Recent Updates

Furar Danko 25

 


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗




           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣5️⃣




........Fuska Lulun ta sake tsukewa, yayinda sakatariyar ta risina tana gaishesa dan basan ko wanene tunda ba yau ya fara zuwa ba. 

      “Jeki abunki.”

Ya cema sakatiyar yana kaiwa zaune. Sakatariyar ta ɗan kalli Lulu a tsorace, sai kuma ta dubesa cikin girgiza kai kamar zatai kuka. Shima Lulun da ke faman haɗa takardun gabanta ya kalla, sai kuma yay ɗan murmushi. “Madam please taje?”. Harara ta ɗago ta balla masa, ta sake maida kanta ga abinda take yi. Ƴar ƙaramar dariya ya ƙarayi mai fidda haƙora, tare da yima sakatariyar nuni da hannu alamar taje. Da sauri ta fice har tana neman cin tuntuɓe. Idanunsa da ke ma sakatariyar kallon ƙasa-ƙasa ya janye ya maida ga Lulu... “Miyasa ka biyoni?”. Ta katse maganar da yay yinƙurin mata. “Idan masoyi ya biyo masoyiyarsa laifi ne Mawaddat. Please ki daina wahal damu haka mana, ko so kike sai na kai ƙasa ne?”.

       “Bani da matsala da kaiwarka ƙasa Tajuddeen, matsalata ɗaya shigarmin rayuwa da kake yi. Ka bar wahal da kanka dan bazaka taɓa samuna ba. Ko'a baya na amince ma batun su Daddy ne saboda Grandpa kaima ka sani. Amma ban taɓa jin sonka ba, kai bama kai ba, duk wani namiji ban taɓa jin sonshi da sunan soyayya ba a rayuwata. Idan ka cire Daddy na, Grandpa, da Uncle you. Ina baka shawarar ka daina bibiyata dan ina ɗaga maka ƙafa ne saboda zumincin da ke tsakaninmu, idan kuma ka cigaba zan iya fyatoka ta duk inda yay mun bawai hancina kawai ba”. Daga haka ta miƙe hannunta ɗauke da takardun data tattara. Cikin takun nan nata na yauƙi. Tamkar wanda ta danne bakinsa da dannau ya kasa iya furta komai sai binta da kallo da yay cikin tashin hankalin kalamanta. Ya jima da fahimtar bata ra'ayinsa a yanzu, amma bai taɓa tunanin tun farko ma bata taɓa sonshi ba alfarmar Grandpa ɗin su yaci ba. Hannunsa ya kai saman goshinsa ya shiga murzawa, dai-dai nan sakatariyar Lulu ta shigo. Ɗagowa yay yana kallonta, ta ɗan rissina da girmamawa ta ce, “Sorry sir ta ce na rufe mata office ɗin”.

     Idanu ya ɗan lumshe ya sake buɗewa akan matashiyar yarinyar mai tarin nutsuwa. Sai kuma ya saki murmushi da jinjina mata kansa ya miƙe kawai. “Sorry sir” ta sake faɗa dai-dai yana fita. Hannu kawai ya ɗaga mata batare da ya juyo ba ya fice abinsa zuciyarsa fal damuwa. Koda ya fito ƙurar motarta kawai ya samu alamar ta fice. Ya kalla Smart da ke jigine jikin motarsa da waya a kunne alamar magana yake. Tsaiwar jiransa yay har ya kammala. Bayan ya kammala wayar ya juyo idonsa akan Tajuddeen da fuskarsa ta nuna alamun ɓacin rai da damuwa, kai tsaye ya furta, “Inaga zan wuce gida dan wani uziri ya taso min”. Cikin damuwar dake shimfiɗe a fuskarsa ya gyaɗa masa kai da ɗan ɗage kafaɗa. “Ba damuwa ai itama ta sake tafiyarta”. Sam shi Smart bai ga fitar Lulu ba, dan haka ya kallesa cikin son ƙarin bayani. “Ina magana ne akan ogarka bakaga fitar ta ba?”. Smart ya kai dubansa ga inda ya ga motarta tun shigowarsu, wayam babu ita. Sai kawai ya dawo da dubansa akan Tajuddeen ɗin yana mai girgiza kansa da ɗan furzar ya huci. A taƙaice ya ce, “Bara na wuce”. Ba yanda Tajuddeen ɗin baiyi ba akan ya bari ya kaisa amma yaƙi. Dole sukai sallama ya fito domin samun napep.....


         ★★★


      Sosai ran Tajuddeen yake a dagule, dan haka maimakon office da yay niyyar zuwa sai ya nufi companyn mahaifinsa da yake da tabbacin yana can. Koda ya isa gaisuwar ma'aikatan wajen ma bai iya amsawa da ƙyau, hannu kawai yake iya ɗaga musu. Sun sha mamaki dan sun san shi mutum ne mai saukin kai sosai ga fara'a. Sam baida wulaƙanci, wani lokacin ma idan yana jin barkwancinsa ya shigo Companyn bazaka taɓa cewa ɗan oga bane ba. Kai tsaye office ɗin mahaifin nasa ya nufa batare da jiran sakataransa yay masa iso ba. Alhaji Sulaiman Sufi Garko da ke tsaka da tattaunawa da babban yaronsa da ba'a jin sirrinsu a tare suka zuba ma Tajuddeen ɗin ido har ya ƙaraso inda suke. Hannu ya Bama yaron mahaifin nasa mai suna Isyaku, sai dai ana kiransa da Malami. Malami ya gaida Tajuddeen ɗin da girmamawa duk da kuwa zasu iya sa'anni, to amma ai baba ma da babansa. Alhaji Sulaiman dai kallon ɗan nasa yake kawai bai dai tanka ba, sai wani inkiya da yayma Malami da ido. Kai ya gyaɗa masa dan babu wani yaren jiki na Alhaji da bai haddace ba. Ko tari yayi yasan mi yake nufi. Fita yay ya bama ɗa da mahaifin waje...

         “Auta wani abu ya faru ne na ganka a haka?”.

    Alhaji Sulaiman ya faɗa cike da kulawa ga tilon ɗan nasa namiji kuma auta a cikin ƴaƴansa. Cike da damuwa Tajuddeen ya sake tsuke fuska, sai kuma ya kalla mahaifin na sa da idanunsa da suka kaɗa sosai. “Abba Please ina son zancen aure na da Mawaddat ya motsa mana. Wlhy bazan iya daina sonta ba, dan na gwada hakan amma na kasa”.

             Murmushin manya Alhaji Sulaiman yayi tare da ajiye pen ɗin hannunsa idonsa ƙyar akan Tajuddeen kamar yana son tabbatar da gaskiyar furucinsa... 

    “Abba Please say something mana”. Tajuddeen ya faɗa kamar zai saki kuka.

          Alhaji Sulaiman ya furzar da huci yana mai haɗiye sauran murmushin fuskar tasa da ya rage. “Tajjudeen in ce maganar nan ta wuce ai ko?”.

      “Abba bata wuce ba wlhy, dan nikam ina sonta kuma zan zauna da ita a duk yanda take. Dan ALLAH kayi haƙuri ku sasanta da Uncle Isma'il ni dai a auramin ita. Kaga zuwa jibi Grandpa zai dawo da ga Umra ɗinsa, ni dai zan samesa da zancen a karo na biyu tunda har yanzu bawai ta tsaida wani mijin bane. Nima kuma na kasa kallon kowacce mace da sunan soyayya dan ita kaɗai nake so tun ina yarona”.

      “Humm Tajuddeen sasantawa tsakanina da Isma'il abune mai matuƙar wahala. Kuma nasan zai iya wulaƙantani fiye da da saboda ƴarsa. Amma zan iya komai a kanka kamar yanda shima yake jin zai iya komai akan tasa ƴar. kuma kafin ma Baba ya dawo jibin yau zan fara masa zancen a waya”.

     Sosai farin ciki ya baibaye zuciyar Tajuddeen. Miƙewa yay yaje ya rungume mahaifin nasa. Shima fuskarsa da murmushi ya amshesa hannu biyu. Kusan mintuna biyu Tajuddeen ya ago. Cikin komawa serious ya ce, “Abba wai dan ALLAH miye ya haɗaku kai da Uncle Isma'il? Nasan dai sanda ina yaro ba haka kuke ba. Kuna ƙaunar juna kamar ƴan uwa na jini, kuna mutunta juna matsayin surukai. Amma abin mamaki sai ga mijin ƙanwarka uwa ɗaya uba ɗaya ya juye ya zama maƙiyika! Abba Please ka heal min miya haɗaku ko zan iya wani abu mana.”

              “Tajuddeen wannan ba huruminka bane, kai dai ba kana son auren Mawaddat bane? To ka saka a ranka kamar ka samu dan koba komai ita ɗin ɗiyar ƙanwata ce Isma'il bai isa canja wannan tarihin ba. Dan haka jeka ka cigaba da harkokinka Mawaddat ta zama matarka nan da sati biyu kacal.”

       Sosai maganar farko ta tsaya masa a rai, sai dai ta ƙarshe ta masa matuƙar daɗi da sakashi a farin ciki dan haka bai musa ba yay masa sallama ya fita cike da ƙwarin gwiwar ya kusa malaskar Mawaddat.


Ni dai is born hummmm😵‍💫. Kufa masu karatu ya kuka gani🤷?.


       ★★★....★★★


   Kallon mamaki yake ma kill rate akan furucinta. Fahimtar hakan ya saka Aunty Saliha sake faɗin, “Wlhy da gaske nake Sweetheart bata nan fa. Alamu ma ya nuna ta jima da barin gidan nan kamar.” Sosai ran Uncle Yousuf ya sake dugunzuma. Dan haka ya cije lips ɗinsa da ƙarfi batare da lie komai ba. Ture shayin gabansa yay tare da miƙewa ya fice a falon. Cike da tausayin mijin nata ta bisa da kallo. Baba maigadi ya gaishesa da girmamawa duk da ganin yau fuskar ubangidan nasa babu walwala. Hannu kawai ya iya ɗaga masa. Sai kuma ya furta “Baba ko akwai wanda ya fita a gidan nan ne bayan yara da suka wuce school?” 

      Baba maigadi da ya ɗan daburce ya shiga in-ina da inda-inda. “Baba tambayarkafa nake? Bana son kwane-kwane ka faɗa min”. Uncle Yousuf ya faɗa da ɗan jin haushi a muryarsa. “Kayi haƙuri Alhaji, abunne dai kamar da ruɗewar kai. Hajiya Muwaddat dai ta fita kam tunda duku-duku kafimma yara su wuce, sai dai abinda ya ɗauremun kai da hargitsani ni banga shigowarta bane shiyyasa na fara tunanin ko junnu ne ke son buɗe min idanu n....”

      Takaici ya saka Uncle Yousuf yin gaba batare da tsayawa jin ƙarashen labarin da yayma kallon na soki burutsu ba. Sai dai harga ALLAH shi baba maigadi iya gaskiyarsa da yake faɗa. Sosai hankalin Uncle Yousuf ɗin ke'a tashe, dan zuciyarsa ta fara masa wasi-wasin karfa taƙi zuwa gida. Yana shiga key ɗin motarsa da ke a dining kawai ya bama aunty Saliha umarnin bashi, bai ma ko saurareta akan magiyar yazo ya ƙarasa break fast ɗinsa baiyi ba ya sake ficewa abinsa. Sai ƙarar buɗe gate da fitar motarsa kawai tajiyo. Addu'ar isa lafiya kawai tai masa dan bata da yanda ta iya tunda tasan ƙaunar da yakema ahalinsa dabance a rayuwa. Bai haɗa son su da komai ba. Ita hakan bai taɓa zame mata matsala ba dan itama suna nuna mata ƙauna a cikinsu. Basu taɓa wareta ba ko nuna mata bambancin kasancewarta bare garesu. Hasalima suna ɗaukar mahaifinta matsayin uba garesu a yanzu fiye da kowa har danginsu na Jiƙamshi. Dan haka bazataima ALLAH butulci ba sai dai ma ta tayashi son danginsa itama tare da musu fatan alkairi musamman akan Mawaddat data zame musu tamkar zakka.........✍️





_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments