Furar Danko 55
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣5️⃣
......Daga nan gidan Daddy suka ɗunguma ɗaukar amaryar ƙamshi. Lulu lu'u-lu'un Jiƙamshi family, tauraruwa abar buƙatar son ganin kowa.
“Ya arrahaman!” Ango Smart ya ambata a hankali lokacin da Hussaini ke fitowa da ga gidan riƙe da hannun Lulu. Ni kaina masu karatu sai da alƙalamina yay adungure ƙasa da ƙyar na kamosa na cigaba da muku burutun. Amarya da tayi jiƙaƙƙen ƙyau, idan nace muku ƙyau ina nufin ƙyau maƙurar ƙurewa a cikin ƙarshen ƙure. Wani irin shegen material ne golden color da aka ƙawata da adon fararen stones masu walwali da ɗaukar idanu. An masa ɗinkin gown data kama mata jiki, sai aka ɗaura wani ƙawataccen alƙyabba fara da adon golden kuma a sama, ta rufe jikinta gaba ɗaya tana ɗan jan ƙasa kaɗan. Ɗauri iya ɗauri, ga shi kwalliyar da akai mata ƴar dai-dai misali da bata ɓatar da ainahinta ba a yanzu. Kayan yari komai yaji, ƙamshi kam ba'a magana wayyoni ALLAH kai jama'a. Yaufa Lulu ƙamshi a ƙamshin take ɗan gaske. Takalman ƙafarta su kansu abin kallo ne, suma farare ne da kwalliyar golden sai pos ɗin ta itama farace da kwalliyar golden stones. Kamar shock ne ya jasu a lokacin da Hussain ya kamo hannun Smart ya saka masa na Lulu. A tare suka zabura zasu janye amma tsabar muguntar Hussain ya sake riƙewa gam ya hana hakan. Duk sai sukai diri-diri da idanu (kamar an kama suruki a ɗakin ƙawar kakar matarsa😂😜) cikin wani irin malalacin yanayi ta sakar ma Smart kasalalliyar Harara. Sai kawai ya samu kansa da ramawa shima. Shi Hussain ma sai abin ya bashi dariya. Amma sai ya danne daƙyar baiyi ba ya sake matse hannayensu cikin na juna da faɗin, “Yayana Aliyu Hydar Zakin zaki ga amanar ƙanwata na baka, har abada bana son ka saki wannan hannun ya kasance cikin laluben naka dan ALLAH”.
Smart da Adams apple ɗinsa keta kaikawo a maƙoshi ya saki murmushi mai sanyi da faɗin, “In sha ALLAHU Yaya Hussain. Na kuma gode”. Murmushin jin daɗi Hussain ya saki jin Smart ya kirashi da Yaya, duk da kuwa yasan Smart ɗin zai iya girmarsa da kusan shekaru biyar ma. Hannayen nasu ya saki yana kallon fuskar Lulu da tai wani irin yin takwaf-takwaf tana neman zame hanunta dake cikin na Smart shi kuma ya hana faruwar hakan ta hanyar damƙesa da kyau, kansa ya girgiza mata da ɗan lumshe idanu alamar lallashi irin na yaya da ƙanwa. Dole ta haɗiye abubuwan da ke mata kaikawo a zuciya da maƙoshi a tare, Hussain ya buɗe musu motar da Ahmad ke ciki yana jiransu a mazaunin driver. Ita ta fara shiga, sannan shima Smart ɗin ya shiga, sai kawai Hussain ya shiga gaba dan Uncle Yousuf ne duk ya tsara musu hakan saboda dai kar mutuniyar ta bada ƙafa🤣 dan tabbas zata iya maida hall ɗin kudanci da ga gabashin da yake a gine😂. Ganin Hussain ɗin kam ya sake saka mata nutsuwa da ƙwarin gwiwa harda sauke ajiyar zuciya kamar Smart ɗin yazo ɗauketa kenan😂. Bata ƙara yarda ta kallesa ba duk da harga ALLAH ya matuƙar canja mata tamkar bashi ba. Ta kuma saka pos ɗin ta a tsakkiyarsu alamar karma yace zai raɓeta. Shima dai dama baiyi niyyar hakan ba, shiyyasa yay zamansa sosai jikin ƙofa suka bada gaf sosai a tsakkiyar. Da ga Ahmad har Hussain sai da suka ji dariya a zukatansu saboda yanayin zaman amarya da angon. Ga shi kowa ya juya kai ya kalli waje tsabar babu ruwan wani da wani ma kenan. Sai da suka fara tafiya Hussain da Ahmad suka gaisa. Da ga haka sukacigaba da ƴar hirarsu a hankali su biyu har suka iso. Wajen fita ne fa dole dai Lulu ta haƙura Smart ya fara fita, dan shine ya buɗe mata da kansa ya kuma miƙa mata hannunsa alamar ta ɗora nata. Ƙaramar Harara tai masa tana ɗauke kanta, sai kawai ya cije lips ɗinsa tare da ranƙwafowa gaba ɗayansa yana tattare hannun rigarsa bayan ya cire link ɗin, miƙa hannun yay alamar zai ɗauketa. Da wani irin bala'in sauri ta waro duka manyan idanunta waje da faɗin, “Kuttt! Mi zakayi?!”.
“Ɗaukarki mana. Ba haka kike buƙata ba Madam”. Ya faɗa cikin salon ɗage gira ɗaya da kashe ɗayan idon. Tsabar abinda ya tokare maƙoshin Lulu sai taji kamar ta buɗe dukan muryarta ta ƙwala ihun da kowa da ke hall ɗin sai ya fito ma. Ta tsani wannan Madam ɗin da yake kiranta da shi tun daga randa sukaje duba shi. Ganin yanda ta fara cika ya sashi ɗage duka hannayensa (alamar wanda yay surrender) da gyara ranƙwafar da yay yana dungure kansa da faɗin, “Kai Aliyun nan ka nutsu a gaban Madam kake”. Sai kawai ta ƙara watso masa harara da tura baki gaba. Da sauri ya ɗauke idanunsa dan harga ALLAH sai da ƙassan jikinsa suka amsa akan tura bakin nan. Hussain dake dariyar drama ɗin tasu ne ya katsesu da faɗin, “Sorry kinjin Sister bashi hannun kinga su Baba duk suna ciki shigowarku ake jira kawai a fara abinda ya tara mutane”. A hankali ta ɗago yatsunta uku batare data kallesa ba. Shima sai ya saka nasa ukun tsakkiya kamar yanda tayin yana ɗan taɓe baki kamar yanda tayi, sai da ya riƙo hanun nata baki ɗaya sannan ya rumtse cikin nashi. Koda ta fito bai yarda sun bar jikin motar ba sai da yasa ɗayan hannunsa da kansa ya gyagygyara mata rigar alƙyabbar da ƙyau yanda ta sake suturta kuma hakan bai hana fitar ƙyaun da tai ɗin ba. Da ga haka suka ƙarasa inda abokan ango dana amarya ke jira suka tafi a nutse kamar yanda ake raka amarya da ango ƴan gata zuwa ga hi table. Matuƙar birgewa sun burge mutane da yawa, yaro da babba ƴammata da samari. Taro ne da ya haɗa harda manyan mutane da iyaye da kakanni shiyyasa babu wata shiririta ko baɗala a cikinsa. Amarya da ango ma tunda aka kaisu mazauninsu hatta cake a zaunen suka yanka shi. Koda ta ɗibo danta bashi maimakon yin hakan saita lakata masa a hanci. Abin ya burge mutane da basu dariya, dan yanda tayi ɗin sai ka ɗauka duk cikin soyayya ne, itako tayi hakanne danta bashi haushi.
Shima daya ɗibo ya kai mata baki, buɗewa tai tana shiryama ranta muguntar gallara masa cizo a yatsun dake riƙe da cake ɗin, amma sai da yaje gab da bakin nata sai ya juya hannun ya lunƙuma a nashi bakin yana mata gwalo. Ai hall ɗin kamar zai fashe dan dariya saboda yanda ta sakankance zatayi mugunta amma aka rusa mata plan. Pos ɗin hannunta ta ɗan buga masa a damtsen hannu tana hararasa kamar zatayi kuka dan haushi.
“Aliyu abin tausayi wannan harara dai ka banu da ita kai kam. Anya an taɓa angon da yasha harara a ranar aurensa sama da ni?” ya faɗa yana mangare kansa da kansa. Karan farko ya bata dariya amma sai ta gimtse, tama ɗauke kanta gefe tana ɗan taɓe baki, dan yau sam bata da ƙarfin yin masifa kuma. Da ƙyar aka samu hall ɗin ya lafa da dariyar batun cake aka cigaba da abinda ya tara mutane. Ko sau ɗaya Smart bai yarda ya tashi ba hakama Lulu bai bari ta tashi ba. Da an buƙaci ganinta a wajen fili zai riƙe mata hannu ya girgiza kansa, itama ɗin dama bata da sha'awar tashin, saita fisge hanunta tana harararsa dan yau ita kaɗai aketa faman antaya masa buhu-buhu. Har fa dai MC ya fahimci ango bai san amaryarsa ta tashi kamar yanda shima bai tashi ba. Masu musu liƙi ma dai sai dai su samesu anan. Alhamdullah duk wanda ya shigo wajen nan zai tabbatar maka yaci ya ƙoshi har ma da ƙullar takeaway, Smart ya gaisa da mutanen da bai taɓa tunanin ganinsu koda a zahirin rayuwa ba, dan ƴan siyasa sun halarci taron nan matuƙa da manyan ƴan kasuwa. Har akai aka tashi bayan cake ɗin nan da ruwa baici komai ba a wajen, hakama Lulu ita daman cikin nata ya riga ya naɗe abincin ba damunta yay sosai ba. Ganin dare yayi dan sha biyu ta gota sanda aka tashi Uncle Yousuf yace su Smart ɗin suje gida abinsu zai koma da Lulu gida, dan tun a hall ɗin ya ga Smart nata faman dafe kai alamar bayajin daɗi dauriya kawai yake yi. Yako ji daɗin hakan da Uncle Yousuf ɗin yay musu, itama kuma mai gayya mai aikin taji daɗin hakan, dan ko sallama bata tsaya sunyi ba tai gaba tai shigewarta mota tana zare alƙyabba ɗin tata datai mugun damunta ita da ɗaurin ɗan kwalin....
*_WASHE GARI_*
Washe gari safiyar Lahadi aka tashi da shirin kai amarya Lulu. Dan haka da safe Uncle Yousuf ya ɗauketa da kansa ya kaita gidan Baba. Inda yayye da ƙannen mahaifiyarta suka taru domin mata nasiha. Alh. Sulaiman ne kawai babu, sosai zuciyar Lulu tai matuƙar rauni, dan mahaifiyarta ce kawai babu a wajen bayan mahaifin Tajuddeen. Ita kaɗai suka taɓa rasawa a cikinsu........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
No comments