Furar Danko 30
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣0️⃣
.......Bayan yay sallar la'asar barci ya sake sha har kusa da magrib batare da kowa yasan yana a gidan ba. Dan sanda su Ahmad suka maidosa basu ga kowa a ƙofar gida ba. Wanka yay da alwalar magrib ya fito. Yanayin yanda yake jin jikinsa babu ƙarfi ya sashi yin sallarsa a ɗaki. Bayan ya idar ya fita zuwa cikin gidan. A kallo ɗaya zaka iya fahimtar baida lafiya ƙarfin hali ne kawai. Sai dai hakan bai hanashi leƙa duk ɗakunan gidan ya gaida su Mama ba. A ɗakin Umma ya samu babban yayansu Salim yazo gidan shima. Sama-sama suka gaisa Salim ɗin na wani cika da batsewa shi adole mai naira a gida. Ko'a jikin Smart dan shi ba wannan shirmen ne a gabansa ba. Yana juya baya zai fita Salim ɗin da Umma suka raka bayansa da harara. Oho baima san sunai ba shi dai.
A falo ya samu ƙannen nasa duka. Sai Nasreen dake ta faman tsalle-tsalle ita da autar Aunty Amarya. Gaisheshi suka shigayi, ya amsa yana zama tare da ɗan dafe kansa da har yanzu bai gama saki ba. Ammah da tun shigowarsa take kallonsa ta ajiye littafin addu'oin da ke a hanunta da faɗin, “Baka da lafiya ne Hydar?”. Hannun ya janye da ga goshinsa ya ɗan furzar da iska. “Kaina ne ke ɗan ciwo kaɗan kawai Ammah, na kuma sha magani ma. Ina yini”. Maimakon amsawa sai ta cigaba da kallonsa cike da nazari. Ganin yanda ta kafesa da ido ya sashi duban Hawwah cikin son kauda hankalin Ammah ɗin ya ce, “K babu wata damuwa dai ko?”.
Kanta ta jinjina masa itama da ɗan damuwar ganin yanayin nasa. “Ba komai Yaya Hydar. Sai dai kamar ba ciwon kan bane kawai ke damunka. Ka wani zabge a lokaci ɗaya kamar wanda ya kwanta ciwo.”
Baiyi mamakin jin furuci nata ba. Dan a duk lokacin da ciwon ya bugesa ba ƙaramar fyaɗa yake masa ba. Ya ɗan sake furzar da iska yana tashi zaune da ƙyau da kamo hannayen su Nasreen. “Ciwon kai ne kawai kin san bai min da wasa”. Badan sun gamsu ba dai suka yarda da hakan. Maryam ce ta kawo masa abinci da faɗin, “Ko sai kayi sallar isha'i”.
Nan ma iskar ya ɗan furzar da duban kular abincin. Yasan dai shinkafa ce dan ya ga Salim na ci a wajen Umma. Shi kuma sam shinkafa bata da farin jini a wajensa sai dai kawai ya cita dan yunwa. “Ai banama jin zanci abincin nan ɗauke kawai. Ko kuna da ƙullin kamu ki ɗan dama min kaɗan”.
“Eh akwai. Dama na kunun gyaɗa da Ammah tasa aka markaɗo ɗazun ko shi za'a dama makan”.
“Yauwa dama min shi ɗin kawai bara naje massalaci na dawo”...
