Fara Wuta Book 2 Complete
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*01*
~~~~~~
_I've met alot of people, but nobody feels like you!_ _-Ali Gatie._
**
*Shekaru Goma da suka wuce.*
Lokacin sanyi ne, hazo ya lulluɓe garin ruf ta yadda ba zaka ce safiya ce a sannan ba, don hatta motoci da fitilu a kunne suke yawo koina, na ƙasa kuwa baya ganin abinda ke gaba ko yaya tazararsa dashi take.
A cikin motar dake tafiya kan titin expressway na barin gari, Ma'aruf ya zare earpice ɗin dake kunnensa ya sake shi a jikinsa sannan ya juya ya kalli Jamal dake tuƙin motar.
"Let me drive dan Allah."
Jamal ya girgiza kansa.
"Kaima ka san there's no way da zan baka motar nan, yaushe kayi ƙwarewar da zaka hau babbar hanya?"
"Kusan shekara daya fa kenan Yaya dana fara koyon tuƙin nan, ko wace irin ƙwaƙwalwa ce dani ai ya isa na iya haka."
"Da da Muhammad muka zo sai ka gaya masa hakan, amma ni na sanka Ma'aruf babu abinda yake gabanka banda karatun likitan nan, shi yasa kaƙi barin kanka ka koyi komai, ba don wannan babar taka ma ta dage ba ai da yanzu baka ma fara koya ba, something so shameful!"
Ma'aruf yayi dariya yana É—auke wayarsa daga tsakanin cinyarsa kafin yace.
"Na sha gaya maka makarantar ne ba ƙaramin tsauri ne dasu ba, ƙanwar Havard fa ake ce mata, ba kowa suke ɗauka ba and in my own case da nake baƙar fata dole in dage inyi karatu, babu ruwansu da komai sai abinda ka iya."
Wani mai mota yazo yasha gabansu a lokacin, Jamal ya kalle shi cikin takaici yana girgiza kai kafin yace.
"Kai kuma ka dage dole sai nan, Universities nawa zaka je ka zama likitan ƙwarai Ma'aruf."
Ma'aruf yayi dariya yana kallon gefen hanya ta cikin gilashin motar dake É—aukar ido saboda sabunta, don kwanakin motar biyu kawai da siya bayan Baffa ya gama yi wa Jamal din tsiya akan ya canja tsohuwar motarsa, sai gashi da ya tashi yaje ya siyo wadda tasa kowa gyada kai cikin mamaki.
"Wai likitan ƙwarai, you are too much Yaya, sannan dan Allah sunanta Mami, ba 'babarka' ba."
Jamal ya cije leɓɓensa a wannan lokacin yana kallon gabansa a lokacin da suka gota wani ƙauye suka fara barin gari, yayin da shiru ya ratsa motar kamar yadda hakan ke faruwa a duk lokacin da Ma'aruf ya ƙalubalanci wani abu da Jamal ɗin zai faɗa akan Hajiya Kilishi.
Ba tun yau ba ya sani babu jituwa tsakanin yayan nasa da matar da yake mata kallon mahaifiya akan wani dalili da bai sanshi, don da ace tun daga farko yabi ta Hajiya kilishin ma, baza a taɓa samun shaƙuwa irin haka tsakaninsa da Jamal ba, sai dai soyayyar ƴan uwantakan dake tsakaninsu tafi karfin mizanin yadda yake jin matsayin Mamin a ziciyarsa.
"B... Haka suke maka a makaranta ko?"
Muryar Jamal ta katse shirun motar kamar yadda koyaushe ya saba daidaita al'amura a tsakaninsu. Sai ya juyo da murmushi ya kalle shi.
"Kai a duka friend's É—inka ba wanda yake kiranka da Bakori?"
Jamal ya girgiza kansa.
"Man, ni sunana mai daɗi ne babu wanda yake jingina min sunan wani ƙauye."
Ma'aruf yayi dariya yana sake maida kansa baya, kafin Jamal din ya sake magana.
"Ka gaya min bayan zama likita mai kake son kayi a rayuwarka?"
Ma'aruf bai taso da kansa ba, idanunsa na kallon rufin motar ya cije leɓɓensa alamun tunani, sai kuma ya girgiza kansa yace
"I don't know, let me just start figuring out that tukunna. (Ban sani ba, bari na dai fara gamawa da hakan tukunna.)"
Jamal ya gyada kansa har yanzu idonsa na manne da titin kafin yace.
"Ina so ka sani Ma'aruf ba kowa zaka dinga yarda dashi a duniyar ba, wani lokacin mutanen dake kusa da kai suna iya zamewa abinda makiyanka, ba a kowacce fuska mai murmushi ake samun so ba, ba a kowanne ido mai kyalli ƙauna take ba, wani zai maka murmushi Ma'aruf amma wuƙa yake caka maka baka sani ba, kuma ba lallai ka gane ba sai a lokacin da komai ya ƙure, ka san irin takun da zaka yi tare kowa. Kar ka tambaye ni me yasa nake gaya maka haka, kawai naji ina so ka sani ne don watakila zai amfane ka a gaba."
Sai a yanzu Ma'aruf ya sauko da kansa daga kallon saman motar, ya kalle shi sannan ya gyaÉ—a kansa.
"Its a good advice, (shawara ce mai kyau.) Nagode sosai."
Shima ya juyo ya kalle shi, wani irin kallo da Ma'aruf yaji kamar yana ratsawa har cikin ruhinsa, kamar bai gama gaya masa komsi ba, kamar akwai sauran wasu bayanan da bai gama kwancewa a cikin kalamansa ba, amma sai kawai shima ya gyaɗa nasa kan sannan ya juya ba tare da yace komai ba. Yawu ya zarce cikin maƙogwaronsa kafin ya juya shima ya kalli titin dake bangarensa.
"So are you letting me drive?" (Zaka bani tuƙin?)
Jamal ya girgiza kansa.
"Idan ka kashe mu fa?"
Ma'aruf yayi murmushi ya na cije gefen leɓɓensa.
"Shikenan, sai aje a gayawa su Baffa munyi hatsari mun mutu gabaÉ—aya. The end."
A yanzu shima da nasa murmushin Jamal yace.
"Idan kuma ni na mutu kai ka rayu fa?"
Tambayar ta doka wata irin fargaba a ilahirin a jikin Ma'aruf lokaci guda, amma sai yayi kokarin kore ta da sauri ta hanyar yin wani murmushin kafin yace.
"Sai in ajiye dukkan burin rayuwata a gefe in karbi matsayinka, inyi irin rayuwarka ta yadda kowa zai ga cewa Ma'aruf ne ya mutu ba Jamal ba."
"Har da ambition É—inka na zama likita?"
Ma'aruf yana jin wani iri a ƙirjinsa yace.
"Har dashi, ai ba zan iya rayuwa da wannan nauyin ba, komawa zanyi kamar kai in kashe wannan Ma'aruf É—in don bashi da amfani idan har babu kai."
"The man behind the shadows!"
Jamal ya fadi sunan wani film da yayi shige da abinda Ma'aruf din ya faɗa, film ɗin da a tare suka ganshi a cikin jirgi lokacin da Ma'aruf ɗin zai raka shi Cairo karɓo wasu takardunsa na makaranta, kuma tuno film ɗin yasa su yin dariya a lokaci guda kuma a tare.
"Naga wasu sababbin kaya a cikin leda a É—akin ka jiya, a ina ka siyo? Na daÉ—e ina neman irin Hoodie É—in nan."
Ma'aruf ya É—an tsaya alamun tunani kafin ya iya tuno kayan.
"Ohh! Ruƙayya ce ta kawo min, ban san inda ta siyo ba amma dai zan tambaye ta."
Jamal ya sake shafo gashin kansa, wani abu da yake É—abi'a kuma halayyarsa da kowa ya sanshi da ita.
"Yarinyar nan tana yawon kawo maka kyauta Ma'aruf."
"Na sani,." Itace kawai amsar da ta fito daga bakin Ma'aruf É—in bayan ya juya yana kallon titi.
"Ka san me? Ka san tana sonka?"
Ba shiri Ma'aruf ya juyo yana kallonsa.
"Yarinyar Æ´ar secondary Yaya? Ni kuma da nake shirin fara karatu a yanzu mai zai kawo wannan zancen? And the last time I checked kaine mai bani shawara cewa kar inyi saurari mata a yanzu."
Ya rufe bakinsa daidai lokacin da Jamal ya gama rage gudun motar ya sauka zuwa gefen titin a hankali sannan ya juyo shima ya kalle shi.
"Do you still wanna drive? (Har yanzu kana son kayi tuƙin?)"
Kuma murmushin da Ma'aruf ɗin yayi shi ya tsaya a matsayin amsarsa ya kuma kashe maganar Ruƙayyan da suka fara.
"Kuma kar ka kashe ni!"
Shine kalma ta ƙarshe da Jamal ya faɗa kafin ya buɗa ƙofar motar ya fita, shima Ma'aruf ya buɗe tasa ya zagayo don su canja mazauni, dukkaninsu suna dariya.
Minti goma bayan hakan, motar tayi katantanwa akan titi ta nufi cikin daji!
****
*Present Day.*
*Bakori Enterprises*
*10:05 am*
"Well since everyone is here, let's get started."
( Tunda kowa ya hallara, mu fara kawai.)
Ma'aruf ya faɗa a lokacin da mutum na ƙarshe ya zauna a zagaye teburin cikin Office din, kuma yana rufe bakinsa Daniel ya mike tsaye, Ya tafi gaba yayi connecting flash dinsa a lokaci guda da bayanan cikin slide dinsa suka nuna tar akan farin screen din wajen.
Ma'aruf yayi baya a kujerarsa yana saurarensa kamar yadda sauran mutane goma sha ukun dake zaune a round table din suka yi suma.
Meeting ɗin kamar kowanne ne da suka saba yi, bayani Daniel din din yake yi akan Growth and Development din kamfanin da suka fara cicciɓowa a ƴan watannin nan, kowacce kalma da Daniel ɗin ke fada da kuma diagrams din da yake nunawa daga slide din abubuwa ne dake faranta zuciyarsa suna sawa yana jin kamar ƙwaƙwalwar sa na daɗa washewa ne daga matsalolinsa, don tabbas daga bayanin da kuma yadda komai ke yin sama kowa a wajen ya san cewa sun yi mutuƙar kokari, mutukar kokarin da tun a yanzu a cikin kansa yake jin addu'o'in da Baffa zai yi masa a lokacin da ya kai masa report ɗin.
Yana zaune kyam yana cigaba da sauraren komai kamar wannan shine lokaci na farko da yaje jin bayanan, don baya son ko kalma guda ta wuce shi, baya ko kifta idanu yayin da hasken slide ɗin ke nunawa a fuskarsa, daga gefensa Faruk ne ke nasa danne-dannen a computer yana kokarin hada nasa presentation din da zai yi akan Compensation and Benefits. Ayyukan da suka riƙe shi tun jiya su suka sa bai kammala ba har yanzu, Allah ya sani yana ganin kokarinsa, don Faruk mutum ne mai himma da hazaka, don da babu irinsa a kusa dashi ya sani cewa dole ne labarinsa zai canja.
Tafin da Office É—in ya karaÉ—e dashi a lokaci guda ya shaida karshen bayanin Daniel, idonsa na tsaye akan percentage É—in da Daniel ya nuna na karshe akan screen din yayin da murmushi ya subuce a nasa lebben ba shima kamar sauran mutanen, don sun wuce kuma sun kere adadin nambobin waccan karon da suka zauna meeting.
"... Lastly I will like us to give this credit to our Diligent Manager Mr. Ma'aruf Mansoor Bakori, because without him, we wouldn't be where we are today."
(Daga karshe ina son mu mika jinjina komai ga hazikin shugabanmu, Mr. Ma'aruf Mansoor Bakori, don ba don shi ba, ba zamu ƙaraso wannan gaɓar a yau ba.)
A lokacin ne kowa ya juyo yana kallonsa yayin da sautin wani tafin ya sake karadewa, hatta Faruk sai da ya tsaya da aikin da yake yi shima ya shiga tafin tare da kifta masa ido.
Sai kawai ya mike tsaye yana sunkuyar da kansa alamun godiya, kuma a wannan lokacin ne kalamansa tare da na Jamal suka haska a cikin kansa.
_Idan kuma ni na mutu kai ka rayu fa?_
_Sai in ajiye dukkan burin rayuwata a gefe in karbi matsayinka, inyi irin rayuwarka ta yadda kowa zai ga cewa Ma'aruf ne ya mutu ba Jamal ba!_
This is you Yaya! (Kaine wannan Yaya!)
A hankali ya furta abinda yake fada a duk lokacin da ya zama sanadin samar da wata nasara a Kamfanin.
***
"Ka san ƙoƙarin da muka yi da mutanen RTL ɗin nan shine babban abinda ya sake ɗago da percentage dinmu."
Faruk ya faÉ—a bayan kammala meeting É—in suna zaune a cikin office dinsa. Faruk É—in ne zaune akan kujerar Ma'aruf É—in yana neman abu a cikin desktop din kan teburin yayin da Ma'aruf din ke zaune daga tsakiyar office din inda aka zagaya da wasu cushion chairs guda hudu da kuma tebur a tsakiyarsu, waya ce kare a kunnensa kuma da lama dukkan abinda yake saurare daga cikin wayar mai muhimmanci ne.
Kuma jin shirun da yayi bai amsa ba yasa Faruk matso da kujerarsa zuwa karshem teburin yana barin inda screen din ƙatuwar desktop din da ta kare fuskarsa. Kuma yanayin fuskarsa kadai ya gani ya san tare da wa yake wayar.
"Ka tabbata sunan da ya gaya maka kenan?"
Ma'aruf din ya tambaya fuskarsa babu wannan annurin da ya cika ta a Æ´an mintuna kadan da suka wuce wajen meeting din nan.
Aka sake wani bayanin a cikin wayar da yasa shi cije leɓɓensa sannan yace.
"Ku cigaba da rike shi kawai, zuwa gobe zamu yi waya."
Daga wannan maganar, Faruk ya riga ya san wa yake nufi ya kuma san ina zancen ya dosa, don shi yayi nasarar gano address din accountat din wadannan kamfanin da a baya suka gano cewar ta daliilinsu kamfanin Bakori yayi wannan asarar da aka kasa gano tushenta, wanda daga baya suka gano cewa kamfanin ne suka cuce su da alert din kudin karya bayan an gama yarjejeniyar komai, suka gabatar da shaidun biyan kuÉ—in ba tare da kuÉ—in ya shigo ba.
Don haka sanin cewa basu da hujjar zasu tunkare su kai tsaye yasa suka shiga neman accountant É—in mutanen wanda yake kan aiki a lokacin da abin ya faru Mr. Ishmael Grahm, kuma da kyar ya iya gano address É—insa a jiya bayan tafiyar Ma'aruf din Jigawa, kums a jiyan tun ya a can ya kira shi ya shaida masa hakan kuma bai jira komai ba ya nemi Æ´ansandan da ya sani suka hada shi dana garin Delta inda suka gano mutumin anan yake suka je suka kama shi duk a jiyan, don haka a yanzu ya tabbata dasu yake wayar suna shaida masa wani bayanin.
Ma'aruf ya sauke wayar daidai lokacin da Faruk É—in ya taso ya taho zuwa kujerar dake gabansa ya zauna.
"Me ya faru?" Ya tambaya yana kallon yanayin fuskar Ma'aruf din.
"Me muke dashi akan wannan Mr. Okafor din?"
Faruk ya girgiza kansa.
"Babu komai, har yanzu mutanen dana saka basu gama gano inda yake ba."
Sai kawai ya cillar da wayarsa akan tueburin dake tsakiyarsu kafin yace.
"Dole ne mu nemo mutumin nan Faruk, don duk amsar da muke nema tana wajensa, har yanzu na kasa gane yadda tsohon nan shi kadai ya shiga rayuwata da yawa haka."
"Me ya faru?"
Faruk É—in ya sake tambaya yanayin kan fuskarsa na jira bai tafi ba. Kuma sai da Ma'aruf É—in ya zura hannunsa a cikin gashin kansa sannan yace.
"Wahalar banza muka yi tayi Faruk, wannan dai Mr. Okafor din shi ya san komai, bai kamata ma mu cigaba da binciken ba bayan tafiyarsa, da ace mun dage wajen nemansa da watakila tuni mun gama da case din nan. Yanzu shi wannan mr. Ishmael din yayi musu bayani cewar Mr. Okaforn ne ya shirya musu komai a kamfanin, shi ya hada su da wani computer hacker daya turo mana da alert din kudin nan ba tare da kudin sun shigo a gaske ba, mu kuma a lokacin muka dauki kayan muka basu ba tare da anyi confirming ba, sai daga baya aka nemi kudin aka rasa shi yasa akayi wannan babbar faduwar.
Kuma har yanzu bamu da hujjar da zamu kai su kamfanin kotu tunda a baki ya shaida mana komai. Dole ne mu nemo shi Mr. Okaforn ya hada mu da wanda yayi musu aikin ko baza'a same shi ba a sami wata takarda da zata tabbatar mana da abinda suka yi wadda zasu tsorata su dawo mana da kudinmu ko kuma alkali yayi amfani da ita idan mun kaisu kotu a karbar mana ta hanyar shari'a."
Faruk ya haɗe girarsa biyu waje guda yana nazarin kowacce kalma da Ma'aruf ɗin ke fada cike da zurfin bincike irin wanda ƙwaƙwalwar sa ta saba akan abubuwa, kuma sai da ya gama fahimtar komai sannan yace.
"Idan haka ne B, idan wannan mutumin shi e a bayan komai me yasa yazo da kansa da a farko ya same ni yace zai shaida min abubuwan da muke nema? Idan har shine ƙusar aiwatar da komai me yasa zai bayyana kansa da wuri har yayi kokarin fallasa sirrinsu kai tsaye?"
"Ni kaina abinda nake tunani kenan."
Ma'aruf ya fada yana lashe leɓɓensa na ƙasa da yaji yana neman bushewa.
"Watakila a ranar da naje wajensa, da ban ga Hamida a gidan ba, da ace na zauna na saurare shi munyi magana watakila da tuni mun kawo ƙarshen wannan maganar, da tuni mun gama da case ɗin nan komai yazo hannunmu."
"Dole akwai abinda yake a ƙasa B, don ni yanzu jikina ma ya fara bani ba mu kadai muke neman wannan mutumin ba."
"Nima tunanin da nake yi kenan, don dole ne sai mun yi da gaske..."
Ya É—anyi shiru sai kuma ya É—ago ya kalle shi da sauri.
"Ka san me za'ayi? Ka nemo mana appointment da Yakubu kawai. Kar ya wuce yau zuwa gobe."
Faruq ya zare idanunsa.
"What?? B Yakubu? Yakubu dai Yakubun SS? Ka san kudin da mutumin nan yake karɓa kuwa yanzu?"
"Na sani, da kudina zan biya shi Faruk bada na kamfani ba, 'Cox a yanzu ban ga wata hanya da zamu iya neman mutumin nan cikin sauki ba tunda har su Salihu suka kasa, dole irin Yakubun zamu nema tunda dama shi irin aikinsa kenan, ko ni da kai muka tafi ba lallai muyi abinda shi zai yi ba."
Faruk ya gyaÉ—a kansa a hankali alamun ya fahimta daidai lokacin da wayarsa tayi kara daga can kan teburin, don haka ya miki yaje ya É—auka, kuma ganin number data fito a jiki yasa shi fadin.
"Excuse me." Sannan ya nufi kofa ya fita.
Kuma hakan ya tunawa da Ma'aruf missed call din Ishaq da ya gani a wayarsa shima har guda biyu, don haka ya jawo wayar ya shiga kokarin kiransa.
"Kana ina Kano ko Jigawa?"
Itace tambayar da Ishaq din ya fara yi bayan ya dauki wayar, kuma a lokaci guda kalmar Jigawan ta gifta masa da fuskar Amina, wani abu ya fada a zuciyarsa yana tuna masa da cewar rayuwarsa akwai canji a yanzu, a ƙalla duk bayan wannan hargitsin yana da wani waje da zai samu nutsuwa.
A dazu lokacin da suna hanya, lokacin da ya sata ta kwafar masa wasu lambobi daga cikin wayarsa zuwa daya wayar, yana tukin yana kallonta, yana kallon yadda ta nutsu sosai tana aikin da ya saka tan, kuma a wannan lokacin ne ƙwaƙwalwarsa ta fahimtar masa cewa irin abinda yake ji a zuciyarsa duk lokacin da yahe asibitin sa na MMB-6 haka yake ji idan yana tare da ita, wani irin buɗewa zuciyarsa take yi yana jin yana manta kowa dama komai sai iya abinda zai iya kawai.
Kuma ya san dalili, saboda ya fahimci duk abinda yace kawai shi take yi, duk abinda ya gaya mata shi zata yi ba irin Rulayya bace ita, Rukayya tana da ra'ayi tana da choices da expectations masu tarin yawa, shi yasa ko a lokacin aurensu da ya sa rai cewa zai samu nutsuwa a tare da ita, sai abubuwa suka canja, suka yi juyin waina don ita kullum cikin tuna masa da abubuwan da ya bari a rayuwarsa ta baya yake yi, abubuwan da yake a Ma'aruf É—in da ta sanshi dasu wanda baya yi yanzu, shi yasa shi da ita basu taba daidaitawa ba, don yana son barin baya ne ita kuma tana jawo shi.
Amma Amina da a yanzu bata san waye shi a baya ba, bata san komai game dashi ba, bata da tunanin komai balle har tasa ran cewa zaiyi abu baiyi ba sai yake jin hankalinsa na kwanciya duk sanda yake tare da ita, zuciyarsa tana kara amsawa da abinda ya fara ji akanta tunda daga ranar farko da ya ganta.
"Mun dawo É—azu."
Ya amsawa Ishaq din dake jiran amsarsa a cikin wayar.
"Honeymoon din har ya kare?"
Ba shiri ya zare idonsa.
"Ni na gaya maka abinda ya kaimu kenan?"
"Sai ka gaya min? Wane sabon labari ne wai baka son tuƙin dare, inaga har Kaduna munje ni da kai bayan isha."
Sai kawai ya koma da baya ya kishingiÉ—a da kujerar da yake kai yana guntun murmushi, ya cusa yatsunsa É—aya cikin gashin kansa.
"To ka gama aibata ni sai ka gaya min dalilin da yasa naga missed call É—inka har guda biyu."
Daga cikin wayar Ishaq yayi magana da wani don alama tafiya yake yi kafin yace.
"B kana sane jibi ne zaman shari'ar nan?"
"Yes, na sake duba takardar, na sani."
"Kuma har yanzu kana nan akan bakan ka ba zaka nemo kowacce irin shaida ba?"
"Eh." Ya tabbatar yana gyada kansa.
"Har yanzu baka gaya min dalilinka ba." Ishaq din ya sake fada a lokacin da yake tura kofar wani waje, don yaji karar da kofar ta bayar a cikin kunnensa kafin ya fara magana.
"So nake naga iya abinda zasu yi shi yasa na ɗauki wannan matakin Ishaq, Hamida ƴata ce, idan har zan rike ta it should be in a respectful way, bana son wani yaga cewa nayi amfani da ƙarfi ne na karɓe ta har ita Rukayyan kuwa, don idan hakan ta faru wasu abubuwan zasu biyo baya ka sani.
Shi yasa ba zanyi wani yunkuri ba Ishaq, don kamar yadda ka fada ne a yanzu doke shari'ar zata fi karkata ne a ɓangarensu ba. Wannan wasan nasu ne su suka kawo ƙarar nan don haka mu basu filin da zasu taka rawar su ba tare da mun ɓata musu ba, Cox idan na tashi nawa shirin Ishaq, ina tabbatar maka zanyi komai ne ta hanyar da za'a sami fahimta tsakanina da kowa, tunda a yanzu ina gujewa duk wani abu da zai jawo min tashin hankali Ishaq."
Tun daga farkon bayanin, aganganun ƙarshe su suka ɗauki hankalin Ishaq ba duka sauran abinda ya faɗa ba.
Kalmai ne kaɗai, amma tasirin da suka yi a zuciyar Ishaq suna da yawa, don shi ya san waye Ma'aruf, yana tare dashi tsawon lokaci tun daga shekarun farko na ciwonsa har zuwa yanzu, kuma a baya babu irin naci da ƙorafin da baiyi ba akan ya dinga duba yanayin ciwonsa kafin ya aikata abubuwa, amma rashin yin hakan shine babban abinda ya kawo su ga matakin ciwonsa na yanzu.
Sai dai ya fahimci cewa tunanin Ma'aruf ya fara canjawa tun daga ranar da ya farka a London ya gaya masa matakin da ya kai a cutarsa, ya lura ya fara canja abubuwa da yawa a rayuwarsa tun daga wannan lokacin, kuma a yanzu da yayi wannan auren nan, ya ƙara fahimta cewa yana samun nutsuwa tare da yarinyar nan fiye da aurensa na farko, duk da har yanzu ba zai iya cewa ga takamaimai tunaninsa game da ita ba.
Sun ƙarasa wayar yana yarda da tsarin Ma'aruf ɗin ba wai don zuciyarsa taso ba ko kuma a matsayinsa na lauya hakan ya san hakan daidai ne, sai don ya san cewa kome zai faɗa a wannan lokacin ba zai canja tunanin Ma'aruf din ba.
****
*Karfe biyar da rabi na yamma.*
Ƙafafun Amina suka fito daga cikin toilet ɗin ɗakin bayan ta gama yiwa kanta faɗa da gargadin wankan yamma, amma babu yadda zata yi ne, don a yinin ranar kaf wannan shine kaɗai lokacin da ta iya samu na yin wankan, wankan da take jin kamar ya zame mata dole ne don karkade tarin abubuwan dake yawo a cikin kanta, sai dai duk yadda ta kai ga goge jikinta tare da zubar ruwan bata jin ko kalma guda ta fara koɗewa a cikin dubunnan dake kanta balle tasa ran cewa zasu fita.
Idonta ya kai kan wayar dake yashe a gadon É—akin, wayar Ma'aruf ce da ya bata a safiyar yau bayan yasa ta debe masa nambobinsa zuwa cikin daya wayar tasa, bai ce ya bata ba har yanzu, amma zuciyarta na ayyana mata cewa hakan ce zata kasance.
Ta zauna daga gefen gadon ta ɗauko ta, ƙirar Samsung ce kamar sabuwa ma, ta tuna yadda tayi nacin samun wata Samsung kamar ba gobe lokacin da take ganin hotunansu a wayar Aminu, amma yau gata da Samsung ɗin a hannu kila ma wadda tagi waccan amma zuciyarta fayau take, babu ɗigon wani abu da zata iya dorarwa akan wayar koma wani abun a gefe.
Ta dawo ta tarar Tvn gidan ma an hada ta, an siyo reciver da komai jiya da basa nan an haɗa, Samirah ce ke gaya mata a ɗazu da ta shigo kawo mata jakarta da ta manta a ɓangarensu, don a ɗazu bayan fitowarta daga dakin Hajiya Kikishi rike da magungunan nan a hannunta, bata jin jijiyoyin dake cikin kwakwalwarta sunyi aiki mai kyau har ta iso ta dawo bangarensu.
Allah ne kawai ya taimake ta bata hadu da kowa a hanya ba kasancewar sagiya ce, in banda masu wanki da ta jiyo tarin hayaniyarsu daga can gefe da kuma su Mama Rabi dake shiga bangaren Inna Danejo suna gyara kasancewar yau zata dawo kuma cikin sa'a dukkansu basu kula da ita ba.
"Tarko biyu ta É—ana miki Amina."
Abinda Amma ta fara fada a wayar kenan bayan ta ƙaraso ta kira ta kuma ta gama sauraren dukkan bayaninta.
"Baki fahimce ni ba na sani kamar yadda kika kasa fahimtar hakan tun lokacin da kina gabanta.."
Muryar Amman ta cigaba da fitowa a lokacin da hatta yawun bakinta ya tsaya cak! saboda ruÉ—ani.
"Tace miki a yanzu magungunan sa sun dawo hannunki Amina, amma ta É—auko sauran da yake sha ta baki su? Ko kuma shi ta gaya masa cewa zai dinga karbar maganinsa a hannunki?"
Kuma tambayar ta wuce da wani shiru mai tambarin nazari kafin ta iya amsawa a a hankali.
"A'a Amma, wadannan din kawai ta bani."
"To kiyi tunanin ki gani Amina, da sunan maganin me zaki dauki waddannan ki bashi kai tssye? Wane bayani zaki yi masa da zai gamshe shi ya karɓa? Idan ma ya karɓa ɗin yasha kuma ciwon nasa ya biyo baya me kike tunanin zai faru? Daga shi har sauran jama'ar dake kewayensa me zasu yi tunanin akanki Amina?"
"Kowa zai zarge ni Amma."
Amsar ta fito kai tsaye tun daga zuciyarta, don babu wuya ta zaƙulo ta daga cikin tarin abubuwan dake yawo a cikin kanta, kuma kai tsaye itama Amman ta cigaba.
"Tabbas kowa zai zarge ki Amina, ai babu wani kewaye-kewaye akan hakan. Kilishi mugun ice ce na gaya miki, irinsu ne mutanen da zasu sa ka kashe kanka ba tare da ka san kana soka wuƙar ba, kuma na gaya miki tun farko, dole ki maida ƙwaƙwalwar ki ta koma irin tata Amina, dole ki dinga tunani irin wanda take yi idan ba haka ba a kurkusa zata dulmiyar dake ba tare da kin ya fahimta ba.
A yanzu ta baki iya wadannan magungunan ne don ta gwada ki, taga ta yadda zaki cika umarninta kuma ki kare kanki a lokaci guda, taga ta yadda zaki iya bashi magungunan ba tare da kin shafawa kanki jan fenti ba kema. Tunaninki take son ta gwada, taga idan har zurfinsa ya kai ta saka ki cikin lamuranta, sannan kuma a lokaci guda ta tabbatar idan har da gaske kin goyi bayanta kamr yadda kika ce, kuma ina tabbatar miki Amina, idan kika fadi ko guda daya a cikin wadannan tarkon nata biyu, shikennan kin fara rusa darajarki a wajenta.
Ba zata kore ki a lokaci guda ba, amma zata dauki wani mstakin kwatankwacin yadda tayi wa Aminu don ta ƙara tsorata ki, sannan zata ƙara gwada ki, idan akayi rashin sa'a a karo na biyu kika sake faduwa shima, zata juyo kanki ne a lokacin, zata lahanta ki ta yadda zaki ji a jikinki ki san da gaske take sannan ta sake gwada ki...."
Muryarta ta É—an tsaya kafin ta cigaba.
"... a karo na karshe ne Amina, idan ta sake baki wani abin kika kasa, ina tabbatar miki da cewar Kilishi zata iya rufe kawar dake gabadaya!"
A wannan lokacin Amina taji sanda zuciyarta ta buga a kirjinta kafin fatar bakinta ta shiga maimaita kalaman hasbunallahu wa ni'imal walkil da fatar babu tsayawa, kuma sai da Amman ta tabbatar kalaman sun gama shigewa cikin kanta wucewar wasu sakanni sannan ta cigaba.
"Amina, wannan abin da nake gaya miki gaskiya ne, don mutane irin Kilishi suna aikata abinda yafi haka ba tare da sunji ko É—ar! a ransu ba, shi yasa nake son tun a yanzu ki tattara hankalinki waje guda ki saurare ni, kiyi duk abinda nace, ki yarda da maganata ta cewar da kifi ake kama kifi, kin fahince ni ko?"
Ta san ta ɗaga kanta a lokacin kamar Amman na kallonta, amma bayan hakan ba zata iya tantance yadda zuciyarta ta dinga tsere a ƙirjinta ba, ta san kawai ta damƙe wata kwalbar turare dake gefenta a lokacin don tattara dukkan nutsuwarta, kuma bata san ya akayi hakan yayi tasiri ba, don tayi nasarar ture dukkan hargitsin daje cikin kanta ta cigaba da sauraren mahaifiyar tata.
"Ki narka magungunan a cikin lemo Amina ki bashi yasha ba tare da ya sani ba, ki kwantar dashi kamar yadda ta gaya miki ba tare da shi kansa ya sani ba Amina, ki nunawa Kilishi da gaske kike kin goyi bayanta, ki buɗe mata zuciyarki ta yadda zata sakanksnce ta karɓi yardarki, ki nuna mata zaki iya, zata ga hikimarki, zata jinjina miki, kuma zata jawo ki jikinta. Wannan shine matakin farko da zamu fara cin nasara akanta Amina."
Ta sani cewa ta yarda da dukkan maganganun mahaifitar tata, ta san haka ne, ta san gaskiya ne... Ta san wannan itace sahihiyar mafitarsu, amma zata iya? Zata iya? Idanun Ma'aruf kawai idan ta hango sai zuciyarta ta ƙara nanata mata cewar ba zata iya ba, ba zata iya ƙarawa akan wahalar da yake sha yanzu a rayuwarsa ba, idanunsa kadai idan ta kalla tana jin kamar zata iya tsinto tarin abubuwan dake damunsa ɗaya bayan ɗaya, yana yawo dasu a kirjinsa da kuma kafaɗarsa.
To ta yaya kuma zata iya zama karin wata matsalar bayan duk bayanin da yayi mata jiya cewa yana son samun sauƙi a wajenta? Bayan haka ma idan tana tare dashi ta lura cewa ƙwaƙwalwar ta bata iya tuna duk wannan hargitsin sosai mantawa take da komai kawai sai shi da ka nasa maganganun.
Wani abu ya wuce ta makogwaronta da ba ta san meye ba, taji hannayenta da ta rike wayar dasu duka biyun suna rawa, sai kawai ta ajiye ta a gefe sannan ta mike, man da take shafawa tun zuwanta gidan ta dauko akan mudubi, har zata bude sai kuma ta tsaya tunanin anya ba fari yake sata ba kuwa, don ita kanta taga ta canja kwana niyu sannan ma Aminu yana ta tsokanarta cewa tayi haske, kuma ta san wannan ba sharrinsa bane.
Don haka ta shiga duba jikin robar kuma gabaÉ—aya babu inda aka rubuta hakan sai ma wasu abubuwa dake shaida mata tsadarsa, har yaushe zata dinga tunawa ne cewa masu kudi ta aura? Don tabbas a cikin wannan auren nata mazajen biyu ne, Kilishi da Ma'aruf sannan matan ma biyu ne ita da Amma, kuma kowa da irin rawar da yake takawa.
Sai kawai ta cije lebbenta da murmushi tana tuno kalaman Hajiya Kilishin na ƙarshe kuma mafiya tasirin da suka fi zama a zuciyarta.
_Ba zan hana iya Ma'aruf kula ki ba idan har yayi niyya, amma ba zan dauki wani abu wai shi ciki ba...!_
Bata shaidawa Amma wannan zancen ba don ta yarda daga Kilishin har Amman wannan ba huruminsu bane, wannan yaƙinta ne kamar yadda Amma ta gaya mata, kuma ta yarda ba komai Amman zata iya mata ba, don kamar yadda ta fada mata ne ita hanya kawai take nuna mata amma duk wani taimako da zata yiwa kanta yana hannunta, dole ne sai ta tsaya da kafarta ta fuskanci nata yakin, don haka ba zata dorawa Amma wannan nauyin ba.
Kuma Hajiya Kilishi bata isa ta yanke irin wannan kaddarar tata ba, wannan huruminta ne, hakkinta ne, idan ta yarda da Ma'aruf, bata jin akwai wani mutum kuma a gefe da zai gaya mata yadda zata yi da jikinta ko ma abinda zai zama rayuwarsu a gaba.
Wani murmushin ne ya sake subucewa a bakinta da wannan tunanin, wai rayuwarsu? Ma'aruf din da har yanzu bata dan me take ji game dashi ba, ta san dai kawai zuciyarta ta narke jiya da tayi bacci a cikin hannunsa, kuma bata gama bushewa ba sanda ya sake rungume ta a yau, amma a cikin wannan gulbin zata tsinto cewa tana tsananin ganin kwarjini da kuma girmansa, watakila shi yasa take manta komai idan yana gabanta.
Wata doguwar riga ta É—auko (flowy and Maxi) kalarta fara ce, a jikinta anyi mata prints É—in lilac flower kalar Pink da kuma Pitch, hannunta ya bude har zuwa rabin nata hannun, kalarta tayi kyau sosai da kuma É—aukan hankali, amma ita ba wannan yasa ta dauko ta ba, rashin nauyin ta ne tasa ta zabo ta don shafal take sosai, tana daga cikin kayan da Aunty Safiyya ta bata, kuma ko sanda ta bata É—in sai da su Aunty Ma'u suka yi ta É—aga ta suna fadin laushi da kuma rashin nauyinta.
Don haka abinda ta tuna kenan a yanzu ta lalubo ta, don tare da nauyin dake zuciyarta dama cikin kanta bata jin zata iya da wata atamfa ko makamancin hakan. Tana da mayafi shi fari ne gabadaya, ta sake taje gashinta ta daure shi sannan ta daura mayafin akanta.
Hannayenta har yanzu rawa suke, amma ta san tunda basu yi komai ba tun sanda tana girkin da tayi da kyar a cikin tarin tunaninta, to yanzu ma babu abinda zai same su.
Bata ko saka slippers din da take yawo dashi a cikin gidan ba ta fita daga ɗakin, sanyin tiles din gidan na ratsa fatar ta har ta isa falo, idonta ya kai kan ƴar jar fitilar Tv da ta kama tana tuna mata cewa zata iya kunnawa a yanzu, amma bata hango kallon ko a ƙarshen lissafinta na yau, don haka ta juya Kitchen don karasa abinda ke gabanta.
_....ina son É—anwake ma._
Shine abinda ya gaya mata jiya a cikin abincin da yafi so, shikenan sai ya zama saukinta itama, Samirah kawai ta kira a waya tace a taimaka mata da kanwa da kuka, nan da nan kuwa ta gama abinta, dama tana da yaji mai daɗi da Samiran ta kawo mata tun kwanaki, ta yanka vegetables a gefe guda don bata sani ba ko yana so, sannan ta hada haddadden zoɓonta da ta kusan shanye rabi kafin ta zuba a jug.
Yanzu ma fridge ta buɗe ta sake debo shi a kofi da niyyar ta koma ɗaki ta fito da kayan da ta tara na wanki kafin magriba tayi, kuma ta fito daga kitchen ɗin daidai lokacin da taji ƙarar ƙwanƙwasa kofar gidan, ƙara guda uku da yatsa daya, don haka ta riga ta san ye duk kuwa da cewar bata ji karar bude gate ba.
Sai kawai ta ajiye kofin hannunta a gefe Tv wata zuciyar ta gaya mata cewar ta kwance mayafin ta yafa shi amma wata zuciyar ta kore hakan kai tsaye.
****
Da wuri ya bar Office yau, don yana yin sallar La'asar ya fito tunda sun riga sun gama dukkan abinda zasu yi na yau, dawowar Baffa a gobe kawai ake jira a gabatar masa da komai kafin su fara fuskantar wasu sababbin ayyukan.
Kuma bayan shigowarsa gida kai tsaye ciki ya nufa, yayi minti goma da kyar a ɓangaren Hajiya Maimuna kafin ya fito ya nufi inda yafi wayo, a falo ya kuwa tadda Mamin ita kadai tana zaune tana waya da wani faffadan murmushi a fuskarta, kuma har ya zauna bata gama ba sai dai ya lura bata ƙara cewa komai ba bayan sauraren da take yi.
Ta ajiye wayar yana tsokanarta cewa Allah yasa kwangila ta samo musu kafin su gaisa, sunyi hirar shari'ar Hamida dake shirin faruwa a jibi inda ta dage akan cewar kar ya yarda ya mayar musu da ita gwara ya dawo da ita wajensa kamar yadda ta jaddada masa tun farko, kuma haka kurum sai ya samu kansa da amsa mata kawai ba tare da ya baiyana mata irin tsarin da yayi ba.
Daga nan suka shiga hirar wani sabon gidan gona da take son buɗewa, tana cewa zata ɗora shi a matsayin manajan wajen yana roƙonta ta taimaka ta rufa masa asiri abubuwan dake gabansa sun ishe shi.
"Mami Slides É—ina ne zasu haÉ—e dana kaji, sai nazo ina presentation a meeting kawai in buÉ—e kaji suna cin abinci. Baffa will sack me for days."
Dariyar da take ƙyalƙyale da ita, dariya ce dake fitowa tun daga ƙasan zuciyarta, kuma shi kansa ya sani cewa ko tare da Baffa bata irin wannan nishadin balle kuma duk wani wanda zai biyo bayansa, shi daban ne a lissafinta ba sai ya rantse ba ya sani, ya san Mami na kaunarsa da dukkan irin ƙaunar da uwa ke yiwa ɗanta, wani abu na gaya masa cewa zuciyarta tana yin fiffike ne ta tashi sama ta zagaya a duk lokacin da yake zaune a gabanta irin haka, shi yasa a kullum yake addu'ar Allah ya bashi ikon faranta mata a tsawon rayuwar da zaiyi.
Ya baro cikin gidan da wannan farin cikin a zuciyarsa ya iso bangarensu, kuma har zai buɗe ƙofar da mukullin dake jikin na motarsa, sai kuma ya fasa kawai ya kwankwasa, sau daya biyu, uku yayin da yake tsaye dab da ƙofar hannayensa harde a kirjinsa. Kuma ba'a wani jima ba, aka murɗa handle din a hankali sannan jikin ƙofar yayi baya.
Ba shiri Ma'aruf yaji wani murmushi ya sauka a lebbensa, don duk yadda zuciyarsa ke hassaso masa yadda zai dawo ya ganta, a yanzu ta wuce hakan, a lokaci guda kalolin rigarta dama yadda ta rigar ta zauna a jikinta suka É—auki hankalinsa, yaji wani abu ya motsa a cikin kirjinsa, sai kawai ya cije lebbensa yana murnushin kafin yace.
"Assalamu alaikum."
"Wa'alaikum salam."
Ta amsa a hankali tana sakin hannun ƙofar, ƙafarta tayi taku biyu zuwa ciki amma sai ya cigaba da tsaiwa bai shigo ba, kuma har tana kokarin juya ciki jikinta ya bata cewa a tsaye yake don haka ta juyo ta sake kallonsa, yana tsaye a yadda yake, ya harde hannuwansa a ƙirji yayin da wayoyinsa da kuma muƙullin motar da ya rike ya fito ta kowanne gefe, mamaki ya nuna akan fuskarta don haka ta dawo ta tsaya kuma kafin tayi magana sai kawai yace.
"I'm sorry, ina neman wata ne mai suna Amina, ance min anan take, zaki ganta wata ƴar ƙarama haka tana da idanu masu kyau, kuma ta iya murmushi."
Ba shiri murmushin ya suɓuce a bakin Amina, murmushi da ya fito tun daga zuciyarta saboda da gaske ya bata dariya, yadda yayi da fuskarsa idan tare da wani ne zai rantse cewa da gaske kwantancen yake yi, kuma haka kurum sai taji wani abu a cikin ranta yana wucewa, don haka ta girgiza kanta a hankali tace.
"Bana jin na santa."
"Saboda me?" Muryarsa ta fito tare da godiyar biye masan da tayi.
"Saboda ni kaÉ—ai ce Amina anan, kuma ni duk ban kai yadda ka fada ba."
Ta sake faÉ—a a hankali tana murza yatsunta. Ya kalli yatsun nata sannan yace.
"Zaki yi mamaki idan nace miki a yanzu kinfi ƙarfin kwatance na ma, you look stunning Masha Allah."
Amon muryarsa na fitowa da zurfi.
Murmushin ta ya ƙaru a lokacin da take kallonsa har yanzu da mamaki a fuskar ta, sai kuma yayi saurin girgiza kansa kamar ya tuna wani abu sannan yace.
"I'm really sorry na manta ban tambaye ki ba idan Aminar da nake nema matar aure ce, kar in kwana a inda ban shirya ba."
Murmushin ta ya sake karuwa kafin ta É—aga kanta sau biyu tana cije lebbenta.
"Ya Salam!" Ya faÉ—a yana sakin hannayensa.
"Saurin me kika yi haka? Me yasa zaki yi aure tun yanzu?"
Sai da ta zare idanunta tana dariyar da bata san daga ina take fitowa ba kafin tace.
"Saboda me?"
A lokaci guda ya karaso, ya tako zuwa cikin falon, ya tsaya dab da ita sannan yace.
"Cox I want you, bai kamata ki auri wani ba, ko Allah ya san nine mijinki."
Sai da Amina ta cije lebbenta sannan ta rufe idanunta tana murmushi, kuma kafin ta buÉ—e idon ya sunkuyo daidai gefen fuskarta yace.
"I apologize if this is a little bit forward, but you just look so.... Woww!"
Abinda taji kenan kafin taji ta a cikin hannayensa. Numfashinta ya yanke daga huhunta a lokaci guda, ƙafafunta suka karbi hannayenta wajen rawa, zuciyarta ta sake komawa ruwa, ta sake komawa irin duniyar jiya, duniyar da take manta komai sai Ma'aruf kawai da irin abubuwan da yake nuna mata.
Ya tallafi fuskarta kaÉ—an yana sawa ta kalle shi, don ko kaÉ—an ta kasa rufe idanunta ma yanzu, idanunsa cikin nata yace.
"You are making my world so much more beautiful Amina."
(Kina kara ƙawata duniyata Amina.)
Shikenan! Sai komai a cikin kan Amina ya sake rushewa, kalaman Hajiya Kilishi har ma dana Amma dake kokawar miƙewa, dukkan wani abu mai hankali a cikin kanta ya shiga gaya mata cewar da gaske ne ba zata iya taba lafiyar Ma'aruf ba!
*****
A cikin dakin, a cikin wayar, muryar Hajiya Kilishi ta ratsa da tsananin yaƙinin dake fitowa daga zuciyarta.
"Mahaifinta shine a lissafi Awwalu, munyi wata ya shaida min cewa sun dawo É—azu, don haka gobe zai fita aiki ina so ka fara bibiyarsa tun daga safiya, duk inda zaije ka kasance tare dashi kuma a shirye, wa'adin lokacin zuwa yamma ne kamar na yaron nan. Idan har ban sami abinda nake so zuwa sannan ba, zaka ga umarni na."
Daga cikin wayar Awwalu yayi dariya mai cike da mamaki yace.
"Mutumin nan fa shine ɗanuwanki Kilishi, ina laifin ki sake taɓa wani daga cikin ƴanuwan nata kawai? kuma shi bashi da wata matsala ma naga, let the man be! Ki duba iyalinsa ki kyale shi."
Ko bai ganta ba ya san ranta a hafe yake sanda tace.
"Tun yaushe muka fara la'akari da wani abu a cikin lamuran mu Awwalu? Ka amsa min kawai, bana buƙatar dogon surutu."
Sai ya sake kyalkyalewa da wata dariya mai armashi irin tasa sannan yace.
"An gama Hajiya, umarninki shine abin aikatawa ta!"
**
_Ku gaya min cewa Amina tana shirin kaimu ta baro..._
_Ko kuma laifin na Ma'aruf ne?_
_Ga dai mafita tiryan-tiryan Amma ta fitar, amma kamar Amina kuma kuna ganin cewa da matsala?_
_To wace matsalar kuka zaba?_
_Ta Amma dake cikin mafitar?_
_Ko kuma ta Kilishi da zata biyo baya?_
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:49 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*02*
~~~~~~~
_The act of love is Confession._ _- Unknown_
**
*Shekaru Goma da suka wuce.*
*Ƙarfe takwas na safiya.*
A bakin titi ne, daidai bayan dogon banki wajen da Babu mutane sosai musamman a safiya irin haks, motar da Hajiya Kilishi da kuma Awwalu take tana daka fake a gefen titi an zuge duka gilasanta da bakin tint mai duhun gaske, don musamman don wannan fitar Hajiya Kilishin tace da Awwalu yaje ya saka tint É—in.
A cikin motar, Kilishin taja tsaki tana kallon agogon tsakiyar dashboard kafin tace.
"Mutanen nan sun fara vata mana lokaci Awwalu, saninka ne fa ko Baffa bai san na fito ba."
Awwalun dake gaba mazaunin direba ya gyada kai shima yana kallon titin yace.
"Ki bari kawai, ni kaina ina da aji ƙarfe takwas ɗin nan, kuma wallahi mai muhimmanci ne."
"Aji?" Da mamaki a fuskarta ta tambaya.
Sai ya juyo ya kalle ta.
"Au na manta ban gaya miki ba, na koma makaranta fa, Bayero na samu ina yin English saura shekara É—aya ma na gama."
Kilishi taji ranta ya kara baci, har tana shirin bude baki tayi masa korafin ta yadda har ya shekara biyu a University ba tare da ta sani ba sai kuma taga meye damuwarta a ciki? Rayuwarsa ce, zata hana shi ne idan har hakan ba shafarta zaiyi ba, kuma ma tun asali ta san Awwalu mai son karatu ne, don tun yana yaro farkon zuwansa almajiranta da kudinsa yasa kansa a makaranta har ya gama firamare kafin daga baya kakarta ta shiga tallafa masa, kuma shekaru biyu bayan ta gama shima ya fita daga sakandiren, don haka karatunsa bai kamata ya dame ta ba.
Ta juya tana kokarin kallon wani mai teburin shayi daga can nesa dadu dake ta kokarin hada wutar itacensa, amma itacen yaƙi bashi hadin kai duk kuwa da iskar sanyin da ake hurawa a lokacin. Ba shiri taji murmushi ya subuce a bakinta, zuciyarta ta cika da jin dadin yadda dattijon ke ta goho yana firfita wutar, tana son irin wannan abin, tana son taga wani nata wahala akan neman bukatunsa har sai zuciyarsa ta ƙeƙashe ta daina rauni, shi yasa ko kallo bata cika yi ba, don bata ganin amfanin yadda mutane ke tsara finafinan su cewa mai kirki ne zai ci galaba a kodayaushe.
Taja tsaki bayan wutar ta kama babu daɗewa, ta dawo da idonta cikin motar tana ƙoƙarin lalubo wayarta, sai kuma ta tuna ai ta kashe ta don kar ma a neme ta, kuma a daidai wannan lokacin sai ga wata mota katuwa ƙirar jeep Prado tazo ta sha gabansu, nesa kadan tayi fakin ta tsaya.
"Ina ga gasu nan Hajiya."
Cewar Awwalu yana kallon motar.
"Fita zanyi kenan?"
Ya gyaÉ—a kansa.
"Ai bana tunanin shi ne zai fito."
Sai ta kuma jan wani tsakin.
"Mutanen nan suna cin alfarmarta da yawa Awwalu, ba don dole Jamal ya bar duniyar nan ta hanyarsu ba, bubu abinda zai hana ni zaba musu irin tasu ƙaddarar su ma."
Awwalun ya juyo yana kallonta.
"Haƙuri zaki yi Hajiya minti biyar ne ba su isa su sake ganin fuskarki ba har abada, harbin tayar mota tana gudu ba aikin kowa bane banda irinsu da suka san duk wani tactis na abin...."
Bata ko jira jin ƙarshen zancen nasa ba ta sauke nikabin da ta daura a fuskarta sannan ta janyo wata ƴar madaidaiciyar jaka dake gefenta tare da wata farar takarda ta bude kofar motar ta fita.
Kanta tsaye ta isa wajen motar ta tsaya daga daidai ƙofar baya, kuma daga inda Awwalu ke zaune yana hango sanda aka zuge gilashin ita kuma tasa hannu ta sake ɗage nikabin nata.
Wani mutum ne zaune a ciki, fari tas dashi irin farin da yake komawa tamkar zabiya, sannan ilahirin fatarsa kaf, koina akwai wani ɗigo-ɗigon bakin wani ciwo da ya fito ya warke. Idanunsa na sanye da wani katon gilashi baƙi ta yadda ba'a ko ganin kwayar idanunsa, a lokaci guda yayi wani murmushi da ya baiyana jerin haƙoransa wanda rabinsu suna rufe da ƙarfe ne irin wanda ake cewa hsƙorin makka kalar ruwan gwal don haka sun haska tar a cikin hasken safiyar.
"Barka da zuwa Hajiya, sai haƙuri da irin aikinmu na gaya miki ni bana mu'amala da jakada, shi yasa kika ganni nima da kaina."
Hajiya Kilishi bata yi murmushin ba, tana kallonsa idanunta a tsaye tace.
"Tun da har ka ganni anan ai ka san wannan maganar ta wuce kuma."
Sai ya É—aga mata girarsa daya cikin duniyanci irin nasa sannan ya nuna jakar hannunta yace.
"Sune wadannan?"
Sakan ɗaya biyu tana kallonsa hankalinta na kokarin danne takaicin dake yawo a zuciyarta kafin ta ɗago jakar ta miko masa, ya kuwa karɓa ya zura ta cikin motar sannan ya buɗe, idanunsa suka yi nazarin kuɗin dake ciki.
"Kince yau da misalin karfe tara zai fita sannan shi kadai ne a motar ko?"
Ta gyada kanta sau É—aya sannan ta mika masa wannan farar takardar hannun nata.
"Ga lambar motar koda wancan text É—in ya gige."
Ya karbi takardar ya kalla sannan ya sake É—agowa ya kalle ta.
"Hajiya zan so ace babu magana biyu a cikin wannan al'amarin namu, zamu ƙirga kudin nan idan sun cika zaki ga aiki, idan kuma akwai matsala, to kuwa za'a sami matsalar da gaske."
Sai da ta É—auke kanta gefe cike da takaicin yadda yake mata maganar sannan tace.
"Idan kuma har babu matsalar ta yaya zan tabbatar da cewar zaku yin?"
Ta dawo da idonta kansa lokacin da yake sake wani murmushin.
"Tabbaci kike nema?"
Bata amsa ba, shima kuma bai jira amsar ba, sai kawai ya É—aga yatsansa É—aya a iska yana cigaba da murmushi.
Kuma bata gama tunanin me Ke shirin faruwa ba lokacin da ta wata irin ƙara ta baƙunci iska, tsananin karfin ƙarar yasa duk dauriyarta sai da ta firgita, kafafunta suka yi baya yayin da tasa hannayenta duka biyu ta toshe kunnuwanta lokacin da idonta ya kai kan wasu maza da suka juya da gudu bayan sun karyo kwana, sannan ta hango wannan mai shayin ma ya kwanta a gaban teburinsa yana kakkarwa, tabbas ƙarar ta bindiga ce ba wani abu ba.
"Wannan shine tabbacinki Hajiya, yarana basa wasa da aikinsu, hannu kawai nake É—agawa shikenan duk abinda nace zai wakana ko akan waye kuwa."
Bayaninsa yazo daidai da lokacin da idonta ya sauka akan tayar motarsu ta gaba, gabadaya ta dagargaje ta kuma wargaje a lokaci guda, motar ta tuntsira tayi gefen titi, yayin da Awwalun dake ciki ke kokarin buÉ—e kofarsa don ya fito kar ta kara hantsilawa dashi.
"Na barki lafiya."
Ta sake jin muryar mutumin kuma ko kafin ta juyo ta kalle shi, direbansa yaja motar sun yi gaba da wani irin saurin da har sai da tayar motar ta gurzu da titi ta bada wata irin ƙara.
Babu shiri murmushi ya subuce a bakin Hajiya Kilshi karo na farko a wannan safiyar, tabbas ta bakin Awwalun ne, mutanen nan sun iya aikinsu, rainin hankalinsu ne kawai a gefe. Taji murmushin nata na sauka har cikin zuciyarta da tunanin cewa ba za'a samu akasi ba, a yau Jamal zai bar duniyar nan, ai ta gaya masa... ta gaya masa lokacin da ya juya mata baya zai tafi.
_"Na so zan yi dukkan shirina in bar cikinku ba tare da na taba wani ahalin Baffa ba, nayi maka katanga mai yawa Jamal, na daɗe ina kange ka daga sharrina, amma ka rufe idonka ka tsallako ka iso... Ina jiye maka takaicin barin duniya da ƙuruciyarka, ina taya ka alhinin barin duniyar nan a lokacin da ya kamata ka fara cin ganiyarka, don daga yanzu ni da kai, mutane ne da baza su taɓa iya rayuwa a lokaci guda cikin duniyar nan ba."_
Ta sake wani murmushin tana cije leɓɓenta, zata so ace zai tuna wadannan maganganun nata a lokacin yake bin ruhinsa da kallo zuwa sama. Awwalu ya karaso wajenta a lokacin da nasa murmushin shima, fuskarsa na ɗauke da yanayin da ko bai furta ba ta san me zaice.
_"Me na gaya miki? Mutanen nan zasu iya aikin ki."_
Sai kawai ta juya ta kalli motar tasu a lokacin da Jama'a suka fara taruwa suna ƙoƙarin zagayeta.
"Zaki yi waya a kawo mana wata motar ne?"
Ya tambaya, ta girgiza kanta.
"Baka da zurfin tunani Awwalu, ta yaya hatsarina zai zo rana daya dana Jamal? Tsaftataccen aiki nake yi a kodayaushe ka sani, bana yin sajacin da zan bari ko da É—igon baki da zai kawo zargi a zuciyar wani na."
Awwalu ya gyaÉ—a kansa yana cigaba da wani murmushin kafin yace.
"Na yarda dake wallahi Hajiya."
""Kaje ka siyo wata tayar, a daura sai mu tafi."
Kuma wadannan kalaman nata na lokacin sune tushe, shine sanadin faruwar wasu abubuwan da har a yau ba'a warware su ba, don Awwalu ya dauki tsawon lokaci kafin ya iya samo sabuwar taya da kuma mai daurata kasancewar safiya ce lokacin, don haka kafin su koma gida matafiyan nan sun tafi.
"Mami, Ya Ma'aruf ya shigo yace ya kira wayarki a kashe, yace idan kin dawo in gaya miki ya bi Ya Jamal zuwa Abujan, zaku yi waya idan kin dawo."
Kalaman da Salma ta faÉ—a mata kenan bayan ta koma gida da misalin karfe goma saura na wannan safiyar.
Kuma a tarihin rayuwar Kilishi kaf! Idan zata misalta kalmar tashin hankali, zata kwatanta ta ne da wannan ranar, ranar da zuciyarta ta buga a kirjinta, kafafunta suka zube gar a ƙasa yayin da idonta ya shiga hasko mata gawar Ma'aruf din da bata tsara a lissafinta ba tare da ta Jamal!
***
*Present Day.*
"Halima."
Alhaji Sulaiman dake zaune a cikin É—akinsa ya kira sunan matarsa dake shirin sa kai ta fita bayan ta ajiye masa flask din ruwan zafin da ta dafa a dawowarsu yanzu da safen.
Tsintsiya ce a hannunta wadda ta dauka don zuwa ta kara share falo inda aka kwantar da Aminun, taso ace tun jiya su Maryam sun zo sunyi sharar kafin su dawo, amma haka kurum ta kasa kiran iyalan gidan Kawu Malam inda su Maryam suka tafi da wannan umarnin, tana da kawaici akan Æ´aÆ´an ta kowa ya sani, abinda mutane basu sani ba shine tana ajiye wannan kawaicin a gefe idan har aka zo gabar da za'a cutar mata dasu.
A kofar dakin ta saki tsintsinyar sannan ta juyo ta dawo ciki, don daga yanayin amon muryar Baban ta san magana ce mai muhimmanci zasu yi.
Ta sami waje gefensa ta zauna yayin da idanunta farare irin na Amina sak ke kallonsa, kallo na saurare da kuma jiran umarni.
"Jiya na hango ki kina waya da Æ´arki."
Ta gyada kanta sau É—aya bayan ta gane cewa Amina yake nufi.
"Akwai wata matsala ne da take fuskanta a gidan?"
Mamakin tambayar tasa ya kamata, sai kawai ta sunkiyar da kanta kasa a hankali, a shekarun zamanta dashi kaf! ya sani ko da sau É—aya bata taba zuwa ta bashi labarin wata matsala ba walau ta danginta ko kuma ta wani da ya shafe ta ba kuma shima baya taba tambayar abu makamancin hakan ba sai idan har zancen ne yazo a dole su fade shi, don haka abinda ba'ayi a baya ba, ba za'a fara shi yanzu ba.
Amina yarsa ce, ta san yana da hakki akanta amma a tunaninta ya riga ya gama taka rawarsa akanta, yayi ruwa yayi tsaki wajen kaita rayuwar da babu ta hanyar da bata kalubalance shi ba. Shi da kansa ya fada cewa ba zai iya tuna ranar da tayi masa musu akan wani abu ba, amma bai ko duba wannan kawaicin nata na tsawon shekaru ba, da yake shi namiji ne ya rufe idonsa ya juya mata baya, ya dora yar tasa a wani mizani da dole nasa umarnin zata dauka.
A yanzu anyi hakan, komai ya wuce ba tare dacta nuna fushinta ba, kuma gashi sun fara fuskantar kalubalen da ta guje musu shi, to don me yasa zai tambaye ta kuma?
Ta fahimci har yau Sulaiman bai gama buɗe halayenta ba, don da ya san wacece Halima da bai ɓata bakinsa ma wajen tambaya ba, bata gori, bata cewa 'dama na fada...' zata yi iya kokarinta ne a farko don ganin ta kawar da matsala daga karasowa gare ta, idan kuma ta kasa, sai ta fara shirin tunkararta ta hanyar da zata iya kawar da ita, wannan shine babban abinda ke riƙe da zaman lafiyar gidanta dama zamanta tare dashi. Shi kansa idan zai tuna yana da zafi da kuma zuciya a lokacin kuruciyarsa har zuwa aurensu, amma da wannan halayen nata ta canja shi a lokacin da bai ma sani ba.
Don haka sai ta gyara zamanta kawai a hankali sannan ta girgiza kai.
"Babu wani abu, wata yar matsala ce kawai tamu ta mata."
Ya kalle ta tsawon wasu mintuna kafin ya sake kiran sunanta.
"Ina fata a yanzu kin daina ganin laifina Halima, don kowa shaida ne daga ganin yarinyar nan an san tana cikin nutsuwa."
Babu shiri murmushi ya subuce a bakin Amma, mazan kenan! bata jin har abada za'a zo lokacin da kwakwalwar kowanne namiji zata bude game da al'amarin mata, suna ikirarin sun san komai a kullum, amma tarin abubuwan da ake lullube su a ciki suna da yawa, wanda hakan na ɗaya daga cikin abubuwan dake juya duniya, don da zasu san kowacce kissa da dabara irin ta matan to da zaman auren ma zai gagari kowa ce ƙabila a duniyar nan.
Tun a lokacin da aka jawo kayan kefen Aminan kallo ɗaya tayi wa akwatunan da aka zuba kayan kwalliya zuciyarta ta ɗarsa mata wani abu da sai a yanzu take ganewa. Kilishi ta narka maƙudan kuɗaɗe na gaske wajen siyan tsadaddun kayan gyaran jikin da zasu karbi fatar Amina, ta yadda a waje kowa zai sanya ta cikin layin nutsuwa da kwanciyar hankali da kallo daya, yadda komai zurfin da zuciyarta zata yi babu mai iya gano hakan don za'a shagala da kallon canjawar fatarta maimakon damuwarta, gashi kuwa hakan ya fara aiki har akan mahaifinta da ya kawo ta duniyar nan, wai sau nawa ne zata fada? Kilishi mugun ice ce da gaske!
Sai kawai tayi wani murmushi a hankali sannan ta gyada kanta tace.
"Haka ne."
Shima ya gyada nasa kan.
"Sai dai mu bisu da addu'ar dorewar zaman lafiya.
"Tabbas kuwa."
Amman ta sake fada tana jin wani abu kamar raha na ratsa zuciyarta, tana ƙara yarda cewa mata duniya ne, Allah ya basu damar juya namiji duk girma da tsufansa a tafin hannunsu, kawai da yawa ne basa amfanin da danarsu.
"Mun yi waya da Kawu Mallam yanzu, yace za'a rako su Maryam din anjima, tunda kike ta kallo na a hanya na san abinda kike so kice in tambayo miki kenan."
Ta girgiza kanta.
"Ni ban aike ka ba, idan zasu kara kwana ma ba zan damu ba."
Kice zaki iya bacci babu Hafsatu a gidan nan?" Ya tambaya
"Kafin in same ta fa?"
"Kina da Amina."
Sai kawai ta mike tana dariya, ta ɗauki tsintsiyarta ta fita. Alhaji Sulaiman ya bita da kallo yana jin zuciyarta wani iri, kamar bai gama yarda da kalamanta ba, amma kuma babu yadda zaiyi, matarsa daban ce a cikin mata ya sani, halayenta wani abu ne da ba zai taba iya kwatanta su ba, juma abinda bai sani ba shi e matarsa iri daya ce da kowacce mace, natan ne kawai basa gane cewar nutsuwar zuciyarsu a kowanne fanni na rayuwarsu taba zaune cikin ƙwaƙwalwar su.
Awanni biyu bayan hakan ya baro cikin gidan, Ya fito ya nufi titi don tafiya ga sana'arsa.
Daidai lokacin da Awwalu dake zaune cikin motarsa a can gefen layin ya tada motar shima yabi bayansa.
****
*A wannan safiyar.*
Ma'aruf ya tako cikin gidan a hankali, hannunsa daya na sanye cikin wandon shaddar dake jikinsa kalar ruwan toka yayin da ɗayan ke rike da wayar dake kare a kunnensa, kayan jikinsa kalar ruwan ƙasa ne wanda ta haska cikin safiyar, ƙafafunsa na tahowa cikin falon a hankali yayin da yake saurarar bayanin da Faruk ke yi masa a cikin wayar.
"Mutumin nan sh*ge ne B, Ƙarfe biyun dare ya kira ni wai shi daga sannan yake amsa waya, wallahi har na zata yan fashi ne suka shigo mana."
Yayi murmushi kaÉ—an.
"Baka da hankali Faruk dan fashin ne zai fara kiranka a waya ya gaya maka cewa gashi nan zai shigo tukunna? ka gaya min yaya kuka yi dashi kawai?"
"Yes, ya karba. But sai mun bashi wani abu tukunna, kuma ka san shi cash yake baukata, kuma gayen yana da matsala wallahi don yace dole yau yake bukatar kuÉ—in, shi yasa tun farko ni raina bai kwanta da mu saka shi cikin al'amarin nan ba."
Ma'aruf ya girgiza kansa.
"Kar ka damu, zanje na ciro kuÉ—i anjima sai ya gaya mana inda zamu same shi."
"Shikenan, I will talk to him zuwa yamman, zan gaya maka."
Da haka wayar tasu ta kare, daidai lokacin da Ma'aruf ya shiga hanyar koridon zuwa kitchen, inda ƙarar motsin kwanuka ke tabbatar masa da cewar tana ciki.
Da gaske yake abinda ya faɗa mata jiya cewa tana ƙara ƙawata duniyarsa, don duk da har yanzu bata gama sakin jikinta dashi ba, ya sani cewa shigowarta cikin rayuwarsa ya fara samun wata nutsuwa da shi kansa baya gane mata, abinda kawai ya sani shine abinda yaji tun daga ranar da ya fara ganinta shi yake jan ragamar sa akanta.
Tsakanin jiya da yau kaɗai yana jin sunyi sabon dashi da Ruƙayya basu sami hakan a ɗan kankanin lokaci ba, ya nuna mata cewar da gaske yake wajen gyara alakarta dashi, kuma hakan bai bashi wuya ba don da gaske ne yarinyar bata da matsala, tana da hankalin da bai san da me zai kwatanta shi ba, tana da hankalin da ya fahimta sosai a cikin dukkan amsoshin da ta bashi don sunyi hira sosai a jiya, yayi mata tarin tambayoyin daya fahimci kusan rayuwarta gabadaya a dunƙule.
A lokacin ne kuma ta juyo ta kalle shi, hannunta daya rike da plate din da take wankewa a cikin sink, lbakinta yayi masa murmushin nan nata dake tafiya har cikin zuciyarsa. Wani abu daya lissafa shi cikin nasarorinsa na kwanakin nan kenan, yana gaya masa cewa da gaske yayi kokarin da ya fara rusa wasu abubuwan dake tsakaninsu, shi yasa a jiya ya daure yayi mata tambayar da yake fatan amsar da zai samu amsa daga gare ta, amsar da yake fatan ta zama abu na karshe da zai cire duk wani hijabi a tsakaninsu.
"Sannu da zuwa" Muryarta ta fito a hankali.
Bayan asuba ya sake fita wajen ƙarfe bakwai na safe, ya tafi can yamadawa inda ya halarci janaizar wani abokin Baffa da ya rasu a daren jiya, da Baffan suka yi waya a jiyan ya gaya masa cewa yaje ya wakilce su shi da Baba Usman tunda basa gari, sai gobe ne suke shirin dawowa daga Kadunan.
Don haka can ya tafi kuma har bayan an kai mutumin sai da ya sake komawa gidan don bai shiga ciki yayi musu gaisuwa ba, ya san matarsa guda É—aya, don a shekarun baya kafin ya auri Rukayya daga ita har mijin nata sunyi kokarin hada shi da wata Æ´ar su Nafisa, kuma shima saboda hankalinta ya so yarinyar a lokacin amma sai naci da kuma dagiyar Rukayya ya tsallake nasu.
Yanzu ma da yaje yaga yarinyar, tana zaune a gefen mahaifiyar tata riƙe da wani yaro mai kama da ita sak wanda hakan ya shaida masa cewar tayi aurenta itama, kuma sunji mutukar dadi na ganin nasa, don bai san me yasa ba kai tsaye yake iya fahimtar farin ciki da kuma yabawa a fuskar mutane, kamar yadda a jiya ya fahimci daɗin da Amina taji a lokacin da yake godiya da kuma yabawa girkin da tayi masa.
Ya karaso cikia hankali sanda da ta kashen famfon tana rike da kofi na karshe a hannu ta.
Ya tsaya a gabanta.
"Anyi jana'izar?" Ta tambaya bayan ta kalle shi ta sunkuyar da kanta. Ya daga nasa kan kafin ya amsa.
"Anyi tun É—azu, makabartar babu nisa da gidansa." "
Yaga kamar ta hadiye wani abu a makogwaronta kafin tace.
"Allah ya jikansa."
"Ameen."
Ya amsa yana cigaba da kallonta, kuma abinda yake gani a fuskar tata bai tafi ba, don da alama mutuwar ta ɗan taɓa ta duk da bata san mutumin ba, yaga hakan a fuskarta tun daga lokacin da ya gaya mata inda zai je da safe bayan ya shiga dakinta ya same ta zaune akan dardumar ta har a lokacin.
Kayan dake jikinta a yanzu wata doguwar riga ge ta atamfa Green, kuma akwai wani abu a cikin kalar rigar da yayi mata kyau yake kunna wani abu kamar wuta daga ƙasan zuciyarsa tun sanda ta shigo kitchen din.
"Har kinyi breaskfast?" Muryarsa ta tambaya da wani irin amonta mai sanyi yana katse shirun dake son faruwa.
Ta girgiza kanta a hankali sanin cewa kofin hannunta yake kallo.
"A'a, nayi amfani dashi ne."
Ya zaro wayarsa daga aljihu ya kalli lokaci.
Ƙarfe goma har da kwata.
"Dama ba kya cin abinci da wuri?"
Ta sake girgiza kanta.
"A'a ya danganta kawai."
Sai taji yayi wani abu kamar murmushi kuma kafin ta É—ago ta kalle shi ya sunkuyo da fuskarsa kusa da tata yace.
"Ya danganta da lokacin da na dauka a waje kina jirana kafin na dawo?"
Wani irin abu ya lullubeta a lokaci guda tun daga kai har ƙafa, ta dago ta kalle shi idonsa yana kanta kamar yadda ta sani.
"Ki gaya min gakskiya dan Allah ba zan fadawa kowa ba... kawai ce miki zanyi nagode." Ya roje ta a hankali.
Bata san lokacin da tayi wani guntun murmushi ba sannan ta daga kanta sau daya tana cigaba da kallonsa.
Wani abu da yasa a lokaci guda Ma'aruf yaji wasu abubuwa kamar chemical concoctions na zubewa a cikin zuciyarsa.
"Now I feel like posting it on my Facebook wall."
(Naji kuma yanzu kamar inje in rubuta a shafi na na Facebook.) Ya fada muryarsa can ƙasa.
Sai kawai tayi wani murmushin mai fadi sannan ta juya, ta nufi wajen da take ajiye kofunan a kitchen din ta ajiye na hannunta sannan ta debo wasu containers da ta juye su Madara da Milo a ciki ta juyo, ya jingina da gefen sink É—in har yanzu yana kallonta, kamar yana son yace wani abu.
"Sauran kayan suna falo."
Ta fada tana nufin sauran kayan breakfast din, kuma da haka ta taho zata wuce ta gabansa, amma kamar yadda zuciyarta ta ayyana mata zai faru, sai ya tsayar da ita, ya riko hannunta ya dawo da ita gabansa.
"Baki bani amsata ta jiya ba Amina."
Kai tsaye ya fada yana karbar kayan hannunta ya ajiye su akan sink din.
Sai ta kasa kallonsa wannan karon, ya riko hannunta É—aya sannan muryarsa ta cigaba da magana a hankali.
"yunda na tashi da safe tunanin da nake yi kenan har naje na dawo, ko aikina da tarin mutane ke karkashina baya damuna kamar yadda a yanzu jiran abinda zaki ce ya dame ni, I always have the last and final say a kamfaninmu, but zuciyata bata damuwa da abinda zan fada kamar yadda a yanzu ta damu da abinda zaki fada min, so Please save me from this boredom and just say it now. Na gaya miki ko a yaya amsarki tazo zan karbe ta a hakan ba tare da wani tunani ba, I just want to hear your mind out." ( So nake kawai inji abinda yake a zuciyarki.)
A lokaci guda Amina taji makogwaronta ya bushe, taji tana shakar wata busashshiyar iska tana wucewa har cikin cikinta yayin da maganganun da ya fada mata jiyan ke dawowa cikin kanta.
"Amina ban san tunanin ki gane dani ba har yanzu, auren mu daban ne da irin wanda kowa yake yi, ban taba ganinki ba sai a ranar da kika zama matata kuma na san kema haka, kowanne mu bai san yaya É—aya yake ba balle halayensa har aka haÉ—a rayuwarmu tare, bamu da wannan sanin ko kuma fahimtar junar da mutane da yawa ke samu kafin aure.
Sai a yanzu ne muke fara gina tubalin da muka baro a baya, kuma ba zan boye miki ba I think I have started falling in love with you since from day one da na ganki a cikin gidan nan, ban san me yasa ba I just did... Kuma a yanzu da na ƙara sanin ki nake sanin komai game dake Amina, zuciyata ta bani tabbacin cewa da gaske ne ina son ki ba tunani nake yi ba, zuciyata tana godewa Allah a kodayaushe da ya zamo kece wacce Mami ta zaba min a matsayin matata.
Saboda da bake bace Amina da labarin zai canja, ko sau ɗaya kar kiyi tunanin cewa da kowacce mace aka kawo cikin gidan nan zan karɓe ta kamar yadda na karɓe ki. Na san me nake so Amina na san abinda bana so, kuma ina da tsarina a kowanne ɓangare.
Don haka kema ina son inji tunaninki game dani, bana son in matsa miki da komai Amina, idan zamu gyara alakarmu mu cire komai a tsakaninmu ina so ya zama da yardar dukkaninmu ne, bana so ya zama don ni ina so ke kuma ya zane miki dole, so nake mu ajiye duk wani tunani a gefe tare mu karɓi junanmu da zuciya daya, I want us to ignite our hearts together and get lost because we wanted to, shi yasa a jigawa nace miki not there, not then, sai lokacin da zuciyarki ta amince kuma kika bani dama Amina."
Allah yaso a jiyan da yake fada mata hakan cikin duhu ne, lokacin da bai nemi shawarar ta ba ya shigo dakinta bayan ta barshi a falo yana kallon zancen wata siyasar America, tayi masa sallama da cewar sai da safe zata je ta kwanta, kuma ya amsa mata suka yi sallamar Allah ya tashe su lafiya, sai gashi minti goma bayan hakan ya shigo dakin bayan yaje ya canja kayansa zuwa na bacci.
Ta rufe idanunta alamun bacci take yi har sanda taji ya hawo gadon, amma lokacin da babu zato taji ya naÉ—e hannunsa daya waist dinta kafin ya jawo ta cikin jikinsa a hankali, babu shiri ta bude idanunta tana kallonsa, kuma a lokacin ne ya gaya mata wannan maganar, a yanzu kuma da safiyar Allahn nan yake neman amsarta.
Kuma abinda take ji a yanzu ya wuce duk yadda zata iya fassara shi, yadda ya rike hannayenta duka biyu kadai tana jinta ne kamar wani kwan fitila da ya kama tar! Sannan tana jinta kamar tana shawagi a iska, kuma cikin hakan ne taji lokacin da ya saje cewa
"Duk abinda zaki fada ina son kiyi considering cewa ba kowa ne zai baki irin wannan damar ba Amina, Allah ina da kirki sosai."
Bata san lokacin da wani murmushi mai kama da dariya ya subuce a bakinta, yace ya bata damar da zata fadi ra'ayinta amma kuma ya fara yiwa kansa campaign tun bata ma ce komai ba. Sai ta dago tana kallonsa sanda shima yake murmushin. Shima ya sani ai, amsarta ba zata canja daga abinda yake fata ba, ya riga ya gama daure ta da jikyoyinta, kamar ya sace zuciyarta tun a farkon zamansu ya kulle ta a wani keji, kuma bai bude ta ba sai da ta gama sabawa dashi ta yadda a yanzu da ya baya muƙullin da kanta don ta bude kanta ya san ba inda zata iya zuwa... Dole da ta fito ta tashi zata dawo ne ta faɗo cikin hannayensa.
Don Allah ya sani ko ba ita ba, bata ga macen da zata iya kallon Ma'aruf a wannan lokacin tare da kyawawan halayensa tace bata son sa ba, idan kuwa har an samu yo tabbas ko waceve za'a iya jeranta ta cikin masu karancin sa'a a duniya.
Don haka a wannan lokacin Amina ta daure dukkan wani tunani a zuciyarta, ta ture komai gefe, a karo na farko a rayuwarta tayi wani abu kai tsaye da zuciyarta ta gaya mata ba tare da tunanin komai ba, don a wannan lokacin ta ma manta kowa É—in kuma ta manta komai, babu wani kokonto a ranta ko kuma tunanin hakan bai dace ba, abinda ta sani kawai shine Ma'aruf ya tambaye ta abinda ke zuciyarsa ne kuma zata fada masa gaskiyar zuciyar tata.
Shi kansa bai yi zato ba sanda ta tattaro dukkan dauriyarta a hankali ta ƙara tsawonta kaɗan ta hanyar miƙewa kan kafafunta sannan ta kai fuskarta daidai kunnensa, muryarta ta fito ne a hankali da kalaman da ita kanta sai a wannan lokacin taji su.
"You’re the piece of me I didn’t know was missing untill now."
(Kaine wani ɓangare na da ni kaina ban san bani dashi ba sai yanzu.)
Ta sauke ƙafafunta a hankali tana kallon fuskarsa dake ɗauke da tsananin mamakin da ita kanta take jin yana lulluɓe ta, taga yadda ya haɗiye wani abu a cikin maƙogwaronsa kafin ya gyaɗa kansa a hankali.
"Nagode Amina, insha Allah ba zan taɓa sawa kiyi dana sanin sanina a rayuwarki ba, zan kare dukkan hakkokin ki da Allah ya rataya min a wuya na, ba zan taba cutar dake ba, ina da tabo mai girma a cikin rayuwata, ina da abubuwa da yawa da ba zaki so saninsu ba, I'm a mess just like I told you, amma idan kika bani dama nayi miki alkawarin komai zai tafi daidai Insha Allah."
Kuma bai bari ta sake wani tunani ba ya haɗe tazarar dake tsakaninsu, ya rungume ta a jikinsa da wata irin shiga da taji kamar yana son kange ta ne daga dukkan wani hargitsi na duniyar nan, wani abu daya dawo da ragowar hankalinta jikinta yana tuna mata da zagayen halin da take ciki, fuskar Amma da kuma ta Hajiya Kilishi ta haska cikin kanta a lokaci guda, dukkanninsu suna kallonta da jiranyen da ta san yana zagaye da ita, sai dai Ma'aruf bai bar hakan yayi nisa ba lokacin da ya sake riƙe ta a jikinsa sannan a hankali ya lalubo kunnenta ya raɗa a cikin kunnenta.
"Thank you so much Doll, I was dying to do this..."
Kuma bai ɓata lokacin wani tunani ba, lokacin da ya dawo da fuskarsa saitin tata sannan ya hade dukkan wata tazara tsakaninsu, his lips were rough and urgent, sannan tana iya jin dukkan wani sakon da yake bata a cikin hakan, kuma cikin wannan sakon ne Amina ta samarwa kanta mafita itama, wata mafita da a lokaci guda ta haska a cikin kanta, wata mafita da zata jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya!
Tsuntsu biyu, ba guda daya ba!
*****
Aka kwankwatsa kofar É—akin sau daya, biyu, uku....
"Who the hell is that?"
Muryar Jamal ta daka tsawa daga ciki yayin da yake naÉ—e cikin bargon makeken gadonsa.
Zainab, Æ´ar aikin gidan dake tsaye cikin uniform dinta na masu aikin gidan ta zabura kaÉ—an tayi baya saboda yadda muryar ta firgita ta, ta saba a lokuta da yawa irin haka idan tazo dama da sigar da take samun amsar sa kenan, amma ta kasa sabawa har yanzu, ta kasa sabawa tun sanda ta fara aiki a gidan.
"Hajiya ce tace in gaya maka tana nemanka."
Ta fada da karfi kaÉ—an yadda zai jiyo ta. Jamal yaja tsaki yana shafa kansa da duka hannayensa duka biyu. Ya tsani yarinyar nan, ya tsane ta har cikin ransa, matan mahaifinsa uku ne, suna da ma'aikata fiye da hamsin a gidan kuma kusan rabinsu arna ne, idan ma akwai musulman to babu bahaushe ko É—aya a cikinsu.
Don haka ya rasa dalilin da yasa mahaifiyarsa ita kadai ta fita zakka ta ɗauki irinta aiki, shi baya hausa ma tare da ƴan aiki amma akan yarinyar nan ya fara. Kuma tun daga ranar da ya fara ganinta a ɓangaren mahaifiyar tasa, sanda suka ci karo ta zuba masa miyar data dauko a kwanon hannunta yaji ya tsane ta har cikin zuciyarsa.
Har ya buÉ—e baki zai bata amsa ya tuna ko yayi turancin ma sai yazo ya fassara, don haka zata cigaba da tsaiwa a wajen tana kara maimaita masa abinda ta fada, ilai kuwa kafin ya gama tunanin yaji da wannan shakakkiyar muryar tata ta sake cewa.
"Hajiya ce tace in gaya maka tana nemanka."
Wai wa ya gaya mata cewar Sunan Mamah Hajiya ne ma?
Ya ja tsaki kafin yace.
"Ina zuwa."
Shirun da yaji bayan wasu sakanni yasa ya fahimci cewa ta tafi, don haka ya kara jan wani tsakin kafin ya jawo wayarsa a gefe, karfe sha É—aya da rabi na safe, laifin me aka cewa Mamahn ya sake yi da zata turo a tashe shi da sassafen nan? Missed call É—in Haro ya gani har guda tara don ya saka wayar a silent, gayen bashi da hankali wani lokacin.
Yana shirin sake maida wayar ya ajiye sai ga shigowar wani kiran nasa na goma. Ya ɗauka ya ƙara a kunnensa.
"Ina ka shiga ne J? Ka bar gari ne?"
"Yes, ina gida."
"Dole ka baro Abuja yau Jawad, don na gano hanyar da zamu lalata yarinyar nan?"
Ba shiri Jawad ya miƙe zaune yana sake rike wayar a kunnensa, kusan bakinsa na rawa yace.
"Me ka samo? Me zamu yi?"
Daga cikin wayar Haron ya ƙyalƙyale da dariyar shakiyancinsa kafin yace.
"Ma'aruf Mansoor Bakori!"
**
_Me kuke tunani ya zama karshen hatsarin nan shekaru goma da suka wuce?_
_Wace mafita kuke tunanin Amina ta samo?_
_Ga dai Awwalu can na bin Baba..._
_Me ya Haro yake nufi da sunan Ma'aruf a matsayin hanyar da zasu hukunta Ruƙayya?_
_After all this, what do you think about the love Birds??_
_I'm here singing Confession Song by Omah lay..._
_Ku shirya ganin wasu Confessions ɗin daga MMB...😅_
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:49 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*03*
~~~~~~~
_The best part is, I wasn't looking when I found you._ _- Unknown_
**
*Shekaru goma da suka wuce.*
Lokacin da aka shigo da gawar, lokacin da gidan ya sake hargitsewa da tarin jana'ar dake da ta shigowa da kuma masu kuka da salatin da muryarsu ke É—agawa, lokacin Hajiya Maimuna ta bude fuskar gawar danta da aka shimfude a falon Baffa, hannunta ya rike zanin atamfarta da aka nannaÉ—o shi a jiki, danshin jinin dake jikin atamfar ya a ratsawa har tsakiyar kanta, a lokacin ne kuma abinda ya faru tsakaninta dashi jiya ya dawo cikin kanta.
"Mimi...
Muryarsa lokacin da ya shigo cikin gidan ta ratsa kunnuwanta a jiyan. Tun da yayi sallama da Ladi ta bude masa ƙofar yake kwala kiran har ya shigo gidan, a lokacin tana kitchen, ta jiyo shi tana ta amsawa ama shi bai jiyo ta ba gashi babu kowa a gidan, don safiya ce dukkan yammatan gidan sun tafi makaranta, don haka tana jinsa sai da ya zagaye kusan kowanne daki a gidan yana kiran sunanta a yadda shi kadai yake gaya mata wato Mimi, kafin ya dangana da kitchen din.
Kuma shirun da tayi bayan ya buɗe kofar kitchen ɗin ya saka ta juyowa daga tukin tuwon da take yi. Ya tsaye riƙe da hannun ƙofar kawai yana kallonta, ta manta rabon da ta ganshi da manyan kaya, kullum cikin kananun kaya yake sune shigarsa a kodayaushe, don shekara wajen biyar ya shafe a Cairo yana karatu don haka dasu ya saba.
Amma yanzu da ya dawo gida kuma ya karbi aikin kamfanin Bakori wani abu da yake burinsa kuma mafarkinsa tun yana yaro, sai ya zama dole manyan kayan su zasu zama kayansa.
Jamal yafi kowa kyau a gidan, hakan wani abu ne da ba sai an lissafa ba, tun daga kan yayanta har zuwa na Kilishi babu wanda yake ko kama dashi, tun yana yaro mutane da yawa na cewa ma ba ita ta haife shi ba duk da cewar itama fara ce, amma baya kama da ita kuma baya kama da kowa banda hancinsa da wasu suka ce yana shige da na Baffa don na Baffan ma dogo ne kamar nasan, akwai lokacin da yana shekara bakwai har sai da jama'a suka sa mata kokonto a ranta game dashi itama ta shiga tunanin ko anyi mata canjansa a asibiti ne sai da Baffa ya dakatar da ita tukunna.
"Raina yana ta tashi har nayi zaton ko bakya gidan ne, muryarsa mai zurfi ta fada yana kllonta,.
"Allah ya sawwake maka, ta ina rai yake tashi Jamal?"
Ta faÉ—a tana dariya kafin ta juya.
Ya karaso ciki ya tsaya a kusa da ita yana kallon tukunyar dake jan gas din da take tuka tuwon da ita.
"Mimi kice min wannan miyar waken ce?"
Ya tambaya sanin cewar ta gaya masa tana da miyar tun jiya.
"Itace dai yanzu zan dauko ta daga freezer, kawai tashi nayi yau ina sha'awar tuwon."
"Alhamdlilah." Ya fada yana zura hannunsa cikin gashin kansa.
"Dama banci komai ba wallahi, ina tashi naga wai yaran nan dankali aka soya musu."
Shi baya son duk wadannan kayan cimar na zamani, abu kadan yake ci a cikinsu yafi son abincin gargajiya duk kuwa da zamansa a kasar waje, bama shi kadai ba kusan duka yayanta haka suke, har Ma'aruf idan bata manta ba.
A lokacin ne ya zaro wasu kudi daga cikin aljihunsa ya ajiye a gabanta, gaban flask din da ta gama kwashe tuwon a ciki, kuma ganin yawan kudin shi ya tsayar da ita cak daga karasa abinda taje yi.
"Baffa ne yace in kawo miki."
Ya fada da sautin muryarsa da ya canja a yanzu, tana iya tuna yadda wani irin daci ya mamaye kirjinta a lokaci guda kafin ta yi kokarin ture hakan, hannunta ya kai kudin tana fadin "Allah ya saka da alkhairi', amma sai Jamal yasa nasa ya dafe nata kafin ta dauka.
"Kudin cefane ne ko?" Ya tambaya, muryarsa na shaida irin bacin ran dake cikinta, bata amsa ba ya cigaba.
"Tunda Baffa ya bani kudin nan bake binsa da kallo, baice min komai ba amma na fahimci baya miki magana tun last week, kuma na tambaye shi amma bai bani amsa ba, bana son inyi komai akan zargi Mimi, ki gaya min abinda nake tunani haka ne?"
"Jamal..." Ta fada tana kallonsa.
"Dan Allah." Yayi saurin katse ta.
"Ki gaya min gaskiya, ki san gyarawa zanyi, kin san ba zanyi abinda bai dace ba."
Wucewar wasu sakanni kafin ta gyaÉ—a kanta a hankali tana cigaba da kallonsa.
"Akan zancen zuwa hutun su Munaya ne a Abuja, yace bai yarda ba kuma suna son zuwa, shine nayi masa maganar cewa ta kanaya suje din, amma sai bai fahimta ba, sai laifin ya dawo kaina, yace sun fara girma sun fara raina maganganunsa ni kuma ina biye musu."
Ya kalle ta tsawon waucewar wasu mintuna kafin ya zura hannunsa cikin gashin kansa.
"Kiyi hakuri Mimi, insha Allah duk irin wadannan abubuwwan sun kusa zuwa karshe, na sha gaya miki akwai sa hannun wani a irin wadannan abubuwan dake faruwa tsakaninki da Baffa amma nq kusa gyara komai a gidan nan da yardar Allah, rayuwarmu ba zata cigaba da tafiya a haka ba."
Sai ta girgiza kanta.
"Nima na sha gaya msaka cewa ka daina irin wannan tunanin Jamal, ka daina saka zargi a zuciyarka, wannan matsala ce dake faruwa a kowanne irin aure ba wai wani abu ba, duk sanda kayi naka zaka fahimta kaima. Amma babu ruwan kowa a wannan al'amarin, kana gani dai ko Kilishi da muke kishoyoyi bata da matsalar komai to waye kuma zai saka mu a gaba? Akan me?"
Ya zura hannunsa daya cikin gashin kansa.
"Matsalar kenan Mimi, ba kya bari zuciyarki ta bude abinda yake kasan zuciyar mutane, shi yasa ba kya yarda dani a kodayaushe, amma insha Allah kwanan nan zan nuna miki wani abu da zaki san ba zargi nake yi ba Mimi, so nake kawai in tabbatar in dai ina raye komai ya kusa zuwa karshe insha Allahu."
Haka ya fada a lokacin, amma ita kallo sa kawai take yi tana son gaya masa cewa a wannan lokacin ba wannan ne fatanta ba, ba wannan ne buri ta ba, burinta bai wuce cewa yayi kokarin jawoata Ma'aruf zuwa kusa da ita ba, tana fatan hakan daga yadda take ganin alakarsu na tafiya, fon tun a wancan lokacin maganganun ƴ ƴanuwanta dun fara zama a zuciyarta, musamman a lokacin da Ma'aruf din ya kammala karatun secondry dinsa, tana ganin ma'anar kowacce kalma da suka sha fada mata game da alaƙarta da ɗan nata.
Sai gashi kwata-kwata awannin da hakan ya faru basu karfin na kwana guda ba, yace in dai
Ina raye... Kamar wani abu a lokacin na gaya masa cewar zai iya rasa ran nasa da wuri.
Tana jin kukan su Shukra da sauran jama'ar gidan daga wajen falon, tana jin tashin kukan kowanne a cikinsu yayin da mazan dake wurin ke ƙoƙarin basu baki, don an hana kowa shigowa a wannan lokacin, Baffa yace babu wanda zai ga gawar a wannan yanayin sai an shirya shi tukunna, itama ta shigo ne don ita mahaifiyarsa ce, babu wanda zai iya kallon idonta yace ba zata ganshi ba.
Idanunta na kallon gawar da tayi kaca-kaca da jini, kirjinsa ya dagargaje, ance bishiyar da suka daka shi ta soke don a saitinsa take, kuma har a yanzu ma akwai wasu kananun itacenta da suka hade da jikinsa da aka kasa cire su, jini yana malalowa a hankali har yanzu daga jikin gawar yana jika kayanta a lokacin, don tana tsugunne a gabansa, sanye da wani tsadadden leshinta da tayi shirin zuwa biki dashi a ranar.
Tana jin yadda danshin jinin nan ke jiƙa kayanta, yana gaya mata cewa jinin Jamal ne, ɗanta guda na farko a duniya, ɗan dake mutukar sonta fiye da komai a duniya, ɗan da tun yana karaminsa zuciyarta ke cin buri akansa, wannan kyakkyawan Jamal ɗin da kowa ke yabawa, kyakkyawan ɗan da take alfahari dashi a kowacce, a yanzu vabu wannan kyan, babu kamanninsa ma ko kadan, dogon hancinsa ne kawai ake iya ganewa a cikin kumburar da fuskarsa tayi ba. A cikin kunnenta muryarsa kawai take ji yana ce mata...
_Zafi nake jin Mimi, ko'ina a jikina ciwo yake yi..._
Haka yake ce mata duk lokacin da bashi da lafiya a makaranta idan suka yi waya.
"Limamin ya iso."
Taji wani a cikin mazan dake bayanta yana faÉ—a, sannan taji muryar Baba Usman yana cewa.
"An kira waya yanzu, ance an shiga da Ma'aruf din tiyata, likitocin sun ce anyi sa'a babu internal bleeding."
Sannan taji wani a cikin mutanen na tambayar su waye a wajensa.
"Mami ta tafi tun dazu."
Amsar da ta fito daga bakin wani, itace a amsar da tun a wannan lokacin ta bawa Hajiya Maimuna wani tabbaci na cewar shikenan tayi biyu babu.... babu Jamal É—in kuma babu Ma'aruf din! Don bata jin bayan addu'a tana da wani sauran fata a duniyar nan na dawowar Ma'aruf wajenta.
***
*Present Day.*
Tun da Munaya ta shigo tace da Hajiya Maimuna wai Ma'aruf ne ke zaune a falo yana jiranta hannayenta ke rawa wajen shiryawa, karfe goma sha É—aya na safiya a lokacin sai kallon agogo take tana karawa.
A tarin shekarun da lissafinta ba zai iya ta tancewa ba, ta manta yaushe rabon da ta sanya idanunta a cikin na Ma'aruf din a wannan lokacin, iyakarta dashi bayan tsawon wasu kwanaki ne da zai shigo ya gaishe ta kawai, zuciyarta ta daɗe da haƙura dashi game da wasu abubuwa da ta san cewar hakan ne ya kamata, ta dade da ɗaga kasan ruhinta ta binne dukkan wasu al'amuransa, shi yasa har a yanzu dukkan maganganun ƴanuwanta game da hakan basa damunta sosai.
Sai dai duk da dauriyarta, ta sani cewa bata isa ta canja cewar ita uwa ce ba, bata isa ta daure wannan kewar da zuciyarta ke ciki shekara da shekaru game dashi ba. Basu saba ba, É—awainiyarsa kaÉ—an ta sani, abinda take gayawa kanta kenan a kullum wajen tausar kanta, amma ta sani cewar babu wani abu a duniyar nan da zai yi daidai da dawainiyar rainon cikinsa da kuma haihuwar sa da tayi, shi yasa har abada a duniya uwa É—aya ce, kuma babu girman wani abu da ya isa ya canja matsayinta.
A zaune a falon kuwa ta same shi baysn ta fito, hannunsa rike da wani dan karamin kwano mai kyau, yayin da idonsa ke manne da Tvn dake nuna tashar CNN.
Ya juyo ya kalle ta daidai lokacin da ta karaso hannunta yana danna buttun É—in tsayawa jikin keken tayar.
"Barka da safiya."
Muryarsa ta gaishe ta ba tare da wata inkiya ba kamar yadda yake yi kullum, kuma a wannan lokacin dai taji hakan bai dame ta ba kamar yadda take ji a baya, ganinsa kadai a wannan lokacin ma ya isa ya mamaye dukkan tarin abubuwan da take lissafawa a kansa.
"Barkanmu dai, kun tashi lafiya?"
Ta amsa farin cikin dake zuciyarta na nunawa akan fuskarta.
"Lafiya kalau, ya ƙarfin jiki?"
"Alhamdulilhi mun gode Allah."
Har yanzu idanunsa na ƙasa bai dago ya kalle ta ba, kuma tayi zaton iya abinda zaice kenan kamar yadda suka saba a kodayaushe, amma sai kawai taga ya dago ya kalle ta sannan yace.
"Kwanaki Baffa yace mun Abdurrahim ya kusa dawowa ko?"
Ba shiri ta daga kanta da murmushi.
"Eh, nan da sati biyu insha Allah."
"Ashe har ya tsayar da rana, the last time da muka yi magana yace mun bai saka rana ba tukunna."
Mamaki ya shiga cinye ta a yadda take zaune, amma sai ta daure tace
"Yanzu ya kammala komai ai, don ma baya son taro ne amma ni da nayi niyyar wasu suje masa convocation din."
Sai ya gyada kansa.
"Haka yace mun nima, har Ishaq ma ya tambaye shi amma sai yace masa wai ba wani abu za'ayi ba."
Ta sake yin murmushi.
"Rigimarsa tafi shi ai, nace masa ko kewar mu baya yi."
Shima murmushin yayi ba tare da ya sake magana ba, yana tausayin kannin nasa ya sani, duk sanda suke magana ta hanyar text idan ya tuna cewar ba zai taba iya kiransa ba yana jin wani iri a ransa. Wani iri kamar yadda yake ji a yanzu da yake zaune gaban mahaifiyar tasa yana hira da ita, hirar da ba zai iya tara shekarun da aka rufa kafin ta iya tuna lokaci na karshe da suka zauna irin haka ba.
Kai tsaye yaji wani ɓangare na zuciyarsa ya shiga godewa Amina da tayi sanadin zuwan nasa, don yadda ta kalli idanunsa ta roƙe shi da Allah ya san ba zai taba iya kin ce mata A'a ba.
Kuma a wannan lokacin ba kallon Hajiya Maimunan yake yi ba amma sai jikinsa ya bashi cewa robar dake hannunsa take kallo, kuma yaji shigowar sako a cikin wayar dake aljihunsa, ya san Faruq ne, shi yake jiransa don haduwarsu da Yakubu (mutumin da zasu tura nemo musu Mr. Okafor.)
Don haka sai yayi saurin tasowa ya miko mata robar dake hannun nasa.
"Wai zogale ne na bayan gidan ta tsinko ta dafa shine tace in kawo miki Munaya tace mata kina so."
Yadda shiru ke ratsawa waje a lokaci guda ya kashe ƙarar komai haka Hajiya Maimuna taji a cikin kanta lokacin da ta karbi robar, kalaman suka shiga cikin kanta amma suka tsaya cak! Ta riga ta fahimci wa yaje nufi da itan ba sai ya fassara ba, amma hakan wani abu ne da bata taba tunanin faruwarsa a cikin lissafinta ba.
Ta kalli robar ta sake kallonta, ba wani abu ne mai yawa ba, amma wannan lokacin tana jin kamar nauyin zogalen nan daje ciki yafi girman dukkan wata kadara da take shi, kwalla ta cika ramin idanunta a lokaci guda, don haka bata É—ago ba sai kawai ta daga kanta a hankali.
"Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi Ma'aruf, Allah ya ƙara haɗa kanku, Allah ya baku zaman lafiya, ya kade dukkan sharrin da zai shiga tsakaninku, Allah ya baku zuri'a dayyiba."
Mami tasha yi masa addu'a, kala-kala ma, har da wadanda idan ta fada zai kara kallontasau biyu kafin ya amsa, amma Allah ya sani ya dade baiji addu'ar da ta shiga har cikin zuciyarsa ta tabo wani abu da bai san da zamansa ba irin wannan. Kalaman Mami daban ne da irin wadannan, yawanci addu'arta tana tsayawa akansa ne kadai babu wani a gefe da ya shafe shi, don haka tmya sani tun bayan lokacin daurin aure sa da Baffa da kuma Baba Usman suka yi musu makamanciyar wannan addu'ar, zai lissafa wannan a karo na biyu da yaji irin wannan addu'ar daga bakin wani.
Makogwaronsa ya bushe a lokaci guda, amma yayi kokarin hadiyr wani abu a hankali kafin ya amsa sannan ya tsugunnna yana yi mata sallama, bai kara iya kallonta ba itama kuma baya jin ta sake kallon nasa, don wataƙila suna raba abu iri ɗaya ne a zuciyarsu daga shi har itan.
Kuma karo na farko a wannan ranar bayan ya shiga wajen Hajiya Kilishi yaji haka kurum baya son dadewa don ransa bai gana daidaita ba har a lokacin, yaji hirar da take yi masa ba fahimta yake yi sosai ba, don haka yayi mata sallama ya fito, sai dai kafin ya bar cikin dakinsai da yayi mata wata tambaya dake yawo a cikin kansa tun bayan lokacin sa Amina ta bashi robar zogalen nan.
"Mami kina son zogale kuwa?"
Ta kalle shi kamar tana son gano wani abun kafin tayi murmushi tace.
"Haba ka manta ne Mai gaskiya, amma bana son zogale tun asali."
Sai ya gyaɗa kansa kawai sannan ya ƙara yi mata sallama.
_"Dan Allah zaka miƙawa Hajiya wannan? Zogale ne na bayan gidan nan tsinko na dafa, Munaya tace min Hajiya tana so, amma Mami ita bai dame ta ba."_
Haka ta gaya masa lokacin da ta tsaya a gabansa rike da robar tana ta juya ta a hannunta. Wani abu ne ya faru smdashi bai gama gabe masa ba har yanzu, ya san dai kawai ba laifi suka yiwa Mamin ba amma kuma duk da haka yana jin wani iri.
Ya zaro wayarsa ya duba bayan ya shiga mota, sakon da ya shigo dazu ba daga Faruk bane, daga mutane kamfanin RTL ne da suka yi dasu akan cewar gobe zasu je shi da wasu daga cikin board trustees É—insu su karbo kudin da suka siya dilolin kaya a hannunsu, haka kurum wanna karon ya yanke shawar cewa baza su karbi kudi ta account ba gwara su karbi cash kawai, tunda an cuce su wancan karon kuma har yanzu basu gama da gano matsalar ba.
Sakon yana bayani ne kan wajen da zasu hadun da kuma lokaci da sauran abubuwa, ya kashe wayar ya tada motar daidai lokacin da kiran Faruk ke shigowa, ya san ya riga shi isa wajen kenan kuma yanzu zai dame shi, don haka ya danna motar ya nufi hanyar titi daidai lokacin da idonsa ya kai kan robar zobo mai sanyin da Amina ta ajiye masa daga kasan dashboard din motar wajen da akayi musamman don ajiye roba dama.
Babu shiri wani murmushi ya subuce a bakinsa, yana da plan dama tarin tsaruka na ydda zai saita rayuwarsa tare da yarinyar nan, don tabbas ya gama yarda cewa ita din alkhairi ce a rayuwarsa, kuma mafi dadin abin shine ya same ta ne a lokacin da ba nema yake ba.
Wani abu da alokacin bai sani ba shine kwance a cikin zobon nan, sinadirin kwayoyin maganin Hajiya Kilishi ne ke yawo tun daga sama har kasa.
****
*Abuja.*
*No. 1146 C west, Maitama.*
A cikin ƙaton falon, baka jin komai sai ƙarar A.cn dake hurawa ta kowanne bangare na falon, akwai manya-manyan royal chairs set uku da aka rarraba falon zuwa waje uku dasu. Jawad yana zaune daga kujerun gefe masu kalar ruwan madara, gajeran wando ne a jikinsa kuma wata t-shirt kalar ruwan kasa, a gabansa wani tebur ne da aka cima da kayan abincin safiya, hannunsa na rike da kofin mug yana kuɓar shayin ciki yayin da mahaifiyarsa dake gefe Hajiya Mardiyya ke kallonsa tana sake maimaita maganganun da ba jinsu yake yi ba.
"Yanzu Babana ko don wadannan makiran matan mahaifin naka ba zaka saurare ni ko sau daya a rayuwarka ba? Kana ganin irin banbancin da ake nuna mana a gidan nan, kuma da nayi magana sai kace dani ba zaka yi ba babu kyau, bayan shi kansa mahaifin naku ai ya san abinda su Suraj din ke yi, kawai bai damu bane kuma yana sane yake barinsu. Kowa na diban kason sa amma kai so kake mu mu tashi a tutar babu? Ba don ma Perm Sec. ya shiga zancen mahaifin naku ba kai ka sani da yanzu bama kan wannan kujerar.
Wallahi idan na shiga lissafo maka kadarorin da matan nan suka tara yanzu zaka rike baki Jawad, amma ni gida uku fa kawai nake dashi har yanzu, ba don nayi fafutuka ta ma ba da bana jin ina da ko daya ai, kai kuwa banda motarka bana jin ka tara wani abu, karfi da yaji ka maida mu talakawa alhali muna iyo a cikin kudi Jawad?"
Ya lumshe idanunsa a hankali lokacin da ta kai karshe sannan ya juyo ya kalle ta.
"Mamah amsata ba zata canja ba kema kin sani,abinda nake gaya miki kullum shi zan kara gaya miki a yanzu, ba zan saci kudin mahaifina ba ba zan dauki abinda ba nawa ba, shi yasa nake aiki kin sani, su sauran matan nasa da yayansu ke zuwa su debo musu ai basu suka saka su a gaba suka roke su ba, kowa ganin damarsa ce tasa shi yin hakan, don haka me yasa ni zaki takura min, ba ga su Khairat nan ba? ( Kannensa mata biyu) Ki koya musu wata hanyar da zasu samo miki mana, ai ba maza ne kadai suka iya samowa ba."
Ya ajiye kofin hannunsa sannan ya mike tsaye, sannan yace
"Zanyi bako anjima, Dan Allah Mamah ki sa ayi mana abinci, wadannan duk basu yi min ba."
Ya fada yana nufin tarin cimar dake kan teburin daya tsallake, kuma bai jira abinda zata ce ba yayi gaba, ya zaro wayarsa ya kira Haron da suka yi akan lallai ya shigo Abujan don ta nan ne zasu hau jirgi zuwa Kano, ya gaya masa shi ba zai yi tafiyar mota ba.
Kuma awa guda bayan hakan sai gashi ya iso, suka zauna daga falon kasa na ɓangarensu yayin da Haron ke ta mita akan tason shi da yayi babu shiri.
"Kaifa kake bukatar abin nan J, amma ni ka takurawa na taho rana tsaka, ina ga dole mu maida harkar nan ma taciniki don na fahimci ni zan sha wuya a banza."
"Ko nawa ne ka san zan biya ka, I never regret anything indai akan Rukayya ne ka sani."
Haron ya kalle shi lokacin da ya tsiyaya wani lemo mai sanyi a daya daga cikin tambulan É—in da aka kawo musu sannan yace.
"Shi yasa ni kuma nake iya kokarina don inga na ciro ka daga wannan masifar, Haba ka kalli fa inda kake rayuwa, ni ban ma san kun canja wannan gidan ba, amma ka kallafa ranka akan wannan shashashar yarinyar, in the first place ni ban san ma me yasa zaka neme ta ba idan har ka san aurenta zaka yi."
Jawad ya gyada kansa alamun ya fahimta yana kallonsa sannan yace.
"Ina ga duk mun wuce wannan stage din Haro, mun karaso wajen da kace zaka taimake ni, ni kuma nake jiran inji ta hanyar da zaka taimake ni din."
Cike da takaici Haron yana kallonsa kafin ya buÉ—e briefcase din da yazo da ita a gefensa sannan ya zaro wasu hotuna guda uku ya miko masa, ba tare da bata lokaci ba kuwa Hawad yasa hannu ya karba.
Hotunan mutum daya ne a mabanbantan llokuta har guda uku, na farko kamar ranar daurin aure ne, don a cikin jama'a yake sanye kuma da kaya masu babbar riga, na biyu kamar hoton wajen aiki ne, yana sanye da suit da kuma sumar gashinsa wadda aka gyara cikin wani style mai kyau, sai na karshe a bakin titi ne yana waya, hoton yayi kama da cewar a boye aka dauke shi sosai.
Kuma ba sai Haron ya sake yi masa bayani ba, ya riga ya fahimci waye tun da wuri, don idan zai iya tunawa ma ya tabacganinsa sau daya a wani taron harkar kasuwanci da ya halarta shekara guda baya, idonsa ya manne akan fuskar sa yana son ya gano banbancin dake tsakaninsa dashi, wannan banbancin da yasa Rukayya ta juya masa baya, banbancin da yasa ta rufe idanunta akan tarin kyautatawar da yayi wa rayuwarta ta kasa ganin kokarinsa, ko ma rabewar da zuciyarsa ke yi a lokacin da take gaya masa cewa bata dauke shi komai ba face abin wasa kawai, abin wasanta!
"Na gama samun duk wani background information akan gayen, ashe har aure ma ya sake yi..."
"What?"
A lokaci guda ya katse Haron da ke kokarin fara bayaninsa. Fuskarsa na kallonsa da tsananin mamakin da ya kasa tantance daga ina yake fitowa yana shiga jikinsa.
"Yes, ya sake aure Æ´an kwanakin bayan nan, amma naji ance kamar bashi matar kawai akayi don tare akayi auren dana sauran yanuwansa."
Sai kawai ya gyada kansa a hankali ba tare da ya san me zai ce ba, hakan yasa Haron ya cigaba da maganarsa.
"Ka san ni bana sanya a al'amarina, so na samu labari ance min zai hadu da wasu mutane gobe, na samu details É—in da komai daga bangarensu, so kawai zamu yi masa aiki ne a lokacin."
Jawad ya dago ya kalle shi."
"Aiki? Wane irin aiki?"
"Plan dina shine mu kama shi for now, kar ka tambaye ni me zai faru bayan nan, mu fara gama wannan din tukunna."
Jawad ya kalle shi tsawo sakanni biyu.
"Ba zan tambaye ka ba, amma ka sani cewa I wont sign for any shit, idan har kashe shi ne plan dinka..."
"Wa yake maganar kisa anan J? biyu babu muka ce zamu sa yarinyar nan tayi, you want to make her pay ko ba haka ba? Then we are just going to make her pay kamar yadda kake so, ka yadda dani kawai."
Jawad ya sake kallonsa na wani lokaci kafin ya gyaÉ—a kansa.
"To meye plan din?"
"Ba ma zamu bari ya isa wajen mutanen da zai hadu dasu ba, kafin ya isa za'a tare shi kawai sannan a juyo da motar, yaran da nasa sun nemo titin da komai har ma da daidai wajen da zasu tsaida shi din, shi yasa nace maka dole mu bar Abuja yau."
Jawad ya gyada kansa alamun ya fahimta.
"Idan har babu zancen kisa a al'amarin nan, I think hakan yayi daidai."
Haro ya girgiza kansa.
"Wannan gayen ba irin mutanen da za'a kashe su maganar ta wuce kamar iska bane J, daga shi har mahaifinsa suna da tarin connections din da ban san iyakarsu ba, don haka wasa kawai zamu yi dashi mu cimma manufarmu."
Kalaman ƙarshe suka tafi kai tsaye cikin zuciyar Jawad suka yi masauki.
Wasa kawai zasu yi dashi, wasa... Ya cije lebbensa na kasa yana sake maimaita kalmar a ransa. Yanzu yake ji cewa da gaske Haro ya dauko hanyar cimma manufarsu, tunda har zsi bashi damar da zai nunawa Rukayya cewa mutumin da take wa kallon duniyarta, take wulankanta shi akansa shima bai fi karfin ya zama abin wasan a wajen sa ba.
Yana jin Haron na kokarin yi musu booking jirgin da zai tashi zuwa Kano lojacin da ya miƙe don zuwa dakinsa ya fara shiri, a lokacin ne kuma yaci karo da ita, wannan yarinyar, wannan yarinyar da ya ƙi jinin ganinta, 6ar aikin mahaifiyarsa, tana tsaye daga koridon dake jikin falon haunnuta rike da wani katon faranti da ta shako kayan abinci dasu, kuma ba sai tace komai ba, rawar da hannayenta keyi tare da kwanukan abincin shine abinda kai tsaye ya shaida masa cewa tsaf taji dukkanin shirinsu!
***
Karo na ba adadi Amina ta kalli agogon dakin, zuciyarta ta kara yin nauyi a kirjinta, rawar hannayenta ya karu, amma sai tayi saurin danne hakan ta hanyar daukan wani ƙaton mangwaro dake gabanta.
A bangaren Inna Danejo suke wadda bayan fitar Ma'aruf Samirah tazo ta gaya mata isowarta don haka ta ƙulle gidan suka taho tare, inda ta tadda dukkan sauran jama'ar gidan kowa yazo don saukarta.
Kuma ba'a dade ba aka shiga hayaniyar rabon tsaraba kamar yadda ta fahimci ana yi duk sanda Inna Danejon tayi tafiya ta dawo, su Msma Rabi dama wasu da bata san su waye ba sun zo ana ta faman kwance tsaraba kala-kala, Samirah ce ke gaya mata cewa in dai Inna Danejo taje Bakori to ba gidan kadai ba, tun daga farkon layinsu har karshe kowanne gida sai an kai masa tsarabarsu, abubuwa ne kala-kala har da wanda ita bata taba gani ba ma sai faman rarrabawa ake yi bisa umarnin da Inns Danejon ke bayarwa.
Kusan ita dasu Mama Rabi ne ma ke ta aikin don Samirah ita nata na amfanin gida kawai take ta warewa, tana yi suna fadansu ita da Inna Danejon akan cewar tana diban komai da yawa, Munaya kuma tsince-tsincen duk abinda ta san zata iya ci take yayin da Surayya ke ta aikin danna wayarta taje ta nanike a jikin Inna Danejon dake ta nan-nan da ita, wanda sai a lokacin Amina take jin wai sunan maman Inna Danejon aka saka mata, shi yasa duk gidan tafi shiri da ita akan kowa.
