wata bane?”.
Da farko bata fahimci tambayar tasa ba, dan haka taɗan ɗago ido ta kalleshi, ganin ya tsareta da idanu tai saurin janye nata, cikin in ina tace, “A'a, ƙila ya manta ne”.
Baice komaiba yazo ya sake raɓata ya fice.
Tana jiyoshi ya buɗe gida ya fita, hakan ya sata sauke ajiyar zuciya itama ta ɗauki fitila ta fita duk da tana ɗanjin tsoro.
Tana cikin alwala mijin ɗayar matar gidan ya fito, ganinsa da ga shi sai gajeren wando yasa Rumana saurin duƙawa tana wanke ƙafa, bata ce masa komaiba shima baice mata ba ya shige bayi, itama tai saurin faɗawa ɗaki.
★★★★★
Ana idar da salla Ahmad ya shigo, kasancewar massalacin a ƙofar gidan yake, Rumana na zaune saman abin salla tana azkar.
Yanda yay sallama ciki-ciki haka ita ta amsa masa a hankaki, baice mata komaiba yazo ya sake hayewa gadon ya kwanta.
Rumana ta ƙarasa azkar ɗinta sannan tace, “Ina kwana”.
Kamar bazai amsa mataba sai kuma taji ya amsa da “Lafiya”.
Daurewa tai ta sake cewa “Ya jikin?”.
Nanma dai shirun yayi, harma sai da ta fidda tsammanin zai amsa sai kuma yace, “Alhmdullh”.
Daga haka kowa yay shiru, shi dai barcine ya sake kwasheshi, saboda maganin bai gama sakinshi ba.
Itako duniyar tunani ta faɗa, a ranta sai ƙara girmama hukuncin ALLAH takeyi, yanzu nan Yah Ahmad matsayin miji yake a gareta? Wata zuciya tace, “To gashi ma kun kwana a ɗaki ɗaya”.
Nannauyan numfashi ta sauke, wanda har Ahmad ya jiyota sama-sama a ɗan barcin da ya figesa.
Umm-Rumana na zaune a wajen har gari ya fara haske, ɗakin kawai take bi da kallo daki-daki, Ahmad dai nata barcinsa, wanda daga inda take tana iya jiyo saukar numfashinsa a hankali.
Sama-sama ta fara jiyo motsin matar gidan da yarinyarta dake kuka, sai kuma zuwa can tajiyo maganar mijin shima suna fira.
Idanu ta lumshe tana tuno gidansu, yanzu tasan gidan nacan da hayaniyar yara daga kowanne sashe, musamman ma sashensu da ke da ƙananun yara da sashen baba ilyasu.
Barcine ya sake saceta a kan abin sallar itama.
Sallamar Zainab ce ta farkar da Ahmad, ya buɗe idanunsa kafin ya tashi zaune yana amsawa, yakai idonsa kan Rumana da ko motsi bataiba, janyewa yay ya bama Zainab ɗin izinin shigowa.
Sai da ta sake yin sallama sannan ta shigo, ta sauke tiren kanta da aka ɗora kofin silba babba da kwanon silba guda biyu akai.
“Yaya ina kwana” ta faɗa lokacin da take kaiwa ƙasa durƙushe.
Amsa mata yay yana ƙoƙarin sakko da ƙafafunsa ƙasa.
Tace, “Gashi inji Ayyah, tace yaya jikinka? Idan kaci abinci dan ALLAH kasha magani, idan kasha zataji a zuciyarta kasha, idan kuma bakashaba ma zataji bakashaba”.
Guntun murmushi yayi badan ya shiryaba, a ransa yana kuma jin ƙaunar Ayyah sosai.
A hankali ya furta, “Kice mata zansha insha ALLAHU”.
“To yaya zan faɗa” Zainab ta amsa tana taɓa ƙafar Umm-Rumana yanda Ahmad bazai luraba.
Shi baima san tanaiba, ƙoƙarin sakkowa yake daga gadon.
Dai-dai nan Rumana ta buɗe idanunta.
Zainab ta matsa kusa da ita tana ƴar dariya, Ahmad kam buta ya ɗauka ya fita ya barsu suna gaisawa.
Bayan tafiyar Zainab da Rumana taita roƙon ta zauna taƙi, acewarta ance karta daɗe.
Rumana tahau gyaran ɗakin dan Ahmad bai dawo ba, sai da ta gama shara ne ta fito danta share waje sai taga butar a jiye, kenan nan ya ajiye ya juya ya fita.
Share tsakar gidan tayi gaba ɗaya, tana ƙoƙarin wanke banɗaki matar gidan ta fito ɗauke da kwanikan da suka karya.
“A'a amaryace dayin shara da safen nan? Harda su wankin bayi?”.
Murmushi Rumana tayi, cikin girmamawa tace, “Ina kwana”.
“Lafiya lau amarsu, ya amarci da angon naki?”.
Kasa amsawa Rumana tayi, saboda jin kunya, matarma tayi dariya kawai tana ajiye kwankan bakin rijiyar dake gidan.
Rumana ma ta fito daga bayin riƙe da botiki, gaban rijiyar ta ajiye tana faɗin, “Rijiyar akwai ruwa kenan”.
“Eh akwai ruwa Amarya, sai dai babu guga wlhy, jiya da safe Ahmad ya jefashi cikin rijiyar saboda tsabar rashin jinsa”.
Kallon rashin fahimta Rumana tai mata, jin ta ambaci sunan Ahmad.
Matar data farga da kallon sai tayi dariya, “Au yi haƙuri, na manta sunan mai gidanki kenan Ahmad, bashi nake nufiba, yaron wajena shima sunansa kenan, sai ƙaramar Faɗima muna kiranta Amatullahi”.
Rumana tai murmushin jin kunya tana cewa, “ALLAH ya raya mana su akan sunna”.
“Amin ya rabbi Amarya, amma ke yaya sunanki? Ni sunana Husna, amma yanzu dai anan anguwar anfi sanin maman Ahmad”.
“ALLAH sarki, ni Umm-Rumana, sai dai ni zanke ce miki Maman Amatullah to”.
“To babu damuwa Umm-Rumana amaryarmu, ai dole a ɓoye sunan mai gida, kije ga ruwa can a banbuna ki ɗiba kafin Abban Ahmad yazo ya ɗakko gugan”.
“Nagode sosai”
Umm-Rumana ta faɗa tana nufar Banbun ruwan kalar ganye dake ƙofar ɗakin Maman Ahmad.
Wanka tayo da ruwan data ɗiba, tayi alwalar walha kamar yanda ta saba ma kanta tun tana gida.
Kayanta da aka jera cikin Wadrobe ta buɗe ta ɗauki zani da riga na leshi ta saka, sama-sama ta shafa mai saboda zafi da aka fara, batai wani kwalliya ba sai fauda data shafa da kwalli a idonta.
Ta fara jin yunwa, dan haka ta matsa gaban tire ɗin da zainab ta kawo ta buɗe, Fankasu ne da yay luhu-luhu a kwanon silban farko, sai miya a ɗayan kwanon tana ta ƙamshin manshanu, kofin kuwa kunune na tsamiya shima sai ƙamshin kayan yaji yake, tana rufewa Ahmad na shigowa da sallama, kanta a ƙasa tai masa sannu.
Ya ajiye ledar hannunsa da kofin roba mai murfi madai daici yana amsawa.
Zama yay a bakin gadon idonsa akan kwanikan data gama buɗewa yace, “Miye wannan a ciki?”.
“Fankansu ne da kunu”.
Baikai ga amsawa ba wayarsa tai ring, fiddota yay daga aljihun jallabiyarsa ya duba.
“Manyan ƙasane haka suka tuna damu?” yay maganar wayarsa a kunne.
Daga can Zaheedah tai dariya tana maida masa amsa da “Ai kune manyan ƙasa Shema, yanzu gudun namu da akeyi har takai ai bikinka babu gayyata?”.
Murmushi yayi mai sauti, wanda har ya saka Umm-Rumana satar kallonsa da mamaki, ta daɗe bataga Murmushi a fuskarsa ba, duk da dama can itadai bayi mata yakeba sai da taga yanayi a majalissar abokansa ko idan yana tare da Samina, maganarsa ta sata sake maida hankalinta garesa batare da tasan dalilin hakanba.
“Bani da bakin kare kaina kam, amma dai ina roƙon amin uziri, nasan dai Sufyan ne ya sanar miki, kuma inada tabbacin bazai gaza miki bayani ba”.
“hhh hakane kam ango, ai banyi fushiba, yanzu ma dai taya murna na kira nayi, ALLAH ya sanya alkairi, yasa nanda wata tara muzo suna tunda ba ai biki da muba”.
Sai da ya saci kallon Rumana dake wasa da yatsun hannunta kanta duƙe ya lumshe ido, sannan yace, “Humm, kina lafiya? Ya mutan gida?”.
“Lafiya lau kowa da komai yake” Zaheedah ta amsa duk da taso ya bata amsar maganarta ta farko.
Sun ɗan taɓa hira kaɗan, a cikin hirar take faɗa masa sai tazo ganin amarya.
Bayan ya ajiye wayar ya kalli Rumana da har yanzu kanta ke a ƙasa, “Zubamin kaɗan, sai ki haɗamin shayin nan, anjima nasha kunun”.
Da to ta amsa tana miƙewa, ƙaton banbun ruwanta da aka zuba kwanikan amfani ciki ta buɗe ta ɗauki filet da cokali da kofi, dukda a wanke suke fes sai da ta sake ɗaurayewa sannan ta dawo inda take, sai faman gyara gyalenta dake zamewa take harta kammala haɗa masa shayin, ta zuba fankasu uku yace,
“ya isa haka, zuba miyar a kai kawai”.
Da “to” ta amsa.
Bayan ta gama taɗan kallesa, a ɗarare tace, “Ko a saka Sallaya a ƙasa”.
Kai ya ɗaga mata yana cigaba da danne-dannensa a waya.
Ganin zai fara cin abincin sai ta miƙe zata fita.
“Kefa?”
Yay maganar ba tare da ya kalleta ba.
“In....in..ba banajin yunwa” tai maganar cikin in ina tana sosa gefen kunne.
Manyan idanunsa ya ɗago ya kalle, hakan yasata saurin maida nata ta risinar.
“Dawo ki zauna ki karya ko ranki ya ɓaci”.
Dawowa tai tabi Umarninsa, zata zuba wani fankasun yay mata nuni da wanda ta zuba masa.
Duk jikinta tsuma yake, itace yau zataci abinci kwano ɗaya da Yah Ahmad?.
Yanda ta takure kanta duk yana kula, amma sai yay kamar baisan tanayiba, yaci gaba dacin abincinsa duk da baya masa daɗi sosai a harshe saboda zazzaɓin da yayi, ga damuwar Samina tana nan daram a ransa babu abinda ya ragu a ciki.
Bai sake tanka mata ba har suka cinye ukun data zuba masa, wanda shine ya cinye kaso mafi yawa a ciki, buɗe kwanikan yay ya ƙara wasu ukun ya saka miya, Rumana dai na kallonsa batako motsaba, gabanta ya tura filet ɗin ba tare da yace uffanba.
Ta kallesa da sauri suka haɗa ido, yanda ya sake tsuke fuska ya sata maida kanta ƙasa da sauri ƙirjinta na lugude, tadai fahinci itace zata cinye wannan kenan?.
Yanda bai sake bi takansa ba itama ta kasa kallonsa, ya ajiye kofin tea ɗin da ɗan saura a ciki alamar dai ya ƙoshi, miya tuna kuma oho masa, sai taga ya jawo ledar da madara ke ciki ya fasa ɗayan sacet ɗin ya zuba a kofin da sukari sai nescafe, ya zuba sauran ruwan zafin kofin ya motsa, gabanta ya ajiye ya miƙe nanma bai tanka ɗinba dai.
Da kallo ta bisa har ya ɗakko ledojin jiya ya ajiye inda ya tashi, ya buɗe banbun da kwanika ke ciki ya ɗauki kofi, sannan ya buɗe ƙaramin banbun danya ɗeba ruwa amma wayam babu komai.
Miƙewa Rumana tayi tana faɗin, “Babu ruwa ai, naje zan ɗiba a rijiya wai gugan ta faɗa jiya, bara nasamo maka wajen maman Amatullah”.
Baice komai ba ya miƙa mata kofin.
Bata jimaba ta dawo ɗauke da ruwan leda a filet.
Koda ta ajiye a gabantsa sai ya tsirama ruwan ido kawai ba tare da ya ɗaukaba.
Hakan ya saka Rumana tsayawa tana kallonsa itama.
“Babu ruwane a gidan sai wannan?”. Ya faɗa yana nuna filet ɗin.
“Na tambayeta ne shine ta bani wannan wai na rijiyar baida daɗi sosai suma wannan suke sha.
Filet ɗin ya tura gabanta, da alamun ɓacin rai a fuskarsa kaɗan yace, “Bani wancan haka nan”.
Tamkar Umm-Rumana zata fasa kuka haka taji, yanzu mata tai musu abin alkairi kuma sai yace ta maida? To mi zata ce mata ita kuwa?.
“Zaki ɗauka ne? ko sai kin gama tunanin?”.
Kafin ya rufe baki ta sungumi filet ɗin ta fice cikin sassarfa..............✍🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*(12)*
............Jiki a sanyaye ta koma ƙofar ɗakin maman Amatullah.
Maman Amatullah dake zaune tana ɗura zoɓo a gorori na saidawa ta amsawa Rumana sallama tana faɗin “shigo mana Amarya”.
Kunya duk ta lulluɓe Umm-Rumana, ta ajiye filet ɗin ruwan tana magana cikin in ina “Dan ALLAH kiyi haƙuri, wai ya fi son na rijiyan”.
Murmushi maman Ama tayi, tace, “Amarya karki damu, haka maza suke, abinda suke buƙata kawai suke so, bara na ɗiba miki wannan yafi ɗan sanyi to”.
Rumana dai batace komaiba, ta amsa ruwan tana mata godiya ta fice.
Inda ta barsa nan ta iske sa yana danna waya, ta ajiye kofin ruwan a gabansa “Ga shi”.
Bai ce komaiba ya ajiye wayar.
Tana cin abincin da aka sakata dole tana satar kallonsa yanda yake shan magani kamar zaiyi kuka, sai yayi kamar zai sha sai ya fasa yana matse ido, idan kuma ya jefa a baki da ƙyar yake haɗiyewa kamar zaiyi amai.
Ba sabon abu bane a wajenta tunda tasan baya son magani, ya ɓata lokaci sosai kafin ya gama shan maganin da bai wuce kwayoyi shida ba.
Ficewa yay, mintuna kaɗan sai gashi ya shigo, botiki ya ɗauka ya fita tare da ƙaramin banbunsu.
Hakan yasa Rumana miƙewa itama ta shiga tattare kwankan da suka gama, ta ɗakko wani filet ɗin ta juye kazar jiya ta ɗora a tiren da zainab ta kawo abinci ta ajiyesu gefe.
Mamaki ya bata ganin yana ɗibar ruwa, da alama dai gugar ya fiddo dan ga ƙugiya nan a gefe ya ajiye.
Kwanikan ta ajiye gefe ta koma ɗakin, tana ƙoƙarin shiga ta tsinkayo muryarsa yana faɗin, “Ki kwashe kwanikan nan shima ki fiddosa”.
“To” kawai ta iya cemasa.
Yanzu ita ina zata saka waɗannan kwankan haka? Duk da basu da yawa ɗakin babu wani fili mai yawa daya rage, kuma dai bata ce zata jerasu a ƙasa ba ai.
Haka dai ta gama fiddasu ta ɗauki banbun takai masa, sai da ta ɗauraye shi sannan ta ajiye.
Ya ɗauki wanda ya cika da ruwan ya kai ɗakin, itako sai kallonsa take, dan banbun yanacin kusan boket huɗu.
Ruwan ta ɗiba a ƙaramar roba ta koma gefe tana wanke kwanikan, shi kuma ya ɗauki banbun data ajiye ya maidashi ƙofar ɗakinsu ya ajiye, idan ya cika botiki sai yaje ya juye.
Hakan da Rumana ta ganine ya sata miƙewa tabar wanke-wanken, idan ya cika botikin sai taje ta juye, a haka har suka cika banbun da botikan uku, biyu na roba ɗaya na ƙarfe.
Ƙarasa wanke-wanke tazo tanai, shikuma ya ɗauki ruwan botikin ƙarfen ya nufi bayi.
A lokacin kuma Maman Ama... Ta fito riƙe da Amatullah tana kuka.
Rumana tai murmushi tana kallonsu da faɗin, “A'a Amatullah yaya dai?”.
“Rigima kawai mara dalili, ɗan zoɓon dana rage na ƙasan botiki ta zubarmin a ɗaki, shine kuma bazan gogeba sai na bar mata tai wanka a ciki”.
Rumana tace, “Lallai hajiyar ɓarna kenan, ina Yayana shi? Ban ganshiba tunda na tashi?”.
“Wannan ai tun jiya bama ya gidan, da ƙanwata tazo jiya da yamma ya maƙale mata sai da ta tafi dashi”.
“ALLAH sarki, to ALLAH ya dawo dashi lafiya”.
Rumana ta faɗa tana kama Amatullah data rarrafo wajenta.
Ɗaukarta tayi, ta zauna a bakin rijiyar tana mata wasa, ahaka Ahmad yazo ya wucesu.
Ƙin shiga ɗakin Amatullah tayi, har sai da ya leƙo, kamar ance ta ɗago sai suka haɗa ido, “Zonan” ya faɗa kawai yana sakin labulen.
Miƙewa tai ɗauke da Amatullah ta nufi ɗakin.
Tsaye ta iskeshi yana taje sumarsa a gaban mirror, tace, “Gani Yaya”.
Bai tankaba sai da ya gama, ya ajiye kum ɗin yana faɗin, “Bara naje can gida baba na kirana, naga babu abin girki ko?”.
Tai jimm saboda bata gane kan tambayarba.
Katse mata tunani yay da cewar, “Risho nake nufi ko abin gawayi”.
“Eh babu, amma inaga zasu kawo yau sukace”.
“Okey” kawai ya faɗa yana ƙoƙarin ɗaura agogo a hannunsa, mikuma ya tuna sai taji ya ja siririn tsaki tare da kuncesa ya buɗe jakar daya ɗauki kaya ya jefashi ciki, ya zaro wani ya saka, kumatun Amatullah dake miƙa masa hannu tanason ya ɗauketa yaɗan shafa ya wucesu batare da yace komaiba.
Rumana tai ajiyar zuya bayan ya fice tana ɗan girgiza kai, aranta tana tunanin ko yaya wannan zama nasu zai kasance kenan oho?.
Fitowa tai tsakar gida tanama Amatullah wasa, inda maman Ahmad ke ɗan mata hira daga kicin ɗinsu tana girkin rana.
Ita dai Rumana murmushin ta yafi hirar yawa, dan dama can ita bamai yawan magana bace, ta kuma kula Mama Amatullah akwai surutu.
A haka su Fa'iza sukazo suka iskesu, sosai Rumana taji daɗin ganinsu.
Suka shiga ɗaki sai shaƙiyanci suke mata, harda tambayarta wai yaya jiyan? Dan sunga Yah Ahmad a gida yanata ƙyallin angwanci.
Duka takai musu, suka kauce suna dariya, haka sukaita tsokanarta, kazar kuwa da suka gani sai da ta ɗiba musu, suka kuwa ci suna faɗin, “Tunda ke tsoro ya hanaki kici muko ci mukayi, Rumana wai dan ALLAH da wuya kamar yanda ake faɗa?”.
Rumana ta kalli Salima mai maganar tana faɗin, “Minene?”.
Gado Salima ta nuna mata da yin magana ƙasa-ƙasa kamar mai munafunci.
Tashi Rumana tayi tsaye, “Oh ni ALLAH ya shiryeku, ni dai babu ruwana wlhy, kuje ku tambayo Yah Ahmad ɗin mana”.
“Kutumelecy amma baki da man kai Rumana yasin” cewar Fa'iza.
Salima tace, “A'a so take ya maidamu niƙaƙƙiyar gyada ta ƙuli-ƙuli alkur'an, kinga kuwa yanzu da muka haɗu dashi a gida sai wani cin magani yakeyi, niko a raina har gulmarsa nayi, nace waishi Yah Ahmad yamayi auren bazai canjaba ne?”.
Dariya Fa'iza da Rumana suka sanya, Salima ma mai maganar ta tayasu tana sake cewa “Wlhy na zata yau zan ganshi fuska a washe, Rumana ko dai baki bada kai bane?”.
“Wai Salima yaushe kika koma hakane? To ALLAH ya gyara lamarinki da wuri, kema dai na kula auren kikeso”.
Fa'iza tai saurin faɗin, “Mi takeci na baka na zuba, Wlhy Malam yace muma mu kawo mazan aure, wai muna gama jarabawa aure za'ai mana, abinda Yaya Samina tayi ya tada hankalin kowa, bazasu sake yarda ƴaƴansu suyi zurfi a karatuba sai dai idan mijinka naso ya kaika da kanshi”.
Cikin marairaice murya Rumana tace, “Kuma godema ALLAH kuda gashi zaku ƙarasa, ni kam nasan ai nayi kenan”.
“Karkice haka wlhy, tunda Yah Ahmad nason karatu zai barki ki ƙarasa, ALLAH dai yasa kar bebin mu yay shigar sauri kawai”.
Hararta Umm-Rumana tayi.
Suka sanya mata dariya.
Daga nan suka koma hirar Samina, tare da iskance-iskancen data tsuro dasu a gidan a safiyar yau.
Rumana tace, “ALLAH ya ƙyauta to, ALLAH ya shiryeta”.
Amin dai, su Fa'iza suka faɗa a tare.
Su Fa'iza na gidan har Sadiya da Na'ima ƙanwar Rumana suka kawo abincin rana da ƴan tarkacen kwanika da aka ƙara saima Umm-Rumana, harda ƙaramin risho da abin gawayi, sai Abu dake biye dasu da ƙatuwar jakkar Ahmad ta kaya da tarkacensa.
Sannu Rumana tai musu, suma suka zauna aka ɓalle hira, Abu nata zuba musu shirme suna kwasar dariya, yaran anguwa kuma nata shigowa jefi-jefi ganin ɗakin amarya, harma da mata maƙwafta ƴan gutsiri tsoma, dan yanda auren ya kasance duk ya shiga kunnensu.
_________________________
Ahmad kuwa koda ya fita dauriya kawai yakeyi, dan bayajin ƙarfin jikinsa sam, ga zuciyarsa har yanzu a cunkushe take, kansa kuma bai daina masa ciwo ba.
A majalisar abokansa ya fara yada zango, ya zauna suka gaisa yana sake musu godiya, sukuma suna tambayarsa jikinsa da amarya.
Yaja kusan minti talatin a wajensu kafin ya miƙe ya ƙarasa gidansu, sashen su Malam ya fara shiga suka gaisa, Malam nata saka masa albarka, hakama tsoffin da aka bari ƴan shema su huɗu da Iya, yaɗan daɗe anan ma, ya fito yana murmushin ƙarfin hali na tsokanarsa da sukeyi irin dai wasan jika da kaka.
Sashen Baba Ilyasu ya shiga, ya gaida matansa sannan ya fito zuwa Sashen su Rumana.
A tsakar gida ya iske Ammi da Mama gaje, kowa na hidimarsa, ya risina ya gaidasu tamkar yanda ya saba, Ammi ce kawai ta amsa masa cikin jin nauyinsa da batayi da, Mama gaje kuwa ɗaki ta shige bata amsashiba.
Bai damuba ya miƙe ya fito abinsa.
Ya shiga sashensu, ƴan biki duk sun kama gabansu, sai ƙanwar gwaggo kawai data rage bata wuceba inna Asma'u.
Da Ayyah ya fara cin karo a tsakar gida suna ƙoƙarin kwance zare a ƙafar ɗaya daga agwaginsa ita da Mudan.
Ya ƙarasa gabansu yana faɗin, “Ayyah miya sameta ne?”.
“Wlhy ɗan albarka zarene ya sarƙe ƙafarta, gashi nama lura kamar ƙafar tata ciwo take tun jiya wajen taron nan, to ALLAH baisa nasamu kamata ba suka fice sai yanzu abun ya faɗomin arai, shine nashiga nemanta sai kuma na ganta jikin kejin kajincan a takure kamar wadda aka ɗaure, ashe zarene ya dabai baye ƙafar”.
“To, bai dai ji mata ciwo ba ko?”.
“Eh bai jiba, amma Yaya ina ganin gara a saidasu kawai, kwanan nan naji ana maganar agwagi suna fama da murgwi, na gidan malam kalla sai mutuwa suke suma”. Madan dake maganar ya faɗa idonsa akan Ahmad.
Ahmad yace, “To Mudan saika cigita mai sayen muga idan zasu ɗanyi daraja, amma abar guda biyu, dan nagama wata fara mai yarfin baƙi kamar ƙwai takeyi”.
Ayyah tace, “Ai naga kamarma fa ta fara ƙyanƙyasa da safenan indai ƴar budurwar nance...”
Kafin Ahmad ya bada amsa Inna Asma'u ta fito daga ɗakin Gwaggo riƙe da kayan wankin Gwaggon.
“A'a, ango ɗan gidan Ayyah ne a gidan? Jiki yayi sauƙi kenan?”.
Maida hankali gareta Ahmad yayi, ya taka zuwa inda take yana risinawa ya gaisheta, ta amsa cike da kulawa tana tambayarsa jikinsa.
Ya amsa da cewar da sauƙi.
“To Alhmdllh, ai haka muke son ji, Ina ɗiyar tamu amaryar ƙamshi?”.
Kansa ya kuma sunkuyarwa ya amsa da cewar, “Tana lafiya itama”.
Daga haka ya miƙe ya shiga ɗakin Gwaggo.
Tana zaune Zainab durƙushe gabanta tana cire mata abu a haƙori, sai yarfa hannu take tana kukan shagwaɓa na autanci.
Zama yay yana kallonsu, Gwaggo da sallamarsa kawai ta amsa ta bige hannun Zainab dake riƙe nata, “Idan bazaki tsaya ba tashi kiban waje, ji iskanci saikace ina cire miki rai”.
“ALLAH Gwaggo da Zafi fa” Zainab tai magana tana share hawaye.
“To jeki kicire da kanki mana”.
“Yi haƙuri to zan tsaya ALLAH kuwa” Zainab ta bama Gwaggo amsa.
Ahmad dake kallonsu baice komaiba ya lumshe idanu yana cewa “Ina kwana?”.
Amsawa Gwaggo tayi kamar yanda ta saba masa, sai dai ta tambayi yaya jikinsa da Rumana?.
Yaji daɗi sosai, ya amsa mata murya a raunane.
Ita dai sharesa tayi, duk da kuwa ɗunbin tausayinsa da ga shi har Rumanar nacin ranta.
Shiru babu wanda ya sake tankama wani, har Gwaggo ta gama cirema Zainab haƙorin makka data sa ya maƙale yaƙi fita, tashi yay ya fito da ga ɗakin yaje ɗakin Ayyah suka gaisa itama.
Sai jero masa tambayoyi take akan jikinsa, yay murmushi saboda ganin yanda damuwa ke kwance a fuskarta, kwanciya yay a gadonta dan wani sabon zazzaɓi yakeji.
Ayyah dake kallonsa ta ɗora hannunta saman goshinsa tana faɗin, “Ɗan albarka wani zazzaɓinne fa? Anya kasha magungunanka?”.
A hankali yace, “Nasha Ayyah, bani bargo sanyi nakeji”.
Babu musu ta ɗakko Bargo ta rufa masa, ahaka barci yay awon gaba dashi.
Sai da aka kira sallar zuhur Ayyah ta tashesa dan yayi salla, yay alwala ya fito shi da Mudanseer, a soron gidan sukaci karo da Samina taci kwalliya zata fita, kallo ɗaya yaymata ya ɗauke idonsa, hakan yasa taja siririn tsaki.
Kasa jurewa Mudan yayi yay saurin kallonta yana cewa, “K da ubanwa kike?”.
Baki ta taɓe tana tauna cingam yay ƙara ƙas-ƙas tai fari da idanu, “Da wanda ya tsargu man....”
Bata kai ƙarsheba ya sauke mata mari, zai ƙara na biyu Ahmad daya juyo ya kallesu ya dakatar dashi da faɗin, “Kai wuce muje mana”.
Samina kuwa sai ta fashe da kuka dafe da kunci, da gudu ta juya cikin gida tana kwalama mama gaje kira.
Ahmad sun dawo salla suka iske marin da Mudan yayma Samina ya zama Hayaniya a gidan, dan kuwa mama gaje hannun Samina ta kamo har sashen su Ahmad akan bazata yarda ba, wai Ahmad yasa Mudan ya daki Samina.
Gwaggo uffan bata ceba, sai Inna Asma'u ce ta tanka, sai ko Ayyah data idar da salla itama ta fito ta taya inna Asma'u, nanko abu ya zama hayaniya Mama gaje nata daddatsa magana wa jama'ar gidan, har Malam da Iya bata bariba, Ammin Rumana kam ai tafi kowa shan Zagi da su Ayyah.
Ahmad ya raɓa ta gefensu ya shige ɗakin Ayyah ya sake kwanciyarsa, ko kallon ɗaya a cikinsu baiyiba.
Hakan da yayi ba ƙaramin ciwo yayma mama Gaje da Samina ba, dan sunso ya tanka su hau kansa.
Mudanseer kam cayay inhar Samina bata bar sashenba wlhy dukan mutuwa zai lakaɗa mata, abinda ya ƙara rura hayaniyar kenan, Gashi su baba basa nan, sai da Iya ta shigo tai magana su Ayyah sukai shiru, Mama Gage kam ai kamar tunzurata akayi, taita zuba tsiya har sai da ta gaji tai shiru dan kanta............✍🏻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*(13)*
..............Koda Ayyah ta shigo ɗaki nasiha tai tayima Ahmad akan wannan sabon lamari da ya shigo musu cikin gida.
Ahmad dake jin zazzaɓi yace, “Karki damu Ayyah, ni wlhy abunsu bai damuna, dan ALLAH kuma kubar biye musu, shima Mudan ɗin zan masa magana yabar shiga harkarta, tunda bata da kunya, duk yanda yake tunanin da da yanzu akwai banbanci”.
“Humm su dai suka banbanta da son zuciyarsu ɗan albarka, indai duniya ce kuma gasu gata nan, wanda ma bai zoba jiransa takeyi, wanda kuma duk yasai rariya yasan zata zubda ruwa, ni lalacewar wannan aurenma tsakaninka da yarinyarnan alkairine, dan kuwa na lura duk halin uwarsu ta kwashe, kuzo ku haihu kanaji kana gani ƴaƴanku su tashi ba tarbiyya, yanzu kuwa ALLAH yay maka sauyin alkairi, gidannan kaf babu mai cewa ga halin Umm-Rumana na banza, hakama uwarta, duk fitinar Gaje tayi ta barta, tunda ita dai ba tanka mata zataiba saboda haƙuri da kawaicin da ALLAH yay mata, dan haka ka kwantar da hankalinka akan yarinyarnan, insha ALLAHU wataran sai kace gwamma da akai hakan”.
Idon Ahmad a lumshe duk yana jiyo nasihar Ayyahn sa, wannan itace shawarar da kowa ke bashi, tare da faɗin gamma da akai, shidai jinsu kawai yakeyi, dan bazasu gane yanda Samina ta mallake dukkan zuciyarsa bane, yasan kozai shekara kwatanta musu irin mugun sonta da yayma zuciyarsa dabai bayi ba fahimta zasuyiba, gaskiya so bai masa adalciba, da yasan a haka wannan soyayyar tasu zata ƙare da ya roƙi ALLAH mutuwa kafin wannan lokacin, kawai dauriya ya keyi, dan mutane karsu kallesa mara zuciya ne kawai, amma ko yanzu Samina ta yarda zata zauna dashi zai saki Umm-Rumana ya sake auren Saminar.
Humm, turƙashi Ahmad, lallai zuciya batai maka adalciba kam.
_________________________
Anayin Sallar la'asar Ayyah tacema Ahmad ya tafi gida ya kwanta, dan su Fa'iza ma sun dawo anbar Rumana ita kaɗai.
Badan ya soba ya fita Sufyan ya kaisa gida yauma a mashin ɗin.
Rumana na sharar ɗakin Ahmad ya shigo.
Yanda ya shigo kawai yasata gane babu lafiya.
Matsawa tai gefe ya shigo, tai masa sannu.
Hannu kawai ya iya ɗaga mata ya haye saman gado hannunsa dafe da kansa ya kwanta.
Cikin damuwa ta kwashe sharar data tattara a ƙofar ɗaki, taje ta zubar ta dawo.
Ya lulluɓe har kansa da bargo, hakan yasa ta zauna ta zuba tagumi kawai tana kallonsa, tausayinsa na sake kamata...
A wannan halin tajiyo sallamar Sufyan, leƙowa tai suka gaisa, yace mata yazone da likitan da zai duba Ahmad.
Izinin shigowa ta basu, koda suka shiga saita fito ƙofar ɗakin ta basu waje.
Zuwa wasu mintuna Sufyan ya leƙo ya kirata, shiga tai ɗakin, saita iske za'a ɗaurama Ahmad ɗin ƙarin ruwane ashe, ƙusa suke nema da zasu rataya ledar ruwan.
“Aiko Yah Sufyan babu ƙusa a ɗakinnan, amma bara na tambayi maman Ama... Ko za'a samu”.
Har zata fito Sufyan yace, “Kinga bartama, bara mugwada ko tsahon zaikai jikin mirror ɗinan”.
Gwadawa sukai sai sukaga yama kai, hakan yasa suka ratayeshi acan, sai da ya fara shiga jikinsa komai yay dai-dai sannan suka fice bayan likitan ya nunama Rumanan yanda zata saka ɗayan idan wannan ya ƙare, dan leda biyu za'a saka masa.
Suna fita sai kawai rumana ta zauna ta hau rusar kuka.
Ahmad na jiyota sama-sama, sai dai baice mata komaiba har barci ya kwashesa mai ƙarfi.
Har magriba ruwan bai ƙareba, saboda a hankali suka sakashi, alwala tayo tazo tai salla, bayan ta idarne ta tashi ta saka masa ɗayan ruwan kamar yanda suka nuna mata, duk da dai a tsorace tayi komai, lokacinne kuma Maman Ama.. Ta sake shigowa danta dubashi.
Maman Ama na fita Abu ya shigo gidan da sallama, maman Ama dake ƙoƙarin fita ta amsa masa tana bashi hanya ya shigo,
“To, abun ya kai harda ƙarin ruwa kenan?”. Abu ya faɗa yana ajiye kwanikan hannunsa
Rumana ta share hawaye tana faɗin wlhy kuwa Yah Abu, ni tsoroma nakeji kar wani abune ke damunsa ba'a saniba, garama akaisa asibiti tunda dai wannan ba likita bane babba”.
“Karki damu Umm-Ruman, zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu akaga jikin yaƙi daɗi ai gara aje asibitin, ga tuwo nan inji Ayyah, bara naje na sanar musu dan basusan an saka masa ƙarin ruwa ba”.
Kai kawai Rumana ta iya ɗaga masa.
Ya fice da hanzarinsa, ita kuma ta koma ta zauna ta zuba tagumi.
Koda aka kira sallar isha'i da ƙyar ta iya tashi tayi, tana ƙoƙarin ninke abin sallar tajiyo sallamar matan gidansu, da sauri ta amsa tana ɗaga labule, ganin da gaske sune sai daɗi ya kamata, sai da suka gaisa da maman Ama sannan suka shigo ɗakin.
Ayyah ce da matan baba Iliyasu, Gwaggo da mama gaje da Ammin ta ne basu zoba.
Tabarma ta saka musu suka zauna, ta durƙusa ta gaishesu, suka tambayeta mai jiki tace da sauƙi.
Ta miƙe ta zubo ruwa a kofi ta kawo musu, Ayyah tace, “Rumana waye ya saka masa ruwan?”.
“Ayyah tare da yaya Sufyan daya kawosa sukazo, leda biyune, da ɗayan ya ƙare shine na saka ɗayan kamar yanda suka nunamin”.
“ALLAH ya ƙara afuwa” suka faɗa kusan a tare.
Sun daɗe a gidan sunata jajanta abun, har Mudanseer ya shigo da baƙar leda a hannu, shima har cikin ɗakin ya shigo suka gaisa da Rumana, ya tambayeta jikin Ahmad ɗin yana ajiye ledar hannunsa.
“Ga wannan kananzir ne tun ɗazun yace na kawo shaf na manta wlhy, saboda ɗinki ya ɗauke hankalina, kawo risho ɗin a haɗa”.
Miƙewa Rumana tayi ta ɗakko kwalin ƙaramin risho da su Fa'iza suka kawo ta ajiye gabansa, buɗewa yay ya fiddoshi daga ciki, ƙaramine amma yanada ɗan ƙyawunsa, suna nan zaune harya gama zira lagwanin ya haɗa komai yasa kananzir ɗin, sai da yaga tankin ya cika ya miƙa mata sauran yana faɗin, “Sai ki adana wannan ko”.
Amsa tayi cikin girmamawa kamar yanda aka koyar dasu ga dukkan yayyensu.
Su Ayyah suka miƙe suna faɗin bara su wuce kar dare yayi, idan ya tashi tai masa sannu.
Tamkar Rumana zatai kuka haka taji, ta rakasu har soro tana share guntun hawayen da suka cika mata ido.
Umma tace, “Haba Rumana miye abin kuka anan, kowa da haka ya fara kinji, ALLAH ya baku zaman lafiya dai da haƙuri da juna”.
“Amin” Ayyah ta amsa, Umma babba kam baki taɗan taɓe tana wani mosan mugunta, kusan dai ƙawar mama gaje ce.
Ayyah na kallonta amma tai kamar bata ganiba suka fice, Rumana ta koma cikin gida tana share sauran hawayenta.
Zama tai suna ɗan hira da Mudanseer, dan dama can shi yana sake musu ba kamar Ahmad ba, sannan mutum ne mai yawan barkwanci ga kowa. Shine ya sakata dole taci tuwon da Abu ya kawo, sannan yace ta bashi tukunya da ruwa ya dafa musu ruwan zafi, idan Ahmad ya tashi sai kawai ta juye masa yay wanka tunda ALLAH yasa akwai filas.
Tashi tai ta ciro tukunya daga kayanta, ta ɗauraye ta zubo ruwa ciki ta kawo masa ƙofar ɗaki inda ya maida risho ɗin yana ƙoƙarin kunnawa, ta ɗauko filas ɗin shima ta wanke dan su Fa'iza duk suka kawoshi tare da risho.
“Bara naje na dawo kafin ruwan yayi” Mudan ya faɗa yana ƙoƙarin fita.
To ta amsa masa, shikuma ya fice.
Bai jimaba sosai ya dawo da leda a hannu, ya miƙa mata tare da buɗe tukunyar, ruwan nata ƙoƙarin tafasa ne, dan haka ya buɗe murafan filas ɗin ya matso dashi kusa. Yana tafasowa kuwa ya kwashe sa, sai da ya cika sannan ya miƙa mata bayan ya rufe, ya kashe risho ɗin ya ɗako da kansa ya maido mata ɗaki.
“To Umm-Rumana bara naje gida dare ya farayi, idan ya tashi ki tabbatar dai yasha magani, amma ki haɗa masa tea yasha zaiji daɗin jikinsa, ALLAH ya ƙara afuwa, da safe idan ALLAH ya kaimu zan dawo naga yaya ya tashi, idan munga babu wani canji sai aje asibiti ALLAH ya rufa asiri”.
Kanta ta ɗaga masa, ji take kamar tace ya tsaya karya wuce shima, amma bata da ikon hakan, tana kallo ya fice ya barta ita kaɗai sai Ahmad daketa barcinsa dan Mudanseer ya cire masa ƙarin ruwan tun ɗazun saboda ya ƙare.
Tun tana kallonsa harta fara gyan gyaɗi, ahaka Ahmad ya farka kusan ɗayan dare ya ganta, ɗakinsu buɗe ga hasken fitila ƙau saboda sabon batiri dake a ciki, idanunsa yaɗan lumshe ya buɗe a kanta, sai ta bashi tausayi, an haɗata da aikin da sam bai dace da itaba.
Bargon ya janye ya sakko daga gadon, yaɗanji ƙarfin jikinsa saboda ƙarin ruwan da aka saka masa.
Motsin saukarsa ya saka Rumana buɗe idanunta, cikin ɗan rikicewa take masa sannu, ya amsa murya a dushe.
Buta ya ɗauka ya fita, itama saita miƙe ta fara zuba ruwan sanyi a botiki kafin ya fito taji idan zaiyi wankan, a haka ya fito ya sameta, kanta a ƙasa tace, “Yaya Ko zakayi wanka?”.
Kamar bazai amsa ba sai kuma yace, “Inason yi amma akwai sanyi”.
“Ruwan ɗumine ai”
Kallonta yayi sosai, ganin haka yasata saurin cewa, “Eh ai Yah Mudan ya kawo kananzir ɗin, shine ya dafa maka”.
Janye idonsa yay akanta yana jin ƙaunar ƙanin nasa, da hannu yay mata nuni data haɗa masa, ya miƙe ya hau cire kaya.
Da sauri ta fita da ruwan takai masa bayi, a tsakar gida suka haɗu yana sanye da jallabiya, ta wuto shikuma ya shiga bayin,
Tea ɗin ta haɗa masa kamar yanda Mudan yace tayi, ta shimfiɗa abin salla ta ajiye shayin a gefe da biredi, sai ƙwai da Mudan yasa aka soya masa shima ta juye a filet ta rufe.
Ahaka ya shigo ya sameta, ya ɗauki buta ya sake fita, babu jimawa ya dawo, sai da ya kulle ɗakin sannan ya ƙaraso, Rumana na gefe zaune kanta a ƙasa ya tada salla.
Kafin ya ƙarasa ramuwan sallar magriba da isha'in har Barci ya fara kwasar Rumana a wajen, ta riga da ta saba da barcin wuri.
“Ki tashi kije ki kwanta” nutsatstsiyar muryarsa ta daki kunnenta.
Buɗe ido tayi da sauri tana gyara mayafinta, ta ɗaga masa kai tana ɗan matsowa gabansa, buɗe shayin tai da ƙwan ta matsar gabansa sosai,
“Su Ayyah sunzo dubaka da Umma ƙarama da Umma babba, hakama yah Sufyan yazo sake dubaka baka tashiba”.
“Na gode” ya faɗa a hankali.
Shayin ya ɗauka ya fara sha saboda yunwa yakeji dama, Rumana ta miƙe ta ɗakko ledar magungunansa ta ajiye gabansa, tabarmar data kwanta jiya ta ɗauka zata shimfiɗa a ɗayan lungun gadon tunda Ahmad na zaune inda ta kwana jiya sai ya dakatar da ita.
“Ki hau gadon ki kwanta”.
Yanda yay maganar a dake tasan babu zancen musu, sai dai jikinta har rawa yake kaɗan, taya zata iya kwana dashi bisa gado ɗaya?.
Kamar mai tsoron a saceta haka ta ɗofana a bakin gadon ta cure jikinta waje ɗaya.
Ahmad na kallonta baice mata komaiba, ya gama shan shayinsa yasha magani da ƙyar, Rumana dayake ta juya masa baya batasan hidimar da yakeba.
Ya daɗe zaune a wajen har barci ɓarawo ya sace Rumana dake kwance a ɗofane.
Jin barci na neman sake ɗaukarsa saiya miƙe ya ɗakko filo daga gadon da bargo, jallabiyarsa ya cire ya kwanta akan abin sallar yana rufa da bargon duk da kuwa garin akwai sirkin shigowar zafi.
★★★★★
Yau dai kam duk yanda yaso fita a gidan bayan sun gama karyawa hakan ya gagara, dan sosai ciwo ya kaishi ƙasa, daga ƙarshe dai sai da Rumana ta amsa wayarsa ta kira Mudanseer.
Babu ɓata lokaci yana zuwa suka wuce asibiti.
Sai ga zance kamar wasa ya zama babba, dan kuwa dai gado aka bama Ahmad.
Kowa ya tausaya masa, dan kuwa dai ansan ciwon abinda Samina tai masane ya kasa barinsa.
Samina ko koda taji labari ko a jikinta, dan ko sau ɗaya bata taɓa leƙa Ahmad asibiti ba har yagama kwanakinsa shida aka sallamesa ya koma gida.
Duk ya rame choco color ɗin fatarsa ta sake wani irin fayau, sai hancinsa da ya sake fitowa raɗau da manyan idanuwa.
Bayan yayi wanka da ruwan da Rumana ta dafa masa ya fito jiki duk babu ƙwari, su Ayyah duk suna daga waje zaune ya shiga ɗaki ya shirya, itama dai Rumana wajen ta fito ta zauna zaman jiransa.
Bayan ya kammala saka kayan ya kira Mudanseer daga cikin ɗakin.
Shiga yay, mintuna kaɗan shima Mudan ɗin ya leƙo ya kira Ayyah da Rumana.
Shiga sukayi, Rumana ta zuba masa abincin da Yaya Maryam ta kawo masa, duk da bayajin daɗinsa haka Ayyah ta takura masa tana basa a baki, sai da yaci fin rabi sannan ta ƙyesa, aka koma dagamar shan magani, dan kuwa da ƙyar yasha sa hardasu yunƙurin amai.
Ranar dai duk anan suka yini sunata tarairayarsa, sai gab da magriba duk suka tafi aka barsa shida Rumana kawai.........✍🏻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_**ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuoeSgXuo
*(14)*
.............Shuru ɗakin yayi bayan tafiyar su Ayyah, babu wani sabo a tsakaninsu na shaƙuwa tun can baya, sai dai girmamawa irin ta yaya da ƙanwa da kowa ya sani, yayanma irin wanda ake shakka sosai ɗinnan.
Umm-Ruman tana zaune da ga kan tabarma inda ta idar da salla ta zabga tagumi, gaba ɗaya kewar gidace ke addabarta, musamman ma yau da duk ƴan uwanta suka kasance a gidan tare dasu.
Ahmad kam yana daga can ɗayan gefen kwance saman sallayar da shima ya idar da salla, dan rashin ƙwarin jiki ya hanashi tashi yaje massalaci.
Yanayinsa zaka kalla kawai shima kasan tunanin yakeyi, dan ya ƙurama silin ɗin ɗakin idone ko ƙyaftawa bayayi, gashi sai taunar lip ɗinsa na ƙasa yakeyi da haƙori.
Kiran sallar isha'i da aka ƙwalane a masallacin kusa da su ya saka Ruman miƙewa ta fita, Ahmad kam ko motsi bai yiba.
Koda ta dawo tayi kamar zata masa magana amma sai ta fasa ta kabbara sallarta, harta idar bai dawo hayyacinsa ba, ta sauke numfashi a hankali, cike da tausayinsa ta matsa gabansa,
“Yah Ahmad!”
Shiru nanma bai motsaba, ta sake kiran sunansa kusan sau uku shiru, dole ta miƙa hannunta zata ɗan bugi filon daya jingina jikin Wadrobe ya saka kusan rabin bayansa da kansa, amm sai a mistake hannunta ya gogi kafaɗarsa.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, yayinda Rumana kuma taja hannunta da sauri tana cusashi cikin hijjabi, jikinta sai tsuma yakeyi, sai kace wadda ta taɓa wani mugun abu.
Kallonta yayi da idanunsa da suka canja kala, ga ramar da yayi ta fito sosai saman fuskarsa, “Lafiya dai?”
Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa.
Rumana dake ƙoƙarin matsawa baya cikin in ina tace, “Dama salla har an idar wasu masallacin”.
Yunƙurawa yay ya tashi zaune sosai, bai ce mata komaiba ya fita ya sake ɗauro alwala.
Koda ya idar ɗinma zaman shurun suka koma, a haka mijin maman Ama.. Yay sallama a ƙofar ɗakin, tashi Ahmad yay yafito suka gaisa yana sake tambayarsa yaya jikinsa?.
Cikin mutuntawa ya amsa masa akan da sauƙi, kowa ya koma wajen iyalinsa...
Yau ɗinma dai cayay ta hau gado ta kwanta, shi kuma ya kwana a ƙasa saman tabarma.
________________________
Haka zaman nasu ya cigaba babu tsangwama babu sakin jiki wa juna, har dai jikin Ahmad ya ƙara sauƙi, yanzu kam alhmdllh ya wartsake, sai dai ciwo irin na zuciya da ya ƙi barinsa, wannan kam kowa yasan abune mai wahala ace ya barshi da wuri, musamman idan aka ƙiyarsata da irin son da yakema Samina.
Tunda yaji ƙarfin jikinsa ma ba zaman gidan yakeba, barcine kawai ke kawosa, zuwa goma sunyi karin kumallo ya fice shago, bata sake ganinsa sai uku na rana, yay wanka yaci abinci ya sake ficewa, daga nan kuma sai sha ɗaya na dare ko goma da rabi zai shigo.
Wajen barci kuwa tana saman gado shiko yana ƙasa a tabarma, babu wani abu na muzgumawa da yake mata, sannan babu najin daɗi, itako tsakaninta da shi sai girmamawa kamar yanda ta saba tun can da suna gida.
Duk da ta lura hankalinsa baya gareta hakan bai damunta, ba itaba ai dama kowa dai yasan Samina yake so, to miyasa zata ɗaɗara kanta da ƙasa akan sai ya sota.
Kuma dama bawani saurayine da ita ba data ƙwallafa ma rai balle yanzu sonshi ya damu zuciyarta.
Yana fita zata dawo tsakar gida suyita hirarsu ita da Maman Ama, kokuma ta ɗakko Ama taita mata wasa ita da Ahmad da take kira yayanta..
Yauma tunda ya fita gidan nasu ya zarce, sai da ya shiga suka gaisa da malam da iya sannan ya shiga sashensu, Ayyah kaɗai ya iske a gidan Gwaggo ta fita, ya gaidata cike da girmamawa yana zama a gefenta.
Gwaggo ta kallesa da kulawa, “Ɗan albarka yaya dai? Naganka wani iri”.
Murmushin yaƙe yayi kaɗan yana duƙar da kansa, kamar bazai ce komaiba daboda nauyin maganar a harshensa sai kuma yaja numfashi, a ɗarare yace, “Ayyah! Sonake nabar garinnan, inaga hakan zai bani ƙyaƙyƙyawan nutsuwa, har yanzu nakanji zuciyata sam babu daɗi a cikinta, komai baya burgeni, komai baya sakani nishaɗi, koma bai sakani farin ciki wlhy Ayyah”.
A yanda ya ƙarasa maganar sai tausayinsa ya kama Ayyah, ta dafa kafaɗarsa tana faɗin, “Ɗan albarka na sani, nasan kana cikin damuwa har yanzun, musamman ma da rayuwar gidannan take neman juyewa zuwa wani abu daban, banƙi kabar garinnan ba, sai dai ka tuna yanzu bakai kaɗai bane, gashi yarinyarnan gaba ɗaya bata wuce sati biyu ba, anya tafiya ka barta a wannan yanayin bazaisa mutane su fassara abun da butulci ba?”.
“Hakane Ayyah, nima nayi wannan tunani, amma a ganina tafiyar shine mafita, ita kanta yarinyar maybe a yanda nake kallonta zai canja”.
Shiru Ayyah tayi tana nazarin maganarsa, bawai bata yarda dashi bane, ta gamsu da duk bayaninsa ɗari bisa ɗari, amma Umm-Rumana take tausayi, bai kamata a haɗa mata zafi uku ba a ganinta.
Ta sauke nannauyan numfashi tana mai kallon Ahmad ɗin kamar baƙonta, “ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi to, mu miƙa lamarin hannun UBANGIJI, idan tafiyar tafi alkairi ALLAH ya tabbatar, idan ba ita bace ALLAH ya canja maka da mafi alkairi”.
“To amin ya rabbi Ayyah, sai ki tuntuɓi baba da zancen shima muji mizaice”.
“Babu damuwa, insha ALLAHU zan masa maganar, itama Gwaggo zan sanar mata ta tayamu da addu'a”.
Kansa kawai ya iya jinjina mata, daga nan suka ɗora da wata hirar, duk dama Gwaggo ce ƙarfin maganar, Ahmad kam sai ihhm da a'a.
Shigowar su Fa'iza daga makarantar allo ya sakashi miƙewa ya fice, shago ya shiga domin ya samu ya rage ɗinki, dan babu laifi sun ɗan tara da yawa.
Yana tsaka da yanka wata atanfa fallatsetsiyar mota tazo gaban shagon ta faka, kallo ɗaya yay ma motar ya ɗauke kai saboda hango Ma'aruff da yay a ciki.
Sai dai kuma ya kasa daurewa, dan yasan dai dole Samina yake jira, ilai kuwa sai gata ta fito cikin kwalliyar duguwar rigar Material datai mata masifar ƙyau, rabonsa da ganinta tun washe garin aurensu, ta ƙara fari da alama man bilicin ɗin ta cigaba da shafa a binta, bai iya daina kallonta ba har ta shige motar Ma'aruff yaja suka bar anguwar, yanda ya bulo ƙasa zaka tabbatar da biyu yayi hakan saboda Ahmad.
Ahmad yaja dogon tsaki yana ɗauke kansa, hakan yasa Mudan dake ɗinki ɗagowa ya kallesa, danshi tunda yayma motar kallo ɗaya bai sakeba saboda takaici.
Kamar Mudan zaiyi magana sai kuma yay shiru ya cigaba da ɗinkinsa, shima Ahmad ɗin dai yankansa ya cigaba da yi dukda zuciyarsa babu daɗi sam.
★★★★★★
Ma'aruff kam yana barin wajen dariya suka kwashe da ita shi da Samina, cikin dariyar yake faɗin, “Mutuminki fa ya shaƙa, kinga harar da yake wulloma motarnan, na tabbata ji yake kamar zuciyarsa zata faɗo dan baƙin ciki”.
“Manta da shi luv ɗina, ni ko kalloma bai isheniba wlhy, yanzu ina zamuje?”.
Gefen titi ya samu ya gangara yay fakin, hakan ya saka Samina kallonsa da faɗin “yaya haka kuma? Miyasa muka tsaya anan?”.
Juyowa yay sosai yana kallonta da wani murmushi a kan fuskarsa, ya ɗan matsota idanu a narke, cikin raɗar magana yace, “Babyna bazaki ganeba, ina cikin wani haline”.
A ɗan ruɗe Samina ke faɗin, “Miya sameka?” tana maganarne tana dube-duben jikinsa”.
Hannu ya ɗora a kafaɗarta yana kuma narke murya, “Bafa ciwo najiba, damuwar a nan ne” ya kamo hannunta ya ɗora saitin zuciyarsa.
Ƙoƙarin janye hannun tayi amma sai ya riƙe sosai yanda bazata ƙwaceba, ya fara murzashi kaɗan-kaɗan cikin nasa hannun mai taushi, “Haba babyna ki gane mana, wai sai yaushene zaki ban dama koɗan rage zafi munayi, kinfa san kece zan aura, aurenma nan da kwana kaɗan, kinaso ace yau ga mijinki a gidan karuwai ko yana huɗɗa da karuwa?”.
Da sauri ta girgiza masa kai, ya lumshe ido yana hura mata iska kaɗan-kaɗan akan fuska, ganin ta lumshe nata ya sake kai fuskarsa dab da tata har suna shaƙar numfashin juna.
“Baby karki hanani kanki, namiki alƙawarin babu abinda zai shiga tsakaninmu inba ɗan kiss hakaba, shima dan na samu nutsuwa ne kawai kar wata ta lalata miki ni, dan harga ALLAH a matse nake, shiyyasa banson aurenmu ya gaza wata ɗaya, amma gashi kekuma kince muyi haƙuri ki ƙarasa karatunki nanda watanni shida, niko yamun nisa Samin ɗina”.
A hankali ta buɗe idanunta da suka shige cikin nasa, tsigar jikinta sai tashi take saboda dama itama a bukacen take, duk yanda taso ta hanashi hakan sai ya gagareta, saboda wani tsantsar sonta take hange cikin ƙwayoyin idanunsa, itama idan son samun tane suyi aurensu nanda wata ɗayan kamar yanda ya buƙata, amma sai mama gaje tace tajashi harta gama makaranta dansu ƙara tatsar kuɗaɗen da zasuyi mata hidimar biki na garari da sai ya tsayama ƴan gidansu a rai da Ahmad, wannan shawarar ce ta saka Samina cemasa ya bari ta gama makaranta kawa......
Saukar laɓɓansa kan natane ya sakata ƙanƙame jikinta, dan wannan shine karo na farko a rayuwarta.
Duk hanyar da Ma'aruff ya ƙware akai sai da yabi Samina ta sakar masa jiki yay kissing ɗinta sosai, sai da ya gaji dan kansa sannan ya barta.
Koda suka dai-daita kunya hanata kallonsa tayi, yaje da ita wani wajen motsa baki, duk yanda yaso taƙi fita su shiga tare, dan gani take kowa zai gane abinda sukayi, Ice-cream da gasashshiyar kaza da kayan ciye-ciye ya lodo mata ya dawo, daga nan gida ya maidota, inda ya hanata fita suka cigaba da hirarsu a mota.
Koda Ahmad ya fito da ga shago zaije masallaci sallar magriba kallo ɗaya yayma motar yay gaba abinsa, zuciyarsa na wani irin ƙuna tamkar zata fito waje.
Har suka dawo sallah Ma'aruff da Samina na'a motar, hakanne ya saka Ahmad shiga cikin gida ya amsar musu tuwo shi da Rumana ya fito domin tafiya gidan.
Har abokansa na tsokanarsa akan yau da wuri haka zai wuce?.
Murmushin yaƙe kawai ya iya musu ya wuce abinsa yana tsaida mai napep.
_________________________
Yau gidan namu ya kasance na mutum Uku, dan kuwa amarya za'a kawo mana, amma dai bazawara ce kamar yanda Maman Ama ta sanar min.
Tun da hantsi ƴan uwanta sukazo sukai mata jere, hakan yasani yini a ɗaki dan ni bancika son sakewa cikin mutane da yawaba, musamman ma waɗanda ban saniba.
Ban sami nutsuwar zaman wajenba sai da suka wuce bayan la'asar, sannan ne na fito nai wanka, na dafa taliya dai-dai cikina dan nasan Yah Ahmad ba dawowa ci zaiba, tunda ya cemin yau yana da aiki sosai a shago, maybe shi da gida sai dare.
Daga nan ƙofata na fito na saka kujera ina duba buks ɗina na makaranta, dan ban fidda ran Yah Ahmad zai barni na zana koda ssce ne ba.
Jefi-jefi nakan amsa maganar Maman Ama da duk rabinta gulmar dangin baƙuwar amaryarmu ne da sukazo sukai jere.
Ni dai ban yarda nace komaiba, iyakata dariya ko nace ALLAH ya ƙyauta, daga ƙarshema da naga zata takurani sai na ɗauki kayan karatun na shige ɗaki kamar zanyi wani aiki a ciki, zama na nai, ban sake fitowa ba sai da aka kira magriba, nazo nai alwala na koma ɗaki, dan baƙi sunɗan fara shigowa, da alama dai dangin angone da zasu tarbi amarya.
Ni dai gaishesu kawai nayi nai shigewata.
Zan kabbara salla biyu a cikinsu suka leƙo wai na taimakesu da buta suyi alwala, miƙa musu nayi na kabbara salla ta, ina cikinyi suka shigo, ganin salla nake suka shinfiɗa tabarma suma suka tayar.
Koda muka idar basu fita ba, sai hira suke jana da ita, duk tambayoyin nasu dai akan son sanin nima amaryace?, ina ɗan amsa musu abinda zan iya saboda naga sun girmemin sosai.
Muna idar da sallar isha'i ne Yah Ahmad ya shigo da sallama, ganin bani kaɗai bace sai ya koma da baya ba tare da yace komaiba.
Hakan da suka ganine ya sakasu miƙewa suna min godiya, a tsaye suka iskeshi, suka gaidashi suna barin wajen zuwa ƙofar ɗakin maman Ama da sauran ƴan uwansu suke can sukai salla.
Sannu nai masa ina amsar leda viva dake hannunsa, wadda Ayyah ta sako masa kwanikan tuwo a ciki.
Da yauwa ya amsa yana zama a bakin gadon, “Waɗannan fa?” yay tambayar yana kallona.
“Uhm baƙine ƴan tarbar amaryar da zata tare a gidannan yau”.
Kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru, saboda wayarsa da tai ring, ɗagawa yay suna magana, wadda na fahimci dai akan ɗinkine.
Kwanikan abincin na fiddo a ledar, koda na buɗe naga tuwo sai bance komaiba na maida na rufe.
Dai-dai ya ajiye wayar, hakan yasashi faɗin, “Da ruwan zafi a gidannan?”.
“Eh, akwai wanda na dafa ɗazun”.
Miƙewa yayi tsaye yana ƙoƙarin cire maɓallan rigar jikinsa mai dogon hannu, “Juye min shi naɗan watsa, zafi ya isheni banzo nayi wanka ɗazun ba”.
Da “To” kawai na amsa masa, na shiga bin Umarninsa tamkar yanda ya bada.
Bayan na haɗa ruwan bayin naje nakai masa, lokacin dana dawo harya cire kayan ya saka jallabiya, ya ɗauki kwandon soso da sosan sa ya fice. Ni kuma sai na kwashe kayansa da ya cire ya ajiyemin saman gado, a raina inata tseguminsa, wani lokacin sai naita ganin kamar Yah Ahmad bai karatu mai zurfi ba na boko, dan sam bashi da irin son gayunan da ƙwalisar samarin yanzu masu irin shekarunsa, yana dai da tsafta gwargwado, amma itama tunda abunnan ya faru tsakaninsa da Samina sai tayi rauni, jiba fa, rabonsa da wanka tun ƙarfe uku da wasu mintuna na yammar jiya, sai yanzune kusan takwas da rabi na dare zai sakeyi, inba sa'a ba daga haka kuma sai gobe da yamma.
“To ke ina ruwanki?” wata zuciyata ta faɗa cikin gargaɗina.
“Haka nefa wlhy” na faɗa a fili kamar mai bama wani amsa.
Kafin ya fito najiyo hayaniya ta ɗan fara cika gidan, da alama dai tawagar amarya sun fara shigowa...........✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WhgANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*(15)*
...............Shigowa yay yana jan tsaki, da alama dai hayaniyar gidance ta bashi haushi, ni dai bance komai ba na amshi kayan wankan na fito waje danna zazzage ruwan jikin soson, ta wani ɓangare kuma na bashi damane ya kimtsa.
Ina kallon wasu suna nunani, da alama dai ana gulma tane, oho basu dameni ba, sai ma na ɗauke kaina daga garesu.
Guɗar data cika soron gidan ne ya tabbatar mana da cewar dai amarya ta iso, ilai kuwa sai gasu sun shigo da ita.
Ni dai ina daga ƙofar ɗaki ina kallonsu, har aka shige da ita ɗakinsa suna callara guɗa abinsu.
Murmushi na ɗanyi, dan sun tunomin da randa nima aka kawoni gidan ina rusar ihun kuka.
“Sai kin gama kallonsu zakizo ki bani abinci ne?”.
Muryar Yah Ahmad ta maidoni hankalina, da sauri na girgiza masa kai ina faɗawa ɗakin jikina har ɓari yake.
Zaune na iskeshi saman tabarma, ya cire jallabiyar yana sanye da wando dogo mai taushi da riga, da alama dai na barcine.
Tuwon na zuba masa miyar kuɓewa ɗanya sai ƙamshi take, dukda babu nama a ciki girkin tsoffin mata irinsu Ayyah daban yake, musamman ma akan abinci irin na gargajiya da a yanzu yake gagarar matan hausawa, wata sai tai maka tuwon masara kaji tamkar ya jiƙe saboda tsabar rashin bashi nutsuwa.
“Kaɗan zaki saka” yay maganar idonsa nakan wayarsa.
Na amsa da to ina ƙoƙarin saka masa dai-dai misali a filet ɗin.
Koda na kammala sai na koma gefe zan zauna, amma sai ya katseni da cewar, “K mi kika ci?”.
“Da yamma na dafa taliya naci da mai da yaji, yanzu banajin yunwa”.
Baice min komaiba ya fara cin tuwonsa hankali kwance, kallo ɗaya zakai masa kasan yanajin daɗinsa sosai.
Yana tsaka da cin tuwon niko ina zaune gefensa kaɗan ina sauraren hayaniyar da gidan ya ɗauka mukaga an ɗaga labulen ɗakin kamar da gayya, da sauri na kalli ƙofar sai naga matashiyar mace ce ma, kafin nayi magana ta katseni da faɗin, “Mai ɗakinnan ruwan sha zaki sammin dan ALLAH”.
Miƙewa nai ina faɗin, “To” hakanne ya sakata shigowa gaba ɗaya tana kalle-kalle kamar ta ajiye wani abu a ɗakin, sai kuma naga ta fita da sauri tana cewa, “Ya salam, kuyi haƙuri dan ALLAH, wlhy bansan maigidanki na nanba”.
guntun Murmushi kawai nai mata na miƙa mata ruwa waje.
Ta amsa tana cewa “Na gode”.
Ni dai komawa nai ciki na zauna inda na taso, kallo ɗaya kuma naima fuskar Yah Ahmad na fahimci yaji haushin abinda matar tayi.
Ni dai bance komaiba, kamar yanda shima bai tankaba ya cigaba da cin tuwonsa.
Bayan ya kammala yace na bashi ruwan wanke hannu.
Muƙewa nai na ɗebo a madaidaiciyar roba na kawo masa ya wanke, na fita naje na zubda, matar data roƙi ruwa ta bani kofina tana sake godiya.
Yanda naga ya ƙwanta da wurine na fahimci akwai damuwa, dan kuwa dai nasan ba barci yakeba tunanine kawai, kuma bazai wuce akan yaya Samina ba.
Haka kawai yau sai naji raina ya sosu, amma saina danne na maida kun nena ga ƴan kawo amarya daketa ƙoƙarin tafiya.
Zuwa wani lokaci gidan yay tsit, fita nai nayo alwalar barci na dawo ɗakin, na tura ƙofar na rufe da addu'a a bakina, na raɓa ta gefensa na haye gado nai kwanciyata.
Banma san lokacin da shima ya tashi ya kimtsa ya kwanta ba, ni dai tuni na jima a duniyar barci.
Kamar yanda na saba da safe nai ƙokarin fara sharar tsakar gidan, lokacin Yah Ahmad ya koma barcin safe dana kula ya iya, kuma tunma yana gida dama yakan taɓa wani lokacin.
Dariyar da naji a bayana ya sakani ɗan waigawa, wadda nake ƙyautata zaton amaryace naga sun fito daga ɗakinta da angonta, kallo ɗaya zaka fahimci suna a cikin nishaɗi, tana ɗaure da zanine sai tawul data yafa, shikuma jallabiya yana riƙe da botikin ruwa.
Janye idona nayi daga garesu, sai da sukazo gittani ne na gaishesu.
Duk sun amsa min sannan suka wuce Bayi a tare, babuko kunyata suka shiga bayi suka rufo suna cigaba da dariyarsu ta nishaɗi.
Ni dai sharata kawai na cigaba dayi ba tare dana sake bi takansu ba har suka fito suka wuceni zuwa ɗakinsu tana masa shagwaɓa wai ya ɗauketa ya kai har ɗakinsu.
Tofa, yau naga abinda ya girmeni.
Na faɗa a zuciyata ina kwashe sharan dana tattara.
Daga haka na ɗiba ruwa na wanke bayi shima kamar yanda na saba, sannan na fara jan ruwa a rijiya na zuba a banbuna na ɗaki dana waje duk da dama ina da ruwan.
A lokacinne maman Ama ta fito, muka gaisa na tambayi lafiyar yara ina ƙoƙarin shigewa ɗakina, dan na lura bakinta da magana sosai, niko banason wannan halayyar sam.
Ƙofar ɗaki na kawo risho ɗina kamar yanda na saba na ɗora ruwan zafi, yana tafasa na juye a filas na saka ɗumamen tuwo shima, kwanikan dattin na zubasu a roba babba a nufina bayan mun karya saina haɗa duka nayi.
Ina gama ɗumama tuwo na juye a kula na kashe risho ɗin na zuba ruwan wanka abina.
Lokacin nake jiyo gulmar da Maman Ama keyi da mijinta daga kicin ɗinmu da ita kawai ke amfani dashi, danni tunda nazo gidanma ban taɓa koda leƙashi ba balle akai ga amfani dashi.
Kaina naɗan girgiza ina mamakin wai maza ma sun iya kananun magana, ni dai na wuce bayi nayo wanka nazo na shige ɗakina kawai.
Yanda kukasan mara gaskiya haka naita ƙumu-ƙumun saka kaya a cikin hijjabi, duk da nasan dai Yah Ahmad barcinsa ma yake, na gama ina tsaka da shafa mai ya farka, zaune ya tashi fusaka duk babu walwala, na ɗan saci kallonsa na kauda idanuna ina shafa kwalli a idona.
Tashi yay ya fita bayan ya ɗauki brush ɗinsa da ya sakama makilin akan madubi, hakan yasa na miƙe da azama nahau gyaran gadon, dan nasan maybe ya jima bai dawo ɗakinba, ilai kuwa harnai shara ma da sauri-sauri bai shigo ɗinba, sai da ina kwashe ƴar ƙurar dana tattarane ya dawo, matsa masa nai ya shigo ni kuma na fita zubar da sharan.
Koda na dawo bakina da nashi bai saɓa ba, nagama jera abincin a gabansa, duk da dai kulan tuwon dana ɗumama ne kawai sai filas ɗin shayi da kofi, sai ko guntun biredin jiya dake a leda da saurin sukarin da ya siyo gwangwani ɗaya, sai madara sacet uku nescafe guda uku shima duk a ledar.
Gani nai ya miƙe bayan ya ɗora idonsa akan ledar biredin dana ajiye, ya ɗauki wandonsa daya cire jiya ya ciri kuɗi ya fita.
Da kallo kawai na iya binsa, danni wannan halayyar tasa tana damuna bata damuna, abinda yasa nace haka dama can na saba babu wata shaƙuwa ta zaman hira ko abinda ya danganci hakan a tsakaninmu, nasan ko ba ƙaramin abu bane ace yanzu da wuri mun saki jiki wa juna da yanda naga ma'aurata nayi, abinda yasa take damuna kuwa shine kaɗaici, a gidan dai shi kaɗai nasani, ko yaya ina buƙatar sassauci daga garesa kodan nima naji sanyi a raina, na tabbata da aunty Samina ya aura da ba'aga haka daga garesa ba, dan bazasuyi kalar wannan zamanba saidai na farinciki fiyema da yanda naga amarya da angoncan yau.........
“K wai tunanin mi kikeyi haka?”.
Maganarsa aɗan zafafe ta katseni daga dogon tunani na, bansan ya dawoba sam wlhy, ina fiki-fiki da idanu nace, “Ba komai”.
Banza yaymin bai tankaba, hakan yasa nima na shiru na fara ƙoƙarin haɗa masa shayin da akema shan dai-dai ruwa kawai.
Nasan tunda akwai tuwo bazai ci biredi ba, dan haka na saka masa tuwon na tura gabansa, niko na haɗa tea ɗin nasha da biredin daya rage, na ɗan ɓalla a wanda yaje ya siyo saboda wancan guntune.
Abinda ya bani mamaki koda muka gama karyawa yau bai fitaba, zamansa yay a gidan, sai ma waya da ya ɗauka ya kira Yaya Mudan ya kawo masa wasu kaya zai yanka a gidan.
Ni dai ƙala banceba, sai dai zuciyata nata zungurata akan nai masa maganar wanka.
Na daɗe ina mulmula maganar kafin da ƙyar na iya fiddata, “Yaya ko zakai wanka tunda akwai sauran ruwan zafi a filas?”.
Shiru banji ya amsaba, hakane ya sakani satar kallonsa, sai naga ashe ni yake kallo shima, jinai duk na daburce, dan kallon dai irin na kinma samin idon nan ne, to amma ya zanyi tunda nai suɓutar baki.
Banyi zatoba naji yace, “Haɗa ruwan”.
Ai zumbur na miƙe kamar dama a ɗofane nake, ina kallonsa ya kauda kai yana murmushi, da alama dai yanda nake a tsoracene ya bashi dariya shima.
Duk da ya kauda idonsa kar naga murmushin naji sanyi a raina sosai, dan na jima banga hakan daga garesa ba.
Ina dawowa daga kai masa ruwan na haɗa wanke-wanke na fice abina gaban rijiya.
Ina ƙoƙarin farawa yazo ya gittani ya shiga bayi.
Kamar jirana maman Ama take sai gata itama ta fito dana wanke-wanken daga ɗaki tazo ta tsira kujera gefena ta fara.
Da farko tsokanar Amatullah na fara muna dariya, sai ta rage murya ƙasa-ƙasa tana faɗin, “Amarya anya kuwa wannan amaryar jiyan zamu dai-daita da ita? Babu wanda zaice gidanan ga yanda daren farkonki ya kasance saboda kunsan kanku daga ke har mai gidanki, amma ita jiya ihu taitaima mutane na rashin mutunci, ita ba budyrwa ba balle ace”.
Sosai gabana ya faɗi jin ta ambaci daren farkona, gefe kuma ina mamakin wannan saka ido irin na maman Ama, wato ita idonta na kammu ashe akan taji yaya mukai daren farko? Tab anya kuwa zaman gidannan bazai canja saloba?.
Ban samu bata amsa ba naji motsi a bayanmu, da sauri na waiga sai naga Yah Ahmad ne, da alama dai yama ji duk mi maman Ama ta faɗa, dan wata uwar harara ya zabgamin yana ƙaramin tsaki ya shige ɗaki.
Innalillahi kawai na iya ambato a raina, na kai kallona ga maman Ama dake cigaba da zabga surutu ita koma lura da yah Ahmad ɗin bataiba......
“Amarya wai yanaga kinyi shiru....?”
Murmushin yaƙe nayi ina girgiza mata kai, “Babu komai maman Ama, kawai dai banda abin faɗane, ni kitsoma nakeson naje, nasan kuma Yaya bazai barni naje gidaba, ko akwai maiyi anan kusa?”.
Nai maganar domin kauda surutanta marasa ma'ana.
Tace, “Eh to sai dai nan gidan matar Ali, ta iya kitso kam sosai wlhy, dolene kikayi oga sai yayi biyan da bai shiryaba”.
Nanma Murmushi kawai nayi, hakan kuma yay dai-dai da sallamar Yah Mudanseer daga soro. Na gane muryarsa shiyyasa na amsa masa ina faɗin “Ya Mudan ka shigo mana”.
Ya shigo da sallama, ya gaida maman Ama ba tare da ya kalli inda muke ba ya shige ɗakinmu.
Nima tashi nai na zubar da ruwa dan na gama sai tukunya, itama a tsaitsaye nai wankinta na kwashi kayan nabar maman Ama a wajen.
A ɗaki na iske Yah Mudan suna hira da Yah Ahmad, sai tsokanarsa yake yana murmushi, nima ina shiga ya dawo da tsokanarsa kaina, dariya kawai nayi na ajiye kwandon wanke-wanken dana ɗora a tire ina gaidashi, a kuskure muka haɗa ido da Yah Ahmad dake duba littafi turamen zani kusan shida ajiye a gabansa.
Babu shiri na ɗauke kaina, shima sai ya ajiye buk ɗin yana kallon Mudanseer.
“Mudan zokaje can wajen kaɗanyo mana cefane kafin ka wuce, dan yankannan zai iya ɗaukata dogon lokaci ban iya tashi nayo ba”.
“To yayana ɗan gidan Ayyah, angon ƙanwata Umm-Ru ma na”.
Ya ƙarasa sunana da ɗai-ɗai saboda hararar da Yah Ahmad ya banka masa.
Fita yay yana dariya, Yah Ahmad yace, “Shashasha kazo ka amshi kuɗin”.
Daga bakin ƙofa yace karka damu akwai kuɗi jikina, ƙanwata mi za'a sayo?”.
Kallon Yah Ahmad nayi dan nima dai bansan mi za'a sayo ɗinba tunda ba taɓa tambayata yay ba idan zaiyo cefane shi, niko kullum abincina baya wuce taliya da mai da yaji saboda shegen kwaɗaina, sai shinkafa da wake, ko dafa duka.
Shima da ya kalleni sai ya janye idonsa ya maida ga Yah Mudan ɗin, shine ya lissafa masa abinda zai sayo, ya miƙa masa ɗari biyar yana cewa, “Ka ƙara da wannan tunda cefanen da yawa”.
“A'a kabarsa yaya, akwai kuɗin ɗinki da yaron malam ya bani yanzun nan zanzo nan, bara naje na dawo”.
Yah Ahmad ya maida kuɗinsa a aljihu, Yayinda Yah mudan ke ficewa shi kuma.
Ni dai duk ina zaune gefe ne ina saurarensu, tsarinsu na ƙara birgeni, dama can kowa yasan akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu.
“Zo nan” na tsinkayo muryar Yah Ahmad.
Kallonsa nayi, dan banyi zaton dani yake ba ganin dai muna zaune ba wani nesa sosai da juna ba, yanda ya tsatstsareni da idanu yasa na miƙe zuwa gabansa na tsugunna.
Yace, “zauna da ƙyau”.
Zaman kuwa nayi cikina na sake ɗurar ruwan tsoro.
Kallona yay sosai ko ƙyaftawa bayayi, ga fuskarsa babu alamun wasa yace, “Ina wasa da ke?”.
Da sauri na girgiza masa kai idanuna na cika da ƙwalla, dan bansan mi nayi ba, sai matse hannuwana nake cikin na juna.
Ya cigaba da faɗin, “Kinsan daga yau ɗinnan da nake miki magana, idan har na sake ganinki zaune da matarcan kuna wata doguwar hira bayan gaisuwa sai na miki shegen duka a gidannan, wato ma har labarin daren farko kika bata....?”
Da sauri na girgiza masa kaina ina faɗin, “Wlhy A'a Yaya, ALLAH ban taɓa ba tunda nake”.
“Ba gashi tana miki hirarba, ke har kinkai girman sanin akwai wani abu shi daren farko ga amarya daman?”.
Hawayen da suka zubomin a saman fuska na share ina cigaba da girgiza kai dan na kasama magana.
Ahmad dake haɗiye dariyar yanda Umm-Rumana ta rikice da ƙyar ya kuma zazzaro mata idanunsa, danshi duk yana yine danya ƙwaɓeta da wuri karta saka kanta a wannan masifar ta shegen gulma, shiyyasa tunda suka tare a gidan ɗabi'un maman Ama basu masaba har mijinta, sam bayason mu'amularta da Umm-Rumana ɗin.
“Kinga daga yau, bama itaba, ko wannan da aka kawo jiya karnaga wata aminta ta haɗaki da kowace shegiyar mata ama anguwarnan ba gidannan kawai ba, inko hakan ta kasance kema kinsan sauran, tashi ki ban waje”.
“Kayi haƙuri dan ALLAH Yah Ahmad, zan kiyaye insha ALLAHU, amma dan ALLAH ka yafemin”.
Duk da ta bashi tausayi sai cayay kawai, “Ya rage naki”.
Tashi Umm-Rumana tai ta koma gefe tana cigaba da sharar hawayenta.
Ahmad dake buɗe zani ɗaya zai fara yanka yace, “Wlhy kika bari Mudan yazo yaga waɗannan hawayen ko, saina sassafaki a ɗakinnan”.
Babu shiri Rumana ta goge hawaye tsaf, sai ko ga Mudanseer ya dawo ɗauke da leda yellow mai layi-layi.
Yana ajiyewa ko zama baiyiba yace zai koma yana da aiki a shago, gashi zaije makaranta da yamma.
Godiya nai masa yay mana sallama ya fice.
Haka na tashi na fidda cefanen, Yah Ahmad nata yankan ɗinkinsa da duk ya maida hankalinsa wajen. Sai da zan fita waje girkine yace nayi anan ƙofar ɗaki basai na fitaba.
Duk da nasan zafin wuta zai ƙarama ɗakin zafi haka nabi umarninsa tunda risho ɗin ba hayaƙi yakeba, kayan miya kawai na fita na wanko tare da ɗanyen kifi da Yah Mudan ya sayo mana a waje nazo ɗaki na niƙa a gireta, kifin kuma nai ƙoƙarin sashi a wuta danna ɗan tafasa da kayan ƙamshi na rage masa ƙarni.
Maman Ama kawai kake iya jiyowa a tsakar gida da yaranta, amaryarmu kuwa suna ɗaki sai dai kajiyo sautin dariyarsu.
Da yake girkin bawani mai yawa bane dan danan nagama girka mana shinkafa jalof, wadda a ido kawai dolene ta birgeka saboda aikin nutsuwa ne, na kwashe a kula gaba ɗayanta na gyara wajen kamar banyi komaiba.
Har lokacin kuma Yah Ahmad nata yankan kayan, sai lokaci-lokacine yake amsa waya idan an kirashi, nama lura mafi yawa abokansane ke tambayar lafiya? Sunga bai fitaba, saiko Customers masu amsar ɗinki ko masu kawowa............✍🏻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*(16)*
.............Kiran sallar zuhur da akeyine ya saka koda na gama gyara wajen sai ban zauna ba, na ɗauki buta na fita.
Ina fitowa Amaryar jiya da mijinta suka fito daga bayi da alama wanka sukayo tamkar ɗazun da safe, harga ALLAH ban kawo komai a raina ba, saima sannun da sukaimin na amsa na shige banɗakin.
Na fitone idona ya sauka akan mama Ama dake leƙe ta Windown ɗakinta, sai dai ganin kamar na ganta ya sakata saurin sakin labulen, kaina kawai na girgiza, na zauna bakin rijiya ina alwala.
Sai ko gata itama zumut ta fito da buta a hannu, tazo gab dani take faɗin, “Amarya an tashi kenan?”
Kallonta nayi da ƴar fara'a nace, “Ai dama ba barci nakeba, aiki nake yima a ciki”.
Tai wata ƴar dariya idonta ƙyam akan jelar gashina, “Ai najiyo ƙamshi har nake zance da zuciyata akan yau kuma amarya a ɗaki ake girki? Ko kayan daɗi za'aci tunda naji ƙamshin kifi na tashi”.
Nace, “A'a, kawai dai dan Yah Ahmad na gidane na zauna saboda na tayashi hira”.
Buɗar bakinta sai cewa tai “Ku hirar kuke, wasuko da ranar ALLAH suna gado suna murzar juna, wannan matar inaga da bamu da maza a gidannan lallai da munsha kallo, aini yau naga bariki wai wanka da miji da tsakar rana”.
Shiru nayi danni sam maganar tata tazomin a baibai, na farko dai ban gama fahimtar gundarin maganar ba, na biyu kuma bansan minene matsalarta da wannan amarya ba, miye laifi idan tayi wanka da mijinta? Bayan malamin islamiyyarmu ya taɓa bamu wata ƙissa da MANZON ALLAH ke wanka da *Nana Ai'sha (R.A)*.
Zaram na miƙe saboda fitowar Yah Ahmad daga ɗaki, a duƙe na ƙarasa alwalar maman Ama na tsaye a kaina, tana jiran Yah Ahmad ya gotamu ta ɗora maganarta daga inda ta tsaya.
Da azama na bar wajen ganin ya nufi bayi, na faɗa ɗakina ba tare da na sake koda waiwayenta ba.
Gaskiya matarcan lamarinta na bani mamaki da ɗaure kai, shikenan kai bazaka damu da rayuwarka ba sai ta wani, dole nazo na roƙi Yah Ahmad komawa makaranta kodan gujema halayyar maman Ama ta son kafa da'irar gulma a gidannan.
Ina idar da salla ne na fara kimtsa kayan danaga ya kammala yankawa, sai biyu suka rage bai taɓaba, na tattare ƙyallayen na saka a leda suma na share ɗakin dan ya samu wajen cin abinci.
Ranar dake a tsaye tasaka garin ɗaukar wani mugun zafi, da ace ina da dama kayan zan cire nasha iska wlhy.
Haka dai na gama shirya masa abinci a tabarma na ɗauki kofi ina zuba ruwa, bisa tsautsayi na ɗan zubar, wanda na gama zubawa na ɗauka nakai gaban abincin nasa, sannan na dawo ina duba tsumma danna goge wanda na zubar.
Abinka da sabuwar leda, ashe na ɗan ɗisar da mangyaɗa a wajen sanda nake girki, koda na goge wajen kuma ban lura da nanba,, ga ruwa ya zuba, ina ɗora ƙafata da dube-duben inda ruwan ya zuba kawai naji na tafi gaba ɗayana, sai gani ƙasa.
Fashewa nayi da kuka saboda wani azabar zafi daya ratsa ƙashin ƙafata da ƙuguna.
Sosai nake kuka dan na kasa tashi, bansan yaya akai kunnen maman Ama ya jiyoniba, sai gata ta shigo jiki na ɓari tana tambayata lafiya?.
Ganina ina kuka rike da ƙafa da hannu ɗaya, ɗayan kuma na riƙe ƙugu ya sakata faɗin, “Faɗuwa kikayine?”.
Kaina kawai na iya ɗaga mata ina cigaba da kukana, takai hannu zata taimaka min danna miƙe sai ga Yah Ahmad yay sallama ya shigo.
Da mamaki ya kalli maman Ama ɗin sannan ya kalleni fuska babu walwala, “Miya faru?”.
Maman Ama ta buɗe baki zata bashi amsa nai saurin katseta....
Kuka na kuma saka masa wanda ni kaina nasan harda taɓara nace, “Faɗuwa nayi”.
Hannuna dake cikin na maman Ama ya kalla, ba tare da ya kalleta ba yace, “Barta kawai zan tada ita”.
Koda ta sakeni a zatona zata fita, sai naga matarka ta gyara tsaiwa tana kallonmu sai kace wasu tv ɗinta.
Wannan abu da Maman Ama tayi ya zafi Ahmad a zuciya, dan haka da gayyar cusa mata baƙinciki ya rungumi Umm-Rumana ya ɗagata cak zuwa saman gado, tunda ya fahimci matarnan muguwar ƴar sa ido ce.
Aiko tamkar ya sani, dan tsayawa tai taga yaya za'a kwashe, daga ita har mijinta sun fahimci Ahmad bai taɓa taɓa Rumana ba, har gulma suke akan hakan, wai baya son Rumana hankalinsa nakan Samina har yanzun.
Wani irin zaro idanu tayi na tsagwaron mamaki, maimakon ganin hakan ya sakata fita saita sake maƙalewa.
Rumana kuwa tunda Ahmad ya ɗauketa jitai hawayen sun gudu saboda tsabar al'ajabi, sam bata kawo hakan a ranta ba, jitai kawai jikinta na wata irin tsumar tsoro, dan a rayuwarta hakan shine na farko gareta.
Ya kwantar da ita a gadon sai dai rabin jikinta na saman jikinsa, a hankali yace, “A inane kika buge?”.
Hawaye Rumana ta matso da suka cika mata idanu, ta nuna masa ƙafarta, ƙugun kuma kunya takeji shiyyasa ta kasa nuna masa dukda nan yamafi ƙafar buguwa.
A mamakinta sai gani tai ya tura hannunsa cikin rigarta ya shafa ƙugun yana faɗin, “Shinan bakison a taɓane ragguwa?” ya ƙare maganar da matsa wajen.
Jikin Rumana har rawa yake ta ƙankame Ahmad ba tare da ta shirya hakanba, ga wani siririn kuka data sakar masa na jin zafi, bai bartaba yanata matsa wajen yanda ƙashin zai saki.
Ita ko ta ruƙunƙumesa tamkar zata koma masa ciki. Dauriya kawai Ahmad yakeyi, amma gaba ɗaya jinin jikinsa yamutsawa yakeyi ta kowacce kafa, tsigar jikinsa yanda ta tashi ya saka kowanne gashin jikinsa fitowa ta ɓularsa. Karo na farko a rayuwarsa da ƴamace ke a jikinsa kwance, abinda ya jima yana kissimawa da Samina kawai, a yau sai ga saɓanintace kwance a jikin nasa. Kasancewarsa gwanin kamewa yasa baka fahimtar yana a mawuyacin hali koda a fuskane, saima kalmar Sorry da yaketa ambatama Umm-Ruman a hankali yana cigaba da murza ƙugun”.
Saɗaf-saɗaf maman Ama ta fice a ɗakin wani abu na tokare mata maƙoshi, dan ita gani tai soyayya suke a gabanta kawai.
Duk yanda Ahmad yaso daurewa ya kasa, hakan yasashi zamewa ya kwanta yana saka Rumana sosai a jikinsa, wai shinan duk azuwan gyarane, taƙi tsayawa ya matseta, wannan damar Rumana da azabar matsa gurin ciwo ya isheta ta kuma mannema Ahmad sosai tana kuka da roƙonsa dan ALLAH ya bari hakanan, akwai zafi sosai.
Sam shi baima san tanaiba kam a yanzu, dan ɗiff kunnensa ya toshe, salon yanda yake matsa mata wajenma kawai zai baka tabbacin ya fara canja tasha ne.
Har maman Ama taje ɗakinta sai ta kasa daurewa, tsabar hassada nacin ranta ta kasa zaune ta kasa tsaye, maganin zafi ta ɗauka ta dawo ɗakinsu Umm-Rumana, tunda ta ɗaga labule taga yanda suke mai makon ta koma da baya sai catai “Yauwa ga maganin zafi kozata shafa a wajen insha ALLAHU zai saki”.
Yanda tayi maganar da ƙarfine ya dawo da Ahmad hayyacinsa, ya buɗe idanun da suka canja launi da ƙyar, kafin ya yunƙura ya tashi zaune da Umm-Ruman a jikinsa, ita tanata shashshekar kukane, shiko sai ajiyar zuciya yake saki a jere kamar jaririn dake neman abinci bai samuba.
Fuskarsa mugun tamke yakai dubansa ga maman Ama, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa saboda yasan muryarsa zata iya fallasa tsantsar buƙatar dake a tare dashi a halin yanzu.
Maman Ama ta ajiye musu maganin zafin gefen gadon ta fice kamar gaske, amma saita maƙale a bakin ƙofa.
Umm-Ruman ta raba jikinta da nashi tana share guntun hawayenta, murya a matuƙar shaƙe yace, “Sannu, kawo ƙafar muga itama”.
Rumana ta marairaice idonta na sake cika da ƙwalla, “Yaya dan ALLAH ka bari na huta sannan, ALLAH akwai zafi”.
Kansa ya girgiza yana kamo ƙafar, “Waya ce miki idan aka barshi anjima bazakiji zafinba, saima kinfiji fiye da yanzu” ya ƙara maganar yana matsa ƙafar itama.
Nanma ta ɗanyi kuka tana rirriƙe masa hannu saboda ƙafarma ta ɗan bugu, sai da ya tabbatar ta matsu sosai ne ya sauka a gadon, jakkarsa ta kaya ya buɗe ya fiddo maganin zafi, dan ko kallon wanda maman Ama ta ajiye baiyiba, a ƙafar ya fara shafawa kafin ya kalli Rumana cikin ɗan ɗaure fuska yace, “Juyo bayan ki ɗaga rigan”.
Cike da jin kunya Rumana tabi umarninsa, shiko yay mursisi yana shafa mata a wajen. Bayan ya kammala ya miƙe tsaya yana cewa, “Kwanta kiɗan huta na minti biyar maganin ya shiga wajen sosai”.
Babu musu ta kwanta tana gyara rigarta, shiko ya ajiye man zafin saman mirror ya koma saman tabarmar ya zauna.
Yunƙurawa tai zata tashi tana faɗin, “Bara na saka maka abincin”.
“Barshi zan zuba kawai”.
Yay maganar yana buɗe kular abincin.
Dole Rumana ta koma ta kwanta, Ahmad kuma ya zubama kansa a binci a filet ɗin da Umm-Ruman ta ajiye.
Sai ya samu kansa da yawan kallonta, kaɗan-ƙadan idonsa sai ya kai gareta.
Rumana kuwa barcin wahala ne yay gaba da ita ba tare da ta shiryama hakanba.
Maman Ama dataji shiru sai ta kama gyaran murya, da faɗin, “Sannu amarya kinji” Ahmad duk yana jinta, amma sai yay kunnen uwar shegu da ita, jin anƙi bata amsa taja ƙafafunta ta koma ɗaki.
★★★★★★★
Koda na farka bayan la'asar kaina kawai na gani a ɗakin, babu kayan da ya yanka, sai kular da abinci kawai ke ciki da kofin ruwa, filet da ƙaramin kofi da yay amfani dasu ma can na hangosu ya saka a robar da nake tara wanke-wanke.
Sakkowa nai daga gadon, dukda har yanzu ina ɗanjin zafin amma ba kamar ɗazunba, takarda dana gani saƙale a hannun kofin ruwan na zare ina warwarewa.
_Idan kin tashi kici abinci, ga maganinan kisha kuma._
Iya abinda kawai aka rubuta kenan a jiki, nai murmushi kawai, a raina nace da mijin Novel ne bazaije ko inaba saina tashi, ya bani abincin da kansa da maganin, ƙilama har wanka zai mini.
Ayyana hakan da nayine ya saka ni tuna yaya Samina, sai nayi saurin faɗin “ALLAH ka ciremin wannan ragon tunanin a raina, dan kuwa suma marubutan suna saka wani abunne kawai dan nishaɗi, wani abun kuma dan ƙara ilimi da gyaran zaman takewar aure, amma ga irinsu yaya Samina nan mai makon su duba abu mai muhimmanci su ɗauka a ciki sai suka ɗaura rayuwarsu bisa mara muhimmancin, na tuna randa naji tana faɗama mama gaje itafa auren irin mijin Novels shine burinta, kuma sai ta cikashi, maimakon naji mama gaje ta kwaɓeta sai cewa tai shi mijin novel ɗin yaya yake ne? Samina!.
Ina jiyosu Yaya Samina na bata labari tiryan-tiryan na wani littafi da take karantawa suna dariya.
Na girgiza kaina kawai ina murmushi, daurewa nai na fita ɗauro alwala.
Maman Ama dake jan ruwa a rijiya ta kalleni, sai naga kamar fuskarta babu fara'a, amma sai ban kawo komaiba, sai dai kuma maganar da tayice ta sakani kallonta.
“Oh ni Amarya sai yanzu aka tashi?”.
Murmushi na mata, “Wlhy kuwa Maman Ama bansan barci ya kwasheniba, ashe har anyi sallar la'asar”.
“Ina kuwa zaki sani, daga gyaran ciwo an koma soyayya, ni shiyyasama na fito na baku waje, dan naga kun manta dani a ɗakin. dama su maza idan kana amarya ai jinka suke kamar ƙwai a cokali, sai an fara haihuwa ɗaya biyu sai labari ya canja salo” ta ƙare maganar da ƙyalƙyalewa da dariya tana cigaba da faɗin, “Muma fa duk anmana mafiyin ma wannan tarairayar, shiyyasa da ake muku yanzu sai muga abun kamar maimaici”.
Murmushi kawai na sake iya yi mata, nace, “ALLAH sarki” kawai nai wucewata bayi.
Duk da Maman Ama ta girmeni, kuma rayuwar gidanmu ba irin haka bace, ba kuma wasu ƙawayene daniba bayan su Fa'iza na fahimci alamar jin haushin kulawar da Yah Ahmad ya nuna a kaina cikin maganar maman Ama, sai kuma yanzune zuciyata ta sake gane yawan tsogumi da maman Ama keyi akan amaryar gidan, dan taga mijinta na bata kulawa, to ALLAH ya ƙyauta, ashe shiyyasa yaya Ahmad yaymin gargaɗi ɗazun.
A bayin ma nayo alwala ta dankar na tsaya wajen nazo na gittata tana ɗibar ruwa da yin wakar barmani choge.
Wuceta nai kamarma na manta da ita a wajen na koma ɗaki.
Koda na idar da salla duk yanda yace nayi haka nayi, bayan nasha maganin na gyara ɗakin sosai dan ɗazun bawani gyara mai kyau nai masaba saboda yah Ahmad, turaren wuta na tsinke na kunna a ɗakin, na ɗiba ruwa naje waje nai wanke-wanke.
Ina cikin yine Amaryarmu ta fito rakkiyar mijinta da alama fita zaiyi, sunyi gayunsu abin sha'awa, har soro ta rakashi sannan ta dawo.
Inda nake ta nufo, hakan yasa nai mata murmushi, ba wata babba bace itama, da alama dai irin sakin wawan nanne, baka daɗe da auren farkoba a sakeka.
Ta zauna saman rijiyar tana faɗin, “Kuyi haƙuri bamuyi gaisuwa da kowaba a gidannan irinta sanayya”.
Cikin faɗaɗa murmushi nace, “Ayya ai babu komai, keda kikazo jiya da dare, ai ya kamata amiki uziri”.
Sosai tai dariya, sannan muka gaisa, tace, “Ni sunana Kausar, kefa?”.
Nace, “Kausar suna mai daɗi, ni kuma Umm-Rumana”.
“Woow Nice name” ta faɗa cike da iyayi.
Ni dariyama ta bani, dan haka na dara kaɗan, sai ga Maman Ama dake wanka ta fito tsilim tana cewa, “Mi ake tattaunawa haka amaren gidanmu?”.
Mu duka kallonta mukayi muna cigaba da dariyarmu, ni dai bata samu amsa a wajena ba, sai Kausar ce ta bata amsar.
Yanda Maman Ama ta nuna son Kausar sai abin ya bani amamaki, wato dai matarnan kwararriyar ƴar barikice, koda ta shiga ɗaki kayan ƙwalliyar waje ta ɗebo ta dawo dasu, ta zauna a kujera ƴar tsugguno, a haka aka cigaba da hira, wadda su biyune keyi, iyakata dariya kawai, saboda firar ta koma akan abinda yafi ƙarfin girma na ne.
Har Kausar na fadin miyasa ni banson cewa komai?.
Nanma dariyar kawai nayi, sai maman Ama ke cewa “Ai indai amaryace haka take, inaga batason bamu nata sirrin”.
Nace, “Maman Ama ni wane sirri gareni, ai sai dai ku manyan yayye”.
Da haka na miƙe ina share ruwan wajen, kausar tai dariya tana bani amsa da cewar, “Kema kin shiga layin manyan ai tunda har aka kawoki ɗakin miji”.
Maman Ama tai saurin cafe zancen “Kema dai ƙya faɗa Kausar, koda yake itafa ƴar gatace, angon nata rainonta yakeyi har yanzu, kusan sati uku kenan da aure kuma”
Kausar tace, “Tab, dama har a wannan zamanin akwai waliyan maza irin waɗannan da suka rage? Ballema saurayi da kamar ji suke su ƙwata tun a waje?”.
“Aiko dai gashi an samu a gidanmu kausar, nima dai ina jinjina ƙoƙarinsa, mu ƴan zamanin shekaru kusan takwas ma ba'a ɗaga mana ƙafaba balle na yanzun?, randa aka kawoni gidan da muka fara zama ALLAH tun farkon dare baban Ahmad yana gida, kamar jira yake ƴan kawoni su wuce ya hau sassafata”.
Dariya suka kwashe da ita, ni dai na ɗauki ruwan wankana na nufi banɗaki ba tare dana ce dasu uffanba.
Ina jiyosu suna cigaba da hirarsu wadda ni kunyama take sani dukda bana a kusa dasu, dan Maman Ama tiryan-tiryan take zayyanoma Kausar daren farkonta, itama tana faɗa mata nata suna kwasar dariya.
A haka nazo na shige ɗakina ina ɗingisa kafata mai ciwo.
Ban sake fitaba duk da ina cigaba da jiyo hirar tasu kuwa, wadda naga tayi zurfi sosai dan har maman Ama tafara kiran ta shiga ɗari lokaci yaja bata dora abincin dare ba.
Kausar take cemata “Kai dama zakiyi abinci kika biyemin, tashi ki ɗora kam gaskiya dan mu saimun gama cin amarci, Amarya dai tunda ta shige tai bulum a ɗaki”.
Dariyar maman Ama na jiyo tana bata amsa da “Ai ƙyaga da yawa indai amarya ce, sam bata gajiya da ƙumshe kanta a ɗaki kamar wata maijego”.
“Zata barine, har yanzu da sauranta ne ai” cewar Kausar.
Ni dai ko tari banyiba balle susan yaya nake.
______________________________
Ɓangaren Samina kuwa a hankali Ma'aruff ya fara cin galaba a kanta, yanzu kam babu fashi duk randa yazo hira wajenta saiya moreta da Romance, tun tanajin tsoro har itama idonta ya fara bushewa saboda jin daɗin hakan da takeyi, dan zuciyarta ta yarda da Ma'aruff ɗari bisa ɗari akan bazai cuta mata ba, a ganinta tunda aure zasuyi kuma ai babu wani abu, da yaje yayi da wata kamar yanda ya faɗa gara yayi da ita tunda kowa yasan akwai maganar aure a kansu.
Kuɗi kuwa da sayayya ya kara haukacewa da yi mata, hakan ya ƙara saka izza da dagawa a zuciyar mama gaje da Saminar kanta, kullum cikin yima Ammin su Rumana da su Ayyah habaici ake, haka zasuyita ciye-ciyen kayan daɗi gaban su Ammin Rumana, amma ko guntu ba'ai musu tayi.
Duk abinda ke faruwa baba Yusha'u ya sani, ya taɓa ma Samina faɗa sau ɗaya akan shiga motar Ma'aruff, amma sai malam Rabi'u mahaifinsu yace karya ƙara ya sakama Samina da uwarta ido kawai. Saboda a randa yay maganar tujara sosai Mama gaje ta zubar a gidan, har su malam ɗin sai da ta zaga babu kunya babu jin tsoron ALLAH.
Komai kuwa a kunnen Ahmad dake gidan yazo gaida su Ayyah ya faru, ƙala bai ceba akan zancen, daga ƙarshema ya baro gidan kawai.