Ana idar da sallar isha'i ya sake dawowa. Anan yasha kunun gyaɗar da Maryam ɗin ta dama masa Ammah harda badawa a sayo masa ɗanyar awara dan tasan yana so sosai, kasancewar bata da yawa duk kafin ya dawo har an soya. Kusan ma tare suka cinye awarar da Nasreen da ke ta faman zuba masa surutu. Murmushi kawai yake mata cikin ƙarfin hali. Ammah dai da ke ɗan kallon tv duk tana lure da shi. Cikar agogo ƙarfe tara yasa Amma maida channel zuwa NTA, su Maryam ba wani son kallon labaran suke ba sai dai dole. Musamman ma Asma'u. Tashi yay ƙoƙarin yi shima sai dai kanun labaran suka ja hankalinsa. Inda rahoton farko ya kasance akan yanda shari'ar matashin nan Emanuel da aka kama a anguwar Yakasai akan lalata yara ƙanana maza da ya ɗauki tsawon shekaru uku yanayi. Kusan wata huɗu kenan ana tafka shari'ar sai a yau ne aka yanke masa hukuncin bisa jajircewar lawyer ɗin da ke tsaye akan bibiyar hakkin yaran da al'amarin ya shafa. Har tsakkiyar kansa yaji saukar muryarta tamkar a gabansa take kamar ko yaushe. Yanda take magana cikin nuna takaici da kuma jin daɗin samun nasara a shari'ar ya sashi kasa ɗauke idonsa ga tvn. Tambayar da ɗan jaridar yay mata akan miyasa a duk irin waɗan nan cases ɗin in dai tana a cikinsa da wahala bata samu nasara ba, anya ba tana saye bakin alƙalan bane ba ta bayan fage.
Ƙaramin murmushi da ke sake fidda loɓawar kumatunta duka biyu ta saki tare da yamutse fuska kamar yanda ya santa musamman idan tanajin masifa. Cikin izzar nan tata ta bama ɗan jaridar amsa da faɗin, “Mi zaisa sai na sayi alƙali akan abinda yake gaskiya. Ashe ma karatun da nai akan harkar shari'a da wahalhaluna sun zama a banza kenan in har sai na sayi alƙali akan gaskiya ta. Nasarata itace gaskiyata. Dan bana tsayawa mutum sai na tabbatar da gaskiyarsa. Na kumayi alkawarin cigaba da yaga mutunci da rayuwar duk wanda ya kasance bunsuru mai halayen dabbobi akan mutuncin yaran mutane. Dan ni duk wanda zai iya ƙwatar mutuncin yarinya ta ƙarfi ballema wadda take ƙanƙanuwa bashi da wani suna a gareni face Dabba alade. Yanzu shi wannan da na kai ƙasa ma ai yafi matsayin alade a gareni bamma san mizan kirashi ba. Shege ya baro yankinsa yazo yana ɓarna a namu yankin saboda suna ganin muna haihuwar yara mu saki a titi kamar bamu san ciwonsu ba. Indai akan harkar fyaɗe ne nai alƙawarin ni Mawaddat Isma'il Ibrahim Jiƙamshi sai na hana waɗannan aladun shan ruwa da numfashi cikin salama. Dan nan gaba kaɗan abinda suke lalata yaron mutanen da shi zan koma datsewa da almakashi ƴan ƙaniya. Idan aure kuke so uwarmi kuke jira da bazakuje kuyi ba ko ku tafi gidajen karuwai Mtsowww!!”.
Ɗan jaridar ya ce, “Turƙashi. Da alama dai Barrister Mawaddat Jiƙamshi ta fusata a wannan karon, masu halin binsiraye sai ku kama kawunanku, inba haka ba za'a sake maimaita gilli da girma bayan wanda akasha da ƙanƙanta. Sai dai a yayin da wannan zantuka na Barrister wasu ke nuna goyon bayanta wasu ƙalubalantarta suke musamman akan zance gilli da zata fara da kanta. Dan haka a yinin yau zantukan barrister suka ɗauki ɗumi da zagaye kafafen yaɗa labarai harma dana yanar gizo aketa tafka mahawara. Ballema da wasu ƙungiyoyin mata masu yaƙi da wannan ɗabi'a ta fyaɗe suka fito muraran da cewar sumafa suna bayanta. Dan zasu sayi nasu almakasan su fara sakawa a jakuna dumin tayata aikin gillin. To ALLAH dai ya ƙyauta, kowa rai yayma daɗi ai baran mai shi ne. Shi dai wannan gashi zai ƙare shekaru talatin cif a gidan kaso bisa tasa mummunar aƙidar mai muni, tare da biyan maƙudan kuɗin da za'a fuskanci lafiyar yaran da ya ɓatama rayuwa”.
