Furar Danko 41
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣1️⃣
.......Mawaddat da ke da burin amsar saƙo ta kallesa fuska babu wasa. “Malam miye na canja hanyar? Dalla ka koma tacan ina buƙatar amsar saƙo”.
Shiru kamar bazai tanka mata ba sai kuma ya bata amsa a taƙaice. “Akwai holdup ta canne, ga shi lokacin sallah ya kusa bana buƙatar rasa jam'i”.
“To ɗan iya wannan kuma matsalarka ce. Bai kuma damen ba. Ka koma ta inda nace bana buƙatar sharhi”.
Hanyar ya canja batare da ya sake cemata komai ba, amma kuma ba wadda dai take son abi ɗin ba dai ce. Dan zuciyarsa ta bashi kayan shaye-shayen nata ne zata amsa. Takaici ya turniƙe Lulu. Dama ga gajiya na nuƙurkusarta, ai tuni ta balbale sa da masifa amma yay biris da ita kamar yanda ya saba, bai ƙara tari ba har suka iso gida. Buɗe motar tai a fusace ta fito, dai-dai da shima yana fitowar da nufin buɗe matan. Ta zabga masa uwar harara da wani banzan kallo. Nunashi tai da ɗan yatsa tare da tattaro dukan ƙarfinta na zazzage masa abinda ke a ranta amma ko kalma guda ta gagara fita mata a harshe saboda yanda ya wani tsareta da idanunsa data raɗama suna irin na macizai. Sai lips ɗin ta ne kawai ke rawa kamar wanda ya ɗaureta da idanun nasa. “Kaje na koreka, da ga yau bana buƙatar sake ganin wannan shashashar fuskar taka illiterate velleger...!”
A hankali ya lumshe idanun nasa sai kuma ya sakar mata wani shegen murmushi da ya kusa fisge mata numfashi gaba ɗaya. Jitai kamar zata zube a wajan tsabar wani ƙudu dun takaici da murmushin sa ya haifar mata. Dan bata fassarashi a komai ba face na rainin wayo. Fahimtar ya samu nasarar ƙular da itan da yake buƙata ya sashi matsota a hankali, cikin ƙasa da murya da wani maidata can ƙasan maƙoshi ya furta, “Oh! Kin fison sake ganin angon naki kawai a ɗakin barcinmu ke nan AMARYA, ba damuwa a bani albashina dan da shi zan biya sadaki”.
“What!!!” ta faɗa da ƙarfi tare da kai ma fuskarsa mari da gaba ɗaya ɗan sauran ƙarfin da ya rage mata a jiki. Baya yay cikin wani salon da ta samu iska shuuu, ya ɗago yana murmushi tare da kashe mata ido ɗaya, sai kuma ya nuna fuskar tasa da yatsa yana ɗan sake matsota harda ranƙwafowa kaɗan. “Duk randa wannan hannun ya sauka kan wannan fuskar da sunan mari to kisa a ranki MAZA sun faɗi, faɗuwa irin ta MUTUWA. dan itace kawai damar da ƘYANWA zata iya samun yin birgima a gaban ZAKI yanda take so”. Ya ƙara kashe mata ido ɗaya yana ɗaga mata yatsu biyu da faɗin, “Bye *MATAR ILLITERATE*”. Yay gaba abinsa.
Yuuuuu!! Lulu ta dinga jin hajijiya na neman kwasarta, wato itace ma ƙyanwar yake nufi. Dariya sosai Uncle Yousuf da ke cikin motar dake a kusa da su batare da sun san akwai mutum a ciki ba ke tuntsurawa harda ƙwalla. Ashe zaton da yakema yaron nan ya wuce nan. Kai jama'a har ya fara tausayin ƴar tasa gaskiya. Dan tabbas akwai babban wasa a wannan tafiya yanzu ne kuma za'a fara. Ganin yanda ta wuce tana haɗa hanya ga hawaye sun wanke mata fuska ya sashi daina dariyar ya buɗe motar ya fito, sai dai duk yanda yake son binta ya haƙura dan lokacin sallah yayi. Ya kai dubansa ga su Smart da ke alwala sai kawai ya nufesu yana gyara yanayinsa kamar bashi ya gama kwasar dariya ba a mota...
