Furar Danko 60
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣0️⃣
........Koda Smart ya kai kayan nan kitchen ya adana wanda zai iya lalacewa a fridge sai ya nufi ɗayan ɗakin kasancewar duk yasan sirrikansu, hasalima key ɗin ɗakin na hannunsa dan a rufe yake tun da aka gama shirya masa kaya aunty Saliha ta damƙa
masa ko ƴan ganin gidan amarya babu wanda ya leƙa cikinsa. Shima nan ɗin kayane lafiyayyu aka shirya, dan shine ma matsayin master bedroom. Ɗakin yayi ƙyau sosai, komai ya zauna a inda ya dace. Duk da gajiyar da yake ji bai kwanta ba sai ya zare rigarsa da ga shi sai dogon wandon da singlet ya nufi bathroom. Bai jima ba ya fito da alamar alwala yayi, lafiyayyen carpet ɗin gaban gadon ɗakin ya hau dan yin salla. Sallar isha'i yay da shafa'i da wutri. Bayan ya idar yay zaman yin addu'a mai tsayi kafin ya miƙe. Har ya zauna a bakin gadon sai kuma ya miƙe, zuciyarsa ke ayyana masa ya kamata ya binciketa ko tayi sallar isha'i, ya kuma duba ko zazzaɓin ya sauka. Sai dai me, yana taɓa ƙofar ya jita a kulle. Shiru yay yana kallon hannunsa da ke saman handle ɗin, sai kuma ya ɗage kafaɗunsa alamar ko oho ya juya ɗakin da ya fito yay kwanciyarsa dan barci yake ji matuƙa. Dan shi a tunaninsa ko Lulun tayi hakanne dan kar ya nema wani abu a gareta.....
No comments