Zuwa yanzu takai karatun Samina ya fara walagigi, dan bata da burin daya wuce Ma'aruff yazo ya ɗauketa a mota su more rayuwarsu da shan minti, hakan yafiye mata zaman aji muhimmanci.
Kowa ya kawo ido ya zira mata, yayarta Bintu da iya kishiyar kakarta Inna mari ne kawai ke faɗama Saminar gaskiya, sai dai sam batama saurarensu, saboda a yanzu duk mai faɗa mata gaskiyar kallonsa take maƙiyinta, mai baƙinciki da cigabanta kai tsaye.
Gefe kuma zugar su Nafy akan haduwar Ma'aruff na sake tunzurata da zuzutata a ƙaunarsa.............✍🏻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*(17)*
..............Harna fito alwalar magriba basu tashi a wannan hira ba, dan maman Ama ma tana kicin ne tana girkin dare.
Ni dai nai alwalata na shige ɗaki ina tsokanar Amatullah dake barbazamin duwatsu a ƙofar ɗaki tana wasa.
Basu tashi ba sai gab da isha'i, shima mijin kausar ne ya shigo, sai lokacin naji wai tana fadin ta shafa'a batai sallar magriba ba.
Ni dariyama ta bani, shiyyasa naɗan murmusa ina cigaba da azkar ɗina.
Yah Ahmad bai dawo gidanba sai goman dare, na tashi daga kwanciyar da nai ina amsa masa sallamar sa, ledar hannunsa ya ajiye idonsa a kaina.
“Yaya jikin?”
Ya faɗa murya ƙasa-ƙasa.
Nace, “Alhmdllh, ya mutan gidan?”.
Shiru yay bai amsaba, harma na fidda rai dan na miƙe kawo masa ruwa sai na tsinkayo muryarsa yana fadin, “Lafiyarsu lau, suna gaisheki”.
Murmushi kawai nayi naɗan rissina na bashi ruwan dana ɗebo.
Amsa yay idonsa akan ƙafata da nake ɗingisawa, sai da yasha ruwanne sannan yace, “Ki duba ledan nan akwai magani saiki sake sha, insha ALLAH zai saki gaba ɗaya”.
Kaina na jinjina masa ina godiya, na tambayesa abinci yace ya ƙoshi, abincin da yaci ɗazun ya tsare masa ciki.
Shiru nai ban sake cewa komaiba, inason masa magana ko zaiyi wanka nima na gwada na ƴan gayu amma inajin tsoro, hakan yasa nai ɓan da bakina har muka kwanta.
_________________________
Haka rayuwar wannan gida ta cigaba da tafiya mana, inda nake ganin sabbin salon ɗabi'u daga matan gidan, dan a hankali dai maman Ama kejan kausar jikinta, kullum kuma babu fashi sai sunba junansu labarin maganin mata da sukai amfani dashi da dare, harma da gwargwadon aikin da yayi akan mazansu, gefe kuma maman Ama na zuge Kausar akan Uwargidanta, dan tanada kishiya a wani gidan da ban.
Lokaci ƙanƙani saiga amintaka mai ƙarfi ta ƙulle a tsakaninsu, inda kuma idan ɗaya na ɗaki yazama ina tare da ɗaya a waje kaji yana sukar ɗan uwansa da gulma.
Kamar yanda Yah Ahmad ya ƙwaɓe ni babu ruwana to haka naja kaina, iyakata dakin gama nace ALLAH ya ƙyauta kawai nabar miki wajen, koma kina cikin faɗar nasan dabarar da zanyi na bar wajen.
Basa iya riƙe sirrinsu, kowacce cikin zayyanema ƴar uwarta halin da take ciki suke, hatta da abinda sukaci da dare idan miji yaɗan sayo saisun bama juna labari, wani lokacinma na lura da biyu akeyi saboda ni, sai kuma lamari yaso juya akala kan maman Ama, dan kuwa dai Kausar tafi zaƙewa akan sayayya irinta ƙwalam da naƙulashe da mijinta ke mata, dan da safe har sauran naman kaza ko tsire ko balangu ake kasowa a filet ni da maman Ama duk dan mugani, tun ranar farko Yah Ahmad ya takan birki akan amsa, dan haka na bama Kausar amsa da ni bama nacin nama kwata-kwata, sai ta koma bama Maman Ama kawai, itako maman Ama zata amsa taci amma hakan na sakata baƙin ciki, dan zakiga tanata fushi da kawomin sukar Kausar wai tana badawane dan ace ta fimu jin daɗi wajen miji, nidai bancewa komai.
A kwana biyunnan kuma sai naga itama maman Ama ta fara ɗabi'ar kaso abu ta bamu wai a zuwan tsarabar kasuwa baban Ahmad yazo dashi, itama dai bana amsa saboda gudun ɓacin ran Yah Ahmad.
Ƙiri da muzu sai gulmarsu ta koma kaina, yayinda a gefe kuma suke kishi da juna, ni lamarin nasuma dariya ya koma bani, duk da sun gimeni amma idonsu na kaina, ni kuma bawani abu gareni na nunawa a garesu ba, tunma danazo gidan inaga sau uku nasan naci nama, biyu nama ɗaya kifi, suma duk na abincine da ake saye bai kuma wuce na ɗari biyu.
Zuwan da yaran gidanmu ke yawan yine yake ɗaukemin kewa, muyita hirarmu a ɗaki, sai kuma sukace na fara musu wani abu na saidawa kamar alawar madara ko aya ko iloka da makamantansu.
Banyi musuba nace su bari idan Yah Ahmad ya dawo zan sanar masa, idan ya amince to zan ringa yi musu.
Tun daga wannan ranar na fara sana'ar abubuwan yara, dan kuwa Yah Ahmad koda na gaya masa sai bai musaba, ya bani dubu ɗaya da ɗari biyar yace nayi jari, godiya nai masa sosai.
Abun har yayta bama Ahmad mamaki, domin kuwa yakan tuna Samina da kuɗi kaɗan kansata tayi fushi, idan ta tambayesa 3k ya bata 2500 aka tai haƙuri bashi dasu, to ranar kam sai tayi fushi dashi akan 500 da babu koda zata amsa 2500 ɗin kuwa, sai idan ya cika mata ɗari biyar ɗinne zasu dawo dai-dai.
Amma yau gashi ya bama Umm-Ruman 1500 kawai matsayin jari tanata masa godiya kamar ya bata 100k.
Yaji daɗin hakan sosai, musamman ma da yaga ta bada himma akan sana'ar, dan kuwa gida ta aika dasu Ammi ta sai Gyaɗa da aya aka soya aka ƙullo daga can, ƙannenta suka ɗauki wata sauran aka aiko mata nan gidan saboda yara masu shigowa.
Akan wannan sana'a ba ƙaramin dariya Kausar da maman Ama sukayiba, acewar Kausar ita yanzu ai bata da time ɗin wata sana'a, yaushe ma ta gama morar amarcinta da har zata takura tunaninta wajen wasu ƙulle-ƙulle.
Maman Ama kuwa tace ai ita bama zata iya sana'ar naira biyar ba, domin sana'ar yarace.
Rumana dai batace komaiba, sai ma murmushi da tai musu kamar yanda ta saba.
Duk kuma wannan abun da suke Ahmad na ɗaki kwance yana jiyosu, su kuma basuyi tunanin yana nanba, dan da takalmansa ya shige ciki bayan ya dawo sallar juma'a, lokacin da ya shigo duk suna cikin ɗakunansu.
Koda Rumana ta shigo ɗakin baice mata komaiba game da maganar, dan shima takaicin abinda Samina ta masa yau ne a gidansu ya sakashi zuwa ya kwanta.
______________________________
Bayan sallar isha'i Ahmad ya fita zuwa gidansu, dan tun dawowar da yay bayan sallar juma'a bai sake fitaba sai da zaiyi sallar magriba, daga nanne kuma bai komaba har akai isha'i ya wuto nan.
Ƙannensa dake cin abinci a ƙofar Ayyah duk suka gaishesa.
Amsa musu yayi cikin rashin sakewa, hakanne ya sakasu fahimtar yana cikin damuwar abinda ya faru ɗazun har yanzun kenan.
Daga can ƙarshen tabarmar da suke zaune ya zauna, a haka Ayyah ta fito daga lungun Baba ta sameshi..
Da damuwa sosai a fuskarta tace, “Ɗan albarka dama kana nan?”.
Kansa ya ɗago yana kallonta, ya girgizashi kaɗan yana faɗin, “A'a Ayyah, ai tun tafiyar da nai ɗazun ban dawo ba, yanzu ma nazo wajen baba ne”.
“To lafiya dai ko?”.
“Lafiya lau Ayyah, magana kawai nakeson muyi, amma inaso ma ace kema kina wajen”.
“Shike nan tashi muje ai yana ciki”.
Tashi yay tsaye, Ayyah na gaba yana biye har lungun baba dake zaune a ƙofar ɗaki saman tabarma, kwanika na gefensa da alama abinci ya gama ci, dan hannu ma yake wankewa lokacin da suka shigo.
Zama sukai suka jirashi ya ƙarasa, ya ajiye butar yana fesar da ruwan bakinsa da ya kurkure, sannan ya jawo da baya ya zauna sosai.
Gaishesa Ahmad yayi, ya amsa cike da kulawa yana tambayarsa Rumana.
“Tana lafiya baba, tace ma a gaisheku”.
“Muna amsawa, amma lafiya na ganka haka kamar mai fama da ciwo?”.
Kan Ahmad a ƙasa yay murmushi, murya a sanyaye yace, “Lafiyata lau Baba, kawai dai yanayin garinne”.
“Amadu yanayin gari kokuwa abinda ka kasa yakicema ranka?, bara na faɗa maka gaskiya, inhar baka cire yarinyar nan da halayenta a ranka ba bafa zaka zauna lafiya cikin salama ba, ka cire duk wani abun da ya faru ko yake faruwa a gidannan ka fuskanci matar da ALLAH yay maka zaɓi madadin son zuciyarka, Ahmadu idanfa kai saken da yarinyar nan Rumana ta farajin ciwon wannan shirmen naka har taso guje maka wlhy zakayi *GUDU DA WAIWAYE....*, kasan kuwa da ga karshe iyakarka mugun zato, amma baka da karfin ɗaukar mataki, ina saka maka idone kawai dan naga iya gudun ruwanka, to na lura bamai sanin zuru bane kai, yanzu abinda akace yarinyar nan ta maka yau a gaban saurayi da mutanen anguwa idan kai da mai zuciyane bai cancanci ka ɗauke kanka daga gareta ba har abada?........”
“Ayi haƙuri dai malam, ai kowa yasan yanzu hankalinsa baya a kan Samina, sai dai mu tayasa da addu'a kuma, kasan dama irin wannan fitarsa a rai sai dai a hankali”.
“Kayya Ruƙayya, ke dai bar lamarin shirmen wannan ɗan naki, inda har bai saka abun a ransaba ai da yabar damuwa da lamarinta, ya kuma tashi ya nema ma kansa mafita ko”.
Ahmad da kansa ke a ƙasa yace, “Baba kuyi haƙuri ku gafarceni, yanzu ma haka nazone da wata mafitar, fatana dai ta zama mai amsuwa a gareku”.
Baba yace, “To babu laifi, muna saurarenka”.
Sai da Ahmad ya kuma luliya maganar a zuciya kafin yace, “Baba dan ALLAH inason a bani izini na bar garinnan”.
“Kabar gari kuma? To zuwa ina kenan?”.
“Duk inda ALLAH ya rubuto mani, inason fita nema ne kawai, bawai dan anmin gorin rashin arziƙiba, ba kuma dan ban godema ALLAH da sana'ar da ya baniba, hakan zaisa zuciyata mance komai dai insha ALLAHU”.
Baba dake jinjina ka sa yace, “Banƙi ta taka ba, amma dai abin dubi anan ita matar taka fa? Duk auren naku kwanansa nawa? da za'ace ka tafi wani waje ka barta, sai naga kamar akwai wauta”.
Shiru Ahmad yay, dan haka baba yace, “Jeka tsakar gida ka jiramu, amma ka turo mani Suwaiba”.
Ahmad ya amsa da to yana miƙewa ya fita, da kansa ya leƙa ɗakin gwaggo ya sanar mata kiran baba.
Batace dashi komaiba ta kashe redion da takeji ta tashi ta fito amsa kiran.
Koda tazo ta zauna Baba yay mata bayanin komai da Ahmad yazo dashi, bata ce komai ba a kai, dama sunsan bazata ce ɗinba, sai Ayyah ce ta bama baba amsa da “Niko malam sai naga kamar babu komai insha ALLAHU, musamman dai da itama Rumana tamuce, kuma itama barinsa garin zai kawo mata salama harya fuskanceta, sannan kuma bamusan alkairi. da ke cikin wannan tafiyaba da yaketa ambato, amma duk hukuncin da ka yanke akan hakan mu masu biyayyane akansa, dan abinda ka hango mu bazamu hangosa ba sam”.
Baba dake sauraren Ayyan ya sauke nannauyan numfashi, kafin yace, “Tunda har kun aminta da hakan kuma ai Alhmdllh, ni dai dama ba matsala bane, tun kuma maganar farko da kikaimin na sanar da su Iya, suma basuyi jayayyaba, sun dai ce na dakata har sai ya sake kawo maganar da kansa, to tunda yanzu ya sake maganar ai ina ganin sai kawai mu bisa da fatan alkairi ko?”.
Cikin faɗaɗa murmushi Ayyah tace, “Hakane malam, mun kuma gode da wannan amincewa, sai aita tayamu da addu'a kuma”.
“Addu'a ai dolece Ruƙayya, shi mai yara inhar da hankali jikinsa ai kuma isasheahen barci ya kare masa kenan, ALLAH dai ya cigaba da mana jagora da tsare mana su baki ɗaya”.
Amin ya rabbi, Ayyah da Gwaggo suka amsa a tare.
Ayyah ce ta leƙo da kanta tai kiran Ahmad, dan haka ya tashi ya koma.
“Amadu mun amince kaje, amma da sharaɗi”.
Ahmad ya ɗago yana kallon baba, don san jin minene sharaɗin.
Baba ya cigaba da faɗin, “Sharaɗin shine karka yarda dogon lokaci ya riskeka baka ziyarci gidaba, sannan inhar kai dawowar farko naga ka canja daga Amadun dana sani to lallai bazaka sake komawa ba”.
“Baba na amince da dukkan sharaɗin, fatana dai kuci gaba da min addu'a”.
“Za'a cigaba dayi insha ALLAHU, yanzu yaushene kake shirin tafiyar?”.
“Eh to asan samuna insha ALLAHU ranar laraba, zanyi ƙoƙari na kammala dukkan ɗinkunan mutane dake hannuna, daga nan na damƙa komai a hannun Mudanseer, sannan inason itama Rumanan ta koma makaranta tunda sun kusa fara jarabawa, inaga hakan zai rage mata kaɗaicin”.
“E lallai kayi ƙyan kai, ALLAH yasa haka shine mafi alkairi, duk da ni yanzu karatun bokon nan ma tsoro yake bani, to amma ita rayuwa ba'ai mata kuɗin goro, dan wani ya bijire dalilin hakan bazakai imani cewa kowama zai kasance hakanba, ALLAH ya cigaba da tsare mana ku baki ɗaya, yanzu kafin ka wuce saika sanarma su Iya duk yanda mukai, nima zuwa safiya zan shiga mu tattauna harma dasu Yusha'u akan batun”.
“To Baba nagode ALLAH ya saka da alkairi, ya kara muku lafiya da tsahon kwana”.
Su duka da amin suka amsa. Daga nan Ahmad yay musu sallama ya tafi, sai da ya shiga Sashen su Iya kankanninsa, bayan sun gama ɗan wasansu na jika da kaka ya zayyane musu komai, babu wanda ya musa a cikinsu, saima albarka da fatan alkairi da nasara sukaita saka masa, zuwa kusan sha ɗaya malam yace ya tashi yaje dare yayi haka nan.
_________________________
Lokacin daya shigo gida Umm-Rumana har tayi barci, hakan yasa bai tadata ba shima ya kimtsa ya kwanta, ya daɗe yana tunani kafin barci ya ɗaukesa.
Washe gari da safe suna karyawa ya sanarma Umm-Ruman maganar tafiyarsa, duk da tasan ba wata soyayya a tsakaninsu ɗan zaman nan da sukai shakuwa ta fara tasiri a garesu, hakanne ya saka duk sai taji babu daɗi.
Amma tayi farin ciki da yace zata koma makarantar ta, hakama islamiyya duk zata koma, dan bayason tanama zama a gidan balle ta koyi halinsu maman Ama.
Duk da ya gindaya mata sharaɗin saka dogon hijjab da niƙaf a makarantar hakan bai ɓata ranta ba sam.
A gaba ɗaya kwanakin da suka biyo baya na shirin tafiyar Ahmad ne, yay ƙokarin kammala ayyukan jama'a daya amsa, sannan yaje makarantar su Rumana yay maganar dawowarta da faɗar matsayinta na matar aure a yanzu tunda makarantar ta ƴammatace, hakama islamiyyarsu yaje ya daidaita mata komai, acewarsa bazata shiga ta matan aure ba, mafi yawan makarantun matan sunfi maida hankali ga saida abubuwa da gulmae juna.
Daren da zai tafi ya zaunar da Rumana yay mata Nasiha sosai, tare da kafa mata shariɗɗa na zaman gidan, duk kuma abinda takeso ta tambayi Mudanseer zai kawo mata, sannan Fa'iza da Salima zasu dawo nan su ringa tayata kwana.
Taji daɗin zancen dawowar su Salima, dan har akan fuskarta sai da yaga haka, amma sai yay tamkar bai fahimceta ba.
Dama tun da daren yay sallama da kowa nasa, iyayensa kakanninsa abokansa dama duk wanda yasan suna huɗɗar mutunci dashi.
Dan haka yana dawowa sallar asuba ya shigo gidan bayan sunyi sallama da mazajen su maman Ama, jakkarsa daya zuba kaya kala uku kawai ya ɗauka, dan ko wanka baiyiba, sai kuma Umm-Rumana taji hawaye na zuba mata.
Tsayawa yay kawai yana kallonta, shi kansa baisan shaƙuwa ta shiga har haka a tsakaninsuba sai yau, ya tako a hankali zuwa gabanta, babu tsammani ya jawota jikinsa kawai ya rungume, ƙanƙamesa tayi tana mai fashe masa da sabon kuka, baice komai ba ya shiga bubbuga bayanta a hankali yana mai lallashinta ta hakan, ganin zata ja masa makara sai ya ɗago kanta ya sumbaci goshinta, murya ƙasa-ƙasa cikin kunnenta yace, “Haba Ƙanwata kuma amaryata, kimin addu'a kinji, amma ba kukaba, ALLAH yay miki albarka, insha ALLAHU lokaci zaiyi da zaki mallaki Ahmad da komansa, ke dai ki zama mai yawan haƙuri da yanayinsa na yanzu kawai”.
Ƙara faɗawa jikinsa Rumana tayi tana wani kukan, yay murmushi mai sanyi yana janyeta a jikinsa, taimaka mata yay ta hau saman gado, ya lulluɓa mata bargo tare da ƙara sumbatar goshinta, yace, “Karki manta dani duk runtsi”.
Abinda kawai ya faɗa kenan ya juya ya fita yana ja mata ƙofar.
Lokacin data jiyo ƙarar rufe ƙofar gidan sai ta kuma fashewa da sabon kuka mai cin rai da tsuma zuciya, tasan dai ba soyayya bace a tsakaninsu, amma tanajin wani ɗacin na wannan nisan nasu.
Ahmad kam Sufyan ya iske yana jiransa da mashin a ƙofar gida, dan haka ya haye suka ɗauki hanyar tasha.
Koda suka isa sai suka iske mota ana mata lodin zuwa garin porthercout, babu wani tunani aran Ahmad ya faɗa bisa shawarar Sufyan, motar dama dai ta gama cika, gurin mutum ɗaya ya rage rak, Ahmad na shiga suka tashi, har motar ta fice a tashar suna ɗagama juna hannu shi da Sufyan...............✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*_GDW_*
*(18)*
...........Taci kuka sosai harta godema ALLAH, dole masu iya magana suce sabo akema kuka ba mutuwa ba, harta fara jiyo motsin maman Ama da yaranta a tsakar gida ita batai ko yunƙurin tashiba, ahakama barci ɓarawo ya sake saceta, saboda jiya sun daɗe basu kwanta ba.
Gaba ɗaya barcin nata sai ya kasance mafarkin Ahmad ne.
Kusan goma Kausar ta fito daga ɗakinta zatayi brush, tabi tsakar gidan da kallo kafin takai dubanta ga maman Ama dake can ƙofar ɗakinta tana haɗa zoɓonta na saidawa.
“Yau gidan namu bai samu ƴar sharar safenba kenan? Ko gimbiyar tamu babu lafiya ne?”.
Ƴar dariya Maman Ama tayi, taɗan taɓe baki cikin iya gulma tana faɗin, “Zaune dafa'an murar kwaɗo, inaga dai kewar tafiyar maigidace ta hanata fitowa”.
“Yo ina mijin ya tafi?” cewar Kausar tana matsowa kusa da maman Ama.
“Uhum wai neman kuɗifa, Kausar nifa wlhy mijin yarinyarnan sai naga tamkar bai taɓa riƙe biroba balle akai ga zaman aji, amma waifa nan inda yake digiri garai”.
Cikin tsantsar hassada Kausar tace, “Yo digirin banza, maman Ahmad ai yanzu wannan ruwan dare ce, ALLAH ma yasa ko a ajin ba na ƙarshe yake ɗaukaba, ita da ba uwar wani abu ya taɓa mataba ma miye na damuwa dan ya tafi mtsooow”.
Dariya sosai Maman Ama keyi, tace, Kijiki da wata magana, idan baiyi mai gaba ɗaya ba, kika sani ko yanayin ƴan kananun ayyuka, duk namijin dai da zai kwana da mace ɗaki ɗaya bai iya mata komaiba ai idan kaji gangami da labari, ALLAH sai dai idan bashi da lafiya ne”.
“Nimafa nayi wannan tunanin wlhy, ko ogana da ina bashi labari cayaymin sai dai idan mijin baida lafaiya, amma wane lusarine za'a kawoma budurwa kamar wannan ya iya kallonta ya kauda kai kuma su kwana lafiya su tashi a ɗaki ɗaya”.
“Kin daiji magana, wlhy hasashenmu duk ɗayane, inaga baida lafiya dai sai yake fakewa da damuwar dan waccan ta ƙisane”.
Sosai suka kwashe da dariya, har suna haɗa baki wajen faɗin “Tamɓele kenan”.
Duk wannan shagali da suke Rumana ma batasan sunaiba, barcinta take abinta.
Bata farka ba sai kusan sha biyu, ta tashi a firgice da mamakin barcin da ta sha, brush da buta ta ɗauka ta fito, Kausar da maman Ama na tsakar gida zaune, Kausar na tsifar kai daga ƙofar ɗakinta maman Ama kuma na tsince shinkafar da zata girka.
Su duka zubamata ido sukai tamkar yaune suka fara ganinta, Rumana ta gaishesu tana tambayar inasu Ahmad.
“Suna ƙofar gida, amma lafiya kuwa da barci har rana Amarya?”.
“Lafiya lau maman Ama, kainane kawai kemin ciwo kaɗan-ƙaɗan”.
“Ayya to ALLAH ya sauwaƙe”. Mama Ama tai maganar suna kallon juna da Kausar kowanne na taɓe baki.
Kausar tace, “Amin, to Amarya ko dai mun samo baby ne?”.
Murmushi kawai Rumana tai mata ta ajiye brush ɗin ta ƙoƙarin shiga bayi ta tsinkayo maman Ama nabama Kausar amsar tambayarta......,
“Hhhh kema Kausar akwaiki da son zance dai, kin taɓa ganin gonar da ba'a taɓa mata ko gewaya ba ta fidda tsirrai? Dama kin tsaya a abinda ta faɗa ɗin yafi”.
Naɗan ciza leɓena dukda ban gama fahimtar zancen nasuba nasan akwai shaƙiyanci a ciki, yanda suka kwashe da dariya kawai ya tabbatarmin da hakan.
Sosai ƙyanƙyami ya kamata ganin bayin duk datti, dan bata tashiba baza'a samu wanda zai tsaftaceba, sai kace ita kaɗai ke amfani dashi, waje ta dawo tai brush ta koma ɗaki abunta.
Bata zauna ba ta hau gyaran ɗakinta, sai da ta kimtsa komai tsaf tayo shara ta goge ledan da ruwa da omo tasa turaren wuta sannan ta dawo sharar waje, har lokacin kuma su maman Ama ana zaune ai ana gulmar maƙwafta, wance tayi kaza wance tace kaza.
Rumana dai bata saka musu bakiba harta kammala sharar tsakar gidan taja ruwa a rijiya, tana ƙoƙarin fara wanke ƴan kwanikan da sukai amfani dasune mijin Kausar ya shigo gidan, gaidashi sukai ita da maman Ama.
Maman Ama na ganin Kausar da mijinta sun shige sai ta ɗakko boket tazo gaban rijiya ɗibar ruwa.
Dama ina kallon yanda take hararar ledar hannun mijin Kausar kamar idonta zai faɗo ƙasa.
Tana zira gugar ne take faɗin “Amarya bakiga mutuniyarki ana karya ƙugu su miji ya kawo cefane ba, batasan munsan komaiba yanzu, sai abinda kishiyarta tace miji keyi”.
Murmushi kawai nayi amma bance uffanba, maimakon maman Ama taji haushi tai shiru itama sai ta cigaba da zaro zance akan Kausar, azamar kammala abinda nake nayi nabar wajen ina faɗin, “ALLAH ya ƙyauta to”.
Ina kallo ta bini da wata harara tana taɓe baki, na girgiza kai kawai na ɗauki ruwa da omo naje na tsaftace bayin sannan nazo na ɗiba ruwan wanka a rijiya.
Har lokacin kuma Kausar basu fitoba, maman Ama na zaune tana facing ɗin ɗakinsu tamkar mai hango abinda sukeyi a ciki.
Lokacin dana fito wanka sai haɗiyar zuciya take, harda dukan Amatullah.
Ni dariyama ta bani, na shige ɗaki abina inayin kayata a zuciya.
Ƙin fitowa nai, ina shirin ɗora taliya a ɗaki sai ga sallamar Zainab.
Ta shigo ɗauke da kwanon silba.
Cikin ɗokin ganinta nake faɗin, “Ga autar gwaggo ga autar Ayyah”.
Itama dariyar takeyi da cewa, “Kai Yaya Rumana, sai kace wadda tazo daga legas”.
“Lallai yarinya, kinsan kuwa yanda nakejin daɗi idan na ganku, daga ina haka?”.
“Daga gida nake, Ayya ce tace na kawo miki wainar rogo da mukayi”.
“Kai-kai kice yau daɗi kukeci a gidan malam ɗin?, duk ni kaɗai wannan?”.
“Eh mana” Zainab ta faɗa tana ƴar dariya.
Na kashe rishon ina cewa, “Aini to nama fasa dafa komai, wannan kam tama isheni”.
Zainab data kwanta a tabarma tace, “Ai aunty fa'iza ma tace anjima zasu taho itada aunty Salima nan, tace karkiyi girki zasu yo muku taɓa ka lashe”.
“To ALLAH ya kawosu lafiya”.
Haka Rumana ta zauna taci wainarta ta rogo tai nak, sunata hirarsu da Zainab, har aka kira sallar la'asar sannan ta miƙe alwala, itama Zainab alwalar tayo sukai sallah, bayan sun idar ta bata naira talatin kuɗin napep da aya da gyaɗa tace taje gida kar a nemeta.
Godiya tai mata ta wuce, itako ta jawo littatafan makaranta ta hau dubawa.
_______________________________
Ahmad kam tunda suka ɗauki hanya ya jingina kansa da kujera yay shiru yana tunanin rayuwa da abinda ya zamo masa sanadin barowa gida, wani sa'in idan ya tuna rayuwar da sukai da Samina a baya sai yaji kamar zai yarda da maganar wasu mutane dakan ce asiri akai mata, sai dai wani sashe na zuciyarsa na saurin ƙaryata wannan magana, sai ya bijiro masa da ainahin gaskiya aka lamarin Samina ta gujesa ne kawai saboda burin banza da wofi da son duniya, wanda a wannan zamanin mafi yawan ƴammata shine yake ruɗarsu ya halakasu, wasu zaka samu da taimakon iyayensu, wasuko sun zubda tarbiyyar iyayen ne sun ɗauki ta ƙawaye ko samari, san zuciyane kawai kesa a zagi ilimin boko, amma wlhy bashi da alaƙa da lalacewar yaranmu, lalacewar kawai tafi yawa daga zuciya ko tarbiyya da dai sauransu.
Yayi zurfi a tunaninsa sosai, har sukai tafiya mai nisan zango dashi kansa baisan adadinta ba, sai da na kusa da shine ya taɓasa lokacin da suka iso wani gari aka tsaya domin yin salla sannan ya dawo hankalinsa.
Bayan salla suka sai abinci kamar yanda yaga abokan tafiyarsa nayi, dan duk inda ya saka ƙafa tarene suke da makwafcinsa da suka zauna kusa da juna.
Bayan sun dawo kuma sai ƴar fira ta fara shiga tsakaninsa da abokin zaman nasa, wanda yace shi sunansa Nura, shima dai neman arziƙi ya kaisa rayuwar garin porthercout.
Tun Ahmad bai sake masaba dai harya saki jikinsa kular da yay kamar Nuran baida yawan hayaniya, ahaka har suka isa garinna port gabannin asubahi.
Dole Ahmad yabi Nura masaukinsa da safe kamar yanda ya buƙata, dan kuwa inma yaƙi dai bashi da wajen zuwa, tunda ba kowa ya saniba balle yace zai nemeshi.
Masaukin na nura dai bawani waje bane face gidan biredi, inda sukan maƙala ƴan kayansu su wuce wajen sana'a, idan sun dawo su yada zango a ƙofar wani shago da ire-irensa su rage dare, zuwa ƙarfe goma su nufi gidan biredi su kwanta, asubar fari kuma za'a tashesu saboda za'a fara aiki.
Sana'ar kuma Nura Shu-shaina ce, dan haka koda Nura yayma Ahmad bayani sai bai jayayya ba yace shima zaiyi, tunda bada wani jari yazo ba balle yace, dama iya kuɗin motane, sai kuɗin da suka rage masa a aljihu naira dubu ɗaya da ɗari bakwai.
Da waɗannan kuɗinne Nura ya rakashi ya sayi ƴan abubuwan bukata da zai fara wannan sana'a, a ranar babu hutu suka fara zagayawa kuwa.
Ahmad yasha matuƙar wahala, duk da ya saba da wahalhalun talla ba irin wannan baneba, saboda banbancin gari da jama'ar garin, sauƙinsa ɗayama yayi karatu, shine ya taimakesa wajen furta magana da mutane, dan inhar kaji hausa to sai dai idan suna tare da bahaushene waɗanda suka kasance ƙalilan a garin kuma.
Sai yamma lis suka dawo yanata yaƙe, ga ƙafafunsa sai ciwo suke, harya yi aniyar cema Nura shi dai bazai iyaba, sai kuma wani tunani yazo masa a rai, idanma yace bazaiyiba to yanada jarin yin wata sana'arne bayan wannan? Wannan tunanin shine ya danne dukkan yunƙurinsa ya sama zuciyarsa haƙuri.
Hankalinsa bai kuma tashiba sai da sukazo kwanciya, yaga kowa na ƙokarin jera kwalin da zai kwanta, ƙwalla ne suka cika masa idanu, dukda kasancewarsu talakawa ko kwanan tabarma bayi yakeba sai ta kama, ko yaya dai sunada ƴar katifar barcinsu.
Shi aranarma sun manta basu sayo masa kwalinba, sai na Nura suka gitta suka kwanta iya ƙirjinsu kawai wai dansuji ɗan taushi, ƙafafu kuma na saman suminti, Ahmad da ya saba rufa zai iya barci sai gashi yau babu abin rufar, aiko duk yanda yaso yin barci kasawa yayi, ta ko ina babu daɗi, zuciya sai tuna masa matarsa da iyayensa harma da Samina take.
ƙarfe uku da rabi aka tashesu, har lokacin kuma Ahmad bai rintsaba, haka suka fito kamar awaki, kowa yaɗan samu waje a waje ya maƙale dan ya ƙarasa daren, wasuko basu kwantaba suka hau hidimar shirin fita kasuwa sai kace fataken dare.
Wannan ƴar kwanciya dasu Ahmad suka samu ƙofar wani shago ce ta jawo masa barci yaɗan figesa, sai da Nura ya tashesa da asuba da ƙyar.
Gaba ɗaya komai ya rikiɗema Ahmad, dukya fita hayyacinsa tamkar ma wanda baisan A ba, gaba ɗaya ya rikiɗe matsayin ɗan ciraninsa, kwanansa huɗu sannan ya samu damar kiran ƴan gida a waya.
Yaci faɗa wajen baba saboda ƙin kira ya sanar ya sauka da baiyiba, sai da yayta bama baba haƙuri sannan ya sakko.
An bashi ya gaisa da kowa, harda Mudanseer, yace masa yaje da dare ya kaima Rumana waya su gaisa.
Aiko kamar yanda ya buƙata da daddare ya kaima Umm-Ruman waya, lokacin su Fa'iza masu tayata kwana suna gidan. Gaisuwa kawai sukai ya tambayata babu dai wata matsala ko? kuma ta daina kukan?.
Ta faɗa masa eh tana haɗiye kukanta.
Daga haka bai ƙaraba yay mata sallama, itako ta mikama Mudanseer wayar.
Tun daga ranar bai sake neman Rumana ba, sai dai duk kwana biyu yakan gaisa da baba, idan yaga kuɗin zasu isa a haɗashi dasu Ayyah, idan bazasu isaba shikenan yace baba ya gaishesu kawai.
Tun Ahmad na jigata harya saba da sanar tasu, ya dake zuciyarsa sosai, komai ya zame masa jiki.
Kafin wani nisan zango sai ga wata ɗaya ta shuɗe babu labarin Ahmad balle dawowarsa, da yake yakanyi waya da Madan ya sanar masa ƴan kuɗin ɗinki da ake samu suna riƙesu har Rumana sai hankalinsa yakan ɗan kwanta, amma ya turama Mudanseer kuɗi sau biyu duk da basu da yawa kuwa.
Baba ya fara magana akan zuwansa gida, hakan ya saka Ahmad shiga damuwa, dan shidai alokacin baima fara fahimtar komaiba game da abinda ya fito nema balle kuma ace yaje gida, ko kuɗin mota kawai sun isa gayya.
A haka wata ɗaya ya kuma shigewa suka zama biyu, dukda takurawar baba yanata jansa da ban haƙuri shidai tare da wasu dabaru.
Wannan sabuwar rayuwarce ta fara saka zuciyar Ahmad mantawa da wata Samina, dan shi kansa yakan manta da kansa balle ita, ibadar ALLAH da sana'arsa ce kawai damuwarsa, sai ƴan uwasa da basa barin zuciyarsa a koda yaushe, Umm-Rumana ma takan faɗo masa arai lokaci-lokaci, musamman ranar dazai taho da taita kuka ta kasa barin ransa, sai kuma randa tai targaɗe a ƙafarta tayi masa kukan taɓara.
Yakanyi murmushi idan hakan yazo masa a rai kuwa.
A hakane kuma suka samu aikin gadi shi da abokinsa Nura, babu musu suka amsa, dan kuwa mai wajen da zasuma gadin yay musu alƙawarin biyansu kuɗi masu ɗan tazara, dan duk wata dubu talatin su biyu su raba.
Ahmad yay murna, dan tun zuwansu bai tara kamar waɗannan kuɗinba.
Da rana zasuyi yawon tallarsu, da dare kuma suzo su kwana yin gadi a wajen.
_________________________
Ɓangaren Samina kuwa yanzu abubuwa sunyi nisa tsakaninta da Ma'aruff, kamar yanda mama gaje take buƙata Ma'aruff na kashema Samina kuɗi tamkar baisan ciwonsu ba, amma kuma yana lalubeta kullu yaumin a mota, yanzuma abin yakai har gidan gonar nan yake kaita susha masha'arsu.
A sheɗanci kuwa shigartane kawai bai taɓa yiba, amma duk wani ƙazamin romance Ma'aruff yanayi da Samina, idan ta dawo gida kuwa ko ranar abubuwa sukai masa yawa bai zoba to ka'idane zata shiga bayi taita ɗauka masa hoton kanta tsirara tana tura masa, har video sakata yake yana faɗa mata abinda zatayi, koya kirata video call ahaka zasu gamsar da junansu😭.
Sanda taji Ahmad yayi tafiya tsakima tayi, acewarta sun rage ƴan saka idon anguwa masu zuwa lahira da ƙoƙwan dambu, waɗanda talauci ya zautar da kwakwalwarsu basa fahimtar komai sai saka ido ga abinda bai shafesuba.
Maimakon Mama gaje ta kwaɓeta saima ta kama dariya kamar wata zautacciya.
Kullum kuma cikin yima Ammin Rumana shaguɓe ake akan ɗawainiyar da Ma'aruff kema Samina.
Sam idon mama gaje ya rufe takasa fahimtar ƴarta na cikin wani hali, abinda kawai tasani ƴarta tana fitane zuwa makaranta, idan kuma Ma'aruff ya fita da ita to sunje ya mata sayayyane kawai.
Bata taɓa tunanin bincikar wayar Samina ba, musamman yanda Saminar bata barin kowa ya taɓa mata waya har ita mama gajen kuwa, ƙannenta ko dasun taɓa ne zata mammakesu ta amshe kayanta, maimakon mama gaje ta fara tunanin akwai abinda Saminar ke ɓoyewa a waya amma sai tayi biris da hakan.
Ita dai kawai da an kawo mata kuɗi da kayan makulashe da zannuwa masu tsada shikenan.
Iyayen Saminar maza da kakanninta kuwa taje ta dafko musu asirin daya rufe bakin kowa a gidan babu mai ma Samina faɗa akan komai, sai idanu da suka zuba mata duk da abinda take yana cin zukatansu kuwa.
Dan wataran baba yusha'u har kuka yi yakeyi akan halin da Samina ta jefa kanta sanadin son zuciya..
Kowa yasan zuwa yanzu idanun Samina sun ƙara buɗewa, ta fetsare sosai, dama karatun islamiyya kam ta ajiyesa gefe, na bokonma da take fakewa dashi yanzu bayi takeba, tunda da taje Ma'aruff ke zuwa ɗaukanta, wani lokacinma ko cikin makarantar bata shiga, kai tsaye gareshi take tafiya, abun yakai har Company dinsu Ma'aruff Samina zuwa take Office ɗinsa susha sha'aninsu.
Gaba ɗaya ta manta da wani halitta Ahmad balle rayuwarsu ta baya da ƙoƙarin gina rayuwarta da yayi, gaba ɗaya ita a dole yanzu ta zama babbar yarinya, budurwar babban yaro da ya fi mijin novels komai.
Abinda yasa Samina taƙi yarda ta bama Ma'aruff kanta 100% saboda tana tuna yanda marubuta kansa amarya tasha gata wajen minjinta a daren farko saboda budurcinta daya samu, amma yanda yasha kawo farmakin amsa da tuni ta bashi.
To tanason dai itama taga wannan gatan shiyyasa.
_________________________
Rayuwa a wannan gida a yanzu babu abinda zance kam, dan bazance ina a ƙuntace ba bazance kuma inajin daɗiba.
Sauƙina ɗaya yanzu tunda safe damunyi kari muka gyara ko ina makaranta muke nufa, bayan na saka Uniform nakan saka hijjan dina har ƙasa da niƙaf, ba ruwana da malamanmu, harma wani girma suke bani, hakan kansa ƴan ajinmu suyitamin shaƙiyanci, iyakata dariya kawai, sai ko su Salima dakan taremin.
Idan aka tashi daga can gida su Fa'iza suke wucewa, nikuma na wuto gida nima, nakan tadda su maman Ama a ɗaki ɗaya zaune suna hira, ko a tsakar gidan wadda na tabbatar bata wuce gulma ba, dama ni tunda na sanar musu zan koma makaranta suka dasa yi dani, nakanji har dariya suke wai tundafa miji ya rainani ai dole ya maidani cikin ƴammata, tunda bani da maraba dasu.
Da farko bana fahimtar zancen, amma a hankali saina gane manufarsu, sam ban damuba dan kuwa ni abinda suke nufin ba shine damuwataba, koda zamu shekara goma Yah Ahmad bai nema komai daga gareniba bazan taɓa ɗaukarsa komaiba.
Dan laulayin ciki da kausar ta farane ya kan kawo a zauna anamin shaguɓe a kansa, tunma bana fahimta harsu Fa'iza suka ankarar dani, banji komaiba a raina, sai ma mamakin rashin ya kamata irin nasu maman Ama nake gani, su miye damuwarsu dan yaya Ahmad bai taɓa mu'amulantata a shimfiɗaba to?.
Zanyi ƙokarin mana girki nasa a kula, la'asar nayi zan shirya na wuce islamiyya, daga can muke haɗuwa mu dawo gida da su Salima idan an tashi.
Ko mun dawo kuwa muna ɗaki abunmu, idan kinga mun fito kuwa ban ɗaki zamuje ko yin abu mai muhimmanci, hakan ya saka su Kausar sake maidani naman cinsu, duk da a hakan kuma suma basubar junansu ba.
Yanzuma likafa ta cigaba har gidan maƙwafta suke zuwa suma suna zuwa nan.
Babu ruwana da kowacce mace bayan gaisuwa.
Lamarin Yah Ahmad kuwa bai cika damuna ba, duk da bawata waya mukeyi da shiba, tundama ya tafi baifi sau uku na taɓa waya da shiba a wayar Yah Mudanseer.
Duk abinda na buƙata Yah Mudan na ƙoƙarin kare mani mutunci ya saya mani, idan kuma yafi karfinsa zai sayo dai-dai ƙarfinsa.
Nima bamma faɗar wanda yafi ƙarfin nasa sam.
Zuwan Ayyah gidan biyu dan taga yanda muke, hakama Yaya Maryam da yaya Sakina da Raheenatu, suma duk sunzo mani harma da yaya bintu yayar Samina.
Suma duka zuwansu ya sakani farin ciki, duk wanda ya ganni kuma zai shaida hakan a fuskata.
Kullum dai nakanbi mijina da addu'ar fatan alkairi da kariyar UBANGIJI aduk inda ya tsinci kansa, ALLAH kuma ya azurtashi da halalinsa komai kankantarsa, ya tsaresa daga haramun komai yawanta da ribar da zaici a cikinta.
A farkon tafiyarsa naji kewarsa, amma zuwa yanzu sam babu hakan a raina.............✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*_GDW_*
*(19)*
..............Tun su baba na saka ran dawowar Ahmad a kusa har abin ya fara basu tsoro, dan kuwa gashi ya shiga wata na huɗu da tafiya.
Wata ranar alhamis Ahmad ɗin ya shiga wani shago na masu sai da yari, saboda kiran da mai shagon yay masa zai wanke masa takalmi, dan yanzu ya gama sanin gari ba tare suke yawo da Nura ba, kowa yana fita neman nasane, da yamma su haɗu a inda suke zama, zuwa dare su wuce wajen gadinsu.
Tunda Ahmad ya zauna wanke takalmi mai shago ke binsa da kallon ƙurilla, tun Ahmad bai fahimta ba harya fahimci kallon da mai shagon ke binsa dashi.
Ɗan ɓata fyska yay, hakan yasa mai shagon yin murmushi, yace, “Na dameka da kallo ko? kayi haƙuri, mamaki nike kamarka fine Boy da wannan sana'ar”.
Ahmad dai baice komai sai murmushin yake da yay, harya kammala ya tattare kayansa zai wuce mai shago ya mika masa ɗari biyu yana faɗin, “Inda zaka yarda dana koya maka wannan sana'ar tamu ta yari?”.
Shiru Ahmad yay yana kallonsa cikin nazari,
Mai shago ya sake cewa, “Karka zurfafa tunani ƙanina, haka kawai haɗuwar jini ta sakani maka wannan maganar duk da kuwa yauce rana ta farko dana fara ganinka, amma dai kamin kamanni da bakatsinen barume hakanne ya sakamin ƙaunarka ta musamman, idan har ka aminta zakayi na baka dama ka samo jarinka kazo insha ALLAHU zan taimakeka”.
Kai kawai Ahmad ya jinjina ya fita bayan ya amshi kuɗinsa.
Koda ya koma ya sanarma Nura sai yay murna, yakuma bashi ƙwarin gwiwar karɓar tayin Alhajin, dan acewarsa wata damace dasu basu samuba tazo masa dukda bai jima da zuwa garinba kuwa. Amma maganar jari ya jira wanda sukema gadi ya biyasu sai yayi amfani da kuɗin.
Ahmad yaji daɗin shawarar Nura, dan haka ya aminta sosai, washe gari yaje ya sanarma Alhajinnan komai, Alhaji ya amsa da babu komai shidai yana jiransa.
Kwanaki goma dayin haka suka jira a basu albashi shiru, har haƙurinsu ya ƙare sukaima mai wajen magana, amma ƙiri da muzu ya hanasu yama yi musu korar kare.
Wannan abu ya saka su Ahmad a takaici, harya hanasu talla a wannan ranar sukai yinin baƙin ciki.
Da abokansu suka dawo daga tasu sabgarsu suma sai suka sanar musu, suma ransu ya ɓaci, nanne wani ke basu shawarr idan zasu iya aikin sauke kaya suzo suje, shi mutumin kullun yake biya adadin kuɗin aikin da kayi.
Da farko Ahmad ya musa, amma da Nura ya lallashesa saiya yarda washe gari sukaje.
Wajene kamar kamfani, ana kawo kaya sukuma za suke jigilar saukewa daga motar zuwa store. A sati ana sauke kayan sau biyar ne.
Duk da wahalar dake cikin aikin haka Ahmad ya dage, bayan sun kammala na ranar kuwa aka biyasu haƙinsu, sunsha ciwon jiki saboda rashin sabo, dan daƙyar sukai barci ranar, amma daɗin kudin da aka biyasu ya saka washe gari suka sake komawa.
A hankali sai gasu sun zama ƴan gida, dan kuwa harma sun saba komai anayi dasu na harkar dako a ma'aikatar.
Duk kuɗin da suka samu Ahmad kan kai nashine wajen Alhajin nan yana tara masa, a randa suka cika sati na huɗune kuma sai kawai ogan wajen ya basu sanarwar duk wanda yazo gobe yaga sunansa an kafe to karya sake zuwa aiki, an koresa kenan
Hantar cikin su Ahmad ta ɗuri ruwa, dan kuwa suna samun alkairi a wajen babu laifi.
Washe gari duk a cikin damuwa sukazo, sai yazam gaba ɗaya waɗanda aka cire hausawan ne, kukane kawai Ahmad baiyiba, suna shirin tafiyane kuma matar mai gidan ta dakatar da Ahmad, acewarta wanan ƙyaƙyƙyawan babu inda zaije, dole ogan ya maida sunan Ahmad kuwa.
Duk da yaji dadi ya nuna damuwarsa na rashin Nura, haka ya cigaba da aikin har tsawon sati huɗu sannan ya bari saboda yaga dai Alhmdllh yaɗan tara wani abu da zai ishesa jari.
Lokacin da zai wucene sai matar ogan ta nuna rashin jin daɗinta, hakan yasa tai masa tayin gadi a gidansu, zasu kuma bashi ɗakin mai gadi ya zauna.
Nanma bai bata amsaba sai da yazo ya shawarci Nura, Nura kuwa ya bashi kwarin gwiwa akan hakan.
Ahmad bai amsa zaiyiba sai da ya koma wajen Alhaji aka fasa asusun kudinsa na dako da ya tara Alhaji ya haɗa masa kwabar ƴan kunne ta hannu, aka zuba kaya dai-dai kuɗinsa sannan, ya bashi tare da sanar masa dabaru akan sana'ar.
Daganan kuma ya koma ga ogansa ya sanarma matar zaiyi gadin, amma zaike zuwa sana'arsa da rana.
Babu musu suka amince, a cewarsu aiba zaman gidanma sukeba da ranar.
Tundaga wannan ranar rayuwa ta sake sauyama Ahmad, dan kuwa a cikin watannan gaba ɗaya saiya cinyesa a yawon tallar ƴan kunne da gadi, koda ƙarshen wata yay yaga yaɗan farfado sai ya fara tunanin zuwa gida, lokacin yanada wata shida cif a garin porthercout.
Babama har yayi fushi da rashin zuwansa ya haƙura yabar masa magaba.
Tun daga randa yay aniyar zuwa gida yaɗan fara sayen tsaraba yana ajiyewa wadda zai fuskanci gida da ita, haka kawai kuma sai yakejin ɗokin ganin Umm-Rumanan sa.
_________________________________
Zuwa wannan lokacin maganar Ma'aruff ta shiga gidansu Samina, yayinda alakarsu ta sake ƙazanta sosai, dan tunda aka tsaida bikinsu wata biyu kacal sai yazam babu abinda Ma'aruff ke burin samu daga gareta sai jikinta.
Har takai dai yau yaci galabar rabata da budurcinta a gidan gonarsa, tasha kuka iyakar iyawa, shiko ya katsatstsareta da lallashi da daɗin baki akan ai babu komai tunda shine zai aureta, kuma bikin nasu duka saura wata ɗaya ne kacal ai.
Tun tana kuka da ƙarfin zuciya har ta aminta da daɗin bakinsa, ya tainaka mata ta gyara jikinta, tare da saka abokinsa ya kawo mata magunguna da allurar rage raɗaɗi, ya kuma kaita Shop rite yay mata shopping na hauka da bai taɓa mata irinsaba, ya maidota hargida tare da bata maƙudan kuɗi.
Mudanseer dake shago Shi da Abu yana kallon yanda Ma'aruff keta saukema Samina kaya niki-niƙi, baki kawai ya taɓe ya ɗauke kansa danshi yanzu babu abinda ya damesa da ita.
Maimakon lokacin da aka shiga da kayan Mama gaje ta fahimci halin da Samina take ciki sai idonta yafi karkata ga manyan ledojin.
Duk uwa mai hankali aka taɓa mata yarinya, kuma yarinyar ta dawo gareta a randa abin ya faru dolene ta fahimci akwai matsala, dan duk macen da aka raba da budurci komai tsahon shekarun da take dashi babu aure wlhy sai taji daban, idan ko babu aurene fargabar fara yinta bata hanyar daya daceba koda itace takai kanta saikin sameta tattare da ita, iyaye kalubale ne agareku, dan yanzu har sai ƙaton banza ya gama lalata miki ƴa a waje ta ɗau ciki ta zubar bama ki saniba saboda sakaci da sakarci kosan duniya irin namu.
Da wannan damar rashin kulawar tamu samari keta lalata yara ta yanar gizo da zahiri ba tareda kun fargaba, damuwarki kawai ki gyarama mijinki kanki dacin kwalliyar tafiya biki domin ki birge mata ƴan uwanki, idan kishiyace dake hankalinki na kanta, saikiga ƙanin uban yarinya ko ƙaninki ko wani na kusa daku ya gama warware tufkar tarbiyyar da kukayi kina nan shatata da baki, sai rashin mutunci ya saka saurayi sakin videon baɗalar da yay da ƴarki a yanar gizo ki haukace har takaiki da faɗawa wani hali ki kamu da ciwon hawan jini kona zuciya, bayan kuma kinbar gini tun ran tubani.
A tunanina duk uwa datasan ƴarta budurwa nada wayar yakamata tazam mai saka mata idanu akan wayar, kodama bata da ita ki saka mata ido tunda akwai ta ƙawaye.
Tanan suke shiga yanar gizo su haɗu da ƴan iskan facebook, ko istagram, ko litatafan batsa dake yawo a kowacce irin kafa ta yanar gizo, ko ƙawa ta sakata a group da sunan group ɗin matan aure wanda idonsu ya rufe basajin tsoron ALLAH duk abinda yake haramun shine abun kallonsu, wanda yake haramun shine abin furtawarsu da jinsu a zuwan wai koyan rayuwar aure, ke wane kidahumancin ya baki tunanin sai an ɗakko shaiɗancin tsiraicin wani kin ganine zakisan yanda zaki rayu da mijinki?, wlhy matan aure kaiconku da wannan wawancin mai toshe ƙofofin hasken zuciya da kashe gani.
Ƴammata da yawa daga shiga irin waɗannan groups suna canja suna komai ke fara tabarɓare musu, idan k uwa baƙya bibiyar lamarinta daga haka sai kiga komai da kika gina ya tarwatse.
Wlhy kuzama masu kulawa kafin ku riski ranar kuka da nadama akan ƴaƴanku, domin sai ALLAH yay miki tambaya dalla-dalla akan tarbiyyarta.
Wannan sakacin ne ya hana Mama gaje fahimtar komai akan Samina har Ammin su Umm-Rumana ita ta lura, ba ƙaramin ruɗani ta shigaba, sai dai tana tsoron tace wani abu aga zaƙewarta.
Samina kuwa kwanciya tai wahala ta sakata barcin dole, bata tashi farkawaba sai bayan sallar magriba, agaban mama gaje ta dafa ruwan zafi taje tai wanka dashi ta sake gasa jikinta kamar yanda taga ana cewa a novels, koda ta fito sama-sama taci abinci ta sake kwanciya, kobi takan kayan da mama gaje ta baza a ɗakin bataiba saboda ita tasan wahalar da taci kafin ta samo kayan.
Haka Samina taita jiyyar jikinta har kwana biyu, ko ɗaga wayar Ma'aruff batayi idan ya kirata saboda haushinsa da takeji, amma taji daɗin yanda ya nuna damuwarsa a kanta, sai turo mata massegea yake kamar hauka, wannan yasa a cikon kwana na huɗu ta kulasa.
Yako kalailayeta da daɗaɗan zantuka ranar, haryaci galaba a kanta tafito makaranta taje Office ɗinsa ta samesa, acan yakuma lallaɓata ya ƙara na biyu, ranarma taci kuka dan tasha wahala, amma daya lallaɓata da mayaudaran kalamanasa saita goge hawayenta saboda ta yarda dashi.
Tun daga wannan ranar ya maidata kamar wata matarsa, a gefe kuma yanata sakar mata kudi itada ƙawayenta suna shirin biki. Sati na biyu da kauda mata martabarta aka kawo lefenta daga gidansu ma'aruff akwati ashirin da huɗu cif, tare da katuwan jakkuna uku manya-manya, ɗaya na babanta, ɗaya na Mama gaje, ɗaya na danginta.
Ranar dai kam su Ayyah sunsha kallo, sun kumasha gori wajen mama gaje da danginta, ƴan anguwa kam ai kamar sa fasa gida kallon kaya, harda ƴan gayyar soɗi, dan ko su Maman Ama sai gasu sunzo ganin ƙwaf daga jin su Salima na sanarma Umm-Ruman cewar gobe za'a kawo lefen Yaya Samina.
Shine mutanenku sukai shiri Rumana bata saniba sukazo wai yimata kara tunda ita har yanzu bata fara zuwa gidaba baba Yusha'u ya hana, yace tai zamanta har Ahmad ya dawo ya bata izinin hakan, makaranta kawai take fita, shima kuma jarabawama suke zanawa ta ssce.
Ranar su Nafy ƙawayen Samina haka sukaita yawo da wannan lefe a social media, yayinda ya tadama ƴammata da yawa hankali da fatan suma sai an musu irinsa koma wanda ya fisa.
Harda masu takaicin inama sune, irinsu Kausar.
Koda sukaje suna bama Rumana labari tasha mamaki, dan ita bama ta kawo can sukajeba, amma sai batace dasu komaiba akan hakan dukda taji haushi.
_________________________________
Baba ne ya gindayama Ahmad sharaɗin ya tabbatar yazo gida anyi bikin Samina dashi, tunda shine namiji babba a gidan bai ƙyaitu ace baya nanba.
Dukda baiso hakaba dole yabi umarnin baba, tunda yanzu dai Alhmdllh, duk da bawasu maƙudan kuɗi ya samuba babu laifi tafiya tai riba, dama kuma ya gama shirinsa tsaf.
★★★★★★
Umm-Rumana duk da bata da tabbacin zuwa gidan bikin haka ta wanke kanta Salima ta yarfa mata kananun kitso, suka kawo ƙawarsu har gida tai mata ƙunshi mai ƙyau, haka kawai ta tsiri juya fasalin ɗakinta.
Tako tsare su Fa'iza suka tayata, komai suka canja masa muhalli ya koma kamar wani sabon ɗaki, aranar kuma su Samina ke shirya fatin ƙunshi a wani haɗaɗɗen hotel tsadajje.
Su Fa'iza duk sun gudu sunbarta ita kaɗai a gidan, dan haka bayan tai wankanta tai kwanciyarta tana kwasar barcin gajiyar aikin da sukayi.
★★★★★★
Ƙarfe kusan huɗu su Ahmad suka iso cikin garin kano, ya jigatu sosai saboda tafiyar dare sukayo, tun a tasha sukai sallama da Nura da shima yazo ganin gida, ya loda kayansa a napep ɗin da yay shata suka nufi gida.
Ƴammatane danƙam da ƙofar gidansu, ga galla-gallan motoci sun jeru domin kwasarsu zuwa wajen kamu.
Mai napep ya samu ɗan wajen maƙalewa yay fakin.
Kallo ɗaya Ahmad yayma motocin ya ɗauke kai, dan koba a faɗa masaba dai yasan ƴan bikine.
Yana fitowa idon Mudan dake ɗinki a shago ya sauka kansa, cikin matuƙar mamaki ya fito, dan babu wanda yasan da dawowar Ahmad ɗin sai baba.
“Yah Ahmad!” Abu ya faɗa da ƙarfi shima tare da sakin butar da ya ɗeboma Mudan ruwa daga cikin gida, sheƙawa yay da gudu ya koma dan kai rahoto.
Kafin kace mi yara sun zagaye Ahmad anata murnar ganinsa suna kwasar kaya zuwa cikin gida, hakan ne ya sakashi farin ciki, inda kuma hankalin ƙawayen Samina ya dawo kansa, dan kuwa su Nafy tuni sun fara rattafo labari akan da shine zai auri Samina ai.
Da yawansu ƙyawunsa ya ɗau hankalinsu, sai dai sunce rashin ƴan canji ya kwafsa masa.
Ahmad da baisan mi sukeba tuni ya nufi cikin gida riƙe da hannun Mudan suna dariyar tsokanar da mudan din ke masa akan yayo ƙiba kamar ba shiba.
A ƙofar soro sukai karo da Samina da taci ado cikin wani arnen farin les, ƙawayensu kusan biyar na tare da ita, da alama dai zasu fita ne domin a kaisu wajen kamun.
Kallo ɗaya Ahmad yay mata ya ɗauke idanunsa yana cigaba da murmushinsa da ya ƙara haska choco color ɗin fatarsa mai ƙyalli ta asalin rumawa.
Haka kawai Samina ta samu kanta da faɗuwar gaba, tuntuɓe tayi zata faɗi ƙawayentan sukai saurin tarota, da kallo ta bisa har suka ɓacema ganinta, sosai taga ya canja mata duk da ma babu kwalliya tare dashi, dan wandon jeans ne da t-shert mai gajeren hannu a jikinsa, duk rigar ta yamutse alamar sunsha zaman mota.
Siririn tsaki taja tana faɗin, “Ɗan wahala kawai” a fili.
Mutum biyu a ƙawayen nata da sukasan komai suka kwashe da dariya kuwa, suma idonsu a kansa, sai daifa harga ALLAH sun yaba da wannan ƙyaƙyƙyawar halittar.
A cikin gida kam an rikice da dawowar Ahmad, harma ya rasa sannu da zuwar wazai amsa, ƴan uwansa da yaran anguwa duk sun zagayesa, kunsan yaro dason adawo daga tafiya a bashi tsaraba koda ta biredi ce😂.
Fahimtar hakan da Ahmad yay ya sakashi jan ledar biredi ɗaya ya miƙama Sadiya data ajiye masa ruwa yace ta raba musu.
Aiko kowa yana samu aka bashi sai ya fita cike da ɗoki kai rahoto gidansu.
Bakin Ayyah gaba ɗaya yaƙi rufuwa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, Gwaggo kuwa babu mai cewa ga yanayinta, sai dai cikin ranta ita kaɗai tasan sanyin da takeji na dawowar Ahmad ɗin.
Bayan yasha ruwa suka gaisa da mutanen da suka shigo ƴan biki masa sannu, wasuko dai ƴan son ganin ƙwaƙwaf ne.
Bayan an gaggaisa suka fita, shima sai ya samu gaisawa da nasa iyayen da ƙannensa.
Yana shirin kishingiɗawa a tabarmar da aka shimfiɗa masa Ayyah tace, “Ɗan albarka badai anan ba, maza tashi ka wuce wajen matarka ka huta acan”.
Cikin shagwaɓa ya narke murya yana faɗin, “Kai Ayyah na, nifa kamarma kin daina sona nake gani?, yanzu abincimafa kince bazaki bani naci ananba”.
“Aiko wlhy ban baka, gashi dai zan zuba a kwano auta tazo ta bika dashi gida kaci acan, maza tashi, baiwar ALLAH ai tayi haƙuri ƴarnan”.
“To Ayyah zan tafi, amma ki bari mu gaisa da baba to”.
“A'a idan ka dawo anjima kwa gaisa, dan malam ma baya nan kusa yaje Dawanau ne”.
Dole Ahmad ya miƙe domin bin Umarninta, jakkar kayansa kawai da jakka ɗaya da leda ya ɗauka, sauran kayan kuwa duk nan aka barsu a ɗakin Ayyah kamar yanda yace su Sadiya su shiga dasu.
Shi kuma Mudanseer ya ɗauka kayan ya fito ƙofar gida domin tarar napep.
Su Samina amare har an wuce, sai abokan Ahmad dake jiran fitowarsa.
Nanma fa wata sabuwar murnarce ta sake kacamewa a tsakanin abokan amana tun ƙuruciya, da ƙyar Ahmad ya ƙwaci kansa akan zaije ya kimtsa ya dawo.
Ya shiga napep ɗin da mudan ya saka masa kayansa suka wuce.
Cikin barci naji muryar Zainab na faɗin, “Yaya Rumana ki tashi ga Yah Ahmad ya dawo”.
Da ƙyar na iya buɗe idanuna saboda ba ƙaramin barci nayiba ashe, ganin Zainab zaune kusa dani ya tabbatar min da ba mafarkin dana saba yi bane.
Tashi nai zaune sosai, sai kuma na miƙe zumbur jin muryar Yah Ahmad dake amsa gaisuwar su maman Ama.
Kasa haƙuri nayi, na nufo ƙofa domin tabbatarma kaina.
Sai dai ashe ya kawo jiki zai shigo sai mukai karo harna bige kaina a ƙirjinsa, nai baya zan faɗi yay saurin ruƙomin hannu..............✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*_GDW_*
*(20)*
...............Sassanyan numfashi na sauke jin ALLAH ya taimakeni bansha ƙasaba, sai dai jina a jikinsa saboda jawonin da yayi ya saka gabana faɗuwa nai saurin son matsawa bayan again.
Sakinta Ahmad yayi saboda ganin Zainab a ɗakin, shima jinta da yay jikinsa ba ƙaramin bugawa ƙirjinsa yayi ba, ya raɓa ta gefenta zai wuce murya na Rawa tace, “Sannu da zuwa Yaya”.
Idanunsa ya ɗan lumshe yana ƙoƙarin zama a bakin gadon, ya ɗago ya kalleta sosai murya ƙasa-ƙasa ya amsa da “Yauwa, kema sannunki”.
Ruwa Umm-Ruman ta ɗibo a kofi bayan ta ɗauraye, ta kawo gabansa ta ajiye tare da durƙusawa tana sake masa sannu da zuwa, tana a duƙen take gaishesa cikin girmamawa.
Daƙyar Ahmad ke ƙoƙarin amsawa dan sosai Rumana ta canja masa, sai yaga ta sake girma, ko dan dai kafin tafiyarsa ba wani kallon ƙwarai yake mataba, sannan bata yarda ta zauna babu hijjab, yau ko ya rutsatane babu hijjabin.
Sanye take da siket da riga na wani yadi mai kama da atanfa, siket ɗin 8-fisis akai masa, hakan yasa ya matseta kaɗan daga sama ya buɗe sosai a ƙasa, ga rigar fitet ita kuma, sai hannunta ne daya buɗe sosai daga ƙarshe.
Mudanseer ne yay musu ɗinki, a lokacin har Ahmad ɗinma na faɗan yanda Mudanseer yay wulaƙanta kayan da ɗinkin manyan gayu.
Yadin bai kai sun sami ɗan kwaliba, sai wani kalan suka saya, itako Rumana bata cika son ɗan kwali mai santsiba, shiyyasa ko yanzu gyalen jallabiyane ta yana akan nata, hakanne ya bayyana haɗaɗɗen kitsonta ta gaba, sai jelar da yake iya hangowa kaɗan idan ta duƙa saboda tanada tsahon gashi, kusanma duk yaran gidansu ALLAH ya basu suma harsu mazan.
Duk da yasha ruwa a gidansu baiƙi shan wanda ta kawo masaba, dan ganinta ya haddasa masa wani sabon ƙishirwan.
Yana cikin shan ruwanne Zainab ta miƙe saboda gargaɗin da Ayyah tai mata akan tai maza ta dawo karta zauna.
“Uhm Yaya Rumana bara naje gida, Ayyah tace karna zauna saboda magriba ta kusanto”.
Ji Rumana tai kamar ta hana Zainab wucewa, dan kallon da Ahmad ke mata duk ya sakata ruɗewa, kamar zatai kuka tace, “Ki zauna su Fa'iza su zo mana, ƙilama Yah Madan yazo anjima saiki bisa”.
Zainab taɗan ƙwalalo ido waje tana fadin “Kai, Yaya Rumana ALLAH Ayyah dukana zatai, gara dai na tafi, gobe zan dawo”.
Ahmad dai duk yana jinsu amma uffan bai ceba, yama ajiye kofin ruwan ya koma latsa wayarsa daya sake, dukda ba sabuwa bace tayi ƙyau dan batasha wahalaba sosai.
Hamsin Rumana ta bama Zainab, “Tunda kinƙin Zee shikenan, gashi saiki hau napep”.
“Kima barshi Ayya naira sittin ta bani kuɗin zuwa da komawa, kin gani” zainab ta ƙare maganar da nunama Rumana sauran talatin ɗin tana ƙoƙarin fita.
Ba yadda Rumana ta iya dole a gaban idonta zainab ta wuce.
Kanta a ƙasa tanata faman gyara gyalen danya rufe mata ƙirji ta maida hankalinta ga Ahmad da har yanzu bai daina latsa wayarba.
“Yaya a saka ruwan wankane ko zaka fara cin abincin?”.
Ba tare da ya bar abinda yakeba yace, “Sakamin ruwan, dan zafi nakeji”.
Da “To” ta amsa, ta sanshi dason wanka da ruwan zafi dan haka ta ɗakko na filas data saba ajiyewa ta juye a botiki ta fita danta sirka masa.
Da sauri Maman Ama da Kausar da suka haɗa kai suna gulma a ƙofar kicin suka hau washe baki kamar gaske.
“A, Amarya barka fa ƴan tafiya an sauka lafiya”.
Umm-Ruman ta amsa da “Yawa, ngd”.
Tasan dai gulmarta sukeyi, tunda kullumne babu fashi, har maƙwafta surutu suke zuwayi akan wai Yah Ahmad ya watsar da ita tsahon wata shida yaƙi dawowa, ƙilama ya gudune, idan iyayenta sukaji zasuzo su kwasheta itada kayan tunda mai gidan haya dai ba lamuni zaiyiba idan shekara ta ƙare.
Yanzukam gulmarta suke akan wai ashe tasan mijinta zai dawo shiyyasa taketa ɓare-ɓaren gyara jikin tarbarsa, amma da suka tambayeta sai tace kwalliyar bikice.
Kausar harda cewa, “Yo kwalliyar iyakar fatar ido dai zata tsaya tunda ba wata uwa zai iya mataba”.
Sosai maman Ama taita dariya da faɗin, “Wa yaga lagwani” shinema Rumana ta fito ta ritsasu.
Sai da taɗan sake ɗauraye masa bayin sannan ta ajiye ruwan ta fito.
A ƙofar ɗaki ta iskesa zai fito, hannunsa riƙe da abin wanka da brush da ya sakama makilin, ta matsa ya wuce bayan ya ajiye takalman daya fiddo na silifas.
Aiko harya shige banɗaki su maman Ama na binsa da kallon ƙurilla, so suke suga abin kushewa a samu nayi, sai basu ganiba, dan saima wata ƙiba data ƙara masa cikar zati da kwarjini ya ƙaro.
Sai suka koma faɗin, ba dole ya narko ƙibaba yanacan yanacin daɗinnsa ya bar Rumana anan cikin wahala daga fara da mai sai wainar filawa.
Karaf sai zance a kunnen Umm-Ruman data fito ɗauraye filet ɗin da zaici abinci.
Kanta kawai ta girgiza tana mamakinsu ta koma ɗaki abinta dan gulma ta rufe musu ido basuko farga da itaba.
Koda Umm-Ruman ta koma ɗaki sai ta ɗauki turaren tsinke ta sake kunnawa, duk da dai da safema ta kunna, kuma Alhmdllh ƙamshin ya kama ɗakin saboda nacin saka turaren da takeyi ga firishina ta haɗawa da yaya maryam ta kawo mata mai ɗan yawa, tanata ɓoyen abunta sai kaɗan- kaɗan take sakawa har turaren wutarma, na tsinkenne dai kullum saita kunna saboda da yawa aka kawo mata su..
Tana ƙoƙarin kunna fitila saboda duhun magriba da garin yayi Ahmad ya shigo ɗakin da sallama, Amsawa tai ba tare data juyi ta kallesa ba saboda kunya, duk da tasan akwai jallabiya a jikinsa kuwa.
Batai auneba taji hucin mutum a bayan, cikin ɗan hanzari ta juyo, Ahmad dake tsaye a bayanta ya miƙa hannu zai ɗauki robar mai dake saman madubin, gefe Rumana ta matsa, duk da hakan kuma jikinsa na taɓa nata saboda lungun wajen baida girma sosai.
Baice da ita komaiba, duk da ya lura da yanda taketa zare idanu, ya ɗau mansa ya zauna abakin gadon danya shafa, ganin taƙi wucewa ya ɗago fararen idanunsa ya ɗan kalleta.
Saurin raɓashi tai ta fice, ya bita da kallo kawai yana girgiza kansa.
Tana alwala a bakin rijiya yazo ya wuce zai fita massalaci, ta shaƙi ƙamshin turaren daya saka tana binsa da kallo, sosai taga canji daga garesa, sai taga kamar an wani canja matashi, dan yanda jikinsa kawai ya murje zai baka amsar tafiya tayi riba.
Da wanna tunanin ta shiga ɗaki itama ta kabbara salla.
Ana idar da sallar magriba sai gashi ya dawo, a bakin gado ya zauna dai-dai tabarmar data ɗora kayan abincin, waya yakeyi, dan haka ta matso ta fara zuba masa abincin a filet, harta kammala zubawa yana wayarsa, sai dai idonsa na kanta kamar ya samu talabijin, dukda tanajin yanda idonsa ke yawo a jikinta tunɗazun ita bata yarda ta kallesanba.
Kauda kwanikan tayi gefe yanda zaiji daɗin sakewa a wajen sosai, ta yunƙura da niyyar ta miƙe kawai babu zato taji ya ruƙo mata hannu, kafin ta gama tantance gaskiyar lamarin ta tsinci kanta ɗare-ɗare bisa cinyarsa.
Kasa magana tayi dan matuƙar al'ajabinsa, ga jikinta sai wani yamm yakeyi, Ahmad ya ajiye wayar gefe tare da kallonta sosai, yanda yake kallon fuskarta babu wani alamun jin ba daidaiba ne ya sakata kasa jurewa ita, gashi fuskarsa sam babu walwala, kamar dai yanda ta saba ganintane acan baya.
Hannu ya saka ya ɗago da haɓarta yana ƙoƙarin zare hijjab ɗin, bata hanashi ba, dan batagama fuskar yin hakan daga garesaba, sai sake matse hannayenta take waje ɗaya illahirin jinin jikinta na gudu cikin kowacce jijiya da sauri.
Ya ajiye hijjab ɗin saman gadon ba tare daya tankaba, goshinsa ya ɗora saman nata, mutuniyarku saita sake ruɗewa, cikin in ina tace, “Ya..ya a...b in ....cin za..i zai huce fa”.
Ahankali ya furta “idanma ya huce bakece kika ja ba?”.
Babu shiri ta ɗago idanunta sai suka afka cikin nasa, dan har yanzu goshinsa nakan nata, hancinsu gab da juna suna musayar numfashi, hakama bakinsu babu wata tazara duk da ita Rumana taɗan duƙar da kantane ba kamar yanda nasa yake daret ba.
Ƙasa ta sake maida idanun dan bazata jura kallon cikin nasaba, cikin muryar da ita kanta batasan tana da itaba tace, “Yaya ni kuma?”.
Ahmad da muryar Rumana ta saukar masa da kasala yace, “Uhum mana, ke haka aka koya miki tarbar miji ne? Wata shidda bama tare amma sam banga wani murnar ganina ko kewata a tare da keba”.
Karon farko da kanta ya kasa ɗaukar kalamansa, domin batai tsammanin wannan furucin daga garesa ba. Saita kasa bashi amsa, wasa dai taketayi da hannayenta dake bisa cinyarta, itako tana saman tasa zaune ko nauyinta bayaji.
Hannunsa dake zagaye da ƙugunta ya janye ya kamo hannayenta da taketa cuɗawa waje ɗaya.
Sosai jan lallen da akai mata wanda ya gaurayu da zanen baƙi yayma choco fatarta dake kama da tasa ƙyau, ya janye kansa daga goshinta yana sauke sassanyan numfashi tare da murza yatsun hannun nata duka cikin hannayensa.
“Tunda bakiyi murna da dawowar tawa ba, ɗagani na koma inda na fito”.
Da sauri ta girgiza kanta idonta na cikowa da ƙwalla “ALLAH yaya ba haka baneba fa, nayi murnar dawowarka mana”.
Tsura mata ido yay, yanda idanunta suka kawo ruwa suna fidda wani ƙyalli saboda hasken fitilar sun ƙayatar dashi, ɗan yatsa ya ɗora kaɗan ya dangwalosu yayinda suka gangaro kaɗan saman furkarta, “Har yanzu kina nan a shashasharki dai?”.
Baki Rumana ta kumbura kaɗan wai ita dole taji haushi ya cemata shashasha.
“Haushi kikaji?”
Yay maganar cikin kunnenta yana sunsunar dokin wuyanta dake kamshin khumrar data shafa.
Da sauri ta sinne kai ƙasa, jikinta na ɗaukar ƙyarma saboda sabon al'amarin da yakeyi mata.
Baki yaɗan taɓe yana saka hannu ya ɗago haɓarta suka kalli juna, “Oh jan ajine komi?”.
Kasa jure kallon tayi tana janye idanunta, “A'a kawai dai banyi zaton dawowar taka bane ba yanzu”. Tai maganar cikin sarƙewar halshe.
Karon farko yayi murmushi har haƙoransa na bayyana, ya yunƙura tare da miƙar da ita shima ya miƙe, harkan tabarmar suka isa hannunsa riƙe da nata, ita dai ji take tamkar ta tsilla da gudu, sai da suka zauna sannan ya saki hannun nata, yakai hannu ya jawo filet ɗin abincin gabansa ya faraci ba tare da ya sake cewa komaiba.
Rumana dai na zaune duk a takure, addu'a take ALLAH ya kawo mai belinta yanzun nan, sai dai addu'ar tata bataci ba, dan kuwa har ya kammala cin abinci babu wanda ya shigo, sai motsin matan gidan da suke jiyowa daga tsakar gida.
Shikam Ahmad yanacin abincine idonsa akanta, musamman ma ƙushinta data gama tsole masa idanu tun shigowarsa gidan, amma da yake jarumin dakewane bazaka taɓa fahimtar hakan akan fuskarsa ba.
Ya kammala cin abincinsa tsaf sannan yasha ruwa yana yin hamdala, dai-dai nan aka fara kiraye-kirayen sallar isha'i.
Wayarsa ya ɗauka yay kiran wani da taji yana ambata da Nura, kusan mintuna biyu suna wayar sannan ya kashe, miƙewa yay tsaye yana zira wayar cikin aljihun jallabiyarsa, “Bara naje salla, daga can zanje gidan dan bamu gaisa dasu baba ba”.
Kan Rumana a ƙasa tace, “Saika dawo a gaishesu”.
“Uhum” ya faɗa yana ficewa daga ɗakin.
Sai da Rumana ta jiyo fitarsa daga gidan gaba ɗaya sannan ta sauke numfashi tana murmushi, ta kalli hanunta sosai da yasha murza a nasa ta lumshe ido, wai yau itace bisa cinyar Yah Ahmad zaune ɗane-ɗane, yana mata magana cikin taushin murya da sanyi.
Duk da tasan ba sonta yakeba hakan ba ƙaramin daɗi yay mataba, salla ta miƙe ta gabatar sannan ta zauna ta cinye sauran abincin da ya rage a filet ɗin tana mai jin wani tsagwaron nishaɗi...
★★★★★★
Koda aka idar da sallar isha'i Ahmad gidansu ya nufa, inda ya samu damar gaisawa da kakanninsa da iyayensa maza, waɗanda yayi mamakin baiji sun rufeshi da faɗan rashin dawowarsaba, dukda yayi tsammanin hakan kuwa, ko baba baice dashi komaiba akan hakan.
Yanzun kam har ɗaki ya shiga ya samu gwaggo ya sake gaisheta, duk da bata sake masaba sai da ta jero masa tambayar ya hanya da sauransu.
Yaji daɗin kulawarta, dan haka ya amsa yana faɗaɗa fuskarsa da fara'a.
Ba tare data kallesa ba tace, “Kai yanzu nan kana ganin abinda kayi mai ƙyaune? Ka tafi kabar ƴar mutane har tsahon wata shidda? Kana ganin inda badan gida bane iyayenta zasuyi shiru su zuba mana idanu?”.
“Nasan ni mai laifine Gwaggo, amma dan ALLAH ku gafarceni, wlhy inda ALLAH yay zaman nawa mai nisane, sannan harna kwashe kusan watanni uku bana fuskantar komai a sana'ar tawa, saboda bada jari najeba, lokacin ko kuɗin motar dawowa aikine a gareni, amma insha ALLAHU bazan sake kwatanta hakanba, kuma ALLAH ya huci zukatanku, itama zan bata haƙuri na kuma nema gafararta”.
Shiru gwaggo tayi kamar bazata amsashi, sai kuma zuwa can tace, “Shikenan, ALLAH ya yafe mana baki ɗaya, abu na gaba shine karnaji wani abu daban agareka cikin hidimar bikinnan, babu ruwanka da sabgar yarinyarnan komi zasuyi, ka kama kanka ka kama girmanka, suma su Mudanseer ka sake gargaɗinsu akan karnaji karna gani”.
“Insha ALLAHU gwaggo an wuce wannan wajen yanzu, babu wani abu saɓanin mai daɗi da zakiji, ni yanzu babu wani abu daya shafeta da yake a gabana sam”.
“Hakan ya fi”.
Gwaggo ta faɗa a taƙaice, daga nan shiru ɗakin ya ɗauka babu wanda ya sake cewa uffan a cikinsu, shi dai Ahmad badan hirar ta ishesa bane, haka ita gwaggon, tadaiyi shirune saboda dama tun fil azal babu irin wannan sabon na doguwar hira a tsakaninsu.
Kusan mintuna biyar saima ta miƙe ta fice tabar masa ɗakin gaba ɗaya.
Sassanyan murmushi yayi yanajin ƙaunar mahaifiyar tasu cikin ransa, maimakon tace ya tashi yaje, shi yaga ta koresa shine ita ta bar masa ɗakin dan kar ace ta saka ɗan fari a ɗaka suna hira.
Kai shikam bazai yarda Rumana taima ƴarsa ko ɗansa na fari wannan abunba gaskiya, dan kuwa akwai cutuwa, yanzu shi badan gwaggon ta samu Ayyah mai ƙyaƙyƙyawar zuciya ba da yaya kenan?.
Miƙewa yay yaje ya haye gadonta ya kwanta kamar yanda yakeyi a ɗakin Ayyah.
Gwaggo dake tsakar gida tana ƴan kaye-kaye saboda ganin hadari sai zuba ido take taga ya fito amma shiru, gashi Ayyah na sashen baba saboda yau itace da girki, yaran kuwa duk sun fice wajen kamu sai Zainab kaɗai a gidan itama tana sashen su Samina.
Ɗakin ta dawo dan taga mi yakeyi a ciji da bazai fito ya tafi gidaba gashi har goma tayi, dan taskar labaraima akeyi a redio.
Sosai mamakin ganinsa saman gadonta ya kamata, dan sam koda yana yaro ba ɗabi'arsa bace hawar mata gado, sai da ɗakin Ayyah.
“Kai lafiyarka kuwa? Wace irin ɗabi'ace wannan?”.
Dariyace taso kufcema Ahmad dako motsi baiyiba, amma sai ya daure ya haɗiye da ƙyar yana faɗin “Oh gwaggo bakiso na hau sai ƴaƴanki kawai su Mudan? To nima ai suna hawa gadon ɗakinmu idan sun shiga shiyyasa na rama, kuma wlhy ki tambayi Ayyah kiji”.
Ayyah dake tsaye bakin ƙofa ta kwashe da dariyar shaƙiyancin Ahmad, “ALLAH ya shiryeka ɗan albarka, ammafa kamin dai-dai, maza ka rama mana kuwa muma hawar mana gado da ƴaƴanta keyi ehe”.
“Yauwa Ayyah ta, shiyyasa kike burgeni akan faɗar gaskiya”.
Harara Gwaggo ta bankama Ahmad tana cije baki, “Tashi ka fitarmin a ɗaki fitsararren banza kawai”.
Kasa daurewa Ahmad yay ya sakko yana dariyar yanda Gwaggo ta haɗe gabas da yamma kamar zata makesa, yayinda Ayyah ke tayashi daga waje tana faɗin, “Kaga fito kama tafi gida karta makemin kai daga dawowa”.
“Aifa ganinan Ayyahna”.
Gwaggo dai bata tanka musu ba, duk da tana jiyosu suna mata dariya a tsakar gida har su Fa'iza suka shigo.
Haɗe fuska Ahmad yay yana kallonsu, dukansu sunsha jinin jikinsu duk sai sukai tsaye suka kasa ƙarasowa.
“Daga ina kuke a wannan lokacin!?”.
Tuni jikin Sadiya ya fara ɓari, hakama Salima uwar tsoro, sai Fa'izace cikin ƙarfin hali tace, “Yah Ahmad wajen kamu”.
“Kamu?, har zuwa wannan lokacin da yake baku da hankali?”.
Guri ɗaya duk suka cure saboda tsawar da yay musu.
Ayyah tace, ”Wlhy nima tun ɗazun abin ya dameni, babanku ma sai faɗa yakeyi, namazo ne nai maka maganar kozaka tura Abu yaje ya kirasune”.
Sosai ran Ahmad ya ɓaci, yace, “Okey sabon iskancin da yazo muku a kai kenan saboda bana gidan?”.
“Wlhy A'a yaya, dan ALLAH kayi haƙuri bazamu sakeba”.
Mudan dake shigowa ta bayansu ya tallare ƙeyar Sadiya dake farko shima yana masifa, “Yah Ahmad karka wahal da kanka ai tun acan saida na basu maruka bibbiyu marasa mutuncin”.
“Oh kace kainema kaje ka taho dasu?” cewar Ayyah.
“Wlhy kuwa Ayyah, tun kusan takwas nake zuba idon ganin sun dawo amma shiru, har tara shiyyasa nai azamar ƙarasa ɗinkin danake nabisu har can, sun miƙe ƙafafu sam basuma da alamar tahowa”.
Ƙwafa Ahmad da takaici ya isa yayi, ya nunasu su duka yana faɗin, “Wlhy daga yau wanima cikinku ya sake zuwa fatin saina kusa halakashi a gidannan, ƴan iska kuwuce kuba mutane waje kawuna kamar sheƙar angulu”.
Da gudu suka shige ɗakin Gwaggo dake saurarensu daga ciki, babama duk yana jiyosu, ya kumaji daɗin yanda Ahmad da Mudanseer sukai musu, baida haufi akan tarbiyyar ƴaƴansa, koda baya numfashi su Ahmad garkuwar ƙannen sune.
Ganin iskar hadari ta fara tasowa Ayyah tace, “Ɗan albarka maza gida kafin wannan ruwan ya sakko kaji, ka gaida ɗiyar tamu”.
Sallama yay musu ya tafi, bayan ya leƙa yayma su Iya ma sallama, wadda ta bashi wani abu a robar swan tana faɗin, “Ungo wannan ka kaima Rumana, tashashi yanzu kafin ta kwanta”.
“To Uwargida ran gida za'a bata ta gode, amma minene haka kamar zuma?”.
“To shugaban matambaya ba zuma bace, maganin shawarace da naji su Salima nata ƙorafin bata gajiya da kwanciya, shiyyasa na haɗa matashi kartazo wajen taron nan taita langaɓe-langaɓe, tasha kamar kashi ɗaya bisa huɗu”.
Dariya Ahmad yayi yana cewa, “Oh kajimin iya, kina nufin matata raguwace dai kawai a fakaice?, karki damu nan gaba kaɗan ƙofar gidannan saita mata kasaɗan”.
“Dako nayi farin cikin hakan ɗan ƙwal uba kawai, kaima ai gakanan ka ɗakko sanwar fara kiban kamar iliyasu”.
Fita Ahmad yay yana dariya Malam dake kwance yana tayashi.
A waje yay sallama da abokansa dake shirin shigewa gidajensu, ya tari Napep zuwa gida saboda harma an fara yayyafi.
A lokacinne kuma motocin su Samina ke isowa, da alama dai lokacin aka tashi daga kamun nasu da yasha banban dana saura.
Dan kowa dai yasan da yamma ake kamu tare da dangin amarya, dangin mijima ƙalilan suke zuwa, to ita nata dangin mijin sunfi yawa, danginta ɗaiɗaikune iya ma ƴan uwan mama gaje ne, sai tarin ƙawayenta.............✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*_GDW_*
*(21)*
...........Napep ɗin daya ɗakko Ahmad na tsayawa a ƙofar gidan ruwan na ƙara ƙarfi, ɗari biyu ya miƙa masa, baiko tsaya amsar canji ba yace yatafi kawai.
Kusan tare da mijin Kausar da shima ya iso yanzu suka shiga, sama-sama suka gaisa yanama Ahmad barka da dawowa kowa ya shige ɗaki saboda saukar ruwan mai ƙarfi.
Rumana da tun ɗazun tai shirin barcinta, harta gaji da jiransa ta ɗauki wani novel tana karantawa, zaune take saman gado ta jingina da fuskar gadon fitilar da batir yay sanyi na a kusa da ita gab yanda zataga rubutun.
Ajiye buk ɗin tai tana masa sannu.
Kallonta yay yana amsawa ya janye idanunsa, ƙoƙarin cire doguwar rigar jikinsa yayi yana faɗin, “Kina ganin ruwa amma bazaki rufe ƙofaba?”.
Kanta a ƙasa saboda ganin zai cire riga tace, “kayi haƙuri Yaya, dan karna rufene kuma barci ya ɗaukeni kazo kaita bugawa banjiba”.
Baice komaiba sai ƙoƙarin rufe ƙofar da yakeyi, hasken fitilar ɗakin bai wani wadata ba, dan haka ya ɗauka wayarsa ya kunna fitilarta, sosai Umm-Ruman ta kuma takura, amma ta lura shi ko a jikinsa.
Ganin yanda ta takura kantane ya sakashi buɗe jakkar kayansa ya ɗauki farar t-shart ya saka, duk da yasan idan zai kwanta saiya cire saboda hakan ya zamar masa sabo.
Sai a lokacin Rumana taɗan samu sukuni, dukda ba iya kallonsa taiba daret tadai samu zarrar miƙewa ta kawo masa ruwan sha.
Amsa yay yasha, dan ɗan gudun shigowa gida da yay maƙogwaronsa harya bushe, kallo ƙasa-ƙasa ya bita dashi, ta canja kayanta ta saka doguwar riga mara nauyi ta barci har ƙasa, sai ƙamshi ne mai daɗi ke fita daga jikinta.
Dan duk yanda Yaya Raheenatu da Sakina suka koya mata bata mantaba, sun tabbatar mata koda wasa karta bar jikinta babu ƙamshi musamman da daddare idan Ahmad na gari, hakan ne data tuna ya sakata bayan fitarsa taje tai wanka duk da tana kallon su Kausar na gulmarta bata kulasuba, tazo ta shafa mai sama-sama saboda zafin hadari daya ɗaure garin, tabi lungu da saƙo na jikinta da khumra sannan ta zira doguwar riga tai zaman jiransa tana karatu......
“Yaya zaka ƙara cin abincine?”.
Tai maganar tana durƙushe a gefensa.
Bai bata amsaba, sai hannunsa daya miƙa ya kamo nata ya miƙar da ita, batai masa musuba, saboda tun fil azal babu wannan wasar tsakaninsu, kusa da shi ya zaunar da ita har jikinsu na gogar juna, hakan ya saka Rumana ɗan takure jikinta.
Abinda Iya ta bashi ya miƙa mata, “Gashi inji iya kisha”.
Sai da ta kallesa, ganin shima ita yake kallo tai ƙasa da nata idon tana amsar robar dake cikin baƙar leda, ta cire ledar tana jujuya goran a hannu, Ahmad ya katse tunaninta da faɗin tace, “Kisha ɗaya bisa huɗu”. Daga haka ya miƙe tsaye.
Rumana nason tambayar minene amma tanajin tsoro, sai kawai ta buɗe goran ta miƙe ta ɗakko kofi ta zuba, yanda abun ke zuba a kofin da kauri sai taga kamar zuma, sai dai wannan ƙamshin kayan yaji yake tunma kanta kai bakinta, ganin yayi dai-dai da yanda iyan tacene yasata rufewa takai kofin bakinta, sosai zaƙi taji, dan haka mamaki ya isheta, amma da yake dama can ita sha zumamuce wajen ƙwaɗayin abu mai zaƙi saita shanye kayanta harda suɗe kofi😂.
Shi dai Ahmad tuni ya haye gadon yana kwance yana danna wayarsa, sai dai rabin hankalinsa naga kallon Rumana.
Tashi tai ta ɗauraye hannunta da kofin cikin roba sannan tasha ruwa, ta gyara labulen da iska ke ɗagawa ta dawo cikin ɗakin sosai tana ɗaukar tabarma danta shinfiɗa a ƙasa, tunda taga Ahmad ya hau gadon, itama kuma a ranta tanaji ya cancanta ta barmasa ya kwanta kodan daɗewar da yay bai hauba, dukda itama ba hawan takeba, dan tunda ya tafi a ƙasa suke kwana dasu Salima, sun fara kwana a gadon tare, amma randa yaya Maryam tazo taita musu faɗa akan hakan da sukai ai tsageranci ne, gadon da yayansu ke kwana zasu hau su jeru suna malelekuwa akai? Karta sake ganin haka, su dinga kwanciya a ƙasa.
Tun daga wannan ranar basu sake hawaba, sai dai bata gajiya da gyaransa kowacce safiya........
“Ruman! wai tunanin mikike ana magana ma baƙyaji?”.
Firgigit Umm-Rumana ta dawo hayyacinta jin maganar Yaya Ahmad dab da ita babu zato.
Ta kallesa tana ɗan yin baya da sauke ajiyar zuciya, sai kuma yanda ya kira sunan natane ya tsaya mata a rai, gashi ya tsatstsareta da waɗannan idanun nasa masu kama da ƙwai ga shegen haske kamar ba namijiba.
Duk saita nema daburcewa ma, tasan dukansu gidansu suna kamane da juna, amma dole wani ya ɗara wani ƙyau, to lallai ta fannin ido kowa yasan Ahmad ya zarta kowa, akwai idanu masha ALLAH, gasu da haske da cikar gashi, amma idan ransa ya ɓaci tuni suke komawa jajur tamkar bashiba, shiyyasa mafi yawan lokuta ta idanu ake gane ɓacin ransa ko damuwarsa........
Jin hannunsa tai kan nata, ta sake kallonsa a ɗan tsorace, tabarmar hannun nata ya amsa ya ajiye kawai, ya nuna mata gadon alamar ta kwanta yana faɗin, “Bansan tunanin mikikeba haka nikam?”.
Murya a sanyaye Rumana tace, “Babu komai fa”.
Bai tanka mataba, taje ta hau gadon daga can gefe inda ta saba kwanciya, ita duk zatonta shine zai kwanta a ƙasan.
Dan haka lokacin da zai cire riga ta rufe idanunta tana gyara kwanciya.
Ahmad ya kammala kimtsawa lokacin ruwan na sake ƙarfi sosai ya haye gadon abinsa, zai kai haƙarkarinsa ne yaji abu a wajen, buk ɗin da Rumana ke karantawane, dan haka ya janyosa yana kwanciya da ƙyau, samun kansa yay da haska wayarsa yana duba buk ɗin.
Abinda ya karanta a shafin data tsaya ɗinne ya sakashi juyawa ya ɗan kalli bayanta data juya masa, wanda tunda ya hawo gadon gabanta ke luguden daka, dan sam batai zaton yau ɗin a guri ɗaya zasu kwanta ba.
Ɗauke kansa kawai yay yana girgiza kai, yaɗan ƙara karantawa, yanzu kam sosai ya zubama bayanta idanu, yace, “Juyonan”..
Gaban Rumana ya sake ƙarfin gudu, tasan dai da ita yake, kuma bazai maimaita abinda ya faɗaba tunda yasan tajisa sarai, kamar mai tsohon ciki haka taita motsi da ƙyar harta juyo tana fuskantarsa, sai dai ta kasa kallonsa sam.
Littafin ya miƙa mata tare da wayarsa, “Amshi karanto min wajen nan har zuwa ƙarshen shafin”.
Babu shiri Rumana ta waro nata manyan idanun itama a kansa tana ɗora hannunta saman baki kamar wadda ta faɗi abu ba daidaiba.
“Malama karki cinyeni da waɗannan idanun, oya amsa”.
Amsar tai jiki na ɓari, sai dai tasan abinda yake buƙatar yana da nauyi a gareta, dan sun taɓa karanta buk ɗin dasu Fa'iza, maimaitawa kawai takeyi, inda kuma yakeson ta karanta sam ɗanba sauƙine, dan kuwa daren farkon ma'auratan littafinne, duk da marubuciyar bawai ta buɗe komai bane, salon soyayyar wajenne dole ta tsuma ma'abocin karatu, tareda jin kunya ga irinta da batasan komai dangane da hakanba......
“Kina ɓatamin lokaci fa” yay maganar gab da ita ba tareda tasan ya matso ba ma.
Kallonsa taɗanyi, tai azamar janye idonta saboda kusancin da suka samu dab sosai.
Cikin ɗan rawar murya da marairaiceta tace, “Yaya kayi haƙuri dan ALLAH....”
Ahmad ya katseta da faɗi, “Laifin mi kikaimin, karatu kawai nace kiyi”.
Haɗiye busashshen yawun daya kasa wuce mata tun ɗazun tai da ƙyar, cikin haɗo kalmomin bakinta da ƙyar tace, “Ai a..i ka ra tunne ban iya a fili ba”.
“Uhyimm, tom saiki fara koya da ga yau, kina ɓatamin lokaci”.
Idanun Rumana cike da ƙwalla ta fara ɗan karanto masa, yayin da taje layi kusan na biyar a shafi ai ina saita kasa, dan kuwa dai da kunya wlhy.
Ahmad da idanunsa ke a lumshe yana saurarenta ya buɗesu jin tayi shiru,
“Yaya dai? Cigaba mana”.
“Yaya dan ALLAH kayi haƙuri, na tuba bazan sakeba”.
Kamar zaiyi murmushi amma sai ya dake, idonsa a kanta yace, “To wayace kinyi laifi? Nidai karatu kawai nake buƙatar ji, inba hakaba kuma ni na karanta miki nawa labarin”.
Rumana da sam bata fahimci inda ya dosa ba ta miƙa masa buk ɗin jiki na tsuma tace, “Eh yaya dan ALLAH to gashi”.
Baiyi musuba ya amsa buk ɗin, sai dai juyawa yay ya ajiye a bayansa ya juyo gareta yana amsar wayarsa ya kashe fitilar, hakan ya saka Rumana saurin shirin juyawa amma sai ya dakatar da ita da faɗin, “Waya gaya miki ni a littafi zan karanta? piratical ne aini nawa”. Yay maganar yana jawota jikinsa gaba ɗayanta.
“Tashin hankali, wanda ba'a sa maka rana” inji Rumana da dukkan illahirin jikinta ke amsa kuwwar karkarwar tsoro, firgici, harma da gigita mai gauraye da tsuriya🤣.
Ya matseta sosai cikin jikinsa yana lumshe idanunsa, yayinda hancinsa ya sauka saman dokin wuyanta yana magana cikin wata irin murya da Umm-Rumana bata taɓa sanin yanada itaba.
“Ashe kin girma ban saniba Ruman?”.
“Wlhy Yaya ban girma ba”.
Cewar Rumana murya na rawa alamar tahowar kuka.
Sake matseta yay da ƙyau, ya maido fusakarsa kan tata yana haɗa hancinsu waje guda, a hankali ya sake furta, “Ga zahiri na gani kuwa, tunda kin iya karatun littatafai irin waɗannan?”.
“Yaya na rantse ba nawa bane, su Salima ne sukazo dashi, shine na ɗauka ina dubawa ganin baka dawoba”.
“Kinga da ki fara ɓata lokacin karantawar gara ni na karantar dake ai ko?”.
Nanma ya sake faɗa muryarsa na sake shigewa cikin maƙoshi, ga ruwa kuma anata zabgawa tamkar da bakin ƙwarya.
Komai ya ɓacema Rumana, tambayar kanta take anya kuwa Yah Ahmad ne wannan kokuwa wani daban?.........
Saukar laɓɓansa saman nata babu zato ko tsammani ya ida rikitar da guntun tunanin nata, daga nan kuma komai ya canja salo, magiya, kuka, roƙo, ban haƙuri, babu wanda Rumana batayiba, amma sam Ahmad baimasan tanaiba, dan kuwa tuni yama rasa jinsa da ganinsa shi, abinda duk yazo masa a rai kawai yake gudanarwa da iya basira da ƙwarewar da ALLAH yay masa wadda shi kansa baimasan yanada itaba sai yau ya keyi🤨😆🚶🏻♀️.
Lallai Umm-Rumana taga daren alkairi na haƙiƙa, dan Ahmad baije da wasaba, sosai ya nuna gwarzantakarsa a zahiri ba tareda tunawa da wadda yake a filin dagarba, gashi ya hanata dukkan damar da zatai kukan da wani zaiji, dukda ma ruwan da ake zubawar kuwa bazai bar wani jin nata ba.
Haɗiyar zuciya kawai take a jikinsa dan zuwa yanzu kukanma ya gagara zuwa da hawaye, shi kansa yayi laushin da ko hannu ya kasa ɗagawa domin lallashinta, ya dai turata jikinsane tamkar zai maidata ciki, idonsa na zubarda hawayen da shi kansa baisan dalilinsu ba, kawai saukarsu yakeji akan kumatunsa.
A haka wahalallen barci ya sace Umm-Ruman dake ta sauke tagwayen ajiyar zuciya har lokacin, yaja kusan awa ɗaya bai iya taɓukama kansa abun ƙwarai ba balle ita da yakejin illahirin jikinta ya ɗauki zafin zazzaɓi, haka ya daure ya janyeta a jikinsa tare da bargon ya sakko daga gadon yana layi na rashin ƙwarin jiki saboda faruwar sabon al'amari da gaɓɓansa basu taɓa fuskantaba a rayuwarsa.
Ya ɗauki filas ɗin shayinsu kozai samu ruwan zafi, sai dai wayam, dan ɗazun dashi Rumana tai masa amfani, tsaye yay yana nazarin mafita, dan kuwa dai ya zame masa tilas taimakama Rumana tun a daran kodan yanayin gidan da suke ciki, basai da asuba yace zaita faɗi tashiba ana ƙare musu kallon ƙurilla.
Dole ya ɗauki shawarar zuciyarsa ta ƙarshe ya kunna risho ya saka ruwa a tukunya ya ɗora.
Babbar roban Rumanan daba fitama take da itaba sai zatai wanki ya ɗauka ya ajiye a tsakar ɗakin, sai da ruwan yay zafine sannan ya juyesa ya sake ɗora wani ya nufi gadon.
Har yanzu ajiyar zuciya kawai Rumana ke saukewa cikin wahalallen barcin daya ɗauketa, ya janye bargon da take ciki yana ƙoƙarin ɗagota, amma koda ta buɗe ido saita fashe masa da kuka saboda azabar da illahirin jikinta ke mata.
Yatsansa ya ɗora saman bakinta yana faɗin, “Shiiii” dole tai shirun kuwa tana haɗiye kukan da ƙyar.
Sosai yay mata gashin datasha kuka kuma taji daɗinsa, sannan ya nuna mata yanda zatai wankan tsarki dukda bashida haufi akan ta iya tunda suna zuwa islamiyya.
Kafin ta kammala ya koma gaban gadon ya kunna fitilar wayarsa ya haska zanin gadon, bawani ɓaci yay sosaiba, amma dukda haka yasan za'a iya ganewa, dan haka ya yayesa gaba ɗaya, dirowarsu ya buɗe ya ciro ɗayan da dama guda biyune kacal zanin gadon, ɗaya mai tsada ɗaya mai ƙaramin kuɗi, shiya shinfiɗa, dai-dai Rumana daketa hawaye ta kammala tsarkale jikinta, da kansa yazo ya taimaka mata ta fito a roba, sai faman kare ƙirjinta take da hannu wai karya gani😜.
