Recent Updates

FARASHIN TASIRI Complete Hausa Novel


 

[30/08 à 21:47] MRS SADAUKI 💫: 🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
*FARASHIN TASIRI*🪺
        ```celebrity```🌬️
         🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
     *Gajeren labari*🕊️

MRS SADAUKI 💫✍️

FCWA ☀️

Special gift fo my VIA FANS 🪷

❌Don Allah duk mai so ya fara daga farko,in kuma kin karanta ki yi share domin wasu su amfana

Page 1

“Ban...gane ka na asibiti ba? Mike faruwa? ”

“Na ce miki Sadiq Allah ya karɓi ransa ya riga mu gidan gaskiya ,yanzu haka ana ƙoƙarin yi wa gawarsa wanka”

Tamkar wacce aka buga wa ƙaton dutse haka na ji saukar furincinsa,ban san lokacin da na saki wayar ba na yi faɗuwar ƴan bori.Abu na farko da ya fara faɗo min a rai shi ne yadda yayi ta sambatuna a daren jiya ya na shaida min ni ce macce ta farko da ya taɓa kusanta a rayuwarsa .

Hawaye masu mugun zafi suka zubo min a kumatu,na sani ni karuwa ce duk abin da nake domin na samu kuɗi nake yinsa amma Sadiq shi na daban ne,ya so ni tsakani da Allah tun a lokacin da nake tallaka.Muguwar rayuwar da na saka kaina bai sa ya daina sona ba.
“Ki na da kyau! Wannan sana'a ba ta dace da ke ba.Zan so Allah ya nuna min ranar da zan aure ki,komai naki ya zama mallakina ni ɗaya” shine furincinsa na jiya bayan na ci galaba a kansa har ya kwanta da ni.

Ringing ɗin wayata shi ya maido da ni daga halin alhinin da ruhina ya lula.
“Alhaji Nera” shine sunan da ke yawo,da sauri na goge hawayen ina mai ɗaga wa.
“Baby na shigo gari ina son ganin ki a central hotel,a ɗakin da mu ka saba haɗuwa” shi ne abin da ya faɗa .
“Ban cikin yanayi wlh ,rasuwa aka yi mana” na faɗa kamar zan yi kuka.
“Subahanallah! Wa rasu?”
“Wani saurayina ne!” na basa amsa kai tsaye.
“Hhh! Wata sabuwa in ji ƴan caca! Meelat yau ke ce ke kuka akan namiji? Hum! Kar fa ki manta ke Cele ce wannan ba girman ki ba ne damuwa da wani can banza”

Cikin wata marainiyar murya na ce “Sadiq ne fa!”
“Sadiq? Talakan saurayin ki wanda ke ƙin karɓar kuɗin kin nan?”
“Shi fa dai” na furta wasu hawayen na zubo min shaaa.
“Allah jiƙansa! Amma Baby please ki ƙoƙarta ki zo ,na yi miki tanadi mai kyau” Alhaji Nera ya faɗa ya na mai yin dariyarsa ta shaƙiyanci.

Jin furincinsa ya saka na ji ɗan ƙwarin gwiwa,wayar na ajiye bisanin na shiga ban ɗaki na feso wanka.Kalolin turaruruka na shafe jikina da su sannan na fesa na baki bisanin na saka riga da wando jeans tare da ɗora hullar gashin doki.

Ban yi kwalliya ba hakan ya saka farin fuskata fita da kyau.Man leɓe na shafa bisanin na ɗauki key ɗin motata bayan na saka takalmi masu tsini.
Ina tafe ina rausaya kamar bishiya,mai gadi na ganina ya ruga ya buɗe gate.
Baƙar motata na shige na yi mata key, ina tafe ina sauraren kiɗa.

Wayata ta ɗau ringing,na ja uban tsuki ina masifa “jarababbe ni fa ban son jarr...” maganar ce ta gintse ganin sunan Heelat.
Ina ɗaga wa ta ce “Meelat ki na ina ne har yanzu ba ki ƙara so ba?” ta faɗa.
“Ban ƙara so ina ba?” na tambaye ta.
Ina jin mamaki a maganarta lokacin da yake ce min “ki na nufin ba ki san Sadiq ya rasu ba?”
“Na sani mana” na bata amsa.
“To mi kike jira da har yanzu ba ki zo ba? Kin ganmu nan fa duk abokanmu kowa ya zo”
Na ɗan taɓe baki na ce “zan zo ni ma,akwai wurin da zan je mai muhimmanci”
“Meelat duk uwar sadaukarwar da Sadiq yayi a kan ki har akwai abin da ke da muhimmanci da ya wuce ki hallarci zana'dar shi?”

“Heelat!” na furta cikin wani salo daidai nan na kawo hotel ɗin.
“Okay!” ta furta tare da kashe kiran.

Fitowa na yi bayan na gama parking,motar Alhaji Nera na gani a parker.Na saki murmushi tare da kutsa kai ciki,direct sama na hau inda ya saba kama mana ɗaki.
Knowking na yi,ya zo ya buɗe ƙofar.Uban tumbinsa na ƙurawq ido ina jin takaici,amma kasancewar mayyar kuɗi ce ni na share.
“Ya na ga ka na min wani kallo?”
“Kyau kika ƙara Babyna!” Alhaji Nera ya faɗa ya na washe baki.
“Ok na gode sosai!” na faɗa ina mai zama bakin gado.
Kusa da ni ya zauna ya fara shafata,sai dai ban biye masa ba saboda furincin Heelat da ke ta min yawo a kwanya.
“Baby don Allah ki cire mutuwar nan a ranki,shi fa ya riga da ya mutu to tunanin mi za ki yi?” Alhaji Nera ya faɗa ya na ƙoƙarin raba ni da kayan jikina.
Ban hana shi ba,haka kuma shawarar shi ta yi aiki kaina na ba da kai bori ya hau.
Bayan komai ya lafa ne yake ce min “kin ƙara zama ta musamman mene ne sirrin?” ya faɗa tare da kashe min ido ɗaya.
Ban basa amsa ba na tashi na shiga toilet na yi wanka,ina fitowa na mayar da kayana.
Ina tsaka da ɗaura igiyar takalmina ya miƙo min waya Android iPhone tare da wani turare wanda zai kai darajar dubu ɗari.
Na karɓa ba tare da na gode ba na miƙe tsaye,“zan tafi”
Yayi min kiss a goshi bisanin na fito.

Cikin aljihun mota na saka wayar da turaren bisanin na maida akalar motata hanyar gidansu Sadiq.
A daidai lokacin da nake fitowa daga mota,a kuma daidai wannan lokacin ne aka ɗauko gawar Sadiq za a saka a mota.
Ga dai duk jinkinsa rufe da likafani amma hakan bai hana ni ganin idonsa ba ya na fitar hawaye.Kukan jini Sadiq yake,yayin da kuma nake jin amon muryarsa ya na cewa “Meelat mi na yi miki har haka da za ki sayar da ruhina?”

Na zabura tare da yin ƴar ƙara jin an taɓa ni.Heelat ce,“lafiyar ki? Mene ne na gan ki cikin ruɗani? ”
“Ba komai !” na faɗa,ina mai sake kallon motar da  tuni an shigar da gawar Sadiq wanda kuma ke yi min magana cikin ɗaga murya “Meelat ki cece ni kar ki bari a tafi da ni,ban mutu ba” motar na bi da kallo har suka ɓacewa gani na.

“Meelat ki rasa kayan da za ki zo da su gidan makoki sai wannan?” Heelat ta faɗa,na ɗan dube ta .
“Wai lafiya kike? Ya na gan ki wata iri? Ai ban yi tunanin mutuwar Sadiq ta shige ki har haka ba” Heelat ta sake faɗa.
Yayin da kuma sauran ƙawayenmu suka ƙara so ,gidansu Sadiq yayi ƙaramtar da ba zai ɗauki mutane  sosai ba wannan ya saka duk suka tsaya waje.

“Gida zan koma!” na faɗa ina shirin tafiya Heelat ta riƙe ni,“ki jira mu yi ta'aziya mana .Yanzu za mu shiga amma don Allah bari na ba ki kallabina ki yafa ”
Ta faɗa tare da ciro kallabinta da ke ƙasan hijabi ta bani.
Karɓa na yi don kaf cikinmu ni ɗaya ce mai shigar banza duk da akwai uwanda ba su saka hijabin ba.

Ciki mu ka shiga don babu laifi mutane wasu sun ragu.Kamar wacce aka ce ma ga wadda ta kashe ɗanki haka Mamar Sadiq ke kallona da jajayen idonta ta kafe ni da su ko ƙyaftawa ba ta yi .
Da sauri na sunne kai ina jin zuciyata na mugun bugawa,lamurran da suka faru da ni a waje sai yawo suke min a kwanya.Har yanzu ban gaskata cewa abin da Sadiq ya faɗa min gaskiya ne ba.

Heelat Malama ce wannan ya saka ta wakilce mu ta fara jero addu'a'o'i mu kuma mu na amsawa da Amen .Duk da kaina a sunne yake amma har yanzu ina jin idon mahaifiyar Sadiq su na yawo a jikina.Na ɗan ɗago domin tabbatar wa,karaf mu ka haɗa ido da mugun sauri na mayar da su na sunne.

Wayata ce ta fara rigingin na katse kiran da sauri,sai dai yadda wani kiran ke ta shigo wa fiye da goma ya saka ni ɗaga wa,cikin ikon Allah daidai nan Heelat ta gama addu'a duk muka fitowa.

“Hello!” na furta,cikin ƙaraji yake min masifa tare da yi min furinci da ya kusa saka bugun zuciyata bugawa.
Tsabar kaɗuwa ya saka na riƙe Heelat gam ina mai sake tambayar Alhaji Nera “meeemm..me ka ce?”

“Ki sakar min gabana wanda kika sa yake ta fitar da jini,wato Meelat a kaina za ki gwada tsafi? Kin san wane ne ni ? Kin zata ni ɗin kanwar lasa ne?”
“Gaba kuma?” na sake tambayarsa a lokacin tuni injin da ke kula da ganina ya fara yin ƙasa.
Cikin gwanjin kuka,ban sani ba ko ya fahimci ban ma san abin da yake son sanar da ni ba yake cewa “Meelat ki yi wa Allah ki sakar min gabana ke ce kawai na yi amfani da ita duk yau,ki taimaka ki bar min abat1 wlh sabon aure zan yi.....”


*is not for free*😮‍💨
[31/08 à 11:01] MRS SADAUKI 💫: 🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
*FARASHIN TASIRI*🪺
        ```celebrity```🌬️
         🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
     *Gajeren labari*🕊️

MRS SADAUKI 💫✍️

FCWA ☀️

Special gift fo my VIA FANS 🪷

Page 2

Yadda Alhaji Nera ke gwanjin kuka a waya ya tabbatar min da gaskiya ce abin da yake faɗa.
Ina jin muryar wata na cewa “wannan ai baƙin ciki ne,ta ya za ki saka babban mutum cikin wannan mawuyacin hali? Ki taimaka ki saki kurwarsa kar jininsa ya ida.”
Na lumshe ido yayin da wasu zafafan hawaye kuma suka soma yi min zuba,key ɗin motata na baiwa Heelat na ce “mu je ki sauke ni gida don Allah ba zan iya yin driving ba.
“Mike faruwa Meelat? ”
“Mu je zan sanar da ke ” wayata ce ta ƙara yin ringing style Alhaji Nera ne.Ƙin ɗaga wa na yi ,a ƙarshe kuma na kashe wayar.
Heelat ce ta yi driving ɗina zuwa gida,sai dai tun kafin mu ƙarasa na ga motar ƴan sanda da kuma Hajiya Turai matar Alhaji Nera .

Yadda suka yi wa motata ƙawanya na san ban da wata mafita,“Meelat ƴan sanda ! Lafiya laifin mi kika yi?” Heelat ta faɗa a ɗan rikice ta na mai saurin taka burki.

Ban bata amsa ba na fita,daidai nan Hajiya Turai ta nuna ni ta na mai cewa “ga ta nan ku damƙeta ita ce ta kame kurwar mijina”
Ba su yi wani jira ba suka haɗe hannuwana tare da saka min akwa tare da jefa ni a motar su .

Heelat ta fara kuka ta na kiran sunana amma haka mu ka tafi mu ka barta nan tsaye.
A harabar asibiti motar ƴan sandar suka yi parking kafin a fito da ni.Ciki mu ka shiga har ɗakin da aka kwantar da Alhaji Nera ,har yanzu likitoci na kansa su na bakin ƙoƙarinsu.
Yadda al'aurar Alhaji Nera ke ta zubar da jini abun ya ƙara ɗaga min hankali,yayin da furicin likita kuma ya jefa ruhina cikin cakwakiyar fargaba .
“Zai iya mutuwa idan jinin bai tsaya ba nan da minti ɗaya”

Hajiya Turai ta min wani uban dundu ta na mai “don ubanki ki ƙetara shi ko kurwarsa ta dawo jikinsa,don wlh in kika bari mijina ya mutu da hannuna zan kashe ki”

“Meelat kin cuce ni,kin ci amanata...” Alhaji Nera ne ya soma magana sai kuma ya kasa ida wa sai gurnani da yake na fitar rai.
“Ya mutu!” wannan furincin na likita yayi daidai da tsayarwa igiyar da ke tafe da numfashina,ban ƙara sanin abin da ya faru ba sai tashi na yi na tsinci kaina a gadon asibiti.

Na lumshe idona da nake jin sun yi min nauyi,yayin da kwanyata ta yi balaguro zuwa shekarun baya ta na hasko min ainahin tarihina.


Jameela shi ne sunana na yanka,iyayena tallakawa ne.Mu na rayu a wani ƙauye da ake kira da Takalmawa.Noma da kiyo shi ne aikin mahaifina,yayin da sana'ar sayar da koko ya karɓi Innata.
Raheela ita ce babbar ƙawata,ajinmu guda a makaranta.Tun daga collège har zuwa lycée,bayan mun ci jarabawarmu ta ƙarshe wato BAC sai iyayenmu suka yi ta fafutukar yadda za mu shigo birni mu yi karatun University.

Ban da kowa a birnin Maraɗi sai abokin mahaifina wanda suke cinikin shanu, raƙumi da sauransu wato Alhaji Nera.
A ɓangaren Raheela kuwa ita a cikin hostel take karatunta tun da akwai ɗakuna inda ɗalibai ke kwana.

Tun ranar farko da mu ka fara zuwa makaranta mu ka raina kanmu,yadda ƴan matan birni ke cin uban ado yayin da mu kuma kayan jikinmu duk tsofi ne sannan ba wasu masu yawa ba.

“Jar uba Raheela dube min yadda ake ɗaukar wanka sai kace za a yi zaɓen fidda gwani” shi ne firucina yayin da nake ta ganin ƴan mata da samari na ta shawagi cikin sutura mai kyau.
“Jameela kar ki wani damu da kayan jikinsu,kin manta mu ɗin ƴan baiwa ne Allah ya yi mana ni'imar ilimi? Godiya ya kamata mu yi masa kasancewar mu ma mun shiga tarihi a cikin jerin ƴan matan Takalmawa da suka zo jami'a ”

“Haka ne kam! Su Lauratu ai tuni an yi masu aure ba tare da sun samu ilimi ba” na faɗa ina mai yin gaba,Raheela ta yi ƴar dariya ta ce “ke ma fa da yanzu ki na goyon yaro na biyu”
Na kai mata dundu ina cewa “Allah kiyaye min ,duka shekaruna 21 fa”
“Ƴan sha biyu ma an yi masu aure ballantana ke ƙatuwa? Mu je na gwada miki ɗakina ” cewar Raheela kafin mu wuce wurin kwanan ɗalibai.
Ɗaki ne ɗan madaidaici,mai ɗauke da gadajen ƙarfe biyu .

Bayan na ga ɗakin nata mu ka wuce ajin karatu,nan fa kallo ya dawo kanmu yadda mu ka fita daban da sauran ƴan mata.Bai hana wasu samari yi mana dariya ba ana zunɗenmu, kasancewar ban da haƙuri ya sa ni cewa “uban wa kukawa dariya ihiii? Sheguna masu ƙattan kanu ”
Ban san yanayin maganar ƙauyenmu zai basu dariya ba sai da na ga kusan mutanen na darawa su na “wlh ƴan ƙauye ne”

“Eh su na mi shikai in daga ƙauye na zaka ( na zo)?”
Tamkar abar wasa haka suka dinga tsokanata,a ƙarshe da na fahimci maganar ƴan ƙauyen ce basu dariya na yi banza da su.
Sosai Raheela ta yi ta danna ƙirjina,a haka har malamin da zai koyar da mu ya shigo.Nan ne fa suka raina kansu yadda suka ji ina ta ɓarin ilimi kusan ni da Raheela duk mun fi  amsa tambayoyin malam .

Lokacin cin abincin yayi,ni da Raheela mu ka je mu ka sayo dambu mu ka zauna mu na ci.
“Assalamu aleykum ” wani matashin saurayi ya faɗa,Raheela ta amsa masa sallamar kafin ya ce.
“Don Allah mi sunan ƙawar ki?”
Sai da Raheela ta kalle ni sannan ta ce “Jameela”

“Su Jameela abun babu Bismillah?” ya tambaye ni haɗi da tsure ni da ido,“Kar ka kuma ambaton sunana”
Na furta ina harerensa zan ci gaba da yin magana na ƙware nan na shiga tari.
Ruwan da ke riƙe da hannunsa ya miƙo min na karɓa na sha ,“yau na ga masifa! Wlh ko maye ne kai kurwata ta fi ƙarfin ka” na faɗa ina goge hawayen da ke min zuba don sosai na ƙware.

Shi da Raheela suka shiga yi min dariya,bisanin ya zauna su na hira.Don dole ni ma na saki jiki aka yi hirar da ni,a nan ne na san sunan shi Sadiq.
Tun daga wannan lokaci mu ka yi sabo da Sadiq wanda bai ɓoye min ba ya nuna min so da ƙauna,don abokinsa Hafiz har tsokanarsa yake da mijin baƙauya.

Adadin watannin da na yi a jami'a iya adadin yadda girman burina ke daɗa ƙaruwa a ruhina.Ina son ganin na yi rayuwa irin ta wayayyun mata,na saka kaya masu kyau,na hau mota mai tsada da kuma zuwa wuraren ƴaƴan masu kuɗi.
Sam ban iya ɓoye muradina,a kullum in mun fita na ga mota mai kyau sai na nuna kwaɗayina akai yayin da Sadiq da Raheela ke iya ƙoƙarin su wurin ganin na cire wannan dogon burin sai dai ina,aka ce wanda yayi nisa ba ya jin kira.

Yau ne aka bamu hutun farko, wannan ya saka mu ka fara shirin zuwa can ƙauye.Hajiya Turai wacce a gidanta nake zaune sai wani ɓata rai take don ba ta so na tafi saboda tun zuwana ni ke yi mata wankin kaya da sauran aikace-aikace.

Bayan na gama shirya komai Alhaji Nera ya ɗauke ni a mota ya kai ni can tasha.Tun kafin na sauka na hangi Raheela zaune ta na zaman jirana,ƴan kuɗin kashi ya bani bisanin ya ce min “in kin je sai ki gaishe da Abban ki”
Da “to” na amsa kafin na fito da ƙullin kayana cikin ɗan buhu gari yayi zafi.
Mu ka rungume juna ni da Raheela bisanin mu je mu shiga mota.

“Babu wuri kujera ɗaya ce ta yi saura,ina ga mu fita mu jira wata” na faɗa ina dubawa ko zan samu wata kujerar .
“Ki zo nan ga wuri nan” cewar wata Hajiya daga can ƙarshen mota,da murna na ce “yawwa Raheela ke zauna nan ni bari na je can”
“To babu damuwa amma na so a ce mun zauna kusa da juna” Raheela ta furta duk yanayin fuskarta ya nuna rashin jin daɗi.

Ni kuwa ƙetara wa na yi,na zauna kusa da matar ina mitar “to tun da ba motar gidanmu ba ce ai dole mu yi haƙuri,nan ina ce in kin ji ina faɗar ina son na yi kuɗi na shiga mota mai kyau ya kwatsa ta kike”

Zama na gyara ina mai rungume buhun kayana,direba ya fara jan mota hajiyar da ke kusana wacce ƙamshin turarenta duk ya cika min hanci ta ce .
“Ƴan mata mi sunan ki?” na dubeta a mamakance,ta ci gaba da cewa “na ji kin ce ki na son ki yi kuɗi shi ne nake son na ji ta bakin ki in ki na son na taimaka miki ”
Jin ta sosa min inda yake min ƙaiƙayi ya sa na washe baki,don kallo guda za ka yi mata ka gane mai kuɗi ce ita irin sosai ɗin nan don hauren Makka biyu ne jere ras a bakinta .
“Hajiya da gaske za ki taimaka min na yi kuɗi?” na tambaye ta.
“Ƙwaran gaske ,yanzu haka ina da yara sa'anin ki masu aiki a ƙarƙashina duk sun yi kuɗi ta dalilina.Ina da motoci sama da biyar,yanzu ma ra'ayi ne ya saka ni shiga motar kasuwa sannan yadda kika san shiga ɗaki haka na mayar da jirgin sama ”
Romon bakan da take yi min suka ƙara zautar da ni,sai ƙasa-ƙasa take da murya ta na bani labarin rayuwarta da ƙasashen da ta taɓa zuwa a haka har mu ka sauka.

“Ga lambar wayata in kin samu lokaci sai ki kira ni, wannan kuma ki sayi ƙaramar waya da su” wani ɗan ƙaramin kwali ne mai ɗauke da number ta sai 10k sabuwa dal.
Hannuna har rawa yake na karɓa, lokacin da hannuna suka samun contact da kuɗin nan tamkar wacce aka yi wa wankin ƙwalwa haka na ji burina ya ƙara bunƙasa.

Bayan mun sauka, Raheela ta ce “wai hirar mice ce kuke ta yi da hajiyar nan?”
“Labaran duniya,kin ga ki saki ƙafa mu yi sauri mu ƙarasa gida na matsu na ga Innata” na faɗa tare da canza akalar zancen.
Haka kuwa aka yi ba ta sake yi min zancen ba,mu na tafe ta na min hirar Hafiz abokin Sadiq yadda ya nuna ya na sonta kuma aurenta zai yi.

A bakin ƙofa na tarar da Inna da ƙaton bokitin kokon da take sayar wa.Mu ka rungume juna cikin murna bisanin ta ja ni zuwa cikin ruɓaɓen ɗakinmu wanda ina yin tozali da shi na ji raina ya ɓace don a ɗan zamana birni na saba cikin villa.

Bisa tabarmar kaba na zauna,Inna ta kawo min ruwa haka na daure na shan ruwan rijiya bisanin kuma na fita zuwa shagon ɗan Idi mai sayar da waya.Dubu shidda ya sayar min da wata ƙaramar waya sai kuma ya ban layin airtel kyauta.Shi ya daidaita min komai bisanin ya saka min ita a caji don gida ba mu da wuta.Kamar abun tsiya haka na zauna na yi ta zaman jira har sai da ta ida cika sannan na karɓa na nufi gida.
Lambar Hajiya na loda tare da kira,bugu biyu ta ɗaga ta na ƴar dariya “dama na san za ki kira....”
[31/08 à 12:51] MRS SADAUKI 💫: 🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
*FARASHIN TASIRI*🪺
        ```celebrity```🌬️
         🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
     *Gajeren labari*🕊️

MRS SADAUKI 💫✍️

FCWA ☀️

Special gift fo my VIA FANS 🪷

*Masu buƙatar littataina na kuɗi ku zo na yi maku bonus maimakon 500 za ku iya biyan 300 domin samun littafi complete wacce ta shirya ta min magana ta WhatsApp* +22795045822

Page 3

“Eh Hajiya! Duk na kasa sukuni shine na je na sayi wayar”

“Dama na sani ai ! Yaushe za ki koma Maraɗi?”

“Hutun kwana goma ne ba zo yi” na bata amsa .

“Ayya! Ni kuwa ina cewa gobe za mu je kanti ki sayi kayan da kike so sai mu wuce wurin gyaran jiki.” Hajiya ta faɗa cikin wata irin murya mai jan hankalin mai muradi.

Cike da zumuɗi da kuma son banza na ce “ai zan iya zuwa in kin min sayayyar sai na dawo ko ya kika ce?”

“Har dai ki zo ɗin zan san yadda za mu tsara komai” ta furta.
“To Hajiya amma ya za a yi na gan ki”
“Kin ji wani shirme kuma,ke da kike da wayar hannu kawai kira na za ki yi sai na aiko direbana ya ɗauko ki”

Na washe baki jin an ambaci mota don ta na ɗaya daga cikin manyan burina.
“To Hajiya Allah saka da alkhairi ” na furta cikin jin daɗi.
“Amen! Sai an jima zan yi wani aiki” ba tare da ko ta jira abin da zan ce ba ta kashe kiran.

Na ja ajiyar zuciya bisanin na kwanta kan tabarma.Ina nan zaune Inna ta shigo da langa ,a gabana ta ajiye ta na mai cewa “ga alala nan ki ci,a zubo miki kokon?”
“A'a Inna alalar ma ta isa” na faɗa ina jawo langar na fara cin alalar a zuci kuma faɗi nake ina ƙari ‘ nan da wani lokaci za mu yi hannun riga da duk wani abincin tallakawa,mu rinƙa shan madara da ƙwai da haƙarkarin kaji’ sai kuma na yi dariyar kaina .

Gurbin zuciyata ya cika fam da dogon buri wanda a yanzu dab yake da cika.
Ina gama ci na sha ruwa sannan na jawo matashin kai na rungume,lambar Sadiq na kira wacce ta daɗe a kaina.
Ya na ɗagawa mu ka gaisa sai kuma kuɗin suka ida,shi ya sake kirana ya na mai cewa “Jameela ina kika samu waya?”
“Tawa ce,yau na saye ta” na basa amsa.
“Madallah! Na ji daɗi sosai yanzu kin ga sai mu yi ta shan hira kafin ki dawo.Da ina cewa Hafiz ya ban lambar Raheela sai mu rinƙa waya”

“Hum! Saurayinta ya saya mata waya kai kuma ka dinga yin hira da budurwarka ko?” na cikin jin haushi saboda satin can da ya wuce Hafiz ya saya wa Raheela ƙaramar waya.

“Jameela kin san da ina da kuɗi da tun tuni na saya miki,wlh ni ma ba a son raina ba ne.”
“Ba wani har ce min ka yi za ka bani tsohuwar taka muddin ka canza amma kuma daga ƙarshe ka ƙi”

“Jameela tun ranar nan na faɗa miki Mama ce ba ta ji daɗin jikinta ba shi yasa na sayar da ita na sayo mata magani ”

“Hum! Na ji masu Mama”

“Ke ma ai Mamar ki ce,ya ne ya ƴan gidan fatan kowa lafiya?”

Na amsa da “ alhamdullah! Abba ya tafi gona Inna kuma na waje ta na sayar da koko”

“Ke kuma ki na me?”
“Kwance ina huta wa!” na basa amsa.
“Hhh! My Jamee in kin samu gidan hutu sosai za ki ƙara kyau farin ki ya fito,shi yasa nake ta fafutukar neman kuɗin auren ki”

Dariya ya ban sosai,saboda bai wata sana'a sai shap-shap wani sa'in kuma ya kan taɓa kabu-kabu domin samun kuɗin da zai sa mai a babur ɗin.

“Kai da ke zaune gida shine za ka ce ka na fafutuka? Wai ina katin da kake sayarwa ne? A turo min na 200 ”

“Yanzu kuwa” ya faɗa tare da kashewa,500 ya turo min na yi masa text na godiya bisanin na fara kiran duk wanda na san ya na da waya.

Wuraren magrib Abba ya dawo gida.
“Ah su Jameela ƴan makaranta ,yanzu Innarki ke ce min kin zo hutu ”

“Eh wlh Abba ,sai kuma na samu kira daga can makaranta gobe za mu zana wata jarabawa dole zan koma” na faɗa ina mai shararo masa ƙarya.

“Allah taimaka,ya kika baro mutanen can ɗin?”
“Lafiyarsu lau Abba ,Alhaji ya ce ma a gaishe ka”

Nan mu ka soma yin hira bisanin na fita na yi alwalar sallar magrib,a bakin murhu na bar Inna ta na ta ƙoƙarin dafa Ganda.
Bayan na gama sallah na rakuɓe na lula duniyar tunanin in na yi kuɗi yadda zan yi rayuwata,ina nan zaune aka kira isha'i na tashi ita ma na sauketa bisanin na fita tsakar gida.
Abincin mu ka ci,Inna sai labarin ƙawayena uwanda suka yi aure bayan tafiyata.

Washegari
Tun safe na yi wanka na shirya,don sam ban yi wani baccin kirki ba.Sallama na yi masu kafin na je tasha na hau mota,tun a hanya na sanar da Hajiya  .
Cikin ikon Allah mu ka sauka lafiya,ina ƙoƙarin kiranta na ji muryarta “ga ni nan”

Na washe baki tare da isa wurinta na gaisheta,ta amsa tare da buɗe bayan wata farar mota ta ce “shiga” na kuwa shige sannan ita ma ta shiga.

“Ya hanya?”ta tambaye ni.
“Lafiya lau alhamdullah ! Ashe har kin zo ki na jirana ” na faɗa ina ɗan dubanta.
Ta murmusa ta ce “eh saboda ina son mu wuce kanti ki yi sayayya”
Na ɗan sunne kai ina godiya yayin da ita kuma ta na min wani kallo da na rasa na mene ne don har sai da na ɗan tsargu.

Ina cikin saƙar zuci har mu ka isa mall ɗin,mu biyu kawai mu ka shiga yayin da direba ya tsaya cikin mota.
Tamkar wacce yau ne ta fara shiga birni haka na yi ta ƙauyanci,tun ina mamakin yadda Hajiya ke zaɓa min kaya har na bari na bar wa kaina kan cewa saboda ita ɗin mai taimakon jama'a ce kuma mai kuɗi.

Tun daga kayan sawa,takalmi,hijabai da kuma turare babu abin da ba ta saya min ba.Har mota aka kawo mana kayan kafin mu wuce gidanta,nan na tarar da ƴan matan da ta yi min hirarsu a jiya.
Cikin sakin fuska duk suka tarbe ni,bisanin Hajiya ta ce “ga ƴar uwar nan na samo maku abokiyar aiki,ku taimaka mata ta tsefe kitsonta sai ku kaita salon”

Ƴan mata biyu ne suka miƙe su na cewa “to Momah yanzu nan kuwa”
A kunyace na zauna aka tsefe min kitso,ɗaya daga ciki kuma ta haɗa wasu abubuwa ta shafe min jiki da shi an ɗauki minti talatin sannan na shiga na yi wanka da ruwan ɗumi nan fa na ga fatata ta yi wani uban kyau.

Cikin kayan da Hajiya Momah ta saya min na zaɓi ɗaya na saka.
Su biyun nan dai suka min rakiya zuwa salon,yau ne karon farko da aka sa min apple hakan ya sa na yi ta ƙauyancin yadda gashina yayi taushi da tsayi.

Musamman da aka fito da ni daga madafar gashin sai ya ƙara yin tsayi aka shafa min mayuka da kuma saka min ribob.
Gida mu ka dawo,Hajiya Momah da ta ga yadda na sauya ta ce “an gaishe da Munayya da Rumy ”
“Da girman kujerar ki Hajiya Momah” suka furta su na murmushi.

Abinci mai rai da lafiya aka zuba mu ka ci,har sauri nake domin na gama na koma can Takalmawa na nunawa Raheela yadda na koma sai na ji Momah na cewa “in kun gama cin abinci ku kaita ɗakin hutu ta kwanta,na san duk ta gaji irin wannan zirganiya”
Ban ce komai ba duk da ina son komawa gidan,amma haka na bi bayansu na kwanta ba kuwa jima ba bacci ya ɗauke ni.
Ina farkawa da Hajiya Momah na fara cin karo hannunta riƙe da wani ɗan ƙaramin kasko sai hayaƙi ke tashi sama yayin da ƙamshi haɗi da wani ƙauri suka garwaye ɗakin.

“Meelat kin tashi? Ki na jin yunwa ko?” ta tambaye ni.
Jin ta canza min suna ya saka na ɗan murmusa don na fahimci Hajiya ta na son bariki sannan kuma wayayyar mace ce.

Ta ci gaba da cewa “Munayya kawo mata madararta ta sha sai ta je ta yi wanka”
Munayya wacce ke gefena ta na game ta miƙe ta buɗe frigine ta ɗauko wata tasa,miƙo min ta yi na karɓa.Madara ce mai sanyi sai ƙamshi ke tashi,abun ka da baƙauya haka na kafa kai na shanyeta tasss.
Momah sai wani murmushi take ,ni kuwa toilet na shiga na fara wanka.

Tamkar wacce ake yi wa sauyin massarafar gangar jiki haka na soma jin duk wata gaɓa ta jikina na saki,yayin da kuma  nake jin wani yanayi da ban taɓa tsintar kaina a ciki ba.
Ban shirya ba na ɗauki towel na ɗaura,idona har wani lumshewa suke ina ganin dishi-dishi.

Turus na yi ganin Hajiya da Munayya duk ba sa nan sai mutumen da na ɗauka matsayin Uba na biyu wato Alhaji Nera.Da wani mugun sauri na yi baya na jingina da ƙofa,a ɗan sauran ganin da ya rage min nake hango Alhaji Nera na tafowa gare ni.......
[31/08 à 15:22] MRS SADAUKI 💫: 🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
*FARASHIN TASIRI*🪺
        ```celebrity```🌬️
         🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
     *Gajeren labari*🕊️

MRS SADAUKI 💫✍️

FCWA ☀️

Special gift fo my VIA FANS 🪷

❌Duk wacce ta san ba ta karantawa kar ta shigar min groupe

#Mafarin ƙaddarata
Page 4

Lokacin da Alhaji Nera ya iso gare ni bai yi wani ƙasa da gwiwa ba wurin jawo ni jikinsa. Ba bacci nake ba amma madubin idona ya dishashe ta yadda ban gani tarau.

“Jameela dama na san ke zazzafa ce! Yadda kike da shaf mai kyau ya tabbatar min cikin mata ke ajin farko ce ,dubi yadda fatarki ke sheƙi” ya na yin furicinsa ne haɗi da ƙoƙarin raba jikina da farin towel ɗin da ke ɗaure a ƙuguna.
Jikina babu wata attakar da zan hana shi,hakan ya sa ya ci nasarar zare masurturcin  jikina haɗi da ɗaukata kamar ƴar tsanar roba ya ajiye kan latifa.
Gangar jikina yake sarrafawa wacce ban san dalilin da yasa nake jin saƙonsa na shigata ba,sai dai ba zan iya mayar masa da martani ba saboda jikina duk a mace yake.
Lokacin da Alhaji Nera ya ci nasarar raba ni da abu mafi daraja a wurin ko wace mace,sai na ji wasu hawaye masu gumi su na zubo min.Duk uwar azabar da nake ji bai sa na iya yin wani kataɓus ba,don kuka ma iya hawaye ne kawai suke iya fita.

Na ɗan ware idona kaɗan da har yanzu ba su ida dawo normal ba.Alhaji Nera ke tsaye ya na mayar da kayan jikinsa,a gaban idona ya fice sai kuma Hajiya Momah ta shigo.Wannan karon ita da Rumy ne fuskarsu ɗauke da murmushi sai kace abun arziki ne aka aikata gare ni.
Momah ta zauna ta na mai ɗago kaina yayin da ita kuma Rumy ta buɗe min baki ta fara zuba min wani shayi mai ɗan ɗumi,ɗanɗanason sam babu daɗi amma haka nake sha kamar wacce aka yi wa dole har na shanye.

Na lumshe ido,sannu a hankali gangar jikina ta fara dawowa normal.Sai a lokacin na fashe da matsanancin kuka,Momah ta shafa kaina ta na cewa “yi shiru mana,ai komai ya wuce yanzu burin ki zai cika za ki hau mota ,kayan jiki kuwa sai dai ki baiwa wasu”
Jin ta ambaci mota ya saka na ji nauyin zuciyata ya ɗan ragu,dakyar na yunƙura na tashi zaune ina mai kiciniyar suturta jikina da dara.
“Momah ki taimaka ki gasa mata jikinta mana,don wannan ban ce za ta yarda da na yi mata wankan ba” cewar Rumy ta na wani kwaɓe baki.
Dakyar na iya taka ƙafata zuwa toilet,sosai Momah ta min gashi mai kyau wanda ya sha magunguna.Sai kuma ta bar ni cikin wasu ruwan ɗumin,ina nan zaune na fara tunanin abin da ya faru da ni da tsakar rana.

‘Alhaji Nera !’ shi ne sunan da na aiyyana a rai,ina tunanin ranar farko da na sauka gidansa irin kallon da yake min kamar na son tantance wani abu.
Na lumshe ido can ƙasan zuciya na furta ‘mugu! Wato tuggu ya shirya min ya kawo ni tashar mota ya haɗa ni da muguwar can?’
Ɗaya ɓangaren zuciyata ne ya ban amsa da ‘to ai sau ɗaya ne tak! Kuma muradin zuciyarki ya cika yanzu za ki hau mota!’
Ban san lokacin da murmushi ya suɓuce min ba,ina hango yadda zan dinga parker motata a cikin jami'a ina kuma saka tsadadun kaya tare da shiga wurin manyan mutane.

“Wai har yanzu ba ki gama wankan ba? Likita na waje ya na jiran ki zai duba ki” Rumy ce ta turo ƙofa ta na kallona.
Da sauri na jawo towel sannan na miƙe,babu laifi yanzu ina ɗan takawa da ƙarfi.

