Daurin Boye Complete Hausa Novel
DAURIN BOYE* 🧣🧣
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
HASKE WRITERS ASSO
(home of expert and perfect writers)✍
*_Dandano daga littafin DAURIN BOYE_*
0⃣1⃣
Sake gyara tsaiwarshi yayi jikin machine din nasa samfurin lifan kirar MOTO B,agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ya kalla yana sake qiyasta mintocin daya kashe tsaye a qofar gidan,tabbas banda wani babban dalili babu abinda zaya sanyashi zaman jira har kamar haka,babu abinda ya tsana a rayuwarshi kaman jira,mutum ne shi mai kiyaye qa'ida wanda bai yarda da samfurin wannan maganar da hausawa ke bawa lokaci ba na african time.
Sauke hannun nashi yayi ya maida dubansa ga madaidaicin get din dake maqale da katangar gaban gidan wanda ya kasance shine kofar da zai sadaka da ainihin cikin gidan,kaman jiran hakan kuwa ake qofar ta soma yunkurin budewa,cikin sakannin kadan matashiyar dake yunqurin bude qofar ta bayyana.
A hankali take takowa zuwa inda yake,sanye cikin dinkin atamfa riga fitted da skert wanda ya zaunawa jikinta das,ta lullube jikinta da mayafi wanda baikai matsayin medium ba,a hankali yayi kokarin mamaye fuskarshi da murmushi duk da yadda fuskarta take kadaran kadaham hakan bai dameshi ba duk da yana ankare,ba fara'a sannan ba kuma a daure take can ba,kallo take kare masa tun daga nesa kaman yadda ta saba masa duk sa'ilin da ya ziyarceta,shirt ce jikinsa ruwan makuba da bakin wando jeans mai matsakaicin kudi,kafafunsa saye da takalmi budadde dinkin hannu na kasuwar kofar wambai,fes yake hakanan kayan sun masa kyau babu laifi,sumarshi kanshi zuwa sajensa a gyare a taje wanda hakan ya sake bayyana sirrin kyan da Allah ya bashi,ba shakka banda wani abu guda tak muhammad ya cika mijin aure wanda za'a iya nuna shi a ko ina,saidai wannan abun daya rasa din ya sanya ta cireshi daga tsarin mutumin daya cancanci aurenta.
"Barka da fitowa gimbiya zulaiha" ya fada cikin sassanyar muryarsa wadda na daya daga cikin abinda ke burge zulaihan tare da shi,duk da bata jin zata iya bashi damar kasancewa cikin rayuwarta,yana ci gaba da nazarin yanayin fuskarta a fakaice sanda ta amsa masa
"Barkan ka" ta fada cikin wani salon shan qamshi da basarwa
"Har na fidda rai ai,na tsammaci yau bazan samu ganinki ba"
"Kusan da hakan ce ta kusa faruwa,saboda zamu fita ne da maama,sannan ma kuma bansan zaka zo din ba,yanzun ma zuwa nayi na gaya maka.....don Allah ya kamata ace duk sanda zaka zo ka fara sanarmin tukunna kafin kazo din"ta fada kanta tsaye tana yamutsa fuska murmushi ya saki gami da dan duqar da kanshi qasa yana wasa da duwatsun dake shimfide a qofar gidan,baice komai ba sai murmushin da yaci gaba da fitarwa yana tattaunawa shi da zuciyarsa,tabbas yasan wannan rana na nan tafe,fiye da haka kuma na nan zuwa nan gaba kadan,wannan ba baqon lamari bane a gareshi,zulaiha ba itace mace ta farko da makamancin hakan ta faru tsakaninsu ba,saidai bazai yanke mata hanzari ba,zai jirata har zuwa ranar da zai zata furta kota yanke alaqar dake tsakaninsu da bakinta,sai bayan daya kammala wannan tunanin sannan ya dago ya dubeta
"Shikenan....babu damuwa...kiyi hakuri" ba tare data tanka ba ta juya tana niyyar komawa cikin gidan nasu
"Ki gaida maaman idan kin shiga"
"Zata ji" ta fada gami da jan qaramin tsaki can qasa ta shige gidan gami da rufe qofar gidan garam.
Kai ya girgiza bayan shigewarta cikin gidan yana sakin murmushi tare da cije lebansa na qasa,cikin qwarewa ya haye saman babur din bayan ya tadashi ya figeshi cikin gudu ya fice daga layin,zuciyarsa cike fal da tunani da mamaki,mamakin da har yau yaqi barinsa,tsahon shekaru kenan wannan abu na daure masa kai,da gaske haka rayuwa ta koma?,ya gode Allah da baiyi gaggawar yiwa hukunci wa rayuwarsa ba.
Titi ya hau ba tare da yayi wata doguwar tafiya ba ya soma sauka daga kan kwaltar zuwa gangaren titin,daf da wasu jeran baqaqen motoci da farare a qalla guda biyar ya soma qoqarin tsaiwa,wanda tun kafin ya kai ga tsaiwar wasu matasa kimanin su bakwai sanye da coat baqi da fari suka doso shi,kowanne fuskarshi manne da baqin gilashi wanda hakan ya sanya baka iya ganin qwayar idanunsa,ya kuma qara musu kwarjini qwarai,daya daga cikinsu shi ya riqe babur din sanda ya sauka,yayin da dayan ya matso kusa da shi yana bude masa qofar daya daga cikin motocin wadda duka ta fisu kyau da girma,sai da yaga ya shiga sannan ya rufe masa qofar,sauran suka zagaya suka shige ragowar motocin nasu,yayin da daya daga cikinsu shi kuma ya haye babur din ya bisu a baya.
"Ya dai,akwai wani sauyi ko ci gaba kuwa yau?" Wani kyakkyawan matashi wanda aqalla zaiyi shekara talatin da hudu dake zaune daga corner motar riqe da magazine ya fada yana dubanshi,fuskarshi na nuna alamun dariya yakeson yi,takalman qafarsa ya soma yunkurin cirewa gami da agogon hannunshi ba tare daya dubeshi ko ya amsa masa ba,ya dannan wani madanni dake gaban sit dinshi,wani qaramin akwati ne ya fito ya zuba agogon takalmin harda wayar dake hannunshi qirar VIVO bayan ya kasheta,ya maida akwakwun muhallinsa ya jingina da makarin kujerar sannan ya waiwaya ya dubeshi
"Me kake tunani mahmoud?,ita dinma kaman sauran,abun ma kamar yana sake lalacewa ne" ya qarashe maganar yana lumshe idanunsa tare da sauke numfashi
"Duk inda xaka je ka dawo dai shawarata ce kan hanya,na sha gaya maka ka sauqaqewa kanka walaha,ka laluba cikin familynka,akwai gomayyar 'yammatan dake sonka ka zabi daya cikinsu ka huta,kaga wannan babu wani fargaba tattare da kai,duka ana tare". Kansa yaci gaba da girgizawa ba tare daya bude ido ya kalli mahmoud ba,tsahon sakanni tamkar bazai amsa mishi ba sannan ya ware idanunsa yana duban sit din dake gabansa
"kana tunanin qaramin abu ne ya sanya na guje musu dukkaninsu na xabi inbiyo ta wannan hanyar?,su dinma kusan duka abu guda ne,babu wani banbanci,halayyar daya ce dai kaman yadda sunansu yake daya,abu guda dukkaninsu suke wa,manufarsu guda ce......" Maganar tashi ta katse sakamakon shigowar kira wayar tasa,ya maida qwayar idanunsa ahankali kan wayoyin dake zube a gefansa,kusan lokaci guda idanunsu shida mahmoud suka sauka kan wayar RAMLA sunan dake yawo kenan bisa screen din,murmushi mahmoud ya saki ganin ya kau da kanshi tamkar ba cikin wayarshi kiran ya shigo ba
"Yallabai ka daga mana?"
"Qyaleta kawai" ya bashi amsa kai tsaye gami da danna wani madanni,wani dan qaramin abu mai kama da fridge ya bayyana,cikinsa nau'ikan abubuwan sha ne masu sanyi da duka duka basu wuce gwangwanaye da kwalba goma sha biyu ba,daya a ciki ya dauka hadi da cup ya maida abun muhallinsa ya koma ya jingina da kujera ya tsiyaya yana kaiwa bakinsa ba tare da yabi ta kan qorafin daga waya da mahmoud ke masa ba,a maimakon hakan ma sai ya maye gurbin qorafin nasa da tambaya
"Jirgin qarfe nawa zamu bi ne?" Tunda ya masa hakan yasan bai bukatar xancan,saboda haka shima ya tayashi
"Yanzun airphort din muka nufa ai,tunda duka duka awa guda da 'yan mintuna ya rage lokacin tashin jirgin ya cika"
"Ok,kafin nan mu biya na sauya kayan jikina"
"Ba matsala" ya fadi yana gayawa driver inda zasu fara zuwa kafin su isa airphort din.
🧣🧣🧣🧣
A nutse ta miqe daga saman abun sallar tana sakin 'yar qaramar hamma tare da furta "a'uzu billahi minash shaidanir rajim" gami da ninke daddumar ta mata ma'ajiya a muhallinta,zare hijabin jikinta tayi tanayi tana duba agogon dake maqale a bango saboda gudun makara,qarfe shida na safiya ya nuna mata,hakan ya mata dadi ta tabbatar kafin lokacin tafiyarsu makaranta ta kammala dukkan abinda zata yi din,gyara dankwalin kanta tayi wanda ke niyyar zamewa saboda santsinsa da kuma santsin sumar kanta,sannan ta zura slippers ta bude qofar dakin nata ta fita a hankali.
Makekan falon nasu shiru yake tamkar babu halittar kowa cikin gidan,bugu da qari mamaye yake da dan sauran duhun asuba da bai gama yayewa ba,babu motsin kowa,don hatta da masu aikin gidan basu tashi ba,kunna qwayayen falon tayi take haske ya game ko ina ya kuma bayyana asirin kyan da falon ke da shi,sannan taci gaba da takawa a hankali ta doshi wani corridor wanda a nan kitchen dinsu yake.
Kitchen ne na alfarma wanda ya mallaki dukkan wani nau'in kayan amfani da kitchen ka iya buqata,kai tsaye ta nufi jikin wani dan qaramin Allo wanda ke dauke da timetable na abincin da gimbiyar gidan ke buqata kowacce rana,alhamis ce saboda haka ta sauke idanunta kan THURSDAY dake rubuce baro baro,ta kuma karanta abincin dake qarqashin ranar,kanta ta jinjina saboda yau aikin nata kaman mai yawa ne,gashi a jiya bata samu ta duba me zata girka ba yau sakamakon bacci fa yayi nasarar saceta tana tsaka da karatun test da zasuyi a safiyar yau,cikin hanzari ta bude freezer ta fiddo dukkan abinda zata buqata,sannan ta wuce store dake cikin kitchen din ta fiddo kayan amfani,sannan ta soma aikinta cikin hanzari da qwarewa.
A qalla ta shafe kusan mintina talatin sannan ta jiyo motsi alamun ana niyyar shigowa kitchen din,fuskarta qunshe da murmushi wanda ya sanya dimple dinta dake dukka kumatunta lonawa,tunkan ta qaraso tasan wacece,ita kadai ke tashi ta kama mata aiki,ita daya ce matar da hakanan Allah ya hada jininsu take qaunarta,ita daya ce take ganin qauna daga idanunta,irin qaunar data rasa,irin qaunar da take buri da fata ta ganta daga wajen wadda tayi silar kawota duniya saidai har yau abu yaci tura,a wajenta ne kawai take ganin kulawa qauna da kuma sassauci.
Ita dince kuwa,daya daga cikin masu aikin gidan ce inna laraba,fuskarta fadade da fara'a tace
"Yanzu inna laraba yau dinma ba zaki kwanta ki huta ba?,ina cewa jiya da qyar kika samu ciwon qafar nan ya barki?" Itama fuskarta qunshe da fara'ar tace
"Banda abinki shatu ai kema kinsan ban saba da wannan baccin bayan sallar asubar ba,kuma na tabbatar kina nan ke daya kina fama da kacaniya" ta fada tana qarasowa kusa da ita,murmushi ta saki sannan cike da girmamawa ta gaida innar kaman yadda take kiranta tare da tambayarta ya qafar tata,amsa mata tayi itama cikin kulawa kafin ta matso da niyyar kama mata aikin,duk yadda taso hanata amma innan sam taqi,haka ta sakar mata suka ci gaba da aikin tare suna hira.
Bata ankara ba taga lokaci ya ja,har qarfe tara saura na safiya,idanu ta zaro don tun jiyan da daddare anty asma'u ta ja mata kunne cewar qarfe tara zata fita,kuma driver ba tsayawa jiranta zaiyi ba,ruwanta ta shirya da wuri ruwanta karta shirya ta samu mai ajjiyeta makaranta"hakan ya sanya ta tattare komai a gurguje ta soma shiryawa saman qawataccen teburin cin abincin dake sashe na musamman dake cikin falon.
Plates da spoons suka rage suta dauko ta dawo da niyyar ajewa daga nan ta shiga ciki ta shirya itama,duk da cewa ita sai goma zata fita,amma dole ta shirya tabi asma'un koda qarfe bakwai asma'un zata fita,tsaye ta tadda ta shirya tsaf cikin wata doguwar rigar material,ta zuba makeup sosai,hannunta maqale da 'yar madaidaiciyar hand bag mai azabar kyau,kafadarta rataye da mayafinta wanda wanda haka qa'idar saka mayafinta yake,qwayar idanunta saye da tafkeken sun glasses wanda ya kusan cinye rabin fuskarta,table din take qarewa kallo har sanda aysha ta qaraso wajen tana dora plates din saman teburin gami da gaida asma'un.
Bata damu da amsa gaisuwar da take mata ba saima tambayar data jefo mata
"Waima baki shirya ba?" Ta fada cikin bacin rai tana zare glass din fuskarta kasancewarta mace wadda qanqanin abu sai ya bata mata rai ko ya tunzurata
"Yanzun zan shirya in sha Allahu" ta fada a tausashe,cikin hasala asma'un tace
"Kada ma ki shirya wannan ya rage naki,ni dama na soma gajiya da tafiya dake gaskiya,ya kamata daddy ya barni haka nan ya raba mana tafiya tunda babu dole.....ina cewa tun jiya na sanarmiki lokacin da zan fita,amma saboda tsabar raini da salon ki jawa mutum fada baki tashi kin gama komai a kan lokaci ba"
"Kai...kai me yake faruwa haka da sassafen nan kuma lafiya?" Cikin bacin rai asma'u ta juya tana kallon mahaifiyarta dake saukowa daga stairs,shirye cikin tsadajjen lace na alfarma,hannayenta da wuyanya duka sanye da jewels da banguls masu tsada
"Mommy nida yarinyar nan ne mana,wai ki duba fa jiya gabanki na gaya mata when zan fita shine wai har yanzu bata shirya ba"
"Garin yaya ke ayshatu?...." Jin tambayar tayi banbarakwai,tunda dukkaninsu sunsan me ya tsaidata,hidimar abincin safen asma'un ne,wanda dukkansu sun kwana da sanin cewa don ta itama a soke abincin safe,totally ma ba damuwarta bane abinci
"Ya kuma kika tsaya,jeki ki shirya,idan kuma har ta gama baki fito ba sai ki samu napep ya kaiki" ta fada itama tana jan daya daga cikin kujerun dining din da alama karyawa zatayi akwai muhimmiyar fita kenan.
Juyawa tayi a hankali ta doshi corridor din da dakunansu suke,sam batayi mamaki ba tunda ba yau bane farau,hajiya sa'adatu irin matan nan ne da basu cika ganin aibu ko laifin dansu ba,bugu da qari tana da attitude na idont care kan lamuran da ba nata ba,tayi ma rawar gani yau data tanka,idan da taso Allah ya kyauta kawai zata ce tayi zamanta ta hau hidimar gabanta ya tasu koma ya zasu qarke ohon mata,indai hakan bazai shafi shalelen tata ba ko kuma ita bazai kawo mata wani cikas ba.
Duk da cewa a gurguje ta shirya amma hakan bai sata ta samu nasarar tadda asma'un ba,saima hajiya sa'adatu data samu tana yunqurin bude murfin mota zasu fita ita da drivanta,kallo daya tayi mata tace
"Gashi har asma'un ta wuce tun dazun,saidai ki qarasa titi kibi ta haya" ta qarashe maganar tana shigewa motar tare da yunqurin rufewa
"Ba komai zan qarasa din mommy,a dawo lafiya"
"Allah yasa" ta masa sanda drivern ya fara jan motar suna niyyar ficewa daga gidan ba tare data damu da yadda ayshan zata kai kanta makarantar ba.
Tana nan tsaye har motar mommy ta fice sa'annan ta soma takawa a hankali cike da nutsuwar data zama tambarinta tabi bayan qurar motar ta fice daga gidan ta 'yar qaramar qofar dake maqale jikin get din.
Duk da yake akwai 'yar tazara kadan tsakanin gidan nasu da bakin titi amma sam bata ji tafiyar ba,hakan ya faru ne sakamakon yadda qwaqwalwa da zuciyarta baki daya sukayi zurfin tare da nisan kiwo wajen tunani,tunani qwaya daya da ko yaushe bata gajiya da shi,hakanan batasan randa babin tarihin rayuwarta zai rufe ba,hakan batasan meye qarshen nasa ba,yaya qarshen nasa zai kasance?,wata iriyar cukurkudaddiyar rayuwa da tayi take kuma kanyi ita ke mata kai kawo cikin qwaqwalwarta.
Sam ta sha'afa sai data tsaida mai napep sukayi cinikin nawa zai kaita sannan ta laluba jakarta cikin fargabar ta fito da kudi?,Allah ya taimaketa jakar a ciki ta sanya kudaden da daddy ya bata sanda zaiyi tafiya,ta sauke ajiyar zuciya a hankali tana hamdala cikin zuciyarta.
Kusan babu wanda ta tarar cikin ajin,sakamakon akwai tazarar awa guda daga lokacin da za'a shiga lacture din da sanda tazo,guri ta samu na musamman inda tafi sha'awar zama ta zauna,sa'an nan ta zaro handout dinta taci gaba da dubawa kafin lokacin da zasu zana test din ya cika.
*mrs muhammad ce*👑
[09/01, 4:17 PM] +234 803 238 4602: 🧣🧣 *DAURIN BOYE* 🧣🧣
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
HASKE WRITERS ASSO
(home of expert and perfect writers)✍
0⃣2⃣
Kusan rabi da rabi take karatun,fiye da rabin hankalinta ya ta'allaqa ne akan wayarta,wadda ba komai take kalla ba sai wasu numbers wanda ke rubuce da sunan MAMA NA,ta kallesu yafi sau shurin masaki,ta kwatanta kira fiye da irgen yatsun hannunta saidai ta kasa hakan,ba wani abu bane ya jawo haka ba illa tsoro da fargabar abinda kiran zai biyo baya,taji ance bata ji dadi ba,tana so ta kirata ta mata sannu da jiki,saidai bata da wannan damar,ba qaramin qunar baqin wake take ba duk sanda tayi jarumtar kiranta,wanda hakan daga qarshe baya haifar mata da d'a mai idanu.
"Qawata sarkin sammako" taji an ambata ta gefanta,wayar ta rufe ya dago kai fuskarta qunshe da murmushi tana duban Aliya dake sauke jakarta daga kafada kana ta yiwa kanta mazauni kusa da ayshan itama tana murmushi
"To ya za'ayi" ayshan ta maida mata amsa tana gyara zamanta
"Hala yauma uwar masu gidan zata fito da wuri ne kika kwaso qafa kika biyota?" A maimakon ta bata masa murmushi ayshan ta saki,tasan halin rigima sarai irin na Aliya.
'Yar tsama suke qwarai da asma'u,basa hada hanya da ita,saboda banbancin halaye qwarai dake tsakaninsu,bugu da qari tana jin haushin yadda take mu'amalantar ayshan wadda ta zame mata qawa kuma aminiya a dui fadin makarantar,sosai Aliya keson aysha sabo managartan halayenta,nutsuwa haquri gami da kunya,uwa uba ayshan na daya daga cikin daliban da sukayi fice a duk fadin department dinsu,kai bama iya tsangayar tasu kadai ba a duka makarantar ma.
Kai Aliya ta kada cikin takaici,saidai ayshan bata bata damar cewa komai ba ta tareta
"Kinso yau ki makara qawata,ya akai haka?"
"Hmmm,wlh yau mama ta tsaidani sai dana hadawa ya khalil breakfast,Allah ne ya soni na masa sharp sharp na fece,da Allah ne kadai ya san makarar da zanyi" duka tana zancan ne sanda take ciro handout dinta daga jaka,kafin su sake cewa komai lacturer din ya shigo ajin.
Qarfe uku na rana ta kammala duk abinda zatayi cikin makarantar,hakan ya sanya ta tattara komai nata ta fito don ta qarasa inda zata samu asma'u,saidai koda taje wayam taga wurin babu alamun motarta,hakan ke nuna bata cikin makarantar,bata wani damu ba ta soma takawa da qafa don zuwa bakin get din makarantar don ta sami abun hawa,don yau Aliya ta rigata tafiya gida,ita ta tsaya ta dudduba wasu karatuttuka.
Jin qarar mota a bayanta ya sanyata sake rabewa don bawa motar damar wucewa,a sannan idonsu ya hadu da drivern,asma'u ce,ita da wasu mutum biyu a motar,da alama qawayenta ne,dauke kai asma'un tayi tamkar bata ganta ba,sai tama qarawa motar wuta tayi hanzarin wuce ayshan,sam hakan bai dameta ba,saboda ba yau farau ba,babu abinda asma'un ta tsana nan gidan duniya irin alaqar da zata bayyanar da cewa ayshan jininta ce,gida daya suka fito ko suna da dangantaka,tunda ayshan ta fahimci hakan sai itama take baya baya da duk wata alaqa da zata hadata da asma'u cikin bainar jama'a.
Kai ta jinjina kawai taci gaba da takawa zuwa qofar makaranta,wannan abun na asma'u zata iya cewa bai bata ranta ko kadan,idan ma ya bata din bai wuce digo daya cikin dari ba,a yanzu qyamatar da take fuskanta take kuma bata mamaki ta shafe ko wacce iriyar qyama da qiyayya da dukkan wata halitta zata nuna mata a doron duniya,dukkan wata tsana saidai ta biyo bayan waccar,da wannan tunanin ta tsaida wani dan sahu dake niyyar gifatata ta masa kwatance inda zata ta fada ciki.
Kamar kullum yauma a qalla ya kusa shafe mintuna ashirin yana tsaye yana jiranta,har sai data kaishi ga qosawa ya haye saman babur din da yazo da shi ya zauna,saboda rashin sabo saura kadan babur din ya tuntsira da shi Allah ya taimaka cikin zafin nama yayo gaba ya dawo ya zauna dai dai,mahmoud dake zaune cikin motarsu dake fake a wani layi ya tuntsire da dariya harda duqawa,ba don ba dabanba da ya fito ya masa vedio ya ajjiye saboda tarihi,saidai yana tsoron tashin balli tilas ya zauna cikin motar kamar yadda yayi masa umarni.
Sake duba agogonsa yayi yana qissimawa ranshi mintinan da zai qara wanda matuqar bata fito ba zai qara gaba,a gajiye yake,daga airphort yake ko gida bai isa ba ya sauya kaya ya canza akalar tafiyar tasa zuwa gidansu,bayan ya yiwa daya daga cikin yaranshi waya ya kawo masa babur din,kwanaki goma ya kwashe a qasar da yaje,bai kuma samu damar kiranta ba tunda ya tafi saboda gudun tonuwar asiri,don kada ta tsammaci ya janye hakan ne ya sanyashi tahowa kai tsaye gidansu.
Kamar ko yaushe yauma haka fuskarta take,ta qaraso inda yake saidai a yau waya take amsawa,ganin ta iso gareshi yasa ta bada uzurin zata sake kira ta kashe wayar ta lanqwasheta a hannunta yauma tana sake qare masa kallo a kaikaice
"Allah ya baka kyau na nunawa sa'a,saidai hakan ba zaiyi tasiri a raina ba saboda kana da babban naqasu na rashin hatimin nasara" duka take wannan maganar a ranta,sama sama suka gaisa tamkar baqin juna,shi kansa yana jin wani irin cikin ranshi,duk yadda yaso kawo sabo da shaquwa tsakaninsu zulaihat taqi bashi dama.
Shiru ya ratsa tsakaninsu bayan ya gama iya maganganun da yaga sun kamata,saidai rashin samun gamsashshiyar amsa yasa maganganun nashi basuyu tsaho ba
"Ammm...dama akwai abinda nakeson gaya maka" ta fada tana gyara yafen mayafinta
"Uhmmm...babu damuwa,yi maganarki"
"Cewa nayi don Allah daga yau ina son ka janye daga zuwa wajena da kake....saboda ina da buqatar space"qaramin murmushi ne ya subucewa fuskarsa,abinda yake zato yau zai tabbata kenan
"Amma wani laifi na aikata ne haka" kai ta kada tana dan tabe baki
"Ko daya,kawai na gaji da alaqarmu ne haka.....har yau jiya iyau,kai ba qaruwa ake da kai ba" ta qarashe furucin qarshe can qasan maqoshinta,saidai abinda bata sani ba shine,yana daga cikin jinsin mutanen da Allah ya musu kaifin ji matuqa,murmushi ya kuma saki mai dan sauti,ga mamakinta taji yace
"Shikenan....in sha Allahu daga yau din zan janye....amma" ya fadi yana sanya hannunsa cikin aljihun trouser dinsa,american dollers ya ciro daga aljihun nasa wanda baisan ko na nawa bane,takawa yayi a hankali har ya isa inda take jingune rungume da hannayenta ya soka mata su tsakanin hannayenta yana ci gaba da jifanta da murmushi
"Na gode da lokutanki na baya da kika aramin.....sai wara rana" ya fadi yana juyawa,binsa tayi da kallo galala,duk wata tasha ta tunaninta ta dauke tsaf,har ya isa bakin wata baqar mota wadda bataji sanda ta iso inda suke ba,gidan baya ya bude ya shige kana ya rufe,sai data ga motar ta bar layin nasu sannan hankalinta ya dawo jikinta,tabi dollers din dake liqe a jikinta da kallo,sabbi kar suna fidda wani irin qamshi dake cakude da sassanyan qamshin turarensa da har rana irin ta yau ta rasa gane wanne irin turare yake amfani da shi,cikin sauri kaman wadda aka yiwa allura ta juya cikin hanzarinta shige gidan su,bata tsaya ko ina ba sai parlourn gidansu,inda tabar qawarta barratu na jiranta
"Ya akayi,kin sallami dan anacen naki" maimakon ta amsa mata saita miqa mata dalolin dake hannunta
"Wadannan fa daga ina?" Barratu ta fada tana zakudawa gami da gyara zamanta tare da tattara dukkan hankalinta kan zulaiha,mayafinta ta yage sannan ta zauna hannun kujera tana baiwa barratu labarin abinda ya faru,ta rufe da cewa
"Tsoro na daya barratu,kada ya kasance irin mijin da nake muradi ne na koreshi da kaina,kinga irin motar daya shiga kuwa" ta fada fargabarta na fitowa fili qarara,murmushi barratu ta saki tana karkada kudaden
"Kinga malama....kwantar da hankalinki....tundan yau kin gano haka ai baki makara ba,waskewa zakiyi,ai kiransa zakiyi kawai ki nuna ke bakison kudinsa yazo ya amshi abinsa,ke gwadashi dama kike yi" bata tsaya ta gama jinma qarshen zancan ba ta zaro wayarta cikin hanzari ta soma laluba inda ta jefa lambar tasa,can cikin black list ta ganota,cikin hanzari ta cireta daga black list din sannan ta soma kiransa.
Dai dai lokacin yana lafe a bayan motar suna tafe, mahmoud nata tambayar sa ya akayi a gefe guda kuma yana sheqa masa dariya,qarar wayar ita ta sanyashi bude manyan idanunshi da suke a rufe,waya ce da ita daya keda number,wadda dama dominta ya siya wayar da layin,hannunshi ya kai ya daga wayar ya kara a kunnensa ba tare da yace komai ba
"Ka dawo ka amshi kudinka,ni basu nake so ba,gwadaka dama nake,kuma alamu sun nuna kaci wannan jarrabawar" irin maganganun data ringa jerowa kenan duk a niyyarta nason amintar da shi da gamsar da shi,murmushi kawai ya sake mata wanda ya ratsa kunne da qwaqwalwarta
"Am sorry to say,ida na wuce aji bana maimaita shi.....sai wata rana" ya qarashe fada yana cire wayar daga kunneshi,bai tsaya a nan ba sai daya cire layin ya karyashi gida biyu,ya sauke glass din motar qasa kadan ya watsar ta window sannan ya maidashi yadda yake ya koma jikin kujerar motar ya sake lafewa ba tare daya bi ta kan dariyar mahmoud ba,hannayensa ya saka ya rufe kunnuwansa saboda yadda mahmoud din ya hanashi sakat,daga bisani da yaga baida niyyar barinshi ya huta ya shammaceshi ya kai masa naushi,Allah ya taimakeshi ya kauce yana cewa
"A'ah,karka lahantani,haka kawai bani na kar zomon ba ai,danma ka samu wai ina rakoka,tunda an kasaka ba shikenan ba sai ka sake sabon lale....amma fa ka riqr a ranka,'yammatan zamani indai zaka ci gaba da zuwa musu a haka za'a dade ana kasaka" dariya ce ta subucewa khalipha ba tare saya shirya ba,suka dan dara tare da mahmoud din,shi kansa lamarin na bashi mamaki gamibda daure masa kai,karo na uku?,karo na uku duk tafiyar ta kasance iri guda?,sai yaushe?,sai yaushe zaiga sauyi,zaya so yaga wannan rana qwarai.
*_HUGUMA_*
0⃣3⃣
Tsaye yake cikin tafkekan dakin taron a gaban wani hamshaqin teburi wanda yake dauke da aqalla ma'aikata kimanin mutuk arba'in,hannunsa guda dafe yake da gaban teburin yayin da daya hannun yaketa wulwulgashi cike da gwanancewa duk da baisan yana yi ba,da alama bayanin da yakewa ma'aikatan da suka bashi dukkan nutsuwarsu ya dauki zafi,lokaci lokaci yana daga daya hannun nasa dake dafe da teburin yana duba agogon hannunsa,wannan kadai ya isa ya nuna maka mutum ne mai kiyaye lokaci da kuma alfanunsa.
"Is there any problem?...." Ya qarashe jimlar tasa ta qarshe yana duban fuskokin ma'aikatan,saidai kowanne ya gamsu girgiza kai suka dinga yi daya bayan daya,ganin haka ya sanya shi ya soma tattare kayanshi dake saman teburin tare da bada umarnin a rufe taron da addu'a kaman yadda yake a qa'idarsa.
Shine mutum na farko da ya soma fita,shahid ya rufa masa baya suna magana qasa qasa,a bakin hall din daya daga cikin mutanen dake tsaye a wajen ya karbi kayan hannunsa sannan yabi bayansa har cikin elevetor wadda bata saukesu ko ina ba sai hawan qarshe na kamfanin inda office dinsa yake.
Mahmoud ne kawai zaune cikin office din ya tasa computer a gaba da alamu wani aiki yake ragewa mai muhimmanci Hannu mahmoud ya baiwa shahid suka gaisa cike da alamun cikakkiyar sanayya a tsakaninsu bayan security din dake riqe da kayan khaliphan ya aje ya fice,yayin da khalipha ya wuce kai tsaye bakin freezer ya dauki ruwa ya sha bayan ya rage suit din jikinsa kana ya shige toilet,alwala ya daura sannan ya dawo cikin office din ya tadda shahid da mahmoud suna hira,wadda fiye da rabinta abinda ya shafi kasuwancinsu ne,daya daga cikin wayayoyinshi wadda ke dauke da lambobin dukkan mutanen daya baiwa muhimmanci a rayuwarsa lambarsu ke ciki,kai tsaye ya nufi bakin daya daga cikin windows din dake cikin dakin office din wanda kai tsaye zaka iya kiransu da qofa saboda kadan ne ya rage basu kai girman qofar ba,saidai glass ne zalla a jiki wanda hakan zai baka damar gano ainihin farfajiyar companyn daga sama har qasa.
Bugu biyu aka daga wayar,ya sauke ajiyar zuciya sallamar matar na ratsa kunnensa,cikin sanyin murya kaman yadda halittar muryarshi take ya amsa sallamar sannan yace"Anni...barka da warhaka"
"Barka kadai khalipha,kun fito daga taron ne?"
"Mun fito ammi,saidai aci gaba da yi mana addu'a Allah yasa mu dace"
"Ubangiji ya dafa,ya shiga lamarinku,ya zama jagora a gareku,ya albarkaci rayuwarku". Cike da jin dadi yaketa amsawa da ameen,idanunsa lumshe yana shafa qirjinsa yana jin zuciyaraa wasai
"Ya jikin anni?,kinsha maganinki na rana,naga lokaci yayi"murmushi ta saki cike da qaunar yaron nata
"Khalipha kenan baka gajiya?,kaman ba awannin da suka shude muka gama waya da kai ba,jiki alhamdulillah,magani kuma ina gama sha kiranka ya shigo"cikin murmushi ya amsa
"Ya za'ayi na gaji da jinki anni....Allah ya qara miki lafiya mai dorewa"
"Allahumma amin khalipha,Allah yayi albarka"
"Ameen anni...sai na dawo"
"Allah ya tsare" ta sake ambata cikin nuna kulawa da qauna,ya amsa sannan ya kashe wayar yana murmushi,abubuwa da yawa na dawowa cikin kwanyarsa game da annin tasa,zai iya cewa baiga uwa irin tashi ba,kuma baya zaton za'a samu,anninsa da taban ce ko cikin halittun ubangiji,da wannan zancan zucin ya qaraso inda su mahmoud suke.
🧶🧶🧶
Zaune yake gaban annin tashi cikin shigar qananun kaya na t shirt da trouser,qafafunshi tanqwashe gabanshi kuma plate ne wanda ke dauke da tuwon shinkafa miyar water leaf da ogu wadda ta wadata da ganda busashshen kifi da kuma tsokar nama,a nutse yake cin abinci gefe guda suna hira da anni,hirar dake nuna tsantsar shaquwa dake tsakaninsu,kallo daya zaka yi musu ka tabbatarwa kanka lallai akwai saboda da shaquwa mai qafi tsakaninsu
"Khalipha..." Ta ambata a hankali wanda hakan yasa ya dago kanshi yana dubanta sannan ya amsa
"Wai sau yaushe zan daina jiran ganin zuwam surukata?" Murmushi ne ya subuce masa,sai ya aje cokalin hannunsa ya fasa kai lomar da yayi niya,cikin kulawa da qauna yake dubanta sannan yace
"Kwanan nan anni,karki damu....addu'arki nake buqata kawai...ina son na kawo miki surukar da zata kulamin dake,surukar da zata daukeki a matsayin uwa....surukar da zakiji dadin zama da ita fiye dani yadda zanji" murmushi ya subuce mata,sai ta kada kai tana dubanshi
"Allah ya baka mace ya gari wadda zata zame maka majingina.....amma banda abin khalipha kana tunanin akwai irin wannan surukan yanzu?" Ta qarashe managanar tana dariya qasa qasa,don har ga Allah bata dauki burinta ta cillashi har haka ba,kullum dai addu'arta Allah ya bashi wadda zata soshi tsakani da Allah,nagartacciyar matar aure,dan marairaicewa yayi kadan sannan yace
"Anni,kin sha gayamin ba'a fidda rai da rahamar Allah"
Kai ta jinjina cike da gamsuwa tace"wannan haka yake,ubangiji ya maka zabi ja gari"
"Ameen" ya amsa yana daukar cokalinsa dinci gaba da cin abincinsa sannan yace
"Cikin sati na gaba haidar zai dawo gida hutu" murmushi tayi kaman ko yaushe
"Sun kammala jarabawar kenan"
"Eh sun samu hutu na wata biyu"
"Allah ya kai mana rai"
"Ameen" ya amsa yana daukar cup din daya cika da ruwa ya soma sha.
🧶🧶🧶
Da sauri sauri take tafiya hadi da duba agogon hannunta,qarfe tara da rabi na safe dai dai,mintuna talatin zata qara ta makara wanda hakan dai dai yake da rasa lacture dinta har na tsahon awa biyu.
Turus tayi gabanta na dan dokawa ganin asma'u zaune dafa'an cikin falon sanye da kayan barci wanda hakan ke nuna ko wanka bata yi ba bare a kai ga shirin fita,hannunta daya riqe da cup na tea tana kurba a hankali,daya hannun kuma wayarta ce samfurin iphone 8 take latsawa,jikinta sanyaye ta qaraso gefanta ta tsaya
"Ashe baki shirya ba anty asma'u?" Sai data shaqi iska kafin ta amsa
"Eh....sai eleven"
"Gashi goma lacturer din yake shiga..." Ta fada adamuwance,saboda daddy yana gidan,kusan yasan lokutan fita lactures dinsu daya ne,tare suke fita su kuma dawo tare a iya saninsa kenan,idanu ta daga ta kalleta ta watsa mata wani kallo
"Naga alamun raini na son soma shiga tsakaninmu aysha duk don saboda sharing abun hawa da muke ko...to ki shiga taitayinki,ke kanki kinsan wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,banda game game irin ja daddy da sunan zumunci saidai ki dinga hangoni ta cikin glass,to banson zura kai in zaki wuce kije ki hau abun hawa na haya ki wuce,dama dashi kika fi dacewa kuma dashi kika saba" tana kaiwa nan ta maqala earpiece a kunnenta da alama kira ne ya shigo mata zata amsa.
A kasalance take takawa a harabar gidan,zuciyarta cike fal da tunani,tana tsammanin kyautatawa na sanyawa kaso mutum koda baka sonshi,saidai ta gefan asma'u sam ba haka bane,mommy kuwa har yau ta kasa fahimtar a wanne aji take?,banbancin rayuwar data baro da wannan baya wuce sauyin muhalli,sutura da ilimi data samu ba,amma baya ga haka zata iya kiran yanayin da SAMMAKAL a wajenta
"A'ah,ina zaki a qafa aishatu?" Ta tsinkayi muryar daddy dake fitowa daga babban falonshi da yake ganawa da baqinsa,wanda sam bata lura da shi ba saboda zurfin tunanin da tayi,cikin hikima tayi qoqarin saisaita yanayinta,ta qaraso cike da girmamawa
"Ina kwana daddy..." Ta soma da gaisheshi,don yau duka basu samu damar haduwa ba,kasancewar jiya wajen goma na dare ya dawo qasar,ya kuma buqaci mommy ta tasota saidai tanajin sa'adda da tace masa ai ayshan tayi bacci,bayan idanunta biyu a sannan litattafanta ne a gabanta take dubawa,har lokacin data shiga dakin asma'u ta tadata kan ta fito daddynsu ya dawo amma asma'un tayi qememe tace ta gaji sa gaisa gobe,haka mommyn ta fito tace masa itama din tayi bacci
"Ina zaki aysha?" Ya sake jeho mata tambayar bayan sun gama gaisawa,bata da wata qarya da zata masa don kare asma'un wannan karon,saboda haka kai tsaye tace
"Makaranta" agogon wayarsa ya duba sannan yace
"Ina asma'un.....ina kuma drivern naku?"kanta ta duqar qasa sannan tace
" yau akwai banbancin lokacin fitar namu ne"
Kai ya jinjina,tun da can shi ba mutum bane mai yawan sanya ido da takura ba,hakan ya sanya abubuwa da dama kan gudana cikin gidan ayi musu kwaskwarima a sauya musu salo a bashi a haka ya karba ba tare da ya sani ba.
Dai dai sannan usama drivansa ya turo get din gidan ya shigo,saboda ga tsammaninsa a sannan zasu tafin,hakan ya sanya daddyn ya sallameta bayan ya miqa mata sabbin 'yan dubu dubu guda biyar da sukayi saura a hannunsa wanda da alama ya gama sallamar masu neman taimako ne wadan nan suka rage,tasan baya kyauta a dawo masa da ita hakan ya sanya tasa hannu biyu ta amsa tana jero masa godiya.
Ko cikin motar tunanin karamci irin na daddyn take,har abada kuma har ta mutu ba zata taba manta alkhairinsa da karamcinsa gareta ba,qarar wayar usama ta dawo da ita hayyacinta,daga jin yadda yake amsa wayar cikin daburcewa tasan akwai magana
"Kiyi haquri ranki ya dade,yanzu zan ajeta na dawo,na dauka yau bazaki fita bane...kiyi haquri" kalmar yayita maimaitawa,saidai hakan bai hana asma'u yi masa tas ba harda alakoron zagi ta kuma katse wayar
"Kaga....ajjiyeni usama kaje ka daukota saina qarasa wani abun hawan" yana bala'in ganin qimar ayshan saboda yadda take girmamashi tamkar yayanta,hakan ya sanya yace
"Barshi kawai na qarasa dake aishatu,koda na ajekin ma na koma daukota ba tsira zanyi ba" kai ta kada
"Ka ajenin babu komai...laifin ai zai ragu idan kace mata ajjiyeni kayi ba kamar ka kaini ka dawo ba" haka ya gangara gefan titi bada son ransa ba ya ajeta ya juya ya koma,ta tsaida adaidaita sahu ya qarasa da ita,idan da sabo ta jima da sabawa da halayen asma'u,ta haddacesu tsaf,shi yasa ba komai ke bata ranta ba.
*mrs muhammad ce*👑
🧣🧣 *DAURIN BOYE* 🧣🧣
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
HASKE WRITERS ASSO
(home of expert and perfect writers)✍
0⃣4⃣
Qarfe daya ta fito daga library dake cikin makarantar don ta qarasa masallaci tayi sallah,tattaunawa suka sakeyi da sauran dalibai 'yan uwanta kan lacuture din da suka gama yi,qoqarinta da yadda kanta keja yasa yawa yawan dalibai ke maqale mata saboda ta sake ganar da su abinda basu fahimta ba,ta kammala alwalar tana gab da shiga masallacin wayarta tayi tsuwwa,dakatawa tayi ta ciro tana duba mai kiran,gwaggwo asabe ce take kiranta qanwa ga mahaifiyarta,mace daya tak da ko a baya tayi qoqari wajen ganin ta taimaki rayuwarta,tana daya daga cikin jerin jama'ar da bazata mance da su ba cikin rayuwarta,gefe ta samu ta jingina da wata bishiya dake wajen bayan ta katse kiran ta kirata da kanta don kada ta cinye mata kudi,gaisawa sukayi bayan 'yan tambaye tambayen lafiyar juna da suka biyo baya tace da ita
"Indo hala bakisan malam baida lafiya ba ko?"
"Kai haba?,tun yaushe gwaggwo?"
"Sati kusan biyu kenan,har a asibitin cikin gari ya kwanta,amma alhamdulillahi yanzu jikin nasa da sauqi an sallamoshi yau kwana uku yana gida ma"
"Ayyah,Allah ya sawwaqe ya bashi lafiya,in sha Allah zan shigo garim cikin qarshen satin nan,kiyi masa sannu kafin na iso"
"Zaiji,saikinzo Allah ya kawoki lafiya"
"Ameen gwaggo na gode,ki gaishemin da su lami"
"Zasuji" daga haka ta kashe wayar ta maidata cikin jakarta tana sauke ajiyar zuciya,ta tabbata ba don gwaggwo asaben ba babu lallai tasan da rashin lafiyar malam din,ta rasa wanne irin baqin abu ta aika har baqin jini yake bibiyarta wajen danginta na uwa da uba?,me tayi musu haka da kowa ma bai damu da rayuwarta ba?,a hakan ma takan iya cewa alhamdulillah da yadda ta tsinci kanta a yanzu akan shekaru kusan bakwai zuwa goma baya da suka shude,wanda abun yayi tsananin da har bata marmarin tunawa?,saidai har yau akwai wawakeken tabo da gibi cikin rayuwarta wanda batasan ranar da wannan gibin zai cike ba,batasan randa wannan babban jigon zai rabeta ba,batasan yaushe zai waiwayo ya dubi rayuwarta duba irin na idon rahama ba kaman yadda sauran 'ya'ya ke samu daga wajen uwayensu,da wannan tunanin ta qarasa cikin masallacin ta tada sallarta.
🧶🧶🧶🧶
Cikin nutsuwa ya kammala sanya maballan t.shirt dinsa wadda kudinta ya kama naira dubu biyu ita da wandon jeans dake jikinsa,har ya dauki turarensa zai fesa sai ya tuna,maidashi yayi wajensa,ya sake miqa hannu ya dauko wani daban wanda kallo daya zaka masa ka qiyasta kudinsa bazai wuce naira dubu guda ba idan yayi wuta ya fesa a jikinsa,duk da qarancin kudin turaren kuma bai cikin jinsin irin turarukan da yake mu'amala da su amma hakan bai hanashi jin dadin qamshinsa ba,saboda turare ne sanyi dake fita a hankali ba tare da ya daga hankalin wanda yake shaqa ba.
Gaban mudubi ya qarasa yana duban kansa,sai murmushi ya subucewa fuskaraa,duk da arhar kayan amma sun masa kyau
"Gwanjo" ya fada yana shafa gaban rigar dake jikin nasa zuwa saman cikinsa,yana tuna can wani lokaci baya daya shude,wani zamani da yayi tafiyar ruwa da dukkan farincikin rayuwarsu,wani qarni wanda basu taba tsammanin zaya wuce babinsa ya shafe kaman bai taba wanzuwa ba cikin littafin qaddararsu ba,tunanin ya saka ya zarce da sake gyara sumarshi da tayi matuqar yi masa kyau.
Kafin ya kai ga aje comb din hannunsa aka turo qofar dakin hade da sallama,mahmoud ne ya shigo idanunsa na kan khalipha,daga gani tambayoyi ne fal cikin qwaqwalwarsa wanda tun kafin ya zauna ya jefo masa daya
"Me haka ne malam?,ban fahimceka ba" juyawa yayi yana ci gaba da gyara kansa kafin ya bashi amsa
"Na zaci shigata kawai ta isa ta baka amsar abinda yake faruwa ko?"
"Wai har yau baka haqura ba?,baka kuma daina ba?" Ajjiye comb din yayi ta tako kusa da mahmoud din ya dauki qaramar vivo din dake aje kusa da shi ya bude bayanta ya soma qoqarin sanya mata layi
"Na sake haduwa da wata,kuma na fuskanci kaman wannan karon ina tare da nasara" dariya sosai mahmoud din ya bushe da ita harda kwantar da gadon bayansa saman gadon khaliphan,san dariyar mahmoud din bata dameshi ba saima yunqurin kunna wayar da yake bayan ya kashe nashi tsadaddun guda uku ya jefa cikin wata 'yar kyakkyawar briefcase dake nuna alamun da ita zai fita
"Me yasa kake wahalar da kanka ne babu gaira babu dalili my man.....ka saki kudi kawai ka auri duk kalar macen da kakeso kada ba jinsinka bace ba 'yar qasarka ba,kowa ya sani cewa mata yanzu kudi kawai suke so,mai kudi suke nema koda baida hali koda bai cancanta,koda ba saurayi bane koda ba kyakkyawa bane,koda jahili ne,to bare kai da babu abinda Allah bai baka ba,c'mon muhammad khalipha ka aje wannan game din a gefe ka fuskanci reality,ba irin matan da kaketa serching a yanzu,baka gani duk inda ka soma farauta daga qarshe sai kaga no signal?".
Hannu yasa ya dauki briefcase dinsa tamkar bada shi mahmoud ke magaba ba ya doshi qofar fita ba tare da yace masa ci kanka ba,hakan ya sanya shi miqewa da dan tsallensa ya biyo bayansa,saidai bai sake biyo ta kan wancan maganar ba ya sauya topic,yasan ko yaci gaba ma ba amsa zai samu daga gun khaliphan ba
"ka rakani mu shiga na gida anni"
"Daga nan ni sai inda na nufa,idan ka fito daga wajenta ka kwashe su jibril duka ku wuce kamfani na tadda ku a can,ni da mota daya zan fita,bana buqatar gayya" ya fada yana gaba yana ci gaba da dubo lambar sabuwar budurwar tashi don ya sanar mata da tahowarshi.
Yana fita duka suka taso inda yake,da hannu ya tsaidasu kafin ya daga kai ya dubesu
"Mota daya ta isheni da driver,zaku jira mahmoud tare zaku tafi,zan taho daga baya" kai auka jinjina suna janyewa,yayin daya bude motar da kanshi ya shige gidan baya,drivan motar ya shiga ya tasheta suka bar harabar makeken gidan.
Layuka biyu suka rage kafin ya qarasa layin gidan nasu ya bashi umarnin ya saukeshi ya kuma jirashi a nan,ba musu ya tsaya kaman yadda ya umarceshi,ya bude ya fice.
Sannu a hankali yake takawa,shi kansa yana jin dadin takawar da yake,saboda ko banza ya motsa gabbansa,ba kamar baya ba da motar ita ta zame masa qafafunsa,sauqin abun daya bai da lalaci,duk safiyar duniya sai ya shiga dakin dake bangarensa,wanda ke cike sa nau'in qarafuna da na'urori na motsa jiki da qara lafiya.
Plashing yayi bugu biyu ya katse,shi kansa sai da dariya ta subuce masa
"Shame on you khalipha,wai yau kaine da yin plashing,Allahu yahdik" ya furta a zuciyarsa yana sakin murmushi gami da ranqwashin tsakiyar kansa,fitowarta ita yasa ya maida hankalinsa ga qofar gidan,tayi kwalliya sosai cikin atamfarta
"Sannu da zuwa" ta furta tana wuwwulga ido kaman mai neman wani abu,amma sai ta basar saboda jin kanta da take a mace mai aji
"Yauwa barka da fitowa"
"Ina kuma abun hawan yau?" Ta tambaya kai tsaye tana dubanshi,wani abu mai kama da mamaki yaso mamayarsa amma sai yayi hanzari kau da shi yace
"Kinsan qarfen nasara bashi da tabbas,yau yaqi tashi kawai sai na yanke na taho a na haya"
"Kan bala'i,ana wata ga wata" ta furta qasa qasa,sarai ya jita amma sai yace
"Na'am,me kika ce?"
"Babu komai,shigo daga ciki" ta fada ranta a alamun bace,bai musa ba yabi bayanta har setting room din gidan,duk da cewa ba baqonsa bane gidan da zuwanshi kusan na uku kenan,kallon farko zuwa na biyu zaka yankewa maxauna gidan ajin rayuwar da suke ciki,ba alamun suna cikin talauci,dukkan wata alama ta rufin asiri akwaita a gidan,kaman yadda ya tsammaci akwai tarbiyya gwargwado gidansu khadijan.
Nan ta masa sauki ta gabatar masa da abun motsa baki kamar kullum,saidai abinda ya fuskanta abinda aka kawo masa jiya idan ya sake zuwa yawansu da tsadarsu kan ragu,idan cake da doghnout da lemo yaci to zuwa na gaba doughnout da lemo kawai zai samu,yasan bai taba baiwa khadijan komai ba,haka itama bata taba roqarsa ba,saidai amma ya lura duk sanda sukayi sallama zai tafi ba tare da ya miqo komai ba yakanga bacin rai qarara a fuskarta,har idan ya koma gida ya kirata da zummar gaya mata ya iso bata dagawa,saidai duk ya share wannan bai sanyashi a babin komai ba.
Tun kafin aci talata da laraba a hirar tasu ta gyara zamanta tare da sake lanqwashe murya
"Ammm....dama muhammad akwai maganar da nakeso muyi"
"Ina saurarenki" ya fada yana harde qafafunshi waje guda tare da zuba mata idanunsa,haka nan taji ya mata kwarjini,abinda take yawan tunani kenan,me yasa yake yawan cika mata ido,wanda wannan dalilin yasa tun zuwansa na farko dana biyu data fuskanci ba kalar wanda take lalube bane ta kasa masa bayani,janye qwayar idanunta tayi cikin dakiya tace
"Dama.....biki zamuyi na wata qawata,so an fidda anko nakeso ka yimin" janye yatsansa dake saman lebansa yayi ya dan motsa jikinsa kadan sannan yace
"Kaman nawa ne kudin how much?" Sai da tayi rolling qwayar idanunta sannan tace
"Dubu talatinma is enought,idan son samu ne kuma 40k" murmushi ya qwace masa saidai iya shi da zuciyarsa,ba kudin data tambaya bane suka bashi mamaki don ba matsalarsa bane,don a yanzun haka akwai ninkinsu a wajensa,wanda ya fito da su ne yau dan ya mata kyauta matuqar ta sake tsallake yau din bata nemi komai daga wajensa ba,mamakinsa shine yadda yarinya budurwa da bata rasa ci sha da sutura daga gidansu ba take iya duban qwayar idon namiji ajnabinta ta roqeshi kudin da zata dinka suturawa jikinta haka kanta tsaye ba kunya,tamkar ta bashi ajiya ne,kai yake kadawa a hankai zuciyarsa na gaya masa bata gama cin jarabawa ba ba shakka
"Ya naji kayi shiru ne?" Ta tambayeshi tana dan bata rai gami da fiddo ido waje
"A'ah babu komai,kawai....gani nayi kudin basuyi yawa ba?" Tsaf ta dinke girar sama da qasa
"Just 30 to 40k dinne sukai yawa?,ko iyawa ne ba zaka yi ba?,thank god da ba'a gaban qawayena bane da nake cika musu kanka da naji kunya" murmushi ya saki yana miqewa tsaye
"Ba zakiji kunya ba in sha Allahu zan shiga na fita,amma sai kin danmin haquri kadan kinsam abinka da almajiri mai nema"
"Ba damuwa indai zasu samun,amma kar su wuce nan da one week don Allah" ta qarashe maganar a shagwabe,kai kawai ya iya jinjinawa mamaki na kasheshi,haka tayi masa rakiya har qofar gida yau cike da kulawa sannan ta juya ta koma,shi kuma yaci gaba takawa yana juya abinda ya faru tsakaninsa da khadijan har ya isa bakin motar,wanda tuni driver ya bude masa ya shige shi kuma ya maidata ya rufe sannan ya shiga mazauninsa ya tada motar suka bar unguwar.
"Ashe duk kanwar jaa ce?" Ya fada qasa qasa cikin sigar tambayar kansa da kansa bayan ya ciro sabbin kudaden dake aljihunsa ya qare musu kallo ya watsasu cikin wata ma'ajiyar dake motar ya maidata ya kulle yana sauke ajiyar zuciya,kansa ya shafa sau biyu yana kiran sunan Allah sannan ya maida idanunsa ya lumshe yana aje numfashi
*DAURIN BOYE*
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
HASKE WRITERS ASSO
(home of expert and perfect writers)
0⃣5⃣
A hankali take takowa bayan fitowarta daga kitchen dauke da babban tray data shiryo abincin daddy a kai zuwa inda yake zaune yana faman rubuce rubuce cikin wasu takardu,yayin da gimbiyar tasa hajiya sa'adatu mommy ke zaune gefanshi cikin kwalliya tana aikin duba tashar da zata dace da kallonta.
Duk da yawan ma'aikatan dake gidan hakan sam bai damu ayshatu ba ko ya tsone mata idanu,takan bata lokaci aduk sadda take da dama tayi girkin da zata ciyar da mutanen gidan,musamman daddy mutumin dake da qima a idanunta,mutumin da take masa kallon mahaifi,kai tana iya cewa abinda yayi mata ko mahaifin da yayi silar kawota duniya baiyi mata shi ba,don ba zata iya cewa yau ga dadin da mahaifi yake da shi ba.
Gabansa ta aje tray din cikin nutsuwa a ladabce,ya dan daga kansa ya dubeta fuskarshi washe da fara'a
"Sannu indon baffale" murmushi ta saki saboda kiranta da wani suna daya shude can baya cikin tarihin rayuwarta,sai ta duqad da kanta ta koma can baya ta rabe daura da momy,tana jira ya bata dama ta sanar masa tafiyarta qauye da takeso tayi gobe asabar ta dawo litinin tunda bata da makaranta ranar litinin din.
Asma'u ce ta fito daga dakinta sanye da dogon wando da riga 'yar qarama mai gajeran hannu,sai ta dora top wadda takai har saman gwiwarta,kunnenta sanye da earpiece kaman yadda yake kusan al'adarta kenan ko da yaushe,kanta babu dankwali sai yalwataccen gashinta mai tsaho dake fake cikin ribbom,a shagwabe ta qaraso gaban iyayen nata ta zube a gaban daddyn
"Daddy....tun shekaran jiya ka dawo har yau zuwa fa banga alqawari na ba"
"Hmmm,bake kadai ba,nima shiru nake ji har yau ba'a cemin komai ba,safina ma tayo waya tana jira amma duk daddy ka mana shiru"inji mummy sa'adatu ta fada tana ci gaba da sauya tasha,takaddun ya tattara gefe daya kana daga bisani ya cire gilashin idanunsa yana murmushi
" kowa sai daya min qorafin saqonsa shiru,ayshatu ce har yau banji ta fadi komai ba"murmushi aysha tayi tana sadda kanta qasa,ita awa?,wanne saqo ma ta baiwa daddyn?,iya alfarmar da ya yiwa rayuwarta kadai ta isheta har abada,ta gefan asma'u kuwa fuska ta kwabe tana dan bata rai,ta tsani daddy ya dinga hada yarinyar da su sam,tana ganin bata cancanci jerawa da su ba,yayin da hajiya sa'adatu ta dan tabe baki gami da dauke kai a fakaice,wanda ba kowa bane zai kula da hakan,bai sake cewa komai ba ya kira waya ya bayar da umarni,cikin mintina biyu daya daga cikin amintattun yaran gidan ya shigo jaye da akwati da kuma wata babbar jaka ya dire a falon ya juya ya fice.
Saukowa yayi qasa carfet din ya janyo jakar ya soma kici kicin zugeta hadi da fadin
"Ai gwara na sallameku na huta kada ku cinyeni danye" dukkansu sai da sukayi dariya,kasancewarsa mutum mai barkwanci a wasu lokutan,amma fa idan ya murde sam bashi da dadin sha'ani.
Wayoyi ya fito da su guda biyu irin wanda asma'un ta zaba tace tana so iri daya sak komai da komai,wayace sabuwar shigowa mai dan karen tsada da kyau ya miqawa asma'un,cike da murna da zumudi ta amsa tana jujjuyata ranta fari qal,saidai tuni murnarta ta koma ciki sanda taga ya miqawa aysha irin tata wayar sak,farincikin dake kan fuskarta ya koma bacin rai,ya sake fito da wasu dogayen riguna masu azabar kyau guda shida ya raba musu uku uku,cikin sanyin jiki da fargaba aysha ta miqa hannu zata amsa,yayin da idanunta ya sauka kan mommy da asma'u,mommyn dai ta share kaman bata gani ba,yayin da asma'u idanunta ke kan ayshan,haka ta amsa cikin sanyin jiki tana jerama daddyn godiya da addu'ar Allah ya qaro budi,wasu kayan ya sake fitarwa ya turawa mommyn yana cewa
"Ga kayan su safina nan,saiki san yadda zaki gobe ki aika musu da saqonsu nima na huta"
"Tohm" ta amsa wanda ga duk wanda yai tsai da hankalinsa zai fuskanci ranta a bace yake,muqullin mota sabuwa dal ya ciro ya miqa mata yana fadin
"Ga taki tsarabar saiki barni na sarara" sai a sannan fuskarta ta washe ta koma kaman da,cike da murna tasa hannu biyu ta karba tana masa godiya
"Ta wajenki saiki barwa su asma'u da aysha su ajje tasun ko?"
"Kan uba" kalmar data subuce daga bakin asma'u,motar data jima da ciwa burin daddyn nata yasa mommy ta bar mata shine yanzun zaice wani wai ita da aysha?,wallahi ko sama da qasa zasu hadu ba zata yi sharing motar nan da ita ba
"Me kike fada asma'u?" Daddyn ya tambayeta yana mai zuba mata ido don yaso yaji kalmarta ta farko
"A'ah mamaki nake daddy,mun gode Allah ya qara budi"
"Ameen" ya fada yana rufe jakarsa,aysha na gefe baki daya a takure
"Alla ya qaro arziqi daddy mun gode,Allah ya saka da alkhairinsa" ta furta a sanyaye
"Amin aisha....amin" ya fada cikin jin dadi,a tajure take,saboda ji take kaman idanun mommy da asma'u na kanta har yanzu,hakan ya sanya ta miqe tare da fakewa da cewa zata duba farfesun naman kan ragon da takewa mommy a kitchen tayi shigewarta kitchen din,zamanta tayi a can tana duba farfesun tare da sake gyara freezer din da suke zuzzuba kayan girke girke da suke da saurin lalacewa har naman ya nuna,zuwa sannan bata jiyo muryar kowa a falon,hakan ya tabbatar mata sun bar gurin kenan,don haka ta juye naman a warmer ta gyara wajen ta baro kitchen din.
Asma'u kadai ta taras ta nutse cikin kujera,idanunta saman t.v saidai ba ita take kallo ba,ta cika tayi fam,ta soma gajiya da yadda daddyn ke dai daita da 'yar qauyen yarinyar a komai nata,da kafin zuwanta duka batasan irin wannan ba,ita kadai ta rage a gabansu sai abinda ta zaba ake mata,komai nata daban yake ba tare da an hadata da kowa ba,kallon baqin ciki tabi aysha da shi wadda ta giftata ta nufi dining ta dora warmer din.
Tana saukowa daga wajen mommy na shigowa falon,cikin hanzari asma'u ta miqe ta gyara zamanta sosai cikin bacin rai ta soma fada kaman zata saki kuka
"Yanzu fisabillilahi mommy ni an kyauta min kenan?,babu dama nace ina son abu sai daddy ya hadani da yarinyar nan,yanzu kaman ni ace in saka kaya iri daya da nata,na riqe waya irin tata,mu shiga mota daya tayi driving nayi,mu shiga makaranta a gani ai wallahi sai friends dina su rainani" mommyn dake shirin zama nan wajen tace
"To ya zakiyi husna,sarai kinsan halin mahaifinku,idan yayi niyyar abu babu kai hanashi" ta sake narkewa kaman mai shirin fidda qwalla tace
"Ni wallahi na fahimci kawai daddy ya shurya zubda min mutunci na da ajina,ke ba sai kiyiwa tufkar hanci ba mommy,gaskiya bazan yarda ba nidai kawai ki karbi wayar kya siya mata wata,koni na saka hamid ya kawo mata dai dai ita daga kamfaninsu tunda sun fara qananun wayoyi daga 50k zuwa sama"
"To ai shikenan indai kinsan zaki kawo mata watan,banson ne daddynku ya fuskanci bata hannunta ya daga ma mutane hankali....aysha" mommy ta qwala mata kira wadda ita tuni har ta isa dakinta ma tana shirin daura alwala tayi shafa'i da wutiri,sai ta fasa ta fita kiran mommyn
"Wayar da daddynku ya baku dazu zaki kawomin na ajjiye miki wajena,za'a kawo miki wata wannan bai kamata ki fara amfani da irinta ba tun yanzu" cike da rashin damuwa ta nunawa mommyn inda kayan suke,don tunda aka soma dramer tasan akwai abinda zai biyo baya shinyasa ma bata debe kayan ba,asma'un ita taje ta birkita kayan ta dauko wayar tana jifan ayshan da harara kamar ita ta cewa daddyn ya aikata hakan ko tana da masaniyar zai aikata din
"A'ah dawo ki debi sauran kayan mana ya zaki barsu nan?" Mommy tace da aysha wadda take niyyar komawa dakinta,bata ce komai ba ta dawo ta kwashesu tana fadin
"An gode".
" ke kawo....zonan mu ga"asma'u ta fada cikin hargagi,ba musu ta dawo da baya ta sake zube kayan a gabanta,hannu ta saka ta bibbirkita ta ciro doguwar riga guda daya wadda bata da kalarta cikin wadda daddyn ya raba musu,gefanta ta jefa tana cewa
"Jeki wannan ta yimin,kamar ma tafi tawa tsada,ina da wata idan na shiga daki zan dauko miki a amadadinta" Tsaki asma'u taja bayan ayshan ta shiga dakin
"Rigima ce fa kawai irin ta daddynku,ita kanta yarinyar na fuskanci rayuwa bata dameta ba,yarinyar data taso a qauye saika dinga siyan kaya na manyan kudi kana bata,harda abinda batasan darajarsa ba ma....miqo min wayar" mommy ta fada tana miqawa asma'u hannu,saita noqe
"Namecy zan bawa ita mommy please" dan zare ido mommy tayi
"Ke bana son sakarci bani nace" cikin shagwaba tace
"Habba mana mommy,kinsan 'yar waye ne cikin garin nan?,wallahi nasan na bata wannan wayar as a gift ba qaramin daga min aji kyautar zatayi ba" harara mommyn ta watsa mata
"Yar banza,sai shegen son suna da tara qawaye"
"Thank you my mommy,i love you so much" ta fada tana tsalle hadi da faduwa saman kujerar cikin farinciki,ta tabbata gobe zatayi abunda kowacce saita kalleta cikin qawaye,haka nan husna zata sake ganin darajarta da yadda da irin kudin nasu gidan,duk da qawaye ne amma gasa ce sosai a tsakaminsu,kowacce so take tayi abinda zata burge daga,kowacce so take 'yar uwarta taga ta fita,kowacce so take ta ganta itace a gaba ta baro daya a baya,su kansu basu san cewa abota suke mara ma'ana ba,har hassada da qyashi da kishi ya shigo cikin tarayyarsu yayi kane kane ba tare da sun sani ba,abu daya ne ya hana mommy amshe wayar jin cewa 'yar wani za'a bawa,kasancewarta mace mai son mu'amala da manyan mutane,tana son a ganta tana mu'amala da wani,wanin ma da yayi suna ya kuma shahara,haka dabi'arta take a jininta take,kusan ba'a qasa yaranta suka dauki wannan dabi'a,za'a iya cewa duk cikinsu mutum daya ce ta banbanta da su,halayenta kusan irin na mahaifinta ne,hakan ya sanya babu jituwa ko alaqa mai qarfi tsakaninta da asma'u,saboda banbancin ra'ayi da hali.
A hankali yake kurbar lemon dake cikin tambulan din qarau na glass sake gabanshi,yayi kyau cikin shigar da yafiyi shigar suit musamman idan ranakun aiki ne,yanayin zamanshi a wajen da yadda yake kai lemon bakinsa lokaci lokaci kadai ya isa ya gaya maka nutsuwar da yake sa ita uwa uba aji da kyau da Allah ya bashi,kusan babu budurwar da zata shigo wajen bata kalleshi ba,masu rawar kan cikinsu kanyi sha'awar dosar sa su taya hajarsu saboda alamun malasa da suke hangowa tattare da shi,saidai basu iya qarasawa saboda kwarjinin da yake da shi suke karya kwana su sauya hanya.
Agogonsa ya sake dubawa ya yarfar da hannu gami da jan tsaki,banda haduwarsu da mas'ood yau ta zama dole baiga abinda zai sashi zaman wajen ba,sam wajen baiyi masa ba,akwai yawaitar cakudedeniyar maza da mata abinda yafi tsana,yana da kishi qwarai duk da cewa kuwa baida qanwa mace,a zahiri zaka ce bai damu da motsin dake faruwa a wajen ba,saidai a badini yana zaune ne yana sake.nazarta da karatun halayyar 'yammatan zamani,abubuwa da yawa sun faru da suka bashi mamaki suka kuma sake sa mishi tsanar zaman wajen,yana mamakin yadda yammatan ke shigowa,wata tsakiyar maza biyu wata namiji daya,ba wani kunya ko takatsantsan da aka san diya mace da ita,ta zauna cikinsu suci abinci ko abinsha suna hira kaman zasu tafa,wasunsu ma sukan kebe can baya suje susha shisha,wanda shi a wajenshi bata da maraba da taba wiwi da sholisho,hakan take ko a wajen malaman lafiya,zuqa daya ta shishar dai dai yake da ka zauna kasha karan taba sigari guda dari biyu,yana da yaqinin mafi yawansu ba nan suka cewa iyayensu zasu ba,suna iya qarya da sunan mabanbantan wurare da sunan cewa can suka nufa,su binne iyayen har su zo su koma basu fuskanci komai ba.
Dogon tsaki ya kuma ja yana niyyar dauke kanshi wata mota ta shigo wajen,hakanan yaji ta dauki hankalinsa,bawai don kyanta ko bai taba ganin irinta ba,a'ah,hasalima shekararsa uku da hawanta,duk da ba ita yake kallo kai tsaye ba amma hankalinshi na wajen.
kaman a mafarki yaga khadija na fitowa daga gaban motar bayan matashin dake tuqa motar ya zagayo ya bude mata,yana iya ganin sanda ta sauya hijabin jikinta da mayafi sannan ta fito,tare suka jero har zuwa kan daya daga cikin kujeru da teburan dake wajen suna wa juna magana.
Sosai mamaki ya kamashi,don bai tsammaci ganinta a ire iren guraren nan ba tare da wani namiji,da kuma shiga irin ta jikinta,aljihunsa ya laluba sai yaji wayarshi da yake kiranta da ita,yaji dadin hakan,don dama ya taho da ita ne saboda yana da plan din daga nan ya leqa wajenta.
Miscal wajen hudu yana hangota daga inda yake,tana ganin kiran take dauke kanta,daga bisani ta soma tsaki,yana hango saurayin na mata magana kan ta daga,sai a kira na shida sannan ta daga din,sallama ya soma mata ta amsa da qyar tana wani basarwa
"Hala na katse miki wani abu mai muhimmanci...."
"Kusan haka ne,don bacci nake...na dawo daga makaranta na gaji ina buqatar hutu don Allah....ko kudin sun samu ne?"
"A'h...muryarki dama kawai nake da muradin ji"
"Ohk....idan sun samun zaka iya kirana saika gayan ranar da zaka zo" ko kafin ya kashe tashi wayar tuni ta datse nata layin,yana iya hango yadda take yatsina fuska sannan daga bisani ta wurga wayar jaka ta sake tattara hankalinta ga saurayin.
Yana shirin dauke idanunsa ya hangi sanda ya amshi jakarta ya saka mata kudi a ciki,kanshi ya kawar sannan ya miqe tsaye bayan ya ciro wayarshi yaba laluben number mas'od ranshi a bace,shi yasa ya tsani jira,badon mas'ood din ya tsaida shi da alqawarin yana hanya ba da bai zauna wajen har idanunsa sun gane masa abinda ya gani din ba
"Afwa boss,afuwa don Allah"
"Is too late....nayi cancel schedules dina na yau na zauna jiranka duk da muhimmancin da lokacina yake da shi.....saidai wani lokaci kuma idan na samu chance....na kiraka ne na gaya maka karka qaraso baka kuma sameni ba" ya qarashe fada yana shigewa bayan motarshi da jibril ya bude masa sannan ya kashe wayar ya ajeta gefanshi,idanunshi na kansu har sanda driver ya soma jan motar suka soma barin wajen,idanunsa ya lumshe sanyin A.cn dake cikin motar yana ratsashi,sosai zuciyarsa na zafi...dukkan wani hope nashi yana sake raguwa sosai fiye da kowanne lokaci,sunayen Allah yake jerowa daya bayan daya cikin zuciyarshi kamar yadda ya saba duk sanda yaji bacin rai,bai yadda ya zauna zuciyarshi na soyuwa hakanan ba tare daya kira Allah ba.
*mrs muhamma ce*👑*D B*
*0⃣6⃣
*Wannan littafin na kudi ne meso ya karanta ya nemi wannan number 08030811300*
Washe gari ita mommy ta baiwa tsaraban yaran nata dake aure ta hadata da driver ta kai musu,duk da cewa tana da makaranta amma ita sam wannan ba matsalarta bace,damuwarta shine ta idar mata da nata aiken koma ya zatayi ba matsalarta bace,hakan ya sanya a gurguje taje ta miqa musu,ba wani zama tayi ba,ko dama can ba wani sabo ke tsakaninsu ba,tsakaninsu da ita idan bautarsu da tashi,gidan anty safiyya kawai ta dan zauna har ta sha ruwa,kasancewar duk ta fisu sakin fuska da janta a jiki.
Ranar bata shigo gida ba sai qarfe biyar na yammaci,duk da haka bata zauna ba sai data shiga kitchen ta shiryawa daddy abincin dare da taimakon inna laraba,data gama dinma dai ba zama tayi ba,kayanta ta soma hadawa wanda zata je gida gobe da su,tsaf ta shirya kayan nata cikin matsakaiciyar jaka,kaman yadda ta saba ta tsinci wasu daga cikin kayan nata ta zuba daban da niyyar yin kyauta da su kaman yadda ta saba.
🧶🧶🧶🧶
Tafe suke shida drivansa cikin motar tasa baqa wul,wadda kallo daya zaka mata kasan ba qananun kudi aka sanya aka sayeta ba,yana lafe bayan motar sanyin raba na kadashi,sanye yake da suit suma baqaqe wadanda suka dace da kalar fatarshi wadda ainihin hutu da jin dadi suka ratsashi,dirarsa kenan cikin qasar,wanda a yanzu haka yana hanyarsa ne ta isa gida,lokaci lokaci yakan lumshe kyawawan idanunsa dauke da zara zaran gashin ido,hakanan yake jin kasala da gajiya sun masa dabaibayi,Allah Allah yake ya isa gida yaga anninsa ya kuma kwanta ya huta.
A hankali qaramar wayarshi da bai wuce mintuna goma da kunnata ba ta dauki qarar qaraurawa,ko bai daga ba yasan wacece,ita kadai zata kirashi ta cikin wannan wayar,saboda don ita kadai ya saka layin ciki,hakanan daya bude yaci karo da tarin saqonninta tun na kwanaki bakwai da suka wuce,wato kwananshi biyu kenan da barin gidansu,kwana daya kuma da ganinta da yayi a wancan eatery din,wanda yayi dai dai da tafiyar data kamashi zuwa china sai a yau ya samu dawowa,a kasalance ya saka hannu ya daga wayar gami da karata a kunnesa
"Na gode da wulaqancin da ka yimin,duk ni na saiqa kaina koma meye ka yimin khalipha" idonsa ya sake lumshewa ya bude yana jin yadda taratsin maganarta ke ratsa kwanyarsa
"Afwan dija na"ya fada cikin qarfi halida danne bacin ranshi a kanta wanda ya haifar da sanyi a muryarsa,sanyin muryar da ta kashe mata jiki tare da sauke kaso hamsin cikin darin bala'in data so yi
"Ni baka da abinda zaka gayamin,wannan wanne irin cin fuska ne,tun ranar da kazo gidanmu na qarshe gaba daya aka daina samunka a waya,kuma kai baka neme ni ba,haka ake soyayyar?"boyayyen murmushi kawai ya saki,shi yasan ba wannan ne maqasudin fadanta ba,a baya bata taba nemansa ko damuwa da duk kwanakin daya dauka baije gidansu ko ya nemeta ba,idan ya nemeta falillahil hamd,idan ma bai nemeta ba duk daya wai mamaci ya karye
"ai nace kiyi haquri ko?,wayar tawa ce ta samu matsala,sai yau na samu na karbo daga wajen mai gyaran" ya qarshe maganar yana istigfari cikin zuciyarshi,daga can bangaren khadija dummm tayi,tana sake ji cikin zuciyarta da jikinta lallai muhammad din bai dace da ita ba sam,baiwar kyau kawai Allah ya masa,wanda bazata bari kyansa ya rudeta ba ta shiga gidan da bashi take da buri ba,wanne irin gyaran waya fisabillilahi,wayar tashi da ko tata wayar ta fita tsada,don ranar farko data fara ganin wayar sai data sake kallonta,gaba daya ba zata wuce dubu goma ba
"Kawai ka fadi me ya hanaka dawowa,ko babu waya ai qafafunka zasu iya kawoka,ko kudinne ba zaka iya bani ba shi yasa ka janye jiki?" Maganarta ta bashi dariya,baisan murmushin da yayi ya fito fili ba sai data ce
"Dariya na baka?" Cikin waskewa yace
"A'ah....ba haka bane,gani nayi kin kusa canko abinda ya hanani dawowa.....kawai dai kudin ne basu samu ba,kuma ina kunyar nazo miki haka" ranta yayi qololuwar baci,a haka zata aureshi?,mutumin da ya kasa mata kyautar naira dubu talatin kacal ina zai samu kudin aurenta,a gabanta kowacce cikin qawayenta suka dinga karbar alert na kudade daga samarinsu,mai qaramin kudi cikinsu itace wadda aka turowa dubu talatin,sai ita zata tashi a tutar baya?
"Kana nufin duk jiran da nayi ya tashi a banza kenan bazan samu ba?" Sake gyara kwanciyarshi yayi bayan motar sanyin A.C na ratsashi,cikin kwantar da murya kaman gaske yace
"Ni bance ba zaki samu ba,ai Allah shine mai bayarwa,shike kuma azurta bawa a duk sanda yaso,ina nan ina qoqari cikin satin nan ina saka ran Allah bazai hanani ba" shiruuu tayi bacin rai na ratsata
"Ai shikenan" abinda ta iya fada kenan ta katse kiran,wayar ya cire a kunnensa yana kallonta,ya sake sakin murmushi kawai yana girgiza kai,baiyi ko yunqurin nemanta ba ya aje wayar gefanshi saboda baison sauran hayaniya hutu yake nema kuma,har suka isa gida yana tunanin rayuwa da irin darussan daya samu masu tarin yawa dangane da halayyar 'yammatan zamanin nan.
A nutse yayi sallama cikin parlourn alfarma wanda yake mallakin mahaifiyarsa,parlour ne daya wadata da dukkan wani nau'i na kayan morewa rayuwa,dattijuwa anni na zaune cikin daya daga cikin kujerun tana sauraron hadisai saga tashar talabijin ta saudi sunna tare da kallon masallacin ma'aiki da suke nuno lungu da saqonshi,a hankali ta cira kai tana amsa sallamar tashi fuskarta qunshe da fara'a,yayin da bakinta ke furta masa marhaban lale,cikin qauna irin ta d'a da mahaifi ya iso gabanta,suka shiga gaisawa cikin nunawa juna kulawa
"An dawo lpy"
"Lpy alhmdlh anni cike da nasara"
"Alhamdulillahi rabbil Aalamin" ta fada tana hade hannayenta waje daya kaman mai addu'a,kansa ya sake dagawa ya dubi saudi sunnah sannan ya kuma duban anni cikin murmushi
"Ko yaushe cikin shauqin wajen nan kike anni" murmushi ta sake masa mai sanyi irin na manyan dattijai sannan tace
"Banda abinka khalipha wannan waje ko sau nawa musulmi zaije ai bazai rabu da shauqinsa ba,ba zaiqi ya dawwama a nan ba har ranar mutuwarsa"
"Gaskiya ne,inaga ki soma shiri zan sa khalid ya shirya miki komawa can cikin watan nan,ko sati hudu kije ki sake yi" murmushi ya sake yalwata kan fuskarta,farinciki tare da alfahari da tilon dan nata ya sake mamayarta,bai wasa da duk wani abu data nuna tana muradi ko da iya kan fuskarta ya fuskanci haka,kwata kwata watanta uku cikin na hudu da dawowa daga umrar
"Ba matsala khalipha?" Murmushi ya saki
"Har abada anni ina fata mun tserewa matsala,ko sau nawa mike da buqatar zuwa ki fadi kawai,yaronki a shirye yake da ya kaiki,uwace ke da ba kowanne d'a yake dace sa irinta ba,har abada bazab manta sadaukarwarki garemu ba"
"Alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi ta timmus salihat,Allah yaci gaba da yiwa rayuwa albarka,ya tsareka ya maka jagora,Allah ya zama gatanka kaida 'yan uwanka,ya hadaka da mace ta gari"
"Amin ya Allah anni,Allah ya qara lafiya da nisan kwana"
"Amin amin" ta fada tana murmushi,ya bude bakinsa zai sake magana yaga shigowarta falon,hannunta riqe da wani kyakkyawan kwando kwanon tangaran,tana sanye cikin shadda gezner ruwan hanta wadda aka yiwa dinkin buba da ado mai kyau tun daga sama har qasa,tayi daurin zamani tare da buga kwalliya sosai,suna hada idanu ta soma jifansa da murmushi,janye idanunsa yayi a hankali ya maida kan anni yayin da take qarasowa kusa da su,ta aje kwanon gaban annin sannan ta zauna tana fadin
"Barka da dawowa ya khalipha"
"Yauwa,sannunki amal"
"An dawo lpy ya hanya?" Ta fada tana murza yatsunta kanta a qasa alamun jin kunya,ya sake dubanta ya dauke kai sannan ya miqe yana cewa
"Alhamdulillah,yasu momma?"
"Lafiyarsu qalau suna gaidaka"
"Ma sha Allah,anni zan shiga nayi wanka na huta" daga kanta amal tayi da sauri tana dubanshi
"Ya khalipha ga abinci can na shirya maka fa" ta fada a narke tana dubanshi
"Am ok,nafi buqatar na huta" ya fadi yana soma motsawa alamun zai wuce ne
"A'ah ai ba'ayi haka ba,kaje kayi wankan saita miqo maka ko a can sai kaci" cewar anni wadda bata so amal din taga kaman ya gwasale qoqarinta ne,saboda tunda ya kira annin yace mata sun taso take rawar qafa
"Ba damuwa anni" ya fada yana daukar safarshi daya cire yayi gaba.
Sai daya kashe wayoyinshi kaf sannan ya rage kayan jikinsa ya fada bandaki,mintina talatin yayi sannan ya fito,ya shirya cikin jallabiya mai gajeran hannu,yana cikin fesa turarensa ya jiyo knocking daga can qofar falonshi,ya aje turaren yana daukar wayarsa qwaya daya ya kunnata sannan ya fita zuwa falon.
Amal ce ita da mai aikin anni raliya,wadda ke dauke da kwanukan abinci,sakin qofar yayi,amal ta amshi kayan abincin daga hannun raliya ta shigo ciki,kasancewar ta sani baiso kowa na shigo masa bangare barkatai,a gabanshi ta dire kwanukan abincin a sanda yake waya da P.A dinshi,kafin ya kammala harta gana zuba masa komai ta samu gefanshi daya daga cikin kujerun ta hakimce tana satar kallonshi,ba qaramin so takewa khalipha ba,ji take kaman ta bude ido taga ya zama nata,komai nashi yayi mata,sak irin mijin data sha zanawa a mafarkinta,kyakkyawa mai qirar qarfi,mai aji mai kudi kana mai dimbin ilimi.
Hada idanu sukayi sanda ya dauki plate din data cika da fried rice da gasashshiyar kaza a gefe,daga cikin dabi'unsa sam baison kallo,a nutse yana juya abincin yace da ita
"Akwai wani abu da yayi saura ne amal?,kina iya tafiya" shagwabe masa tayi tana noqe hanci
"Haba ya khalipha,wanne irin na tafi bayan hira nakeso na tayaka?yaushe rabon da mu hadu don Allah,amma kai ko irin nunawa ma baka yiba" fararen idanunsa ya watsa mata yana tauna abincin bakinsa a hankali,sai daya hadiye sannan yace
"Indai zaman hira kika zo yi yanzu kam bazan iya ba,kinsan ban iya cin abinci ana min surutu ko?"kai ta sadda qasa
"Kayi haquri to" sai ta dan bashi tausayi kadan,banda ya riga ya gama da farke layarsu ita da mahaifiyarta bai tunanin zai iya tsallakewa tarkon ita yarinyar a yadda take binshi sau da qafa
"Is ok,kije ciki idan nayi bacci na tashi zan shigo,sai muyi hirar ko?"
"Tohm" ta fada tana miqewa tare da ficewa daga parlourn bayan ta ja masa qofar,kai ya girgiza yana ci gaba da cin abincinsa a hankali,har yau bai manta da mahaifiyarta ba wato momma zinat,har yau bai mance irin kyara tsana tsangwama da kallon qasqanci da ta dinga jifansu da shi shida mahaifiyarsu ba a wani zamani baya can da ya shude,sai gashi cikin qanqanin lokaci momma zinat din ta koma daya daga cikin gagga gaggan masoyansu,abun da mamaki da kuka daure kai a wajenshi,saida ga duk wanda baisan abinda ya faru shekara kusan goma sha biyar baya ba zaiyi zaton soyayyace daga Allah momma zinart din ke musu,da wannnan tunane tunanen ya kammala,a nan kan doguwar kujerar da yake kai ya miqe,kan wani lokaci bacci yayi awon gaba da shi kasancewar tafiyar da yayi bai samun isashshen baccin da ya kai awa hudu ko biyar
🧶🧶🧶🧶
Tunda suka shigo siririn titin da zai sadaka da ainihin qauyen nasu tunaninta ya rarrabu kashi kashi kaman yadda ta saba kowanne lokaci,ina zata sauka?,a wanne gida zata fara yada zango?,gidansu mahaifinta ko gidansu mahaifiyarta?,ko kuma gidan gwaggwo lami?,ason ranta gidan gwaggwo lami tafi sha'awar ta sauka,saidai hakan ka zama tamkar ta aikata wani laifi ne aduk sanda labarin zuwanta ya iske gidansu mahaifiyarta harma dana mahaifin nata,zasuyita mata fassara daban daban kaman yadda suka saba,duk da cewa ada bawai sun damu da rayuwarta bane,saidai a yanzun suna son nuna sun damu da rayuwar tata ko don dan qaramin alkhairin da take riqowa tazo musu da shi,wanda hakan ya dan sauya yanayin mu'amalarsu da dangantakarsu,sauyin da bai taka kara ya karya ba,sauyin kuma da bashi da wata ma'ana ko alfanu a gareta.
Itadai a baya tasan ba wanda ya damu da rayuwarta,babu wanda ya damu data rayu kota mutu,ba wanda keson ta rabeshi,kowa gani yake rab'uwarta da shi wani kayan nauyi ce,idan kuwa ya zama dole ta rabi mutum din yana ganin ya yiwa rayuwarta gagarumar alfarma ne,koda kuwa babu wani abu da yake iya tsinanawa rayuwartata
Umarni ta baiwa mai motar da ya daukota tun daga tashar takai saboda asma'u ta fice da motar da daddy ke fadin wai ya basu,wai mana tunda bata taba shigarta ba itakam,hakan kuma bai dameta ba,mommy kuma ta kasa bada koda qarama cikin motocinta biyu a kawota kasancewar babu idon daddyn,tun da sassafe ya sallameta sukayi sallama ya fita,tace drivan ya sauketa qofar gidansu mahaifinta,tunda duk tsiya da uba ake ado,yaran da sukayi tsaye gaban motar su suka daukar mata jakarta zuwa cikin gidan,sai data biya direban sannan tabi bayan yaran zuwa cikin gidan,lokaci lokaci gabanta na faduwa tare da tunanin me kuma zata taras wannan karon.
Kamar ko yaushe,kamar kuma kowanne lokaci irin wannan,dukkan matan sassa sassa dake gidan na gindin qatuwar bishiyar dake tsakar filin gidan,wadda kusan itace ta zama wajen hutawarsu a duk sadda rana ta qwalle a sararin subhana,nan ne dai wajen zaman,masu sana'a nayi,masu gulma da sa'ido ma duka suna yi,masu ayyukan gida ma duk sukan jibge a nan,wasu bisa shimfidar tabarmar kaba,wasu kan kujera 'yar tsuguno,yayin da wasu ke a tsaye suna surfe ko wani aikin ma daban,bishiya ce da Allah ya mata yalwar inuwa da kuma iska,har wani bai takurawa wani,wajen zaman ya ishesu a wadace.
Tunda aka shigo da jakarta yanayin hayaniyar dake wajen ta ragu,kowa ya maida hankalinsa kan ganin shigowarta,mata ne a qalla sun kusa su goma kowacce idanunta a kanta tana qare mata kallo,ta saba da wannan kallon tun a sanda yake muguwar guba ce a rayuwarta,balle yanzu da kaifin wannan gubar ya ragu saidai abinda ba'a rasa ba,fuskarta a washe ta zauna gefan tabarmar da tatuwa take kai ita da faccalarta karime ke kai suna irga soyayyar tunkuza wadda da alama basu jima da kammala aikinta ba,saboda yanayin maiqon dake jikin zannuwansu da rigunansu,kowacce da yanayin data amsa mata,zuciyar kowannensu da abinda take saqawa.
Tsahon mintuna tayi a cikinsu tana tattambayar 'yan uwanta dake gidajen aure da iyayenta maza wasanda dama ta tabbatar suna goba suda yaransu maza wadanda suka tasa sai qananu da aka bari a gida,matan kuwa matasan da basuyi aure ba na wajen talla,kana daga bisani ta tambayi kakarta wadda take mahaifiya ce ga mahaifinta hafsatu wadda suke kira da inna yelwa
"Tana rumfarta tana hutawa" cewar lami wadda ta maida tabaryarta cikin turmi bayan ta watsa dawar da zata surfa,tasan dama a rina,kasancewarta mace mai shegen mulki ga duk wanda ke qasanta da nuna isa,bata cas bata as cikin gidan,yawanci irin wannan lokutan tana rumfarta zaune saidai ta wurgo umarni kuma dole abi,walau 'ya'yan nata ko matansu ko su kansu jikoki.
Ilai kuwa a sanda ta daga labulen dake rumfartata sai ta sameta zaune saman tabarmar karauninta,falon nata a share qal wanda tasan aikin daya daga cikin surukan nata ne,wanda duty duty suke,qafafunta miqe abinda,haule daya daga cikin surukanta tana murza mata goro a magogin qarfe tana watsawa bakinta,bawai don bata da haqora ba a'ah da saura,tsabar mulki ne da ganin dama.
Fuskarta a sake tayi sallama yayin da inna kululu ta dago kai tana dubanta
"Hala kinji zuwan waccar uwar taki shine kika kwaso qafa kika taho,bayan kin san babu abinda zai sauya,zuwanki banza zamanki banza" sosai kalaman suka soki zuciyarta,duk da cewa ta jima tana jin ire iren wadan nan kalaman daga bakin inna kululun,saidai har yau ta kasa sabawa,ta rasa sai yaushe wannan DAURIN BOYEN zai warware?,sai yaushe komai zai gyaru?yaushe zatayi dariyar farinciki da zata ratsa har qasan zuciyarta kamar kowacce 'ya?.
Bata amsa mata ba har ta zauna gefan tabarmar da take kai tana gaida haule,ta amsa tana miqewa tare da gyara daurin zaninta da alama ta gama murza goron,kallonta inna kulu tayi
"Ki kiramin karime"
"Toh" ta amsa tana ficewa,sai data fitan sanann innar ta maida kallonta kan aysha
"Uwarki kika biyo ko?" Ta sake maimaitawa bayan ta amsa gaisuwar da ayshan ta mata,kai ta kada ranta na tabuwa
"Kibar wannan maganar inna yelwa,ni baffa nazo dubawa ance min baida lafiya"
"K'nnnnn,lallai Allah yasa da gaske kike,ya kika baro su sa'adatun,ince dai bakya musu wani mugun halin naki ko?" Ta fada tana tsareta da ido,ya ilahil Aalamina,daga durowarta?,ba'a tambayeta komai daya shafeta sai zancan su mommy?,koda yake hakan ba komai bane,abinda yafi hakan ma zata iya gani
"Suna lafiya lau,tana gaisheki"
"To madalla".
Shiru ne ya biyo baya kaman wadansu baqin juna,ita innar bata ga damar sake magana ba har karime ta shigo ta fita,yayin da ayshan ta rasa abun cewa saboda ba wani sabo bane tun fil'azal tsakaninsu,bugu da qari tunanin daya rinjayi zuciyarta ta gefe guda najin mahaifiyara dake aure a lagos wai tazo,ba zata iya tuna yaushe rabon data sanyata a idanunta ba,idan zata tuna tun sanda zata bar qauyen zuwa gidan daddy rabonta da ita,shekara aqalla kusan takwas kenan,rabuwar da har yau tana tuna yadda suka yita,a duk sanda ta tunada lokacin sai qwalla ta cika mata idanu
Ta tafi tana roqon ta kalleta sau daya,ta tafi tana kukan ta kira koda sunanta sau daya taji da kunnenta,ta tafi tana kwadayin taji tayi mata addu'a ko sau daya ne tak a rayuwarta,saidai dukka wannan burin nata bai cika ba.
Sai qarfe biyu saura ta miqe daga zaman kuramen ta rataye mayafinta ta dauki butar inna kulun ta zagaya don kama ruwa da daura alwalar sallar azahar
🧣🧣 *DAURIN BOYE*🧣🧣
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
HASKE WRITERS ASSO
(Home of expert and perfect writers)
0⃣7⃣
Bayan ta kammala sallar tana zaune saman abun salla,yaran gidan na shigowa da daya da biyu,wasu tana nan aka haifesu wasu bata nan,wasu ta tafi a sanda suke da qananun shekaru wanda zuwa yanzu sun girma,sa'anninta kuwa suka taso tare wanda taci wuya wajensu yanzu babu kowa cikinsu,kowacce tayi aure tana gidan aurenta da yaranta,duk yaron daya shigo bata rasa dan abinda zata bashi,a haka har uku na rana ta kusa ba wanda yabi ta kanta,sai bayan ukun sannan innan ta tura mata wata langa wadda ke dauke da shinkafar hausa fara qal da man gyada da yaji,ta dan soma curewa waje daya saboda tayi sanyi sanyi,bata damu ba ko dama can ita ba mai damuwa bace taja ta tsakura ba da yawa ba ta rufe kwanon,inda Allah ya taimaketa a halittarta ita din ba ma'abociyar son cin abinci bace,lamarin daya taqaita wahalarta qwarai da gaske a shekarun baya da suka shude.
Mayafinta ta rataya tare da maqala 'yar jakarta bayan tasha ruwa ta wanke hannunta tana duban innar
"Inna zan qarasa gidansu inna kulu" wani kallonta watsa mata sannan tace
"Zaki dai je ganin uwarki ko?,uwar da bata damu da rayuwarki ba" Kanta ta kada can qasar zuciyarta tana jin babu dadi,komai lalacewar uwa uwace,sam bata jin dadin kalaman dake fitowa daga bakin inna kulu ko yaushe akan mamanta,batasan wanne irin rashin jituwa bane haka a tsakaninsu tsahon shekaru tun tasowarta amma har yau bata sauya zani ba
"Bansan ma sunzo ba inna,zanje na duba jikin kawun ne" baki innar ta tabe tana ci gaba da abinda take ba tare data tanka mata ba,har ta gaji da tsaiwa haka nan taja jikinta a hankali ta fice daga dakin ba tare data sake cewa komai ba itama.
Wannan karon tsakar gidan nasu babu jama'a sosai sai yara jefi jefi,kowacce tayi sashinta masu wankan da ba'a yiba tun safe nayi,da masu shara da wanke wanke,ba zasu sake hallaraba wajen ba kuma sai bayan sallar la'asar,hakan shinya bata damar ficewa hankali kwance daga gidan ba tare data sake jin wani abu da bazaiwa kunnuwanta da zuciyarta dadi ba,tun tasowarta haka taga gidan nasu,wannan zaman dai sai an yishi a kulli yaumin.
Da gudu yaron ya biyo tayarsa da yake garawa wadda bata tsaya ko ina ba sai gaban aisha,dafe tayar tayi ta daga kanta tana duban yaron,kallo daya ta masa ta tabbatar jininsu ne,don yana kama da umminta sosai,kana dubanshi kasan daga duk inda ya fito ba waje bane na wahala,sanye yake da wando da t.shirt wadda ta dace da kayan nashi,duk da sun debi qura da jar qasa kadan sanadiyyar wasan da yake faman yi babu ji babu gani amma kana kallonsu kasan masu tsada ne,kallonta yayi sai ya dauke kai yaci gaba da gara tayarsa alamar bai santa ba,ita dinma bata sanshi ba,amma bata tantama shine yaron data ji labarin ummin nata ta haifa bayan shekararta daya da komawa gidan daddy zuwanta na farko ziyara qauyen
"Laaaa,anty indo" taji an ambata qasa qasa,waiwayowa tayi tana duban mai kiran sunan nata,wanda tasan masu kiran nata da wannan sunan wasu kebantattun mutane ne.
Basma ce wadda a qa'idance zata kira da qanwarta,saidai a zahirance kai ba zaka ce qanwar tata bace musamman a shekarun baya da suka shude,gwara a yanzun da yanayin rayuwarta data basman ta saje,mutane da dama wadanda basu sansu ba kan sheqe da dariya idan ta nunata tace qanwarta ce saboda banbancin yanayi na rayuwa da tazara mai tarin yawa a tsakaninsu,saidai a yanzu da rayuwa ta soma zuwa mata da wasu daga cikin sauye sauye zaka gasgata cewa qanwarta ce karon farko saboda yanayi na daidaikun kamanni data dan debo nata.
Fuskar yarinyar qunshe da murmushi kamar yadda fuskar aysha ki cike da fara'a ta qaraso gabanta ta kama hannayenta
"Anty indo dama kina nan?,yaushe rabon dana ganki anty?,tunda kika koma inda kike sai a dade ba'a ganki ba me yasa?"
"Inda na koma din ba cikin garin nan bane basma,kuma makaranta nake zuwa bako yaushe nake da lokacin zuwa ba....yaushe kuka zo?"tayi dukka maganar tata cikin fara'a
"yau kwananmu uku,gobe ko jibi abbu zaizo ya daukemu" cike da zaquwa tace
"Harda ummi?" Kai basma ta kada
"Harda ita,tana cikin gida ma,shigo muje ki ganta"ta fada tana dan jan hannun ayshan, faduwar da gabanta yayi shi ya tilasta mata lumshe idanunta kafin daga bisani ta budesu,Allah ya sani tana sonta,tana son ganinta,tana son ta rabeta,amma bata san me yasa duk bata da wannan damar ba,batasan me ya haifar da wannan babban gibin da baraka dake tsakanin dangantakarta data mahaifiyarta ba da kuma gidansu mahaifinta,a hankali ta bude idanun ta dafe hannun basma dake cikin nata
"kije zan shigo,kinsan me zai biyo baya idan ta ganmuntare aiko?" Fuskarta a bace ranta a hade ta kada kai
"Shikenan,amma don Allah anty karki koma ki shigo din"
"Yanzun nan kuwa kada ki damu,zan leqa gidan mero ne".
A haka suka rabu ta shiga layin gidan meron,tayi hakanne kuwa don tana jiyewa basma hukuncin da zai biyo baya idan ummin ta gansu tare,ba qaramin aiki bane a wajentan ta lakada mata dukan da zata ji a jikinta,tunda tun kafin takai hakan take dakuwa wajenta matuqar zata gansu tare,ko zata ga ta bata wani abu,wani lokaci idan ta tsawaita tunani kan wadan nan cakudaddun al'umaran takanji kanta tamkar zaya tsage,bata da amsa bata kuma da mai bata amsar,sai tarin tsana da tsangwama da take fuskanta aduk sanda tayi yunqurin tambayar wani makusancin lamarin kan meya faru a baya?,meye sanadi?,mai ya haifar da haka,wasu sukanyi gaba su barta a nasu tunanin tasan komai,tsabar rainin wayo ko wahala ce ta soma taba qwaqwalwarta,da wannan tunanin na tsohon shafin rayuwarta ta qarasa gidan qawarta ta quruciya wato mero.
Cikin farinciki suka rungume juna ita da mero,da qyar suka samu wajen zama kowa na zumudin ganin dan uwansa,abota ce da ba zasu taba mantawa da ita ba,abota ce data yiwa aysha rana,abota irin wadda ta kasa samunta daga yan uwanta a wancan lokacin
"Indo....ashe komai na rayuwa mai wucewa ne...kin ganki ko indo kin zama matar birni,don ma har yau babu qibar da kika qara" mero ta fada tana kama habarta,qaramar dariya aysha ta saki tana kada kai
"Mero har yau halayyarki ba zata sauya ba kenan....komai na rayuwa mai wucewa ne mero,amma banda abu guda,wanda bana tsammanin zai wuce" ta qarashe maganar fara'ar fuskarta na raguwa,da alamu maganar da take cikin zuciyarta ta taba ranta sosai,hannu meron ta aza bisa kafadar aysha tana cewa
"Ba abinda ke tabbata a duniya sai ikon Allah indo,kici gaba da sakawa ranki salama,kici gaba da sawa ranki cewa watan watarana zai zama labari tamkar ba'a yiba,umminki mutum ce kaman kowa,zuciyarta na hannun ubangiji,kuma yana da ikon sata ta sauya aduk sanda yaga dama koda bata so yin hakan ba" cike da gamsuwa take gyada kanta gami da sanya yatsunta ta dauke qwallar data sauko mata,zuciyarta na samun nutsuwa da kalaman mero
"Haka ne,na gode qwarai Allah ya qara zumunci"
"Ba wannan tsakaninmu indon baffale,yanzu mutuminki zan dafa miki ko kuwa?,yau ban dora sanwa ba a gidan nan duka yaran suna gidan gwaggwan habu shi yasa ban dafa komai ba" dariya indo ta saki saboda tuno wani abu da tayi
"Hoooo,meron habuwalle,bada kanki a sare...waima yana ina" dariya mero ta saki
"Zaku taba diramar taku ne?,yau tun safe ya tafi hungu ina jin kuma bazai shigoba sai gefin magariba,amma ai tunda kina nan zaku hadu ne" ta fada tana yunqurin tashi
"Kinga yi zamanki karki wahal da kanki,ban jima da cin abinci ba na fito" komawa tayi ta zauna tana dubanta
"Wanne abinci ko muna abinci,sun baki wannan busashshiyar shinkafar tasu da ke kika jima da yin bankwana da cin irinta,ni bansan meke damun jama'ar gidanku ba,ga arziqin abinci gar abinci amma su basu raba kansu da cimar da kowa cikin karkarar nan ke fatan bankwana da ita ba" dariya aysha tayi kawai tana jin mitar mero,itadai indai aka taba indo tofa za'aji kansu da shi koda waye ma,zata iya cewa su biyu ita da aliya bata taba samun soyayya kamar tasu ba,tabbas idan wani ya qika wani zai soka haka rayuwa take.
Ledar data zabo mata atamfofi cikin nata ta miqa mata,ta daga tana ta murna da godiya,duk da cewa bata rasa komai gidan mijinta ba,habu mutum ne mai zuciyar kula da iyali wanda irinsa daidaiku ne cikin karkara a halin yanzu.
Sun dan jima suna hira sannan sukayi sallama da alqawarin gobe idan bata samu taje gidan gwaggwo asabe zata dawo susha hirarsu.
Tamkar mara gaskiya haka ta dinga taka dogon soron gidan kakannin nata,ba komai ya haifar da hakan ba illa tunani da zaton mahaifiyarta a halin yanzu na cikin gidan,tsakar gidan fetal yake babu kowa,bata ji motsi ko hayaniyar kowa ba,hakan shi ya sake bata qwarin gwiwar kutsa kai cikin gidan bakinta dauke da sallama,inna kulu dake qasan rumfar da suke girki ce zaune gaban murhu tana ta aza wuta bisa dukkan alamu wani abu mai buqatar wuta da yawa take dafawa,waiwayowa tayi tana amsa sallamar kafin daga bisani ta dan washe fuskarta tana fadin
"Indo....yaushe kika shigo garin?"
"Wallahi inna dazu dazun nan"
"To maraba,qarasa daki nima gani nan tasowa"
"Toh" ta amsa idanunta na satar kallon kebantaccen dakin da tasan cewa mahaifiyarta na sauka ciki duk sanda tazo garin,dakin a bude yake saidai an dan karashi hakan yasa ba zata iya gane da mutum ko babu ba da haka ta sanya kanta cikin dakin inna kulu dake falle daya dauke malale da leda da labulaye gami da lailayayyen gadon qarfe da doguwar kujera qwaya daya wanda dukkan wannan gyaran aikin ummin nata ne.
Tana shirin zama gefan gadon inna yelwan qamshin turaren ya ziyarci hancinta,qamshi ne data san cewa ba irin wanda inna kulu ke amfani da shi bane,hakan ya sanya ta soma baza idonta cikin dakin,tashin farko jikinta ya soma rawa har ta kasa hayewa saman gadon qarfen mai tudu wanda ya sha katifa,ta zame baki daya zuwa qasan ledar dakin ta zube ragwaf cikin rawar jiki,umminta ce zaune kan kujera qwaya daya dakin,sanye take cikin wani legos lace mai kyau da tsada peach wanda aka yiwa dinkin buba qarama da plain zani,hannunta sanye da awarwaro da zobe,haka wuyanta da kunneta sanye da sarqa da dan kunne,tayi fresh tayi kyau fiye da yadda ta santa ma ashekarun baya,tunda aqalla yanzu ta kusa shekara biyar rabon data sanyata a idanunta,daurin dankwalinta dai dai da zamani,idanunta na kan wayarta qirar samsung torching dake hannunta tana shafawa,cikin rawar murya ta hada lafazin
"Ina wuni ummi...." Shiru taji kamar yadda ta zata,tamkar babu wata halitta a dakin bayan ita,ko motsi ummin bata yi ba bare ta saka ran amsawarta,kai ka rantse da Allah bata san akwai halitta cikin dakin ba
"Ummi bar....ka da yamma....an yini lpy?" Ta sake maimaitawa,saidai kaman waccan karon wannan karon ma ko motsi bata yiba bare ta amsa,abu guda ne ya banbanta yanayin shigowar 'yan matasan yara maza guda biyu a guje daya yana bin daya cikin dakin suka afka jikinta suna rigima kan wani abun wasa,sai sannan ta dagonta rungume wanda ya fado jikintan tana duban babban dake tsaye
"A'ah,a'ah abba yaya?,bana hanaku irin wannan guje gujen bane wai?"
"Ummi....."
"Kul na sake jin wannan sunan a bakinka"
"Mami nawa ne fa,ya bar nashina gida tun shekaran jiya da zamu taho na sakoshi cikin trolly na,shine yanzu ya dauke yace wai nashi ne"
"Shine zaka biyoshi haka?,bana son sakarcin banza...oya maza wuce daki kaje ka canza wadan nan kayan daka bata" ta fada tana ware masa idanu,haka nan ya juya ya fita yana cuno baki,shi kuma wanda ke jikintan yana ta dariya abinsa alamun ya samu nasara.
Idanunta ta maida kan basma daketa kallon aysha dake takure gefe guda kanta a qasa tana son yi mata magana amma tana shakkar ummin tasu,tsawa ta katsa mata
"Fice a gun,kar na sake ganin qafarki tsaye a wajen nan"
"Amma mami......"
"Ubanki nace....kama hannun yusra ku wuce daki ki gyara sauran kayanku da baki gama hadawa ba" kamar zata fashe da kuka haka basma matashiyar dake da shekara goma sha hudu ta kama hannun qanwarta dake da shekaru goma suka fice,sai data ga ficewarsu sannan ta daga yasir dake jikinta ta kama hannunshi suna niyyar ficewa a dakin,sai a sannan aysha ta daga kanta tana duban mahaifiyar tata da idanunta dake cike fal da qwalla,cikin rawar murya tace
"Ummi....ki yafemin don Allah duk abinda nayi miki...wanda na sani da wanda ban san......"
"Idan kika qara yimin magana Allah ya isa ban yafe ba" ta fada cikin tsawa sannan taja hannun yasir,cike da tsantsar tashin hankali ta bita da kallo qwalla na silalo mata suka ratse inna yelwa dake tsaye da kwano a hannunta
"Kuma ga naman naki binta"cewar innar
"samin a daki na" ta fada tana yin gaba,haka nan ta juya kuwa tabi bayanta.
Sanda ta dawo har aysha ta gama cin kukanta ta gode Allah,sai tuquqi da zuciyarta ke mata kadai,muryarta a shaqe suka gaisa da inna yelwa,ta kuma tambayeta jikin kawu ta sanar mata da sauqi,ko kadan bata tada zance abinda ya wakana tsakaninta da umminta ba,wannan ba shibe karo na farko ba da irin hakan ta taba faruwa ba,shi yasa sam aysha batayi mamaki ba,inna kulu na haka ne saboda ba ita ta haifi umminta ba?,koko tana haka ne saboda alkhairin da take samu daga wajen ummin nata kada ta yiwa kanta sanadi,saboda ta sani tsaf zata yanke duk wani alkhairi da take mata matuqar zaka shiga maganar data hada da ayshan,biyayya kusan duk wanda yaga yadda take mata za'a ce takewa binta,wanda hakan kusan kowa ke ganin bai rasa alaqa da abun duniya da take samu daga wajenta,zuciya da jikinta duka babu dadi hakan ya sanya bata iya tsaiwa taga dawowar kawu ba bare ta dubashi tayi sallama da inna yelwa da zummar ta dawo gobe.
Tana tafe tana share hawaye,sam bata ka biyo ta hanyar da jama'a suke wucewa sosai ba don bata da buqatar tsayawa tayi magana da kowa,kasancewar tunaninta bai tare da ita hakan shi ya bashi nasarar shan gabanta ba tare data lura ba,sai jan baya da tayi da sauri sabida ganin inuwar mutum a gabanta ta hasken farin wata,a nutse ta qare masa kallo haqoranshi a waje kamar yadda ta sansu yana washe mata baki shi a dole fara'a
"Indo matata.....yau a gari?" Kalma mafi muni data tsana taji ta kenan daga bakin dan ladin tun a shekarun baya zuwa yau,bata taba ganin dan akuya mara kunya irinsa ba,tun a baya neman tsari take da shi balle a yanzu da ta soma samun sa'ida da sauqin wahalar rayuwa,ta kuma san inda duniya ta dosa,bata iya amsa masa ba illa ce masa da tayi
"Dan matsa min malam na wuce sauri nake"
"Haba indo,yanzu fusabilillahi ke ba zaki haqura ki karbeni a matsayin miji ba kije ku zauna tare da 'yar uwarki,naga dai 'yar uwarki ce,abu shekara da shekaru amma kin kasa haqura,duk abinda na dinga yi miki sharrin shaidan ne da zuciya" bacin ransa da wanda ta qunso ya taso ya tokareta,cikin zafin nama da zafin zuciya ta kewayeshi fuu tayi gaba,binta yaci gaba da yi yana magiya saidai banza ma ta fishi a wajenta,don sam bata masa kallon mai hankali,ta sani cewa tsantsar kidahumanci da jahilci kadai sun isa su maidashi mahaukaci tuburan,bare ga shegiyar mai saurin tarwatsa rayuwar koma waye wato qwaya da yake afawa lokaci lokaci,bata taba zaton inda yana da cikakken hankali zai iya tararta ya dubi qwayar idonta ya mata magana ba,bai qyaleta ba sai da yaga shigarta cikin gida sannan ya haqura ya juya yana jin takaicin rasa indon da yayi,tana qiyasta yadda tayi kyau ta goge da tuni yana can yana mora,yanzu gashi yana can yana fama da ladidi.
*_WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER ( 08030811300)_*
*DAURIN BOYE*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
0⃣8⃣
Kebantaccen waje ne da yake ganawa da muhimman mutanensa,wanda a siffa yafi kama da lambu.
Waje ne mai kyau daya qawatu da shuke shuke da kujeru irin na kaba,daga gefe guda wani magangarar ruwa akayi mai kama da qorama,zakayi zaton ba cikin companyn yake ba saboda yadda aka tsarashi,kallo daya zaka ma wajen ka fuskanci dan qaramin taro aka gama yi a wajen,saboda yadda grass carfet din wajen ya baci da robobin kayan ci da na sha,khalipha na tsaye cikin mutanen wanda baqi ne daga qasar waje wanda zasuyi hadin gwiwa wajen bude wani kamfani,da sauri daya daga cikin yaranshi wanda ke riqe da wayoyinshi ya matso inda yake tsaye,ya tsaya daga bayanshi kadan cikin girmamawa
"Sir,ana kiranka" hannunshi kawai ya miqa ya amshi wayar yana ci gaba da magana da mr james,vivo dinsa ce yasan mai kiran koda bai duba ba,amma duk da haka saiya duba screen din,khadija ce kamar yadda ya zata,bai samu damar daga wayar ba har sai da suka kammala maganarsu da su mr james sukayi sallama da su suka shiga motocinsu suka fice daga companyn baki daya.
Da sauri daya daga cikin yaran ya sake matsowa da niyyar amsar wayar ya adana ta,daga masa hannu khalipha yayi sanda ya danna kiran khadija sannan yaja baya jikin wasu flowers da aka yiwa ado mai kyau
"Muhammad...ni kake qin dagawa waya?" Abinda ta soma fada kenan,kadan ya cije lips dinsa kana yace
"Afwa....ina wani uzuri ne....mun tashi lafiya?"sai data ja iska kafin ta amsa masa
"Lafiya lau.....ya ake ciki ne wai?,gaskiya jiran fa yayi yawa...har yau kana nufin kudin basu samu ba?" Danne bacin ranshi yayi cikin dakiya yace yana kada kai tare da tabbatarwa kansa itama khadijan ta fadi,bata kai labari ba,bata kuma cinye jarabawar ba
"Su naketa qoqarin hadawa basu samu ba....dubu goma ce kawai ta samu" can qasa yaji ta ja tsaki tana qunquni sannan tace
"Ka kawon dubu goman na toshe wata kafar,da babu gwara babu dadi"
"To shikenan"
"Kar ka wuce qarfe hudu saboda inason in fita"
"To babu damuwa" qit ta kashe wayar,ya cirata daga kunne yana kallonta gami da kada kai,har yau dai jiya iyau,dukkansu kaman tare aka haifesu tsabar kamanceceniyar hali,ya talaka yake wanda baida komai kafin ya samu macen aure a wannan zamanin?,ya talaka mara abun hannunsa yake kafin ya samu soyayyar gaskiya?,da wannan maganar zucin ya miqawa jibril wayar,ya amsa yana miqo masa daya daga cikin kebantattun wayoyin nashi wanda kira yake ta shigowa tun dazun,bai bashi bane ganin wata wayar yake amsawa,karba yayi ya kara a kunnesa kana ya soma takawa yana barin wajen,yana fita ma'aikata suka shigo suka soma kintsa wajen da kawar da duk wata dauda ko shara komai qanqantarta.
♦♦♦♦♦
Kusan jiran da ya saba yi mata na yau ya wuce na ko yaushe,bai damu sosai ba saboda maganar da yake cikin waya tun dazun ta dauke masa hankali,ya jima tsaye qofar gidan sanye da wani yadi mai sauqin kudi wanda aka yiwa dinkin riga iya gwiwarsa da gajeran hannu,irin yadikan nan ne da ake saidawa kan farashi mai sauqi,duk da haka yadin ya masa kyau saboda baiwar qira da Allah yayi masa,daga takalmin qafarsa har zuwa hularsa masu qaramin kudi ne duka baqaqe,mota uku ce ta masa rakiya saidai yau sun shigo har cikin layin,amma suna tsaye bayanshi qofar wani gida wanda a qalla daga gidan zuwa gidansu khadijan gidaje hudu ne a tsakanisu,waya ya daga ya kirata
"Gani nan" ta fada sannan ta kashe tana jan tsaki
"Kaman wani kudin arziqi ya kawo min,sai kyau iya kyau amma babu abokan tafiya,wannan da kyan da yake da shi da shine kudin shi kuma mummuna da da sauqi,kyau ba kudi ai wahala ce tunda ba dashi zaku rayu ba,ba kuma kyan zaka loqa a goshi kayi yawo da shi ba" ta fadi ita kadai tana mita sanda take gyara yafen mayafinta.
Babu wata cikakkar fara'a a fuskarta haka ta iso
"Mun yini lafiya"
"Lafiya lau ya mutanen gidan"
"Suna lafiya....." Ta amsa ciki ciki
"Ina saqon?" Ta buqata kai tsaye saboda tana tantamar idan ka ya kawo din
"Gasu nan" ya fada hannayensa na harde a qirjinsa ba tare da ya motsa ba yana karantar yanayinta lamarin na sake bashi tsoro da mamaki,sai ya cire hannunsa daya ya saka cikin aljihun wandonshi,ganin haka ya sanyata tadan saki ranta sannan tace
"Ok....mu shiga daga ciki mana" ta fada tana duban qofar gidan sannan ta maido idanunta kanshi,kafadunsa ya daga duka biyun yana ci gaba da qoqarin zaro kudin,ba tare daya dubeta ba yace
"Ba sai na shiga ba,abinda kika fi buqata na kawo miki kawai muyi sallama na wuce" bata fahimci komai ba haka bata ce komai ba,saboda hankalinta dukka yana kan kudin daya ciro a aljihunsa,wanda kai tsaye bata ce ga adadinsu ba,bandir bandir ne sababbi kar a miqe na 'yan dubu dubu guda biyar,sai 'yan dari biyar biyar kuma daban,wadan can ya maida aljihunsa ya irga 'yan dari biyar biyar din dubu goma ya miqa mata yana kallonta
"Lissafa kiga sun kai?" Amshewa tayi,cike da zumudi qasan ranta tare da fatan samun qari ta lissafa cikin qwarewa sannan tace
"Sun cika" sai ya kada kai ya sake ciro wadancan bandiran yana dubanta yace
"Nawa kika ce kina buqata a baya?" Farrrr tayi da ido dadi na ratsata,addu'arta ta karbu cikin zumudin daya kasa boyuwa tace
"40k kawai nake buqata,ina zaton zata isheni komai da komai" sai ya miqa mata dukkan kudaden hannun nasa yace
"Zaki iya gane nawa ne nan ko?" Cikin zumudi bakinta a washe tace
"Yes,duk bandir daya dubu dari ce,duka wannan five hundred thousand kenan"kai ya gyada hannayensa soke cikin aljihunsa,ya dan shaqi iska sannan yace
"ki riqe duka na baki" idanunta ta waro baki daya tana jujjiya kudin cikin rudewa tace
"Kai muhammad please da gaske kake?,dama ka samu kudin kake ta min wasa da hankali haka,oh my god sweetheart na gode na gode,dama ni na sani ba zaka barni naji kunya ba,dama ashe wasa kake min"
"Eh....gwadaki nake.....kuma kinyi failing....baki ci wannan jarabawar ba khadija,kin fadi warwas har abada" sai kuma ta dan saurara daga murnar da take tana dubansa cikin mamakin kalamanshi
"Kamar yaya wacce iriyar jarabawa?"murmushi ya fidda mai kyau wanda ya sake fitar da kyan surarshi,sai taga yau taga yafi kullum yi mata kyau,ya zaro wayarsa yana dannawa wadda khadijan ta bita da kallo,idan bata manta ba wancan satin ta taba tambayar kudin wayar taji tafi qarfin kanta,don har saurayinta ta tamnaya ya siya mata ita a sannan yace bata da hankali,ashe ba qananun kudi ta baro masa ba, cikin burgewa take bin wayar da ido,idanunsa na kan screen din wayar yace
"Kudi kike so khadija bani ba,kudi sunfi miki soyayyata,sune gaba da komao a wajenki....gasu nan na baki su a madadina...as from today ki saka a ranki baki taba sanin wani mai suna muhammad ba a rayuwarki ko mai kama da shi,kisawa ranki kamar a mafarki alaqarmu ta taba wanzuwa....." Ya qarashe maganar yana kashe wayar tare da maidata aljihunsa fuskarsa qunshe da murmushi wanda take cakude da mamaki,haushi al'ajabi da takaicin halayyar 'yammatan yau,yayin data saki baki kawai tana binsa da kallo saboda lissafinta dake neman dagulewa lokaci guda.
Kunya da tsoron rasashi a sanda ta fahimci wayeshi suka dabaibayeta,tsoron subucewarsa daga hannunta a sanda ta gane cewa type dinta ne shi suka cikata,cikin qoqarin kare kai ta bude baki da niyyar bawa kanta kariya,saidai isowar motocinsa wajen yasa ta kasa furta komai,a gabanta ilyas daya daga cikin yaranshi ya bude masa bayan motar ya shige ba tare da ya sake koda waiwayarta ba,tana kallo suka janye motocin suka fice daga layin suka barta tsaye riqe da rafas din kudi.
Har suka bace daga layin tana tsaye tana bin kyawawan baqaqen motocin da kallo mamaki ya daskarar da ita,da gaske wannan shine ainihin muhammad ba wanda ta sani ba?,shin mafarki take ko gixo idanunta ke mata,saita maida idanunta kan kudin tana jujjuyasu tare da qare musu kallo,qwaqwalwarta a daure take tamau,ta rasa me zata aiwatar,takai hancinta ta shanshanasu,wani irin lallausan qamshi suke fitarwa irin mai kwantar da zuciya,take nadama da dana sani suka lullubeta,ya akayi ta kasa boye zalamarta?,ya akayi ta kasa gane cewa muhammad ba qaramin mutum bane?,iya motoci kawai data gani na biye da shi da kyautar daya mata a yanzu sun isa bata amsar cewa shi din wani ne,shi din isashshe ne,sam bata jin zata iya haqura da shi,asarace da ba zata iya jurewa ba,samun irinsu muhammad a wannan zamanin tamkar gudun yada qanin wani ne ga 'ya mace,mai rabo ke samu,zata san yadda zata lallabashi ta dawo da shi cikin rayuwarta,tabbas sai ya zama mallakinta cikon burin rayuwarta kenan,jiki a salube ta juya ta shige gidan tana gyara riqon kudin a hannunta zuciyarta cike da zulumi da fargabar kada ta rasa muhammad daga rayuwarta.
*_WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER (08030811300)_*
*DAURIN BOYE*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
09
A gaggauce ta tsame hannunta daga cikin flour din da take kwabawa ta dauraye hannunta ta goge jikin towel sannan ta fita a kitchen din don amsa kiran da mommy sa'adah keta qwala mataba tare da tayi la'akari da aikin data sanyata take yi ba
Cikin bedroom dinta ta taddata,tana zaune gefan gado,daga daura da ita kayan turarukan wuta ne lodi guda da alama lissafinsu takeyi,yar lelen nata kuma na gaban madubi tana ta shafe shafe da qalqale qalqale,saboda yau fita ce ta musamman zatayi,dinner ake na wata cikin qawayenta na makaranta da take aure,qawaye ne irinta 'yan ji da kai da daukar duniya da fadi,su kansu kayan da zata sanya a ranar order dinsu aka yi mata bayan an musu dinki na musamman,ba'a maganar jaka da takalmin da zata sanyawa qafafunta na kudade masu yawa.
"Mommy gani" aysha ta furta tana rusunawa gefan mommyn,wayarta ta aje sannan ta dubeta
"Saura me da me ki kammala ne?,qarfe shida na yamma fa zasu soma taron,kuma nasan tana can tana jira"
"Mommy na gama komai da komai,doghnout din ne naga kamar bazai isa ba shine zan dan qara yawanshi"
"Zaikai kamar nan da minti nawa?" Ta tambayeta bayan ta kalli agogo
"Awa daya ko minti hamsin"
"To kiyi sauri ki gama din,saboda ke zan aika ki kai matan"
"To mommy" ta fadi tana miqewa tare da qoqarin ficewa daga dakin
"Idan kin gama ki debi komai kimin packaging,ki hada masa dambun kazar nan da kika ma daddy last week,yau nake xaton hamid zai dawo gobe zai shigo waje na" cewar asma'u dake goga jambaki kan lebanta,wanda ta bada umarni ne kawai ba tare data waiwayo ta dubi wadda ta bawa umarnin ba
"Toh" shine abinda aysha ta fada tana ficewa daga dakin cikin ranta tana fadin autan maza,hamid shine saurayin asma'u data zaba cikin dubban samarin da Allah ya bata a matsayinta na budurwa 'yar qwalisa wadda har ranta takejin duniya na damawa da ita,me ji da kyau aji ado da gata takowanne fanni,hamid ya yiwa asma´u dari bisa dari,tana jin ya dace da tsarinta ya kuma yi dai dai da ra´ayinta,hamid matashin saurayin dan kasuwa ne maiji da gata da kuma dukiya,mutum ne shi mai shegen son girma,son matsayi da qyamatar mu'amala da duk wani wanda baikaishi arziqi ba,tafiyarsu tazo dai dai da asma'u saboda katarin hali da akayi yazo guda,soyayya ake bugawa sosai,wani irin so asma'u take masa wanda yake baiwa kowa mamaki,irinson da ba'a taba ganinta ta yiwa wani d'a namiji shi ba,saboda ta jima tana jan maza a qasa,tana daga musu kai da hura musu hanci saboda baiwar kyau da Allah ya bata da iya kwalliya,uwa uba gata data samu daga wajen uwa da uba kasancewarta auta a gidansu,saidai tashin farko ta matowa hamid,ya rushe duk wani plan nata ya tafi da zuciyarta,a yanzu haka babu wanda baisan da zaman soyayyarsu ba,haka nan ta tsaidashi a matsayin wanda zata aura,saidai iyaye duka basu shiga ciki ba,saboda tana da plan din sai ta gama degree dinta sannan a soma maganar aurensu,shi dinma hakan ya masa shi yasa komai ke tafiyar musu dai dai,suke kuma gudanar da soyayyarsu hankali kwance.
Sam jinin aysha da hamid zan iya cewa bai hadu bane ko kuma banbancin halayya ya sanya hakan,tsakaninta da shi gaisuwa,sai ko idan yazo ta miqa masa kayan maqulashen da asma'u ke sawa ta hada masa ta kama gabanta,yana da ji da kai girman kai da kuma daga kai da jin shi wani ne,wannan halayyarsa ce a jininsa.
Cikin awa gudan ta kammala komai ciki harda wanka,ta shirya tsaf cikin lace bayan ta nannade jikinta da laffaya wadda ta dace da shigarta,ita ba ma'abociyar son kwalliya bace,hakan ya sanya kaso hamsin na kyawunta ke boyewa idan ba ka mata kyakkyawan kallo ko kyakkyawan sani ba,ita dai barta da qamshi,tana son qamshi,kuma dukkan turaren da take amfani da shi ba mai hayaniya bane,saika matsa kusa da ita zaka dinga jin tashinsa,kuma a hankali,yawanci tafi ta'ammali da turaren kaya haka sai rollon body spray masu kyau da dadi tamkar wata babarbariya.
A parlour ta tadda momy tsaye tana amsa waya,dai dai sanda asma'u ta fito,ba banza ba ta kashe awa guda tana kwalliya,ba qaramin kyau tayi ba,duk wanda ya ganta kuma dole ya sake juyawa ya kalleta,ankon lace din yayi masifar karbarta,uwa uba make up din da tayi
"Hey momy sai na dawo" ta fada tana ficewa cikin hanzari tana kada muqullin mota,itama hannu mommyn ta daga mata cikin dan daga murya take cewa
"Kiyi qoqarin dawowa kafin daddynku ya dawo kinji na gaya miki" daga haka ta maida wayarta taci gaba da yi,hannun kujera aysha ta samu ta zauna idanunta kan film din da ake haskowa a tashar zee world hannayenta rungume a qirjinta tana jiran mommy ta gama wayar ta bata umarnin tafiya,sai data gama din sannan ta dubeta
"Na saka usama ya sanya komai a cikin mota,a motar asma'u zakuje saboda ta fita a tawa,na mata bayanin komai ki gaisheta idan kinje"amsa mata tayi ta miqe ta fice daga falon yayin data bar mommy na zama saman kujera tare da qwalawa daga cikin 'yan aikinta kira ta kawo mata drinks.
Hajiya laraba qawa ce ta qut da qut ta momy,saidai akwai banbancin halaye tsakaninsu,hajiya laraba macace mai kirki da mutunci qwarai da jan mutane a jiki,faran faran da rashin girman kai duk da arziqin da suke da shi,sanda ta isa da kayan ba qaramin murna ta nuna ba ta bubbuda tana cewa
"Kai ma sha Allah,wannan da gani aikin indo aisha ne ko?" Murmushi aysha tayi cikin jin kunya har fararen haqoranta na bayyana bata ce komai ba
"Sannunki da aiki,lallai hajiya sa'adatu na morar mai girki"
"Yauwa mama" ta amsa mata tana matsa yatsunta
"Gashi dukka su muslima tun shekaran jiya suka gudu gidan bikin suka barni a gidan saini kadai sai 'yan mazan,maza kuma kinsan ba zama suke ba,gidan babu dadi duk saini daya" ta fada sanda mai aikin mama ke aje mata kayan motsa baki,ruwa kawai ta zuba tasha tana sauraren maman data daga waya tana kiran yaronta,sai data gama wayar take dan jan ayshan da hira,bata da saurin sabo a wasu lokutan amma tayi qoqarin sakewa maman suna dan taba hira.
Sallamar matashin saurayin ce ta katse musu hirar da suke jefi jefi
"Banda abin ahmad kuma saika zauna,kasan amfani za'ayi da kayan,ka hanzarta don Allah ka miqa mata" ta fadi tana miqa masa muqullin mota bayan ta miqe ta nufi dakinta tana cewa
"Bari na baka wadan nan kudin ka kai mata,ni inajin sai wajen gobe zan samu shigowa qafar nan yau ta matsanta min" amsa mata yayi yana gyara zamanshi saman kujerar idanunsa kan aysha wadda ta gaidashi a sanyaye kamar yadda haka yanayinta yake,ya amsa mata yana tambayarta mommy,daga haka falon ya sake daukan shiru har mama ta fito ta sallameshi ya wuce.
Sam hanata tafiya maman tayi har sai data yi sallar isha'i ta kuma tilastata taci abinci,kyautar turare maman tayi mata da agogon hannu mai kyau kafimn su wuce,hannu biyu tasa ta karba tana mata godiya,hakanan aishatu ke burge maman saboda yanayin nutsuwarta da tarbiyyarta.
Suna gab da shiga unguwarsu wayarta ta soma ringing,da mamaki ta cirota daga jakarta tana duba mai kiran,saboda tasan bata da wani mai kiranta a irin wannan lokacin,bama wannan lokacin ba,da wuya ka zauna da ita kaji kira ya shigo wayarta,saboda bata da mai kiran nata bata da wanda ya damu da ita baya ga Aliya a cewarta,idan kaga kiran mommy kona asma'u cikin wayarta to qaruwarsu ce.
Ilai kuwa asma'un ke kiranta,tana shirin sallama saidai bata tsaya ta saurari sallamar ba bare ta amsa ta soma magana,da alamun bacin rai cikin muryarta
"Mommy tace min ta aikeki gidan mommy laraba,ki bar abinda kike ku sameni keda usama a meena event" qit ta kashe wayar daga haka,wayar aysha ta sauke daga kunnenta tana qoqarin maidawa cikin jakarta tace da usama
"Usama meena event center zamu je,kasan wajen?" Dariya ta bashi har ya dan murmusa cikin sautin murmushin nasa yace da ita
"Na sani mana aisha wanne dan kano ne baisan wajen ba....sai irinku kifin rijiya" itama murmusawar tayi,tana ganin meye hadinta da wajen me zata jeyi?,a yadda ma taji Aliya na fadin haduwar wajen tasan ba tsarar shigarta bane
"Amma me zamuyi a wajen?" Usama ya jeho mata tambayar
"Yaya asma'u tace muje,halan daukota zamuyi"
"Amma da motarta ta fita ai,me zamuyi a can"
"Ban sani ba nima usama" ta bashi amsa tana dan dafe kanta tare da maida kanta ga titi,ba ma'abociyar son doguwar magana bace sam,hakan yasa sau tari asma'u kan soketa da kalmar macijin sari ka noqe,taqi yarda har yau cewa a halittarta ne.
Ba wanda ya sake cewa komai har suka isa wajen taron,wajen adana motoci usama yayi parking sannan aysha ta soma kiciniyar kiran asma'u,jifa jifa tana bin wajen da kallo wanda yake da haske saidai ba tarwai ba,amma hakan bazai hanaka ganin yadda hadaddun maxa da mata ke kaikawo a wajen ba cikin ado da qawa.
Kusan sau biyar tana katsewa ba tare da asma'un ta dauka ba,sai ana shidan ta daga,shima kunnuwanta cike da kidan dake tashi daga cikin ainihim rufaffen dakin taron taje tsinto muryar asma'un
"Wai meye ne?" Abinda ta soma cewa kenan
"Muna wajen mun iso" tsaki ta doka
"Bana son qauyanci fa,daga zuwanku sai nabar abinda nake...ku jirani malama" daga haka kashe wayar,itama kashe tata wayar tayi sannan tace
"Ammm...usama tace muyi jiranta"
"To,bari na zaga nima nadan kama ruwa"
"Ba damuwa" ta furta tana bude data din wayarta,cikin qanqanin lokaci ta soma browsing tana duba abubuwa masu amfani dake da alaqa da karatunta.
Jira sukayi na tsahon awa biyu,har a sannan ba asma'u ba dalilinta
"Tayar motar nan kamar tayi faci aishatu,ko zaki fito na sauya wata kafin ta fito?"taji usama na fada saitin window din da take zaune
"Toh ba matsala"ta fadi tana maida wayarta jaka sannan ta bude murfin motar ta fito,idanunta ta sake sanyawa tana qarewa filin kallo,komawa tayi jikin motar ta jingina tana ci gaba da kallon wajen jifa jifa.
Cikin minti goma usama ya gama canza tayar yace ta koma ciki,amma sai tace ya barta anan saboda ta gaji da zaman cikin motar.
A gurguje yake takowa daga bangaren nasa zuwa bangaren anninsa,shigar baqaqen kaya yayi gaba daya har takalminsa hight top sai ratsin ja jifa jifa,agogon hannu yake daurawa hakan yasa sam bai lura da zeenart ba,qiris ya rage suyi gware,da sauri ya ja da baya yana ci gaba da daura agogonsa,yayin da zeenart ke qare masa kallo cike da sha'awa da burgewa,ya mata kyau sosai haka shigarshi ta burgeta matuqa
"ya khalipha badai fita zaka yi ba"murmushi ya saki kadan bayan ya dubeta yana ci gaba da gyara wuyan rigarsa
"Xan dan leqa dinner din wani abokin kasuwanci na"a shagwabe tana dan buga qafa tace
"Kai ya khalipha,amma ka sani already na hada maka dinner yana kan dining ko?"
"Dont mind,bazan jima ba zan dawo"
"Kayi alqawari?" Ta fada tana langabar da kai,murmushi ne ya qwace masa,yaran na bashi mamaki matuqa,wai sun mata baya ne?,ko sani ne basuyi ba saboda qanqantar shekaru?,ko sun sani takewa sukayi
"Nayi" kawai ya fada,binsa tayi suka jera har zuwa bangaren anni.
A parlour suka taddata kamar ko yaushe tana zaune saman kujera sanye da hijabi hannunta riqe da carbi,haka al'adarta take musamman da yake ba'a jima da gama sallar isha'i ba,amal ce zaune gefanta tana shan fruits,idanu suka hada ta sakar masa murmushi,bai iya disgi ba hakan ya sanya ya maida mata ya qarasa gefan anni ya zauna a qasan carfet kamar yadda al'adarsa take idan annin na sama bai zama a sama shima
"Ka fito khalipha"
"Eh anni na fito......ina su haidar ne?"murmushi annin ta saki tana dan tabe baki
"Nan yaci wanka ya fice,yace yaga alama saiya kawomin surukata har gida sannan zaka farka" murmushi ya saki shima yana shafa sumarsa cikin jin kunya,yasan jirwaye annin ke masa me kama da wanka,bai maida amsa ba yace
"Anni zan leqa wajen bikin mus'ab"
"Ikon Allah....lokacin har yayi kenan?"
"Eh wallahi...."
"To Allah ya sanya alkhairi,ka miqa masa saqon taya murnata"
"Zaiji in sha Allah...sai nadawo"
"Allah ya tsare hanya" amsawa yayi da amin sannan ya miqe zai fice,zeenart ce ta rufa masa baya,tsam amal ma ta miqe ta biyosu.
Gab da zasu isa jikin motocin ya jiyo muryar amal na tsaidashi,dakatawa yayi yana dubanta har ta qaraso,bata damu da zeenart dake wajen ba cikin shagwaba tace
"Yaya...amma nace ka kaini shopping kace baka da lokacin fita da dare..kuma...."
"Wannan uzuri ne daya kama dole...later ma fita ko" ya katsi qorafin data soma jerowa
"Yauwa yaya na na gode" ta fada cikin farincikin,tasan cikin ruwan sanyi ta rama abinda zeenart din tayi mata dazu na karbe girkin da ita tayi niyyar yiwa khaliphan.
Har motoci ukun da zasu fitan tare suka bar harabar gidan suna tsaye,sai da suka gama ficewa sannan zeenart taja tsaki tayi gaba zuwa cikin falon cikin gudu gudu sauri sauri,amal ta bita da harara sannan tabi bayanta suka shige ciki.
Ranta a bace ta hau step ta yiwa amarya sallama da niyyar sai gobe,don sam ba yanzu taso barin wajen ba,amma mommy ta katse mata hanzarinta ta kirata kan lallai ta biyo su aysha su dawo gida yanzu yanzu,saboda daddynsu ya dawo yana tambaya ta masa qaryar ta aikesu su duka gidan hajiya laraba.
Cikin takunshi dake nuna baiwar da Allah yayi masa ya hawo mazaunin ango da amaryan don ya shigo a makare,mus'ab din kuma yaqi karbar uzurinsa ya kafe lallai sai ya qaraso nan ya bada uzurinsa wajen amarya.
Sakkowa take a hankali saboda yanayin tsinin takalmin dake qafarta,dab da zasu gota juna idanunsa ya sauka a kanta,yanayin hade ranta abu na farko daya soma jan hankalinsa,tafiyar nutsuwa da adonta,da hanzari ya qarasa wajen ango suka gaisa sannan ya juya yace masa yana zuwa.
Ita kadai ke sakin tsaki jifa jifa saboda komawarta gida da bataso ba,yana biye da ita tare daci gaba da karantarta a haka har suka kusa isa parking space din dake wajen sannan ya qara hanzarinsa har ya cimmata,a bayanta ya tsaya sannan yayi mata sallama,ta dan tsorata hakan yasanya ta waiwayo tana dubanshi,da fari taso gaya masa magana ne saboda yadda ta tsorata,amma tashin farko sai ya mata wani irin kwarjini,kyan fuskarsa ya dakushe tsiwarta,saita sake ajiyar zuciya tana dubanshi tace
"Meye haka malam?,haka kawai ka tsorata mutane" murmushi ya saki cikin sassauta tsare gidansa da ragewa kwarjininsa kaifi
"Kiyi haquri ranki ya dade,banyi zaton zaki tsorata ba"
"Naji...lafiya?"kai ya girgiza
"ba lafiya ba" ido tadan fiddo waje
"Ba lafiya ba kamar yaya?"
"Idan ba zaki damu ba ko zamu matsa daga gefe?"
"Ba buqatar hakan don ni sauri nake,fadi matsalarka"
Cikin nutsuwa ya soma fadi mata sunanshi da abinda ke tafe da shi,kallo ta dinga qare masa tun sanda ya soma maganar har ya gama
"Kai din waye?" Ta furta tana son sanin waye shi din har zuciyarta,shafa kanshi yayi kamar wani mara gaskiya
"Ba kowa bane ni,hasalima qarqashin wani nake,shine ubangidana kuma shi na rako nan wajen" dariya ta saki cikin ranta tana jin haushi da takaici,tana ganin ya gama raina mata wayo,ya kuma fado da ajinta,ta yaya yaron wani zaice yana sonta?,maici a qarqashin wani?,me na sama yaci ballantana na qasa,toko gashin kanshi yake ci ai bata jin zai samu soyayyarta ta sauqi bare yaron wani,abu guda ne zai hanata ci masa mutunci,tsantsar kyau da kwarjinin da yayi mata,sai kawai taja siririn tsaki ta juya ta soma takawa a hankali da niyyar barin wajen
Cike da hanzari da zafin nama ya sake binta,daf da zasu isa inda su aysha ke jiranta ya sake shan gabanta,tsam tayi tana dubansa har ya gama maganarsa,tsiwa takeso ta masa amma ya mata kwarjini,yayi mata tako ina ya hadu,kai tsaye ma zata ce yafi hisham
Kyau kwarjini da cikar zati,namiji ne mai irin kyan da takeso,mai surar da takeso,saidai bai mallaki abinda zai bashi damar shiga jerin masoyanta ba,abu guda tak daya fada yasa taga sam bai dace tayi tarayya da shi ba,wato lafazin uban gidansa ya rako
"Kar ka sake bina pls,ka saurara min" lafazin da aysha ta iya jiyowa sun fito daga bakin asma'u kenan,tana iya hangoshi tar ta cikin hasken,a hankali ta janye idanunta daga kansu tana yunqurin komawa cikin motar ganin asma'un ta doso su tun kafin tazo itama ta sauke mata nata kason,tana matuqar mamakin yadda asma'un keda zarrar tsayawa gaban maza tana musu yadda taga dama ba tare da damuwa da shekaru ko darajar koma waye ba.
Garam ta rufe murfin motar ba tare data dubi usama ko aysha ba tace
"Muje" kai tsaye
Ita daya ta dinga mitar biyotan da akayi aysha na jinta bata ce komai ba,tana ganin kamar ya rage mata aji ne daya biyoya ma,kiran wayar hamid ita ta janye hankalinta har suka je gida suna waya,a cikin mota ita dai ta barta ta wuce ciki.
Kan dining ta samu daddy shi da mommy suna cin abincin dare,a nutse ta qarasa,tana shirin gaida daddy mommy tayi caraf cikin salon data saba amfani da shi koda yaushe tace
"Ina kuka tsaya tun la'asar sai yanxun?" Kanta a qasa tace
"Hajiya ce tace sai munci abinci zamu taho"
"Ina ita husnar?"
"Tana mota" ganin tambayoyinta sun qare yasa ta waiwaye bangaren daddyn ta gaidashi cike da ladabi da girmamawa,shima ya amsa mata cikin kulawa,tana shirin miqewa ta wuce asma'u ta shigo,a shagwabe take qarasowa zuwa wajen
"Ke ba zaki ci abinci ba?"mommy sa'adah ta fada ganin ayshan na niyyar wucewa,ga idanun daddy a wajen
"Na qoshi,naci wajen hajiya"har ta soma takawa daddy ya kira sunanta,sai duka hankalinsu ya koma kansu daddyn duk da magana suka soma yi a tsakaninsu,a ladabce ta dawo ta durqusa
"badai wata matsala ko?" Murmushi ta saki dan kadan,to wacce matsala ita din take da bakin cewa tana da ita?,a yanzu bata ganin wata matsala tattare da rayuwarta idan ta kwatanta da rayuwarta ta baya
"Eh daddy babu"
"Kin tabbatar?" Ya sake jaddadawa don har ga Allah yana qaunar yarinyar yana tausayin rayuwarta,sam bata da marsala tunda har yau duk abu irin na sa'adatu bata taba kawo masa qararta ko qorafi a kanta ba,duk da cewa bata taba yabonta ba,amma hakan ya alamta masa bata da wata matsala,yqsan halin matarsa sarai,da tana da damuwa yarinyar tofa duk sanda suka zauna hira ta dinga sakin qorafin akanta kenan,duk da ba zata fito kai tsaye ta kawo masa qararta ba,haka nan nutsuwarta ta daban ce
"Na tabbatar daddy" ta amsa masa muryarta can qasa idanunta na duban tiles din dake shimfide a qasan falon
"To Allah yayi albarka ya kuma yi jagora"
"Ameen daddy na gode,Allah ya saka da alkhairi"
"Ameen" ya amsa cikin jin dadi,miqewa tayi bayan ya sallameta,asma'u na zabga mata harara a fakaice tana ayyana munafuka cikin zuciyarta,yayin da haushi da takaici ya tuqe mommy sa'adatu,saidai sam ba zaka ce haka ba don ko kan fuskarta bata nuna ba,sai abinci da take diba kadan kadan.
A gajiye take liqis,cikin kasala ta dinga warware lafayar jikinta sannan ta shiga bayan gida ta hada ruwa mai zafi tayi wanka,mai ta shafa ta feshi jikinta da turare sannan ta zira rigar bacci doguwar mai taushi da kauri,bacci kawai take buqata tayi,saidai qarar wayarta ta dakatar da ita,ta qarasa ta cire wayar daga chargy tana duba mai kiran,asma'u ce,ta shafa ta kara a kunnenta
"Fito ki daukomin kayan da nace ki ajemin" ta fada da salon muryar data saba yi mata magana,aje wayar tayi ta zira hijabinta ta fice zuwa kitchen.
*_WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER (08030811300)_*
*DAURIN BOYE*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
HASKE WRITERS ASSO
(Home of expert and perfect writers)
10
A tsaye ta sameta cikin kitchen din riqe da cup tana shan yoghourt,fuskar nan a hade,fridge din ta bude ta ciro mata kayan,saidai bata ga dambun kazar ba
"Ina dambun?" Ta tambayeta tana duban kayan
"Ban sani ba nima cikin freezer din na ajjiye"
"Wacce iriyar banzar magana kike fada,banson iskancin banza waye zai dauka?" Ta fada a dan zafafe,da alama dai akwai wata a qasa,cikin sanyin muryarta kamar yadda yake a halittarta tace
"Wallahi ban sani ba anty asma'u,dana gama na saka a ciki mummy ta aikeni gidan mummy laraba", shigowar mummy cikin kitchen din shi ya katse muhawarar
" hayaniyar me nake ji?"ta tambayesu tana aje warmers din abincin da daddy ya gama ci
"Wannan yarinyar mummy nason ta fara rainani,sumumu kasau macijin sari ka noqe,na sata ta hadamin kaya amma tace wai bata ga dambun da nace ta yimin ba?"
"Banson tashin hankali da daren nan ki kira mana hankalin babanku,ta sake miki wani,wancan nayi baqi na basu" ta fadi tana ficewa a kitchen din,shiru tayi kafin ya kwashe kayan ta fice itama bayan ta aje mugun tsaki.
A qalla ta shafe kusan minti goma kafin itama ta soma takawa a hankali tana ficewa daga kitchen din,bata san me ya taba zuciyarta ba batasan tana hawaye ba saidata shafi fuskarta,tana goge hawayen tana addu'ar bacci da haka ta kwanta bayan taja bargonta zuwa kafadunta.
Ta jima a kwance tana nazarin rayuwa kafin ta tattara dukka lamuranta ta sake miqawa Allah.
Ya dan jima tsaye shida drivansa yana qarewa gidan kallo,haka kawai yaji zuciyarsa ta nutsu ta aminta da gidan,yana jin gamsuwa da nutsuwa har cikin zuciyarsa,yana son mace mai kamun kai da jan aji,yana ganin kamar akwai alamun hakan tattare da ita,yanayin arziqin gidansu yana ganin kaman bazai sanyata qyamatar mai qaramin qarfi ba,kamar zata amsheshi haka yakeji,amma hakan bazaizama dalilin da zai sanya ya kasa jarraba ta ba kamar sauran,a nutse ya yiwa drivern nasa umarnin su wuce.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Qarfe biyu na rana suke takowa zuwa cikin layin nasu daga bakin titi zuwa gidansu ita da asma'u dake qunquni kamar zata fashe,taci alwashin bata sake hawa motar,duk da ba tsufa ne yasata yin hakan ba,uban motar da take ci ne kawai da kuma halin tsiyar qarfen nasara,inda Allah ya taqaita saida sukazo kwanar gidan nasu ta kakare musu a nan,itakam aysha na gefanta,baki daya bata ga abun bacin rai ba,don dai yau kadai.
"Malam ka cikani,Allah bazan biya ba"
"Wallahi saika biya kaji na gaya maka,ba inda zan sakeka kaje" hayaniyar mutum biyu kenan data cika kunnensu gab da zasu qarasa qofar gidansu,hayaniyar na tashi ne daga wani dan case dake maqale da gidan maqocinsu dake kallon nasu gidan,case ne da mai gadin gidan ya bude yana saida katin waya da sauran 'yan qananun abubuwa da ba'a samu cikin unguwar sai sunje waje mai nisa saboda yanayin unguwar tasu,dukkansu hankalinsu yakai wajen,asma'u ta ganeshi tsaf,yayin da aysha taso ta shaida fuskar,da sauri asma'u ta dauke kanta,hakanan taji gabanta na faduwa,ta yaya akai yasan gidansu?,me yake a layinsu?,fatanta daya kada Allah yasa ya nuna ya santa,don ta fuskanci yana da wata zarra da rashin fargaba.
Saidai ko daya addu'arta bata ci ba,don kafin tayi qwararan taku guda goma ya samu isa gabansu,murmushi yake jifanta da shi wanda ya haddasa mata faduwar gaba,babu shakka ba qarya yana da kyau wanda ko gasa ya shiga idan baizo na daya ba zaiyi na biyu,saidai baida makamin da zai tayashi yaqin shiga inda yakeso
"Ranki ya dade....ashe nan ne gidanku?" Ya fadi yana qarewa gidan nasu kallo kamar da gaske yau dinne ya soma tozali da shi,itama gidan ta kalla kaman yau ta soma gani sannan ta maido dubanta gareshi,cikin tsiwa da tsaurin ido tace
"Nan ne,sai yaya?" Murmushi ya saki sannan yace
"Nayi farinciki sosai.....hakan ya nuna Allah yana sona" tana niyyar maida masa habu mai trader da suka tarar suna taqaddama ya qaraso yana sakw fadin
"Mallam ka sallameni ka biyani kudina zan koma bakin aikina"
"Karka damu yanzu za'a biyaka...." Sai ya dubi asma'u dake dubansu galala tana tabe baki
"Ranki ya dade taimaka ki ranta min wasu kudi mana 'yan kadan ba masu yawa ba" kallon banza tayi masa,wani bacin rai na tokare wuyanta,yanzu ita asma'u har tayi arahar da saurayi mai cin bashi wajen masu qananun akurkin shaguna zai tsaya kafada da kafada da ita yana magana?,baqinciki yasa ta kasa magana illa dogon tsaki da taja ta wuce zuwa bakin wangalelen get din gidansu kamar zata saki kuka,koma meye motarsu ce ta jawo mata,da bai isa ya ganta ba bare ya tsaya da ita.
Binta sukayi da kallo duk su ukun har ta shige cikin gidan kafin kowanne ya maido idanunsa inda suke,idanu suka hada shida ayshan,sai kuma ta danyi turus cikin rashin sabo ganinta gaban maza har biyu abinda bata saba da shi ba,sai a sannan ta soma tuhumar kanta name ta tsaya yi a wajen,a hankali ta ciro jakar ta dake rataye a kafadarta ta bude tana fatan samun wani abu a ciki,cikin sanyin muryarta ta daga idanunta ta dubi habu mai trader
"Nawa ne kudin naka?"
"Eh...ammm....dari biyar.....dari biyar ce" dubu daya ta ciro ta miqa masa
"Gashi bani da canji....ka bashi canjin dari biyar din ya riqea hannunshi" tana gama fadi ta maida jakarta kafadarta ta nufi cikin gidan,tana ganin rashin kyautatawarta qarara,tana gani tunda har ya karya billensa ya tambaya buqata gareshi,bai kamata kana da shi ka hana wanda baida shi ba,batasan dalilinsa na tambayarta ba.
Tun kan ta isa parlour din take jiyo banbamin fadan asma'u,tsaye ta sameta gaban mommy sa'adah da alamu labari take bata da kuma nuna bacin ranta
"Sannu da gida mummy..." Aysha ta furta tana dan rusunawa cikin girmamawa
"Yauwa.....ina ke kuma kika tsaya?" Ta tambayeta tana dubanta
"Ta tsaya tana kallonmu salon ta sake samun damar rainani.....munafuka....waya sani ma ko kin sanshi....koma kece kika turoshi?" Bata ce komai ba ta juya ta nufi bangaren da dakinta yake,tana iya jiyo muryar asma'un tana ci gaba da cewa
"Banza baqauya kawai....Allah mommy cikin satin nan indai daddy bai sauya min mota ba Allah na bar zuwa school,ai ba girma na bane a ganni mota tana bani matsala...haba don Allah mommy...sau biyu fa tana min haka" kai ta kada kawai,sau tari tana mamakin halayya irin ta asma'un,itakam har yau cikin duniyar nan bata ga wani abu da zai burgeta ya shiga zuciyarta da yawa har irin haka ba,me ta nema?,meta rasa?,amma ko yaushe qari take nema,ko yaushe so take taga ta zama perfect,ko yaushe so take taga komai nata yafi na kowa,ko yaushe yadda ta tsara ma kanta haka takeso taga ya kasance,tafi dukkan sauran 'yan uwanta mata uku buri da kai kanta can wata uwa duniya,duniyar da ma'abota buri da hangen duniya da tsaho suke yunqurin isa.
Dukka tana wannan tunanin ne tana cire kayan jikinta don wanka take da buqatar yi saboda tsananin ranar da ake kodawa,da wannan tunanin ta shiga bandaki ta sakarwa kanta ruwan shower mai sanyi ba tare data sirka da ruwan dumi ba,koda sanyi ake indai ba tsananta yayi ba tana iya wanka abinta da ruwa mai sanyi,saboda sabo da tayi da wata iriyar rayuwar da tayi can a baya.
Dari biyar din habu mai gadi ya miqa masa yana cikin rusunawa tamkar bashi ya gama cin kwalarsa dazu ba yana cewa
"Gashi yallabai...." Daga kai khalipha yayi ya dubi kudin sannan hannayensa zube cikin aljihun wandon jeans din jikinsa 'yan gwanjo wanda ya ara wajen habun ya dora kan t.shirt dinsa da ainihin wandon jikinsa
"Bakai aikin da kyau ba habu" cikin fargabar ko kada yadda ya ringa cacimarsa ne ya bata masa rai yace
"Tuba nake yallabai...." Murmushi khalipha yayi ya amshi dubu dayan da yake miqa masa yana cewa
"Nan gaba kayi da gaske,ka daina tuna waye ni,kayi kaman ka kama mutumin da yaci bashinka shekara guda ya tsere yau ka kamashi" dariya ya bawa habun har sai daya dara,yana mamakin sauqin kai irin na khalipha,dama akwai masu kudin dake da sauqin kai haka,amma mamakinsa meye dalilin da yasa khaliphan ya maida kansa talaka a idanuwansu?.
Isowar wani matashi cikin shigar coat baqaqe dauke da briefcase wajen ya sanya habu tsagaita dariyar da yake,briefcase din mutumin ya zuge ya miqowa khalipha,dubu dayan daya karba ya jefa cikin sabbain bandiran kudin dake cikin jakar,sannan ya zaro bandir din 'yan ashirin ashirin ya miqawa habu,cikin rawar jiki da murna yace
"Duka wannan nawa ne yallabai?" Kai ya gyada masa sannan yace
"Next term zanci bashin credit....karka manta"
"Allah ya kaimu yallabai...yaushe zakazo"
"Ba lokaci....saika ganni kawai" ya fada yana amsar wayoyinsa daga hannun matashin tare da duba miscal din daya tara zaman da yayi wajen habun,sannan ya soma takawa a hankali zuwa wajen motocinsa dake can bakin layin suna jiransu.
Mai kawai ta shafa ta zura doguwar rigar atamfa a jikinta,bacci takeji sosai saboda jiya bata samu tayi isashshen bacci ba,tayi karatu sosai hakan ya hanata bacci da wuri,kan gadonta ta koma ta janyo wayarta ta soma lalubar lambar aliya wadda bata jin dadi bata samu ta shigo ba,ringing uku aliyar ta daga tana fadin
"Yanzu nake zancanki cikin raina" murmushi ta saki mai dan sauti,tana jin dadin yadda aliyar ke nuna mata qauna
"Nima kina raina,lactures ne yau sunyi zafi da yawa aliya,kaina har ciwo ciwo yake wallahi" ta qarashe maganar da sanyin muryarta,dariya aliya tayi
"Tofa....alhuda huda yau da kanta take fadin haka?,lallai yau kun gasu" 'yar dariya itama tayi
"Eh lallai jiki yayi kyau tunda har kike da bakin tsokanata....to Allah ya qara lafiya"
"Amin sashin(haka take kiranta wasu lokutan),naso na shigo makarantar yauma,mama ce tace na bari na qara jin dama zuwa jibi da muke da lacture"
"Allah sarki mama...ki gaidamin ita don Allah"
"Keee....wai me kike nufi?...banfa dauke miki dubiya ba" dariya ce ta qwacewa aysha ba tare data shirya ba
"To kuma me kika ji nace?"
"Baki ce ba amma i know you in and and out eesha....bakyason zuwa gidanmu bakison zuwa gidan kowa....bansan me yasa ba..ko kina tantamar qaunar da nake miki" tabbas ba qarya aliya take ba,hakanan take jin kaman bata dace data rabi kowa ba,bata kai matsayin hada alaqa da kowa ba tunda har uwarta mahaifiya ma bata da buqatarta
"Kiyi haquri sashin...gobe zan shigo in sha Allahu"zaro ido aliya tayi kaman tana gabanta cikin mamaki da doki
"What...da gaske kike?"
"Na taba miki qarya?" Ta amsa mata cikin dariya dariya
"Heee....Allah ya nuna mana gobe....breaking news yau a kunnen mama...kinga bari naje na soma shiri tun yau...sai anjima" ta fadi cikin zumudi gami da katse wayar tabar aysha da dariya,tasan dole aliya taji dadi saboda yadda take qaunar ayshan,bugu da qari tunda suke zuwanta gidansu daya sanda mamanta bata da lafiya wannan shine na biyun.
Wayarta ce ta sake ruri a karo na biyu,sake jawo wayar tayi tana tsammanin aliya ce ta sake kira,idanunta ta zaro zuciyarta na bugawa ganin sunan wadda ke yawo saman screen din wayarta,a zabure ta miqe ta zauna sosai saman gado bugun zuciyarta na qaruwa,UMMI NA sunan data yi serving number mahaifiyarta dashi shike yawo saman wayar,tunda take karo na farko da lambar wayar ummin ta soma yawo akan wayarta ba tare da ita tayi gangancin kiranta ba,cikin zumudi farinciki cakude da wani irin tsoro ta amsa kiran tana mai cike da fatan ummin tata ce da gaske.
Gauruwar ajiyar zuciya ta sauke sanda tajiyo muryar Basma
"Anty indo...basma ce" ta fada cikin zumudi
"Wai...yau kin tuna ni basma" ta fada tana jin dadi cikin ranta,ko banza yarinyar na sonta cikin 'yanuwanta
"Anty bani da waya shi yasa bana kiranki.....yanzu ma ummi na wanka na dauka bata sani ba"
"Ina ummi basma...tana tunawa da ni?...tana zancena?...." Ta fada cikin karyayyiyar murya
"Ummi bata son ana........."
"Basmah!" Aysha ta jiyo murya ummin na kiran sunan basman cikin tsawa,da alamu ma kusa da ita take
"Uban wa kike kira?"ta sake tambayar yarinyar cikin hargagi
"Kiyi haq....haquri um...mi..." Abinda aysha ta jiyo kenan wayar ta katse,sauke wayar itama tayi daga kunnenta cikin fargaba,muryar mahaifiyarta Kawai data jiyo da fadanta ya sanya jikinta yin laushi tare da tsoro tamkar tana gabanta,zuciyarta ta karye sai hawaye ya soma sintiri saman kuncinta
"Ya Allah" ta furta a sanyaye tana kwantar da kanta saman pillow,fatanta daya Allah yasa kada ta yiwa yarinyar irin mugun dukan data saba,bata taba mance yadda dukan ummin nasu yake,bata mancewa da irin fushinta,bata manta yanayin hukuncinta,gefe daya zuciyarta na saqe saqe kala kala irin wanda ta saba,tasha qaryata mutane da kanta cewa ummin mahaifiyarta ce,saidai an sha gaya mata,kowa ma hakan yake gaya mata itace mahaifiyarta sau shurin masaki,ita ta tsugunna ta haifeta,saidai garin yaya?,me yasa?me ya faru?me tayi mata?,Allah masani har yau bata samu wannan amsa tata ba,ta dade tana kuka saman gadon ita daya har baccin data kwanta dominsa yazo ya sureta
*_WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARINH,IDAN KINA DA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER (08030811300)_*
*HUGUMA*
11
Washegari kusan wunin kitchen tayi,tana yi tana duba agogo kar lokacin da ta yiwa Aliya alqawarin zata je ya wuce,duk wani snacks da sukeyi su ajjiye cikin freezer dinsu sai data yisu dama ita keyi,tayi packaging dinsu kamar yadda ta saba sai suya a duk sanda buqatar hakan ta taso.
Tana fitowa a kitchen din anty safiyya ta shigo,inna laraba dauke da yaronta al_amin,ba laifi duk cikin yaran mummy sa'adatu ta fisu kirki,tana da dadin mu'amala da son jama'a,tana da fadin gsky saidai tana da fada idan akai ba dai dai ba,cikin fara'a aysha ta qarasa ta karbe al'amin daga hannu inna,ta dosana kan hannun daya daga cikin kujerun falon ta zauna tanawa al'amin wasa ta basu dama su gama gaisawa da mummy sa'ada dake baje a falon cikin takardu tana lissafe lissafen business dinta
"Aysha indo 'yammata....,ba'a ganinku sai anzo gidanku ko?" Cewar anty safiyya tana duban aysha cikin murmushi,itama murmushi tayi ta soma gaidata ba tare data amsata ba,tana cikin tambayarta sauran yaranta asma'u ta sauko daga sama,tayi kwalliya sosai cikin wani irin yadi wanda cikin tsarabar daddy ce,tayi masifar kyau,don dama itadin ba baya bace wajen kwalliya
"Mara mutunci" anty safiyya ta fadi tana gasa mata harara,narke fuska asma'un tayi tana cewa
"Mummy ki mata magana Allah,kinga daga zuwanta ko?"
"Hala wancan me shegen jin kanne yazo" ta sake fadi tana jifanta da harara
"Allah mummy kiyi mata magana.....duk yadda yake ganin mutuncinki shine zaki gaya masa haka?"ta fada cikin bacin rai shimfide saman fuskarta,miqewa aysha tayi ta miqa mata al'amin daya soma neman nono ta soma barin wajen sanda anty safiyya ke cewa
" to basai ki rama masa ba....tunda na zagi qanin mummy"
"Ya isa haka safiyya...ke kullum qorafinki kan hamid ne....kinsan kuma indai ita tana wajen baida aibu" fuuuu asma'un ta wuce ranta naci gaba da baci,babban takaicinta ma yadda anty safiyyan tayi mata a gaban ayshan,yarinyar da taqi jini,ta kuma qi jinin ta rainata ko a disgata agabanta.
Bayan komawarta daki wanka ta sauya ta soma shiryawa,madaidaiciyar kwalliya tayi,tayi kyau cikin laffayar data nade jikinta marron mai adon baqi,tana cikin fesa turare aka turo qofan,asma'u ce ta dubeta
"Ki tambayi lantana kayan da na saka a hada min ki dauko ki kawo min,muna gefan garden"
"To" kawai aysha tace ba tare data dubeta ba,saboda babu abinda ta tsana a rayuwarta irin hamid din yazo asma'u tace taje ta kai musu wani abu,batasan me yasa takeson mata hakan ba,ko da yake hakan baya rasa nasaba da yadda ko yaushe bata da burin daya wuce taga ta qasqantar da ayshan ta kuma nuna cewa ita ba kowa bace a wajenta,hakanan ita din ba jininta bace iqirarinta kenan koda yaushe.
Harta tura qofar dakin sai kuma ta sake dawowa tace
"Ke" tana dubanta,fararen idanunta kawai ta daga ta dubeta
"in zaki zo ki nemi hijabi ki saka,karki zomin a haka" tana gama fadi tayi gaba,hakanan taga ayshan tayi mata kyau,yadda marron din laffayar ta zauna saman fatar farar bufalatanar mace hakan ya sata qyashin ganinta a haka.
Sai data gama komai ta dauko jakarta ta fito baki daya sannan ta qarasa kitchen ta amshi kyakkyawan farantin da aka cika da kayan motsa baki ta nufi inda ta gaya matan.
Suna zaune daf da juna kan fararen kujerun da aka aje a wajen saboda zama da shan iska,isowarta wajen baisa sun gyara zamansu ba,idanun hamid jifa jifa nakan asma'un rabi na kan wayarshi,yayin da asma'un ta tattara dukka nutsuwarta da idanunta a kansa,sallama tayi ta dire sannan tace
"Ina yini" kai ya daga ya dubeta sannan ya maida kan wayar kafin ya amsa,juyawa tayi tana qoqarin wucewa
"Sai yanzu kika ga damar kawo wa?..." Ta fadi da saigar tambaya,tsaiwa kawai tayi ba tare data amsa kota ce wani abu ba,tsaki ta saki sannan tace
"Me kika tsaya kuma yi....aisaiki wuce ko malama" nan bata tanka ta ba ta juya tabar wajen,halayen asma'un ba baqo bane wajenta,koma waye tana iya masa haka idan taso,abu daya ta sani kome mutanen gidan suke mata suna da qima a idanunta,na farko koba komai sun riqeta suna zaune da ita,ta samu ingantuwar rayuwarta wadda abaya bata zaceta ba bakuma ta tsammaci samunta ba,na biyu kuma girma da qimar daddy ya shafe komai,ya danne duk wani abu da za'a mata,karamcinsa a gunta ba abune mai yiwuwa a manta da shi ba.
Ciki ta koma kawai tayiwa mommy sallama ta amsa mata,tana shirin juyawa zata fita a falon sukayi karo da ahmad dan gidan hajiya laraba,murmushi ya sakar mata itama saita maida masa tana matsawa gefe
"Ina zuwa haka da wannan yammacin?"
"Ina yini" ta zabi gaidashi maimakon amsa mishi tambayarsa
"Mu qarasa ciki saimu gaisa ko?....ko zan bata miki lokaci?" Ba haka taso ba,amma sai ta kada kanta kawai tana juyawa zuwa cikin.
Da fara'a mommy ta tarbeshi,aysha na gefe ta gaidashi sannan ta miqe
"Shiga ciki ki samo masa wani abun" cewar mummy,duk da cewa ko cikin kitchen din akwai masu aiki dake aikin abincin dare.
Miqewa yayi ya soma yiwa mummy sallama sanda aysha ta sake ficewa da niyyar tafiya
"Saurin me kike haka ina zuwa?" Tajishi daga bayanta yana fadi,ahmad ne,murmusawa kadan tayi tana noqewa baya kadan saboda qarasowa da yayi yana niyyar jerawa da ita
"Zani dubiyar wata qawata ne" ta amsa masa
"Ohk...muje na saukeki mana" kai ta kada
"A'ah...na gode....zan qarasa na hau napep"
"Amma ina duka drivers din gidan?,bansan gidan nan ana hawa abun haya ba..."
"Wataqila basa nan"ta fada cikin zaquwar ya tsaya daga nan,don sun kusa isa wajen aje motoci,ga asma'u data hango daga nesa idanunta na kansu
"Fine....tunda wataqila basa nan muje ni na saukeki"
"Allah ka barshi"
"Bakison na samu ladar gaida mara lafiya kenan?"
"A'ah ai....."
"Indai ba haka bane muje na kaiki" ya katseta,batasan me kuma zata sake ce masa ba,hakan ya sanya tilas ta bishi wajen motarshi.
Tana gefen sit din driver amma jinta take a matuqar takure ,jinta take kamar wadda ta aikata babban zunubi,kanta na qasa ta jiyoshi yana cewa
"Malama aysha....ya makaranta ya kuma samari?" Banbarakwai ta ji maganar,itakam tsahon rayuwarta ba zata iya tuna wani qwaqwaqwaran saurayi data taba yi ba,tun tana qauye zuwa yanzu,dama makarantar yace dai,kusan yanzu bata da wani abu da ya wuce makarantar a wajenta
"Ya kika yi shuru?" Ya sake tambayarta yana kallonta kafin ya dauke kai
"Makaranta alhmdlh" ta fada tana sauke boyayyar ajiyar zuciya
"Ma sha Allah,samarin fa?" Ya fada yana murmushi
"Hmmmm" kawai tace
"Hmm...kardai kice min babu?" Ya fada cikin sigar zolaya,gaba daya a takure take,sam batason maganar,jinta take kaman ta girmi kanta,bata ma da muhalli ko gurbi sam a rayuwarta ta yanzu,buri gareta na karatu mai zurfi,wanda zai zameta qaqqarfar garkuwa da zata tare duk wani abu mai cutarwa daka iya ci gaba da kawowa rayuwarta farmaki
"Idan har da gaske ne babun?...me zai hana ni a bani dama na shiga layi kuma mutum na farko ko?"shiru tayi tana jin zuciyarta na bugawa,kaman yaya me yake nufi?
"Uhmmm aysha?,kinyi shiru?,ko na barki kiyi nazari?"
"Eh" ta fadi da sauri,saboda shi daya ne mafitar a yanzu don bata da amsar bashi
"Ayi tunani mai kyau" ya fada yana karya kwanar da zasu shiga bayan ta masa nuni da yatsa.
Qofar gidan ya tsaida motarsa tana yunqurin fita ta masa godiya
"Ki daina saurin godiya haka,saboda zan dawo daukarki" kai ta girgiza
"Na yafe wallahi...bansan ma lokacin da zan koma gida ba karna wahal da kai"
"Na gane dai bakison na dawo....fine...samin phone number dinki" ya fada yana miqa mata wayarshi,da ka ta saka masa number sannan ta miqa masa yayi serving,sai data shige cikin gidan sannan yaja motarsa yabar wajen.
Tana shiga aliya tayi tsalle ta riqeta
"Ke...waye ya kawoki?" Murmushi ta saki mai sanyi cikin siririyar muryarta tace
"Wannan itace tarbar da za'amin dama?"
"Yi haquri sashen...wallahi dadi ne ya sakani fadin haka....yau naga abinda ban taba gani ba"
"Rakani na soma gaida mama tukunna"
"Mama bata nan,amma kafin ki tafi zata dawo" ta fadi tana jan hannunta zuwa kan kujerun falon.
Sai data cikawa aysha gabanta da kayan ciye ciye kala kala harta rasa wanne zata ci?,bata barta ba sai data ci tasha sannan suka shiga hira,yawanci aliya ke baiwa ayshan labarai kala kala,ta kuma kwaso mata hotuna ta kalla har ta gaji,daga bisani ta sake tada mata zancan,bata boye mata komai ba don aliya qawa ce ta gari
"Aysha....ki bashi dama ina ganin..bakisan me Allah zaiyi ba,ki manta da da rayuwarki ta baya...ki manta dake wacece ki ki amshi sabuwar rayuwarki" zame hannunta tayi daga na aliya qwalla na cika idanunta
"Ta yaya Aliya zan manta wace ni?,kin manta har yanzu akwai tabo cikin rayuwata,Aliya....mahaifiyata...ta yaya zanyi aure?,ta yaya zan sanarwa da wanda zan aura bahagon labarin dake wanzuwa tsakanina da mahaifiyata...ta yaya zan fahimtar da shi...da wanne ido zan kalleshi na sanar masa?koda na mance komai komai ya wuce banda wannan aliya" ta qarasa tana girgiza kai qwalla na bin kuncinta,can qasan zuciyarta tana jin suya,hannu aliya ta saka tana share mata hawayen fuskarta
"Kinzo gidanmu maimakon ki samu farinciki saiki qare da kuka?,banason haka sashin" murmushi ta saki wanda qasan sa ciwo ne da radadi
"Kinsan me?.....bari na kira ummi kiji ki sake tabbatarwa da maganata na kan hanya" ta fadi tana zaro wayarta,duk da yadda zuciyarta ke bugun uku uku tana mata gargadin kiranta amma bata fasa yunqurin kiran nata ba.
Dab da zata tsinke aka daga,sallamar ummin ta bayyana cikin muryarta,shuru ayshan tayi ta kasa cewa komai har sai data ce
"Wake magana ne?"
"Nic....ce...aysha ce"
"Wace ayshan?" Ta tambaya a dan gintse saboda hasashen da zuciyarta ta mata
"Aysha indo"
"Bakiji me na gaya miki ba ko?.....ke wacce iriyar yarinya ce mara zuciya?....koda yake ba mamaki jininsu sama'ila yake yawo a jininki,gargadina dake na qarshe karki sake nemana na gaya miki" daga haka ta yanke wayar,a matuqar sanyayar jiki aysha ta sauke wayar daga kunjeta,murmushi mai ciwo na tashi saman fuskarta
"Kin ji kuma kin gani ko aliya?" Ta fada a rarrabe muryarta na rawa,saman kafadarta aliya ta dora ayshan sai kuwa ta fashe da kukan data jima tana so tayi bai fita ba,sai qunci da takurar zuci da take fama da shi,babu wanda zata zauna gabanshi tayi kuka har haka,idan ma akwai aminiyarta ce qwaya daya da tayi mata nisa tana nata muhallin a qauyensu.
Tausayin ayshan ya hana zuciyar aliya sukuni,haka ta dinga share qwalla itama,itakanta mamakin wannan lamari take wanda bama ita ba,ayshan ma baki daya batasan daga inda ya somo ba,sai data gama don kanta sannan ta goge fuskarta aliyan na lallashinta da kalamai masu dadi cike da qauna da tausayawa
A gajiye ya koma gida a ranar,hakan ya sanya hatta da abincinsa a dakinsa yaci,hakanan tsakanin amal da zeenart ba wadda ya baiwa damar ganinsa,wanka kawai yayi yayi dai dai qasan carfet yana cin abinci,qwaqwalwarsa cike take da lissafe lissafen ayyukan dake jiransa gobe da kuma cikin satin,a matuqar gajiye ya jawo briefcase dinsa don ya ciro system dinsa,sunyi da wani abokin kasuwancinsa da zasu fara harkar fita da wasu samfurin duwatsu masu daraja zuwa china zasu qarasa maganarsu a lokacin.
Har ya kammala cin abincin amma yana kan system din,sai dayaji bacci na rinjayarsa sannan ya kashe yana zuba hamma,ya bude brieafcase din ya maidata,inda ya aje kudi ya bude ya soma zarasu,don sunyi magana da haidar zai aikashi gidan kawunsu dake da buqatar kayan abinci,dubu dayan ce ta fado,cikin mamaki ya saka hannu ya dagata yana kallo,don har ga Allah ya mance da ita,a hankali ya tuno inda ya sameta,murmushi ya saki yana tuna abinda ya faru,shi kansa abun ya qayatar da shi,tamkar a majigin film,wai shine aka ci kwala ana tuhuma da cin bashin naira dari biyar
"Ya Allah" ya fada yana maida bayansa jikin kujera ya jingina,yadda komai ya faru yana dawo masa fes kamar yanzu abun ke faruwa
"Ita din wacece?" Ya tambayi kanshi,baisan ko wace ba,amma abinda tayin ya burgeshi,hakan yana nuna tana da zuciya mai kyau,ta gefe daya tsiwar asma'u da dagiyarta yana dan burgeshi,yanayin son ajinta,adonta,yana son mace mai ado bawai kwalliya ba,to ita ya fuskanci duka ta hada,a hankali bacci barawo ya saceshi a yadda yake zaunen.
Kiran sallar farko ya farka kaman yadda ya saba,sosai wuyanshi ya riqe saboda yanayin kwanciyar da yayi,da addu'a a bakinsa ya shiga bandako,wanka ya soma sannan ya daura alwala,jallabiyya ya zira bayan ya wadata jikinsa da tsadajje kuma daddadan turarensa mai sanyin kwantar da hankali,idanunsa ya lumshe yana sheqar qamshin turaren yana tuna masa da wata rayuwa can baya,rayuwar da tazo ta wuce musu tamkar a mafarki,dalili biyu yasa yake amfani da turaren lokaci lokaci,na farko yana son qamshinsa,na biyu kuma dukan daya taba ci dalilin turaren a hannun yaya ibrahim,yaya ibrahim din da a yanzu shine gatansa,rayuwa na bashi tsoro,yanayin yadda rayuwa ke garawa tana qara sashi jin tsoron Allah kadaitashi da kuma imani da shi,da ire iren wannan tunanin ya tada sallar nafila kafin zuwan lokacin asubah
.
A kullum babu wata rana da zata zo ta wuce khalipha baiyi ire iren wannan tunanin ba,wani abu ne daya shafi rayuwarsa,abu ne daya tana rayuwarsa ya kuma shiga cikin tarihinta.
Baccin da yaso komawa bayan sallar asubar bai samu ba ya hau net yana rage ayyukan dake gabanshi,qarfe takwas ya fito daga wanka,yana tsane jikinsa da towel kira ya shigo wayarsa,ya qarasa yana duba mai kiran,ramla ce,dauke kanshi yayi kamar bai ganin kiran,yasan tatsuniyar gizo bata wuce ta qoqi,yasan bai wuce ta gaya masa cewa zata zo ba,abinda shi kuma baiso kenan,matsalar daya anni....baisan mai yasa ba....anni nada zuciyar mantuwa da yafiya,ta fishi sanin yaran su su waye suba wajensu suda iyayensu,amma tanayi kamar ta manta koma bata sani ba kwata kwata baki daya,suna zuwa su zauna mata suyu mata hidima,bayan yasan kowacce akwai manufarta cikin zuciya,shikam baijin zai manta ba kuma don bai yafe ba,a'ah..sam,amma iyaye daban suke,duk wani abu daya taba illata ko jirkita duniyar jin dadinsu baijin dan halak zai manta da hakan,dalili kenan daya sanya daga shi har haidar da salim ba wata qwaqwqwarar jituwa ko shaquwa a tsakaninsu da dukka yaran,baiga kuwa dalilin da zai saka ya zabesu a matsayin matan aure ba.
Kiran nata na katsewa kiran P.A dinshi ya shigo,a ladabce ya gaidashi shi kuma ya amsa a mutunce,nan yake sanar masa yau nefa tafiyar
"Wacce kenan haris?
" yallabai south africa din,na tura maka komai jiya ta email dinka da watsapp amma naga kaman baka gansu ba"kanshi ya dafe yana ambatar sunan Allah,shaf ya manta baki daya,don har yau yana da agender tare asma'u a capterian makarantarsu,amma dole ya aje komao saboda tafiyar nada muhimmanci
"Qarfe nawa ne tafiyar?"
"Jirgin qarfe daya ne sir"
"Is ok....ba damuwa" ya fadi yana katse wayar.
A nutse ya shirya cikin qananun kaya da sukai matuqar fidda sigarsa,sun masa kyau sosai,slippers ya saka ya fito izuwa sashin anninsa.
Ko ina agyare yake tsaf yana fidda qamshin turaren wuta na icce tamkar ba safiya ba,manyan abubuwa da yake jinjinawa anninsa da shi kenan,yake ganin da wuya ya samu mace wadda keda kaso daya cikin ukun halayenta,tsanani ko wuya,samu da talauci basu taba sanya annin nashi qazanta ba dai dai da qwayar zarra.
Tamkar ba safiya ba haka falon yake,kai baka ce ana zama cikinsa ba,dakinta ya wuce kai tsaye,a falonta dake manne da dakin gadonta ya sameta,wanda ita da iyalinta kawai ke zama a can,tsaf ya sameta kamar kullum,sanye da atamfar super riga da zani plain,dinkin jikinta yayi dai dai da shekarunta ya kuma yi mata kyau sosai,hannunta riqe da cup na tea na tangaran tana shan dafaffen shayin na'a na'a,yayin da daya hannun nata ke riqe da casbaha tana ja,qamshin falon nata daban da wanda ya baro,cikin fara'a ta aje kofin hannunta a gefe tana masa maraba da zuwa,cike da qauna ya isa gefanta ya zauna gabanta yana lanqwashe qafafunsa
"Barka da safiya anni...."
"Barka kadai muhammadu.....mun tashi lpy?"
"Lafiya lau,ya qarfin jiki?"
"Mun godewa Allah"
"To Allah ya qara lafiya da tsahon kwana mai amfani"
"Amin don isar annabi da alqur'ani....hala yau ba zaka fita bane"
"Zan fita anni....amma sai wajen azahar haka...inasu haidar ne?"
"Salim dai bai jima da ficewa motsa jiki ba,haidar kuwa kasan yana can yana bacci" sumarshi ya shafa sannan yace
"Mtswee....ya kamata na maidasu kamfani hakanan anni...zaman hutun ya isa haka"
"Ya kamata kam...nima ina shirin tuna maka....".
Amal ce tayi sallama ta shigo falon cikin dinkin doguwar rigar atamfa,tayi kwalliya a fuskarta tamkar ba safiya ba,ta laqanci khalipha sosai,me yakeso meye baya so,kanta a qasa cikin nuna yanayin jin kunya ta qaraso,khalipha ta soma gaidawa wanda hakan sam bai masa ba sannan ta gaida anni,jima kadan tace
" me xaka ci ya khalipha"son samu yace babu komai,amma annin ta hanashi hakan,ko baya sha'awa tace ya karba,don kada ya sosa ran dan uwanshi musulmi yaga kaman ya gwasaleshi
"Bani tea mara madara"
"Kawai?" Ta tambaya cikin salo,kai ya kada mata,sai ta miqe ta fice
"Muhammadu ya maganar da mukayi abincin da za'a kai gidan kawunka?"kai ya kada idanunsa na kallon qasa yace
"Anni....anni keta daban ce....kin manta komai kenan?" Murmushi tayi mai dauke da ma'anoni da dama sannan tace
"Muhammadu...duk wanda Allah ya doraka a kanshi ka riga ka fishi kenan har abada baida yadda zaiyi....sannan rama alkhairi gamai cuta ba illa ne ba.....baida amfani a lokacin daka tserewa wani abu ka dinga qoqari da fadi tashin tunawa da shi,da kuma maida hannun agogo baya...rayuwa idan ta wuce ta wuce kenan har abada,ka kalli gaba...ka kumayi qoqarin gina gaban...ka manta baya...zuciya mai yafiya ita Allah yakeso yake maraba da ita,zuciya mai manta sharri,zuciyar dake manta alkhairi itace abar neman tsari,koda yaushe ka zama mai manta sharri,mai saka cuta da alkhairi ina fata ka fahimta"
"Na fahimta anni....madalla da samun uwa irinki...koda yaushe ina godewa Allah daya bamu ke a matsayin uwa....dai dai da rana daya baki taba umartarmu da yin wani abu ba dai dai ba komai tsanani komai wuya"ya fadi yana gyada kai
"Burin uwa ta gari muhammadu ko yaushe ta dora diyanta kan tafarkin tsira duniya da lahira"
"Haka ne....yau za'a kai in sha Allahu,zan baiwa haidar ya kai masa"
"Allah ya albarkaceka kai da 'yan uwanka duniya da lahira....ya jiqan mahaifinku"
"Amin summa amin anni",ya jima suna hira shida ita har haidar da salim suka shigo suka samesu a haka,baibar wajenta ba sai da sha daya na safiya tayi,yana matuqar jin dadin zama da mahaifiyar tasa,macace mai hikima dattako da sanin ya kamata,idan ka zauna da ita ko yaya saika amfana ko ka qaru da wani abu mai muhimmanci da baka sanshi ba.
A dan gurguje ya shirya cikin shigar suits,wanda kallo daya ya isar sanar maka da awanne aji take,yana cikin gyara tie din wuyanshi gaban madubi idanunsa suka sauka kan vivo dinshi dake aje gefan madubi,murmushi ya subuce masa sanda ya tuna agender dinsu da haduwarsu ta qarshe da asma'u,dariyar data dinga masa shida wayar tana masa kallon wani shashasha gaula,tuni ya gama gane inda ta dosa,saidai game din da suke bugawa shida ita hakanan ke burgeshi tare da bashi qawa,yakan raya a ransa tunda har take tsaiwa suyi magana koda ba mai dadi bace watan wata rana zata saurareshi,zata fuskance shi,za kuma ta zama tashi,hakanan yayi sha'awar kiranta,sai ya kunna wayar yana ci gaba da shiryawa tare da jiran ta kawo.
Yana takawa harabar gidan wayar na ringing alamun tana shiga bayan yayi sallama da anni,yaranshi suka bude qofar motocin suna jiran qarasowarshi,ganin haka ya dakata daga dan nesa kadan,ta daga wayar saidai bata amsa ba,hakan ke alamta ta gane cewa shine
"Assalamu alaikum ranki ya dade"
"Ya akayi yaron oga?" Ta fada cikin isgili tana dariya dariya,baki daya ta daukeshi kaman wani abun wasa a gareta,don tasan cewa babu hadin kifi da kaska,babu abinda ya hada kashi da fura,sam tafiyarsu ba daya bace,hanyar jirgi, mota bata isa tabi ba,murmushi ya saki,kafin yace komai tace
"Naga alama kai kam da gaske kake.....tunda har haka ne....kazo ka sameni ina son ganinka" sosai maganar ta bashi mamaki,saidai baiji komai ba,cikin salo yace da ita
"To babu damuwa,saidai yanzu haka oga ya aikeni ne,ya turani wani waje,aqalla zanyi sati biyu haka,idan na dawo zan iya zuwa?"
"Baka da case" tace da shi tana katse wayar,kashe wayar yayi baki daya yana dan nazari,murmushi yake kadan kadan,daya daga cikin yaranshi nazir ya qaraso ya amsa ya mata waje.
Murmushi take bayan ta kashe wayar,babbar aminiyarta husna ta dubeta tana mata wani irin kallo
"Asma me kike nufi ne wai?,mutuncinki kikeson zubarwa kome?,mace irinki maisu hamid su hisham me zaki da wanda ke qarqashin gashin wani....haba asma" dariya ta saki tana duban husna
"Husna...husna...shi yasa nake sonki...tunaninmu daya,ra'ayunmu daya,saidai a wannan karon abinda na hasaso daban da naki,kinsan meke faruwa ne?" Ta fada tana gyara zamanta tare da fuskantar husna sosai
"Saikin fada" ta ambata tana duban asma'un sheqeqe
"Wannam guy din ya hadu tako ina....Allah ya masa baiwar kyau da qira....abu guda ya nakasheshi....bai mallaki hatimin da zai sanyashi mallakar zuciyata ba....amma kowanne mutum da ranarsa.....muhammad namiji ne da zaki shiga da shi kowanne waje da maza masu aji da jin su wasu ne ki kuma kankarowa kanki qima da mutunci....abu daya ne kawai,ki sama masa suttura ki bashi abun hawa duk sanda zai rakaki wani waje...." Kai husna take kadawa
"Maganarki haka take....amma asma'u,gani daya nayi masa naga kaman bazai biyu miki yadda kikeso,a ido kawai tsayayyen namiji ne,yana da wani irin kwarjini da cika ido,anya asma?" Dariya ta saki tana kada key din motarta dake hannunta
"Husnaaaa....kudi sune qarshen zance kin manta?" Murmushi ta saka tana gyada kai tare da gamsuwa da bayanan asma'u,ita kanta ya burgeta qwarai,saidai ba ajinsu bane shi saboda bai mallaki abinda za'a nuna shi ba.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Cikin sati biyun ya nemi duk wata hanya da zai dinga tuna mata da shi,batasan ya akai ba,batasan yadda ya samu number dinta ba,sai kiranshi da take samu babu qaqqautawa,bata iya wulaqanta mutum ba kaf rayuwarta,don itama bata saka kanta a lissafin mutane masu daraja ba,bugu da qari alfarma ya nema a wajenta,hakan ya sanya bata qin daga wayarshi koda na zata ce komai ba,ba zata iya cewa komai game da shi ba,don a yanzun zuciyarta tana jin kamar bata mutum ba,batajin zata karbi wani abu da ake kira soyayya,soyayyar da taje jin bata a duniyarmu,bata jin gaske ce,don bata taba dandanata ba bare ta adar da komai a cikinta.
🧣🧣 *DAURIN BOYE*🧣🧣
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
HASKE WRITERS ASSO
(Home of expert and perfect writers)
12
Qarfe daya da rabi na rana suka fito daga babban meeting na duka ma'aikatan kamfanin nasa,kai tsaye shida motocinsa suka wuce katafaren gidan abinci na purple palace da yake cin abinci don suci abincin rana,tafiyar minti sha biyar ce tsakanin kamfanin nasu da wajen suka isa sukai parking,tuni nazir ya bude mishi qofa,yana shirin fitowa vivo dinsa dake can gefan set din da yake zaune ta hau qara,shaf ya mance da ita,ya waiwayo yana dubanta,yasan mutum daya ne zaya kira asma'u,ita dince,wayar ya daga ya kara a kunnensa
"Kana ta wajen ina?"ta fada kai tsaye ba tare data damu da yin sallama ba
"Ina wajen aiki"
"Ohk....kazo purple palace restaurant ka sameni" ta fadi kanta tsaye kaman wani yaronta sannan ta kashe wayar,wayar ya sauke daga kunnensa,daya daga cikin yaranshi ya kira da hannu,qarasowa yayi cikin girmamawa ya masa nuni daya matso,cikin kunne ya masa magana ta mintina,kai ya gyada ya wuce zuwa cikin wajen cin abinci,minti biyu ya dawo ya sanar masa da abinda ya aikashi yi,kai ya gyada,sake kiran daya daga cikin yaran nasa yayi ya sukai magana,cikin mintuna sai gashi ya dawo riqe da baqar leda ya bashi,ya amsa,sannan a nutse ya soma cire suits dinshi na saman guda biyu ya bar ta ciki,takalmin qafarshi ya sauya zuwa mai sauqin kudi bayan ya kira daya daga cikin yaran shi ya dauko masa cikin boot din daya daga cikin motocin nasu,eye glasses dinsa ya cire ya kashe wayoyinsa ya ajjiye ya dauki vivo din ya riqe a hannunsa hadi da cire agogon hannunsa shima ya aje sannan ya fito daga motar,da kallo suka bishi,suna yunqurin binsa ya tsaidasu
"Ku janye motocin nesa kadan da nan wajen,karku biyoni ina dawowa"
"Yes sir" dukkansu suka ce,a nutse suka janye motocin suka musu muhalli a wajen da zasu iya ganoshi.
Ita daya ce zaune kan teburin cin abincin tana danne dannen waya, tasha ado cikin gown ruwan bula,ta yane kanta da mayafi ruwan powder mai turuwa,fuskarta sanye da sun glasses daya kusa mamaye fuskarta,da sallama ya qarasa wajen,hannunsa guda zube a aljihunsa,dayan riqe da baqar ledar,kai ta daga tana amsa sallama,ya mata kyau a idanunta sosai,saidai har yanzu bata gaza ganin aibunsa ba
"Kin yini lafiya ranki ya dade"
"Lafiya lau....zauna magana zamuyi" ba musu yaja kujerar da hannu daya sannan ya zauna,ya hade yatsunsa waje daya ya zuba mata idanunsa bayan ya aje ledar a tsakaninsu,kafin wani a cikinsu yace komai daya daga cikin waitress din wajen ta qaraso riqe da purple din leda mai tambarin gidan cin abincin ta miqawa asma'u ta amsa
"Kana kusa kenan dama?"
"Eh....naje wani aike ne na oga nan kusa"
"Yayi yaron oga...."
"Ga wannan,naga ni a hanya ne na miki tsaraba" ya fada yana miqa mata ledar,janta tayi gabanta sannan ta bude,abinda ta gani ciki ya bata takaici fuska a yamutse ta dubeshi
"Meye wannan?"
"D'ata,yalo,guava"takaicin daya qumeta shi ya hanata magana
"dauki muje" ta fadi tana nuna masa ledar da ma'aikaciyar wajen ta kawo tana miqewa bayan ta masa nuni da ledar da aka kawo mata,dariya ce taso subuce masa,sai kawai ya dauki ledar ya bita.
Nasiru shi ya soma tahowa da sauri da niyyar amsar ledar hannusa bayan ya hango fitowarsu,cikin zafin nama ya sanya hannunshi ta baya ya dakatar da shi,hakan ya sanya suka tsaya cak suna kallonsu har suka isa motar asma'un,ta masa izinin ya shiga itama ta shiga sannan ta tada motar.
Shiru ne ya ratsa motar jin hakan ya sanyashi cewa
"Ina zamuje ne?,kar oga ya nemi ni fa"
"Karka sake kawo min irin wancan tarkacen...ko na maka kama da maicin irinsu?" Dasauri ya sauya yanayin fuskarsa ganin ta waiwayo inda yake zaune,ya ragewa fuskar tasa kwarjini da tsare gidan da yayi
"Kayan marmari ne fa"
"Irin naku na talakawa?" Ta fada kai tsaye,cik yaji kalmar ta caki zuciyarsa,an taba gaya masa makamanciyarta cikin wani yanayi can baya daya kasa barin ransa,shiru yayi ya lula wata tsohuwar duniya,hakan ya wanzar da shiru a tsakaninsu har suka iso inda suka niyyaci zuwa.
Qaton botique ne wanda da alamu ke nuna na manyan yara ne,kai tsaye wajen suturun maza ta nufa tana dubawa yana biye da ita,bata masa magana ba,ita da kanta ta dinga zabar t.shirt zuwa trousers masu matsakaitan kudi tana miqa masa hadi da cewa ya duba ya gani,dariya ya dinga yi shi kadai yana biye da ita,duk abinda ta miqo cewa kawai yake yayi,yana yi yana duba price din kowanne riga da wando,a qalla ya manta yaushe rabon daya saka kaya masu wannan farashin,shi yake zabar kayan da yake so da kanshi,saidai ba cikin ire iren wadan nan qananun batique din ba.
Kaya ne kala biyar takalmi qafa biyu,kai tsaye wajen biya suka nufa aka mata total ta cire ta biya,jimillar dubu ashirin,yana biye da ita da kayan har zuwa cikin mota,dubanshi tayi kafin tace
"Ka fara amfani da wadan nan,ranar juma'a ka zabi daya daga ciki ka sanya,zaka rakani wata dinner"
"Ayyah...kinsan oga baya barina inje nan da can,sannan ni kaina bana yawon dare" wani kallo tayi masa
"Ka hadu ta halittar da Allah ya maka,saidai ka kwafsa tako ina,yaushe zan iya zaman aure da kai tabdi" ta fada cikin zuciyarta,amma a fili sai tace
"Kaman kai kace baka son yawon dare...sometimes idan kana wani abun kaman baki karatu ba" ta fadi cikin mamaki,murmushi kawai yayi yana dauke kansa,itama bata sake magana ba ta tada motar tana wani tsare gida suka tafi,saidai tana wassafa yadda zata dinga shiga da shi ne manyan gurare,cikin abokai da sauran 'yan uwa ko don ta kankarowa kanta mutunci wajen abokan takun saqa
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Har qarfe shida na safe tana saman abun sallah bata koma baccinta ba,saboda breakfsat da zata shirya na asma'u.
Shida da minti goma ta nufi kitchen din,saidai yau sabanin ko yaushe tun kafin ta qarasa ta jiyo kwarafniya a kitchen din
Lauratu ta taras mai aikin mummy,a mutunce suka gaisa,akwai zaman mutunci da girmama juna tsakaninta da duka yan aikin gidan sabanin asma'u
"Yau kinyi sammako lauratu"
"Wallahi,alhaji ne yace amin magana,mu sama masa tuwon acca da safen shi zaici" murmushi aysha tayi,tasan daddy yana sane baisa an gaya mata ba,tasan yayi hakanne don kawai ta huta
"Idan kin gama hada komai ki barmin zan dafa" aysha tace da lauratu
"Kai...aikin bazai miki yawa ba....bakya gajiya da girki?"
"Girkin daddy ne fa lauratu ko kin manta"
"Af....anyi haka fa,na manta ba'a shiga tsakaninku" dariya sukai baki daya kowa ya kama nashi aikin.
Na asma'u ta fara kaiwa dining saboda taji yau zata fita makaranta da wuri,tun sanda asma'u ta soma cin abincin asma'u taqi abincin duka masu aikin gidan,sautari ayshan itake girkin ta dama na gidan wasu lokutan,bata taba gajiya ko nuna damuwarta ba
Zuwa goma ta gama na daddy shima,ta shirya komai tsaf ta diba zuwa saman dining ta shirya a can,tana niyyar barin wajen taji shigowarsa
A ladabce ta qarasa ta gaidashi ya amsa mata sannan ta gaida mummy sa'adah da suka fito tare
"Ke suka barwa girkin indo?" Cewar daddy yana murmushi,murmushin itama kawai tayi
"Sannu indo bakya gajiya,Allah yayi albarka kinji"
"Amin daddy" ta fada cikin jin dadi,don har ga Allah tana jin dadi idan ya sanya mata albarka,tana jin albarkarsa tamkar ta mahaifinta da ba zata iya tuna yaushe da yaushe ya saka mata ita ba.
Tana tsaka da shiryawa bayan tayi wanka wayarta ta dauki ringing,a nutse ta duba sai taga ahmad ne,ta danji dadi kadan tunda ko babu komai zai debe mata kewa,wata rayuwa ta taso ta kadaici tun da can zuwa yanzu,duk da cewa gidansu na can cike yake da jama'a amma ita kusan ita daya take rayuwarta,ba qawa ba aboki ba masoyi,sai daga baya qawa qwaya tak ta shigo rayuwarta.
tunda tayi sallama hirar tata ta koma eh da A'ah,kusan ahmad ya saba da wannan halayya tata har baya damuwa,yakan ce bai taba ganin mace mara magana ba irinta,itakam saidai tayi murmushi,sun jima suna hira saidai magana ta qarshe daya gaya mata ta sanyata cikin matsananciyar faduwar gaba da fargaba har ta kasa amsa masa
"Aysha ina son a tambaya min daddy izinin zuwa wajenki,inaso na kafa gwamnatina sosai,na gaji da bulayi ta layin waya".
Sosai take jin tsoro da fargaba suna shigarta,kaman tayi tsaurin ido ko?,haka take ji zuciyarta na gaya mata,saidai wace hujja ta riqa da zata dakatar da ahmad din?,kan wannan batun sukayi sallama da ita,bai damu da jin cikakkiyar amsa daga bakinta ba,tunda ya sani magana wuya take mata.
*_BAYAN SATI DAYA_*
Xaune take dai dai cikin dakin nata gabanta cike da tarin litattafai,karatu take tuquru saboda jarabawa dake doso su.
Kiran mummy sa'adah ne ya shigo wayarta,a mamakance take kallon wayar don iya saninta indai tana cikin gidan masu aikin gidan take aikowa suyi kiranta,don ita ba ma'abociyar zaman falon gidan bace,zaiyi wuya ka sameta a falon indai ba wani abun zata yiwa mummyn daddy ko asma'u ba.
" kizo falon daddy yana nemanki"
"Toh" ta amsa,ta aje wayar cikin sanyin jiki,don tunda take zata iya irga shigarta falon daddyn,hijab ta lalubo cikin kayanta ta zura ta fice.
Yana zaune yana kallon labarai tare da shan coffe,yayin da mummy ke hakimce zaune a gafensa tana amsa wayar halimatu babbar diyarta,shi kadai ya amsa sallamar ta samu guri gefe daya ta zauna har mummy ta gama amsa waya.
"Aysha...na kira ki ne kan maganar ahmad yaron wajen hajiya laraba......sunxo sun sameni kan na bashi daman zuwa wajenki,yaya kike gani?" Ya qarashe maganar yana duban asma'u dake shigowa falon"shiru tayi kanta a qasa,rashin sabo kunya gami da tsoro suka baibayeta,shiru ya ratsa falon,yayin da agefe guda takaici ya kama asma'un,har yaushe ahmad ya soma son aysha?,yarinyar na nufin zata auri wani mai abun hannu kenan kamar ita?,sam ba zata taba bari hakan ta faru ba,sam ayshan bata cancanci shiga familyn alhj uba ba,don ta sani cewa ko su ba zasu nuna musu arziqi ba,ganin har lokacin bata ce komai ba ya sanya daddy yace
"Naga alamun kamar ba zaki sake kiyi magana sosai ba,bayan ke da asma'u duk daya kuke a wajena....shikenan kije ki duba ki gani?,idan har kin aminta da shi saiki sanarmin,ko ki sanarwa mummynku idan ma kina jin kunya saita sanarmin sarkin kunya,tashi kije koda wani abun?" kanta a qasa cikin kunyar tata ta kada kai alamun a'ah sannan ta miqe ta fice tana cewa sai da safe,duban asma'u daddy yayi
"Auta...ya akayi?" Cikin shagwaba kamar wata qaramar yarinya tace
"Daddy motata....daddy wahalar dani kawai takeyi,daddy ina buqatar canji"
"Motarki ko motarku keda aisha" mummy tayi saurin cewa don kada asma'un ta kwaba musu,itakam har ga Allah ma ta manta wai da wata aysha aka basu motar
"Yanzun ya kikeso ayi" ta samu abinda takeso,hakan ya sanya ta sake shagwabewa
"Daddy...canzata mukeso ayi mana"
"Amma baki fadi haka ayshan na nan muji nata ra'ayin ba" ranta ya baci a take,gani take kamar a yanzu aysha tafi matsayi a wajen daddyn fiye da ita,komai zaiyi tsakaninshi da ita sai ya sako ayshan,ko misali zai mata da wuya ya tsallake kan ayshan
"Banda abin daddy....ai kasan kunya gareta,ko tana nan dinma babu abinda zata ce"
"To mummyn yara" ya fada yana murmushi,shiru yayi na dan sakanni sannan yace
"Shikenan....yanzu kinsan abinda za'ayi?" Kai ta kada cikin zumudi
"Akwai wani abu da nake jira nan da qarshen watan nan,idan har komai yamin yadda nakeso,na muku alqawarin motoci ke da ayshan kowa tashi daban...kinga sai ku daina sharing haka nan" sosai albishir din ya faranta ranta,saidai ra gefe guda kuma baqin ciki nason hana murnar tata tasiri jin cewa wai ita da aysha za'a siyawa motar,bayan ita tazo ta roqi alfarmar
"Qwace goruba a hannun kuturu bazaiyi wuya ba" ta raya hakan a ranta,hakan data tuna ya sanyata warewa sosai ta yiwa daddy godiya cikin farinciki,sannan tayi musu sallama ta fice.
Saidai bata wuce dakinta ba,dakin mummyn ta koma ta zauna bakin gado tana jiranta bayan ta kunna t.v plasma tana kallo cikin tashar zee world,tasan lallai mummyn zata dawo ta shirya kafin ta koma dakin daddyn,awa guda cur kuwa saiga mummyn ta shigo,duban asma'un tayi cikin tana ciro kayan bacci
"Ya akai?,me kike har yanzu a nan baki kwanta ba?"
"Mummy....magana nakeso muyi"
"Uhmmm...ina jinki"
"Mummy....ya za'ayi ahmad din mummy laraba ya rasa yarinyar da zaice yana so da aure sai aysha?,haba mummy,wannan ai abun ayi daku ne cikin da'irar qawayenku,kuma wallahi wasu ma sai sun zageki suga kaman kin cutata masa saboda ba yaronki bane zako hadashi da wancan yarinyar da duniya bako daya ta juya mata baya ta rasa mai tallafarta sai mu"
"Na rigaki wannan hasashen,na kuma yi maganin matsalar....lokaci kawai nake jira,don duk wanda keda jibi da ni bazan taba bari ya aureta ba,bazan ce kada tayi aure ba,amma taje can ta samu dai da ita,dai dai ruwa dai dai qurji,amma familyn alhj baba ai ya tsere ma sa'anta"
"Yauwa mummy....ashe kema kin fahimci hakan...ammm sannan mummy....zancan siya mana mota tare" sai ta marairaice murya
"Mummy wallahi daddy yana saidamin mutunci ko cikin qawayenki mummy....ya za'ayi a dinga mana abu iri daya nida 'yar ruqo fisabilillahi mummy,ina laifin ya hada kudin motocin biyu ya siya min qwaya daya 2019?"
"Kina westing time dinki ne kan wannan maganar,kin riga da kin sani tunda har yayi niyyar saiya babu wata hujja da zata dakatar da shi,wancan issue din zan iya kuma zan maganinsa cikin ruwan sanyi wannan kam saidai kiyi haquri" kamar zata saki kuka tace
"Please mummy mana...ni kadaice fa kuma haka ya kamata naci gaba da kasancewa,mummy bai kamata na dinga abu iri daya da yarinyar riqon gidanmu ba,duk halaccin da muka yi mata kuma saita dinga shiga rayuwata haba mummy ki duba ki gani mana?"
"Alright,zanyi wani abu a kai,amma banso ki nuna masa komai koda ya riga daya siyo motocin"
"Thats my mom,shi yasa ko yaushe nake cewa nafi kowa sa'ar mummy a duniya"
"Uhummm,da yake nayi accepting duk abinda kike so ko?"
"Noooo mummy...duk abinda nazo da shi ai dai dai na fadi,kuma ci gaban 'yar autarki ne ko?" Ta fada tana rungume mummyn ta bayanta
"Naji ni barni na shirya wuce kije ki kwanta"
"Ok mummy,gud nyt"
"Allah ya bamu alkhairi".
Tana ratsa falon tana murmushi,duk plan dinta ya tafi yadda ta tsara yadda takeso,a rayuwa tana haushin aysha,ji take ayshan ta kai mata ko ina ta tsare mata wani abu,duk da azahiri babu wani abu da ayshan ta tsare mata,kyau irin na ayshan da sanyin hali nagarta da haquri sune abubuwan da suka tsonewa asma'un ido ba tare data san da hakan ba,a karan kanta tana ganin ayshan bata mallaki komai ba bare tayi hassada da ita,ita din ita keda komai,ita ta mallaki komai.
*_WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER (08030811300)_*
*DB*
13
*_BAYAN SATI BIYU_*
"Daddy game da maganar ahmad da aysha" mummy sa'adah ta fadi tana lanqwasawa daddy hular da zai fita da ita
"Uhmmm...ina jinki...tace wani abu ne?"
"Eh....maganar gaskiya yarinyar nan daddy sai nake ga kaman bata sonshi...bata fito kai tsaye ta furta ba....saidai yanayinta yadda ya nuna tana cikin damuwa,kasan kawaici irin nata ba zata fito kai tsaye ta fada ba" shiru daddyn yayi kadan yana nazari....yayin da mummy keci gaba da taimaka mishi yana shiryawa,bakinta fal da addu'ar Allah yasa zancan nata ya samu gurbi,don maganar gaskoya ba zata so ace dan hajiya larabar ya auri ayshan ba,ko don kare qimarsu a idanun sauran qawayensu
"Bari naje na dawo...sai muyi maganar"
"Shikenan.....amma dai gaskiya daddy kar muyi abinda zamu cutar da yarinyar,kaga tamkar amana ce a wajenmu"
"In sha Allah" yace mata.
Tana zaune cikin kujerun roba dake tsakiyar flowers din da aka qawata gidan da su,cikin kwanakin duk ta takure kanta saboda jarabawa,hakan ya sanya bata da wani cikakken lokacin kanta,tana jin bata da wani gata daya wuce karatun shi yasanya ba zatayi wasa da damarta ba,ta sani cewa duk randa ta kammala karatunta zaiyi wuya idan ba qauyensu zata koma ba,don bata ga wani dalili da zai ci gaba da zaunar da ita cikin gidan ba tana zame musu nauyi bayan duka dimbin halaccin da sukayi tsawon shekaru suna yi mata,don haka ba zatayi wasa da damarta ba,zata tsaya tsayin daka taga ta samu abinda ta samu wanda zata tsira da shi koda ta komawa can din.
Ko kadan bata ji tahowarshi ba saboda yadda hankalinta yayi gaba,daddyn shi ya soma ganota,a nutse ya karanceta,sai yaga ta rame din,wanda yake a badini karatun da take tuquru ne ya kawo hakan,bai mata magana ba ya wuce ganin tayi nisa cikin karatun ta.
Qarar bude get da fitar motar daddyn ita ta dawo da ita,ganin ya riga daya fice saita maida kanta taci gaba da karatunta.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Qarfe sha biyu na rana yayi sallama da anninsa a filin tashi da saukan jirgin saman malam aminu kano,wadda zata wuce saudiyya don yin umara,shi da sulaiman da farouq suka rakata suka juyo,kan hanyarsu ta komawa company ya bawa drivansu umarnin su wuce jami'ar bayero don yiwa wani abokinsa zuwan na zata,Dr mansur amini ne da har gobe khalipha baya mance halaccinsa a gareshi,hakan ya sanya yake matuqar girmamashi.
Duk inda motocin su suka ratsa sai idanu sunyi kansu saboda kyau da yadda suke daukar idanu,guri na musamman suka aje motocin nasu,yana yunqurin fitowa ya hango tahowarta daga nesa,cikin hanzari ya maida qafarshi tare da rufe murfin motar,ta cikin baqin gilashin motar ya zuba mata idanu har tazo ta wuceshi bata sani ba,su uku ne ita da wasu yammata kamarta da alama qawayenta ne,sai data wuce sannan ya fito suka nufi office din DR kai tsaye.
Sosai yayi murna da zuwan bazatan da khalipha yayi masa,sun jima suna hira har haidar ya qosa ya fice acewarsa zai shiga capteria yaci abinci kafin su gama,don baiyi breakfast ba suka fito
"Saika dawo...amma karka bata mana lokaci,muna da abubuwan yi da yawa da muka baro a company ka sani"
"Zan dawo da wuri in sha Allahu" ya fada yana fita da dan sauri yana wulga qafarshi kamar zaiyi ball da wani abu.
Ita daya ce zaune saman table din,hannunta riqe da littafi tana dubawa,duk da rabin hankalinta na wajen aliya data zaunar da ita a wajen,kwata kwata zata iya irga yawan zuwanta wajen,don sam ba wajen zuwanta bane,jinta take duka a takure.
Bata ankara ba taji fallatsowar abu ta gefan fuskarta zuwa hijabin jikinta mai sanyi,da sauri ta daga kai dai dai sanda haidar ke fadin
"Subhanallah....sannu don Allah" sosai lemon ya bata jikinta,amma ba wannan ne ya dameta,ta handout dinta take,ganin bata dubeshi ba ya sanyashi sake cewa
"Am sorry pls madam kiyi haquri don Allah,wallahi ban sani ba...."
"Babu komai..." Ta fada cikin hanzari tana miqewa ganin yadda hankula suka soma dawowa kansu abinda bata so kenan
"La la la.....aysha garin yaya?" Aliya dake takowa zuwa wajen ta fadi tana duban haidar dake tsaye cikin rashin jin dadi,sam aysha bata kula da ita ba da tuni ta tareta,saboda sarai tasan halin aliyan
"Bai sani ba aliya...muje kawai" ta fadi tana son janye aliyan
"Amma dai malam baka kyauta ba....duba yadda kayi mata da jiki fisabilillahi"
"Aliyaaaaa....bai sani ba ya kuma bada haquri...muje don Allah" ta fada tana janye da hannun aliyar
"Am so sorry kiyi haquri" ya sake fada yadda zata jiyo
"Is ok" ta amsa ba tare data waiwayo ba,sauke ajiyar zuciya yayi bayan yaga sun fice,duk da aliya saidata juyo ta watsa masa harara,sam bai zaci zatai sauqin kai haka ba,yayi mamakin yadda ta nuna babu komai cikin sauqi tayi tafiyarta,dama har yanzu akwai yammata irinta?,komawa ya sakeyi reception ya sake order din wani abun shan yace su hado masa da abincin da yace yana so.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Zaune take gaban daddyn tana sauraron bayaninsa,wanda batasan daga inda aka samo wannan hikayar ba
"Badon mummynki ta ankarar da ni ba aysha ai zan tsammaci kin aminta da ahmad dinne....tunda dai haka ne babu takurawa zan musu bayani su janye...Allah ya kawo miki wani na gari ya hada hankulanku waje daya" amsa masa kawai da amin,don bata da wani abin cewa,miqewa tayi zuwa dakinta tana jujjuya maganar daddyn,hakanan taji babu dadi har ranta,ita dai abinda ta sani batayi maganar kowa da ahmad ba baya ga aliya,bata ce tana so ko bata so ba,a daren abun ya dan dameta,amma da yake ba wani sanyashi tayi can cikin ranta ba zuwa safiya ta rage tunawa da abun,ta saka karatunta a gaba,wanda yake final exam ce suke dab da fara zanawa.
Wannan abu shi ya kusa kawo baraka tsakanin mummy sa'adah da mummy laraba,mummy sa'adah taso wanke kanta,amma da yake ba abinda mummy laraban bata sani ba na mummy sa'adan kallonta kawai tayi,hakan bai hana ahmad ci gaba da kiran ayshan ba.
Cikin wata guda suka kammala jarabawarsu,komai yazo mata a saqi fiye da yadda ta zata,saidai ba abun mamaki bane hakan saboda ita kanta tasan ba qaramin karatu tayi ba,sai fatan samun sakamako mai kyau ta yadda zata samu damar dorawa daga inda ta tsaya
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Qarfe biyar da rabi na yammacin ranar,tana kan hanyarta ta dawowa daga gidan anty halima babbar diyar mummy data aiketa,bata wani jima ba ta dawo don sam babu sabo ko sakewa tsakaninta da ita,saboda kusan halayyarta daya da asma'u,abinda ya rabasu kadan ne,kusan photocopyn ta ce asma'u.
Dan uban horn aketa maka mata tunda ta sauka daga napep ta gangaro layin su,a dan sace ta waiwaya,mota ce qirar pilot baqa wul,tun daga glasses har jikin motar baqi ne,sheqi kawai take da daukar ido,tsoro ne ya kamata saboda yanayin layin nasu da bai cika jama'a ba,hatta da habu mai trader da ba'a rasashi qofar gidan da yake aiki yau baya nan,hakan ya sanyata qara dan uban sauri cikin yunqurin isa gida ko zata samu ta tsere,saidai haqanta bai cimma ruwa ba,tana dab da qofar gidan ya samu nasarar tare mata hanya,cak ta tsaya tana maida numfashin tsoro har zuwa sanda mamallakin motar ya bude ya fito,matashin saurayi ne wanda kallo daya zaka masa kasan kudi ilimi da hutu sun ratsashi yadda ya kamata,sanye yake cikin dinkin shadda jamfa da wando kanshi babu hula,fuskarsa dauke da murmushi ya zagayo inda take tsaye
"Kinga na kamaki babu inda zaki kuma guduwa tunda kinqi tsayawa" tsoro ne ya sake kamata,ya kamata kamar yaya,idanunta ta dan zaro tana satar kallon gefe da gefenta ko zata samu wanda zaya ceceta,mahaukacin horn din da aka danna daga bayansu wanda ko qarar tahowar motar ita bata ji na ya sanyata zabura saboda tsoro,waiwaya sukayi duka su biyun ita da wanda bata mako san sunanshi ba suna dubanta,asma'u ce ta fito,tana sanye da doguwar riga ta atamfa mai gajeran hannu,wuyanta nannade da dan qaramin mayafinta,yayin da qafafunta ke saye da hillshoes,glass din fuskarta daya kusa mamaye rabin fuskarta ta zare tana dubansu tare da takowa inda suke
"Hafiz....." Ta ambata da alamun mamaki,bai amsa ba kuma baida niyyar amsawa,don shidin ba wani ganeta yayi sosai ba
"Ke aysha me kike a nan....dalla wuce gida" ta fada cikin hargagi,daman jiran hanya take,sam tsaiwar bata yi mata saboda rashin sabo,saboda haka da hanzari ta nufi get din gidan ta tura ta shige,ajiyar zuciya ta sako sannan taci gaba da takawa a hankali zuwa ciki.
A falo ta tadda mummy zaune cikin lesukan da take saidawa
"Kin dawo?"
"Eh na dawo mummy....tana gaidaki"
"Lafiyarki qalau kuwa?"ta fada tana qare mata kallo
"lafiya lau" ta fadi tana miqa mata kudin data ciro daga jakarta ta soma yi mata bayani.
Suna tsaka da lissafi asma'u ta fado falon tana huci
"Mummy....ki jama yarinyar nan kunne,tana neman ta janyowa kanta abinda yafi qarfinta don bazance yafi qarfinmu ba" maida hankalinta mommy tayi kan asma'un tana dubanta
"Wani abu ne ya faru?"
"Sai data zauna ta jefar da jakarta gefe sannan tace
" kinsan da waye na gansu a tsaye kuwa?"
"Waye ne?" Mummyn ta sake tambaya tana yatsina fuska idonta kan asma'un
"Fahad mummy dan gidan IG fa?,batasan bata kai can ba?,zata debo abinda zaya zo yafi qarfinta,koda yake ita daya zaya dama wallahi,ke har kin isa tarayya da maza irin hafiz?,kinsan yawan matan dake sonshi,kyau da kudi?" ta qare maganar tana duban aysha da wani wulaqantaccen kallo,ajiyar zuciya mummy ta saki wanda ke nuna bata zaci abun baikai can inda take tunani ba,yayin da aysha ke rabe zaune a gefe guda kanta na kallon qasa,gaskiyar asma'u zalla take gani cikin maganganunta,gaskiya ne,ita din ba kowa bace,ita din batakai matsayin kowa ba,don me zata tsaya da wani?,don me zata tsaya da wanda ya amsa sunan wani?,to amma abu daya ya kamata a mata uzuri a kai,bata bashi dama ba,bata kuma saurareshi ba
"Ko aure zaki indo baki kai ki auri dan gidan IG guda ba,ko yace yana sonki bai san ainihin wace ke ba,koda ya sani kuwa to yaudararki yake.....ki bari miji dai dai ke yazo miki amma ba irinsu hafiz ba,don wannan yafi qarfin kanki" ta rufe maganar tana bayyana inda ta dosa kai tsaye daga qarshe
"Allah ya kyauta...ke saiki kiyaye" cewar mummy tana ci gaba da lissafinta,gefe guda na zuciyarta tana ganin dacewar abinda asma'un tayi
"In sha Allah" shine kawai abinda tace tana miqewa hadi da daukar jakarta ta wuce daki.
Kallo mai kama da harara asma'un tabi bayan ayshan da shi,taso tattauna zancan da mummyn amma sai ta fuskanci hankalinta na kan business dinta,bata wani tsawwala ba ta wuce nata dakin tunda ta cika burinta.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Yammacin ranar lahadi ne wanda yake dai dai da kusan watanni uku da kammala jarabawarsu,sanye take da riga da skert na atamfa brown wadda aka yiwa ado da yarfin yalo,hijabi ne a jikinta wanda ya sauko mata iya gwiwarta,fuskarta babu adon komai sai powder da man lebe data shafa bayan ta kammala yiwa daddy da ya yini yau a gida abincin dare,ita daya ce zaune cikin lambun gidan saman wani lilo dake daure tsakiyar shukokin dake cike a wajen,sosai takeson wajen yana kuma burgeta,yana debe mata kewa ba kadan na,takan iya shafe tsahon a wanni a wajen ita daya bata komai sai tuna rayuwarta mataki zuwa mataki,har zuwa bigiren da yau ta kawota kai,sau tari idan aka nemeta aka rasa cikin gidan to tana maqale ne a wajen,wajene da mutan gidan basu damu da shi ba,ta alaqanta hakan da basu san sirrin dake wajen ba da irin ni'imar daya tara ba,yakan tuna mata rayuwarta ta qauye sosai,duk da cewa ba wani abun burgewa sha'awa ko dadi a ciki da zata iya dorarwa,a yanzu ma lilawa take kadan kadan,idanunta na kafe waje guda tana kallonshi,wayarta dake saman cinyarta tana fidda sautun karatun kitabuttauhid na malam ja'afar mahmud adam,ta nutsu sosai tana jin karatu hadi da fahimtarsa kamar tana gaban malamin,mayyar karatun addini ce,tana da bibiya da kuma kiyayewa,babu wani karatu da idan tana saurararshi yake sakata nishadi irin karatun addinin islama,kada ma ace hadisi take saurara,wanda yawanci tafi son taji karatun Dr ahmad BUK.
"Ke...kizo daddy na kira" ta tsinci muryar asma'u a tsakiyar kanta,batasan yaushe ta shigo wajen harta qaraso inda take ba,kanta ta daga tana duban asma'u dake sanye da fitted gown,kanta babu dankwali sai gashinta mai santsi dako yaushe ke cikin gyara yake matse a ribbom,kunneta maqale da earpiece wanda sanyashi ya zame mata kamar al'adarta,hakan kuma baya rasa nasaba da yawan jin kade kade da take da shi
"Tom" ta amsa tana tsaida karatunta
"Yauwa...idan mun shiga ki yiwa daddy godiyar mota" tana gama fada ta juya abinta ta wuce,sam ta mance wacce mota ma,sai data zo shiga cikin gidan data sake ganin motocin ta tuna,motocinsu ne da daddy ya musu alqawari ya kuma cikasu guda biyu ita da asma'un,tuni asma'u ta soma hawa tata,saidai ita ko lasisin zuwa kusa da motar bata samu ba bare ta hau ta tuqa,kasancewar a sanda motocin suka iso daddyn baya nan,tafiya ta kamashi na sati hudu,andai danqa mata muqullin ta riqe sau daya,bata juyashi sau biyu ba mummyn ta karba daga hannunta,daga ranar ba'a sake mata maganar ba,taga dai asma'u na hawa tata har makaranta sai data shiga da ita,ko sau daya bata sake tunawa da wani batun mota ba,bata a cikin lissafinta ko sau daya bare ta damu da lamarinta,bata manta ba a qauyensu ko jaki sai ta manta rabonta da hawanshi balle mota,tana can cikin uqubar data fi ta kurkuku,yaushe ma zata tuna da wani abu.
"Indon baffale" daddy ya fada a sanda ta gama gaidashi yana murmushi,sau tari yakan kirata da hakan Idan yana cikin nishadi ko yana son jefa murmushi bisa fuskar ayshan,duk da sunan yana da babban naqasu nashi na qashin kansa,amma har kwanan gobe tana farinciki da alfahari da shi,tunda ko babu komai DA UBA AKE ADO.
yadda daddyn ya maida yanayinshi kadai ya isa shaida maka cewa muhimmiyar magana ce zaiyi da su,hakan ya sanya kowa ya bashi hankali da nutsuwarsa a sanda ya soma magana
"Na godewa Allah daya nunamin lokacin da kuka kammala karatunku cikin nasara,ba shakka nayi alfahari da hakan yadda kuka kama kanku da mutuncinku,alhamdulillahi....toh,dukkaninku ina zaton ba wadda bata haure shekara a shirin ba...saboda haka abu na gaba da nakeson kowaccenku ta sani shine....aure nake da burin naga kunyi,a yanzu shine abinda ya rage muku,duk da ke indo bamuyi haka da ahalinki ba,munyi dasu zan maida musu dake a duk sa'ilin da aka kai wannan bigiren,amma na tabbatar da cewa ba zasu qi ko suyi jayayya da wannan batun da nake muku a yanzu ba,don suma ina da yaqinin shine hukuncinsu na gaba a kanki" a hankali taja hanci tana dauke tagwayen qwallar data ziraro daga idanunta,bata jin sun damu da rayuwarta bare suyi wani kyakkyawan tunani game da makomarta,ba wanda ya biyo sahunta tunda ta taho,ba wanda ya damu yasan inda take rayuwa,babu wanda ya damu da sanin wani hali taci gaba da kasancewa bayan barowarta mahaifarta,duk da tasan cewa basa maraba da hakan amma a qalla zata ji dadi idan wani ya bibiyeta da sunan ahalinta ne shi,ita dai tana godewa Allah da yaji qanta ya dubi rashin gata da galihu irin nata,ya jefo mata da daddy cikin rayuwarta a lokacin da take cikin tsananin buqatar matallafi,wanda zai jibanci lamuranta,bangon da zata dafa taji dadi
"Ammm....auta" ya kira asma'u
"Na'am daddy" ta amsa cikin fara'a
"Ina fatan kin samu wanda kikeso kun kuma daidaita kanku" kai ta kada cikin sauri
"Eh daddy...ka manta da hamid?...dan gidan alhj kutama?"
"Af....anyi haka,ja'ira ko kunyata bakiji ko?,ba zaki bari mamanku ta gaya min ba?" Fuskarta ta rufe da tafin hannunta tana dariya,shima dariya daddyn yayi kafin yace
"To ma sha Allah,babu damuwa,hamid ai dan gida ne,sananne ne...amma duk da haka zanyi bincike,zan nemeku daga baya ke da shi duka"
"Toh daddy" ta fada cikin murmushi,wani farinciki ke ratsata na daban,tana jin kadan ya rage mafarkinta ya tabbata,saura kadan ta shiga sahun manyan mata,wadanda za'a kira ko a nuna ace matar wane ce ko surukar wane ce,ahalin alhaji kutama ko qaramin yaro yasan nasibin da suke dashi bare babba,lallai zata tserewa sa'a nan kusa.
"Indo aisha.....kinsan hafiz?....hafiz yaron gidan IG...." Mummunar faduwar gaba ce ta ziyarci asma'u,ashe hafiz bai bar aysha ba,duk abinda ta fada mishi kan ayshan kenan bai masa tasiri ba,meke shirin faruwa?,lallai dole tayi wani abu,bai kamata aysha ta auri kwatankwacin wanda ita ta aura ba,har abada aysha na qasansu kuma zata ci gaba da tabbata a qasansu,ba zata yarda ko ta bari suyi gasa ko komanceceniyar jin dadin rayuwar gidan aure ba,yayin da qwaqwalwar ayshan ta tafi binciken mai sunan da daddy yake fadi,don ita harga Allah ta mance da babinsa
"Au hafiz daddy bai yarda ba?....kinji aysha ashe bai yarda da abinda kika gaya masa ba" ta fada cikin dariya dariya tana duban ayshan
"Kamar yaya?,me yake faruwa?" Daddyn ya fada fuskarsa na nuna alamun neman qarin bayani idanunsa tsakanin aysha wadda kanta ke qasa da asma'u
"Daddy kunyar aysha tayi yawa,dama na sani ba zata iya gaya maka ba,hafiz kafin yazo gareka ita ya soma samu yace yana so....to already akwai wanda takeso suka jima suna soyayya....infact sunma juna ma alqawarin aure,ta sanar masa shi kuma yace bai yarda ba,lallai shi ya ganta yana sonta,ba ruwansa da soyayyarta da wani tunda ba aure aka daura musu ba,tofa shine ya biyo ta wajenka" kai daddyn ke kadawa
"A'ah ba za'ayi haka ba....,ba yadda zanwa aysha auren tilas,shi wancan din ya sunanshi?,waye shi?" Tashin farko khalipha shine wanda ya fado ranta,babu wanda ayshan ta dace da shi irin khaliphan,ta tabbatar idan ta aureshi ayshan ta daina tarayya da ita cikin komai,tana da yaqinin bashi da qarfin da aysha zata samu jin dadin rayuwar aure makamanciyar tata ma bare irin tata,ba shakka yaron oga shine dai dai da aysha,qwarya tabi qwarya
"Sunansa muhammad abba"
"Ba komai...ki bani number dinsa,ni zan kirashi da kaina mu zauna nasan wayeshi" cikin sauri ta fiddo wayarta ta dauki wayar daddayn ta soma loda masa number khalipha.
Ji take kaman ba kanta ake maganar ba,tunda ita iya saninta dukkan maganganun da ke wanzuwa tsakanin daddyn da asma'u ba wanda tasan ya faru akanta,bata gane cewa da ita ake ba saida daddyn ya soma magana cikin tsokana
"Wannan kunyar indon baffale har yanzu bata ragu ba,fulatancinki na jikinki...kinje jami'a amma babu abinda ya ragu,yanzu badon Allah yasa ma'u tayi bayani ba na miki auren dole fa?" Ya qarasa maganar cikin sigar zolaya,wani sanyi taji yana ratsata a sanda ta fuskanci kanta ake dukka wadan nan maganganun,qwaqwalwarta ta tsaya da tuna komai bare ta samu abin fada,hakan ya sanya ta sake dunqulewa waje daya,yar dariya daddy yayi ga zatonsa tsabar kunya ke dawainiya da ita,kusan bata kuma gane meke gudana ba,daga qarshe dai ta fahimci daddy ya sallamesu,asma'u ta kama hannunta ta miqar tana zolayarta cikin kissa da kisisina,zolayar datake ganinta kamar a majigin kallon fina finai,saboda tsahon zamanta da rayuwarta da asma'un bata taba ganin murmushi kan fuskarta zuwa gareta ba,idan ko tayi murmushin to na mugunta ne ko cimma nasarar wani muradi a kanta
"Indon nan har yau daddy taqi ta waye wallahi,har yau indon qauye ce,na rasa ta yadda zan canza ta,tashi mu tafi karki nutse a wajen" ta ambata tana jan hannunta tana dariya,binta kawai tayi kamar wata shashasha har suka fice daga falon suka doshi nasu gefen.
_gaisuwa da godiya a gareku masoya na cikin grps namu na zafafa paid grp,da daurin boye grps_🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_HUGUMA_
*WITSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA MAI BUQATAR WADAN NAN LITATTAFAI SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
(08030811300)
*DB*
14
Tun basu shiga bangaren nasu ba ta saki hannunta tana dubanta
"Gata nayi miki fa....ruwanki kibar batun a haka ruwanki ki warware,amma ina tabbatar miki koda kin warware kece a ciki" tana gama fadar haka tayi gaba abinta ta barta a tsaye a wajen tana qoqarin gayawa kanta abinda ke faruwa,sam ta kasa tabuka koma
Wai meye haka ke shirin faruwa da rayuwarta?,ya ilahi wanne laifi ta yiwa asma'u haka?.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Tun yana toilet yana brush yake jiyo sautin qarar wayarshi,mutum daya ce ke kiransa ta layi asma'u,cire wayar yayi daga chargy ya koma saman sofa ya zauna sannan yabi kiran,plashing ya mata kamar yadda ya saba sannan ya aje wayar gefanshi yana ci gaba da tura saqonnin da suka hanashi kowamawa bacci bayan sallar asuba ta cikin system dinsa,ba'a rufa minti guda ba cikakke ta biyo kiran.
"Yallabiya kin tashi lafiya"
"Lafiya yaron oga"ta amsa kaman yadda ta saba masa,duk da yau akwai sakewa sosai cikin muryarta babu cunkushewa
"Yasu daddy?"
"Shi yakeson ganinka ma" sam bai tsammaci jin maganar ba daga bakinta
"Allah yasa ba laifi nayi ba" ya furta yana maida wayar handsfree ya ajeta kusa da system din nashi yana ci gaba da aikinsa
"Lafiya qalau....zaka sameshi da daddare ne bayan sallar isha'i"
"To Allah ya kaimu" bata amsa ba ta katse kiran kawai.
Aikinsa yaci gaba da yi jifa jifa yana tambayar kansa dalilin kiran,sai ya tsaida aikin nashi ya lalubi wayarsa yana neman wata lamba,bugu hudu aka daga bayan sun gaisa ya bada sautun kayan gwanjo riga da wando da takalmi mai sauqin kudi,a ladabce ya amsa masa sukayi sallama,ya sauka ya masa transfer din kudin daya gaya masa.
Knocking din qofarshi aka soma yi,da fari yayi shuru yana zaton zeenart ko amal ne,daga bisani ya fara jiyo tashin muryar al'amin
"Boss....kar kace min bacci kake har yanzu" miqewa yayi ya isa bakin qofar ya bude al'amin ya biyo bayanshi
"Tun asuba nake zaune aikin nan nakeson qarasawa....kawai nayi zaton cikin yaran can ne banason takura" ya qarasa fada yana miqawa al'amin din hannu suka cafke
"Mtsweew.....yara na binka komai yaji,zuqa zuqa da su amma kana musu haka....i swear da nine hadasu zanyi na auresu" harara khalipha ya watsa masa sannan yace
"Allah ya sawwaqe...an gaya maka kowa ma na mamajo ne irinka" dariya al'amin ya saki bayan ya gama hada coffe ya dawo gefan gadon khaliphan ya zauna suna facing juna
"Ba zancan na mamajo....dama ce Allah ya baka ba sai ka dama ba"
"To basuyimin ba....kai ba wannan ba.....na samu kira fa"
"Kai boss....duwatsun sun samu kenan?"
"Ba maganar wannan kamfanin ba....asma'u dazu ta kirani babanta yana son ganina,ina tsammanin na cimma gaci fa" kai al'amin yake kadawa yana dariya
"Kai mutumi na...zanso ganin qarshen wannan game din"
"Tare zamuje ka shirya anjima....but karka sakamin manyan kaya ina fata ka gane"
"Kana nufin....har baban nata a haka zamu je masa?"
"Qwarai kuwa...inason in samu 'yar gidan dattawa ne wadanda mutunci da addini suke duba ba dukiya ba" ya furta yana miqe qafafunshi saman center din dake gabanshi bayan ya ture system din gefe guda
"Yes!,Allah ya nuna mana anjima" daga nan suka fada batun harkokin kasuwancinsu.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Tunda suka taho a mota al'amin ke kallonshi yana diban dariya,kayan gwanjonsa abinsa sunsha wanki da guga,duk da araharsu da suka nuna amma basu kasa yi masa kyau ba,sun fito da ainihin xatinsa
"Ango....ango" al'amin kawai ke fada,shima dariyar yake yana cewa
"Ka fadi da kyau....ban taba zaton yarinyar zata ci wannan gwajin ba al'amin"
"Eh....ai ba daga nan take ba"
Kusan a qalla sun kusa mintina goma tsaye bakin gate mai gadi ya hanasu shigowa,suna tsaye daddy ya dawo daga masallaci sallar isha'i,yana shirin wucewa ya lura da su saidai bai zaci gidan suka zo ba,zai shige mai gadi ya masa bayani ya bashi umarnin ya shigo da su falon baqi.
Dukansu shida al'amin din na zaune saman carfet din suna dakon shigowar daddy,sallamarshi ita ta sanya khalipha sake gyata zamanshi tare da duqar da kanshi qasa har daddy ya qaraso,cikin girmamawa suka soma gaidashi kan khalipha a qasa
"A'ah....ku taso muyi musabaha ai tafi lada ko" al'amin shi ya soma zuwa sannan khalipha,sai a sannan ya dubi daddy
"Alhaji!" Khalipha ya furta cikin tsantsar mamaki tare da maida hannunshi da yake niyyar miqawa daddyn
"Alhaji dama kana nan?"
"Muhammadu...kaine?" Daddy shima ya furta cikin fara'a yana mamaki,gaisuwa ta musamman sukayi kowanne fuskarsa qunshe da fara'a kafin khalipha yace
"Na jima alhaji ina nemanka,har na gaji na haqura"
"Allah sarki muhammadu...ya bayan saduwa?,ya jikin maman naka?"
"Anni tana nan lafiya alhaji,tana raye tana kuma cikin qoshin lafiya sanadiyyar taimakonka"
"Ma sha Allah...ma sha Allah...naji dadi qwarai....kaine ko abokinka ke neman auren diya ta?" Kunya ta saka khalipha duqar da kanshi yana murmushi,al'amin ya fansheshi
"Shine alhaji" ya fada cikin sigar zolaya yana dariya,shima daddyn dariyar ya danyi,a zahiri yaji dadi sosai,koba komai yasan aysha zata shiga hannu na gari,yasan khalipha tun kafin ya kai haka,sanin farko daya masa a rayuwarshi nagartarsa da kyakkyawar halayyarsa ita ya soma gani tattare da shi"
"Ma sha Allah....ma sha Allah,lallai aysha indo ta dace....ta dace da miji da yayi dai dai da irin halayyarta" a hankali ya daga kai suka hada idanu da al'amin cikin mamaki,yana son yaga ko shi kadai yaji daddy yace aysha indo,kamar ko daddyn yasan tantamar da yakeyi sai yace
"Khalipha...ga indo nan na baka don bani da wani sauran neman shaida game da halayenka,ni kadai na ishi kaina shaida,ka dauka amana na baka saboda haka ka riqeta amana,Allah yasa albarka a rayuwarku....banason wasu dogayen bidi'o'i,magabanta kawai nakeso ka turomin"
"Madalla daddy...mun gode Allah ya saka da alkhairi" al'amin ya fada ganin khaliphan ya kasa cewa komai
"Shikenan khalipha.....sauran hira sai komai ya kammala mun samu zama sosai ni da kai ko?,amma ina fata zuwa yanzu kana da sana'ar da zaka iya riqe aysha"
"Alhamdulillah...Allah ya kawo duk wani wani rufin asiri cikin taimakonsa"cewar khalipha wanda qwaqwalwarsa tayi nauyi saboda tunanin daya cuno kai ya cunkusheta lokaci guda kamar qiftawar walqiya,tambayoyi fal kansa
"to ma sha Allah..masha Allah"da taimakon al'amin sukaiwa daddy sallama,suka rabu cikin karamci da mutunci yana tsokanarsa bazai tsaya yaga ayshan tasa ba ko kunyarsa yake ji,shidai yaqe kawai yake kusan al'amin shi ya karbi ragamar tafi da komai.
A sanda suke takawa zasu fice daga harabar gidan lokacin asma'u da nata gwanin hamid ke shigowa cikin gidan,shima yazo ne don amsa kiran daddy,dauke kanta tayi tamkar bata taba sanin wani mai kama da khalipha,da yake hakan kusan halayyarta ce sai ta karbeta,hakan ya sanyawa khalipha yaji har cikin ranshi cewa akwai wata a qasa,yana kuma buqatar qarin bayani,shin wace aysha?,wace ayshan da ake cewa an bashi ita,a ina take?,ya take?,ita din ta sanshi?,ko kuma itace tace tana sonshi,ko duka ma ba haka bane asma'u ce mai suna biyu?,kusan wadan nan sune maganganun da yake gayawa al'amin sanda suke cikin mota a hanyarsu ta komawa gida
" khalipha....inaga wannan al'amarin fa sam bazaiyuwu ba,tayaya zaka iya kunce DAURIN BOYE?,ka koma ka yiwa dattijon nan bayanin bakasan kan wace aysha yake magana ba kai asma'u kake neman aure"
"Al'amin kafin komai ina buqatar jin ta bakin asma'u"
"Eh hakan nada kyau" hannunsa ya saka cikin aljihun kayanshi ya zaro vivo dinsa ya soma neman layin asma'u,dai dai lokacin da take kitchen ta tasa aysha a gaba tana hadawa hamid kayan motsa baki,kallo daya zaka mata ka karanci ramar data qara bayan wadda take da ita,maganar nata cinta zuciya da ruhi saidai bata da wanda zata gayawa damuwarta,bata da abokin shawara bata sa abokin magana,bata da wanda zata gayawa matsalarta sai ita kadai a karan kanta,ba wanda ya damu da ita,ba wanda ya damu da rayuwarta,aliya ce bata nan ta mata nisa,nisan da batasan ranar dawowarta ba,bata samunta ko a waya,tunda suka kammala jarrabawa tayi sallama da ita ta wuce nijer can wajen dangin mahaifiyarta,ta sanar mata idan taje ta sayi layi zata kirata,saidai har yau shiru bata kira tan ba.
Tana ganin khalipha ne ta daga wayar ta kara a kunnenta tana dariya gami da cewa
"Yaron oga how far?"
"Asma'u...ban fahimci dukan abinda ke faruwa ba" ya fada cikin muryarsa da yau daya taji ta sauya mata,
"Ohk...kana buqatar qarin bayani kenan?"
"Haka nake son nace miki" ya maimaita cikin amon data ji ya mata kwarjini
"Ba wani abu bane,mata nayi maka"
"Ni na gaya miki ina da buqatar hakan?" Ya fada cikin zafin da ya fara bayyana har cikin muryarsa,hakan ya karya lagonta,ya kuma rage kaifin tsiwarta
"Karka damu fa....yar uwata ce" ta fadi tana duban aysha gami da tabe baki
"Koma wace bana so....sannan ki tanadi abinda zaki gayawa mahaifinki a yammacin gobe idan na sanar masa cewa bansan da maganar ba,saboda haka....get ready" ya kashe wayar yana jin zafinta irin zafin da bai taba jin irinsa ba daga gareta
"Man...ka shirya kawai gobe ka koma ka gaya masa komai...fine an wuce wajen" shuru khalipha yayi ranshi na dada baci,batasan wayeshi ba,dama da siffar daya zo mata da ita yasa ta rainashi tayi zaton wani gaula ne,batasan waye khalipha na asalin ba ba wannan fake khalipha ba,tana zaton ita din wata abace ko wata tsiyar ce ita,amma yaci alwashin gobe zai nuna mata real muhammad khalipha.
Tsaki tayi tana yatsina bayan ta kashe wayartata,bata jin komai hakanan bata jin ta aikata ba dai dai ba ko sau daya,bata saurari aysha ba ta kira daya daga cikin ma'aikatan gidan ta daukar mata kayan don tuni ayshan ta fice sanda take amsa wayar.
Da maganar ya kwana ya tashi,saidai a safiyar ranar tafiya ta sameshi wanda babbar qaruwa ce sa samuwa a gareshi da kamfaninsu baki daya,a qalla tafiyar zata daukeshi tsahon satittika biyu zuwa uku,hakanan ya shirya ya tafi ba tare daya samu isa zuwa ga daddy ba.
Cikin kwanakin gaba daya zaman gidan taji ya fice mata a kai,sam bata jin dadinsa duk da a baya ma ba dadin take ji ba,saidai abun ya sake sauya salo,a wancan lokacin idan zasu hadu da asma'u idan taga dama ta mata kallon banza,idan bata ga dama bama bata kallon nata,sai bada umarni ko hani,amma a yanzun da wuya su hadu bata bita da dariya ba,dariyar da batasan meye musabbabin yinta ba,yanayin yadda take jin gidan ya sanyata shirya kayanta ta nufi takai,a hakan tana zaton zata samu dan sassauci komai qanqantarsa,duk da tasan cewa yaudarar kanta kawai takeyi,hakan ce kuwa ta kasance,a can dinma ba wanda ya damu da tambayarta meye damuwarta ko meye matsalarra,hatta da karatunta data gaya musu ta kammala bata samu wani daga cikin gidansu mahaifinta ko na mahaifiyarta daya tayata murna ba koda na washe haqora ne idan ka dauke qawarta guda daya tak mero,qwarai tayi qoqarin yakice damuwar dake ranta saidai hakan ya faskara,wannan itace damuwa ta farko data jita da girma cikin ranta baya data mahaifiyarta tun bayan data fice saga qangin rayuwar data taba tsintar kanta,sati biyi cur data diba cikin garin tana fama da damuwarta ita kadai,daga qarshe ta tuqe gaban mero ta sanar mata da komai tare da neman shawararta.
Qwarai ran mero ya baci sosai,fada ta dinga tana jin inama itace,shawara ta qarshe da take ganin itace taje ta yiwa daddy bayani kai tsaye,ta amsa mata ne kawai don bata jin tana da qwarin gwiwar zuwa ta fuskanci daddy da maganar,tana tsodon dukan tambayoyi da bacin ran da zai biyo baya cikin gidan,ta sani sarai bacin rai kowa za fuskanta ba qarami ba,yana da sauqin kai saidai fushinsa baida dadi,baya kuma tafiya cikin sauqi.
Sati hudu tayi ta tattara ta dawo gida ba tare data samu wani sauyi ko ci gaba na yanayin da take ciki ba.
Daren data dawo mummy tayi kiranta
"Aisha...gobe da wuri nakeso ki tashi zamuyi baqi kaman sha daya na safe,a hada musu breakfast da dan sauran abun tabawa,duka kayan snacks na gidan nan sun qare tun tafiyarki,su lantana ba iyawa sukai ba haka freezer din ke zaune babu komai ciki....amma dai a soma wannan din daga baya kyayi na gidan baki daya"
"Toh" kawai tace ta miqe ta fice,tana mamakin yadda ko a fuska bata ga alamun mummy tasan meke faruwa ba,hutunta ba damuwarta bane bare tace ta huta tunda a yau yau din ta dawo daga tafiya,baqinta na gobe sune kawai damuwarta,zata iga ba zata iya ba,yata baro qauyen duka ba'a gabanta yake ba.
***************
Goma na safe ta kammala dukkan abinda ya kamata tare da taimakon lantana,a bakinta taji cewa magabatan hamid ne zasu zo neman auren asma'u,sun gama komai sun killace waje daya,tana shirin barin kitchen din asma'u ta shigo,sanye take da kayan bacci tana amsa waya murya qasa qasa,ko ba'a gaya mata ba tasan da hamid take wayar,a haka ta qaraso inda kayan suke killace ta soma bubbudawa tana gani daya bayan daya,kashe wayar tayi sannan ta dauki plate daya cikin ma'ajiyar farantai ta soma diban duk abinda taga yayi mata,aysha bata tanka ba tunda tasan ta gama nata,sai ta saka kai kawai ta fice ta bar mata kitchen din,a nan asma'u ta zauna ta cika cikinta,cikin ranta tana yaba dadi da tsaruwar girkin,saidai koda wasa ko sau daya bata taba daga baki ta furtawa wadda ke bautar ba.
Daga nan dakinta ta koma ta fesa wanka sa kwalliya,yau jinta take kamar mai yawo cikin duniyar sama,ji take duk duniya a yau babu wata halitta data kaita farinciki,mallakar hamid shine cikar mafarkin rayuwarta,ita kanta batasan irin son da take masa ba,bata kuma tsammaci zata so wani namiji irin haka ba.
Sha daya na safiya da minti bakwai motocin gidansu hamid suka soma jerin gwano a harabar gidan daddy,a sannan aysha na tsaka da karyawa,duk sa cewa ba wani abun arziqi take iya ci ba tub da can ma bare yanzu da maganar ta mata karan tsaye cikin rayuwarta,take kwana ta tashi da ita,kullum kwanan duniya maimaita shawarar mero take cikin zuciyarta,ko yaushe gwada yadda zata doshi daddy take,saidai har yanzu ta kasa samun qwarin gwiwa,dalili kenan da ya sanyata ta duqufa da yin istihara,don bata fatan ko dai dai da sau daya a rayuwarta ta biyewa son zuciyarta da zai sanyata nadama a gaba.
Iya motocin da suka jere kawai ya isa ya gaya maka lallai ba qananun mutane bane,irin buri da mafarkin asma'unne.
Kiran da mummy ke qwala mata ya sanyata aje cup din tea da tun dazun take qoqarin tursasa kanta taga ta shanyeshi kosa bata ci komai ba saidai yaqi tafiya,a hanzarce ta sauko ta tadda mummyn cikin kitchen tana duban kayan da asma'u ta bubbude ta diba
"Wanne irin abu ne haka?" Mummyn ta fada fana hade rai
"Anty asma'u ce ta diba" ta fada cikin sassanyar muryarta dai dai sanda asma'un ta sake dawowa tana naeman mummy cikina adon da tasha tamkar yaune bikin nata
"Wanne irin shashanci ne wannan,ayiwa baqi abu ki bude ki diba?,ce miki akai su qananun mutane ne.....lantana....ku dauka ku kai musu hakan tunda raini kikeson siya mana" a shagwabe ta dira qafa tana hade hannayenta waje guda
"Am sorry mummy....wallahi sha'awa suka bani shi yasa na diba"
"Ja'irar yarinya" ta fada tana jifanta da harara ita kuma tana dariya
"Aysha ku gyara kayan su lantana su dauka su miqa" ta fada tana juyawa ta wuce asma'u tabi bayanta,tsayawa tayi ta sake gyarawar kamar yadda ta umarceta sannan ta koma dakinta ta bar su lantana suna kwashe kayan zuwa babban falon baqi na gidan.
Zuwa azahar tana iya jiyo maganganun asma'u cikin farinciki,jifa jifa da maganar mummyn tana ta waya tana sanarwa,an kawo kudin asma'u naira miliyan daya,bakin mummy kam yaqi rufuwa,zallaf farincikinta yaqi ya qare.
*****************
Qarfe bakwai na daren ranar jirginsu ya sauka daga qasar china,ya tsuke yayi kyau sosai cikin suit dinshi baqaqe baki daya,idanunsa saye da sun glases daya sake fitar da hancinsa daga tsakiya,ga kuma sajensa daya kwanta yayi kyau ya sake fidda adon fuskar tashi,sati biyar din da yayi sai yaji kaman ya jima sosai baiga anninsa ba,hakan ya qara masa daukin zuwa ya ganta.
*****************
Tara na dare yana gaban anninsa,daga shi sai ita a parlourn,sau tari idan suna irin wannan zaman baka ganin kowa daga shi sai ita,saika rantse sa Allah shine auta ba sulaiman ba,tsabar shaquwa ce da qauna ta musamman da Allah ya sanya tsakaninsa sa ita fiye da duka sauran yaranta.
Abinci yake ci yana bata labarin yadda tafiyar tasu ta kasance har ya kammala cin abincin nasa wanda yayi dai dai da shigowar sulaiman cikin kwalliya da alamu daga wani waje ya dawo
"Daga ina kake haka?,ya zaku fita ku barta ita kadai cikin gida daga ita sai masu aiki?" Cewar khalipha
"Ban jima da fita ba ma,tunda ka tafi idan muka fita ita kadai take zama"
"Inasu amal din?" Ya tambaya yana dubanshi
"Washegarin tafiyarka suka tafi suma"
"Ohk....ohk..." Ya fada yana kada kai tare da hasashen wani abu,tabbas yasa ba yadda barewa zatayi gudu danta yayi rarrafe,saboda shi kenan suke zaune cikin gidan hakan ya sake tabbata ba domin mahaifiyarsa ba kaman yadda zeenart tasha nunawa
"Yanzun daga ina kake?" Khalipha ya fadabyana kurban tataccen ruwan inibi
"Ni yaya?" Ya fada yana shafa kanshi,murmushi anni tayi
"Kai din ga,nima so nake insan ina kaje" ta fada cikin salon zolaya
"Anni...kinfa sani...wata 'yar unguwa ce"
"Kadai fadi gaskiya....muhammadu idan bakai da gaske bafa 'yan uwanka zasu rigaka tashi....ya kamata dai ka maida kai,shekaru jaa suke,hakanan lokaci baya jira".maganarta ita ta sake tuna masa da case din daya tafi ya bari bai kashe ba
"Kwanan nan in sha Allahu anni....kici gaba da yimin addu'a" ya fada cikin sanyin murya,yana jin ya kamata ya kawo qarshen komai matuqar ya kashe wannan matsalar yana jin dama kawai zai bata ta zaba masa matar aure,yana da yaqinin ba zata zaba masa baragurbi ba,yana kuma saka ran cewa zaiyi dace.
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA MAI BUQATAR SIYA ZATA TUNTUBI WANNA NUMBER*
0803811300
*DB*
15
Qarfe takwas da rabi na daren ranar yana tsaye farfajiyar gidan,cikin sanyin san nan mai cike da nutsuwa yake qarewa wajen kallo tamkar mai wani nazarin abu na daban,sanye da shadda wannan karon sabon dinki daya siya ready made fara qal wanda kudinta bazai wuce naira dubu takwas ba baki daya,saidai kayan sun masa kyau ainun,haka Allah ya halicceshi wani irin jiki ne da shi mai kyau,komai arahar kaya ya saka suna amsarsa.
"Ah,muhammad ya ka tsaya daga nan?,kaifa dan gida ne daga yanzu ko ka manta?" Daddy da yayo tattaki tun daga parlournsa ya fito tarbarsa yake fadin haka,murmushi khalipha yayi,sai yaji kunya ta kamashi,ya dan sadda kanshi qasa yana shafa qeyarsa
"A'aha....kodai ba wajena akazo bane na koma?" Ya fada cikin zolaya yana murmushi
"A'ah....a'ah daddy" ya fada cikin yanayin kunyar,yana tuna karamcin mutumin wanda ya sani tun wasu shekaru baya da suka shude,da alama har kwanan gobe haka yake yana nan da karamcinsa,ba abinda ya sauyashi
"Ba damuwa ma koba wajena aka zo ba,muje ciki mu gaisa tukunna" a baya yabi daddyn suka taka har zuwa cikin parlournsa,cikin girmama juna suka gaisa ya tambayeshi anninsa da jikinta,ya amsa mishi lafiya lau take yanzu
"Ina fata dai komai lpy babu wata matsala ko?" Nauyi da kunya suka hanashi furta dukkan abinda yayi niyya,duk wani plan dinsa sai yaji ya ruguje,ya nemi dukkan hanzarinsa ya rasa shi,sai a sannan ya dinga tuna waye daddyn,wane irin halacci yayi musu a rayuwa?,banda shi da ya tabbatar ya rasa anninsa,banda shi a wannan rana da tuni yanzu yana gidan prison,banda shi da tuni yanzu bai a wannan bigiren da yake kai a yanzu,zaiyi wuya ya iya furta masa buqatarsa,idan da amana ruwa bazai dafa kifi ba,kuma rama halacci sai dan halak,bashi da manta alkhairin mutum a gareshi komai qanqantarsa
"Babu daddy alhamdulillah"ya ambata yana son tursasawa kanshi amsar duk wata qaddara da zata fadowa rayuwarsa
"To ma sha Allah...ni bari na kira maka indon da kaina" ya sake fada cikin zolaya yana ciro wayarsa daga aljihu ya lalubi mummy yace ta turo ayshan falon baqi.
Lantana ce ta shigo ta shaida mata lokacin da take tashi saman abun sallarta bata kai ga ko ninkewa ba,hakanan ta samu faduwar gaba duk da batasan dalilin kiran ba,kwanaki biyun hankalinta ya soma kwanciya kadan saboda ganin babu ta inda maganar aurenta ta sake tasowa,kowa harkar gabanshi yake,abun sallar ta aje hakanan ta fito da hijabin sallarta a jikinta tana takawa a hankali cikin fargaba.
Cikin sanyin nan nata da nutsuwa ta kutsa kai falon muryarta dauke da sallama,dukkansu suka amsa saidai khalipha bai iya dagowa ya dubeta ba saboda taraddadin wace ce indo,gefe guda ta samu ta gaida daddyn da baqonsa,baqon da bai dago ya kalleta ba,koda ya dago din batajin zata gane wane
"Ga baqonki nan indo.....kinsan da zuwanshi kika barshi tsaye a waje?...next time idan kika sake saikin bani ladar shigo miki da shi" ya fada da tsokana cikin amonsa sannan ya miqe yayi hanyar fita yana cewa
"Toh malam muhammadu...a gaida gida"
"Na gode daddy" abinda ya iya cewa kenan daddyn ya fice a falon aka barsu iya su biyu,shuru na ratsa falon,kowa najin baqunta tattare da shi,kowa da abinda zuciyarsa ke kai komo a kai.
A hankali ya daga kanshi dai dai da sanda itama ta tada kanta don ganin waye din duk da yadda zuciyarta ke luguden bugu,tare da yi mata gargadi da nuna mata kuskuren aikata hakan,a tare suka sauke idanunsu cikin na juna,karon farko ya tuna wace ce duk da cewa gani daya tak ya taba mata a rayuwarsa,saidai alkhairi bai mantuwa kamar yadda sharri bai mantuwa,yarinya ya gani wadda shekarunta basu kai na asma'u ba,hakanan shekarunta basu kai na amal zeenart ko rahama ba,farar bafulatana wanda bata da jiki sam,sai manyan fararen idanunta da suka sauka cikin nashi,daga haka bazaice yaga komai ko yaji komai ba,daga nata bangaren bata ganeshi ba ko daya,saidai abu guda da taji shine tausayin kanta da wani nauyi na musamman,ta san bata da wata daraja ko qima data rage mata a rayuwa,sadakar ko kyautar ta asma'u tayi ba tare da sanin daddyn ba,saidai ta yaya zata qaryatata bayan ita din tana jin kanta dai dai da baiwa maras 'yanci,wadda bata da ikon fadin albarkacin bakinta.
Kusan shuru shi ya biyo baya babu wanda ya sake cewa da dan uwansa komai,kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarsa,haka nan khalipha yaji duk abinda yayi niyyar fada baida wani muhalli ko gurbi,me zai gaya mata da zata fahimta,basu san juna ba bare a kai ga batun fuskantar juna har a fahimci me abokin magana yake fada?kusan haka suka qarar da lokacin kamar masu gasar nuna tsantsar iya rashin magana,yana da abinda zaiyi da yawa hakan ya sanya ya miqe ya doshi fita,yana gab da ficewa ya tsaya hannayensa zube cikin aljihun rigarsa yana dan nazari kadan,kaman zaice wani abu sai kuma ya fasa ya rufe da
"Sai anjima" yasa kansa ya fice,ta jima zaune a wajen ta qurawa waje daya ido tana jin yadda zuciyarta ta kacame da lissafe lissafen da basu da tushe bare makama,ta sani cewa bata da wani abun yi saidai ta zubawa sarautar Allah ido,haka ta gaji da zaman ta miqe zuwa cikin gida.
Tana gab da dakinsu asma'u na fitowa cikin hanzarin da batasan na meye ba daga nata dakin,saita ja birki tana duban aysha kafin ta soma mata dariyar data saba qasa qasa
"Yaron oga ya tafi?....ina fata kun gayawa juna kalamai masu dadi ko?,ina tayaki murna fa aysha kinyi dace da samun kyakkyawan miji,ko banza zaki more kyau.....kinga fa nayi taimako,bakiyi biyu babu ba,wato ba kudi kuma babu kyau,kin tsira da abu daya a nan......" Bata tsaya ta gama jin kalaman banzanta ba ta sa kai zuwa cikin dakinta,tana iya jiyo dariyar shaqiyancin ta kafin ta gaji tayi gaba.
Gefan gado ta zube tana dafe da kanta,wasu hawaye masu dumi suka soma bin kuncinta,karo na biyu kenan.....karo na biyun da saura qiris yayi kamanceceniya dana baya,wai shin ko bata da rabon zabin abokin rayuwa ne,bata da rabo a soyayya?...me yasa take rasa soyayyar mutane da dama?me yasa qaddararta ke fadawa hannun mutane kala daban daban suna juyata yadda suka ga dama haka?,wai ita din ba mutum bace yar adam tamkar kowa?,ko bawa tana tunanin yana da yancin kansa ko yaya ne ta wasu fannin,a haka ta sulale ta kwanta hawaye na fita daga idanunta,tana jin kanta cikakkiyar marainiya,cikakkiyar mara gata wadda tafi duk wani mara gata rashin gata,ba dangi suna nan amma akawai ya babu,babu uba ga uwar da bata da maraba da wadda babu wanzuwarta a doron duniya tsahon shudewar lokutta,iskar kadaici na ratsata da narkakkiya kuma karyayyar zuciyar da da take tsammanin samuwar daidaituwarta taci gaba da zama cikin dakin ita daya har dare ya soma nisa bata sani ba,saida lokacin tashinta yin sallar dare yayi sannan ta ankara ta miqe ta shige bayi ta daura alwala kamar yadda ta saba tun wani zamani can baya,tun a sannan batasan muhimmancin abinda take ba,tun a sannan bata da yaqini kan abinda take tazo ta hau saman abun sallarta.
*******************
Sau uku yana sako kai parlour din zai shigo sai yaja ya koma,muryoyin da yake ji ne sam baya son ganinsu,duk randa suka hadu gaba da gaba kuwa saidai tsautsayi da qaddarar ranar zasu ganshi,a duk sanda ya gansu ko yaji muryoyinsu wasu abubuwa marasa dadi da suka faru shekarun baya ke masa tariya akwanyarsa fes,tariyar da baya buqatarta,da yana da hali zai dawo da rayuwarsa baya ne ya cire wannan wajen don ya daina tunawa da shi gaba daya,yana mamakin ma yadda sukan iya shigowa har cikin gidan nasu su dubi idanun anni suyi magana da ita.
Wannan karon daya koma din sai daya bada tazarar awa guda sannan ya sake shigowa sashen annin,ga sa'ar daya ci kuwa sun tafi.
Da sallama ya shiga annin na zaune qasan carfet qafafunta miqe tana jan carbi da alamu ciwon qafarta ne ya motsa,da kallo ta bishi tana son karantarsa saidai ya basar yaqi yadda hakan ta faru
"Sai yanzu ka dawo daga cewa bari kaje kayi wanka?"
"Wallahi anni na...."
"Bance ka rantse min ba...ga abincinka can" ta fada tana dubansa,miqewa yayi yaje ya zuba ya dawo gabanta ya zauna kamar yadda ya saba koda yaushe,saidai wannan karon babu hirar da suka saba yi,saboda duk yadda yaso ya manta da tunanin dake katse masa hanzari hakan ya faskara,yana da damuwa ga zuwansun gidansu ya qara masa wata damuwar,ya tsani su rabi gidansu sam saboda yana jin babu alkhairi sam tattare da su,ya bayyana qarara ba don Allah suke sonsu ba
"Ya maganar kudin registration din ibrahim...naji har yau shuru" lomar dake bakinsa ce ta tsaye masa,sai da yayi dagiyar hadiyeta sannan ya lumshe idonsa ya bude su kan annin
"Saboda shi suka zo?" Idan saboda shi ne karsu sake zuwa don girman Allah....zan dinga tura musu,haidar yazo ya bisu da shi"ya fada yana laluben number qanin nasa,bacin rai nason taso masa yana danneshi don baison annin ta gani,ido anni ta zuba masa,halin ruqo ba halin khalipha bane,amma wani sauyin yanayi da jama'ar da suka fada rayuwarsu sun sanya ala dole yana kwatanta halin a kansu,ita kanta badon koyarwar ma'aiki ba batajin akwai wani abu da zai sanya ta sake tada kai ta dubi idriss da iyalansa bare har taimako ya shigo ciki,saidai wasu dalilai da koyarwar addini su suka mata burki...hakanan ita din uwa ce,duk abinda ta aikata zai zama abun kwaikwayo ne ga tsatsonta a kansa zasu tashi,ajiyar zuciya ta saki bata sake tada masa zancansu ba don tasan radadi da yake ji a duk sanda aka masa zancansu,har haidar ya shigo khalipha ya masa transfer din kudin yace ya tsaya a atm ya cira ya kai musu,sai daya fice sannan annin ta sako wata hirar wadda ta mantar da shi damuwarsa,duk da tunaninsa na kasuwa....yana so ya sake komawa daddy...yana son su zauna ya fahimtar da shi yadda maganar take,amma kuma zamanshi da anninsa ya shafe komai.
*******************
Karo na biyu ya sake dawowa wajen daddyn,saidai girman halaccinsa da yake masa yawo cikin ido da qwaqwalwa yasa ya kasa furta masa wata magana makamanciyar wadda yake zuwa da ita,a wannan karon bai nemi ganin aysha ba,ya nuna sauri yake daddyn kawai yazo gaisarwa,saidai ita din ta ganshi sanda take cikin garden,ta kuma baro ciki ne saboda asma'u da qawayenta dake karakainarsu sake ba qaidi,uwa uba bata son hayaniyarsu wadda take ratsowa har cikin dakinta,hirace mara ma'ana da sam bata da buqatar jinta,ko kadan basu da kintsa bakinsu,har yazo ya fita din tana zaune wajen,shima din ya ganota,saidai yayi tsammanin bata ganshi ba.
Sau uku khalipha na zuwa saidai ya gaza furta komai,wani arashi kuma duk sanda zaizo tana hangoshi shigarsa da fitarsa,shi dinma yana ganota daga cikin garden din data mayar muhallin zamanta,baisan meke zaunar da ita a wajen ba,saidai yana zaton ko yanayin tsirran dake wajen ne ke qawatar da ita,amma bbai taba ganin tana wani abu da zai nuna hakan ba.
A zuwa na hudu ne ya nemi ganinta,yana son yayi aiki da shawarar da zuciyarsa ta bashi,ya fara sanin wace ita halayyarta da dabi'unta,hakan shi zai dorata a mizanin hukunci daya dace,yana tsoro kar yaje ya tafka kuskure,kar yayi gudun gara ne kuma ya tadda zago,sanda akai kiran nata wannan karon daga wanka ta fito akace mata tazo tayi baqi,mamaki ya mamayeta,ita din?,baqi kuma?,ina take da mutanen da suka damu da ita har zasuyi tattaki zuwa wajenta,aliya dai bata nan bare tace itace,bugu da qari ko kadan bata qaunar fitowa sararin gidan baki daya saboda yau sarkin isa da taqama hamid zaizo,hakan ta shafa mai ta zira atamfa riga da zani ta dora hijabinta ta fito.
Tun daga falo take duba baqin saidai bata ga kowa ba,lantana ce ta gaya mata yana can cikin lambu
"Waye" take tambayar kanta,kamar wadda ke a tsorace haka take takawa har zuwa cikin lambun,har ta isa tsakiya bata ga kowa ba,hakan ya sanya ta tsaya dude dube,sai data gaji ta juya da niyyar fitowa a nan ta hangoshi kan wasu kujeru dake can gefe guda na lambun,yana zaune da waya a hannunsa yana dannawa,dauke idanunta tayi daga kanshi gabanta na faduwa,wani irin kwarjini taga yayi mata irin wanda babu wani namiji data taba gani yayi mata,sai taji kaman ya cika wajen,kamar wani tsoro tsoronsa haka taji tana ji cikin jininta,duk da cewa itaba ba ma'abociyar kallon maza bace,bama maza ba ko mace 'yar uwarta bata iya irin wannan kallon ba.
Bayan daya daga cikin kujerun ta tsaya tamkar mai tsoron wani abu,idanunta zube saman teburin dake gabansu
"Salamu alaikum" ta furta cikin muryarta mai sanyi wadda ta soma rawa rawa alamun ko yaushe tana iya sakin kuka,kujerar da take tsaye kusa da ita ya tura mata idanunshi a kanta yana karantarta,ta fuskanci me yake nufi ga kuma nauyi da taji idanunsa sun mata a kanta,hakan ya sanya bata jaa ba ta matsa kusa da ita ta zauna tana curewa waje daya kamar zai cutar da ita,sai data zauna din sannan ya amsa mata sallamar
"Suna na muhammad khalipha...kefa?" Ya tambaya yana maida vivo dinsa aljihun gaban rigarsa
"Aishatu...." Idanunsa ya dan lumshe kadan sannan ya budesu saboda girman da darajar sunan da yake gani,sunan anninshi ne hakan ya sanya yake ganin qimar duk mai sunan da shi sunan kansa,gyaran murya yayi bayan ya hade yatsunshi waje guda
"Ban sani ba...ko kina da masaniya kan abinda yake faruwa...abinda 'yar uwarki tayi da abinda ke shirin faruwa a garemu gaba daya,da amincewarki?..da saninki?...ko da sa hannunki?"
"Ina mai baka shawarar ka bijirewa auren aishah,saboda bakasan wacece ita ba....sanin wace ita ya sanya asma'u shirya abinda ta shirya din" ta fada kanta tsaye,rauni da dakiya na tarayya cikin zuciyarta lokaci guda,abinda bata taba zaton yana haduwa cikin zuciyar dan adam cikin lokaci daya ba,idanu ya tsira mata cike fal da mamakin wacce iriyar mutum ce ita?,a yadda tayi maganar ya tabbata da shi matsoracin namiji ne babu abinda zai hanashi miqewa ya nemi arcewa,bai taba gamo da mutumin dake baiwa mutane shawarar su gujeshi ba komai girman laifin da yake aikatawa ba,amma fuskarta kawai ta karantar da shi akwai wani lamari mai girma dake cin zuciyarta wanda bazaiso yanke hukunci ba sai yasan meye shi,idanunshi ya janye daga kanta ya saki ajiyar zuciya bayan ya sarqafe yatsunsa na hagu da dama waje guda.
"Sannunku masoya" muryar asma'u cikin sautin amon dariya yayi kutse cikin nazarin da kowannensu ya fada,a tare suka daga kai suka dubeta ba tare da kowannensu yace komai ba
"Yaron oga an samu damar bullowa kenan?....hakan yayi kyau" ta qara fada cikin dariya dariyar da tafi gama fa izgili
"Allah ya barku tare,musha biki" ta kuma fadi tana dai dariyar izgilanci
"Ammm....yaron oga....ina muku fatan alkhairi fa a auren da zakuyi....saidai ina fatan ta gaya maka cewa ita din ba jinin gidan nan bace....sannan yana da kyau ka shirya zuwa qauyensu ka gano tushenta....don kada ma ta yaudareka tace maka nan ce mahaifarta ko daddy na shi ya haifeta ni sistern ta ce...na barku lafiya" ta fada tana ficewa daga lambun,yanayin kwalliyarta kawai ya isa ya gaya maka cewa hamid ne yazo,khalipha shi ya fara dauke idanunsa zuciyarsa na tafasa,yana jin kaman ya tashi ya nunawa asma'u true colour dinsa,yana jin kaman ya hukunta asma'u a wajen,mahaifinta shi ya fado masa a rai,tunashin da yayi shi ya katse masa dukkan wani hanzari nasa,tilas ya tattara duk wani fushi da bacin rai daya taso masa ya lanqwameshi ta hanyar sakin ajiyar zuciya mai tsaho,yana mamakin yadda ta zamto jinin daddy 'yarsa tsatsonsa,ba shakka Allah dama ya fadi yana fitar da rayayye daga matacce ya kuma fitar da matacce daga rayayye,wani bari na zuciyarsa yaci gaba da tausarsa da danneshi yana gaya masa cewa AKWAI LOKACI.....
Idanunsa ne suka sauka kan fuskar aysha wadda tuni ta jiqe da hawaye,bakinsa ya bude zaiyi magana ta daga hannunta da sauri ta dakatar da shi
"Har abada tushena shine abun alfahari na koda kuwa wa na zama cikin doron qasa....har abada inason iyaye na komai lalacewarsu sune silar zuwa na duniya....har abada dangina sune dangina bani da makwafinsu da zan sauya su da su komai girman sabani ko rashin fahimta,ni aisha har abada ina son qauye ina taqama da shi saboda shine asalin kowanne dan adam koshi waye saidai idan shi din ya zama kaza ce ci ka goge bakinka" wadannan kalamai su suka sauka cikin kunnuwan khalipha da asma'u dake shirin ficewa a wajen,kamar zata tanka saita tuna hamid data bari yana jiranta kada ranshi ya baci yayi tafiyarsa,hakan ya sanya ta waiwayowa ta kalleta da niyyar bata gargadi,sai kuma tayi rashin sa'a idanun ayshan bai kanta ta sanyasu tsakiyar tafin hannunta kamar mai qayyade adadin jijiyoyin dake kaiwa hannun nata jini da dawo da shi,dole ta juya ta fice ba tare data samu damar maida raddi ba.
Wani irin abu shi ya shiga kaiwa da kawowa cikin zuciyarsa idanunshi a kanta,karon farko da ya yiwa wata mace kallon qurilla tsahon girmansa
"Bana buqatar sanin ko ke wace ce?....ki riqe tarihin rayuwarki naki ne."jiqaqqun idanunta da suka jiqa har gashin idanunta suka qara fito da tsahonsu da baqinsu
"Ya zama dole kasan wace aysha matuqar zaka karbi aure na....rashin sanin wace ce ni ya ta'allaqa ne da hukuncin daka yanke wa karbar aurenmu"
"Kinsan waye daddy kuwa a wajena?,kinsan me ya taba yiwa rayuwata?"
"Kamar yadda bakasan waye ba a wajena da abinda ya yiwa tawa rayuwar yake kuma kan yi mata....indai haka ne dole kasan wace ni" ta fada hawayen idonta naci gaba da zuba.
"Suna na aishah umar sanda,hafaffiyar wani qauye cikin qaramar hukumar takai dake jihar kano takai,mahaifiyata sunanta naja'atu,mahaifina cikakken bafulata ni ne,hakan ya sanya sunansa na asali ya bata saidai a kirashi da baffale,mahaifiyata kuwa 'yar manoma ce amma dukkansu mazauna qaramar hukumar takai ne,duk da irin wakaci ka tashin dake faruwa tsakanin manoma da makiyaya amma haka Allah ya qaddara aurensu,saidai irin abubuwan dana dinga gani bayan an haifeni na soma girma nasan cewa ba qaramin kai ruwa rana akayi da iyayen baffana ba kafin su yarda ya auri ummi na.
Ni kadai mahaifina ya haifa har ya rasu,nayi wata iriyar rayuwa daga tashina zuwa girmana,wanda tunda na girman baisan wani abu waishi qauna tausayi ko jin qai ba,bansan soyayya ba,bansan lallashi ba,bansan kula ba,rana tsaka na tashi na girma na gani a matsayin 'YAR TSAKAR GIDA,da wahala na budi ido,da bauta na saba,da bin umarni ko hani nake aiki koda yaushe,babu mai cemin sannu,babu me cemin na gode,babu me cewa me yake damunki,babu mai cewa me kikeso meye bakya so?,mahaifiyata ta bar gidan ta barni da qananun shekaru,ta barni tun bani da wayo sanin ciwon kaina,bana ce ga abinda ya faru ba don bani da masaniya,a hannun kakata inna yelwa ta barni,saidai kuma hakan a baki kawai yake,mahaifina yana da yayye uku qanne hudu,dukkansu cikin gidan suke suda matansu da 'ya'yansu,duk cikinsu babu mai mace daya,daga mai biyu sai mai uku,ga tarin yara da suke da shi,tunda na tashi nafi kowa rashin gata cikin gidan,kusan a tsakar gida nake qare rayuwata,hakanan duk wani aikin wahala na gidan yana wuya na,nice lungun baba auwalu,nice lungun baba sani,nice lungun baba salisu,nice na baba rabi'u,khamisu tasi'u,sabi'u,babu wanda ban gararamba a lungunsa yaransu na zaune,kuma ban isa nayi kuskure ko inyi ba dai dai ba,yadda akeso haka zanyi komai sauqi komai wuya,ba ruwansu da zafi sanyi rani da damina,kuma kakata tana kallo,asali ma sai na lura da babu abinda ya shafeta,ita kanta idan ta kama sai ta jani ta daka iya son ranta,duk cikin jikokinta ni tafi tsana,duk wanda zai hukunta ni koda hukuncin yafi girman abinda na aikata din ba damuwarta bane,saidai ta tayasu ma da jifana da miyagun kalmomi kala kala
"Shegiya ta gado baqin hali irin na gidansu uwarta naja,tur da jinin gidan saluhu,jinin fitsara jinin kafirar zuciya" wannan kalmar tun ban fahimtar me take nufi har nazo na ganeta,na kuma haddace ta ta zauna daram a kaina,bansan me nayi musu ba,bansan wanne girman laifi ne dani cikin gidan ba da kowa bai qaunata,yaqi jinina,tsangwamar bata tsaya iya cikin gidanmu ba,koda sauran mutane sai suke min abinda suka ga dama ganin bani da wani tsayayye wanda zai tsayan,ko cikin yara sa'anni na ina cin duka,kyara da tsangwama,musamman daya zamto nafi kowa qazanta na kuma fi kowa rashin gata,a lokacin mahaifina yana raye,bashi da abin cewa duk da cewa shima na lura bai wani damu dani sosai ba,yafi nuna kulawa ga sabuwar matarsa mai suna kuluwa,zuwan kuluwa gidan sai ya sake zama tamkar sabuwar babin azaba ne a tare da ni,yar kulawar da baba na ke nunawa kaina sai na rasa,ta janye hankalinsa tsaf,hakanan hatta da kakata ta koma qarqashin iko da mulkin kuluwa,a da babana kan zauna dani mu danyi hira,yakan yawaita cemin na yafe masa,zuwan kuluwa gidan da komawar inna yelwa qarqashin ikonta sai ya haddasa sababbin jam'iyyu kala kala a gidanmu da kuma kishin bal bal mai azabar zafi a tsakanin faccalolin,nidai a sannan bani ga tsuntsu bani ga tarko,ta rayuwata nake,duk inda na tattala ta sai anga an rushe,walau baba kuluwa ko sauran faccalolinta,kowa yagata yake figata yake,ina da son tsafta,ina son karatu kaman me,ina son gayu amma duka sun gagareni,duk da kaf cikin yaran gidan babu wanda ya damu da karatun saini daya,walau arabi ko boko,kuma babu wandaya matsanta musu kan hakan,son karatu na sai ya zama kamar wani sanabe ne ko iyayi ne a ganinsu da ganin ina nuna ai ni nafi kowa,hakan yasa aka qara qaimin datsemi duk wata qofa ta ilimi,tun sallar asuba idan na tashi nake bauta cikin gidan ba wanda ya damu da tsaftata ci na sha na suturata ko karatuna har dare ya shiga sannan ya maida haqarqarina na kwanta,da qyar nake samun sauran abinci naci ko sau biyu ne kacal a rana,haka zan hada guntu guntunsu duk lalacewarsa naci,watarana na kwana tsakar gida gefan dakin inna yelwa,watara na na kwana gefan turken awaki idan ta koreni daga qofar dakinta,watarana kuma ta barni daga cikin dakin nata amma daga bakin qofa komai sanyi komai damuna,kayan sawata kuwa a wani tsohon kwandon qarfe na shara suke,idan damina ta sauka haka zasuyita jiqewa ina matsewa ina shanyawa,dama gashi ba cikakken wanki suke samu ba.
Wani abu da Allah ya doramin shine son mahaifiyata da qulafucinta,saidai abinda ya soma girgixa hankalina fiye da dukkan abinda yake faruwa dani shine...." Tsinkewa maganar tayi daga harshenta,saboda wani daci da abu mai tauri daya riqe mata maqoshi,kuka nason kufcemata,aduk sanda ta tuna wannan gefan na rayuwarta bata iya jurewa
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA MAI BUQATAR SAYA ZATA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
0803811300
*ko kuma*
07067124863
*DB*
16
A duniya babu abinda ta tsana ta gani kamar ni,ban taba ganin tsana qarara daga idanun wani dan adam zuwa wani ba irin wadda nake gani daga idanun mahaifiyata zuwa gareni"ta fada muryarta na rawa alamun gabar da tazo tana taba zuciyarta matuqa gaya fiye da duk labarin dukka wahal halun data sha a baya
"tunda ta bar gidanmu......" Sai ta kasa ci gaba saboda kukan daya qwace mata,tayi matuqar qoqarin riqe sautin kukan saidai ta kasa,hakan ya sanya ta qudundune kanta cikin hijabi ta soma sakin kukan nata bayan ta toshe bakinta.
Shuru khalipha yayi tamkar baya wajen,saidai idanunsa idan ka kalla har sun soma sauya kala kadan,wani abu yake hadewa mai daci daga harshensa zuwa maqogoransa,labarinta ya taba wani sashe mai girma na tashi rayuwar,saidai babban abun al'ajabin yadda qiyayya mai qarfi ta qullu tsakanin uwa da 'yarta,garin yaya?,meye sanadi?,zaya so yaji amsa,baice da ita komai ba hakanan bai tsaidata ba har sai data rage kadan daga cikin radadin da take ji cikin zuciyarta,ta sanya hijabin nata ta soma goge fuskarta,hannunsa ya saka ya laluba aljihunsa da yake baya rabo da hanki,zaro shi yayi ruwan madara mai kyau da taushi da qamshi ya aje a tsakiyarsu,sai data kalleshi da idanunta da suka dan tasa saboda kuka sannan ta saka hannu ta dauka cikin sanyi tace
"Na gode" sai data goge fuskarta sosai sannan ta miqa masa,kai ya kada alamun ta riqe,bata sake cewa komai ba ta dunquleshi a tafin hannunta sannan ta miqe tsaye tana cewa
"Ina zuwa" bai ce mata komai ba har ta juya ta fice daga lambun,tana fita wayarsa daya boye cikin aljihun wandonsa ta dauki vibration,a hankali ya zarota yana duba mai kiran nashi,P.A dinsa ne da suka zo tare,ya latsa ya kara a kunnensa
"Sir.....har yanzu baka gama ba....we r waiting"
"Kuna iya zuwa wani waje kafin na gama,idan na gama zan kiraku"
"Okey sir" ya fadi suka katse wayar baki daya sannan ya maidata aljihun wandon ya sake hade yatsunsa cikin junansu kamar yadda yake a baya.
Daga nesa ya hangota dauke da gorar ruwa data lemo hade da cup,gabanshi ta qaraso ta zauna a inda ta tashi sannan ta tsiyaya ruwa da lemon ta aje gabansa,turasu yayi suka koma gabanta,yana nufin ta dauka ta sha,sai ta kauda kanta kadan don ba zata iya shan abu gabansa ba,don ba sabonta bane hakan bata iyawa,ganin bata dauka din ba ya sanyashi cewa
"Uhmmm...." Ta gane manufarsa,hakan ya sanya ta dora cikin muryarta mai sanyi
"Tunda ta bar gidanmu bata taba wucewa ta qofar gidanmu ko bayan gidanmu ba,gaba daya ta daina bin layinmu,hakanan duk wani abu daya hadata alaqa da gidanmu ta barshi,sau tari idan aka aikeni zan lallaba na tafi gidansu ummina,na tsaya soro ina leqenta,saboda nasan idan na shiga me zai biyo baya,duka ne kuma na shashi babu adadi,hakanan idan labari ya kai kunnen inna yelwa cewa naje gidan nan ma itama tana kamani ta daka iya son ranta,harda dungurin kai,akwai sanda irin haka ta faru,ummi na ta kamani ta nada sannan ta gaggayamin maganganu da a sannan na kasa gane kome take nufi,ina komawa gida da aiken da inna yelwa ta yimin itama ta kamani ta yimin duka,ina tsugunne kusa da turken awaki ina kuka sabira 'yar kawu auwalu wadda ta dan girmemin tazo shiga bayan gida,tsaki taja bayan ta dunguren kai na
"dama zaki haqura ki daina bibiyar waccar tsohuwar taki mai baqar zuciya da shegen ruqo,don ba zata taba sonki ba saidai zaki koma cikimta ta haifoki cikin wani ahalin ba wannan ba" maganar tata ta tsayan a raina,nayita jujjuyata saidai na kasa fano bakin zaren,a sannan akwai quruciya tattare da ni saidai manya manyan laguzzan dana haddace basu da iyaka wanda ake gayan,wasu ina girma ina ganesu ina warwaresu,wasu kuwa har kwanan gobe bani da amsarsu bani damai zaunar da ni ya warwaren.
Qiyayyar da mamana kemin tayi grman da kaf qauyenmu sunsan me ake ciki,da yawan mutane abun na basu mamaki da al'ajabi,sai wasu suka soma min qazafin anya ba shege na tayi ba koma shine sanadiyyar sakinta da akayi asirinta ya tonu,kalmar shegiya na santa tun a qananun shekaruna....saboda akwai wata 'yar qauyenmu data taba cikin shege ta haife,irin tsangwamar da naga ana nuna mata da 'yar data haifa qarsge ma tabar garin nasan cewa ba qaramin mummunar abu bace,saidai gakan ya taimaka min qwarai wajen kare kaina da kare mutuncina wanda ba wanda ya damu da shi,kusan kalmar shegantaki daga gidanmu ta fito,daga bakin kakata ta soma fitowa.
Kullum ta Allah saina je gidansu ummi na labe a soro komai jibgar da zan sha idan ta ganni bai dameni ba,wataran naci kuka na na qoshi idan na hangota a tsakar gida,abu daya ne ya sanya na rage zuwa na janye jiki sanda ta furta cewa zata tsinen idan ba rabu da ita ba,na kuma san illar tsinuwar itaye wa yaransu ta sanadiyyar makarantar dare da na saka kaina nake satar jiki naje da daddare idan aikeni,inacin duka a nan ma da dunguri duk sanda naje na jima din,inda Allah ya taimakeni ba'a taba gani na ba cikin daliban bare aje ace an ganni a hanani zuwa tunda babu wanda yake zuwa cikin yaran gidan.
Allah ne ya hada jini na da malamin makarantar darenmu malam musbahu,yanayin rayuwar da yaga ina fuskanta ya sanyashi tausaya min sosai,yana taimakamin gun karatuna,dalili kenan daya sanya na zama zaqaqura cikin daliban,sau tari yakan ban sabulun wanka dana wanki,saidai baya bani zallar kudi,sabulu dai yana taimakan da shi,hakanan yana bani shawarwari wanda hakan ya taimakan qwarai wajen saitan rayuwata,shi ya tsayamin ya nema min makarantar gwamnati dake cikin garin takai,manyan daya hada inna yelwa da su shi ya sanya ta haqura badon son ranta ba ta barni,amma fa wani lokacin ma sai an fita break nake zuwa,watarana ma idan taso tana hanani zuwa,duk da hakan na samu karatu sosai.
A sannan aka tada zancan aurara da yara matan gidanmu wadanda suke sa'anni na ne,kowacce tana da nata saurayin amma banda ni,a sannan ma na sha cari da maganganu kala kala,sam ban damu ba don ba wanda nake kulawa ko ince ba wanda ke kulani saboda rashin gata da kuma qazafin shegantaka da aka yimin,nima hakan ya yimin,saboda babban burina shine naga na kammala primary na naci gaba,haka aka soma shirye shiryen auren su su biyar.
To ashe suna qwafe da malam musbahu,ranan da naje karbar sabulu wajensa wanda ban taba haka ba amakaranta yake bani bayan an tashi,ranar ma na matsu ne zan wanke unifoarm dina da ban samu damar wankewa ba saboda gobe monday.
Ihu muka ji wanda bamusan daga inda yake ba,ashe talle ce faccalar inna kulu,tana daga cikin masu matsanta min fiye da kowa
Tana kishi da ummina ko sanda tana cikin gidan fiye da kowa,hakanan suna shiri sosai da inna kulu,duk da shirin ba don Allah da ma'aiki bane,hakanan bai kai har zuci ba.
Kalaman da mukaji yana fita daga bakinta shi ya daga mana hankali dukanmu nida malam musbahu
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'una,malam musbahu....indo....ashe masha'arku kuke aikatawa?....dama abinda kukeyi kenan shi yasa ko yaushe kuke liqe da juna?...wannan wacce iriyar masifa ce....yauni talle naga masifa quru quru da idanu na" kafin kace meye wannan ta tara mana jama'a,fadi take
"Wallahi na gansu.....na gansu da idanuna turmi da tabarya" abinka da qaramin qauye dake mamaye da duhun jahilci cikin qwaqwalen mafi yawa daga cikinsu nan suka yarda,suka soma mana tofin ala tsine harda masu shirin dukanmu,ba shiri aka miqamu hannun mai gari a can gidan na kwana,a ranar naga tashin hankalin dama jima banga irinsa ba,duk da ban wani damu sosai ba saboda ni nasan cewa muna da gaskiya babu abinda mukayi,har wayewar gari zuwa yammaci maganarmu ake zuzutawa ana yayatawa cikin qauyenmu da kewaye,mai gari masanin ilimin addini ne,hakan ya sanya baiyi hukunci da ka ba saida yayi kyakkyawan bincike
Kowa ya shaidi malam musbahu hakan shi ya wankeshi ya wankeni a idanun wasu,yayin da wasu suka zauna daram kan zancan inna talle ciki harda ahalin gidanmu kafff,hakan ya sanya ma wasu daga cikin jahilan iyayen yara suka soma janye 'ya'yansu daga makarantar,hakan ba qaramin bata ran malam musbahu yayi ba,dalili kenan daya sanyashi tarkata ya nasa ya nasa yabar garin,wanda hakan niba qaramin sake sakani yayi cikin halin ha'ula'i ba,don dama tun kafin yabar garin aka hanani zuwa makarantar,ko nan da can ma an hanani fita,ina turke a daki kamar akuya daure cikin mari,komai saidai a wurga min haka zan dauka naci komai muninsa idan naji yunwa ta kamani qwarai,duk wannan abun da ake ummina na cikin garin tana gidansu amma tamfar ma batasan me yake faruwa ba,ba motsinta ba gilminta,wannan shine abu na biyu daya sake dagulamin lissafin rayuwata,kuka nake ba dare ba rana,ina zaune a daki a daure,ba wanka ba wanki ba sallah,haka na dinga zama a dakin tsahon kwanaki.
Nasan zakayi mamakin ummina ko?,kace ina mahaifanta?,su basu isa su gaya mata taji ba?,mahaifinta Allah yayi masa rasuwa,tunkan rasuwarsa kuma mahaifiyarta ta rasu don itama ita kadai ta haifa,ta taso a hannun matar ubanta,duk yadda dangin mamanta dake jahar kaduna sukaso daukarta tun a lokacin babanta yaqi,haka suka haqura suka bar masa ita,itama ta danci wuya hannun matar ubanta,saidai ba wata mai yawa bace kasancewarta mai baki,tana iya qwatar kanta,kuma bata barin ta kwana bata yadda a danne ta ba,hakan kusan shi ya ceceta.
Inna kulu matar babanta macace mai azabar son abun duniya,ko yaya zaka bata to kaine mai daraja da mutunci,tana iya take gaskiya saboda kudi ko abun duniya,tana ganin dai dai indai kana miqa mata sai ta gaza gaya maka ko gyara maka haka rayuwarta kenan,dalili daya sanya sanda mahaifiyata ta soma girma tana amfanarta ya sanya bata iya yi mata gyara ko gaya mata gaskiya,saboda ko bayan rasuwar baaba taci gaba da zama a gidansu ne ba gidan wanda ta koma,cikin makusantan ummi da wanda ya isa da ita dama wanda bai isa ba ba wanda baisa baki ba kan abinda take gwadamin wanda ni bansan mafari ba,saidai duk wanda ya mata maganar tamkar ya kawo qarshen alaqarsa ne da ita,tun ana yi har aka gaji aka zuba mata idanu.
Ina cikin wannan halin labarin yin auren ummina ya sameni,na tsinceshi ne ina daga kurkukun da aka sakani,zaman da matan gidanmu keyi qasan bishiya na kisan dabe daga safiya zuwa yammaci,an baje kolin maganar kowa na tofa albarkacin bakinsa,a nan naji cewa a legos zata zauna,ta samu mijin ne cikin dangin mamarta dake birni,kusan duk wanda zai bude baki yayi magana a kai ba alkhairi zai fada ba,sai mugun abu yarfe da sharri,duk da cewa na danji kishin wani da zata aura bayan ga baba na amma na mata murna jin zata samu ci gaba ne,duk da bata damu da rayuwata ba,haka aka sha biki cikin garin na kece raini da tsone idon 'yan adawa,yako tsone din,don zama na musamman akayi cikin gidan har na kwanaki biyu ana tattauna abinda aka gani wajen bikin da abinda ya faru,don faccalolinta banda inna talle da tata adawar ta bilhaqqi ce ba wadda bata je ba bata kuma riqo tsarabar gidan bikin ba,ina daga daki ina jiyo qarar motocin da suka zo suka dauki ummina tabar garin takai zuwa legos,a sannan kamar nayi tsuntsuwa naje na taresu na ganta koda ba zata min magana ba,koda zata dakeni,koda zata tsinemin din kamar yadda tace,don ban sani ba shin zan sake ganinta ko mun rabu kenan?,a haka ina hawaye har na daina jiyo sautin motocin.
Tun daga ranar ban sake ganin ummi na ba sai idan tazo garin ganin gida,duk sanda ko zata zo din zan saki jiki na jima a soron gidan baba ina kallonta,koda kuwa waye ya aikeni,ko aiken waye a hannuna,a sannan duka sa'anni na suna gidan aurensu,a masu shekaruna ni kadai na rage cikin gidan.
Wani zubin kuma hanyar da take bi nake zuwa na zauna,ina sane nake fitowa wai yadda zata ganni ko ta manta da ni ne,sau tari idan muka hada ido harara take cilla min ko taja min qwafa,ta rage duka na,don wani bin har tazo ta tafi ba zaka ga ta dakeni ba,hakan kuma ina zaton baya rasa nasaba da girma da taga na fara,saidai ban isheta kallo ba,ko muhalli kuma bata yarda mu hadanikam kallonta kawai nake yadda ta canza lokaci daya tayi kyau,a yadda naji mutanen gidanmu na gulmar mijinta yana da shi,tana kuma jin dadi fiye da gidanmu data bari nesa ba kusa ba.
A haka rayuwa taci gaba da garamin,ga girma na fara yi,a lokacinne na samu mutum daya yake kulani saboda qazanta ta da rashin gyara wato dan ladi,babu mutumin dana tsana a rayuwata sama da shi,saboda tantirin dan iska ne,haka nan cikakken dan shaye shaye,babu nau'in abun mayen da baya sha kaf cikar fadin garinmu an sanshi,a hakan kuma 'yan gidanmu tayani murna suke an samu mai sona,idan dan ladi zai shekara bina da yimin magana bazan kulashi ba saboda haushinsa nake ji,a haka dai bai haqura ba yake bibiyata,duk da shima wani lokaci idan ya gaji yaba min maganganu yake
"Dalla can donma na rufa miki asiri nace zan aureki?,waye ma ya taba cewa yana sonki?,aibu fal tattare dake,uwarki ma data kawoki duniya gudunki take amma ni na bugi qirji nace ina sonki,banza mara rabo,kuma wallahi saina aureki inga ta tsiya" iren iren wadan nan kalaman yake jifa na da shi koda a hanya muka hadu gaban mutane,bama irin ranar da yake a cakensa.
A haka ummi na tayi haihuwar farko ta haifi mace,duk sanda tazo garin saina aika yara a zuwan qawarta ke aikowa a bani yarinyar ta dade a waje na,ina son yarinyar ina qaunarta sosai,inajin kamar ota kadai nake da ita a duniya,hakan ya sanya basma ta saba da ni ta shaqu da ni,sam ummi bata farga da hakan ba sai da basma ta soma wayo ta fara yawaita yi mata zancena,a nan naga tashin hankali,tayimin duka ta kuna koran gargadi mai qarfi babu ni babu ita,itama basman bata qyaleta ba,saidai ko gezau bamuyi ba,duka kuwa muna shanshi bama ya kamar sanda basman ta sake wayo,take debo kayan bayarwa cikin na mamanta da nata take kawo min,ranar dukanmu ta hada ta daka ta kuma jefoni waje tare da aikawa gidanmu ayimin gargadin zuwa gidansu tunda ba gidanmu bane,haka inna yelwa ta dinga bala'i da masifa,shikenan duk sanda tazo gari bani ba sake fita har sai tabar garin.
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKO SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*DB*
17
Tashin hankali na gaba dana sake fuskanta shine shirin aurar da ni da ake ga dan ladi,wanda babu wanda ya tambayeni ko ya tsaya jin ra'ayina aka bada ni gareshi,tamkar auren sadaka zance aka shirya yimin,domin babu abinda dan ladin ya kawo gidanmu da sunan kudin zance kayan sa rana da sauransu,hasalima sake tunzurashi ake akan cewa ya taimaka su rabu da qaya,domin wai na tasamma tsufa a gabansu,duk da cewa duka duka a sannan ban wuce shekara goma sha uku cikin ta sha hudu ba,duk da lalacewa irin ta dan ladi wai mahaifiyarsa qyama take ya aureni,tana cewa za'a joganawa danta ni,danta yafi qarfin aurena,amma da yake dai Allah ya hukunta cewa sai na shiga gidansu na dandani tasu kalar azabar haka aka daura aurena da shi,babu wani abu dake nuna cewa bikin yarinya budurwa ake,duk wani gata da akewa budurwa yayin auren fari ni ban sameshi ba ban ganshi ba,a wannan lokaci nayita zuba idanu ko zanga ummi na amma shiru,bama ganinta ba,naso ace ko wani motsi nata da zai nuna tana sane da ni ko tana sane da aure na nasamu daga gareta amma maqatau,hakanan dangin mamata suka hado kayan da zasu iya dai dai qarfinsu suka kawo amma inna yelwa ta aje gefe tace sam ita da taba kayan zuri'ar gidansu ummina,ta hadamin buta tukunya da kwanukan cin abinci,sai katifa da labulaye da fulalluka iya abinda aka jera min kenan aka daukeni ziqau babu gyara aka kaini,hana rantsuwa dai ranar an sakani nayi wanka da kyau.
Tunda aka kaini dakina qwaya daya wanda aka jawa katangar kara da makewayi kusa da shi nake zaune ina raba idanu,santin dakin nake a raina saboda sau dubu yafi bolar da nake kwana kyawun gani,tun ina jiyo hayaniyar jama'a har gidan ya dauki shuru,ina nan zaune bansan sanda tsohuwar gajiya ta sanyani na sulale nabi lafiyar ledar da aka malalawa tsakar dakin ba.
Faduwar abu da naji yif a kaina shi ya farkar da ni a zabure nayi yunqurin miqewa,saidai nauyin da yake kaina ya fi qarfina,sai dana lura da kyau naga ashe dan ladi ne,wanda maganganun da yake furtawa kawai sun isa su gaya maka a make yake qwarai..."qasa aysha tayi da kanta,cikin jin nauyi da kunya tace
"Nayi alqawarin bazan boye maka komai ba.....idan nace komai ina nufin harda rayuwar aure na da danladi....a wannan daren dan ladi ya nemi karbar haqqinsa ta qarfi,saidai sam naqi yarda,haka muka dinga artabu da shi cikin dakin,wanda daga qarshe da yaga ina neman gajiyar da shi ya kamani ya yimin duka dan gaske wanda sai da naji a jikina,duk da na saba da duka kusan ni jakarsa ce amma wannan ya shiga jikina matuqa,saboda an yishi ne cikin fitar hayyaci,kafin kace meye fuskata ta kumbure haka jiki na,yadda naga rana haka naga dare,amma duk da hakan ban fasa tashi sallar asuba ba yadda na saba,bayan na gama na samu na rabe gefe guda ina maida numfashin wahala,idanu na kan dan ladi dake baje saman katifata,ni kuwa gani kwance kan dandanyar ledar daki.
Bashi ya farka ba sai tara na safe,zuwa lokacin har tsakar gidan gidan ya cika da hayaniya kala kala ta yara da manya,da alama kowa ya shiga sabgarsa,tashi yayi yana hardewa wanda hakan ke nuna bai gama wartsakewa ba ya dubeni ya watsan harara gami da jan qwafa,da alama yana sane da abinda ya faru jiya kuma yana qufule da ni,ficewarsa yayi,tunda ya fice din kuwa ba wanda ya nemi ni hatta da shi kanshi,sai da sha biyun rana ta kusa naga yunwa na shirin hallakani na miqe na debi ruwa na shiga makewayi nayi wanka,na cika kofi da ruwa na sha,na danji dama dama a jikina sannan na saka hijabina na fito cikin gidan,gida ne kamar namu na mutane da yawa,matan yayye da matan qanne da uwar miji,haka aka dinga bina da kallo wanda nasan baya rasa nasaba da sanin wace ni da kuma kokawarmu ta daren jiya da.nasan mafi yawa sunyi zatan wani abu ne ya faru,nidai na gaidasu na wuce wajen mamar dan ladi da suke kira da fatsi,tun daga yanayin amsa gaisuwarta nasan cewa akwai wata a qasa,ilai kuwa hakanne,domin kuwa na sake fadowa jahannama ta biyu ce,duk wata bauta ta gidan kusan a kaina take,zagi hantara da gori kuwa babu kalar wanda ba'a yimin,babu wanda ban haddace ba cikin qwaqwalwata,gefe daya kuma idan dare yayi mu hadu da dan ladi wanda kullum sai yayi yunqurin karbar haqqinsa ni kuwa naqi bada hadin kai,saboda bala'in qyanqyaminsa nake ga tsoro dake tattare da ni,uwa uba qiyayyar da nake masa,idan ya gama yunqurinsa haqarsa bai cimma ruwa ba sai ya kamani yamin duka,wansa hakan bazai hana gobe da sassafe na tashi aikin gida ba koda wanne irin ciwo naji wannan ba ruwan mama fatsi bane,sau tari takanmin habaici da gugar zanar ita bata ga me nakeyi a gidan ba bata ga amfani na ba,ashe rashin tarbiyyar dan ladi ta kai ya gaya mata cewa har yau bai karbi haqqinsa a wajena ba,randa na gane hakan takaici kunya da baqinciki sun sakani kuka mai yawan gaske.
A haka naci gaba da zama cikin wannan uquba,ko qofar gida ban taba leqawa ba bare nayi tunanin zuwa gida,duk da suma gidan ba ruwansu da ni,ba wanda ya taba takowa inda nake idan ka debe yan qananun yaran gidan da basu san me ake ba,idan yawonsu ya debosu zasu shigo gidan,a nan zanta jin dadi in riqesu ina aiki muna hira ina tambayarsu mutanen gidan suna bani labarin abubuwan da suka faru da bana nan,koyaya dan uwa yake yana da dadi,hakan na yimin dadi kuma yana deban kewa.
Ranar data zamemin ranar yayewar wani bangare na hijabin rayuwata shine ranar da dan ladi ya yimin wani irin duka wanda da qyar na qwaci numfashina,naji ciwo matuqa na sha wahala,hakan ya sanya da asuba na gudu zuwa gudanmu karon farko,abinda ban taba yi ba,kusan da qyar na kai kaina gida ina nishi ina numfarfashi,sanda na shiga ana sallar asuba,dakina na shiga nada na lafe a can,har baccin wahala ya daukeni ba tare da na sani ba,salatin da naji a kaina shi ya farkar da ni na bude idanuna,mutanen gidanmu na gani a kaina inna yelwa na akan gaba,ita ta saka hannu ta finciko ni sai gani a filin tsakar gidan,idanuna basu sauka akan kowa ba sai kan dan ladi da mama fatsi,yana wani cika yana batsewa,ashe abinda ban sani ba shine zuwa sukai nemana,wai na yiwa dan ladi sata na gudu,ba wanda yayi duba da ciwukan jikina sanoda tsabar sonkai kowa ya hau tofin ala tsine
"Gata nan munafukar Allah,inda zaka san cewa babu gaskiya ba wanda yasan da shigowarta cikin gidan....kayi haquri don Allah don annabi dan ladi ka dauketa ku koma" inji inna yelwa kenan
"A'ah...ku riqe yarku,don ni banga abinda aurenta ya qarawa dana ba sai jaraba da masifa" cewar mama fatsi tana tafa hannu da yada baki gefe,nan suka hau roqonsu har suka amince zan koma,ni kuwa a sannan na tubure kan babu abinda zai sanyani komawa,abinda ban taba aikata makamancin irinsa ba tsahon zamana da su su duka
"Dauketa dan ladi koda tsiya,uwar me zaki tsinana mana,dauketa ku tafi" inna yelwa ta fada cikin nuna qyama tamkar ba jininta ba,haka dan ladi ya dinga figata cikin bainar jama'a har zuwa qofar gida,inda ya cilloni ya biyo bayana da niyyar sungumata mu tafi.
Bansan ya akai na fada jikinsa ba,bansan ya akai na rarumeshi ba da hancina dake digar jini saboda jana da dan ladi ya dinga yi yana wujijjigani,dattijo ne mai kimanin shekara hamsin da biyar,tsam ya tsaya yana duban dan ladi dake takowa inda muke cikin isa da qafafa tamkar shi ya haifeni,dakatar da shi daddy yayi da hanashi tabani yana son jin ba'asi,matata ce daya fada ya sanya daddy bashi ni,har ya juya zai tafi sai yaji zuciyarsa bata aminta ba,hakan ya sanya ya dawo ya nemi jin ba'asi,yanayin shigar da suka gani tattare da shi ya sanya jama'a yi masa bayani na gaskiya game da rayuwata....magana ta gaskiya....tsaiwar da daddy yayi yasa alqali ya tilastawa dan ladi ya sakeni kawai ko iya ita kadai daddy ya yimin bani da abin ce masa a rayuwa,karamcinsa mai tarin yawa ne,alkhairinsa har yau bai daina bibiyata ba,ya karbi takardata ya kuma zauna da yan uwan mahaifina yace zai tafi dani,da sunso su turje,amma da yabi kowanne da hasafi cewa sukayi sai mun dawo,inna yelwa ce kawai taso taqi,yaranta suka tanqwarata ta amince
Daddy shi ya tsayan tsayin daka daya fuskanci ina son karatu,ya hadani da malamin dakewa asma'u lesson nima yake min,na zana common entrance na samu shaidar kammala primary,naci gaba da lesson na zana placement sannan aka kaini makarantar da asma'u ke zuwa,ya hadamu aji daya na fara daga ss one,har na kammala na samu shaidar kammala secondry,takarduna sunyi kyau fiye da zaton daddy,direct na samu wucewa B.U.K wadda ban jima da kammalata ba.
Zuwa na gidan daddy na fuskanci tsangwama qarara da qyama daga wajen asma'u da mummy,saidai ita na mommy har yau bai bayyana ba,bana zarginsu bana kuma jin haushinsu...saboda a wajensu na samu rayuwa irin wadda dangina suka kasa bani....na samu 'yancin da a baya ban samu kwatankwacinsa ba,na hutu na gangar jiki koda ruhina bai samu wannan hutun da nake kwadayi ba...."idanunta suka cika fal da qwalla wadda bata iya adanata ba sai data gangaro
"Har kwanan gobe ina fatan na samu hutu na ruhi,ina son na samu salama a ruhina....amma ba zata taba samuwa ba har sai ranar dana samu soyayyar mahaifiya...har sai ranar dana san dadin dumin mahaifiya wanda tunda na tashi ban sanshi ba....tunda na tashi bansan dadin soyayyar uwa ba,saidai na hangota daga nesa,kona ganta daga wajen wasu uwayen zuwa yaransu" kanta ta kwantar saman teburin muryarta na rawa,hawayenta na qaruwa zuciyarta naci gaba da karyewa
"Wannan ita ce aisha....itace ainihin aysha,aishan da kakesom cusa taka rayuwar cikin tata qazantacciyar rayuwar,ka taba cin karo da mutum mai tarihin baqar rayuwa irin tawa?....ka taba ji?" Ta qarashe maganar tana sakin kuka mai cin rai,duk da yadda taso danne kukan.
A hankali tamkar mai sanda ya miqe daga kan kujerar kana ya zare jikinsa ya soma takawa a hankali yana barin lambun,taji a jikinta tafiya yake kuma bata da sha'awar daga kai ta kalleshi,me ya rage dama me yayi saura?,babu mutum mai hankali da zaiji gundarin rayuwarta yayi sha'awar zama da ita,shin idan an zauna da itan ma me za'a qaru da shi,me ta mallaka wanne abun sha'awa ne ko jan hankali cikin rayuwarta,har ta daina jin takunsa bata daga kai ta dubi gurbin da ya tashi ko yabi ya wuce ba.
Batasan yawan lokacin data dauka a wajen ba,har sai data ji sautin dariya bisa kanta
"Ya arce ne shima yaron ogan yaga bazai iya ba?" Ta tambaya cikin izgilanci,bata motsa ba bare ya nuna mata taji don ba itace a gabanta ba,har ta gama babatunta tayi gaba nan ta barta.
Bai nemi komai ba ha dinga takawa a hankali hannayensa zube cikin aljihunsa,duk taku daya yana tariyar labarin da ya gama saurara ne a yanzu,labarin da yake jinsa tamkar hikaya,haka ya dinga takawa har ya isa inda ya bar mutanensa,cikin hanzari suka nazir ya iso cikin girmamawa ya bude masa murfin motar ya shiga sannan ya rufe,PA dinsa nata masa magana ta window din motar bai amsa ba sai hannu da ya daga masa,hakan ya sanyashi komawa cikin daya daga cikin motocin yabi bayan sauran motocin.
"Gida zan koma" ya furta a hankali ganin sun nufi hanyar kamfani,wanda hakan ya tsara da farko,saidai baijin a yanzu zai iya,yana buqatar kebewa baya son hayaniya,hakanan drivern ya sauya akalar motar zuwa gida.
Ta qofar baya ya shiga gidan,don bai shirya haduwa da anni yanzu ba,ya tabbata da zarar ta ganshi zata karanci sauyin yanayi tattare da shi,yanzun itama zata shiga damuwa ta kuma nemi jin ba'asi,sam baisan da harshen da zai fahimtar da ita ba.
Kacibus sukayi da zeenart yaja baya da sauri suna duban juna,ita dressing din jikinsa take kallo cikin mamakin kayan jikinsa,yayin da shi kuma rashin jin dadin ganinya yayi,a irin wannan shigar idan yayi baiso kowa ya ganshi bare ya tambayeshi ba'asi,yanzun ma bai kaucewa tambayar zeenart din ba
"Bro....lafiyanka kuwa?" Dan hade rai yayi kadan ya qarawa fuskarsa kwarjini saboda baison tambayar tayi tsaho
"Me kika ga?"
"Ka duba kayan nan da kyau kuwa kafin ka saka?" Ta fada tana dudduba jikinsa da idanunta kamar mai neman wani abu,sake duban kanshi yayi kamar baisan kayan da ya saka din ba sai data fada
"Meye a ciki?.....ammm..idan kin shiga ciki karki cewa anni na dawo....zan shigo nan da anjima akwai abinda na dawo yi" ya qarashe fada yana gewayeta gami da wucewa yayin data bishi da kallo har ya bacewa ganinta bai waiwayo ba,tunda taga haka tasan yana nufin abinda ya fada din,hakan ya sanya tasa kai ta wuce itama inda ta nufa.
Kayan jikinsa ya fara cirewa sannan ya wuce direct zuwa toilet,yana tara ruwa yana dafe da bathtube din,labarinta yake jujjuyawa cikin kwanyarsa daya bayan daya,a haka ruwan ya cika ya shige ciki,kusan mintina talatin ya dauka kafin ya baro bayin ya dawo cikin dakinsa,shiryawa yayi cikin riga da trouser,hakanan yaji kasalar data sanyashi tilas ya koma saman gadon ya kwanta dai dai,tamkar yanzu take bashi labarin haka ya dinga ji yana dawo masa kansa
"Haka rayuwar take,kowa kansa ya sani,kowa son kai yayi masa yawa,wacce iriyar uwa ce wannan?,wacce iriyar uwa take da ita?,wanne laifi tayi mata mai girma data wofantar da rayuwar diyarta?,wanne irin dangi ne haka,me yasa ahali suka zama haka?,wanne irin dangi Allah ke jarabtar mu dasu a yanzu,wadanda basu san damuwar kowa ba sai tasu,mirginawa ya dinga yi daga wannan gefe na gadon zuwa wani gefen,cak ya miqe daga kwanciyar da yayi tamkar wanda aka tsikara,agogo ya duba,qarfe biyar da mintina ashirin da takwas na yammaci,dirowa yayi daga saman gadon ya zira takalmansa ya fito daga sashen nasa.
A hankali yake takawa har zuwa sashen anni,a parlour ya sameta zaune ita da zeenart,amsa sallamarsa anni tayi tana dubansa,tana son tambaya amma tasan babban dalili ne zai dawo dashi gida ba lokacin dawowarsa ba,rusunawa yayi ya gaidata sannan ya miqe kai tsaye ya wuce samanta ba tare daya zauna parlourn ba,hakan shi ya nuna mata yana son magana da ita mai muhimmanci,saidai bazai iya tada ita ba tunda ya sameta a zaune ita da zeenart
"kaiwa yayanku abinci sama"anni ta fada tana duban zeenart,tsam ta miqe ta shiga kitchen,tani ta yiwa umarnin ta hada komai,tana tsaye ta gama hadawar ta dauka tayi saman da su.
A miqe ta sameshi kan doguwar cusion dake falon yana latsa waya,a gabansa ta aje fulasan cikin kissa tace
"ya...ga abincinka na zuba maka?"
"Bana jin ci yanzu...barshi zuwa anjima" ya amsa mata ba tare daya dubeta ba,labarin aysha na yawo ya dawo masa kaf da tabon dake cikin tashi rayuwar tamkar yanzu komai ke gudana,wannan ya sanya ko kallon zeenart din baya son yi
"Ka daure yaya kaci"
"Later" ya sake fadi a taqaice,taga alamar 'yan miskilancin ne suka motsa,indai kuma yana cikin wannan mode din baya son dogon zance,hakan ya sanyata ta miqe ta fice daga falon.
Tana qoqarin sauka anni na hawa,ta wuce ita kuma ta shige ciki,yunqurin tashi yayi ya zauna sanda yaji sallamarta,idanunta a kansa saita kadar ta kalli kayan abincin da bai taba ba,bata ce masa komai ba ta isa gaban abincin da kanta ta soma kiciniyar zuba masa,da hanzarinsa ya taso ya karbeta yana murmushi,itama murmushin tayi sannan ta sakar masa yaci gaba da zubawa,ta koma da baya ta samu waje ta zauna tana cewa
"Ah to...naga alamun 'yan sarautar ne yau a kusa" murmushi kawai yayi bayan ya gama zuba dai dai yadda zai iya ci ya rufe komai ya koma gabanta ya zauna ya soma ci
"Uhmmm....ina jinka ya akayi?" Ta tambayeshi kai tsaye kaman daman ya gaya mata zasuyi wata magana ne,murmushi ya saki yana jin dadi har cikin ransa,mahaifiyarsa ta karanceshi fiye da kowa a duniya,aysha ce ta fado masa a hankali fara'ar fuskarsa ta dan ragu,ya motsa bakinsa yana duban annin yace.
*DB*
18
"Bansan ta ina zan fara ba anni...matar aure aka bani,bansan me zance ba" abinda ya iya fara fada mata kenan saboda shi kansa baisan ta ina zai fara ba,idanunta ta saka tana kallonshi saboda yadda taji maganar tashi banbarakwaii,tana tunanin tayaya haka ta faru,saidai koma meye ta sani cewa zaiyi mata bayani,hakanan bazai taba yin wani abu daba dai dai ba kozai haifar da dana sani,zamanta ta gyara tana qoqarin fahimtar dan nata kamar yadda al'adarta take,bata yankewa koma waye hukunci kai tsaye,murmushi ne bisa fuskarta
"Matar aure a ina?,kaji gorin haidar kenan?" Murmushi shima ya danyi yana ture kwanon abincin gefe duk da ba wani mai yawa yaci ba
"Zaki iya tuna alhajin nan da na taba tsintar wallet dinsa,wanda ya taba biya miki kudin aikin da aka yi miki shekara goma da suka wuce?" Kai take kadawa
"Qwarai kuwa....ya za'ayi na manta muhammadu?irin wadan nan mutanen dan halak bai manta halaccinsu a gareshi"
"A gidanshi take...shine mariqinta"
"Ikon Allah" ta ambata cikin mamaki,a hankali ya zauna ya warware mata komai,babu abinda ya boye mata,tun daga yadda ya dinga neman aure ta sigar DAURIN BOYE,har zuwa neman asma'u yadda mu'amalarsu ta kasance sa kuma yadda ta qulla lamarin shi da aysha,sannan yazo ya bata labarin rayuwar ayshan kamar yadda itama ta bashi.
Ta jima anni tana jinjina kai,falon ya jima shuru shi da ita babu wanda yace wani abu,labarin ratsata yake tun daga kanta zuwa tafin qafarta,lallai duniya,inda ranka kasha kallo,idan kana da rai babu abinda ba zaka gani ba,tsahon wasu mintuna ta dauka kafin ta dubeshi
"Koda baka karbi aurenta ba,ko babu niyyar haka a zuciyarka khalipha ina mai baka umarnin ka aureta khalipha....,Allah ne kadai yasan manufarsa daya kawo silar haduwarmu da ita ta wannan sigar,me yiwuwa Allah ya turomu ne muma cikin rayuwarta,aurenta shine hanaya daya tak da zata zama bamu damar sauya mata rayuwa" Ta fada tana jin lafuzan nata har cikin zuciyarta,wani irin tausayi da qauna ta ayshan na na ratsata duk da bata ganta ba,duk mutumin daya fuskanci rayuwa irin wannan abun a tausaya masa ne,a dubeshi a kuma juyawa a dubeshi,sun taba dandanawa da kalar tasu daban,ba zasu taba mantawa ba.
Kanshi yake jinjinawa,shi kansa yana jin cikin zuciyarsa tamkar haduwarsu daga Allah ce,tamkar Allah ya tsara komai ne don ya sama ma rayuwarta farincikin da bata taba dandanarsa ba tun tasowarta
"Allah ya bani ikon sauke dukkan haqqin mai haqqi dake kaina...." Ya ambata,saidai wani bari na zuciyarsa yana fasalta yadda aure zaiyuwu babu soyayya,bayaso ta amincewa zama da shi saboda ta samu matserar rayuwarta bawai don ta nutsu da hakan har zuciyarta ba.
Kafin kowa yace wani abu a cikinsu zeenart ta shigo falon fuskarta qunshe da fara'a
"Anni...alhaji yazo" tana nufin mahaifinta kenan
"Toooh....maraba" ta ambata tana miqewa daga zaman da take,shima khaliphan miqewa yayi ya sakata a gaba zeenart na bayanshi suka sauko zuwa qasan.
"Ku haka kuke qulewa kubar gida ba kowa.....ba don zeenatun na kusa ba kenan saidai ka gaji ka koma....yo ai wannan gwara da take zaune a gidan ma" ya fada yana saba babbar rigarsa,idonsa na kan khaliph wanda fuskarsa take ba yabo ba fallasa,idanunshi na kam anni bai dauke ba sai da yaga ta zauna sannan ya dauke nashi idanun ya samu hannun kujerar da take kai ya zauna yana sauraren gaisawarsa da anni
"Barka da yamma" khalipha ya fada,waiwayowa alhajin yayi yana dubansa
"Kai wato ba'a isa a ganka gidan kowa ba saidai a naku gidan ko?" Murmushi ne ya subuce masa,sai ya kada kansa kawai yana duban alhajin,idan maye yaci ya manta uwar da ai ba zata manta ba,shi alhajin ya manta furucinsa na qarshe a garesu kenan
"To ni gani nazo da kaina da nacewa zeenatu tace ina nemanka kayi funfurus kaqi zuwa" alhajin ya sake fada yana tsatstsareshi da ido
"Yanayin aiki ne,ba kowanne waje yake barina naje ba....gani...Allah yasa ba laifi nayi ba" ya qarashe maganar ta sigar gatse,gyara zamanshi yayi bayan ya gyara zaman babbar rigarsa
"Wato muhammadu so kake kafi qarfinmu ko?,ka tasamma qin aure qiri qiri kasa qafa kayi fatali da sunnar ma'aiki,kana girma shekarunka na ja qannanka na tasowa,ga 'yar uwarka nan jiddin tana gidan nan tana qaunarka amma ko wannan baisa ka duba ba?....yanzu haka ka zaba kenan?" Murmushi ya sake yi,abubuwa masu yawa na dawo masa cikin kwanyar kansa,yana sake godiya ga Allah kan komai da yayi masa a rayuwa,baiwa masu tarin yawa da shi kansa baisan adadinsu ba,miqewa yayi tsaye hannayensa zube cikin aljihunsa,idonsa ya sauka kan zeenart da kanta ke sunkuye tana wasa da yatsunta ita ala dole kunya sai faman zuba murmushi take
"Kayi haquri alhaji ba haka na zaba ba.....idan Allah ya kaimu ranar asabar kwana biyu masu zuwa za'a kaimin kudin aure harma da sadaki....shikenan?" Baki ya soma budewa,yana jin zallar farinciki,ga tunaninsa komai ya fada ne tsakaninsa da zeenatun,amma maganar da khaliphan ya dora da ita a sanda yake yunqurin barin falon ita ta kadar da duk nutsuwarsa ta kuma sanya gumi ya soma karyo masa
"Duk da ban sanar da mahaifin yarinyar ba,amma zanyi qoqarin shaida masa yau zuwa gobe in sha Allahu" daga haka ya fice ya bar alhajin cikin rudani
[1/6, 11:50 AM] Om Muhammadiyya: Shiru ne ya ratsa falon kafin daga bisani kukan zeenart ya karade falon,kuka take sosai mai sauti tana raba ido tsakanin mahaifinta da anni,hakan ya sake tunzura alhajin wanda yaketa qoqarin share gumin goshinsa,miqewa tsaye yayi cikin banbami yake cewa zeenart
"Ke,tashi mu tafi....tashi nace maza....mu za'a yiwa wulqanci aci mana mutunci?,mu za'a nunawa qaryar arziqi,dadin abin ai tun kafin ayi daran akai kwandi" a tausashe anni ke dubansa
"Haba bashir....abun baikai haka ba don Allah...ka zauna"
"In zauna inyi me hajiya A'i?....me zan zauna inji?,ina cewa a gabanki ya fadi komai baki dakatar da shi ba...ina tsammatarma hadin baki ne kukayi saboda kada a auri yaranmu...to babu komai....shi yasa zumunci ya shiga halin ni 'yasu,dole zumunci ya lalace,tashi ki wuce mu tafi" kada kai anni take can qasan zuciyarta mamaki na kaikawo na maganganun da alhajin keyi,duk da haka ta danne
"Kayi haquri dai duk da haka,ka barmin zeenatun"
"Mai zata zauna tayi muku...ai magana ta riga ta qare"ba yadda annin bata yi ba amma ya qeqashe qasa yaqi,tana zaune tana kallonsu ya tasata ta hada kayanta suka zo suka fice,ajiyar zuciya kawai ta saki,me hali baya fasa halinsa,lallai khalipha shi yasa meya gani...shi yasan wanne tunani yayi daya sanyashi qin duk wata yarinya dake cikin ahalin nasu.
Khalipha ne ya sake dawowa falon,harararshi annin tayi sai ya saki murmushi yana takowa inda annin ke zaune,duk sanda yaga ta harareshin yasan ya aikata mata laifi kenan
"Kaji dadi.....ka hadani da dan uwan mahaifinka" gabanta ya qaraso dariya tana kubce masa,kan gwiwoyinsa ya durqusa ya kama hannayenta
"Ki cire dukkan wata damuwa anni dangane da mutanen nan,kin dade da sanin cewa babu wani abu da zakiyi ki fita a wajensu,Allah shine shaidarki,mutane masu adalci suma sun shaida hakan....banda ke anni da wata ce ko kallo basu isheta ba bare su jibanceta ko su jibanci nata yaran,anni.....bazan iya auren kowacce yarinya data fito daga zuri'armu ba ko daga sama ta sauko kuwa....kiyi haquri karki tambayeni dalili saboda suk duniya kinfi kowa sanin dalilin....ki manta da su da lamuransu....kici gaba da duk abinda kikega zaki iya kuma shine dai dai hat a gaban mahaliccinmu" shiru tayi tana tunani,ba shakka duk maganar khaliphan haka take tana bisa hanya,ita kanta tafi kowa sanin wuyar data sha da shi kafin yaci gaba da mu'amala da dangin nashi,amma a yanzun saika rantse babu komai tsakaninsu basu taba aikata musu komai ba,don indai anni ta bada umarnin yayi abu zai cikashi duk wuyarshi
"Yanzu ina kayan abincin da za'a kaima baffan ka"
"Wannan maganar an gamata....haidar kawai nake jira yazo ya kai" ya qarasa fadi yana duban idanunta
"Yanzu jibin za'a je gidansu yarinyar?"
"Eh anni...in sha Allah...inason mutanen nan ne su qyaleni suda yaransu...koda kika ga zeenat ta tafi ina mai tabbatar miki zata dawo...ko bata dawo ba wata na nan zuwa"kai take kadawa sannan ta bude baki
"shikenan,Allah ya sanya alkhairi yasa a yi a sa'a ya kade dukkan fitina.....saika gayawa dukan wanda ya dace kada wani yaji daga baya yayi qorafin bai sani ba"
"Ko sunzo ma mota daya zan bada,sauran suje a motar haya.....har yau bani da komai sai rufin asirin Allah da shi zanci gaba da neman aurenta idan har zata iya zama da ni a haka" dariya ya bawa anni...khaliphan ya fita daban da matasan zamani...matasan dake neman kayan aro da zasu sanya ariqa musu kallon masu arziqi su yaudaro yarinya su aureta,yau shi gashi da dukkan wani abu da ake da buqata amma boyesu yake yana maida kansa ruwa da zubin maqasqanciyar rayuwa,bai bar falon ba saida haidar din yazo ya miqa masa saqonnin duk wadanda za'a kaiwa abincin sannan ya fice zuwa gidan babban wan mahaifinsa suyi maganar zuwa gidansu ayshatun.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
A daren washegari daddy ya kira mummy sa'adah ya sanar mata zuwan masu neman auren ayshan,a zahiri ta nuna zumudi da farinciki,amma a badini baki kawai ta tabe,madadin ta gaya mata tayi musu tanadin abin tabawa kamar yadda aka yiwa maneman auren asma'u sai taja bakinta ta tsuke,taqi ma shaida mata bare tayi qoqarin yin wani abu,sai asma'u data gayawa,dariya asma'un ta dinga yi tana cewa
"To dama mommy me za'a bawa wadan nan?,...nasan yadda dansu yake suma haka suke..qilan ma gwara shi sau dubu a kansu....,mummy ki shirya kina da gagarumin biki....don wallahi tun yanzu ma kisan ya zakiyi da daddy Allah karma ya wani ce zai hada mana biki,don bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane ehe" fuskarta qunshe da murmushi saidai tana harararta,don itama harga Allah tafiso a barta a bikin auta su raqashe,ba zata yarda ya hade musu biki da ayshan ba ya jawo musu zubewar mutunci
"Saiki gayawa daddyn naku ai" buga qafa tayi tana duban mummyn
"Allah mummy yace zai hada mana biki fasa auren zanyi,sawa sweet hamid zanyi yacewa daddyn ya qara wata daya ko biyu ai dole ya haqura"
"Kwantar da hankalinki,babu mai hada mana biki ma" tsalle tayi ta ruqunqume mummyn
"Sai mummy na...." Dariya suka sanya baki dayansu.
***** ***** ***** **** **
Sha daya na safe tana kitchen tana hada breakfast din asma'u wadda takeson fita da safen,sam bata masan da cewar yau za'a zo wani neman aurenta ba,ta riga ta bayar da cewa khaliphan yayi tafiyarsa ne abinsa,saboda tayi imanin babu yadda za'ayi mutum yaga mace kamar asma'u,wayayya mai kyau nasaba da dukiya sannan ya zabeta,ita hakanma yafi mata,zuciyarta tafi nutsuwa sosai,don batasan ya lamarin zai kasance ba idan har ya karbi auren nata ba,ta yaya zasu zauna bayan babu wata kalma data jibanci soyayya wadda ta taba shiga tsakaninsu,basu taba za su yi magana mai taken ta fahimtar juna ce a tsakaninsu ba,basu suka zabi juna ba,ba wanda yasan kowa sani tun daga na halayyar zuwa na ra'ayi,wannan gambizar dame tayi kama?,tafiyarsa tana jin maslaha ce kawai a rayuwarsu su duka,gabaki daya a duniyarta a yanzu ta zurfafa karatunta shine kawai burinta,ko sau daya bata taba darsawa kanta tunanin yin aure,wannan ta baiwa kanta cewa sai cikakkun mata masu abinda zasuyu tutiya da shi,itakam me take da shi?,me ta mallaka,taji ma da tarin tulin matsalolin dake neman shaqe rayuwarta su kaita kushewarta wanda har yau bata samu magani ba.
Motsin data ji shi ya sanyata juyowa,mummy ce ta shigo,ta rusuna cikin girmamawa ta gaidata,ta amsa kana ta juya ta fice ba tare data dauki komai ba,daddy ke maganar baqi sun iso a kawo musu abin tabawa,ta shigo ta kuna rasa me zatayi,ayshan zata roqa ta rufa mata asiri ko ko yaya?,itakam bata san ma me ake ba,daga bisani dai taga daya daga cikin masu aikin gidan ta shigo ta shirya lemuka da ruwa kan faranti ta fita da su,itama tana gama hada break din ta diba zuwa dining ta soma shiryawa a can.
Tana tsaka da gyara wajen taji muryar daddy yana shigowa falon,da alama waya yake,takun takalman asma'u suka karade falon,kai tsaye ta nufi dining din ta ja kujera ta zauna tana duban ayshan fuskarta qunshe da fara'ar da batasan ya meye ba,kallo daya ayshan ta yiwa fuskarta ta dauke kai,hakanan taji fara'ar bata gamsheta ba
"Me kika dafa?" Ta fada tana latsa wayarta,bata ce komao ba ta bubbude kwanukan,sai data daga kai ta dubesu sannan tace
"Zuba maza da sauri fita zanyi" faranti ta jawo ta soma zuba mata dai dai sanda daddy ya gama wayar suka soma magana da mummy
"Mun gama sun tafi"
"Nawa suka kawo?"
"Dubu talatin ne" daddy ya fada yana ciro kudin da suka kawo din daga aljihunsa,wani sanyi ya ratsa mummy a badini tana jin cewa lallai Allah ya yiwa diyarta gyadar dogo,yayin da a zahiri kuwa ta cunkushe fuska tana cewa
"Haba daddy...yanzu kai ya za'ayi ka bada auren yarinya akan dubu talatin kaman wata atamfa....haba sai kasa a zagemu ace muna sane"
"Babu komai sa'adatu...albarka auren ake nema ba tarin dukiya ko qyale qyale ba,yaron kuma yana da dukkan nagartar da za'a iya bashi auren kowacce diya wannan kawai ya isa"
"Amma aysha indo a dubu talatin daddy" saida mummy tayi furucin qarshe sannan ta ankara,mummunar faduwar gabanta tazo dai da sanda asma'u ta bushe da dariya har tana neman qwarewa da farfesun da take diba da cokali tana sha
"Wai.....dubu talatin....kudin takalmi na" asma'un ta fada tana dariya qasa qasa don kada daddyn ya jiyota,sosai jikin aysha ke rawa da jin abinda bata tsammata ba haka nan bata shirya masa ba,aure?...aure a irin wannan lokacin?.....wanne irin mutum ne shi da ya amince zai aureta a haka?.
Abincin da bata gama zubawa ba kenan ta saki sarving spoon din ta wuce dakinta.
Kuka ta zauna sosai tayi a bakin gado,tsoro da firgici yana kamata,tunanin makomarta take,ya kuma rayuwarta zata sake juya mata,auren da babu soyayya a karo na biyu,auren da babu sanayya sabo ko fahimtar juna,ya sunan zamansu?,ya zata kasance shine kawai abinda ta dinga juyawa cikin ranta,wayarta ta jawo,a yau tana jin buqatar abokin shawara fiye da kullum,yau tana fatan idan ta kira aliya ta sameta a waya,ba kamar ragowar kwanakin ba da bata samunta,saidai yau dinma data kira haka aka sake gaya mata layin a kashe yake,jikinta a sanyaye ta aje wayar ta qura mata ido,bakinta cike fal da addu'ar neman yayewar qunci da haskawar lamuranta baki daya.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Tun safiyar ranar bata sake takowa falo ba bare ta leqo wajen gidan,tana nade kan gado,sallah kawai ke sauko da ita data gama zata koma ta sake kwanciya.
Qarar bude qofar dakinta ya sanya ta daga kanta tana duban bakin qofar,inna laraba ce,da sauri ta miqe ta zauna saman gadon fuskarta qunshe da murmushi tare da nuna zumudi take saukowa daga kan gadon
"Inna....yaushe kika dawo?"
"Ban wuce minti talatin ba cikin gidan nan...komawa kuma zan sakeyi ma" ta fada tana murmushi,tunda babbar 'yar mummy cuta aka kai inna laraba take can gidan,ba qaramin kewarta aysha keyi ba,don kusan da ita kadai take zama ta taba hira cikin gidan,saboda yadda inna ke janta a jiki tare da nuna mata qauna,haka nan jininsu ya hadu sosai da innar,gaisheta ta fara yi innar ta amsa tana cewa
"Baqo gareki fa 'yata....inajin surukin namu ne yazo....yau bakina har kunne nazo na tadda abun alkhairi...ubangiji yasa abokin arziqin ki ne"kanta a sunkuye jikinta a matuqar sanyaye ta amsa
" ki maza ki fita...idan ban koma ba kafin ki gama ma gaisa sosai"
"Toh inna" kawai ta fada innar ta fice ta barta tsaye gaban kayan sawarta tana neman hijabi,bawai don bata ga hijabin bane,hakanan jikinta yayi wata iriyar mutuwar ga fargabar data cika mata zuciya.
Har zata fice a falon sai ta koma kitchen ta qofar baya,ta hado masa lemo da ruwa ta dora cup ta wuce da shi.
Daga nesa ta hangoshi,ya baiwa qofar shigowa baya,qafarsa daya na saman kujera daya tana qasa,bata iya hango abinda yake amma dan duqe yake gwaiwar hannunsa kan gwiwar qafarshi,takowa take idanunta a kanshi,gabanta na faduwa duk sanda nisan dake tsakaninsu ya ragu
"Assalamu alaikum" tayi sallama tana tsaye daga bayanshi kanta na kallon qasa,a nutse ya sauke qafafunshi sannan ya waiwayo inda take tsaye,dubanta yayi sau daya sannan ya amsa sallamar yana nemawa kanshi wajen zama,bata motsa ba har sai data tabbatar ya zauna sannan ta dora farantin,tq bude robobin duka ta zuba masa ruwa da lemon sannan taja kujerarta can baya ta zauna
"Ina yini" ta furta a hankali cikin sanyayyar muryarta da sai ka zaci da gayya take yinta,idanunsa ya dauke daga kan kofunan ya maidasu saman fuskarta da take kallon qasan wajen ya amsa mata da lafiya lau,daga haka shuru ne ya biyo baya,ya zuba mata idanunsa yana karantarta,yayin da tausayinta ya dinga ratsa zuciyarshi,sai ya dinga kwatanta ace qaramar qanwarsa ce haka a gabansa ta fuskanci rayuwar data bashi labari koma take kan fuskanta,hajar ya tuna,harbkwanan gobe bai mantawa da ita,bai manta yadda ta tafi ta barsu,tabon yana nan a zukatansu bai goge ba.
Duk da bata kalleshi ba hakanan take jin idanunsa a kanta,tunda take bata taba ganin namijin da yake mata kwarjini irinsa ba.
Batasan yaushe ya taso ba,sai tsintsarsa tayi zaune saman teburin,hannayensa sarqafe da juna,tazarar dake tsakaninsu bata da yawa,hakan ya sanya zuciyarta soma bugawa da sauri da sauri,don kaf rayuwarta ba zata iya tuna sanda ta zauna haka da namiji tsakaninta da shi da qaramar tazara ba.
Kamar ya karanci zuciyarta ya dan sake ja baya tare da bada wata tazarar a tsakaninsu
"Bansan da sunan da zan dinga kiranki da shi ba....saboda sunan mama na kenan" ya fada cikin nutsuwa,shuru ne ya biyo baya kamar yana jiran yaji abinda zata ce,hakanan itama bata ce komai ba saboda bata da abinda zata ce din...tsahon sakanni sannan ya dora
"Sai kikaji an kawo kudi ba tare dana sanar miki ko na nemi jin ra'ayinki ba" ya sake furtawa still idanunshi a kanta,yanzun ma shuru yaga tayi ba tare da tace komai ba bayaga motsa jikinta kadan da tayi gami da cewa
"Uhmmm"
"Duk da banji ta bakinki ba amma bata baci ba...idan ba zaki iya aurar mutum irina ba kina iya fada saboda 'yancinki ne....kin ganni talaka ne ni bani da komai sai rufin asirin Allah,bamai kudi bane ni haka nan ni ba wani bane.....naga ba irinmu asma'u keso ba ban sani ba kema ko ra'ayinku daya"
"Asma'u kace....kana magana ne kan yara masu gata...masu nasaba.....masu kudi....masu kyau...."
"Da ace kema duka kina da wadan nan zabinki zaizo dai dai da nata kenan?" Ya tari numfashinta ba tare daya bari ta gama fadin maganarta ba,kai ta kada
"Rufin asiri da mutunci shine biyan buqatata,da ace ina da 'yancin zabar kalar mijin da nakeso to miji na gari zan roqa....." Har cikin tsakiyar zuciyarsa kalaman ta suka sauka,sai yaji maganganunta sun burgeshi qwarai,yanayin yadda kalamanta ke a tsare kadai ya bayyana masa tsantsar nutsuwar da Allah ya mallaka mata,sai yaji yana son hirar tasu ta dore saboda haka yace
"Bayan kin samu miji na garin alal misali,taya zaki zauna da shi koda baku taba soyayya ba?" Shuru tayi tana juya tambayar tasa,itakam gaba daya soyayya ba matsalarta bace,abinda kawai ta sani shine mutunta juna,tausayi da jin qai,qauna ta haqiqa su take buqata,inama zata samu hakan?,take qiyastawa a ranta
"Soyayya Allah ne yake jefata cikin zukatan bayinsa,duk da ban dan danata ba amma nasan da haka,tunda na samu soyayyar inna laraba da Aliya ba tare da sun zamo jinina ba....amma mutunci da karamci sanin qima suna daga cikin jigon dake riqe zaman tare" baisan sanda murmushi ya subuce masa ba,ta iya magana ta hikima taqaitacciya kuna dunqulalliyar dake isar da saqo a dan qaramin lokaci
"Humaira.....zan kiraki da shi idan babu damuwa.....daga sanda aka daura mana aure sunanmu miji da mata a idon duniya....."katseshi tayi
"Ina mamakin ta yadda zaka iya aure na wai....." Girgiza kai take duk da ba dubansa take ba
"Kada ka yaudareni kada ka yaudari kanka.....ba aurena zaka iya ba...." Qaramin murmushi ya sake
"Ni dake gaba daya lamarinmu na hannun ubangiji,bamusan yadda zaiyi ba....ban taba kawoki cikin qaddarata ba kamar yadda kema nasan hakan ne.....bazan boye miki ba,hajiyata ita ta yimin izini neman aurenki,wanda na tabbata ta hangi abinda mu kanmu babu lallai mu hangeshi" shuru tayi tana jinjina qarfin hali da jarumta irin na mahaifiyar tasa,ita a karan kanta hankalinta da shekarunta da iya abinda take gani tasan uwa na nufin wani abu mai girma a rayuwar dukkan wani abu mai rai,duk da cewa ita din batasan dadin hakan ba amma tasan ita din ba qaramin abu bace....
"Zaki iya rayuwa da talaka?"ya sake fada yana katse mata tunaninta
"Ni din wace?"
"Hajiya ce mana" ya fada yana murmushi,itama batasan sanda siririn murmushi ya qwace kan fuskarta ba,abinda ta jima rabonta da shi,sai kuma ta maida fuskarta ta gintse,miqewa yayi tsaye yana zuba hannayensa cikin aljihunsa sannan ya sake cewa
"Daddy ya saka rana gashi ni kuma ban shirya ba,infact ma ban soma shiri ba,kinsan abun talaka,lefe ma kawai aiki ne a wajenmu....ga wajen zama....toh..Allah muna gareka" ya fada yana dan daga kanshi sama,murmshi ta saki,ita din daba kowan kowa ba,ita din da aka cusa masa,ita ayshan daba wani gata ba,ita dinma tana ga Allahn,bata ga abinda zai damu kanshi ba akai wai wani lefe da wajen zama,tana daga kai suka hada ido da shi,ya jima yana dubanta ya kuma.karanceta tsaf ba tare data sani ba,sai ya dauke idanun nasa yana jin tausayinta,har ya danyi gaba sai ya dawo ya dauki lemon,irin lemonsa ne da yake yawan sha
"Bari naji zan iya shan kalar wannan,kinsan abinka da baka saba ba" ya fada yana kurbar lemon,bai aje ba sai daya shanye sannan ya aje cup din
"Zan wuce gida.....amma ba lallai ki sake gani na nan kusa....saboda muna tare da oga koda yaushe....kinsan qarqashin wani nake" yayi shuru yana jira ko zata ce wani abun a wannan gabar,saidai babu abinda tace illa
"Karka takura kanka....."
"Ki gaida mutanen gidan"ya fada yana takawa zai bar wajen
"Ka gaida hajiya" ta furta ba tare data shirya ba,sai data fada din sai kuma tayi shuru tana raba ido kanta a qasa,tana jin kamar tayi azarbabi,gabanta na faduwa sanda taji tsaiwarsa,zuciyarta na kwabarta na ta cika azarbabi da yawa
"Zataji na gode" ya fada har cikin zuciyarsa yaji dadin kulawar data nuna.
_ina godiya a gareku,kuci gaba da yimin uzuri kan yanayin gajeran typing don Allah,na gode_
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
*KO KUMA*
07067124863
*DB*
19
Cikin sati hudu mummy ta soma shirye shiryen bikin 'yarta don bana ce shirin bikinsu ba,ta bangaren aysha sam babu abinda ya dameta,kallon komai ma take a matsayin almara,har sannan gani take koda yaushe ma muhammad kamar yadda tafi kiransa,duk da cewa cikin ranta ne bata taba kiransa a sarari ba zai janye shima,bata taba duba da wai cewa baida komai ba,ko bai taba bata wani abu ba,hatta da katin waya bai taba tura mata ba ko na naira biyar,hakanan duk sanda zaizo kayan gwanjo yake sakawa a wanke a goge a kawo masa ya saka,ko ya sayi shadda ready made mai sauqin kudi,wataran yasa a taho masa da babur ya amsa daga can qasan layinsu ya qaraso da shi,wataran kuma ya sauka daga bayan layin ya tako da qafafunshi ya qaraso,vivo qarama itace wayarshi,kama daga hula da takalmi dukka kudinsu bai taka kara ya karya ba,ko sau daya hakan bai taba damunta ba ko a fuska,bata ma daga kai ta kalla bare har ta tantance,wataran yakan jima yana satar kallon fuskarta ko zai fuskanci wani sauyi tattare da ita,saidai sam ko alama bai taba ganin wani abu ba daya danganci hakan.
Daddy da kanshi ya zauna da mummy,tayi masa lissafin duk abinda ake buqata na asma'u,daya tashi gaba daya ya hada ya bata dana aysha dai dai dana asma'un,abun ya qona ranta sosai,wannan karon tamkar zatayi magana,da qyar ta samu ta danne ta karbi komai daga hannunshi ba qorafi ko nuna ba'ayi dai dai ba.
A sannan asma'un na zaune cikin kitchen tana charting,aysha na tsaye bakin gas tana soya mata wainar fulawa,idan ta cire saita saka mata a plate ta miqa mata
"Mummy..kin fito?" Asma'u ta fada tana cire earpiece din dake kunnenta,wanda ba komai take ji ba sai waqe waqen 'yan kudu
"Na fito" ta amsa mata tana jingina da jikin qofar kitchen din
"Ya kukayi mummy...Allah yasa duk komai yadda na tsara hakan ya bada" ta sake fada tana sauke qafafunta qasa wanda daa suke nade a saman kujerar plastic din da take kai
"Eh haka ya baku" idanu ta zaro tana duban momyn
"Momy?....ya bamu ni da wa?"
"Dawa kikasan yana bakun?"
"Haba momy haba,why...why?...komai sai an hadani da wani,wannan abun fa gaskiya ni ya isheni mommy...kenan har dubai din tare zamu wani kwashi jiki muje?,salona rainani,wannan idan akaji labari ai ajina ya gama zubewa,ince mun tafi tare dawa dina?....wallahi mommy ban yarda ba,tsakani da Allah fa ni ba'a yiwa rayuwata adalci" ta fada cikin fushi tana cika kamar zata fashe,aysha na jinsu,tana kuma sane da cewar da ita ake,saidai ko daya ita ba wannan ne ma a gabanta ba,result dinsu data samu labarin ya fito takeso taje ta duba taga me ta samu
"Ke aysha....zamuje dubai siyayyar kayan aurenku....inaga don ayi serving kudin jirgi dana hotel da kuma abinci da zamu dinga ci kiyi zamanki kawai ki bada list na abinda kike so" mummyn ta fada bayan tana sane da daddyn ya bada kudin duk wani abu da zasu buqata,sai a sannan ta waiwayo ta dubesu
"Ba komai mummy....duk abinda kika siyo yayi" dan jim sukayi baki dayansu,don basu tsammaci sam zata ce hakan ba,duk da sunsan halinta indai aysha ce ba abinda yake damunta,duk yadda aka kai ga cusguna mata tana iya shanyewa saman fuskarta,koda bai mata dadi ba cikin zuciya,wani lokaci sukanyi mamakin hakan,su dauka ko zuciya ce bata da ita ko kuma mene
"Au haushi kika ji?" Inji mummyn ta fada tana son tabbatar da ainihin yanayin aysha,da sauri ta waiwayo fuskarta qunshe da murmushi
"Haba mummy....nima fa tamkar asma'u ce a wajenki,na daukeki kamar mahaifiya ce ke a waje na,ta yaya kuwa uwa zata cutar da diyarta,kawai gani nayi ko banje ba indai ke ko anty asma'u kunje duka daya ne kamar ina wajen ne,sannan gidan ma bai dace mu barshi babu kowa a ciki ba" baki asma'u ta tabe tana jin haushi,yadda duk takai ga son cusguna mata taga bacin ranta hakan yaci tura,bata bari wani abu ya qona mata rai komai girmansa,koda ya qona matan zata iya cewa basu taba gani su a nasu idanun ba
"Shikenan....hakan yayi" cewar mummyn ta juya ta fice,sai asma'un ta miqe tabi bayanta,bata bar wajen ba bata kuma je ko ina ba,ci gaba tayi da soya mata wainar tana ajewa cikin warmer cikin hanzari saboda makaranta da takeson ta shiga.
A bakin matattakala asma'u ta cimma mummy
"Mummy....kawai ni inaga ba sai an wani auno mata kaya daga wani waje ba.....kiyi waya kawai zoo road inda anty halima ta siyawa 'yar aikinta kayan gado lokacin aurenta,ai suma sun iya su kawo kawai set biyu a zaba,bata kudine kawai da asarar kudi a siya mata kaya masu tsada,tunda ko da can ba saninsu tayi ba bare tasan darajarsu,sannan shi kansa mijin ma bashi da qarfin da zaiyi ginin da zai dauki kayan,kinga anyi asara kenan" ta fada tana duban mummyn
"Haka nake tunani nima....kuma akwai siyayyar da nakeso nayi nima,kudina bazai kai ba,to cikin kudin nata nakeso na cika" murmushi asma'u ta saki
"Yauwa mummy yaushe zamu tafi....inason na yiwa hamid magana zan karbi wasu kudade a hannunsa"tunani tayi kadan sannan tace
"inaga nan da next week ko upper week"
"Allah ya kaimu....bari naje nayi wanka zan shiga school naga result dina"
"Ya kamata....don babanku ya qagu ya gani shima dazu muke maganar" ta fada tana haurawa sama,asma'un kuma ta juya ta nufi dakinta.
Tsaf ta shirya cikin shigar hijabi abinta,tayi kyau sosai cikin hijabin,dama ita tunda can yana mata kyau kai baka ce hijabi bane a jikinta,ta iya ado da shi sosai,a falo suka hadu da asma'un itama ta gama shiryawa,tare suka fito saidai ita parking space ta nufa ta dauki motarta,motar da har yau ta aysha ke rufe cikin tampol bata taba zuwa kusa da ita ba bare ta hau,da daddy yayi magana sai mummy tace ayshan ce tace a aje mata ita ba yanzu zata hau ba,hannunta bai gama fadawa ba,da kansa daddyn ya kirata yace lallai lallai taje ta koya motar a cikin satin,yasa mummyn ta kira wanda ke koya musu mota a gabansa aka yi masa magana,saidai har yau babu shi babu dalilinsa sai tashin zancen,ba kuma kowa ya hanashi zuwa ba sai asma'u,itama hakan yafi mata kwanciyar hankali,don ko sau daya bata taba sha'awar tuqa mota ko mallakar mota ta kanta ba,bata taba wannan burin ba,don ko yaushe tana daukar kanta nan kusa kusa,bata taba barin kanta tayi wani dogon buri ko dogon mafarki ba.
Tana bakin titi a tsaye asma'un tazo ta wuceta motar na tashin kida,duk da taga ayshan tun daga nesa amma bata nuna hakan ba,hasalima baqin gilashin motar ta zuge sama abinta ta wuce,itama ayshan dauke kanta tayi,bata jima ba ta samu napep ta hau.
Kyan da result dinta yayi ya sanyata kuka sosai harda hawaye,tasan cewa tayi karatu tuquru ta kuma yi addu'a,amma bata taba zaton zata samu wannan result din ba,farincikin da take ciki ya shafe komai dake ranta,saidai bata da wanda zasu raba wannan farincikin tare,gefe taja ta dinga trying lambar Aliya amma amsar kamar koda yaushe ne a kashe take,hakanan ta dinga takawa zuwa bakin makarantar fuskarta a washe fes,saidai kana kallon idanunta kasan tayi kuka.
Ta gefan asma'u kuwa tarin carry overn data tarar tana da ita ta dagula lissafinta,ba qaramin tashi hankalinta yayi musamman sanda ta samu labari tun a cikin makaranta kyan da result din aysha yayi,duk da akwai banbancin courses a tsakaninsu,ba haka taso ba,bata son ma hamid yasan ta samu C.O bare ya raina qwaqwalwarta,ta tabbata kam yanzun dole ya sani kenan,hakan ya sanya ta baro makarantar a fusace kamar wani ne yayi mata.
Tun daga nesa kafin ta qaraso take ganin kamarshi,zaune yake dai dai saman babur din,yana sanye da kayan gwanjo kamar kullum shirt da trouser,takalman qafarsa budaddu ne dinkin hannu na kasuwar qofar wambai,hannunsa riqe da wayarsa da yake zuwa da ita yana dannawa,a zahiri ita yake dannawar,amma a badini yana wassafa halayen asma'u wadda tazo ta wuceshi yanzun cikin motarta ta tayar masa da qura,sosai zuciya take ciyoshi amma yana dannewa ta wani gefan,ya tabbatar ba qaramin haquri aysha keyi da su ba,akwai abubuwa masu yawa da bata gaya masa ba gameda da zamantakewarsu shi ya sani,ya tabbatar halayyar asma'un ba qaramin mai haquri bane xaya zauna da ita ba tare da anji kansu ba.
Da sassanyar muryarta tayi sallama daga gefansa,kusan satinta biyu bata ganshi ba,tun zuwan qarshe da yazo ya kawo mata carrot,dama duka duka idan yazo din baya wuce minti talatin ya wuce,saboda dukansu basu san me zasu gayawa juna ba,gwara shi yakanyi qoqarin janta da hira ko yaya irin ta wa da qanwa,saboda yana so ne ta sake da shi,ta dinga sharing matsalarta da shi,kanshi ya daga ya dubeta yana yunqurin maida wayar aljihunsa,duba dayan da yayi mata ya karanci yau tana cikin farincikin da bai taba ganinta cikin wannan yanayin ba,duk da baisan sila ba sai ya danji dadin hakan,ko ba komai yau yaga sauyin yanayin da ya saba gani kan fuskarta
"Ina yini" ta gaidashi tana dan rusunawa kadan
"Mun yini lafiya...ya gida?"
"Lafiya qalau" ta fada tana murxa yatsunta,shuru ya dan ratsa tsakaninsu,yayin da yake karantarta a fakaice kafin yayi magana
"Me muka samu yau?" Sai ta dago tana dubanshi kafin ta kauda idonta,don ba wani dogon kallo take iya masa ba
"Kamar me...,me ka gani?"
"Labarin zuciya a tambayi fuska inji hausawa?...fuskarki ta labarta min wani abu" murmushi ya subuce mata karo na farko daya taba ganin hakan qarara saman fuskarta,sai yaga ta sauya masa,jerarrun siraran fararen haqoranta suka bayyana,wushiryarta ta fito,haka dimple din dake kwance hagu da dama na fuskarta ya loba,tana son kaifi da saurin ganewarsa,yana da saurin karantar mutum,yana da alamun iya mu'amala
"Result dinmu ne ya fito"
"Ma sha Allah....duk yadda akai an samu abinda ake nema" kai ta kada fuskarta na sake fidda murmushi
"Ma sha Allah....kinga da yayan naki wani ne daya dauki nauyin ci gaban katatun naki" shuru tayi ba tare da tace komai ba,har yanzu kanta na a qasa,shirunta shi ya tabbatar masa da burinta kenan na gaba,saidai yanayin halayyarta ba zata barta ta iya fadi masa ba,murmushi kawai yayi yana kada kai wanda ya ratsa kunnen aysha,sai ya dauke kanshi gefe .
Ya bude baki da niyyar cewa wani abu lantana ta qaraso ta shaida mata asma'u na kiranta zata hada mata abinci zatayi baqo
"Yanzu zan shigo lantana" aysha ta fada,amsa mata tayi sannan ta juya ta koma ciki,khalipha aysha ya kalla wanda ya zuba mata idanu yana son yaga reaction dinta,ya fuskanci ba kadan ba asma'u nada izgili raini da wulaqanci,ta raina ajawalin aysha sosai,hannayensa rungume a qirjinsa,ta soma motsawa sannan tace
"Zan shiga ciki"
"Ni kuma ban gama abinda ya kawoni ba" da mamaki saman fuskarta ta kalleshi,sai kuma ta dauke kai da sauri donbata saba masa irin wannan kallon ba na kai tsaye,duka duka dama zaman da yake idan yazo din baya wuce irin wanda yayin yanzu,girarsa daya ya daga yana so yaga iyakar asma'u ne shi yasa yace haka
"Kina mamaki ne?,ita waccan awa nawa suke da nata sahibin idan yazo?,....ko da yake ni ba sona ake ba ko?" Kunya sosai maganar tashi ta bata,har batasan sanda tace ba
"Me kuma ya kawo zancan soyayya" kafada ya daga yana dan murmushi don yau ta bashi dariya
"Au....haka ne fa" qarar sake bude gate ita ta dauki hankalinsu,asma'u ce ta fito cikin taku dai dai tana jifansu da wani irin kallo na raini da qasqanci,kai tsaye ta nufi kusa da aysha
"Ke....yaushe na zama sa'arki da zan aiko a kiraki har tsahon wasu mintina baki zo ba?"
"Kiyi haquri anty yanzu nake shirin shigowa" aysha ta fada a sanyaye
"Ki wuce kije dalla karki batawa mutane lokaci"
"Bata gama abinda take ba tukunna" khalipha ya fada idanunsa zube fes a kanta,a fusace ta waiwayo da niyyar sauke masa qarshen tsiwarta,amma ga mamakinta sai taji bakinta ya kasa,wani kwarjini na musamman taji yayi mata,sai kawai ta maida idonta kan aysha
"Karki shigo don Allah kici gaba da zama" ta juya cikin bacin rai ta koma ciki,cikin wani irin zafin nama ya diro daga saman machine din nasa
"Macace...ba kuma girmanka bane kai da kanka...saidai kasa ayi maka" wani sashe na zuciyarsa ya tunasar da shi,tilas ya dunqule hannunsa kowanne waje guda ya zirashi cikin aljihunan wandonshi yana hadiye fushinsa tare da qoqarin saita kanshi.
Tuni idanunta ya cicciko da qwalla,duk da bashi take duba ba yakaranci hakan daga sanda ta soma jan hanci
"ka gaida gida" ta furta a hankali
"Kin tabbatar kin gama duk uzurinki?"
"Ka barni naje...koda banje bama sakamakon..." Sai ta kasa qarasawa,da hanzari yace
"Jeki...Allah ya bamu alkhairi" duk da ba haka yaso ba,so yayi yaga iya gudun ruwanta a yau,saidai kuma kome yayi yunqurin yi tare zai barsu da ayshan,koma meye a kanta zai qare ita kadai,yana nan tsaye idanunsa biye da ita har ta bude qofar gidan ta shige.
*oum muhammadiyya*
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
20
Cikin satittikan da suka biyo baya duka mummy shirin biki take haiqan,ba qaramin buri ta ciwa bikin ba,bama ita kadai ba har sauran yayyen asma'un,karma su aunty halima suji labari,gwara ma aunty safiyya ita da yake ba shiri tsakaninta da amaryar sosai,babu wanda yake ta aysha...babu wanda ya damu da lamarinta,anty safiyya ce kawai mai tsomota cikin lamarin.
Da yammacin wata ranar laraba anty safiyya tazo gidan,suna zaune a parlour ita da mummy da asma'un,mummyn na cinikin wasu magungunan mata da asma'un tace tana so,ta kira matar takanas kuwa har gida ta kawo mata,saboda tasan cewa zata maida uwar kudinta cas harma da riba,mummy na dauka asma'u na duddubawa tana zaba da kanta,anty safiyyan na gefe tana kallon ikon Allah,tun tana shuru har ta gaza yin shirun kasancewarta mai zafi da rashin son raini da wargi,kai tsaye ta yiwa asma'un magana saboda tasan idan ta mummy ne ma aikin banza ne a wajenta
"Wai asma'u meye haka?,wannan wacce iriyar muguwar dabi'a ce?"kai ta daga tana kwabe fuska saboda tasan halin anty safiyyan tsaf
" yanzu kuma meye nayi?,tunda kika zo gidan nan na kasa qwaqqwaran motsi na sake saboda nasan ki da dan banzan chellang din mutane da cin gyaransu"
"Akan gaskiya ba....ke ko kunya bakiji ki zauna kina zabawa kanki magungunan mata gaban babarki?" Matar ce ta saki dariya tana cewa
"Yo hajiya meye?,ai yanzu haka akeyi,idan ba'a mata a gidansu ba waye zaiyi mata?,'yammatan yanzu ma kansu ya waye,idan ba'a miki ba ni da kansu suke zuwa su siya abinsu kafin bikin suyi amfani da shi...meye a ciki ai gwara su gyaggyara ko" dauke kai safiyya tayi daga bangaren matar,donta fuskanci ita kudinta takewa campaign da kayanta,ba ruwanta da batun kunya ko al'ada ta dubi mummy
"Mummy....ko magani za'a bawa asma'u ba irin wannan take buqata ba,maganin sanyi da basir ya kamata ace an soma nema mata,baya ga haka ma akwai abubuwa da yawa daya kamata ace su aka fara dora ta akai bawai magani zalla ba da sauran qyale qyale,akwai abubuwa data rasa,mummy ina mai tabbatar miki babu abinda asma'u ta iya dafawa,hana rantsuwa indomie,komai a gidan nan yiwa asma'u ake bata san ta yiwa kanta komai ba,a haka zata zauna gidanta duka ba'a kula da wannan ba,wannan gata ne mummy?,duk macen data shiga gidan miji a haka ko hurul'een ce ita ba zata taba daraja ba" bacin rai qarara ya fito a fuskar asma'u,badan badan ba da tace anty safiyya na cikin 'yan baqincikinta,don dai kawai ciki daya suka fito,ta jima rabon da aci mata fuska irin haka,badan tasan bata daukar wargi ba ba abinda zai hanata gaggaya mata magana kota sheqa mata ma zagi
"Banda abinki safiyya duka mai ya kawo wannan maganar kuma,zancan koyon aiki kema kinsan inda zata je ai,bata da matsalar girki da sauran gyaran gida tana da masu yi mata"
"Barta kawai mummy,don ke baki da mai aiki kinqi daukar kowa kin hadawa kanki wahalar aikin gida kowa haka zai zauna kamar wani dan wahala?,already mun gama magana ni da hamid ina da masu yimin komai baya buqatar na wahal da kaina wajen dauke koda tsinke ne" asma'un ta fada cikin bacin rai tana ci gaba da duba kwalin magungunan abinta
"Idan kana da kyau asma'u ka qara da wanka,ni yar uwarki ce dole na gaya miki gaskiya koda kowa ya kasa gaya miki saboda tsoron ko shakkar rashin kunyarki,duk arziqin mijinki akwai wani abu da yake buqata matarsa ta iya tayi masa ita da kanta,ba burgewa bace kana jibge kaman kayan gwanjo wata ke miki aikin gidanki,duk ladarki kin tattara kin bar mata,bautar ubangijin da akace zakiyi cikin aure ke baki ma santa ba kenan,saidai kici ki sha kiyi wanka"
"Au dama bauta aka ce miki no zanje nayi?,tabdijan su bauta manya,ni gidan 'yanci zan shiga gidan soyayya"ta fada tana tabe bako,don ta soma kaiwa bango,gab take da yiwa mata rashin kunya,bata son ayi fito na fito da ita kwata kwata kan nata ra'ayin,tafiso a qyaleta tayi yadda takeso ta kuma tsara
"Rayuwarki ce kiyi duk yadda kike ganin ya dace,amma karki kuskura kimin rashin kunya,kin sanni bani da dadi wallahi" ta fada cikin fushi qarara bayyane a muryarta
"To ya isa haka don Allah,ni bana son wannan rigingumun naku" mummy ta fada tana turawa matar kayanta,tattarewa tayi ta soma maidawa cikin jakarta suna lissafi da mummy,tashi safiyya tayi ta wuce kitchen saboda bacin rai da takaici,kome asma'u zatayi batasan me yasa mummy bata iya tsawatar mata ba,ita a ganinta sam wannan ba soyayya bace,duk duniya kowacce uwa na son danta,amma duk sanda kikayi sakacin da baki iya tsawatar masa a sanda ya aikata ba dai dai ba to la shalla zakiyi kuka gaba da hawayenki,bahaushe yace ka saka danka kuka kafin shi ya saka ka,hakanan kaza tana sane take take danta badon bata sonshi ba,a'a sai don ta koya masa darasin rayuwa.
Sanda ta fito daga kitchen din matar ta wuce,hakanan asma'un bata falon,zama tayi kusa da mummyn dake latse latsen waya
"Mummy...don girman Allah ki daina biyewa asma'u a duk lamuran da tace tana so,mummy wannan fa ba gata bane,gidan wani zata je fa,yadda kika saba mata haka zata ce zata yi musu,bayan ita rayuwa ba tabbas gareta ba"
"Kai safiyya kai...wallahi kin cika qorafi...magana ta riga ai data wuce ko,maganin duka qwaya biyu na daukar mata sai kuma meye yayi saura?,nifa kinsan bani son takura kwata kwata" kai ta jinjina
"Shikenan mummy...kiyi haquri" daga haka ta soko maganar data kawota gidan,kan wani abun adon daki da za'a yiwa asma'un,saidai yadda taga mummyn na lissafin na mutum daya ne
"Mummy aysha fa...nayi zaton duka daddy ya bayar?"
"Eh...ina da uzuri da nata kudin ne,idan na samu wasu kudin ko kafin biki ne ayi mata tunda kamfani ne ba za'a rasu su available ba koda yaushe" shuru kawai safiyyan tayi,tunda ta fadi haka kawai ta sani banda ita,batasan me yasa mummy take irin haka ba,aysha ta cancanci a siya mata ma ahana asma'u,don yadda mummy ke morar aysha mo asma'un bata mata rabin wannan morar ko kusa ko alama.
(To gareku mata masu riqon yaran wasu,walau marayu dan kishiya ko masu iyaye...mu sani rayuwa bata da tabbas,baki da tabbacin kema zaki rayu da naki,idan kin rayu da naki jikonki fa?,duk abinda ka yiwa yaro na cutarwa yana sane abun yana kanshi,komai dadewar shekatu wallahi Allah yana sane da abinda kayi masa,wani ma a sanda zai tuna miki tsufa ya cimmaki ko qarfinki ya qare kema kina qarqashinsa ko qarqashinta,a sannan shi kuma Allah ne kadai yasan arziqin da yayi masa,a lokacin da zai tuna mikin Allah ne kadai yasan kunyar da zaki sha idan ma kina raye kenan,idan ma bai yada maganar a sanda kike qarqashin qasa ba,wallahi duk wanda ka zalunta duk qanqantar zaluncin Allah bazai taba yafe maka ba sai ya fiddawa kowa haqqinsa,da kike fifita yaranki a kanshi shima haihuwarsa akayi iyayensa na sonahi,qila da suna tare da shi gatan da zasu nuna masa yafi wanda ke kike nunawa naki yaran,hakanan yaranki na kallon me mike kina koya musu aqidar banza ne idan Allah ya basu aron rai suma akai zasu dora,shi sharri dan aikene maishi yake dawowa,hakanan alkhairi danqo ne baya faduwa qasa banza,Allah yasa mu dace,yasa mufi qarfin zukatanmu)
A tsakanin wannan lokacin mummy suka tafi dubai ita da asma'u da anty halima,batasan me da me suka tsarawa daddy ba,saidai baiyi fada kan tafiyar da sukayi babu ita ba,itama sabgarta kawai take,a yanzu gaba daya addu'o'inta sun karkata ne kan Allah ya sanya auren ya zama alkhairi a gareta duniyarta da lahirarta,bata jin motsin wani daga cikin 'yan uwanta bare yace wani abu kan aurenta ko zata ji dadi,tasha tasa wayarta a gaba tana kallon lambar umminta,ta sha kwatanta kiranta,tasha qissimawa a ranta inama ta wayi gari watan wata rana ta tsinci koda miscal ne akan fuskar wayarta,zata so Allah ya gwada mata wannan mafarkin nata koda sau daya ne tak a rayuwarta kafin tayi qaura wa duniya,abun mamaki da lantana mai aiki suka tafi,tana jin mummyn na cewa
"Gwara muje da itan,saboda daukar kaya da sauran 'yan wahalhalu" bata sani ba kota fadi hakanne saboda kar ayshan ta zargeta,itadai ko oho bata masa inda zancan nata ya dosa ba,don bata iya riqe magana ba a rai,ita kadai suka barwa gidan sai mai gadi,a lokacin daddy shima yayi tafiya,tana tsoron gidan sosai amma haka ta zauna babu yadda ta iya,idan tayi addu'a ta koma dakinta bata sake fitowa sai safiya,
Ba qaramar siyayya suka yo ba,har jikokinta sai data yi musu tasu tsarabar,kayan fitar biki nata dana asma'u,hakanan ta jido kayan business dinta,saidai babu ko tsinke da Allah yasa aysha taga gilmawarsa da sunan nata ne,kaya masu yawa haka aka jibgewa asma'u a store din gidan,a haka ma da wasu suna nan qarasowa.
Kwana biyu da dawowarsu taji mummyn na waya da wani mutum dake amsar kayanta a kantin kwari kan tana son kaya,da daddare sai gashi ya kawo din kuwa,a sannan yasha tana daki tana gyaran kumbarta lantana ta shigo ta kirata,kaman ko yaushe ta saka hijabinta ta fita
"Aisha ga kaya nan saiki zabi kalar wanda kikeso,daddynku ne yace a siya muku na fitar biki" kai ta tada ta dubi kayan
"Duk wanda kika dauka min yayi"
"A'ah A'ah ni babu ruwana kinsan halin daddynku,tare da asma'u muka je ta zabi wanda takeso to saboda kayan kar suyi yawa suja kilo shi yasa ba'a sai naki ba,dalili kenan daya sa nace nuraini ya kawo miki daga shagonsu kema ki zaba da kanki,tunda suma kayan su masu kyau ne"
"Mtsweew....mummy sai dana ce miki ba sai kin kirata ba,ina laifi ba ma da za'a siya mata,kawai ki zaba ki aika dasu wajen dinki ta bada size dinta,amma ai bama girma bane ki tsaya kuna wani maida magana ke da ita"
"Shikenan zabar mata,'yar uwarki zata zabar miki"
"Na gode" ta fada kawai tana miqewa tabar wajen,asma'un ita ta zaba mata atamfa da laces,kusan kayan ma mummyn ce ta sarosu kudin ya sake dawowa inda ya fita kenan,dinki ne kawai mummyn ta kai inda ake mata bayan ta dauki hotunan kayan ta turawa daddy da sunan kayan da aka siyowa asma'u ne da aysha.
Satin da suka dawo kwana hudu tsakani aka soma shirin amsar lefen asma'un,ko ba'a fada ba mai karatu yasan waye a gaba idan ba hanci ba,tun ana sauran kwana biyu a kawo lefen aka hana ayshan tsugunnawa,tamkar wasu jinin hurul ini ne zasu zo haka ake tsara komai,a randa zasu zo din kuwa kayan masu kawo lefe kawai da aka hada abun a tsaya a kalla ne,komai cikin girma harma da nuna fariya a lamarin haka aka jibge musu kaya ana jiran isowarsu.
Tabbas hamid yayi lefe irin wanda ya dace da tsarin asma'u,akwati talatin ne cif,goma pink,goma purple,goma brown,kowanne danqare yake da sutura ta alfarma,sai kayan sakun lalle,kama ga buhunhunan shinkafa,suger gero da sauran kaya,'yan uwan asma'u kaman su taka rawa banda anty safiyya data kama kanta tun sanda taga yadda 'yan uwan hamid ke bubbuda hanci suna kallon ko ina da kowa d'ai d'ai,don ko zama ma basuyi ba atsaye akayi komai,tukuicin kuwa da aka basu cewa sukayi sun gode basu amsa ba,wanda kana ganin yadda sukayi din sun raina ne,saidai da anty safiyyan ta fada asma'un rigima ta saka tace dama can bata qaunarta ita da hamid shine yanzu zata yiwa 'yan uwanshi sharri,ita ta rasa me yasa tana 'yar uwarta bata qaunarta,ta lura da da hali canzata zatayi da ayshan don ta lura tafi sonta da ita,sai abun yaso ya koma kaman ashan ce tayi da yake tafi rainata akan kowa,shuru kawai tayi musu daga qarshe saboda yadda taga sun dauki zancan tsakanin asma'un dasu anty halima,babu ma wanda ya kula da abinda ita tace ta hango din,duk idanunsu ba wannan yake kalla ba,abinda kawai suka dubawa dukiyar da aka jibgowa asma'un.
A sannan aysha na falon ta zuba ma anty halima da anty kubra abinci ta aje musu,saboda basu tafi ba har isha'i suna falon suna hirar yawan kayan da kyansu tare da yi musu d'ai d'ai suna sake kalla,tana shirin juyawa anty kubra tace
"Ke yaushe ne kawo naki lefen?naji har yau baki ce komai ba" Kanta a qasa tana murza tafin hannunta tace
"Idan zai kawo din zai fada.....dama ya riga daya gayamin zaiyi bakin qoqarinsa ne idan sun samu,saboda ranar bikin da aka sama tayi mishi gajartar da zai iya shiryawa a tsukin" wani mugun tsaki anty halima ta saki sanda take kai lomar abincin bakinta
"Kema kubra da neman magana kike wallahi.....har wani lefe kike jira a kawo mata....saikiyita jira ai....ke tashi ki bamu waje" ta fada tana hade rai gami da kafeta da ido,asma'u dake zaune gefe ta samu nayi,dariya ta dinga harda qyaqyatawa
"Yaron oga ne fa,sai abinda oga ya gutsuro ya bashi da shi zaiyi hidiman bikin,ku bishi dai a hankali kar ya fece,dai dai ruwa dai dai qurji"
"arziqi da talauci dai duka na Allah ne,kuma zaman lpy da mutunta juna ake nema ba tarin dukiya ba"cewar anty safiyya aysha ta jiyota tana fada,a sannan tuni ta isa qofar kitchen tayi shigewarta abinta,itakam ko cikin tunaninta bata wani saqa zancan lefe,mata masu 'yanci suke bidar lefe,ita wani abu ne ya rage mata,sam bama shine damuwarta ba a yanzu.
Washegari da daddare daddy na falonshi zaune ana nuna masa kayan,asma'un na zaune gefenshi suna kallo tare,duban mummy yayi
"Banga aishatu ba yau....ina tayi ne?" Baki mummyn ta tabe
"Allah dai ya kusa raba yari da barawo" ta furta a ranta
"Tana ciki.....ka santa gwanar zama a daki sam batason zaman falo bansan me ya sa ba" asma'u ya kalla
"Jeki kira min ita" hakanan ba don taso ba ta miqe ta tafi kiran ayshan,sanda taje ayshan na kwance rub da ciki saman gadonta tana karanta wani littafin addu'o'i,ta qara yawan haddar addu'o'inta sosai saboda kariya da ingantuwar tata rayuwar
"Saiki taso kizo....kwarkwasa fidda mai giji" ta fada tana watsa mata harara sannan ta juya ta koma,a nutse ta miqe ta sanya hijabinta sannan ta zura slippers ta fito.
Cike da nutsuwa tayi sallama hannunta dauke da jug na glass wanda ke cike da lemon guava data hadashi dazun nan,fuskar daddyn ce kawai qunshe da murmushi,ta isa gabanshi ta aje cikin nutsuwa
"Daddy sannu da hutawa"
"Yauwan indon baffale....sannu kadai" ya furta yana duba jug din
"Yau kuma me na samu?" Murmushi ta saki tana sunkuyar da kanta sanda take komawa da baya tana lalubar mazauni,da kanshi ya zuba sannan ya soma kurba yana kallon kayan da asma'u ke dagawa daya bayan daya,ganin shuru daddyn baiyi magana ya sanyata fara yunqurin miqewa a zatonta ba wani abu bane sai ya dakatar da ita har sai da suka gama kallon kayan tsaf,duk da aysha jifa jifa take daga kai ta kalla ta maida kanta qasa ta saddar.
"Ma sha Allah....yanzu sai biki kenan gaba daya ran ashirin ga wata" dif sukai daga mummyn har asma'un saboda anzo wajen,anzo wajen da ba zasu yarda daddy ya hada musu biki da ayshan ba,ko komai sun daure basa jin zasu haqura da wannan din
"Daddy" aysha ta kirashi cikin sanyin nan nata
"Na'am aishatu..."
"Daddy don Allah ina neman alfarma..."
"Tame indo?" Dan jim tayi kadan sannan tace
"Ina neman alfarmar idan babu damuwa a qyale anty asma'u tayi nata bikin ashirin ga wata din...ni ranar litinin din da aka gama bikinta ina son na tafi qauye ayi nawa bikin a can,daddy......" sai kuma ta danyi jim
"Inason idan an tashi daukoni a daukoni daga tushena...inda na girma na kuma rayu a can".
Shiru daddy yayi yana auna kalamanta,yarinyar nada nutsuwa sanin da kamata,ya tabbata da wata ce cikin 'yammatan zamanin nan masu son abun duniya son qyale qyale da qyamatar tushe babu abinda zai sanyasu yin zancan asalin nasu ma bare akai ga batun zuwa can biki
"Kin tabbatar haka kikeso,baki kuma da matsala da hakan?" Daddy ya tambayeta yana dubanta
"Eh daddy.." Ta fada tana gyada kai alamun tabbatarwa
"Shikenan to,babu damuwa" kanta ta duqar qasa
"Na gode daddy...Allah ya saka da alkhairi ya qara girma"
"Amin amin aishatu" ya amsa yana jin dadin addu'o'inta,ficewa tayi ta barsu a nan.
Tana shirin tada sallar wutiri bayan ta gama shafa'i wayarta ta dauki tsuwwa,dakatawa tayi don bata riga ta tayar din ba ta duba mai kiran,Aliya ta gani...take hannunta ya fara kakkarwa tana kokawar daga kiran kamar wadda ke dambe da wani tsabar rudewa da jin dadi,lallai Aliyar tazo mata a dai dai sanda tafi buqatarta fiye da kowanne lokaci
"Aliya.."
"Aysha" suka kira sunan juna a tare,qatuwar ajiyar zuciya aysha ta sauke,sannan cikin mutuwar jiki ta koma gefan gadonta ta zauna tana cewa
"Haba Aliya...haba..ya zakimin haka don Allah fisabilillahi.....bayan kinsan duk duniya bani da abokin shawara..kin tafi a lokaci mai tsada da muhimmanci a rayuwata kinyi dif kamar baki duniya...?" Ta qarashe fada lafuzanta na bayyana tsantsar damuwar dake maqare a zuciyarta
"Kiyi haquri sashin...wallahi dake nake kwana nake tashi...saboda ke naqi zama a nijer,kin ganni shigowata gida kenan ko zama wallahi Allah banyi ba na soma da kiranki....gayamin meke faruwa?"ajiyar zuciya ta sauke,cikin karaya tace
"meye ma bai faru ba,babu abinda ma bai faru ba sashin" idanu Aliya ta zaro kamar tana wajen cikin fargaba
"Me ya faru dake 'yar uwa gayamin"
"Wai aure zanyi,aure na ya kusa"
"Kaman yaya?,how comes?...labarin daya cancanci ace ni zan bada shi ni ake baiwa....aysha ban fahimceki ba....wanne irin aure?ina fatan babu cutarwa a ciki" dan qaramin murmushi daya fidda sauti ta saki,duk da cewa tsoro fargaba da alhini ne danqare a qasan zuciyarta
"Maganar tafi qarfin waya Aliya.....idan kin samu lokaci kyazo"
"Wanne lokaci ne zan samu?...ki jirayeni gobe da sassafe in sha Allahu"
"Allah ya nuna mana....ki gaida mama"
"Zata ji" da haka sukai sallama,aysha ta jima zaune riqe da wayar tana kallonta,jifa jifa tana sauke ajiyar zuciya,haka kawai take jin nauyin da take ji a qirjinta ya dan ragu duk da bata ce komai ba,lallai ba shakka rashin abokin shawara(aboki na gari mai addini) ba qaramin nakasu bane a rayuwar mutum.
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
*KO KUMA*
07067124863
*DB*
21
Goma na safiya ta kammala duk abinda take,saboda ta sani tsaf zata iya ganin Aliya a lokacin,cikin dakinta ta zauna tana 'yan gyare gyaren da suke maganin zaman banza da kuma hana kai tunani,don babu wani abu qwaya daya dake buqatar gyara cikin dakinta,tana da bala'in tsari komai nata a jere yake daki daki,tana da tsafta komai nata kal yake kaman ba'a zama cikin dakin,tun da can tana da son tsafta,koda bata da sabulun wanki ko wanka,haka zata dibi toka tayi wanka,ta sake saka tokar ta sabe kayan sawarta duk da cewa ba wai fita suke ba amma tana rage dauda,kuma tana jin dadin sanyasu a jikinta a hakan.
Sha daya na safe wayarta dake aje gefanta ta dauki ringing,da sauri ta duba aliya ce
"Ina bakin gate zo ki shigo da ni..."haka ta fada mata,yawancin lokuta indai tazo din ayshan take kira tazo ta shiga da ita duk don kada wai su hadu da asma'u tayi mata kallon banza da wofi,don ba qyaleta zata yi ba.
Murmushi suka sakarwa juna sannan suka tako zuwa cikin gidan tare,gab da zasu shige sashen dakin ayshan sukayi kacibus da asma'un sanye da kayan bacci zata shiga kitchen,da alama yunwa ce ta tasheta,don tana iya kaiwa azahar a daki tana kwance kurum kamar ruwa,har ta gota sai ta dawo da baya tana duban aliya
"a'ah....anzo shirye shiryen bikin ne?" Ta furta cikin siga ta izgilanci tana dariya dariya
"Ai gwara a bada himma...mai kwarmin ido da wuri yake fara kukansa ko?,duk da yake ma a qauye za'ayi komai,ta kwana gidan sauqi" ta qarashe tana dariya,da sauri aysha ta matsa hannun Aliya tana mata nuni da kada ta kulata kenan,aliyan ta fahimci haka,saboda haka ta watsawa asma'un kallon banza sannan tace
"Kinci sa'a cikin gidanku nake.....ki tareni a waje" ta fada a zafafe tana jan hannun aysha sukayi gaba
"Ba komai....duk nasan meke damunku" ta fada tana dariya tayi kitchen,iska ta furzar daga bakinta bayan sun shiga dakin ayshan,bata iya zama ba ta dubi aysha
"Har yau wannan mara mutuncin tana nan tana iskancin nan nata....abun ma kamar gaba yake sakeyi saboda rashin taka mata burki da bakyayi ko?" Murmushi aysha ta saki tana gyara ma aliyan wajen da zata zauna bawai don akwai datti ko kaya a wajen ba
"Karki damu.....duk abinda take ba shine a gaba na ba...saboda baki taba gani an gutsuri naman jikina saboda haka ba....hasalima qimarta nake gani har kwanan gobe....saboda jinin daddy ce ita....daraja ba qarya bace...ko a lahira wani yana cin darajar wani....karkuma ki manta cewa ni din ba kowa bace....face yarinyar da hatta mahaifiyarta ta gujeta"ta qarashe cikin karayar zuciya
"wannan ba hujja bace" aliya ta fada hannunta riqe da qugunta tana kada kai
"Manta da wannan.....zauna muyi hirar yaushe gamo" ta fada tana murmushi tamkar ba abinda ke damunta a rayuwa,saidai can qasar zuciyarta tana jin tafi kowa matsala a rayuwa
"Ba hirar yaushe gamo zamuyi ba aysha....mu tattauna maganar dake gabanmu" ta fadi tana zama,yayin da ayshan ta yiwa kanta mazauni itama kusa da ita.
Kaf babu abinda ta boye mata ta zayyana mata komai,shuru ne ya ratsa dakin yayin da aliya ke hadiyar yawu idanunta fes kan fuskar ayshan
"Aysha..." Ta kirata still tana kallonta
"Na'am" ta amsa tana dubanta
"Kin gamsu har cikin ranki zaki auri wannan mutumin zaki zauna da shi?" Tayi mata shigen tambayar da khaliphan ya taba yi mata,kai ta jinjina don ta tabbatar idan tace bata so tsaf aliya zata rusa komai,to idan ta rusa dinma me zata zauna taci gaba da yi cikin gidan?,meye amfanin zamanta?,a gaba wa zata hadu da shi?,gwara wannan ya nuna alamu na tausayi a gareta
"Shikenan....addu'a zamu ci gaba da yi Allah yasa kin dace...ina fata kuma asma'u idan ma tayi da niyyar mugunta mugun abinta ya koma mata kanta,auren mai kudi ba shine dacewa ba,aurwn mai kudi ba shine samun kwanciyar hankalin gidan aure ba,auren mai kudi bai cikin manyan jigon dake sawa a auri namiji,ni'ima ce da idan Allah yaga dama zaiwa wanda yaga dama bawai don yafi sonka cikin halittarsa ba,hasalima ba kowa ke dacewa kan hakan ba,amma sashin abu daya bana son kice zaki rage na hidimar biki da akewa kowacce diya mace budurwa,don kema ita ce....saboda haka zamuyi komai kamar yadda akeyi" dariya aysha tayi ta karyar da kai tana duban aliya
"Kiyi haquri sashin karki dora min abinda bazan iya ba,wallahi Allah bana sha'awar yin komai....kin manta cewa muhalli kawai zan sauya ba wani abu ba....ni haka nake ji a jikina bawai aure zanyi ba"
"Sai kuma kiyi..." Aliya ta fada tana tura dankwali gaban goshi,hakan da tayi ya sanya aysha qyale maganar don bata fiya son jayayya ba,saidai har cikin ranta bata jin tana buqatar yin wani abun.
Hira sosai suka sha da aliya,wanda tana yi tana jefo maganar biki da wani abun da za'a gudanar,itadai murmushi aysha take,komai ma ganinsa take kamar almara sani ne aliyan batayi ba take zancan wani biki,wayar aliyan ce ta fadi tunda ta sauka anijer din,bata kuma haddace lambar aysha ba,mamanta kuma itama bata gari bare ta aiko a karba mata lambar ta tura mata.
Sai qarfe uku aliya ta shirya tafiya,tare suka fito tana tako mata har wajen gate,daga can ta hango kamar shi,yana tsaye gaban mai saida agwaluma da goba irin masu turowa a baro din nan yana siya,kanta ta dauke har zasu gota shi taji ance
"Sannunku" tare suka waiwaya,ayshan ta saki dan qaramin murmushi
"Barka da yamma" ta furta a hankali,har yau bata sakewa da shi jinsa take kamar baqonta
"Barkanki..."ya amsa mata yana miqa mata ledar agwalumar daya siya mata a baqar leda
"Na gode,bari na dan raka qawata" ta fada bayan ta saka hannu biyu ta karba a mutunce
"A dawo lafiya...amma ai ba haka ake ba...bari ni nayi karambani....qawa ni suna na muhammad khalipha....nine sabon yayan aishatu" duban ayshan aliya tayi don bata gane me yake nufi ba
"Sabon yayanta da za'a daura musu aure...." Ya sake bata haske,qasan ransa yana dariyar yadda ta kasa gane zancan da farko
"Ohk....kacemin ango ne" ta furta cikin fara'a,sannan suka gaisa,nan suka barshi su kuma sukayi gaba,sosai aliya ta damqe hannun aysha
"Sashin....wannan kyau haka?....haka yake da kyau....ke ni kaman ma na san fuskarshi wallahi,kamar na taba ganinsa amma na manta a'ina....gaskiya kyakkyawa ne" itakam murmushi kawai tayi,don bata iya qare masa kallo bare ta rarrabe da kyansa ko muninsa
"Gaskiya kin dace...da alama sashin yana da kirki....saidai abinda ban gane ba....meye na wani cewa yayanki.....yana nufin a hakan zaku tafi wa da qanwa?" Ajiyar zuciya aysha ta saki
"Koma mene ni indai zai sanyani cikin ahalinsa,su zauna da ni zuciya daya su riqeni kamar daya daga cikinsu,na samu walwala da kwanciyar hankali magana ta qare" kai aliya take kadawa sannan ta dan dakata da tafiyar da take ta dubi aysha
"Ban yarda da wannan alaqar ta tafi a haka ba aysha....kisa a ranki aure zakiyi kamar kowa" murmushi tayi tana rausayar da kai bayan ta kallo gefe guda
"Nima ai ba kamar kowa bace aliya ki duba fa ki gani....ba wanda ya nemeni don zanyi aure...ban taba tattauna maganar dake damuna da kowa ba saike...kina nufin da ni 'yar gata ce...kina nufin da ana sona dukkan abinda ya faru din nan zai faru?" Ta qarashe tambayar idanunta cikin na aliya,da alamar akwai abunda ke taba ranta qwarai,kama hannunta aliyan tayi qasan zuciyarta cike fal da tausayinta
"Karki damu da kowa....karki damu da komai aysha...koba kowa mu muna tare...ki koma ki jirayi lokacin zuwa gyaran jiki....kin bar angonki kuma a tsaye,idan wata tazo wucewa kuma ta qyasa kanshi ba ruwa na,tsaf zata qwaceshi a hannunki da wannan sanyin naki" ta qarasa fada cikin sigar zolaya,dariya ta baiwa aysha har sai da tayi ta fito,har yau ba zata iya tantance wannan kyan da aliya ke fada ba
"Amma fa karki tsorata....don bai fiki kyau ba qawata" dariya sosai wannan karon ta baiwa ayshan,wanne kyau ne da ita?,yaushe ta samo kyan,mamaki take duk sanda aliya tace mata tana da kyau
"Ki gaida mama" suka qarke sallamar sanda wani mai napep yazo wucewa aysha ta tsaida mata shi suka tsadance yaja suka tafi.
A jingine ta sameshi jikin katangar qofar gidan hannayensa rungume a qirjinsa,ta saci kallonsa tana son gano kyan da aliya ke fada saidai hada idanun da sukai ya hana hakan tasiri,tana jin nauyin ya ganta tana kallonshi ba tsari hakan a wajenta,kauda kanta tayi sannan tayi gaba zata shige
"Da kin tsaya mun gaisa....wucewa zanyi daga aiken oga nake karyaga na jima ban dawo ba" bata ce komai ba ta dawo da baya,nesa dashi ta tsaya kamar yadda suka saba,a fakaice yake karantarta kamar yadda ya saba,yana mamakin halayenta sosai,sam.bata damu da wasu qyale qyale ba na rayuwa,tunda yake zuwa kulli yaumin cikin hijabi yake tadda ita,bata da yawan kazarniya ko rawar kai irin ta 'yammatan yanzu,bata da surutu bata da kallo,zai iya zuwa ya tafi baifi ta kalleshi sau biyu ba,shi dinma bawai ta kalli cikin qwayar idanunsa ba kai tsaye,dama ba wani hirar arziqi suke ba,yana zuwanne kawai saboda anni dake yawan cewa yaje din bai kamata ba,bataso tazo taqi sakewa da su,ya zamana bata saba da kowa ba
"Biki yanata qaratowa kinjini shuru ko?" Ya fada yana shafa sajen fuskarsa,ba abinda ta fada har ya gama jiran amsa ya dora
"Ina can ina fafutuka ne....duk abinda Allah ya hore zaki jini in sha Allahu...me dame zakiyi ne da bikin?,a ina zakiyi taki walimar?" Dan motsawa tayi kadan hannayenta rungume a qirjinta ta cikin hijabinta
"Karka matsa da yawa....qauye ma zan tafi a satin bikin" cikin mamaki yake dubanta
"Qauye kuma?.....me zakiyi a can?" Sai a sannan ta daga idanunta ta zubesu fes a kansa kafin ta sake janyesu ta maidasu qasa
"Can ne tushe na...kuma daga can nakeso a dauko ni....bani da inda yafi can" tayi shuru tana jiran jin me zaya fadi,gaba daya ta gama burgeshi,a wannan zamani da yawancin mutane ke bala'in gudu da qyamatar qauye....suke jin haushi da takaici idan an kirasu 'yan qauye,suke bata rai idan 'yan qauye sun rabesu,a sannan ita ta zabi ta nuna su a matsayin danginta,ta zabi kowa yaje ya ganta a cikinsu,take daga hannu tana gayawa duniya daga inda take
"Babu matsala.....duk da haka za'ayi abinda ya samu da yardar Allah....sakamin number wayarki don Allah koda buqatar kiran zai taso" ya fada yana miqa mata vivo dinsa da ya baiwa nasir dazu ya saka reza ya jijji mata ciwo,saika dauka tsabar dadewa ne ya saka ta qoqe,idanu ya zuba mata sanda ta amsa ko zaiga qyama daga gareta ko wani abu makamancin haka,saidai fuskarta na nan a yadda take ta soma jera masa lambobin,saura lamba biyu ta gama sakawa wayar ta dauke dif,yasan da faruwar hakan amma sai ya nuna kamar bai kula ba,cikin damuwa ta dago ta dubeshi
"Ta dauke wayar ko chargy ne babu?"
"Subhanallah....,dama yau tun safe take haka....miqo in gani,Allah yasa ta tashi,gashi oga zai iya kirana kowanne lokaci" ya karba yana cire batirin,ya sake maidawa ya kunna duk da yasan ba sake tashi zata yi ba,ai kuwa bata tashin ba,fuskarsa cike da damuwa yace
"Idan akwai paper da biro taimaka ki rubutamin nayi maza na wuce nakai masa saqon tunda taqi tashi"
"Mu gani" tace tana miqa hannunta,wayar ya miqa mata kamar yadda ta buqata,sai yaga ta bare batirin ta ciro layin dake kai,dama babu memory a ciki,wayarta ta bude ta cire nata layukan ta dora nashi ta kunnata ta tasheta sannan ta miqa masa
"Kayi amfani da wannan,zai iya kiranka kafin ka qarasa inda yake yaji a kashe,zai kuma ji dadi....me yiwuwa ka sabawa dokar aiki ka biyo ta inda ba wajen aikinka bane a lokacin aiki" mamaki fal saman fuskarsa yake duban wayar data miqo masa,bawai mamakin tsadar wayar ba,don ya jima rabon ma daya riqe waya mai qaramin kudi kamar ta,mamakin yadda ta bashi wayar kanta tsaye yake,baya manta sanda asma'u ta soma ganin wayar hannunsa,sanda ya bata wayar yace ta saka mishi numbers dinta,sai tada ci dariya sosai kafin tace
"Wai wannan waya ce?" Ya amsa mata da eh,ta bude baki kamar zata sake magana sai kuma ta fasa,ta miqa hannu a qyamace zata amshi wayar sai kuma ta fasa
"Karta bata min hannu da Allah,bari na karanto maka digits din" da toh ya amsa mata,ta dinga karanto masa yana sakawa,sai da ya gama lodawa sannan tace
"Pls duk sanda muke tare ka dinga qoqarin boye wayarka,kar daya daga cikin friends dina su gani ka zubar min da mutunci"
"Ke dame zakiyi amfani?" Ya katse tunaninsa ta hanyar tambayarta
"Karka damu dama ba wani abu nakeyi da ita ba,ina da qaramar nokia zan saka layina a ciki" hannu ya sake miqa wa yana cewa
"Kawo waccar to ko Allah zaisa ta gyaru" kai ta kada
"Karka damu.....akwai wanda zaizo anjima ya karba za'a gyara" sai ta soma takawa tana cewa
"Ka wuce karka yi laifi.....sai anjima ka gaida hajiya".
Ya dan jima a tsaye a wajen yana juya wayar a hannunsa kafin ya soma takawa yana barin layin zuwa layin da motocinsa ke jiransa,duk a tafiyar mamakin abinda tayi ne ya masa rakiya,ya dinga jujjuya halayyarta yana hadata data asma'u,bai manta ranar data ciro dubu daya guda ta bashi da niyyar biya masa bashi duk da batasan waye shi ba
"Irin wannan sharp sharp haka yau...."cewar mahmoud dake danne danne a system din dake saman cinyarsa
"ka manta ina kan hanyar aiken oga"ya fada yana murmushi sanda motocin suka soma dagawa suna barin layin zuwa saman kwalta,dariya mahmoud ya saki sosai sannan yace
"Allah ya shiryeka khalipha....Allah ya nuna min ranar da qaryarka zata qare" bai amsa mishi ba sai wayar data bashi daya zaro ya jefata inda yake ajiye ajiyensa cikin motar,yana shirin maida locker ya rufe sai ya cireta kuma daga ciki ya hadata da wasu dacument nashi da zaije gida da su.
Wayarshi ya dauka bai ko saurari zancan da mahmoud ba ya soma duba miscal din da ya tarar,sai daya gama sannan ya lalubi wata number mai dauke da sunan anty ruqayya akai,tana shiga aka daga ba tare da jinkiri ba
"Manya.....yanzu nake shirin nemanka ai" murmushi ya saki sannan yace
"To ya akayi....ya ake ciki?"
"Komai ya kammala,yaushe zaka shigo ka gani?"
"Ba lokaci anty....amma zan duba idan na samu chance zan shigo"
"To shikenan...ka cema anni inata kiran layinta bai zuwa"
"Annin?" Ya tambaya yana dan fiddo ido kaman yana gabanta
"Bari na dubata" ya sake fadi da sauri yana katse kiran,kai tsaye annin tashi ya kira,ba jimawa kuwa ta daga ,ajiyar zuciya ya saki har sai data jiyoshi
"Ya akayi khalipha?,lafiya dai ko?"
"Anty tace tayi kiranki bata sameki ba...." Murmushi ta saki mai dan sauti,tasan ya kira ne yaji da gaske ne ko kuma wani abu ne ya faru
"Sharrin qarfen nasara ne....amma wayar a kunne take"
"To alhamdulillah....sai na dawo"
"Allah ya tsare"
"Amin" ya amsa yana jin dadi har cikin ransa sannan ya aje wayar.
"Wai me aka shirya mana ne?" Mahmoud ya sake tambayarsa lokacin da yake laluben number jibril jagoran tafiyar tasu zai tura masa texs
"Name fa?"
"Biki mana....kana nufin ba zamu gwangwanje ba?" Wayar ya aje bayan ya gama tura masa inda zasu yana murmushi
"Kasan wani abu ne mahmoud?....yarinyar ba irin sauran 'yammata bace ba....tayi universty amma saika zaci 'yar secondry ce...akwai ciwo a rayuwarta da yake hanata sukuni....,saidai ina fata haka halayyarta take bawai plan bane....saboda mahaifiyata mahmoud bana son abinda zai taba mahaifiyata" kai mahmoud yake jinjinawa cikin nazari sannan yace
"Na yadda da kai khalipha....kana da zuciya da mu'amala mai kyau,in sha Allahu ubangiji bazai bari wani ya cutar da kai ba.....yanzu yaushe za'a kaini wajen amarya?"
"Zaka iya saka kayan gwanjo?"
"Kai....kai ina....bazan iya ba magana ta gaskiya,ina laifin cikin kaya na na lalubo mai sauqi sauqi" harara khalipha ya watsa masa
"Sai kasha zamanka...don dama koni bata gama sabawa da ni ba"
"Aurenku na bani mamaki.....karon farko da na taba ganin auren da akayi babu soyayya tsakanin ango da amaryar amma duka sun amince zasu zauna da juna" ya fada yana dariya dariya,murmushi ya saki khalipha idanunshi na kallon titi
"Kawai abinda na sani shine....zan aureta ne a matsayin taimako da kallonta da nake kaman qanwata dana rasa a baya,zan aureta don in canza mata family...zan aureta don in bata farincikin da iyaye ke baiwa 'ya'yansu koda ba duka ba nasan zata samu wani bangare daga wajen anni....ina mata kallon qanwa ne bawai matar aure ba...koda na aureta zan bata 'yancin rayuwa irin na budurwa....saidai zan tsare mata mutuncinta"
"Zai yuwu?" Mahmoud ya tambaya yana kallonshi
"In sha Allah" shima ya bashi amsa bayan ya waiwayo sun hada idanu,kafada.mahmoud ya daga bayan ya danyi nazari kadan sannan yace
"Well....Allah ya bada nasara" bai amsa masa ba saboda sun iso wajen da zasuje din,babban wajen siye da siyarwa ne wanda ba nau'in suturar da basa saidawa masu kyau da tsada na qasashe daban daban,a wajen dukka motocin sukai parking,suka dunguma zasu bishi ya dakatar da su sukayi gaba shi da mahmoud da jibril sai nasir.
"Khalipha....khalipha" yaji ana ambaton sunansa da sauri sanda yake gab da shiga wajen sautin kuma na sake matsowa inda yake,cak ya tsaya sannan ya waiwayo a nutse yana duban inda kiran ke fitowa,zulaihat ce ke takowa cikin sauri idanunta a kanshi tana qare masa kallo
"Ashe haka khaliphan yake?" Abinda take ayyanawa kenan a ranta,wani irin kyau da kwarjini na musamman taga yayi mata
"Lallai talauci masifa ne...ko siffarsa ka ara saiya sauya maka kamanni bare ya kamaka da gaske" ta sake fada sanda take qarasowa inda yake tsayen,tana qarewa motocinsa da suka faka a wajen kallo a dabarance,saidai ta makara,gwani ne wajen saurin karantar mutum wannan baiwa ce da Allah yayi masa,duk kuma wanda ya dan jima tare da shi yasan da hakan,da idanu ya yiwa su jibril alamar su shige,yayin da ya zuba mata narkakkun idanunshi hannayensa zube a aljihun wandonsa,idanunta ta dan kautar saboda kaifi da sukayi mata,kyau da kwarjininsa suka cikata,zuciyarta ta karye har cikin ruhinta tana jin haushin wautar data tafka,da tuni yanzu wannan nata ne,da tuni mallakinya ne inda ta iya mallakar kanta ta boye zalamarta
"Yanzu muhammad haka rayuwa take don Allah?" Ta fada bayan tayi namijin qoqarin tattara dukkan qarfin halin da take da shi,bai amsa ba yadai ci gaba da kafeta da ido,ganin baida alamun amsawa ta sake hada wasu kalaman duk da ta soma karaya saidai tana fatar haqanta ta cimma ruwa
"Ba wanda baya kuskure fa....kuma ni banyi da wata manufa ba...kawai dai kuskure aka samu" ta qarashe maganar cikin lanqwashe murya tana duban cikin idanunsa da wani salon kallo da take fatan ta tafi da hankalinsa,saidai ko gezau,mahmoud ya soma tabashi kadan yana son samun qarin haske ko kuma shi khaliphan yace wani abu,sai a sannan ya dauke idanunsa daga kanta,yana murmushi can qasan ranshi mamaki na sake rufeshi....yana kuma sake baiwa kansa yaqinin babu soyayyar gaskiya a doron duniya...idan ma akwai tayi da nisan da ba kowanne dan adam ke iya kamota ba,hannu ya dagawa mansur daya daga cikin yarashi,ya gane me yake nufi,saboda haka ya tako ya iso gabanshi da jakarshi ya budeta sannan ya miqa masa,hannu ya saka ya bude,kudi ne sabbi a miqe suka bayyana,bandir biyu ya ciro ya sannan yace masa ya rufe jakar,rufewar yayi sannan ya juya da ita ya bar wajen
"Sau daya dama take zuwar ma wani mutumin a rayuwa...kuma hakan ce ta faru da ke" hannunsa ya miqa a nutse ya soka mata kudin jikin jakar hannunta dake maqale a gwiwar hannu yana murmushi
"Ina fata wannan ya zama karo na qarshe da zaki nuna kin taba sanin khalipha a duk inda zaki ganshi....ki huta lafiya" ya fada yana juyawa mahmoud ya bishi a baya ba tare da yace komai ba.
Qwallar da suka cika idanunta sai a sannan suka silalo,kunya ta cikata na mutanen dake wucewa jifa jifa ta inda suke tsaye,gefe guda baqinciki da tarin takaici sun cikata...ba wannan take so ba.....muhammad takeso ya dawo yaci gaba da sonta kamar yadda suke a baya,ya kuma aureta burinta ya cika.
"Ban taba sonta ba.....da fari nagartar ta da na gani a fuska ita ta soma jana....ga zatona zamu dai daita daga baya na koyawa kaina yadda zan sota.....ashe ma tafiyar ba mai nisa bace" ya fada a taqaice wanda yasan ya isa amsa wa mahmoud,saqon ya isa kuwa,don ya gane daya daga cikin yammatan daya nuna yana so ne a baya,ba shakka ya tabbatar batasan waye khalipha,idan yabar abu ya barshi kenan har abada bai waiwayarsa,yana da sauqin kai tausayi da son jama'a,saidai baison yaudara da ha'inci,indai kana son tafiyarku da shi tayi tsaho tilas ka kiyaye wadan nan,sau tari idan ka karanceshi bai bai zaka daukeshi a mara kirki..kuma mutum mai tsauri da dokar tsiya,saidai yafi komai dadin zama da sauqin kai idan ka fahimceshi.
Bai wani jima a ciki ba,kaya ya zabarwa anni kamar yadda ya saba duk bayan wani dan lokaci,ya biya da kanshi kamar yadda bai yadda wani ya yiwa annin siyayya saishi ya dauko kayan da kanshi suna hira da mahmoud jifa jifa suja fito suka bar wajen.
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
22
Ta kowanne bangare daya shafi asma'u hidima ake tuquru ta bikin autar mummyn,babu wata rana da zata fito ta fadi ba'a tsara wani abu dangane da shirin bikinta ba, tamkar mummyn zata aurar da yara uku haka take ji.
Tun saura sati hudu bikin mai gyaran amare ke zuwa gidan,takanas mummy ta biyata kudin sati hudun take zuwa take gyara asma'un,cikin qanqanin lokaci kuwa ta sake wani kyau,fatarta tayi fes kyanta ya sake fitowa,duk wannan hidimar da ake dai dai da sau daya ba'a taba karar tsoma aysha a ciki ba,itama kuma duka bai cikin lissafinta,don sam tasama ranta aurenta ba irin nasu asma'u bane,irinta yaran gata su ya cancanci suyi irin wannan hidimar.
Kullum ta kwanta fatanta da burinta daya Allah yasa umminta tazo bikinta...Allah yasa a wannan karon umminta ta kulata...Allah yasa umminta zata rungumeta wannan karon a jikinta taji duminta kamar sauran yara,zuciyarta takanyi fari tayi haske a duk sanda wani sashe na zuciyarta ya bata qwarin gwiwar koya hasaso mata kanta kwance a cinyar ummin tata suna hira.
Tun biki saura sati uku aka je ganin gidan,gidan asma'u aka soma zuwa,itadai aysha ba'a gayyaceta ba saboda haka bata je ba,bata ma da sha'awar zuwa,don kullum sake jan jikinta take da gujewa duk wani abu da zai iya zama laifi,ta dai zauna gida tayi abincin baqi,sanda suka dawo nan falo suka baje suna hirar irin gidan alfarma da hamid ya ginawa asma'un,itakam tana tsakiyarsu tana hura hanci farinciki kamar ya kasheta,dama tasan duk wanda yaje yaga ginin sai ya yaba kafin ma akai gayi mata jere,don kusan lokaci lokaci yana daukarta suna zuwa ganin ginin abinda baiyi ba tayi magana a rushe a sake maida mata yadda takeso da haka aka kammala ginin,wanda kafin a gama din ba qaramin hasara aka dinga yi ba saboda an rushe gurare da dama an sauya da wasu plan din.
Kwana biyu tsakani mummy ta sameta a kitchen a sannan tana hadawa daddy abincin dare kamar yadda take lokaci lokaci akai akai musamman idan 'yar mulkin ta sakar mata mara ranar babu abinda ta sakata dafawa
"Ya kamata ki yiwa wancan yaron magana me yake da suna?....za'a je aga inda zaku zauna saboda asan yanayin kayan gadon da za'a siya,kada a siya kuma azo ayi asara,suyi yawa ko suqi shiga"
"Toh mummy" ta fada kawai,ita batasan ma ya ake cewa ba,batasan ta yadda zata gaya masa wai za'a je ganin waje ba.
Har washe gari bata yi yunqurin yin komai ba,bai kuma zoba don yakan dauki lokaci kafin yazo din,a daren kwana na uku da maganar mummy ta sake tuntubarta a sannan asma'u na wajen
"Ke idan zaki masa magana ki masa,idan baki iyawa ni ina da lambarsa sai na kirashi na shaida masa" cewar asma'u kanta tsaye,ganin bata kulata ba ta sake cewa
"Abinda dai kike gudu duk tsiya sai anje an gano"bar mata wajen tayi,don ita duka bata da lokacin ire iren wadan nan.
Tana tsaka da goge kayan sawarta data wanke dazun wayarta ta dauki tsuwwa,a sannan yana zaune cikin valcony dinsa sanye da farar t.shirt qal mai qaramin hannu da farin trouser,aiki yake cikin system dinsa idonshi ya kai kan wayarta data bashi,sai a sannan ya tuna ma da abinda ya faru,rabonshi kuma da ita tun ranar,ko ya kira yayi pretending kan vivonsa daya baro a hannunta baiyi ba,hakan yasa shi yanke shawarar kiranta,wannan karon da layinsa da yake amfani da shi ya kira ba layin daya ware ba,cikin sanyin nan nata tayi sallama,idanunsa ya dan lumshe kadan sannan ya budesu,karon faro daya soma kiranta a waya tunda suke tare,amsa sallamar tata yayi sannan shuru ya biyo baya dukkansu
"Baki gane dawa kike magana ba kenan?" Ya tambaya a sake,murmushi ta saki kadan,sai daya kuma magana ta gane waye
"Na gane mana" ta fada cikin sanyi
"To waye?" Dan shuru tayi kadan sannan tace
"Yaya ne"
"Kin yarda kin bani matsayin yayan kenan?" Murmushi kawai ta saki,don harga Allah kallon yayanta take masa,bai damu da amsarta ba ya dora da
"Kira nayi na baki haquri kan rashin kawo lefe....kayanne har yau basu gama haduwa ba...kiyi haquri inaga sai bayan an daura aure za'a kawo ko a aje miki can gidan da zaki zauna"
"Babu komai...babu wata damuwa....ni dama ban saka hada lefe ba" ta amsa masa a nutse
"Au...haka ake auren budurwa...ko da yake ni yaya nake...amma duk da haka ai miji nake a idon duniya ko?,xan qoqarta nayi miki dai dai qarfina in sha Allahu bazai gagara ba"
"Ba damuwa...yanzun ma mummy ce...." Sai kuma ta kasa qarasawa,hakanan take jin nauyin fadi,biron hannunsa ya aje ya miqe qafafunsa yana shafa kansa da hannu guda
Haka nan yake jin dadin sautin ta
"Uhmmm....mummy ce meye?,Allah yasa ba wani matsalar bace ta faru" kai ta girgiza kaman yana wajen
"A'ah....wai zasuga gida ne"
"Ya salam...toh" ya furta kaman da gaske ya dan rude din,duk sai taji babu dadi....tana kallon kaman zai taimaki rayuwarta ne shi kuma gashi ana son qureshi da sanyashi cikin takura da matsala duk don saboda ita
"Babu damuwa.....kamar ranar yaushe suka ce zasu je?"
"Ban sani ba nima....kawai dai yau kwananta uku da gaya min"
"Is ok....shikenan....zuwa anjima ko gobe zan kiraki na gaya miki ranar da zasu zo din"
"Tohm..." Ta fada cikin sanyinta da ya sakashi lumshe ido,haka kawai yakeson yanayin muryarta kamar ta yara saboda zaqinta.