Ya maida mata rigarta yana zaunar da ita saman gadon, sai mutsu-mutsu take saboda zafin da takeji zaman neman gagararta yakeyi, lura da hakan da Ahmad yayine ya sakashi faɗin, “Sorry”.
Banza tai masa, shiko ya dubo paracetamol a kayansa yazo ya zauna gefenta riƙe da kofin ruwan daya ɗebo ya bata, dayake bata da matsala da shan maganin saita amsa tasha, ya taimaka mata ta kwanta ya lulluɓeta.
Shima tsaftace jikinsa yayi a ɗakin, ya buɗe ɗakin ya watsa ruwan dan har lokacin ruwa ake makawa sosai, goge duk inda suka jiƙa yay tsaf, ya maida komai inda ya ɗakko sannan yasaka abin salla yay nafila raka'a biyu yana miƙama UBANGIJI sinƙi-sinƙin godiya, ya daɗe yana zubama ALLAH kirari da doguwar addu'a ga Rumana harma da iyayensu da suka kasance sanadin komai.
Kafin shima yasha paracetamol ɗin daƙyar dan wani zazzaɓine ke neman rufesa shima ɗin, cikin barci Umm-Rumana tajisa cikin jikinta dake zafi zau da zazzaɓi, da yake shima nasan ya ɗau zafi sai baiji natanba sosai, haka ya kuma maƙalƙaleta yana gyara musu bargo............✍🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*_GDW_*
*(22)*
...............Da asuba Ahmad ne ya fara farkawa, ya buɗe idanunsa da ƙyar saboda nauyin da sukai masa na rashin samun isashshen barci, Umm-Ruman na kanannaɗe a jikinsa, sai dai su duka zazzaɓin ya sauka.
Wayarsa ya lalubo ƙasan filo ya kunna fitilar, gaba ɗaya ɗakin ya gauraye da haske, ya shafa kan Rumana dake lafe saman ƙirjinsa a hankali, komai na daren jiyane ya shiga dawo masa, ya sauke sassanyan numfashi yana faɗin, “ALLAH yay miki Albarka” akan laɓɓansa.
Cikin rashin son ya tasheta ya ƙoƙarin zameta daga jikinsa, tako sake riƙeshi dan sanyin da takeji bataso ta rabu da koma miye ta maƙalƙale.
Murmushi ya sauke a hankali tareda busa mata hucinsa cikin kunne, ɗan sautin hucinne ya sakata motsawa kaɗa.
Ganinfa da gaske ba tashin zatai ba sai ya kai bakinsa saman kunnenta ya fara magana, “Ruman kibar Yayanki ya tashi lokacin salla yayi”.
Sarai Umm-Ruman taji maganar Ahmad cikin kunnenta, dan tunda ya kunna fitila ta farka, amma kunya ta hanata koda motsin da zai gane.
Sake shige masa jiki tai tana faɗin, “Uhm-uhm”.
“Uhm-uhm ko? to ai nasan maganink......”
Kafin yakai ƙarshe tai azamar raba jikinta da nashi, ta matsa baya tana juya masa baya.
Sosai abin ya bashi dariya, dan haka yay murmushin da har take jiyo sautinsa.
Bargon ya yaye yana zura ƙafarsa ƙasa da faɗin, “Matsoraciya da ki tsaya mana”.
Ita dai batako motsaba harya buɗe ɗakin ya fita bayan ya zira doguwar riga.
Har lokacin ana ɗan yayyafi, shiyyasa Ahmad da yayo alwalan sai ya dawo ɗaki.
“Wai bazaki tashiba?” yay maganar idonsa akan Umm-Ruman da har yanzu take naɗe akan gadon, ita duk wayonta sai ya tafi salla zata tashi, amma jin ya dawo ɗakin ya bata tabbacin anan zaiyi shima.
Tashi tai da ƙyar, dan har yanzu gaɓɓanta ba daina mata ciwo sukaiba, ga ɗan zafi har yanzu tanaji, bata yarda tama kalli sashen da yakeba koda wasa, shiko yana tsaye saibin ta da kallo yake sabida ganin yanda take tafiya da ɗan ɗingishi, duk da ya lura da ɗunbin jarumtar da takeson nunawa dan ganin tafiyar ta tafi dai-dai.
Sai da ta ficene ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa da buɗewa lokaci ɗaya.
Cikin dauriya da ƙarfafa kanta take taku saboda ruwan da akasha, danma tsakar gidan nasu duk sumintine, alwala itama tayi bayan ta shiga bayi ta fito.
Lokacin data dawo ɗakin yana zaune yana jiranta, miƙewa yay idonsa a kanta, itako taƙi yarda yanzun ma ta kalli ko sashen da yake, baice da ita komaiba harta kimtsa tazo inda yake tunda taga alamar jiranta yake ya jasu sallar.
Hakan kuwa akai ya jasu suka sallaci asubahi, bayan sun idar yaja dogayen addu'oi a garesu da al'ummar musulmi baki ɗaya.
Koda suka shafa Rumana na zaune a bayansa batako motsaba, kanta dai a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.
Zamansa ya gyara ya jingina da jikin hado yana mai fuskantarta, sai dai baice komaiba kallonta kawai yake tamkar ya samu tv.
Ai sai jikin mutuniyar taku ya nemi fara tsuma, cikin salƙewar halshe ta fara gaishesa,
“Uhm u..hm Yaya ina kwana, ya gajiyar tafiya?”.
Guntun murmushi yayi yana ɗora dukkan hannayensa saman gadon cikin miƙar dasu, har sannan kuma idon nasa a kanta yake.
“Lafiya lau Amaryar Ahmad, ya ƙoƙari?”.
Shiru tai dan bata fahimci ƙoƙarin mi tayi ba.
Ya sauke hannayensa tare da kai na damar ya ɗago haɓarta, “Kalleni nan” yay maganar babu wasa.
Dolenta ta ɗago idanunta a hankali ta saka cikin nasa daya kafeta da su.
“Bakin ya mutu ne?”.
Yay maganar yana matso da fuskarsa daf da tata.
Itakam ta rasa yaya zatai da Yah Ahmad, shi baisan kunyarsa takeji bane halan? Tun daga dawowarsa jiya ya koma mata tamkar bashiba a komai.......
Iskar daya busa mata saman idanu ya sata lumshesu sosai tsigar jikinta na tashi, ya jawota gaba ɗaya jikinsa, ya cire mata hijjabin tare da faɗin, “Yaya jikin?”.
Baki taɗan kumburo masa kaɗan da faɗin, “Nidai lafiyata lau fa Yaya”
“Oh ALLAH? Shike nan kinga to bara mu maimaita”.
A zabure tace, “Yah Ahmad mi?”.
Yanda tai maganar hawaye na zubowa lokaci ɗaya saman kumatu ne ya sakashi yin dariya, yaja hancinta kaɗan tare da dungure mata kai yace, “Mai raki kawai, iya tasan har ita kika kira saboda ragwantakarki saita miki dariya”.
Cusa kanta tai a jikinsa tana murmushi, jiya kam a ƴan gidansu ai babu wanda bata lissafo ba, har Tahir dake shan nono bata mantaba, yo taji azaba, ashe abun da gaske babu sauƙi........
Ahmad ya katse mata tunani da faɗin, “Kinga tashi kije ki kwanta, wannan barcin da muka ɗau bashi idan bayinsa akaiba zai haddasa ciwon kai”.
Da ƙyar Rumana ta bar jikinsa ta miƙe, bata yarda ta kallesa ba taje ta haye gadon ta kwanta, shima da yake binta da kallo tashin yay yacire rigarsa ya hau gadon.
Jinsa a jikinta ya saka sabon tsoro bijiroma Rumana, ta lafe tamkar mai barci tana sauraren mizai biyo baya, sai bataji komaiba, hakan ya sata sauke ajiyar zuciya a hankali.
Ahmad daya jita ya murmushi kawai.
★★★★★★★
Basu farkaba har kusan goma, har lokacin kuma dai garin ana yayyafi irin yaf-yaf ɗinnan, hakan yasa garin ɗaukar shiru kowa yana cikin ɗakinsa, sai irinsu maman Ama ƴan gutsiri tsoma da ake yawan leƙa waje aga wazai fara fitowa, dan ita dukda yayyafinnan tuni mijintama yabar gidan.
Kausar ma dake fama da ciki kusan tara ta fito ɗaura musu abin kari, ananne suka haɗu da maman Ama.
“Waisu waɗannan bazasu tashi bane? Garin ALLAH ya waye amma ƙofa a garƙame?”.
Dariya Kausar dake sauraren mama Ama tayi tana gyara buhun ledar data ɗora saman kanta saboda kar yayafi ya jiƙata, tace, “Ke ko sai an nuna manafa miji ya dawo jiya ko”.
Baki maman Ama ta taɓe, “Saikace wata tsiya mijin ke iyayi matan”.
Kausar ta sake yin dariya tana juye shayi a kofi mai murfi, “Ko baiyiba ai yaɗan lalubi abinda zai iya, wlhy ni idan nice ita tuni zan tona maka asiri na kashe auren, banga amfanin namiji gareni bai iya taɓukamin komaiba, ai ko ganga batason ajiya burinta kullum a kaɗata ta bada sauti balleni da ƙuruciyata da komai”.
“Ke kika san dokar ai” ‘Cewar maman Ama tana harar ƙofar ɗakin su Rumana da basusan sunaiba ma’.
Rumana ce ta fara tashi, ta janye jikinta da yay mata nauyi daƙyar daga na Ahmad ta sakko, barcinsa yake sosai dan haka baiji saukarta ba, ƙofar ta buɗe ta fita bayan ta cika buta da ruwan zafin daya ajiye a filas ta fita da brush a hannu, tsakar gidan babu kowa, dan sun gaji da leƙe-leƙen sun zauna waje ɗaya, hartayi brush ɗinta taje bayi tai tsarki sosai ta fito babu wanda ta gani, taji daɗin yin tsarkin kuwa, dan sai taji kamar an mata gafara.
Ɗakin ta koma, ta maido risho bakin ƙofa daga ciki ta kunna domin nema musu abin kari.
Tana cikin juye ruwa filas ɗin Ahmad ya farka shima, lalubawa yay kozai jita sai yaji wayam, ya buɗe idanunsa yana tashi zaune, ganin tana aiki sai yaɗanji sanyi a ransa, bata yarda ta kallesa ba harya sakko a gadon, ya ɗauki brush da buta ya fita baice da ita komaiba.
Lokacin daya dawo harta gama kwashe ruwan ta kashe risho ɗin, daga bakin ƙofa ya miƙo butar ya ajiye ya juya ya fita.
Ganin hakanne ya saka Rumana ƙoƙarin fara gyaran ɗakin, da yake aikin ba wani mai yawa bane dandanan ta kammala, tana shara Ahmad ya dawo riƙe da leda ƙarama a hannunsa.
Matsa masa tai ya shige, ita kuma ta fita da sharar waje, koda ta dawo saita iske yana fito da kayan tea daga jakkar da yazo da ita, batace komaiba ta kawo kofuna kamshin ƙwai soyayye dukya gauraye ɗakin.
“A ledar nan akwai bired”. Yay maganar yana cigaba da maida kayan daya fiddo daga jikkar.
Cikin sanyin murya Rumana ta amsa da “to”.
Bayan ya kammala zama yazo yayi, da taimakonsa ta haɗa musu shayin, ita dai duk taƙi yarda su haɗa ido, duk da shi Ahmad yanata buƙatar hakan.
A takure tai wannan kari, har suka kammala ta tattare komai ta fita da wanke-wanke, shi kuma ya ɗiba ruwan wanka ya sirka da wanda ta zuba cikin filas ɗin ya nufi bayi.
Tana bakin rijiya ya wuce, hakan yasa ta bisa da kallo, dan batasan zaiyi wankanba aida ta haɗa ruwan takai masa.
A lokacinne Kausar ta fito daga ɗakinta, sai da ta harari Rumana data juya mata baya kafin ta ƙaraso tana ƴar dariya, “Oh ni su amarya anyi bulum a ɗaki saboda yau oga ya dawo?”.
Murmushi kawai Rumana tayi, ba tare data bata amsaba tace, “Ina kwana”.
Nanma saida Kausar ta harareta ta wutsiyar ido sannan ta amsa, zuwa yanzu garin yayi ɗaf babu yayyafin, sai wani ɗan hasken rana daya hasko mai ɗumi.
Kausar tasan dama Rumana ba biye mata zatai suyi surutuba, amma sai ƙoƙarin janta take da hira, Maman Ama da taji motsinsu sai gata wuff ta fito daga ɗaki tamkar an jefota.
Itama Rumana gaidata tayi da tambayarta lafiyar yara, maman Ama ta amasa suna gulmar Rumana da ido itada Kausar, ahaka Ahmad yazo zai shigesu suka shiga gaishesa.
Amsawa yay kawai, ba tare da ko kallonsu yayiba ya shige ɗaki, sunata surutunsu ita dai Umm-Rumana na wanke-wankenta, tana kammalawa kuma ta miƙe tama bar musu wajen, da tabbacin Ahmad ya gama shiryawa ta shiga ɗakin, sai kuma ta iske saɓanin hakan, yadai gama shafa mai yasa singlet da boxer yana kwance a gadon ƙafafunsa a ƙasa.
Shigowarta ce ta sakashi buɗe idanunsa ya zuba mata, yayinda ita kuma dukta dabarbarce tana neman juyawa ta koma saboda yanda ta gansa.
Katseta yay da faɗin, “Zonan”.
Tamkar zata fasa ihu haka taji, ta matso shikuma yana tashi zaune sosai, saurin riƙo hannunta yay ganin tana neman durƙusawa, “K wai nazama surukin kine?”.
Yay maiganar yana ɗorata saman cinyarsa.
Kanta ta girgiza masa.
Yace, “Magana da baki nakeso”.
Daƙyar tace, “A'a”.
“Eh mana, ba gashi bakison kallona ba, idan ina ɗakinnan duk sai kibi ki takura kanki”.
“To kayi haƙuri, bazan sakeba”.
“Inma banyi haƙurinba ya zanyi Ruman, kinga tashi na gwadaki naje shago naɗan sama miki kayan da zakije wajen bikin gobe, yau dai ki kwanta ki huta”.
Idanunta suka cika da ƙwalla, danta saka ran zai barta taje tun yau, da ƴar shagwaɓa tace, “Amma Yaya miyasa bazan fara zuwa tun yauba?”.
Kallonta kawai ya tsayayi, kamar zai shareta sai kuma yace, “Gobenma na gadama bazaki jeba”.
Bakinta taja ta tsuke, bata sake koda tariba.
Ya miƙar da ita daga cinyar tasa shima ya miƙe, tef ya ɗauka yazo gabanta ya tsaya, karon farko dazai gwadata dan zai musu ɗinki, hakan bai taɓa faruwa ba, dan baya gwadasu sai dai yace su kawo kayansu yay amfani dashi.
Salon da ake gwada ɗinkin ya saka tsigar jikin Rumana keta tashi, badai ta yarda ta motsaba saboda yanda ya haɗe fuska, tasan dai haushin maganar bikice da tayi, itama saida ta furta ne taga wautarta.
Yanayi yana rubutawa, harya kammala ya ɗauki kayansa ya saka, sabuwar shaddace mai ƙyau kalar ruwan sararin samaniya, duk da bamai tsada bace tai bala'in masa ƙyau, ga ɗinkin ya zauna ɗam cikin ƙyaƙyƙyawar surarsa, ainahinsa na Barumen bakatsine ya fito masha ALLAH, ballema yayi aski da gyaran fuska, ƴar ƙasumbar daya ajiye ta sake fiddo taswurar nutsatstsiyar fuskarsa, hannunta daya kamone ya maidota hayyacinta, ya saka mata turare a hannun.
Kallonsa ta ɗanyi sai ya nuna mata jikinsa alamar ta saka masa.
A ɗan kunyace ta fara fosa masan, sai da ta tabbatar ko ina yaji sannan ta dakata, hannunta ya kama ya jata gaban gadon, shi ya zauna ita kuma tana tsaye a tsakanin ƙafafunsa idanunta a ƙasa tana kallon hannayensu.
Yace, “Kina jina”.
Kanta ta ɗaga masa, sai kuma tai saurin cewa, “Eh” saboda tuno gargaɗinsa.
Ya murza hannun nata yana cigaba da faɗin, “Ki kwanta ki huta, bance kije cikin matannan ki zauna ba, zan aiko Abubakar ya kawo miki abinda zakici, sannan abinda ya faru tsakanina dake sirrinmu ne, koda wasa naji bakinki na bama wani labari koda su Fa'iza ne bazakiji da daɗiba, ki kama bakinki”.
Cikin rawar murya Rumana tace, “To yaya, insha ALLAH zan kiyaye”.
“Good” ya faɗa yana miƙewa, matsota yay jikinsa ya rungume yana sumbatar kanta da shafa bayanta, a hankali ya furta, “ALLAH yay miki albarka”.
Rumana dake lafe jikinsa tana shaƙar ƙamshinsa ta amsa da amin a cikin zuciyarta tana ƙoƙarin maida ƙwallar da suka cika mata ido..
Ɗago kanta yay ya kama fuskarta ya saka cikin tafin hannunsa yana kallo, ganin taƙi kallonsa sai ya ɗora goshinsa kan nata, “A kalleni mana madam”.
Kunya ta sake kama Rumana, taɗan saki murmushi da a maƙoshi kawai taji sautin kayanta, shima ya sumbaci laɓanta ya ɗago ya sumbaci goshinta sannan ya saketa.
Ɓaƙar ledar daya ajiye gefe ta viva ya ɗauka yana faɗin, “saina dawo mizan zo miki dashi?”.
“Ba komai Yaya” ta faɗa tana ɗan satar kallonsa.
Kaɗa kansa yay yana nufar ƙofa bayan ya zira takalmansa baƙeƙe a ƙafa, “Shikenan saina dawo”.
“Ka gaidasu, ALLAH ya tsare”.
“Amin” ya faɗa yana ɗaga labulen ya fice.
Kausar da maman Ama da har yanzu suna inda Rumana ta barsu suna gulmarta duk suka zuba masa ido a kaikaice, harya fice kowacce da abinda take saƙama ranta.
Shiko baima san sunaiba, dan basu ishesa kalloba.
Yana fita Rumana ko bakin gadon ta zauna tana sauke numfashi a hankali daɗan murmushi, yanzu kam ta yarda Yaya Ahmad natane bana yaya Samina ba kamar yanda kowa ke faɗa a baya, abinda bata taɓa kawowa ba koda a mafarkinta, ALLAH kenan, mai tsara yanda yaso, ga kuma wanda yaso.
Miƙewa tai ta ɗora ruwan zafi a risho danta samu tai wanka, bata fitoba saida ta juyo a botiki, matan gidan nata ƙoƙarin ɗora sanwar rana, batace da kowa komaiba ta shige bayi.
Sai da ta fitone maman Ama ke tambayarta wai ko zataje gidan bikine?.
Murmushi Rumana tayi dan tasan tambayar da biyu ce, sosuke suji ko Yah Ahmad zai iya barinta taje?.
Sai kawai tace, “Mizai hanani zuwa, zan dai jira su Fa'iza suzo mu wuce”.
“A'a, toshi angon bacan ya nufaba da bakibishi kun tafi tare ba?”.
Karon farko Rumana taji zata iya maida murtani, dan haka tace, “Maman Ama mi kikeci na baka na zubane?”.
Shiru kuwa bakin maman Ama ya rufe ruf, suka kalli juna itada Kausar cike da mamakin Rumana, itako batabi takansu ba tai shigewarta ɗakinta tana jan tsaki a zuciyarta.
Har tai shirinta bata sake jiyo tarin kowa a cikinsu ba, sai ga sallamar Abu, taji daɗin ganinsa, ya ajiye mata ledar dake hannunsa yana tsokanarta da faɗin, “Wannan ai kece amaryarma ba waccan fanɗararriyarba”.
Dariya Rumana tai masa, “Kai Yaya Abu wace fanɗararriya kuma?”.
“Amaryar gidanmu mana mai kan goba” ya faɗa yana miƙa mata ledan hannunsa, “Gashi inji Yah Ahmad”.
Amsa tai tana godiya, ga ƙamshi dukya cika ɗakin, dagaji kasan kazace.
Abu da ko zama baiba yace, “Bara na fece amaryar Yaya”.
“Yah Abu ina zaka fece, “dan ALLAH kazo muci”.
Dawowa yay da baya yana rage murya kamar zaiyi gulma, “Hajiya takice ke kaɗai, tamu nacan a shago ina faɗa miki a ƙyafe, gara naje kafin Yah Mudan ya handame rabi ya banni da ƙwala idanu”.
Dariya sosai Rumana takeyi, Abu ya fice shima yana tasa.
Zama Rumana ta gyara taci kazarta tai nak tana lumshe idanu, ta ɗora da maltinar da aka sakko mai sanyi kunnuwanta a mimmiƙewa sama, rabonta dacin nama harta manta lokacin, sai taji wani ƙaunar yaya Ahmad na girmama a ranta, sauran ta ajiye gefe tai kwanciyarta a tabarma kamar yanda ya buƙata.
________________________________
A gidan su Ahmad kam bikin dai daga danginsu ƴan shema babu wani armashi, dan inna marwa ce kawai da iyalanta sai sukazo, sai maza da zasuzo ɗaurin aure gobe, dangin mama gaje ne kawai suketa zuwa, waɗanda da yawansu kasan da biyune, dan sai habaici suke kala-kala, amma babu wanda ya kulasu hatta da Ammin su Rumana.
Koda Ahmad yazo gidan saida ya shiga har sashen ya gaida Ammin su Rumanan, aiko dangin mama gaje da ƙawayen Samina da ita kanta saminar tamkar zasu cinyesa da kallo, kowa ya gansa yansan hankalinsa a kwance yake, gashi yau shar yake da ƙyallin angwanci na gaske, fuskarsa ta sake yin wasai abin son kallon kowa ba tare da kaso ya gusa daga gareka ba.
Shikam koma kallon basu ishesa ba ya fito zuwa sashensu, dan sashen su iya ya fara shiga dama suka gaisa.
Bayan ya gaisa dasu Gwaggo da Ayyah su Fa'iza sukazo duk suka gaishesa, sai satar kallonsa sukeyi saboda ƙyawun da yay musu, su baba dai duk sun fice wajen nema.
Ɗakin Ayyah ya shiga suka buɗe kayan da yazo dasu aka fiddama kowa tsarabarsa a gidan gwargwadon bajintar da ya nuna ta ƙarfin aljihunsa.
Amma abin birgewa kowa aka bamawa sai murna yake da nuna jin daɗinsa, sunata jera masa godiya.
Koda ya shiga ɗakin gwaggo ya ajiye mata kuɗi sai cewa tai “Ita Yaya ka batane”.
Kasa haƙuri yay saida ya kalleta, yasan Ayyah ta wuce gaban raini a garesa, kuma duk abinda ya siya musu tare ya sai musu, kuɗinma ya bata itama, amma saiya ɗan ƙarama Gwaggo wani abu matsayinta na mahaifiya, duk da yasan halinta dakamar wahala ta amsa, dan itama Ayyah idan su yaya maryam sukai mata alkairi inhar babu na Gwaggo bata amsa, sai dai idan ta raba musu dai-dai........
“Magana nake maka ka zauna kana kallona”.
Murmushi yayi yana duƙar da kansa, yace, “Eh Gwaggo na bata”.
“To ALLAH ya saka da alkairi, ya ƙara buɗi na alkairi”.
“Amin ya rabbi” ya faɗa cikin jin daɗi sosai.
Daga haka sake dawowa yay wajen abokansa ya basu tasu tsarabar, yaɗan zauna suka taɓa hira bayan sun dawo sallar zuhur, ya jima sosai a wajen suna shan shafta irin tasu ta abokan da suka shaƙu tun ƙuruciya kafin ya tashi shi da Sufyan su nufi shago dan yanason yanka ɗinkin Rumana ya samu kafin dare ya haɗa mata.
Yana aikinsa suna hira da bama juna labarin yaushe gamo...........✍🏻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭👏🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*_GDW_*
*(23)*
............Kusan ƙarfe biyar na yamma Rumana na bakin rijiya tana ɗibar ruwa Ahmad ya shigo gidan da sallama.
Ita da Kausar dake wanke-wanke a wajen ne suka amsa, maman Ama dake kicin tai zumut ta fito sai kace mai jira dama.
Rumana bata yarda ta kallesa ba tace, “Sannu da dawowa”.
Ahmad da ya ja birki a gabanta ya amsa yana binta da kallo ƙasa-ƙasa, ko damuwa dasu Kausar baiyiba.
Ledar hannunsa Rumana ta miƙa hannu zata amsa, ya riƙe bai bataba, sai ranƙwafowa da yay wajen kunnenta yana magana ƙasa-ƙasa,
“Sai kin kalleni tukkuna ko kuma na ɗauke ki gaban ƴan sa idon nan har ɗaki”.
Babu shiri Rumana ta kallesa cikin zaro idanu da mamakinsa.
Gira ɗaya ya ɗaga mata yana kashe ido murmushi shimfiɗe saman fuskarsa.
Ai da ɗan gudu Rumana tabar wajen itama tana murmushi.
Dariya ta bama Ahmad, dan haka yayi kaɗan har haƙoransa na bayyana, “Yarinya idan na ɗaukar miki ruwan nan akwai tara”. ‘Ya faɗa daɗan ƙarfi yanda Umm-Ruman dasu maman Ama da ke hangame da bakuna duk suka iya jinsa’.
Ruwan ya ɗauka ya nufi ƙofar ɗakinsu har sannan baibar murmushinba, yayi kuma tamkar baisan dasu Kausar a tsakar gidanba.
“Sannu barewa” ya faɗa yana ajiye ledar hannunsa idonsa akan Rumana data kawo masa ruwa.
“Yaya barewa kuma?” tai maganar a ɗan shagwaɓa.
Haɗawa yay da hannunta da ruwan ya riƙe yana tsareta da idanunsa masu hasken tsiya, musamman ma yau da yake tare da farin ciki babu sirkin komai a cikinsu, har wani ƙyalli sukeyi, “Eh mana, tunda kin gudo kin barni da waɗancan matan gidan naku masu shegen sa ido”.
Rumana tace, “Yaya sune basu da aikinyi ai, ni basa gabana balle halinsu”.
“Da kyau Babyna haka nake sonki, kizama maiyin rayuwa dan kanki badan wani shashasha ba, ashe dai kema A ce”.
Kauda kai Rumana tai gefe tana dariya, shi ba'ace masa A ba sai ita.
Hannun nata da ruwan ya haɗa yakai bakinsa, sai da yasha ruwan sosai ya janye yana sauke numfashi.
Tausayinsa ya kama Rumana, dan ta lura dama ƙishin yakeji, kofin ta ajiye ƙasa ta juya zata fita yace, “Zo mana”.
Dawowa tai da baya, zata durƙusa gabansa ya riƙota ya zaunar kusa dashi.
“Yaya jikin naki?”.
Ƙasa tai da kanta tana murmushi da wasa da yatsun hannunta, “Yaya babu wata damuwa, komai Alhmdllh”.
“Da gaske?”. ‘Yay maganar ƙasa-ƙasa kamar mai raɗa’.
Yanda yayin sai da tsigar jikin Rumana ya tashi kuwa, ta ɗaga masa kanta kawai dan ta kasa magana.
Hancinta yaja kaɗan yana faɗin, “Ashe matar tawa ba ragguwa bace”.
Yanda yay maganarne da jan hancin nata ya saka Umm-Ruman ƙyalƙyalewa da dariya tana rufe fuska. Shima murmushi yayi, dan sosai yakeson ya ganta cikin farinciki, baya ƙaunar ganinta a takuren nan sam......
Ita ko yanda yau ya sake mata sai takejinta daban, tanaji a ranta ashe itama dai mace ce, ba kamar yanda su maman Ama ke nuna mata sun fita ba........
Ganin tayi shiru Ahmad ya kamo hannunta yana faɗin, “Tunanin mi kuma?”.
“Ba komai Yaya, dama cazan miza'a dafa”.
“Babie R waya faɗa miki amarya mai martaba irinki na girki a wannan ranar? Ai sai kinyi sati kina hutawarki, hidimata kawai zakikeyi”.
“Babie R” ta maimaita sunan a zuciyarta, sai kuma tai guntun murmushi, shima Ahmad dake kallonta murmushi yayi yana lumshe idanu.
A waje kuwa tunda su Rumana suka shige Kausar data rakasu da muguwar harara tace,
“Hum sabon sallo wai tusar liman bayan sallame salla”.
tai maganar cikin hura hanci.
Maman Ama ta tare numfashinta da faɗin, “Ai wannan ya wuce sabon sallo sai dai bariki, shikuma a neman kuɗin abinda ya ƙaro ilimi kenan?”.
Kausar ta ajiye sosan da take wanke-wanke ta miƙe da ƙyar saboda ciki tana jan tsaki, “bokon za'a nuna mana a yanzu, aiko bazamu ɗauki ƙananun iskanciba, sai dai in gaba zasu ƙara sayi a wani gidan amma ba nanba”.
“Kausar faɗi ki ƙara da wayyo, dan baza'a lalata mana yara ba kuwa da watsewa”.
Su dai kaɗai suke banbamin hassadarsu, Rumana ma batasan sunaiba, tana can cikin sabon shauƙi da yayanta da a yau yazo mata da sabon salon sabuwar rayuwa mai tsafta da riƙe zuciya.
Ahmad kuma bai barta ta sake ko leƙo waje ba har sai da aka kira sallar magriba ne ya fito riƙe da buta, a gaban idonsu yay Alwala, Umm-Ruman ta fito ta amshi butar, koda ya bata saiya matsa ya sumbaci gefen kuncinta na dama yana faɗin, “Saina dawo babie na”.
Duk da kunya ta gama rufe Rumana haka ta daure saboda ganin yanda aka zubo musu idanu, itama cikin sanyin murya tace, “ALLAH ya tsaremin yayana”.
Fita yay yana murmushi, itako ta shige bayi abinta batako kalli sashen su Kausar da suka sake cika da baƙin cikiba.
Koda ta fito kowacce ta shige ɗakinta, Rumana tai dariya a zuciyarta da faɗin, lallai aiki ya sameku.
★★★★★★
Sai da akai isha'i ya dawo gidan, yazo musu da abinda zasuci, sannu Rumana tai masa, ya amsa yana zama a tabarmar dake shinfiɗe yana faɗin,
“ALLAH yasa da ruwan zafin wanka a gidan nan?”.
“Eh akwai, a zuba ne?”.
“Eh to barsa naci abinci first”.
Tace, “to”.
Tare sukaci suka ƙoshi, duk da dai Rumana najin kunya, shiko ko'a jikinsa kai tsaye yake komansa babu wani risini, sai yanzun take sake yarda da maganar mutane dake faɗin mutum mai shiru-shiru baida sauƙi idan yaso abu, duk da ba koda yaushe ya cika fara'a ba bata damuba, dan itama ba fara'arce da itaba.
Ruwan wanka ta haɗa masa ta tafi kaiwa, ta juyo zata fito sukaci karo dashi a ƙofar bayin, tsare hanyar yay ya hanata fita, cikin dauriya tace, “Yaya ga ruwan nan”.
“Na gani ai” ya faɗa yana jan hannunta, ya tura ƙofar bayin.
Da sauri tace, “Yay...”
“Shiii bansan surutu” yay maganar babu wasa a fuskarsa.
Dole taja bakinta ta kulle, tanaji tana gani ya cire mata kaya kamar yanda shima ya cire jallabiyar da ya sako kawai a jikinsa, babu shiri Rumana ta rufe idanu ruf, jikinta har tsuma yake saboda tsagwaron kunyar data mamayeta, mamakinsa ne ke sake girmama a ranta, wai dama haka Yaya Ahmad ɗinnan yake?.
Haka akai wannan wanka babu wani sakewa daga Umm-Rumana, suka fito yana riƙe da kayanta ita kuma botikin wankan.
A yanzun kam taji daɗi da babu ko ɗaya daga matan gidansu a waje, sai dai bata saniba mijin maman Ama ya gansu, jikinsa kuwa har ɓari yake wajen zuwa ya bama matarsa labarin abinda ya gani.
Lokacin da take leƙensu ta Window Ahmad na tsaye yana brush a wajen, ga iskar hadari data fara kaɗawa, Rumana ma fitowa tai domin yin brush ɗin, cikin zuciyarta tanajin daɗin canjawar yayanta, dama tasan tun can da shi mai tsaftane, ruɗanin Samina kawai daya sakama ransane ya nema susutar dashi.
Tana kammala alwalar barci isaka mai ƙarfi ta taso, cak Ahmad ya ɗauketa ita da butar yay ɗaki dasu suna dariya saboda tsorata da tayi wai catake iskarce tai sama da ita.
Kausar dake ƙoƙarin rufe ɗaki dan yau mijinta a gidan Uwargida yake tace, “Watsatstsu kawai” Tana jan tsaki.
Ahmad kam sai da ya dire Rumana a tsakkiyar ɗakin sannan ya juya ya rufe musu nasu ɗakin.
Ko a wajen shirin barcinma dai Rumana nata muƙu-muƙu, a zuciyarta tana ƙunƙuni akan figaggar rigar da Ahmad ya ciro cikin kayansa ya bata wai ta saka, dan ƙyau rigar tayi ƙyau, sai dai dole kaji kunyar sakata a gaban wanda bake matuƙar ganin girma.
Kodata saci kallonsa sai taga ko'a kwalar rigarsa, shi boxer ma kawai ya saka ya haye gado a hakansa ya kwanta yana kallonta, dan yace idan ta gama tazo gabansa yaga yanda rigar tai mata.
Ita dai tasan inhar a haka za'a cigaba ta bani da Yah Ahmad a gidannan, tunda ta lura shi babu ruwansa da kawaici agaban kowa, duk abinda yazo masa a rai shi yakeyi.
Dole tabi umarninsa dan babu wasan jayayya a tsakaninsu, shiko ya ware ido yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, daga ƙarshe yajawota ta faɗo jikinsa ya mirgina tsakkiyar gadon da ita yana sauke mata tagwayen kisses.
_________________________
Ɓan garen Samina kuwa sosai ganin Ahmad ya zauna mata a rai, duk da ƙoƙarin turesa da take a rai hakan ya gagara, yau daren ɗaurin aurenta da Ma'aruff amma Ahmad yazo ya cunkushe dukkan tunaninta, koda sukaje wajen party ɗin da suka shirya iyakar su ƙawaye da abokansa kasa sakewa tai, duk da shima Ma'aruff ɗin ta lura tunda aka fara hidimar bikin nan yaketa wani ɗaɗɗaure mata, abinda yasa batabi takansa ba saboda duk kuɗin data buƙata bata yake, abinda kawai ta kawo a ranta rashin son auren nasu da Mahaifiyarsa ta nuna ƙuru-kuru ne, dukda yana ƙoƙarin son ganin bata fahimtaba.
A yau kuma asabar aka wayi gari safiyar ɗaurin aure, gidan nasu ya cika saboda isowar ƴan shema, ga kuma dangin mama gaje na nan cikin gari da ƙawayenta sun ƙaru.
Bakajin komai sai ƙamshin girki da hayaniyar data cika gidan, dan girke-girke ake na garari, su dai su baba iyakar ƙarfinsu suka bada, amma mama gaje tace sunfi ƙarfin dafa wannan abincin a bikinsu, gefe ta ajiye kayan dasu baban suka bada ta fiddo tasu sayayyar, dama ta raba wasu ayyukan gidajen ƙawayenta.
★★★★★
Kusan sha ɗaya na safe su Kausar ana tsakar gida ana sana'ar ta gulma, wata maƙociyarsu maman Aysha ta shigo suna mata gulmar Rumana sai ga Rumana da Ahmad sun fito cikin gayun daya nema zauta zukatansu.
Rumana na sanye da les ruwan makuba daya haska choco ɗin fatarta, an masa kwalliya da kalar ruwan zuma kaɗan, gashi Ahmad yay mata ɗinkin daya zauna mata sosai a jiki tamkar irin matan manyan nan dake ji da hutu, tasha awarwarayenta da sarƙa masu ƙyau da tsari, tundaga kan takalma zuwa mayafi da bag duk sabbine, Ahmad ma na sanye da sabuwar shadda ruwan zuma sai maiƙo take, ko angon sai dai ya nuna masa tsadar kaya amma ba tsarin kwalliya ba, ƙamshin khumran da Rumana ta shafa da turaren Ahmad ɗin sun gauraye sun bada wani ƙamshi mai tsayama maƙiyi a maƙoshi.
Yana riƙe da bag ɗin Rumanan a hannunsa sai leda mai ɗan girma baƙa itama, ta rufe ɗakin ta juyo suka haɗa ido suna sakarma juna lallausan murmushi, ido ya kashe mata ita kuma taɗan murguɗa masa baki.
“Ni ko?”. Ya faɗa yana matsota.
Baya taja tana sassanyar dariya da gyara mayafinta, “Yi haƙuri ba kaiba” itama ta faɗa a hankalin.
Ƴar ƙwafa yay ya nufi hanyar fita riƙe da bag ɗin da ledar ba tare daya bataba.
Ita kuma ta ƙarasa gasu maman Ama tana faɗa musu ta tafi wajen biki sai sun ƙaraso suma.
Da ƙyar suka iya amsa mata su duka har maman Aysha ɗin, ta kaɗa kanta ta bi mijinta suka rakata da harara.
Ba ƙaramin tsaya musu a rai wankan Umm-Ruman yayiba, dan ko makaho ya laluba yasan sunyi ƙyau sosai, kamar sune akema bikin.
A soro ta iske Ahmad tsaye yana jiranta, ya miƙa mata bag ɗinta, amsa tayi tana cewa, “Thanks yayana”.
Baice komaiba sai kallo da yake binta dashi, shi kansa ganin matar tasa yake kamar ba itaba, dan kuwa ya kuma tabbatarwa jikin Umm-Ruman nason abu mai ƙyau, kamar yanda mutane ke faɗa akansa shima.
Cikin katse masa tunani ta miƙa hannu zata amshi ledar hannunsa, saiya janye yana girgiza mata kai, ya nuna mata hanya yana faɗin, “Ke kanki badan kar ace na cika rawar ƙafaba da ɗaukarki zanyi bazakisha wahala ba”.
Gaba Rumana tai da sauri tana murmushi, yayanta wlhy yafi mijin novel ɗin da Samina ta tafka kuskure akan nemansa.
Duk inda suka gitta kallonsu akeyi, hakan kuma saiya zafi Ahmad a zuciya, ya tsaida musu napep suka shiga yana jan tsaki.
Da mamaki Rumana ta kallesa, sai ya galla mata harara yana faɗin, “Da nasan kowanne banza zai nema ɗora idonsa akan matata wlhy da hijjab zaki sawo Mtsoww”.
Gefe Rumana ta maida kanta tana ƙoƙarin haɗiye dariyar dake neman kufce mata, tofa kishifa kenan? Dan idanunsa harsun kaɗa saboda ɓacin rai.
Kallo bai dawo kansuba ma sai da suka iso ƙofar gidansu, gaba ɗaya mutane sukai musu caa da idanu, abokan Ahmad kam wani ihu suka saki harda masu fito tamkar anci ƙwallo suna haɗa baki wajen ambatar “Sai mai zafin mu!!”.
Daƙuwa Ahmad yay musu yana cije baki.
Ba tare da yasan mi yayi ba yaja hannun Rumana sukai cikin gida wai duk dan mutane subar gane masa mata.
Murmushi baba ilyasu da Baba Yusha'u dake ƙofar gidan suma sukayi suna girgiza kawunansu, Baba kuwa ai shi harda kunya yaji, dukda yaji daɗin ganin ƴaƴan nasu cikin aminci da kuma kishin Rumana daya hango a fuskar Ahmad ɗin kodan abunda yayi.
Rumana nason tace ya saki mata hannu amma tanajin tsoro, a haka suka shigo har cikin gidan sashensu, inda yake cike da ƴan Shema matan da akazo dasu ɗaurin aure.
Aiko abokan wasa sukai musu caa da sheri, shi saima lokacin ya fahimci tsiyar daya tafka, gashi sunyi ido huɗu da Gwaggo da Ayyah dake tsaye suna magana, gwaggo dai kallo ɗaya tai musu ta ɗauke kanta, Ayyah ko saita hau dariya mai nuna tsagwaron farin ciki.
Gasu Yaya Maryam daga gefe suma suna dariyar da kare su Ahmad ɗin daga sherin da abokan wasa suke masa akan ya kamo Rumana kamar yana tsoron kar wani ya ƙwace masa.
Murmushi kawai yayi ya saki mata hannu a hankali, ya sosa gefen wuyansa tare da takawa zuwa ga iyayensu ƴan shema dake wajen.
Rumana kam ai tunda suka tsaya kanta ta sunkuyar kawai ƙasa, jitake inama ƙasa ta tsage ta shige saboda kunya, bata iya ta motsa ba sai da Ayyah tazo ta kama hannunta sannan, amma sai tafiya take a hahharɗe.
Ayyah ta ƙarasa da ita inda Ahmad ke durƙushe yana kwasar gaisuwa da saka albarkar dangin mahaifan nasu, durƙusawa itama Rumana tayi kanta a ƙasa bata yarda ta kalli kowa ba ta shiga gaishesu.
Wata dake matsayin yayar su babansu ce ta jawo hannunta tana faɗin, “Wannan ƴar tawa anya babu ajiyar mijina ko kishiya anan?.
Nanfa kowa ya shiga faɗin albarkacin bakinsa, Ahmad dai tunda ya saci kallon Rumana saiya miƙe dan yaga su Wasila abokan wasansu ba ɗaga masa ƙafa zasuyiba, shi kuma ba iya maida murtani yakeba dama can.
Wajen Ayyah ya nufa suma ya gaishesu yanata wani soshe-soshen kai, ita Ayyah ma saiya bata dariya.
★★★★★★
Samina na tsakkiyar ƙawayenta ana rangaɗa mata kwalliya wasu ƙawayenta biyu da suka iso kusan tare dasu Rumana suka shigo musu da labarin soyayyar da suka gani a waje na wasu sabbin ango da amarya, dansu basusan Ahmad ɗinba.
Tsigil wata ɗiyar ƙanwarsu mama gaje tace, “Aunty Samina Ahmad nefa da Rumana”.
Wani irin faɗuwar gaba Samina taji har tana kaɓe hannun mai kwalliyar, tayi kicin-kicin da fuska dan zuciyarta sai zallo take tamkar zata faso ƙirji ta fito, a yanda ƙawayenta ke bada labarin lallai show ɗin ya ƙayatar kuwa, ganin zata sauka a layi Nafy tai saurin ƙwaɓarta.
Duk yanda taso dai-daita kanta saita kasa, dan kuwa ahankali maganar abinda Ahmad ɗin yayi yaketa fitowa daga bakunan mutane, wasu suna ganin yayine dan kawai ya nuna yanzu Samina bata ransa, wasu kuma na faɗin kawai tsantsar ƙaunar dake tsakaninsa da matarsane ya nuna kishinta.
Samina jitake kamar ta fara dannama duk wanda ya ambaci sunan Rumana da Ahmad zagi a wajen............✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*_GDW_*
*(24)*
..............Su Rumana dai an shige cikin dangi, kowa sai haba-haba yake da ita, iya kuwa harda guɗa ta callara akan Umm-Rumana, hakan ya jawo kallon Rumana ya ƙara armashi cikin taron, dangin mama gaje da hassada keci sai kusheta suke, ƴan uwanta kuwa dana mahaifiyarta daɗin ganinta cikin shigar kamala duk sai ya lulluɓesu, ko ba komai dai Ahmad ya tabbatarma duniya ya amshi zaɓin ALLAH kuma yabi umarnin iyayensa.
Babu wanda yay tunanin ganinsa cikin taron bikin sai gashi harda matarsa, kuma abin birgewa cikin aminci da cikar haiba aka gansu, ba kamar yanda su mama gaje suke tunanin soyayyar Saminar ta cigaba da wajiga rayuwarsa ba har a wannan lokacin.
Dan bokanta ya tabbatar mata Ahmad tsiya-tsiya zai dawo daga neman kuɗin daya tafi, kuma bazai taɓa shiga gaban Samina ba ita zatai ta kasancewa a samansa, haka Rumana kuwa bazai taɓa ya kusanceta ba sai dai iyayenta su gaji su kashe auren.
Itama Umm-Ruman tun tana sinne-sinnen kunya harta saki jikinta acikinsu, dukda kuwa jitake kamar kowa yasan miya shiga tsakaninta da Ahmad, gashi dama bawani gama jinta tai dai-dai ba, irinsu Ayyah tsoffin mata dasu Iya kallo ɗaya sukaima yanayin tafiyarta suka harbo jirgin.
A ƙofar gidama ga Ahmad dolene abun ya burgeka, harkokin gabansa kawai yake cikin abokansa, sam babu wata damuwa ko kaɗan a saman fuskarsa, shaftarsu sukesha cikin nutsuwa suna kwasar dariya.
Yanda ya nuna halin ko in kula ba ƙaramin burge iyayensa da abokansa yayiba.
Shiko harga ALLAH yanzu Samina bata gabansa, dan ƴan labaran daya samu akanta gameda rayuwar data zaɓama kanta da Ma'aruff ba ƙaramin tsanarta ya cusama ransa ba, balle yanzu da suka zama abu guda shida ƴar ƙanwarsa Umm-Ruman, saima ya kula dama can so yama rufe idanunsa bai kula Rumanan tafi Samina komai ba.
Har aka gama taruwa babu ango babu dalilinsa, hakama waliyansa, ga lokaci yanata ja, an tara mutane dukda sunada uzurorin gabansu, abokan ango dai sun iso, sai kiran wayar Ma'aruff ɗin suke amma tsabar wulaƙanci yaƙi ya ɗaga.
Sai da mutane suka gama ƙuluwa da takaici, wasuma harsun fara miƙewa sannan sai gashi, ko neman afuwar kowa baiyiba kuwa, da yake tare suka iso da waliyan nasa kawai ɗaurin auren akayi.
Kamar mutane akan ƙaya suke ana ɗaurawa suka fara watsewa, shi kansa angon dagashi har abokansa basu zaunaba suka ƙara gaba.
Aiko wannan abu ya zama ƙananun magana sosai a cikin gida, dan irin ƴar gaisuwar iyaye da anguna kanshiga yi su Ma'aruff basuyiba, balle amarya tai tunanin zasu ɗan ɗauki hoton tarihi haryaga kwalliyarsa ita taga tasa ya zamo musu ranar tunawa wata rana a gaba.
Samina ranta ya ɓaci, ta kira Number Ma'aruff amma yaƙi ɗaga mata, daga ƙarshema data jera masa kira kusan baƙwai sai ya kashe wayar gaba ɗayanta.
Wannan abu yaso ɗimauta tunaninta kam, sai dai Nafy na tausarta saboda idon mutane.
A ƙofar gida kam yaran anguwa suka haɗa dj na shaƙiyanci, da waƙar MATAR JAMI'A ta Naziru Ahmad suka fara wadda kowa dai ya fahimci habaicine ga samina, daga nan suka cigaba da saka waƙoƙi kala-kala da dai ke gargaɗi ko magana akan butulci.
Ahmad da abokansa kuwa tuni sunbarma anguwar suma, dan dama sunada wajen zuwa auren kawai suke jira a ɗaura su ƙara gaba.
★★★★★★
Maganar farin ciki dai a wannan buki kam ƙalilanne, dan komai kaga yazo saika samesa a dagule da ɓacin rai, danma dai sunata ƙoƙarin rufe wani abun dan kar a fahimta ai musu dariya.
Da daddare ma sai da rai ya ɓaci akan ƴan ɗaukar amarya kafin abokan ango su iso, tsabar iskanci kuma dukda sun iso a makare sai sukace ƴammatan amarya kawai zasu ɗauka banda tsaffi.
Da ƙyar aka samo wani mai motar hayar taxi a anguwar ya ɗauki wasu a cikin iyayen Saminar tunda bazai yuwu ace ankai amarya babu danginta ko guda ba.
Abinda kuma basu saniba daga nan gidanma bawai gidanta aka nufaba da ita, hotel ɗin da zasuyi dinner abokan ango suka nufa, shiyyasa ashe sukace ƴammata kawai zasu ɗauka.
Ran wasu a cikin iyayen da suka bisu ya ɓaci sosai, dan dangin Ma'aruff ɗin sai kallon banza suke musu.
Ganinfa ana nemam wulaƙantasu suka zaro jikinsu suka fito domin dawowa gida.
Ga Samina kuwa duk ɓacin ran data shirya nunama Ma'aruff tana ganinsa sai taji ta daburce ta kasa ko tari, sai ma damuwa data shiga dangane da shashsharetan da yakeyi.
Har aka tashi wannan dinner bataga fara'arsa ba, sai dai idan abokansa ko danginsa sunzo kusa dasu yin hoto ko magana dashine zataga yana murmushi, amma ita magana ma idan tayi saiya ja lokaci yake bata amsarta, wata kuma ya share abunsa kamar bai jiba.
Ƙarfe ɗaya aka tashi, kowa ya kama gabansa bayan sunma Amarya da ango rakkiya gidansu, dan tsaruwa kam gida ya tsaru, dolene Samina ta kira kanta gwarzuwar shekara a wannan lokaci.
Sai dai suna shiga yaga abokansa sun wuce da ƴan uwansa ya saki hannun Saminar, ɗakinsa ya nufa ya barta a falo tsaye, tun tana tsammanin fitowarsa harta ƙosa ta bishi, tsabar rainin hankali iskesa tai harya shiga wanka, ɗakin ba baƙonta bane, tunda ansha kawota cikinsa a aikata abinda akeso da ita a ciki, sai dai an canja kayan cikinsa, waje ta samu ta zauna tana tsumayen fitowarsa.
Koda ya fito ya ganta kallo guda yay mata ya ɗauke idanunsa, cigaba yay da shirinsa kamarma baisan tana ɗakinba, ita dai Samina mamaki sai kuma ɗaure kanta yake, gani take tamkar ba Ma'aruff ɗinta bane mai sonta da ƙaunarta tare da tattalinta ga komai.
Bayan ya gama shirinsa tsaf yazo ya zauna a bakin gadon yana kunna lap-top, ga kofi daya ciko da fresh milk ya ajiye gefensa.
Kasa jurewa Samina tayi ta miƙe ta koma kusa dashi ta zauna tanata zabga ƙamshi mai daɗi kuwa.
Murya a raunane tace, “Wai lafiya kuwa Sweet?”.
“Mi kika gani?” yay tambayar ba tare daya kalleta ba.
Da ƙyar ta haɗiye busashshen yawun bakinta tana zuba masa mayun idanunta irin nasu Ahmad, “Sweet ka canja min, sai kace ba kaiba, kamar baka ɗokin ganina a gidanka matsayin amarya matarka ta sunna? Yanzu wane angone za'a kawoma amarya amma hankalinsa nakan aiki”.
Wata ƴar dariyar rainin hankali yayi ya juye gaba ɗayansa yana kallonta, yayinda yake kai kofin madararsa a baki yana sha.
“To ke kuwa banda abunki wane zumuɗi kike son ganina a ciki? Babu wani abu baƙon a gareni daga wajenki ai, kokuwa wannan faudar da zanen ƙunshin zan zauna kallo?” yay maganar yana lakato kwalliyar fuskarta a ɗan yatsa.
Wani mugun tsorone ya kuma dirar mikiya a fuskar Samina, tai galala da baki tana kallonsa ba tare da ta iya furta komai ba.
Bakinsa ya taɓe yana kauda kansa daga kallonta, “Miye abun mamaki a zancena, kema dai kinsan kowane ango yana rawar jikine ga amaryarsa saboda abunda zai amsa mai muhimmanci a gareta, to ni kuma an bani tun a waje ai, mizanma ɗoki kuma yau?”.
Hawaye masu azabar zafi suka fara gudu bisa fuskar Samina saboda kalaman da Ma'aruff yake gasa mata akan abinda shine yafi ƙarfinta ya amsa ba itace ta bashiba, hasalima tabi duk hanyar da zatabi danta tsare abunta sai irin wannan ranar amma saida ya ruguza mata shirinta.
Tashi tai ta fita da gudu tana kuka, ya bita da kallo yana taɓe baki, sai kuma yaja tsaki yana faɗin “Kajimin wawuyar yarinya, ballaga kawai mtsowww”.
Samina kuwa ɗakinta ta shiga tunda dama ta sansa, ta faɗa kan gado tana fashewa da wani kuka mai ciwo, farawa da iyawa kenan, daga tarewarta Ma'aruff ya rasa dami zai tarbeta sai wannan rashin mutuncin?.
Kuka tasha bana wasaba, ga maganin matan da aka ɗirka mata sai cizonta yake, har mararta ta fara mata ciwo.
Ganinfa zata halaka kanta kusan biyu na dare ta sake miƙewa ta koma ɗakin Ma'aruff.
Kwance ta iskesa hankalinsa kwance yana barci, cikin sanɗa ta haye gadon tare da ɗaga bargon ta shige cikin jikinsa ta ƙanƙamesa.
Cikin jan tsaki Ma'aruff daya farka yace, “K wane salon iskancine wai haka ina barci zakizo ki tadani?”.
Banza tai masa ta fara masa salon data san yana saurin ruftawa, da zafin nama ya tureta daga jikinsa.
“K banason rashin mutunci fa, mike damun tunaninkine?”.
Kuka mai tsuma zuciya Samina ta fashe masa dashi tana roƙonsa ya taimaketa karta mutu, sai faman riƙe mara take tana matse baki, ga hawaye wasu na bin wasu.
Shiko kallonta yakeyi da maɗaukakin mamaki, shi sai yau yake fahimtarma abinda mahaifiyarsa ke faɗa masa akan rashin dacewarsa da wannan yarinyar......
Katse tunaninsa Samina data manne masa a jiki tayi, ya janye jikinsa yana hararta, “Wlhy ki kama kanki, ni na aikeki kisha abinda zai hanaki zaman lafiyar? Can kije kiji da matsalarki ni dai barci nakeji, dan haka tashi kibarmin ɗaki kokuma na fitar dake wlhy”.
Sabon kuka Samina ta fashe dashi tana durƙusawa a gabansa tana roƙonsa, amma sam yaƙi saurarenta saima faɗi yake ta fitar masa a ɗaki, inba hakaba wlhy zai lakaɗa mata duka, abinda take son shi baida ra'ayinsa yanzun.
DAREN FARKO ya zama DAREN WAHALA, Inji amarya Samina dake neman shiɗewa saboda azabar ziwon da mararta take mata, ruwan sanyi kam harta gaji da sheƙa ma jikinta ta sadaƙar mutuwa zatayi kawai kafin wayewar gari, tayi nadamar biyema su mama gaje da suka dinga ɗirka mata magunguna duk dan ta burge Ma'aruff, kuka kam tayi harma ta rasa hawayen zubarwa, Ahmad ya faɗo mata a rai, yanda yay wani irin murjewa ga wani sheƙi da choco fatarsa keyi, kawai saita shiga kawosa cikin ranta a wani irin yanayin daya sakata kuma fashewa da kuka, dan kuwa tana ƙiyastashi a rantane zuciyarta na hasko mata Ahmad tare da Umm-Ruman.
Jitai tamkar numfashinta zai bar gangar jikinta lokacin da hakan yazo mata a cikin rai.
___________________________________
Ahmad ma kam baisan tanaiba, dan tun sanda ake dambarwar abokan ango sunce bazasu ɗauki tsoffi a motaba ya shigo gidan ya kaɗa kan matarsa suka ɗauki hanyar gida.
Tana sashensu sunashan hira da Amminta da ƙannen Ammi da sukazo bikin Zainab taje ta sanar mata saƙon kira daga Ahmad akan tazo su wuce gida.
Sam bataso wannan tafiya ba, dama ga tsoro a ranta na abinda ya faru a daren shekaran jiya, Ammi tai mata tsawa ganin taƙi ko motsi balle shirin tafiyar.
Tashi tai tana matsar hawaye ta kimtsa ta fito, a sashensu ta iskesa suna faɗan da suka saba shi da Sakina, tun suna ƙanana idan tace masa ƙaninta sai ya ɓata rai saboda bayaso, to har yanzu da take a gidan aure ga ƴaƴa ba dainawa sukaiba, dan ko gidanta yaje sai sunyi.
Ta girmesan amma tsiran bawani baneba, shiyyasa hakan ke bashi haushi.
Su Yaya Maryam nata musu dariya Rumana ta shigo, ya zubama kan Sakina ranƙwashi yay saurin nufar hanyar ƙofar gida yana faɗin Rumana ta samesa a waje.
Sosai yanzu kowa ke musu dariya har Ayyah da Gwaggo, dan kuwa Sakina taji zafin ranƙwashin nan sosai.
Ya tsaya mana inba tsoroba, kuma zata kamashi saita rama.
Ita kanta Rumana abun nasu ya matuƙar bata dariya, dan haka tabisa da kallo tana murmushi.
Sallama taima su Ayyah dasu Yaya Maryam ɗin ta fita, lokacin anata hayaniya a ƙofar gida da abokan ango, dube-duben inda zataga Ahmad takeyi, duk da kuwa ƙofar gidan akwai hasken wutar nefa da aka kawo.
Jin an kama hannunta tai saurin juyowa, ganin Yah Ahmad ne ya sakata sauke ajiyar zuciya a hankali, baice mata komaiba yaja hannunta suka bar wajen.
★★★★
Duk da Ahmad ya lura da fushin da takeyi sai ya shareta kamar bai fahimci abinda take jima haushin ba, lokacin da suka shigo gidan shiru dan kowa ya shige ɗaki ya kwanta, Ahmad ya buɗe musu ƙofa suka shiga.
Kayan jikinsa ya rage itako Rumana ta samu waje ta zauna tanata kumbura fuska.
Baibi takanta ba ya haɗa ruwan wanka ya tafi yowa, har ya dawo ɗakin tana a inda ya barta, murmushi yayi kaɗan yana girgiza kai, yasa tawul ya goge ruwan jikinsa ya shiga shirin barci.
Sai lokacin itama ta miƙe ta ɗeba ruwan ta fita, da kallo kawai ya bita amma uffan bai ce ba.
Itama dai wankan tayo, lokacin data shigo harya kwanta, sai dai ba barci yakeba waya yakeyi, Rumana ta kalli agogon ɗakin sannan ta kallesa, duk da bataji da wa yake wayarba hakan ya bata haushi, tako sake tsuƙe fuska waje guda.
Duk abinda take Ahmad na lure da ita, ta kammala mutsu-mustun shirinta tazo gefen gadon nesa dashi ta kwanta a takure.
Dai-dai nan ya ajiye wayar shima, matsowa yay tsakkiyar gadon ya jawota ta dawo jikinsa.
Hancinsa saman dokin wuyanta yana hura mata iska yace, “Kodai mu koma ne kima amaryar zaman ɗaki?”.
Tasan baƙa ya faɗa mata, dan haka tai shiru, murya a shaƙe ya sake faɗin, “Dake fa nake magana”.
“A'a” ta faɗa tana ƙanƙame jikinta saboda abinda yake mata da hannunsa a cikin jiki.
Bai sake magana ba sai sabon salo daya canjama kwanciyar tasu.
“Yau ɗinma dai babu sauƙi” cewar Umm-Rumana a zuciya tana share hawaye bayan ta gama gurzuwa a hannun jaruman mazaje.
Da taimakon Ahmad yau ɗinma ta kimtsa jikinta tanata masa kuka, da yake kukan da biyune harda haushin ƙin barinta ta kwana gida sai na yau ya nema finma na shekaran jiyan, shi dai Ahmad idanuma ya zuba mata, sai dai a ƙasan ransa yanajin tausayinta dan shi kansa yasan shiɗin bana wasan yara bane, tunda yana a ganiyar ƙuruciyarsa ne, kuma yanzunma aka fara wasan🤭.
Yanata lallashinta ta sigar shafa mata baya har barci ya kwashesu a haka su dukansu.
★★★
Washe gari Ahmad na gida har azahar bai fita ko inaba, hakanne ya saka Rumana fahimtar itama dai bazataje ko inanba kenan.
Bataga fuskar tambayaba kuma dan haka tai shiru da bakinta sai haushi dake cinta a zuciya.
Bayan anyi sallar azhar ɗinne Zainab da Ni'ima ƙanwarta sukazo, taɗanji daɗi, dan kayayyakin bikine wanda Ayyah ta haɗo tace a kawo mata, a wajensu takejin ai suma su Yaya Maryam duk sun tafi gidajensu ma, gidanma sai iya dangin mama gaje ne kawai da suke shirin zuwa buɗar kai gidan Samina.
_________________________________
Ko wacce amarya tana saka daren farkonta a jerin tarihin daren tunawarta koda takai tsufa saboda muhimmancinsa a gareta, sa ɓanin Samina daya zame mata daren baƙin ciki da wahaltuwar ciwo, da safe tashi tai tamkar wadda aka tsamo daga bakin kura, tayi wujiga-wujiga cikin azabar ciwo, ga kukan wahala datasha idanu sunyi luhu-luhu.
Har lemon tsami sai da ta samo daƙyar a kicin ɗinsu tasha amma bataji yanda takeso ba, sai da taɗan samu kanta kaɗan harta sami damar gyara jikinta tai wanka, bataga ko ƙeyar ma'aruff ba a gidan kuma bataji motsinsa ba sam, gashi koɗan abincin da akan kawo daga gidan surukai washe garin kai amarya ita babu wanda ya kawo matashi.
Ƴar kazar amarcin da ango yake kawowa nanma bata sameta ba a daren jiya.
Komai ya dagule mata ta kowanne fanni, har zuhur bataga kowa ya leƙotaba ga yunwa ga damuwa ga ciwon mara, falo ta dawo ta kwanta cikin kujera tana hawaye, a lokacinne taji ana ƙwanƙwasa ƙofa.
Tashi tai bayan ta ciri tissue dake saman center table ɗin falon ta goge hawayenta taje ta buɗe, ƴan uwan mahaifiyartane da sukazo buɗar kai.
Matsa musu tai suka shigo tana musu sannu da zuwa, su dai sai binta suke da kallo.
Duk da sunsha mamakin ganinta ita kaɗai a gidan sai basuce komaiba, yanda akasan amarya da farin jini sun zata kodai dangin mijinta sa iske wasu a ciki, duk da dai sun kula ƴan gayune kowa rayuwarsa yake babu ruwansa data wani, kuma yanda mijin nata yake firi-firi babu alamar kunya a idonsa ma ya hana kowa raɓarsu.
Yanayin da suka ganta wujiga-wujiga basu kawoma kansu tana cikin damuwa baneba, ca suke kawai dai angone ya mori amarcinsa musamman lura da yanda take tafiya da sukayi, ita kuma ciwon marane ya sakata tafiya a dudduƙe😣🤭.
Bata iya faɗama kowa halin da take cikiba har suka gama hidimarsu bayan la'asar sukai shirin tafiya, a lokacin kuma motar ma'aruff ta shigo cikin gidan.
Ya fito daga mota sai wani tsume fuska yake tamkar baiga waɗanda suke a gidanba, kamarma zai wuce bazai gaidasu ba sai kuma dai miya gani oho masa, ya tsaya ya gaishesu cikin rashin girmamawa ya wuce abinsa.
Wannan abu kuwa ya saka kowa a cikinsu yaye baki suna binsa da kallo harya shige, ita kanta Samina abin ya sosa mata rai.
Su dai duk sun tafi zuciya a saɓule, yayinda wasu suka gumtsi abin faɗa da yaɗawa kuwa.
Samina na shiga falon taci karo da Ma'aruff tsaye yana cika yana batsewa, harara ta zuba masa tana jan tsaki zata wucesa.
Baice mata komaiba ya fisgi hannunta ya jata ɗakinsa saikace wata abun banza, saman gado ya wurgata kawai ya afka mata.
Sosai Samina taji warin giya a jikin Ma'aruff, hankalinta yay matuƙar tashi, duk da a buƙace take dashi sam batajin daɗin yanda yake mu'amulantarta yanzu, ga warin giya ya addaba ma, tsabar baisan abinda yakeba kuma danna mata bakinsa kan nata, yunƙurin amai samina ta fara tana kuka wiwi, Ma'aruff ya cire bakinsa jin zatai masa amai yako kaftama fuskarta mari.
Kuka mai tsuma rai Samina ta saki, dama gashi da mugunta yake kusantarta saboda baisan ina hankalinsa yakeba, kuka take tana roƙonsa yayi haƙuri, ta tuba.
Cikin maye yace, “Ba ke kike buƙatata tun jiyaba, dan uwarki kin samu ma shine zakimin yanga” ya ƙare maganar yana sake kafta mata marin daya sake gigitata.
Yana samun nutsuwa kuma ya kwarayo mata amai a jiki mai azabar wari ya koma gefe yana sauke numfashi...............✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*_GDW_*
*(25)*
..............Samina ma aman ta shiga kwararawa.
Ma'aruff ya tashi zaune da ƙyar yana faɗin, “Kai wai k dan uwarki amai kikemin ma a ɗaki? To aiko saikin shanyeshi shegiya sauran titi, ƙilama bani kaɗai kike baiwa ba” ya ƙare maganar yana kai mata wani bahagon bugu.
Dan wuyama Samina yanzu kasa kukan tayi, babu ko ɗigon tausayinta a ranshi ya tashi yashiga lakaɗa mata duka, ta ƙwaci kanta da ƙyar zata gudu, yace wlhy idan ta fita sai ya mata mafiyinsa tazo ta gyara masa gado da ɗaki, uwartace zatazo ta goge wannan aman?.
Dole Samina ta tsaya dan duk a birkice take, ga tsoronsa ya kuma tasiri mata arai, tana kuka ta nannaɗe zanin gadon, shiko yana tsaye ƙyam a kanta da belt ɗin wandonsa.
Haka ta haɗa ruwan morping tazo ta tsaftace gadon zuwa tsakar ɗakin, Ma'aruff kuwa na tsaye a kanta, sai da yaga komai yay masa need sannan yace ta haɗa masa ruwan wanka, kuma saita wanke bayin, danshi ya kula wai batada tarbiya, toshi zai koya mata tasa a gidannan😂🤭.
Duk uban aikinnan da Samina keyi a bubbuɗe take tafiya saboda ɓarnar da Ma'aruff yay mata na afka mata, duk yanda yakeso haka tayi, tana hawaye harta kammala komai ta saka masa wankakken zanin gado ta feshe ɗakin da air parishioner.
Zata fice ya kuma dawo da ita, “K dan uwarki juyo bayanki, ubanwa zai wanke miki wannan zanin gadon? Zoki ɗauka karkuma kibari na tashi barci na ganshi da dattin nan”.
Dawowa tai ta ɗauka ta fita dashi tana sharar ƙwalla.
Shiko yaja tsaki yana nufar ban ɗaki, koda yayo wanka zuwa yay ya kwanta abinsa, barci mai nauyi kuwa ya sacesa hankali kwance.
A ɗakin tama data koma kuka taitayi rurus, ga warin zanin gadon dana giyar daya goga mata ya addabeta, dole ta ajiye batun zaman kuka gefe ta miƙe ta hau wankin zanin gadon hanci a toshe, sai da ya fita fes ta ajiyeshi gefe itama ta fara tsaftace nata jikin, ta shiga ruwan zafi kozataji nutsuwa akan baƙar muguntar dayay mata.
A daren jiya ta wahaltu da buƙatarsa, sai gashi bata samu nutsuwar fitar abinda ya dametanba saima baƙar wahala data shawo, wahalar kuma ta mantar da ita buƙatar da take ciki gaba ɗaya.😣⛹♀
Tsakar gida taje ta shanya zanin gadon da ƙyar, ga yunwa nacin hanjin cikinta, ga damuwa, kayan cincin da aka kawo mata na gara wanda mama gaje tai bajintar yi saboda za'a kawo ƴa gidan masu kuɗi Saminar ta ɗiba, sai dai kuma tuno warin aman Ma'aruff da haɗa bakinsu da yayi ya faɗo mata a rai, saurin ture filet ɗin tai gefe saboda sabon amai da taji yana zuwa mata.
Kanta ta dafe tana hawaye da faɗin, “Nashiga uku ni Samina, wace rayuwace na jefo kaina a ciki?”..
Bata da mai bata amsa dan haka ta cigaba da raira kukanta a falon.
“Masu karatu ban saniba ko kuna da amsar bata”💁🏼♀️.
Ni dai Bilynku bani da🤩🤪⛹♀⛹♀⛹♀
★★★★
Ma'aruff bai farka ba sai kusan tara na dare, normal ya miƙe, yay wanka yay shirinsa mai nuna alamar na fitane, a falo yaci karo da Samina dake kwance a galabaice ko sallar la'asar, magriba, isha'i bata samu yinsu ba saboda rashin ƙarfin jiki, yunwa tacita ta cinye.
Tsayawa yay kawai yana kallonta da mamaki, “Lafiyarki kuwa?”.
Ganinsa cikin hankalinsane ya saka Samina tunanin roƙonsa kozai tausaya mata, ta miƙa masa hannu tana fashewa da kuka.
“Dan ALLAH ka taimakeni kar yunwa ta halakani”.
Tsabar rashin mutunci irin na ɗan giya dan baisan yama aikata mata duk wancan abunba sai ya riƙota yana faɗin, “Wai dama bakici abinciba?”.
Ganin ya amshi abun da muhimmanci Samina ta kuma langyare masa tana fashewa da sabon kuka, kwantar da ita yay yana miƙewa, “Kinga ina zuwa”.
Samina ta bisa da kallo harya fice, batai zaton zai dawoba, dan kusan awa ɗaya sannan sai gashi da abinci ya kawo mata, shine ya tadata zaune ya fiddo mata daga leda ya bata, jikin Samina har rawa yake taga abinci, aiko ta fara masa cin hannu baka hannu ƙwarya kamar bata taɓa cin abinciba a duniya, tana gamawa ta miƙe da gudu xuwa banɗakin falon ta shiga yin amai saboda yunwar data gama cinye mata hanji.
Da kallo kawai Ma'aruff ya bita amma ko gezau baiyiba ballema ai tunanin zai bita ya taimaka mata.
Yana wajen zaune ta dawo tana tafiya da ƙyar da fidda huttan numfashi suma da ƙyar ɗin, kujerar ta koma ta kwanta.
Ma'aruff ya kalleta aɗan yatsine yace, “Lafiya dai ko?”.
“Amai nayi” tafaɗa a marairaice.
“Tofa, to ALLAH ya kiyaye, kibar zama da yunwa dan yanzu kinga sakamakon ta”.
Da mamaki ta kallesa hawaye wasu na korar wasu, “Hakama zakace nabar zama da yunwa bayan kaine sanadin komi, jiya aka kawoni gidanka ashe abinda ka shirya min kenan Ma'aruff? Wannan shine sakamakon son danai maka da sadaukarwa?......”
“K Samina kinga dakata min, mina miki mara ƙyau a gidannan, idan batun abinci kike baga komai nan a kicinba, miya hanaki shiga ki girka? Naga dai gidannan ba baƙonki baneba, idan kuma maganar daren jiya kike nima saikimin uziri, sam babu buƙatar abinda kike ƙulafici daga gareni a sannan, to tayaya kike tunanin zan iya mu'amulantarki yanda kike buƙata......?”.
Cikin katsesa Samina tace, “Eh amma ai ka mu'amulanceni ta hanyar da bantaɓa maka zatoba, yanzu dama ashe kana shan giya?”.
Tsaki yaja yana taɓe baki, “To miye dan ina shan giya? Rayuwatace fa, kuɗina, ra'ayina kuma, please karki kawomin wannan ƙananun maganar dan bazan ɗaukaba”.
“Dolene na maka magana akan shan giya Ma'aruff, domin a sanadinta yau ka dubi yanda ka nema halakani, idan a haka zamu cigaba a gidannan watarana gawata za'a tarar, jiba yanda ka farfasa min jiki da duka, bayan rashin tausayin daka nuna mani da baida banbanci fyaɗe....”
Kansa ya dafe, sai kuma ya ɗaga mata hannu yana faɗin, “Ya isa haka Please, kiyi haƙuri ni bansan na mikiba, kuskure aka samu”.
Tsayawa kawai tai tana kallonsa hawayenta suna sake ƙarfin gudu.
Yace, “Kin tsareni da ido, banace kiyi haƙuri ba”.
Koba komai taji ɗan sanyi a ranta, ta share hawayenta tana amsa masa da “Shikenan ya wuce, amma dan ALLAH Sweet wannan ya zama na farko na ƙarshe, dan ALLAH kabar sha kaji”.
“Shikenan ya wuce, ki ɗauki ɗayan abincin sai ki sake ci kije ki kwanta, ni bara na fita saina dawo”.
Da sauri Samina ta tashi zaune, “Sweet fita kuma? A wannan daren?”.
Kamar bazai kulata ba, mikuma ya gani oho masa ya juyo ya kalleta, “Kinga bawani jimawa zanyiba zan dawo, akwai abinda zanyine, nima fitar ta zamemin dolene”.
Kasa ce masa uffan tayi, sai baki da hanci data saki tana binsa da kallo harya fice.
Hannu kawai Samina tasa a ka ta dafeshi, zuciyarta na zallo tamkar zata faso ƙirji ta faɗo ƙasa dan tashin hankalin da take hange a gabanta.......
____________________________________
Haka rayuwa take juyi-juyi, lokacin da Samina ke cikin wancan tashin hankalin gasu Ahmad kuwa farin cikine mamaye dasu shida ƴar Rumanan sa.
Dan bai fita a gidanba sai bayan sallar la'asar, yayi wankansa yaci gayu cikin ƙananun kaya da sukai masa ƙyau sosai, Rumana kanta ta kasa ɗauke idanunta a kansa, sai satar kallonsa take, da taga zai juyo sai tai azamar ɗauke kanta daga sashensa.
Ɗan murmushi yay yana girgiza kai, ya tako a hankali inda take zaune a saman tabarmar, hannunsa yasa ya miƙar da ita, hannunsa ɗaya a ƙugunta ya mannata da jikinsa, ɗayan hannun kuma ya ɗago haɓarta yanda zasu kalli juna.
“Hajiyata wannan gulmace, ki kalli mijinki kanki tsaye saboda nakine ke kaɗai” ya ƙare maganar da hura mata iskar bakinsa a fuska.
Murmushi tayi idonta lumshe, ya ɗora goshinsa akan nata shima yana murmushin, “Babie R murmushi na miki ƙyau, amma sam baƙyasonyi saikin gadama”.
Idonta ta buɗe dan mamakin zancensa, to shikuma fa daya fita iya ƙin son yin murmushin.
Ɗan mintsininta yayi a hannu, hakan ya sakata sake manne masa a jiki tana ƴar dariya, “Yaya ALLAH da zafi?”.
Shima dariyar yayi yana sumbatar kumatunta, “K ai jarumace Babie R nasan ɗan zafin nan bazai damekiba, bara na ƙara”.
Tai saurin riƙe masa hannu tana dariyar, “A'a wlhy na yafe, naji niba jaruma bace”.
Sakinta yay yana dariya sosai da cewa “Aini nasan inda jarumtar babie na take”.
Rumana datasan inda ya dosa tai saurin rufe fuskarta da ɗan kwali.
“Kiyi tuwo gaskiya na gaji da waɗannan kayan maiƙon, bara naje idan na samu yaro zan aikosa da cefane, idan ban samuba kuma saina ƙarasa gida sai Abu ya kawo”.
“To a dawo lafiya, tunda ni dai an hanani komawa”. Ta ƙare maganar a hankali yanda bazaiji ba.
Sai dai kuma sarai ya jita ɗin, ya dai sharetane ya ida ficewa abinsa fuskarsa ƙunshe da murmushin da su Kausar sukaci karo dashi.
Baiko dubi inda sukeba ya nufi hanyar fita daga gidan, da kallo suka bisa kafin su kalli juna suna taɓe baki.
Maman Ama tace, “Nifa mutanen nan yanzu maɗaukakin mamaki suke bani, munafukan da kamar bazaka saka musu yatsa a baki su cizaba amma yanzu ji salon bariki kala-kala”.
Tsaki Kausar taja tana cigaba da saka lallin da take a yatsun hannunta, tanaji a ranta itace ya kamata ta samu wannan rayuwar soyayyar da take gani wajensu Rumana, dan mijinta duk yafi mazan gidan arziƙi.
Itama dai maman Ama abinda ke ranta kenan, gani take tafisu komai, kuma ta girmesu, ya kamata ace koman su ta dinga sani.
Rumana dai da batasan sunaiba ɗakin ta kuma kimtsowa ta fito itama dan wanke ƴan kwanikan abincin da sukaci, tana zama su Fa'iza na shigowa gidan da cefanen da Ahmad ɗin yace zai aiki, da alama a hanya ya gamu dasu dai, cikin mutuntawa suka gaida su maman Ama dake binsu da kallon ƙurilla suka amshi wanke-wanken Rumanan suka ƙarasa suna hirar data shafesu ba tare dasun damu da su Kausar dasuka kasa kunne suna saurara ba.
Suna gamawa suka koma ɗaki suna baje babin firarsu musamman akan candyn su dake matsowa, dan jarabawa uku kacal ta rage musu su ƙarasa.
Rumana na girki daga ƙofar ɗaki sukuma suna daga ciki ake hirar
harta kammala tayo wanka sannan ta koma ɗakin suka cigaba da shaftarsu.
Sunayin sallar la'asar suka wuce islamiyya abinsu aka bar su Kausar iyayen gulma sunayi, tunda su basu da aikinyi basu kuma kallon matsalolin gabansu saina wani.
Kusan tare suka shigo gidan da Ahmad, dan ya daidaita lokacin dawowar tasune dama, su Fa'iza daga can gida suka wuce, ita kaɗai ta dawo gida, yanda suka shigo tare gidan saika ɗauka tare suke dama.
Rumana ta buɗe musu ɗaki, shi Ahmad ma bai shigaba ya amshi buta yay alwalar magriba ya sake fita.
Yanzu Umm-Rumana ta lura baisan kaiwa dare a waje yanzu tunda ya dawo, idan kinga ya daɗe to zuwa sallar isha'ine zai shigo.
Wani lokacin suyi kallo a wayarsa wani lokacin kuma ma tana karatune shi yana latse-latsen wayar, inda bata ganeba ta nuna masa yay mata ƙarin bayani.
★★★★★
Wannan tafiya dai kam ta zamewa Umm-Ruman alkairi, dan kuwa dawowarsa ta canja tsarin zamansu gaba ɗaya, babu abinda zatacema ALLAH sai dai godiya akan hakan.
Dan yanzu Yah Ahmad hankalinsa baki ɗaya akanta yake, yana ƙoƙarin ƙyautata mata, suci kuma mai daɗi koda dai bamai yawabane.
Gefe kuma ya ƙara mata jarin dubu biyu akan nata nada ta ƙara kayan maƙulashe na yara da take saidawa a gida, wanda a hankali zuwa yanzu yaran anguwar sun gane, sukan shigo su saya.
Satin Ahmad uku yay haramar komawa porthercout, tafiyar tasa tai dai-dai da kammala jarabawar su Umm-Ruman da kwana biyu kacal.
Da farko baba birkicewa yay akan Ahmad bazai sake komawaba, tunda a tafiyarsa ta farko ya saɓa masa alƙawarin zai zo gida da wuri amma baizo ɗinba saida ya kwashe wata ɗai-ɗai har kusan shida, to yanaga idan kuma ya sake tafiya yanzun sai nan da shekara guda kuma.
Ahmad yay magiya yayi roƙo da nuna nadamarsa tare da bayanan da zasu fahimci abinda ya jawo daɗewar tasa a wancan karon amma sunƙi fahimta sam.
Harma ya haƙura da komawar ya kira Nura yace ya tafi kawai sai kuma ana gobe kamar yanda ya shirya Baban yace ya shirya yaje saboda malam yay masa magana akan ya barsa ya koma kawai, dan basusan alkairin dake cikin hakanba, gashi tun a zuwan farko sunga canji daga Ahmad ɗin.
Sai da baba yaja masa dogon gargaɗi akan amma wlhy karya wuce wata biyu.
Ahmad yayi godiya sosai, tun a daren yay musu sallama da abokansa ya nufo gida.
Tunda ya sanarma Rumana maganar tafiyar sai duk tai laƙwas, dan a yanzu tamafi jin zafin rabuwar tasu fiye data farko.
Ganin yanda duk tai la'asar saiya shiga kwantar mata da hankali, tare da kalamai masu sanyi, bayan soyayya mai tsayawa a rai daya nuna mata a wannan daren.
Kiran sallar farko na asuba ya tashi yay wanka, ya kimtsa tsaf sannan ya wuce masallaci, ana idar da salla bai zaunaba ya shigo gidan, duk yayma mazan gidan da suka dawo daga masallaci tare sallama.
Tunda ya dawo Umm-Ruman taki yarda ta kallesa saboda hawayen da takeyi, shi kansa dauriya kawai yakeyi, ya cire sim card ɗaya daga wayarsa ya bar ɗaya, gabanta yaje ya zauna a kan sallayar suna kallon juna, dukda ita ta duƙar da kanta taƙi kallonsa.
Ya haɗiye abu mai ɗaci daya tokare maƙoshinsa tare da kamo hannunta ya riƙe cikin nasa yana murzawa a hankali.
“Haba Babie R, maimakon na samu ƙwarin gwiwa daga gareki saikiyita kuka kuma? Na zaunefa baiga gariba, akwai abubuwa masu muhimmanci a gabanmu, idan ban tashi na nemaba wazai bamu?, maganar karatunki kwanan nan zakiga jarabawarku ta fito, fatanmu kufita da results masu ƙyau, dukda su baba sunce su Fa'iza aure zasuyi inhar mazansu sun amince zan ɗauki nauyinsu kutafi makaranta, dan yanzu anzo zamaninda sai kanada ilimi ake yi dakai, kimin addu'a kinji, namiki alƙawarin insha ALLAHU wannan karon bazan daɗeba zan zo, dan tunaninkima bazai bar zuciyata ta hutaba da har zan iya jan lokaci mai tsayi ban gankiba, nangaba kaɗan duk inda zan saka ƙafa kema taki na wajen, dan bazan iya nisa dakeba sam kinji”.
Ba tare data ɗagoba tace, “Kayi haƙuri yaya na daina kukan, ALLAH ya tsare mini kai aduk inda ka tsinci kanka, ya azurtaka da samun halali mai albarka, ya nisantaka daga haramun komin farincikin da zata kawo maka, ALLAH ya kareka daga sharrin duk wani abu mai sharri, ya baka ikon cika alƙawari a sauke nauyinmu dake kanka”.
Ahmad yay sassanyan murmushi yana sakin hannunta ɗaya ya ɗago fuskarta, hawayen ya share mata yana faɗin, “To kukan ya isa haka ko, nagode da addu'arki gareni”.
Kanta ta jinjina masa tana haɗiye kukan tare da masa murmushi.
“Yauwa Babie na kokefa, ga waya nan insha ALLAHU kullum zakijini karki damu kanki”.
Da mamaki ta kallesa ta kalli wayar, “Yaya yazaka ɗauki wayarka mai tsada ka bani, kaikumafa to?”.
Murmushi yay mata yana shafa fuskarta, “Umm-Ruman duk tsadar wayarnan batakai ko darajar yatsan hannunkiba balle ke kanki tafi ƙarfinki, karki damu ALLAH zai buɗa, insha ALLAHU zan sai koda ƙaramace kafin muga abinda ALLAH zaiyi, kinga zata ɗan ɗauke miki kaɗaici kina ɗanyin kallo idan babu abinda kikeyi kinji, wannan karonma duk abinda kike buƙata Mudanseer zai kawo miki, ga wannan dubu ukun ki riƙe a hannunki saboda wani abun nasan ba iya tambayarsa kikeba dan dukya gayamin komai, ALLAH yay miki albarka kinji”.
Godiya sosai Rumana ta shiga yimasa, farinciki da kaunarsa na sake mamayeta, haka ya mike ya ɗauki ƴar karamar jikkarsa daya saka abinda zai buƙata, itama mikewar tai ta rakosa har soro tana cigaba da share hawayenta.
Har zai fita ya dawo da baya, hannu biyu ya kamo fuskarta ya haɗe bakinsu, kusan minti ɗaya sannan ya saketa cikin sauke numfashi da sarƙewar halshe yace, “zanyi missing ɗinki sosai Umm-Ruman, zanyi missing ɗinki da komanki”.
Jikinsa ta faɗa tana fashe masa da sabon kuka, dan kalmar daya furta tazo matane a bazata, bai taɓa furta mata itaba sai yanzun, bayanta ya shafa yana murmushi, kafin ya janyeta daga jikinsa a hankali ya juya ya fice zuciyarsa na suya.
Rumana ta jingina da bango tana cigaba da kukanta, ta ɗauki kusan minti biyar a wajen sannan ta koma cikin gida..............✍🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*https://youtu.be/HFjVgQVnmn0
*_GDW_*
*(26)*
............Gaba ɗaya yinin ranar haka ta yini sukuku fuska babu walwala, su maman Ama sunyi gulmar harsun gaji, har dare bata iya sakin jikintaba, dan koda su Salima sukazo bata shiga sabgarsuba, tunma suna tsokanarta har suka koma tausayinta da lallashi.
Washe garima dai zuciyarta duk babu sukuni ta tashi, gashi ta gwada Number ɗayan layinsa daya cire amma bai shigaba, hakan ya tabbatar mata dai yana a ƙasa ɗin tunda dama babu waya ya tafi.
Su Salima na gama tayata aiki suka tafi gida, ita kaɗai suka bari tunda yanzu babu makaranta, sai islamiyya.
Kwanciyarta tayi a ɗaki, alwala kawai ke fiddota, abincima ƙin dafawa tai sai shayi ta haɗa tasha ta sake kwanciya.
Kusan bayan la'asarne tana kwance tajiyo hayaniya a tsakar gidan, bata motsaba balle ta fita, dan daga ɗakin tana iya jiyo komai, kishiyar Kausar ce tazo gidan ashe take ciwa maman Ama mutunci akan munafunci data saka Kausar ta ƙulla musu wajen mijinta akan biyan kuɗin makarantar yaranta.
Hayaniya dai sosai har maƙwafta suka shigo, wasa-wasa dai saiga gida ya cika, dan yanda nakeji ana hayaniyar sosai kamar za'a fasan bangon ɗaki kawai ya isheni amsa.
Har sukaci suka tsire bayan mijin maman Amatullah ɗin ya shigo aka raba daƙyar ban leƙaba, sai fatan shiriya da nake nema musu kawai.
Tun daga wannan ranar maman Ama da Kausar suka shiga gaba, babu mai kula wani a cikinsu, nidai nawa kallone, duk da kowannensu yana neman laɓewa ya shigo jikina danya soki ɗan uwansa, sam bana basu fuska nikam, danaga ma abin zai zama takura saina koma yin har wanke-wanke a babbar robata a cikin ɗaki kawai, dama dai shike fiddoni tsakar gidan harna daɗe asamu damata, wani lokacin kuma su Fa'iza keyi.
Ranar da Yah Ahmad ya cika kwana goma da tafiya ina kwance a ɗaki bayan sallar zuhur ina kallon film ɗin da Abu ya turomin a waya kira ya shigo, ɓaro-ɓaro Number Yah Ahmad da yay save da suna *My N2* ta bayyana, wani farin ciki ya kamani, na lumshe idanu ina haɗiyar numfashi da sauri-sauri, kamar maijin tsoron taɓa wayar haka na danna alamar amsawa, kafin nakai wayar kunnena a hankali.
Dagani harshi babu wanda yay magana kusan Seconds goma.....
“Babie R” ya Ahmad ya faɗa a hankali cikin katse shirunmu.
Idanu na sake lumshewa ina murmushi, nima na amsa a hankali da faɗin, “Uhyim Yayana”.
“Har yanzu dai Yayan?” ya sake faɗa cikin sanyaya murya.
Dariyace taso kufcemin yanda yay maganar irin kamar a shagwaɓa ɗinnan, na danneta da ƙyar, amma sai jinai yace, “Dariyama kike mani ko? Babu damuwa zan rama ai nima”.
“Ba dariya nakeba fa Yaya, ina yini?”.
“Badai haƙura zanba saina rama, ina fatan kina cikin ƙoshin lafiya?”.
“Alhmdllh Yaya, sai dai kewarkafa”.
Daɗi ya kama Ahmad jin furucin Rumana, yay murmushi mai sautin da har take jiyowa, “Nima hakan take Babie R, gaskiya kice na dawo gida”.
Dariya Umm-Ruman ta sanya masa, dan yanzun kam ciki shagwaɓa yay furucinsa na ƙarshe, tace, “Tab ai yayana idan ta nice ka dawo da gudu ma, to amma kuma banason ka wahala, kai zamanka ina nan ina maka addu'a”.
“Da gaske Babie na?”.
“ALLAH kuwa yaya” tai maganar da alamun jin kunya.
“Tom shikenan ta hannun damar, yanzu miye labari?”.
“Labarai kam da yawa yayana”.
“To wanne zan samu daga ciki?”.
“Saika zaɓa ka darje”.
Yace, “Inye kaga Ahmad ɗan gatan Ruman, to abani na soyayya”.
Siririyar dariya Rumana tayi tana rufe fuska kamar tana gabansa, tace, “Kai yaya ALLAH sai nake ganin kamar ba kaiba”.
Dariya sosai ta bashi shima, dan haka ya shigayin kayansa, “Wato kamar ba niba ko? To ai kece kika maidani hakan Babie R, shiyyasa nake yaba ƙoƙarin ki, dan na kula da zafinki kikazo dan kin tsare ko ina babu wasa”.
“Nagode Yayana” Rumana ta faɗa tana share hawayen jin daɗi dake silalo mata saman fuska.
“Nine ya kamata na gode miki babie na, yanzu dai ki huta abinki, muna kasuwane, dama nakirane saboda yanzun nan na ɗora layin akan waya, idan muka tashi zan kira kinji”.
“To Yaya ALLAH ya bada sa'a, sai anjima”.
“Okey babu damuwa, amma idan na sake kira karnaji wannan Yayan”.
Murmushi Umm-Rumana tayi, koda ya yanke saita sumbaci wayar tana rungumeta a ƙirji.
Tun daga wannan kiran sai yazam kullum da daddare Yaya Ahmad saiya kirani, nikuma nakan kirashi da safe na gaishesa.
Ɓangaren su Maman Amatullah kuwa sunyi gabarsu ta kusan sati uku suka koma suka sake ɗinkewa kuwa, a raina nace kudai aiki ya sama.
Tunda kuma suka ƙyalla ido suka ganni da babbar waya a hannu duk sai hankulansu ya tashi, a daren ranar muna jiyo Kausar na tafka rigima da mijinta akan sai ya saya mata babbar waya.
Shiko yace baida kuɗi yanzu, idan zatai hakuri da tata tayi, idan bazataiba to saita sayama kanta shidai baida.
Wannan furuci ya kawo musu rigima sosai, dan har cemasa take mijin Umm-Ruman ɗan balaguro da bai kaisa komaiba gashinan ya sayama matarsa tana ɗaga musu hanci a gida da ita, wlhy bazata cigaba da riƙe waya mai madannaiba itama ƴar shafi ɗinnan takeso mai shan jini.
Wannan al'amari ya daɗe yana bani mamaki, da safe koda na gaisheta ƙin amsani tayi, nasan ban mata komaiba dan haka na watsar da lamarinta, ita dai hassada ga mai rabo ai takice.
Ita dayake Maman Ama tafita bariki da wayo sai bata nuna ko a fuskaba, amma abun na sassakar mata rai sosai, da tanada dama saita kaɓe shegiyar wayar waran a ƙasa ta kwararratse muga tsiya.
_______________________________
A sati ukun nan da Samina ta ɗauka a gidan Ma'aruff komai ya gama susuce mata, soyayyar da take tunani yay mata tanadi ko alamarta ba gani takeba, ashe Ma'aruff riƙaƙƙen ɗan giyane, sannan kullum dare sai ya fita ta rasa ina yake zuwa?.
Karfe taran dare nayi zai fice daga gidan, bazai dawo ba sai ɗaya, wani lokacinma ɗayan ta wuce yake shigowa, lokuta da dama kuma cikin mayen giyane, yazo yayta mata amai mai wari, yakumace saita gyara, idan tai masa gaddama ya kusanceta da ƙarfin ƙwanji na tsantsar mugunta ya lakaɗa mata duka dole tayi tana kuka.
Idan gari ya waye kuwa yayta bata haƙuri akan shi baisan yayiba, zata zauna tai masa nasiha yay shiru kamar ya ɗauka, cikin kulawar juna zata taimaka masa ya shirya ya wuce office, idan ya dawoma zaka gansa normal, har ya nuna mata ƴar kulawa suyi ɗan soyayyarsu idan yanada buƙatarta ya sauke nauyi, amma taran dare nayi duk wayon dazai mata yabar gidan ya sanshi.
Gaba ɗaya ta rasa a ina matsalar take?, ga mahaifiyarsa ƙiri-ƙiri take nuna bata sonta, hakama ƙannensa, sauƙinta ɗaya sunajin shakkarsa kuma ba zuwa gidanma sukeba sai idan ta kama dole.
Amarya nayin ƙiba itadai rama tayi, sai wani haske take ƙirjinta ya cika yay fam, ga shegen kwaɗayi dake yawan damunta, sauƙinta ma idan tace ya sayo mata abu yakan sayo, sannan bai rageta a ci da shaba ta kowanne fanni, jin daɗi da kayan more rayuwa na cikin gida komai bata rasaba, dolene idan kazo gidanta ka kirata mai sa'a, sai dai matsalar tanaga farin ciki, dan kuwa kaso ɗaya bisa uku kawai take samu, shima wani lokacin batama samun.
Ƙawayenta fa kullum cikin zuwa suke ganin ɗakin amarya kashi-kashi, kowacce tanaji inama itace cikin wannan daular.
Idan suna ma kansu addu'ar samun ya tata saitai ta kallonsu kawai, dan kuwa kallon kitse sukema rogo.
Ƙannenta ma suna zuwa, hakama dangin mama gaje da ƙawayenta, sauran yaran gidansune dai har yau bataga ƙeyar kowaba, hatta da yayarta binta da suke ciki ɗaya batazo mataba.
A koda yaushe mama gaje da inna mari cikin aiko mata da kayan mata da ƴan ƙulle-ƙullensu na wurin malamai suke, kuma duk tana ƙoƙarin yi, amma ta kula Ma'aruff shegen taurin zuciyane dashi, wani lokacin idan tai wani abu sai taga kamar ya kamashi idan yana kwantar mata da kai, har sai ta fara murna sai kuma komai yazo ya burkuce.
Babu abinda ke ɗaga hankalinta irin shan giyar da yakeyi, ta tsani warinta, ga aman da yake mata mai azabar wari, har kasa cin abinci take idan ta tunosa.
Yau ma dai haka ta tashi batajin daɗin jikinta sosai, ta daure da ƙyar ta haɗa masa breakfast duk dan ta sakashi farin ciki, ga kuma maganin da inna Mari tace ta zuba masa wai zai ƙara lalacewa a kanta, duk dai tayi yanda akace tazo ta jere abincin a dani.
Da taimakon dattijuwar mai aikinta ta gyara gidan, dayake ba anan take kwanaba, zatazo da safe ne da yamma sai ta koma gida.
Hakanne ya ƙara kawoma Samina rufin asiri har yanzu babu wanda yasan halin da take ciki na ƙunci game da halayen Ma'aruff, danta daure ko mama gaje bata sanarma ba har yanzu.
Wanka taje tayi tai ƴar kwalliya dan sam batajinta dai-dai, dama dai tunma tana gida ba isashshiyar lafiyarne da itaba, tana daurewane kawai a zatonta zirga-zirgan bikine, to yau dai sosai takejin ciwon a jikinta.
Ɗakin Ma'aruff ta shiga, yana kwance cikin bargo yana kwasar barcin da giya ta haddasa masa, tunda tazo gidan kullum sai ta tashesa da safene yakeyin sallar asuba, to sanda ake sallar shi hankalinsa bai gama dawowa jikinsa ba ta ina zaiyita?.
Yanzunma da ƙyar ta iya tadashi dan kar yayi lattin Office, ya tashi yana mata masifa, da yake harta fara sabawa sai batace komaiba ta taimaka masan dai har bayi inda ta haɗa masa ruwan wanka.
Bayan ya shiga dawowa tai da nufin ta gyara masa ɗakin kamar yanda ta saba amma sai hakan ya gagara saboda jiri dake kwasarta, dole ta duƙa gaban gadon ta kifa kanta kan gadon.
A wannan yanayi Ma'aruff ya fito ya Sameta, kamar zai shareta sai kuma ya matso yana yarfa mata ruwan hannunsa, “K lafiyarki kuwa? Kina zaman miye da baki gyara ɗakinba? kinsa na fito inata taka datti”.
Samina bata iya bashi amsaba, bakuma ta ɗago ta kallesa ba, shima saiya watsar da ita yay haramar yin sallar asuba, lokacin takwas ma fa ta wuce🤦🏻♀.
Yana cikin yin sallarne Samina tai baya yaraf ta faɗi.
Saurin idarwa yay ya matso yana taɓata, jin ta suma sai abun ya bashi mamaki, ya shiga kiran sunanta yana murza tafin hannunta, amma ina ko motsi bataiba, ruwa ya tashi ya ɗebo a gaggayce ya yayyafa mata, sai lokacin ta kawo numfashi, “Lafiyarki kuwa? Miya sumar dake haka?”.
Da ƙyar Samina ta buɗe baki tace, “Sweet banda lafiya wlhy”.
Hannu ya aza bisa wuyanta, yaji zafi sosai, “Tabbas ga jikinki da ɗumi ma, ni saima yanzu na lura kin rame da yawafa, baƙya cin abince halan?”.
Murmushi kawai Samina tayi tana haɗiye kukan da yake shirin taho mata, shi tunaninsa abincine ke kawo ƙiba kawai babu kwanciyar hankali?.
“Kinmin shiru ina miki magana?”.
Kallonsa tayi, sai kuma tayi murmushi tana girgiza masa kai, “Inaci mana”.
“Shikenan bara na shirya muje asibiti, idan kuma bazaki iyaba bara na kira Adam ya dubaki kawai”.
“Ka kirashi ɗin to kawai”.
Kamata yay ta koma saman gado ta kwanta, shikuma ya ɗakko wayarsa ya kira abokinsa Adam daya kasance likita.
Kafin Adam yazo ya gama shirinsa na fita, a ɗakin ya barta yaje yaci abincin data shirya a dani ɗin, yana tsaka dacin abincinne Adam ya iso.
Bayan sun gaisa ne yayma Adam ɗin tayin abincin amma sai yace yayi breakfast shi.
Umarnin shiga ɗakinsa kawai ya bashi yaje Samina na can, babu wani alamar nuna kishi koda a fuskarsa, cigaba ma yay dacin abincinsa hankali kwance Adam kuma ya shige ɗakinsa.
Samina na kwance Adam ya shigo mata saƙaƙa babuko sallama, wannan abu ya sosa mata rai, ta kumaji zafin Ma'aruff, domin dai ya nuna bama ya kishinta matsayinta na matarsa ta sunna, tsabar takaici ma saiga Adam zaune ɗane-ɗane a bakin gadon da take kwance, sirrinsu kuma dukda bata taɓa kwana a kansa ta daɗin raiba.
Haushin hakanne ya sakata ita ta sauka ƙasa, amma ko a fuska Adam bai nuna ya damuba, saima tsokanarta da cewar “Amaryarmu kinsha ƙamshi”.
Murmushin yaƙe kawai tai masa.
Tambayoyi ya shiga mata, yanda take bashi amsane ya sakashi kafeta da idanu, daga ƙarshe ya bata tsinken gwajin ciki yace taje tayi.
Bata musaba taje tayo yanda yace, ta fitone ta iske Ma'aruff ya shigo, yana zaune kusa da Adam suna magana, sai dai ta lura kamar Ma'aruff ɗin a rikice yake, tsinken ta miƙama Adam ta koma kan sofa ta kwanta.......
“My friend da gaske fa akwai cikin nan”.
Wata zabura Ma'aruff yayi yana faɗin, “Kai bazai yuwuba Adam, duka yaushe akai aurenma da za'ace ta ɗauki ciki?”.
“Kaga Calm down Please, bara na ɗiba jininta yanzu zanje na dawo”.
Ma'aruff baice komai Adam ya ɗiba jinin Samina da suka ɗaure mata kai tama kasa cewa komai balle tunanin inda suka dosa.
Tunda Adam ya tafi Ma'aruff ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai kai kawo yake a ɗakin, ita Samina ma barci ya kwasheta a wajen.
Ba jimawa kuwa sai ga Adam ya dawo, tun a yanda Ma'aruff yaga fuskar Adam ɗin ya tabbatar akwai dai cikin.
Adam ya miƙa masa result ɗin, jikinsa har ɓari yake wajen amsa ya duba.
Takardar ya jefar a tsawace yace, “Impossible Adam, cikin wata biyufa!!?”.
Yanda yay maganar a tsawace ne ya farkar da Samina mai barci, a kunnenta yake faɗin,
“Ai koda cikinnan a gidan nan ta samesa ba'a wajeba wlhy ban shirya haihuwa yanzuba ballema ɗan shege, dolene a zubar dashi yanzun nan”.
Sosai Samina ta ƙwalalo idanu waje, “Sweet wace irin maganace wannan haka kakeyi? Ni dai to baza'a zubarmin da cikiba inason kayana, tayaya za'ai mu ɗauki laifi biyu bayan na zina kuma ga kisan kai?”.
Harara ya maka mata yana sake harzuƙowa kamar zai maketa, “Ke dabbar inace da baki fahimtar abinda muke faɗa?, kina tunanin zan bari ki haifa mana ɗan shege ne a cikin zuri'armu ki gurɓatata? To idanma barci kike ki farka wlhy, ɗan halak ɗinma ban shirya amsaba balle na shege, inhar wannan cikin nawane bawani daban yayisaba dolene a zubar dashi....?”