Bayan an idar da salla kusan a tare suka fito. Uncle Yousuf ya dakatar da Smart da ke sallama da su maigadi akan ya jira su wuce tare. Kamar zai ce a'a sai kuma dai yay shiru dan kiran da Abba yay masa suna ƙoƙarin shiga massalaci akan idan ya dawo gida ya sameshi falonsa yanzun nan. Yasan maganace da Abban, shi kuma da yayi niyyar bama masu bin san nan a baya dama dan ya tabbatar ba haƙura sukai ba su kamashi dan yana son yin magana da koma waye ya turosun. Babu yanda ya iya dole yabi Uncle Yousuf ɗin, shiko ya ƙaunaci ALLAH ya kaisa har gida yau. Tunda suka fito kuma yaga motar nan sai dai ba napep ɗin yanzu, motar dai ce ke cigaba da binsu yanzu ma. Suna isowa titin anguwarsu yaga sun dakata cikin takaici direban motar na kaina sitiyari duka alamar ba haka sukaso ba. Sai dai kuma abinda bai sani ba shima Uncle Yousuf ya san da su shiyyasa ma ya ɗakkosa ya kawo har gidan.
“Alhaji yau na saka ka aiki, Nagode sosai”.
Murmushi Uncle Yousuf da idonsa ke kan mirror yana kallon mutanen nan ya saki, tare da faɗin, “Har yanzu dai ina a Alhaji na? A tunani na na zama Uncle yanzu tunda ƴa zan bayar duk da auren wucin gadi ne”. Yanda Uncle Yousuf ɗin ya ƙare maganar ne ya saka Smart kallonsa, sai kuma ya ɗauke kansa yana sakin murmushi ya ce, “To ayi haƙuri Uncle”.
“Shike nan na haƙura, dan dama ba'a san iyaye da fushi da ƴaƴansu ba. Ina fatan zaka samu Abba da maganar yau ko?”.
“Da wuri haka?”.
Smart ya faɗa da mamaki yana kallon Uncle Yousuf ɗin.
“Dole ne muyi da wurin, dan ɗazun Baba ya sake kirana akan zuwan M Atik Kumo shima yana nemawa ɗansa aurenta, sannan Alhaji Sulaiman da ɗansa sun gama ƙulla matakin da zasu ɗauka a gobe idan ALLAH ya kaimu.....” tsaf ya zayyane masa komai shima. Mamaki ne ya sake lulluɓe Smart, yayinda a ƙasan zuciyarsa yake ta lissafi akan yanda zai canja salon wasan a yanzu tsakaninsa da Alh. Sulaiman. Kafin yanzu shi bai wani ɗauki zancen da muhimmanci ba, dan har ya gama ƙulla yanda zai kuɓuce wa al'amarin, sai dai a yanzun nan ya canja sabuwar shawara. Duk da bai san minene dalilin Alh. Sulaiman ɗin ba ya kamata ace ya nuna masa shima tsageran kansa ne a wannan gaɓar. Bai damu da zancen MM Atik Kumo ba.....
“Aliyu kayi shiru!”
Uncle Yousuf ya katse masa tunani. Iska ya ɗan furzar kaɗan sai kuma ya fuskanci Uncle Yousuf ɗin. Cikin sake furzar da wata iskar ya ce, “ Please Uncle kozan iya sanin yaya kuke da shi Alh. Sulaiman ɗin?”.
“Yerh babu damuwa Aliyu. Alh. Sulaiman Sufi Ado Garko ɗane ga Alhaji Sufi Ado Garko. Sannan Yaya ga mahaifiyar Mawaddat uwa ɗaya uba ɗaya. A shekarun baya ɗan uwana mahaifin Mawaddat abokai ne da Alh. Sulaiman na ƙut-da-ƙut, dan sun haɗu ne tunkan ya auri mahaifiyar Mawaddat ɗin adalilin shi Baba da ya ja Yayana jikinsa. Sai dai a yanzu ba haka bane, dan bamu san minene ya shiga tsakanin wannan amintaka ba abokan biyu suka zama maƙiyan juna ta yanda ko inuwa ɗaya basa sha. Iya tambaya na yima Yaya amma yaƙi faɗa min komai. Shi iyakarsa fita harkar Sulaiman, amma shi Sulaiman a bayyane yake nuna tsanarsa garesa da mu ma ahalinsa gaba ɗaya shiyyasa Yayana yay ruwa yay tsaki wajen hana aure tsakanin Tajuddeen da Mawaddat dan yace akwai manufa. Wannan shine iya abinda na sani gaskiya”.
Kai Smart yake jinjina wa cike da gamsuwa. Sai da Uncle Yousuf yay shiru sannan shima ya bashi labarin kamasan da Alh. Sulaiman ɗin yayi a randa yazo shi da Ahmad suka roƙesa ya koma aiki, ya kuma sanar masa aikin da yace ya koma yay masa tare da nuna masa motar yaran Alh. Sulaiman da ke tsaye a bakin layinsu kasancewar suna iya hango su da ga nan ƙofar gidan su Smart ɗin da ke a bakin titin.”
Sosai al'amarin ya girgiza Uncle Yousuf ɗin, ya kuma tabbatar masa da shima dalilinsa na kawoshi gida yanzun. Dan tunda suka kammala waya da Baba yaji a ranasa Alh. Sulaiman zai iya ɗaukar mataki kowane iri ne akan Smart shine ya saka wani ɗan sanda zuwa office ɗin Lulu ya saka masa ido, ɗan sandan ne ma a Napep ashe, sai ko gashi bayan tahowarsu gida ɗan sandan ya tabbatar masa ana binsu... “Wato Aliyu idan na fahimta tun fara aikinka da mu Alh. Sulaiman na biye da lamarinka kenan? Kuma bana raba ɗayan biyu a wajen Tajuddeen ya sani. Lallai ya kamata musan dalilinsa danni zuwa yanzu har Tajuddeen ɗin ma na saka masa alamar tambaya”.
“Sanin dalilinsa abunne mai sauƙi Alhaji, yanzu dai barshi na fara masa duka a ciki, bayan cikin ya ƙulle zai amayar da duk abinda ke a ransa da kansa. Sannan Tajuddeen bai zama lallai yasan komai ba, zata iya yiwuwa amfani uban keyi da shi batare da shi ma ya sani ba”.
Murmushi Uncle Yousuf yayi tare da bubbuga kafaɗar Smart, dan tsaf ya fahimci inda zaurancen nasa ya nufa game da duka a ciki. Murmushi shima Uncle Smart ɗin yayi tare da buɗe motar yay masa godiya ya shige gida, shi kuma yaja motar yana ƙara jin ƙaunar yaron har tsakkiyar ransa. A rayuwa yana matuƙar ƙauna da son jarumin mutum. Musamman ma matashi irin Smart mai tsayyar zuciya. Wannan nagartar tasa ya fara hanga a filin ƙwallo ya shige masa zuciya, faruwar ƙaddarar data nema dakushesa da ga cikar burinsa ta fara sakashi jin tausayinsa da laluben hanyar da zai iya taimaka masa. Bayan yin dogon nazari ya yanke shawarar kusantosa gefensa domin ƙara tabbatar da halayensa kafin ya ja hannunsa hanyar da ya gama shiryawa domin kaisa ga cikar burin nasa. Sai kuma ga al'amarin ƴar ɗan uwansa ya gitta a cikin labarin tamkar bakangizo a tsakiyyar gagarumin hadarin da ke gab da zubda ruwa. Fatansa kawai ta kasance bakangizo mai amayar da ruwan da ta shanye bamai haɗiyewa ba har abada.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
No comments