Ina fitowa dadaɗan ƙamshin turare ya bugi hancina,yayin da kuma tuni an canza darar da ke shimfiɗe wacce da idona na ga duk ta ɓace.

Momah ta ce “kwanta likita ya duba ki kar aje kin ƙaru ”
Mutumen da ke sanye da wata farar riga irin ta likitoci na duba,fari ne sol mai farin saje shekarunsa za su kai arba'in da biyar.
Kamar zan yi kuka na kalli Momah na ce “hajiya namiji zai duba ni ? Da dai a bari gaski....” kallon ta jefo min ya saka ni haɗiye sauran maganar.

Kan katifar na kwanta ya duba ni,wanda da ace na san abin da zai faru da tabbas zan koma a toilet na rufe kaina.
Momah ta fice ta rufe ƙofa daga can baya yayin da shi kuma likitan na ga ya na ƙoƙarin cire kayan jikinsa.
Zuciyata ta buga da bala'in ƙarfi,ina mai tashi zaune na ce “mene ? Me za ka yi min?”
Wata dariyar shaƙiyanci yayi bisanin ya ce “mi kika gama yi yanzu kafin na zo na duba ki?”

Ban basa amsa ba sai wasu yawu da na haɗiye muƙut na tsoro,ina ji ina gani likita ya far mini.Wannan karon kuwa kuka har da kururuwa haka na yi shi amma kusan a banza.
Bayan ya gama cutar da ni ya yi min allura,“Allah ya isa!” na furta ina hararensa da idona da suka kumbura suka yi ja tsabar wuya.

Uffan bai ce min ya fice,kamar abun arziki sai ga Momah ta na cewa “Meelat a haka za ki cim ma nasararki ki na zagin costomer?”

“Costomer dai?” na furta a fili ina jin zuciyata na min ɗaci.
“Eh ! Ko har yanzu ba ki fahimci hanyar kasuwancin naki ba?”

Rararas ! Zuciyata ta tsinke.
“Karuwanci?” na jefo mata tambayar ba tare da na shirya ba.
“Madallah! Kwanyar ki na kawo wuta.Ga kuɗin ki na wurin likita,shi kuma ɗayan ya ce gidanku ɗaya za ku gyara kan ku” ta yi furicin ta na mai aje min kuɗi kusan kaina ta yi tafiyarta.

Na jawo pilow na rungume gam tare da fashewa da matsanancin kuka.Sai da na yi mai isata bisanin na je na yi wanka,na gasa jikina da ke min mugun ciwo.

Ledar kayana na jawo na zaɓi wata doguwar rigar abaya baƙa na saka.Na zauna tare da jawo kuɗin ,dubu ɗari ne cicif.
Aka turo ƙofa,mai aikin gidan ce wannan karon hannunta riƙe da abinci ta ajiye a gabana ta fice.
Yunwa nake ji hakan ya sa na fara cin shinkar wacce aka ɗora ƙatuwar kaza daga sama.Sai da na ci na ƙoshi sannan na je na ɗauko ruwa masu sanyi na sha,tunanin makomata na fara don ko giyar wake na sha ban turki zuwa Takalmawa ba dole Inna za ta fahimci abin da ya faru da ni.

Ina nan cikin halin ƙaƙanikayi,wayata da tuni na mance ina da ita ta fara tsuwa.Sabuwar lamba ce,na ɗaga ina mai kaiwa kunnena ba tare da na ce komai ba.

“Baby gani a ƙofar gida na zo ɗaukar ki,yanzu mu ka gama waya da Abban ki” shi ne abin da ya ce.Sarai na gane muryar,Alhaji Nera ne.Ban ce komai ba na kashe kiran,rigar ɗazu wacce na cire na ɗauki abata na saka a leda haka ma kuɗin bisanin na fito.

Har ƙofar gida Momah ta yi min rakiya sai daɗin baki take min da ƙara hura wutar muradina,ta yi min alƙawarin samo min costomer a duk lokacin da na buƙaci haka.
A gaba na zauna don shi ne ya buɗe min ƙofa,sai da ya hau titi da kyau sannan ya jawo hannuna ya ce “ya jikin naki?”
Cike da shaƙiyancin da ban san yaushe na koye shi ba na ce “wane jiki? Ce maka aka yi banda lafiya?”

Dariya yayi irin tasu ta ƴan duniya ya ce “baby duk fushin ne? To ki yi haƙuri da sannu zan cika miki muraden ki” ya jawo aljihun mota ya ciro min waya ƙirar Samsung ya ci gaba da cewa “ki saka layin ki a nan na saya miki Moov ya na ciki har ma  na buɗe miki WhatsApp ”
Ganin waya na sheƙi ya sa na yi saurin karɓa sai dai ban san yadda ake amfani da ita ba .
Sai da ya samu wuri yayi parking sannan ya saka min ɗayan layin nawa tare da nuna min yadda ake amfani da wayar .
A nan mu ka shiririce waje har aka yi sallar isha'i,a mota sosai Alhaji Nera ya yi bidirinsa da jikina.

Mu na zuwa gidansa Hajiya ta tarbe ni da murna,bisanin kuma ta ɗan ɓata rai ganin irin canjin da na yi wanda sam bai ɓoyiwa.

Alhaji Nera ya ce “ke fa kika ce na je na dawo miki da ita ko ba ki yi murna ba”
“Na yi mana Alhaji ,na gode” ta furta , Alhaji kuwa yi yayi tamkar a gasken ƙauye ya je ya ɗauko ni.

Ɗakina na shiga na tsarkake jikina na zo na yi sallah,bisanin na fara taƙilar wayata.Kira ne ya shigo da wata baƙuwar lamba,ina ɗaga wa Raheela ta ce “Ke wace jaraba wa ce aka yi yau? Na je gidan ku aka ce ba ki nan kin koma Maraɗi?”
“Wa ya baki lambata?” ita ce tambayar farko da na yi mata.

“Hafiz,yau da mu ka yi waya yake shaida min wai kin yi wayar hannu shine nace ya cewa Sadiq ya turo masa lambar ki shine shi kuma ya ban”

“Hum! To me yasa ba ki tambayi Hafiz ɗin ba ya faɗa miki jarabawar da aka yi ɗin?”

“Hum! Jameela na san babu wata jarabawa akwai dai abin da ya maida ki ”

Shiru na yi ina ɗan tunani can ƙyarƙyaro ƙaryar “wlh ban iya zama ne babu fanka shi yasa na gudo ”
Dariya Raheela ta yi sosai ta na mai cewa “shi fa ɗan ƙauye bai iya waye wa ba”
Ni ma dariyar na yi ina mai ce mata “sai ma in kin ga yadda na yi kyau,sosai Hajiya Turai ta ji daɗin dawowata yanzu haka tuni ta fara yi min sayayya ta kai ni salon an wanke min gashi in kin ganni sai kin yi santi ”

“Wai gaske ko wasa?”
A yanayin yadda na ji ta yi magana tuni na fahimci tata cutar ta motsa,wato hassada.
Cikin tabbatarwa na ce “da ace babbar waya ce gare ki kamar ni da na turo miki hotunana kin gani”
“Ok yayi sai an jima” shi ne abin da ta faɗa ta na mai kashe kiran.

“Shegiya munafuka ! Sunan Malama ce amma hassada na ciciyar ruhinta mtsw! In ma mutuwa za ki yi sai dai ki mutu don nan kusa kaɗan zan zama babbar yarinya”  na furta a fili ina juyi kan katifata.

Da dare misalin sha biyun dare text ɗin Alhaji Nera ya shigo wayata don sam na kasa bacci sai faman yin hotuna nake.
“Ki kunna data” shi ne abin da ya ce min.
Na yamutsa fuska don sam ban jin daɗin WhatsApp ɗin ba iya lambarsa ce sai ta Hajiya Momah kawai ke kan wayata,Sadiq kuma ƙaramar waya ce da shi balle mu yi hira.
Ina kunna data kiransa ya shigo,sanye yake cikin kayan bacci na maza duk muninsa ya ida fitowa.
Halshe ya fiddo cike da shaƙiyanci bisanin ya tambaye ni “ba ki yi shirin bacci ba?”
“Shi bacci har shiri ake yi masa?” na tambaye shi .
Kai ya jinjina ya na mai cewa “eh mana da wannan rigar za ki kwanta?”
“Eh ai ban daɗe da saka ta ba”
Wata dariya tuntsire da ita bisanin ya kashe kiran ya fara turo min hotunan ƴan mata cikin kayan bacci.
“Su kuma uwannan su waye?”na tambaye shi .
“Ƴan Matana ne!” ya ban amsa.
“Duk kai ɗaya sama da mace biyar?”
“Akwai ma uwanda ban turo miki ba,ki na son irin kayan jikinsu?”
“Eh ina so” na basa amsa .
“Ok gobe sai ki shirya mu je ki zaɓo ”
“A'a ni ba za ni ba sai dai ka kawo min,Hajiya zan yi wa wankin kaya”
“Ok ba matsala,amma don Allah cire rigar ki zauna haka nan yanzu zan kira ki ina son ganin ki”
Wani haushi ne ya kama ni,wato in na fahimta Alhaji so yake ya mayar da ni karuwarsa......
[01/09 à 07:59] MRS SADAUKI 💫: 🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
*FARASHIN TASIRI*🪺
        ```celebrity```🌬️
         🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
     *Gajeren labari*🕊️

MRS SADAUKI 💫✍️

FCWA ☀️

Special gift fo my VIA FANS 🪷

My book is only 300 via 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank,sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822. Ko kuma katin MTN,ƴan Nijar kuma carte airtel ta 300f

Page 5

Ina ƙoƙarin kashe data hotunansa suka shigo wayata,duk na tsaraicinsa ne.Ban san mi yasa ba ,kawai sai na shiga buɗe su abun takaici har da videos.Da dai na fahimci Alhaji Nera na son dole ya mayar da ni cikakkiyar ƴar iska sai na kashe data tare da saka wayar caji.Ina ƙoƙarin kwanta wa na ji text ya shigo,na duba.Sadiq ne ya turo min good nigth my dear,na ɗan murmusa bisanin na mayar masa da thanks kawai na kashe wayar.

Washegari

Kiran sallar asubah farin na yi wanka na yi sallah sannan na fito na fara wankin kayan Hajiya wanda tun jiya ta fitar da su.
Ina wanki ina tunanin sabuwar rayuwata har na gama.Hajiya Turai sai washe baki ake an samu banza,abincin breakfast ta kawo min har ɗakina.Na zauna na ci na ƙoshi sannan na zauna na kunna wayata,text ɗin Alhaji Nera ne birjit kai kace ya ban ajiya.Nan na shiririce wurin karanta saƙonninsa masu nuni da yadda yayi kewata,yadda na fita daban cikin ƴan matan da duk yake tarayya da su.Haka kawai na ji wani kishi kamar mijina,bisanin na koma duba text ɗin Sadiq .Yadda ya tsara min kalaman soyayya ya saka ni saurin kiransa ban shirya ba,ya ɗauka muryarsa a dishashe alamun daga bacci ya farka.
“Manya masu gari har yanzu ba a tashi ba?” na tambayesa.
“Wlh na gaji ne sosai ,jiya wuni na yi ina aiki shi yasa ma kika ga ban kira ki ba”
“Aikin me?” na tambaye shi ,ya ɗan yi shiru bisanin ya ce “Kadiro na je na yi dako,wlh so nake kafin ace mun je hutun ƙarshen shekara na tura magabata na ko baiko ne a yi ma mu kafin na haɗa na lefen”

Gabana ya faɗi,sai na ji kuma ban son maganar auren.To in ma an yi mi zan kai masa? Sauran mazan? Sai na ce “Sadiq don Allah ka mayar da hankalin ka kan karatu,duka fa yanzu ne mu ke shekarar farko cikin shekaru huɗu da za mu yi muna karatu”
Ya ja wata doguwar ajiyar zuciya ya ce “Ke ma haka za ki ce? Hum! Mama ma da na yi mata maganar ki ta ce na fara gama wa da karatu tukunna.Jamee wlh ina tsoron abin da zai raba ni da ke,ina tsoron kafin nan da shekara huɗun nan ki waye sosai ta yadda za ki fin ƙarfina”

Na yi ƴar dariya na ce “mace har ƙarfin namiji take?”
“Sosai kuwa! Jamee don ba ki san irin baiwar da ke tattare da ke ba ne shi yasa kike ɗaukar kan ki ƙaramar yarinya,amma ke ɗin ta daban ce”
“Kai ma ai haka kake ”
“Hum! Ba dai kamar ke ba,ina son ki don Allah ba don kyawun ki ba.Amma na san nan gaba duk wanda zai so ki to tabbas kyawun ki ne zai jan shi”

“Yanzu dai sai an jima,ka ci gaba da yin baccin ka” na furta tare da yanke kiran na lumshe ido bisanin kuma na miƙe kamar wacce aka tsikara na fita zuwa ɗakin Hajiya Turai.
Ba ta nan ciki,ƙarar ruwan da na ji a toilet na fahimci wanka ne take.Gaban dressing mirror na tsaya ina ƙare wa kaina kallo.Doguwa ce ni amma ba sosai ba,haka ba za a kira ni da siririya ba saboda shaf ɗina da ya fita kamar coca cola.Manyan idona masu dogayen gashi na ƙyafta haɗi da yin wani fari da su ina ɗan murmusa,dimple ɗina ya lotsa.

Tun ina yarinya babu abin da ke burge ni sama da rawa, wannan ya saka na ɗan fara girgiza irin yadda indiyawa kan yi rawa.
Hango Alhaji Nera na yi a tsaye bakin ƙofa ya harɗe hannuwa ya na kallona, “ci gaba!” ya furta min.
Zan yi magana Hajiya Turai ta fito daga toilet ɗaure da zane.
“Ke mi kike yi ɗakina? Alhaji mene ne za a ci gaba?” ta tambaya sai dai tun kafin na kai ga cewa wani abu Alhaji Nera ya ce “yanzu na shigo waya ce nake,lafiya ina za ki je na ga kin yi wanka”
“Ke kuma mi kika tsaya ki na yi?” Hajiya ta faɗa ta na kallona,na ɗan sosai kai nace “dama madubi nake so don Allah ki ban ko da guntu ne”

“Iyeee! Abu ga Fulani ! Bari na duba miki” ta faɗa tare da jawo tiroirs ta ban wani ɗan madaidaicin madubi da murna na karɓa na fice.

Ɗakina na koma ina ta kallon fuskata wacce ko maƙiyina yayi kaɗan ya ce banda kyau.
Wayata ta ɗau ringing na ɗaga,“don Allah ki fito na yi miki ganin ƙarshe ina son fita,sannan ki faɗan lambar bra da pant ɗin ki sai na sayo miki” Alhaji ya faɗa ina jin ƙarar mota.
“A'a na gode zan saya da kaina,don Allah Alhaji ka yi haƙuri ni ban son abin da kake yi min”
“Au! Kin fasa cika muradun naki na hawa motar kan ki da kuma rayuwa mai kyau?”
Shiru na yi ,sai kuma nace “amma hakan ka na ganin ....” sai na yi shiru saboda yadda Hajiya Turai ta shigo ɗakin ,ta kuma wani kafe ni da ido kamar mai zargin wani abu.

“Meelat ki mori ƙurciyar ki daga Kano sai Abuja ,don Allah kar ki bani kunya ko fito ina jiran ki” Alhaji Nera ya sake faɗa.
Murya na ɗan rawa na ce “Sadiq don Allah ka fahimce ni,karatu ne a gabana yanzu ba aure ba ka ga ma Hajiya nan tsaye ta rutsa ni ina waya” fuskar Hajiya ta ɗan sauya ta style ta na mai ci gaba da kallona.
Alhaji Nera gogagen ɗan duniya ne,ya tuntsire da dariya don ya fahimci abin da na son sanar shi ya ce “ok babu damuwa zan sayo miki kayan baccin” sai ya kashe.

Na ja tsuki ina mai mayar da hankalina ga Hajiya Turai na ce “hajiya ko da wani aiki da zan yi?”
“A'a babu,wane ne Sadiq?”
“Wani ɗan makarantar mu ne da yake sona,wai har ya far maganar aure sai kace wasar yara”
Hajiya ta washe baki ta ce “to in ba abun ki ba Jameela nan za ki zauna babu aure? Kawai ki amince masa ya fara zuwa zance!”
Cike da ladabi na amsa da “to Hajiya ” bisanin ta fice,na bi bayanta da harara.

HAJIA TURAI

Sanin halin Alhaji Nera na akuyanci ya saka kullum take kakau da Jameela,ko ba komai yarda ce ta saka mahaifinta kawota gidan karatu ba tare da ya san Alhaji Nera akuya ce da fatar kura.
Ba ta taɓa damuwa da ƴan matan Alhaji ba saboda ta san bai haihuwa balle ace ya yi wa wata ciki ta ji kunya,sannan ta na zaune da shi ne saboda kuɗinsa mutuwarsa kawai take jira ta ci gado.
Ɗaki ta koma ta ƙara kashe ɗaurin kallabinta na less ,sosai ta yi kyau . Kitchen ta shiga ta ɗora girkin rana.

Ɓangaren Alhaji kuwa sosai ya so Meelat ta fito su yi ban kwana,wani irin mugun sonta yake ji a ransa.So ne na sha'awa ba wai aure ba,hakan ya sa bai wani ji zafi don ta ambaci sunan Sadiq .

Sadiq
Ko da Meelat ta kashe waya tashi yayi ya je yayi wanka ya shirya tsaf ya tafi gidansu Hafiz.Cikin ƴar rumfar shaƙatawar da ke tsakar gida suka zauna.
Hafiz ya ce “ya na gan ka cikin damuwa?” Hafiz ya tambaya.
“Ba dole ba! Son Jameela yayi min kamun sandar makauniya.Wlh abokina mugun sonta nake,amma talauci ya min iyaka da cikar burina”
“To ai da zarar ka gama karatu aiki za ka nema,ka ga da ka samu shikenan”
“Amma kai auren ka da Raheela zuwa yaushe ne?” Sadiq ya tambaye shi.
Hafiz ya ce “jiya mun yi magana da Daddy,ka san tun can dama ya ce zai buɗa min kanti amma na ƙi to shine yanzu na amince.In ya so zuwa ƙarshen shekarar nan sai a yi auren ”

“Masha Allah! Nan da wata shidda kenan? Amma kun yi magana da ita Raheelar?”
“Eh! Ɗazu ma har Mamarta ta ban mu ka gaisa ”

Su na nan zaune su na ta hirar rayuwa motar Daddyn Hafiz ta shigo.Da sauri suka je suka gaishe shi,ya amsa ya na tambayar Sadiq Mamar shi ya amsa da ta na lafiya bisanin su koma su zauna.
“Abokina ya kake ganin in na fara zuwa da motar can ta Daddy makaranta?”
Cike da murna Sadiq ya ce “wlh za mu ji daɗi,ka ga sai na ajiye babur ɗina dama wani sa'in na mai na yi min wahala”

“Da mun sha yawo kuwa,jiya Raheela ta kira ni akan na saya mata babbar waya don Allah mu je ka yi min rakiya ”
“Ok to babu matsala”

Nan suka tashi suka je Tof Galaxy gidan sayar da waya.Tecno Pop2 Hafiz ya saya kala biyu iri ɗaya sannan suka fito,tun a hanya ya cire layinsa ya baiwa Sadiq tsohuwar tashi ya ce “ga wannan ka sa naka layin tunda na yi sabuwa ni da masoyiyya ” tsabar murna ya saka Sadiq idonsa cika da hawaye ya na ta godiya.