Da sauri Samina ta katsesa da faɗin, “Kamarya ba wani yayisaba? Bayan kai na taɓa mu'amula da wanine?”.
“Ubanwama yasani ko kin taɓayi ballagaza, tunda har kika iya bani wanima zaki iya bashi ai, ciki dai ko uwarki mai kwaɗayinan tazo nan bata isa hanashi yabi sokawe ba yau dinnan”.
Hawaye masu ɗumi suka shiga bin kumatun Samina, ta nuna Ma'aruff itama tace, “Wlhy sai dai uwarka mai baƙar zuciya......”
Jikake “Tatasss!!” saukar lafiyayyen mari a kumatun Samina, ta dafe kuncin tana sake fashewa da kuka.
Adam dake kallonsu yay saurin riƙe Ma'aruff dake zaro belt ɗin wandonsa.
“Kaga ku nutsu dan ALLAH karka taɓata”.
“Adam in bartafa kace?, wannan karuwar gidance har ta isa ta zagarmin uwa dan ubanta?”.
“Nasan batai dai-daiba, amma dan ALLAH ka barta muyi kawai abinda ya dace, kekuma tunda yace bayason cikin kibari kawai a zubar dan ALLAH a zauna lafiya, lokacin daya shirya na tabbata bazai hana ki haihu ɗinba.......”
“Dawa zan haihu? Bar wannan saɓon dan ALLAH Adam, ai babu tsarin haɗa zuri'a da wannan ballagazar yarinyar a daga gareni, haka kawai a haifamin ƴaƴa masu bin maza, saboda ƙwaɗayifa tabar saurayin daya gama mata wahalar duniya kuma ɗan uwanta, tokai ta yaya zanyi fatan tazama uwar ƴaƴana a haifamin fanɗararru waɗanda idan nace ga yanda nakeso suce bazasuyiba, saboda haka uwarsu taima ubanta itams”.
“Ya isa haka dan ALLAH, haba MJ”.
Shiru Ma'aruff yay yana ƙwafa, ya nuna Samina dake kuka rurus saboda baƙaƙen maganar daya jefa mata yana faɗin, “Garama ki tsaya da arziƙi, dan wlhy inba hakaba dukan mutuwa zan miki kuma a zubar da cikin”.
“Sai dai ka kasheni, amma bazan yarda a zubarmin da cikib......”
Maruka biyu ya sauke mata a lokaci ɗaya, nanma sai da Adam ya riƙeshi yana bashi haƙuri sannan.
Adam ya haɗa allurar dazai mata, Samina naji na gani Ma'aruff ya matseta Adam ya danna mata allurar zubda ciki, tana wani kuka mai tsuma ran mai saurare.
Mintuna sha biyar kacal dayin allurarnan jini yaɓalle kuwa.
Tun tana sanin halin da take ciki har ta rasa jinta da ganinta baki ɗaya.............✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*_GDW_*
*(27)*
..............Jini sosai ya ɓallema Samina, abinda ya tsorata su Ma'aruff kenan suka ɗauketa zuwa asibiti, gaggawar fara ƙoƙarin shawo matsalar Aliyu ya farayi, da ƙyar aka samu komai ya dai-daita bayan baƙar wahalar da yasha.
Ma'aruff sai jan tagwayen tsaki yakeyi, ya kasa zaune ya kasa tsaye har sai da Adam ya fito sannan.
Kwantar masa da hankali yayi akan an samu dai-daiton komai, yanzu haka zasu kai Samina ɗakin hutune.
Numfashi ya sauke a hankali, sai lokacinne ya tuna da batun aikinsa, waya ya ciro yay kira Mama gaje ya sanar mata akan tazo asibitin ta samesu.
Hankalinta ya tashi sosai, da yake batasan ina zata gano asibitinba saboda private ne sai ta tasa ƙanin Rumana gaba Kamalu suka tafi dan ya rakata, bata sanarma kowaba saboda a ƙofar gida ta gamu da Kamalun ta iza ƙeyarsa suka tafi.
Koda suka iso suna gaisawa da Ma'aruff ya kaita ɗakin da aka kai Samina sai yay mata bayanin ɓari Samina tayi, daga haka yay musu sallama ya tafi akan shi zaije Office ne saiya dawo.
Yanda Samina ta rame ya tadama mama gaje hankali, amma data tuna ɓari akace tayi saita danganta ramar da kwaikwan ciki, sai dai a ƙasan ranta tana mamakin miyasa Samina bata taɓa sanar mata ta samu cikiba koda wasa? Yanzu kuma auren sati uku ne har an samu cikin da zai iya zubewa?.
Batai zurfi a wannan tunaninba ta watsar da shi gefe kawai ta ɗakko wani.
Kamalu shine ya koma gida ya sanar musu Samina na asibiti babu lafiya, kowa yasha mamaki, amma da yake ba biyema shirmen mama gaje sukeba sai sukai shirin zuwa su dubata.
Yayinda yaran gidan suka fara tafiya kaima yayyensu na ma'auri labarin.
Harsu Ayyah sukazo duba Samina asibiti tana barci bata farkaba, kowa yayi mamakin ganin ramar da Samina tayi a sati uku da aure kacal, hakama zancen ɓarewar ciki ya tsayama kowa a rai.
Ammi ce kawai data daɗe da fahimtar Samina nada shigar ciki tun tana gida abun bai bata mamakiba, sai dai tana tausayin mama gaje akan ƙarancin rashin kulawa da saka idanu akan yaranta.
Basu baro asibitinba sai gab da magriba, har zuwa lokacin kuma babu ko ɗaya daga dangin mijin Samina daya leƙo, shima kansa Ma'aruff ɗin bai dawo ba, sai Inna mari da Iya da sukaje, sai ko dangi ɗai-ɗai irin na kusa da labarin yaje musu suma suka ɗan lalleƙo.
Har zuwa lokacin kuma Samina nata barci bata farkaba, su dai sallama sukai musu suka taho akan sai kuma gobe idan ALLAH ya kaimu, dan malaman asibitin sun fara maganar sunyi yawa, da sun tsaya har sai Saminar ta farka suma.
Bayan dawowarsu gidane suma su Baba suka tafi duba Saminar, sun isa babu jimawa ne ta farfaɗo.
Da ihu da fisge-fisge Samina ta farka, sai ambatar sunan Ma'aruff take akan itafa tanason cikinta karsu zubar mata, babu wanda bai shiga ruɗaniba, su sam sunma kasa fahimtar mi Samina ke faɗa.
Dr Adam yace duk su fita daga ɗakin Please.
A daidai wannan lokacinne kuma Ma'aruff ya dawo, daka gansa zaka san hankalinsa kwance, kuma daga gida yake, dan bakayan ɗazun da safe banema a jikinsa, babu tausayi ya wankama Samina dake cikin halin rashin sanin mi takeyi mari,
“K dan ubanki duniya kike faɗama yanda aikai ne?”
Da sauri Adam ya janyesa yana masifa, “Wai kai MJ mike damun kankane? Yarinyar dama batasan ina a hankalinta yakeba kakema wannan Marin? Kaji tausayin halin da muka sakata mana, wlhy badan tanada sauran shan ruwaba a ɗazun zata iya rasa ranta, kai baka da wani abin birgewa sai dukan mace? Wannan fa matarkace ta sunna ba matan banza daka sabama wannan rayuwarba, Mtsoww, baka sha giyarba ma rasa hankalinka ake......”
A fusace Ma'aruff ya dakatar da Dr Adam, “Malam karka faɗamin babu daɗi mana, bansan shishshigi kaima ka sani”.
Banza Dr Adam yay masa, ya shiga ƙoƙarin ganin Samina da numfashinta ke fita da ƙyar bama taimakon gaggawa, dole dai allurar barcin ya sake mata saboda sam bata a cikin hayyacinta, a ƙasan ransa yana dana sanin biyema Ma'aruff akan wannan aikin.
Acan waje kuwa su mama gaje na iya jiyo hayaniyar su Ma'aruff, sai dai basajin mi suke faɗa, tuninsu ma duk ruɗewar halin da Saminar ke cikine ya jawo hakan, hakan yasa suma suka sake rikicewa ainun.
A fusace Ma'aruff ya fice daga ɗakin, ko kallon su Baba dake wajen dasu mama gaje baiyiba balle su sami mutuncin a gaishesu, su duk ganinsu halin da matarsa ke cikine ya sakashi a ruɗani🥺.
Basusan ma yana fita daga asibitin zuwa yay ya tanaji giyarsa ba tare da tsaleliyar budurwa suka nufi gida, tunda yau babu Samina a cikinsa anan zai warwasa abinsa😢.
★★★★★★★★★★★
Ina bakin rijiya zaune ina wankin ƙarfin hali saboda kaina dake mani wani azabar ciwo, gaba ɗaya kwanakinnan haka nake fama da wannan ciwon kai, abinda kawai nasaka a raina basir ne yaymin mugun kamu da malleriya, sallamar yaran gidanmu ta sakani ɗago idanu na kallesu, ni kaɗaice dama a gidan, Kausar taje asibiti wai yaron cikinta na dawo mata a ƙirji, maman Amatullah kuwa tana gidansu sunan ƙanwarta data haihu, su Fa'iza kuwa tun da safema suka tafi gida yau.
Sallamarsu ta amsa fuskarta dai babu walwala.
“Ku kuma daga ina? Da wannan tsakar ranar khadija?”.
“Yaya Rumana daga gida mukefa, Yaya Samina ce bata da lafiya tana asibiti”.
Ajiye hijjab ɗin danake cuɗawa a cikin ruwan kumfar nai ina faɗin, “Ya salam, miya sameta haka?”.
“Muma bamu saniba, amma dai su Ammi ma duk sunacan sunje dubata”.
“Wayyo, to ALLAH ya bata lafiya, zan kira Yah Ahmad kuwa nasamu zuwa anjima naje na dubata”.
Haka Rumana ta cigaba da wankinta su khadija na tayata da hira, duk da ma ita ba saka musu baki takeba dan kanta dake ciwo, da yake wankin baida yawa dan danan ta kammala, tana share ruwan wajen Kausar ta shigo tana ɗaga ƙafa da ƙyar saboda ciki, duk da yanzu bata min magana hakan bai hanani mata sannu ba.
“Uhumm” kawai tace min ta buɗe ɗakinta ta shige.
Ban damuba, nima na haɗa robobin danai wankin na nufi nawa ɗakin, muna shiga na bama su Khadija kantu daya rage a kayan sana'ata nace suje gida kar'a nemesu, dan nagaji da surutunsu nikam.
Da murna suka amsa suka wuce, nikuma na shiga duba magani dan nasha sai dai ma ashe ya ƙare, ƙaramin tsaki naja na haye gado na kwanta kozan samu sassauci.
Ring ɗin wayartane ya tasheta daga nannauyan barcin datai nisa a ciki, ta kai dubanta ga agogon ɗakin tana ƙoƙarin lalubo wayar a ƙasan filo.
Ƙarfe biyar na yamma, agogon ya nuna, tashi nai zaune a rikice dai dai na gama ciro wayan, Yaya Ahmad ne, kafin na ɗagama ta tsinke.
Ina ƙoƙarin sakkowa ya sake kira, dakatawa nai na ɗaga ina kaiwa kunne.
“Kina lafiya kuwa? Tun ɗazun nake kira amma babu amsa”.
Cikin yanayin wanda ya tashi a barci nace, “Kayi haƙuri Yaya, wlhy barci nake”.
Daga can yace, “Barci kuma? Lafiya dai ko?”.
“Lafiya ƙalau, kaina ne kawai kemin ciwo dan wankima na gama”..
“Na rasa wannan ciwon kai na miye haka? Kusan kullum yanzunfa sai kinyi?”.
“Wlhy kuwa Yaya, amma karka damu inaga basirne, zan aika iya ta bani magani”.
“ALLAH ya ƙara sauƙi, yanzu kinsha magani ko?”.
“A'a maganin ya ƙare, jira nake anjima idan Yah Mudan yazo sai ya sayo mani”.
“Bara kawai na kirashi sai ya kawo miki yanzun, ina zama da ciwo yaga daɗi”.
“To Yaya na gode, itama Yaya Samina ma bata da lafiya”.
Shiru yay kamar bai jitaba, hakan yasa tai tunanin baijinba ta sake maimaita masa.
Cikin halin ko in kula yace, “ALLAH ya ƙarama kowa lafiya”.
“Amin yaya, ammafa abin serious ne fa, dan tanama asibiti, na shirya naje na dubota dan ALLAH?”.
A hasale yaja tsaki yana faɗin, “Malama kiji da naki ciwon kinji, inada abunyi sai anjima” ƙit ya kashe wayarsa.
Shiru nayi a wajen tamkar ruwa ya cinyeni, na zame wayar a hankali ina kallonta kamar zan hangosa ta ciki, dama tun jiya nasan haushina yakeji saboda su Fa'iza sunce zasuje gidan Yaya Samina, nima saina tambayesa dan naje nagano ɗakin amarya daga nan mu wuce gidan sunan ƙanwar maman Ama da akeyi.
Aiko naci masifa, dan Yah Ahmad na asali dana sani ya komamin, tamkar zai jawoni daga wayar ya daka, daga ƙarshe ya kashe wayarsa ma baki ɗaya, na gwada kira yafi sau hamsin amma switch up, ni kuma yanzu sam banyi zaton abin zai ƙara ɓata masa raiba tunda dai ciwo akace.
Damuwa fal raina na tashi na fita, dan ko sallar la'asar banyiba, tsakar gidan shiru kamar babu mutum, dama dagani sai Kausar ne, mai raya gidan maman Ama ce kodan saboda ƙiriniyar yaranta.
Bayan na idar da salla na ɗauki waya na kirashi, amma harta yanke bai ɗagaminba, na kuma kira ban gajiba, sai da na jera masa kira goma sannan ya ɗaga.
A hasale yace, “Ke wai bakisan ina kasuwa bane? Idan kika takura min da maganar nan zan ɓata miki rai wlhy”.
Bai jira ma mizan ceba yanzun ma ya sake yanke min wayar, hawaye masu ɗumi suka shiga rige-rigen fitowa a idanuna suna silalowa bisa kumatuna, ni bansan lokacin da ya farama Yaya Samina irin wannan baƙar tsanarba? nima dai na shagala wajen mantawa murɗaɗɗen halinsa ne, darajar aurenmu yasa na fara ganin haƙoransa a waje, suma ɗin a wannan zuwan.
Zamewa nai na kwanta ina cigaba da hawayena.
Sai bayan isha'i yau su Salima sukazo, dan sune ke a gidan saboda su Ammi sunje duba Yaya Samina a asibiti.
Yanda suke bani labarin halin da Yaya Saminar take ciki sai tausayinta ya kamani, na mata addu'a dan nasan tunda yace bazan jeba to bazanje ɗinba, dan sunan ƙanwar Maman Ama da yace bazanjeba jiya gashi banje ɗinba.
Sai da zan kwanta ne danaga har lokacin bai kiraniba nai masa text message na ban haƙuri da kalamai masu sanyi na tura masa.
Haka na kwanta cikin damuwa, da ƙyar barci ya ɗaukeni kuwa, dan ya sabamin duk dare ko bazamuyi hira mai tsaho ba dai zamu gaisa yaji lafiyata naji tashi kafin na kwanta.
Da safe ko da su Fa'iza sukace na shirya muje dubota, canai musu suje kawai banajin daɗi, danma karsu zargi wani abu sai nace jiri nake gani.
Sannu sukaita jeramin kafin su wuce, nace suce ina gaisheta dan ALLAH.
Bayan wucewarsu na ɗauki wayata na sake dubawa, a zatona ko zanga reply ɗin Yah Ahmad, amma sai naga wayam, tagumi nayi na zubama wayar ido kawai.
Duk da motsin Kausar da nake jiyowa a tsakar gida ban fitaba sai da zanyi sallar zuhur, dan kafin su Salima su wuce komai sunmin har ɗibar ruwa.
Banga Kausar a wajeba yanzun, ta shige tuni, na laru dai batajin daɗi kwana biyunnan, ɗakinta na nufa nai sallama, sai da nayi kusan uku sannan ta amsa min, ban damuba na shiga ciki, kwance take a ƙofar ɗaki, ɗakin kaca-kaca babu gyara, na zauna a kujera ina mata sannu da tambayarta yaya jikin?.
Nanma da ƙyar ta amsamin cewar da sauƙi.
Duk da nima ba ƙarfin nakeji ba haka na tashi na fara kimtsa mata ɗakin, dan yayi datti da yawa, da alama dai tama daɗe batai gyaransa ba, wanke-wanke kansu cike da babbar robarta ta tara, bayan na gyara gadon nace ko zata koma can.
Bata musaba ta yunƙura zata tashi amma ta kasa, taimaka mata nai ta miƙe ta koma saman gadon, nikuma na ƙarasa kimtsa ɗakin harda morping duk nai mata, na kwashi wanke-wanken na fita dasu.
Har la'asar ina ma Kausar hidima, sai da naga komai yayi fes sannan nace mata ta daure tayi wanka zataji ƙarfin jikinta, kanta ta ɗagamin kafin ta fara jeramin godiya.
Nai murmushi da faɗin babu komai karta damu, koda na fito nai alwalar la'asar ɗaki na koma, ban sake fitowa ba sai da Maman Ama ta dawo gab da magriba.
Sannu da zuwa nai mata tare da ALLAH ya raya, na kuma bata haƙuri akan rashin ganina da bataiba.
Ta ɗanyi dariya tana bina da kallon ƙurulla, “Babu komai Amarya, ai dole nai miki uziri tunda ban saniba ko ogane ya murɗa kambunsa, dan ba kasafai suke son yawan fitarba”.
Murmushi nai nace, “A'a bama shi bane, kawai dai jiya na yini ne da ciwon kai wlhy”.
“Ayyah, to UBANGIJI ya ƙara lafiya”.
Da Amin na amsa ina tsokanar Amatullah dake cin biscuit.
________________________________
Ɓangaren Samina kam sai washe gari ta farfaɗo cikin hankalinta, taƙi magana wa kowa sai hawaye, hakan ya saka Inna mari fara mata masifa akan ai ba kanta aka fara ɓarin ciki ba, idan tayi haƙuri ALLAH ne zai bata wani.
Ita dai batace uffan ba, sai da taga ƴan dubiya nata zuwane sannan ta daurema ranta ta daina kukan, sai tsoro ya kamata sosai da lamarin mutane, dan wasu idan akace ɓari tai sukan jinjina maganar, harda masu cewa ikon ALLAH, yanzu cikin sati uku har yakai ai ɓarinsa?.
Wannan furuci da mutane ke yawan yi sai ya fara ɗarsama mama gaje da inna mari shakku suma a ransu, ga mamakin rashin dawowar Ma'aruff asibitin, tun daren jiya daya fita cikin fushin abinda Aliyu yay masa su kuma suka ɗauka damuwar halin da matarsa ke a cikine, sai kuma rashin ganin danginsa da basu zo duba Samina ba.
Koda mutane suka tsagaita zuwa yamma inna mari kasa haƙuri tai sai da tai maganar rashin dawowar Ma'aruff ɗin da rashin zuwan danginsa.
Uffan Sanina dake kwance bata ce ba, duk da kuwa taji mi Inna Mari ɗin ta faɗa sarai.
“Wai Samina bakiji mina faɗa bane halan?”.
Kallo ɗaya Samina tai mata ta janye idanunta gefe, “To idan najiki mizance Inna mari? Naga dai kwance nake anan ta yaya zansan lafiya ko saɓanin hakan”.
“Kefa dama baki da kunya Samina, daga tambaya minene namin baƙar magana dan rashin arziƙi”.
Shareta nanma Saminar tayi, saima ta rufe ido kamar mai shirin barci.
Har suka kwanta babu Ma'aruff babu dalilinsa..........✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻[7/27, 5:12 PM] Jidder 2: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*_GDW_*
*(28)*
.............Yau ɗinma har na kwanta banga kiran Yah Ahmad ba, duk da abin nacin raina haka na danne nima na sharesa kawai.
Washe gari da safe na fito zanyi wanke-wanke sai naji Maman Ama da Kausar na gulmata wai bilicin nake, saboda nayi wani mugun haske fatata har ƙyalli take.
Ni dariyama suka ban, toni tunma ina budurwa bayan basilin zanma iya rantsewa ban taɓa siyan wani mai dan na sama jikina ba, ina naga kuɗin sayen to, sai dai idan munje kamar gidan yayunmu mun ganine mukan shafa wani lokacin......
Maganar Kausar dake cewa, wai jiya da nake mata aiki itafa kasa ɗauke kanta tai daga kallona, saboda nayi ƙiba ga fari, anyama mai nake shafawa kuwa ba allura naje akaiminba na kumasha maganin ƙiba dan ace inajin daɗi wajen miki? Dan inda maine da ƙafata saita nuna, amma dukfa jikinane yay hasken.
Kaina na girgiza kawai ina murmushi, fitarma da zanyi saina fasa na koma ɗaki na kwanta, dama ruwa zan ɗiba.
Bansan lokacin da suka tashi a wannan gulma tasu ba, lokacin dana fito alwala kuwa idanunsu tamkar zasu faɗo saboda kallona.
Ni wlhy zuwa yanzunma rayuwar waɗannan matan tausayi take bani, to ace kai baka kula da matsalolinka ba saina wani, ga nauyin cin naman ɗan uwanka da kullum kake azama kanka?, ALLAH shi kyauta to.
Koda na idar da salla tsakar gidan na dawo nima na fara ƴan ayyukana, kallo kam sukeda lokacin yinsa, nakan ɗan jefa musu baki a hirarsu idan sun sakkoni, amma fa ban saki baki ba kamar wadda bata da aikinyi.
_______________________________
Ɓan garen Samina kuwa dai har yammar ranar basuga ƙeyar Ma'aruff ba, sunma Samina tambayar duniya a kansa taƙi kulasu.
Sai bayan magriba suna shirin kayansu kamar yanda Doctor yace suyi dan zai basu sallama sai ga Ma'aruff yazo, abin mamaki babu wanda ya gasar tsakanin Inna Mari da Mama gaje, sai ma faman hura hanci yake yana wani ɗaɗɗaure fuska.
Mama gaje ko jiki na ɓari take gaidashi, ya amsa a cinkushe babu wani alamun girmamawa agareta.
Wannan abu ya saka Samina tsantsar takaici, shiyyasa da aka sallamesu zasu wuce tace ita gidan Inna Mari take so ta wuce, sai taji ƙarfin jikinta zata koma.
Da farko Ma'aruff yaso yin gardama, mikuma ya tuna oho masa yace taje amma sati ɗaya kacal.
Ta yarda da hakan, maimakon ya ɗibesu ya kaisu gidan a motarsa sai kuɗin napep ya danƙa musu wai shi akwai inda zaije ana jiransa.
Baƙin ciki tamkar Samina ta haɗiyi zuciya ta mutu, amma dai sai batace dashi uffanba.
Tunda suka shigo gida iya keta haba-haba dasu, ita ta dafama Samina ruwan zafi tai wanka dan taji daɗin jikinta, tare da nuna mata dabarun da zata gyara jikinta duk da kuwa ɓari tayi.
Uffan inna mari bata ce dasuba, dan ita abinda Ma'aruff yay musu ne kecin ranta, so take ta gano ina malar take suyi ƙoƙarin gyarawa kafin Saminar ta koma, dan sosai ta fahimci akwai matsala, to kafin mutane su farga gara suyma tufƙar hanci.
Aiko da dare Samina na kwance bisa gadonta, itako tana ƙasa zaune mama gaje ma haka dan bata wuce gidaba wai sai da safe inna Mari ta jefoma Samina tambaya a bazata.
“Anya Samina wannan mijin naki akwai zaman lafiya a tsakaninku?”.
Da mamaki Samina ta kalli inna mari, “Inna miyasa zakimin wannan tambayar?”.
Sosai Inna mari ta kalli Saminar, “K ƴarnan barmin wani ɓoye-ɓoye, fito fili ki faɗi damuwarki kafin ki koma malam ya maido miki shege akan layi, kafin ƴan bakin ciki da sa ido su farga”.
Ajiyar zuciya Samina tayi tana ɗauke kanta ba tare da ta faɗi abinda suke bukatar jinba, bawai bata son faɗar bane, kawai dai tana tsoron faɗarne maganar cikinta ya shigo, kuma inhar zata faɗar sai wannan labarin ya shigo.
Suma ƙyaleta sukai basu sake magana akaiba har kwanaki uku da dawowarta.
A hakanma basuga ƙeyar Ma'aruff a gidanba, gashi tabar wayarta acan gidanshi, kayama da take buƙatar a kawo mata tanaji tana gani sai haƙura tayi.
A kwana na huɗune Inna mari tai shirin zuwa wajen malaminsu, Samina catai zata bita, batai musu ba suka shirya suka tafi tare.
Aiko ranar yini guda a wajen malamin suka yisa, ya haɗo mata abubuwa sosai akan Ma'aruff, na binne-binne da wanda zata bashi yasha ko yaci a abinci.
Mama gaje kuwa a can gidansu Ahmad catai Samina ta koma gidanta, harshi baba Yusha'un abinda tace dashi kenan.
Babu wanda ya damu da bin ƙwaƙwƙwafinta, dan kowama tasa ta ishesa a ɗakinsa.
_________________________________
Tsawon kwanaki huɗu Yah Ahmad na haushi dani akan kawai na tambayesa zuwa duba Yaya Samina, wannan abu nasa ya daɗe yana bani mamaki.
A ranar cikon ta huɗun ina cikin gyara kayana a drawer sai ga kira ya shigo min, bamma kawo shiɗin bane na zata ko Yah Mudan ne.
Ganin sunansa na yawo ɓaro-ɓaro a waya sai mamaki ya kamani, cikin hanzari na ɗaga saboda tana gab da tsinkewa.
A sanyaye nai sallama dan shi yayi shiru da ga can.
Yanda ya amsa da ɗan dama sai naji sanyi a raina, na tambayesa ya kasuwa da jama'a?.
“Alhmdllh, ya jikin naki?”.
Da ɗan murmushi a fuskata nace, “Na samu sauƙi ai Yayanmu”.
Daga can Ahmad ya lumshe ido kewarta na cigaba da zungurinsa, cikin sanyin muryar datai kwana biyu bata jiba daga garesa yace, “Yanzu mikikeyi?”.
Daɗine ya kamani, nai murmushin da nakeji a jikina yayi tasiri a garesa, ƙasa na kuma maida muryata nace, “Ina gyaran kayane Yayana”.
Yaɗan sauke numfashi kaɗan daga can, “Sannu da ƙoƙari” ya faɗa a ƙasan maƙoshi.
Tunda nace yauwa sai mukai shiru mu duka, nice na katse shirun da cewa, “Yaya kayi haƙuri dan ALLAH na ɓata maka rai ranar, insha ALLAH bazan sakeba”.
“Ya wuce”.
Ya bani amsa a takaice, daga nan muka sake yin shirun na wasu sakwanni kafin ya kuma kauda shirin namu da cewar, “Ki zaɓa cikin gidajen su Yaya Maryam ina kikeason zuwa?”.
Wani daɗine ya kamani, cikin zumuɗi nace, “Ko gidan Yaya Maryam ɗinma yayi”.
“Ki shirya sai su Salima su rakaki gobe idan ALLAH ya kaimu kimata yini, saura kukai har dare acan”.
“Na gode Yayanmu, insha ALLAH zamu dawo da wuri”.
Yanda ya jiyo tana zumuɗi sai tausayinta ya kamashi, amma sai bai nuna mataba yay mata sallama akan idan ya koma gida zai kirata, yanzu yana kasuwa ne, kafin ta bashi amsa ya yanke wayar.
Sosai naita zumuɗin wannan fita, su Salima na zuwa na gumtsa musu bayani, dariya sukaita min, niko ban damuba dan ni kaɗai nasan daɗin da nakeji, tunda akai aurenmu ban taɓa zuwa gidan kowaba a cikin yayyenmu, aiko tun a daren na gama kimtsa hatta kayan da zan saka saboda tsabar zumuɗi.
Da daddaren ma ya kirani, duk da dai sama-sama yanzunma muka gaisa naji daɗi, koba komai dai inaji a jikina ya daina fushi dani.
Ƙarfe goma mun gama shiri, ko nace na gama su Fa'iza da suka je gida su faɗa nake jira su dawo mu wuce, sai kallon agogo nake ina zuba tsaki, aiko basu dawoba sai kusan goma da kwata, sunsha harara kamar idona zai faɗo.
Sukaita zubamin dariya, ban kulasu ba muka fito na kulle ɗakin, Mama Ama ce kawai a tsakar gidan, kausar na ɗaki inaga dai jikin nata babu daɗine, ganin takalmin mijinta yasa mukaima maman Ama salama kawai muka fice abinmu, duk da neman zance da take na tambayar “Su amarya yau kuma ina aka nufa?”.
Banko bata amsaba bayan murmushi da cewar “Zan ɗan fitane saimun dawo”.
Muna fitowa su Salima ke faɗin, ”Wai ita matarnan bazata canjaba?”.
Suma ban basu amsaba, muka tare Napep dai sukai ciniki sannan muka shiga.
Farin cikin da nai na fitar sai muka iske mafiyinsa a wajen Yaya Maryam, gaba ɗaya ta gama rikicewa da murnar ganinmu, ta kasa zaune ta kasa tsaye.
Gashi dama ita kaɗai muka iske a gidan kishiyarta wai tayi tafiya zuwa Zamfara biki.
Sosai ranar na tsinci kaina a farin ciki, domin na yini cikin ƴan uwana munsha zuminci, Yah Ahmad ma ya kira suka gaisa da Yaya Maryam har take masa faɗan wannan karon baizo gidanta ba harya koma.
Bansan wace amsa ya bata ba, naga dai ta kalleni tana dariya da faɗin, “Zahiri kuwa ɗan ƙanina”.
Munsha yini cir, sai kusan biyar muka baro gidan, inaji ina gani muka biya ta ƙofar Gidanmu su Salima suka shiga suka ɗakko abu sukazo muka wuce amma ni sai dai kallo, sai da naji hawaye sun cikan idanu, banda aure waye ya isa maka katanga da gidanku? sai lokacin da akaso kaje.
__________________________________
Haka rayuwar taci gaba da shuɗawa, wasu abubuwan na wucewa wasunsu na biyo baya, wataran masu daɗi wataran saɓaninsu.
A wannan yanayin Samina ta koma gidan ma'aruff bayan sun masa shiri na musamman daga wajen malaminsu, tsafi gaskiyar maishi, a cewarsu sunga canji daga Ma'aruff ɗin, dan kuwa da kansa ma yazo ya buƙaci komawar Saminar.
Da farko ta tirje wai ita jan aji saboda taga yana lallaɓata, sai da Inna mari tai mata kaca-kaca akan ta zauna shirme ta lalata komai.
Aiko babu shiri ta dawo hankalinta ranar da yazo da dare ta shirya suka koma.
Tunda ta koma gidan ba'ace babu daɗiba, dan kuwa dai tana samun kulawa fiye da da, sai dai bai fasa shan giyarsa ba balle neman mata, yawan dukantane dai ya bari sai idan ya nemeta ne taƙi saboda warin giyar da bataso shinefa zai lakaɗa mata duka ya kumayi abinda yakeso koda ta ƙarfine, daga ƙarshe kuma yay mata wanka da amai mai uban wari.
Data lura gardamarta ke kawo irin waɗannan matsalolin saita fara sauke rawar kai koda yazo a bugen idan ya nemeta bata hanashi kanta, haka za'ayi tana toshe hanci, babu zancen jin daɗi ko farin ciki daga gareta, kawai ta miƙa kantane ya samu biyan buƙata dan gujema buyaginsa.
Sannan kullum safiya bayan sunyi breakfast sai ya bata ƙwayoyin hana ɗaukar ciki tasha a gabansa yanzu, idan tai gardama tasha mari kuwa, kuma tilas tasha.
Wannan abu na tadama Samina hankali ainun, su da sukeda burin ta haihu dashi amma shi shine yake gudun hakan?.
Ta rasa hanyar da zata ɓullowa al'amuran, tana son faɗama su Nafy tana tsoro saboda gargaɗin da Inna mari tai mata akan riƙe sirrinta ga ƙawaye.
Gefe ga tsangwamar dangin miji, ko wata sabga ake ya kaita gidansu komawa take kamar wata mujiya a cikinsu, babu mai mata kallon arziƙi, to ana harkar masu kuɗi ita talaka ɗiyar talaka wane damar hura hanci gareta?.
Waɗannan matsalolin ne suka tarumata akai ko ƙibar kirki balle murjewar kwanciyar hankali bataiba, ga dai gida iya gida da kayan alatu amma babu wadataccen kwanciyar hankali a cikinsa.
Wani lokaci idan Ma'aruff ya tafka mata wata tsiyar takan ji a ranta da Yah Ahmad ne hakan bazata faruba sam, har kuka takanyi akan hakan duk da bataji a ranta har yanzu ta aikata ma Ahmad ɗin ba daidaiba.
★★★★★
Ga Umm-Ruman kuwa tanajin sabbin abubuwa a jikinta, musamman son kaza da jin bata sha'awar kaza, yawan barci da saurin fushi, lokuta da dama shi kansa Yah Ahmad ɗin sukan haura sama ta waya, yakanyi mamakinta tunda tun fil azal yasan batada kwaramniya balle akai ga rashin kunya gana gaba.
Tayi wata irin murjewa, fatarta kuwa tai luff har ƙyalli take, sannan tai haske sosai kamar yanda su Maman Ama ke yawan gulmarta yanzu akan wai bilicin takeyi.
Shirmen ƙuruciya baisa Rumana ta fahimci wasu abubuwan da takeyi da sukai canji ko mata nisa a yanzu ba, da abun ya fara tsamari saita koma danganta hakan da wai shawara ke damunta😂.
Wata hikima ta UBANGIJI kuma sai ALLAH ya toshe ji da ganin Kausar da maman Ama akan fahimtar komai daga halin da Rumanan ke ciki.
Koda yake ita dai Kausar ma lafiyace ta mata ƙaranci, to maman Ama ma dai da alama laulayin sabon ciki takeyi, dan yanzu ko zamanma basa yawanyi sai lokaci-lokaci, shima zakiji gaisuwace sama-sama kowa ya samu waje ya kwanta.
Wannan yanayin ne ya kawoma gidan su Rumana yawan shiru, inba su Ahmad da Amatullah ke wasaba, gasu dai matan gidan babu mai ƙarfin yin wani motsi mai girma.
_________________________________
Ga Ahmad komai yana tafiya Alhmdllh, sai dai ƙalubalen kasuwa na yau da kullum, wataran a samu yanda akeso wataran saɓanin hakan, amma ko dai yaya ba'a rasa na abinci Alhmdllh.
Zuwa yanzu ya shiga wata na uku da dawowa, tun yana yawo da ƙaramar kwaba har ya ƙara neman babba data fita, sai kuma ga ɗan waje dukda bawani mai yawa bane, dan alfarma wani yay masa ta hanyar alhaji yaɗan bashi gaban shagonsa yake jingina kwabar, shi leda yake sayarwa mai shagon.
Hakan ba ƙaramin cigaba yazoma da Ahmad ba, dan yana ganin hasken zama wajen sosai.
Bayason ya cika wata uku baimaje gidaba, dan haka ya fara tunanin zuwa anan kusa kodan cika alƙawarin da yayma iyayensa, ga kewar matarsa kuma a gefe na cinsa a kowacce magudanar jini.
Ranar wata lahadi ya koma gida da wuri saboda kansa dake masa ciwo, gashi irin wannan ranarma kasuwar zakaga duk shiririta tafi yawa saboda masu garin ranar komai yakan tsaya ne agaresu a irin wannan ranar, magani yasha ya kwanta, da yake masu gidan sun fita ziyara basu kai ga dawowa ba daga sai shi kaɗai a gidan.
Da ƙyar ya tashi yay sallar magriba, sai lokacinne masu gidan suka dawo, tashi yay ya buɗe musu gate suka shigo da motarsu, ya tsaya har suka fito.
Gaisuwa sukai cikin girmama juna, dan matar tana son Ahmad sosai, tana kuma ƙyautata masa duk da ba addini ɗaya suka fitoba ba kuma yare ɗayaba, hasalima ko zo zan kasheki bata saniba da yaren hausa, UBANGIJI ne dai kawai ya haɗa jininta da Ahmad ɗin, sai kuma ƙyawunsa dake ɗaukar hankalinta, (kunsan ƙabilun nan dason abu mai ƙyau☺️).
Ciki suka shige shi kuma ya zauna a ƙofar ɗakin mai gadi da yake kwana dan yasha iska saboda zafi.
Wayarsa daya samu ya sake saya yaketa danne-danne a cikinta, yana a wajen har kusan takwas.
Ganin lokacin Salla yayine saiya miƙe ya koma ɗaki yay sallar isha'i.
Tun yana cikin sallar yakejiyo kukan yarinyar iyayen gidan nasa sama-sama, babanta sai ƙoƙarin lallashinta yake amma taƙi daina kukan.
Da farko baki Ahmad ya taɓe saboda yarinyar bata sonshi, gata ƙatuwar budurwa amma idan tana taɓara saika ɗauka wata ƴar shekara bakwai ce.
Jin hayaniyar naɗan ƙaruwane ya saka Ahmad leƙowa dan yaga mike faruwa?.
Kuka ya iske Happy nayi rurus, iyayen duk sun rikice sunata lallashinta amma taƙi saurarensu, tayi zaune a ƙasa dirshan duk ta jefar da abubuwan jikinta irinsu gashi da abun hannu da takalma saboda tsabar rashin man kai.
Kamar zai koma sai kuma ya tambayi ko lafiya?.
Baban ne yayma Ahmad bayanin wai Assignment na makaranta aka basu, su kuma duk sun kasa koya mata tun jiya, saboda basu iya Mathematics ba, wanda kuma yake koya mata baya nan, shinefa take wannan shirmen.
Kai Ahmad ya girgiza yana mamakin wannan taɓara, yace idan bazata damuba tazo shi zai koya mata.
Da mamaki duk suka kallesa, itako yarinyar harda hararsa wai miya sani da har zai koya mata?, Hausawa ƴan arewa da basa karatu hauka zai koya mata ko?.
Murmushi Ahmad yayi kawai, bai kuma ce mata komaiba ya juya zai koma ɗaki abunsa.
Saurin tsayar dashi maman tayi sannan taima Happy magana da yarensu akan ta gwada bashi tunda yace zai iya ɗin.
Bai musaba ya dawo, gani yay Happy ta miƙo masa buk ɗin tana hararsa, fuska a ɗaure ya amsa danshi dama bamai son wargi bane tun fil azal, shiyyasa sam baya barin Happy taga fara'arsa, duk da tana masa kallon ƙasƙantacce bahaushe ɗan arewa da wahala ta kawosa yankinsu cin arziƙi.
Kallon Questions ɗin yay ya taɓe bakinsa, hannu ya miƙa mata ta bashi pen ɗin nanma tana hararsa, baibi takantaba ya amsa, zama yay a ɗan dandamalin da aka zagaye flowers ɗin gidan ya fara mata aikin.
Dukansu idanu suka zuba masa cike da mamaki, cikin mintuna sha biyar ya kammala mata shi tsaf cikin ƙwarewar Handwriting ɗinsa mai bala'in birgewa, ba tare daya ce mata uffanba ya miƙa mata buk ɗin yana tsashi tsaye.
Amsa kuwa tai tana kallo, da salon rubutunsa mai cike da nutsuwa ta fara cin karo, sai kuma aikin, baki buɗe ta ɗago ta kalli bayansa daya juya dan tuni yama bar wajen, jiki a saɓule ta maida dubanta ga iyayenta tana faɗin, “Mommy yayi fa”.
Amsar buk ɗin sukai suma duk suka duba, mamaki ya kamasu, sam basu taɓa kawowa a ransu wai Ahmad yayi karatuba, kasa daurewa Dadyn yarinyar yayi yace, “Dama kayi karatu?”.
Ahmad ya tsaya cak, sai kuma ya juyo ya kallesu yana guntun murmushi, yace, “Har matakin degree kuwa oga, ku a tunaninku Hausawa basa karatune? Kodan kunga muna zuwa yankinku neman na kanmu?”.
Dukansu babu wanda ya iya bashi amsa saboda mamaki da kunyarsa, shiko ya juya abinsa ya shige ɗakinsa ransa na ƙuna saboda yanda aka ɗauki yarensa a ƙasarsa.
Washe gari saiga Happy har ɗakinsa cikin tsantsar farin ciki, ita da ke ƙyanƙyaminsa sai gata harda rungumesa, saurin tureta yay a jikinsa yana mata tsawar karta sake masa haka bayaso.
Farin cikin data take ciki ya sakata bashi haƙuri tana miƙa masa buk din data kwafi aikin da yay mata jiya.
Kamar bazai amsaba sai kuma ya amsa a yatsine yana jan ƙaramin tsaki.
Taci 100/100, ya ɗan taɓe bakinsa yana miƙa mata buk ɗin.
Ko haushi batajiba ta shiga bashi labarin itace ta taci ɗari bisa ɗari a kaf ƴan department ɗinsu.
Cikin halin ko in kula yace mata “Congrat” a taƙaice ya ɗauke kansa.
Ita dai bata kula da basarwarsa ba ta sanar masa kiran da Dad dinta ke masa.
Binta yay suka shiga cikin gidan.
Yaune karan farko da zai shigo cikin gidan har ma falonsu, tsararren falone da yaji kayan more rayuwa, dama ya daɗe yana hasashen hakan kuwa.
Iyayen gidan nasa na zaune fuska ɗauke da murmushi, zai zauna a ƙasa sukace ya hau kujera, bai musaba kuwa ya hau ya zauna, yanda suke jera masa godiya tamkar ya musu wani gagarumin abu sai mamaki ya kamashi.
Miye na wani godiya akan Assignment kawai da yayma ƴarsu? Shida suka bashi wajen kwanafa, sannan suke biyansa duk ƙarshen wata dukda aikin nasa iya darene kawai.
Dad ɗin Happy yace, miya karanta ne?.
Ahmad ya faɗa masa.
Sosai mamaki ya sake kamasu, a take kuwa yace inhar yana bukatar aiki ya kawo takardunsa, dan kuwa ƙaninsa babbane a ma'aikatar man fetur ta NNPC zai sa ya nema masa aiki.
Sosai mamaki ya bayyana a fuskar Ahmad, a yau ya yarda da batun mutane da suke cewa Alheri danƙone baya faɗuwa ƙasa banza, sannan da gaske ƙabilun nan basu da baƙin ciki wasunsu.
Da ƙyar Ahmad ya haɗiye yawu yana jinjina kansa, yace, “Mizai hana inhar babu damuwa nanda sati ɗaya yaje ya kawo dan suna gida”.
Dad ɗin Happy yace babu wata damuwa zai iya zuwa ya kawo, koda nanda sati biyune, sai dai karya wuce hakan.
Godiya sosai Ahmad ya shiga yi musu, sukam sukace karya damu, tunda baiyi baƙin cikin taimakon ƴarsu ba su mizaisa suyi baƙin cikin taimaka masa.
Farin cikin da Ahmad ya tsinci kansa a wannan rana faɗinsa ɓata lokacine, a daren ya kira Nura ya sanar masa, sosai Nura ya tayashi murna da tabbatar masa lallai shikam yazo Porthercout da ƙafar dama.
Tun a washe gari kuwa Ahmad ya fara shiri, dan so yake ya wuce gida nanda kwana biyu, kodan yaje ya samu damar tattara takardunsa waje ɗaya ya juyo da wuri.............✍🏻
*_Afuwan! Afuwan!! Afuwan Please, kunjini shiru kwana biyu, kusan jiki da jini an binciko file ɗinane, amma Alhmdllh lafiya ta samu, inama kowa fatan alkairi🥰🥰🥰🥰🙏🏻_*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
[7/27, 5:12 PM] Jidder 2: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*_GDW_*
*(29)*
..............Wannan karon ma bai sanarma kowa zuwansa ba, harma baban baisan da zuwan Ahmad ba.
Cikin amincin ALLAH wannan tafiyar da yake tafiyar wuri sukayo sai gasu kusan sha biyu sun sauka.
Yau ɗinma dai gidansu ya fara sauka, ba ƙaramin bazata yay musu ba, yara nata murnar ganinsa, hakama su Ayyah ɗin kansu.
Bayan ya gaggaisa da jama'a Ayyah ta korashi akan yaje gida ya huta, bai musaba kam, dan dama cike yake da zumuɗin son ganin ƴar matarsa, anan ya bar musu tsarabarsu ya ɗauki iya kayansa da tsarabar Rumana ya tafi.
Umm-Rumana kam haka kawai yau bayan tashinsu barcin safe ta tashi da ƙulafucin son cin alala, wakenta ta gyara ta bama Ahmad ya kai mata markaɗe nan makwaftansu, dayake fa'iza sun wuce gida tun ɗazun, yanzu akwai wajen koyan saƙa da suke zuwa sai lokacin islamiyya suke tasowa su biyoma Rumana, duk da yanzu wataranma ita da kanta take cewa bazata jeba batajin daɗi.
Sai da ta kammala ƙulla alalan ta ɗora a wuta sannan ta share ɗakin ta wuce wanka, shigarta babu jimawa Ahmad ya shigo gidan.
Kawai muryarsa ta jiyo yana amsawa maman Ama dake masa sannu da zuwa, cikin mamaki a zuciyarta take faɗin, “Da gaske yaya Ahmad ko dai kunne nane baiji da ƙyau ba?”.
Sake jiyo muryarsa tai yana ma yaran da suka shigo masa da kaya godiya.
Mamaki ya kuma kamata da wannan bazata tashi, kofa daren jiya sunyi waya, ita kuma sam bataji alamun tafiyar motaba.
Haka dai ta kammala wankanta ta fito tana tunane-tunane da mamakinsa. Da takalmansa ruwan makuba dake ajiye ƙofar ɗakin ta fara cin karo, maman Ama ta fito daga kicin tana faɗin, “Ohni amarya an iya sema ƙunshe dai? To barka ƴan tafiya an sauka lafiya”.
Murmushi kawai nai mata ina amsawa da ngd, dan nasan ko bayanin bansan da zuwansaba nima nai mata ba fahimtata zataiba, alwala na ɗaura sannan na shiga ɗakin da sallama.
Yah Ahmad dake kwance bisa gado yayi filo da hannayensa ƙafafunsa duka a ƙasa ya ɗan ɗago ido yana kallonta.
Canji ya sake gani a jikin ƙanwar tasa na musamman fiye da waccan dawowar da yayi.
Rumana dake ɗan sisinne kan kuwa tace, “Sannu da zuwa Yayanmu”.
Yunƙurawa yay ya tashi zaune sosai idonsa a kanta ko ƙyaftawa bayayi, saurin riƙe hijjab ɗin da take ƙoƙarin sakawa yayi saboda daga ita sai ɗaurin ƙirjine da ƙaramin gyale data yafo, bata yarda ta fita tsakar gidansu daga ita sai zani, dan tasan ko yaushe wani zai iya shigowa daga sauran mazan gidan.
Manyan idanunta da suka ƙara wani haske na musamman ta ɗago tana masa kallon mamaki.
Yanda shima ya kafeta da nashi sai ta kasa jurewa tai ƙasa da nata tana murmushi.
Tsaye ya miƙe kawai ya jawota jikinsa ya rungume, a tare suka sauke nannauyar ajiyar zuciya kowanne na sake mannema ɗan uwansa.
Ahmad da idanunsa ke a lumshe yace, “I miss you so much Babie R”.
Murmushi Umm-Rumana tayi har yanajin hucinsa a ƙirjinsa, ta ɗago kanta a hankali ta manna masa sumba a ƙirjinsa.
Ƙankameta ya sakeyi yana sauke numfashi da kyar, dan ba ƙaramin isa saƙon Rumana yayiba a dukkan sassan jikinsa da magudanar jininsa.
Itako dauriya kawai tai wajen aikata hakan, shiyyasa tana yi ta kuma cusa kanta a jikin nasa.
Da ƙyar ta yarda ya ɗago kanta da hannayensa duka biyu, idanunsa ya fara bazawa akan fuskarta yana binta da kallon ƙurulla tamkar yaune ya fara ganinta, itako sam taƙi yarda ta kallesa.
Iska ya hura mata a fuska yay ƙasa da muryarsa tamkar mai raɗa yace, “Lallai Babie R ɗina ta girma da gaske”.
Da sauri tace “Ni dai ban girmaba”.
Yanda tai maganar da shagwaɓa ne ya sakashi yin murmushi, ya matsar da bakinsa saitin kunnenta, a hankaki ya furta, “Tunda kika iya ɗaukar nauyin Amadin Ayyah ai kin gama girma”.
Saurin ƙanƙamesa tai saboda girman maganar tasa da sanin inda ta dosa.
Aiko Ahmad ya ƙyalƙyale da dariya shima yana rungumetan da ƙyau.
Itama dai murmushi taketa zubawa tana jin ƙaunarsa mai zafi na ƙara tasiri a ranta.......
Daga waje maman Ama ta katsesu da fadin, “Amarya abincinki fa na ƙauri”.
Da ƙyar suka iya rabuwa da jikin juna, ta ɗauki hijjab ɗin daya hanata sakawa ta saka ta fice domin duba abincin.
Babuma wani ƙaurin kirki da yakeyi, tsabar kutsugune irin na maman Ama, dan ruwan data tsumbula ledojin alalarne yake kumfa yana tasowa da ɗiga a rishoɗin, shinefa yake ɗan hayaƙi, hayakin kuma na ƙauri.
Buɗe murfin tai ta duba, ganinma alalar tayi sai kawai ta sauke ta ɗora man da zata soya, ɗakin ta koma ta kaima Ahmad ruwan sha sannan ta dawo ta tsame alalar ta kashe risho ɗin.
Ba tare da ta shiga ɗakinba ta ɗaga labulen ta ɗan leƙa kanta, “Yaya azuba ruwan wanka?”.
Ahmad ya ajiye ruwan da yasha yana ɗaga mata kai alamar eh.
Sai da takai masa har bayi sannan ta dawo ta sake leƙawa danta sanar masa ta kai ruwan, hannunta kawai yaja ta faɗa ɗakin sosai.
“Wannan dojewar ai nasan inda ta dosa, oya maza cire min kaya, infa ba'a tarairayata kamar ƙwai a cokali kayana zan ƙulle na koma....”
“Da gaske?” Rumana ta faɗa cikin waro masa idanu waje.
Hancinta yaja kaɗan yana murmushi da faɗin, “Mizai hana ƴar ƙyaƙyƙyawa ta”.
Umm-Ruman tai murmushi tana ƙoƙarin cire masa maɓallin shirt din jikinsa, duk yanda yaso haka tai masa, da taimakonta ya cire komai, ta barsa da kayan ciki kawai ta koma ƙoƙarin ɗakko masa jallabiyya a drawer.
Ta juyo zata bashi ya wani tsareta jikin drawer ɗin yana bata fuska, “Kai gidan hayama bai yiba, a yanda na gajinnan wankanma buƙatar aimun nakeyi”.
Rumana ta ɗora hannunta kan baki tana murmushi.
“Oh dariya ma kikemin ko? Aiko zan manta da kowa kuwa muje dole kiyim ɗin”.
Sosai ta kwalalo idanu tana faɗin, “Yaya rufamin asiri, aiko to har gidanmu sai matan gidannan sun kai gulma”.
Ƙaramin tsaki yayi yana amsar rigar da cewa, “Sun daɗe basu kaiba masu kawunan talo-talo”.
Ita dai Umm-Ruman dariya tayi, shikuma ya fita domin yin wankan.
Dole taje ta sake yo alwala ta dawo ɗaki, aiko sake alwalar nan ba ƙaramin tsone idon maman Ama tayi ba, harda jan tsakinta tana faɗin, “Iya nan kukafi afana daga ke har lusarin mijin naki da baya amfana miki komai”.
Nace, “Oh su maman Ama problem😹🌚”.
Koda Umm-Ruman da batasan maman Ama nayiba ta koma ɗaki sai tai azamar fiddo kaya ta saka kafin ya fito, ta shafa mai ta ɗan murza fauda da kwalli harda janbaki kaɗan sannan ta saka turare ta tada salla.
Tana cikin sallar ne Ahmad ya fito, shima botikin ya ajiye ya ɗauka butar data ajiye masa yay alwalar sannan ya shigo.
An riga an idar da salla a massallaci, dan haka yay ƙokarin gabatarwa a ɗakin, lokacin Rumana ta idar sai ta bashi abin sallar ita kuma ta miƙe domin shirya masa abinci.
Yana idar da sallar mai yaɗan shafa ya saka wando iyakar gwiwa da t-shirt mara nauyi mai guntun hannu, zama yay inda ta shirya abincin, da mamaki yake kallon Alalar da keta tashin ƙamshi, yanda yakeson alala yasan duk wanda yay tarraya dashi zaisan haka balle ita da suka tashi a gida ɗaya.
Kallonta yay, “Babie anya bakisan zan dawoba kuwa?”.
Murmushi Rumana tayi da faɗin, “Yaya baka sanarmin ba yaya zan sani? Amma miyasa kamin wannan tambayar?”.
Ba tare da yayi magana ba ya nuna mata alalar.
“Nayine kawai saboda na tashi da sha'awar cinta ALLAH”.
Idanu ya lumshe ya buɗe a kanta, yace, “Hakan ya sake tabbatar min zuciyoyinmu suna fahimtar yaren juna koda basa a ƙarƙashin inuwa ɗaya Ruman”.
Sosai kalamansa sukai mata daɗi, ta duƙar dakai tana murmushi, shiko ya fara cin abincinsa dake masa tsagwaron daɗi.
Sai da yay lauma kusan biyar sannan ya kai ta shidan bakinta, ta kallesa shi kuma ya ɗaga mata gira alamar ta amsa.
Babu musu ta buɗe bakin ya saka mata, a haka suka cigaba dacin alalar yanaci yana bata har saida sukayi nak sannan, ita tama rigasa ƙoshi.
Taji daɗin yanda yaci sosai kuwa, ya fita ya kuskuro bakinsa yazo ya haye gado yana fadin, “Bara naɗan rage barci kafin la'asar”.
“A tashi lafiya yayanmu”.
Harya rufe idanunsa ya buɗe yana kallonta, ”Bazaki tayaniba?”.
Kanta ta girgiza alamar a'a.
Yaɗan ɗage gira sama kaɗan yana fadin, “Shikenan zan rama”.
Ita dai Rumana Murmushi kawai tayi batace dashi komaiba, ta tattare kayan da suka gama cin abincin ta fita tsakar gida danta wanke, shiko babu jimawa barcin ya kwashesa dan dama shine fal idonsa.
Daga ita saisu Ahmad a tsakar gidan, mamansu ta fice tun ɗazun, Kausar kuwa tana ɗaki saboda yanzu tayi nauyi, gashi bata da isashiyar lafiya tunda cikin yakai watanni bakwai, yanzu ma inba sune suka lekata ba baka taɓa ganinta tsakar gidan sai alwala ko wanka ko fitsari ya fiddota dole.
Tana ciki. wanke-wanken ne Maman Ama ta shigo, tasan dai daga gidan maman Aysha take gulma, batabi takanta ba taci gaba da aikinta.
Koda ta kammala sai ta koma ɗaki abunta ta zauna tana ƙarema Ahmad dake barci cikin nutsuwa kallo, sosai ya kara canjawa, daka gansa kaga nutsatstsen matashi mai sassanyar ƙwalisa, ya kumayin haske ga ƙibar da yayi jikinsa ya kuma murjewa sosai, hakan saiya ƙara masa kwarjini sosai, ga ƙasunbar daya ajiye tun wancan zuwan ta kuma fidda sirrin kyawunsa kai kace irin ɗan yankin utopia ɗin nanne.
Ajiyar zuciya Rumana ta sauke a hankali, ta ɗauka wayarta ta cire hasken camara ɗin ta lallaɓa ta gabansa tai masa hoto, sosai kuwa hoton yayi ƙyau tamkar ba barci yakeba.
Tana nan zaune har aka kira sallar la'asar, a kiran farko da aka ƙwala Ahmad ya buɗe idanunsa.
Barcin dai ba isarsa yayi ba, amma yaji nauyin jikinsa ya ragu Alhmdllh.
Kallon Rumana data fara gƴangƴaɗi yayi yana murmushi, daga gani bata san barcin ya figeta ba, bai tadata ba ya sauka a gadon ya fita yo alwala, sai da ya dawone ya taɓata ta tashi shikuma ya saka jallabiya ya fita masallaci.
Bayan an idar da sallar la'asar ɗinma ya jima bai shigoba, har kusan mintuna ashirin bayan sannan ya shigo.
Sannu tai masa ya amsa yana nufar drawer, kaya ya ciro wando da riga na farin yadi ya saka, ɗinkin ya masa kyau dan iyakarsa cinyarsa, gashi fitet akaima rigar, yana ƙoƙarin saka link ɗin hannun yake fadin, “Ruman bara naje na gaggaisa da mutane, idan na dawo kuma akwai labari mai daɗi”.
Cikin zumudi Rumana tace, “Yayanmu da gaske?”.
Sai da ya kama hannunta cikin nasa sannan yace, “Sosai ma kuwa babia na, ke dai ki tanaji goro mai daɗi da saka kunne miƙewa”.
Tai ɗanyi walai da idanunta cikin salon jan hankaki tace, “Ka ɗauka ka samu Yaya na, mi zan dafa da dare?”.
Matso da fuskarsa yay kusa da tata ƙasa-ƙasa yace, “Ke kaɗai kin isheni ai”.
Da sauri ta ƙwace hannunta ta juya masa baya, yay ƴar dariya yana rungumota ta baya da mata abinda ya sake tsundumata a kunyar da tafi ta farko, ga tsigar jikinta da tai wani yarrr.
Shiɗinma ganin zai ɗakkoma kansa dala babu gammone ya sakashi sakinta yana sauke numfashi a harhaɗe ya fice da fadin, “Saina dawo”.
“Uhum” ta iya ce masa kawai, hakanne ya sakashi juyowa ya kalleta.
Saurin juyawa tai wani sashin, shi kuma ya fice yana murmushi mai sauti.
__________________________________
Duk da yace kartai komai bata zaunaba, ta diba ayar da take saidawa wadda ba'a soyaba ta fita ta gyara, dama tanada kayan kunun ayarta datai tanadi akan duk randa zai dawo zatai masa sai kuma ya shammaceta.
Abu taima filashin, babu jimawa kuwa ya kirata dan shima yanada ƴar jagwal dinsa, roƙonsa tai akan ya sayo mata kwakwa ƙwallo biyu idan babu tsada ya kawo mata sai ta bashi kuɗin, idan kuma da tsada ya sayo ɗayama zata isheta, sai ƙankara kuma dan ALLAH.
Kafin ta kammala gyaran ayar kuwa sai gashi, ashema yana kusa da anguwar tasu yazo sayen kayan ɗinki.
Leda ya miƙa mata yana tsokanarta akan Yau daɗi zasuci kenan?.
Rumana tai dariya tana faɗin, “Kai Yah Abu wane kayan daɗi fa?, ɗan kunun ayane kawai zanma Yayanmu tunda ya mana zuwan bazata”.
“Wlhy kuwa, ai Yah Ahmad ya iya wayo, kofa a gida babu wanda yasan da zuwansa, ganinsa kawai akayi”.
Rumana tace, “Lah wai harsu baba ma Yah Abu?”.
“Aikam harsu in faɗa miki. bara naje Yah Mudan jirana yake nakai masa, sai mun dawo shan kunu”.
“To ALLAH yasa da gaske kakeyi, zanko ajiye dan ALLAH ka dawo”.
Yana gab da fita yace, “Wlhy wasa nake karki ajiye, yau aiki garemu a shago na masu biki”.
Roƙonsa ta shigayi akan ko cikin su Kamalu ne ya aiko su karɓa masa, shidai ya fice yana jaddada mata karta ajiye.
Koda ta haɗa markaɗen Ahmad ta aika ya kira mata Aysha yarinyar maƙwaftansu, ta bata tayo mata markaɗen, zama tai ta tace abinta ta haɗa duk abinda ake buƙata ta saka ƙanƙara bayan ta juye a ɗan boket na plastic ta rufe abinta, ta sake kimtsa ɗakinta tai wankanta gab da magriba ta shige ɗaki bayan ta sake kunna turaren wuta na tsinke, ta fito ta samu garwashin uwatar da maman Ama tai girki ta diba taje ta saka turaren wuta na tsugunno tayi kamar yanda yaya maryam ta koya mata sannan ta zuba na ɗaki a sauran rushin, salla ta fara gabatarwa kafin ta gyara jikinta, wasu siket da riga daya kawo mata wancan zuwan ta saka, sunko mata ƙyau sosai, dan dama sawarta ɗaya tun yana nan, bayan tafiyarsa kuma ta ninkesu da sauran ta ɓoye abunta, a tsarinta dama dai tafi son taringa kwalliyar dare dasu idan yana gari.
Bayan sallar isha'i kaɗan kuwa sai gashi ya shigo, lokacin ta kammala zuba masa kunun ayar a kofi tana goge wanda taɗan zuzubar a ƙasa ne.
Sannu da zuwa tai masa, ya amsa yana ajiye ledar hannunsa dake ta ƙamshi idonsa a kanta.
Kayan sun zauna mata ɗas ajiki, musamman yanzu datai ƴar kibarnan.
Ita kanta yanda yake binta da kallo sai da kunya ta kamata, ta kai tsunman waje ta ɗaurayo hannunta ta dawo.
“Wai miye sirrin ƙyawun nan ne ta wajena?” Ahmad dake kallon Umm-Rumana ya faɗa.
Tace, “Kai Yayanmu, kai ba'a tambayeka sirrin ƙyawun da kaiba sai ni wane ƙyau nayi?”.
Hannunta ya riƙo ya ɗorata saman cinyarsa, “ALLAH Babie karkiji batun wasa kin wani haɗu sosai, kinyi ƙiba da haske kamar ina kusa dake”.
Hannu tasa ta rufe fuskarta tana faɗin, “Wlhy kana bani kunya Yaya”.
“Kwantar da hankalinki, anjima kaɗan zaki bani kunyata ai yarinya”.
Tashi tai a jikinsa tana dariya, ta ɗakko filet ta buɗe ledar daya shigo da ita, gasasheshen balangune daya samu tsafta da iya gashi, ga tumatur da albasa da cucumber yasha sunata bada ƙamshi mai daɗi, ta ajiye a saman tabarma kusa da juk ɗin data zuba kunin ayar.
Tashi yay ya cire rigarsa ya zauna da dogon wandon da singlet, itama ya nuna mata gefensa.
Bata musaba ta zauna, ta tsiyaya masa kunun ayar a karamin kofi ta ajiye a gabansa, ɗauka yay yasha yana lumshe idanu.
Ya buɗe a kanta tare da fadin, “Babie na kinaji dani fa”.
Guntuwar dariya Rumana tayi ita dai, tace, “Goron albishir ɗinne ai kafin ama fadamin na bayar”.
“Ina my Ruman, bashi nake so matsayin goron albishirba, ki ɗauka wannan na sannu da zuwane kawai, goron albishir ɗina na musamman nakeso da gwauro baya samunsa”.
Ƙasa tai da kanta tana ƙara mamakinsa a ranta, idan ya zubo magana saika ɗauka bazai iyaba.
Cikin nutsuwa ya zayyane mata abinda ya kawoshi kamar yanda yayma su baba bayani a gida, farin cikin daya lulluɓe Rumana batasan sanda ta faɗa jikin Ahmad ba ta rungumeshi.
Cikin dariyar da yake mata ya samu damar lalubo bakinta ya manna nashi...........🌚🤫😝✍🏻
*_Masu bin littafin ƙwai cikin ƙaya kuwa, saina tattare part 1 zan turo duka insha ALLAH, na gaji da wannan asha ruwan tsuntsayen nima, zaku iya ganina a koda yaushe da izinin UBANGIJI🥰🥰🙏🏻_*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*_GDW_*
*(30)*
.............A yanda salon yazo tuni Umm-Ruman ta bada haɗin kai wa yayan nata cikin nata ilimin data ƙara samu akan nada, ta mance da wata aba wai ita kunya, sai dai Ahmad yay liɓis a zaunen nan sannan ta iya ƙoƙarin janye bakinta tana ɓoye fuskarta a ƙirjinsa.
Ya lumshe idanu yana jingina da bango da sake kanannaɗeta a jikinsa yana sauke numfarfashi.
Kusan mintuna biyu suna a haka kafin ya iya buɗe baki da ƙyar yace, “Da gaske dai Ruman ta girma”.
Shiru Umm-Ruman tayi tana sake lafewa a jikinsa, ita kanta tasan yau ta zaƙe da yawa, ba komai ya jawo hakanba kuma sai missing ɗinsa.
Tace, “Nidai Yaya ban girmaba”.
Murmushi yayi yana kai hannu ya zame ɗan kwalin kanta, sumarta dake a ɗaure babu kitso ya shaga shafawa a hankali, kafin ya zame ribbon ɗinma gaba ɗaya ya saki gashin nata mai tsawo da cika, yanason gashi sosai, dan yana ɗaya daga cikin abinda yaso tattare da Samina, ashe baima saniba Rumana tafi Saminar,
“Miyasa babu kitso Babie R?”.
Yunƙurawa Rumana tai ta tashi daga jikinsa, kanta a ƙasa batason su haɗa ido tace, “Zafi nakeji”.
“Zafin kitson?” yay maganar murya a shaƙe.
Fuska taɗan ɓata tana langaɓe kai tace, “Eh wlhy Yaya”.
Yayi wani ɗan moso mai sauti yana kai hannunsa kan gashin, “Miyasa wani lokacin ke raguwace? Yanzu nan kitsone keda zafi?”.
Babu shiri ta kallesa da ƙyau, dan ita dai tasan zafin kitso babu sauƙine, “Yaya kitsonne babu zafi?”.
Shima idanun ya fiddo kamar yanda tayi yana cewa, “Duk zafinsa ya kai randa kikai tamin raki”.
Yanda ta ɓata fuska tai gefe da ita na alamar shagwaɓa tsagorontane ya saka Ahmad ƙyalƙyalewa da dariyar da bai niyyaba, ya jawota ta dawo jikinsa, “Kinga wasa nake gwal ɗina, ba ke baceba gaskiya”.
“Ni babu wani wayo da zakaimin bayan kanata faɗa”.
“To na daina faɗar, haba zinariyar zuciyar Ahmad”.
“Naƙi wayon” Rumana ta faɗa tana ɗan dukan ƙirjinsa na wasa.
Dariya sosai ya shigayi yana ƙoƙarin riƙe hannayenta amma taƙi bari.
Karaf kuwa wannan wasa nasu a kunnen mijin maman Ama daya shigo gida a lokacin, shiga yay ɗakinsu yana tsaki, maman Ama ta kallesa da mamaki tace, “Lafiya Abban Ahmad?”.
“Mtsoww mutanenki mana, wai yaushema har ya fara abinda mazan ƙwarai keyi?”.
Itama tsakin maman Ama tayi tana taɓe baki, “Ko baiyiba ai ayi mana bariki dan muce anyi, karma kilakinsu ya dameka, hakama wancan zuwan sukaita wannan abun sai kace wani namijin gaske”.
To su dai su Ahmad ma basusan sunaiba, sunacan suna firarsu cikin nutsuwa da nunama juna zallar aminci ba tare dasun damu da kowaba ko lamarin kowa a gidan, dan in zaka karsu basa faɗa maka yanda kowacce take rayuwarta a gidan ba da mijinta.
Suko anbi an saka musu idanu ko wanne motsinsu abin ayi tsogumine.
Tana kwance kanta bisa cinyarsa yana wasa da gashinta, wayarsace a hannunta take kallon hotuna suna firarsu cikin nutsuwa.
Har kusan goma da rabi sannan Ahmad yace su tashi haka nan su kwanta barci yakeji.
Batai musuba ta tashi tai kaye-kaye tayo alwala da brush kamar yanda shima yayo, sanda ta shigo haryayi shirin barci ya haye gado, itama kimtsawa tayi bayan ta kashe fitilar ɗakin har Ahmad na mata tambayar lafiya.
Ca tai masa babu komai.
Murmushi kawai yayi yaɗan girgiza kansa yana gyara kwanciyarsa.
Sai da ta gama ƙumshe-ƙumshenta sannan ta hawo gadon.
Yau ɗinma dai sun gwangwaje juna da soyayya mai tsayawa a rai, duk da dai Rumana ta yabama aya zaƙinta, dan Yah Ahmad ɗin bana wasan yara bane.
Shi kansa yasan tayi laushi bana wasaba, yau ma wankansu sukai a roba ya fita ya zubda ruwan ita kuma ta goge inda sukaɗan ɗiɗɗisar da ruwan.
Aiko tunda suka kwanta Rumana batai ko juyiba tsabar gurzuwar da tayi, a hakan kuma bayan sunyi sallar asuba ya sake nuna buƙatarsa, babu yanda ta iya dole ta amince kodan gujema fushi.
Aiko harda ƴan ƙwallanta, dan ita kam jarumtarsa tsoroma take bata, inhar haka za'a cigaba dayi lallai akwai jan aiki a gaban mata kenan?.
Da ƙyar Umm-Ruman ta iya tashi bayan sunsha barcinsu kusan goma na safe, haka ta daddage ta miƙe domin haɗa musu abin kari.
Shima tashin yayi, ya zira jallabiya ya fita, babu jimawa sai gashi ya dawo, lokacin tana ƙofar ɗaki ta kunna risho.
Ciki ya wuce, ita kuma ta cigaba da ayyukanta, bayan ta ɗora ruwan cikin ɗakin ta koma, yana kishingiɗe a tabarma dan haka ta samu ta gyara gadon, ta ɗan share ɗakin ta gewayeshi, har tsakar gidan ta share ta wanke bayi, duk wannan hidimar da takeyi kuma Maman Ama bata gidan, tunda Kausar tai nauyin da bata iya zama suyi gulma to bata iya zaman gidan, to dama ita mijinta ƙarfe bakwai yabar gidan, shiyyasa sam bata kallon irin wannan lokacin matsayin safiya.
Rumana dai ta gama haɗa kalacinta, ruwan wanka ta sirka taje tayo, sai da ta fito sannan ta haɗama Ahmad.
Koda ta faɗa masa ga ruwan wanka bai musaba ya miƙe yaje dan ya yo, saboda shima a damuwar son tsarkake jikinsa yake.
Kafin ya fito Rumana harta shirya, ta mulke jikinta da ƙamshi.
Koda ya shigo itace ta taimaka masa ya shafa mai kamar yanda ya buƙata, duk da tanajin nauyinsa haka ta daure danta lura bayason yace ai masa abu ake masa gardama.
Itako yanda yake sakewa da ita a yanzu ai bata fatan taga ɓacin ransa sam.
Iya gajeren wando da singlet kawai ya saka ya zauna sukai breakfast, bayan sun kammala yace ta fiddo masa kayan da zaisa, dan Sufyan zaizo suje makaranta ne.
Taji daɗin wannan girmamawa tashi, dan haka ta zaɓo masa kayan da tasan idan yasa suna ƙara masa kwarjini da ƙyau, da taimakonta ya saka hardasu hula, tsaf ya fito asalinsa na bahaushen arewa, ta saka masa turare.
Kuncinta ya sumbata yana miƙa mata agogonsa da faɗin, “Thanks”.
Kanta ta jinjina masa tana ɗan murmushi, ta kama hannunsa ta ɗaura masa agogon.
Ji take kamar tace ya zauna kawai taita kallonsa......
Ya katse mata tunani da faɗin, “Bara muje inaga ya iso ga kiranshi nata shigowa, sai mun dawo”.
“Tom Adawo lafiya, amma mi za'a dafa?”.
“Komaima ki dafa, Abu zaizo, ki duba a kayan dana cire zaki samu kuɗi saiki bashi yayo cefane”.
Yana gama faɗa ya fice, ita kuma ta bisa da addu'ar dawowa lafiya.
Ajiyar zuciya taɗan sauke bayan fitarsa, ta zauna a bakin gadon tana cije baki, wlhy jikinta sai ciwo yake mata, “kai Yah Ahmad babu sauƙi” ta faɗa a fili tana matsa cinyoyinta.
Dole ta sake daurewa ta tashi ta sake kimtsa ɗakin da kyau, sai da taga komai ya mata yanda takeso sannan ta samu nutsuwa, barci ne sosai a idonta amma haka ta daure ta zauna jira Abu.
Shima babu jimawa yazo saboda kiransa datai ta waya, kuɗin ta ɗakko ta bashi kamar yanda Ahmad ya faɗa, ta lissafa masa abinda zai sayo.
Da yake aiken na mai hankaline bai jimaba ya dawo, itama ta miƙe batai son jikiba tai abincin.
Dan danan ta kammala ta tsaftace wajen tamkar batai ba, alwalar azhar tayi ta shige ɗaki, har lokacin su Ahmad basu dawoba, aiko tana idan da salla kasa jurewa tai tasa filo ta kwanta a wajen, cikin mintuna ƙalilan barci yay gaba da ita.
__________________________________
Hajiya Samina matan masu hannu da shinu, yanzu kam babu laifi tana ɗan samun yanda takeso wajen angon nata, sai dai fa shan giyarsa da ɗura mata maganin hana ɗaukar ciki yana nan yanayi bai fasaba, idan tai masa gardama taci dukan banza.
Matsala ɗayace yanzu taso tasota a gaba, wato maganar ƙara aure da mahaifiyar ma'aruff take yawan yi masa, duk da shi dai bai amsa zaiyiba hakan na tada hankalin Samina matuƙar tiƙewa.
Dole ta lallaɓasa akan tanason zuwa gidansu cikin satin nan, dama baifi sau biyu ta taɓa zuwaba a cikin kusan wata huɗu da aure, amma gidan iyayensa kam dukda ana hantararta haka yake sakata taje dole, gidansu kam ya hanata, data ambata zaice mizataje tayo? Bayanma ba wani buƙatar ganinta sukeba ƴan gidan nasu, idan kuma kannenta sukazo yayta fushi yana faɗin shifa bayason wannan shigi da ficin.
Hakan na mata ciwo a rai, amma tana dannewa dan a zauna lafiya.
ALLAH ya dorata a kansa kuwa yau ya barta, amma yace sai ranar talata, batai musuba ta amince tunda dai ai nanda kwana biyune kacal.
___________________________________
Sai bayan la'asar su Ahmad suka dawo, tare da Sufyan suka shigo gidan, amma sai Sufyan ya tsaya a ƙofar ɗaki sai da Ahmad ya fara shiga saboda sunyi sallama basuji Rumana ta amsaba.
Kwance Ahmad ya isketa tana barci, da alama ma ko sallar la'asar batayiba.
Wani ɗan tsigunno yayi a gabanta yakai hannu ya shafa fuskarta, jikinta da ɗan zafi kaɗan, bai kawo komai a ransaba game da ɗumin jikin nata, ganinsa kawai dan tana a cikin ɗakine.
A hankali ya fara kiran sunanta yana cigaba da shafa fuskarta, “Umm-Ruman;”
A hankali ta buɗe idanunta a kansa, ganinsa tsugunne a gabanta ya sakata sake buɗe idanun nata sosai tana kallonsa, murya a sanyaye tace, “Yaya kun dawo?”.
Kansa ya ɗaga mata, ya miƙa mata hannunsa ta kama ya taimaka mata ta tashi.
“Koma salla bakiyiba halan?”.
“Eh wlhy Yaya banma san anyiba, banyi zaton barcin nawa zaiyi nauyi hakaba”.
Hijjab ɗin daya ɗakko yake ƙoƙarin saka mata, “Ai gara da kikayi ƙyaji daɗi, tare muke da Sufyan”.
Tayashi saka hijjab ɗin tai tana faɗin, “Yana ina to?”.
“Gashi a ƙofar ɗaki, munyi sallama ne baki amsaba shiyyasa ya jira na shigo naga lafiya?”.
“ALLAH sarki, kuyi haƙuri banjiba wlhy, ya shigo to”.
Izinin shigowa Ahmad ya bama Sufyan, ya ɗaga labulen ya shigo sallama ɗauke a bakinsa.
Rumana tai masa barka da zuwa ya amsa yana zama da tsokanarta.
Fuskarta ɗauke da murmushi ta ɗauki tiren data shiryama Ahmad abinci takai gabansu tana gaida Sufyan ɗin, koda suka gaisa saitai yunƙuri durƙusawa zata zuba musu abincin.
Ahmad dake latsa waya yana saurarensu ya ɗago ido ya kalleta, a hankali ya furta, “Jeki abunki zamu zuba”.
Yanda fuskarsa babu walwala yasa bata musaba tama fita domin yin alwala.
Lokacin data shigo harsun fara cin abinci, sallarta ita dai ta kabbara, koda ta idar saita fita tabarsu sunacin abincin suna hirarsu.
Koda suka kammala ma tare suka sake ficewa daga gidan Sufyan nata mata santi, ita dai murmushi kawai takeyi kanta a ƙasa har saida suka fice.
Ta tattare kwanikan ta fita dasu danta wanke, tana wanke-wanken suna ƴar fira da Kausar data fito take shan iska a ƙofar ɗakinta, Maman Ama dai bata gidan tana gidan maman Aysha.
A haka tazo ta samesu, kawai sai gani sukai ta ɓata fuska, ko zato take gulmarta sukeyi? Bata san su firar tasuma akan haihuwar Kausar ɗin bace..
Tunda Rumana taga yanda tayi saita miƙe abinta dama ta gama wanke-wanken ta koma ɗaki kawai.
★★★★★★
Yauma anayin sallar isha'i Ahmad ya shigo gidan, ledar daya sayo musu kayan fruits ta amsa tana masa sannu da zuwa, kwalliyar datai yakebi da kallo dan ta mata ƙyau, itama ta lura da kallon da yake mata tun shigowarsa.
Ta katsesa da faɗin, “Yaya a haɗa ruwan wanka?”.
A taƙaice yace, “Uhm”.
Sai da takai masa har banɗaki sannan ta dawo ta sanar masa, ya miƙe ya cire kayansa ya saka jallabiya ya fita.
Kafin ya dawo ta saka fruits ɗin a filet mai ɗan girma, tana fiddo masa kayan da zaisa ya shigo.
Da taimakonta ya shirya dukda dai ita takasa sakewa dashi yanda ya kamata har yanzu, sosai takejin nauyinsa, abinda yasa take daurewa saboda ta lura yana son tattali, nuna kulawarta a garesa sosai ke sakashi sakin mata fuska tana ganin fara'arsa, a ganinta ta wannan hanyarne zata cusa masa sonta a rai koda bata samu kwatankwacin abinda Samina ta samuba na soyayyarsa, itama ta samu wani yanki a ciki.
Sai dai abinda Rumana bata saniba shine tuni tayi mamayar da Samina batai koda kwatankwacinta ba a zuciyar gwarzon nata, kawai dai bai furta baneba.
Yau ɗinma bai ɗaga mata ƙafaba, danshi dai ji yake ta sake canja masa fiye da wancan karon, shiyyasa baya gajiya da ita.
Rumana dai kam dauriya kawai takeyi, dan batajin daɗin jikinta sam, da safe kuwa luɓus ta tashi harda su zazzaɓi, to dama can ba isashshen lafiyarne da itaba shikuma yazo ya sake nuƙurkusarta.
Duk yanda yaso kuma suje asibiti tace ita kuma a'a, har sai da yakai da zazzaga mata masifar dabai niyyaba, sai kawai ta saka masa kuka.
Abin nan ya bama Ahmad haushi, dan baiga abin kuka a wajen ba shi dai.
Ƙyaleta yay yama shirya ya fice daga gidan dan jiya bai kammala uzirirorinsa ba shida Sufyan.
Yau ɗinma tare suka tafi da Sufyan ɗin a mashin ɗinsa.
Sai dai duk abinda yakeyi zuciyarsa nakan Rumana daya bari kwance duk da haushin data bashi.
Rumana kuwa kusanma sha biyu sai taji ta ta dawo dai-dai, sai dai ciwon jikin da Ahmad ɗin ya haddasa matane kam bai bartaba.
Abincima ta tashi tayi sannan ta gyara jikinta.
Lokacin da Ahmad ya shigo gidan sai ya isketa da su khadija ƙanwarta sun kawo mata kayan sana'arta da akayo daga can.
Ya ɗanji sanyin ganinta haka, amma sai bai sakar mata fuskaba.
Yaran suka gaidashi itama tai masa sannu da zuwa, duk amsawa yay a dake har ita ɗin.
Da kansa ya ɗiba ruwa ma ya tafi wanka baice ta haɗa masaba, koda ya fito ta gama shirya masa abinci, su Khadija kuma ta basu aikin data kauda hankalinsu suka dawo waje.
Ganin yaƙi kallon ko inda ta ajiye abincin sai ta daure tace, “Yaya ga abinci”.
Kamar bazai tanka ba, sai kuma ya juyo yaɗan. kalleta ya ɗauke kansa, “Na ƙoshi, ke da baki da lafiya kuma waya aikeki yin abinci?”.
“Dan ALLAH kayi haƙuri Yaya, naji sauƙi, dama kuma bawani yayimin zafi bane zazzaɓin”.
Bai amsata ba, dukda ta bashi tausayi, ya canja kayansa, da alama dai wanima wajen zai sake fita.
Sai da ya kammala tsaf sannan ya zauna ya buɗe abincin data ajiye, matsowa tai tana jin sanyi a ranta da zaici, ta zuba masa, tana ƙokarin komawa gefe yace, “K kinci?”.
“Naƙoshi” ta faɗa kanta a ƙasa.
Cokalin ya ajiye yana yunƙurin mikewa, “Cin nawa baida amfani kenan”.
Saurin katseshi tai har tana dafa masa hannu, “Yi haƙuri yaya Please zanci wlhy”.
Sai da ya zuba mata harara sannan ya koma ya zauna.
Daga ƙarshe dai a tare sukaci abincin sannan ya fice yana faɗa mata bara yaje baba na jiransa zasuje wata gaisuwa.
A dawo lafiya tai masa.............✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻https://youtu.be/N2nbw8zn9Jk
*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*_GDW_*
*(31)*
...............Cikin sauke ajiyar zuciya Umm-Ruman tace, “Kai Yah Ahmad ko daru” idan ƴan arziƙin sukazo ayi, idan ƴan tsiyarne ya koma mata Ahmad ɗin data sani a gida.
A cikin kwana biyun nan dai kam ya bala'in maida kansa busy, hankalinsa bai samu zama waje ɗaya ba sai da ya haɗa kan duk abinda yake buƙata sannan.
A daren jiya malam ya tashi da mura ta rashin jin daɗin jiki, abunka da jikin tsufa, zuwa safiya sai abun yaso yin ɗan tsanani, tunda safe sukai kiran Ahmad koma barci bai tashiba kiran ne ya tadashi.
A gurguje yay brush ya canja kaya ya fice.
Tunda ya fita Umm-Ruman tai tagumi kawai tana ma kakan nasu addu'ar samun afuwa.
Ahmad na zuwa basu ɓata lokaciba asibiti suka wuce, shi da Mudan sukai ta shigi da fici saboda sune dai manyan ƴaƴa maza a gidan, iyayensu kuma ba karatu sukaiba, suma kuma suna bukatar a taimaka musun.
Dukansu dasu akaje asibitin, amma dai su Ahmad ɗinne keta kai da kawo har aka bama Malam gado sannan sukaɗan samu nutsuwa.
Rumana tun tana jiran dawowar Ahmad harta fara damuwa sosai, ta gyara ko ina dai tayi musu breakfast, sai dai ta kasa ci.
Tana zaune jugum har kusan ƙarfe ɗaya sai gashi ya shigo, jiki a sanyaye ta miƙe tana masa sannu da zuwa.
Ya kalleta yana ɗan lumshe ido ya jinjina mata kai kawai, dan jikinsa yayi luɓus saboda kai kawo da sukaitayi, ga yunwa na cin hanjinsa.
“Yaya ya jikin nasa?”.
Kaɗan ya sauke numfashi yana zama a bakin gadon, “Da sauƙi sosai, sunata ƙara masa ruwane dan yaji ƙarfin jikinsa”.
“Wayyo malam ALLAH ya ƙara lafiya yasa kaffarane”.
Da amin Ahmad ya amsa yana miƙewa ya fara cire kayansa, hakanne ya saka Rumana fita danta haɗa masa ruwa.
Tana dawowa shi kuma ya fita zuwa bayin, koda ya fito yaga ta ajiye kayan shayi sai ya kalleta da mamaki.
“Kina nufin zama kikai jirana baki karyaba?”.
“Yaya banji yunwa bane shiyyasa”.
Baice komaiba ya ɗauke kansa, ya kimtsa ya fita massalaci domin gabatar da sallar zuhur.
Itama Rumana abinda tayi himmar yi kenan, bai kuwa jimaba sai gashi ya dawo ɗauke da ɗanyan indomie a leda.
ledar ya miƙa mata yana faɗin, “Tashi ki dafa wannan”.
Amsa tai cikin girmamawa, kafin ta kammala yaɗansha tea dan yunwa yakeji bata wasaba, koda ta gama da ƙyar ya sakata taci abincin, ya lura batason cin abinci yanzu, ga wani tsarce-tsarcen yawu daya lura tanayi a kwana biyun nan.
Bai dai ce mata komai akan hakanba yace dai ta shirya suje asibitin ta duba malam.
Taji daɗi sosai, ta shirya tsaf ta kawo hijjab ta saka, maman Ama na tsakar gida suka fito, sai da Rumana ta kammala rufe ƙofarta kafin tace mata saisun dawo kakansu aka kwantar a asibiti.
Addu'ar samun lafiya maman Ama tai musu tanabin Rumanan da kallon ƙurilla, itafa saima taga kamar mai ciki.
Tsaki taja tana faɗin, “Toni bandama abuna waye yay cikin? matar da ko namiji bata taɓa saniba ta ina zata samo ciki?, inaga dai dagaske maganain ƙibar sukasha ita da mijin”.
🤣Maman Amar mu ta mutunci kenan, ido bai gani baki ya ƙyalle saiya tofa, ALLAH ya gyara mana ke da masu irin halinki🤸🏻♀😂 .
Rumana tayi mamakin ganin ashe da mashin ɗin Sufyan Ahmad ɗin yazo.
Sai da ya hau ya tada sannan ya kalleta ganin tayi tsaye tana kallonsa kamar ta samu tv,
“Kona wuce ne?” Ya faɗa manyan idanunsa a kanta.
Da sauri ta ƙaraso, dole sai da ta dafa bayansa sannan ta hau.
A zuciyarta take faɗin, “gaskiya roba-roba inba mijinkaba ai baida daɗin hawa”, to diba yanda duk ta koma jikinsa, ballema ita matsoraciyarnan dama.
Babu mai cema ɗan uwansa uffan har suka isa asibitin.
Samina dake jikin motar Ma'aruff da ALLAH ya ɗorata a kansa ya kawota duk da dai akwai manufa a ransa, dan soyake yakai yarinyarsa gida suɗan huta, shiyyasa ya ɗakkota da kansa ya kawota gida kamar yanda yay alƙawari, sai dai suna zuwa aka sanar musu malam na asibiti, duk matan gidanma basu daɗe da tafiya ba sai yara kawai.
Da kansa yace tazo ya kaita asibitin itama, idan ya ajiyeta sa dawo gida da ƴan gidan nasu, da daddare kuma zai dawo ya ɗauketa.
Wani sama taji kanta kuwa, shiyyasa akai shiri na alfarma, yanzu haka sun shiga sun dubo malam ɗinne tazo rako Ma'aruff da zai wuce.
Tun shigowar mashin ɗin su Ahmad akan idontane, gabanta yay wata irin faɗuwa zuciyarta sai fatt-fatt take da masifar ƙarfi.
Ma'aruff dake magana batajiba ya kalli inda tabi da kallo kamar idonta zai zubo ƙasa.
Akan Ahmad dake faka mashin ɗin ya sauka, Umm-Ruman ta dafa bayan Ahmad zata sauka shida baima san su Samina nayiba ya ɗan juyo ya kalleta yana faɗin, “Babie R karki karyani fa”.
Murmushi mai ƙayatarwa Rumana tayi, ta ƙarasa sauka tana bashi amsa,
“Oh Yaya, da nice fa yanzu kacemin raguwa”.
Shima saukar yay yana murmushi da ƙoƙarin ajiye mashin ɗin da ƙyau, ya juyo yana ɗan ranƙwafowa ya lakaci hancinta da faɗin, “Yo ai ragguwarce”.
Yanda Rumana ta ɗan ɓata fuska a shagwaɓe ne ya bama Ahmad dariya, dan haka yace, “Zaki wuce mu tafine ko saina ɗaukeki?”.
Baya ta matsa tana masa harar wasa, ta tofar da yawun daya taru mata a baki kaɗan tana fara tafiya.
Hannu ya kai zai riƙota tai wani ɗan taku mai hanzari kamar zata ruga.
Dariya Ahmad yayi har haƙoransa na bayyana, yace, “ALLAH zan kamakine Yarinya”.
Wannan kalma tashi karaf a kunnen Samina da Ma'aruff dake binsu da kallo kamar idanunsu zasu faɗo ƙasa.
Sukam su Ahmad ma basu lura dasu ba har suka shige.
Ma'aruff ne ya fara taɓe baki yana faɗin, “To shi wannan faƙirin yaushe yay ƙiba haka? Ko shima sha ka fashe ɗin da mata ke sha ya sha?”.
Banza Samina tai masa, dan ita kaɗai tasan sukar da takeji a zuciyarta, badan ta baro handbag ɗinta wajen mama gaje na a ciki da wlhy bazata koma ba.
Shiko Ma'aruff Umm-Ruman ce ta tafi da zuciyarsa, harya kasa haƙuri sai da yay ma Samina tambaya, “Wai dama wannan aka aura masa?”.
Guntun tsaki Samina tai, a taƙaice tace, “Uhm”.
Babu zato taji Ma'aruff yace, “kai amma ƙyaƙyƙyawa da ita, wlhy tama fiki ƙyau da nutsuw....”
Sai kuma yay shiru bai ƙarasaba ganin kallon da Samina tai masa a hargitse.
“Kinga malama daina watsomin waɗanan idanuwan, indai nine ma kinga tafiyata, kice ina gaidashi shida ƙyaƙyƙyawar matarsa dan ALLAH”.
Hawayene kawai suka shiga sakkoma Samina a kumatu, wanda ita kanta batasan na minene ba, da ƙyar ta iya tsaidasu tabi bayan su Ahmad, dukda tsantsar kishin Rumana daya doki ƙirjinta bazata iya daurewa ba sita sake ganinsa ko zataji sassauci.
Su Ahmad kam tunda suka shiga iyayensu mata duk suka zubama Rumana ido, sukam basu fahimtaba, cikin girmamawa duk suke gaishesu daga Rumanan har Ahmad.
Tsagwaron farin cikine ya bayyana a fuskar Ayyah, hakama Gwaggo da Ammi sai dai su sun shanye a zukatansu, su dai su Yaya maryam sun kasa ɓoye farin cikinsu duk da hasashe suke ba tabbatarwa sukaiba, Mama gaje kuwa zuciyarta sai gudu take da sauri-sauri.
Ahmad da Rumana dai suka shiga inda Malam ke kwance danta dubashi, barci yakeyi, shi kaɗaine a ɗakin har yanzu kuma ana saka masa ruwa, likatanne yace duk su fito dan ba'ason ana masa yawan hayaniya.
Basu jimaba a ɗakin suka fito, Ahmad ya nufi wajen likita dan yaji ya ake ciki yanzu?, ita kuma Rumana ta zauna wajen iyayensu mata da yayyanta.
Lokacin Samina ta shigo, dan haka Rumana ta gaisheta da bata haƙuri akan rashin zuwa dubata da bataiba, tace alokacin itama batajin daɗine.
Cikin ɗan taɓe baki Samina tace, “Karki damu” daga haka taja bakinta tai shiru.
Itama Rumanan sai bata sake cewa komaiba, su Ayyah ma duk suna saurarensu amma babu wanda ya saka baki.
Tashi Samina tai ta nufi office ɗin likita wai bari taje taji yaya ake ciki? Babu wanda ya tanka mata sai mama gaje, dan tunda tazo asibitin taketa nuna isa ita adole matar mai arziƙi, har cewa tai za'a canjama malam asibitin iya tace a'a nanma ya Isa, Ahmad nata iya bakin ƙoƙarinsa hakanma su ya wadatar.
Yanzu kuwa data tsiri zuwa Office ɗin likita kowa ya fahimci Ahmad ta hango ya shiga ƙila.
Babu kuma wanda ya tanka mata akan hakan.
Yanda Rumana ta kasa zama taketa fita zubda yawune ya saka amaryar baba iliyasu tai magana cikin murmushi,
“Rumana kiringa samun ko cingam ne ko wata alewa haka kina sakawa a bakin, zai rage miki tara yawun kinji”.
Rumana da bata fahimci al-amarinba tace, “To Umma, ni wlhy nama rasa miya kawo hakan, sam ban iya haɗiye yawun yanzu, idanma nai kuskuren haɗiyewa sainaji kamar zanyi amai ko zuciyata taita tashi”.
Su dai iyayen da suka fahimci tsagwaron wautar Rumana duk sai sukai murmushi, sai su Yaya Raheenatu ne suke mata dariya sosai.
Ahmad na zaune suna magana da Doctor Samina ta shigo ko neman izini babu, kallo ɗaya Ahmad yay mata ya ɗauke kansa yana sake shan toka, zama tai a kujerar dake kallon tasa, hakanne ya saka Ahmad miƙewa yana bama Doctor hannu sukai musabaha yana masa godiya.
Ya tsallakota zai fice ba tareda yama nuna yasan ƙurar data kwasota ba, gudun kar taji kunya yasata tasowa da sauri tabiyosa, nanma baiko dubeta ba dukda yana jin takunta gab da shi, kusan a tare suka iso wajen, aiko Rumana da ganinsu tare ya sosa ranta karaf sai suka haɗa ido da Ahmad.
Yanda ta juya idanun ta ɗauke daga kansane ya bashi mamaki, dan tsagwaron kishi ya hango a cikinsu, saima yaga ta miƙe ta fita.
Ayyah da duk ta kula da abinda ke faruwa tai dariya a zuciyarta, kallon Ahmad ɗin tai tana faɗin, “Ɗan albarka ya kamata a samowa Umm-Ruman wani ɗan abu ta saka a bakinta koda alewane ko cigam, wannan zubda yawun baida daɗi, ta kasa zama waje guda ta huta”.
Da kallo yabi Rumanan data dawo yanzu ta zauna, shi kansa abin ya fara basa mamaki, yace, “To Ayyah bara na samo mata, zama muje taga likitane, ni kaina narasa mike damunta”.
“Allazi an ƙara kenan” cewar Sakina tana dariya.
Harararta Ahmad yay dan dama tunda ya shigo basuyi faɗan da suka saban ba.
“Allazi an ƙara me? Kekuma?”.
Sakina tace, “Haba ɗan ƙanina miye na fusatar?”.
Hannu ya kai zai ranƙwasheta ta matsa tana faɗin, “ALLAH kana taɓani akan matarka zan rama, a maganata dai ai ban ambaci sunkaba ka tsargune kawai”.
Dariya kowa ke musu, dan babu wanda baisan wannan ƴar tsamar dake tsakanin Ahmad da Sakina ba, inhar suka haɗu faɗa sau goma su shirya yamusu kaɗan.
Shi yaƙi yarda ta girmesa, ita kuma bazata fasa faɗar shi ƙaninta bane🤣.
Ƙwafa yay zai bar wajen, tace, “Iye kaga su Amadi masu mata, saboda nace zan rama a kantane ka haƙura kenan, a lallai soyayya ruwan zuma”.
Wucewarsa yay bai tanka mataba, ya saki lallausan murmushi saboda iya shegen da Sakina ke masa har yanzu shida Rumana.
Babu abinda zuciyar Samina keyi sai zallo, adai fahimtarta suna nufin Rumana ciki ne da ita, cikinma na Ahmad ɗinta.
Wata irin tsuma jikinta keyi, numfashinta kuwa da ƙyar take fusgarsa wajen fitarwa.
Ana cikin haka sai ga Ahmad ya dawo da leda mai ɗan girma, har gaban Rumana yaje ya miƙa mata ledar, ta amsa kanta aƙasa saboda nauyin iyayensu da yayenta, shiko ta kula koma ajikinsa, kansa tsaye yake komai.
Saboda neman magana irin na Sakina ta amshe ledar daga hannun Rumana tana dubawa, “Iye kwali-kwali fa ya siyo, Amadi bara na raba nima naɗan ɗib.....”
Ai bata ƙarasaba taji saukar rankwashi mai zafi a kanta, ya kuma fisge ledar yana fadin, “Ko kece ƙwalan ta kankia bazaki lashi ko ledar abu ɗayaba”.
Aiko mi za'ai inba dariyaba, Sakina kuma ta dafe kanta kamar zatai kuka, tace, “Kam balastin, aiko ka jama matarka, kanta zan rama”.
Sake juyowa yay ya kama hannun Rumana yace, “Basai idan ta zauna inda kikeba zaki raman”.
Rumana duk da kunyar da ta nema halakata tanaji tana gani Ahmad yaja hannunta suka bar wajen.
Sakina tace, “Matsoraci kawai”.
Gwalo ya juyo yay mata yace, “Oho dai”.
Basu Ayyah ba hatta dasu Baba sai da sukai dariyar wannan rikici na Sakina da Ahmad.
Samina kuwa tsaki tayi zuciyarta na mata zafi da turiri, wannan itace ƙauna da soyayya da riritawar datai tsammanin samu daga Ma'aruff, amma sai gashi tana ganinta wajen wanda takema kallon gara, faƙiri.
Ta haɗiye wani yawu mai kauri tana binsu Ahmad dake ƙoƙarin shiga Office ɗin doctor da kallo, kuma har suka shige bai saki hannun Umm-Ruman ba, jitai wata irin tsanar yarinyar na ƙara mamaye duk illahirin zuciyarta.
Mama gaje tsaki tayi, sosai maganar cikin nan na Rumana ya tokare maƙoshinta, a ganinta Samina ta cancanci wannan cikin, babu wanda yabi ta kansu dan bama asan sunaiba.
Su Umm-Ruman kuwa a office ɗin Dr suka yada zango, dama bayanin da Ahmad yaje ɗazun yay masa kenan, bayan sun zauna Rumana ta gaida likitan ya amsa da ƴar fara'a yana tambayarta yaya jikin.
Sai da ta kalli Ahmad sannan tace, “Nifa banajin wani ciwo a jikina Yaya”.
Murmushi Doctor ɗin yayi, danshi tun shigowarsu ya fahimci Rumana nada ƙaramin ciki.
Shine ya katse musu kallon da sukema juna, Ahmad na harara-harara, Rumana na kallonsa a tsoro-tsoro.....
“Hajiya ai dama bamuce muma wani abu na damunki ba, jininki kawai zan ɗan ɗiba yanzu.
Dole ta amsa da to, saboda yanda Ahmad ya tsuke fuska.
Kiran waya Doctor yayi, babu jimawa wata Nurse ta shigo, ita yasa ta ɗiba jinin Rumana ta fita dashi zuwa lab.
Tashi sukai suka koma wajensu Ayyah, dan Doctor yace sai nan da kamar awa ɗaya zai basu bayani idan result ɗin ya fita.
Ahmad bai zaunaba suka wuce massalaci dasu baba, Rumana kuwa tazo ta zauna wajenta nada.
Tun tana sauraren hirar yayun nata har itama ta fara saka baki, Samina ce dai ta koma gefe ta tsume taƙi shiga cikinsu, a ganinta ta wuce da ajinsu, gefe kuma mugun haushin Umm-Ruman takeji dama su kansu ɗin da suke tarairayarta.
A haka su Ahmad suka dawo, baba yace su tashi duk su wuce gida hakanan anbar yara su kaɗai, su zasu zauna har malam ɗin ya farko.
Rumana sai addu'a take ALLAH yasa Ahmad yace ta bisu, tanata satar kallonsa amma shi yaƙi kallon inda take sai faman latsa wayama yakeyi, a bazata baba yace Samina da Rumanan suma suje can idan mazajen nasu sun tashi sa biya su ɗaukesu.
Dama ita Samina can zata koma, Rumana ce ke a cikin ƙila wakala, shiyyasa baba na faɗa wani daɗi ya ratsa ranta da zuciyarta.
Aiko tana ɗago ido ta tsinci na Yah Ahmad dake antaya mata harara.
Fuskewa tai ta ɗauke kanta kamar ma bata ganshiba, takobi su Ayyahn.
Tun a wajen asibitin Mama gaje da Samina suka raba hanya dasu Ayyah, dansu daga nan wajen malaminsu suka nufa Inna mari nacan na jiransu dama tun ɗazun.
Babu wanda ya damu da lamarinsu kuwa, dan suma su Sakina ayarin ƴan gidan nasu sukabi kowa nason ƙarasa yininsa a gida, hakama bintu yayar Samina gida tabi ƴan uwanta tanama mahaifiyarsu da ƴar uwarta fatan shiriya a wannan rayuwa.
★★★★★★
Ba ƙaramin daɗi Rumana ta tsinci kantaba na ganinta a gida cikin ƴan uwanta, su Fa'iza harda mata sherin wai akuyar ɗaure ta samu sake.
Daƙƙuwa kawai tai musu tana dariya.
Abinda ya tsayama Rumana a rai yanda kowa ke mata magana akan ta kula da kanta sosai, sannan tabar zama babu wani abu a bakinta saboda hanama kanta zubda yawu. Ɗan tsarguwa ta farayi a ranta jin Yaya Bintu na faɗin, “ALLAH dai ya raba lafiya wannan ɗan gatan dangi ya fito duniya musha shagalinmu”.
Rumana tai kasaƙe tana tunani, idanfa har zata ɗora maganganunsu a mizani kamarfa suna dangantata da cikine na haihuwa? To amma haka ake cikin dama babu wani wahala? Ita dai bayan ciwon kai dataita fama dashi kwanaki batajin wani ciwo a jikinta sai na rashin jin daɗin jikinta, tanajin komai na sauya mata a jiki kam sai wannan zubar da yawun shima baifi kwana biyu kenanba ya fara addaba mata.
Kauda zancen tai kawai a ranta da yaƙinin ba haka bane, ta cigaba da hidimarta hankali kwance............✍🏻😑
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻https://youtu.be/HFjVgQVnmn0
*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*_GDW_*
*(32)*
............Bayan tafiyar su Rumana Doctor yake sanarma su Ahmad sakamakon gwajin da akai mata, ya tabbatar musu tana ɗauke da ƙaramin ciki ɗan watanni uku.
Daga su Baba har Ahmad bayyana farin cikin da suka tsinci kansuma a ciki ɓata lokacine, bakin kowa ya kasa rufuwa, wannan aure da suka haɗa yayi riba, dan sun sake tabbatar da ƴaƴansu sun amshi ƙaddarar UBANGIJI da hannu biyu.
Ahmad sai sinne kai yake yana murmushi, shi adole kunyar su baba yakeji, Su Mudan ne dai suketa shirmensu shi da Abu da sauran ƙannensu.
A wannan yanayin farin cikin abokan Ahmad suka iskesu, suma sunzo duba Malam.
Aiko sunajin abinda ke faruwa suka tasa Ahmad da sheri, baiko ɗaga musu ƙafaba ya shiga ramawa.
Gaba ɗaya Ahmad ya kasa daina mamakin abun a ransa, wai shine yau da ɗa, Umm-Rumana zata haifa masa ƴa ko ɗa mallakinsa.
Ya lumshe ido yana haɗiyar wani tsinkakken yawu da sauri-sauri, taɓasan da Sufyan yayine ya sakashi buɗe ido yana kallonsa.
Sufyan yay murmushi tare da faɗin, “Kai Alhaji duk murnarce? Badanma ka tsaya jamana ajiba ai da wannan watanne watan haihuwa”.
Ƙaramin naushi Ahmad ya kaima Sufyan, da sauri Sufyan ya kauce yana dariya, Ahmad ya faɗaɗa murmushin sa yana harar Sufyan ɗin, “Ɗan sa ido kawai, nakula ka fara lalacewa kaje kai aure?”.
Rabi'u yace, “Iye kaji masu aure, mikakeci na baka na zuba, muma muna nan tafe insha ALLAH, dan da yawanmu bazamu wuce shekarar nanba”.
“Da nayi farin ciki kuwa, ko yaya nasamu sauƙi daga iskancinku” Ahmad ya faɗa yana hararsu.
Nanma dariyar suka ɗanyi kaɗan.
Suna a asibitin har kusan tara na dare, a lokacinne kuma cikin amincin ALLAH malam ya farka, kowa yaji daɗin yanda ya farka daɗan ƙarfinsa, kuma a hayyacinsa, dama can Malam bayason asibiti, hakanne yasaka shi yanzuma ya tijare musu akan bazai kwana ba su maidashi gida, da a hayyacinsa yakema bazai yarda a kawosa nanba.
Duk yanda su Ahmad da abokansa sukaso lallaɓa tsohon nan sam yaƙi harda shirin musu kuka yake.
Babu shiri Doctor ya basu sallama akan zai dinga zuwa da safe yana dubashi insha ALLAHU.
Sunji daɗin karamcin wannan likita, dan haka suka nufi gida da ƙwarin gwiwa.
★★★★★★★
Lokacin da suka iso gidanma Rumana ita har tayi barci a ɗakin Amminta, ta kwantane da fatan ALLAH yasa karsu Ahmad su dawo da wuri yau ta kwana gida, koba komai ta huta da fitinarsa ma.
Sai dai kam addu'arta bataci ba, dan su Ahmad suna kai malam ɗaki yaga komai ya dai-daita sashensu ya shiga.
Ayyah da Gwaggo sukai masa sannu da zuwa.
Amsawa yay yana zama kan dutsin dake kusa da kwatanniyar ruwan agwaginsa, gaishesu yayi suma, suka ƙara masa ya mai jiki, yace Alhmdllh, dan kuwa kowa yaga malam yanzu bazaice shine aka fita dashi shataf ba ɗazun da safe.
Ayyah tace, “Ɗan albarka a kawo tuwo ko?”.
“Ayyah anya kuwa zanci tuwon nan yau?, gaba ɗaya a gajiye nake kwanciya kawai nake buƙata yanzu, ko ma yunwar banaji sam”.
“Sannu kaji, zirga-zirgace wlhy, jiki da jini ai yana buƙatar hutu, to inko bazaka ciba kuzo ku wuce gida dare nayi, dan itama wannan yanayin nata bai buƙatar yawace-yawacen daren nan kodan shaiɗanu, tunda baikai ƙwariba har yanzun”.
Murmushi kawai Ahmad yayi, dan ya lura dai iyayensa mata su dukma sun gama fahimtar yayi ajiya ashe.
Gwaggo dai duk na zaune ta kunna redio tana sauraren taskar labarai, tana kuma jinsu sarai, amma yanda ta ɗauke kanta saika ɗauka batasan hidimar da akeyiba.
Sadiya ya ƙwalama kira, ta amsa daga ɗakinsu tana fitowa, da alama ma harta kwanta ya tasota.
“Jeki ki kira min Ruman mu wuce gida”.
Da “to” Sadiya ta amsa tana wucewa.
Shi kuma ya miƙe ya ɗauki buta ya shiga bayi.
Dai-dai nan baba ya shigo shima, daga Ayyah har gwaggo sannu sukai masa, ya amsa yana faɗin, “Su Amadu sun wuce dai ko?”.
“A'a yanzu dai suke shirin wucewar, yana bayi” Ayyah ta bama Baba amsa.
Baice komaiba ya shige sashensa.
Ahmad na fitowa Rumana da Sadiya suka shigo suma, sai kumbura fuska Rumana take saboda barcin data fara aka taso ta, ji take tamkar ta fasa ihu.
Ahmad ya sauke idanunsa a kanta, ta ɗan hasken farin watan daya gota sha biyar, hakan ya saka ƙyawunta kuma bayyana masa a cikin ido, ya sauke ajiyar zuciya kaɗan yana maida idonsa gasu gwaggo da Ayyah.
“Tom bara mu wuce sai da safen ku”.
Ayyah tace, “To ALLAH ya huta gajiya ɗan albarka, Umm-Ruman ALLAH ya ƙara lafiya kinji, aita addu'a dai ALLAH ya inganta mana ya kuma raba lafiya”.
Sadiya ce kaɗai ta amsa, Ahmad da Rumana kunya ta hanasu cewa komai, hakama Gwaggo da tunda aka fara zancen cikin bata tofa nata ba, tana dai cikin tsantsar farin ciki a cikin ranta.
Itama Rumana tai musu sallama tabi bayan Ahmad da yay gaba.
Sai da sukaje soro ne ya juyo, hannunta ya riƙo ba tare daya ce komaiba, dan ya lura kamar barcin data fara bai saketa ba.
A ƙofar gida sukaci karo da motar Ma'aruff yazo ɗaukar Samina, amma sai masifa yake mata akan tun ɗazun yazo kusan mintuna talatin yana jiranta, itako sai faman lallaɓashi take dan karya ɗaga murya ƴan majalissar abokan su Ahmad su ji.
Fitowar su Ahmad ne ta saka ma'aruff yin shiru yana kafe Umm-Ruman da ido tamkar idanunsa zasu faɗo ƙasa, suko koma kallonsu basuyiba duk da su Ahmad ɗin sunji jarabar da yakema Saminar, sun gittasu Ahmad yajiyo warin giya ya buso, mamaki ya kamashi warin giya daga ina haka? Yasan dai mu al'ummar arewa kasantuwarmu mafi yawa musulmai bamu cika huɗɗa da giyaba musamman yankinmu da Hausawa sukafi yawa, sannan shi baima taɓa jin warin giyaba a ƙofar gidan nasu sai yau, to lallai yana zargin kamar mijin Samina ne kenan?.
“ALLAH ya ƙyauta” ya faɗa a zuciyarsa yana ajiye tunanin gefe guda dan ba damuwarsa bace. Napep ya tare musu suka shiga.
Rumana da idonta ke cike da barci ta kwantar da kanta akafaɗar Ahmad, kaɗan ya juyo ya kalleta, idanunta lumshe suke, hakan saiya kuma fiddo ƙyawunta sosai, ga kalar hijjab ɗin data saka ya kuma fiddo da ƙyawun fusakar tata ainun.
Hannu yakai ya shafa kumatunta a hankali, ta ɗan buɗe idanun nata tana kallonsa, nasa idanun ya lumshe mata shima yana faɗin, “Karkiyi barcifa fa, banida ƙarfin ɗaukarki”.
Fuska ta kumbura dama can haushinsa takeji yasa Ammi ta tada ita, dan tace ace ya barta ta kwana kuma Ammi ta hauta da faɗa dole ta taso.
Kansa yaɗan jingina jikin nata yace, “Ni bana faɗa yau”.
Murmushi tayi mai sanyi ta maida idanunta ta lumshe tare da riƙe nasa hannu sosai tana shaƙar ƙamshin turarensa na tun ɗazu dake manne da jikinsa.
Shima murmushin yayi idonsa akan hanya.
Shi dai mai napep yana daga gabane yana kallon ikon ALLAH ta madubi saboda fitilar daya saka a cikin napep ɗin dake haska su Ahmad.
Koda suka isa gida bayan sun biyashi kuɗin, bai wuceba har sai da suka shige gidansu, Mai Napep yace, “ALLAH ka haɗamu da masoyan ƙwarai, kana gamo da irin wannan masoyan ai tuni kake tada ƙayar baya a gidanku ai maka aure yasin”.
Kunji mara man kai, sai kaje ka tada din😂⛹♀.
Ahmad ya amshi key ɗin ɗakin wajen Rumana ya buɗe, bata shigaba, hannu kawai ta zira ta ɗauki buta taje tayo fitsari sannan ta koma ɗakin, Ahmad na ƙoƙarin cire kaya ya tashigo, hijjab ɗinta kawai ta cire ta jefa saman gadon zata bishi ya riƙota.
“Daure muyi wanka saiki kwanta baki ɗaya kinji Babie R ɗina, maman kuma Babie na mai zuwa insha ALLAH”.
“Yayah Please wlhy barci nakeji, nidai yau bazanyi wankanba”.
Ya kula yau dai shagwaɓa takeji, sakata yay a jikinsa sosai suka zauna a bakin gadon a haka, cikin tausasa harshe yace, “Sorry Gwal ɗina daure kinji, zan saya miki sweet mai daɗi fa”.
“Kai yaya, wannan wayone fa wlhy”.
“Tab, waneni da yima Gwal ɗina wayo, ai kece Boss sai yanda kikeso za'ayi”.
Da wannan lallaɓar ya samu yaci galaba akanta harya cire mata kayanta, ya haɗa ruwan wankan da kansa ya tasata a gaba zuwa bayi.
Ita dai da ƙyar tai wannan wanka, suka fito kowanne yay alwalar kwanciya barci da brush, wajen shirin barcinma sai da yasha daga da ita, dan bil haƙƙi da gaskiya barcine taf idonta, to yau bata samu tayi ko barcin safe ba balle akai gana rana.
Duk ƙwazabar Ahmad kam ai dole yau ya ɗagama Rumana ƙafa sukai barcinsu, shi harma tsoro yake karya koma can kuma baya samu hakan ya damesa, duk yanda yaso dauriya da asuba kuwa ai bata yuwuba, sai da yaɗan rage zafi sannan yajisa dai-dai.
Shafin sabuwar tarairaya Ahmad ya buɗe ga Rumana, ita kanta abun har mamaki yake bata, data motsa zaice inane ke mata ciwo? Mi take so taci ko ta sha?.
Abun na bata dariya ainun, idan taso tsokanarsa har langare nasa take, sai ta gama tsurar dashi sannan ta dawo taita masa dariya.
Yakance babu komai i zai rama wataran, ta ɗauka yanzu itace a ciki shine a kwana, amma wataran zata dawo kwanar shi kuma ya koma ciki.
Dole rayuwarsu ta burgeka, babu sanyi gaba ɗaya, sannan kuma babu zafi mai tsanani.
Wataran ai farin ciki wataran saɓaninsa.
Inda ƴan gidansu abin ke ƙona musu rai, dansu UBANGIJI kan nuna musu farin cikin su Umm-Ruman ɗinne kawai.
Ɓacin ransu kuma suna ƙoƙari dannewa su shanye abinsu a cikin rai da cikin ɗaki, tunda ALLAH yayo Ahmad ɗin bamai hargagi ba, koda ɓacin ranne ya shigo cikin sanyi ake yinsa babu wani faɗa ko cacar baki a ciki.
_________________________________
Samina kuwa bayan wucewar su Ahmad ta jama Ma'aruff tsaki saboda kallon ƙurullar da yake binsu da shi, aiko yana juyowa ya daddage ya ɗauketa da maruka har biyu.
Da ƙarfin masifa ya turata mota ya rufe yana faɗin yau sai ta san ta masa tsaki wlhy.
Wannan abu kuwa duk a idanun abokan Ahmad dasu Mudan dake shago ya faru, sai yaran dake wasa a wajen, sunema suka kai labarin wannan mari cikin gida.
Baiko yi kaffara ba suna shiga cikin gidan ya hau jibgarsa ita kuma tana zaginsa da ja masa. ALLAH ya isa.
Sai da yay mata lilis da duka sannan kuma ya afka mata, taci wuya a hannunsa, dan yau ko aman da yay matama kasa tashi tai ta wankesa.
Washe gari kuwa labarin marin Samina yayta yawo cikin anguwa, Mama gaje taita masifa da cewar ƙaryane, kawai an sakama Samina idone anason ganinta cikin bala'i kuma baza'a ganiba, ƴan baƙin ciki sai dai su mutu.
Babu wanda ya kulata a gidan har taci ta tsire, sai daga baya ta kira Samina dan tasan tabbas da Ma'aruff bai mari Saminar ba da wannan zance bai fitoba.
Aiko Samina ta fashe mata da kuka, tare da zayyane mata dukan daya kara mata ma da suka ido gida.
Mama gaje tace, “Bar ɗan iska ai daga wannan karon dai ta ƙare, kedai kiyi duk yanda malam yace zaici ubansa ne matsiyaci, kuma zan koma zuwa gobe dan wancan cikin na shegiyar can baza'a haifesa ba, Ahmad bai isa samun ƴaƴaba har saikin samu Samina”.
Daɗi sosai yakama Samina, dan dama da baƙin cikin cikin nan ta fito Ma'aruff ya ƙara mata da haushin kallonsu Ahmad ɗin shine ta ƙare da cin duka a wajensa.
Washe gari duk da wuyar da taci a hannunsa sai da ya tsareta tai masa breakfast, yana fita aiki kuwa ta ɗakko abubuwan da malam ya bata ta fara ƙoƙari yin duk yanda yace tayi daki-daki.
Tsafi gaskiyar maishi, tun daga wannan lokacin Samina tace taga canji, dan yanzu kam ta sake kama Ma'aruff a hannu, koda giyarsa ya sha baya dukanta, sannan duk abinda ta tambayesa yimata yake, idan rashin kunyarta ta tashi kuma ta zuba masa gwargwadon iko baya iya ce mata komai.
A yanzu dai ta gama da matsalar ma'aruff kamar yanda ta faɗa, cikin jikin Rumana ne taget dinta na gaba, dan tayi alƙawarin sai yabi rariya, kuma da ga shi Umm-Ruman bazata sake ɗaukar waniba sai dai a lahira idan anayi.
Ni dai bilynku nace, “Hummm”.☹️😏
_____★_★_____★_★______★_★______
A wannan karon kwanan Ahmad tara ya juya, da zai tafinma sai da akasha daru shida mutuniyar, dan kuka taita masa ranarma, shi dai ya samu ya lallaɓa ya gudu yana jin ƙaunarta na mamaye duk illahirin gaɓɓansa da jijiya.
Ya tafi da kwana biyu Kausar ta tashi da naƙuda a safiyar Laraba, ranar dai kam a asibiti ta kwana, su Rumana nata mata addu'ar sauka lafiya.
Tasha wahala sosai kafin ALLAH ya sauketa lafiya ta santalo ƴarta mace mai kama da ita.
Su Rumana na shirin tafiya dubota sai gasu sun dawo ma gida.
Daga ranar kuma aka shiga zaman bakwai, inda abin gutsiri tsoma ya samu ga maman Ama, dan duk abinda ba aima Kausar ba saita tanka, ita dai Rumana nata idone, sai idan dangin Kausar sun bukaci wani abu daga gareta ta basu, tanama ɗaki kwance tana fama da kanta, dan tunda Ahmad ya wuce sai yazam bata cika jin daɗin jikin nata ba, dauriya kawai takeyi tunda dai ba sharkaf take a kwance ba.
A haka aka kwashe kwanaki shida da haihuwar Kausar, inda kuma aketa shirin suna gobe idan ALLAH ya kaimu.............✍🏻
Sai munzo cin rangam ni da Fans Kausar⛹♀
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*_GDW_*
*(33)*
...............Ɓangaren Ahmad kam randa ya isa porthercout washe gari ya damƙama ubangidansa takardunsa.
Sosai kuwa Uban gidan nasa yay mamakin ƙyawun takardun Ahmad ɗin da yaba ƙokari basirar da ALLAH yay masa.
Happy ma tanata santi, dan yanzu itada Ahmad ɗasawa ake duk da yana shareta bai kuma shiga sabgarta, ko ɗan Assignment ɗinta ta kwaso shi take nufa, yana mata kodan darajar iyayenta, wani lokacinma ba Assignment ɗin bane haka kawai zata kwaso buks tace yay mata lesson.
Idan yanada lokaci yakan mata, idan baidashi kuma yace ba lokacinba, wani sa'inma waya zaiyi da Rumana sai yace mata lokacinsa na matarsane yanzu.
Ita sam bata aminta yanada mataba, gani take kawai dai yana faɗane danta bashi waje.
Kasuwarsa kuwa bai fasa zuwaba, yana zuwa kullum kuma Alhmdllh, dama dazai tafi Nura ya miƙama kayan shima yaɗan samu, koda ya dawo yanzun kuma sai ya bashi shawara akan mizai hana yazo shima ya koya harkar.
Nura bai musaba yayma Ahmad ɗin godiya, dan ɗan riƙema Ahmad ɗin da yayi a wannan tafiyar yaji daɗin harkar..
Tun daga wannan lokacin suka kuma kasancewa tare da Nura, dan har zuciyarsa yana son Nura, yana ɗaukarsane tamkar ɗan uwa na jini.
Ubangidansa tunda ya amsa takardunsa bai sake ce masa komaiba a kansu, shima kuma bai sake maganaba ya maida hankalinsa ga sana'arsa kawai.
Sai dai kuma yana fatan dacewa idan da alkairi a cikin aikin, idan babu alkairi ALLAH yama hana samuwarsa.
__________________________________
A wannan safiya dai gidansu Rumana da sunan babien Kausar suka tashi, da yake ƴan uwantane ke komai sai su Rumana suka zama ƴan kallo, sai dai ɗan abinda ba'a rasaba sukan taimaka, koda yake Rumana ce kawai a gefe, Maman Ama ai tuni tayi uwa tayi maɗaukiya, sai ƙara shigewa jikin Kausar ɗin takeyi, da kuma ta koma gefe ta zageta da gulma😹.
Ita dai na Rumana kallone.
An kira Sallar Zuhur Rumana dake ɗaki kwance tana fama da rashin daɗi jiki ta miƙe da ƙyar, ita dai bawai zatace ga inda ke mata ciwo baneba, amma sam jikinta batajin daɗinsa, nata salon laulayin kenan.
Sannu taima matan dake zaune a ƙofar ɗakinta ƴan uwan Kausar ɗin, duk amsawa sukayi suma da mata sannun.
Tana shiga bayi sai wata a cikinsu ke faɗin, “Kai amma ciki yama yarinyarnan ƙyau, jiba yanda ta murje tai haske”.
“Wlhy kuwa Maman hafsa, nima dai tunda muka shigo naketa kallonta, ko gajiyama banayi da kallon nata”.
Maman Ama dake bayansu kaɗan tace, “Inafa ciki anan? Bilicin dai da shan maganin ƙiba”.
Duk juyawa sukai suka kalleta da mamaki, babbar Yayar su Kausar tace, “Aiko dai maman Ahmad idanunku basu gane muku dai-dai ba, yarinyarnan babu wani bilicin da take balle shan maganin ƙiba, cikine wlhy....”
Dai-dai Rumana ta fito daga bayi, hakanne ya sakasu yin shiru, sai dai fa idanun Maman Ama tamkar zai faɗo wajen kallon Umm-Rumana, ita da batasan sunaiba ta duƙa da ƙyar tana yamutse fuska zatai alwala, sai dai ta zubda yawun daya tarar mata a baki sannan ta fara.
Maman Ama ta kuma zaro idanu waje tana faɗin, “Kambu, yasin cikine kuwa, to yaushe akai hakan?”.
Har Rumana ta gama alwala ta miƙe zuwa ɗaki kallonta Maman Ama take harma da wasu a dangin Kausar ɗin, dan wasu labarin yanda akai aurenta da Ahmad ɗin sukeyi ta dalilin bijirewar Samina.
Ita dai bama tasan sunaiba, ta shige ɗakinta kawai ta kabbara salla.
Masu himmar sauke farali a kan lokacine sukai himmar tashi suma, Rumana tai musu allura, tana cikin sallar mutum biyu suka shigo ɗakinta dan suyi anan, ciki kuwa harda ƙawar maman Ama wadda ta kasance ƴan uba suke da Kausar, dama can an ƙulla ƙawancen ne saboda gulmar Kausar.
Lokacin da Umm-Ruman ta idar ne su kuma sunayi, wayarta tai ring, dan haka ta jawota tana dubawa, tayi mamakin ganin Yah Ahmad, dan bai cika kiranta a irin wannan lokacinba saboda kasuwa.
Ɗagawa tai ta saka a kunne da yin sallama murya a sanyaye.
Shima daga can ya amsa cikin lumshe idanu.
“Gwal ɗina kin tashi kenan?”.
“Lah yaya waya faɗa maka ina barci?”.
“Zuciyata mana babie R, aina kiraki, tunda naga baki ɗagaba nasan barci kikeyi”.
Murmushi Rumana tayi har yana jiyo sautinsa, “Tace kai Yaya, to yaya kasuwan?”.
“Kasuwa gata nan munata bugawa, yaya baby ɗina da ƙarfin jikinki?”.
Murmushi taɗanyi tana sake ƙasa da murya saboda ba ita kaɗai bace, tace, “Nidai ƙalau nake”.
“Ai haka akeso Ruman, shi kuma babie na fa?”.
Neman kauda zancen take ya katseta da faɗin, “Ruman nifa banson wannan kunyar, abinda akaimin ban yarda aima ɗana ba uhyim”.
Rumana taɗan kalli yanda matan sukai kasare suna saurarenta dan sun idar, ƙasa ta kumayi da muryarta tace, “Yaya bafa ni kaiɗai bace”.
“Owo keda waye haka?”.
Shiru tai dan tarasa yanda zata faɗa masa ya fahimta, da kansa yace, “Okey yaufa kuna suna ashe?”.
Rumana tace, “Uhm”.
“Ayya to ALLAH ya raya, nima kewarki ce ta isheni, anjima na kira”.
“Na gode yaya”.
Bayan Rumana ta ajiye wayar tsabar son jin ƙwaƙwaf, ƙawar Maman Ama sai cewa tai, Amarya munfa gode, kema ALLAH ya saukeki lafiya muzo i war haka musha suna”.
Murmushi kawai Rumana tayi kanta aƙasa, sai dai batace komaiba.
Suka sake mata godiya suka fito.
Itako alawa ta ɗakko ta saka a bakinta kamar yanda yanzu takeyi saboda batason tara yawun nan.
Ƙawar maman Ama taje har ɗaki ta sameta itama tana salla, tana idarwa ta juyo tana faɗin, “Ƙawata Yaya da gaskene cikinne?”.
“Wlhy kuwa shine ƙawata, muna salla fa mijin ya kira, kinji kuwa yanda ake kashe murya kojin abinda take faɗa bamaji wlhy, kai wannan yarinya akwai bariki anan, idan ta samu shashar kishiya tuni take ƙwace mijin”.
Wata dariya mai nuna tsangwaron hassada Maman Ama tayi, ta riƙe haɓa tana fadin, “Kaini wannan abu ya ɗauran kai, ciki fa? To wai yaushema akayisa?”.
Dariya sosai ƙawar tata ta sanya, “Kai kujimin ƙawata da wani batu, mata da miji har kike tambayar yaushe tai ciki?”.
Ai dolene nai wannan tambayar ƙawata, kinsan mufa wlhy dukma ɗauka muke bai taɓa taɓata ba, ashe munafukan sunsan tsiyar da suke a ɗaki idan sukai bulum, to wlhy babu mai ce miki ga daren farkon yarinyarcan a gidannan”.
“Ƙawa kinsan wasu matanfa akwai dauriya wlhy, koda sunsha wahalar bazasu bada wata ƙofar da wani zai fahimcesu ba, kuma kinga ai tanada iliminta yarinyar ga wayo, kune dai dama kuke raina ajinta, amma irin masu sanyin nan kedai gansu ki barsu”.
“A to lallai na yarda da maganarki wlhy, ohni kujimin wani sabon zance”.
Haka dai maman Ama taita wannan sambatu ƙawarta na mata dariya, ALLAH ALLAH take a gama taron sunan nan ta gumtsama Kausar da maman Aysha.
Rumana kam bama tasan sunaiba, dan tun bayan fitar su kwanciya ta koma ta sake yi, ahaka mutane sukaita ɗan shishshigowa yin salla.
Washe garin da taron suna ya watse kam ai kasuwar yi da cikin jikin Umm-Ruman suka ci, dan ba ƙaramin tsaya musu yayba a rai, saboda yazo musu a bazatar da ko a mafarki basu taɓa kawowaba, aiko duk inda tayi idanunsu na kanta, tunma bata fahimtaba harta fara fahimtarsu, itadai addu'ar neman tsarin ALLAH da sharrinsu tai ta jefa musu, dan tarasa wannan kallon har hanji na minene haka? Ina kuma dalilinsa?”.
Tunda ga lokacin basu da abin magana sai wannan ciki, ita Maman Ama ko nata bata kulaba sai na Rumana, ita Kausar ma ga jego tanayi amma hakan bai hana idonta zama akan wani ba.
_________________________________
Dawowar Ahmad da kusan sati huɗu sannan aka nemesa, ashe tuni ubagidansa ya bada takardunsa wa ƙaninsa.
Cikin fargaba da addu'ar samun nasara suka isa wajen ƙanin ubangidan nasa shi da shi harma da Happy da tai musu rakkiya.
Abunda yaso kaɗa hantar cikin Ahmad ganin shine kaɗai bahaushe a waɗanda aka amshi takardunsu, addu'a yay tayi a zuciyarsa, ya turama Rumana text message akan ta tayashi da addu'a itama.
Koda ta gani murmushi tayi, cikin ranta tana maijin tausayin yayan nata da ƙaunarsa.
Amma su Ahmad interview, kowa a ransa da fatan nasara, ance nanda zuwa kwana uku zasuji sakamako, wanda duk ya haye ya tsira, wanda bai samuba kuma yay haƙuri.
Idan nace muku Ahmad ya bar hankalinsa kwance a kwana ukunnan nai ƙarya, duk ya kira su baba yace su sakashi a addu'oinsu, hakama ƙannensa duk a faɗa musu kowanne yay masa addu'a.
UBANGIJI mai Rahma ne kuma mai jinƙai, a randa kwana ukun ta cika ko kasuwa kasa fita yay da wuri, kusan sha ɗaya saiga baƙo masu gidan sunyi, shidai yaje ya buɗe masa gate ya dawo ya cigaba da shirin fitarsa, yana gab da kammalawa sai ga Happy da gudunta, tunda yaji gudu yasan itace, kaɗan daga aikinta kuma tace zata rungumesa, dan haka ya juyo yana kallon ƙofa a tsume.
Aiko koda ta shigo ɗakin kansa tayi gadan-gadan, yay azamar ɗaga mata hannu yana faɗin, “Kinga tsaya”.
Dakatawa tai tana kumbura fuska.
Yace kinga kiyi haƙuri, mu addininmu da al'adarmu sun banbanta da naku, haramunne a addininmu mace ta taɓa balle ta rungume namijin da ba muharraminta ba, shima namijin haka, sannan babban abin kunyane a al'adarmu ta hausa fulani.
Cikin kaɗa ido da hannu Happy tace, “Okey na fahimta, amma dai kun cika tsauri da yawa”.
Murmushi Ahmad yay mata yana girgiza kai, yace, “Ba tsauri mukai da yawa ba, wannan ɗabi'ace mai ƙyau, domin an daraja macen ma ne anan, kinga ba kowanne shashasha ne zaice zai kai kazamin jikinsa ko hannunsa kanta ba”.
Shiru tai tana kallonsa, da alama dai maganar ta mata tasiri, ya ɗauke kansa shikuwa yana faɗin, “Miya faru kike zuba gudu?”.
Cikin kauda abinda ya faru ta washe baki tare da dirga tsallen murna, tace, dama zuwa nai na maka albishir, “Uncle ɗina da yazo yanzunan yake tabbatar mana ka samu aiki”.
Da sauri ya kuma waro mata manyan idanunsa, “Da gaske kike?”.
“Da gaske mana, Dady yace kazo ma”.
Binta kawai Ahmad yayi, amma yarasa yanda zai musalta farin cikinsa na wannan albishir na Happy, a tare suka isa falon su Happy ɗin.
Dady, Momynta, sai baƙonsu wanda takardun Ahmad ke a hannunsa, kujera Dady ya nunama Ahmad ɗin, ya zauna yana gaishesu tare dama baƙonsu barka da zuwa.
Da ƴar fara'arsa ya amsa yana faɗin, “Ahmed kai mai sa'a ne, duk da kasancewarka bahaushe ɗan yankin arewa kaci nasarar samun aiki, aikinma a gurbi mai daraja”. ya ƙare maganar yana miƙama Ahmad ɗin takardun hannunsa.
Ahmad na buɗewa yagani a gabansu Ahmad ya sauka ƙasa yayma Ubangiji sujda, duk da kallo suka bishi na mamaki, Momyn Happy kasa haƙuri tai sai da tai masa tambaya.
Shiko yay mata bayanin yayi hakanne domin nuna godiyarsa ga UBANGIJINSA domin shine yay masa wannan rahmar.
Su dai dariyama sukai masa, baiko damuba suma yay musu godiya sosai da wannan karamci da sukai masa babu ko sisinsa.
★★★★★
“UBANGIJI mai hikima, kuma gatan bawa, mai bayarwa ga wanda yaso akuma lokacin da yaso, yayana naji farin ciki sosai da wannan cigaba da muka samu, maganarka ta tabbata, da kace na zaune baiga gariba, sannan motsi yafi zama, dan bawa baisan ina alkairinsa yakeba”.
Lumshe idanu Ahmad dake kwance yana sauraren nutsatstsiyar muryar Babie R ɗinsa ta cikin waya yayi, yay sansanyan murmushi yana sake ƙasa da muryarsa, “Ngd Gwal ɗina”.
“Yayana miye abin godiya, fatanmu dai ALLAH ya baka ikon tsare gaskiya a duk inda ka samu kanka. ya kuma baka ikon cin halalinka komai ƙanƙantarta, ya tsareka daga haramun komai yawanta dan bata da amfani”.
“Amin ya rabbi Babie R, yanzu mizan samu goron albishir?”.
Wata ƴar dariya Rumana tayi daga can, takai dubanta gasu Salima dake barci, sannan tace, “Mi kake buƙata Zumana, kuma yaya?”.
Kwanciyarsa ya gyara yana sauke ajiyar zuciya, yace, “Komi na samu zanyi murna Gwal ɗina”.
Numfashi ta sauke a hankali tare da sumbatar wayar cike da salo.
Karon farko da Rumana tai ma Ahmad abinda baiyi zatoba, dan haka ya tashi zaune sosai cikin mamaki yace, “Babie R!”.
A ɗan tsorace Rumana dake dariya ƙasa-ƙasa tace, “Nayi laifi ko yaya?”.
Dariya yaɗanyi mai sanyi shima daga can, “Laifi kuma Gwal ɗina? Ai abinda ban taɓa zato bane akaimin, ngd da wannan goro sosai”.
Murmushi Rumana tayi har yanajin sautinsa, tace, “Ai kafi ƙarfin haka daga gareni Zumana, wannan ma bashi bane Goron, saika dawo zaka samu goro na musamman”.
A take tsigar jikin Ahmad ta fara tashi, ya marairaice mata murya kamar wani yaro yace, “Da gaske Babie R?”.
Tace, “Insha ALLAHU Sweet Yayana, farin cikina, mai hana kukana zuba”.
Gaba ɗaya Rumana ta gama cakar da Ahmad, ji yake tamkar ya rufe ido ya buɗe ya ganshi a gabanta, jininsa sai wani gudu yake da sauri, hakama gashin jikinsa dukya mimmiƙe, sai yake ganin kamar ana ƙara mata wayone kullum.
Kasa jurewa yay ya yanke wayar kafin ya tafka abin kunya, yay luf akwance tamkar wanda akaima bugun tsiya.
Daga Rumana kuwa murmushi taitayi, dukda itama tana masifar jin kewarsa, ta shafa cikinta tana maijin ƙaunarsa da ɗokin zuwansa duniya idan ALLAH ya ƙaddara hakan.
________________________________
Ɓangaren Samina kuwa a yanzu babu abinda ya tsayama rayuwarsu a rai ita da su Mama Gaje kamar cikin Umm-Ruman, da yake yanzu Ahmad kan barta taje gidansu lokaci-lokaci mama gaje jitake kamar ta gatsi Rumana da haƙori idan taje, fahimtar hakan da Ammi tayi ne ya sakata kuma dagewa Rumana da addu'a, dan ranar cikin dare fitsari ya fiddo Khadija ƙanwar Rumana sai taji Mama gaje nata kiran sunan Rumana a tsohon daren nan, lallaɓawa tai ta leƙa ta jikin Window mama gaje, dayake a kwai ɗan haske khadija tai ido biyu da Mama Gaje na busa wani abu a hannunta tana kiran sunan Rumana, hankalin khadija yay masifar tashi, kasa haƙuri tai saida ta bugama Amminsu ɗaki a hankali, ALLAH yasa bata da nauyin barci ta tashi ta buɗe mata, harta farama Khadija faɗa akan hakan da tayi, babba da ita tana abun yara mike faruwa.
Khadija tai ƙasa da murya tana sanarma Ammi abinda ta gani, fitowa tai itama jikinta har rawa yake ta leƙa Window mama gajen, a lokacin ma sunan Rumana dana Ahmad ɗin take kira tana sheƙa abun hannunta a ƙasa saikace mai shiƙar hatsi.
Wannan Abu yay masifar tada hankalin Ammi, a wannan daren kam batai barciba daga ita har Khadija...............✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*_GDW_*
*(34)*
...............A lokacin da mama Gaje ke wancan shaiɗanci Umm-Ruman na kan sallaya tana karatun Qur'an, ta idar da nafilfilinta tamkar yanda ta saba a kowane dare idan har ALLAH ya bata iko, randa kuma takejin nauyin jiki koda ta farka taji bazata iyaba sai taita addu'ointa daga kwance har barci ya sake kwasheta, tama daɗe bata tashi ba a kwanakin nan, saboda yanayin jikinta, amma yau tun kusan sha biyu da rabi sai barcin ya ƙauracema idonta, dole ta miƙe tayo alwala a tsorace ta dawo, shine ta fara gabatar da salla kafin ta ɗauki Al-Qur'ani ta shiga karatu a hankali.
Tabbas taji gittawar abu ta gabanta tamkar iska, sai dai koda ta ɗago ido bataga komaiba, bata kawo komai a rantaba ta cigaba da karatunta kawai.
Tunda Safe sai ga Khadija gidan, yanda ta iske Rumana cikin farin ciki suna karyawa ita dasu Fa'iza ne ya sakata jin sanyi a ranta, bata sanar mata komaiba dasu Salima zasu wuce gidama saita bisu.
Koda ta dawo ta faɗama Ammi Rumana na cikin ƙoshin lafiya sai itama taji sanyi har ranta.
Ta cigaba da mata addu'ar neman kariyar UBANGIJI a koda yaushe.
Randa Rumana tazo gidan kuma saita ƙara bata wasu addu'oi tace ta dage dayi a kullum tana kuma shafe cikinta shima.
Rumana ta amsama Ammi da “To” cikin jin kunya, dan tunda maganar cikin nan ya bayyana Ammi bata taɓa maganarsaba sai yau.
★★★★★★
Su Mama gaje sunta jiran suji sakamakon aikinsu amma tsit, sai ma Umm-Ruman da tazo gidan cikin ƙoshin lafiya, hankalinsu ya tashi, a ranar taje ta sanarma Inna mari.
Sai ta hauta da faɗa akan kodai batayi yanda malam ɗin yaceba, tunda dai gashi aikin da yayma Samina yayi ƙyau, dan yanzu haka tana kan cin duniyartane da allura, duk da dai bawai yabar shaye-shayensa bane, randa kuma tsautsayi ya gifta yakan jibgeta, sannan tun randa yaga Rumana da Ahmad kusan kullum saiya mata maganar Umm-Ruman, har cemata yake da yasan da wannan ƙyaƙyƙyawar a gidansu mizaiyi da ita sauran bilicin.
Wannan abu na sosa zuciyar Samina, shiyyasa take sake jin tsanar Rumana a kowacce daƙiƙa ta rayuwarta, bataƙi ace yau ga gawar Umm-Ruman ba a duniya.
Mama gaje dai ta taima Inna mari rantsuwa akan duk tayi yanda yace, hakan yasa suka koma wajensa washe gari.
Bai ɓoyeba ya sanar musu gaskiya akan samun aiki yaci Rumana ko Ahmad abune mai wahalar gaske, danshi Ahmad ma akwai tsari tare dashi tun yana yaro cikin iyayensa sukaima duk yaransu, shiyyasama ko aikin farko da sukai akansa dan karya samo komai a neman kuɗinsa aikin yaƙi tasiri. shima sai daga baya ya fahimci hakan. Umm-Ruman kuwa bata wasa da ibadar ALLAH, tana cika kowacce salla ta farilla, sannan bata bari lokacinta ya shige akan ganganci sai dai kuskure.
Yace, “Kunsan ba aikin dake bamu wahala kamar na mutumin da bai wasa da salla, mukan daɗe bamuci galaba a kansaba, sai dai idan UBANGIJI ya ƙaddara hakan arayuwarsa. Yanzu gashi matsala ɗaya bata jini saboda ciki, amma da ace tanai sai mubi wannan hanyar musamu nasara. Idan kuma zakuyi haƙuri harta haihune to, randa ta haihuma zamu iya salwantar da yaron ita kuma aikinmu ya shiga jikinta”.
Shiru su mama gaje sukai suna nazarin maganarsa, Inna mari ta katse musu tunani da faɗin, “Babu damuwa mun yarda kawai malam, amma babu yanda za'ai kafin sannan aɗan saka rashin jituwa tsakaninta da mijin nata?”.
Dariya malam yayi yana faɗin, “Badai za'a barta ta hutaba kenan? To zan gwada na gani idan za'a dace, amma ita ƴar uwar tata Samina ta kwantar da hankalinta ta shiga jikinta sosai, ta wannan hanyarne kawai zamu san komai daga gareta har watan cikin nata”.
“To shikenan Malam wannan ba matsala bane zamu sanar mata”.
Sun masa sallama suka taso suka taho gida suna ƙara jin haushin Ammi da Rumana da basu tsare musu komai a rayuwa ba.
★_★“★_★”_★
Da ƙyar su mama gaje suka shawo kan Samina akan shiga jikin Umm-Ruman, dan da da farko taƙi, yanda ta tsani Umm-Ruman ai ko maganarta ta tsana a mata balle har akai ga ta raɓeta, ita yanzu hakama ko za'a kasheta bazata iya gane gidan da aka kaita kafin Rumanan ba.
Ta dai fara karɓar Number Rumana ɗin wajen yayarta Bintu da hakan ya ɗaurema kai, haka kawai hankalinta ya kasa kwanciya da ƴar uwar tata akan amsar wannan Number ta Rumana.
Da farko ma kamar karta bata, sai taga idanma bata batanba ai zataje ta samune wajen wani.
Abinda kuma su mama gaje basu saniba a yanzu duk motsinsu Ammi na hankalce dasu, sannan ta kuma dagewa tuƙuru wajen jefan ƴarta da addu'oi harma da cikin jikinta data lura shi ya tsone musu idanu.
_________________________________
Haka rayuwa ta cigaba da turawa, kwanaki na shuɗewa suna zama satittika, yau da gobe kayan ALLAH har takai cikin Umm-Ruman ya fara fitowa sosai, danma dai cikin fari dama ba wani girma ya cikaba, sannan gata doguwa kuma masha ALLAH.
Ahmad ma dai ta ɓangarensa komai sai hamdala, dan kuwa ya fara zuwa aiki, gefe kuma ga kayan kasuwarsa sun haɗa hannu da Nura, shima duk ranar weekend yakanje kasuwa.
Ya samu ya sake aiko da kuɗin hayarsu, dukda ma tunaninsa ya fara bashi ɗakko Umm-Rumana su taho nan, dan yanzu bazai dinga samun lokaci mai yawaba na zuwa gida ya jima kamar da.
A hakama da ƙyar ya fisge a wannan karon yazo gidan akan zaiyi sati ɗaya kacal.
Kowa yaga Ahmad yasan rayuwa ta fara canja masa sosai, musamman yanda yay ɓul-ɓul dashi ga alamun kwanciyar hankali na musamman tattare dashi, ya ƙara zama Gentleman na gaske, ga gayu tamkar ba shine yay shushaina ba da talla a titi.
Ita kanta Umm-Ruman bata iya ɗauke kanta daga garesa, dan gaba ɗaya ya rikiɗe ya canja mata, sunsha soyayyarsu mai tsafta tare da tattalin da yake nuna mata saboda tausayinta da yakeji a ransa na cikin jikinta, a ganinsama tayi ƙarama da ɗaukar cikin, amma yasan UBANGIJIN daya basu shine zai bata ikon haihuwa lafiya.
Yama su baba maganar tafiya da Rumana amma sai sukace ba yanzuba, ya bari ta haihu dan bazai yuwu ace sun tafi tana cikin wannan halin hakaba, balle cikin nama fari, kowa zaiso ta haihu a gida cikin danginta kodan itama ta samu kulawa.
Baiyi musu da suba ya haƙura duk da bai soba, ya tattara ya koma bayan randa ya cika sati guda.
A wannan tafiyarma sai da tai masa kuka, haka dai ya gudu ya barta.
Tun daga sannan duk ƙarshen wata sai Ahmad yazo gida, wani lokacin yay kwana uku, ko huɗu harma sati yakanyi.
Duk zuwan da yay kuma saisun tsinci kayan haihuwa sun ajiye a gidan yaya Maryam, hakan yasa ƴan gidansu Rumana su Maman Ama ke dariyar gatsatsa, wai gadai Ahmad ya canja amma su basuga wani canjiba, koɗan kayan haihuwar da akan siya a yadda na haihuwar fari basu ganiba ga Ahmad.
Bai iya komaiba sai zaryar dawowa gida saboda fitina na cinsa.
(Kusan har yanzu basusan ya samu aiki ba ƙabayen😹).
🤦🏻♀kuji masifa, bayan da sunce masa lagwani😏😂🤣.
Duk da Umm-Ruman takan jisu wani lokaci bata ko kallonsu, ita dai fatanta a kullum ALLAH ya bata ikon zama dasu da zuciya ɗaya, ya kuma hanata yimusu ƙƴashi ko hassada a komansu.
Duk da wannan abun da suke mata haka zaki ganta da ɗiyar Kausar maƙale wani lokacin, dukda tana fama da kanta har goyata take su fita cikin gari wani lokacin, ta kama hannun Amatullah ga Surayya babyn Kausar kuma a baya.
Akwai randa taje gidansu Ayyah taita mata faɗa akan wannan gangancin goya Surayyan, takuma tabbatar mata karta sake ɗaukama kanta wannan rigimar, ta bari har ALLAH ya sauketa lafiya sai tayi koma miye.
To tunma daga ranarne taɗan ɗaga ƙafa da goya Surayyan, amma hakan baisa tayi fari a idon Kausar ba balle taji kunyar zama yi da ita.
Tun farko dama bata saka lamarinsu a rantaba balle yanzunma ya dameta, harkokin gabanta kawai take da ƴar sana'arta data samu karɓuwa sosai, sai ko rainon cikinta da a kullum take addu'ar fitowarsa duniya lafiya.
___________________________________
Daga Samina har mama gaje sun saka a ransu aikin da Ahmad ya samu ba wani na kirki baneba, harda cewa ƙilama ƙaryane anayine kawai dansu, rashin ɗaukar abun da muhimmanci ya sakasu ƙin saka abun a ransu, sai cikin Umm-Ruman ne kawai yafi zame musu damuwa.
Ranar wata juma'a Samina ta shirya zuwa gidan Umm-Rumana kamar yanda malaminsu ya bata Umarnin ta fara shige mata tundaga sannan, dan cikin Umm-Ruman ya shiga watan haihuwa.
Taci adonta cikin kaya na alfarma, dan kuwa rantsatstsar doguwar rigace da taji adon duwatsu ta saka, komai nata dai ya kasance na matan manya, dan zuwa yanzu ƙawayen data ƙara masu rawar kai irinta sun sake wayar da ita fiye ma da da, ɗaukar kanta take sama sosai, balle gashi Ma'aruff yana a tafin hannunta ne sai yanda takeso za'ayi, uwarsa kanta da ƴan uwansa duk ta bi dasu babu mai mata kallon banza yanzun, shiyyasa take musu rashin mutuncin da duk suma sukai mata a baya, matsalarta dai kawai cikin datake ta zuba ido ya shiga saboda Ma'aruff ya daina bata magani yanzu bulum kakeji babu ko alamarsa, taje asibiti likita ya tabbatar mata cewar lafiyarta ƙalau, abin na tada mata hankali, dan babu abinda tafi buƙata sama da ɗaukar cikin ma'aruff a yanzu, a ganinta haihuwar da zatai dashine zai ƙara mata lasisin mallakar dukiyarsa, dan mahaifinsu ya rasu tuni, kuma ma'aruff ɗinne kaɗai namiji a gidansu, shiyyasa ya tashi cikin gata bana wasaba, duk dukiyar ƙannensa tana wajensa shi yake juya musu, dan Company ɗin ba nasa bane shi kaɗai, shaye-shayen da yakene ya saka duk yarinyar da ya nema auren ke lalacewa, ga neman mata ko bunsuru ya shafa masa lafiya.
Sau biyu ana saka masa ranar aure amma yana lalacewa saboda rashin mutuncinsa, wasu kuma saiya gama lalata musu rayuwa saiya gudu bazasu sake ganinsa ba, idan ma sunsan inda yaken kosun kawo ƙara gidansu a banza, mahaifiyarsa ca take ƙaryane, sharri akaima yaronta baya shan giya, abinda yasa bata saniba ma'aruff baya shan giya sai dare, dayasha kuma gida yake dawowa, da safe kafin ya fita ta sakeshi, to inba tare kake dashiba har barci bazaka san yanayiba, gashi komai da taku yake kayansa, hakan yasa ko ita Saminar bata taɓa saniba.
Sannan ita kanta Samina da shirin yaudararta yaje, daya samu abinda yakeso ya gudu, sai dai kuma su Mama gaje sun masa DAURIN GORO bai saniba, dan saka malam sukai yay ram dashi a hannu akan tilas ya auri Samina.
ALLAH kuma sai ya amsa musu akayi auren dama yake da alamar tambaya saboda cikin da taje dashi a jikinta.
Cikin takunta na gayu ta fito daga ɗakinta tanata zabga ƙamshi, Ma'aruff na kwance a doguwar kujera yana kallo, ya kalleta da mamaki dan shidai baisan zata fitaba.
“Ina zuwa haka?” ya faɗa cikin tsareta da idanu.
Saboda tasan tsiyar data shirya masa saita zauna tana murmushi, “Wlhy so nake naje na duba sister ɗina Umm-Ruman, ance batajin daɗi ne Sweet”.
Jin ta ambaci sunan Rumana sai ya washe baki da faɗin, “Wai kina nufin mutuniyata?”.
Dukda maganarsa ta zafeta sai ta danne itama tana murmushin tace, “Tabbas ita kuwa, ai nama manta ka santa”.
“A to bari kawai na shirya muje tare, tana wane asibitine?”.
“A'a ba asibiti takeba tana gida”. Samina ta bashi amsa zuciyarta na mata zafi.
Babu yanda ta iya ta yarda suka tafi tare, ita ke tuƙa motarma saboda tunda ta sameshi a hannu ta tilastashi ya koya mata mota, duk kuma motarsa datai mata ita take hawa a gidan dukda ya bata wata ƙarama.
Cayay su biya ta shoprite wai suma Rumana tsaraba, Samina bata musaba kuwa suka biya, sayayya ta tashin hankali taga yanayi, itafa lamarin guy ɗinan mamaki yanzu yake bata, tama rasa yanda zata fassara manufarsa akan Rumana, tunda dai shi ai ba mahaukaci bane yasan tanada aure, kuma ƙanuwarta ce uba ɗaya.
Uffan batace dashiba ya gama kwasar duk abinda ya tare gabansa yaje ya biya suka tafi.
Sai da ta kira mama gaje a waya ta sake nata kwatancen gidan sannan, da suka isa ma Ma'ruff cayay dashi za'a shiga gidan, sai da Saminar tace bazai yuwuba, tunda basu Rumanar bane kaɗai a ciki akwai ƴan haya bayansu, ya zauna a mota kawai zata saka Rumana ta fito su gaisa.
Badan yasoba ya haƙura, ita kuma ta kwashi kayan daya takura mata ta shiga cikin gidan.
Umm-Rumana na zaune a ƙofar ɗakinta kan tabarmar data shinfiɗa dantasha iska, aya da Ammi ta soyo take ƙullawa, maman ama na bakin rijiya tana wanke-wanke, sai Kausar daketa kaikawo daga ɗaki zuwa kicin tana dahuwar naman kai anama su Rumana iyayi, hira sukeyi, duk da ma dai maman Ama ne da Kausar ƙarfin hirar, sai anyi abun dariya Rumana kanyi, sai kuma jefi-jefi takan saka baki itama.
Tunda Samina tai sallama duk suka zuba mata idanu, ita Rumana ma bata ganetaba da farko, dan Saminar tayi bala'in sake fari, takumayi ƴar ƙiba ba laifi, gashi ta toshe fuska da glasess baƙi.
Gidan su Umm-Ruman ko ina lailaye yake da suminti, sannan ba wani girmane dashiba da za'ace ya tara baƙar ƙazanta ko tarkace, ko ina tsaf yake abinsa, amma hakan bai hana Samina yin yatsine-yatsine ba.
Rumana ta faɗaɗa murmushinta tana faɗin, “Lale marhabun da Yaya Samina, sannu da zuwa ki shigo”.
Wannan furuci na Rumana ne ya saka su maman Ama fahimtar wacece, dan koda aka kawo Samina gidan a wancan lokacin ai maman Ama bata gantaba sosai, tunda ko kwana batai a gidanba, takuma canja sosai ma yanzun fiye da da.
Dan munafurci harda ce mata Hajiya Samina🤣.
Itako ta amsa tana sake ɗage musu kai tamkar wata matar shugaban ƙasa.
Ita dai Rumana tai mata iso zuwa ɗaki, ko zama basu gama yiba saiga Maman Ama da zoɓo da ruwan leda afilet, wai ta kawoma Samina.
Rumana dukda tasan salon annamimancine hakan bai hanata mata godiya ba.
Samina sai bin ɗakin take da kallo, a ranta tana tuna randa aka kawota cikinsa, ita koma kalar kayan gadon bata shaidaba dan bata tsaya kallon komai na cikinsaba a wancan lokacin.
Ita dai Umm-Ruman ta gaisheta da girmamawa kamar yanda ta saba.
Samina ta amsa cike da yanga tana faɗin, “Uwar biyu ashe kin kusa sauka haka?”.
Murmushi Rumana tayi kawai bata iya cewa komaiba ita dai.
Samina ta harareta kaɗan tana taɓe baki, sai kuma tace, “Yah Ahmad ya haɗaki da aiki ya gudu ya barki, ai wasu mazan dama sam basu da tausayi, abinda kawai suka sani suma macen ciki su aje mata fara da mai suyi gaba, acan kuwa dadinsu sukeci su kiga sunyi ɓul-ɓul.
Rumana dai bata bata amsaba nanma, dan ta gama lura akwai cin mutunci a ciki.
Samina taci surutanta ta tsire sannan ta miƙe akan zata wuce, dama ta anguwar sukazo gittawa shine tacema mijinta bara ta shigo tayi zuminci tunda ita Rumana Ahmad ya hanata.
Rumana ta bata haƙuri akan itama zatazo insha ALLAHU.
“ALLAH yasa to, ga shinan ƙyaɗan sabunta kema inji hubbyna, kizo yana ƙofar gida ku gaisa”.
Jimmm Rumana tayi tana tunani da kallon kayan, dan daga amsar kayan har fita gaisawa da mijin Saminar tasan zai iya zama matsala tsakaninta da Yah Ahmad.
Amma dan kada Samina taga kamar akwai wani abu a ranta saita zira hijjab ta fita, daga zaure ta tsaya Ma'aruff ya shigo suka gaisa, yanda cikin ya ƙarama Rumana ƙyau da murjajjen jiki sai Ma'aruff ya nema zaucewa, ɗan hegiyar sai haɗiyar yawu yake yana lashe laɓɓa, idonsa kam tamkar zai zazzago ƙasa saboda kallonta.
Itako bama tasan yanaiba dan kanta duƙe yake a ƙasa ko kallonsa ta kasayi, suna kuma gama gaisawa tai musu sallama zata shige gida, jikinsa har ɓari yake ya fiddo kuɗi ya bata amma sai taƙi amsa ta shige abinta.
Jiyay kamar ya jawota ya rungume a jikinsa, a fusace Samina ta fisgi hannunsa sukai waje.
Ƙwacewa yay tare da hankaɗata yana jan tsaki, dan yaji haushi sosai..........😝✍🏻
🤸🏻♀Ɗan hegiya, wannan Gwal ɗin Amadidin Ayyah ce, ƙwalelekanka dan uwarka😏🥴😹⛹♀⛹♀
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
*_GDW_*
*(35)*
...............Koda Rumana ta dawo cikin gidan bata koma ɗaki ba, inda Samina tazo ta sameta a ƙofar ɗaki nan ta sake zama.
Su Kausar da suke zuba ido suga mi Samina ta kawo dole suka haƙura.
Su basu sanma Rumana ita neman mafitar da zata ɓulloma Ahmad takeba a cikin ranta, tasan ko giyar wake tasha bata isa tunkararsa da maganar zuwan Samina gidanba balle harda mijinta kuma sun kawo mata abu.
Tasan hakan gagarumar matsala zai kawo musu wadda zai iya haɗa sati yana fushi da ita, idan kuma bata faɗaba yaji a bakin wani ai sai tafi shiga tara ma ba uku ba, to ita yaya zatai kenan?.
Ta ta saƙawa da kwancewa akan neman mafita tana cigaba da ƙulla ayarta, daga ƙarshedai zuciyarta ta bata wata shawara da ita kanta taji ta aminta da shawarar.
Kamar yanda ta yanke shawaran jiran Yaya Mudan yazo ta faɗa masa komai, sai gashi bayan sallar isha'i ya kawo mata fruits da kullum ya jura kawowa, ko wani ɗan abin kwaɗayi haka, idan kaga bai kawoba to baida kuɗine kokuma Ahmad ya dawo gari.
Lokacin da yazo su fa'iza basu kai ga zuwa ba, dan yanzu sukanje majarantar dare, sai an tashesu ƙarfe tara saisu taho nan.
Bayan sun gaisa da Mudan tai masa bayani komai da zuwan Samina da nuna masa kayan da suka kawo da ko buɗewama ita bataiba taga miye a ciki.
Hakan ya bama Mudanseer mamaki sosai, dan shidai yaji a ransa akwai wata manufa a zuciyar Saminar.
Yace, “Kin sanarma Yah Ahmad ne?”.
Rumana ta riƙe haɓa tana faɗin, “Wai, Yah Mudan wlhy tsoro nakeji, shiyyasama na yanke shawarar faɗa maka idan zaka sanar masane to, dan nasan komu bamu faɗaba wani zai faɗa masa musamman matan gidannan dana san saisun sanarma mazansu, sukuma zasu iya faɗa masa, to maimakon yaji a wani waje yaji zafi gara musan abunyi, kasan Yayah nada zuciya akan abinda duk bai masaba”.
Mudan ya jinjina kansa yana sauke ajiyar zuciya, yace, “Hakane kema kinyi ƙyan kai, yanzu dai bara na tafi da kayan, insha ALLAHU zan masa bayani a yanda zai fahimta, ki kwantar da hankalinki kinji, dan kina yanayin da sam ba'a buƙatar damuwa tattare dake”.
Rumana tace, “To Yah Mudan nagode sosai”.
Da zai wuce da kayan ya tafi, Rumana nata zuba ido taji Ahmad yay mata magana akan kayan nan ko zuwa Samina amma shiru, kuma kullum ne babu fashi sai sunyi waya, daga baya saita fara tunanin kodai madan bai sanar masa baneba?.
Kasa haƙuri tayi da Mudan yazo gidan ta tambayesa.
Ya tabbatar mata yako masa maganar, dan shinema yace abama Ayyah kayan ta ajiye a wajenta, kuma harsu Baba ma sunsan komai a kan maganar.
Rumana tayi matuƙar mamaki, amma sai itama ta share abun a ranta taci gaba da harkokinta.
Zuwan su Samina da sati ɗaya Ayyah tazo gidan da kanta, bayan sun gaisa tacema Ruman ta kimtsa kayanta insha ALLAHU nanda kwana biyu zata koma can gidan da zama har saita haihu, dan cikinta ya shiga watan haihuwa, bakuma zasu barta ananba ita kaɗai.
Hakan yama Umm-Ruman daɗi sosai, koba komai ta samu hutu daga su maman Ama.
Koda taima Ahmad maganar da suna waya sai yace mata ai yasan da komawar tata shima, hankalinta ya sake kwantawa sosai, a washe garin ranar kam sai su mama Ama sukaga tanata kimtse-kimtse su Salima na tayata, iya abinda zata iya buƙata kawai ta zuba a jakkuna biyu dan tsabar wauta🤣, sai kace ance ta tafi kenan.
Washe garin da zata wucene ta sanarma matan gidan, dan sai zuwa dare zata wuce, da safen dai su Fa'iza suka wuce da kayanta, wanan abu yama su maman Ama ciwo, sai dai kuma ya suka iya.
Da daddare kuma ta wuce ta basu filin gidan su warwasa da ƙyau🤸🏻♀.
___________________________________
Tunda Umm-Ruman ta dawo gidansu take sake ganin tattali da kulawa musamman wajen Iya da Ayyah, duk wani kulawa da mai ciki kan nema Rumana na samunsa, hatta da gwaggo da Ammi dake nuna kawaici suma sukan kawo nasu taimakon.
Yayanta kuwa yana ƙoƙarin kiranta a duk sanda ya samu lokaci, musamman ma da daddare da sukam shafe dogon lokaci suna fira.
Mama gaje kuwa dawowar Rumana gidan ya sakasu farin ciki, koba komai zasu sami cikar burinsu a cewarta, dan haka ta shiga a jerin masu tattalin Rumana ko kunyar ALLAH bataji, kowa kuma a gidan kallonta kawai yake yi.
Samina kuwa bini-bini tazo gidan, taita kawoma Umm-Ruman abubuwa, duk abinda ta kawo amsa kawai Rumana take tana bama Ayyah na ajiyewa.
Wannan karon dai Ahmad yaja dogon zango bai zoba, dan wata harya mutu an shiga wani bai zoba, sai haƙuri ya abasu akan abubuwa sun masa yawa maybe zaiyi haƙuri sai Rumana ta haihu tunda ta shiga watanta.
Kowa ya amshi uzirinsa da masa fatan alkairi, garama Rumana taɗan masha shagwaɓa akan ita dai tana kewarsa gaskiya.
Dariya yayta mata yana lallaɓata har tace itama ta haƙuran.
_________________________________
Yau Umm-Ruman tana sati na uku a gidansu, har kuma ta shanye watan haihuwarta ta shiga wani, kowa dai fatan sauka lafiya yake mata a kullum, danma cikin ba wani irin girman nan yayiba can sosai.
Yau dai haka ta tashi ba wani walwala, da yake Ayyah tasan wannan yanayin mai tsohon ciki takan tsinci kanta sai takeya lallaɓata.
Tunda akai sallar la'asar takejin wani azababben zafi, Ayyah ta shinfiɗa mata tabarma a ƙofar ɗaki tace ta zauna tasha iska a wajen.
Gidan shiru saboda duk yaran sun tafi islamiyya.
Ayyah ta fito daga ɗakinta ɗauke da kwanika guda biyu, ɗaya ƙwaɗon zogale ne da yaji kayan su tumatur harda cucumber sai ƙamshi yake, ɗaya kwanon kam jiƙaƙƙen zoɓone, tunda Ayyah ta ajiye kwanikan Rumana ta canja fuska, Ayyah dai batace uffanba sai dariyarta data haɗiye.
Tunda Umm-Ruman tazo gidan babu abinda takeso irin kayan ƙwaɗayi, tace wannan, tace wancan, shiko Mudan da Abu da Baba basa gajiya da saya mata, Ayyah taga abin zai wuce gona da iri, dan randa taje asibiti na ƙarshe tare sukaje, Doctor yayma Rumana gargaɗin rage cin nama, harma da wasu abubuwan, ya basu shawaran taɗan ringa cin ganyayyaki haka zasu taimaka mata, wannan abu ya bama Rumana haushi, dan tunda suka dawo Ayyah ta ɗaura ɗammara, kullum da kalar da zata bata safe da rana, abinci ko shima bamai maiƙoba sosai.......
“Gashi nan maza a ci” Ayyah ta faɗa tana katsema Rumana tunani.
Cikin kumbura fuska da tara ƙwalla a ido Rumana tace, “Ayyah banajin yunwa fa”.
“Eh ai wannan basai anji yunwaba dama, zogale ai ba abinci bane maganine, ga jiƙon zoɓonan tun safe na yisa amma ko kurɓa guda baki masaba, kar na gama sharo ɗakin malam baki cinye zogalen nanba, inba hakaba ɗura zan miki yau a gidannan ehe”.
Rumana da idonta ya cika da ƙwalla tace, “Kai Ayyah”.
“Tom ki zauna harna fito ki gani” Ayyah tai maganar tana shiga ɗan lungun Baba.
Gwaggo na daga ɗaki tana jiyosu, tai murmushi kawai abunta.
Kwanon Rumana taja ta ajiye gabanta, dan tana zaune ne ta miƙe ƙafafu, tagumi tayi ta zubama kwanikan idanu....
Dai-dai wannan lokaci Ahmad ya iso ƙofar gidansu, Mudan ne kawai a shago, anguwar babu yawan hayaniya saboda yara duk yawanci suna islamiyya, ko majalisar abokansa ma babu kowa sai Rabi'u kawai shi kuma yana daga cikin shagone baiga isowar Ahmad ba.
Mudan ya rungumesa yana mai nuna tsantsar murna da mamakin ganinsa.
Murmushi Ahmad yay yana faɗin, “Har yanzu dai ana nan da hali bai canjaba ɗan gidan Gwaggo”.
Dariya Mudan Yayi, yace, “Ina da kai Yah Ahmad ai ni kullum shagwaɓaɓɓe ne”.
Murmushi kawai Ahmad yayi, shigewarsa yay yabar Mudan da mai Napep ɗin suna sauke kayan da yazo dashi.
Bai gamu da kowaba a soron harya ƙarasa sashensu, da Umm-Ruman ya fara tozali, ya ɗan wawwaiga ko ina baiji mitsin kowaba, sai ita kaɗai tayi tagumi tare da ƙurama kwanikan gabanta idanu.
Wani tausayinta ne ya sake kamashi, ya tura hannayensa duka cikin aljihun wandon shaddarsa kalar ruwan ƙasa yana murmushi, a hankali ya buɗesu ya sauke akan cikinta daya fito sosai, sai dai kuma bai wani irin girman nan na tsiyaba kasancewarsa cikin fari, gashi ita kuma doguwa ba laifi.
Takawa ya farayi a hankali zuwa gareta, amma sam bataji koda motsinsaba, saboda tayi zurfi a tunani.
Harya iso ya zauna a hankali kusa da ita gab, ƙafarsa ɗaya a ajiye ya ɗora hannunsa, ɗayar kuma ya tanƙwasheta yayi dafe da hannunsa a ƙasa, yanayin zaman sai ya basu kusanci sosai.
Gashi dai ƙamshin rurarensa ya cika tsakar gidan har hancin Rumana, sai dai hankalinta sam baya tare da duniyar mutane.
Sassanyar murmushi Ahmad ya sakeyi tare da matsar da kansa dab da kunnenta, cikin magana raɗa-raɗa yace, “Gwal ai ga abinda kike tunanin kusa da ke”.
Firgigit Rumana ta dawo hankalinta, ta zaro ido waje babu shiri dan ita tsoratama tayi, catake ko aljanine yazo mata a suffarsa...
Da sauri yace, “Surprise”.
Wata nannauyar ajiyar zuciya Rumana ta sauke tana kumbura masa fuska, harda kai masa ɗan ƙaramin naushi kamar gaske, shiko yay saurin matsawa baya da riƙe hannun nata yana ƙaramar dariya.
“Yi haƙuri manyan mata” yay maganar yana sumbatar hannun nata daya riƙe, tare da sakata jikinsa ya rungume.
Sam ta manta a inda suke, dan haka tai luf tana sauke ajiyar zuya.
Ahmad yay murmushi sosai yana ɗagota daga jikinsa, ya zuba idanunsa cikin nata, bata janyeba, dan wani irin mugun kewarsa takeyi, sai cika sukai da ƙwallan da ita kanta batasan dalilinsu ba, hakan sai ya ƙarama idanun ƙyau, fuskarsa ya matsar dab da tata tamkar zai haɗe, hakan ya saka Rumana lumshe idanunta ƙwallan da suka taru a ciki suka gangaro bisa kumatunta.
Bakinta da ta tsuke ya sumbata shima yana lumshe ido, yaɗan janye kaɗan yana ɗora hannunsa saman cikinta, “ALLAH yay miki albarka Babie R”.
Bata iya cewa dashi komaiba sai goshinta data jingina da nashi tana sauke tagwayen ajiyar zuciya, itama ta ɗaura hannunta saman nashi dake kan cikinta, tace, “Yayana nayi kewarka, musamman yau da son ganinka na tashi sosai, ban saniba ko bazan tsallakeba mutuwa zany....”
Gwaggo da taji motsi ta ɗaga labule zatonta ko dabbobine, da sauri ta saki labulen saboda ganin Ahmad da Ruman, ita dai bataji motsin shigowarsa gidanba sam.
Su Ahmad da basusan anaiba Saurin buɗe ido yay yana janye kansa daga jikin goshinta, ƙirjinsa sai wani fat-fat yake alamar tsoro, sam baiyi zaton wannan furucin daga bakinta ba,
Yace, “Gwal karna sake jin haka daga bakinki kinji ko”.
Kallonsa tai, yanda fuskarsa ta nuna alamun ruɗani sai ya bata tausayi, murmushi tai masa, cikin son kauda masa tsoron data hango cikin idanunsa tace, “Wasa nake fa, mutuwa ai tana wuyan kowa, kuma kowa zai iya tafiya a kowane lokaci”.
Duk da maganarta bata kore masa abinda yakejiba hakan bai hanashi mata murmushi ba, ya riƙe hannunta da take shafa masa fuska, shima cikin ƙoƙarin son kauda zancen ya shiga buɗe kwanikan gaban nata.
“Ƴar gata minene aka jera miki anan?”.
Baki ta cona gaba dan ya tuna mata aikin dake gabanta, ga gargaɗin Ayyah.
“Woow Gwal duk ke kaɗai?”.
Da sauri tace, “Dan ALLAH tayani ci yaya kafin Ayyah ta fito”.
Yaɗan zaro idanu yana magana ƙasa-ƙasa sai kace mai gulmar wani kuma baiso a jisa, “Kina nufin ke nan baƙya son ci?”.
“Eh mana” tai maganar tana kuma tura baki.
Yace, “K baƙauyace dama ai” yay maganar yana ƙoƙarin ɗauraye hannunsa da butar kusa da ita.
Ita duk zatonta shine zai taimaketa ya ci, sai taga koda ya ɗebo zogalan da hannunsa ya nufo bakinta. Ta kallesa ido cike da ƙwalla tana narke masa fuska dan yaji tausayinta.
Kansa ya girgiza mata alamar kar tayi kuka, tare da lumshe ido da buɗewa alamar ta daure.
Bakin ta buɗe masa ya zuba mata, ta shiga taunawa a yamutse, shi dai kallonta kawai yakeyi a ransa tana bashi tausayi da dariya.
Kuma ɗebowa yayi ya kuma kaiwa bakin nata, nanma sai da ya marairaice fuska alamun lallashi sannan ta amsa.
Mudan dake laɓe shi da Ayyah suna kallonsu kowa ya saka hannu ya toshe baki yana ƙoƙarin danne dariyarsa.
“Ayyah kinga ɗanki fa, shiru-shiru dashi amma hummm...”
Ranƙwashi Ayyah taima Mudan, har zaiyi ƙara sai kuma yay sauri toshe baki yana shafa inda ta rankwasheshin kawai.
Ayyah dai murmushi take tayi, dan taji daɗin yanda Ahmad ke bama Rumana kulawa.
Gwaggo kam bata sake yinƙurin ko ɗaga labulenba, saima ƙarar redion ta data ƙaro daga cikin ɗaki.
Daga Ahmad har Umm-Ruman shauƙin juna yama mantar dasu wani zai iya shigowa, musamman ma Mudan daya baro da kaya a waje, yana ƙoƙarin sakama Rumana laumar zogalen kusan ta baƙwai su Zainab sukai sallama, wani ihun murna ta saki na ganin yayan nasu.
Hakanne ya maido su Ahmad hankalinsu suka tuna a inama suke, amma duk da haka bai daina bata zogalen ba.
Ayyah da Mudan ma suka fito daga maɓoyarsu ta lungun Baba suna dariya.
Anan ne kunya ta kama Ahmad, yaɗan matsa baya kaɗan daga nanuƙe Rumana da yayi, yay mata nuni da idanu wai ta cigaba daci.
Ita kanta taji kunya, hakan ya sakata duƙar da kai ƙasa.
Ita dai Ayyah sai ta hau masa lale da wannan zuwan bazata danta kauda kunyar dataga ta lulluɓesa............✍🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_36_*
*_Mai gadon kara🥳😲_*
..............Koda Ahmad ya gama gaisawa da mutan gida da ƙannensa harma da iyayensa, yaci ya ƙoshi Ayyah tai masa maganar tafiya can gidan sai ya ɓata fuska.
Tace, “Tofa ɗan albarka yaya dai?”.
“Nifa Ayyah ni kaɗai zan koma can yanzu? Duk kowa yana nan ni sai a wareni?”.
Kasa daurewa Ayyah tayi ta kwashe da dariya, Rumana ma ƙasa tai da kanta tanayin tata, hakama Zainab da suka faɗa cikin ɗaki, dan bazasuyi a gaban saba tunda sunsan sauran.
Harara yaketa zubama Umm-Ruman yana sake kumbura fuska.
Ayyah tace, “To yanzu ya kakeso ayi kenan?”.
“Nima Ayyah ban saniba dai, ki kawo shawara”.
Ayyah tace, “Ga shawarar na kawo nace katafi gida ka huta ka kamamin shagwaɓa”.
Yace, “Toni Ayyah tsorofa nakeji, ni kaɗai a ɗakin ai sai wani abu ya cinyeni kafin safiya”.
Ba Ayyah ba hatta Gwaggo dake ta ayyukanta bata saka musu baki sai da tai murmushi tana girgiza kai, yayta mazurai wa yaran gidan da shan toka, amma idan yana gaban Ayyah jinsa yake tamkar wani ƙaramin yaro.
Zama Ayyah tai tana lallaɓa Ahmad, dan tuni su Fa'iza suka tafi kimtsa masa ɗakin, aiko da ƙyar ya yarda ya tafi.
Rumana ta sauke ajiyar zuciya tana maijin ƙaunarsa har can ƙasan ranta.
★★★★★★
Koda Ahmad ya isa gida ya iske su Salima sun gama komai suna wanke masa bayi ne da duk ya ƙazance, saboda su Maman Ama sai sun gadama suke wankewa, amma fa ba kullum bama saboda kowa na ganin ƙyashin ya gyara wani ya amfana, dai dai da tsakar gidan yasan Rumana bata gidan, dan duk ya fitta hayyacinsa, wani lokacinma Ahmad suke sakawa sharar ɗan ƙarami dashi.
Su Kausar dai mamakin yanda Ahmad kullum ya dawo sai kaga sabon canji tattare dashi sukeyi, harsu fa'iza suka wuce ya shiga wanka basu bar satar kallonsa ba.
Shi baima san sunaiba, saurin kimtsawa yay dan gidan duk babu daɗi yakejinsa, jinsa yake kamar wani maraya da baida kowa, gidan ya masa girma saboda rashin Gwal ɗinsa a ciki.
Sauri-sauri ya gama shiryawa ya sake fitowa, lokacin anata kiran sallar magriba.
Bayan anyi sallar isha'i Rumana na kwance tana kallo a waya bisa gadon Ayyah ƙarami na ƙarfe kawai sai ganinsa tai ya shigo ɗakin da sallama.
Da mamaki ta ajiye wayar ta yunƙura ta tashi zaune tana kallonsa, Yaya dama baka tafiba?.
Zama yay a bakin gadon yana harararta, “Oh baƙyason ganina ne?”.
“Taɓ ni na isa”.
Yace, “Ina su Ayyah?”.
“Su Ayyah sunje gidan Inna mariya wai bata da lafiya, dama da yamma sukaso zuwa dubata sai kuma ka dawo, shine sukace tunda sunyi niyya gwara suje dubata a darennan dan Sadiqu na nan gidan malam ne ya tafi kaisu”.
Gaba ɗayansa ya juyo yana kallonta, yace, “Tun yaushe suka wuce?”.
Rumana bata fahimci bin ƙwanƙwanton maganarba tace, “Yaya yanzun nanfa, dan namayi mamaki da baku haɗu dasu a ƙofar gida ba”.
Wani nannauyan numfashi taji ya sauke, yace, “Su fa'iza fa?”.
“Suma yanzu suka wuce makarantar dare, kusan tarema suka fita dasu Gwaggon”.
Shiru yay yana ƙiyasta nisan inda su Gwaggo suka tafi da lokacin da zasu iya ɗauke. Ita dai Umm-Ruman kallon mamaki taketa masa, gani tai kawai ya miƙe ya kama hannunta yana fadin,
“Kinga sakko muje kiga wani abu Gwal ɗina”.
“Wani abu kuma Yaya a ina?”.
Bai bata amsaba ya taimaka mata ta sakko, haka ya jawo hannunta suka shige ɗakinsu Fa'iza, sam bata kawo komai a rantaba, ta daiga ya sakama ɗaki sakata, dama ɗakin babu fitila da wayarsa ya haska.
Yaja hannunta suka hau saman katifar, danma karta kawo masa togaciya yasha toka.
Tunda ya kashe fitilar wayar tasa kuma sai tsoro ya kamata, tace,
“Yaya wai lafiya?”.
“Shiiii!” ya faɗa yana kwantota jikinsa, da ɗora fuskarsa akan dokin wuyanta.
Duk yanda taso hanashi ta kasa, bawai itama bata buƙatar inda taga ya dosa bane, a'a kunya takeji da tsoron kar wani ya shigo gidan, tunda Abu da Mudan da Baba duk suna a anguwar, sannan su Ayyah ma ai zasu iya dawowa, kokuma wani a cikin gidan, musamman ma Iya da bata gajiya da leƙowa dubata, garama su
Fa'iza da sauran lokaci.
Duk salon da yasan zai mata jikinta yay laushi shi yayta bi, sai da yaga tayi tuɓus ta miƙa wuya sannan.
Bakinta na rawa tace, “Yah Ahmad ba gidanmu bane fa nan, dan ALLAH kayi haƙuri....”
Muryarsa a sheƙe yace, “Idan nayi haƙurin kina da maganin bani ne na samu nutsuwa?”.
Kanta ta girgiza masa, ta sake buɗe baki zata masa bayanin da zai fahimta, ya rufe bakin gaba ɗaya ma........
__________________________________
Tamkar jira, Ahmad na samun nutsuwa ciwo ya tashi daga Umm-Ruman, ta fara da kukan bayanta, mararta.
Saurin saka kayansa yayi itama ya maida mata nata duk ya rikice saboda kukan da takeyi.
Da ƙyar ya samu suka fito daga ɗakin tanata yarfa hannu da ƙara ƙarfin kukanta, dole dai ɗakin Ayyah ya maidata yay saurin nufar sashen Ayyah ya faɗa mata akan taje shikuma ya samo mota su tafi asibiti.
Amma sai Iya ta tsaidashi, a tare suka koma sashen nasu, lokacin sosai Rumana ma ta gama galabaita, dan har wani ruwa ya fashe mata, sai kiran sunan Yah Ahmad takeyi da Ammin ta.
Gabanta ya duƙa ya riƙe hannunta shima muryarsa na rawa yake faɗin, “Kinganni nan kusa dake Gwal ɗina, kiyi haƙuri yanzu zan samo mota muje asibiti kinji ko”.
Cikin kuka rurus take ɗaga masa kai alamar to.
Iya ta korashi waje dan ta kula haihuwace gadan-gadan ta tahoma Rumana.
Koda Ahmad ya fito jingina yay da bango ya lumshe idanu, ji yake kamar ya taya Babie R ɗinsa kuka, dan sosai kukanta ke sukarsa, gani yake laifinsa ne, da bai kusanceta ba ƙila hakan da bai faru ba, shikuma kasa jurewa yay, dan a jigace yake da son jinta a jikinsa.
Dai-dai nan su Ayyah suka shigo gidan, duk sai da gabansu ya faɗi ganinsa a wajen, dan kukan da Rumana keyi idan ba matsowa kai kusaba ba wai zaka jita bane, zuwa yanzu ma ta bar kukan sai nishi da Iya ke cewa tayi.
Kafinma su Ayyah su sami damar tambayarsa suka jiyo nishin Rumana, hakanne ya tabbatar musu haihuwace, jin iya ce a ciki sai Ayyah ta shiga danta taimaka mata, Gwaggo kuma ta fara yunƙurin ɗora ruwan wanka bayan ta shiga ɗakin baba ta ɗakko wasu sassaƙen magunguna.
Kaf gidan babu wanda yasan hidimar da ake sai iya su, ko Abu da yake baida man kai daya shigo cin abinci bai fahimta ba, ya ga dai Ahmad sai kai kawo yake a tsakar wajen cikin damuwa, da yake ba wasa yake da suba sai bai iya ya tambayesa ko lafiya ba?.
Cikin amincin ALLAH mai rahma mai jinƙai ALLAH ya sauki Umm-Ruman lafiya bayan baƙar wahalar data gama sha, duk da a hakanma su Iya sunce haihuwar tazo mata da sauƙi, ballema tana da dauriya, dan bata irin ihun nan kamar ɗiyan maguzawa.
Tunda Ahmad yaji kukan jinjiri ya sauke wani nannauyan numfashi da har Gwaggo sai da ta jiyosa ta kallesa, duk da itama ta sauke ajiyar zuciya, tausayi ya bata daga shi har Umm-Ruman ɗin dake filin daga.
Ayyah ta fito ta ɗauki abu ta koma, tana cema Ahmad ya samu waje ya zauna tunda an sauka lafiya ai.
Nanma ya sake samun nutsuwa, sai bin gwaggo da kallo yake yaga ko zaiga yanda zata nuna, sai dai bai fahimci komaiba daga fuskarta, ta dai ɗauka buta tayi alwala ta shige ɗaki abinta.
Kansa ya duƙar ƙasa yanata cigaba da jeroma ubangiji godiya da kirari akan wannan ƙyauta da yay masa.
A haka su Fa'iza suka shigo gidan suka iskesa, sannu duk sukai masa, a mamakinsu sai sukaga fuskarsa washe da fara'a, su dai ɗakinsu suka shiga dansu ajiye littatafan hannunsu da hijjabai.
Sadiya tace, “Oh ni waye yayma katifarnan haka? Zainab halan kece?”.
Zainab sarkin tsiwa tace, “Kai Yaya Sadiya, ALLAH zai sakamin dan wlhy bani baceba”.
Duka Sadiya ta kai mata, ita kuma ta fita da gudu zuwa ɗakin Gwaggo dan takai ƙara.
Gwaggo dake ƙoƙarin fitowa sukaci karo da Zainab, tace, “K kuma lafiya?”.
“Gwaggo ba yaya Sadiya bace, wai dan mun dawo munga an hargitsa katifa shine wai tace nice, kuma wlhy ni bani bace nama rigasu tafiya makaranta......”
Kafin Gwaggo tace wani abu Sadiya ta fito daga ɗakin tana faɗin, “Nifa Gwaggo daga na tambayeta ne, maimakon tace ba ita bace sh
ine harda wani cewa ALLAH zai saka mata na mata sharri ma kenan?, bakigafa yanda akaima katifarba kaca-kaca kamar wani ya hau yay danbe”.
Fa'iza tace, “ƙilama aljanune wlhy Gwaggo, ni dai yau ban kwana a ɗakin nan”.
Ahmad duk yana zaune yana saurarensu, amma ko kai bai ɗago ya kallesu ba, balle ya nuna yasan wanda yayi.
Gwaggo da batace uffanba ta nufi ɗakin dan ta gani, dai-dai nan kukan ɗan jariri ya kuma cika sashen.
A take su Fa'iza duk suka fiddo idanu waje alamun mamaki, har haɗa baki suke wajen ambaton, “gwaggo Rumana ta haihu ne?”.
Da hannu tai musu nuni da suyi shiru, aiko sai kowacce tai ɓam da bakinta amma tsagwaron murna ya mamayesu, suka kama tsalle tare da afkawa ɗakin suka haye katifar da suke cewa sunajin tsoro, kota kan Gwaggo dake ƙarema katifar kallo basu biba.
Itama sai tai fitowarta bata tanka musuba.
Cikin awa biyu Gwaggo da Ayyah suka kammala kimtsa komai, sannan kusan sha ɗaya na dare, Ayya ce taje cikin dubara ta sanar ma Ammi dan ba'ason faɗin haihuwar sai safiya idan ALLAH ya kaimu.
Addu'a kawai Ammi tayi amma bata zoba.
Ayyah ta kama hannun Ahmad suka shiga ɗakin ya tsaya daga ƙofar ɗaki, jaririn dake nannaɗe cikin zani ta ɗakko masa, dukda da akwai ɗan ƙarni-ƙarni jikinsa, dan zaitun kawai aka shafa masa hakan bai hana Ahmad amsarshiba jikinsa sai tsuma yake, lokacin da idonsa ya sauka akan yaron kuwa sai suka ciko da ƙwalla, ya ɗora bakinsa akan goshin yaron ya sumbata yana murmushi.
Ayyah ma dake murmushi tana kallonsa tace, “Ɗan albarka nayi miji gashi nan tubar kalla masha ALLAH”.
Murmushi yayma Ayyah sai dai bai iya cewa komaiba, jiyake kamar ya maida yaron cikin jikinsa, ya kai dubansa ga Rumana dake kwance a kan gado ta juya musu baya wani wahalallen barci yay awon gaba da ita, Iya ko data sake kimtse-kimtse, dan so take ta ɗaurayema yaron jiki ko yayane, Rumana dai anɗan gargasa matane kafin safiya.
Murya a sanyaye yace, “Ayyah Gwal ɗin fa?”.
Ayyah tace, “Wane kuma Gwal ɗan albarka?”.
Fahimtar suɓutar bakin da yayne ya sakashi miƙa mata yaron ya fita da sauri yana dariya.
Iya da duk take saurarensu tace, “Ɗan jakar uba, a gaban uwar takama Gwal zaka ce? Ashe bamu kaɗai akema rashin kunyar ba, ni dana gama wahalar amsar maka haihuwar wannan raguwar matar taka baka fara tambayata ba sai ita”.
Shi dai bai bata amsaba yama fice daga gidan cikin tsagwaron farin ciki da yarasa a ina zaije ya juyesa ko zaiji sassauci.
Ayyah da sai lokacin ta fahimci inda zancensa ya dosa itama tai dariya tana girgiza kai.
Sai da Iya ta kammala komai tsaf ta fice sanan Ayyah taje har ɗaki ta kamo Gwaggo dan dole tazo taga baby.
Lokacin kusan sha biyu ma.
Gwaggo ta ɗaukesa tai masa addu'a tana mai kallonsa tamkar sanda ta haifi Ahmad, Rumana dai tanata barcinta batasan wainar da ake toyawa ba.
Gwaggo na fita su fa'iza suka shigo, sai santin ɗan yaron suke, sukam, ai sai da Gwaggo ta korasu suje su kwanta sannan.
Ahmad ma da wannan tsagwaron farin ciki ya isa gida, har zai kwanta ya tuna akwai najasa a jikinsa, dole yaje yay wanka tare da ɗauro alwala, saima ya kasa kwanciyar kuma ya hau nafilfilin miƙama UBANGIJI godiya.
A wannan dare haka wannan ahali suka kwana cikin tsagwaron farin ciki mara misaltuwa.
★★★★★★
Asubar fari Ayyah ta fito baba ya taimaka mata suka haɗa wutar ɗora ruwan wanka, lokacin da ake ƙoƙarin shiga massalaci ai harya tafaso cikin amincin UBANGIJI.
Iya na idar da salla nan tayo, ita taima Rumana cikakken wanka mai gamsar da jikin duk wata maijego data samesa, Ayyah kuma taima jinjiri, Fa'iza ta kimtsa ɗakin Ayyah aka kunna turaren wuta ɗaki ya ɗauki ƙamshin jego.
An naɗe yaro a kayan sanyin da aka sakama Ahmad lokacin yana jinjiri shima ruwan ganye da ratsin fari, (kunsan mutan da akwai ɓoyo da bama abu muhimmanci, dama Ayyah tai alƙawarin inhar ALLAH ya kaita da rai, duk randa Ahmad yay aure ya haihu kayan da za'a fara sakama ɗansa ko ƴarsa kenan) to gashi ALLAH ya cika mata burinta kuwa, da yake
kuma kayan saƙace mai inganci da tsari.
Shiko sai barcinsa yake yaji ɗumi.
Kafin gari ya gama haske har gwaggo ta kammala damun kunu da yaji kayan ƙamshi, ga kuma shayi shima yaji kayan ƙamshin.
Mudan ya shigo gaishesu yay gamo da wannan farin ciki, dan shi bai shigo gidanba a jiya yanata dinkin wasu anguna kusan ma kwana yay, da yake kuma ba wani ɗaga murya sukeba sai baisan mi ake cikiba, ko fitar Yah Ahmad bai ganiba, ya daiga shigowarsa bayan sallar isha'i.
Gaba ɗaya farinciki ya gama rufesa, ya ƙwaƙume jinjiri tamkar zai maidasa ciki, koda baba ya shigo a lokacin dan shima sai yanzune zai gansa da ƙyar Mudan ya bashi, ita dai Rumana kanta na a ƙasa ko Mudan ɗin ta kasa amsawa santinsa balle kuma ga baba ya shigo.
Ta dai gaidashi, ya tambayeta yaya jikinta? Ta amsa da ƙyar.
Jariri daketa barci yaji daɗin wanka yasha addu'oi wajen baba, Mudan ko ya fice nemi kayan shayi da Ayyah ta faɗa masa.
Babu daɗewa ya dawo harda soyayyen ƙwai.
Sai a lokacin kuma Iya ta dage ta callara ghuɗa domin tabbatarma kowa dai anyi haihuwa.
Ba ƙaramin faɗuwar gaba wannan ghuɗa ta saka mama gaje ba, itace farkon isowa sashen su Ahmad kafin sauran matan gidan.
Sai dai yanda suka iske mai jego tsaf ya tabbar musu da haihuwar bata yanzu bace, nanfa aka shiga taya juna murna da tsokanar jariri kasancewarsa jika a wajensu.
Mama gaje dai ta ciki na ciki, dan duk a rikice tace tana ƙoƙarin danne wane kawai.
Gida dai ya kacame da murna, duk da farar safiyar nan yaran gidan haka sukaita rige-rigen bin gidajen yayunsu dan sukai musu labari.
Sanda Ahmad ya iso gidan kuwa, duk yanda yaso shiga ɗakin Ayyah su gaisa da Rumana hakan gagararsa yay, dole ya haƙura bayan yaɗan gaggaisa da matan gidan sukai masa barka da addu'a wa jariri dole ya haƙura ya koma ƙofar gida wajen abokansa da suma suka kacame masa da murna, bakinsa ya kasa rufuwa kuwa sai murmushi yake saki.
Mama gaje kam ɗaki ta koma tamkar wata zararriya, sai ƙoƙarin kiran Number Samina take yaƙi tafiya, sai tsaki take tana faman zagaye ɗakinta da waya a hannu, wani irin zafi na azalzalar zuciyarta🥴...........✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_37_*
*_MATAR AUDU😜🥱_*
.........Lokacin da mama gaje ke a wannan ruɗani na neman number Samina ido rufe tana can suna tafka bala'i da Ma'aruff.
Dan gaba ɗaya a kwanakin nan dama sai a hankula, asirin da ke a jikinsa ya bar jikinsa, hakan yasa sam Samina ta kasa gane kansa a wannan lokutan.
A daren jiya kuma bayan sun gama rigima akan fitar da zaiyi ta dare ta tareshi akan baizai fitaba ya shashsheƙa mata maruka ya fice abinsa, zama tai taci kukanta gwargwadon iko ta haƙura dan kanta, sai kusan ƙarfe ɗaya ya dawo gidan, tana ɗakinta ta kasa barci har lokacin, amma sai bata fitoba dan duk zatonta shi kaɗaine yauma ya dawo a bigensa kamar yanda ya saba.
Sai dai bata saniba tare yake da karuwarsa, kuma sabuwar ƙawarta Basira, wadda suke kira (Basy), suka shige ɗakinsa kuma suka kulle kansu, ranar a nan Basy ta kwana.
Da safe Samina ta fito haɗa breakfast taci karo dasu a kicin babu mai suturar arziƙi tsakanin shi da karuwar tasa, wai yunwa takeji shine ya rakota ta haɗa shayi.
Neman zubewa Samina tayi, ta dafe bango da sauri tana ƙoƙarin maido hankalinta jikinta, dai-dai Ma'aruff da karuwarsa sun juyi zasu fita daga kicin ɗin, shi ɗauke da tiren da suka soya ƙwai da shayi a kofuna biyu.
Gabanta yay wata mummunar faɗuwa saboda ganinma wacece karuwar Ma'aruff ɗin, ko kunyar ALLAH baiji balle fargabar inda ya shigo wanda alamomi sun tabbatar mata a gidanma Basy ta kwana da mijinta, suna maƙale da juna lamarin zattakaici.
Zuciya kuwa ta kwashi Samina ta tare hanyar da za subi tana huci,
“Wannan la'ananniyar kuma daga ina bunsuru?”.
Ma'aruff ya miƙama Basy tiren hannunsa yana kallon Samina, yace, “Bunsuru?”.
Cike da tsiwa tace, “Ashe ka jini, guntun iskancin naka ya kai har ka ɗakko karuwa ka kawo mani cikin gidan aurena ku kwana saboda kai baƙin jahiline babu ilimin arabi a kank.....”
Mari daya ɗauketa da shine ya hanata kai ƙarshen maganarta, ta faɗa jikin drawer kicin dafe da kunci, amma ta daure batai kuka ba, ci gaba tai da zaginsa daga shi har karuwar tasa.
Yako yunƙuro zai sake kai mata duka ta kauce, sai damar shaƙo wuyar budurwar ALLAH ya bata, nanfa kokawa ta ɓarke a tsakaninsu, shi sai ƙoƙarin ƙwaƙule hanun Samina yake daga wuyan basy yana faɗin, “K wai wace irin mahaikaciyace, ki saketa karki min kisan kai a gida!!!”
Ko saurarensa Samina batayi, ta shaƙe Basy sosai sai kakari take idanunta duk sun firfito saboda tsagwaron matsa da taji.
Da ƙyar Ma'aruff ya yakice Samina daga jikin Basy, wadda tuni numfashinta ya rabu da gangar jikinta ta suma.
Dukan Saminar ya shiga yi tana ramawa itama, duk abinda ya tare mata gaba ɗauka take ta kwaɗa masa, a haka har suka fito falo, da ƙyar ta ƙwaci kanta ta afka ɗaki ta kulle tana danƙarama iyayensa zagi shima yana danƙarama nata🤦🏻♀😢.
Kan Basy ya koma yana jijjigata, sai dai yaga ashe ma ta suma, da farkoma ɗaukarsa kota mutu ne, sai da ya zuba mata ruwan sanyi ta kawo nannauyan numfashi.
Kuka ta sanya masa akan wlhy bazata yardaba, dama ya kawota gidansa ne dan Samina taci zarafinta, to wlhy saita ɗauki mataki bazata bar Samina tasha a banza ba.
Duk yanda yaso ta sauraresa sam taƙi, ta shiga ɗakinsa ta tattara kayanta, yana ƙoƙarin riƙeta tana tureshi da faɗin karya sake taɓata.
Yanaji yana gani ta fice daga gidan, ya zube a kan kujera yana dafe kansa ga raunikan da duk Samina tai masa, sun fasa abubuwa da dama na kwalliya da akaima falon, da ace yau zai iya sai ya saki Samina saki uku, to amma idan har ya saketa bai rama wannan abun da tai masa yau ba to lallai baici riba ba ma ashe, sanan shi ba namiji bane, dolene ya tabbatar mata shiɗin da gaske yamafi bunsuru kamar yanda ta ambata.
Samina na kwance ne tanata rusar kuka mai ciwo, tunda ta auri ma'aruff bata taɓa zaman kwana uku dashi ba cikin kwanciyar hankali, idan ta toshe wannan ƙofa sai ya buɗe waccan, sam farin cikin da taima kanta fata a gidansa gaba ɗaya ta kasa samunsa, wace iriyar rayuwace wannan?.
“To Samina, ni dai bily bansan wa kike tambayaba, fans ko kune?🤷🏻♀️.
___________________________________
Duk yanda Ahmad yaso samun ganin Umm-Ruman hakan ya gagara, dan mutanema sake shigowa suke, jinjirinma sai da abokansa sukazone aka kawo musu shi soro sukai masa addu'a, sannan ya gansa a duk safiyar yau.
Yaje maida yaron ne cikin gida yayma Ayyah zancen ya kamata Rumana ta shirya suje asibiti a duba lafiyarta saboda haihuwar gidace.
Ayyah ta gamsu kuwa da maganarsa, ta shiga ɗakinta ta saka Umm-Rumana kimtsawa, Yaya Maryam data fara isowa ta ɗauki jaririn suka fito.
A ƙofar gida suka iske Ahmad yana jiransu, ya sauke idanunsa akan Rumana da itama take satar kallonsa.
Ƙasa tai da nata tana murmushi, dan haka kawai ta tsinci kanta dajin kunyarsa.
Shiko sai yaga ta ƙara masa haske a ido duk da sanye take da hijjab, bai iya cewa komaiba ya nuna musu hanya alamar suje.
Umm-Ruman ta buɗe baki a hankali tace, “Yaya ina kwana?”.
Kamar bazai tanka ba sai kuma yace, “Sai yanzu aka tuna dani?”. Yay maganar yana raɓawa ta gefenta zai wuce.
Binsa tai da kallo tana bin bayansa, dama Yaya maryam ita tayi gaba bata tsaya inda suke ba.
Napep suka shiga ita da Yaya maryam, shi kuma ya hau mashin ɗin Sufyan dake jiransa dama sukabi bayansu.
Koda suka isa asibitin su Ahmad ne sukaita shigi da fici har suka samu ganin likita.
Sai da Doctor ta tabbatar Rumana bata da matsala, sai ɗan ƙari data samu wanda dama tun daren jiyan takema iya complain ɗin zafi, musamman ma da zatai mata wanka da safe, dan kasa zama tai cikin ruwan sai da iya tai mata jan ido, ashe ɗan ƙarine tayi kaɗan.
Duk wani taimakon da ya kama Dr Hajarah ta bata shi, harda shawarwarin yanda zata kula da yaronta, ta rubuta magunguna ta bama su Ahmad akan a sayo ma Rumana.
Amsa yay suka tafi, su Rumana kuma da yaya maryam sukaje inda za aima jaririn allurar Iminazeshon tunda yayi dai-dai da ranar da akeyi.
Sun ɗan ɓata lokaci a asibitin, dan har ɗaya suna can, sai da komai ya kammala sannan suka fito, yaya Maryam da Umm-Rumana suka nufo gida.
Shi da Sufyan suka wuce kwata ya sayo nama mai ƙyau yayo cefane suka dawo suma.
Daga Gwaggo har Ayyah sunji daɗin hakan da yayi, ya iske ƴan uwansa duk sunzo, sunata masa murnar samun ƙaruwa.
Yayinda Sakina ta tasashi gaba da fadin, “Inye su ɗan ƙanina an girma, abun mamaki wai Amadi da ɗa”.
Harara ya zabga mata kawai ya wuce, tako cigaba da kunnashi har sai da yay mata ƙwafa sannan, amma dai baice komaiba😂.
Barcin da baiyi isashsheba a daren jiya shiya addaba masa, dole ya shiga ɗakin su Mudanseer ya kwanta kuwa.
Umm-Ruman taji daɗin zuwansu asibitin sosai, dan magungunan da aka bata sun taimaka ma jikinta ta kumajin ƙarfi, bata sake ganin idon Ahmad ba har bayan sallar magriba.
★★★★★★
Bayan sallar isha'i Ahmad ya shigo gidan, da gani dai yaje gida yayo wanka, dan yanzu sanye yake da ƙananun kaya da suka ainahin fidda ƙuruciyarsa da kwarjini saɓanin yanzu da yake sanye da yadi.
Sai da ya shiga sashen baba suka gaisa, acanma ya iske Gwaggo, dan dama tunda Rumana ta dawo gidan Ayyah ta barma Gwaggo mijin, iyakarta tayi abinci kawai.
Bayan ya gaidasu duka suka ɗan tattauna da baba, yay masa maganar yima yaro huɗuba.
Ahmad yace, zaije yanzu yayi, dan da safe ya shigo zaiyi ya iske mutane sunyi yawa.
Gwaggo dai na jinsu bata tankaba har Ahmad ya tashi ya fita zuwa ɗakin Ayyah dake ƙofar ɗaki zaune ita da Mudan dake cin abinci suna hira.
Sannu sukai masa ya gaida Ayyah.
Fuskarta faɗaɗe da murmushi ta amsa da ce masa ya shiga abincinsa na ciki.
Ɗakin ya nufa ya shiga da sallama, su Fa'iza dake zaune suna taya Umm-Ruman hira duk suka miƙe, raɓawa sukai suka fice suna gaidashi.
Sai da duk suka gama fita yana tsaye idonsa kafe akan Rumana dake cin farfesun da Ayyah tai mata na naman da Ahmad ya kawo ɗazun.
A hankali ya taka zuwa gaban gadon inda ɗan jaririnsa ke kwance naɗe a cikin zani, zama yay ya ɗaukesa ya aza bisa cinya.
Rumana dake satar kallonsu tace, “Sannu da shigowa”.
Kallonta yay kaɗan yana maidawa ga yaron tare da amsa mata, yay masa kiran salla a duka kunnensa yana faɗin, ALLAH ka raya *_HAMZA, Sunan Uncle ɗin MANZON ALLAH, jarumtarsa yasa akan masa laƙani da zaki,(ALLAH yasa kaima ka kasance magajinsa a wajen addini da jarumta) sannan magajin Baba, (ALLAH yasa ka kasance mai kwaikwayon halayya na ƙwarai irin na baba) dan haka alkunyarka itace (Haysam, ma'ana Lion) kenan, ALLAH yasa ya zama zaki mai kare martabar addininsa a duk inda ya tsinci kansa, ya sanya albarka da alkairi a rayuwarka my lion har ƙarshen numfashinka, ALLAH ya hanaka kasancewa a cikin masu aikata fasadi a ban ƙasa, ka zama ɗa na garin abin alfaharinmu, abin alfahirin MANZON ALLAH a ranar da ya ambata al'umarsa su zama_*
Rumana dake saurarensa kanta a ƙasa tace, “Amin ya ALLAH Yaya, ALLAH ya Rayasa akan turbar addini”.
“Amin Gwal ɗina, amma banji kin maimaita sunanba”.
Murmshi Rumana tayi tana ɗan ɗago ido ta kallesa, ya ɗaga mata gira da wani salo.
Ɗauke idonta kawai tayi, tace, “To ALLAH ya raya Haysam”.
“Muna godiya Umm-Haysam ”.
Nanma murmushin tayi, ya ciro dabinon dake aljihunsa ya saka a baki ya tauna sannan ya zare hannun da yaron ya saka a baki ya haɗe bakinsu bayan yay bismilla ya zuba masa.
