Furar Danko 57
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣7️⃣
........Wajen ƙarfe tara ALLAH ya kawo aunty Bilkisu ɗakin zata ɗauki kayan biki data ɓoye dan bama facalolinta da zasu wuce. Da sauri ta ƙarasa gaban gadon tana ambaton sunan ALLAH. Ta kai hannunta a goshin Lulu dake barci. Zafi zau har tana jin harbawar jijiyoyin kan nata. Bargo taja ta lulluɓa mata, sannan ta kwashi abinda tazo ɗaukar ta fice. Bata san yin kwakwazo hankalin mutane ya dawo nan, dan haka ta sallami facalolin nata sannan ta koma cikin raɗa ta sanarma Ammah da ke a cikin danginta da zasu kwana. Hankalin Ammah ma ya tashi, ta miƙe cikin hikima ta shiga bedroom ɗin, itama dai tattaɓa goshin nata tai, sai kuma ta juyo tana kallon Aunty Bilkisu.
“Yanzu ya za'ayi kenan? Dan nima bana son kowa ya fahimta baki baka san yanda na wani yake ba”.
“Hakane Ammah, to kodai a kira Hydar, sai ya samo mata magani”.
Ɗan jimm Ammah tai na tunani, sai kuma ta ɗan sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Kirashi ɗin to. Ki kuma turomin Auntynku”.
Da to Aunty Bilkisu ta Amsa tana fita, sai da ta fara zuwa tai kiran aunty Amarya da Ammah tace kafin ta wuce sashen samarin gidan. Duk suna waje wajen dj balle ga ƴammata dama cike da gida, dan kusan duk ɗakunan ma a kulle suke, sai ɗakin Smart ne da ya nuna haske ke tabbatar da mutum a ciki. Sallama tayi aka amsa mata sannan ta shiga. Shi da Ahmad ne kawai a ɗakin, dan abokansu su kam yau duk kowa ya kama gabansa tunma da safe kasancewar gobe idan ALLAH ya kaimu Monday kowa zai koma kan aikinsa. Ahmad da ke zaune yana shan fura ya dubi aunty Bilkisu da murmushi yana faɗin, “Aunty Babba ke da kanki”. Murmushin ta mayar masa da faɗin, “To ya na iya Ahmad, amaryarku ce babu lafiya”.
“Ya Salam! Miya faru?”.
Ya faɗa da sauri. Dai-dai nan Smart ya fito da ga toilet da alama wanka yayi, sai dai sanye yake da jallabiya sai ƙaramin towel yana goge sumar kansa. Su biyun duka ya kalla saboda jin abinda Ahmad ya faɗa, da son jin amsar da Aunty Bilkisu zata bada. Cikin damuwa ta ce, “Zazzaɓi ne da ciwon kai mai zafi. Gata can cikin bargo tanata rawar sanyi ma”.
Smart ya ɗan lumshe ido ya buɗe, sai kuma ya ɗauki turare ya ɗan fesa da faɗin, “Inaga hayaniyar nan ce....”
“Hakama Ammah tace, shiyyasa ma tace a kiraka”. Aunty Bilkisu ta katsesa da sauri. Ɗan Basket ɗin da yake ajiye magunguna ya ɗauka, sai kuma ya dubi Ahmad da faɗin, “Ina zuwa”. Kai ya jinjina masa da mata addu'ar samun lafiya. Su kuma suka fice. Cikin gidan da sauƙin mutane dan duk ana waje wajen dj, sai ƴan tsofaffin ne da suka gaji sukai zamansu. Aunty Amarya ce ta taresu tun a farkon shigowa tace su biyota. Binta sukai sashenta, falon babu kowa sai yara da aka kwantar, kuma duk yaranta ne, dan ita danginta ma duk sun wace sai ƙanwarta budurwa da zata kwana tana kuma tare da su Maryam. Kai tsaye bedroom ɗin ta suka shiga, Lulu da aka maido nan tana kwance a gado cikin bargon da Aunty Amarya ta lulluɓa mata. Aunty Bilkisu tace “Yauwa nan aka maidota ashe?”. Amsa Aunty Amarya ta bata da “Eh nan ɗin yafi ƙarancin hayaniyane”. Sai kuma ta kalli Smart da ya zubama gadon idanu kawai batare daya ƙarasa ba. Katseshi tai da faɗin, “Hydar ƙaraso, Bara a samo ruwa tasha magani, sai dai banajin ma tunda aka kawota gidan nan taci wani abu. Ko a ɗan samo mata abinci? Ko tea haka ko”.
A hankali ya ce, “Ko tea ɗin dai zaifi”.
Babu jimawa Aunty Amarya ta dawo da tea da ruwa. Tana ajiyewa suka fice ita da aunty Bilkisu, sai lokacin ya ƙarasa gaban gadon. Da ga tsaye ya kai hannu kan bargon ya ɗan yaye kaɗan idanunsa suka sauka akan ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Kamar ko yaushe yau ma babu kwalliya, sai wani irin sirrintaccen ƙyawu data ƙara fiye da yanda ya santa. A karo na biyu bayan ranar dinner daya riƙe mata hannu ya taɓa jikinta yanzu ma. Saukar hannunsa mai sanyin danshin ruwan wankan daya fito ya sata buɗe idanu kamar a ɗan zabure. Cikin sa'a kuwa suka faɗa cikin nasa saboda shima kallonta yake. Sake waro idanun tai da ƙyau, sai kuma ta kai hannu ta buge masa nasa hannun da har yanzu ke akan goshin nata tana hararar sa. Cikin ƙarfin hali ta ce, “Kai kuma waya gayyatoka nan?”. Yanda tai maganar da son yin masifa sai dai babu ƙarfi yaso bashi dariya, amma sai ya danne abarsa baiyi ba, sai ma kaiwa zaune da yay a bakin gadon har jikinsu na gogar juna sai dai ita a bargo take, kanta ya ɗan kifo yana raba hannayensa gefe-da-gefenta ta kasance a tsakkiya. Idanunta data sake rufewa ta buɗe da sauri jin saukar numfashinsa saman fuskarta duk da akwai ƴar tazara a tsakaninsu, ta sake watsa masa harara ta ce, “Kai kuma wai miye haka? Kake yi”.
Karan farko cikin ɗan lumshe idanunsa da buɗewa a lokaci guda ya motsa lips ɗinsa dan shima dai ciwon kansan nan na tare da shi a yau ma yini guda. Dan ma yanata addu'a da shan addu'oi wajen Malam sannan Abba yay masa kamu ɗazun da magrib shine ma ya ɗan samu barci sai yanzu ya tashi yay ɗan wanka zaiyi sallar isha'i da shafa'i da wutri aunty Bilkisu taje. “Zan dai yi Madam. Amma first ina son sanin mike damunki?”. Yay maganar cikin tausasa harshe sosai.
“Meya ruwanka malam nifa bana son shishshigi ka sani”. Itama ta faɗa cikin tsiwa da takurar yanayin kusancin nasu.
“Inafa na sani, sai dai yanzu da kika faɗa zan kiyaye. Amma yanzu dai ni ba faɗa nazo muyi ba, tashi kici abinci kisha magani”.
“Nace maka ina buƙata ne?”.
“Basai kina buƙata ba ai”. Ya bata amsa yana ɗaura hannunsa saman bargon zai yaye. Tattaro bargon tai ta da sauri ta tattaro cikin hannunta zata fisge daga nashi. Hakan yasa ya ja shima, itama ta ja, ya ƙara ja, itama ta fisga cikin sake fusata duk da bata da wani ƙarfin kirki a jikinta. Ga bakin masifar sai motsi yake alamar magana take son yi amma bata fita. Da ɗan ƙarfi yaja kasancewar ƙyaleta kawai yake dama, aiko ya ɗage bargon. Gaba ɗaya ta tattaro da hannunsa da bargon ta fisgo cikin takaici sai kawai ya biyo su shima ya faɗa mata a jiki fuskokinsu kan na juna kowa na shaƙar numfashin ɗan uwansa, lips ɗinsa a kan nata. Sosai zukatansu suka hau dokawa da sauri-sauri a tare, sai dai kowanne da dalilinsa. Lulu da wani shuɗaɗɗen al'amari mai matuƙar zafafa zuciya da ƙonata ya fara son hasko mata a memory tasa dukan sauran ƙarfinta ta turesa jikinta na rawa. Hakan bai sakashi yin ko gezau ba, sai dai shima ya matsar da fuskarsa da ga kan nata, sai kuma ya ɗagata jininsa na wani yamutsawa. Zaune ta tashi tana ƙoƙarin sauka a gadon kamar wadda ke neman rasa nutsuwarta dan jikinta rawa yake, yay saurin dakatar da ita cikin sassarfar harshe shima. “Ina kuma zaki je?”. Ganin tana cigaba da janye bargon zata saukan ya riƙota da sauri. Harara ta watsa masa da idanunta da suka kaɗa sosai. Ga jikin nata rawa yake da gasken fa. Magana take son yi amma ta kasa, sai idanunta dake cikowa da ƙwalla. Mamaki sosai hakan ya bashi, amma sai ya sake yinƙurin riƙota.
Hannunta ta fisge, sai kuma ta dafe kanta wasu hawaye masu zafi na sake wanke mata fuska. Idanu ya zuba mata ganin yanda jikinta ke ƙara ƙarfin rawa, hakan ya matuƙar sake ɗaure masa kai da zuciya, dan yanayine bawai mai nuna ƙin da take masa ba matsayin wanda bata so ko tafi ƙarfin aurensa, ba kuma kuya bace. Al'amarin nata kamar dai like wadda ta tuna wani mummunan al'amari mai firgitarwa da ciwo a zuciyarta da yay kamanceceniya da yanayin da suke ciki. Kanta ta sake girgizawa da sake yinƙurawa zata ƙarasa sauka ya miƙe da sauri ya zagaya gabanta. Cikin nuna kulawa da son maidota a nutsuwarta ya ce, “Kinga Please relax, ko mima zuciyarki ke son ayyana miki ba haka bane ba, koma ki kwanta kinga baki da lafiya”.
“Idanunta da sukai masifar kaɗawa da ja ta ɗago ta zuba masa. Sai kuma taja da baya da ga kusa da shi har yanzu dai da alamar bata samu nutsuwar da yake buƙatar ba. Shima sai ya matsa ɗin da kallon ƙofa ya kuma sake maido idanunsa kanta. “Kin gane bana son wani ya fahimci akwai wani abu a tsakaninmu saɓanin abinda suke kallo a bayyane. Ki daure zuciyarki na roƙeki koma mi kike tunani ki ajiyeshi gefe”.
Yaraf ta koma saman gadon ta zauna, hannunta dafe da kanta muryarta na fita da rawa da ɗan kaushi ta ce, “Ka kira min wata a cikinsu bazan iya zama da ga ni sai kai a ɗakin nan ba in har dole sai jikinka ya taɓa nawa”.
“Wancan ma mistake ne, bakuma za'a sake ba, Kinga ga tea kisha sai kisha maganin ki kwanta”.
Tabbas yanda yake mata magana a nutse ya taimaka ma ƙwaƙwalwarta wajen dawo da ita hayyacinta kan cewar bafa abinda ke mata kai-kawon bane ba. Sannan kuma tunda take da shi bai taɓa aikata mata makamancin hakan ba, lallai ta yarda mistake ɗinne kamar yanda ya faɗa. Hakane, ƙwarai hakanne mistake ne. Zuciyata ta shiga sake tabbatar mata. Sai ta fara sauke numfashi a hankali a hankali jikinta na ƙara samun ƴar nutsuwa. Gadon ta koma ta zauna ta jingina da fuskar gadon bayan taja bargon ta rufa, sai ya koma shima ya zauna a baki-baki da ƴar tazara a tsakaninsu yana sauke ƙaramar ajiyar zuciya ya miƙa mata kofin shayin da har ya ɗan fara hucewa..........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
No comments