MEELAT

Tun fitar Hajiya Turai na zauna ina latse-latsen waya.Kiran Hajiya Momah ya shigo kamar ba zan ɗauka ba sai kuma na ɗaga.Gaisheta na yi ,ta ce “Su Meelat fushi ake da Momah ? Ko ɗan text ɗin nan na Barka da safiya?”
“Hum!” na ja ƙyaci.Ta ci gaba da cewa “to tuba nake ,dama kayan bacci ne Alhaji Nera ya ban kuɗi ya ce mu je sai na saya miki,yaushe kike da lokaci sai mu je?”

Cikin zumuɗi na son abu mai kyau na ce “jira gani nan zuwa” ta yi ƴar dariyarta da ta saba,sannan ta kashe wayar.
Sai da na sake yin wanka na shirya tsaf na fito.A kitchen na samu Hajiya Turai,“hajiya zan fita sai na dawo”
Ta juyo ta dube ni ta ce “Ah! Ah! Irin wannan uwar kwalliya ko dai wurin Sadiq ɗin za a je?”
Na ɗan sunne kai na ce “eh wai za mu je gun wata ƙanwar babarsa ne”
“Ok to ki kula da kan ki banda shashanci a hanya” cewar  Hajiya .

Ina fitowa na tsayar da mai taxi ,dama ina da kuɗi ADS nace ya kai ni can unguwar su Hajiya Momah .Ya na sauke ni na shiga gidan kai tsaye,yau falon tsit ba kowa sai Hajiya da wata sabuwar fuska.
Na gaisheta kafin na samu wuri na zauna,gasashen kifi ta sa aka kawo min da kuma jus.

Na kuwa ci don akwai ni da son daɗi.Bayan na gama ne sai Hajiya ta dube ni ta na cewa “ jira  ya na hanya”
Na dube ta da ɗan mamaki amma ban ce komai ba.Ko minti biyar ba ayi ba sai ga Alhaji Nera,sai wani rarraba ido yake ya dube ni ya dubi kuma baƙuwar fuskar da na tarar zaune wacce take wata zankaɗeɗiyar budurwa.

Kuɗi ya miƙa wa Hajiya ya na cewa “ga shi sai ku zaɓo masu kyau, Allah sa kafin ku dawo lokacin na gama”
Hajiya ta karɓa tare da miƙewa wannan ya saka ni ma na miƙe ina duban Alhaji Nera da bai da niyyar tafiya,don har mun fito daga falon.
“Hajiya shi kuma Alhaji fa? Mene ne yake maganar zai gama?” na tambayeta lokacin har mun shiga mota.

Ta yi ƴar dariya ta ce “matsalata da ke kenan Meelat ba ki iya cin ƙwan makauniya ba,sai kace ba ƴar hannu ba to mi zai yi bayan ya kwashi Gara.Ki gode wa Allah duk cikin ladies kin fita daban ke ce ƴar gaban goshi ”
Ban sake cewa komai ba har mu ka isa mall ɗin.Kayan bacci,pant,bra,kadar mata da kuma turare mu ka sayo bisanin mu jiyo .

Lokacin da mu ka isa gidan Hajiya Momah ,ko zama ba mu yi ba Alhaji Nera ya fito daga ɗakin nan na jiya ya na gyaran azargagin wandonsa.....

Just 300 via 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank,MD +22795045822
[01/09 à 13:56] MRS SADAUKI 💫: 🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
*FARASHIN TASIRI*🪺
        ```celebrity```🌬️
         🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
     *Gajeren labari*🕊️

MRS SADAUKI 💫✍️

FCWA ☀️

Special gift fo my VIA FANS 🪷

My book is only 300 via 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank,sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822. Ko kuma katin MTN,ƴan Nijar kuma carte airtel ta 300f

Page 6

Kallon sheƙeƙe na yi wa Alhaji Nera ,ina ƙoƙarin kawar da kaina ita ma budurwar sai gata ta fito. Kallo guda za ka yi mata ka san ta gurzu ba laifi don yanayinta ya canza sosai,jan bakin duk babu, kwalliyar fuskarta kuwa duk ta dame.

“Har kin fito? Ina cewa na haɗa miki ruwan wanka” Hajiya ta faɗa.
Ta ɗan yi dariyar yaƙe ta na mai zuge zip ɗin jakarta ta ɗauko 2k ta baiwa Hajiya Momah .
Wani mugun kallo hajiyar ta yi mata ta ce “kar ki ɗauke ni ƴar iska mana! Mu je ciki” ta ja hannunta ƙiiii suka koma ɗakin.

Alhaji Nera ya yi dariya ya na mai cewa “hajiya Momah manya” bisanin ya zauna kusa da ni ya ce “Baby ya na ga sai cin magani kike? Ko wani ya ɓata miki rai ne uhum?”
Zan buɗe baki na yi magana wayata ta ɗau ringing,sunan Sadiq ne ɓaro-ɓaro ke yawo a kan screen ɗin.
Ban damu da Alhaji Nera da ke kusa na ba na ɗaga,cike da murna Sadiq ke shaida min yayi babbar waya har ma ya turo min hotunan shi ta WhatsApp na hau online na gani.

Na ɗan saki murmushi na ce “yaushe? Ah ! Kace ka faso gari ?”
“Ni ma fa Hafiz ne ya ban wayar,yau ya sayi sabuwa shi da Raheela ”
Tuni na fahimci Raheela ta yi masa ƙorafin Android shi yasa ya saya mata.
“Ok zan duba ,yanzu ina wani aiki ne ” na faɗa tare da kashe kiran.
“Wai don Allah waye Sadiq ɗin nan? Na ji ɗazu sunansa kika ambata don lurar da ni Hajiya ta shigo ɗakin ki”
Labarin Sadiq na basa da yadda yake mugun sona har yayi min alƙawarin aure .
Ga mamakina sai na ga fuskar Alhaji Nera ta canza,“ke da ke karatu ya zai yi miki maganar aure yanzu? Kuma ma mi kika rasa?”

“Yanzu dai sai an jima zan wuce gida” na faɗa tare da tashi tsaye.
“Ko kayan ba za a nuna min ba?”
“Mene ne na sauri kai da za ka gansu sanye a jikina?” na faɗa cike da kissa.
“Eh kuma haka ne fa,ni ɗin ne na cika sauri kamar sabon ango” ya faɗa ya na yaƙe haƙora.

Ɓangaren Hajiya su na shiga ta dubi Na'ilah ta ce “ban son sakarci mi zan yi da dubu biyu? Sanin zai baki kuɗi da yawa ya saka na haɗa ki da shi amma shi Alhaji Nera ya fi son sabuwa dal a leda tausayin ki yasa na rakuɓa ki wurinsa”
Na'ilah ta ce “duka fa 10k ne ya ban”
“Wlh ƙarya kike! Alhaji Nera ƙaramin biyansa talatin ne abin da ya haura sama,sannan kayan matan da na ɗirka miki fa kin zata kyauta ne?”
“Hajiya ɗan tsumin ma sai na biya?”
Hajiya ta kece da dariya ta ce “tun da nake da ke na taɓa baki maganin mata? Ina ce dai ke kike saya da kuɗin ki, wannan ma da na baki cikin na Meelat ne jiya Alhaji ya bada kuɗi na gangamo mata su ”
“Ai kam su na da kyau sosai ni kaina abun ya min daɗi ba kamar kullum ba”
“Hhh! Kayan Sokoto kenan,ita kanta Meelat ɗin ba ta fara aiki da su ba yau na aiki direba ya ɗauko min su tashar mota”

Na'ilah ta ce “don Allah Hajiya ki ɗan ƙulla min a leda yau ma ina son fita,ga 5k ki haɗa da 2k ɗin farko”
Hajiya Momah ta karɓe kuɗin ta ce “sai dai na baki lambar Hajiya Fatimah mai gyaran aure can ki saya,kayanta ba su da tsada ga kuma biyan buƙata(duk mai son ingantattun kayan mata masu kyau irin ƴan Sokoto sai ya tuntuɓe ta ga lambar nan +234 816 788 8934)”

Na'ilah ta yi godiya suka rakayo falo.

“Meelat ina kuma za ki je ?”
Har na kai bakin ƙofa na ji muryar Hajiya Momah ,na bata amsa da “gida zan je mana”
“Hajiya ita ce Meelat ɗin?” budurwar nan na ji ta tambaya.
“Eh ita ce! Meelat ga Na'ilah nan ko za ku yi ƙawance ne?” Hajiya ta faɗa ta na wata ƴar dariya wacce ta saka na yi zargin ko gulmata suka yi.
“Bani lambar wayar ki” cewar Na'ilah.
“Banda da ita” na bata amsa don ban ga dalilin da zai sa na ƙula ƙawance da ita ba.
Fita ta yi yayin da Hajiya kuma ta ɗauko min wasu garin magani kala biyu ta bani wai na rinƙa sha in ina gida.Duk da ban fahimceta ba haka na karɓe na saka a jaka,kafin na fice na bar Alhaji Nera nan.

Ina isa gida Hajiya Turai ta tarbe ni da fara'a,ledar kayan na zube ta shiga dubawa sai ta ce “uwannan ai sai dai na aje miki su har auren ki ya tashi” ta kwashe kayan baccin ta bar min pant da bra da turare” mi zan ce baya ga dariyar yaƙe,ina ji ina gani Hajiya ta kwashe kayan ta kai su can ɗakinta.

Nawa ɗakin na wuce,na haye katifa tare da kunna data.Hotunan Sadiq na fara cin karo da su,babu laifi duk sun yi kyau.Na yaba bisanin ni ma na tura masa nawa,aka yi katari shi ma ya na online .
“Jamee wai don Allah ina son na tambaye ki ina kika samu Android ?”
“Saya na yi” na  basa amsa .
“Ina kika samu kuɗin? Ko kin sayar da Akuyar taki?” ya tambaya cikin zolaya don na taɓa faɗa masa ina kiyon Akuya.
Na yi ƴar dariya ina mai ce masa “ka ji ka da wani zance,babbar waya ce fa ta kai 80k” ya wani waro ido ya ce “sabuwa ce ma kenan?”
Kwalin wayar na ɗauka hoto na tura masa,maimakon ya yaba sai ma kirana yayi.

Na ɗaga sai dai yadda ya jero min tambayoyi ya saka na yi zuciya na kashe kiran,ya na ta maido wani amma na ƙi ɗaga wa sai kuma ya koma turo min saƙo.
Da na ga zai dame ni sai ma na fice zuwa falo na shiga kallo nan na ɓata lokacina,sallah ma a nan nake yi har aka kira magrib.

Ɗaki na koma na yi wanka sannan  na yi sallah,ina nan kan sallaya na ji muryar Alhaji Nera.Ban san mi yasa ba haka kawai na ji ina ra'ayin yin kwalliya sai dai banda kayan.Wayata na ɗauka na yi masa text na sannu da dawowa,an ɗauki lokaci kafin ya maido min da yawwa my Baby.

Sai da aka yi isha'i sannan na fita falo,kamar kullum a zaune na tarar da su suna cin abinci a plate guda.
Hajiya ta ce “ga abincin ki can a kan table”
A ladabce na amsa bisanin na je na zauna,ina cin abinci sai ga saƙon Raheela ya shigo min ta WhatsApp.

Labarin da ta bani ya saka abincin fice min a rai,ita kuwa cike da murna take ta aiko min ɗan ƙaramin akwatin da aka kawo wai na baikon ta da Hafiz .
Ko ganin ban ce komai ba ne ya saka ta kira ni oho! Ɗaga dai kiran na yi.
“Jameela wlh kamar da wasa iyayen Hafiz sun zo an kawo kuɗin tambayar aure,nan da wata uku za a kawo lefe”
“Raheela wai ki na nufin aure za ki yi ki bar ni ? To karatun fa?” na tambayeta muryata na ɗan rawa.
“Zan ida can gidansa,ashe iyayen Hafiz kuɗi ne da su kin ga motar da suka zo da ita? Hafiz ɗin ma ya min da zarar an koma makaranta da ita zai dinga zuwa sannan zai koya min”
“Ni ma zan koyi motar in sha Allah ” na faɗa cike da jin haushi.
Ta yi dariya ta ce “ba dai da motarmu ba”
“Au! Har ta zama taku? To yayi masu mota” na faɗa ina mai yanke kiran kai kace ni na kirata.

Cike da baƙin ciki na koma ɗaki,ina nan kwance har dare yayi sosai.Kiran Alhaji Nera ya shigo,shaf na manta ban kashe data ba.Video call ne ya turo,dakyar na ɗaga ina ɗan ware idona da nake jin su na yi min ƙaiƙayi.
“Baby ya haka har yanzu ba ki shirya cikin kayan baccin ba?” Alhaji ya faɗa .
“Su na wurin Hajiya ta karɓe,wai za ta aje min sai na yi aure” na basa amsa.Cikin masifa ya ce “iskancin banza! Uban waye ya ce mata ki na buƙatar ta ajiye miki?” sai kuma ya kashe kiran.

Hotunan Sadiq na shiga duba wa,ina ayyana wa a raina ina ma ace shi ne ke da kuɗin Alhaji Nera? Da na ji daɗi.Ina cikin wannan zullumin bacci ya ɗauke ni.

Alhaji Nera kuwa sosai ya ji takaicin abin da Hajiya Turai ta yi masa.Hakan ya saka ya fita zuwa ɗakinta,a kwance ya tarar da ita kan bed ta na latsa waya.
Kayan baccin da ta saka ya bi da kallo sosai suka karɓeta ,amma kasancewar ba ta da lafiya bai kai tunaninsa ba nesa.

“Alhajina!” ta furta ta na mai tashi zaune.
“Hajiyata mai abun ikon Allah!” ya faɗa ya na mai ɗan sakin murmushi.
“Ah Alhaji ya haka kuma kake abu kamar wani yaro?” ta faɗa ta na janye hannunsa da ya ɗora a ƙirjinta.
“Kusan shekara uku kenan ba mu haɗa shimfiɗa ba,kin ce min ba ki lafiya amma har yanzu ban taɓa gani kin nemi magani ba” Alhajin ya faɗa ya na mata kallon ƙasa-ƙasa.

‘Ina zan yarda da kai ,garin neman matanka ka kwaso cuta ka ƙaƙaba min’ Hajiya ta faɗa a zuci,a zahiri kuma cewa ta yi “wlh Alhaji ko ruwan zan kama ba na iya saka hannu na wanke wurin saboda yadda ƙuraje suka addabe ni,har sabulun infection fa na saye ka ga shi can a ajiye”
“To Allah kyau! Ni bari na koma daga ciki,ina son yin kallo” ya faɗa ya na baza ido nan kuwa yayi arba da ledar kayan Meelat.
“Ki zo ki rufe ƙofa” da “to” ta amsa masa shi kuma ya fice.

Ɗakin Meelat ya wuce kai tsaye,dama ba wani key take sawa ƙofar ba.Ya tura ya shigo,can ya hangeta ta na bacci.Sai da ya ƙare mata kallo da kyau sannan ya ƙarasa ya zare wayar da ke hannunta.

Firgigit na tashi jin ana taɓa ni,ina buɗe ido na yi tozali da Alhaji Nera.
“Lafiya mi kuma ka zo yi ɗakina?” na tambaye shi ina mai jingina ga bango.
“Baby ina buƙatar ki ne,a nan za mu yi ko mu je ɗakina ?”
Na waro ido na ce “alhaji cikin gidan ka fa mu ke! Gaskiya ba zan iya ba ”

“Za ki iya kuwa! Gobe fa nake son kai ki wurin koyon mota shi ne ba za ki faranta min rai ba?” Alhaji Nera ya faɗa ya na shafar kumatuna.
Na washe baki na ce “da gaske Alhaji? Kar fa ace wasa kake min”
Bai bani amsa ba sai romance ɗina da ya fara,bisanin ya zarce zuwa mai kankat.
Ya na gamawa ya ficewar shi,ni kuma na shiga toilet na tsarkake jikina.

Washegari kuwa Alhaji Nera ya biya min kuɗin koyon mota,ƙaryar zan je karatu can makarantarmu na yi wa Hajiya .A haka har na ida kwanaki takwas ɗin da muke hutu a koyon mota,babu laifi na ɗan iya amma ba sosai ba.

Yau ta kama Monday,ranar da za mu koma makaranta.Cikin abaya blue na shirya tsaf na maida gashin kaina a tsakiya na ɗaure sannan na jawo wani a gefen goshina.
Ƙarfe shidda cicif na fito,motar nan wacce aka biyan 100 ta ƴan makaranta na je na yi tsaye ina jira har ta zo na shiga.

Ina zuwa makaranta direct aji na nufa,saɓanin da can baya da nake zuwa wurin Raheela.Tun ranar da ta sanar da ni zancen aurenta ba mu yi wata hirar da ita ba.
Ina nan zaune sai ga ta kuwa ta shigo,yadda ta yi wani turus shaye da mamakin ganin canjin da na samu ya sa sakar mata murmushi nace “amarsu ta ango!”
“Wai ke ce? Kin ga yadda kika yi kyau?”
Shigowar Hafiz da Sadiq yasa hirarmu ta gimtse.Su ma da ɗan mamaki suke kallona kamar sauran ƴan ajin,Hafiz ne ya gayyace mu zuwa waje inda ya parker mota.....

Only 300 via 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank,DM +22795045822
[02/09 à 09:34] MRS SADAUKI 💫: 🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
*FARASHIN TASIRI*🪺
        ```celebrity```🌬️
         🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
     *Gajeren labari*🕊️

MRS SADAUKI 💫✍️

FCWA ☀️

Special gift fo my VIA FANS 🪷

My book is only 300 via 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank,sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822. Ko kuma katin MTN,ƴan Nijar kuma carte airtel ta 300f

Page 7

Ni da Raheela mu ka zauna a baya,yayin da Hafiz ke tuƙi Sadiq na gefensa.
A ranar na ga ikon Allah yadda Raheela ke nuna min ƙiri-ƙiri motar saurayinta ce,sai wani shagwaɓe masa take ta na ƙirƙiro wasu sabbin abubuwa da ban santa da su ba.Amma na ajiye wannan a ma'adanar sirrina akan ƙila don an yi masu baiko ne.
Sadiq kuwa sai satar kallona yake ta madubi,ni kuma na share na yi kamar ban ganinsa.

Wayata na ciro na fara dube-dube ,ni ce WhatsApp ni ce cikin Gallerie.Raheela ta ce “wayar na da kyau sosai nawa kika saye ta?”
“Saya min aka yi fa” na bata amsa.
“Wa fa?”
“Alhajinmu” da yake haka nake kiran Alhaji Nera tun can asali.
“Ko son ki yake? Amma ai na ga bai haihuwa”
“Haihuwa ai ta Allah ce!” na faɗa ina mai ɗagowa na maido hankalina gare ta.

“Haka ne kam! Amma ke ki na son shi?” Raheela ta sake jefo min tambayar.
“Ina dai son kuɗin shi amma mi zan yi da tsoho?”
Daidai nan Hafiz yayi parking a Bouzou City ,duk mu ka fito.
Ciki mu ka shiga Hafiz ya saya wa kowa biscuits da cake duka kuɗin dai ba za su wuce 10k ba amma Raheela sai wani ɗagawa take.Na ji haushi sosai wannan ya saka na ƙudirci aniyar sai na shayar da ita mamaki tun yau ba sai gobe ba.

Mu na tsaka da tafiya na cewa Hafiz “don Allah ka biya da ni wurin Madugu mai Kaji yunwa nake ji zan karɓa ”
Da farko shiru yayi bai ce komai ba sai kuma ya juyo ya na kallona,idonsa ya sauka kan jakar kuɗina da zuge shagu ƴaƴan banki jere ras.
Dama ba wani nisa ke da kwai ba,haka Hafiz ya canza akalar mota ya na mai cewa “Jameela hutun nan da aka je ya mayar da ke ƴar gayu sosai,bayan canjin launin fata da kika samu wato har sabuwa bariki kika tsiro ta cin Kaji?” cikin raha yayi maganar hakan yasa ban jin zafi ba.

“A'a gyara sunan Meelat! Yaushe rabon wata Jameela! Wlh kuwa ka san an ce dare ɗaya Allah ya kan yi Bature ! Ni da kaza wani irin ƙawance mu ka ƙulla” na yi maganar ina dariya tare da satar kallon Raheela ta gefen ido .Yanayin fuskarta duk ya canza ,baƙin ciki ya hana ta cewa komai har mu ka isa.
“In babu damuwa za mu iya fita mu ci abincin sai mu dawo,na ɗauki nauyi” na faɗa,a cikinsu Sadiq ne kawai bai ga kuɗin Meelat ba lokacin da ta ce ta na son kaza sai da ya ji kamar zuciyarsa ta kama da wuta don takaici.Tun da dai ya san shi bai da ko ƙwandala ta saya mata ,dole dai Hafiz zai biya.
Yanzu kuma da ya ji banzar furincinta ya saka shi saurin juyowa.
Ido huɗu mu ka yi da Sadiq da yake min wani kallo da ban fahimci mi yake nufi ba,fita na yi daga motar don tuni Raheela ta fita ita da Hafiz .
Sadiq shi ma ya fito,mu na shiga ciki masu kula da wurin suka fara gaishe ni saboda a yawon da nake na koyon mota mu na haɗewa da Alhaji Nera a nan.

“Babyn Alhaji ina kwana! Mi za a kawo maku?”
Cike da kuri da yanga na faɗa masa ya haɗa mana couscous da kaza plate huɗu da kuma ruwa masu sanyi na cikin bidon.

Wuri mu ka samu mu ka zauna,ko wanensu yayi shiru kamar ruwa sun ci shi har abincinmu ya iso.
Ni da Hafiz kawai ke cin abincin nan cikin jin daɗi da walwala,saɓanin Raheela da Sadiq da ko wane nake zargin abin da ya hana shi sakin jiki.Ita dai baƙin ciki ne da kuma ba ta yi zaton haka ba,shi kuwa Sadiq ina tunanin kishi ne da kuma tambayar ina na samu kuɗi.

Bayan mun gama na zaro kuɗi na biya kusan 30k don ƙarfin hali da za a ban canjin da yayi saura ce masa na yi ya riƙe.
Hankali kwance na shiga mota na zauna sai ma lumshe ido da nake zuciyata fari tasss.Wannan karon babu mai magana a motar har mu ka isa makaranta.
Ina shirin shiga aji Sadiq ya fizgo ni na yo baya,kamar wata ɗiyarsa haka ya ja hannuna zuwa gefe.“Jameela mene ne haka? Irin wannan uban kuɗin da kika kashe ai sai ki sa a fara zargin ki. Ina kika same su? Ko aiken ki aka yi ?”
Na fizge hannuna na ce “mene haka Sadiq ? ”
“Yi haƙuri raina ne a ɓace ban yi hakan da niyyar kaina ba”
“Daga yau kar ka sake riƙe min hannu,dubi yadda ake kallonmu” na faɗa ina mai barinsa nan a tsaye na shige aji.

Kusa da Raheela na zauna wacce ta game ban da can.Ni ma na shareta ina mai duba saƙon Alhaji da ya shigo min,na saki murmushi tare da kiransa.Buga guda ya ɗaga, “da gaske Alhaji har ka buɗe min account?” na tambaye shi saboda tun jiya na yi masa ƙorafin riƙe kuɗi a hannuna Hajiya za ta iya shiga ɗakina ta yi bincike.
“Eh tun tuni,yanzu haka na saka miki kuɗi ma a ciki”
“Ok to babu damuwa yau in na fita koyon mota sai na biya Bank na ajiye na ga hannuna”
“Ok babu damuwa amma kafin nan ina son mu je hotel mu ɗan huta”
“Ok babu damuwa,yanzu dai ina cikin aji na ga ɗalibai sun fara shigowa ƙila malamin da zai mana darasi ya tawo” na faɗa tare da yi masa sallama farin ciki fal raina.

Ina ajiye waya kuwa malam ya shigo,darasinsa ya fara kamar kullum yau ma ina ta bada amsoshin tambayoyi.Canjin da na samu hatta malumaina sun fahimci haka don wasu su na nuna mamaki a fuska wasunsu kuma har tambayata suke.

Bayan mun gama ko wane darasi na fito ina daddana waya,muryar Raheela na ji a bayana “yanzu sai gida?” na juyo na dubeta,sarai na san abin da take son sani saboda lokacin da na ajiye waya malam ya shigo babu damar ta tambaye ni shine yanzu ta biyo ni.

Na ɗan rausayar da kai cikin kurin magana da salon da Hajiya Momah ke koyar da ni nace “zan je restaurant na ci abinci sai na wuce inda ake koya min mota”
“Allah taimaka” ta faɗa tare da yin gaba.Sosai na ci dariya yadda Raheela ta nuna min ta ji haushi babu ko ɓoye wa.

SADIQ

Sam ruhinsa ya ƙi samun salama,hankalinsa duk ya tashi.Ya na son Jameela sosai ta yadda ya kasa ɓoyewa mahaifiyarsa ita.Su na tafe cikin motar Hafiz amma sai jan tsuki yake shi ɗaya.
“Abokina haƙuri za ka yi tun da dai ba ka kai kuɗin aurenta ba,sannan yadda ta waye ɗin nan Allah sai ta ƙara kyau ai farin ciki ya kamata ka yi” Hafiz ya faɗa ya na riƙe da sitiyarin mota.

“Murna? Ni wlh na fi son ta yi zamanta a ƴar ƙauye zai fin min nutsuwa.Ka na dai ganin uban kuɗin da ta kashe mana ko a kwalar rigarta,kuma inda ka ga wayar hannunta Galaxy ce ”

“Hhh! Kishi dai kake! Amma fa alamu sun nuna kamar soyayya take da wani Alhaji ,tun da na ji ma'aikacin gidan abincin nan ya na kiranta da Babyn Alhaji”

“Hafiz kar ka sa zuciyata ta buga don Allah,ya isa haka ta je ta yi ta soyayya da shi ɗin.In ya na da kuɗi ni kuma ina da Allah zan ta kai kukana wurinsa har ya bani ita”

“Wai har haka kake son Meelat?”
“Fiye da yadda kake tunani,wlh yanzu haka ji nake kamar zan kama da wuta”
“Ka zage dantse wurin ganin ka samu soyayyarta fiye da shi wancan ɗin” Hafiz ya faɗa daidai nan ya kawo ƙofar gidansu Sadiq da yake nan unguwar Maraɗawa.
“Na gode abokina sai an jima” Sadiq ya faɗa tare da fita.
Ya na shiga cikin gida ko sallama babu ya shige cikin ɗakinsa.
Da sauri Mama ta biyo bayansa ta na tambayarsa lafiya amma ya ƙi faɗa sai ce mata yayi “ba komai Mama ”
“Ƙarya kake yanayin ka ya canza! Ba haka ka saba shigowa gida ba.Dole da wani abu,ka faɗa min ka ji”
Duk yadda ya so ya ɓoye wa Mama kasawa yayi saboda a soyayyar Jameela shi ɗin mai rauni ne kawai sai ya fashe da kuka ya ce “Mama Jamee ce...” sai kuma ya kasa ida maganar.

“Cewa ta yi ba ta son ka ko? Irin wannan nacin da kake yi mata ai dole ta faɗa.Yo ayi mutum babu jan aji kullum cikin amayar da abin da ke cikinka kake”

“Mama ba fa haka ba ne,soyayya take da wani”
Mama ta shiga taɓa hannuwa ta ce “shine kuma kake kuka maimakon ka yi tunanin hanyar da za ka raba ta da shi? To Allah kyauta!” ta na gama faɗa ta fice.

Sadiq yayi zaune kan yamutsatsar katifar shi ya rabka uban tagumi ya na tunanin mafita.

MEELAT

Taxi na ɗauka na tafi can auto-école,cike da girmamawa aka tarbe ni bisanin mu shiga motar da ake koya min da ita.Sai da mu ka hau titi sannan ya bani,ban sani ba ko don ina son mota ne sosai ya saka na yi saurin iyawa oho.

“Masha Allah ki na kula da komai yadda ya kamata, Allah dai ya nuna mana ranar da za a baki lasisin ki” cewar wanda yake koyar da ni.
“Amen na gode sosai”

Sai da mu ka yi yawo sosai sannan na wuce hotel ɗin da Alhaji Nera ke zaman jirana.
Tuni an tanadar min abinci,ya na ƙoƙarin taɓa ni na dakatar da shi saboda ina buƙatar yin wanka.
“Ki fara da abincin Baby sai ki yi wankan” cewar Alhaji Nera.

Na buɗe abincin,ƙamshi ya bugi hancina idona sun rufe da zalama sam ban lura da garin maganin da aka barbaɗe abincin ba.Ina gamawa na shiga na yi wanka,ko da na fito tuni Alhaji Nera ya shirya,ya na kwance kan bed babu kaya.
Na ɗan harare shi nace “wai don Allah wannan tumbin naka ba ka iya sha masa magani ya baje?”
“Don Allah Baby ki bar maganar tumbin nan,ki zo ki kula da ni” yayi maganar ya na jawo ni.
Bayan mun sheƙe ayarmu na kwanta luf ina lumshe ido,yau kwana goma sha ɗaya cicif da na shiga sabuwar rayuwar da nake jin daɗinta zuwa yanzu.
Na yi fari na yi kyau,shap ɗina ya ƙara buɗe wa ya fito da kyau.
Dogon hancina Alhaji Nera ya ja ya ce “my Meelat ƴar fullo”
Na yi murmushi kawai,“ya Sadiq ɗin ko shine ake tunani?”
Na ɗan yamutsa fuska nace “don Allah daga yau ban so ka na min zancen shi”
“Ok babu damuwa gimbiya,in kin tashi tafiya ga kayan baccinki nan na sayo”
Da ƴar murna ta na tashi ina cewa “Ah! Ah! Yau Allah yayi nufi kenan?”
Ya washe baki ya na miƙo min ledar na fara dubawa,“sun yi kyau amma dai wanda Hajiya Turai ta ɓoye sun fi kyau sosai”
“Zan bincikosu su ma,don Allah yau ki saka wannan ina son ki kwana a ƙirjina” ya faɗa ya na nuna min wasu farare.
“A'a in fa Hajiya ta shigo ɗakina ta gan ka? Na faɗa ma haka kawai cikin dare sai na ga ta faɗo min”
“A ɗakina za ki kwana,in za ki zo sai yi kuna pampon toilet ki yi wa ƙofar key kin ga ko ta shigo za ta yi zaton ki na ciki ne”
Na dube shi da kyau na ce “wai Alhaji ina kake samo irin wannan dabarun?”
Dariyarsu yayi irin tasu ƴan duniya ya ce “ke dai tashi ki yi wanka na kai ki gida”
Haka kuwa aka yi,bayan duk mun yi wanka mu ka kimtsa sannan mu ka fito Alhaji ya kai ni bank na ajiye kuɗina,sai kuma ya sauke ni a ƙofar gida.

Kiciɓis mu ka yi ni da ƙawar Hajiya Turai,ban kawo komai a rai ba na gaisheta kafin na wuce.
Mabaruka ta na fitowa ta ga Alhaji Nera a zaune,ga kuma Meelat ta shiga gida nan zargin kar dai ace tare suke ya sakata yi wa Hajiya Turai voice lokacin da ta isa gida.

Ina shiga na gaishe da Hajiya ta ce ga abincina nan nace mata a ƙoshe nake bisanin na shige ɗaki na yi ta baccin wahala.Wuraren sallar la'asar na farka,Hajiya Turai na gani ta na ta bincikar min akwatin kayana.
“Ina wuni Hajiya ?”
Da sauri ta juyo ba ta yi tsammanin zan tashi ba.“Jameela kin tashi? Nace halan a ƙafa kika dawo kike wannan mugun baccin?”

Zama da maɗaukin kanwa shi ke sa farin kai.Kasancewar ina tare da Hajiya Momah da kuma su Rumy tuni na halbo jirgin wato Hajiya zargina take.
Sai kuwa na ce mata “Wlh kuwa Hajiya ,halan Alhajinmu ya sanar da ke ya ɗauko ni, lokacin har na ma kusa kawowa gida.Yayi faɗa sosai ya ce miyasa ban tambaye ki kuɗin taxi ba ai ba za ki hana min ba,ni kuma wlh Hajiya kunya nake ji yadda kuke ta ɗawainiya ina laifin ciyar da ni da kuke hakan ma alkhairi ne.”
“Amma kuma shi alhajin bai ma shigo ba,to wai ina saurayin ki ba kin ce makarantar ku ɗaya ba?”
Na yi saurin dirowa daga kan katifa na ce “yawwa don Allah Hajiya ina neman alfarmar ki roƙa min Alhaji kan Sadiq ya dinga zuwa zance”
Hajiya ta washe baki ta ce “ke babu damuwa kawai kar ki damu” sai kuma ta fice,na bi bayanta da harara ,na ɗauki waya na shaidawa Alhaji komai kafin na shiga toilet.

HAJIYA TURAI

Ta na fita daga ɗakin Meelat ta kira ƙawarta Mabaruka,“ina ga babu komai a tsakanin su kawai ya sauketa ne kawai yayi”
“Ki dai ci gaba da kulawa kamar yadda kika ce ɗin,amma yadda baƙauyar yarinyar nan ta yi mugun canzawa da wuya in ba ta san maza ba”
“Zan kula,kin ga sai an jima bari na kira alhajin na ji shi mi zai ce” ta na gama faɗar haka ta kashe ta kira Alhaji .
Kamar yadda Meelat ta shaida mata shi ma haka ya ce a ƙarshe kuma ya fake da yi mata faɗan mi yasa take barin Meelat babu kuɗi ko ta manta ita ɗin amanarsu ce.
Hankalin Hajiya Turai sai ya ɗan kwanta ta basar.
Sai da na gama sallah sannan na fito falo riƙe da takardun karatu ina dubawa yayin da kuma Hajiya ta wuce kitchen.
Ina cin abinci na miƙe na cewa Hajiya sai da safe gobe zan zana jarabawa ina son yin karatu sosai.

Babu laifi sai wuraren sha ɗaya na tsaya da karatun da nake don wayata ma kasheta na yi.Wanka na shiga bayan na fito na shafe jikina da mai,sannan garin da Hajiya Momah ta ban na ɗauko shi na zuba madara na sha .Ina kunna waya Alhaji Nera ya kira ni,hira sosai mu ka yi ta tayar da hankali don har video call ya min ya na nuna min kansa.
Kayan baccin na saka farare sannan ɗora dogon hijabi a sama,na kunna pampo na ƙage ƙofar kafin na fita zuwa ɗakin Alhaji .

Hajiya Turai kuwa sam ta kasa bacci,tunaninta na kan Meelat hakan ya sa ta fito .Jin tsit babu muryar Meelat wacce ta yi ta ɗaga wa ɗazu ta na karatu ya saka ta saurin isa ɗakin. Wayam babu kowa kan katifa sai tarin takardu da kuma ƴar ƙaramar waya,Hajiya ta ƙara sa ta ɗauki wayar ta na mai kallon toilet da take jin motsin ruwa.Fitowa ta yi har za ta shiga ɗakinta sai kuma tace bari ta dubo Alhaji Nera.......

Mu haɗe💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
My book is only 300  3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank,sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
[03/09 à 08:33] MRS SADAUKI 💫: 🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
*FARASHIN TASIRI*🪺
        ```celebrity```🌬️
         🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
     *Gajeren labari*🕊️

MRS SADAUKI 💫✍️

FCWA ☀️

Special gift fo my VIA FANS 🪷

My book is only 300 via 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank,sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822. Ko kuma katin MTN,ƴan Nijar kuma carte airtel ta 300f

*Last Free page 8*

“Tok! Tok! Tok”

Na yi saurin tashi daga kan ƙirjin Alhaji Nera ina mai duba ƙofar wacce zuwa yanzu an dakata.
“Ka ga abin da nake guje wa ko? Hajiya ce fa ke buga ƙofa ” na faɗa ina mai jawo kayan baccina zan maida Alhaji yayi saurin riƙe ni ya na mai cewa “ƙofar a rufe take ba za ta shigo ba,kuma ma fa ke ce ke damun kan ki Hajiya ba ta da matsala ta sani sarai ina harakar mata”

Idonsa na kalla ko kunya ba ya ji,shi fasiƙancin ma ado yake da shi.
Jawo ni yayi ya ci gaba da cewa “kin ga har ta yi tafiyarta ko? Zo Baby ki saki jikin ki”
Ba wai tsoron Hajiya nake ba,a'a kawai ban so ace ta tarar da ni da mijinta cikin wannan halin shi yasa na ƙara zillewa.
Nan na ga fushin Alhaji Nera ƙarara ya na cewa “wlh in ki na tsiyar zan iya buɗe ƙofar nan ta gan ki kin ga shikenan sai mu bar ɓoyon nan”
Fahimtar ƙaramin aikinsa ne ya saka na yarda mu ka ci gaba da masha'a.
Bayan komai ya kwana na mayar da kayana,a gabana Alhaji ya jawo system ya na duba Camera da ya saita a falo,sai kuma ya shiga ta ɓangaren Hajiya Turai ta na kwance kan bed ta na sharara bacci.

Na dube shi da mamaki,shi kuma ya ɗagan gira ya na cewa “kin zata haka nan kawai na ce ki fito ɗazu? Sai da na tabbatar ba ta falo ”
“Ka ce kuma ba ka tsoronta” na faɗa ina hararensa don wlh zuwa yanzu na yi mugun raina Alhaji .

Ya ɗan bugu kumatuna da yatsunsa biyu ya ce “ita ɗin matata ce,rigar mutumcina .Ta dalilinta ake min kallon mutumen kirki,nan da ace ban ajiyeta ba to ina mai tabbatar miki da tuni sunana ya ɓace a gari”

“Shi yasa kake zuwa hotel kenan? Can sunan naka ba zai ɓace ba kenan?” na tambaye shi ina mai tsure shi da ido.
“Yanzu dai wuce ki koma ɗakin ki,zan kira ki”
“Kiran mi za ka min kuma? ” bai ban amsa ba ya je ya buɗe min ƙofa na fice.

Ina komawa ɗaki na ɗaga katifa na ɗauko key na buɗe toilet.Tsarkake jikina na yi sannan na fito na kwanta,kamar yadda na yi tsammani Hajiya ta ɗauki wayata wacce babu ko layi a ciki,kwanciyata na yi ban ɗau lokaci ba kuwa bacci ya ɗauke ni.

Hajiya Turai

Dama kusan jefi-jefi ta na duba Alhaji don kar ya fahimci zaman kuɗi take ba wai don ta na son shi ba.Wayar Meelat ta bincike sai dai babu komai a ciki wannan ya saka ta yi kwancinta.Sai tsakar dare wuraren asubahi ta farka,wayar Meelat ta je ta mayar inda ta ɗauke ta.

Washegari

Kamar kullum tun safe na shirya tsaf cikin shiga mai kyau.Ƙaramar wayata na gani na ɗauka ina murmushi,zuwa yanzu na fahimci duk wacce ta ɗauki harakar duniyanci to ta na buƙatar abubuwa na dabaru.
Takardu na ɗauka tsaf na fito,kamar yadda na yi tsammani ta na kitchen.Na leƙa na gaisheta,ta miƙo min abinci  cikin kwano mai kyau ta na mai cewa “ga shi ki tafi da shi tun da ba ki iya jira”
Na sunne kai na ce “eh saboda kar mota ta bar ni ne”
“Oh! Na manta bari na ɗauko miki ko da 1k ne” cewar Hajiya kafin ta fice daga kitchen ɗin.

Hajiya na shiga ɗaki ta ɗauki kuɗi bisanin ta fito.
“Jameela ga wannan ki hau mota sauran ki ci abinci” na karɓa tare da yin godiya na fita.
Maimakon na tsaya jira Bus kamar kullum kawai sai na samu kaina da tafiyar ƙasa,ina tafe ina tunani a bayana na ji Horne.
Na tsaya tare da ɗan juyowa,a hankali aka sauke glass ɗin idona yayi tozali da wani matashi a ƙalla zai haura shekara arba'in a duniya.

“Hajiya an tashi lafiya?” ya furta cikin muryasa mai shegen daɗi.
“Alhamdullah” na amsa ina wasa da ido.
“Sai ina?” ya tambaya ya na kallon takardun hannuna,na masa wani kallo kafin na ce “suyar awara”
Ban sani ba ko ya fahimci baƙar magana ce ba,sai ya ƙyalƙyace da dariya ya ce “ai kuwa fatar jikinki ba ta yi kama da mai raɓar wuta ba ,ta fi dacewa da masu zama ƙasan ac.Am...in ba damuwa ki shigo na ajiye ki mana”
Sai da na ɗan yi jim bisanin na je na shiga,“sunana Bashir Sudan,Kano-kano nake zuwa ina da mata ɗaya da yara biyu fatan ban miki tsufa ba?”

“Daga rage min hanya sai nace ka yi min tsufa?” na faɗa tare da basarwa na yi kamar ban fahimce shi ba.
“Mi sunan ki?”
“Meelat!”
“Wato Meelat tuntuɓe na yi da sonki ƙaunarki kuma ta min dabaibaye tun a kallon farko”
“Allah sarki” na faɗa ina ƙare masa kallo,fari ne tass ya na da ƴar ƙiba ga saje da jan leɓo sai na ji ina sha'awar sumbatar su.

“Don Allah ki taimaka ki amince min”
Na saki makirin murmushina wanda na koya gun Momah tare da ƙanƙance ido ina tara wasu ƙwalla na ɗauke hankali,na karyar da wuya na ce “Allah shige mana gaba”
Cikin jin daɗi Bashir ya karɓi lambar wayata,sai a lokacin na sanar da shi kuma University zan je.

Daidai ƙofar makarantar ya ajiye ni tare da fiddo dumbujen kuɗi ya zaro min 20k ras,ko irin ɗan jan ajin nan ban yi ba na karɓe shegu.Ina ƙoƙarin fita ya ce “mi zan sayo miki matsayin tsaraba,sannan please ina son zuwa gidan ku tun yau”

Kalmar zai zo gidanmu ya saka ni jin wani mugun daɗi,nan na yi masa kwatance cewa Zariya ta uku nake.
“Abin da zan sayo miki fa?”
“Duk abin da ka sayo Meelat na son shi” na faɗa ina murmushi.
“Don Allah turo min hoton ki kafin ki tafi”
“Bari na tura ma ta WhatsApp kawai tun da ka ban lambar ka” na faɗa tare da kunna data,ban tafi ba sai da na tura masa hotuna.

Ina shiga ciki na zame ɗakin Raheela inda take kwana.A kwance na tarar da ita ta yi wanka ta shirya ta na duba takardu .
“Jameela babu ko sallama?” ta faɗa tare da tashi zaune,cike da murna na zauna kusa da ita ina cewa “Heelat na yi babban kamu yanzun nan bisa hanyata ta zuwa makaranta na haɗu da wani kyakkyawan saurayi fari mai saje”
“Shine sai ki shigo babu sallama?”
Na tamke fuska na ce “ke fa matsalata da ke kenan! To maganar sallama ba ta wuce ba,in ba ki ji daɗin ganina ne ba sai na fita na bar miki ɗakin ki”  na faɗa cikin fushi.

“Allah baki haƙuri ina son dai sanar da ke ne muhimmancin sallama” Raheela ta sake faɗa.
“To sai ki yi ai !” na faɗa tare da fara danna waya sai na ga Bashir shi ma ya turo min hotunan shi.
“Masha Allah! Kyakkyawa kuwa da shi amma Jameela wannan kamar ya na da mata” Raheela ta faɗa.
“Ina ruwana da matar shi tun da ba auren shi ba zan yi! ”
“Jameela...” na yi saurin katse “Meelat za ki ce ban son sunan Jameelar nan”

Sai da Raheela ta yi dariya sannan ta ce “sunan kuwa na ƴan gayu! Amma don Allah da gaske ba auren shi za ki yi ba?”
“Kuɗinsa kawai zan ci.Heelat dubi laɓansa uwannan sai sun yi daɗin sumbata” na faɗa ina cije leɓena na ƙasa.

“Kin ce ba auren shi ba za ki kuma ki na zancen sumbata”

“Au! Aure kawai yake sa a sumbaci mutum Heelat?”
“Wai ni ce Heelat ɗin?”
“Eh ko bai yi daɗi ba?”
“Yayi sosai ma.Mu tashi mu tafi ko ƙarfe bakwai har da minti ashirin ” ta faɗa ta na kallon agogon wayarta.

“Ina wacce kuke kwana ɗaki guda?” na tambaya.
“Ta fita tun ɗazu wai motsa jiki”
Na miƙe ina cewa “ba ta son ta yi ƙiba ne halan?”
Ba ta ban amsa ba har mu ka fito ta rufe ɗakin,mu ka nufi ɓangaren da ake karatu.

Duk ko wane ɗalibi sai duba takardu ake,mu kam zama mu ka yi ina ta baiwa Raheela labarin Alhaji Nera yadda yake kashe min kuɗi amma ban sanar da ita ya na nemana ba.Mu na nan zaune sai ga Sadiq da Hafiz ,ko wane facing budurwar shi ya zauna kafin mu fara taɓa hirar da su.

Shigowar malamarmu ya sa kowa ya nutsu,kamar yadda mu ka yi tsammani ita ma jarabawa ta rubuta mana ta na mai cewa “Ya kamata ku dage sosai ku ƙara hazaƙa don kun kusa tafiya stage za a kai ku asibitoci ku ga yadda aikin likita ke gudana”

Cike da murna na cewa Heelat “na matsu na saka farar rigar nan”
“Za ta yi miki kyau sosai,amma ai ba sai mun sa ba”

Malama ta ci gaba da cewa “ku yi shiru ku ci gaba da aikin gaban ku,in an tashi kowa sai ya nemi farar rigar likitocin ” sai kuma ta fara zagayen ajin.
Duk tambayoyin na san su hakan ya saka na riga kowa idawa na baiwa Madam na fice.
Alhaji Nera na yi text na shaida masa ina jin yunwa,ya kuwa ce na jira zai kawo min.An ɗauki kamar minti ashirin sannan ya zo,har cikin makaranta ya shigo na je na karɓo sannan na zauna kan dakalin nan mai kamar kujera da ake yi cikin makaranta.

Ina tsaka da cin frite da dunƙulalar kaza, Heelat ta fito.Zama ta yi mu ka ci gaba da ci,dai hirar jarabawar mu ke.
Bayan mun gama mu ka hauda da exotic,sai a lokacin na sanar da Heelat cewa Alhaji Nera ya kawo min.

“Ƙawata Alhajin nan na ji da ke gaskiya,to amma ya za ki yi da Bashir?”
“Kowa da matsayinsa” na bata amsa.
“To wa kika fi so?” dariya kawai na yi na ce “so? Tabbb ! Ba ki taɓa bani labarin soyayyar ki da Hafiz ba”
“To ai a gaban ki ake komai” cewar Heelat ta na mai fara duba wayarta sai kuma ta ci gaba da cewa “jarabawar ta yi wa Habibyna wuya bawan Allah ”
Ci kan ki ban ce mata ba na yi kamar ban ji ba,don na ga alamu irin rawar kan amare ce take son nuna min .
Bayan kowa ya fito sai kuma mu ka ci gaba da yin cours har lokacin tashi yayi .Yau ban je koyon mota ba direct gida na wuce,a falo na tarar da Hajiya ta na cin dambu,“Jameela har an sauko? Ina kwanon da na zuba miki abinci?”
Gabana ya faɗi don kuwa na manta shi a motar Bashir,ban sani ba yawan shirun da na yi ne ya saka ta ce “kar ki min ƙarya”
Hakan yasa kuwa na faɗa mata gaskiyar inda na manta shi sai na ƙara da cewa “ya ce zai zo yau ,in sha Allah zan ce ya biyo min da shi”
“Ya na da kuɗi sosai kenan?” Hajiya ta faɗa ta na washe baki,ganin haka ya sa na zauna ina ta bata labari har da kuɗin da ya ban.

“Ah to yanzu na ji zance! Shi wancan faƙirin yaron ki fita harakar shi,yo yaushe ya gama karatun har ya nemi aiki har ku yi auren” cewar Hajiya ta na mai ƙara ƙawata min auren mai kuɗi.
Da na gaji dai na je na yi wanka sannan na zo na ci abinci.



Da dare misalin ƙarfe tara Bashir ya zo.Ya samu kyakkyawar tarba gun Hajiya don har ciki ya shigo ya gaisheta bisanin mu koma can waje cikin motar shi.
“Ɗazu sai kika bar wa mijin ki abincin breakfast” ya faɗa ya na murmushi.
Na ce “Eh wlh manta wa na yi sai da na dawo gida sannan Hajiya ta tuna min”
“Abincin yayi daɗi ga kwanon nan na gode”

Nan mu ka fara yin hira sama-sama har motar Alhaji Nera ta zo ita ma.Duk da ya na dare akwai hasken ƙwan fitila,yadda yayi tsaye ya na kallonmu ya saka Bashir cewa “bari na fita na gaishe shi” bai jira cewa ta ba ya je ya gaishe da Alhaji ,shi ya shiga gida yayin da Bashir ya dawo.
“Gida zan shiga na ga dare ma ya soma yi” na faɗa zuciyata na ɗan dokawa.

“Daddyn ki na da tsanani halan? Allah sa dai kar ya min iyaka da ke” cewar Bashir kamar zai yi kuka.
“Kar ka damu” na faɗa tare da ɗaukar kwanon na buɗe mota.Bashir ya miƙo min wata leda na karɓa na shige gida.

“Sarai kin san yarinyar nan amana ce aka kawo mana shine za ki barinta fita zance to daga yau sai yau kar na sake ganin wani ɗan iska ya zo min gida” shine abin da kunnuwana suka jiye min tun kafin na shiga cikin ɗakin.
A falo na tsaya na sunne kai ina sauraren masifar da Alhaji ke yi wa Hajiya kafin ya dawo kaina,da ya gaji kuma ya shiga cikin ɗakinsa.
Hajiya Turai ta ce “kar ki wani damu! Yo jiƙa ki za mu yi mu sha! Kawo mu gani mene ne ya kawo miki ”
Ledar na miƙa mata ta buɗe,ɗinkuna ne na atamfa guda uku sai gizner wacce ba a ɗinka ba da kuma less.
“Masha Allah! Ki na ji yanzu in kin shiga ɗaki ki kira shi ki ce saura kuɗin ɗinki in ya bada sai na kai miki gun tela a yi miki ɗinkin ƴan gayu ”

Sosai na ji daɗin yadda Hajiya ta ɗaure min gindi,ina shiga ɗaki na gwada kayan duk sun yi min cicif sannan na ɗauki waya na ce masa saura kuɗin ɗinki ko? Kawai ya kira ni.
“Su sauran ba su yi miki ba ne?” ita ce tambayar da ya fara yi min.
“Sun yi mana sosai ma”
“Shine ba za ki iya yi min godiya ba? ”
Ji na yi kamar ya watsa min petur,cikin masifa na ce “ka zo ka karɓi kayan ka in ka bani ne don na dinga ƙasƙantar da kaina wurin ka....” sosai na yi ta masifa.
Bashir ya ce “Meelat? Meeeela!” sai kuma na yi tsit,yadda ya kira ni cikin salo na fizgar rai sai na ji wani abu ya caki ruhina.

Da kuma na tuna da huɗubar Hajiya Momah kawai sai na fashe da kuka ina jan majina.Ina jin yadda Bashir ke sauke ajiyar zuciya.
“Yi shiru mana my Meelat! Ban son kukan ki! Amma don Allah ina miki kyauta ki dinga cewa kin gode”
A shagwaɓe nace “na ƙi ɗin! Kuma wlh sai na cije ka tun da ka bari na yi kuka”
Ya saki murmushi mai sauti ya ce “oh! My shagwaɓaɓiya irin wannan ai sai ki sa na zauce na dawo gidan ban shirya ba”
Cak na tsaya da kukan sangartar na ce “wai gaske ka na sona sosai?”
“Fiye da tunani! Yanzu dai sai da safe zan shiga gida ki kula da kan ki”
Haka kawai na ji haushi,amma na danne na ce “kai za ka kai ni makaranta gobe”
“Ok babu damuwa,zan fito zuwa shidda da rabi hakan yayi”
“Eh sai da safe” ƙittt na kashe kiran.
Text ɗin Alhaji Nera ne ke ta shigowa,ni dariya ma ya ban yadda yake nuna kishinsa a kaina ƙarara.
Ciki da izgilanci na tura masa “Ni ka yi wa faɗa ko? To yau babu inda zan je sai dai ka rungume pilow”
Ina gama tura masa saƙon ko minti ɗaya ba ayi ba ya kira ni,na ɗaga.
“Wallahi! Wallahi in ba ki zo ba in na fasa fita yanzu na je na shaida wa Hajiya Turai ke karuwata ce Shege Kuluwa ta haife ni.Wato Meelat ba ki son zaman lafiya! Duk gama ni da Sadiq bai ishe ki ba sai kin rakito min wani farin buzu wanda ka na ganinsa ka ga jarababe ”
Na tuntsire da dariya na ce “au! Buzaye jarababu ne kenan? Hum! Alhaji ni ka kira da karuwa? ”
“Ki dai fara shirya wa yau tun ƙarfe goma nake son ganin ki a ɗakina ”
“Ba zan zo ba”
“Sai kin zo!”
“To sai na gani in dole za ka yi min”
Ina gama tura saƙon na kashe wayata na je na yi wanka,cikin kayan bacci na shirya tsaf na kwanta tare da rungume pilow na fara tunanin Bashir .
Na lumshe ido ina ayyana cewa shi ne na rungume,tarau na buɗe ido tuna ya na tare can da matar shi na ja tsuki a fili na ce “wlh ba zan so ka ba!” sai kuma na turo baki gaba ina jin haushi.
Cikin wannan tunanin bacci ɓarawo ya ɗauke ni,jin ana hura min iska a fuska ya sa na fara buɗe idona a hankali da Alhaji Nera na ci karo durƙushe a gabana,ina shirin tambayarsa lafiya kawai ya sukuce ni yayi waje da ni.

Ina kiciniyar direwa mu ka yi kiciɓis da Hajiya Turai wacce ta fito daga kitchen,ruwan da ke hannunta ta saki yayin da shi kuma Alhaji Nera ke gyara min zama a ƙirjinsa.
“Alhaji mi nake shirin gani?”
“Abin da idon ki ya gane miki ai ba baƙon ki ba ne” ya gama faɗa ya nufi ɗakinsa da ni,kunyar duniya ta ishe ni tuni na fara hawaye. A ranar na tabbatar idon Alhaji Nera a ƙyanƙyashe suke,na yi tunanin Hajiya Turai za ta tayar da hankali ta zo ta yi ta kishin ƙofa sai kuma na ji tsit.A ranar ɗakin Alhaji Nera na kwana,mun kashe arna fiye da tunani inda a ƙarshe yayi min alƙawarin zai canza min gida na koma can da zama .

Washegari
Bayan na yi wanka a ɗakin Alhaji na saka doguwar rigarsa na fito,ɗakina na shiga na shirya tsaf tare da haɗa duk wasu kayan jikina da takarduna kamar yadda Alhaji ya faɗa.
Bayan na gama komai na fice zuciyata duk babu daɗi,duk da Alhajin ya tabbatar min ita Hajiya ko a kwalar rigarta zaman ta ci mai kyau ta sha mai kyau ne take da shi ta kuma rufa wa kanta asiri .

Sai na zo bakin titi sannan na kunna wayata ,nan kiran Bashir ya shigo ya tabbatar min ya na hanya .Ko da ya zo na shiga motar,ban cikin yanayi mai daɗi Bashir kuma ya fahimci haka don ya na ta tambayata amma ban basa amsa ba kawai sai ya wuce da mu filin ƙwallo na Maraɗi yayi parking mota ya ce na fito.
“Mene ne wai? Kin shigo mota kamar kurma,ina tambayar ki kuma kin yi shiru!” ya faɗa ya mai jingina da mota.
Ido na zuba masa nan na ƙara yarda da mai kyau ne na ƙarshen lamba,an ce so ya na shiga a kallo ɗaya kamar shigar sarɗe to ni ma hakan ce ta faru da ni.Ban san ya zan yi ba kawai na faɗa jikin Bashir ina mai fashewa da matsanancin kuka......

#Mafarin ƙaddara Meelat da Bashir

Nan zan tsaya da page na kyauta wato free page,duk mai so za ta biya kuɗin karatu only 300 via 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma katin MTN,ƴan Nijar carte airtel ta 300f.

❌Kawai ki yi transfer don Allah ko kuma ki turo da kati👏🏻

NB: da zarar na kammala book 500 ne
[04/09 à 16:07] MRS SADAUKI 💫: 🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
*FARASHIN TASIRI*🪺
        ```celebrity```🌬️
         🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
     *Gajeren labari*🕊️

MRS SADAUKI 💫✍️

FCWA ☀️

Special gift fo my VIA FANS 🪷

My book is only 300 via 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank,sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822. Ko kuma katin MTN,ƴan Nijar kuma carte airtel ta 300f

*Zuwa goma zan tsaya duk mai so ya biya kuɗinsa*🌚

Page 9

Duk yadda Bashir ke ƙoƙarin cire ni a jikinsa amma abu ya cuttura, saboda ba ƙaramin ƙanƙamesa na yi ba.
Wani abu nake ji wanda ban taɓa ji a ko wane namiji ba,a can ƙauyenmu na yi samari nan ma birni amma karon farko da na taɓa jin wannan lamari wai shi ƙwayar so.

A hankali na sassauta riƙon da na yi masa na ɗago jajayen idona da suke ta shatatar da hawaye.Gashin idona ya jiƙe sosai,shi yasa nake ganin fuskar Bashir dishi-dishi.Da mugun sauri na lumshe su jin ya na hura min iskar bakinsa bisanin ya sa tattausan hannunsa ya fara goge min ƙwallar.

Na ja da baya kaɗan amma za mu iya jin hucin juna.“Dubi yadda kika ɓata kwalliyar ki? Faɗa min mene ne ke damun ki?”
“Alhaji ne! ” sai kuma na yi shiru tuna Bashir kallon mahaifina yake yi wa Alhaji Nera.
“Wane Alhaji?” ya tambaye ni ya kamo hannuna.
“Daddy mana! Bai son na fara zancen soyayya ya fi son sai na gama karatu! Amma don Allah kar ka rabu da ni ina son...son ..kaaa !” Na yi ƴar gargada a kalmar ƙarshe saboda yau ne karon farko da na furta wa wani ita .

Daɗi sosai ya bayyana a fuskar Bashir ,a ɗan ruɗe ya fara tambayata “Meelat da gaske ki na sona? Za ki aure ni ? Wayyo Allahna! ”

Kai na jinjina masa ina murmushi sai kuma ya buɗe min mota na shiga,shi ma ya hau mazaunin direba.
Mu na tafe mu na tsara yadda rayuwarmu za ta kasance tare da yin soyayya a ɓoye ba tare da Alhaji ya sani ba har mu ka iso makaranta.Da zan sauka ya ban 2k don na ci abinci,yau ɗin ma ban yi masa godiya ba sai ce masa da na yi “sai an jima ka kula da kan ka!”
Ya saki murmushi mai sauti ya na cewa “na gode my Meelat ke ma ki kula min da kan ki banda kula samari”
Na yi ƴar dariya kafin na wuce ɗakun Raheela.

A tsakiyar ɗaki na tarar da ita ta baza kaya,“lafiya sai kace an fasa dilar Makka ?” shi ne abin da na faɗa daga shiga ta.
Yau ba ta yi ƙorafin sallama ba ta ce “yawwa don Allah Meelat zo ki taya ni zaɓar kayan da zan saka,kin san yau zan je gaida mahaifiyar Hafiz”

Na ɗan taɓe baki bisanin na taya ta duba kayan,don zuwa yanzu ita ma babu laifi Hafiz duk kusan ya canza mata sutura.Wata atamfa ƴar côte d'ivoire na zaɓa mata,da murna ta shiga shirya wa.
Na dubeta na ce “Yanzu za ki tafi gaishe ta ɗin?”
“Eh mana ko ba ki son yau babu makaranta ba?”
“Don me?”
“Oh! Na manta ban sanar da ke ba,jiya kin yi saurin tafiya ne SG ya sanar ba a makaranta ko zaɓen mi za su yi”

Jin haka yasa na yi kwanciyata ina cewa “madallah dama a gajiye nake”
Heelat ta dube ni ta ce “aikin mi kika yi?”
Sai na ƙyalƙyace da dariya ina tuna moments ɗin mu na jiya ni da Alhaji ,sai na ce mata “babu komai! Hafiz ɗin shi zai zo ya ɗauke ki ko yaya?”
“Eh haka ya ce,ya na ma gidan su Sadiq ,na manta ma ban tambaye ki ba ya jikin nasa?”
“Jikin wa?”
“Sadiq mana! Ba dai ba ki san bai da lafiya ba?” Heelat ta tambaye ni.
“Bai faɗa min ba” na bata amsa.
“Kuma fa ke ce sila! Duk a son ki ne,Sadiq na bala'in kishin ki.”
Na taɓe baki na ce “mene ne amfanin soyayyar tunda ko sisi bai da ballantana a yi zancen aure”

Heelat ta ce “ko Hafiz fa Daddynsa ne ya biya komai amma ai shi ma bai da ko sisin ”
“To shi nasa mahaifin ya mutu,bai bar masa komai ba sai wani guntun gidan laka ” na faɗa ina mai fara daddana wayata.

Dariya Heelat ta yi sosai bisanin ta ce “wlh Meelat ba ki da mutumci,shi gida har da guntu ke da kwai? ”
“I ba ki da labari?”
“Ko ma dai mene ai guntun gatarinka ya fi sari ka bani”

“Kar ki ɗora min ciwon please,bari na hau facebook na ga wace wainar ake toyawa a can” na faɗa tare da shiga yanar gizozo,yayin da kuma Heelat ke ta ƙoƙarin ganin ta yi kyau sosai.

Uwanda suka turo min saƙon ƙawance na fara mayar wa sama da mutum ashirin kuma duk maza ne.Kamar jira suke mu ka fara masayar kalma,a ƙarshe kuma wasu cikinsu suka tambaye ni lambar da nake WhatsApp na kuwa basu.
Sosai na shagala cikin wannan duniya,sai na ji muryar Heelat na cewa “zan tafi sai na dawo”
Na juyo ina watsa mata mugun kallo na ce “wa za ki bari yayi miki tsaron ɗaki? To tare za mu je Malama duk tsiyar ki yau sai na ci abincin gidansu Hafiz ”

Kai ta girgiza ta ce “mai hali dai bai fasa halinsa! Tun farko na so na tambaye ki ko za ki yi min rakiya,to sanin halin ki ya saka ban furta ba”
Na yi ƴar dariya ina mai maida wayata a jaka na ce “to mu tafi”
Mu ka fito ta rufe ɗaki kafin mu fita,gidan baya na zauna ita kuma ta shiga gaba.

Har mu ka kai gidan Hafiz hirar Sadiq ce yake min,akan na tausaya wa abokinsa na so shi kamar yadda shi ma yake sona kar na ci amanar ƙauna.Heelat ma ta daddage ta na kama masa sai goyon bayan Sadiq suke,tun ban jin haushi har ya kai na yi banza da su ina mai duba sabon group ɗin da aka saka ni à WhatsApp wanda iya sunansa kawai za ka fahimci babu abin arziki a ciki.

Ina shiga kuwa na ga sai abubuwa maras kyawu ake turowa,na fito ina dariya a zuci na ce ‘ana hau duniya!’
Gidansu Hafiz mai kyau ne,tun daga waje har cikin gida.Shi yayi mana iso har ciki,mahaifiyarsa da ƙanensa su na zaune.Mu ka gaishe su sannan mu ka samu wuri mu ka zauna, Heelat sai wani sunne kai take.

Mahaifiyarsa babu ruwanta don irin ƴan bokon nan ne,haka ta yi ta jan mu da hira bisanin ƙanwarsa ɗaya ta kawo mana ruwa da jus da kuma yankarkar ayaba,da gwada.
Ɗayar kuma abinci ta kawo cikin kwononin madubi don ka na iya hango lakaɗeɗen kifin da ke bacci a gashe abinsa.

Tashi suka yi suka bamu wuri,hatta Hafiz ɗin wanda kafin ya tafi ya ce “ku ci ku ƙoshi nan fa gidan ku ne”
A zuci na ce ‘kar ma ka yi ɓarnar bakinka don ko ba ka ce ba sai na yi narrr ’

“Wlh ni kunya nake ji,don Allah Meelat kar mu nuna ƙauyanci mu ci kaɗan ” Heelat ta faɗa ta na ɗaukar ayaba.
Na jefe ta da mugun kallo na ce “dalla can malam! Ga abincin sai na zauna da yunwa eh lalle!” ai kuwa na buɗe kifin da tun da aka aje shi yawuna suka tsinke plate na ɗauka na zuba acake da sauran kayan haɗin.

Kamar ƙaton da ya dawo daga gona haka na zuba na ci na ƙoshi, Heelat kuwa sai tsakura take ita ala dole ta zo ta zo gidan surukai.
Na dube ta da kyau na ce “kin ga Malama ki saki jiki ki ci abincin ki don dai in sun fito ba za su gane kaɗan kika ci ba”
“Na fa ma ƙoshi” ta faɗa ta na cire hannunta ta saka sabulu ta wanke hannunta a ruwan da aka kawo cikin wani kwano.

Don wulaƙanci sai ta koma gefe ta na danna waya,ni kuwa ban damu ba bayan na gama ci na fara shan kayan marmarin na ɗora da ruwa.
Sai a lokacin ƴar aikinsu ta zo ta kwashe kayan,Hafiz ya dawo ya mai cewa “ku taso ku duba kayan” ba tare da sanin kayan mi ba mu ka bi bayansa.
Wani ɗaki mu ka shiga mai shegen kyau sai ƙamshi ke tashi,tozali na yi da akwatinan aure kusan shidda ko wace a buɗe take da kuma kaya a ciki .

Ba ƙaramin ƙoƙari na yi ba wurin haɗiye abin da na ji ya zo min a maƙogoro .‘Wato dai Heelat aure za ta yi ta bar ni alhalin ko can a ƙauye ita ke kore min samari ta na aibatasu don duk kar ni na yi na bar ta,shi ne yanzu za ta ci amanata?’ na yi zancen zucin.

Dakyar na cira ƙafata na matsa na fara duba akwatinan,less,atamfa da duk wasu abubuwan da ake sawa cikin lefe hatta kayan bacci da bra da pant duk an saka.Turare da man shafawa trollynsu daban ta musamman.
Sarƙa da ɗan kunnai kuwa ba a magana sai ƙyalli suke.
Hafiz sai faɗa yake ya na ƙarawa “in da akwai abin da babu ku faɗa,don ina ga yau za a kai kayan ”

“Meelat komai yayi ko?” Heelat ta tambaye ni ta na min wani murmushi mai cike da ma'anoni,a cikin kallonta zan iya hango irin na yi miki zarra na wuce ajin ki.
“Duk sun yi Allah sa alkhairi ” na faɗa ina murmushin yaƙe.
“Amen! Shi yasa nake son yanzu na kai ku can Takalmawa tun da gobe ma babu makaranta sai ku yi shagalin taya murna ku da sauran ƙawayen ku”

“Tunanina da na ka sun zo ɗaya Habibi , Meelat ai za ki tafi ko?” ta dube ni ta na tambayata.
Na ce “a'a zan yi Bashir magana sai mu tafi tare”
“Wane Bashir kuma?” Hafiz ya tambaya ya na turniƙe fuska.
Na yi ƴar dariya ina mai danna wayata na shiga yi wa Bashir ɗin text babu jimawa ya kira,na yi saurin fitowa don sosai nake jin zuciyata na zafi in ina ganin trollyn nan.

Bayani na yi masa a ɗan takaice,ya shaida min ga shi nan zuwa.Tsabar takaici a waje na fita ina jiransa tun da an yi katari ya na kusan unguwar.Ina nan tsaye na tsinkayi motar shi daga nesa,idona har rufewa suke na soma tafiya direction ɗin.

A gaba na zauna ina mai sauke nauyayyar ajiyar zuciya,ganin fuskar Bashir kawai ya saka na ji nauyin zuciyata ya ragu.
A ɗan shagwaɓe na ce “shikenan ƙawata za ta yi aure ta bar ni,a duk faɗin ƙauyenmu mu biyu ne kawai manya” shaaa sai hawaye.

“Ikon Allah! Meelat ke kam hawaye ba su miki wuyar zubar wa? Mene ne na kuka to? Shi aure ai lokaci ne kamar mutuwa kowa da nasa lokacin,murna ya kamata ki yi mata” Bashir ya faɗa cikin rarrashi.
“To tun da haka ne mi yasa can baya ita ta hana ni na yi auren? Kullum cewa take ta fi son ayi aurenmu ɗaya rana,kenan ƙarya ce take min dama can saboda ita ba ta da mashinshini” na faɗa ina kuka bilhaƙi.

“Oh my god! Meelat duk wacce kika ga ta yi aure lokacin yinsa ne yayi,ke ma can baya saboda Allah bai sa naki lokacin ba ne shi yasa ba ayi ba.Amma babu wani mahaluki da ya isa ya hana faruwar wani abun da ya tsara,kuma ma da kike cewa haka in da kun yi auren ina za ki samu santalelen yaro ɗan fari kama ta?”
Yadda yayi maganar cikin zolaya ya ban dariya,ganin murmushi a fuskata ya ci gaba da kawo abin da zai sa na daɗa yin wani.

“Meelat ya na ji ki na zancen ƙauye,kenan dama ba ƴar nan ba ce?”
“Eh! Karatu ne na zo nan amma asalin iyayena su na can ƙauyen Takalmawa,ina son mu je ka gaishe su” na faɗa ina ƙure shi da kallo sai na ga yanayin fuskar shi ya canza.
“Lafiya ko ba ka son ƴar ƙauye?”
“A'a ba haka ba ne,sai dai kin san da zarar kin gabatar da ni a wurin iyayen ki za su iya yi min maganar aure ni kuma gaskiya ban shirya ba”
“Kamar ya ba ka shirya ba? Haba Bashir sai kace sai ba ka sona? ”

“Kar ki sake faɗar haka! Ina mugun son ki sosai,amma kin san komai ana son a bisa a hankali musamman zancen aure abu ne ba na wasa ba.Dole ne ki karanci halayena,ni ma haka sannan mu fahimci junanmu”

Wani mugun tsoro ya shige ni jin furucinsa,tare da saka min saƙe-saƙen zuci da tunanin kar dai a je ya fara bincike a kaina.
“Ya na ga hankalin ki ya tashi?” Bashir ya tambaya.
“Babu komai,kawai dai na fahimci ba za ka aure ni ba” na faɗa kamar wata mai maraicin Uwar da Uba.
Bashir ya gyara zama ya ce “ki na ji na Meelat? Ba wai kuɗin aure ne banda ba,a zahirin gaskiya ko milliyan ne sadakinki ina su a ƙasa.Matsalar guda ce matata! Shekararmu biyar da yin aure har yanzu ba ta taɓa ko da ɓatan wata ba,in ta ji zan ƙara aure hankalinta zai tashi ta ga ko don ba ta taɓa haihuwa ba ne ni kuma ba zan so haka ba saboda na yi mata alƙawarin ba zan sake aure ba sai ta haihu”

Ji na yi kamar ya caka min mashi a ƙahon zuciya,dakyar na haɗiye ƙodagon baƙin cikin na ce “amma ka ce min ka na da yara biyu”
“Eh da matata ta farko ba,yanzu kuma ba ma tare har ta sake wani auren yaran kuma su na gun ta”
“To mi zai hana ka karɓo su ka baiwa wannan matar in ya so sai mu yi auren”
Dariya yayi ya ce “kin taɓa ganin inda aka yi kyauta ɗa? Ta yaya ma za ki kawo min wannan zancen?”
Cike da jin haushi na ce “kenan ko shekara goma za ta yi muddin ba ta haifu ba shikenan za mu jira ta sannan mu yi aure?”
“Don Allah ki bar faɗar haka! Yanzu ina ne zan kai ki gida koko can Takalmawa?”
Ban basa amsa ba na buɗe ƙofa na fita cikin fushi,ina jin ya na kiran sunana na yi banza da shi.
Dama babu nisa da kwalta,na samu adaidaita na shige.Wayar Alhaji Nera na kira ,na tambaye shi in ya kwashe kayan nawa ya kuma tabbatar min da eh ya kwashe har ya kai min su gidansa na Gao.
Direct gidan Hajiya Momah na yi tsinke,cikin rashin sa'a na ci karo da wannan shegiyar Na'ilah don jininmu bai haɗu ba.

Hajiya Momah ta tarbe tare da yin min kirari,nan na ji zuciyata ta yi fess yayin da kuma Na'ilah ke ƙoƙarin saka min wani baƙin cikin.
“Hajiya ki bar zuga ta ,kar ta ɗauka ta fi kowa shi dai abin nan ko wacce ta na da shi ....” na yi saurin katseta ta hanyar ce mata “ke dallah rufewa mutane wannan shegen bakin naki mai wari” ban rufe baki ba ta kai min duka nan mu ka shiga jibgar juna dakyar Hajiya ta raba mu.

Mu na nan mu na cacar baki sai ga Alhaji Nera,ya tambayi ba'asi Hajiya ta shaida masa komai .A gabana ya shiga yi wa Na'ilah masifa ya na cewa “rashin uwa shi ke sa ayi uwar ɗaki,amma ke na fahimci ba ki son zaman lafiya .Akan Baby ko Hajiya Momah zan iya cin uwar juna da ita,ke kuma wuce mu je” ya kama hannuna za mu fita na ji Hajiya Momah na cewa Na'ilah “shikenan kin yi wa kan ki ga shi nan yayi tafiyarsa kin yi biyu babu”

Alhaji kamar wata ƴarsa haka ya saka ni a mota ,ya na driving ya na min faɗan kar na kuma zuwa gidan Hajiya Momah mi ma ya kai ni can shi bai son ya na gani na can.Abin da na fahimta Alhaji Nera mugun tantiri ne,biyar mata ya mayar da shi ruwan sha .A haka dai har mu ka isa wani ɗan madaidaicin gida,yayi horne mai gadi ya buɗe mu ka shiga ciki.

Babu abin da babu na more rayuwa,komai tsaf.Duk yadda nake cikin ƙunci sai da Alhaji Nera ya sauke maganin da ya sha a kaina wanda kuma can farko akan Na'ilah ne ya tanade shi.
Key ɗin gidan ya ban ya na cewa “daga yau babu takura shikenan za mu yi rayuwarmu hankali kwance”
Ban basa amsa ba,nan ya fahimci kamar ina da damuwa ,ya tambaye ni.Cikin kuka na sanar da shi auren Heelat,hatta kuma hirar da mu ka yi da Bashir .Cikin kuka na ce “don Allah ka taimaka min Bashir ya fito ayi auren nan tare da na Heelat in ba haka ba... ” ban rufe bakina ba Alhaji Nera ya ce “kar ki wani damu kan ki in dai auren ƙawar ki ne ba za ayi shi ba muddin ina da rai”
Duk da fahimci abin da yake nufi ba sosai bai hana ni jin daɗi ba har ta kai da na rungume ƙaton tumbinsa.......

My book is only 300 via 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma katin mtn,ƴan Nijar carte airtel ta 300f

Nan duk shimfiɗa ce har yanzu ma mu kamo kanun labarin ba,ki zo ki biya naki Hajiya kar ayi babu ke🌚
[05/09 à 08:15] MRS SADAUKI 💫: 🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
*FARASHIN TASIRI*🪺
        ```celebrity```🌬️
         🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
     *Gajeren labari*🕊️

MRS SADAUKI 💫✍️

FCWA ☀️

Special gift fo my VIA FANS 🪷

*Page ɗin ƙarshe ta kyauta 10*

Bayan fitar Alhaji Nera na duba wayata,saƙon Sadiq na gani ya na min barka akan kuɗin auren Heelat da aka kai.Abun ma haushi ya ban kawai na tura masa “kai kuma ƙaton banza babu zuciyar da za ka yi niyya ka tara kuɗin auren ballantana ka kawo gidanmu ko?”  ina ta jiran ya maido min amma shiru.
Na tashi na shiga toilet na yi wanka,bayan na fito na shiga kitchen na dafa taliyar leda don duk ya ajiye min komai.Kifin gwangwani uku na fasa na zube a ciki ,sosai girkin yayi daɗi.

Ina shiga WhatsApp group kawai na ci karo an turo videos BF na kuwa kunna ina kallo,abun ka da wacce ta saba sex nan hankalina ya tashi sosai.Wannan karon sha'awar Bashir na ji don shi ne wanda nake so,duk fushin da na yi da shi haka na haƙura na mayar masa da saƙon ban haƙurin da yayi ta turo min na share.

Ya na ganin saƙona ya kira ni,nan na dagargaje ina ta zuba masa shagwaɓa tare da ce masa ina son ganinsa.Yayi min alƙawari bayan sallar magrib zai zo yanzu ya na wani aiki.
Tamkar wacce aka yi wa albishir da gidan aljanna haka na tashi na ƙara gyara gidan na fesa turare,sai kuma na yi wanka na shirya cikin riga da siket iya gwiwa.Zumbulun hijabi na saka na fito,mai gadi na zaune bakin ƙofa ya na sauraren radiyo.
“Hajiya fita za a yi?” ya tambaye ni.
“Eh ina son zuwa bakin hanya ne yanzu na dawo” na basa amsa kafin na fice.
Taxi na shiga na je na siyo banana da tufa,ina kan hanya aka fara kiran sallah.
Bayan na dawo gida na samu madara da na zuba garin da Hajiya Momah ta ban na saka a ciki,sai da yayi minti biyar sannan na shanye.
Sai duban hanya nake,dakyar na yi sallah bisanin na fara saffa da marwa kamar kazar da ƙwai ya fashe wa a ciki.

Can sai ga kiran Bashir ,na ɗaga tare da yi masa kwatancen gidan.Ina nan zaune ya ƙara kirana ya shaida min ya zo,da sauri na fita kamar zan tashi sama haka na isa inda yake zaune cikin mota.Gidan gaba na buɗe na shiga,sannan ya fara tuƙawa direction ɗin da na fito.

“Nan kuma gidan su wane ne kika dawo?” cewar Bashir lokacin da ya daidaita parking a ƙofar gidan.
“Mu shiga ciki dai ka gani” na faɗa ina mai fita,ina gaba Bashir na biye da ni bayan sun gaisa da mai gadi.
Ina shiga falo na cire hijabin na ajiye shi kan salon,Bashir yayi suman tsaye ya na kallona tare da haɗiyar yawu.
Dakyar ya furta “Meelat ya za ki zauna a haka kuma?”
“Kai dai samu wuri zauna bari na kawo ma ruwa” na faɗi haka ina mai nufar kitchen,kan tray na ɗora butalin ruwan sanyi da kuma fruits ɗin da na yayanka.
Na fito ina murmushi na ajiye gaban Bashir ina cewa “barka da zuwa sabon gidan Meelat! Ga ruwa ka sha ” ya karɓa hannunsa na rawa,gefensa na zauna na ɗauki ayaba ina ci.
“Meelat kin san hakan ba daidai ba ne ko? Irin haka sai ki sa mutum ya zauce don Allah ki mayar da hijabin ki”
“Saboda in faranta maka da rai na yi fa,na ga ɗazu kamar ka yi fushi” na faɗa ina  zagayo hannuna kan cikinsa.Bashir ya dube ni cikin ido ni kuwa ganin haka yasa na ƙanƙance nawa tare da ƙara shagwaɓe su.
Lips ɗinsa da na jarabta na kai wa sumba kamar wata kura,a tare mu ka sauke ajiyar zuciya.Bisanin mu fara sumbatar juna haɗi da romance,a ranar Bashir ya shayar da ni zuma wacce ban taɓa sanin akwai banbanci tsakanin wanda kake so da kuma wanda kake yi don kuɗi.

Sai bayan komai ya lafa ne Bashir ya dube ni da kyau ya ce “Meelat ina kika kai budurcin ki?”
Na sunne kai har da hawayen kissa na ce “fyaɗe aka min Bashir ”
“Amma ba ki gaya min ba alhalin har maganar aure ta shiga tsakaninmu”
“Ka yi haƙuri!” na furta ina mai lafewa jikinsa.

Zuciyar Bashir wani irin bugawa take da ƙarfi, ya na son Meelat sosai amma sam yanzu ya fara zargin da lauje a lamarinta.Ya na ƙoƙarin tashi na riƙe shi,duk yadda ya so tafiya na hana shi sai da mu ka je zagaye na biyu.Toilet ɗin falo ya shiga yayi wanka,bayan ya fito na saka hijabi na yi masa rakiya har cikin mota.

“Oh Allah! Sama da appel goma,ana ta kirana ashe” ya faɗa tare da cire wayar a caji,nan kuma wani kiran ya shigo.Ya ɗaga yadda wayar ke da ƙara sosai ni ma ina iya jiyo abin da ake faɗa.
“Bashirrr! Mon amour farin cikina tun ɗazu nake kiran ka ba ka ɗauka na sanar da kai babban albishir ina ci..ki yanzu na yi test na gani wayyo daɗi don Allah ka zo ka kai ni asibiti a ƙara tabbatar min” in kunnena ya jiyo min daidai shi ne abin ta faɗa.
Cike da murna ya ce “da gaske masoyiyya? Yawwa gani nan tafe” ƙittt ya kashe kiran ya dube ni “Meelat zan tafi matata ce ta kira ni zan kaita asibiti”
Cike da murna na ce “to Allah sa gaske ne ,kar ka manta ka kira ni” sai na fita na koma cikin gida cike da murna.

BASHIR

Ikon Allah kawai ya kaisa gida,don soyayya mai zafi suka yi shi da Mariya kafin su yi aure.Ya na zuwa gida tuni ta shirya  hakan yasa suka wuce asibiti .Dr yayi gwaji ya kuma tabbatar masu da ciki ne ɗan wata biyu,sosai suka yi murna Bashir kuwa ya manta da zancen wata Meelat.

A can ƙauyen Takalmawa kuwa sosai aka yi shagalin tarben kayan auren Heelat.Innar Meelat kuwa tuni ta shiga zullumi wannan ya saka ta ga ita ma gwara ta aurar da tata ƴar can ta sai ta ƙarasa karatunta a gidan mijin.Ta samu Abba da zancen shi kuma ya nuna mata bai san wannan ba dole ƴarsa ta ida karatu tunda saura shekara uku nan gaba.
Heelat tamkar sallah haka take ji sai wani fifiko take yi wa ƙawayenta uwanda suka yi aure nan ƙauye kasancewar duk sun zo tarben lefen.
Heelat ba ta koma Maraɗi ba sai washegari,direct makaranta ta yi tsinke.

MEELAT
Jin matar Bashir na da ciki ba ƙaramin daɗi yayi min ba,murna kawai nake saboda samun cikin nata ya nada alaƙa da samun nawa auren.Ina ta zaman jiran Bashir ya kira ni shiru,kuma ban so na kirasa kar ace ya na tare da matar shi kawai sai na haƙura.
Washegari kamar kullum Bashir ya kira ni akan zai zo ya kai ni makaranta,ban sanar da shi ba mu yi ba sai da na bari ya zo.
“Jiya ina ta jira ka kira ni ka shaida min yadda ake ciki amma shiru” na faɗa ina shafa dogon gemunsa.
Ya kashe motarsa sannan ya ce “murna ce ta min yawa amma ai gashi yanzu na zo ko?”
“Masha Allah kenan dai yanzu akwai cikin?”
“Eh haka likita ya ce watansa biyu ”
“Alhamdullah ! To ya maganar aurenmu yaushe za a yi?” na tambaya cike da murna.
“Aure kuma?” ya tambaye ni kamar bai san da zancen ba.
Na ce “eh mana! Ko ka manta ka ce sai in matarka ta haifu?”
‘Da yake banda hankali sai na auri matar da na sani tun a waje ta rabewa ƙatai jikinta’ Bashir ya faɗa a zuci amma a zahiri sai ya ce wa Meelat “in ba abun ki ba Baby daga samun ciki shikenan sai na kawo zancen aure yanzu? Bari za mu yi har ta haifu”
Maganar da Bashir yayi sam ban yarda da ita ɗari bisa ɗari ba,amma na share na ce “to Allah kai mu”
Ya amsa da “amen” sai kuma duk mu ka yi shiru.
Hannunsa na ji jikina ban hana shi ba saboda ina sonsa,an ce kuma duk inda ke da so to sha'awa na yi masa sanɗa ne.
Tsabar rashin ta ido Bashir ya nemi mu shiga daga ciki,ni kuwa na biye masa mu ka shiga ya gama abin da zai yi ya fito.Tun daga wannan ranar Bashir ya mayar da ni matarsa ta biyu,da zarar na yi masa maganar aure kuma sai ya ɓata rai.Gefe guda kuma Alhaji Nera mu na sheƙe ayarmu sai dai a hotel ne bai zuwa nan,ɓarin kuɗi kuwa ta ko wane ɓangare ina samunsu.Cikin ƙanƙanen lokaci na ƙara waye wa na goge na fito sak ƴaƴan madara rairafan capet.
Ni da Heelat wa'azi ne ke shiga tsakaninmu don zuwa yanzu duk ƴan makaranta sun fahimci rayuwar da na saka kaina.Wasun su ma guduna suke,Sadiq kuwa ya na ta bakin ƙoƙarinsa aikin ƙarfi yake ya na tara kuɗin aurena wanda har asusun ya nuna min.

Ba sau ɗaya ba sau biyu ba a gabana Hafiz ya sha yi masa faɗa kan cewa ya rabu da ni,amsa ɗaya yake basa a kullum “ ita soyayyar gaskiya ba ta sauyawa ina sonta a haka da zarar na aureta shikenan” furicinsa ya saka na basa wani keɓaɓen wuri a sashen zuciyata.


NA'ILAH POV

Tun bayan cin mutumcin da Meelat da Alhaji Nera suka yi mata ta lashi takobin sai ta aure shi sannan ta raba shi da duk biyan sauran matan banza.Ba ta ɓata lokaci ba wurin neman bokaye da malamai ba,babu shiri Alhaji Nera ya fara yi mata ɓarin kuɗi tare kuma da zancen soyayya.Babu jima wa maganar aure ta shigo don har an yi komai.

★ Yau ta kama Monday ranar da za mu fara zuwa stage a asibitocin da ke kewaye da nahiyar maraɗi.
Riga fara na saka tare da baƙin wando jeans,ƙananun kitson da aka yi min na tattare wuri guda na tubke.Ina ƙoƙarin fita Alhaji Nera ya shigo,da mamaki na dube shi na ce “alhaji lafiya?”
“Lafiya lau! Dama mota ce na zo na kawo miki ni zan yi tafiya zuwa Dubai”
“Wai dai ko gaske ne aure za ka yi?” na tambaye shi ina mai kafe shi da ido,ya ƙyalƙyace da dariya ya ce “Meelat kenan ! Ko ma auren zan yi mene ne? Ina ce har da maza kike shigo min a gida duk na yi shiru ban ce komai ba” ya na faɗa haka ya fita na bi bayansa,bayan na rufe ɗaki.

Farar mota ce sai ƙyalli take an yi mata wanka,motarsa ce bai jima da sayenta ba yanzu kuma ya ce ya bar min ita.
Key ɗin ya miƙa min ya ce “mu je ki ajiye ni gidan Bus ” da murna na karɓa na shiga,ni na yi driving nasa har mu ka isa can.Kuɗi ya ban sannan na wuce asibitin Ali Shebu inda a nan ne zan yi nawa stage ɗin.
Ko da na isa na tarar da Heelat kasancewar wuri guda aka kawo mu.Na parker mota na fito,ƙiri-ƙiri ta nuna min hassada don kasa ɓoye wa ta yi har sai da tace “yo wa za a yi wa kurin mota ai ni ma dai na iya”
Na yi dariya na ce “ke ai iyawa ce kawai kika yi ni kuma ina da motar”
“Hafiz ya ce zai saya min matsayin tukuicin daren farko” shareta na yi don na fahimci ta na son yin magana kullum kan daren farko sanin ni banda abin da ko wace amare ke taƙama ta baiwa mijinta.

“Ya na ga har yanzu sauran ba su zo ba? To wai nan za mu tsaya?” na tambayi Heelat ina ƙare wa asibitin kallo.
“Sai shugaban asibitin ya zo,shi ne zai damƙa mu ga ma'aikatan ”

Ina shirin buɗe baki na yi magana sai ga motar Bashir ta shigo,ban kauda idona ba har sai da sai da matar ta fito wanda a gaban idona yayi kissing ɗin goshinta.
Wani ƙaton dutse ne ya zo kan zuciyata ya zauna daram,ji na yi kamar na je na shaƙo shegiya don na fahimci matarsa ce wacce akan ta samu ciki ya fasa aurena don yanzu na fahimci Bashir ba zai aure ni ba.Kimanin sati ɗaya currr nake binsa akan ina son ganinsa ya ƙi,a ƙarshe ya faɗan maganar da har in mutu ban zan manta ba “in na aure ki mine ne za ki ban wanda yanzu ba ki ban ba?”  shine furucinsa na ƙarshe a gare ni.

Na rumtse ido lokacin da kyakkyawar matar tasa ta zo wucewa ta gabanmu.
“Ke lafiyar ki?” Heelat ta tambaye ni,ban kai gabata amsa ba wata nurse ta kira mu.
Mu na zuwa sai mu ka tarar da sauran abokan karatun mu ashe tun ɗazu su na ciki.

Da tsiya da jaraba sai da na san yadda na yi na je ɓangaren ƴan awon ciki,nan na samu mata sun yi layi sosai ban sha wuya ba wurin hango matar Bashir .Kamar wacce aka yi wa allurar baƙin ciki haka na shiga mota na je pharmaci na siyo maganin zubar da ciki na dawo.
Cikin ladabi na je ina kamawa matar aiki har aka zo kan matar Bashir ,a gabana ta kwanta Madam nurse ta mata scanning ɗan cikin sai juyi yake .
Bayan an gama aka ce na bata maganin masassara don jikinta na da zafi da kuma wasu sauran magungunuka,cike da dubara na bata na zubar da cikin wanda in ta sha shi da wuya ma in mahaifarta za ta ƙara ɗaukar ciki da wuri.
“Allah raba lafiya” na faɗa ina murmushin ƙeta .

Sai wuraren sallar la'asar mu ka tashi,ni na ɗauki Heelat cikin motata direct gidana mu ka wuce.Tsoro ya bayyana ƙarara kan fuskarta ta ce “Meelat duk yadda nake tunanin ki ashe kin wuce nan?”
Na yi murmushi kawai na wuce kitchen, Heelat kuwa sai dube-dube take kamar baƙauyar da ta shigo birni.

Jus da kayan motsa baki na kawo sannan na kunna kayan kallo,Heelat na ci ta na min wa'azi inda a ƙarshe take cewa “Meelat kan wannan sana'ar da kika sa kan ki tun da kin ce saboda kuɗi kike yi mi zai hana ki buɗe shafin Tik Tok yadda kike da kyawun nan na san za ki samu followers,cikin ƙanƙanen lokaci za ki zama *CELEBRITY* ”

Na yi shiru ina tunanin maganarta,sai na ce “a can zan samu kuɗi?”
“Milliyoyi ma kuwa”
Furincin Heelat ya saka na sauke app ɗin Tik Tok ita ta nuna min yadda ake yi komai ta ce wurin wacce suke kwana ɗaki ɗaya duk ta koya .Kamar da wasa na buɗe shafina da sunan *MEELAT ƳAR FULLO*  .
Wanka na yi na saka wata baƙar riga marar hannu tare da wando,Heelat ta min video farko a rayuwata na ɗora.

Sama da awa biyu har Heelat za ta tafiya sai kuma ta ce “Shiga mu ga su wa suka yi like da comments”
Hannuna har rawa yake wurin dubawa,caaa haka na ga an yi min tuni na samu followers da comments na ban mamaki.Daɗi na ji kamar zai kashe ni,mutanen da suka nemi na yi masu video sun fi ɗari.Tun daga lokacin na ji kaina ya fara hayaƙi,buri da muradin zama CELEBRITY ya danne zuciyata.......

*Yanzu ne kawai mu ka shigo labarin mun fita daga shimfiɗa,da sannu za mu ji yadda ta zama CELEBRITY wanda in ba ku manta ba farkon labarin tuni Meelat ta fara biyan FARASHIN TASIRI saurayinta Sadiq ya mutu,ga kuma Alhaji Nera gabansa na fitar da jini.Shin wace ce Meelat bayan ta fara rayuwar Tik Tok? Har mene ne ya jaza mata wannan masifar da duk in ta yi mu'amala da namiji yake mutuwa? Ya za ta yi kenan a yanzu da ake tuhumar ta da ta kashe Alhaji Nera?*

Sai mu haɗe a PAID GROUP,only 300 ne via
3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank , shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ,ƴan Nijar carte airtel ta 300f.

NB: 300 kuɗin shiga group ne,daga lokacin da na kammala shi zai koma 500

5/9/23

MRS SADAUKI NIJAR

No comments