Ɓata fuska yay yana motsa baki, hakan ya saka Ahmad ƙura masa ido yana murmushi, ya yafito Rumana da hannu alamar tazo ta gani.
Bata musaba kuwa ta taso zuwa garesu, har lokacin fuskar yaron a yamutse take yana dai cigaba dajin sabon ɗanɗano a harshensa, sai kuma ya koma motsa bakin alamundai shanye kayansa yake.
Murmushi sosai Rumana takeyi itama.
Ahmad ya ɗago yana kallonta shima yana murmushi, “Gwal kinga ƙwaɗayin da kikayi ko? Duk kin gogama yarona”.
“Ni wlhy a'a, shidai yasan inda ya kwaso kayansa”.
Dariya Ahmad yay yana sumbatar kumatunsa, yace, “My Lion kaji Ummienka ko? Karka damu zamu rama”.
Ita dai Rumana kallonsu take cike da sha'awa, ya kuma sumbatar goshinsa.
Tasowa yayi yazo gabanta ya durƙusa, tare da ɗora mata shi saman cinya, ba tare da ya janye hannunsa ba ya ɗago ido yana kallonta, duk yanda taso janye nata ya hanata dama, murya ƙasa-ƙasa yace, “Please gwal, yi feeding ɗinsa na gani”.
Tana ƙoƙarin janye idanunta yay saurin jawo hannunsa daga cinyarta ya riƙe haɓarta.
“Haba babie R sai anja mani aji”.
A ɗan shagwaɓe tace, “Nidai Yayah ALLAH kunyarka nakeji”.
Gira ɗaya ya ɗage yana mata wani kallo mai saka zuciya nutsuwa, “Gwal zuman ki ne fa, wace kunya kuma ta rage miki bayan kin haifomin My Haysam duniya Huyim?”.
Yanda yaketa wani marairaice matane ya sakata bin umarninsa tayi yanda yakeso.
Yanda take ta matse baki da yaron ya kama ne ya sakashi yin murmushi, “Miya farune Gwal ɗina?”.
Cikin ɗan yarfe hannu tace, “ALLAH akwai zafine Yah Ahmad”.
“Oh sorry, to kona tayashi”.
Babu shiri ta buɗe idanunta tare da zarosu waje.
Dariya yay yana matsawa baya, “Kinga wasa nake karki hanani barci da waɗannan idanun hajjaju”.
Itadai shiru ta masa, shiko ya koma kan tabarma ya jawo tiren dake gefe yana buɗewa dan yasan abincinsa ne.
Yanda ya ƙureta da idone ya sakata janye yaron tana gyara rigarta, dama ta gaji, dan tsakanin daren jiya zuwa yau ta kula yaron nan cin tsiya zaiyi, dama da daddare da kuka Ayyah ta tirketa ta bashi nonon, yauma ɗin sai an tuna mata kokuma yana kuka sannan.
Yaron ta gyarama zanin da yake a ciki ta miƙe zuwa ɗan katifarsa mai net dake babban gadon Ayyah ta sakashi sannan ta dawo ta zauna.
Yanda tai shirune ya saka Ahmad kallonta yana fadin “Malama wai na zama surukinki ne?”.
Rumana tace, “Eh mana”.
Tsayawa yay yana kallonta, yace, “To miyasa?”.
Fiki-fiki tai masa da idanu tana ɗauke kanta bata bashi amsaba.
Yay ƙaramar ƙwafa da faɗin, “Zan kamakine yarinya”.
Ita dai murmushi kawai tayi.
Koda ya gama cin abincin sai da Ayyah tai masa magana yazo ya wuce gida sannan ya fito yana ɓata fuska.
Ita dai Umm-Ruman sai dariya take ciki-ciki, ya harareta da mata alamar wai zai kamatane ai sannan ya fice.
★★★
Washe gari wajen goma na safe sai gasu maman Ama, sunzo barka ita da Kausar, sunzo da ɗan ƙullin Omon su, ita dai Rumana ta amshesu hannu bibbiyu.
Sunata santin yaro da fadin sun rasa da wama zasuce yana kama, ita ɗin ko Ahmad.
Ita dai batace dasu komaiba, kusan yini sukai a gidan, dan sai bayan zuhur sosai suka wuce.
____________________________________
Ɓabgaren Samina kuwa Basy na fita ta kawo musu ƴan sanda tayi, tsabar ta fisu rashin mutunci tasa har Ma'aruff ɗin aka kama sukaje suka garƙame kuwa.
An tafi dasu babu jimawa ƙanwar Ma'aruff tazo gidan, mai gadi ya zayyane mata komai daya faru, hankalinta tashe ta kira Ummansu ta sanar mata, acan suka haɗu police station ɗin da sauran ƴan uwanta.
Da yake ƙasar tamu ta zama mai kuɗine mai faɗa aji, ƴan sanda sunajin sunan Ma'aruff jikinsu har ɓari yake suka fiddosa suna bama su Ummansa haƙuri.
Shine yace a fiddo Samina ma, amma Ummansa tace sai dai itama a nemi iyayenta su fiddata.
Baiko musaba yabi maganar Ummansa suka tafi suka bar Samina a station.
Samina naji tana gani Ma'aruff da ƴan uwansa suka fice suka barta a station ɗin, dukda kasancewarta matarsa ta sunna, su kuma matar ɗan uwansu.
Wani cikin ƴan sandan yaji tausayin Samina, shine yace ta bada Number wani cikin ƴan gidansu a kira.
Rasama tawa zata bada tayi, sai ta basu ta mama gaje, an kira yafi sau biyar bata shigaba, tai shiru tana tunani, ta bada ta Ahmad ne kokuwa ta babanta?.
Wata zuciya tace ki bada ta Baban dai, koba komai mahaifinki ne zai rufa asirinki, amma Ahmad ya samu ƙofar miki dariya ne.
Wannan shawarar tabi tabada ta Baba, bugu biyu kuwa ta shiga.
Kasa magana tai sai ɗan sandan ta bamawa ya sanarma Baba yusha'u halin da Saminar ke ciki, da kuma a inda take............🧐✍🏻
*_Jiya wayatace ta zafafani shiyyasa nima na saku a zafi, sai da nagama wahalar typing kusan 2pages sannan komai ya goge, kaina cakewa yay nama rasa mizan sake rubutawa, kawai sai na kunna waƙa naitaji dan takaici😔😏._*
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_38_*
*_BULKUMA🤫_*
...........Baba Yusha'u da baba suka kalli juna, dan a hansfree ya saka wayar tasa, kuma suna tare da baba zau,ne a ƙofar gida.
Takaici ya hana baba Yusha'u magana, ransa a ɓace ya tura wayarsa aljihu yana faɗin, “Wlhy sai dai ta shekara dubu acan”.
Da kallo kawai baba ya iya binsa, cikin ransa yana tunani to miya kai Saminar police station da aurenta kuma?.
Kansa kawai ya girgiza ya ciro wayarsa daga aljihu ya shiga neman number Ahmad, yanata maimaita sunan station ɗin a ransa dan karya manta.
Ahmad na gida lokacin yana shirin fitowa zasu fita shi da Sufyan kiran baba ya shigo masa, ɗagawa yay cikin girmamawa ya gaishesa.
Baba ya amsa yana faɗin, “Amadu kana inane?”.
“Baba gani a gida, amma ina shirin fitowa ne”.
“Yauwa to maza kazo gida ka sameni yanzun nan kaji ko”.
“To Bana, ALLAH yasa dai lafiya?”.
“Sai kazo dai”.
Ahmad dake sanye cikin baƙar shadda daketa maiƙo sabuwa dal ya sauke numfashi kawai, bazamuce mai azabar tsada bace, dai-dai ƙarfin talaka mai abunyi a hannu, shaddar ta masa ƙyau sosai, sai kace wani ɗan masu hannu da shuni, ga ɗinkin da akai mata na zamani ya kuma fidda cikar haibarsa da haska choco fatarsa da jindaɗi ya kuma gogewa har wani ƙyalli-ƙyalli take.
Hula ya ɗauka kalar golden da akai adon gaban rigar da ita ya saka, zuciyarsa sai kuma mamakin kiran baba yake, yana zancen zuci ya ɗauka link ɗin hannun rigar shima golden ya saka sannan ya fesa turare a gurguje yasa wayarsa a aljihu ya fito.
Kausar ce kawai a tsakar gidan tanama ƴarta wanka, tabi Ahmad da kallo harya fice, zuciyarta na mamakin irin wannan ɗaukar wanka da kullum Ahmad keyi sai kace wani ɗan wani da wata, su dai sun saka ido suga shin neman nasa jikinsa kawai yakemawa kokuwa harda Rumana?, dan sudai randa sukaje barka basuga wani sabon abuba daga Rumanan.
Shidai Ahmad da baisan tanaiba yana fita ya hau mashin ɗin Sufyan da yazo dashi, sosai mashin ɗin ya masa ƙyau, duk budurwar data gani dole ta ƙyasa harda masu burin auren mijin novel (🥴😂⛹♀).
“ƴammata a kula, wannan garan na anguwarku dake zuwa miki da koɗaɗɗun kaya, babu mota, babu ƴan canji, da kin kama abunki kin riƙe wlhy kece zaki saitashi yafi mijin novels ɗin da kike hange komai, dan mazanmu ba banbanta sukai da mazan novels ba, sunma fisu komai idan baki saniba, bar hangen abinda yake gaibu kama zahiri ki amfana duniyama ta amfana, ƙyalƙyal banza shirmene, ƴammatan wajema sun isheki, dan waɗannan da kike hange masu siffar mazan novels ɗin mafi yawansu a rigane wlhy, babu hali babu tarbiyya, sai ƙalilan daga cikinsu, dan duk inda aka samu na banza to akwai nagari, sannan ko wane namiji da kika gani komin garancinsa yanada izzarsa, dan wannan cikin jinin maza take, saikin saka ido zaki ranfo cikar haiba naki shima, kwarjini, isa, taƙama, harma da tsagwaron sarauta daga jinin gwarzonki, zan faɗa a fili, na faɗa ɓoye, na faɗa da kuwwa, agaban kowa kuma, wlhy mazanmu sunfi mazan novels ɗin da ragwayen zukata ke ɗauka wani abin burin samu, ƴammata harma da wasu matan auren a kula sosai, da rarrafe yaro kan tashi, duk wani mai arziƙi ko shugaba, mafi yawansu da zaki bibiyi tarihinsu sai kinci karo da gwagwarmayar da sukaci a rayuwa kafin sukai ga mtsayin, kema idan kin auri wannan ɗan dakon wataran shine zai biya jirgi ya masa dako, daki auri wanda ya tara gamma ki auri wanda zaku tara tare, ko mata ɗari zai kalla bayanki suke, sannan kimarki a wajensa daban take koda shine shugaban ƙasar Nageria kuwa🤸🏻♀🤫, lamarin fa duk bugene😹🤷🏻♀️⛹♀⛹♀⛹♀.
A ƙofar gida Ahmad ya iske baba na jiransa, ya kafe mashin ɗin yana nufar wajensa.
Sai da ya durƙusa ya sake gaishesa sannan baba ya faɗa masa abinda ya faru.
Tuni fuskar Ahmad ta canja, kansa a ƙasa yace, “To baba ina mijin nata?”.
Murmushi baba yay idonsa akan Ahmad ɗin, “Amadu bar zancen kowa je kaima zumincin ALLAH”.
Kai Ahmad ya jinjina tare da faɗin “To baba”.
Cikin gidan ya shiga, dan ya saka a ransa sai matarsa ta fara ganinsa kafin wata shashashsa.
Umm-Ruman na saka kaya ya shigo, dan fitowarta wanka kenan, jaririn kam barcinsa yakeyi shima an masa wankan tunda farar safiya.
Bata juyoba tadai amsa sallamarsa, tana ta ƙoƙarin jan zip ɗin rigarne sama yaƙi tafiya, ashe wani zarene ya shige ciki.
Ahmad ya matso kusa da ita tare da ɗora hannunsa bisa nata, baice komaiba ya janye natan yaja zip ɗin, sai dai shima bai wuceba, jansa yay ya koma ƙasa sannan ya duba, ganin zarene yaɗan ranƙwafo yasa haƙori zai tsinke, maimakon ya tsinke zaren sai ya kama busa mata iska a gadon baya.
Babu shiri Rumana ta juyo tana fuskantarsa..
Ɗagowa yay shima yana wani kallonta idanu a narke,
“Kai Yaya, haka ake sa zip ɗin?”.
Ransa a dagule yake da aikin da baba ya sakashi, hakan yasa sam fuskarsa babu walwala, sai ɗanyatsa da yakai ya lakaci hancinta yana ɗage mata gira ɗaya.
Kafin ta samu damar magana ya jawota ta manne da jikinsa, dukansu suka sauke ajiyar zuciya, zip ɗin yaja yay sama yana mata magana a cikin kunne.
“Babie R mizan samu?”.
Yanda yay maganar kamar akwai damuwa a maƙoshinsa ne ya saka Rumana janye jikinta daga nasa ta ɗago ta kallesa.
Murmushi tayi dan duk alamominsa ya nuna mata yanada damuwa, batace komaiba ta ɗora hannunta a ƙirjinsa tana gyara masa wuyan rugarsa da cire wani zaren ɗinki daya maƙale a surfanin, ta koma kan hularsa itama ta gyara mata zama da ƙyau, shidai kallonta yake kawai.
“Zumana kayi ƙyau, sai kace wani sabon ango?”.
Kaɗan ya murmusa yana ɗora duka tafukan hannunsa a fuskarta, ya matso da goshinsa kan nata yana faɗin, “Gwal ɗina ni angone mana, angon ƙarni Abu Haysam ”.
Murmushi Rumana tayi, ta sumbaci laɓɓansa tana lumshe idanu, tace,
“Hakanefa Zumana, yanzu daga nan sai ina kuma?”.
Guntun tsaki yayi yana cire goshinsa daga kan nata, “Share kawai babie R”.
Batace masa komaiba harya ƙarasa inda Haysam ke kwance a babban gadon Ayyah yana barci, an naɗesa cikin kaya masu kauri ruwan hoda, harda showal ɗin da yake ciki, kaɗan ya janye showal ɗin ya sumbaci goshin yaron, “Sadauki na kai baka da aiki sai barci? Har yanzu kaƙi naga idanunka, ko duk jarumtarce?”.
Dariya Rumana dake kallonsu da saurare tayi, hakanne ya saka Ahmad juyowa yaɗan kalleta.
Ta ɗauke kanta tana faɗin, “Jarumta ko ragwantaka”.
kafin ya samu bata amsa Ayyah ta shigo ɗakin da kunun da aka damawa Rumana.
Hakan yasashi ɗauke kansa ya maida ga Haysam.
Ayyah tace, “Ɗan albarka ga yaro can Sufyan ya turo ya kiraka”.
Saida ya sake sumbatar Haysam ya gyara masa rufar kamar yanda ya gani sannan yace, “To Ayyah na, sai na dawo”.
Addu'a tai masa itama, ya nufi hanyar fita yana amsawa cike dajin daɗi, sai da ya kama labule sannan Rumana tace “ALLAH ya tsare”.
Juyowa yay ya kalleta, yay mata ƙaramar harara, itakuma tai masa gwalo.
Ida ficewa yay yana murmushi.
___________________________________
Sun iso station ɗin su da baba da baba Ilyasu, ganinsu tsaf-tsaf ya saka akai musu tarbar mutunci.
Sun musu bayanin wadda sukazo fiddawa.
Ogan ya bama ɗan sanda ɗaya umarnin fiddo Samina, sannan aka bama Ahmad inda zai saka hannu.
Ƙinyi yay sai da baba yay masa magana, fuskarsa babu walwala yaja buk din tare da ɗaukar biron da aka ajiye masa, dai-dai nan aka fiddo Samina.
Babu ɗankwali a kanta babu takalmi, tayi wani ziru-ziru ga ƙananun ciwuka da taji lokacin da suke faɗa da Ma'aruff.
Akan Ahmad dake rubutu ta fara sauke idanunta, wani sama numfashinta yayi da ƙyar ta fisgosa, sai maimaita sunansa take cikin zuciya, ya ajiye biron yana tura buk ɗin gaban ɗan sandan tare da yima Samina kallo ɗaya ya ɗauke idanunsa yana sake tamke fuska.
Ƴan sandan sun mata gargaɗi akan ta kiyaye gaba, dan tana dai gani dangin mijinta duk da sunada arziƙin da waya kawai zasu iyayi a fiddata amma sukazo har station ɗin suka fidda ɗansu ita suka barta.
Ita dai kanta a ƙasa, saboda kunya da baƙin cikin Ahmad yanajin sirrinta.
Shiko tamkarma baisan anaiba, ya ɗauke kansa daga garesu baki ɗaya yana danna wayarsa daya ciro a aljihu.
Koda aka sallamesu shine farkon fitowa ma, lokacin da suka fito suma jingine da mashin suka iskesa yana waya da Happy data kirashi.
Zuciyar Samina sai sake tsitstsinkewa take, gaba ɗaya Ahmad ya canja mata a komai, ya rikiɗe ya zama wani hamshaƙin namiji.
Ita dasu baba napep suka shiga, Ahmad da Sufyan kuma suka hau mashin dan daga nan inda suka fito dominsa zasu wuce, su baba kuma su wuce da samina gida.
★★★★★★★
Tunda suka fito daga Napep ƴan anguwa dake kai kawo jefi-jefi da yara suketa kallon Samina, ta shige gida tana rufe fuska da mayafi.
Da Mudan taci karo a soro ya fito daga sashensu, ya bita da kallon mamaki harta shige sashinsu itama.
Ƙaramar dariya yayi ya ida ficewa yana faɗin, “Ankusa fara wasan kenan”. dan dama yanajin sanda baba kema Yah Ahmad bayanin zuwa su amso Samina daga station.
Mama gaje da batasan hidimar da akeba ganin Samina kawai tai ta shigo, ta ajiye robar hannunta dake ɗauke da kayan miyar da zata ɗora abincin rana tana kallon Samina.
Ammi ma dake wanki daga ƙofar ɗakinta da kallo tabi Saminar harta shige.
Hakanne ya saka mama gaje jan tsaki tana faɗin, “To kurwarta dai kurr wlhy, wannan kallon ƙurulla har ina”.
Ammi dai batace komaiba ta cigaba da wankinta, mama gaje na ƙoƙarin bin bayan Samina baba Yusha'u daya shigo gidan ya dakatar da ita a zafafe.
“Ina wannan lalatacciyar? Maza zoki fitarmin daga gida, wlhy su Yayanma su suka fiki da sukaje suka amsoki daga wajen ƴan sandan, ai ni sonai yanda mijin naki da danginsa suka barki acan suma su barki ki ƙare rayuwarki a kulle, ki fito nace ki fitarmin a gida ko”........
Fitowa Samina tai tana hawaye, dai-dai nan su baba da suka biyo bayan Baba Yusha'u suma suka shigo suna masa magana.
Sai dai sam yaƙi sauraren kowa, ya kafe akan Samina saita bar masa gida.
Wannan ƙaramar hayaniyace ta fargar da sauran jama'ar gidan harma da maƙwafta da katangarsu ke jingine da gidan nasu Ahmad.
Hankalin mama gaje ya tashi saboda jin fallasar da Baba Yusha'u ke musu a bainar Nasi, dan faɗin komai yake babu rufi, su Ayyah duk sun shigo an haɗu anata bashi haƙuri, amma sai sake jerama mama gaje ALLAH ya isa yake akan ɓata masa rayuwar ƴa datai, yakuma tabbatar mata wlhy badan ƴan uwansa da iyayensa da suka hanashiba da tuni ta tsufa a gidansu itama.
Mama gaje fa taji babu mafita sai kawai ta saka kuka, wai Baba Yusha'u dai dama ya shirya cin zarafintane.
Abu dai ya nema yin tsamari har sai da iya ta shigo sashen ta tsawatar sannan.
Baba Hamza kuma yace, Samina ta zauna har sai Ma'aruff yazo sun nuna masa kuskurensa sannan ta koma.
Da wannan aka kashe maganar kowa ya fito, Mama Gaje da Samina suka shige ɗaki ransu a dagule.
“Keko Samina miya kaiki wajen ƴan sanda?” Mama gaje ta faɗa hankalinta a tashe.
Kuka Samina ta sanya tana kallon mama gaje, ta shiga zayyanema mama gaje duk abinda ya faru, harma abinda basu saniba dangane da shan giya da Ma'aruff keyi.
A matuƙar firgice mama gaje tace, “Samina giya fa?”.
“Wlhy da gaske nake mama”.
Kasa magana mama gaje tayi, tasaka hannu bibbiyu ta rabga tagumi kawai tana kallon Samina.
Yaya bintu dake tsaye daga ƙofar ɗaki basu saniba tai murmushi mai ciwo, “Wannan shine abinda na hango miki Samina, ni nasan bai zama lallai ki samu abinda kike hangenba ɗari bisa ɗari kodan girman butulcin da akaima Ahmad, farin ciki shine abin buƙatar ɗiya mace a gidan miji ba dukiyaba, mama kun tafka babban kuskure wlhy, ku........”
“K binta ki kiyayeni wlhy!!!”.
Mama gaje ta faɗa a matuƙar tsawace.
“K wace irin wawuyace mara kishin ƴar uwarki, ni nasan yanda Ma'aruff kesan Samina wlhy sai dai idan asiri akai musu, kuma ba kowa bane sai dai wannan annamimin yaron Ahmad ko baƙar dagarcan (Amin su Rumana take nufi), suna baƙin cikin ta fisu ta wuce da saninsu, shine suka ƙulla mata dan tarasa zaman lafiya a gidan aurenta”.
Murmushi kawai Bintu tayi tana girgiza kai, tace, “Wannan shine ake kira da suna *GUDU DA WAIWAYE....* mama, gashi tun ba'aje ko inaba harya fara kawo muku *mugun zato*, ina Ahmad yaga wani lokacin ma Samina asiri balle Ammi da abinda yake gabanta kawai takeyi, abinda ta zaɓane ALLAH ya bata kawai. Godiya ya kamata kumasa dan a yau ɗinma kuɗinsa ya saka ya fiddota, badan mahaifinsa ba kuma sai dai ta dawwama a hannun ƴan sandan”.
Tana gama faɗa ta fice abinta tabar musu ɗakin.
____________________________________
Anta ƙananun magana akan wannan al'amari daya faru da Samina, harda masu ƙara gishirima a kai, tana ji tana ganin shigowama sashen su Ahmad taga jariri ya gagareta, saboda ƴan barka masu shige da fici.
Lamarifa ya taru yayma su mama gaje yawa, ga baƙin cikin haihuwar Rumana, ga tashin hankalin abinda ya faru da Samina, ga surutan mutane dake tashi harda abindama ba ayiba.
Sunason fita wajen malaminsu baba Yusha'u yace konan da zaure Samina ta fita inhar ba mijinta yazo gidanba to tabar gidan kenan har abada, itako mama gaje inhar ta fita to abakin aurenta.
Dan randa inna mari tazo barkane yaji suna ƙulla yanda zasuje wajen malam su sanar masa abinda ke faruwa, musamman ma a kan aikin Rumana da basuga ya wani ciba, tunda gata daram ita da jaririn ta, ga ruɗanin daya ɓillo a cikin auren Samina wanda su basu san da shiba.
Ranar da Umm-Ruman ta cika kwana biyar da haihuwa, Samina nada uku a gidan sai kawai akaga su yaya maryam da akwatina guda huɗu set guda kenan, sai kuma babba guda ɗaya kalarsa da ban da ƴan tarkace irin na jarirai.
Tofa, kallo ya koma sama, aka gama shigo da kaya kafin a tattara zuwa sashen su Rumana akai a dire, dan gwaggo da Ayyah harma da baba dama duk sun gani sunkuma san da shirin.
Tun fitar Ahmad ta farko neman kuɗi, yaɗan fara zuwa da kaya yana ajiyewa ɗakin baba acewarsa zai haɗama Rumana lefen da ba'ai mataba, hakan yasa duk zuwan da zaiyi sai yazo da wani abu yaɗan yadda, ranar da suka karɓo Samina fitar da sukai akwatina suka sayo suka kaisu gidan Yaya maryam, dama acan yake tara kayan haihuwa, waɗanda ya tara anan kuma kullum idan zata wuce gida saita ɗauki wasu ta tafi dasu, a haka aka fidda kayan daya tara a ɗakin baba.
Ba wani uban kaya na fariyya Ahmad ya danƙara a akwatunanba, amma dai Alhmdllh ya cancanci yabo, dan kuwa ko maƙiyi yaga wannan lefe dolene ya yaba, ga kuma kayan barka na jariri da kayan ƙamshi na al'ada da iyaye mata kan haɗa Ayyah ta haɗasu rankakakaf, sai ɗan akuya gasashshe na al'ada shima na ƙauri da baba yayi.
Mama gaje na tsakar gida su Sakina suka shiga, Samina kuwa tana wanka.,
Suka sauke akwatina a ƙofar mama gaje saboda aima Ammin Rumana irin kawaicin nan, a baɗini kuwa harda son ƙularwa ga mama gaje da Samina.
Aifa nan dangin Ammi dake gidan suka shiga callara ghuɗa.
Su Yaya Maryam dake tayasu suka shiga musu bayani, Sakina tace, “Waɗan nan kayan barkane na al'ada da kowa ya san wajibine yima mai jego idan ta haihu, musamman ma haihuwar fari, waɗannan akwatina kuwa saƙone daga Ahmad, yace a faɗa muku kayan lefene na Umm-Ruman da baiyiba a baya, ga sunan ayi haƙuri dai babu yawa”.
A take waje ya sake kacamewa da sabuwar ghuɗa.
Basu jira mama gaje ta fara buɗewa ba, hakan ne ya saka mama gaje da ƙirjinta ke lugude kamar zai fito yin tsaki, ta fara sakin maganganu akan duk barikin dai da za'ai na banzane, dan ko kama ƙafar lefen Samina dai wannan lefe baiyiba.
Babu wanda yabi takanta, dansu ba yawan bane matsalarsu, albarka suke fata, da bajintar da Ahmad ya nuna ba tare da kowa yayi zaton hakanba.
Tuni gida ya kacame, maƙwaftama sunata shigowa ganin kaya.
Samina data fito wanka ta samu ta raɓa ta shige ɗaki tana haɗiyar zuciya.............✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻.*_39_*
*_ZAFAFA NE_*🤫🥳
..............Umm-Ruman ta rasa da bakin da zatama Ahmad godiya, ta dai samu lokaci ta rubuta tsararren text messege ta tura masa, dan tunda kayan suka shigo gidan bata sake ganin ƙeyarsa ba, ko abune yakeso sai dai ya aiko wani ya amsa.
Wannan lefe na Umm-Ruman ya tsayama mutane da yawa a rai, yayinda wasu kuma ya sakasu farin ciki.
Har gida aka kaima su Maman Ama gulma, da farkoma ƙaryatawa sukai, dan haka suka ƙirƙiri zuwa gidan su Rumana akan sunzo sake gaisheta ne, tunda basa samun zuwa kullum.
Ita dai murmushi kawai tayi, tace musu babu komai, dan taji a ranta dai akwai dalili, amma ba gaisheta ba.
Har sashensu tasa aka rakasu dan kayan suna ɗakin Ammin ta.
Aiko komai sai da aka buɗe musu suka gani, sai sauke tagwayen ajiyar zuciya suke hassada fal ransu.
Su da sukace zasu zauna har yamma a fara rage aikin abincin suna sai suka kasa, suka kwasa zuwa gida acan aka buɗe dandalin gulma da maƙwafta, sai faman kushe kayan suke, Kausar harda faɗin ALLAH yasa Ahmad ba arowa yay ba (Oh ALLAH, ALLAH ka rabamu da ciwon hassada dai to😂).
Ita dai Rumana da batasan sunaiba ma tana can ana mata kitson suna da ƙunshi, wanda suka sake fiddo mata ƙyawun da jego yay mata, gashi ƴar ƙibar datai ta ciki tana nan bata saukaba, hakan yasa tai dumurmur da ita saboda kulawar da take samu ta musamman daga iya da Ayyah, dan gyara suke mata maiban mamaki.
_________________________________
Yau aka wayi gari ranar suna, bayan sallar asuba aka raɗa sunan yaro da yaci sunan baba, wato *HAMZA*.
Kowa nata addu'a wa jinjiri tare da fatan samun rayuwa mai albarka.
A cikin gidama dai sunata hada hadar girki, dan su Yaya Maryam anan suka kwana, to wannan shine karon farko da za'ai sunan jika na ɗa namiji a gidan, tunda sudai duk a gidajensu ake na ƴaƴansu.
Abu ne ya kawo musu sunan yaro, tare da sanar musu alkunyarsa shine *Haysam* kowa nata addu'ar ALLAH ya raya Haysam.
Rumana na daga ɗaki tana karyawa duk tana jiyosu, taci kwalliyarta cikin atanfa data samu zaunannen ɗinki da Mudan yay mata.
Tata zaton Ahmad zai shigo kafin gidan ya cika amma sai taji shiru, sai da rana ta ɗaga ta jiyo maganarsa a tsakar gida zasu fita da raguna biyu na yankan suna.
Kaɗan ta leƙa ta kafar labule, daga shi sai jallabiya ma a jiki, yadaiyi gyaran fuskar data kuma fiddo nutsuwarsa, taɗan sauke ajiyar zuciya tare da komawa ta zauna kawai, batasan wane wasan ɓuya yake da itaba haka? kwana biyunnan.
Da gaske dai wannan suna shiri akai masa na musamman, dan taron da su Rumana basu samuba a biki gashi a taron sunan Haysam an yi musu shi.
Ƴan shema ma da ba'ai zatoba sai ga mata sunzo mota biyu, nanfa gida ya ƙara kacamewa da hayaniya, Umm-Ruman masu jego ansha kyau har an gaji, sai shiga take tana fita cikin ɗunkunan da suka tokare zukatan maƙiya irinsu mama gaje dasu maman Ama.
Bayan sallar zuhur Ahmad ya shigo gidan cikin dakakkiyar shadda fara tas da taji ɗinki na musamman, daka gansa saika ɗauka sabon angone a ranar ɗaurin aurensa, nanfa gida ya ɗauki sowa musamman abokan wasa da su Sakina.
Shi dai murmushi ne nasa kawai.
Umm-Ruman ta fito itama cikin dakakken less dayay mata ƙyau sosai, ga Haysam shima an masa gayunsa tsaf.
Kallo ɗaya Rumana taima Ahmad ta duƙar da kai, shiko ko kunya baiji ya kasa daina kallonta, dan sun masa masifar ƙyau ita da zakin sa.
Yaron ta miƙa masa kamar yanda aka umarceta, dan tare yake da mai hoto.
Ya haɗa da hannunta da yaron ya amsa, sai da ta kallesa sannan ya sakar mata hannu yana murmushi, ita dai batace komaiba ta koma gefensa ta tsaya aka ɗaukesu.
Daga nan dangi sukaita zuwa harma da Gwaggo da Ayyah, su Ammi da matan baba iliyasu, Mama gaje koda aka kirata ƙin zuwa tai, wai ace ta shiga wanka (Mama gajenmu ta mutunci kenan😂).
Samina kuwa dama babu wanda yaga idonta tunda garin ALLAH ya waye.
Har sashen su iya Rumana da Ahmad sukaje akai hoto da malam shima da Iya.
Bayan an gama shan hotuna da ƴan cikin gida Ahmad ya fita da Haysam waje inda zasuyi da abokansa.
Ba kuwa a maido yaronba sai da ya fara kukan neman abincinsa.
Zuwa yamma gida ya kacame sosai da hayaniya, duk da ma ƴan shema sashen Baba iliyasu suka koma.
Kowa dai a wannan suna sai dai yace Alhmdllh, sai ko maƙiya irinsu maman Ama daketa kushe akan Rumana sai ɗaga kai take wai🤣.
Hidima ta ishi baiwar ALLAH bazasu barta taji da kantaba, duk da kuwa tayi iya bakin ƙoƙarinta dan ganin an karramasu yanda ya kamata suda matan anguwarsu da sukaje tare, amma hakan bai hanasu ƙananun magana ba, gashi ita maman Ama ma na fama da ciki tirtsai-tirtsai.
Cikin amincin ALLAH dai taro ya tashi lafiya yanda maƙiya basu soba, komai kuma anyisa a wadace daidai ƙarfinsu babu fariyya ko nuna su masu shine.
Da ƙyar Rumana ta samu ta watsa ruwa saboda gajiya da barcin dake cin idanunta.
Tanaji Haysam na ƙananun kuka amma ta sharesa tai kwanciyarta.
Inna baraka ta shema ce da suke tattare kwankan da aka bazar a tsakar gidan, ta leƙo tanama Rumana magana akan tanajin kukan Haysam kuwa?.
Cikin kunbura fuska Rumana tace, “Inna ki barsa idan ya gaji yayi shiru, shi baisan mutum ya gajiba ne? Babu abinda ya tara sai cin tsiya yaron nan yasin”.
“Kinci gidanku Rumana, maza tashi ki basa nono, kajimin ƴar ƙwal uba kai, daga sanda kuma ka haihu ai barci ya ƙare maka isashshe, sai dai haƙuri da abinda ya samu.
Kamar Rumana zatai kuka haka ta tashi ta ɗauki Haysam, aiko harda dungure masa kai kafin ta bashi.
Shi dai baisan tanaiba, yana samu ya cafke kayansa daman kukan yunwane.
Dai-dai nan, Ahmad ya shigo ɗakin da sallamarsa, Rumana taja witsiyar gyalen jallabiyar dake kanta ta rufe Haysam dan kar Ahmad yaga jikinta, sannan ta amsa sallamarsa.
Shikam tsaye yay kawai yana kallonsu, a duk sanda ya ganta manne da yaron yakanji farinciki ya sake girmama a zuciyarsa, dan ba ƙaramin ƙyau suke masa ba.........
“Yaya ina yini”.
Rumana ta katse masa tunaninsa, ƙaramar ajiyar zuciya ya sauke tare da cigaba da takowa inda suke, ya zauna a bakin gadon ƙafafunsa a ƙasa, saɓanin ita da take a gadon baki ɗaya.
Yanda ya zauna kusa da ita sosai har jikinsu na gogar juna sai taketa addu'ar ALLAH yasa kar Ayyah ta shigo ta gansu, dan faɗa take mata.....
Gyalen da ya janyene ya dawo da ita hayyacinta, tai saurin riƙewa zata maida ya harareta,
“Malama mikike ɓoyewa to?”.
Fuska ta kumbura masa kaɗa sai dai ta kasa kallonsa.
Yasa hannu ya ɗago haɓarta suka kalli juna, sai wani narke idanu yake kamar wanda ke a maye, “Miye za'a ɓoyemin wanda ban sanshi ba anan Gwal ɗina?”.
Yanda yay magana a hankali cikin tsananin sanyin murya ya saka Rumana lumshe idanunta tausayinsa na tsargata, dan ta tabbata yana a yanayin buƙata......
Saukar sumbatar da yay mata a kumatu ce ta sakata buɗe idunta, fuskarsu gab da juna suna musayar shaƙar numfashin juna, taso matsawa amma sai ya hanata damar hakan.
Yace, “Mizan samu babie R?”.
Cikin son kauda abinda ta hango a idanunsa tace, “Yunwa kakeji Yayana?”.
Kansa ya ɗaga mata yana wani luuu da idanu, yace, “Sosai ma”.
Ta gyara Haysam dake ta shan mamansa baisan iyayensa sun sashi tsakkiya suna ƙonewa ba😂🤭.
“Bara to na haɗa maka tea, kokuma na shiga cikin gida idan za'a samu abinci”.
Janye fuskarsa yay yana ɓata fuska, “Ni ba wannan abincin ba”.
Rumana ta danne dariyarta da ƙyar tace, “To wanne?”.
Kallonsa ya maido gareta ya kafeta da idanu, kafin ya janye ya maida kan Haysam.
Lura tai ba Haysam ɗin yake kalloba, dan haka ta janye yaron ta gyara rigarta.
Ahmad ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya yana faɗin, “Bara nazo nabar garin nan da gaggawa kafin ta kife dani wlhy”.
Yanda yay maganar cikin tsagwaron damuwa yasa Rumana kasa daurewa sai da tai dariya.
Ya kai mata cafka sai tai saurin ɗora masa Haysam a cinya tana ja baya.
Ƙwafa yay kawai ya maida kallonsa ga yaronsa dake ƙyalla ƴan idanu saboda hasken fitilar dake ɗakin.
Sallamar Ayyah ta sakasu kallonta su duka.
Tace, “A'a, ɗan albarka wai dama kana nan?”.
A kasalance yace, “Wlhy kuwa Ayyah, wajenki mafa nazo sai na iske baƙya ɗakin”.
Rumana tai saurin kallonsa, sai kuma ta janye idanunta tana haɗiye dariyarta da ƙyar, dan ko rantsuwa tayi babu kaffara Ahmad ya canja zancen ne kawai dan kar Ayyah tai faɗa.
Ayyah kanta tasan ba haka bane, amma sai tace, “To gani ɗan albarka a shafamini bayani”.
Dariya kawai yaɗanyi. itama Ayyah haka, Rumana dai saima ta ɗauki buta ta fita bayan ta saka hijjab.
Koda ta dawo ta iske Ayyah nama Haysam shirin barci. Ahmad kuwa yana faɗa mata alkairan da mutane sukai masa, sai godiya take da faɗin Haysam yayi goshi.
Rumana dai ta haye gado tai kwanciyarta dama barci takeji, dan haka batasan sanda Ahmad yabar gidanba.
*_Washe gari_*
Washe gari baƙi kowa ya kama gabansa, aka bar su Umm-Ruman masu jego da kewa, inda ita kuma tasha barcin gajiya.
Suna da kwana uku Ahmad ma ya tattara ya koma wajen aikinsa, wannan tafiyar ma dai Rumana sai da taɗan matse hawaye, su Fa'iza kuwa suka tasata da dariyar mugunta da tsokana.
Ta cigaba da samun cikakken wankan jego mai ƙyau da kulawa ta musamman hannun iyayen nata.
Ya yinda a koda yaushe take maƙale da waya suna soyewarsu itada Zumanta.
Tayi ƙyau sosai hakama Haysam yayi ɓul-ɓul abunsa saboda nonon Rumana nada ƙyau Alhmdllh.
Suna cikin sati uku dayin suna Ma'aruff ɗin Samina yazo, dan kuwa Inna mari ce tasa aka yomata farautarsa ganin zai sakasu jin kunya, da ƙyar ta samu yaje can gidan, taita roƙonsa akan yayi haƙuri Samina ta koma kar suji kunya hannanun maƙiyansu.
Babu kunya yayta yanka mata magana, daga ƙarshe dai ya amince da ƙyar.
To shinefa yau yazo bayan kusan kwana huɗu da kiran inna mari.
Ƙiri-ƙiri yaƙi bama su baba haƙuri, saima ƙarya da yayta narka musu akan Samina na masa abubuwa, aiko suka kirata a gabansa akai mata faɗa sosai sannan ya ɗauketa suka tafi.
Tunda suka tafi bai mata maganaba, duk yanda taso takalarsa da maganar kuma ya hanata kowacce ƙofa, dan yayi kicin-kicin da fuska tamkar an aiko masa mutuwarsa.
A ƙofar gate ya tsaya yace ta fita shi yanada inda zaije.
Jiki a saɓule ta fita, shiko yaja mota yana mata tsaki.
Gidan yayi futu-futu da ƙura alamat baya zama cikinsa, haka ta daure ta hau gyarawa, har dare tana wannan tiƙar aiki, sai da gidan ya dawo hayyacinsa ta samu nutsuwa, sai dai kuma harta kwanta a gajiye babu alamar Ma'aruff.
Da safe ta zuba idon ganinsa amma shiru kakeji wai malam yaci shirwa.
Wasa-wasa dai sai da Ma'aruff ya kwashe kwanaki takwas kafin ta sakashi a idonta, shima da daddare yazo mata a buge, tana masa magana ya maketa yabi ya taushe, sai da yay mata biji-biji a wajen sannan ya barta tana cin kuka.
Safiya nayi kuma ya sake barin gidan, sai bayan kwana uku ta sake ganinsa.
Yau dai cikin hankalinsa ya shigo mata, tana zaune a falo tana yankan farce.
Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta, shima cikin taɓe baki ya wurga mata ƙaramar ledar hannunsa ya wuce ɗakinsa.
Sai da ya shige ta ɗauki ledar ta duba, invitation ne guda kusan ashirin a ciki, ta ciro ɗaya tana dubawa.
“Ƙundugurun buhun ubannan kayyasa” Samina ta faɗa a matuƙar firgice, ganin invitation ɗin auren Ma'aruff ne da wata ɗiyar ƙanin babansa.
Jifa tai da ledar ta nufi ɗakinsa, yana kwance a kan gado ta faɗo masa tare da buga ƙofa da ƙarfi.
“K mahaukaciyar wane ƙauyece zaki shigomin ɗaki a haka?”.
“Matsalarka ce wannan Ma'aruff, wannan katin miyake nufi?”.
Tsaki yayi ya maida kansa ya kwantar yana faɗin, “Kinci kuɗin tara a banza ne da baki fahimci abinda ke cikiba?, to katine na ɗaurin aurena nanda kwanaki baƙwai kacal, na samu tsaleliyar yarinya dai-daini mai tarbiya kuma”.
“Wlhy baka isaba Ma'aruff, kuma da kake faɗin mai tarbiya nima ɗin da abuta ka ganni, kaine ka gurɓatamin ita da taka rashin tarbiyyar macuci azzalumi kawai, ɗan giya bunsuru”.
Wata dariyar ƙularwa yay mata ya koma ya gyara kwanciyarsa yana faɗin, “Bani da lokacinki yanzu nikam, karyar titi”.
Cigaba tai da gaggasa masa magana har takaisa da sheƙa mata maruka biyu ya fice ya bar mata gidan.
Tashin hankali na gaske Samina ta shiga ranar, tayi kuka tamkar ranta zai fita, ta kira mama gaje ta zayyane nata komai dake faruwa, itama hankalinta ya tashi sosai, suda suke shirin shawo hankalin matsalar Saminar ta samu zaman lafiya shine yanzu kuma Ma'aruff ɗin ya ɓaro musu wani aikin, gashi Baba ya hanata fita a gidan.
Duk wanda yasan mama gaje yasan a tsakanin nan tana cikin matsanancin tashin hankali, sai bushewa take a tsaye kamar kilishi.
Kwana biyu da wannan abu saiga ƴan jere, ɗayan sashen dake gidan sukaima amarya jerenta na girma, dama can shine ainahin sashen matar da zata zauna a gidan, inda Samina take Ma'aruff yayisa ne kawai saboda baƙi ko wata sabga idan ta tashi mutane su sauka anan.
Tasha masa tambaya akan wancan sashen amma yana ce mata aikine bai gamaba sai ya gama zata koma, ashe yasan tsiyar daya shirya mata.
Shi kansa an tsara masa ɓangarensa dake cikin wancan sashen tsaf.
Dangin Ma'aruff sukaita yankama Samina baƙar magana, tunda dama aurene na zuminci, ranar sai kulle sashenta tayi, dukta susuce tayi firingai-firingai da ita...........✍🏻
*_Muna barar addu'arku ga miss xoxo ALLAH ya bata lafiya😢🙏_*
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_40_*
*_GDW_*
...........Haka aka shiga hidimar biki ba'a sakata cikin kowacce sabga, to ganin angonma yafi komai mata wahala a gidan, dan tun randa ya kawo mata invitations ɗinnan bata sake ganin ƙeyarsa ba.
A danginta kuwa babu wanda yaje mata kara, dan mama gaje sun rufe sunƙi sanarma kowa za'aima Samina kishiya, sai a shanun ƴan talla jama'a ke jiyo labarai suna kawoma ƴan gidan gulma.
Yanda bata faɗaba babu wanda yay yunƙurin zuwa balle ya nuna mata yasan ma halin da ake ciki.
Ansha hidima ta alfarma, dan yanzune kam a kaima Ma'aruff auren gata kamar yanda danginsa suke faɗa, ranar asabar bayan kammala gagarumar dinner ɗin da har gidan tv suka nuna aka kawo amarya ɗakinta.
A lokacin Samina tana cikin wani hali, dan kuwa duk taga wannan shagali a tv, yanda Ma'aruff yake rawar ƙafa da washe baki, da yanda danginsa ke ɓarin dukiya kamar ba wahala sukai suka taraba ba'ai koda kwatankwacinsa a nata bikinba, hakanne ya sakata zaman dirshen a kafet tasha kukanta..
Duk yawan ƙawayen data tara babu wanda ya tuna inda take balle yazo, hatta dasu Nafy bata ganiba balle sababbin datai na yanzun.
Har ƴan kawo amarya suka kammala ghuɗe-ghuɗensu da arerewarsu Samina na zaune a wajen ta zuba uban tagumi abin tausayi.
Kafin wani lokaci gidan ya koma yay tsit, tun tana tsammanin shigowar Ma'aruff harma ta fidda rai, dan yanayin shirun da garin yayi sai haushin karnuka ya tabbatar mata dare ya tsala, sai tunaninta ya fara bata ƙilama Ma'aruff ɗin yanacan make cikin giya baizo gidanba.
Lallai tunanin Samina yazo da ruɗani a gareta, ya kuma karanta mata ba dai-daiba, dan kuwa dai yau ango Ma'aruff ko lemon bai damu da shaba balle akai ga giya, yana manne da amaryarsa da sukasha soyayyarsu, duk da dai daga ƙarshe abin yazo masa da ruɗani, dan kuwa dai amarya a fafake take ba budurwa bace, wani ya ɗana.
Ance wanzami baya son jarfa, hakan yasaka hankalin Ma'aruff tashi matuƙa, ya hauta da bala'i ta taka masa birki nan take, dan ta tabbatar masa bazata ɗauki haukarsa ba, harda tambayarsa wai shi dama budurcinta ne matsalarsa?.
Wannan tambaya ta ƙonama Ma'aruff rai, sai dai ya gaza cewa uffan saboda wani shegen tsoron Mufida yaji ya mamayesa.
“Aiki ga mai ƙareka”😂⛹♀
___________________________________
Su Umm-Ruman masu jego kam an kammala wanka, tayi dumurmur da ita kamar ka sace ta ka gudu, hakama Haysam abin sha'awa, ga ƙyawun yaro da yay gado uwa da uba nata fitowa, dama iyayen kamarsu ɗaya, hakan yasa bama a iya banbance dawa yake kama a cikinsu, wasuma sukance ya ɗara iyayen ƙyau.
Ita kanta Rumana takan zauna taita kallonsa idan babu kowa kusa, a ranta tana ƙiyasta yanzufa wannan mallakinsune ita da Yayanta.
Hakan na saka zuciyarta farin ciki sosai, shi kansa Ahmad idan ya kira labarinsa mafi yawa nakan Haysam, wataran Rumana har nuna kishinta take a fili, shiko yayta mata dariya, hotunan Haysam kam ai kullum sai an masa an tura masa, idan ita batayiba ma Mudan zaiyi ko Abu da aka sayi waya shima ya shigo gari da ƴar mai shan jininsa😂.
Umm-Ruman ta fara ƙoƙarin zagaya dangi ziyara, wanda da farko da Ahmad yaso kawo tirjiya Ayyah ta taka masa birki akan dolema yasama ransa haƙuri tunda haka al'adar take, sannan tunda Rumana tai aure ina yake barinta zuwa? Tanada dangin mahaifiya a gari suma kuma ai suna buƙatarta, ga dangin gwaggo suma ya kamata ta ringa shiga.
Dole yay shiru yabi umarni kam, aiko saiga su Rumana har shema ita dasu fa'iza, kwannansu huɗu suka dawo da tarin alkairi, dan ƴan Shema sunji daɗin wannan ziyara sosai.
Cikin ƴaƴan ƴan uwa kuwa wani ya maƙalema Fa'iza, kuma da gaske yake babu ƙarya, itama dai Fa'izan ta amsa, dan yay mata, sai dai fargabarta batason zama Shema kamar yanda ta sanarma su Rumana.
Sun bata shawarar addu'a kawai da neman zaɓin ALLAH, dan yafi kowa sanin abinda ya tsara.
Da zaman wankan Rumana, da ziyarce-ziyarcenta kusan watanni biyu da wasu ƴan kwanaki da tafiyar Ahmad.
Dan haka ya fara shirin zuwa gida, sai dai a wannan karon yasha banban da zuwan baya, dan kuwa zaizone domin ɗauke matarsa da ɗansa su koma kusa dashi kamar yanda iyayensu sukai masa alƙawari.
Ranar juma'a kwatsam babu zato sai gashi, kowa yayi murnar ganinsa kuwa, musamman yara da sukasan zasuci tsaraba kamar yanda ya saba kawo musu.
Ita dai Rumana duk wannan bikin murnar dawowar Ahmad da ake tana sashensu tanaji amma bata zoba, yaga dai Haysam dake goye a bayan Zainab yana barci.
Bayan yasha ruwa ya miƙe kamar yanda ya saba domin gaida matan gidan dasu iya.
Sashensu Iya ya fara shiga, ya gaisa da kakanninsa daketa tsokanarsa da cewar angon zumuɗi.
Shi dai dariya kawai yakeyi, dan kuwa dai sun gama ranfosa.
Koda ya fito sai ya shiga Sashen baba iliyasu, nanma ya gaisa da matansa sannan ya nufi sashen su Umm-Ruman, dan tunda bai gantaba asashensu yasan tana nan.
Sai dai anan ɗinma bai gantanba harya gama gaisawa da Ammi, ita mama gaje ma bata gidan.
Duk kuma Rumana na jinsu, dan tana ɗakin baba tana masa shara, hakan yasa taita leƙen Ahmad ta window ba tare daya saniba.
Shima dai haka kawai zuciyarsa da idanunsa suka karkata ga ɗakin baban, sai yakeji kamar akwai abunsa mai muhimmanci a cikin ɗakin.
Yana fita kuwa Ammi ta ƙwalamata kira.
Fitowa Rumana tai da sharar data kwashe tana amsawa.
“Ammi gani”
“Na ganki ai, k bakiji mijinki ya dawo bane?”.
Shiru Rumana tai bata iya cewa komaiba, ta dai duƙar da kai ƙasa, itama Ammin bata sake ce mata komaiba tama ɗauke kanta daga gareta baki ɗaya.
Sai da ta kammala abinda takeyi sannan ta nufi sashen su Ahmad ɗin a kunyace, dan Ammi sai antaya mata harara takeyi.
Tunda tai sallama Ahmad dake zaune riƙe da Haysam daya tashi barci ya zuba mata idanu, itako taƙi kallon sashensa.
Ayyah tace, “Ɗiyata aida yanzu zanje biko, dan ko abinci na hana mijinki nikam sai kinzo”.
Murmushi Rumana tayi, aɗan in ina tace, “Shara naima Baba Ayyah”.
Ɗauke kai Ahmad yay daga kallonta ya maida ga Haysam, ji yake kamar ya haɗiye ɗan yaronsa, a ƙasan ransa kuwa yana tuno yanda yaji akan ɗakin baba, ashe kuwa tana ciki.
Duk wannan hidima da akeyi Gwaggo na ɗakinta, tunda suka gaisa da Ahmad tai shigewarta ɗakinta.
Umm-Rumana ta taka inda yake, kujerar dake gefensa kaɗan taja ta zauna, “Sannu da zuwa Yaya, ina yini?”.
“Sai yanzu aka san dani?”.
Yay maganar yana wasa da hannun Haysam.
Ita dai tunda tasan tayi laifi sai tace yayi haƙuri kawai, ta miƙe ta amso abincin da Ayyah ke kiranta ta ɗauka masa takai ɗaki.
Sai da ta shiga da kusan mintuna uku sannan ya shiga ɗauke da ɗansa.
Tana ƙoƙarin zuba masa ya shigo, hakan yasa bata fasaba bakuma ta kallesu ba shida ɗan nasa.
Shiko ya kasa ɗauke idonsa a kanta, dan ƙyawun data ƙara da ƴar ƙibar datai mata ƙyau sunyi mugun tsole masa idanu.
Gabansa ta tura komai sannan ta ɗago ta kallesa, irin kallon da yake binta da shi na ƙurulla ya sakata jin kunya, tai murmushi tana ɗauke nata idon, “Yaya wai kallon fa?”.
Ajiyar zuciya ya sauke kaɗan yana janye idonsa da salon lumshewa.
Bai iya cewa komaiba, sai cokali daya ɗauka zai fara cin abincin.
Katsesa tai da faɗin, “Kawoshi to yanda zakaji daɗin cin abincin”.
Bai musaba ya buɗe hannayensa alamar ta ɗauki Haysam ɗin dake kan cinyarsa, sai faman watsal-watsal yake da ƙafafu na lafiya da ALLAH ya bashi.
Tasowa tai ta duƙo domin ɗaukarsa, hakan ya basu kusanci sosai ita dashi, dan har suna iya jin saukar numfashin juna, kowa na shaƙar daddaɗan ƙamshin jikin ɗan uwansa, gashi yanda wuyan rigar yake daɗan girma ya samawa idon Ahmad abinci.
Ita dai tsigar jikinta na tashi ta ɗauki Haysam a kasalance ta matsa baya.
Ajiyar zuciya Ahmad ya sauke ya fara cin abincinsa.
Kamar jira Haysam keyi ta ɗaukesa ya fara ƙananun kuka, banza tai masa, a ranta tana fadin, “Kujimin yaro da neman dalili?”.
Ahmad ya ɗago ido ya kalleta da mamaki, ga yaro na kuka amma tayi biris, kafin yay magana Ayyah dake waje tace, “Waishi wannan alhajin baza'aji da shi bane Rumana? Kema kinsan yunwa yakeji tunda barci ya tashi dama”.
Rumana tace, “Ayyah rigimace fa kawai, gashi nan zan bashi ruwa”.
Ayyah tace, “Ruwan ƙaniya, ki bashi nono kafin nazo kanki”.
Rumana ta dingure kan Haysam sannan taja hijjab ta saka wai batason Ahmad ya ganta, a haka ta fara Shayar dashi, shiko yaro kamar yasan za'aima ubansa buƙulu yaƙi amsa saboda zufar dole da aka ƙirƙirar masa.
Cikin haushi ta cire hijjab ɗin tana faɗin, “Kai wai ba a sirri da kai dan maigarin garinku?”.
Murmushi kawai Ahmad yayi yana ɗauke idonsa daga kallonsu.
“Yaga za'a cuci masa Abbansa a hanashi ganin halalinsa ba dole yay boreba” Ahmad yay maganar ba tare da ya kalli Rumana ba.
Baki ta kumbura, amma bata tankaba, sai harar Haysam takeyi kamar yasan tanayi😝.
Shidai Ahmad ya samu tv, yanacin abincinsa yana kallo.
Rumana dai kasa jure wannan kallo tai, ta samu da Haysam yaɗan sha ta ciresa tana gyara rigarta, dai-dai lokacin Mudan ya shigo ɗakin bayan yayi sallama sun amsa Ahmad ya bashi izinin shigowa.
“Ashe da gaske yaran nan suke kaiɗinne dai?”.
Murmushi Ahmad dake Kallon Mudan yayi, yana ƙaunar ƙanin nasa sosai, hakama Rumana dake ƙoƙarin miƙewa ta basu waje.
Mudan ya amshi Haysam daga hannunta yana gaishe da Yayansa, ita kuma ta fice a binta.
Bata sake shiyowa ɗakinba. suko sunata hira abinsu, sai da aka kira sallar magriba Ahmad yabar gidan zuwa can gidansu, dan tun shigowarsa su Fa'iza suka tafi gyarawa.
Maman Amatullah kawai ya iske a tsakar gida tana shara, sai maman Aysha data shigo suke ƴar gulmarsu, kuma kamar an saita sunayi da Rumana ne akan wai taƙi dawowa.
Sai su Ahmad dake wasan ruwa a bakin rijiya shi da Amatullah.
A bazata sukaji sallamar Ahmad, wanda sarai yaji kalmar maman Aysha ta ƙarshe saboda bata magana a hankali ita dama.
Duk sai suka daburce wajen gaishesa da masa sannu da zuwa, shi dai ya amsa kawai ba tare da ko kallonsu yayi ba, Mudan yasa makulli ya buɗe masa ƙofar suka shiga.
Ko zama Mudan baiyiba ya fito yabar Ahmad.
A zuciyar Ahmad godiya yakema UBANGIJI da ya tsame matarsa ga wannan muguwar al'adar, shi sam bata birgesa tun ma yana yaro, sai kuma ALLAH ya soshi Ayyah da Gwaggo babu ruwansu da irin wannan tsogume-tsogumen ma.
Ya fito wanka yana alwala Kausar ta shigo itama, ashe gidan sunan ƙawarta taje, gaisawa sukai tana binsa da kallo.
Shi dai da baisan tanaiba ma tuni ya miƙe ya saka butar ɗaki ya fice abinsa.
Aiko kamar jira take ta nufi kicin inda maman Ama ke girki.
“Maman Ahmad wannan matar kuwa zata dawo? Ƙiri da muzu ta maida miji gwauron ƙarfi da yaji”.
Maman Ama ta fito tana taɓe baki, “Wlhy maman Siyama yanzu muma muka gam ni da maman Aysha, yanzu dai ai zamusha kallo, tunda ta gama wanka ga kuma miji ya dawo maji ma gani”.
Baki Kausar ta taɓe tana ƙoƙarin sauke Siyama dake goye a baya ta tashi barci, taja kujera ta zauna alamar koma ɗakin bazata shigaba balle tunanin yin salla.
Nanko suka sake buɗe babin gulmar Rumana da batasan sunaiba.
___________________________________
Ɓangaren Samina sam abubuwa babu sauƙi, komai sake rikice mata yakeyi, dan yanzu idan har kikaga Ma'aruff a sashenta to tabbas Mufida bata gida ne kokuma sunyi faɗa, ko yazo mata a buge ta korosa, dan tace bazai taɓa zama mata a sashe yan warin giya ba, bai dametaba yaje yay ta sha shiya sani, amma babu maganar raɓarta.
Tofa shine sai kiga ya taho wajen wadda ya raina Samina, ita kuma da bakinta bai iya mutuwa saboda azabar tsiwa da yace kule zatace cas, kafin kace mi sunyi sama, yako bubbugeta babu abinda yasha kansa.
Ya saka mai gadi ya hana kowa zuwa wajenta saboda zugar Mufida, ashe lokacin bikima shine yasa aka hana ƙawayenta shigowa gidan, sai da ta kira Nafy tana mata tsogumi shine ta sanar da ita komai daya faru, ran Samina ya ɓaci suka haura sama da Ma'aruff, ranarma sunci uban faɗa a gidan Mufida nata kwasar dariya.
Dolene duk wanda yasan Samina ya ganta a tsakanin nan ya tausaya mata, tayi figi-figi da ita kamar wadda aka ƙwato daga bakin kura, gashi saboda man bilicin ɗin data daina shafawa saboda ƙarewar nata ƙuraje sun mata futu-futu da fuska, nan yayi baƙi nan yayi ja, fuskar tai wata iri kamar wadda ta tashi daga jiyyar ƙuna.
Duk ɓarin kuɗin da yake mata da yanzu ya daina, sai abinda mufida tace akeyi a gidan.
Da kuka na maganin damuwa da tuni Samina yayi mata, sunan Ahmad kuwa ai babu fashi a rana saita ambata sama da sau goma, abu kaɗan Ma'aruff yay mata saitace da Yaa Ahmad ne da ba hakaba.
Ga rashin mutuncin dangi miji, sosai surukarta ke nuna fifiko tsakaninta da Mufida.
__________________________________
A randa Ahmad yazo a ranar yayma iyayensa tuni akan maganar abinda ya kawosa nason tafiya da iyalansa, dan yace kwana uku zaiyi kacal ma su juya.
Babu wanda yay musu a cikinsu, tunda dama kowa yasan da zancen, dan haka shiri kawai suka somayi.
Sai kuma Rumana duk ta shiga damuwa, ta roƙesa dan ALLAH su tafi da Zainab tunda ta gama firamare ɗinta, idan sukaje can sai a sata sakandire.
Da farko dai yay shiru kamar bazai amince ba, amma da yaga tana kuka sai yace zai tun tuɓi su baba idan sun amince, idan sunce a'a tofa sai dai tayi haƙuri, tunda da dai ga Haysam nan ya ishe ɗauke kewa.
Ita dai tata addu'ar ALLAH yasa a dace, da dare ya samu baba da maganar bayan ya fara sanarma Ayyah dama.
Baba yaso tirjewa, hakama gwaggo, amma da Ayyah ta saka baki sai suka amince, koda suka sanarma malam da iya fatan alkairi sukayi, iya tace dama tanada niyyar magana akan abama su Rumana wata a yaran gidan.
Ana gobe zasu tafi Rumana taje can gidansu, su mama Ama na soro zaune suna hira da makwafta, mamakin ganinta ya kamasu, dan a zatonsu kota dawone, har wata maman Salim na faɗin, “Maman Haysam masu jego na dawowar dare ke ta rana kike?”
Murmushi tayi amma bata bata amsaba sai da ta zauna, suka amshi Haysam dake bayan ƙanwarta khadija suna yaba ƙyawun da yaron ya ƙara.
Sai da ta gaisa da kowa kafin tace, “Ba dawowa naiba, munzo muku sallamane dan da sassafe zamu wuce”.
Cikin mamaki duk suk kalleta, maman Ama ta ɗora da tambayar “Yo ina kuma zakuje amarya?”.
Kafin Rumana ta bada amsa khadija ta amshe da faɗin, “Porthercout zasu tafi ita da yayanmu”.
Kallon kallo aka koma. Kausar tace, “Yawon shaƙatawa za'a kenan Amarya?”.
Nanma Khadija dai ta bata amsa da faɗin, “A'a zasu koma can dai da zama sai dai suzo mana yawo”.
Tsitt soron yayi, sai maman Aysha ce cikin yaƙe ta katse shirun, “A to lallai su marya gara wasai, kice guduwa za'ai kudu a barmu, su Haysam ashe ƴan kudanci za'a koma”.
A yanda take maganar kawai ya isa tabbatarma da mutum bada daɗin rai takeyiba.
Su kuma sauran sai famar yaƙe sukeyi, ita dai Rumana miƙewa tai ta nufi ɗakinta, shigarta babu jimawa sai ga Ahmad shima ya shigo.
Ya wuto su maman Ama Haysam na wajensu.
Rumana ta amsa masa sallama tana cigaba da abinda takeyi, shima amsawa yay yana zama a bakin gadon idonsa a kanta, daure zuciyarsa kawai yake harsu tafi ba tare daya nema ruwan dazai kashe ƙishinsa daga gareta ba.
Itama ta lura da hakan, shiyyasa taketa addu'a da fatan harsu wuce kar yace yana buƙatarta, dan ita dai bazata sake maimaita abin kunyar da sukai a ranar da naƙudar Haysam ta dole tazo mataba.
Tana kimtse-kimtsenta yana binta da kallo, hakan yasa ta ƙwalama khadija kira, sarai Ahmad ya fahimci dalilin kiran khadijan, hakan yasa ya cije baki a ransa yana faɗin duk wayon amarya dai sai ansha manta, kuma zaki gane baki da wayo yarinya.
Ita dai batasan yanaiba, ta gama komai yanda ya dace dan yace dagasu sai kayan sawa zasu tafi, sai ɗan abinda ba'a rasaba da Rumana ta ɗauka.
Gab da magriba suka bar gidan tana jaddadama su Kausar kalmar a yafi juna.
A fili dai sunce suma a yafe, amma ƙasan zukatansu tamkar zasu kama da wuta haka sukeji, sunajin baƙar hassada akan wannan tafiya ta Umm-Rumana, ita kanta ta fahimci yaƙe kawai suke mata da dariyar gatsatsa wadda tafi kuka ciwo. Duk da ita sai takejin wani iri babu daɗi saboda sabo............✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻[8/21, 12:41 PM] Nadady: *_41_*
.............Washe gari suna idar da sallar asuba motarsu ta tashi, Rumana sai share hawaye takeyi, Zainab kam ko a kwalar rigarta murna taketayi, su kaɗaine a motar dan shata Ahmad ya ɗauka duk da kuɗin daya kashe hakan yafi musu sauƙi, dagasu sai kayansu, direba da Ahmad a gaba, zainab da Rumana da Haysam a baya.
Kuka sosai Rumana takeyi haka ƴan uwanta, duk dauriyar Ammi sai da tayi hawaye itama, tunda motar ta wuce gidan sai ya koma tsit, kowa yanajin kewarsu a ransa, dan Ahmad ya zama wani jigo abin alfaharinsu.
Mama gaje kuwa babu abinda kecin ranta sai baƙin ciki, ko fitowa ba taiba lokacin da kowa ya fito ƙofar gida har iya domin ganin tafiyarsu.
Babu wanda ya damu da lamarinta, sukabi yaransu da addu'ar fatan alkairi sudai.
Sunyi tafiya mai nisa Rumana tana kuka, yayinda Zainab barci yay gaba da ita, dama Haysam tunda suka taho shi barcinsa yakeyi.
Ahmad da direba ma ba wata hira sukeba, saboda hankalin Ahmad naga Rumana, itama dai barcinne ya saceta.
Ajiyar zuciya a Ahmad yayi kaɗan, yana maijin tausayinta na tsigota da yay daga cikin dangi, bashi da wata mafita bayan wannan, duk da kasancewarsa ƙaramin ma'aikaci yanada ƙyau ya maida hankalinsa ga aikinsa tuƙuru, gashi karatu yakeson komawa, zai sake zama busy sosai, kuma koba komai yana buƙatar jinta a kusa dashi, itama karatun ya keso ta koma kafin yara su fara mata nauyi.
Da ga Rumana har Zainab sun jigatu da wannan doguwar tafiya da basu taɓa riskaba a rayuwarsu, Haysam kam kuka yayta tsilalawa, musamman da lokacin da aka saba masa wankan yamma yayi, sosai ya rikice, Ahmad dai shi yayta taimaka mata, dan a gajiye take, ga kuma ruɗatan da Haysam yayi, dan bai taɓa mata makamancin kukan nanba da suna gida, yayi kukan dare kam sosai amma da yake Ayyah ce ke kwana dashi ita dai nata kallone, wani lokacinma sai yayi kusan rabin kukan take farkawa.
Iya galabaita dai kam sun galabaitu da wannan tafiya, dan ko abincin da sukan tsaya ci ita da zainab basa wani iya ci, Zainab amanta biyu ma ita.
Wannan yanayinne yasa Rumana bazasu iya ƙarar da komai da suka gani a hanyaba, ALLAH dai ya saukesu lafiya gabannin asubahi.
Gidane ƙarami da aka bama su Ahmad ɗin ƙananun ma'aikata su zauna, falone sai ɗakuna biyu a falon, babba guda ɗaya da kuma ƙarami da baikai girmaba, sai ko kicin da sito shima ɗan fit, kowanne ɗaki da bayinsa a ciki.
Ginin gwamnati ba ginine na mugunta ba, komai akanyisa da inganci, dan haka dolene gidan ya burge mutum, duk da dai kamar a kwatas suke, babu wata hayaniya kamarma babu mutane a wajen.
Ita dai Rumana ma bata kallon abubuwa takeba, burinta ta samu ta zauna ta huta, hakama Zainab data maƙale jikin Ahmad saboda rashin ƙwarin jiki, gashi ɗauke da Haysam a kafaɗa barcin wahala ya sacesa.
Nuni yay musu da su shiga ciki bayan ya buɗe ƙofar da key ɗin daya ciro a aljihu, har sannan Zainab na jingine dashi, Rumana tai gaba shikuma ya shigo da yaran, yayinda direban keta ƙoƙarin sauke musu kayansu.
Ɗan gidan ya sake birge Rumana, daɗinma da taji sune a can ciki jikin katanga.
Babu komai a falon sai wani kafet da aka shinfiɗa daga gefe akan tayis ɗin, dan haka suka zauna anan, zainab ma kwanciya tayi, Ahmad ya ɗorama Rumana Haysam a jiki ya fita domin shigo da kayan.
Sai da suka gama shigo dasu tas sannan ya fice domin yo salla tunda da massalaci a wajen.
Yacema su Rumana ma suje suyi sallar.
Da ƙyar ta lallaɓa Haysam ya kwanta ta miƙe, ɗakin daya nuna mata ta shiga, tabi ɗakin da kallo saboda akwai nefa, katifa ce kawai a ciki sai tarkacensa na kaya da abinda ba'a rasaba, sai ƙamshi ke tashi kuwa mai daɗi.
Ta nufi ƙofar da take ƙyautata zaton bayine, ilai kuwa shine, alwala tayo dan akwai fanfo, ta dawo ɗaƙin bayan taje falo ta ɗakko akwati ɗaya ta canja zani saboda ƙyanƙyamin na jikinta da takeyi.
Harta idar da sallar Ahmad bai shigoba, sai bayan kusan mintuna talatin garima ya fara haske sannan sai gashi da sallama.
Tunda yaga bata a falo sai ya nufo ɗakin, Rumana na ƙoƙarin cire hijjab ya shigo.
Kusan a tare suka haɗa baki wajen yima juna sannu, Ahmad ya nufi bayin yana faɗin, “Wanka ya kamata ki musu kema kiyi saina samo abin kari ku kwanta ku huta, dan na kula duk bakwa hayyacinku”.
Da “To” ta amsa umarninsa, ya saka musu hita a ruwa sannan ya fita zuwa kicin, dan yanada ƴan kayan abincinsa da yakan dafa wani lokacin.
Ƙamshin ƙwai kawai Rumana take jiyowa, amma sai bata leƙaba tazo ta tada Zainab da tai barci, da taimakonta zainab ɗin tai wanka, ta cire mata kaya a kayan sawarta sannan ta ɗauki Haysam shima tana cire masa.
Dai-dai nan Ahmad ya shigo da tire ɗan babba ya ajiye idonsa akan Zainab.
“Zainab yaya jikin?”.
A marairaice ta kallesa tace, “Yaya naji sauƙi, barci dai nakeji”.
“To bara ki karya saiki kwanta kinji ko”.
Kanta ta ɗaga masa tana cigaba da saka kayan, Rumana ma na jinsu tana ƙoƙarin cirema Haysam kayan jikinsa.
Ganin ta miƙe Ahmad ya kalleta, “Zaki iya masa wankan kuwa Ruman?”.
“Lah yaya zan iya, ai tun a gida ana sakani na masa saboda irin wannan ranar dama”.
Kansa ya jinjina mata, ita kuma ta wuce bayin.
Tana farama Haysam wanka ya fara ƙwaɗa kuka, hakan yasa Ahmad miƙama Zainab shayin daya haɗa mata da sauri ya miƙe zuwa bayin, shi duk gani yake Rumana bazata iya wankanba.
Amma ganin tanayin dai-dai sai hankalinsa ya kwanta, da taimakonsa aka kammala ma Haysam wankan, tace yayi shima kafin ta shiryashi.
Bai musaba kuwa, itama saita fito.
Har ta gama shirya Haysam ta shayar dashi sannan ya fito, Zainab kam tuni ta gama karyawan ta kwanta barci yay gaba da ita, tashi tai ta shiga itama, ta barsa yana shiri.
Sai da suka kammala komai daya dace, suka karya suma sannan Umm-Ruman ta kwanta, Ahmad kam shiri yay ya fita ya barsu bayan ya kullesu ta baya.
★★★★★★★
Su Rumana ansha barcin gajiya, kusan kwana uku suna hutawarsu, abinci ma Ahmad ke sayo musu, bai kuma nema komai daga gareta ba duk da yana cikin tsananin buƙatar hakan.
Da yamma randa suka kwanaki na ukun sai gashi shida nura a mota da kujeru, dama ya daɗe da bayarwa ayi wajen wani kafintan bahaushe da suke kira malam na kano, yana irin sana'ar gwangwan ɗinnan ne, sai yazam yanada yara masu aikin kafinta, Ahmad ya sanshi ne sanadin Nura, malam na kano yanason ƴan uwansa hausawa, dan haka yake taimaka musu da abubuwa da dama, dan ya kuɗance da sana'ar gwangwan ɗin nan sosai, a hankali Ahmad yayta biyansa, yanzu hakama bawai ya kammala biyan bane, duk da kujerun ba wasu masu shegen tsada bane, dai-dai ƙarfi dai akayisu.
Mamaki ya kama Rumana sosai, ita dai tana kallonsu ne har suka gama tsara kujerun a falon, kafet din da yake ajiye da shi kaɗai a falon a ka maidashi tsakkiya, sai ƙaramar katifa da aka sakama zainab a ɗayan ɗakin itama, ya umarci Rumana akan ta maida mata kayanta duka a can.
Sun daɗe da Nura a gidan, dan sai dare ya wuce, da yake yanzu shine a gidan su Happy ya maye gurbin Ahmad tun lokacin da aka bashi gidan nan.
Da daddare bayan sun kammala hira da cin abinci zainab ta shige ɗaki wai barci takeji ita dai, Ahmad na zaune yana danna waya bai tankaba, sai ita da Rumana ke maganarsu dama can, sai idan ya gadama yake jeho tashi.
Haysam na goye a bayanta yana barci.
Bayan shigewar Zainab Rumana ta kalli Ahmad ɗin, “Yaya zakasha shayin ne yau? dan nima kwanciyar kam zanje nayi”.
Idanunsa ya ɗago ya kalleta, ya ajiye wayar yana wani sake ƙanƙance idanu kamar wani bachaine.
“Eh kawo”.
Ya faɗa kamar wanda bayason magana.
Tashi tai ta nufi kicin, babu jimawa ta dawo da kofin shayi yana tururi.
Koda ya amsa idonsa na kanta, ita dai ta ɗauke kai kamar bata fahimcesa ba.
Ɗaki ta nufa tana faɗin bara ta kwantar da Haysam kafin ya shigo. Da uhum ya amsa mata.
Koda ta shiga ta kwantar da Haysam a ƴar katifarsa mai net saita cire kaya ta shiga wanka, dukkan dabarun dasu Yaya Maryam suka ƙara mata karatu a kai shitayi kafin shigowar Ahmad, dan tasan yau dai batada mafita, wannan narke fuskar da yake faman yi yakai maƙurar da bazai iya ɗaga mata ƙafaba.
Kamarko tasan abinda ke ransa kenan, dan yana kammala shan tea ɗin tashi yay ya nufo ɗakin bayan ya kashe fitilar falon da fanka, dan basu da kayan kallo.
Isketa yay tanama Haysam addu'a, bai ce komaiba ya nufi bayi, ita kuma ta daka hijjab ta nufi ɗakin Zainab.
Itama tayi barci tuni, addu'a tai mata sannan ta gyara mata kwanciya ta fito.
Tana shigowa Ahmad na fitowa, yace, “Daga ina?”.
“Addu'a na yoma Zainab”. ‘Ta faɗa tana zama bakin katifarsu’.
Baice komaiba ya ƙarasa shirinsa, ita kuma ta cire hijjab ɗin ta kwanta.
Sai da ya duƙa wajen Haysam ya zira hannu yaɗan shafa kumatu yaron yana murmushi kafin ya taso yana faɗin, “Sadaukina banda kukan dare yau, Ni da Mommyn filin daga zamuje”.
Kallonsa Rumana dake daga kwance tayi cikin mamaki, sai dai harya kwanta ya sakata jikinsa bata iya cewa komaiba.
Ya hura mata iska a cikin kunne yana magana a hankali, “K idan ance yau ranar barcice sai ki yarda?”.
Rumana taɗan ƙanƙame jikinta saboda tsigar jikinta data yamutsa gaba ɗaya, shi kansa jikinsa rawa ya farayi saboda tsananin kewarta da yayi.
A yanda duk sukai laushi zai tabbatar maka kowa kewar ɗan uwansa na damunsa, dan yau ajiye kunya Rumana tai ta tabbatarma yayanta da gaske shiɗin natane, kuma ya karɓu a gareta karɓa ta har abadan.
Hakan ba ƙaramin neman zauta Ahmad yayiba, dan baitaɓa zato daga Gwal ɗinsa ba sam, duk da ta jigatu ta daure domin ganin ya samu farin ciki daga gareta, kodan tarin alkairan da yayi mata kashi-kashi tun daga haihuwarta zuwa yau da bazasu lissafuba.
Bata samu kuɓuta daga garesaba sai da kukan Haysam ya tsaida komai, a gurguje suka tsarkake jikinsu tazo ta ɗaukesa ta bashi abinda yakema kukan.
Ahmad harda dungurema Haysam kai, wai baiji nasihar da yay masaba ashe😂.
Ita dai Rumana tai murmushi kanta a ƙasa dan taƙi yarda su haɗa ido saboda nauyin abinda ta aikata yau, shiko ko'a jikinsa, saima wata ƙaunarta ta musamman dake sake shigarsa ta kowacce ƙofar gashin jikinsa.
Da asubama bayan yay sallar asubahi sai da ya sake komawa filin daga injisa.
Tun daga wannan ranar abubuwa suka sake canjawa tsakanin Ahmad da Umm-Ruman, dan yanzu kam kaso mafi yawa daga kunyarsa ajiyeta take gefe sai sun gama ƙonuwa a soyayyarsu sannan ta maido ta ta lulluɓa, hakan nama Ahmad daɗi aynun, dan shi dama haka yafi buƙata.
Dolene zamansu ya birgeka, akoda yaushe cikin waya suke da ƴan uwa da abokan arziƙi da suka baro, satinsu huɗu a garin Ahmad ya ɗauki su Rumana ya kai har gidansu Happy.
Sosai sukaita mamaki, dan sufa da basu yarda Ahmad nada aure ba.
Aiko kamar su haɗiye Haysam dan so, yaron yay bala'in birgesu, dan haka Mummy ta sakasu sukaje wani ƙaton super maket taima Haysam siyayyar kaya masu ƙyau.
Wannan abu yabama Rumana mamaki, duk da ba wata hira tai da suba saboda su basajin hausa, ɗan turancin bakinta kuma baida yawan da zasuje doguwar magana, sai dai ta lura mutanen sunada kirki, Ahmad koda yazo yaga hidimar da sukai musu yayta godiya.
Sai dare suka koma gida, Happy tace sai tazo itama.
_________________________________
Tafiyar su Ahmad da kwanaki biyar Ma'aruff ma ya ɗauke Mufida suka tafi Honeymoon kamar yanda mahaifiyarsa ta umarcesa, a cewarsa ƙila daga nan sa samo rabo.
Wannan abu yay masifar taɓama Samina zuciya, dan har sai da tazo gida.
Mama gaje taita lallashinta da ƙarfafa mata gwiwa saura kaɗan Ma'aruff yazo yay gurfane a gabanta yana neman gafara, ita dai tayi haƙuri ya gama rawar kan amarcin kawai.
Da wannan lallashin ta sama zuciyarta salama, sai lokacin taji labarin tafiyar da Ahmad yay da Rumana wajen aikinsa, sai taji zuciyarta ta sake dagulewa, babu shiri ta miƙe tana faɗin zataje gidan inna mari daga can saita wuce gidanta.
*_BAYAN WATANNI BIYAR_*
Zuwa yanzu abubuwa da dama sun faru na cigaba a wajensu Rumana, dan duk wata Ahmad ya amsa albashinsa zai ɗan tsintar musu abinda basu dashi a gidan ya saka musu, dan danan gida ya haɗe yay tsaf dashi, su kansu sunajin daɗin yanda komai ya zama ɗas a muhallinsa, a watani biyar ɗinnan zuwan Ahmad gida biyu yay kwana uku a na farko, na ƙarshen nan kuwa satinsama guda, amma banda su Rumana, hakan yayma iyayensa daɗi, dan ya tabbatar musu tafiya da iyalansa can bazaisa ya manta da waiwayarsu ba kenan.
A gefe kuma yanata shirye-shiryen komawarsa makaranta, hakama Zainab an sama mata wata secondary anan kusa da kwatas ɗin nasu, zata ringa zuwa da wata yarinyar maƙwaftansu da bata wuce sa'artaba, duk da dai ba hausawa bane kuma ba musulmai bane, amma basu da matsala dai, dan a hankali sukaita shiga jikinsu Rumana har sabo yay ƙarfi a tsakaninsu ana gaisawar mutunci, sai islamiyya da Ahmad ya samar mata sanadin ogansa na ɗan kunne, duk weekend take zuwa ita kuma.
Haysam kam kullum ƙara wayo yake, yanzu haka yana zama abinsa, da ɗan rarrafe duk da dai bai nunaba rarrafen, yaron ya ƙara ƙyau sosai da cikar haiba maiban sha'awa, kowa yagansa saiya tanka, dan haka Ahmad ya dage da tofe kayansa da addu'a, itama Rumana yakance tai masa.
Duk sanda zaije gida sai taji kamar tai tsuntsuwa ta bisa, sai dai babu dama, har ƙwalla takeyi, Zainab kam bata damuba, balle tana gaisawa dasu Gwaggo a waya akai-akai, ita daɗinma garin takeji sosai da sosai.
______________________
Ɓangaren Samina kuwa sai da su Ma'aruff sukai watanni biyar cif sannan suka dawo, saiko ga Mufida ta dawo da fatan surukarsu, dan ta dawone tana laulayin ciki, hakan ya tada hankalin Samina, musamman yanda kowa ke nuna ƙaunar wannan ciki hatta da shi kansa Ma'aruff ɗin.
Har takai ta kasa haƙuri sai da tai masa magana, aiko suka hau sama dashi, harda faɗin wai baƙinciki Samina ke masa saboda taga ya samu ƙaruwa, to sai dai ta mutu kuwa, duk baƙin cikinta shi dai ya rigada yayi mata rata, idan kuma tai masa hauka yanzu zata nufi gidansu da jan kati.
A harzuƙe tace, “Saime idan ka sakenin, wlhy ni murnama zanyi na rabu da ƙaddararern auren mashayi mazinaci”.
Sai da yay mata wata dariya mai ƙularwa sannan ya haɗe rai, yace, “Aiko tunda kika nema saki da kanki bazan sakekinba, shashasha kawai sauran titi”.
Samina ta kwashe da dariya itama duk da maganarsa ta doketa, tace, “Nida kai ɗinne dai duka sauran titin, kuma hukunci ɗaya ALLAH zai mana, garama ni na tuba.....”
Bai ƙarasa jin abinda zata faɗaba ya fice.
Samina ta fashe da kukan takaici tare ɗunbin nadama da kaico na abinda Ma'aruff ke jifanta dashi a kullum na kiranta sauran titi..........✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
[8/21, 12:42 PM] Nadady: *_42_*
.............Su Umm-Ruman nada watanni na bakwai a port wani abin farin ciki da cigaba ya sake riskarsu, dan kuwa dai karatun da Ahmad keta ƙoƙarin komawa ya samu gurbin yinsa a ƙasar Saudi-arebia.
Cikin tsantsar farin ciki ya iso gidan, lokacin Rumana na kicin tana girkin dare, Zainab na Assignment ɗin makaranta a falo, sai Haysam da suketa rigima saboda rarrafe da yake yanason hanata abinda take, idan ta janye buks ɗinta sai ya haye mata saman wuya yana ƴar ƙara ta wasa da akasan yara dashi.
Rumana na jiyosu daga kicin ita dai.
Zainab ta amsama yayan nata sallamarsa tana masa sannu da zuwa.
Amsa wa yay da fara'ar data bata mamaki sosai, sallamar Ahmad ɗin ta saka Haysam dake riƙe da kayan wasansa da Zainab ta bashi dan ya barta shima rarrafawa da hanzarinsa ya nufesa, kasancewarsu basu da yawa a gidan, kuma ba wani waje ake fita da shiba yasa duk yasan ƴan gidansu, ko Zainab ta dawo makaranta haka yake mata, gashi da wayo masha ALLAH, bazaka taɓa ɗauka watanninsa taraba kenan, har tafiya yaɗan fara gwadawa, sai dai tsoro kan hanashi miƙewa shi kaɗai sai ya dafa kujera ko bango.
Ahmad ya ajiye takardun hannunsa ya ɗaukesa yana murmushi, “Oh my king yoyoyo”. Yay maganar da sumbatar kuncin yaron, zama yay a kujera Haysam na jikinsa, ya kalli Zainab yana faɗin, “Ina auntyn taki?”.
Zainab dake ƙoƙarin miƙewa tace, “Yaya tana kicin, bara na kirata”.
Wasa ya cigaba da yima Haysam, Zainab kuma ta nufi kicin kiran Rumana sai ma sukaci karo a hanya, dan dama Rumanan na jiyosu, kawai tana dai mamakin miya maidosa gida da wuri haka?.
Cike da shauƙi Ahmad ke kallonta, inba an faɗa makaba bazaka taɓa ɗauka itace ta haifi Haysam ba, musamman ma yanzu da Port ɗin ta kama jikinta, ta sake kyau dayin dumur-dumur abinta alamun samuwar kwanciyar hankali mai inganci.
Hannunsa ta taɓa, hakan yasashi kawo numfashi a hankali.
Ta ɗanyi murmushi tana faɗin, “Wannan kallonfa Zumana?”.
Sashin da Zainab take yakai dubansa, duk da dai yasan da wahala ace tana nan dan inhar yana falon bata zama sai indan sune suka kirata.
Umm-Ruman ma inda ya kalla tabi da kallo, sai kuma ta maido idonta kansa, dai-dai shima ya juyo idanunsu suka shige cikin na juna.
Cikin tare numfashinta yace, “Gwal ɗina kodai na sake yin ajiya ne?”.
Babu shiri ta waro idanu waje da faɗin, “Ajiya kuma Yaya? A ina?”.
Sai da ya shanye ruwan data miƙa masa sannan ya bata amsa yana nuna Haysam dake wasa da kwalliyar gaban rigarsa.
“Ƙanuwar Haysam mana”.
“Yaya rufamin asiri na mutu maza su kaini ba mataba, yaron da ko shekara baiyiba”.
Murmushi yayi yana shafa kan Haysam, yace, “Matsoraciya kawai, baki tambayeni na dawo da wuri ba?”.
“Wlhy da wannan mamakin na fito My boss, sai ka mantar dani da wannan ƙyaƙyƙyawar fuskar taka”.
“Kin rainani wlhy” ya faɗa cikin faɗaɗa murmushin fuskarsa har haƙoransa na bayyana.
Itama murmushin tayi, kafin ta sake magana ya miƙa mata takardun gefensa.
Amsa tayi cike da ɗunbin mamaki, shikuma ya tsura mata idanu yaga yaya zatai.
Cikin tsagwaron mamaki ta ɗago tana kallonsa bayan kammala duba takardun guda uku, “Yaya dan ALLAH yimin ƙarin bayani, ban fahimci komaiba bayan sunan Saudia kuma da naka”.
Kunnenta yaja har saida ta riƙe hannunsa tana ƴar ƙara sannan ya saki yana dungure mata kai, “Ashe a banza aka cima su baba kuɗin tara”.
“Ba komai ai sun yafe” Rumana ta faɗa tana dariya.
Shima dariyar yayi yana amsar takardun daga hannunta.
“Kinsan takardun minene?”.
“Abinda nake jiran ji kenan Zumana”.
Sai da ya sauke Haysam dake ƙoƙarin sauka daga jikinsa ƙasa sannan ya cigaba da faɗin, “Na makaranta nane, ammafa a ƙasar Saudi-Arebia”.
Sosai Umm-Ruman ta waro manyan idanunta waje, “Yaya wasa ko gaske dan ALLAH?”.
Hannunsa ya miƙa mata ta kama, yay mata nuni daya taso, babu musu kuwa ta taso ɗin ya ɗorata bisa cinyarsa, cikin magana a hankali kamar mai gudin a jisu yace, “Indai haihuwar Haysam bata zama wasaba haka shima wannan ba wasa bane Babie R”.
Rungumesa Ruman tayi cikin murna tana dariya, hakan ya saka Zainab fitowa dan taga dariyar mi suke haka?.
Da sauri ta nema komawa baya amma sai Ahmad ya kirata, dole ta dawo kanta a ƙasa saboda a yanda suke, ya miƙa mata hannu itama alamar tazo, har lokacin kuma Rumana na jikinsa ya hanata tashi.
“Kinsa mi Auntynki kema murna?”.
Kanta ta girgiza har sannan ta kasa kallonsu.
Sanar mata yayi itama, babu shiri Zainab ta faɗa jikinsu tana ihun murna itama, hakan ya saka Haysam fashewa da kuka saboda tsoratan da yayi.
Sakinsu Ahmad yayi suka maida hankalinsu gareshi, ganin yanda ya raɓe jikin kujera kamar wani marayane ya basu dariya.
Aiko suka shiga masa dariya, Zainab ta ɗakkosa itama tanayi.
Ahmad ya amshesa yana faɗin, “Sorry Abbanmu, kayi fushi kai ba'a faɗa makaba ko?, to tuba muke Sadaukina”.
Zainab da Rumana dai dariya sukeyi har sannan, Rumana ta kalli Zainab tana faɗin, “Zainab haɗo masa abincinsa inagama yunwa yakeji”.
Da to ta amsa ta nufi kicin, Rumana kuma ta nufi ɗakin barcinsu domin haɗama Ahmad ruwan wanka.
Bayan ta kammala haɗawa ta leƙo ta faɗa masa ga ruwa.
Amsa mata yay yana miƙama Zainab data fito Haysam.
Koda Ahmad ya shigo ɗakin Umm-Ruman saita sake rungumesa, alamar dai har sannan tana cikin farin cikin, ta haɗe bakinsu waje ɗaya, su oga Amadi dama kaɗan ake jira, koda Rumana taso janye bakinta sai yaƙi, ya kuma ƙanƙameta cikin sauke numfashi yake faɗin, “Yarinya ai kuma baki isaba, kin kawo kanki ai”.
Za tai magana ya kuma maidawa, dole tai shiru ta koma amsar saƙwanninsa masu tsayawa a rai.
Daga ƙarshe dai tare sukai wankan🤫.
★★★★★★
Sati ɗaya da samun wannan takarda Ahmad ya tafi gida, wannan karon Rumana ta saka ran zaije dasu, amma sai yace saboda makarantar Zainab, dole ta amshi uzirinsa ta haƙura ya tafi ya barsu da kewa.
Ya zoma ahalinsa da farinciki mai yawa, yayinda maƙiya abin ya zafesu a zuciya, dan mama gaje yini tai haɗiyar zuciya, gashi ta kira Number Samina a rufe, da yamma kuma tace zataje gidan inna mari baba ya hanata.
Washe garin zuwan Ahmad aka sanya ranar su Fa'iza, dama akan hakan ne baba ya kirasa, sai kuma ga dalilin zuwan nasa akan tafiya karatunsa.
Wata ɗaya aka saka kacal, saboda Ahmad ne zaiyi komai, gashi kuma watan gobe idan ALLAH ya kaimu zai wuce idan yakai tsakkiya, nanda kwanaki 45 kenan kacal.
Bai bar kano ba saida ya tabbatar ya rage kaso mafi yawa na abubuwan buƙatar hidimar bikin ƙannen nasa guda biyu, kwanansa shida ya dawo akan sai biki kuma, zai ringa turoma Mudan kuɗi a hankali ana cigaba da rage hidimomi.
Ya tafi iyayensa na sanya masa albarka, tare da tsarabar da aka shiryama su Rumana.
Kasancewar tasan yau zai dawo da wuri tai gyaran gidan komai yay ƙal, dama ta wanko kanta a wani saloon dake nan kusa dasu, Haysam ma an masa aski daya ƙara fiddo ƙyawunsa, dan shima akwai suma ya gada uwa da uba.
Zainab dama tayi kitso kwanaki biyu da suka wuce saboda makaranta.
Alala tai masa mai daɗi, dan tasan shine abinda yafi so a rayuwarsa sai kuma tuwo, tai kwalliyarta cikin shadda siket da riga, inda shima Haysam akai masa gayunsa, zainab kam bata dawo makarantaba, dan lokacin ƙarfe sha biyu da kusan rabi.
Saboda tafiyar yamma yayo jiya sai gasu sun iso da wuri, a gajiye ya shigo gidan saboda zaman mota.
Yay sallama shiru babu amsa, sai idanunsa daya sauke akan Haysam dake barci a falo, yay murmushi yana ƙarasowa ga yaron, gaban kujerar ya durƙusa tare da ranƙwafawa ya sumbaci kumatunsa da goshinsa, yayinda hancinsa ke shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren da yaron keyi.
Umm-Ruman dake bayansa tsaye bai saniba tai murmushi, sai da ya miƙe ta matso jikinsa ta rungumeshi ta baya tana ɗora kanta a bayansa, a tare duk suka sauke ajiyar zuciya, Ahmad ya ɗora hannunsa akan nata data zagaye cikinsa yana firzo iskar bakinsa, zagayo da ita yay gabansa yana ƙarema kwalliyar tata kallo.
“Gwal ɗina kinsan kuwa ke sarauniyace ko a cikin matanma?” yay maganar yana ɗora goshinsa akan nata.
Murmushi tayi tare da dora laɓɓanta akan nashi ta sumbata kaɗan ba tare da tace komaiba.
Yana ƙoƙarin maida laɓɓansa akan nata zainab ta shigo da sallama, dukansu baya sukaja kowa yabar jikin ɗan uwansa.
Zainab dama bata lura da yanda sukeba tahau ɗokin ganin yayanta ya dawo, sannu da zuwa tai masa kafin ta ƙaraso ta duƙa tana gaisheshi da tambayarsa jama'ar gida.
Fuskarsa da ɗan murmushi ya amsa mata yana zama cikin kujera, ya tambayeta karatu tace Alhmdllh, saƙon gaishe-gaishen da duk aka aiko mata ya shiga lissafa mata, dai-dai nan Rumana ta dawo ɗauke da ruwa a kofi.
Gefensa ta zauna kaɗan ta tsiyaya masa ta bashi.
Amsa yay yana wani narke mata fuska cike da salo, ita dai ta kauda kanta tana murmushi, saima ta tashi zuwa ɗaki domin haɗa masa ruwa, harta gama ta dawo suna wajen shi da Zainab, Haysam dai bai tashiba yanata barci.
Kusan mintuna uku sannan ya miƙe zuwa ɗaki, Zainab ma ta nufi ɗakinta tana faɗin bara tazo taci abinci yunwa takeji, Rumana tai dariya cikin tsokana take bata amsa da, “Ai yau keda ɗanki banyi girki da kuba, iya yaya kawai zaici abincin gidannan”.
Zainab taja birki cikin shagwaɓa take fadin, “Mi mukayi aunty?”.
“Ku kuka sani, idan ya tashi ki tambayesa tsiyar da yaymin yau a gidannan, bugu yaci kafin nai masa wanka yay barcinnan”.
Saurin dawowa Zainab tayi, ta duƙa gaban Haysam tana tattaɓashi da faɗin, “Kai aunty Rumana, dan ALLAH da gaske bugunsa kikayi?”.
“Oh kin ɗauka wasa nake kenan?”. Rumana ta faɗa tana shigewa ɗaki.
Zainab kamar zatai kuka taketa shafa kan Haysam dake barci lokaci-lokaci yana sauke ajiyar zuciya, yayinda haushin auntyn tata ya kamata.
Tana fiddoma Ahmad kayan da zaisa idan ya fito sai gashi ya fito ɗaure da tawul, ta baya ya rungumeta dukda laimar ruwan dake jikinsa, Rumana ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin, “Wayyo Yaya jikinka sanyi”.
“Da gaske?” yay maganar yana shinshinar wuyanta tare da goga mata gashin ƙasunbarsa dake jiƙe da ruwa.
Tuni tsigar jikinta tahau tashi, babu shiri ta juyo tana fuskantarsa, ta ɗora hannayenta a wuyansa suna mai kallon juna ido cikin ido, kowanne fuska ɗauke da murmushi, Ahmad daya ɗan ranƙwafo saboda finta tsaho da yayi ya sumbaci kuncinta,
“Malama ƙarasamin” ya faɗa yana juya idanu.
Rumana da bata fahimcesa ba tace, “Mizan ƙarasa?........”
“Kiss ɗina na ɗazu mana” yay maganar cikin tare mata numfashi.
Dariyar data sake narkar dashi tai tana ƙoƙarin zille masa, yay azamar turata jikinsa gaba ɗaya yana dariya, “Baki da man kai Babie R, karma ki ɗauka zan yafe sai kinyi, dan ɗazun naji kamar na make Zee ɗincan datazo ta katse min jin daɗi”.
Sosai yanzunkam Rumana ke dariya, tace, “Autar Gwaggon zaka bige? Aiko da an cika tara”.
“To ai ita ɗince tazo min a lokacin da bai daceba”.
Rumana ta zame jikinta tana cigaba da masa dariya, “Nidai ka shirya kazo ga abinci karya huce ma, kasa a ranka daga goman dare har safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu duk nakane lokacin”.
“Uhyim wayo ko Gwal? Shikenan na amsa, ALLAH yasa na jefa ƙwallona a raga to”.
“Nikam wannan fata da kakemin Yaya ka bari, sai Haysam ya cika shekara huɗu”.
“Humm haba yarinya wasan yara kenan, insha ALLAH nanda shekara huɗun kin yaye min babie gal ɗina mai kama dake”.
Fita Rumana tai dan ta kula idan ta biyesa zasu kwana a wajenne.
Tare sukai zaman cin abincin su uku, har suka gama Haysam bai tashi ba, Ahmad ya shige ɗaki ya kwanta danya ɗan huta.
Bai samu ganawa da Haysam ba kuwa sai da ya tashi, cikin ɗoki da kewar juna ya rungume yaronsa yana mai jin farin cikin ganinsa cikin ƙoshin lafiya.
Shima yaron da ALLAH ya bama wayo tamkar ba ɗan fariba sai maƙalƙale Abbunsa yake
___________________________________
A ɓangaren Samina abubuwa sunyi tsamari sosai, dan kuwa kullum cikin takalarta fitina Mufida take, tun bata biye mata saboda cikin jikinta harta shiga tanka mata, kuma koda itace da gaskiya idan Ma'aruff yazo sai ya goya da bayan Mufidan.
Akwai randa sukai wani faɗa shari'a har gidansu Ma'aruff ɗin, amma ƙiri da musu mamansu Ma'aruff ta goyama Mufida baya duk da Samina ce da gaskiya.
Abinnan ya ƙonama Samina rai harta tafi gida, koda taje ta sanarma Mama gaje sai taita lallaɓata akan ta koma, dan yanzu idan maƙiyansu sukaji dariya zasuyi musu, tayi haƙuri watarana sai labari, akwai kuma wani sabon malami da sukajiyo zasuje mata wajensa, daga mufidan har Ma'aruff ɗin sun kusa maganinsa.
Samina ta ɗanji daɗi, dan haka ta koma ɗakinta da ɗan ƙwarin gwiwa.
__________________________________
Kwanci tashi babu wahala wajen UBANGIJI, dan kuwa lokacin bikin su Salima yazo, ana saura kwanaki huɗu su Rumana suka taho kano.
Cike suke da ɗoki tamkar waɗanda akaima gafara, wannan karonma dai sunsha wahalar ita da Zainab, Haysam kam abin mamaki ko gezau yaronnan, hakan yasa Ahmad yayta musu dariya akan Haysam ya fisu ƙarfin jini.
Sosai gida ya kacame da murnar zuwan su Umm-Ruman, kowa yana mamakin dunbin canjin daya gani a garesu cikin watanni takwas kacal, musamman ma Umm-Ruman data fara zama matar manya, ga Haysam ya zama ɗan saurayi, hakama Zainab ta ƙara girma.
Umm-Ruman nata addu'a akan kar Ahmad yace su tafi can gidan, sai bayan magriba takeji wajensu Fa'iza akan ai an kwaso kayanta daga can gidan, akwai wani ɗan fili a lungun su Iya an haɗesa da wani ƙaramin ɗaki, Ahmad ya gina musu ɗaki a wajen, yanzu haka kayansu duk suna can.
Duk da taji sanyi a ranta sai kuma taga da kunya, yanzu kenan gaban iyayensu zasu zauna ko yaya? Koda yake tana ganin dan dai ba zama zasu rinƙa yiba yanzu shiyyasa.
Bayan isha'i kuwa Ayyah ta kora Rumana can.
Ɗakine guda ɗaya, sai dai babba dan yafi ɗakinsu na gidansu Maman Ama, wannan kuma yayi musu ƙaramin banɗaki na wanka a ciki, sannan anja katanga a gaban ɗakin babu mai ganin wani suda su Iya.
An jera kayanta duka anan, ɗakin yay ƙyau sosai.
Juyowa tai tana kallon Ahmad daya fito daga bayi, yay murmushi yana faɗin, “Surprise Babie R”.
Jikinsa ta faɗa tana dariya, “Wlhy da gaske kuwa ka shammaceni, yaya koda wasa baka taɓa sanarmin mun baro gidancanba”.
Bayanta ya shafa yana faɗin, “Ai dama nace sai kinzo ƙya gani, na gaji da ganinki cikin magulmatan matancan ne, duk da dama dai yanzu ma ta ƙare, tunda ko bamu baroba ba zaman garin mukeba”.
“Hakane Yayanmu, amma gaskiya wannan dabarar tayi, kaga kuɗinma hayar ai sun isa su kare mana wata lalaurar, ɗakin yayi tsari da ƙyau sosai”.
“Da gaske?”.
“ALLAH kuwa yaya”.
“Kinga kuwa malam ne ya kawo wannan shawarar wlhy”.
“ALLAH sarki tsoho mai ran ƙarfe, wlhy hakan yayi, ALLAH ya sanya alkairi”.
“Amin gwal ɗina”.
Har washe gari su Rumana suna amsar ƴan sannu da zuwa da ƴan ganin ƙwaƙwaf..........✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
[8/21, 12:42 PM] Nadady: *_43M_*
.............An tsunduma cikin hidimar biki da Ahmad keta samun ALLAH shi albarka, dan kuwa ya taka rawar gani sosai, shine yayma amare kayan ɗaki na gado, ya kuma ajiye isashen abincin da akaci gwargwadon ƙarfinsa, sannan ya danƙama Gwaggo kuɗaɗe masu dama itama akan taima Fa'iza siyayyar kayan kicin ta hannun ƙanwarsa Raheenatu.
Iyayensa suma dai sun ɗauki girman sun tattara sun bashi, dan shine ya bada auren ƙannen nasa.
Hakan ba ƙaramin ƙayatar da mutane yay ba, Ahmad kam sai yaji kamar yay kuka, dan abun ya masa girma da yawa.
Bayan kammala ɗaurin aure mata suka cigaba da hidima a cikin gida, amare dai suna ɗakin Umm-Ruman, sunsha ƙyau harsun gaji.
Gida cike da mutane, anata kaikawo da taya juna murna, inda abokan wasa suka saka Mudanseer a gaba da magana akan saura shi.
Shiko da ko budurwa baida sai abun yayta bashi dariya, duka nawa yake da za'a ishesa da wani zancen aure, Yah Ahmad yaushe yay aurenma duka-duka, shima sai ya shana sosai kafin yayi.
Su Rumana duk suna a sashensu Ahmad anata hidima, saboda girma da ake bama Baba Hamza sai yazam kamar komai anan akayi, sannan ma Ahmad shine ya ɗaura auren, ga kuma dangin Gwaggo dana Ayyah, can ɓangaren su Salima sai yazam dangin mamantane kawai da abokan arziƙinta, ƴan shema kuwa duk suna a sashen su Samina, amare da ƙawayensu na sashen su iya inda su Umm-Ruman suke yanzu suma.
Rabon da taga Ahmad tun kusan goma na safe, ko wankama ba anan yayiba, ɗibar kayan yay ya fita tunda safen.
Bayan kammala ɗaurin aure kuma Mudan ne ya fita da abincin abokansa da yace ta ɗiba ta ajiye. Sai Abu daya aiko ya amshi Haysam shima.
Samina ta shigo sashen, duk ta rame, sai farin bilicin daya maidata kamar wata aljana, tunda aka fara hidimar bikin nan sai yanzu ake ganinta a gidan, dan bata leƙoba ko sau ɗaya sai yau.
Tunda tazo kuma suna ɗaki ita da su mama gaje, sai da binta yayarta taje ɗakin kaima su Inna mari abinci take mata faɗa akan ita bazatazo ta gaisa da dangiba, bayan anata tambayarta.
Kamar bazatazo ba, sai dai mitagani oho mata ta taso ta fito.
Sai yauƙi take ita a dole matar mai kuɗi duk da kallo guda zakai mata ka fahimci rayuwarta a wajige take, sai dai idonta na sauka akan Umm-Ruman saita raina kanta, dan ita taƙama da sutura kawai takeyi.
Amma Umm-Ruman murjewar jikinta da ƙyawun data ƙara shine babbar amsar dake nunama duk mai kallonta tanajin daɗi, sannan tana tattare da tarin kwanciyar hankali a gidan aurenta.
Shigowarta abokan wasa sukai mata ca da maganar ai su sun zata batazoba ko tayi nauyi ɗan baba ya hana.
Sosai maganar ta soki ƙahon zuciyar Samina, cikin yaƙe kawai take gaisawa da mutane.
Koda ta iso wajen yayunta ta gaisa da kowa amma banda Rumana, koda Rumanan ma ta gaisheta da ƙyar ta amsa mata.
Ko a jikin Umm-Ruman, dan a halin Samina ai babu baƙonta kuma.
Duk yanda Samina taso barin wajen hakan ya gagara, dole ta zauna kodan neman ɗebe kewar damuwarta a hirar da ƴan uwanta keyi cikin kwanciyar hankali abinsu.
Sukam hankalinsu kwance suke hirarsu da dariya, har Rumana data nunama bata damu da abinda Saminar tai mataba sam.
Shigowar Ahmad dake ɗauke da Haysam a kafaɗa yana barci ya sakasu kallonshi su duka.
Yayi masifar yin ƙyau cikin dokakkiyar shadda kalar ruwan ƙasa mai duhu, sai maiƙo take da ɗaukar idanu, hular kansa ma dai kalar shaddar, hakama takalmasa, babu wanda zai kallesa yace Ahmad ɗin nan ne daya jigatu a soyayyar Samina, komansa ya sake canjawa, sai wani annurin kwanciyar hankali fuskarsa ke fiddawa musamman saboda gyaran da sajensa yasha.
Cikin tsokana wasu daga cikin iyaye ke faɗin ga “Uban amare ga uban amare”.
Murmushi kawai yake faman yi, saboda masu maganar duk yayun Ayyah da Gwaggo ne da ƙannensu.
Samina da tun shigowarsa idonta ya sauka a kansa tai ƙasa da kai tana haɗiye wani busashshen yawu mai kauri, gashi Rumana kusa da ita take zaune, sai ma an wuceta za'a kai ga Rumanan.
Shiko da idonsa ke kan matarsa yace, “Haba Gwal, kina ganinmu bazaki taso ki tarbemu ba?”.
Dariya su Yaya Maryam suka saka musu, Ruman dake murmushi ta miƙe ta nufoshi.
Samina da zuciyarta tai duhu da baƙin ciki ta maimaita sunan “Gwal” a zuciyarta da Ahmad ya kira Umm-Ruman dashi ko kunyar mutane baijiba, da ƙyar ta iya maida ƙwallar data cika mata idanu tana satar kallonsu ta gefen idanu.
Rumana kuwa data isa garesa hannu ta miƙa masa danta amshi Haysam ɗin, amma sai ya girgiza mata kai da ƴar harara,
“Haba Babie R wanda ke barci za'a ɗauka? Ko dai goyo”.
Ɓata fuska tai cikin marairaicewa tace, “Yaya goyo kuma? Salon ya ɓatamin kwalliyata”.
Sosai yay murmushin da har haƙoransa suka bayyana, cikin ƙasa da murya yace, “Duk kwalliyar da bani akaimawa ba ai bata da wani amfani Gwal ɗina, kuma ina kishin duk wanda zai ganta koda matane”.
Karaf maganar a Ahmad a kunnen Samina, saboda a kusa da ita suke, ji tai tamkar ta fasa ihu, da tasan zai shigo wajen nan da bazata taɓa zuwansa ba, Ahmad ɗinta data girma da soyayyarsa ne a gabanta yake furta kalami masu daɗi ga watanta ba itaba........
Wata ƙanwar Ayyah ce ta matso tana faɗin, “Ɗan gidan Ayyah kaga kawosa kaji”.
Murmushi yayi yana miƙa mata Haysam da cewa, “A lallai yau ango zai more bayan uwargidansa”.
Dariya tayi itama tana cewa, “ai bazanyi a batiba, idan ya tashi saina ranƙwashi kansa sau goma sannan, wane mijine haka babu kuɗin cefane babu ɗinki”.
Dariya su Yaya Maryam suke musu da kare Haysam ɗin.
Yayinda Umm-Ruman da Ahmad suka koma murmushi sudai.
Barin wajen Ahmad yay zuwa ga iyayensa yana gaggaishesu, yayinda su kuma suke masa taya murnar an ɗaura aure, da ALLAH ya sanya alkairi, sai addu'a akan hidimar da yay.
Yaja wasu mintuna kafin ya dawo inda su Rumana suke, idonsa akan Umm-Ruman yace, “Gwal ɗina yunwa nakeji fa, a taimaka a bani abinda zan sakama hanjina, ke da Ayyah duk kun manta dani yau nikam”.
Sosai Umm-Rumana kejin kunyar wannan Gwal da yake ambata a gaban iyayen da yayunta, amma yaya ta iya, tunda shi taga ko a jikinsa.
Miƙewa tai tana faɗin, “Yaya abincin gidannanfa duk ya zama saura, gashi bana tunaninma akwai tuwo duk sai shinkafa ta rage”.
Yace, “Nikam shinkafarnan bana sonta gaskiya, bincika mani idan da fura ko ita sai na sha”.
Amsawa tai da to, shi kuma ya nufi hanyar fita yana cewa idan ta samu ta bayar a kai masa yana waje wajensu Sufyan.
Ahmad na fita Samina ta miƙe tabar wajen, dan idan har tace zata cigaba da zama komaima zai iya faruwa da ita, dan bazata iya riƙe damuwarta ba.
Babu wanda ya damu da ita, kowa harkar gabansa yakeyi.
Rumana ta samo fura ta bayar aka kaima Ahmad ƙofar gida kamar yanda ya umarta.
★★★★★★★★
Bayan sallar isha'i aka shirya kai Salima ɗakinta, itako Fa'iza sai gobe idan ALLAH ya kaimu za'a nufi Shema da ita, daga can sai Katsina ta dikko ɗakin kara, dan can angonta zaizauna saboda acan yake aiki.
Salima ansha kuka kuwa, inda ta samu rakkiyar dangi da yawa saboda mijinta ɗan napep ne, sukazo kuwa gayya guda ɗaukar amarya, sai da kowa ya samu waje isashe kafin a saka amarya ita a mota a ɗinguma.
Umm-Rumana da ƙyar Ahmad ya barta wai zata kwasoma Haysam sanyi, ALLAH ya taimaketa Ayyah ta amshi Haysam ɗin ta goya hakan yasa ta samu damar tafiya.
Ɗan gidan Salima mai ƙyau ita kaɗai abunta, dan gidan kansane ba haya yakeba, aiko nan dangi aka shiga ƙananun magana akan ai abun ba'a dukiya bane zuciyace kawai, kowa yasan wannan habaici ana yinsa ne wasu Samina, wadda ita bama ta zoba tana gida abunta sai Binta ce taji zafin abun, sai dai tasan gaskiya mutane ke faɗa ai, tun barowar Samina wajen su Rumana tai zamanta sashensu bata sake fitaba, amma kowa ya ganta yasan tana cikin damuwa, dan har bayi ta shiga tasha kukanta, wani irin masifaffen son Ahmad takeji a ranta, musamman ganin datai masa yau shida matarsa da ɗansu, hakan ya kuma tada hankalinta, ɗan yaron mai ƙyau, da yanzu ita ta haifesa fa.
Mama gaje ta fahimci Samina tai kuka, sai dai bata da damar tambayarta saboda taron mutane.
Basu daɗeba aka kwasosu aka dawo dasu gida, sai kuma ALLAH ya kaimu gobe tafiya kai Fa'iza.
*_Washe gari_*
Washe gari akai shirin miƙa fa'iza, tunda wuri aka gama kimtsawa, itama tasha kuka fiyema dana Salima, bayan an kammala mata faɗa suka ɗunguma zuwa shema, dan sai anyi biki suma a can yau zuwa gobe su miƙata cikin katsina su juyo.
Kaf su Rumana ba'abar kowaba dasu aka tafi, Samina ce kawai batajeba, a ranar ma ta tarkata kayanta ta koma gida, dan inhar tace zata cigaba da zama a gidan zuciyarta zata bugane idan tana ganin Ahmad.
Tarba ta mutuntawa suka samu a shema, dan auren zumincine da kowa ke murna dashi, anta musu hidima sosai kamar a goyasu.
Haysam ya nema takurama Rumana da kuka ta banka masa maganin da yasakashi dogon barci, dan ya hanata rawar gaban hantsi bayan itama tana buƙatar taɗan warwasa😂.
Faɗa yaya Maryam taita mata kuwa akan haka, ita dai tai tsit tunda tasan bata da gaskiya.
Sun kwana sun hantse washe gari aka ɗauki Fa'iza suka sake ɗunguma cikin Katsina, itama ɗan gidanta mai ƙyau kuma ita kaɗai, kowa yanata sam barka.
Salla kawai sukai aka ɗan gyagygyara mata waje, dayake aikin yawane dan danan suka kammala, ƴan shema sukai gida, ƴan kano suma suka nufo kano cike da kewa da fatan alkairi ga ƴar uwarsu.
Sai takwas na dare suka iso kasancewar tafiyar yamma lis sukayo, Ahmad na kwance a ɗaki duk yanajin hayaniyarsu, tunda ya dawo sallar isha'i yay kwanciyarsa saboda gajiyar hayaniya.
Rumana bata shigo ɗakinba sai kusan goma, dan batai tsammanin yanama gidanba, da yamma sunyi waya kafin su taho yake faɗa mata sunje wani waje shida Sufyan.
Sannu yay mata, ta amsa tana kwantar da Haysam dake barci kusa dashi, bata zaunaba ta faɗa wanka dan shi take buƙata fiye da komai.
Bayan ta fito tai sallolin da suka riskesu a hanya na magriba da isha'i, har lokacin Ahmad na kwance barcima ya fara ɗaukarsa bayan ya gama tattaɓe Haysam.
Tashi tai ta fita neman ruwan zafin da zataima Haysam wanka, dan tasan inma batai masaba saiya farka, kuma hanasu barci zaiyi tunda ta rigada ta sabar masa da wankan kullum kafin barci.
Ahmad ma baisan ta fitaba sai motsin dawowarta yaji, idanu ya buɗe yana kallonta har tazo ta ɗauki Haysam ta cire masa kaya.
“Bakijin akwai sanyi garin nan Ruman, kibarsa da wankan nan” yay maganar muryarsa da alamun son barci.
Tsayawa tai daga ƙoƙarin zame wandon jikin Haysam, tace, “Yaya wlhy jiƙe yake da fitsari a panpas ɗinnan, sannan rabonsa da wanka tunda safe a shema da Yaya Raheenatu tai masa, komun kwanta zai tashemu da rigima anjima”.
Numfashi ya sauke da fadin, “To kardai ki zuba masa ruwa bisa kai, dan mura zata iya kamashi”.
Da to ta amsa tana miƙewa zuwa bayi.
Tana zuba masa ruwa a jiki ya hau mata kuka, bata kulasaba saida ta kammala tazo tai masa shirin barci, tea ta haɗa ta bashi, dan yarigada ya fara girman da har tsoro take yace zaisha nono, dayakema baida damuwa komai aka bashi ci yake, sai dai yasha ya ƙoshi sannan itama ta miƙe tana shirin barci, shi kuma ya rarrafa jikin Ahmad dake barci-barci ido biyu.
*_BAYAN KWANA GONA_*
Tafiyar Ahmad ta gama kankama, zai fara yin gaba kafin yaga abinda ALLAH zaiyi game da iyalinsa da yakeson su bishi, yana tare da damuwa game da karatun Zainab data fara za'a datse mata, dan bazai yuwu su koma can su kaɗai su zaunaba, amma da yay shawara da su baba sai sukace aje da Abu can porthercout ɗin sai ya zauna dasu Rumanan har aga abinda ALLAH zaiyi.
Kowa yayi na'am da wannan shawara.
Tare sukai shiri suka koma port, suka sake barin ƴan gidansu da kewa, kowa kuma nabin Ahmad da addu'ar fatan alkairi da ɗunbin nasara.
Duk jarumtarsa sai da ya share hawaye, dan yanaji a ransa kamar bai zama lallai ya sake ganawa da wasunsu ba, koshi ya mutu, kosu wani ya mutu.
Wannan tafiyar harda Abu aka yita, hakan yasa Ahmad da Umm-Ruman suka zauna a baya, Abu da zainab kuma na gaba dan shata ya ɗauka wannan karonma.
Sun isa gidansu da sukaima yajin sati biyu, a ranar da suka isan dai babu abinda suka iya tsinanawa saboda jigata, dan wannan tafiyarma tiɓis su Rumana suka isa, hatta da Abu kansa dan shima bai taɓa doguwar tafiyaba irin haka.
Haysam kam wannan karonma ragal yake yaronnan, sai dai yayi barci ya farka.
Washe gari kasancewar Abu ba mutum mai ganda ba da taimakonsa Umm-Ruman ta gyara ko ina ya ɗauki haske, Ahmad kam ma tunda safe ya fice gidan, bai dawoba sai yamma tare da Happy.
Duk da Rumana tayi mamakin ganinsu taren sai batace komaiba, ta tarbeta da mutunci kamar yanda ta saba, sai da suka shiga ɗaki Ahmad ke sanar mata anan Happy ɗin zata kwana.
Murmushi kawai Rumana tayi batace dashi komaiba, ya riƙo hannunta yana tsatstsareta da idanu.
“Naji bakice komaiba?”.
“To Yaya mizance? Tunda da dai ga ɗakin Zainab basai tai kwanciyarta ba”..
Baice komaiba ya sake mata hannu, ta fice shikuma ya bita da kallo kawai yana girgiza kai, akan laɓɓansa ya furta “Kishi kenan Gwal?” babu mai bashi amsa, dan haka ya taɓe baki kawai.
Washe gari ranar tafiyar Ahmad, bayan ya gama kimtsawa suka rankaya domin masa rakkiya a motar daddyn Happy da sukazo.
Kallo ɗaya zakaima Umm-Ruman kasan ta ƙwaɗi kuka a daren jiya, shi kansa Ahmad wannan tafiyar jiyake kamar yayta kukan, Haysam nata barcinsa har suka isa Airport ɗin.
Zaman da baifi na mintuna talatinba aka fara sanar da shela akan matafiyan, nanfa ran Umm-Ruman ya sake dugunzuma.
Ahmad dake zaune kusa da ita ya sauka yay durƙuso a gabanta tare da kama hannayenta duka cikin nashi, yau ko kunyar Abu da Zainab baijiba.
“Haba Babie R ki daure Please, insha ALLAHU kuma nan bada jimawaba zaku bini, saboda inason ku kasance kusa dani yasa na zaɓi ƙasar saudia domin yin karatunnan koda aka bani zaɓi, saboda inason yarana su tashi da cikar burina, insha ALLAH bazan ɗau lokaciba zaku matso kusa dani kuma kinji, ki kulamin da Sadaukina, idan kuma nayi ajiyar ƙanwarsa anan itama a bata kulawa”. ya ƙare maganar da shafa cikinta
Kanta ta ɗaga masa tana share hawayenta da murmushi a lokaci ɗaya, ya miƙe tsaye tare da sumbatar goshinta yana saka mata albarka shima da murmushi shinfiɗe a tashi fuskar.
Barin gabanta yay yaje ya sumbaci Haysam dake barci a bayan Zainab, itama ya kuma mata gargaɗi akan karatu.
Ya matsa yayma su Momyn Happy sallama yana sake musu godiya, sai ga Happy na hawaye, badan tasan bayaso ba da babu abinda zai hanata rungumeshi.
Ya bama Abu hannu shina yana sake jaddada masa ya kula sosai, cikin girmamawa Abubakar ke amsawa yayan nashi, tare da jera masa addu'oin fatan alkairi da nasara.
Harya tafi ya dawo wajen Umm-Ruman da duk suka miƙe tsaye ya rungumeta, dole Abu da Zainab sai ƙasa sukai da kansu.
Jin sunansa da aketa ambatane ya sakashi sakinta ba tare dayace uffnba ya juya ya fita.
Momyn happy tazo ta rungume Rumana a jikinta tana lallashi, da ƙyar suka samu tai shiru.
Sai da jirgin su Ahmad ya lula sannan suka bar airport ɗin, har gida su Dadyn Happy suka maidasu sannan suma suka wuce.
Umm-Rumana ta shiga ƙunci akan tahowar Ahmad porthercout balle barin ƙasa baki ɗaya, ranar har Haysam saida ya shaida tana fushi, dan ƙiri da muzu taƙi bashi nono sai tea sukaita banka masa da abinci.
Ƴan gida sunata kiranta harda amare su Fa'iza, sanda suke waya da Ammi saita saka mata kuka, Ammi ta yanke wayar kawai.
Haka ma baba kuka taitai masa, shidai ya allasheta da kalamai masu daɗi akan tabi mijinta da addu'a ba kukaba, kalaman babane suka sanyaya ranta harta daina kukan..............✍🏻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻[8/24, 12:08 PM] Nadady: *_64244456G_*
..............Ahmad an sauka ƙasar saudi-arebia, ƙasa mai tsarki, mahaifar MANZON ALLAH (tsira da amincin ALLAH su ƙara tabbata a gareshi), wajenda ɗakin ka'aba yake, gari mai farin jini da tarin al'umma, mai tarin ni'ima da burin zuwa ga kowa.
Jirginsu ya sauka a filin jirgin birnin Dhahran, Baisha wata wahala ba saboda haɗashi da yaron ogansa daya koya masa sana'ar ɗan kunne da akai tunkan ya taho, shima yana karatu anan ne, sai dai shifa ustazu ne na gaske, dan yana karatune ɓangaren islamic, an kwankwaɗi madarar ilimi sosai, sai dai muyi fatan ALLAH ya bada ikon amfani da shi, da amfanar da sauran al'umma.
Kasan cewar an tura masa hoton Ahmad shima kuma Ahmad ɗin yana da hotonsa sai babu wahala suka gane junansu.
Cikin al'ada irin ta larabawa suka rungume juna kafin suyi musabaha kamar yanda ustaz ya nuna yafi buƙata, kowanne fuskarsa ɗauke da murmushi shinfiɗe, bazasu gaza sa'annin junaba, dan shima ɗin dai kwanan nan akai masa aure aka turo masa matar nan.
Suna riƙe da hannun juna har lokacin Ahmad yace, “Muh'd Gaddafi Umar ko? Idan banyi mantuwa ba”.
Murmushi yay masa shima yace, “Hakane abokina, kaima Ahmad Hamza Rabi'u.
Ahmad yay ƙaramar dariya yana jinjina masa kai, abinka da masu ilimi, sai suka sake da juna dandanan kamar sun daɗe.
A gidan Muh'd Gaddafi Ahmad ya samu masauki, inda akai masa tarba ta mutunci da bazai taɓa mantawa ba, duk da amaryar Muh'd na fama da laulayin ciki haka ta shirya musu liyafa, Saudia taima Ahmad ƙyau, musamman birnin Dhahran da ya sauka, jinsa yake a yau tamkar wani sabon mutum, har suka iso gidan Gaddafi idonsa bai daina kalle-kalle ba.
Bayan sunci sunsha aka kaisa inda zai kimtsa ya hutama ransa, yakoji daɗin hakan dan hutun yake buƙata dama sosai, sai dai koda ya kwanta sai tunanin ahalinsa ya hanasa rintsawa, ya tabbata yanzu Rumana nacan cikin damuwa har yanzu, tafiya iya porthercout kawai ta saka kanta a matsananciyar damuwa inaga yabar ƙasarma baki ɗayane, ko Haysam zaiyi kuka in bai gansaba oho.
Yata tunane-tunane kafin barci ya sacesa.
Rayuwar gidan Gaddafi ta birge Ahmad sosai, dan ya fahimci akwai tsantsar ƙauna a tsakanin ma'auratan da soyayya mai tsafta, hakan sai ya tada masa nasa tsumin akan tashi gimbiyar da a yanzu ta zama wani sashi na rayuwarsa, sai murmushi yake saki tare da ƙara jin ƙaunarta da begenta mai tsanani.
Ya ƙanƙame filo a ƙirjinsa yana sauke nannauyan numfashi tare da rumtse idanunsa da kiyasto Baby R ɗinsa a yanayin da yazame masa sirri mai daraja da mutuwace kawai zata iya masa shamaki da tunawar.
_________________________________
Kwanaki Biyu Rumana na a sukuku da ita, kafin kuma ta saki jikinta ta koma normal, dan Ahmad ya kirata a ranar da Safe da wayar Gaddafi, tayi farin ciki sosai kuwa, yanda yake bata labarin kansa a saudia sai taji kamar tai tsuntsuwa ta ganta acan.
Su Zainab ma duk sai da ya gaisa dasu, hakama Haysam an saka masa wayar yanaji hayaniyarsa duk da shi yaron baisan anaiba ma.
Gidama Ahmad ya kirasu dan su sami kwanciyar hankali, aikam duk sunji daɗin hakan sosai, sunata jifansa da addu'oin fatan alkairi.
Cikin jin daɗi da tsantsar kewarsu yake amsawa har yanajin ƙwalla ta taru masa a idanu, ahalinsa suna da muhimmancin da bakinsa bazai iya furtawaba a rayuwarsa, yana addu'a rabbi ya azurtashi da halalinsa mai albarka da zai tallafi rayuwar sauran ƙannensa masu tasowa, suma su sami ilimi wadatacce kamarshi, ba dole sai na boko ba, na addini shine jagaba akan komai, shine kuma ake ribantuwa dashi a duniya da lahira, dan haɗuwa da Gaddafi ya sake tada masa kwaɗayi akan son sake zurfafa ilimin addini a rayuwarsa, sannan yanama ƙannensa sha'awar hakan suma.
___________________________________
Duk wani shigi da fici na karatun Ahmad da taimakon Gaddafi da yasan gari yayisa, sosai jami'ar *_King Fahd University of Petroleum & Minerals_* ta ƙayatar da Ahmad, ya zama ɗan ƙauye a cikinta, “kaga gini tamkar ba hannune yayisa ba malam Gaddafi?”.
Gaddafi dake kallon Ahmad yay murmushi yana mai sake bin makarantar da kallo shima, yace, “Ai Birnin Dhahran yana cikin manyan birane na duniya masu ƙayatarwa, shiyyasa da yawan Universitys da sauran makarantu dake wannan birnin zaka samesune a ƙawace, birnin da fadar saudiyyarfa yake kenan, kasanko ai dole komai na cikinsa ya ƙawatar”.
Ahmad ya sauke numfashi yana faɗin, “Lallaikam, cigaban da ya gagari namu ƙasashen kenan, kowa da ga aljihunsa saina ƴaƴansa da iyalansa ya sani, ALLAH ka azurtamu da jannatulfirdausi maɗaukakiya”.
“Amin ya rabbi abokina”
Gaddafi ya faɗa yana maijin takaicin al'ummarmu da suka dauki zalunci ƙaramin abu da bazai taɓa komai na rayuwarsuba, balle ya ragesu, sun manta da inda ake biyan zalunci komin ƙanƙantarsa da ayyuka, ranar da kowa ayyukan yafi buƙata ruwa a jallo, ranar da in baka da ayyukan kwarai a taskarka zunibin wanda ka zalunta za'a ɗiba a maka maka (Ya rabbi ka rabamu da rufaffiyar zuciyarda shaiɗan ke gadinta, ka azurtamu da ganin gaskiya komai dacinta garemu, ka hanamu zalintar duk wanda ALLAH ya haɗamu zama dashi koda ba'amuhalli dayaba, ka hanamu hassada da ƙyashi wa kowa, ka hanamu ƙuntata zuciyar kowa a rayuwarmu, ka hana maisan ƙuntata mana samun nasara a kayinmu😭🙏🏻).
Har suka isa gida suna cigaba da tattauna matsalolin ƙasarsu ne da suka baro.
Cikin kwanaki kaɗan komai ya kankama na karatunsa, Gaddafi ya ɗaukesa sukaje har makkah yay addu'oi ɗakin ka'aba na neman nasara da haske a dukkan al'amuransa, makkah ma ta ƙawatar dashi ainun, yay ziyarce-ziyarce sosai kafin ya fara zuwa makaranta, shine har Madina bisa jagirancin Gaddafi dai.
Aiko Alhmdllh, dan tunkan ai nisan zango yafara cin karo da hasken, dan kuwa yanda ya kamata yana fahimtar karatun da yazo dominsa.
Satinsa biyu a gidan gaddafi ya samu wajen zama shima, hakan yasa ya tattara ya koma can, gashi abin jin daɗi kusa da makarantar.
Kwaɗayin son faɗaɗa ilimin addini dan amfani da damar da ALLAH ya bashi, ya sakashi ma Gaddafi maganar son komawa makaranta, sosai Gaddafi yaji daɗin wannan al'amarin, kuma Ahmad ya birgesa, babu bata lokaci nanma ya shiga shigi da fici har Ahmad ɗin ya samu shiga wata islamiyya ta dare da aka buɗe domin magidantan da basu da lokacin kai da rana da irinsu Ahmad da karatu ke cinyema lokaci, nanma dai Ahmad ya fara karatunsa cike da nasarori kuma ya maida hankali dan kuwa masu iya magana sunce gemu baya hana ilimi.
Kullum da dare sai yayi waya da iyalinsa, Rumana taita masa shagwaɓar da ke tada hankalinsa dajin buƙatar son ta matso kusa dashi.
Haka kwanaki sukaita jaa, abubuwa nata faruwa, inda kafin kace kwabo Ahmad ya ja watanni huɗu da tafiya, tun yana ƙaraminsa mutum ne shi mai zuciyar nema, hakan yasa ko a ƙasar ta saudia bai zauna ya dogara da karatunba kawai, dukda duk watan duniya albashinsa na shiga asusunsa, wanda aciki yake fidda hidimar iyalansa da ahalinsa.
Shawara ya nema wajen Gaddafi akan son fara yin wani abun, Gaddafi yay murna da wannan zuciya ta Ahmad, nan take ya bashi shawara ƙyaƙyƙyawa kuwa, da taimakonsa suka haɗa ƙarfi da ƙarfe duk da dai na Gaddafin sunfi suka fara kasuwanci, dan dama shi Gaddafin yanayi.
A lokacin da Ahmad yake watanni na goma sha ɗaya sai dai muce Alhmdllh, dan kuwa dai-dai gwargwado yasamu rufin asirin da zai iya maido su Rumana nan, babu ɓata lokaci yasa aka fara musu shirin tahowa harda Zainab, Abu kuwa anan porthercout ɗin yasa ake nema masa admission, dan dama yana zuwa wajen Nura tare suke zama wajen sana'ar kayan yarinsu Ahmad ɗin.
Randa Ahmad ke sanarma Rumana suyi shirin tafiya kano tayi farin ciki sosai, dan tafiyace dake nuni da sun tafi kenan daga can jirginsu zai ɗaga zuwa saudia.
Harda Abu suka taho kanon, amma shi zai dawo ne tunda komai na karatunsa ya gama kammala.
Sosai Rumana kum taji kewar Port, zuwa yanzu kuma babu inda Haysam baya zuwa da ƙafarsa, yayi wayo sosai har magana yakan ɗan dagula duk da bata fita da ƙyau sosai, ta kuma yayesa ba tare da kowa ya saniba hatta da shi Ahmad ɗin kuwa..
Kowa yayi farin ciki da wannan zuwa nasu, sai dai banda irinsu mama gaje da har yanzu suka kasa samun mafita balle damar cutar dasu.
Haysam ɗan dangi, kowa sai ɗaukarsa yake da jinjina saurin wayon yaron.
Dukda Rumana taɗan rame saboda rashin mijinta a kusa hakan bai hanata sake yin ƙyauba, fatarta sai ɗaukar idanu take.
Wannan zuwan bata zaunaba, ta shiga ziyarce-ziyarcen dangi dayin sallama, itace har katsina wajen Fa'iza dake fama da cikin da har ya fito, da alama dai kusan lokaci ɗaya suka samu ita da Salima ma, duk da sun huta sosai sunci amarci kafin ALLAH ya kawo cikin.
Fa'iza tayi farin ciki matuƙa da zuwansu, ranar sunsha hira sosai, suka kwana suka hantse washe gari da yamma suka taho suka barta cike da kewarsu.
Wannan karon ta samu har tsohon gidansu taje domin gaida su Maman Ama, sai dai tayi rashin sa'a ta iske maman Ama bata nan, wai tayi yaji saboda faɗa da sukai da mijin akan zai ƙara aure ya faffale fuskarta da maruka.
Kausar kawai ta iske sai waɗanda suka kama hayar ɗakin da suka zauna yanzu, sosai Kausar ta ruɗe da ganin yanda Umm-Ruman ta sake canjawa, tamkar ba ita bace ta zauna a gidan nasu, gashi ta girke ta zama mace sosai, keko shekara kusan biyu kenan basuga junaba, tun arba'in ɗin Haysam da gashi yanzu yana takawarsa.
Duk sai Kausar ta raina kanta, tanatama Rumana Gulmar maman Ama, ita dai Rumana bata tofa tataba sa ALLAH ya ƙyauta da tace, da tagama abin zai wuce makaɗi da rawa tai musu sallama ta taho, ta barsu da tafa hannaye na mamakin wai yanzu Saudia su Rumanan zasu koma?.
Aiko maman Ama na dawowa bayan kusan sati da zuwan Rumana da labarin zuwan Umm-Ruman ɗin Kausar ta tarbi maman Ama duk da a yanzu basa shiri anyi uwar watsi tuni, harda ƙara gishiri da magi😂.
Maman Ama taji takaici na rashin ganin Umm-Ruman, dan haka ta ɗau aniyar sai tazo har gida taganta tunda Kausar tace sai nan da sati biyu Rumanan zasu wuce.
Sai dai kuma an taki rashin sa'a, dan kuwa kwanaki huɗu da zuwa Umm-Ruman maganar tafiyarsu ta tashi, haka sukai sallama da ƴan uwa da abokan arziƙi, suna kuka itama tanayi sukai mata rakkiya airport ita da Haysam da Zainab suka lula abinsu.
__________________________________
*_SU UMM-RUMAN A JIRGI ZA'A BAR ƘASA🥴😹_*
Cike zuciyarta take da kewar ahalinta, gefe kuma na cike da farin cikin zuwa ga mijinta da tai kewa tsawon watanni takwas, tare da ɗunbin ɗoki zuwa ƙasar da kowa ke fatar ganinsa a ciki.
Ahmad na filin jirgin tarbarsu tun kusan awa ɗaya saura su sauka, yana cikin tsagwaron zumuɗi da baki ma bazai iya furtawaba, Gaddafi da matarsa Jiddah da ƴarsu data haifa mai suna Subayya sunata masa dariyar zumudin da yake famar yi, bai kulasu ba, idonsa akan ƙofar jirgi da mutane ke fitowa
Can kuwa saiga taurarinsa guda uku na fitowa, Umm-Ruman ɗauke da Haysam a hannu tana cikin jallabiya ruwan siminti datai mata masifar ƙyau, ta naɗa gyale ruwan ƙasa da yay dai-dai da adon duwatsun da akai kwalliyar rigar mai zubin bubu dasu, sai Zainab dake sanye da wando da riga itama ta ɗora baƙar afterdress a sama, ta sake zama budurwa abinta, dan yanzu tana a shekara ta goma sha uku ne, Haysam kuwa yana sanye da wandon jeans da t-shirt mai ƙyau, shima ya ƙara girma sosai a idonsa yaron, ga kamaninsu da suka sake bayyana tattare da yaron musamman ma shi.
Ahmad ya sauke wani sassanyar ajiyar zuciya yana lumshe idanu, duk yanda yaso yin haƙuri su ƙaraso kasawa yay, ya shiga takawa zuwa garesu.
Inda itama Umm-Ruman idonta ya sauka a kanshi lokacin da Zainab ke faɗin, “Lah aunty Rumana kinga Yaya”
Da ƙyar Rumana ta iya haɗiye yawu da zuƙar numfashi saboda canjawar da Yayan nata kuma mijinta ya sakeyi, ya sake girma da ƙiba tare da wani ƙyawu mai ban mamaki saboda canjin wajen zama daya samu, sai kace baima taɓa aureba balle tunanin ajiye ɗa kamar Haysam.....
Jitai kawai an rungumeta ita da Haysam ɗin, hawaye suka silalo mata akan kumatu saboda buɗe ido datai ta sauke akan Ahmad dake rungume dasu su duka har zainab ɗin da itama ta ƙanƙamesa cike da farin cikin ganinsa.
Dukansu shida Rumanan sun kasa magana, sai ɗagowa yay suka zubama juna idanu tamkar baƙin ganin juna, ya ɗage mata gira yana cizar leɓensa na ƙasa, murmushi tayi tana duƙar da kanta ƙasa saboda kunya.
Shima ya murmusa yana maida idonsa ga Haysam daketa kallonsa, shi dai ya manta da Abban nasa, amma koda ya miƙa masa hannu bai musaba yaje garesa, ya shafa kan Zainab itama yana mamakin canjawar da duk sukai masa.
Gaddafi da Jiddah da suka matso ne suka katsesu, suka shiga yima su Umm-Ruman barka da zuwa.
Ansan juna a waya, dan suna gaisawa da junansu, hakan yasa babu tambaya Rumana ta ganesu, amsar Subayya dake hannun Jiddah, tayi tana mai yaba kƴawu da girman da yarinyar tayi a watanni bakwai da haihuwarta.
Gaddafi ma ya miƙa hannu domin amsar Haysam a hannun Ahmad, amma sai yaƙi, dariya suka sanya, Gaddafi yace, “Wato shi Abbu duk da ka daɗe baka gansaba ka gane abunka? Niko da baka saniba shine zakamin ƙiwa?”.
Dariya Ahmad yay yana kallon Haysam dake wasa da ƙasumbarsa, yace, “Sadaukina Uncle nefa, wanda ya baka mata tunkan kazo gata nan”.
Amamakinsu sai sukaga Haysam na dariya kamar ya fahimci abinda ake nufi, hakanne suma ya sakasu darawa baki ɗaya.
Motar Gaddafi suka shiga gaba ɗayansu domin tafiya gida...........✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
[8/24, 12:14 PM] Nadady: *_54465452386_*
.............A gidan Gaddafi suka yada zango, dan Hafsat tace itace mai tarban.
Sun iske abinci kuwa mai rai da lafiya na musamman da aka shirya domin su, yanda Rumana ta sake da Hafsat sosai ya faranta ran Ahmad, dan ya kula Babie R ɗinsa ta sake wayewa sosai fiye da sanin da yay mata kafin tahowarsa.
Sai kuwa satar kallon juna suke ita da shi suna sakarma juna murmushi.
Bayan sunci sunsha kowa yay nak sukai shirin tafiya gidansu suma.
Gaddafi dake miƙewa yace, “Ai sai dai ku tafi ku biyu, amma ni nan a barmin ƙanwata Zainab da yarona kuma surukina Haysam sumin kwana biyu kafin su biyo bayanku ko Zainabu?” ya ƙare maganar da kallon Zainab.
Babu musu Zainab dake riƙe da Subayya ta amsa cikin ɗoki, dan batason a rabata da ƴar ƙyaƙyƙyawar yarinyar dama.
Murmushi Ahmad yayi, dan sarai ya fahimci abokin nasa kuma ɗan uwansa a wannan ƙasa dama ya basu suje su more kewarsu shi da Gwal ɗinsa.
Da alama kuma shirin harda Hafsat a ciki, dan ɗaki ta janye Rumana ta bata wasu abubuwa akan suna zuwa gida yanzu kartai sanya tai amfani dasu.
Murmushi Rumana tai tayi tanama Hafsat godiya, dan Hafsat zata iya girme mata, saboda ita tayi karatu har matakin masters ma kafin ALLAH yay aurenta da Gaddafi, amma da yake tanada ƙaramin jiki bazaka taɓa kawo cewa ta girmi Rumanan ba, kasancewar ana cikin yanayin jin daɗi kuma Hafsat akwai gaye da tsafta.
Wayo akaima Haysam suka gudu, to saima akai sa'a shi bai farga da fitar tasu ba, hankalinsa na kan Baby Subayya gaba ɗaya.
★★★★★
Ahmad dake tuƙa motar Gaddafi da suka taho a ciki sai faman murmushi suke suna shaƙar ƙamshin juna shi da Gwal ɗinsa.
Amma abin mamaki bakunansu sun gaza furta komai, yakan juyo dai ya kalleta lokaci-lokaci, itama dai satar kallonsa taketayi ta gefen ido.
A cikin wannan yanayin dai ALLAH ya kaisu gida lafiya, sosai gidan yayma Rumana ƙyau, duk da kasancewar madaidaici kuma basu kaɗai bane, amma sashen kowa daban dan ɓangare ukune a gidan, kuma duk haya suke a ciki.
Bayan Ahmad yay fakin ya zagaya ya buɗema Rumana itama.
Wannan girmamawa ta ƙayatar da ita sosai, tai murmushi tana miƙa masa hannu kamar yanda ya miƙa mata nasa shima.
Babu wanda baiji wani sabon yanayiba tsakanin a jikinsa ba shi da ita lokacin da suke rumtse hannayen cikin juna, amma sai ko wanne ya fuske abinsa saboda tsaro ba tsoro ba😎🥺.
Sai da ya ɗauki wasu kayan sannan ya nuna mata hanya alamar suje, tai guntun murmushi itama tana ɗaukar akwatin Zainab daya rage dan basu wani kwaso kayaba kamar yanda yace mata, akwatinta babba ita da Haysam, sai na Zainab ɗan madaidaici, sai Handbag ɗinta da wata jikka itama dai madaidaiciya.
Kansa ya girgiza mata alamar ta ajiye zai ɗauka, amma sai ta noƙe kafaɗa tare da girgiza masa kai itama.
Ya lumshe ido yana kaɗa mata kai alamar suje to.
Gaba yay tana binsa biye har ciki. Sosai gidan ya kuma ƙayatar da Rumana, dan ya haɗu babu ƙarya masha ALLAH.
Rayuwa kenan, duk mai rai baya yanke ƙauna da rahmar ALLAH, ko a mafarkinsu basu taɓa tunanin zuwa wannan matsayinba a rayuwarsu........
Rungumetan da taji anyine da zare a kwatin hannunta ya sata kawo numfashi mai ƙarfi tana dawowa duniyar mutane, kallonsa tai, shima idanunsa a kanta.
Ya zare handbag ɗin hannunta yana kuma mannata da jikinsa, su duka sauke numfashi suke a gurguje saboda tsigar jikinsu dake mimmiƙewa.
Umm-Ruman ta ƙanƙame Ahmad itama tana sake masa wani kuka mai tsuma zuciya da ruhin masoyin ƙwarai daya fahimci na shagwaɓane kawai.
Murmushi Ahmad yayi yana ɗagota jikinsa, idanu kawai ya zuba mata ganin yanda take hawaye harda shashsheka, ya sake murmusawa yana haɗiye abinda ya tokare maƙoshinsa maiɗan ɗaci tare da jinginata da bangon da suke gab dashi.
Hannunsa yasa ya ɗago haɓarta tare da ɗora bakinsa kan nata......😚🤫
Komai cak ya tsayama musu, ji da ganinsu gaba ɗaya baya tare da duniyar mutane, takai har ƙafafunsu na neman gaza ɗaukarsu, ganin suna neman zubewa a wajen Umm-Ruman ta janye da ƙyar tana faɗawa ƙirjinsa ta ƙanƙamesa.
Bashi da zaɓin da ya wuce shima ya ƙanƙametan, suka durƙushe ƙasa a tare suna sauke huttai tamkar waɗanda sukai gudu a sahara.
Sunja kusan mintuna biyar a wajen basu iya tashiba, babu abinda suke faɗama juna sai irin kewar da sukayi da nisan da ya jawo hakan.
Ahmad dake kallon bakin Umm-Ruman tana zubo masa bayani ɗunbin kewarsa da tayi ya shafa fuskarta yana haɗiye ƙwallar data taru masa a idanu na tausayin kansu.
“Gwal ɗina ke ta dabance a duniyata, bakina yayi kaɗan wajen furta miki kalaman godiya ko kewa da ƙishirwar jinki a kusa dani dana tsinci kaina a wattani goma sha ɗayannan, kinriga da kin zama Ahmad, Ahmad ya zama ke tuni, kece zuciyata, kece jinin jikina, kece farin cikina da komaina matata, ashe kema haka kike sona?”.
Sake ƙanƙamesa Rumana tayi tana dariya yanzu, shima dariyar yake mata, da ƙyar suka miƙe a wajen manne da juna.
________________________________
Bayan sunyi wanka Ahmad ya fita gabatar da sallar magrib da Isha'i, yabar Rumana itama zatayi anan.
Kafin ya dawo duk abinda Hafsat tace tayi sai da tai abunta, dama gashi kafin su tahi Ayyah da Iya sun mata tsumawa ta musamman, Yaya Maryam ma da tata gudunmawar, banda wanda itama taima kanta a bayan fage.
Kasancewar cikinsu taf yake basa tare da yunwa Ahmad ya shigo musu hannu rabbana, dan jiya duk wani sayayya data dace ya yita a gidan na kayan abinci, to sai yazam harda fruits duk ya ajiye gwargwadon ƙarfinsa.
Koda ya dawo ɗin zaman gaisawa sukayi da tambayar ƴan uwa da abokan arziki.
Daki-daki kuma take sanar masa da saƙon gaisuwar kowa yake masa.
Yaji daɗi kuma yanata amsawa da godiya, daga ƙarshe dai hirar ta canja sabon salo zuwa......🤫.
😚to babu ruwana, su o'e an buɗe kunnuwa aji, salon aje wajen malam ace Bilyn Abdull ce ta hiɗi😌😏🤣⛹♀⛹♀⛹♀.
★★★★★
Rumus Umm-Ruman ta tashi a wannan rana, dan da gaske dai Ahmad ya fanshe watanninsa na kewa.
Kallo guda zakai musu ka fuskanci ɗunbin farin cikin da suke ciki, ALLAH ya sosuma ranar tazo a ranar hutu bazaije makaranta ba, amma ya dace yaje wajen business dinsu da sukeyi da Gaddafi kamar yanda ya saba a duk randa baida karatu.
Sai dai ba zai iya hakanba, to tunma da safe Gaddafin ya kirasa akan ya hutashshesa basai ya fitoba.
Hakanne ya saka Ahmad sake bararrajewa sukai ramuwar barcinsu na dare da ya gagara.
Koda suka tashima tare suka shiga kitchen suka haɗa abincin rana dan ba'ace masa breakfast ba dai😹.
A wannan yini dai gaba ɗayansa a kogin soyewa da rushewa waɗannan ma'aurata sukayishi, suna manne da juna kowa na bama ɗan uwansa labarin abinda akai a watanni 11 da basa tare, sai kiran ƴan gida da Ahmad yayi suka gaisa.
Washe gari ma har rana Ahmad na gida, sai da ƙyar da yamma ya iya fita makaranta saboda yanada lecture ɗin yamma.
Kwannan su Umm-Ruman biyar da zuwa saudia sannan su Haysam suka dawo nan gidan, familyn Ahmad ya dunƙule waje guda kamar yanda ya daɗe yana kewa.
Dan danan shaƙuwa ta shiga tsakaninsa da Haysam sosai, dan yana jansu a jiki shi da Zainab dansu sami farin ciki daga tsamosu a dangi da yayi, soyayya kuwa shida Gwal ɗinsa ai ba'a cewa komai.
Suna da watanni biyu da zuwa saudia Ahmad ya nemawa Zainab makaranta, shima Haysam kuwa aka sakashi, duk da ma dai Gaddafi ne ya ɗauki nauyin saka Haysam makaranta dan yana ƙaunar yaron, haka zasuzo su ɗaukesa yaje can yay musu kwana biyu.
Wannan yasa Haysam yazama mai gida biyu, yau yana gidansu gobe yana gidan Gaddafi, idanma akai kwanaki ba'a kaisaba sai yayta kuka yana kiran sunan Ubaya, (Subayya kenan yake nufi😂).
Itama dai Umm-Ruman ɗin Ahmad yanada burin sakata makarantar, danshi dama can mai sha'awar son ganin iyalinsa sunyi zurfi a karatune, hakan yasa yaji bazaiyi ƙasa a gwiwa ba, dukda shi bamai ƙarfi bane zaiyi ƙoƙari da abinda ALLAH ya hore masa insha ALLAHU, tunda da dai karatune ya kawosa ƙasar ba kasuwanciba, amma duk da haka babu abinda zai cema UBANGIJI sai Alhmdllh.
A gefe kuma yanata zuba ido yaga gwal ɗinsa ta fara laulayi, dan Ahmad yay ƙwarin da ko ciki ta samu a yanzu basu da wata damuwa, ballema yaron yanada girman jiki, hakan yasa ta yayesa tun yanada shekara ɗaya da rabi, gashi yanzu har yanada skekara biyu da wata ɗaya.
Tom ALLAH dai bai kawo ɗinba, sai dai a cigaba da fata.
_______________________________
*_NAGERIA🇳🇬_*
_Ya kamata mu waiwayi Samina matar manya😉😌_⛹♀
Lamari ya sake caɓewa sosai a gidansu Samina ko nace gidan Ma'aruff, dan tunda Mufida ta haihu komai ya ƙara canja salon taku.
Irin shagalin da akai wajen wannan haihuwa da ɓarnar kuɗin da Ma'aruff yayi abin har ba'a cewa komai.
Dan mahaifiyar ma'aruff kanta lamarin ya girgizata, hakama ƴan uwansa tunda kowa yasan ba haƙƙinsa bane shi kaɗai kuɗin da yake ɓaragaza dasu, amma saboda son ƙuntatama Samina sai basu nunaba balle zance ya fito, kowa ya haɗiye abun a ransa, dan dai kam tabbas Mufida bawai tabar Ma'aruff hakanan bane duk da kuwa mahaifiyarsa ta tsaya tsayin daka akan sai ya auri mufidan.
Rabonda Ahmad ya shigo sashen Samina da ƙudirin sauke haƙƙinta harta manta watan, dukta fige, dan ko lokacin bikin su Fa'iza a wannan tashin hankalin tajesa, to bayanma bikinsu Fa'izar sai abubuwa suka kuma taɓarɓarewa.
Dan ganin Ahmad a wajen taron bukinnan ya dawo mata da sabuwar zazzafar ƙaunar da take masa, wanda kwaɗayi da son duniya ya danneta a wancan lokacin, kullum shine a mafarkinta, shine tunaninta, saboda shi duk dare saitayi kuka mai yawan gaske, ga tashin hankalin gidan miji, gadai ci da sha amma babu miji babu farinciki babu ƙauna daga ahalinsa, ya kuma hana kowa zuwa gidan a ƙawayenta, wannan yasa ta haɗu ta kuma lalacewa, ko gidansu batason zuwa, indai ta fita iyakarta gidan inna mari, acan suke haɗuwa da mama gaje, mutanen gida kuwa duk sun ɗauka ko laulayin ciki Samina keyi shiyyasa ta ɗaukema gidan ƙafa, amma kuma basuji wani labariba har tsawon watannin da zuciya zata iya ɗauka wannan hasashe.
Ta amshi Number Ahmad, daga baya kuma sai aka sanar mata ai bamaya ƙasar, dan ita batasan zai tafi saudia ba, mama gaje bata sanar mataba gudun kar ranta ya ɓaci😹.
Babu kalar ƙulle-ƙullen da basuyiba amma asirin nasu yabar tasiri a halin yanzu, sun rasa a ina matsalar takene?.
Basusan matsalarsu itace Mufida ba, dan itama sai da tai duk wani yunƙurin daƙilesu kafin ta kafa nata shaiɗancin tsubbun ga Ma'aruff da ahalinsa.
A yanzu babban tashin hankalinta shine Ma'aruff kullum cikin zarginta yake akan wai maza takebi, dan watannin daya ɗauka baiyi tarayya da itaba bazai yuwu ta iya haƙuriba tunda yasanta ita karyace.
Tamasa rantsuwa yafi shurin masaƙi amma yaki saurarenta, abinda kuma bai saniba komai yawan bukata na ɗan adam inhar yana cikin tashin hankali bayama tuna wata sha'awa, musasaman ma mu mata da muke da rauni, ƙaramin ɓacin rai kan gusar da sha'warmu muji bama bukatar namiji.
Wasa-wasa abu ya fara tsamari tsakaninta dashi akan wannan magana, to abune lamari na kwakwalwar ɗan giya da babu Mathematics sam aciki, balle ga sammu na ɗawainiya da rayuwarsa.
Yau da su Rumana ke cika wattanni biyu da tafiya rikici ya ɓalle tsakanin Samina da Ma'aruff akan saita faɗa masa da wa suke cin amanar aurensa, dan da daddare ya shigo gidan a make Mufida ta hanashi shiga sashenta shine ya nufo nan, ya iske Samina nata sambatu akan begen Ahmad.
To da yake a make Ma'aruff yake sai ƙwalwar kansa ta bashi wani abu daban, tun a daren ya fara dukanta sai dai abun bai nisaba ta gudu bayi ta ɓuya, shine ALLAH ya taƙaita abun.
Da safe kuma bata fitoba har yabar gidan, ya kumaje ya yini da abun a ransa ko a office ɗinma, shinefa yana dawowa abinci kawai yaci a sashen Mufida yanufo sashen Saminar ɗauke da yarinyarsa da Mufida ta haifa masa.
Sai kuma gashi ya taki babbar sa'ar isketa a falo kwance tana tunanin Ahmad da ayanzu ya zamemata abokin rayuwa.
Ganin yana cikin hankalinsa yasa tai tsamanin babu abinda zai faru, sai dai ina, batasan a yanzunnema zai farunba.
Basu yarda ta ɗaukar musu yarinya, dan haka yanzuma kallo ɗaya tai musu shida ƴar tashi ta ɗauke kanta, sai dai tambayar daya jeho mata makamanciyar ta jiya ya sata tashi zaune a rikice.
Tun ana zancen da fatar baki har takai ya ajiye yarinyar ya maƙure Samina, dan ya tabbatar mata idan bata sanar masa dawa take tarayyaba sai ya halakata.
Tashin hankalin da Samina take cikine ya sata birkice masa itama, yana kai mata duka tana ramawa, kafin kace kwabo sun kaure.
Sosai hayaniyarsu ta kaure gidan, a kuma lokacin ne Afrah ta rarrafa zuwa ga wata kwalbar ruwan lalle da Samina ta ajiye gefen kujera ta ɗauka ta saka a baki, sunata danben bala'i itako tana wasa da ita har ALLAH ya bata nasarar buɗewa ta juye ruwan cikin bakinta ta shanye.
Mufida duk tana sashenta tanajin wannan bala'i, sai kwasar dariya takeyi, daga ƙarshe ta fito da nufin zuwa tasha kallon zahiri baji da kunneba, sai dai ta iske kallon zahiri kuwa wanda batai zatoba ko tsammani.
Dan daidai baby Afrah na shure-shuren mutuwa ne ga dafara na fita a bakinta fara tas ta kumfa, ihun da ya dawo da hankalin Ma'aruff da Samina ta ƙwala tana nufar Afrah, suma duk sai suka kalli wajen.
Ma'aruff shima ya isa da gudu suna jijjiga Afrah tare da Mufida, daga ƙarshe dai ya fisge yarinyar ya fita da gudu da ita waje, Mufida da Samina suka take masa baya a matukar tashin hankali.
*_RUBUTACCIYAR ƘADDARA_*
Tabbas wannan yanayi ya cancanci a kirashi da suna Rubutacciyar ƙaddarar Samina, dan kuwa bayan ankai Afrah Asibiti, likitoci na amsarta mufida na kuka ta kira ƴan sanda akan bazata yardaba Samina ce tai yunƙurin kashe mata ɗiya, mai makon Ma'aruff da yasan gaskiyar lamari ya hanata, tunda dagashi har Samina basusan mi Afrah taci ba ko yay sanadin shigarta wannan hali, sai yay shiru Mufida ta kira ƴan sandan.
Samina na gida cikin matuƙar tashin hankali, dan basu bari ta biyosu ba, bayan tafiyarsune kuma ta fahimci abinda Afrah tasha ɗin.
Ƙaddarar dake biye da ita ta sakata ɗauke kwalbar ruwan lallen tasa a shara tare da goge wajen wai dan kar Mufida ta juya abun kota zargeta🤦🏻♀.
Batasan hakan datai shine babban kuskuren data tafkaba a rayuwarta kuwa.
Dan tana kammalawa babu jimawa sai ga Mufida da ƴan sanda, basu wani tsaya jan zanceba suka wuce da Samina tana kuka da rantsuwa akan ita ba ita ta aikataba.
Sai dai sunƙi saurarenta, haka suka wuce da ita station.
Kafin aɗauki dogon lokaci kuma magana ta fara baje dangi, har gidansu Samina takai.
Babu kuma mai faɗin gaskiyar lamari sai cewa ake Samina ta bama ɗiyar kishiyarta fiya-fiya ta mutu saboda ita tana baƙin cikin bata haihuba.
A asibiti kuma babu wani bayani dangane da jikin Afrah daga likitoci, sunata dai shigi da fici ɗakin da aka kwantar da yarinyar saboda Adam da ya tsaya tsayin daka akan komi...............✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻[8/24, 12:14 PM] Nadady: *_6446446J_*
............Komai ya hargitse, gaskiya ta gaza fita a bakunan mutane, kowanne furuci ya fito na zargin Samina ne kai tsaye.
Ca ake bata ɗauki ranta a bakin komaiba ita kanta dama, dan ta taɓa shan fiya-fiyan shiyyasa yanzu ma ta bama ƴar mijinta.
Mama gaje ta koma tamkar ƙaramar mahaukaciya, hakama inna mari, ga baba Yusha'u yace babu hannunsa a ciki, Babansu Ahmad da Mudanseer ne keta shigi da fici station ɗin amma ko ganin Samina an hana misu, dan ƴan sanda sunci kuɗi sunyi haniƙan wajen Mufida data sake ɗaure komai da wasu zantuttukan, Ma'aruff kuma ya gaza kare Samina ko sau ɗaya.
Afrah bata mutuba, amma yarinyar na cikin mawuyacin hali, harma takai sai an mata aiki a ciki saboda ɓannar da ruwan lallen yay mata a wani sashe na kayan hanjinta.
Yanzu ana maganar shiga kotune, dan haka akace su baba suje kawai su nema lauya😢.
*_YARO TSAYA MATSAYINKA, KADA ZANCEN ƳAN DUNIYA YA RUƊEKA_*
Wannan kalma itace dai-dai da abinda ya dace a ambatama Samina ko zata zamo mai tuna mata baya.
Dan kuwa a yanzu babu mai goyon bayanta, kowa ALLAH wadai yake furtawa a gareta tareda bada shaidar munanan halayyarta, abun mamaki dukkan iskancin da sukayi da Ma'aruff saiga zantuka nata fitowa.
Har takai wani video ya fita nasu amma ba'a ganin fuskar Ma'aruff ɗin saita Samina, sai dai duk wanda yasan ma'aruff yanajin muryarsa dake fita a videon yasan shine, kuma gashi a gidan gonarsane.
Hankalinsa ya tashi matuƙa, dan waɗannan videos ɗin da sukaitayi da Samina duk a cikin tsohuwar lop-top ɗinsa ya adanasu, data samu matsala ya gaza fiddasu sai yay tunanin ƙilama sun goge, shiyyasa bai damuba, saboda ya rasa muhimman abubuwansa da yawa a cikin lop-top ɗin, to ashe wasu bidiyo ɗin sun maƙale🤦🏻♀.
A watan jiya daya shuɗe Mufida ta roƙesa ya bama ƙaninta lap-top ɗin zai gyara yay amfani da ita, saboda babbar lop-top ce kuma batasha wahalaba, kuɗine kawai dake ɗawainiya da Ma'aruff shima ya sakashi ajiyeta.
Baiyi musu ba ya bashi, ashe acan wajen gyara ƙanin Mufida sukaga wasu daga cikin bidiyo ɗin da basu gama fitaba shida abokansa, sai dai ya karɓe ya ɓoye, bai kuma taɓa sanarma kowaba har Mufidan, sai yanzu da wannan abun ya taso saboda son tozarta Samina yaron ya saki videos ɗin shi a tunaninsa Samina ce kawai zata tozarta banda Ma'aruff, tunda a ko ina babu fuskarsa sai muryarsa, wani wajen kuma Saminar cema kaɗai a bayin gidansu tai masa video ta tura masa.
Abu kamar wutar jeji yayta yawo a kafafen yanar gizo da wayoyin mutane, tare da hoton bikin su Saminar da wata budurwar da ma'aruff din ya taɓa yaudara itama ta ƙara, hakama irinsu Basy da wasu tarin ƴammatansa suka samu hanyar sake tozartashi.
To lamarifa sai ya sake canja salo, dan ahalin Ma'aruff ɗansu kawai suke ƙoƙarin karewa da son kare mutuncinsa.
Ranar a gidan su Samina duk wanda kaga baiyi kukaba to lallai sai dai idan bai mallaki hankalin kansa da zai fahimci halin da ake ciki bane, wannan tashin hankalinne ya saka jikin malam rikicewa aka kwashesa zuwa asibiti.
*_SAUDIYYA_*
Ahmad na makaranta kiran baba ya riskesa, bai ɗagaba dan sannan suna lecture, sai da ya bari ya fito sannan ya kirashi.
Tun a yanda yaji muryar baba hankalinsa yay masifar tashi, Baba yana share hawaye ya sanar masa abinda zai iya, dan bai iya buɗema Ahmad komai ba a zancen.
Shiru Ahmad yay kawai yana sauraren baba, bayan sun gama wayar da Baba sai ya kira Mudanseer, ko gaisawa basuyiba ya tambayi Mudanseer abinda ke faruwa.
Komai Mudan bai ɓoyema Ahmad ba, har maganar cikin da akece Samina taje dashi gidan Ma'aruff ɗin, da duk shaiɗancin da suka dingayi a titi lokacin shi yana cikin mawuyacin hali na ƙulafucin sonta.
Babban tashin hankalin Ahmad halin da akace malam yana ciki da Baba Yusha'u, haka ya koma gida a wani irin yanayin da Umm-Ruman ta gaza fahimta.
Tai masa tambayar duniya yana bata amsa da babu komai, daga ƙarshe sai kawai ta zuba masa ido tana kallo, dan ita dai tsagwaron damuwa take hangowa tattare dashi, gashi babu wanda ya sanar mata da abinda ke faruwa ita kam daga mutanen gida.
Koda lokacin ɗakko Haysam yayi daga makaranta sai itace ta fita ta ɗakkosa, alhalin inhar yana gida ca yake ta zauna ya ɗakkosa.
Da suka dawo duk maƙale masan da Haysam yake bai kulashi ba, daga ƙarshema da Haysam ya fara fitinar kuka akan bazaici abinciba sai da Ahmad ɗin kamar yanda ya sabar masa, sai Ahmad ya daka masa tsawa kamar zai dakesa.
Yaro bai saba da ganin Abbunsa hakaba, tsoro ya kamashi ya ƙanƙame Rumana yana kuka da ɓoye fuskarsa.
Ɗauke kai Ahmad yayi duk da baiji daɗin yanda yayma yaronba, tunda shi minene laifinsa a ciki?.
Aiko har yamma Haysam bai sake bin koda sashen da Ahmad yakeba, itama Zainab tana shigowa gidan ta fuskanci akwai matsala, dan har Rumanan ma bata cikin walwala sam.
Zuwa sallar magriba ya samu wani kiran daga Nigeria, hankalinsa tashe ya ɗaga, dan tun ɗazun girarsa ke rawa gabansa na faɗuwa tamkar wani abu zai faru dashi, hakama Rumana ta tsinci kanta a cikin wani irin tsoro.
Koda ya ɗaga a tsorace sai yaci karo da tashin hankalin abinda dama yake jima tsoron, wato dai ALLAH yayima Malam kakansu rasuwa😭.
Sakin wayar kawai Ahmad yayi ya zube cikin kujera hawaye masu zafi da ƙarajin tsanar Samina na tasiri a ransa, yasan mutuwa dolece akan kowa, sannan kuma dama ALLAH ya rubuta yau malam bazaiyi kwanan duniyaba, amma tabbas Samina ce sanadi, dan ɓacin ranta shine sanadi.
Ta zubar musu da kimar gida, ta kunyata ƙoƙarin tarbiyyar da iyayensu suka gina a garesu da saka shakku a cikin ta ƙannensu masu tasowa gaduk namijin da zai iya neman aurensu.
A ruɗe Ruman ke tambayarsa miya faru? Sai dai ya gaza bata amsa sai hawaye yake irin waɗanda ya jima baiyiba a rayuwarsa.
Barin wajen tai taje tai kiran gida itama, sai dai daƙyar ta samu Number Salima, itace ta sanar mata komai dake faruwa da yay sanadin barin malam duniya dukda dai dama kwanansa ya ƙare.
Ranar sunsha kuka ita da Zainab, har sai da Ahmad ya dawo lallashinsu.
__________________________________
Bayan rasuwar malam da kwana huɗu za'a shiga kotu, har sannan kuma Samina bata da lauya, hakan yasa baba kiran Ahmad akan maganar, duk da ɗacin wulaƙantarwar da Samina ta jamusu a idon duniya.
Ƙiri da muzu Ahmad ya bama baba haƙuri akan shi babu ruwansa akan wannan maganar, zai biya kuɗi dai a canjama Baba Yusha'u asibiti kawai.
Tun baba na masa faɗa harya koma lallashinsa, da ƙyar ya yarda akan a samo lauyan to, idan kuɗin da zai buƙata baifi ƙarfin aljihunsaba ya biya, idan sunfi ƙarfinsa sai dai mama gaje itama ta kawo wani abu.
Dole aka yarda da wannan magana ta Ahmad, dan koda aka samo lauya sai ya noƙe ya bada abinda baifi rabin kudin da lauyan ya buƙataba, dole mama gaje ta fidda wata kaddarar acikin wadda suka saya suka tara da kudin ma'aruff din ta saida.
A wajen rasuwar nan ta malam babu abinda ake mata ita da Samina sai ALLAH wadarai, ko fitowa batason yi saboda kunya.
Tayi wani firi-firi da ita saboda damuwa da tashin hankalin da take a ciki.
Washe garin addu'ar Malam ta uku aka shiga kotu.
Su Mudan hankalinsu yakai ƙololuwar tashi lokacin da aka iso da Samina kotun. dan dagani kasan taci ɗan banzan duka na fitar hankali a wajen ƴan sanda.
Ko gani idonta ɗaya bayayi saboda kumburi.
Yanda akaima Samina ɗauri tamau akan wannan al'amura yasa ko a kotun komai yay tsamari, dan kuwa sun ɗauki kwararren lauya da yaci kuɗi na tashin hankali, saboda dangin Ma'aruff ma suna goyen bayan Samina ta shiga wani halin da zai kaita jail saboda mutuncin ɗansu.
Aiko sai gashi hujjojin da duk sukazo daga mutane da ƙwarewar lauyansu ta saka wannan shari'a ɗaukarsu ga nasara.
Ruɗanin da Samina take ciki yasa duk tambayar da akai mata take badata cikin zurma kanta, daga ƙarshe shari'ar sai bata bada wahalaba kai tsaye alƙali ya yanke hukunci wa Samina.
Ɗaurin shekara bakwai a gidan yari, saboda yunƙurin kisan kan ƙaranar yarinyar da batajiba bata ganiba da tayi, sai tarar kudi mai tsoka da za'aima Afrah aiki da kula da rayuwarta har ta samu sauƙi.
Daga haka kotu ta tashi.
Duk da Ahalin Ma'aruff sunso ace ɗaurin rai da rai akaima Samina shekara bakwai ɗinma tai musu daɗi, dan koba komai dai tayi nesa da rayuwar ɗansu.
Kafin a wuce da Samina Ma'aruff ya bata takardar sakinta uku cif, ta damƙeta a hannu tana wani irin kuka mai ciwo da cin ƙahon zuciya, musamman yanda taga Baba hamza na share hawaye da gefen babbar rigarsa, haka aka sakata mota aka wuce.
Sai dai kuma abinda dangin Ma'aruff basu saniba tana ƙasa tana dabo acan kuma tsakaninsu da Mufida.
Dan kuwa dai ana gama wannan case sabuwar masifa ta tashi tsakanin Ma'aruff da Mufidar, wanda ta rikiɗe ta zama faɗan family ɗinsun gaba ɗaya ma.
__________________
Ɓangaren su baba kam sun shiga matsanancin tashin hankaki da wannan hukunci da akaima Saminar, sai dai basu da yanda zasuyi su hana, suna gani tana kuka aka sakata a mota domin kaita prison.
A take wajen mama gaje ta yanke jiki ta faɗi, sai asibiti aka wuce da ita.
A tsakanin nan kam wannan ahali nasu Ahmad basu da abin faɗa sai dai Alhmdllh kawai.
Hakan yasa Ahmad ya zage da addu'ar ALLAH ya sama musu sauƙi, dan har ɗaukar su Umm-Ruman yay sukaje Makkah sukai addu'oi a ɗakin ka'aba.
Dan suma duk da suna can suna a yanayin da yake dai-dai da wanda mutanen gidansu ke ciki a najeriya.
A hankali al'amura suka cigaba da lafawa, dukda dai zukata sun gaza mantawa dasu sam, baba yusha'u yanata samun sauƙi, hakama mama gaje ta samu sauƙi, sai dai ta rame matuƙa, damuwa ta maidata tamkar wata zararriya, haka zaka sameta zaune jigum tayi tagumi saboda tunani.
Ranar da akai addu'ar arba'in ɗin malam akai zaman mitin a gidan, wanda Baba Yusha'u ya roƙa akan ayisa.
Yana hawaye yake neman gafarar ƴan uwansa akan dukkan abinda ya faru ta sanadin iyalinsa, hakama mahaifiyarsu iya ya nema gafararta itama, kowa yace ya yafe masa, tunda ai ba shine ya aikataba, suma da suka aikata ɗin ALLAH ya shiryesu ya ganar dasu gaskiya harma da ƴan baya masu kalar tunaninsu.
Bayan gama tattaunawa da neman gafarar juna baba Yusha'u ya maida kallonsa ga mama gaje da tai jigum tun zamansu mitin ɗin, uffan bata iya furtawaba sai kallonsu kawai take kamar doluwa.
Yace, “Gaje bazan iya cigaba da zama dakeba duk yanda naso jurewa, wlhy ganinki kaɗai sakani takaici yake da tashin hankali, kece sanadin komai, kece kika rusa mana zuri'a, tun daga aurenki har zuwa yanzu ban tsinci wani abun alkairi bayan na haihuwaba tattare dake, to acikin haihuwarma saida kika haddasa komai na baƙinciki wa rayuwata da ahalina, alhakin yaronnan Ahmad kawai ya isa hana rayuwarki samun salama, Samina ta tsinci kanta a halin da yafi wannan ma, yaron nan yashiga ƙuncin rayuwa a dalilin butulci, hakama iyayensa, amma suka danne zukatansu basu raba zuminci damuba, sanadin Ahmad kika dawo gidannan Gaje, a wannan gaɓar kuma dolene ki barshi, bari na har abada, dan haka kije gida na sakeki, na katse sauran igiyar data rage a tsakaninmu dama ƙwara ɗayace.........”
Cikin hanzari baba Hamza ya katse baba Yusha'u da faɗin, “Haba Yusha'u, wannan wane irin maganace? Miyasa zaka saketa? Koma dai miye ya rigada ya faru, ya kamata kuma mu ɗaukesa matsayin jarabawar da babu hannun da ya isa gogeta a duniya, sam banji daɗin wannan hukuncin nakaba, bankuma yi zato ko tsammanin zaka yankesa ba........”
Baba Iliyasu yace, “Yaya wannan hukunci yayi dai-dai wlhy, lokaci yayi da zamu dawo cikin hankalinmu, kaine babban yayanmu, wanda muke kallo tamkar uba, tayaya zamu cigaba da kallo a koda yaushe ana cuta maka kaida zuri'arka?, tun daga zamanin ƙuruciya har wannan ranar da muke yau iyalanka haƙuri kawai suke a gidannan, babu kalar haɗin masifa da ba'ai musuba, shikenan kuma dan ALLAH yasa kun kasance masu kawaici sai a maidaku juji? Wlhy bama gaje ba, kowacce ƴar iskar mata yanzu a gidanan inhar bata dai-daita sahuntaba mu zamu daidaita matashi, dan munsan gaje tanada mabiya masu koyi da munanan halayenta a gidannan.......”
Nanma dai babane ya sake katse baba iliyasu, dan (Kowa yasan baba iliyasu da matarsa yake shima).
A mamakin kowa sai akaga mama gaje ta miƙe bata cema kowa uffanba ta shiga ɗaki, mintuna baifi gomaba ta fito sanye da hijjab ta fice daga gidan nanma bata tankama kowaba.
Da kallo duk suka bita, dan zukatansu sun fara basu ƙwaƙwalwarta kamar ta fara samun matsala.
Babane yace Mudan ya bita yaga wane hali take ciki, koda Mudan ya biyota sai yaga ta tari napep tana faɗa masa ya kaita anguwar su inna mari.
Gida Mudan ya koma ya sanar musu, hakan ya saka baba Yusha'u faɗin, “Dama kune kuke ɗaukarta mai matsala, amma ni nasan wacece gaje, tajecan ta ƙarata, nidai na yanda ƙwallon mangwaro na kuma huta da ƙuda”.
Shiru kowa yayi, sai iyace tai gyaran murya, dan haka kowa ya maida hankalinsa gareta.
Nasiha ta shiga musu, tare da nuna musu muhimmancin zumunci da sakamakon mai wargazashi, takuma sakasu suka ƙara neman gafarar juna, taima su Ayyah nasiha akan su ƙara haƙuri da kowa su cigaba da ɗaukar girman da ALLAH ya ɗora musu, insha ALLAHU zasu cigaba da zama masu ribane har abadan.
_________________________
A saudiyya ma dai abubuwa sunyi sauƙi, sai dai abinda zuciya ta gaza mantawa, dan a tsakaninnan ba ƙaramar tsanar Samina Ahmad ke ƙara jiba a ransa sosai.
Ko gida ya tuna sai kaga ɓacin rai ya mamaye fuskarsa, abu kaɗan zai kama faɗa a kansa, ranar tsautsayi na bin Haysam Rumana ta ajiyema Ahmad ɗin tea zaisha da daddare wajen tsalle-tsallen yara na wasa ya ɓarar dashi, aiko Ahmad ya kama faɗa hardasu zane Haysam yayi.
Agaban Rumana komai ya faru, amma sai ta ɗauke kanta tankarma batasan sunaiba, sai Zainab ce keta kuka tana roƙon Ahmad yayi haƙuri, daga ƙarshema Rumana sai tabar masu falon kawai.
Ranar Haysam yaci kuka yaronan abin tausayi, daga ƙarshe yay barcin dole.
Tun daga lokacin ya koma tsoron Ahmad ɗin, ko sallamarsa yaji zakiga ya gudu ya ɓuya koda a bayan Rumana ne ko Zainab.
Sai kuma abun ya fara damun Ahmad ɗin, ranar ya dawo daga makaranta da wuri ya iske Rumana kwance bata da lafiya, duk da dai taƙi sanar masa, dan takai sati uku tana fama amma ganin yanayin da yake ciki na saurin fushi a wannan tsakanin saita danne tai gum da bakinta.
Yau ɗinma koda ya fahimci bata da lafiyar sai ta fuske abinta.
Shine ya kasa haƙuri ya tambayeta da cewar, “Ruman lafiya kuwa?”.
Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta tana cewa, “Babu komai”.
Duk yanda yaso jin damuwarta taƙi faɗa masa, tama haɗe fuska taƙi sake masa kamar yanda ta saba.
Numfashi ya sauke kawai ya shiga bayi yayi wanka, harya fito bata motsa daga kwancen da takeba a gado, ya zira jallabiya fara yana mai satar kallonta, “Bara na ɗakko Sadauki a makaranta”.
“Uhum” kawai tace masa ta ɗauke kanta.
Ya kalleta da ƙyau yanajin mamaki a ransa, amma ganin taƙi kallonsa sai ya fita kawai.
Koda Ahmad yaje makarantar su Haysam ɗaukarsa Haysam sai yaƙi yarda dashi, anyi lallashin duniya yaronnan yace shi sai dai Ummien sa ya keso.
Badan malaman sun san Ahmad ba, kuma ga tsananin kamar da Haysam keyi da shi da sai suce kodai dama ba mahaifinsa bane?.
Lallashi da wayo irin wanda akema yara babu wanda ba'aima Haysam ba amma yaƙi kallon ko Ahmad ɗin.
Wannan abu yay masifar sosama Ahmad rai, har ya gano kuskuren daya tafka ga iyalan nasa da basu da laifin komai akan damuwarsa.
Daga ƙarshe dole sai ɗaukar Haysam Ahmad yayi yaron na kuka tamkar za'a yankashi, sauƙinsama makarantar kusa da gida take, bawani uban nisa bane mai yawa tsakaninsu.
Har sukaje gida Haysam na turje-turje da kuka.
Umm-Ruman na bayi tana amai suka shigo, ta kuskure bakinta ta fito jikinta duk babu ƙwari, ga fuskartama ta nuna alamun a wahale take.
Ahmad ya sauke Haysam yana kallonta, itako ta ɗauke kanta ta haye gado ta sake kwanciya tana jan bargo.
Haysam kuwa da Ahmad ya sauke da gudu yaje ya maƙalƙaleta yana ɓoyewa cikin bargon data lulluɓa.
Jikin Ahmad sai ya sake yin sanyi, ya zauna a bakin gadon yana mai zuba musu ido ranshi na ƙuna.
Har washe gari Ahmad na tare da wannan damuwa, dan da safenma Haysam ƙin yarda yay ya kaisa makaranta, gashi Rumana na kwance babu lafiya sosai, ko breakfast ma sai Zainab ce ta haɗa musu saboda tana ƙoƙarin koyama yarinyar duk abinda ya dace.
Dole sai Zainab ce ta ɗauki Haysam ɗin, Ahmad na biye dasu a baya har majarantar, daga can itama ta wuce shikuma ya dawo gida..............✍🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
[8/24, 12:15 PM] Nadady: *_670774475737Y_*
...............Zama yay a bakin gadon yana mai kai hannu ya yaye bargon da Rumana ke ciki, duk tana jinsa, amma rashin ƙwarin jiki da take fama dashi saboda yawan amai ya hanata koda kallonsa.
Hawowa yay gadon ya kwanta bayanta tare da mannata a jikinsa, ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe ido saboda zafin da jikinta ya ɗauka.
Itama ajiyar zuciyar ta sauke amma ko motsawa batayi ba.
Murya ƙasa-ƙasa yace, “Haba Gwal ɗina, yanzu wannan rayuwar da kika zaɓa mana kina ganin ta dace kenan? Ace kina fama da ciwo amma kinƙi yarda muje asibiti?”.
Murmushi ƙaɗan Rumana tayi jin furucin yayan nata, batace dashi komaiba itadai.
Shima tashi yay zaune ya yaye bargon gaba ɗaya, sannan ya ɗagota jikinsa yana faɗin, “Please muje namiki wanka, kuma banason musu”.
Bata musa masanba kuwa, dan tana buƙatar wankan, rashin jin ƙwarin jikine ya hanata tashi, da taimakonsa tai wanka da ruwa mai ɗumi sosai dataji ƙwarin jikinta kaɗan, koda suka fitoma shine ya taimaka mata ta shafa mai ta saka doguwar riga.
Shima shiryawar yayi ya ɗakko kayan karin da Zainab ta haɗa musu ya kawo ɗakin, amma sai Rumana tace bazata iya ciba ta ƙoshi, da ƙyar ya takura mata tasha shayi babu madara, aiko tana gamawa sai amai.
Da gudu ta tashi zuwa bayi shima ya bita, ta bashi matuƙar tausayi, sai kuma ya fara zargi a ransa kodai cikine da Gwal ɗin tashi?.
Wani irin ɗoki ya ziyarci zuciyarsa, dan haka suna fitowa cayay mata asibiti zasuje, duk yanda take masa magiyar ya barta, bai sauraretaba ya saka mata gyalen jallabiyar dake jikinta, dole ta yarda suka tafi kuwa.
_______________________________
Rayuwar jail da Samina ta tsinci kanta a ciki rayuwace da sam bata da daɗi, dan ALLAH ya haɗata zamane da wasu mugaye dake azabtar da rayuwarta.
Cikin ƙanƙanin lokaci komanta ya canja, tai wani irin baƙi saboda man bilicin da fuskarta bata samu, gashi tayi gida-gida tamkar ta ƙone, ga ƙuraje.
Yayinda zuciya take azabtuwa ta tarin ƙaunar Ahmad da baisan tanayiba, tunda take a rayuwarta bata taɓa jin son Ahmad mai masifar zafi irin a wannan tsakaninba, ji take idan bata rayu da shiba tamkar zata iya rasa ranta, kullum cikin tunaninsa take da roƙon ya dawo gareta dan ALLAH.
Samina Ahmad baya jin wannan kirayen naki sam, sai dai haƙuri kinji😢🤒.
Tana ambaton kalmar data sani gameda Sanin Ma'aruff fiye da sau dubu a rana, tare da ɗunbin jin zafin mahaifiyarta da kakarta da tafi tsana fiye da kowa yanzun a duniya, dan a ganinta kakarta inna mari ce silar komai, sai ƙawayen banza mugaye irinsu Nafy, tare da son zuciya da ruɗi na neman wayewa da son duniyar da baida amfani, domin ita dai gashi bai mata amfaninba.
_______________________________
Su Ahmad suna isa asibiti a gwajin farko aka gano cikin da ke jikin Rumana ɗan watanni biyu, wanda Ahmad yake hasashen zuwan su Rumana Saudiyya babu jimawa ta sameshi.
Yayi murna sosai da farin ciki, inda harya kasa haƙuri sai da ya kira Yaya Maryam ya gwargwaɗa mata.
Itama kuma Rumana lokacin tanata barci saboda Ruwan da aka saka mata.
Awarsu kusan shida a asibitin sannan aka sallamesu, lokacin da ruwan da aka sakama Rumana ya ƙare, yanda taga fuskar Ahmad ɗin a washe ya bata mamaki.
Duk da ita ta daɗe da sanin ciki gareta, tunda taga wata ya shige batai jini ba tasan abinda Ahmad ɗin ke fata ya samu, yanda ya koma mafaɗacin ƙarfi da yajine yasa ta danne abunta a rai taƙi sanar masa.
Murmushi ya sake sakar mata yana lumshe idanu, ya jawota ya saka jikinsa yana sauke tagwayen ajiyar zuciya, kafin ya ɗago fuskarta yay mata sumba kusan huɗu a goshi da kumatunta.
Turesa ta ɗanyi tana faɗin, “Yaya wai mike faruwa hakane?”.
“Kina nufin bakisan mike faruwa bane? Wlhy nasan kin san da abin farin cikinnan kika ɓoyemin Babie R ɗina”.
“Ni bansan komaiba” Rumana ta faɗa tana ɗauke kanta gefe’.
Hannu yasa ya maido da fuskar tata inda take, yace, “Gwal ɗina ke ɗinnan ko, shikenan dai bara sai munje gida kawai”.
Shiru tai bata iya cewa komaiba, suka fito zuwa gida saboda an basu sallama, takumaji daɗin jikinta sosai yanzu babu laifi, sai da suka biya ta makarantar su Haysam suka ɗaukesa, yau ɗinma dai ƙin yarda yayi da Ahmad, sai da yaga Ummien sane saiya gudu ya maƙalƙaleta.
Rumana tai murmushi tana riƙe hannunsa da faɗin, “Oh Sadaukin Abbunsa kana lafiya?”.
Yaron ya faɗa jikinta yana dariyar farin cikin ganinta, koda Ahmad ya miƙa masa hannu sai ya noƙe kafaɗa alamar bazaijeba.
Ahmad yay guntuntun murmushi kawai.
Har suka isa gida Haysam nata bama Rumana labarin abinda take masa tambaya a kai cikin rashin ƙwarewar maganarsa, dan yanzun yanda yake magana da larabci yafi masa sauƙi akan hausar, danma suna ƙoƙarin masa dan basa buƙatar ya manta da yarensa, to dama dai Ahmad ɗinne maijin larabcin sosai a gidan. Sai itama Zainab da yanzu Alhmdllh ta fara ji saboda makaranta, Rumana kam sai jefi-jefi irin na islamiyya da wanda take tsinta annan.
A gida duk yanda Ahmad yaso sakewa da Haysam kamar da can baya sam yaƙi, zai fara kiran ƴan uwa ya baza musu tana da ciki ta fara roƙonshi akan dan ALLAH karyay hakan, badan yasoba dole ya haƙura yabi yanda takeso tunda yasan dai Yaya Maryam ta riga da taji ai.
Cikin hikima kuma ya cigaba da jan Haysam a jiki, da masa wasa tamkar da, sai a hankali kuma yaron ya koma sakewa da shi tamkar da can baya, shaƙuwa ma ta sake shiga tsakaninsu tunda yanata ƙara wayo.
Haka Umm-Ruman ta cigaba da rainon cikinta dake ɗan wahal da ita, dan wannan karon da Amai yazo mata, sai dai tanata jurewa dan kar Ahmad yace bazai nema mata makaranta ba sai ta haihu.
Shiko da yaga kamar da sauƙi yanzu sai ya cigaba da cuku-cukun makarantar tata da taimakon Gaddafi, dan matar Gaddafin ma jin ɓangaren islamic Rumana keson faɗaɗa karatunta, sai itama taji sha'awar komawa karatun, duk da kuwa tayi karatu har matakin masters, to a ganinta hakan bai zama ya wadatarba dan islam shine babban tushen da zaka karanta kai alfahari da shi a duniya da lahirarka, boko kuwa aikin alkairin da zakai ta dalilin karantarsane zai amfanar da kai a duniya da lahira.
Komai tare akai musu, Gaddafi ya bada gudunmawa sosai saboda yafi Ahmad ƙarfi sosai.
Randa Ahmad yazo mata da bayanin komai, tare da takardunta sun kammala, jikinsa ta faɗa tana kukan daɗi, bata taɓa zato ko tsamanin irin waɗannan nasarorinba a rayuwarta, amma gashi a dalilin yima iyaye biyayya tama wuce inda kowa yake zato, dalilin haƙurin da tai da Ahmad a farkon aurensu ya jawo mata alkairin da hasashen zuciya bai taɓa kaiwa nanba.
Ahmad dake shafa bayanta yay murmushi yana magana a hankali cikin kunnenta.
“Gwal ɗina tawace ni kaɗai, hakama farin cikinta nawane ni kaɗai, kin cancanci nasarar data kere haka a rayu Umm-Ruman, duk wanda yay haƙuru da jarabawa da ƙyaƙyƙyawar zuciya badan jiran sakamako ba to lallai sai ya kasance mai tarin nasara a nan gidan duniya ko a lahira, karkaga ka wahala iya wahala a rayuwa baka samu nasarar sakamako irin na labarin novels ba ka ɗauka shikenan kai ka rasa, ɗan uwa/ƴar uwa! Kun manta akwai wata sabuwar rayuwar da tafi ta gidan duniya komai? Labarin littattafai misaline kawai wa rayuwa ake nunawa, Iyakar daɗewar ɗan adam a duniya shekaru ɗari ne kacal, amma ka tuna tun zamanin annabawa ake mutuwa, saika shekara talatin kacal a duniya ka mutu kaje kai shekara dubunnai a barzahu kafin a tashi kiyama, mi kake tunani a iya zaman barzahu kawai idan har baka aikata alkari ba a ƙanƙanuwar rayuwarka ta duniya😭, miyasa haƙuri da juriyar jarawar shekarun da bazasu taɓa haura ɗari ba, su gagareka jurewa? Miyasa daɗin da bai taɓa tsallake shekara ɗari na a duniyarka zai ruɗeka ka manta da dubbunan shekarun dake gabanka na barzahu kawai?, miyasa daɗin dake ƙalilan na duniya zai ruɗeka ka manta da ranar hisabi ranar da bata da kwatankwaci ko misali😭?, ranar rarrabe gaskiya, ranar tonon silili, ranar da uwa ke gudun ɗanta, ranar da ɗa ke gudun iyayensa, ranar da kanka kawai ka sani, ranar buɗe ɓoyyayun sirrika😭 (Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un) ƴan uwana! Ƴan uwana! Mi muke tunani haka da zurfine? Mi muke buri haka da yawane? Mi muke fatan samu haka da yawane? Mi muke ƙoƙarin mallaka haka da yawa ne? Mi yake canjamu haka da yawane? Mi yake ruɗarmu haka da yawa ne? Mi muke taƙama dashi haka da yawa ne? Da mi muka dogara haka da yawa ne? Suwa muke tunanin ko zaton sun tsaya mana haka da yawa ne? Ina mukabar imaninmu tafiya haka da yawa ne? Ina muka bar zukatanmu haka da yawa ne?😭😭.
“🙏🏻😭Ya rabbi ka gafarta mana badan halinmu ba”.
Umm-Ruman ta sake ƙanƙame Ahmad tana zirar da hawaye, jikinta na sake yin sanyi game da komai ma, shi kansa da yake maganar hawayen yakeyi......
“Abbu! Kuka kakeji?”.
Sukaji maganar Haysam a kansu a bazata.
Saurin sakin Rumana Ahmad yayi, ya goge hawayensa cikin dabara kafin ya duƙa gaban Haysam dan ya daidaita tsahonsa da shi, ya dafa kafaɗun Haysam ɗin yana murmushi.
“A'a Sadauki na, ba kuka nakeji ba, abune ya faɗamin a ido sai Ummineka take ciremin fa”.
Haysam yay shiru kamar ya yarda, sai kuma ya sake jehoma Ahmad tambaya,
“To Abbu itama ai naga ruwa na fita a idonta?”.
Kai Ahmad ya dafe, yasan Haysam yarone mai matuƙar wayo da basira, kullum ta ALLAH kuma ƙwalwar kansa faɗaɗa takeyi, ya sake girgiza masa kai, ƙasan ransa na tunanin wace amsa zai bashi ya huta.....
Durƙusawar da Rumana itama tayi kusa da shine ya sakashi kallonta, ta dafa hannun Ahmad dake a kafaɗar Haysam tace, “Babana tausayin Abbunka nefa ya sakani hawaye, kaga abu ya faɗa masa cikin ido, amma kuma sai yake gayamin naji tsoron ALLAH a duk inda nake, karna ringa shiga maganar manya, karna ringa shiga abinda ba'a sakaniba, karkuma na saɓama UBANGIJINA, idan nayi akan kuskure na nema gafararsa, dan dukkan mai saɓama UBANGIJI to ƙarshensa baya ƙyau, hakama mai saɓama iyaye baya gamawa da duniya lafiya, wuta ake sakashi, sannan MANZON ALLAH baya cetonsa a ranar kiyama.......”
“Ummie!” Haysam ya kirata cikin katseta.
Ta amsa da “Na'am Haysam”.
“Ummie ita lahirar to a ina take?”.
Kallon juna Ahmad da Umm-Ruman sukayi, sai kuma duk suka maida kallonsu ga Haysam ɗin.
Ahmad yace, “Lahira ba'a ganinta, sannan babu wanda zaice maka yaje ya ganota balle ya baka labarinta, sai dai UBANGIJIN al'arshi ya bamu labarinta a littafinsa mai tsarki na AL-QUR'ANI, a wajaje daban-daban, yayi mana bayanin abubuwa masu yawa da zasu faru a cikinta, duk wanda ya mutu a yanzu yana barzahu ne, sai ranar da za'a busa ƙahone kowa zai tashi yaga kansa a lahira, harda ƙwari da dukkan nau'in kowacce halitta da UBANGIJI ya taɓa rayawa a doron duniya”.
Nanma dai shiru Haysam yayi, dan maganganun sun masa girman da bai fahimci komaiba a cikinsu sai ƙalilan, kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru saboda chocolate ɗinsa daya hango, dama ita yazo ɗauka.
Jikinsa ya zame daga garesu yaje ya ɗauki abarsa ya dawo jikin Ahmad ya zauna yana bashi akan ya ɓare masa.
Amsa Ahmad yay ya ɓare masan, yana amsa ya miƙe yafice yana ƙwala kiran sunan Aunty Zainab.
Da ga Ahmad har Umm-Ruman ajiyar zuciya mai ƙarfi suka sauke suna kallon juna, Rumana ta kwanto jikin Ahmad shiko ya rungumeta.
“Abu Haysam!”
Ta kira Ahmad murya a narke.
Idonsa a kanta ya amsa da “Uhyim Umm-Haysam!”.
“Daga yau karmu sake ɓoye masa abu mai muhimmanci da ya shafi rayuwa ko addininmu, ƙwaƙwalwarsa a yanzu a wanke take, komi muka sanar masa zai zauna a cikinta, zama irin na har abada, zai kuma riƙesu a ransa su amfanesa harma da yaran da zasuzo a bayansa”.
Kanta Ahmad ya shafa tare da sumbatar laɓɓanta, sai ya zarce da kissing ɗinta, da ƙyar ta samu ta ture kansa tana faɗin, “Yaya wlhy yaronnan zai iya dawowa”.
Murmushi yayi yana lumshe idanunsa da har sun kaɗa sun canja launi.
★★★**★★★★★**★★★
Haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa, yau fari gobe tsimma, su Umm-Ruman anata karatu da rainon ciki, sunyi ƙawaye da suke ƙaruwar juna, kafin wani dogon zango larabci ya zauna raɗam a bakin Umm-Ruman.
Wannan cikinma ya sakata tayi ƙiba fiye da na Haysam, hakan yasa ta zama wata babbar mace ga ƙyawun da ya sakata, Ahmad kansa idan suna zaune bai gajiya da kallonta, kowane motsinta idonsa na kanta, ita harma kunya abin ke bata.
Ba kowa yasan Rumana nada ciki ba, dan Yaya Maryam tai gum da bakinta akan maganar, saboda gudun shaiɗancin su mama Gaje wadda tana gidansu kam cikin wani irin yanayi mai wahalar fahimta.
Suna waya da mutanen gidan kuma kullum babu fashi, sai dai yawan rashin lafiyar da takance tanayi wasu ke zargin ko cikinne.
A haka dai a kwana a tashi cikinta ya cika watannin haihuwarsa, wata safiyar Juma'a ta tashi da naƙuda, Ahmad na ƙoƙarin shirin yin massalaci dole ya ajiye ya kira Gaddafi suka ɗauketa a motarsa harda matar Gaddafin suka nufi asibiti.
Suna isa ma akaga haihuwar ta rigada ta taho gadan-gadan, dan danan aka shiga bata taimakon gaggawa.
Wannan haihuwar Rumana taci wahala, kafin ALLAH yasa ta sunkuto ɗanta namiji mai kama dasu sak.
Murna wajen wannan ahali ba'a magana, kafin su baro asibitin har labari yakai Najeriya, kowa yanata mamakin wannan al'amari tunda dai ba'asan Umm-Ruman nada cikinba hasashene kawai wasu keyi.
Hotunan yaro kam sunata yawo a wayoyin ƴan uwa, anatama juna barka da arziƙi.
Bakin Ahmad kam ai yaƙi rufuwa, ita Rumana ma har mamaki take, sai kace yaune aka fara masa haihuwa.
Kasancewar jikinta Alhmdllh zuwa safiya aka sallamesu suka koma gidansu, Jiddah matar Gaddafi ita ke tsaye akan Rumana da komai, sai wata dattijuwar balarabiyar ƙasar Morocco da suke a ɗayan sashen gidan, itama taketa gyara Rumana tamkar ƴar uwa ta jini, dacan sukan gaisa, idan taga Haysam taita jansa, wani lokacinma jikokinta kanzo su ɗauki Haysam ɗin. to amma wannan haihuwar ta Umm-Ruman sai ta sake ƙarfafa zumincinsu sosai fiye da da can.
Tun randa Ruman ta haihu Ahmad yayma yaronsa huɗuba da suna Yusha'u, sunan ƙanin babansa, kuma mahaifin Umm-Ruman, zasu ringa masa alkunya da *_Abu-Talib_* Uncle ɗin MANZON ALLAH (S.A.W).
“To sai muce ALLAH ya raya Abu-Talib”.
Ba'ai wani taron sunaba, amma dai sunɗanyi walimar cin abinci ta abokan Ahmad na karatu dana Gaddafi, sai maƙwaftansu.
Hakama ƙawayen su Umm-Ruman na makaranta sunzo suma.
Jama'ar gida nata ALLAH ya raya mai sunan baba Yusha'u.
Haka Rumana taci gaba da rainon yaronta Abu-Talib tare da karatunta, shima yaron dai masha ALLAH, yana kama da Haysam, rayuwa ta cigaba da shuɗawa komai na sake cigaba gasu Rumana, rayuwar gidansu abin sha'awa da burgewa, hakama ƴaƴansu kamar ka sace ka gudu, idan saɓani yazo a saɓa, a kumazo a fahimci juna komai ya wuce.
Kafin wani dogon zango Abu-Talib ma ya kai girma, shima Rumana ta yayesa ba tare da Ahmad ya saniba, dan tasan zai iyayin faɗa.
Ranar da akai yayen gudunma kar yay mata kuka ta banka masa maganin barci tace mura yakeyi, da yake Ahmad a gajiye yake daga makaranta sai bai kawo komai a cikin ransaba ya yarda, washe gari ma haka taima Abu-Talib, sai da ta jera kwana huɗu tana haka, ta dai fahimci yaron ya ɗan manta da nono sannan................✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻[8/30, 3:10 PM] Nadady: *_GDW_*
*_8448_*
...........Sai a ranar da Abu-Talib ke cika sati ɗaya da yaye Ahmad ya fahimta, kasancewar Juma'a ce babu makaranta, sun dawo daga massallaci shi da Haysam sai yayo musu tsaraba irin ta yara, to anba Abu-Talib nashi amma kuma na hannun Haysam yakema zari, dan haka yaketa ƙoƙarin kwacewa, shi kuma Haysam ya hanashi.
Su dai su Rumana na kallonsu suna dariya, saboda yanda ake kicimillin rigimar dolene kai dariya, Abu-Talib akwai rigima, ga zafin nama na hanzari da ALLAH yaba yaron, ko zazzaɓin haƙora yake inba yakai matukar kaisa ƙasaba, baya hanashi yin wasa, sai dai su suyita jin tausayinsa. Zainab kuwa tana ɗaki kwance tasha magani saboda zazzaɓi da takeyi.
Can rikici yay rikici Haysam yaji zafin tsole masa ido da Abu-Talib yayi wajen son amsar abun hannunsa, shi ko ya tureshi ya faɗi, aiko ya fashe da kuka dan yaji haushi.
Rumana ta ɗauki Abu-Talib ɗin tanama Haysam faɗan abinda yayi.
Ganin yaƙi yin shiru bisa lallashin da Ruman ke masa Ahmad yayma Rumana magana akan ta bashi nono mana ƙila yay shiru.
Murmushi kawai tayi tana cigaba da lallashin Abu-Talib.
Ahmad da yay zaton batajisaba ya sake maimaitawa, nanma sai tai murmushin tana faɗin “Karka damu Yaya zai shiru, ya riga ya girma da nono ai”.
Da mamaki yake kallonta, tare da nuna alamun bai fahimceta ba.
Yace, “Wai kina nufin mikenan? yayesa zakiyi?”.
Tace, “Ai nama yaye ɗin”.
Ahmad yay masifar tsura mata idanu, sai dai fuskarsa ta nuna alamun ɓacin rai, hakan yasa Rumana da ta fahimta sai ta ɗauke kanta, dan tasan dama za'ayi hakan ai inhar ya sani, ko na Haysam ma dan baya ƙasarne.
Baice mata komaiba a lokacin, sai dai kuma hirar da akeyi yabar yinta, daga ƙarshema ya ɗauki Haysam ɗin tare da amsar Abu-Talib da ga hannunta suka fice.
Ajiyar zuciya ta sauke tana girgiza kai, ita dai bataga abin fushi ananba ai, shekara ɗaya da wata bakwai miye laifi idan ta yaye Abu-Talib dan ALLAH?.
Bata da mai bata amsa dan haka ta share ta cigaba da harkokin gabanta kawai.
Tun tana tsammanin dawowarsu kusa har magriba babu labarinsu, ta taso Zainab dake kwance saboda magriba.
Haka tai zaune ita kaɗai shiru har tara na dare, dan Zainab ma ta sake komawa ta kwanta.
Tana shirin barci suka shigo, ya kwantar da Abu-Talib dake a kafaɗarsa yana barici, Haysam kam ido ras, sai zuwa yay ya rungume ƙafafun Rumana yana fadin, “Ummie oyoyo”.
Juyowa tai tana murmushi, tace, “Babana kun dawo?”.
Tai maganar tana satar kallon Ahmad da ke ƙoƙarin shiga toilet fuska babu walwala..
Haysam kuwa na ƙoƙarin bata amsa, da labarin inda sukaje.
Sam hankalinta baya a kan yaron har Ahmad ya fito, yazo ya ja Haysam ya cire masa kayan jikinsa sannan ya ɗaukesa zuwa bathroom, tana nan zaune suka fito yayi masa wanka, ita dai batace komaiba harya gama shiryashi ya tafi kaisa ɗakin Zainab inda yake kwana yanzun.
Yaɗan jima kafin ya dawo, tasan yanacan yana lallaɓa Haysam yay barcine.
Ita kuma lokacin tanama Abu-Talib wankane yana kuka, ta kammala ta fito tai masa shirin barci shima ta bashi tea, ƙinsha ma yayi, data fahimci a ƙoshe yake saita ƙyalesa kawai ta kwantar dashi.
Alokacin ne Ahmad ya dawo ɗakin, nanma ɗindai bai kalli inda takeba, ita dai ta daure ta tambayesa ko akwai abinda yake buƙata?.
Sai cayay mata a'a.
Shiru kawai tai tana kallonsa, ya shiga bayi yayo wanka ya fito yay shirin barci, har lokacin idonta biyu kuma tana zaune.
Koda ya kammala shirinsa sai ya kwanta tamkar baisan tanayiba.
Zuwa can itama ta gaji da zaman da tunane-tunane ta matsa jikinsa ta kwanta tana gyara musu bargo.
Ahmad najinta amma sai baiyi ko motsiba, tai guntun murmushi kawai tana lumshe idanu, hannunta nakan ƙirjinsa tana yawo dashi.
Tace, ”Haba Zumana, minayi haka da zafi ake irin wannan fushin dani ne wai?”.
Shiru yay mata tamkar bai jiba, bata gajiba dai ta sake maimaitawa, nanma yay shiru, itako bata fasaba ta cigaba da neman harmutsa masa tunani.
Da Ahmad fa yaji yana neman hawa Network gashi yana fushi sai yay saurin riƙe mata hannu, “Miye haka wai Ruman? Ki barni barci nakeji”.
“Yaya ya za'ai na bari bayan kana fushi dani? Yanzu yayen da nayi shine laifi dan ALLAH?”.
