Furar Danko 48
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣8️⃣
........Bai nuna ma ya jita ba balle ta samu amsa. Sai ma sake tattara hankalinsa da yay ga Deen. Uncle Yousuf ne yay mata nunin ta zauna cikin harara. Zaunen ta kai a ɗofane gefen katifar kaɗan badan taso ba. Bayanin da Smart ke masa na cewar su Daddy sunzo da twins da Mubeen har da su Suhaib sun dubashi babu ma jimawa suka wuce ya sashi maida hankalinsa garesa.. har cikin rai yaji daɗin hakan, dan baiyi zaton Yayan nashi zai yi wannan abin kirkin ba. Da ga haka suka cigaba da ƴar hira jefi-jefi. Kusan mintuna goma Lulu dai na zaune tana bin ɗakin da kallo ƙasa-ƙasa, sai dai duk ta matsu su wuce amma taga Uncle Yousuf baida niyyar ma hakan. Dan hankali kwance suke hirarsu kamar ma sun manta da ita a ɗakin. Deen kuwa yay matashin kai da ƙafarsa yana buga game ɗin ball da yace ya kunna masa dama shine tushen amintakarsa da yaron tun farkon fara aikinsa. Kiran wayar Uncle Yousuf da akai ta katse musu hiran, tashi yay ya fita a ɗakin domin amsawa.
Shiru ɗakin ya ɗauka baka jin komai sai hayaniyar game ɗin da Deen ke bugawa. Dan tvn ma da ke aiki dama ƙasa-ƙasa ƙararta take. Sosai yanzun kam ya zuba mata ido duk da iya bayanta da ɗan gefen jikinta zuwa fuska kawai yake iya gani, ƙasa-ƙasa yay ƙwafa da ɗaukar ƙaramar wayarsa da ke gefe yay ɗan danne-danne ya kai kunne. Ana ɗagawa da ga can a cinkunshe ya ce, “Bama Nasreen ta kawo min hijjab”.
Da mamaki Maryam ta ce, “Yaya Hydaar hijjab kuma?”. Ƙitt ya yanke kiran batare da ya amsa mata ba. Kafin ya ajiye wayar kira ya shigo, Uncle Yousuf ne dan haka ya ɗaga. Kafin ma yace komai da ga can Uncle Yousuf ɗin ya ce, “Aliyu am sorry ina ɗan zuwa bazan jima ba uzirin gaggawa ne”.
“To Uncle ALLAH ya tsare sai ka dawo”. Da ga haka ya ajiye wayar. Dai-dai nan Nasreen tai sallama. Duk da ƙarancin shekarunta bata shigo ba sai da tace, “Uncle in shigo?”.
“Eh Angel”.
Ya bata amsa idonsa a kan ƙofar. Lulu da muryar yarinyar ta ɗauki hankalinta itama ta zubawa ƙofar ido. Sai ko gata ta shigo hanunta ɗauke da gogaggen hijjab fari da keta tashin ƙamshi. Ɗan tsayawa tai tana ma Lulu da ta zuba mata ido kallon rashin sani. Sai kuma ta ce, “Aunty ina kwana”. Batare data jira amsawarta ba ta nufi Smart, sai dai tana tafiyar tana ɗan waigowa ta kalli Lulun, dan ita dai ƙaton gilashin data toshe fuska ne mafi ɗaukar hankalinta. Karan farko Lulu ta saki murmushi tun shigiwarta ɗakin, sai kuma ta sa hannu ta cire gilashin dan sosai ƴar yarinyar ta tafi da hankalinta. Kodan basu da baby girl kamarta a gidansu ne oho. Sanda su Afrah suke kamarta kuma bata Nigeria. Zamanta ta gyara ta yanda zata fuskanci Nasreen da ƙyau, hakan kuma sai ya bata damar fuskantar Smart, dan ta fuskanci katifar ne kai tsaye shi kuma yana a gicciye ne.
“Baby Girl how are you!”.
Ta faɗa tana kai hannu ta kamo na Nasreen da ta gama miƙama Smart hijjab ɗin da ta kawo. Yarinyar sai da ta kalli Smart fuska a ɗan ƙwaɓe, ya ɗaga mata kai ciki lumshe idanu alamar taje sannan ta dawo da kallonta ga Lulu a hankali ta ce, “I am fine”.
A zuciya Lulu tace (tofa ashe tana jin turanci) a zahiri kam sai ta matso ta jikinta. Ga dai yarinya fess kuma ƙyaƙyƙyawa, amma batai zaton samunta wai tana jin yaren turanci ba. da turancin ta sake tambayarta sunanta. Nan ma ta amsa mata tsaf, ta tambayeta shekararta nawa, ajinta nawa kuma a makaranta. Nan ma ta bata amsa dai da turancin. (Ikon ALLAH) ta sake faɗa a zuciya. A karan farko kuma ta dubi Smart da ya zuba musu idanu. Da farko dai magana tai niyyar yi, sai kuma tuna dawa take a ɗakin ta fasa dan yanda ya zuba musu ido ga kayan jikinsa da haka kawai suka sakata jin wani iri, ɗauke idanunta tai da ɗaukar Nasreen cak ta maida saman cinyarta ta zaunar. Nasreen ta kallesa a ɗarare ta ce, “Uncle wacece ita auntyn nan ban santa ba?”.
“Kema wacece ai bamu sanki ba?”.
Cewar Deen cikin tare numfashin Nasreen cike da haushin hawa masa cinyar Aunty Lu da tayi. Aiko Nasreen ta balla masa harara shima ya rama yana kaina ƙafarta tsunguli. Doke masa hannu Lulu tai da faɗin, “karka taɓa min Baby”. Baya yaja yana tura baki. Smart ya riƙosa yana murmushi. “Kaga ƙyalesu kaima ba gaka da ni ba”. Dariya yaron yay da faɗin, “Yes Uncle” sai kuma yayma Nasreen gwalo. Itama ramawa tai da faɗin, “Ai dai Uncle ɗina ne, kuma yafi so na”.
“Mai ƙarya yafi sona. Ko Uncle Smart?”.
Deen ya faɗa kamar zai yi kuka. Murmushi Smart yay masa da gyaɗa kai. Cikin raɗa ya ce, “Ai namiji na namiji ne, mace kuma ta mace. Itama ga aunty ta samu. Kaga 1-1 kenan. Dan haka kuyi gaisuwa banda faɗa”. Dariyar jin daɗi Deen yayi, tare da miƙama Nasreen hannu. Sai yarinyar ta maƙe kafaɗa da faɗin, “Halamun ne gaisawa da maza, a islamiyya an faɗa mana duk mai gaisawa da maza za'a sashi wuta. Ka gaisheni dai a haka. Ko aunty?”.
Matuƙa gaya Nasreen ta burge Lulu, fuskarta da murmushi mai ƙayatarwa ta gyaɗa mata kai. “Hakane sweet heart”. Cikin jin daɗi Nasreen tace, “Kaji ko”.
“Ai nima an faɗa mana a Islamiyyar mu”. Cewar Deen shima. “Lah da gaske? Zo muje to kaga littafaina”. Nasreen ta faɗa itama. Babu musu Deen ya miƙe yana ajiyema Smart wayarsa akan jiki. Itama sai ta tashi suka fice a tare.
A hankali Lulu da ke binsu da kallo cike da sha'awa ta wani lumshe ido fuskarta da murmushi har sannan. Idanunsa masu kaifi ya zuba mata, sai kuma a hankali ya motsa lips ɗinsa wajen faɗin, “Kin fara tunanin kema nan da 5years kina da kamarsu ne?”.
Idanun ta buɗe da sauri a kansa tana haɗiye murmushin fuskarta. Sai kuma ta balla masa harara tare da ƙoƙarin miƙewa. Sai dai yanda rigar tai mata masifar ɗam-ɗam a jikin yasa sai da tai ƙoƙarin dafa kujera. Fuska ya sake tamkewa da miƙo mata hijjabin. Batare da ya bata damar cewa wani abu ba duk da ya fahimci akwai abin faɗar a bakinta ya tareta da faɗin, “Haramunne matar aure ta fito a shiga mai bayyana ainahinta ga wasu, kai koda ma mara auren ce. Dan haka ki kiyaye inada kishi mai zafi. Wannan kuma ya zama first and last dan ban shirya rabarma kowanne sankaran ido ba, duk abinda akace nawa ne to nawa ɗinne ni kaɗai koda bana ra'ayinsa”.
Tuni wani irin tuƙuƙin takaici ya maƙure maƙoshin Lulu. Cikin kaushin murya da jifansa da wani malalacin kallon sama da ƙasa ta ce, “Kai a matsayin wa? Da ka isa hanani yin abinda yake ra'ayina!”.
“Ni a mijinki da ya biya sadakinsa”. Ya bata amsa cike da gadara da kaushi ga idanunsa da ya wani tsatstsareta da su kamar zai cinyeta.
Rasa abin faɗa dan takaicin da ya ƙulleta ya sata faɗin, “Mtsoww! To baka isa ba. Kayi tsararo Shash.....”
Bata kai ƙarshe ba ya tareta da faɗin, “To ke da kike jin kin isa ki sake sakawar ki fito ɗin zan tabbatar miki isar tawa kuwa.” ya ƙare magana yana jefa mata hijjab ɗin a saman cinya ya maida hankalinsa ga cire ruwan da ake ƙara masa dan ya ƙare. Mamaki ne, ko takaici, ko tsoro ne ya saka Lulu yin sagade tana kallonsa oho itama bata gama tantancewa ba. Idanunta sunyi masifar kaɗawa ga tarin masifar da take tattarowa na mata kai kawo a ƙirji. Ƙarasa miƙewa tai tana hucin bala'i, hakan yasa hijjabin ya faɗi ƙasa. Shima miƙewar yay duk da baya jin ƙarfin jikinsa, sai kawai ganinsa tai a jikin ƙofa yana saka mata key”.
“Kai wai mika ɗauki kanka ne?”.
“Duk yanda zuciyarki ta baki”.
“Mtsoww banda lokacin ka ban hanya na wuce”
“Idan kinbi abinda nace kenan. Saɓanin hakan na nufin cigaba da zama a ɗakin nan matsayin kinzo ke nan”.
“Mtsoww kana buƙatar ganin likita. Wlhy kaban hanya kona illataka”.
“Muyima juna illa dai. Dan wlhy idan kinga kin bar ɗakin nan to kin saka hijjab kuwa. In ko ba haka ba kimayi kiran waya gida tun yanzu a fara tattara miki kayanki a aiko miki”. Ya na gama faɗa ya bar wajen ƙofar yana zira keys ɗin cikin aljihun 3 quarter ɗinsa, sai ma ya shige toilet abinsa. Karo na biyu kenan da take jin an mata wulaƙanci mafi muni, randa ya kaita dawanau da kuma yau. Wai ita illiterate drivern nan nata zai ce ma sai ta saka hijjab sannan ta fita a ɗakinsa. Uncle You duk ya ja mata wannan rainin da tozarcin. In ba haka na velleger ɗin nan ko'a hanya yama isheta kallo ne bare har ya kalla cikin idonta wai ya bata umarni. Lallai dole ne ma wannan drama ɗin ya tsaya a haka. Dan bazata iya wannan auren contract ɗin ba kuwa.....
Motsin fitowarsa ya katse mata tunani. Ta buɗe idanunta da suka gama kaɗewa da ɓacin rai ta ɗan bisa da kallo. (Ƙaton banza) ta faɗa a zuciyarta tana mai kauda idanun nata da ga kansa. Saman katifarsa ya koma ya zauna, jug ɗin kununsa ya buɗe ya zuba a cup, sai kuma yasa sugar kaɗan da madara ya juya. Jan jikinsa yay baya ya zauna da ƙyau ya fara shan abunsa hankali kwance tare da ɗaukar wayar tasa ya fara sana'ar buga game ɗin ball tamkar ma ya manta da ita ne a ɗakin.
Fiitt yaji an warce wayar. Sai ya ɗago a ɗan zabure ya kalleta yana wani ɗan buɗe baki. Harara ta watsa masa kai kace Luulu eyes ɗin nata zasu zubo ƙasa ne. Kansa ya shafa yana wani ƙasa-ƙasa da nasa idanun. “Madam ni fa hararar nan tana sani tunanin kamar nayi wani abu, gaskiya in dai ana son a rabu lafiya to a daina, kin san abinka da ba sabin ba tuzuru da mata”. Ya ɗan sake ɗago ido ya kalletan sai kuma ya maidasu ƙasa kamar mai jin kunya.
Iya matuƙar kunnuwa kam Lulu ta kai maƙurar kunnuwa. (Mi wannan abin yake nufi?) Ta ayyana a zuciyarta, tsaf kuwa ta fahimtar da ita inda ya dosa. Wani irin waro idanu tai da faɗin, “What! Wait! Wait! Wai mi ma kake nufi?!”. Tsabar yanda take jin masifa da ɓacin rai takaicinsa jikinta har wani tsuma yake yi. Ya samu yanda yake so, dan kuwa ta kunnun fiye ma da yanda yake buƙatar. Idanun ya sake ɗagowa ya kalleta cikin son sake kaita maƙura ya ce, “Ni fa Madam ina jin kunya ne, amma idan kince na nuna miki a aikace sai na rufe ido, kema Please ba sai kin kalle ni ba sai ma mu kashe fitil......”
Wani irin mugun wawura ta kaima filos ɗin saman sofar ɗakin ta shiga jefa masa su ɗaya bayan ɗaya. Hannu ya sa ya dinga kare kansa. Ta ce, “Kai har ka isa ma yin wannan tunanin a kai na, har abada kai gaban abada ma ƙazamin yatsar hanunka ma bai isa zuwa ko kan veil ɗina ba ma illiterate velleger!”.
Dariyar da ke neman kufce masa ya keta faman dannewa. Dan muryarta har rawa ya ke na matsanancin takaicinsa, filos ɗin da ta gama loda masa a jiki da jifa ya shiga janyewa yana faɗin, “Ba sai kin ƙirƙiri hanyar maidani asibiti ba. Ni dai ina tsoratar miki ganin aikin jahilin baƙauyen nan a aikace. Dan kin san mu idan muka ɓalle ba'a iya taro mu saboda ƙazamin hannun nan da wahala idan zaiji bari fa. Sannan ki bar fassarani in da banje ba karki lalatama Ammah yaro tun ban tafasa ba ki ƙona ni Aliyu ba inda kike nufin na nufa ba”..........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
No comments