Recent Updates

Furar Danko 58

 


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗




           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣8️⃣




........Kai ta girgiza masa alamar bazata sha ba. Sai ya ce mata “Please ko kaɗanne! Kinga magani zaki sha”.

     Yanda yay maganar da ɗan dafe kansa shima ya sata amsa dan har yanzu dai tafi buƙatar ya fitan ko zata fi samun daidaito yanda ya kamata. Kwankwaɗar shayin tai kamar ruwa kawai duk da akwai ɗan sauran zafin. Tasha kusan rabi ta miƙa masa kofin, amsa yay baice mata komai ba ganin ta ɗan sha. Ba tsoron magani take ba, dan haka ta amsa tasha shima salin alin, sai kuma ta zame ta kwanta tare da lulluɓe duk jikinta har kanta ta juya masa baya. Idanu kawai ya zubama bargon da take ciki, har yama rasa mizai hasaso game da abinda ya farun yanzu. Rashin makama ya sashi miƙewa da Basket ɗin magungunan, ya ɗan tsaya a kanta yay addu'ar da ake son yima mara lafiya da kuma ta barci ya tofa mata dan yasan idan yace zai tofa mata a hannu ta shafa bazasu wanye lafiya ba. Dan haka yay yanda zata fisheshi sannan ya fice. 

      Su Aunty Bilkisu na falon zaune da alama dakon fitowarsa suke, bai zauna ba ya ce, “Tasha maganin ta kwanta nima zanje na kwanta sai da safe”.

     “ALLAH ya tashe mu lafiya”.

Suka faɗa a tare, yana ida ficewa yake amsawa da Amin. Koda ya koma ɗakin nasa ya samu Ahmad na wanka, dan haka ya zauna jiransa sai da ya fito ya shiga ya sake alwala ya fito. Sallar isha'i ya rama da yin shafa'i da wutri yay karatun Alkur'ani kaɗan dan wancan kiɗan na waje damunsa yake yi. Bai dai ce komai ba yay kwanciyarsa bayan sun ɗanyi magana da Ahmad dake tambayarsa yaya jikin Lulun. Ya amsa masa da cewar da sauƙi zazzaɓi ne. Daga haka ɗakin yay shiru, Ahmad na kallo a MBC Action shi ko yay luf tamkar mai barci, sai dai idanunsa biyu abinda Lulun taine ɗazun ke masa kaikawo a rai. Tabbas akwai abinda ya firgitata a dalilin abinda ya faru a tsakaninsu. Yana kuma tunanin kamar hakan ya tuna mata da wani abu ne da ya shuɗe a rayuwarta ko kuma.... Sai kuma ya ɗan furzar da iska kaɗan, hakanne yasa Ahmad jiyowa ya kallesa.

        “Kai wai dama ba barci kake ba?”

     Idanunsa ya ɗan buɗe ya kalla Ahmad ɗin. Shi kuma sai ya saki ƴar dariya da faɗin, “Oh dama likimo kayi, to kodai mun tauyeka ne da rashin baka amaryarka? Ai bata ɓaci ba yanzu ma sai a kawo maka ita nan ko kuma ku tashi ku wuce karma ku mana abin kunya an.....”

    Bumm!! Yaji saukar filo akan bakinsa. Filon Ahmad ya riƙe yana murza bakin, sai kuma ya kalla Smart dake harararsa ya bushe da dariya. “Kufa dama masu shiru-shirun nan wlhy abin tsoro ne wajen ƙulafucin mace. To maida wuƙar yau ne kawai gobe i war haka kuna can manne.....”

     Sake jawo wani filon Smart yay zai jefa masa yay saurin ɗaga hannu sama alamar surrender yana faɗin, “Yi haƙuri nayi shiru Zakin zaki. Haka kawai kamun dogon baki na kasa samun mai aurena nima”.

     Ƙwafa Smart yayi ya ajiye filon, sai kawai yaja bargo ya lulluɓa yana juya masa baya ma. Dariya Ahmad ɗin ya cigaba da yi masa ta shaƙiyancin a kaikaice. Shi dai bai sake kulashi ba dan sosai abinda Lulu tai yanzu yay masa tsaye a rai yaƙi wucewa.....


          *_WASHE GARI_*      


    Washe gari safiyar litinin kusan kowa ya tashi da ƙyar musamman ma ƴammatan nan da sukasha rawa da su Abdull da suma suka cashe kam basu tashi ba sai wajen sha ɗaya da ƙyar. Baƙi fa nata haramar tafiya musamman ma na nesa dangin Abba. Dan haka buɗar kai ma da wuri za'ayi. Alhmdllh amarya Lulu ma ta tashi garas babu zazzaɓin, sai dai damuwar son shan kayayyakinta da ke ƙara tsikararta. Tare suka kwana da su Amrah a ɗakin aunty Amarya. Koda aka kammala haɗa break fast Asma'u ce takai musu. Yanda ta gaishe da Lulu cike da girmamawa da kiranta aunty yay matuƙar mata tasiri a zuciya, sai taji ƙaunar Asma'un ya shigeta, gata ƙyaƙyƙyawa, kamanninta kuma sosai a bayyane suke da Smart. Tun jiya sun jone da su Afrah dan zasu iya zama sa'anni, sai dai Asma'u ta fisu nutsuwa a bayyane, su kuma sun fita wayewa. Dan haka ta basu hannu suka gaisa kowanne nama ɗan uwansa murmushi, a take kuma hira ta ɓalle a tsakaninsu sai Lulu ta zama ƴar kallo. Asma'u na tare da su har sai da Amal tazo tai kiranta sannan tai musu sallama da cewar zata dawo idan tayi sallar walha.

     “Wannan kuma ina kuka samota?”

Cewar Lulu bayan fitar Asma'u. Kai tsaye Amrah ta bata amsa da “Aunty Lu ƙanwar Uncle Smart ce fa, tace mana itace auta a ɗakinsu. ALLAH yarinyar tana da daɗin zama bakiga yanda suka dinga karramamu jiya ba, mutanen gidan nan nada kirki”.

         Shiru kawai Lulu tai tana kallon Amrah ɗin har na wasu sakkani, sai kuma ta ɗauke idanun nata sakamakon kiran wayar Afrah da akayi. Mommy ce, tana ɗagawa tace a Bama Lulu. Amsa tai cike da ɗokin jin Mommy, ta gaisheta da faɗin, “Good morning Mommy”.

     Daga can Mommy ta amsa mata da kulawa da kuma tambayarta yanda suka kwana a baƙon guri da bin ba'asin babu dai wata matsala ko?. Samun kanta tai da amsawa Mommy ɗin da “Eh babu wata damuwa Mommy.”

        “To Alhmdllh haka akeso. Sai ku zama cikin shiri gasu Auntynku nan tahowa buɗar kai, zasu kuma maidaki gidanki In sha ALLAH”.

    Duk da bawani ta damu da zuwa can ɗin ba ko ɗaukar hakan da muhimmanci ta amsawa da Mommy ɗin da to. Da ga haka ta miƙawa su Amrah wayar ta ƙarasa shirinta dan tayi wanka harma ta saka kaya.....


