Furar Danko 28
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣8️⃣
_Ya rabbi ka gafartama *Sheikh Abubakar Giro Arugungun*. Ka yafe masa kurakuransa, alkairan da ya isar garemu na wa'azantarwa da koyarwa kasa ya amfanar da mu duniya da lahira. ALLAH ya albarkaci zuri'arsa. Suma iyayenmu ALLAH ka gafarta musu, damu baki ɗaya 😭✍️_.
........Wata nannauyar ajiyar zuciya Smart ya saki mai ƙarfin gaske lokacin da malam ya shafa masa ruwan addu'oi da yayi tofi a ciki, sautin karatun suratul Naazi'aat da ɗaliban malam ce ta fara shiga cikin kunnensa da wani irin ƙarfi tamkar a iya cikin kunnen nasa akeyi. Ya sake sakin ajiyar zuciya sai kuma ya kai hannunsa ya dafe goshinsa dan kansa wani irin ciwo yake kamar zai tarwatse. Uncle Yousuf ne ya fara ambatar sunansa, dan haka ya sake yunƙurin buɗe idonsa a karo na biyu sai dai ya kasa. A rikice duk suka dubi malam. Ya karkaɗa musu kansa da faɗin, “Kamar yanda na faɗa muku tun wancan karon ku sake jajircewa wajen addu'a da sadaka akansa, dan al'amarin nasa akwai ruɗani kamar na sihiri mai ƙarfi. Sai dai ban tabbatar ba dan UBANGIJI shine kawai masanin gaibu. Amma gaskiya al'amarin nasa yana nuna kamar bugewar junnu ne. Na fara baku ruwan addu'oi a wancan karon amma sai aka daina zuwa a karɓa kwata-kwata, dama ba komai bane face addu'oin karya sihiri wanda ya kamata ma ace duk musulmi kan dingayi a gidansa domin shi da iyalinsa koda lafiya lau ake dan rayuwa kake baka san mike biye da al'amarin ka ba. Koba sirihi akwai baki (kambun baka) da yafi sihiri kaifi a wasu lokutan. Koda ma bazaku juri zuwa nan ɗin a karɓa ba to ku dage da yi masa a gida dan ALLAH”.
A tare suka amsa da “In sha ALLAH malam” sai kuma suka ɗora da godiya. Ganin yanda Smart keta faman jujjuya kansa malam ya ƙara masa addu'a tare da basu umarnin kaisa asibiti mafi kusa. Godiya sukai masa dan a wancan karon ma haka yay musu. Suka ajiye masa sadaka shi kuma ya basu ganyen magarya da ayoyin da zasu karanta da ga cikin Alkur'ani mai girma. Kai tsaye asibitin suka nufa kuwa, inda aka bashi gado dan a kallo ɗaya idan kai masa dole ne ya baka tausayi, kai kace ba a yanzu kaɗai ya kasance a kwance ba yanda yay sharɓan. Sun bashi taimakon gaggawa har sai da ya samu barci suka ɗan samu nutsuwa. Sun yanke shawarar sanar da gidansu amma sai coach ya ce adai ɗan dakata idan basu sallamesa zuwa yamma bane sai a sanar musun. Hakan ya musu, dan haka sukai yunƙurin fitowa aka barsa da Ahmad ya zauna da shi kafin suje su dawo.....
★★★★★
Duk yanda taso cigaba da gudanar da al'amuran gabanta na wannan yinin hakan sai ya nema gagararta. Ba ƙaramin tsaya mata a rai abinda drivern nata yay mata yayi ba. Dole ta hakura da tattara bayanan case ɗin da zata fara tunkara a safiyar litinin kan dukiyar wasu marayu da wan mahaifiyarsu ke ƙoƙarin handamewa dan zuciyarta a cinkushe take matuƙa. Steering da take murzawa ta kaima duka a karo na babu adadi. Ta cije lips da masifar ƙarfi da faɗin, “Sai na koya maka hankali!”. Kalmace data ambatata yafi sau shurin masaƙi. Ga takaicin daren jiya da ma na cigaba da ci mata rai dan a duniya tai masifar tsanar wani namiji ya raɓeta da sunan taɓata ko soyayya. Shiyyasa shima Tajuddeen lissafinsa ya shiga cikin jerin lissafin abubuwa masu ƙuna da ajiyewa a kudin tarihinta na wannan yinin da take ganin yazo mata a birkice. Office ta koma, inda ta tarar da baƙi kashi-kashi na jiranta. Tabbas batajin magana, sai dai a ɓangaren aikinta ita ɗin jajirtacciya ce, dan ma ɗabi'arta ta shaye-shaye na matuƙar maidata baya a lokuta da dama, dan badan wata hikima ta UBANGIJI ba da Lulu ta jima da daina zuwa wajen aikin ma gaba ɗaya ne. Mummunar hallayya mafi muni tattare da Mawaddat shine sakaci da addini, sam babu abinda ta sani akan addininta sai abinda ba'a rasa ba sakamakon karatun ta na lawyer. Bata san a kira salla ta tashi tayita akan lokacinta ba, to idan ma tayin babu maganar yinta a yanda MANZON ALLAH ya koyar damu. (Kuyi haƙuri ba Lulu kaɗaice a wannan matsalar ba. Wlhy da yawan mutane sunayin salla ne ba'a yanda MANZON ALLAH ya koyar ba. Dan bawai fa muna nufin Lulu bata san salla ba, a'a itama ta tashi ne a yanayin yanda akeyi kawai nakeyi batare da samun ilimin yinta ba kamar yanda da yawa mutane suka kasance. Mafi yawanmu idan da zaman tsayawa akan ibadarmu ta salla za'ai tun daga tsaiwarta ma zamu fara samun gyara. Please Dan ALLAH a wannan gaɓar kowanmu ya nutsu ya kalla sallarsa da kuma bincike akan yaya ake salla kamar yanda MANZON ALLAH S.A.W ya koyar mu gani ko zamu ribantu da gyarawa). Sanda ta gadama take salla, tana kuma yin tane a yanda kawai taga anayi kasancewar karatun addinin ma gatan mahaifinta ya zame mata cutarwar da bata samesa ba. Masifarta kam wannan halitta ce, wani mai haƙuri wani saɓani haka. Sai ɗabi'ar shaye-shayen data jima tana binnewa wanda har yanzu bamu san tushen farawarta ba ko dalilinsa. Wulaƙanta mutane da takasu a duk yanda taso kuskuren mahaifinta ne da ya ɗorata a turbar komai take so zata samu. A duk sanda ka nunama yaro komai yake so zai samu tofa kansa zai ƙara girmane da tunanin yafi kowa daraja da power a rayuwa, sannan akan komai shine sama da kowa. (Iyaye sai mu kula hakan ba soyayya bace)....
Yanda ta zube wayoyinta da zama jagwab cikin lallausar kujerar office ɗin nata ya sake bayyanar da ɓacin ranta akan fuska. Hand bag dinta ta jawo tare da fiddo key ɗin drower ɗin jikin decks ɗinta da bata yarda kowa ya taɓa saboda abinda take ajiyewa a ciki ta lalubo. Tana ƙoƙarin buɗe drower ɗin sakatariyarta ya shigo office ɗin da sallama. Wani takaici ya sata ɗago idanunta da suka kaɗe da gajiya. Sai dai gaba ɗaya tama kasa mata masifar da ta saba yi mata a duk sanda tai mata kuskure. Da sauri sakatariyar ta ce, “Please am sorry maa. Wlhy abinda matar can tazo da shi ne yay matuƙar tayarmin da hankali. Jiya ma tazo nace mata ta dawo yau dan kina up 2days sai yau ne zakiyi res.....”
Hannu Lulu ta ɗaga mata alamar gajiya da saurarenta. Murya a shaƙe ta ce, “Zainab ba wanda zan iya saurare a yau koma minene akazo da shi. Ki sake bama duk wanda ya dace sabon appointment banda yau da gobe. Duk case ɗin da kuma kika sani bani da buƙatarsa a teburina karma mai shi ya shigomin office ok”.
Zainab da damuwa ta bayyana ma a fuska ƙarara ta gyaɗa kanta da ke ƙasa. Sai kuma cikin rawar murya dan har ta fara hawaye ta furta, “Aunty matar can fa mijinta ne yayma yarinyarta da taje agolanci da ita gidansa fyaɗe. Kuma yarinyar shekararta tara kwata-kwata. Sunje asibiti da yarinyar amma anƙi karɓarsu tun jiyan wai sai da ƴan sanda. Taje police station ɗin kuma ƴan sandan nata mata yawo da hankali. Wlhy bakiga a yanda sukazo da yarinyar ba a jiya da yamma abin babu ƙyan gani....”
Wani irin matse idanu da damƙe kujera Lulu da jikinta ya fara tsumar mazari tayi. (Mawaddat calm down. Mawaddat calm down. Mawaddat calm down). Wani sashe na zuciyarta ke ta ambata mata. Sannu-sannu ta fara sassauta damƙe kujerar da rumtse idanun nata da tai, sai kuma ta buɗesu gaba ɗaya sunyi jajur matuƙa kamar wadda tasha wani abu a lokacin.
“Shigomin da ita”.
Ta faɗa ƙirjinta na ƙara ƙarfin sukar da yake mata. Ga jikinta bai daina tsumar da yake ba. Da ace tanada ilimin addini da addu'a tafi cancanta da harshenta a irin yanayin. Amma sai aka samu akasin hakan a gareta. Da sauri sakatariyar ta ta fice cikin matuƙar sassarfa. Minti biyu basu rufaba sai gasu sun shigo. Matar dai da ka ganta kaga wadda ke'a cikin mawuyacin hali, sai dai da zata samu kulawa ƙyaƙyawar mace ce dirarriya. A lamarin Lulu da talaka a teburin aikinta kawai suke iya shan inuwa ɗaya, shima akan abinda ya shafi aikintane kawai babu ruwanta da rayuwarka. Har ƙasa matar ta kai ga alamun ciki da ya turo a jikinta zata gaida Lulu. Bata hanata durƙusawar ba amma dukkan hankalinta na gareta, sai kuma katseta da ga gaisuwar data fara da tai...
“Kinga wannan gaisuwar baida amfani faɗamin ina yarinyar take?”.
Cikin gyaɗa kai da share hawaye matar ta ce, “Tana gidan ƴar uwata da ta rakoni nan jiya, saboda yanda jikin nata yake ne ƴar uwar tawa tace na dawo yau ita ta kula min da ita”.
“Wane police station kukaje domin kai ƙarar?”.
“Na nan unguwarmu ne sai kuma da mukazo nan wajen ƴar uwar tawa itama ta kaimu na nan ɗin. Sai dai shima basu ɗauki abin da muhimmanci ba shiyyasa ta ce zata rakoni nan inda take da tabbacin za'a share mana hawaye. Hajiya dan ALLAH ki taimakeni kamar yanda ALLAH ya taimakeki. Yarinyar nan marainiya ce mutuwar mahaifinta ta sani auren wannan tsinannen da tunda na aure shi ban sake farin ciki a rayuwata ba......”
Cikin jan tsaki da takaici Lulu ta katseta da faɗin, “Kika zauna da shi kuma har ya miki ciki. Malama ni ba rayuwar aurenki nake buƙatar ji ba. Ki tashi kuje zan haɗaki yanzu da wanda zaku sameni a asibiti”. Ta ƙare maganar tana miƙewa cikin matsanancin ɓacin rai. Waya takai kunnenta, da ga can aka ɗaga. Kirari aka fara mata ta katse da faɗin, “Musa ka sameni a office yanzu kai da Shu'aibu Please inada emergency case.”
“An gama ranki ya daɗe”.
Musa ya faɗa ransa fes dan yasan yau aljihunsu zai kasance a cike. Dan aiki da Lulu yafi masa zaman cikin station aita kayan hamma balle tsaiwar kan titi amsar na goro. Ɗan rubutu tai a takardar data yago ta miƙama sakatariyar ta dake tsaye har yanzu. “Idan sun zo ki basu wannan, suje da ita sai su sameni a wannan asibitin dana rubuta. Kibasu 5k da zasu saka mai a mota”. Daga haka ta fisgi hand bag dinta da ɗayar wayarta da key tai waje...
Batako kalli sauran mutanen da ke zaune a inda table ɗin sakatariyarta ya ke ba ta fice. Taja ƙaramin tsaki lokacin da take dana unlock ɗin motar tunkan ta ƙarasa gareta. Bazata iya jure wannan zirga-zirgar tuƙin ba fa gaskiya. Dan tun farko ita dama ba gwanar sonyi driving bace. Cikin ƙara jan tsaki lokacin da take ficewa a gate ɗin ta dannama Uncle Yousuf kira. Sai da ta shiga ta tuna abinda ya faru jiya da wasan ɓuyan data ƙudiri aniyar farayi da shi. Da sauri ta rarumi wayar zata katse sai dai harya ɗaga. Babu alamar wasa a muryarsa ya ce, “Lafiya?”.
Kamar ta fasa ihu haka taji, amma sai ta dake cikin pretending da ƴar shagwaɓa ta ce, “Uncle Barka da safiya. Dama no ɗin mutumin nan zaka turamin koka kiramin shi Please ya sameni a Shira's hospital”.
Ɗan jimmm yay kamar bazai amsa mata ba sai kuma cikin dakewar da takan bata tsoro a Duk sanda yayita ya ce, “Wane mutumin?”.
Yanzu kam sai da taji bugawar zuciya. Da ɗan rawar harshe ta ce, “Driver fa my papa”.
Har zaiyi yi mata tambayar yaya akai bashi ya kaita office ba sai kuma ya fasa saboda tare ya ke da abokinsa Hameed. “K kina ina yanzu?”. Ya faɗa cikin goce tunaninsa.
“Ina hanyar Shira's hospital ɗinne ”.
“Sai kin ƙaraso”.
Ya faɗa kawai yana yanke kiran.......✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
No comments