Yana katse layin ya soma lalubar wata number da ya tanadeta saboda irin wannan ranar,yana kira babu jinkiri aka daga,bayan sun gaisa ya bashi umarnin sama masa gida tare da gaya masa irin yanayin gidan da yakeso,unguwannin ya lissafa masa ya zabi daya daga ciki,daga bisani sukai sallama ya aje wayar yaci gaba da aikinsa yana murmushi,shi kansa idan ya tuna yadda plan dinsa ke tafiya dariya yake baiwa kansa...bai zaci abun zaiyi tsaho har haka ba,haka kawai yaji sha'awar ci gaba da yi,har zuwa yau kuma baiga komai tattare da ayshan na raini ko qyama ba,duk da cewa bashi da yaqini ko tabbas itama a kanta,bai sani ba ko yanayin rayuwarta ne yasa ta zame masa hakan,amma koma meye saura qiris komai yazo qarshe...kuma lokaci zai nuna.
Sai daya kammala komai yazo kwanciya sannan ya tura mata texs din cewa gobe ko jibi idan sun shirya suyi masa magana yazo ya rakasu,ya kashe wayar tasa ya soma addu'ar bacci,yana cikin shafawa wayarshi wadda ita kadai ta rage bai kashe ba ta soma haske,ramla ce ke kiransa,sharewa yayi yaci gaba da abinda yake,saidai har ya gama din bata daina kiran ba,tilas ya sakashi dagawar ya kara a kunnensa.
Ajiyar zuciya ta saki kafin tace komai,don har ta fidda ran zai daga,khalipha na wahalar da rayuwarta....bata taba tsammanin zata masa irin wannan soyayyar ba da bata bari abinda ya faru ya faru a baya ba
"Ya khalipha...."
"Yaya akayi?" Ya tambayeta ba tare daya amsa ba,harga Allah taba takura masa fiye da kowa a cikinsu,baya son mace mai naci sam
"Kayi haquri don Allah,laifin wani fa baya shafar na wani a rayuwa...ina sonka ya khalipha ka sani ina tsananin sonka....please ka bani dama mu zama abu daya....mu shimfida rayuwa mai kyau da inganci"
"Kiyi haquri bacci nake ji,idan na tashi i will call you back" katse layin yayi ya kashe wayar baki daya sannan ya kwanta,saidai maimakon bacci yazo sai rayuwar da suka tabayi a gidansu ramlat din wasu shekaru can baya suka dinga dawo masa daki daki,cikin lokaci qanqanin idanunsa suka kada,yana kwance rigingine hannayensa harde a qirjinsa sai ya canza yanayin kwanciyar tasa zuwa hannun damanshi yana ta'awizi don kore shaidan daci gaba da tunzurashi da tuna masa abinda ya riga ya shige,a hankali temper din nashi ta dinga sauka,gajiyar ranar ta lullubeshi,nutsatstsen bacci ya sauka a idanunshi.
Saidai bai jima da fara baccin ba yayi mafarkin aysha na kuka....kuka take sosai ba tare da tace wani abu ba,abinda ya sake tashinsa kenan,alwala yaje ya daura ya tada sallah yana jujjuya mafarkin cikin ranshi,tabbas akwai abinda yake damunta haka zuciyarshi ta bashi,tausayinta sosai yake yana jin tamkar qanwarshi,da wannan bacci yayi awon gaba da shi.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Tunda aysha tace za'a je ganin gida asma'u ta hana kanta tsaye ta hana kanta zaune,motsi kadan sai tace zasuje suga mansion house din aysha,har sai da mummy ta gaji da ji ta kwabeta.
Ranar da za'a din itace tayi driving dinsu,su anty halima ne...anty kubra,sai anty lubabatu,sai inna laraba,anty safiyya ce kawai bata samu zuwa ba saboda al'amin data kai asibiti ranar baya jin dadi,babu wani danginta ko daya,babu wani da zata kirashi nata qwaya daya,haka tanaji tana gani asma'u ta sanyawa motar key suka fice bayan ta saki waqa cike da nishadi.
Da kashi yaso zuwa,da kansa yaso ya musu rakiyar,saidai kuma a ranar yana da baqi da zasu zauna meeting da su,tilas ya wakilta daya daga cikin manyan yaranshi ya musu jagora,qaramar camera ya bashi wadda ya jonata da system dinsa,ta yadda zai dinga ganin duk abinda yake faruwa har su dawo.
Misalin qarfe uku da mintina suka shiga unguwar,tun daga farkon layin asma'u ke tabe baki tana fadin
"Tab..." Unguwa ce data tara marasa shi qwarai,kusan babu wani gida qwaya daya da zaka nuna wanda zai alamta maka akwai maiqo ko dukiya a gidan,wasu daga cikin gidajen ma qofar buhu ce daure ko labule a jikinta.
Qofar wani gidan qasa dan rakiyar ta tsaya,hakan ya sanya asma'u itama tayi parking,sannan suja fiffito gaba dayansu suna qarewa unguwar kallo cike da qyama kafin daga bisani su maida idonsu kan gidan da dan rakiyar ke kici kicin budewa.
Ginin qasa ne wanda yasha shafen sumunti da makuba,qofar katako irin ta da ta katako sosai maqale da katangar gida wanda ke nuna ta nan zaka shiga zuwa ainihin gidan,kallo daya zaka yiwa gidan kasan cewa ba sabon gini bane,kowanne idanunsa kan gidan suka isa bakin qofar,asma'u ce ta dubi dan rakiyar
"Kaga malam basai kayi wahalar saka muqulli ka bude wannan rubabbiyar qofar ba,da qafa ma budeta zamuyi" ta qarasa fada tana daga qafarta ta daki qofar,qasa da qura suka biyo qofar suka yo kanta,hakan ya sanya tayi saurin ja da baya,ita kanta mamaki take cikin zuciyarta,sam batayi tsammanin talaucin yaron oga yakai har haka bama,wani bacin rai ya sake lullubeta da haushinsa,yasan haka yake har ya zubda mata ajinta ta jera da shi?,ta hada muhallin zama da shi,lallai iya zaman da yasa tayi da shi ba qaramar cutarta ma yayi ba,batasan mutane nawa ne da suka santa suka kuma sanshi suka gansu tare ba,ta tabbata wasu sun mata dariya.
Da qyar ya iya samu qofar ta bude ya tura kai ciki suka biyo bayanshi,tsukakke kuma dogon soro suka fara taraswa mai dauke da rufin azara irin ta da,idan kaci gaba da jumurin cusa kai zuwa cikin gidan kuwa,tsakar gida ne mai fadi da yalwa wanda aka yiwa daben qasa,duqurqushin bandaki jere kusa da kitchen,sai dakuna manya falle biyu
"Ummm....indo ba'a manta gida ba" cewar anty halima,daga kai kawai inna laraba tayi ta kalleta ta dauke kanta....wato shi dan qauye ba mutum ba?...tana da yaqinin harga Allah daddy baisan duka wainar da ake toyawa ba,duk da cewa bata gidan amma tana katarin riskar wasu abubuwan,ta yaya aysha yarinyar da tayi jami'a take zaune cikin birni shekara da shekaru zatayi aure cikin wannan gidan ta kuma zauna a ciki?,ta ina zata iya taimakawa rayuwarta ta fidda ta?
"Hhhhhh,ai tazo inda ya dace da ita" cewar asma'u tana yarfa hannu tare da takawa cikin gidan tana qare masa kallo.
Ba abinda dan rakiyar yace saboda ba'a umarceshi da cewa komai ba,kuma ya tabbatar duk abinda ke wakana boss din sa yana ji kuma yana gani,bai furta komai din ba har suka gama isgilancinsu suka gama suka tako zasu fita ya rufa musu baya,yana maida muqullin zai rufe asma'u ta dubeshi
"Kana wahalar da kanka ne kawai....banda abinka wai meye abun qwaqumawa wannan kangon kwado kayita wani rufeshi,da ka barshi ma a bude don baida maraba da kango" kallo daya yayi mata ya maida kansa yana ci gaba da ruge gidan,ranshi fal da mamakin me ya hada boss da wannan gidan me zaiyi da shi?,sannan kuma meye gaminsa da wadan nan matan?,ko da ya gama rufe gidan tuni sun hau kwalta sunyi gaba abinsu.
Cikin motar ma zancan gidan sukeyi,kowa na tofa albarkacin bakinsa,anty lubabatu ce tace
"Anya ko asma'u wannan plan din baiyi worst ba....talaucin mutumin nan fa kamar yayi yawa" dan tsaki ta ja saboda sakuwarta ce
"Kinjiki kema da wani irin zance....to daga ina ita din ta fito?....ina cewa irin wannan gidan anan taci ta sha,banda ma tsaurin ido irin na talaka daga an riqeka a waje sai kace lallai sai kayi rayuwa irin tasu?,kuma wa ya hanata musanta zancan tun yana farkonshi...wai ita saliha a dole baiwar Allah.....munafuka inaga ma kyanshi ta gani ta kasa cewa bata sonshi....so ni banga wani worst ba da yayi,ungulu ce kawai zata koma gidanta na tsamiya" tabe baki anty halima tayi,sai a sannan tayi magana
"Lubabatu a yadda yarinyar nan take gani tana da kyau idan ta auri wani kan mage ne zai waye,uban kowa ma neman taka shi zatayi,irinsun nan ki gansu haka haka ba qananun 'yan iska bane idan suka samu waje...Allah ne kadai yasan manufar jaki da bai bashi qaho ba....daddy nema haka kawai ba dangin dangiro kaje ka jajubo yarinyar mutane....ta gama abinda ya kawotan ma maimakon ka maidata a'ah ka daukama ranka saika aurar da ita....bayan ko uwarta bata ta tata saikai" ta qarashe maganar da tsaki
"Shi yasa nakesonki anty halima....kinfi kowa fahimta"
"Mu ai da yake jakai ne ko?" Lubabatu ta fada tana hararta,dariya tayi tana cewa
"Bance ba".
Nannuyar ajiyar zuciya ya saki ya soma latsa system din bayan ya gama gani da jin duk abinda ya gudana tun daga qofar gidan shigarsu ciki zuwa barinsu unguwar,tunani ne cikin qwaqwalwarsa kala daban daban,mamakin baqar zuciya da mugunta irin ta wasu mutanen,buri da fatan jefaka a rana koda baka takawa kowa komai ba,aysha dai aysha ba'a son ci gabanta a rayuwa kwata kwata?,shikam wanne irin gata zaiyi mata daya dace da ita wanda zai bada mamaki ya girgiza zukatan maqiya
[1/14, 1:37 PM] Om Muhammadiyya: Mamakin abinda aysha tayi wanda ya tsarewa asma'u a rai yake,me tayi mata mai zafi da taketa yunqurin daqile duk wani ci gabanta,wacce irin macace asma'un?,bama ita kadai ba,hatta da 'yan uwanta ya fuskanci haka suke,ta ina suka gado wannan halayya?,wato da da gaske shi din haka yake zasu fi kowa farincikin dawwamarta cikin wahala kenan?.
Kusan wunin ranar baki daya abinda ke masa kai kawo kenan a zuciya,har sanda yake zaune gaban anni yake cin abinci abunda ke tsinkulinsa kenan
"Muhammadu lafiya dai?gajiya ko kuma aikin?" Dan murmushi yayi sannan a nutse ya bata labarin dukkan abinda ya faru,kai take jinjinawa cike da mamaki da.nazari
"Muhammadu yarinyar nan tana buqatar wani ginshiqi da zai tallafeta....inama ace kana mata soyayya mai qarfi wadda zata zame mata jigo?....saidai duk da haka ina jin qaunar zama da ita...sai nake jin kamar a maida daurin auren gobe ka dauketa daga cikinsu,me yasa mutane zuciyoyinmu suke ciki da kishi qyashi da hassada?...Allah ka shiryamu ka gyara mana zukatanmu"ta furta cikin sanyin jiki
"amin ya Allah....amin"
_kuyi haquri da wannan don Allah_
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER (08030811300)_*
[ 🧣🧣 *
*DB*
23
Tunda suka dawo babu zancan da suke sai na gidan ayshan mommy na ji bata dai tanka komai nata ciki ba,a sannan anty safiyya ta dawo daga kai al'amin asibiti,ganin ta gama da wuri sai ta zarto gida,nan ta taras da su ta kuma ji duk abinda suke fadi din,babu wanda ta cewa uffan sai tayi ma kamar batasan me yake faruwa ba,har suka gama sha'aninsu kowacce ta wuce gidanta suka bar safiyyan a gidan
"Ke yaushe zaki wuce...kowa ya tafi ya barki?"
"Mommy dukansu fa sun riga ni zuwa,kuma ma sai nayi sallar isha'i abban al'amin zaizo mu wuce tare"
"Ai shikenan..." Ta fada tana ci gaba da aikin gabanta.
A nan tayi sallar isha'i taci abinci,bata jima da kammalawa ba daddy ya shigo gidan,mintina goma ta bayar ta kwantar da al'amin sannan ta wuce zuwa falon daddyn.
Yana zaune saman kujera sanye da jallabiya,da alama daga wanka ya fito yayi shirin cin abinci,da murmushi a fuskarshi suke gaisawa,saboda duk cikin yaransa bayan asma'u itace ta biyu a wadanda yake so,itama asma'un don itace auta shi yasa ta rigashi zuwa,tana da halaye irin nashi,sauqin kai da fahimta gami da rashin daukar komai da zafi
"Amma ace tun safe kima gidan nan me mike baki koma gidanki ba safiya?" Murmushi tayi tana dubansa sannan tace
"Magana nakeso nayi da kai ne daddy" ta qarashe maganar yana dan satar kallon mommy,bisa dukkan alamu batason yin maganar tana wajen kenan,ya fahimceta,hakan ya sanya ya dubi mummy dake kici kicin zuba masa abincin darenshi wanda aysha ce ta girka yace
"Jeki hadamin coffe sa'adatu"
"Toh" tace tana aje serving spoon din hannunta ba tare data fahimci komai ba ta miqe ta fice.
Sai data gama fita din daddy ya kalli safiyya
"Ina jinki safiya ya akayi?"
"Daddy.....kasan wanda aysha ta kawo zata aura kuwa baida wani qarfi?...daddy kaman ma dai bazai iya riqeta nake gani"
"Indai zai iya bata ci da sha da suttura da muhallin zama ya kiyaye haqqoqinta da mutuncinta da lafiyarta safiya shi ake bida a aure,amma duk da haka akwai wani abu da larabawa ke cewa khafa'a wato dacewa da juna ta wajen aure,ko musulunci ya yadda da khafaa'ah....nasan halayen yaro kuma na binciki lamarinsa naga yana da ikon da zai iya riqe mace....yana da aiki duk da qarqashin wani yake,na gamsu da bincike na shi yasa na bashi ita" lallai daddy qila akwai abinda bai fahimta ba ko ya shige masa duhu,hakan ya sanya ta sake hada nutsuwarta tace
"Daddy....yaufa aka je ganin gidan da aysha zata zauna daddy...gidan qasa fa?" Shuru yayi yana nazarin maganarta,sai yaji shima bai gamsu data zauna a gidan ba,don idan yayi hakan tamkar baiyi adalci ba
"Gidan qasa safiya?..." Ya sake tambayarta don tabbatarwa
"Eh daddy" shuru ya sake shi da ita ba wanda ya sake cewa wani abu,ajiyar zuciya ya sauke sannan yace
"Da kanta ta kawo yaron tana sonshi bata yadda za'ayi na hanata wanda take so,idan nayi mata haka kaman banyi mata adalci bane,amma shikenan babu komai...ki tashi kije Allah yayi miki albarka....zanga yaron zanyi wani abu akai in sha Allahu"
"Na gode daddy....Allah ya qara girma" ta fada tana miqewa,dai dai sanda mommy ta dawo dauke da coffen,hakan ya sanya daddy ya sake basar da zancan
"Ina abokina ne...ko kin soma barinshi gida shima?" Dariya tayi mummy ta amsa masa
"Yau abokinka ba lafiya,haqori ya sakoshi gaba...yana daki yana bacci"
"Ashsha...Allah ya sawwaqe,a gaida babanshi"
"Zaiji in sha Allahu....mummy ni zan wuce,sai da safe"
"Ki gaida gida da sauran yaran" da haka ta fito daga falon daddyn tana jin dadi har cikin ranta,tana jin kamar ta sauke wani nauyi,sam tana jin bai dace subar aysha ta rayu cikin gidan qasa ba ba adalci bane sam,batasan me yasa duk yadda yarinyar ke da hankali da nutsuwa ba basa gani
"Allah ya kyauta" ta fada tana amsa wayar abban al'amin daya kirata ta fito su tafi.
Yayi mamakin ganin kiran daddy da kanshi kan cewa yana son ganinshi,a ladabce ya amsa mishi,saidai yace ya bashi uzuri zuwa gobe,ya fadi hakanne saboda a ranar yaje abuja za' dauki hoton yatsunshi zai sauya passport dinsa.
******************
Qarfe biyar na yammaci yana zaune falon daddyn cikin shigar yadi wanda aka fi kira da mamar ruwan bula mai haske,cikin mutunta juna suka gaisa shi da daddyn,ya dan bawa khaliphan space ya kurbi lemo duk da bamai yawa ya sha ba sannan yace
"Malam muhammadu....ya gida ya hidimomi" yana dan shafar kansa yace
"Alhmdlh daddy komai lafiya" zamanshi ya gyara bayan yayi gyaran murya
"Nasan zaka yi mamakin kiran ka da nayi ko"
"Hakane" khalipha ya amsa
"Ba wani abu bane babba yasa na kira ka ba....ammm kasan cewa tun ba yau ba na daukeka kaman matsayin d'a a gareni...to haka yake har yanzu,musamman da zaka auri diya ta...inaso nayi maka kyauta ne kamar yadda mahaifi zai yiwa dansa" ya saurara da maganar yana ciro wasu kudi daga gefan inda yake zaune,rafa ce ta 'yan dubu dubu guda goma ya aje a gaban khaliphan
"Ga wannan.....ka karba kayi amfani da su....duk wani abu da kasan baka samu ka qarasa ba kayi da sh,ka gaya muhallinku da dan abinda zakuci" can qasan xuciyarsa qina da mutuncin daddyn yake sake gani,tabbas ya kai maqura wajen nuna talaucinsa,hakan kuma bai sanya daddyn kai tsaye yace bazai bashi aure ba,saidai kamar yana son taimaka masa ne a fakaice ba tare daya furta ba,yasan mai yiwuwa labarin gidan aka zo aka bashi.....ko kuma ita ayshan talaucin taga ya mata yawa ta soma kokwanto?,kaman daddy yasan tunanin da yake yace da shi
"Tunanin me kakeyi?....kar kayi shakka ko kokwanton karba...babu wanda yasan na baka wannan kudin ko munyi maganar da kai,daga ni saikai sai Allahn daya haliccemu,karka damu ni na baka ba tambaya kayi ba,kuma har abada qimarka na nan a ido na" boyayyar ajiyat zuciya ya saki sannan yace
"Na gode na gode daddy qwarai da karamcinka na batun yau ba,Allah ya saka maka da mafificin alkhairinsa...amma daddy... Am sorry to say bazan iya karbar wadan nan kudaden ba,zanyi dukkan abinda ya dace iyakacin iyawata da yardar Allah daga iya abinda Allah ya horemin....don Allah kar kace saina karba daddy..." Kai yake gyadawa cike da mamaki da alfahari da wadatar zuci irin ta khaliphan wadda ya santa ba tun yau ba,lallai akwai wadatar zuci mai yawa tattare da shi,hakanan daddyn ya sanya hannu ya janye kudin yana cewa
"Shikenan...Allah ya taimaka yayi jagora....yayi albarka a zamanku"
"Amin ya Allah...na gode daddy" ya fada yana miqewa sukai sallama,yayin da daddy ya bishi da kallo,har ga Allah yaso ace ya karbi kudin ko muhallin da ayshan zata zauna ya gyara musu,saboda yayi yaqinin mutumin da bai karbi kudi ba ko gida ya bashi bazai karba ba,yaso ace ya karbi kudin ma sai yayi dabarar da zai bashi gida kudin yayi wata sabgar da ita,ajiyar zuciya yayi cikin zuciyarsa yana jin bari qurar bikin auren ta lafa dole ya inganta rayuwarsu bazai qyalesu a haka ba.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Saura sati daya bikin a yadda aka tsara aliya tazo ta tasata a gaba zasu je gidansu za'a soma mata gyaran jiki
"Don Allah sashin ki bar wannan zancan,meye wani gyaran jiki don Allah?....ni kunya ma kike bani wallahi"
"Kya gama jin kunyarki ki miqe mu tafi...."
"Don Allah sashen ki barni...."
"Idan kika sake wata maganar Allah ni dake ne...ki shirya kawai" hakanan ta miqe ta shiga bayi wanka ba don tana so ba.
Tana shiryawa aliya na mata mitar tana maida kanta koma baya,har sai da ayshan ta juyo yana dan bata fuska a shagwabe kaman qaramar yarinya,wanda ta riga data saba kusan dabi'arta haka lokaci zuwa lokaci
"To kuma don Allah sashin ba ya riga ya wuce ba gashi ina shiryawa...."
"Oho dai...ina gaya miki ne donma gobe kar kice zakimin musu....don sati za'ayi ana yi"
"Haba kaman wata kaya"
"Whatever...." Aliya ta fada tana watsa hannu.
Tsaf ta shirya ta saka hijabinta sannan suka fito,ta shiga dakin mummy ta sanar mata
"Saikin dawo" kawai ta fadi ba tare data damu da yaya abun zai gudana ko waye zai biya ba.
Suna harabar gidan zasu fice khalipha ya fito daga wajen daddy,zuba ido aliya tayi taga reaction na kowannensu,wucewa ayshan tayi kamar zatayi da sauri aliya ta damqi hannunta ta tsaidata,dai dai sanda khaliphan ya qaraso wajen,duk da yana dan gaggawa ya wuce saboda ya baro baqi a tahir amma saiya rage saurinsa sanda ya iso wajensu
"Ango kasha qamshi..." Aliya ta fada cikin salom tsokana,ya fahimci tana da sauqin kai da barkwanci,hakan ya sanya yayi murmushi
"Qawar amarya...ina zaku haka?"
"Gyaran jiki....da qyar na jajibo wannan amaryar taka" ta fada tana yima aysha da kanta ke qasa dariya
"Wai haka...?" Ya tambaya yana dan kallonta a fakaice
"Ina yini" ta gaisheshi a maimakon bashi amsa,ya fuskanci tana da hanyoyi da dama da take guntule zance idan bata son tsawaitarsa,shima din yana da abinyi hakan ya sanya ya kawo qarshen tsaiwar tasu
"Gashi kuma yayan naki gurgu ne babu abun hawa da.na kaiku"
"Babu komai ango....zamu qarasa a napep babu nisa daga nan" hannunsa ya sanya cikin aljihun wandonshi ya soma zaro kudi,cikin hanzari ya maidasu bayan ya duba yawansu,Allah yasa basu gani ba
Daya aljihun ya sake saka hannunsa,'yan dari biyar biyar ne hade da 'yan dari bibbiyu,baisan adadinsu ba,yana son ya qirga nawa ne amma ya kasa kasancewar bai saba hakan ba,miqa musu yayi
"Ga wannan kyayi wani abu da shi.....saidai fa haquri angon bashi da komai talaka ne" dariya aliya tayi ta sanya hannu zata amsa,ta daya bangaren aysha ta riqe hannunta,saidai bata kula da ta amsa din tana cewa
"Ba komai...Allah ya amfana wannan din"
"Amin...." Ya fada yana yabawa nagartar qawancen aliyan da aysha.
Shi ya soma yin gaba,aysha ta dubi aliya
"Me yasa zaki karba aliya....yanzun haka kudinsa fa kenan?" Murmushi ya saki sanda ya jiyo abinda ayshan ke fada,wani lokaci halayyarta na masa kamanceceniya da halayyar hajar....wata halitta mafi soyuwa a garesu da bazasu taba mantawa da ita ba,kusan yanayinsu da halayyarsu na gogayya da juna,da wannan tunani ya qarasa ficewa daga gidan ba tare daya ji qarshen muhawarar tasu ba.
"To meye don na karba din.....ya kamata ko yaya fa yasan zaiyi aure ne,za'a bashi mace kuma budurwa,bawai ya aureki kaman an bashi sadaka ba" kai aysha ta kada ta soma takawa sai aliyan tabi bayanta
"Har kullum aliya bana son ki dinga sani ina jin ni dinma kamar kowa nake bayan ba hakan yake ba"
"Ni kuma na gaji da maimaita miki wannan karatun na kema kamar kowa kike,da dama ma kin fisu a wajen Allah"kanta itama take girgizawa,tausayin aysha na rinjayar zuciyarta,ko sai yaushe zata yarda itama 'yace kamar kowa?,sai yaushe zata sake tayi rayuwa yadda kowacce mace take?,oho...Allah masani...wannan itace amsar da aliya ta baiwa kanta,haka suka dinga tafiya tamkar kurame.
Ganin ayshan nason motso damuwarta wadda zata iya shafar wuninsu na yau,sai aliya ta qara sauri ta jera da ita tana sako mata zancan makaranta da yadda result dinsu ya kaya,hakan sai ya sanyayar da zuciyar aysha,suka ci gaba da tattaunawa,har ta zabi su taka a qafa tunda wajen ba wani nisa bane can da shi,aliya bata musa ba ta biye mata suka dinga takawa a qasa suna hirarsu
"waccan 'yar qarunar naga kaman bata wani damu da carry overn data samu ba ta aure take....naji labarin ta samu c.o ko?duk da ba'a gaya min ba don kada nayi sharhi...to sai nayi,zancan duniya kuma bai buya" Aliya ta fada tana qunshe dariyarta,don ita hakan yayi mata dadi,ko banza asma'u zatasan da cewa duk inda kakai ga zama wani a duniya dole kayi lacking wani abu a rayuwarka ko kai waye.
Harararta da aysha tayi yasa ta dauke kanta gefe guda tana dariyarta hankali kwance
"Kai.." Aliya ta fada lokaci daya dariyarta tana daukewa,saita waiwayo ta dubi aysha
"Aysha.....kaman angonki fa na gani hakimce cikin motocin can" ta fada tana nuna mata motoci ukun da suka wuce a jere iri daya,bin motocin tayi da kallo kafin ta maida idonta kan aliya tana murmushi
"Dama kina gulmar wata ba dole idonki ya dinga miki gano miki abinda ba haka ba....mutumin da muka rabu da shi yanzu yanzu a gida"
"Allah seriouse aysha shi na gani...don har mun hada idanu sai naga ya dage glass din motar" wannan karon sai da aysha tayi 'yar qaramar dariya
"Idan shi kika gani yaushe ya zama haka?...yaushe ya sayi dukkan wadan nan motocin yanzu yanzu kenan daga fitowarsa daga gidanmu ko?,may be shi da oganshi ne,don kusan ko yaushe yana gaya min suna tare" Ja aliya tayi ta tsaya,yanayinta ya koma da gaske take irin yanayin da tasan ayshan zata fahimceta
"Wallahi Allah da gaske nake miki aysha khalipha na gani a cikin motocin can,kuma alamu duka sun nuna cewa ba wani yake ja ba shi ake ja motarshi ce,kayan jikinsa fa ba irin wanda muka ganshi da su bane yanzu" shiru dukka sukayi aliya na kallon aysha cikin tantama,yayin da aysha ta soma shiga tunani gami da shakka,ajiyar zuciya aliya ta saki sannan tace
"Allah aysha tun asali sam khalipha baiyimin kama da wanda ke cikin babu ko yake samu a qarqashin wani ba....kin taba qare masa kallo da kyau kuwa tun daga kanshi har zuwa tafin qafa?" Dariya ce ta kubcewa aysha duk da yanayin fargaba data soma shiga
"Aliya ta yaya zan iya kallon wani namiji haka tun daga kansa zuwa qafa koda kuwa mijina ne?" Idanu aliya ta zaro
"Mijinki?...kina nufin ba zaki iya masa wannan kallon ba....lallai aysha akwai aiki a gabanki" qaramin murmushi ta saka tana kada kai
"Muje don Allah....shi din talaka ne kamata hakan shi ya qara min qwarin gwiwar amincewa zama da shi....ba da sunan miji ba...da sunan yaya dan uwa...'yan uwan da na rasa nake fata wannan karon nayi gam da katar da su kuma managarta,bana jin akwai wani ha'inci ko qarya tsakanina da shi"
"Idan kuma abinda idanuna suka gani gaske ne kinga shikenan...shikenan kaya sun tsinke a gindin kaba" aliya ta fada tana dariya
"U r mad aliya...ba don wannan zan zauna da shi ba...na amince ne saboda naga irina ne shi,kaman yanayin rayuwarmu daya ne...idan kuma har da gasken ne....bazan iya shiga cikinsu ba na zauna,ban masa qarya ba ban boye masa komai nawa ba,ban boye masa wacece ni" dukan kafadarta aliya tayi tace
"Shutup my friend....bana son wannan maganar taki ma...muje don Allah" daga haka suka ci gaba da takawa ba tare da sun sake bi ta kan maganar ba.
Numfashi ya sauke gami da lumshe bayan sun wucewa ganinsu aliya,yana sane ya sha mur ya dauke kai gamida dagr glass din sama don tayi tsammanin cewa bashi bane idanunsa ya bude sannan yace
"Jibril"
"Na'am sir"
"Daga yau bana son a sake saukemin glass din mota qasa idan bani na bada umarni ba"
"Yes sir,in sha Allahu" daga haka motar ta dauki shiru,addu'a yake cikin ranshi Allah yasa basu ganeshi ba,don ba yanzu ya shirya bayyanar komai ba.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Biki saura kwanaki uku gidan mommy ya soma cika da jama'a 'yan uwa da abokan arziqi,kowa zancan bikin asma'u kawai yake,da yawansu ma basusan cewa itama aysha nata auren za'ayi ba,idan sun tambaya ma takan ce a can qauyen iyayenta za'ayi,eh haka ne ayshan take cewa,don itama ta matsu ta wuce qauyen nasu,ko banza naka naka ne.
Cikin kwanakin zuwa gyaran jikin sai ya soma yi mata wahala saboda hidimar baqin dake gidan,awanninta kaso mafi yawa a kitchen take yinsu,duk da itama hakan ya mata dadi don bata ga meye na wani yin gyaran jiki ba,hakan kamar wani rawar kaine a wajenta ko wuce gona da iri,don haka sai take noqewa take fakewa da cewa gidan cike yake da baqi,hakan ya fusata aliya kan zasu maidata 'yar aikinsu,ta dage kan sai ta tattara kayanta ta dawo gidansu,da qyar ta shawo kanta ta nuna mata ranat juma'a ma zasu wuce takai baki daya tunda asabar ne daurin auren.
Tun ranar laraba aka fara gudanar da bikin,gidan kuwa ya cika ya tumbatsa da 'yan uwa da hamshaqan qawayen asma'u,tun ranar ta soma shiga ta kece raini,bridal shower suka fara yi sannan sauran events din suka biyo baya,ayshan kam mafi yawan lokaci idan bata tana kitchen ko dakinta,don data je gyaran jikin da aliya ta tilastata take dawowa,yawanci da aliyan suke zuwa,saidai ita bata shigowa gidan tunda aka fata bikin a qofar gida suke rabowa ta koma ta wuce nasu gidan.
*_WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER (08030811300)_*
*KO KUMA*
(07067124863)
*DAURIN BOYE*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
24
Ranar laraba da safen mommy ta kirata dakinta,sanda ta shiga akwai qannen mummyn a ciki da wasu daga cikin 'yan uwanta zazzaune,wasu a gefan gado wasu saman tiles,binta sukayi da kallo sannan suka soma qus qus a tsakaninsu,hakanan jikinta ya bata da ita suke duk da bata iya jin me suke fada amma jikinta ya bata,tana iya jin sautin dariya dariya qasa qasa daga bakunan wasu daga cikin 'yammatan dake cikin dakin,saidai batasan meye abin dariyar ba,jikinta dai atamfa ce riga da zani sai hijabi data dora iya gwiwa kanta babu dankwali,sai tudun gashinta dake matse a cikin ribbom.
A ladabce ta tsugunna a bayan mummy wadda ke gaban wardrobe tana fidda kayan da zata sanya anjima,ba tare data waiwayo ba tace
"Gobe wasu daga 'yan uwanki zasu zo daga qauye,za'a je ayi miki jere....ya kamata ki sanar da shi zuwan nasu,ya bayar da muqullin gidan ko ya rakasu,don ba lallai su su sake gane hanyar gida ba bare gidan kanshi"
"Kawai mummy ya rakamun" inji nusaiba qawar asma'u tayi caraf ta fada,cikin muryarta kana iya jiyo sautin dariyar dakeson fitowa,nusaiban 'yace ga yayar mummyn,qawancensu yayi daidai saboda hali da yazo daya,tana son harkar girma itama,tana son fantamawa,tana son kuma mu'amala da masu hannu da shuni
"Ko yazo ko ya samo wanda xai rakaku...don ko su halima sunce ma ba zasu iya gane hanyar gidan ba" dariya nusaiba ta sake da alama tasan komai ko an bata labari,sai ta kuma waske tana wa farida cousin dinta dake zaune kusa da ita magana
"Toh mummy" ta fada tana miqewa jiki a salube,tana qirga iya kwanakin daya rage zata sake shiga wata sabuwar rayuwar,ko ya zata kaya da ita ita kuma?.
Zata fice sukayi clashing da naana,qawa ce ga asma'u,amma ta zama kamar 'yar gida saboda yadda ake buga qawance,duban juna sukayi naana ta saki dariya,abinda tsahon sanin da aysha tayi mata bata taba yi mata ba,face kallon banza da kallon raini dake shiga tsakaninsu,saboda asma'u ta riga ta gama dorasu kan turba
"Amarya amarya" naanan ta fada,kallo daya aysha tayi mata ta dauke kanta ta wuce,karon farko da hawaye taji sun cika idanunta,karon farko data ji damuwa ta sosa zuciyarta,gefan gadonta ta zauna,tana qoqarin tsaida hawayen,saidai bata da wannan ikon,saboda zuciyarta na buqatar rage nauyin da ta jima tana dauka,cikin muryar kuka ita kadai cikin daki take cewa
"Ya Allah...kaine mafi jin qan masu jin qai...kaine mafi tausayin masu tausayi...kaine mai tallafar raunana...ya Allah...ka fini sanin wace ce ni...ka fini sanin dalilinka na sanya rayuwata a wannan bigiren,ka fini sani gobe da jibina har zuwa qarshe na,Allah kai kace mu roqeka zaka amsa mana,ya Allah....kayi ruqo da hannayena...ka yiwa rayuwa ta jagoranci...Allah karka barni dai dai da qiftawar ido ya Allah...." Ta qarashe addu'ar tana fashewa da kuka wanda ya tilastata cusa kanta cikin fulalluka don gudun fitowar sautin kukan nata.
Ta jima tana kokawa ita kadai....ta dade tana fitar da ruwan hawaye kafin ta lallashi zuciyarta.
Qarfe shida na yammaci sanda 'yammatan amarya ke shirye shiryen zuwa bridal shower aka ce mata ta fito ga 'yan uwanta nan daga takai,gabanta na dukan uku uku ta zira hijabinta ta tako zuwa falon gidan inda aka aje su don bana ce aka saukesu ba,duba da yadda yawanci mutanenmu na birni ke raina mutanen karkakara,bayan mutane ne da Allah ya musu baiwa iri daban daban masu tarin yawa fiye da mu din,fargabarta na su waye suka zo?,yaya zasu zauna da su a muhalli guda ba tare da bacin rai ko samun wata tangarda ba?.
Murmushi mai tafe da hawaye ne kan fuskarta ganin mutanen da suka zo matan,mero ce da gwaggo asabe,sai inna kulu da kuma karima matar kawunta
"Sannunku da zuwa gwaggo kunsha hanya" ta fada itama tana zama qasan carfet cikinsu kamar yadda ta samesu zaune a nan,ko banza taji dadin gani masoyan nan nata biyu meronta da kuma gwaggo asabe,akace naka naka ne hakan take,sai ta dinga jin dadi da nutsuwa har cikin ranta,bakinta yaqi rufuwa gata ga meronta,falon jama'ar dake kai kawo sunyi yawa,hakan ya sanya ta kwashesu zuwa cikin dakinta,ba wanda ya damu da su don ba wanda ya qara bi ta kansu ma,hira suka balle sosai da ita,kusan duk rabi labarin na garinsu ne,kamar aliya tasan da zuwansu saiga wayarta,ta gaya mata zuwan nasu take tace gata nan zuwa,babu jimawa sai gata kuwa da kulolin abinci,duk da gidan basu da damuwar abinci amma bata son aysha ta damun kanta wajen sai tayi girki,don dama ba'a son ranta ana mata gyaran jiki take shiga kitchen ba cewar aliya.
Sanda ta qaraso gidan an ragu sosai duk an dode zuwa wajen da za'a gudanar da bridal shower din,hakan yasa ta dan jima suna hira da su,da yake itama sam bata da qyamatar mutane,hakan tana da fira fiye da aysha da kuna saurin sabo.
Sunzo mata da gudunmawar da aka tara mata,wanda duka duka abinda suka kawo din bai kai ya kawo ba,ba kuma don basu da shi bane,a'ah...,qarfin abinma dai gwaggo asabe ce da mero,har cikin zuciyarta sai taji dadin gudunmawar duk da qanqantarta,wannan ce rana ta farko da zata bigi qirji tace ga wani abu da suka taba yi mata,dalili kenan data ji dadin abun ta kuma bashi girma.
Dukkan abinda yake gudana kusan yana sane da shi ana gaya masa,kama daga events na bikin da yadda komai na gidan ke wakana,hakan ya sanya qarfe tara na dare yayi kiranta,a sannan tana gyarawa su gwaggo wajen kwanciya suna dan taba hira ita da gwaggon da mero,don karime babu wani sabo tsakaninsu,har gwara inna kulu a kanta,don bata taba fito da muguntarta tsirara ba a kanta.
Bata samu ta dauki wayar ba har sai data gama gyara musu wajen sannan ta duba mai kiran,bin kiran tayi don tana da credit wanda daddy ne yakan sanya mata lokaci lokaci,a cewarsa bata iya tambayarsa komai koda tana da buqatar hakan,ita kuma bata saba bane,tun tasowarta bata saba ayi mata abu na,shi yasa ma bata tambaya
"Anata hidimar biki ko ke babu ke...kiyi haquri" abinda yace da ita kenan bayan sun gama gaisawa
"Yayan naki talaka ne...." Ya sake fada a karo na biyu
"Uhmmm" kawai tace tana gyata tsaiwarta,don ita gaba daya tama mance da ana wani abu a biki banda asma'u na nata taron,dan bata sha'awa ma koda zatayi ma wa zata gayyata wa take da shi?,ita duka wannan ba damuwarta bane
"Kinje wajen ne?" Ya tambayeta karo na farko,don yasan ba lallai tayi magana illa kudin wayar da zaita tafiya a haka
"A'ah" ta amsa masa a taqaice
"Saboda me?"
"Iyayena sunzo daga takai...mummy tace na shaida maka gobe zasu zo jere"
"Gashi kuma inaa..." Katsewa yayi da hazari jin ya kusa baranbarama
"Ohk....shikenan...babu damuwa,Allah ya kaimu,zan aiko wani dan uwa na sai ya rakasu"
"Tohm" ta fada kana tayi shuru tana saurare ba tare data ce komai ba,shima jin shirun daga nashi bangaren yasan hirar tasu ta qare saboda haka ya katse kiran,aje wayar tayi suka ci gaba da hirarsu dasu gwaggo.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Tun tara na safe motar kayan jeran aysha take tsaye qofar gidan wanda kayan ta siyesu ne a zooroad maimakon dubai kamar yadda daddy ya tsara a siya musu kowacce set biyu daga waccar qasa,yayin da wadanda zasu jeran suke shiryawa,wanda yawancinsu ba don Allah zasu je ba,zasu je ne kawai saboda gulma,duk da cewa yau ne dinner din asma'un.
Goma da minti biyar kira ya shiga wayarta da baquwar lamba,cikin mamaki ta daga wayar ta kara a kunneta
"Ranki ya dade nine wanda yallabai ya aiko nayi wa 'yan jere rakiya" cikin mamakin yanda yayi maganar cike da girmamawa tace
"Ohk...to zakayi haquri kadan jirasu na mintina,bari na sanar musu"
"To babu damuwa..." Katse kiran tayi sannan ta dubi inna wadda shigowarta dakin kenan tana taya su mero hada kayan da za'a tafi jeran da su
"Inna...." Ta fada a sanyaye
"Na'am indo"
"Wai wanda zai rakasun ya iso yana bakin gate"
"Toh...toh bari a sanar da su" ta fada tana sakin jakar baccon da take zugewa kana ta fice.
Shiru ayshan tayi kanta a qasa,duk da tana sauraren hirarsu gwaggo asabe jefi jefi,saidai faduwar gaba da damuwa sun mata yawa,fargabar auren take qwarai,gani take kamar zata koma 'yar gidan jiya,yayin da gefe guda na zuciyarta ke cike da damuwa,ina mahaifiyarta ta shiga?,shin ko labarin aurenta ya isa kunnenta?,tasan aure zatayi kuwa?,tana son tambayar gwaggo asabe tun jiya tana jin nauyi da fargaba,Allah kadai shi yasan yadda take ji a zuciyarta
"Ya dai indon baffale?,ko fargabar auren ce irin ta amare?" Mairo wadda ta dafa kafadarta ta fada qasa qasa yadda su kadai zasu ji cikin murmushi,kai ta daga cikin qarfin hali ta maida mata murmushin
"Karki damu....zaki dace in sha Allahu wannan karon" murmushin kawai ta sake mata,kafin tace wani abu muryar inna laraba ta tsaidasu
"Zasu qarasa shiryawa ne saimu wuce".
Har suka gama shuryawar su wadan can 'yan rakiyar basu gama ba,har suka zauna suka huta bayan sun gama nasu aikin suka taba hira shiru kake ji,a qalla saida sukayi jiran awanni biyu sannan suka ce sun gama din su fito.
Da mamaki inna laraba take duban 'yan zuwa jeran,ko a mafarki bata taba tunanin zasu taka gidan aysha ba bate suyi mata jeran aure,dadewarta a gidan ya sanya zata iya fadin halin kowanne daya daga cikin dangin mummy,kai kawai ta gyada cikin ranta tana tabbatarwa kanta cewa akwai lauje cikin nadi,akwai dalilin wannan gangankon nasu,to koda ma saboda Allah zasun 'yammata irin wadan nan masu ji da kai da yauqi ina zasu tsaya yin wani jere,haka dai ta barwa ranta suka shiga motocin da zasu kaisu wajen wanda yawancinsu motocin 'yammatan ne suke ta shewa,duk su qi shiga motar da khalipha ya aiko da sunan wadda zata kaisu sun raina ajinta,sai inna laraba da su gwaggo asabe ne suka shiga.
Yana gaba saman babur dinshi lifan motocin dake dauke da kaya da su inna na biye da shi har suka isa unguwar
"Ya haka?,ya zai kawo mu wata unguwar daban kuma?" Cewar anty halima cikin fushi,da yake gwanar fushi ce ita din,abu kadan yake tunzurata
"Nima dai kamar ba unguwar da asma'u tace mana bace" inji farida tana wulwulga idanu,saboda ita kanta unguwar na daya daga cikin burinkanta a wajen zama.
Shiru ne yaci gaba da wanzuwa har zuwa sanda ya tsaida babur dinshi qofar wani katafaren gida,wanda idan ka tsaya ka qarewa gine ginen kallo kaf layin ba gidan da ya kai girma da tsaruwarshi,suma bakin gidan suka tsaida motocinsu
"Ku zauna...basai kun fito ba" ya fada yana zaro wayarshi daga aljihu,daddadannata yayi sannan ya kara a kunnenshi,waya yayi ta sakan biyar,ba'a cika sakanni goma ba katafariyar qofar gidan ta wangale,mai gadi cikin unifoarm na musamman ya bayyana,daga bayanshi kana iya hanho.
hango makekiyar harabar gidan,wadda ta qawatu da grass carfet da fitilu gami da furanni na alfarma da fitilu dake kunne,da hannu ya musu alamun su shigo,hakan nan suka dinga cusa motocinsu ciki wanda suka tashi laqwam a wajen,ba wanda ya iya magana cikinsu har suka gama dai daita motocin nasu kusa da wadansu kyawawan sabbi fil din motoci guda biyu
"Wai ina ne nan ne?,ina ya kawomu?,karfa yace yana nufin ya kawomu gidan uban gidan sa ne mu soma gaisheshi,an gaya masa mu mabarata ne?....ko qarqashin wani muke ci?" Cewar anty halima sanda suke fiffitowa daga motocin kowa yana qarewa harabar gidan kallo,daga yadda ta tsaru tun daga waje ya isa ya gayawa mutum cewa akwai kallo a ciki ba qarami ba
"Kaga malam mufa ba wasa ne ya kawomu ba muna da abinyi....ba gaida uban gidansa muka zo yi ba wannan matsalarsu,ka kaimu gidan qasa muje mu juye mata kayanta mu wuce"
"Kwantar da hankalinki hajiya....nan ne gidan amaryar" tofa!....sai aka soma kallon kallo tsakaninsu,yayin da murmushin farinciki ya subuce a fuskar mero inna laraba dama gwaggo asabe,duk da mamaki daya cika zuciyarsu fal suma
"Kaman yaya?...mu ba wannan fa gidan ya soma kaimu ba,bashi muka sani ba,sannan yanzu ace nan ne?,hasalima fa wancan gidan gidan qasa ne"
"Gidan qasa?" Mutumin ya fada cike da mamaki yana musu wani kallo
"Boss ne zai zauna cikin gidan qasa?....ai ko masinjansa ke ko mai masa wankin mota yafi qarfin zama cikin gidan qasa ko talauci irin haka,ina tsammanin dai a mafarki hakan ta faru kikai zaton a gaske ne"
"Uwar mafarki nayi....nace maka uwar mafarki nayi ba mafarki ba" ta fada cikin hasalar abu biyu,na farko yana son nuna mata raini raini gaban qannenta,na biyu ta yadda khalipha ya raina musu wayo ya rufesu,tashin hankali ta dinga ji yana rufto mata,ta tabbatar ko asma'u gidanta bai qarasa wannan ba,duk kyan gidanta tasan da zata ga wannan din shi zata fi so,ta yaya hakan ta kasance a kan aysha?
"Allah ya baki haquri hajiya....abun duk baikai ya haka ba...ni dan aike ne....kuma boss yace na girmamaku saboda akwai iyayenta a ciki....ga wadan can" ya fada yana nuna saitin sababbin motocin dake qasan rumfa
"Na amarya ne....ga muqullan idan kuna buqata a baku kukai mata" ya fadi yana ciro muqullan daga aljihunsa,dukkansu mutuwar tsaye sukai ba wanda ta iya magana a cikinsu,baki dayansu ba wadda batasan nawa ne kudin mota duk guda daya ba a ciki
"A'ah ka maida masa ya aje mata....duk randa aka kawo masa ita ya bata da hannunsa" cewar inna laraba da saurinta saboda tsoron karsu amshi key din wani abu yaje ya dawo,sam bata damu da kallon da suka soma jeho mata ba
"To shikenan" ya furta yana maida muqullan aljihun nasa
"Mu qarasa ciki ko?" Ya fada yana yin gaba gami da ciro wasu muqullan daban,inna laraba,mero,gwaggo asabe sune kan gaba,ba abinda bakunansu ke furtawa sai
"Ma sha Allah...alhamdulillah...kai Allah abun godiya" musamman inna laraba da tasan zaman aysha a cikin gidan,muryarta tafi ta kowa dagawa,kuma da biyu take da gayya take,ba qaramin farinciki bane a zuciyarta,ta tabbatar da cewa Allah baya zaluntar bawa saidai bawa ya zalunci kansa,hakanan ubangiji baya mantuwa,karamcinsa baiwarsa da kuma kyautarsa yawa gareta.
Qofar falon kawai tun daga nan suka sallama,inda suka gama miqa wuya sanda suka shiga falon zuwa dakunan baccin dake gidan,gini ne mai kyau mai daukar hankali wanda aka yishi cikin hikima da fasaha,tun daga falon gidan zuwa dakuna zuwa kitchen babu abinda bai saka ba na alatun rayuwa harda ma qaari
"Kai Alhamdulillah...Aysha Allah ya miki baiwa....Allah ya zaba ya baki....Allah ya tabbatar dake cikin wannan gida...yasa tsohuwar gida ce" abinda inna laraba ke fada kenan cikin farinciki suna kewaye gidan,mero ba abinda take cewa ita da gwaggo asabe sai
"Amin...amin" cikin farinciki.
Ta gefan su anty halima kuwa bakuna zuwa jikkuna sun mutu murus,kowacce cikin 'yammatan zuciyarta ta tafi,xasu iya cewa tsahon zamansu da burikansu basu taba shiga gida irin wannan ba....duk cikinsu babu wadda bata ji inama inama ace itace zata shigo gidan ba
"Kutumar uba....mutumin nan fa DON ne wallahi da alama"cewar mufida qanwar mijin anty halima sanda take qarewa gidan kallo karo na barkatai,batasan sau nawa ta kalli gidan ba,babu lungu ko saqo na gidan da bata kashe selfie ba....bama ita kadai ba har sauran yammatan
"amma asma cin kai ce....tace mana fuqara'u wal maskin ne shi?....inaga dai bata gano dai dai ba wallahi" inji nusaiba
"Ni gani nake anya wannan baifi hamid kudi ba?,ko a ina ta somashi?" Fatima qanwar mummy ta fada
"Da Allah ku yiwa mutane shiru kun cika mana kunne da surutan banza da wofi......." Anty halima ta fada cikin zafi da qunar rai,lallai ba shakka khaliphan DAURIN BOYE NE,yazo musu ne a duqunqune kenan?,ita a karan kanta tasan cewa babu gami tsakanin khalipha da hamid,hamid eh lallai yana da kudi....saidai duka basu kai yadda suka zata ba,sun zaci yafi haka,fariya da dagawa da son a sani ya qarawa arziqin nasa ado ake masa kallon yafi haka,yayin da khalipha ya iya takunsa,yake dora komai a muhallinsa da mizanin hankali da nutsuwa.
Hannun nusaiba ya kai kan wani daki wanda shi kadai ne basu buda ba bayan na mai gidan,dakin na manne da bedroom din ayshan,binta sukayi duka a baya "gwara mu kashe qwarqwatar idanunmu...kai....wlh ji nake kamar a mafarki....indo?,indon da tazo daga qauye wai itace da wannan gidan?,anya ba qarya mutumin nan yake mana ba raina mana wayo kawai yake don ya burge ya kawomu gidan jama'a?" Inji anty kubra
"Nima tunanin da nake kenan" anty halima ta fada cikin sanyin jiki gami da tausayawa qanwarta,tasan yanzun zata tashi hankalinta matuqar taji cewa gidan ayshan ya kerewa nata.
Daki ne guda wanda aka shiryawa sif ta jikin bango kowanne gefe da tarin hangers na maqale sutturu,sutturu ne sabbi a dinke iya ganinka babu kalar wanda babu
"Innalillahi....oh my god" nusaiba ta fada tana rufe bakinta da hannunta tana fiddo idanunta,abun yayi masifar burgeta da tafiya da ita,ba ita kadai ba kusan duk wadanda suka shigo dakin,saidai hassada data cika zuciyar wasu daga ciki hakan ua gaza tarihi
"Na shiga uku.....indo ina zata kai wadan nan sutturu?....wannan kuwa zata gama saka su harta mutu?" Cewar mero tana dafe qirji,dariya inna laraba ta saki
"Suttura ai itace mutum kuma bata yawa....kuma bai kai mata lefe ba bawan Allah ashe haka ya tsara zaiyi mata" ta fadi cikin murmushi,kayan suka dinga bi daya bayan daya suna tabawa dubawa da fadin kudin wadanda suka san kudinsa,wanda basu sani ba kuwa saidai hasashe kawai da suke,tun suna dubawa suka gaji suka koma kan jakankuna takalma da mayafai,qarshe haqura sukai da qwaqwqwafinsu suka fito daga wajen bayan sun gama daukar hotuna,a falo suka tadda anty halima zaune wanda tunda ta saka kai dakin sai ta fito da sigar amsa waya bata kuma komawa ba,gefanta kubra ce zaune itama cikin sanyin jiki,bala'i ta hausu da shi kan uban meye suka a wajen,kamar basu taba ganin kaya ba?.
"Halima ina zaton saimu koma haka harda motar kaya ko?,tunda naga gidan babu abinda yake buqata ko cokali kuwa"cewar inna laraba,wani banzan kallo ta juyo ta watsawa matar data darawa ma mahaifiyarta a shekaru
"Ke kinga inna laraba,na gama fuskantar take takenki fa...tunda muka shigo gidan nan kike rawar qafa kina neman gindin zama....shine zaki gayawa mutane magana a fakaice,butulu shekararki nawa kina cin arziqinmu daga ke har indon?,ina cewa badon muba da tuni ana qauye ana fama da kirci da faso?,to mu duk girman arziqi bai rudarmu don mun saba gani ba yau farau ba" maganar ta yiwa inna laraba ciwo qwarai,a ganinta ko babu komai haliman ta girmamata ko don furfurarta,cikin murmushi da danne bacin rai tace mata
"Ki adana fushinki don bani nayi ba Allah ne ya nuna ikonsa a kai....duk wani abu da kuka hana aysha sai gashi yau Allah ya bata ninkinsa....duk abinda kuke zaton bata cancanceshi ba sai gashi yau Allah ya bata sama da shi,kun hanata mota qarama qwaya daya sai gashi Allah ya bata manya biyu,kun bata daki mafi qanqanta a gidan sai gashi Allah ya bata masarauta guda....kun siya mata kayan daki a qasar nan maimakon qasar waje kuma saiti daya sai gashi Allah ya bata wasu fiye da daya fin biyu ma,ya qawata mata gidan aurenta da jin qansa da rahamarsa....kinga kenan ba yina bane yin Allah ne...idan kunga dama ku aje abinda ke ranku ku rungumi yarinyar da bata taba taka muku ba bare ta zubar muku,ba sawa ba futarwa sai ku da kuke amfana ma da ita,baky dubi maraicinta ba,baku dubi rauninta ba kuke gallaza mata da gasata a ruwan sanyi ba tare da duk wani mara dogon nazari da tsinkaye ya fuskanci hakan ba,kun manta cewa Allah ke daukaka bawa a duk sanda yaso,kun manta cewa talaka da mai kudi duka Allah ne ya haliccesu badon yafison wani ba sai wanda yafi biyayya a gareshi,kun manta cewa dan kauye mutum ne mai daraja shima kamar kowa....qauye muhalli ne mai daraja tun a zamanin annabawa?,tunda ko annabinmu an bada shi raino a can,ya rayu da su bai kuma taba qyamatarsu ba,halima wannan ishara ce a gareku,ruwanku ku gayara ruwanku ku dora daga inda kuka tsaya,aysha dai tayi gaba amma zaku iya biyota a baya"miqewa anty halima tayi ta soma zuba ruwan bala'i,duk wani bacin rai dake ranta take furtashi a sannan,su anty kubra ke riqeta amma bata ji bata gani,murmushi inna laraba tayi
"Iyaka a dakatar dani bakin aiki ko?....ki sama ranki to daga nan zan wuce cikin nawa ahalin,karki manta yarona da qafarsa yazo zai tafi da ni mahaifiyarku ta dakatar da shi,ta roqeshi ya barni saboda sabo,ina fata baki manta ba?,abu daya zan gaya miki kafin na wuce shine...kibi ko ince kubi duniya a sannu,a yanzu ishara daya tazo muku...idan baku sauya ba sauran isharorin na nan tafe,bikin indo kuwa har qauyen takai in sha Allahu,na barku lafiya" ta fada tana juyawa nan ta fice ta barsu,anty halima naci gaba da kumfar baki.
*mrs muhammad ce*👑*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN BAKI BIYA BA DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING_*
*_LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_SAFIYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*_,IDAN KINA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER (08030811300)_*
*KO KUMA*
(07067124863)
*DB*
25
Bin kowannensu da kallo kawai asma'u take sanda suke zayyanawa mummy yadda suka samu gidan ayshan,jin abun take kamar almara,ji take kaman mafarki,tsaye kawai take ta kasa tabuka komai kamar wadda aka zarewa duk wata laka ta jikinta
"Qarya ne....qarya kuke waini zaku zolaya,ta ina yaron oga zai samu irin wannan gidan?,ni zaku tsokana bayan nafi kowa sanin wayeshi,mtseww" Ta fada tana banka musu harara,nusaiba ce tayi caraf ta ciro wayarta ta soma gwadawa asma'un selfie din da suka sha cikin gidan
"Kanbu" asma'u ta lailayo ashar din kai tsaye cike da baqinciki takaici cakude da hassada,zama tayi da sauri gefan gado kusa da nusaiba
"Who is khalipha?" Ta fada tana tambayar kanta,tabbas babu shakka akwai wani daurin boye dangane da al'amarin,tabbas wannan khaliphan ba shine wanda ta sani ba,akwai wani khaliphan boye a bayan khaliphan data sani,ta yaya zata yadda,ta yaya zata amince aysha ta auri wannan khaliphan?bayan duka yaqin da tayi a baya kan hana faruwar hakan,abinda ya dinga kai komo kenan a zuciyarta,cikin fushi da hanzari ba tare data cewa kowa komai ba ta fice daga dakin,tana jin kamar iska ke tafe da ita ba qafafunta ba.
"Aisha....kinga baiwar da Allah yayi miki kuwa?,kinga gidanki aisha?,dama mai kudi zaki aura?" Mero ke fadin haka cikin tsantsar farinciki tana riqe da hannun aishan,sosai takejin dadi kamar ita zata zauna cikin gidan.
Sam bata kawo komai ba tayi murmushi
"Mai rufin asiri dai mero,shima talaka ne kamarmu" idanu mero ta zaro tana dubanta
"Talaka?,alqur'an kada bakinki ya sake fadin cewa shima kamarmu yake,kinsan yadda sama ta yiwa qasa nisa?,to kwatankwacin haka tazarar mu da shi take,kinga gidanki kuwa indo?....bari kigaa a wayata duk da bai dauku da kyau ba" mero ta fada tana ciro 'yar qaramar torching dinta da mijinta ta saya mata wancan wata bayan ya saida amfanin gonarsa ya samu riba mai yawa.
Dariya take kawai a sanda ta karbi wayar don tana zaton zuzuta abu ne kawai irin na meron,a ido gidan ya qayatar da ita sanda take kallon hotunan,saidai sam bata kawo kanta a ciki ba
"A ina kika samo wadan nan hotunan mero?" Aysha ta tambayeta
"Hotunan gidanki ne da muka je yanzu indo...indo ki godewa Allah,Allah ya miki ni'ima da baiwa wallahi,ba shakka Allah ya fanshe miki wahalarki ta shekara da shekaru,yanzu haka kaf kayan jeranki mun dawo dasu saboda babu wajen da zamu zuba su,hasalima wadanda muka tarar jere a gidan sai namu ya tashi kaman a bola muka tsintosu" dariya sosai aysha ta saki,labarin sai ya nishadantar da ita,don har ga Allah bata yarda da gaske mero take ba,ta daukeshi kawai a shaci fadi ko nishadi takeson sanyata saboda taga alamun damuwa tattare da ita tun dazun kafin su fita,ita kuma ba wannan ne a ranta ba,ummanta take son gani,labarin ummanta takeson ji,kulawa take buqata ta gani daga wajen umminta komai qanqantarta.
Mummy ce ta turo qofar dakin dai dai sanda aysha ke wannan dariyar,dubanta mummy tayi sai ranta ya quntata,tana tunanin tasan komai da hadin bakinta yaron ya lullubesu,ta ayyana a ranta yanzu haka tana dariyar farinciki ne da samun nasara,idanun aysha ya sauka kan mummy sai ta miqawa mero wayarta tana miqewa cikin nutsuwa tace
"Me kike da buqata mummy,da kinyi magana sai nazo basai kinzo da kanki ba" kai ta girgiza ranta na baci,a zatonta tana bacin rai ne saboda aysha sun rufeta,saidai abinda bata sani ba shine tana bacin rai ne saboda ayshan ta samu daukaka da muhallin da autarta bata samu ba,hassada kecin ranta ba tare data farga ba
"Wannan ai yafi qarfin kizo saidai ni nazo da kaina....godiya na taso takanas nayi miki,wato duk zaman da mukeyi dake da yadda muka riqeki ashe ke ba haka bane cikin ranki,kallon maqiyiyarki kikemin,kallon abokiyar adawarki abokiyar gabarki wadda bata son cin gabanki kike min,har ku hada baki da yaron nan ku rufe mana komai sai munje ganin jeranki sannan mu gani,kinsan mai arziqi ne baki gaya mana ba,amma ya zowa a sma'u a wanda baida komai saboda wani baqin nufi dake ranshi,ko ba komai da munsan waye ya bayyana kanshi xamuyi duk shirin daya dace yadda ba za'a ji kunya ba,to na gode da sakayyar da kika yimin Allah ya saka da alkhairi" ta juya tana shirin fita,iya qololuwar tashin hankali aysha ta shige shi,dama ita gwanar hawaye nan da nan ruwan hawaye ya soma layi a fuskarta,bata gane kan me mummyn ke magana ba,me take nufi ne ?batasan sanda ta isa gaban mummy ba ta tareta cikin kuka tana fadin
"Wallahi mummy ba mai kudi bane...talaka ne shima kamata,idan da mai kudi ne anty asma'u ita zata soma sanin hakan,tunda ita ta hadani da shi,ta hanyarta komai ya tabbata har kawo yau...ki tambayeta kiji" ta qarasa fada muryarta na sarqewa
"Ke dalla matsa....dake da asma'un dukanku lusarai ne...kada ma asma'un taji labari.....kunsan waye muhammad abdulhakim mai goro?,kunsan wanne irin arziqi ke gareshi,dukanku baku sani ba,cikin 'yan sa'o'in aka gayan wayeshi,aisha kin nunan iyakata kuma ina godiya" ta qarasa fada tana kewayeta gami da ficewa daga dakin.
Kuka aysha ta saki har sai da gwaggo asabe sake zaune tana kallon ikon Allah ita da mero suka taso suka riqeta gami da zaunar da ita,tsoro ne fal cikin zuciyarta,ta yaya zata shiga familynsa bayan ya soma dayi mata qarya?,a hakan zai roqeta?,a hakan zai cika alqawarin daya dauka,tana tsoro,tana tsoron faruwar wani abu,don me zai yaudareta,akanme zai ninketa yazo mata da siffar daba tashi bace,yanzu gashi ya hadata da mummyn,ya hadata da mutanen da suka zauna da ita da dadi babu dadi,ba kamar danginta da suka kasa zama da ita ba saboda wani banzan dalilinsu maras tushe wanda baici ace ya shafi rayuwarta ba.
"Ohni sadiya..wai wannan wane irin lamari ne haka yake faruwa?,indo wadanne irin mutanene haka kike zaune da su?,tunda muka zo daga wannan sai wancan?" Cewar gwaggo cikin bacin rai da tashin hankali.
Miqewa tayi tsaye ta dubi su mero
"Ina zuwa" ta fada kawai kana ta fice,da hijabin data idar da sallar azahar a jikinta don haka bata da buqatar sanya wani abun.
Parlourn daddy ta nufa kai tsaye,tayi qoqarin daidaita nutsuwarta sannan tayi sallama ta kutsa kai,su biyu ne zaune a falon shi da anty safiyya,da alama wata magana suka gama tattaunawa ko suke kan tattaunawar,dukkansu shuru sukayi ganin shigowarta falon,kai tsaye ta isa gaban daddy ta duqa tana hawaye
"Daddy don Allah ka kirashi ki bashi haquri ka gaya masa ka fasa bashi aurena,daddy bazan aureshi ba,bazan iya zama cikinsu ba" anty safiyya zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu sannan ya maida hankalinsa wajen aishan
"Saboda me?" Ya tambayeta
"Daddy....yazo min da siffar daba tasa ba,ya yaudareni daddy,wannan ha'inci ne daddy,a haka zanje na zauna da su?" Kasa daurewa safiyya tayi sai data furta
"Aisha,anso kashe rayuwarki ne Allah ya raya ta,an hadaki dashi saboda ana tsammanin bashi da komai Allah sai ya kaiki hannun mai komai din,wannan kadai bai isa ki godewa Allah ba?,wannan abun da kike fada tamkar butulcewa Allah fa kikeso kiyi"da hanzari ta daga kai tana kallon anty safiyya,akwai wani abu,akwai wani data sani kenan game da yadda auren ya qullu?
"Aisha" daddy ya kira sunanta bayan ya dakatar da safiyya
"Me yasa baki gayamin tun farko yadda abun yake ba kika ja bakinki kika yi shuru,kina zaton da an tafi a haka na hadaki aure da shi Allah bazai kamamu ba mu duka?"fada sosai daddy ya dinga yi irin wanda bai taba yi ba,alama ranshi ya baci sosai,kuka ta dinga yi tana bashi haquri,yace sam nauyin bakinta baiyi masa ba,haquri ta bashi da alqawarin ba zata sake ba,daga bisani ya kwantar mata da hankali da bata labarin farkon sanin daya soma yiwa khalipha a rayuwarsa.
"na sanshi can shekarun baya masu yawa ta sanadin faduwar jakar kudadena,kudade ne masu yawa wanda banda kudaden akwai muhimman takarduna harda na kamfani na,sosai na shiga tashin hankali a sannan,saboda matuqar kudaden suka bace a sannan tsaf zan iya shiga talauci bana wasa ba,cikin ikon Allah kwanaki uku da faruwar haka aka kira wayar kamfani na akace ni ake nema kan kudina dana yar,nayi murna sosai na buqaci inda zanje mu hadu da wanda ya tsinci kudin,ba bata lokaci ya bani adress din gidansu,yace nayi haquri,yana da wani uzuri ne da baya barinsa ya fita daga gida da da kansa zai kawomin,nikam a sannan kota kan hakan baibi ba,saboda ko a qafa yace min na tafi wata qasar na amso zuwa zanyi
Sanda na isa gidansu nayi matuqar mamaki,gashi dai gida har gida irin ginin masu kudi da wadata na sannan amma kana masa kallon farko zakasan babu da talauci ta tasamma yi masa raga raga,mamaki na bai sake qaruwa ba sai dana shiga na tadda matashin dan shekara ashirin na jiyyar mahaifiyarsa magashiyyan rai a hannun Allah da qannenshi maza guda biyu,kana kallonsu kasan kuka suka gamayi dukansu,sanda na amshi kudin na tambayeshi nawa yakeso ga mamakina sai yace min babu komai,alfarma daya yake da buqata na biya kudin aikin mahaifiyarsa ta rabu da zafi da radadin ciwon da take fama da shi,na zaci zai buqaci sama da haka,amma sai yace min buqatarsa kenan,matsanancin ciwon suger take fama da shi wanda shi har takai ga ya taba mata qoda za'a mata aiki.
Muna tsaka da wannan maganar saiga 'yan sanda katsama kanmu,miqewa naga khaliohan yayi yayin da suka yo kanshi kamar kura ta samu nama syka cukuikuyeshi,yayin da yajeta rantsuwa yana fadin bashi bane,matashi dake bayansu yana cewa
"Karku saurara masa,qarya yake ku dakeshi"ni na miqe na musu magana,sannan na tambayi ba'asi,nan dan samdan yace ana tuhumarshi ne da yiwa yarinyar wan babanshi fyade,kuka yake sosai a sannan yana rantsewa da duk abinda yasan me girma ne kan bashi bane,yanayin nagartar yaron ya sakamin tantama kan zancan,naja daya daga cikin 'yan sandan waje nace ya gayamin gaskiyar magana,na masa alqawarin kudade mai tsoka,nan yace ba shakka bashi bane,amma alhj idris da yaronshi ibrahim su suka biyasu kan kada au saurara idan sunzo su kamashi,daga nan su kaishi kotu ma birsin sukeso yayi,don ya matsa kan maganar gadonsu,a take na gaya masa sunana sai yayi sororo,na kira sauran 'yan sandan na sallamesu duka da wani abu,nan ibrahim yahau min hauka,nace koya wuce kona makashi kotu kan ya yiwa khalipha qazafi,haka ya wuce don kada allura ta tono garma,kuka sosai ya dinga yi mahaifiyarsa dake kwance tana tayashi,haka qannensa maza guda biyu,a sannan naso jin labarin rayuwarsu amma sai naga bashi yafi muhimmanci ba,lafiyar mahaifiyarsa itace gaba,muka je asibitin na biya duk wani abun da za'a buqata a aikin,hatta da abincin da ita da su zasu ci,cikin nasara akayi aikin aka gama lpy ta kuma samu sauqi,ina da niyya da shirin taimakon rayuwarsu tafiyar gaggawa ta sameni russia,wanda ban dawo ba sai bayan watanni shida,dana dawo su na soma nema sai na tadda sun saida gidan sun tashi,kuma ba'asan ina suka koma ba,dole na haqura da neman nasu naci gaba da saka yarona addu'a,don gaskiya nasp na riqeshi d'ana,saboda gaskiya amana da hankali da nutsuwar da naga yana da ita,uwa uba yadda naga yanason mahaifiyarshi yana tattalinta,nasan lallai sai yaro na gari ne kawai zai hada wannan nagartar"
Dukansu shiru sukayi suna jinjina labarin,yayin da zuciyar aysha ta soma kuma rabuwa gida biyu,
"Kije kici gaba da addu'a ina da tabbas kan khalipha aysha...Allah ya baku xaman lafiya" anty safiyya ce ta amsa ayshan ta miqe cikin sanyin jiki tabar falon.
Sosai ranta ya dinga baci,hassada nacin ranta ba tare data sani ba,ta yaya ma aysha zata samu irin wannan gidan?,wayarta ta ciro ta soma neman tsohuwar lambarsa da suke waya,so take taji ta bakinsa,so take taji dalilin raina mata wayon da yayi tunda fari,saidai amsa daya ake bata is switched off,gani take ma kamar akwai wata a qasa,kaman ayshan ita ta shirya komai,wani irin gumi take ita kadai qwaqwalwarta na kaikawo,hakan ya sanya ta tashi don fitowa daga dakin sukayi kacibus da mummy a bakin qofa,duban asma'un tayi
"Kina jin sunan muhammad abdulhakim mai goro?" Kai asma'un ta kada,sosai ta sha jin sunan ko a bakin hamid ma
"Shine khalipha yaron da zai auri aysha" cikin qanqan da idanu take duban mummy,kamar tana zaton mummyn zata sauya zancan data gaya mata
"Mummy da gaske?"
"Ina wasa dake?" Ta fada itama a dan zafafe,sai kawai asma'un ta kewaye mummy ta fice da hanzari zuwa dakin aysha.
A sanyaye ta koma dakinta,su mero suka zuba mata ido saidai ba wanda ya iya tambayarta komai,bankado qofar dakin da akayi shi yaja hankalinsu su duka suka daga kai suna kallon bakin qofar,gabanta ta qaraso yau qarara muraran take jin haushinta da kishi da ita ba tare kuma da tana da wani sahihin dalili kan hakan ba,wayarta ta cilla mata saman cinyarta
"Ke saka mana number khalipha wadda yake using da ita" a natse ta daga kai ta kalleta,tunda suke da ita yaune karo na farko data kirashi da khalipha sak ba yaron oga ba
"Waye khalipha?"harara ta watsa mata sannan tace
"yaron oga nake nufi"
"Ke da kika soma hadani da shi inaga ke zaki fi kowa samun lambarsa" ta furta anutse sannan ta miqe ta nufi toilet,wanda sanadiyyar tashin nata wayar ta subuto ta fadi qasa,hakan ba qaramin bata ran asma'u yayi ba
Cikin zafin nama da salo na huce haushi da takaici asma'u ta damqo hijabin aysha tana cewa
"Dawo dan uwarki...." Wani wawiyar fincika aysha ta yiwa hijabin nata cikin bacin rai da quna,duk yadda take da mahaifanta bata sake a zagesu,duk yadda suke duk kashinsu dai iyayenta ne,hakanan ba'a sauyawa tuwo suna,wani kallo ta watsawa asma'u,wanda hakan ya dan firgitata,saboda yadda lumsassun idanun ayshan masu kama dana wanda kejin bacci suka bude sosai a yau
"Karki kuskura ki sake zagemin mahaifiya....wannan shine kuskure na farko da zakiyi dana sanin aikatashi a kaina" tuni mamaki ya kashe asma'u,yau itace aysha ke maidawa magana haka gatsal kai tsaye,ayshan dako duka zata kai.mata ba zata daga kai ta dubeta ba,lallai abinda take gudu yana gaf da afkuwa,wato daga jin labarin wanda zata aura har ta soma komawa haka kenan?,lallai dole ta gaggauta daukan mataki tun wankin hula baikaita dare ba
"Ni aisha ni kikewa haka?" Ta fada cikin tsananin mamaki tana nuna kanta,bata tanka mata ba ta juya ta shige bandakin,itama asma'un sake juyawa tayi ta fice fuuu daga dakin zuwa falon daddy.
"Daddy ka dakatar da shi,kar kayi kuskuren aurawa aisha shi,mayaudari ne kuma maqaryaci ne shi,labarin haka yanzu ya zomin,daddy ka dakatar da aurensu" tsai dadddyn yayi yana kallonta ya kafeta da ido harta gama,bai taba tsammanin haka halayyar asma'un take ba sai yau,yaushe ta debo dukkan wadan nan dabi'un oho bai sani ba
"Jeki kiramin mahaifiyarki ku taho tare" ranta ne yayi sanyi,tana zaton zata cimma gaci taje ta taho da mummy,saidai kalaman daya soma furtawa da bude mata dukkan plan din data qulla kan aishan har Allah ya qaddara zata auri khalipha ya girgizata,ga akayi daddy yasan da dukka wadan nan abubuwan?,ya mata tas har hakan ya sanyata kuka mai yawa,tare da qara mata tsanar aisha,sosai yayi mata kaca kaca bai saurara ba,mummy tayi tsumu tana jinsu,ta kasa sanya baki saboda ita batasan ya zasu qarke ba ita da shi.
Haquri ta dinga bashi ta dinga bashi,tare da yi masa alqawarin ba zata sake maimaita kuskure makamancin hakan ba,ya umarceta taje ta nemi yafiyar aysha duk da Allah yayi mata sakayya,bayan ya sallameta mummy ya dirarwa,wanda hakan ba qaramin bacin rai ya haifar ba,ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba,ta nuna masa ita batasan meke faruwa ba,ya qalubalanceta ya kuma bata laifinta,haquri itama ta bayar cikin kissa tare da kwantar da kai,saboda bata son wani abu mara dadi ya bullo da zai bata bikinsu,tilas daga qarshe yayi haquri tare dayi mata gargadi mai qarfin gaske ta kuma amsa dukka laifin.
Shigarta toilet din alwala ta daura ko zata ji sauqin bacin ran dake yankar zuciyarta,saidai har ta fito hawaye bai yanke saman fuskarta ba,gefan gadonta ta zauna kai tsaye ta dauki wayarta,wannan karon babu fargaba ta kira mahaifiyarta,gab da zata tsinke aka daga
"Waye?" Aka tambayeta kamar yadda ta saba,alamu dake nuna har yau bata da matsayin da zati serving na numberta
"Nice ummi...Aisha ce 'yarki"
"Sau nawa zan fada miki ki daina kirana kafin ki gane abinda nake nufi?" Ta fada cikin salon tambaya,kafin aysha tayi yunqurin cewa komai ta ja tsaki gami da yanke wayar,kuka aysha ta saki mai sauti idanunta akan gwaggo asabe,a hankali ta tashi zuwa inda take ta zauna gabanta sosai tana dubanta
"Batasan zanyi aure ba...ba zata zo bikina bare na samu kowacce albarka da diya ke samu a wajen mahaifiyarta duk lokacin data tashi tafiya gidan miji,duk wata matsalata ni kadai na santa,ban taba dan dana dadin uwa ba,gwaggo...ke kadaice fata na na qarshe,ke kadai nake saka ran zan samu amsata daga bakinki...gwaggo...don girma da daraja ta annabin rahama ki gaya min...me na yiwa ummi na?,me na aikata mata haka daya saka ta tsaneni?,meye laifina meye kuma aibuna?" Ta qarashe maganar tana fashewa da kuka mai fidda sauti gami da kifa kanta saman cinyarta,hannu gwaggo asabe ta dora saman kan ayshan,tana jin dukkaninsu basu kyauta,dukansu masu laifi ne,suma kuma suna da tasu gudunmawar da suka taka wajen baqincikin da ayshan ke hadiya,a yau tana jin zata gayawa aysha dalilin wannan wakaci kaa tashin dake faruwa tsakaninta da mahaifiyarta,dukkaninsu a lokacin duk da sunji zafin abun basu zaci zaiyi tsanani har haka ba,ita kanta gwaggo asaben da take 'yar uwa ga ummin nata abun na bata haushi da takaici gami da mamaki,tamkar sake rabasu akayi bayan wancan dalilin daya zama silar wanzuwar komai
"Na roqeki gwaggo ki fiddani daga duhu izuwa haske,ki warwaremin wannan DAURIN BOYEN,na jima cikin zullumi tashin hankali tsoro da firgici saboda irin qiyayya qarara da nake ganowa daga idanun mahaifiyata....me yayi zafi gwaggo?" Ta qare da sigar tambayar kamar zata shide numfashinta zai tsaya
"Yau xan baki labari indo...yau in sha Allah ba zaki sake kwana da tunanin kin aikatawa mahaifiyarki wani laifi ba" ta fada tana sauke ajiyar zuciya,mero da ita tayi saura a dakin saboda karime tana waje bata shigo ba,saboda kusan itama tabi sahun 'yan takaici da jimami,dubanta gwaggo asabe tayi
"Zauna mero.....baki zama wata bare ba ko baquwar al'amarin"komawa tayi ta zauna tana tattara hankalinta wajen gwaggo asabe kamar yadda aysha tayi,shuru ne ya ratsa dakin kafin daga bisani gwaggo tace.
"kamar yadda kika sani cewa dangin mahaifinki fulani ne gaba da baya,yayin da mu dangin mahaifiyarki muka kasance manoma ne,har kakanki kafin Allah yayi masa rasuwa ya kasance sarkin noma na qauyenmu,fadan manoma da makiyaya fada ne daya jima yana wanzuwa tsakanin wadan nan mutane guda biyu,fada ne daya janyo asarar rayuka da dama,ya janyo asarar dukiyoyi rashin kwanciyar hankali da lumana,ya kuma janyo gurbacewar mu'amala tsakanin manoma da makiyaya,to wannan abu ya shafi qauyenmu,duk da cewa mu ba'ayi kashe kashe ba,amma rashin jituwa ya shiga tsakani da sabani mai girma,kowa ya tsayawa bangarensa,kowa yana goyan bayan dan uwansa da yake jin labari a can wani yanki an kashe ko anci zarafinsa,hakan ya kawo silar daya zama manoma da makiyaya basa ga maciji a tsakaninsu,a irin wannan ne Allah ya hada soyayya tsakanin mahaifinki baffale da mahaifiyarki,suna tsananin son junansu qwarai da gaske,sam basuyi duba da abinda kaje ya kawo ba,basuyi la'akari da abinda ke faruwa tsakanin jinsin biyu ba,soyayyarsu kawai suka saka a gaba,sanda soyayyarsu ta bayyana,kowa cikin gidansu sunja daga kan daya bazai auri daya ba,duk wata hanya ta rabasu anbi amma sunqi su rabu,junansu kawai suke so,bana mantawa mahaifiyarki ansha jibgarta a gabana amma bata sauya zani ba,a haka suka ci gaba da gudanar da soyayyarsu ba tare da sun yarda da qudurin raba su ba.
Sanda suka tada maganar aure gagarumar rigima ta barke cikin qauyenmu,abu har ya kai gaban alqali,inda yaja kunnen iyayen da su qyale yaransu suyu aure tunda suna son junansu,mai yiwuwa hakan ya zama silar kawo zaman lafiya a tsakani.
Toh tun asali mahaifiyarki macace mai zafi fada da kuma fushi,tana da wuyar saukowa a fushi idan ranta ya baci,hakanan bata yarda a take haqqinta ko waye zata qwaci kanta a hannunsa,tana da riqo idan ka bata mata,saidai takan sauko idan ka nemi yafiyarta,dalili kenan daya sake taka rawa wajen kawo hatsaniya tsakaninta da matar babanta inna kulu,kowa cikin fadin garin yasan ta da wannan hali,hakan ya sanya kaf 'yan matan qauyenmu ba yarinyar dake kawo mata wargi,mahaifiyar baffale ta miqe ta fadi wannan halaye nata,ta kuma ce ko donsu ba zata bari danta ya aureta ba,ba zata hada jini da ita ba.
An buga sosai kafin daga bisani Allah ya qaddara cewa sai baffale ya aureta,biki akayi sosai kasancewar tana da dangin mahaifiya a nan cikin birni,an mata komai na gata,jeran da babu tamkarsa,hakan ya sake hura wutar kishi a zuciyar faccalolinta tun kafin ta shigo,don duk cikinsu ba wadda ta samu irin gatan data samu,hakanan yadda baffale ke take take a kanta babu wadda ta samu irin wannan soyayyar.
To wani irin zama zance tayi cikin gidansu mahaifinki,tsakaninta da mijinta salamun salamun,zaman lafiya suke da qaunar juna,hakanan yana nuna mata qauna ko a gaban waye,nan fa qananun maganganun cikin faccalolinta da gutsiri tsoma suka soma yawa,kowacce kishi take da ita,saidai sunsan halinta duk wadda ta tareta gaba da gaba ta gaya mata maganar banza tofa itama ranta sai ya baci,ba zata qyale mace ba,suka dinga gutsura magana suna yiwa surukar tasu nuni data saka ido a rayuwar gidan baffale,suka karanta mata da alama ta mallakeshi,kasancewarsa shine qarami hakan yayi tasiri a ranta nan da nan,sannan uwa uba ga kuma kallon da take mata na yarinya mara kunya mara dagawa kowa qafa fitsararriya,nan fa aka fara sa toka sa katsi tsakanin su,mahaifiyarki ita kadai tsakanin faccaloli da uwar miji,amma da yake jarumar gaske ce duk ta iya da su,ta tare iskancin kowa,kuma bata fasa nuna soyayya da kulawa mijinta ba,tana matuqar sonshi hakanan tana kiyaye duk abinda baiso gami da bashi amanna,ta bashi yarda ta sakankance kan cewa bazai taba tozartata ko wulaqantata ba,mu kanmu a sannan mun jinjina mata da irin qoqarin zaman da tayi,a haka ake zaune har tsahon shekara guda,bata taba haihuwa ba sai bari da take yawan yi a kai akai,da wannan kuma suka samu dama suka tasa ta a gaba da habaici da gori,ba uwar mijin ba ba faccalolin ba.
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
(08030811300)
26
*DB*
Duk wadda ta gaya mata baqa kan rashin haihuwarta saita maida masa martani,inna yelwa kawai take dagawa qafa,itama randa ta gaji ranar ta maida mata,daganan cacar baki ta barke a tsakaninsu,har baffale ya dawo ya taddasu haka
"Na gaji da zaman wannan yarinyar mara mutunci a cikin zuri'ata,yarinyar kamar 'yar fata,kamar 'yar Allah bani?,to lallai lallai saidai ka saketa ta koma gidansu,yau dai ba zata kwana cikin zuri'ar modibbo ba" kai baffale ya kwantar yana bata haquri amma sam inna yelwa tace batasan wannan zance ba,tace saidai ya zaba ko matarsa ko ita,hakanan baffale yana ji yana gani yayi mata saki daya,tana kuka ta tattara kayanta ta dawo gida
Zaman nata a gida nan ma ba wani dadi ne dashi ba,saboda adawa suka dinga sosai da inna kulu,kusan ta wani janibin idan aka karanci halayyar mahaifiyarki lafiya lau za'a zauna da ita,duk da tana da wuyar sha'ani amma tana da dadin zama,duk da baffale ya saketa sai ya zamana kamar ba'a rabu ba,kullum suna tare kusan idan baida wani uzurin da zai gabatar to suna tare da ita,tuni ya maidata da baki,gidanne kawai bai maida ta ba,sanda labari ya kai kunnen inna yelwa tayi tashin hankalin rabasu amma ina sam haqanta yaqi cimma ruwa,a sannan ma ashe tana da ciki tun kafin ta baro gidan mahaifinki,bai bayyana kansa ba sai a sannan.
Tofa sai sabon rikici ya kunno kai,inna yelwa ta kafe kai da fata kan cewar ciki bana danta bane,yayin da mero ta kafe itama ciki na baffale ne,a sannan baffale baya nan,ya tafi neman kudi garin legos,rigima taqi ci taqi cinyewa,inda alqali ya sake shiga karo na biyu,yace a jira har sanda Allah zai dawo da baffale aji ta bakinsa,hakanan mahaifiyarki ta dinga rainon cikinta a gida,har sanda cikinta ya isa haihuwa baffale bai dawo ba,da yawa suna cewa zaunar da shi inna yelwa tasa akayi don kar ya dawo sabo da ita,haka dai zance keta yamadidi.
Wata tara da kwanaki ta haifeki,kama ta bayyana ta zahiri,kama irin ta ahalin gidan moddibo,ran kwana bakwai aka saka miki sunan aishatu,ba ragon suna ba rigar sakawa,babu kuma wani daga gidansu mahaifinki,a sannan naja'atu bata damu ba,tasan cewa da masoyinta ya dawo komai zai dai daita.
Watanki takwas sannan mahaifinki ya dawo,ranar daya dawo bai zarto ko ina ba sai wajen naja'atu,yayi murna matuqa da samunki sannan ya sake jaddadawa naja'atu cewa zata dawo dakinta ranar juma'ar da zata zagayo,a haka suka rabu,daga bangarenshi ba wanda yasan da wannan magana,ita kuwa tuni ta shaidawa 'yan uwanta ta kuma soma shiri,labari yakai kunnen inna yelwa,ta kuma ci alwashin daukar mataki,wanda shi ya kaita ga barin garinmu na kwana biyu sannan ta dawo,ba wanda ta gayawa me tayi,babu kuma wanda ta gayawa imda taje,ta dai dawo ta ja bakinta tayi shiru.
Ranar juma'ar kuwa aka yi mata rakiya,saidai inna yelwa ta tsare qofa ta hana a shiga da ita ciki,ta cika ta tunzura da taimakon zugar faccalolin ta,budar bakinta ma cewa tayi ita sam bata yarda da cewa ma diyar baffale bace goye a bayanta,tana shakka,tunda shi tunda ya dawo bai nemesu ba bai kuma yi maganar 'yar ba,bai kuma ce tashi bace,yayin da naja itama ta dage kan ba zata koma gida ba...gidan mijinta yau zata kwana,tunda shi ya maidata,babu dalilin komawarta gidansu,sannan 'ya ta baffale ce ko sama da qasa zasu hadu shi ya san da hakan,a nan inna yelwa ta bazama yara nemanshi sai gashi kuwa,tsatstsareshi tayi da ido tana tambayarsa yaushe ya maida naja bai nemi yardarta ba,rudewa yayi ba irin wadda ya saba ba duk sanda yayi mata laifi,ya kuma hau kame kamen cewa naja din ce ta dage kan komawarsu,abinda ya bata mamaki kenan ya daure mata kai,itadai tasan tare sukai maganarsu,ya kuma nemi ta koma din ya kuma amince,to amma duka ba wannan ne babban abinda ya girgizata ba,yadda inna yelwa ke shegantaka masa yarinya tana ba cikinsa bane yayi gum da bakinsa bayan yasan nashi ne,a nan fa halinta na qwatarwa kai 'yanci ya motsa,tace ba zata yarda ba,ta garzaya wajen alqali wanda ya saba shiga rigimar tasu,nan ya tattarasu ya tambayesu,sai a nan baffale ya amsa kaman yana dari dari da inna yelwa,da alamu dai akwai wata a qasa kenan,ganin ya amsa alqali ya kashe case din,naja'atu ta koma dakinta,saidai abinda baffalen yayi ba qaramin bata mata rai yayi ba.
Bayan komawarta sai zaman nasu ya sauya salo,ba wani jituwa can tsakaninsu,haka ma jama'ar gidan abun nasu ya sake qamari,bata shiga sabgar kowa suma basa shiga tata,duk wanda ya sake ya shiga gonarta kuwa zata nuna masa kurensa,bata barin kota kwana,hakan ya sake saka rashin jituwa mai qarfi tsakaninsu,baffale kam tana zaune da shine kawai saboda darajar soyayyar da sukayi a baya bata manta wannan ba,kasancewarta mace wadda bata da saurin mance abu.
Al'amarin ya fara ne lokacin da naja'atu tayi watanni hudu da dawowa gidanta,a sannan kika cika shekara guda a duniya,mahaifin naja'atu da muke kira baffa salihu ya hada mata gara mai yawa,garar haihuwa ce wadda ba'a yi mata ba saboda bata dakinta a sannan.
Ranar kai garar ina cikinsu,a sannan nima ina goyon suwaiba,naja batasan da zuwanmu ba,saboda haka tana sashinta,da sallamarmu gami da guda muka shiga gidan,duk matan gidan suna qasan bishiyar nan da sukan zauna kulli yaumin,sai aka rasa mai amsa mana sallamarmu sai ido suka bimu da shi,ganin haka rakiyar mai bin naja tace mu wuce bangaren najar kawai,kai tsaye can muka dosa,sanda muka shiga gidan mun isketa a sashenta tana dinkin hula,fes da ita ita da sashen nata kasancewarta gwanar tsafta,da farincikinta ta shinfide mana tabarma a tsakar gidanta tana fadin
"Amma kun yimin ba zata,da kun iske ni kuma bana nan fa?"
"Saimu koma da kayanmu mu cewa baffa salihu kince bakiso" dariya aka saki baki daya sannan tace cikin farinciki
"Kayan baffa ai bana mayarwa bane".
Kayan muka soma nuna mata,sai ta dakatar da mu tace bari ta kira sauran matan gidan,tayi hakanne saboda haka ake,a qa'ida ma su zasu tarbemu,uwar mijin kuma ita zata saukemu a wajenta,tana shirin fita da goyonki a bayanta saiga inna yelwa afujajan cikin fushi,sauran surukanta matan 'ya'yanta biye da ita,da kallo naja ta bisu da shi,duk sanda irin hakan ta faru tasan Allah ne kadai yasan sharrin da aka yi mata wajen inna yelwa,Allah ne kadai yasan me akaje aka gaya mata,tasan cewa yau babu zaman lafiya kenan,ta quduri aniyar komai ta fanjama fanjam ba zata lamunci a taka ta ba
"ku tashi ku fito munafukai algungumai irin masifa jinin tsiya,manufukar data gaya muku babu abinci a gidan nan qaryarta tasha qarya...tun kafin ayi daran akai kwandi....tun kafina a haifi uwar mai sabulu balbela take da farinta,bamu gaji yunwa ba bamu santa ba,kuma zuwanta cikinmu bazaisa a fara yunwa ba,ku kwashe tsiyarku ku koma da ita tun rayuka basu baci ba" baba ladi dattijuwar cikinmu,wadda take yaya ce ga baffa salihu tace
"Haba yelwa...haba ke kuwa....idan ana harkar arziqi ai tsiya bata shigo ba,gara ce ta jikarki da aka saba yi wadda bamuyi ba wancan karon saboda najar bata dakinta yanzu muka biya ta..." Tsawa inna yelwa ta daka mata gami da kiranta tsohuwar banza tayi wa mutane shiru,hakan shi ya sake tunzura zuciyar naja itama ta tanka
"Karki sake kiran uwata da tsohuwar munafuka...akan meye ne inna duka wannan masifa da bala'in?,tunda na auri danki ban huta ba...wai duka dai akan baffale ne wannan?"
"Eh...a kansa ne idan kin haifu cikin uwarki sahura da ubanki salihu ki barmin dana kiga idan baqar magana ma zata sake shiga tsakanina dake har abada....kai manu...matsa kuyimin koli koli da kayan wadan nan matsiyatan na daina ganinsu" ta baiwa matasan jikokinta umarni,kafin qiftawa da bismillah yaran sun soma diban kayan suna watsawa farfajiyar gidan,wadda ki cike da kwatami da qazanta,haka suka dinga watsi da duk abinda muka zo da shi yana dilmiya cikin tabi da gulbi muna kallo,tsabar baqinciki naja kuka ta saka ta dora hannu a ka,ana tsaka da wannan abu baffale ya shigo,ranta sai ya danyi sanyi tayi wajenshi tana zayyana masa abinda yake faruwa ga zatonta zai dakatar da su,sai yayi wajen mahaifiyarsa wadda ta dubeshi kai tsaye ta bashi umarni
"Ka saketa baffale idan ni na haifeka,saki biyunta nakeso ka qarasa mata" juyawa yayi ya dubi naja,kai take kadawa cikin kuka
"Karka aikata abinda zai zama dana sani a garemu...karka karya alqawarin daka yimin..."
"Bazan taba dana sani ba don na rabu dake.....naja na sakeki saki biyu....kai manu ku shiga dakinta ku fitar mata da kayanta" ya sake baiwa yaran umarni,kafin kace kwabo kayan ta sun soma watangaririya,tun daga tsakat gida har zuwa katangar bayan gida ta nan suka dinga jefa wasu sai da muka zagaya muka tsince,hatta da suturarta ta sawa basu damu da wankinta da guga ba haka suka dinga watsi da ita.
Mun jata kan ta wuce kawai mu tafi don wasu kayan ma ba zasu debu ba amma ta doje,ta koma ta dubi innayelwa daje tsaye ita da surukanta,wanda kowaccw farinciki take yau naja tabar gidan tsabar hassada da kishin banza mara amfani
"Yelwa....saboda danki kika yimin haka?....burinki ya cika danki ya sakeni....amma ki sani akwai ranar nadama,idan danki ne na barshi kenan har abada,ba danki ba duk abinda ya danganceku ma..." Ta qarashe maganar tana kwantoki daga bayanta,a sannan kina bacci duka bakisan abinda ke faruwa ba,shimfide musu ke tayi,tana shirin juyawa inna yelwa ta saka dariya
"idan kin haifu ke cikakkiyar 'yar halak ce ki sallama mana ita kiga idan ba zata rayu ba" wani irin kallo ta juya tayiwa inna yelwa,ta yiwa baffale nashi sannan ta qaraso cikinmu cikin matsanancin fushi mukayi gaba,a sannan babu wanda yaga rashin dacewar barinki saboda bacin ran abinda suka yi mana,a sannan babu wanda ya zaci wannan qiyayyar zata shafeki ta raba tsakaninki da mahifiyarki,babu wanda ya zaci lamarin zaiyi dogon zango har ya cimma wadan nan shekarun,yadda naja tace ta bar baffale har abada hakan ce ta faru,hatta da qofar gidan ta daina wucewa,hakanan duk wani lamari daya danganceki ta shafeshi a babin rayuwarta,bata zancanki bata yarda ayi mata zancanki,bata rabarki bata yarda ki rabeta.
Hankalinmu bai dawo jikinmu ba sai sanda labarin wahalar da kike ciki ta riskemu,a sannan duka bakifi shejara hudu a amma yadda ake tafi dake tamkar wadda ta shekara goma,duk da tun sanda mahaifiyarki tabar gidan hankalin baffale kacokam ya koma kanki,kulawarsa duka tana gareki,a hankali sai ya soma bagarar dake kema,wanda mutane da yawa sunyi amannar an kawar da hankalin baffake ne daga kanki da mahaifiyarki,ba'a hayyacinsa yake aiwatar da komai ba,a sannan mukayi yunqurin karbowa naja 'yarta amma taci alwashin duk wanda ya taka gidanma babu ita babu shi har abada,a sannan baffa Allah ya masa rasuwa.
Hankalinmu bai sake tashi ba sai da kikayi wayo kika soma bibiyarta da kanki,amma wata iriyar tsana kyara da hantara ta dinga giftawa a tsakaninku,ba wanda bai mamakin wannan al'amari ba,har aka dinga zaton anya ba jinnu ne suka shiga jikin naja sukai amfani da abinda ya faru ba suka farraqaku,saidai daga baya muka fuskanci ras take bata da wata matsala,taja kunnen duk wani wamda yake ganin ya isa ya kawo daidaito kan lamarin,akwai wadanda sanadiyya daidaita lamarinku har yau babu jituwa tsakaninsu da mahaifiyarki,da tawa daga cikin 'yan uwa jin haushin abinda take miki yasa suka fita sabgarku gaba daya ke da ita,suna ganin kunfi kusa ai,duk yadda zasu soki basu kai ya uwar data haifeki ba.....to kinji indo...wannan shine sila kuma mafari"gwaggo asabe ta qarashe fada tana sauke numfashi.
Kuka sosai aysha takeyi,tausayin mahaifiyarta na ratsata sosai na irin wulaqanci da cin zarafin data fuskanta....yayin da wani bari na zuciyarta ke qalubalantar matakin data dauka akanta,ita meye laifinta,ba itace sila ba,ya akayi mahaifinta da mahaifiyarta qarshensu yazo da haka duk sa irin soyayyar da gwaggo asabe ke fadin sun yiwa junansu,anya kuwa batayi kuskuren amincewa da khalipha ba kan cewar zai mata riqo irin wanda yayanta ciki daya zai mata,zai bata family da zatayi farinciki da su,zai bata dama da 'yanci duk kalar wanda ya dace?,ga masoya yadda suka qare...ina ga ita da zatayi rayuwar alfarma a qarqashinsa,ina ga ita da take da tabbacin ba soyayya ce ta hadasu ba,ba itace jigo ba...tausayi ne da taimako da zaiyi ma rayuwarta.
mero ma dake gefe tayi mutuwar zaune tana juya lamarin,ba shakka tana iya tuna wasu abubuwa da suka dinga biyo baya,irin shige da ficen da faccalolin ummin suka dinga yi suna yada cewa aysha shegiya ce,wanda banda Allah nasom baiwar tasa da tuni ya bita,sai ubangiji ya dakushe hakan daga qwaqwale da bakunan al'umma cikin lokaci qanqani da soma yada qaryar.
Kuka take sosai,tana sake tilawar labarin cikin kwanyarta daya bayan daya,tana fidda kuskuren kowan kowa a ciki,sosai tsoron maza ya kamata,firgici lokaci guda ya shigeta,tana ganin wautarta da kuskurenta na aminta da zama da ahalin khalipha,da wanne ido zasu dauketa wanne kallo zasuyi mata,ashe tabon dake cikin rayuwarta ya wuce iya yanda ita take tunani?.
Sai data ci kukanta sosai ba wanda ya tsaidata a cikinsu,domin dukkaninsu sunsan ba abu bane mai sauqi kashe irin wannan wutar,ba kuma qaramin al'amari bane gyara barnar da tayi shekara da shekaru da afkuwa ko ace tana afkuwa ma,a hankali ta dinga baiwa kanta baki,ta dinga qoqarin tsaida hawayenta,da kumburarrun jajayen idanunta ta dubi gwaggo asabe
"Na gode qwarai gwaggo,na gode da fidda ni da kikayi daga duhu xuwa haske,na gode da kika budemin abinda na jima ina neman sani a kai,na gode da kika kwancemin DAURIN BOYE" tana kaiwa nan ta miqe ta shiga bandaki,alwalar sallar magariba ta daura wadda ta gabato sannan ta fito ta soma shirin salla
"Kici daga da addu'a indo...komai mai wucewa ne da yardar Allah" cewar mero dake duban aysha cike da tausayi,murmushi mai ciwo wanda kai tsaye za'a iya kiranshi dana yaqe ta saki sannan tace
"Na sani mero...kuma ina fata wataran hakan ya zama tarihi"
"Amin ya Allah" ta fada itama tana shiga bandakin don daura alwalar.
Tana saman abun sallarta bayan ta idar,tunaninta ya rarrabu kashi kashi,daga nan inda take tana iya jiyo hayaniyar 'yan biki wadanda ke shirin tafiya dinner din asma'u,wayarta da tayi qara ita ta yanke tunaninta,ta waiwaya ta jawota sannan ta daga ta kara a kunneta,aliya ce tayi sallama cikin tsokana,wannan karon ranta cunkushe yake shi yasa bata samu damar maida mata ba
"Gobe ne tafiya qauyen ko?" Aliyan ta tambayeta bayan sun gama gaisawa
"Ke da kika ce ba zaki ba?....." Ayshan ta tambayeta a sanyaye
"Haba sashen,ko mafarki kikayi nace haka zaki yarda?....wasa nake miki...ko ramin kurege kika shiga ai naa shiga,haushi kika bani da kika qi yarda ko dan jan lalle ayi miki,na rasa wacce iriyar amarya ce haka?"
"Ta buzuzu mana..." Ta bata amsa qaramin murmushi na subucewa daga kan lebanta,sanadiyyar tuna aurenta na fari da tayi,wanda ko wankan arziqi bata yi ba randa za'a kaita bare a kai ga wani gyaran jiki da lalle,gwara wannan ta samu gyaran jiki yadda ya kamata,lallen ma itace bata so ba,jin abinda ayshan ta fada yasa aliya bushewa da dariya
"Au dariya ma kike?.....ni son ganinki ma nake fa akwai maganar da zamuyi"
"Har kin sani zumudi....Allah yasa ta samu" karyar da kai ayshan kawai tayi tana tuna yadda al'amrin ya kasance,tana tuna ayanzu waye khalipha na ainihi...hakan ba qaramin fadar mata da gaba yake ba
"Ko na taho yanzu?" Aliya ta katse mata tunaninta ta hanyar tambayarta
"A'ah....ki barshi kawai...ki bari ma tattauna gobe idan zamu wuce takai"
"To Allah ya kaimu"
"Amin....ki gaida mama"
"Zataji wlh...ai ran daurin aure tare zasu taho takai din da abba"
"Kice mata karta wahalar da kanta...ba komai ma za'ayi ba acan din,kawai nima dai inason asan asalina da tushena...kuma nima na jaddawa kaina wace ni...kar duniya ta rudeni"
"Koke ba zakiyi komai ba mu zamuyi malama....sai da safe" ta fadi tana katse wayar,itama aje wayar tayi,batasan wani matsayi zata baiwa aliyar ba,batasan wanne irin qauna take mata ba,tasani kawai Allah shi ya hada qaunarsu,ba wai don tana da wani abu da za'a qaunaceta ko a sota dominshi ba.
Bata bar kan abun sallar ba sai datayi isha'i,zuwa sannan hayaniyar gidan ta ragu saboda 'yan biki yawancinsu sun tafi sai dai daiku,jifa jifa mero na janta da hira don ta saki jiki tana kuma hada musu kayansu da zasu juya gobe da safe,anty safiyya ce ta shigo da sallama dakin,fuskarta qunshe da fara'a cikin ankon lace wanda sukayi iya su hudu 'ya'yan mummy yayyen amarya,tayi kyau sosai kasancewarta gwanar ado ce da kwalliya,duban aysha tayi tadan bata fuska
"Haba aysha...ya na ganki zaune kuma?,dinner din fa,kowa fa ya wuce iya mu mukai saura" murmushi ta dan saki,ina ita ina wannan waje?,ko giyar wake aka bata tasha ai ta wartsake
"Bana dan jin dadi ne sosai anty....bazan iya zuwa ba...afwa don Allah"
"Ayyah me ya sameki?"
"Dan ciwon kai ne kadan...amma na sha magani ma nasan zai sauka in sha Allahu"
"Sannu Allah ya sawwaqe yasa kaffara...kin kusa tafiya gidanki ki huta baki daya in sha Allah....amma ki miqe ki daure ki saka kayan da akace zaku saka yau din saboda masu shigowa" dan tunani ta shiga kadan wanda tuni har anty safiyya ta dagota
"Karki cemin cikin kayan da daddy yayi muku ba'a kawo miki komai ba?...." Shuru ita dai tayi ba tare data amsa ba,juyawa tayi fuuu zata fice,da sauri ayshan ta cafko hannunta,tayi narai narai da fuska idanunta sukai qwalqwal kamar zata fidda hawaye,dama har yanzu zuciyar a karye take
"Don Allah anty safiyya ki bar zancan nan karki tada komai....kinga dai yau duka abubuwan da suka dinga faruwa...karki silar tashin wani abu kuma,kiyi haquri" cikin sanyin jiki take duban ayshan,tana da sanyin rai da kyakkyawar zuciya,tana da nagarta da dattako,tana mata kaykkyawan fatan tayi dace da abokin rayuwa mai irin halayenta
"Shikenan aysha..ubangiji yayi miki kyakkyawan sakamako....yasa kin dace har abada"
"Amin amin anty safiya" cewar mero,bata sake cewa komai ba ta juya ta fita ranta sam babu dadi,bata jin dadin wasu daga cikin halayen mummyn dana 'yan uwanta,batasan meye laifin yarinyar ba,bata da wani mummunan hali qwaya daya tak,kawai don Allah ya yita cikin jinsin talakawa?,kawai don Allah ya sallada zata zauna qasansu taci arziqin da basu suka baiwa kansu ba,Allah ne ya ara musu donsu tallafi bayinsa mabuqata,gashi cikin ikonsa da buwayarsa ya soma yi mata baiwa da kyauta daga cikin ni'imominsa,tana fatan nagartacce ne wanda zata huta ta manta dukkan wata wahala ta rayuwarta.
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
*DB*
27
*Dimbin godiya a gareku masoyan da basu manta halacci da alkhairi*🙏🏽🙏🏽🙏🏽
_Alhamdulillah,wato haka rayuwa take,a duk sanda ka dage kan ka karya wani ko kaga bayanshi matuqar Allah na tare da shi aikin banza kake,matuqar zuciyarsa a tsarkake take zaiyi wuya kaci galaba a kanshi,koda dukka mutanen duniya aljanu da bil'adama masu taimaka maka ne wajen ganin durqushewar wani,a sanda ake fafutukar fidda litattafanmu kota halin qaqa,sai hakan ya zame mana tamkar wata silar alkhairi a garemu,a lokacin ne wasu jama'a ke ninka farashin da muka sanyawa kowanne littafi namu ninkin baninkin su sayeshi a haka saboda sanin daraja da mutuntuka,da kuma zuciyar da bata manta alkhairin mu a garesu a baya,DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI_
Qarfe sha daya na dare ta fita da kwanukan da su baba asabe suka ci abinci,ta bari ne zuwa sannan tana zaton ba kowa falon,idan ma sun dawo daga wajen dinner din tana tsammanin kowa ya tafi makwancinsa,ganin yadda kitchen din yake a hautsine sai ta kasa tafiya ta barshi haka,ta tsaya tana kikkintsa shi tare da gyara abinda zai gyaru a sannan tunda dare ya riga yayi.
A haka lantana daya daga cikin masu aikin gidan ta shigo ta tadda ta
"Lallai indo a gaisheki da qoqari,amarya guda da gyaran kitchen?,lallai" ta fada tana kama habarta alamar mamaki,da murmushi a fuskar aysha ta juyo ta kalli lantanar
"Banda abinki lantana wannan kitchen haka komai a hautsine,ta yaya zakuji dadin yin aikin?" Baki ta dan tabe tana aje farantan hannunta
"Wallahi gajiya nahi aisha....tun safe kana tsaye...ka gyara a bata,kowa kuma da kiran da zai maka....dama kuma kece mai juriyar,nikam nayi iya yina na gaji"
"Allah ya rufa asiri"
"Amin....ai gwara kiyi mana ma na bankwana,zamuyi kewarki wallahi indo" inji lantana tana nuna alhininta a fuskarta zuwa zuciya,sun saba da ayshan saboda sauqin kanta,hakanan sau tari takan amshe ayyukansu tayi idan tana da lokaci,ba ruwanta da qyamar mutum ko girman kai,ba kamar asma'u ba da basu taba jin dadinta ba,ayshan bata ce komai ba sai murmushi da tayi,wanda banda lotsawar da kumatunta yayi ma ba zaka gane hakan ba,kama mata lantanar tayi suka soma gyaran tare.
Basufi mintuna goma ba suka soma jiyo tashin hayaniya daga falon gidan,a hankali muryar anty safiyya tafi ta kowa fitowa
"Mu zasu nunawa iskancin banza iskancin wofi...mu zasu nunawa arziqi?,dama tun ranar kamu nake kula da take takensu,kai tun ranar kawo kaya,ina ruwanmu da wani familynsu ko arziqinsu,abinda muka sani kawai shine mun basu auren 'yar uwarmu,hakanan muma ba'a talauce suka ganmu ba bare suyi mana dagawa" ta qarashe fada tana huci
"Ke kinga yadda suke wani daddaga hanci da kallon kowa d'ai d'ai kamar kansu aka fara kudi,kina fa gani da muka shiga yiwa ango da amarya liqi sauka sukayi daga kan stage dinfa...." Anty kubra ta fada cikin jin haushi itama
"Su taka a hankali mi tsaf zan kora musu jawabi wallahi...ai muma ba tsiya suka ga tana binmu ko?....koma tsiyar ce a haka dansu yaga yarmu yace yana son aure" anty hajja wadda take qanwace ga momy ita ke binta ta fada.
"Kowa ya sayi rariya ai yasan zata zubda ruwa....tun daga yanayin halayyar yaron ya kamata su gane kowanne tsuntsu kukan gidansu yakeyi,don dai kai kawai baka isa ka fada bane baka da ikon gin magana" lantana ta fada,itadai aysha bata ce komai ba,tunda ba huruminta bane,har suka kammala ta wanke hannunta ta yiwa lantana sallama ta juya tabar kitchen din.
A kacame ta tadda falon,asma'u na kumfar baki anty safiyya nayi,da alama wani abun ne ya sake faruwa,tana jin anty safiyya na cewa
"Nikam babu matar data isa na sake jera kafada da ita bare ta wulaqantani bayan Allah bai wulaqantani ba,kije ku qarata ke dasu ke kika zabarwa kanki...banda shi mara mutunci ne har yace ki baiwa yan uwansa haquri sannan ya saurareki?" Cikin kuka asma'u tace
"Kinji ko mummy....wallahi ki mata magana,kinga zata jawo min matsala ko....nasan halin hamid wlh tsaf zai tsiri fushi da ni qarshenta ma sai wani satin za'a qarasa wani abun...nidai ki mata magana kawai"
"Ai na haifu,kuma 'yar halak ce ni...kije Allah ya bada sa'a" anty safiyya ta fada tana barin falon,ta haura sama dakin da suka sauka ita da sauran 'yan uwanta.
"Maganar gaskiya asma'u nima fa naji haushi...kuma hamid ya bani mamaki...ban zaci haka yake babu kwalli a idanunsa ba,giyar kudi na dibansa kenan?" Cewar anty kubra wadda sakuwa ce ta asma'un
"Kinga don Allah bana son qananun maganganu,nice dai zan aureshi na zauna da su,kuma naji ina son abina a haka ko yaya yake tunda shima yana sona" ta fadi cikin fada tana tasowa kubrar kamar zata doketa
"Allah ya bada sa'a" itama ta fada tana barin wajen,sai asma'un ta fada jikin mummy tana rushewa da kuka,duk sun hada mata zafi,gaba daya bikin yana neman juye mata,yaqi zuwa mata a dadin rai yadda taso,ga wannan tirka tirka da takeao ta kunno kai tsakanin dangin hamid din da nata,gefe guda kuma maganar aysha har yau na cin ranta,ba kamar yauma da take sake tambayar hamid waye muhammad abdulhakim mai goron,a yadda yake gaya mata waye shi ta tsorata matuqa,tana tsoron faruwar wani anu,tana tsoron kada reshe ya juye da mujiya,batason abinda zai sanya ta kasance itace a qasa har abada,koda yaushe tafison taga itace a sama sama da kowa.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Qarfe goma na safiyar washegari suka kammala shirinsu na wucewa takai,a sannan har aliya itama ta iso,ta ishi aysha da tambaya kan maganar data ce zasuyi,murmushi tayi kawai tace
"Me kike ci na baka na zuba?,zamuyi ai".
Sallamar lantana ita taja hankalinsu
"wani ne a waje yake jira wai an turoshi zai kaiku takai" cikin mamaki aysha ke kallon lanta
"Mu kuma?...takai?" Ta fada tana tunanin waye haka zai aiko?,iya tunaninta bata gane ko waye zai mata wannan karamcin ba,hakan yasa dole ya zira hijabinta tace
"Zo muje aliya inga ko waye" suka fice daga dakin.
Tun daga nesa ta gane baquwar mota ce ba irin ta gidansu ba,saidai bata iya ganin waye a ciki har ta qarasa gaban motar ta tsaya,murfin motar ne ya bude,wani matashin dan kimanin shekaru arba'in ya fito,cikin girmamawa yace
"Ranki ya dade boss ne ya aiko ni....ina fatan kun kammala shiryawa"
"Wanne boss?" Murmushi yayi sannan yace
"Wanne boss ne bayan muhammad khalipha?" Hannunta ta daga
"Ohk....ka koma kawai,zamu bi motar haya" ta fadi tana kama hannun aliyar dake binta da kallon tambaya suka juya.
Tana gab da shiga falon wayarta ta dauki ruri,dubawa tayi K ce ta bayyana kamar yadda tayi serving number dinsa
Numfashi ta aje sannan ta daga wayar ta kara a kunneta
"Me ya faru tsakaninki da sani,yace min wai ance ya tafi"
"Bbu komai,zamu bi motar haya ne kawai...."
"Bai dace ba aysha...maida hannun alkhairi baya fa kenan?"aliyata fada tana tsaye daga gefanta
"Aliya....kin san waye?"ta fada tana kallon hanya ba tare data dubi aliyan ba
"a'ah"ta bata amsa tana girgiza kanta dukka idanunta da hankalinta na kan ayshan
" khalipha ne fa aliya,wanda zan aura"
"Arrrrrrhhhhh" aliya ta fada tana rufe bakinta da tafukan hannayenta duka biyun kamar mai maitsoron kar wani yaji ihunta,idanunta a waje hakanan fuskarta qunshe da murmushi
"How comes sashen....tell me pls" juyowa tayi tana duban aliya,hannayenta harde a qirjinta,fuskarta a hade tsaf
"Khalipha ya saka min shakku mai yawa a kansa aliya....ta yaya zaizo min da wata fuska?,ta yaya zaizo min da wata siga?....a yadda khalipha yazo min aliya ashe ba haka bane....wannan ba yaudara bane?"
"Ya salam.....haba...ni nasan kaman na taba sanin face dinshi a wani waje wlh...kaman ya taba zuwa wajen abba na...oh my god...ina zuwa" aliya ta fada tana zame hannunta daga riqon data yiwa aysha,da sauri sauri kaman wadda zata tashi sama ta koma qofar gida,da idanu aysha take kallonta tana mamakin saurin me take ina zata?,me yasa bata ga alamun jimami ko tayata bacin rai kan abinda khaliphan ya aikata ba?.
Tana nan tsaye kaman sakarya har aliyan ta dawo fuskarta washe da fara'a ta kama hannun aysha ta jata zuwa ciki,a parlour suka ga asma'u zaune sanye da kayan bacci,kaman ko yaushe tana saqale da earpiece a kunnenta da alamu ma waya take,harara ta danqara musu wadda kowaccensu ta ganta,wata fara'a ta musamman aliya ta qirqira tana sake riqe hannun aysha sosai tana cewa
"Kinsan me goro family kuwa aysha?....ai ke Allah ne ya tarfawa garinki nono,dare daya dama Allah kanyi bature..." Ta qarashe fada suna tura qofar dakin ayshan suka shige,hannunta aysha ta cire bayan sun shiga din tana kallon aliya gami da kallon qofar dakin nata kaman wani zai shigo,dariya aliya ta bushe da shi har tana duqawa kadan
"Banson fitina aliya kin sani ko?" Ayshan ta fada a narke kamar mai shirin sanya kuka,bata tanka mata ba sai taja hannunta zuwa bakin gadon ayshan ta zaunar da su a tare sannan ta kalli gwaggo asabe
"Gwaggo kiyiwa aysha fada taiwa kanta fada...mijin da Allah ya bata da don jama'a da dama ne ba zata sameshi ba,bama shi ba gwaggo ko mai gadin gidansa ba zasu yarda ta aura ba....duk bata duba haka ba zata tsaya tana wani goce goce maras tushe ko dalili?,khalipha kaman wani tsanin ki ne na fita daga tsangwamar da kika dade kina fuskanta tsahon rayuwarki,Allah ya sani baki ma sanshi ba bare kiyi kwadayin abun hannunshi koda jama'a zasu fadi hakan,ke kinfi kowa sanin kanki,kinfi kowa sanin wacece ke" ta fada tana duban idanun ayshan kai tsaye sannan ta dafa kafadarta
"So pls aysha....ki nutsu ki fuskanci gabanki kawai...." Ta fadi tana sauke hannunta sannan ta cewa su gwaggo
"Ku shirya da sauri gwaggo....angon ya turo driver shi zai kaimu har qofar gida"
"To ma sha Allahu....kinga mun huta hawa ta haya kuwa" gwaggwon ta fada cikin farinciki,sannan daga bisani tayiwa ayshan dan fada da jan hankali,itakam kawai tana zaune tana jinsu,amma harga Allah tana da fargaba...su asma'u kawai sun isheta isharar tsamiyar talaka da mai kudi bata jiquwa waje daya...masu kudi basa qaunar talaka sam,kansu suke so,isu isu suke mu'amala da junansu,amma koma meye ta miqawa Allah zabinta.
Tana zaune waje daya kawai tunda ta gama nata shirin tana binsu da ido wayarta ta dauki qara,ta duba batasan number ba sai ta daga ta kara a kunneta tayi shuru ba tare data ce komai ba taji waye
"Assalamu alaikum warahmatullah" ta jiyo muryar wata mace dattijuwa,cikin mamaki ta amsa sallamar tana son taji wace
"Ina fata aishatu ce" a ladabce ta amsa saboda yadda muryar ke nuna shekarun mai maganar
"To ma sha Allah....me ya faru na saka khalipha ya turo muku driver ya kaiku,sai naji yana waya da driver yana gaya masa ya dawo kawai?" A take ta gane wace,anni ce duk da cewa baifi sai biyu ta taba jin sunanta daga bakinsa ba,diriricewa tayi gami da tsorata kamar wadda ta yiwa sarko qarya har hakan ya bayyana saman fuskarta,aliya dake gefe wadda ke jin duk abinda ke faruwa saita amshi wayar,gaisawa sukayi sannan tace
"Qawar aysha ce,bamu gane waye ya turoshi ba sai daga bisani....amma yanzun haka ma gab muke da gama shiryawa mu wuce"
"To madalla...na zaci daga khalipha ne...Allah ya tsare hanya...a gaida mutanen gidan"
"Amin zasu ji,mun gode" daga haka ta katse wayar itama aliyan ta sauke tana murmushi qasa qasa,hannu ta saka ta daki bayan ayshan
"Saikin biyani ladan yin lauya....haka zakije ki dinga musu wannan sanyin naki da tsoro?...uwar mijinki ce fa ta kira" idanu aysha ta zaro tana duban aliya
"Ke...uwar mijin wa?...mamana zaki ce,a matsayin yayana yake ni da shi babu zancan miji da mata" idanu aliya ta saka tana kallon ayshan,sai kuma tayi turus ayshan tana duban dakin,Allah yasa su biyu ne su gwaggo sun soma fita da kayansu ana kaiwa mota
"Kaman yaya ban gane ba,yimin bayani...."
"Share kawai" ta fada tana miqewa gami da saba jakarta a kafada,itama aliyan tashi tayi tana rataya tata
"Wallahi baki isa ba yarinya kinyi kadan,tunda kika fara fada dole ki fada duka" murmushi tayi tayi gaba...itama tasan hakanne,ba wani boye boye tsakaninsu,idan ta boye dinma tana da wanda zata gayawa ne daya fita.
A parlour aliya ta toge aysha ta haura sama yiwa mummy sallama
"Mummy zamu wuce...sai mun dawo"a watse ta amsa tana sabgar gabanta,bata damu ba ta miqe ta fito,nan suka ci karo da anty safiyya,da fara'a take dubanta
"yanzu shikenan haka zaki tafi ba dan rakiya?"
"Ba komai anty muna tare da aliya da mero,ga gwaggo asabe ga baaba karima"
"Shikenan....sai ranar lahadin kenan"
"Eh in sha Allahu" ta fada tana duqar da kanta qasa kadan alamar kunya
"To Allah ya nuna mana,don Allah ki gaidasu ,abinne ya hade mana lokaci guda"
"Zasuji anty" har ta juya anty safiyyan tace
"Ammm...aysha zo aliya ta kawo min qararki" waiwayowa tayi ta dawo rana taraddin me ya faru,a tausashe take mata magana
"Bana son inji wata baraka tsakaninki da khalipha,tunda ba wani mugun hali nashi ya boye miki ba sai yanzu ya bayyana,abinda ya farun me yiwuwa haka tsarinshi yake,yaso daukar asma'u amma Allah ya duba ba kalarshi bace bata dace da shi ba sai ya hada tsakaninku,kinsan komai basai na miki bita ba,kuma koda baki fada ba da bakinki kin sani cewa Allah ne ya qwata ya baki,ya lullube asirin komao bada wayon khalipha ko plan dinsa ba,wannan shirin Allah ne,so don Allah aysha banson jin komai"
"In sha Allahu anty...na gode"
"Yauwa Allah ya tsare hanya"
"Amin anty" daga haka suka rabu ita ta sauko qasa ita kuma ta wuce dakin mummy.
Lafiyayyar mota ce data amsa sunanta,hakan ya sanya sukai tafiya mai dadi wanda har mero ta dinga santin ashe hanyar garinsu bata wani rube sosai ba rashin kyawawan motoci yasa suke shan wahala.
Qarfe biyu da mintina takwas suka isa qofar gidan nasu,a hankali aysha take qarewa gidan nasu kallo tana mamakin jama'ar data gani anata shige da fice a gidan,sai tayi tsammamin wani abu ke faruwa don ko kusa ko alama bata kawo cewa bikin aurenta yasa mutane taruwa ba har sai data fito daga motar taga jama'a sun soma yanyameta tare da yi mata maraba lale gami da kiranta da amarya,da mamaki kawai dubansu kamar wasu masu shirin wasan kwaikwayo,kafin kace meye kayanta da aka fito dasu daga booth har an samu masu sunguma sukai cikin gida da shi sannan ita kuma da sauran mutanen da suka tsaya gaban motar suka dunguma zuwa cikin gidan.
Sosai tunani da qwaqwalwarta suka daure da sauyin data taras cikin gidan nasu koma tace a unguwar baki daya,kowa indo yakewa marhaba,kowa indo yake tare,kowa indo yakeson nunawa kulawa,kowa.indo yake so ya raba,kowa ita yakeso ya yiwa magana,shin me ya haifar da wannan gagarumin sauyi haka dare daya?,me yake faruwa ne koko daya daga cikin ire iren mafarkan data saba yi ne tau take yinsu ido biyu,ba aysha kawai ba ba mero da gwaggo asabe da suka san meke faruwa ba hatta da aliya wadda labarin aysha ne kawai ya isketa sai data yi mamakin sauyin data gani.
Mamaki bai sake kamata ba sai sanda inna yelwa ta miqe da kanta ta tareta,ta tareta cikin yanayin da tunda ta budi idanu tasan duniya da abinda ke cikinta bata taba ganinsa ba,cikin kulawa da fara'ar da bata taba ganin makamanciyarta ba daga gareta,da idanu take bin rumfar inna yelwa da ido tunani yana zagaye ilahirin qwaqwalwarta,yadda aka gyara rumfar fes kai baka ce ita bace,aka sabunta ta aka sauya mata kamanni,ta sha leda...ta sha fenti da labulaye harma da kujeru
"Wai meke faruwa?" Ayshan ta tambayi kanta da kanta tana duban aliya kamar ita zata bata amsa,kafada aliya ta daga sannan tace
"Ina zan sani sashen....wannan abun akwai ayar tambaya a kai" tana kaiwa aya wayar aysha dake hannun aliya ta kada qaraurawa alamun shigowar saqo,dubawa tayi don ba komai irin haka a tsakaninsu sun saba
"Karki wani damu da sauyin da zaki gani,anni tayi duk wani abu daya dace saboda ki samu walwala ki sake" aliya ta karanto saqon a fili don mai wayar taji abinda ya qunsa,shuru tayi tana tunani
"Me tayi daya dace?,me ya sauya mutanen nan haka?" Ta sake aikawa da qwaqwalwarta da wannan tambayar,bata kai ga samun amsarta ba matan kawun ta suka soma shigowa,kowacce baki har kunne aka sake sabuwar gaisuwa a gurguje kar inna yelwa ta shigo ta riskesu don ta gargadi kowaccensu da karta shigo bare ta damesu,abun mamaki shine godiyar da suketa sheqa mata kafin kowacce ta miqe ta fice
"Aliya don Allah ki fahimtar da ni abinda ke faruwa mana" ta kama hannun aliya tana fada cikin rudu,don ita har ga Allah tsoro.ma abin yake bata,ko wani abun suke qullawa?,ko wani shiri ne sukayi na daban wanda batasan da shi ba,domin bata tunani akwai abinda zai sauya wadan nan mutanen lokaci guda kai kace umarni ne daga sama
"Babu komai sai alkhairi aysha...karki damu...saqon daya shigo daga khalipha yake,kuma na tabbatar su su khaliphan bazasuyi abinda zasu cutar da ke ba" maganar ita ta kwantar da hankalinta,saidai idanu data sanya tana lura da motsin komai da yadda komai yake gudana,tana iya jiyo shewar cincirindon matan qauyen dake tsakar gidan gidan nasu,sanda aliya ta miqe zata alwala ta daga labule a nan taga manyan tukwanen dake girke a tsakar gidan suna cin wuta,da aliyan ta dawo dubanta tayi
"Na kusa gane abinda anni tayi,anya ba siye mutanen sukai ba?anya ba kudi ne suka sauya komai ba?,aysha shanu biyu aka shigo da su a yanke,ga tarin abinci kala kala a wancan rumbun dake kusa da makewayinku,sannan kowanne cikin gidan nan cikin walwala yake da burin zuwan gobe ranar daurin aure" daga idanu tayi ta kalli aliya sanda take maida pad din data ciri daya zata sauya cikin jakarta
"Hakan ma zata iya faruwa aliya,kin manta ni ba komai bace...zasu iya sadaukar dani saboda abinda baikai wannan bama...." Ta fada tana sauke idanunta qasa qwalla nason qwace mata,dafata aliya tayi sannan tace
"Idan kika lura a yanzu kin zama mai daraja aysha,baki lura da yadda suke kaffa kaffa dake da dukkan lamuranki ba?...dubi kwanukan abinci kin taba gani an jere miki su haka a gabanki daga sashe sashe?,ko wannan ya isa ya gaya miki daraja su anni suka siya miki...kuma ina miki fatan kici gaba da kasance mai daraja ta sanadiyyarsu".
Sai da suka zo kwanciya bayan inna yelwa ta saka musu maganin sauro an yada musu dandamemiyar katifa da bargo sannan dukkansu suka dago manufar sauyi da suka samu
"Indo ina kika samu miji mai arziqi haka?....ashe dai zamu dandana arziqinki....bama 'yan gidan nan ba har maqota...kinsan kaf gidan nan babu wanda yanzu bashi da jari mai tsoka?...sannan kaf dinmu mu da maqota ba wanda bai samu sabon dinki ba da zai saka a gobe?bayan manyan buhunhunan shinkafa da aka bi aka raba musu,sannan rumbunan gidan nan uku kowanne cike yake da cima ta 'yan birni,guda daya yace ayi hidimar biki da shi...saura namu ne muci mu qara idan sun qare za'a dado wasu....ke kanki yasa mun fadi yadda muke bukukuwanmu na al'ada ya biya komai gobe kwana za'ayi ana cashewa,ke ni fa da nake kakarki har kudin liqi sai da aka zubemin in gaya miki,kudina sabbi fil a miqe...." Kanta kawai ta juya daya barin,babu abinda ya burgeta a zubar da inna yelwa keyi,sun sake saida mata dan guntun mutuncin da yayi mata saura,bata sake cewa komai ba tana jin inna yelwar da aliya na sake bugun cikinta tana jin yadda abubuwa suka kasance,mota guda ashe aka yi musu ta saqonsu.
Tashi inna yelwar tayi ta janyo wata babbar akwati ruwan makuba(marroon mai adon dark blue)tana sumbatu
"Ga uban kayan da yace a aje miki indo ko zaki buqata,idan kinzo a baki,kaf karkarar nan da maqotanta ba wadda ta samu adaka irin taki cike da suturu haka,na biye ne saboda masu dauji dai dai nace sai kinzo na danqa miki abarki" kusan aliya ce kawai ta bude tagani,kaya ne aqalla kala goma sha biyu dinkakku,wanda amsa sunansu,takalma jaka mayafai zuwa sarqa da dan kunnaye kowanne kaya da kalar daya dace dashi,kayan kwalliya da duk wani nau'in abu da zata buqata akwai a ciki,jinjina kai aliya take tana qissima tsadar iya wadan nan kayan,sannan a ido kawai kyansu dole ya burge mutum,ba yadda batayibda aysha ta tashi ta gani amma taqi koda motsawa haka ta gaji ta haqura ta qyaleta.
Washegari da dagewar aliya da mero ta shirya cikin a tamfa,duk da cewa ba wani kwalliya tayi ba amma sosai tayi kyau,komai sabo ta saka daga cikin dinkin da asma'u ce ta zabi kayan har zuwa dinkin,hakanan taji tana sha'awar sanya kayan da daddy ne ya dinka mata,ta kasa taba kayan khalipha kwata kwata,komai a sukuku take yinsa,don hatta da karyawar safen da aka kawo musu tea da bread da chips da wainar qwai wanda batasan wanda ya hada ba bata iya ci ba,sosai aliya ta dinga sako hira da zance don ta sako jikinta amma ita kadai tasan ya take jin zuciyarta.
Goma na safe inna kulu ta aika tazo,da fari inna yelwa taso tayi gaddama amma daya daga cikin yaranta maza ya jata daki sukayi magana,batasan me ya gaya mata ba tace suje amma ta dawo kafin lokacin daura aure,tare suka fita da aliya don mero ta koma gida zata shirya kafin lokacin daurin auren yayi,don sai qarfe uku na yamma za'a daura,suna tafe aliya na yaba yanayin gari tare da tambayar indo wasu abubuwan,kusan tasan kowanne waje da abinda yake wajen kasancewarta sha gwagwarmaya ce.
Babu zato ba tsammani suka ga an sha gabansu gami da karta adda a qasa,a tsorace suka ja baya dukansu suna riqe da hannun juna,sai data duba sosai sai taga ashe dan ladi ne
"Indo baki isa kiyi aure ba idan ina raye...kin manta ke tawace?,har yanzu ke matata ce kuma ina sonki,babu wanda ya isa ya rabani dake"wani wawan tsaki taja sannan taja hannun aliya zasu wuce,don ta lura a buge yake ba cikin hayyacinsa yake ba,sake shan gabansu yayi
" na gaya miki ina sonki,babu inda kuma zaki daga nan sai gidana"ya fada cikin salo na maye,isowar wasu matasa wajen suka cakumi dan ladin sukai musu gefe da shi yayiwa ayshan dadi,haka suka wuce aliya na waigen dan ladin
"Waye wai wannan aysha..."
"Tsohon mijina ne"
"Dan ladi?" Kai kawai ta gyada mata,don tunawa da rayuwar datayi da shina qona mata rai yake,dariya aliya ta bushe dashi tana duban ayshan,tana son ta kalleta itama ta tsokaneta amma sai taga ayshan ta basar,da alamu har yanzu ranta ba'a sake yake ba,ganin haka itama ta share har suka isa gidan.
Ga mamakinta a canma jama'a ta samu zoqar ana shirye shiryen yinin biki sosai,a nan dinma maraba ake da ita,duk da bata wani ji abun har cikin ranta ba amma ta dan saki jiki albarkacin gwaggo asabe,saidai duk da haka nata ido,wuni bikinsu suke sosai,tana zaune tana binsu da kallo,lokaci lokaci tana share hawayen fuskarta,koda ace ba har zuciya suke mata wannan hidimar ba,koda ace ba don Allah suke yinin bikin ba,koda ace abun bai burgeta amma zata so ace mahaifiyata na wajen...zata so ace mahaifiyarta tazo...zata so ace tana ganin wulgawarta a wannan bigiren koda kuwa bata farinciki da ganin nata ko auren da take yi.
Qarfe daya na rana zayyanu dan qanin babanta yazo ya kirata,tana jinsu suna 'yan maganganun kiran itadai ta miqe suka wuce ita da aliya da wasu daga cikin 'ya'yan qannen umminta,sanda suka isa qofar gidan nasu ya soma cika damqam da jama'a,kusan kowa cikin shadda yake fara,matan kuma sanye da tasu shaddar light purple har zuwa cikin gidan haka kalolin suke,da alama dinkawa akayi kowa da kowa,hakan take kuwa,saboda tana shiga tsakar gidan dake cike da mata suka saki guda a tsakiyar kanta suna yabawa gami da godiya da dinkin shaddodin da aka yiwa kowa a cikinsu,ciki da wajen gidan,aliya ce ta ja mata mayafinta ta rufe mata fuska,kuka ne ya qwace mata,tana ganin komai kamar a mafarki,idan suka kirata amarya sai taji banbarakwai,tana ji kaman da gaske auren gaske zatayi bana samun 'yanci ba,ba yadda aliya batayi da ita tayi shuru ba amma hakan ya gagara,don ita kanta tasan bata da ikon tsaida wannan kukan,a haka aliya ta matsanta ta mata ta sake sauya wasu kayan,tayi kyau sosai saidai fuskarta duka tayi jajir ta tasa saboda kukan data kasa dainawa.
Kafin lokacin daurin auren gidan ya cika danqam da jama'a,ci da sha ake tako wanne fanni cikin walwala da dariya,saika rantse da Allah tun usuli ita din diyar gata ce a cikin gidan,tun tana kallon kowa cikin mamakin har ta daina mamakin ta zubawa sarautar Allah ido,wato a rayuwa idan kana da shi kaine wani?,kai ne abin so?,kaine abun taqama abun a nuna?,kai akewa biyayya?,kaine abun girmamawa koda baka biyayyawa mahaliccinka?,wadan nan tambayoyin ta dinga yiwa kanta suka dinga kai kawo da amsa kuwwa a kunnenta da kwanyarta.
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
*ko kuma*
07067124863
*DB*
28
Kafin a kammala daura auren tuni zazzabi da ciwon kai ya saukar mata mai zafi,haka ta samu can lungun gadon inna yelwa ta lafe,wanda da qyar ta yadda ta hau,gado ne da iya tsahon rayuwarta bata taba hawanshi ba koda da qiriniya irin ta quruciya saidai taga 'yan uwanta na hawa,kusan duk abinda ke faruwa daga cikin dakin zuwa farfajiyar tsakar gidan tana iya jiyowa,hayaniya ce kala kala cakude da muryoyin mawaqa da kidan qwarya wanda tun safe idan waccan ta tashi wata sai ta dasa nata,tana mamakin irin cikar data ji garin yayi,kusan gaba daya qauyen ya hade da hayaniya da dumin maganar daurin auren,duk wanda baka gani ba a wajen to bai kusa ne ko bai cikin garin,gayyar sodi kuwa ba'a maganarsu
"Sai yau kuttun farinjinki ya fashe ne indo?" Mero keta fada cike da al'ajabin halayyar dan adam,karadin maroqa kuwa har wani bai gane na wani,a haka ne ta jiyo sanarwar daurin aurenta daga bakin daya daga cikin maroqan wanda yafi kowa karadi da zaqin murya.
Idanunsa ya lumshe sanda aka kammala karanto siga aka shafa fatiha,yana jin kaman gaske wani b'ari na zuciyarsa na gaya masa ba gaske bane,Koma meye yana jin dadi cikin zuciyarsa,ko babu komai ya cikawa anni burinta na kawo yarinyar cikin ahalinsu,burin annin shine nashi,bai fatan taso wani abu guda daya da bazai iya bata shi ba koda kuwa rayuwarsa ce,ta damu da ita sosai kaman ma bashi yazo da zancanta ba itace tazo da shi,kullum zancanta take da sauran kwanakin da suka rage mata da zata bar gidan daddyn ta dawo cikin nasu gidan,ta dokanta sosai,tana ganin kamar hajar dinta ce zata dawo,ya tabbatar zatayi farinciki a sanda labarin daurin auren ya isa kunneta,yanajin wannan farincikin ne yake tayata shima.
Wasu sabbin hawaye ne suka gangaro mata ta gefan idonta,ta cusa hannunta qasan filo ta ciro wayarta,lambar wayar umminta ta lalubo sannan ta shiga wajen rubuta saqonni ta fara rubuta mata
_duk da na sani bani daga cikin yara masu 'yanci...bani daga cikin yaran da za'a nemawa albarka saboda laifukansu ga iyayensu...na sani fadar bata da wani amfani a gareki,amma a dai dai wannan lokaci ina neman alfarma a gareki karo na biyu a rayuwata,ki sakawa rayuwata albarka a ranar da aka dauran igiyar wani...ki nema min afuwa da albarkar rayuwa wajen ubangijinmu,koda cikin zuciyarki ne keda ubangiji...koda wannan ce alfarma ta farko kuma ta qarshe da zaki yiwa rayuwata,na barki lafiya,daga 'yarki mai mafarkin watan watarana zaki rungumeta kamar sauran zuri'arki_
Tura mata tayi,sai data tabbatar yaje sannan ta maida wayar qasan filo ba tare data saka ran samun amsa ba.
Duk yadda aka dinga hada hada da shigowar tawagar ango cikin gidan tayi luf babu inda ta motsa,duk da tana jiyosu suna cigiyar angon,har sukai suka fice taqi ta fito ko nan da can,kusan aliya ce ta zama uwa ta zama makarbiya.
Qarfe hudun yamma inna laraba mai aiki ta iso,tuni maman aliya suka juya ita da abbanta bayan ta saka mata kudi masu yawa a hannunta tace ta riqe,da hanzari aysha ta diro daga gadon ta rungume innar tana sakin kuka,lallashinta ta dinga yi tana mata fadan kukan da tayi daya sauya mata fuskarta ga zazzabi a jikinta,sai data nutsu sannan tayi mata nasiha gami da jan hankalinta,nasiharta tayi mata tasiri matuqa saboda ta tunasar da ita abubuwa da yawa,wannan shi ya taimaka ya riqeta har zuwa dare bata sake zubda wata qwalla mai yawan da zai mata illa ba,saidai kawai gatanan ne sukuku,wanda mutanen qauyen da yawa ke ganin rashin ganin mahaifiyarta da kalar alaqar dake tsakaninsu ne yake haifar mata da sanyin jiki.
Tun daga zuwansu zuwa dawowa yake karantar abubuwa da dama daga cikin rayuwarta,yaga gaskiya zalla,yaga ainihin labarinta da take bashi qarara kusan a aikace,baya manta zuwanshi na farko tattakin da yayi yaje qauyen nasu cikin gidan nas a zuwan mai bincike kan wace indo ba tare da sunsan kowaye shi ba,maganganu marasa dadi da yaji a kanta da mahaifiyarta daga bakunansu,abubuwan daya karanto daga idanunsu,amma ga mamakinsa zuwa na biyu da yaje da sabanin abinda yaje muau da shi da farko sai gashi ta farad daya komai ya canza,cikin qanqanin lokaci ya siya mata qauna da soyayya mai tarin yawa,duk da idean anni ce wadda Allah ya sallada mata qauna da soyayyar ayshan duk da bata taba sanyata a idonta ba,da gaske ne kaso mafi yawa na mutanen duniya sun sauya,babu mutunci babu qauna babu soyayya,komai suna aunashi ne kan mizanin me kake da shi?,me ka mallaka?,waye kai?,waka sani wa yasanka?,zaka iya siyan komai idan kana da kudi,zaka iya mallakar komai komai yana iya zama naka idan kana da abun hannunka,yakan kwatanta yanzu da rayuwarsu ta baya,sai yake ganin banbaci na zahiri mai tarin yawa,ya sauya abokan rayuwa da yawa,da rabu da wasu mutane da yawa ya sauyasu da wasu...saboda walqiyar da akayi suka ga kowa quru quru,kusan shirunsa yafi maganarsa yawa cikin motar,saboda tsohon ciwon kansa dake son ya tashi,wanda hayaniya da kuma tarin tunanin dake cunkushe a kwanyarsa keson tayar dashi,da fari mahmoud bai gane ba,ya addabeshi da tsokanar kodai kewar amarya yake,bai samu ya ganta ba,sai daga bisani ya gane matsalar ciwon kan nashi ce keson tashi,tilas ya tsaida ayarin motocin suka koma mota daya shida khaliphan iya su biyu,yadda hakan zai bashi damar hutawa sosai.
***********************
Qarfe takwas na safiya suka gama shirin komawa gidan daddy wanda haka su inna yelwa suka zartar a cewarsu a gidan mutumin daya riqeta kamar diyarsa za'a dauketa a miqata gidan mijinta,itakam bata da wani tsari sai yadda suka tsara,wannan karon ma ce musu kawai akayi su fito ga mota,wannan karon bata musa ba bata ce komai ba suka fito,motocin guda biyu ne wannan zuwan,guda daya ita da aliya ne da mero sai larai da bahijja yayan baba auwalu,daya motar kuwa gimbiya inna yelwa ce da inna kulu ga mamakin aysha inna yelwan bata ce komai ba ko tayi wani abu na tada hankali kan an hadasu muhalli daya da inna kulun ba,sai kuma lanti matar baba sadisu da kuma qannen ummi mata su biyar jimillar wajen su goma suka nufo gidan daddyn.
Kamar wancan karon wannan ma tafiyar bata wani wahal dasu ko sunga nisanta ba,cikin mintoci zuwa awa guda suka isa gidan,suma gidan a cike yake da 'yan yinin biki,hakanan suka ratsa zuwa cikin gidan ayshan na musu jagora,bata wuce dakinta ba sai da suka soma zuwa wajen mummy don su gaisa,sama sama ta karbesu kafin daga bisani su wuce zuwa dakin ayshan su yada zango.
Qarfe biyu na rana ya shiga bangaren annin,ya kasa daurewa duk da yawan jama'ar dake gidan da sunan 'yan biki da kuma ciwon kanshi da yakeson ya dawo,ciwo ne daya sameshi kusan shekara goma baya bisa wani dalili,tun jiya rabonshi daya ganta abinda bai saba yi ba indai yana gari ko yana qasar,a kasalance yake takowa zuwa bangaren nata sanye da farar shadda riga iya gwiwa mai dogon hannu da wando da alama masu hade babbar riga ne,wanda ya barwa mahmoud ajiyarta a guest house dinshi da suka sauka shi da sauran abokanshi da suka halarci bikin,duk da ba yadda baiyi dasu suyi zamansu ba amma kowanne sai dayazo mishi,kanshi babu hula hannunsa daya saye cikin aljihun wandonsa,yayin da daya hannun yake riqe da hular da bai saka din ba,duk inda ya gifta ido ake binsa dashi kaman yadda akasan amarya da ango da farinjini haka aka dinga tsokanarsa,murmushi kawai yake wanda kusan na yaqe ne saboda ciwo da kanshi keyi,yakan tsaya wani wajen su gaisa wani wajen kuma ya wuce abinsa,da yake yasan kowa yasan kuma dalilin da yasa mafi yawancinsu suke tarayya da su,a haka ya cimma anni a falon ta zaune ita da sauran 'yan uwa kowa na sabgar gabansa,falon ya cika da hayaniya da surutu dalili kenan da yasa yaji bazai iya zaman falon ba bayan sun gama gaisawa ya miqe,inda wasu mata dake zaune su uku kowacce idonta ke kasa taba qissima abinda zata fada wanda zahiri abinda kecin zuciyar kowannensu ne,inna maryam wadda kusan tafisu rashin haquri kuma mahaufiya ga zeenart tace
"Kadaiqi 'yan uwanka khalipha qarfi da yaji...duk dadin bare ai dan uwa ya fishi ko?,da cikin 'yan uwanka ka auri daya kai kanka kasan yanzu farinciki da ake yafi haka...." Murmushin gefen baki yayi wanda yafi kama daya motsa fuskarsa ne kawai,baisan me yasa wasu mutanen sam Allah bai halicci kunya aqwayar idanunsu ba,baisan me yasa wasu suke da saurin manta bara ba,bai cancanta idan ka aikata sharri ka mance da kayi ba,domin shi din dan aike ne,duk daren dadewa watarana zai dawowa mai shi,ta manta lokacin da 'yan uwan suka kasa tabuka komai ga rayuwarsu?,ta manta sanda suke gudunsu kowa ke qyamar hada muhalli da su?,ta manta cewa bare...baren da basu san daga ina ya fito ba shi ya tallafi rayuwarsu?,ya musu abinda kaf dinsu suka kasa yi musu?zaiso ya jefa mata dukka wadan nan tambayoyin saidai kuma a yanzu baijin yana da lokacinta,sai kawai ya saka kai ya shige dakin gadon anni.
Saman gadonta ya xube plat yana tallafe da qeyarsa da tafukan hannunsa daya hada guda biyu waje daya idanunsa a lumshe,kunnuwansa na masa tariyar kururwar maroqa dake faman kiransa da angon aysha a wancan awannin da suka shude,yana tariyo yawan jama'ar da suka halacci wajen,manyan mutane a qasar nan da wajenta,mutanen da bai taba tsammatar a rayuwarsa zaiyi tarayya da wasunsu ba.
"Lafiya dai khalipha?" Yaji muryar anni na ratsa dodon kunnensa,idanunsa da suka dan kada ya bude ya kalleta da su,sannan ya miqe ya zauna sosai saman gadon
"Ba komai....kaina ne yake dan ciwo kadan..."
"Hayaniya ko?....dama nayi xaton faruwar hakan..kasha magani?"kai ya gyada
"nasha...."
"To Allah ya sawwaqe"
"Amin"
"Batun dauko amarya...." Anni ta fada tana dubansa,baisan sanda murmushi ya subuce masa ba mai sauti,shi shaf ya manta da agender ta gaba ma ta dauko amarya
"Anni....kina son yarinyar nan da yawa...Allah yasa itama haka ne" murmushi tayi
"Khalipha yarinyar ta wahala da yawa...ya kamata zuwa yanzu tasan akwai soyayya qauna da tausayi a ban qasa....ya kamata taji yadda sauran mutane suke ji idan suka samu mai nuna musu qauna....kasa a ranka amana ce zaka riqe saboda Allah,kar ka sanya cutarwa ko matsantawa a tsakaninku,ka bata 'yancinta wanda bai sabawa addini da shari'a ba" hakanan yaji zuciyarsa na bugawa da kalaman anni...yanajin kaman ta dora masa wani qaton dutse saman kanshi,sai kawai ya miqe
"Qarfe nawa zasu je tahowa da itan"
"Kaman biyar ko shida"
"Ba damuwa......" Tare suka fito da annin ya fice daga sashen nata ya koma nashi bangaren don yana buqatar kadaicewa baya son hayaniya ko zai damu ciwon kan nashi ya sauka,bai jima da shiga ba bacci yayi awon gaba dashi mai nauyi,bai tashi farkawa ba sai qarfe hudu da rabi,subhanallahi ya ambata ganin lokacin sallah ya qwace masa,da sauri ya dira daga gadon ya wuce toilet ya kama ruwa yayi alwala ya fito ya tada sallah.
Yana tsaka da azkar din yammaci biyar saura mahmoud ya kirashi
"Wai ina ka shiga ne?"a kasalance yace
"Ina cikin gida"
"Anya kuwa?....irin wannan murya kodai amarya ce...." Tsaki khalipha yaja,mahmoud yana magana kaman baisan komai kan auren ba
"Me yake faruwa?" Ya jeho masa wata tambayar daban
"Maganar dauko amarya fa?....sai yaushe?"
"Biyar zuwa shida anni tace"
"Toh ba damuwa...ciwon kan fa?"
"Da sauqi dai...baikai na dazu ba"
"Allah ya qara afuwa...zan sake nemanka"
"Okey" ya fada yana katse wayar yaci gaba da azkar dinsa kafin daga bisani ya lula duniyar tunani.
Qarfe biyar da rabi yana shirin shiga wanka ko zaiji qarfin jikinsa kiran mahmoud ya sake shigowa
"Mun fito da dukka motocin nan fa yau ne yafi cancanta ayi amfani da su,dasu xamu tafi daukota" idanuwa ya zaro yana mamakin mahmoud
"What....mahomud dukka sababbi ne...kasan me zanyi da su,wai kana nufin duk yawansu dasu zaku tafi kaman zaku taron president?"
"Tafi president ma" ya fadi yana katse kiran,sauke wayar khalipha yayi yana binta da kallo cike da mamaki,kada kai kawai yayi ya shiga toilet din ba tare daya sake bi ta kan mahmoud ba.
Gaba daya layin ya dinke tsaf da jama'a,koda bakasan wajen ba idan kazo wucewa zaka san cewa biki ake,daga cikin gida kuwa bangaren asma'u amarya an gama shiryawa tsaf,ko irin kunyar nan tsoro da fargaba na amare babu ita tattare da ita,kwalliya ta tsara sosai kamar ranar ne ma ake dinner din tata,qawayenta 'yan bana bakwai kewaye da ita suna sake tunzurta tare da hirarrakinsu,lubna qawarta wadda itace ta biyu baya ga mai sunanta husa ta shigo tana cewa
"Guy din nan ya gama fitowa dake asma...ke kinga sabbin motocin da suka jere a layin nan kar da su,da alamu ma ba'a taba hawansu ba,iya ganinka sune kala daya yadda kikasan za'a rakiyar shugaban qasa?,wata boyayyar ajiyar zuciya ta saki sannan a fili tayi far da ido,dukkan fargabarta na tafiya,ta boye dukkan wani gata da aysha ta fita tsoronta kar a barota ranar da za'a kaisu,ta toshe duk wata kafa da zata fidda labarin aljannar duniyar da aysga ta samu,tana tsoron kar a daukan amarya suyi shirin da zai rusa nata,wanda kallo zai koma sama,maimakon a kalleta ya zama ayshan itace abar kallo,ashe da wasa hamid yake mata daya gaya mata cewa mota biyu xai kawo shi baya son hayaniya azo a cika masa gida a bata masa waje,tunda ya fada ta kasa challanging dinsa don kar yayi fushi,amma kuma a farga take na kada ya aiwatar da abinda ya fada din,ashe ma wasa ne
"kice yau muma ranarmu ce...idan da rabo muma sai kiga mun dace da wani don din fa" inji nusaiba wanda maganarta ta farantawa da yawa a wajen rai,shewa suka saka sannan suka shiga tafawa cikin walwala da nishadi,asma'u kam ji take kaman ta shide don dadi,kanta ya sake fasuwa,taji ba komai bane don aysha ta fita da gida tundaya kankarota a nan,kuma zata ci gaba da toshe duk wata hanya da qawayenta zasu san mijinta sama yake da nata mijin.
Ta bangaren aysha kuwa tana yin komai ne bisa umarnin aliya,tun dazun da daddy yazo ya musu nasiharsa da bankwana na qarshe take jin kamar idan ta fita daga gidan ba zata dawo ba,kaman tace ta fasa auren...kamar tace ta fasa tafiya,suyita zamansu dasu asma'un tana daurewa halayyarsu,tabbas sabo mugun abu ne,sabo turken wawa ne,batasan da wanne baki zata yiwa daddyn godiya ba,batasan cikin addu'o'i wacce addu'a ya cancanta tayi masa ba,saidai kowa tayita roqa masa gafara da rahamar ubangiji har qarshen rayuwarta,tana zaune saman doguwar kujera a gaban mudubi aliya na shiryata,sunyi fada yafi sau nawa,duk abinda ta saka mata sai ta cire,duk abinda ta goga mata saita goge,saida aliyan ta nuna fushinta sannan ta tsaya ta mata madaidaiciyar kwalliya wadda ba qaramin kyau tayi wa ayshan ba,kamar ka sace ta ka gudu,kwalliya mai sanyi babu hayaniya ba cin waje,tana tsaka da fesheta da turare wayar aliya ta dauki ruri,da hannu daya ta daga saboda dayan ya baci da hoda ta kara akunneta
"Okey...okey to shikenan" ta ambata,wayar ta datse tana fidda murmushi idonta akan aysha
"Ko iya haka aka tsaya khalipha ya faranta min....na gode masa qwarai" saita dubi 'yan uwan ayshan dake dakin tace
"Duk motar da kuka gani baqa mai dauke da wani tambari a jikinta motocin daukar indo ne...ku shiga duk wadda kuka ga dama,ko kowacce mutum mutum daya zata dauka motocin sun mana yawa....duk wanda ya muku magana koya gaya muku maganar banza ku mayar masa" dariya suka sanya aysha na binsu da kallo,tun jiya aliya ta zige su baki daya,sun kuma hau,kowa yasan yanayin yadda wasu yaran karkarar suke bare yanzu da aliya ta sake tunzurasu,murya qasa qasa don sam bata son magana tace
"Aliya....kin zama babbar kwabo...ke kike sake tunzurasu" idanu aliya ta fito da shi tana tsayawa daga rolling mayafinta da take tana duban aysha
"Kin manta abinda hausawa suka ce?...rana dubu ta barawo rana daya tak tamai kaya...shekara nawa ana abu daya...so ba ruwanki malama ki barmu yau mu huce takaici" bakinta kawai taja ta tsuke,tasan tunda ta niyyata sai sun adar,tana kallon aliyan ta fice daga dakin.
A corridor ta samu mamanta wadda daga dakin mummy take tayi mata Allah ya sanya alkhairi,aliya na ganinta ta mele baki
"Kai mama...sai da kika mata Allah ya sanya alkhairi bayan baso take ba na 'yarta kawai takeso" daquwa maman ta watsa mata
"Gidanku ja'ira...koma meye ba daga yau ya qare ba?,Allah ya qaddarawa kowa qaddararsa?"
"Shikenan mama....ga masu daukan ayshan can sunzo bari na yiwa su gwaggonta magana....."
"To shikenan...bari na shiga mu gaisa".
Wayarta ta daga ta kira mahmoud wanda suka jone a matsayinsa na babban abokin ango ita kuma babbar aminiyar amarya,bakin daya daga cikin motocin ta qarasa tana qarewa motocin kallo a fakaice,ita kanta abun ya qayatar da ita,yawansu da kyan motocin da yadda suke daukar ido,magana sukayi da shi ta gaya masa duk matar data shiga motarsu gidan aysha za'a wuce kawai sannan ta dawo ciki,tun daga farfajiya zuwa falon godan take jin ana zancan motocin da suka zo daukar asma'u,kowa na zuzutasu hadi da yabawa,dariya take sosai cikin ranta tana qissima yadda dramer zata kaya,lallai yau akwai film guda a sanda asma'u ta fahimci meke faruwa,yau zata gane a rayuwa kafi wani ne wani ya fika,kuma dole kai qasan wani kake komai kyanka,iliminka dukiyarka ko nasabarka.
Sanda ta shiga dakin bata taddasu aysha ba,su gwaggo sun miqa ta wajen mummy da nufin suyi sallama,kalaman da aysha tayi ga mummy ba ita kadai ba har wanda ke wajen ya tabasu,wannan karon duk da yadda mummyn kejin zafin aysha...jin zafi mara dalili ta daure tayi mata fatan alkhairi,kuka take sosai cikin mayafinta,kukan rashin uwa,uwar da zata tallafeta ta rungumeta,kukan rashin uwar da zata gaya mata dokoki da hanyoyin zaman gidan auren,uwar da zata nuna alhinin na haqiqa saboda sun raba muhalli...uwar da zata roqa mata salama da samun tabbatuwa da zaman lafiya a sabon muhallin da zata soma rayuwa,yau jinta take cikin matsanancin quncin da zata iya cewa tamkar ninka mata shi akayi,a haka take takawa tana ficewa daga gidan,kuka na sarqe numfashinta kamar zata shide.
Kowa ya san yadda mata keda kwadayi da rububin zuwa gidan amarya,hakan ce kuwa ta kasance sanda aka soma bude motocin daukar aysha,dangi da 'yan uwan da kaso tara cikin goma na asma'u ne suka soma duruwa ciki,suna tsammamin motocin rakiyarta ne,don da yawa daga cikinsu suna da kabarin irin mijin da ayshan zata aura,basu da labarin yadda lamari ya sauya lokaci daya,so babu wanda ya kawo cewa mijin nata zai iya aiko da wadannan motocin bare suyi tunanin nata ne,a haka labari ya bazama cikin gida masu son zuwa kai amarya wadanda basu da ababen hawa suka soma fitowa.
Farida ce ta shiga dakin da asma'u da qawayenta suke ta sanar musu an soma tafiya fa,a sannan wata yayar mummy ta shiga ta kai asma'un wajen mummy don suyi sallama,ba wata sallama bace ko wasu kalamai illa kuka da suka dinga yi,saida aka riqe asma'u wanda kusan rabi pretending ne,don dai kawai kar aga rashin kunyarta,bata tunanin don zata koma zama da masoyi kuma ya zame mata abun kuka,a haka aka lullube asma'u aka dannata cikin daya daga cikin motocin daukar amarya da zasu gidan aysha ba tare da sun sani ba.
*_Ya Allah,ya ubangiji ka rabamu da sharrin mutum da aljan_🙏🏽🙏🏽*
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑🏡🏡🏡💋💋💋💋💋💋
[10/02, 8:40 PM] +234 810 044 6653: *_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
*KO WANNAN NUMBER*
07067124863
*DB*
29
Ita kadai da qawayenta ne suka shiga motar,saboda a cewarta idan aka hadata da tsofaffi zasu hanasu sakewa,suna shiga ta yaye lullubin kanta tana kallon cikin motar,ita mayyar mota take ta burgeta,tayi mata kyau sosai komai yaji,tana ji a ranta ita ko irinta zata sa mahmoud ya siya mata,nan suka rare cikin motar abinsu kamar ba amarya ba,ta yiwa driver magana ya saka musu waqa,saida suka zaba daya daga cikin waqoqin mutanen kudu
"Asmaa....haka friends din hamid suka hadu?....ke kinga wani guy dana gani a cikinsu kowa....ke inaga rabo ke kira na nazo bikinki" cewar husna duk girman kanta da fadin ranta,dariya suka sheqe da ita gaba da
[10/02, 8:40 PM] +234 810 044 6653: qawayenta mutum uku,baya son qorafi baya son kuma ya qarajin wani abu ya biyo baya,tasan daddyn har yau na ciki da ita kan maganar aysha,tilas ta haqura,aka dauki yayarta daya yayar daddy daya,qawayenta biyu,qawayen asma'un biyu,abun mamakin shine sanda suka fita da amaryar akwai motoci kusan guda takwas,saidai biyu ne kawai nasu saura dangin hamid ne mata,wanda a qa'ida su zasu shiga su fito da amarya amma suka qame cikin mota ba wadda ta tako waje har aka saka asma'un cikin motar aka soma tafiya.
Qarfe tara na dare ayarin motocinsu khalipha da abokanshi suka shigo gidan,daga inda take zaune tana iya jiyo qararsu da maganganu sama sama,duka duka ba'a fi mintuna goma sha biyar ba taji motocin sun sama ficewa daga gidan,cikar mintuna ashirin taji dif alamun babu kowa a harabar gidan.
[10/02, 8:40 PM] +234 810 044 6653: tsantsar bacin ran dake fuskarta na nunawa,duk da qoqarin danneshi da take
"Motoci biyu?...motoci biyu kuma?" Mummy ta tambaya tana yatsine fuska
"Ki aika a gano miki" anty safiyya ta fada tana cire mayafinta ta wuce bandaki,don ita bata jin zata ma iya zuwa.
Kai tsaye dakin asma'u mummy ta wuce tana tambayarta zancan motoci biyu da aka ce,ta tabbatar mata haka ne,nan mummy ta hau masifa tana fadin idan ma qyashin bada motocin suke su zasu bada wadanda zasu isa
"Mummy.....kiyi haquri kawai don yace baya buqatar mota sama da biyu",wannan batun shi ya tunzura mumnyn,tana ganin kawai hamid ya shirya wulaqanta su ne,ta taya har aisha zata fisu yawan 'yan rakiya da ababen hawa?,ganin yadda mummyn ta hau sosai taqi sauka daga qudurinta na qara motoci,sannan ita ta sani idan haka ta kasance komai zai iya faruwa,saboda haka tayi hanzarin kiran daddy ta gaya masa komai,kashe wayar yayi ba tare daya ce komai ba ya nemi mummyn da kanshi ya bata umarnin ta bada yarinya a tafi kaita,a hadata da manya mutum uku
[10/02, 8:40 PM] +234 810 044 6653: ,bata iya bata amsa ba sai hannunta data kama suka shige motar anty haliman suka tada ta,tilas saura suka sake hawa motocin da aka kawosu akayi jigilar maidasu.
Tun cikin mota ta dinga jin ta muzanta,duk da cewa ba wadda ta sake ce mata komai amma saitaji a karan kanta ta tsargu da kanta,ba abinda ke mata yawo cikin idanu da kwanya irin gidan aysha,ita kanta ta tabbatar da cewa khalipha ya yayiwa hamid fintikau ya tsere masa,tako ina WUTSIYAR RAQUMI tayi nesa da qasa(daya daga cikin littafan zafafa biyar na billyn abdul),yau BURI DAYA (zafafa biyar mamuhghee)da take da shi ya cika,saidai ta raina cikar burin nata,ashe abinda take hangowa akwai sama da haka?ta yaya akai haka ta faru?,inama ace zata samu SAUYIN QADDARA(zafafa biyar na hafsat rano). Sai takwas na dare sannan ya kirata ya sanar mata zuwan motocin,anty safiyya ce ta fita sai gata ta dawo ta dubi mummy
"Sai a zabi wadanda zasu je kaita"
"Kamar yaya....kowa zaije kamar yadda aka je na indo"
"Da motoci biyun?" Anty safiyya ta fada
[10/02, 8:40 PM] +234 810 044 6653: Duk yawan motocin tsaf harabar gidan ta lanqwame su,a jere daya bayan bayan daya suka jeru sannan jama'ar ciki suka fara fitowa,kowa ka kalla ido a waje yake duban gidan,kowa tanka kyau da tsarin gidan yake,tun daga harabar gidan zuwa cikin gidan,a sannan asma'u na cikin mayafi farinciki kaman ta taka rawa,tana tsammamin ana magana ne kan gidanta,sai a sannan ta soma zagin su nusaiba cikin ranta,wato qarya suke mata da suka wassafa yadda gidan aysha yafi nata kyau kenan?,so suke su haukatata kenan saboda sunsan yadda ta tsani tayi qasa a rayuwa.
Aysha na mota tana addu'a kafin fitowarta,a sannan tuni asma'u ta isa ga katafaren falon gidan ta yiwa kanta mazauni kan daya daga cikin kujerun falon masu tsakanin laushi da taushi,ranta na haske da maganganun kodawa da yabawa gidan da take iya ji daga bakin 'yan rakiyar dake ta kunno kai cikin gidan.
Cikin nutsuwa da fargaba take takowa cikin gidan da taimakon aliya da mero
"A'ah amarya asma'u ...ya haka?,ko rakiyar qanwar taki aysha kika zo?"
[10/02, 8:40 PM] +234 810 044 6653: dayansu,nusaiba tace
"Ke husnee....bake daya ba ni kaina wlh da sakin asma zanyi na shiga motar wani guy dana gani wallahi ya tafi da ni,muna zuwa zan sauka na ware nemanshi babu sanya wallahi" kan asma'u kamar zai fashe,tana fari da idanu tace cikin magana qasa qasa yadda driver bazaiji ba wai kar tayi baran barama
"An gaya muku a banza na dagewa hamid dina....ke shifa bai mu'amala da qananun mutane wlh,kaf mutanen da yake harka da su sun isa yadda ya kamata" shewa suka sake sawa suna ci gaba da hirarrakinsu.
Duk inda motocin suka gifta sai sun dauki hankalin mutane,tambarin dake jikin motar ya sanya duk traffic jam din da suka he wucewa ake basu hanya su wuce ba tare da an tsaidasu ba,da yawa da basu san motcin waye ba zato suke wani muhimmin mutum ne ya kawo ziyara qasar,su asma'u sun lura da haka,farinciki kamar ta taka kan shege,tana sake gayawa kanta lallai batayi faduwar baqar tasa ba yadda take zato,ko a yanzu ta gayawa jama'ar unguwarsu dana garinsu ita asma'u tayi aure.
[10/02, 8:40 PM] +234 810 044 6653: bare tayi tozali da irin falon da take mafarki yau gashi ya zama mallakin aysha,ko a harabar gidan duk yadda taso ta hana idanunta ganin komai hakan ya gagara,iya fitilun da suka haske harabar gidan tarwai kamar rana kawai abun kallo ne,cikin fushi ta ciro wayarta ta soma neman lambar hamid,dama yasan ba ita ya kawowa motocin ba,yasan da haka amma yayi shuru baice komai ba,ya janyo mata abun kunya,me xai kata taka gidan aysha?,yqnzu yarinyar zata dinga tutiya da jin ita asma'u da kanta ta rakota gidanta kenan,sai data kusa tsinkewa sannan ya daga
Qoqarin controlling fushinta tayi don kada qilu ta jawo bau,duk zafin kantabtasan inda take tasan halin hamid din sarai
"Haba hamid....ya zaka yimin haka don Allah fisabilillahi....?"
"Lafiya?....keda wa?"
Ya tambaya cikin halin ko in kula,tasan halin kayanta sarai,shariya da halin idont care
"Munbi motocin daukan aysha munyi zaton ni ka aikowa da su?"
"Ni na gaya miki naki ne?...." Shuru ta danyi sannan tace
"Yanayin abunne nayi zaton nawa ne"
[10/02, 8:40 PM] +234 810 044 6653: "Ni na gaya miki naki ne?...." Shuru ta danyi sannan tace
"Yanayin abunne nayi zaton nawa ne"
"Amma ai already na gaya miki cewa motoci biyu xan kawo,kuma da sunzo din xan kira ki na sanar miki ko?"
"Habba dear ka rufamin asiri don Allah...motoci biyu kaman za'a rakiyar kaza....ai ba girma na bane...kaga motocin rakiyar aysha ne?"
"Ke bana son rainin wayo malama....haka nakeso haka na tsara...bana son hayaniya da hauka aje a batawa mutum waje ba'asan nawa ka kashe ba...ni xaki hada da muhammad mai goro?" Ya qarashe maganar ta sigar tambaya wanda bata fahimci me yake nufi ba
"Am sorry" ta fada a sanyaye
"If kina son zaman lafiya da kwanciyar hankali kibi dokata,ban kuma lamince a qara wata motar kan wadda nace ba" daga haka ya kashe kiran,shuru kawai tayi tana duban su nusaiba dake tsaye gabanta,duk yadda taso ta daure saida kuka ya qwace mata,hamid yana son ruguza ta da gadar mata da abun kunya kuma abun fada,ta yaya za'ayi rakiyarta da mota biyu kacal,anty halima ce ta qaraso wajen tana tambayar meke faruwa
[10/02, 8:41 PM] +234 810 044 6653: hakanan ko waye khaliphan da ake zuzutawa tasan bazai iya tasar ayarin motocin nan ba azo daukar aysha...ayshan data cusa masa ita tunda tasan ba ita yakeso ba ita asma'u yakeso
Ko sau daya aysha bata bari addu'a ta subuce daga bakinta ba,hannunta yana matse gam cikin na gwaggo asabe,haka mayafinta na saman kanta,saidai hawaye kam ba'a magana kamar barinsu ake,tun gwaggo na mata magana da bata baki harta haqura tayi shuru ta qyaleta.
Da yawa daga cikinsu basu gane gidan da aka xo b,saboda da yawa basu samu zuwa yi mata jere ba,hamid ya riga ya fadi adadin mutanen da yakeso suje jeran a sannan don karsu bata masa tsarin gida a cewarsa,asma'un ta biye masa saboda tsanin qauna,hakanan ta tsara mummy,ita kuma ta biyewa tsarin nasu saboda farincikin autarta qalilan daga cikinsu ne wanda basufi mutum hudu ba suka so su gane saboda banbanci qarara dake bayyane tun daga gate din gidan,suma basu kai ga yin magana ba saboda sun zaci haka aka tsara har aka shiga cikin gidan.
[10/02, 8:41 PM] +234 810 044 6653: Aliya ta fada tana murmushi,wani anu ne ya daki zuciyar asma'u,ta yamutae fuska ta cikin mayafinta tana sauraren bugun zuciyarta dason gane me kalaman aliyar ke nufi,bata kai ga wannan gacin ba muryar anty halima ta karade ilahirin falon
"Ke asma'u garin yaya kuka hau motocin rakiyar aysha?,ko haka dama aka tsara?,kin batmu muna can bilayin nemanki badon Allah yasa fatima taga fitarku ba" anty haliman ta furta da alamun bacin rai qarara ga fuskarta ta ratso falon wadda ta shigo afujajan
"What?!" Asma'u ta fada a zabure tana yaye mayafin kanta tana ware idanunta,da daya da daya idanunta ya dinga sauka kan kowanne lungu da saqo na falon tana qarewa dukiyar da aka xuba kallo a fakaice,a lokacin anty halima na fadan kuskuren da aka samu wanda da biyu take masifar,basu saurareta ba tuni suka sada aysha da daya daga cikin dakunan baccinta.
Bata iya tsayawa ta gama kallon dakin ba ta miqe a fusace ta baro falon,zuciyarta kamar zata fito,ranta na tafarfasa,sai data gwammace bata yaye lullubinta ba.
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
*KO WANNAN NUMBER*
07067124863
*DB*
29
Ita kadai da qawayenta ne suka shiga motar,saboda a cewarta idan aka hadata da tsofaffi zasu hanasu sakewa,suna shiga ta yaye lullubin kanta tana kallon cikin motar,ita mayyar mota take ta burgeta,tayi mata kyau sosai komai yaji,tana ji a ranta ita ko irinta zata sa mahmoud ya siya mata,nan suka rare cikin motar abinsu kamar ba amarya ba,ta yiwa driver magana ya saka musu waqa,saida suka zaba daya daga cikin waqoqin mutanen kudu
"Asmaa....haka friends din hamid suka hadu?....ke kinga wani guy dana gani a cikinsu kowa....ke inaga rabo ke kira na nazo bikinki" cewar husna duk girman kanta da fadin ranta,dariya suka sheqe da ita gaba da
dayansu,nusaiba tace
"Ke husnee....bake daya ba ni kaina wlh da sakin asma zanyi na shiga motar wani guy dana gani wallahi ya tafi da ni,muna zuwa zan sauka na ware nemanshi babu sanya wallahi" kan asma'u kamar zai fashe,tana fari da idanu tace cikin magana qasa qasa yadda driver bazaiji ba wai kar tayi baran barama
"An gaya muku a banza na dagewa hamid dina....ke shifa bai mu'amala da qananun mutane wlh,kaf mutanen da yake harka da su sun isa yadda ya kamata" shewa suka sake sawa suna ci gaba da hirarrakinsu.
Duk inda motocin suka gifta sai sun dauki hankalin mutane,tambarin dake jikin motar ya sanya duk traffic jam din da suka he wucewa ake basu hanya su wuce ba tare da an tsaidasu ba,da yawa da basu san motcin waye ba zato suke wani muhimmin mutum ne ya kawo ziyara qasar,su asma'u sun lura da haka,farinciki kamar ta taka kan shege,tana sake gayawa kanta lallai batayi faduwar baqar tasa ba yadda take zato,ko a yanzu ta gayawa jama'ar unguwarsu dana garinsu ita asma'u tayi aure.
hakanan ko waye khaliphan da ake zuzutawa tasan bazai iya tasar ayarin motocin nan ba azo daukar aysha...ayshan data cusa masa ita tunda tasan ba ita yakeso ba ita asma'u yakeso
Ko sau daya aysha bata bari addu'a ta subuce daga bakinta ba,hannunta yana matse gam cikin na gwaggo asabe,haka mayafinta na saman kanta,saidai hawaye kam ba'a magana kamar barinsu ake,tun gwaggo na mata magana da bata baki harta haqura tayi shuru ta qyaleta.
Da yawa daga cikinsu basu gane gidan da aka xo b,saboda da yawa basu samu zuwa yi mata jere ba,hamid ya riga ya fadi adadin mutanen da yakeso suje jeran a sannan don karsu bata masa tsarin gida a cewarsa,asma'un ta biye masa saboda tsanin qauna,hakanan ta tsara mummy,ita kuma ta biyewa tsarin nasu saboda farincikin autarta qalilan daga cikinsu ne wanda basufi mutum hudu ba suka so su gane saboda banbanci qarara dake bayyane tun daga gate din gidan,suma basu kai ga yin magana ba saboda sun zaci haka aka tsara har aka shiga cikin gidan.
Duk yawan motocin tsaf harabar gidan ta lanqwame su,a jere daya bayan bayan daya suka jeru sannan jama'ar ciki suka fara fitowa,kowa ka kalla ido a waje yake duban gidan,kowa tanka kyau da tsarin gidan yake,tun daga harabar gidan zuwa cikin gidan,a sannan asma'u na cikin mayafi farinciki kaman ta taka rawa,tana tsammamin ana magana ne kan gidanta,sai a sannan ta soma zagin su nusaiba cikin ranta,wato qarya suke mata da suka wassafa yadda gidan aysha yafi nata kyau kenan?,so suke su haukatata kenan saboda sunsan yadda ta tsani tayi qasa a rayuwa.
Aysha na mota tana addu'a kafin fitowarta,a sannan tuni asma'u ta isa ga katafaren falon gidan ta yiwa kanta mazauni kan daya daga cikin kujerun falon masu tsakanin laushi da taushi,ranta na haske da maganganun kodawa da yabawa gidan da take iya ji daga bakin 'yan rakiyar dake ta kunno kai cikin gidan.
Cikin nutsuwa da fargaba take takowa cikin gidan da taimakon aliya da mero
"A'ah amarya asma'u ...ya haka?,ko rakiyar qanwar taki aysha kika zo?"
Aliya ta fada tana murmushi,wani anu ne ya daki zuciyar asma'u,ta yamutae fuska ta cikin mayafinta tana sauraren bugun zuciyarta dason gane me kalaman aliyar ke nufi,bata kai ga wannan gacin ba muryar anty halima ta karade ilahirin falon
"Ke asma'u garin yaya kuka hau motocin rakiyar aysha?,ko haka dama aka tsara?,kin batmu muna can bilayin nemanki badon Allah yasa fatima taga fitarku ba" anty haliman ta furta da alamun bacin rai qarara ga fuskarta ta ratso falon wadda ta shigo afujajan
"What?!" Asma'u ta fada a zabure tana yaye mayafin kanta tana ware idanunta,da daya da daya idanunta ya dinga sauka kan kowanne lungu da saqo na falon tana qarewa dukiyar da aka xuba kallo a fakaice,a lokacin anty halima na fadan kuskuren da aka samu wanda da biyu take masifar,basu saurareta ba tuni suka sada aysha da daya daga cikin dakunan baccinta.
Bata iya tsayawa ta gama kallon dakin ba ta miqe a fusace ta baro falon,zuciyarta kamar zata fito,ranta na tafarfasa,sai data gwammace bata yaye lullubinta ba.
bare tayi tozali da irin falon da take mafarki yau gashi ya zama mallakin aysha,ko a harabar gidan duk yadda taso ta hana idanunta ganin komai hakan ya gagara,iya fitilun da suka haske harabar gidan tarwai kamar rana kawai abun kallo ne,cikin fushi ta ciro wayarta ta soma neman lambar hamid,dama yasan ba ita ya kawowa motocin ba,yasan da haka amma yayi shuru baice komai ba,ya janyo mata abun kunya,me xai kata taka gidan aysha?,yqnzu yarinyar zata dinga tutiya da jin ita asma'u da kanta ta rakota gidanta kenan,sai data kusa tsinkewa sannan ya daga
Qoqarin controlling fushinta tayi don kada qilu ta jawo bau,duk zafin kantabtasan inda take tasan halin hamid din sarai
"Haba hamid....ya zaka yimin haka don Allah fisabilillahi....?"
"Lafiya?....keda wa?"
Ya tambaya cikin halin ko in kula,tasan halin kayanta sarai,shariya da halin idont care
"Munbi motocin daukan aysha munyi zaton ni ka aikowa da su?"
"Ni na gaya miki naki ne?...." Shuru ta danyi sannan tace
"Yanayin abunne nayi zaton nawa ne"
"Ni na gaya miki naki ne?...." Shuru ta danyi sannan tace
"Yanayin abunne nayi zaton nawa ne"
"Amma ai already na gaya miki cewa motoci biyu xan kawo,kuma da sunzo din xan kira ki na sanar miki ko?"
"Habba dear ka rufamin asiri don Allah...motoci biyu kaman za'a rakiyar kaza....ai ba girma na bane...kaga motocin rakiyar aysha ne?"
"Ke bana son rainin wayo malama....haka nakeso haka na tsara...bana son hayaniya da hauka aje a batawa mutum waje ba'asan nawa ka kashe ba...ni xaki hada da muhammad mai goro?" Ya qarashe maganar ta sigar tambaya wanda bata fahimci me yake nufi ba
"Am sorry" ta fada a sanyaye
"If kina son zaman lafiya da kwanciyar hankali kibi dokata,ban kuma lamince a qara wata motar kan wadda nace ba" daga haka ya kashe kiran,shuru kawai tayi tana duban su nusaiba dake tsaye gabanta,duk yadda taso ta daure saida kuka ya qwace mata,hamid yana son ruguza ta da gadar mata da abun kunya kuma abun fada,ta yaya za'ayi rakiyarta da mota biyu kacal,anty halima ce ta qaraso wajen tana tambayar meke faruwa
,bata iya bata amsa ba sai hannunta data kama suka shige motar anty haliman suka tada ta,tilas saura suka sake hawa motocin da aka kawosu akayi jigilar maidasu.
Tun cikin mota ta dinga jin ta muzanta,duk da cewa ba wadda ta sake ce mata komai amma saitaji a karan kanta ta tsargu da kanta,ba abinda ke mata yawo cikin idanu da kwanya irin gidan aysha,ita kanta ta tabbatar da cewa khalipha ya yayiwa hamid fintikau ya tsere masa,tako ina WUTSIYAR RAQUMI tayi nesa da qasa(daya daga cikin littafan zafafa biyar na billyn abdul),yau BURI DAYA (zafafa biyar mamuhghee)da take da shi ya cika,saidai ta raina cikar burin nata,ashe abinda take hangowa akwai sama da haka?ta yaya akai haka ta faru?,inama ace zata samu SAUYIN QADDARA(zafafa biyar na hafsat rano). Sai takwas na dare sannan ya kirata ya sanar mata zuwan motocin,anty safiyya ce ta fita sai gata ta dawo ta dubi mummy
"Sai a zabi wadanda zasu je kaita"
"Kamar yaya....kowa zaije kamar yadda aka je na indo"
"Da motoci biyun?" Anty safiyya ta fada
tsantsar bacin ran dake fuskarta na nunawa,duk da qoqarin danneshi da take
"Motoci biyu?...motoci biyu kuma?" Mummy ta tambaya tana yatsine fuska
"Ki aika a gano miki" anty safiyya ta fada tana cire mayafinta ta wuce bandaki,don ita bata jin zata ma iya zuwa.
Kai tsaye dakin asma'u mummy ta wuce tana tambayarta zancan motoci biyu da aka ce,ta tabbatar mata haka ne,nan mummy ta hau masifa tana fadin idan ma qyashin bada motocin suke su zasu bada wadanda zasu isa
"Mummy.....kiyi haquri kawai don yace baya buqatar mota sama da biyu",wannan batun shi ya tunzura mumnyn,tana ganin kawai hamid ya shirya wulaqanta su ne,ta taya har aisha zata fisu yawan 'yan rakiya da ababen hawa?,ganin yadda mummyn ta hau sosai taqi sauka daga qudurinta na qara motoci,sannan ita ta sani idan haka ta kasance komai zai iya faruwa,saboda haka tayi hanzarin kiran daddy ta gaya masa komai,kashe wayar yayi ba tare daya ce komai ba ya nemi mummyn da kanshi ya bata umarnin ta bada yarinya a tafi kaita,a hadata da manya mutum uku
qawayenta mutum uku,baya son qorafi baya son kuma ya qarajin wani abu ya biyo baya,tasan daddyn har yau na ciki da ita kan maganar aysha,tilas ta haqura,aka dauki yayarta daya yayar daddy daya,qawayenta biyu,qawayen asma'un biyu,abun mamakin shine sanda suka fita da amaryar akwai motoci kusan guda takwas,saidai biyu ne kawai nasu saura dangin hamid ne mata,wanda a qa'ida su zasu shiga su fito da amarya amma suka qame cikin mota ba wadda ta tako waje har aka saka asma'un cikin motar aka soma tafiya.
Qarfe tara na dare ayarin motocinsu khalipha da abokanshi suka shigo gidan,daga inda take zaune tana iya jiyo qararsu da maganganu sama sama,duka duka ba'a fi mintuna goma sha biyar ba taji motocin sun sama ficewa daga gidan,cikar mintuna ashirin taji dif alamun babu kowa a harabar gidan.
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
*KO KUMA*
07067124863
*DB*
30
Annin na xaune saman kujerun falon tana nunawa magajiya da larai masu aikinta guraren dake buqatar gyaran,ko kadan bata iya zama cikin qazanta duk taron da akayi sai taga gidan ya daidaita take samun sukuni,amal ce ta ukunsu tare suke gyaran falon,duk da cewa dauriya ce kawai take nunawa,ita kadai tasan ya take ji cikin zuciyarta,tana amfani da shawarar sayyada ne kawai qawa a gareta,yau khalipha yayi aure ya auri wata ba ita ba?.
Sallamarshi ta sanya anni daga kai cikin mamaki tana amsawa idanunta a kansu,tun kafin ta qaraso jikinta ya bata ayshan ce,amal dake duqe tana goge glass din center table ta dago da hanzari jin muryarshi tana binsa da kallo itama,gabanta yayi mummunar faduwa ganin mace biye da shi,sai tayi sauri ta koma taci gaba da aikinta,saidai rabin hankalinta da dukkan kunnenta na inda suke.
Miqewa annin tayi har suka iso inda take,ta kama hannunta tana yunqurin zaunar da ita saman kujera,qasan carfet ayshan ta sulale ta zauna,da sauri anni tace
"A'ah...tashi mana,ya zaki zauna a qasa?" Bata damu da wannan ba ta soma gaida annin cike da tsantsar nutsuwa,har a sannan bata bude fuskarta ba bate annin ta ganta,cikin kulawa anni ta amsa sannan ta maida kallonta kan khalipha dake zaune dai dai saman kujera,gajiyar da yayi na bayyana qarara
"Lafiya khalipha,me ya fito daku cikin wannan daren?" Yan aikin dake falon ya kalla sannan yayi gyaran murya,jiyowa sukayi suna dubanshi ya musu inkiya da su wuce,duka suka fice daga falon har amal wadda ta aje duster din hannunta ta haura saman anni,saidai kasa wucewa tayi ta tsaya daga can step din qarshe yadda zata iya jin duk abinda ke faruwa daga parlour din.
"Ta zabi zama a nan anni"shiru annin tayi tana duban ayshan cike da mamakin yadda taqi nata gidan ta zabi zama tare da su,sannan ta daga kai ta dubi khalipha
"Anya khalipha....ita da kanta ta zabi haka?"
"Gata nan anni ki tambayeta,Allah bani nace ba..." Ya fada yana dan bata fuska alamun da gaske yake
"Aysha....yaya zaki qi gidan da akayi donminki?..." Shuru ayshan tayi,tana kunya da nauyin annin duk da bata taba ganinta ba
"Shikenan kuje ku huta...zuwa safiya saimu gaisa tunda naga diyar tawa kunyata take ji" ta fada tana murmushi,harga Allah taji dadin hakan,kodon zaman kadaici da yadda takeson ayshan ta dauketa kamar mahaifiya ta kuma saba da ita,daya daga cikin masu aikin ta kira tace takai ayshan wani dako a bata duk abinda take buqata,a nutse ayshan ta tashi tabi bayanta tabar khaliphan da annin a falo.
"Khalipha anya kuwa babu takura ga yarinyar nan?"
"Ina shiga gidan abinda tace min kenan anni"
"Shikenan saida safe ma tattauna,jeka kaima ka huta nima tashi zanyi" amsa mata yayi sannan ya miqe yana ficewa daga falon,shima burinsa kawai ya samu waje ya huta,don har yanzu ciwon kan bai sake shi ba.
A sanyaye ta juya tabar wajen zuwa dakin anni dake sama hawaye nabin kuncinta,kenan a gidan matar khakiohan zata zauna?,anya kuwa zata iya ci gaba da zama da su?,anya ko burinta zai cika?,da wannan tambayoyin amal ta qarasa dakin ta samu waje ta zauna tana qoqarin controlling hawayenta.
Yana shiga dakin kayan jikinsa kawai ya fidda ya shige toilet,haka ya sakarwa kansa ruwa idanunshi na rufe ruwan na kwaranya tun daga saman kashi zuwa qafafunshi,sanyin ruwan na ratsashi yana masa dadi a jiki saboda zafin da ake dan tabawa kwana biyu,sai a sannan ya soma jin qwaqwalwarsa na komawa kan saitinta,nauyin daya dinga ji saman kanshi da qirjinsa na sauka,nutsuwa ta soma ratsashi,ya jima sosai qasan shower din sannan ya fito ya tsane jikinsa ya sauya kaya kawai yabi lafiyar gado,don hatta shafa'i da wuturin ma ya kasa yi yau,hannunshi saman kanshi yana shafawa kadan kadan,yana son hana kanshi yin kowanne tunani burinsa kawai bacci yayi awon gaba da shi.
Qarar wayarshi da ya manta shaf ba manta ba ta katse shi
"Ya salam" ya fada cikin salo na qosawa,ya saba idan yana so ya huta yakan kashe wayarshi ne a dare har sai gari ya waye don kada wani abu ya bullo da zai hanashi samun hutu,miqewa zaune yayi ya miqa hannunshi saman side drower ya dauko wayar,number ce babu suna,a gajiye ya daga ya kara a kunnenshi,kuka ya soma ji kafin daga bisani ya gane wace,zeenart ce,kuka take masa sosai
"Meye haka ne zeenart...me kike yi ne haka?" Ya fada cikin baci bacin rai
"Yanzu ya khalipha tsakani da Allah saboda bare shine ka gujemu ka zabi bare a kanmu?...mu 'yan uwanka ya khalipha?..." Ta qarashe maganar tana sake fashewa da kuka
"Stop it zeenart.....bana son shirme don Allah da tsakiyar daren nan" yana gama fada ya katse wayar yana sakin dogon tsaki,ba don anni bama da duk cikinsu a yanzu babu wanda ya isa ya rabo kusa da shi,baijin akwai wanda zai sake kalla a cikinsu koya mu'amalancesu.
Yana shirin sake kwanciya wata wayar ta sake shigowa,tsaki ya sake ja kaman bazai daga ba sai yaga lambar data jibanci kamfaninsu ce
"Am verry sorry sir...." Ya fada cikin ladabi mai maganar ya fadi haka
"Ba matsala joe....me ya faru?"
"Sir...ka duba email dinka,zancan kwangilar nan ne nake ga kamar akwai matsala,na tura maka komai ka duba ka gani"
"Ohk...ohk" ya fadi da sauri yana kashe wayar,sannan ya sauka a nutse ya binciko inda ya aje system din nasa,sai daya kunnata sannan ya koma saman gadon ya zauna.
Aiki yayi sosai mai yawan gaske,tun yana yi cikin marmari har idanunsa suka soma nauyi suna lumshewa,tilas ya katse duk wani aiki ya zube saman gadon ba tare daya ma samu ya kashe cumputer din ba.
Daga bangaren aysha kuwa tunda mai aikin anni ta kaita dakin tana zaune daga bakin gadon,saidai zuwa yanzun ta janye mayafinta baya sosai yadda zaka iya hangen fuskarta,a hankali take qarewa dakin kallo...,dakine falle daya mai hade da toilet,akwai gado mirrow da wardrobe a ciki,komai na dakin ruwan madara ne hakanan tsarin da aka yiwa dakin dole ya burgeka,sosai ya yiwa aysha kyau ba kadan ba,shi kadaine a rea din sauran dakunan suna daga farko.
Amal ce data kasa zama tafe a gaba,kishi sosai take ji yana cik zuciyarta saidai tana qoqarin danneshi,ji take sam ba zata iya kwana ba bataga fuskar amaryar ba,tana fata bata fita da komai ba saboda watan watarana ta fata itama ta zama mata a gareshi,mai aikin anni na biye da ita dauke da kwanukan abinci,kayan tea da flask din ruwan zafin da anni tace a kawo mata ko zata buqata.
Qarar bude qofar ya sanyata saurin sunkuyar da kanta,idanun amal qyarrrr a kanta tayi sallama aysha ta amsa,suka qarasa gabanta mai aikin ta aje kayan ta fita,kusa da ita amal ta zauna cikin salon barkwanci tace
"Haba matar ya khalipha,ban taba ganinki bafa,nima rowar ganin fuskar taki zakiyimin,ai ni ba baquwar kunyarki bace saiki bude fuskar taki na gani" ta fada tana ja mata mayafin baya fuskar ayshan ta fito,sosai gabanta ya fadi sanda aysha ta dago suka hada idanu fuskarta qunshe da murmushi,bata taba tsammanin ganinta haka ba,lallai tabbas dole khalipha yaqisu kafataninsu,ko ita da take mace ba qaramin kyau ayshan tayi mata ba balle da namiji,ba shakka ko itace zata qisu din ta zabi ayshan,da qyar ta hadiye wani abu daya tsaya mata a wuya ta miqe tana cewa
"Ni suna na amal,cousin sis din ya khalipha,ga abincin nan ko zaki buqata,akwai toilet gashi can cikin dakin,akwai kayan bacci a wardrobe,ki kwanta ki huta matar ya khalipha" ta fada taba murmushin yaqe tare da juyawa zata fice daga dakin,banbarakwai aysha taji da sunan da amal din ta bata na qarshe,wai matar khalipha
"Na gode" ta fada a hankali,sai amal din ta juyo tana kallonta, sannan tace
"Babu komai" ta qarasa ficewa daga dakin gami da ja mata qofa,kuka sosai ta rushe da shi sanda ta shiga dakinta,bata ga wata hanya ba,bata ga wata kafa da zata shigewa khalipha ba,ko ina a toshe yake.
Aysha kuwa bandakin ta shiga tayi fitsari sannan ta daura alawa,bata buqaci kayan bacci ba ta ware mayafinta da yake babba ne mai kauri tayi shafa'i da wuturi ta maida kanta ta kwanta,tana jin gajiya na nuqurqusarta,duk da cewa ba wani zirga zirga tayi ba don bata dauki hidimar da dumi ba.
To sai nace asuba ta gari ahalin gidan mai goro .
************************
A gurguje ya shirya ganin har sha daya na safe bai fita cikin gida ba,bashin baccin kwana da kwanaki ya tabbata shi ya danneshi,cikin qananun kaya ya shirya ya fito yayi tsaf da shi kamar kowanne lokaci,sannan ya zira takalminsa half cover ya fito zuwa sashen annin.
Falon nata shuru babu kowa,hakan ya alamta masa wataqila itama gajiya ta hanata fitowa da wuri,yana shirin wucewa zuwa dakinta sai gata ta fito,fuskarta wasai da fara'a ta tarbeshi,cikin girmamawa kamar yadda ya saba ya gaidata
"Yau duka munyi nauyin bacci,don har masu aikin basu jima da gama abincin kari ba,yanzu nake shirin kiranka a waya dama,mun bar baquwa ita kadai bamu bata abun kari ba,bamu san yaushe ta saba cin abincin safe ba" murmushi kawai yayi don ko shi dinma baisan yaushe take karyawa ba,kar yaje yayi magana kuma ya kwafsa shi yasa ya zabi yayi shirun
"Dubata khalipha ta fito mu karya baki daya ko?,hakan zaifi" ba haka yaso ba amma bazai iya cewa a'ah ba,saboda haka ya aje wayoyinsa ya wuce zuwa dakin.
Fitowarta kenan daga wanka tana gaban mudubi bayan ta gama shafa mai tana gyara dogon gashinta,wanda ba yadda aliya vatayi da ita a biki ba suje ayi mata gyaran kai amma sam taqi,tafi ganewa ta gyara abinta a gida da kayan gyara na gargajiya,tunda yana santsi da tsaho abinshi,jin ana kiciniyar bude qofa ya sanyata yayar mayafinta ta yabawa kanta baima yafu a dai dai ba,tayi tsan tana jiran taji wanda zai shigo.
Da sallama ya shigo suka hada idanu kasancewar idonta na bakin qofar,amsawa tayi tana saukar da idonta qasa,idanunshi yakai kan saman goshinta dake kwance da sumar da bai taba gani ba,tunda ko yaushe cikin hijabi da dankwali take bata bari sumarta ko daya ta fito,dauke kanshi yayi yana jingina da bango
"Ina kwana" ta gaidashi da muryarta mai sanyi,masa mata yayi da
"Lpy lau ya kwanan baqon waje....anni tace ki fito mu karya"
"Toh" ta bashi amsa,saidai bata iya motsawa ko ina ba saboda tana son ta qarasa shiryawa ne,ya karanceta sai ya juya yaba yunqurin bude qofa yace
"Idan kin gama ina qofar dakin" ya qarasawa fice,a gaggauce ta daure gashinta ya daura dankwalinta sannan ta gyara yafen mayafin nata ta fito.
Yana gaba ne tana binsa a baya har zuwa cikin falon,kallonta anni take fuskarta qunshe da murmushi ,tausayinta ayshan na sake ratsa zuciyarta
"Kyakkyawar yarinya mai shekarun da basu haura a shirin ba,ya ilahi ko meye aibunta oho?" Anni ke tambayar kanta,tamkar aysha zata nutse haka taji sanda anni ta miqa mata hannu suyi musabaha,sai ta rasa inda zata tsoma kanta,khalipha na jingini saman kujera kamar mai shirin yin kwanciyar rigingine yana noticing abinda yake faruwa,murmushi anni tayi
"Ki daukeni kamar uwa wadda ta haifeki aishatu kinji,daga yau nan gidanku ne,bana so ki sake tuna wani abu daya faru dake a baya,ya zama tarihi daga yau da yardar Allah" kai ta gyada cikin tsananin kunya,har yanzu ta kasa kallon annin
"Muje muci abinci.....bansan me ya hana amal fitowa ba har yanzu,duba min ita khalipha" ba'a son ranshi ba ya miqe zuwa dakinta,a lokacin tana zaune saman kujerar mudubi bayan ta fito daga toilet data shiga ta wanke fuskarta saboda kukan data ci,knocking yayi mata ta tambayi waye
"Ki fito inji anni,tym for breakfst" daddadar muryarshi ta daki dodon kunnenta,saita lumshe ido kamar yana tsaye a gabanta,lumshe idanun daya fito da wasu sabbin hawayen,tuni yayi gaba bai tsaya jin me zata ce ba,saidata sake wanke fuskarta ta goga hoda da kwalli sannann ta fito.
Dauke idanunta tayi da sauri sanda idonta ya sona tozali da aysha daje zaune saman kujerar dining idanunta a qasa ta kasa sakewa,fresh skin dinta,manyan idanuwa da zara zara eye lashes,qaramin bakinta komai dai dai kamar wadda ta zana,kai ko ita ta zana bata jin zata zana mai kyau kamar wanda Allah ya bata din,sai data zo gab da su sannan ta iya dauke idanunta,ta qaqalo murmushin dole ta sorawa fuskarta tana jan kujera daya wadda ke daura da khalipha ta zauna tana fadin
"Amarsu ta ango" kunya maganar ta baiwa aysha,gaisawa sukai sannan amal din ta gaida anni,annin na tamabayarta ko gajiya ce ta hanata fitowa,amsa mata kwai tayi da eh amma ita kadai tasan meke cin zuciyarta,kusan dai cin abincin su uku suka yishi banda aysha,ta kasa taba komai,ji take kamar kowa ma kallonta yake,amal dinma kawai qarfin hali take tana tsakura tare da basarwa,har suka gama babu abinda aysha ta iya kaiwa bakinta,anni nata qorafin hakan khalipha na jinsu,kusan baida wata idea kan halayyarta shi yasa baida abun tofawa.
Sanda ya miqe ne anni tace masa
"Ya kamata ka wuce sashenka da ita sai ta samu taci wani abin a can tunda a nan ta kasa sakewa taci komai,zan turo muku badi'a ta tayaku gyaran wajen ko?"
"Ohk...zanyiwa kamfani magana ma akwai gyare gyaren da za'a yiwa wajen"
"Ya kamata....aysha kuje yanzun zan turo badi'a"amsawa tayi sannan ta miqe tabishi a baya suka fice.
Kamar mai tsoron wani abu haka take biye da shi a baya,tana jin fargaba da tsoro hakanan,a haka suka isa sahen nashi ba wanda yace komai da dan uwansa.
Kallon farko wajen ya burgeta sosai,komai a tsare a tsaftace kamar sashen mace,qamshi yake fiddawa sosai da alama qamshin ya kama wajen,babban parlour wanda ke tsare da kujeru blue black,rugs da curtains dun falon duka kalarsu kenan,sai kayan kallo daga gefe daya wanda aka musu bango gudada yasha ado mai daukan hankali,daga kowanne kusurwa na falon manyan hotunan khalipha ne window size kaman zaiyi magana,wanda suka fitar da ainihin halittar da Allah yayi masa,kowanne hoto akwai murmushi kan fuskarshi,akwai dakuna guda uku,daya bedroom ne biyun suna rufe batasan ko meye a cikinsu ba,saidai dayan dakin study room ne da wanda ya maidashi kaman qaramin office dinshi na gida wanda aka daga bayanshi aka yiwa wata qofa ta glass da zaka iya habgo bayan gidan dake cike da shuke shuke,isaka mai kyau takam shigo masa shi yasa yake jin dadin zaman wajen sosai,dayan kuma ya barshi ne a dakinsa na motsa jiki wanda shima yana da wata qofae daban bayan ta cikin falon.
Dubanta yayi har yanzu fuskatta na qunshe yace mata
"Ga guri ki xauna....." Soma takawa tayi a hankali wanda ada tana tsaye daga bakin qofar falon,cikin rashin sani santsin door mat din dake bakin qofar ya debeta
"Subhanallahi" ya fada da sauri,Allah ya taqata ta dafe qofar qirjinta na bugawa,tsayawa yayi cak sannan ya sake dubanta
"Ki cire wannan lullubin haka....ni wanki ne ba wani abu ba" ya fada ranshi daya
"Me dame kike buqatar a dauko miki a can gidan?" Ya tambayeta yana jin banbarakwai don bai saba hada daki da kowa ba bare mace bayan ta zauna kan daya daga cikin kujerun
"Kayan sawa na suna nan cikin akwati"
"Kawai?" Ya sake tambayarta,kai ta kada masa sai ya juya ya fice,dai dai sanda mai aikin ta sako kai da kayan abincin,cak ta tsaya ta duqar da kanta cikin girmamawa ba tare da tace komai ba,hannu ya sa ya karbi farantin daga hannunta ta juya ta koma dama tasan dokar ba'a shiga mishi bangare.
Da sallama ya sake shiga ta amsa tana dubanshi,sai suka hada ido,ta sake jan mayafin nata gaba kadan,tabe baki yayi cikin ranshi yana fadin
"Sai wani faman rufe fuska kaman mara gaskiya,ko tana tunanin ina kallonta ne?" Itako cikin ranta cewa take
"Me yasa yakemin hidima da kanshi" ta fadi haka ne saboda matsayin data lura yana da shi,saman dan teburin dake daura da ita ya dora farantin sannan ya juya ya fice.
Sashen anni ya koma,tana zaune yanzun saman kujerar falo,dubanshi tayi
"Sai ina kuma?,zama ya kamata kayi khalipha sosai da ita har ta sake damu,na lura tana da baqunta sosai"agogonshi ya duba sannan yace
"Ba abinda aka taho dashi daga can gidan anni,dole naje naga me za'a dauko din kafin agama gyaran nan,sannan kuma ma ina da baqo.....na masa alqawarin zamu hadu yau,ina zaton kin sanshi abokin hudar abba ne tun yana raye....saidai kaman yaro yake a wajenshi,so sun saba tun a sannan abba na ara mishi kudade daga bisani ya maidowa abba da kudinsa idan ya juya an samu riba,to yanaso ne yanzun yaci gaba da wannan mu'amalar da ni,ina da dan alamun tambaya ne akan kasuwancin nashi,sannan ina tantama kan yiwuwar harkar tamu da shi saboda yanayin yadda na lura da rashin iya tattalinsa,da kuma rashin qwarewarsa wajen juya kudi gaskiya akwai matsala"ajiyar zuciya anni ta sauke
"Tunda har yana hurda da mahaifinka a baya bai kamata ka hanashi ba,abinda zakayi shine ka bashi a matsayin gwaji...sai kaga me zai biyo baya ko?" Kai ya gyada
"Haka ne anni....sai aci gaba da yi mana addu'a"
"In sha Allah....Allah yayi jagora"
"Amin" ya amsa sannan sukayi sallama ya fice.
Ruwan tea kawai ta iya sha cikin kayan da aka kawo din don ba kasafai ta fiye ciye ciye ba,hakanan ma ita sam yau bata jin yunwa,da haka ta hade kayan waje guda ta jingina da kujerar,zuciyarta da gangar jikinta najin gajiya na sauka kadan kadan daga jikinta,idanunta na gilmawa cikin falon tana yaba tsarinsa da kyansa,kwata kwata baiyi kama da falon namiji ba,da daya da daya tana kallon komai har idanunta ya sauka kan hoton khalipha wanda yake opposite dinta.
Yana sanye da kufta ruwan hanta,da hula dara da rufaffen takalmi,yayi murmushi sosai yana kallon kyamarar ya daga hannun damanshi sama kaman yana yiwa wani bye bye,sosai take kallon hoton tana qarewa khaliphan kallo,karo na farko data taba tsayawa ta kalleshi tun daga kanshi zuwa qafa
"Fatabarakallahu ahsanul khaliqin" ta furta a ranta,sai yanxu ta yadda da zancan aliya data ke gaya mata khalipha mai kyau ne,irin kyan da ba kasafai ake samun maza da shi ba,banda yau da zata iya rantsewa shacu fadin aliya ne tunda bata taba tsayawa ta kalleshi haka ba,a karan kanta taji tana jaddawa dawa kanta tayi iyakar iyawarta wajen tsayawa a matsayin qanwarsa,tabbas koba dade koba jima matar khalipha na tafe.
Daga wannan tunaninta ya gangaro kan mahaifiyarta,tunanin da rana bata fitowa ta fadi ba tare data yishi ba sau babu adadi,a hankali take nazarin labarin da gwaggo asabe ta bata,tana tuna duk wata kalma guda daya ta cikin labarin bata bari ta subuece mata ba,umminta tayi nisa,nisan da ba'ajin kira,abun ya ratsata shekarun da aka dauka ba wasa bane,wa zata kama?,wa zai taimaketa,wa zai taimaka mata ta dawo da umminta hayyacinta?,a qalla a yanzu ta samu sauqin wasu abubuwan ta wasu fannin,tunda har gashi dangin ummin da dangin mahaifinta suka iya tarayya waje guda lokacin bikinta,abinda iya zamanta bata taba gani ba,kusan yanzu babbar matsalarta shine yadda zata farkar da ummin nata,yadda zata samu soyayyar uwa kamar kowanne d'a
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil,wa ufawwidu amri ilallah,innallaha basirun bil ibaad" ta shiga maimaitawa sau babu adadi kan Allah ya kawo mata dauki,a haka bacci yazo yayi awon gaba da ita.
Bata tashi farkawa ba sai dai dai lokacin sallar azahar,duka sai take jin wani iri babu dadi jikinta saboda bata saba zaman dabe ba haka ba a gida,toilet ta laluba a nan parlourn ta daura alwala ta tada sallah.
Daga can wajen anni kuwa duka hankalinta na wajen aysha har sanda aka kammala abincin rana,da kanta tasa aka shirya komai tacewa mai aikinta ta dauka ta kai mata,karba amal tayi ta wuce da shi don tana son sake tabbatarwa da kanta haka ayshan take?
Tana shirin fita daga kitchen din haidar ya shigo,baya ta danja kadan ya samu ya shigo din saboda tasan halinshi sarai,haka nan yaqi jininsu batasan dalili ba,saidai dalilin kusa yayi shige dana khalipha ne,a sanda dukkan abinda ke faruwar ya farun haidar nada dan sauran wayo,yana tuna wasu abubuwa daga ciki,yana da zuciya sosai shi yasa shima ya kasa mantawa,dalili kenan ma da sukaqi zaman gidan gaba daya da aka tashi hidimar bikin,suka koma gidan wani abokinsu shi da mus'ab dake bayan layinsu.
A ladabce kaman yadda suka saba ya gaida anni
"Ina mus'ab ne?,ai an gana bikin sai ku dawo gida hakanan ko?"
"Yau in sha Allahu....munyi missing dinki anni..." Murmushi kawai tayi tana dubanshi sanda yake duba abinda aka dafa,donshi ba daga nan ba wajen son abinci musamman mai dadi,kusan halayensa suna mata kamanceceniya dana khalipha.
Sanda ta shiga tana zaune saman abun sallah data samu kan hannun kujera,da murmushi kan fuskar ayshan ta amsa mata sallamar,amal din ta qaraso ciki idonta na kan ayshan wadda,ranta yacu gaba da suya irin na kishi gami da fargaba,lallai adazune ma bata kalleta sosai ba qila saboda kada wani ya gano kallon qurillar da take mata
"Ya bakici komai ba?" Amal din ta fada tana bubbuda abincin,murmushi ta sakeyi
"Naci mana"bata sake cewa komai ba don bata jin zata iya sake cewa din ta aje mata wancan kwandon ta dauki dayan ta fice,sai ayshan ta bita da kallo saboda ta fuskanci kaman ta dan sauya,gabanta ya fadi taji babu dadi a ranta,wataqila taji rashin dadi ne saboda bata ci wani abu ba a dazun,ita kuma taci iyakar cikinta kenan,bazata so ta soma bata musu ba daga kwana daya tak cikin gidan,saboda haka ta sauko ta zuba abincin cikin plate,ita kanta tasan ba zata iya cinyewa ba amma haka ta dinga cusawa har sai data ji tana son yiwa kanta illa sannan ta rufe.
Ba dadi haka cikinta yayi mata,hakan ya saka ta tashi ta soma dan kade kade a falon da goge ko zai zazzage,abinka da wadda ta saba sai kawai ta zarce da shara,ta gyara falon sosai duk da ba'a hargitse yake ba,amma komai nason gyara take ya sake kyau da qyalli,sanda ta gama uku ta gota,sai ta sake alwala ta kuma zama tana jiran sallar la'asar,ita irin wannan zaman sam bata saba da shi ba,shi yasa take jinta kamar cikin kurkuku.
_Ya Allah ka rabamu da sharrin mutum da aljan_
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
*KO KUMA*
07067124863
*DB*
31
Ana gama sallar la'asar mai aikin anni tayi knocking qofar,bata tambayi waye ba don tasan koma waye dan cikin gidan ne
"Anty....anni tace in duba mata lafiyarki" murmushi tayi tana jin dadi har cikin ranta,ganin ta sake samun dadin masoya a fadin duniya
"Lafiya lau...ko zaki yimin jagora na koma ciki?"
"Babu damuwa" itama ta amsa sauqin kan aysha na burgeta,takalmanta kawai ta zira ta maida qofar ta rufe kamar yadda ta sameta tabi bayan mai aikin suka jera
"Anty meye sunanki ne na gaskiya"
"Aisha sunana....zanfi jin dadi idan kika kirani da shi" bako ta kama sannan tace
"Wane mutum...uwar masu gida ce fa,ni na soma sunan anni kenan ai" murmushi aysha tayi har cikin ranta taji dadi,haka suka ci gaba da takawa raliya na sakowa ayshan hira jifa jifa.
A falo suka tadda annin,da fara'a take kallon aysha
"Raliya karkicemin tasota kikai"
"A'ah wallahi hajiya...ita tace min zata taho"
"Auho....shikenan to,tafi ki qarasa aikinki" wucewa kitchen tayi yayin da aysha ta zauna qasan carfet kusa da annin,annin ta lura kamar dabi'arta kenan,batayi mamaki ba duba da yanayin halayyarta da rayuwar data taso,zataso ta saki jikinta da ita,ta dinga jinta kamar mahaifiyarta
"Aishatu ya zaki zauna a qasa?,na gaya miki nan fa kamar gidanku ne" murmushi tayi kanta a qasa ta girgiza shi
"Nan ma yayi na gode"
"Kinqo sakin jikinki dani har yanzu 'yata,bana son ki dinga kunyata,so nake ki saki jikinki kamar khalipha kike a wajena"
"Na gode" ta furta a hankali tana mamakin sauqin kai da son jama'a irin na annij,duk da dukiyar da suke da ita amma sam bata ganinta.
A hankali anni ke jan aysha da hira duk don ta saki jikinta,saidai maganarta bata wuce eh ko a'ah,a haka amal ta cimmasu,zaman nasu sai ya dan taba ranta,da dane ita annin zata nema,amma gashi tun ba'a je ko ina ba kwana daya kacal annin ta soma sauya sheqa,hakan ya sanya tayi shuru bata fiya sakawa hirar tasu baki ba da yawa,duk da anni na sakota,saita dauki remote kawai ta canza tasha,saidai rabin hankalinta na kan hirar tasu.
Biyar da rabi na yammaci ya dawo gidan,da sallama ya shigo parlour din dukkansu suka amsa masa,idonshi ya sauka akanta,yadda take zaune a darare ya kalla sannan ya maida dubanshi ga anni,itama shi take kalla tare da yi masa sannu,ya samu daya daga kujerun ya zauna yana zare takalmin qafarsa yana dan cije lips saboda yadda yaji yatsunsa sun riqe,dora qafarshi yayi saman daya cinyar tasa yana lanqwasa yatsun nashi,a sace aysha ke kallonsa,abinda ta karanta cikin qanqanin lokaci kamar shine jigon gidan,bata taba ganin mahaifinsa ba hakanan bata taba tambayarsa ba game da mahaifinsa,sai taji kamar bata kyauta ba,yasan komai game da rayuwarta,ya damu da komai nata amma itabtaba taba karar tambayarsa komai nasa ba,duk da cewa ta sani a sannan data tambayeshin ba lallai ta samu gaskiyar abinda take son ji ba,tunda ta sigar daya zo mata daban,haduwar tasu tazo ta wani bahagon yanayi,bayan daurin boyen daya qulla yazo da shi a haka da fuskar daba tasa ba,har yau tana mamakin me yasa ya aikata hakan kuma tana son taji dalili,a sacen ya dubeta shima yana jin rashin kyautawarsa na wuni guda ya kamata ko sau daya ya kira yaji yata wuni a baqon guri,sai suka hada idanu,dukansu kowa ya janye idonsa daga dan uwansa,yaci gaba da matsa yatsunsa sannan yave
"Ya kika wuni ya baqunta" anni ce ta amsa
"Takwarata kam akwai baqunta,har yanzu ta kasa sakin jiki muyi hira" sake satar kallonta yayi,iya zamanshi da ita yasan cewa ba kasafai taje iya buda baki tayi hira ba,murmushi kawai ya yiwa annin a matsayin amsa,ido suka hada da amal,ya dan jefa mata harara ya kauda kai,tasan me yske nufi yswi jinin tayita kallon nan nashi,sai ta basar kamar bata gani ba
"Ya khalipha wannan ai aikin amarya ne ko" amal ta fada taba son kota yaya khliphan ya kulata,Allahvyasa anni na amsa waya bata ji me ta ada ba,tsuke fuskarshi yayi kadan,ya fuskanci sassaucin da taga yana matan ta dauka wani sauqi ne,take ta shiga taitayinta,sai ya miqe yana cewa anni
"Zan shiga na watsa ruwa"
"Ba laifi...saika fito,abinci fa?"
"A kawomin anni na gaji bazan iya fitowa ba inajin sai sallar magariba"
"Allah ya nuna mana" ya amsa da amin ya dauki socks dinshi ya fice a parlour din.
Amal ce ta miqe da hanzari ta shige kitchen ta hado dukkan kayan abincin ta fito da shi,dubanta anni tayi,ko zata qyalesu akan komai banda wannan,daga daren jiya zuwa wunin yau taga matar autwn khalipha tattare da aysha,ta gano haske da albarka mai tarin yawa tatare da ita,saboda fadar ma'aiki annabi muhammad S A W da yace"ita kunya dukkaninta alkhairi ce"duk inda kaga kunya to akwai alkhairi biye da ita(qalubale gareku 'yammatan wannan zamanin da suka watsar da al'adar kunya da akasan diya mace da ita,da kin nuna dabi'ar kunya take sai a fassara hakan da cewa rashin wayewa ce take damunki,to ki sani ita kunya ado ce a wajen diya mace,kai ba yammata ba har wasu matan auren yanzu ba ruwansu da kunya,duk mace macace,hakan ita take maida kanta gold ko kuma juji idan taso,ita ke saiwa kanta mutunci ko akasinsa,Allah yasa mu gyara ko ma samu dacewa amin),to amma kome zatayin tasan sai tayishi cikin hikima,dole ta shiga tarayyar khaliphan da aysha ba tare da sun gane ba,dole tati wani abu akai
"Ai daga yau Allah ya hutassheku amal,tunda tsohon tuxurun yayan naku yayi aure,baiwa aysha ta miqa masa kawai" har cikin ranta bata ji dadi ba,amma ba yadda ta iya haka ta miqa mata,tasa hannu ta amsa.
Cike da fargaba ta tura qofar gami da sallama,tsit falon yaje alamun ba owa ciki,saitayi tsai tana tunanin inda zata aje kayan kada tayi ba dai dai ba,qarar bude daya daga cikin qofofin falon yaja hankalinta,khalipha ne ke fitowa daga dakin,boxer ne a jikinsa da singlet da alama baiyi zaton samun mutum a falon ba,don ruwa ya fito dauka,da hanzari ya koma ya dan tura qofar sannan yace ta aje saman tebur,ta jira fitowarshi,jikinta na dan bari tayi yadda yace
din,muqulli ya sanyawa qofar ya cire kayanshi ya shiga wanka.
Kusan awa guda kafin ya sake fitowa cikin shigar qananan kaya,ba qaramin kyau sukayi masa ba,sai qamshin turare mai sanyi ke tashi daga jikinsa,turaren yakai mata ko ina saidai ta kasa daga ido ta dubeshi,har ya zauna qasan carfet kaman yadda ya sameta,tayi zaton abincin zai fara tambaya sai taji yace
"An kawo miki kayanki....ki duba idan akwai abinda babu saikiyi magana...babu baqunta ba nauyin baki....kinga anni ta soma damuwa da rashin sakewarki,bana son kuma ta zargeni,kiyi qoqari ki zama normal"
"Toh..na gode" ta fada tana wasa da yatsunta,kallonta yake yana karantarta,ya lura halayyarta kenan,sai ya dinga kwatanta yaya take iya zama da asma'u,mai surutu rawar kai wulaqanci da isgili
"And..." Sai kuma ya danyi shuru sannan ya dora
"Bakisan komai a kaina ba,baki taba kuma tambaya ba,duk da may be baki da interest ne akai,amma ya zama dole for now kisan wasu abubuwan,ni ne d'a na fari wajen anni,ina da qanne guda uku,maza biyu mace daya...saidai macen Allah yayi mata rasuwa" ya qarashe maganar da wani irin tune wanda ke nuna akwai abinda ya soki zuciyarsa
"Allah yayi mata rahama" ta furta itama tana tuna nata mahifin
"Amin ya Allah....mu hudu ne a gidan saidai bamu hudun muke zaune ba,akwai cousins dina yaran yayye da qannen mahaifina 'yammata dake yawan zuwa,yawancinsu suna da manufarsu ta zuwa,daga yanzu kuma zuwa kowanne lokaci zaki iya ganin wata ko wadansu sunzo,main point din shine,bana so ki sake da kowa don banson raini,banson kiyi hira da kowa ki gaya mata matsalarki ko wani abu daya shafeki ko ya shafi rayuwarki,and bana so ki dinga nuna rashin sabo ko baqunta tsakanina dake,let pretend like husband and wife that r loving each other....ina fatan kin fahimta?"kai ta gyada mishi gefe daya na zuciyarta tana tunanin wanne DAURIN BOYE ne shi kuma tsakaninsa da danginsa
"Idan lokaci yayi xaki san komai" ya furta kaman yasan me take qissimawa ranta,tunanin ta katse ta gabatar masa da abincin,ta zuba masa komai ya fara ci yana sauya tashar t.vn dake ci zuwa wata wadda kusan duka labaran kasuwanci suke.
Baiyi nisa da soma ci ba ya dubeta ta gefan ido,baisan ko taci abincin ba ko bata ci ba,saidai baisan ta yaya zai tambayeta ba,baiso taga kaman ya takurata,amma sai yakejin idan bai tambayetan ba kamar bai sauke nauyin daya daukowa kanshi ba
"Kinci naki ne?" Kai ta gyada masa bayan ta dan dubeshi kadan tana jin dadi cikin ranta,yau wani ya damu da cin abincinta,taci ko bata ci ba,kalmar da bata taba jinta daga bakin wani nata ba,shuru yayi bai sake magana ba,baici da wani yawa ba taga ya ture,ya tsiyayi wani ruwa mai dumi wanda batasan na meye ba don bai kama da ruwan shayi ba yasha,bedroom ya koma ya sake dauro alwala,ya fito yana goge hannayensa da suke da lemar ruwa da handkherchief
"Zan fita sallah...ki jirani idan na dawo zamu fita dinner,haka al'adar gidan take" kai ta gyada masa ya saka kai ya fice.
A inda tayi sallar magariba taci gaba da zama,duk jikinta bata jin dadinsa saboda ta riga ta saba da wanka sau biyu,gashi tun kayan jiya ne a jikinta bata cire ba bare ta sake wani wankan,kayan nata da yace an dauko bata gansu ba da ko kayan saita sauya,sai da aka idar da sallar isha'i taji shigowarsa yana waya,ta lura yana da yawan mu'amala da waya,sai daya gama sannan ya dubeta kadan ya kau da kai
"Wadan nan kayan basu isheki ba hakanan,ina tunanin tun na jiya ne ko?" Ya fada cikin basarwa yana ci gaba da latsa wayarshi,kunya taji ta dan kamata,yanzun haka sai ya tsammaci ita din qazama ce,sai ta rasa abun cewa
"Ina tunanin ba haka amare suke ba washegarin randa aka kaisu,let me ask" ya fada yana lalubar wata lambar a wayarsa,bugu uku ta shiga suka gaisa sannan ta jiyoshi yana tambaya daga can bangaren aka bashi amsa
"Thanks" yace yana kashe wayar
"Ce mishi akayi ban sani ba da zai tambaya" ta fada a ranta.
Bai ce da ita komai ba ya sake kiran wani layin,magana yayi da batafi ta second ba ya kashe,yana tsaye yana ci gaba da latsa wayarshi akayi knocking,ya zura wayar a aljihu ya nufi qofa ya bude.
Qaramin akwati ne ya shigo da shi baby pink da adon golden me azabar kyau da daukar ido,gabanta ya aje yana gyara hannun rigarshi yace
"Ki shirya sai mu fita,kina iya using bedroom toilet dina" jim tayi kaman ba zata ce komai ba,nauyi take ji tana raya kada dai ace kallon qazama yake mata koko meye?,amma maganarshi akan hanya take bai kamata taci gaba da zama haka ba,ita kanta tasan akwai matsala tunda baquwa take wajen al'ummar gidan karsu zaci haka dabi'arta take.
A nutse ta miqe ta dauki akwatin wanda ya danfi kit girma da kadan ta nufi qofar bedroom din daya nuna mata,cike da baqunta kamar zata tadda wani abu ta tura qofar ta shiga,babban bedroom mai kyau tsari da daukar hankali,kallon farko taji ya bugeta,babu tarkace babu kaye kaye aciki,furnitures din cikin ba wasu masu girma bane medium amma kyansu dole ka kalla ka sake kalla,gadon fes qal a mulmule kaman na amarya,a sanyaye ta aje akwatin saman mirrow don kada ta bata mishi gado,ta bude shi,wani lace ne mai azabar kyau a ciki butter colour,wanda aka yiwa dinkin riga fitted da zani simple,akwai dankunne da sarqa a ciki da abun hannu,zai wani.plate din takalmi dake maqale da mayafi dukka kalar da zasu shiga da lace din,sai body cream da powder da sauran tarkacen kayan makeup duka na kamfani guda,shafa lace din ta sake yi karo na kusan uku,ko baka san kudin kaya ba kaganshi kasan cewa ba qarami bane,jikinta yayi sanyi tana jin shakku cikin zuciyarta,anya ko bata zura kai da yawa ba kuwa?,zama tayi sosai tana ci gaba da kallon kaya,bata iya tuna wata rana guda data saka kaya kamar haka masu kyau da tsada,a qalla ta kusa kashe minti goma kafin ta iya tashi ta debi kayan ta shige toilet din da su,don ba zata iya fitowa ba ta shirya cikin dakin.
A toilet dinma sai da wasu abubuwan suka bata mata lokaci da batasan ya zatayi operating nasu ba,daga bisani ta gama wankan ta tsane jikinta ta saka wadancan,har shafa man duka a bayi tayi ta gyara gshinta,sai data gama ta dawo gaban madubi ta shafa powder ta dan goga jambaki kadan daya qarawa lips dinta colour pink dinsu ya sake fita,ninke wadancan data cire tayi ta maida cikin akwatin,tana shirin rufewa taji knocking,wuri wuri tayi da idanu tana duban mayafin da aka hada mata cikin kayan,sam bashi da wani kauri,jin ana turo qofar ya sanyata ala dole taja mayafin ta yane kanta.
Dubanta yayi sanda ya shigo na tsahon minti daya,kanta na qasa tana rufe akwatin,dagowa tayi suka hada ido saiya basar,yana tuna sanda anty ruqayya ta dauko lace din ta dinga kodashi da fadin zaiyi ma mutum kyau,a sannan shidai kawai yana biye da ita ne,saboda indai ba anni ba bansan ya zai sayawa mata kaya ba,gashi dai maison ado ne da kwalliya amma baisan ya zai saya ba,kodan bashi da 'yar uwa mace,wani abu ya taba zuciyarshi a lokacin daya tuna da hajar,har hakan yasa yanayin fuskarsa ya dan sauya,duk sanda zai tuna da ita da yadda ta tafi ta barsu komai walwalar da yake ciki sai yanayinsa ya sauya
"Mu tafi" ya fada yana fita daga dakin,gaba daya jin dakin yake kaman ba nashi ba,saboda tsahon rayuwarshi ba macen data taba shiga masa daki idan ka dauke anni,takalman ta duqa ta zira a qafarta sannan tabi bayanshi,yana gaba tana bayanshi,suna dab da shiga sashen annin ya tsaya sai itama ta tsaya
"Qaraso kusa" ya fada ba tare daya waiwayo ba,kusa da shi ta qaraso din dab da bayanshi,sai ya sake matsowa baya suka dai daita tsahonsu sannan suka ci gaba da takawa zuwa ciki.
Mutum biyar ne cikin falon,anni amal da wasu maza biyu da mace daya da aysha batasan su waye ba,da fara'a anni ta amsa sallamar tasu tana yiwa aysha sannu,yayin da amal ta zubawa ayshan idanu tana dubanta ita da daya baquwar,duk kunya saita kama ayshan na yadda anni ke karramata haka,bayan ita din ba abar karramawa bace a ganinta
"Kai.....kaddai kece auntyn tamu?" Haidar ya fada fuskarsa cike da fara'a da kuma mamaki,dubanshi sukayi su duka,mus'ab yadan tabe fuska
"Yanzu zaka ce ka santa ko?"
"Qwarai kuwa"
"A'ina?" Amal tayi saurin tambaya,hararta yayi sannan ya amsa
"A school....,gaskiya yaya kayi zabe mai kyau,she was verry kind and innocent wallahi...."
"Tell us ya akayi kasan hakan?" Daya baquwar da batayi magana ba ta fada cikin yauqi,sai a sannan khalipha ya dora idanunsa a kanta,idonta daya ta kashe masa sannan tace
"Yeah...muna buqatar mu sani,angon da babu gayyata gashi mu mun kawo kanmu"
"Anni....ya kamata muci abinci haka dare yana yi" ya furta yana duba agogon hannunshi,ko daya baiji dadin zuwan rahama ba gidan,ya santa yasan halinta sarai,gwara amal sau dubu da ita,baya son takura baya son sa ido duka rahama ta hada su
"Ya kamata" anni ta fada tana yunqurin miqewa,wanda hakan ya saka kowa ma ya miqe zuwa dining area,saidai rahama data danyi jinkiri tana ta bayan khalipha
"Ya khalipha...kaman bakayi murna da gani na bako,bayan laifin boyemin bikinka da kayi baka sanarmin ba,ina niger ina nigeria?"
"Tunda kin sani yanzu no need of qorafi....."
"Amaryar tamu ma sha Allah....baka gabatar mata da ni ba"
"Da wuri haka?..." Ya bata amsa a kaikaice,bakinta taja tayi shuru kawai ba tare data sake cewa komai ba,tana gudun kada ajinta ya zuba a idanun aysha,a haka suka qarasa wajen,amal dake ankare da duk abinda ke faruwa tana tsaye kishi ya hanata zama,har sai da kowa ya zauna sannan ta soma serving din kowa da abinda ranshi keso,kala biyu suke girki duk dare,saidai basa yin mai yawan da zai zama asara,suna yinsa dai dai da yadda za'a iya cinyewa,rahama wadda tunda suka zauna take satar kallon aysha,ba haka taso taddata ba sam,saidai duk da haka tana jin ba wani abu da zai rageta da shi
"Har yanzu anni kuna girkin kun nan kala biyu?"
"In sha Allahu" anni ta bata amsa,sai ta dauke idonta ta maida kan aisha
"Wannan tsarin ya khalipha ne,yana da son abinci mai dadi diffrent colurs...Allah yasa amaryar tamu expert ce ta wannan bangaren" shuru teburin ya dauka kowa da tunanin daya zo masa,khalipha ne ya katse shurun da cewa
"Abu na farko data soma sani kenan game da ni.....wai ke yaushe kika zo?,wa kika barwa karatun naki?" Idanunta ta juya sannan tace
"Sun tafi strike ne na sai baba ta gani,so shi yasa na samu chance na zuwa na tayaku murnar biki...amma amaryar taka kamar bata magana" ta qarshe maganar idanunta kan aysha,da alama ta tsaye mata a rai,wanda ayshan batasan dalilin haka ba,banda faduwar gaba ba abinda takehi,addu'a take kada Allah yasake jarrabtarta da jama'ar da zasu hanata sukuni,jama'ar da zasu zame mata tarnaqi a rayuwarta
"Kirkinta ne yayi yawa yaa rahama.." Haidar ya sake fada yana murmushi,khalipha ya daga kai ya kalleshi yana tunanin a ina ya santa ne wai?,duk suna son dagula masa lissafi baki daya baison yana cin abinci ana damunshi da hira barkatai,tunda rahama tazo kuma sai yadda hali yayi
"Ya khalipha ka tuna sanda muka shiga makaranta ganin wani abokinka lacturer bayan mun tashi daga office nace am starving,zanje na nemi abinci naci?" Kai ya gyada masa.
Daki daki ya bada labarin duk abinda ya faru tun daga shigarsa,watsa mata lemo da qarasowar aliya zuwa fitarsu daga wajen,shuru kowa yayi a wajen,sai a sannan aysha ta daga kai ta dubeshi,tabbas ta tuna abinda ya farun,saidai fuskar tashi ce ba zata tuna ba banda ya fada din,tabe baki rahama tayi,don ita gaba daya abun bai burgeta ba
"Kaman wani labarin arziqi ka ishemu da karadi" hararta yayi itama duk da ta girmeshi
"Idan kece i know saikinyi tashin hankali sosai kaman yadda qawarta taso tayi,musamman idan aka jiqa wannan foundation face din naki" dariya suka kece da ita gaba daya,banda anni dake qoqarin tsawatar musu,sai kuma khalipha daya dan murmusa kadan yana kada kai kafin ya tsuke tashi fuskar,aysha kam baka gane yanayin fuskarta,har kowa ya nutsu amma banda amal,sosai abun yayi mata suger,ta tsani zuwan rahama da zeenart gidan sam,karma rahama taji labari da take musu gani gani,ita daga bangaren anni take,da yake tana da tarihin me ya wakana tsakanin anni da su dangin baban khalipha,sai ya zama kamar ta samu wani abune da take yawan yi misu shagube da shi
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
32
Khalipha ne ya soma miqewa daga zaman cin abincin,anni ta dubeshi
"Ka gama kenan?"
"Eh..ban jima da cin abinci ba ai..."
"Ko amarya dai ta cika maka cikinka?" Rahama ta fada da salon bin qwaqwqwafi,wani kallo yayi mata kawai ya dauke kai ya soma sauka daga wajen,ture plate din aysha itama tayi wadda bata ci wani abun arziqi ba sam,don ko yunwar ma bata ji batasan me yasa ba
"Aishatu kardai ace kema kin qoshi?" Kai ta gyada a kunyace
"Don dai ya khalipha ya qoshi ne shi yasa" amal ta fada can qasan ranta tana jin kishi,dariya suka saka tsakanin mus'ab da haidar,murmushi anni tayi sannan tace
"Saiku wuce hakanan ku samu ku huta ko muhammadu?" Anni ta fada
"Ohk...ohk" khalipha ya fada cikin dan daburcewa kadan wanda ba lallai ka lura da hakan ba,yayi zaton anni zata bata daki ta wuce ta kwana a nan,amma sai ya raya a ransa me yiwuwa saboda idon yaran ta gwada hakan
"Aishatu wuce ku tafi sai da safe"kunya ta sakata ta kasa motsawa daga nan,idon rahama na kanta haka ma amal na satar kallonta,tsaf anni ta lura kunya take,sai tace da khalipha
"Wuce amal ta rakota"
"Ohk to..." Ya fada yana jin dadi cikin ransa,don baisan yadda zai kwana daki daya da mace ba.
Yana fita daga falon anni ta dubi amal
"Qarasa ci ki rakata.."
"Toh" ta amsa wani abu yana dunqule mata a maqoshi,hakanan amal ta dinga yangar cin abincin da gayya tana sani,bata gama ba har sai da khalipha yaci wajen awa daya da tafiya sannan ta sha ruwa ta miqe hakanma ba don taso ba
"Allah ya bamu alkhairi"
"Amin" aysha ta amsawa anni.
Kaman tafiyar kurame haka sukayi,ita aysha baqunta amal kishi har suka isa qofar part din nashi,amal na shirin juyawa aysha tayi qarfin halin cewa
"Ba zakiqaraso ba?" Idanu ta waro tana dubanta
"Ko da can ba'a shiga masa sashe any how ina ga yanzu?,sai da safe" ta fadi tana yin gaba,sai dataga wucewar amal din sannan ta tura qofar ta shiga tana tunani
"Komai nashi a tsare take sarkin tsari me da alama wannan mutumin" bashi a falon sai wasu jaridu dake zube gefe daya da alama dubasu ya gama yi ya tashi,daga can wani side din idanunta suka gamo mata qyallin wasu akwatuna,irin wanda ya bata dazu sak saidai su manyansa ne guda goma sha biyu,gefe daya ta samu ta zauna qasan carfet na tsahon minti talatin sannan aka turo qofar bedroom din aka fito,sanye yake da jallabiyya baqa sai zabga wani qamshin yake daban,dan tsaiwa yayi da ganinta a zaune,ya zaci anni ta riqeta kenan?,hannun rigarshi dake nade ya soma saukewa yana jin wani bawai,ya saba bararrajewarsa shi daya a sashensa ta yaya zai iya zama da wata,agogon dake maqale a bangon falon ya kalla,goma da arba'in sha daya saura kenan,din shirin kwanciya ma yake ya dawo cirar wayarsa ne
"Ammm..." Ya fada kana yayi shuru
"Inaga muje wajen anni ko akwao wani dakin spare ki kwana a can,zuwa lokacinda zanga ya za'ayi a gyara inda zaki zauna a nan" ya qarashe yana goge gargasar jikinsa dake jiqe da ruwa da qaramin towel.
Yana gaba tana baya har sashen anni,babu kowa a falon,sun kashe ma duka wutar falon alamun sun kwanta saishi ne ya kunna,saman anni suka haura kai tsaye har zuwa qofar dakinta yayi knocking,daga ciki ta bada izinin shigowa,tana zaune saman abun sallah da hijabi a jikinta,haka take duk dare bata wani barcin arziqi,tana raye darenta da salloli da addu'o'i ma yaranta da mai gidanta daya rasu,shi yasa yawanci take bacci tsakanin sha biyu na rana zuwa azahar haka hakadan,wanda irin wannan baccin sunna ne,annabi S A W yayi umarni da yinsa,yace saboda shaidan baya irin wannan baccin,yawanci hausawa muna kiransa da qailula,da ido ta bisu sannan daga bisani ta saukewa khalioha kallon baki daya,dai ya dan dirirce daga jisani ya tattara hankalinsa yace
"Anni...cewa nayi akwai sauran dakin da za'a ara mana zuwa sanda za'a gyara sashen nawa?" Wani irin kallo tayi masa kafin ta dauke kanta ta.mayar kan casbahar gabanta me dubu da take ja
"Babu,saidai wannan nawan da nake ciki"
"Subhanallah"ya fada a ransa cikin fargaba
"sai da safe"ya fada da sauri yana duban aysha tare dayi mata umarnin ta taso su tafi,batasan me yake faruwa ba itadai ta tashi ta bishi,a son ranta itama a samu inda zata kwanna a can,har su fita ta qwalo masa kira,shi kadai ya koma aysha ta jungina da makarin silver na matattakalar
"Daga yau karka sake yawon neman dakin da zaka aje matarka...karkayi kuskuran dako sau daya zata ji cikin ranta ita ba komai bace a cikin gidan nan,bata da cikakken matsuguni,bangarenka shine nata,shine cikakken 'yancinta,yanzu ba mallakinka bane"
"In sha Allahu anni" ya fada cikin nuna ladabi
"Tashi ka bani wuri sai da safe"
"Na gode" ya fada yana fita,suna tsaka da ficewa suka jiyo muryar rahama
"Yawon me angwaye suke haka alokacin daya kamata ace suna tsaka da morewa lokacinsu?" Ta tambayesu tana qarasowa cikin kayan bacci,dauke kai khalipha yayi ya juya baya kafin ya bata amsa
"Ina tunanin tsananin sa idonki ne ya hana kowanne saurayi tararki yace zai aureki sanoda yana gudun shegen qwaqwqwafinki" tilas ba don ya shirya ba yasa hannu ya damqo hannun aysha,ya hade yatsunsa da nata ya jawota yana fadin
"Sai da safe idan kin gama tambayoyin kya iya tafiya" sukayi gaba suka fice daga falon.
Bai saki hannunta ba duk da yadda wani abu ke ratsashi tun daga yatsanshi zuwa qwaqwalwarsa don yana gudun sa idon rahama,tsaf zata iya leqensu,sai da suka shiga falonshi ya maida muqullin ya rufe sannan ya zame hannunshi daga nata,wanda zuwa wannan tuni ta daskare a wajen,bata taba aikata hakan ba bata kuma tabajin irin hakan ba,tsoro da fargaba jikinta har dan rawa yake saboda tsoro da rashin sabo,guri ta samu ta zauna ba shiri zuciyarta na bugawa,tuni ya wuce bedroom sai ya tsaya ya rasa me zaiyi,tafin hannunsa ya duba kamar me neman amsa sannan ya hadashi da daya hannun nasa ya murza su sosai ko zai daina jin abinda yake ji idanunsa a lumshe yana furzar da iska mai dumi daga bakinsa,tsahon minti biyar yayi a haka sannan ya haura gadonshi ya ciro blanket da pillow qwaya biyu,yana jin bai kamata ita ta kwanta a falon ba saboda yadda anni ta nuna kulawa a kai shima ya kamata yayi komai saboda annin
"Ki shiga ki kwanta" yace da ita yana zube pillows din a qasa tare da shimfida blanket din kan kujera,kanta ta daga ta dubeshi,har ya gama shimfidar ya dora pillow bata motsa ba
"Nace ki shiga ciki ki kwanta" ji tayi hakan bai dace ba sam,karon farko data bude baki
"Babu komai zan kwanta a nan kai ka kwana a dakinka"
"Ba zaki iya ba"
"I can do it...ka manta,daa a tsakar gida nake kwana ma gaba daya kusa da turken dabbobi?" Ta fada qwalla ma shirin taruwa a idonta,sai ya daga kai kawai yana dubanta jin abinda ta fada,baisan me ya tuna mata da wannan rayuwar ba a dan tsukin nan,kawar da kallonshi yayi daga gareta sannan yace
"No,kiyi kaman yanda nace miki" zamanshi yayi saman daya kujerar yaja magazine din yana dubawa,wanda talla ne na wasu kamfanunuwa da sabbin gine gine ake masa,a nutse ta miqe ta nufi dakin gadon a karo na biyu,sai data shiga ta maida qofar ta tura ta yadda ta ganta,gadon ta qarewa kallo sosai,bata jin zata iya hawa gadon daba nata ba ta kwana bayan ta kori mai gadon zuwa falo,tana jin kamar tayi zalunci ne,bargo itama ta cira ta shimfida a qasan gadon ta saka pillow,tana dora kanta tunanin mahaifiyarta ya dawo mata sabo fil,'yan sa'o'in data yi da anni da khalipha tafa yadda uwa ke nuna qaunawa yaranta,taga yadda uwa ke zama wani abun alfahari a wajen yaranta,duka cikin abinda ya zama musabbabin faruwar komai bata ga laifinta ba ko qwaya daya,me yasa abun yafi shafarta fiye da kowa?,me yasa abun yafi illatata,sakamakon ya koma gareta duka da nauyin laifin daba ita ta aikata ba,bata bada shawarar kan kasancewar haka ba?,idanunta ta lumshe hawayen dake maqale a gashin idanunta ya sauko zuwa kuncinta.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Tunda ta idar da asuba idanunta biyu bata koma ba tana ta rabo ido cikin dakin nashi,ba abinda bai burgeta ba a dakin,komai sai data qare masa kallo kafin ta dauke kai,bata taba gasgata zata kwana a irin dakin ba a rayuwarta,qarfe takwas na safiya tayi karambanin shiga wanka,sanda ta fito taga wani qaramin akwatin da yafi na jiya girma a gefen gado,batasan ya akayi ya shigo dakin ba,amma koma.meye tana da buqatar kayan sawa,data bude komao da komai akwai a ciki,saidai sabanin na jiya wannan harda soson wanka water soap,brush da toothpaste,sai setin rollon,body spray powder da sauran tarkacen kwalliya da qamsasa jiki,mai ta shafa kawai da powder,sai jikinta data bude da turare saboda qaunarta da qamshi itama,kayan dake cikin akwatin ta buda tana dubawa,qarshe ta zari wata atamfa ta saka set da mayafinta da komai.
Ita kanta data tsaya a jikin mudubi sai taga kaman ya zira jiki da yawa,ba wata kwalliya tayi ba amma kyanta ya fito sosai,atamfar holland ce pink me adon fari da blue zanan manyan ganye,cikin ranta take tasbihi da godiya ga ubangijinta wanda yake sauya mata rayuwa daga wannan bigiren zuwa wani a sanda baka zata ba,maida komai muhallinsa tayi ta gyara dakin zuwa bedroom din sannan ta maida mayafinta ta fito.
Babu kowa a parlour din sai tarkacensa da kayan shimfidarsa na jiya,saidai tana iya jiyo motsi cikin daya daga cikin dakunan dake falon,wala'alla tayi tunanin yana ciki,gyare falon tayi tas har ta gama bata daina jiyo motsin ba,saboda haka ta bude qofar kawai tayi cikin gida,don yau batason wannan wunin waje guda,ita sam takura take tunda bata saba da shi ba.
Tana shiga falon anni tayi kacibus da daya daga cikin me share sharen gidan riqe da mopper,cikin girmamawa ta gaida aysha ta amsa tana jin kunyar yadda tayi matan tare da mamakin ta santa ne?
"Anni ta tashi?" Kai ta girgiza
"Ai sai goma da rabi sannan take saukowa qasa ayi karin safe idan ba yunwa kaji ba ko uzuri gareka" kai ta jinjina sannan ta tambayeta kitchen,jagora tayi mata zuwa kitchen din ta qofar ta nan cikin falon zuwa wani corridor na musamman inda kitchen din yake.
Mutum biyu ta tadda suna aikin abincin safe,suma gaidata sukayi cikin girmamawa ta amsa musu kaman waccan karon,sai taja kujera ta zauna tana kallon yadda suke gudanar da ayyukansu,take kewar gida ta taso mata,sabo turken wawa,da tuni i yanzu itama tana can tana tata sabgar,duk motsinsu tana biye da su,a nan taga kurakurai da dama daya kamata su gyarashi yayin girkinsu,saidai bata ce musu komai ba saboda tana ganin hakan bai kamata ba daga zuwanta a matsayinta na baquwa bazatayi musu shishshigi ba.
Tana nan zaune har suka gama komai,saidai duk abinda sukeyi suna yine cikin tsafta daya daga cikin abinda ya burgeta kenan,da alama sun horu da tsafta daga wajen anni,dawowa sukai suna gyara wajen da wanke kayan da sukayi amfani da shi,zata kama musu saida kowa ya zabura suna fiddo da ido
"Ki rufa mana asiri...inamu ina saka matar boss aiki,kiyi haquri don Allah" suka fada a marairaice,karo na farko da aka soma girmamata a rayuwarta,karon farko da aka nuna ita din mutum ce mai wata daraja ta daban,dariya suka so bata,lallai qaramin sani qunqumi,lallai basu san ita din wace ba da basu wani gigice haka ba.
Katsam saiga anni a kitchen din ta shigo riqe da wani jug a hannunta,cikin ban girma aysha ta miqe ta amshi jug din daga hannunta tana shirin gaidata annin tace
"Aysha harkin tashi?"
"Ai hajiya ta jima a zaune a nan tana kallon aikin girki"kallonta annin tayi
"An tashi lafiya ya baqunta" kamar zata nutse haka taji,ita annin ke gaidawa,russunawa tayi sosai ta gaidata ta amsa tana jin dadi a ranta,kallon daya daga cikin masu aikin tayi
"Atika karbi jug din ki hadamin wani,kinsan ina gama cin abinci nake sha"
"Toh hajiya...da alama kinji dadin jikinki"
"Sosai ma...kedai Allah ya biyaki"
"Ameen hajiya" ta fada cikin farinciki
"Bari naje nadan watsa ruwa kafin sarakan baccin su tashi muyi break"
"A fito lafiya" aysha ta fada cikin girmamawa annin ta amsa sannan ta juya ta fice.
Inda ta tashi ta koma ta zauna tana kallon atika na yin wasu hade hade cikin jug din,ta gane me take hadawar saidai taga kamar akwai kura kurai a ciki,taso yin shuru sai kuma ta kasa
"Ko zaki dan aramin jug din kadan naga ko na iya hadawa?" Waiwayowa tayi tana duban ayshan tana murmushi
"Kai hajiya wannan hadin mutanen qauye mu muka fi saninshi ai,ina ku kuma ina qauye" murmushi tayi kawai tana saukowa daga saman kujerar da take kai ta nufi inda take
"Ba wanda bashi da qauye...duk wanda yace baida qauye ka tuntubi asalinsa" sosai zancan ya yiwa atika da sauran biyun dadi,basu zaci haja daga gareta va,sun saba ganin qyama da kallon banza daga gun duk baquwar fuskar data zo gidan,abinda ke kwantar musu da hankali da sake basu qwarin gwiwar zama da mutanen gidan shine basu taba jin ko ganin maganar banza ba daga wajensu
Cikin minti goma kacal ta gama hadawa,atika duka na kallonta cikin mamaki
"Kai hajiya....ya akayi kika iya wannan hadin kamar ma yafi nawa kyau?" Murmushi kawai ayshan tayi ba tare data bata amsa ba,kusan tasan magunguna sosai,saboda inna yelwa tayi sana'ar saidasu kala kala,kuma babu maiyin wahalar sai ita,wani lokaci ma ita ke shiga jeji ta sassaqo abinda ya kamata,ta gada ne itama daga wajen mijinta wato kakan ayshatu bayan rasuwarsa,wanda ya rasu ne tun kafin a haifi umminta.
Tana aje jug din rahama na shigowa cikin kitchen din,ta tsuke cikin shirt da dogon skert tana takawa dai dai,ganinta duk sai su atika suka nutsu,suka soma gaidata tana amsawa dai dai tare da cewa
"Ku samamin wani abun,duka abinda kuka dafa din yau bana jin cinshi" kai aysha ta daga tana dubanta cikin mamaki,a qalla an dafa abu yakai uku kuma duka tace babu na cinta a ciki?,idanunta ne ya sauka kan ayshan,ta dan kalleta na minti biyu,yanayin halittarta tayi mata sosai,ta yabawa tsarinta saidai tana kishinta
"Amaryarmu...ya da fitowa da safe haka?,ke daya kika bar angon naki?"
"Tare muka fito nina rakota saboda ta damu taga anni,komawa nayi in dauko wasu takardu dana manta" muryar khalipha ta ratso kitchen din a sanda take takowa zuwa kitchen din,cikin yadin kufta baqi wanda iyakar rigar qasan gwiwa sai dogon hannu da take da shi,aikin sarauta aka yi masa sosai wanda ya dace da hula dara dake kansa,ba qaramin kyau suka yi masa ba,sai ya tashi tamkar wani jinin sarauta,kwarjininsa ya qaru sosai,sunkui da kansu atika sukayi sannan suka rusuna suna gaidashi,ya amsa musu suka lalubi qofa suka fice,kitchen din ya rage saura su uku,hannyensa harde a qirji ya zubawa rahama ido,wanda a take ya ladabtar da ita,ta dauke kanta tana basarwa
"Princess" yayi qarfin hali fada yana duban aysha,sai tayi wuri wuri da ido cikin mamaki da tambayar kanta dawa yake,hakan sai yayi kama da kamar ta kada mishi idanunta ne a ganin rahama,hannunshi ya miqa mata yana cewa
"Muje muyi break anni tace na kiraki" dubanshi take,ta fuskanci abinda yake nufi,amma sai take jin ba zata iya ba,har yanzu kallonta yake yana fatan ta dago abinda yake nufi ko don rahaman,iya matakin da zai dauka a kanta kenan ta rage sawa rayuwarsa ido da matsanta masa,ganin ayshan nason karya plan din sai kawai ya saqalo tafin hannunta ya janyota zuwa kusa da shi tamkar zasu hade,sannan ya soma takawa ba shiri itama tabi sahunsa yana fadin
"Rahaman kike jin kunya....idan baquwarki ce toni ba baquwata bace...muje kici wani abu na lura bakison cin komai,bana son wannan baquntar taki fa" da idanu rahama ta bisu ranta na suya,bata taba sanin haka khalipha yake ba sai yau,ashe duk sauqin kanshi da take gani da sakin fuska ta wani fannin baida kirki,ita zaiwa haka?"qwalla ce ta cika mata ido tayi hanzarin maida ta,a hankali ta soma takawa tabi bayansu,ta fasa canza abun karin,zama taci ko meye.
Gab da zasu isa qofad da zata sadasu da ainihin falon taso ta zame hannunta,turasu yayi ita da shi cikin wani daki wanda sai da suka shiga taga store ne na kayan abinci,idanu ya tsareta da shi sannan ya soma cewa
"Na gaya miki tun ranar farko ni dake,karkiyi wani abu da zai saka baqin fuskar dake yawan zuwa gidan nan su dora ayar tambaya a kanki ko akanmu,ke matata ce wadda na aura saboda ina sonta,ta aureni auren 'yanci da soyayya kuma akan radin kanta,a haka kike a idon family na....kiyi qoqarin ci gaba da kasancewa a haka,bana son ki bada qofar zargi" kalma ta qarshe data shiga kunnen rahama kenan wadda tazo wucewa,tsai tayi tana jira ko zata sake jin wani abu,saidai ba abinda khaliphan ya sake cewa,illa handkherchief daya ciro daga aljihunsa ya miqawa ayshan yana cewa
"Goge hannunki da kyau,baki tsaya kin wanke ba muka fito,ga gefan fuskarki ma ya dan baci kadan" a sanyaye ta saka hannu ta karba ta goge duk inda yace din,gefan bakinta ne kawai bai gama goguwa da kyau ba,dole ya karba ya sake matsawa gabanta kadan yasa handkherchief din akan yatsanshi ya soma goge mata,numfashinsu ne ya soma gauraya da juna saboda kusancin da hakan ya kawo tsakaninsu,idanunta ta daga saita saukesu fes cikin na khaliphan,ja baya yayi da sauri kaman wanda aka jonawa shock,cikin aljihunsa ya saka handkherchief din sannan ya juya ya soma yunqurin ficewa,hakan ya sanya rahama qara wuta tabar wajen kafin su fito su cimmata.
Duk kowa na saman tebur din kusan kaman qarasowarsu ake jira,ja mata kujera yayi ta zauna kafin shima ya zauna,hakan ya yiwa anni dadi sosai,yayin da amal ta dauke ido zuciyarta kaman zata fito,rahama kam hararar khalipha take a fakaice,wanda ko giyar wake tasha tasan bata isa ta harareshi ba gaba da gaba,haidar ne ya soma gaidata sannan mus'ab,dukkansu ta amsa cikin fara'a da jin kunya,don dukkansu sun girme mata amma suke girmamata kamar itace gaba da su,shikam haidar ganin qimarta yake tun waccar rana a capteria,abinda tayi ya tabbatar masa ita din nutsatstsiyar macace,sai gata a amatsayin matar wanshi hakan ya masa dai dai,a nutse ake cin abincin babu yawan surutu kaman jiya,tsakiyar shurun muryar rahama ta ratso
"Ya kamata amarya ki fadi abincin da kika fiso tunda kin shigo cikin iyalin da kowanne lokaci ake daukar abincin da kowa yafiso a girka"
"Karki damu....abun mamaki duka choice din anni akan abinci irin na aysha ne...." Ta wutsiyar ido aysha take satar kallonshi,itadai tasan basu taba magana makamanciyar haka ba,hasalima koda za'a titsiyeta batasan choice din anni ba a yanzu,dan sauya fuska rahama tayi sannan tace
"Haba ya khalipha...ka barta ta fadi da kanta mana...,wai haka ne?"murmushi ta saki wanda dan fitar sautinsa yasa khalipha daga kai ya dubeta sannan ya maida kan plate din gabanshi yaci gaba da juya abincinsa
"haka ne"ta bata amsa a taqaice,kafada ta daga tana tabe baki
"sai kace mutuniyar qauye?...."
"Suba mutane bane?,abincin da suke ci duka yafi namu lafiya,mu kusan duk kame kame muke,ko a qarfi idan kija hada yaron qauye saiya kada na birni guda uku shi kadai" anni ta bawa rahama amsa tana murmushi tare da son nusashsheta,sosai amsar ta yiwa aysha dadi ta kuma qarawa anni qima da martaba a idonta,khalipha ma yaji dadin hakan,saboda baison aysha tayi wani abu da zaisa rahama ta dauki haske kan wani abu daya shafeta ko ya shafi rayuwarta,daga haka bata qara tankawa ba kowa yaci gaba da cin abincinsa.
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
*KO KUMA*
07067124863
*DB*
33
Bayan sun kammala break din hira ta balle,wanda kusan haidar da mus'ab ne suka hada rudun,sun saka rahama gaba sai cakar da ita suke,itakam tayi kicin kicin don bata son raini,nan ma saida khalipha ya tsawatar,qarshe tashi tayi ya basu waje,amal itama ta miqe tana sauka qasa don zuwa kitchen ta samu ruwan da zata sha.
Mus'ab kewa anni qorafin motarsa tare da roqarta ta bashi daya cikin wanda ya khalipha ya bata,wasa qasa yake maganar saboda yadda khalipha ke harararshi "Shikenan....a baiwa diyata dayar,kai kuma ka dauki daya,amma fa aro..." Ta qarashe fada tana dubanshi,dan tsalle yayi kadan saboda yasan ta fadi ne kawai qarshe dai ta zama tashin halak malak
"Yes my anni!.....thank you" hannunshi khalipha ya saka a aljihu ya ciro muqullan mota yana fadin
"Kin tunamin kuwa anni....ina haidar...idan kun samu lokaci ko zuwa dare ne kuje ku dauko motarta dake wancan gidan...wacce zata yi amfani da ita kenan anni?"
"A debosu duka ta dinga hawa wadda takeso ko 'yata" kunya ce sosai ta kama aysha da wani irin nauyi,ita dako rage hanya ba'a qaunar ayi mata a rayuwa yau ita ake cewa ta dinga hawa mota bama daya ba har guda biyu?,itakam wacce irin qauna mutanen ne ke mata ne
"Allah ya saka da alkhairi ya jiqan magabata ya qara lafiya..na gode"
"Amin...amma babu godiya saboda tamkar 'ya kike kema,ku bata muqullanta ta soma hawa duk sanda takeso" dan dubanta khalipha yayi sannan ya maida dubanshi ga anni yana miqewa
"Banjin ta iya driving...."
"Faduwa tazo dai dai da zama....sai na koya mata kawai" mus'ab yayi hanzarin fada,harara khalipha ya maka masa wadda ta sanyashi ya nutsu sannan ya dubi anni
"Zan fita amma bazan jima ba zan dawo"a dawo lafiya suka yi masa gaba dayansu.
Ranar a nan ta wuni gaba daya,ko da su atika zasu shiga girkin dare a lokacin bata jima da gama sallar la'asar ba binsu tayi kitchen din,kusan ranar gaba daya ita tayi girkin daren sai tattaimaka mata da suka dinga yi da wasu abubuwan,da fari qin sakar mata sukayi suna tsoro suna dari dari,daga bisani dole suka sakar mata din ganin yadda take komai cikin qwarewa,a nan suka saba sosai dasu atikan kamar sun jima tare,qarfe shida suka gama ta baro kitchen din ta koma sashensu ta shiga wanka.
A hankali ta tura qofar dakin kaman yana nan duk da tasan baya nan din,gefan akwatunanta ta nufa ta bude,doguwar riga ta ciro ta ajeta saman akwatin sannan ta shiga bandakin ta tura qofar ta sama tara ruwan dumi,ba jimawa ya cika ta soma wankan tana jin dadin dumin ruwan da yadda yake bada qamshi shi da kansa ruwan,ita kadai cikin ranta take jinjina gayu irin na khalipha da son qamshi.
Shida saura ya shigo gidan kamar yadda ya saba sai daya biya yaga anni kafin ya wuce sashensa,annin tana ta qorafin wunin da yayi yauma a waje,dariya kawai yake yana jinjina yadda anni keso ayshan,ya sani duk don saboda ita yayi hakan,tabe baki rahama tayi bayan ya wuce wadda ke zaune gefan annin tana latsa waya ta kalleta
"Nikam wannan auren soyayya akayi?,ango da sai kayi satima kuna gida daya baka ganshi ba amma shi kwana biyu kacal ya soma fita yana wuni?,kodai bata iya kula da miji bane?"
"Banda abinki rahama wannan ai zancanku ne keda yayan naki" anni ta fada tana miqewa don da wuri take daura alwala kafin a kira sallah ta shige toilet abinta,hada ido sukayi da amal,saita saka dariya wadda tayi ne kawai don ta qular da rahaman itama ta miqe ta bar falon ta shige dakinta
Cikin satin aysha ta soma koyan mota sosai ta hannun aliyyu,wanda sam khalipha ya hana mus'ab yace haidar din ya fishi nutsuwa,tun tana dari dari da su har ta soma sakin jiki,haidar nada kirki qwarai,yana da daraja mutum,yadda yake bata girma abun har kunya yake bata,idan taga yadda yake tsarewa rahama da amal gida idan baiga dama ba sai abun yayita bata mamaki,suna kamanceceniyar halayya da khalipha ta wani fannin,zamanta cikin gidan sai ya soma yi mata dadi,ta soma sakewa musamman idan tana tare da anni,duk wata kunya da surukuta anni ta soketa tsakaninsu,sukan zauna su taba hira duk da har yanzu bata iya bude baki sosai tayi magana yadda ya kamata mai tsaho,saidai tana qoqari matuqa wajen ganin ta saba dasu din.
Sati uku da biki ta soma warwarewa sosai,janta a jiki nuna mata ita watace da mu'amala mai kyau shi ya taimaka wajen samuwar wannan sauyin,saidai abu daya da bata jin dadinshi shine yanayin yadda rahama take mu'amalantarta,takan bata girma dai dai gwargwado,hakanan bata shiga sabgar da bata shafeta ba kamar yadda haka halayyarta take tun a gida,saidai duk wani motsi na ayshan a idonta yake kamar wadda aka baiwa gadinta,hakanya sanya itama ta iya takunta take matuqar taka tsantsan da ita.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Parlour din asma'un cike yake da qawayenta na makaranta wanda ta gayyacesu suzo gidanta kwanaki sati hudu da tarewarta,manyan qawayenta ne da take ji da su ko ince a kullum take qoqarin yin abinda zata burgesu su fahimci cewa ita din ba qaramar mace bace,a ranar ta baiwa yarinyar da aka kawo mata a matsayin 'yar aiki qwaya daya 'yat qabilar igbo umarnin ta dafa musu abinci har kala uki,baya ga snacks da lemuka da aka jibge tsakiyar falon,anaci ana kwasar shafta.
Gaba daya hankalinsu yayi gaba babu wadda taji kota lura da shigowarshi,fuskarshi tamke yake bin kowacce da kallo,sai a sannan suka ankara da shigowar tasa,nusaiba itace ta soma masa magana cikin wasa irin na qawar amarya
"Ango kace kana kusa da dawowa ma kenan.....dama kai muke jira ai" maimakon ya sake mata su gaisa kaman yadda suka saba yi a lokacin hidimar biki saitaji yaja tsaki tare da yin gaba ya haye sama,dukansu baki galala suka bishi da kallp har ya gama hawan
"Ke....haka naki mijin kuma yake?" Cewar daya daga cikin qawayen tana riqe da haba cikin mamaki
"Wannan ko anya asma'u?,kinga kallon raini da wulaqancin da yake mana kuwa?"dayar ta kuma fadi
" ni ban gaji wulaqanci ba wlh,oya ku tashi kawai mu wuce"cewar husna babbar qawar asma'un da take ji da ita,sai a sannan da taga suna shirin miqewa asma'u da wani baqinciki ya qumeta da azabar kunya ta magantu
"Babu wannan maganar don Allah kuyi zamanku ina zuwa....yana da fushi ne zai iya yiwuwa a waje aka bata mishi rai bari naje" ta fada da sauri tare da miqewa tayi hanyar stairs ranta na bala'in baci.
Tura qofar dakin tayi,saita sameshi yana tsaye ya kwabe rigarshi saura singlet yana shirin cire dogon wandonshi ta shigo,cikin nuna bacin rai da fusata ta kalleshi
"Haba hamid....ya zaka kunyatani gaban qawayena don Allah?,me suka taba yi maka zaka yi musu wannan wulqancin?,so kake suje gaba su samu abin bada labari?" Bai tankata ba har sai daya cire wandon saura gajeran wando kawai sannan ya dago ya dubeta cikin qanqan da idanu
"Ke,an gaya miki bansan ciwo kudi ba?,ko an gaya miki tsintosu nake?,ohk kin zaci za'a ci gaba da yadda aka saba ko?,toni ba haka nake ba,nasan ciwon kudi nasan mutunci da darajarsu,haka kawai ki taramin garadan qawayenki ki kwaso abinci da abun shan da a qalla zamuyi sati muna ci ki jibge musu don tsabar burga?,to wallahi kiyi gaggawar zuwa ki sallameshi ki kuma kwashemin kayan abincina ki maida store" tsantsar bacin rai da mamaki ne qarara ya bayyana a fuskar asma'u,tana jin ya xama lallai ta nunawa hamid bacin ranta qarara saboda gaba
"Me kake nufi hamid?,qawayen nawa?,to wallahi babu inda zasu,kayan abinci kuma da kake magana ai daga gidanmu aka hadoni da shi ko?" Dawowa yayi da baya maimakon daa da yayi gaba zai shiga wanka
"Haka kika ce?,don an kawo wadan nan matsoyatan kayan abincin kike gaya min haka?,ohk fine....ki gayamin nawa na kashe miki wanda sunyi ninkin baninkin kudin kayan abincin da aka kawo min?,koni na gayawa iyayenko ina da buqatarsu ma?,a matsiyaci kika aureni?,tunda ba zaki iya sallamarsu ba ni zan iya" ya fadi yana nufar qofa,da mamaki ta soma tsaidashi saboda singlet da gajeran wandon dake jikinsa amma ko juyowa baiyi ba bare ya saurareta.
Kaf dinsu saida kowacce ta miqe tsaye a tsorace ganin mijin qawar taso a haka,dubansu yayi sannan ya soma magana
"Kafin na qirga biyar kowacce a cikinku ta kwashi matattun qafafunta tabar min gida tunda yunwa ce ta kawoku,kada wadda ta sake zuwa min gida tasha min koda ruwa ne bare abinci,ku cika cikinku a gidajen ubanku kafin kuxo" cikin bacin rai husna da take jin tafi qargfin wulaqanci ta soma maida masa martani,kanta yayo wanda hakan ya sanya suka qarasa ficewa a guje ba shiri ba tare da sun tsaya daukan kayayyakinsu ba,bayansu yabi cikin daga murya yake baiwa inyamurin mai gadinsu umarni cikin karyayyen turanci
"Maza ka sakar musu karnukan nan su qarasa rakasu" jin abinda yake fada ya sakasu qara mai,taimakon da Allah yayi musu daya motar da suka zo cikinta tana qofar gidan basu shigo da ita ba saboda motocin hamid guda uku dake harabar wajen data asma'u daya data zo da ita ta cike wajen.
A tsaye a falon ya tadda asma'u tana qwallar takaici tare da tunanin anya kan hamid daya kuwa?,lafiyarsa qalau?,kodai ya soma bin hudubar yayyensa mata randa sukazo da sunan sunzo ganin amarya da sukaji suna gaya masa
"Wannan matar taka sai kayi da gaske,makarantarsu daya da nabihat,bata da kirki batason talaka,dagawa gareta da girman kai,hakanan kudinka takeso tosai kayi tsayin daka idan ba haka ba rainaka zatayi wallahi" abu daya ne bata sani ba,hamid mutum ne mai shegen son abun dunuya,yana da dukiya amma ta cinsa ne iya shi kadai,ko sanda yana gida wani abun sai ya rataya a jikin mahaifinsa yayi masa bazai taba qwandala tashi ba,irin yaran nan ne dako.iyayensu basa iya taimakawa banda Allah yasa mahaifin nasa yana da wadata shima,saidai matsalarsa daya mahaifin nasa,mutum ne da bashi da tattali,yana da son nunawa duniya shi wani ne ko nawa zai kashe akan haka zai iya,ya kuma yi nasara don sunansa ya dan fita,sakamakon yadda yake nuna qaryar arziqi don baikai nan ba.
A parlour ya taras da ita zaune tana gunjin kuka,kota kanta baibi ba ya wuce zuwa sama abunshi ya dauki wankanshi.
Minti talatin ya sake saukowa,ya tsuke cikin qananun kaya,yana dannan waya ba tare daya dubeta ba koya kula da kukanta yace
"Ina abinci na?" Shuru tayi masa da fari har na tsahon minti uku
"Ina abinci na!" Ya sake tambayarta karo na biyu cikin qaraji da fushi wanda ya kada mata 'ya'yan hanji ta soma qwallawa rebacca kira
"Ohkey.....wai na tambayeki mana?,na kawo mai aiki ne donta kula dani ko don ta tayaki aiki?"
"Duka gaba daya" ta bashi amsa cikin bacin rai,cike da fushi yake nuna kanshi
"Ni kike baiwa amsa haka kai tsaye?"
"Waikai hamid me yake damunka ne?,ya za'ayi mu rabu lafiya da kai sannan kazo kana min wasu abubuwa kaman dan qwaya?" Dariya ya saki
"Au bakisan dam qwayar bane ni?,yau zakisan ni cakken dan qwaya ne tunda baki iya zama da miji ba" ya fada a sanda rebacca ta gama jera abincin ta fice,don kusan duk a kunnenta ake komai,zama yayi ba tare daya sake dubanta ba ya take cikinsa da abinci sannan ya miqe yasa kai zai fice,har yayi gaba ya dawo da baya
"Ina canjin cefanen da lado yayi dazu?" Cikin mamaki take kallonshi,a arziqinsa bata taba tunanin zai tambayi wani canji cefane ba wanda baifi dubu daya ba,ita a wajenta dubu daya ba komai bace
"Dubu dayan kake tambayata?"
"Ita ba kudi bace?...ko satowa nakeyi?,tashi malama ki dauko min" bacin ranta da mamakin sauyawar hamid dare daya suka sake yawa
"Bazan bayar ba,wannan wane irin nuna talaici ne?,dubu daya kawai?" Mari ya kai.mata Allah yasa tayi gaggawar kaucewa
"Ni zaka mara hamid?"
"Na nuna miki kadan daga abinda zan iya yine idan har na dawo baki nemo min dubu dayata ba duk inda kika kaita" daga haka ya juya ya fice abinsa,da kallo ta bishi hadi da hawayen takaici,a rayuwarta tunda taje ta taba daukar koda dubu dari ta riqe hamid zai magana akao bare dubu daya?,tunda take rayuwar gidansu ta taba baiwa dubu qwaya daya wani muhimmanci mai yawa?anya lafiya ko hamid yake?,kanta bazai iya daukar wannan abun ba haka ya sanya kai tsaye ta soma kiran lambar mommynta
Tana dagawa mummyn ta fashe da kuka,a rikice mummyn ke cewa
"Ke...lafiya asma'u,me ya faru?"
"Mummy hamid ne..."
"Hamid?,me ya sameshi?" Nan ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar mata,take mummyn ta cika tayi fam
"Lallai yaron nan mugun dan iska ne,ce masa akayi baiwa aka kawo masa da zaice zai dakeki?,to wallahi daga yanzu ba yarda ba,duk sanda ya sake yunqurin dukanki ki tattara ki taho gida,idan yaso babanki ya masa jan kunne mai qarfi"
"A'h mummy,basai na taho ba,kinsan ma halin daddy baya yarda da irin wannan"tasan sarai ba wai daddyn take dubawa ba kawai,tsabar son miji ne
"Karki sake ki yarda dai ya dakeki wallahi ban lamunta ba,duk abinda ya sake faruwa ki sanarmin don bazan lamunci wannan iskancin ba" da haka suka rabu da mummyn ta aje wayar tana dakon dawowar hamid din.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
A hankali ta turo qofar falon tamkar wadda ke sanda,idanunsa ya dago daga saman screen din system din da yake aiki akai,qwayar idanunshi wanda suke cikin farin gilashi da yake aiki da shi lokaci zuwa lokaci idan zai jima yana kallon screen ta fito tarwai,saidai ta danyi ja kadan gami da lumshewa saboda gajiya da kuma bacci da yake ji,a hankali ta janye tata qwayar idanun kamar yadda shima yayin ya maida kan screen din,cikin muryarta mai sanyi tayi sallama tana takowa cikin falon,tun dazun ya shigo don shi baima zauna ba a falon bayan sun gama cin abinci ya yiwa anni sallama yace yana da aiki da yawa yau,a can ya barta tana jin caftar su haidar tana kwasar dariya a ciki,ta sake sosai yau saboda rahama bata nan ta tafi gidan qanin anni zata musu kwana uku
"Zo" taji ya fadi sanda take shirin gifta shi,saita dawo da baya ta samu waje nesa kadan dashi ta zauna bayan ta nade qafafunta a qirjinta ta rungumesu kamar wata 'yar mage,bai dago ba har sai daya kammala tura wani saqo sannan ya rufe cumputer din ya zare gilashin fuskarsa yasa handkherchief ya goge idanun nasa sannan ya dubeta,kusan a tare suka kalli juna kowa kuma ya janye idanunshi,baisan me yasa sau da dama sukan kalli juna lokaci guda ba su kuma janye lokaci guda
"Meye babban burinki yanzu a rayuwa?" Ya jeho mata tambayar kai tsaye,shuru ne ya ratsa dakin tamkar ba kowa a ciki,ya kafeta da idanu yana karantarta,yayin da ita kuma take kallon tafin hannunta tana matsawa kamar wadda yakewa ciwo,abu biyu,abu guda biyu ne yake mata kai kawo a ranta,burinta na farko a duniya ta samu kusanci yarda da aminci na mahaifiyarta,burinta na biyu na biyu shine ta samu ilimi mai zurfi,ilimin da zai sauyata,ya zamewa rayuwarta garkuwa,karatun da tayi har yanzu bataji ta qoshi ba,har yanzu tana da qishirwarsa,har yanzu bata jin ta cimma gaci.
"Mahaifiyata....ina da burin naganni ni da ita tamkar kowacce 'ya da uwa" sai tayi shuru tana hadiyar zuciya kadan kadan,tana son danne mikin daya taso mata
"Bayan wannan fa?"
"Karatu" shuru ya sakeyi yana nazari,kafin daga bisani ya jawo wata paper ya danyi rubutu ya ninketa
"Kina da jamb?" Kai ta gyada da sauri
"Eh last year nayi,ta na nan"
"Good,kina da zabin makarantar da kikeso?"kai ta kada
"Duk wadda na samu inaso,matuqar dai makaranta ce" kai ya jinjina na tsahon wasu mintuna kafin yace
"Is ohk,zakije wudil?" Kai ta jinjina itama da sauri murmushi na qwacewa daga fuskarta,ganin mafarkinta na nesa na shirin zuwa kusa,burinta na gab da cika
"Ba damuwa" ya fada ta sigar dake nuna ya sallameta,da hanzari ta miqe tayi daki,cike da farinciki ta dira saman carfet din dake gefe guda wanda ta maidashi makwancinta,don ko da wasa bata taba hawa gadonshi ba,murna take sosai ita kadai a dakin,ba don dare yayi ba da ba shakka saita kira aliya ta shaida mata,don ba'a boyewa abokin kuka mutuwa.
Sai data gama dararta sannan ta soma sauya kayan jikinta zuwa na bacci masu kauri da taushi,ta saka dan qaramin hijabin da take kwana da shi wanda iyakarsa qirji ta shiga toilet ta daura alwalar kwanciya bacci(yana da kyau mu kasance cikin alwala a duk sanda zamu kwanta bacci,domin hakan ba qaramin kariya bace a garemu daga sharrin shaidanun mutane da kuma shaidanun aljanu,bama lokacin bacci ba kawai,a wuninmu gaba daya yana da kyau mu dinga zama da alwala,Allah yayi mana tsari,yasa mu dace duniya da lahira amin summa amin).
Tana zaune tana karanto addu'ar bacci taji ana knocking qofar,sai a sannan ta tuna bata rufe ba,tsuru tsuru tayi da ido ita batayi magana ba hakanan bata miqe ba,jin shuru yayi yawa yasanyashi turo qofar ya dubeta yana kauda kai
"Am sorry zan dauki blanket ne" sai kuma ya dawo da kanshi inda ya ganta,zai magana sai kuna ya fasa,ya isa ma'ajiyarsu ya dauki daya hadi da pillow sannan yace
"Me yasa kika zabi kwana a qasa?"
"Babu komai" ta fada a sanyaye,baice komai ba ya juya ya fice daga dakin,ta qarasa addu'arta ta koma ta kwanta ranta fari qal idan ta tuna batun ci gaba da karatunta.
Qarfe shida na safe ta gama shiryawa tsaf cikin lafaya,ta nade jikinta sosai kamalarta ta fito,fatarta data sake kyau da qyalli sakamakon isashshen hutu ta sake bayyana sosai cikin kalar tufafin dake jikinta,ranta fari qal,yau ita daya tasan farincikin da take ciki,duk zumudi ya cikata sakamakon screening da zata wudil,a haka ta fito parlourn ta tadda shi tsaye yana kurbar ruwan dumi a cup,wanda sabonshi ne hakan duk safiya kafin yaci komai,don yana wanke duk wani system na jikin mutum tare da inganta lafiya,ido ya dan xuba mata ganin yadda take ta faman zumudi,fara'ar fuskarta tafi tako yaushe,wanda hakan ya sake bayyana mishi irin yadda take qaunar karatu a rayuwarta,gaidashi tayi ya amsa taci gaba da tsaiwa tana jiran jin me zaice,sai daya gama shan ruwan sannan ya aje cup din
"Ban sanarwa da anni ba....bansan ya zata dauki zancan ba"duk sai taji daukinta ya tsaya,kuzarin data fito da shi ya ragu,dan soma takawa yayi ya nufi qofa a sanyaye tabi bayanshi.
A parlour suka tadda haidar riqe da muqullin mota kamar yadda khalipha ya tsara shi zai kaita,da alama magana suke da anni,dubansu take har suka qaraso cikin falon,aysha ce ta soma gaidata sannan haidar itama ya gaidata,daga bisani ta koma gefe ta lafe tana ji suna gaisawa da khalipha
"Me zasu yi a wudil da safiyar nan?"
"Screening zasu....zan miki bayani anni"
"Screening?" Ta maimaita tana danyi shuru kamar mai nazari,kada kai tayi daga bisani sannann tace
"Haka zaku tafi kenan baku karya ba?"agogo haidar ya duba sannan yace
"Zamu karya a hanya karmu bata lokaci,amma ban sani ba ko anty zata ci wani abun"
"Na qoshi" ta fada da sauri wanda har hakan ya sanya khalipha waiwayowa ya dubeta,yayin da anni ta saki murmushi saboda ta karanci zumudin da takewa tafiyar,duk da bata gama fahimtar tafiyar ta meye ba
"Allah ya kiyaye hanya,saikun dawo" anni ta fada suka juya suka fice khalipha na jawa haidar kunne kan tuqin ganganci.
Dubanta ta dawo dashi kanta,filon dake saman kujerar ya janye mata alamun ta zauna,babu musu ta zauna din tana hade hannayenta waje daya,shima ya zauna daura da ita kansa na dan kallon qasa
"Kiyi haquri anni,naso muyi maganar dake kafin wannan lokacin amma na sha'afa saboda yawan hidimomin dake shigo min.....na samu wata dama ne daga wani kamfani dake da reshe a mafi yawancin qasashen duniya....to amma wannan dama daci gaba ba zasu tabbata min ba har sai na sake qaro karatuna,wanda hakan zai zamemin kamar jifan tsuntsu biyu da dutse daya ne,zan kai wani mataki mai girma cikin reshensu dake qasar nan,sannan namu kamfanin zai sake samun ci gaba da daukaka da yardar Allah,karatun duka zai daukeni ne tsahon shekara biyu....mun dauko humaira daga ainihin inda suje ruqonta don mu samawa rayuwarta nutsuwa jin dadi da kuma ci gaba,sai na tattauna da ita game da meye burint,ta sanarmin karatu ne,hakan ya sanya nayi tunanin me zai hana na maidata makaranta yadda take da buqata,nq bata zabi ita da kanta ta zabi waccar makarantar,tunda dama can ta cike first choice da second choice dinta,dalili kenan da yasa na tura ta can din....amma nasan hakan bai kamata ba,ya kamata na fara yin magana dake kafin duka na yanke wadan nan abubuwan" kai ta jinjina,ta tabbatar duk abinda khalipha zaiyi yana zurafafa tunaninsa kafin yanke komai,hakanan baya aiwatar da komai saida dalili,sannan tunda suke ita da shi bai taba yanke wani hukunci ba tare daya shawarceta ba,bai kamata don an samu akasi a wannan karon ta manta baya ba ta tuhumeshi
"Tunda har haka takeso babu damuwa,Allah ya bada sa'a ya taimaka,saidai kai din kar ka manta cewa da da yanzu ba daya bane,zaka tafi har tsahon shekara biyu wata uwa duniya?"
"Zan dinga zuwa duk sanda aka samu chance...."shuru ta sakeyi sannan daga bisani tace
"Shikenan..amma dai kayita istikhara ka barwa Allah zabinsa,idan alkhairi ne dukkan abubuwan daka zayyana Allah ya tabbatar da su,idan babu alkhairi kuma ina roqon ubangiji yayi maka musaya da mafi alkhairi,sannan kayi shawara da matarka"
"Amin ya Allah anni na gode...Allah ya jiqan magabata"
"Amin amin"
"Zan shiga ciki inason na sake hutawa kafin goma na wuce office..."
"Allah ya nuna mana" har ya miqe ya soma taku ta kira sunanshi,dawowa yayi da baya ya zauna hannun kujerar daya tashi a kai
"Khalipha...na baka shawara?" Cikin mamaki ya daga kai yana duban annin,lafazin nata ne ya dan bashi mamaki,kai ta kada
"Qwarai kuwa shawara,domin kuwa abinda ya shafi rayuwarka ne kai kadai" sai ya samu kanshi da kada kai
"Ka riqe aysha da kyau,don ina tsammatar ita din matar aure ce ta gari irin wadda kowanne namiji yakeso" iya abinda ta fada kenan taja bakinta ta tsuke,ya tabbata ta fadi hakanne ta bar mishi saura yaje yayi nazari a kai
"In sha Allahu" kawai ya fada yayi mata godiya ya miqe ya fice.
Har ya nufi sashensa sai ya sauya akala zuwa sashensu haidar,ya tura qofar ya shiga ya ratsa falonsu sai ya wuce dakin mus'ab,yana kwance dai dai saman abun sallah yana kwasar bacci abinshi,da alama yau baije masallaci ba a daki yayi sallah,hannu khalipha yasa ya daka masa duka a qeyarsa,miqewa yayi a zabure da har zai soma masifa ga zatonshi haidar ne sai kuma yaga khalipha tsaye a kanshi hannayensa harde a qirjinsa yana dubanshi,kai ya sadda yana gyara zamanshi
"Wato duk fadan da nake maka kan salla bisa jam'i baka ji ba ko?"qeya ya soma sosawa cike dajin nauyi da kunya
"wallahi ya khali...."
"Shutup.....kasan muhimmancin sallar asuba da isha'i a jam'i kuwa?,annabi S A W yace idan kaga sallolin nan guda biyu sune mafiya nauyi akan munafukai,suna yiwa munafuki wuya da nauyi, sallar asuba da isha'i,sannan ya sake cewa da mutane sunsan me yake cikinsu da sunzo musu koda dajan gindi ne...ka shiga taitayinka,karka sake ka shiga sahun wadancan mutanen,annabi S A W a lokacinsa yace badon mata da yara dake cikin gidajen wadanda basa halartar sallah asuba ba,da ya umarci wani yaja mutane sallah,shi kuma ya dauki itace ya zagaya gidajensu ya kunna musu wuta,ibn ummu makhtum mai yiwa annabi kiran sallahn farko makaho ne,ya nemi uzuri wajen annabi S A W kan bashi da d'an jagora,sannan hanya akwai kwazazzabai a hanya shin ya iya zama a gida yayi sallar asubarshi?,har annabi ya bashi daman ya zauna har ya tafi yayi kiranshi ya dawo,ya tambayeshi daga gida yana iya jiyo kiran sallah?,yace masa eh,yace to lallai lallai dole ya taho masallaci ya halacci sallah cikin jam'i,saikai da baka da wuni uzuri?,saika kai sha biyu na dare kan waya daya na dare,ka kasa tashi sallar asuba wace hujja zaka gayawa Allah" sosai jikinsa yayi sanyi,a hankali yace
"In sha Allah hakan bazai sake faruwa ba ya khalipha nayi alqawari"
"Ka kiyaye karna sake ganin irin haka ya faru,kada na sake zuwa masallaci ban ganka ba"
"In sha Allahu" ya fada cikin nadama
"Ka tabbatar ka fito qarfe goma zamu fita ni da kai,haidar ya wuce wudil,karka sake na rigaka fitowa" ya fadi yana bude qofar fita daga dakin
"In sha Allahu yaya" daga haka ya fice zuwa nashi dakin.
Koda ya shiga ya cire jallabiyyar jikinsa ya kwanta don ya sake ri tsawa sai ya kasa,maganganun anni ke dawo masa,ya kasa gane ina ta dosa,duk wata kulawa da yayi alqawari yana baiwa ayshan,ba wata takura cikin rayuwarta sam,ya kasa gano komai haka bacci yaqi daukarsa,dole ya haqura ya miqe ya sauya kayan jikinsa zuwa wanda yake amfani da su idan zai shiga gym dinshi ya fice zuwa dakin motsa jikin.
*mace nayin soyayya da dukkan zuciyarta,yayin da namiji keyin soyayya da dukkan qarfinsa*
34
Kwance take saman doguwar kujerar falonta tana kallo,tun dazu ta aika drivern gidan tare da hamid zai taho mata da shawarma don ita take kwadayin ci,saidai ta tashi babu kudi a hannuna,kasancewar ko naira biyar hamid bai bata a hannunta,hakanan ko cefane akai zaibi ba'asin ragowar canjinsa,kudinta dake accnt dinta takeso taje ta cira a atm saboda kwata kwata bata saba zama babu kudi a hannunta ba,batasan babu ba sam,mummynta ta tsaya mata bata taba neman abu ta rasa,har gwara daddy wani lokaci yakan hanata ko ya bata ba yadda ta buqata ba(qalube gareku iyaye,bawai burgewa bace ace komai yaro ya nema saika bashi,irin haka akwai matsala mai yawa a rayuwar yaro,baka da tabbas na cewa zaka ci gaba da rayuwa da shi har abada,koda kaci gaba din baka da tabbacin zaka dawwama cin wadatar da zaka dinga yi masa duk abinda yakeso,irin haka takan fara ne tun daga sanda yaro yake qarami,bani biyar bani goma bani ashirin,randa baki bashi ba ya zauna yayita yi kiki kuka,ba zaki barshi ba yaci kukansa har ya haqura saboda ya gane ba duk abinda kakeso kake samu ba,A'ah,sai kice ya isheki da kuka ungo ni ka barni na huta,daga ranar ya gane haka duk randa kika hanashi kuka zai saka miki har sai kin bashi din,diya mace 'yar gudan wani ce,idan ta saba duk abinda ta buqata zata samu kina da tabbacin wanda zata aura haka ne?,kina da tabbacin zaku rayu tare kici gaba da yi mata yadda takeso?,don Allah iyaye muyi qoqari mu gyara,kaza tana taka danta ne badon bata sonshi ba,a'ah saboda ta koya masa darasin rayuwa,yana kukan bakiso bakijin dadi har cikin ranki amma saiki danne don mi koya masa lallai abinda kikeso shiza'ayi ba abinda shi yakeso ba,Allah ya shirya mana zuri'a baki daya amin).
Driver dinne yayi sallama hannunshi riqe da baqar leda wadda taketa maiqo,miqewa tayi daga kwancen da take ta zauna sosai tana yatsina gami da cewa
"Miqo" ya qarasa ya miqa mata dariyar mugunta fal cikinsa yana dannewa,budewa tayi maimakon shawarma sai ta hangi wainar fulawa wadda ko wadataccen manja babu a ciki bare albasa,wurgi tayi da ledar cikin fushi
"Meye wannan malam zailani?,wannan wanne irin iskanci ne da rashin mutunci?,nace shawarma ka kawomin wainar fulawa a qaqqandare?" Cikin kwantar da murya yace
"Hajiya ba laifi na bane.....wallahi Allah muna cikin tafiya da shi muka biyo ta wani layi yaga ana soyawa,da kansa ya bada umarnin na tsaya naje na siyo miki....ita kanta yarinyar da ganin motar har kyautawa tayi ta sako gyara" miqewa tayi cikin fushi ta soma zazzageshi da masifa kamar zata cinyeshi danye ko kamar shi yayi mata,sake kwantar da murya yayi duk da dariya na cinsa a ciki,wulaqancin data taba yi masa rannan har yanzu bai manta ba yace
"Haka zaki haquri hajiya kici tunda duka da wancan da wannan din duk dangin fulawa ne"
"Malam zailani,ka tashi ka fiya ka bani wuri tun ban zagi uwarka ba" hannu yasa ya rufe bakinsa cikin tsananin mamaki,don bai zaci isgilancin nata yakai har nan ba
"Allah ya baki haquri" ya fada yana miqewa gami da ficewa daga dakin,komawa tayi saman kujera ta zauna kamar zata saka kuka tsabar baqinciki
"bari daddy ya aikomin da kudin da yayimin alqawari,naga wanda ya isa ya hanani cin abinda raina keso"gaba daya hamid ya sauya kamar bashi ba,a baya duk abinda tace masa tana da buqata kona miliyan nawa ne yi mata yake babu musu,sai gashi yanzu biyar tashi sai tayi da gaske take cinta,hatta da cima ya soma canza musu,don shi ba kasafai ma ya fiya cin abincin gidan ba,sam yadda ta dauki auren ba haka ta sameshi ba,ta zaci wata sabuwar duniya zata balle,ta dauki cewa rayuwar 'yanci ce fiye data gidansu,jin dadi zaman lafiya da kwanciyar hankali daya ninka na gidansu,rayuwar kece sa'a da tserewa sa'a,sai gashi komai yana zuwa mata a baibai,koya aysha?,tunatan datayi sai dariya ta qwace mata,hala itama tana can tana karbar nata gashin,ita da aka aureta ma ba so babu qauna,aka aureta ba tare da an shirya ba.
Tana tsaka da wannan bacin ran taji knocking,kafin ta bada izini an turo an shigo,yayyen hamid ne guda biyu da qannenshi su uku duka mata,da yake su biyu ne maza a gidansu shi da qaninsa,hakanan ta aro fara'a ta dorawa fuskarta,kana gani tasan bata saba hakan ba,haka yake don bata da experience na yadda ake taryar baqo,kujerun suka samu suka zazzauna suna bubbuda hanci da qarewa gidan kallo fes,aka rasa wanda zai fara gaida wani,su suna ji da girman kai,yayin da ita kuma batasan ya akewa baqin ba idan sunzo,don a gida abinda ta sani shine ta qwalawa mai aiki ko aysha kira ta kawo lemo da ruwa wani lokaci da abinci,to yau mai aikin nata tunda ta tafi gidan qanwar babanta bata dawo ba tun safe,kusan tare suka fita da hamid,ita kuma ta qyuyar tashi,koda ta tashin ma basu da wani abun azo a gani,ruwanta ne data siya cartoon uku takesha ba kuma zata iya basu ba,sai lemon da hamid ya shigo dasu jiya qwaya uku yace mata kuma nashi ne kar a taba masa,tanajin girman kan ta taba masan don karya rainata shi yasa ko kallonsa batayi ba
"wacce iriyar mace hamid ya aura ne wadda bata iya gaida mutane ba?" Babbar yayarsu ta fada tana yatsina baki,kallonta asma'u tayi,sai a sannan ta ganeta cewa itace babba a gidan,dole yasa tace mata ina yini.ita kadai ta amsa da qyar aka ci gaba da kallon kallo da zaman kurame,kowa da abinda yakeji dashi cikin ransa,qaramar qanwarsu ce kuma autarsu wadda a qalla ta kusa shekara sha biyar ta saka kuka tana cewa
"Tun a hanya nakejin qishirwa maman salima kika ce na bari mu iso,gashi mun iso din kuma banga alamun ruwa ba"
"Ki bamu ruwa tunda saimun roqa" wadda daga ita sai autar tasu ta fada,miqewa autar tasu tayi tana cewa
"Ta barshi idan ma bazata bani ba ai nasan kitchen din,tunda gidan yayana ne" ta fada tana nufar kitchen din asma'u,take zuciya ta ciyo asma'un,ta miqe da hanzari ta janyo ta tana cewa
"Bana daukar raini ko rashin kunya,karki kuskura ki shigarmin kitchen nada izinina ba,idan kina taqamar gidan wanki ne me ya ajiye a gidan?,wani abun arziqi yake bani?" Salati babbar yayar tasu ta saka,sanda auta ramla ta saki kuka
"Lallai hajiya tazo ta ganema idonta 'yar gudan butulu,tun daga aurenki har kawoki gidan nan kike laqwame dukiyar dako mahaifiyar data haifeshi bata ci ba,shine yanzu zaki bishi da sharrin bai aje miki komai?,ku tashi mu tafi maza kafin muma ta jefe mu da wani sharrin" tana nan tsaye har suka gana ficewa daga falon,ta bisu ta bame qofarta ta tsaya tana maida numfashi gami da tambayar kanta meye haka ne?,sai ta dafe kanta tana son ta gane me hakan yake nufi?,wai dama haka rayuwar auren take ne wai?,wannan shine jin dadin da hamid ya dade yana mata dadin bakin yayi mata tanadinshi?,kuka ta saki ta sake daukar wayarta tana neman layin mummy,saidai cikin rashin sa'a a kashe wayar take,haka ta zauna taci kukanta daga bisani ta haura sama tayi wanka saboda gumi data yi,sakamakon yanayin zafi da aka shiga,don gidan babu wuta,hakanan engine dinsa baya kunnawa sai ya dawo gida,shima na iya mintinan da zai zauna a falo ne,daya tashi yin bacci zai kashe yayi kwanciyarsa,a sanda suke zuwa ganin gini ya nuna mata kayan hada solar inverter,amma daga baya bayan sun tare suna tsaka da amarci ya kwashe ya saida yace babbar wannan zai saka,gashi yanzu a qalla watanni uku ba ita ba dalilinta,babu ma wannan maganar,mutumin da duk wani alatun rayuwa ya janye shi daga gidan sai abinda ba'a rasa ba wanda bazai iya rayuwa babu shi ba.
Falon qasan ta sake dawowa bayan ta gama wankan ta zauna tana sauke ajiyar zuciya,yunwa take ji ta kasa cin komai,Allah ya taimaketa aka kawo nepa,a nan ta kwanta sosai iskar A.c na kadata tana jin dadin iskar duk da zuciyarta a cunkushe take,tana ta son ta lalubo dalilin sauyawar hamid amma ta rasa,tana son tasan shin dama tun ainihinsa haka yake ko kuwa sauyawa yayi.
Kana kallonshi kasan a fusace ya shigo falon yana wani daddaurewa yana cin magani,a baya farkon fara hakan sanda bata saba ba duk sanda ya shigo din takan aje girman kanta ta bishi ta rissina masa tana neman jin ba'asi da lallashi yana fuffurjewa,daga bisani itama ta watsar ta nuna masa sam itafa ba haka aka raineta ba,batasa daukar wulaqanci ba,ba'a sakata saidai ita ta saka,idan ta nema dole ta samu,yadda ta tsara ahaka ake aiwatarwa,abinda shi kuma yake kallonshi a amatsayin shi da babu duk daya.
Har ya wuce ya soma taka matattakala ya dawo da baya yana dubanta
"Na lura iskancinki da rashin mutuncinki qara gaba yake,takai ma ban isa kimin sannu da zuwa ba ko?" Banza tayi da shi kamar bata ji me yace ba,saima gyara kwanciyarta da tayi,kai ya kada ya haye saman,ta bishi da kallon banza taja tsaki,gaba daya auren dashi hamid din kansa ya fice mata a rai,minti arba'in ya sake saukowa ya sauya kaya da alama wanka yayi,duk sanda ya dawo haka yakeyi,daga yaci ya qoshi zai sake fita ba zata kuna ganinsa ba sai sha daya da rabi ko sha biyu na dare
"Ina wainar fulawar da malam zailani ya kawo miki?"
"Tana shara" ta bashi amsa cikin gadara,sosai yaji wani bacin rai ya kamashi,shi zata yiwa almubazzaranci bayan kudi ya saka ya siya mata
"Ina abinci na?" Sai a sannan ta dubeshi
"Mai dafawar ai kafi kowa sanin bata nan,tunda kai ta tambaya sanda zata fice yawonta"
"Saitana nan zanci abinci a gidan nan?"miqewa tayi ta zauna sosai don dama qule take da shi,ta dubeshi sosai
"Eh mana,meye amfaninta?"
"Ke nake aura ko ita?,baiwar uwarki ce ita da kullum ita zata dinga dafa muku abinci" sosai lafazin nashi ya bata mamaki,yau ita hamid ya zaga kanshi tsaye ba wani damuwa kamar ya zagi banza
"Baiwar uwata?,idan ita din ba baiwar uwata bace ni baiwar uwarka ce?,ko yarjejeniyar da mukayi kenan da kai kafin aurenmu?,ka wargaza komai ka saba duk wani al....." Bata samu damar qarasawa ba ya kasheta da mari sannan ya nunata da yatsa
"Kin tabbata cikakkiyar mara tarbiyya wadda ba'a koya mata tarbiyya ba daga gidansu,uwata zaki zaga?,tun kafin ma dawo gidan nan labarin wulaqanta min 'yan uwa da kikayi ya iskeni,da mike zancan na karya duk alqawarin da nayi an gaya miki bansan don me mike sona ba?,bansan samari nawa kikayi ba kafin ni duk kika qisu saboda kina tunanin na fisu arziqi?,dama an gaya min din me kike sona yanzu gashi kuwa ya tabbata,wannan aishan da kike qi kike gayamin maganganu kullum a kanta din na tsaneta tota fiki,na tabbatar da ita na aura bani da matsalar komai kome zan ciyar da ita kowanne umarni zan bata,saboda haka ta fiki wawiyar mace wadda bata iya komai ba,kuma duk kudin dana kashe miki da asarar da siyayya masu tsada da kika dinga roqa ina miki duk sai na fanshe abuna,an gaya miki ni sakarai ne bansan ciwon nema ba?,to idan baki sani ba bari in gaya miki yau free,ba'a cin kudina haka siddan koda kai ka kawoni duniyar,bare ke da mika tsinceni da haqorana talatin da hudu cif" hannu ya zura cikin aljihunsa ya fito da envalope ya farkesu,kudi ne suka zubo daga ciki,ya qirgasu ya zari wani abu daga ciki ya watsa mata sauran
"Gashinan inji tsohonki,mun hadu a banki naje kai kudi shima tasa ta kaishi,na cire kudin wainata da kikamin asara,canjin zanje naci abincin da baki girka ba" ya fada yana maida uban kudin daya zara da sunan kudin wainar fulawa,sannan ya isa gaban dustbin din data ce ta jefa wainar ya zura hannu ya laluba ya cirota a keda ya fice ya jefawa karnukansa,ba bata lokaci suka hau ci don ya koya musu cin komai,babu abinda basa ci.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Cikin qanqanin lokaci komai da komai ya kammala na karatunta,sunanta na gaba gaba cikin jerin sunayen daliban da suka samu admission,kusan tana zaune akayi mata komai,zirga zirgar da tayi bata kai ta kawo ba abinka da wadanda keda masu gidan rana,ta riga data zabi zaman hostel,ba don komai ba donta samu yin karatu sosai yadda ya kamata,sannan tanason hankalinta ya ttara waje guda,saidai kuma zata dinga zuwa gida duk weekend.
Sam anni bataso haka ba,don zuwa yanzun ayshan kusan itace mai kula da komai na annin,hatta da kayan sawarta,kitsonta abincinta da sauransu,uwa uba sabo daya shiga tsakaninsu,tana matuqar jin dadin zama da ita,duk yadda take hasashen ayshan saita karanci ta wuce nan,wata baiwa Allah yayi mata ta daban wadda ko ita ba lallai tasan da ita,saidai annin bata nuna rashin jin dadin nata ba don kada ta rage mata qwarin gwiwa ko taji babu dadi,don ta fuskanci sosai takeson karatunta,gefe guda kuma amal na dan tabukawa kada ta fuskanci ta raina qoqarinta ne itama.
Ranar da komai ya kammala ya sameta a falon anni,ta riga data saba bacci ne kawai ke maidata nasu sashen,tana zaune saman kujera annin na qasa tana lallabe mata kanta,zanen hausa take mata guda shida duk bayan kwana goma,da yake annin akwai gashi tubarkalla kasancewarta buzuwar bafulatana har bayanta jelar ke fitowa.
Dukkansu suka mishi sannu da zuwa yayin data maida kai tana ci gaba da gyarawa anni kai,shi kuma suna hira da annin,jifa jifa yakan daga kai ya dubeta sannan yaci gaba da abinda yake,tunaninsa daya ya take ji cikin ranta a yanzu haka data rasa soyayyar mahaifiya?,shi kadai yasan dadin da yake ji aduk sanda ya zauna suna hira da anninsa,ita kuwa bata taba samun irin wannan damar ba tsahon rayuwarta,amma har ta iya jure hakan ta hadiyeshi cikin zuciyarta
"Sannu takwara....kije ki nemi abinci kici kuma hakanan,tun dazun banga ko ruwa kinkai bakinki ba" murmushi tayi tana goge hannunta a kunyace tace
"Azimi nake" duban khalipha anni tayi
"Ah...amma kasan tana azumi baka gayamin ba bare a tanadar mata wani abun?" Dan dawurwura yayi sannan ya sake kallon ayshan kafin ya dubi anni,ya bude baki zaiyi magana ta rigashi
"Ban sanar mishi ba anni,saboda hanani zaiyi" ajiyar zuciya ya saki donta qwaceshi,ya bude bakinsa ne kawai ba tare da yasan me zai gayawa annin ba
"Ma sha Allah....bari nasa su atika sumiki wani abun haka"
"A'ah anni duk abinda suka dafa zan iya ci" tana gama fadin haka ta tsinkayi muryar khalipha yana qwalawa laure kira daya daga cikin ma'aikatan,cikin sakan goma ta bayyana a falon
"Idan akwai garin flour kiyimin dan wake yanzun,ayi mishi hadin salad pls"
"In sha Allahu yallabai" ta fada cikin girmamawa gami da miqewa ta juya zuwa kitchen da hanzarinta,yana waiwayowa suka hada ido da ayshan,saita sadda kai tana mamakin ya akayi yasan abincin da take matuqar so?,sau tari a gida takai duk sanda akayi danwake ko za'a daketa saitaci,hakanan koyaya aka bar ragowa bata barinsa saita bi ta cinye komai sanqarewar da yayi shida dafaffen wake(qulu),sharewa shima yayi kamar baiga kallonshi data sata ba,janyo jakarshi yayi ta office daya shigo da ita ya bude ya fito da da wasu takardu ya miqawa ayshan yana mata bayani
"Komai ya kammala,on 29 zaku fara lactures in sha Allah,yau saura sati daya kenan"tuni hawaye ya cika idanunta,kuka yana son qwace mata tana yunqurin danneshi,ta rasa me zatayi me ya kamata tayi,kaman wannan ne karo na farko da zata soma karatu haka take ji,sai ta zamo daga saman kujerar ta durqushe a gabansu shida annin
"na gode,ubangiji ya saka da mafificin alkhairi,Allah yayi muku sakamako da aljannarsa madaukakiya,Allah y...."
"Ya isa haka ayshatu...wannan addu'ar duka kina iya mana ita a zuciya,tashu ki tafi abinki,ki saka a ranki kamar a gidanku aka miki hakan" da qyar ta iya miqewa saboda kuka,inama ace a gidan nasu ne,inama ace ahalinta ne ke mata haka,duk wata soyayya da zata gani daga garesu a yanzu ba shakka akwai dalilin da yasa suke mata ita,ba haka kawai bane,da wannan kukan takai kanta sashensu ta zube saman kujera tana ci gaba da rerashi.
Gab da magariba yabar wajen annin don zuwa ya daura alwala ya wuce masallaci,tura qofar yayi bakinsa dauke da sallama,saman kujera ya hangota nannade waje guda,sheshsheqar kukanta da jan majina na fidda sauti kadan kadan,tsaiwa yayi yana dubanta duk da baya iya ganin fuskarta,duk sanda wata mace mai shekarun hajar ke kuka sai ya dinga jin kamar itace take kuka awancan lokacin da har yau ya kasa bacewa daga qwaqwalwarsa,lokacin daya sakawa suna da baqin lokaci,shi yasa a yanzun kukan nata ke sokarsa sosai,takawa ya soma yi zuwa wajen da take sai kuma yaji ana knocking,hakan yasanya ya sake juyawa zuwa wajen qofar ya bude,larai ce dauke da kayan kwanukan abinci,nuni yayi mata data aje,ta aje din kuwa a ladabce ta juya tabar wajen,ya sunkuya ya dauki kwanukan dai dai sanda ake qwala kiran sallar magariba,saman tebur din dake daura da ita ya aje
"Kukan ya isa haka,idan kuma a fasa makarantar ne kuma toh" da sauri ta tashi zaune tana hadiye kuken gami da qoqarin goge kyawawan idanunta da suka dan rine saboda kuka,ganin haka ya sanyashi wucewa ciki ya barta nan.
Sanda ya fito zai wuce masallaci tana zaune a wajen,jiranshi take ya fito ta shiga ta wanke bakinta,don idan daya yana cikin dakin dayan bai shiga har sai ya fito,har gwarashi wani lokaci zuwa lokaci yakan shiga idan akwai uzurin da bazai iya zaman jira ba,kaman zai wuce office yayi mantuwa zai dauki wani abu da makamantansu,dukkansu suna jin nunansu kaman baqi,saboda ba wanda ya taba rayuwa da wani jinsi daba nashi ba amuhalli guda sai wannan lokaci.
A bakin gate suka hadu da mus'ab da haidar,tun fadan daya yiwa mus'ab din bai sake kamashi da laifin rashin zuwa salla isha'in ko asuba ba,tare suka jera abinsu gwanin sha'awa,akwai qauna da fahimtar juna mai tarin yawa tsakaninsu,duba da wahalar da suka sha a baya wadda ita ta sake haifar da danqon qaunar junansu,haidar ke bare dabino yana ci khalipha ya kalleshi,yasan ma'anar kallon,da sauri yace
"Sorry yaya,kasan yau azumi mukayi ni da anty,ban samu na tsaya nayi bude baki ba kar jam'i ya wuceni,kuma ba'ason asha ruwa baka kai komai bakinka ba" bai sake cewa da shi komai ba,saidai yana mamakin yadda duk 'yan gidan keji da ayshan,yasan lallai ita rinjayi haidar ya soma azumin,don kwata kwata basa shiri da azumi.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Tun daga cikin dakinta take jiyo muryar hamid yana qwala mata kira,sosai kiran nashi ya bata tsoro har tana tuntube garin sakkowa saboda qara dage murya da yake wajwn kiran nata,a kitchen ta sameshi a tsaye,yayin da me aikinsu itama take tsaye gefe guda kantaba qasa kamar kazar da aka jiqa a ruwa,tana shiga ya dago mata kwalin lipton dinsu yana dubanta,sam bata fahimci me yake nufi ba sai da yayi magana
"Ya akayi ganyen shayin nan ya qare tun yau?"
"Kaman yaya?" Ta tambayeshi cikin takaici tana yamutsa fuska
"Tunda baki gane ba bari nayi miki bayani dalla dalla,sanda na kawo lipton din nan na qirgashi a gabanki na kwana sittin ne,ya akayi ya qare kwana ashirin kacal" hannayenta ta saka ta riqe qugunta duka biyun tana kallon hamid,itakam yanzu abun nashi bayan haushi ma tsantsar mamaki yake bata,koda wasa wani yace zaiyi abinda yake din yanzu sai anji kansu
"Ganyen shayin banza ganyan shayin wofi da zaka dinga yimin wannan kiran mafarautan saboda shi,kai yanzu hamid bakaji kunya ba saboda ganyan shayi kake daga jijiyar wuya haka,ohkey toni ban gaji tsiya ba,bazan bi wani lissafin ganyan shayi ba wallahi"
"Eh saboda ai bakisan ciwon kudi ba bakisan ciwon nema ba,yadda nayi almubazzaranci a waje haka ma yanzu kikeson naci gaba?,toba kudin banza gareni ba,lipton kuma saidai kici gaba da siya da kanki har kwana sittin ya cika" ya qarashe fada yana wurga kwalin a shara ya juya fuu ya fita daga kitchen din da alama ma ficewa xaiyi daga gidan donya shirya fes abinshi cikin suit kai baka ce shike magana kan lipton ba,binsa tayi da sauri tana tsaidashi,bai tsaya din ba har sai daya shiga motarsa yana shirin tada ta
"Man shafawa ta ne ya qare....inason wani irin na cikin kayana shine ya karbeni" dariya ya saki yana kallonta kamar yaga mahaukaciya
"Da Allah matsamin kina batamin lokaci kar baqina su wuce kija min asara,don na fuskanci ke bakisan darajar kudi ba"
"Wai hamid lafiyarka kuwa anya na asiri akayi maka ba?" Ta fada cikin harxuqa da mamaki,dariya ya sakeyi sannan ya ziro qafarsa daya waje kaman wanda ya fasa tafiya ya kalli cikin idanunta sosai
"Asma'u,kudi kika fiso a rayuwarki su na saka na shigo dake gidana,kin zaci ni wawa ne wamda baisan ciwon kudi ba saboda.ina da su ko?,toko dana tara bana almubazzaranci bane,kuma kaina na tarawa ba wani ko wata ba,idan zaki koyi rayuwar akwai da babu ki koya,shine kawai zaisa mu samu zaman lafiya ni dake matuqar ko zakici gaba da tambayata wani abu daya shafi in kashe kudina baki gayyaci zaman lafiya a gidan nan ba" yana kaiwa nan yaja murfin motarsa ya rufe ya kunnata ya dannawa mai gadi horn yaja motarshi ya fice.