      Ƙarfe kusan sha biyu dangin Lulu suka iso gidan su Smart da shatara ta arziƙi na kayan gara dana rabo. Acewarsu waɗan nan iya na nan gidan su Smart ɗin ne nashi kayan garar ankai can gidansu. Koda Abba da aka kira yazo kai tsaye yace musu baza'a amsa ba kayan sunyi yawa. Haƙuri su Aunty Saliha sukaita bashi amma fir yaƙi, ya daice an amshi kayan rabo suyi kamar yanda al'ada ta tanadar amma kayan abinci kam a'a sunyi yawa. Wanda aka kaima Smart ɗin sun wadatar. Dole aka haƙura da sauke kayan daga motar da aka ciko da su sai iya na rabon kawai. Duk abinda ake Lulu taji, hakan kuma ya matuƙar bata mamaki, sai dai batace komai ba. Anyi rabo na bajinta daya tsayama su Umma arai, dan a kaf aurarrakin ƴaƴansu maza ko rabin hakan ba'ayi ba, hatta ƙannen Smart da ke ɗakunansu har ƴaƴan Aunty Amarya sai da aka basu abu, daga haka akai ɗan abinda al'ada ta tanadar ciki harda kai Lulu gaban surukinta Abba da tsirarun ƴan uwansa datai ƙyau cikin lass pitch color da yay matuƙar mata ƙyau skert da riga da mayafinsa, ga kayan sarƙa ta ɗora sai ɗaukar ido take duk da kwalliyar kaɗan ta yarda su Amrah sukai mata. Fuskarta a lulluɓe take, ta gaishesu kamar yanda aunty Saliha ta sanar mata tayi tunkan su fito daga ɗakin aunty Amarya. Abba yay mata tarba irin ta uba da ƴa, ya saka mata albarka sosai da yimata nasiha tare da addu'a, hakama ƴan uwansa. Daga nan ɗakin Ammah aka kaita. Itama dai kamar Abban ne, ta mata nasiha da sanya albarka a wannan aure tare da fatan alkairi. Hakama ƴan uwanta. Sai ɗakin Umma da taso yin abin kunya sai da ƴarta ta kwaɓeta, a hakan ma dai sama-sama tace ALLAH ya sanya alkairi. Hakan bai damu su Aunty Naja'atu ba, dan sun fahimci Umma sai a hankali, mace ce da bata iya ɓoye hassadarta. Sai wajen Mama. Ita dai ta matuƙar dannewa dan ƴaƴanta ita na ƙoƙarin ƙwaɓarta idan sukaga zatayi wata ƙwaɓar, ta tarbesu da yima amarya nasiha a taƙaice itama tai addu'a kuma. Sun koma ɗakin aunty Amarya itama tai fatan alƙawari sosai da addu'a. Sannan aka sake maidata ɗakin Ammah, da ga canne aka ƙarasa abinda ya rage na yima juna godiya da fatan alkairi sannan suka ɗauki Mawaddat domin maidata can gidan da zasu zauna. Baƙi na nan kuma suka ƙarasa shirinsu na tafiya dan jiya duk an kaisu sunga gidan amarya bisa tsarin Abba dan yau kar ta zama sun takura musu.


       Sun iso gidan amarya lafiya, Lulu ta buɗe idanu da ƙyau tana kallon ko'ina tunda dai daga ita sai ƴan uwanta. Komai batace ba akan gidan da tsarinsa, ita babbar damuwarta a yanzu kawai ta samu kayan shaye-shayen ta ne, dan shine ya haifar mata da zama shiru-shiru da rashin ƙarfin jiki. Sarai aunty Saliha ta fahimci damuwarta, sai kuma yanzu ta sake gane hikimar Uncle Yousuf da duk ya tsara hanyar toshe mata inda zata iya samun komai da zata sha, dan a dalilin hakan gashi nan sun samu tayi laushin da kowa ke iya controlling ɗinta batare da an samu ko ƙaramar matsala ba. Suna shiga takai kwance a falo ta dunƙule jikinta waje guda ta rufe idanu. Suko suka shiga ɗan gyara abinda zasu gyara su Amrah nata santin yanda gidan ya tsaru duk da bai kasance katafare ba. Sai da suka daidaita komai yanda ya kamata, Aunty Naja'atu ta sakata yin sabon wanka wajen ƙarfe shida na yamma, kafin ta fito sauran mutanen dake gidan duk suka wuce, aka bar su Aunty Saliha kawai sai su Amrah dake ta ƙara goge inda aka ɓata da sassaka turaren wuta. Tsaye sukayi a kanta ta shirya cikin wasu ubansun yadi mai taushi da ɗaukar ido, sai yi take kamar zatayi kuka amma suna lallashinta dan sun fahimci matsalarta, sai dai kowa da yanda ya fahimta ɗin kasancewar aunty Naja'atu bata san Lulu na shaye-shaye ba, dan duk da tamafi samun damar yi idan taje wajensu a Abuja amma iya takunta yasa basu taɓa gane komai ba da ga ita har Uncle Khamil. Sai da suka tabbatar komai ya dai-daita a yanda suke buƙata sannan suka zare jikinsu suka fito a ɗakin, ita dai tana kwance a tunaninta zasuje falo ne, koda taji gidan yayi tsitt barcin dake rinjayar idanunta yasa bata kawo komai a ranta ba ta cigaba da saƙa ta yanda zata samu abinda take muradi........✍️

    



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments