Recent Updates

Furar Danko 47

 


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗




           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣7️⃣



.......*_WASHE GARI_* da asuba da ƙyar Lulu ta iya tashi sallar da Uncle Yousuf ya sa aunty Saliha ta tadata yi. Dan kuwa dai daren jiya suna gama hira da Aunty Saliha ta shige ɗaki sakamakon dawowar Uncle Yousuf gidan a gajiye ta samu sirof ɗin ta da wani ya kawo mata a gidan bayan sallar isha'i ta fita a sulale ta amso bada sanin aunty Saliha ba har kwalba uku tasha. Dan yanda kanta yau ya ɗauki zafin nan ta tabbatar sai tazo kwanciya komai zaita dawo mata a rai ta kwana cikin damuwa. Sam bata buƙatar hakan kuma. Ga shi dama abin yazo mata a dai-dai wato weekend. Dan dama fa duk weekend kusan sune ranakun da tafi ƙwalewa son ranta ta sha barcinta. Kafin a gane tana shaye-shaye sai aita ɗauka gajiyar aiki ce ke sata mahaukacin barcin da take sha. Balle ma Daddy kan hana a tadota  a cewarsa a barta ta huta. Hakan na bata dama ƙwarai da gaske ita kuma ta sha abinda take son batare da sun gane komai ba.

       Sabon barci ta sake dasawa har kusan sha ɗaya sai da Uncle Yousuf nan ma yasa Aunty Saliha tadata. Tun a yanda ta fito ya fahimci wani abu ta sha a jiyan, bai ce komai ba kan haka duk da zuciyarsa tayi babu daɗi sai cemata da yay ta koma ta shirya yana jiranta zata rakashi wani waje. Kai kawai ta gyaɗa masa da komawa ɗakinta dan tana da ɗaki dama a gidan. Ta jima a toilet ɗin kafin ta fito tanata ƙamshin shower gal mai ƙamshin tsiya, dan anan bata da turarrukan wanka duk ta ƙarar da su ta kuma manta ta kawo ta ajiye dan bata iya cikakken sati biyu batazo nan ta kwana ba ko yin weekend. Tana tsaka da shiryawa Deen ya shigo. “Akku mai bakin magana kenan”. Ta faɗa tana kallonsa. Ai ko yay zaman dirshan ya fara tsiyaya mata surutu itako tana biye masa dan kaf ƙannen nata tafi ƙaunar yaron fiye da kowa. Shima kuma yana son aunty Lu ɗinsa. Sai da ta gama shirinta tsaf cikin doguwar riga ta atamfa da tai masifar lafe mata a jiki kamar wadda akaima fenti. Dan Lulu koda ta saka kayan hausawa irinsu lass atamfa material zaka samesu dai babu wani ɗinkin mutunci a tare da su. Shiyyasa ma kayan basa wuce fitet gwan ne. Dan ko skert da riga ba sosai ta cika yi ba, inma tayin zaka samu suma dai sai sun mata ɗamm kamar zatai nishi su yage. Kasancewar kuma tana da ƙyaƙykyawar sura sai sukan mata ƙyau kamar an haliccesu a jikin nata ne. Dan telan nata kam ƙwarone wajen iya ɗinkin shegantaka. Ba kuma kowa ya haɗata da shi ba sai Nadiya. Yau ma ko takan ɗan kwali ba'abi ba dan dama Amrah ce a mafi yawan lokaci kan mata ɗauri idan tai irin wannan dress ɗin. Sirrin mayafi milk color da ya shiga da zanen atamfar ta yana kawai bisa kai aka ɗora ƙaton google tare da dogayen takalmanta. Dan ƙyau kam tayi ƙyau ga wani mahaukacin ƙamshi mai ɗaukar hankali na tashi. Uncle Yousuf bai fito ba harta kammala breakfast da ba wani na kirki taci ba. Dan shaye-shaye ya gama cinye Lulu ko abincin kirki bata iya ci a rayuwarta. Barta da son cin chocolate kamar shazumamu, dan ko a handbags nata baka rabata da su bayan ƙwayoyinta na shaye-shaye. A tare aunty Saliha da Uncle Yousuf suka sakko da ga sama. Dan haka su duka suka zuba mata ido. Aunty Saliha ce ta fara faɗin, “Babyn Uncle badai da kayan nan zaki fita ba musamman ma ɗan mayafin nan?”.

        Sosai mamakin furucin aunty Saliha ya sata waro idanunta manya da suka juye. Sai kuma ta kalla kanta. Dan tasan dai ba yau ta saba fita a kahaba ai. “Mamy miye laifin kayan nan kuma?”. Ta faɗa fuska a turɓune. Murmushin aunty Saliha tayi da faɗin, “Haba dai Mawaddat ai yau ba jiya bace. Ko kin manta yanzu ke matar aure ce”.

       Wani mugun yamutse fuska tayi dan ita tama manta da wani batun auren. Musamman da ya kasance abinda tasha a daren jiyan ya mantar da ita duk wata damuwarta. Kamar Zatai magana sai kuma tai shiru jin Uncle Yousuf yay gyaran murya da faɗin, “Kinga barta kawai muje ai a mota ne, kuma babu inda zata fita sai a can”.

     Sosai aunty Saliha ta zubama mijin nata ido da mamakin abinda ya faɗa. Dan abu ne da batai zaton ji daga garesan ba sam. Kasa sake magana tai har suka fice Lulu na mata bye ita da Deen da ya maƙale zai bita. Ta ja ajiyar zuciya da faɗin, “Ai masa sannu sai kun dawo”. Da kai kawai Uncle Yousuf ya amsa mata yana ficewa. Yasan abinda yay ɗinne ya ɗaure kanta. Sai dai shima yanada hikimarsa tayin hakan bawai bai san abinda yake yi bane. 


        A motar tuƙinsa yake tayi, yayinda ita da Deen suketa surutunsu da dariya. Dan indai Lulu da Deen ne kam babu mai shiga tsakani. Sai ya ƙulleta da haushi ta mammakesa da kiransa mai shegen surutu kamar akku. Sun tsaya a wani ƙaramin super market Uncle Yousuf ɗin ya fita shi ɗaya. Bai jima ba ya dawo, sai kuma a wajen masu fruits, nan kam da ga motar ma yay bayanin abinda yake so aka kawo masa ya bada kuɗin suka cigaba da tafiya. Lulu dai bata tambayi ina zasuje ba. Hasalima hankalinta gaba ɗaya naga Deen ne. Sai da motar ta tsaya ne sannan hankalinta ya dawo ga inda suken. Kallon anguwar take a ɗan yamutse, duk da ba wani datti bane ko makamancin hakan, hasalima titi ne shimfiɗe da ya miƙe samɓal kasancewar gidan su Smart na a farkon shiga layinne. Sai dai yanayin gine-ginen da kai kawon mutane dana ababen hawa riiiii yasa zaka tabbatar dai irin tamu ce dangin malam Shehu....

       “Papa nan fa?”

   Cewar Lulu a gatsine.

Maimakon bata amsa wayar da yake dannawa ya kai kan kunne. Ta daiji yana amsa gaisuwa, sai dai bata fahimci mi ake cewa da ga can ba. Sai kuma taji Uncle Yousuf ɗin na cewa, “Kai dai kaɗai ne a ɗakin ko? Okay gani nan shigowa”. Daga haka ya yanke wayar tare da buɗe murfin yace, “Oya ku muje”.

        “Uncle.....”

    “Shiiiii...” yay saurin katseta tare da mata alamar zip a baki. Dole ta haɗiye abinda take son fadar dan babu alamar wasa akan fuskarsa. Shi da kansa ya kwashi ledojin, ita kuma ta fito riƙe da hannun Deen tana ta faman yamutse fuska. Sauƙin ma babu kowa a ƙofar gidan. Wanda ke iya hango su kuma ba sosai suke iya ganinsu ba duk da harda masu leƙe saboda son gulma irin ta mutane. Soron ta dinga bi da kallo duk da shima dai fes yake gashi kuma lailaye da sumintinsa. Hakama koda suka shigo gidan ko'ina fes babu wani datti, ga gidan shiru babu yawan hayaniya sosai dan yaran sun wuce ismaliyya, sai ma matan anguwa da wasu a dangi dake ta faman shigowa yin ALLAH ya sanya alkairi da auren Smart ɗin da ba'a san da shi ba. Sai kuma wanda suka san baida lafiya na ɗorawa da jajanta yaya jiki musamman maƙwafta. Anan dai ta inda suke basu haɗu da kowa ba har suka shige sashen ɗakunan samarin gidan da ke a farkon shiga. Anan sun ɗan haɗu da wasu. Bakowa bane kuma sai Mubarak da kema Smart wankin kayansa na ciki, sai Abdull a gefensa yana kallon film a waya da eirpiese a kunnensa. Mubarak ya shiga musu sannu da zuwa cikin girmamawa dan ya gane Uncle Yousuf, itako Lulu dama kallo guda tai musu ta ɗauke kai gefe a ranta tana ƙunƙunin ina ne nan Uncle You ya kawosu. Duk da dai gidan babu wani makusa tare da shi a ɓangaren tsafta a ginensa dai na masu ƙaramin ƙarfi ne. Ita ba hakanne ya dameta ba, kawai bata cika son zuwa irin wajejen nan bane, shiyyasa ko aikinta ya ratsa da hakan zaka ganta cikin rashin sakewa da son a gaggauta abar wajen. Abdull da Mubarak ya zungura shima ya shiga gaishesun. Duka dai Uncle Yousuf ne ya amsa da tambayarsu ko Aliyu na nan? Duk da yasan yana nan tunda dai yayi waya da shi. Sun amsa masa da girmamawa Abdull ya tashi yay musu iso.

        Tunda Uncle Yousuf ya ambaci Aliyu ta kafesa da idanun son jin ƙarin bayani, sai dai bai kulata ba yay gaba dole suka bisa a baya. Yana zaune a saman katifarsa da ƙarin ruwan da doctor ya ƙara saka masa babu jimawa saboda rashin ƙarfin jiki da ya tashi da shi. Wando ne 3 quarter a jikinsa da ƙaramar t-shirt data kama masa jiki sosai. Ainahinsa na tsayayyen mutum ya fito sosai. Fes ɗakin yake ga ƙamshin turaren wuta mai daɗi da Maryam ta saka masa bayan ta share. Gefensa kaɗan flaks ɗin shayinsa ne da cup da ya sha sai kayan tea a wani basket mai ƙyau harda bread alamar dai nan ɗin ne wajen ajiyarsu. Sai kuloli biyu da jug mai riƙe zafi da aka dama masa kunun gyaɗa. Sallamar Abdull da ta Uncle Yousuf ta sashi ɗago idanunsa da ke kallon tv ya zubama ƙofar tare da amsawa. Abdull ya fara shigowa da faɗin, “Yaya Smart baƙi ne”. Kalmar baƙin ta bashi ɗan mamaki, dan shi a tunaninsa Uncle Yousuf ɗin ne kaɗai kasancewar su Daddy basu jima da tafiya ba su. Kafin ya kai ƙarshen tunaninsa Abdull ya gama ajiye ledojin da ya amsa a hannun Uncle Yousuf Deen ya shigo, Uncle Yousuf biye da bayansa Lulu a ƙarshe. Harga ALLAH sai da gabansa ya faɗi, bawai na tsoro ko makamancin hakan ba, shi dai kawai ya samu kansa da jin bugawar ƙirji. Sai dai kuma abinda bai sani ba bashi kaɗai ba. Ita kanta Lulun sai da nata ƙirjin ya harba. Hannu ya miƙama Deen yana faɗin, “Welcome my little handsome”. Cike da farin ciki Deen ya nufesa shima yana murnar ganinsa. Zama Uncle Yousuf yay a sofa ɗin ɗakin ƙwara ɗaya yana murmushi, yayinda Lulu ta wani cakuɗe fuska da yamutse ta duk da taji shock ɗin ganin inda Uncle You ɗin ya kawo ta ta danne, dan tunda tai masa kallo ɗaya a yayin shigowarsu bata sake ba. 

          Smart da ke sauraren surutun Deen da ya karaɗe ɗakin ya dubi Uncle Yousuf cike da girmamawa ya ce, “Uncle Barka da safiya”.

      Shima cike da kulawa yake kallonsa da tausayawa. Amsawa yay da “Barka dai Aliyu yaya jikin naka?”.

       “Alhmdullah ai na miƙe”.

   “Kana dai dauriya Aliyu ga shi harda su ƙarin ruwa. ALLAH ya baka lafiya yasa kaffara ne”.

    “Amin ngd”.

Ya faɗa can ƙasan maƙoshi yana bin Lulu da ta dogare tsaye da kallo ƙasa-ƙasa. A take wani abu ya tokare masa maƙoshi akan shigar jikinta. Lallai yasan akwai babban yaƙi a tsakaninsu. Dan shifa bazai yarda da wannan shigar shegantarkar ba gaskiya. Uncle Yousuf da shima ya juya yana kallon Lulun ya nuna mata gefen katifar yana faɗin, “Zauna mana kikai mana tsaye a kai Mawaddat. Ba kuma kiga Aliyu babu lafiya ba?”.

       Kamar zata fasa ihu taji, ta sake yamutse fuska da ɗaureta a taƙaice ta ce, “Uncle nan ma it's ok”. Sai kuma ta dubi Smart fisha cike da gatsali ta ce, “Sannu fa”.......✍️



        *_Kuma sannu fa🙋 dangin Smart 😂🤣🤩. Dangin mu Lulu's team Barka da rana😚😘😉._*



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments