Furar Danko 56
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣6️⃣
........Kuka ne sosai ya kufce mata, dan matuƙa tana so da begen mahaifiyarta. (Dan Lulu ta kasance irin yaran nan ne masu ƙulafucin uwa, sai kuma gashi ALLAH bai ƙaddara zata rayu da ita ba) kukan nata ya sake karya zuciyar iyayen nata, haka ma Baba duk da dauriyarsa sai da yaji ƙwalla sun cika masa ido. Hannunta ya kama ya zaunar a kusa da shi tare da ɗora kanta a kafaɗarsa ta dama yana ɗan bubbuga bayanta alamar lallashi. Sai da suka samu taɗan tsagaita kukan sai ajiyar zuciya da take faman saki sannan baba ya fara mata nasiha. Bayan ya gama kowa a falon yay tasa. Kakarta da suke kira Dada ma dai ta danne abinda ke ƙasan ranta na ƙiyayyar auren tai mata nasiha sama-sama, dan ta ɗauki alwashin sai inda ƙarfinta ya ƙare wajen raba wannan auren ƙaddarar. Komai da suke faɗa yana shiga kunnen Lulu, sai dai zuciyarta na fassara komai da gargajiyanci da kuma tsauri da yawa saboda ita tunaninta daban da nasu kasancewar babu ilimin addini a tare da ita. Kuka ma da sukaga tanayi na tuna mahaifiyarta ne kawai babu na aure dan a wawtarta auren nan dai na wata ɗaya ne kacal. Duk wata ƙyauta da iyayen nata suka shirya bata anan wajen suka bata ita kamar yanda tsarin family ɗin yake. Bayan an gama Uncle Khamil da Uncle Shu'aib suka ɗauke ta suka maida gidan Daddy dan Uncle Yousuf yana ajiyeta ya juya. Acan ɗin ma dai bayan sallar azhar Daddy da Uncle Yousuf, Mommy aunty Saliha da gayyar iyaye ƴan jiƙamshi suka zagayeta da tasu nasihar, duk da dai Daddy baice komai ba, sakamakon gaba ɗaya yanayinsa ya sauya, jikinsa duk a sanyaye yake alamar damuwar rabuwa da ƴar tashi. Sai dai yana ƙoƙarin dannewa amma hakan ya gagara. Bayan tashi da ga wannan zaman aka cigaba da kimtse-kimtsen tafiya da amarya, yayinda Aunty Saliha ta sake ɗaukar Lulu ta kaima matan nan masu gyarata suka sake murjeta tas da kayan gyaransu na musamman da tarin ƙamshi kala-kala. Ba kuma a maidata gidan Daddy ba sai huɗu na yamma cikin shirin miƙata gidan iyayen mijinta. Tayi ƙyau matuƙa cikin atamfar da Aunty Saliha ta bata ta saka. Aka kuma ɗora mata alƙyabba ƴar ubansu baƙa mai kwalliyar golden da fari kaɗan, sai stones da suka sake ƙawatata. Shara-shara alƙyabbar take. Takalmanta yau ma flat ne baƙaƙe. Babu kwalliya ko ɗis a fuskarta dan tace bata so. Sai dai hakan bai hanata zama mai cika ido da kwarjini irin na amare ba, ga gyara tasha na fitar hankali dama fatar nan ta sake wani irin ƙyau kamar madara a sabuwar ƙwarya (Dangin Smart ban son jealous 🥱😉) Hankalin Lulu bai tashi ba sai da taga Daddy na hawaye sanda aka fito da ita yana riƙe da hannunta zai sakata a motar da Hassan zai ja, dan sune zasu mata rakkiya shi da Hussain da Mubeen. Sai motar ƴan rakkiyar amaryar su biyosu a baya. Duk da abokan ango sunzo kasancewar amaryar ƴar dangi ce akwai zugar motoci da ga family ɗin biyu na Jiƙamshi da Garko da zasu bisu da nasu motocin. Ba Daddy kawai ba Uncle Yousuf kansa yana can falon Daddyn yana sharce hawaye yamaƙi fitowa shi. Lulu da duk taji karaya tamkar ba ita ɗin nan ba ta rungume Daddy ta saki kuka mai ban tausayi. Itafa auren nan baisa taji komai, amma wasu abubuwa da ga zuri'ar tata kansa zuciyarta ta motsu. Da ƙyar Uncle Khamil ya janye Lulu a jikin Daddy aka sanyata a mota, Hussain da Mubeen suka sata a tsakkiya, gaba kuma Amrah da Afrah ne sai Hassan da zaija motar.
Masha ALLAH motocin rakkiyar Lulu sun ratsa kwaryar Kano ne tamkar wata gwamna zata gitta dan gatan da zuri'arta suka nuna mata. Duk inda suka ratsa sai anso jin wanene haka? Koda babu mai bada amsa. A haka suka iso anguwar fagge layin su Smart. Yanda aka jera motocin tun daga ƙofar gidansu har kusan ƙarshen titin ya sake ɗaukar hankali matuƙa, hatta mata dake cikin gidaje fitowa suke leƙen wannan sabon lamari, lallai an sake shaida Smart kam dai ya ɗakko ƴar gidan madara.
Smart da ƴan uwansa mazan gidansu suna falon Abba daya tarasu su duka amaryar ta iso. Daga ɗakin suna iya jin surutai da gidan ya ɗauka da kambama yawan motocin da suka rako amarya. Balle ma motar da aka kawota ciki ta musamman ce da Daddy ya saya mata matsayin gift na aure. Tasha adon ribbon kuwa da balun masha ALLAH. A hankali Smart da ke kusa da Rufa'i mai bi masa babban ɗan Mama ya lumshe idanunsa yana jin wani irin yanayi mai wahalar fassara na saukar masa. Addu'a ya shiga karantowa game da wannan aure nasa mai cike da rikici takowane ɓangare. Ita kanta amaryar da nata.. Addu'ar Smart kamar an saita dai-dai da fitowar Lulu amaryar ƙamshi da ga mota Mubeen riƙe da hannunta. Fuskarta rufe take ruff da hular alƙyabbar dan haka ba'a iya ganinta tako ina sai hannunta mai ƙawace da adon zanen lalle ja da baƙi. Da wani sirrintaccen ƙamshi na musamman mai ratsa ɓargo da jijiya. Har cikin gida Hassan da Hussain da Mubeen da su Afrah sukai mata rakkiya, hakan ya matuƙar sake burge mutane da kallon al'amarin matsayin shaƙuwa ce ta kawo hakan tsakaninsu. Sun kaita har ƙofar falon Ammah da ke cike da ƴan uwanta itama, da ga nan Aunty Saliha da Aunty Naja'atu suka kama hannunta suka ƙarasa da ita cikin falon Ammah. Da ga haka su Hussain suka juya cikin sanyin jiki da basu taɓa tunanin zasu iya ji akan Mawaddat da sukai ƙololuwar tsana a cikinsu ba dalilin fifitata da mahaifinsu yay sama da su da mahaifiyarsu. Mubeen ma sai kawai ya kama hawaye....
Sauran ƴan rakkiyar amarya sun ɗura ciki suma. Wasu farin ciki ya kawosu wasu ko gulma da jinjina inda ALLAH ya kawo Lulun. Duk irin yanga da jin kai da izza irin tata ta ƙare da aure a getto eria irin haka? Kai lallai da mamaki koda yake tarihine ya maimaita kansa tunda haka itama mahaifiyarta tayi, sai dai akwai banbanci sosai a yanayin tsarin auren. Wasu ma harda dariyar mugunta wasu ko tausayinta suke ji a nasu ganin taci baya gaskiya. Wasu ko tayata farin ciki suke ALLAH ya kawota matakin da ko wacce ɗiya mace ke jin alfahari da ɗaukaka. Abu mafi ɗaukar hankali tarbar mutuntawa da suka samu daga ahalin ango duk da yawansu. Ammah kam da ga ciki su Aunty Nasara na shiga da Lulu ta taso ta rungumeta a jikinta. Haka ma ƴan uwanta sai faman musu lale marhabun akeyi. Ajiyar zuciya Lulu ta dinga saki da sake lafewa aikin Ammah, dan wata irin nutsuwa taji tana ratsa mata sassan jiki da ɓargo batare data san dalili ba. Duk da bata san wacece ita ba, ba kuma ta gani fuskarta abinda matar tai mata ya sata jin ƙaunarta. Bayan kakarta Dada Ammah ce mace ta biyu datai mata runguma irin ta mahaifiya, a hankali hawaye suka shiga ziraro mata daga cikin hular alƙyabbar tsigar jikinta na wani irin tashi. Adda Fati babbar yayar su Ammah da suke uba ɗaya ce tazo ta kama hannun Lulu aka shiga da ita ƙuryar ɗakin Ammah da aka gyara dama dan tarbar amaryar, shiyyasa kowa ya fito aka dawo falo da ɗayan ɗakin dan kowance a gidan dama ɗakuna uku ne a falonta.
Gida ya sake amsar harami tako ina, dan ƴan kawo Lulu basu wuce ba sai kusan biyar da rabi na yamma. Lulu na can ƙuryar ɗakin Ammah tare da su Amrah dan ita dai fa babu ƙawa, dama da lafiya-lafiya ne da Nadiya ce zata kasance da ita. Sai dai ta riga ta jingine tarayyarsu a matsayin tarihi ita kuma idan ta ɗana tarkon tafiya bata waiwaye. An tara musu abinci da abin sha kala-kala har da su fura mai ƙyau da tsafta. Aiki su Amrah suka shiga cin nama da furar nan dan sun musu da ɗi. Da farko dai Afrah zata fara wani iyayi Amrah tai mata gargaɗi da tuna mata kashedin da Mommy tai musu. Hakan yasa ta dawo hankalinta, sai da suka buɗe abincin kuma taji ɗanɗano sai ta ware ta hau ci. Duk abinda suke Lulu na kwance lamo a gadon Ammah tana kallonsu kawai. Kanta ke mata wani irin masifar ciwo, dan tana cikin matsanancin buƙatar kayan shaye-shayen ta matuƙa. Kwana bakwai fa kenan bata sha komai ba, kai ai tayi ƙoƙari matuƙa. Har ji take ana mata mutsu-mutsu a brain, ga hayaniyar bikin nan na matuƙar caja mata kai itama. Dan ma nan ɗin da aka kawosu su kaɗai ya mata daɗi, duk da sunajin hayaniyar amma da sauƙi ba kamar suna a wajen ba. Su Aunty Saliha basu wuce ba sai bayan magriba su, ƙin shigowa sukai mata sallama dan karsu takalo ta, bayan wucewarsu ma cikin gidan ta fara lafawa da mutane, dan dj da su Mubarak suka sa ya kwashi mata duk anyi waje. Tuni su Amrah ma da ke jiyo sautin kiɗa suka gudu suka barta ita kaɗai a ɗakin. Batace musu komai ba sai lumshe idanunta da tai barci ya kwasheta, cikin mintina ƙalilan zazzaɓi mai zafi ya rufeta ruf ta hau rawar sanyi, ga fanka na juyawa a ɗakin ta kasa tashi ta kashe ta. Barcin take a wahale ga mafarkin mahaifiyarta........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
No comments