“ALLAH yay ma wannan yarinya albarka da iyayen ma da suka kawo ta duniya”.
Furucin Ammah a bazata ya maidosa hankalinsa. A tare Hawwah da su Asma'u suka amsa da amin. Har Asma'u na faɗin, “Ammah nima in sha ALLAHU lauya zan zama. Wlhy tun randa na fara ganin matar nan kan case ɗin nan nake jin ƙaunarta da sha'awar nima na zama kamarta.....”
(Ba Amin ba a ɓoyayyar halayyarta) ya faɗa a zuciyarsa yana miƙewa batare da ya ƙarasa jin zancen Asma'un ba. Sallama yay musu ya fito acewarsa zai sha maganin ciwon kai ne ya kwanta. Sun masa addu'ar samun lafiya, yayinda Ammah ta dakatar da shi da faɗin yazo ta kama masa kan. Gabanta ya dawo ya zauna. Ta kai hannun nata saman goshinsa da ke da ɗumi har yanzu. A hankali ya sauke ajiyar zuciya da har ta iya jiyosa, sai dai batace komai ba dan tun ɗazun zuciyarta ke bata kodai lamarin nasa ne ya motsa bai son faɗa, ko kuma yana son ya motsa ɗin. Sosai tai masa addu'a yanata faman sauke ajiyar zuciya kafin ya miƙe yana jin wata nutsuwa ta musamman na ratsa masa jini da ɓargo. Koda ya koma ɗakin ma magungunan da malam ya bashi ya shashsha sannan ya kwanta. Maimakon barcin sai abinda ya gani a tv ya shiga dawo masa tiryan-tiryan. Shi yama rasa a mizai fassara wannan yarinya. Ita dai gata nan rabi mutum rabi muna mutum. Sai dai kalaman nata na yau sun matuƙar tasiri garesa har yana haɗasu da na jiya data dinga faɗa cikin shirmen buguwar ita ba ƴar iska bace. Bawai ya gamsu da hakan bane. Dan babu ta yanda za'ai irinta mai ƙwalewa da kayen maye ta iya furta ita ƙillatacciya ce ya yarda. A yanzu hakan ma wani sashe na zuciyarsa na kallon kalamanta na ɗazunne kawai a gurbin fuska biyu irin na halayyar ɗan adam na yanzu. Ya ɓoye zahirinsa na mutumin banza, ya shiga gaba-gaba wajen bayyanama duniya shi na kirki ne na ALLAH. Guntun tsoki yaja da lumshe idanunsa yana fatan barci ya ɗauke sa.....
★★★
★.★.★★
Tabbas a daren jiya yanda yaga rana haka yaga dare dan ko sau ɗaya bai rintsa ba. Sai faman bulbulama cikinsa hayaƙin cigarette da yay tayi dana shisha. Baya taɓa neman abu ya rasashi, haka ma bai taɓa harar mace sau biyu ba ta zille masa sai a kanta. Duk da ɓacin ran da ya tsinta kansa dalilin rasata a jiya bai ji ko ɗigon sha'awarta ya ragu masa a rai ba. Sai ma ƙaruwa yay yana sake azalzakarsa da sake tunzura buƙatarsa. Neman hanya ta uku ya tsunduma a tunani, sai dai zuciyarsa ta rabu gida biyu. Ɗaya na tabbatar masa ya nema aurenta kawai itace hanya mafi sauƙi. Ɗaya na tabbatar masa bazata amince ba, dan haka kota halin ƙaƙa kawai ya kore ƙishirwarsa, kai koda sakawa a sace masa itane. Ganin ya rasa makamar riƙewa sai kawai ya yanke shawarar neman shawarar abokinsa. Gabanin asuba yay kiransa, bugu biyu kuwa aka ɗaya dan shima a lokacin yana cikin club ne a Abuja..........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
No comments