A lokacin ne kuma Samirah ke gaya mata cewar gobe Amaren da akayi bikinsu tare zasu zo, don haka duk tarin taraddadin dake zuciyarta, sai taji itama tana murna da zuwan nasu, don aƙalla koyaushe tana jin hirarsu kala-kala a bakin su Samiran.
Ta cakuda hannayenta duka biyu waje daya lokacin da Mama Rabi ta karbi aikin da take yi tace taje ta huta, Inna Danejonnkuma ta miko mata wata damammiyar fura mai gardi a cikin roba tana yi mata nata sannun itama, kuma duk da yadda take murmushi akan fuskarta hakan bai ƙarasa har cikin zuciyarta ba, don bai isa ya kore halin da zuciyarta ke ciki ba.
Ta samowa kanta mafita ta sani sai dai duk da hakan mafitar bata canja daga umarnin Amma ba don ba zata taɓa iya kin bin maganganunta ba, itace gatanta ta sani kamar yadda ta san maganganunta sune fitilar da zasuvgitar da ita daga duhunnda taje ciki, don haka a dole ta tsamo kanta daga rudanin zuciyarta ta yanke hukuncin aiwatar da umarnin Amma tare kuma da samawa kanta mafitar da take ganin zata jefi tsuntsu biyu ne da dutse daya.
Zata yi abinda Amma tace, zata aikata umarnin Kilishi ta hanyar samun gaskiya da kuma yardarta, sannan zata yi jinyar Ma'aruf ta hanyar da hakan zai ƙara shaƙuwa tsakaninsu, a yanzu zuciyarta ta riga ta karɓe shi da dukkan iyawarta, don haka zata ajiye komai a gefe ta gyara rayuwarsu kamar yadda ya roƙe ta, kamar yadda yake so... Idan tayi hakan ta san zata samu sauƙi a zuciyarta na ganin laifi da kuma rashin kyautawarta.
Hannayenta suka kara rawa lokacin da ta tuno yadda suka kasance dazu da safe, dama abinda ya rada a kunnenta kafin ya fita bayan tambaya karbi robar zogalen nan.
_You are really making me insane, and I like it..._
Tana iya tuna yadda wasu abubuwa ke harbawa a cikin kanta wannan lokacin, dama yadda jikinta ya dinga rawa a cikin hanayensa kafin ya janye ta a hankali yana gaya mata cewar zai fita a cikin kunnuenta.
Sai dab da magariba sosai sannan komai ya natsa, suka gama haÉ—a kan tsarabar nan tsaf, sannan ta samu tayi sallah, har kowa ya tafi sai ita kadai a bangaren Inna Danejon, don bata san me zata koma bangarensu a wannan lokacin tayi ita kadai ba, jira take amma bata san ma abinda take jira din ba, dawowar Ma'aruf ko kuma akasin sa??
Kuma da misalin karfe bakwai da rabi daidai, sai dukkan wani tunaninta dama kokwanton ta yazo kan gaɓa, sannan fatanta dama duk wani tsarinta ya tafi daidai lokacin da kiran Hajiya Kilishi ya riske ta.
Mama Rabi ce ta shigo ta gaya mata sakon, kuma bayan hakan bata ce komai ba don haka Inna Danejon ma bata yi wani tunanin komai tayi mata sallama ta fito tare da tata katywar ledar kayan tsarabar.
A harabar gidan ta hango Mamin, tana tsaye a jikin motar ta kirar Camry yayin da Malam Sani direba ke ciki ya kunna motar, hasken gitulun danjojinta na haskawa ta kowanne gefe, tafiya kawai take yi har suka karasa tare da Mama Rabin dake fadin.
"Hajiya ashe har kin fito."
Kuma Mamin bata amsa ba, sai ta kalli kayan hannun Aminan kawai sannan tace da Mama Rabin ta karba ta tafi dasu.
Kwatanta yadda zuciyar Amina ke bugawa a kirjinta wannan lokacin wani abu ne da ba zai bayyanu ba, don kafafunta ma bata jinsu a jikinta kwata-kwata, yayin da jikinta yayi shafal kamar fallen takarda.
"Amina..."
Hajiya Kilishin ta kira ta cikin sautin muryarta da ya fito tar a shirun harabar compound din.
Bata amsa ba don bata san me zata ce ba, tana kallonta ne kawai da dukkan taraddadin dake yawo akanta, kuma ga mamakinta kawai sai taga tayi wani irin murmushi mai fadi da ya tabo har cikin idanunta kafin ta fadi abinda ya tsayar da duk wani hargitsin kanta cak!
"Ma'aruf yana asibiti, yanzu Ishaq ya kira ni yake shaida min!"
Maganganun suka fito tar cikin muryarta, kuma bata jira komai ba sai ta miko mata wata takarda da sai a yanzu ta kula da ita a hannunta.
"Ga nawa albishir din Amina, kamar yadda kema kika bani naki."
Bata san tsawon sakanni nawa ne suka wuce kafin ta ita sa hannu ta karbi takardar amna idonta da kwakwalwar ta basa gane ko meye a jiki balle har ta kai ga fahimta, kuma abinda Mamin ta gane kenan saboda haka tace.
"Appointment ne na wani asibiti a Indiya, za'a kai Aminu a gyara masa kafafunsa, na biya komai, saura shi da mai raka shi su fara fafutukar visa."
Ta fadi hakan sannan ta yi shiru tana kallon yadda hannun Aminan ke rawa tare da takardar, sai kawai ta sake wani murmushin sannan tace.
"Me na gaya miki ne Amina? Komai mai sauki ne umarni na kawai zaki bi, shikenan sai in mayar miki da duniyarki kamar aljanna."
Abinda bata sani ba shine a wannan lokacin Amina ba jinta take yi ba, kwata-kwata bata saurarar abinda take fada take yi ba, maganganun Amma mahaifiyarta ne kawai ke yawo akanta.
_"... A tafin hannunki zaki dora Kilishi Amina, a tafin hannunki zaki dinga juya ta ba tare da ta sani ba, duk abinda kike so har ma da wanda baki roka ba zata yi, da kanta zaki sa tayi ta haƙa ramin binne kanta har sai yayi zurfin da zai rufe ta!"_
***
_Me ya faru da Ma'aruf?_
_Kun fahimci cewa mun fara wasa da hankalin Kilishi?_
_Kun fahimci kudirin Amina?_
_Kun fahimci inda rayuwarsu ke shirin kaimu?_
_Me zai faru game da tsarin su Jawad?_
_Me ke shirin faruwa da Zainab? ( Ƴar aikin gidan su Jawad.)_
_Allah yasa baku manta da Hameda da kuma mamanta Rukayya ba... Suna nan tafe._
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:50 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*04*
~~~~~~~
_There are feelings that can't be explained._ _- Unknown_
**
A cikin asibitin, daga cikin wani dogon korido mai É—auke da kofofin kala-kala, Hajiya Kilishi na tsaye ita da Faruk yayin da daga gefenta kan kujerar masu jira na asibitin Amina ce ke zaune suna sauraren bayanin da Faruk din ke yi.
"Wallahi Mami mun gama duk abinda zamu yi, munyi sallama lafiya kalau da shi har ma da wanda muka hadu dashi din, kowa ya hau mota muka rabu a wajen round about din nan, to ni nayo gaba kawai sai go slow ya tare ni kafin inyi nisa, anan naji wasu mashin da suka karaso suna hirar fadan da suka baro ana yi a baya, daya yana cewa wai ai ya san mai dukan sunansa Ma'aruf yana aiki tare damu a kamfani, naji yana bawa abokinsa labarin daya incident din a ya faru dashi da Daniel.
Da kyar na fita da go-slown nan na koma, kuma lokacin da naje ma har an raba su an dawo da Ma'aruf din motarsa mutane suna ta rike shi, ina masa magana amma kamar bai gane ni a lokacin ba, shine na kira Ishaq, sai da ya karaso sannan da kyar yasa shi ya yarda ya baro wajen, amma tunda naje abu daya yake ta fada wai a barshi ya karasa kashe mutumin yana da sakon da zai bashi."
Hajiya Kilishi tayi ajiyar zuciyar dake shaida tsananin damuwarta kafin tace.
"Kuma ko bayan fitar tasa ma munyi waya sai kuma na kira shi daga baya bai dauka ba."
"Ai Mami gabadaya wayoyin nasa ma da wallet da komai an kwashe, da yake bude motar kawai yayi ya fita a lokaci guda, to a wannan hayaniyar ɓarayi suka samu dana suka kwashe komai, har mukullin motar sun tafi dashi, ita kanta motar ma don baza su iya dauka a lokacin bane."
"Tana ina yanzu?" Kai tsaye ta sake tambaya.
"Tana wajen, nasa wasu dai sun tura ta zuwa gefen titi, sannan na basu kudi su kwana a ciki saboda ban ma san inda za'a nemo spare key dinsa a dauke ta ba."
Duk wannan bayanin da Faruk ke yi, Amina dake zaune daga kujerar baya ta masu zaman jira a asibitin idanunta na manne ne da kayan Faruk din, farar shadda ce a jikinsa wadda gabadaya gabanta ya ɓaci da jini har zuwa kowanne hannun na rigar, zuciyarta na bugawa da motsin dake shaida girman laifinta da a yanzu take ganinsa karara, yayin da kalaman ke yawo a cikin kanta, tana yarda da kowacce kalma ɗaya bayan daya dake maimaitawa daga cikinsu.
Suna gaya mata cewa tabbas babu abinda dan adam zai samu a duniyar nan cikin sauƙi, sannan kuma babu wani abu da mutum ya kamata ya fito yayi takama dashi a duniyar nan, don ana zuwa gabar da rayuwa ba zata baka zabi ba, zaka zo kayi wani abu da ko a mafarki ba zaka taɓa tunanin aikata shi ba.
A baya zata rantse da Alkur'ani wajen karyata duk wanda zai zo ya shaida mata cewar zata iya aikata wani abu najamancin wannan, amma sai gashi a yanzu da hannunta ba tare da tursasawar kowa ba tayi abinda take jin tambarinsa ya É—arfanu a zuciyarta ta hanyar da ba zai taba goguwa ba, don idan har za'a lissafa da sunanta a cikin wanda suke da kamasho a yau wajen faruwar wannan tashin hankalin, wajen zama sanadin da har mutane biyu ke kwance a asibiti, da kuma fitar jinin da take kallo har a jikin Faruk yanzu, to kuwa ta tabbata bata da kalaman da zasu wanke ta ko a gaban waye.
"Ka ce bai ji ciwon sosai ba ko?" Sai a wannan lokacin muryar Mamin ta shiga kunnenta, tana tambayar Faruk din da ya gama amsa wata waya wafda da alama fuk akan abinda ya shafi al'amarin ne.
Ya daga kansa sau daya.
"Ba sosai ba, na wancan mutumin ne yafi yawa, tun a can muke fatan Allah yasa bai fasa masa ido ba, don dukansa yayi tayi Mami, yana cewa a kyale shi ya kashe wai yana da sakon da zai bashi."
"Inalillahi wainna ilaihir raju'in... Bari na kira Baffa."
Ta faÉ—a amon muryarta na fitowa da tsananin damuwar da babu wanda zai kasa shaida hakan, Amina ta bita da kallo baya ta juya ta bar wajen, kuma a wannan ya lokacin ne wata Nurse dake cikin É—akin da suke jira a kofarsa ta fito, hannunta dauke da farantin kayan dressing wanda ya cika fal da tarin auduga mai jini.
Idanun Amina ya sake bin hannunta da kallo har ta ɓacewa ganinsu, abinda take ji a ranta yayi yawa a lokacin don haka sai kawai ta damƙe hannayenta biyu duka waje daya ta a shirin kore kwallar dake taruwa a idanunta. Munaya wadda suka taho tare da ita ta karaso daga fitar da tayi tana gama waya da Hajiya Maimunan da ta sake kira tana tambayar halin da ake ciki.
Taji sanda ta zauna a gefenta bayan tayi sallama da Hajiyan don haka ta juyo ta kalle ta.
"Za'a barmu mu ganshi yanzu?"
Sai ta girgiza kanta.
"Wallahi ban sani ba, amma ko sun ce ma ai inaga Mami ce kadai zata shiga."
Idon Amina ya nuna da mamaki kafin ta tambaya.
"Saboda me?"
"Saboda idan yana wannan yanayin bai kamata aje kusa dashi ba, Mami ta fada mana hakan tuntuni."
Bakin Amina ne ya bude a lokaci guda, mamakin dake idonta ya karu tana kallonta.
"Waye yake kula dashi kenan?"
"Yaya Ishaq ne, yawanci ma ba anan suke zama ba, akwai asibitin da yake ganin likita a London, can suke tafiya sai ya sami sauki tukunna. Amma lokaci kadan ne, da mood din nasa ya dawo zaki ga koma daidai."
A lokaci guda sai taji hankalinta ya kasa ɗaukan maganganu da Munayan ke faɗa, kallonta kawai take yi yayin da take jin kamar kwakwalwarta na washewa, komai yana gogewa, don bata san yadda zata dauki wannan al'amarin ta ƙara akan sauran tarin abubuwan dake kanta ba.
Tunaninta ya kasa lissafa wace irin zuciya ce da Hajiya Kilishi, a kowanne irin ma'auni na duniya ta rasa a wanne iri za'a dora zuciya irin ta Kilishi tayi kama da ta mutane... Abubuwan da ta aikata a rayuwarta kaf idan za'a tara su waje É—aya bata jin duk raunin imanin mutum a duniyar nan za'a sami wanda zai kalla bai ji zuciyarsa ta motsa ba.
Ta shigo cikin rayuwar mutanen nan da ƙarfi da yaji, ta gurgunta mahaifiyarsa, ta ƙwace shi daga gare ta, ta shuka tarin ƙananun abubuwa a cikin rayuwarsu da watakila ita kanta ba zata iya lissafawa ba, kuma duk da bata sani ba tana tunanin wataƙila itace sanadin ciwon nasa ma amma duk wannan bai ishe ta ba sai ta daƙile shi kuma a dukkan ɓangare na kulawa irin wannan.
Bata san irin ciwon Ma'aruf ba, bata san komai game dashi ba, amma tayi imani cewar babu wani ciwo a duniyar nan da baya bukatar kulawa, ko da na hauka ne kuwa, to ta yaya za'a ce ayi nesa dashi a lokacin da yake tsananin bukatar kulawa?
Farkon zuwanta gidan tana ganin komai ne daidai, tana sha'awar mu'malarsu da komai shaƙuwarsu na mata yawo a ido kodayaushe, amma sai a yanzu take ganin tarin ramukan dake gewaye dasu, sai yanzu take fahimtar cewa ba daidai komai yake tafiya ba kamar tunaninta.
Mutane ne su masu hankali, Æ´an boko kuma masu ilimi, amma Kilishi ta dauke su gabaÉ—aya ta sanya a wani rami da babu mai iya haurowa, tana daga sama sai iya amon muryarta da kuma umarninta kawai suke ji, suna yin dukkan abinda ta furta ba tare da sun sani ba, ba tare da sun san ma me saka su ba. Taji zuciyarta ta matse a lokaci guda wani abu a cikin kanta yana gaya mata cewa wannnan yana daya daga cikin abubuwan da zata fara canjawa.
Tana jin Munayan na cigaba da waya da wata classmate dinta a lokacin, tana jin suna tattauna wani abu da ita ba fahimta take yi ba har sanda Mamin ta dawo, ta shiga gayawa Faruk da ya dawo cewar yaje gida ya canja kayansa, don mutanen dake wajen duk wanda zai wuce sai ya kalle shi, amma yace mata bari likitan ya fito tukunna su ji abinda zai ce, don har ga Allah baya jin zai iya tafiya ba tare da ya san halin da ma'aruf ke ciki ba.
Zuciyarsa ta yage har karshe tun daga lokacin da yaga yadda yake rike Ma'aruf a wajen nan yana yi madmsa magana amma babu alamun ya a gane shi alhsli yanzu-yanzun nan suka rabu lafiya, lokacin da al'smarin Daniel din nan ya faru a Office zuciyarsa tana bada wani kamashon laifin ga Daniel din, yana ganin har da laifinsa wajen tunzura Na'aruf din, amma abinda ya gani yau, yafi karfin dukkan wani tunaninsa.
Don haka yana tsaye har lokacin da Ishaq ya bude kofar wajen ya fito, kayan jikinsa kalar maroon ne amma duk da haka ana ganin inda ya samu nasa rabon ɓacin jinin shima.
"Ishaq me ake ciki? Me suka ce?"
Mami ce ta fara jero tambayoyin cikin zaƙuwa. Kuma da muryarsa a hankali kamar kodayaushe yace.
"Mami ki kwantar da hankalinki, ciwonsa ne dai ya tashi, dama munyi sa'a ne kwana biyu mood din nasa ya saisaita, kuma ban san me ya tada shi yanzu haka a lokaci guda ba. Sai dai na yi musu duk bayanin da suka bukata kuma sun bude file sun rubuta hakan, yanzu an bashi alluran bacci yana hutawa."
"Abinda zasu iya yi masa kenan?" Ta tambaya.
Ya gyada kansa.
"Mami ai ko irin magungunan nasa na basu dasu anan, guda daya kawai aka samu, so na gaya musu zamu taho da na wajenmu zuwa gobe su kara duba su tukunna, ina tunanin insha Allah iya nan komai zai tsaya, ba sai mun koma London ba. Don allurar da suka yi masa ma iya ta zuwa gobe ce."
Hajiya Kilishi ta gyaÉ—a kanta alamun fahimta sannan ta sake furta kalmar inalillahi wainna ilaihir raji'un fuskarta na nunaea da abinda za'a kashe wani akansa cewar damuwa ce.
"Likitan ya fita, yanzu zasu kaishi É—akin da zai huta, sunce nambar dakin C0-9."
Mamin ta gyaÉ—a kanta.
"Zamu je mu ganshi kafin mu tafi...."
"Mami zan zauna."
Babu zato muryar Amina ta katse abinda Hajiyan Kilishin ke shirin fada. Dukkaninsu suka juyo suka kalle ta a lokaci guda, wani guntun mamaki ya haska a fuskar Hajiya Kilishi kafin tayi saurin kore shi da murmushi.
"Toh shikenan, sai ki zauna zuwa gobe."
Ishaq ya gyaÉ—a kansa shima.
"Zanje in ɗauko masa wasu kayan da za'a canja masa don waɗannan na jikinsa sun ɓaci. Sannan zuwa gobe zan dauko reports dinsa gabadaya na asibitin don na san familyn wancan mutumin zasu iya shigar da kara, dole ne mu sami backup a hannu."
Faruq ne ya fara gyaÉ—a kansa kafin yace.
"Allah ya kaimu, I need to talk to you please kafin in wuce." (Ina so muyi magana kafin mu wuce.)
"Okay toh muje." Cewar Ishaq din suna yin gaba.
"Kin tabbata kina son ki zauna?"
Munaya ta tambaya tana kallon Amina lokacin da wata Nurse ta karaso tana mikawa Hajiya Kilishi wasu takardu na É—akin da aka kai Ma'arf É—in, kuma tana jin wani abu kamar damuwa na yawo a cikin muryar tata.Sai ta gyada kai tana kallon hannayenta.
"Babu abinda zai faru Munaya Insha Allah, bai kamata a barshi shi haka shi kaÉ—ai bane ba."
Hajiya Kilishi ta juyo riƙe da takardun nan a hannunta ta miƙowa Munaya su.
"Munaya je ki fara dubo mana dakin gamu nan."
Wannan karon muryarta ta fito da sanyi kalau, kamar na iskar wajen dake hurowa daga A.c, kuma Munayan bata yi tunanin komai ba ta mike tsaye ta karbi takardar amsawa da Toh.
Hajiya Kilishi ta bita da kallo har ta bace a dogon koridon wajen sannan ta juyo ga Aminan da har yanzu kanta ke sunkuye a kasa tana wasa da yatsun hannunta.
"Naji dadin abinda kika yi fiye da tunaninki Amina, na baki wannan aikin ne don in gwada hankali da kuma tunaninki ba wai don ba zan iya ba kin sani, kuma ba zan boye miki ba zuciyata ta yaba da irin hikimarki, musamman a yanzu da nazo naji cewa daga Mai gaskiya har wadannan abokan nasa basu san komai ba, shi kansa bai san cewar ya sha magani ba balle har ya dora zargi akanki.
Na san zaki iya Amina, na san zaki iya tun daga ranar dana fara ganinki a duniya jikina ya bani hakan, shi yasa nayi amfani da Aminu na zaburar dake don ki fahimci cewa zaki iya din ba tare da kin bata min lokaci ba, amma kamar yadda na nuna miki ne, komai zai wuce kamar ba'ayi ba, zan sa ki manta da abun da ya faru dashi kwanan nan insha Allah.
Shima Ma'aruf din zai tashi, kwana biyu ne dama wanda kafin nan na gama dukkan abinda zanyi akan RTL, don haka abu daya nake so dake yanzu, ki rage wannan damuwar dake kan fuskarki, kin riga kin shigo cikin tsarina Amina, kuma ni bana tafiya ina barin shaidar takuna a baya, ina wucewa ta cikin sahara ne ba tare dashi kansa yashin wajen ya san na taka ba. Kin fahimce ni?"
RTL! Sune kalaman da Amina ta fara rikewa a cikin kanta kafin maganganun Amma su gufta cikin kanta.
_ki ƙasƙantar da kanki a gabanta ta sigar da ba zata taba iya haska cikin zuciyarki har tayi wani hasashe ba..._
Me ya same ta ne? Me take shirin yi? Tayi saurin tambayar kanta, tayi komai, ta samu yardar Kilishi a yau kadai tun ba'aje ko'ina ba, sannan kuma a yau din tana neman tayi wasa da haka? Yawu ya zarce cikin maƙogwaronta babu shiri, Amma bata nan, hasali ma zata iya kirga iya lokutan da ta taba ganin Hajiya Kilishi a rayuwarta, amma kamar ta karance ta ne tsawon shekaru, dukkan maganganunta suna zuwa akan kowacce gaɓa na tunanin Kilishin. Saboda haka sai tayi saurin girgiza kanta sannan tace.
"Mami, damuwata ba akan abinda ya faru take ba, tunanin nake yi idan har da gaske kike game da abinda kika fada akan Aminu, ina son Æ´anuwana fiye da komai Mami, kuma zanyi komai kamar yadda kika fara gani yanzu indai akansu ne, shi yasa nake ta fatan samun saukin sa kamar yadda kika fada."
Ta fadi hakan bayan ta É—ago tana kallonta, kuma ga mamakinta sai kawai tayi murmushi mai kyallin dake tabowa har cikin idanunta kafin tace.
"Kar ki damu Amina, kin riga yarda dani amma baki gama tabbatarwa bane, abinda nake so kawai shine ki kwantar da hankalinki, duk wata gaggawa bata ɓullewa ga nasara, don haka mu bi komai a hankali. Ina tabbatar miki da sannu zaki fahimci wacece Kilishi da kuma hukuncinta!"
Amina ta kalle ta da nata guntun murmushin da a dole ya sauko kan sannan ta daga kanta kawai.
_Ina tabbatar miki idan kika tsallake matakan farko Amina, komai zai zo miki bi da bi kuma saukake, yardarta kawai muke nema a yanzu._
Tabas! kalaman Amma gaskiya ne, gwara da ta daure zuciyarta ta bi umarninta, don tun a yanzu ta fara fahimtar cewa babu wahala juya tunanin Kilishi,
Taji zuciyarta na ƙara yarda da kalaman Amma na cewar kissa da dabara sune makamin kowacce mace a duniyar nan, ba namiji kadai ba, hatta mace ƴaruwarta yanzu zata ci galaba akanta da waɗannan abubuwan duk kuwa da irin takama da ikonta, ya danganta kawai daga yadda macen ta yarda ta bude kwakwalarta, ta yarda cewa Allah ya halitta mafitar kowacce matsalarta a cikin kwakwalwarta, kuma idan ta dogara dashi ta yarda cewar zaki iya ɗin, shikenan ta rusa dukkan wata katanga dake gabanta.
Kuma lokacin da suka isa É—akin, kwata-kwata su Mami basu fi minti biyar ba suka tafi bayan Mamin ta furta kalmar Allah ya sawwake sau daya, wadda ta san itama ta fada ne saboda Munayan dake tsaye, wadda ita kuma ta kasa dauke idonta daga kan Ma'aruf din tun bayan shigarsu, tana kallonta har sanda suka zo fita sai da ta waiwayo ta sake kallonsa.
A wanan lokacin ne kuma zuciyarta ta kasa iya auna irin don da Hajiya Kilishi ke ikirarin taba yiwa Ma'aruf, duk da cewar ita kanta shaida ce, tana kaunarsa ta wata siga da babu mai iya kwatanta ta cikin hankali, don babu hankalin da zai yarda da so da kuma cuta a lokaci guda, ta yaya za'a yarda tana sonsa amma zuciyarta bata jin komai wajen cutar dashi? Ita gabadaya saninta dashi na yaushe ne, amma da yaya ta daure zuciyarta ta aikata komai kuma yanzu yaya take ji a ranta?
Sai ta matsa a hankali zuwa gaban gadon bayan fitarsu, kuma da kowanne taku tana jin kamar tana tafiya ne da nauyin laifukanta a gabansa, laifukan da a yanzu zuciyarta ke shan alwashin gyaransu ta duk hanyar da ta san zata iya, tunda ta riga ta fara yin mai wuyar.
Kafafunta suka tsaya a gaban gadon tana kallon fuskarsa, kuma yanayin yadda fuskar tasa tayi so innocent ya daki zuciyarta taji tana ƙoƙarin hadiye wani abu da ya kasa barin makogwaronta.
Wasu abubuwan suna faruwa ne ba'a yadda bawa ya tsara su ba, wasu nasarorin suna samuwa bayan ka daure zuciyarka wajen aikata wani abu da kake da yakinin samun nasararsa a gaba.
Gashin kansa a barbaje yake sosai, sannan fatar bakinsa ta rabu da Æ´aruwarta ta yadda tana iya jin fitar numfashinsa ta duka hanci da baki daga inda take tsaye, sai ta tsugunna a hankali idanunta na cigaba da kallonsa.
Kuma bata san ta yadda zata hana kanta ba sanda hannunta ya sauka akan gefen fuskar tasa, yatsanta daya ya taho a hankali daga gefen fuskarsa zuwa karshe, kumatunsa ba cikakken bane kuma ba ramamme ba kawai dai wani abu ne a tsakiyar hakan, da sauri ta janye hannunta ganin ta karasawa kusa da bakinsa sannan ta mike tsaye.
Wayarta da ta ajiye akan kujerar dakin tun bayan shigowarsu taje ta dauko, missed din Amma har guda biyu ya shiga idonta. Bata san lokacin da ta kira va don wayar ta shiga silent,kuma dama ko bata kira din ba, ita take shirin kira don tun safe ya kamata ace sunyi wayar amma hayaniyar dawowar Inna Danejon nan ta É—auke hankalinta.
"Assalamu alaikum."
Muryar Amman da ta fito a hankali kuma cikin sanyinta kamar kodayaushe tasa ta jin kowacce tsigar jikinta na tashi, tasirin al'amarin na da kuma abinda tayi na kara kamata, ta rufe idanunta a hankali kafin ta iya tattaro dauriyarta ta fara gaishe ta, wanda bayan hakan ne dukkan sauran hirarsu ta biyo baya.
Hirar da a cikinta kalaman Amman da kuma umarninta ya kara inginza zuciyarta, suna buÉ—e mata wani sabon kwarin gwiwar da bata san tana dashi a baya ba!
***
*Washegari.*
*07:30am.*
"Doll..."
Muryar ta shiga kunnenta a hankali, ta jiyo amonta kamar daga can nesa, kamar a cikin wani fili da ita take ƙarshensa muryar kuma tana daya karshen, don haka bata motsa ba ta tsaya a hankali tana saurare ko zata kara jinta,bdon bata yarda cewar wanda take tunani zai kira ta da hakan a halin da yake ciki ba. Ilai kuwa bayan sakan daya biyu kuwa sai amon ya sake cika kunnenta da wannan sabon suna da a duniya kaf ta san mutum daya ne ya taba gaya mata.
Babu shiri ta bude idanunta, amma hasken da ya shiga cikinsu a lokaci guda ya hana ta ganin komai, sai da ta maida shi ta rufe tasa hannunta ta mutsikka sannan ganin nata ya dawo daidai, a cikin É—akin asibitin nan ne, don kafar gadon da take fuskanta itace abu na farko da ya tuna mata cewa tana kwance ne akan carpet din dakin tun bayan da tayi sallar Asuba kuma ta gama yiwa Ma'aruf dukkan addu'o'in da Amma ta shaida mata jiya a wayarsu.
"Doll..."
Muryar Ma'aruf da ya kira ta yasa idonta ya kai kansa a lokaci guda, yana kwance irin yadda take ta gefe daya a saman gadon, idanunsa duka a buÉ—e suke kallonta.
Mamaki ya ratsa ilahirin jikinta gabaɗaya don bayan dawowar Ishaq jiya da daddare yace mata likitocin sun ce ba lallai a yau ma a samu ya farka ba don allurar tana da karfi sosai, sai kuma ta tuno addu'o'in da tayi har bacci ya dauke ra, a lokaci guda tajintana kara yabawa ƙudira da kuma ikon ubangiji, don haka ba shiri ta mike zaune kuma bata jira komai ba ta ja ƙafafunta ta ƙarasa gabansa.
"Why are we here?" (Me yasa muke anan?)
Ya tambaya amon muryarsa na fitowa a hankali yayin da yake kallonta, gashinsa a barbaje kamar yadda yake tun jiya sannan idanunsa ke lumshewa alamun fada yake yi da kansa wajen bude idon. Tausayinsa da ta kwana dashi a cikin zuciyarta ya sake tasowa a ranta, taga idonta na nuna mata cewa kamar ya rame daga jiya zuwa yau kaÉ—ai.
Tasa hannunta a hankali ta gyara dankwalinta da yayi baya da yawa, ta jawo shi ta rufe gashinta sannan tace.
"Baka da lafiya, jiya su Ishaq suka kawo ka."
Taji muryar tata ta fito kamar wani yana karta farce akan katako don haka ta shiga kokarin yin gyaran murya kadan sanda ya girgiza kansa a hankali.
"I don't want to be here." (Bana son zama anan.)
Ta daga kanta a lokaci guda.
"Tohm, bari nayi wa Nurses din magana su zo sai mu tafi gida."
Ta fadi haka da niyyar mikewa amma a lokaci guda ya kamo hannunta, taji yatsunsa da suka dauka dsuka da sanyin A.cn sun ratsa sun nad hannun nata, numfashinta ya dan katse a kirjinta kafin ta dawo ta tsugunna akan gwiwoyinta sanda idanunsa sun sake rufewa.
"Kar ki kira su."
Bata ce komai ba, yayi ƙoƙarin sake bude idonsa sannan yace.
"Ina wayata?"
Tambayar tasa a lokaci guda ta tuna abinda Faruk ya fada a jiya cewa an dauke duka wayoyin nasa har dasu wallet, don haka sai kawai tace bata san inda take ba, ya sake yin shiru yana kallonta, lumsassaun idanunsa suka tsaya akanta ba tare da yace komai ko kuma ya kifta su ba, zuciyarta ta shiga tsere a kirjinta, don duk da ta san rashin lafiya ce tasa idanunsa suka koma hakan, tana jin tasirin yanayinsu har kasan zuciyarta.
"Kin goge numbers É—in nan?"
Ya sake tambaya a hankali, tayi shiru na wasu sakanni tana son ta tuno wadanne nambobi yake fada kafin ta tuna ranar da yace mata ta kwashe wasu nambobi daga wayar da ya bata zuwa ta hannunsa lokacin da suna hanyar dawowa daga jigawa.
"A'a suna nan a cikin wayar har yanzu." Ta faÉ—a a hankali, kamar idan ta É—aga muryar tata tana tsoron zata fama masa wani ciwon ne.
Kuma saboda kokari sai da ya daga kansa sau biyu sannan yace.
"Akwai number Ishaq a ciki, ki kira shi kice masa yazo ya fitar dani daga nan."
Ta daga kanta sau daya sannan tayi kokarin zare hannunta daga cikin nasa a hankali kafin ta mike yayin da ya maida idanunsa ya sake rufe du.
Akan kujerar dakin ta ajiye wayar tun bayan da alarm din Asuba ya tashe ta, don haka ta dauko ta ta shiga nenan nambar Ishaq din. Bugu daya biyu, uku aka dauka.
"Ma'aruf..."
Taji muryarsa ta kira sunan da manaki da kuma kuma kokwanto bayan saurin dske cikinta. Sai idonta ta koma kan Ma'aruf din da har yanzu idanunsa ke rufe sannan tace.
"Ba shi bane, amma dai ya farka."
Jin muryar tata yasa taji kamar yayi ajiyar zuciya kafin ya sake tambaya.
"Kin tabbata ya farka?"
Ta daga kanta.
"Eh, shi yace in kira ka ma kazo ka maida shi gida, yace baya son zama anan."
"Kin kira Nurses din wajen?"
"A'a kai yace in fara kira tukunna."
Yayi shiru na wasu daƙiƙai kafin yace.
"Bashi wayar."
Sai ta taso a hankali ƙafafunta na taka laushin carpet ɗin wajen kafin ta isa ta tsugunna daidai gabansa, kuma kamar yaji ta ya sake buɗe idanunsa wannan karin sosai a cikin nata.
"Zaiyi magana da kai." Bata san lokacin da fatar bakinta ta fadi hakan ba.
"Kin gaya masa abinda nace?"
Har yanzu sautin muryarsa a hankali yake fitowa, ta daga kai tana kasa janye idanunta daga cikin nasan, sai yace.
"Ki kashe wayar kawai."
Ta dan tsaya kaÉ—an don ta tabbata Ishaq din daje cikin wayar yaji, amma ga mamakinta sai kawai taji shima yace.
"Rabu dashi gani nan zuwa."
Daga haka bai kara cewa komai ba kiran ya katse. Ta ajiye watar a gefe tana ganin yadda fatar idanun nasa ke sauka a hankali girmansu na kara raguwa, amma kuma duk da haka ita yake kallo.
"Zaka ci wani abun? Ko tea?" Ta tambaya tana ganin wautar ta, don a yanayinsa kowa ya kalle shi ya san bai gama dawowa haiyacinsa ba, kuma sai ya sake girgiza mata kansa sannan yace.
"Just stay Amina..."
Abinda ya fada kenan kafin idanun nasa su ƙara rufewa a lokaci guda, ta tsaya kusan sakanni biyar tana kallonsa kafin tajo tana son sake rike hannun nasa, don bata san me zata yi ba ma idan ta tashi.
Don haka haka ta miƙo shi ta riko nasa a hankali, kuma ga mamakinta sai taji ya kara rike su shima, yana ratsa yatsunsa tsakanin nata sanyin dake jikinsu ya ratsa farar ta kamar dazu, sai kawai ta matso da kanta ta kwantar dashi a gefe gadon itama, tana kallon fuskarsa yayin da idanunta ke ƙiftawa a hankali.
***
*Awanni biyu bayan hakan.*
"Mami ni na san Ma'aruf, wallahi idan ya farka ya sake ganinsa a wajen nan abinda zai biyo baya zai fi muni akan wanda ya faru jiya."
Ishaq ya fada lokacin da yake tsaye a kofar dakin, yayin da daga ciki wasu Nurses ne guda uku matsbiyu da namji daya ke kokarin dora Ma'aruf akan wani gado mai taya da za'a fita dashi.
Amina na tsaye daga gefensu riƙe da jakar ƴan kayayyakin da aka kawo musu idonta yabi hannun ɗaya Nurse din da ta riko kansa da kallo, tana kallon yadda hannunta ya nutse cikin gashin kansa, wani abu ya motsa a cikin zuciyarta.
Sai kawai ta juya tana sauraren Ishaq É—in dake cigaba da yiwa Mami bayanin da yasa dole ya nemi sallamar wa Ma'aruf, yana rokonta akan ta kira Baffa tayi masa bayani akan cewar ya bari a dawo da Ma'aruf gida don yanzu suka gama waya dashi yan fadan cewar don me ya biyewa Ma'aruf É—in yace a sallame shi, saboda kawai yace baya son zama a asibitin.
Kuma bai sani bane amma ita kanta Mamin bata so hakan ba, da zata sami dama nata ƙorafin zata yi itama. Don kamar yadda ta faɗa mata a yau ne zata aiwatar da koma meye kudirinta, kuma abu na karshe da zata so shine ace Ma'aruf baiyi nisan daga gare ta ba ta yadda ba zai iya kawo mata giftawar wata matsala ba komai kankantar ta.
Ta maida wayarta jaka lokacin da Nurses din nan suka shiga tura gadon da suka É—ora Ma'aruf É—in dake bacci har yanzu, don tun bayan wannan farkawar, bai kara bude idanunsa ba.
"Amina."
Muryar Ishaq da ya karaso cikin É—akin bayan fitar Nurses fin tasa ta dawo dq hankalinta kansa.
"Bai ce miki komai ba bayan sakon da kika bani lokacin da ya farka?"
Ta girgiza kanta a hankali.
"Cewa kawai yayi in gaya maka kazo ka fitar dashi, kuma bayan kiran ya katse ma bai sake cewa komai ba."
Ta gyada kansa yana maida wayarsa cikin aljihu.
Shiru ya ratsa na dakika biyu kawsi kagin ymuryarsa ta sake fitowa.
"Mun gode sosai da abinda kika yi Amina, this is the first time da wani ya taba zama da Ma'aruf a irin wannan yanayin bayan ni."
Bata san me zata ce ba, don haka ta gyada kanta a hankali tana kallon jakar hannunta da ta rike. Ya juya ya fita daga dakin har a lokacin bata dago ba, rayawa take a zuciyarta cewa idan har daga yanzu za'a fara yi mata godiya akan duk abinda zata yi, watakila za'a zo lokacin da za'a rasa wajen ajiye godiyar ma.
****
Hajiya kilishi ta tsirawa sakon da ya shigo wayarta ta nambar Awwalu ido, ta karanta ta sake karanta yadda yake gaya mata dukkan tsarindu ya tafi daidsi lokaci kawai yske jiracda kira ta kafin wani irin murmushi ya subuce a bakinta.
Me yasa take mantawa ne wai? Itace fa, itace wannan Kilishin da ba ta taba saka abu a gaba bata cimmasa ba, to don me kuma a yanzu take iya saka kokwanto a ranta? Me yasa take yiwa komai tunani biyu bayan gashi Aminar ma ta riga ta sami kanta.
_Saboda faruwar komai yana sauri da yawa..._
Wani gefen tunaninta ya ambata mata amma sai tayi cilli dashi gefen da ya fito a lokaci guda, ai yarinyar ta gama tsorata da ita ta sani, ta gaya mata cewar taɓa dan'uwanta da tayi ba karamin abu bane da ba za ta so a sake irinsa ba, don haka ta riga ta gama yarda da ita, tunda har ta iya aikata wannan umarnin da ta bata a kudundune, umarnin da yaci sunan lauje cikin nadi, amma kuma tsaf cikin hikimarta ta ware nadin ta fidda laujen cikin sauki.
Don haka bata da sauran matsala ta sani, ko an dawo da Ma'aruf gidan umarni kawai zata bata na cewar kar ta sake ta bari ya fito, da wannan ta san zasu iya gama komai ita da Awwalu kafin jibi, tunda ko Baffa sai gobe zasu dawo suma.
Ta sake wani murmushin a hankali tana hango lissafinta. Tazarar fa kaɗan ce, saura kaɗan su ƙarasa ga ƙarshe inda komai zai fashe, taji tana taya Amina murnar shigowa cikinsu, don wahalar da zata yi kadan ce, ita da Awwalu sun daɗe suna tsarawa da gina komai bi da bi.
Wayarta tayi kara a lokacin, Awwalu ne, ta dauka ta kara a kunnenta,
"Hajiya ki fito yanzu komai ya kammala."
Ta gyada kanta ba tare da ta amsa a fili ba.
Ta kashe wayar tana wani murmushi sannan ta jawo mayafinta, ita da dawowa gidan kuma sai lokacin da ta kammala kaso mafi yawa na cikar burinta.
Abinda bata sani ba shine, ubangiji ya kadarta tafiyarta a wannan lokacin ne don faruwar wani abu da tunaninta bai taba hango mata ba.
****
*Karfe biyar da rabi na wannan ranar.*
Karo na farko a rayuwar Ma'aruf da ya taɓa bude idanunsa cikin irin wannan yanayin yaga ƴanuwansa zagaye dashi fal, Awa kusan uku kenan tun bayan farkawarsa amma har yanzu zuciyarsa ta kasa ƙarasa yarda da ganinsu gabadaya tare dashi kuma ba a ko'ina ba a cikin gidansa.
Samira ce ta gaya masa cewar Amina ce ta sanar dasu an dawo gida don haka tun da rana kafin ya farka suka zo har dasu Salma, Shukra da Safiyya wanda suka zo a ranar, ga dadin dadawa Inna Danejo da itama Mama Rabi ta rako ta tun daga cikin gidan har nan.
Tana zaune daga gefensa inda aka kwantar dashi a falon tana ta karanto tarin addu'o'i daga cikin carbin ta take ja tana gaya masa cewar rubutu zata sa ayi masa na Alkur'ani gabaÉ—aya don ita ta gaji da yawan maganin asibitin da har yau bata ga amfaninsa ba.
Kuma tun da Ma'aruf yake a rayuwarsa, tun daga lokacin da ya sami ciwon nan, idan har bashi da lafiya ya sani cewar sai dai ya farka ya ganshi a London asibiti ko kuma tare da Ishaq a gefensa.
Ko lokacin da yana tare da Rukayya baya bude idonsa ya ganshi a gida kuma ko shi a baya bai taba ganin wani abu game da hakan ba, don idan ba zai manta ba a cikin hira Mami tasha gaya masa cewar hakan shine daidai, bai kamata ya dinga mu'amalantar kowa ba har sai yanayinsa ya sauko ya daidaita.
Shi yasa a karo na farko da ya farka a yanzu yaga mutane zagaye dashi sai yake jin wani iri a zuciyarsa, wani irin yanayi da bai san dame zai fassara shi ba, kallonsu kawai yake yi tun bayan da ya bude idanun nasa, kowanne da murmushi a fuskarsa suna tambayar lafiyarsa da kuma yadda yake ji.
"Ya MB kace min ka warke dan Allah, ni ban san haka ciwon ka yake ba wallahi, ban taba ganinka a haka ba."
Shukra ta fada tana gyara glasses din dake fuskarta tana kallonsa. Kuma sunan da ta kira shi dashi ya tuna masa da dadewar da yayi bai gansu ba tun bayan aurensu, ya san dai kowaccensu ta kira shi sau daya sun gaisa amma bai kara jinsu ba bayan hakan, dukkaninsu sun canja, musamman Safiyya da tayi wata irin kiba a watanni biyu kawai tana gaya masa cewar da wuri zasu tsufar dashi idan ska kalle su aka cewa su kannensa ne.
Kuma maimakon ya bata amsar abinda ta tambaya sai kawai yace.
"Ya project work É—in naki kuwa Kin gama?"
"This is your answer ya warke kenan, don ni na tabbata da yace miki da sauki to wallahi Yaya bai warke ba."
Cewar Salma tana karasowa rike da kwanon furar da Inna Danejo tasa taje har bangarenta ta dauko shi. ta zubo wani potate É—in dankali a ciki daga kitchen, tana karasowar kuwa Inna Danejo dake gefensa ta karba tana fadin.
"Muhammadu juyo nan kasha wannan, na gaya maka ni ban yarda da wannan she*gen ruwan da ake sawa ba ace wai shima abinci ne, gashi nan tunda ka farka ai kake ta shan ruwa da yana aiki ai ko shi ba zaka nema ba."
Ya juyo ya kalleta, ta debo abincin da niyyar bashi, sai kawai ya girgiza kansa yace.
"Ni ba haka matata take bani abinci ba."
Su Salma suka kyalkyake da dariya ba shiri yayin da kafin Inna Danejo ta kai karshen salatin ta Surayya ta shigo tana fadin cewar ga wani likitan nan ya karaso da sakon cewar Baffa ne ya turo shi, don a dazu bayan farkawarsa sun yi waya da Baffan har ma da Baba Usman suna tambayar yaya jikin nasa, kuma a cikin muryarsu kaÉ—ai ya fahimci su ma sunji dadin yadda wannan karon ciwon nasa bai tsawaita ba.
Inna Danejo ta ajiye farantin hannunta tana fadin ace masa ya shigo, Ma'aruf ya juyo yana ce mata ta bashi furar tace ai kuma yayi wa kansa kenan ya zauna da yunwar cikinsa idan matar tasa tazo ta bashi.
A lokacin ne kuma yadso ya tambayi inda Aminan take don tun bayan lokacin da ya farka sau daya ya ganta sanda da ta kawo masa ruwan farko da ya tambaya, amma kafin ya bude baki Shukra ta matso tana dariya ta É—auki plate din tana faÉ—in ita zata bashi.
A lokacin ne kuma Zahra da Sahla da suka fito daga hanyar koridon dakunan gidan.
"Ina Aunty Amina?"
Suka tambaya a tare muryarsu na shaida murna.
"Me kuka je kuka yi mata a daki?"
Safiyya ce mai tambayar tana kallon hannun Sahla data boye a baya.
"Babu komai, kawai tambayarta zamu yi wani abu."
Salma ta kalle su tace.
"Makaryatan banza ai idan bincike ne kun iya shi, na gaya muku duk ranar da zaku zo gidana walkahi ku gaya min kulle koina zanyi ku zauna a falo.
Munaya dake zaune a gefe ta kalle ta.
"Har yanzu baki san abinda ke tsakaninku da Samirah bane, shi yasa kike ganin na wadannan yaran wani abu suke yi."
Da sauri Salman ta juyo tana rokonta ta gaya mata abinda Samiran ta daukar mata amma tace ita ba zata fada ba ba, ta bari duk ranar da Allah ya tashi tona mata asiri zata gani da kanta yayin da Inna Danejo ke fadan hada husuma babu kyau.
"Wai ina Samiran ne ma, ni tazo in bata sakon cupcakes."
Safiyya ta tambaya daidai lokacin da Surayya ta shigo tare dasu Faruk da kuma likitan nan, hannunta na dauke wani dan karamin yaro da a lokaci guda Ma'aruf ya gane cewar Aarif ne É—an gidan Faruk, kuma bai gama tunanin ba Shaida natar Faruk din ta shigo biye da sauran Æ´aÆ´ansu biyu mace da namiji.
"Yaya, su Aunty Shaida ne duka zo."
Cewar Surayyan kasancewar dama ita tun da ta san Shaidar don yayar ƙawarta ce.
Kowa ya amsa sallamar su da fara'a yayin da Munaya ta taso a lokaci guda tana kokarin daukar Aarif din dake ta mika hannu zai koma wajen mamansa alamun kyuiya yake yi.
Shahida ta karaso har gaban Inna Danejo tana gaishe ta yayin da likitan nan ke kokarin cire allurar drip din daje hannun Ma'aruf din, shima ta gaishe shi sannan ta gaya masa cewa Faruq din yana waje tare da Ishaq wanda shima ya karaso a lokacin.
Da haka ta juya wajensu Safiyya tana gaishe su da tambayar Yaya mai jiki. Tambayar da tasa sai a lokacin hankalin kowa ya lura cewar Amina bata wajen kuma kowa ya tabbatar da cewar bai ga lokacin da ta fita ba.
Sai dai kafin hakan ya kai ga nisa, kofar falon ta bude, kuma Aminan da ake nema ta shigo a lokacin tare da Samiran da suka fita tare, sai dai duk wanda ke É—akin basu yake kallo a lokacin ba.
Wadda ke zaune akan kujerar da Samira ta turo zuwa cikin falon a hankali ce... Hajiya Maimuna.
Shiru ne ya ratsa ilahirin falon a lokaci guda kafin kowannesu ya rufe da kiran sunanta, hatta Inna Danejo sai da tayi murmushi tana kallonta, don a tarin jama'ar gidan kaf, kowa ya san kawaici irin na Hajiya Maimuna, ba karamin kokari Amina da Samira suka yi na sawa tazo ba, tunda tun rana ta san inda dukkaninsu suka taho amna bata ce zata zo ba.
Ma'aruf ya kasa rufe bakinsa a lokacin da yake kallon Hajiya Maimunan dake Samirah ke turota tana karasowa gabansa. Keken tayar ya hawo har kan carpet din ta iso daidai gabansa da kuma Inna Danejo wadda ke fadin taso Baffa yana gari yau yaga Maimuna a gidan Ma'aruf, don ko sanda yana tare da Rukayya har suka rabu bata taba takawa gidansa ba.
A lokaci guda wani abu kamar kwallar da bai san dalilinta ba ta cika idanunsa lokacin da Hajiya Maimunan ta gama gaishe da Inna Danejo ta juyo tana tambayar yaya jikin nasa, bai ma san da wadanne irin kalamai ya amsawa tambayarta ba, ya san kawai a wannan lokacin idanunsa na kallon Amina ne dake can tsaye a baya da murmushi a fuskarta tana gaisawa da Shahida tana kuma kokarin daukar Aarif da ya gudo daga hannun su Munaya ya koma wajen Shahidan.
Zuciyarsa yaji tana gaya masa cewa ko da iya wannan alkhairin nata na yau kaÉ—ai, zai kyautata duniyarta da dukkan iyawarsa.
***
*Ƙarfe tara da rabi na dare.*
Kowa ya tafi a lokacin, hatta su Ishaq bayan ya takura musu sun shaida masa dukkan abubuwan da yayi missing dinsu a ranar, farko shine shari'ar Hamida da shi kansa ya manta da ita a yau,Ishaq din ya gaya masa cewar yaje ya dauko yarinyar ya tafi da ita kotun, kuma duk iya kokarinsa a gaban Alkalin, ba'a je koina ba alkalin ya yanke hukunci da cewar yarinyar ta koma wajen mahaifiyarta idan yaso tunda ya bada uzurin mahaifin nata bashi da lafiya, ya yanke hukunci cewar duk sanda ya warke zai iya sake shigar da kara sai a zauna a sake tattaunawa.
Na biyu kuma shine zancen haduwarsa da mutanen RTL din nan, Faruq ya gaya masa cewar babu yadda baiyi yayi contacting mutanen ba amma ya kasa samun su kuma suma basu ce masa komai ba. Sannan Ishaq ya shaida masa cewayasa snyi deactivating gabaÉ—aya cards dinsa da aka É—auke kuma barayin basu sami danar fitar da komai ba.
Har suka tafi Faruk yana ta kokarin ya kwantar da hankalinsa akan cewar ya san ba wani issue ne babba ba amma har suka kammala zancen suka tafi jikinsa bai bashi haka ba, kawai ya ajiye zancen ne a gefe sanin cewar idan ya saka a ransa tabbas abin zai hadu ya dame shi tunda wancan case din ma har yanzu basu karasa shi ba, don haka ya hakura ya barwa karin samun saukinsa komai.
A yanzu gidan daga shi sai Amina ne, kowa ya tafi, su Salma tare suka koma cikin gida tare dasu Inna kuma ya san zuwa yanzu ma duk sun tafi. Kuma Hajiya Maimuna da har ta tafi fara'ar fuskarta bata ɓoyowa, kuma yana jin sanda taje ta addu'a da sawa Amina albarka daga can bakin kofa inda suke sallama.
Hatta Faruk sai bayan da suka yi sallar Isha ma sannan suka tafi don suna ta hira tare da Ishaq, yayin da Amina ke tare da Shahida a kitchen don dukkaninsu basu tafi ba sai bayan da suka ci abincin dare, har Samira ta dawo daukan wayarta da ta manta tana ta korafin me yasa basu kirata ta taya su ba.
A yanzu fitowarsa kenan daga wanka yanzu tunda ya samu a dazu sunyi jam'in sallah tare dasu Ishaq.
Yana zaune daga bakin gadon dake dakinsa, safa yake kokarin sakawa a ƙafarsa saboda sanyin da yake ji yayin da zuciyarsa ke kara hasaso dukkan abinda ya faru a yau yana ganin kamar a wata guda akayi komai ba yau kadai ba.
Kofar É—akin ta buÉ—e a hankali, ya juyo da kansa lokacin da Amina ta shigo hannunta dauke da wani dan madaidaicin tray a hannuta.
Tun bayan tafiyar kowa bai ganta ba, kuma tun a adibitin nan da ya farka yace ta kira masa Ishaq basu kara magana ba, jayan jikinta suka shaida masa cewa itama tayi shirin ba ci don doguwar riaga a jikinta wadda bara sauka sosai, ba, wani abu acikin kansa ya shiga gaya masa cewa yana missing wadannan siraran kafafun nata kamar me.
Ta karaso gabansa a hankali, idanunsa na kallon kowanne takunta, kaginnya maida su fuskarta.
"Yaya ka kara ji da sauki?"
Muryarta ta tambaya kamar wani abu dake tashi sama a hankali.
Kuma baiyi tunanin komai ba yace.
"Ke kike ta bani reason din da nake jin saukin ai."
Sai kawai tayi murmushi kaÉ—an sannan ta tsugunna a gabansa, ta durkushe kafafunta daga ganinsa, hannunta ya buÉ—e plate guda É—ayan dake kan tray din tana fadin.
"Na san yanzu zaka iya cin wani abu ko?"
Bai amsa ba ta sake cewa.
"Inna Danejo tace kar in bari ka kwanta haka baka ci wani abu."
Ta karasa sanda ta saka cokali a cikin plate din hadadden potate din dankali da alaiyahun dake ta ƙamshi a hancinsa.
Ta dago ta kalle shi, har yanzu idanunsa na kanta, kuma ga mamakinta sai taga kawai ya sauko kasan shima ya zauna daidai gabanta, sannan ya riko hannunta daya da bata rike plate din dashi ba, kamar koyaushe ya ratsa yatsunsa a tsakanin nata. Ta kalli hannun nata daya rike ba tare da tace komai ba sannan ta É—ebo abincin ta shiga bashi, yana ci tana gaya masa yadda akayi kafin likitocin asibitin nan su sallame shi.
Kuma bayan sun gama ne yace ta dauko masa wasu magungunan gargajiya da ya taba siya ya ajiye a saman drawer dakin, kamar zata iya sai da taje gaban drawer sannan taga da saura dosai kafin tsawonta ya Kai, don haka ta shiga neman abinda zata taka, amma kafin ta motsa tajinsanda ya karaso daidai bayanta sannan kai tsaye hannayensa duka biyu suka zagayo ta kasan cikinta kuma kafin ya hade su waje daya tana jin irin rawar da suke yi alamun har yanzu jikinsa bai gama kwarin da zai tsaya haka ba.
Don haka bata san lokacin da ta juyo ta fuskance ba da sauri idanunta na haskawa da mamaki.
"Me yasa ka taso? Zan iya daukowa fa..."
Sai ya girgiza kansa yana sake rike ta a jikinsa.
"I want to talk to you."
Har yanzu ji take yi kamar basu gama tsayawa daidai ba don haka tasa hannunta duka biyu ta rike gaban rigarsa kadan tana cigaba da kallonsa, kuma bata ce komai ba ya cigaba.
"I'm sorry game da abinda ya faru Amina, I'm sorry for how you saw me, (Ki yi hakurin yadda kika ganni) Na gaya miki dama I'm a mess..."
Sai tayi saurin girgiza nata kan itama tana cigaba da kallonsa.
"You dont need to be, lafiya da rashinta ba mallakin kowa bace, Allah yana bamu ita ne a lokacin da ya ga dama ya kuma karɓe ta a lokacin da yake so don wanke zunubanmu, saboda haka ba kaifinka bane, ba laifin kowa bane, don kowan bai wuce ya wayi gari shima an karbi tasa ta wata sigar ba.
Insha Allah abinda ya same ka kaffara ne ga wasu abubuwan da ba lallai ka san dasu ba ma. Don haka daga kai har mu ba abinda zamu yi da ya wuce addu'a kamar yadda kowa da ya taru anan yayi tayi maka..."
Tayi shiru tana kallonsa kafin ta karasa a hankali.
"... abinda kake bukata kenan."
Taji hannayensa sun sake rike ta sosai kafin ya karadso da fuskarsa a hankali ya dora goshinsa akan nata.
"Ban san me zan ce miki ba Amina, duk abinda kike yi, duk kike fada yana wuce dukkan tunanina, bana jin a duniyar na bayan Mami akwai wanda yake fahimtata yanzu sama dake."
Ambatar sunan Hajiya Kilishi da yayi yasa numfashinta yin rawa kafin ta rufe idanunta a hankali, tana jin nasa numfashin shima na sauka akan fatarta, sai kawai ta tatraro dukkan dauriyarta tace.
"Nima bana son kowa yafi ni fahimtarka, nafi son na zama mutum ta farko da zaka nema a kowanne lokaci walau na ɓacin rai ko farin ciki."
Bata sani ba ko kallonta yake yi amma taji sanda ya kara rike ta a jikinsa yana gaya mata dukkan wasu kalaman godiya, sai kawai ta ture dukkan wani tunanin a cikin kanta a lokacin ta mika hannunta daga saman kirjinsa zuwa bayan wuyansa, ta rike shi kwatankwacin yadda shima ya rike ta. Wani abu da ya bashi mamaki don taji sanda ya dantsaya a cikin hannayen nata kafin ya kira wannan sunan nata a hankali.
"Doll..."
Kafin tama yi tunanin amsawar yace.
"Wannan ma yana daya daga cikin amsata na ranar?"
Ya rufe bakinsa daidai sanda ta daga kanta alamun amsa, taji yayi wani murmushin mai sauti sannan ya matsar da fuskar sa kadan daidai saitin kunnenta ya rada abinda a lokaci guda ya sata dunƙule yatsun kafarta akan tiles din dakin.
"I want to kiss you again dan Allah..."
Ya faɗi hakan sannan ya janye fuskarta daga tata, yayi baya sosai yana kallonta. Amina taji lebbenta ya shiga rawa tare da hannayenta sai kawai ta ƙara tsawon kafarta a lokaci guda, ta kai fuskarta daidai gefen tasa kuma ba tare da jiran komai ba tayi pecking gefen kumatunsa.
Ta sake jin sautin murmushinsa kafin ya kara sunkuyowa cikin fuskar tata ya kwaikwayi sak abinda tayi yayin da take jin murmushinsa akan fatarta, kuma sai da ya matso dab da bakinta sannan ya tsaya, wani abu da yasa a lokaci guda ta buÉ—e idanunta tana kallonsa.
"I want to ask you something? (So nake in tambaye ki wani abu.)
Kafin ta amsa yace.
"Naga kin fara kwarewa a wannan karatun, shekarar ki nawa? 'Cox I don't want us to stop, bana so mu tsaya kuma bana so a kama ni da laifin child abuse."
Amina bata san lokacin da bakinta ya subuce da wata irin dariya ba, ta rufe idanunta gabaɗaya sautin dariyar na fitowa tare da tsananin kunyar da maganganun dake lulluɓe ta.
****
_Wani abu yana shirin konewa anan.😅🥰🤩_
_Ina kuke tunanin Hajiya Kilishi ta tafi ne?_
_Me suka shirya ita da Awwalu?_
_Ruƙayya da mahaifiyarta sun samu nasara, Hamida ta koma wajensu, kun tuna mataki na biyu a tsarinsu?_
_Yaya kuka ga kokarin Amina na farko wajen hada kan gidan Alhaji Muhammad Mansour Bakori?_
Sai naji dukkan sharhinku..🥰��
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:50 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*05*
~~~~~~~
_If it's not you, it's not anyone._ _- Unknown_
***
*Abuja.*
*No. 1146 C west, Maitama.*
*Ƙarfe tara da rabi na safe.*
A cikin harabar gidan, daga can gefe inda akayi shuke-shuken wasu bishiyu dama fulawowyi, Jawad ya shafo kan hancinsa da daya hannunsa wanda baya rike da wayar da yake yi kafin yace.
"Na gaya maka naga motar, daga can gefen inda muke ta tsaya kuma ni naga mace da namiji a ciki, fuskokinsu ne kawai ba zan iya tantance maka ba."
"Babu ji, wannan mai sauki ne in dai har ka tabbatar number motar da ka faÉ—a daidai ne. Zanyi kokarin nemo bayani akan plate din sai muyi tracing , tunda na san dake zuwan nasu yana da alaka da dalilin rashin zuwan Ma'aruf wajen."
Jawad ya gyaÉ—a kansa a hankali yana cije lebbensa.
A jiya bayan sun shiga Kano, tsarinsu ya tafi daidai, sun yi komai kamar yadda Haro ya tsara kuma ma sun isa wajen da suke saka ran ganin Ma'aruf inda zai hadu da wadannan mutanen, sai dai sunyi tsawon jiran da har mutanen suka zo babu Ma'aruf din babu alamarsa, kuma suna wajen har lokacin da motar mutanen ta juya suka bar wajen.
Kuma sai a yanzu Jawad ya tuna da motar da suka wuce akan titin kafin su sami wajen tsayawa, don haka ya kira Haron a waya yanzu yake gaya masa, don a jiyan bai ko bari ya kwana a Kano ba yayi booking jirgin dare ya dawo gida,yana da abubuwa da yawan da ba zai iya wasa da lokaci wajen kuɓucewaru ba.
"Kar ka damu J, ai ba ƙasar ya bari ba, muna da lokaci muna dashi mara adadi, wannan opportunity din ma don naga yayi kusa ne nace muyi amfani dashi kawai, amma yanzu damar ta fara Jawad kai ma ka sani."
Ya gyada kansa.
"Na sani, na san akwai lokaci Sadiq, fata kawai nake ne kar Rukayya ta shammace mu."
Haro yaja tsaki a cikin wayar.
"Haba Jawad, a cikin kwakwalwar wannan dakikiyar yarinyar har akwai abinda zata yi ne da zai fi namu? Kawai ka cigaba da harkokin ka, ba za'ayi dedewar da kake tunani ba insha Allahu, su kuma WaÉ—annan mutanen zan saka a nemo mana su insha Allah."
Da haka suka gama wayar, Jawad ya kalli mintunan da duka gama fitowa a jikin screen din kafin ya kashe ta ya zura a aljihu, yayi abu guda biyu da ya É—anawa tarko a safiyar yau bayan dawowarsa, saura na ukun wanda har cikin zuciyarsa yake jin tasirin faruwarsa, game da yarinyar nan, Æ´ar aikin nan.
Jiya bayan ya fito ya gan ta a wajen nan kuma ya tabbatar da cewar taji dukkan maganganunsa da Haro, baiyi mata magana ba, bai ce komai ba, don ko Haron baya son ya san hakan, abinda zuciyarsa ta gaya masa shine dole ya san yadda zai yi ya rufe bakinta kawai don baya hango yadda alakarsa da mahaifiyarsa zata kasance idan har koda wasa ne ta fadi hakan a gabanta.
Ya zura wayar a aljihu, sannan kai tsaye ya fito daga wajen ya nufi hanyar da zata zagaya dashi baya zuwa ɓangaren masu aikin gidan, bangaren dashi kansa gida ne guda mai ƙatuwar haraba da kuma shuke-shuke, ba zai iya tuna rana ta karshe da ya taka kafarsa zuwa wajen ba, kawai dai ya san kafin su kai ga tarewa a gidan da suka zo gabaɗaya tare da mahaifinsu da kuma sauran ƴanuwansa maza, sun zagaya koina har nan kuwa.
"Good morning sir... Good morning."
Wasu ƴan aikin guda biyu dake shanya tarin kayan wankin yara suka tsugunna suna gaishe shi, ya gyaɗa kansa alamun amsawa sannan ya tsaya yana kallonsu, ya rasa ma me zai ce musu saboda ko sunan yarinyar bai sani ba, ya san dai ya taba ji Mamah ta taɓa kiranta a gabansa, watakila fiye da sau ɗaya ma amma baya jin zai iya tunawa.
"You want something sir?" ( Kana bukatar wani abu ne yallabai?)
Daya daga cikin ma'aikatan ta faÉ—a, sai dai kafin ya buÉ—e bakinsa yayi magana idonsa ya hango masa ita, ta karyo kwana ta shigo wajen, hannunta dauke da wani katon farin nokiti da ta ciko kayan miya a ciki, ko daga nesa ya san bokitin yayi mata nauyi daga yadda yake kokarin rinjayarta ta gefe guda.
Sai kawai ya juya ya nufi wajenta, kuma har ya taho bata lura dashi ba sai da ya iso daidai gabanta tukunna, da farko idanunta basu shaida shi sosai ba, watakila ko bata taba zaton ganinsa a lokacin kuma a wajen bane, amma a lokaci guda sai idanun nata suka haska da tsananin mamaki da kuma fargaba.
Yana ganin yadda ta saki bokitin da sauri zuwa kasa kafin itama ta bishi kasan ta durkushe kan gwiwoyinta sannan tace.
"Ina kwana... Barka da safiya."
Duka kalar gaisuwar guda biyu shi kaɗai, kuma har ya buɗe baki zaiyi magana sai idonsa ya kai kan wasu mata daga ginin dake gabansu sun leƙo ta window suna hangensu, wani tunani ya gifta a cikin ransa don haka sai kawai ya maida kalaman da yayi niyyar faɗa yace.
"Me kuka dafa a bangren Mamah?"
Tambayar ta shiga kan Zainb da tsananin mamakin da ya fi na farko, don ta tabbata ba abinda ya kawo shi kenan ba, ya za'ayi ya bato bangaren ya taho tun daga can har zuwa nan don ya tambayeta kawai abinda aka dafa? Mutumin da idan hr ba fita zai yi ba kowa ya haddace cewar baya tashi sai rana ta miƙa, amma ƙarfe nawa yanzu? Tara da mintuna...
Ta yaya ne ma yake mata magana muryarsa a ƙasa, ta zata ai idan har ba tare da mahaifiyatsa yake ba baya iya magana babu hantara. Sai tayi saurin hadiye abu a bakinta sannan tace.
"Ba'a gama abincin duka ba, an dai yi wasu."
Ya gyada kansa.
"Ki debo wanda aka gama ki kawo min."
Da haka bai kara cewa komai ba yayi gaba. Zainab tabi bayansa da kallo gabanta na faduwa kafin ta mike a hankali.
Kuma minti goma bayan hakan, ta kwankwasa kofar É—akin nasa É—auke da farantin kayan abincin, kallon da sauran manyan Æ´an aikin gidan suka dinga binta dashi bayan ta gaya musu inda zata kai abincin.
"Shigo."
Muryarsa ta fada daga ciki, kuma karo na farko ta murda hannun kofar ta shiga, dakin kamar yadda ta zata ne, ƙato mai cike da hadaddun kayan kamar na sauran ƴanuwansa mata, sai dai har gwara nasu ma yafi kyale-kyale akan wannan da komai tsilla-tsilla ne. Yana zaune daga gaban gadon dakin a tsakiya, ya dora hannayensa kowanne akan cinyoyinsa yana kallonta, kuma da yatsu biyu kawai yayi mata alamar cewar ta karaso.
Ta taho É—in, amma muryarsa ta tsaida ta.
"Koma ki rufe kofar."
Gabanta ya sake faduwa, amma babu yadda ta yi ta koma É—in ta rufe ta a hankali sannan ta sake juyowa, tana ta tahowa bai ce ta tsaya ba, kallonta yake yi ta sani amma ita idanunta na kan farantin.
Sai da ta karaso nesa dashi kadan sannan ta tsugunna ta ajiye farantin a saitin gabansa, kuma kafin ta mike kamar yadda daga shi har ita suka san shine abu na gaba ya sake magana.
"Zauna."
Ta hadiye wani kullutun abu a makogwaronta sannan ta gyara tsugunnon nata a hankali alamun ta zauna É—in, tambayarsa ta gaba ta kada Æ´aÆ´an hanjinta a lokaci guda.
"Daga ina kike?"
Sai ta dago ta kalle shi.
"Nace daga ina aka kawo ki?"
Ya sake maimaitawa, ya sake maimaitawa yana fadada tambayar da ta riga ta fahimta din kuma ta san ina take dosa.
"Sunan garinmu Yakura, a kusa da Kaduna yake." Muryarta tana rawa.
Ya gyada kansa.
"Waye ya kawo ki nan?"
"Abokin babana ne."
"Ina baban naki?"
A hankali tace.
"Ya rasu."
"Ina babarki?"
Sai da ya lura ta hadiye wani abu sannan tace.
"Tana nan, matarsa ce ita yanzu."
Kalaman suka daki kirjinsa da wani abu da bai san meye ba, amma dai ya san nazarinta yake yi, nazarin shekarunta da ya kasa ƙiyasinsu.
"Ita me yasa bata hana shi kawo ki ba?"
Sai ta sake dagowa ta kalle shi, idanunta na nuna wani abu da ya kasa tantancewa, idan ma tunani take cewa muryarsa ta fito da damuwa ne, zai goge mata hakan yanzun nan.
"Bashi da kirki, Naani baza ta iya hana shi ba."
Kalmar Naanin da ta fada ya fahimce itace mahaifiyarta don haka kai tsaye ya sake tambaya
"Yaya sunanki?"
Wannan karon da mamakin da yafi nasa ta kalle shi, bai san sunanta ba? Bai san sunanta ba yake tambayar labarinta?
"Sunana Zainab."
Sai ya sake gyaÉ—a kansa yana kallonta.
"Zainab, I know you heard us...."
Maganar tasa ta katse tuna cewar a banza zai yi bayanin ko ta cigaba.
"Na san kin ji mu ranar nan, kinji duk abinda muka fada ni da wanda yazo...."
Ta riga ta sani dama, tasan zancen da zai yi mata kenan, ta san ta shiga uku, ta san karshen rayuwarta a gidan nan tazo tun daga wannan lokacin, Allah ya sani tana jin daÉ—in zaman gidan nan fiye da sauran gidaje biyu da tayi aiki dasu a baya saboda yadda mahaifiyarsa ke kyautata mata, amma tun daga ranar da ta ci karo dashi har ta zuba masa miya a kaya, tun daga ranar hannayenta suka fara lissafin kwanakin barinta gidan, sai gashi ta samu talalar wasu watannin kafin shekanjiya ta tabbatar mata cewar wa'adin kwanakin nata yazo karshe.
Don haka taji yadda iska ta wuce cikin busashshen makogwaronta kafin ta tattaro dukkan karfinta ta daga kanta sau daya.
Jawad ya gyaÉ—a nasa kansa shima.
"Good. Shi yasa na kira ki nan."
Ya fadi hakan sannan ya gyara zamansa.
"Ba zaki so in zama abokin babanki na biyu ba Zainab balle kuma har in fi shi, don ina rabbatar miki zan iya kuntata rayuwarki fiye da yadda bakya tunani idan har kika zabi yin wasa dani.
Abinda kika ji sirrina ne, kuma duk da babu yardata ya iso gare ki, na baki amanarsa a yanzu, kuma in so ki barshi a cikin ranki, ki barshi kamar yadda yake a tsakanin mu yanzu, idan har shiga kunne na biyu musamman kunnen mahaifiyata Zainab..."
Yayi shiru yana cije lebbensa kafin ya fadi abinda yasa ta zare idanunta a lokaci guda ta dago tana kallonsa, hannayenta dama ilahirin jikinta gabaÉ—aya suka shiga kakkarwa yayin da idanunta ke haskawa da tsoron da bsta lissafa dashi ba a duk wani lissafinta na ukubar rayuwar da take tunanin fuskanta!
****
*Kano.*
*No. 58 Mafara Street, NNDC SharaÉ—a Quaters.*
*Ƙarfe Goma na safe.*
A cikin dakin, cikin uwar dakin Hajiya Kilishi ta dubi kawarta Hajiya Salamatu wadda isowarta kenan a wannan safiyar bayan fitar Mama Rabi wadda ta shirya musu abun motsa baki fal a wani katon faranti.
"Kinyi min nisa da yawa Salamatu, china tayi min nisa tunda ni ba harkar social media din nan nake yi ba. Na kulla abubuwan da yawa wanda babu tayawarki a ciki balle har mu kai wa tufkar ƙarshe mai daukar ido."
Hajiya Salamatun ta cire dankwalinta ta ajiye shi a gefe, mikakken gashin kanta da yasha gyara ya shiga nuna maikonsa cikin hasken dakin kafin tace.
"Ni iyaka ta dake ai shawara Kilishi, wasu ma ba É—auka kike ba idan na fada, to don me zaki yi kewata? Yanzu kawai ki gaya min me ya faru? Me ya faru daga inda na barki."
Hajiya Kilishi ta juya idanunta tana murmushi sannan ta kalli aminyar tata dake zaune daga bakin gadon dakin tace.
"Abubuwa da yawa Salamatu, don haka mu kyale ƙananan ma a gefe, mu fuskanci manyan.
Na riga na gama da yarinyar nan, ta san komai kuma ta yarda da komai..."
"Haka cikin sauki?"
Salamatun ta kasa daure namakin da yasa ta katse ta wajen tambaya.
Sai kawai ta É—auki kofi guda akan farantin, ta tsiyaya lemo a ciki ta mikowa Hajiya Salamatu kafin ta bata amsa.
"Ba cikin sauki bane, nayi abinda ba zata iya bijire min bane kamar yadda ta fada da bankinta. Kin sani Salamatu, kin san yadda bana wasa da dukkan abinda nasa a gaba, kuma kin san yadda nake bawa abinda nake so muhimmanci."
Hajiya Salamatu ta kurɓi lemon sannan tace.
"Na sani Kilishi, ba sai kinyi wannan bayanin ba, na yarda kin samu yarinyar bayan ita kuma sai me?"
Tayi wani sassanyan murmushi tana kallonta.
"Sai burin da na É—anawa tarko, burin cike kan wadannan kudaden."
"An samu?"
Ta tambaya bayan ta ajiye kofin lemon.
"Kwarai, an samu Salamatu, wani ciniki suka yi na makudan kudaden da har suka fi gejin da nake nema ma."
"Kince min ya gano waccan hanyar taku ta hacking account din kamfanin da akayi aka tura musu da alert din bogi. To wannan karon me kika yi?"
Kai tsaye Kilishin tace.
"Kwantar dashi nayi kamar yadda na saba kuma zaki yi mamaki ta hanyar yarinyar nan hakan ta faru."
Wannan karon da mamaki Hajiya Salamatun ta kalle ta kafin ta kyalkyale da dariya.
"Irinki basu da yawa a kowanne ƙarni Kilishi, shi yasa nake gayawa duk mai takura min akan rayuwa cewa ya kyale ni kawai, da nayi niyya zan rayu a duniyar nan kamar a aljanna ne saboda ke." (Waiyazubillah.)
Kilishi ta gyada kanta tana daukan cake guda a cikin farantin fake gabansu.
"Ni kaina na sani Salamatu ina da laushi fiye da dukkan tunanin mai zato, laushin da zan iya ruɗar ko waye a duniyar nan ya dulmiya zuwa cikin tarko na da bashi da ƙarshe. Shi yasa tun farko na gaya miki cewa ita kanta yarinyar na shirya mata, kuma gashi tun amba'aje koina bakan ta tabbata r miki da abinda na fada cewar babu wata mace da ta isa tayi tasiri a zuciyar Ma'aruf sama dani, a yanzu na gama yi mata shirin da ba zata taɓa iya bari Ma'aruf din yayi tasiri a zuciyarta ba balle har ta iya tsallake umarni na.
Na tsorata ta, kuma ta gama tsoratar akan al'amarinsa, zata ganshi ne kamar yadda na haska mata shi, zata ganshi a matsayin wani abu daban ba mijin aure ba, don ko ciki bata isa É—auka ba."
Salamatu tayi dariya.
"Na san zaki aika ai Kilishi, kawai dai a farko ne nayi tunanin ke kanki baki gana sanin halin yarinyar ba na jiye miki wannan tsoron, amma tunda har kin taka matakin nasara akanta tun ba'a je koina ba, mu cigaba a inda muka tsaya, ki gaya min ta yadda kika sami kudaden nan."
Kilishi ta daga kanta sau daya sannan ta cigaba da magana.
"Kwantar dashi nayi kamar yadda na gaya miki sannan Awwalu ya sanya min yaran sa suka fara binsa tun daga lokacin da ya bar gida, muka sa wani yaje ya daki motarsa sannan kuma ya zage shi don in tabbatar idan har yarinyar nan ta bashi maganin, ilai kuwa nan da nan mood dinsa ya rikice ya kama dukan mutumin, a wannan hayaniyar wasu da muka saka suka samo min wallet dinsa har dama wayoyinsa wanda muka yi amfani dasu."
Hajiya Salamatu ta girgiza kanta.
"Ban gane ba, kuka yi amfani dasu ta yaya?"
Kilishi ta ajiye cake din da har a lokacin bata kaishi baki ba, ta gyara zamanta sosai tana kallonta sannan tace.
"Ma'aruf yana da wayo da dabara sosai Salamatu, na sha gaya miki tun bai kai haka ba. Don haka bayan sun gama wannan bincijen shi da wannan abokin aikin nasa, sun gano cewar tabbas alert din da suka samu na bogi ne, sai ya canja shawara, yace wannan karon cash zai karbi kuÉ—i ta hannun mutanen da suka yiwa aiki ba ta account ba kuma da kansa yadda zai je ya saka a banki don kar a sami ma wata matsala ba.
Abinda bai sani ba shine, tunanin Kilishi da nasa ba daya bane, a cikin maganganunsa kawai na gane abinda yake shirin aikawmtawa tun kagin ma su gama aikin a saka ranar karbar kudin, shi yasa na tsara komai, na tsara iya kwanakin da zasu ishe ni har in tunkari Amina ta gama shawararta tazo ta amince dani da kuma iya kwanakin da zata sanya masa gubar har ya kwanta kafin ranar.
Kuma na sami komai Salamatu, I.D cards da kuma wayar Ma'aruf É—in kaÉ—ai muka nunawa mutanen nan da kuma wani dan bayani kaÉ—an suka yarda suka bamu kudin a madadinsa, kuma mun karbo ba tare da wata matsala ba Salamatu, Ma'aruf kuma yana nan a kwance duk da ance min ya fara samun sauki amma wannan ba damuwata bace, ko yanzu idan ina son ya kara komawa, umarni kawai zan bata, muna zaune anan zaki ji komai ya kara rikicewa."
Hajiya Salamatu ta girgiza kanta.
"Ba kya tunanin idan ya tashi ya tuntubi mutanen zasu iya shaida masa abinda ya faru da kuma yanayinku? A tunanina ba kya É—anyen aiki Kilishi."
Itama ta girgiza kanta.
Ba tunanin kike ba Salamatu, tabbas bana danyen aiki, don wannan É—in ma gasashshe ne. Wani saurayi muka samo daga Prison, wata na biyu Salamatu ina barar da kudi a prison din nan ina neman kafa, don kawai a ara min shi na rana guda yayi wannan aikin kuma da kyar muka samu.
Awwalu ne yayi masa I.D card din kamfanin sak a matsayin babban ma'aikaci, don haka muka tura shi a matsayin hakan ya karbo mana kudin da bayanin cewa shi maaikacin wajen an aiko shi ya karɓi sakon ne bayan ya nuna musu kayan Ma'aruf harma da wayarsa don haka nan da nan suka yarda.
Suka bashi dukkan kudin mu kuma muka bashi rabonsa tare da na iyayen gidansa muka maida shi inda muka dauko shi. Shi yasa nace miki aikin gasashshe ne Salamatu tunda kin san duk naci da binciken Ma'aruf babu ta yadda zai kamo mutumin dake cikin Prison duk kuwa iya bincikensa."
Hajiya Salamatu ta kyalkyale da wata irin dariyar da bata shirya mata ba tana girgiza kai.
"Zama dake alheri ne Kilishi, na sha gaya miki yadda kike bude nin kwakwalwata akan abubuwa, yana bani saukin warware nawa matsalolin gabana na nima."
Kilishi ta gyada kanta.
"Abinda na gayawa Saratu kenan ai, kowacce mace tana da irin tata dabara da kuma mafitar matsalarta a cikin kanta, yanzu da ta saurare ni ba gashi nan daga ita har Æ´aÆ´an ta mijin ya tafi dasu Egypt din ba, amaryar da ake takama da ita da farko wata daya tayi ya dawo da ita.
Kawai jahilci ne yasa mutanen farko ke bin wasu bokaye da suke maza ma don samun biyan bukatar fa bata dorewa. Kowa ta sani cewa tunda aka halicci duniyar nan har kawo yau, ƙarya ne a samu aikin wani bokan da ya zama mai dorewa har abada.
Amma idan mace tayi amfani da dabara da kuma tunaninta wajen kwatarwa kanta Æ´anci ko a wajen waye, ina tabbatar miki wannan abin ba mai gogewa bane balle har ya lalace, akwai abubuwa da yawa da suke É—amfare da tare da halittar mu, kawai bama barin kanmu mu gansu ne.
Kwakwalwar mace kamar littafi take, dauke da tarin abubuwan da tana bude shafukan gaba tana kara fahimta, wadda bata bude ba kuma zata yi ta jallon bangon ne kawai ba tare da ta taba sanin meye a ciki ba.
Salamtu ta kara gyada kanta tana yarda da dukkan maganganun kamar yadda Kilishin ta dade tana ambata mata.
"Na taya ki murna kwarai na samun wannan burin da kika daÉ—e kina lissafinsa a É—an kankanin lokaci Kilishi, kin tafi zuwa gaba kuma saura kiris ki kai ga cimma msnufarki gabadaya. Sai dai yanzu na san baza'a sake samun irin wannan aikin a kusa ba, za'a dauki tazara koda baza'ayi dadeear da nake tunanin ba. Don haka meye a gabanki yanzu?"
Tambayar ta yiwa Hajiya Kilishi dadi, me yasa ne take buÉ—ewa Salamatu cikinta dama? Me yasa take gaya mata dukkan tsarinta duk sanda ta tambaya? Ba saboda tana gaya mata daÉ—aÉ—an maganganunn dake wanke zuciyarta suna bata kwarin gwiwa a kodayaushe bane?
"Hamida ce target dina na gaba Salamatu.."
Ta faÉ—a kai tsaye tana kallonta.
"... wannan yarinyar, wannan ƴar ta mai gaskiya, ina son Ma'aruf amma bana son duk wani abu da zai zana nasa, don hakan ba karamin naƙasu zai jawo min a zuciyarsa ba.
Rukayya bata taba damunsa ba shi yasa nima bata taɓa damuna ba har tayi yayinta ta tafi, amma wanna ƴar tata Salamatu, naga wani abu a cikin idanun Ma'aruf a ranar da yake riƙe da ita a asibiti, na ga wani abu da ban taba ganin irinsa tare da kowa idan ba ni ba Salamatu. Shi yasa tun awanvan ranan na rufe idanuna naso kawo karshenta, amma Allah yayi da sauran ruwanta a gaba shi yasa ban samu nasara ba, amma a yanzu ina jin cewa ko ta halin
ƙaƙa zan iya canja kaddarar yarinyar nan Salamatu. (Waiyazubillahi!)
Ta rufe bakinta daidai lokacin da kofar dakin ta bude, Samirah ce ta shigo jai tsaye hannunta rike da wata ƙatuwar jaka kalar Pink mai kyau, dukkaninsu suka bita da kallon yayin da kafin Hajiya Kilishin tayi magana Surayya kuma ta biyo bayanta, hannunta dauke da ƴar yarinyar da a lokaci guda kamanninta suka doka wata irin fargaba zuciyar Hajiya Kilishi.
Hamida ce, riƙe a hannun Surayyan ta makalkale ta yayin da take zare manyan idanunta irin na maifinta sak! akan kowannensu.
"Mami yanzun nan direban gidansu ya kawo ta, wai cewa akayi akai ta wajen Ya Ma'aruf."
Murmushin da ya sabuce a bakin Hajiya Kilishi wani murmushi ne da ya taɓo har acikin zuciyarta... Tana son mutane masu saukaka mata ayyuka, a rayuwa, Allah ma ya sani.
****
"Inalillahi wainna ilaihir raji'un..."
Sune kalaman da suka fito daga bakin Ma'aruf a lokacin da yake zaune kan kujerar falon yana sauraran bayanin da Faruk ke masa a cikin wayar, kayan jikinsa dogon wando ne baƙi da kuma wata riga kslar ruwan toka mai haske.
"Wallahi sun nuna min evidence da komai cewa kai ka turo mutumin da ya karbi kudin, don har I.D Card dinka da sauran credit cards dinka ya nuna musu a matsayin shaida."
Ma'aruf ya cije lebbensa.
"Na kasa ganewa Faruk, na kasa gane wanda zai sace kayana a wannan lokacin kuma har ya san ina da appointment da mutanen a wannan wajen kuma a wannan time din."
"Saboda already sun san hakan ne, sun san kana da wannan appointment din shi yasa suka tare ka a wannan wajen kuma suka kwashe dukkan wayoyi da wallet dinka."
"Are you thinking this is all planned?" (Kana tunanin duk wannan abin haÉ—awa akayi?)
"Ba tunani nake ba, ina ƙoƙarin tabbatarwa ne, don tun safe muke waya da Ishaq, ya gaya min mutumin da rigimar ta hada ku har yanzu baiyi filing case ɗin ba, tunda ka san da sun yi dole za'a neme shi, ka duba al'amarin nan ka gani hankali ba zai dauka ba Ma'aruf ace kayi masa wannan abin amma ko shi ko ƴanuwansa basu dauki wani mataki ba."
Yayi shiru kafin yace.
"Amma har da nawa contribution ɗin Faruq, ta yaya kake tunanin zasu iya saka ni nayi abinda ban yi niyya ba, ina shan magani na cikin ƙa'ida sannan ina kiyaye dukkan ƙa'idojin da aka rubuta a wannan takardar. To ta yaya zasu iya controlling emotion dina?"
Faruk yayi shiru shima kafin ya amsa.
"Da wannan kuma B, amma zamu gano komai a hankali idan muka bincika. But there's no way da zan yarda cewa wannan al'amarin accident ne kawai."
Ma'aruf ya rufe idanunsa, ya dafe goshinsa da hannu daya yana rarraba Æ´an yatsunsa akan goshin. Abubuwan dake yawo a cikin kansa basu da iyaka, motsin kowannensu kawai yake ji yana ihu tare da Æ´anuwansa, yana jin kamar tafiya suke yi akan fatar kan nasa suna zagayawa da karfin da yafi na kadawar iska a cikin sakanni.
Me yasa ne sai su? Me yasa ko waye su ya zaba yana bibiyarsu? Me yasa ko sau daya bai taba tunanin ya barsu su huta ba? Kamar dukkan fafutuka da kuma ayyukan da suke yi na da sauki a wajensa, kamar a rana É—aya kawai suke kammala komai ta yadda gake diban dukiyarsu hankalinsa a kwance, yana jin cewa zuciyarsa ba zata tafi da nauyin wahalarsu da ma guminsu ba.
"Na gaya maka B, na gaya maka ka bari sai ka dawo office tukunna ma tattauna, but you still insist. Gashi nan yanzu naji alama you're changing, bana so na jawo maka wata matsalar kaima ka sani. So mayi magana kawai anjima."
Da haka wayar ta katse kuma Ma'aruf bai sauke ta daga kunnensa ba, ya cigaba da rike ta kawai idanunsa a rufe yayin da kwakwalwarsa ke juyawa da son tantance dukkan wata kalma da ta fito daga bakin Faruq din.
Bashi da wanda zai zarga, babu wannan mutumin a cikin lissafinsa, amma ya san a yanzu zargin kamar dole ne, don ta haka ne kawai za'a iya samun hanyar da zasu fara tunanin kawo ƙarshen wannan al'amarin.
Anyi haka ba sau dayaba, ba sau biyu ba... An daɗe ana irin wannan abin a kamfanin tun kafin ya kai ga karbar wannan muƙamin, anyi a farkon fara aikinsa ma, watannin daBaffa da Baba Usman suka dora dukkan wani fatansu akansa na cewar abubuwa zasu canja da zuwansa, amma babu abinda ya canja ɗin banda adadin kudin da suka ninku wajen bata ma fiye da baya.
_Ina so ka sani Ma'aruf ba kowa zaka dinga yarda dashi a duniyar ba, wani lokacin mutanen dake kusa da kai suna iya zamewa abinda makiyanka, ba a kowacce fuska mai murmushi ake samun so ba, ba a kowanne ido mai kyalli ƙauna take ba._
Kalaman Jamal sula haska akansa tun bayan wani lokaci, a shekarun baya ya kan tuna su fiye da cikin masaki, amma da wucewar lokaci da kuma hargitsin rayuwa ya manta lokaci na ƙarshe da ya tuna su sai yanzu da suka dawo kansa a lokaci guda, yana iya tuna cewa a wancan lokacin Jamal ya gayamasa cewa bai san dalilin da yasa ya fada masa hakan ba, kawai tunani yake cewar zai iya amfanarsa a gaba...
'Gaban' tana da ma'ana da yawa, zata iya zama shekarun baya da suka wuce, zata iya zama shekaru masu zuwa a gaba, zata iya zama kuma yanzu, yanzun da yake jin kamar maganar tana É—oruwa ne akan halin da yake ciki.
Ya ajiye wayar a hankali daga gefen kujerar sannan ya mike a zuwa hanyar kitchen inda ya baro Amina ya taho amsa wayar, ya san ma ta gama aikin nata a yanzu, don tun kafin ya fito ta kusa karasawa.
So yake yayi distracting kansa, so yake ya juyar da tunaninsa a yanzu gabaÉ—aya daga kan wannan al'amarin, ya samu wani abu da zai É—auke hankalinsa ya manta da abinda ya gama ji, don bai san me zai faru ba idan ya cigaba da kasancewa cikin hakan a yanzu, abinda ya sani kawai shine koma waye a bayan wannan al'amarin zaiyi dana sanin da wani mahaluki bai taba irinsa ba duk ranar da yazo hannunsa.
Don haka yayi kokarin maida tunaninsa kan Aminar a yanzu, yana kuma tunawa kansa da dukkan abinda ya faru jiya, jiyan da a cikinta kadai ya kara yarda cewa da gaske ƙaunar yarinyar nan, zuciyarsa ta manta da dalilin da yasa ya aure ta don baya ko saka ranar fara wannan binciken, tunda ya taushi kansa da cewar sai ya saba da ita tukunna shikenan ya ajiye hakan a gefe.
Baya iya wani tunani sai na yadda kusan komai nata ke burge shi, halaiyarta, saukin kanta da kuma kunyarta wadda bata hana ta abinda take so, ya kara fahimtar hakan a jiya sosai, a jiyan da yaso abubuwa su fi haka a tsakaninsu, amma baya jin dadi, baya jin kwarin jikinsa kuma baya son yin komai a wannan yanayin, don bai yarda da kansa ba, bai san ta yaya ma komai zai kasance ba.
Ya karasa cikin kitchen din idanunsa na nuna masa cewa babu kowa a ciki, sai kayan girkinta da ta gama ta jera komai tsaf akan table. Karfe sha daya ne na safiya a lokacin, basu dade da tashi ba, don ita kanta ya kula ta gaji jiyan, kwanan asibitin nan da suka yi ba wani mai dadi bane, shi yasa ya sake rike ta a jikinsa bayan sunyi sallar asuba, tana ta gaya masa cewa zata tashi da wuri amma ya ture bayaninta ya kashe bakinta.
A haka wani baccin yayi awon gaba dasu su duka biyun wanda basu tashi ba sai ƙarfe goma saura, shi ya fara tashi ma, kuma yana yin motsi ta farka, shikenan sai baccin ya kare.
Kofar kitchen din ta baya da take a buɗe ta shaida masa cewa fita tayi wajen, don haka ya nufi wajen kuma tun kafin ya ƙarasa ya hango ta, ta wanke wasu ƴan kananan dusters na kitchen ɗin tana shanya su a jikin igiyar da bai san lokacin da ta ɗaura ta ba.
Wannan rigar ce a jikinta, wannan rigar da bata rufe kafafunta ba, da safen nan bayan tayi wanka ya roke ta da Allah da ta saka don zuciyarsa ta gaji da hasashen kafafun nata da yake jin kamar ya shekara bai gansu ba, kuma da kyar ta yarda ta maida kayan da ta dauko ta saka din tana fadin ita ta bacci ce, abinda yasa shi tunanin zai siyo wanda ba na baccin ba kenan.
Amina ta shanya tawul na gaba a hannunta yayin da take jin zuciyarta tayi wani irin wasai a yau, farin cikinta na karuwa da kowanne wucewar lokaci idan ranta ya tuna abinda ya faru jiya, kokarin da tayi wajen hada al'ummar gidan nan kaf a gaban Ma'aruf bayan tashinsa, ciki har kuwa da mahaifiyarsa da sai dagabaya ma zuciyarta ta bata shawarar hakan, wani abu da ta san babu wanda bai ji dadinsa ba, don ko su Shukra kafin su tafi suna ta fadin zasu tambayi Ma'aruf ya barta tazo inda suke suma, yayin da Salma ke fadin cewa zata zo su saka labule, tayi ta binsu da murmushi kawai tana amsawa har suka tafi, Shahida ma matar Faruqa a jiyan kadai ta sake da ita har sunyi exchanging numbers, musamaman da ɗan ƙaramin ɗanta Aabid yaki kowa duk a tarin jama'ar nan ta jiya sai ita da kuma Inna Danejo... Har Innan na ta tsokanarsa cewa jinin tsofaffi ne dashi don wai tana da kishiya data rasu mai suna Amina.
Sannan ga Ma'aruf ma, yadda ya dinga yi mata jiya kadai ya isa ya shaida mata irin nasa jin dadin, don har godiyar yayi ta radawa a kunnenta, godiyar ma da daga baya ta kasa tantance gabadaya ta mecece. Yanzu babban abinda ya rage shine ta roke shi ya barta taje gidansu kafin Hajiya Kilishi ta sake É—ago da wani abun ko kuma ita ta cigaba da nata takun.
Don Allah ya sani tana kewar Æ´anuwanta fiye da yadda zata iya misaltawa, shi yasa ko a jiyan da suka yi waya da Fati da kuma Maryam a wayar Fatin, bata ko sake yi musu zancen zuwansu ba, don ta yiwa kanta alkawarin da kanta zata zo sai dai su biyo ta daga baya.
A wanan lokacin ne kuma Ma'aruf ya karaso ta bayanta, ta san shine don a lokaci guda ya hanayensa zuro ta gefen cikinta duka biyun ya rungumota ta baya, fuskarsa ta sauka akan kafadarta guda É—aya yayin da É—umin fatarsa da kuma na hannayensa suka ratsa jikinta a take... Zazzabi ne kuma ya kama shi?
Babu shiri ta juyo da sauri tana kallonsa, sai yayi mata wani guntun murmushi sannan yasa yatsansa ɗaya yana taɓa gashinta da ya fito ta gaba kamar yana karkaɗe mata wani abun, a lokaci guda taji zuciyarta kamar ta fashe a kirjinta, dumin hannayensa ya shiga ratsa fatar goshinta yayin da numfashinta ya fara rawa a kirjinta, ta zata ta fara sabawa... Sai kawai ta buɗe baki tace.
"Zazzabi kake... yi?"
Ya girgiza kansa a hankali.
"Lafiya ta kalau, na gaya miki na warke tun jiya, ko baki yarda ba?"
Ta girgiza kanta itama.
"Jikin ka da zafi har yanzu."
Sai kawai ya jawo duka hannayenta biyu dake É—auke da kowanne dusters É—in nan jikakku, ya kara su duka biyun akan kumatunsa sannan yace.
"Kina jin zafin har yanzu?"
Tayi wani guntun murmushi sannan ta girgiza kanta.
Ya cije lebbensa kaÉ—an.
"Na so kince A'a, don ina da wasu hanyoyin da zan nuna miki cewa lafiyata kalau BabyDoll."
"Me yasa kake kirana haka nr?"
Yace.
"Saboda kina min kana dasu, wadanannan siraran Æ´antsanan da nake gani su Sahla suna wasa dasu da."
"Zanyi kiba kwanan nan, kar ka damu."
"Da gaske?"
Ya tambaya ysna kara matso da fuskarsa kusa da tata.
"... Me zai saki kiyi kibar?"
Tana murmushi har yanzu ta É—auke hannyenta daga fuskars ta dan ture shi baya ta kafadunsa sannan tace.
"Idan nayi zaka gani."
Yayi baya ya dawo sannan ya girgiza kansa.
"Ki gaya min idan akwai gudunmawata kinga sai na fara shiryawa tun yanzu."
Yadda yake maganar ya sata yin dariya kafin tayi kokarin juyawa a hankali don karasa shanyar na hannunta, amma ya dawo da ita.
"Seriously idan kiba kike so na san ta yadda zamu samo ta, kawai ki gaya min."
Ganin da gaske yake yasa ta kara ture shi tana dariya.
"Nan fa waje ne, beside rana tana tayi ma bamu yi breakfast..."
Muryarta ta katse sanda ya dora goshinta a saman nata, idanunta suka shiga haskawa da mamaki da kuma tsoro tace.
"Wani zai iya shigowa fa..."
Ya girgiza kansa, motsin na tafiya da nata kan.
"I don't care, let them... koma waye ban damu ba 'cox i'm trying to find my inner peace here." (Kwanciyar hankalina nake nema anan.)
Ya rufe bakinsa daidai lokacin da ya sinkuyo da fuskarsa cikin wuyanta yayin da tasa duka hannayenta biyu masu rike da jikakkun duskter din nan ta riƙo gaban rigarsa saboda yadda take ji jikinta na rawa kamar zata fadi.
Kuma a daidai lokacin ne, wannan kofar bayan nan dake ɓullewa zuwa hanyar cikin gida ta buɗe, Hajiya Kilishi ta fara shigowa sanye da wani dogon hijabinta na sallah sannan ƙawarta Hajiya Salamatu ta biyo baya, daga bayansu, Sameera ce riƙe da wannan jakar Pink, yayin da Surayya ke binta ɗauke da Hamida.
***
_Watakila bani da abinda zance game da chapter nan, ku gaya min ra'ayinku kawai._
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:50 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*06*
~~~~~~~
_You will know when it's love, real love, 'cox you will start believing in destiny._
**
"A hankali zaki kwantar da ita ta gefe."
Amina ta faÉ—a lokacin da Surayya ke kokarin kwantar da Hamida da tayi baci a jikinta kan gadon a hankali.
Surayan ta sunkuyo tana kokarin ajiye ta dadai inda Amina ta sake shimfida bargo da ta ninke gida hudu akan gadon.
"Kar ki sake ta sai ta taɓa gadon."
Amina ta sake faɗa a hankali lokacin da ta kai ƙarshe da ita kuma a hankalin Surayya ta ajiye ta sosai akan bargon sannan ta zare jikinta da kadan kadan, da farko Hamidan tayi kamar zata tashi amma kuma sai ta koma ta kwanta alamun baccin ya dauke ta da karfi, Amina ta karaso rike da wani farin mayafinta dan karami ta rufa mata a jikinta, suna kallo su duka biyun har fuskarta ta saki jikinta sosai akan bargon.
"Kar ki damu insha Allah ba abinda zai canja da zuwanta, kawaidai maganar da su Mami ke tayi alsn rashin kyautsawarsu ne da suka kawo ta da sassafen nan babu wani bayani."
Cewar Surayyan tana cigaba da kallon yarinyar. Amina tayi murmushi itama tana kallon yarinyar kafin ta sunkuyar da kanta a hankali tana kallon yatsun hannunta, ba wai zancen Hamidan ne ya dame ta a yanzu ba, tunanin tarin abubuwan da bata gama saninsu bane game da al'ummar gidan dama Ma'aruf din kansa, sannan kuma tunanin halin da ta lura Ma'aruf na ciki tun sanda taje falon.
Tayi zaton a yau sau É—aya zuciyarta zata tsorata kamar yadda tayi a dazu, a dazun da taji karar buÉ—e kofar nan ta baya, Samirah ta taba gaya mata cewar kofar tana kara ta samu mai ta saka mata, amma bata taba tunanin cewar mantawar da tayi zaiyi amfani ba sai a dazun da karar buÉ—ewar tata ta cika wajen, wanda a lokacin guda ta ture Ma'aruf daga jikinta ta ruga ta koma cikin gidan ta kofar kitchen din dake bayansu.
Bata san waye ba amma tun a lokacin zuciyarta ta gaya mata cewa koma waye din bai dace ya gansu a wannan yanayin ba, sannan bayan rashin dacewar ma ta sani hanya ce da al'amura zasu iya cakude mata tun yanzu, ilai kuwa sai ga mutanen da bata taba zato ba, Hajiya Kilishi da kanta har da wata da ta kira Aminyarta da kuma su Surayyan.
Ta tuno yadda hannayenta suka dinga rawa lokacin da take kokarin zaro dogon hijabinta daga cikin abin sallarta bayan ta taho da sauri zuwa daki, da kuma yadda Hajiya Kilishin ta dinga bin hijabin nata da kallo bayan ta fita gaishe su, kamar tana son É—age shi ne don ta gano wane irin kaya ne a jikinta.
Kuma kamar yadda Mamin take haka matar da ta kira kanta ƙawarta take, duk da cewa tana ta faman addu'a da sanya fatan alkhairi a cewarta bata sami zuwa biki ba, sai dai daga ita har Ma'aruf don a wannan lokacin ba jinta suke yi ba, Ma'aruf din na can tsaye a hanyar kofar fita daga falon kusa da window yana waya da Ishaq rike da yarinyar da Surayyan ta shigo da ita yayin da nata idanun ke tafiya kansu duk bayan wucewar sakan guda tana jin zuciyarta na sake yin rawa a kirjinta.
"Sunanta Hamida Amina, Æ´arsa ce."
Abinda Mamin ta fada kenan bayan lurar da tayi da kallonsu da take yi da kuma cewar wayar Ma'aruf É—in ba mai karewa ba ce a kusa.
Tana tuna yadda zuciyarta ta doka a ƙirjinta kafin ta haɗiye wani dunƙulen abu tana wasa da yatsun hannunta.
"Nayi zaton ai a cikin surutan yaran nan sun gaya miki zancenta, tunda tun kafin bikin ku ake ta case din dawowar tata wajensa."
Sai ta girgiza kanta a hankali yayin da Surayya ke cewa.
"Mami hirar ce dai bata taba zuwa ba idan muna tare, amma ai ko daga colander bakin Samirah zata iya ji."
Amina bata ce komai ba har sanda Hajiya Kilishin ta sake cewa.
"Kuma shima ban ce ya gaya miki bane shi yasa duk aka taru aka manta."
Ta fadi hakan muryarta na haskawa da wani irin yakini da kuma izza wadda wanda ya santa irin sanin da tayi mata ne kawai zai fuskanci manufar kowacce kalma dake bayan maganar tata, da kuma dabarar cewa itace mai juya duk wani al'amari da ya shafi mutanen gidan. Kuma Amina tana tuna yadda wata busashshiyar iska ta shiga wucewa ta makogwaronta kafin ta gyada kanta.
Samirah ta tafi a lokacin don tace kitchen ta baro ta taho, don haka ko da ta gama gaishe dasu bata zauna a falon ba, ta miƙe ta dawo ɗaki, a bakin gadonta ta zauna tunaninta na zarya kan tarin abubuwan da bata san yawansu ba a cikin kanta yayin da take jin muryoyinsu daga nan Ma'aruf ya dade yana wayar nan kafin taji ya gama su dawo magana dasu Mamin, tana jin muryarsu amma bata san me suke cewa ba har zaman shirun ya ishe ta, gashi wayar nantana hannunsa balle ko ba ta kira Amma don ta sanar mata ba, ta kira taji ya jikin Aminu.
Sai kawai ta fito da wasu mayafai da hijabanta da har yanzu ke cikin akwatunan lefen nan ta fara ninke su tana samo musu waje a gefen inda take sa kayanta, a haka Surayyan ta karaso ta same ta É—auke da yarinyar da tayi bacci.
"Ki kyale Mami kawai Amina, na san Ya Ma'aruf zaiyi miki bayanin komai, ita ba lallai taga hakan a matsayin wani abu bane."
Surayyan ta ƙara faɗa wannan karon tana kallonta, kuma ba shiri itama ta dago da fuskarta ta kalle ta.
A zagayen tunaninta kaf dama yadda ta fahimta tayi zaton ai babu mai iya ganin rashin daidain Hajjiya Kilishi balle har a su fahinta, amma da sigar da Surayyan ke mata magana a yanzu sai taga kamar tana nuna cewar bata ji dadin yadda Mamin tayi mata maga a dazu bane wanda ita ta san dalili, Ma'aruf baya zaune a wajen... ƙawarta kuma Hajiya Salamatu ta riga ta san da abin dake tsakaninsu da alama, Surayyan kuma dake zaune bata damu da abinda zata yi tunani ba.
Lokacin da suka fita zuwa falon babu kowa, su Mamin sun tafi Ma'aruf kuma bata san inda yake ba, Surayya tayi mata sallama ita kuma ta kwashe kayan lemonta da basu taɓa ba ta koma kitchen.
Zuciyarta na ta sake-sake tana maida kayan wajensu lokacin da taji shigowar Ma'aruf yana waya, kuma daga sautin muryarsa ta ji ya wuce zuwa hanyar daki don haka ta dauko kayan breakfast dinsu da ta riga ta haÉ—a ta taho zuwa dakin.
"Ka bar ta kawai Ishaq, ka barsu kawai... tunda ka tura musu da wannan shikenan I have my plans against them. Sun yanke wannan hukuncin, na karba, zasu ga me zai biyo baya kuma."
Muryarsa ta fito ne a hankali da tsananin damuwar dake kwance fal a cikin ransa, damuwar da tun a dazu ta san da ita, amma yawanta a yanzu ya ninku ta yadda take jin da zata iya, zata ƙwace wannan wayar ne don kowa ya daina kiransa yana ƙara gaya masa abubuwan dake hargitsa shi.
Yana zaune daga gefen gadon ya sunkuyar da kansa hannunsa ɗaya riƙe da wayar ɗayan kuma ya zura hannunsa a cikin gashinsa yana magana. Ta karasa ta ajiye tray din hannunta akan bedside drawer dake gefen gadon.
Ya dago ya kalle ta sau daya sai kuma ya cigaba da sauraren bayanin da Ishaq din ke yi ta cikin wayar. Tana jin yadda jikinta babu nauyi kwata-kwata ta shiga kokarin hada tea a kofi guda bayan ta zuba dankali da kwan da ta soya a plate ta ajiye a gabansa, lokacin da ta gama haÉ—a tean ta juyo don ta miko masa ya gama wayar.
"Kin zuba naki?" Muryarsa ta fito a hankali yana kallonta.
Sai ta girgiza kanta.
"Yanzu zan zuba, ka fara karɓa tukunna."
Sai kawai ya miƙo hannunsa ya riko kofin, ya hada har da hannunta gabadaya, ya zagaye yatsunsa a jikin natan.
"Mami ta miki bayanin komai?"
Komai? Idan har komai É—in yana cikin kalma biyun da ta faÉ—a cewar yarinyar Æ´arsa ce to kuwa tayi mata bayanin, abinda ya rage kawai shine a fahimtar da ita don bata gane ba, babu abinda ta gane a zuwan nasu da sassafen nan har kuwa rare da Aminiyarta da kuma yarinyar da aka zo ala shimfide a gadonta, amma sai bata ce komai ba, don bata san ta yadda zata fara gaya masa tarin tambyotin dake cikin kanta ba.
Yana riƙe da hannunta da kuma kofin lokacin da ya fara maganar da a farkonta bata gane komauba.
"Rukayya kamar Family freind dunmu ce tun da dadewa, mahaifinta abokin Baffa ne, sunyi aiki tare kuma sunyi kasuwanci tare kafin kowa ya buÉ—e nasa kamfanin. Ita kadaice a gidansu mace tana yayye da kuma kanne maza, amma tun a wancan lokacun ba ma shiri da sauran Æ´anuwan nata saboda ra'ayinmu da ya banbanta.
Ita kaÉ—ai ce a gidansu kowa yake shiri da ita, kuma tun a wannan lokacin ra'ayinta ya karkata sosai a kaina ta yadda take kyautata min fiye da kima har sai da kowa ya fahimci cewa she's interested in me. To sai wani abu ya faru a wannan lokacin da ya zama mafarin ciwo na, rayuwata ta canja gabadaya ta yadda na tashi daga yadda kowa ya sani zuwa wani abun daban.
Amma duk da haka bayan mun kammala karatu sai ta dage akan bakanta, and I've no right da zan iya cewa A'a, saboda ko Baffa a lokacin ya matsa da cewar inyi aure kuma ni ba wannan ne a gabana ba, ina wani bincike ne da nake ganin cewa zan iya gama shi a wancan lokacin saboda haka above all the girls a sannan sai Rukayya tafi kowa zama wadda ya dace na aura.
Bayan auren mu, da shekara biyu, sai zaman yazo karshe, lokacin Hamida tana Baby...."
Yayi shiru yana shafa hannunta akan kofin kafin ya cigaba.
"Na yarda na bar yarinyar a wajenta ne a lokacin saboda karama ce kuma ko baka haka ba dole a wajenta ya kamata ta zauna dama, sai dai duk da haka munyi wani sharadi a lokaci da zai bani damar É—aukarta bayan na kammala abubuwan gabana.
Lokacin da ake shirin fara aurenmu dake, lokacin naga Hamida a wani waje da bai dace ba tare da wata Christian wai ita take kula da ita, da na dauke ta na kai ta wani creche ne tunda ba zan iya kawo ta gida a lokacin ba kuma a can ta zauna har bayan kin zo gidan nan.
Mami tace in dawo da ita nan amma banyi hakan ba saboda nafi son komai ya tafi a hankali, don ni dake ba mu gama fahimtar juna ba a lokacin, so I have my plans yadda komai zai tafi daidai amma sai gidan su Rukayyan suka kasa jira na suka kai zancen kara kotu wanda a jiyan ya kamata inje amma ban samu zuwa ba, Ishaq yaje kuma basu yarinyar kamar yadda muka san dama hakan ce zata faru.
Amma kawo ta da suka yi a yau ban san dashi ba Amina, Dukkaninmu babu wanda ya san dalilin da yasa suka yi hakan, abu daya kawai na sani shine, Hamida tazo wajena kenan Amina ba zata taba komawa hannunsu ba ko me zasu yi a duniyar nan kuwa."
Yayi shiru yana kallon yanayin fuskarta, yadda idanunta ke nuna cewa kwakwalwarta tana daukan dukkan maganganunsa a wani ma'auni da ya kasa tantance shi, don haka sai kawai ya karasa jawo ta gabansa a hankali, har yanzu kofin na rike a hannunsu su duka biyun. Kuma saura kadan goshinsa ya hadu da nata yace.
"Doll, zaki taya ni mu rike ta?"
Muryarsa a hankali ta fito, da wani amo da kamar auna shi ne ya tabbatar zai kassara kowanne abu mai kwari a jikinta da kuma cikin kanta, numfashinta kawai take ji yana fitowa da saurin da yafi daidai, kuma ta san ya fahimci hakan amna da yake a kowanne yanayi Ma'aruf shi din ne dai sai ji tayi yace.
"Idan tunani kike zata hana mu wani abin Doll kar ki damu, I will always find a way, na miki alkawari."
Bata san lokacin da ta ture shi baya da hannu daya sannan ta miƙe tsaye, ya rike kofin data bar masa, ya kalle ta da murmurshi a fuskarsa lokacin da wayarsa ta sake kara.
Ta juyo ta kalle shi kamar zata ce wani abin game da wayar, ya daga mata gira É—aya yana kai kofin bakinsa, sai kawai ta kasa cewa komai din ta juya zuwa wajen wardrobe É—inta.
"B, yanzun nan É—aya daga cikin mutanen RTL ya sake kira, ya bamu details akan mutumin nan da yazo ya karbi kudin."
Abinda Faruk ya faɗa kenan, bayanan layi biyu da a cikin sakanni biyu kawai da suka da suka yi ƙoƙarin goge duk wani dukkan hargitsin da ya tashi dashi a safiyar yau, bakinsa ya furta hamdalar da bai san lokacin da taji bakin nasa ba.
Yaji zuciyarsa na washewa da yakinin fawwalawa Allah al'amarinsa, a yau kaÉ—ai ya tashi da matsaloli har guda biyu wanda suke jigo kuma manya-manya a rayuwarsa, amma sai gashi tun kafin ya kai breakfast bakinsa ya fara samun rabi na waÉ—annan matsalolin sun fara gushewa.
Idonsa ya sauka akan Amina data dauko wani farin abu dan karami ta karaso kan gadon daga daya gefen tana ƙoƙarin kara rufawa Hamida dake motsi kamar sanyin fankar dakin ne ke damunta.
"Alhmdlilah."
Ya furta a hankali yana cigaba da kallon halittu biyun da yake ganin sun zama wani jigo naduniyarsa a yanzu.
Abinda bai sani ba shine, akwai wasu lokuta da bawa ke kaiwa gabar da karshen wahalhalunsa a duniya ke karewa, akwai gabar da mutum ke zuwa inda komai zai tsaya, komai din da ya danganci dukkan wani kunci da hargitsin rayuwar da ya fuskanta, akwai gabar da mutum ke girbe tarin hakurinsa da ya shuka, akwai gabar da mutum ke fahimtar cewa Allah na karbar dukkan addu'o'in sa, sannan akwai gabar da mutum ke iya canja karin maganar bahaushe da cewar...
Rana dubu ta barawo... Rana dubu ma ta mai kaya!
***
_Ina ga mun tatttaro dukkan ksn matsalar mu a yanzu, so wa shiryawa fara samun revenge?_
_Waya shiryawa ramuwar gayya da ake cewa tafi ta gayyar zafi?_
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:52 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*07*
~~~~~~
_She didn't love easily, it took alot for her to fall, but when she loved it was with such intensity it could be felt from a mile away, it shook the earth and made the ocean roar. And when he felt it,it made him questioned if he'd ever known love at all... - Unknown._
**
"Mammy bata ce wajenki zan zo ba..."
Hamida ta faÉ—a tana kallon Amina dake gabanta, tashinta kenan daga bacci kuma sai da Aminan ta sha faman tambaya kala-kala kafin ta samu a yanzu tayi maganar. Maganar da a lokaci guda tasa Amina yin murmushi don in har ce wani abu to komai zai zo da sauki, saboda haka ta gyada kanta a hankali tana murmushin sannan tace.
"Na sani, wajen Daddy tace zaki zo ko?"
Sai ta gyaɗa kanta alamun ta ƙara warewa daga baccin da ta tashi.
"Daddy ya fita yanzu Hamida, amma zai dawo anjima kadan kinji."
Bata ce komai ba ta cigaba da kallonta kawai, sai tace.
"Zaki ci abinci kafin ya dawo?"
Yanayin idonta ya canja da cewar maganar tayi tasiri akanta amma duk da haja sai da taji ta sake tambaya tukunna sannan ta daga kanta a hankali.
"To taso muje a wanke fuska tukunna tunda daga bacci kika tashi ko?"
Wannan karon a lokaci daya ta gyada kai sannan ta miko mata duka hannayenta biyu alamun ta dauke ta, Amina ta sake yin murmushi ganin hakan kafin ta mika hannu itama ta É—auke ta a jikinta.
Kamshin turaren ta mai daÉ—i ya shiga hancinta a take, daga gani tabbas tana samun kulawa don haka tunanin dalilin da yasa suka kawo ta kamar yadda su Ma'aryf keyi ya É—arsu a ranta, suka shiga toilet din dakin har a lokacin kallonta kawai Hamida take yi.
Ta ajiye ta a kasa tana fadin bari adebo ruwan kafin ta samo dauko kofin dibam ruwa ta taro mai dumi kadan daga fanfon. Ta tsugunna a gabanta har ysnzu tana murmushi tace.
"Muyi wasan ruwa?"
Ga mamakinta sai ta girgiza kai.
"Mariya tace babu kyau wasan ruwa."
Sai murmushinta ya karu tana daga kai tace.
"Good, ashe kina da ƙawa mai hankali."
"Mariya tsohuwa ce, ba ƙawata bace"
Sai da Amina ta dan tsaya kafin tace.
"Babba ce?"
Ta gyda kai tana cigaba da kallonta. Sai ta girgiza kanta.
"Ba sunanta Mariya ba ai Hamida."
Alamun mamaki da kuma tsoron laifi suka nuna fuskarta kafin tace.
"To ai haka su Mammy ke ce mata."
Amina ta sake girgiza kanta.
"Su Mami sun manta ne amma Mama Mariya sunanta, watakila ma idan kinyi bacci suna fada baki sani bane kawai."
Bata ce komai ba, sai ta kara yin wani murmushin da tace.
"Tana da Æ´an yara ksmar kibharda mnya ma kamar su Mammmy da ni kinga ai ta zana Mama ko?"
Sai ta gyada kanta a hankali alamun ta gane amma bata ce komai ba, Amina tayi murmushi ta wanke mata fuskar sannan suka taho kitchen, acan yna ta dinga janta da Æ´ar hira a hankali har sai da ta fahimci ta dan fara sakewa da ita, duk da cewa tana ta tambayar inda Ma'aruf ya tafi da kuma lokacin dawowarsa, har Surayya da ta kawo ta ta tambaya tace mata itama zata dawo.
Ma'aruf ya fita a É—azu ne bayan yasa Faruk ya turo masa da direba yazo ya dauke shi da motar Oficce kuma duk kawaicinta sai da taui kokarin nuna masa cewa bai dace ya fitan ba saboda yanayin jikinsa, amma ya gaya mata cewar fitar tasa ta zama dole ne don abinda Faruk din ya samo, wani abu ne da a yadda yake jin kansa ya san ba zai iya barin kansa bai fita ba, sannan kuma du Baffa ma zasu dawo a yau, wanda ka'ida duk sanda suka yi tafiya doguwa irin wannan da sun dawo a kamfanin suke fara sauka tukunna kafin gida.
Don haka babu yadda ta iya dashi haka ya shirya ya fitan, bayan ya roke ta da Allah cewar tayi masa tuwo da miyar wake, don haka aikin da take tayi kenan yayin da Hamida ke zaune tana cin abincinta da kuma tea din da ta hada mata.
"Kema Daddyna daddynki ne?"
Taji ta tambaya lokacin da take kokarin wanke naman da ta fito dashi daga fridge, ta juyo ta kalle ta da murmurshi sannann ta É—aga mata kai, amma sai Hamidan ta kara haÉ—e ranta.
"Ni bana son inyi sharing Daddyna da ke."
Murmushin ta ya karu sosai don maganar ta bata dariya, sai ta gyada ksnta sannan tace.
"Toh shikenan na bar miki Daddynki ke kadai, ni zan dinga dafa muku abinci kawai kuna ci ko?"
Ta daga kanta da sauri a jere alamun ta yarda sannan tace.
"Kuma ki dinga min English, Mammy tace bata so bana yi."
"Insha Allah Princess."
Yadda ta fadi hakan kai tsaye kuma ta kira ta da Princess yasa karo na farko Hamidan ta danyi murmushi itama sannan ta juya ta cigaba da cin abinta, itama ta koma aikin ta. Bayan ta wanke naman ta dora, ta sake duba tukunyar farar shinkafar da tayi ƙal a cikin tukunyar kafin ta rufe ta ɗauko wayarta.
Kamar yadda take ta gwadawa tun safe, nambar Amma ta kara dannawa amma ssi bata shiga, Allah yaso ta kira Babba dazu sin gaisa yace mata watar ba caji ne amma ya baro zata bawa Maryam ta kai mata, don haka ta tabbatar ba'a karbo ba kenan, ga shi ta fatima ma ta samu matsala da ta kira ta ita suyi magana da Amma tana nan.
Idonta ya kara kallon wayar, sabuwa ce dal kirar Samsung don ɗazun nan kafin fitar wani mai delivery ya kawo su guda biyu, ya dauki daya ya bata daya sannan ya karɓi tsohuwar ta hannuta wadda ya fita da ita, don sabuwar ma tana ɗaki yace sai ya fara yin welcome back na sauran layikan nasa tukunna, kuma kyan wayar yasa take ganin har yanzu kamar ba tata bace.
Ta maida ita jikin caji wanda ta jona a kitchen din sannan ta cigaba da aikinta, tana yi tana juyawa tana kallon Hamida dake cin abincin har yanzu a hankali, kamar ba zata ci ba... Har tean ta san ya gama yin sanyi yanzu, a ranta ta kudirce cewa zata gyara wannan cin abincin nata.
"Finished."
Taji muryarta lokacin da take tuka tuwon, ta juyo ta kalle ta, ta dora habarta akan table din ta harde hannayenta daga kasa kuma tana shilla kafafunta, haka kurum ranta yayi daÉ—i ganin plate É—in babu komai ta cinye.
"A taimake ni da plate din a cikin sink Princess din Daddy."
Ta kalle ta alamun bata gane me tace ba sai tayi murmushi tace.
"Ki kai min su plate din cikin sink Princess din Daddy."
Watakila sunan ne kawai yayi mata dadi, don kamar bata yi niyya ba sai ta mike a hankli ta dauki kofin da kuma plate din, da taje wajen sink din sai da tayi dage sannan ta iya cilla su a ciki.
Amina tayi murmushi sannan ta juya ta cigaba da aikinta, ƙasa da minti daya bayan ƙarar da Hamida ta ƙwalla ta cika koina a gidan, bata san lokacin da ta saki tuwon ba ta juyo.
Daga can karshen kitchen din ta ganta a tsaye, rike da wani dan karamin bowl da ta zuba soyayyen msnjan da ta rage a ciki.
"Mammy jini, Mary! Mary!"
Amina bata san wa take kira ba ta karaso ta karbi bowl din sannan ta shiga ƙoƙarin kwantar da hankalinta tana gaya mata cewar ba jini bane, mai ne kawai, amma ko kadan ba saurararta take yi ba, don haka ta dauke ta gabadaya kawai suka yi toilet.
Ta cire mata kayan ta ajiye su a sink sannan ta saka ruwan dumi ta shiga dauraye wajen da manjan ya taba ta, daga baya ma sai suka yi wanka kawai gabadaya, kuma ba su fito daga toile din ba sai da Hamida tana kyalkyala dariya saboda yadda ta dinga tsokanarta da ruwan fanfon shower.
Kuma a lokacin da suka fito ne abin ya faru, a lokacin da ta É—auko jakarta don samo mata wasu kayan, ta dauko su har ma ta sanya mata, gyara su kawai take yi zuciyarta na kiyasin adadinsu da tunanin dama sun kawo ta ne da niyyar zama lokacin da idonta ya kai kan wata bakar leda a can kasan kayan, har zata maida su sai taji cewa bari taga meye a ciki.
Hannunta ya ɗauko ta yayin da ta saki duka sauran kayan, ta taɓa wani abu kamar kwalba a ciki don haka ta zaro ta yi a hankali, kwalbar ce kuwa ƴar karama, baƙa kamar ta turare, ta kalli Hamida a lokaci guda da taji zuciyarta ta buga.
"Turarenki ne?"
Yarinyar ta girgiza mata kai itama tana kallon kwalbar, sai kawai tayi tunanin budewa taji wane iri ne sai dai tana taba kan taji ya ɓalle, idonta ya leka ciki, yana tabbatar mata da cewar ba turaren ne a ciki ba wani farin abu ne kamar takarda, ta tsaya tana wani tunani na sakanni kafin tace da Hamidan.
"Bari naje na dawo, ki zauna anan."
"Inyi kwalliya?"
Muryarta ta tambaya tana mikewa, idonta ya kai kan dressing mirror da take nunawa, sai kawai ta dawo ta dauke dukkan abinda ta san zata iya ɓata jikinta dashi tasa a drawer ƙasa ta ƙulle sannan tace mata tayi
Can waje ta fita bayan kitchen É—in nan sannan ta É—auko intelock guda daya a gefe ta fasa kwalbar da shi, kuma abinda ta gani shi yasa a lokaci guda zuciyarta ta shiga rawa tun kafin hannayenta su fara yi...
Laya ce... Laya fara ƙal!
An nannade ta gabdaya da farin zare!
***
*Bayan Magriba.*
M'aruf bai san iya mintunan daya kwashe kofar dakin yana kallonsu ba, gabadayansu sun juya masa baya ne yayin da suke jera kayan Hamida da suka baje a dakin cikin wardrobe din dashi take kallo daga inda tsaye.
Ya gaji, gajiyar da har da rashin komawar jikinsa daidai, amma duk da haka yaji yana son ya cigaba da tsayawa a wannan wajen har zuwa karshen inda lokaci zai kai su. Wani irin abu mai dumi yake ji yana bi cikin jijiyoyinsa gabadaya, tun daga farkonsu har karshe.
Tun daga ranar da ya fara ganin Hamida yana jin wani irin abu yana ratsawa har can bangon zuciyarsa, yana fito da tarin kaunar daya daɗe da binne ta, yawan ƙaunar dake sashi ganin irin ƙoƙarin da yayi a cikin shekaru biyu nayin nisa da yarinyar, yana sa shi alaƙanta abinda yake
ji da cewar haka sauran iyaye ke ji idan suka kalli abinda yake gudan jininsu. A yanzu kuma da hotonta ya hadu dana Amina a gefenta, sai yaji komai yana ninkuwa, adadin komai É—in na karuwa a cikin ransa da yawan da bai san ta yadda zai fassara shi ba.
A lokacin da yake tare da Rukayya, lokacin da Hamida tana ƴar ƙarama, baya jin ranakun da ya dawo ya ganta a hannunta zasu wuce kirgensa, kullum zata ce masa tana wajen mai aikinta sai dai in a karbo masa ita daga baya, don haka a yanzu bai san da wane sikeli za'a iya auna abinda yake ji a zuciyarsa ba.
Ya yarda har cikin ransa cewar cikar kowannen namiji yana karkashin kulawar mace ta gari! A yau kadai, sa maganar da yayi mata kadai, ta karbi Hamida cikin rayuwarta gashi tun ba'aje ko'ina ba alamu sun nuna masa cewar ita kanta yarinyar ta fara sakin jikinta da ita.
"Wannan da wannan da wannan Uncle Jawad ne ya siyo min."
Hamida ta faÉ—a tana nuna wasu kaya har da wanda Aminan ke sakawa a wardrobe din.
"Wanene Uncle Jawad?" Muryarta ta tambaya a hankali, wannan muryar tata mai taushi. Sai yarinyar ta girgiza kanta.
"Kawai wajen Mammy yake zuwa."
Sai Aminan ta gyada kai sannan tace.
"Allah ya saka masa da alkhairi."
Shirun da Hamidan tayi yasa ta juyo ta kalle ta.
"Baki ce Amin ba."
Sai da ta sake wani shirun sannan tace.
"Ameen."
"Yawwa Princess din Daddy."
Idanunsa suka sake tsayawa akan Amina da kuma murmushin fuskarta. Ta canja kayanta zuwa wata riga ƴar kanti kalar yellow, a zaune take don haka bai san tsawon rigar ba, amma kalarta ta haska wajen gabaɗaya kamar ranar dake kwallewa a sama, babu dankwali akanta sai wannan gashin nata mai laushi data daure karshen sa da katon ribbon baƙi. Kuma bai sani ba ko hasashensa ne kawai, amma daga inda yake kadai yana jin kamshin turarenta irin wanda yaji a jikinta da safe.
Ta saka kwalli a idanunta wanda ya fito raÉ—au ya fito da kamanninta yana haska fuskarta da tayi fayau a cikin hasken É—akin, shi kansa bai san tasirin da shigar tata tayina ransa ba, ga san dai kawai numfashinsa ya kara yin nauyi a kirjinsa yayin da yaji wani abu kamar gumi na tstsafowa daga tafin hannunsa, sai dai kafin yayi wani tunanin ta juyo ta kalle shi, idanunta suka sauka akansa, gashin samansu mai tsawo har yana tabo girarta, lebbenta ya tale da murmurshin da yaji kamar yana narka zuciyarsa.
Sai dai kafin yace wani abu ko ita tace, Hamida ta juyo ta kalle shi, kuma a lokaci guda ta taso da gudu ta taho tana fadin .
"Daddy!"
Sai ya rasa wanne a cikin biyun nan zai dauka ya bawa alhakin narkewar zuciyar tasa, ya san dai kawai a wannan lokacin ya manta dukkan bayanan da ya tattaro a cikin kansa na Office ya karbi abinda lokaci ya bashi, saboda haka sai kawai yayi ƙasa ya durƙushe akan gwiyoyinsa yayin da Hamida ta karaso da sauri ta shige cikin hannayensa.
Amina ta miƙe tsaye a hankali, tana kallonsu, kuma a lokacin ne idon Ma'aruf ya sauka akan ƙarshen rigar, iya gwiwa ce... Ya salam!
"Kin tashi daga baccin Baby girl?."
Ya kira ta da sunan da yake gaya mata tun a creche din nan wanda ya sata murmushi.
"Har tea na sha ma da chips."
"Really? Kince kinyi karfi kenan."
Ya faÉ—a suna mikewa tsaye, ta kyalkyale da dariya tana É—aga masa kai. Amina ta matso gabansu kadan.
"Sannu da zuwa, ya aikin?"
Ta faÉ—a muryarta na saukowa kamar wani fiffiken dake saukowa kasa a hankali yayin da Idanunta ke kallonsu da nata kalar sha'awar da bata san da ita ba.
"It was fine, ba laifi an samu abinda ake so."
Ta gyaÉ—a kanta.
"Alhmdlilah."
Sai kawai ya kasa daurewa zuciyarsa yace.
"You look breathtaking Doll, kamar idan na kalle ki da yawa zan daina numfashi."
Da dan guntun murmushi a lebbanta ta cigaba da kallonsa, ya gyaÉ—a mata kai yayin da Hamida ta juyo tana kallonsu. Wani abu yake ji a lokacin kamar wuta ya harba daga tsakiyar bayansa zuwa kafafunsa, yaji yana so ya rungume ta kamar yadda yayi wa Hamidan, kuma kai tsaye zai iya yin hakan amma bai san yaya zata karbi hakan ba a yanzu.
Ta juya ta koma can wajen wardrobe din rike da rigar nan a hannunta sanda Hamida ke cewa.
"Daddy, wannan Auntyn tace ta bar min kai ba zamu yi sharing ba, kawai zata dinga dafa mana abinci."
"Haba dai?" Ya tambaya da sauri da kuma alamun mamaki, sai kuma yace.
"Wasa take miki, kice wasa kike mata dan Allah Doll.
Yadda muryarsa ta fito, yadda amonsa ya furta wannan sunan da kuma taushin muryar tasa ya taba har fatar kunnenta ba ma can ciki ba, ta juyo ta kalle shi tana dariya kuma kafin shi da ita su sake cewa komai, Hamida tace.
"Sunanta Doll?"
Ya gyada kansa yana cigaba da kallon ta.
"Eh mana amma ba wanda kika sani ba, wannan special one ne."
Sai ta gyada kanta itama alamun ta gane kuma daga wannan ta shiga tambayarsa yaushe zai sake maida ita wannan creche din da ya É—auko ta, tana gaya masa cewa su je kitchen taga irin bowl É—in da ake zuba mata abinci a creche din, kuma da haka ta ja shi suka bar dakin tana ji taba gaya masa cewa wai jini ne a cikin bowl din har ya bata mata kaya.
Sai ta hadiye wani abu da bata san sunansa ba a maƙogwaronta, har yanzu ta kasa samun Amma a waya, Allah-Allah kawai take anjima tayi ta kira Baba idan ya koma gida, don duk da ta ƙona wannan layar dazu a bayan fulawoyin gidan har yanzu hankalinta bai kwanta ba, har yanzu zuciyarta bata nutsu ba.
Ta zazzage dukkan kayan Hamidan yafi sau biyar tana sakewa, tun tana tambayarta me take nema har ta gaji ta tsaya tana kallonta kawai, sai da ta gaji ta tabbatar babu wani abu da ta sake gani sannan ta zauna suka shiga ninke su suna saka su a kasan drawer.
A yanzu ta riga ta sami amsar da kowa bai sani ba, ta gane dalilin da yasa suka kawo yarinyar haka kwatsam bayan faruwar komai, akwai wani abu da suke son cimma ne wanda bata san takamaimai asirin akan waye ba, amma duk da haka bata jin cewa ya dace ta sanar da Ma'aruf tun a yanzu, shi yasa take son samun Amma a waya ta shaida mata komai don ta san yadda zata ɓullo musu suma, don ta yarda idan har zasu yi yunkurin cin galaba akan Kilishi to wannan ma ba komai bane, kawai tsoronta shine kar ya zamo da wani abin da bata sanshi ba ko kuma bata yi daidai ba wajen ƙona layar nan.
Lokacin da ta gama ta koma falon, Hamida na zaune ita kadai tana kallo, don haka ta fahimci Ma'aruf yana dakinsa kenan, sai kawai ta koma kitchen ta debo dukkan kayan abincin data hada ta fito dasu falon, Hamida tace ba zata ci tuwon nan ba, don haka tayi mata wata Æ´ar jollof din taliya da kifi. Kuma tana miko mata ta karba ta fara ci,ta fahimci yarinyar tana son abinci kawai dai bata iya ci da sauri bane.
Sai dai tana fara ci din tace a cire mata ƙayar kifin, don haka ta bar sake kokarin kiran su Amman da take yi tazo ta zauna daga gefenta a kujera tana kokarin cire mata ƙayar tsakiya na kifin da fork din da take ci. Kuma a lokacin ne Ma'aruf ya fito, ya canja zuwa wata gogaggiyar jalallabiya kalar milk data fito da ɗan hasken fatarsa kadan, yayi fresh din da ba sai yayi bayanin daga wanka yake ba, amma duk da haka Hamida ta tambaya.
"Kayi wankan?"
"Yes, nayi wanka."
Ya amsa yaba tahowa idonsa akan kafafunta da ta rasa me yake gani a jikinsu yake kallo, jallon da yasa zuciyarta tayi fayau a kirjinta.
Ya ƙaraso a hankali ya tsugunna a daidai gabanta hannunsa riƙe da wani abu da bata gani sosai ba, kuma tun kafin yace wani abu Hamida ta sake fadin.
"Daddy naku tuwo ne kai da Auntyn, ni bana ci shi yasa nake cin wannan."
"For real?"
Ya dawo da ganinsa kan Aminan, don shi har ga Allah ya manta da zancen tuwon da yayi.
"Da gaske na samu tuwon nan?"
Tana murmushin yadda yake tambayar ta gyada masa kai, sai ya zura hannunsa daya a cikin gashinsa yana kallonta ba tare da yace komai ba.
Sai kawai tayi murmushi ta mike zuwa wajen da ta ajiye food flasks din tana gaya masa cewa har da na dumame ma duk zai samu, yayin da Hamidan ta shiga tambayar meye É—umamen.
"Eeeewwwww!" Ta fada da karfi bayan Ma'aruf yayi mata bayanin.
Suka yi dariya dukkansu kafin Ma'aruf ya taso zuwa wajen da take zuba masa abincin, kamshin miyar ya ratsa hancinsa yana yaba girkin tun kafin ya kai bakinsa don ko daga yadda miyar bata yi mai sosai ba ma hakan ya burge shi, kamar ta san yadda yake son komai.
Ya tankwashe ƙafafunsa a gabanta yana kallonta yana kallon yadda take zuba miyar, yadda take komai... Allah ya sani baya jin gar ya bar duniya zai taba manta wannan alkhairin na Mami na kawo masa Amina cikin rayuwarsa.
Wannan wani alkhairi ne da yake tunanin har a kabarinsa zai tuna shi.
****
"Ƙarfe tara da rabi.*
Hamida tayi bacci a lokacin, kuma har a sannan Amina bata sami damar samun su Amma ba don wayar Baban shima bata shiga yanzu.
Ma'aruf ya shiga cikin gida wajen Baffa, kusan awa guda kenan, tun daga masallacin isha'i yace mata zai wuce. Ya gama cin abincin yayi santi kala-kala da tun tana daurewa har ta dinga dariyarta a fili, kuma bayan hakan ya gode mata lokacin da ta kwashe kayan zuwa kitchen.
A cikin kunnenta ya dinga raÉ—a wasu abubuwa da ita kanta idan ta tuna yanzu sai ta runtse idonta don kunya, Ba wai maza ta sani sosai ba amma ta yarda Ma'aruf daban ne, shi da kansa yau ya gaya mata cewar baya ji, kuma itama ta yarda da hakan.
Babu wanda zai yarda zai aikata dukkan abubuwan da yake yi, idan ka ganshi a fuska very responsible and so stiff akan dukkan abinda ya yanke, amma yafi kowa sanin tarin hanyoyin da zai ruÉ—a mace a lokaci guda.
Kamar kullum wajen da ya riƙe ta har yanzu tana jin kamar shatin yatsunsa a wajen, kamar lokacin da ya riƙe ta yatsunsa sun ƙona wajen ne sai a yanzu iska ke kaɗawa tana son dawo da fatar tata daidai.
Ta ajiye abin sallar da ta idar da isha'i a lokacin, gyaran kitchen din da tayi ta kuma tsaya yiwa Hamida Brush da canja mata kaya tana gyangyadi shi ya cinye lokacinta sai yanzu ta samu na sallar.
Ta tafi zuwa gaban mudubi ta dauko wani kwando tana kwashe dukkan abinda ta san Hamida zata iya sawa a ido ko ta bata jikinta dashi, tana yi tana yabawa kanta yadda tayi kokari wajen kula da yarinyar da kuma sawa ta sake a gidan ysu daya kawai, Surayya na cewa sati guda, idan ta shigo gobe zata sha mamaki.
A lokacin ne kuma kofar dakin ta bude, ta dago da idonta ta cikin mudubin tana kallon Ma'aruf din da ya shigo, fuskarta ta haska da murmushi tana masa sannu da zuwa.
Ya karaso a hankali yana zuwa inda take, kuma ba tare da ya jira komai ba ya rungumeta ta baya, kansa ya sauka a gefe wuyanta sannan ya karkato da kansa gefe yayi kissing kumatun ta kafin yace.
"Har guda nawa zan dinga samun wannan sannu da zuwan ne?"
Tayi kokarin tsaida numfashinta a hankali.
"Duk lokacin da ka fita ka dawo, kana da guda daya?"
Sai ya gyada kansa sannan ya ƙara karkata shi zuwa cikin wuyan nata, ba shiri ta damke kwandon nan dake gaban mudubin, tana jin kamar wannan karon kusan tayi yawa.
"Yaya jikin naka?"
Ta tambaya a hankali don ji take yi kamar har yanzu da É—umi a jikin nasa. Yayi shiru jamar ba zai amsa ba tsawon wucewar sakanni sannan yace.
"I'm sorry Doll."
Mamaki ya dan kamata.
"Na me?" Ta tambaya.
Sai kawai ya mike tsaye sosai ya juyo da ita tana fuskantarsa, sannan yace.
"Sorry da nake saki damuwa akaina."
Ya sunkuyo a hankali ya sake kissing daya gefen fuskar tata sanan ya sake cewa.
"Sorry da zuwan Hamida."
Ya sake kissing gefen bakinta.
"Sorry da dukkan flaws din da kika zo kika tarar a rayuwata."
Wannan karon saman bakinta ya sake kissing sannan ya É—an matsar da fuskarsa baya kaÉ—an yana kallon idanunta yace a hankali.
"Sorry da na bata miki dukkan rayuwar da kike tunanin zaki samu idan kinyi aure..."
Kafin ya ƙarasa, kafin ya sake cewa wani abu tasa hannunta da sauri ta rufe bakinsa sannan ta girgiza kanta.
"You don't have to be... Babu abinda na taba tsarawa a rayuwata a wannan stage din, babu wani hasashe da na taba yi, so dukkan abinda ke faruwa a yanzu shine duniyata kuma shine fantasy dina."
Ya rike hannunta da ta rufe bakin nasa dashi, yayi kissing cikin tafin hannun nata kafin ya janye shi a hankali.
"Ban gane ba Amina, ki kara yi min bayani sosai."
Sunanta da ya fito daga bakinsa da kuma yadda sautin muryarsa yake yasa jikinta yin rawa kadan, ta hadiye wani abu a makogwaronta har yanzu tana kallonsa sannan bakin ta ya furta.
"Ma'aruf Mansour Bakori, kai ne duniyata kuma kaine duk wani fantasy dina a yanzu, I really love you so much and I mean it."
Kuma da haka bata jira komai ba ta kara tsawon kafafunta tayi kissing gefen bakinsa kamar yadda yayi mata dazu,da farko bai ko yi motsi ba, yana tsaye ne kawai kamar baya numfashin amma tana kokarin maida kafafunta ta koma taji ya furta kalma guda biyu rak!
"Ya salam!"
Kuma da haka bai jira komai ba yasa duka hannunsa biyu ya jawo ta jikinsa.
"I love you." Muryarta ta kara fada a fuskarsa, yayin da a cikin zuciyarta take mika dimbin godiya ga mahallicinta jalla wata'ala daya kyautata rayuwar ta da mutum kamar Ma'aruf.
Kafin tayi tunanin komai, hasken dakin ya tafi gabadaya, kuma daga wannan gaɓar bata ƙara gane komai ba, abinda ta sani kawai shine ta riga ta yiwa kanta alkawarin cewa da yardar ubangiji daga wannan lokacin, Ma'aruf ya daina sanin wani ɓacin rai a rayuwarsa sai dai idan har abu yafi ƙarfinta.
Dukkan wadannan matsalolin da yake fuskanta da sannu zata buɗe masa su daya bayan daya, don in dai har a wajen Hajiya Kilishi matsalar take, tayi imanin zata warware masa su ne hankali kwance ba tare da ita kanta Kilishin ta fahimta ba kamar yadda Amma ta gaya mata a wayar da suka yi ta ƙarshe.
_"Mun riga mun gama haddace dukkkan wani takun matar nan Amina, don haka dasu zamu yi amfani daya bayan daya wajen kassara ta, ba zata taba tunani ba, ba zata taɓa hange ba saboda tana da yaƙinin hakan tunaninta ne ita kadai kuma saboda mun saka mata imanin cewa ke baiwarta ce, baki da wata mafita ko dabara sai tata kawai!"_
**
_Wannan shine takunmu na farko akan Kilishi... Shine takun farko! Gabatarwa kawai, introduction..._
_Shine play button na Game É—in, don yanzu za'a fara wasan, yanzu komai zai fara, yanzu zaku san mene ainihin suna da kuma ma'anar labarin FARAR WUTA ( A lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai!) Don Amina itace Farar wutarmu ba Kilishi ba kamar yadda kuke tunani tun daga farkon labarin._
_Amina itace FARAR WUTAR da Kilishi bata taba lisaafinta ba!_
_And Ehem ehem, kun kula cewa yau Ma'aruf muka ruda??_
😅😅🤣
*Asuba ta gari!*
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:52 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*08*
~~~~~~
_I need you to tell me it's okay._ _-Unknown_
**
"Ma'aruf..."
Muryar Amina ta fito a hankali cikin shirun dakin a hankali, ƙarfe bakwai da rabi ne na safiya, don tun bayan sun idar da sallar Asuba basu koma bacci ba. Kuma jin yayi shiru yasa a hankali ta dago da kanta ta kalle shi.
Idonta ya sauka akan fuskarsa, ya rufe idanunsa gabadaya kamar ya koma bacci amma ta san ba baccin yake yi ba, wani tunani mai daÉ—i ya sauka a cikin zuciyarta na tunanin cewa daga daren jiya zuwa yau ya daÉ—a tabbata shi mijinta ne don dukkan wahalar data sha ma da yadda take jin jikinta baya gabanta a yanzu, kawai zuciyarta na kara narkewa ne da tunanin dukkan abinda ya faru.
Daga yadda yake rike da ita kadai a yanzu tana jin cewa kamar a duniya kaf babu wani waje da zata taɓa zama a killace sama da cikin hannayensa, musamman a yanzu da ya fara bata labarin rayuwarsa, tana jin yadda kowacce kalma da yake fada ke ratsawa cikin kanta har zuwa zuciyarta.
Rayuwarsa mai kyau ce, cike take da wani irin gata da kuma jin dadin da ita bata taba saninsa ba ma, don ko a tsakanin yan uwan nasa, rayuwarsa daban ce, Hajiya Kilishi ta kyautata rayuwarsa da wani irin gata da kuma jin daɗin da a yanzu take jin zuciyarta na ƙara dasa aya kan wace irin ƙauna ce wannan da zata so shi irin haka kuma ta dinga cutar dashi.
Sai dai bayan duk hakan kuma a yanzu yazo gabar da yake gaya mata labarin yadda ya rasa ɗanuwansa Jamal, ya gaya mata yadda komai yake tsakaninsu, shaƙuwarsu dama dukkan wani buri da kuma ƙudirin Jamal ɗin bayan ya dawo daga karatu, a yanzu yana gaya mata lokacin da suka yi wata tafiya ne zuwa Bakori don ɗauko Inna Danejo, kuma duk da bsi karasa ba, tunaninta ya gaya mata cewa a wannan lokacin ne wani abu ya faru, shi yasa bayan yayi shiru bata ce komai ba, tana jinsa kawai yana cigaba da wasa da yatsunta daga kasa bargon da ya lulluɓe su, sai da shirun ya tsawaita tukunna sannan tayi magana.
Ya bude idanun nasa a hankali ya lumshe su yana cigaba da kallonta yayin da ita nata ke ware akansa. Kuma a hankali cikin rashin hasken É—akin muryar sa ta cigaba da cewa.
"Shi ya bani tuƙin a lokacin, kuma abu na karshe da ya gaya min shine kar in kashe shi, bayan mun canja waje na hau titi bamu kara magana ba saboda ya shiga ansa call din wani abokinsa Liman, suna ta magaba ni kuma nayi focusing hankalina akan titin, wallahi wallahi banyi wani abu ba daidai ba, I was driving safely lokacin da abin ya faru."
Ya sske yin shiru, shirun da ba sai wani ya gaya mata cewar yana shirin gaya mata cewa yana shirin gaya mata dukkan memories din dake binsa shekara da shekaru bane.
"Kawai naji sitiyarin ya ƙwace daga hannuna ne sannan naga motar tana wullawa akan titin, ina jin salatin da yake yi amma ni ban ma san me nake cewa ba, hannunsa yana ta kokarin ya kama sitiyarin amma juyin da motar ke yi yasa buguwa kawai muke yi kotawanne bangare, lokacin da motar ta sauka daga kan titi ta nufi cikin daji, daga ni har shi babu wanda yaga karyayyiyar bishiyar dake gabanmu har motar ta dake ta, ta dake ta daidai saitin inda Jamal yake da karfin da yasa ta faso ta cikin gilashin ta soke a ko'ina na kirjinsa."
Ya sake yin shiru, idanunsa na kallon tsakanin girarta guda biyu yayin da suke haskawa da wani irin abu da Amina ta kasa tantance shi a lokacin, sai kawai ta ɗago da hannunta daya da bai riƙe ta dashi ba zuwa gefen fuskarsa, a hankali dogwayen yatsunta suka ratsa tsakanin gefen fuskarsa da kuma wuyansa, wani abu da yasa ya sake lumshe idanunsa nasa kafin ya sake cewa.
"Likitocin sunce zuciyarsa ta fasa a lokaci guda shi yasa tun a wajen ya rasu..."
Bata ce komai ba ya cigaba.
"Ya rasu yana kallona Amina, idanunsa akaina suka tsaya har lokacin da jama'a suka karaso suka rufe motar ana kokarin fito damu, don tankin mai ya fashe tana shirin kamawa da wuta, ba'a iya fito da Jamal ba sai da aka sare reshen bishiyar nan daga jikinta, aka fita dashi dasu a jikinsa.
Ban ma san ta yaya aka zaro ni ba, na san dai kawai ban ƙara fahimtar komai ba bayan hakan sai farkawa nayi na ganni a asibiti, and that was the beginning na farawar ciwo na, I was depressed, emotionless and even out of my mind."
Taga alamun ya haɗiye wani abu a maƙogwaronsa sannan ya cigaba.
"Kusan haukacewa nayi a wannan time din Amina, bana gane komai bana fahimtar komai, wannan ranar ita kadai take ta maimaitawa a cikin kaina, tun daga safiyar da na ganshi zaiyi tafiyar, har tahowarmu mu, da maganganun da muka yi da kuma yadda hatsarin ya faru.
Su Mami, kowa da kowa sunyi mutukar kokarinsu wajen tallafa min Amina, musamman Ishaq, Ishaq yayi mutukar kokarin da ban ma san adadinsa ba Amina, kusan shi kaÉ—ai yake tare dani a kodayaushe, dashi muka yi ta yawon zuwa asibiti a London, shi yake tare dani a gida kodayaushe, su Mami suna zuwa duba ni amma ba kodayaushe ba, ina samun support dinsu da tarin addu'o'i.
A cikin wasa muka yi magana da Jamal cewa zan iya canja rayuwata zuwa tasa idan har wani abu ya faru, amma duk da haka bayan naji sauki sai naji ba zan iya rayuwa a matsayin Ma'aruf da wannan nauyin ba, saboda haka sai na ajiye dukkan wani buri na a gefe na fara sabuwar rayuwa.
Tun ina yaro burina ne in zama likita, kafin accident din na sami admission a wata makaranta a lokacin amma bsyan na warke ban sake bi ta kan admission din ba na dage wajen canja makaranta dama course din gabadaya, Baffa ya iya kokarinsa don hana ni amma na gaya masa cewa in dai ba karatun business ba ba zan yi karatun ba gabadaya, a lokacin ne Mami tasa Ishaq ya dawo wajenmu bayan rasuwar iyayensa muka tafi London tare muka yi karatun.
Bayan wannan abubuwan da na canja a rayuwata suna da yawa Doll, this isn't me, mafi muhimmanci shine wannan matakin da nake kai, burin Jamal shine ya karanci harkar kasuwanci kuma riƙe ragamar kamfanin Baffa kamar yadda nake yi yanzu."
Ya sake yin shiru yana kallon yadda ta kame gabadayanta, har yanzu hannunta na kan fuskarsa,babu abinda take sai numfashi da kuma jiran ya cigaba.
"Kin fahimce ni Doll, kina ganewa?"
Ya yanke shawarar tambaya, sai tayi kokarin É—aga kanta a hankali tana son tayi maganar amma ta kasa, ta kasa don bata ma san me zata ce ba, ya gyada kansa shima ba tare da ya damu da jin abinda zata fada din ba, kuma tana ji yana cigaba da wasa da hannunta kafin yace.
"Bani na kashe Jamal ba Doll, ni na san bani na kashe shi ba don haka bayan abubuwa sun fara tafiya daidai sai na fara bincike akan wannan accident din, kuma sai da na shekara uku ina bin wannan hanyar ina tuntubar mutane kafin na samu wasu mutane biyu da suka tabbatar min cewa wasu mutane ne suka harbi tayar motar mu a lokacin da nake tuƙin, da silencer suka yi amfani a bindigar ta yadda babu wanda yaji wata ƙara sai kawai ta fashewar tayar.
Bayan nan, nayi iya binciken da zan iya don gano mutanen da suka yi wannan aikin, ina living rayuwata ina kuma yin binciken don ban taba amma duk hanyar da na bi bata ɓullewa bana samun komai, kuma duk lokacin da hakan ya faru I felt emotionally high, sai ciwona ya tashi, sai inji komai ya tsaya, abu kadan yana bata min rai kuma idan ran nawa ya baci bana jin ina son komai sai tsananin yadda zan iya wanke kaina a wajen Jamal.
Kuma abu daya ne kawai yake zuwa kaina cewa zan iya aika masa da sako, shi yasa duk wanda ya bata min rai, sai inji ina son in kashe shi kawai, in kashe shi in bashi sakon cewa ya gayawa Jamal abinda ya faru bani na kashe shi ba, this is crazy! I'm crazy na sani Amina, na san banbancina da mahaukaci a irin wannan lokacin bashi da yawa, amma wallahi hakan ne kaÉ—ai abinda nake so shi yasa nake tunanin idan har na samo wanda suka yi abin nan watakila zan iya jin sauki a raina."
Amina ta hadiye wani abu da bata san sunanshi ba a maƙogwaronta, tana jin yadda maganganun ke zagawa cikin kanta kowanne da tarin ma'anar da yake fitowa da ita, kowanne da nauyinsa kuma kowanne da tasirin da yake zama dashi a zuciyarta. Kuma bata sab lokacin da hawaye ya cika a idanunta ba sai zubuwarsa taji a gefen fuskarta.
"Wannan ciwon shine dalilin rabuwata da Rukayya, ta bata min rai a ranar da nima nawa ran yake a bace, so bana cikin hankalina sanda na karbi Hamida daga hannunta tana Baby lokacin nayi wulli da ita, ita kuma nayi mata dukan da ba don Allah ya kawo Ishaq a lokacin ba ban san me zai faru ba.
Ba zan ɓoye miki ba Amina, duk yadda nake jin zuciyata na sakewa dake wallahi ina tsoron ranar da ciwona zai iya tashi akan ki, shi yasa lokacin ayrenmu na aika miki da wannan takardar don ki fasa, bana son in sake abinda nayi tare da Rukayya ..."
Ya kara kallonta sosai, yana kallon idanunta da suka cika da kwalla kafin ya ƙarasa.
"... Na yarda ƙaddarar haduwa dake itace bata sa na mutu ba tun a wancan lokacin, sabida haka idan har wani abu ya same ki ta dalilina yanzu, na tabbata wannan karon nima mutuwa zanyi, don ba zan taɓa iya sake wata rayuwa a duniyar nan ba idan har na kara sanadin rasa abu nsi muhimmanci irinki..."
Wadannan kalaman suka tada tsigar jikinta a lokaci guda, taji wani abu ya ratsa tun daga zuciyarta har zuwa bayanta. Sai kawai ta sake matso da kanta cikin jikinsa sosai, tana rike da fuskarsa har yanzu ta shiga girgiza kanta a jikin fuskarsa.
"Babu abinda zai sake faruwa, babu abinda zaka yi min Insha Allah, babu wanintashin hankalin da zai kara samunka, sauran da suka faru ma, sun faru ne saboda haka Allah ya tsara komai ya kasance, amma Allah ba zai kara kawo su cikin rayuwarmu ba insha Allah, all I care is that ba kai ka kashe Jamal ba kuma na san shima ya san hakan, da zai dawo nayi imanin zai gaya maka hakan, zai gaya maka cewa ya san ba laifinka bane."
"Laifin waye Doll? Har yanzu na kasa gane laifin waye, ko zai dawo É—in ta yaya zai yarda dani?..."
"Zaka sani insha Allah, nayi imanin idan ka cigaba da nema zaka sani, Allah ba azzalumin bawansa bane Ma'aruf, ya sani cewa ko su waye sun cuce ja kuma sun hargitsa rayuwarka, zai maka sakayya ta hanyar tona musu asiri insha Allah."
Maganar ta fito tare da tahowar wani hawayen mai dumi daga idanunta, sai kawai ya sake sunkuyo da fuskarsa kan goshinta yayi kissing idanun nata duka biyu yayin da ta rufe su.
"Insha Allah Doll, fatan da nake yi kenan a kodayaushe."
Wasu hawayen suka sake biyo bayan na baya suka fito masu É—umin gaske. Abinda ta sani kawai a wannan lokacin shine idan har da sa hannun Hajiya Kilishi a mutuwar Jamal, to tabbas kuwa Ma'aruf ya kusa samun amsar sa.
***
*Ƙarfe tara da rabi.*
Tunda suka tashi take iya kokarinta wajen ganin tayi komai kamar yadda suka saba, yau asabar ce don haka ta san vabu inda zai je, wajen karfe takwas ta fito ta sake yin wanka sannan ta shiga aikinta, tana jiyo shi daga daki yana ta waya kuma bayan taje kai masa daya wayarsa da ya bari a falo wadda ake ta kira, ta ganshi ya fito da system har guda biyu yana ta faman dube-dube. Basu yi wata magana sosai ba amma yayi mata murmushi fiye da yadda zata kirga a iya safiyar kawai.
Ta kammala hada breakfast din tana dauraye kwanukan da tayi amfani dashi ne lokacin da ihun Hamida ya ziyarci kunnenta, ta tashi tana ta kiran sunan Mary.
Ta fahimci Mary ce Æ´ar aikinta da kullum suke tare, kuma takaicin da ya kasa barin zuciyarta shine na yadda sunan arniyar ya zauna a bakinta, ko mahaifiyarta bata kira sama da ita, yanzu ma ace yaro ya tashi daga bacci babu kiran sunan Allah sai wata arniya... Da sannu zata canja mata hakan a hankali.
Kuma ko da ta isa dakin har ta sauko daga gadon tana shirin fitowa, don a bakin kofa ta tarar da ita. Kuma cikin siga da dabararta sai da ta sa ta fadi addu'ar tashi daga bacci kafin su wuce zuwa bandaki inda tayi mata brush da wanka gabadaya.
Bayan sun fito ta shirya ta cikin wata Æ´ar doguwar rigarta mai kyau pink colour sannan suka fito falo,inda anan suka tarar da Ma'aruf har ya fito shima ya É—ebo kayan breakfast din da kansa zuwa falo ya zuba yana ci.
Yana ganinta ya fara bata hakuri cewa yunwa yake ji shi yasa ya kasa jiransu, Hamida ta makalkale shi tana gaya masa cewa tayi mafarki da Unicorn, wani shirmen mafarkinta irin cartoon din da kullum take gani.
Wannan lokacin yayi dadi a zuciyar Amina ba kadan ba, sai take ganin yadda yarinyar ta dada sawa gidan ya zama lively a tsakaninsu, har wayar Ma'aruf ɗin ta dauke lokacin da Faruk da wani Josh ke ta kira babu kakkautawa, sai da ya roƙe ta da Allah ya gaya mata cewar wani suke nema da yayi musu satar wasu tarin kudi masu yawa a kwanciyar nan da yayi na kwana biyu kawai sannan zancen ya dake ta da wani irin yanayi ta bashi wayoyin.
Ya fita zuwa barandar waje duk da suna jin dukkan abinda yake cewa, kuma ko kafin ya dawo Hamida tasa ta canja mata daga tashar CNN din da yake kallo zuwa Disney Junior dinta, ita kuma ta kwashe kayan nan zuwa kitchen ta shiga karasa wanke wankenta da bata gama ba.
A lokacin Ma'aruf ya shigo cikin kitchen din, ya karaso har inda take sannan ya rungumeta ta a hankali cikin hannayensa.
"Hey Angel."
Ya faÉ—a a cikin wuyanta, a lokaci guda numfashinta ya katse a kirjinta kafin tayi kokarin saita kanta zuwa tambayar dake bakinta.
"Me yasa zaka fita yau weekend?"
Tayi tambayar don taji sanda yake gayawa Faruk cewa gashi nan zuwa. Taji yayi murmushi a cikin wuyan nata kafin ya lalubi daidai kunnenta yace a hankali.
"Saboda babu yadda zanyi Doll, dole ne muyi abin nan da gaggawa mu samo mutumin nan, babu wanda ya san abinda ya faru a kamfanin har yanzu, ni da Faruk da kuna Josh ne kawai, sai wadanxan mutanen daya kamfanin. Kuma bana son ayi dadewar da dole zancen zai fita balle har Baffa ya sani... Idan hakan ta faru rayuwata zata sake taɓuwa ne na sani."
Tana jin yadda jikinta ke yi kamar ya kama da wuta, sannan tana jin murmushin da yake yi a jikinta alamun yana jin dadin rikita tan da yake yi, kuma kafin daya daga cikinsu ya sake cewa wani abu, sallamar Samirah da kuma Munaya daga falo ta shiga kunnensu.
Ba shiri tayi kokarin matsawa amma yaki sakinta.
"Su Samira ne suka zo..."
Ya gyada kansa.
"Naji su, me za'ayi?"
Ya tambaya da gaske, hannusa daya na kokarin kwance dankwalin kanta, babu shiri tasa nata hannun duka biyu ta damƙe shi sannan ta juyo tana kallonsa.
"You are busy ka manta kace fita zaka yi yanzu, suma kuma yanzu zasu shigo nema na har nan."
Ya girgiza kansa yana ƙara jawo ta jikinsa.
"Na fasa, I want this busy yanzu more than anything."
Ya fadi hakan idanunta na kan kofa don daga yadda take jin Samirah na kiran sunanta ta san yanzu zata shigo, sai kawai taji ya shiga kissing gefen kumatun ta yana jawo hankalinta daga kofar zuwa kansa.
"Dan Allah ka tafi kar su shigo." Muryar ta ta fito kamar zata yi kuka.
Ya janye fuskarsa baya sannan murmushi mai kama da dariya kafin yace.
"Yanzu kike shirin roko na kar in fita yanzu kuma kina korata saboda waÉ—annan yaran, wai laifi muke yi ne ko me?"
Girgiza kai kawai take tana kallonsa cike da roko, kuma kafin ta iya cewa wani abun muryar Samirah ta doso kitchen din tana fadin.
"Matar gidan tana nan ne..."
Ai bata san lokacin da tasa dukkan karfinta ba ta fita daga hannun Ma'aruf ta dawo gaba ta tsaya da sauri tana kokarin daukan wasu kwalayen sugan data juye a jar ta bar kwalayen anan kan worktable din dake tsakiya, kuma kafin Samiran ta shigo tana jin sanda ya juyo shima ya sake tsayawa a daidai bayanta sannan kafin tayi tunanin komai ya sunkuyo daidai gefen kunnenta yace.
"Kina nufin in zuge miki zip din rigar? Dama wancan karon da na taya ki din nan kamar ba daidai muka yi ba ko?...."
Bakinta ya faɗi har ƙasa yayin da numfashinta ya dauke a lokaci guda, sai kawsi ya kyalkyale da wata dariya a hankali sannan yayi gaba ya wuce ta zuwa hanyar kofa, kuma sai da yaje daidai kofar sannan ya juyo yace.
"Na tafi inda kika kore ni, kiji dasu, amma akwai lokacin da bakin ki ma bai isa yayi magana ba."
Yana fadin haka ya kifta mata idonsa daya yana murmushi sannan ya fita daidai lokacin da taji Samirah bna cewa.
"Ashe kaima kana nan Yaya..."
Sai kawai ta saki wani numfashi a hankali sannan bakinta ya tale da murmurshin da ta kasa tsaida shi.
***
*Karfe goma sha É—aya.*
Ƙarar ƙwankwasa kofar ta karaɗe gidan gabadaya, Amina ta taho da sauri daga cikin daki inda ta bar Hamidah na ƙoƙarin taje girarta a gaban mudubi, yarinyar na son kwalliya da alama, don ko ɗazu da ta raka ta toilet tayi fitsari tana kallonta lokacin da take gyara hularta a jikin mudubin jikin sink.
Allah ya sani a yanzu tana jin son yarinyar nan yana ƙaruwa a cikin ranta, kwana biyu kawai amma duk sanda ta kalle ta da waɗannan idanun nata irin na Ma'aruf sak, sai taji wani abu na yawo a cikin ƙirjinta, don ita kanta yarinyar ta ƙara sakewa da ita sosai.
Tafiyarta a hankali saboda yadda take jin jikinta ta karaso bakin ƙofar, kuma haka kurum sai taji gabanta ya faɗi, taji farin cikin da ta tashi dashi a yau na yayewa, taji zuciyarta tayi fayau yayin da jikinta yayi shafal a lokaci guda kamar fallen takarda.
Sai kawai ta karanto hasbunallahu wa ni'imal wakil sau uku sannan ta bude kofar daidai lokacin da aka ƙara kwankwansawa.
Kuma a lokaci guda idanunta ya shiga na cikin Hajiya Kilishi dake tsaye a wajen.
***
"Me tace?"
Muryar Amma ta tambaya a cikin wayar da Amina ke yi awanni biyu bayan hakan. A hankali taji wani abu na zarcew cikin maƙogwaronta yayin da idonta ke kallon Hamida da tayi bacci a cinyarta.
Kalba take yi mata a cikin gashinta mai tsananin laushi amma kuma babu yawa, laushinsa ne kawai irin na Ma'aruf amma bai yo yawan nasa ba, saura guda daya su gama don haka ta daÉ—e da yin baccin don tun a farko tayi abinta.
"Me ya kawo ta Amina?"
Amman ta sake tambaya jin tayi shiru, tun dazu suke wayar, tun dazu Amman ta kira take shaida mata cewa ashe a airplane su Hafsa suka sa mata wayar tun jiya shi yasa bata same ta ba, kuma bayan ta kashe ta sake kira ne ta shiga zayyano en mata zuwan Hamida da kuma layar da ta gani a cikin kayanta.
"Kinyi daidai wajen ƙona layar,don nsyi imanin idan har ba da sunanki aka yi ba to da nasa ne, don da alama asirin kusa ne,sai yana tare da mai shi sannan zai ci, suna da tasu manufar tabbas, amma nafi danganta hakan da cewar kome take son taui ita mahaifiyar yarinyar, shi yasa suke son su jawo hankalinsa kanta ko kuma ke su kore ki, amma bamu da tabbas, don haka ki dage da addu'a, ki kuma cigaba da kiyaye dukkan wani abu a gidan.
Zasu zo, ni na tabbata zasu zo miki don asirin bai fara ci ba tukunna, ki zuba ido kawai ki saurari zuwansu, wannan matsalar mai sauki ce don nasu tunanin bashi da fadi don haka a lokaci kankani zaki gama dasu.
Amma yarinyar, ki cigaba da rike ta da wannan kulawar da na sanki da ita Amina, Kilishi ba zata kawo miki ita a banza ba amma tunda bata ce komai ba mu saurare ta tukunna, wanda kafin nan ki cigaba da rike ta da zuciya daya don wannan ba karamar kofa bace da zaki ƙara bude wata darajar taki a zuciyarsa, kar ki manta kullum ina gaya miki takamar kowacce mace a duniyar nan zuciyar mijinta ce, samun nasararki akan Kilishi dama duk wani abu da zai biyo baya ba zai kai darajar kyautata rayuwar aurenki ba."
Da wannan suka kammala zancen Hamida da kuma batun layar nan, sannan Amman ta shiga bata labarin cewa Hajiya Kilishi ta turo da wasu mutane an dauki Baba da Aminu zuwa wajen da za'a fara musu fafutukar visa don kaishi asibiti a india kamar yadda ta shaida musu.
"Suna nan suna ta yabonta Amina, Babanku da ƴanuwansa har ma dasu Asma'u (ƙannenta) kowa yana ta sambarka, basu san cewar umarninki bane Amina, don wannan bashi da maraba da cewar umarnin hakan kika bata, umarnin da ita kanta bata sani ba."
"Tazo É—azu Amma."
Kai tsaye bakinta ya fadi hakan, don a wannan lokacin ta kasa daurewa tarin hargitsin da kuma ruÉ—anin dake cikin kanta.
"Me tace?"
Sune kalmomi biyu da Amman ta furta wanda taji su a cikin ranta kamar baron da aka cika da ƙasa mai nauyi yake rike a hannunta kuma tana shirin hawa tudu dashi, don bata san ma ta inda zata fara ba, bata san ta inda zata fara dauko zancen ba, amma shirun wayar dake tafiya yana shaida mata jiran sauraren da Amma ke yi tasa ta hadiye abinda ke bakinta sannan tace.
"Akan Hamidan ne."
Amma bata ce komai ba har ta ƙara haɗiye wani abun a cikin maƙogwaronta sannan ta cigaba.
"Kamar yadda kika fada tace bata kawo min ita a banza ba, bata tsallake kowa tace ni zan rike ta ba sai don tana da dalili, dalilinta kuma shine bata bukatar yarinyar ta zauna a cikakkiyar mutum, ta gaya min da farko tayi niyyar a kawar da ita ma gabadaya, amma kuma sai taga cewa gwara ta bar Ma'aruf da wani abu ko guda daya ne a rayuwarsa bayan ta tafi.
Bata gaya min inda zata je ba, amma tace daga ni har ita mun kusa barin rayuwar Ma'aruf don ta kusa kammala burin da ta shigo dashi gidan, burin da yasa tayi fafutukar auren Baffa tun a shekarun baya, don haka tace min ko bayan bata nan bata son ya zama akwai wani abu mafi soyuwa a rayuwar Ma'aruf sama da ita.
Tafi son ya zama zuciyarsa na tunawa da ita da matsayin da yafi na kowa a wajensa, don ta gaya min cewar tafiyar da zata yi ma zata tafi ne ba tare da sirrinta É—aya ya fita ba, zata tafi ne ta barsu suna begenta har karshen rayuwarta don hakan shine babban burinta kuma ta riga ta tsara yadda zai kasance tuntuni, kawai tana jiran kammala cike abinda ke gabanta ne.
Don haka ta gaya min cewa tana so ta makantar da Hamida ne ta kuma gurgunta ta ta yadda ba Ma'aruf kadai ba, babu wani mahaluki da zai kalle ta da daraja a duniyar nan kuma zata yi haka ne ta hanyata, ta gaya min da hannu na zanyi hakan Amma."
Muryarta ta kai ƙarshe da tsananin rawar da take fitowa kamar kuka ne ke shirin kwace mata,amma kuma duk da haka sai taji kamar ta ɗauke wani dutse ne daga kirjinta, nauyin maganganun da ta furta na barinta kamar yadda iska ke ɗiban yashi.
Kuma shirun da ya ratsa a cikin wayar, mai tsawo ne, tsawon da ba zata iya tantance shi ba don har sai da Hamida ta motsa a cinyarta ta gyara kwanciyar ta, daga bangaren layin gidan wayar kuwa, ta san bakinsu na ta washewa na ganin adadin cinikin da suke yi dasu, kuma abinda Amman ta furta bayan tsawon wannan lokacin shine.
"Alkawarin me tayi miki wannan karon?"
Ta shaki wata busashshiyar iska a cikin hancinta kafin tace.
"Na'am Amma?" Alamun bata gane ba.
"Alkawarin me tayi miki idan har hakan ya cika?"
Ta gane yanzu, amma bata gane me yasa shine abu na farko da Amman ta tambaya ba, amma duk da haka sai ta hadiye mamakinta sannan muryarta ta fito.
"Tace zata canja muku gida sannan ke da Baba zaku je aikin hajji wannan shekarar."
Sai kawai ta jiyo murmushin Amman kafin tace.
"Ashe ina da rabo a wadanda Allah ya kira zuwa dakinsa wannan shekarar Amina."
"Amma ban gane ba..."
"Kar ki damu zaki gane komai Amina, abinda zan gaya miki a yanzu kawai shine cewa babu abinda zai faru, babu abinda zai sami yarinyar nan, amma kuma a idanun Kilishi komai zai faru, zaki cika mata wannan aikin nata sannan kuma zata kaimu Makkan har da wannan canjin na gida ma!"
"Amma..."
"Kar ki ce komai a yanzu, bar ni kawai da tunani na har zuwa lokacin da zata kawo miki umarnin farko na abinda zaki yi. Yanzu ki gaya min ta tambaye ki wani abu game dashi a yau din?"
Amina ta haÉ—iye tarin kalamai da kuma rudanin da bata san adadinsu ba a cikin kanta sanin cewa tunda Amman ta faÉ—i haka babu wani bayanin da zata kara samu daga Amman a yanzu. Kuma abinda ta fada yanzu ta san shi din da take nufi Ma'aruf be, don bata taba kiran sunansa saboda haka sai kawai ta É—aga kanta kamar tana kallonta sannan tace.
"Eh ta tambaye ni inda ya tafi kasancewar yau asabar."
"Sai kuma me?"
"Na gaya mata cewar suna bincike ne shi da abokin aikinsa game da wani abu da ya faru a kamfanin su."
"Me ya faru?"
"Yace min wani mutumi suke nema da yayi musu satar wasu tarin kudi masu yawa a kwaciyar nan da yayi na kwana biyu kawai."
Murmushin da Amma tayi wannan karon ya amsa sosai a vikin kunnen Amina kafin tace.
"Kin fahimta? Kin fahimci wannan ne aikin da Kilishi tace miki tana son yi a wajen aikinsa wanda tace miki bata bukatarsa a sannan?"
Ta gyada kanta da sauri.
"Na gane Amma nima na fahimta, shi yasa da ta tambaye ni na gaya mata gaskiya din nsji abinda zata ce, amma kuma abinda ta fada din ban gane masa ba."
"Me tace?"
Ta sake maimaita kalma biyun nan na É—azu. Amina ta gyara zaman wayar zuwa É—aya kunnenta kafin tace.
"Dariya kawai tayi, tace wai ai da sun daina wahalar da kansu abinda suke nema yana wajen da ba zai taba fitowa ba, kuma sai da nayi tunanin sannan na gano cewa wajenta take nufi tunda ba zata taba faÉ—a ba."
Amma ta sake yin shiru na wucewar wasu lokutan kafin muryarta ta sake fitowa.
"Me suka samo su game da mutumin?"
"Ban sani ba dai duka amma naji kamar suna waya da wani yana gaya masa cewa an kwatanta musu siffarsa ne kawai"
"Bani minti biyar, ina zuwa Amina."
Abinda ta fada kenan sannan ta kashe wayar ba tare da ta jira komai ba.
Amina ta rike wayar a hannunta, tana sake niya dukkan maganganun nasu kafin a hankali kuma tunaninta ya tsaya kan abu guda daya da bata shaidawa Amman, wannan abun da tun a farko ta boye mata na zancen cewa Kilishi bata yarda da wani zance na samun ciki a wajenta ba, a yau ma ta sake maimaita mata cewar ta cigaba da yin taka tsantsan da zuciyarta akan Ma'aruf, ta kawo ta ne don tayi mata aiki ba don ta zama matarsa ba.
Kalaman da suka kara sata jin wani abu na sauka a zuciyarta yana kara gaya mata cewa wannan yakinta ne, ta ƙyale Amma a ciki ta nunawa Kilishi nata kalar kissar da lulluɓin da bata isa ta yaye ba.
Da wannan tunanin, zuciyarta ta koma wajen jiran da Amman tace tayi, fiye da komai zata so su fara samun mafita kamar yadda tayi alkawari wa rayuwar Ma'aruf, komai ya tsaya cak akanta, hatta hanyenta dake rawa a yanzu sun daina, ta kasa ko sake taba kan Hamida balle ta karasa kalbar dake jiranta, jira kawai take yi yayin da idanunta kallon wucewar lokaci a agogon wayar.
Minti goma bayan hakan wayar ta shiga gurzawa a hannunta da ƙarfin vibration din dake jikinta, kuma ba tare da ta jira komai ba, ta danna wajen amsa kira ta kara ta a kunnenta.
"Amina..."
Muryar Amman ta fito da wani irin yanayi da ta kasa fassara shi.
"Na'am.." ta amsa a hankali tana jin yadda nauyin da take murna da tafiyarsa a ɗazu ya sake dawowa kan ƙirjinta kafin kalaman Amma su fito da tasirin da yasa komai tsaya cak a cikin kanta.
"Idan ya dawo, ki san ta hanyar da zaki gaya masa cewa su nemi mutumin da suke nema har a cikin Prison!"
***
_Na gaya muku Kilishi ta fara ganin ta kanta!_
_Kun fahimci cewa Amma ta mayar da Kilishi ne kamar boyi-boyinsu?..._😅
_Hausawa sunce idan baka iya kama ɓarawo ba, shi barawon sai ya kama ka..._🤣🤣
*Muje zuwa dai, an fara kunno wutar!*
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta. Ko
3/15/22, 15:52 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*09*
~~~~~~
_There was love and then there was your love, and that was entirely different._ _-Unknown._
**
*Shekarar 1997*
"Ga kanun labaran bi da bi....
A jiya laraba ne mai girma shugaban ƙasa General Sani Abacha ya ƙaddamar da taron karɓar sababbin kayan ayyuka na aikin wutar lantarki a yunƙurinsa na samar da ɗorewar wutar lantarki a faɗin Nijeriya bakiɗaya...."
Rediyon dake yashe a tsakar gidan ke fitar da labaran yayin da mace É—aya tal don dake tsajar gidan ke tsugunne daga can gefe tana wanke-wanke. Da misalin karfe goma sha boyu ne na rana, ranar kuwa ta hasja a sama kwal alamun lokacin na rani ne. Daga gefe guda na tsakar gidan akwai wutar itace daje ci bal- bal yayin da tukunya ke tafasa akanta.
"Assalamu alaikum."
Muryar Amma ta wancan lokacin tayi sallama daga bakin kofar tana shigowa, hannunta daya dauke da wata ƴar karamar yarinya mai kama da ita sak! Kuma sautin muryarta da ya fito tare da sallamar, yasa wannan matar juyowa riƙe da kwanon silbar dake hannunta, fuskarta ta haska da tsananin murna da kuma farin cikin ganin nata.
"Maraba lale da Halima, marhaba bikum."
Amon muryar tata ya fito da labarin kan fuskarta yayin da ta mike da sauri tana kara yi mata sannu da zuwa.
"Shigo, shigo Halima, jiyan nan ai muke zance da Sani nace mun kwana biyu bamu ga juna ba zan sami lokaci inje in gano halin da kuke ciki, ashe kya ce ma kuna tafe."
"Wallahi Hajiya iya, muna hanya kam."
Amman ta fada da nata murmushin itama bayan shigarsu dakin.
Hajiya iya ta karbi yarinuar dake hannunta kafin Amman ta zauna kan tabarmar da aka shimfida a saman ledar dakin.
"Anya kuwa ba zan dawo da kishin nan ba, da nace na haƙura muyi zaman salama amma wannan kyan da kike zubawa Aminatu zan yarda kuwa?"
Ta faɗa tana kallon yarinyar data kira Aminar, wadda ke shirin ɓangalewa da dariya kamar ta gane maganar da take mata, sai ta cigaba da cewa.
"Kodayake idanu ne kawai, wannan hancin ba tasowa zaiyi ba."
Amma tana ta dariya har lokacin da itama Hajiya iyan ta nemi waje ta zauna kan wani kushin dake fuskantar tabarmar riƙe da yarinyar.
Hajiya iya ƙanwar mahaifinta ce, dattijuwa ce mai kirki da kuma sanin ya kamata, bata taɓa haihuwa ba, amma akwai wani ɗan mijinta guda ɗaya Sani da ita ta rike shi tun yana yaro, don haka kusan su ƴanuwanta duka sun san shi, tana yawan zuwa dashi wajensu idan har zata je.
Amma a Nigeria ta tashi tare da sauran Æ´anuwanta, amma bayan rasuwar iyayenta ita ta koma Niger yayin da sauran Æ´anuwanta biyu suka zauna a wajen yayarta Zahra'u (Tanti) wadda tayi aure a lokacin. Amma da Allah yayi dole bata da rabon zama a Niger É—in dole aure ya sake dawo da ita Nigeria, kuma aka kawo ta unguwa guda da Hajiya iyan, don haka kusan kodayaushe suna cikin ziyarar juna tunda ita kadai ce Æ´aruwar iyayenta mafi kusa.
"Kuna lafiya Halima?"
Amma ta gyaÉ—a kanta a hankali har yanzu da ragowar murmushin a fuskarta.
"Maigidan naki da nasa Æ´an uwan suma duk kalau?"
Ta sake gyada kanta.
"Lafiya lau Hajiya Iya. Alhmdlilah."
Sai ta gyada kai itama tana sake kallon Aminan dake hannunta.
"Wannan kuma ba sai na tambaye ta ba, daga wannan kumatun nata ma na san kalau take."
Dukkaninsu suka yi wani murmushin yayin da Amina ta bangale da dariya alamun ta fahimci da ita ake. Kuma karar tafasar tukunyar nan daga waje ya katse Hajiya ita daga maganar da zata yi, ta mike da sauri tana fadin bari tazo, Amma ta karbi Amina yayin da ita kuma ta fita.
A wannan lokacin ne kuma tayi bakuwa, wata kawarta ce mai suna Inna Hajara tazo, a tsakar gidan suka gaisa kafin ta dauro alwalarta sannan ta shigo dakin, suka gaisa da Amman dake shayar da Amina dake kokarin bacci sannan ta tayar da sallarta a gefen tabarmar.
Ta shara-sharan labulen Amina na kallon yadda take kai kawo a tsakar gidan har ta kammala tuka tuwon masararta ta kwashe, tana yi tana kiran suyi mata hakuri.
"Yawwa, na san idan nazo na zauna ne, aikin tsayawa zai yi, amma kinga yanzu ai komai ya kammala sai ci kuma."
Ta fada bayan ta dawo dakin rike da kwanukan data zubo musu abincin, ta ajiyewa Amina a gefenta tana zaunawa a inda ta tashi, Amina tayi bacci a jikin Amman lokacin, tayi lamo sai numfashi kawai take fitarwa a hankali yayin da bakuwar tata ta idar da sallarta.
Tana jin yadda hirarsu ta cigaba bsyan sun gyara suna cin abincin wanda tun ba'ayi nisa ba Amma ta gane tsaf akan abinda suke maganar don hira ce da ta riga ta zagaye fadin arewa a wannan lokacin kaf, kasancewar labarin wani abu ne da babu wanda ya taɓa jin makamancinsa, wata mata ce da aka kama da laifin hayar wasu mutane da sula je har gida suka kashe ywar mijinta saboda irin takurwar da matar tayi mata.
Ita kanta taji, kuma ko da ta tambayi mijinta ce mata kawai yayi su bar zancen don baya ko son ambatarsa.
"Ai sai jiya aka koma shari'ar, sai jiya suka sake zama."
Cewar Inna Hajarar tana kai lomar tuwo bakinta kafin ta cigaba.
"Da yake ta kwana biyu a wajen hukumar tana jin matsa shi yasa ba'a je koina ba ta amsa laifinta kuma ta fadi inda ta samo mutanen da ta saka suka yi mata aikin."
Hajiya iya ta dauko salati tun farko har ƙarshe ta dire sannan tace.
"Su kuwa wadannan mara sa imanin daga ina suke."
"Wai a Prison tasa aka samo mata su..."
Amsar Inna Hajaran ta fito daidai lokacin da Amma ke shirin shimfide Amina don ta tashi tayi tata sallar itama.
"... Hajiya Ladi ta gaya min haksma suke yi dama, duk mai son ɓoye aikinsa gidan yari yake zuwa yayi cuku-cukun da za'a bashi wanda zasu yi masa, da sunyi sun koma shikenan babu mai sake ganinsu. A sallami iyayen gudansu suma a siyo musu ƴan kayan buƙata shikenan, aikin ka ya rufo kamar yadda na kwance a kabari yake rufe."
Hajiya iya ta jinjina kanta.
"Ita da tayi rashin sa'a aka kama guda a cikinsu shi yasa komsi ya caɓe mata kenan..."
Maganganun Hajiya iyan, suka zama na ƙarshe da suka taho tun daga wancan lokacin zuwa a yanzu da take tsaye riƙe da wayarta a hannu.
Kwakwalarta ta sake tariyo wannan ranar a cikin kanta tana sake biya kowacce kalma daga bakin Inna Hajara cikin nutsuwar da take jeranta su da kalaman da Amina ta gaya mata a yanzu cewar abinda su Ma'atuf ke nema da sun daina wahalar da kansu abinda suke nema yana wajen da ba zai taba fitowa ba.
So take yi ta haɗa abubuwa guda biyun waje guda sai dai kuma kwakwalarta na ayyano mata tazarar shekarun dake tsakanin zamani biyun da cewar tabbas abubuwa na iya canjawa, amma kuma a lokaci guda sai tunaninta ya cilli kan watarana da yamma lokacin da ta hau adaidaita sahu don zuwa gidan ƴaruwarta Tanti, a cikin adaidaita sahun aka ɗauki wani mutumi da suka shiga hira shi smda ɗan adaidaita sahun kan halin da ƙasa ke ciki a yanzu, kuma ba zata manta ba ya rantse fiye da kirgen da zata iya tunawa cewa fiye da rabi na masifar da ake ciki da sa hannun shuwagabanni.
"... Wai kana ina za'a shiga gidan yari a debo masu laifi duk a basu bindiga É—an kare, to rabin masu garkuwa da mutanen nan da kuma wadannan Æ´an bindigar duk waye ya sansu, wani ya shekara homa a gidan yari za'a dauko shi ya fito yayi wani aikin, da sun ga al'umma sun natsa an fara gano su shikenan sai a maida du inda suka fito, wa ya isa ya gano su a inda ba zasu taba fitowa ba?..."
Kalaman suka kai ƙarshe tare da tabbatarwa da kuma yakinin kowanne abu dake cikin kanta, yaƙinin da take jin sa har ƙasan zuciyarta don haka ba bata sake bata wani lokaci ba hannunta ya sake lalubo nambar Amina a take.
"Idan ya dawo, ki san ta hanyar da zaki gaya masa cewa su nemi mutumin da suke nema har a cikin Prison!"
***
"Ban gane ba, kin ga yarinyar bayan tsawon kwanaki da ɓacewarta, har a gaban alkali an baki ita kuma kice min kin dauke ta kin sake mayar da ita hannunsa? To meye hikimar Rukayya?
Na zata shi kike so, shi kike so ya dawo rayuwarki, kuma Allah ya mallaka miki Æ´ar da ta dalilinta zaki hillace shi ya dawo gareki, amma sai ki É—auke ta ki mika masa ita ke ki koma gefe?
Wane irin tunani ne wannan Rukyy? Wane jahilin ne yace miki..."
"Mahaifiyata ce."
Ksi tsaye Rukayyan ta katse kawarta mai suna Hanan dake wannan zancen ta cikin wayar.
"Kin san ni ba shashasha bace Hanan, tunda kika ga nayi hakan,kin san da dalili,kuma shi ya kamata ki fara tambaya ba ki shiga ƙoƙarin aibata ni ba."
Ba ganinta take yi ba, amma zata rantse Hanan ɗin ta taɓe baki wani abu da yake al'adarta kafin tace.
"Ni ba aibata ki nake yi ba,amma koma meye shirin naku ina tabbatar miki wannan shirme ne,da kin tambaye ni tun farko da ba haka..."
"Ke na tambaya ai tun farko Hanan..." Ta katse ta muryarta na dagawa.
"Ke na tambaya tun kafin in gama iddar auren Ma'aruf, zuciyata tayi nadama tun a sannan, amma ke kika ce kar in bashi hakuri don in koma Hanan, kuma ke na tambaya kika bani shawarar auren Alhaji Ahmad, kuma ke na tambya lokacin da su Maamah suka hada ni da Jawad, ke kika nuna min cewa in biye masa muyi wannan rayuwar zan manta komai, amma na manta din Hanan? Sannan ke na tambaya kika hada ni da Mary Æ´ar aikin Hamida... Hanan ki gaya min a cikin tarin wannan shawarwarin naki wanne ne ya juye zuwa alkhairi? Wanne ne ya juye zuwa alkhairin da har yanzu nake mora?"
"Ban gane ba Rukayya, me kike nufi? Me kike nufi dani?"
Muryarta ta fito ne da harzukin dake keto wayar yana dukan kunnen Rukayya.
"Ina nufin ke ba ƙawar arziki bace Hanan, na fahimci babu wani abu mai kyau da ya taba faruwa dani a tsawon zama na dake."
Kuma daga haka, bata jira komai ba ta katse wayar, ta rike ta a hannunta tana kallon adadin mintinan da suka É—auka a wayar.
Da dukkan maganganun da ta furta a wayar nan ta kwana a ƙirjinta, dasu ta kwana suna yawo a zuciyarta, don a cikin tarin tunanin dake yawo a cikin kanta ta iya nemo wannan kawai ta jera shi daya bayan daya ta fitar da karshensa, kuma abinda bata gama sani ba shine bayan Hanan, mutane nawa ne kuma bata yi sa'ar kasancewa dasu ba a cikin rayuwarta.
Hannunta ya fita daga bangaren kira na wayar tata, ta shiga wajen sakonni, bayan na banki, sunan Jawad ne a kasa, sakon sa na karshe daya tura mata kafin su yi wannan haduwar.
_I madly love you Barbie, me yasa kike hukunta ni? Pick my call please..._
Haka kurum taji a ranta cewa shirunsa a yanzu yana da nasaba da wani abu, Jawad mai naci ne, mai wani irin rufaffen nacin da baya ji kuma baya gani idan har ya dora ransa akan wani abu, ta san wannan ba tun akanta ba, tun akan aikinsa don hakan shine babban abun da yasa cikin ƴan shekaru kadan matsayinsa ya kere kowa a wajen, to ta yaya don kawai tayi masa wannan bayanin zai haƙura komai ya cigaba da tafiya daidai?
Wayarta tayi kara tun kafin tunaninta ya kai karshe, Mahaifiyarta ce Hajiya Nafisa, ta É—auka daga haka tasa a speaker.
"Ki sauko kasa, muna magana ne akan wadda zata je gidan."
Wadda zata je gidan, ba sai Maamahn ta fasa ba, wadda zata je gidan tana nufin gidan Ma'aruf, yarinyar da zata je ta kwance asirin nan, asirin da kamar yadda suka tsara komai a yau ba sai gobe ba aikinsa zai fara, Ma'aruf zai tsani koma wacece yarinyar dake cikin gidan nan a matsayin matarsa, tsanar da a cikin kankanin lokaci zai rabu da ita, don ta riga ta san ko waye Ma'aruf, idan baya son abu baya son sa har cikin ransa kuma babu wanda ya isa a duniyar nan ya canja ra'ayinsa game da hakan hatta Baffa kuwa, shi yasa shi kansa Baffan baya saka baki akan al'amarin wani hukunci da ya yanke.
Sai kawai tayi wani murmushi mai fadi tana hango yadda rayuwa zata maida ita bigiren da ta yarda babu kamarsa duk duniyarta.
Ta yi mu'amala da maza da yawa tun kafin aurenta, amma babu wanda ya kamo kafar Ma'aruf a cikinsu shi yasa ta dage har ta aure shi a sannan, kuma bayan zuciya ta ruÉ—e ta ta fito, har yanzu bata ga wanda ya kama kafarsa a komai ba... Jawad yana ji da kansa wajen iya kulawa da kuna tarairayar mace, amma ta tabbata zai zubar da dukkan makamansa idan da zata hasko masa kwana É—aya kawai a rayuwar aurenta da Ma'aruf kafin abubuwa su canja a tsakaninsu.
Wayarta ta sake ƙara, Maamah ce, sai kawai ta sake wani murmushi mai fadi tasa hannunta duka biyu tana gyara dogon gashinta zuwa baya.
Bata san wane irin zama Ma'aruf ke yi da sabuwar matarsa ba, amma koma wane iri ne, yau zata zama rana ta ƙarshe da hakan zai zo ƙarshe.
***
"Meye wannan?"
Ma'aruf ya faɗa a hankali yana laluben gefen fuskar Amina dake tsaye a gabansa, a jikin wardrobe ɗin dakinta ya same ta, tana kokarin samowa Hamida kayan da zata saka sakamakon bata nan jikinta da tayi da hodar ta fasa gabadaya kuma ta zube a jikinta, duk yadda ta kai ga kwashe kayan kwalliyar nan bai hana ɓata kayan nata da take gudu ba.
Dawowarsa kensn daga cikin gida, don can ya fara shiga baysn ya dawo, bata ssn wajen wa yaje ba amma tana tunanin wajen Baffa ne don yau ma yans gida. ÆŠazu bayan gama wayarta da Amma, Ssmirah tazo sun shiga sun gaishe shi, har da Hamida da taki zuwa wajensa ta makale a hannunta, wani sbu da ya taba zuciyarta a lokscin yayi mata dadin da kuma yabawa kanta na cewar yarinyar ta fara sabawa da ita.
Kuma sai da numfashinta ya katse a yanzu daya zura hannun nasa gefen fuskarta, tana jin yadda yatsun nasa suka ratsa kunnenta, sanyin jikinsu na bi ta kan fatar ta.
"ÆŠan kunne ne, baka sanshi ba?"
Ta fada tana kallon cikin idanunsa hannunta rike da kayan da ta dauko, ya gyada kansa a hankali yana cije lebbensa kafin yace.
"Na sanshi, kawai bana son shi ne."
"Saboda me?"
"Saboda damuna zai dinga yi."
Sai da ta dan tsaya tana kallonsa kafin tace.
"Ta yaya zai dame ka?"
Bai ce komai ba ya fara kokrin zare shi a hankali, ya karkato da fuskarsa dab da tata yana kallon ta yadda zai cire kuma bata ce komai ba ta tsaya kawai jiran taga abinda zai yi, ya cire na bangaren dama, sannan ya karkato da kansa daya gefen ya cire na hagun shima, ya hada su a hannunsa sannan ya kamo nata daya a hankali, na hagun da bata rike kayan dasu ba, ya bude tafin hannun ya dora mata su a ciki.
"Please in dai saboda ni kike sawa ki daina, bana son su, takura min zasu yi 'Cox bayan kafafunki, I like this curve of your body best."
Numfashinta ya tsaya cak a ƙirjinta yaki fita yaki shigactsawon wasu daƙiƙai, dama kafafunta burge shi suke? Inalillahi! Ai bata taba tunani ba, ko lokacin da ta saka wannan yaluwar rigar sai da tayi ta ayyana yadda yake kallonsu a ranta amma bai ce komai ba, sai yau Allah ya budi bakinsa ya fada kenan.
Sai kawai ta rufe idanunta ta bude sannan tace.
"Insha Allah."
"Insha Allah me? Baki karasa ba..."
A hankali tana kallonsa tace.
"Me zan karasa?"
"Sunana..."
"Ma'aruf?"
Ya girgiza kansa.
"Wannan na kowa ne, though I like the way kike fadan 'R' din sunan, amma na fi so ki samo min wani daban, da ke kadai zaki dinga fada."
Ta danyi shiru tana cigaba da kallonsa, kwakwalarta na gaya mata cewa sun bar Hamida a can falo amma wani gefen na gaya mata cewa tunda kallo take yi vabu komai.
"Kamar me toh?"
Innocence din cikin muryarta ya fito tar, yayin da idanunta ke cigaba da kallon sa. Sai kawai yayi dariya yana zura hannunsa cikin gashinsa sannan ya girgiza kansa, kuma maimakon ya bata amsa sai kawai ya juyo da ita, tana fuskantar É—akin, ya tsaya daga bayanta sannan ya sunkuyo da fuskarsa cikin wuyanta, bakinsa daidai kunnenta ya rada a hankali yace.
"Call me the first thing you see..."
(Ki kira ni abu na farko da kika gani.)
Ta cije lebbenta tana murmushi, kuma a hankali idonta ya sauka akan robar sukarin da ta É—auko É—azu tayi amfani dashi a wani kayan gyaran fuska da akace mata sai an hada da sukarin.
"Sugar..."
Muryarta ta fito a hankali, sai yayi wani irin murmushi mai sauti a cikin wuyan nata yace.
"Yes! I know I'm that sweet Sunshine."
Sai kawai ta juya tana nata murmushin itama ta kalle shi, kuma a wannan lokacin ne kwakwalarta ta gaya mata cewa shine damarta na gaya masa sakon da take jin nauyinsa a cikin ƙirjinta.
"Ina so ne in gaya maka wani abu."
Bakinta ya yanke shawarar fadar abinda ke zuciyarta kai tsaye tun kafin kwakwalarta ta canja tunani.
Sai ya gyada kansa yana kokarin rike ta a cikin hannunsa alamun yana saurarenta, ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta a hankali tunaninta na ƙara gaya mata muhimmancin abinda zata fada.
"Ka yarda dani?"
A lokaci guda taga yanayin fuskar sa ya canja, ragowar murmushin na barin kan fuskar tasa, ya zama so serious ɗin da taji zata iya zagin kanta inda har da ba abu mai muhimmanci zata faɗa ba. Ya ƙara gyada kansa sau daya yana kallonta kafin yace.
"With every cell of my body Doll, na yarda dake."
(Da kowanne kowanne abu dake jikina Doll, na yarda dake.)
Kalaman suka bata jwsrin gwiwar da a lokaci guda ta fara magana.
"Dazu da ka fita ina ta tunanin akan maganar da ka fada min, akan maganar wannan mutumin da kuke nema, nace me yasa baza ku duba har wajajen da ba'a tunani ba kamar irin su Prison, saboda wani lokacin mutane suna wasa da hankali ne kawai su yi abinda suka san ba za'a taba zato ba..."
Ta yi shiru, kamar ta kai ƙarshe kamar kuma akwai sauran abinda zata fada. Shima yayi shiru bai ce komai ba, tsawon wucewar wani lokaci yana kallonta kafin muryarsa ta fito.
"All this while ina ta underestimating dinki ne ashe Doll, naga alama abubuwan da kika sani sunfi karfin tunani na, amma insha Allahu lokaci zai bude min su daya bayan daya.
Abinda kika fada yanzu was amazing, kinyi tunanin da ba ni va har su Faruk wani a cikinmu bai taba yi ba. Tabbas ana amfani da prisoners a irin wannan harkar sosai,mun sani amma Allah bai taba sawa munyi tunanin hakan ba, thank you so much da kika tuna min, Allah ya saka miki da alkhairi Amina kuma Insha Allah a yau zan kira Faruk, kuma daga gobe zamu fara binciken nan, muna da details din yadda siffar mutumin take da komai, so in har a gidan yarin yake, ba zai yi mana wahalar kamawa ba insha Allah."
Ta gyada kanta tana jin kamar wani abu zai fashe ne a cikin zuciyarta saboda jin dadin yadda ya fahimce ta a cikin kankanin lokaci yayin da shi kuma ya cigaba da kallonta, kuma kafin tayi wani tunani taji ya sunkuyo da fuskarsa dab da tata sannan a hankali yace.
"I want to borrow a kiss right now Doll, don in nuna miki godiyata, amma nayi alƙawarin zan dawo miki dashi Allah."
Bata san lokacin da ta kyalkyale da dariya ba tana kokarin ture shi, amma sai ya kara rike ta yana fadin.
"Da gaske nake Allah, yanzun nan zan dawo miki dashi, kawai ki ara min."
Da ƙyar ta samu ta fita daga hannunsa, ta koma falon ta barshi anan yana amsa wayar Ishaq, zuciyarta cike fal da daɗin yadda ta isar da saƙon Amma cikin ƙanƙanin lokaci kuma ta samu fahimtarsa, ta gama da wannan babin insha Allah.
Kilishi ta jirayi abinda zai biyo baya, zata sha mamakin yadda asirinta zai tonu alhali ta san bata budewa kowa sirrinta ba, tunda ko ita ta san bata gaya mata ba, kawai sunyi amfani da kalamanta ne akanta. A yanzu saura abu na gaba da take da yakinin zai fi wannan... Abinda Amma tace ce.
_'...babu abinda zai faru, babu abinda zai sami yarinyar nan, amma kuma a idanun Kilishi komai zai faru, zaki cika mata wannan aikin nata sannan kuma zata kaimu Makkan har da wannan canjin na gida ma!_
Allah ya sani zuciyarta a tsaye take wajen jiran faruwar hakan.
"Zoben Sofia za'a fauko a cikin wannan ramin."
Hamida ta faÉ—a tana nuna mata cartoon din da take kallo a cikin Tvn, ta juya ta kalli ramin da take faÉ—a kafin tayi dariya tana gaya mata cewa rijiya ce ba rami ba.
A daidai wannan lokacin ne kuma taji karar buɗewar Gate alamun sunyi baƙi don ta san da daga cikin gida ne ta baya za'a shigo.
Ta gama canjawa Hamida rigar sanda aka kwankwasa kofar É—akin alamun koma waye ya karaso.
Don haka tayi saurin ajiye rigar a saman kujera sannan ta nufi wajen ƙofar, hannunta ya buɗe a hankali daidai lokacin da fuskar matar ta shiga idanunta, tana tsaye da dogon hijabi tayin da fuskarta ke dauke da wani faffadan murmushi, kuma kafin kwakwalarta ta fara tunanin inda ta santa, taji muryar Hamida daga bayanta tace.
"Mariya???"
***
"Mun yi magana da mutanen, sunce hodar zata samu zuwa jibi, mutumin da zai kawo jirgi zai biyo don haka ka shirya gobe zaka tafi lagos, don bana son ta ko kwana a hannunsu, kudin dana kashe akanta da yawa, ba zamu yi sske na dage ba."
Hajiya Kilishi ta faÉ—a a cikin wayar da take yi. Awwalu ya nisa alamun a kwance yake kafin muryarsa ta fito.
"Daga wace ƙasa ma kika ce za'a kawo?"
"Mexico." Ta bashi amsa kai tsaye.
"To wai ta yaya ma za'ayi amfani da ita ne.?"
"Ba kai zaka yi ba, me yasa kake tambaya ta?"
"Saboda na lura tunda kika shigo da yarinyar nan cikin al'amarin nan na fara rage sanin wasu abubuwan. Kuma kina ganin kamar ban cancanci hakan ba."
Sautin muryar tasa ya fito ne da wani irin kauri alamun akwai layin harzuka a ciki. Sai kawai tayi murmushi sannan tace.
"Kar mu fara wannan Awwalu. Ka soke wannan tunanin a cikin ranka, ka kori shaidan daga gefenka. In dai akan wannan hodar ne ka bude kunnenka ka ji.
A cikin kwallin yarinyar za'a saka, a hankali take aiki, ana saka mata yau da gobe zata fara da ciwon ido, ciwon idon ne zai ta ƙaruwa ana kuma cigaba da saka mata a haka har idon ya rufe gabaɗaya ba tare da ko likitoci sun gano dalilin hakan ba."
Ta kai ƙarshe ba tare da yace komai ba, kuma jin shirun nasa yasa ta ƙara da cewar.
"Idan mun gama da wannan sai kuma mu koma kan ƙafarta, na tabbata lokaci zaiyi mana daidai da sanda zan gama da abinda ke gabana, kaga kenan zan tafi ba tare da na bar kowanne dutse a kife ba."
"Haka ne, Allah ya bamu sa'a, zan siya ticket É—in jirgi anjima insha Allah."
Yadda ya fadi hakan a lokaci guda, kai tsaye, kuma yadda kalmar Allah har sau biyu ta fito a bakin Awwalun yasa ta tsayawa da nata shirun kafin a hankali a furta kalmar 'Ameen.' din da bata jin ta kai ƙarshe sanda ya katse wayar.
Wayar ta katse tare da katsewar numfashinta da kuma tsayawar idanunta akan mudubin da taje kallo a gaban ta.
Me Awwalu yake nufi?
Me ke shirin faruwa ne?
Wake shirin girgiza mata tebur ne?
***
_Kun yarda da tunanin Amma? Kun gamsu da yadda ake amfani da zurfin tunani wajen samun mafita?_
_Ina so in dan haska muku wani abu anan, abubuwa da yawa na faruwa a cikin rayuwarmu da zasu wuce ba tare da mun basu wani muhimmanci ba, wani hira ce wani kuma actions ne._
_Amma kuma a cikin abubuwan nan akan samu abubuwan dake ɓullewa zuwa abinda zai zame mana mafita a wasu matsalolin namu na rayuwa. Ba komai zamu dinga mantawa ba, ba komai zamu dinga shashantarwa ba... Komai kankantar abu zai iya zame mana mafita a wani babban al'amarin na rayuwarmu._
_An halicci ƙwaƙwalwa da fadi, don haka bude ta ki zuba tarin abubuwan da baki san lokacin da zasu amfane ki ba._
_And kuna tunanin Amina ta gane wacece Mariya kuma daga ina take?_
_Ku taya ni gayawa Ma'aruf cewa ɗan kunne yana da amfani a adon mace...😅_
_Sannan team Kilishi, me Awwalu yake shirin jawo muku ne?_😅
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:53 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*10*
~~~~~~~
_A love so wasted._ _- Unknown_
**
"What?"
Ma'aruf ya faÉ—a da tsananin mamaki yana kallon fuskarsa a cikin mudubin É—akin dake fuskantarsa.
"Baka ji ni bane ba? Nace maka auren Munaya nazo nema."
Mamaki ya nuna tar akan fuskar sa yana shafa gashinsa ta baya.
"Wallahi da na iya zagi zan É—ura maka wanda zaka kwana kana juyi Ishaq."
Daga cikin wayar Ishaq yaja tsaki sannan yace.
"Ai na gaya mata raini zata jawo min, amma tace in fara tambayarka tukunna, da wallahi sai dai kaji zancen."
Ma'aruf ya girgiza kansa.
"Let's talk serious, me kake nufi wai?"
"Da gaske nake B, ina son kanwarka, zan aure ta, kuma na gaya mata itama ta yarda, da Baba Usman zan gayawa amma wai sai tace in fara gaya maka tukunna, ban san me yasa yaran nan suke girmama ka har haka ba."
Tsabar mamaki bakinsa ya kasa rufuwa, sai kawai ta sake girgiza kansa sannan yace.
"Wallahi ban san baka da kunya ba sai yanzu Ishaq, ni kake tambaya wai kazo neman auren Munaya Ishaq?"
"Allah ya tsinewa kunya in dai taka zanji Ma'aruf, kai kanka ina ka ganta da za'aji maka? Maimakon ka fara godewa Allah ma kun samu mutumin kirki kama ta sai ka fara aibata ni? Ni dama na san wallahi raini Peaches zata jawo min kawai don tayi insisting ne."
Ma'aruf ya gyaÉ—a kansa.
"Wato Peaches Ishaq, Munayan ce Peaches? Ƴar mutane ce fa..."
Dariyar da Ishaq yayi a cikin wayar, dariya ce da ya dade baiji yayi irinta ba kafin yace.
"Kai ta gidanka ba Æ´ar mutanen bace ba? Malam in zaka shige min gaba muje wajen su Baffa kayi magana."
"Ba zanje ba, baza'a baka ba."
"Nagode Babban Yaya, Allah ya ƙara girma."
Da haka ya kashe wayar, Ma'aruf ya cije lebbensa yana jinjina al'amarin a cikin kansa, yana jin kamar ba gaske ba, wani iri, kamar a labari cewa wai Ishaq ne ke son Munaya, yarinyar gabadaya shekararta nawa? Shekara ta biyu take fa a Jami'a, kuma a ɓangaren karatun da take yi na densistry bai taɓa zaton cewa zaiji wannan al'amarin a kusa ba, Allah kaɗai ya san yadda akayi Ishaq ya hure mata kunne.
Sai kawai ya zura wayarsa a aljihu sannan ya fita daga dakin da niyyar zuwa gobe yaje ya same shi suyi maganar hankali.
Tun daga korido yake jin maganganu alamun ƙaruwar wani a gidan, don haka ya karasa a hankali tafin kafarsa na taka tiles ɗin wajen, ya ƙarasa daidai lokacin da Amina ke kokarin ajiye tiren ruwa da lemo a gaban wata mata yayin da matar ke kallon Hamida tana faɗin ta taho wajenta, ya tsaya daidai inda su baza su ganshi ba amma shi yana gano su.
"Au ba zaki zo ba sauraniyar Mama? Ba tafiya zanyi dake ba, kinga kaya ne nan ma Mammy tace in kawo miki."
Hamida ta matse kafadarta daya tana cigaba da kallonta ba tare da tace komai ba.
"Haba Princess din Daddy, Mama Mariya ce fa... Har labarinta fa kika bani."
Cewar Amina da murmurshi a fuskarta, amma duk da hakan Hamidan ta matse kafadarta.
"Ai shikenan kyale ta, da kanta zata zo,ni kujera ce ai."
Dukkaninsu suka yi dariya kafin Amina ta koma ta sami waje a kujerar da Hamidan ke zaune, suka gaisawa da matar da har a lokacin Ma'aruf bai gane daga ina take ba.
"Ai maman tata ce tace inzo in kawo mata wasu kaya da aka manta ba'a hado dasu ba, har da na wasanta ma."
Ta faɗa tana miƙo wata jaka dake gefenta.
Kuma yana ganin yadda Amina bata karɓi jakar ba, amma fuskarta da murmushi tace.
"Ai kuwa ƙika tana kewar kayan wasan nan, don tunda tazo kallo kawai muke ta sha."
Matar ta sake dariya kafin tace.
"Sai kuma wata mantuwa da akayi, a cikin waccan jakar tata wai akwai wani kayanta data manta shine take son in taho mata dashi yanzu."
Mariyan ta fada har yanzu da murmurshi a fuskarta, murmushin dake tsayawa iya fatar bakinta kawai ba tare da ya ƙarasa ko'ina ba, don a wannan lokacin tana jin muryar Rukayya tana amsawa a cikin kanta da umarnin data bata kafin tahowarta, umarnin da ta bata bayan tasa ta shafe hannunta da wani bakin ruwa.
_"Idan kika gaya mata haka ta dauko miki jakar, zip din farko zaki bude, akwai wata bakar leda a ciki. Kina zaro ta sai ki bude kamar zaki tabbatar da abinda ke ciki, budewar kawai nake so kiyi Mariya, da kin bude shikenan kin gama cika aikin ki, sai ki kulle ta kawai ki dawo, ki dawo min da ita ki karbi kudinki. Cif dubu hamsin babu ragi."_
Tana iya tuna yadda zuciyarta ta cika da murna a lokacin, ta cika da wani irin ɗoki da kuma farin ciki, albashinta dubu ashirin ne kowanne wata idan an cire alkhairin da take samu a gidan, kuma ta kwashe shekara da shekaru tana aikin, don haka idan har ba adashi ta ɗauka ba, ƙarya ne ta tuna ranar data riƙe dubu hamsin a lokaci guda ta kanta.
_"Zip É—in baya zaki bude ledar tana ciki, babu mai ganinta sai ke da kika wanke hannunki da wannan ruwan don haka kar ki tsaya komai, kina budewa zaki ganta .."_
Maganar da Hajiya Nafisa ta sake jaddada mata ta shiga kunnenta. Sai tayi saurin gyada kanta lokacin da Aminan ke miƙewa da niyyar zuwa ɗauko jakar.
"Who's she?"
Ma'aruf ya tambaya lokacin da ƙafafunta suka tsaya a gabansa, fuskarta na nunawa da mamakin ganinsa da tayi a wajen. Sai kawai ta matso dab dashi sannan a hankali tace.
"Daga gidansu Hamida take, saƙo ta kawo."
Tana faÉ—in haka kawai ya girgiza kansa.
"Dan na kawo miki Hamida bance har da Family É—inta ba, babu ruwanki dasu, don me yasa zaki buÉ—e mata kofa?"
Yadda yayi maganar yana ƙoƙarin ɗaga muryarsa yasa tayi saurin dago da hannunta ta rufe bakinsa. idanunta na haskawa da wani abu kamar mamaki, wani abu da yasa shi fahimtar cewa ransa ne ke ƙoƙarin ɓaci, don haka sai kawai ya girgiza kansa yana riƙe hannunta data fora akan bakinsa sannan yace.
"She's leaving." (Tafiya zata yi.)
Tafiya? Saboda me? Ta yaya zai ce yace mata ta tafi? Sai dai kafin tayi magana yace.
"I have my plans against mutanen nan, babu wanda zai sake ganinta for the meantime a cikinsu, don haka kar ki sake buÉ—ewa kowa kofa idan har kin san daga nan suke."
Muryarsa ta fito ne da wani irin kauri da kuma ikon da bata taɓa ji ba yayin da fuskarsa take ɗauke da wani irin yanayin da har yanzu bata san shi ba. Sai ta gyaɗa kanta, amma duk da haka ta daure tace.
"Yanzu zata tafi, amma dan Allah ka bari in É—auko mata sakon tukunna, É—auka kawai zata yi sai ta tafi."
Idan har bai bari ta ɗauko mata jakar nan ta duba taga cewar babu abinda suke nema ba, bata san me zata ƙirga a matsayin nasararta da kuma sakonta da zai isa gare su ba, ya tsaya kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya gyada kansa a hankali yace.
"Ki É—auko ta tafi, I'll be out in two minutes, idan na fito ganta zan mata duk abinda yazo kaina wallahi."
Tana jin haka tayi saurin gyaÉ—a kanta sannan ta saki hannunsa da sauri ta karasa dakin, bata ko tsaya rufe wardrobe din ba ta dauko jakar ta fito, ta samu baya wajen don haka kai tsaye ta karasa cikin falon.
"Ai tace saƙon itama ba nata bane, wai can Adamawa za'a kai, sai da aka zo tafiya dashi ta duba taga yana nan wallahi."
Cewar Matar tana ƙarɓar jakar har yanzu da murmurshi a fuskarta, ta miƙa mata da nata murmushin itama sannan ta zauna a kujerar dake fuskantar ta tana cugaba da murmushin dake nunawa tar a fuskarta.
_...wasa da hankalin mutane yana daya daga cikin abubuwan mafiya daÉ—i a duniyar nan, ina jin dadi duk lokacin da na koma baya na kalli fuskokin mutanen da na É—aure su tamau da hannayena ba tare da sun sani ba._
Wannan na daya daga cikin maganganun da Kilishi tayi mata ranar da ta fara bude mata ko ita wacece, amma ta manta su, basu sake zuwa cikin kanta ko sau É—aya ba sai a yanzu, sai a yanzu da take kalllon fuskar Mariyan dake bayani tana kokarin neman zip din da aka kwatanta mata, da sanda ta gane shi, da sanda ta buÉ—e, da kuma sanda hannunta ya shiga ciki kafin yanayin fuskarta ya canja a lokaci guda jin babu komai.
Sai kawai wani murmushi mai faɗi ya ɓalle daga bakinta, tabbas mata masu wayo dole ne su ji da kansu.
***
"Tunda bank statement dinki za'a bayar, dole za'a haÉ—a da affidavit da kuma I.d card dinki wanda yake dauke da signature."
Muryar Muhd, wani ma'aikaci a wajen da ake harkar shige da fice na visa ya fada cikin wayar dake kare a kunnen Hajiya Kilishi.
Hajiya Kilishi ta nisa sannan tace.
"Babu damuwa Muhd, duk zasu taho dasu, idan nasa kudin da zasu isa a cikin account din shikenan komai zaiyi daidai ko?"
"Eh, amma idan da hali Hajiya ki dan bar wani abu ko da dubu dari ne."
"Shikenan babu matsala, nagode."
Da haka ta katse wayar, tana tashi ta dauko wata jaka da ta fito da ita a gefen wardrobe din dakin, ta koma kan gadon ta zauna sannan ta fito da dukkan takardun ciki, a cikinsu ta dauko wata Æ´ar karamar takarda mai dauke da rubutun nambobi ta kwafi nambobin masu shaida wata account number sannan ta tura iya adadin kudin da ta san zasu isa a komai da komai na tafiyar su Aminu har kuma da dorin da muhd É—in yace.
Ta tura kuma bayan an turo mata da sakon kwasar kudin, bata san sanda tayi murmushi ba ganin yadda wani É—an mitsitain adadi ne kadai ya sauka akan zunzurutun kudin dake cikin wannan account din.
Jiya ta turawa da Æ´anuwanta kudin da take basu a karshen kowanne wata suma, amma duk da haka gani take kamar bata taba kudin ba... Kudin da take da yakinin ko Baffa bashi da adadinsu a yanzu, bama shi ba, kamfaninsu gabadaya da suke takama dashi na Bakorin bata jin adadin da suke dashi ya kai jimlar na accounts dinta gaba daya.
Ita kanta ta sani cewa tayi kokari kokarin da ba kowacce mace irinta ce zata iya shi ba, ganin tsawon shekarun da aka dauka tana cika rantsuwa da kuma burin data daukarwa kanta tun zuwa gidan nan, tun bata da komai sai zuciyarta da tanadinta, gashi har an rufa shekarun da ta tara manya-manyan Æ´aÆ´an da har ta aurar da biyu a ciki.
Wani abu ya ratsa zuciyarta na cewar ƴaƴan da take wa rabin wannan hidimar ma har yanzu basu da masaniyar komai, matsalarta kenan, wajen da take ganin faduwarta kenan... A kokarin binne komai don ta tafi a tsaftatacciyar hanya, bata taɓa nunawa waninsu kalarta ba, har gwara Salma, a kwanakin baya ta kan gaya mata cewa tanadin da take yi musu mai kauri ne, don haka idan har akwai wani abu da zata iya kira da ƙalubalen da take shirin fuskanta, shine na yage su Samirah da zata yi daga wannan gidan da kuma mahaifinsu.
Ta nisa a hankali, tana lissafi a cikin kanta. Komai yana tafiya daidai, ta riga ta gama da dukkan wata harkar kashe kuɗi a shirye-shiryen tafiyar mahaifin Amina da kuma ɗanuwanta Aminu, so take su tafi har su isa can a fara yi masa aikin kafin ta tunkari Amina da hodar da Awwalu zai karɓo mata a lagos, don ta haka ne Aminan zata sami kwarin gwiwar yi mata aikin.
Da taga komai ya fara kuma, zata san ta yadda zata yi ta siya musu gida, wannan zai bawa Aminan ƙwarin gwiwar cigaba da yi mata aikin, sai kuma ta biya musu kudin aikin hajji ta kuma basu adadin kudin da zasu iya buƙata, idan tayi hakan ta tabbata babu makawa Amina zata cigaba da yiwa yarinyar amfani da hodar har lokacin da idanunta zasu rufe gabadaya.
Ta gama wannan tsarin ta ajiye shi a gefe sannan ta jawo na ɓangaren sauran adadin kudin da take son ta lahanta kamfanin Bakori dasu.
Gobe litinin, Ma'aruf zai koma aiki, ta san zai cigaba da bincike akan mutumin nan da ta tabbata yanzu an gaya masa kamanninsa kuma sun fara nemansa, baza su taɓa ganinsa ba kamar yadda har yanzu basu iya gano inda wannan Mr. Okafor yake ba don haka a ajiye hakan a gefe, ta san Ma'aruf, ta san cewar wannan abin ba zai sa ya tsaya da aikinsa ba, zasu cigaba da aiki ne kamar wancan lokacin kuma suna cigaba da binciken su, don haka meye kwangilarsu ta gaba?
Ta jawo wani file ta buda cikinsa, ta dauko takarda ta karanta, sunan wani kamfani mai suna Rotel& Co ta shiga idanunta, sai tayi wani murmushi mai fadi, ta san kamfanin don lokaci bayan lokaci suna yawan yin aiki dasu Baffan, kuma basa wasa da harkar biya ko shi Baffan ya gaya mata.
Lissafinta yayi kwana zuwa wani lokaci na gaba, lokaci mai zuwa, lokacin da har su Ma'aruf zasu gama yi musu aiki azo gabar karbar kudi, idan zata lissafa ba zai fi cikin wata guda mai zuwa ba, don haka me zata yi a wannan lokacin da zai dauke hankalin su kudin su shigo hannunta?
Wace hanya zata bi ta karbi kudin kuma wace hanya zata bi ta fara karkato hankakin Æ´aÆ´anta don ta sami wannan kudin ta san ta kassara kamfanin Bakori kenan har abada, babu ta yadda za'ayi su iya tasowa tunda bata sani ba amma zata iya rantsewa cewa a yanzu da ragowar kudin Ma'aruf zai yi amfani wajen karbar wannan kwangilar, to idan suma suka narke me kuma zasu sake samu suyi wani aikin.
Ta ajiye wannan lissafin a gefe ta shiga lalube a cikin kwakwalarta wajen neman mafita, a lokacin wani tunani ya haska a cikin kanta cewar zata iya samowa kanta hanya guda É—aya da zata cimma wadannan abubuwan guda biyu, hanya daya da zata dauke hankalin kowa kudin nan su shigo hannunta kuma hanya guda da zata sa ko Æ´aÆ´anta baza su ja da ita ba idan lokacin tafiyarsu yayi...
Hanya daya,
Daya kacal!
Jifan tsuntsu biyu da dutse daya...
Hanyar da zata ƙarkare komai kuma zata kawo ƙarshen komai...
Hanya É—aya...
Jigo kuma ginshiƙin komai...
Bango...
Meye Bangonsu?
Meye Bangon da zai jijjiga kowa?
Me zai rikito da komai?
Meye abinda zai taɓa kowa ya ɗauke hankalin kowa?
Meye zai taba har zuciyar Æ´aÆ´anta su yarda cewa basu da wani zabi banda nata?
Idan har za'a je ƙarshe, to dole ne ta tabo komai tun daga tubali.
Meye tubalin?
Meye mafari kuma ginshiƙinsu?
Meye Bangon da kowa ke jingina a jikinsa?
Baffa....!
Tabbas Baffa!
Alhaji Muhammad Mansour Bakori.
Mutuwarsa zata zo daidai da rikicewar kowa a gidan kuma daidai da samun nasararta!
Mutuwa...
Ta ɗan tsaya tana nazari a cikin kanta amma kuma sai wani tunanin nata ya kore wannan nazarin, ta taɓa sonsa ne? Tun da suke tare taba jin wani abu mai kama da son sa koda kuwa ɗan burbushi...
Mutum ɗaya zuciyarta ke so, mutum ɗaya zuciyarta ta taɓa russuna akansa, kuma mutum ɗaya ne ruhinta ya taba kallo da wannan sigar, Ma'aruf...
Amma kuma son nasa yazo mata ne ta haramtacciyar hanya, haramtacciyar hanyar da duk kaifin basira da kuma wayonta bata isa ta mallake shi ba. Da wannan karyayyiyar zuciyar take rayuwa a kodayaushe kuma da ita take ganin yadda wasu saɓanin ita ke samunsa.
Shi yasa take yin duk abinda ta san zata faranta masa kuma zata zauna a zuciyarsa, kuma take kore dukkan wani abu da zai É—ara matsayinta a ransa. Ta yarda da wannan, ta yarda iya shi kaÉ—ai zata samu, ta yarda shi kaÉ—ai ne nata, shi yasa take kare hakan da dukkan iyawarta.
Ba zata taɓa bari wani abu a duniyar nan ya keta ta a cikin zuciyarsa ba... Duk sanda ta tashi tafiya kuma zata barshi ne da ragargajajjiyar zuciya irin tata ta yadda ba zai taɓa samun wata dama da wani abu msi kyau zai sake tasiri a ransa ba.
Zata kashe mahaifinsa,
Zata nakasta Æ´arsa,
Zata kassara jarin kasuwancin da suke taƙama dashi,
Zata raba shi da Aminar da yaga kamar hankalinsa ya fara karkata zuwa kanta.
Idan tayi haka, me ya isa ya sake ratsa cikin zuciyarsa kuma?
Dole ne kowa ya biya bashin rashin samunsa da ba zata yi ba.
Hannunta ya É—auki wani biro a gefe, a saman takardar Rotel&Co ta rubuta talatin ga watan yuli.
30th July.
Wasu abubuwan zasu fara kafin wannan ranar, wasu abubuwan kuma zasu faru ne a wannan ranar.
Abinda Kilishi bata sani ba shine, wani lokacin Bawa da hannunsa yake rubuta lokaci da kuma ƙaddararsa!
***
"Ni ba jahili bane Sadik, na gaya maka nafi shekara goma ina tanadi akan matar nan. Da ni take shirya komai, na san duk irin butulci da kuma cin amanar da take shiryawa makusantan ta, to ni waye da zan yi tunanin cewa zata ware ni?"
Awwalu ya faÉ—a yana kallon abokinsa Sadik, suna zaune ne a tsakiyar falon gidan Awwalun, inda a kodayaushe Sadik É—in ke zuwa suna hira.
"Me kake tarawa? Kana tunanin abubwan da kake tarawa sun isa su tozarta ta a idon mutanen nan, kai da kanka fa kake bani labarin irin yardar dake zuciyarsu game da ita."
Awwalu ya jinjina kansa, ya dauki kwalbar lemon dake gabansa ya kurɓa sannan yace.
"Ina da CDs na recording É—in bayanan da take yi min sun fi guda ashirin Sadik, dukka a cikinsu bayanai ne masu mutukar muhimmanci na abubuwan da tayi, a wayata nake recording sai in bayar a mayar min dasu cikin Cd, sannan ina dasu a duka computers dina ma.
Kuma na dade da sanin cewa sune sanadin arzikina, don ni ba mahaukaci bane da ina kallo zata sami waɗannab maƙudan kuɗaɗen kuma in tsaya kawai ta gutsirar min wani abu a ciki? wane tabbaci ma nake dashi na cewar zata bani ɗin? So hanyarta take gyarawa kawai nima ina gyara tawa."
A lokaci guda Sadik ya É—uro wani zagi yana dariya, sannan ya jinjina kansa yana faÉ—in.
"Sh*gen duniya! To amma baka tsoron idan kayi mata wannan barazanar ta saka a far maka kaima?"
Awwalu ya kalle shi sosai sannan yace.
"A wannan ɓangaren matar nan dakiƙiya ce Sadik, don duk wadanda ka san suna mata aiki ni nake nemo su. Shi yasa nayi mamaki a yanzu da har ta sami wasu a Mexico tayi cinikin hodar nan dasu ba tare da na sani ba, kaga hakan ya nuna min cewar ta fara shirin juya min baya da ta sami wani connection ɗin.
Allah yaso dama zuciyata a tsaye take tun daga lokacin da ta shigo da yarinyar nan cikin wannan al'amarin, don na sani babu ta yadda za'ayi mu'amala mutum uku dole sai biyu sunfi jituwa... Kaga kenan da banyi wa kaina wannan tanadin ba ai na shiga uku."
Sadik ya jinjina kansa kafin yace.
"To me kake so? Fiye da abinda zata baka?"
Wannan karon dariyar ta Awwalu ce, ya ƙyalƙyala ta iya son ransa sannan ya dago ya kalle shi.
"Duka abinda ta tara Sadik, Duka!"
Ya fadi kalmar karshen yana daga murya.
"A irin abinda ta shuka, cin amana da kuma butulcin da tayi, bata cancanci taci kuɗin nan ko ƙwandala ba Sadik, ban ma san me zata yi dasu ba, matar nan ta tsufa sannan ƴaƴanta duka mata ne, ub*n me zata basu da zai fi ta aurar dasu, kawai dai an halicce ta ne da wani irin son zuciyar da ban san ta yaya zan misalta shi ba.
Ni namiji ne, yanzu zan fara rayuwata, aure zanyi in tara iyali, don haka ka gaya min wa yafi cancanta da wadannan kudaden?"
Sadik ya jinjina kansa yana cije lebbensa kafin yace.
"Kaine, kai zaka ci su, kuma nima dole in taya ka mu same su ko ta wace hanya ce, don nima in samu abinda zan samu!"
***
_Inaga a wannan babin mun samu amsar wasu abubuwa da muke nema tun farkon labarin nan._
_Bayan hakan, ban san ma me zan ce ba, ku san min ra'ayinku kawai..!😅_
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:53 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*11*
~~~~~~~
_She will listen to your words, but your actions will say more._ _- Unknown_
**
*Abuja.*
*No. 1146 C west, Maitama.*
A cikin ƙatuwar harabar gidan wadda duk girman wajen ya cika taf da al'umma da koma motaci, baka jin komai sai tarin hayaniya, mata da maza ne fal da lokaci zai dauke ka da yawa wajen ƙirga su ke ta zirga-zirga, kowa sanye da ƙarshen akwatinsa sai ƙyalli kawai kake gani a kowacce kusurwa, musamman ga matan da mafiya kayansu walƙawa kawai suke a cikin fitulun compound ɗin, irin dai kayan da mafi yawan mata ke amfani dasu wajen halartar taron biki na dare, (Dinner).
Taron bikin ƴaƴa biyu mace da namijin da ake gudanarwa a gidan wanda suka kasance ƙannen Jawad din dake tsaye daga barandar ɗakinsa a lokacin yana kallon hayaniyar mutanen dake fita a jerin motocin dake layi, amma duk da haka kamar ba ɗibansu ake yi ba, tunda a cikin tarin ƴanuwansu kaf kowa ya tattaro ya dawo gidan da sunan zama har a gama bikin.
Kananun kaya ne a jikinsa daga wandon har rigar duka farare, kuma gama wayarsa kenan da Haro wanda ke ƙara gaya masa sababbin hanyoyin da ya sake samowa na yadda zasu kama Ma'aruf a hannunsu.
Hannunsa ya koma wajen kira ya sake danna nambar mahaifiyarsa da yake yi a cikin wayar amma har ta sake katsewa ba'a ɗauka ba, karo na shida kenan daga 6uta har ƙannensa biyu babu wanda ya ɗauka, mukullin motarsa da ya bari a ɓangaren nasu yake nema, don shima ba zai zauna ba, nan da minti talatin ya sani kowa ya bar gidan don haka shima yana da inda zai je ba zai zauna ba, dalilin fitowarsa kenan barandar ya tsaya ko zai hango ɗaya daga cikinsu yayi musu magana su kawo masa muƙullin, amma babu alamarsu.
Ya ja tsaki a hankali sannan ya juya ya koma cikin ɗakin, akan gadon ya jefa wayarsa sannan kai tsaye ya nufi kofar dakin, ya fita zuwa koridon dake kaiwa hanyar matatattakala ya sauka zuwa falon ƙasa, a jikin falon daga can ƙarshe akwai wata kofa dake fuskantar babbar kofar da za'a fita zuwa waje, ya buɗe ta ya taka cikin koridon dake bullewa zuwa ɓangaren mahaifiyar tasa, ya buɗe a lokaci guda da hayaniyar wajen ta cika kunnensa.
Allah ya sani ya rasa tunani irin na mahaifiyarsa, a kullum kawai yana É—ora alhakin É—abi'unta da rashin karatun ta ne, don labari ne da kowa ya haddace shi cewa irin fulanin dajin nan ce mahaifin nasa ya auro ta, idan ba haka ba bai ga dalilin da zai sa itama tayi tata gayyar har kuwa da Æ´an kwana ba don ana bikin Æ´aÆ´an kishoyoyinta.
Ya shiga cikin falon inda mutane da yawa suke, suna ta gaishe shi ya amsa sama-sama don kaÉ—an daga cikinsu kawai ya sani wanda sune manyan, wata yayar mahaifiyar tasa ta tsayar dashi suka yi magana akan aikin da take son ya samowa danta a wajen aikinsu kafin ya shige kai tsaye zuwa É—akin mahaifiyar tasa.
"Wallahi kinyi kyau, babu wadda ta isa tayi miki kallon raini a cikinsu, babu wadda zata yada miki maganar cewa ba kya fantamawa kamar su."
Abinda ya fara ji kenan yana fitowa daga bakin wata Aunty Nana kafin hoton mahaifiyar tasa ya shiga idonsa, ta saka wata doguwar riga ta lace da zai rantse da Allah babu wajen da yatsa ɗaya zai zauna ba tare da taɓa tarin dutsunan dake ƙyalli ba, sai walƙawa suke suna haske kota'ina.
Ba shiri ya haÉ—e ransa a take sanda mutanen É—akin ke kiran sunansa da korafin tun safe suke nemansa.
"Naje aiki ne."
Shine amsar da yabi kowanne su dashi bayan gaisuwa.
"Mamah mukullin motata nake nema."
Ta tambaya kai tsaye sanda ya isa gabanta, sai tayi murmushin da ya nemi karya zuciyarsa a lokaci guda, murmushin da yasa ba shiri duk wannan haÉ—e ran nasa yabi iska.
"Haba Babana, yanzu ba zaka ce nayi kyau ba...?"
Yasa yatsansa daya ya shafo kan hancinsa, sannan yace.
"Mamah kinyi kyau... Kinyi kyau sosai."
Sai kuma ya kara da.
"Sai dai na so don ra'ayinki kika yi wannam kwalliyar ba don wani ko kuma wasu ba."
Murmushin da take bai bar fuskarta ba tace.
"Ka kawo min mata ka gani wanda zanyi don kai bashi da iyaka Babana, har sai ka rufe idonka."
Murmushin da bai shirya ba ta sake saka shi kafin ya gyaÉ—a kansa yace.
"Allah ya kaimu, key É—in motar yana wajenki?"
Daidai lokacin da Zainab ta shigo dakin a lokacin, hannunta dauke da wani katon kwando, yana jin yadda sauran Aunties ɗin nasa na ɗakin suka samu damar korafin jiran bikin nasa da suke yi suna faɗin so yake yi su haɗa shi da ƙannensa su Khairat tukunna, amma hankalinsa baya kansu tun sanda ta shigo dakin, hannunta na ɗauke da wani ƙaton kwondo da ta ciko kayan da bai san na menene ba dasu, idonsa ya bita da kallo sanda taje har can ƙarshen ɗakin ta bude wardrobe tana saka kayan.
"Zainab anyi namu wankin?
Wata ta tambaya a cikin mutanen dakin, sai ta É—aga kanta da sauri tana murmushi tace.
"Eh suna cikin dryer ban ƙarasa dasu ba, amma yanzu zan kwaso."
Wata da ya san sunanta Aina'u tace.
"Kafin mu tafi ki kwaso min kayan da kika kai mota É—azu, na fasa barinsu anan."
Bata amsa ba wata tace.
"Zainab an karɓo min saƙon kuwa?"
"Yanzu zan karbo Aunty, ban samu lokaci bane tun dazu."
Sai ta gyaÉ—a kanta tace.
"Babu komai, ai kina kokari ma, tun safe kike tsaye."
Daga inda Hajiya Mardiyya ke ƙoƙarin lalubo mukullin motar Jawad ɗin tace.
"In dai Zainab ce ai ba daga nan ba,bata zama sam."
Duk maganganun da ake yi idanun Jawad na kan yarinyar, yana kallon yadda take saka kayan cikin wardrobe da sauri da kuma yadda hannayenta ke rawa, wani abu ya gifta cikin zuciyarsa da bai san menene ba.
Ta gama saka su tazo wucewa daidai lokacin da Hajiya Mardiyya ke miko masa muƙullin motar, kuma bai ji me take cewa ba kawai ya karɓa sannan yabi bayan ta, suka fita daga ɗakin tare.
Kwandon da ta juye kayan ne a hannunta tana ta ratsawa ta cikin mutanen dake É—akin har waje, hannayensa duka cikin aljihun wandonsa yana bin bayanta har suka fita wajen, tayi kwana zuwa hanyar inda É—akunan kwanan su suke,kuma bai tsaida ita ba har suka fara shiga wajen suka bar hayaniyar mutanen nan a baya sannan ya kira sunanta.
"Zainab."
A lokaci guda ta tsaya cak kafin ta juyo da sauri, idanunta suka zare a lokaci guda da ganinsa, tasirin mamakin ganin nasa ya haska ƙarara a fuskarta kafin ya lura cewa rawar da hannayenta ke yi sun ƙaru. Sai kawai ya taho ya ƙaraso dab da ita ya tsaya. Hasken fitilun wajen ya nuna masa yadda fatar bakinta ta bushe sosai ksmar yadda ya hango.
"Kinci abinci?"
Ya tambaya kai tsaye yana kallon ta, bashi take kallo ba ta sunkuyar da kanta ƙasa kawai, kuma jin tambayar yasa babu shiri ta shiga ɗaga kanta da sauri, ɗaga kan da a cikinsa ya fahimci cewa amsaawa kawai take don ta tsorata amma hakan ba gaskiya bane.
Sai ya ja tsakin da bai shirya masa ba, ƙararsa ta fito ƙarara, sannan yana kallonta ya sake maimaita abinda ya fada.
"Ba wasa nake miki ba, nace kin ci abinci?"
Wucewar sakan daya ,biyu kamar ba zata amsa ba sai kuma ta girgiza kanta a hankali alamun A'a. Ya cije lebbensa yana gyada kai sannan yace.
"Biyo ni."
Ya fada ba tare da ya matsa ba, ta É—ago ta kalle shi sannan ta girgiza kai har yanzu idanunta na nunawa da tsoro.
"Akwai aikin da zanyi da yawa, su Hajiya suna ta jira na, dan Allah ..."
Bata ƙarasa ba saboda tasirin yadda idanunsa ke kallonta, kuma ganin ta dakatar da kanta da kanta yasa shi lumshe idanunsa a hankali sannan ya juya, har a lokacin hannayensa sanye cikin aljihunsa, ya juya ya fara tafiya.
Zainab ta kalli bayansa, yadda ƙaramar rigar ta fito da fadin kafaɗunsa, zuciyarta ta kara nauyi a ƙirjinta, sai kawai ta haɗiye wani abu a makogwaronta sannan ta bi bayan nasa itama.
Ta cikin mutanen nan suka wuce, tana tsayawa nesa dashi kadan duk sanda ya tsaya magana da wasu, kuma kusan sau biyar yana juyowa ya tabbatar idan tana bin nasa har suka ƙarasa ɓangarensa, ya buɗe kofar da mukullin da ya zaro a aljihunsa sannan ya shiga ciki yana barinta a buɗe.
Ta sake yin karfin halin danne zuciyarta kafin ta taka kafafunta ta karasa zuwa ciki, har yanzu tana riƙe da wannan kwandon, hannunta ya saki kofar bayan ta shiga cikiba tare da ta rufe ba, kuma har ta yi taku biyu a ciki taji muryarsa a cikin kanta.
"Koma ki rufe kofar."
Ta juya gefen da taji muryar, wajen kujerun falon dake gefe, yana kwance akan guda É—aya three-sitter dake fuskantar Tv ya mike kafafun sa.
Sai ta juya a hankali ta koma, ta tura kofar a hankali har ta rufe, amma kuma sai ta kasa juyowa, ƙafafunta suka tsaya a wajen, hancinta na shaƙar daddaɗan kamshin air freshener da ta fesa da kanta yayin da hannayenta ke rawa riƙe da wannan kwandon.
"Ki ajiye wannan abin ki shigo ki ci abinci "
Ya faÉ—a ba tare da ya bata damar shawara da zuciyarta ba, sai ta juyo ta sake kallonsa, shima ita yake kallo daga yadda yake kwancen.
"Wallahi akwai abinda zanyi da yawa, suna jirana kuma... kuma Hajiya zata min faɗa, alƙur'an..."
"Me?" Ya katse ta a lokaci guda yana kallonta.
"Me kika ce?"
Ba tare da ta fahimci abinda yake nufi ta sake cewa.
"Alqur'an faÉ—a zata yi min..." Rantsuwa ta sake fitowa daban da yanayin fuskarta, babubta yadda wani zai ce ma ita ta fada. Sai kawai ya girgiza kansa.
"Kar in sake ji kin fadi wannan rantsuwar. Bana so, kar ki sake faÉ—a."
Ta hadiye yawu a makogwaronta sannnan ta gyada kanta a hankali alamun ta ji kuma ta fahimta, shima ya gyada nasa.
"Good, now enter."
Bata ji me ya faÉ—a ba amma dai ta san yana nufin ta shigo ne, sai duk da haka ta kasa motsi daga wajen ta tsaya a tsorace kamar wani zaiyi motsi ta juya da gudu ta koma.
Kusan minti guda taba tsaye a haka kafin muryarsa ta sake ratsa kunnenta.
"Zaki yi dana sanin tsaiwa anan, idan na taso."
Sautin muryar tasa ya fito iri ɗaya dana kwanakin baya, ranar da ya gaya mata cewar idan ta sake ta bayyana wannan sirrin nasa da taji, ba ita zai taɓa ba, mahaifiyarta da ta baro a ƙauye zai sa a lahanta.
Don haka abinda bata gane ba yanzu shine meye manufarsa kuma yanzu akanta?
Wani yawun da bata shirya masa ya wuce a bakinta sanda ta tuno maganar mahaifiyarsa, maganar da tayi sanadin kawo ta cikin wannan ƙullin.
_"Ki saka min ido akansa sosai, shi yasa nake aika ki kuma nake saka ki gyaran ɓangaren sa, duk wani abu da kika gani daban a dakinsa ki kawo min, ko waya yake yi ko kuma yana tare da abokansa ki tsaya ki saurara, dole yana ƙulla wani abu na sani Zainab, don haka idan banji komai daga gare ki ba, matakin da zan ɗauka zai shafi har iyayenki!"_
Allah ya sani a yanzu bata san meye mafitar ta ba, ta san dai kawai ko waye zai fassara halin da take ciki da Gaba kura, baya sayaki.
***
"Ina jinka..."
Tattausar Muryar Ma'aruf ta faɗa a cikin office ɗin, a cikin wayar da yake yi zaune akan teburinsa, hannunsa ɗaya na kan wata ƙatuwar jotter da yake rubutu akai. Daga cikin wayar muryar Yakubu ta cigaba da cewa.
"Na sami former address É—in sa da komai ance anan gidan ya zauna directly da suka taho daga Kano, amma kuma satinsu uku a gidan suka tashi.
Kuma na fahimci kamar wani abun ne yasa suka tashi don ance min cikin dare suka bar unguwar babu wanda ya sani sai mutumin da suke hayar gidan a hannunsa, to shima jiya munyi kusan 3 hours tare ya rantse min da ubangijinsu cewa bai san inda suka tafi ba, sai dai ya san mai taxi É—in da ya É—auke su daga nan unguwar.
To da safen nan munje gidan mutumin amma kuma sai matarsa muka tarar ta, gaya mana cewa wai wasu mutane sun dauke shi haya zai kaisu wani ƙauye a can hanyar Uyo, kuma wai kwana uku zasu yi sannan ya dawo dasu,to da har naui niyyar daukar mai mota naje can sai kuma banga tunda ba dadewa zaiyi ba ai zamu iya jiransa don kwana uku kawai, amma what do you suggest?"
Ma'aruf yayi shiru yana kallon abinda ya rubuta, idanunsa ya haska da nazarin da kwakwalarsa ke yi, sai kawai ya ajiye biron hsnnun nasa sannan ya shafo saman kan hancinsa.
"Kar ka bi shi, ka barshi sai ya dawo din, and idan ya dawo din kayi duk yadda zaka yi ka samu wani bayani daga gare shi, Dan Allah Yakubu ko nawa yake bukata ka bashi kawai ko nawa yace."
"Banda dai ko nawa Ma'aruf, don ina gaya maka mutanen nan idonsu a buÉ—e yake game da harkar kudi."
Ma'aruf ya girgiza kansa.
"Mani da wani choice ne yanzu a harkar nan Yakubu, wani abu ya sake faruwa da idan banyi tackling É—insu gabadaya ba ban san ya zan sami kaina ba, saboda haka I'm willing to give everything, wallahi zan iya bada komai nawa idan har zan samu wani gamsashen bayani daga ko waye, so kar ka ja dashi dan Allah."
"Baka da matsala, zanyi abinda ya dace... Ka tabbata dai kawai zaka biya ni a ƙarshen komai."
"Ka san bani da matsala."
"Na sani, shi yasa ma na yarda zanyi maka aikin."
Da haka ya kashe wayar ba tare da ya sake cewa komai ba.
Ma'aruf ya ajiye wayar shima yana kallon rubutun da yayi a jikin jotter nan, bai san da yaya zai kira wannan bayanin na Yakubu ba, Nasara ko kuma akasin haka? Sai kawai ya koma da baya ya jingina da kujerar sannan ya rufe fuskarsa da duka tafukan hannayensa, fatansa guda É—aya ne... Nan da kwana uku Yakubu ya iya samo wani kwakwkwaran bayani akan inda zasu sami Mr. Okafor.
"And guess what?!" (Ka canki wani abu!)
Faruq ya faɗa da ƙarfi yana banko ƙofar Office ɗin, sautin muryar tasa yasa shi ɗagowa yana kallonsa.
"License daga wajen ƴan sandan ya ƙaraso."
"Ka bari dan Allah." Ya fada yana kokarin tashi tsaye, ya ƙaraso ya miƙo masa takardar hannunsa da nasa murmushin shima.
Ya karɓa a lokaci guda da idonsa ya shiga karanta abinda ke jiki.
"Ishaq ya aiko da nasu license din yau da safe, É—azu nayi printing dinsa, kaga mun hada komai kenan sai kawai mu fara aiki."
"And details din mutumin are ready?"
Ya tambaya bayan idanunsa sun bi dukkan rubutun jikin takardar da kallo har karshe,ya kuma tabbatar da dukkan abinda yake nema. Sai dai maimakon Faruq ya bashi amsar abinda ya tambaya sai kawai ya ja kujerar gabansa ya zauna, sannan yace.
"Naga alama hannunka a sake yake game da harkar nan, na dade ina gaya maka cewa ina son motarka, so yaushe zaka bani muƙullinta?"
Ma'aruf ya girgiza kansa sannan ya koma ya zauna shima kafin yace.
"Zan iya bar maka gate É—in gidana a buÉ—e da kuma mukullinta a jiki, sai kazo da daddare ka É—auka."
"�arawo ka mayar dani kenan...?"
Maimakon ya bashi amsa sai yace.
"Dan Allah ka gaya min Faruq, bani da haƙuri akan wannan harkar ka sani."
Kuma sanin hakan yasa kai tsaye Faruq din ya ajiye zancen komai a gefe yace.
"Nayi convincing wannan mutumin ba RTL, wanda yaga saurayin da ya karbi kudin,wanda dai yayi mana bayanin kamanninsa, na gaya masa mun sami license É—in Æ´ansanda da kuma na kotu, na gaya masa akwai tsaro sosai don haka ya yarda cewa zai bi mu yawon zuwa Prisons din mu nemi mutumin. Kaga babu ruwanmu da ma wani bayanin takarda,ya tabbatar min cewa yana ganinsa zai gane shi."
Murmushin da ya sauka a fuskar Ma'aruf a lokaci guda, irin murmushin da mutum baya shirya masa ne, irin murmushin dake fitowa tun daga ƙasan zuciya a lokacin da farad daya mutum ya tsinci labarin mai daɗin da bai taɓa lissafinsa ba.
A yanzu tabbas ya yarda cewa zai kirga wadannan bayanai guda biyun da ya samu ne a matsayin nasara, don Allah ya sani har a ƙasan zuciyarsa yake jin cewa watakila sun zo gaɓar da zasu taka matakin nasara a tsawon shekarun da suka ɗauka suna gwagwarmayar da bata da iyaka.
***
*Ƙarfe huɗu da rabi na yamma.*
A cikin É—akin Munaya, Amina tana tsaye a gaban mudubin É—akin kare da waya a kunnenta tace.
"Mun shiga cikin gida, ka taho ne?"
Muryarta ta fito a hankali, kuma duk da yaji ta Ma'aruf bai ce komai ba, yana kishingiÉ—e ne kawai ta baya akan arm chair dake cikin office É—in Faruq inda suka gama wani aiki.
"Ka taho?"
Ta sake tambaya a hankali, duk da haka baice komai ba.
"Baka ji ba? Mun shiga cikin gida, na ƙulle gidan kuma."
Ya sake lumshe idanunsa kawai yana jinta, sakan daya, biyu ta wuce sai kawai tace.
"Sugar..."
Ba shiri yayi murmushi a lokaci guda sannan yace.
"Yanzu kike magana Doll, da ban san sa wa kike ba ai."
Ya jiyo ƙarar murmushin ta a hankali daga cikin wayar.
"Shi yasa ka min shiru?"
Sai ya girgiza kamar tana kallonsa.
"Ki sake fada dan Allah, just say it once."
Tayi shiru kamar ba zata fada ba sai kuma tace.
"Sugar-Boofy..."
"Ya salam.."
Ya fada a lokaci guda yana dariya.
"Me gashina ya miki kuma?"
"Ba komai,yana maka kyau."
"Yana min kyau ko yana miki kyau?"
"Duka biyun." Muryarta ta sake fitowa a hankali tana jiyo hayaniyar dake tashi a can falon data baro.
Sai ya gyaÉ—a kansa kafin yace.
"So yanzu ki gaya min, kwana nawa kenan da aka saka sunan?"
"Wanne suna?"
"Wanda kike fada."
Yana jiyo sautin wani murmushin nata kafin tace.
"Biyu, ko?"
Ya gyaÉ—a kansa.
"Yes, biyu... Kenan ranar Asabar zamu yi suna?"
"Suna kuma?" Tambayar ta fito da mamakin dake nunawa a muryarta.
"Yes, idan an saka suna ba ana yanka rago baysn 7 days ba? Nima zan siyo bawa ranar Asabar mu yanka tare, kinga sunan ya tabbata kenan."
Sai kawai tayi dariyar dake fitowa mai dadi sannan tace.
"Baka gaya min ba, ka taho din?"
"You miss me that bad?"
Bata amsa ba yace.
"Shi yasa kika kira ni?"
Ta girgiza kanta.
"So nake in gaya maka muna cikin gida ne."
"Wajen Mami?"
Kai tsaye yayi tambayar da tun É—azu take dakon jiranta, sai ta girgiza kai tana cije lebbenta kafin tace.
"A'a muna wajen Hajiya."
"Baku je wajen Mami ba?"
Ta sake wani murmushin jin daɗin nasarar da take fara samu ta wannan ɓangaren, ɗaya daga cikin manya-manyan takun da ta tsara a yanzu shine zata yi amfani da duk lokutan da Kilishi bata nan wajen kokarinta na haɗa kan al'ummar gidan.
Kamar yadda Amma tace ne, kar ta taba bawa Kilishi damar da zata zarge ta don haka ta sani idan har ta fara yawan zuwa wajen Hajiya Maimuna a gabanta, dole zata iya bata wata damar da zata zarge ta da wani abun, amma idan har bata nan, to wannan ce damarta da zata yi komai ba tare da ta bawa ita kanta Kilishin damar ganin laifinta ba, tunda bata da hujjar da zata kafa a gaban kowa game da hakan.
Shi yasa a yanzu ta taho bangaren Hajiyar kuma ta kira har su Samirah ta hanyar dabarar cewa su koya mata wani cin-cin da suka dade suna bata labarinsa... Sannan tayi iya kokarinta da har Hamida ta saki jikinta da Hajiya Maimuna, a yanzu ma ta baro su ne Hajiya Maimunan na kokarin koya mata su alifun ba'un É—in da tace mata bata san su ba.
Shi yasa ta kira Ma'aruf shima da dabarar da zai sa ya taho nan É—in, don ta tabbata da kyar ne idan yazo gaishe ta tun bayan warkewarsa. Saboda haka kai tsaye ta girgiza kanta sannnan tace.
"Mami bata nan, mun shiga aka ce bata nan, shi yasa muka zo gaishe da Hajiya."
Ya gyaÉ—a kansa kai tsaye alamun gamsuwa da hakan sannan yace.
"Ban taho ba, akwai aikin da zamu karasa da Faruq, ina tunanin sai bayan magriba ma tukunna."
Itama ta gyaÉ—a nata kan.
"Allah ya kaimu, Allah ya baku sa'a. Zamu jira ka anan É—in Insha Allah."
Ya san jam'in da ta saka yana nufin ita da Hamida ne, don haka ksi tsaye yace.
"Ni nace miki ku jira ni anan? I'm badly missing you Doll, ta yaya zaki hukunta ni da idanun Hajiya."
Tayi murmushi mai faÉ—i tana kallon hannunta da yayi buÉ—u-buÉ—u da fulawa kafin tace.
"Ba hukunta ka zanyi ba ladan gaishe da ita zan sa ka samu."
Yayi murmushi a hankali.
"Na sani Allah ya saka da alkhairi, amma da gaske ina missing É—inki, ki tsara sunan waÉ—anda zaki kira tun yanzu, last time Amma kaÉ—ai kika yi ta kira..."
"Inalillahi wainna ilaihir raji'un...."
Shine abinda ya fito daga bakin Amina babu shiri kuma ba tare da ta sani ba tana saka É—aya hannunta ta rufe bakinta don bata san me zata ce ba bayan hakan, Ma'aruf yayi dariya sosai yana rufe idanunsa sannan ya sake cewa.
"Kar ki damu BabyDoll, da mun fara Printing kema zaki fara taya ni wannan hirar."
A lokaci guda yaji É—ib, wayar ta katse.
***
*Ƙarfe shida da rabi na yamma.*
A cikin duhun magaribar, Hajiya Kilishi ta gyara zaman niƙabin fuskarta tana kallon mutumin dake tsaye a gabanta, ta jinjina kanta a hankali sannan tace.
"Recording muryata yake yi?"
Sadik dake tsaye ya gyaÉ—a kansa da murmushi yana kallonta.
"Tabbas, da bakinsa ya gaya min cewa yana da Cd's sun fi guda ashirin da yake nafe muryarki sannan kuma yana dasu a kwamfutocinsa gaba É—aya, sannan ma ya gaya min duk hanyoyin da zai bi yaci galaba akan ki."
Murmushin da ya sauka a fuskar Kilishi a lokaci guda, irin murmushin da mutum baya shirya masa ne, irin murmushin dake fitowa tun daga ƙasan zuciya a lokacin da farad daya mutum ya tsinci labarin mai daɗin da bai taɓa lissafinsa ba. Sai kawai ta gyaɗa kanta a hankali tana cigaba da murmurshin sannan tace.
"Aikin ka yana kyau Sadik! Ka cigaba da bibiyarsa ka cigaba da kasancewa amininsa, ai bamu samu komai ba tukunna!"
***
_Kuyi haƙuri, ku jira faɗuwar Kilishi, ƙaddarar labarin nan tayi alƙawarin wanke muku zukatanku insha Allah. Mu bita dai zuwa talalar da ubangiji ke yiwa ire-irenta a doron ƙasa. Sakayyar mai girma ce insha Allah._
_Wai me Ma'aruf yake nufi da Printing ne?_😅
_kun fara kaunar labarin Zainab da Jawad?_
_Ku gaya min Awwalu ya shiga uku.!_😅🤣
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:55 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*12*
~~~~~~
_ You don't always have to make sense of it all, sometimes you just follow your happiness._ _-Unknown._
***
*Bayan wasu kwanaki.*
"Ayiryiryiryiriiiiiiiiiii.....!"
Wata tsohuwa ta rsngaÉ—a guda a lokaci gyda da jama'ar dake dawowa daga wajen daurin auren suka shigowa gidan, mazs ne fal samari da dattijai suna ta sauka daga motocin dake shigowa suns parking a harabar compound din, kusan kowannensu sanye da fararen kaya sai fara'a suke yi yayin da ksmshin turarensu ke gaurate iskar wajen yana haduwa dana matan dake waje suma cikin kwalliyarsu da kuma wadanda ke fitowa don tarar angwaye biyun dake zagaye fal cikin abokansu.
Kidan algaita da kuma kirari ga angwayen dama guda kawai kake ji a tsayar hayaniyar da wani baya jin wani.
Daga cikin morarsa wadda yayi parking a can gefe bayan ya shigo gidan, Jawad ya tsaida idonsa akan screen din wayarsa yana kallon lambar da har a bayan kwakwalarsa bai taba tunanin ganin kiranta ba.
Barbiee ( Rukayya.)
Missed call daya ne, daga shi babu kari balle kuma sako ya biyo baya, ya cije lebbensa a hankali, mamaki yake na yadda skaui har yanzu nambarta take cikin wayarsa s tunanimsa ya goge tun a ranar da ya baro waken da suka hadu na karshe, amma kuma sai ya tuna cewar yayi saving nambar tata ne fiye da sau biyar a wayar tasa da garafai daban daban.
Don haka kai tsaye tafi zuwa kan nambar, ya danne ta ya goge, sannan ya koma vikin layin contact din nasa, ya nemo dukkan harafan da yayi saving nambar tata ya goge su gabaÉ—aya.
_"... Ka taimaki kanka ka manta dani Jawad.."_
Haka tace, haka ta gaya masa, dune harafan da suka fi kowanne ɗagawa a cikin maganganun da ta fada masa, sune harafa da a kowacce rana zuciyarsa ke maimaita masa su fiye da kirgensa, kuma tun daga wannan lokacin zuciyar tasa ke neman abun da zai sa ta manta da ita din, kuma Allah ya sani ya gwada tarin abubuwan da bai san iyakarsu ba tun daga wancan lokacin a ciki har da ƙudirinsu shi da Haro na shirin daukar fansa akan Ma'aruf, amma duk cikin tarin abubuwan nan, babu wanda yake jin yana tafiya har cikin zuciyar tasa kamar yarinyar nan.
Tsanar da yayi mata mai yawa ce a kwanakin baya, amma yanzu baya jin hakan ko kadan, wani abu yake ji da bai ma gama lissafa shi ba, abinda ya sani kawai shine, duk sanda zai gan tan zai ji kawai yana son ta cigaba da kasancewa a wajen, shi kadai ya san yadda abinda ke zuciyarsa ya dinga bin iska shekaranjiya daya tsare ta taci abincin nan a ɓangaren sa, kuma bai san me yazo kansa ba sanda ya riƙe hannunta ya maida ita baya lokacin da take kokarin fita shi kuma ya hango wani ɗanuwansu Ahmad da yazo zai shigo ɓangaren nasa.
Ba abinda zai faru don ya ganshi da ita, ba abinda ya isa yace, amma haka kurum yayi saurin kamo hannunta ya dawo da ita ciki, kuma itama hango shin da tayi yasa bayan ya dawo da ita, ta shige bayan ƙofar ta tsaya jikinta na rawa.
Kuma bayan ya sallami Ahmad din ma da kyar ta fito, ta tsorata sosai bai san me yasa ba, watakila shi yasa tun wannan lokacin bata kara bari sun haÉ—u ba, tun wancan satin ske bikin amma sau daya ya ganta kawai daga windon dakinsa taba hoye dawani yaro sannan ga wata yarinya kuma a hannunta tana yi mata wasa.
Kwankwasa kofar gilashin motar da akayi ya katse tunaninsa, ya juta yaga wani ƙaninsa ne Mukhtar, sai ya zuge gilashin ƙasa a hankali, tarin hayaniyar wajen ta shiga kunnensa a lokaci guda.
"Nace dan Allah akwai mutanen da zaka É—auka a motarka ne?"
"Zuwa ina?" Ya tambaya da mamaki.
"Wajen reception din, yanzu da angwayen sun fito za'a juya ai."
Sai kawai ya girgiza kansa.
"Bana jin zan je, sai dai in baku motar."
"Thank you so much bro, su Na'im zan dauka dama wallahi na rasa mota."
Da haka ya fito, ya miƙo masa mukullin motar sannan ya nufi cikin gidan, a ƙa'ida bangarensa ya kamata ya tafi ya kwanta don tunda aka fara hayaniyar bikin ya manta yaushe rabon da ya samu wani isasshen bacci ba, amma haka kurum tunaninsa ya gaya masa cewa ya tafi bangaren mahaifiyarsa ya nemi abinci, babu mai kawo masa a cikin wannan hayaniyar, ba tunawa dashi zasu yi ba ya sani.
Ya isa ɓangaren yana fara cin karo da kanmensa mata da kuma tarin kawayendu fal a falo, har yanzu ya kasa lissafin yadda kowa ke dokin wannan bikin, shi mutun daya kawai ya gaiyata wani ɗan office ɗinsu, shima ba gayyatarsa yayi ba akan table dinsa ya ga katin yace masa shima yana da ɗaurin aure a masallacin kuma a ranar don haka zai zo, kuma bai ganshi ba ma.
Ƙawayen su Khairat din suka hada baki wajen sirranta muryoyinsu su suna gaishe shi, ya amsa jai tsaye sannan ya nufi wajen wasu cousins din nada mata dske wajen dining, a cikinsu har da Ibrahim wanda aka yi masa maganar ya nemo nasa aiki, bayan sun gaisa da kowa suka shiga magana da Ibrahim din akan interview din da zai zo yayi, yana fada masa abubuwan da ya kamata ya duba.
Kuma sanda Ibrahim din ke masa wani bayani ne ta fito daga dakin, Zainab... Hannunta dauke da wani ƙaton tray da ta ciko tarin plates da kuma cokula a ciki.
Ta yo hanyar cikin falon alamun fita zata yi, daidai sanda wata mata da bai san wacece ita ba ke cewa.
"Zainab har yanzu kina nan? Kowa ya shirya ke baza ki je ki shirya ba gashi har Æ´an É—aurin aure sun dawo..."
Da murmushinta a fuska tace.
"Maman Nasir yanzu zanje, kwanukan nan na tsaya debowa idan ba haka ba yanzu zan neme su in rasa."
Kwata kwata bata lura dashi a wajen ba, dai da wata Maryam daga bayansu ta kora sunanta.
"A kawo mana alala idan ya gama."
A lokacin ne ta ganshi, idonta ya shiga cikin nasa kuma ya haska da wannan tsoron fiye da wannan lokacin da yabi ta a baya, wannan karon babu mamakin, wani abu ne kamar tsoron kawai shi kadai, irin tsoron da ya gani lokacin da ya riko hannunta da kuma sanda ta tsaya daga bayan ƙofar nan, sai kawai ta ɗauke kanta da sauri tana amsawa Maryam ɗin, kuma ba tare da ta jira komai ba ta nufi hanyar ƙofa da niyyar fita amma kafin ta kai ga fitan ya kira sunanta shima yana tsayar da ƙafafunta a lokaci guda.
Da tazara mai dan yawa tsakanin wajen dining don da yake tsaye da kuma can bakin ƙofar, kuma ba daga murya yayi ba, amma a cikin hayaniyar dakin ta jiyo shi tsaf kuma ta sake juyowa a hankali, sai dai wannan karon bata kalle shi ba, idanunta na kan kwanukan data riƙo ne.
"Ki kai min abinci side dina yanzu."
Ya fadi abinda banda ita, bai shallake tunanin kowa ba.
***
Kusan minti goma kenan yana zaune akan kujerar falonsa yana jira, hayaniyar gidan ta ragu sosai don mazan duk sun tafi wajen reception, sai kiɗan ƙwarya kawai da yake juyowa daga can nesa.
Ƙofar ɗakin ta buɗe a lokaci guda, a hankali tana gaya masa waye tun ma kafin ya ɗago ya kalla.
Kuma bayan tayi sallama bata ce komai ba tayi kwana ta nufi hanyar dining da kayan dake hannunta, shima bai amsa sallamar ba ya mike yabi bayan nata, ko ta san yana binta bata juyo ba sai da taje har gaban teburin ta ajiye tray din hannunta tukunna.
"Why are you avoiding me?"
Kai tsaye ya tambaya yana lura da cewa hannayenta rawa suke tun kafin ma yace komai.
Sai ta juyo da sauri tana ƙara yin baya da ƙafafunta saboda yadda ya tsaya dab da ita, kuma tuna cewar bata fahimci abinda yace din ba yasa shi saurin gyara zancen nasa.
"Me yasa kike guduna?"
Kanta na ƙasa ta shiga girgiza shi.
"Wallahi ban ganka bane tun rannan, aiki nake tayi kullum... Mutanen da yawa."
"Kuma ke baiwar kowa ce da sai kinyi musu duk abinda suke so?"
Kai tsaye ya sake tambaya.
Ta sake girgiza kanta.
"Yawanci É—awainiyar yaransu ce, kuma yaran ne suke ta zuwa waje na."
Ya tuno sanda ya ganta da goyo da kuma wata yarinya a hannu, sai a yanzu tunanin Allah kadai ya san yaransu da take goyawa a rana ya kama shi, ba shiri yaja tsaki mai ƙarfi.
"Kar na sake ganin kin dauki yaron wani daga yanzu."
Bata ce komai ba yace.
"Kin ji ni?"
Muryarsa na ɗagawa kaɗan, sai tayi saurin daga kanta alamun ta gane, har yanzu hannayenta rawa suke, yaji kamar ya kamo su ya rike a cikin nasa, amma kwakwalarsa ta gaya masa cewa bayan ƙara rikita ta da zai yi watakila zata iya yi masa ihu ma idan yayi hakam. Don haka sai kawai ya canja zancen da abinda yake son tambaya.
"Kinyi wanka?"
Tambayar ta tayar da wani dan karamin bom a cikin kan Zainab da yasa ba shiri ta ɗago ta kalle shi tana zare ido, kuma shima ya lura da hakan don hannunsa ɗaya yasa ya sosa ƙeyarsa sannan yace.
"Ina nufin me yasa bakya canja wannan kayan, me yasa kowa yayi kwalliya banda ke?"
Sai tayi kokarin hadiye wani abu a makogwaronta sannan tace.
"Ba komai dama... dama yanzu zanje in shirya."
Tunda bakinta ya furta 'dama' har sau biyu ta san ya fahimci ƙarya take yi, ilai kuwa ba shiri ya hade ransa irin yadda take tsoro sannan yace.
"Zaki gaya min gaskiya ko kuwa?"
Ƙwalla ta taru a idanunta kafin tayi ƙarfin halin fada masa sbinda ke cin ranta tun kwanaki, maganar da ta kasa gayawa kowa tunda bata da wanda zai saurare ta sai shi din da ta san ba zai yarda da karyarta ba.
"Bani da kaya ne."
"Baki da kaya?..." Mamaki ya fito a cikin muryar tasa.
"Last week ina zaune Maamah take gaya min cewa anyi wa kowa a gidan nan kaya set hudu na bikin, ke ba'ayi dake ba?"
Ta girgiza kanta.
"Ni nawa ma guda shida ne Hajiya ta bani."
"Ahaan..."
Ya fada alamun neman ƙarin bayani, tayi shiru kamar ba zata ƙarasa ba sai kuma tace.
"Su Janifa ne suka ƙona nawa..."
"What?"
Yadda muryarsa ta sake ɗagawa yasa ta ƙara rikicewa, ta dago tana kallonsa tana kara yin baya da ƙafafunta kafin tace.
"Wallahi bani nace suyi ba, ina cikin gida na dawo da daddare suka ɗebo su suka ƙona su a gabana, dama duka sauran kayana ma haka duke yi musu guda biyu kawai suka bar min, dan Allah kar ka fadawa Hajiya..."
A lokacin da take fadar hakan ta kai ƙarshe da bangon wajen dining din kuma rawar da hannayenta ke yi ta ƙaru, Jawad ya kasa daure kansa da abinda yake ji na tsoratar tata sai kawai ya ƙarasa gabanta ya riƙo hannun nata, ai kuwa kamar yadda ya zata ta buɗe bakinta zata ƙwallara ihu amma yasa ɗaya hannun nasa ya rufe shi da sauri.
"Shut it, kar ki sake ki min ihu."
Ya faÉ—a hannun nasa rufe da bakinta dayan kuma rike da nata duka biyu, ta shiga daga kanta da sauri alamun ta fahimta kafin ta hadiye shi a cikinta, dukkaninsu suka yi ajiyar zuciya a tare kafin a hankali ya dauke hannunsa daga fuskar tata yana kallon idanunta.
"Su waye su Jennifer? Kuma su nawa ne?"
Muryarsa ta fito ne a hankali saboda yadda yake kusa da ita. Zainab ta haɗiye ƙullutun wani abu da har a lokacin bai gama barin maƙogwaronta ba tana jin hannunsa riƙe da nata da kuma ƙamshin turarensa da ya zagaye ta kafin tace.
"ÆŠakinmu É—aya dasu, suma aiki suke yi. Su uku ne."
"Ya sunansu?"
"Da Janifa, da Uchi da kuma Amaka."
Ya ɗaga kansa a hankali alamun ya fahimta, amma bai matsa ba ya cigaba da tsayawa riƙe da hannunta kawai yana kallon fuskarta, ita ma tana kallonsa da nata idon da yake cike da tsoro da kuma rudani, sakanni suka wuce kafin tayi magiyar dake rubuce a ko'ina na fuskar tata dashi baya gani.
"Dan Allah..."
Ta faÉ—i hakan ba tare da ta san ma me take roko ba, amma ga mamakinta sai magiyar ta fito kamar ta tuna masa da wani abu, kamar ta dawo dashi cikin hayyacinsa, yayi saurin sakin hannayenta sannan yayi baya ya juya, sannan ya koma cikin falon inda ya É—auko wayarsa da ya bari akan kujera.
Tana ganin haka gabanta na dukan uku-uku ta nufi hanyar waje da niyyar fita, amma ya katse ta ba tare da ya ko juyo daga inda yake tsaye ba.
"Ki koma ki zauna kici abinci."
Yana fadin haka ya kara wayar a kunnensa sannan ya juyo yana kallonta daga inda yake a cikin falon.
Magiya da duk wani bayanin da zata yi na banza ne ta sani, don haka sai kawai ta juya hankali ta koma.
"Ki zuba nawa nima."
Ya faɗi abinda ya sake saka ƙafafunta tsayawa, idan tace ta shiga uku, tana ganin kamar tayi wa halin da take ci rashin adalci, don Allah ya sani zuciyarta na dokawa da tsoron rashin sanin manufar mutumin nan akanta ne a kowacce rana tun daga wancan lokacin, idan aka ƙara da taraddadin alkawarin da shi da mahaifiyarsa suka ci alwashin yi mata tare da mahaifiyarta dake can gida cikin wata uƙubar kuma, sai ta tabbatar cewa ko ita kanta ba zata iya kwatanta halin da take ciki ba.
Ta karasa inda ta ajiye kwanukan a hankali lokacin da muryarsa ta ƙara shiga kunnenta.
"Kana wajen reception din ne?"
Daga cikin wayar aka bashi amsar da ya sake cewa.
"Okay, akwai wani aiki da nake son kayi min ne da zarar ka dawo."
Gajeriyar amsar da ba ciki ya bashi yasa shi kai tsaye ya cigaba.
"Akwai wasu da nake son ka kor ñnña daga aikin ku ne... I don't care waye ya kawo su ko kuma wa suke wa aiki kawai ka tabbatar sun bar gidan nan a yau..."
"... Su uku ne, Jennifer, Uchi da kuma something Amaka."
Plate ɗin tangaran ɗin da Zainab ta riƙe a hannunta ne ya fadi har ƙasa tarwatse a wajen!
***
*NO. 38 Ramie Street, Nassarawa GRA, Kano.*
"Ke ma kanki Nafi kin san babu haufi a zancena, da matar da kuka aika taga wannan layar da yanzu wani zancen muke ba wannan ba, amma tunda har an samu akasi..."
"Akasi?"
Rukayya ta faÉ—a tana katse Hajiyar Sudan É—in dake bayani a gabansu, dukkaninsu suna zaune a falon dake saman gidansu ne suna tattauna matsalar bacewar layar nan da Mariya bata gani ba a cikin jakar Hamida, don tun bayan da al'amarin ya faru, sai a yanzu suka sami Hajiyar Sudan suke shaida mata kasancewarta mace mai tarin hidimomi akanta.
Kuma a yanzun da Rukayya ke tunanin zata basu wata kalwakkwarar hujja akan al'amarin, sai kuma taji tana kiran kalmar akasi, wane akasi za'a fara lissafi tun ba'aje koina ba?
"Nayi zaton kince babu wanda zai ga layar sai wanda ya wanke hannunsa da wannan ruwan? To wane akasi za'a samu idan har abinda kika fada gaskiya ne?"
Ta tambaya ranta a ɓace kamar yadda a kwanakin nan ta saba kasancewa a cikinsa. Hajiyar Sudan ta haɗe nata ran itama sannan tace.
"Abinda na fada gaskiya ne,wannan aikin ba'a kanku aka fara yinsa ba, kuma duk wadanda nake bawa, babu wanda ya taɓa yi min ƙorafin ba'a sami daidai ba, to kuwa ai dole akasin daga gare ku yake... Kuma wannan shine karo na ƙarshe da zaki kara ɗaga min murya kin ji ni ko?"
Kafin Rukayyan ta sake cewa wani abu, mahaifiyarta Hajiya Nafisa tayi magana tana ƙoƙarin shiga tsakaninsu.
"Yi hakuri Sadiyavranta ne ya ɓaci na sani, kwana biyu a haka take ne, nima tunda Mariyan ta dawo ai abinda nake ta faɗa kenan, nace duk yadda akayi matsala aka samu wajen sakawar, fatanmu dai shine ace layar ɓata tayi ba, kar ya zama ita yarinyar ce ta gani."
Ta janye idanunta a hankali daga kan Rukayyan da har a lokacin ke kallonta sannan tace.
"Wannan ba matsala bace, ko yarinyar ta gani ko bata gani ba akwai wata hanyar da za'a bi ku sami abinda ake so ba tare da illar wancan ya shafi wannan ba."
"Yauwa Sadiya, na san ai kowacce dama bata faduwa ƙasa banza a wajenki, shi yasa na dage sai kinzo din. Allah na tuba ba don ke ba ai da bamu san hanyar da muke bi ba a yanzu, ki ƙyale wautar Ruƙayya kawai a gefe, na tabbatar miki damuwa da kuma tunani ne kawai suka sa ta yin hakan."
Ta faɗi hakan lokacin da Rukayya ke sunkuyar da kanta cike da takaici, ta kusa kaiwa bango, ta kusa ƙurewa, daga mahaifiyar tata har Hajiyar Sudan ta kusa daina saurararsu, ta kusa fara bin hanyarta, don bata ga inda suke motsi ba a wannan gaɓar... Amma lokacin da Hajiyar Sudan tayi ajiyar zuciya tace.
"Aikin gaske zamu yi mata, Nijar zata shirya mu tafi, akwai wajen da idan muka je ina tabbatar muku babu haufi akan komawarta."
Sai kawai wani murmushi ya suɓuce a bakinta, irin wannan aikin take so tabbas! Wanda za'ayi kamar da gaske ake yi, don ita da gaske take yi, da gaske take har cikin ranta, ba ma ta ƴarta take yi ba, wannan lissafin daga baya ne, fatan ta kawai ta sake mallakar Ma'aruf a karo na biyu kuma ko tawacce hanya!
***
*Karfe tara da rabi ba dare.*
Amina ta sake gyara kwanciyarta akan gefen kafadar Ma'aruf, film din da suke "The life we had" wanda sai a yau Allah yayi zasu sami damar kalla baiyi ko rabi ba, amma Ma'aruf yayi korafi yana kushe shi da tun tana ƙirga shi har ta daina.
Karfe tara da rabi na dare ne a lokacin, Hamida ta gama nata kallon tayi bacci akan kujerar dake gefensu, don yau tasha zirga-zirgar da bata saba ba, Ma'aruf ya kaita makaranta anyi dukkan wani process na registration an gama shi a yau da cewar ranar monday zata fara zuwa, sai murna take yi tun yanzu duk da su Hajiya basu so hakan ba, musamman Inna Danejo da suka shiga wajenta dazu, tana ta korafin cewa islamiyya ya kamata a fara saka ta zuwa wata shekarar tukunna.
Hajiya Maimuna ce kadai bata ce komai ba, amma ko Mami bata so ba sai dai bata hana ba duk da ta fahimci cewar sai da Ma'aruf din yayi shawara da ita tukunna, don tans kara saninsa ne tana kara sanin cewa kusan kashi tamaninn na al'amarim rayuwarsa tare da Mamin yake fara yin shawara.
Yau tunda ya dawo daga office yana tare dasu Baffa akan zancen dawowar Abdurrahim gobe sai wajen takwas ssnnan ya shigo gidan yana gaya mata dalilin dadewar tasa, ta san Abdurrahim dun a lissafin jerin ƴaƴan gidan amma bata san komai akansa ba don basu yi hirar dasu Munaya ba kuma Mami bata taɓa gaya mata komai akansa ba,da alama wani abu bai taba hado hanyarta dashi bane.
Mami, Hajiya Kilishi... Hajiya Kilishin da har yau bata sake ce mata komai ba, ko É—azu da suka shiga wajenta, sun gaisa ne kawai amma bata ce komai akan zancen Hamida ba da take jira ba, ta kula kamar wasu abubuwa sun fara shan gabanta ne ba zancen Hamidan ne a lissafinta ba ko kuma na bincikar waÉ—annan pills din magungunan da tace ta dinga sha, wanda ko a satin da ya wuce ta tambaye ta game da hakan har sau biyu kuma ta tabbatar mata da abinda take son taji cewar tana sha É—in... Jitmra kawai take yi lokacin da amsar da zata bata ta gaske ta fito.
"Doll seriously na gaji da film din nan, I want something else..."
Muryar Ma'aruf ta janyo ta ta daga tunaninta, idanunta akan Tv ba tare da ta É—ago ta kalle shi ba tace.
"Something kamar me?" Muryarta ta fito a hankali cikin duhun dakin da hasken Tvn ne kawai akwai, don Ma'aruf ya kashe sauran fitulun dakin saboda suna damun Hamida a baccinta, tana ta juyawa sai da aka kashe tukunna ta nutsu.
Sai ya juyo bangarenta a hankali sannan yace.
"Kamar..."
Shirun da yayi bai karasa ba yasa ta haƙura da kallon Tvn ta juyo da fuskarta itama tana kallonsa, tazarar dake tsakanin fuskokinsu bata jin ta kai ta inci guda don tana kwance ne a jikinsa sosai, idonsa ya sauka zuwa kan lebbenta a hankali, kuma ganin haka yasa tayi saurin juyowa ta dawo da fuskarta yadda take da farko a saman kafaɗunsa, kumatun ta na shafar saman dogon hancinsa kafin ta juya din.
A lokaci guda kuwa yasa hannunsa É—aya ya dawo da fuskar tata tana fuskantar tata sannan ya É—ora goshinsa akan nata yana kallon idanunta bakinsa É—auke da wani guntun murmushi amma bai ce komai ba, sai ta dago da hannunta na dama ta dora akan gefen fuskar tasa itama, dogwayen yatsunta na shigewa cikin gashin kansa, hakan tasa shi lumshe a hankali idanunsa kafin yace.
"Ishaq ne yake gaya min cewa wai yana son Munaya."
Muryarsa ta fito a hankali yana kallonta, kuma bata san me yasa ba amma wani abu a cikin muryar tasa ya gaya mata cewa itace mutum ta farko da ya fara gayawa hakan, hakan yasa a lokaci guda wani murmurshi ya sauka a fuskarta.
"Da gaske? Wow! Masha Allah. Nayi farin ciki sosai wallahi, this is a good news Allah ya sanya alkhairi."
Ya fadi Amin din a hankali sannan kawai yayi shiru yana kallonta, sai tace.
"Me ya faru? Are you not happy?"
Sai ya girgiza kansa.
"Kawai ban san me nake tunanin bane, gani nake Munaya har yanzu yarinya ce, level two take fa..."
Gira guda É—ayan da Amina ta dage ne yasa shi yin shiru ba tare da ya shirya ba.
"Yarinya? Munayan? Sa'a ta ce fa."
"Da gaske?"
Ya tambaya kamar bai sani ba, sai kawai ta cije lebbenta sannan tace.
"Kuma aka ka gaya masa?"
Yadda take ƙoƙarin hade fuskarta yasa shi sake girgiza kansa.
"At first na gaya masa hakan, amma É—azu a office yazo mun sake magana har mun tsayar cewar zan je in fara samun su Baffa ma in gaya musu."
Ta gyada kanta a hankali.
"Nayi zaton haka kace masa, da nima idan naje gida gobe kaga sai inyi zamana ince maka ni yarinya ce."
Murmushin da yayi mai fadi ne kafin ya saje hade goshinsu waje daya.
"Our story is different, labarinmu daban ne Doll, ni na san yadda zanyi handling É—inki, na san yadda nake sace zuciyarki cikin ruwan sanyi..."
"Da gaske? Ta tamvaya.
"Ta yaya kenan?"
Muryarta ta sake fitowa a hankali tana kallonsa kuma maimakon ya bata amsa sai kawai taji hannunsa a bayanta, kusa da wuyanta sosai, kuma kafin tayi wani tunani ya zura hannunsa cikin wuyanta a hankali sannan ya shiga zana wasu abubuwa a gefen wuyan nata, jikinta ya shiga rawa sannan numfashinta ya fara haɗewa, tayi niyyar sake magana amma ta kasa, sai kawai ta rufe idanunta a hankali gabaɗaya tana saurarensa, har zuwa sanda taji wani abu kamar tashin zuciya da ya sata saurin riƙe hannunsa.
"Saboda me?..."
Muryarsa ta fito cike da ƙorafi ba tare da ya fahimci dalilinta ba.
"Wai meye ban gani bane?"
Tambayar ta saka ta kyalkyala dariya, wata ƴar siriiyar dariya kafin ta ture shi gabadaya ta miƙe, ya bita da kallo daga kwancen da yaje yana cije lebbensa, ta dauki Hamida a hankali sannan tayi hanyar ɗaki tana cigaba da yi masa murmushi, kuma kafin yayi wani motsi sai wayarsa dake gefe tayi ƙara, ya mike zaune ya jawo ta daga kan centre table ɗin dake gabansa.
Nambar Yakubu da ta fito ɓaro-ɓaro akan screen din ta motsa zuciyarsa kafin yayi saurin danna wajen amsa kiran ya kara ta a kunnensa.
"Na sami mutumin, gashi nan a hannu na."
Shine abinda Yakubun ya fada kai tsaye bayan ya dauka.
Hannunsa ya shiga cikin gashin kansa a take kafin muryarsa ta fito fili.
"Ka ganshi Yakubu? Ka ganshi? Mr. Okaforn da gaske?"
Yakubun ya gyada kansa.
"Kwarai gashi nan ma É—aure gabana, dashi da iyalinsa bakidaya... Kuma ya gaya min iya abinda ya sani, labarin mai tsawo ne amma yace sunan mutumin dake saka su aikin Awwalu.!"
Awwalu!
***
_Kuna tunanin Awwalun Kilishi ne??_
_Ku gaya min me ya sha kan Kilishi ne da har yanzu bata bawa Amina hodar nan ba?_
_Ina kuke hango tafiyar Jawad da Zainab? Allah yasa kar in shallake tinaninku!_😅
_Wannan tashin zuciyar na BabyDoll ɗin Sugar...?_�😅
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:55 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*13*
~~~~~~
_"If you want to keep a secret, you must also hide it from yourself." –George Orwell, 1984_
**
Ƙafafunsa suka shigo cikin tangameman falon a hankali, kai tsaye ya shiga wuce tarin wajajen dake cikin falon har zuwa inda ya san zai sami mahaifin nasa, yana bi ta kan tausasan carpet ɗin dake wajen kala-kala har ya karasa wajen a daidai lokacin da idonsa ya shaida masa mutanen dake zaune bayan mahaifin nasa.
Mahaifiyarsa, matar mahaifinsa ta biyu mai suna Yagana, sai kuma shugaban ma'aikatan gidan Joshua, yana kallon yadda kayan Hajiya Yaganan ke ƙyalli tare da na mshaifiyarsa a cikin fitulun wajen kamar masu shirin tafiya fadar shugaban ƙasa.
Ya karasa da sallama sanda mahaifin nasa ya sauke jaridar dake fuskarsa sannan shirun da suka yi dukkaninsu ya tafi tare da amsawar sallamar daga mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa su kaÉ—ai yayin da Hajiya Yaganan ta shiga jefo masa hararar da sau É—aya ya gani ya É—auke kansa.
"Barka da Safiya Abba."
Ya gaishe da mahaifin nasa yana zama kusa da Joshua.
"Yawwa mun tashi lafiya?"
Amon muryar mahaifin nasa ya fito babu yabo kuma babu fallasa.
"Lafiya kalau Alhmdlilah." Ya amsa kafin mahaifin nasa ya sake cewa.
"Ai ban san kana gari ba ma har akayi bikin ƙannenka, sai yau da na tashi da ƙorafin ka da aka kawo min."
Kafin ya amsa muryar Hajiya Yagana ta cika falon da cewar.
"Ƙorafi? Ai ba ƙorafi bane Daddyn su Amal, laifi ne yayi kuma shi kansa ya san da hakan."
Ta kira sunansa tana kebanta shi da Æ´aÆ´an ta saboda Hajiya Mardiyyan dake zaune. Kuma maimakon mahaifin nasu yayi maganar katse shin da tayi a zancensa, sai kawai yace da Jawad É—in.
"Me yasa ka korar mata Æ´an aiki har mutum uku Jawad?"
Jawad ya gyara zamansa yana fuskantar inda zancen ya dosa kafin yace.
"Ni ban san Æ´an aikinta bane, laifi suka yi min nace da Joshua ya kore su, kuma ko a karkashin wa suke aiki a gidan nan haka zan ce."
Alhaji Bashir ya gyaÉ—a kansa alamun ya fahimta.
"Laifin me suka yi?"
Kai tsaye ya sake cewa.
"Wata yarinya suka ƙonawa kayan sawarta gabadaya, sunanta Zainab."
Amsar ta fito da zare idon da Hajiya Mardiyya tayi a lokaci guda tana kallonsa da kuma kallon haushi dana takaicin da Hajiya Yagana ke jifansa dashi.
"Ita wannan yarinyar a ina take da har kake yanke wannan hukuncin saboda ita?"
Kai tsaye ba tare da wata shakka ba Jawad ya sake bada amsa, idanunsa na kallon adon carpet din dake gabansa, yace.
"Anan gidan take, Æ´ar aikin Maamah ce."
Wannan karon ba matan kaÉ—ai ba, hatta Alhaji Bashir din da kuma Joshuan dake zaune a gefensa sai da mamaki ya haska a fuskokinsu.
"Zainab Jawad? Zainab din dake wajena?"
Da alama Hajiya Mardiyyan dake tambaya bata shiryawa hakan ba, sai dai kafin ya bata amsa mahaifin nasa ya kawo tasa tambayar shima.
"Meye tsakaninka da ita kenan?"
Jawad ya girgiza kansa.
"Babu komai, I just like seeing her around me." ( Babu komai, kawai ina jin dadin ganinta a kusa dani ne.)
Ba wai sabon abu bane, duka wanda ke zaune a wajen hatta Joshua daya ɗebi shekaru a gidan, ya san hali irin na Jawad, halin kafiya, jajircewa, naci da kuma rashin boye ra'ayinsa akan abu, halin da tun a baya ya jawo rashin jituwa tsakaninsa da mahaifin nasa don ra'ayinsu ya banbanta sam kan gudanar da harkar mulkin da yake yi wanda ya faro tun daga matakin Chairman. Sannan kuma halinsa wanda ya dace da aikin da yake yi a office wanda ya jawo har ya samu babban muƙami a ƙananun shekaru.
Don haka babu wani ja in ja, Alhaji Bashir din ya sake gyada kansa alamun ya fahimta sannan yace.
"Bayan haka babu wani abu?"
Kalmar wani abun a dunƙule ta fito, ɗauke da tarin ma'anonin da kowa a wajen ya fahimce su, Jawad ya haɗiye wani abu da bai san sunansa ba a maƙogwaronsa, a wannan muhallin amsar sa mai tsafta ce ya sani, amma a wancan ɓoyayyen al'amarin na Ruƙayya, zai iya faɗar amsar da zata sanya kowa sallallami a wajen nan, amsar da zai tozarta mahaifiyarsa ta mafi munin hanyar da ba zata taɓa tsammani ba, wannan shine kadai rauninsa, shine kaɗai rauninsa a duniya ya sani, kuma bai san ma ta yadda zai fuskanci hakan ba.
Wannan karon idanunsa na kan mahaifiyarsa dake kallonsa da tarin wasu abubuwa da ba zai iya fassara su ba yace.
"Babu wani abu Abba, babu komai tsakani na da ita."
Alhaji Bashir ya sake gyaÉ—a kansa kafin yayi magana.
"Daga kai har yayyenka da ƙannenka babu wanda nake takurawa a rayuwarsa kun sani, abu ɗaya ne kawai ba zan taɓa lamunta ba shine hoto mara kyan da har zai iya taɓa siyasa ta, saboda haka ina son labarin nan ya cigaba da kasancewa a yadda ka faɗe shi yanzu Jawad.
Yarinya aiki take yi a gidan nan, kar ka shiga hakkinta, kuma kar ka shiga hakki na da naka na neman wani abu da ya É—ara haka a tsakaninku, ko mai kyau ko kuma akasin sa. Ba zan lamunta ba wallahi!"
Shiru ya ratsa ɗakin sabidya yadda muryar Alhaji Bashir ɗin ta fito cikin ɗagawa da kuma hasala, wani abu da idan har ba a fagen siyasar tasa da yake ji da ita ba, da wuya ne kaga ɓacin ransa irin haka, tsarinsa guda daya ne, yace a cikin iyalansa kowa yana da yanci da kuma damar yin abinda yake so, abu daya ne kawai ba zai taba lamunta ba, idan har al'amarinka zai shafi siyasar sa komai kankantarsa kuwa, balle kuma a yanzu da kujerar tasa ke girgidi kowa ya sani.
Sai dai duk wannan ba shi ya dami Jawad a wannan lokacin ba, ba shine abinda kwakwalarsa ke biyawa ba, kalamansa ne, kalaman mahaifin nasa na ƙarshe masu dauke da ma'anar da ya kasa fahimta balle har ya ajiye su a gefe ya fuskanci ma'anar kallon da mahaifiyarsa ke masa a lokacin.
_... kar ka shiga hakki na da naka na neman wani abu da ya É—ara haka a tsakaninku, komai kyau ko kuma akasin sa..."_
***
Ƙofar falon ta buɗe, ta buɗe a lokacin da Jawad ke magana cikin wayar dake kare a kunnensa, dawowarsa kenan daga ɓangaren mahaifin nasa ya shiga ansa kira daga wani shugabansa na wajen aiki da yake can babban branch dinsu na Lagos. Kuma bai ɗago ya kalli kofar ba don ya riga ya san waye mai shigowar har ta ƙaraso ciki, kamar kodayaushe hannunta ɗauke da tray din kayan abincin da ya zama dolenta wajen kawowa.
"I'll see to it on Monday sir."
Cewar Jawad bayan ya fahimci dukkan abinda mutumin ke faÉ—a ta cikin da wayar.
"Okay, so thank you for your time Mr. Kuliya."
"Thank you too sir."
"You are welcome."
Cewar mutumin kafin wayar tasu tazo ƙarshe, Jawad ya ajiye ta a gefensa sannan ya dago yana kallon Zainab fin dake tsaye daga wajen Dining ɗin bayan ta ajiye kayan abincin, bai sani ba idan kyau tayi ko kuma akasin hakan, kawai dai ta ca'nja, don tana sanye ne da ɗaya daga cikin bunbula-bunbulan dogwayen rigunan da ya bawa wani direba a gidan yaje ya siyo mata jiya, wanda sai bayan ya siyo din sannan yaga wautarsa na bawa namiji ya siyo, don in banda yawo ba abinda take yi a cikin kayan, Khairat zai kira ya bata wani kudin ya san zata siyo wanda zasu yi mata daidai.
"Ina wuni."
Ganin yadda yake kallonta ya sa ta furta gaisuwar da ta san ba amsawa zaiyi ba don bai taɓa ba, amma kuma wannan bai sa ta fasa ba a kullum itama, sai kawai yayi ajiyar zuciya a hankali sannan yace.
"Ga wata jaka nan akan table din dauko ta ki zo."
Ta juya ta kalli jakar daga can gaban inda ta ajiye kwanukan, ta mika hannunta ta dauko ta sannan ta taho, ta karaso cikin falon a hankali har zuwa gabansa.
"Zauna." Ya faɗa kai tsaye bayan ya karɓa, kuma ta riga ta san me yake nufi don haka bata yi wani musu ba ta sami waje a daidai gaban nasa ta zauna.
"Maamah ta ganki kafin ki taho?"
Ya tambaya yana kallonta, sai ta girgiza kanta a hankali.
"A'ah, tun dazu ta tafi ɓangaren Alhaji bata dawo ba."
"Wani ya sake miki wani abu a cikin gidan?"
Ta sake girgiza kanta a hankali tana kallon ƙasa.
Ya cije lebbensa kaɗan sannan ya buɗe jakar ya dauko wani bandeji da kuma wasu kwalabe har da plaster, kuma bai sake cewa komai ba kawai ta ga ya sauko daidai gabanta shima, sannan yasa hannunsa kai tsaye ya janye ƙasan rigarta kadan, kumburarriyar ƙafarta da taji ciwo lokacin da plate din tangaran din nan ya fashe akanta ta fito fili.
"Just stay still." Ya fada a hankali ba tare da ya damu da ta gane ko bata gane ba.
Zuciyar Zainab ta buga a ƙirjinta, mamaki ya riƙe ta a yadda take a zaune, sannan tsoro ya mamaye koina a ƙirjinta, hannayenta suka shiga rawa, amma sai dukkan hakan ya tafi da saukar ruwan wani abu cikin ciwon nata, zafinsa ya ratsa har ƙasan ruhinta ta yadda ba shiri ta runtse idanunta da dukkan karfin da zata iya tana jin yadda yake kokarin bajewa a ko'ina na jikinta amma duk da haka bata motsa daga yadda take ba har ya gama.
Ya ɗaga kafar tata a hankali ya naɗe ta da bandeji bayan ya saka plaster sannan ya tattara sauran kayan ya mayar cikin jakar da ya bari akan kujera sannan ya juyo ya sake kallonta, itama shi take kallo yanzu, manyan idanunta sun buɗe sosai akan fuskarta, kuma yanayin yadda yake zaune yayi kusa da ita sosai amma duk da haka bata yi ƙoƙarin matsawa ba kallonsa kawai take yi da tarin wasu abubuwa fal da bata san ma'anarsu ba a cikin kanta.
"Ni kike yiwa wannan kallon?"
Muryarsa ta fito a hankali shima yana kallonta, kuma muryar ta fito kamar ya daeo da ita cikin hayyacinta don babu shiri ta miƙe a lokaci guda jikinta ya hau rawarsa, sannan tayi hanyar wajen Dining inda ta san aikinta na gaba shine zuba abincinsa.
Sai kawai yayi murmushi a hankali sannan ya miƙe tsaye shima yana nufar inda ya ajiye wayarsa kafin yabi bayanta.
**
A cikin dakin Hajiya Mardiyya tayi wulli da dankwalin kanta akan gadon É—akin yayin da jikinta ke rawa tana rike da wayar hannunta kafin tace.
"Ki taimaka min Aunty Sadiya kizo gidan nan yau, tsoro na Allah tsoro na Annabi sce wannan yarinyar tana da alaƙa dashi."
Daga cikin wayar yayarta mai suna Sadiyar tace.
"Baki da hankali ai Mardi, na daÉ—e ina gaya miki har yanzu baki da wayo balle hangen nesa idan banda haka, me yasa zaki dauki yarinyar nan aiki? Tun farko da kika ji ance daga Garun Albasu take me yasa zaki rike ta har ki sakar mata kamar yadda nazo na tarar kina yi?
Garun Albasu ƙauye ne, mutanen cikinsa ba wani yawa ne dasu ba, idan har ma yarinyar nan ta kasance ƴaruwarsa wani abun mamaki ne?"
Hajiya Mardiyya na faman girgirza kanta tace.
"Ba zai yiwu ba, ba zai taba kasancewa ba, dan Allah Aunty Sadiya kizo mu zauna akan zancen nan...!"
***
*Kano.*
*Bakori Enterprises.*
*10:30am.*
"Ina Faruk É—in yake?"
Yakubu ya tambaya ta cikin screen É—in computer dake gaban Ma'aruf wanda suke video call ta jiki, Ma'aruf ya girgiza kansa kafin yace.
"Baya nan, ya tafi wani aiki ne."
Yakubu ya gyaɗa kansa yana cije leɓe.
"I wish yana nan, da na nuna masa proof na kokwanton da yake yi akan aikina."
Ma'ruf ya gyaÉ—a kansa kusan sau biyar a jere.
"Ya sani Yakubu, ai munyi maganar dashi tun sanda ka kira ni, let's just get straight to the point dan Allah, ina yake?"
"Ka kwantar da hankalin ka yanzu zasu shigo dashi, bana garaje a aikina ka sani,ko so kake yi yazo a sigar da ba zaka sami wata amsa ba?"
Ma'aruf ya haÉ—e tafukan hannayensa biyu akan fuskarsa sannan ya fitar da iska ta bakinsa, kusan awa guda kenan da Yakubun ya kira shi cewa zai haÉ—a shi da Mr. Okaforn ya tambaye shi duk abinda yake so ta wayar video call kafin su yanke hukuncin abinda zasu yi dashi.
Kuma tun a lokacin suke magana da Yakubun ta wayar ba tare da ya ga Mr. Okaforn ba don kamar yadda Yakubun yace ne yana hannun wadanda zasu lallasa shi ta hanyar da ba zaiyi taurin kai ba.
Tunani kawai yake a cikin kansa na yadda zasu sami karin bayanin da zai kai su ga ko waye wannan Awwalun da ya faÉ—a, kuma ko a ina yake, don a yanzu haka har an fitar masa da list din duk wani ma'aikaci dake karkarshin kamfanin nasu mai suna Awwalu, da wadanda suka yi aiki suka bar wajen har da ma wadanda applying kawai suka taba yi ba'a dauke su ba tukunna.
Ance idan rakuminka ya bata ka duba har cikin tulu, a yanzu ya koyi buɗe idanunsa sosai wajen nema, maganar da Amina ta fada masa na cewar su nemi mutumin nan har a cikin prison ta bude tarin wasu abubuwa da yawa a cikin kansa, ta sa shi ya daɗa fahimtar cewa bai kamata yayi limiting nemansa a iya wani waje guda ba, watakila tun farko abinda yasa suke ta zagaye suna dawowa kenan... Da wannan tunanin yake ƙara godewa ubangiji a kodayaushe da ya azurta shi da mace kamar Amina a cikin rayuwarsa.
Ƙofar dake bayan Yakubu a cikin videon ta buɗe a lokacin, wasu mutane biyu suka shigo, dogwayen jikinsu kawai ya gani kafin Yakubun ya juya yaga mutumin da suke rike dashi.
Kuma ba don ya tabbatar da cewar Mr. Okaforn da suke jira ne za'a shigo dashi ba, zai rantse ba shi bane wannsn saboda fuskarsa ta kumbura gabaÉ—aya, idanunsa sun shige a fuskar tasa sannan hancinsa da bakinsa na fitar da jini. A lokaci guda ya shiga girgiza kansa yana kallon Yakubun.
"This is not what I ask of him Yakubu, ( ba abinda nace kuyi masa ba kenan) mutumin nan yana da iyali..."
"Just ask your questions."
( Kawai kayi tambayoyin ka.)
Cewar Yakubun yana katse shi, daidai lokacin da mutanen nan biyu suka ajiye Mr. Okaforn a gaban camerar sannan suka juya suka fita.
Ma'aruf ya haɗiye wani abu a maƙogwaronsa yana girgiza kansa sanda Mr. Okaforn ya shiga magiya yana haɗe hannayensa biyu cikin kuka. Sai kawai yayi karfin halin saita muryarsa sannan ya shiga magana da turanci.
"Komai zai koma daidai idan har ka bamu hadin kai akan dukkan abinda muka tambaye ka, ba zan bari su sake taɓa ka ba, za'a maida kai gida cikin iyalanka lafiya, hatta ƴarka Mary zan yafe mata laifin da tayi min akan ƴata, kuma ba zamu sake tuntubarka bayan nan, zaka cigaba da rayuwarka cikin kwanciyar hankali idan har ka fada min dukkan abinda ka sani Mr. Okafor."
Kuma bai bashi damar da zai tsaiwaita godiyar da ya fara ba yace.
"Ina jinka."
Babu musu balle tirjiya Mr. Okafor ya gyada kansa da sauri alamun zaiyi hakan kafin muryarsa dake cike da kuka ta fara magana cikin nasa yaren na Pidgin English.
"Kamar yadda ka sani Yallabai ni mai shara da goge goge ne a kamfaninka,to watannin baya da suka wuce, sai wani abokin aikina mai suna Sani ya same ni da labarin cewa ya samo mana hanyar da zamu yi kuÉ—i mu daina wannan bautar, ya gaya min cewa akwai wani mutumi mai suna Isa, bayarbe ne amma kuma musulmi, yana harkar computer hacking da duk wani abu da ya shafi harkar technology na yanzu.
Rana É—aya yazo yace min wai wasu mutane sun same shi da rokon cewa zasu bashi miliyan daya idan har ya shiga ofishinka ya samu wasu nambobi a cikin computerka, to shi bai san harkar komai na computer ba shine yazo ya same ni yace zai bani rabin kudin dubu dari biyar idan har na taya shi aikin, ya gaya min sau É—aya cewar sunan mutumin da ya saka su aikin shi da Isa Awwalu amma bayan nan bai kara gaya min komai akansa ba.
Kuma sai a ranar da nake da aikin gyaran ofishin naka ne sannan muka yi waya da daya mutumin mai suna Isa, shi ya kwatanta min inda zan shiga a computer taka in kwafo wasu security numbers wanda sune na account din kamfanin, kuma na sami sa'a har naje na samo nambobin ba'a kama ni ba.
Kuma Sani ya gaya min cewa da wannan nambobin suka yi amfani akayi hacking account number kamfanin har aka turo muku da alert din ƙarya alhali kuɗin sun tafi ne zuwa wani account daban, kuma sunyi haka ne ta hanyar da ko banki baza su gane balle idan kun je ku sami wata gamsashshiyar amsa daga gare su.
Bayan mun gama aikin da sati ɗaya sai shi abokin aikin nawa ya kawo min kuɗi dubu dari kawai yace min wai shima basu bashi yadda suka fada ba, amma idan sun bashin zai ciko min. Daga nan bai ƙara yi min mgna har tsawon lokaci kuma na tuntube shi amma yaki saurarata.
Ni kuma hakan sai nayi kokarin É—aukan matakin da zan tsorata su su bani kudina, shi yasa naje na sami sbokin aikin ka Yallabai Faruk na gaya masa cewa ina da masaniyar abinda ya faru, nayi recording hirar mu a wayata sannan naje na sami abokin aikin nawa Sani da niyyar in nuna masa hakan.
Sai dai ina zuwa gidansa na tarar ya mutu har ana jana'izarsa. Sai na tsorata na dawo gida, bayan kwana biyu sai Isa ya kira ni da cewar inyi hankali watakila wadanda suka kashe Sani suna da alaka da wadanda suka samu aikin nan, a wannan ranar ne kai kuma kazo gidana Yallabai, sai dai bamu samu munyi magana ba ka dauki wannan yarinyar ka tafi.
A washegari kuma na tsinci labarin mutuwar Isa shima, shi yasa ba shiri na haɗa iyalaina muka gudo nan garin ranka ta daɗe, kuma nayi maka rantsuwa da kabarin babana tun daga wancan lokacin ban ƙara jin wani bayani daga kowa ba ranka ya daɗe."
Mr. Okafor ya kai ƙarshe a lokacin da Ma'aruf da kuma Yakubun suka cigaba da kallonsa, kallon da Ma'aruf ke yi masa daban ne, kallonsa yake yana kuma saurarensa da dukkan wani abu mai hankali dake jikinsa, kwakwalarsa na fahimtar kowacce kalma dake taruwa tana fitar da jimla guda a bayanin nasa, kuma bayan ya kai ƙarshe, abu na farko da ya fara yi shine jawo wayarsa. Hannayensa suka lalubo nambar Martha a lokaci guda.
"Ki duba min a kananun ma'aikatan dake aiki akwai wani Sani da ya mutu kwanakin baya?"
"Okay sir." Ta amsa da sauri fahimtar cewa shima saurin yake yi a cikin muryarsa, kuma daga inda yake zaune yana jin karar keyboard din computer ta da take dannawa, cikin abinda bai fi rabin minti ba tace.
"Akwai yallabai, sunansa Sani Madugu, wani danuwansa ne yayi reporting mutuwarsa wata hudu da suka wuce, kuma har an bawa iyalinsa garatutinsa wancan watan."
"Thank you."
Kawai ya faÉ—a sannan ya ajiye wayar, idonsa ya sake dawowa kan Yakubu da kuma Mr. Okaforn dake jiran abinda zai ce ta cikin computer, zai so kwarai yace a sake shi ya tafi ga iyalansa amma ba zai iya ba, bayani kawai suka samu daga wajensa babu wata shaida ko kuma kwakwaran bayanin da zai kaisu ga wani abu har yanzu, don haka sakinsa zai zama tamkar saki na dafe ne wanda ba zai fara hakan ba.
Saboda haka yayi ajiyar zuciya mai nauyi kamar ta cikinta ne zai fitar da tarin abubuwan da yake jin nauyinsu a cikin kansa sannan yace.
"A cigaba da rike shi Yakubu, amma kar ku sake taba shi..."
"Sir pleeeease, pleeese sirrrr, abeg naaaa, help me sirrrr pleaseeeeee....."
Magiyar Mr. Okaforn ta sake cika oficce din a lokaci guda kafin Yakubu ya daga murya ya kira mutanen nan, kuma suka shigo a lokaci guda suka É—auke shi suka sake fita dashi yana ta magiyar yana rokon Ma'aruf.
"Kar ka damu, duka iyalan nasa ma suna nan tare damu, zan cigaba da rike su har lokacin da kace, 'Cox ina da wani aiki da zsn yi anan garin ma."
Ma'aruf ya gyaÉ—a kansa.
"Nagode sosai Yakubu it's a pleasure to work with you. Zan sake turo maka da wasu kudin insha Allah to keep things going."
Yakubu ya gyada kansa shima sau biyu a jere sannan kiran ya katse. Ya katse a lokaci guda da saƙon Amina ya shigo wayar Ma'aruf dake gefe, ya dauko ta ya duba, abinda ta rubuta dan guntu ne.
"Sugar, zanje kitso dan Allah..."
Yana gama karantawa wani saƙon nata ya kara shigowa akai.
"Ba nisa..."
"Kusa da gidansu Fatima ne..."
Gidansu Fatima, wannan kawar tata da yake yawan ji tana faɗa, dazu tare suka fito ya sauke ta s gidansu tare da Hamida kafin ya tajo office, shima ya shiga ciki sun gaisa da kowa, don saura kwana biyu kawai tafiyar mahaifinta da kuma kaninta Aminu zuwa India, har da kansa ya yiwa Mami godiya da yaji labarin cewa ita ta ɗauki nauyin tafiyar, ƴanuwanta ne ya sani amma haka kurum sai yaji kamar saboda shi tayi hakan, shi yasa shima a yanzu da yaje yayi musu irin tata kyautatawar wanda da kyar suka karɓa, abinda basu sani ba shine, zuciyarsa na gaya masa cewa zaiyi tarin abinda yafi haka ma indai akan Amina ne.
Saboda haka kafin wani saƙon ya sake shigowa ya shiga typing amsar sa da take jira.
"Ki tabbatar an rubuta sunana a jikin kitson nan Doll."
Sakon ya tafi a lokaci guda tare da shigowar kiran Faruk, don haka ya fasa cigaba da rubuta abinda yayi niyya ya É—auka.
Muryar Faruk É—in ta fito a lokaci guda da ya kara wayar a kunnensa.
"Muna High Prison, mun sami mutumin nan B, yana ganinsa ya gane shi, yanzu haka ma ya fadi duk wadanda suka saka shi ya fita daga Prison din suma an tafi za'a fito dasu don dukkaninsu ma'aikatan wajen ne."
"Alhmdlilah, Alhmdlilah, Alhmdlilah...."
Itace kalmar dake fitowa daga bakin Ma'aruf tunda yaji abinda Faruk ɗin ya faɗa na farko. Ya miƙe tsaye a lokaci guda ya fito daga kujerarsa ya dawo tsakiyar office din hannunsa a cikin gashin kansa yayin da zuciyarsa ta kasa tsaida kanta waje guda a tsakanin murnar wannan nasarar da kuma taraddadin abinda yake shirin tambaya.
"Ya gaya maka wani abu Faruk? Any clue na su waye mutanen da suka sa shi aikin kafin yaje ya karbi kudin?"
Ya tambaya muryarsa a tsaye kyam!
A can bangaren,Faruk ya girgiza kansa yana kallon hayaniyar dake faruwa a gabansa wadda ma'aikatan Prison ɗin suka tayar na Cewar baza'a tafi da ogansu ba kasancewar har da sa hannunsa al'amarin,tarin ƴan sandan da suka zo dasu na ta ƙoƙari wajen hana su haurowa inda su suke tsaye ana shirin fito da mutumin, sai ya girgiza kansa a hankali sannan yace.
"Ko waye Awwalu ya shiga uku Ma'aruf, don gayen yace min mutum daya ya gani da ya saka shi aikin, shi ya bashi wallet dinka da wayoyinka ya kuma fada masa duk abinda zaiyi, kuma yace sunansa Awwwalu."
"Awwalu." Ma'aruf ya furta ba tare da ya san ya fada ba.
"Awwalu." Ya sake faÉ—a a hankali.
****
"Awwalu."
Hajiya Kilishi ta faÉ—a tana kallon Aminiyarta Hajiya Salamatu.
"Ni Awwalu zai yaudara ya mayar mara hankali Salamatu? Wai har ni Awwalu yake kokarin cin amana a harkar nan?"
Ta sake faɗa amon muryarta na fitowa cike da takaici. Suna zaune a cikin falon gidan Hajiya Salamatun ne,inda bayan su kaya ne fal na sabbabin atamfofi da kuma lesuna tsibiri-tsibiri an zube su kamar banza kasancewar dawowar Hajiya Salamatun kenan daga ƙasar da take yo siyayyar kaduwancinta.
Hajiya Salamatu ta girgiza kanta.
"Wannan ai ba komai bane Kilishi, ki duba fa ki ga yadda kike cin amanar wadannan mutanen dake tare dake, to har dan abokin aikin ki wanda kullum yake ganin abinda kike yi ya kwaikwayi hakan sai kiji wani zafi? Kamata yayi ace daman kin dayde da shirya masa.
Kilishi dake kallonta tace.
"Maganganunki sunyi zafi Salamatu, amma haka ne, tabbas abinda kika faÉ—a haka yake, wannan ba komai bane don Awwalu ya nemi ya bauÉ—e, daÉ—in shine na daÉ—e ina shirya masa dama, kuma a tunaninsa ya koyi irin taku na yana shirya hanyarsa bai san cewa sawun giwa ya take na rakumi ba kuma ko a gidan giya akwai babba, sannan sama tayi wa yaro nisa sai dai ya É—aga kai yayi kallo."
"Wannan haka yake, nice ta farko da zan fara yi miki wannan yabon bayan ke Kilishi, yanzu ki gaya min a ina kuka tsaya tare dashi."
Kilishi ta kurbi lemon hannunta tana kallon Salamatu ta cikin gikashin kofin, kuma bata ajiye ba sai da ta shanye shi tas sannan tace.
"Tun daga ranar da ya kawo min hodar nan daga lagos bai sake ce min komai ba nima kuma ban kira shi ba, dukkan abinda yake ciki ina jinsa ne ta hanyar wannan Sadik din dana tura ya zama abokinsa a kwanakin baya, saboda haka na riga na daɗe da gama shirya masa, yanzu jira kawai nake yi ya nunawa Sadik inda ya tara Cd's din da yake ɗaukar muryarta, ya riga ya ganoinda computers din suke, da mun samu Cd's din, zan sa ya ƙona komai ne gabaɗaya sannan inje in fuskance shi.
Zan gaya masa dukkan shirinsa da na san yana yi da kuma yadda akayi na kama shi, kafin in aiwatar da nufi na akansa."
"Me zaki yi masa?"
Kai tsaye Salsmatun ta tambaya tana wulli da wani leshi dake kan cinyarta zuwa cikin kayan dake baje a dakin.
"Haukata shi zanyi Salamatu, ba zan kashe shi ba, Haukata Awwalu zanyi ta yadda zai kare rayuwarsa yana biyan bashin cutar da yaso yayi min."
Salamatu ta gyada kanta tana taɓe baki kafin tace.
"Shi kuma Sadik din fa?"
Kilishi tayi shiru tana nazari kafin tace.
"Sadik irin mutanen da basu da ra'ayin kansu ne Salamatu, kuma daga Ghana yake kin sani saboda haka wani kaso kawai zan bashi ya koma kasar su, da ya koma ya cigaba da shaye-shayensa shikenan bani da wata matsala dashi na sani."
Salamatu ta gyada kanta tana murmushi sannan ta sake cewa."
"Victoria Island dai na can na jiranki Kilishi, kafin ki kammala komai na tabbata an gama gine-ginen nan."
Girgiza kanta kawai Kilishi tayi kafin tace.
"Bar wannan zancen tukunna yanzu Salamatu, jikina ya bani cewar Ma'aruf ya dage akan binciken kamfanin nan nasu, bai ce dani komai ba amma na fahimci hakan ne kawai, shi yasa na tsayar da komai nake son inyi in gama da Awwalu akan kari.
Tunda kin san indai har sun sami mutanen nan duk abinda zasu samo zai kaisu ne kawai ga Awwalun tunda shi kadai suka sani, kin ga idan na kammala abinda zanyi dashi kafin su nemo shi, zasu je su same shi ne a haukace, haukan da ba zai taɓa warkewa ba. Daga nan sai in dawo in fuskanci batun yarinyar nan da kuma Baffa, yadda zan tsara mutuwarsa a ranar da kudi na gaba zasu shigo kamfanin."
Dariyar da Hajiya Salamatu ta kyalkyale da ita tana debo wani zagi wata iriyar dariya ce da babu shiri Kilishin ta shiga taya ta itama, muryoyinsu suka karaɗe falon cikin wani irin amo mai ɗauke da tsananin nishadi da kuma taƙama, taƙamar da a cikinta Kilishin ke jin kanta zuwa wani mataki da take jin cewa bata da takwara a duniyar nan.
Abinda bata sani ba shine, alƙalami ya riga ya bushe akan wata ƙadddara da zata wanzu cikin kwanakin da take lissafawa kanta da wani labari da yasha banban da wasiƙar da zuciyarta ke biya mata!
Kuma zaren labarin ya fara ne a daidai wannan lokacin kuma a cikin wannan dakin!
***
_Wanne irin sirri kuke tunanin Hajiya Mardiyya na ɓoyewa akan Jawad? Kuna tunanin sirrin yana da alaka da halayyarsa?_
_Sannan ta ina kuke tunanin labarin Jawad da Zainab yana da alaƙa da ɓangaren su Kilishi?_😃
_Ma'aruf ya tattaro kowanne ɓangare na matsalarsa, kuna tunanin ya fara taka matakin nasara?_
_Ga kuma tsarin da Hajiya Kilishi ke yi tun kafin su kai ga ƙarshen binciken nasu, matar nan A ce!_😅
_Amma ya kuke tunanin hakan zai kaya??_
_Ina gaya muku BabyDoll din Sugar ta tanadar mana wani surprise mai daɗi a babi na gaba._��🥰🥰
_Muje zuwa!_😅
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:56 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*14*
*Tarin Addu'o'in ku da kuma fatanku na alkhairi na É—aya daga cikin abinda ya farfaÉ—o dani, bani da bakin da zan ce Nagode, don ina ji kamar kalmar tayi kadan in dora ta a mizanin goriyar tawa... sai dai ince Allahu ya saka muku da alkhairi ya kyautata rayuwarku ta duniya da kuma lahira.*
*Nagode da tarin ƙauna.*
~~~~~~
_I'll hold you when things go wrong..._
_I'll be with you from dusk till dawn..._
_Baby, I'm right here... -ZaynMalik & Sia._
***
Hannun Inna dake riƙe da cokali ya juya wani kwadon zogalen da yaji kuli-kuli da kuma su tumatir daga can tsakar gida inda take zaune yayin da a lokaci guda da Amina dake zaune a gɗaki ta sauke wayar hannunta daga kunnenta.
Idonta ya tsaya akan Amman yayin da kalamanta na yau suka shiga dawowa cikin kanta. A dazu bayan fitar Baba, sun fi ƙarfin awa guda suna magana, magana sosai irin wadda tun bayan tafiyarta basu yi irinta ba kasancewar wannan ba'a waya bane ba, sun sake tattauna tarin abubuwan da suka gudana a baya sannan ta gaya mata cewar ta cigaba da rike Hamida hannu biyu kafin ta ga abinda su Rukayya ke shirin sake shiryawa, wanda har a yanzu ta jaddada mata da cewar kar ta bari Ma'aruf ya sani.
"... Ki cigaba da tafiyar da al'amarin gidanki kan turba mai kyau Amina, daga shi har yarinyar kar ki basu kokwanton wani abu yana faruwa daban tare dake, ki barshi yaji da matsalar wajen aikinsa da yake fuskanta yanzu, kuma kar ki taɓa tambayarsa wani abu idan har ba shi ya gaya miki ba, don tambaya hanya ce mai ce miƙakƙiya ga zargi... Don haka ki kyale shi da dukkan wata tambaya da ta shafi binciken da yake yi, kwanciyar hankali shi yafi buƙata daga gare ki yanzu, idan har muna buƙatar wani bayanin, akwai hanyar da zamu samu abinda muke nema daga gare shi, zai faɗa miki duk abinda kike so ba sai ma kin tambaya ba."
Tana tuna yadda ta dinga juya maganganun a lokacin, yadda Amma ta gata mata dukksn hanyoyin da mace zata bi idan har tana son samun amsar wani abu daga wajen mijinta, ba tare da shi kansa ya fahimci tambayar tata da kuma abinda take nema ba.
"Rayuwar mace gabaɗaya dabara ce da kuma kissa Amina, idan da har bayan ibada kowacce mace zata ɗauki waɗannan abubuwan guda biyu ta riƙe su a kowanne fanni na rayuwarta, da tabbas mata da yawa zasu sami rabin aljanarsu ta duniya."
"Kin san ranar nan kuwa Jamila tazo nemanki?"
Maryam dake zaune a gefenta riƙe da Hamida wadda ta ɗane kan cinyarta tana zana mata fulawa da abin Rani ja kan fararen hannunta ta fada.
Amina ta kalle ta, tana tuno Jamilan da take fada, wata ƙawarta ce da a islamiyya ce da babu gaira ba dalili ta tsiri daina yi mata magana, har Amma sai da ta shiga cikin al'amarin a lokacin wajen tambayarta abinda ya faru amma tace babu komai.
"Da gaske? Me tace kuma?"
"Wai taji labari ance kinyi aure ne shine tazo yin murna, wai a rakata inda kike ku gaisa."
Amina tayi murmushi tabya jinjina kanta alamun mamaki kafin Maryam din ta cigaba.
"Amma tace wai ai sai ta saka rana tazo a raka ta, shine ta karbi nambar wayar Amman wai zata kira, ni kuwa na bata wrong number, ranar da ta gaji ta tako ƙafarta tazo, kwanciya zanyi ince bani da lafiya?"
"Saboda me?" Amina ta tambaya tana dariya.
"Dan Allah ki rako ta ko kuma ki bata namba ta, kinga ai a kawo karshen gabar tata."
Maryam ta girgiza kanta tace.
"Wallahi Yaya wannan yarinyar ba mutunci ne da ita ba, haka kurum taje ta jawo miki wata matsalar..."
"Haba dai, ai bata isa ta jawo min wani abu da yafi karfin wanda nake ciki ba Maryam, tunaninta bai isa yafi na mutanen da nake tare dasu ba."
Ta fadi hakan fuskar Kilishi na haskawa a cikin kanta.
"Bata sake yi kiranki ba har yanzu?"
A dazu da suke magana da Amma haka ta tambaye ta, ta girgiza kanta kafin tace.
"Bata sake yi min magaba ba tun daga lokacin Amma, na kula kamar kwana biyu hankalinta ya rabu ne kan wani abun, tana yawan fita sannan bata maida hankali kan abubuwan gidan sosai."
Amman ta gyada kanta a lokacin sannan tace.
"Watakila ta fahimci binciken da suke yi ya fara doso ta ne, watakila kuma tana da tsarin wasu abubuwan bayan sha'anin yarinyar shi yasa tayi miki shiru.
Kilishi tana da tsari, ta san me take yi... Wasu abubuwan take saitawa kafin ta waiwaye ki, ba zata baki aikin a lokacin da ta san hankalinta baya kanki sosai ba, watakila kuma tsuntsu biyu take neman jifa da dutse É—aya, abu biyu zata haÉ—a a lokaci guda. Ba lallai ki iya sani ba, amma idan kin ga alamar wani abu ki gaya min watakila zamu iya samo wani abun a cikin takunta."
Ta gyada kanta a lokacin sannan ta É—ago ta kalle ta sosai kafin tayi tambayar da ta daÉ—e tana ci mata rai a zuciyarta.
"Amma idan har ta kawo maganin ta yaya zanyi amfani dashi? Lokacin da muka yi magana kince komai zai faru amma kuma ba abinda zai faru? Kince a idonta kawai Hamidan zata makance amma ba a gaske ba."
Murmushin da Amman tayi mai fadi ne a lokacin kafin tace.
"Kar ki damu, har na fara wannan shirin Amina, na gaya miki takunta zamu ɗauka kamar yadda muka fara yanzu, zamu shammace ta ne ta hanyar da take shammatar mutane, ta hanyar da take ganin tata ce itace mai ikonta, don haka ki bari lokacin yazo zaki san komai, nafi so a yanzu ki tsaida hankalinki akan gidanki tukunna, nan ne ɓangare mai girman da yafi kowanne bukatar tallafawarki a yanzu."
"Wani abu kike ciki yanzu a gidan?"
Tambayar Maryam ta dawo da ita duniyar zahiri, sai tayi saurin girgiza kanta.
"Ina nufin tunaninta bai isa yafi na mutanen gidan da yanayin wayewarsu da komai ba, na gaya miki yadda su Samiran nan suke, yanayin rayuwarsu ta banbanta da namu ta hanyoyi da yawa."
Ba tare da ta fahimci komai ba Maryam tace.
"Shi yasa bana son zuwa ai, kin san ni duk inda za'a wulankanta ni ko a raina ni ba son zuwa nake ba, wallahi ko da su Amma suka tafi Jigawa kai Aminun nan da muka je gidan Kawu Mallam baki ji yadda na dinga ji ba, na tsani a dinga min iko da abu."
Sanin wannan halin nata sarai yasa Amina bata ja zancen ba tace.
"Allah ya taimake ki kar Baba ya miki irin nawa."
Sai ta girgiza kanta tace.
"Wallahi ba zan iya ba Yaya, ba zan taba iyawa, nifa kinga ko kayan gidanki da na san da yawa nasu ne, zasu sa zuciyata ba zata nutsu wani ya shigo ya gaya min magana...Don ma dai Hajiya Kilishi ce, da sauki ta saba mana alkhairi, shi yasa ma banji komai sosai ba ko a wannan tafiyar dasu Baba zasu yi."
Amina tana murmushi tace.
"Allah ya shirye ki Maryam."
A wajenta dukkan wannan abin da take faÉ—a tatsuniya ce kawai, don bata san tarin kalolin da rayuwa ke haskawa É—an adam ba.
Daga haka idonta ya jai waje inda Amma ke zaune da kwano a gabanta da kuna Hafsa da ta shigo a lokacin daga islamiyya tana tambayar.
"Har yanzu su Yaya suna nan?"
"Wai ina Aminun yake ne ma?" Amina ta tambaya.
Maryam ta tabe bakinta tace.
"Abokanansa ai ba sa kyale shi tunda ya dan ji saukin nan, yanzu zaki ji sallama sun shigo sun gara wheelchair din sun fita dashi musamman yanzu da suka san jibi za'ayi tafiyar nan."
Kafin Amina tace wani abu Hamida dake kan cinyar Maryam din ta taso da sauri tana nuna mata kunshin da aka gama da murnarta.
"Babydoll yayi kyau?"
Wani abu ya ratsa cikin kan Amina, ta rasa ta yadda zata yi yarinyar nan ta daina kiranta da haka, Ma'aruf ya vuvi kwakwalarta da yawa, kuma kagin ta amsa idon ta ya gano mata Hafsa, sai kawai tayi wajen da sauri tana fadin,
"Aunty Hafsa come look, zo ki gani me aka min
..."
Mamaki ya kama dukkaninsu. Maryam ta gyada kanta tace.
"Ina gaya miki Hafsa ta ƙar rashin mutunci yarinyar nan, yanzu wai daga zuwanku har ta san ta gaya mata sunanta Aunty Hafsa...? Bari Adam yazo kuma mu ji Uncle Adam."
Dukkaninsu suka yi dariya Amina na fadin,
"Ni na san kamar fuska kawai muke yi da Hafsa ai, amma ina zan iya da halinta."
Maryam tana mikewa tace.
"Yarinyar nan zata kunyata ki a cikin mutane watarana, gwara ma ki gaya mata ba sunanki BabyDoll ba..." Ta dan yi shiru sai kuma tace.
"...Amma kuma ya iya zabar suna."
Dardumar dake gefenta Amina ta É—ebo ta cilla mata tana faÉ—in.
"Ranki zai ɓaci wallahi...!"
Wayarta tayi kara a lokacin, Fatiman da take ta jira ce.
"Haba Fati, wai bokiti guda ake soya mana ne?"
Daga cikin wayar, a gaban ƙawarta dake soyar waina Fatiman tace.
"Kin san mutanen da aka tsallake ake yi mana ne kike ta kwala min kira, to wallahi ko sun zo daukar ki ne sai sun tsaya mun ci wainar nan Allah."
"Wa ya gaya miki tun yanzu zan tafi? Ni kawai na ƙagu ne, bakina sai tara yawu yake."
Fatiman tayi dariya tace.
"Ki cewa É—an Baban yayi hakuri, gani nan a hanya."
A lokaci guda kalaman Fatiman suka tafi cikin kan Amina dake zaune suka buga wani abu, wani abu da taji dirarsa har cikin ƙirjinta, wani abu da yayi mata kama da tashin hankali a lokaci ɗaya, taji ma'anarsa na yin fadi a cikin zuciyarta tana so tafi karfin kalmar kokwanto.
Hannunta ya kai kan cikin ta a lokaci guda da kalmar Fatiman ta furta akan lebbenta, kwana biyu bata jin dadin jikinta sam, tana ta yin komai ne amma bata fahimta ba sai da ta fara jin tashin zuciya, haka kurum take ji kwana biyu bata son kamshin wasu abubuwa,ko a yanzu ma zogalen da Amma ke haɗawa ne yasa ta kasa tashi taje wajenta, tun daga nan take jin cewa bata son ƙamshinsa, sannan kuma yadda take ji kamar wani abu a cikin cikinta na rawa na jiran wainar fulawar da Fatiman ta tafi siyo musu, yafi karfin yadda take son wainar a kodayaushe.
Amma tsaya, haka da wuri komai yake faruwa? Kai tsaye kawai? Idan zata tuna lokacin da Aunty Ma'u ta sami cikinta na farko ba irin wahalar da ita da mijinta da kuma Amma basu sha ba.
Don ta kusa sati uku kwance a asibiti, kuma Amman ce mai kwana da ita a lokacin, to ta yaya ita yanzu tana zaune komai zai faru ba tare da ta ma sani ba? Sai kawai ta ture zancen Fatima a gefe ta mike ta fito daga falon lokacin da ta kula Amma ta rufe kwanon zogalen.
".... Suna gidanmu gabaÉ—aya, zaki zo? Har da Barbie nake da."
Ta jiyo Hamida na lissafowa Hafsa kayan wasan ta yayin da take zare ido cike da É—oki tana kallonta. Tana juyowa suka haÉ—a ido da Inna dake kallonta tunda ta fito daga falon sai dai kafin tace komai Maryam ta fito daga É—aki da hijabi tana fadin ta tafi.
"Ina zaki je?"
"Kuɓewa zata siyo anan bayan layi gidan su Aisha, ita kaɗai ce ba'a samo ba a kayan naki."
Amma ta faɗa tana jawo wata leda mai yalo da baƙi da aka cika taf da kullin bakaken leda.
"Ga Kuka anan, wannan kuma busashshen zogale ne ga yajin sannan ga dakakkiyar citta da tafarnuwa anan..."
Ta shiga lisaafin kowacce leda daga ciki yayin da Amina ke kallonsu, zuciyarta na bajewa da wani daɗi da kuma ganin daraja ta girman Uwa, tabbas dole ne wanda ya rasa ta yayi kuka da idanunsa kullum a duniya, don ƙarya ne ka sami mai kulawa da kai tun daga ƙasan ruhi a duk duniyar sama da ita, sai dai kuma ubangiji kan ɓoye wasu tarin hikimomin nasa ga rayuwar wadanda ya karbi tasun, hukuncinsa daidai ne a kodayaushe.
Ɗazu kafin ta tafi gidan kitson a hira kawai take tambayar idan har yanzu gidan wata mata mai suna Salamatu akan layin nasu tana sayar da kuɓewa, tace duk bata dasu sai gashi har Amman ta tanadar mata komai a yanzu. Da murmushin da godiyar ba zata misaltu ba tace.
"Madallah, Allah ya saka da alkhairi."
Amman ta amsa da Ameen sannan hannunta ya dauko kwanon zogalen nan ta miƙo mata, bata ko bude murfin ba, amma ƙamshinsa ya tafi a tsaye har cikin hancinta, ba shiri ta juyar da kanta da sauri, sannan ta shiga girgiza kanta.
"Amma madallah, Fati zata kawo mana wainar fulawa yanzu."
Amman ta kalle ta na wasu sakanni kafin ta dauke kwanon tace.
"To ita zaki iya ci?"
Da murmushin ta ta kalle ta tace.
"Amma wainar fulawa ce fa."
"Wannan ma ai zogale ne kuma kina cin sa a da."
Fassarar da Amina ta yiwa kalaman Amma daban a cikin kanta, don haka a lokaci guda idanunta suka kaÉ—a ta shiga sake girgiza kanta.
"Wallahi Amma ba wani abu nake nufi ba, kawai ji nayi bana son ƙamshinsa, ya za'ayi in ƙi ci haka kawai..."
Amman ta gyada kanta tana katse ta.
"Na sani ai, na san da lalurar shi yasa na tambayeki... Kin fada masa ma tukunna? Don ban ga alamun kun je asibiti ba?"
"Asibiti?..."
Amina ta tambaya kai tsaye tana kallon mahaifiyar tata, idan ka shigo a wannan lokacin ka kallesu, su biyu zaune akan tabarmar nan, zaka yarda an ƙirƙiri wani mudubi ne dake zabge shekaru yana kuma ƙara du a lokaci guda, don kamarsu daya sak, yanayin sirantar jikinsu da idanun da hancin, dama yawan gashin kan mai laushi duk da na Amina ne kawai a buɗe, banbancinsu kawai shine shekaru da kuma hasken fatar da Aminan tafi Amman a yanzu.
"... Lafiyata kalau fa Amma ba abinda ya same ni..."
Murmushin da Amman tayi shi ya katse ta daga sake magana, ta juya da kanta bata kalle ta ba sannan tace.
"Baki san kina da ciki ba?"
A lokaci guda tambayar ta janye Amina daga gangar jikinta, ta jita tana tashi zuwa wata sama mai nisa, tana barin gidan, tana batin unguwar, tana barin garin tana barin ƙasar, tana barin nahiyar ma gabadaya... tana ganin kowa da kuma komai a cikin kanta kafin ta faɗo a lokacin guda, ta taho tun daga wannan lulukin a tsaye, babu wani hijabi har inda take zaune, kuma ƙarar dirar tata ya cika kunnwanta bakidaya!
***
A cikin motar dake tafiya, Ma'aruf ya kalli Faruk dake zaune a gefensa bayan ya ajiye wayar da suka yi da wani jami'in Æ´an sanda yace.
"Yana da wayo Faruk, ko waye Awwalun nan yana da wayo, tunda har daga wadannan mutanen har Mr. Okafor bai taba waya tare dasu ba."
Faruk ya girgiza kansa yana komawa da baya ya jingina sosai da kujerar da yake zaune kafin yace.
"Shi yasa na gaya maka zama zamu yi sosai kawai mu fara sabon bincike, gobe dole ka fito early, sai mu ga ta inda zamu fara."
Dawowarsu kenan daga Police headquarters na Bompai inda aka garkame duka mutane hudu ma'aikatan prison din dake da sa hannu akan fitar wannan mai laifin, inda har a yanzu daga mutumin har da mutanen kowannensu ya tsaya akan rantsuwar wani mutumi mai suna Awwalu kawai suka sani akan al'amarin, a yanzu haka an sami nambar da suka yi magana da shi Awwalun a lokacin, an mika ta hannun IT department, kuma zuwa gobe suke sa ran samun bayani daga wajensu idan har za's iya tracking wani waje da za'a iya samun Awwalun ko kuma wani bayanin da zai ksi su gare shi.
Ma'aruf ya dunkule hannunsa akan bakinsa kafin yace.
"Kana tunanin mu shigo da Yakubu wannan ɓangaren shima?"
Faruk ya girgiza kansa.
"Yakubu ya iya aiki B, amma ka san yana da nasa matsalolin... Yana aikin ne tare da mutane da yawa kuma ban san me yasa ba amma haka kurum jikina yake bani cewa neman Awwalun nan yana bukatar sirri, sannan ya gaya maka cewa akwai aikin da yake yi yanzu haka shi yasa har zai cigaba da kula da wannan Mr. Okaforn, ka ga we have no time da zamu jira shi kenan.
Kawai kaje gida ka huta, gobe early in the morning mu san ta inda zamu fara kafin mu sami bayani daga IT members din, zan taho da Æ´an bayanan da na hada sai mu gani."
Ma'aruf ya gyaÉ—a kansa sau biyu kafin yace.
"Gobe Abdurrahim zai dawo and I think ni da Ishaq zamu dauko shi daga airport, but insha Allah zamu yi komai."
"Wow! Allah ya kawo shi lafiya..." Cewar Faruk É—in kafin ya cigaba.
"Da safe kafin in kira ka, munyi magana da mutanen Rotel&co (kamfanin da zasu yi aiki dashi na gaba) na gaya musu ranar da muka yi fixing zamu zauna dasu... Amma yanzu da wannan abubuwan da suka taso, ina ji kamar a kira su mu ƙara ɗagawa..."
Ma'aruf, ya sake girgiza kansa.
"Let them, zamu iya Insha Allah Faruk, kar ka manta duk wannan fafutukar da muke yi Baffa bai sani ba, so abinda kawai zai sani shine idan muka tsayar da aikin mu, har zuwa karshen shekarar nan fa bamu da wata kwangila a gaba, wannan ce damu kawai, may be idan muka yi aiki mai kyau, zamu iya sake wani contract da wasu."
"Haka ne."
Cewar Faruk ɗin kafin wayarsa ta fara ƙara, ya dauka ya kara a kunnensa ya shiga waya da makanikensa wanda zai zo ta dauki motarsa data mutu a ƙofar Prison din nan da suka fara zuwa.
"Canja ta zanyi kawai Aminu, kawai dai a fara gyarawa mu gani tukunna..."
Faruk ɗin ya shiga magana, sai kawai ya dunƙule hannunsa guda dunkule akan bakinsa yayin da har a lokacin yake kallon titi.
Wani iri zuciyarsa ke masa, wani iri yake ji a dukkanin jikinsa gaba daya, kowannan tukin ymda yake yi ji yake kawai kanar a cikin wani zagaye yake tafiya da idan suka yi gaba suna sake, tunanimsa yq kasa hango masa waye wannan Awwalun da kuma dalilinsa na kassara su, yadda yake amfani da kwakwalwa dana kudinsa don ganin kawai ys tarwatsa su.
Zai rantse har da Allah dalilin wannan abin bai taru kawai akan kuɗi ba, dole akwai wani labarin dake ƙarƙashin komai.
A haka har suka karasa kofar gidan Faruk din ya sauke shi.
"Ka huta sosai B dan Allah idan kaje gida, ka barwa gobe komai, let your mind rest."
Abinda Faruk din ya fada kenan bayan ya fita ya tsaya daga wajen motar, kuma da ya kalle shi sai yaga kamar yana kallon mudubi ne wanda ke hasko masa irin tarin gajiyar dake tattare dasu, idanun Faruk din kadai sun kada kamar nasa, don banda ruwan da suka siya bayan sunyi salkar La'asar babu wani abu da ya shiga cikinsu a tsayin ranar yau din.
Sai dai kafin ya buÉ—e baki ya bashi amsa, kofar falon gidan daga can barandar dake fuskantarsu ta buÉ—e, yara biyu mace da namiji suka fito da gudu suna ihun.
"Daddy! Daddy!"
Kafin matarsa ta baiyana itama riƙe da hannun karamin ɗansu Aarif wanda ya fara tafiya, sai kawai yayi masa murmushi sannan ya ja motar zuwa can gate inda maigadin dake tsaye bai rufe ba kasancewar ya gaya masa yanzu zai iso. Da a yau bashi da inda zai je ya huta gajiyarsa kamar Faruk, baya jin zai iya hana ciwonsa tashi kotawacce hanya.
*
Siraran hannun Amina suka kwankwasa kofar bandakin a hankali, idanunta na kallon tiririn daje saman ƙofar inda wajen glass ne maimaikon katakon dake kasa.
"Come in..."
Muryar Ma'aruf ta faɗa daga ciki, sautinta ya fito lazily kamar yadda yanayinsa yake tun lokacin da ya shigo, ta tsaya kamar ba zata bude ba sai kuma tasa hannunta daya da baya riƙe da ɗan karamin towel din da ta riƙo, ta murda handle din a hankali, kofar ta rabu da wata ƴar siririyar hanya amma sai ta kasa karasa buɗewa, ta tsaya rike da handle din kawai tana shakar daddadan dimin dake fitowa hade da ƙanshin sabulunsu.
Baifi sakanni biyar ba Ma'aruf yaja kofar daga ciki ya buÉ—e ta gabadaya, yana tsaye daga shi sai towel din dake jikinsa na wankan da yayi, gashin kansa a jike yake gabadaya ya barbaje wasu kuma sun manne da fatarsa, tana kallon idanunsa da suke a lumshe sosai don kusan rabinsu je kawai a buÉ—e kanar mai jin bacci, sai kawai ta karaso ta rufe takun biyun dake tsakaninsu, tasa towel din hannunta akansa sannan ta shiga goge masa gashin a hankali da duka hannunta biyu.
Ya rufe idanunsa duka biyun a lokaci guda da hannayensa suka zagaye ƙugunta yana rike ta sosai a jikinsa... Yana jin yadda siraran yatsunta ke motsi a cikin gashin nasa ta jikin towel ɗin. Sai kawai tayi ɗage da kafafunta ta ƙara tsawo daidai shi sannan ta dora goshinta akan nasa, ta janyo hannayenta daga saman towel din ta zura su ta kasan sa, numfashinsa ya kara nauyi akan fuskarta sanda yatsun nata suka shiga cikin gashinsa gabaɗaya, tana jin yadda ya ƙara riƙe ta a jikinsa, ɗumin jikin nasa da kuma ƙamshin sabulun na mamaye ta gabaɗaya.
"Are you feeling better?"
Muryarta ta fito a hankali, a hankalin da shi kansa da yake jikinta can kasa yaji ta sosai.
"Abinda nake ji yafi karfin Better Babydoll, you are healing me..."
Kalaman suka sata murmushi, suka kuma bata kwarin gwiwar yin É—age da kafafunta a hankali kafin tayi kissing dinsa, bai ce komai ba da farko sai da yaji da gaske take sannan bakinsa ya furta.
"Damn it!"
Da haka ya sake riƙe ta sosai a jikinsa yana tuna mata da banbancin dake tsakanin abinda zata iya da kuma wanda shi zai yi, tsawon mintuna kafin ta janye zuwa baya a hankali tana kallonsa.
"I love you." Muryarta ta fito kamar wadda ta tsaya a tsakiyar gudu.
"I love you too Noor."
Ya fada tasa muryar hankali kwance. Sai tayi murmushi mai fadi jin sabon sunan da ta samu kafin a hankali ta janye towel din daga kansa ya fado zuwa wuyansa sannan ta saka hannunta na dama ta shiga gyara gashinsa zuwa baya a hankali.
"Da zan iya tsaida lokaci zan tsayar da wannan daren yayi ta sake faruwa Sugar, har sai ka dawo daidai, sai na tafiyar da gajiya da kuma damuwarka gabadaya, this is our own happy place, ni da kai kawai."
Ta fada idanunta na kan gashin nasa da kuma yadda take gyara shi, ya sake rike ta a hannunsa kafin ya gyada kansa a hankali sannan muryarsa ta fito.
"Nima haka BabyDoll, I wanna see the sun rise on your skin kullum, amma kar ki damu da nayi settling abubuwan da ke gabana we're going on a honeymoon, somewhere far away, just me and you." (Da na gama da abubuwan da dake gabana zamu tafi yawon amarci, wani waje mai nisa daga ni sai ke kawai.)
Ta gyada kanta tana kallonsa da murmurshi a fuskarta, sai ya sake cewa.
"Yaya kika bar su Amma?"
Su Amma, sunan ya tuna mata da gida da kuma dukkan abinda ya faru a can, sai taga kamar taje wata duniya ne ta dawo, rayuwarta a can da kuma a wannan gidan tana da tarin banbanci, a gidansu a gaban iyayenta da kuma Æ´anuwanta, ita Amina ce, Aminar da kowa ya sani Aminar da ita kanta ta san kanta a ita, amma idan ta dawo gidan nan sai taji ta koma wata daban, wata suruka a gidan Æ´an gayu da kuma É—an gayun mijin dake sawa taji kamar sune ma'aurata mafi sa'a a duniya, bata jin kanta a komai sai a matsayin Babydoll din da yake kiranta. Fuskar Hajiya Kilishi ce kawai mai ruguzo da ita tana tuna mata cewa ba'a aljanar duniya take ba.
Amma kuma bayan hakan a yanzu, karo na farko sai taji cewa kamar an ƙulla wani zare ne da ya haɗe waccan duniyar tata da wannan, kalaman Amma, bata tabbatar ba, ba wai bata yarda ba... Kawai kokwanto ne a cikin kanta har yanzu...
Kokwanton da ta kasance a cikinsa tun daga wancan lokacin, don bata sake cewa Amma komai ba, basu sake maganar ba gar suka taho, kawai dai kowa ya san yanayinta ya canja, tunanin ya cika kanta, tunanin da a cikinsa babu komai sai na yadda zata gayawa Ma'aruf hakan, fon a tsarin da tayi, a tsarin da tayi na kokarin boyewa kowa, kowan da Hajiya Kilishi ta zamo sila babu Ma'aruf, hasalima shine daya hannun da zai talkafa mata wajen cimma dukkan abinda ta tsara din, tsarin da ko Amma bata san shi ba...
Amma kuma tun kafin tazo gaban nasa, sai ta rasa ta yadda ta yadda zata iya harhado kalaman da zasu tashi ma'anar da zata gaya masa, ta kasa tunanin konai, tana jin kwakwalarta dama zuciyarta fayau, don haka ko a yanzun babu abinda ta iya cewa sai kawai ta shiga bashi labarin gidan nasu da kuma yadda Hamida ta sake da Æ´anuwanta.
Har ya shirya suka koma falo inda ya cika cikinsa da abincinta kafin Hamida ta cika kansa da nata surutun, har suka yi bacci, tana rungume a jikinsa tana jin numfashinsa a hankali kafin ya koma mai nauyi alamun gajiyar dake jikinsa tafi ƙarfinsa.
Har Asuba da tayi, ya fita masallaci ya dawo ya same ta akan tata sallayar, tana zaune gaban Mahaliccin data idar da ibadarta yayin da zuciyarta ke karanto tarin addu'o'in da basu da ƙarshe.
Daga bayanta ya tsugunna akan gwiyoyinsa, sannan ya zuro hannayensa duma biyu ya kara su a bayan nata, ya tsayar dasu yadda ta yi wa nata wajen addu'ar sannan ya ɗora haɓarsa a saman kanta.
Tayi murmushi a hankali tana jin ƙamshin sabon turaren da ya fesa a jikin sallayarta na shigar mata har cikin kai, ƙamshin mai sanyi ne, amma ita tana jin ƙarfinsa har cikin kanta, ta kai ƙarshe a addu'ar kuma yana ganin ta motsa hannunsa ya haɗe su da nasa gabaɗaya suka tafi kan fuskar tata.
"Ameen ya Allah Noor."
Ya faÉ—a daga saman kan nata sannan ya juyo da ita gabaÉ—aya tana fuskantarsa, a lokacin ne ta rasa dukkan wani tunanin kanta, yadda yake kallonta a cikin duhun dakin ya warware dukkan wani lissafinta, a lokacin ne bakinta ya furta abinda ya zama mafarin bude wata sabuwar rayuwa a tsakaninsu.
"Ma'aruf..."
Bakinta ya furta sunan ba tare da ta san ma me ta fada ba, kuma kafin ya amsa sauran kalaman suka biyo baya, bi da bi, wani na tunkude wani akan lebbenta.
"I think we're pregnant....!"
( Ina tunanin muna da ciki...!)
****
*No 1856L, Sulaiman Crecent Kano.*
*Gidan Hajiya Salamatu.*
"Kar ki damu Hajiya, gobe-goben nan zan sako miki su a mota, an riga an haÉ—a sun cika cif, laces guda talatin da biyu ne, atamfa arba'in, sai materials É—in guda takwas Nylon da kuma cotton guda goma..."
A cikin wayar dake kare a kunnen Hajiya Salamatu take wannan bayanin, tana zaune ne a barandar gidanta, daga ƙasan rumfar yayin da iskar yammar ke kadawa a kowanne ɓangare na harabar gidan.
A gabanta akwai wani dan karamin tebur da ta ajiye jotter da kuma biron da take karanto adadin kayan da take lissafawa a ciki, bayan jotter akwai jug mai garai-garai yana É—auke da lemo kakar yalo tar da kuma kofinsa wanda aka zuba lemon a ciki.
Ta kai ƙarshe a wayar tata, sannan ta sauke wayar, kuma kai tsaye hannunta ya lalubo nambar Hajiya Kilishi wadda taji shigowar nata kiran a lokacin da take waya.
"Ina tare da mutane na ne ranki ya daÉ—e..."
Ta fada kai tsaye bayan Kilishin ta ɗauki waya daga nata ɓangaren.
"Na sani ai shi yasa ban takura ba... Saratu ta kira ni da safe take gaya min cewa zasu dawo kasar nan kunyi waya?"
Hajiya Salamatu ta gyaÉ—a kanta tace.
"Mun yi tun jiya, nake cewa komai labari ne, yaushe take ta daga hankalinta akan yaƙi tafiya da ita gashi har ya dauke ta da ƴaƴan nata kuma zasu zo hutu."
Hajiya Kilishi tayi murmushi mai kama da dariya kafin tace.
"Da ta biyo ta hanya ta ba, a baya ta tashi hankalinta a banza, amma da ta fahimce ni ta ja da baya ta zama macen kanta ba gashi yanzu komai ya dawo hannunta kishiyar tata ma ta kama gabanta ba."
"Wallahi kuwa..." cewar Hajiya Salamatun kafin ta canja zancenta da cewar.
"Kin samu kayan ne?"
Hajiya Salamatun ta tambaya tana kurbar lemon hannunta.
"Wai sai Jibi zasu iso, abinda nake ta tunani kenan Salamatu, karo na farko da zuciyata ta kasa kwanciya akan wani abu, haka kurum nake jin cewa kamar jibin nan ba zata karasa ba wani abu zai faru."
Hajiya Salamatu tayi dariya kafin tace.
"Ki kwantar da hankalinki Hajiya, kin san hausawa sun ce aski idan yazo gaban goshi yafi zafi, gangarar kawai kika zo shi yasa kike jin haka, ban da abinki ma daga ni sai ke fa muka san wannan abin da kike shirin yiwa Awwalun nan, kuma ni dai kin san ko yanka ni akayi baza'a iya fitar da sirrinki daga cikina ba ko?"
Kilishi ta gyada kanta.
"Na sani Salamatu, kawai ban san me yasa ba bana gane komai ne a yanzu sai na fara gamawa da Awwalun nan, É—azu munyi waya da Maigaskiya yace min yana office abubuwwa sun yi masa yawa, bai ce min komai bayan hakan ba amma na fahimci kamar binciken nan suke yi kuma sun gano wani abu Salamatu, da ba Awwalu na dora akan harkar nan ba da na bari ko sau daya ne dun ganni da tuni inaga abubuwa sun canja kala daga yadda nake kallonsu."
Salamatun ta girgiza kanta itama.
"Ki daina wannan tunanin, ki fuskanci abinda ya rage kawai bayan Awwalun, zancen yarinyar nan tasa Hamida sai kuma mutuwar shi mai gidan naku da har yanzu baki tsara yadda zata kasance ba."
"Na tsara komai Salamatu, zan gaya miki da zarar mun hadu, a yanzu bayan wadannan biyun kuma ina so da Amina idan ta gama yi min aiki akan yarinyar in raba ta da mai gaskiya itama, a fuskokinsu kawai zaki gane kamar rayuwa na tafiyar musu daidai, ba zan iya basu wannan farin cikin ba Salamatu... Ba zan iya barin Ma'aruf da wani abu mai haske a rayuwarsa ba, so nake har ƙarshen rayuwarsa ya dauwama yana tunanin ni kaɗai ce haskensa."
Hajiya Salamatu ta taɓe bakinta kaɗan kafin tace.
"Ba zaki canja tunaninki akan yaron nan ba Kilishi, amma wannan É—in ma daidai ne, ai bai É—ara daga cikin aikin ki ba, sai dai tsaya... Wane tabbaci ma kike dashi cewa har i yanzu yarinyar nan bata É—auke da wata hamidar ko kuma Hamidu?"
Kilishi tayi murmushi mai fadi kafin tace.
"Na dade da bata magani Salamatu, kuma a yadda yarinyar nan ta yarda dani ba zata saba min alkawari ba, abinda zanyi musu ma idan ta gama yi min wannan aikin na Hamidan zai rufe musu ido ba zasu ga komai a rabuwar tasu ba daga iyayenta har ita din. Kuma yadda zan raba sun babu wuya, ni na san abinda zanyi, na san abinda zanyi yadda Mai gaskiya ba zai sake kallon yarinyar nan a duniya ba."
Hajiya Salamatu ta gyada kanta.
"Na fahimci har yanzu da saura a harkar nan Kilishi, shi yasa kika ce zuciyarki ta kasa kwanciya... Amma kar ki damu, tunda kin iya da tarin abubuwan da kika shallake a baya waɗannan ma ba zasu yi miki wahala ba, ki cigaba da tsarinki kawai, ina garin nan har sai kaya na sun ƙare, don haka kar kiji komai."
Da haka wayar tasu ta ƙare.
Hajiya Salamatu ta ɗauki jotter da kuma bironta sannan ta miƙe tare da wayarta ta shiga ciki tana barin jug ɗin lemon anan, kuma shigarta kenan bata ko yi minti biyar ba, wata ƴar aikinta mai suna Sadiya ta shigo, ta durkusa har kasa tace.
"Hajiya kinyi baƙo, yace wai mai karbar kaya ne shi yasa maigadi ma ya barshi ya shigo."
Ta ɗan kalle ta tsawon wasu sakanni tana son tuna wadanda suka yi alkawari dasu a yau cewa za'a zo a karɓi kaya, bata tuna ɗin ba don haka sai kawai tace.
"Je ki shigo dashi."
Ta tashi ta juya ta fita, idonta yabi ta da kallo har ta fita daga ƙofar falon nata da yake na biyu a jerin tsarin gidan.
Minti guda bayan haka Sadiya ta dawo, biye da ita Wani ne da bata ga fuskarsa a karo na farko ba kasancewar ya saka riga irin ta sanyi mai hula ya rufe kusan rabin fuskar tasa, don haka bata sallami Sadiya ba ta tsaya tana kallonsa, idonta akan kofin lemonta wanda ta baro a waje dake rike a hannunsa yanzu, kuma kafin tayi magana yasa hannu ya cire hular zuwa baya, a lokaci guda fuskar Awwalu ta baiyana a gabanta.
Yana murmushi ya kai kofin bakinsa ya kurɓa, sai kawai ta ɗagawa Sadiya hannu alamun ta sallame ta, Sadiyar ta juya ta tafi shi kuma ya karaso ya zauna a kujerar dake gefen tata.
"Me ya kawo ka wajena Awwalu?"
Ta tambaya fuskarta a hade tana kallonsa, da murmurshi a fuskarsa ya sake kurbar lemon sannan ya taso ya fuskance ta sosai yana rike kofin da duka hannayensa biyu.
"Ni ba mutumin banza bane Hajiya, na san ƙawarki, na san Kilishi tun bata da komai a duniyar nan sai ku biyu ke da ɗayar da bata magana Saratu... Yau sati guda kenan Kilishi bata kira ni ba, tun bayan da na karbo mata wannan hodar a Lagos, don haka dole na san akwai abinda yake faruwa kuma na san ba zan sami bayani a ko'ina ba sai a wajenki ko kuma wajen wannan ɗayar yarinyar da ta shigo da ita cikin al'amarin.
Don haka zuwa nayi ki gaya min ta inda Kilishi ke shirin kashe ni..."
Hajiya Salamatu ta kalle shi tsawon sakanni, cike da mamakin yadda akayi yasha jinin jikinsa game da Hajiya Kilishin tunda ta gaya mata cewa bata bashi wata dama da zaiyi tunanin cewa tana shirin juya masa baya ba... Kuma ko mutumin da ta saka ya kusance shi mai suna Sadik bai bada damar da zai zarge shi ba har yanzu. Sai kawai ta haÉ—iye yawu a makogwaronta sannan ta girgiza kanta.
"Ban san komai ba Awwalu, ka tashi ka fitar min daga gida."
Ta ƙarasa tana nuna masa hanyar kofa, sai kawai ya saje wani murmushin yana kallonta, ya girgiza kansa sannan ya sake kai kofin lemon bakinsa, wannan karon ya shanye shi tas! Sannan ya ɗago ya sake kallonta.
"Na gaya miki ni ba mutumin banza ne bane Hajiya, ina da abinda zaki miko min Hajiya Kilishi yanzu ba sai anje koina ba."
"Me kenan?"
Ta tambaya tana kallonsa cikin ido. Ya sake wani murmushin yana kallonta cikin ido shima kafin bakinsa ya sake motsi.
"Kina da labarin inda É—anki yake?"
Mamaki ya bayyana tar a fuskarta, mamaki irin wanda ke sauka a fuskar mutum lokaci guda, ba shiri bakinta ya furta.
"Wane É—an nawa?"
Awwalu yana sake wani murmushin da shi kadai ya san ma'anarsa kafin yace.
"ÆŠan da kika haifa tare da mijinki na farko, wanda ya mutu a asibiti ranar da kika haife shi!"
***
_Ku gaya min me yake shirin faruwa ne?_
_Me Awwalu ke shirin haddasawa tsakanin aminan guda biyu?_
_Me ya faru a wancan lokacin?_
_Me Amma ke shiryawa game da tsarin Hamida?_
_Su Ma'aruf zasu sami Awwalu kuwa?_
_Ta yaya kuke tunanin faÉ—owar Kilishi zata fara?_
_Gashi tana ta lisaafo wasu sababbin tsarikan...😅_
_And yes! BabyDoll think they are Pregnant!😃.... Ta yaya ake ɓoye ciki ne wai😅?_
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:56 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©�AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*15*
*Ina mika ta'aziyyata ga al'ummar musulmi na rashin babban malamin da muka rasa a yau, Dr Ahmad Bamba BUK. Allah ya jimansa ya kyautata namu zuwa Ameen.*
~~~~
Awwalu ya cije lebbensa, kansa yana gyadawa... Gyadawar da shi kansa bai san yana yi ba, idanunsa sun canja, dun cika kuma sun yi fayau, suna tsaye akan fasashshen gilashin kofin dake gabansa, kofin da ya tarwatse tun daga lokacin da Hajiya Salamatu ta feÉ—e masa biri har wutsiyarsa game da dukkanin shirin Kilishi akansa.
"... Haukata take shirin yi Awwalu, tace zaka ƙare rayuwarka ne kana biyan bashin abinda kayi niyyar yi mata, ta shirya komai tare da abokin ka Sadik, zai saka maka maganin bacci ne a cikin wani abu da ka sha ka fita daga hayyacinka zasu ɗaure ka, akai ka cikin gidan gonarja da yake Janguza, anan zata je ta same ka, zata yi maka bayanin komsi idan ka farka sannan zata saka Sadik yayi maka wasu allurori a gabsn idonka, tace guda takwas ne, suna nsn tayi odar su zuwa jibi zasu iso, kuma bana tunanin zata bata wani lokaci idan har sun iso din, don tana da tarin wadu abubuwan da zasu yi bayan naka..."
A lokaci guda yaji wani abu na cika idonsa, kuma kafin ya lissafa dumin hawayen dake tahowa ya shiga saukowa kan kuncinsa... Yana jinsu, yana jinsu duna fitowa wani na bin wani, cikin gudun dake son kwatantawa da yadda zuciyarsa ke masa a wannan lokacin, cikin gudun da zaiyi daidai da rawar da yatsun hannayensa ke yi a gabansa.
"Babu abin hawaye anan Awwalu, abinda kuka yi kai da ita yafi karfin hawayen a wasu zukatan, ko ka manta suma wadancan mutane ne kamar ku?"
Hajiya Salamatun ta tambaya tana kallonsa kai tsaye a gabanta. Sakanni kusan biyar kafin ya girgiza kansa a hankali.
"Baki san komai ba Hajiya, baki san abinda nake ji ba, ba zaki iya kwatanta zuciyata ba watakila sai kin ji naki tukunna...Kilishi ta cuce ni, ta cuci dukanninmu, ta cuci tarin al'ummar da har yau bana hango kwakwkwaran dalilinta na yin hakan, na dade da dawowa daga rakiyarta, na dade da nadamar abinda son kuÉ—i na ya jawo min, shi yasa na daÉ—e da fara gyara rayuwarta.
Ba tun yau ba na san Sadik yaron Kilishi ne, na san ita ta aiko shi ya kusance ni tun daga lokacin da ta kula na fara canja mata, ina sane na biye masa na ja shi jikina kamar yadda take so kuma nake gaya masa dukkan sirri na, ina sane na gaya masa cewar na shirya kwace dukiyar da take tarawa kuma na tara hujja ta akanta, ina sane na gaya mata hakan don in san irin tunaninta akaina.
Amma ba wannan ne shiri na ba, don ko kudin da nake samu a wajenta na dade da daina cin su, suna nan a banki ina tara su don na san ba halali bane, bayan na gama karatu na sami aikin koyarwa a wata makaranta, da albashi na nake rike kaina bana taba wadannan kudin ko kadan.
Kuma nayi niyyar kawo karshen komai ne saboda na gaji, shi yasa na gayawa Sadik wannan maganar don in san in tsayar da abubuwa a tsakaninmu kuma in kawo karshenta. Kilishi ta cuci tarin mutane a duniyar nan Hajiya, ta cuci al'umma ta hanyar da bana tunanin ubangiji zai ƙona ta a wuta iri daya da ta sauran mutane, tayi abubuwan da idan ina tuna su a cikin kaina, na kanyi kokwanton idan har ba wani ɓangare ne na shaidan ya sauko duniyar nan ba."
Ya juyo ya kalle ta a hankali, hawayen dake fitowa a idanunsa sun tsaya, sai shatinsu daya rage akan fuskar tasa.
Hajiya Salamatu kallonsa kawai take yi da abinda ba zata iya fassara shi ba a cikin kanta, duk abinda yake faÉ—a game da Kilishi ta sani, ba tun yau ba ita kanta ta sha wannan tunanin a cikin kanta, tasha fada mata hakan ma cikin magana, amma daga wannan tunanin zuciyarta bata kara komai, tana É—aukan komai dinne a matsayin labari kawai, bata jin wani emotion ko feeling na tausayi ko kuma na jin ciwon abun a zuciyarta, zata cigaba da harkokin ta ne kawai kamar babu wani abu da ya faru.
Don haka a yanzu ma ba wani abu taji ba, ita ba ta wannan take ba, zuciyarta na rawa ne tare da kuma hankoron bayanin da Awwalun ke shirin bata, bayanin da yayi mata alkawari kafin tayi abinda take jin kamar tasa hannu ne ta kashe aminiyarta tata a gabansa.
Kuma har yanzu zuciyarta bata gama kokwanto ba, bata gana kokwanton cewa idan har bs zata dsuki nasa bayanin ta kai mata ba, don Kilishi kamar wani barin ta ce, bata taba tunanin akwai wani abu da zai sa ta iya sarayar da sirrinta cikin sauki haka a duniyar nan ba, amma idan ta duba ba saukin bane, babu sauki a cikn soyayyar uwa ga danta, ga abinda ta haifa ko da kuwa bata taɓa tunanin da wanzuwarsa anan duniya ba.
Awwalu yasa tafin hannunsa duka biyu ya share hawayen fuskarsa sannan ya sake kallonta.
"Na san har yanzu kina kokwanton ki dauki maganata ki mayar mata, idan na gaya miki naki bangaren labarin, kwalwarki zata fahimta, watakila ko kadan ne, zaki ji irin abinda naji a zuciyarki, watakila hoton Kilishi zai iya canjawa a zuciyarki da siffar da kike kallonta."
Kuma bai bari ta ce komai ba ya cigaba da cewa.
"Shekaru talatin da hudu da suka wuce idan baki manta ba a lokacin kika yi aurenki na farko, watanni kadan da kuka kare karatun sakandirenku, ke kika fara aure a cikin ku ukun, kika auri Alhaji Ibrahim Shanawa, mai kudin da kowa ya sanshi a wannan lokacin.
Kuma a sannan ne amincina da Kilishi ya fara, don kamar yadda kika sani ni almajirin kakarta ne inda ta taso, a gidan nake aiki ana biyani da kuma bani abinci. Mun yi sabon da a wannan lokacin ta ksn gaya min yan kananun damuwarta, kuma tun daga lokacin auren naki, da taga irin kudin da aka kashe da kuma gidan da aka kai ki ta fara shiga damuwa.
Ta gaya min cewa duk a cikin ku ukun itace iyayenta masu karamin karfi, ta gaya min sanadin abotakar taku ma ya samo asali ne daga taimaka mata da kuke yi ta hanyar kudin makarantar da kuma sauran abubuwan buƙata, saboda haka tace min tun a wannan lokacin tayi alkawarin samun dukiya itama,ta sa a ranta cewa zata yi kuɗin da zata kere ku duka, amma a lokacin sai gashi bata sami komai ba ke kin taka wasu matakan nasarar kala-kala.
Taji zafin hakan a lokacin sosai ta hanyar da sai da ya zama a kullum tsakani na da ita bamu da wata hira sai taki, har ta kai tana gaya min cewa zata iya komai don ta tsayar dake daga cigaba da samun nasarar da tafi tata.
A haka har lokacin da kika sami ciki, zan gaya miki tayi baƙin cikin da duk duniyar nan bata iya nunawa kowa sai ni, kuma wannan shine mafarin lokacin da Kilishi ta fara jawo ni cikin zunubanta, a irin kuɗin da take samu a wajenki tayi min alkawarin wani kashi idan har zan taimake ta, na yarda ba tare da na san abinda take shirin yi ba sai a watan da zaki haihu, ta same ni ta gaya min cewar ba zata iya jurar ganin kin samu magajin a wannan gidan ba, don haka tana son mu san yadda zamu yi mu kashe jaririnki bayan kin haihu kuma tun a asibitin.
Sai dai bamu sami wata mafita ba har zuwa ranar da kika haihun, ranar da aka kira ta cewa kina asibiti, a wannan ranar ne Kilishi ta sami mafitar da ta dade tana nema, bayan mun isa asibitin ni da ita ta sami hadin kan wata Nurse da ta yarda ta musanya miki dan da kika haifa da wani matacce na wata mata mai tabin hankali da wasu mutane suka taimaka suka kawo ta asibitin ganin tana nakuda.
Ta shaidawa mutanen cewa dan matar ya mutu kuma za'a bayar a binne shi a asibitin sannan ta dauko gawar jaririn ta kawowa mijinki da kuma yanuwanki, dan da kika haifa kuma ta danka shi a hannun Kilishi a blye ba tare da kowa ya gansu ba. Idan zaki tuna Kilishi bata asibitin a wannan ranar da kika haihu.
Ni da ita muka hayi mota muka fita har bayan gari tare da jaririn, a wannan wajen ta dage cewar mu kashe yaron, amma sai tausayinsa ya kama ni, ganin yadda aka dauko shi daga haihuwa, jikinsa duk jini don ko lokacin goge shi ba'a samu sosai ba, ana miko wa Nurse din shi bayan ta faki idon mutane ta canja shi da wannan mataccen, amma duk da haka baya ko kuka har muka isa bayan garin nan.
Saboda haka da kyar na shawo kanta ta bani yaron nan ta fasa kashe shi, nayi mata alkawarin zan dauke shi zuwa wajen da babu wanda zai taba sanin daga ina yake balle kuma asalinsa. A wajen ta bani kudin mota muka rabu, sai na kora wani abokina da yake almajiri shima na shaida masa komai,sai yabani labarin wata kanwar mahaifiyarsa dake aure a wani kauye yace min babu shakka ya san zata karbi yaron, fon haka muma tafi tare dashi.
A tasha muka sayi madarar jarirai na samu na bawa yaron da kyar, sannan muka hayi mota guda zuwa wani kauye a hanyar Kaduna, wani kauye da ake kira da Garun Albasu, amma yanzu ance sunansa ya canja zuwa Yakura, anan muka sami matar kuma kamar yadda Ila ya shaida min ta karbi yaron babu wani musu, nayi godiya sosai na bata kuÉ—i daga na hannuna sannan muka juyo.
Bayan na dawo na jinjinawa Kilishi komai kuma ta yaba min, daga wannan ranar ban sake komawa ƙauyen nan ba, ban sake tunawa da yaron ba sai bayan shekaru biyu, lokacin da naje wani aiki da Kilishi ta tura ni a Kaduna.
Lokacin ne naje har gidan matar, aka shaida min cewa ta rasu shekara guda da ta wuce, na tambayi zancen yaron sai aka ce min babu wanda ya sanshi, sai da nayi bayani sannan da kyar aka sami wadda ta shaida min cewar tun a washegarin ranar da na kawo shi aka sami wasu mutane da suka zo suka tafi dashi Abuja, da na ji haka sai kawai na share zancen na baro kauyen kuma ban kara bi ta kansu ba. Amma ina da tabbacin cewa da na kara bincikawa tsaf zan iya sanin inda yaron yake a Abujan."
Awwalu ya kai ƙarshen dogon bayanin yana kallon fuskar Hajiya Salamatun da ko sau daya bata yi kokarin katse shi ba, kallonsa kawai take ui da idanunta da har yanzu basu canja ba, basu canja daga yanayin da suke tun a lokacin da ya fara magana ba har zuwa yanzu, kallonsa take yi kamar kalma guda kawai ya furta tana jiran ya fara bayanin ne.
Amma a cikin kanta hotuna ne kawai suke wucewa, hotuna masu tarin yawa, tun daga wadannan shekarun da Awwalun ya dauko, lokacin da ta haihun aka shaida mata cewar ta rasa danta, lokacin da ta rike gawar yaron a hannunta, lokacin da take jin wani daci na sauka daga makogwaronta yana mamaye dukkanin jikinta, har lokacin da aka raba ta da abinda take tunanin shine natan, da yadda Æ´anuwanta suka taya ta wannan bakin cikin da fuskar Kilishi da tafi kowa nuna alhinin hakan,da irin hidimar data sha akanta don ganin ta dawo daidai.
Da yadda jama'a hatta ysnuwanta suka dinga yabawa abotarsu, da yadda bayan shekaru biyu ta kamu da wata matsananciyar rashin lafiya bayan tayi barin wani cikin, rashin lafiyar data taba mata mahaifa, da hoton fuskar likitsn dake yi musu bayani a wancan lokacin cewa da wuya ne idan har zata sake hsihuwa a rsyuwarta.
Da tarin rigingimun da tasha da wannan mijin nata kafin ya sake ta da cewar ba zai zauna da juya ba, wani abu da ya zamo mafari kuma tushen tsanar maza a zuciyarta har ta kai duka aure biyun da tayi bayan nan ta kasa tsaida zuciyarta wajen hakurin zama musamman da mijinta na ƙarshe Alhaji Shamsu. Gaɓar da har ta kawo ta cikin wannan rayuwar da take kai, rayuwar da tun iyayenta na da rai suke kokarin hana ta har suka koma ga mahallincinsu.
Ashe duk wannan abin, aminiyarta ce sila? Kilishi ce silar da kalolin rayuwarta suka bambanta da buri da kuma tarin mafarkanta na zama uwa kuma mata a gidan mijin da zata taso da nata ikon itama, ashe zalunci da kuma cin amanar Kilishi da kullum take yiwa hangen nesa ba'a kan kowa ya fara ba illa ita?
A lokacin ne ta rufe idanunta a hankali, tana jin zuciyarta na bugawa, da wani irin bugu da bata danganta shi da komai ba sai na cewar ita uwa ce yanzu, ita uwa ce... Ta zama wannsn uwar da a kodayaushe taje mafarki, Allah ya mallaka mata wannan dsnar ya dawo mata da matsayin da kubce daga hannunta tsawon shekarun da taje jin nauyinsu a kirjinta. Kuma abinda ta sani a wannan lokacin shine ko zata ga dan nata ko ba zata ganshi ba, zata yi abu guda daya ne da take jin kamar Allah ya bar mata numfashinta tsawon wannan lokacin don ta zama sanadinsa.
_... haka kurum nake jin cewa kamar jibin nan ba zata karasa ba wani abu zai faru._
Kalaman Kilishi a dazu da suka yi waya ya dawo cikin kanta, tabbas ta yarda da kalaman Awwalu, ta yarda Kilishi kamar wani rabin shaidan be ya fado duniyar nan, jikinta ya bata wani abu zai faru tun kafin Awwalu ya shigo gidan nan tun kafin ita ta san komai.... Abinda kawai bata sani ba shine ashe ta hanyarta din, ta hanyar ita din da take gayawa karshenta zai fara.
Zaren labarin ya fara ne tun daga wannan ranar da tazo cikin gidan nan take gaya mata sauran tsarukan da take shiryawa, tun daga wannan lokacin da suke wannan dariyar take jin zuciyarta na yin wani iri akan al'amarin aminiyar tata duk kuwa da a sannan tana jin cewa ba zata taɓa iya tona mata asiri ba, sai gashi ba'aje ko'ina ba a wannan ɗakin, a wannan ɗakin dai da suka zauna tare nan ɗin shi zai zama mafarin ƙaddarar da bata taɓa lissafawa da ita ba.
"Na san da wuya ne ki yarda dani..."
Muryar Awwalu ta cigba da magana, sai kawai ta girgiza kanta a hankali tana katse shi, kuma tare da ta buÉ—e idanun nata ba, kalamanta bakinta suka fito, sautinsu ya fito da wani amo a hankali amma kuma wanda ya karaÉ—e falon...
"Ka kaini muje ƙauyen Awwalu, idan har na tabbatar da abinda kake faɗa, zan taya ka mu tonawa Kilishi asiri a idon duniyar nan...!"
Ta faÉ—i haka a daidai lokaci guda da adadin mintunan kiran dake tafiya a cikin wayar Hajiya Salamatu ya katse dib!
***
*No 38 Ramie Street, Nassarawa GRA, Kano.*
Karo na biyar kenan da Ruƙayya ke sake kiran nambar, amma da ya tafi kamar zai shiga sai ya katse kawai, ba sai wani yayi mata bayani ba, ta san ya rufe layinta ne daga shiga cikin wayar tasa, tunda dazu ta gwada da wani sabon layin ta kuma ya shiga, sai dai ba'a dauka bane.
Sai kawai tayi wulli da wayar kan gadon da take kai, ta tafi kamar zata fadi zuwa É—aya karshen sai kuma ta tsaya bata karasa ba, hannunta ya dauko daya wayar tata dake gefe, ta sake lalubo nambar Jawad din a ciki, har zata sake danna nambar da niyyar kira sai kuma ta tsaya, wata zuciyar ta gaya mata cewa babu dalilin da zata cusa masa muryarta idan har ya nuna cewa baya so, sanin cuwon kai a rayuwa ma wani abu ne.
Don haka ta nufi bangaren rubuta sako, cikin abinda yake kasa da minti guda ta rubuta dalilin nemansa da take yi. Sakon ya tafi a daidai lokacin da mshaifiyarta ta turo kofa ta shigo dakin.
"Wani abu kike yi?"
Ba shiri ta girgiza kanta tana kallonta, sai ta gyada kanta sannan ta karaso ciki,da kowanne taku da take yi Ruƙayya na jin zuciyarta na bugawa sanin cewa bata da amsar abinda tazo nema din.
"Yazun nan muka gama waya da Hajiyan Sudan, ta gaya min cewa ta gama shirya komai tafiyar taku jibi ce."
Cewar Hajiya Nafisan va tare da ta zauna ba, daga kan gadon daga inda kafafunta suka lume gabadaya a cikin lallausan bargon Rukayya ta daga kanta sannan tace.
"Nima ta gaya min Maamah, É—azu da safe ta kira ni a waya ta ce min tayi settling komai sai tafiyar mu kawai."
"To kin fito da kudin?"
KuÉ—in. Abinda take gudu kenan, tambayar da take gujewa kenan, kwanaki hudu kenan da mahaifiyar tata ta tuna mata da wasu kudi da ta taba bata ta ajiye mata a bankinta, kudade ne masu yawan da a yanzu ta manta ainihin lissafinsu, sai skayi rashin sa'a a lokacin ta samu matsala da bankinta na ajiyar kudi, don haka ba tare da tunanin komai ba ta bawa Jawad da cewar shi ya saka a É—aya daga cikin bankunansa zuwa sanda zata tashi nema.
Ya karba din tun a lokacin kuma ya ajiye, sai dai daga shi har ita sunyi mantuwa da hakan ta sigar da bata sake tunawa ba sai a yanzu. Sai a yanzun da mahaifiyarta ta gaya mata cewa ta fito da kuÉ—in dasu zasu yi komai, shi yasa a yanzu bata san ta yaya zata fara yi mata wani bayani ba da ta san ba fahimta zata yi ba, don haka ta gyaÉ—a kanta da sauri sannan tace.
"Anjima zan fita Mamah, anjima zan dauko su gabadaya."
Sai ta gyada kanta alamun ta fahimta sannan tace.
"Yau Daddynku zai dawo kin sani, ki saki jikinki ki nuna masa kin hakura a yanzu da zancen Hamidan, idan ba haka ba kuma zai É—auki matakin da zai lalata mana al'amari kin sani. Kuma kar ki sake ko da wasa ki bari ya san da zancen tafiyarki, ni na san abinda zan ce masa."
Sai tayi kokarin fito da wani guntun murmushi daga siririn lebbenta sannan ta gyada kanta.
"Ba zan yi komai da zai kawo matsala ba Mamah kin sani, idan nayi haka na san kaina na ɓata."
"Sannan duk wanda ya kira ki da zancen Hamida kice musu kawai ta fara zuwa wajen mahaifinta ne hutu. Kar ki kara komai daga haka."
"Me yasa ma sai an gaya musu hakan Maamah, ba dai daga ɓangaren Daddy bane masu tambayar, ni babu wayar wanda zan daga."
Hajiya Nafisa tace.
"Na gaya miki ne ko da zaku yi magana da wani..."
Bata karasa ba wayar hannunta ta shiga kara, don haka ta dauka ta kara a kunnenta sannan ta juya ta fita daga ɗakin taiba magana, Rukayya ta bi ta da kallo, wani abu ya zarce a makogwaronta, ta san halin mahaifiyarta sarai, ba son dukkan wata mu'amala da ta danganci Ma'aruf take ba, kawai tana yin komai ne saboda ita kawai don haka idan har zata yi saken da za'a kasa samun kudin nan akan lokaci,komai zai iya tsayawa m, zata iya yin wasa da damarta ta ƙarshe a yanzu.
Ta jawo É—aya wayar tata ta duba tarihin asusun da take dashi a yanzu na banki, kudin ciki basu fi rabin abinda Hajiyan Sudan ta nema ba, babu mai bata kudi a cikin Æ´anuwanta ta sani, Ashraf ne kadai zai iya kallonta da wannan rahamar amma shima a yanzu wannan fetsararriyar matar tasa da baya yin komai sai da shawararta ba zata bari ba.
A wajen mahaifinta ne kadai zata iya samun wani abu amma shima ta sam wanda bai taka kara ya karya ba, don tunda yayi ritaya ya shiga hsrkar buga-bugar kwangila baya son fitar da kudi sam wanda hakan halinsa ne tun a baya, kawai suna da wadatar da ba'a ganewa ne... Kuma hakan ba daya daga cikin wani babban dalili da yasa mahaifiyarta ke dagewa kan ta auri mai kudi, don su samu ta wani ɓangaren tunda ita mai son busasha ce.
Ta dafe kanta da duka hannayenta biyu, yatsun hannayen nata na shiga cikin gashin kanta, Jawad ya sha bata kudi, yasha bata kudin da tana tarawa ta san ta wuce wannan lissafin a yanzu, amma bata karba din ne da hujjar cewa ba lada take nenya a wajensa ba, don ta yarda da cewar mu'amalarsu na tafiya ne saboda haka take so, saboda ita take amfani dashi ba shi ba, saboda kuma bata son ya kalle ta da wani ƙasƙanci ko na kaɗan.
Tayi ajiyar zuciya a hankali tana sake kallon text É—in da ta tura wa Jawad, ita kanta ta sani a bayan wannan neman da take masa kuma akwai wani abu kamar damuwa, damuwar da bata san dalilinta ba, a baya ta danganta hakan ne da shirunsa kawai, amma idan har zata yiwa kanta adalci ta san akwai wani abu ksmar kewsrsa a can kasan ranta, kawai tana danne shi da tarin dalilin da take bawa kanta a kullum.
Sai kawai ta mike tsaye iskar dake shigowa daga winfon dakin na kada lallsusar rigar baccin da 'ke manne a jikinta, idonta ya ksi ksn siffarta acikin mudubin ɗakin, waye zai taɓa cewa tayi aure har da haihuwar ƴa? Ai ko don kyawunta ta san ba zata taɓa asara ba, shi kansa Ma'aruf ɗin bata son zubar da ajinta a wajensa ne shi yasa ba za ta tunkare shi ba.
Taso ganinsa lokacin shari'ar nan amma tunda har abubuwa sun canja, jiran nasa ne a yanzu, shi zai jira har zuwa lokacin da zai kasa lissafa asarar da yake yiwa kansa, tayi murmushi a hankali, siraran lebbenta suna talewa, da ta samu Ma'aruf ko meye a cikin tata zuciyar zai manta da Jawad shima.
Sai kawai ta kada kanta tana sake yin baya da gashinta sannan ta nufi bandakin dake cikin É—akin.
***
*Abuja.*
"Bata da lafiya kamar yaya?"
Jawad ya tambaya tsaye daga kofar É—akin, yana kallon wata yarinya mai suna Kristy dake tsaye tana gaya masa hakan.
"Eh Yallabai, baya da lafiya tun jiya bai fita ba, as a matter of fact ma snce ne yau zata tafi gida."
Yarinyar da ta fadi haka cikin gurbatacciyar hausarta jin ceqar tambayar da yayi matan da Hausa ne, ya cije lebbensa yana kallonta, wani tunanin ya gifta a cikin kanta na sakanni biyu, tun jiya bai ganta ba ance masa tana aiki sai wata banzar inyamurar aka aiko ta kawo masa abincin da bai ci ba don mukullin mitarsa ya dauka ya bar gidan kuma bai dawo ba sai dare, a yau ya farka ne babu tunanin komai akansa sai na son ganinta, to kuma ta yaya zai zo ace bata da lafiya? A cire ma maganar tafiyarta a gefe, wannan bai san dashi ba kuma babu ta yadda za'ayi ya faru.
Don haka bai jira komai ba sai kawai ya gyaÉ—a kansa sannan yayi gaba zuwa hanyar dakin dake bayanta.
Ba shiri yarinyar ta juya ta bishi da kallo, idanunta na zarewa da tsananin mamakin ganin ya nufi hanyar kofar shiga dakunan wajen, idan aka cire lissafin cewa tunda take bata taba ganin wani dan gidan walau mace ko namiji ya shigo bangaren nasu na masu aiki ba... Babu ta yadda kuma za'ayi ace an samu wani da ya shiga har cikin dakunan nasu... Saboda haka da ita da sauran Æ´an aikin dake harkokinsu a harabar wajen, suka bi bayansa da kallo har sanda ya taka kafarsa zuwa ciki.
Wajen dogo ne yana É—auke da kofofin dakuna kusan biyar don haka yaja ya tsaya ba tare da ya san inda zai shiga ba, muatan dake wajen duk suka tsugunna a lokaci guda suna gaishe shi, idanunsu na nunawa da mamakin da ba sai sun furta.
"A ina Zainab take?"
Ya tambaya kai tsaye cikin harshen turanci don ya san babu wani karin bayani, du duka sun san wacece Zainab din tunda babu wata bayan ita, ta farko ce ta nuna kofar dakin dake gabansu tana fadin.
"She's inside here sir..." (Tana cikin nan ranka ya daÉ—e.)
Zainab na kwance akan katifarta daga can karshen dakin, ta kudundune a cikin hijabin sallarta, jikinta yayi zafin da babu makawa ta san zazzaɓi take yi, amma ko kaɗan ta san wannan ba damuwarta bace, taraddadin dake cikin ranta daban ne, kalaman da Hajiya Mardiyya ta kira ta jiya ta gaya mata su ke ta yawo a cikin kanta...
"Babu wani abu kika yi min ba Zainab, Allah ya sani naji dadin zama dake da kuma aikin ki. Tafiya zanyi zuwa wata kasar kuma zan debe tsawon watanni shi yasa nake ganin ya dace ki koma gida, tunda babu wanda zaki zauna kina yiwa aiki, kuma babu amfanin zamanki cikin kabilun nan, gobe zan saka direba ya mayar dake har garinku, ga kaya nan cikin wancan akwatin duk naki ne, ga kuma kudi nan isassau zan bawa Hajiya Mairo da ta kawo ki ta kaiwa iyayenki, nace ta roke su ayi miki aure Zainab, kar su sake tura ki wani wajen gwara ki tafi dakin mijinki ke ma ki samu kwanciyar hankali...."
Tana tuna kowacce kalma da ta faɗa har yanzu a cikin kanta, tana jin nauyinsu da kuma irin razanarwar da suke yiwa zuciyarta... Komawarta gida a yanzu kamar yana nufin zuwa karshen rayuwarta ne ta sani, babu ta yadda za'ayi mijin mahaifiyarta ya yarda cewa ba wani abu tayi aka dawo da ita ba, idan kuma har yaji wannan saƙon na cewar ayi mata aure ta tabbata za'ayi ɗaya ne cikin biyu, ko dai ya karɓe kuɗin ya sake tura ta wani wajen ko kuma yayi mata auren da wanda ranta ba zai taba so ba kuma a wajen da zata wahala.
Tana kwance tana hango fuskar mahaifiyarta, Allah ya sani bata san me ta fito nema ba, ta san ba wani yanci ta taho samu ba amma haka kurum zuciyarta na jin cewa kamar zata koma ne da wani abun da zata samawa mahaifiyar tata sauki, kamar zata koma da wani abu da zai cire su daga kangin wahalar da suka faÉ—a tun bayan mutuwar mahaifinta... Sai gashi mafarkinta dama burin nata yana shirin bajewa a iska, ba zata koma da komai ba sai wannan jakar da Hajiya ta nuna mata, jakar da ta san ko meye a ciki bai kai ya canja rayuwarsu ba.
Daga yadda take kwancen tana jin hayaniyar sauran matan dake zirga zirga a waje, ita kaɗai ce a cikin dakin, kuma tun jiyan ƴan kadan ne a cikinsu suka kula da yanayinta kuma tunda suka tambaye ta tace musu bata da lafiya shikenan babu wanda ya kara bi ta kanta, amma gwara su sau dubu akan ɗaya ɓangaren data baro, inda anan anfi samu wanda suka tsane ta kuma suke mata mugunta da gaske.
Ta rufe idanunta a hankali tana jin yadda yadda zuciyarta ke rawa a jikinta, taradaddin barin wajen ne kawai ke kamata, yana ƙarawa akan halin da take ciki. A lokacin kuma taji muryoyinsu daga waje suna gaisuwa, kowa yana fadin barka da zuwa yallabai, don haka ta bude idanunta da sauri cike da mamakin da bsi je koina ba wanda idanunta ya sauka akan mutumin da ya shigo cikin dakin, zuciyarta ta buga a ƙirjinta.
Jawad, Jawad ne tsaye daga bakin kofar taba sanye da wasu kaya bakake, irin kayan da yake sawa a kullum wanda ba manya ba, wadanda suke zama a jikinsa daidai, kansa har da hula wadda ta dace da kayan, sannan a hannunsa akwai mukullin motar kamar fita zaiyi, Allah ya sani tun a jiya ta manta da lissafinsa kwata-kwata, taraddadin da take ciki har shi ya haÉ—a ya shanye baki daya.
Kafin tayi wani yunkuri ya karaso har inda take, kafafunsa da takalmi na bi ta kan katifun sauran Æ´an dakin da basa nan, yayin da gefen idonta ya É—auko mata yadda wasu suka shiga lekowa ta kofar dan karamin dakin wani abu da ya haddasa rikicewarta a lokaci guda don ta san ta riga ta shiga uku kenan a wajen mutane da maganganu kala-kala, jikinta ya shiga rawa a karkashin hijabin yayin da idanunta suka zare a kansa, amma babu alamar ya kula da hakan ya tdugunna a daidai gabanta idanunsa na kare mata kallo.
"Me ya same ki?"
Shine abinda ya fara faɗa kafin ƙamshin turarensa ya zagaye ta, kuma duk da rikicewar da take ciki, sai da amon muryar tasa yasa taji wani abu kamar tayi kewarsa tsakanin jiya da yau din kawai, don haka gaisuwar da take da niyyar yi bata fito ba, sai kawai ta girgiza kanta tace.
"Babu komai zazzaɓi kawai nake yi... Na, na warke ma, kawai ban fito bane yau shi yasa ban kawo maka abincin ba...."
Bayanin da ta fara cikin rawar murya ya katse a lokaci guda da Jawad yasa hannunsa akan wuyanta, sanyin fatarsa ya ratsa har cikin kanta, jikinta ya tsaya cak, numfashinta ya ƙame a cikin wuyanta, ya sake motsa hannun nasa yana ƙara zura yatsunsa cikin wuyanta...
"Wane magani kika sha?"
Muryarsa ta sake tambaya, tana kokarin dawo da ita cikin haiyacinta, sai kawai ta haÉ—iye wani abu a makogwaron ta a hankali sannan ta girgiza masa kai, bai dauke hannun nasa ba ya cigaba da kallon ta da idanusa daue kara rikita ta sannan yace.
"Maamah ta san baki da lafiya?"
So take yi ta tashi amma ko yaya bata son yin motsin kar hijabin jikinta ya zame, rigar dake jikinta yar ƙarama ce, irin ta bacci da ƙanwarsa ta bata, da ita ta kwana sai da taji sanyi da asuba sannan ta jawo hijabin ta lulluɓa, don haka sai ta sake girgiza kanta a hankali idanunta na kallon kasa.
Kamar ba zai É—auke hannun nasa ba sai kuma ya cire shi a hankali m, tana jin yadda yatsun nasa ke barin fatar ta.
"Taso mu tafi."
Ya fada yana miƙewa kuma maimaikon ya juya sai ya tsaya akanta yana kallonta, kallon da yasa ba shiri ta mike tana kokarin riko hijabin nata kotawanne bangaren amma saboda yadda jikinta yake rawa kafarta ta take shi garin mikewa ba tare da ta sani ya kuwa tafi kasa gabadayansa.
Zuciyar Jawad ta buga a lokaci guda da idanunsa suka gane masa kayan jikin nata, sai kawai ya juya da sauri gabaɗayansa yayin da ta koma ta zauna da sauri tana ƙoƙarin sake tattaro hijabin nata.
"Idan kin shirya ina waje."
Ya fadi hakan ba tare da ya sake juyowa ba sannan ya nufi hanyar fita, tana ji wadanda suka tsaye daga waje na yi masa a sauka lafiya, amma tsabar kunya, takaici da kuma rawar da jikinta yake yi ta kasa ko É—agowa.
Kuma fitarsa ke da wuya, abinda take jira ya faru, sauran matan nan suka shigo suka zagaye ta, masu shewa irin tasu ta ƙabilu nayi masu tsokanarta nayi, har da masu cewa ta fada musu kalar asirin da take amfani dashi suma su samu.
Zuciyarta ta sake matsewa da takaicin maganganun su, tana jin cewa da zata iya asirin, da zata samu asirin da wanda zai canja rayuwarta gabadaya zata yi, wanda zai canja rayuwarta tun daga tushe ba a rana tsaka ba.
***
"Me yasa lokacin da suka fita baki zo kin gaya min ba?"
Hajiya Mardiyya ta tambaya tana kallon wata yar aikinta dake tsugunne a gabanta.
"Ai Hajiya na zata tafiya zasu yi, don tace min yau zata koma garinsu shi yasa nayi tunanin gida kawai za'a kaita."
Ta faÉ—a cikin harshen turancinta na Pidgin, Hajiya Mardiyya tayi shiru tana kallonta ba tare da ta san me zata ce ba, sai kawai ta tashi ta mike daga falon, ta nufi cikin dakinta inda ta bar wayarta akan mudubi.
Dole ne ta takawa Jawad birki, bai isa ya tozarta ta a idanun duniya ba, bayan sun gama shawara da ƴar uwarta akan ta haƙura da yarinyar kawai ta maida ita garin su tun abubuwa basu ɓaci ba, sai kuma yazo ya fara shirin warware tufkar da take yi? Me yasa yake son rikito da duniyarta ne a kodayaushe? Me yasa ko sau ɗaya a rayuwarsa ba zai taɓa bata matsayinta na mahaifiyarsa ba?
Hannunta ya kai kan wayar tana jin zuciyarta na fitar da zafin da sanyin A.cn dakin bai isa ys kore shi ba, kuma kai tsaye hannunta ya danna nambar Jawad a cikin wajen kira sannan ta kara a kunnenta, tana jin karar bugun dake shiga cikin kunnenta kamar ba za'a É—auka ba...
"Assalamu alaikum Maamah..."
Muryasa ta shiga kunnenta a gabar da saka rai da tsinkewar kiran.
"Wa'alaikum salam... Jawad kana ina?"
"Ina asibiti." Ya bata amsa kai tsaye.
"Kai da wa?"
"Ni da Zainab, bata da lafiya Maamah kin sani?"
Wani takaici ya taso ya kara lullube zuciyar Hajiya Mardiyya, ashe da gaske ne daukanta yayi suka fita har asibiti, da taji muryarsa bayan ya É—auka sai taji kamar zai ce mata yana office ne ko kuma wani waje daban.
"Jawad a wani hurumin zaka É—auki yarinya ka kaita asibiti? Ni ban san bata da lafiya bane sai kai?"
Hannunsa ne ya tsaya daga ƙoƙarin karbar receipt din da wata cashier ke kokarin miko masa bai karba din ba kawai ya tsaya yana sauraren mahaifiyar tasa a lokacin da ta cigaba da cewa.
"Bata gaya maka cewa yau zata koma garinsu bane? Ko bata gaya maka iyayenta sun aiko suna nemanta bane ko kuma kai baka da aikin da zaka tafi yi ne?"
A hankali idanunsa suka juya yana hango Zainab din da ya bari daga can kan wasu kujeru na jira, dogon hijabi ne sanye a jikinta, kalar ruwan hoda, fitilun wajen sun haska fuskarta tar da kuma manyan idanuwanta dake ta zarewa tana kalle kallen mutane da kuma abubuwan asibiti, kamar koyaushe, kamar duk lokacin da zai ganta wani abu ya motsa a zuciyarsa, sai kawai ya girgiza kansa sannan yace.
"Bata gaya min ba Maamah, abinda na sani kawai shine bata da lafiya yau don haka a ƙyale ta, idan ta warke ni da kaina sai in kaita ta gaishe su..."
"Ba dawowa zata yi ba Jawad, aure iyayenta zasu yi mata..."
A lokavi guda shiru ya ratsa wayar a lokaci guda tsawon sakanni bai ce komai ba, wannan matar dake miko masa receipt ta fasa ta ajiye shi kawai akan tebur É—in sannan ta juya ta cigaba aikinta, idanunsa suka tsaya akan Zainab din da a yanzu take kallonsa, yanayin fuskarta na nuna alamun tambaya tana son taji idan yana so ne ta taso.
Sai kawai yayi murmushi yace.
"Shikenan Maamah sai mun dawo."
Yana faɗin haka ya kashe wayar ya maida ita cikin aljihunsa, sannan ba tare da ya sake tunawa da matar da kuma receipt ɗin ba yayi gaba kawai, ƙafarsa ta ɗauke shi har gaban Zainab ɗin da tayi saurin miƙewa ganin ya taho.
Ya tsaya a daidai gabanta, yana kallon yadda ta sunkuyar da kanta bayan ya tsaya a gaban nata, yadda zuciyarta ke bugawa a cikin ƙirjinta tana ji kamar zata fito ne ko kuma zai ji ta, Allah-Allah kawai yake yi yace su juya su tafi gida, don duk yadda zuciyarta ta san cewa yana kyautata mata ne har yanzu tana tsoron kasancewarta tare dashi, don bata san wane irin hukunci zata fuskanta a wajen mahaifiyarsa ba idan har ta san irin yadda yake kulawa da ita.
Sai dai a lokacin da take tunanin zai fadi abinda take jira ɗin, sai wasu kalaman suka fito saɓanin hakan, wasu kalaman da suka dasa aya akan a wannan bangaren na rayuwarta.
Wasu kalaman da daga ita har Jawad din basu da masaniyar cewar tasirinsu yafi ƙarfin dukkan wani ƙalubalen da kwakwalarsu zata iya hangowa... Wasu kalaman da sune ƙarshen dukkan wata wahala da wani ahali suka daɗe suna fuskanta! Kuma wasu kalaman da sune sune karshen talalar da ubangiji ya kaddara akan wata halittarsa!
"Zainab zaki aure ni?!"
***
_Kun yarda da Labarin Awwalu?_
_Kuna ganin zai tabbatarwa da Hajiya Salamatu zancensa?_
_Me ya faru ne a cikin wayar Hajiya Salamatu? Wane kira ne kuke tunanin sai a lokacin ya katse?_
_Ku gaya min Jawad na shirin kwance tarin abubuwan da shi kansa bai san adadinsu ba..._
_Kalaman da kwakwalarsa ta yanke masa a lokaci guda suna shirin bude mana tarin abubuwan da muka dade muna jira a labarin nan... Insha Allah._
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:56 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*16*
*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka, akwai wata member ɗin group ɗin nan da ta rasa mijinta sati biyu da suka wuce, ina rokon mu saka shi cikin addu'o'in mu Allah ya jiƙansa da rahama ya bata haƙurin rashi da kuma bayan ɗaukan marayu, mu kuma Allah ya kyautata namu zuwan. Ameen.*
~~~~~
_I'm seeing the pain, seeing the pleasure...I love to hold you close, tonight and always..._
*#Tariyar baya.* *(Flashback.)*
"Na fahimci har yanzu da saura a harkar nan Kilishi, shi yasa kika ce zuciyarki ta kasa kwanciya... Amma kar ki damu, tunda kin iya da tarin abubuwan da kika shallake a baya waɗannan ma ba zasu yi miki wahala ba, ki cigaba da tsarinki kawai, ina garin nan har sai kaya na sun ƙare, don haka kar kiji komai."
Da haka wayar tasu ta ƙare. Hajiya kilishi ta mikie ba tare da ta kula da cewar bata kashe kiran ba ta fita daga dakin, kai tsaye falon ta nufa inda anan take jiyo hayaniyar da bata san dalilinta ba, ilai kuwa isarta ke da wuya ta tarad da su Zahra da Sahla tare da wasu kawayensu da suke makota su biyu suna faman bare kayan decorations daga cikin ledodinsu, kaya ne gasu nan fal-kala, sai faman ɗaga su suke yi suna kokarin ganin ta yadda za'ayi amfani dasu.
"Duk wadannan abubuwan na meye?"
Kai tsaye muryarta ta katse su ganin har ta tsaya a falon basu kula da ita ba. Dukkaninsu suka juyo a lokaci guda, ƙawayen nasu suka shiga gaishe ta yayin da Sahla tace.
"Mami, Ya Samirah ce tace mu fito mata dasu, za'ayi decoration din tarar Ya Abdurrahim ne gobe...."
"Abdurrahim!
Sunan yayi amsa kuwwa a cikin kan kilishi a take, kwata-kwata ta manta da lissafin zuwan nasa, tinda suka ui maganar da Baffa bata kara tunawa ba sai yanzu, abubuwan dake saman kanta dama cikinsa suna da yawa, kuma ta riga ta sani cewa yaron ba matsalarta bane a yanzu, ko zai dawo ne da irinsa guda dari ta sani bai isa ya tsaya mata ko a gefen hanya ba balle ya tare mata wani abun.
Don ma an samu akasi ne, kwakwalarsa taso ta taɓa tun a wancan lokacin, wannan kwakwalar tasa da tun yana karaminsa babu abinda take kange shi daga ganewa.
Tana tuna wannan ranar, tana tuna ta kamar jiya, lokacin da taje har makarantarsu ta islamiyya a lokacin, ta haÉ—a baki da maigadin makarantar, idanunta na hango mata yadda hannyensa ke cusa damin kuÉ—in da ta bashi cikin aljihunsa, da yadda bakinsa ke washewa yana faÉ—in bata da matsala ya gane yaron da take biÉ—a, yana bayanin yana kallon idanunta dake boye a bayan niqabin fuskarta, bai ko damu da sanin kamanni ko wani abu nata ba.
Har ya kawo mata yaron ta É—auke shi kamar yadda tace a motar da tazo tare da wasu Æ´an daba guda biyu da Awwalu ya haÉ—a ta dasu, don ko Awwalun a wannan lokacin bata yarda ya san abinda take shirin yi ba.
_"Kar ku kashe shi, so nake kawai ayi min abinda ƙwaƙwalarsa zata taɓu..."_
Haka ta gayawa mutanen a wancan lokacin, don bata yi niyyar kashe shin ba, kuma haka suka yi mata, don bayan ansha nema hankalin jama'ar gidan dama na malaman sa gabaÉ—aya ya tashi, an tsince shi ne yashe a cikin wani kango a sume jini na fita ta hancinsa da kuma kunnensa.
Aphasia.
Haka likitoci suka kira cutar da ta same shi, sunce gefen kwakwalar sa dake aiki da bangaren magana ne ya sami matsala sakamakon toshewar jini zuwa wajen, farkon rashin lafiyar tasa yana iya magana amma a gutsirtsire, cikin sautin da ba'a ma fahimtar abinda yake cewa duk da cewar da kankantarsa a lokacin.
Likitoci sun bada shawarar yadda za'a dinga taimaka masa maganar da yadda harshensa zai koma daidai don sun tabbatar da cewar babu wani magani kwakwara game da cutar amma da yake shi yaro ne mai zuciya, tun a lokacin yaƙi bada haɗin kan hakan, ya daina maganar ma gabaɗaya babu yadda ba'ayi ba amma haka ya taso kowa yana kiransa Kurma, don ko makarantar da yake yi a can ƙasar ma ta kurame ce irinsa.
"Mami fulawa ta kare, kuÉ—in drawer kuma sun kare su ma..."
Muryar Samirah da ta fito daga kitchen ta fada a gabanta tana dawo da ita daga tunaninta. Ta juyo ta kalle ta.
"Sati É—aya kenan fa dana ajiye kudin nan Samirah,yanzu har kin karar dasu?"
Da murmushi a fuskarta tace.
"Wallahi Mami, abubuwan ne wannan week din da yawa, kinga munyi abincin sadakar uku na jikar Mama Rabin nan data rasu, sannan ga wannan shirye-shiryen dawowar Ya Abdurrahim É—in kuma, surprise party muke haÉ—a masa tunda ya hana kowa zuwa can.."
"Amma ni duk ban san da wannan ba."
"Mami kwana biyu fa ba kya ko zama a gidan nan, kamar wani abu yana damunki shi yasa kawai muka ƙyale ki..."
Da murmushi a fuskarta sanda ta faÉ—i hakan, amma da ta san tasirin da kuma yadda suka shiga cikin kan Hajiya Kilishi da watakila bata yi wannan murmushin ba.
_.... Kamar wani abu yana damunki shi yasa muka kyale ki..._
Wannan wajen ya maimaita a cikin kan Hajiya Kilishi fiye da yadda zata iya ƙirgawa a cikin sakannni kawai, ƴarta ce wannan, ƴar da ta haifa a cikinta... Itace take gaya mata cewa sun ƙyale ta saboda tana cikin damuwa, sun ƙyale ta ba tare da sun damu su ji abinda ke damun nata ba a matsayinta na mahaifiyarsu.
ƙwakwalarta ta tariyo mata wani abu a lokacin, tabbas ba zata iya tuna rana guda da wani a cikin ƴaƴan nata ya taɓa damuwa da damuwarta ba, Ma'aruf ne kawai... Ma'ruf ne kawai ke taɓa nuna damuwarsa akanta idan har wani abu ya same ta, ko a yau ma s gajiye ya dawo yadsa ta fahimta daga muryarsa, smma ssi da ya kira ya gaishe ta ya gsya mata ya gaji ba zsi iya shigowa ba kafin ya shiga gidansa, amma a vikin yan shekarun nan ba zata iya tuna rana guda da ta taɓa ganin wata damuwa mai zurfi daga wajen ƴaƴan nata ba har kuwa waɗanda ta yiwa aure yanzu, su kan dauki lokaci basu kira ta ba sau da yawa sai dai taji su suna waya dasu Samira.
Wani abu ya wuce daga makogwaronta yana son dasa mata wani abu da ba zsta taba yarda ba, don haka sai kawai ta gyada kanta sannan tace da Samiran dake tsaye tans kallonta.
"Bari na kawo miki, har da na cefanen wannan watan ma jiya Baffa ya aiko dashi kun fita."
"Yawwa Mami, Madallah."
Abinda tace kenan kawai sannan ta juya tana gayawa su Zahra abinda zasu yi. Sai itama ta juya tana jin kamar zuciyarta tayi nauyi da abinda ya faru, amma kuma
kwakwalarta ta cigaba da gaya mata cewa hakan ba komai bane, da zarar lokacin da zata kammala komai yazo, su da kansu zasu gane gatan da ta daɗe tana yi musu, yaushe aka taɓa halittar ƴaƴan da suka juyawa uwarsu baya a duniyar nan? Shaidan ne kawai ke kokarin cin galaba akanta.
Ta isa cikin dakinta lokacin da idonta ya kai kan wayar da ta bari akan gado, mitunan kiran na da suka yi da Hajiya Salamatu na nunawa akan fuskar wayar har yanzu, mamakin yadda akayi bata kashe ba kuma itama Salamatun bata lura ba ya kamata, sai kawai ta ƙarasa ta ɗauke ta, har zata kashe sai kuma taji wani abu kamar murya na magana don haka ta kara ta a kunnenta kuwa daidai lokacin da ta jiyo muryar Hajiya Salamatun daga can ciki tace.
_...a idon duniyar nan...!"_
Mamaki ya gifta a ranta na ma'anar hakan, amma sai wani gefen tunaninta ya bata cewar watakila hirarta ce kawai da wasu mutanen tunda gidan nata baya rabo da jama'a, don haka sai kawai ta kashe kiran ta ajiye wayar akan gadon sannan ta tafi daukowa Samirah kuÉ—in.
Da ace dan adam yana da ikon dawo da lokaci baya zuwa sanda yake so, da tabbas Kilishi zata so dawo da wannan ranar kuma wannan lokacin fiye da sau dubu a rayuwarta.
***
*Ƙarfe tara na safiya.*
Amina ta kunna gas ɗin da ta ɗaura frying pan da mai a cikinsa, idanunta suka tsaya akan man har lokacin da ya fara zafi, yayi zafin yama fara shirin ƙonewa kafin ta farga ta zuba haɗin ƙwan da ta haɗa akai.
Minti talatin kenan, minti talatin tun bayan dawowarsu daga asibiti, don a É—azu da asuban nan bayan ta gaya masa abinda take tunani yace ta shirya su fita, ya kira Munaya yace tazo ta dauki Hamida zasu fita.
Tun gari bai gama haske ba ta shigo ta dauke ta zuwa cikin gidan tana bacci ma bata san me ake yi ba, kuma tana ta tambayar inda zasu je amma bai ce mata komai ba sai da suka tsaya a gaban wani É—an karamin Private asibiti da a samansa aka rubuta 24hours, (awa ashirin da hudu.).
A asibitin aka haÉ—a ta da wata Nurse bayan ya yi musu bayani, kuma minti takatin bayan hakan aka tabbatar musu da abinda suka zo nema cewar da gaske tana da cikin.
Ta sani, tunda Amma ta gaya mata ta yarda kuma tana ji a jikinta ma, amma a wannan lokacin sai take ji kamar wani sabon labari ne, kamar an tabbatar mata da wani abu ne da a baya yake yawo a iska, kuma tun a cikin asibitin nan ta sani kwatanta irin murnar da ta gani a idanun Ma'aruf, wani abu ne da bata tunanin yana da geji, sai kuma tazo ta tankwaɓe komai a lokaci guda da ta gaya masa cewa bata so zancen ya fita ko'ina tafi son ya barshi a tsakaninsu.
Bata so ayi wani na ukunsu da zai sani, ta gaya masa tana da dalilinta kuma zai san hakan a gaba, amma bai fahimce ta ba, tayi kokarin ƙara yi masa bayanin amma sai kawai yace ta kyale shi kuma a wannan lokacin da ta kalli idanun nasa ta san babu abinda ya fi dacewa illa ta kyale shin, don ta kasa tantance tsakanin farin ciki da kuma rashin fahimtar tata wanne yafi yawa a cikinsu.
Ta ƙarasa soya ƙwan gabaɗaya, ta fito da dankalin da ta soya a deep fryer, ta hada komai waje guda tare da kayan shan tea, sannan ta koma ta kwaba fulawa da kwai da butter tayi wani pancake da yayi taushi sosai guda uku.
A hannunta ta É—auko woven tray É—in da ta jera komai akai tana barin flask É—in ruwan zafin a kitchen din, kafafunta suka fita daga kitche É—in har zuwa hanyar koridon É—akunansu, wata doguwar riga ce a jikinta ta atamfa, dinkin jikinta mysi kyau ne don ko ranar da ta fsra saka ts su Samirah sun yaba dinkin sosai, ta daura dankwalin kawai a gaban goshinta, bayan É—aurin ya tokare da tudun gashinta mai laushi da yake a tsefe ya fito ko tawanne gefe ana ganin sa.
Fuskarta fayau take, don duk da halin da take ji suna ciki akwai murna kuma a ƙasan ranta fal, godiya ga mahallicinta kawai take mikawa a cikin ranta, tana jin cewa kamar babu wani abu a duniyar nan da zai iya daukar irin farin cikin dake cikin zuciyarta.
"Assalamu alaikum..."
Muryarta ta faɗa bayan ta murda kofar dakin nasa, labulayen da iska ke motsawa ta fara gani a idanunta kafin shi, yana zaune daga ƙarshen gadon ɗakin kusa da bedside drawer dake kunne da fitila akanta, hasken fitilar da shi kaɗai ne a cikin ɗakin, kasancewar labulayen windunan sun hana hasken ranar da ya fara fitowa a waje shigowa ciki kuma sauran fitulun dakin duka a kashe suke.
Faffadar kafadarsa da kuma bayansa su ke kallo ta yayin da kamar kodayaushe hannunsa daya na riƙe da wayar dake kare a kunnensa.
Taji kamar ya amsa amma bata tabbatar ba don maganar da yake yi ma bata jin ta sosai, kafafunta suka taka a hankali zuwa ciki kuma maimakon ta samu waje ta ajiye tray din hannun nata sai kawai ta tafi gabansa ta tsugunna gabaɗaya da kayan a hannunta, idanunsa suka kalle ta kuma kafin ta gama tantance idan fushi yake yi ko akasin haka, sai kawai ya kamo hannunta guda daya ya riƙe shi a cikin nasa.
"Zuwa 11 na fito Insha Allah, ina ga muna da two hours kafin lokacin da zanje É—auko Abdurrahim..."
Ya fada a cikin wayar da ta san ba da kowa yake yi ba Faruq ne. Idanunta suk cigaba da kallonsa yana sauraren bayanin Faruq ɗin, ba ma sai yace mata ba, tana iya karantar cewa ransa a ɓace yake a cikin idanun nasa da kuma yadda jijiyoyin gefen wuyansa ke fitowa suna motsi su kaɗai, gashin kansa ma wani bayanin ne ƙarara, gabadayansu a hargitse wasu sun durƙusa kamar zasu yi sujjada.
Sai kawai ta zame farantin daga hannunta ta ajiye shi a ƙasa sannan ta miƙe zuwa gabansa ta zauna akan cinyarsa a hankali, da yatsan hannunta da bai riƙe ba tta shiga shafa gefen wuyansa a hankali kuma tana jin yadda makowagronsa ke tamkewa da taɓawar da take yi, sai kawai ta karya wuyanta ta cusa fuskarsa ta gabaɗaya a cikin nasa wuyan, tana jiyo muryar Faruq ɗin dake bayani tar daga cikin wayar.
"... Yaron bashi da hankali B, yana gaya min wai baya tunanin nambar ma wani ya taɓa yi mata rijista? Akwai layin da yake amfani babu rijista ne?..."
Hannunta ya tafi daga wuyan nasa zuwa bayansa kuma a hankalin ta shiga zana masa harafan da ba lallai ta san ya fahimta a lokaci guda ba, don haka ta shiga yi tana ƙara sakewa... SORRY.
Har a lokacin kanta yana cikin wuyansa, tana jin yadda ko'ina a jikinsa ke amsawa da abinda take yi amna kuma bai ce komai ba, baiyi wani motsi ba ko kuma ya kalle ta tun bayan riƙe hannunta da yayi.
"Zan kira ka Faruk ina zuwa."
Taji ya faɗa a cikin wayar muryarsa na fitowa wani iri, kuma tana jin wayar ta tsinke sai ta ƙarasa da fuskarta daidai kunnensa tace.
"I'm sorry Sugar, dan Allah kayi hakuri."
Muryarta ta fito da sautin da taji da ace dare ne zata iya tayar da hasken taurari su haska masa fuskarta sosai don ya fahimce ta, ta fadi hakan sannan ta janye kanta a hankali zuwa baya tana kallon fuskar tasa, kallonta yake yi kawai babu alamun zai ce wani abun amma duk da haka tana iya jin yadda zuciyarsa ke bugawa kamar tata.
Komai fushin da zaiyi da ita, bata jin zai karasa har cikin zuciyarsa, ita mai rangwame ce akanta ta sani, sai kawai tasa tafin hannunta duka biyu ta rike kowanne gefen fuskar tasa.
"Ba fushi nake yi ba, me yasa kike bani hakuri?"
Ya yanke shawarar fada muryarsa na fitowa da wani irin amo da bai yi nata dadi ba, amon da yasa babu dalili a lokaci guda taji hawaye ya cika idanunta, bai fahimce ta ba har yanzu, bai fahimci dukkan bayanin da tayi masa ba, bata taɓa tunanin kuma zai kasa fahimtar tata irin haka ba.
Zuciyarta ta matse da tunanin irin fassarar da yayi mata tun kafin ma ta sani, tana jin wani abu na narkewa a cikin jikinta kamar ƙarfen da ake ƙonawa a cikin wuta, wannan yaƙinta ne ta daɗe da gayawa kanta hakan, babu wanda ya san wannan manufar tata a duniya bayan shi, ko Amma bata furtawa ba, shi kaɗai ɗin ne ta san ya zama dole ya sani kuma shi kaɗai take tunanin zai fahimce ta su rufawa junansu wannan asirin duk da bai san komai ba, amma idan har yana yi mata wani tunani na daban nasarar me taci kenan?
Sai kawai ta girgiza kanta tana cigaba da kallonsa.
"Da zan iya zan tattaro komai a duniyar nan Sugar, zan tattaro du gabaɗaya in jera a gabanka don su zama shaida cewar ba zan taɓa yin wani abu da na san zai bata ranka ba, so nake kawai ka fahimce ni, ba zaka gane yanzu ba na sani, kuma lokacin da zaka gane ɗin ma na tabata ba sai na sake yi maka bayani ba.
Roƙon ka kawai nake yanzu ka bani haɗin kanka, bayan shi bana son komai Ma'aruf, kaine inuwata kuma kaine tallafi na, bani da wani mai kare ni a duniyar nan da ya wuce kai, bani da wani da zan dogara dashi a duniyar nan bayan ubangiji da ya wuce kai, kuma ba zan taɓa daina godewa Allah ba da ya kawo min kai cikin rayuwata a lokacin da ban tsara ba kuma ban taba tunani ba, I will always love you in a way that I will never hurt you..."
A yanzu bata jin wannan kwallar data taru a cikin idonta, wani abu take gani a idanunsa take kuma ji a jikinta kamar kwarin gwiwar da ya sata ƙarasa maganarta.
"Zamu haifi babyn nan cikin kwanciyar hankali insha Allah Sugar, babu abinda zai faru, ka cire tunanin komai a ranka dan Allah ka yarda dani, kamar yadda kake yarda da Faruq É—in nan."
Sai kawai ya girgiza mata kansa a lokaci guda sannan yace.
"Kar ki taɓa haɗa kanki dashi Babydoll, matsayinki da nasa daban ne a cikin zuciyata, there's no way ma da kuka zo kusa."
Ya fadi hakan yana matso da ita jikinsa, kusa dashi sosai ta yadda take jin ƙarar bugun zuciyarsu ya haɗe waje guda akan zare guda, sanyi da zafi, mai nauyi da mara shi da kuma siririn da ya yake haɗewa cikin dan'uwansa.
"Na yarda dake Noor, na yarda I'm just curious ne, abubuwa be suke neman haÉ—e min haÉ—e min waje É—aya matsalar office da kuma..."
Ya faÉ—a hannunsa na kokarin lalubo zip din rigarta a hankali, wani abu da yake son wasa dashi a kodayaushe. Sai kawai ta girgiza mata kanta a hankali.
"Babu ruwan gidan nan da office my Ranger Handsome, ka bani damar da zan sa idan ka dawo wajenmu kaji kamar wata duniya daban ka shigo, kamar mun koma Mars ne mun bar musu duniyarsu da hayaniyarsu."
A lokaci guda murmushi ya suɓuce a fuskarsa yana kallonta.
"Really BabyDoll? Kamar me kenan?"
Ya tambaya yana ɗaga mata gira ɗaya, sai ta cije lebbenta na ƙasa alamun tunani kafin tace.
"Zamu zama iyaye nan da watanni masu zuwa..."
"Alhmdulilah." Ya katse ta yana gyaÉ—a kansa.
Bata tsaya ba ta cigaba.
"... Kuma yau muka sani, yau aka gaya mana... So let's celebrate!"
Ya ƙara gyaɗa kansa murmushinsa na ƙara yawa, yayin da a cikin kanta take godewa Allah ganin yana dawowa yanayinsa na Ma'aruf ɗin ta.
"We should BabyDoll, me kike so muyi yanzu? I think ina da two hours kafin in fita."
Ya fada yana ɗora goshinsa akan nata, hancinsa na taɓa saman nata.
Ta sake cije leɓɓenta tana kallonsa sannan ta girgiza kai, duka fuskarsu ta girgiza a tare.
"Yanzu lokaci yayi kaÉ—an, kayi breakfast ka fita, celebration É—in zai fi daÉ—i da daddare."
A lokaci guda hannunsa ya tsaya da taɓa zip din rigarta da yake yi, ya janye fuskarsa daga tata yana kallonta sosai, da idanunsa da take jin kamar yana sace ruhinta daga jikinta, har a lokacin da murmurshi a fuskarsa yace.
"Tabbas zai fi daÉ—i sosai Babydoll..."
Ta gyada kanta itama.
"Zan nemo restaurant hadadde wanda suke da fitulu sosai 'cox we are going to take pictures na tarihi wanda zasu zauna har tsawon shekar...."
Bata ƙarasa ba lokacin da Ma'aruf ya kyalkyale da dariya yana ɗora kansa a gefen kafadarta ta dama.
"Menene? Me ya faru?"
Ta tambaya tana murmushin da bata san na meye ba yayin da hannunta ke kokarin É—ago da fuskarsa. Tana jin yadda jikinta ke girgizawa da dariyar da yake yi.
"Na kasa ganewa, wai menene?"
Ta ƙara faɗa sanda tayi nasarar dago da kan nasa, ya kalle ta sosai yana girgiza kansa kafin yace.
"Babydoll da kika ce celebration kuma kika ce da daddare, abinda nake hangowa daban..."
Bata san lokacin da ta ture shi ba tana kiran sunan sa, sunansa gabaÉ—aya.
"Ma'aruf Mansour Bakori..... ka dinga tunani irin na mutane a cikin kanka dan Allah."
Ta fada tana ƙoƙarin miƙewa, bata je koina ba kuwa ya jawo ta suka koma kan gadon gabaɗaya.
"Zo ki koya min irin yadda ake yi tunanin mutanen..."
Abinda ya faÉ—a bayan hakan ya saka ta kyalkyala dariya tana cusa kanta a cikin wuyansa, abinda ya cigaba da faÉ—a kuma ya sata faÉ—in.
"Inalillahi wainna ilaihir raji'un... Ma'aruf!"
Dukkaninsu suka kyalkyale da dariya, kuma abinda dukkaninsu basu sani ba shine, za'a É—auki wata tazara mai tsawo kafin sake faruwar irin wannan ranar a rayuwarsu!
****
*Abuja.*
*No. 1146 C west, Maitama.*
Ta san dakin, amma idanunta suna kallonsa ne kamar bata taɓa ganin sa ba, idan ma akace ta ƙirga bata san sau nawa zata kirga adadin data share kuma ta gyara shi ba, shi kaɗai ne a ƙasa bayan falon, kuma tasha tambayar kanta dalilin da yasa aka hada shi har da komai da komai alhali mai wajen baya amfani dashi ko kaɗan.
Bayan haka kuma zuciyarta tasha hasko mata yadda zata ji daɗin kwanciya akan gadon da yake dakin, don kalar labulayen cikinsa da kuma zanin gadon ɗakin da suke suke dukka kalar yalo, suna faranta zuciyarta haka kawai, tana jin kalar na shiga idanunta da tasirin da take jin kamar tana samun ƴancinta ne a ciki, kamar zata samu wani fiffike da zai miƙar da ita sama ta tsaya da kafafunta irin yadda take fata a kullum.
Amma yau da take tsaye a cikin dakin rike da ledar kayan dake hannunta bata jin dukkan waÉ—annan abubuwan, bata jin komai, zuciyarta fayau take kamar fuskarta.
_"Zainab zaki aure ni?"_
Sune kalaman dake maimaitawa kawai a cikin kanta, amonsu take ji yana ratsa ko'ina na tunaninta, tana ji kamar shaƙuwar data kwace mata a lokacin zata sake dawowa, don shaƙuwa kawai ta dinga yi yayin da idanunta ke ƙara zarewa akansa, kuma bai sake cewa komai ba sai kawai ya kai hannunsa ya shafa kansa sannan ya juya ya bar wajen.
Bai sake cewa da ita komai ba har suka gama dukkan abinda za'ayi a asibitin ya karɓo mata magani, binsa kawai take yi tana so ta tsayar da shaƙuwar da ta kasa tafiya, ya barta a mota ya shiga wani waje da ta kula cewa magunguna ake sayarwa, kuma bayan ya dawo ne ya shigo motar ya miko mata robar ruwa har a lokacin bai sake cewa da ita komai ba.
Tana tuna yadda ta shanye ruwan gabadaya kasancewar ba wani girma ne dashi ba amma har a lokacin shakuwar bata tafi ba, sai kawai taga ya sake miko mata wata robar daga cikin ledar maganin, a lokacin har sun fita daga cikin asibitin sun hau titi. Kuma ga wani mamakinta ba gida suka taho a lokacin kamar yadda ta zata ba, idan zata tuna ma taga sanda suka wuce hanyar gidan suka tafi kai tsaye har wajen aikin sa.
Wajen da ya ƙara rikita ta, ya kara sawa ta raina kanta ta san cewa ita ba komai bace a duniyar nan, tun daga waje ginin wajen ya daki zuciyarta har suka shiga ciki, don bai bata wani zabi ba yace ta biyo shi, suka tafi har office din wata mata da taji yana kira da Aunty Mary, dattijuwa ce amma kuma arniya, ta saka kayan da basu matse kayion jikinta ba sannan tayi kitson ƙarin gashi.
Tana da tsananin fara'a da kuma kirki, anan yace ta zauna zai je ya dawo, kuma bayan ya tafi haka tayi ta mata magana duk da ta fahimci ba ganewa take sosai ba, don idan ma zata gane É—in, taraddadin dake cikin zuciyarta na tunanin Hajiya Mardiyya da nemanta da za'ayi ba zai barta ba, a haka ta zauna cikin tunani da tsoro har sanda wani ma'aikacin wajen ya shigo rike da leda mai dauke da abinci da kuma magungunan da aka siyo.
_"Hajiya ga shi yace ki ci abincin kuma ki sha magungunan."_
Tana tuna fuskar mutumin da ya kira ta da Hajiyar, zata iya rantsewa zai kai sa'an mijin mahaifiyarta da ta baro a gida, amma kamar bai ga kankantar ta ba ko kuma dogon hijabin data zura wanÉ—anda basa shaida wani abu na Hajiyar da ya kira ta.
Matar nan da kanta ta gaya mata cewa lokacin sallah yayi, ta buÉ—e mata banÉ—akin cikin office É—in ta shiga tayi alwala sannan bayan ta fito ta shimfida É—ankwalinta akan carpet din wajen tayi sallah, haka ta zauna idanunta na cigaba da zarewa har sanda ya dawo, kuma a lokacin kallonsa kawai tayi taji shakuwar É—azu ta dawo, haka ta dinga yinta tana kokarin boyewa har suka koma motar kuma ya sake miko mata wani robar ruwan ba tare da yace komai ba, wani abu da duk rikicewarta sai da ya saka ta murmushi a lokacin.
Sun dawo gidan jikinta na rawa kamar yadda zuciyarta ke yi na tarin abinda ta san zata tarar, abinda ke jiranta wanda kwakwalarta ta kasa hasaso mata shi, amma bai ko bari tayi hanyar wajensu ba yace ta biyo shi bangarensa.
Kafafunta sai da suka tsaya cak jin hakan yayin da wani shiru ya ratsa ta tana jin yadda komai ya É—auke a cikin kanta amma bayan yayi gaba ya sake juyowa ya kalle ta da wadannan idanun nasa sai kawai ta kasa cewa komai ta biyo bayan nasa suka shigo har bangarensa, ya buÉ—e mata kofar wannan dakin ya bata ledar kayan dake hannunta a yanzu yace ta shiga ta shirya.
Ta shirya. Shiryawar da bata san ma'anarta ba har yanzu, kallon É—akin kawai take yi kamar a cikinsa zata samo amsoshin da take nema.
Ta tsugunna a hankali har ƙasa, ta buɗe ledar hannunta ta zaro kayan ciki, wata farar riga ce mai tsawo da kuma laushi, akwai wani dogon wando kakar adon jikinta pink, sannan da hijabi fari tas wanda ta san zai kai mata ne har ƙasa, mamakin inda ya samo kayan ya kamata, Allah ya sani bata san me yake nufi ba, bata gane komai ba har yanzu, so take kawai ya barta ta fita ta samu Hajiya Mardiyya ta gaya mata duk abinda ya faru ta kuma roƙe ta gafara, don ƙwakwalarta na shaida mata cewa itace gatanta ba Jawad da al'amarinsa ba.
Kusan minti talatin tana zaune a kasan carpet ɗin ɗakin ta jingina bayanta da jikin gadon yayin da kwakwalwarta ke ta faman lissafin wucewar lokaci tana jira yazo ya sallame ta tafi, kuma saboda gajiya da kuma zazzaɓin da bai gama barinta ba har a lokacin, sai ta fara gyangyadi zaune a wajen har zuwa sanda aka kwaknkwasa kofar dakin, sau biyu kawai kafin kofar ta buɗe.
Idonta ya sauka akansa tana ƙoƙarin wartsakewa, yana tsaye sanye da wata jallabiya baƙa, hasken fatarsa ya ƙara fitowa sosai alamun wanka yayi, yayi shirin da ita bata yi ba.
Jawad ya tako har ciki yana kallonta, da alama inda ta tsaya bayan ya barta a dakin a wajen ma ta zauna, Babu alamun ta matsa ko'ina, me yasa take so ne ta kara masa matsala bayan tarin abubuwan da yake fuskanta?
Shi kaɗai ya san yadda ya daurewa kansa yayi aiki a office yau, zai rantse da Allah bai taɓa ganin tsoro a idanun kowacce mace a duniyar nan ba kamar yadda ya gani a nata lokacin da ya tambaye ta idan zata aure shi, shi yasa ko da ya barta a Office din Aunty Mary, sau biyu yana kiranta yaji idan tana nan bata gudu ba, wannan shakuwar kaɗai da ta dinga yi tayi yawo a cikin kansa ta yadda da ƙyar ya goge ta yayi aikin dake gabansa.
Da gaske yake, da gaske yana ganin zai iya aurenta shi yasa har ya tambaya, don bai taba jin wani abu da ba zai taɓa kasancewa ba sai a lokaci da Mamah ta gaya masa cewar wai aure iyayenta zasu yi mata, ya sani bashi da iko akanta fiye dasu ko ma wani a duniyar nan, amma a lokaci guda yaji cewar babu mahalukin da ya isa yasa hakan ta kasance, babu wanda zai bari yayi nasarar dauke ta daga gabansa, shi yasa a lokaci gudan ya yanke shawarar tambayarta idan har zata aure shi.
Don a wannan lokacin yana ji kamar idan ta amsa shikenan komai ya tabbata, shikenan ta zama tasa sun kaucewa dukkan wasu abubuwa.
Burinsa kawai ya cigaba da wayar kowacce safiya yana ganinta a gefensa ko da ba zai iya taɓa ko yatsanta ba, ya riga ya fahimci a yanzu rauninta yake so, shine babban abinda ke jan hankalinsa akanta, wannan rauni da kuma rikicewarta da suke banbanta masa ita da Rukayya, Rukayya mai ji da kanta da kuma taƙamar tsayawa da kafayrta a kodayaushe, komai nata yayi hannun riga da Zainab, shi yasa tun a farko zuciyarsa ta fara tsayawa akanta don yana neman duk wani abu ne da zai sa ya manta da Rukayya a lokacin.
Da lokaci ya cigaba da tafiya kuma sai yake jin zuciyarsa ta saba da wannan banbancin sabon da baya jin a karo na biyu kuma zai bari ya sake rasa wani abu irin haka a rayuwarsa.
Tun kafin ya karasa shigowa ɗakin ta miƙe hannayenta na ƙoƙarin fara rawa riƙe da rigar da ta ɗauko a cikin ledar, ya cije lebbensa kaɗan yana daurewa abinda ke ƙoƙarin tasowa daga zuciyarsa.
"Me yasa baki shirya ba?"
Ya tambaya kai tsaye yana kallonta, ta girgiza kanta da sauri kafin tace.
"Ba komai, so nake in koma É—akinmu dama sai in shirya acan."
"You are not going back to that place..."
Idanunta suka tsaya akansa da kallon rashin gane abinda ya faÉ—a duk kuwa da yadda take a tsorace, sai ya É—an kalli gefe alamun mantawa da hakan sannan ya sake juyowa.
"Anan zaki zauna, ba zaki koma can ba,idan akwai abinda kike bukata a cikin kayanki sai ki saka a dauko miki.."
Ai tun kafin ya ƙarasa kwalla ta cika idanunta ta shiga girgirza kanta da sauri.
"Dan Allah kayi hakuri ka barni in tafi, wallahi Hajiya faÉ—a zata yi min, yau ma tace za'a mai da ni gida kuma..."
"Babu inda zaki, idan kin warke zan kai ki gidan ki gansu sai mu dawo."
Ya fada yana sawa ta tsaya cak tana kallonsa, don hatta kwallar data taru a idanunta bata zubo ba.
"Ba dawowa zanyi ba idan na..."
"Dawowa zaki yi, 'Coz babu inda zaki je ki zauna a duniyar nan da ya wuce nan."
Ya faÉ—i hakan kamar cikin tursasawa don har yanzu a tsaye take cak tana kallonsa, sai kawai ya shafo kansa da duka hannayesa biyu shima yana kallonta, yayi kokarin saita kansa sannan muryarsa ta saje fitowa.
"Babu abinda zanyi miki Zainab, wallahi babu abinda zanyi miki, baki ga har hijabi na siyo miki ba? I just want to feel you close to me... So nake kawai in dinga jinki a kusa dani. Shi yasa na tambayeki idan zaki aure ni saboda zan je har wajen iyayenki ne in nemi aurenki, babu ruwana idan ma akwai wanda suka tsara zasu baki Zainab, ko shari'a zan iya yi da kowa idan akace za'a hana ni aurenki..."
Ya faÉ—a yana kallon yadda take kallonsa har a lokacin, a tsaye kyam amma kuma idanunta na haskawa da dukkan wata ma'anar tsoro na duniya kamar ma bata fahimce shi va, ba sai kawai ya girgiza kansa sannan yace.
"Ko ke baki da zaɓi yanzu Zainab, zan aure ki ko baki gama yanke shawara ba, idan yaso daga baya zan koya miki yadda zaki so ni."
Yana faɗin haka ya juya yayi hanyar kofar dakin, sai dai taku huɗu kawai ya tsayar da kafafunsa kafin ya ƙarasa, ya juyo ya sake kallonta, tana tsaye yadda take har yanzu kamar tana jira ne wani ya taɓa ta ta faɗi, sai ya juyo ya dawo da saurihar gabanta, kuma bai jira komai ba ya janye hijabin kanta zuwa ƙasa, gashin kanta da akayi wa wasu manyan kitso mai suna 'Doka' guda uku suka baiyana da jelarsu ƴar gajeriya a baya.
Sai dai shi ba ta su yake ba ma, hannyensa yasa duka biyu a wuyanta, yatsunsa dukkansu suka zagaye dan siririn wuyan nata har zuwa baya, dumin jikinta ya ratsa zuwa tasa fatar a lokaci guda da ta rufe idanunta gabaÉ—aya, wannan kwallar da ta taru tana samun damar zubowa.
Dukkaninsu suka sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya a tare yayin da Jawad ke kallon fuskarta yana ji kamar ya ƙarasa da tasa ya haɗe goshinsu waje daya, amma ya daurewa kansa ya haɗiye wani abu a kirjinsa sannan muryarsa ta fito, a hankali cikin sautin da baiyi kama da wanda ya gama magana dashi yanzu ba.
"Maganin ki yana wajen dining, ki ci abinci ki sha, zan je wajen Maamah yanzu zan dawo, kinji?"
Kuma ga mamakinsa sai kawai ta ɗaga kanta sau ɗaya bata ƙara ba kuma har yanzu idanunta a rufe suke, ya cigaba da kallon fuskarta na tsawon sakanni idonsa na sauka akan siraran leɓɓenta yana jin yadda kwakwalar sa ke kokarin saita kansa daga abinda yake tunani kafin ya zare yatsunsa daga wuyanta a hankali.
Kuma bai ƙara cewa komai ba ya juya ya nufi hanyar kofa fitar, zuciyarsa na goge hoton ta da na mahaifiyarsa a cikin idonsa, Hajiya Mardiyya... missed call dinta ne a wayarsa kusan goma sha biyar, bayan wayar da suka yi sau hudu yana gaya mata inda suke da kuma sanda zasu dawo, yanzu ma ya tabbata bata ji shigowar motarsa bane da tuni ya ganta tazo.
"Jawad dan ub*nka a matsayin me ka dauki yarinyar nan ka kaita har wajen aikin ka?"
Haka take gaya masa lokacin da yace mata suna office tare.
Bata taba zaginsa ba, zai rantse bai ma taɓa jin kalmar zagi a bakinta ba, sunansa kadai akan shafe watanni bata furta ba, a kullum kuma a gaban kowa shi baban ta ne, amma yau da girman sunan da take ji da komai ta haɗa ta zage gabadaya.
Ya hadiye wani abu a maƙogwaronsa lokacin da ya fita zuwa waje gabadaya, haka kawai yake jin kamar ko ita bata isa ta shiga tsakaninsa da yarinyar nan ba.
Yana isa ɓangaren nata kannenta ya fara tararwa tare da wasu cousins dinsu sun zo gidan, sun haɗu akan wani katon tray da suka dafa wata tarin indomie da kifi a ciki, kowacce ta tattare kayanta sun baje suna ci ga wasu manyan-manyan jugs na zoɓo a gabansu.
Gaisuwarsu ta amsa a cikin kansa cikin amo É—aya na siririyar murya, kuma bayan ya amsa bai jira komai ba kafafunsa suka karasa zuwa hanyar koridon da zai tarar da dakin mahaifiyar tasa.
Kofar a buɗe take, ya tura ta a hankali ya shiga ciki da sallamar da ta tsaya iya maƙoshinsa, sai dai idonsa bai gane masa kowa ba alamun bata ciki, kuma har ya juya zai koma lokacin da kunnensa ya jiyo masa muryarta daga cikin banɗakin ɗakin wanda kofarsa bata rufu sosai ba.
"Yanzu duk ba wannan ba Aunty Sadiya, mu fuskanci maganar nan, ina jin kamar zan iya komai don in gyara abubuwa su koma daidai, ba zan yi wahalar banza ba tsawon shekarun nan Aunty Sadiya, na kaÉ—e idan har Jawad ko waninsa ya san cewar ba ni na haife shi ba....!"
****
_Yau na haɗe muku lovebirds ɗin mu a Chapter ɗaya..._🥰�
_Ina kuke tunanin muna tafiya?_
_Kun san na saba wasa da tunaninku...😅_
_Ku shiryawa abinda ke shirin faruwa... Ku shiryawa alkawarin da na daÉ—e ina daukar muku..._
_Komai mai sauki ne idan har kun yarda dani._
_ƙullin ba gab! da kwancewa._
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:57 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©�AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*17*
~~~~~~~
_Hope is a waking dream._ _— Aristotle_
***
"Yanzu duk ba wannan ba Aunty Sadiya, mu fuskanci maganar nan, ina jin kamar zan iya komai don in gyara abubuwa su koma daidai, ba zan yi wahalar banza ba tsawon shekarun nan Aunty Sadiya, na kaÉ—e idan har Jawad ko waninsa ya san cewar ba ni na haife shi ba....!"
Haji Mardiyya ta fada tana dafa sink din daje gabanta a cikin banÉ—akin, daga cikin wayar, yayar tata mai suna Aunty Sadiyan tace.
"Duk ba za'a kai ga wannan ba insha Allahu, yanzu dai kawai abinda nake so shine kiyi kokari ki samu ki raba shi da yarinyar kawai, idan har ta tafi sauran mai sauki ne.
Kawai lokaci zamu ja sai idan ya takura mu samu wani kauyen mu kaishi, da mun fan sunna wa wasu a cikin garin yan kuÉ—aÉ—e sai ya same su a matsayin iyauenta kawai ace masa ta mutu, kinga wannan dole ya hakura ai, komai fa dabara ne Mardiyya, rayuwar mace gabadaya akan dabara take tafiya, idan kika iya ta ina tabbatar miki babu ruwanki da tashin hankali akan abubuwa da yawa, kina daga zaune zaki dinga gyara matsololinki hankali kwance."
Hajiya Mardiyya ta gyada kanta.
"Na dade da haddace wannan karatun naki ai Aunty Sadiya, yanzu na aika a kirawo shi don haka ko yazo ma, ba zan nuna masa kai tsaye cewa ya rabu da yarinyar ba, kawai zan nuna raina ne ya baci ta yadda ba zai fuskanci komai....."
Kalaman ta suka gutsire a iska sakamakon juyowar da tayi a zacen nata, juyowar da tayi a lokaci guda kuma kai tsaye siffar Jawad ta shiga idanunta, yana tsaye rike da hannun kofar banɗakin, yana tsaye yana kallonta da tarin abubuwan da ba zata iya lissafa su ba a jikin idanunsa, tarin abubuwan da suka sa babu shiri wayar dake hannunta ta zame daga kunnenta ta tarwatse a ƙasa!
***
A cikin tangameman ɗakin baccin, Alhaji Bashir ya sauke wayar dake kunnensa daidai lokacin da matarsa ta biyu Hajiya Yagana, kwallin idanunsa kuma shalele duk a cikin matansa uku ke miƙo masa plate din data zuba abincin a ciki tun bayan farawar wayar tasa tsawon mintuna da suka wuce
Kallon da take masa wani kala ne, wani kala ne da duk sanda ta yin yake zabge shekarunsa da nata a zukatansu gabaÉ—aya, lokaci ya ara musu wata dama da a cikinta suke É—anÉ—anar ruwan zumar da baya duba da yaro ko kuma babba.
"Ayi hakuri mana Shalele, aikin his excellency ne, ni ban isa ince ba zan saurare su a yanzu ba."
Ya fada yana kallonta da murmushi, sai ta turo bakinta kaÉ—an alamun ba inda fushin nata yaje kafin tace.
"Kwana biyu ne an shiga hakkina da yawa ranka ya daÉ—e, a lalace nayi kusan wata ban same ka ba, duk ranar da kwana na yazo sai tafiya ta taso ko kuma wani abu ya faru... Hatta su Amal sun fahimta."
Ya sake yin murmushi mai armashi yana kallonta kafin yace.
"Kar ki damu, wannan duk labari kike bayarwa, yanzu dai ba gani ba kuma ga ki? ai zance ya ƙare kuma tsawon kwana ukun nan ni naki ne, ko office ba zan fita ba Yagana, idan ƙasar ma kike son mu bari ki zabi inda zamu je mu kwana biyu sai mu dawo..."
Idanunta suka wulkito tana sake kallonsa yayin da dadi ke ratsawa har cikin zuciyarta, a duniyar nan bata da wani lissafi da ya wuce a kullum ta samu tarin hanyoyin kuntatawa kishiyoyinta, duk wani abu da zata yi su ji haushi shine kawai alkibilarta, don haka ta gyaÉ—a kanta tana murmushi sannan tace.
"Garin masoya zamu tafi Daddy, (Paris) ina son inga hasken fitulun garin nan na haska min fuskar ka a idanuna...."
Dariya da Alhaji Bashir yayi wannan karon mai sauti ce, dariya ce dake fitowa tun daga cikin zuciyarsa, kuma har ya buɗe baki zai yi magana lokacin da kararrawar (doorbell) ɓangaren gabaɗaya ta ɗauki ƙara, sautin ta ga mamaye ko'ina da amon da zaka san tabbas ba an danna ta ne sau ɗaya ba.
"Waye wannan kuma..."
Hajiya Yagana ta furta tana ƙoƙarin danne zagin da taji ya biyo bakinta. Kuma kafin ta karasa wata karar ta sake biyo baya, Sai kawai Alhaji Bashir dake gefe yayi murmushi yace.
"Je ki buÉ—e ko waye na gida ne ai."
Kamar ba zata tashi ba, don sai dai ta kirga wasu sakanni zuciyarta na biya tsinuwar dake tafiya ga ko waye a bayan kofar nan kafin tayi kwafar da ita kadai taji ta ta mike, ta miƙe sanda Alhaji Bashir ke fadin.
"Zan same ku anan falo."
Kafafunta suka dauke ta zuwa cikin falon da shi zaka fara tararwa bayan ka fito daga É—akin, ta wuce ta isa ga falo na karshe a bangaren sannan ta kama handle din makekiyar kofar ta buÉ—e bayan ta murda mukullin, kuma fuskar wanda ke tsaye daga wajen, fuska ce da ta sake bakanta ranta a lokaci guda, tasa zuciyarta matsewa a kirjinta... Wai har yaushe Jawad ya fara shiga rayuwarta ne? A kodayaushe ita mantawa take dashi ma a lissafin dukkanin Æ´aÆ´an gidan don ko zama a gidan bai cika yi ba, to don me yasa yanzu zai dawo ya saka ta a gaba kuma?
Tayi niyyar gaya masa magana amma sai yanayin fuskarsa ya tsaida ita, don duk da ba wani sanin halinsa tayi sosai ba, ta sani cewa bata taɓa ganinsa a irin yanayin da yake yanzu ba, fuskarsa fayau take yayin da idanunsa ke haskawa da wani abu da bata san meye ba, sai kawai ta saki kofar sannan ta juya ciki ba tare da tace dashi komai ba.
Ta juya daidai lokacin da Alhaji Bashir ke fitowa, nasa idanunsa shima suka sauka akan Jawad din dake shigowa, yana kallon yadda bai ko cire takalman kafarsa ba, balle ya rufe kofar da ya baro a bayansa.
Kuma ga mamakin Hajiya Yagana, tana juyuwa da niyyar biyo bayansa su dawo cikin falon sai kawai ya É—aga mata hannunsa guda.
"Ki shiga ciki Yagana, zan shigo."
Ita kanta ta sani cewa a yanayin Jawad din, babu ta yadda za'ayi ya faɗi abinda ya kawo shi a gabanta, bata jin ma ko da gaishe da mahaifin nasa ne zai yi idan har tana wajen, don haka bata ce komai ba sai kawai ta juya ta koma ciki, kuma ta shiga cikin ba tare da ta rufe ƙofar ɗakin gabaɗaya ba.
Alhaji Bashir ya ƙaraso cikin falon ya samu waje ya zauna, kuma sai da ya zauna ɗin sannan Jawad ya ƙarasa ƙarasowa cikin shima, ya sami waje a daidai jikin kujerar dake fuskantarsa ya durkushe har ƙasa kan lallausan carpet ɗin dake shimfiɗe a wajen.
Alhaji Bashir ya kalli yadda ya zaune a gabansa, idanunsa na cigaba da nazarin fuskarsa, zai kafa hujja da cewar tunda yake bai taɓa ganinsa a irin wannan yanayin ba, don haka sai kawai ya ajiye wayoyinsa da ya fito dasu a gefe sannan ya kira sunansa.
"Jawad, me ya faru?"
Muryarsa ta fito ne a hankali, cikin wani amo irin na manya, irin na manya a lokacin da suka fuskanci wata matsala game da Æ´aÆ´ansu ko kuma duk wani wanda suka san zai iya samun mafita daga gare su.
Sai dai abinda Jawad É—in ya buÉ—i baki ya fada a wannan lokacin, wani abu ne da ya shallake dukkan tunani da kuma hasashen Alhaji Bashir, wani abu ne da idan za'a tattaro dimbin abubuwan dake kansa a jera sunya tabbata ba za su taba kaiwa ga magana irin wadda ya fada a wannan lokacin ba...
"Ƴan sanda zasu zo gidan nan, nan da minti kaɗan Daddy, babu wanda zasu taɓa kuma babu wanda zasu kama, kawai so nake ta gansu ta tsorata ta gaya min gaskiya, tace ni ba ɗanta bane ba ita ta haife ni ba, don haka so nake ta gaya min su waye iyaye na kuma meye asalina... Wannan kawai nake so in sani Daddy!"
***
*Ƙauyen Garun Albasu ( Yakura).*
*12:15Pm.*
Awwalu ya gyara zamansa a gaban motar da suke ciki, motar dake tafiya cikin wani tsukin lungu na ƙauyen da suka shigo kusan awa gyda da ta wuce, kuma a wannan lokacin suka shafe suna faman tambayar gidan wata mata mai suna Hanne kamar yadda Awwalun yace itace wadda a wancan lokacin ta shaida masa cewar yaron da yake nema yana can Abuja, kuma a cikin awa gudar an kaisu ga gidajen mata masu sunan Hanne fiye da goma, kowacce Awwalu yana fadin ba ita bace da zarar ta fito.
Lokacin da suka shigo cikin kauyen kai tsaye ma yace zai iya gane gidan da ya sami matar a wancan lokacin, amma tun kafin tafiyar tayi nisa, canje-canje da kuma sabbin tsarin da aka samu a koina ya shaida masa cewar abinda ya sani a wadancan shekarun da kuma yanzu daban ne, don haka suka shiga tambaya, tambayar da ta kaisu ga lissafin mutane kusan tara kafin a samu wanda ya faÉ—a musu cewa matar ta daÉ—e da barin garin amma akwai wata Talatu da zata iya basu labarin inda take.
Tun a hanya Hajiya Salamatu ta sani cewar zai iya yiwuwa matar ta mutu, zai iya yiwuwa su zo su sami labarin wucewar wasu shekaru da mutuwarta, ace musu ta rasu tare da labarin abinda suka zo nema, abinda shine zai zamo ginshiƙin canjawar rayuwarta da ma ta adadin wasu masu yawa.
Amma bata san me yasa ba a yanzu zuciyarta ke gaya mata cewar bai kamata ta biyewa Awwalu rana tsaka ba, bai kamata ta yarda da wani daban akan aminyarta da suka shafe tarin shekaru tare ba, waɗannan shekarun da a cikinsu baza ta taɓa cewa ga rana guda da wani abu ya shiga tsakaninsu ba, kokwanton kawai guda daya ne... idan ta tuna cewa sauran mutanen da take azabtarwa wanda suma haka zasu buɗi baki su ce.
Sannan kuma har yanzu Awwalu bashi da wata shaida, bashi da wata shaida ko guda ɗaya da zata tabbatar mata da dukkan labarinsa, zai iya yiwuwa yazo yayi amfani da ita ne don kawai ya sanarwa kansa mafita, idonta ya sauka akansa daga gaban motar, shi kansa ba abin yarda bane, shekara nawa ya shafe yana aiki tare da Kilishin, shekaru nawa yayi yana taya ta wajen kuntata rayuwar wasu? Me yasa bai taɓa tuba ba sai a yanzu? Shekaru sun fara ja masa amma ko aure bai taɓa tunanin yi ba, bashi da wani mutunci ko kuma wani abu kwakwkwara da rana tsaka kawai zata yarda dashi.
Sai dai idan har bata yarda da Awwalun ba, to tabbas kuwa ba zata yarda cewa Kilishi ba zata iya aikata abinda Awwalun ya faÉ—a ba.
Lungun da suke bi a yanzu wani ɗan tsuki ne da ba don direban nata yace zai iya bi ba, zata ce su fita su tafi a ƙasa ne, don a yanzun ma dukkan mutane da kuma samarin dake zaune sai da suka mike suka dage bencinan da suke zaune akai don bawa motar waje, idanun kowa na binsu da kallon rashin sani kamar yadda suke gani a koina duk inda suka tsaya tambaya.
"Wancan kwanar ce, yaron yace kwana ta farko zamu karya."
Awwalu ya fada yana nunawa direban kwanar dake damansu, zuciyarsa fayau take a kirjinsa, yana jin kamar allon kirjin nasa baya É—auke da komai, kamar iska ce kawai ke yawo a cikin gangar jikinsa da take fanko, yana jin yadda bugawar zuciyar ke amsawa a cikin kunnuwan shi.
Rayuwarsa gabaɗaya a yanzu ta ta'allaka ne ga inda zasu je da kuma abinda suka taho nema, nasararsa da akasinta tana ga irin amsar da zasu tarar ga tambayarsu, idan har bai samu gamsaahshen bayanin da zai tabbatarwa da Hajiya Salamatu ba, bai san me ya kama ba, bashi da wata mafita ko zaɓi illa ya tattara komai nasa ya bar garin Kano zuwa wajen da ya tabbata Kilishi ba zata taba riskarsa ba.
Kuma wannan ba shine babbar matsalarsa ba, ya san yana da ilimi da kuma takardun da zai iya neman aiki a koina, kuma ya san yana da yan kuɗaɗen da zai iya gina sabuwar rayuwar da zai fara a ko'ina, amma wannan ba shine burinsa ba, ba shine fatansa ba... Bashi da wani jin daɗin da zai wuce ya ga faɗuwar Kilishi, ya ga tarwatsewar ta tare da dukkan mafarkanta, yana so ko sau ɗaya ne Allah ya bashi damar da zai zama sanadin da Kilishi zata ɗanɗani ko da rabi ne na irin baƙin cikin da ta shafe rayuwarta tana jefa al'umma a ciki.
Bayan sun shiga kwanar, motar ta tsaya a daidai gida mai bunun da akayi musu kwatance, kuma daga Hajiya Salamatun suka fito suna barin direban a ciki, kafafun Awwalu suka ƙarasa da sassarfa ya ƙarasa wajen wasu samari dake zaune a kofar gidan ya shiga yi musu bayanin abinda suka zo nema.
Akan idon Hajiya Salamatu wani saurayi ya miƙe ya shiga cikin gidan bayan yayi wa Awwalun bayanin cewa zaiyi masa iso da matar da suke nema, tana ganin yadda Awwalun ke juyowa yana kallonta daga inda yake tsaye, sai kawai ta juyar da kanta gefe guda ba tare da tace dashi komai ba, sharadi ne sun rifa sun yi sho tun kafin su taho.
Zata yafe masa,ba zata ce komai ba, ba zata ce komai ba,ba zata tona shi a gurin Kilishi ba, zata barshi yaji da neman hanyar tsira da rayuwarsa,komai zaiwuce kamar bai faru ba, niyyar taimakonta da yayi zata kore duk wani sharri da da zata iya shirya masa, amma idan har akasin hakan ce ta faru, komai ya tabbata zuwa gaskiya... to tabbas zata nunawa Kilishi wata sabuwar siffar cin amanar da a tsawon rayuwarta kaf! bata taba saninta ba.
Cikin abinda yake kasa da minti biyar, wannan saurayin ya fito yana faÉ—in ance su shiga ciki. Awwalu ya juyo ya sake kallonta alamun ta taho kuma bata ce komai ba har a lokacin ta gyada masa kai kawai.
Suka nufi ciki inda bayan sun wuce soron bunun ƙatuwar haraba ce irin ta gidajen ƙauye, akwai tarkace mai yawa wanda ya haɗa da tarin tirame da kuma wasu abubuwan da baza su lissafu ba, ginin ƙasa ne a ciki na ɗakuna kala-kala kowanne na fuskantar junansu yayin da wasu suke daga can gefe, mata guda hudu suka tarar a tsakar gidan, uku da hijabi a jikinsu da alamun shigowarsu ce ta sa suka sanya sai kuma wata tsohuwa daje surfe daga can gefe, dukkaninsu suka amsa sallamar su.
Wannan saurayin da ya shige gaba shi ya jagorance su har wani daki dake can karshe, kuma tun kafin su shiga suke jin muryar dake ciki na faÉ—in.
"Maraba, maraba... Sannun ku."
Hajiya Salamatu ce ta fara shiga ciki kafin Awwalun ya biyo bayanta, É—akin bashi da girma sosai, akwai gado da kuma wasu kayan tarkace na kwanuka daga gefe, sai daga gaban gadon kuma aka shimfiÉ—a wata sabuwar tabarma, matar tana daga gefe sanye da hijabi itama sai washe baki take yi tamkar ta sansu.
"Barkan ku dai, maraba..."
Ta sake faɗa bayan sun zauna, Awwalu bai shigo ciki ba don ko takalminsa bai cire ba, tsugunnawa yayi kawai daga ƙofar ɗakin yana amsawa kamar yadda Hajiya Salamatu ke yi.
"Ai Yakubu da ya shigo ya gaya min abinda ke tafe daku, yace bayanin Inna Hanne kuka zo nema ko?"
Awwalun yayi saurin gyaÉ—a kansa da sauri.
"Tabbas, indai itace Hanne, to ita É—in muka zo nema, wani Malam Tanimu ne ya kwatanta mana nan gidan yace ke Æ´arta ce zamu sami bayanin inda take a wajenki."
Matar da har a lokacin basu san sunanta ba ta gyada kanta sannan tace.
"Tabbas, ai da yake ta jima da barin ƙauyen nan, tayi wani aure ne a can Hayin Shehu, wani kauye dake gabas da nan, hi isa mutane da yawa ta ɓace musu."
Hajiya Salamatu ta gyaÉ—a kanta kafin tayi magana, maganar da ta zarce ga abinda ya kawo su kai tsaye don har yanzu ita bata ga dalilin shigowar su gabaÉ—aya da kuma tarbar da matar ke yi musu ba.
"Shi yaron yayi miki bayanin abinda ya kawo mu?"
Sai kuwa ta gyada kanta a lokaci guda da amon muryarta ya canja.
"E, yace nemanta kuka zo yi..."
"Ƙauyen Hayin shehun kawai zaki kwatanta mana da kuma gidan wa zamu nema idan har mun je."
Awwalu ya faɗa yana katse abinda take shirin faɗa. Sai ta girgiza kanta a hankali idanunta na kallonsa, sannan ta faɗi kalaman da yake gudu, kalaman da yake tserewa, kuma kalamai na ƙarshe da zai iya tunanin ba da ransa akai idan har zai iya tare su daga fitowa daga amon kowanne mutum a duniyar nan.
Kanta ne yayi sama ya koma ƙasa alamun gyadawa sannan sautin muryar tata ya fito fili.
"Haka ne, sai dai Inna Hanne ta riga ta rasu shekaru shida da suka wuce!"
***
Ƙarfe shida na yamma, Awwalu ya buɗe kofar falon gidansa, kuma bai jira komai ba ya shigo har ciki ba tare da ya ko cire takalman kafafunsa ba.
Ya wuce falon ya tafi har cikin ɗakin kwanansa, inda ansn ma ma bai bata lokaci ba hannunsa ya janyo wani akwatinsa da yake yawan tafiye-tafiye dashi, ya shiga ya baɗe drawer ɗakin a gurguje yana kwaso gogaggun kayansa dake nibke a ciki yana jefa su cikin akwatin, kuma sai da ya tabbata ya kwashi fiye da rabi sannan ya rufe akwatin da ƙyar ya sake jawo wata jaka irin ta matafiya daga ƙasan wardrobe din.
Ya buɗe zip ɗin cikinta ya tabbatar da tarin cd's ɗinsa dake ciki suna nan sannan ya wawuro wata computer dake ajiye kan bedside ɗin gadon ya cusa ta a ciki itama ya shiga ƙoƙarin rufe zip ɗin.
Wayardmsa da ya cillar akan gadon dakin ta shiga kara tana nuna wata sabuwar lamba, da sauri ya dauko ta ya kara a kunnensa.
"Eh nine, ni ne wanda ya kira ka yanzun nan... Dan Allah ka taimaka in samu ticket din nan... Eh, na Lagos... To shikenan ina son na Lokojan... Nagode ka samar min shi É—in kawai, gani nan yanzu zan karaso."
Ta fadi dukkan wannan bayanin, zuciyarsa na rawa tare da amon muryarsa, burinsa da ma fatansa ya ta'allaka ne a tanzu kawai kan barin garin nan, babu iya kokarin da baiyi ba wajen kokarin fahintar da Hajiya Salamatu iya gaskiyarsa don ta yarda da dukkan bayanin da yayi mata, amma bata saurare shi ba sam! Hasali ma ta gaya masa ne cewar zata yi masa alfarmar rufe sirrinsa a wajen Kilishi don niyyar taimakon da yayi mata, kuma bata ko sake ɗauko shi motar ta ba ita da direbanta suka juya suka tafi suka barshi tsaye a ƙofar gidan Bunun nan.
Haka ya fito daga cikin ƙauyen nan ya samu ya isa tasha sannan ya ɗauki shatar mota guda saboda tun akan hanya zuciyarsa ta gaya masa cewa bashi da isasshen lokaci da kuma kwanciyar hankali daga yanzu, gobe ne... gobe ne ranar da Kilishi ta gama tsarinta akansa, gobe ne dukkan wannan bayanan da yaji su a matsayin labari zasu tabbata idan har bai samarwa kansa mafita ba.
Don haka a yanzu zai dauki dukkan wasu abubuwansa masi muhimmanci ne ya var garin nan, idan yaso daga baya,zaiyi magana da dillalin da zai sayar da gidan ya kuma É—aukar masa sauran kayansa... Burinsa da fatansa kawai shine ya bar cikin Kano a yau, yayi nisa daga inda Kilishi zata iya samunsa kafin yayi nisa daga gare ta gabadaya, nisan da ba zata taba iya samunsa ba, don idan har shi baiyi nasara akanta ba, to kuwa ba zai taba bari ita tayi akansa ba.
Bayan ya ajiye wayar ya zaro wallet dinsa ya kalli adadin kudin ciki da kuma tarin cards É—insa na banki, ya tabbatar komai yana nan daidai sannan ya sake mayar da ita aljihunsa.
A hannayensa duka biyun ya ɗauko jakar ya kuma riƙo akwatin da guda ɗaya, ƙafafunsa na sassarfa ya fito daga ɗakin ya sake biyowa ta cikin falon ya nufo hanyar fita waje inda motarsa da ya bude ke jira, sai dai da taku biyu kaɗai ya rage tsakaninsa da kofa lokacin da abin ya faru...
Kofar falon ta buɗe da wani irin ƙarfin da yafi na hankali, kuma a cikin sakanni biyun da suka biyo baya, idanun Awwalu suka ɗaukar masa hoton mutanen da suka fado ciki...
Ya san su, ya gane shigarsu, kayan jikinsu da kuma yanayin yadda suke rufe ba tun yau ba, ba kwanan nan ba, a shekaru masu yawa da suka wuce, shekaru goma da suka wuce.... Sai dai kafin kwakwalwarsa ta tariyo masa inda ya san su da kuma a ranar da ya gansu ɗaya daga cikinsu ya karaso da saurin da suka faɗo gidan dashi ya buga masa wani dogon abu da yake riƙe dashi.
Wata tsawa tare da wani farin haske suka ratsa kunnuwa da kuma idanun Awwalu a lokaci guda! Yaji kamar ruwa na bi ta bayansa, kamar yana sulalewa zuwa wata duniyar daban, taji sanda kafafunsa suka yi rawa suna durkushewa a wajen, kuma kafin idanunsa su tafi su rufe gabaÉ—aya, yaga sanda da yawansu ke shigowa cikin gidan suna yanyame shi.
****
"Kun gama?"
Ma'aruf ya tambaya a cikin wayar dake kare a kunnensa yayin da yake zaune cikin daga office din Faruk.
Amina dake tsaye ya gaban mudubin dakinta ta daga kai kafin tace.
"Eh yanzu ta fita, ta gaya min duk abinda zan dan kiyaye ne kuma tace babu wani abu tunda anui scanning a asibitin babu wata matsala, kuma nace mata babu abinda nake ji."
Ma'aruf yayi shiru yana kallon tarin takardun dake gabansa da kuma Faruk É—in dake can jikin windon office É—in yana waya, an kammala dukkan wani binciken da gidan waya je yi akan lambar da suka samu ta Awwalu, sun sami tarin bayanin da tun dazu ake turowa Faruk É—in yana printing dinsu daga computersa, a yanzu abu É—aya kawai suke jira, so suke yi a turo musu da address din inda yake wanda aka samu daga cikin wayarsa tare da wani shekaru uku da suka wuce yana bayanin canja gidan da yayi.
Yaron da zai turo musu da report É—in hakan ne ya tafi wani meeting tare da sauran shuwagabannin su, don haka tun É—azu Faruk É—in ke rike da kan waya yana jiran dawowarsa tare da kuma samun wasu bayanan daga sauran ma'aikatan wajen.
A gabansa kuma tarin takardu ne na meeting din da zasu shiga da kamfanin Rotel&co gobe, kwangilarsu ta gaba... Babu yadda Faruk bai yi dashi akan su daga ranar zaman nasu ba amma yace masa A'a dole zasu ajiye komai a gefe su yi hakan, don baya son bawa Baffa kowacce irin dama da zaiyi tunanin cewa suna kasawa a wani abu, sannan su kansu kamfanin sun samu kwangilarsu ne da kyar, akwai tarin kamfaninnika da yawa da suke neman samun yin aiki dasu don tabbas kowa shaida ne cewar biyansu ya banbanta da na wasu kamfanikan da yawa.
Don haka ko yaya suka basu wata dama, kai tsaye zasu iya tuntubar wasu su manta da zancensu, fon haka ya dage cewar dole su tsaya kan alkawarinsu, amma kuma duk da
Wadannan tarin ayyukan dake gabansa tunaninsa ya kasa mantawa da matarsa da kuma sabon al'amarin da suke ciki, gani yake kamar ba haka bane, kamar abinda ita da kuma asibitin nan suka gaya musu ba gaskiya bane, ba don komai ba sai don yadda abin yake iya tsakaninsu kawai har yanzu.
Lokacin da yana tare da Rukayya, lokacin da ta sami ciki, zai iya cewa shi da Malam sani direba sune na ƙarshe a sani, don yayi tafiya a lokacin har aka kwantar da ita a asibiti ta kwana babu wanda ya kira shi a cikin ƴanuwanta tunda ita tana bacci a lokacin, sai da safe da Mami zata je asibiti wajenta sannan ta kira shi tana gaya masa, a lokacin suka ji tare da Malam Sanin da zai kaita.
Kuma Allah ya sani a wancan lokacin da zuciyarsa ta riga ta gama sarewa da al'amarin Rukayya, don baya jin ko sau daya ya taɓa nuna damuwa da abinda ke cikin nata, ya san dai ya bata dukkan kulawar da zai iya, bayan haka bai damu ba da dawainiyar cikin ba kamar ita, kamar itama da a lokacin bata ɗauke shi a komai ba.
Sai a ranar da Hamida tazo duniya, ranar da ya riƙe ta a hannunsa sannan wannan ƙaunar da iyaye ke ji a lokacin da suka kalli gudan jininsu ta mamaye komai, ta rufe wasu abubuwan ta kuma bude tarin wasu a zuciyarsa, tarin wasun da duk karfin da suka yi basu iya saita rayuwarsa daidai a lokacin ba, don ƙaunar da yake bukata, zuciyar da yake bukata ta fahimce shi tafi tafi karfin ƴar karamar dake bugawa a kirjinta.
Amma wannan karon, haka kawai yake jin kamar komai daban ne, tunda rayuwarsa ta canja, yana cikin nutsuwa da kuma kwanciyar hankalin da yake ji hannayensa zasu iya buɗewa su riƙe wani abun fiye da wanda yake iya kokarinsa wajen kula dasu a yanzu, shi yasa haka kurum bayan yazo office ɗin ya kira wata likita dake aiki a asibitinsa na can Abuja, ya kira ta yace taje gidan ta sake duba ta tunda sunyi magana tace masa tazo Kano ita da Familyn ta hutu.
Saboda haka ya sake gyara zamansa yana zura hannunsa cikin gashin kansa kafin yace.
"BabyDoll kin tabbata babu abinda kike ji?"
Amina ta girgiza kanta a hankali tana neman wajen zama daga bakin gadonta.
"Ba abinda nake ji da gaske, kawai kamshin wasu abubuwan ne suke damuna ka sani..."
Ya gyaÉ—a kansa yana kallon Faruk É—in da a yanzu ya tafi can gaban teburinsa yana karanto wasu lambobi daga cikin wayar tasa zuwa cikin wayar dake kare a kunnensa.
"Kiyi list dinsu gabaÉ—aya ko menene we are getting them out of the house da zarar na dawo... Kinji."
Ta cije lebbenta taba murmushi, don list É—in farko da ta fara hangowa kusan rabi na turarukan da yake amfani dasu ne, sai kawai ta gyaÉ—a kanta sannan tace.
"Insha Allah Sugar."
Yayi shiru na wani lokaci, itama tayi shiru bata ce komai ba, tana jin muryar Farouk din dake magana daga cikin wayar.
"Kina son wani abu?"
Ya tambaya a hankali yana katse shirun, sai ta girgiza kanta kamar yana kallonta kafin tace.
"A'a."
"Ni ina son wani abu..."
"Wani abu me?" Ta tambaya tana cije lebbenta sanin halinsa, amma sai taji yace.
"Dan Allah ki min tuwo yau..."
Tuwo. Kalmar ta dira akanta duk da yadda ya fade ta a hankali, ba wani jin daÉ—in jikinta take ba, kawai daurewa take tana gaya masa babu komai tunda ta san tarin ayyukan dake gabansa da kuma abinda yake fuskanta. Bata tunanin ma zata so kamshin kowacce miya da zai ce yana so.
Amma ya zata yi? Ba kullum ne zata fyskanci abinda take so a cikin auren ba ma ta sani, ta sani a cikin kanta cewa wannan matakin da suke ciki mai wucewa ne ma, yau da gobe tafi ƙarfin komai, rayuwar ba tatsuniya ba ce ba, ko a tatsuniyar ma akwai lokacin da abubuwa basa tafiya daidai, tana lissafi da ranar da zata zo Ma'aruf zaiyi mata abinda zai ƙona ranta, tana lissafi da ranar da zata fara fuskantar irin hakurin da kowacce mace ke yi a gidan aurenta, saboda hakan shine auren shi yake mikewa ya cigaba da haifar da fahimtar juna da kuma shaƙuwa a tsakani, idan har babu hakuri a ginshikin aure, da tabbas duk wani nau'i na jin dadin duniya ya ƙare.
Saboda haka sai kawai ta gyaÉ—a kanta a hankali sannan tace.
"Insha Allah Sugar, kayi aikinka ka dawo, muna nan muna jiranka da tuwonmu a ƙofa..."
Tana jiyo murmushin da yayi mai kama da dariya.
"I love you so much Noor..."
"Love u too."
"Ki saka min wannan rigar kafin in dawo."
"Wacce?"
Ta tambaya girarta biyu na gadewa waje guda alamun bata gane ba.
"Wadda ba sai na sha wuya ba..."
Dariyar da ta kyalkyale da ita ta katse sauran maganganunsa, yayi shiru yana juya biron hannunsada nasa guntun murmushin shima.
"Da gaske nake."
Sai ta girgiza kanta sannan tace.
"Kar ka damu, zaka so wadda zan saka fiye da wadda kake tunani ma..."
Ya girgiza kansa a lokaci guda
"The day is rough Babydoll, and you are making me go crazy..."
(Ranar yau sai a hankali Babydoll, kuma kina kara rikita ni....)
Amina ta cije leɓɓenta a hankali tana murmushi, kuma sanin halinsa da abinda zai iya faɗa a gaɓa, yasa tayi saurin yi masa sallama, wayar tasu ta ƙare da hakan.
A daidai lokacin da Ma'aruf ya sauke wayar daga kunnensa daidai lokacin da Faruk ya tsaya a gabansa yana miƙo masa takardar dake hannunsa, kuma murmushin dake kan fuskarsa shine abu na farko da ya fara shaidawa Ma'aruf abinda bai furta ba.
"Mun same shi Ma'aruf, ga address dinsa nan, ka shirya mu tafi... ko waye wannan Awwalun yau dubunsa ta cika!"
***
_Su wa kuke tunanin sun kama Awwalu?_
_A wane lokaci kuke tunanin su Ma'aruf zasu isa gidansa?_
_Tare da mutanen nan?_
_Ko bayan sun tafi da Awwalun?_
_Ina Kilishi?_
_Kuna tunanin Hajiya Salamatu ta hakura da zancen dan ta?_
_Ta yaya Jawad zai gano mahaifiyarsa?_
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:57 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©�AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*18*
~~~~~~
*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka, ina mika ta'aziyyata da kuma jaje ga dimbin al'ummar musulmi da ma jama'ar Kano game da tashin hankalin da muka fuskanta a cikin satin nan na kisan gilar da aka yiwa ƴar ƙaramar yarinyar da bata da laifin komai a duniyar nan, ina rokan Allah ya bawa iyayenta haƙurin rashi, Allah ya ƙara kare mu da iyalanmu, Allah kuma ya kawo mana karshen dukkan tashin hankalin da muke ciki lafiya. Ameen.*
***
Motoci guda huɗu zaka fara gani a ƙofar gidan kafin idanunka su lura da cewar kofar motar guda ɗaya a bude take hade da mukullinta a jiki.
Don a lokacin da suka tsaya, tunanin Ma'aruf da kuma duk wata nutsuwarsa tayi kaura daga cikin kansa, fatansa kawai shine su sami mutumin da suka zo nema a cikin gidan nan, Awwalu!
"Nan ma baya nan...!"
Ƴan sanda na ƙarshe da suka dawo daga bayan gidan suka fada suna shivowa cikin falon inda dukkaninsu ke tsaye, sun duba koina a gidan sun duba koina, kuma hasashen Ma'aruf na cewar babu mutum a cikin gidan tun sanda ya tako ƙafarsa ciki shine ya tabbata.
Babu kowa, babu kowa a cikin gidan banda shatin tayoyin motar da suka tarar a jikin kasar waje ta compound É—in gidan, shatin da Æ´an sandan suka tabbatar da cewar bai daÉ—e ba, babu daÉ—ewa da fitar mota a gidan.
Bai san lokacin da yayi baya ya zauna kan wata kujera dake cikin falon ba yayin da hayaniyar Æ´an sanda da kuma sauran tanen da suka zo dasu ta tafi kan wata jaka da suka tsinta a cikin falon, wata jaka da babu komai sai tarin wadu CD's da kuma computer guda daya.
Yana jin abinda suke fada, yana jin suna fadin cewa kayan ba karamar kadara bace da zata iya kaisu ga abinda suka zo nema, amma shi ba wannan ne a ransa ba, ba hakan yake do ba, ba kuma hakan yayi fata ba. Burinsa yaga ko waye wannan Awwalun, burinsa yaga fuskarsa yaga WAYE SHI, ya ga waye wanda ya daÉ—e yana cutar dasu a duniyar nan ya kuma san dalilinsa.
So yake ya tambaye shi me suka yi masa? Me suka yi masa shi da mahaifinsa da dauki aniyar tarwatsa su? Wane irin laifi duka yi ko kuma ta ta yaya suka cutar da rayuwarsa da yake bata lokacinsa yana kuma sadaukar da dukiyarsa da fasaharsa don ganin karshensu? Abinda yake so a wannan lokacin kenan, so yake ya riƙe wuyansa a cikin hannayensa ya tambaye shi me suka yi masa... So yake ya dake shi, ya mare shi, ya naushe shi har sai yaga haƙoransa suna biyo jini suna fitowa....
"Kusan duka Cd's É—in are write-protected, sai mun je office zan iya aiki akansu."
Cewar wani a cikin ƴan sandan nan yana ƙoƙarin danne-danne a cikin computer dake hannunsa bayan ya gwada CD guda ɗaya a ciki, kuma bayan hakan yana ji mutum biyu da suka buɗe computer hannunsu suna faɗin itama a ƙulle take da password.
Wayarsa tayi kara a lokacin, hannunsa ya zaro ta a hankali daga aljihunsa, Ishaq ne.
"B kana ina? Tun dazu nake kiran wayarka taƙi shiga, gani har nazo Airpot daukan Abdurrahim, ka manta ko?"
Sai kawai ya cusa hannusa gabaÉ—aya cikin gashin kansa.
"Wallahi na manta Ishaq, ina nan ina wajen aikin nan ne, amma bari mu gani, may be kafin jirgin nasu ya sauka I'll be there."
Ishaq dake zaune a cikin motarsa a harabar filin airpot din ya gyada kansa.
"Kayi kokari Dan Allah Ma'aruf, don kafin in fito Baffa yayi fadan me yasa baka gida bayan ka sani."
Ya sake gyada kansa a lokacin da Faruk dake tsaye tare da wani É—an sanda ya matso daidai inda yake zaune.
"Zan zo yanzu insha Allah, bari mu kammala."
Kuma da haka wayar tasu ta kare, ya sauke ta san da Faruk din ke cewa.
"Kar ka damu Ma'aruf, zamu sami wani abu a cikin waÉ—annan kayan insha Allah, kuma zasu saka security daga yanzu za'a saka ido akan gidan nan 24/7, we are close to finding them Insha Allah."
Abinda dukkaninsu basu sani ba shine, amsar da suke nema a yanzu tare da mabuÉ—in da zai bude komai ya kuma kawo karshen komai É—in yana dab da taka kasar Nigeria!
***
"Naira miliyan tara!"
Muryar mutumin ta furta a hankali yana kallon wanda ke gabansa, a zaune yake akan doguwar kujera da ta cika kusan rabi na dakin, don bayan ta miƙe ta zagayo ta bari ɗaya cikin wani shape mai kama da C, kalarta milk ce kamar yadda tattausan carpet ɗin da aka baje a ɗakin yake, akwai labulaye da suke kalar brown, kalar da ta dace da fentin ɗakin da kuma sauran kayan furnitures ɗin da kyawunsu ke ƙara haska haduwar ɗakin.
Mutumin na zaune ne daga shi sai gajeren wando da kuma wata yaloluwar T-Shirt yayin da teburin gabansa ke cike da wasu kwalabe da kuma kule-ƙullen da ba sai an tona ba kowanne mai hankali zai san cewa abubuwa ne da ya kamata a liƙa musu ayar tambaya.
"Naira miliyan tara ba wasa bane..."
Mutumin ya sake faɗa yana ɗora kafafunsa duka biyu akan teburin dake gaban nasa wanda hakan yasa wasu abubuwa dake kan teburin suka faɗi. Awwalu dake zaune daga can ƙarshen ɗakin hannuwansa da kafafunsa duka a ɗaure, idanunsa suka bi kayan da suka fadi sannan ya sake dawo dasu kan mutumin.
"Munyi yarjejeniya da kai Awwalu, ka san ni, na sanka kuma ka san ba'a a cin kuÉ—ina a kwana lafiya..."
Ya faÉ—i haka sannan ya É—ago daga kishingiÉ—ar da yayi, a gefensa katinan bankin Awwalun ne wanda suka samu a cikin wallet É—insa, ya É—ebo su guda uku sannan ya watso su, suka taho tun daga inda yaken har zuwa kan fuskar Awwalun kafin su tarwatse a jikinsa.
"Babu komai a cikin waÉ—annan accounts É—in, mun duba gidanka ma babu ko sisi..."
Mutumin ya hade hannayensa biyu sannan yace.
"Bana so in taba ka Awwalu ka sani, ka san wannan ne dalilin da ya sa na daga maka kafa tsawon watanni, ka san wannan ne dalilin da yasa na dade da yi maka shiru kuma ka san shine dalilin da yasa ni da kai muke kallon juna a yanzu..."
Ya kai idanunsa kan agogon dake manne daga can saman dakin sannan yace.
"... Zuwa nan da ƙarfe shida, zaka iya zama tarihi Awwalu, don zan gwammace in kashe ka da ace ni da kai muna cigaba da rayuwa a duniyar nan kuma babu kudina a tsakaninmu."
Ya kai karshe a lokacin da Awwalun ke kokarin gyara zamansa don duk abinda yake fada gaskiya ne ya sani, ÆŠantaro abokin huldarsa ne da suka daÉ—e suna harkar cinikayya tare, a yanzu kudin da yake faÉ—a miliyan tara, kuÉ—in wasu kayayyaki ne da ya karba a wajensa ya aikawa da wani kaninsa dake can garinsu don ya fara kasuwanci, kuma ba wai ya hana shi kudin saboda wani dalili bane ba, bai bayar bane saboda ya manta, a kwanaki biyun nan da al'amarinsa da na Kilishi ke cakudewa, kwakwalarsa ta manta da tarin abubuwan da bai san lissafinsu ba.
Lokacin da mutanen ÆŠantaro suka shigo gidansa, yanayin shigar kayansu da yadda suka rufe fuskarsu, ya bashi tunanin cewa mutanen Kilishi ne don wannan ne kadai tunaninsa a yanzu, abinda yake gujewa kawai kenan, ya gansu ne da tunanin ire-iren mutanen daya taba hada ta dasu ne wanda suka kashe Jamal.
Sai a lokacin da ruwan da aka watsa fuskarsa ya farkar dashi daga suman da yayi, ya bude idanunsa akan Ɗantaro da kuna yaransa sannan ya fahimci cewa zaren kaddarar tasa da saura, bai kai karshe ba har yanzu, yana da lissafin wasu kwanaki kafin a zo gabar da sa'ar da ya dade yana talawa zata ƙare, don ya riga ya sallama a yanzu, tunda har bai samu abinda zai bashi yardar Hajiya Salamatu ba shikenan duk wani shiri da kuma fatansa ya kare, don a tsarinsa yana so yayi amfani da Hajiya Salamatun ne su boye laifinsa wajen tonawa Kilishi asiri.
Amma tunda bashi da wani mataimaki a yanzu, to ya san babu ta yadda za'ayi yaje ya tunkari iyalan Bakori don tonawa Kilishi asiri ba tare da ya bankada nasa ba shima.
Don haka fatansa kawai shine ya bar garin Kano a yanzu, yayi nisa da arewa ma gabaÉ—aya, ya tafi inda ko yanuwansa baza su sani ba, idan yaso da ya sami lokaci sai ya zauna ya gyara wadannan CD's din da ya dade yana recording muryar Kilishi a ciki, ya cire duk inda ta ambaci sunansa da kuma muryarsa, idan yayi haka, sai ya turawa da Ma'aruf hakan yana daga inda yake, ya tonawa Kilishi asiri ba tare da kowa ya sanshi ba, idan yaso duk binciken da za'ayi idan basu gano shi ba, za'a karyatata ne a dora laifin akanta ita kadai.
Don haka a yanzu da ÆŠantaro ya kama shi zaiyi amfani da wannan danar ne kawai ya kwana biyu a wajensa, zai bari su rike shi ne har zuwa lokacin da hankalin Kilishi zai karkata daga kansa don ya san ÆŠantaro karya yake ba iya kashe shi zai yi ba, shi É—an kasuwa ne kawai mugu, amma muguntarsa ba ta tsallake wani geji.
Babban tashin hankalinsa kawai a yanzu shine wannan jakar da ya rasa, tunaninsa dama duk wani lissafinsa suna kanta ne, don idan har ya rasa ta bai san me ya kama ba a rayuwarsa, dukka wani tanadi dama kuma nadamarsa zasu tashi ne a banza. Don haka a lokaci guda da ÆŠantaro ya watso masa waÉ—annan katinan a fuskarsa a lokaci guda wata dabara ta haska a cikin kansa.
Dabarar da ya san ba makawa itace kadai hanyar mafitarsa a yanzu, hanyar da zai tserar da kansa.
"Kayi hakuri ÆŠantaro..."
Ya fada kai tsaye yana kallonsa.
"... wallahi banyi niyyar cutarka ba kuma ba guduwa nake shirin yi ba, kawai kwana biyu na shiga wani al'amari ya É—auke min nutsuwata gar na manta. Amma yanzu zaka sami kudinka, wadanannan kananun accounts ne da katinansu ma sun dade da lalacewa, akwai wadanda nake ajiyar kudi masu yawa a ciki, su kusan duka dukiyata ma suna cikinsu ne, amma na barsu a cikin jakar dake hannuna lokacin da suka buge ni,ku duba ciki zaku gani."
Dantaro ya kalle shi tsawon lokaci, ya kalle shi sosai yana nazarin sa, sai kawai ya murza yatsunsa biyu a iska suka fitar da wata kara ba mai yawa ba, amma duk da karancinta a lokaci guda kofar falon ta bude, wani katon mutumi ya shigo, Awwalu ya gane shi a matsayin daya daga cikin wadanda suka kamo shi, banbancin kawai shine a lokacin fuskarsa a rufe take a yanzu kuma ya buÉ—e ta.
ÆŠantaro ya nuno shi kafin ya ce da mutumin.
"Kun ga jaka a hannunsa?"
"Eh yallabai, mun ga jaka amma babu komai a ciki sai wasu kaset don haka bamu taho da ita ba..."
"Ku koma gidan dauko ta."
Ya fadi hakan yana katse sauran bayanin mutumin kai tsaye wanda yayi saurin gyaÉ—a kansa sannan yace.
"Yanzu kuwa yallabai."
Da haka ya juya ya fita. ÆŠantaro ya sake juyowa ya kalli Awwalu idanunsa akansa yace.
"Wannan gidan gona ta ne Awwalu, a bayan gari muke don haka idan har na gane cewa karya kayi min, ka sani cewa zan iya yi maka duk abinda na ga dama anan in gama ba tare da ka sami mai taimakon ka ba."
Awwalu ya gyada kansa.
"Babu dalilin da zani sa inyi maka ƙarya Ɗantaro, ka yarda dani idan har an samo wannan jakar baka da matsala."
Sai dai abinda daga shi har Awwalun basu sani ba shine, matsalar da yake faÉ—a kuma matsalar da kowannensu ke gujewa, tana dab da taka kasar Nigeria a lokacin!
***
Wayar dake hannun Kilishi ta katse a karo na ba adadi da take danna lambar tana katsewa.
Idonta ya sauka akan tanadin data gama yi akan Awwalun, tanadin da yazo a safiyar yau da aka kawo mata har airport taje ta karba, a cikin kwali yake a rufe, amma duk da haka sai da ta bada dubu dari biyar ga ma'aikatan wajen na toshiyar baki sannan aka bata shi ta taho, don duk da basu san meye ba, jikinsu ya basu cewar ba abu ne da hukuma zata yarda dashi ba, tunda ko daga can kasar da aka kawo shi ma, cikin sirri wani ma'aikacin jirgin ya fito dashi.
Babu wanda ya san menene, kuma kudin data basu ya toshe musu bakin tambaya, sai a yanzu da ita ta bude sannan ta ga meye a ciki ta kuma karanta komai dalla-dalla.
Allura ce, allura ce da ruwanta a cikin wata yar karamar kwalba da sai da ta saka gilashinta ta ita karanta rubutun dake jiki.
Ruwan dake ciki high dose ne na Ritalin, cocaine, Adderall, da kuma wasu amphetamines Alcohol Hallucinogens Opioids, dake tafiya kai tsaye zuwa cikin kwakwala su lalata wasu ɓangare a cikinta ta yadda hankali zai gushe.
Bayan haka ta gama tsara komai, ita kadai ba tare da taimakon kowa ba, tasa an kama mata hayar wani gida acan hanyar Na'ibawa inda zata kira Awwalun can, sannan ta samu wasu inyamurai guda biyu da zasu taimaka mata. Tunda har da kudi komai ba matsala bane a wajenta.
Idan komai ya kammala kuma, ita da Sadiq zasu je gidan nasa su ɗebo duk wani abu da yake taƙama dashi akanta sannan su goge duk wani abu da zai iya bawa jami'an tsaro wani bayani akanta tunda ta san dole al'amarin zai haɗa da hukuma idan har Awwalu yayi kwanaki baya gidansa.
To amma idan har ta gama wannan tsarin me zai sa kuma ta nemi Awwalun a yanzu ta rasa, lebbenta ya cije ta gefe guda ganin kiran ya sake tafiya kuma ya katse, ƙarya ne ace Awwalu ya iya gano cewar tana yin shiri akansa, mataimakinta ne ta sani, amma bata bashi damar da zaiyi wannan tunanin ba, zuciyarsa da ta ruɗe shi ta ja shi wajen tunanin bijire mata bata isa ta haska masa wani abu akanta ba.
Hannunta ya lalubo lambar Sadik a cikin wayar, wanda bugu É—aya biyu ya É—auka.
"Kana ina?"
Daga cikin wayar Sadik yace.
"Ina Yankaba Hajiya."
"Yaushe rabonka da gidan Awwalu?"
"Ai Hajiya tun ranar da kika ce kar na koma idan bashi ya kira ni ba, to shima kuma bai kira ni ba shi yasa kawai na shiga harkata."
Ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya.
"Ka tafi gidan yanzu Sadik, ka gano min me yake faruwa, yana nan ko baya nan."
Sadik din ya gyada kansa.
"Shikenan Hajiya, amma nima ina son in tuna miki fa cewa lokaci fa yana ƙara tafiya, naji shiru kuma, gashi ni ina son hada kaya in bar kasar nan kin sani Hajiya."
Kilishi ta gyada kanta kusan sau biyu a lokaci guda.
"Kar ka damu Sadik, ina tunanin daga yau zuwa jibi ma mun kammala komai na sallame ka, kai dai kawai yanzu kaje ka nemo min Awwalun, da mun same shi shikenan, rabin matsalar mu ta warke m u ma."
Sadik ya danyi shiru kafin ya gyda kansa yace.
"Shikenan, Normal Hajiya, sai kin ji ni."
Yana faÉ—in haka ya kashe wayar gabaÉ—aya. Kilishi ta sauke tata daga kunne tana sake yin wata ajiyar zuciyar, fata take da dukkan abinda ke cikin ruhinta na ta sami Awwalu a yanzu... Don taga alamun komai na shirin tsaya mata ne idan har ta rasa mafita a wannan al'amarin nasa. Shi yasa a É—azu bayan ta fita zuwa airport ta dawo, bayan ta tabbatar maganin nan yana hannunta, zuciyarta ta lissafa mata cewa ta fara rage sauran abubuwan dake gabanta kawai.
Don haka a karo na biyu kafafunta suka sake kaita zuwa ɓangarensu Ma'aruf, Su Samirah na can na shirye-shirye a cikin gida don haka ta tabbata babu wanda zai neme ta har ta gama abinda ya kaita.
Tana tuna yadda idanun Aminan suka yi a lokaci guda bayan ta buɗe ƙofar taci karo da ita, yarinyar ta riga ta gama tsorata da ita ta sani, shi yasa bata da wata fargaba akanta yanzu, ta san zata yi duk abinda ta sanya ta don tsirar da lafiyarta da kuma ta iyayenta da ƴanuwanta.
Abu biyu kawai ya rage mata a yanzu, abu biyu kawai, idan har tayi mata aikin Hamida sai kuma ta kwantar mata da Ma'aruf nan gaba kadan lokacin da zata gama da Baffa, da anyi hakan, ita ta san ta yadda zata yi kuma ta raba aurenta da Ma'aruf É—in kafin tafiyarta, don babu ta yadda za'ayi ta tafi ta barta a cikin rayuwarsa, ta haska shi da ita ne kawai don cikar nata burin ba don nasa ba.
Ita kadai take so Ma'aruf ya zama yana tunawa a kodayaushe, ita kadai take so ya dauwama yana danganawa da duk wani abu taimako da kuma jin dadi na rayuwarsa
_"Wannan shine maganin da zaki yiwa Hanifa amfani dashi Amina, gashi nan kamar kwalli yake, ki tabbatar kin sanya mata shi a idanunta kullum, abinda kawai nake so daga ke kenan, idan har naga tasirinsa a cikin kwanakin da suke a lissafe, a cikin waÉ—annan kwanakin iyayenki zasu mallaki sabon gida Amina..."_
Abinda ta gaya mata kenan bayan ta mika mata garin da yake baƙi a cikin wani hadadden kwanson sa kamar kwalli, kuma a idanunta ta lura da cewar kamar yarinyar ta canja amma sai zuciyarta ta kasa danganta hakan da komai sai na canjin waje da kuma jin dadin da take ciki sabanin gidan iyayen ta.
Ta wullar da abinda tunaninta yake so ya fara, don ko kwanaki Aminar da kanta ta kai mata sachet din magungunan hana ɗaukar cikin da ta bata da bayanin cewar ya ƙare... Kuma da hannunta ta dauki wani ta bata da ta san shima babu makawa zata shanye shi ne gabaɗaya, don haka bata ce komai ba bayan zancen maganin Hamidar har ta baro wajen.
Ta dawo tana lissafin yadda abubuwa ke fara gara mata, yadda komai ke kara tafiya cikin tsarinta da kuma hangenta. Abinda bata sani ba shine, tsarinta dama damar ta take gani kuma take taƙama da ita sun kawo wata gaɓa da zata kai ƙarshen kowannensu.
Ta gama rufe maganin da ta buɗe a cikin kwalinsa, sannan ta mike ta mayar dashi cikin kayanta, bangaren nasu sgirun yake ba kowa, don su Samiran gabaɗaya sun tattara sun koma ɓangaren Hajiya Maimuna inda suke shirin tarbar Abdurrahim din a can, tana ji Surayya na waya da Amina tana gaya musu cewa da ta gama nata aikin zata shigo itama, wani abu da ya daɗa tabbatar mata da cewar bata da wata matsala da yarinyar nan zata yi duk abinda tace hankali kwance.
Ta mayar da murfin wardrobe ɗin ta ruɗe a lokaci guda da wayarta ta ɗauki ƙara. Sanin ko waye yasa ta dawo da sauri kuma sunan Sadik da ya haska a kan fuskar wayar yasa ta ɗauka babu ɓata lokaci, kamar yadda babu bata lokacin muryarsa ta kwararo cikin kunnenta.
"Hajiya akwai matsala fa, motocin Æ´ansanda ne gasu nan zagaye da gidan, na tsaya daga gefe ba zan iya karasawa ba...."
Muryar Sadik din ta faÉ—i kalaman da a lokaci guda suka dako zuciyar Hajiya Kilishi da wani irin tasirin da tunda take a rayuwarta bata taba jinsa ba.
Abinda bata sani ba shine, wani abu da zai zama sanadin tarwatsewar zuciyar tata gabaÉ—aya yana dab da taka kasar Nigeria a lokacin!
****
"Ta kawo min maganin Amma..."
Muryar Amina ta fada tsaye daga cikin kitchen din tana kallon tukunyar tuwan data tarawa ruwa a cikin sink É—in dake gabanta.
"Tace yana aiki ne a lokaci ƙanƙani, tace ba zai ɗauki lokaci ba komai zai fara, don haka zata saka ido ta gani, idan har komai ya tafi daidai, alkawarinta ba zai canja daga yadda ta faɗa a farko ba."
Amma dake zaune a tsakar falonta tayi murmushi mai fadi kafin tace.
"Kar ki damu Amina, ki kwantar da hankalinki komai ya riga ya fara ai... Dama ita kadai muke jira!"
***
_Meye yake dab da taka kasar Nigeria?_
_Me kuke tunani zai zama jam'in dukkan waddanan gibin?_
_Kuna tunanin abinda Amma ke shiryawa yana da alaka da tonuwar asirin Kilishi?_
_Muna dab da faÉ—awa cikin ramin dai...!_
_Kar ku manta da Jawad fa, tasa gudunmawar na nan tafe soon Insha Allah._
_Ku gaya min ƙiyamar Kilishi ta tsaya!_
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:57 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*19*
_The fight between your heart and your mind is never easy..._
~~~~~~
"Mami..."
Sabon sunan da Hamida ta raÉ—awa Amina ya ratso ta cikin hayaniyar kitchen din. Shigowarta kenan bangaren bayan ta gama aikin nata tuwon ta kuma gama waya da Amma, wayar da ta sanya ta farin ciki a lokaci guda, ya kore dukkan fargaba da kuma damuwar da Kilishi ta saka a ranta bayan ta bata maganin nan.
Zuciyarta ta wanku tas da tsarin da Amma ta fitar musu, tsarin da babu shakka duk wayo da kuma hange irin na Kilishi bai isa ya tsallake dabarar tasu ba, don kamar yadda Amman ta fada ne...
_"Na gaya miki takunta zamu bi Amina, da kifi ake kama kifi,kamun da baya ganewa har sai ya ji shi a cikin komar masunci... Idan kika bi irin takun da take bi, to kin riga ki gama tsallake tunaninta har abada._
_Tun kwanaki na gaya miki cewa na fara shiri akan hakan, na gaya miki yarinyar zata makance a idanun Kilishi ne kawai amma ba'a zahiri ba. Don haka tsarin da nayi shine akwai É—an gidan Baffa Saliyo abokin mmahaifinku na unguwar Sharada, kin gane shi?"_
Kuma a lokacin kwakwalarta bata sha wahala ba wajen hasko mata fuskar saurayin da Amman ke fadi ba, shine Babba a gidan abokin mahaifin nasu kuna kwanan nan ya kammala karatunsa na likita har ma ya samu aiki a asibitin malam Aminu Kano. Don haka ta gyada kanta da sauri tana gaya mata cewa ta gane shi.
_"Shi nasa aka kira min har cikin gidan nan Amina, sati guda da ya wuce, kuma yazo ya same ni da daddare har cikin falon gidan nan... Nayi masa bayanin komai ta sigar da ba zai fahimci cewa matsalar daga ina take ba amma kuma ya fahimci dukkan kudirina, kuma ya gaya min zai taimaka, don haka yanzu duk bayan kwana biyu zai dinga rubuto takardar magunguna daga adibiti na yara da suke shaida ciwon ido, a hankali, a hankali ana yin gaba yana kara rubuta cewa ciwon yana habbaka._
_Maryam zata dinga kawo miki takardun duk bayan wani lokaci kina kai mata da cewar yarinyar ta fara ciwon ido... Rayuwar mace dabara ce Amina kuma Kilishi shaida kawai take nema a yanzu ba zahiri ba Amina, Kilishi tana wani matakin da ba zata saka ido akan al'amura ba yanzu, saboda ko ba'a faÉ—a ba kin san binciken da suke yi akanta yayi nisa. Don haka a yanzu kamar tana kokarin tattare abubuwa ne don tayi ta gama karasa manufarta kawai._
_Bayan haka kuma, idan kin lura al'adar Kikishi cewar bata da bin diddigi, da ta fahimci abinda take so ya faru shikenan kawai zata gama da wannan babin, na fahimci haka tun daga ranar da ta yi miki alkawarin tafiyar su Aminu India a lokacin da aka kira ta da bayanin Ma'aruf yana asibiti kafin ma ta ganshi.Don haka ki kwantar da hankalinki Amina, komai zai tafi daidai insha Allah."_
Kuma da wadannan kalaman hankalin nata ya kwanta, don kamar yadda Amman tace ne a yanzu hidimar dake gaban kilishi daban ce ita kanta ta lura, don ko a yanzu ma bata gidan tun dazu ta fita ba tare da kowa ya san ina ta tafi ba, wani abu da ya bawa kowa mamaki kenan, don da wuya ne idan ana hidima irin wannan ta sanya kafarta ta fita, hatta Æ´anuwan Hajiya Maimuna da suka zo kowa sai da yayi ta tambayarta ana sa ran dawowarta da wuri amma har yanzu.
Wani abu da a wajen Amina yayi mata daÉ—i sosai, don a kullum tana son irin wannan tazarar ta dinga faruwa tsakanin Kilishi da kuma farin cikin ahalin gidan.
Sai da ta kammala komai a bangarenta sannan ta taho cikin gidan, inda anan ta tarar har wasu daga cikin Æ´anuwan Hajiya Maimuna sun iso ana ta hidimar tarar Abdurrahim É—in da Ishaq yayi waya yace ya sauka gasu nan a hanya.
Basu yi waya da Ma'aruf ba tun dazu, bai kira ta ba kuma itama bata kara kira ba, don ta fahimci kwana biyu aiki yana yawan yi masa yawa, shi yasa bata so ta zama sanadin katse shi a komai, kamar yadda Amma ta gaya mata ne kamata yayi ta zama nutsuwar da zai dinga hanƙoro a duk lokacin da hankalinsa ke juyowa zuwa gida.
Don haka ko a yanzu ma da aka ce sun taho, bata kira shi ba ko kadan, aiki suke tayi na kokarin haÉ—a miyar taushen da aka manta da ita kwata-kwata, anyi masar tun rana amma sauran sha'anin su Samirah ya mantar dasu miyar sai a yanzu sannan aka hadu gabadaya ake kokarin gamawa kafin karasowar tasu.
"Mami...."
Hamida ta sake kira sanda ta karaso gabanta da gudu. Amina ta juyo daga yankan alaiyahun da suke yi ita Munaya.
"Su Aunty Sahla sun ce dan Allah in tambayeki su canja min kaya?"
Ta fada muryarta na fitowa kamar haki alamun ta dade tana neman nata cikin mutanen gidan.
"Kaya Hamida? A ina suka sami wasu kayan?"
"Su suka É—inka a School É—insu...!"
Ta faÉ—a da sauri tana katse ta. Kuma kafin tayi magana Munaya tace.
"Wannan shirmen nasu zasu saka miki Hamida... wannan karkatacciyar rigar da suka dinka?"
Tana fadin haka Amina ta gane kayan da take nufi, don itama har wajenta suka shigo suka nuna mata da murnarsu, rigar bata yi kyau ba sam!
"Wallahi Aunty Munaya tana da kyau... Pink ce fa!"
"Hamida ki bari idan Dadynki yazo sai ki tambaye shi kinji? Zai fi so ki fara tambayarsa tukunna.."
Amina tayi mata wayo ta tsaya kanar bata yarda ba sai kuma ta gyada kanta sannan ta juya da gudu.
"Har yanzu ina mamaki da akace wai yarinyar nan tana da cutar rashin son mutane da yawa, gashi nan yanzu tagane kowa a gidan nan kuma ta saki jikinta."
Munaya ta fada tana kallo ta ta cikin ymgayaniyar sauran mutanen dake shige da fice a kitchen din du Mama Rabi, sai kawai Amina tayi murmushi tace.
"Bata son ta rabu da ita ne kawai, kin san É—a da uwa."
Munaya ta taɓe dan karamin bakinta tana gyara zaman glass dinta tace.
"Ba wani kula fa take yi da ita ba, ba zuwa muke yi ba amma mun sani, atbfirst ma ba'a hannun Æ´ar aiki Yayan ya samo ta ba? Sai gashi kuma sun dawo da ita da kansu, sannan ko ita yarinyar ba kya ji tana nemansu."
"Haka ne." Amina ta fada a hankali idanunta na hasko mata hoton wannan layar, da kuma fuskar matar da aka aiko takanas har cikin gidanta, har yanzu basu sake cewa komai ba, basu sake yin wani abu ba, bata sani ba ko haƙura suka yi ko kuma suna shirya wani sabon shirin ne, zata so idan har ma basu haƙuran ba su cigaba da ɗaga musu ƙafa har zuwa lokacin da abubuwa dake gabanta a yanzu zasu yi sauki, don haka gudun kar Munaya ta cigaba da maganar yasa ta tsokane ta da cewar.
"Ina fata dai kin ajiyewa Yaya Ishaq nasa special abincin?"
Kuma murmushin da Munayan tayi yasa ba shiri ta taya ta itama.
Da misalin ƙarfe tara daidai na daren, motoci guda biyu na Ishaq da kuma Ma'aruf suka shigo gidan, a lokacin sun kammala komai, jiran baƙon kawai ake yi,bakon da sai a yau Amina ta fahimci irin kewarsa da al'ummar gidan suka dade suna yi bakidaya,a da yadda kowa ke harkokinsa ba'a zancensa sai jefi-jefi sai taga kamar basu saba dashi bane ko makamancin hakan, amma yanzu ko zuwan wasu daga cikin yanuwan Hajiya Maimuna kaɗai ya tabbatar mata da matsayinsa a zuciyarsu.
Tana kitchen ita da wasu Æ´aÆ´an Yar Hajiya Maimuna sanda suka shigo gabadayansu bayan sun baro bangaren Baffa inda nan suka fara danganawa dashi. Taji yadda falon Hajiya Maimuna ya ruÉ—e da hayaniyar murna kala-kala wadda bata ko gane me ake cewa.
Hannunta riƙe da farantin da aka jera kofunan kemo suka fito tare da sauran, kuma a lokaci guda idanunta suka lalubo Abdurrahim din, fari ne, fari ne sosai duk da bai kai Jamal din da take ganin hotonsa a wajen Ma'aruf ba, sannan yana kama da Ma'aruf din sosai, yanayin idanunsu da sumar gashin kansa da shima ya tara, sai murmushi yake yi zaune a kusa da Hajiya Maimuna dake kan kujera yayin da kowa ya yanyame shi da sakon gaisuwarsa.
Ma'aruf na tsaye daga bayansu riƙe da Hamida wadda ta makalkale shi, idonta ya kai kansu sanda Hamidan ke lalubo kunnesa tana rada masa wani abu da ta san ba zai wuce zancen rigar ba, a idanunsa kaɗai ta fuskanci tarin gajiyar da ba sai ya furta mata ba.
Sai kawai tayi masa murmushi ta karaso cikin falon suka gaisa da Abdurrahim din, bata ji muryarsa sosai ba amma taji kamar ya amsa da 'Lafiya' a hankali, kuma da yake bai santa ba shikenan abinda tace sannan ta juya kitchen din da niyyar dauko wayarta, a lokacin Hamida ta taho da gudu zuwa gabanta.
"Mami, Daddy yace inje a saka min kayan kuma yace dan Allah shima ki zo ki canja masa kayans..."
Hannunta tasa da sauri ta rufe bakinta don da ƙarfi take maganar sannan ta juyo tana kallon Ma'aruf din da ya juya yana yiwa Ishaq da ya shigo a lokacin magana, ta yaya zai gayawa yarinya wannan maganar?
Hamida bata jira taji me zata ce ba ma ta fita daga hannayenta ta tafi wajensu Sahlan da saƙonta tana murna, a lokacin ne kuma taji muryarsa yana tambayar Surayya da tazo wucewa.
"Ina Mami?"
Tambayar ta fito daidai lokacin da wani al'amari ya faru daga can falon Baffa, inda yake zaune a gaban talabijin ɗin dake ci a gabansa yana kallon labaran NTA na ƙarfe taran dare, a hannunsa guda robar robb ce da yake shafawa a ƙafarsa ta hagu.
Zuciyarsa a cike take da tsananin murnar dawowar Abdurrahim, a kowanne dare da kuma wayewar garin Allah fatansa baya wuce ganin iyalansa sun haɗu waje guda, a kodayaushe yana daga cikin addu'arsa cewar kar Allah ya ɗauki rayuwarsa ba tare da ya ga haduwar iyalansa waje guda ba, duk da cewar ya san akwai wani giɓin da har abada ba zai taɓa cikewa a zuciyarsa da ma ta sauran al'ummar gidan ba... Jamal.
Wayarsa tayi ƙara daga kan kujerar da yake jingine a bayansa, ya miƙa hannunsa ta gefe ya dauko ta, sabuwar lamba ce da b sant ba don haka ya ɗauka yasa a speaker...
Muryar wani dattijo ta fito daga cikin wayar a lokaci guda.
"Barka da dare yallabai... Ina magana ne da Alhaji Muhammad Mansour Bakori?"
"Barkanmu dai, Eh Ni ne Mansour."
Ya faÉ—a yana ajiye robar robb É—in dake hannunsa... Kuma kalaman da suka biyo, kalamai ne da babu shiri suka tsayar da duk wani tunani a cikin kan Baffa.
"Ranka ya daÉ—e suna na DPO Umar Nasir, matarka Hajiya Kilishi tana nan tare dani!"
***
*Washegari.*
*Ƙarfe shida da rabi na safiya.*
Motar na tafiya ne a wani irin yanayi da Zainab ta ƙasa gane gudu Jawad ke yi ko kuma akasin sa, idanunta na manne da titin dske gabansu yayin da take ji zuciyarta na bugawa a kirjinta da sautin da zata iya rantsewa cewa yana iya jinsa daga inda yake zaune.
Hannnusa ne guda akan sitiyarin motar ya danne shi da ƙarfin dake baiyana a ido, yayin da ƙafafunwansa ke ƙara take motar suna shillawa akan titin da bata san ina zai dangana dasu ba. Ƙarar sautin shigowar kira a wayarsa yafi ƙirgen da zata iya tunawa, bai ɗauka ba, bai kashe kiran ba ko ma wayar gabaɗaya, yi kawai take tana sakewa kamar ƙarar motar agaji,(ambulance).
Ta hadiye rawu a cikin maƙogwaronta a hankali tana sake matse yatsunta a cikin hijabin dake jikinta, wannan dogon hijabin sabo da ya bata, shi ta saka tayi sallar asubahin yau, sallar da tana sallamewa Jawad ya shigo dakin, kuma bai jira komai ba yace ta taso ta biyo shi.
Bata san me yake nufi ba, bata san ina zasu ba don haka ta taso ta biyo shi É—in zuwa cikin falon da komai yana nan kamar yadda yake a jiya, kayan abincin dake kan dining suna nan har a sannan babu wanda yabi ta kansu, bata ko buÉ—a su ba tun a jiyan, daga su har ledar magungunan da yace mata taje tasha suna nan a wajensu.
Don babu yadda za'ayi ƙafafunta su iya dauko ta daga inda ya bar ta a jiyan zuwa cikin falon, tasirin maganganun da ya gaya mata kafin ya fita su suka manne ƙafafunta a inda ta tsaya kuma suke ta maimaitawa a cikin kanta, maimaitawar da duk zagayen da tunaninta ke yi ya dawo a waje guda yake tsayawa, waje gudan da har a yanzu da garin Allah ke kokarin wayewa abubuwan da ta gane a ciki basu da yawa, don bayan ma kankantar tasu, ita shaida cewa ko giyar wake aka taru aka sha a garin tunaninta baya hango kasancewarsa.
Aure ba ƙaramin abu bane ta sani, ana yinsa kullum, cikin kowanne sati na duniya, amma duk da haka yana da wani irin girma da kuma darajar da ubangiji ya ɓoye a cikinsa, shi yasa har kullum yake kamar baƙo a zukatan al'umma, idan za'a gama yau a fara wani gobe, na goben zai zo ne da wani sabon farin ciki da kuma doki a zukatan masu yinsa.
Aure abu ne da rayuwar mutum ke tafiya gabadaya akai, rayuwar da zata mamaye farko har zuwa ƙarshe na kwanakin ka a duniya, shi yasa har yanzu bata ga dalilin Jawad na cewar zai aure ta ba don bata ga wani abu da take dashi a duniyar nan da zai iya hada rayuwarsa da tata ba.
Bayan haka ma, ita bata jin cewar tana sonsa, zuciyarta ta riga ta gama tsorata da tarin abubuwa, tun daga rayuwar da ta baro har zuwa wadda take yi a yanzu, sannan shi kansa tsoronsa ya fara dasawa a ranta, tsoron da a yanzu bata san ta yaya zata iya juya shi ya koma wani abu daban ba....
_"Ko ke baki da zaɓi yanzu Zainab, zan aure ki ko baki gama yanke shawara ba, idan yaso daga baya zan koya miki yadda zaki so ni..."_
Ta rufe idanunta a hankali tana tuna sanda suka iso wajen motar tasa yace mata ta shiga, a lokacin ne kafafunta suka tsaya waje guda cak! Ta tsaya daga daidai bayansa tana tambayar ina zasu tafi? Ina zai kaita a wannan safiyar ba tare da Hajiya Mardiyya ta sani ba ko kuma ta bata izini.
Abinda tayi dana sanin tambaya kenan tun daga kirgen wancan lokacin har zuwa yanzu, don yadda ya tsaya a gabanta ya rike hannayenta duka biyu da iya karfin da take tunani nasa ne, ya gaya mata cewar baya son baya son sake jin muryarta kawai tayi dukkan abinda yace, da wani yanayi ne da zata rantse bata taɓa gani a fuskar wani mahaluki ba, don sandan hannayenta duka biyu suna zafi da tasirin riƙon da yayi mata. Shi yasa bata ƙara cewa komai ba har a yanzu da suka yi nisa cikin tafiyar da bata san ina ne ƙarshen ta ba.
Zuciyarta na faman bugawa ne cike da tsoron irin tarin laifin da yake kara mata a wajen Mahaifiyarsa, Hajiya Mardiyyan da tun a jiya ta bata umarnin haÉ—o kayanta don ta maida ita garinsu, da kuma Deluwa matar da ta kawo ta gidan, don bayan rashin mutunci Dekuwa gar azaba tana yiwa duk yarinyar da ta kai gidan aiki ta gudu...
Tunaninta ya tsaya a lokacin da motar ta tsaya kusan a lokaci guda, kusan a lokacin gudun da tasirin hakan yasa tayoyinta gaba daya suka fitar da wata ƙara da ta cika kunnuwan su da suke ciki ma, kuma kafin Zainab ta sake wani tayi wani tunani ya ɗauki wayarsa da har a lokacin ke ƙara ya jona da wata waya dake jikin motar.
"Jawad, Jawad... Jawad..."
Muryar Aunty Sadiya ta cika speakers É—in dake cikin motar a take, daga bayanta hayaniya ce mai yawa ke tashi yayin da sautin kukan da babu shakka na Hajiya Mardiyya ne ke barazanar fin muryar tata karfi. A lokaci guda Zainab taji cikinta ya hautsine.
"Jawad kana ji na? Kana ina? Ina ka tafi?"
Tambayar ta shiga kunnen Jawad da sigar rainin hankali, ina ta tafi? Ina suke tunanin zai tafi bayan inda suka gaya masa?
A daren jiya har wajen ƙarfe biyun dare ana case din da yake gani da jin sa tamjar a mafarki, bayan ya shaidawa Alhsji Bashir komai, shi da kansa ya karbi wayar hannunsa, ya kira ƴansandan da shi ya kira ya tsayar daau daga zuwa gidan. Sannan shi da kansa ya kira mijin Aunty Sadiya yace ya kawo ta gidan a lokacin, bayan haka, ya kira dukkan sauran ƴanuwan Hajiya Mardiyyan da suke a garin yace suma yana bukatar ganinsu, kuma cikin abinda bai haura awanni biyu ba dukkaninsu su huɗu suka hallara, mata biyu da yayyensu maza biyu.
Hajiya Mardiyya itace ta karshe a kiran Alhaji Bashir din, alokacin ta kira wayar Jawad dake rile a hannunsa fiye da kirgen mai kirga, don tana ta nemansa a cikin gidan, bangaren Alhaji Bashir ɗin ne kawai bata zo ba don watakila tana tunanin bata da kwarin gwiwar fuskantarsa a wannan lokacin, amma sai gashi kafafun nata sun kawo ta, kuma a lokacin da ta shigo tayi arba dasu, ƴanuwanta har su hudu cikin wannan dare da kuma shi da Alhaji Bashir ɗin dake mata kallon da babu bukatar asarar kalmomi, sai gashi ta samu kwarin gwiwar ƙarasowa har gaban nasu.
Kuma a jiyan yaji komai, yaji dukkan wani bayanin daga bakin ita da kuma Aunty Sadiyan da suka fahimci tabbas dubunsu ta cika zuwa wata dubun.
Sun tunawa da kowa shekarun da Hajiya Mardiyya ta shafe babu haihuwa s gidan alhali dukkan sauran kishiyoyinta na tara Æ´aÆ´a, da kuma yadda ita Aunty Sadiyan ta dinga ziga ta akan shawarwari kala-kala, wadda bata dauki kowacce ba sai ta cewar tayi karyar tana da ciki, ta raini abinta kamar gaske idan lokacin haihuwarsa yayi, zasu samo jaririn da zata dawo dashi daga asibiti bayan sun tafi su biyu ba tare da kowa ba.
Kuma hakan suka yi, don kafin lokacin aka bawa Aunty Sadiyan labarin wata ungozoma acan wani kauye dake irin wannan harkar ta siyar da jarirai idan ta karbi haihuwa don a kaidar aikinta ta idan ta karbi haihuwa yaro bai zo da rai ba, ita ke binnewa, wai ladan aikinta kenan saboda jahilci irin na mutanen wannan ƙauyen a lokacin, don haka idan har ta samu masu nema, to tana basu ranar da zata karbi haihuwa ne su zo, ita kum idan har ta ciro dan, to akwai wani lakani nata da take yiwa jarirai da tun kukan farko basa kara wani, zasu yi ta bacci ne mai tsawo har zuwa wani lokaci ta yadda za'a yarda da ita dewar sun mutu.
Da wannan dabarar take shaidawa nmasu haihuwa cewa dansu ya rasu, da sun ganshi sai a bata gawa ta taho da ita gida, inda daga nan zata samu hanyar da zata yi ta dauko jariri ta kawowa masu bukata su bata kudinta.
Aunty Sadiya tayi bayanin haka ce ta faru dasu, a ranar da suka yi karyar naƙudarta ta tashi a ranar suka ɗauki mota su biyu kawai ita ke tuƙawa suka nufi can wannan ƙauyen da a lokacin ake ce masa Yakura, amma a yanzu ya koma Garun Albasu, anan suka sami matar da babu wani bata lokaci suka bata kudinta ita kuma ta basu yaro, inda murnarsu ta ƙaru ganin namiji ne.
Daga nan suka kama hanya suka dawo da cewar ta haihu kuma har an sallamo ta daga asibiti, kuma babu wanda ya zarge su aka shiga murna da shagalin suna... Kuma tun daga wannan lokacin suka binne wannan abin a tsakaninsu su biyu kawai ta yadda ko sauran ƴanuwansu basu taɓa sani ba sai a yanzu da ƙwaryar da suke riƙe da ita ta faɗi har kasa ta tarwatse.
Yana iya jin muryar Hajiya Mardiyyan a cikin kansa har yanzu, yana jin yadda take magiya da kuma kukan gayawa Alhaji Bashir cewa wallahi sauran ƙannensa mata da ta haifa shekaru biyar bayan shi ƴaƴan su ne na cikinta, ita da ƴaruwarta sunyi garaje ne kawai na tunanin bata haihuwa na tsawon shekaru bakwai kafin lokacin da ta sami cikinta na gaske.
Ya rufe idanunsa a hankali ya buÉ—e su kafin ya amsawa Aunty Sadiya da abinda take jira.
"Ina hanyar Kaduna..."
"Kaduna?"
Ta tambaya a lokaci guda.
"Inalillahi wainna ilaihir raji'un.... Haba Jawad me yasa zaka kama hanya da sassafen nan? Tun ɗazu muke nemanka, ina zaka tafi? Aƙalla ka saurare mu mana..."
Ina zai tafi? Ta yaya zai cigaba da zama a gidan nan alhali tun a daren jiya labarin komai ya zagaye gidan daga bakin Hajiya Yagana da bashi da tsntamar cewar ta ji dukkan tattaunawar da akayi.
Ta yaya zai kara zama yana kallon idanun kowa ba tare da wani bayani mai gamsarwa da zai iya kare kansa a wajen su ba? Bai ce ba zai dawo ba don ko Alhaji Bashir da yaje yiwa sallama abinda ya gaya masa shine zai dawo bayan ya sami Æ´anuwansa, kuma shi bai hana shi ba ko yace masa yayi garaje sai su....?
"Ka yiwa Allah da ma'aikinsa ka dawo Jawad, ka sani a cikinmu babu wanda ta taba cutarka, kuma bamu yi komai don mu cuce ka ba, to me yasa ba zaka saurare mu ba Jawad? Me yasa ko sau ɗaya ba zaka ji daga bakin mahaifiyarka ba... Tunda komai ya fito fili ka tunanin zamu sake ɓoye maka wani abu ne?"
Ya girgiza kansa a hankali kamar tana kallonsa.
"Kar ku damu Aunty Sadiya zan dawo...."
Abinda ya faÉ—a kenan kawai sannan yatsun hannunsa suka ni kashe kiran, sai dai muryarta ta sake kwararowa kafin hakan.
"Ina wannan yarinyar Jawad? Ina Zainab?"
"Tana tare dani."
Amsar ta fito cikin tattausan amon muryarsa da tsabar ruÉ—ani da kuma tashin hankalin da yake ciki ya haifar dashi.
Kuma daga shi har Zainab É—in, suna jin salatin da Aunty Sadiyan ta ruÉ—e dashi kafin ya kashe wayar.
Ɗib kiran ya katse a kunnen Zainab, yana sake tonawa kanta sautin zuciyarta dake bugawa a ƙirjinta, kuma bata juyo ba, bata juyo ta kalle shi ba, kanta na sunkuye tana kallon yatsunta dake girgizawa akan cinyoyinta, nemanta suke yi ita ta sani, shi tasa ko baccinta na jiya ta cika da mafarkai masu nauyi... Watakila gani suke tana da hannu a duk abinda Jawad ke yi.
Kuma ta sani ko a gaba suka sa ta bata da yadda zata iya yi musu bayanin cewa bata san komai ba, bata san me yake yi ba ko kuma su abinda suke yi, kamar koyaushe a rayuwarta babu wanda ya taba bata zabi a rayuwarta, komai faruwa kawai yake a gaban idanunta yayin da take jin tamkar an rufe bakinta an kuma daure hannayenta, kamar tana tsakiyar wani waje ne da bata da mafita kotawanne ɓangare,kamar tana cikin kwale-kwale ne a tsakiyar teku ta yadda ruwa ya zagaye kowanne bangarenta... Don haka bata da wani zaɓi illa ta zuba ido taga yadda Allah yayi da ita kawai.
Tana ji sanda ƙarar wani kiran ta cika motar, sannan taji sanda muryar wani namiji ta amsa.
"Oga sir.."
Shine abinda ya fara faÉ—a bayan sallama. Ta gefen idonta taga sanda ya dafe kansa yana yin baya dashi kafin ya amsa.
"Sulaiman ina ga a location dina saura bai fi minti biyar ba na kusa isa zuwa garin, ka tabbata mutumin da zaka hada ni dashi É—i yana nan a gari?"
Daga cikin wayar Sulaiman din yace.
"Yana nan Yallabai, bai fi minti biyar ba .a da muka yace min ya riga ya fito bakin titi yana jiranka, sunansa Nura, na gaya masa kalar motarka to da ka iso zai gane ka kawai."
Ya gyaÉ—a kansa sau biyu yana faÉ—in.
"Shikenan, nagode."
Sannan ya kashe wayar. Taji ƙarar sanda ya ajiye ta a gefen dake tsakaninsu kafin abinda bata yi zato ba ya biyo baya...
"Zainab zaki ci wani abu?"
Muryarsa a hankali ta fito,cikin amon dake shaida mata cewa nasa ne, ya dawo daidai ba kamar É—azu da ta tabbata baya cikin hayyacinsa ba.
Sai kawai ta rufe idanunta a hankali tana jin É—umin kwalla na kokarin cika su.
"Kina jin yunwa?"
Ya ƙara tambaya a hankali, sai ta girgiza kanta a hankalin itama ba tare da tace komai ba, shiru ya sake ratsa motar na wasu sakanni kafin ya kunna ta su sake hawa kan titin, kuna tafiya yar kadan ta isar dasu cikin wani tsohon gidan mai da ya koma kasuwa kuma maciyar mutanen hanya, wajen da ya hada da tarin kantinan da kusan duk wani abinda matafiyi ke bukata zai samu.
Bai kashe motar ba ya barta a kunne har da mukullin a jiki sannan ya bude ƙofar motar ya fita, Zainab ta bishi da kallo ta cikin mutanen dake wajen, kayan jikinsa wani kalar yadi ne mai ruwan toka, tafiyarsa kadai ta banbanta da tarin mutanen wajen har zuwa sanda ya bacewa ganinta, Idonta ya shiga yiwa cikin gidan man kallon sani amma nan da nan ta ƙaryata kanta, ta dawo da idonta ya dawo kan mukullin motar.
Zuciyarta ta ayyana mata yadda zata koma mazaunin direban ta murda shi, da zarar ta tashi sai tashi sai ta juya kanta ta fita daga wajen, ta komawa dukkan hanyar da suka biyo a baya har zuwa cikin gidansu. Wataƙila idan tayi hakan zata iya wanke kanta a wajen Hajiya Mardiyya da kuma Deluwa, watakila zasu iya yafe laifinta su mayar da ita gida wajen mahaifiyarta komai ya ƙare, komai... Har dashi kenan? Wani bari na zuciyarta ya ayyana mata, kuma rashin sanin amsar yasa ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta.
Cikin abinda yake ƙasa da minti goma Jawad ya dawo har a lokacin tana sake-saken a ranta, bata ko ganshi ba sai ji tayi an buɗe ƙofar gefenta, kuma kafin ta dago ya ajiye tarin ledojin hannunsa akan cinyarta sannan ya mayar da kofar ya rufe.
Idonta yabi ledojin da kallo tana jin kanshin kayan abinci kala -kaka da kuma nauyin robobin ruwa dana lemo da suke cikin tasu ledar daban, a cikin wata ƴar karamar leda fara, ta gano magunguna, irin magungunan da ya siyo mata jiya sak wanda suka bari a falon ɓangarensa.
Mamaki ya kamata, tsananin mamakin wani irin mutum ne Jawad da kuma halayensa, sai dai wannan mamakin bai kai koi'ina ba sai a lokacin da suka isa kofar shiga garinsu 'Garun Albasu' minti biyar bayan barinsu daga gidan man nan, a lokacin da ta ɗago kanta jin ya rage gudu suna kokarin sauka daga titi, lokacin da ta ɗago da idanunta suka sauka akan kasuwar ƙauyensu ta bakin titi kafin ka dangane da cikin garin, da kuma fuskar ɗanuwanta Nura, (ɗan mijin mahaifiyarta) yana washe baki yana tunkaro motar tasu da saurinsa.
A wannan lokacin abinda taji yayi kama da fadowar zuciyarta a cikin kirjinta, taji kamar ta faɗo ne ta fice ta ƙasan motar, tayoyin baya kuma suka bi ta kanta suka tarwatsa ta, jininta ya fallatsa a koina na jikin motar!
***
A cikin harabar tsakar gidan, mata ne kala-kala da kuma yara dake wasan su, matan na ayyukansu na yau da kullum wanda ya haɗa da girke da kuma surfen hatsi kala-kala, kusan rabinsu na goye ne da ƙananun yara a bayansu yayin da suturarsu kaɗai idan ka kalla, banda gini kasan dake zagaye da tsakar gidan zai shaida maka cewa mutanen karkara ne.
A wannan lokacin ne kuma sallamar wani dattijo ta karaÉ—e koina a tsakar gidan, sau daya ya furta sallamar amma a lokaci guda yanayin wajen ya canja, yara suka mike a guje suka nufi kasan rumfar dake barandar dakuna suka taru waje daya gabadayansu yayin da matan kowacce ta mike tsaye suna amsawa, yan tsofaffin dake zaune suna aikin busa ne jadai basu mike ba.
Mutumin ya shigo sanye da vabbar rogarsa wadda ta banbanta da yar ciki, hular kansa mai kyau ce wadda dattin dake tattare da ita ya boye hakan.
"Ina Talatu? Talatu, Talatu....!"
Kakkaurar muryar tasa ta fada yana karasowar ciki. Matar dake amsa sunan Talatun tayi saurin sakin itace da ta debobdon kara wutar girkinta tayo gaba tana faÉ—in.
"Gani Malam.."
Kuma tsaye ya nuna ta yana fadin.
"Wato Talatu rashin mutincin naki bai kai karshe ba dama? Sakin da na dannewa zuciyata ban yi miki wancan karon ba shi kike nema?"
Ba shiri Talatun ta dafe goyon Æ´ar dake bayanta sakamakon faÉ—uwar gaban da taji ta ratsa har ta bayanta tana shirin kwance goyon.
"Inalillahi wainna ilaihir raji'un Malam me kuma ya faru? Wallahi Malam vabu abinda na kara yi."
"Babu abinda kika kara yi? Karya nake yi miki kenan? Ko kuma shi wancan ƙaton Gardin da Nura ɗan gidan Malam Sadi ya rako min shi har majalisa suka zo nema ki dake ƙaryar suke? Dududu kwana nawa kenan da kika shigar min da mutum har ɗakin aurenki? amma ace duk uw*r tarzomar da aka sha baki hankalta ba? Allah wadaran auren jinin Hanne wallahi...!"
Ya fada muryarsa na dagawa, dagawar da tasa sauran matan dake gefe murmusawa suna kallon junansu. Talatu ta sake talkafe goyon bayanta tana girgiza kanta.
"Wallahi Malam, bani da masaniyar komai, ni ban san me suke nema a wajenta ba, ban san ma me yi musu kwatancena ba..."
"Ina zaki sani Talatu? Dama ina zaki sani... Muna zaune a majalisa kawai mota ta faka aka ce wai gidana ake nema, kin kunyata ni a cikin jama'a, ace ina zaune a gida da mata amma wasu maza daga waje suna zuwa nemanta? Wallahi darajar Malam da na karbi aurensa a wajenki kawai kike ci Habiba, amma anyi na farko anyi na biyu, na rantse da kabarin ubana aka sake samun wani É—an kaza-kazan da zai zo nemanki sai kin bi shi, billahillazi kafar sa kafarki, na gama zaman aure dake..."
Talatu ta gyada kai cikin amincewa da sauri sannan kafafunta suka durkusa har kasa cikin kasar wajen tana neman afuwa. Kuma sai da ya gama cikarsa ya bayse sannan yayi kwafa yace.
"ÆŠauko hijabinki, suna soro muje inji me ke tafe dasu."
Sai ta girgiza kanta, tana kallonsa tace.
"Wallahi Malam ba sai na fita ba, waɗancan mutanen da suka zo sun bar lambar wayarsu suka ce in kira su idan na samu wani labari, to indai suma Hanne suka zo nema zan basu lambar su nemi waɗancan su gaya musu komai, ka yarda dani Malam wallahi bani da wata alaƙa dasu."
Muryarta na rawa cike da tsoro yayin da yake kallonta idanunsa na haskawa da dimbin bacin rai da kuma fushin da a zuciyarta take kirga adadin kwanakin da zasu wuce kafin ta sake samun fuskarsa.
Muryarsa cike da ba'a, yace.
"Akwai abinda zasu nema ne da ya wuce Hannen? Duk danginku akwai mai jawo muku tsiya ne kamar ita?"
Talatu bata ce komai ba tana tsugunne a gabansa, hannayenta dake tallafe da goyon ƴarta na rawa a ƙasan goyon, kuma bata san lissafin da yake yi ba tsawon wucewar wasu mintuna kafin yace.
"Tashi ki ɗauko lambar, wannan shine na farko da kuma na ƙarshe a lamarin nan na gaya miki Talatu..."
Ba shiri sai ta miƙe tsaye, kuma bata ko damu da karkaɗe kasar da ta ɓata kafafunta ba, ta miƙe da sauri ta nufi ƙofar ɗakinta, kuma cikin abinda bai wuce minti guda ba ta dawo riƙe da wata farar takarda da take a miƙe samɓal, ya fizga tamkar zai yaga sannan ya juya ya nufi hanyar fita.
A ƙofar gidan ya tadda Jawad da kuma Nura dake tsaye suna jiransa, ya juya ya kalli motar da suka bari a can gaban gidan, wannan yarinyar dake ciki har yanzu tana nan, ta juyo tana kallonsu idanunta na na kallonsu a zare, sannan ya kalli tarin yara har da matasan da suka tsaya daga can nesa suna kallo su, don labarin maƙudan kudin da aka bashi ya danna a aljihu bayan ya fara fadan babu mai ganin matarsa ya kusa biye kunnen duk wanda ya sanshi a lokacin.
Ya ja tsaki mai tsawo yana fadin.
"Allah wadaran munafukai...!"
Sannan ya juyo ya sake kallon Jawad É—in dake a gabansa.
"Yallabai, matata tace bata da wani bayani da zata yi maka don Hanne ta rasu shekaru shida da suka wuce, amma ga wannan lambar, idan ka kira watakila zaka sami wani bayani a wajensu, don suma kamar kai sun zo nemanta kwanaki."
Idanun Jawad na kallonsa har yaje karshen zancensa, ba haka yaso ba ko kadan, yaso akalla yaga Talatun yaji bayanin komai daga wajenta, tunda sun sha tambaya tare da wannan matashin Nura amma babu wanda ya gane Hannen da suke nema sai da kyar aka samu wanda ya faÉ—a musu cewa matar ta daÉ—e da barin garin amma akwai wata Talatu da zata iya basu labarin inda take.
Kamar zai yi magana, amma sai zuciyarsa ta shawarce shi da cewar yabi mutumin a haka, don ya lura idan ya matsa za'a iya samun matsala, yau ya fara nema ba lallai ya samu komai a yau ba dama... Don haka sai kawai ya gyada kansa sannan hannunsa ya karɓi takardar kafin bakinsa ya furta godiyar da bai san ta wace sigar kalamai suka fito ba... Idanunsa suka manne da suna da kuma nambobin dake rubuce a jikin takardar lokacin da mutumin ya juya yana zagin jama'ar dake shirin taruwa a kodar gidan bunun.
Hajiya Salamatu.
080673....
****
Ruwan da ya sauka akan fuskar Awwalu mai tsananin sanyi ne fiye da na farko da ÆŠantaro yasa aka watsa masa awanni kaÉ—an da suka wuce.
Ya buÉ—e idanunsa cikin tsananin firgita, yana kallon wadanda ke tsaye a gabansa, da farko inuwoyi idanunsa suka fara nuna masa kafin fuskar ÆŠantaron dake saitinsa ta fito tar cikin hasken safiyar dake ratsawo cikin fankon É—akin da aka kawo shi aka kulle tun a daren jiya.
"Ni zaka yiwa shunen Æ´an sanda Awwalu? Ni zaka sa in aika yarana gidanka alhali ka aika Æ´an sandan can? Ni zaka yaudara Awwalu?"
Ƴan sanda! Kalmar Ƴan sandan ta doka wata irin tsawa a cikin kan Awwalu a lokaci guda tana sa shi wartsakewar da ba shiri.
"Ƴan sanda suka gani a gidan nawa?"
Muryarsa ta fito tare da shakku da kuma tashin hankali da baya neman tabbacinsa, kuma Ɗantaron bsi yi maganar ba sai kawai ya girgiza kansa sannan yayi wa yaransa biyu daje tsaye da bokitai alama da su karasa zuba masa ruwan bokitan dake hannunsu wanda ɗaya na zafi ne ɗaya kuma na sanyi, mai rike da na zafin ne ya fara juye masa tun daga saman kansa sannan na sanyin ya kwara masa shima har ƙasa.
Tasirin zafi da kuma sanyin da suja ratsa jikinsa suka sa dukkanin jijiyoyinsa riƙewa bakiɗaya, ya shiga kokawa da dawowar numfashinsa a kirjinsa kafin ya muryar Ɗantaron ta ratsa kunnensa.
"Kai baka isa ka tona min asiri ba Awwalu, wallahi, wallahi daga yau taka ta kare!"
Kuma ga mamakin Ɗantaro sai kawai Awwalun yayi murmurshi, murmushi mai fadi sannan ya girgiza kansa, don abinda Dantaron bai sani ba shine su duka biyun ne tasu ta ƙare! Tunda ya riga ya jawo shi jikinsa shikenan tasu ta kare gabaɗaya!
***
_Me kuke tunani ya haÉ—a Kilishi da É—an sanda?_
_Kuna tunanin hakan wani shirinta ne?_
_Shirinta na gaba wato kashe Baffa?_
_Ko kuma wata kaddarar ce daban?_
_Me kuke tunani ya faru lokacin da su Jawad suka shigo Garun Albasu?_
_Zainab bata shaida masa Garinsu bane? Ko kuma Nuran da yazo bai gane ta bane?_
_Jawad ya samu lambar Hajiya Salamatu, me zai biyo baya?_
_Mabudin komai dai, ya riga ya iso!_
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:58 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*20*
_Inch by inch. Life is a cinch. Yard by yard. Life is hard._ _—John Updike, Rabbit Redux_
~~~~~~
*Tariyar Baya.( Flashback)*
"Hajiya akwai matsala fa, motocin Æ´ansanda ne gasu nan zagaye da gidan, na tsaya daga gefe ba zan iya karasawa ba...."
Muryar Sadik din ta faɗi kalaman da a lokaci guda suka dako zuciyar Hajiya Kilishi da wani irin tasirin da tunda take a rayuwarta bata taɓa jinsa ba.
Bugun zuciyar tata ya cika kunnuwanta a lokaci guda da sauran bayanin Sadik din ya ɓace daga cikin kunnuwanta, ba shiri dukkan jikinta ya shiga rawa yayin da ta nemi gefen gadon nata ta zauna, hannunta daya da baya rike da wayar ya kamo zanin gadon don neman tallafi.
"Kana ina yanzu Sadik, ka bar wajen?"
Ta tambaya da sautin da taji kamar ba nata ba saboda ƙarar buguwar zaciyar tata da shi kaɗai take iya ji har a yanzu. Tun da rana da ta daga labulen dakinta ta kula da gajimaren da ya baibaye sararin sama, ya rufe ta kusan bakidaya saboda haka babu kadawar iska sosai, amma bata tabbatar da hakan ba sai a yanzu da take jin gumi ko tawanne ɓangare na lulluɓe ilahirin jikinta.
"Ina daga gefe Hajiya, na leƙa layin ne sai na dawo daga baya nake kiranki."
Wannan karon, muryar Sadik É—in ta amsa tar a cikin kanta.
Sai ta mayar da wani abu dake shirin tasowa daga makogwaronta kafin tace.
"Motocin Æ´ansanda ne kaÉ—ai a wajen Sadik?"
Ya girgiza kansa.
"A'a akwai wata karamar mota kirar Accord."
Accord. Accord... Kalmar ta rangaɗa a cikin kan Kilishi ta sigar tashin hankalin da ba'a saka masa rana ko lokaci. Accord motar Ma'aruf ce! Me yake shirin faruwa? Ta yaya zasu gano Awwalu? Ta ina? Ta ina tunaninsu zai iya samo Awwalu? Ba shi yaje ya miƙa kansa ba ta tabbata, don idan haka ne a ƙofar dakinta waɗannan motocin ƴan sanda ya kamata su tsaya ba'a gidan Awwalu ba.
"Sake komawa Sadik, sake komawa yanzun nan ka karanto min lambar karamar motar..."
"Hajiya..." Sadik ya furta muryarsa na shaida fargaba.
"Laifi ba'a manne yake a goshi ba Sadik, babu wanda ya sanka kuma babu wanda zai gane ka, ka koma ka karanto min lambar."
Yadda muryarta ta fito a kausashe tana shaida tsananin tafasa da kuma rudanin da take ciki yasa Sadik haÉ—iye maganar dake bakinsa sannan yace.
"Shikenan, bani minti biyu..."
"Kar ka kashe wayar..."
Ta katse shi da sauri, don bata sani ba idan har kofofin hancinta zasu iya shaƙar iska tsawon lokacin da zata jira shi. Tana jin ƙarar takunsa, zuciyarta na bugawa tare dasu har zuwa lokacin da ya isa wani waje da hayaniyar mutane ta shiga kunnenta a lokaci gyda, taji shi yana ratsawa ta cikin mutanen kafin muryarsa ta fito da harafan nambar motar Ma'aruf cikin amon muryarsa da Kilishi ta sani cewa har bayan ranta ba zata taɓa mantawa da ita ba. Don a wajenta, a bangarenta wannan lokacin shine mafarin komai, shine mafarin wata rayuwar da a yanzu bata santa ba.
***
*Current Situation...* *( Halin da ake ciki.)*
"Ta farka?"
Sune kalamai na farko da suka fara shiga cikin kanta, sune abinda ta fara ji kuma cikin amon da yake mafifici a wajenta, amon muryar da take tunanin ko a bayan kasa take babu ta yadda za'a yi ta kasa tantamce shi. Ma'aruf. Ma'aruf...
Zuciyarta ta biya sunan sau biyu kafin wata murya a cikin kanta ta ƙwallara kara, Ma'aruf? Me ya kawo Ma'aruf inda take? Me yazo yi a wajenta a wannan lokacin? Tsaya wane lokaci ne ma? Sannan a ina take tukunna? Tayi yunkurin bude idanunta amma kai tsaye sai wata zuciyar ta hane ta da hakan kai tsaye don haka ta fasa a daidai lokacin da muryar wata mace ke cewa.
"Gashin idonta yana motsi, da alama yanzu zata farka..."
"Tun É—azu abinda kike fada kenan, just go and call the Doctor."
Taji Ma'aruf ya sake fada yanayin muryarsa kamar a hasale.
"Yallaɓai na san aikina fa, idan da bukatar kiran likitan ai..."
"Ni zaki gayawa kin san aikin ki? Kin san aikin ki tun 8 kike zirga-zirga anan ta tashi ne?"
"B, Calm down ta san me take yi mana..."
Muryar Ishaq tayi saurin katse shi.
"Wannan tabe-taben banzan ne ta san abinda take yi Ishaq?"
Ya sake faÉ—a muryarsa na cigaba da É—agawa cikin fushin dake fitowa karara, kuna matar bata yi shiru ba ta sake cewa.
"Amma dai ka san mu bamu isa mu tashe ta ba idan har..."
"I don't f*cking care! Idan har me?all I know is mun kawo ta nan ne don ta sami lafiya."
Ƙarar sakin wani abu ta cika iskar dakin kafin muryar matar ta sake cewa.
"Then ga ka nan gata ai, sai ka bata lafiyar."
Da haka taji matar ta juya karar takunta na yin nisa daga inda Kilishi take a kwance yayin da maganganun su Ishaq ɗin ke ƙara shiga kunnenta, sai dai ba su Hajiya Kilishi ke saurare a wannan lokacin ba, tunaninta yayi baya ne yana tarewa ga abinda ya faru jiya don ta fahimci abinda ke faruwa yanzu.
Abinda ya faru bayan Sadik ya kira mata lambar motar Ma'aruf a ƙofar gidan Awwalun, cewa tayi ya jira ta a wajen gata nan zuwa. Don a lokaci guda kwakwalarta ta gaya mata cewa tunda har ƴansanda suka zo neman Awwalu basu same shi ba, to tabbas dole ne ita ta fito su san yadda zasu yi su nemi inda Awwalun yake a wannan daren ita dashi don ta gama da babinsa kafin komai ya caɓe mata.
Don haka tayi saurin yin transfer wasu kudade daga bankinta na ajiya zuwa na amfaninta da kowa ya sanshi da ita sannan ta debi kayan waɗannan allurorin ta zuba a leda ta fita, ta fita a lokacin da kusan duk jama'ar gidan ke ɓangaren Hajiya Maimuna na murnar dawowar Abdurrahim, ta fita babu wanda ya ganta don ko Maigadi bata samu a gate ba shima.
Da kafarta ta taka har bakin titi inda ta samu wani mai keke napep É—in da ya sauke ta a shagon wani mai POS ta ciro dubu dari biyar daga account din ta zuba su a wannan ledar don ta riga ta gama shirya yin asarar ko nawa ne a jiyan don samun inda Awwalu yake.
Tana iya tuna yadda zuciyarta ta dinga bugawa a kirjinta a lokacin, tana iya tuna yadda ta kasa zama waje guda cikin keke napep ɗin zuciyarta na cikowa a ƙirjinta,
har ƙoƙarin tsugunnawa tayi ta kuma yi ƙoƙarin tashi tsaye, daga baya ma taga kamar mutumin baya gudu sosai don haka tace dashi ya tsaya, ta sauka ta bashi kudinsa sannan ta tsaya neman wani, tana tsaye tsabar ruɗewa da kuma yadda kanta yake juyawa sai taga kamar daya barin titin an fi samun keke napep ɗin da babu kowa.
Kuma a lokacin ne abin ya faru, a lokacin da tazo tsallakawar ne motar ta buge ta, taji lokacin da ta tashi sama, numfashinta na biyo ta sannan taji lokacin da ledar hannunta ta suɓuce, tana gaya mata cewa kuma abu na ƙarshe da zata iya tunawa kafin numfashinta ya yanke shine taji hayaniya da kuma salatin mutane da yawa a saman kanta.
A yanzu a asibiti take kenan, asibiti ne daga maganganun da taji suna yi a saman kanta.... Salatin da bakinta ba zai iya ba shi zuciyarta ta karanto ta kuma sake karantowa, ina ledar dake hannunta ina kuma wayarta? Me yake shirin faruwa ne? Wane irin mummunan mafarki ne wannan? Ta yaya Allah zai jarabce ta da hadarin da har zai kai ga kwanciya a asibiti a wannan halin da take ciki? Ina ledar hannunta ina wayarta? Inalillahi wainna ilaihir raji'un... zuciyarta ta ambata tana sakewa, don abu na ƙarshe da zata so yanzu shine ace ledar hannunta dama wayarta tana hannun da bai dace ba, hannun da zsi iya tona asirinta ba tare da wata wahala ba.
Tayi kokarin yin motsi kaɗan, a lokacin ne taji yadda kanta ke juyawa kotawanne ɓangare, jikinta yayi tsami kamar anyi mata duka.
"Har yanzu akwai ƴan sanda a ƙofar?"
Taji muryar Ishaq ya tambaya, tambayar da ta haddasa dokawar ƙirjinta a lokaci guda, bugawar da ta nemi dagargaza zuciyarta, bakinta ya sake karanto kalar wani salatin da bata taba sanin ta iya shi ba... Ƴan sanda? A ina?
"Suna nan baza su tafi ba ai, Baffa yace babu yadda baiyi dasu ba, amma har sun tura maganar sama, don haka babu yadda za'ayi a rufe case din tunda shi DPO din da ya kade ta ma yaki saurarar Baffan su sake magana."
DPO? DPO'n Æ´an sanda ne ya kaÉ—e ta? Kuma yaga abinda ke cikin ledar hannunta? Yaushe duniya ta tsuke har haka?
Muryar Ma'aruf ta fito da kaushi, kaushin dake shaida tsananin ɓacin rai mai haɗe da tashin hakalin da baya ɓuya. A cikin kanta ta kintaci cewa ya girgiza kansa kafin ya cigaba da cewa.
"There must be a mistake dole Ishaq, me Mami zata yi da allurar ƙwaya irin wannan? Sannan har da kudi five hundred thousand a cikin leda? Na yarda framing dinta kawai wasu ke ƙoƙarin yi tunda ko Baffa ma bai san da fitar ta ba... Kuma ban san me yasa ba amma jikina yana bani cewa wannan al'amarin yana da alaka da case ɗin da muke yi, shi yasa nake so ta farka tayi bayanin komai waɗannan ƴan i*kan su bamu waje."
A wannan lokacin ji tayi kamar ta miƙe zaune ta girgiza kanta, ta gaya musu cewa ba zai yiwu ace komai ya caɓe mata a wannan lokacin ba...
Ba zai yiwu ba, tana da sauran lokaci, damarta bata taba karewa ta sani, tsarinta kullum daidai yake tafiya don haka ko a yanzu da take iya jin tsananin damuwa daga muryar Ma'aruf ta sani zaren bai ƙare mata ba, tana nan a Mamin da take a idanun kowa abunda ya rage kawai shine ta bude idanunta ta ture wannan ƙalubalen ta cigaba daga inda suka tsaya... Zata san yadda zata yi ta fidda kanta ta sani... Sun ga ledar a hannunta amma hakan ba zai basu tabbacin komai ba tunda babu wayarta.
Wayarta, babu wayarta, basu same ta ba, don haka ba shiri ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta, komai da sauki, komai zai zo da sauki kenan, ba'a kama Sadik ba, tana da sauran fata ta san yadda zata yi komai ya tafi daidai, ta sani.... Ita Kilishi ce kuma ko a wani hali tana da mafita...
"Ka cire tunanin wadannan mutanen a ranka B, babu inda zasu je idan har ba umarni aka basu daga can ba."
Ishaq ya faÉ—a daidai lokacin da ya daga wayarsa kuma ba sai yayi wani bayani ba daga gaisuwa kawai Kilishi ta fahimci cewa da Hajiya Maimuna yake magani.
"Mami baza su barku ku shigo ba, mu ma da I.D cards É—inmu muka yi amfani, yanzu ma so muke mu samu ta farka watakila komai zaiyi sauki..."
A lokaci guda hankalin Kilishi ya dugunzuma ya ƙara tashi, ak'amarin ya kai har a hana nakusantan ta ziyartar ta? innalilahi wa'inna ilaihir raji'un! Ta ina zata fara neman mafita idan har al'amarin ya kai haka? Me zata fara kamawa a yanzu? Ta ina zata fara bayanin inda ta samu allurar da kuma wajen da zata je? Wannan wane irin mummunan tashin hankali ne? Me yasa komai zai ɓare a lokacin da bata shirya ba? Me yasa sai a wannan nisan sannan ƙalubalenta zai zo? Don ta yarda har yanzu wannan ƙalubale ne, babu ta yadda za'ayi ace wannan shi zai kawo ƙarshen ta, tana da mafita a komai na rayuwarta, tana da ita ta sani! Kawai zata fuskanci wahala ne kafin ta daidaita komai.
"Hajiya ce, wai su Samirah ne har da kuka zasu taho..."
Taji Ishaq ya faÉ—a bayan ya ajiye wayar da yake yi.
"Babu wanda zai zo, su bari mu san me ake ciki ma tukunna, idan sun zo me zasu yi?..."
Cewar Ma'aruf yana jin tasirin abinda ke zuciyarsa na yin yawa, kuma Ishaq din bai ce konai ba, shiru ya ratsa dakin kafin wayarsa tayi kara, kuma yana jin ya dauka ya fara waya zuwa office ɗinsu, sai kawai ya miƙe, ya miƙe tsaye ya nufi kofar ɗakin, kuma bai kira komsi ba ya kama hanya ya fita.
Missed call É—in Faruk guda biyar ne, duka bai san lokacin da ya kira ba sai kuma na Amina guda biyu.
Amina ya fara kira kafin Faruk É—in, kuma sautin muryarta, wannan sassanyar muryar tata, shine abu na farko da ya tuna masa da irin tarin wahala da kuma gajiyar dake jikinsa, wanka kawai yayi a jiya lokacin da Baffa ya kira shi da zance mafi tashin hankalin da hafi ba zagayen halin da yake ciki, cewar wani dan sanda ya kira shi da cewar ya kade Mami akan titin hanyar gidan Gwamna, sannan sun tsinci wasu miyagun kwayoyi a cikin ledar dake hannunta.
Yana iya tuna magiyar da ta dinga yi masa a lokacin, magiyar cewar ya fada mata abinda ke faruwa, amma bai iya ba din,rigar da take miko masa a lokacin ya karɓa kawai ya zura a jikinsa sannan ba tare da ya damu da taje barbajajjen gashin kansa ba ko kuma ya shafa mai ya dauki mukullin motarsa kawai ya fito, ya fito ya barta ita da Hamidan dake binsa a baya da nata tambayoyin da kuma kwanukan tuwon nan da yaci burin huce gajiyarsa dashi kamar me...
"Babydoll...."
Muryarsa ta fito a hankali bayan ya shige cikin motarsa. Kuma maimakon ta amsa sai tace.
"Ya jikin nata? Hajiya tace har yanzu bata farka ba."
Hannunsa daya ya miƙa cikin barbajajjen gashin kansa sannan ya rufe idanunsa gabaɗaya yana jingina da kujerar motar.
"Bata farka ba, amma soon insha Allah."
Amina ta gyada kanta, tana zaune ne akan kujerar falon gidan tare da Hamida tmda tayi bacci akan cinyarta, basu dade sosai da dawowa daga cikin gida ba, don kamar kowa suma kusan a zaune suka kwana ana jimamin abinda ya farun, a yanzu ma ta dawo ne ta yiwa Hamidan wanka ta kuma bata abinci, wanda bayan ta gama ne bacci ya dauke ta.
"Kana tare da ita ne?
Ta sake tambaya a hankali. Ya girgiza kansa a hankalin shima.
"Na fito,ina mota yanzu."
"Dan Allah ka dawo gida kafin ka tafi wani waje... Baka ci komai ba fa.." ta fada ksmar zata yi kuka.
Yayi shiru kaÉ—an kafin yace.
"Kina ganin zan iya cin wani abu yanzu?"
Ta gyaÉ—a kanta a hankali.
"Zaka iya Sugar, saboda babu abinda zai faru insha Allah, komai zai tafi daidai kawai jiran sakamakon ne mai wuya..."
Ya gyaÉ—a kansa a hankali.
"Na sani Noor, da wuya sosai... Mami kamar mahaifiyata ce, ina jin ta har cikin raina wallahi hankalina ba zai taɓa kwanciya ba ace wasu sun saka ta a cikin wannan halin, babu abinda ya same ta amma har yanzu bata farka ba Amina, bamu san meye matsalar ba har yanzu, amma kuma duk da haka ace gaan saka ƴan sanda suna gadinta sun hana kowa shiga..."
Ƙwallar da ta cika idanun Amina ta gangaro zuwa kumatun ta, Allah ya sani tsoro take ji, tsoro take ji sosai na ranar da Ma'aruf zai san wacece Kilishi, don bata san yadda za'ayi zuciyarsa ta iya daukar masa hakan ba, bata sani ba ma idan har zai iya daukan...
Sai ta share su da bayan hannunta É—aya sannan tace.
"Babu abinda zai faru Insha Allah Sugar, alkhairi kaÉ—ai Allah zai azurta rayuwarmu dashi insha Allah."
"Insha Allah." Ya faÉ—a a hankali yana buÉ—e idanunsa sannan yace.
"Zan aiko direba ya karɓa min abincin, ba zan iya dawowa gida yanzu ba Babydoll, ayyukan dake jira na a office suna da yawa, yanzu ma na ga missed call din Faruk kusan biyar ban dauka ba."
Ta cije lebbenta kaÉ—an na ba hakan ta so ba, amma tasirin uzirin da ta san dole ne tayi masa ya danne son ran nata don haka tace.
"Shikenan Allah ya kaimu yazo É—in..."
"Kar ki sake yin komai, ki bar min É—umamen tuwon nan kawai."
Tayi murmushi jin daÉ—in cewa har yanzu bai manta da tuwon ba sannan ta gyada kanta a hankali.
"Insha Allah Habibi albi."
Ma'aruf ya sake lumshe idanunwansa yana jin tasirin muryarta da kuma sabon sunan a jikinsa. Yayi shiru kawai ba tare da yace komai ba, itama tayi shiru bata sake cewa komai din ba, kuma a cikin shirun yake yake jin kamar dukkan gajiya da kuma damuwarsa suna bin iska ne, sai dai hakan baiyi nisa ba sakamakon shigowar kiran Faruq da ya sake shigowa, ya É—ago da wayar ya kalla kafin ya sake maida ita kunnen nasa.
"Babydoll ki min hakuri please, zan É—auki kiran Faruq."
"Ba komai, kaje kayi aikin ka kawai, amma dan Allah ka turo direban da wuri."
"Insha Allah thank you so much for ur care." ( Nagode sosai da kulawarki.)
"Aiki na ne Sugar."
Ta faɗi abinda ya saka shi murmushi ba shiri, murmushin da yake ɗan mitsitsi amma ya taɓo har cikin zuciyarsa.
Kiran Faruq É—in ya É—auka ya kara a kunnensa.
"Faruq..." Ya furta muryarsa na fitowa yadda take.
"Ma'aruf kana ina?"
"Ina asibiti. Har yanzu bata farka ba."
Ya faÉ—a yana kallon rubutun 'Amenity 4' É—in dake can gabansa kamar yana son ya tabbatarwa kansa da hakan.
"Kazo office yanzun nan Ma'aruf, ga Brothernka anan yana buÉ—e mana aiki..."
Ba shiri ya miƙe zaune sosai yana buɗe idanunsa.
"Wane brothern? Waye? Me ake yi?"
Ya jero tambayoyin a lokaci guda harshensa da ma muryarsa na ƙoƙarin karyewa wajen tambaya.
Daga cikin wayar, Faruk yayi murmushi mai sautin da ya ji shi kafin yace.
"Brothernka da ya dawo jiya Abdurrahim, yaron nan wuta ne B, kazo ka ga aikin da yake yi, gabadaya forensic department din da muke dasu baza su iya ba B... Walkahi kowaye a bayan aikin nan, alƙiyamarsa ta tsaya!"
Faruk ya faÉ—i hakan a lokaci guda da kwakwalar sa ta tuna masa abinda Baffa ya gaya masa da safoyar yau.
_"Abdurrahim ya fita yace zai fara zuwa kamfani, inaga daga nan zai zo ya ganta shima idan zasu bari ya shiga...!"_
***
A ƙofar wani ƙaton Gidan ƙasa Jawad ke tsaye a jikin motarsa, idanunsa na kan ƙifar gidan ne wanda tarin mutane ke ta fitowa ta cikinta kamar gidan tururuwa.
Har yanzu lissafi kwakwalar sa kawai take yi na yadda abubuwa ke faruwa dashi bi-da bi, yadda duniyarsa ke tsukewa tana waje guda tarin abubuwan na bayyana gare shi, É—aya bayan É—aya kuma kowanne baya yin nisa da guda.
Kusan minti talatin kenan a dazu da Zainab ta gaya masa cewa garinsu ya kawota, garinsu,inda gidansu yake kuma inda mahaifiyarta take. Mamakin hakan ya harba cikinnkwakwalwarsa da tasirin wani abu da bai san shi ba, tsayawa kawai yayi yana kallonta yayin da hannunsa ke kan sitiyarin motar yana kokarin juyawa, bayan sun rabu da Nura ne, wannan saurayin da yayi masa rakiya har gidan da ya samo lambar da bai tabbatar idan zata amfane shi ba.
A lokacin har sun sauke Nuran ya juya kan motar suna shirin barin garin, kanta yana ƙasa tana wasa da yatsunta, sai kawai ji yayi tace.
"Dan Allah zaka kaini gida kafin mu tafi?"
Muryarta ta fito ne tana rawa, tana rawa sosai ta yadda da ƙyar ya gane me take cewa, ku.a ba shiri a lokaci guda ya tsayar da motar, Allah yaso ba gudu yake har a lokacin ba, ya juyo ya kalle ta har a lokacin kanta yana ƙasa,
"Me kika ce?"
Ya tambaya da sauri yana kallonta.
"Gidanmu, a can hanyar yake babu nisa, dan Allah ina so in ga Naani."
Ta sake faÉ—a wannan karon hannayenta na rawa fiye da É—azu. Kuma kalmar Naanin ta haska a kansa da wata ma'ana da ya taba sanin cewa ya rike a cikin kansa cewar haka take gayawa mahaifiyarta. Don haka ba shiri yace.
"Gidanku? Anan garin kike dama?"
Ta daga kanta.
"Nan ne garinmu, da muka zo nayi zaton gida Hajiya tace ka kawo ni, sai kuma naga ba haka bane... Wanda ya nuna maka gidan da kuka je sunansa Nura, shima na san shi, a gidan da mamana take aure yake."
Ba shiri hannunsa ya kai saman kansa yayin da bakinsa yake a buÉ—e, kuma a lokaci guda ya tuno da ranar da ya fara tambayarta sunanta da kuma inda take...
_"Sunan garinmu Yakura, a kusa da Kaduna yake."_
Haka ta fada muryarta tana rawa, sai kawai ya gyada kansa yace.
"Zainab kin san shi? Amma ya akayi baki yi magana ba shima kuma baice komai ba?"
Ta kai hannu ta share kwallar da ta cika idonta a lokacin, sannan ta girgiza kai har a lokacin bata kallonsa.
"Bai gane ni ba, bai sanni sosai ba, lokacin da na tafi ma baya garin ance ya tafi ci rani."
Sai kawai ya haÉ—iye wani abu da bai san sunansa ba a makogwaronsa yana kallonta, yana kallon yadda take sunkuye da kan ta da kuma yadda take share hawayen fuskarta, bai san kukanta na meye ba amma ya fahimci tsoro take ji, tsoron tambayarsa take yi don taje ta ga mahaifiyarta, shi É—in da ba kowa bane har yanzu a rayuwarta, wani abu da yake ji kamar ya fi tausayi girma shi ke gilmawa a zuciyarsa a lokacin haÉ—e kuma da mamakin yadda abubuwa ke kasancewa bi da bi a rayuwarsa.
Ya murɗe kan sitiyarin motar suka juya, kuma yana tambayarta da kwatance har zuwa ƙofar gidan da a yanzu yaje tsaye yana jiran fitowarta, yana jiran yayin da kwakwalwarsa ke cike da lissafi da kuma tarin tunanin abubuwan da bai san adadinsu ba.
A karo na ba adadi hannunsa ya sake danna wannan lambar da aka bashi, kuma ta shiga har zuwa bugu na ƙarshe kafin ta katse kamar kodayaushe, tunda ya tsaya a wajen yake kira, zai iya ƙirgawa kiran ya tafi kusan sau goma daga lokacin da ya fara zuwa yanzu, sai kawai hannunsa ya shiga bangaren sako ya rubuta abinda ya san ko waye zai karanta ba zai dauki neman da yake yi masa da wasa ba.
Kuma sai da ya tura sannan tunanin ko bai kwafi lambar daidai ba ya haska a ransa, sai kawai yasa hannu a aljihunsa ya zaro wannan takardar, ya kalli lambar jiki da kuma wadda yake kira yaga daidai ne sai kawai ya duƙunƙune ta yayi wulli da ita gefe, yayi wulli da ita daidai lokacin da ƙafafun wani dattijo suka fito daga cikin gidan.
Sanye yake da riga da babba Æ´ar ciki wadanda suke daban-daban, fuskarsa a murtuke take babu alamun fara'a ko kaÉ—an, kuma da kallo É—aya da yayi masa ya fahimci wanene shi, Mijin mahaifiyarta, mijin mahaifiyarta wanda tace shine sanadin tahowarta aiki, naganganu da kuma hoton wannan ranar da ya fara tambayarta sunanta ya sake dawowa cikin kansa.
_"Waye ya kawo ki nan?"_
_"Abokin babana ne."_
_"Ina baban naki?"_
_A hankali tace._
_"Ya rasu."_
_"Ina babarki?"_
_Sai da ya lura ta hadiye wani abu sannan tace._
_"Tana nan, matarsa ce ita yanzu."_
_Kalaman suka daki kirjinsa da wani abu da bai san meye ba, amma dai ya san nazarinta yake yi, nazarin shekarunta da ya kasa ƙiyasinsu._
_"Ita me yasa bata hana shi kawo ki ba?"_
_Sai ta sake dagowa ta kalle shi, idanunta na nuna wani abu da ya kasa tantancewa, idan ma tunani take cewa muryarsa ta fito da damuwa ne, zai goge mata hakan yanzun nan._
_"Bashi da kirki, Naani baza ta iya hana shi ba."_
Wadannan maganganun suka dawo cikin kansa a lokaci guda, a cikin sakannin da mutumin bai kai ga karasowa inda yake ba, don haka zuciyarsa ta ɗauke shi ta ajiye shi a wani mazauni na daban daidai lokacin da mutumin ya ƙaraso har zuwa gabansa ya tsaya kuma kai tsaye tambayar bakinsa ta fito.
"Yawwa, nace kaine Jawad É—in?"
Jin haka yasa shi gyara tsayuwarsa kadan sannan ya amsa, yana ƙoƙarin ture abinda ke cikin ransa.
"Eh ni ne, Barka da fitowa."
Sai ya gyaÉ—a kansa ba tare da ya amsa ba sannan yace.
"Ni ne mahaifin wannan yarinyar Zainab da ka kawo..."
Ya faÉ—a yana kallonsa don yaji me zai ce, amma baiyi maganar ba sai kawai ya cigaba da kallonsa, don haka shima ya cigaba.
"Ta gaya min tare kuke daga can gidan da take a Habujan... To an gode madallah zaka iya tafiya yanzu."
Kallonsa kawai Jawad yaje yi daga inda yake tsaye yana jin maganganun na shiga cikin kansa suna fita ta É—aya gefen,kuma sai da ya kai karshe sannan ya girgiza kansa.
"Nima nagode Baba, amma a yadda na sani mahaifinta ya rasu, kuma ni ban kawo ta ne don ta zauna ba, hasalima wani abu daban ne yazo damu nan kafin in san cewa anan mahaifiyarta take."
Mutumin ya sake kallonsa a sheke sannan yace.
"To ni nake auren mahaifiyarta kuma shi din wanda ya haife ta abokina ne don haka ka gaya min ta yadda ban zama mahaifinta, sannan a wane hurumin zamu sake daukan yarinya yanzu mu baka? Tunda dai ta zo gida ba shikenan ba, dama ita Deluwa da ta kai ta ai ta gaya mana cewa uwargijiyar tata,ta gaji da halinta tace zata dawo da ita gida..."
Jawad ya sake girgiza kansa yace.
"Ba gajiya suka yi da ita ba, zasu dawo da ita ne kawai saboda ni, saboda sun fahimci cewar ina son in aure ta, kuma da gaske nake ba da wasa ba..."
Dariyar da mutumin yayi ita ta katse shi daga kasa ƙarasawa, ya tsaya a lokaci guda yana kallonsa.
"Ai Zainaba tana da mijin aure tuntuni, itama ta san da wannan zancen, tun ubanta yana da rai muka hada su da É—an waje na Nura, baya zaman gari ne shi yasa itama muka tura ta don ta tara kuÉ—in kayan aikinta kafin ta dawo...."
Nura, Nura. Nura.... Sunan ya ɗarsu a zuciyar Jawad tare da hoton saurayin da suka sauke daga farkon garin yanzu, wannan saurayin da yake sanye cikin wasu dukunannun kaya riga da wando yana washe baki a lokacin da ya miƙa masa dubu biyu, sai kawai ya girgiza kansa yana kallon mutumin, wannan wani abu ne da ba zai taba yiwuwa ba, ba zai taɓa faruwa ba koda kuwa bayan babu ransa... Zainab tasa ce, tasa ce har abada, me yasa kowa baya ganin tambarin hakan da shi yake gani a tare da ita?
Ya sake girgiza kansa ya a kallon mutumin kafin yace.
"Kayi hakuri Baba, amma bana tunanin a yanzu kana É—aya daga cikin mutanen da zasu hana ni aurenta, saboda..."
"Saboda me? Nace saboda me? Ita bata gaya maka da alƙawari akanta bane tuntuni? To bari in gaya mska kaf dangin uwarta babu wanda ya damu dasu da nace zan auri uwar tata ma gode min suka yi don babu wanda yake bukatar nauyinsu sai ni da nace na ji na gani.
Dangin ubanta kuwa babu inda zaka same su, ko wuka ka dora akan uw*r tata ba zata iya gaya maka ba, daga ci rani yazo arewa bai koma ba... don haka bari in gaya maka babu wanda yafi ni iko da Zainaba a yanzu a duniyar nan don haka ka kama hanya ka bar min kofar gidana, ta gode da alherin da kuka yi mata acan da kuma wanda kayi niyya.
Yarinya ta dawo gida ba fitowa zata yi ba, kai bari in ƙarƙare maka ma ita da sake fitowa daga gidan nan sai idan zata tafi gidan Ɗana, ɗin mahaifiyar tata ma da take taƙama da ita, ta mutu yau kwanaki takwas kenan!"
"Ta mutu yau kwanaki takwas kenan!*...
Waɗannan kalaman sune ƙarshen abinda Jawad yaji kafin fuskar Zainab da kuma tunanin halin da take ciki a yanzu ya cika idanunsa bakiɗaya!
*****
"Aunty... Aunty... Aunty."
Amira É—iyar Yayar Hajiya Salamatu wadda ke yawan ziyartar ta idan tana gari ta faÉ—a tsaye daga bakin kofar dakin baccinta. Tana sanye ne da wata matsatstsiyar riga fitted gown data bi fukkan lunguna da kuma tudun jikinta yayin da ta sangala É—an karamin mayafinta daga gefe É—aya na kafadar, daya hannunta navrike da jakarta da take Æ´ar mitsitsita kamar ita.
Hajiya Salamatu ta yaye bargon da ta lulluɓe jikinta dashi, ta ɗago kaɗan tana kallonta ta gefe.
"Na tafi." Cewar Amiran.
"Yau ma da karatun ne?" Ta tambaya muryarta na fitowa a disashe.
"Eh Aunty, 2-4 ne lectures din, za'ayi na 4-6 ma amma ba zan tsaya ba."
Sai ta gyaÉ—a kanta.
"Daga can zaki wuce gida?"
Ta gyada kanta.
"Eh, amma idan kina gari zuwa jibi zan dawo."
Sai ta mike zaune a hankali kafin tace.
"Ina nan, bana jin daÉ—in jikina, bana tunanin zanyi tafiya kwanan nan..."
Ta É—an tsaya kadan tana kallonta kaÉ—an.
"Momi me ya same ki wai? Sadiya tace jiya ko abinci baki ci ba..."
"Na sha fruits, bana jin daÉ—in jikina ne kawai Amira, kije sai kin dawo."
Kuma daga hakan Amiran ta san cewa babu wani bayani da zata sake yi mata don haka sai kawai ta tabe bakinta kaÉ—an cikin siririyar muryarta tace.
"Bye-bye."
Sannnan ta juya tana jan hannun kofar da siraran hannunta da kusan dukkaninsa yake a waje. Hajiya Salamatu ta sauke ajiyar zuciya a hankali sannan ta dafw kanta da duka hannayenta biyu.
Bata jin dadi, abinda take fadawa kowa kenan tun a kwanakin da suka wuce,haka take gayawa kowa, daga wadanda suka kira ta don cinikayyar kaya har ma da wasu daga cikin Æ´an uwanta.
Kuma ba karya tayi ba, da gaske bata jin dadin, bata ji dadi tun daga wannan ranar da Awwalu ya furta mata maganar da ta darsa wani irin fata a zuciyarta, wani fata da ya zabge tarin shekarunta na duniya, ya mayar da ita zuwa wani lokaci na can baya, lokacin da take ɗauke da cikin ɗanta, lokacin da take jin abinda kowacce uwa ke ji a lokacin da abinda ke cikinta ya kusa karasowa duniya, wannan hanƙoro da kuma ɗokin, zata rantse irinsa take ji tun daga ranar da Awwalu ya bata sabon fatan da bata taɓa lissafawa dashi a rayuwarta ba.
Ta miƙe a hankali bayan ta yaye bargon dake jikinta, wayarta da ta ajiye akan mudubi ta jawo tana kunna ta, 10 missed calls daga wata sabuwar lamba ya nuna tar akai, sai kawai ta ajiye ta sannan ta nufi toilet, minti kusan ashirin a ciki tayi wanka hade da wanke bakinta sannan ta fito.
Bayan ta shirya ta ƙwalawa Sadiya kiran ta kawo mata abinda zata karya sannan ta koma kan wayar tata ta ɗauko ta, ba tare da tunanin komai ba hannun ta ya danna wannan lambar da ta tarar da kiran nata...
Ta shiga har sau biyu ta tsinke ba'a dauka ba, don haka bata sake kira ba, sai dai kafin ta kai ga ajiye wayar wani kiran ya shigo, lambar Salma ce Æ´ar gidan Kilishi, mamaki ya É—an kamata kafin ta É—auka, ta kara ta a kunnenta haÉ—e da sallama.
"Salma kuna lafiya?" Bakinta ya furta hakan kai tsaye.
"Aunty Mami tana asibiti, bata cikin hayyacinta tun jiya.!"
Saƙon ya fito tare da bugawar zuciyarta a lokaci guda, ba shiri ta karonto salati tun daga farko har karshe a bakinta.
"Gani nan Salma, gani nan zan zo gidan yanzu."
Ta faɗi hakan tana jin sauran hayaninyar dake tashi a cikin gidan kafin Salma ta kashe wayar,cgirman sakon na lulluɓe zuciyarta, har yanzu Kilishi aminiyarta ce, bata samu wata hujja da zata yi watsi da ita ba har yanzu, Awwalu baiyi nasara ba... Tana son ta ƙaryata shi duk da cewar zuciyarta tafi son ta bashi gaskiyar, amma har yanzu ba komai, bata da wani abubda zai nuna mata gaskiya ko akasinta...
Ta sauke tata wayar daga kunnenta daidai lokacin da idonta ya kai kan wani sakon da bata lura dashi ba sai a yanzu, saƙon text message ne, daga wannan lambar... lambar da ta kira a yanzu ba'a dauka ba. Idonta ya sauka akan harafan saƙon, harafan da suka canza rayuwarta da na duniyarta a lokaci guda!
_Assalamu alaikum, an bani wannan lambar ne da fatan zan samu bayanin wata mata mai suna Hanne, iyaye na nake nema a wajenta, please idan saƙon nan ya shigo contact me._
***
Ƙarar iskar dake kadawa ta shiga idanun Awwalu a lokaci guda da mutumin dake tsaye akansa ya kwance ƙullin da aka rufe fuskarsa dashi.
Ya rufe idanunsa saboda tasirin iskar da kuma na ƙasar dake tashi a wajen yayin da mutumin ya sunkuya yana kokarin kwance wayar da aka ƙulle hannayensa da ita ta baya, jijiyoyinsa suka saki bayan an kwance hannun ya shiga mutsikka su duka a lokaci guda, sannan ya murza idanunsa kagin ya buɗe su a gaban motar dake fake a gabansa.
Ya kalli kowanne gefe a inda suke, cikin daji ne mai fili gaba da baya, bishiyun da yake iya hange tsilla-tsilla ne.
Ya juyo da kallonsa zuwa cikin motar dake gabansa ƙirar Odessy sabuwa, idonsa ya sauka akan Ɗantaron dake zaune a kujerar tsakiya wadda aka zuge zuwa baya, gajeren wandon da yake sanye dashi tun jiya shine a jikinsa har yanzu, sai kuma baƙar T-shirt.
Yasa hannu ya zare gilashin fuskarsa sannan ya kalle shi.
"Ni ba ɗan i*ka bane Awwalu, ba zan zauna tare da kai ba alhali na san ƴan sanda suna nemanka ba, ina da ƙura a lamurana, idan na bari mutanen nan suka risko ni ba zan ji dadi, don haka ga ka nan na sake ka... Idan kun gama daidaitawa dasu, idan har baka mutu ba zan dawo gare ka don haka ka tanadar min kuɗina kafin nan!"
Yana faɗin haka yayi wani guntun murmushi sannan yaronsa ya rufe kofar motar ya zagaya zuwa gaba ya shige, cikin abinda yake kasa da minti guda motar ta tashi... Suka bar wajen suna tayar da ƙurar da ta bade fuskar Awwalu baki ɗaya.
Sai dai wannan ba shine abinda ya dame shi ba, ba shine tunaninsa ba... tunaninsa É—aya ne, he's free at last! Don haka ta ina zai fara??
***
_Ta ina kuke tunanin kowa a wannan babin zai fara?_
_Ta ina Kilishi zata fara?_
_Ta ina Jawad zai fara?_
_Ta ina Hajiya Salamatu zata fara?_
_Sannan ta ina Awwalu zai fara?_😅
_Wai ina Rukayya ne??_
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:58 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©�AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*21*
_Sin makes its own hell, and goodness its own heaven.-Mary Baker Eddy_
~~~~~~
Ƙarar tashin jirgin ta ragu a cikin kunnen Jawad, yana jin yadda tafiyar jirgin ke ƙoƙarin daidaita a sararin samaniya, yana jin kamar kafafunsa na bin gudun jirgin ne zuwa garin da suke dosa, yana jin yadda tasirin tazararsa da Kaduna ke yagewa a jikinshi, zaren na yin tsawon da bai san ta yaya zai kwatanta shi da wani sunan ba face cewar yana barin Zainab ne a baya, yana barinta a cikin halin da bai sani, halin da bai ko iya ganin fuskarta ba balle ya iya kintata halin da take ciki.
Sai kawai ya koma da baya ya rufe idanunsa, yayin da a hankali bi da bi abinda ya faru awannin da suka wuce tsakaninsa da Nura ya shiga dawowa cikin kansa.
*
"Karya yake..."
Abinda Nura ya fada kenan yana kallonsa a lokacin da yake tsaye a gabansa. Shi din da ya dawo ya sake nemansa lokaci kadan bayan rabuwarsu, don a tunaninsa tun bayan lokacin da suka sauke shi sun dade da barin garin, sai gashi cikin abinda yake kasa da awa guda kiransa ya sake shigowa wayarsa da tambayar yana ina? Kuma bai bata lokaci ba ya shaida masa inda taken duk da mamakin da ya kama shi, wajen da cikin abinda yake kasa da minti goma yazo ya same shi.
Tun kafin ya tsaya ya hango motar don haka ya taho ya iske shi a daidai jikinta bayan ya fito.
A wannan lokacin Nura zai rantse da Allah duk da ya dade da sanin halin mahaifinsa ba karamin mamaki ne ya sake lulluɓe zuciyarsa ba lokacin da Jawad din ya shaida masa abinda ke faruwa.
Farko, yayi mamaki sosai da ya kasance yarinyar ta zama Zainab ɗin da ya sani cewar a kwanakin nan an rasa zaman lafiyar gidansu saboda ita, ya san ya kalle ta a lokacin da ya fara haduwa dasu amma baiyi mata kallon da zai gane wacece ita ba don a tunaninsa matarsa ce, matar aure ce, matar da babu dalilin da zai sa shi kare mata kallo, don duk buɗewar idanunsa duk irin tarin zunuban da yatsunsa zasu lissafa ya aikata a rayuwarsa babu harkar mata a cikinsu, a kodayaushe a kowanne hali yana daraja mata, yana basu ƙima da kuma darajar da ya san Allah ya halitta su da ita, don haka mace ko wace iri ce ba saka ta a ransa.
Mamakinsa na biyu akan mahaifinsa ne, mamakin yadda kai tsaye ya haɗa ƙarya irin wannan don kawai ya kore alkhairin da ya san cewa ba zai shafe shi ba... Don halin da yake ciki bashi da alaka da zuwan Jawad ko rashinsa kwata-kwata, kawai yayi hakan ne don son zuciya da kuma ƙoƙarin kuntatawa yarinyar da ko maraicinta ba zai kalla ba don ya sassautawa rayuwarta.
Satin sa biyu da dawowa garin lokacin da mahaifiyarta ta rasu... Ya dawo ya tarar bata da lafiya kuma zai rantse kafin mutuwar tata akwai ranar da kunnensa yaji tana roƙon mahaifin nasa akan ya dawo mata da ƴarta don tayi jinyarta, wanda sai a sannan shi ya tuna cewa ma tana da ƴa guda daya da tsohon mijinta, kuma a lokacin ne ya fahimci inda yarinyar take don da kunnensa yaji mahaifin nasa na gaya mata cewa idan yarinyar ta dawo bai san kuma da wanne kudi za'a dinga samu ana siyo mata magunguna ba don shi bashi da shi.
Rigimar da ake ciki kuma a gidan ta fara ne tun bayan rasuwar mahaifiyar tata inda yanuwanta da suka zo suka nemi yarinyar kai tsaye kuwa sauran matan kuma suka shaida musu cewa ai mahaifin nasa ya kai ta can birni aikatau.
Saboda haka tun kafin a kai ga share makoki aka fara sa'in sa a tsakaninsu, suka tsaya akan cewar sai ya dawo musu da yarinyar, da kyar aka sulhunta wajen bashi wasu kwanaki da cewar ya dawo da ita, kuma basu ko tsaya an kai kwanaki bakwai ba ana share makoki da kwana uku gabakidayansu suka koma kauyensu.
Sai dai shi tun daga kan haka bai kara bi ta kan zancen ba yaji inda aka tsaya ya shiga harkokinsa, don haka a yanzu da ya riski wannan labarin daga bakin Jawad, har da kuma sunansa da zancen cewar shi zai auri yarinyar dashi ko kammaninta ba zai iya zanawa a zuciyarsa ba, kafafunsa sunyi mutuwar tsaye ne na wucin gadi yayin da zuciyarsa ke maimaita kowanne batu É—aya bayan É—aya kafin ya girgiza kansa a hankali yana kallon Jawad É—in.
"Ƙarya yake, wannan zancen ba haka yake ba, a gaskiya babu wani alkawarin aure tsakani na da yarinyar nan, ya faɗa maka hakan ne don ka rabu da ita kawai..."
Wadannan maganganun su Nura ya faɗa masa bayan ya ƙare masa dukkan wani bayani, kuna sune magan ganun da a lokaci guda suka ciccibo shi daga wata duniyar suka dawo dashi wata, yaji kamar ya saka hannu ne ya sauke masa wani tarin nauyi da yake yawo dashi a kirjinsa. Yana kallonsa lokacin da ya cigaba da fayyace masa komai...
"Ka gane... Da shi da mahaifinta abokan juna ne, to bayan rasuwar mahaifinta nata ne sai ya auri mahaifiyarta, a lokacin kamar daga ita har yanuwanta sunyi tunanin zata samu sauki ne a wajensa ko kuma sun ga cewa sun sanshi ne sai kawai suka amince, to ni ban san me yake faruwa ba bsyan na tafi amma dai na fahimci bata jin dadin auren, kuma da ya tashi tura yarinyar aikatau ya hana ta gayawa yanuwanta kamar dole yayi musu ne ya tura ta irin yadda yake yiwa sauran Æ´aÆ´an nasa.
To sai bayan rasuwarta ne a yanzu sannan suka dage akan cewar ya dawo musu da ita, sai kuma gashi yanzu kun zo, to ina tabbatar maka da cewar yanzu can wajen yan uwan mahaifiyar tata zai maida ita, kai kuma ya kore ka ne don ya san da zarar ya mayar da ita ba zai amfana da kai ba shi yasa yayi amfana da wani abu naka ba, shi yasa yayi amfani da sunana ya gaya maka wannan labarin amma ina tabbatar maka duk abinda ya faÉ—a babu gaskiya a ciki, don ni yanzu ma babu batun aure a gabana."
Tun daga farkon bayanin har zuwa karshe ya saurare shi ne da dukkan nutsuwarsa, da dukkan hankalinsa da kuma tunaninsa wajen tantance gaskiya ko kuma akasin kalaman nasa, sai dai duk iya nisan da hasashensa ke kaiwa, dawowa yake yi wajen gaskata shi da kuma yarda dashi, idan aka cire muryarsa a idanunsa kaÉ—ai yana ganin tabbacin kowacce kalma da yake furtawa.
Yana jin yadda zuciyarsa da kuma kowanne abu mai hankali a jikinsa ke yarda dashi, don haka a lokacin da ya kai karshe, bai ɓata lokaci ba ya shaida masa abinda yake son yayi masa bayan Nuran ya shaida masa cewa mutumin ba zai ɗauki lokaci ba wajen sa wa a maida ita wajen yanuwan nata tunda har an riga an ƙaiyade masa wasu kwanaki da sharaɗin ya dawo da ita.
"So nake kayi kokarin da zai mayar da ita wajen yanuwan nata da wuri, sannan ka bi su har can ka gano ƙauyen sai ka kira ni ka gaya min, zan biya ka ko nawa ne Nura..."
Yana tuna alkawarin da Nuran yayi masa, tarin alkawarin cewa komai zai tafi daidai kuma bai san me yasa ba haka kurum ya yarda dashi, ya ɗebo adadin wasu kudade daga cikin wanda ya fito dasu a cikin dashboard ɗinsa ya bashi da cewar ya kula da ita har zuwa lokacin da komai zai daidaita, kuma bai sake bukatar komai ba ya juya motarsa ya bar ƙauyen, ya riga ya fahimci cewa gaggawa shine mataki na farko da zai bata hanyar mafitarsa.
Bashi da wani ƙarfi ko kuma wani iko akan mutumin nan ya sani, babu yadda zai iya dashi a yanzu tunda har Zainab ta riga ta shiga hannunsa, don haka zai bi shawarar Nuran, zaiyi hakuri har zuwa lokacin da zata bar cikin ikon nasa, wanda yake saka ran saka ran hakan da wuri kamar yadda ya gaya masa, shi yasa bai ko damu ba a yanzu kafin tasowarsa da Nuran ya sake kiransa a waya ya shaida masa cewar mahaifin nasa ya ajiye Zainab ne a can cikin dakin uwargidansa inda ba zai iya zuwa ba don haka ba zai iya hada shi da ita a waya ba kamar yadda suka yi kafin rabuwarsu.
Wani abu ya wuce ta makogwaronsa a hankali yayin daya tuna babban al'amari na biyu dake shirin faruwa da rayuwarsa, bai san takaimaimai me zai faru ba, bai san na abinda zai je ya tarar a garin Kanon da yake nufa a yanzu ba, abinda ya sani kawai shine, tun kafin haduwarsa da Nura, bayan ya baro kofar gidan mutumin nan, kira ya shigo wayarsa da wannan lambar da aka bashi,lambar da yake saka ran ko yaya ne zata bashi hanya ta kuma saukaka masa wahalar tafiya neman abinda ya fito dashi har hakan ya shafi rayuwar Zainab.
Sai dai kuma ya fahimci kamar yadda yake neman wani abu haka ma matar da ta amsa wayar take, bai tabbatar ba don wataƙila baya cikin haiyacinsa a lokacin amma ya fahimci ba lallai ne idan tana da wata kwaƙƙwaran bayani da zata iya bashi ba, zai je ne kawai don ya sami wani abun akan iya abinda yake dashi, don ya tabbata ita ta daɗe tana nema, don haka tabbas zai samu wani abun da zai fi nasa.
Shi yasa ya yanke shawarar tahowa inda ta gata masa take a lokaci guda, ba zai koma Abuja ba, hatta wajen aikinsa ya riga ya rubuta takarda tun da asubahin yau ya tura musu na daukar hutu tsawon wasu kwanaki, kuma ya sani bashi da matsalar hakan don a shekaru biyu da suka wuce ko hutun karshen shekara da ake bawa kowanne ma'aikaci shi bai taɓa karba ba.
Su Hajiya Mardiyya kuwa bai ƙara ganin kiran daya daga cikinsu ba tun dazu, ya gaya musu zai dawo, kuma ya san hakan kadai ua ishe su su fahimci cewa ya riga ya yanke hukuncin da babu wani kuma da ya isa ya saka shi ya canja, tunda sun sanshi, sun san halinsa da kuma abinda zai iya tun kuruciyarsa.
Matar ta turo masa da address É—in inda take, a tunaninta a garin Kano yake shima, don kai tsaye ta gaya masa cewa zata jira zuwansa a yau din, shi yasa ya tabbatar da cewa itama nema take kamar shi.
Ya bude idanunsa a hankali sannan ya zura hannunsa cikin aljihun rigarsa, rigar da ya canja a cikin garin Kaduna inda ya nufa bayan rabuwarsa da Nura, Gidansu wani abokinsa Hashim ya nufa kai tsaye inda yaci sa'a Hashim din kuwa na nan, a gidan ya bar motarsa sannan yayi wanka ya canja kaya zuwa wasu riga da wando da ya tsaya a wani boutique ya siya, rigar kamar ta sanyi ce amma bata da nauyi, tana da hula mai girma wadda ya jawo ta ya rufe kansa da ma kusan rabi na fuskarsa, bayan kayan babu abinda ya dauja sai wayarsa da kuma wallet dinsa inda ya jera mint din kudaden da ya ciro.
"Maigida..."
Saurayin dake zaune a kujerar gefensa ya faÉ—a a hankali, ya juya ya kalle shi yana yin baya da hular rigarsa, wanda hakan yasa Saurayin ya kara yin murmushi kafin yace.
"Nace dan Allah ko zaka taimaka ka dan dauke ni a hoto, this is my first time hawa na jirgi, so ina so nayi posting a acconuts dina na social media ne..."
Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙo masa wayar hannunsa, babu yadda zai yi sai kawai ya gyada masa kai sannan ya karbi wayar ya danyi baya kadan yayin da saurin ya gyara zamansa a jikin kujerarsa dake kusa da taga, ai kuwa yayi masa hotuna guda biyar masu kyau sannan ya mika masa.
"Nagode, Nagode sosai, It means alot sir!"
Cewar saurayin yana murmushin jin dadi har da hade tafukan hannayensa biyu, kuma bai san me yasa ba sai kawai ya nuna masa kwalin wani abu a hannunsa da ska rubuta 'Free-dat' sakon kai abun ne yasa mutanen da suke do suka bada kudin jirgi a kawo...
"... Idan ba haka, babu abinda zai sa in hau jirgi a wannan matakin da nake a rayuwata."
Bai san lokacin da murmushin da bai shirya masa ya subuce a lebbensa, ba wai kuma murmushin abinda ya fada bane, murmushin jiye wa matashin dadin rayuwarsa yayi, dadin wannan lokacin da yake ciki da bashi da wata damuwa mai yawa, tazarar shekarunsa bata da wani yawa sosai ya sani, amma shi yanzu ne lokacin da komai yake hargitse masa, rayuwarsa ma gabaɗaya ta canja a cikin kwanakin da basu fi ƙarfin ƙirgen yatsunsa ba. Ya rasa identity ɗinsa sannan kuma yana shirin rasa yarinyar da yake ganinta a matsayin wani ɓari na rayuwarsa.
Ya tabbbata laifinsa ne ke bibiyarsa, ko ma ya fara, don shi da kansa ya sani cewa wanda ke aikata laifi irin nasa karya ne rayuwarsa ta dinga tafiya daidai,karya ne ka sabawa Allah akan haninsa kuma ace baka fuskantar wani kalubalea ruywarka, idan kuma hakan ta faru to kuwa tabvatas ka ji tsoron haduwarka da shi... Don ko hausawa sun ce 'Alhaki kwikwiyo ne, duk inda kayi sai ya bi ka.'
Ya sani cewar ya biyewa shedan a rayuwarsa,ya aikata rarin abubuwan da sanari da yawa a wannan zamanin ke ganin cewar ba laifi ne, kamar suna halattawa kansu ne ma wasu sabon Allahn a cikin lissafin morewarsu ta duniya, amma zai rantse da ubangijinsa tun daga lokacin da zuciyarsa ta fara fuskantar Zainab da kuma al'amarinta, ko shisha bai kara dandanawa a bakinsa ba, yana jin kansa ne kamar ya zama commited na tarin irin abubuwan nan da yake ganin bashi da lokacinsu, ko abokinsa Haro a yanzu su kan dade ma basu yi waya ba ganin yaki maida hankali game da shirin da suke yi akan Rukayya.
Rukkaya. Ya lashe lebbensa kadan sabida ambatar sunan da zuciyarsa tayi, tana ina a yanzu? Me ke faruwa a cikin tata rayuwar? Don ya tabbata ba shi kadai ne yake fuskantar sakamakon laifin da suka dade suna aikatawa a rayuwarsu ba, kwarai ko da ga nesa ne zai sp sanin halin da take ciki don ko layin da take samunsa dashi ma a yanzu baya wajensa, ya daÉ—e da bawa wani masinja a Office É—insu kyautarsa tare da sabuwar waya bayan ya kawo masa korafin rasa wayarsa da yayi.
Jirgin ya sauka a Kano da misalin ƙarfe 7:24 na yamma, yayi sallama da wannan saurayin mai sakon Free-dat sannan bai bata wani lokaci ba kasancewar bashi da kaya ya fito daga wajen, a cikinnairpot din ya samu mai motar da yayi haya har zuwa address ɗin gidan da matar ta turo masa.
***
*No 1856L, Sulaiman Crecent Kano.*
*Gidan Hajiya Salamatu.*
Babu irin sake-saken da Hajiya Salamatu bata yi a zuciyarta ba bayan sun gama waya da mutumin da ya tabbbatar mata da cewar shine ya turo sako cikin wayarta game da matar nan Hanne, kuma ya tabbatar mata da cewar zai same ta har inda take a yau.
Ta dauki wayarta da niyyar kiran tarin mutane amma tana fasawa, sai karshe da tunaninta ya tsaya kan kaninta mai bi mata da shima yake zaune anan cikin unguwar da take sannan ta kira shi, kuma a wayar ta kasa shaida masa komai sai da yazo gidan tukunna.
Kallon da yayi mata bayan ta gama yi masa dukkanin bayanin da Awwalu yayi mata da kuma yadda suka je har Garun Albasu nemsn Hanne da ma sakon da ta samu a yanzu,kallo ne da bata taba gani a idanunsa ba, kamar yana shirin cewa watakila ta samu cutar tabin hankali ne ko kuma zaiyi mitar ta taso shi akan abinda yake kamar almara, amma sai ya girgiza kansa sannan muryarsa cikin kokarin kwantar mata da hankali yace.
"Zamanin nan babu abinda ba ya iya faruwa Ya Salamatu, mutane sun haukace akan kudi yanzu, babu ta hanyar da ba za'a biyo ba don a yaudare ka yanzu, kar ki bari wasu suyi wasa da hankalin ki. Ni shaida ne da Kawu Muhammad da Yaya Murtala Allah ya jikansu, su suka binne jaririn da kika haifa matacce tun a wannan ranar...."
Saita girgiza kanta taba katse shi tun kafin ya karasa.
"Wallahi Nasir tun a wannan ranar da na rike jaririn da aka bani ban ga kamanni na ko kuma na Ibrahim a fuskarsa ba... Kuma banji komai ba, banji sani abu da ya danganta ni da wannan yaron ba."
Yana kallonta sai kawai yayi dariya ya girgiza kansa.
"Ba fa jiya ko shekaranjiya muke zancen al'amarin nan ba Ya Salamatu, shekaru kusan talatin da nawa kenan... ?"
Sai ta ƙara Daga kanta alamun amincewa sannan tace.
"Shikenan naji mu ajiye zancen nan Nasir, yanzu dai ai ba abinda ya kai ga faruwa, mutumin zai zo kuma zai same ni ne ni da kai saboda haka idan ma har akwai wani abu a ciki sai ka taya ni ganewa."
Da haka ta rufe bakinsa, bai ƙara cewa komai ba, suka zauna jiran mutumin da a cikin zuciyarta bata da tabbacin cewa zai zo ɗin, don haka tayi tarin sake-saƙen da bata san iyakarsu ba har lokacin a ya tafi sallar magariba a masallacin wani gida dake makotan ta ya dawo.
Yar aikinta ta kawo masa tarin abincin da yana ci yana kallon wasan ball a Tvn falon nata, hankalinsa kwance kasancewar ya gayawa matarsa inda yake, amma ita nata hankalin ya kasa kwanciya ta shiga daki ta fito har compound din wajen ta dawo yafi kirgenta, gani take yi kamar mafarki ne, kamar ba gaske bane abinda ke shirin faruwa, don hatta hasken fitulun gidan nata gani tayi sun disashe a idanunta, sun koma yanayin da mutum ke gani kamar a mafarki, kana ganin abu amma ba kamar daga nesa ba tar ba.
Hatta Nasir din sai da yace ta kwantar da hankalinta, idan basu ga kowa ba Allah ya tseratar da ita kenan, sannan a agogon falon nata ya nuna mata adadin mintunan da zai iya karawa a gidan don a kunnenta mutane har biyu sun kira shi da cewar suna jiransa.
Sai dai ƙarfe takwas da minti uku daidai, lokacin da wayarta tayi kara, zuciyarta ta buga tare da amon sautin kiran sannan numfashinta yayi nauyi a kirjinta ta yadda da kyar ta sauke shi ganin lambar da take jira ce ke kira, Nasir yayi mata alamun ta ɗauka. Kafin ta sake fitar da wata ajiyar zuciyar ta kara ta a kunnenta.
"Assalamu alaikum..."
Jawad ya furta daga can ɗaya bangaren, muryarsa can ƙasa ta fito, tana shaida masa tarin gajiya da kuma tarin lissafin dake cikin kansa.
"Wa... Walaikum salam."
Hajiya Salamatu ta amsa a hanzarce.
Daga wajen wani madaidaicin gida kuma mai farin gate din da yake tsaye, Jawad ya kalli plate number dake jikin katangar kafin yace.
"Ina kofar gidan da kika bani address É—in... Shine 1856L Sulaiman Crecent ko?"
Zuciyarta ta faÉ—a har cikin cikinta kafin ta sa
"Nan ne, bari nayi magana su shigo da kai."
Da haka ta kashe wayar, hannunta na rawa ta shiga neman lambar maigadi.
"Gashi nan ya iso Nasir, yanzu zai shigo."
Ta fada, kuma lokacin da Maigadin ya dauka bayan bugu daya, taji ne kamar tayi ihu wajen saka masa albarka.
"Akwai bako a waje ka shigo dashi yanzun nan."
"To Hajiya."
Ya amsa da sauri shima jin yansyin muryarta, Hajiya Salamatu ta ajiye wayar sannan ta tafi da sauri wajen tagar dakin dake fuskantar saitin bakin gate ta buÉ—e labulen, tana ji Nasir na cewa kar ta fita ta bari ya karaso tukunna.
Akan idonta maigadin ya fito daga dakinsa, ya bude kifar gate din ya fita sannan bayan sajanni uku kofar ta sake budewa suka shigo tare, tana hango su suna tahowa zuwa ciki kuma tun daga can zuciyarta ta shaida mata cewa ba wani babban mutum bane kamar yadda ta zata,matashi ne yaro daga shigar dake jikinsa ta wando da riga mai hula da kuma ƙirarsa ma, suna kara matsowa tana kara ganin tsawonsa kamar na daɗuwa, tsawon da a lokaci guda tasirinsa a idanunta ya zarce cikin zuciyarta ya sami mazauni.
Nasir ya riga ta tafiya ga kofar falon a lokacin da suka karaso, don bayan ta saki labulen ta juya da sauri ta tadda shi hana kokarin bude kofar tin kafin ma su buga.
"Yallabai barka dai, barka... Dama Hajiya ce tace a shigo dashi, bakonta ne."
Maigadin ya fada a lokacin da kofar ta bude a gabansu, tana tsaye daga bayan Nasir É—in sanda Maigadin ke fadar hakan sai dai ta tabbata daga ita har Nadir din bashi suke kallo ba, idonsu na kan matashin ne da ya saka hannu ya ture hular da ya rufe kansa, fuskarsa ta fito tar a cikin hasken fitilar wajen.
Ibrahim.
Shine mutumin da Hajiya Salamatu ta gani tsaye a gabanta.
Ibrahim Shanawa.
Mijinta na farko a duniya, mijin da ta fara zaman aure tare dashi, shine sak a tsaye! Cikin shekaru da kuma ƙuruciyar da ta aure shi, wannan lokacin da kyawunsa da kuma dukiyarsa suka rufe mata idanu daga ganin kowa a duniyar saɓanin shi... Amma ta yaya zai cigaba da kasancewa a haka bayan ita ta tsufa ta manyanta?
Wannan tunanin shine ya daki tsakiyar kanta a lokaci guda yana son tabbatar mata da cewar abinda take gani ba daidai bane, sai dai muryar Nasir da ta fito a lokaci guda ta katse wannan tunanin daga tabbatuwa, ta gaya mata cewa ba ita kaÉ—ai take ganin abinda idanunta ke nuna mata ba...
"Innalilahi wa'inna ilaihir raji'un...!"
***
*Bakori Enterprises*
*Administrative Office.*
_Zan iya fara restarting wani amma still shima ba lallai sautin ya buÉ—e ba sai da Frea-dat É—in._
Idon Ma'aruf ya karanta abinda Abdurrahim ya rubuta a fuskar wata Tablet da koyaushe tana hannunsa da ita yake nagana ta hanuyar rubuta dukkan abinda zai ce da dan yatsansa, ya karanta yaje har karshe sannan ya gyada kansa da sauri.
"Kar ka damu, just carry on yanzu zai ƙaraso insha Allah."
Ya faɗi hakan sannan ya juya gefe, daga can barndar katon ofishin da suke ciki inda Faruk ke tsaye yana faman magana a cikin waya, maganar da bata komai bace illa bayani da kuma kwatance wa wani mai online shop guda ɗaya da suka samu da suke da Fre-dat ɗin da Abdurrahim yake nema, wani abu da su basu taɓa saninsa ba don haka a yanzu Faruk ɗin na waya dasu ne don su san yadda za'ayi a kawo.
A safiyar yau ƴan sandan da suke aiki tare dasu suka kira Faruq da cewar basa tunanin akwai wani abu a cikin wannan tarin jakar cd's din da suka samu a gidan Awwalu, suka gaya masa cewar sun yi iya bincikensu amma basu iya ganin komai a cikin kowanne CD ba, don haka ba tare da ɓata lokaci ba ya aika a aka dauko masa jakar don shi ya riga ya yarda cewa ba zai taɓa yiwuwa ace an tara Cd's fal a cikin jaka guda ba tare da wani amfani ba, don haka suka bar wa yan sandan sauran aikin na nemo mai motar da ya ɗauki Awwalun kamar yadda mutumin nan da suka samu a unguwar ya shaida musu cewa ya gane lambar motar.
Faruk yasa an dawo da Cd's É—in office ne da tunanin idan komai ya natsa zasu nemo wajen da zasu iya kaiwa a buÉ—e musu ko a wacce kasa ne, sai gashi tun ba'a je ko'ina ba, tun ranar da akayi hakan bata kai ga faduwa ba, tun shi kansa bai kai ga zuwa ma yaji me ake ciki ba, Allah ya kawo Abdurrahim cikin wajen, kuma kamar da wasa Faruk yace hannunsa ya kai kan jakar ya buÉ—e ta yana zaro guda É—aya a lokacin da suke hira game da kamfanin da kuma dawowarsa.
Yace kallo É—aya kawai yayi wa Cdn ya rubuta masa sunansa da kuma abin da ake yi dashi, sannan ya tambaye shi me suke boyewa a cikinsa... Kuma dogon bayanin da yayi masa shi ya kaisu ga kokarin da Abdurrahim din ya fara yi da Computersa wajen kokarin bude cikinsa.
Kuma kafin karasowar Ma'aruf, kafin zuwansa wajen yayi nasarar bude guda daya da ya fara dauka har sun ji muryar dake ciki, sai dai sakanni goma sha biyar ne kawai a cikinsa inda shiru ya cike fiye da sakanni goma sha biyu, sai a cikin sakanni ukun karshe ne kawai suka ji wata murya daga can nesa tana magana da wasu kalmomi da ba wanda ya iya fahimta a cikinsu balle ma su tantance sautin.
A yanzu yana kokarin buÉ—e na biyun ne wanda a cikinsa har ya gano cewar anyi amfani da kusan minti talatin na sauti, don haka a yanzu yana kokarin buÉ—e kowannensu ne yadda da ya samu Free-dat É—in da suke nema, za'a karasa bude su nan take.
"A Kaduna suke ashe mutanen nan, flight nake dubawa daga Kadunan zuwa nan, sun ce zasu aiko da wani yaron su ya kawo..."
"Ba lallai ne a samu flight da wuri kafin yamma ba, mu duba wani wajen kawai..."
Ma'aruf ya fara fada amma Abdurrahim yayi saurin katse shi ta hanyar riko hannunsa sannan ya rubuta masa a cikin Tab dinsa cewar.
_"Nasu original ne, ba'a ko'ina ake samun abin nan ba, wasu zasu iya faking É—insa."_
Sai kawai Ma'aruf ya zura hannauensa gabaÉ—aya cikin gashin kansa sannan ya gyada kai kafin yace da Faruq.
"Shikenan kayi musu booking Flight din zamu jira..."
Ya fadi hakan wani abu na wucewa ta makogwaronsa da vai san meye ba,kuma a cikin wannan ofgice din suka shafe awanni suna cigaba da aikin tare da Abdurrahim din dake iya bakin kokarinsa wajen ganin yayi decrypting kowanne CD, har sai da ya zama kusan duka aikin tare suka yi shi su uku, wasu awanni da a cikinsu Ma'aruf ya kara fahimtar tarin abubuwa da yawa game da Abdurrahim din wanda ko a baya idan kowannensu yazo gida hutu bai sani ba kasancewar basu cika zama waje guda ba, a kullum shi yana tare da Hajiya Kilishi ne yayin da shi kuma Abdurrahim din ba zuwa nan yake ba.
Kuma a cikin awannin nan Ma'aruf ya kira wayar Baffa da kuma Ishaq wanda a yanzu su uku ne har da Baba Usman a wajen Hajiya Kilishi fiye da ƙirgensa, hatta mutanen gida sunyi waya dasu yana shaida musu halin da ake ciki gane da Mamin kasancewar bayan zuwan wani likita an sake shiga da ita wata tiyatar tunda sunce ta farka amma still bata iya bude idanunta.
Sau ɗaya suka sake magana da Amina, bayan ta aiko musu da abincin da yaga banda tuwonsa har kuma da karin wasu girke-girken guda biyu duk da yace mata jar tayi, sai dai sunyi amfani mutuka don dasu Faruk da Abdurrahim suka cika cikinsu tunda ba inda suka fita, daga sallar la'asar har ta magriba anan cikin office din suka yi jam'insu, bayan haka bata kara kiransa ba, bata ƙara cewa komai ba tayi masa uzuri kamar yadda ta fahimci yana buƙata wanda shi kaɗai ya san daɗin hakan da yaji a zuciyarsa.
Kuma bayan Sallar magaribar ne saƙon ya iso, wani matashi dashi aka aiko da Free-dat ya iso har cikin office din bayan Faruk ya tura anje an dauko shi daga airpot din.
Ya iso yana ta godiya da kuma murna kamar ya san su dama, a cikin drawer office fin Fatuk din Ma'aruf ya ƙirgo dubu arba'in yace ya sake booking wani jirgin ya koma suma sun gode. Kuma bayan godiya har sai da yayi abinda yasa dukkaninsu yin murmushi kuwa duk da irin zagayen halin da suke ciki.
Bayan fitarsa ne Abdurrahim ya gama installing Free-dat ɗin nan a cikin labtop dinsa sannan ya shiga saite-saite da kuma taɓe-taɓe cikin kokarin bude CD na farko da suka saka a ciki.
Karfe takwas da rabi na dare a sannan, kuma a wannan lokacin tabbas ne da za'a auna jinin kowannensu zai yi sama fiye da zatonsu, idanunsu gabadaya yana kan labtop din yayin da koren layin ke tafiya a hankali zuwa inda zai kai karshe kafin sautin ciki ya buÉ—e.
Idan ka É—auko hoton office din daga sama sai ka kalla sosai sannan zaka iya gane inda suke ma, don a hargitse yake gabadaya da tarin takardu da kuma wayoyin abubuwan da aka jojjona a cikin computer Abdurrahim, sannan ga kwanuka da flask din abincin da suka ci kowanne ya kalli hanyar garinsu.
Wannan koren layin na kan lamba ta 75 lokacin da wayar Ma'aruf tayi kara a aljihunsa, ya zaro ta hannunsa na wani abu kamar rawa ya kalli sunan da ya fito... Ishaq ne.
"Hello... Ya akayi?"
Bai ma san hakan ya faÉ—a ba lokacin da ya kara ta a kunnensa.
Ishaq ya shafo nasa gashin daga can cikin asibitin da yake tsaye, idonsa ya kai kan Baffa da kuma Baba Usman dake kokarin shiga office din wani likita da yasa akayi kiransu kafin yace.
"An fito daga aikin Ma'aruf...."
"Alhmdlilah...."
Muryarsa ta faÉ—a da karfin da yasa daga Faruq har Abdurrahim din juyowa su kalle shi.
Ishaq ya girgiza kansa daga can kafin yace.
"Mami ta rasa idanunta B, bata gani...."
Muryar Ishaq din ta fada a daidai lokaci guda da wannan koren layin ya kai karshe a jikin Computer Abdurrahim, kuma babu wani bata lokaci sautin dake kai ya shiga playing tar a cikin office, cikin murya guda da hatta Abdurrahim da ya debi shekaru baya gida kai tsaye zai shaida cewa Hajiya Kilishi ce, Mami... Mami dai! Mamin Ma'aruf!
_"...A banza na sa aka kashe min Jamal Awwalu? Ko kuwa a banza na rufe idon Ma'aruf daga ganin kowa hatta uwarsa kuwa? Ba duk akan wannan burin nawa bane ko kuwa ka manta kaima É—in alfarmar burin nawa kake ci har yanzu... To ta yaya zaka ce min mu dakata tukunna?_
_Ka sanni bana jira Awwalu, bama ni da kwanakin dazan sake wani jiran.... Ishaq ya kira waya yace Ma'aruf ya farka, kuma Baffa ya gaya masa cewa duk yadda zasu yi likitoci su sallame su tsakanin gobe ko jibi su taho don haka bani da lokaci Awwalu, ka nemo duk mutanen nan dole ne kuÉ—in kamfanin Bakori su shigo account dina a goben nan....!_
A daidai wannan lokacin ne daga can waje wani mai adaidaita sahu ya faka a gaban ginin kamfanin, Awwalu ya fito daga ciki idanunsa na kallon dogon ginin wajen da ya haska tar! da fitulu....
A wannan lokacin ne kuma daga can unguwar Nasarawa GRA, Ashraf ya buɗe ɗakin nahaifiyarsa Hajiya Nafisa, tana tsaye daga jikin mudubin dakin tana feshe jikinta da turare sakamakon shirin da take yi na zuwa wajen mijinta wanda ya dawo ƙasar a wannan ranar.
BuÉ—ewar kofar tasa ta juyo ta kalle shi a lokaci guda kuma sakewar fuskarta na canjawa da yanayin mamaki sakamakon yadda ta ganshi kusan a birkice.
"Lafiya Ashraf daga ina?"
Ta tambaya, sanin cewar a dazu ya bar gidan bayan yazo yayi wa mahaifin nasa sannu da zuwa.
"Mamaah ina kika ce Ruƙayya ta tafi?"
Wani asibitin kawarta a Abuja, don a duba ta sakamakon ciwon kan da take yawan fama dashi.... Haka tace musu a É—azu bayn da kowa ya hallara a falon mahaifin nasu suna murnar tarbarsa, har Ahmad na cewa dole tayi ciwon kai tunda ta saka damuwa a ranta,mahaifin nasu kuma yace a kirawo ta a gaya mata ya dawo don haka itama ta dawo.
Fuskarta a É—aure kaÉ—an tace.
"Ba munyi zancen nan da ku É—azu ba? Me zata yi maka?"
Sai kawai ya É—ago wayarsa dake hannunsa ya nuna mata.
"Abokina ne ya turo min hotunan wani hatsari da ya haÉ—a da kawunsa a Niger dazu... Mamaah har da Rukayya a ciki....!"
Ya fadi hakan a lokaci guda da idonta ya sauka akan hoton Rukayyan dake kwance a gefen titin tare da alamun mutane kwance a gefenta, taba sanye da wata doguwar rigarta da ta sani ta atamfa wadda ta yayyage ta kuma ɓaci gabaɗaya da jini, idanunta a rufe suke yayin da fuskarta take a daddauje wajaje da yawa,yanayinta bashi da maraba da na sauran gawawwakin daje zube a wajen...!
***
_Ƙarshen tika tika.......!_
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:58 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*22*
_People pay for what they do and for what they allowed themselves to become, simply by the lives they lead.- Edith Warthon._
~~~~~~
Haske ya ratso cikin É—akin, ta tsakanin labulen dake dagewa a hankali sakamakon iskar dake kada su kasancewar windon a bude yake.
Farko hasken rangwame ne kafin a hankali cikin abinda bai minti biyar ba ya shiga karuwa a hankali, yana yin yawan da ya fara damun fuskokin mutane biyun dake kwance akan doguwar kujerar falon, Amina da kuma Hameeda duka su biyun sun kudundune ne cikin sigar da a kallo daya zaka san cewa bacci ne ya dauke su a wajen ba tare da sun shirya masa ba.
Hasken yasa Amina ƙifta idanunta a hankali kusan sau hudu kafin ta bude su,ganinta na sauka akan Hamidan da kanta yake daf da tata fuskar ta yadda saman gashin kanta kawai take iya gani.
Idanunta suka tsaya a layukan dake tsakanin kalbar kanta tana ƙoƙarin saita tunaninta kafin ta tuna dukkanin halin da suka shiga a daren jiya.
Ma'aruf bai dawo ba, babu shi babu kuma su Baffa, da misalin karfe goma na daren jiya suka fara buga wayoyinsu ita da mutanen cikin Gida, ta Baffa da kuma Baba Usman basa shiga kwata-kwata, wayar Ishaq da kuma Ma'aruf ɗin kawai ake samu suna shiga suna katsewa har ƙarshe amma babu wanda yake dauka.
Da farko suna kira ne don su ji halin da Hajiya Kilishi ke ciki amma ba'a fi minti goma ba sai ya koma suna kiran ne don su san halin da su É—in ma suke ciki.
Hankalinsu ya tashi zuwa nisan da ba zai kwatantu ba, sai daga ƙarshe da Munaya tayi tunanin a kira Malam Sani sannan suka samu shi ya dauka a bugun farko da bai katse ba, kuma kai tsaye ya gaya musu cewa ai sun riga sun baro asibitin tare dasu Baffa, ya gaya musu cewa bai san dai me ya faru ba amma ya fahimci kamar wani ne ya kira su da cewar su taho kamfani don tare har da Ishaq suka taho kamfanin yana bin bayansu a motarsa.
Da magiya Hajiya Maimuna ta roke shi akan ya hau zuwa saman ya bawa É—aya daga cikinsu wayar amma bayan yaje É—in yace kofar koridon da take kaiwa ga ofishin da suke ciki ma gabaÉ—aya a kulle take don haka ba zai iya shoga ba.
Wani abu da ya kara tsurar dasu kenan, suka yi firgi-firgi dukkaninsu mata kawai a cikin gida don hatta su Hamida dake harkokinsu tare dasu Sahla sai da suka sami waje suka nutsu... Hajiya Maimuna tace tafiya zata yi, tasa Munaya ta kira wani É—an yayarta da suke kira da Abdoul akan yazo ya dauke su su tafi.
Sai dai inda Allah ya taimaka, minti biyar bayan hakan kiran Baffa ya shigo cikin wayar Hajiyan, tana tuna idanun kowannensu a lokacin nan, da kuma sautin karar bugun zuciyarsu da bayan nata da ya cika kunnuwanta tana jin kamar tana jin na Surayya da kuma Samiran dakezaune a kowanne gefenta.
Kuma sai Allah ya taimaka suka ji abinda dukkaninsu suke fata, Baffa ya shaidawa Hajiya Maimuna cewa babu komai ba abinda ya faru gasu nan zuwa, a lokaci guda sai hankalinsu ya kwanta kowa ya shiga hamdala yana godewa ubangiji, amma tun a lokacin haka kurum taji cewa ita bata gamsu da hakan ba, jikinta bai sake ba kamar yadda na su Samira yayi a lokacin.
Tayi niyyar su zauna acan har ƙarasowarsu amma sai Inna Danejo tace dare yayi, gwara Ma'aruf yazo ya same ta a gida bayan dukkan gajiyar da yasha, don haka su Munaya suka rako ta tare da Hamidan da tayi bacci a lokacin, kuma sai da suka shigo suka koma sannan ta tuna da wayarta da ta bari a cikin gidan.
Da tunanin dawowar Ma'aruf cikin abinda ba zai fi ƙasa da minti talatin ba yasa bata yi niyyar komawa ba, ta canja kayan jikinta zuwa na bacci sannan ta canjawa Hamida ma, tun rana take jin wani abu kamar zazzabi na shirin kamata, ko abinci bata ci mai yawa ba don haka kurum taji bata son kamshin miyar da aka yi a cikin gidan, tana da ragowar abincin da tayi wa su Ma'aruf aka kai musu amma ta saka a fridge ta sani yayi sanyi yanzu.
A yadda take jin kowacce gaɓa a jikinta tayi nauyi sai kawai taji gwara ta hakura da abincin don haka ta dawo falo ta kwanta, kuma tun tana kirga minti biyar da goma har ta koma sha biyar da ashirin, har idanunta suka fara rufewa babu alamun dawowar Ma'aruf, kuma a lissafin da take yi na komawa cikin gida ta dauko wayar bacci ya dauke ta, bata farka ba sai karfe biyu na dare da kukan Hamida ya tashe ta, kafafunta na sasarfa ta koma dakin inda ta same ta zaune akan gado tana kiran sunan 'Mammy'.
Sunan da tana ji ta san mahaifiyarta take nema tunda ba haka take gaya mata ba, da kyar ta lallaba ta ta koma baccin, wanda a lokacin ne kuma tashin hankali ya daki tsakiyar kanta da tunanin halin da ake ciki da yasa Ma'aruf bai dawo ba har a sannan.
Ta zura hijabinta sannan tayi hanyar kitchen da niyyar nufar cikin gidan, amma tana buɗe ƙofar baya ta kitchen ɗin, da duhun daren lokacin ya shiga idanunta da kuma shirun dake waje, sai ta kasa fita, ta rufe ta sannan ta dawo zuciyarta na gaya mata cewa dukkan halin da ake ciki zata sani idan garin Allah ya waye.
Sai dai bayan ta dawo ta zauna din, ko da wasa bacci ya kasa daukarta, hankalinta ya kasa kwanciya, ta dinga zama tana canja waje, tayi sallah raka'a biyu kuma ta kasa kara wata daga hakan, tana zaune kawai akan sallayar zuciyarta da yatsunta cike fal da lissafin abinda zai iya faruwa, a haka Hamida ta sake farkawa tana kuka, wannan karon sai da ta É—auke ta suka dawo falo sannan ta sake komawa, kuma minti biyar bata yi ba ta sake tashi da wani kukan.
Wani abu da ya sake tsorata ta kenan don tun sanda tazo gidan ko sau É—aya bata taba tashi cikin dare ba, hannayenta na rawa ta samu da kyar ta bata lemo sannan tayi shiru kwance a jikinta, abinda ya hana ta sake tashi kenan saboda tana tsoron idan ta yi motsin da zai tashe ta ba lallai ne ta sake komawa ba, kuma zaman waje É—ayan yasa dukkan tarin bugun da zuciyarta ke yi da kuma saka da warwarar dake ranta bacci ya sace ta a cikinsu wanda bata farka ba sai yanzu.
Sai a yanzu da idanunta da kuma zuciyarta suka cika da wani irin nauyi da bata taɓa jin sa ba a rayuwarta, ta miƙe da sauri wanda hakan ya farkar da Hamida da kanta ya sauka daga jikinta.
Karfe bakwai da minti uku na safe...
Lokacin da agogo ya nuna a ciki idanunta kenan, ta kalli ko'ina a falon, su kadai ne har yanzu babu Ma'aruf kuma babu alamun wani ya shigo, wani abu ya zarce ta makogwaronta yana ƙoƙarin zana kalar tashin hankalin da take shirin fuskanta a cikin kirjinta, wajen da ta bar wayarta ta tabbata su Samira zasu gani, idan komai lafiya kamar yadda Baffa yace ya kamata ace su Samira sun kawo mata wayar, ko ma wani ya shigo ya gaya mata dalilin rashin dawowar Ma'aruf din.
Wani tunanin ya daki kwakwalar ta a lokaci guda, me yake shirin faruwa ne? Ko ma me ya faru din? Sai yanzu take ganin me yasa Inna Danejo zata ce a rako su su dawo gida a jiya bayan su Baffan basu iso ba? Idan da gaske ne komai lafiya yake me yasa har yanzu Ma'aruf bai dawo ba? Ko kuma a kawo mata wayarta? Manta ta tayi ma ko kuma me ya faru?
Ba shiri bugun zuciyarta ya karu a lokaci guda, duk wata alama da zata tabbatar mata da cewar ranar yau daban ce ta shiga haskawa a idanunta, hatta yanayin hasken ranar ta ganshi daban da yadda ta saba saninsa a irin wannan lokacin, me yake shirin faruwa ne? Mutuwa akayi? waye ya mutu? Hajiya Kilishi? Idan ita ce me yasa za'a boye mata.... tsaya! Ko dai Ma'aruf ne?
Ba shiri ta É—aga kafafunta zuwa daki don ta dauko hijabinta tayi nufi cikin gidan,don duk da hankalinta na neman barin jikinta ta sani ba zata iya fita a haka ba, rigarta bata ko kai gwiwa ba, duka kayan baccinta haka suke, haka take saka su don ta fahimci cewa zata iya raba soyayyar da Ma'aruf yake yi mata da kuma wadda yake yiwa kafafunta daidai.
Sai dai me? Tana motsa kafar tata wani irin jiri ya ɗebe ta, da kyar ta iya ƙokarin tsayawa akan kafafuwanta kafin ta fahimci yunwar da take ji, don siraran yatsunta har rawa suke yi banda jikinta da take jinsa yana komawa kamar fallen takarda, ba shiri ta fasa tayi hanyar kitchen Hamida da ta farka a lokacin itama ta biyo tana mutsikka ido.
Tana shiga kitchen din ta buÉ—e fridge ta zaro container da ta zuba abincin a ciki, jollof din shinkafa da taliya ne sai tayi sauce din nama da vegetables, bata ko tuna da sauce din ba a yanzu ta nufi tukunyar da tayi girkin da ita jiya, har yanzu tana kan gas din bata wanke ba sakamakon kiran da Samira tayi mata a jiyan cewa an sake shiga da Hajiya Kilishi tiyata.
Sau ɗaya ta dauraye ta ɗora ta akan wuta, ta zuba abincin akan na ciki wanda ya kama, jikinta na rawa ta tsaya tana kallonsa kuma sai zuciyarta ta gaya mata cewa ba zata iya jira ya ƙarasa ba don kamar za'a zare numfashinta haka take ji, sai kawai ta kashe wutar sannan ta dauko tukunyar gabadaya ta zauna a kasa, akan tiles din wajen tasa hannunta ta fara cin abincin a haka tana ci hannunta na rawa bata ko jin sanyin dake jikinsa.
"Mammy zan ci nima.."
Hamida ta fada tana zama itama a gabanta har da tankwashe kafa, ta shiga bata a baki da hannunta, babu wanda ya gama wartsakewa a cikinsu babu wanda yayi ko brush, wani abu da yasa hawayen da bata da tabbacin na meye suka gangangaro kan kumatunta duka biyu a lokaci guda, babu abinda ta gani, babu abinda taji amma ta riga ta sani cewa ba sai wani ya gaya mata ba, ba sai ta jira komai ba, faruwar al'amari irin wannan da kuma yadda jikinta yake mata tun a jiya alama ce ta cewar wani babban al'amarin ya faru... don ko a wasan kwaikwayo ta sani cewa abubuwa basa tafiya daidai idan komai yazo ƙarshe.
Tasa ɗaya baya hannunta ta shiga share hawayen amma kamar ta ziga shi ne sai yawansa ya ƙaru, ya cika idanunta taf ya zama bata ko iya ganin Hamidan dake gabanta sai dishi-dishinta tsayuwarta a wajen, sai kawai ta kifa kanta a jikin tukunyar ta fashe da kuka gabaɗaya.
Kukan da a cikinsa da kuma tambayoyin Hamida ta tsinci bugun kofar da ake yi daga waje.... Ba shiri ta ajiye tukunyar ta sauko daga saman da take, Kafafunta na sassarfa ta fita daga kitchen ta karasa cikin falon.
Bata san me take jira ba kuma bata san me ta zata ba har sanda hannunta ya bude kofar, kuma siffar mutane biyun dake tsaye a waje, Munaya tare da wata Æ´ar uwar Hajiya Maimuna da suke kira da Auntyn Sama, kallon da suke mata kadai yasa zuciyarta ta kulle tamau waje guda, komai ya tsaya a cikin kanta cak!
Ba abinda take iya gani sai fuskar Auntyn Saman da take a birkice da kuma kumburarrun idanun Munayan dake shaida cewa har a lokacin kuka take itama... Shikenan! Abinda take hasashe ya faru....
Sai kawai kafafunta suka kasa daukanta ta sulale a lokaci guda zuwa dandaryar ƙasan wajen.... Kuma kafin komai ya ɗauke daga idanunta tana iya tuna cewa taga fuskar su Munayan akanta suna girgiza kai cike da ƙarin tashin hankalin da ya ninku a idanunsu sannan taji muryar Hameeda na kiran sunanta.
***
"Babu wani labari har yanzu..."
Abinda Baba Usman ya faÉ—a kenan a cikin wayar dake kare a kunnensa, ya gyada kansa sau É—aya sannan yace.
"Eh, shi DSP É—in yanzu yace an samu mutum daya yanzu a can wajen hanyar kura da yace yaga wucewar motar, wai wani mai mashin ne ya dan hada go-slow akan hanya to idan motoci sun taho suna tsayawa amma yace ita motar taba zuwa kawai sai tayi kwana ta biyo ta cikin mutane, yace ta kan kayayyakin sa da yake siyarwa anan bakin hanya tabi ta kai shi yasa har ya iya ganin lambar dake jikinta, shi kansa ma yace sauran kwanansa a gaba ne yasa bata bi ta kansa ba..."
Yayi shiru yana sauraren bayanin da ake yi a cikin wayar kafin ya sake cewa.
"To, yace dai an saka Æ´ansanda a kan hanya har zuwa Kuran, to amma tunanin da muke yi shine ba'a sani ba idan iya nan suka tsaya, ko kuma sun wuce ma Kuran..."
Ya gyaÉ—a kansa sannan yace.
"Gaskiya ne... Yanzu dai alfarma muke nema ka saka baki a sake bamu wasu ma'aikatan kamar na division biyar haka, babu matsalar payment, za'a basu ko nawa ne."
Ya fadi hakan daidai lokacin da Ishaq ya shigo cikin falon na Baffa.
Kuma ko daga nesa idanunsa kadai zaka kalla ka san cewa duniyarsa ta birkice ne a lokaci guda tsakanin joya da yau, yana cikin tashin hankalin da zai rantse har da ubsngijinsa za'a samu fiye da kutane dubu da zasu zo duniya su gama rayuwarsu har su koma ga mahaliccinsu ba za su taba fuskantar irinsa ba.
Jiya watarana ce da babu daya daga cikinsu da zai yi tunanin zata shafe daga tarihin rayuwar ahalinsu bakiÉ—aya ba ma su kaÉ—ai ba.
Faruk ya kira su a waya bayan lokacin da ya kira Ma'aruf yake shaida masa result din da aka samu game da tiyatar da aka yiwa Mamin da suke wajenta tun safe, bai samu wata kwakwarar amsa a wajen Ma'aruf din ba wayar ta katse, bayan kamar minti goma a lokacin da su Baffa suka gama da likitan nan suke shirin komawa gida, a lokacin Faruk ya kira shi da rokon cewa kar ya bari su Baffa su tafi ya kawo su Kamfani a yanzu-yanzu...
Kuma da ƙyar ya samu su Baffan suka yarda suka bishi, a cewarsu halin da ake ciki da kuma jiran da mutanen gida suke yi zai tsayar da ko meye a kamfanin, sai da Baba Usman ya saka baki da cewar ya san su Ma'aruf baza su kira su akan wani abu da bashi da muhimmanci ba sannan Baffan ya yarda suka tafi.
Yana tuna yadda suka shiga cikin administrative office É—in suka same su komai a barbaje, koina kaca-kaca kafin ma su kai ga fahimtar abinda ke faruwa, kuma shi kansa a yanzu ba zai iya banbance tsakanin bayanin mutumin da suka tarar wa a cikin Office É—in mai suna Awwalu wanda ya san su Ma'aruf sun dade suna nema da kuma bayanan muryar Hajiya Kilishi dake cikin wasu tarin CD's da Abdurrahim yayi ta sakawa É—aya bayan É—aya wanne ya fara ji ba.
Idan wani zai ce ya kwatanta tashin hankalin da ya shiga da kuma mamaki a wannan lokacin ya sani cewa a matsayin sa na lauya shi kansa ba zai iya kare kansa ba,
Balle kuma su Baffan da ya san al'amarin yafi shafarsu akansa, kowannensu kasa magana yayi, baya iya tuna kalma guda da wani ya furta a wannan lokacin banda Baffa da ke maimaita 'Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un' cikin amon muryarsa dake ratsa zuciyarsu ta kowanne bangare, bayan haka kuma sai lokacin da Faruk ya kira Æ´ansanda a waya da cewar su tafi da Awwalun da ya kammala yiwa su Baffa duk bayanin da zai yi a lokacin.
Wanda a sannan ne kuma Ma'aruf ya miƙe, babu wanda ya san inda za shi a lokacin don shi bai maganshi ba sai da ta isa wajen kofar office ɗin, babu wanda yayi wa magana, babu alamun ma ya san da su zaune a wajen don baya tuna cewar ko bayan da suka shigo tare dasu Baffa ya ɗago da kansa, su Abdurrahim ne kawai suka yi musu magana kafin tashin hankalin dake yawo a cikin ɗakin ya ziyarce su.
Kuma babu wanda yayi tunanin su tsayar dashi a lokacin, babu wanda yayi tunanin komai sai bayan fitarsa da minti biyu sannan shi da yake zaune hankalinsa ya dawo jikinsa, ya fita da sauri ya bishi amma bai ga komai ba sai maigadi da ya hango daga can yana ƙoƙarin maida gate din wajen zai rufe... A lokacin ya san cewa dukkanin su sunyi babban kuskuren da zai shafi al'umma da yawa a wannan daren.
Ilai kuwa! Ƙasa da minti talatin bayan hakan, a lokacin da Baffa ke ƙoƙarin kwantarwa dasu Hajiya dake can gida hankali, a lokacin kiran DSP ya shigo wayarsa da sakon cewa Ma'aruf yayi wa mutane biyar jina-jina a asibiti ciki gar da ƴansandan sa guda biyu sannan kuma ya ɗauki mara lafiyar da suke gadi wadda suke zarginta da ta'ammali da mugayen kwayoyi kuma ya har yayi nasarar fita da ita daga asibitin ba tare da an iya tsayar dashi ba.
Ishaq ya sani cewa idan za'a zaunar dashi zai kwana yana saka hannu a takardun da zasu bada tabbaci na cewar Baffa mutum ne jajirtacce irin wanda bai taɓa gani ba a rayuwarsa, a iya abinda ya sani na tarihin rayuwarsa yana da lissafin tarin wasu abubuwan da ba kowa ne zai iya fuskantarsu a duniyar nan kuma rayuwarsa ta cigaba da tafiya daidai ba, amma Baffa ya fuskance su, yabi ta cikinsu ba tare da wani abu guda daya ya goce daga rayuwarsa ba, ko a iya harkar kamfaninsa kadai akwai tarin abubuwan da mutane da yawa zasu iya kasawa a bugu daya, amma da kafafunsa ya tsaya, ya jajirce, har komai ya kawo matsayin da yake a yanzu.
Amma a lokacin da DSP ya kira shi da wannan bayanin, a jiya cikin wannan daren faduwa yayi har kasa daga yadda yake mike bayan ya amsa wayar Hajiya Maimuna, babu wanda ya gani babu wanda ya lura, sai da ya kai har kasa wanda hakan shine kalubale na biyu da suke fuskanta, don tun jiyan bai farka ba, sun kwana dashi a asibiti bayan likitoci sunyi kokarin dawo da numfashinsa, amma tun a daren jiyan Hajiya Maimuna take magiyar a dawo dashi gida, don haka a dole likitan da ya kwana dasu a asibiti ya biyo su gida dab da sallar asubahi aka kwantar dashi a dakinsa tare da sauran hade-haden da akayi masa a asibitin.
Sunyi masa allurar bacci mai ƙarfi da aƙalla zata ɗauke shi tsawon kwanaki biyu don likitan ya tabbatar da cewar idan har ya farka a yanayin da yake komai zai iya faruwa, saboda halin da zuciyarsa ta shiga.
A yanzu haka kuma cikin gidan ya koma tamkar gidan makoki ne don iya abinda suka ji ya tayar da hankalinsu mutuka, tunda dama tun a jiyan sun kwana ne a zaune.
Yanzu dashi da Baba Usman da kuma su Faruq suke ta fafutukar neman Ma'aruf da kuma Mamin ko ta wacce hanya, kuma hankalinau na tsaye ne kamar yadda suma suke a tsaye, Abdurrahim na kan Computer tun a daren jiyan yana kokarin gano signal din wata karamar waya mai É—auke da layin Ma'aruf din na biyu wadda ake tunanin cewa tana cikin motarsa, saboda ana ta kira ba'a dauka wani lokacin ma bata shiga.
Sai dai duk kokarinsa ya kasa kama signal din wayar har yanzu saboda matsalar Nigeria da ba koina ake samun service ba idan har ba mutane bane a wajen... Faruk kuwa yana can sunyi hanuar Kuran tare da Æ´an sandan, shima a yanzu dawowarsa daga asibiti kenan wajen mutanen da Ma'aruf É—in yayi wa rauni a daren jiya, dole ana bukatar sa hannun wanda yake da alaka dashi ne a wadu takardu da za'a cike a asibitin don haka DSP din ya kira waya yace a tura wani.
"Su biyar din ne kamar yadda suka ce?"
Baba Usman ya tambaye shi bayan ya karaso cikin falon Baffan inda ya same shi, kuma shima bayan ya gama wayar da yake yi. Kansa a sunkuye ya daga shi.
"Eh, bayan Æ´ansandan biyu sai maigadin kofar wajen da aka ce yayi kokarin hana shi shiga,sai kuma wani Nurse guda É—aya."
Baba Usman ya gyada kansa tare da ajiyar zuciya sannan yace.
"Nayi magana da sakataren IG É—in, ina ga kamar ya karbi case din da muhimmanci don haka yace da zarar ya shigo office zai yi magana dashi a sake bamu wasu ma'aikatan."
Lebbensa a bushe kamar makogwaronsa Ishaq ya gyada kansa a hankali sannan yace.
"Mun yi waya da Faruk Baba, yace min sun wuce Kura ma yanzu wai wani manomi yace musu yaga shatin tayar mota a cikin gonarsa kafin ya fito, don haka zan bi bayansu..."
Idan ka kalle su a wannan lokacin daga Baba Usman din ha Ishaq din ka san kawai kowanne yana amsa sunansa ne na 'Namiji' amma bayan hakan babu abinda zai hana su fitar da tarin hawauen dake kwance a cikin kirjinsu, kuma a wannan lokacin ne, kafin Baba Usman É—in ya buÉ—e baki ya bashi amsa suka jiyo wani sabon kukan daga cikin gida wanda kafin ya iso inda suke Hajiya Madina matar Baba Usman ta kira shi da cewar Amina ta faÉ—i!
***
_Komai dai yazo ƙarshe, ina kuke tunanin Ma'aruf ya tafi da Kilishi?_
_Me zai faru?_
_Me zai faru?_
_Masu iya magana kan ce a lokacin da baƙi ciki ke samun waje da kuma bigiren yaɗuwa a lokacin ne kuma a wani wajen, farin ciki ke kafa tasa tutar..._
_Wasu zuciyoyin na bushewa ne yayin da ruwan damina mai danshi ke mamaye wasu zukatan..._
_Kuna tunanin gangarar nan zata zama mai dadi ga kowanne bangare?_
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:58 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©�AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*23*
_And those who burdened muslim men and women, without them doing anything (wrong) hsve burdened themselves with false accusations and open sin.- Surah Al-ahzab, Ayah 58._
~~~~~~
"Anan wajen ya mutu Mami..."
Ma'aruf ya faÉ—a da sautin muryar dashi kansa ya sani baiyi kama da nasa ba, a zaune yake a cikin motar idanunsa a manne da wata katuwar bishiyar dake gabansu, daga bayan motar, kujerar baya Hajiya Kilishi ce zaune kanta a sunkuye yayin da idanunta suka yi jawur da tsananin tashin hankalin da baya mata kama da zahirin da mutane ke rayuwa.
Tashin hankalin da ya canja kamanninta, ya mayar da lissafin kammanin ta wani irin da da wuya ne ka gane ta a lokaci guda, don hatta jikinta ya canja a cikin kwanaki biyu kaɗai! Ta rame ta sirrance sannan tsufa da kuma shekaru ta da a kullum kwalliya da murmushin ta ke ɓoye su sun baiyana tar!
"Anan wajen ya mutu bayan ya gaya min kar na kashe... Shine abu na karshe da ya gaya min Mami bamu sake magana bayan hakan ba, yana amsa waya lokacin da kaddarar da kika halitta mana ta faru... I was driving safely, na sani cewa tun a wancan lokacin banyi wani abu ba daidai ba.
Kawai naji sitiyarin ya ƙwace daga hannuna ne sannan naga motar tana wullawa akan titin, ina jin salatin da yake yi a wannan lokacin Mami, sannan ina ganin hannunsa yana ta kokarin ya kama sitiyarin amma juyin da motar ke yi yasa buguwa kawai muke yi kotawanne bangare, lokacin da motar ta taho cikin dajin nan, daga ni har shi babu wanda yaga wannan bishiyar dake gabanmu har motar ta dake ta, ta dake ta daidai saitin inda wani reshenta yake a karye sannan daidai saitin inda Jamal yake da karfin da yasa reshen ya faso ta cikin gilashin ya soke shi a ko'ina na kirjinsa...."
Muryarsa tayi ƙoƙarin shaƙewa amma ya cigaba.
"... Ya rasu yana kallona Mami, idanunsa akaina suka tsaya har lokacin da jama'a suka karaso suka rufe motar ana kokarin fito damu, kuma ba'a iya fito dashi ba sai da aka sare reshen bishiyar nan daga jikinta, aka fita dashi dasu a jikinsa.... Har akayi masa wanka aka kaishi kabarinsa da itacen bishiyar nan a jikin sa Mami.
Kina tare dani a asibiti a lokacin, kin san wannan ranar itace sanadiyar samun ciwo na, ciwon da ya tauye tarin abubuwa da yawa a rayuwarta, kin san dukkan wahalar da na sha Mami, kusan haukacewa nayi kin sani, bana gane komai bana fahimtar komai, wannan ranar kadai ke maimaitawa a cikin kaina, tun daga safiyar da na ganshi zaiyi tafiyar, har tahowarmu mu, da maganganun da muka yi da kuma yadda hatsarin ya faru...
Na dade inabincike Mami, na daɗe ina bincike fara bincike akan al'amarin, sai da na shekara uku ina bin wannan hanyar ina tuntubar mutane kafin na samu wasu mutum biyu da suka tabbatar min cewa wasu mutane ne suka harbi tayar motar mu a lokacin da nake tuƙin nan, na gane cewa da silencer suka yi amfani a bindigar ta yadda babu wanda yaji wata ƙara sai kawai ta fashewar tayar.
Bayan nan, nayi iya binciken da zan iya don gano mutanen da suka yi wannan aikin amma har aka zo gaɓar da hankalina ya karkata ga aikin kamfani da kuma binciken wata ɓarakar da kike haifarwa acan ban sami komai ba Mami, duk hanyar da na bi bata ɓullewa kamar yadda a binciken kamfanin ma bana samun komai, kawai ina ƙarewa ne da tarin bacin ran dake sawa ciwona ya tashi, komai ya sake tsayawa a rayuwata ta yadda bana jin ina son komai sai tsananin yadda zan iya wanke kaina a wajen Jamal, in kuna kawo ƙarshen komai, wanda hakan shi ke kara baki dukkan wata dama da kike kassaramu da ita...."
Wani abu ya wuce a makogwaronsa da bai san meye ba, yayin da yake jin tasirin kowacce kalma da ya furta da kuma yanayin tare da tashin hankalin dake zagaye dasu na haddasa wani abu a ƙirjinsa da bai san meye ba, kuma a lokacin ne ya juyo ya kslle ta, har yanzu bashi take kallo ba, kanta a juye ysketana kallon waje, idanunta auna tafiya zuwa wani nisan da bashi da karshe, idanunta da har yanzu basa nuna masa kamanin Mamin da ya sani, baya ganinta a tare da matar dake gabansa kwata-kwata.
Har yanzu a gaban bishiyar motar take, bishiyar da ta shiga cikin wani ɓari na rayuwarsa, ɓarin da ya riga ya zama tambarin da a kodayaushe a kowanne waiwaye shi zai fara kalla a rayuwarsa.
Ƙarfe shida na safiya, ƴan mintuna kaɗan bayan sallar asubahi lokacin da suka ƙaraso wajen, yana tafiya ne da karfin gudun da tun daga nesa wani magidanci dake tahowa akan keke daga hanyar shiga kauyensu ya hango ta, hasken fitilun gaba ya fara gani kafin kurar dake bin ta a baya ta cika idanunsa.
Ba shiri ya dawo da idanunsa kan gonakin dake gaba, gonaki kusan biyar dake dauke da sabbin shukoki da suka fara fitowa, kuma kafin ya gama lissafin abinda ke shirin faruwa, motar ta karaso ta zarce ta cikinsu da tsananin gudun da tayoyinta har dagawa suke saboda tudun kunya-kunya dake gurin, tana wucewa tayoyinta na murje shukokin da matukin cikinta baya ko ganinsu balle yaji alamunsu daga ciki.
Hannunsa akan sitiyarin suke kawai yana danne shi wajen kara nausawa ciki, dogwayen bishiyun da idanunsa ke gani kadai yake iya kaucewa bayan haka baya ganin komai, baya jin komai sai tarin maganganun dake tarewa a cikin kansa suna sake dawowa.
Maganganun dake sa wa tun yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa, yana jin huci da kuma dumin wani abu na ratsa kirjinsa zuwa cikin idanunsa, har ya daina.... Ya zama baya jin komai... Baya jin komai sai sautin muryarta dake fitowa daga cikin wadannan CD's din a lokacin da yake tsugunne a gaban computer Abdurrahim.
Yana tuna kowacce kalma da ta shiga kunnensa yana tuna su bi da bi saman kwakwalwarsa na tsara masa su daki-daki a yadda al'amarin ya faru a yadda komai ya kasance... Sannan bayan haka daga can ƙarshen kansa muryar Awwalu ce ke amsawa, dukkan bayanan da zai iya tunawa yaji lokacin da yake shaidawa su Baffa tarin abubuwan da suka daɗe suna binne su a cikinsa.
Ya sani cewa zuwan Awwalun da kansa a wannan lokacin da kuma abubuwan da yake fada abu ne mai mutukar mamaki duba da tsawon lokacin da suka shafe suna nemansa, amma mamakin sautin muryar Mamin da kuma tarin abubuwan da dake fitowa daga muryar tata ya shallake dukkan wani abu a cikin kansa bayan hakan duk da cewar bayanan Awwalun wani abu ne da ya ƙara basu dukkan tabbacin da zasu nema, don Allah ya sani zai iya ƙaryatawa.
A wannan lokacin zai ce ba haka bane, zai ce dukkan abinda yaji karya ne... Zai yarda da dukkan wata hujja da zata gaya masa cewa impersonation ɗin Maminsa aka yi, Mamin da ya sani mai ƙaunarsu ce, zuciyarta a buɗe take ga kowa, ba zata taba ko iya hada hanya da wanda zai cuce su ba balle ta saka hannu, balle kuma ace itace ja gaba wajen faruwar munanan abubuwa da yawa a rayuwarsu....
Sai dai me? Bai ma yi wannan fatan ba, baiyi ma yi wannan tunanin ba aka tafi har zuwa gaɓar da komai ya tabbata, komai ya tabbata ta sigar da basu da wata kafa ko kuma hujjar ƙalubalantar abinda suka ji.
Kuma ba ga shi kaɗai ba, ya sani dukkansu a yanzu dalili zasu so sani, dalilin da yasa tayi hakan, ta aikata tarin abubuwan da baya jin ko akan fatar bakinsa zai iya furta su, dalilin da yasa ta shigo rayuwarsu tun farko ma, dalilin da yasa basu taba ganin komai ba sai tarin murmushi da kuma dimbin kaunar dake nunawa akan fuskarta mai kaifi, kaifin da take amfani dashi tana huda zuciyoyinsu a tarun lokutan da ko sau daya wsni a cikinsu bai taɓa waigawa yaga makamin da hannayenta ke rike dasu ba.
Wani? Akwai wanin da ya dace ne bayan shi? Akwai wanin da ya kamata ace a cikin ɗinbin shekarun da ya rayu tare da ita ace ko sau ɗaya idanunsa ko kuma tunaninsa basu taɓa haska masa wani abu da ya kamata ya ɗorawa ayar tambaya akanta ba?
Hannunsa ɗaya ya shiga cikin gashin kansa a lokacin da ɗayan ke kara danne kan sitiyarin suna ƙara nausawa cikin dajin, a cikin hannunsa ya shake likitan da aks ce ya jagoranci ƴar karamar tiyatar da akace anyi mata an tabbatar da makantar idanunta, kuna ba'aje koina ba a cikin hannun nasa likitan ya gaya masa cewa ita ta nemi da yayi mata hakan ya fadawa kowa cewa ta makance bayan tayi masa alkawarin tarin wasu kuɗaɗen da ba zai iya ƙin tayin ba.
Kuma daga idanunsa kaɗai ya san ta sani, ta san ya san komai, tun kafin ma ya faɗa shi yasa bata ce komai ba har yanzu, har suka ƙaraso wajen da bai manta hanyar ba, don ba zai taɓa manta ta ba, yazo fiye da sau goma kuma a zuwan farko ne kaɗai yayi bilinbituwar da ta ɗauke shi awanni kafin ya iya gane ba wajen, bayan haka baya jin ko a mafarkinsa ya taɓa kauce hanya.
A lokacin da suka ƙaraso, idanunsa sun tsaya akan bishiyar da kuma gudun da motar ke yi a cikin hannunsa, yaji wani abu na yawo a cikin kansa kamar wancan lokacin, shekaru goma da suka wuce, lokacin da hannayensa dama duk wani abu mai tsini a cikin kansa suka kasa tsayar da motar dake nufar bishiyar da yake kallo a yanzu, da sanda suka tafi suka dake ta, suka dake ta a yanayin ba zai taɓa fita daga kansa ba...
Sai kawai ya danna birkin motar a yanzu da ƙarfi, da ƙarfin da ya fitar da sauti mai ƙara daga waje, ƙarar ta karaɗe cikin dajin zuwa nisan da ba zai iya kintata ba, kuma duk da karfin birkin, motar bata tsaya ba sai da taje dab da bishiyar, dab da ita sosai ta yadda bai fi tazarar taku biyu kawai ba a abinda ya rage
Tayoyin na tsayawa ya buɗe ƙofar ya fito, ya fito ya buɗe ta baya idanunsa na kaiwa kan Hajiya Kilishin da har yanzu bata kallonsa, kanta na juye daga gefe tana hangen wani wajen daban, da tafiyar da suke yi da ma karfin birkin da ya faru a yanzu babu daya da ya canja ta daga mazauninta, idonsa ya tsaya akan fuskarta, awanni kadan da suka wuce, awanni da basu fi kirgen yatsunsa ba, duniyarsa a tsaye take game da rashin lafiyarta, yana jin komai ya birkice masa yana jin rayuwar ba daidai take tafiya ba tun kafin ma ya san sakamakon abinda ya same ta.
Amma a yanzu gashi tsaye a gabanta sai dai a yanzu bashi É—in bane, ba Ma'aruf É—in da yake a jiya bane, ba Ma'aruf É—in da yake a shekarun baya bane... Baya jin kansa a matsayin kowa da kuma komai, jin sa yake a wani sabon mutum daban, sabon mutum É—in da babu komai a zuciyarsa illa tarin abubuwan da yaji ya kuma sani daga daren jiya.
A karo na farko, yaji wani abu kamar kwalla na shirin ziyartar idanunsa, sai kawai ya juya ya koma mazaunin direban ya juya ya buÉ—e booth É—in baya na motar... idanunsa suka tsaya akan rediyon motar yayin da yake jin zuciyarsa na girgizawa tamkar yadda yatsun hannayensa ke yi, sai kawai ya danna ya play buttun a jiki kuma a take sautin dake fitowa ya karaÉ—e kowacce speaker dake cikin motar.
_"Ka yi masa magana kawai Awwalu, na yarda zan bashi hakan, babu abinda ba zan bayar ba saboda wannan aikin... Ya kamata ka sani tun da har na kashe Jamal babu abinda ba zan iya ba akan cikar burina..."_
Tashin hankalin da ya daki tsakiyar kan Hajiya Kilishi a lokacin ba abu ne da zata iya misaltawa ba, tun daga lokacin da ta farka a daren jiya, lokacin da ta gama jin hirar dukkanin abinda ya same ta, ta daɗe kwance a wajen tana tsara hanyar mafitar da zuciyarta ke saƙa mata, ta da yadda zata wanke kanta a idon kowa ta kuma fita daga ƙullin ƴansandan nan... Kuma tsarin nata ta tafi daidai a cikin kanta, ta ƙirga komai ta fitar da dukkan hanyoyinta kamar yadda ta saba, hatta kuɗin da zata kashe ta lissafa da kuma yadda bayan hakan tsarinta zai cigaba da tafiya daga inda ta tsaya.
Ta sami wani likita da ta farar-ɗaya ya amince da buƙatar ta jin makudan kuɗin da a take tayi masa alkawari. Tana tuna murmushin da tayi bayan fitarsa, murmushin jin dadi da kuma jinjina wa kanta na yadda a kodayaushe mafita ke zywar mata, sai dai me? Ashe bata sani ba wannan murmushin shine na karshe da zata yi a wannan karnin watakila har ma da me zuwa a gaba... Don wadannan lokutan na jiya ta sani cewa har abada su zata lissafa a matsayin lokuta na ƙarshe da suke daidai a rayuwarta.
Tana iya tuna maganganun da suka yi da Baffa kafin nan, sun shigo wajenta shi da Baba Usman, kuma dukkan maganganun da zasu kwantar da hankalinta su suka zanta, suna tabbatar mata da halin da kowa a can gida yake game da ciwonta da kuma cewar ta kwantar da hankalinta abubuwa zasu daidaita, wasu maganganu da suka ƙara saita hankalinta waje guda bayan tabbatarwar da tayi cewa abubuwa suna nan a yadda ta san su har a lokacin.
Sai dai tun daga lokacin da tayi ido hudu da Ma'aruf bayan ya shigo ya fizge bandejin da aka rufe fuskarta dashi, da kuma mutanen da ta gani a ƙasa a kofar ɗakin a lokacin ta fara fahimtar cewa tabbas abubuwa sun fara karewa mata, rayuwarta ta birkice a daidai ƙarshen da bata taɓa hangensa ba, kuma abinda Ma'aruf ya fada kai tsaye na cewar ta biyo shi yana kallon cikin idanun nata da zuwa wannan lokacin ta tabbatar da cewar an kai musu sakon makancewarta shine mataki na farko da ya fara tabbatar mata da cewar, rayuwa tana ɗauke da mabanbantan kaloli kuma ba a kodayaushe ne abubuwa ke tafiya kamar yadda ɗan adam yake tsarawa a rayuwarsa ba.
"Babu kowa a duniyar nan, mu kaÉ—ai ne Mami... Babu kowa mu kaÉ—ai ne a wajen nan... Kuma na kawo ki ne don ki bani wata hujja kwakwara Mami, Me muka kasa baki a rayuwar nan? Me tasa zaki kashe Jamal? Me Hajiya tayi miki kika gurgunta kafafunta? Me Abdurrahim yayi kika dauke muryarsa? Me yasa kike kwashe dukiyar Baffa?
Me zaki yi da ita Mami? Ina zaki je ina zaki kai ta? Ƴaƴanki da su kansu kike rufe su da halaiyarki kike tarawa? Me zasu yi da ita Mami? Me suke nema a duniyar nan da basu samu yanzu ba? Me zasu nema ban gaba da ni ko Baffa zamu kasa Mami? Me yasa kike hukunta ni da soyayyar karya Mami? Me yasa kika sa na baki matsayi da kuma girman UWA a zuciyata? Me yasa kika kassara rayuwarmu kotawanne fanni Mami?...."
Muryarsa ta jero tambayoyin da dukkanin dauriyar da yake jin zai iya wajen saita kansa yayin da idanunsa ke kallon fuskarta, har yanzu bata kallonsa kuma bata ce komai ba, baiyi tunanin zata yi magana ba dama don baya zaton idan za'a tara kalmomin duniyar na kaf zata sami wadanda zata iya kare kanta dasu, sai kawai ya juyar da kansa yana sake kallon bishiyar dake gabansu, a lokacin hawayen da yake dannewa suka sulala kan fuskarsa.
Yana jinsa ne fanko, kamar wani ya zazzage dukkanin abubuwan da ya sani da kuma abinda yayi mu'amala dashi a rayuwarsa, kamar wani ya shafe dukkan tarihinsa komai ya zame masa sabo, yana jin kamar bai san ina ya nufa ba bayan nan, kamar bashi da wani takamaiman wani abu da zai sake yi a rayuwarsu, sai kawai ƙwallar dake danne a idanunsa ta fito tana gangarowa kan fuskarsa.
Kuma a lokacin ne dukkaninsu suka jiyo jiniyar motocin Æ´an sanda dake tahowa daga bayansu, motocin guda biyu ne yana hango su tun daga can nesa ta gilashin motar suna tahowa, daga gefensu motar Faruk ce ke tahowa, sai kawai ya sake juyo da fuskarsa ya kalli Hajiya Kilishin da har a lokacin take zaune bata motsa ba.... Kuma sai a sannan ne idonsa ya gane masa hawayen dake gangarowa kan fuskarta...
Wani abu da ya saka shi murmushi a lokaci guda kafin ya sake juyawa, dogwayen yatsun hannunsa suka rufo kofar motar yayin da dayan ya murda mukullin mitar yana kunna ta.
"A tunanina, nan wajen shine mafari Mami, shine mafarin dukkan wani abu da kika dade kina ƙulls mana, daga kan Jamsl kuka fara, don haka daga kansa zsmu tsaya."
Yana faɗin haka bai jira komai ba ya ƙarasa tayar da motar sannan ya danne kanta, a lokaci guda ta figa da tsananin ƙarfi kai tsaye tana nufar Bishiyar nan....
Kuma ta cikin gilashin dake gaba idanun Ma'aruf na kan fuskar Mamin da ta ɗago tana kallonsa fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye sanda motar ta karasa ta daki bishiyar da wani irin ƙarfin da karasa ta karade ko'ina!
Ƙarar da ta sanya Faruk taka nasa birkin motar sannan ba tare da jiran komai ba ya buɗe kofar motar ya tafi da gudu zuwa wajen, sauran ƴan sandan dake bayan motoci biyu suka diro da nasu saurin suka rufa masa baya!
***
*NO. 38 Ramie Street, Nassarawa GRA, Kano.*
"Basu kira ba har yanzu?"
Hajiya Nafisa ta tambaya da idanunta da suke a zare tana kallon ɗan ta Ashraf wanda ke rike da waya a hannunsa, a cikin falon da suke akwai Ahmad ma, yana zaune daga cikin kujerun falon yana hannayen sa duka biyu dafe akansa yayin da yake sauraren Ashraf ɗin dake riƙe da waya yana amsa kiran mutane daban-daban ɗin da suke fatan su isa ga abinda suke nema... Rukayya.
A yanzu bincike da kuma dukkan hasashensu ya kai ga abinda suke nema, an basu tabbaci na cewar Hoton da suka gani Rukkayya ce kuma a cikin gawarwakin da aka fito dasu daga wata mota dake nufar wani kauye a can kasar Niger.
Idon Ahmad ya koma kan mahaifiyarsu, Hajiya Nafisan dake ta zarya a cikin falon idanunta shabe-shabe da hawayen dake fitowa wani na bin wani akan fuskarta.
Ashraf ya girgiza kansa sannan yace.
"Bai kira ba Maamah, kiran da nayi masa kusan na biyar kenan ya ce suna hanya, bana don inyi ta kara kiransa..."
Hajiya Nafisa ta girgiza kanta.
"Ka kira shi Aahraf... Ka sake kiransa, ya san al'amari irin wannan ai, ya san ba zamu iya jira ba, dole ne hankali ya tashi...."
Ahmad dake zaune ya girgiza kansa.
"Maamah ki jira yanzu zasu isa kar muyi abinda..."
"Kar muyi abinda me? Kar muyi abinda zamu tashi hankalinsu? Saboda kai naka bai tashi ba? Ƴaruwarka tana can a halin da babu wanda ya sani amma kai kana zaune babu abinda ya shafe ka?"
"Babu abinda ya shafe ni? Babu ya shafe ni zaki ganni anan Maamah? Ni na tura ta Niger din ko kuma idan Allah ya ga damar É—aukar ta zan iya wani abun da zai hana ne...?"
"Ahmad..."
Ashraf ya katse shi yana juyowa kansa. Sai kawai ya mike tsaye.
"Me nayi? Nayi laifi ko? Ni kullum mai laifi ne a gidan nan, Ruƙayya ce ta tafi yawon barbadancinta har Niger amma ni da nake zaune anan nine mai laifi?"
Ashraf ya girgiza kansa fuskar sa ɗauke da tsananin ɓacin rai muryarsa a sama yace.
"You are crazy! Baka da hankali Ahmad me yasa kai a kullum kan ka kawai kake gani? Me yasa baka taba considering mutane a kowanne hali da ake ciki?..."
Sai kawai Ahmad ɗin ya miƙe, shima cikin daga murya yace.
"Saboda nima babu wanda yake considering dina a gidan nan....!"
"Inalillahi wainna ilaihir raji'un!"
Hajiya Nafisa ta faÉ—a tana komawa da baya ta zauna akan kujerar dake bayanta.
"Da wanne zan ji Ashraf?? Da wannan halin da muke ciki ko kuma da fadan da zaku fara? Inalillahi wainna ilaihir raji'un!..."
Ta rufe bakinta daidai lokacin da kiran waya ya shigo cikin wayar Ashraf din, hannunsa na rawa ya É—auka ya kara a kunnensa, Hajiya Nafisa ta taso da sauri ta tsaya a gabansa yayin da Ahmad ya koma ya zauna yana kallon fuskar Ashraf din.
"Eh, eh ita ce.."
Ya fada yana gyada kansa, yayin da hannayen Hajiya Nafisa ke rawa akan fuskarta tana sauraren sa. Ashraf ya sake cewa.
"Eh ita ce Yallabai..."
Sai kuma ya gyada kansa yace.
"Alhmdlilah... Okay toh... Mun gode sir, mun gode mun gode...."
"Me ya faru? An ganta? Sun ganta? Tana da rai Ashraf?"
Tun kafin ya sauke wayar Hajiya Nafisa ke jero waÉ—annan tambayoyin, kuma ga mamakin kowannensu sai kawai ya gyaÉ—a kansa sannan yace.
"Sun ganta, tana da rai Maamah, tana asibitin a kwance..."
"Alhmdlilah... Alhmdlilah."
Dukkaninsu su biyun suka faÉ—a a lokaci guda yayin da Ashraf din ya shiga girgiza musu kansa amma babu wanda ya lura dashi a cikinsu, sai kawai ya kira sunan mahaifiyar tasa kai tsaye.
"Maamah..."
Ta juyo ta kalle shi da sauri, idanunta a zare dauke da wani sabon fatan da a yanzu ya sani cewa maganarsa zata rusa shi ne har garinsa.
"Maamah sun ce ta samu paralysis (mutuwar ɓarin jiki)!"
***
*No 1856L, Sulaiman Crecent Kano.*
*Gidan Hajiya Salamatu.*
"Wallahi Sister Maryam muna gidan har yanzu, abu ne kamar wasa, shekaru kusan talatin da wani abu sai yau Allah ya baiyana shi.. "
Cewar wata dattijuwa da take Æ´aruwar Hajiya Salamatu wadda suke kira da Aunty Bilki. Zuwansu gidan kenan a safiyar yau da suka tashi da labari mai daÉ—i mai kuma cike da dimbin al'ajabi na cewar Æ´aruwar tasu ta samu danta bayan tsawon wasu shekaru, É—an da duniya da ma kowa a cikinsu ya riga ya bada tabbacin cewa ya koma ga mahaliccinsa tun a ranar da yazo duniya.
Sai a gashi a cikin ƙanƙanin lokaci kawai, a cikin wasu kwanaki da hannu zai lissafa su labarin ya canja, ɗan da yake natan na asali ya baiyana a raye tare da kammanin da ko bashi da hujjar labarin da ya bayar wanda yayi daidai da na Hajiya Salamatun, kowa a cikinsu zai shaida ya kuma gasgata cewa shi ɗin da gaske ɗanta ne na asali, don kamarsa ɗaya da mahaifinsa sak! Mijin da ta fara aura Ibrahim Shanawa, komai nasu iri ɗaya ne ta yadda babu wanda ya isa ya musa hakan.
Su kusan biyar ne ƴan uwanta suka zo a yanzu, harda guda biyu da suke a Abuja, tun a daren jiya da ta gaya masu suka yi booking jirgi a safiyar suka taho... Kuma a cikinsu babu wanda ya ƙaryata hakan saboda sun zo ne sun iske tarin hijjojin da ita Salamatun da kuma yaron dake kiran kansa da Jawad suka tanadar ta kowanne bangare, musamman babban al'amarin da ya ƙara girgiza kowa na cewar Jawad ɗin ya tashi ne a gidan Alhaji Bashir wanda yake ƙanin mahaifinsa.
Komai ya faru ne kamar almara, kamar mafarki ko kuma wani labari da ba zai zama gaskiya ba, shi yasa a cikin lokaci kadan zancen ke ta tawo kusufa-kusufa a cikin danginsu har ma da waje, wadanda ke zaune a garin Kanon ma har sun fara zuwa don ganewa idanunsu, don Salamatu kiran kowa take yi, kowa ya kira ta zata ce yazo gidan saboda murnar dake cike fala ranta.
Ko ta zancen ƙawar tata Kilishin da kuma matakin da ya kamata su dauka akanta na irin wannan zaluncin da ta haifar bata yi, sai yayyensu maza uku da suka gama shawara tare da Nasir ne sannan suka yanke shawarar ɗaukan yansanda a tafi har inda Kilishin take, don wanda yake Babba a cikinsu ya ɗauki zafi da yawa ta yadda ya rantse da Allah babu abinda zai hana su zama akan shari'ar.
Wayar da Aunty Bilkin take tare da wata ƙawarta dake can wajen aikinsu ta kare daidai lokacin da Hajiya Salamatun ta bude kofar dakin ta shigo hannunta ɗauke da wata katuwar leda fara.
"Aunty Bilki Yaya Nura zai wuce yanzu."
Ta fada tana kallonta a cikin mutanen dake dakin, da mamaki a fuskarta tace.
"A'a, tafiya kuma ba dauka zasu bari ko zuwa gobe idan komai ya natsa, naji suna zancen za'a je a taho da Kilishin."
Sunan Kilishin da ta ambata ya rage fara'a a fuskarta kafin tace.
"Shi kaÉ—ai zai tafi, su suna nan anjima zasu je tare da Nasir, yace shi yana da meeting din wani contaract da zaiyi a yau."
Ta gyada kanta tana kallon ledar hannunta sai tace.
"Kaya ne nasa aka kawo masa Aunty Bilki, daga Kaduna yake kuma ashe bai zo da kaya ba."
Ta fada tana fito da set É—in kaya guda goma É—inkakku da wani yaronta ya bata lambar irin wajajen É—inkin nan na yanzu masu sunan 'Wardrobe' da suke da kaya dinkakku nasu kyau da zaka je ka siya.
Yadikan dukkaninsu plane masu tsananin kyau da kalolinsu mabanbanta, kowanne anyi masa É—inki mai kyau irin sealed din nan da maza ke yayi.
"Zai daÉ—e ne kafin ya koma?"
Aunty Bilkin ta tambaya, sai ta girgiza kanta.
"Babu inda zai koma Aunty Bilki, tare zamu je kuma tare zamu dawo na gaya masa ne dai kawai ya kira Bashir din ya gaya masa komai."
Ta faɗa da dukkan yaƙinin da zai iya fitowa daga cikin zuciyarta, sannan ta mayar da kayan cikin ledar da cewar zata same shi ta bashi, caraf sai Amira ta miƙe ta karɓa da niyyar kai masa, don haka sai ta samu waje a kusa da Aunty Bilkin ta zauna, tana gaya mata mutanen da suka kira ta a waya suna cewa ayi mata barka.
Sai dai sam ba fahimtar ta sosai take yi ba, ba komai take ganewa a cikin bayanin ba, zuciyarta zagaye kawai take yi taba komawa daren jiya, daren jiya da suka zauna tare da Jawad suka fayyace komai game da al'amarin, tarin bayanin da yayi nusu na yadda yaji labarin komai a cikin kankanin lokaci da ma dukkan abunda ya faru bayan nan,sai dai ba komai ne yafi tsaya mata a rai ba illa sunan Bashir da ya kira a matsayin mutumin da ya rayu a gidansa kuma yake masa kallon mahaifi tsawon shekarun nan.
Mukaminsa da ya ambata na matsayin minister shine abinda kai tsaye ya tabbatar mata da cewar Bashir din da ta sani a rayuwarta ne, kanin mijinta Ibrahim wanda yake kamar yayansa, don tun kafin mijinta yayi aure shi yake da mata uku, tana tare da Ibrahim din kuma ya kara ta uku mai suna Mardiyya, ta san shi ta san matansa sarai! Don sun yi shiri da matarsa ta biyu Yagana. Bayan abubuwa sun lalace a tsakaninsu ne sai itama ta juya mata baya kamar sauran duka danginsa.
Ibrahim yana son haihuwa, sun fara samun matsala ne tun daga lokacin da ta haifi dan da akace musu ya rasu, sannan sai abubuwa suka lalace a tsakaninsu bayan an tabbatar da matsalar da ta samu a mahaifarta, matsalolin da suka kai ga rabuwar aurensu tun a wancan lokacin, kuma cikin wani ikon Allah sai daga ita har shi babu wanda ya sake haihuwa a dukkan aurarrakin da suka yi bayan nan har zuwa lokacin da Allah ya karbi rayuwarsa.
Tana tuna lokacin da aka gaya mata rasuwarsa, shekaru kusan ashirin da wani abu a baya, tana tuna iya zafin hakan da taji tun a wancan lokacin, zafin da bai kai wanda take ji a kirjinta yanzu ba, wanda take ji idan ta tuna cewa Ibrahim ya rasu ne yana tare da É—ansa ba tare da ya sani ba, don a bakun Jawad take ji cewa anan gidan Bashir É—in akayi jinyarsa kafin ya rasu...
"Kukan me kike yi kuma Salamatu? Idan na murna ne ai ya isa haka, idan kuma wani tunanin ne a ranki ki kauda shi gefe dan Allah, ki godewa Allah da ya nuna hakan tun da ranki kafin ki bar duniyar, ki sa a ranki cewa ya so ki da rahama ne tunda har ya baki wannan damar... Ga ki da ranki da lafiyarki da dukiyarki har da kwarinki, ba sai a lokacin da ba lallai ki iya komai ba... Gidewa Allah zaki yi ki kara gode masa Salamatu, ba kullum ne al'amari irin wannan ke faruwa a duniyar ba."
Sai ta sa hannunta tayi saurin goge gawayen fuskarta sannan ta daga kai alamun ta yarda hakan ne... Sannan ta dago daidai lokacin da jikokin Aunty Bilkin yayan wata yarta Muniba da itama ta karaso a lokacin suka taho da gudu suka rungume su... Ta riƙe yarinyar a jikinta tana kallon Muniban data shigo rike da karamin dan ta a hannu yayin da sauran ƴanmatan dakin suka juya suna yi mata magana, kowanne fuskarsa dauke da fara'a...
Sai kawai ta furta kalmar Alhmdlilah a fili tana kara godewa Ubangiji ya daya azurta ta da wannan damar a rayuwa.
*
Jawad yana tsaye daga cikin ɗakin, daga jikin windon ɗakin inda aka saki farar liner dake jikin labulayen ta yadda daga yadda yake a tsaye yana hango wasu motoci biyu da suka shigo gidan mutanen cikinsu na ƙoƙarin fitowa. Hannunsa ɗaya na kare da waya yayin da guda ɗaya ke rike da labulen yace.
"Wallahi mutane take ta kira Haro, daga safiya zuwa yanzu gidan ya kusa cika... They are making me feel uncomfortable, yanzu muka rabu da shi kanin nata Nasir, yana gaya min cewa idan yansandan sun iso tare zamu fita zuwa gidan ita É—aya matar, tsakanin jiya da yau Haro na rasa ma lokacin da zan zauna inyi tunanin cikin kaina..."
Daga cikin wayar Haro yayi dariya kafin yace.
"Kace ka zama wata sabuwar amarya kawai, but I'm really happy for you man! Wallahi kayi sa'a ba kowa ne ke gane irin wannan abun game da rayuwarsa kuma ya samu mafita cikin kankanin lokaci ba... You solved everything out kafin ma mu sani, don ni sai jiya da daddare ne da muna waya da Bello na office dinku yake ce min wai ka dauki hutu a lokaci guda yana fata dai lafiya sannan na san cewar ashe baka gari ma."
Jawad ya saki labulen ya taho cikin dakin yana kare wa kayan cikinsa kallo, a tunanin Haro komai ya faru ne cikin sauki, a lokaci guda ba tare da wani bata lokaci ba, amma shi ya sani halin da ya shiga da kuma wuyar da ya sha a iya wannan ɗan tsukin, idan za'a rarraba ta a zuciyar wani zai ɗauki watanni kafin ya iya kai ƙarshensa.
Shi kadai ya san abinda yaji shi kuma shi kadai ya san abinda ya fuskanta a cikin zuciyarsa da ma jikinsa, sannan ga tasirin dukkan abinda ya faru jiya, na yadda ya samu abinda baiyi zato ba bayan sun bashi tabbacin da shi kansa ba zai iya musantawa ba. kusan hotuna goma Hajiya Kilishi ta dauko masa na mahaifin nasa da takira da sunan Ibrahim Shanawa, kuma tun a hoton farko yaga kamar ya san fuskar kamar ya gane shi duk da cewa suna ta zuzuta kammaninsa dashi.
Sai da ya fara yi mata bayanin inda ya taso sannan komai ya fito fili, wani ikon Allah da kuma wata sabuwar isharar ta fahimtar dashi cewa a tsawon rayuwar da yake tunanin ya shafe a hannun wasu mutane, ashe ba wasu bane, a cikin danginsa yake, a tsakiyarsu ma tunda tun kafin hawan Alhaji Bashir matsayin minista gidansa yake a matsayin centre guda ta family dinsu, kusan kowa yazo zai samu wajen zama babu takura, shi yasa a yanzu da yake matsayin ministan Æ´an aikin dake tafiyar da al'amarin gidan su kansu wajensu daban.
Bai kira kowa ba, bai kira su Hajiya Mardiyya ko kuma wani a gidan ba har yanzu, yafi son sai ya gama tara hankalinsa waje guda tukunna, yafi son sai ya saita iya abinda ke gabansa a yanzu, don ya sani gaggawa ba zata haifar masa da komai ba.
Ya ajiye wayar hannunsa a gefen gadon dakin sannan ya nufi ƙofar toilet ya buɗe... wanka yake so yayi ya canja kayan jikinsa shi yasa yake ta jinkirtawa don ta gaya masa cewa zata sa a kawo masa wasu, hoton fuskar Zainab ya gifta a ransa a lokacin, ba sau daya ba ba sau biyu ba tasha wanke masa toilet, ta haka ya fara gane ta, ta haka ya fara gane cewa an canja masa mai gyara masa daki kafin ma ya fahimci wacece ita.
Ya cije lebbensa kadan yana ƙoƙarin tuno ɗaya zagayen halin da yake ciki, sai dai hakan baiyi nisa ba lokacin da aka kwankwasa kofar ɗakin, sai ya saki ta toilet ɗin da yake riƙe da ita sannan ya matsa gaba ya buɗe.
Wata yarinya ce, tun safe ya ganta a gidan bayan ya tashi daga bacci, don bayan an kawo masa breakfast ma ta zo daga baya ta kawo masa lemo da kuma Pringles tace ya kara, bai ma san wacece ita ba, bai san matsayinta ba,yaji dai kawai suna koran sunanta da Ameera.
Bakinta ya tale da murmushin da yayi daidai a fuskarta.
"Yaya J, hope dai ban katse ka kana wani abun ba?"
Ya zura wayarsa dake hannu a aljihu sannan ya girgiza kansa yana kallonta.
"Kar ki damu I'm fine."
Sai ta sake wani murmushin sannan ta gyada kanta.
"Toh Alhmdlilah... Kaya ne Aunty tace in kawo maka."
Ta fada tana nuna ledar hannunta da yatsanta daya mai dauke da wani zobe dake kyalli a cikin fitilar wajen.
"Nagode." Ya fada yana mika hannunsa fon ƙarba amma bata miko din ba sai tace.
"Can I choose a colour for u? Wanda zaka sa yanzu?" (Zan iya zaɓar maka kala?)
Jawad ya ƙara kallonta, zuciyarsa na kokarin gaya masa wani abu da ba shine ransa ba yanzu, sai kawai ya sake miƙe hannunsa yace.
"Kar ki damu zan É—auki duk wanda yake a sama ne kawai."
Yayi zaton zai ga canji a fuskarta, amma sai jawai ta ƙara yin murmushi mai fadi tace.
"Shikenan, muna jiranka."
Da haka ta miƙa masa kayan sannan ta tsaya tana cigaba da kallonsa da murmushin a fuskarta ba tare da ta juya ba. Wani abu da ya ratsa zuciyarsa kenan yasa duk yadda ya kai ga jinsa wani iri sai da wani guntun murmushin ya sauka a lebbensa.
"Nagode."
Ya faɗa yana rufe ƙofar, ta kaɗa masa yatsu biyu a gefen fuskarta tana cigaba da murmushin kafin ya rufe ƙofar a fuskarta.
Ya rufe kofar daidai lokacin da wayarsa dake cikin aljihu ta shiga kara, hannunsa ya jawo ta da sauri ya duba, sunan Nura ya baiya na tar a jiki don haka ba shiri ya daga ya kara a kunnensa tare da sallama.
Daga cikin wayar Nuran ya amsa da sautin muryar da ya sanya zuciyarsa tsalle tun kafin Nuran ya kai ga faÉ—in abinda ke bakinsa.
"Yallabai an samu matsala, wallahi yau da safe da muka tashi ba mu ga yarinyar nan ba, tun safe ake nemanta har yanzu babu labari....!"
***
_A cikin shafi biyu masu zuwa a gaba, labarin Farar wuta zai kai ga tsayawa insha Allah..._
_Nagode da tarin haƙurin ku, Allah ya sani na fiku damuwa ganin yadda lokaci ke ta jan mu, da kuma yadda nake ta yawo da nauyi a ka._
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:58 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*24*
_There are no happy endings, endings are the saddest part, so just give me a happy middle and a very happy start..._
~~~~~~
"Sai gyada Hajiya, sai gyada ci ko tsaraba.."
Wata yarinya dake É—auke da bokitin tallan gyadanta ta faÉ—a tsaye daga bakin wata hayis dake dauke da fasonjoji wanda mafi akasarinsu mata ne dsuke da yara da kuma wasu a goye, banda hayaniyar cikin tashar akwai ta cikin motar ma da baka jin komai sai sautin muryoyin matan kawai dake ta kacaniya suna kuma ciye-ciyensu kala-kala.
Wani dattijo ya taso ya tsaya daga bakin ƙofar hannunsa riƙe da littafi zai fara karɓar kuɗin mota da kuma rubuta sunaye, wata mata dake ɗurawa yaronta wani farin kunu a leda tace.
"Motar fa bata cika ba..."
Ya gyada kansa.
"Na sani ai Hajiya ba saura mutum É—aya ba, kowa ya fito da kuÉ—in motarsa... Ke ya sunanki?"
Ya faɗa yana ƙoƙarin rubuta sunan mace ta farko dake bakin ƙofar yayin da kowa a motar ya shiga ƙoƙarin binciko kuɗi daga jakarsa, mutumin ya gama rubuta sunan ya dago da kansa daidai lokacin da idonsa ya sauka akan wata yarinya da ta karaso jikin motar sanye da wani farin hijabi dogo.
"Ƴan mata ina zaki je? Jaji ko kuma Kawo?"
"Sameru zanje..." Muryarta ta faÉ—a kusan a shake sautin na fitowa a hankali, sai ya girgiza kansa.
"Ga motocin Sameru can a wancan layin... Kudinki dari takwas ne, amma zan miki ragi, kawo dari bakwai a rubuta sunanki tun daga nan kafin mu isa."
Zainab dake tsaye tana kallonsa ta haÉ—iye a wani abu a makogwaronta kafin ta girgiza kanta a hankali.
"Bani da kudi malam, dan Allah..."
"Baki da kudi?"
Ya tambaya sautin muryarsa na juyewa zuwa wani abu kamar izgili.
"To rawa zaki yi su kai ki Samerun ko kuma ya za'ayi?"
"Haba bawan Allah, kace mata babu mota kawai mana, sai ka bi ta da bakar magana."
Wannan matar ta faÉ—a daga cikin motar, vai saurari daya daga cikinsu ba ya juya kawai ya cigaba da neman sunayen mutanen dake cikin motar.
Wani abu ya sake wucewa ta makogwaron Zainab a lokaci guda da ta shiga murza yatsun hannunta daga cikin hijabin, ƙwalla ta sake cika idanunta a lokaci guda, kafafunta sun gaji, tayi tafiya mai nisa kafin ta kawo tashar, tayi tafiya tun daga cikin kauyensu inda ta fito ta baya har zuwa wannan ƙauyen dake gabansu inda anan babbar tashar da ake samun mota zuwa ƙauyuka daban -daban a wannan hanyar take.
Kuma bayan isowarta kai tsaye aka nuna mata wajen da ake hawa motocin inda take son zuwa, Sameru... Ƙauyen da ƴan uwan mahaifiyarta suke... Wajen da ta san cewa duk duniya bata da inda yafi shi a yanzu, babu wani waje ko kuma wani masaukin da wani zai bata da matsayinsa a idanun al'umma dama nata gabaɗaya zai kai can.
Hadiza, wata yarinya da tayi kusan sa'arta a cikin gidan mijin nahaifiyarta da ta baro ita ke shaida mata dukkan abinda ya faru a lokacin rasuwar mahaifiyar tata, yadda yan uwansu kowa da kowa ya hallara a gidan da kuma tarin rigimar da aka sha da mijin mahsifiyar tata skan aikin da tmya tura ta.
Wani abu da lokacin da tana Abuja babu abinda take tunawa kamar hakan, yadda yanuwan mahaifiyar tata suka yi iya kokarinsu wajen ganin ta basu ita sun rike a lokacin da zata yi aure, amma ta ƙi haksn,tace ta san zsi tike ta da amana kamar mahaifinta tunda amininsa ne, sannan ta kafa hujjar cewa duk duniya ita kadai take da ita a matsayin ƴa kuma bata tunanin sake samun wata haihuwar a yanzu duba da shekarunta, don haka babu yadda suka iya suka bar ta a wajenta.
Kuna tun daga farko zaman gidan baiyi dadi ba sam! Sun sha wahalar da duk da karancin tunaninta tasha lissafa musu mafita ta hanyar mahaifiyar tata ta rabu dashi, amma bata yi hakan ba har karayar arziki tazo ta same shi inda babu bata lokaci ya shiga tura ƴaƴan sa aikatau, wanda daga baya ya hada har da ita da tarin hujjojin da mahaifiyar tata bata iya ƙarewa ba.
Tana tuna ranar da ta tafi, ranar da ta tafi ta barta, tana tsaye daga kofar dakinta tans share hawaye da bakin zaninta, kwana suka yi tana bata hakuri da kuma shawarwarin da zata kare kanta yayin da itama ta shafe daren tana saƙe-saƙe cike da tunanin haƙuri irin na mahaifiyar tata da kuma taraddadin inda zata je da abinda zata tarar.
Ashe dukkan tarin abinda zata tarar din bai kai wanda zata dawo kuma ta iske ba, ƙofar dakin mahaifiyarta a ƙulle da wani ƙaton jwado a daidai lokacin da ta taka kafarta cikin tsakar gidan, da kuma idanun mutanen gidan da yadda suke kallonta da mamaki da kuma wani abu da bata iya fassara shi ba sai a lokacin da mutumin nan yake gaya mata cewa babu mahaifiyarta...
Ta rasu, babu ita a duniyar nan, ta rasu sati biyu da suka wuce... Ta rasu babu wanda ya gaya mata, babu wanda yabi ta inda aka tura ta ya gaya mata. Mahaifiyarta ita kadai take da ita a duniya, guda daya ce babu wata... Amma ta rasa ta babu wanda ya iya zuwa ya gaya mata sai da ƙaddara ta dawo da ita da ƙafafunta sannan ta samu labari, fuskar Jawad ta haska cikin idanunta a sannan, lokacin da ya riko hannunta kafin ta kai ga fita daga motar ya gaya mata cewa yana jiranta, zai jira ta a wajen har ta gama abinda zata yi ta dawo...
_"Ba zan iya tafiya babu ke ba, amma nayi alkawarin zan dawo dake insha Allah Zainab..._
Haka ya faÉ—a da sautin muryarsa da duk da ba ta shi take yi a lokacin ba sai da ya ratsa har cikin zuciyarta, bata san me suka fito nema a lokacin ba, bata san me ya kawo shi har cikin garinsu ba, amma zata kiyasta cewa yana cikin kwatankwacin matsalarta ne a lokacin, ko ma wadda tafi tata.
Kuma ta tabbata abinda ke gabansa shi yasa shi barinta a lokacin, idan ba haka ba ta sani,ta san Jawad ta fahimci galinsa a dan kankanin lokacin da ta sanshi, baya fadin abu sai idan har da gaske yake kuma ya tabbatar dashi har cikin zuciyarsa don idan ya fada É—in, to babu wani kuma a duniya da ya isa ya canja ra'ayinsa, ko a bakin Hajiya Mardiyya tasha jin tana bawa kannensa hakuri akan su hakura da wani abu, tace ko ita tsoro sa take yi idan ransa ya baci.
"Malama idan baki da kudi gwara ki koma gida, alkur'anin Allah babu wanda zai dauke ki har Sameru kyauta a wannan tashar..."
Wannan mutumin ya sske fada a lokacin da ya gama rubuta sunaye ya shiga haɗa kan yan canjin da aka tattara masa, a lokacin kuma wani mutumi ya ƙaraso ya biya nasa kudin aka gama cika mitar,direban ya zagayo ya karbi kudinsa ya cire kamashon tasha sannan ya shiga ya tada motar.
Sai kafafunta suka matsa daga wajen ta koma gefe, gefe kusa da wasu kanti da kuma rumfuna ta tsaya, tana kallo motar ta juya ta fita ta nufi hanyar fita, idonta ya koma kan jerin motocin da akace mata sune ke nufar garin da take son zuwa, mutane na ta hada-hada a wajen ana lodi da kuma jera kaya yayin da masu karbar kudi ke yi.
Bata da ko sisi, bata ma san inda zata same su ba, amma alƙawari ne ta yiwa kanta cewa ba zata sake komawa cikin Yakura a yanzu ba, watakila watarana zata dawo ko don ziyartar kabarin mahaifiyarta, amma a yanzu ta yarda cewa babu abinda zao sake maida kafafuwanta wannan gidan.
Tunanin Jawad ya sake haskawa a cikin kanta,ta san zai dawo zai neme ta, amma rashin samun nata da zaiyi bai dame tasosai akan tunanin samawa kanta Æ´anci da take son yi ba.
_"Babu abinda zanyi miki Zainab, wallahi babu abinda zanyi miki, I just want to feel you close to me... So nake kawai in dinga jinki a kusa dani. Shi yasa na tambayeki idan zaki aure ni saboda zan je har wajen iyayenki ne in nemi aurenki, babu ruwana idan ma akwai wanda suka tsara zasu baki Zainab, ko shari'a zan iya yi da kowa idan akace za'a hana ni aurenki..."_
Abinda ya fada mata kenan da yabayin fuskarsa dake tabbatar mata da kowacce kalma da yake fada a lokacin, don haka ta yarda idan har da gske yana son ta, zai nemo ta a duk ind take tunda ta san va zata yi nisan da hakan zai gagare shi ba.
Tana yawan son korewa kanta nauyi a kodayaushe, ta yarda babu wani ingantaccen abu da rauni ke samawa mutum a duniyar nan, don haka ba zata bari rauninta ya rinjaye ta wajen zama jiran Jawd ba, idan har ta mike da kafafunta, ta tafi wajen da zai tabbatar da darajarta tun kafin yazo da ma bayan yazo din, abubuwa zasu canja daga kalar yadda suke tafiya a baya, shi kansa zai san cewa bai same ta ne a wani hali na rashin gata da madafa ba.
"Har yanzu kina nan?"
Mutumin nan ya fada bayan ya dawo zai wuce, hannunsa babu littafin nan a yanzu. Ya ja ya tsaya a gabanta sannan ya gyada kai.
"Lallai da gaske kike, hala mutuwa akayi muku a can din ko?"
Kalmar mutuwa ta sake dawo mata da zagayen halin da take ciki, sai kawai idanunta suka ciko da kwalla sannan t ja hancinta kadan kafin ta gyada kanta. Sai shima ya girgiza nasa kan.
"Allah ya jikan musulmi, ai kuwa kya so tafiya... Kuma zan taimake ki tunda haka ne."
Ba shiri ta dago ta kalle shi da idanunta da har a lokacin suke rine da kuka, ya sake gyada masa kana alamun ya tabvatar da hakan.
"Akwai shugabanmu anan wajen, wallahi ba wani abu zai yi miki ba, kawai dai taimakon juna zaku yi ki sami abinda kike so, ke fiye da hakan ma zai baki a yau din nan, babu wanda zai sani kuma babu wanda zai ganki."
Wani abu ya doka a kirjinta da jin hakam,don tsaf ta fahimci inda zancen nasa ya dosa, ta zare idanunsa akanta tana kallonsa cike da tashin hankalin da shi bai fahimta ba ya cigaba da cewa.
"Kuma walkahi ma ni a duk wadanda nake kai masa babu irinki, duk yan kauyen nan ne dake kawo tallan kaya cikin tashar nan, to suma baki fa abinda suke samu ba balle kuma ke... Ai ina gaya miki sa'ar da zaki raka yau..."
"Kayi hakuri Malam, amma ba zsn iya abinda kake nufi ba."
Muryarta ta fito a hankali tana katsse shi, kuma dukda hayaniyar cikin tashar yaji abinda ta fada da yake hankalinsa na kanta.
Zainab ta juya zuwa batanta inda wajen yake da rumfa daga gefen wani shagon container ta cire takalmanta ta zauna tana jin yadda hakoran bakinta suka kasa tsayawa waje guda sakamakon kukan da yake shirin kubce mata tana danne shi, mutumin ya kalle ta daga inda yake tsaye, takaicin asarar kudin da yake hangen zai samu a wajen shugaban nasa na bi ta kan zuciyarsa.
Har zai juya yaji ba zai iya dannewa ba, don ba karya yayi mata ba, shi dai ta hanyarsa ya sani cewa bai taba kaiwa Alhajin wata mace kamar ta ba, fatarta kadai wata kala ce dake tsakanin fari da kuma ruwan ƙasa, wata kala mai ɗauke da kuma daukar hankali, bata da shahararren kyan da a lokaci guda zaka gane shi, amma ƙirar jikinta kaɗai da yake gani tun daga cikin hijabin, ya sani ba kowacce mace take haka ba.
Don haka a lokaci guda ya canja shawara, shawarar daya san tunaninta ba zai iya kufce masa ba.
Bai sake cewa komsi ba ya juya ya tafi kuma sai a lokacin ƙwallar dake tare a idanun Zainab ta ganganro kan kumatunta, bata taba yiwa kanta wannan fatan ba, bata taba fatan za'ayi ranar da zata zubar da mutuncinta don biyan wata bukatar ba... Zata gwammace ta koma inda ta fito da tayi wani abu makamancin hakan, a hankali ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta biyu tana kokarin goge hawayen.
Banda Jawad babu namijin da ya taba rike ta a duniya, kuma shi nasa daban ne, baya kallonta da niyyar komai, yawanci fushinsa ne ma ke sawa ya rike ta, fushinsa da take mutukar jin tsoro a lokacin, amma a kwanakin nan musamman tahowar da suka yi, idan ta kalle shi a wannan yanayin, sai taji kamar ta rungume fuskar sa a jikinta tsawon lokacin da ba zai kara ganin komai ba bayan ita...
_"...zan aure ki ko baki gama yanke shawara ba, idan yaso daga baya zan koya miki yadda zaki so ni."_
Wani abu tsaya a makogwaronta a lokacin da ta tuno hakan, Jawad bai sani bane amma halayen rayuwa sun sa tun a yanzu ta fara koya...
"Baiwar Allah..."
Muryar wata mace dattijuwa ta sa ta dago da kanta bayan wucewar wani lokaci, fara ce, farin da bata sani ba idan na gaske ne ko kuma wanda ta samawa kanta, fuskarta dauke da fara'ar da ta sa a lokaci guda tasa bayan hannunts ta goge hawayen dake kan fuskarta.
"Ance min taimakon kudin mota kike nema ko?"
Ta sake tambaya da wani murmushin, kuma kafin ta bata amsa ta cigaba.
"Gidan abinci ne dani anan baya, kuma almajiran dake min wanke wanke bai zo ba yau, idan zaki yi in biya ki kinga sai ki samu kuÉ—in motar ko?"
Babu shawara ta biyu tunanin Zainab ya amince da hakan, bata ga aibun hakan ba, bata ga komai ba... Don hausawa sun ce wanda yake ruwa aka miƙa masa takobi kamawa zai yi, ƙafafunta suka mike a daidai lokacin da nasa suka ƙaraso wajen.
*
"Kace ta san sunan garin ko?"
Jawad ya tambaya a cikin gudun da motar ke yi, gudun da suke yi daga gefen titi wajen da babu komai sai kasar dake tashi a baya da zarar sun wuce.
Nura dake zaune a gefe ya gyada kansa.
"Ta sani, haka Baban ya gaya min cewa ai tun da daÉ—ewa ta san sunan garin.
"Kuma ka tabbata babu wata tasha da ake zuwa garin sai wannan da zamu je?"
Ya sake tambaya yana zura hannunsa a cikin gashin kansa.
Nura ya sake gyada kansa.
"Ita kadai ce a kusa yallabai, ita kadai ce wadda zata iya zuwa, kuma gashi ma Isa ya tabbatar mana da cewar ya ganta akan hanya..."
Jawad ya cije lebbensa na kasa, hannunsa ya sake danne sitiyarin motar da babu shiri suka kara figa da gudu, Abdallah É—an wan Hajiya Salamatu wanda bata yarda da tafiyar Jawad ba sai da ta turo shi ya biyo shi yayi magana daga inda yake zaune a bayan motar.
"Easy mana bro,zamu isa yanzu ai Insha Allah."
Jawad ya girgiza kansa.
"A kowanne lokaci mota tashi take yi a tasha zamu iya sabanin ko kuma minti daya ne Abdallah. Tun yaushe ta fita, tun safe fa yace badu ganta ba."
Nura ya gyada kansa.
"Amma ai da tazarar tafiya,ta dauki lokaci kafin ta isa na san sannan kuma bata da kudi a hannunta, sai da kowa ya caje kudinsa a gidan yau duka bata dauki ko sisi ba, kaga kafin tayi abinda zata samu kudin mota shima wani lokacin ne don haka za..."
"Me zata yi ta samu kudi?!"
Ba shiri Jawad ya katse shi yana daga muryarsa, kafin ya juyo da fuskarsa yana kallonsa.
"Me zata yi ta samu kudi a cikin tasha Nura? "
Kafin Nuran ya amsa, wayar Abdallah tayi ƙara a hannunsa ya dauka ya kara a kunnensa da sallamar da Jawad ya riga ya san ko wacece, Hajiya Salamatu... Don tun daga lokacin da suka sauka daga jirgi a Kaduna suka je gidan abokinsa suka ɗauko motarsa da ya bari a can, ta kira shi da kuma Abdallah fiye da sau goma, sai da ta fahimci shi yake tuƙin motar sannan ta koma kira Abdallahn.
Zai rantse da Allah a lokacin da ya gaya mata cewa zai taho Kaduna a yau, kalar tashin hankalin da ya sauka a idanunta iri É—aya ne da wanda ya gani a idanun Hajiya Mardiyya kafin tahowarsa... Tsoro ne karara da kuma taraddadin rasa shi, wani abu da ya kara bashi tabbaci na cewar da gaske ita mahaifiyarsa ce Uwa wadda babu makamanciyarta a duniya, tunda a kwana daya rak da ta san shi har zata iya tarayya da halin da wadda ta raine shi tsawon shekaru ta shiga wajen tunanin rasa shi.
Har hannunta ya riƙe ya gaya mata cewa zai dawo su tafi can Abujan tare kamar yadda ta tsara har ma da wasu ƴanuwanta, tana gaya masa cewa akwai tarin wasu yanuwan nata da zaau zo wajensa a yau daga Gombe shima yana gaya mata cewa baya fatan abinda zai kaishi ya ɗauke shi tsawon wani lokaci.
Bai gaya mata ba, bai gaya mata abinda zaizo yi ba kamar yadda shima Abdallahn bai gaya masa komai ba, kawai ya tsinci labarin ne bayan sun dauko Nura a cikin irin maganganun da suke yi na zuwa nemanta.
"Bamu karasa ba har yanzu Aunty muna hanyar..."
Abdallah ya faÉ—a a cikin wayar yana dawo da hankalin Jawad kan halin da suke ci kuma a sannan ne suka fara hango tashar, daga can saman wani waje da ya danyi tudu alamar tsanuni ne a wajen tunda hayar tana da hawa da sauka da yawa.
Ya cije lebbensa na kasa hannunsa ya sake danne kan motar a lokacin da Abdallah ke cewa.
"Insha Allah Aunty, insha Allah za'a ganta..."
Ya sauke wayar sannan ya shiga sake tambayar Nura sunan wajen da kuma tazararsa da cikin garin Kaduna, sai dai Jawad baya ko jinsu idanunsa dama duk wani abu mai motsi a jikinsa sun tafi ne ga bakin tashar nan, baya ko damuwa da gudun da yake yi ganin ya fara shigowa cikin mutane.
Tayoyin motar suka tsaya tun kafin ya ƙarasa kofar tashar, kuma ya fito a lokaci guda da motar ta tsaya yana rufe kofar motar, su Nura suka biyo bayansa suka nufi ciki gabadaya, tarin mutane da kuma hayaniyar dake faruwa a ciki ta cika kunnen Jawad kota wanne bangare, wata yarinya ya fara hangowa dauke da kaya, kammaninta suka koma ba Zainab sak a idanunsa.
Har ya fara tafiya sai ya hangi wata irinta itama daga wani gefen, ya ga wata da goyo sannan ya ga fuskoki da yawa daga cikin wata mota duk irin nata, sai kawai ya ja ya tsaya, ya tsaya daidai lokacin da Nura ke tambayar wani inda ake samun motocin Sameru.
"Wallahi maigida nima matafiyi ne ban sani ba, sai dai ko ku gwada tambayar wancan na ganshi da rigar Æ´an union."
Yana faÉ—a yana nuna wani ma'aikaci dake aiki daga can gefe, kuma Nuran ne kadai ya tafi yana ganin kwatancen da mutumin yayi masa tun daga can, kuma tun daga can É—in ya gane, don haka kafin ma Nuran ya dawo ya riga yayi cikin tashar Abdallah na binsa a baya.
Mutum biyu suka samu akan wata mota dake kan layi kuma duk irin tambayar da suka yi musu kai tsaye suka nuna cewa basu ga yarinya mai makamancin kwatancen da suke yi ba.
"Amma bari a kira Sani, sune a wajen da safe, watakila bakuwar taku da safe tazo."
Dayan ya fada yana yin gaba zuwa wani gini daga gefe. Dayan ya kalli Jawad sosai yace.
"Yallaɓai wallahi kar ku saka rai, tashar nan sai mutum dari su zo a kasa da minti goma,wani ko fuskarsa ba zaka kalla ba zaka karbi kudinsa ka tambayi sunansa... Da ka rubuta shikenan kai dashi har abada, to ta yaya za'a iya gane wata yarinya?...."
Bai ƙarasa maganarsa ba sai ga daya ya dawo tare da mutumin da aka kira da Sanin, yana tsayawa tun kafin ma Jawad ko Nuran su ce wani abu ya tambaya.
"Yallabai farin hijabi ne a jikinta..."
Jawad ya daga kansa da sauri yace.
"Ofcourse bata da tsawo sosai..."
Sanin ya daga kansa shima.
"Ai bata je ko'ina ba, bata hau mota ba, tazo inaga kamar bata da kudi ne saai kuna ta tafi. To bayan hakan kuma sai na ganta a zaune a wajen shagon Ashiru, amma wallahi tun É—azu ne, ban sani ba yanzu ko za'a same ta..."
"Ina ne wajen? Nuna mana wajen kawai..."
Cewar Nura.
Mutumin ya shige gaba, dukkaninsu suka bi shi a baya zuwa daya bangaren tashar wajen da ake lodin motocin dake karasawa cikin Kadunan, Jaji zuwa Kawo.
Kuma Ashirun da Sanin ya ambata shi suka fara gani a wajen yana ɗaukan sunayen wasu mutane a cikin mota. Basu san me Sanin yace dashi ba, don shi ya fara ƙarasawa kafin su, idon Jawad na kan Ashirun a lokacin da yake gyada kansa yana nuna wata hanya da ke gefe don haka bai ko ƙarasa wajensu ba ya yi hanyar.
Ya isa daidai jikin wani shago lokacin da idonsa ya hango masa ita a lokaci gudataa mikewa da aamun zata bi wata farar mata dake tsaye a gabanta tana yi mata murmushi.
Ta juya bayanta tana fuskantar matar, bata ga tahowarsa ba balle ta ganshi, don haka bai jira komai ba ya ƙarasa da taku biyu ya riko hannunta, yatsunsa suka lankwasa a tsakanin nata tun kafin ta juyo a lokaci guda da ta kalle shi, ta kalle shi da idanunta a zare da tsananin tsoron da cikin sakanni biyu kawai ya juye zuwa mamaki.
"Jawad...??"
Bakinta ya furta a hankali yayin da zuciyarta ta buga sau É—aya, ta buga da wani sauti da ta tabbatar da cewar dukkan sauran mutanen dake zagayensu sun ji shi. Ba shiri idanunta suka cika da shekin kwallar da bata san ta ina ta fito ba, mamaki take idan shi din ne ko kuma mafarki take yi... Don tunaninta ya kasa bata cewa zai iya zuwa ya same ta a wannan wajen kuma a wannan lokacin.
Sai dai babu wani bata lokaci, yayi abinda ya tabbatar mata da cewar da gaske shi din ne ba wani ba, da gaske Jawad din da ta sani ne...
Hannayensa duka biyu suka zagaye jikinta, ya rungume ta a cikinsu, ya rungume ta a kirjinsa, ya rungume ta a gaban tarin mutanen dake wajen ba tare da tunanin komai ko kuma abinda za'ace ba..
Sai kawai ƙwallar da ta cika idanunta ta zubo kan fuskarta, ta riga ta sani komai ya zo ƙarshe, wahalar da take tunani ta yanke tun kafin ma ta fara, shikenan tayi sallama wa dukkanin wahalarta!
***
*03:15 am.*
Tana tsaye daga jikin tagar dakin, hannayenta duka biyu dafe da gilashin da aka rufe yagar wanda ta manna fuskarsa a jiki yayin da idanunta ke tsaye ƙyam! Akan wanda ke kwance a akan gadon dakin, ance mata Ma'aruf ne, kowa yace mata shine, amma fiye da minti goma da take tsaye a wajen babu wani abu a kwakwalar ta da yatuna mata cewar Ma'aruf din da ta san shi take kallo.
Fuskarsa a kumbure take idan ka dauke katuwar robar zukar numfashin da aka manna a fuskarsa da kuma gashin kansa da aka aske, wannan sumar... Wannan sumar ta Ma'aruf da kullum take tare da hannaensa, yanayin yadda yake cusa su a ciki kadai Kala-kala ne ta yadda ta kan fahmci wani abun da yake nufi idan yayi tun ma kafin ya furta.
Don haka gabaɗaya kamanninsa sun canja ta yadda ko ba'ayi wa mutum bayanin rashin lafiyar dake damunsa ba shi da kansa zai kintata tun daga harafan dake rubuce ɓaro-ɓaro akan gilasan wajen da launin ja... ICU.
Wani abu ya wuce ta makogwaronta lokacin da ta tuna da san da ta farka ta riski labarin komai... fuskar Amma ta fara gani kafin komai, tana zaune daga kujerar dake gefen gadon da take kwance, hannunta rike da wani carbin ta kalar yalo, wani carbi da a cikin su gabaÉ—aya babu wanda zai iya fadar adadin shekarun da suka san shi a hannunta, dashi take lazimi kulum, a kowacce safiya da kuma yammar Allah.
Ta rufe idanunta a hankali sannan ta sake bude shi tana kara kallon Ammar da kanta ke sunkuye tana addu'o'in ta, yanayin sai ya koma mata iri É—aya sak da wani lokaci a can baya, lokacin da Maryam bata da lafiya, lokacin da suke zaman jinyarta a asibiti, haka Amma ke zama a gaban gadonta da wannan carbin tana lazimi.
Fahimtar cewa yau itace ba Maryam din ba ya dawo mata da zagayen halin da take ciki, ya tuno mata da dukkan abinda ya faru kafin sumanta da ma irin tashin hankalin da ta shiga...
Ko kuma tashin hankalin da har a yanzu ta farka a cikinsa, tunda bata san me ya faru ba har a lokacin, bata san ina Ma'aruf yake ba sannan bata san a wane hali yake ciki ba, tun a lokacin aga yanayin fuskokin su Munayan da suka shigo wajenta tunaninta ya gaya mata cewa abinda ya faru ba labari ne mai daɗi ba, sannan a lokacin ta ƙara tabbatar da cewar da gaske tunaninta hakan ne tunda bata ganshi ba.
Ta sake bude idonta a hankali, lokaci ya nuna mata ƙarfe goma sha biyu na safiya wanda hakan ya tabbatar mata cewar har a yanzu tana cikin wannan ranar ne tunda da sassafe ne lokacin da su Munaya suka zo suka same ta.
Ƙofar ɗakin ta buɗe a sannan, Aunty Ma'u ta shigo bayanta goye da ƴar ƙaramar ƴar ta, hannunta da rike da wani a kwandon kwanukan abinci.
Amma ta amsa sallamarta tana juyawa.
"Bata farka ba dai ko?"
Ta tambaya tun kafin ta karaso.
"A'a har yanzu, amma Nurse din da ta fita tace ba zata dade ba zata farka."
Aunty Ma'u ta ajiye kwandon abincin sannan ta sauko hoyon yar tata dake bacci Amma ta karbe ta.
"Su Tanti suna hanya, tace akan kwana suka hadu da Safiyya yanzu zasu taho."
Kuma sai da ta zauna daga gefen gadon sannan tace.
"Ya muka ji da wadannan abubuwa da suka faru Amma? Labari haka rana tsaka babu daÉ—in ji..."
Amma ta gyara kan yarinyar dake cinyarta tace.
"Wallahi Ma'u muma haka muka tashi da kira wai an kawo ta asibiti ta suma, yanzu su Maryam suka koma su ma tare da yariyar dake wajenta Hamida, don likitan yace da ta farka zamu iya tafiya, rashin kwarin jikinta ne yasa suman ya same ta a lokaci guda."
Aunty Ma'u ta gyada kanta tana sake kallon Aminan dake kallonta ta tsakanin gashin idonta.
"Inalillahi wainna ilaihir raji'un... �ari fa akace ta kusa yi Amma, wannan wane irin labari suka gaya mata?"
"Su waÉ—anda muka tarar anan sun ce ai tun kafin ma su san wannnan al'amarin aka kawo ta asibitin. Komai ya rikice ne kawai Ma'u don ita kanta Tantin da muka yi waya ban iya gaya mata wani abu ba tunda har yanzu su ma babu wanda ya gama sanin abinda ake ciki, Munayan tace min sun san dai an tafi da ita Kilshin wajen Æ´ansanda daga asibitin nan, shi kuma an kwantar dashi."
Aunty Ma'u ta gyada kanta.
"Irin wannan sai an kwana biyu dama za'a san me ake ciki tunda su kansu yanzu hankalinsu ba'a jikinsu yake ba."
Amma tace.
"Duk sun taho ma, har da Æ´arta daya Sameerah, suran ne suke can gida tare da wasu yanuwansu don Mama Rabin da na hadu da ita tace gidan ya zama kamar na makoki daga safiya zuwa yau..."
"Allah ya kyauta, ni wallahi banyi mamaki ba Amma, a wannan zamanin jama'ar da suke da fuska biyu wajen cutar al'umma suna da yawa, kuma ba ma wai sai a wani babban abu ba, wani ko ba zai samu komai ba idan ya nuna baya kaunar ka a bayan idonka zai ji daÉ—i, kawai dai ita nata yayi yawa ne, cuta da kuma zaluntar ciki tafi karfin tunanin mutane ire-irenta da yawa.."
Amma ta yi shiru kafin tace.
"Zancen babu daÉ—in ji Ma'u, iya wanda ya fito a yanzu kaÉ—ai balle kuma abinda zai fito daga baya, Æ´an uwanta ma wasu basu yarda ba, abin ne kamar mafarki, kamar labari... Sai dai addu'a kawai."
"Allah ya kyauta, Allah ya basu hakurin É—aukar hakan ya bi musu hakkinsu, sai a godewa Allah don watakila da lokaci ya ja, zata iya aikata fiye da wanda tayi ma a baya."
"Wannan haka yake, don al'amarin yafi karfin tunaninki, Allah ya bata fikira da kuma dabarar da ta bari shaidan ya karbi linzaminsu."
Ƙwalla ta cika idanun Amina a lokacin tana hana mata ganinsu bakiɗaya sannan tunaninta ya cilla kan maganganunsu tan son fahimtar da kanta abinda bata gane ba... su waye suka yi hatsari? Wanda take nufi an kawo asibitin Ma'aruf ne? Abinda su Munaya zasu gaya mata kenan? Abinda ta kasa tsayawa ta ji kenan? An kama wani? Hajiya Kilishi ce? To ta yaya hatsarin ya faru? Komai yazo ƙarshe kenan? A wane hali su Samirah ke ciki? Baffa... Sauran mutanen gidan.... Ma'aruf ma...
Wadannan tambayoyin su suka yi ta haskawa a cikin kanta har lokacin da taji Amman tace.
"Bari na sake lekawa can inda aka kwantar dashi naga me ake ciki dama jiran ƙarasowar ku nake kar a bar ta ita kaɗai."
Ta faɗi hakan sannan ta miƙe tsaye ta juya kan wata kujera daga can jikin bango ta ajiye yarinyar.
Amina bata ga sanda ta fita ba ta dai ji ƙarar rufewar ƙofar da kuma muryar Aunty Ma'un bayan nan tana kwatance wa su Tantin da suka kira ta a waya, don haka bata bude idanunta ba sai a daidai lokacin da ta kai ƙarshe a wayar wanda hakan yasa tana bude idon ta kula da ita
"Alhamdlilah, Amina kin tashi? Sannu..."
Ta faɗa kai tsaye tana ƙarasowa gaban gadon.
"Sannu Amina, sannu...."
Ta sake faɗa tana rike hannunta wanda ba'a saka masa allurar drip ɗin da take ji a jikinta ba, sai tayi kokarin miƙewa a hankali tana kama hannun Auntyn Ma'un sosai.
"Sannu..."
Ta ƙara faɗa tana riƙe ta.
Bakinta a rabe yake kaɗan amma bata ce komai ba... Wani abu ya wuce ta maƙogwaronta tana ƙoƙarin gyara zamanta.
"Bari in zubo miki abinci ki iara jin kargin jikinki.."
Aunty Ma'u ta sake faɗa tana ƙoƙarin juyawa, sai tayi saurin kamo hannunta da sauri tana kallon ta.
"Aunty me ya faru? Su waye suka yi hatsari?"
Muryarta ta fito a bushe kamar yadda lebbenta yake. Aunty Ma'u ta girgiza kanta.
"Bari ki fara cin wani abu Amina..."
"Aunty dan Allah..."
Ta katse ta tun kafin ta ƙarasa. Tana jin yadda wani abu kamar kwalla na kokarin cika idanunta yayin da bugun zuciyarta ke dokawa ta yadda bata tunanin ko yawu zai iya wucewa ta makogwaron nata.
Sai kawai Aunty Ma'un ta dawo ta zauna a gefen gadon ba tare da ta saki hannunta ba sannan tana kalonta sosai tace.
"Ma'aruf ne yayi hatsari tare da Hajiya Kilishi Amina, amma ba wani abu ne ya same shi ba, jikin nasa da sauki, kar ki daga hankalinki sun ce babu abinda ya same shi... Ki samu ki ci wani abu yanzu, Amma tace za'a iya sallamar ki a yau, sai mu je ki ganshi...."
Abinda ta fada mata kenan, abinda ta rude ta dashi har ta kwantar da hankalinta ta iya cin wani abu a abincin da ta kawo ba tare da ta san cewa babu zance É—aya daga da yake gaskiya ba a duk abinda ta fada.
Don bayan Amma ta dawo har kuma an kira likita ya sallame ta, tun daga hanyar zuwa wajen ta fahimci cewar al'amarin yafi karfin yadda ta lissafa shi... Babu kowa a wajen lokacin da suka isa, su Hajiya Maimuna da duk dimbin jama'ar da suka taru a wajen lokacin da aka kawo shi duk sun koma gida, can gidan da a yanzu ya koma kamar gidan zaman makoki saboda ƙarancin tashin hankalin da ya wanzu a cikinsa.
Don haka ita kadai aka bari ta shiga wajen yayin da su Amma suka tsaya daga waje... Kuma Amma ce ma ta danyi mata bayanin abinda ya same da taji daga wajen su Hajiya Maimuna lokacin da tazo ta same su... Likitocin sun ce bugun zuciyarsa baya tafiya daidai, sannan ya farka sau biyu amma duka ba'a haiyacinsa yake ba... Sannan bayan haka numfashinsa ma baya iya fita daidai (Respiratory insufficiency).
Bata san tsawon mintunan da ta shafe tsaye a wajen ba,ta san dai kawai lokaci mai tsawo ya tafi zuciyarta na ta sake-sake da tunanin ayyana halin da Ma'aruf ko kuma sauran ahalin gidn ke ciki kafin wata Nurse ta gaya mata cewa su Amman dake waje suna jiranta.
Ƙafafunta suka dauke ta zuwa waje, dogon koridon asibitin inda t barsu a zaune, dogon hijabi ne a jikinta na Maryam wanda Baba ya dawo daga baya ya kawo mata, ta fita daidai lokacin da su Amman ke gisawa da Ishaq da kuma Abdurrahim wanda suka ƙaraso a lokacin, kuma kallon Ishaq din kawai tayi taji kwalla ta cika idanunta don haka kanta a sunkuye ta karaso gabansu sanda suka shiga gaishe ta da jiki shi da Abdurrahim ɗin da kawai ɗago mata hannu yayi.
Ta share hawayenta da bayan hannu sanda Amma ke gaya musu cewa ta kira su Hajiya Maimuna babu wanda ya É—aga idan yaje yace musu zasu tafi da ita gida zuwa jibi don ta kara jin daÉ—in jikinta tunda Hamida ma na can tare dasu Maryam, Ishaq É—in ya amsa amma ko daga muryarsa kaÉ—ai Amina ta san cewar har yanzu ba'a haiyacinsa yake sosai ba, tashin hankalin da shi da kuma zagayen al'ummar dake gefensa ke ciki ya isa ya sa shi a kowanne irin hali.
Kowanne irin halin da mutum guda daya yayi sandinsa ga tarin mutnen da a yanzu ita kanta bata san adadinsu ba....
Kilishi....!
****
Tana zaune akan kujerar da teburi ya raba ta da wadda É—ansandan dake kallonta ke zaune.
"Hajiya gwara ki buÉ—e baki kiyi bayani kawai, komai yazo karshe, mun kama duk wani wanda kike mu'amala dashi a harkar ki, hatta sabon yaron ki Sadik Awwalu yayi mana kwatance munjeun taho dashi, sannan mun kama likitan da kika hada baki dashi a asibiti ma da cewar kin makance, so ki bude baki ki yarda da laifinki, Shari'a sabanin hankali ce da za'a iya yi miki rangwame, baki da kowa kuma baki da komai a yanzu, don bana tunanin koa cikin iyalanki ko kuma yanuwanki akwai mai bin goyon bayan ki a yanzu.... Zai fi kyau ki sallama ki saukaka mana aiki Hajiya..."
Dan sandan yayi dukkan wannan bayanin yana kallon Hajiya Kilishi, yana kallon fuskarta da take manne da baneji a wajaje da yawa da kuma karyayyen hannunta wanda aka sakale shi ta wuya bayan anyi mata gyara, idanunta a tsaye suke cak!
A tsaye tana kallonsa, tsawon sakan ɗaya biyu, uku... Kafin ya mayar da kansa kan file din dake bude a gabansa wanda akan farar takardar dake kai, jerin laifukan da ake zarginta dasu ne wanda tun farkon suka rubuta bayan an tabbatar da kama ta da kwayoyin nan da kuma wanda a yanzu suka ƙara samu daga bakin yanuwanta bayan hatsarin da ta samu na biyu.
Baki da kowa kuma baki da komai...!
Sune kalaman dake maimaitawa a cikin kwakwalar Kilishi, suk sae dawowa suna komawa baya a lokacin... Tun bayan lokacin da Ma'aruf ya fitar da ita daga asibitin nan, tun daga lokacin tunaninta ya tsaya, komai ya faru ne a idanunta kamar tatsuniya, kamar wani mummunan labarin dake faruwa a cikin mafarkin yaro, bata gama warware zaren daya kulle ta a cikin al'amarin cewa yansanda na jire da ita suna nemanta ba, batagama lissafa hanyar mafitar ta da ta fara budewa ba,bata yi komai ba,tana cikin zagaye guda daya nesa kuma ga abinda zata ya kira da tashin hankalin duniya da kuma lahira ya riske ta.
Jiya rana ce da bata taɓa tunanin tunanin Allah zai haiccce ta ba a duniyar nan, a dukkan tsare-tsare da kuma lissafin da a tsawon rayuwarta bata taɓa hangen irin abinda ta gani ba a jiya, tana tsara komai kuma komai din yana tafiya daidai, kawarta Salamatu ce ma kawai kan tuna mata da cewar a duniya take ba'a aljanna ba cewar wani abun zai iya zuwa mata a karkace, amma ko yazo din, tana daga kwance take sa hannun guda ta gyara shi.
Alah ya bata tarin nasarori a rayuwar nan, bata jin akwai abinda ta taba zanawa zuciyarta da bai faru ba, bata jin ta taba ko da hasashen manufarta ne kuma hakan bai kasance ba, to dan me yasa sai a yanzu da rana tsaka kawa komai zai gargitse mata kuma ta yarda?
Ta yarda ta rasa Ma'aruf, ta rasa shi ta rasa kulawa da kuma ƙaunarsa. Babu kalamansa ko a cikin kanta, ta ji su a lokacin da ya fade su kuma ta barsu a wajen, babu abinda ta dauko sai ciwo da kuma takaicin rasa shi da tayi ta wannan hanyar a raywarta, ta shirya dama, ta shirya barinsa don haka ta dade tana ywa zuciyar tata tanadi na wasu abubuwa da zasu dauke hankalinta bayan ta bar cikin rayuwarsu, amma da hakan ya faru a lokacin da bata shirya ba sai ya dake ta da tsananin tashin hankalin da bata ƙara ganin wani abu da ya tsorata ta ba bayan hakan ba.
Ko sanda ya danna kan motar suka tafi suka daki bishyar nan, bata ji tana tsoron mutuwa kamar tashin hankalin cewa an riga bude ainihin kammaninta a idanunsa ba.
Da kuma sanda ta kalli idanun su Baffa, Baba Usman, Ishaq, abokin Ma'ruf mai suna Faruq da kuma Abdurrahim... Ta kalli idanunsu ne tana jin zuciyar fayau yayin da tunaninta yake wasai, don tunda zuciyarta ta karɓi tashin hankalin wajen Ma'aruf bata tunanin kuma akwai wani abu a duniyar nan da zuciyar tata zata sake rusunna masa, hatta Baffan kuwa, hatta shi din da ya zame mata tsani kuma hanya wajen aikata dukkan abinda ta wanzar a rayuwarta.
Tana kallon kowa ne kawai tana kuma jin abinda suke cewa, amma yadda bata furtawa Ma'aruf ko da kalma guda ba, haka babu abinda tace har wayewar garin yau, abu daya kawai take so ta yarda dashi shine cewar ba zata yi biyu babu ba, ba zata rasa Ma'aruf ta kunyata a idon duniya a rana guda ba sannan kuma ta rasa burin rayuwarta ba, ba zata taɓa iyawa ba, ba zata yarda an zo gaɓar da zata je ƙasa ba kamar yadda ta shar'antawa kanta a baya ba, har yanzu tana da yardar cewar damarta bata ƙare ba, dole ne ta fidda kanta kamar yadda ta sa ba.
Dan sandan yace bata da kowa a yanzu,ta yarda, ta yarda da hakan... Don tun da ta rasa yardar Ma'aruf ta sani cewa ko yardar Æ´aÆ´an ta ba zata samu a yanzu ba, don haka ta yarda zata barsu, zata bar kowa nata sannan zata bar kowa da ta sani, abinda bata yarda ba shine da yace bata da komai, wannan ne zuciyarta bata amsa masa ba don ita ta san tana da abinda zata kare kanta ko a gaban wane alkali ne a duniyar nan.
Amma ba za'a kai nan ba ma, ba zata je gaban kowanne alkalin ba, zata yi nisane da kowa, zata yi nisa zuwa wani waje da zata kafa sabuwar rayuwarta, sabuwar rayuwar da ta san a cikin lokacin da zai ja mata... Dole ne yayanta zasu dawo gare ta, dole ne watarana zasu juyo su waiwaye ta, don meye yake raba ya'ya da uwarsu a duniyar nan?!
Sai kawai ta mika hannunta mai lafiyar ta janyo file din dake gaban ɗan sanda, ya dago ya bita da kallo fuskarsa na shaida mamaki da kuma tunanin abinda take shirin yi, ta ajiye file din sannan ta sake mika hannunta alamun ya bata biron da yake rike dashi, sakan daya, biyu... Kamar ba zai bata ba sai kuma kawai ya mika ma tan, bayan ta karba yana kallon yadda yatsunta dama rubutun da take yi ke rawa, rawar dake shaida rikicewar da yanayinta ke ɓoyewa.
Lambobi ne, lambobi ta rubuta guda goma wanda ba sai ya tambaya ba ya san lambar asusun banki ne (account number), ta ajiye biron akan file din sannan ta sake turo masa shi gabansa.
Idonsa ya kalli lambobin sannan ya dago ya sake kallonta, a lokacin ne kuma tayi magana ta faÉ—i abinda ba ga É—ansandan ba kadai, har ga ita kanta ya tabbatar mata da cewar har yanzu tana nan a matsayin Kilishinta.... Tanan bata canja ba!
"Akwai kudi sama da miliyan dari huÉ—u a cikin account din nan, ka taimake ni in fita daga wannan wajen, ka taimake ni inyi nisa daga dukkan wadannan matsalolin dake rubuce a cikin file dinka, ni kuma nayi alkawarin zan baka rabin kudin da nake dashi, zan gyara rayuwarka ta yadda har ka koma ga ubangijinka ba zaka taba sanin É—acin Babu ba!"
Ta kai karshe a lokacin da idanun É—an sandan ke kallonta da wani irin yanayi mai wuyar fassara a lokaci guda!
***
A cikin ɗakin asibitin ba ka jin komai sai ƙarar kaɗawar iskar Acn da ya kaure ko'ina.
Hajiya Mardiyya ta girgiza kanta riƙe da wayar dake kare a kunnenta kafin tace.
"Kar ku damu Khadija, ki bawa su Innan ma hakuri, tahowarmu ba zata wuce gobe zuwa jibi ba insha Allah, ni ban san haka wannan asibitin yake ba da muka dauko ta wancan na gwamnatin muka kawo ta nan, su bamu refferal kawai abu na neman gagara... Ashraf dai yace yayi magana da likitan dazu, ni ko bai yarda ba zan dauko ta ne kawai mu dawo ba zan jira ba."
Ta gyada kanta sannan ta sake cewa.
"Eh, Ahmad ne ya taho yau, da asuba ya kira ni yace Babansu yace yazo ya kawo min saƙo... Amma shi kadai ya taho banda sauran."
Wadda suke wayar a ciki ta amsa kafin ta ta lashe wayar tana ajiye ta a gefen bedside drawer dake kusa da gadon, kusa da gadon da Rukayya ke kwance idanunta a rufe.
Kusan awa guda kenan da ta samu bacci, awa guda bayan ta farka da tarin surutan da a ciki basa iya gane komai sai sunan Hamida ƴarta da kuma Hajiyan Sudan da take ambata, Ashraf yace zai iya yiwuwa shine abu na ƙarshe da ta dinga fada lokacin da hatsarin ya faru, ta ga Hajiyan Sudan din a wancan asibitin na farko da suka je dauko Rukyya, ita bata ganta ba kuma bata bari ta ganta din ba, babu kowa a wajenta kafafunta na karye duka biyun an nade su da bandeji an kuma dage su zuwa sama.
Tana ji wata Nurse na faÉ—an cewar har yanzu ba'a sami wani danuwanta da zai zo ya biya kudin treatment da akayi mata ba... Bata ce komai ba suka biya kudin Rukayyan kawai suka karbi sallama suka juyo.
Don abu na karshe da zata yi a rashin hankalinta shine ta nuna wata mu'amala tsakaninta da Hajiyan Sudan ɗin a gaban Ashraf, ta sani kashinta ne zai bushe idan har mijinta ya san da hakan... Ya san abinda ta tura Rukayyan yi a Niger kuma tare da ƙawarta. Don haka bata ce komai ba har suka bar asibitin suka kawo ta wannan.
To a yanzu Ashraf din ya dame ta da tambayar wacece Hajiyan Sudan din da Rukayyan ke kira, ta gaya masa cewa itama bata san ta ba amma kallon da yayi mata bayan ta gaya masa hakan ta san ba na yarda bane.
Ta sake kallon Rukayyan, ciwonta da sauki ba kamar yadda suka zata a farko ba, mild stroke ne mutuwar barin jiki wanda likitoci suka tabbatar masu da cewar ba zai dauki lokaci ba zata warke ta koma daidai idan har za'a bi dokin da da kuma kaidojin da suka dace... Ita ta sani dama, ta san Allah ba zai jarraba su ta wannan hanyar ba, kyawun yarta haÉ—e kuma kyawun jikinta wani abu ne da ba zai nakasa ba.
Don haka hankalinta ya dan kwanta ta yadda bata hango komai sai komawarsu Nigeria don su cigaba da jinyarta acan ba tare da asirinta ya tonu ba.
Lokaci ya nuna karfe biyu daidai yana tuna mata da sallar azahar din da bata yi ba, don haka ta mike ta shiga toilet din dakin ta dauro alwala sannan ta shimfida slaya a gefen gadon ta tayar, zuciyarta cike da fatan kafin idarwar tata, Ashraf ya dawo tare da Ahmad din da yaje daukowa daga airpot.
Ai kuwa sai fatan nata ya karbu don a sallamar raka'a ta karshe su ma suka yi sallama suka shigo dakin.
Ta amsamusu a lokaci guda da ta fahimci rashin fara'ar dake kwance akan fuskarsu... Ahmad din ne ke gaishe ta yayin da Ashraf ya samu kujera ya zauna fuskarsa na numa tsananin bacin ran da ta dade rabon da ta ganshi a fuskarsa.
"Me ya faru? Wani abu ne ya faru kuma?"
Ta tambaya tana kallon dukkanninsu... Kuma Ahmad din dake gabanta bai ce komai ba sai kawai yasa hannu ya ciro wata takarda daga aljihunsa ya dora akan sallayar da take kai.
"Sakon da Daddy yace in kawo miki ne."
A lokaci guda zuciyarta ta buga a kirjinta, bata san meye a cikn takardar ba, bama tayi tunanin menene din ba, amma daga yanayin fuskokin yayan nata kadai ta san ba abu ne wanda zata so shi ba, dn hak ta yankewa kanta nisan taraddadin, ta mika hannunta a hankali wanda ke rawa ta dauki takardar, kuma tun kafin ta kai ga buÉ—e ta, taji kwalla ta na neman cika idanunta yayin da kwakwalar ke gaya mata cewa ita ta riga ta karbi sakon tun kafin ma ya iso.
A rubuce a ciki, Hajiya Nafisa ta tadda kalaman da sune abu na karshe da kunnen kowacce mace zai so yaji su daga sautin mutumin da take raba rayuwarta tare dashi!
***
_Ƙaddarar dake jiran labarin nan a gaba ya danganta ga amsar da Hajiya Kilishi zata samu daga bakin ɗansandan nan...._
_Me kuke tunani?..._
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/22/22, 19:33 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*25*
_They tell you to be grateful for what you have, but you are also allowed to be sad for what you have lost..._
~~~~~
*Bayan watanni Shida.*
**
*Kano.*
*Central Prison.*
*03:00pm*
Ruwan ya cigaba da dukan rufin dakin da wani irin ƙarfi fiye da kodayaushe. Karar tsawa da ake yi lokaci-lokaci tana cika iska da sautin da duk karfinsa baya disashe tarin surutun daje cikin dakin, tarin surutun dakin kurkukun wanda yake cike da fuskokin mata kala-kala. Manya -manya da yara farare da bakake, dattojai da yanmata wanda kowanne a cikinsu yake cigaba da rayuwarsa daidai kamar babu wanda yake da digon koda memory guda na wani abu daga bayan dogwayen katangar da suka zagaye su, kamar nan din shine mafari kuma farkon rayuwarsu, kamar basu san akwai wata duniya dake wanzuwa bayan su ba.
Rayuwa bata da adalci, bata dashi ko kadan, wannan shine abinda Kilishi je maimaitawa a cikin kanta da fitowar kowacce rana da kuma faduwarta. Ta yarda rayuwa bata da adalci don babu abinda ke saka ta tsayawa, komai girmansa kuma komai kankantarsa ba abinda ke tsaida ita kamar dai ruwan daje zuba a yanzu, abubuwa suna cigaba da tafiya ne ba tare da wani ma yaje ko kusa da wajen da zai ji labarinka ba.
Damina ta dade da tsayawa ta yadda kusan kullum ake kwara ruwan dake daukar awanni, kuma a duk lokutan da ruwan ke sauka, Kilishi na samun waje ne dab da wata yar karamar taga dake can sama ta zauna, ta zauna tana kallon tasirin zubar ruwan da kuma nauyinsa da take ji a zuciyarta, tana ayyanawa kanta cewa hawayenta ne wannan ke zuba, don irin kukan da ya kamata tayi kenan tunda a kirjinta dama idanunta babu danshi ko kadan balle ayi tunanin hawaye.
Ta kan so ayi ruwan lokacin da suke fita waje don ta zauna a cikinsa ya sauka a jikinta, ya sauka akan fuskarsa ta yadda zata ji sosai kamar hawayen nata... Idanunta a tsaye kyam suna shsida kamannin da ta sani cewa ba nata bane, ba itace wannan Kilishin da tayi wata rayuwa da zata rantse da ubangijin da ya halicce ta babu wata mace a cikin kurkukun nan da tayi makamanciyarta.
Ba itace wannan Kilishin dake samun komai a zama daya da zuciya da kuma kwakwalarta ke sama mata mafita ba, sannan ba itace wannan Kilishin da ta shafe tsawon shekaru wajen gwagwarmayar samawa karshen rayuwarta tare da yayanta wata daddadar rayuwa da bata ko misaltawa ba.
A yanzu ita wata sabuwar halitta ce kawai, wata sabuwar halitta da ta rasa kowa kuma ta rasa komai, amma kuma zuciyarta ta kasa yarda ta karbi hakan, don idan ma zata yarda tana tunanin ya kamata ace ko da rabin mutanen duniya su jajanta mata, amma ba wai rayuwa ta cigaba da tafiya tamkar babu wani abu da ya faru ba.
_A tuhume ta akan kisan ɗana kawai yallaɓai..._
Tun da aka fara wannan tashin hankalin, wannan maganar ta Baffa ita kadai ce abinda ya fitar da hawaye daga idanunta bayan maganganun Ma'aruf, yace a ture dukkan wasu laifukanta a gefe, a tuhume ta kisan Jamal kawai wanda ta san yayi haka ne don ya tanadar mata wani abun daban.
Ko a lokacin da aminiyarta Salamatu ta baiyana a gabanta da tare da yanuwanta game da zancen raba ta da dan ta tsawon shekaru bata ji wsni abu sosai ba,don me take tunanin? Awwalu zai cigaba da lullube duk wani sirri nata da ya sani ne? Bakin cikinta daya ne ma da ya zamana akace Salanatun taga É—an nata, wani abu da duk da mamakin da ya bata sai da taji ciwonsa har cikin kirjinta.
Salamatu bata taba taya ta mugunta ko guda daya ba,hasali ma ta kan kushe mata wasu idan ta kawo su, amma duk da haka tare suka faro tafiyar tana gaya mata dukkan sirrinta da kuma abinda take ciki don haka ko yaya ne yaci ace itama ta karbi nata kamashon bakin cikin, ba'ace ita da Awwalun dai sune kadai zasu dandani zafin shari'ah ba.
A lokacin da dansandan nan yaki karbar tayin kudin da tayi masa, a lokacin da ya kalli nambobin da ta rubuta ya dago ya sake kallonta sannan ya girgiza kansa, a lokacin wata wuta ta kunno a cikin kirjinta, wata wuta dake zafi tana kona duk wani ragowar emotion da take dashi tana kuma kara zafin kunci dake cikin zuciyarta wanda karara yake nuna mata cewa da gaske ne tata ta kare babu wata sauran mafita kuma.
Daga wannan lokacin ta koma kamar wata gunki da aka sassaka ko kuma karfen dake motsi kawai, numfashi kawai take tana kallon tarin mutanen dake zuwa koyaushe wajen mata tambayoyin da bata ko fahimtarsu, ciki har da Æ´an jaridar da tayi zaton zasu watsa labarin nata zuwa kusufa-kusfar da zai sa duniya ta tsaya wajen jimanta mata, amma kamar yadda tace rayuwa bata da adalci, ba abinda ya faru!
Bata yi magana da kowa ba sai da akaje kotun sannan ta amsa dukkan tambayoyin alksli kai tsaye babu wani musantawa ko kuma kokwanto, tana bayar da amsar tana kallon idanunsu Baffa, Baba Usman, Ishaq, Abdurrahim da kuma tarin wadu yanuwanta da acikinsu har da mahaifin Amina, Alhaji Sulaiman.
To don me ba zata amsa ba, ai ba su kawo wanda zasu daure ta da jijiyoyin ta a jikinta ba, basu kawo wanda da yana wajen ta sani bakinta ba zai taba budewa ta amsa laifukan da aka zaiyano a cikin kunnensa ba... Ma'aruf!
Ya sani, ya san komai, ya san komai din da ya zamana ta san baya cikin haiyacinsa ma a lokacin, amma duk da haka da ace yana wajen, yana cikin kotun nan a lokacin da ake sauraren shari'ar, zata rantse da ubangijin da ya halicce ta cewa ko alkalin zai ce a kwantar da ita ana yankar naman jikinta ɗai-ɗai da ɗai-ɗai, ba zata taɓa iya amsa wadannan laifukan a gaban idon Ma'aruf ba.
Amma har Baffa tana kallonsa ne kawai tana amsawa tare da tunanin abinda zai ji amma ba wai ita ba, har aka gama shari'ar aka yanke mata hukucin shekaru goma sha takwas bata jin ko da wucewar sakan guda taji nauyin wani daga vikin mutanen dake wajen nan.
A yanzu ma ƴaƴan ta kawai take tunawa, tana jin yadda rashin ganinsu ke ɓangarar da wani abu a cikin zuciyarta, yanuwanta da yawa sun zo, musamman wadanda take yiwa alkhairi, wasu ma bata ko fita ganinsu saboda bata ga abinda hakan zai tsinana mata ba.
Don haka a yanzu rashin ganin yayan nata shine abu mafi tashin hankali da take fuskanta bata ko lissafin shekarun da zata kwashe a cikin wajen nan,don gani take kamar an fade su ne a kotun nan kawai, kamar an fade su ne kuma an rubuta amma baza su kasance a gaske ba... Gani take kamar zata iya fita, kamar idan ta yunƙura zata samu hanyoyin da zata fitar da kanta.
Amma matsalar shine har yanzu zuciyar tata ta kasa fahimtar komai a wajen na balle har ta fara tunanin hanyoyinta, Baffa yana kassarata da wucewar kowanne lokaci a duniyar nan wajen hana ta ganin fuskokin Æ´aÆ´an ta, ita Kilishi ce, mai zurfin tunani da hangen nesa, shi yasa a lokacin da yace a ture dukkan wani laifi a hukunta ta akan abu daya kawai ta zubar da hawayenta.
Shi mijinta ne, ta san halinsa tsawon shekaru,ta san yadda yake iya hukunta mai laifin dake hannunsa cikin salama ba tare da kowa ya sani va, hukuncinsa mai sanyi wanda zai daskarar da jinin jikinka hankali kwance yadda duk ihunka babu wanda ya isa ya ji ka, shi yasa yake da kai zuciya nesa a komai na rayuwarsa, da wuya kaga ransa ya baci akan wani abu don idan har ya bacin to shi kansa ya sani cewa hukuncin da zaiyi daban ne,ta san wannan... ta san wannan tun a shekarun farko data aure shi.
Shi yasa zuciyarta take rabewa da kowanne motsawar lokaci idan ta tuna hakan, idan ta tuna yadda rayuwar kowa ke cigaba da tafiya babu ita kuma kamar ba'ayi ta din ba, don yanuwanta sun gaya mata cewa har sake gini anyi a gidan an rushe bangarenta.
Mamakin yadda rayuwa ke juyawa dan adam baya a lokaci guda shi ke dada cinye ta, kamar badu saba ba, kamar ba itace mai yarje mata komai ba, kamar ma bata santa ba, ace komai ya ƙare a lokaci guda? Komai din da zai hada har da ya'yanta, banda wannan tarin dukiyar da ta shafe shekaru tana ajiyarta, shi yasa a kullum take fada tana karawa rayuwa bata da adalci, bata dashi ko kankani....
Tana zaune ne kawai a yanzu ba tare da wata mafita ba, abu biyu kawai take hasashe shine watakila idan har ta mike da ƙarfinta da kuma dabararta ba lallai ne ta kai wannan shekarun da aka gindaya mata a kotu ba, amma kuma matsalar shine bata da karfin, a kullum kuma a kowanne wayewar farin Allah Baffa yana kara kassarata ne da hukuncinsa na hana ta ganin yayanta... Shi yasa duk yadda ta kai ga ture wani tunani a zuciyarta tana ji kamar zata yarda dashi akan cewa.
Karshen tika tika dole TIK ne! Dole ne ta yarda cewa komai ya kare mata, kuma dole nrme ta yarda da abinda Ishaq ya kalli cikin idanunta ya fada mata a ranar da za'a kawo ta gidan nan...
*'Wata shari'ar sai a lahira Mami...!'*
Rugugin tsawar da ake yi ya cika iska a lokacin, walkiya ta haska tar ta kuma haskawa a cikin duhun hadarin, sai kawai ta sake ɗaga idanunta tana kallon zubar ruwan ta cikin tagar ɗakin, ta cikin hayaniya da kuma dararrakin mutanen dakin, kuma ba tare da tayi zato ba a lokacin wata guntuwar ƙwalla ta cika idanunta tana gangarowa kan fuskarta, wannan shine karo na uku da taji dumin hawaye a kan fatarta, kuma wannan lokacin shine karo na farko da tambayar da taƙi bari ta yiwa kanta tun a zamanin farko ta ɗarsu a cikin zuciyarta... Wannan tambayar da take gujewa, tambayar da bata taɓa lissafa ta ba balle ta yi tunanin matsayinta na Kilishi zai kai ta ga yinta....
Ta yaya zata mayar da rayuwarta baya shekaru goma da suka wuce?
Dana sani....! Yau Kilishi ce da dana sani!
Dana sani a lokacin da komai ya kure!
Dana sani irin wadda kowanne musulmi ke gudu a duniyar nan!
Dana sani tun ta duniya kafin a je ga ranar da ƙafafunta zasu durƙushe a gaban ubangijin da shaidan ya janye hannunta ga barin umarninsa!
Abinda Kilishi bata sani ba ma shine kamar yadda Ishaq ya faÉ—a ne... Wata shari'ar sai a lahira!
Hakki yana rama kansa ne cikin halaye biyu... Tun a duniyar da kuma lahirar dake jiran kowanne bawa!
Zata karbi abinda yake nata a yanzu, kuma zata karbi abinda yake nata a can, ga rayuwar kurkukun da bata fara ganin komai a cikin ta. Gata nan... ita É—in ce dai Kilishin da take ce, da lafiyarta da karfinta har ma da tunaninta da komai da take takama dashi, kuma a cikin duniyar da take ganin ita da ita aminan juna ne ta kowacce hanya, sai gashi tasirin wasu katangogi kaÉ—ai!
Tasirinsu kaÉ—ai ya hana mata dukkan abinda take takama dashi da kuma iyawarta, tasirin shari'ar duniyar kaÉ—ai, ba ma akai ga mutuwa ba, balle kwanciyar kabari ko kuma tashi a gaban Mahaliccin da ta bijirewa da dukkan iyawarta!
***
*Kano.*
*Mai Æ´aÆ´a Street, Bawo Road.*
*04:30pm.*
_So here we stand in our secret place_
_Where the sound of the crowd is so far away_
_You take my hand, and it fees like home_
_We both understand, it's where we belong..._
An dauke ruwan, amma har yanzu garin da danshi, iskar da take kadawa mai sanyi ce, Zainab tana jinta akan fatar ta da kuma wuyanta yayin da mai kwalliyar dake gabanta ke ta aikinta na fente fuskarta, sassanyar wakar qmwestlife ta queen of my heart kuma na tashi daga cikin Mp3 din studion...
"Kiki, miko min brown liner nan..."
Mai yin kwalliyar ta fadawa wata yarinyarta dake gefe, Zainab ta bude idanunta bayan Aysha ta juya karbar liner, idonta ya gane mata wata ita din daban a cikin mudubin dake kallonta, wata kyakkyawa mai kama da ita din da da take ganin kamar ba ita ba, powder da aka saka da komai ta bi fatar jikinta tsaf ta kwanta tana fito da kowanne tsini da lankwasar sa, musamman hancinta da taga ya ƙara tsawo fiye da yadda da ta sanshi, ga kwsllin da ya fito da idanunta tar yana shaida hasken ƙwayar cikinsu.
Gabanta ya fadi ya kuma faduwa hannunta yayi nauyi yayin da surutun da yan mata biyun dake bayansu ya cika kunnenta, ds kuma muryar Ameerah dake waya can gida akan a kawo mata takalminta da ta manta.
Can gida, can gida yana nufin gidan Hajiya Salamatu mahaifiyar Jawad da kusan komai na harkar bikin da ake yi yake hannunta da kuma yanuwanta.
Watanni shida kenan da Jawad ya same ta a cikin tashar nan, watanni shida kenan da rayuwarta ta canja, don tun daga wannan lokacin tun daga wannan ranar abubuwa suka fara sauki a rayuwarta, Jawad ya mayar da ita har gida can wajen yanuwan mahaifiyarta, inda baya nan aka sha artabu tare da mijin mahaifiyarta akan cewar ya barta ta ɓata, babu wanda ya nuna masa cewa tana can hatta dansa kuwa Nura, sai da hankalinsa ya tashi ya fita daga haiyacinsa bakiɗaya ya tabbatar ana shirin kaishi kotu sannan yazo ya bada hakuri.
A lokacin ya san tana wajensu, kuma ga mamakin kowa sai ya faÉ—i maganganu san ransa sannan ya tashi ya tafi. Kuma tun daga lokacin tun daga lokacin da hankali sa ya fara kwanciya, sannan Jawad din ya koma Abuja ya dawo bayan wasu kwanaki, sai ya zama babu abinda ake yi sai maganar bikinsu wanda ba'a samu wata matsala da yan'uwan mahaifiyar tata ba wajen amincewa.
Kuma sai bayan nan ne sannan ya shaida mata dukkan abinda ke faruwa a tasa rayuwar, abinda ke faruwa tun a lokacin da ya ɗauko ta daga Abujan nan game da rikicewar rayuwarsa da kuma yadda Allah taimake shi ya samu mahaifiyarsa a cikin ƙanƙanin lokaci, dama babban abin manakin na cewar tsawon rayuwar tasa da ya shafe tun daga yarinta a gidan yayan mahaifinsa yayi ta ba wai a wani waje da yake bare ba.
Ta daÉ—e tana mamakin kasancewar hakan, sai dai duk mamakinta bai kai na yadda har a lokacin Jawad ya dage akan aurenta ba, don har a cikin yanuwanta daga mazan har matan waÉ—anda basu furta cewa tayi sa'a ba kadan ne...
Ita kanta ta sani, ta san hakan ne kawai suna tuna mata ne da irin sa'ar da tayi, shi yasa bata da wa ta cewa a dukkanin abinda ake yi, don ta sani bata da wani gata a yanzu idan ba Jawad ba, ko su yanuwan nata da suke faram-faram da ita don na doki ne da kuma tausayawa rashin mahaifiyarta da tayi da kuma wahalar da ta sha a hannun mijin mahaifiyar tata, sannan bayan haka ma ta sani cewa da yawa suna mutunta ne kawai saboda ganin Jawad É—in.
A can garin nasu aka daura auren, yanuwansa da yawa sun je har dasu Hajiya Mardiyya daga can Abuja da kuma dangin sabuwar mahaifiyar tasa, don haka fadar tarin mutanen da ta gani ranar daurin auren nan, wani abu ne da ba ita kadai ba har dangin nata sunyi mamaki... Kuma a ranar ta sha kuka kamar me tayi kukan rashin mahaifiyarta sannan tayi kukan farin cikin da bata san irin yadda zata fallasa adadinsa a kirjinta ba, Tayi hamdala ta godewa Allah fiye da yadda zata iya kirgawa a lissafinta.
Bayan haka kuma tayi kukan fargaba na irin rayuwar da zata je ta tarar a gaba, don ta sani a yadda zata shiga rayuwar Jawad bata da komai kuma bata da iyaye tsayayyyu dole ne ta fuskanci wasu abubuwan daga mutanen dake kewaye dashi wanda na lallai suyi mata dadi ba... don ko a ranar daurin auren nan ta raina kansa a cikin kowanne bangare na yanuwansa sau dubu tana sakewa...
Kuma a wannan ranar ne aka basu ita suka taho Kano yayin tare da wasu yanuwan nata yayin da su Hajiya Mardiyya duka wuce Abuja. Sun taho tare da kuma tarin kayan da su Jawad É—in suka kai wanda har a yanzu bata mayar da hankalinta wajen ganinsu ba kasancewar yadda aka dinga rububin kallon kayan a can garin nasu.
Kuma bayan sun zo ne suka tarad da gagarumin bikin da mahaifiyarsa ke shiryawa wadanda ta ga kamar sun fi karfin tunaninta, don kusan komai an gama shirya shi hatta kayan da zata sa an gama dinka su, sai bayan da tazo aka gwada aka ga wajen da yayi mata yawa sannan aka mayar aka daÉ—a gyara su.
Kallon komai kawai take tana kuma kallon kowa tare da ita da yanuwan nata da suka zo kawai, an hada ta da wata yarinya Ameerah da kusan ita ke jan ragamar komai nata, ita ta gaya mata dukkan shirye-shiryen da suke yi na cewar za'ayi walimar iyaye ne (mother's eve) a yau washegari da safe kuma za'ayi budar kai tare da yini sannan jibi zasu tafi can Abuja tare da Jawad din su kuma tari nasu Hajiya Mardiyya da suke shiryawa suma kafin a dangana ta da sabon gidan da ya kama kusa da wajen aikinsa.
Sai a lokacin da taji hakan ne sannan wani sabon kukan ya sake cike kirjinta, ta sani yanuwan mahaifiyar tata sunyi nasu kokarin, don da karo-karo da kuma gudumawa kala-kala aka hada mata kudi dubu hamsin bayan sadakinta da aka kawo na dubu hamsin din shima da cewar ta siya wasu kayan amfanin idan taje gidanta, ko da kayan kitchen ne aƙalla ta dinga kallon wani abu da yake nata tunda sun sani cewa Jawad ya riga ya dauke musu komai yace zaiyi komai din ba sai sun wahalar da kansu ba.
Amma duk da haka a yanzu da tazo ta ganta a cikin tarin yanuwansa tana jin nauyin da zuciyarta ke ƙara yi da tunanin kowa yana yi mata wani kallo ne daban na cewar an kawo ta ba tare da komai ba kuma a yamzun ne masu niyya zasu kafa mata kahon zukarsu.
Idan Jawad da mahaifiyar tasa dake ta fara'a tana nan-nan da ita suna sonta kuma basa ganin aibunta, hakan baya mufin zadu iya rufe idon kowa daga ganin hakan. Don haka tun da suka zo a É—arare kawai take, idan wani yana yi mata magana hannayenta har rawa suke, gani take kamar zasu daka mata tsawa ne kawai ta tashi ta fara aiki ba wai itace wadda suka taru dominta ba. Daga ita har yanuwan nata kuwa tunda dama itace karfin gwiwarsu a wajen, tunda suka fahimci a tsorace take shikenan su ma basu da ta cewa sai abinda akace.
A yanzu ta baro su ne acan gidan da cewar za'a tafi dasu wajen Partyn da idan an gama yi mata kwalliyar zata je ta same su acan. Ameeran tace mata Jawad ne zai zo ya ɗauke ta idan an gama. Jawad din da tun a can garinsu ranar ɗaurin auren nan bata ƙara ganinsa ba kasancewar tunda suka zo gidan a cike yake da mata fal don haka bata ma san a ina yake ba.
"Rufe idonki..."
Mai kwalliyar ta fada tana dawo da ita daga tunaninta. Ta kuwa rufe idon zuciyarta na kiyasta adadin kudin da aka kadhe a wajen mai kwalliyar kada banda kayan dake cikin wani akwati dasu Ameeran suka taho dashi.
Ƙasa da minti talatin bayan hakan mai kwalliyar nan ta gama fente fuskarta a yanayin da ita kanta da rufe mata ido kawai akayi aka bude zata rantse cewa ba ita bace, Ameerah tare da sauran ƴanmatan nan biyu suka taimaka mata ta zura doguwar rigar wani hadadden material kalar ja mai haske ta kasa, kalar ta dace sosai da kalar fatarta da take wani abu tsakanin fari da kuma brown, daga nan aka shiga daura gwaggwaron da bata san minti nawa aka shafe ana dora hawansa ba.
Lokacin da aka gama tsoro ne ya kamata sosai ganin kanta da tayi a mudubi, wani abu ya wuce ya sake wucewa a wuyanta lokacin da su Ameerah ke ta fadin Masha Allah suna daukar ta a wayoyinsu, ta kasa dauke idanunta daga mudubi koda na sakwan guda, ji take kamar ta tattaro dukkan mutanen da suka santa a hargitsenta don su taya ta shaida cewa ba itace wadda idanunta ke ganin mata ba.
"Ashe dai Yaya J ya san me idonsa ya gano masa."
Ameerah ta faÉ—a tana saka ta murmushin da bata shirya masa ba. Dun dade a wajen, har akayi wa su Amirah tasu kwalliyar sannan mai wajen tayi ta É—aukarta a hoto itama sannan wayar Amirahn tayi kara da sakon Jawad na cewar sun iso wajen, fabanta na dukan tara-tara su Amirah suka taimaka mata suka fita waje Bayan ta yafa wani mayafi shima kalar ja mai shara-shara.
**
"Eh munzo É—auko su yanzu, yanzu zamu taho."
Jawad ya fada a cikin wayar da yake yi bayan ya fito dafa cikin motarsa da ta tsaya a kofar wani gida da akace shine gidan mai kwalliyar dasu Zaunab suka zo. A yanzu haka ma da mahaifiyar tasa Hajiya Salamatun yake waya, da kyar yake jinta a cikin tarin kidan dake can wajen bikin inda kusan duka danginta ne gabaÉ—aya ta tara, yanuwansa na Abuja kaÉ—an ne a wajen, kusan maza ne ma kadai don su ma suna can Abujan da shirin yin nasu bikin da zarar sun koma.
Ya roke su, ya roki kowa a cikinsu Hajiya Salamatun dama Maaman (Hajiya Mardiyya) akan ba sai sun shirya wani gagarumin taro ba idan aka daura aure kawai aka bashi matarsa zai fi kowa jin dadi amma babu wanda ya yarda dashina cikinsu, kowacce tace tana da yanuwanta da dole ne su sani cewa tana bikin É—a, don haka a dole su suka ja tsawon watannin har aka kai yanzu wata na shida kafin komai ya tabbata.
Ya fahimci kishin dake tsakaninsu tun daga ranar da suka koma Abuja shi da Hajiya Salamatu da kuma wasu yanuwanta bayan dawowarsa daga wajen Zainab bayan kuma sun mika case din ƙawar Hajiya Sakamatun da tayi sanadin komai wadda yaji suna kira da Kilishi, wani suna da yayi kama da orin wanda ya kan jina bakin Rukayya lokutan baya, sai dai bai rike komai ba sunan yana da alaka ne da zancen tsohon mijinta da baya son ji a lokacin.
Kuma a yanzun ma bai matsa ba ko kadan, ya san dai Hajiya Salamatun ta gaya masa cewa tuni matar dama tana gaban hukuma sanda suka kai ƙarar, abinda ya sani kenan kawai har su saka ranar da ta maida su farin Abuja, zuwa cikin gidan da a ranar da ya fita ya barshi ko kadan baiyi tunanin dawowarsa a kusa ba, yana hango wucewar shekaru ne wanda kafin nan watakila ziciyar tasa ta iya hucewa game da abinda ya faru.
Sai gashi ya dawo a tsakanin lokacin da hannu ma zai iya kirga shi, ya dawo tare da wani abu da ya É—aure tunanin kowa a gidan, don ba Hajiya Mardiyya kaÉ—ai ba, kusan duka al'ummar gidan a gigice suka taho bangaren mahaifin nasu jin labarin cewa Hajiya Salamatun da suka sani tsohuwar matar Kawu Ibrahim yadda kowa ke kiransa itace mahaifiyarsa.
Babu wanda bai santa ba, daga matan gidan har wasu da suka manyanta a cikin Æ´aÆ´an gidan, kawai zumuncin ya lalace ne tun da ya dade da rabuwa da ita tun kafin rasuwarsa kuma ya auri wasu matan bayan ita sannan kuma dadin dadawa babu zuria a tsakaninsu.
Tun daga wannan lokacin labari ya gama zagaye danginsu gabaÉ—aya, kuma maimaikon a samu shiri tsakanin Hajiya Salamatu da kuma Mardiyya sai wsni abu kamar kishi ya shiga tsakaninsu don kowacce tana ganin tana da nata ikon akansa.
Ko lokacin da suka tafi Yakura dukkaninsu sun je amma kowa da nasa tawagar ne. Ko yanzu Alhaji Bashir ya saka baki cewa su Hajiya Mardiyya su zo nan Kanon, ma ta dage cewa itama uwa ce don haka ita ya kamata azo a samu. Sai kowa ya rabu dasu a hakan, Alhaji Bashir ya gaya masa cewa lokaci ne amma komai zai daidaita a hankali.
"Ka kira su kuwa? Time yana ta tafiya..."
Haro dake tsaye a gefensa ya faÉ—a, kuma kafin ya amsa sai ga kiran Hajiya Mardiyya ya shigo, ba shiri yayi murmushi yana girgiza kansa kafin ya bawa Haro amsa.
"Na kira Ameeran, tace gasu nan fitowa.."
Haro yayi murmushi yana kokarin gyara hular kansa sannan yace.
"Ai sai ka gaya min in gyara Malam."
"Haro, na gaya maka yarinyar nan ba kalar ka bace, yes tana da wayewa amma ba irin taka ba."
Haron ya juyo ya kalle shi, bayan ya kalli sauran abokan nasu ya tabbatar hankalinsu baya kansu.
"To ni an gaya maka mai irin wayewata nake nema? For real? Kana tunanin kai ka samo mai nutsuwa shikenan ni bani da hankali zan auri yaran titi ne? Malam idan zaka bani support kawai gwara ma kayi..."
Kafin ya bashi amsa wani kiran Hajiya Mardiyyan ya shigo sai kawai ya ƙara a kunnensa da murmushi yana faɗin.
"Maamah wallahi jibi zamu taho..."
Daga cikin wayar Hajiya Mardiyya ta kyalkyale da dariya alamun farin cikin da take ciki kafin tace.
"Na sani Babana, kira nayi in gaya maka cewa na aika an sake ɗauko wasu daga cikin yanuwanta don ance min mutum goma sha biyar ne kawai anan, sunyi kaɗan ita kanta yarinyar tana buƙatar yanuwanta..."
Murmushi ya sake yi yana cije lebbensa don ya san tayi hakan ne kawai saboda Hajiya Salamatu... Daga haka ta cigaba da bashi labarin shiryen-shiryen da suke yi wanda a ciki baya hango komai sai tarin gajiyar da shi dama Zainab É—in zasu fuskanta, Kawai babu yadda zai yi ne yce da waninsu ya fasa.
A cikin saurarenta da yake yi, yaji muryar Haro yana fadin.
"Here goes my chance..."
( Ga dama ta nan...)
Don haka yayi saurin juyowa a lokaci guda da idonsa ya nuna masa wata tsantsareriyar halittar da tayi kama da Zainab din dske amsa sunan tasa a yanzu...
Watakila ya fara yarda da idear shirye-shiryen bikin nan....
**
Lokacin da su Zainab suka fito ƙofar gidan, daga can gaba kadan suka hango motoci guda biyu da suka tsaya yayin da mutanen ciki ke tsaitsaye a waje suna jiransu, Jawad na tsaye daga tsakiyarsu yana waya, idonta ya sauka akansa lokaci guda da numfashinta ya tsaya a kirjinta yana sawa ta manta da nata kyan da tayi gaba ɗaya.
Brown shadda ce a jikinsa da kuma dark brown hula, yayi kyau ya gyara fuskarsa sannan tsawonsa ya sake fitowa, sai ta kasa yarda, ta kasa yarda cewa wai a yanzu matsayinta da nasa ya zarta na yadda ta san shi, a yanzu shi din mijinta ne, mijinta shine wanda ya rufe idonsa daga kowa da kuma komai ya zabe ta a cikin tarin mutanen duniyar nan alhali bata da kowa kuma bata da komai.
Sai kawai kwallar da bata shirya mata ba ta cika idanunta tana gangarowa kan fuskarta, yayin da sauran mutanen dake kewayensu suka shiga maganganun da ko kadan ba jinsu take ba, shi din kawai take kallo kamar tana son nemo dalilin sa na aurenta akan fuskarsa, kamar tana so taga wani abu da rayuwa ta tauye masa har ƙaddara ta hukunta shi da aurenta alhali yana da tarin dama a duniyar nan.
"Idan kika cigaba da tsayawa kina kallonsa haka, zan tafi in maye gurbinki yanzun nan..."
Ameerah ta raÉ—a a kunnenta daga gefe, wani murmushin da bata shiryaemwa ba ya sake sauka a bakin ta, ta juyo tana kallonta idanunta cike taf da hawaye, sai kawai ta gyada mata kai tace.
"Alhmdlilah ake cewa..."
Ta gyada nata kan itama sannan a hankali bakinta ya furta kalmar.
"Alhmdlilah."
"Ai gasu nan sun fito ma, Masha Allah..."
Muryar É—aya daga cikin abokan Jawad É—in tasa su juyowa daidai lokacin da Jawad din shima ya juyo har a lokacin wayar kare a kunnensa.
Idanunsu suka hadu waje guda kuma maimakon taga mamakin rashin gane tan da take zato a fuskarsa, sai kawai yayi wani murmushi mai fadi yana cigaba da kallonta, murmushin da ya mamaye fuskarsa gabaɗaya yana sa nata lebben talewa itama har a lokacin da ragowar ƙwallar dake cikin idanunta.
"Alhmdlilah..!"
Bakinta ya sake furtawa a lokacin da kafafunsa ke tahowa gabanta, idanunta kuma na hango mata wata kyakkyawar dake jiranta a gaba...
Tabbas Rayuwa me adalci ce... Bata saka alkhairi da mugunta!
***
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/22/22, 19:33 - Ummi Tandama😇: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*26 (Final Chapter)*
_Madly is the way I love you, forever is how long it will be...!_
~~~~~
Mintina goma da dauke ruwan, aka kwsnkwasa kofar gidan, Rukayya dake jingine akan doguwar kujerar falon ta kalli gefe inda Æ´ar aikinsu ke zaune tana kallon Tvn dake aiki a É—akin, ganin bata nan ya dan bata mamaki don ko kadan bata ji lokacin da ta tashi ba.
"Jummai..."
Muryarta ta kira ta a hankali tana ƙoƙarin gyara zamanta, sai dai da alama Jumman tayi nisa a cikin gidan da ba lallai ne ta jiyo ta ba, ƙarar doorbell din ta sake cika dakin, sai kawai ta mika hannunta a hankali ta jawo ƙarfen da take rikewa wajen tashi da kuma tafiya dashi, hannyenta da har yanzu ke rawa suka damke jikinsa a hankali kafi ta tattara dukkan ƙarfinta akai ta iya mikewa.
Ta mike daidai lokacin da Jumman ta dawo tana fadin.
"Hajiya gani nan, koma kiyi zamanki.."
Ta koma din a hankali ta zauna yayin da Jumman tayi gaba ta bude kofar, kuma da yake kujerar da take zaune itace daidai saitin kofar, sai ya zamana Jumman na buɗewa hoton ƙaninta Ashraf ya shiga idanunta a lokaci gyda da gabanta ya fadi zuciyarta ta buga a kirjinta, ba wai ganinsa ne ya haddasa hakan ba...
Don kusan kullum yana zuwa duba du ita da mahaifiyar tasu tunda suka tare a gidan, kusan koyaushe ya tashi daga aiki nan yake faraboyowa kafin ya wuce gidan nasa, don haka yanyin fuskarsa a yanzun shine ya tsorata ta, wani yanayi ne da rabon da ta ga irinsa a tare dashi tun a lokacin farkon ciwonta, sanda suna Niger kafin ma ayi transfering dinta zuwa asibitin da tayi kusan jinyar watanni biyu a cikinsa anan Nigeria, lokacin da ta farka ta tarar da sakon dashi da kuma Ahmad suka kawo na saki tsakanin iyayen nasu.
Wani abu da tunda ya faru daga su Ashraf din har ƴanuwansu suke ta fafutukar neman yayi hakuri ya mayar da Hajiya Nafisan amma duk yadda akayi, duk kokarinsu baya sauraren kowa yace ya riga ya yanke hukuncinsa, tunda har zata iya rufe idanunta akan saɓon Allah ta kuma tura ƴarta har wata ƙasa wajen neman magani don biyewa bukatun duniya, to tabbas bai ga amfanin zamansa da ita ba.
Ita kanta Rukkayan sau É—aya yaje ya duba ta a asibiti, a ranar a gaban Hajiya Nafisan ya bata hakurin kuskurensa ma cewar bai bata uwa ta gari ba a matsayinta na Æ´arsa sannan yayi fatan cewa abinda ya faru zai zama izna gare daga yanzu wajen gane tarin laifukan da ita kanta tare kuma da mahaifiyar tata suka taya ta aikatawa.
Sannan ya gaya mata cewa ta dawo wajensa da zama duk ranar da aka sallame ta tunda duk wata dawainiya da tsadar asibitin ma shi yake biya amma bayan an sallane tan, sai wannan tausayin da ubangijinke halittawa tsakanin ya'ya da iyayensu musamman ma Uwa... Ya hana ta juya baya ta koma wajen mahaifin nata.
Ashraf ne ya kama musu wannan gidan acan hanyar Tarauni suje zaune, kuma anan mahaifiyar tata tayi jinyarta tare da yanuwanta dake yawan zuwa akai-akai suna taya su kwana, a yanzu ta sami sauki sosai har tana miƙewa tsaye kuma maganarta ma ta fara fitowa sosai.
Sai dai har yanzu bata koma Rukkayyan da take a da ba, bata koma wannan kyakkyawar Rukayyan dake ji da kyan da take ganin ta hanyarsa zata iya samun komai a duniyar nan... Komai din da bai hada da Ma'aruf ba, wanda hakan sho ya rude ta wajen biuewa kowacce irin shawara da mahaifiyarta tata da ƙawarta Hajiyar Sudan suka kawo, tunda ko a karon farko ta sani cewa da ƙyar ta same shi a rayuwarta.
An kawo Hameeda kusan sau uku tazo ta duba ta daga can gidansu Ma'aruf din da a yanzu Baffa ya aiko an shaida musu karara cewa yarinya ta dawo hannunsu tunda su suka kawo ta da kansu amma lokaci bayan lokaci za'a dinga kawo ta suna ganinta, kuma itama yarinyar ko kadan bata nuna tana sha'awar zama ba musamman ganinsu a wani sabon gidan ba inda ta saba ganinsu ba.
Sannan kamar kusan kowa, sun ji labarin abinda ya faru a gidan su Ma'aruf game da Hajiya Kilishi, tayi mamaki amma ba wani sosai ba don tun lokacin da ta zauna a gidan dama ba wani shiri suka yi sosai ba, don haka ta yarda duk abinda aka fada din zata aikata. musamman da su ma suke ji da tasu matsalar sai basu wani daukaki abin sosai ba.
Ashraf ya shigo a lokacin da wannan yanayin na fuskarsa, yanayin da ba ita kadai ba hatta Jamilan da ta buÉ—e masa kofa a hankali ta rufe sannan ta juyo ta fita daga falon tana basu waje.
"Sannun da zuwa, ya aikin?"
Rukkayan ta faÉ—a a hankali tana kallonsa bayan ya ajiye jakar hannunsa.
"Alhmdlilah, bata nan?"
Ta san wa yake nema don haka ta girgiza kanta.
"Tana wanka yanzu zata fito..."
Ta fada sai kuma ta sake cewa.
"Me ya faru?"
Don zuciyarta ta kasa tsayawa waje guda da tunanin abinda ya farun, shima kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya mika hannu ya bude zip din briefcase din da ya shigo da it, hannun nasa ya zaro wani envelope da a lokaci guda ya sa zuciyart bugawa, yaba tuna mata da emwanda ta gani na karshe a hannunsa shi da Ahmad, na sakin mahaifiyar tasu.... Yanzu kuma me ya faru?
"Daddy ne zai yi aure Rukyya,ga kayin daurin auren nan, sati mai zuwa...!"
Ya fadi hakan daodai lokacin da Hajiya Nafisa ta shogo falon, sakon kuwa ya shiga kunnenta yana sa zuciyarta nugawa ta kuma tarwatse a kirjinta!
Rukayya ta hadiye abinda bata san sunansa ba a makogwaronta, shikenan! Kamar ita Mahaifiyarta tayi biyu babu akan mutum guda, ta rasa mahaifinsu ta sake rasa shi kamae yadda itama ta rasa Ma'aruf sau biyu a tata rayuwar... Da gaske Daddy yake kenan, da gaske ba zai mayar da ita gidanta ba...
Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce ka kiyayi zuciyar mai hakuri lokaci aka kaishi karshe.... Mahaifinsu mutum ne mai tsananin hakuri da kuma kawar da kai akan tarin abubuwa, shi yasa tun farko mahaifiyar tasu ta samu sake yin abubuwa da yawa da taga dama... Tunda sau da yawa ma zasu yi abu har su gama bai ma sani ba balle ya hana, baya takura musu baya takura mata, ko lokacin da tayi aure har biyu bayan Ma'aruf, yanuwansa sai da suka nuna bacin ransu na ganin bata wani dadewa take sake fitowa amma shi bai ce komai ba, bai yi mata ko ƙorafi ba ba balle faɗa.
Idan kayi laifin da zaka bashi hakuri ma wani lokacin ba ma sai ka furta ba, alamun niyyar ka kaɗai kan sa ya yafe ma tun kafin ma kace wani abu... Don haka ba ita kadai ba, tabbas kowa ma ya sani cewa da gaske mahaifiyarsu ta kai shi ƙarshen da ba lallai ne ya dawo ba.
A lokaci guda wata kwalla mai dumi ta gangaro kan kumatunta, tana tuna mata da tarin lokutan da suke cikin jin dadi da fantamawa son ransu... Rayuwa bata da adalci...
"Rukayya.."
Ashraf din ya sake kiran sunanta yana sska ta ɗagowa a lokacin da Hajiya Nafisa ta karaso cikin falon ta dauki envelope din katin daurin auren tana dubawa, ta a duba sunan wata mai sa'ar da rayuwa ta zaɓo ta wajen bata kyakkyawar damar da ita tayi rikon sagegeduwa da ita.
"Naga anyi posting daurin auren Jawad a facebook, kin sani?"
Kalaman suka tsayar da tunani dama numfashin Rukayya cak a lokaci guda... Taba jin wani abu na yawo a cikin kanta da bata san menene ba, jiri ya debe ta daga inda take zaune, kanta ya zagaya ya sake zagayawa a cikin ɗakin kafin idanunta su dawo dashi kan Ashraf dake kallonta har a lokacin, sai kawai ta girgiza kanta da ƙarfi a yanzu kwallar dake fitowa daga kowanne idonta tana tarwatsewa a iska...
Tabbas Rayuwa bata da adalci! Musamman ga mata irinta wanda basu da hankalin fahimtar cewa duk kwaɓewar al'amari, namiji yana da damar tsame kansa ya bar macen a cikin rauninta wanda ba zai iya kaita ga matsayin wasu damar dashi zai samu ba...
Zai barta a cikin ƙuncin da zata zauna tana maimaita kalaman Rayuwa bata da adalci!
***
*Abuja.*
*New Horizon Street, Wuse 2.*
*05:30pm.*
Iska ta kaɗa farin labulen ƙaton windon dake manne da wani ƙaton falo, wanda yake a saman benen gidan. Tagogin windon gabaɗaya a bude suke, an wangale su ta kowanne gefe yayin da sassanyar iskar daminar da ake yi ke kada labulayen dake jikinsa kalar ruwan toka, kalar da ta dace da kusan komai na cikin falon da yake da sassaukan ado, (Grey &ash) sai kuma tsilla-tsillan abubuwan da suke kalar baki kamar sauran kayan electronics.
Mintuna basu fi goma kenan ba da ɗauke ruwan samn da aka fi kusan awa guda ana zabga shi, don haka garin a lulluɓe yake da duhun hadari da kuma na yamma wanda a lokacin ƙarfe biyar da rabi ne.... Koina a jike yake sharkaf dauke da danshin dake komawa sanyi-sanyi yayin da bishiyun dake harabar wajen ke ta rangaji a cikin iskar na jin dadin yanayin da kuma jikewarsu.
Falon dogo ne wanda a can ƙarshensa ya hade da wajen dining da kuma kitchen duk a ciki, iri ɗaya sak da tsarin gidajen turawa kamar yadda akayi ginin a haka tun daga waje.
Akwai matattakalar bene daga gefe wadda akayi kusan rabi na jikinta da gilashi fari kamar yadda mafiya abubuwa suke a gidan, matattakalar zata kai ka zuwa sama inda anan zaka tarar da kofofin manya-manyan dakuna guda uku masu dauke da hadddun toilets da kuma walk-in wardrobes...
A watannin farko da suka zo gidan, Amina zata rantse ta shafe fiye da wata guda kafin ta gam sanin komai na gidan ta kuma saba da tsananin kyawunsa da take gani. Har faduwa ta taba yi har kasa watarana data yi alwala ta fito daga toilet saboda tsabar santsin marbles din dake gidan wanda ko mai ta shafa a a kafarta tana jin kamar zata zame.
Watansa hudu kenan a ciki, amma komai yana nan da kyallinsa kamar sabo, hatta kayan kitchen wanda su tafi komai tabawa a gidan balle kuma sauran dakunan da ta kan yi kwanaki biyu ma bata leka ba. Hatta doguwar kujerar falon da Ma'aruf kullum yake kwanciya akai bata taba nuna alamun nauyinsa na nunawa ba, ko kuma tace nauyinsu tare...
Daga cikin falon, Amina na tsaye a jikin sink din dake tsakanin drawers na kitchen din, ta kunna fanfon tana wanke wani farin kwano data dauko yayin da sassanyar iskar daminar ke shigowa tana kada Æ´an kananan gashinta da suka taso sama saboda laushinsa, babu dankwali akan nata sai gashinta da ta daure da wani yalon ribbon, rabon da ta taje shi ma kusan kwanaki biyu kenan.
Rigar jikinta wata loose T-shirt ce ta maza fara kal wadda bata fi rabin cinyoyinta ba, ta tattare duka hannayen rigar zuwa gwiwar hannunta yayin da maɓallan sama ma bata gama rufe su ba.
Ta juyo daga jikin sink din ta dawo kan worktable din dake tsakiyar wajen, ta shiga yanka albasar kanana a cikin wani farin kwano... A lokacin ne wayarta tayi ƙara daga can kan Centre table din dake tsakiyar kujerun falo, da saurita ajiye wukar kafafunta suka dauk ta zuwa can, siraran tafin kafar nata na bi ta kan santsin marbles din dake wajen har ta sauka zuwa falon wada ya danyi kasa da matattakala biyu kawai.
Ƙafarta ta shiga cikin tattausan carpet din da yake kalar grey, kamar kullum yatsun kafarta suka lume ciki kafin ta kara wayar a kunnenta da murmushin da ko mutumin bai tambaya ba zai canki waye mai kiran.
"Amma... Barka da yamma."
Ta fada da murmushi bayan sallama. Daga É—aya bangaren, Amma tayi nata murmushin itama tana kokarin dauke kwanon dambunta da Hamida ke kokarin dauka sannan ta amsa.
"Barkanmu dai, kun yini lafiya?"
Amina ta gyada kanta.
"Alhmdlilah Amma lafiya kalau."
"Ya jikin naki? Ya nasa jikin shima?"
Ta cije lebbenta tana zama akan hannun kujerar dake gefenta, wata iska mai ƙarfi ta shiga kaɗa ta tana ratsa ƴar rigar jikinta tana shiga koina.
"Alhmdlilah Amma dukkanmu da sauki, da sauki sosai."
"Ga Hamida nan an kawo ta yau tazo zata hana ni cin abinci..."
Cewar Amman tana sawa fara'ar dake fuskar Amina ta karu a lokaci guda.
"Hamida tazo?"
"Ɗazun nan da safe aka kawo ta, Abdurrahim ne yace zuwa goben zai zo ya dauke su gabaɗaya har dasu Maryam su zo taren ku. Dambun shinkafa muka yi yau, shine ta hana kwanon kowa saƙat! Yanzu suka gama ci tare da Adam ta dawo kan nawa kuma n tsoro nake kar yayi mata yawa ya bata mata ciki, tunda har a rama Babanku yasa aka saka.'"
Amina tayi dariya.
"Ni ban san yaushe ta koyi haka ba, da fa idan bata san abu ba bata ci kwata-kwata..."
"Hajiya ma haka tace, ranar da suka yi Amala a gidan wai da kyar aka samu ma ta dandana, amma yanzu gashi mu ban t kasa ko zama."
Daga cikin wayar tana jiyo maganganun Hamidan tana fadin a bata da kuma na Hafsa tana cewa ta É—auko plate su ake zubowa tare."
Amina tace.
"Allah Amma nima raina ya biya tun daga nan, dambun nan naki daban ne ai, a gas kina yi ko a mangal?"
Amma tace.
"A mangal ne, Babanku kuma kafin ya fita da safe cewa yayi wai yafi son naki wanda kike hadawa da rama... Shine na bawa Adam ya siyo muka saka kar ya dawo ya sake min gori."
Amina ta bude bakinta kadan tana dariya.
"Baya ci sosai fa idan nayi, Amma kin manta har cewa yayi baya son tsaminta..."
Kafin Amman ta amsa daga cikin wayar Muryar Maryam dake shirin fita daga É—akin tayi magana da karfi tace.
"Missing É—inki yake yi kawai..."
Amma tace.
"Ai nima naga alama, don ko da safe da zai fita sai da ya sake tambaya yau din zaku taho kuwa.."
Kwalla ta cika idanun Amina a take yayin da murmushin ta ya ƙaru.
"Ni tawa kewar tafi taku Amma, ni kadai na san abinda naji a cikin watannin nan."
Ta fadi abinda ya canja akalar hirar tasu a lokaci guda. A lokaci guda da Amma ta gyara wayar a kunnenta sosai kafin ta tambaya.
"Wannan duk ya wuce yanzu Amina, tunda ga dawowar nan tazo, abinda kawai nake so ki bani tabbaci shine kin tabbata dai babu wata matsala har yanxu ko? Ya gama jin sauki gabaÉ—aya?"
Wani abu ya zarce wuyanta a lokaci guda... Yaji sauki? Ma'aruf yaji sauki? Tana da tabbacci?
Tambayoyin da har take yiwa kanta kenan a kullum wayewar garin Allah tunda ya gaya mata cewa da gaske É—in yu zasu koma, don ba sai wani ya gaya mata ba ta sani, duk abinda yazo ya faru a gaba, duk abinda yazo ya same shi zata karbi alhakin hakan ne ko da kuwa duniyar gabaÉ—aya zasu goya mata baya don kare ta.
Watanni hudu kenan da dawowarsu garin Abuja, bayan watanni biyu na zaman jinyar Ma'aruf a asibiti da kuma faruwar wasu tarin al'amura masu ɗaga hankalin da babu wani a cikinsu da ya taɓa sanin irinsa.
Ciwon Ma'aruf yayi tasirin da a karon farko likitocin ke zaton cewa ya rasa hankalinsa bakiɗaya, don kusan mutum uku ne suka sa hannu akan cewar Bipolar diorder dake damunsa ta kai mataki na ƙarshe wato 'Mania'.
Sai da aka samu banbancin ra'ayi a wajen mutune guda biyu sannan Baffa ya bada umarni aka fita dashi zuwa asibitin da yake ganin likita acan London, da Ishaq da kuma Baba Usman su suka kai shi, don har a lokacin hankalin Baffa ya kasu gidaje da yawa, wajen fuskantar tarin shari'ar da ake yi akan Hajiya Kilishi sakamakon wasu laifukan nata da ake ƙara ganowa a hankali ciki har da aminiyarta da take zarginta da raba ta da ɗan cikinta da tayi tsawon shekaru.
Zancen ya sake ta da hankalin kowa a sanda suka ji shi... Don yanuwan nata da ƙarfinsu suka zo da kuma tarin hujjojin da suka sa dole aka hada dasu a cikin shari'ar... Wanda bayan hakan ne, likitocin dake kula da Ma'aruf acan suka yi nasu ƙoƙarin wajen dawo dashi cikin hayyacinsa, sai dai da sharadin cewa dole ne ya samu aƙalla watanni uku a wani waje da hankalinsa zai kwanta ba tare da tashin hankali da kuma yawan ganin mutane ba... Wani waje da zai bashi nutsuwar zuciya da kuma kwanciyar hankalin da zai manta da dukkan matsalolin da ya fuskanta yaji sunyi masa nisa har zuwa lokacin da kwakwalwarsa zata daidaita.
Don haka tun kafin su dawo Ishaq yasa suka kama hayar wannan gidan a cikin garin Abuja, wata kawatacciyar unguwa da kusan tsarinta da komai na kasar turai ne, don tun daga ranar da suka zo Amina ta sani cewa ba kowa ne a duniya yake samun damar rayuwar a irin waÉ—annan wajajen ba.
Da farko ta sha wahala wajen fuskantar tarin abubuwa daga sabon Ma'aruf É—in da a kullum take ganinsa a haka, baya magana baya cin abinci, baya komai sai sallah shima sai idan lokacinta yayi kenan, kuma tsakaninta dashi abu biyu ne kawai zai amsa maganarta da Eh ko A'a, sannan idan zasu kwanta zai rungume ta a jikinsa zuwa safe.
Baya cewa komai baya bata labari, baya mata ƙorafi, baya tambayar kowa baya tambayar aikinsa, ko Hamida bai taba tambaya ba, ita kaɗai ɗin kawai da ya gani tare dashi ita kadai yake kallo yana binta da eh ko a'a idan tayi masa magana, daga baya har tunani tayi itama din kamar bata da amfani a tare dashi, don haka sai ta samu rana guda ta gwada tafiya daya dakin tayi kwanciyarta don ta gani idan har zai kula bata nan ya neme ta.
Fatanta kuwa ya karbu don bata ko kai ga yin bacci ba taji motsin bude kofar dakin, da murmushi a bakinta lokacin da ya hawo gadon ya rufe ta a jikinsa ba tare da yace komai ba, ta dago da kanta tana kallonsa ta cikin dan siririn hasken É—akin dake shigowa daga windo na fitilar waje, idanunsa a lumshe suke yana kallonta dasu kamar a rufe.
_"I'm sorry BabyDoll..."_
Muryarsa ta fito a hankali da sautinsa wanda a lokacin idan zata kirga, bai fi cikin hannunta taji shi ba tun bayan zuwansu gidan, ta kalle shi kusa na wucewar minti guda tana auna daÉ—i da zuciyarta ta shiga kafin a hankali bakinta ya sake talewa da wank murmushin sannan ba tare da ta sake cewa wani abu ba ta kwantar da kanta a saman kirjinsa kawai yana kara rungume ta.
Kuma tun daga wannan ranar, sai abubuwa suka fara yin sauki, ya zama yana magana daya biyu har ma ya tambaye ta wani abu, idan ta kunna T.v baya kashewa, sannan sau biyu a ranakun da yaga bata jin dadi kuma an kwana biyu likitar dake zuwa duba ta bata ba zo yace mata ta dauki wayarsa ta kira ta kasancewar duk lambobin mutanen da zasu nema idan suna bukatar wani abu a wayar tasa Ishaq ya ajiye lambarsu.
Lambobin mutum biyu ma kaɗai tafi kira, daga mai canja musu ruwan dispenser sai mai zuwa ya siyo duk kayan abincin da take bukata, kuma a baya yawanci lokacin da zasu zo din, yana jinta dasu a ƙofa ba zai taɓa tasowa ba... Sau ɗaya ya taba ido ya kalli mai yin cefenen da ya taya ta shigo da ledojin kayan da ya siyo ciki... Amma a yanzu shi da kansa yaje bude musu kofa ya karbi duk abinda suka kawo.
Bayan haka da ta fahimci ya fara sakewa, sai ta fara bashi labarai a hankali a hankali, yan kananan labaran da baza su ja hankalinsa da yawa ba wadanda ke magana akan hakuri da kuma karbar kaddara, ba karara take fito da hakan ba, ko kadan ma bata amfani da kalaman da zasu fito da manufarta, labarin ne kawai zai zo a sigar dashi zai fahimci hakan, kuma da ta kula ya fara tunani na fahimtar abinda take nufi, sai ta kirkiro wani aikin ta tashi ta bashi waje don ya kara fahimtar abinda take nufi É—in.
Sannan ta dinga kokarin binsa jam'in sallah, tana gani ya tayar zata yi saurin yin alwala tazo ta bi bayansa.... Tayi tarin abubuwan da ta san ko taya ya ne zasu iya tsayar da hankalinsa waje guda ya samu ya dawo wannan Ma'aruf din da ta sani, wannan Ma'aruf din da tazo ta tarar dashi cikin kyakkyawar rayuwarsa.
Jinya ce irin tata tayi ta, tayi da jikinta da kuma zuciyarta,tayi dukkan kokarin da zata yi da dabararta da kuma wasu daga cikin shawarwarin Amma har ma da Ishaq wanda a rashin É—anuwan nasa sai ya zama ita yake kira a kullum yaji cigaban lafiyarsa.
Har sai da ta kai Baffa da bakinsa watarana da suka yi waya ya bata shawarar cewa ta dinga saka lemon tsami a ruwan É—umi ta samu yasha kafin ya kwanta, yace mata hakan ba karamin abu bane dake wanke zuciyar É—an Adam...
Hajiya Maimuna kuwa tasa Munaya ta rubuto mata tarin addu'o'in wasu kuma tayi recording da muryarta tana tofawa a cikin ruwan shan sa, wani lokacin har ma da kayan da zai saka kafin ya fito daga wanka. Samirah ma ta sha kiran waya ta gaya mata abincin da ta san yana so tun asali wadanda idan anyi ransa ke jin dadi.
Kowa ya taimaka, kowa ya taimaka da iya abinda zai iya duk kuwa da halin da har yanzu zuciyioyinsu ke ciki, musamman su Samiran ƴaƴan Hajiya Kilishin da ko a idanunsu, baƙo zai shaida damuwar da suke cikinta har yanzu, amma har su Salma dake gudajensu suna kira su ji lafiyarsa.
Don haka duk da ta sani cewa ba da iya taimakonta kadai suka karaso matakin da Ma'aruf din yake a yanzu ba, matakin da take ganin kusan bashi da maraba da warkewarsa gabaÉ—aya, duk da haka tana jin zata É—auki alhakin duk abinda zai biyo baya idan har aka samu wani akasi ga me e da lafiyar tasa.
Kowa yayi kewarsa a gidan nan, tarin kewar da take ganin kamar shine ruhin gidan nasu gabaÉ—aya, don irin murnar data ji daga kowa a gidan a ranar da shi da kansa ya dauki waya ya kira su, wani abu ne da mizaninta ya kasa aunawa.
Tana tsaye daga baya bata ko jin me suke cewa, da amsoshinsa kadai take ayyana tarin murnar da har ƙwalla sai da ta saka ta, sai ta juya masa baya tana sharewa da tafin hannunta yayin da zuciyarta da ma duk wani abu mai hankali a cikin kanta ke ƙara tasbihi ga jalla wata'ala da ya takaita wahalarsa da ma tasu bakiɗaya, don ko daga gidansu Amma tace kowa yayi kwanan farin ciki musamman ma Baba wanda ya matsu ya ga dawowarta.
Bayan hakan Ma'aruf da kansa ya yanke ranar da zasu koma Kanon bayan tarin abubuwan da suka ƙara gamsar da ita warkewarsa, don a yanzu har da Faruk suna waya game da harkokin kamfaninsu, yana gaya masa iri tsarin sababbin securities dn da Abdurrahim ke sakawa a kowanne bangare na kamfanin ta yadda babu wani mai wayon da ya isa ko yaga kaya ma idan za'a fitar dasu daga kamfanin balle kuma kuɗi.
A yanzu haka ma kusan sati guda baya yini a gidan yana can fafutukar rufe asibitinsa MMB-6 da cewar zai mayar dashi can hida Kano inda shi da kansa zai dinga jagorantar komai... A yanzu kusan an gama komai ma kokarin samun masu siyan ginin kawai ake yi... Kuma sai ya zama fitar ma ta kara taimaka masa wajen sake warwarewa don ta sani akwai tarin abubuwan da a zaman gidan kadai zasu cigaba da tuno masa da Kilishi da kuma dukkanin abinda ya faru, amma bai taɓa maganarta ba tunda ya farka, ko da Baffa ko kuma da Baba Usman ɗin da suke waya a kullum.
Sannan bayan tahowarsu Munaya ta gaya mata cewa cikin abinda bai fi sati hudu ba wata guda n canja tsarin gidan bakiɗaya, Baffa ya saka an rushe bangaren Hajiya Kilishi, an haɗe gidan baki ɗaya a waje ɗaya kuma ta kofa guda saboda su Samirah dama dukkanin al'ummar gidan da tabbas ganin ɓangaren nata zai dinga tuna musu da ita a kodayaushe.
Don ko a lokacin da yayi general meeting tun kafin tahowarsu, ba ga ƴan gidan kadai ba har da sauran yanuwa na da kuma na Hajiya Maimuna akan abubuwan da suka faru, yayi ta jaddada cewa dole ne kowa ya cire ta daga cikin zuciyarta saboda trin laifuka da kuma cutarwar duk da cewa an ɓoye wasu da yawa saboda Inna Danejo dake fama da rikicewar tsufa tun daga wannan daren da al'amarin ya faru.
A zahiri yanzu rayuwa ta fara komawa daidai, abubuwa suna tafiya kusan a daidai ga kowa don Baffa yana iya bakin kokarinsa wajen ganin ya daidaita rayuwar tasu ta koma kamar da, amma a cikin zuciyoyin kowa Amina ta sani cewa dole akwai wannnan digon bakin ciki da ba zai taba gogewa ba musaman ga su Samirah Æ´aÆ´anta, wanda ko sau daya Baffa bai bari sunje sun ganta a can kurkukun da aka daure ta ba...
Munaya tace mata wasu daga cikin yanuwansa sunyi kokarin tausar sa akan hakan, amma babu wanda ya san cewa yayi nasa fushin sai a lokacin, don Ishaq ya kira ya zauna a gabansu sannan yace ya zama shaida zai yi shari'a da duk wanda ya ƙara kawo masa magana makamanciyar wannan. Shikenan! Sai zancen ya mutu ko su Samirah basu kara yunkurin hakan ba.
Gobe itace ranar da Ma'aruf ya yanke shawarar komawarsu, bata sani ba ma idan ya gama da zancen asibitin nan, amma ya tabbatar mata cewar zasu koma gida don tun jiya shi da Ishaq suka gama tsara komai, don haka itama tun a jiyan da kuma yau da safe ta gama shirya dukanin kayansu, akwati guda uku ne sai kuma wata jakar dake É—auke da yan kanan tarkacenta, ta tattare komai nasu hatta kayan da zasu saka ta fito dasu, na jikinsu idan sun cire ne kawai zata sama musu waje.
Kuma bata san me yasa ba haka kurum tun jiyan take jin wani iri don haka a yanzu da Amman tayi mata wannan tambayar sai kawai ta sake jin jikinta ya mutu, ta haɗiye yawu a maƙogwaronta kafin ta gyada kanta a hankali.
"Insha Allah Amma ba abinda zai faru, yaji sauki da gaske, kuma idan mun dawo ɗin ma zai ƙara tafiya can asibitin da ake duba shi kafin ma ya koma aiki insha Allah."
Daga cikin wayar, Amma ta yi tata ajiyar zuciyar a hankali.
"Shikenan, Allah ya kawo ku lafiya, Allah ya ƙara sauki. Maganar da nake son mu yi akan yadda zamanki zai cigaba a gidan nan ne... Na gaya miki Kilishi ba itace matsalarki ta ƙarshe a duniya ba, zama yau da gobe tare da kowa a duniyar nan dole yana bukatar hakuri don watarana ma baka san lokacin da zaka batawa wani ba, kina gani ko sanda kina nan a tsakaninku yanuwa ma kuna samun sabani balle kuma a gidan surukai.
Don haka dole ne ki cigaba da yin taka tsan-tsan wajen kyautatawa kowannensu da kuma É—auke kai akan abinda bai shafe ki ba, wadannan abubuwan guda biyu Amina sune abinda mata da yawa suke kuskurensu shi yasa ba ga surukansu kadai ba har a wajen miji suna samun matsala, idan kin dawo zamu sake yin magana insha Allah."
Amina ta gyaÉ—a kanta alamun ta fahimta ta kuma rike kamar dukkan sauran maganganun mahaifiyar tata kafin ta amsa.
"insha'Allah Amma, insha Allah."
"Kice muna gaishe shi, sai goben idan zaku taho kya kira mu."
"Toh zai ji insha Allah."
Har Amman na shirin katse wayar tayi saurin sake magana.
"Maryam tana kusa dake? Zan tambaye ta wani abu ne..."
"A'a bata nan amma ga Adam nan, bari ya kai mata."
"Toh Allah ya bamu alkhairi."
Amman ta amsa kafin ta mika wayar a hannun Adam dake zaune yana game a wayar Aminu, ya mike da sauri zuwa tsakar gida inda Maryam É—in ke kitchen tana sake zubawa su Hafsa da suka tsira mata idanu abinci tana faÉ—in kar su shigar mata daki su bata mata.
Ta karɓi wayar bayan hakan sannan suka shiga tasu hirar akan wasu ɗinkunan kaya da ta barwa Maryam ɗin ta kai mata kafin tafiyarsu, ɗinkunan da take sa ran su zata yi amfani dasu a bikin Munaya da Ishaq wanda aka saka rana watanni biyu masu zuwa... Watakila lokacin da zata haihu da kwanaki kaɗan. Ko can gidan a yanzu shirye-shiryen kawai da ake yi kenan, shine babban abinda ke dan dauke hankalinsu daga al'amarin da ya faru, musamnan su Samirah da Munsyan ke gaya mata cewa suma sun kara sakewa sosai a yanzu.
Aminu ya shigo kafin su ƙarasa eayar da Maryam, yana shirin fita zuwa wajen aikinsa da ya cigaba da zuwa sakamakon saukin da kafarsa tayi. ya karɓi wayar daga hannun Maryam suka shiga tasu hirar kamar kodayaushe yana gaya mata cewa ya cika akwati na uku ya buɗe na huɗu da kayan Baby.
***
Daga kan matattakalar benen dake saukowa cikin falon gidan, Ma'aruf ya sauko, kafafunsa na biyo matattakalar a hankali yayin da yanayin hasken falon ke shaida masa yanayin tafiyar da lokaci yayi don har ya kammala shiryawa da komai bai kalli agogo ba tunda wayarsa ma a falon ya barta tun jiya.
Iskar dake faman kadawa a falon kasancewar bude windows da akayi ta shoga kada shi kotawanne ɓangare yayin da idonsa ya sauka akan Amina dake tsaye daga can wajen kitchen tana zuba fulawa a cikin wani kwano.
Numfashinsa ya tsaya a kirjinsa a lokaci guda ganin kayan daje jikinta, rigarsa ce... Wata loose T-shirt dinsa da yawanci idan zaiyi ball yake saka ta... Fara ce ƙal, ta tattare dogwayen hannunta zuwa can sama, kanta babu dankwali yayin da girman cikinta ya fito sosai a saman rigar... Kafafunta, wadannan siraran kafafun nata da a yanzu suka kumbura ƙaɗan suna yawo ta kasan dan karamin wandon da ta saka wanda bai kai gwiwa ba.
Ba wai yau ya fara ganinta da irin wannan shigar ba, kusan kullum ne, amma kusan kullum din sai zuciyarsa ta cika da wani irin abu mara misaltuwar da yake ganin kamar idan ya kira shi da sunan farin ciki kaÉ—ai bai yi masa adalci ba... a lissafinsa itace duniyarsa a yanzu, ita kadai ce wani abu da har cikin ransa yake ganinta a cikin rayuwarsa a matsayin wani abu da yake so har cikin zuciyarsa ba wani abu da ya karba a matsayin maye gurbi ko kuma don babu yadda zai yi ba.
Yana sonta ta sani, yana sonta saboda kyawawan halayenta, yana sonta saboda kyautatawar ta, sannan yana sonta saboda taimakonta wanda a kullum a kodayaushe yake ƙara ganinsa... Musamman a yanzu da yake ganin wata irin kulawarta wadda duk yadda zuciyarsa ke da tauri a yanzu kai tsaye take wucewa tana taɓowa har can ƙarshe.
Kuma bai san me yasa ba lokacin da al'amarin ya faru, lokacin da komai ya faru, bai sani ba idan wani a cikin yanuwansa ko ma Hajiya Maimuna sun kalle ta da wani tunani, amma shi bai ko tuna ba sai daga baya, bai tuna ma cewa ta shigo rayuwarsa ne ta hanayar matar da a yanzu bai san a wane irin mizani zuciyarsa ke tunaninta ba. Idan ya kalle ta kawai a kullum kuma a kowanne hali baya tuna komai sai cewa itace waje mafi girman da yake samun nutsuwar zuciya.
Lokacin da ta juya dauko wani jug din ruwa a gefe, lokacin idonta ya kai kansa, ta kalle shi a lokaci guda da murmushi ta subuce a fuskarta.
"Wani yasha bacci yau..."
Ta fada a lokacin da ya karasa saukowa daga kan stairs din, ta cire hannunta daga cikin fulawar ta ware su tana murmushi sannan ta ƙaraso da sauri ta rungume shi, ta rungume shi sosai ta yadda har sai da kafafunta suka ɗaga daga kasa kamar ƴar ƙaramar yarinya.
"You miss me this much?"
(Kinyi missing dina har haka?)
Muryarsa ta fito a hankali dab da kunnenta, sai ta dawo baya a hankali tana sauka akan kafafunta sannan tace.
"Nayi missing dinka fiye da haka Sugar.."
Yayi murmushin da fuskarsa tayi mata kyau yana kokarin cije lebbensa.
"Really? Kamar yaya kenan?"
"Kamar cikin malala gashin tinkiya..."
Ta fada tana kama kuncinsa kamar karamin yawo.
Dariyar da yayi ta jefa kansa zuwa baya.
"I can't beleive kina hada ni da tinkiya Babygim.."
Yadda ya fadi abin ya saka ta dariya itama kafin tace.
"Kawai fa salon magana ne, ni na isa nace maka haka, you are the most adorable person to me a duniyar nan yanzu Sugar."
"Mhmmm, Baki ce masha Allah ba..."
Ya fada yana daga gira guda. Ta sake yin wata dariyar sosai kafin tace.
"Dama ana cewa maza Masha Allah ne?"
"Su ba mutane bane?"
Sai ta cije nata lebben yanzu har yanzu daya hannunta akan kafadarsa daya kuma tana rike da gefen fuskarsa kafin tace.
"Idan mazan suna so a gaya musu, su fara fadawa matan tukunna, especially in sun yi kwalliya ba wani dogon turanci ba..."
"Ni ai ba sai na fada ba Babydoll, saboda ni mijinki ne, nawa hanyoyin daban suke ma bayan wannan dogon turancin."
"Really?"
Ta tambaya tana daga duka girarta biyu bayan murmushin da take yi. Sai kawai ya sake sunkuyo da kansa dab da fuskarta sannan a hankali yace.
"Ko in nuna miki? Kinga sai mu ƙara da photocopy a ciki kafin printed one din nan ya fito?"
Ba shiri bakinta ya buÉ—e sannan idanunta suka zare a lokaci guda. Ta cire hannunta dake gefen fuskarsa ta naushe shi sannan ta juya tana fadin.
"You're soooo Bad Ma'aruf Muhammad Bakori!"
Ta maida hannunta cikin kwanon fulawar daidai lokacin da ya zagaye duka nasa biyu a kugunta yana rungume dan karamin cikin nata da ba zaka yarda ya kai watanni har takwas ba. A kusa da kunnenta sosai ya shiga magana.
"Zan fita wajen su Khalid ne yace wasu mutane sunyi masa magana zadu je su ga ginin, kinga idan mun daidaita dasu komai zaifi sauki dama ina nan, idan kuma ba haka ba Khalid din shi zai ƙarasa komai bayan na tafi."
Sai ta gyada kanta a hankali yayin da É—aya hannunta ke zuba ruwa a cikin fulawar tana kara cakuda siraran yatsunta a ciki.
"Zai iya shi kadai? Kuma ka yarda dashi?"
Ta tambaya, tana cigaba da sbinda take yi,daga bayan nata, nasa udanuna a tsaye akan sbinda take yi É—in yace.
"Lawyer ne, abokin Ishaq, kuma gidnsa bashi da nisa da aibitin, saboda haka mai siyan wajen kawai zai samo, jiya muka samu wani kamfani NHC da suka siya duka kayayyakin aikin dake cikin asibitin har sun biya kudin, sannan na gaya miki na gama biyan staffs É—in duka tun shekaranjiya so kin ga kusan babu abinda ya rage kenan..."
Daya hannunta ya kara ruwa a cikin fulawar yayin da iskar da ake yi har yanzu ke cigaba da kada su kotawanne ɓangare kamshin damina da kuma sanyinta na cika gidan. Tace.
"Allah ya taimaka komai ya faru da wuri, Allah yasa hakan ne mafi alkhairi."
Addu'ar tayi masa dadin da har sai da yayi murmushi kafin ya amsa.
"Ameen."
Sai kuma fuskarsa ta koma daidai a lokaci guda, ya kusan hade ransa ma kafin yace.
"Wai meye wannan kike yi?"
Ta dan juyo da kanta ta kalle shi da murmushi jin muryarsa ta canja.
"Fanke..."
Fatar bakinta ta motsa yayin da sautin ya fito a hankali.
"Fanke?" Ya tambaya cikin rashin fahimta karara.
"Fanke da na sani na mutuwa? Me za'ayi dashi?"
Amina ta kyalkyale da dariya ba shiri tana juyar da kanta. Sai kawai ya sake ta sannan ya juyo da ita sosai tana fuskantar sa.
"Seriously da gaske nake, me zaki yi da fanke? Ba sai anyi mutiwa aje raba shi ranar sadaka ba?"
"Sugar waya gaya maka? Koyaushe fa anayi... Har yara ana yiwa su je dashi makaranta sannan mutane suna cinsa as breakfast ma, me yasa sai anyi mutuwa za'aci?"
Yanayin fuskarsa ya nuna alamun ya dan fahimta a lokaci guda, amma duk da haka hannunsa na rike da itan yace.
"Ke me zaki yi dashi?"
"Ci zanyi, kawai na tashi ne naji ina sha'awarsa."
"Me yasa baki ce in taho miki dashi ba? Me yasa sai kin wahalar da kanki?"
Ya tambaya a hankali yana cigaba da kallonta... Sai ta karasa matsowa cikin jikinsa ta mayar da hannayenta saman kafadarsa kamar dazu sannan a hankali tace.
"Saboda nafi son inci wanda nayi da hannuna Sugar, ka daina damun kanka aiki baya wahalar damu, we are strong!" (Muna da karfi.)
Kalmar 'Mu' din da ta furta ta shiga har cikin zuciyar sa a lokaci guda, sai ya sake rike ta a jikinsa yana tallafo ta da duka hannayensa biyu.
"Jamal is strong Babydoll, don haka insha Allah haka little one dinsa ma zai zama..."
A lokaci guda kumatunta suka yi murmushin da take yi a kodayaushe ya fadi hakan, don tun daga ranar da suka ga gender É—in Babyn ya tabbatar mata da sunansa... Jamal.
Fuskar Kilishi ta gifta a cikin kanta a lokacin maganganun da ta faÉ—a mata suna haskawa a cikin kanta.
_"...na san ba zan iya hana Ma'aruf kula ki ba idan har yayi niyya, amma kuma ba zan lazimci wani abu ciki ba don babu shi ko kaÉ—an a cikin lissafina!"_
Murmushin da bata shirya masa ba ya kufce mata, a lokacin ta faɗa ne kamar ita ke da iko a komai, kamar ita ke da ƙaddarar su a tafin hannunta, kamar babu abinda ya isa ya giftawa wannan umarnin nata, sai gashi a yanzu tana duniyar, da lafiyarta da komai, amma bata da ikon ko da ganinsu balle har ta san me suke ciki ko kuma tayi gadarar zartar da wani hukuncin...
Sai ta gyaÉ—a kanta sau biyu tana cigaba da murmushi kafin muryarta ta fito a hankali tana kallonsa, a hankalin da ko da akwai wani a kusa dasu ba kallai bane yaji abinda tace.
"Insha Allah."
Idanunsa suka cigaba da kallonsa tana nazarin tarin abubuwan dake kara canjawa a hankali a hankali game dashi din. Gashin kansa ya taru sosai sai dai har yanzu bai kai na baya ba, ya taje shi sosai yana ƙyalli, don har yanzu da laushinsa, yadin jikinsa kalar dark blue ya kara fito da hasken da fatarsa ta kara yi a kwanakin sakamakon hutun da ya samu akan rayuwarsa ta baya.
"Idan kika cigaba da kallo na haka, ba lallai ne in iya fita ba Babydoll...."
Muryarsa ta fito a hankali yana cigaba da kallonta, sai kawai ta cije lebbenta tana murmushi sannan ta yi É—age a hankali ta kai fuskarta dab da kunnensa.
"Kayi zaman ka kawai, idan nayi fanken nan sai mu siyar, kaga may be ma mu samu fiye da kudin asibitin nan... Naga alama Æ´an gayu basu san fanke ba."
Yayi murmushi sosai yana kallonta.
"Ki rufa min asiri Babygym, ni da nake neman kudin da zan gina miki irin wannan gidan, naga alama kina son shi da yawa..."
Idanunta ya zare a lokaci guda...
"Ni bance ba, ni bance ba Sugar, ka rufa min asiri dan Allah..."
Yadda ta fada tsakaninta da Allah ya bashi dariya sosai, sai kawai yayi baya da kansa kafin ya sake kallonta sosai.
"I'm madly in love with you Amina.."
Ya faÉ—a yana lumshe idanunwansa. Ta sake yin dage akan kafafunta a hankali tana wasa da yatsunta dake sarke da wuyansa.
"Madly? Madly dai wanda na sani?"
Muryarta ta fito kamar wani fiffiken dake fadowa kasa a hankali.
"Idan baki gane ba Babydoll, zan iya yi miki bayani, kin san babu wanda ya san ƙwarewata anan kamar ke..."
Ba shiri Amina ta kyalkyale da dariyar da tana yin baya zuwa gefe, hannunta ya dauko wani mug kalar baƙi an rubuta 'Pa' a jikinsa ta tsiyayo masa ruwan tea ɗin data haɗa a wani flask sannan ta miƙa masa.
"Mutane suna can suna jiranka Pa...."
Da murmushi ya karɓa ya jan kujera a gefensa ya zauna, yana gaya mata wallahi da gaske yaje, zai bata mamaki tunda har bata yarda dashi, yana bayanin tana murmushi tana juyowa tana kallonsa.
Ƙarar wayarsa ce ta katse shi, yasa hannu a aljihu ya ɗauko ta, nambar Maryam ƙanwarta da ya gani ta tabbatar masa da waye tun kafin ma ya ɗauka.
"Dadddddyyyy!!"
Muryar Hamida ta faɗa da ƙarfi daga cikin wayar, ba shiri Amina ta taho da sauri ta karɓa tun kafin ma ya amsa tana tambayarta yadda take, makarantarsu da kuma gaya mata cewa gobe zasu dawo.... Dama a dazun nauyin Amma ne yasa basu gaisa ba, kafin kuma tace Maryam din ta hada ta da ita sai Aminu ya karbi wayar.
Daga inda Ma'aruf ke tsaye yana kokarin karasa shanye tea É—in dake hannunsa ya cigaba da kallonta yana murmushi...
Amina itace rabin rayuwarsa a yanzu ya yarda, itace nutsuwarsa dama dukkan wani fatan samun nasarar sa... Kulawar da yake samu tare da ita, wani abu ne da bashi da inda zai je ya samu idan ba a wajen nata ba.
Komai muƙaddari ne daga ubangiji ya yarda! lokacin da ya amince da aurenta, yayi ne saboda Jamal, saboda ya san alakarsa da ita a lokacin da yaga sunanta har ma da adireshin ta, sai gashi daga baya ya fahimci cewa wannan sunan na wata Aminan ce daban da itama take a wannan unguwar ta gadon kaya, wata Amina ce daban da suka yi makaranta tare a wajen sauran takardunsa na wajen Hajiya Maimuna da bai san dasu ba sai a lokacin da Amina ta haddasa kusancinsu...
Allah ya sani bai san tarin alkhairin da zai lissafa da ya samu ta dalilinta ba tun daga lokacin da ta shigo cikin rayuwarsa zuwa yanzu, kamar tana tafiya ne da wani haske a kafafunta dama hannayenta ta yadda duk inda ta taka ko kuma abinda ta taɓa sai ta haskaka shi.
Ita kaÉ—ai, ita kaÉ—ai ce abinda idan ya tuna cewar ta hanyar Kilishi ya samu, zuciyarsa ke yin sanyi da tarin rangwamen da yake jin cewa zai iya kyale ta da iya hukuncin da take fuskanta anan duniya, amma tabbas ne cewa tsakaninsu da ita wani hukuncin sai a lahira, don ko da giftawar sakan guda baya so ko da fuskarta ne ta gifta a tunaninsa balle kuma wani abu nata.
Adadin yadda zuciyarsa ta so ta shine adadin tsanar da yayi mata a yanzu, tsanar dake tafiya tare da albarkacin Aminar da ta zama inuwarsa a yanzu, don abinda ya sani shine ba don ita din da yake kallo a gabansa ba, ko zai sake yi sau dubu yana kasawa, ba zai fasa ba zai yi ta kokarin da zai aika ta ne har lahirar da danuwansa ya tafi don ta riga shi zuwa da sakon da yake son ya isa ga danuwansa.
Amma saboda Amina, saboda ita da kuma sauran tarin yanuwa da iyayensa da yake ganin kokarin da suke yi akansa wajen ganin daidaituwar lafiyarsa...
Shi yasa a dole yake ta kokarin kai zuciyarsa nesa yana tuna tarin maganganun da kowa ke yi masa wajen ganin yayi hakurin da komai ya daidaita rayuwarsa, sai dai a duk ciki babu abinda yafi rikewa irin kalaman Ishaq da ya gaya masa cewa babu yadda suka iya da Kilishi, babu abinda zasu yi msta da zsiyo daidai da adadin cutar da tayi musu a duniyar nan, dole ne su hakura su kyale ta da iya abinda da Allah ya kadarta a rayuwarta kawai,fon wata shari'ar sai a lahira!
"Tabbas wata shari'ar sai a lahira...!"
Bakin sa ya maimaita hakan a yanzu yana kallon Aminan dake dariya a cikin wayar tare da Hamida...
Shine bai fahimta ba tun asali, Kilishi bata daga cikin mutanen da suka cancanta a rayuwarsa!... Bata cikin su ko kadan.
Sai kawai ya zaro É—aya wayarsa ya shiga kiran mutumin da yake son ya hada shi da agency din da zai sayi kujerar makka guda biyu na Amma da kuma Baba (iyayen Amina).
Fatansa a kodayaushe shine ya faranta ran wannan Æ´ar yarinyar fiye da yadda take gyara tasa rayuwar!
*Alhmdlilah.*
*Ƙarshe.*
***
*Fara Wuta...*
_Ba'a kodayaushe ne Ubangiji ke rama cutar da makiyanmu ke yi mana daidai gwargwado da abinda suka zalunce mu a dashi ba, hakki yana da nauyi kuma yana bibiyar dukkan mai ɗaukarsa, sai dai dukkan wata wahala da kuma azabar da mai zalunci ke fuskanta game da wani hakki da ya ɗauka a duniyar nan baya ƙarasawa ko kaso guda a cikin ɗari idan za'a kimanta sauran hukuncin da zai je ya tarar a gaban ubangijinmu... Don gaskiya ne abinda masu iya magana ke faɗa cewa WATA SHARI'AR SAI A LAHIRA!_
_Ina fatan Allah ya bamu gamawa da kuma wucewa lafiya a duniyar nan ba tare da mun koma gare shi da hakkin kowa ba, sannan ina fatan kuma ba zaku dauki hakkina ba wajen tura labarin nan ga wasu a matsayin kyauta... Don bana fatan wata shari'ar ta hada mu daku a gaban ubangijin da kowannenmu zai koma gare shi._
_Godiya mai tarin yawa ga dukkan hakuri da kuma jinkirinku har zuwa gabar da muka kammala Farar wuta, nayi laifuka masu tari yawa na sani, amma dama da wuya ne kowacce tafiya ta kasance dari bisa dari wajen samun daidaito... Ina fatan dukkan wadanda na ɓatawa rai zasu gafarce ni su yi min afuwa irin wadda zasu so ayi mudu idan sune a matsayina..._
_Nagode ga dukkan masoya rubutuna, nagode da hakurinku nagode da lokacinku, Nagode da kaunarku, idan har zanyi wani rubutu a gaba ina fata ba zai karaso gare ku ba sai a cikakken sa insha Allah._
_Ina fatan Allah ya faranta rayuwarku fiye da yadda zan kimanta... Allah ya bamu ikon amfani da Æ´an darussan dake cikin labarin nan... Jazakallah khairan._
*Aysha Shafi'ee.*
*08067794315.*
03/ 2022
No comments