Recent Updates

Furar Danko 26

 


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗




           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣6️⃣




........Cikin ƙanƙanin lokaci Uncle Yousuf ya isa gidan ɗan uwan nasa. Anan ma sama-sama ya gaisa da su maigadi. Su ya farama tambayar Lulu tazo gida. Sun bashi amsar da ta sakashi sakin ajiyar zuciya mai kauri. Sai kuma ya samu ƙwarin gwiwar ƙarasawa ciki duk da sun tabbatar masa ta fita aiki tunma ɗazu tare da drivern ta. Kusan karo suka ci da Daddy dake ƙoƙarin fitowa har lokacin yana ƙananun magana wa Mommy akan Mubeen bai gaida Lulu ba. Sai dai duk wanda ya sanshi yaga yanda yake faɗan yasan yana yinsa ne kawai amma akwai abinda ke damunsa mai raɗadi ba abinda Mubeen ɗin yayi bane, shi kamar ya taka sahun ɓarawo ne. Ita dai Mommy bata tanka ba sai ma maida hankalinta tai akan cin abincinta da shi Daddy ɗin ya fasa ci saboda Lulu bataci ba. Mubeen ma na zaune cikin ɓacin ran yanda faɗansa ya koma kan Mommy kamar dai dama Daddyn nasu dama da biyu ya ƙirƙiri faɗan dan ya maidasa kanta ne. Gaishesa Uncle Yousuf ɗin yayi, sai kuma ya leƙa ya gaida Mommy da ga inda yake tsaye, acewarsa yana sauri ne dama ya biyo ne yaga Yaya. Mommy tai ɗan murmushi da masa addu'a. Tare suka fito da Daddyn da ya bar faɗan tun ganin Uncle Yousuf, dan yasan yana ji zai fara kare Mommy koma shi ya maida faɗan a kansa. 

       “Yaya magana ce da ni mai muhimmanci”. Ya faɗa cikin rashin walwala. Tsai daddy yay yana kallonsa. Sai kuma ya kamo hanunsa da faɗin, “To muje office ɗina ko naka sai muyi a can ko auta”.

    “A'a Yaya, anan gida ya cancanta muyita dan zatafi dacewa”.

   Komai Daddy bai sake cewa ba sai hannun ƙanin nasa da ya sake ja suka nufi falon baƙi da ke can ta wajen garden. Tsaf falon yake dan kullum sai an gyarashi da saka masa turaren wuta. Bayan sun zauna cikin kulawa da san danne damuwa Daddy ya ce, “Ina jinka mike faruwa Auta? Danni duk ka ɗaga min hankali da wannan yanayin naka wlhy.”

          Numfashi mai ɗaci Uncle Yousuf yaja da gyara zamansa. Kai tsaye ya ce, “Akan Mawaddat ne.”

      “Kuma dai Yousuf? To mi ta sake yi?”. Da ga jin a yanda Daddy yay tambayar kasan ransa a jagule yake. Amma sai Uncle Yousuf ɗin yay biris ya cigaba da faɗin, “Gaskiyar da muke buƙatar gani da ido ce na gani jiya a zahirance. Dan an maido min Mawaddat gida a buge tana warin kayan maye kamar ma harda giya”.

        Tsurru Daddy yay yana kallon Uncle Yousuf, sai kuma cikin rawar murya kamar mai shirin yin kuka ya ce, “Yousuf dan ALLAH ka gayamin gaskiya, dan in har wani yazo ya faɗa maka nasan za'a iyama Mawaddat sharri kasanta da magauta. Na rasa mi yarinyar nan ta tsarema wani a rayuwa. Gashi ita bata damu da kowa ba amma ita an dam........”

      Dakatar da shi Uncle Yousuf yay da faɗin, “Yaya! Kasan dai bazan ma Mawaddat ƙarya ba dan naci riba ko? Kuma ni babu wanda yazo ya faɗa min ni na gani da idanuna. Kuma gashi misawarka tasa na fahimci kai kanka baka san Mawaddat bata kwana gida ba ma. Hakan na nufin dama ba yau ta fara fitar dare ba batare da ka sani ba kuma baka taɓa maida hankali ko damuwa ba akan tabbatar da kowa na gida kafin ka kwanta. Yaya bansan yashe ka koma haka ba, shin dan ALLAH miya canjaka? Anya kuwa son Mawaddat kakeyi da gaske har cikin ranka? Wace irin bahaguwar rayuwace wannan mara fasali. Iyayenmu sun baku tarbiyya gwargwadon iyawarsu kai da Aunty Kareema. Sannan kuma kun bani dan gashi a yanzu ina cin ribarta matsayin nagartaccen mutum da ke banbance fari da baƙi koda a cikin rufewar idanu ne. Sannan sauran yaran ma suna samun irin tarbiyyar dana samu da ga gareku. Shin miyasa komai ya canja akan Mawaddat ne? Miyasa makahon so ya lulluɓe zuciyarka kake ɗorata akan abinda zata iya kaico da kai wataran da tunanin soyayya ce. Ban ce karka sota ba, amma ka dinga dubayya mana. Shin dole ne sai ka nuna mata ƙazamar soyayya zamu san kaso mahaifiyarta kamar haka itama? Ko sai ka mata makahon so zai sanarma duniya ita ɗin ƴar sonka ce da ta fito da ga jikin matar son ka?. Anya yaya ba alhakin Aunty Kareema bane kuwa ke bibiyarku akan Mawaddat kai da mahaifiyarta? Anya ba farkawa ya kamata kayi da ga nannauyan barcinka ba a wannan gaɓar kafin komai ya ƙarasa taɓarɓarewa mu rasa Mawaddat gaba ɗayanta”.

      Sosai jikin Daddy ya ƙara yin sanyi, dan dama harga ALLAH ƙarfin hali kawai yake na son musawa uncle Yousuf ɗin tunda shima ya ga shigowarta gidan a ɗazun da safen batare da ita ko wani ya sani ba. Wannan damuwar ce ya tashi da ita, sai dai ya rasa ta yanda zai tunkari Mawaddat ɗin shine ya huce haushin akan Mubeen da Mommy. A hankali ya damƙo hanun Uncle Yousuf cikin nasa ya ƙanƙame da ƙarfi, so yake ko sau ɗaya yayi kuka akan wannan damuwar ta halin rayuwar da Mawaddat ta jefa kanta a ciki amma ya kasa. Sai dai idanunsa sunyi wani masifar kaɗawa da ja. Cikin rawar murya ya ce, “Nagode ɗan uwana. Nagode da ka kasance mai faɗa min gaskiya komai ɗacinta. Wlhy auta al'amarin Mawaddat shine mafi zama ƙololiwar damuwata a yanzu fiye da komai, dan hanani barci yake yi. Zan faɗa maka gaskiya ko jiya nasan fitar ta a gidan nan, kuma nabi bayanta, sai kuma na samu yaron nan driver da ka kawo shima ɗin yabi bayanta. Dan haka na laɓe a kangwon kusa da gidan data shiga a wajen har kunama ta harbeni jiyan. Ban damu da azabar kunamarba, ni dai burina yaron nan ya fito da ita a gidan lafiya. Cikin amincin UBANGIJI kuwa sai gashi ya fito da ita a mota, na fito zan sake biyosu duk da azabar harbin kunamar da nake ciki idona ya ganemin ɗan gidan tsohon gwamna M Atik Kumo zai shiga gidan shima. Na shiga tashin hankali matuƙa, sai dai ban tsayaba na biyo motar tata dan naga ina yaron nan zai kawota sai naga gidanka ya nufa da ita. Nutsuwar hakan dana samu ce ta sani komawa da baya can gidan ɗin dai na sake tsayawa a mota, abinda ya sake tadamin hankali Yousuf su Alhaji Baita na gani sun fito a gidan nan dai da Mawaddat ta shiga kusan ƙarfe ukun dare. Wlhy tsabar ruɗani bamma san kunamata ta sauka ba. Da ƙyar na iya sake maido kaina gida shine fa ko rintsawa banyi ba har akai sallar asuba, bayan na dawo massalaci naga shigowarta gidan nan”. Ya ƙare maganar hawayen da yaketa son su zubo na sauka a yanzu masu zafi. Sosai shima Uncle Yousuf ya shiga ruɗani da tashin hankali. Dan jin sunayen manyan mutane da duk wanda ka tambaya zai tabbatar maka ɗunbin ganin mutuncinsu da yake a cikin wannan labari na yayansa......

       Daddy ne ya katsesa da faɗin, “Yousuf kaina ya kulle gaba ɗaya akan al'amurin nan, ka kawo mafita inba hakaba ina gab da kaiwa ƙasa akan lamarin Mawaddat”.

          “Yaya mafita ɗaya muke da ita shine yi mata aure....”

       “Aure Yousuf? To da wa? Kasan dai Mawaddat bata kula kowa. Kana dai ganin duk kurari da jan idon Baba (Alhaji Sufi Garko) yayi ya barta akan sanya ranarta da yaron Sulaiman data bijirewa. Har gargaɗin duk randa wani ya sake zuwa garesa domin santa zai aura masa ita koba amincewar ta da mu kammu yay mata amma bata ɗauki hakan da muhimmanci ba saboda bushewar zuciya. Yousuf na rasa da ga ina na kuskure akan Mawaddat. Shin nuna mata soyayya na nufin ba dai-dai ba kenan?”.

     “Humm Yaya wannan harda laifinka kaima ka sani, ba'a hana iyaye su nunama ƴaƴansu soyayya ba, sai dai ba ƙazamar soyayya irin wadda kaima Mawaddat ba da har tazama jagoran hanata fahimtar minene addininta. Yaya kofa salla nagartacciya Mawaddat bata iya ba a wannan shekarun nata balle azo ga sauran al'amuran addini, hakan kuma duk kuskurenka ne da kasa barinta ta samu tarbiyya irinta uwa a wajen Aunty Kareema saboda son zuciyarka..... Amma dai mu ajiye abinda ya wuce mu kalla na yanzu. Yanzu dai bayan tabbatar da aure ne mafitarmu akan lamarin Mawaddat bani da wani idea kuma. Amma dai ka bani lokaci nayi nazari tukunna. Sannan dan ALLAH ka kwantar da hankalinka. Dan lamarin Mawaddat an baro shiri ne tun rani. Amma insha ALLAHU tsayayyen miji a gareta zai jagoranceta da sabuwar tarbiyyarsa irin wadda tun farko ya kamata ace ta samu da ga garemu. Addu'a ya kamata mu duƙufa mata musamman ma kai ɗin nan. Sannan mu dage da sadaka ALLAH ya shiryar mana da ita, ya kuma kawo mana mafita cikin sauƙi. Sannan ka ajiye batun su Alh. Baita ni da kaina zanyi bincike a kansu insha ALLAHU zan gano alaƙarta da su”.

         “Shike nan Yousuf ALLAH yay maka albarka.”

    “Amin yaya”.

   Daddy ya sake nisawa a hankali da faɗin, “Sai dai kabi a hankali a duk wani bincikenka dan a wannan gaɓar da gaske inajin ƙanina, tsoro na gaske nakeji wlhy a wannan gaɓar. Miya kawo su Alh. Baita cikin rayuwar Mawaddat?”.

         “Bana tunanin wani abu saɓanin wanda zuciyata ke kallo yaya. Kasan dai da yawan wasu manyan ƙasar nan sunata taka wata rawa cikin rayuwar lalacewar yaranmu batare da mun farga ba”.

     “Nafika sanin hakan Yousuf. Sai dai al'amarin ya wuce a yanda kai kake kallonsa da hasashensa. Kai dai kamar yanda na faɗa maka inajin tsoro da gaske a yanzu tsoro nake ji irin wanda a baya babu shi a zuciyata.....”

       “Yaya na kasa fahimtar mi kake nufi ka ruɗar dani fa, Miye ke baka tsiro ne wai?”.

   Murmushi Daddy yayi mai nuna tsantsar damuwa a bayyane. Maimakon amsa sai ya dafa kafaɗar Uncle Yousuf tare da ɗan bubbugawa ya miƙe. “Tashi kaje office auta karka makara”.

       Kallo Uncle Yousuf ya bisa da shi mai tsayawa a rai, sai zuciyarsa ke wani irin rawa dan shi kaɗai yasan mi yake iya hangowa game da ɗan uwan nasa, sai kawai shima yaji kamar ya fara jin tsoron. Tabbas akwai ɓoyayyen al'amari wanda ya kamata ace ya sani amma ta yaya? (Bincike akan alaƙar Mawaddat da su Hon. Babale Nakowa) kansa ya jinjina cikin gamsuwa da shawarar zuciyarsa. Dan haka shima ya miƙa ya fice. Da kallo yabi motar Yayansa dake ƙoƙarin ficewa a gidan. Numfashi ya sauke da ƙyar tare da nufar tashi motar shima.



★★★ ∆ ★★★


   

   Smart kam tattara al'amarin Lulu yay ya wancalakar gefe domin fuskantar tasa mai muhimmanci. Gida ya nufa kai tsaye saboda kiran da Abba yay masa. Ya samu gidan da ƴar hayaniyar kasancewar zuwan Sa'id da wasu kawunansa uku. Cikin girmamawa ya gaishesu batare da ya kalla inda Sa'id ya ke gurfane ba kamar mai kuka. Ya maida hankalinsa ga Abba da Hawwah ke a kusa da ƙafafunsa kamar tana kuka itama.

      “Abba gani”.

Ya faɗa cikin dakewarsa. Nisawa Abba yay da nuna Hawwah ya ce, “Kaine ka ɗakko Hauwa'u a gidanta?”.

          “Eh tabbas nine Abba”.

      “Me yasa?”.

  Shiru ya ɗan yi kafin ya nisa. “Abba saboda ta kirani akan ga mahaifiyar mijinta na neman ƙonata da mangyaɗa. Banje gidan da nufin ɗakkota ba sai jin ba'asi na kuma sasanta kamar na baya da akai batare da kun sani ba. Sai dai na samu abin ya wuce yanda nake zatonsa shiyyasa na ɗakkota kafin a cutar da ita tunda mu bawai mun daina sonta bane ba. Ba kuma mun bashi bane dan mun gaji da ita a gidan nan kota gundiremu. Abba abubuwa da yawa sun faru akan auren Hawwah amma ina sasantawa a iya can batare da kai ko Ammah kun taɓa sani ba. Bama ku ba hatta da Aunty Bilkisu ban taɓa sanarmawa ba, kuma na gargaɗi Hawwah sanar ma kowa. Shiyyasa wannan karon na ɗakkota kuma bazata sake koma musu gida ba. Yaje ya auri wadda mahaifiyarsa ke son zama da ita haka nan dan ALLAH kowa ya huta.”........✍️





_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments