Furar Danko 59
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣9️⃣
......Smart zaune gaban su Abba da Ammah suna masa nasiha. Yayi matuƙar ƙyau cikin yadi mai taushi grey color, ga ƙamshi mai daɗi da saka nutsuwa yana yi. Nasiha mai ratsa jiki Ammah da Abba sukai masa sannan suka rufe da addu'oin samun zaman lafiya da nasarar rayuwa. Tare da tuna masa muhimmancin cigaba da tsayawa akan gaskiya da addu'a da ibada. Kar yaga ya koma bayan idanunsu ya aro halin da basu sanshi da shi ba. Ya ji tsoron ALLAH ya riƙe matarsa da zuciya ɗaya bisa koyarwar MANZON ALLAH (S.A.W) karya barta tai kuka akan abinda yanada ikon share mata hawaye. Abba ya miƙa masa wata leda mai ɗauke da magungunan musulunci yana faɗin, “Ga wannan ɗazun naje na amso maka shi, dan yawan ciwon kan nan naka yana damuna. Ka kula dan ALLAH dayin yanda duk suka rubuta a kuma cigaba da addu'a dan itace gaba da komai muma muna muku ALLAH ya kawo iyaka”.
Ya amsa da Amin tare da masu godiya zuciyarsa a raunane. Ashe haka akeji idan za'a bar gida. Ashe ba mata ne kawai ke shiga cikin yanayin damuwa ba yayinda za'a kaisu gidan aure. Ji yake kamar ya saki kuka kawai ya huta. Amma dai ya daure ya cije da ƙyar yay musu sallama ya fita inda Ahmad ke jiransa. Sai da ya koma cikin gidan yay sallama da su Umma da dama abinda take jira kenan, cikin dabara tai masa hoto batare daya sani ba, dama sanda aka kawo Lulu haka tayi. Koda ya fito inda Ahmad yake sai da suka tsaya akai sallar magrib a masallacin anguwar sannan suka wuce. Basu ƙarasa sharaɗa ba sai da Ahmad ya tsaya yay saye-saye irin na rakkiyar ango, shi dai Smart baice komai ba, hakan yasa Ahmad komawa tsokanarsa wai kodai a samo masa mayafi ya lulluɓa kamar yanda amare keyi idan za'a kaisu. Dan ya lura shima ɗin fa kukan kawai ya rage yayi. Kunnen Ahmad ya kama ya murɗa da faɗin, “Kai wai bazaka daina sa ido ba ko”.
Hannun Ahmad ya buge masa. “Mugu ciremin kunne zakai dan kai ka samu ka tsallake.” murmushi kawai Smart yay baice komai ba. Koda suka iso sai da ya fita ya buɗe gate ɗin sannan Ahmad ya shiga, shi kuma ya rufe sannan ya samesa dai-dai yana fiddo ledojin sayayyar da yayi. “Mawashi ya kamata fa gidan nan a nema maigadi gaskiya”.
Cikin taɓe baki da ƴar harara Smart ya ce, “Yayi me idan an nemosa?”.
“A'a gadi mana, kana ganin ya dace ace kaine zaka dinga buɗe gate da rufewa idan kun shigo ko Madam ɗin. Sannan shi amfanin mutum a gida ko tafiya kukayi baku da ɗar akan barin gidan babu kowa.”
Duk da ya gamsu da maganarsa ta ƙarshe sai cewa yay “Kai share wannan batun muje kazo kayi ka wuce dare nayi”.
“A'a nazo dai nayi na wuce na baka fili kawai zakace malam. Kai jama'a wai kowa da yayi aure sai idonsa ya buɗe, bara dai nazo nai mai yiwuwa, in sha ALLAHU nima bazan ƙetare shekarar nan ba”.
“Da yafi maka”.
Cewar Smart yana murmushi. Daga haka suka ƙarasa cikin gidan. Wani irin ƙamshi mai ratsa zuciya ne ya tarbesu, falo kam ya tsaru iyakar tsaruwa dan Uncle Yousuf da gaske ya zuba dukiya a gidan nan ƴar gaske. Zaune Ahmad ya kai, shima Smart sai ya zauna ɗin yana furzar da iska. Ko yaya zata kaya musu a wannan gida cikin wannan rikitaccen aure mai cike da cakwakiya da ƙalubale oho. Yau dai ga shi da ga shi sai Lulu ƙamshi ƴar balaja'un ogar nan tasa da bata raina abin masifa matsayin ma'aurata. Shi yasan akwai babbar ƙura, idan yace ƙura yana nufin ƙura irinta turniƙewar yaƙi da ko tafin hanunka ganinsa bazai yiwu maka ba...”
“Oh oh tunanin mi kuma ka tafi?”. Ahmad ya katsesa. Iska ya ɗan furzar da sakin ajiyar zuciya. Ahmad yay dariyar shaƙiyanci yana miƙewa. “Ƙalau kake kuwa?” cewar Smart da ke kallonsa. Ahmad ya ɗage kafaɗa da faɗin, “Kafin kowa sanin ƙalau nake tunda gashi na rakoka wajen amaryarka. Ni kaga nayi nan asha angwanci lafiya kar dai a karya gado da safe a kiramu neman kafinta”.
“ALLAH ya shiryeka mara mutunci”. Cewar Smart yana miƙewa shima. Yanzun ma shi ya buɗe masa gate ɗin yana faman jera masa godiya. Dan Ahmad yayi matuƙar ƙoƙari a bikin nan. Ko shine angon sai haka. Sai da ya rufe ko'ina sannan ya sauke ajiyar zuciya da bin ƙofofin ɗakin uku da kallo. Duk da biyu a cikin corridor suke ƙaramin ɗakinne a ware shi kaɗai ɗan nesa da su ma. Zuciyarsa tafi kaisa a corridor ɗin dan haka ya nufi can kai tsaye, tafiya yake tamkar wanda ke jin kasala ko gandar takun nasa, hakan yay matuƙar jagorantar steps ɗin nasa wajen kasancewa a tsare, hannunsa ya kai saman handle ɗin ƙofar, sai ya samu kansa da ambaton sunan ALLAH kafin ya murɗa ya shiga da sallama can ƙasan maƙoshi. Hasken ɗakin ya bashi damar hangota naɗe a tsakkiyar gadon, ya ɗan zuba mata ido na wasu sakanni kafin ya ƙarasa cikin ɗakin da shima keta tashi ƙamshi, yana da ga tsayen ya kira sunanta a hankali, idanun ta buɗe da ƙyar dan bata da nauyin barci, ko abu tasha ta kwanta da wuya kaga barcinta yay nauyin da za'ai abu a kusa da ita bata farka ba. Maidasu tai ta rufe tana wani ɓata rai. Duk da yanda tai ɗin sai bai damu ba ya kai zaune a bakin gadon sai dai nesa da ita kaɗan, koba komai yau ai ita baƙuwarsa ce, ada bai kulata ba ma balle yanzun. Hannunsa ya kai saman goshinta, da zafi sosai alamar zazzaɓi yau ma.
“Yau ma zazzaɓin ne?”.
Kamar bazata kulashi ba sai kuma ta ɗaga masa kai kawai. Iska ya ɗan furzar a hankali. Sai kuma ya ce, “Tashi to kici wani abu sai kisha magani”.
Kalamar magani da ya ambata yasa kanta kawo wuta, cikin gamsuwa da dabarar data zo mata ta tashi zaune da ƙyar tana ƙara cin serious, sai da ta zauna sosai bayanta jingine da gadon sannan ta ɗan kallesa ta kauda idonta, ganin hankalinsa nakan wayarsa yasa taji ƴar nutsuwa dan bata ƙaunar kallo. Cikin ƙara dai-daita plan ɗinta murya a karye ta ce, “Nifa paracitemol bayamin maganin zazzaɓi”.
Ɗan ɗagowa yay ya kalleta, sai kuma ya sake maida idon nasa kan wayar yana faɗin, “Sai wanne?”. Handbag ɗinta da ke bedside drawer ta ɗauka ta zaro wata takarda a bayan zip ɗin ta miƙa masa. “Wannan shi nake sha in dai ina irin wannan zazzaɓin, in ba haka ba bana warkewa da wuri”. Harga ALLAH bai kawo komai a ransa ba tunda shi ba likita bane, dan haka ya amsa takardar, ganin rubutun Doctor ya sashi sake yarda. Sai kuma ya ɗan kalli agogo, takwas da kusan rabi dare baiyi ba. Idanunsa ya maida kanta, ta janye nata da ke kallonsa a sace cike da basarwa. “Ya kamata kici wani abu to kafin na dawo ko?”. A ɗan yatsine ta ce, “Karka damu har ka dawo.”
“Okay”.
Ya amsa mata yana miƙewa. Wani irin daɗine ya ratsa Lulu kamar ta fasa ihu dan farin ciki. Wai yayama akai wannan dabarar baizo mata ba tuni take a wannan bala'in. Zamewa tai ta kwanta tana murmushin da kakan daɗe baka gani ba akan fuskarta dan sai ta gadama take yi.
Napep ya samu ta kaisa har ƙofar pharmacy ɗin data kwatanta masa ana iya samun maganin, koda ya basu takardar yaron saida ya kallesa, amma sai baice komai ba ya dai wuce wajen ɗakko masa maganin. Koda ya dawo da maganin ya faɗa masa kuɗin ya cire daga aljihu ya bashi. Napep ya sake samu ta maidashi gida. Yanzu kam sai da ya rufe ko'ina da ɗaukar abubuwan da Ahmad ya siya musu sannan ya nufi ɗakin. Inda ya barta anan ya sameta, sai dai yanzu ta koma ta kwanta. Duk da taji sallamarsa bata motsa ba har sai da ya kai hannu ya yaye bargon data rufa har kanta. Jikinta har tsuma yake lokacin da ya fiddo maganin da ga leda mai tambarin pharmacy ɗin, amma sai tai ƙoƙarin kannewa.
“Yanzu mi zaki ci?”.
Ya faɗa yana ɗagowa ya kalleta. “Ni bana jin yunwa, naci abu tare da Mamy”. Ta bashi amsa idonta akan ledar nan dai. Bai san wa take cema Mamy ɗin ba, sai dai yanda tai maganar cikin serious ya sashi gamsuwa, sai kawai ya cire maganin biyu ya miƙa mata tare da goran ruwa. Bata musa ba ta amsa tasha. Sannu ya sake mata da tattare sauran maganin ya ajiye a bedside drawer da ruwan. Zamewa tai ta sake kwanciya da faɗin, “Sai da safe”.
Murmushi ya ɗan saki ƙasa-ƙasa. Dan ya fahimci korarsa akeyi. Baice mata komai ba ya tattare sauran ledojin ya fice yana rage mata hasken ɗakin. Ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi, sai kuma ta miƙe zumbur da raka bayansa da harara ta dannama ƙofar key sannan ta dawo. Cikin rawar jiki ta fisgi ledar nan ta zazzage kusan ƙwayoyin maganin biyar a tafin hanunta ta afa a baki batare da ruwa ba. Sai da ta haɗiye sannan ta ɗauka ruwan ta kora kaɗan. Wani irin farin ciki take ji na samun kayan nan cikin sauƙi, sai kawai ta faɗa saman gadon cike da jishaɗi tai juyi ta sake juyawa........✍️
_(ALLAH ka rabamu da mummunar ƙaddara. Wlhy irin masu ɗabi'ar nan tausayi suke ban. Dan rayuwar kawai suke batare da sun san ina ta dosa ba, idan sukai nisa sai an dage kafin su bari, ku ga dai, kwana biyu batasha ba amma ta koma kamar mara lafiya. Iyaye dan ALLAH mu ƙara dagewa wa ƴaƴanmu, mu bar aibata ƴaƴan wasu idan muka gamsu a irin wannan halin. ALLAH ka shiryar damu😭🙏)._
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
No comments