A matuƙar fusace ya juyo gareta yana faɗin, “Okey bama abune mara ƙyauba kikayi? Yanzu ace Umm-Ruman ina cikin gidannan harki yayemin yaro ban saniba? Duka shekararsa nawa? Ɗaya fa da wata bakwai, saurin mikikeyi da bazaki barshi ya cika shekara biyunba? Okey ke yanzu kin girma ko? Duk abinda kikaji yuwuwarsa cikin rai baƙya buƙatar kowa a cikinsa, hakafa kika yaye Haysam ban saniba, nai miki shiru a lokacin shine yanzuma kika sake saboda kin gama rainani ga sa'anki ko......?”
Innalillahi kawai Rumana ke ambata, ganin yanda ya birkice da masifa tamkar ba shiba, akan ƙanƙanin abunda ita bata kallesa wani abun kirki ba.
Sai da ta bari ya gama sannan, ita dai batace uffanba, ranar ma kwanciya kowa ƙarshen gado yay barci, tasan ko haƙuri ta bashi sai dai ta sake tunzurashi yay sama, to garama tai shiru da bakinta yafi alkairi, idan ya huce daga baya ta bashi haƙuri.
Da safe kuma yay ficewarsa makaranta bayan yasan tana kicin tana ƙoƙarin haɗa musu karin kumallo.
Koda ta fito taga ya fita hakan ya mata bala'in ciwo a rai, har ƙwalla tayi, ita dai wannan saurin fushin na Ahmad bata sonshi sam wlhy, gashi da mitar fushi, idan yay zuciya takan jima bata shawo kansa sun dai-daitaba, danma dabarun da Iya ta bata tana ƙoƙarin aiki dasu, dan lokacin bikin su Fa'iza da suka ɗan daɗe a gida akwai randa Haysam ya faɗo daga kan gado yana barci, ita dai tasan a tsakkiyar gado ta kwantar dashi, yaronnan wajen mirgina-mirgina ya dawo gefe, daga ƙarshe ya faɗo ita kuma tana waje suna hira da iya, tofa sai faɗowar Haysam tai dai-dai da shigar Ahmad ɗakin, ya nufesa da gudu ya ɗaukesa, yaro yayta kuka, iya ta amshesa tana dudduba jikinsa sai ta fahimci yaji ciwone a hannu, ta kaisa wajen Malam ya duba sai ya tabbatar ciwo yaji, a take malam yay masa gyara saboda ya iya, aka sakamasa magani. To aiko wannan lamari ya zafi Ahmad, danshi a ganinsa laifin Rumana ne data kwantar da Haysam a bakin gadon saboda sakaci, haka ya zauna ya zazzaga mata masifa a ɗaki daga ƙarshe ya koma fushi, Rumana taci kukanta a ɗaki ta share hawaye, kwana biyu basa kula juna Iya na lure dasu, sai dai yanda basu faɗaba itama bata tankaba, sai aranar na ukune suna gab da komawa Porthercout Iya ta zaunar da Rumana tana koya mata dabarun zama da Ahmad ɗin. ta kuma tabbatar mata mafi yawan halayyar Ahmad ya samosune daga kakansu Malam Rabi'u mijinta, shiyyasa idan Ahmad ɗin na abu takan tuna ƙuruciyarsu da Malam sosai. Umm-Ruman taji daɗin wannan shawarwari na Iya, da sune kuma take samun damar fuskantar Ahmad ɗin a duk lokacin da yayisa.
Itama kasa cin komai tayi, sai Haysam da Zainab ne sukaci, shima Abu-Talib ta bashi nashi da yake iya ci sannan sukai shirin fita.
Kwana biyu yana haushi da ita, a na ukun kuma ta ƙara durƙusawa har ƙasa ta bashi haƙuri tana hawaye da amsar laifinta.
Sai da taita masa magiya kafin ya nuna ya haƙura tare da mata gargaɗi sosai akan karta sake.
A take ta rungumeshi, daga nan aka canja tasha zuwa wadda tafi ƙarfina🥱🤫.
“Dama ance faɗan masoya hutu😂⛹♀”.
***********************
Rayuwa ta cigaba da shuɗawa su Rumana ana shekara ta Uku a makaranta, yayinda Ahmad yaketa ƙoƙari akan nasa karatun shima, dan haka sam baya wasa da damarsa.
A lokacin shima Abu-Talib an sakashi a makarantar su Haysam, hakama Subayya ɗiyar Gaddafi, yanzu hakama Jiddahn ciki gareta tsoho itama.
Bayan shuɗawar wasu watanni Jiddah ta haihu namiji, su Rumana akasha hidima.
Itama babu jimawa sai ga wani cikin, nanma dai Ahmad yata murna tamkar ya goyata, inda itakam bataso cikinnan yanzuba kodan karatunsu da ya ɗauki zafi yanzun, amma sai bata nunaba ta godema UBANGIJIN da ya bata, dan inharma Ahmad ya fuskanci hakan daga gareta lallai zasuyi uwarwatsine kawai..
Haka dai ta cigaba da rainon cikin nan, da sauƙi shi bai cika bata wahala ba, sai dai yawan son abu mai sanyi da takeyi.
Zainab ma ta cigaba da karatunta a sashen lafiya a wata makaranta dake Riyadh, dan haka acan take zaune gidan wani abokin Gaddafi balarabe ne shima da matarsa ɗaya da yaransu biyu, su ƴan asalin ƙasar Saudiyya ne, yanzu idan ka ganta wajen su Rumana weekend tazo ko hutu, weekend ɗinma hanata wani lokacin Ahmad yakeyi.
________________________________
A kwana a tashi shekaru sukaita shuɗawa tamkar almara, kafin wani dogon zango abubuwa da yawa sun faru.
Bayan shigewar shekaru huɗu da tai dai-dai da cika shekarun su Rumana bakwai a saudiyya, Ahmad kuwa takwas.
A yanzu yaransu uku duk maza, dan cikin da Rumana ta sake haihuwa shiɗinma dai namiji ne, wanda yaci sunan Baba Ilyasu shima, suna masa alkunya da suna *_Abu-Turab_*, sosai yanzu Rumana ke sha'awar ƴar budurwa, musamman idan Subayya tazo musu weekend, wato yarinyar Gaddafi.
Abubuwa da yawa sun faru na cigabansu, karatunsu da duk suka kammala har Zainab, tare da gurbin aiki da ma'aikatar tace man fetur ta ƙasar Saudiyya taba Ahmad, sam baiso hakanba, dan ƙasarsa shima yake burin zuwa yayma hidima, amma sun ko dage suma sai yayi musu aiki na adadin wasu shekaru kafin su sallamesa.
Da farko yayi takaici, amma da Gaddafi yay masa nasiha akan ya ɗauki hakan shine mafi alkairi a rayuwarsa sai hankalinsa ya kwanta..
Da kuma ya sanarma Baba duk suka sanya albarka a cikin lamarin.
Rumana ma sun kammala karatunsu, amma tanason cigaba saboda daɗin da yay mata, hakama Zainab ta kammala, tanason cigaban dai itama, amma Ahmad yace saita samu miji ya aurar da ita inma zai aminta da cigaba da karatun nata.
To da yake akwai wani abokin karatunta da suke lobewarsu, ɗan asalin ƙasar Eygpt, amma haifaffen nan Saudiyya ne, mahaifiyarsa kuwa ƴar asalin ƙasan Nageriya ce, sunansa *Akeem*, sai kawai ta gabatar dashi garesu.
Ahmad da Rumana sun masa tarba ta mutunci, sun kuma yaba da yaron. sai dai Ahmad yace sai yayi bincike a kansa, idan yaga babu wata damuwa zai kai maganar gida kafin a yanke hukunci.
Daga nan suka fara shirin zuwa Nageriya ganin gida a karo na farko, wanda yay dai-dai da taron bikin Mudanseer da za'ayi.
A yanzu kam kowa yaga Umm-Ruman yasan na gaba yay gaba na baya sai labari, ta ko ina ta zama cikakkiyar mace kamila wadda a kowane irin taro zata iya bugar ƙirji ta kira kanta macen, balle a tsakaninnan da take ɗauke da wani yaron cikin maƙale a mararta, duk da dai ita kaɗai ta fahimci tana da kayanta, dan ko Ahmad taƙi sanarmawa.
Haysam ɗan saurayin yaro abin sha'awa da so ga kowa, a yanzu yanada shekaru takwas da wasu watanni a duniya, yaro mai matuƙar hazaƙa da haƙuri, sam bashi da kwaramniya, ɗabi'un ƴaƴan farin dai na tare dashi.
Sai Abu-Talib manyan ƙasa, kamaninsa da Haysam sun sake fitowa matuƙa, a yanzu yana da shekara biyar da wasu watanni shima a duniya, akwaishi da wayo ga ƙiriniyar masifa, jan faɗa da rashin barin saita kwana kam ai ba'a magana, akwai zuciya irin ta mahaifinsa tattare dashi sosai, dan a hallaya kam ba'a cewa komai wajen gadon Abbunsu, shima ALLAH ya bashi hazaƙar karatu, ga ƙulafucin iyaye, ko yaya Abbunsu bai dawo gida da wuriba yata tambaya kenan, “Ummie ina Abbunmu? Yaushe zai dawo? Ko miyasa bai dawo ba? Kira manashi a waya muji ya taho?” wani lokacin tun tana jurar bashi amsa har taji haushi tai masa banza, idan kuwa Zainab ta kira waya lokacin tana makaranta aka bashi su gaisa yata mata rigima kenan akan ta dawo gida, sai dai taita lallashinsa har a rabu lafiya.
Sai Abu-Turab, ɗan gatan Aunty zee kenan, autan Ummie kuma, duk da dai Ahmad yace shi autansa kam akwai yayu kamar shida a gabansa ma kafin yazo, dan haka da sauran aiki Rumana ta sake zage damtse😅, a yanzu shima yana da shekara Uku da wasu wattani a duniya, shima dai akwai wayon, sannan babu ragi, dan faɗa shi da Abu-Talib kullum ne babu fashi, kowa yana fama da zuciya, shima dai akwa wayo, ga surutu a bakinsa ko tsuntsun akku ya shafa masa lafiya, shifa komansa a rayuwa Aunty Zee, ko abu ya samo aunty Zee ce mai ɓoye masa, idan abun daɗi yaci ya rage zaije ya ɓoyema aunty zee ɗinsa, shima dai suna shirin sakashi makaranta kwannan nan, dan Islamiyya kawai yake zuwa, so Ahmad yake sai sun dawo ganin gida sannan a sakashi.
Sai uwar ƴaƴa Zainab, ta zama budurwa cikakkiya, asalin ƙyawun runawan nan na ɗawainiya da ita, hakan yasa take ɗaukar hankalin ƴaƴan larabawan nan, dan irin fatar su Ahmad tana da birgewa ga ko farar fatane, Zainab akwai tsiwa, amma hakan bai hanata tashi da nutsuwa ba, dan Ahmad da Rumana basuyi wasa da tarbiyyar Zainab ba, da iyayensu suka danƙa musu amana, a yanzu haka tanada shekaru ashirin cif a duniya, ga yanayin garin ya karɓeta, tako ina ta zama cikakkiyar mace abin buƙatar kowanne ɗa namiji.
Sai fa mai gayya mai aiki, Alhajin ALLAH, kamilin namiji kainuwa dashen ALLAH, wato dai angon Umm-Ruman nake magana Amadidin Ayyah Abbun Haysam da su Abu-Talib, yayan Zainaba kuma ba😉, lallai Ahmad kam yanzu ya kama ƙasa, bawai a dukiya nake maganaba, a cigaban rayuwa mai albarka da buƙatar dukkan namijin ƙwarai, dan dukiya dai ba itace mutunci ba, har yanzu Ahmad ba hamshaƙin mai arziƙi bane, yana rayuwarsane a tsaka tsaƙi, cikin rufin asirin ALLAH, zai iya ɗaukar dukkan ɗawainiyar iyalinsa harma data danginsa gwargwadon iko, sai dai bai tara ƙazaman kuɗaɗen dake jibge a bankunaba, sannan bai tara motocin da suka cika harabar gida ba, har zuwa yanzu bai da gidan kansama, dukda dai ya shirya wani gagarumin surprise ga Umm-Ruman wanda bai taɓa sanar Mataba koda a labari.
A yanzu haka an bashi gida da motar hawa a wajen aikisa, sannan za'a ɗauki nauyin karatun yaransa biyu, wato dai Haysam da Abu-Talib, ranar da wannan abin alkari ya riskesu har hawaye Ahmad yayi, yama rasa yanda zai kamanta farin cikinsa, UBANGIJI ya masa komai a wannan rayuwar, dan ko ilimin da ya azurtashi dashi kaɗai ya isar masa abin alfahari duniya da lahira.
Ga matar ƙwarai da ALLAH ya bashi, wadda tasan darajarsa da mutuncinsa, ga ƴan yaransu abin sha'awa da birgewa ga kowa, ya sauke nauyin buƙatun ahalinsa masu yawan gaske musamman akan karatun ƙannensa masu tasowa, ga harkar kasuwancinsu kullum sake haɓaka take shi da Gaddafi, hakama na wajen Nura komai yana tafiya Alhmdllh.
Cikin farin ciki suka tattara suka koma sabon gidansu da suka samu rakkiyar abokan arziƙi da suka tara anan ƙasar Saudiyya, ga kuma waɗanda suke kallo ƴan uwansu da basu da kamarsu, Gaddafi da matarsa Jiddah.
Gidane da ya amsa sunansa gida, ga motar hawa da dukkanin abin buƙata a ciki, su Abu-Talib sai tsalle suke an dawo sabon gida, ballema ga wani ɗan lambun hutawa a gefe da aka shirya wajen wasan yara a ciki, hakan ba ƙaramin ɗaukar hankalinsu yayiba ainun.
Anan dai cikin birnin Dhahran ɗinne suka sake samun wannan sauyin rayuwa, sun tare da sati guda suka shirya zuwa makkah domin yin Umrah ta kwanaki goma.
Duk da kuwa basusan adadin Umrah da sukaiba a rayuwarsu cikin shekarun da suka tsinci kansu a saudiyya, aikin hajji kuwa tunda sukazo saudiyya basu taɓa fashin yinsaba duk shekara, tanan nema suke haɗuwa da ƴan ƙasarsu harma da waɗanda suka sani jefi-jefi, dan akwai wani Alhaji ɗan anguwarsu da Ahmad ɗin ya taɓa gamo dashi, lokacin Ahmad na cikin tsananin rayuwa da neman kuɗin karatunsa har neman taimako ya taɓa zuwa wajen Alhaji, amma a wancan lokacin sai ALLAH bai cida Alhajin nan ya taimaki Ahmad ba, Ahmad ya baro gidan da ɓacin rai saboda korar kare da matar Alhajin tai masa, sai gashi yau kwatsam sun haɗu a saudiyya, shi Alhajin ma bai gane Ahmad ba, amma shi Ahmad ya ganesa, dan haka ya gaishesa kuma ya bashi sani, duk da bai tuna masa da wancan batunba yadai kwatanta masa gidansu. Cikin ikon ALLAH kuwa Alhaji ya gano mahaifin Ahmad ɗin harma da abinda ya taɓa masa a wancan shekarun.
Bayan an kammala aikin hajji kafin lokacin komawarsu Ahmad ya ɗaukesa ya kaisa har gidansa, suka karramashi da tarba ta mutuntawa, hakan ya sosa zuciyar Alhaji har ya gaza haƙuri yayta neman gafarar Ahmad, murmushi kawai Ahmad ɗin yayi yace dan ALLAH subar zancen ya wuce, kowa kuma ai yasan ajizanci na ɗan adam.
Sosai Alhaji yaji daɗin wannan karamci na Ahmad, da ya koma gida Nageriya kuwa har gida yaje yayma su baba alkairi ya kuma basu labarin karramawar da Ahmad yay masa a saudiyya, yayta bama mutane labari kuwa, tun daga wannan lokacin zuminci ya ƙullu tsakaninsa da su baba mai ƙarfi, har takai ya ɗauki su baba su duka ya ɗorasu akan wasu harkokins, dukda basuyi karatun bokoba bazasu cutuba wajen tafi dasu.
“Wannan ma nasarace da Ahmad bazai taɓa mantawa da itaba a rayuwa”.💪🏻😌
Bayan kammala Umrah suka koma Dhahran, kwanakinsu takwas da dawowa suka kammala shirinsu na tafiya ƙasarsu ta haihuwa tsaf, Zainab da Umm-Rumana sai murna suke, suko su Haysam dai suna murnar za'aje anguwane kawai, amma basusan ainahin inda za'aje ɗinba, dan Haysam ya manta da Nageriya kasancewar sanda suka barota bashi da wani cikakken wayo............✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
[8/30, 3:10 PM] Nadady: *_94_*
..............Ɓangaren Ma'aruff abubuwa sam babu daɗi tsakaninsa da Mufida, dan tun bayan barin Samina gidan suka dawo gida zaman lafiya ya gagara a tsakaninsu saboda videos ɗin da aka fidda na abinda ya faru tsakaninsa da Samina.
Asiri yana ɗawainiya da Ma'aruff sosai, hakan yasa yake masifar tsoron Mufida, a lokacin taso ƙwarai da gaske su rabu, sai dai iyayenta suka tsawatar mata saboda akwai wata manufa a ran mahaifinta, duk da mahaifinta ƙanin maman Ma'aruff ne bashi da wani buri da ya wuce ya mallake company ɗin su Ma'aruff ɗin, bayan rasuwar mahaifin su Ma'aruff yaso ya tattare dukiyar yaran ya riƙe a hannunsa akan shi ne zai kula musu tunda dai mahaifiyarsu macece.
Amma sai sam taƙi aminta da hakan, dan gudun kar a salwantar da dukiyar marayu, a lokacin shi ma'aruff yana Germany yana karatu, ya kammala degree ɗinsa na biyu zai tafi na uku ne ta matsa masa akan ya dawo gida dole, yabar karatun wanda yayi ya wadatar.
Badan Ma'aruff yasoba ya dawo Najeriya, daga nan ta danƙa masa dukiyar a hannunsa, shi kuma sai ya gyara company mahaifin nasu na yin takalma kawai aka cigaba da harka.
Wannan al'amari yayima mahaifin mufida ciwo a rai, amma sai ya danne, kullum dai yana neman hanyar da zai mallaki dukiyar har zuwa yanzun, bayan auren Samina da Ma'aruff ya fahimci ƴar uwarsa bata ƙaunar matar ɗansa, dan haka yayta sake tunzurata a ƙiyayyar Samina, yana cusa mata son haɗa zuminci tsakanin ɗiyarsa da Ma'aruff.
Tun abin bai tasiri ga maman su Ma'aruff ba har taji ta aminta saboda basu barsu hakaba, dan bin bokaye wajen maman mufida lamarin sai dai gyaran UBANGIJI, hatta da videos ɗinnan ƙanin Mufida ya sakesune da gayya saboda Samina ta barma ƴar uwarsa gidan, tunda shima yasan dukiyar Ma'aruff mahaifinsu ke ƙulafuci, idan kuma an samu shine zai mora tunda shine namiji babba a gidansu.
Rikicin dake yawan faruwa tsakanin Ma'aruff da Mufida ne ya nema fara susutar dashi, dan sai shan giyarsa ta ƙaru fiye da da, da yake ALLAH ba azzalumin sarki bane sai kuma ya koma begen Samina, da yasha yay ɗaɗil sai yayita ambatar sunanta a cikin shirmen surutansa na maye.
Maman Ma'aruff sam batasan mike faruwa ba, tana can ta saki baki akan tunda Ma'aruff ya rabu da Samina maƙiyiyarsu shikenan ya samu salama a rayuwarsa kenan, yanzu zasuyi zama na arziƙi da ƴar uwarsa.
Sai dai hankalinta ya fara tashine ganin kusan sati uku Ma'aruff bai zo inda takeba, al'halin baya iya kwana uku baizo gidanba.
A lokacin ta danne abin a ranta da tunanin ko ruɗanin tsiyar da Samina ta tafka musune bai sakesuba, tare da videos ɗin dake yawo yakema kunyar zuwa gidan.
Kwanaki sun sake shuɗawa, har kusan sati na shidda babu Ma'aruff babu dalilinsa, ranar wata asabar sai gashi yaje gidan, hankalinta yay masifar tashi da yanda ta gansa, dan ya rame sosai yayi baƙi.
Zaunar dashi tai tana jera masa tambaya akan mike damunsa?, amma sam ya kasa faɗi mata komai, ganin bazai sanar mataba sai ta haƙura, dan a tunaninta dai wancan abunne ke damunsa har yanzun.
A ranar ya wunine anan gidan, ba komai ya kawosaba kuma sai umarnin Mufida akan yazo ya ɗauka mata takardun company ɗinsu, to amma da yazo ya rasa hanyar da zaibi ya ɗauka, dan suna ɗakin mamansune, shikuma ba shiga ɗakin yakeba sai da dalili.
Har dare bai samu yanda yake soba, maman kuma ta sakashi ya tafi gida dole harda bada abu a kaima Afrah, tunda ita batasan dawan garinba.
Tunda ya shigo gidan Mufida taga babu takardun ta hausa da masifa kamar uwarsa, yay shiru kawai yana kallonta, daga ƙarshe ya koma bata haƙuri, amma taƙi koda saurarensa, ganin abin zaiyi yawa sai yay ɗan irin buɗe mata wuta ɗinnan wai ko zataji shakkarsa ta saurara masa, dan duk tsiya da zagin da take masa maigadi na jiyosu.
Aiko sai saukar mari yaji a fuskarsa, ya dafe kunci yana kallonta da ɗunbin mamaki, “Mufida ni kika mara?”.
“An mareka, ko zaka ramane?! Wawa da kai lusari, kana abu tamkar ba namijiba, ɗakko takardu su gagareka a cikin gidanku......”
Raɓata yay ya wuce bai iya sake magana ba, ransa a ɓace ya shige sashen da Samina ta zauna, dukda har ya fara ƙura haka ya faɗa cikin kujera ransa na masa zafi, bai san miyasaba idan yana gaban Mufida bai iya komai a rayuwarsa, sai yabar inda takene zai dingajin ciwon abinda take masa, ya kai dubansa ga kwalaben giyar da ya baza a falon na Samina kaca-kaca, cikin rawar jiki ya miƙe, inda ya ajiye kwalayen giyar kusan biyar ya nufa, ya ɗakko biyu ya dawo ya zauna, ransa na masa zafi ya ɓalle ya hau kwankwaɗa.
Sai da ya jisa mankas sannan ya zube a wajen yana surutai da zagin Mufida tare da begen Samina.
★★★★★★★
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya abubuwa nata sake tsauri tsakanin Ma'aruff da Mufida, kullum tana aikashi ya ɗakko mata takardun Company ALLAH bai bashi ikon ɗakkowaba.
Yanda take matsa masa akan waɗannan takardu haka mahaifinta ke matsa mata itama.
Abu kamar wasa watanni suka shuɗe shekara ɗaya ta kusan haɗuwa, zuwa lokacin hankalin momin su Ma'aruff yakai ƙololuwar tashi da canjawar Ma'aruff ɗin, dan takai hatta da aiki yanzu Ma'aruff sai ya gadama yake zuwa, al'amuran Company sun fara taɓarɓarewa.
Ranar dai tai shiri da kanta tazo gidan, a lokacin Ma'aruff na sashen Samina yayi mankas da giya, da wannan damar Mufida tai amfani ta ƙalama Ma'aruff sherin wajen mahaifiyarsa, ta nuna dai duk wannan abu da yakeyi akan Samina na ne, nan take Mamansa tace ai asiri iyayen Samina sukaima Ma'aruff.
Aiko ta kira mahaifin Mufida ta sanar masa, koda yazo gidan shima sai ya nuna shiga tashin hankali kamar gaske, ya kuma zugata akan suje su saka ƴan sanda su kama iyayen Samina.
Babu musu ta yarda da wannan shawara, sukaje kuwa police station suka kai report, ƴan sanda sunji kuɗaɗe babu wani bincike suka nufi gidansu Ahmad, sai dai koda sukaje an sami akasi, dan a ranar su baba duk basa nan, suda matan gidan duk suna Shema wajen biki, su Mudan ne kawai a gida.
Koda ƴan sanda suka sanarma Mudan dake shago yana ɗinki abinda ya kawosu tsabar iya shegensa sai ya turasu gidan inna mari akan cewar ai iyayen Saminar yanzu sunbar gidan sun koma can.
Ƴan sanda babu man kai suka yarda😂, suka kuwa kwashi ƙafafunsu sai gidan Inna mari bisa kwatancen da Mudan yay musu.
Koda suka isa gidan Maman Ma'aruff taci karo da Inna mari bayan sunyi sallama ta fito dan taga wanene sai cewa tai “Yauwa yallaɓai ga kakarta nan, ku haɗa da ita”.
Inna mari na tambayar ba'asi aka cukuykuyeta zuwa cikin motar ƴan sanda, sannan suka kutsa kai suka tattaro Mama gaje dake tsakar gida zaune zataci abinci, iya kuwa ta fita sayo waken ƙosanta na gobe.
Itama dai kwasarta sukai sai cikin mota, duk da roƙon da take musu da tambaya sunƙi saurarenta.
Babu tausayi babu imani mahaifin Mufida yasa aka jibgi su Inna mari duk da tsufanta, sai da sukai musu lilis sannan suka barsu.
Iya na dawowa ƴan anguwa suka sanar mata abinda ya faru, nan take ta rikice tahau kuka, ta saka aka kira mata ƴarta a waya ta sanar mata komai, hankalinta tashe tazo gidan ita da mijinta, haka suka bazama neman station ɗin da aka kai su mama gaje tare da ƙanin mama gajen shima isa, amma basu samuba har dare, dole suka dawo gida.
Washe garima haka sun fita bin stations suna tambaya, amma duk inda sukaje sai ace ba nanbane, har inda aka kai su inna mari sunje amma ance ba nan bane, a kwana na huɗu sukaga abin yafi ƙarfinsu sukaje suka faɗa gidansu Ahmad.
Shi Mudan ma ya manta da anyi abun, dan bai sanarma kowaba, koda suka dawo daga Shema, sai randa su Iya sukazo.
Kai tsaye Baba Yusha'u yace shikam babu ruwansa, dan baida alaƙa dasu yanzu kam.
Baba Hamza ne ya tsawatar masa akan wannan furuci, ta ya zaice baida alaƙa da mama gaje bayan gasu binta, dole Baba Yusha'u yay shiru.
ALLAH sarki Baba Hamza, haka ya tasa ƙeyar Madan gaba akan suje su bincika suma, su Iya kuma suje gida su huta, amma sai sukace karya damu suje taren kawai.
Da farko Mudan yaso yin yawo da hankalinsu, to amma da ya tuna dashi za'asha wahalar, ga kuma dinkuna jibge a shago suna jiransa ga zuwa makaranta sai kai tsaye ya rakasu station ɗin da yake da tabbacin su Mama gaje nacan, amma a zuwan dai bashi da tabbas dan kar baba yaci ƙaniyarsa.
Suna isa kuwa suka iske maman Ma'aruff a wajen.
Su baba sunsha wahala kafin a basu su inna Mari, dan sai da ya saka Mudan ya kira Ahmad a waya suka haɗashi da d.p.o din wajen, baisan mi Ahmad ɗin ya faɗa ma d.p.o ɗinba ya yarda, kuma da yake shi baba tare sukazo a wancan lokacin da aka rufe Samina akan faɗansu da Basy sai d.p.o ɗin ya sake aminta da maganar da sukai da Ahmad, nan take ya bada belin su Mama gaje.
Hankalin su Baba ya tashi ganin yanda aka fiddo su Inna mari, jiyay ƙwalla sun cika masa idanu, harya kasa haƙuri sai dai yayma dpo ɗin ƙorafin irin wannan duka da sukaima mata haka, matanma tsoffi kamar waɗannan, musamman ma Inna Mari.
Dpo yayta bama Baba haƙuri akan wlhy shi bayanan komai ya faru, hasalima baisan halin da su Inna Mari sukeba sai yanzu, yay taima ƴansandan da sukai abin faɗa tamkar zai cinyesu ɗanyu.
Su dai su baba sun kwashi su mama gaje zuwa asibiti kamar yanda Mudan ya bada shawara, dan tausayi suka koma bashi, harma yay dana sanin bai tura ƴan sandan can gidanba.
A asibiti sosai su Inna mari sukaji ciwuka, gashi duk sun galabaita, dole dai aka basu gado, tare da taimakon gaggawa, komai Mudan ne ya biya na asibitin, dan sai da aljihunsa yay kankat harya haɗa da cin bashi.
An kwantar dasu tsahon kwana uku kafin a basu sallama.
Daga Mama gaje har inna mari sunsha kuka bisa wannan tashin hankali, dan tun daga wannan lokacinma dai Inna mari lafiya ta gagareta, sai da ta kaita da kwanciya cutar ajali, haka zataita rusar kuka da sambatu, tare da kiran sunan Samina ta yafe mata, sai dai ina Samina batajinta, hasalima tana ɗaya daga cikin waɗanda Saminar tafi tsana a yanzun a duniya.
Takai kusan watanni uku tana jiyya ALLAH yay mata rasuwa.
Wannan mutuwa ce ta kuma susuta mama gaje, lamarin da ake tunani na taɓuwar hankali ya sake bayyana a gareta, dan itama haka kawai saita kama surutai, kokuma tai zaune jugum ba im ba im-im, saita haɗa kwana biyu bataima wani magana ba, komai sai dai tayita binsa da idanu.
A lokacin Ahmad har waya yasa aka bata yay mata gaisuwa, sai dai ko Umm-Ruman bai sanarma rasuwarba, dan tana fama da laulayin cikin Abu-Talib lokacin.
Ɓangaren su Ma'aruff kuwa sai komai ya koma yay lif, dan mahaifin Mufida ya fahimci bazasu sami abinda sukeso ga Ma'ruff ta wannan hanyarba, dole ya tirsasa Mufida ta koma lallaɓa Ma'aruff.
Sai dai lallaɓawar sam batai amfaniba, dan shan giyar da yake ta kuma ɓaci sosai, Har takai hantarsa ta taɓu ba tare da kowa ya saniba, a tsaitsaye ya fara ciwo tamkar wasa, tun yana ɗaukar lamarib ba komaiba har abun ya kaisa ga kwanciya, dukda mufida tasan baida lafiya taƙi faɗama mamansa ta kuma ƙi taimakonsa zuwa asibiti, saima takurama rayuwarsa da tai da batun ɗakko takardun nan.
Jikin Ma'aruff yayi matuƙaryin tsamari, har takai ranar ya gaza a yin komai yana ɗaki kwance rijib, yanaji wayarsa na ring tunda farar safiya amma ya kasa ɗauka ya duba wanene mai kiran, gashi sam baiji koda motsin Afrah ba a gidan balle na Mufida.
Hawaye masu zafi suka gangaro masa a kumatu, inda zai iya da tuni ya ɗauki wayarnan ya kira Mominsu ya shaida mata halin da yake ciki ko zai damu taimako daga garesu.
Har kusan azhar babu motsin Mufida, hakanne ya tabbatar masa bama ta gidan, koma bata kwana a cikinsaba, dan tun jiya da magriba dama yaji kamar motsin fitarta, daga nan bai sake jinta ba, to duk zatonsa kodan yayi barci da wurine harta dawo bai saniba, sai dai zuwa yanzukam yaji a ransama bata dawo ba tun jiyan.
Jiyo knocking ƙofar da ake da ɗan ƙarfine ya katse masa tunaninsa, dagaji dai ba bugune na lafiya ba, gashi duk yanda yaso tashi ya gaza hakan, kuma yana tunanin Mufida kullesa tayi....
Bai kai ƙarshen tunaninsaba ya jiyo maganar mai gadi sama-sama yana faɗi musu anya kuwa yana nan?.
Sai kuma ya jiyo maganar Mominsu kamar tana kuka, ya rimtse idanunsa zuciyarsa na sake salon bugu, dan kuwa dai tabbas yaji a jikinsa babu lafiya......
Maganar ƙanwarsa data zagayo ta bayan Window ɗin ɗakinsace ta sakashi jin sassauci, ta shiga sallallami ganinsa kwance a gado da alamar yana cikin mawuyacin haline, da gudu tabar wajen tana ƙwala kiran sunan mominsu da tabbatar musu yana ciki kwance.
Nan take suka fara ƙoƙarin ɓalle ƙifar, cikin amincin ALLAH suka sami nasara da taimakon baba mai gadi.
Yanda suka shigo suka iske Ma'aruff ya kuma birkita dukkanin tunaninsu, suka shiga share hawaye da jera masa tambayoyi, sai dai bai iya basu amsar ko guda ɗayaba shima, sai binsu da kallon tsoro yake ganinsu duk da raunuka a jiki an liƙe da bandeji.
Babu maganar jan dogon zance sukai ƙoƙarin cewa a kaisa asibiti, duk da sunsan basu da ko sisin kwabo tare dasu, amma suna tunanin shi ƙila a samu wani abu a accaunt ɗinsa tunda da alama su Mufida basu taɓa komai na nan gidanba.
Ramar da yayice ta saka suka iya ɗakkosa su uku ba tare da sunji wani uban nauyiba sam, suna shirin sakashi a motane wata motar tai hon, hakan yasa Momi cewa maigadi yaje ya buɗe gate yaga wanene?.
Babu jimawa sai ga baba maigadi ya dawo a kiɗime, momi ta shiga tambayarsa ko lafiya?.
Yace, “Hajiya wlhy wai wasune sukazo suke maganar nan gidansu ne”.
Cikin matuƙar razani ƙannen Ma'aruff da Mominsu sukace, “Gidansu kuma?!”.
“Wlhy kuwa hajiya, gasu nanma zasu shigo......”
Babu wanda ya iya cewa uffan a cikinsu har mutanen suka ƙaraso, sai wani cika suke da batsewa.
Su dai su Momi sun zuba musu idanu kawai.
Ɗaya a cikinsu ne ya fara bayani ko gaisuwa babu balle lura da halin da Ma'aruff yake ciki baiyiba, “Hajiya mune waɗanda suka sayi gidannan, kuma hajiyar da suka sayar mana sun tabbatar mana kafin muzo kun tashi, amma kuma sai gashi mun iske saɓanin hakan”.
Baki buɗe duk suke kallonsu, cikin ƙannen Ma'aruff ɗaya ta samu baki faɗin, “Hajiya kuma? Wace hajiyace ta saida muku gidan bayan ga mai gidan nan shi baisan anyiba?”.
Kallon juna sukai suma, ɗaya yace, “Bamu gane mi kuke nufiba?, to mudai Hajiya mufida sunanta, kuma ita da Mahaifinta suka kawomu mukaga gidan sati uku da suka shige, tun a ranar muka biyasu rabin kuɗin, jiya kuma muka cikasa biyasu sauran suka bamu takardun gida yau ɗinnan da safe”.
Baya kawai momi tai ta yanke jiki ta faɗi a sume, nan take hayaniya ta kaure.
Ma'aruff ya amshi takardun daƙyar ya duba, tabbas takardun gidanne, to amma a garin yaya sukaje hannun su Mufida bayan yasan suna gidan momi?.
Bai samu amsaba saboda tashin hankalin da suke ciki, masu gida kuwa sallama sukai musu suka tafi akan sun basu nanda sati guda su kwashe komansu su basu gidansu suna bukata.
Babu wanda yabi ta kansu, dan suna a ruɗanin da baki bazai iya furtawaba sam.
★★★★★
An karɓi su Ma'aruff cikin gaggawa saboda asibitin su Adam sukaje, hankalin Adam yayi masifar tashi da ganin halin da Ma'aruff yake ciki, ya kwana biyu basu haɗuba saboda shima aiki yay masa yawa a tsakanin nan.
An samu damar ceto rayuwar mamansu Ma'aruff da hawan jini ya nema saka zuciyarta bugawa, yanayin da take na firgici yasa dole akai mata allurar barci danta samu hutu.
Ma'aruff kam gwaje-gwaje aka shiga masa, bayan bincike mai zurfi aka gano hantarsa tayi masifar kamuwa da ciwo harta harbi ƙodarsa, ba komaine ya jawo hakanba gareshi sai giyar da ya maida ruwa🤦🏻♀️ .
Hankalin ƴan uwansa ya kuma tashi kololuwa, basusan yanda zasu fassara wannan tsakaninba a rayuwarsu, a daren jiya ƴan fashi sukai musu dirar mikiya a gida bisa jagirancin mahaifin Mufida da ƙiri da muzu babu kunyar ALLAH yazo musu a zahirinsa, bayan ya gama zayyane musu komai dangane da burinsa a kansu tare da zage momi tas sannan suka ƙwace komai, dukkanin takardun company ɗinsu da dukkanin na kaddarorinsu, ya kuma saka akai musu dukan tsiya, dukan da yay tunanin momi ta mutune suka fice suka barsu.
Sai dai da yake shi rai a hannun ALLAH yake ba wani shegeba, sai ALLAH yasa babu wanda yama samu wani mummunan rauni, sai dai sumar da sukai da kuma ciwuka da targaɗe ga wasunsu.
Da taimakon ma'aikatan gidan aka kaisu asibiti tun a daren, shinefa aketa kiran Ma'aruff bai amsaba, hankalin momi ya tashi ta matsa sai tazo ta ganshi duk da tana cikin halin rashin jin daɗin jiki, amma tana tsoron kar shima su Mufida sun masa wani mummunan abun, shinefa sukazo suka iske wannan musibar kuma ta saida gidan Ma'aruff din dasu Mufida sukayi da halin ciwo da yake a ciki.
*_MAI RABON SHAN DUKA, BAYAJIN ƘWAƁO SAI YA SHA_*
Dolene a kira ahalin Ma'aruff da wannan kalma, dan itace dai-dai da yanayin da suka tsinci kansu a ciki a halin yanzun kam.
Lokacin da duniya ke kai masa babu wanda ya isa faɗa masa giya nada illa ga ɗan adam, yasha faɗama Samina cewar kuɗinsane, jikinsane, sannan ra'ayinsane, sai gashi itama giyar kuwa da dukiyar sun tabbatar masa da su lokacine dasu, sannan shi komai a rayuwa da bawa yakeji dashi wata rana labarine, (watarana ma masu labarin baza'a samuba inji babana😭, haka yakansha faɗa mana cewar duniya labari, watarana masu labarin babusu😭😭🙏🏻, ya rabbi ka gafarta masa da dukkan waɗanda suka rigamu kwanta dama).
Momi dake ganin Samina bata dace da rayuwar ɗantaba saboda ɗiyar talakawace ita, shiyyasa ta aura masa ɗiyar ɗan uwanta wanda batasan shaho bane a gareta, ya daɗe cikin shawagin ganin ya ɗauke dukkan wani jin daɗinta, ga samako nan ya biyo baya wanda ya dace da ita.
Duk tsiyar da Ma'aruff ke aikatawa ta shaye-shaye da lalata ƴaƴan jama'a sarai ta sani, kuma tanaji tana gani amma soyayyarsa ta rufe mata ido ta kasa ƙwaɓarsa saboda karta ɓata masa rai ko makamcin hakan.
Gashi yau babu dukiyar, babu lafiyar, babu komai da suke tunƙahon dashi ko taƙamar, komai ya ƙare, komai ya lalace tamkarma ba'a tarasuba.
Kwanansu Ma'aruff uku a asibiti mummunan al'amari ya sake zuwa garesu, dan kuwa dai ƴamfashin da baban mufida yasa sukazo suka ƙwace komai nasu Momin, shima sun ƙwace komai daya amsa saboda yaƙi biyansu kamar yanda yay musu alƙawari, shinefa suka bishi har hanyar birnin ikkon daya fece wato legas, suka ƙwace komai sannan suka saka tirela tabi takan motar da suke ciki.
Babu wanda ya shura kaf ɗinsu, Baban mufida, mamanta, ƙannenta mata biyu da namijin daya fidda video ɗinan nasu Samina, sai Mufida da Afrah.
Wannan tashin hankalin gawarwaki da Momin ma'aruff ta gani na ahalin ɗan uwanta ya saka jininta ya sake ƙololuwar hawar da ɓarin jikinta ya dakata da aiki.
Saiga Ma'aruff na kuka rurus tamkar wani mace, ƴar ɗiyar ƙwaya ɗaya daya haifa a duniya ya ƙwallafama rai ta tafi ta barshi, ya tuna sanda Samina ke roƙonsa akan karsu zubar mata da ciki amma sukaƙi saurarenta, ya tuna ƴammatan daya saka aka zubarma ciki duk dan gudun karya haifi ɗan shege.
Kuka yake tamkar ransa zai fita, Adam yana lallashinsa, amma ina bama yajin wannan lallashin, sambatu kawai yake da fallasa sirrin abubuwan daya aikata a rayuwarsa ta baya lokacin kudi nakai masa, ga ƙyau, ga lokaci, ga ƙuruciya, ga dama duk shi kaɗai.
Ko a mafarkinsa bai taɓa tunanin riskar irin wannan ranarba, kai kodama kwatankwacinta, gani yake tunda ALLAH ya basu bazasu taɓa zuwa ƙasaba har gaban abadan, komai zai cigaba da zama bazasu rasaba.
★★★★★
Haka rayuwa taci gaba da tafiya Ma'aruff da momi suka cigaba da jinya, tun suna asibiti ana kula dasu har aka tattarasu aka maida gidan, dan Adam ɗinma dake taimakonsu yaji nauyin yamasa yawa dan haka ya sahilema kansa.
Basu da komai sai gidan dasu Momi suke ciki, anan suka cigaba da zama cikin yanayin rayuwa mai tsanani, ƴan aikin gidan duk sun gudu, matsin rayuwa da abinda Ma'aruff ya shukama ƴaƴan wasu ALLAH ya jarabci ƙannensa suma da tsintar kansu a wani mummunan hali, dan kuwa ƙiri da muzu sun zama karuwan cikin gida, saima sun fitane zasu samo musu na abinci, lokacin da Ma'aruff ya fahimci halin da ƙannensa suke ciki yayi baƙinciki mai tsanani, yayi kuka yayi nadama mai yawa akan lalata rayuwar ƴaƴan jama'a da yayi, yakuma tabbatar da ita wannan rayuwar idan ka cutar da wani yanzu tun a duniya ake fara ganin sakamako bama sai an mutuba.
Haka suka cigaba da rayuwa komai na ƙara lalacewa da taɓarɓarewa har tsahon waɗanan shekaru, duk wanda yasan Ma'aruff a yanzu ya gansa bazai yarda shineba, yayi baƙi ainun, ga cikinsa yawani zama ƙato, haka zakaga wani lokacin yayi wata mahaukaciyar kumbura tamkar za'a taɓashi ya fashe, wani lokacin kuma sai kaga yaɗan sauka, lamarin abin tausayi da matuƙar tashin hankali.
Itama dai Momi tanata fama, da kuma ALLAH ya kawo iyakar abin a wani daren lahadi ta amsa kiran UBANGIJIN al'arshi.
Su Ma'aruff sunsha kuka sosai, har shima jikinsa yaso ruɗewa.
Wannan mutuwarce ta girgiza ƙannensa sukace aure zasuyi, ALLAH kuma ya taimakesu suka samu mazan auren a hannu, duk da basu kai yanda sukai fataba, dan inda a dacan bayanema sukazo sukace suna sonsu tabbas zamasu iya cewa zasu halakasu, dan ko ƴan aikin gidansu basu kaiba.
Amma halin rayuwa yau sai gasu matsayin mazan aurensu, haka aka ɗaura auren babu wani shagalin biki sam, aka mimmiƙasu ɗakunansu tamakar auren dole.
Suka shiga gidan auren kuma kowacce tai gamo da sabuwar rayuwa mai ban tsoro, tsangwamar dangin miji data kishiyoyi, harma da rayuwar da ba'ai sabo da itaba🤦🏻♀️.
A yanzu haka dai Ma'aruff shi kaɗaine a gidansu tamkar wani maye, ga ciwo ga kaɗaici, ga rashin abinci, wani lokacinma sai ya fita ya barato abinda zaici, sai kuma maƙwaftan da sukaga ALLAH suka tausaya masa suka kawo masa saura idan sun rage dan karsu zubar.
Haka zai amsa ya cinye tamkar wani maye, wanu lokacinma yanaci yana kuka.
Duk yawan abokansa baya ganin kowa, duk yawan ƴammatansa baya ganin kowa, ma'aikatan da ke ƙarƙashinsa baya ganin kowa, danginsu na wajen uwa dana uba da abaya suke nane dasu yanzu baya ganin kowa.
Yanzu ya sake tabbatar da lallai al'ummar wannan ƙarnin dukiya suke mutuntawa da darajawa ba ɗan adama ɗan uwansuba, idan kanada dukiya zaka taka kowa ya taku, hakama idan kanada mulki, amma daga lokacin da akace kaiba kowan kowa bane zance kuma ya ɓaci kenan, kowanma mantawa yake dakai a sha'aninsa🤦🏻♀️😭.
“Ya rabbi kasa mufi ƙarfin zukatanmu, ka rabamu da mummunar ƙaddara, ka yafe mana kurakuranmu, ka saka duniya a tafin hannunmu karka sakata a zukatanmu😭😭🙏🏻”.
_________________________________
Kowa yabar gida gida ya barsa, wannan itace kalmar da Ahmad ya ayyana yayinda yake zuƙar iskar ƙasarsa ta Najeriya abar alfaharinsa, ƙasar da bashi da kamarta duk duniya, yana son ƙasarsa, yana kuma burin ganin ya dawo rayuwa a cikinta.
Ya shafa bayan Abu-Turab dake kwance a kafaɗarsa yana barci, tare da sake damƙe hannun Haysam dake cikin nasa.
Umm-Ruman da Zainab na biye dashi a baya, sai Abu-Talib da shima yake tare da Zainab ɗin.
Kowa yasan da dawowarsu a wannan rana, sai dai gudun karsu wahal da kansu wajen zuwa tarbarsune ya saka Ahmad yin gum da bakinsa bai faɗi ainahin lokacin da zasu sauka ba, Mudanseer da Abubakar ne kawai suka sani, shima Abu ɗin yazo gidane saboda dawowar su Ahmad ɗin, amma har yanzu yana porthercout abinsa, zamu ma iya cewa shikam yazama ɗan can.
Rumana ce ta fara hango su Mudanseer dake ta kalle-kallen neman inda zasu hangosu, duk da sun canja mata matuƙa dan dukansu sun sake girma da ƙiba, ga gayu irin na samarin zamani, tai murmushi tana faɗin, “Abu-Haysam ai gasu Yah Mudan can ma”.
Inda ta nuna ya kalla shi da Zainab, aiko suma sai idonsu akan su Abu ɗin waɗanda sufa har yanzu basu gansuba sam.
Zainab ce ta gwargwaɗama Abu-Talib magana a kunnensa, dan haka ya ƙirƙira da gudunsa zuwa gasu Mudan.
Ahmad da baisan abinda Zee ta faɗama Abu-Talib ba ya shiga ƙwala masa kira, amma sam yaron nan ko juyowa yaƙi yayi, sai ca yake “Abbu ka jirani ina zuwa”.
Rumana ta dafe kanta da faɗin, “Ni Umm-Ruman! Rabbi ka shirya Abu-Talib, yaro kamar ana kaɗashi da ruwan hanji?”.
Zainab dake dariya tace, “Nicefa na aikesa.......”
Bata gama rufe bakiba Abu-Talib ya isa inda su Mudan suke.
Ji kawai Mudan yay an rungume masa ƙafafu ana faɗin, “Yauwa na Aunty Zee na kama mikishi har kizo”.
Da sauri Mudan da Abu suka kallesa, dan yayi maganarne da larabci, sunan Zainab da ya ambata kawai sukaji su dai.
Ɗunbin mamaki ya kamasu, saboda kama da yaron yakeyi da su, Mudan ya kama hannun Abu-Talib ɗin, “Yaro daga ina?”.
Abu-Talib da dama dai yanajin hausa, duk da dai bazata kai kamar ace ya tashi cikin ƙasarsa da ake yaren a koda yaushe ba, ya ƙurama Mudan idanu saboda ganinsa tamkar Abbunsa.
Hakan yasa Mudan duƙawa gabansa ya daidaita tsahonsu, Abu-Talib ya kai hannu ya shafa fuskar Mudan yana faɗin, “Lah Aunty Zee zo kiga Abbu biyu.....”
Kafin Mudan ya samu ta cewa da lamarin Abu-Talib Abubakar yace, “Kai Yah Mudanseer, kodai yaron Yah Ahmad ne.....?
Shima bai samu amsa ba, saboda kwace hannu da Abu-Talib ɗin yayi daga Mudan ya juya da gudu yana ambatar, “Ummie kema zo kiga Abbu biyu”.
Dariya Zainab ta ƙyalƙyale da shi, yayinda Ahmad yake murmushi saboda jin shirmen Abu-Talib, ya sake kai dubansa gasu Abu da suma yanzu nan idanunsu suka sauka akan Yayan nasu da Ahalinsa.
Ai nan take bakunansu suka washe, suka nufosu cikin matuƙar ɗoki, nan take suka kaure da matuƙar murnan ganin juna.
Mudan dake dariya yana basu labarin abinda Abu-Talib yaje yay musu ya kamo hannun Haysam da shima dai kallonsu kawai yakeyi, shi da yake yayi ɗan wayo dai yasan ba Abbunsu bane ya zama uku kamar yanda Abu-Talib ya koma faɗa yanzu saboda sake kallon Abubakar da yayi yaga shima dai kamarsa ɗaya da Abbun nasu.
Abu ya amshi Abu-Turab dake a kafaɗar Ahmad yana barci suna dariyar shirmen Abu-Talib ɗin.
Basu wani ɓata lokaciba suka rankaya ga motar da sukazo da ita, shi dai Ahmad bai tambayi ina suka samo motaba, amma a ransa yana mamaki kam, baya ya shiga shi da Rumana da Zainab, Mudan ya zauna a mazaunin driver tare da Haysam a cinyarsa tamkar zasuyi tuƙin tare ne, Abu-Turab kam da har yanzu ke barcinsa yana tare da Abu.
Abu-Talib dake baya jikin Zainab ya tubure shima bazai zauna a baya ba sai an sakashi inda aka saka Haysam sunyi tuƙin tare, Zainab nata lallaɓashi amma yaƙi sai turje-turje yake yana bibbige Rumana.
Tun suna masa dariya da cewar yay haƙuri shima zaiyi bayan Haysam yayi tunda shine yaya amma yaƙi, Rumana ta daina tat dariyar ta zuba masa harara tare da daka masa tsawa.
Babu shiri ya nutsu kuwa yana mannewa jikin Zainab, Rumana tai tsaki tana ɗauke kanta da faɗin, “Wlhy ka cigaba dan jikinka ne zai tsami”.
Abubakar ne yay magana Abu-Talib ya dawo wajensa, shi kuma ya miƙa musu Abu-Turab tunda barci yakeyi, dan da idonsa biyuma ba yarda zaiyiba shi ɗinnan da shegen rashin yarda da mutane.
Hakan da akayine ya kawo zaman lafiya, Ahmad yace, “ALLAH dai ya shiryaka Abu-Talib, ko ina saika nuna hali”.
Abu-Talib yace, “Abbu aito Na shiryu, kuma ka tambayi Aunty Zee nayi addu'a da mukaje makkah”.
Dariya su Mudan suka sanya harda Zee, Rumana dai banza tai da su ita da Ahmad, dan ita bama jin daɗin jikinta takeba, tana dauriyane kawai.
Sun isa gida inda suka samu ƙyaƙyƙyawar tarba ta musamman, dan motarsu na tsayawa Abu ya shige gida ɗauke da Abu-Talib ya gwargwaɗa musu sun iso.
Take gidan ya kaure da murna, wasu kasa haƙuri sukai sukayo waje, dan su yaya Maryam duk suna gidan sunzo tarbarsu, duk da basu san taka maimai lokacin isowar tasuba.
Tuni gidan ya rikice, babu maijin zancen wani, kowa na mamakin canjawar kowa, musamman ma Ahmad da yazam babban mutum da ita kanta Umm-Ruman, Zainab kam sai tsiya suke mata wai aure takeso shiyyasa ta zangame da tsaho.
Saboda zafin da akeyine Ahmad yace ma Ayyah a saka musu tabarma a waje kawai, hakan kuwa akayi.............✍🏻
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_GUDU DA WAIWAYE......_*
_(Shi ke kawo mugun zato)_
*_ƘARHE_*
*Kuma babu editin🥱, aradun ALLAH nagaji😜😂*⛹🏻♀️⛹🏻♀️⛹🏻♀️⛹🏻♀️⛹🏻♀️
...........Yanda gidan ya kaure da hayaniya saika ɗauka biki akeyi, maƙwafta sai zuwa suke kallon ƴan Saudiyya, Abu-Talib kuwa yanda ya sake da mutane saika rantse dama a cikinsu ya tashi, Haysam sai laɓe-laɓe yake, yana dai kallonsu ɗai-ɗai, haka yasa mutane keta faɗin saikace Abu-Talib aka haifa anan ba Haysam ɗinba.
Abu-Turab kuwa koda ya tashi shi ai baima aminta da kowaba shima, da an miƙo hannu za'a ɗaukesa sai ya maƙalƙale Ahmad ko Zainab, dan ita Rumana daya raɓeta turesa take saboda takanta takeyi.
Da ƙyar aka samu mutane suka lafa, shima sai da Ayyah ta sakasu suka shige ɗaki dan su samu suci abinci, kuma ta lura Umm-Ruman batajin daɗi, dan da alama dai ba ita kaɗai bace ba.
Zainab kam nacan mamuƙe da Gwaggonta, hakan yasa Abu-Turab binta, ganin Aunty Zee ɗinsa a jikin Gwaggo shima sai ya yarda da Gwaggo ta ɗaukesa ta saka a cinya, amma sai faman kallonta yake.
Gwaggo tace, “Auta wannan ɗan naki kuwa yanajin hausa? Ya zubamin ido kamar yaga kuɗi”.
Dariya Zainab tayi tana kallon Abu-Turab dake zaune a cinyar Gwaggo, tace, “Sunajin hausa Gwaggo, ai duk muna musu yaya baya bari, dan yace idan ba'a musu mukazo gida da wane yaren zasu shiga ahalinsu, sai dai da yake bazai zam sujita tamkar suna anan da zasuyi cuɗanya da yara ƴan uwansu ba”.
Gwaggo dake murmushi ta shafa kan Abu-Turab tana faɗin, “Kunyi dabara kam, tunda mudai nan ba larabcin muke jiba”.
Zainab ta sake yin dariya, tace, “Ai abinda shima yayan ya hango kenan, bara kiji, inba ni nai masa maganaba dama bazai mikiba, sam yaron nan bashi da yarda, yanzunma dan ya gannine ya yarda ya zauna miki cinya”.
“Abu-Turab!” Zainab ta kira sunansa.
Juyowa yay yana kallonta, tare da amsa mata.
“Kasan wacece wannan?”. Tai maganar tana nuna masa Gwaggo.
Kallon Gwaggo Abu-Turab yayi, sai kuma ya girgiza kai ya bata amsa da larabci.
Zainab tace, “A'a da hausa nakeso”.
Shiru yay kamar bazai sake maganaba.
Sai kuma cayay, “Aunty Zee!”
Tace, “Na'am”.
“Inane nan mukazo?”
“Abu-Turab nan shine gidansu Abbu da Ummie da ni, kuma kuma shine gidanku, nanne ƙasarmu, kaga wannan daka zauna mata a cinya, itace maman Abbu, ɗayar maman Abbunma tana nan waje itama (Ayyah)”.
Shiru Abu-Turab yay yana kallon Gwaggo dake murmushi jin Abu-Turab na surutu ashe raɗam, sai ya maida kallonsa ga Zainab ɗin.
“Aunty Zee!, shi Abbu dama yanada Ummie har biyu? Mukuma miyasa tamu Ummie ɗin ɗayace?”.
Babu shiri Gwaggo ta saka dariya ita da Zainab.
Zainab tace, “Kuma ai Umminku biyu, ba ganiba, gakuma Ummie, kaga biyu kenan aiko?”.
Kansa ya ɗaga mata cikin gamsuwa, sai cayay “Aunty zee miyasa su su Ummien Abbu basuje Dhahran ba sun zauna dashi suna kaishi makaranta, suna masa wanka, suna kaishi yawo?”.
Dariya sosai Zainab da Gwaggo keyi, Saiga Sadiyama dake fama da tsohon ciki ta shigo, ta zauna tana tambayarsu miya basu dariya haka?.
Gaya mata Zainab tayi, Sadiya itama tai dariya tana miƙama Abu-Turab hannu yazo, amma sai yaƙi yama maƙale Gwaggo.
Yana lafe jikin Gwaggo yace, “Aunty Zee ita kuma wannan Ummien waye?”.
Zainab tace, “Itama Ummienka ce”.
Shiru yayi yana kallon Sadiya, a ransa kuma dai yanajin kamar abin yayi yawa, kenan Ummin tasa tamafi biyu.
Kafin yay wata tambayar Abu-Talib sarkin hidima ya shigo, ganin Abu-Turab a cinyar Gwaggo shima sai yaje ya ɗane saboda kishi.
Abu-Turab ya shiga turesa akan sai ya tashi, nanko faɗa ya kaure.
Wannan abu ya saka Gwaggo dariya sosai da Sadiya, Zainab tace ai kaɗanma kenan indai su Abu-Talib ne, hayaniyarsu ta saka Ahmad daya fito alwala leƙa ɗakin, dan yasan faɗan da suka sabane sukeyi.
Koda ya ɗaga labulen yaga a jikin Gwaggonsa suke wannan bidigeren sai ya daka musu tsawa, “Wane kalar rainine wannan zakuzo jikinta kuna faɗa? Abu-Talib ba aikoka nai ka kiranin Aunty Zee tazo taci abinci ba?”.
Yanda duk suka nutsu sai suka bama Gwaggo tausayi, ashe Ahmad ɗin na nan bai canjaba ko akan ƴaƴansa, hannunsu ta kama ta maida a cinyarta ta zaunar da duk sun miƙe suna neman wajen ɓuya, tace, “Babu ruwanka kai dai, cjikinka ko nawa?”.
Ahmad yay murmushi da faɗin, “Nakine Gwaggo, amma ai saisu zauna lafiya ba suyita tsallen banzaba, shifa wannanma aikosa nayi amma yama manta”.
Sadiya tace, “To yaya ai gara su more abinsu, cinyar da basu taɓa hawaba cefa, ina Haysam?”.
“Wannan ai shi sai a hankali, yana can maƙale Mudanseer, da Ayyah kawai ya yarda sai Mudan ɗin, gadai wanda ya sake da mutane nan uban hidima”. Ya nuna Abu-Talib.
Dariya sukai har Gwaggo, Ahmad ya saki labulen yana faɗin bara yaje salla ya dawo.
Duk yanda su Ahmad sukaso samun sakewa su gaisa da iyayensu hakan ya gagara, sai dare bayan tafiyar ƙannensa dasu Yaya Maryam sannan suka ɗan samu nutsuwar zama gaisuwa da iyayensu da kakarsu Iya, akayi hirar yaushe gamo har kusan ƙarfe ɗaya, sai da su Baba sukace suje su kwanta hakanan sannan, dan Abu-Turab ma shi tuni yayi barci, su Haysam ne dai ido biyu.
Umm-Ruman ɗakin Amminta ta tafi tai kwanciyarta, Haysam kam da Abu-Talib ɗakin Ayyah, Abu-Turab da Zainab kuma ɗakin Gwaggo, Ahmad kuwa ya kwana shi kaɗai a ɗakinsu na sashen Ayyah.
★★★★
Washe garima dai haka suka tashi da ƴan sannu da zuwa, kowa sai sha'awarsu yake da ƴan yaransu masu kama da larabawan ƙasar Morocco, su basuyi fariba, amma jin daɗi ya saka fatarsu gogewa tana kuma ƙyalli da wani cika idanu.
Abinda kuma ya sake birgesu da yaran duk abinda aka basu ci sukeyi, da wahala a basu abinci suce basa cinsa, duk da wani abun ma basu sanshiba, amma haka zasu amsa, sai dai idan basaso zasuci kaɗan nefa suce sun ƙoshi.
Tsaf Ahmad ya lura basa cin abinci sosai, kuma bakomai bane sai rashin sabo da cimar nanɗin, amma yay biris dasu a cewarsa da haka zasu saba da cin ai.
Itama dai Umm-Ruman bata taɓa cewa komaiba, dan ita takantama takeyi.
Zainab data fahimci komaice take ɗaukarsu a sace taje wajen Yaya Mudan ko Abu tace a saya musu wani abun ko biscuits ne haka.
Kwanansu Uku anan gidan suna gaisawa da ƴan uwa da abokan arziƙi, dan kullum cikin zuwa akeyi, abokan Ahmad sai kawo matansu sukeyi yimusu sannu da zuwa, su Sufyan duk an zama manyan mutane, dan shima yana aikinsa yanzu gashi yayi ƙiba abinsa, yaransa biyu shima yanzun.
Babane yace yakamata su koma gidansu hakanan, dan ya kula ananɗin kamar a takure suke, musamman ma Rumana da kowa ya fahimci laulayin ciki takeyi, banda uban gayyar da saida yaji Ayyah ta faɗa sannan hankalinsa yakai.
Yaji daɗi, amma sai antayama Rumana harara yake akan wai bata faɗa masaba, itako tai biris dashi.
Ita batasan da zancen gidaba, duk da dai taga an gyara gidansu tsaf, kowane sashe yasha gyara tamkar ba gidanba, an rushe sorayen ƙofar gida guda biyu anyi guda ɗaya da shaguna a waje da aka zuba kayan saidawa a dukansu, dan ƙofar gidan nasu ya zama wata ƴar ƙaramar kasuwa maiban sha'awa. Cikin gidan kuma dukda ba gini aka canja masaba yasha gyara sosai daya canja fasali saboda dabarun masu gini daya samu.
Da yamma bayan Mudan ya dawo daga kasuwa ya kwashesu a motarsa har zuwa anguwar da Ahmad yay gini wanda ko a labari bai taɓa sanarma Rumana ba, dukda ahima dai a hoto kawai yake ganin gidan, dan Mudan ne tsaye akan komai har aka gama.
Gidajene guda uku jere da juna, na Ahmad, saina Mudan, sai Abu kuma.
Anguwar sabuwar anguwace, amma kuma dai ta cika da gine-gine sabbi, sai dai babu hayaniya sosai da yake ba kowane ya gama dawowaba, amare ma sunfi yawa a anguwar.
Tunda suka shigo gate ɗin gidan baƙi da kwalliyar gold a jiki Umm-Ruman ta saki baki tana kallon gidan, bawani ƙato bane amma kuma an masa gini mai ƙayatarwa.
Ta kalli Ahmad dake murmushi, gira ya ɗaga mata tare da kashe mata ido yana kama hannunta cikin nasa.
Bata iya cewa komaiba tabisa, hakama yaran binsu sukai suna tsallen-tsallensu.
Mudanseer ya buɗe ƙofar shiga falon yana faɗin, “Kowa ya shigo da addu'a, musamman ke Umm-Ruman dan dagake babu wata a gidanan harma dana Saudiyya”.
Dariya suka sanya, Ahmad yace, “Amma Mudan kai ɗan bukulune, baƙin ciki kake naƙaro amarya?”.
Sosai suke dariya yanzu banda Ruman dake ƙoƙarin ƙwace hannunta tana cika, Ahmad yay saurin sake damƙewa yana dariya da faɗin, “Kinga gimbiyar mata wasa nake, ai kishiya ko a mafarki babuke babu ita”.
Nanma dai dariyar sukayi, banda su Haysam da tuni sun shige cikin falon da gudu sun ɗare kujeru.
An gyara falon tsaf, komai an saka a gidan, dan haka suka shiga zagayawa ko ina, a ƙasa akwai ɗakin Rumana sai ɗakin baƙi saina yara, akwai kuma wani anyi ƙofarsa ta fita can waje shima dai na yaranne idan sunyi girma, sai kicin da kafin ka shigesa akwai dani farko.
Kasancewar falon babbane an shirya kujerune har kashi uku a cikinsa, dolene tsarin ya burge mai kallo.
Sai ƙafar bene da zata kaika can sama inda ɗakin boss Ahmad yake, kafin ɗakin akwai falo guda biyu da kuma wani ɗakin bayan nasa.
Gaskiya gidan yayi ƙyau matuƙa, gashi an zuba komai masha ALLAH, Ruman ta rungume Ahmad tana hawayen jin daɗi, yau sune da gidan kansu bayan wahalar haya da sukai na tsahon shekaru har a ƙasar da ba tasuba.
Dariya Ahmad yakeyi, ya jata jikinsa ya rungume yana lallashinta.
“Haba Gwal ɗina, minene abin kuka kuma anan?”.
“Dolene nai kuka Yaya, UBANGIJI yay mana sutura kashi-kashi da baki bazai iya faɗaba, muna godiya a garesa irin wadda bata yankewarnan a saman harshe, Yaya kayi Surprise ɗina wlhy, koda wasa ban taɓa kawo hakan cikin rainaba”.
“Dolene mu godema ALLAH Ruman, zakuma mucigaba da gode masa har ƙarshen numfashinmu, naso na faɗa miki batun gidan amma sai nace bara dai na bari idan mukazo ƙya gani insha ALLAHU, munrigada munyi yawa yanzu, idan mukace zamu zauna acan zamu takura musu muma mu takura, shiyyasa da Mudan ya samu fili nima sai nace ya bincika mana, to sai aka dace aka samu harma na Abu, a hankali mukaita ginawa ana hutawa har gashi an kammala cikin amincin ALLAH”.
Daɗi yasa Rumana sake rungume Ahmad.
Ya dungure mata kai da faɗin, “Nima ai na rama ne, kina tare da new baby na amma shine ban saniba ko?”.
Dariya sosai Rumana keyi, ta kama hannunsa ta ɗora saman cikinta, “To kayi haƙuri Yayana, ai gashinan kaji yanzu, ya kamata ace kafin kowa ya ringa sanin inada ciki kaine zaka fara ganewa, amma koda yaushe sai an faɗa kake ganewa”.
“To ya na iya, nidai fa naji gimbiyar ta ƙara ɗanɗano, amma sai ban ranfoba” yay maganar a cikin kunnenta.
Fuskarta ta ɓoye a ƙirjinsa suna dariya, shigowarsu Haysam yasa suka saki juna.
Gida suka koma a ranar, sai a washe garine suka dawo gidansu gaba ɗaya bisa rakkiyar ƴan uwa da abokan arziƙi, kowa nata yaba gida da tsarinsa, sai dare kowa ya kama gabansa aka barsu su kaɗai a gidansu, Zainab dai ta maƙale wajen Gwaggo akan itafa tana can sai idan zasu komane.
To yazam ma zaman su Haysam ba sosai ananba, sai aka bar Umm-Ruman da Ahmad kawai, suma wani lokacin can gidan suke yini.
Suna kwana na tara da dawowa Ahmad yaje gidan Alhajin nan na anguwarsu da suka taɓa haɗuwa a saudiyya dansu gaisa yay masa godiya bisa alkairin da yayma su Baba, da kuma tsayawa da yay akan ginin gidajensu, dan shine yay tsaye akan komai har gyaran gidansu saboda sana'arsa kenan saida gidaje.
Alhaji yayi farinciki da wannan ziyara tasu Ahmad, sun kuma karramasu karramawa ta mutunci da girmamawa, sannan ya bama Ahmad dama akan ya ɗauki mota a gidan yaje yay amfani da ita har su tafi, dan baikamata yayta yawo a motar hayaba.
Ahmad yayi godiya da wannan karamci, ya amshi key ɗin da Alhajin ya basa suka koma gidama a motar daya bashin aro.
Satinsu biyu cif da dawowa baba ya zaunar da Ahmad akan maganar Samina, da kuma halin da mama gaje ke a ciki na taɓin hankali, dan yanzu lamarinta ya sake turewa sosai, zata zauna taita surutai tana faɗin tsiyatakun da sukai ita da inna mari, wani lokacin kuma saita haɗa kwanaki batai maganaba, sai dai kallon mutane da idanu.
Ahmad yaji tausayinta sosai, ya kuma aminta zaije ya fiddo Saminar kafin a shiga hidimar bikin su Mudanseer.
Washe gari kuwa tamkar yanda yay alƙawari haka ya shirya shida Mudan da Abubakar da baba ba tare da kowa ya saniba suka nufi prison iɗn da aka saka Samina.
Acan suka tadda Alhaji Hamisu dazai taimaka musu tunda shiɗin sanannen mutumne kuma mai jama'a.
Koda suka iso prison ɗin, Ahmad da Alhaji da babane kawai suka shiga, akabar Abu da Mudan a mota.
Suna nan zaune kusan awa ɗaya da wasu mintuna sai ga Ahmad ya fito ransa a ɓace, ya buɗe baya ya shiga ba tare daya cema su Mudanseer komaiba, sai dai bai rufe murfinba ƙafafunsa duk suna waje ma.
Suma yanayin da suka gansa a cikine ya sakasu yin gum da bakinsu basu iya cewa uffanba.
Suna nan zaune babu mai cema ɗan uwansa komai har kusan mintuna talatin sai ga baba da Alhaji sun fito.
Sam Ahmad baiko ɗago kaiba dukda yaji takun isowar su Baba wajen, yanata danna waya abinsa.
Baba yace, “Sannu sarkin zuciya, Amadu wai sai yaushene zaka rage wannan zafin nakane haka? Daga magana sai kayi fushi ka fito?”.
Murmushi Ahmad yay yana ɗago gansa zaiba baba amsa, sai idonsa karaf akan Yamusashshiyar tsohuwa mai kama da Samina.
Duk yanda yaso daurewa kasawa yay sai da yace, “Baba wannan ɗinfa?”.
Baba yay murmushi mai ciwo yana kallon inda Samina ke tsaye kanta duƙe a ƙasa tana hawaye, ya kalli su Mudan da suma sukai mutuwar tsaye suna kallonta sannan ya bama Ahmad amsa da cewar “Ƙanwarkuce Samina”.
A cikin matuƙar firgici sukace, “Samina fa Baba?!!”.
Ƙasa ta durƙushe tana wani irin kuka maiban tausayi da cin zuciya.
Baba yace, “Kunga kushiga mota muje kunji, wannan ba maganar nan baceba, ɗiyata tashi bar kukannan haka ya isa kinji”.
Kasa tashi Samina tayi, sai da Baba ya taimaka mata sannan ta miƙe daƙyar, ita da Baba suka shiga mitar Alhaji, Ahmad kuma dasu Mudan suna a motar Mudanseer ɗin.
Babu wanda ya iya sake tofa komai har suka isa gida, kowa sai saƙawa da kwancewa kawai yake a cikin ransa, gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi musamman ma Ahmad da sam bai taɓa kawoma kansa ganin Samina a wannan yanayinba, yanda yay matuƙar tsanarta sai tausayinta ya rage wani kaso a ciki.
Abu kam kasa daurewa yayi saida ya share hawaye saboda tausayin ƴar uwar tasu, ko iyayensu da suke tsoffi sunfi Samina ƙyawun gani a ido.
Da suka iso gidanma Samina kasa fitowa tayi a motar saboda kunya da matsananciyar tashin hankali da damuwar da take ciki, taso ace anbar rayuwarta ta ƙare a jail, dan tana jin kunyar haɗa idanu da mutane musamman jama'ar gidansu, tasan dukda tsahon shekarun data ɗauka mutane bazasu gaza tunawa da ta'asar data aikataba a baya, kuma bazasu gaza yin zunɗentaba, sannan babu abu mafi ɗaga mata hankali a yanzu irin ganin Ahmad da tayi.
Baba ne ya kamo hannunta ya fiddota, kasancewar yanzun ƙofar gidan nasu yazama wata ƙaramar kasuwa yasa idanu sukayo musu ca, dukda babu wanda ya gane Saminar saboda fita hayyacinta da tayi.
Lokacin da zasu shiga gidan sai kawai ta fashe da kuka mai ban tausayi, wanda yaso ɗaga hankalin su Ahmad fiye da wanda tayi a baya.
Raɓasu yay ya shige abinsa tamkar abun bai damesa ba, hakan yasa baba ya bisa da kallo yana girgiza kai kawai, yasan Ahmad idan har ya tsani abu tofa ya tsanesa kenan sai kuma ta ALLAH kafin ya sake waiwayensa.
Da lallashi ya samu Samina ta shiga gidan, kai tsaye sashinsu ya wuce da ita, hakan yasa su Gwaggo da sukasan da zuwa ɗakkotan suma hankalinsu ya tashi matuƙa.
Gwaggo ta kama hannun Saminar ta saka a jikinta itama tana hawaye, hakama Ayyah kuka takeyi, iyama da Abu yaje ya kira ganin Samina ya matuƙar ɗaga hankalinta.
Sauran matan gidan babu wanda yasan mike faruwa, sai su Haysam dake gidan da sukai tsaye suna kallon Samina, Abu-Turab ma zuwa yay bayan baba ya ɓoye yana kuka wai tsoron Samina yakeji.
Baba yay murmushi tare da ɗaukarsa yana lallashi, “Haba Iliyasu minene abin kukan to, wannanfa ba abin tsoro bace innarkace kaji”.
Noƙe kafaɗa Abu-Turab yayi yana sake ɓoye fuska a jikin baban.
Baba ya sake yin murmushi yana shafa bayansa.
Ruwan wanka Gwaggo ta haɗama Samina, kasancewar jikinta babu ƙwari sai iya ta shiga danta taimaka mata.
Wanka sosai na haƙiƙa iya taima Samina, kasancewar ruwane mai zafi sosai sai taji daɗin jikinta, har kanta sai da iya ta wanko matahi tas, sai ga Samina an fito daɗan fasali, dukda bilicin ya rigada ya gama lalatata, dukya lalata mata fata ya maisheta tamkar wata tsohuwa, ga wahalar datasha a jail.
Ɗakin Gwaggo aka kaita, zainab ta bata kayanta ta saka, sannana aka kawo mata tea tasha dan hanjinta ya wartsake.
Tana cikin shan shayinne Ahmad daya fita ya shigo gidan, magana yayi akan Saminar ta fito Mudan ya kaita asibiti dan a duba lafiyarta.
Kowa yay na'am da hakan, dan haka Samina na kammala shan shayin da kaɗanma ta iya sha Zainab ta kamota suka fika fito.
Asibiti mai ƙyau Mudan ya kaita bisa Umarnin Ahmad.
Shikuma ya ɗauki Abu-Turab daya maƙale masa suka tafi gida.
Koda yazo gidan bai faɗama Rumana komaiba, sai Abu-Turab ne ke sanar mata yaga ojuju a gidansu Baba.
Ta ɗauka shirmensane kawai, dan haka tai dariya ta share zancen, amma sai Abu-Turab yayta maimaitawa maganar, hardai ta ƙosa ta tambayi Ahmad dake cin abinci yana saurarensu ƙarin bayani.
Kamar bazai tankaba yacigaba dacin tuwonsa, sai da ya gama tsaf yamaje ɗakinsa yayo wanka ya dawo sannan yake sanar mata Samina ce fa da suka ɗakko a jail Abu-Turab ɗin ya gani.
Dukda Rumana bataga Samina ba yanda Ahmad ke bata labari saida tayi hawaye.
Shiko ya tsaya kawai yana kallonta da mamaki, to miye abin kuka anan? Kuma tunma bata gantaba, idan ta ganta kuma sai yaya kenan?.
Baki ya taɓe yana ɗauke kansa gefe, hakan sai ya bama Rumana haushi, dan a ganinta itama bai kamata Ahmad ɗin ya cigaba da riƙe Samina ba har yanzu, yadace ace ya yafe mata komai ya wuce kawai.
Tashi tai ta bar masa falon tana kuka, shiko ya bita da kallo harta haye sama sannan ya sauke numfashi yana girgiza kai da murmushi, irin ita mai ƴar uwarnan ko.
Duk binciken da Doctor yayi baiga wata matsalaba tattare da Samina, sai olsa kawai dake damunta, sai zazzaɓin cizon sauro da jininta daya hau, saiko tashin jin ƙarfin jiki.
A take suka bata gado, aka saka mata ƙarin ruwa.
★★★★★
Kwanan Samina uku a asibiti, tana samun dukkan kulawa ta musamman, dan dukkan abinda ake buƙata Ahmad tsaye yake akai, hatta da abincin da likitan ya bada shawarar a ringa maba Samina haka Rumana kullum ke ƙoƙarin dafawa akaima Samina, dukda dai Ahmad ya hanata zuwa dubata asibitin, a cewarsa saita gama fushin dashi sannan.
Ganin dai da gaske ba barinta zaiyi tajeba saita sakko daga haushinsa da takeji ta bashi haƙuri.
To aranar da yamma yace ta shirya yakaita su duba Saminar.
Taji daɗi, ta shirya tsaf cikin baƙar abaya ta larabawa tare da naɗa kanta da gayalen jallabiyar, tayi ƙyau sosai, har Ahmad yaji kihin barinta ta fita a haka.
Da dai tai masa ƴar shagwaɓa sai kawai ya haƙura suka tafi.
Acan suka iske su Zainab dasu Haysam suma Mudan ya kaisu.
Sosai hankalin Samina ya tashi da ganin ƴaƴan Ahmad da Rumana, da yanzu itace a wannan matsayin, amma gashi son zuciya ya jata takai kanta ga hanyar data gaza ɓillewa, tayi kuka sosai tamkar zata shiɗe, Rumana ta rungumeta a jikinta tana lallashi da tabbatr mata komai ya wuce dan ALLAH tabar kuka, ta ɗauka hakan matsayin ƙaddara kawai.
Ahmad na ɗakin amma ko kallo basu ishesa ba, daga ƙarshema ya fita hannunsa riƙe da Abu-Turab zuwa wajen likita.
A ranar aka sallamesu da daddare, sai kuma lokacin sauran ƴan gidan sukasan da dawowar Samina har Baba Yusha'u, yako tubure Samina bazata zauna a gidanba, anyi lallashin duniya yaƙi sauraren kowa hatta iya.
Fahimtar da sukai ransa a ɓacene yasa baba yace Ahmad ya tafi da samina ta zauna a gidansa harsu shawo kan baba Yusha'u, dan yanzu yana cikin fushine zai iya furtama Samina dukkan abinda yazo bakinsa.
Sam Ahmad baiso hakanba, amma sai yaga Umm-Rumana na ɗokim ita, hakan datai ba ƙaramin haushi ta bashiba, dan haka yasa Mudan ya kaisu gida akan shi akwai inda zaijene.
Rumana sarai ta fahimci dankar ya ɗauki Samina ne, amma sai batace komaiba ta barsa, dan ita lamarin Ahmad ma yanzu al'ajab yake bata, idan ya riƙe abu a rai ya riƙesa kenan, kafin ya sakko asha fama.
Ɗakin baƙi na gidan aka bama Samina, Rumana ta ɗeba wasu kayanta ta bata, dukda sun mata yawa haka taketa zundumawa, tsakaninta da Ahmad kuwa ko kallonta bayayi, idanma ta gaishesa sau ɗaya yake amsawa ya ɗauke kansa, idanko tana falon ƙasa shi baya zama, hakan na masifar damunta, dukda tana nan maƙale da mugun sonsa da yafi na baya yawa tasan yamata nisa a yanzu, danshi mijin ƙanwartane, ƙanwar tatama uba ɗaya, ko matan duniya sun ƙare tasan bata isa kida kallo ga Ahmad ba a yanzun.
Wani lokacinma da gayya yakema Umm-Ruma wani abun a gabanta, aiko hakan yana zafarta a rai, dan takanci kukanta sosai.
Kamar wasa zancen gitowar Samina ya fara zagaye bakunan mutane, da biyu ake zuwa ganinta gidan sai dai a iske batanan, wasu sukance ɓoyewa take, wasu kuma suce tana gidan inna mari ne wajen babarta.
To koma dai miye abin tsegumi bai ƙarewa a bakunan mutane.
An shiga hidimar bikin su Mudanseer, wanda ana saura kwanaki biyu ɗaurin aure Ahmad ya ɗauki su Rumana sukabi jirgi sai porthercout, ashe ita batasan Happy ce amaryar Mudanseer ba.
Wannan al'amari ya ɗaure kan Rumana, to a ina Happy suka haɗu da yah Mudan haka?.
Sun sami tarba ta mutunci maiban mamaki ga ahalinsu Happy, kowa na mamakin canjawar ɗan uwansa, sai da suka sami nutsuwane da daddare Happy ke bama Rumana labarin yanda suka haɗu da Mudan.
Ashe Ahmad take so ita tun kan su wuce saudiyya, amma shi sam yaƙi nuna ya fahimceta, bayan tafiyarsa ta shiga tashin hankali, taita masa messeges da kalaman soyayya amma sai baitaɓa bata amsaba, hasalima idan ta kirashu koshi ya kirata bazai taɓa nuna mata ko messeges ɗin ya ganiba.
Ta shiga damuwa sosai harta samu Abubakar da zancen, Abu yay dariya a wancan lokacin tare da bata haƙuri akan abinda yayansu yay mata.
Itako tace babu damuwa, ita bai taɓa ɓata mata raiba dan ta fahimci yana son matarsane sosai, bayason haɗata da kowa a rauwarsa.
Abubakar ne ya bata shawara akan Mudanseer, yakuma nuna mata hotonsa da tabbatar mata cewa kamannin Mudanseer ɗaya da Ahmad, babu wani banbanci.
Koda taga Hoton yah Mudanseer ta aminta da zancen Abubakar, sai dai bataji son Mudanseer a rantaba, tadai cema Abubakar zatai tunani akai.
Koda suka rabu da Abubakar sai yakoma yayta cusama Mudanseer zancen Happy shima, tun Mudan na zagin Abubakar ɗin harya ɗan fara jin wani abu game da ita, saboda Ahmad ma dai ya shiga maganar, shi kuma Ahmad bason Happy ne bayayiba, har cikin ransa yanaji zai iya aurenta kodan ya tsamita daga duhun da take ciki, amma yana duba yanayin rayuwar da yake cikine, ƙarfinsa baikai ya riƙe mata biyuba a wancan lokacin, idan yace zai aje mace fiye da ɗaya rigima kawai zai haɗama kansa wajen ɗaukar nauyinsu na yau da kullum.
Hakan yasa yaso janta zuwa lokacin da zaiɗan sake ƙwari, to saikuma Abubakar yazo masa da batun Mudanseer, koda Ahmad ya tuntuɓi Mudan da batun yaga lallai ya karɓi zancen kuma yanason Happy ɗin saishi yaji zai iya haƙura ya barmass, dan da kai da kaya ai duk mallakar wuyane.
Da taimakon Ahmad Happy ta fara son Mudan, kafin wani lokaci soyayya tai ƙarfi a tsakaninsu, har Happy ɗin ta dawo karatu nan kano gidan wani uncle ɗinta.
Daga nanfa soyayya ta ƙara ƙarfi da shaƙuwa a tsakaninsu, da farko Gwaggo ta shiga damuwa da wannan soyaya tasu, dan ita a ganinta tayaya Mudan zai auri wadda bata salla?.
Amma sai baba ya zaunar da ita yay mata bayani yanda zata fahimta, yakumace suyi addu'a hankalin Happy ya dawo akan musulunci.
ALLAH mai komai da kowa kuwa da yake yaso Happy da rahama sai gashi ta musulunta a hannun Mudanseer ba tare da kowa nata yasaniba, ta zaɓi sunan Halimatussa'adiyya, Har zuwa yanzu kuma babu wanda yasan ta musulunta a cikin ahalinta, tayi alƙawarin sai tayi aure nauyinta ya koma kan mijinta sannan ta bayyanama iyayenta gaskiya, dan dama daƙyar suka yarda zata auri Mudan, saida aka kai ruwa rana sosai har abun ya sahafi Ahmad, daga baya kuma dai suka haƙura saboda tace zata kashe kanta kota gudu tabarsu har abada.
Rumana ta share hawaye tare da rungume Happy sunayi tare, ta tayata murna sosai da addu'ar fatan alkairi.
Samina ma da yake da ita sukaje har kuka tayi, da mamakin irin wannan ƙauna da Ahmad kema Umm-Ruman, saima ta fara tunanin kidai dama Ahmad yana son Rumana ne tuncan da?.
Bata da mai bata amsa, sai dai rayuwar Happy ta birgeta, ta kuma yarda Ruman ta mata nisa ita da Ahmad.
Ranar juma'a aka ɗaura auren Happy (Halimatu) da angonta Mudanseer, a ranar su Rumana suka taho da amarya nan kano, bisa rakkiyar tsurarun danginta, tanata kukan rabuwa da iyayenta suma sunayi.
An fara kawota nan gidan su Ahmad, mutane nata ƙananun magana akan Mudan ya auri ƙabila.
Washe gari kuma aka ɗaura auren Abubakar da ɗiyar ƙanwar Gwaggo mai suna Zubaidah, daga nan aka haɗe shagalin biki akasha aka more.
Samina nata ɓoye-ɓoye amma hakan bai hana mutane bincikota ba dansu gani, sukda ma taɗanyi fasali haka kaita zunɗenta.
Bayan anyi biki an shashshare aka miƙa amare gidajensu, su Umm-Ruman kuma suka shiga barcin gajiya.
★★★★★★
Bayan biki da sati ɗaya Ahmad suka nufi gidansu Inna mari bisa umarnin baba shi da Mudanseer.
Halin da suka iske mama gaje a ciki ya ɗaga musu hankali matuƙa, suka kwasheta zuwa asibitin dawanau.
Dukan wani taimako na musamman sun bada damar a batashi, cikin amincin ALLAH kuwa tafara samun sauƙi da yake abun baiyi nisaba, amma kuma likitocin sun tanbatar musu lokaci-lokaci ciwon zai ringa motsa mata, dan ɓacin raine ya taru mata a zuciya harya kai ga taɓa mata ƙwaƙwalwa.
An bata magunguna suka ɗakkota suka dawo da ita gida, a lokacinne Ahmad yay tunanin yakamata mama gaje ta koma gidansu kodan ta ringa samun kulawa, dan anan ƙarfin iya ya ƙare sosai, itama ƴarta sotake ta ɗauketa daga gidan, bai kamata kuma abar mama gaje ba kawai hakan zai sake girmama ciwonta.
Koda Ahmad yazoma da baba shawarar saiya aminta sosai, dan haka suka zaunar da baba Yusha'u sukai masa nasiha mai ratsa jiki akan yay haƙuri mama gaje ta dawo gidan da zama anan sashen iya ta ƙarasa rayuwarta, sai Samina ta cigaba da kula da ita har itama ALLAH ya bata miji tayi aure, dansu Ahmad watan gobe zasu koma saudiyya.
Yau ɗinma yaso turjewa, amma da sukaita lallashinsa sai ya yarda, dukda bada zaman aure zata dawo gidanba haka Ahmad yaɗan shirya masu ɗakin da zasu zauna ita da samina, katiface kawai sai kwabar kaya daɗan abin buƙata.
Haka aka dawo da mama gaje gidan abin tausayi, itama Samina akace ta dawo.
Jitai kamar ta fasa kuka, dan koda Ahmad baya kulata ganinsa da take yawanyi acan na saka zuciyarta yin sanyi, haka babu yanda zatayi ta dawo nan gifansu da zama.
Sai dai kuma sam babu jituwa tsakaninta da mama gaje, sai da su baba sukai mata faɗa akan hakan sannan ta nutsu ta fara bata kulawar da ake buƙata tana kaico da ALLAH wadai da rayuwar son zuciya da suka jefa kansu a ciki, da yanzu sune a daular dasu Ammi ke ciki, amma gasunan babu wan babu ƙanin, babu dukiya babu Ahmad, ita yanzu ko sunan ma'aruff ma batason tunawa a rayuwarta.
Tanaji tana gani fita ta gagari rayuwarta, saboda data fita yara zasu fara mata ihu, mazan dake majalissa na zunɗenta da dariya da kiranta *Matar manya*.
Wannan dalilan ya sakata haƙura da fita ko ina a rayuwarta, ga yaran Ahmad sam basa yarda da ita, Haysam ne kawai, shima zakiga yana ɗari-ɗari da ita, wanan abu har kuka yake sakata.
Dan akwai randa ta shigo sashen nasu Ahmad amsar ruwan zafi zata jiƙama mama gaje magani sai taci karo da Abu-Talib dake wasa a tsakar gidan ya faɗi, tai ƙoƙarin ɗagashi ya tashi yaronnan ya saka mata ihun kuka akan karta taɓashi.
Tana ƙoƙarin saukesane Ahmad ya shigo gidan, zuwansa kenan yazo gaushesu dan Abu-Talib ranar anan ya kwana shi da Haysam.
Jikinta har rawa yake wajen sauke Abu-Talib, a ranta tana tsoron kar Ahmad ɗin yay tunanin wani abu taima yaron ne.
Dan taga Ahmad ya tsatstsareta da idanu fuska a ɗaure, cikin rawar baki tace,
“Wlhy babu abinda nai masa, na iskesa ya faɗine shine nai ƙoƙarin tadashi amma yake kukan nan.......”
Hannu Ahmad ya ɗaga mata batare da yace komaiba, ya kama hannun Abu-Talib dake ɓoye a bayansa suka bar wajen.
Hakan yasa Samina juyawa ta koma tana kuka batare da ta shiga amsar ruwan zafinba.
Wannan yasa duk son da take nason jan yaran a jikinta ta haƙura, sai dai ta kallesu daga nesa kawai.
★★★★★★
A wannan tsakanin Sadiya ta haihu ƴan biyu duk mata, su Rumana suka shiga jerangiyar zuwa gidan har akai suna, kwanaki hudu da sunan ƴaƴan sadiya Fa'iza ma ta haihu na uku, suka sake rankayawa katsina, Samina bataso zuwaba amma ƴan uwan sukace ta cire komai a ranta ta ringa shiga cikinsu, haka suka sakata dole taje, cikin ƴan shema ma ta kasa sakewa tanata laɓe-laɓe.
Bayan dawowarsu daga sunan Fa'iza Umm-Ruman ta roƙa Ahmad ya barta suje gidansu da suka zauna ta gaishe da su maman Ama idan suna nan.
Bai musaba ya barta, shima da kansa ya kwashesu amota dukansu ya kaisu.
Tun sallamar da Rumana tai a cikin gidan jikinta yay sanyi, gidan dukya canja kamanni tamkar ba shiba, ga kaya kaca-kaca, wanke-wanke a bakin rijiya ƙuda natabinsu.
Yara sai hayaniya suke suma kaca-kaca dasu babu mai shigar arziƙi.
Sai dai ganin ƴan gayu sun shigo gidansu yasa yaran yin tsit suka zuba musu idanu, Rumana ta sauke idonta akan Ahmad din maman Ama daya zama ɗan saurayi yana wanki a bakin rijiyar, yaron kamanninsa na nan basu canjaba, murmushi tayi na ƙarfin hali tana faɗin, “Ahmad ne wannan halan?”.
Ahmad ya ajiye kayan hannunsa yana mutsika kumfar dake jikin hannun idonsa a kansu cikin ɗari-ɗari ya amsa da “Eh nine”.
Murmushi ya ta sakeyi tace, “mamanka fa?”.
Shiru yaron yayi cikin ƴar damuwa, kafin ya nuna mata ɗakin da Rumanan ta zauna.
“Tana nan ciki”.
Rumana tace, “To ko barci take?, yimata magana kace ga baƙi”.
Ɗauraye hannu yaron yayi yanufi ɗakin, babu jimawa ya fito yace, “Tace ku shigo”.
Zuciyar Umm-Ruman cike da ɗunbin mamaki tabi Ahmad hannunta riƙe da Abu-Turab, su Haysam na biye da ita shi da Abu-Talib, sai kallon gidan suke cike da tsantsami.
Maman Ama dake kwance bisa wata yololuwar katifa ta tashi da ƙyar, gabanta da tsohon ciki, dukta lalace tayi baƙi tamkar mai ciwon yunwa.
Sam bata gane Umm-Ruman ba, amma ganin baƙuwar ƴar gayuce duk sai ta rikice, tai yunƙurin tashi danta nemo aron tabarma wajen kishiyarta amaryar dan sunfi shiri akan ta tsakkiyar amma sai Rumana ta dakatar da ita saboda tausayi.
Taja kujera ƴar tsugunno dake gefe ta zauna tana fadin, “Yi zamanki maman Ama, wlhy nanma ya isa”.
Karon farko da gaban maman Ama ya faɗi. dan kuwa tasan Amarya ce kawai ke kiranta da wannan sunan.
Rumana ma data fahimci bata ganetaba, sai tace, “Niko maman Ama sai naga kamar baki ganeniba, Rumana ce fa”.
Har taune harshe maman Ama keyi wajen faɗin, “Wai kina nufin Amarya matar Ahmad da suka zauna anan ɗakin?”.
Rumana tai murmushi da cewa, “Lallai kam baki mantaniba, itace kuwa”.
Babu shiri maman Ama ta miƙe zumbur jikinta na rawa, tama manta da nauyin cikin jikinta, sai tafa hannaye take jikinta na rawa tana sallalami.
Rumana dai nata dariya, cikin sassarfa Maman Ama ta fice tana ƙwalama kishiyoyinta kira, takuma aika yara su kira mata su maman Aysha duk da yanzu ba shiri sukeba, dan tuni anyi uwar watsi saboda maman Ayshan yanzu ta haɗe kai da kishiyar Maman Ama ta biyun.
Tuni gidan ya kacame, maƙwafta nata shigowa, wasuma dai ƙin yarda sukai Rumanan ce, saida ta rantse musu.
Rumana ta tambayi ina Kausar, anan suke sanar mata ai ALLAH yayma Kausar rasuwa wajen haihuwar ɗanta na huɗu, dama tuni sun tashi daga nan gidan an haɗa da kishiyarta, haihuwarta ɗaya acan ana biyun ta rasu bama ta haifesaba.
Hankalin Rumana ya tashi harda kuka, sai rayuwar ta kuma bata tsoro sosai, da haka da hakafa kowa zai kama gabansa.
Sai da gidan ya natsa aka barta daga ita sai Maman Ama a ɗakin take bata labarin halin rayuwar data shiga itama, yanzu su ukune a wajen mijinsu, kowa haihuwa take kamarmi saboda gasa, yanzu haka yaranta bakwai ga cikin na takwasa, taga wulaƙanci kala-kala wajen mijinsu bayan aurensa na biyu, dan shiya sakata ta dawo nan ɗakin aka saka shikiyarta a nata ɗakin, lokacin Kausar na nan bata koma gidan kishiyartaba, zaman dai babu daɗi damuwar yau daban ta gobe daban, kishiya ta sakata gaba wajen miji, yazo ya saketa taje gida tai zama kusan shekara ɗaya, harma ta kwashe kayanta ta saida, sai kuma ya dawo da ita, kasancewar ta saida kayan ɗakin daga ita sai katifa da ƴan kwanika ta dawo, ta dawo babu jimawa su Kausar suka tashi, tana ɗoki zata koma ɗakin da kausar din ta tashi tunda shima ciki da falone sai kawai mijinsu yazo da zancen zai ƙara wani auren na uku.
Kishiyarta tata tsiya, babu dai yanda zatai ya auro suka zama su uku, da farko sun haɗe mata kai kamar yanda Kausar suka haɗe mata kai itada kishiyarta ta farko, to da zama yay zama kuma sai amaryar ta dawo wajen maman Ama din suke mutunci, yanzu haka ƴaƴan gidan kusan goma sha tara, dan kishiyarsu ta tsakkiya sau biyu tana haihuwar ƴan biyu.
Tace yanzu haka dai gasunan zaman babu daɗi, miji nauyi ya masa yawa yama barmusu nauyin kansu kowa itake cida kanta da ƴaƴanta a gidan, inya samo ya miƙama kowa abinda ya samu, idan bai samoba bamaya zuwa gidan sai sulusin dare, daga sallar asuba kuwa bazai dawoba, dukda wannan halin da suke ciki yanzu haka sunji labarin aure kuma yake nema na wata bazawara.
Maman Ama ta share hawaye da cigaba da faɗin, “Amarya wlhy yanzu haka yaran gidannan babu mai zuwa koda islamiyya, haka suke tantal baɗeɗe cikin anguwa kamar ƴaƴan akuyiyi, Wlhy ki godema ALLAH amarya, ƙyaƙyƙyawar zuciyarku ke da mijinki itace taimuku jagoran zama masu nasara a rayuwa, baku ɗauki duniyar da zafiba, kunyi haƙuri da kaɗan da ALLAH ya baku gashi yau kune ke riƙe da mai yawan, Amarya dan ALLAH ki yafemin abinda nai miki a zamanmu, wlhy nayi nadama, na gane manufar rayuwa a yanzu, dan dukkan abinda mukai miki nida marigayiya Kausar nima saida sukaimin ita da kishiyata, bayan barin kausar gidan kuma kishiyiyi suka kuma min, tun anan na gane mun cutar dake matuƙa, zafin da naji yasa har yanzu na gaza yafema Kausar abinda sukaimin ita da kishiyata a gidan nan.........”
Cikin hanzari Umm-Ruman tace, “A haba maman Ama, dan ALLAH karkice haka, ki yafema Kausar dan ita tata tarugada ta ƙare kuma, wlhy ni dama ban taɓa riƙeku a rainaba, nakuma yafe muku. ALLAH ya gafarma Kausar ya raya abinda ta bari”.
“Hakane Amarya, amin ya rabbi, shikenan na yafe mata, ngd nima da kika yafemin, dan ƙila da wuya nima na tsallake din a wannan haihuwar, ban taɓa ɗaukar cikin dake bani wahalaba kamar wannan cikin”.
“Insha ALLAHU lafiya lau zaki haihu Maman Ama, raiyuwa da mutuwa duk a hannun UBANGIJI suke ai”.
“Hakane amarya, ALLAH ya tabbatar, dan nima ba mutuwar nake soba kodan gudun halin da nake hangoma ƴaƴana zasu shiga”.
Rumana ta tausaya mata sosai, ta saka aka kira mata ƴaƴan maman Ama duka ta gansu, ta saka musu albarka.
Su Abu-Talib kam ai Haysam ne kawai ya yarda maman Ama ta taɓashi da maƙwafta da suka shigo, Abu-Turab kam dama shi babu yarda, hakama Abu-Talib ƙin yarda yayi dukda hararar da Rumana taita antaya masa.
A gidan Rumana ta yini, da rana Maman Ama taciyo bashin gurasa ta kawo mata, Rumana bataƙiciba, su Haysam ne dai saida taimu jan ido sannan sukaci, bayan sallar la'asar ta kira Ahmad akan zataje tai gaisuwa gidansu Kausar.
Ya tambayeta wanene ya rasu?.
Anan take faɗa masa ai Kausar ɗince ta rasu, sosai shima maganar ta daki zuciyarsa, yayta jinjina abin a ransa, yace ta jira yazo sai ya kaisu dan yana ta wajen anguwarma.
Shine yazo ya ɗaukesu harda maman Ama da ganin Ahmad ya sake rikitata, wlhy idan a hanya ta gamu da Ahmad da Rumana sam bazata taɓa ganesuba.
Sunje har gidan su Kausar sukaima mamanta gaisuwa, Ahmad yay musu alkairi tare da alƙawarin aiko da taimakonsa wa ƴaƴan da Kausar ɗin ta bari, suka kuma biya ta gidan auren Kausar din sukaima mijinta gaisuwa.
Daga nan suka maido maman Ama gida Rumana tai mata ƙyauta shima Ahmad yay mata akan zataji saƙo yanzu bashi da kudi sunsha kashi.
A hakanma godiya taitayi kamar zata durƙusa, harda share hawayenta, dan koba komai sun samu kudin abincin kwana biyu, tausayinta ya sake kama Ahmad da Rumana.
__________________________________
Watansu Rumana biyu a Najeriya suka shiyar inasu-inasu suka koma sukabar ahalinsu da kewa.
Ana komawa kuma kowa ya koma makaranta, Ahmad kuma aka duƙufa aiki.
Haka rayuwar taita gangarawa har cikin Rumana ya tsufa ya isa haihuwa.
Ranar wata juma'a ALLAH ya sauketa lafiya ta sambado ƴar babi gal ɗinta mai kama da ita da Amadinta.
Murna wajen wannan ahali ba'a magana, su Abu-Turab anyi ƙanwa.
Ranar suna yarinya taci sunan Ayyah, wato *_RUƘAYYA_*, amma kasancewar sunan Ayyah ne zasuke mata alkunya da *Noor*, to ALLAH ya raya Noor.
Bayan haihuwar Noor da watanni kusan shida sukazo Najeriya bikin Zainab da angonta, dukda kasancewar ɗan saudiyya Ahmad ya ce anan gida za'a ɗaurama Zee ɗinsa aure kamar kowa.
Dole wakilansa uku dashi sukazo nan aka ɗaura auren akai biki kafin ya ɗauka matarsa su juya.
Su Ahmad kuma sai da sukaɗan huta anan kafin suma su koma cikin farin ciki da kewar Ahalinsu.
A wannan zuwan dai Samina ta tari Ahmad tana kuka da roƙon gafararsa ita da Mama gaje, dayake anyi sa'a ƴan hankalin na tare da ita a lokacin.
Bai kulasuba, sai da Rumana taita roƙonsa harda kukanta sannan yace shikenan ya yafe musu, ALLAH ya yafe mana baki ɗaya.✍🏻
“To amin ya rabbi Amadidin Ayyah. angon Rumana baban Haysam😂, nima dai na yafema dukkan wanda ya ɓatamin, nima rabbi ka yafemin nawa kurakuran danayi akan sani ko a rashin sani.🙏🏻😭
*_ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN_*
duka-duka anan na kawo ƙarshen wannan ɗan littafi nawa, kuskuren da nayi a ciki rabbi ka yafe mani, abinda na faɗa dai-dai ALLAH ka taramu a ladan.
Mun gode sosai masoyanmu da suka sayi wannan littatafai na ZAFAFA, ALLAH yabar zuminci, muna muku san so irin wujiga-wujiga dinan, irin trillions dinnan.
Waɗanda baku sayaba kusani ko daga baya kuka karanta muna binku bashi😉, a daure azo a biyamu kar ai sanya, ɗari biyu tafu gaban wasa balle a lokacin corona ɗinan😂🤣😜😲.
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
No comments