Kuka asma'u ta saki ta juya zuwa cikin gidan a guje tana addu'ar Allah ya tasheta daga wannan mummunan mafarki da take,idan kuwa har ya tabbata mafarkin take ita da hamid ko hanya sunbar hadawa,sai data tabbatar cewa ba mafarkin bane ta soma tunanin sihiri 'yan adawa suka mata suka juyar mata da hankalin hamid dinta,banda haka mutum mai kudi kamar hamid ace yana maqo irin haka ba shakka da wata a qasa,hakan ya sanya ta dauki wayarta ta lalubi mommy don kai mata qorafi kamar yadda ta saba,don ko misqala zarratin asma'un bata da juriyar riqe damuwa ko solving matsalolin da duk zasu taso mata da kanta.
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
35
Kusan tunda suka taho ita da shi fuskarta ke a cunkushe,ba don komai ba sai don batasan abinda zata je ta tarar ba a gidan,sam bata wani sha'awar zuwa gidansu hamid din,duk da cewa tunda sukai aure bata taba zuwa ba sai yau daya matsanta mata sai taje,saboda zaiyi tafiya ne shima,gaba daya haushin duk wata tafiya tashi take,a yanzu baya cikakken sati daya a gida,bashi wancan gari bashi wannan,bata isa tayi qorafi ba yanzu zai hauta da gorin yana yawon neman abinda ta aureshi ne saboda shi.
A harabar gidan ya tsaida motar sannan ya kasheta,fitowa yayi hakan ya sanya itama dole ta fito tabi bayanshi tana hade fuska har suka isa falon gidan.
Qannenshi ne zaune gaban t.v suna kallo,maza biyu mata biyu sune wadanda suka rage ba'a aurar ba,mahaifiyarsu na tsakiyarsu,kowanne yaci uban asma'u a girman kai da tabara,hakan ya sanya yayansun kawai suka yiwa sannu da zuwa kowa yaci gaba da sabgarsa,babu abinda uwar tace musu don ko ita bata nuna tasan tare suke da ita ba.
Tana rakabe gefe suna ta hirarsu a qalla wajen minti talatin sannan hamid yajiyo
"Au hajiga ga tare fa muke da ita" gilashin fuskarta tadan saukar kadan ta kalli asma'un sosai sannan ta jashi sama
"Na ganta....sai yau taga damar zuwa?,koda yake ai ba yau muka fara ganinta fuskarta sananniya ce" ta fadi hakan da manufa biyu,don sanda hamid din ke neman aurenta bini bini zai kwasheta suje gidansu,saidai babban abinda ya daurewa asma'un ganin yadda dukkaninsu suka sauya,kaf dinsu ba haka suke mata ba a baya kafin ta auri dan uwansu,hakanan suja sha yata sukaci hitarsu suka godewa Allah,ko ruwa ba wanda ya kalleta da shi,sai daga qarshe ne da hamid din ya cewa qanwarsa ta bashi ruwa ta hado da asma'un,saboda tsabar baqinciki da bacin rai ko kallon ruwan bata yi ba har suka tafi.
Cikin mota ta dinga fushi da kumbure kumbure,saidai ko kallo bata isheshi ba bare ya nuna yasan tana yi ba,har daga qarshe data gaji ta tanka
"Amma dama kawoni gidanku kayi don a cimin fuska?" Wani juyowa yayi ya dubeta ya watsar kafin ya bata amsa
"Kamar yaya?"
"Baka ga abinda akayimin ba kenan?"
"To su kike su tashi suyita rawa suna tsalle sunga halittar da basu taba ganin irinta ba,ni da Allah banason fitina kinji ko?" Nan sa'insa ta kaure a tsakaninsu,bata yi shuru ba har sai data ga yana da niyyar kai mata mangari,koda suka je gida a fusace ta fita daga motar ta buga mishi qofar motar
"Kiyi a hankali,don wallahi idan kika sake kika yimin barna taki zan siyar na gyara" ya fada cikin daga murya yadda zata iya jiyowa.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Kwanaki biyar ya rage su soma lacture ta shirya tsaf don tafiya makaranta,duk wani abu daya dace babu wanda ba'a siya mata ba,siyayya irin ta 'ya'yan gata,itadai kallon komai take kamar almara,kaya kaman wadda zata shekara a can,hatta da ruwan sha khalipha bai bari ba sai daya siya mata,wani abun ma har kunyar kanta da kanta take ji duk da yadda anni ke bata qwarin gwiwa,sai take jin kamar ta zame musu wani kaya ta hadasu da hidimarta.
Tana tsaye a falon sashen nasu sagale da jakarta wadda ta zuba qananun abubuwa irin namu na mata,sai take jin kewa ta soma shigarta,jikinta ya danyi sanyi kamar zata wani garin ta barsu,a haka khalipha ya fito ya taddata,atm card ya miqa mata yana kafeta da idanunshi,a sanyaye ta amsa tana son jin qarin bayani
"Duk sanda kike da buqatar wani abu ki cire kudi ki saya,naki ne accnt dinki ne,sati mai zuwa idan Allah ya kaimu da rai da lafiya nima zanyi tafiya,zanbar qasar na tsahon shekara biyu" saita daga kai tana kallonshi,hakanan zuciyarta ta raurawa,sosai take jin ba dadi,kaman cewa yayi idan ya tafi bazai dawo ba,ganin sun hada ido kaman yadda suka saba sai kowa ya kau da kanshi
"Zan dinga zuwa a duk sanda na samu chance Ya fadi kamar ya karanci abinda yake zuciyarta,kunya ce taji tana neman kamata,kardai ace ya fahimci abinda take saqawa a ranta,saita sunkuyar da kai
"Allah ya bada abinda za'a je nema,ubangiji yayi jagora ya kade dukkan abinqi"
"Ameen kema haka" ya fada a taqaice,kasancewar tun jiya yayi mata duk jan hankalin daya kamata,iya gajeran lafazinsa kawai yayi mata dadi a rai
"Na gode" ta furta a sanyaye.
Qwalla ce fal idanunta sanda suke sallama da anni,har mus'ab ya dinga sheqa musu dariya abinsa,khalipha kam falo ya koma yayi zamanshi abunsa,kewarsu take tun kafin tabar gidan,haka suka rakota har bakin mota,inda haidar zai kaita.
Rufe motar tayi ta daga kai a hankalin,take idanunta suka shiga cikin nashi,yana tsaye bakin window din da take zaune hannunsa harde a aqirji,shima ita yake kallo,sai qwallar da take tattalin kar ta zubo ta silalo saman fuskarta,sakin hannayen nashi yayi ya bar side dinta ya koma mazaunin driver,duqawa yayi ta window din motar dai dai saitin haidar,batasan me ya gaya mishi ba na tsahon minti daya kafin ya miqe yana cewa
"Allah ya tsare hanya,a kula da hanya"
"In sha Allahu yaya" haidar ya fada yana tasar motar,yana nan tsaye hannyensa goye a bayansa har motar tasu ta fice daga gidan.
Kadan kadan taci gaba da fidda qwalla tana qoqarin sharewa,haidar baice mata komai ba har sai da sukayi tafiya ta kusan minti goma sannan ya dan saki dariya
"Nikam kukan nan bansan na meye ba?,anya kukan rabuwa da anni ne bana rabuwa da yayanmu bane?" Dan harararshi tayi tana fidda qaramin murmushi,daga bisani tayi qoqarin controlling hawayenta,saidai duk da haka zuciyarta babu dadi,wayarshi ya zaro ya kira khaliphan,da alama shi ya bashi umarnin yin hakan,miqa mata wayar kawai haidar yayi yana murmushi,hannu ta sanya ta karba gami da karawa a kunnenta ba tare da tace komai ba
"Kina kuka kaman wata baby?,kinason dagawa mutane hankali,ko baki shirya ba adawo dake?" Girgiza kai tayi kama tana gabansa sannan tace
"A'ah"
"Allah ya bada sa'a" ya fada cikin low tune
"Amin na gode"
"Bashi wayar" saita waiwaya ta miqawa haidar dake boye dariyar da batsan ta meye ba,magana sukayi da bata wuce ta minti daya ba ya katse wayar yana 'yar mita
"Sai wani jaddadawa yake nayi tuqi a hankali waishi me mata,muma dai mun kusa in sha Allahu mu fara hura hanci muma" daroya ma haidar din ya bata,ita ta sani kawai dai yana jaddadawar ne saboda dan uwanshi,amma ita yaushe takai nan,haka haidar ya dinga janta da hira har ta dan saki jiki,yana bata labarin makarantar da yake can suka fara yi shi da mus'ab kafin daga bisani khalipha ya fitar da su waje.
Ajiyar zuciya ya saki yana maida wayar aljihunsa,baisan me yasha kanshi da kukanta ba harya buqaci jin yata kasance,hakanan kawai yaji yana da buqatar jin haka,sai ya sake sauke wata ajiyar zuciyar yana duban wami littafinta data dauko ta manta dashi saman kujera.
Awa guda suka isa a haka donsu tsaya cin abinci a wani gidan cin abinci dake hanya,itakam aysha har sannan babu abinda taci saboda dama can abincin safen ba damunta yayi ba,haidar na tare da ita har aka gama shigar mata da kayanta,kulawa ta musamman ta samu daga ma'aikatan dake kula da hostel din,bata san me yasa ba,saidai tuni khalipha ya gama sallamar kowa a cikinsu,hakan yasa suke ankare da zuwan ta,saidai komai ya zama normal ya tabbatar babu wani abu da zata sake buqata kaman yadda yayanshi ya umarceshi sannan yayi mata sallama,sanda zai tafin ma dai kamar zata bishi,hakanan dai ta daure ta juya zuwa ta koma hostel din.
Su uku ne a dakin,saidai sanda taje mutum biyun sun gama shirya kayansu basa nan,da alama ma ba ranar su sukazo ba,kasancewarta ita daya a dakin ya bata dama itama ta zauna ta jera komai nata a muhallinsa yadda take da buqata,koda ta gama an kusa sallar la'asar,sai kawai ta kunna gas ta dora jallop din sphaghetti sannan ta shiga bandakin dake manne da dakin ta dauro alwala.
A cooler ta aje abincin bayan ta gama,ta bude barander dake bayan dakinsu ta wanke komai ta tsaftaceshi,bata jin yunwa sai kewar gida dake damunta,tana gefan gadonta tana qarewa dakin nasu kallo,komai neat gwanin sha'awa,fata kawai take Allah yasa musulmai ne,masu halin qwarai,sai ta kasa zaman dakin,ta zari hijabinta ta zura ta lalubi muqullin dakin tanufi qofa tana duba wayarta,aliya takeson kira,yau kwana uku basu samu sunyi waya ba,kowa yana busy.
Qofar da aka turo saura qiris ta daki goshinta,da sauri taja baya tana duban mai shigowar,matashiyar budurwa ce wadda duka duka shekarunta basufi na ayshan ba,doguwa ce bata da jiki,kalarta choculet ce mai daukan ido da sheqi,tana da doguwar fuska da jerarrun fararen haqoranta,idanu ta zaro tana fadin
"Ah sorry sister....sannu Allah yasa ban bigeki ba" murmushi aliyan tayi,yanayin yadda take magana kawai ya isa ya gaya maka tana da surutu
"Babu komai,baki sameni ba"
"Alhmdlh....kece ragowar room partner dinmu da baki qaraso ba ko?" Ta fadi fuskarta qunshe da murmushi wanda ke nuna haka yanayinta yake,kai aysha ta gyada
"Eh"
"Thank god...amma naji dadi....ni sunana halimatu abdullahi musa,amma anfi kirana da hanan,daga hotoro nake,saidai iyayena duka na zaune a abuja,kefa?"
"Sunana aysha umar modibbo"
"Fulani girl?" Hanan ta tambayeta tana dage gira,dariya aysha tayi,yadda hanan din bata da wahalar sabo yake bata mamaki,kai ta gyada mata again
"Kice na shirya,na kusa koyon fillanci" tare suka sake sakin dariya gaba dayansu
"Well,na tsaidaki da surutu na ko,naga kamar fita zaki da alama uzuri gareki" komawa ayshan tayi da baya ta nemi wajan zama,don zuwa yanzu kuma bata da wani sauran dalilin fita
"A'ah,zaman shuru ne dama yamin yawa nace bari na dan fita naga yanayin hostel din"
"No more loniless tunda na dawo" ta fadi still tana murmushi gami da zube jakunkunan dake hannunta
"Naje na amshi saqo ne daga wajen uncle dina....ga wata azababbiyar yunwa da nikeji...nace ma ya tausayan ya sayan wani abu amma yaqi" ta fada tana kwabe fuska,dariya aysha tayi tana nuna mata cooler din data zu a abinci
"Ga abinci can saiki diba kici" ido ya fiddo
"Kai amma kin taimakeni wallahi,dama maman hunaifa nake saka ran idan ta rigani dawowa na samu daga wajenta,to itama kinga shuru" ta qarasa fada tana bude abincin,qamshin ya daki fuskarta saita lumshe ido
"Tun kafin naci ma nasan zatayi dadi wallahi,sauko muci"
"Kaman a qoshe fa nake"
"Ba wani nan,saidai idan nima bakiso naci ne" jin haka ya sanya aysha ta sauko,hanan ta zuba musu tare suka soma ci tana ci gaba da jan aysha da hira,itadai kallonta kawai aysha take,tana mamakin saurin sakewa irin na hanan,bata da baqunta sam,saidai ta lura tana da kirki matuqa,tana da hankali tsafta sannan uwa uba da ganinta yar qwalisa ce wato gayu,da haka suka gama cin abincin,suna tsaka da wanke hannunsu aka sake turo qofar dakin nasu,wata matashiya ce ta sake shigowa,shigowarta ya sanya hanan yin dif,da aysha suka gaisa sannan ta dubu hanan
"Kin dawo amma koki sanar min?"
"Babu buqatar hakan tunda gashi yanzu kin ganni" hanan ta fada tana miqewa ta bude bandakinsu ta shiga,ta dade matashiyar a tsaye hanan bata fito ba,hakan shi ya tilasta mata tafiya,sai data tafi sannan hanan ta fito tana jan tsaki gami da mita,ita dai aysha naji bata ce komai ba hakanan bata tambayi dalili ba,saboda ba dabi'arta bace.
Hanan na idar da sallah aka sake knocking,wata matar ce ta sake shigowa,fara ce itama qal da ita,ba siririya bace haka bamai qiba ba,tana sanye da doguwar rigar material da mayafinta,a qalla zata girmewa su aysha da shekara hudu haka,hannunta rungume da yarinya wadda bata wuce shekara daya ba,sai jakar mata data ratayo,bayanta security ne mata dauke da jakankuna manya guda biyu,da sauri hanan ta miqe tana fadin
"Oyoyo hunaifa" ta karbe yarinyar daga hannun mamata,murmushi matar take idanunta na kan aysha
"Sannu da zuwa" ayshan ta fada itama tana murmushi
"Yauwa sannunkj,baquwa muka samu ne hanan?" Waiwayawa tayi tana duban aysha cikin murmushi
"Cikon abokiyar zamanmu ne"
"Ma sha Allah,da fatan kinzo lafiya" ta fada fana zama gefan gadonta
"Lafiya alhmdlh" ta bata amsa tana karbar hunaifa daga hannun hanan,karon farko yarinyar ta shiga ranta,tayi kyau cikin overoll pink da hula
"Ummm su mmn hunaifa,daga cewa yanzu yanzu zaki dawo sai kuma yanzu aka ganki,kodai baban hunaifa ne ya riqeki?" Dariya ta danyi tana sake hayewa gadon sosai
"Kedai bari kawai,shima yau zai wuce abuja sai dana tsaya na kintsa shi tukunna" ta fadi tana dariya,itama dariya hanan takeyi
"Kinsan yanzun zamani ya canza,idan baki iya tsayawa kin kame mijinki da kyau ba kina can kin sau baki wata zata kame miki shi,koba haka ba qanwata?" Ta qarasa fadi tana duban aysha,murmushi kawai tayi ta gyada kanta,a hankali ta furta
"Haka ne"dariya hanan ta kuma sawa
"Eh lallai wlh kam da gaskiyarki wallahi maman hunaifa,nifa iya zaman kwana hudu da mukayi dake ba qaramin qaruwa nayi ba,wannan idan na tashi aure gidanki zanzo na tare"
"Muna miki maraba,amma ki taho da glass din sawa idonki,donmu gidanmu duk baqon da zaizo saiya shirya" ihun dariya hanan ta saki yayin da aysha ke kallonsu tana murmushi,abun ya qayatar da ita sosai,haka suka jima suna hira abinsu cikin dakin,daga bisani maman hunaifa wadda asalin sunanta shine raihana tayi qorafin yunwa,saurin da takeyi ya hanata tsaiwa taci,cooler din aysha hanan ta tura mata,dubanta mmn hunaifa tayi
"A ina kika samu abinci?,kekam nasan ba abinda kika tsana irin girki bare nace ke ke kikayi"
Dariya hanan tayi tana cire hijabin sallarta ta maida rolling dinta
"Baquwarmu ce wlh da qoqari,nima zuwa nayi na tadda ta dafa"
"Sannu fa,na gode" maman hunaifa ta fada tana duban aysha,wadda tayi shuru tana mamakin hanan da akace ba abinda ga tsana irin girki,itakam sam bata ga abin wahala ko abin gudu a girki ba,sun jima suna hira a tsakaninsu,duk gaba dayansu 'yan hira ne,idan ka dauke aysha da wani abun saidai tayi murmushi kawai,hakanan yanayinsu taji yayi mata,kuma bisa dukkan alamu zataji dadin zama da su,har wajen takwas na dare suna hirarsu kowa na baiwa dan uwansa labarin dan abinda ya shafi rayuwarsa wanda ya kamata dan uwansa ya sani,itadai aysha nata surutun kadan ne,abun da ya tashi hirar tasu kiran wayar hanan da akayi ta haye gado ta barsu a nan,daga bisani itama maman hunaifa bayan ta gama lallaba hunaifa tayi bacci ta sungumi tata wayar ta haye gado,sai ya zamana aysha ce kawai ta rage,itama saita haye nata gadon ba don tana da abunyi ba,likimo tayi tana juya wayarta gami da tunanin wanda zata kira,daga bisani sai ta gwada wayar aliya,a kashe ta taddata,tilas ta sauya akalar kiran nata zuwa ga layin anni,bugu uku ta daga,muryarta cike da fara'a take cewa
"Yanzu bada jimawa ba muka gama maganarki ni dasu haidar a wajen cin abinci,yau gidan duk sai ya yoye babu dadi,khalipha ya wuce shima zai fara tsayawa a legos,rahama ta tafi gida" murmushi mai sauti ta fitar tana jin kewarsu
"Nima nan ba dadi"murmushin itama anni tayi cikin jin dadi
"To ya za'ayi,ba yadda banyi dashi ya barmin diyata a kusa ba yace min can yafi"dariya tayi
" zan saba ai anni in sha Allahu"
"To Allah ya taimaka yayi jagora,Allah ya hadaki da mutanen zama na qwarai"
"Amin anni na gode Allah ya qara girma" yan mintuna suka qara akan layi wanda yawanci tana tambayar annin jikinta da yadda tayi da 'yan abubuwan da aysha ta dauke mata,tace wani haka ta lallaba tayi wani ta haqura,da yake ba komai takeson masu aiki suyi mata ba,daga qarshe sukayi sallama da annin,bayan ta dan ja hankalinta kan ta kula da mutuncinta,wanda kusan dai duk kaman tana taya khaliphanta ne kishinta.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Tsaki taja bayan ta gama zazzage ragowar madarar data rage a kwalin ta wurgar da kwalin gefe tana masifa da mita a ranta,idan akace mata haka zatayi rayuwa da hamid koda mafarki tayi zata qaryata mafarkin,wannan tafiyar da zaiyi babu abinda bai bar mata ba,ya dan rage maqon nashi kadan wanda ada bai wani dameta sosai ba saboda tana da kudinta a accnt,duk abinda take buqata shi take tabawa ta siya abinta,to wancan satin da sukayi waya da daddy yayi mata fada kan ta rage kashe kudi,ya duba accnt nata yaga kudinta sun soma yin qasa sosai,har yana cewa zai sama mata business ta dinga yi,don baison almubazzaranci da rashin adani,ya kawo mata misali da aysha wanda hakan ya qona ranta sosai,ya gaya mata har yanzu babu abinda ta cira a accnt din daya bude musu,tunawa tayi da daya accnt din nata data bude tun tana gida,bayan ta tare ta bawa a hamid ajiyar atm din,kudin cikin accnt din duk kayan aysha ne da take karbewa wanda tasha alwashin sun daina hada komai iri daya take baiwa mommy ta saka a kayanta ta saida saita karbi kudin,ciki harda wannan sabuwar motar tata da daddy ya siya musu iri daya.
Murmushi ta saki tana ayyanawa a ranta yau ga ranar plan dinta nan,a nutse ta soya qwai guda biyu daya rage mata da sauran kayan cikin data baiwa mai gadi ya kaiwa matarsa ta dafa mata ta dumamashi,don mai aikinta tunda hamid yayi tafiya itama ta tafi,shi yace mata ta tafi tunda shima baya nan,amfanin zamanta idan yana nan tunda asma'un bata iya komai ba,tunda baya nan tayi tafiyarta ita asma'un tasan ya zatayi da kanta,ya gaya mata cewar zai cire kudin aikin kwanakin bazai bata ba,tana ji tana gani ta tafin,ba irin bacin ran da asma'un batayi ba,qarshe mummy ta kira ta yiwa qorafi tana kuka,baqinciki ya hana mummyn magana,itakam har ta soma gajiya da jin matsaloli,ba ranarvAllah da zata fito ta fadi bata ji matsala daga asma'u ba sai dai daikun ranaku,wai dama haka auren masu kudin yake ne ko kuwa?,a'ah ta baiwa kanta amsa,koda wasa aysha bata taba kiranta tayi koda tarin da zai nuna cewa akwai wani abu dake faruwa ba tare da ita mara kyau,hakanan ita karan kanta shaida ce cewa bata taba wani kuka da daddy ba,hakanan mummy ke turo mata lantana ta wuni,itama daga bisani data gaji da wahala da ayyukan asma'un da basa qarewa ta tsiri ciwon qarya,dole aka sarara mata.
A nutse ta gama cin abincinta tana jin nishadi zata ciro kudinta ta kashe sabgar gabanta,don dama tun wancan satin ta rasa ya zatayi,za'ayi bikin daya daga cikin qawayensu,kuma kowacce idan bikinta ya tashi gudun mawa ake bata ta qasaita,samanta ta koma ta fesa wanka bayan ta shirya ta soma duba dakinta don dakin hamid din bai barinsa a bude,ko kasuwa zai fita saiya garqame abinsa ga tagi da muqullinsa bare wannan tafiya ta satittika,cikin sa'a kuwa ta gano atm din,ba bata lokaci ko jiran neman izini ta saka mayafinta ta fice daga gidan.
Sau uku tana tada motar taqi tashi,saidaga bisani ta lura ashe mai ne babu,haka ta sauka ta bada dari biyar aka siyo mata a bakin titi wajen 'yan bututu ta zuba ta tashi motar ta fice.
Ta samu layi sosai a ATM din,babu yadda ta iya haka tayita jira saboda taga mafadata aka hada a wajen har layi yazo kanta,saidai ga mamakinta sai ake cemata babu kudi a accnt dinta
"A'ah!" Ta fadi cike da madaukakin mamaki,ita tasan kudin ciki ya kusa dubu dari takwas da wani abu,sake maidawa tayi aka sake gaya mata hakan,take gumi ya soma yanko mata
"Hajiya kiyi da jiki da Allah,muna da yawa fa" cewar wani matashi dan ci da zuci dake bayanta
"Ba kudi ba a accnt din nata amma tazo ta wani faka mota tana yiwa mutane qarya tazo cirar kudi" inji wanda yafi kusa da ita ya fadi sanda ta fice daga layin da katin a hannunta,waiwayowa tayi da niyyar sille mishi,saboda tana ganin a girmanta ta girmi ayi mata hakan,saidai yadda idanu sukayi mata yawa yasa tayi hanzarin yin gaba ta fada motarta
Bata tsaya ba saidata isa gida,ta fada saman kujera ranta na quna,tana son tayi kuka tana cijewa,to yaushe wai har hamid ya fidda kudaden nan bata sani ba?,a fusace ta dauko wayarta ta nemi lambobinsa,bugu hudu aka dauka,saidai maimakon muryarsa muryar mace taji,a zabure ta daga wayar tana dubanta sai taga an yanke kiran,sake kiranshi tayi harta katse ba'a daga ba,sai data sake bi sannan aka daga,wannan karon shine
"Wace yar iskar ce ta daga wayarka?"
"Au....shi kika kirani kiji uwata?" Tunani ne ya fado mata,idan ta biyeshi suyita ne zatayi biyu babu,gwara ta fara sanin ina kudadenta suke tukunna
"Atm dina na wajenka,na dauka yau zanyi amfani da shi amma babu komai cikin accnt din"
"Anyi amfani dasu" ya bata amsa kai tsaye
"Kaman yaya hamid?,me kake nufi?" Ta tambayeshi tana gimtse fuska tamkar yana wajen
"Abinda nake nufi nace miki nayi amfani da su"
"Kudin nawa hamid?,wannan wanne irin abu ne daga baka ajiya zaka dauki haqqina kaci?"
"Dakata da Allah malama.." Ya katseta ba tare data gama fadin abinda zata fada din ba
"Gori zakimin kome?,karki gayan maganar banzan,nawa ni na kashe miki a rayuwa,nawa kike cimin yanzu?,to na cinye saiki qwata idan kina da qarfi" yana kaiwa nan ya datse kiran,kuka kawai ta saki saboda tsabar baqinciki da takaici,nan saman kujera ta zube duniya nayi mata qunci,wannan wace iriyar rayuwa ce,me ta yiwa hamid yake saka mata da wannan abubuwa?,haka ta dinga qwalla tana tambayar kanta.
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
36
Cikin sati uku kacal ta soma gane kan abubuwa na cikin makarantar,yanayin rayuwar da banbancin muhalli,yanayin jama'a kala kala,banbancin halaye dabi'u jinsi da kuma yare.
Ta fannin abokan kwananta kuwa sai sam.barka,dukkansu mutanen kirki ne kamar yadda take addu'a Allah ya hadata dana gari,hanan matashiya ce wadda zasuyi shekaru daya,haifaffiyar kano saidai iyayenta na zaune akano saboda yanayin aikin gwamnati da babu inda baya kai mutum,'yar gata ce sosai kasancewarta ita daya ce mace cikin yaran da mamanta ta haifa,tana da ilimi nutsuwa da kamun kai,tana da surutu,sauqin kai da saurin sabo da jama'a,batason muce mara kamun kai mara tambayi ko kintsi,yanayin rayuwa da take cikin mutane da suke a waye,uwa uba gata bata rasa komai ba saita zama 'yar ado 'yar kwalliya,hanan badai wayewa da gogewa ba,baya ga tsafta taba da son kwalliya da qyale qyale na mata,duk wanda ya santa a haka ya santa,hanan nada saurayinta Abubakar saddiq wanda aka riga akayi musu baiko da shi aka saka musu rana,shekara guda,wato shekara mai zuwa kenan,suna matuqar son juna irin soyayyar nan mai tsafta.
Sai ruqayya ummu hunaifa,matar aure ce wadda aqalla ta basu shekara hudu ko uku,saidai tana da sauqin kai faran faran da son jama'a,macace wadda itama 'yar gayu ce mai zaman kanta,wanda gayunta ya nuna har a jikinta,shekararta uku da aure yanzu haka tana da yarinya 'yar shekara daya,suna zaune a farawa saidai mijinta na aiki a abujane shima,duk weekend yana dawowa gida yayi da iyalinsa,mijinta nada hali don a revenue yake aiki,ruqayya nada ilimin xama da dan adan da experience na rayuwa mai yawa,sakamakon dan yawace yawace na qasashe da sukayi ada da mijints ibrahim,da kuma tashi da tayi a hannun kakarta,tun zuwan aysha taji jininsu ya hadu,kamar yadda Allah ya hada jininsu da hanan,wannan kenan.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Dakin babu kowa sai ita kadai,ita kadai dince ta dawo saboda hanan da mmn hunaifa duka suna aji,sakamakon banbancin course da suke dashi,kowacce akwai abinda take karanta,rana ake qwalawa sosai,shi yasa tana shigowa ta sauya kaya zuwa doguwar riga mai yankakken hannu,ta nade tulin gashinta daya soma damunta da dankwalin rigar,sannan ta shiga bandaki ta daura alwala ko zata ji sanyi,duk da tana fashin salla,saman gadonta ta dawo tayi rubda ciki,dai dai nan kiran aliya ya shigo mata,ba bata lokaci ta daga don dama kwana biyu basuyi wata doguwar hira ba karatu ya soma sa kowa gaba.
Sun kuwa jima suna hirarsu daga bisani sukayi sallama ta yanke ta kira anni suka gaisa,daga anni ta nemi mero sai gwaggo asabe,wanda daga bisani ta tuqe kan lambar umminta,ta jima tana kallon lambar kamar ta kira haka zuciyarta ke raya mata,tayi kewarta qwarai,tana son jin muryarta koda fada zata yi mata,tana son jin motsinta ko yaya ne,qwalla ce ta cika mata idanu,saidai tayi iya yibta ta maidata jin an turo qofar dakin.
Hanan ce,kallo daya zaka yi mata ka tabbatar a jikace take,haka ne kuwa don litatafan ta watsar a qasa
"Wayyo eesha yunwa" dariya aysha tayi tana saukowa daga saman gadonta
"Aikuwa kin daki gurbi,don yau ban dora komai ba na zaci tun yau zaku tafi gida weekend" ciki ta kama tana yamutsa fuska
"Ki taimako don Allah" dariya tayi ta soma yunqurin kunna gas
"Saikin dan qara haquri" saman katifar ta ta koma ta kwanta tana yar mitar data baiwa aysha dariya,tana tsaka da jajjage maman hunaifa ta shigo dakin,ita daya ce don tun wancan satin tabat hunaifa a gidansu bata dawo da ita ba,ba irin mitar dasu aysha basuyi ba
"Ke kike biye mata aysha,barta don Allah yau tasha yunwarta,saison abincin amma bazata iya tsayawa ta dafa ba" ta fada tana hararar hanan
"Haba surukata(haka take tsokanarta tunda qanin maman hunaifan ya ganta yace yana so),idana gaban nazir ishaaq dinne ma haka zaki fada?"
"Eh mana tunda ke son jiki gareki"
"Karki damu zan koya fa ai aysha zata koya min" ta fada tana miqewa zaune
"Ko ba zaki koyamin ba naga kina bata rai?" Sosai ta baiwa aysha dariya,zama da hanan akwai dadi amma idan baka iya ba saikuyita fada,bata ma kalleta ba bare ta gane hakan da har zatayi mata sharhi
"Zanfi kowa murnar ki koya din,saboda sanwa adon macace"
"Gaya mata dai" cewar mmn hunaifa,haka suka dinga zolayar juna suna hirarrakinsu,har aysha ta gama musu jallop din couse couse data ji kifi suka hadu suka ci.
Qarfe hudu hanan ta fito a wanka,tana saka doguwar rigarta ta dubi aysha
"Ko zaki rakani,naga tunda kika zo baki taba zagayawa ko yaushe daga daki sai aji"
"Ina zaki je" mmn hunaifa ta tambayeta
"Kinsan jibi weekend,ga lallen hannu na ya fita,kaina tun last month rabonsa da retourching zan leqa ayimin"
"Nima fa lallen nakeso wlh,abban hunaifa zai biyo jibi mu wuce gida"
"Za'aci amarci kenan?" Hanan ta fada tana kashe ido cikin son tsokano ruqayya,dariya ta bata ta riga ta saba da halinta
"Allah ya shiryeki hanan,ko kunyata bakiji" ta fada tana shiryawa itama
"Ki shirya muje ko?" Ta sake cewa aysha wadda ke kwance tana duba handout,sauketa tayi daga fuskarta tadan yatsina fuska
"Kuje kawai,nikam ban sha'awa,kaina ma kuma a wanke yake" baya hanan taja tana dubanta
"Nimam aysha mamaki kike bani,kekam kaman ba budurwa ba?,duk wani qyale qyale na mata babu ke a ciki,ko dan saurayi haka ban taba ganinki da shi ba?,to tashi yaukam ko kallo saikinje kinyi" ba yadda ta iya da jarabar hanan,hakanan ta miqe ta daura alwala ta sake shafa mai powder da man lebe ta zizara kwalli,har ta dauki hijabinta zata dora saman rigar jikinta tace bata isa ba,bazata jawo a rainasu ba waje zasu je na masu aji,hakanan ta maida ta ciro doguwar riga tayi rolling da mayafinta,plate shoes ta saka da jakarshi,sai wani agogo dan siriri da yazo a cikin jakar
"Ma sha Allah" mmn hunaifa tace
"Da ina da wani qanin bayan ishaaq da nayi masa kamu wallahi" hakanan taji gabanta ya fadi,saita tuna khalipha,tunda ya tafi basu yi waya ba gashi sunci qarfin semester farko,dariya tayi kawai ta basar da zancan suka fito daga dakin,duk cikinsu babu wanda yasan komai game da rayuwarta,ba wanda yasan tana da aure,har yau kuma batayi maganar da kowa ba cikinsu,kallon budurwa duk suke mata,anni ce babarta,haidar qaninta.
Tunda suka fito duk wanda suka gamu da su saisun kalleta,ta rasa kallon na meye,har hakan ya soma damunta yasa ta fara tsarguwa ko tayi wani abu ba dai dai ba,don yawanci idan zata fita lacture shigar hijabi takeyi wani lokaci harda niqab,jefi jefi hanan ko mmn hunaifa kan tsaya su gaisa da wasu wasu kuma su wuce,mamaki take ya akayi sukasan jama'a haka?,sai da suka fito gate din makaranta suka samu abun hawa suka wuce.
Babban waje ne wanda idan aka ce mata akwaishi a wudil zata qaryata hakan,gurin suna gyaran gashi da jan lalle da baqi,hakanan akwai turarukan jiki dana kaya masu kyau da zabar qamshi,kana shiga wajen ma zakasan eh lallai akwai turare a wajen,hanan aka soma yiwa gyaran kai aka sa mata lalle sai mmn hunaifa,daga bisani hanan din da taimakon mmn hunaifan suka tubure sai an saka mata,hakan ba yadda ta iya ta ware kanta aka soma gyara mata
"La haula fi shi'atillah,ba banza ba bakison gyaran kai,muda bamu da mai yawa muke damuwa dama da shi" inji hanan gana zaro ido,itakam murmushi kawai tayi,sai take jinta a takure kaman tana waje,bayan an gama itama aka saka mata lallen,amma.ja tace tana so,iya yatsun hannu da qafa,data cire kuwa saiga yatsun nata shar da su,lallen yayi marroon a farar fatarta,itakanta sai daya bata sha'awa,don ta manta when last da tayi qunshi irin haka.
Sai magariba suka gama,hanan ta siya turarukan kayan dana jiki leda biyu,da gawayi irin mai saurin kamawar nan ta biya suka wuce,suna zuwa daki ta miqawa aysha daya
"Nima a gun mmn hunaifa na soma gani,yana da kyau idan ya kama jikinki" godiya tayi mata bayan ta amsa din,don tana jin qamshinsa a kayanta yana da dadi sosai,a ranar ita kanta taji dadin yadda kanta yayi kyau,hakan bayan ta gama sallar tayita kallon yatsunta har hanan ta lura ta dinga yi mata tsiya.
Tun daga sannan zuwan itama ya zame mata jiki,ko basu je ba data fita ita zata je a sake mata,cikin lokaci kadan saiga ayshan ta soma koyar wasu abubuwa irin na matan da suke da aji daga wajen hanan da mmn hunaifa,yanayin zamantakewarsu da samari da kuma mijinta,idan suna wani abun kallonsu kawai take,ruqayya badai iya tarairayar miji da shagwabashi ba,hakanan hanan da nata saurayin,wani lokaci ita kunya ma take ji sukuwa ko a jikinsu,har gori suke mata kan tayi zuciya tayi saurayi
"Na aurar dake keda hanan na huta lokaci daya" cewar anty ruqayya,sai abun ya soma burgeta,ta dinga jin inama itace su,ta dinga ji inama zata samu wanda zai nuna mata zallar kulawa kamar ibrahim din mmn hunaifa shida mmn hunaifar,ko hanan ita da saddiq dinta,da alama soyayya zaqi gareta,tana son dandana nau'in wannan soyayyar baya gata sauran mutane gama gari data sameta a yanzu,takan jima tana wannan tunanina ranta.
Cikin taimakon Allah suka gama semester daya har suka soma nisa cikin ta biyun,a sannan ayshan ta samu qarin wayewa da budewar ido,komanta ya soma sauyawa saboda gogayya da mu'amala da mutane iri daban daban,shuru shurunta ya ragu duk da cewar har yanzu akwai wannan kunyar da kamun kan,saidai yanayin ado da kwalliya,qyale qyale,iya magana da sauransu duka akwai sauyi tattare da hakan.
A wani zuwa da tayi weekend anni ta mata maganar zuwa gida,itakanta tana son hakan,don tunda tabar gidan a qalla yanzu watanni kusan bakwai zuwanta daya gidan,babu musu ta shirya,kwalliya tayi sosai abinta,dama gashi ta soma zama expert a wannan bangaren,kwalliya mai sanyi da aji da nuna asalin gayu,ba hauka ba hayaniya,haidar shi zai kaita kaman yadda suka saba yawanci idan zata fita ko zata koma makaranta shi yake kaita.
Ana magariba suka isa gidan,ya sauketa shi ya wuce masallaci don yayi sallah,da sallama ta shiga falon,mutum biyun dake tsaye a falon aka rasa mai amsata,sai mummy ce tayi qarfin halin amsawa tana cewa cikin borin kunya
"Indo ce...maraba" sai ta dubi asma'u wadda ke tsaye,inda tasan aysha ce babu abinda zai tsaidata har tazo suyi tozali da juna,uwa uba kuma ga cartoon na kifi da nama da lantana ke fito mata da su wanda zata tafi dasu gida,don dama tuni hamid ya shafe wannan babin,yace abinci shine dole aci,wadan nan sai idan ta kama aci din,ita kuma bata iya jurewa sam,tunda ta saba a gidansu ko yaushe cikin ci suke,uwa uba kuma bata saba laluba abu taji babu ba
"Bari usama su gama sallah sai ya kaiki,wannan ciki da kwadayi yake gashinan saikiyita ci ai tunda na gidanki baya burgeki,banda abun hamid ma da ya barmiki motarki basai ya wani sauya miki sabuwa ba,dududu motar watan ta nawa ma..." Mummy ta waske don kar suji kunya wajen ayshan,ta wannan bangaren sai asma'un taji dadin waskewar da mummyn tayi,hakan ya sanyata ta dan saki jiki kadan,ta koma daya daga cikin kujerun ta zauna .
Aysha baiwar Allah ita sam bata ma fahimci komai ba,hakanan bata kawo wani abu cikin ranta ba banda ma mummyn tayi magana,fuskarta a sake ta soma gaida asma'un,amsawa tayi tana dage kai kaman dai yadda take mata a baya,saidai duk da hakan bai hanata satar kallon ayshan ba,mamaki da fargaba suna mamayarta,sauyin data soma gani tattare da ayshan,saita kwatanta da kanta,babu komai tattare da ita sai uban koma baya data fara cimmata,tana shirin yi qarkon kifi daga ruwa tana shirin komawa wuta,ba ita kadai ba,ita kanta mummyn a ankare take,saita kasa daina kallon ayshan,komai nata ya sauya,hatta da yanayin maganarta
"Anty asma'u ina yaya hamid?" Aysha ta tambaya bawai da wata manufa ba,da manufa daya,duk sai asma'un ta tsargu,tana ganin kaman ayshan tasan wani abu dake faruwa da ita
"Hamid dan albarka yana nan....baha qasar ne ma,yana dubai,dazu suka gama waya wai ya aiko a dauki motarta ya auno mata wata shine kika jini ina fadan almubazzarancin da yake,bayan ba komai motar tayi ba" biyayyar ajiyar zuciya asma'un ta saki,tasan inda don ta itace masifa zata hau ayshan dashi,wanda qila garin masifar ta tona asirin kanta bata ma sani ba
"Allah sarki....an gode Allah ya qara arziqi"
"Amin amin dai.....ke kuma daga aure miji ya kwashi jiki ya tafi cyprus har yau babu shi ba labarinsa,ya bazamaki makaranta kema kamar karatu aka kawo duniya,don yana ganin hadin asma'u ne ai bai kamata ya wulaqanta ki haka ba ko?,kema saikace ba mace ba,komai sai an miki ko an kwatanta miki?" Sallamar daddy ita ta katse wannan dogon sharhin na mummy,ganinsa ya sanya asma'u miqewa,hankalinsa na kan aysha,cikin walwala yake mata maraba bakinsa a bude,itama zamowa tayo cikin qauna da kulawa ta soma gaidashi,ya amsa cikin kulawa yana tambayarta mutanen gidan da karatunta tace komai lafiya
"Khalipha ana can dai karatu da business ya riqeshi,ai ma sha Allah har yau halayensa dana sanshi da su suna nan,kusan kullum sai ya kirani mun gaisa" kanta ta duqar tana murmushi,cikin ranta tana tambayar kanta me yasa yana neman kowa amma banda ita
"Au baki tafi ba?" Daddy Ya tambayi asma'u dake yana dubanta
"Eh usaman bai shigo ba"wayarshi ya ciro yana lalubar lambar usaman yana cewa
"Ai ya kamata ki koma haka,sha'anin zaman aure sai haquri,kowacce mace da tata jarrabawar"
"Haka yake fa,kowa da tashi,ga ayshan nan ita tunda ya ajeta bai sake dawowa ba,gwara ke yakan dawo gida,kuma dama haka masu kasuwanci a qasashen waje suke,kinganta aysha wai tana qorafi kan hamid ya fiye fita waje" murmushi kawai tayi,tasan mummyn ta jina da sanin wace ita,hakanan yanzu da wayewa da karantar mutane ta cikata saita sake yiwa halayyar mummyn fashin baqi ta sake karantarta sosai
"Neman halak yake,saiki qara haquri,wani ma wannan damar yake nema bai samu ba" sai kuma mummyn tayi shuru tana sin yiwa maganar fassara,tana jin kamar ayshan da biyu ta fadi haka,hankalin daddy bai kansu sai daya gama wayarshi
"Yana waje usaman" ya furta yana ciro kudi daga aljihunsa ya miqa mata
"Aci gaba da haquri,kinji dai me na gaya miki dazun ko?"
"Eh daddy na gode"
"To madalla,zan aiko alqasim ne idan kayan sunzo ya kawo miki,zama babu sana'a babu kyau,Allah ya wuce gaba"
"Amin daddy" ta fadi tana addu'a cikin ranta karya furta wata kalmar da zata sa aysha ta gane komai,haka sukai sallama aysha na mata ta gaida gida,da qyar ta amsa tana jin kishi da qyashin ayshan cikin ranta,batasan me yasa kamar ta fita sa'a ba a rayuwa,miqewa.mummy tayi ta bita bayan ta saka an kwashe mata kayan an bita da su ta barta ita da daddy a falon suna hira,hira suke sosai abinsu gwanin sha'awa,yana jin dadin yanayin daya ga ayshan,yasan cewa da ikon Allah ta sake samun ci gaba ne a rayuwarta,a duk sanda ya tuna yadda ya daukota daga qauye su saiyaji tausayinta,ya kuma sake binta da addu'ar ci gaba da samun dacewa a rayywarta,nan haidar ya samesu,shima ya shiga hirar tasu,sun jima kafin daga bisani suyi haramar tafiya,sai a sannan ta kuma ganin mummy,ta danqa musu tsarabar data yi musu daddy ya amsa yana murna bawai don baifi qarfin abun ba,a'ah,saidon yadda kyauta take da girma da kima koma kafi qafin abinda aka yi maka kyautar da shi,yayin da mummy ta karba kadaran kadaham,duk da cikin ranta tayi farinciki,don wata sarqa ce fashion sabuwar shigowa mai tsadar gaske,ko ita bata kai ga siyanta ba har yanzu,anni ce kuma ta bata tace ta bata a zuwan ita ta saya matan,da biyu kuma tayi hakan tasan saqon zaije yadda ya kamata har cikin jiki da zuciyar mummy,ya kuma je din.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Washe gari da safe suna breakfast anni ta dubi aysha
"Ni kuwa ayshatu jiya zuwa shekaran jiya kunyi magana da khalipha?" Daga kai tayi ta dubeta gabanta na faduwa,tunda ya tafi baifi sau biyu daya ya kirata,batasan me zata ce mata ba,bata so tayi wata magana kuma batasan me khaliphan yace da anni ba karta warware masa,saita gyada kai kawai
"ke kika sakarma khalipha har haka kenan ya jima bai waiwayo gida ba?"gabanta ne ya fadi,sai tayi qoqarin tattara nutsuwarta,ta hade hannayenta waje guda bayan ta aje spoon din hannunta
"Tunda ya zauna anni akwai uzuri,idan baida wani uzuri na tabbatar bazai zauna har haka ba,zai zo da zarar ya samu dama in sha Allahu,aci gaba dai dayi masa addu'a" sosai kalamanta da amsar data bata ta kwanta mata a rai,sake shiga ranta tayi,tana yaba nutsuwa hankali da kuma haqurinta,wanda hatta yaran 'yan uwanta da dangin mahaifinsu khalipha masu zuwa dama wadanda basa zuwa bata ga masu hankali da nutsuwarta ba
"In sha Allahu aishatu,Allah yayi muku albarka" duka suka amsa da amin.
Bayan ta kammala ita ta soma tashi,saboda yau takeson ta yiwa anni gyaran dakinta kamar yadda ta saba duk sanda tazo weekend din qarshen wata,abun na damun amal sosai,amma ba yadda ta iya,kuma ita din ba iya yi zata yiba,hakan ya sanya duk weekend ita kuma take tafiya wajen mamanta har sai ayshan ta koma makaranta.
Haidar ne ya sauke ajiyar zuciya yana duban anni
"Anni....nifa ya khalipha bana ganin yana kiran anty...anya ko da gaske ne abinda ta gaya miki kidai bincika"
"Na sani haidar,ina sane na tambaya din,babu wani cikinku da zai layancemin wani abu,na san halayen kowannenku dai dai gwargwado,amma zan sake tambayarta don na tabbatar din"
"Nikam anni kimin addu'a Allah ya bani matar aure kaman takwararki" haidar ya sake fada yana dan murmushi,itama murmushi tayi tana dubanshi
"Aysha tana da nagarta aliyu,nagarta mai yawa,tana da tarbiyya wadda dai daikun yara a yanzu keda irinta,duk da tarbiyyarta daga indallahi ce,ina maka fatan samun mace kamanta"
"Allah amin" ya amsa yana daga hannu,bata rai mus'ab yayi
"Nifa anni?"
"Kaima haka auta" ta fadi tana murmushi gami da shafa kanshi,sai ya saki dariya yana jin dadin annin ta mishi haka gaban aliyu don yaji haushi fadansu na sako da sako,saidai wannan karon dauke kai yayi kaman bai gani ba.
37
Ta kammala gyaran dakin anni tana shirin fitowa annin ta shigo
"Sannu da aiki ayshatu,Allah yayi ma rayuwarki albarka" sunkui da kai tayi tana murmushi ta amsa da amin,ko yaya annin ta gwada jin dadinta kota yabeta kan wani abu dadi take ji,saboda lafazi ne da bata saba jinsa ba a bakunan al'umma a kanta,cikin karamcin ma da suka yi mata batajin tana da abinda zata saka musu dashi
"Amm...aysha" waiwayowa tayi tana amsawa
"Kikace kuna waya da khalipha?" Kai ta gyada gabanta na faduwa
"Kin tabbata?" Kai ta sake gyadawa kawai ba tare data furta komai ba
"Shikenan jeki,Allah ya dafa mana"
"Amin" ta bata amsa tana ficewa,yayin da annin ta bita da kallo,ta sani cewa samun kaman ya aishan a wannn zamanin abune mai matuqar wahala,sosai take qaunar ayshan tare da fata da kuma addu'ar Allah ya nuna mata wani lokaci da take muradin gani.
Dakinta dake nan sashen anni ta koma tana jujjuya maganar cikin ranta,kaddai ace anni ta dago wani abu ne?,da wannan tunanin ta shiga wanka,bayan ta fito ta shirya,tana son ta debo wasu kayanta daga can sashen khalipha,wanda tunda ya tafi itama ta tafi bata sake leqa sashen ba koda wasa,muqullan ma tunda ta ajesu a locker bata sake bi ta kansu ba,bude locker din tayi ta dauki keys din ta fice zuwa sashen nasu.
Gab da zata shiga wayarta tayi ringing,saita dakata tana dubawa,hanan ce,dariya ta dan saki tasan cewa akwai wata a qasa tunda ta kirata,dagawa tayi da sallama ilai kuwa karadin hanan din ya cika kunnenta,ko gaisawa bata tsaya sunyi ba tace
"Nida saddiq...yace na cikashi da zancan aysha naqi na hadaku ku gaisa,na gaya mishi ba laifi na bane,ke din ce kifin rijiya ce baki zuwa ko ina" dariya aysha tayi
"Bani shi mu gaisa" miqa masan tayi ya amsa suka soma gaisawa,sosai yake da so jama'a kamar hanan din,sun dan taba hira kadan kana daga bisani ya zolayeta kan ta kula mishi da gimbiyarsa,sannan zayazo a raba gardama kan wanda yafi wani son dan uwanshi,shi yace ya fi sonta ita tace shi,da dariya aysha ta katse kiran jin musu na niyyar barkewa tsakanin hanan din da saddiq,tana dariyar abin ta bude sashen ta shiga,abu na farko data soma cin karo da shi daya daga cikin window size na hoton khalipha wanda ya fito tarrr kamar kayi masa magana ya amsa ka,fuskarshi qunshe da murmushi wanda hakan ya sake bayyana kyanshi,gabanta ne yadan fadi,sai taji kaman shine a gabanta yake kallonta,dauke kai tayi taci gaba da shiga sai kuma ta kasa,sake maida kanta tayi zuwa ga hoton,ta soma takawa a hankali zuwa sashen da hoton yake.
Ta jima tsaye gaban hoton tana kallonshi,sai ta sanya hannunta a hankali ta shafi qafafunsa,hakanan tausayinsa taji ya kamata,yabar gida yabar ahalinsa duk saboda ci gaban familynsa,tsahon watanni baiga mahaifiya mafi soyuwa a gareshi ba ko wani dan uwansa,cikin ranta ta soma jera masa addu'ar samun dacewa da nasara a rayuwarsa,ba shakka khalipha wani babban jigo ne a rayuwarta,yana daya daga cikin shika shikan da komai nisan rabuwa komai tsahon lokaci ko zamani bazaiyiwu ta manta da wanzuwarsa ba,iyakacin zamanta a gidan ta shaida jatumtarsa a rayuwa,jarumi ne kuma tsayayye na gaske,zata so taji wani abu daga tarihin rayuwarshi daga bakinsa,ta tabbata akwai gwagwarmaya ba qarama ba,a hankali ta sauke hannunta ta juya,sai hanan da saddiq suka fado mata a rai,murmushi ta saki tana ayyana dadin da soyayya ke da shi,sai ta dinga gwada kanta a matsayinsu,wani tunani ne ya fado mata a rai wanda ya tilastata daga kai ta dubi daya hoton khalipha dake gabanta,wanda yana zaune ne saman wata irin kujera ya dora qafarshi daya kan daya,kai ta girgiza tana gayawa kanta bamai yiwuwa bane,khaliphan?,da hanzarin ta watsar da tunanin ta shiga nazarin sashen,akwai 'yar qura bamai yawa ba,wanda hakan ke alamta ana shigowa a share lokaci lokaci,sosai ta gayara wajen tsaf,take komai ya koma fes,ta rurruf abubuwan da tasan zasu qara qura ta sake dauraye jikinta ta debi kayan da take buqata tabar sashen.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
"Wayyo bayana" aysha ta furta bayan ta dago daga durqushen da tayi tana hada kayanta,ajiye littafin hannunta hanan tayi tana dubanta
"Wai karkicemin wannan satin duk sai kin rigamu tafiya gida?da alama ma dai ni kadai zaku bari,don maman hunaifa ma jiya najita tana waya da abban hunaifa abuja zatayi weekend" Sai data samu gefan gadonta ta zauna tana miqe qafarta sannan ta amsa mata
"Wallahi haka kawai wannan karon duk hankalina yayi gida....ki shirya don Allah mu wuce wajen wankin kan nan sai nayi zan wuce"mirginawa hanan tayi daga kwancen da take zuwa daya bangaren
"Wallahi yau kasala nakeji da gajiya...anya zan iya zuwa kuwa?" Harararta ayshan tayi
"Baki isa ba kuwa,ki tashi kawai ki shirya" hakanan hanan ta miqe a kasalance ta shiga wanka ta fito ta shirya suka fice.
Tare suka jero suna 'yan hirarrakinsu jifa jifa,idan sunga wanda suka sani su tsaya su gaisa wani lokaci har sukan dan taba hira kafin su wuce.
Dab da zasu wuce wata mota hanan ta taba aysha
"Gafa mutumin can,kinga mota zai bude amma ya tsaya satar kallonki"
"Wafa?" Ayshan ta tambaya tana duban hanan
"Waye banda daddy huguma,kinsan Allah gayen ya hadu,a nan makarantar yake geology ya karanta suka riqeshi suka bashi lacturing,da qyar ma idan ba zuwa sabuwar semester ku hadu da shi ba,ki bashi dama kawai aysha wallahi,ya hada komai fa" kallonta ayshan tayi taja tsaki tana kauda kai,gabanta taji yana faduwa
"Kekam hanan kinga dacewar haka?,kinsan wayeshi ne?,pls karki sake wannan maganar" dariya da mamakinta take boyewa,batasan me yasa ayshan ta tsani ayi mata zancan wani ba,ta tsani ace wani na sonta
"Allah ya baki haquri,amma maganar gaskiya karki bari wannan damar ta subuce miki,ina miki sha'awarsa"
"Toh naji" ta fada da alama ta qosa da zancan
"Aysha sai yaushe zaki bawa mutane dama?,waikekam soyayya bata burgeki?,kinsan bakasan dadin rayuwa ba harsai kaso kaima ansoka?,rayuwar da babu soyayya nikam ina tunanin wace iriyar rayuwa kenan?" Hanan ta fada da alamun da gaske take magana,shuru aysha tayi tana saurarenta,saita dinga jujjuya maganar hanan din cikin ranta.
Gab da zasu fice daga makarantar motar saddiq ta sako kai,ja hanan tayi ta tsaya tana dubanshi cikin murmushi sanda yayi parking ya fito
"Wato ba zata kayi niyyar yimin kenan?"murmushi yake yana dubanta
"Tuba nake ranki ya dade,na kasa zama ne kawai naji inason ganinki"
"Yayi kyau,kaman kasan tunaninka nima nake"
"Zuciya daya"
"Ruhi daya" sai suka sanya dariya shi da ita,aysha na gefe tana kallonsu,burgeta suke sosai yadda suke son junansu
"Ranki ya dade" saddiq ya ce da aysha
"Tare da naka..Allah yasa ba zuwa kayi ka hanata rakani ba"
"Ni na isa,ina zuwa?"
"Zamu wankin kaine"
"To bismillah ku shigo nayi rakiya" ba musu suka qarasa jikin motar,hanan ta shiga gaba aysha na baya yaja suka tafi,cikin motarma hirarsu suke,ba komai aysha keji ba,wani lokaci saidai taji dariyarsu har suka isa wajen,cewa yayi zai jirasu,saboda haka tabar hanan cikin motar ita ta shiga aka soma yi mata.
Awa uku aka gama musu komai har lallen,yayi kyau kuwa fiye da ko yaushe ita kanta taga haka,kaman wata amarya haka tayi fes tayi kyau,wannan karon haka tabar gashinta,maimakon daa da ake mata manya kalba guda biyu ko uku,ta saki jelarta kota hadeta da ribbom.
Da suka dawo ma tare ta barsu ta shige hostel din,ta taras maman hunaifa ta dawo harta musu abinci,sallah kawai tayi ta zauna suka ci abincin suna hirarsu har zuwa sanda hanan ta shigo.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Qarfe goma drivern gidan anni ya iso
"Toh sai Allah ya kaimu monday kuma"
"Anya ko zako ma dawo monday din kuwa?" Hanan ta fada tana tsokanarta,waiwayowa tayi tana kallontq cikin harara
"Me kika gani?" Dariya tayi
"A'ah babu komai,wannan zumudi haka,kodai kinyi kamu ne?"tsaki ta saki tana dariya
"baki da amsa"
"Idan tayi wari maji" hanan ta fada tana qyalqyalewa da dariya,har bakin mota hanan din ta rakota sukai sallama,don maman hunaifa tun safe ta fita.
Cikin girmamawa dirvern ya fito xai amshi kayan hannunta ta dakatar da shi
"Yi zamanka malam shehu" ba qarami girmansa take gani ba,saboda a qalla ya kusa haifarta,haka shima ba qaramin girmamata yake ba saboda yadda take ganin mutuncinsa,cikin mota suna tafe suna hira jifa jifa,duk da rabin hankalinta na kan dan qaramin littafin dake hannunta,wanda duka lacture din jiya ce.
Da yammaci suka iso gidan,kaman kullum anni na zaune a falo tana kallon africa t.v 3,dukkansu fuskokinsu qunshe da murmushi,anni ta amsa sallamar ayshan
"Lale da 'yan makaranta"
"Anni sannu da gida" ta fada tana zama qasa kaman yadda al'adarta take yawanci idan annin na zaune kan kujera
"Yauwa ayshatu" gaisawa sukai cikin kewar juna annin na tambayarta hanya da sauran al'amura,daga bisani annin da kanta tace taje ta huta,ba musu kuwa ta wuce dakin ta,wanka tayi tana saman gado zata shafa mai a nan bacci yayi awon gaba da ita,bata farka ba sai la'asar,shi dinma kiran wayar aliya ya tada ta
"Kin dawo kenan"
"Tun azahar ma,wannan satin duka makarantar naji ta isheni gida nakeso"
"Da kyau,ina hanya to ki jireyeni" cikin zumudi ta amsa mata dan sun dan kwan biyu basu hadu da aliyar ba,alwala ta daura ta shafa mai da hoda ta sauya kaya ta tada sallah sannan ta fito falon.
Amal ce kawai zaune a falon da alama bata jima da zuwa ba don har mayafinta na kafadarta,hada ido sukai da aysha,ayshan ta sakar mata murmushi,yayin da gaban amal din ke faduwa,kullum rana ta Allah ayshan sauyawa take kamar wadda ake canzawa,komanta qara kyau da fitowa yake kaman ba ayshan data sani watannin baya da suka shude ba,duk sa cewa ko dacan dinma ayshan a hade take,saidai kanta ya bude sosai fiye da yadda ta santa
"Amal ce?"aysha ta fada tana murmushi
"wallahi" ta amsata a taqaice tana jin kishinta na ratsata,tana satar kallon yadda fatar ayshan tayi kyau,jan lallen yatsunta yayi matuqar zama ado a gareta.
"Kwana da yawa....sau wajen hudu ina zuwa weekend bana samunki"
"Nima makaranta na koma banda cikakken lokacin kaina"
"Ma sha Allah,abu yayi kyau Allah ya taimaka" ta fada cikin fara'a ba tare da ta kawo komai ranta ba ta wuce kitchen.
Atika ta samu a kitchen tana yunqurin hada abincin dare,da fara'a ta tari ayshan
"Habawa,shi yasa tun yau naji gidan ya saki,ashe uwar masu gida ce ta iso" dariya tayi tana zama kan kujerar dake kitchen din
"Baaba atika kina kaini inda banje ba"
"Ai gaskiya ce,na jima banga mutum kamarki ba,Allah ya baki dama kina gida kamar wannan amma baki dauki kanki a bakin komai ba,magana ta Allah ba ganin ido ba halayenki masu kyau ne"idanu ta lumshe,tana qissima inama ace ita da mahaifiyarta ke wannan hirar?,inama ace itace ke yabonta kamar haka?
"Allah ya sanyani na zama mafi alkhairin abinda kuke zato,kuma ina roqon Allah karya kamani da abinda kuke fadi....me zan samu baba banci komai ba"
"Yau dai sinasir na yiwa hajiya,kinsanta da son sinasir,zakici ko a dafa miki wani abun?" Kaita kada
"A'ah baba karki wahal da kanki,kai bawa duk abinda ka samu aici kake,bani sinasir din" murmushi baba atika ta saki ta soma zuba mata,halayyar aysha na burgeta qwarai,kusan tayi gadon anni(kira da jan hankali a gareku masu 'yan aiki a gida ko gurin aikin da kake da wasu a qarqashinka,abinda ke qarawa mutum girma farinjini da kwarjini shine ka nuna qasqantar da kai dakai da tawali'u a inda ka isa kuma kake da girma ka nuna kai ba mai girma bane dai dai kake da kowa dake wajen,wannan abun na qaramin qara soyayyarka yake a zuciyar na qasa da kai ba,kuma dabi'ace mai kyau,koyi ne da halin ma'aiki,yadda yaje zama cikin sahabbansa kai bakace shine ba banda haiba kwarjini cikar zati da kyan da babu mai yashi da Allah S W T ya bashi,Allah yasa mu dace).
A kitchen din ta cinye abincin tas,tana ci suna hira,muryar Aliya data jiyo a parlour ya sata fitowa,tana zaune suna hira da anni da alama bata jima da shigowa ba,amal na zaune gefensu tana chart saidai rabin hankalinta na kansu,bayan sun gama gaisawar anni ta miqe ta koma samanta ta basu waje,dab da aliya aysha ta zauna tana dala mata duka a cinya
"Autar mama....kinga yadda kika koma me mama ke baki kina cinyewa ke kadai saboda rashin amana koki ragen?" Dariya aliyan ta saki
"Wai don karna tambayeki shine kikai riga malam masallaci,me kuke ci a wudil,koda yake nasan aikin anni ne wannan,wannan ai saikisa angon ya kasa shaidaki idan ya dawo" baki aysha ta rufe da hannunta
"Wallahi sashen masharranciya ce ke"
"Errrrhmm....nikam inason tambayarki dama wanne mai kike amfani da shi yanzu,naga kanki kamar ba haka yake ba sanda kikazo gidan nan" cewar amal bayan tayi gyaran murya,duban jelar gashin ayshan take har tasa aliya ta kalla itama
"Ba wani mai,kawai na samu gidan gyaran gashi mai kyau ne"
"Kuma ma dai abun sa'a ne" aliyan ta fada ba tare data dubi amal ba,tunda aysha taga haka tasan neman magana ne ya motsa da biyu aliyan ta fada,kama hannun aysha tayi
"Muje ciki don Allah kisha labari" miqewa tayi suka wuce dakin ayshan,suna shiga aliyan ta dubeta
"Wai har yanzu wannan 'yan zaman kisan daben suna zuwa dama?" Baki ayshan ta tabe
"Eh,ina ruwanki dasu?" Dariya ta saki,tasan halin ayshan sarai da rashin son yin zancan wani
"Tabdi,ai wallahi da nice da tuni na saita musu hanya,suna zaune ina da miji kamar khalipha yana giftasu?" Dariya ta bata sosai saboda yadda ta gwada da hannunta,jan hannunta tayi ta zaunar bakin gado
"Ce miki akayi mijina ne,yayana ne" wata harara aliya ta watsa mata taja tsaki
"Kici gaba da fadin haka,kina zaune zw'a farauce miki shi zakice na gaya miki" dariya ce ta subucewa aysha ganin yadda aliyan ta haqiqance bilhaqqi,aliyan zata maida mata amsa ta katseta ta hanyar daga mata hannu
"Yi haquri anty aliya ina zuwa" ta fada tana dariya sannan ta fice ta samo mata abin motsa baki ta dawo
"rannan naje imam wali dubiya....kinsan wa na gani?" Kai aysha ta girgiza tana zubawa aliya lemo sannan ta miqa mata,amsa tayi tana qunshe dariya
"Wai asma'u a third gate tana jiran adaidata sahu,dama tana hawa motar haya a rayuwarta?" Aliya ta qarashe tana bushewa da dariya,kallonta aysha take sosai,labarin bai mata dadi ba saidai bata ma tunanin asma'un ce
"Anya ko sashen?,anty asma'un,kai hamid ma bazai barta ta hau abun hawa na haya ba" ta fada tana girgiza kai
"Wallahi karkiji zancan wasa ita ce,kinsan muna hada ido tayi maza ta dauke kao kaman bata ganni ba,nayi nayi mu hada ido amma taqi" zungurinta aysha tayi
"Kinga kisha lemonki,banson qarya,wai aliya yaushe kika baci da gulma"
"Allah indai gulmar asma'u ce saina kawo miki,don na tabbata itama tana maraba da taki da zata samu wanda zai kai mata,ban taba ganin mugu maqetacin mutum da baison ci gaban kowa ba sai ita" sai data kai nan ta kurbi lemon sannan ta aje
"Kinsan ma Allah labarin da nake ji cikin BUK?,wai reshe ya juye da mujiya,hamid gasata yake"
"Nikam.ban sani ba,Allah ya shiryeki sashen tunda haka kika koma" dariya take sosai,har ga Allah bawai tana jin dadin halin da ake rade radin asma'un na ciki bane,a'ah,sakayya da isharar da Allah ya soma gwada mata ne ta dace da ita,yadda asma'un tayi qaurin suna wajen wulaqanci da yanqwana jama'a a fadin makarantar,hakan ya sanya labarin halin data fada baiyi wuyar isa kunnuwan Al'umma ba,dama ance idan ka shuka alkhairi shi zaka tsinta a gaba,Allah ya bamu ikon aikata mai kyau.
Har akayi sallar magariba basu sani ba saida suka duba agogo sannan suka tashi sukayi,a nan aliya ke bata labarin soyayyar ta da mahmoud yake nema,duk da batasan mahmoud ba bata taba mu'amala da shi ba,amma ance idan kanason sanin waye mutum ka kallo abokinsa sai tayi mata fatan alkhairi ta kuma ji dadi har zuciyarta,har bakin gate ta rakota bayan anni tayi mata kyautar turare suka rabu suna begen juna.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Washegari ta tashi da gyaran sashen khalipha kamar yadda ta yiwa kanta alqawari duk asabar din qarshen wata idan tazo zata dinga yi.
Gyara na musamman tayi masa,ta share ko ina fes,tsayawa tayi tana kallon wajen yadda ya dauki qyalli tana maida numfashi,klien take buqata kuma babu sashen,don haka ta maida hijabinta ta kona sashen anni ta samo.
Da sallama ta shiga duk sai suka juyo suka kalleta,mus'ab dake saman dining ya gama cin abincin rana yana saukowa ya qarasa saukowa da dan gudu gudu zuwa wajen anni tun kafin ya qaraso yake cewa
"Suprise,suprise please anni" yana isa kusa da ita ya mata rada sannan yace da haidar
"Zomu tafi" binsu sukayi da kallo,sai da sukazo gab da aysha qasa qasa tace dasu
"Adai qulla alkhairi"
"Babban alkhairi kuwa zaki gani anty" cewar mus'ab,shidai haidar dariya yake suka rankaya suka fice,qarasowa tayi anni tace
"Sannu aysha,aiki dai aiki dai bakya gajiya,ki dakata hakanan ki samu abinci kici kiyi wanka maza" murmushi tayi
"Ai na kusa gamawa anni,klien zan dauka toilet kawai ya rage"
"To Allah yayi albarka,madalla"
"Amin anni" ta fada tana wucewa store don ta dauki klien din,a duk sanda annin ta sanya mata albarka tana jin dadi har cikin ranta,har cikin zuciyarta tana jin wani sanyi,sai taga kamar umminta ce.
Sai data ga komai yayi mata yadda takeso,don karambani har wasu abubuwan ta sauyawa waje sannan ta cire kayanta cikin bedroom ta daura guntun towel ta shiga wanka bayan ta bar duka sashen na fidda qamshin irin turarukan wutar da take siya wasu ta baiwa anni,wasu ta aje wajenta.
Fuskarsa qunshe da murmushi yake takowa zuwa sashen nasa,fes yake jin zuciyarsa,tunda ya shigo gidan fushin daya tsammaci gani wajen anni saiya samu akasin hakan,cike yake da zumudin yin wanka ya koma wajen anninsa kamar yadda ta hanashi zama yace yaje ya watsa ruwa tukun,don na qaramar rana ake ba ranar,sauqinta ma cikin raba yake amma duk da haka shima yana da buqatar watsa ruwan.
Ba wani shakka ko fargaba ta fito daga wankan abinta,ta isa gaban mudubi wanda yake kallon qofa ta baiwa qofar baya,ta zare ribbom din kanta ta tsiyayi mai ta soma shafawa kanta,hade haden mayuka ne wanda suka qarawa kanta kyau baqi da sheqi,ba wani kudi mai yawa ta kashe masa ba amma duk wanda ya kalli kan sai ya tsammaci da wani mai me tsada take amfani,tana shafawar tana rera waqar joeboy ta begining to fall in love jifa jifa,sai data tabbatar ya ratsa ko ina man ta feshe kan da turaren kai ta dauko comb ta soma tajewa.
Daddadan qamshin da falon keyi ya sheqa ya lumshe idanunsa,yasan aikin anni ne ita tasa aka masa wannan gyaran duk da baisan waye yayi ba,tasan yadda yakeson qamshi da tsafta wanda daga gareta ya gada,kyakkyawar jakar hannunsa ya aje saman kujera ya nufi bedroom dinsa,saidai dan motsin da yake jiyowa ciki sai ya bashi mamaki,a hankali ya dora hannunshi saman mabudin qofar ya tura qofar dakin.
_Ya Allah ka karemu daga sharrin mutum da aljan_🙏🏽
38
Farin bayanta yake iya gani wanda dogon gashinta ya sauka,tana ci gaba da tajeshi yana miqewa,da fari ya danyi mamaki yayi tsammanin jinnu ne sukeso masa yawo da hankali,saida ya saukar da idanunsa zuwa santala santalan cinyoyinta zuwa qafarta ya tabbatar ba aljana bace amma kuma wacece?,bai gama wannan tunanin ba ta ankara da mutum a bayanta can bakin qofa a tsaye cikin baqaqen suit,wani irin kadawa hantar cikinta tayi,ta zabura gami da qwalla qara ta shige bayi ta danna key tana karanto addu'o'in tsari,ba inda ajikinta baya rawa yana kakkarwa,kasa tsaiwa tayi saboda tsabar tsoro da rudewa saida ta samu gefan bathtube ta zauna,tuni hawaye suka fara tsatstsafo mata,yau ta shiga uku ta lalace,dama akwai aljannu a gidan?,don ta tabbatar tayi imanin babu mai shigowa inda take,bugu da qari ma waye zai iya shigowa dakin da tun daga falo ta sanya mauqulli har dakin gadon,saita barke da kuka mai sauti tana ci gaba da addu'a gami da qanqame jikinta waje daya.
Daga inda yake tsaye haushi ya cikashi taf,wannan wanne irin abu je?,daga ganin mutum shine zata wani zabura kamar taga aljani ta shige bandaki?,wai wace ma har ta samu lasisin shigo masa daki ta bararraje haka?,anya anni ta sani?,Allah yasa ba daya daga cikin yarancan bane da suke addabarsu da bibiyar rayuwarsu.
Parlour din ya koma ya zauna saman daya daga cikin kujerun falon yana dafe da goshinsa da hannu daya ya zaro wayarshi ya lalubi lambar anni,bugu daya ta daga,sai yayi qoqarin saisaita temper dinsa
"Anni,wace take amfani da bedroom dina?"
"Bedroom dinka?,wace banda matarka,aysha ce"
"Aysha kuma?" Ya tambaya cikin mamaki
"Eh ita,wani abu ne?"
"A'ah,ta tsorata ne kawai ta shiga toilet tayi zaton wani ne" yayi saurin fada don karta dago wani abu
"Aifa aysha ba baya ba wajen tsoro,saika gaya mata wane ai" daga haka ta katse wayar,jifa wayar yayi gefanshi sannan ya miqe qafafunshi ya soma zare takalmin qafarsa da socka din duka gaba daya,ya rage daya daga cikin three in one suit din dake jikinsa ya sassauta tie dinsa sannan ya sake komawa dakin,tsai yayi yana qarewa dakin kallo,komai a tsaftace yake,sai towel bressier da pant dake kan gadon,sai kayan gyaran gashi dake saman madubi da cumb din data watsar waje guda saboda tsoronta,dauke kanshi yayi ya shigo ciki sosai ya doshi toilet din.
Daga can taji 'yar qara alamun an sake bude qofar bedroom din,wani tsoron ya sake kamata,sautin kukanta ya sake qaruwa sanda taji ana taba qofar bandakin,yana iya jiyo sautinta kadan kadan,haushi ya kamashi,wanne irin tsoro ne da ita haka,knocking ya fara yi saidai maimakon ta bude sake firgicewa tayi,gabanta yaci gaba da bugun uku uku,ta duba duk bandakin ba wajen tsira,kuma ta tabbata ko ihu tayi ba wanda zai jiyota cikin gidan,ganin ba alamun zata bude sai kukan banza da takeyi ba tare da yasan me takewa kukan ba ya sanyashi bude bakinsa,cikin muryarshin nan yace
"Bude mana" saboda tsoro sam bata iya tantance muryar waye ba,sai kawai zuciyarta ta bata muryar aljanu ce,cikin sautin kuka tace
"Wallahi bazan bude ba"
"Kwana zakiyi a ciki?"
"Nidai kuyi haquri don Allah"
"Mu suwa?" Ya tambayeta cikin qosawa,bata bashi amsa ba sai dif da tayi,ganin tana neman bata mishi lokaci yasa ya koma inda ya aje kayan hannunshi ranshi fal takaici,ya lalubi muqullansa daya amsa a hannun anni ya koma yana gwada na toilet din,jin ana alamun budewa ya sake sawa ta tsure,saikawai ta qarasa shigewa cikin bathtube din ta takure waje daya tana dana sanin zama abangaren ita kadai,dama tun dazun take jin motsi,dazu kuma musa'ab ya gama bata labarin ya taba gamo tsohon gidansu,tana ta dariya da tsokanarshi duk labarin ya dan bata tsoro kadan ashe da gaske yake
Sai daya gwada muqullai kusan uku abinda ya sake gajiyar dashi sannan ya dace dana bandakin,a hankali ya tura qofar ya shiga,can ya hangota ta takure gu daya,gashin kanta da bata samu damar daurewa ba ya bazu ko ina har fuskarta,daga kai tayi cikin tsoro ta dubeshi,sai a sannan ainihin siffarshi ta bayyanar mata,khalipha ne sosai tsaye cikin bandakin,sanye cikin baqaqen suit,saidai a yanzu ya cire sun glasses din dake fuskarshi,ya sake haske da kyau,sumar kanshi data fuskarshi luf da ita tana fidda wani sheqin baqi,ya sake murjewa hakanan idanunshi sun sake kyau,daga tsoro sai yanayin ta ya sauya zuwa kunya da fargaba,ta tafka babban abun kunya,bugu da qari tuna abinda ke daure a jikinta kawai ya sake sawa hankalinta ya tashi,kamar ta bace ya daina gannta haka taji,sai kawai ta maida kanta taci gaba da dunqulewa waje guda gana pretending din firgitar dazu ce bata saketa ba
"Saiki tashi ki koma ciki ki bani waje zanyi wanka" ya fada yana dubanta,duk da qoqarin kauda idanunshi da yakeyi amma hakan ya gagara,jin idanunsa take yake ko ina akanta,batajin zata iya motsawa ta wuce haka ya gabanshi
"Ki tashi matsoraciya kawai ko har yanzu baki gane wane ba?" Ya tambayeta yana harde hannunsa a qirji,shuru tayi don bata da amsar bashi
"Ko ba zaki tashi ba sai nazo na daukeki da kaina?" Jin haka ya sanyata zumbur ta miqe,saidai da qyar take iya daga qafafunta ta fito daga cikin bathtube din ta raba ta gabanshi zata fice daga bandakin,caraf yayi ya riqo hannunta yana sani,a firgice ta dago kai suka hada idanu,saita soma neman wajen buya,wanda abin dariyar jikinsa takeson shigewa ko zai daina kallonta,ba shiri ya saketa yana dariya cikin ranshi,bai fasa kallonta ba har sai data fita din sannan ya koma ya rufe bandakin da muqulli ya dawo ciki ya tara ruwan wanka.
Hawaye ne ya sake qwace mata takaici na cinta na ganinta haka da yayi,gashinan shi yanzu ya saka muqulli ya kulle kanshi zaiyi wanka amma ita asirinta abayyane,qwafa tayi ita kadai tana zumburo baki.
Haka ta shirya tana qananun hawaye a gurguje don kada ya sake fitowa ya taddata a haka,duk da haka bata fasa yin kyau ba,doguwar rigar buba ce ta atamfa shadda baqa mai matuqar kyau da tsada,an mata zanen jajayen flowers manya a jiki,bata nemi dan kwali ba saita yane kanta da madaidaicin jan mayafi bayan ta hade gashinta ya bada jela daya data sauka har bayanta.
Har taje zata fita sai kuma ta kasa,bai kamata ba,ba wani magana da sukai tsakaninsu koda ta sannu da zuwa ce,saita koma kan kujerar falon ta zauna tana murza tafin hannunta a hankali tana tuna yadda abun ya faru,dama tun dazu a tsorace take da labarin mus'ab,shi ya sake tunzurata ta sake tsorata.
Idanunsa lumshe suke ruwan na ratsa jikinsa,tabbas haka ne kowa yabar gida gida ya barshi,wani dadi yake ji gashi a gida,Allah Allah kawai yake ya koma wajen anni susha hira,a hankali ya tuna abinda ya faru dazu mintina kadan da suka wuce,murmushi ya saki abun yana son bashi dariya,bai taba sanin matsoraciya bace har haka bayan sanyin da yasan a baya tana da shi ba sai yau,kai ya kada kafin ya dauraye jikinsa ya fito.
Tunani kadan tayi sai ta miqe ta fice zuwa cikin gidan,ya kamata ace tayi masa wani abu da zaiji dadi,tunda bata jin gidan sun tanadar masa wani abun don ba alamun suna da masaniyar zuwanshi a yau,ta tabbata da anni zata sanar mata,haidar da mus'ab ne kawai a falon suna shigo da jakankuna,dariya mus'ab ya sa yana dan satar kallonta,har ta wuceshi ta share sai ta tuna abinda taji yana cewa anni dazu na suprise,sai ta dawo da baya tana dubansa
"Zan rama fa,kaci bashi ne,yaa haidar harda kai aka hada baki ko?" Ta fada tana duban haidar,murmushi yayi yana daga hannu sama
"Nikam babu ruwana bansan me akeyi ba,yace min ne kawai nazo na rakashi airphort" kai ta jinjina tana wa mus'ab sign na alwashi ta wuce kitchen.
Duka 'yan aikin ma ciki sun kacame da aiki
"A'ah duk girkin meye wannan?" Ta tambayi baba atika
"Mai gida yayi zuwan bazata kinga dole a tashi a shirya masa lafiyayyen abinci" hakanan taji cewa dutynta ne wannan,ita ya kamata tayi masa wannan karramawar,koba komai ta dan nuna dan wani yanki na godiya kan kyautatawarsa a gareta,duk da baikai ya kawo ba amma zata kwatanta
"Bari ku gani,wannan girkin naku ai lokaci zai dauka baku gama ba" cikin qanqamin lokaci ta hado duk abinda take buqata ta dora,ta koma gefe ta niqa abarba tayi mishi pineapple juice wanda kafin ta garma dan qwarya qwarayar girkinta ya dauki sanyi.
Mintina talatin ta gama ta shirya komai kan wani faffadan tray mai azabar kyau,ba wanda yawunshi bai tsinke ba a kitchen din(harda ni mai rubutun 😜).
Tana goge hannunta da zummar idan ta gama ta fita da abincin amal ta shigo,kana ganinta kasan bata jima da yin kwalliyar ba cikin dinkin lace
"Wai baba atika me kuke dafawa baqonmu,qamshi ya cika gidan amma shuru baku gabatar masa da komai ba?"
"Ai aikin uwar masu gida ne,gashinan da kanta ba saqo ba" baba atikar ta fada cikin murmushi wanda hakan yaja hankalin amal zuwa wajen aysha wadda take sake jera kwanukan,cikin yaqe take kallonta,nutsatsiyar kwalliyarta wadda girkin da tayi bai bata ta ba,yadda ta jera kayan abincin da qamshin da suke fiddawa,wani abu mai nauyi taji ya tokare qirjinta,sai ta kasa cewa komai ta juya ta fice cikin sanyin gwiwa.
A nutse take fitowa daga kitchen din zuwa falon,shi ta soma hangowa a gefan anni wanda hakan ya haifar mata da matsananciyar faduwar gaba wadda bata taba jin irinta ba,bata sani ba ko hakan yana da nasaba da abinda ya faru dazun?,fuskarshi fes,kyansa ya sake fitowa sosai,ganin yana niyyar juyowa ya sanyata dauke kai da sauri ta maida kan anni,dubanta yake sanda take tahowa din,sai yaga kamar an canza ta gaba daya,shidai yasan ba wannan ayshan ya tafi ya bari ba wata ce daban,abinda tayi dazun ya dawo mishi,sai yace da anni sanda ta iso wajen tana aje kwanukan
"Yaushe humaira ta koma haka?" Yayi subutar bakin fada ba tare daya shirya ba,sam anni bata fahimci tambayar tashi ba,tayi tunanin kyau da gogewar data qara yake nufi,saita saki murmushi tana jin dadi har cikin ranta,miqewa tayi tana cewa
"Sannu takwara,ki kai masa saman teburi,fita zanyi nima dubiya,drivan ma har ya iso" ta qarasa maganar tana miqewa,sai ya dubeta
"Ba hira kenan anni,kamar ma baki kewata ba?"
"Ni bance haka ba saikai khalipha?,watanka nawa?" Ya gane qorafi takeson yi masa,mafi a'ala kuma yayi shuru kar allura ta tono garma
"A dawo lafiya"
"Allah yasa,ya kamata idan ka huta kaima kaje ka dubashi,don yanzun ma tare dasu haidar zamu je"shuru kawai yayi yadan sadda kanshi,da alama baison zuwa wajen amma bazai iya musa mata ba,miqewa aysha tayi ta amshi jakar hannunta ta bita da ita a baya,suna zuwa qofar falon ta amsa
"bar aikin da ba lada kije kiyi na lada,ki kula da mijinki" kunya kaman zata nutse,kalmar saita mata banbarakwai,ba wanda ya fado mata a ranta a lokacin sai maman hunaifa da baban hunaifa,saita dinga jin girma da wani alfahari na shigarta kadan kadan,wai itama fa matar wani ce akwai igiya a kanta,hakanan taji tana son ta gwada yanda matan aure keyi,juyawa tayi zuwa cikin falon,har ta isa kanshi na qasa da alama tunani ma yake,bata tankashi ba ta kwashe kwanukan zuwa saman tebur wanda motsinta yasanyashi daga kai,saiya tsinci kanshi da binta da kallo,qamshinta daya buso zuwa hancinsa yaji ya burgeshi,ci gaba yayi da kallonta ba tare data sani ba yana jin qimarta na qaruwa cikin ranshi,zaman da sukayi da anni kafin fitowarta labarinta kaf duka kan ayshanne,irin kulawar data samu daga gunta ya tabbata ko shine iyakar abinda zai mata kenan,sai yaji tausayinta ya kamashi,lallai mahaifiyarta batasan baiwar da Allah yayi ma rayuwarta ba na samun nutsatstsiyar diya.
Sai data shirya komai sannan ta daga kai da niyyar duban me yake,sai suka hada ido,murmushi ya sakar mata saboda harga Allah bazai iya boye jin dadin kulawa da anni data yi ba,tamkar an dorawa zuciyarta wani abu haka taji,bugun zuciyarta ya sake yawa,idanunta ta lumshe tana qoqarin maida masa martanin murmushin nasa,sai kuma taji kunya ta mata dabaibayi,yanayin daya ganta da abinda ta masa dazu suka fado mata,ji take kaman qasa ta tsage mata ta shige ciki,a nutse ya taso har zuwa inda take tsaye,yaja kujerar dake kusa da ita ya zauna,saita motsa kadan ta matsa daga kusa dashi.
Ganin shuru batayi niyyar zuba komai.ba bayan shi kuma yunwa yakeji sai ya sanya hannunshi da niyyar bude flask din dake gabanshi,tare hannunsu yaje kai saboda arashin tunanin budewar da akayi yazo daya a qwaqwalensu,da sauri kowanne ya janye hannunshi,khalipha ya dunqule nasa hannun yana jin wani irin abu na masa tafiyar tsutsa a jikinsa
"Uhmmm,a sanmin naci" ya fada qasa qasa ganin taqi ta sake motsawa,sai da tayi qoqarin controlling hannunta dake rawa sannan ta iya zuba masa komai ta miqa masa
"Ka dawo lafiya ya hanya?" Ta fada cikin amfani da irin salon maman hunaifa,wanda ba qaramin kyau yayi mata ba fiye da tunaninta
"Alhamdulillah" ya amsa yana sauke ajiyar zuciya,sai tayi niyyar wucewa,ba haka yakeso ba,hakanan yaji bai gaji da ganinta ba awajen,kwalliyarta ta tsaru,sosai adon yabi jikinta
"Zama zakiyi naji me kika bayan bani nan" ya fada yana kai lomar farko bakinsa,saiya kasa ci gaba da maganar da yayi niyya,dadin abincin na kai masa ko ina,hakanan ta zauna a kujerar da ya nuna mata wadda itake facing dinsa,kanta na qasa shi kuma yaci gaba da cin abincinsa
"A ina kika koyi girki haka?"
"A gida" ta amsa masa a ataqaice
"Tun yaushe?"
"Can da dewa" daga haka bai sake cewa komai ba,yayin da sautin muryarsa daya tambayeta da ita taci gaba da amsa kuwwa a kunnenta,sai take jin kamar ba muryarsa ba,komai nashi ya sauya.
Shiru ne ya ratsa wajen,baka jin komai sai qarar cokalinsa da kuma hayaniyar masu aiki dake can cikin kitchen,daga wata kusurwa ta falon kuma amal ce rakabe tana duban abinda ke faruwa ta bayan labule,agogo yayi niyyar kalla sai ya hangi gefan skert dinta da batasan ya fito ba,qaramin murmushi ya saki cikin ransa yake cewa
"Barewa ba zatayi gudu danta yayi rarrafe ba,lallai hali jini yake bi" a hankali ya sauke idanunsa kan hannunta da take wasa da farcan hannunta da yasha jan lallenta ya koma marroon,tafin hannunsa ya dora a hankali samansu ya damqesu kadan yadda ba zataji zafi ba,da hanzari ta daga kai ta dubeshi don sanin dalilin faruwar hakan,murmushin dake shimfide saman fuskarshi saiya qarasa narkar da ita,qwayar idanunta kawai ya kalla yasan tambaya takesoyi
"Amal" ya furta kamar mai rada ta yadda idan ba ita din dake wajen ba bawanda zai iya jiyo me yake cewa
"Amal kuma?" Ta tambayeshi cikin mamaki,kai ya gyada
"Banason ki dinga nuna rashin sabo ko baqunta tsakanina dake" maganarshi ta dawo mata randa take da kwana guda a gidan,kai ta gyada masa alamun ta fahimta,qoqarin dai daita kanta tayi ya dubeta
"Bani labari dame dame ya faru bayan bani nan" ya qarashe maganar yana miqewa a nutse tare da nufar inda ya hangi amal,aysha ta bishi da kallo a sace tana ganin kaman ya qaro salo da yanga,kominshi shima ya sake sauyawa.
39
Tamkar mai neman wani abu yaje wajen,yayi kaman zai juyo ya take qafarta,wata iriyar azaba ta ziyarceta,sai ta saka hannu ta rufe bakinta dashi tana tunanin zata iya jurewa,sake taketa yayi wannan karon kasa daurewa tayi sai data qwalla qara,baya yaja ya dage labulen yana dubanta
"Me kikeyi a nan?" Tsabar azaba ya hanata magana,sai daya maimaita maganarsa cikin tsawa sannan ta iya amsashi
"Babu komai,abu nake nema...." Tsai yayi ya zuba mata rikitattun idanunta dake sake tsumata cikin soyayyarshi koda yaushe,nauyi sukai mata ta gaza daukarsu,saita sadda kai gabanta na faduwa,kunyar abinda tayi na mamayarta,da kanta ta tona kanta ta hanyar cewa
"Kayi haquri don Allah,wallahi bazan sake ba"
"Daga yau duk sanda muke zaune a falon nan mu biyu kacal ko gilmawarki kar na sake gani,bacemin a gun" ba shiri ta wuce tana dingisa qafarta.
Dariya ce sosai ta zowa aysha,ta kifa kanta a saman tebur tana qunsheta,a nutse ya tako wajen,sai yaja ya tsaya yana dubanta,sam batasan ya dawo ba sai dataji yace
"You,me kike ma dariya?" Ya dage girarshi daya,kai ta girgiza tana qoqarin hade fuskarta daga dariyar da take sadai ta gagara hakan,ci gaba yayi da kallonta yadda take son tsuke fuskarta ya taimaka wajen fito da beauty point din dake kumatunta,wanda ko sau daya bai taba kula dashi ba sai yau,qarar wayarshi ita ta dawo dashi daga duniyar kallon daya tafi,saiya fara laluba aljihunsa cikin basarwa,sai daga bisani yaga a saman tebur ya ar wayar,hannunshi ya miqa ya dauko wanda sauran kadan jikinsu ya gogi juna,hanyar waje yayi yana amsa wayar da alama mai muhimmanci ce.
A hankali ya tura qofar falon ya shiga sanyin ac da qamshin nan na musamman da tun zuwanshi yaji sashen nasa nayi ya daki hancinsa,ba wadataccen haske a falon sosai sai daya sanya hannu ya kunna makunnin qwan falon sannan hasken ya gauraye ko ina,daga can bangare daya na falon ya hangota akwance,sanye da kayan bacci ruwan hoda mai turuwa riga mai dogon da wando mai kauri,sai farin hijabi da take sanye da shi wanda bai wuce qugunta ba,gabanta takardu ne a baje da litattafai,sai torch din wayarta dake kunne da alama karatu take baccin ya sureta,sannu a hankali kamar mai sanda ya isa gabanta yana dubanta fuskarta da tayi fes kamar ba bacci take ba,quruciyarta ta fito sosai,baccin ya mata kyau,murmushi ya saki sanda ya tuna abinda ya faru dazu yana zarar daya daga cikin takaddun gabanta wanda take rubutu akai ya soma karanta rubutun dake jiki daya bayan daya
Dauke idanunshi yayi ya maida kanta yana yaba tarin basirar daya gano sanda take gyara kwanciyarta cikin baccin da alama ta gaji da kwanciyar daya bangaren ne,iya yanda take bayanin aikin da aka bata kawai ya isa ya gaya maka cikin sahun daliban da take,jinjina kanshi yayi yana yaba mata kafin ya durqusa ya maida takardar cikin 'yan uwanta sannan ya tsugunna yana tattare mata takardun waje daya.
Motsin takardun shi ya farkar da ita,zumbur tayi ta miqe ta zauna tana dan matsawa baya,da sauri ya dora yatsanshi akan lebansa yana fadin
"Shshshsh....in kika sake kikamin ihu irin na dazu saina cinye bakin" kunya ce ta kamata daya tuno mata da kuma lafazinsa na yanzu,saita sadda kai tana gyara zamanta a fakaice saboda yadd wandon jikinta ya tattare qaurinta ya fito,maimakon daya gama hada takardun taga ya miqe sai ya koma ya zauna sosai,yana soke yatsunshi cikin na juna idanunshi a kanta
"Uhmmm,bani labarin abinda ya faru da bana nan" yatsunta ta lanqwasa suka bada sauti,cikin muryar wanda ya tashi daga barci wanda ta cakudu da yanayin sanyinta tace
"Ba abinda ya faru" lumshe idonsa yayi saboda yadda tsigar jikinsa ta zuba
"Me yasa baki nemi ni ba tunda na tafi?,haka ake yaya da qanwar?" Idanunta da suka sake haske saboda baccin da tayi ta daga ta zuba mishi su
"Ya salam" ya furta can qasan maqoshinsa ta yadda shi kadai zai iya ji
"Wai me yake damunka khalipha?" Ya tambayi kansa da kansa,baisan me yasa yake jin baqon yanayi tattare da ita ba,komai tayi sai ya bada wani reaction a jikinsa da zuciyarsa
"Kafin nayi serving number din ne ta gudu" sake gyara zama yayi sosai,haka nan yake son hirar tasu tayi tsayi,duk da cewa ya sani shine mai.laifin da bai taba nemanta ba
"Amma me yasa baki amsa ba wajen anni?"
"Hakan na nufin zata fahimci baka kirana kenan" ta sake bashi amsa a taqaice a sanyaye,murmushi yayi yana gyada kai,sai yanzu ya gane dalilin da yasa anni bata taba masa fada ba kan bai taba kiran nata ba,tafin hannayensa ya game waje daya,bashi da sauran abin cewa,gashi kuma baison zaman nasu ya qare da wuri haka,sai ya sake bude takardun daya hada matan ya soma zarosu yana mata tambayoyi kan course din da takeyi,batayi qasa a gwiwa ba ta soma bashi amsa daki daki,saidai abu daya ne da bata so shine ya daga kai ya zuba mata idanunshi,faduwar gaba da daburcewa suke sakata,har ta qare maganarta idanunshi a kanta yana gyada kai
"Ma sha Allah" ya fada sanda ya fuskanci ta gama
"Allah ya taimaka"ya fadi yana miqewa,a gajiye yake sosai don fitarsa dazu ba qaramin yawo sukayi ba
"Ameen,na gode,Allah ya saka da alkhairi ya jiqan magabata"
"Ameen" ya amsa cikin jin dadi ya wuce cikin dakin.
Koda ya fito tuni ta miqe saman doguwar kujera,da alama nufinta nan zata kwana,ita kanta tasan qarfin hali ne kawai takeson nunawa,amma tsoron da takeji Allah kadai ya sani,saboda shi kanshi falon yayi mata girma,batason ne a matsayinsa na baqo kuma muhallinsa ne ace ya kwana a nan
"Ki koma inda kika saba kwanciya ki kwana" kafada ta maqale
"Ka barshi zan kwana anan" bai sake ce mata komai ba ya juya ciki.
Duk yadda jikinsa da idanuwansa suka buqatu da barci amma hakan taqi samuwa,yayi juyi saman gadon yafi sau shurin masaki,tunda ya kwanta take masa yawo cikin idanuwanshi,komai yake dawo masa fes game da ita,yanayin daya ganta dazu zuwa yanzu daya shigo ya sameta tana bacci,tsaki yaja ya miqe ya zauna dirshan saman gadon sanda wayarshi ta soma ruri,
Tunda ya kalli number dake yawo yasan lili ce take kiranshi,hatsabibiyar matashiyar budurwar data takura rayuwarshi da sunan tana sonshi,saidai bayan soyayya da take masa tana da burin suyi soyayya irin ta watsewa wadda ita a wajensu ba wani abun aibu bane,tsaki ya kuma ja yana tuna sanda ta keta parlour dinshi a can ta taddashi har cikin dakin gadonshi,tun daga ranar bai sake yadda yabar gidan a bude ba,kashe wayar yayi baki daya bayan yayi rejecting call dinta,sake juyawa yayi ya kwanta rigingine yana addu'ar Allah yasa bacci ya daukeshi,saidai hakan bata samu ba,dole ya sauko daga gadon wani abu na kaikawo a ranshi,toilet ya shiga da niyyar daura alwala ko Allah zaisa ta sanadin haka baccin yazo.
Gefan gadonshi ya dawo ya zauna yana tsane ruwan alwalar,bayan ya gama ya sauke hannun rigarshin,haka kawai ya kasa sake komawa gadonshi,sai ya zura slippers dinsa ya tako a hankali zuwa bakin qofa ya budeta a hankali.
Idanunshi ya shuga wuwwulgawa cikin falon,can ya hangota lokon kujera a takure waje daya kanta na saman gwiwoyinta,qofar ya saki ya taka zuwa cikin falon
"Hasbunallahu wani'imal wakil" ta fada a zabure tana miqewa sanda taji motsin tsaiwarsa,ta tsorata sosai da sauri ya riqeta yana mamakin tsoro irin nata,ganin taqi nutsuwa waje daya ya sanyashi riqe dukka hannayenta yana fadin
"Calm down nine,khalipha ne" ya qarashe fada da dan qarfi don ya dawo da hankalinta kanshi,ajiyar zuciya ta saki don ta soma bacci ne taji wannan motsin,uwa uba dama a tsorace baccin ya dauketa,bai saki hannunta ba har zuwa dakin sannan ya zame hannayensa,da hannu daya yayi mata nuni na tahau ta kwanta,saita kalleshi sannan ta dubi gadon,ta taka a hankali zuciyarta na bugawa saboda tsoron data ji dazu.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
A nutse ta tura qofar dakin anni bakinta dauke sa sallama don su gaisa,saboda bata samu zama breakfast tare da su ba ta tsaya gyaran sashen nasu,tadai kammala abun karin da tasan zai ishi kowa a gidan ta gyara dining din ta bar sashen,da fara'a saman fuskar anni take sa sallamar tata
"Maraba da takwara" murmushi aysha ta saki har wushiryarta na fitowa,tana yaba yadda annin ke mata,tana jin cewa inama inama ace ita tahaifeta,inama ace itace mahaifiyarta,kanta a qasa saboda ta fuskanci suna wata magana mai muhimmanci ne ita da khalipha wanda ya nutse cikin kujerar dake falon annin yana satar kallonta can cikin zuciyarsa yana mamakin sauyarwarta,waishin dama matan cikin hijabi akwai wani sirri na musamman da suke boyo ne ko kuwa wani abu ne ya sauyata?,iyaka saninshi da ita ba haka take ba,kunnuwanshi na sauraren muryarta da suke magana da anni,ita dinma yana jin kaman ba tata ba,kodai watannin daya diba ne yasa yake ganin komai ya sauya?,har suka gama gaisawa da annin da 'yan maganganunsu baice komai ba,furucin anni na qarshe ne ya dawo dashi
"Karki zauna haka na sanki sarai ki nemi abu kici" kanta ta kada sannan taci gaba da takawa don ficewa daga dakin,sai taji tana son ta harde,ba shakka akwai wani dake kallonta,wani nauyi take ji kamar yau ta saba shigowa falon annin
"Khalipha" anni ta kira sunanshi ganin hankalinsa nai tare da ita,cikin dakewa irin ta gigaggun maza ya soma shafa kanshi kafin ya maida idanunshi a kan annin,cike da basarwa yace
"Anni yarinyar nan tana karatun nan kuwa?" Dariya ke cin anni a qasan ranta,amma a zahiri saita dake gami da bata rai
"Me ka gani?" Kai ya girgiza da sauri,don idan ta tirkeshin kan me ya gani dinma baisan me zaya ce mata ba
"Babu komai"
"Aisai ka fadi abinda ka gani" ta sake fadi tana yin kicin kicin da fuska
"Ba komai anni....na lura bakison laifinta"
"Dole kace haka khalipha saboda kaga na qyaleka kan naka laifin ban tuhumeka ba,duk yadda taso ta boyen nasan abinda ke wakana"haquri sosai ya shiga baiwa annin tare da yi mata bayanin abinda ya kawo tsaikon dawowarshi
"ita zaka je kama wannan bayanin bani ba"ta fada tana miqewa,sai ya miqe tare sa annin yana dariya qasa qasa
"Anni yanzu gwamnatina ta rushe kenan?...."dariya yaso bata,sai taqi cewa komai ta amsa shi a taqaice
"Oho to wa yasani?" Murmushi yayi yana biye da ita duk takunta daya sai daya ga shigarta dakin gadonta sannan yaja mata qofar ya fito.
Tana tsaye cikin kitchen din ta hada corn flakes da madara cikin wani qaramin bowl da alama shi take nufin sha,gefe daya ta dora kankana a kan plate tana yankata qananu qananu itama tana zubata a wani bowl din a haka ya sameta.
Bata ji shigowarshi ba sai inuwarsa data gani a gafenta,jan mayafinta tayi dake niyyar sabulewa daga kanta saboda santsin gashinta,gashin nata ya kalla sannan yaci gaba da kallonta ta gefan fuska,duk saita ta kura,batasan wanne jarabar kallo bane haka wanda da can data sanshi bata sanshi da kallo ba,kafin a daura aurensu idan yazo mata tsahon minti talatin din nan yafi ta'allaqa idanunshi kan wayarshi,a nashi gefan kuwa wani abu daya faru bayan barinsa gida shi ya dinga dawo mishi a kai,nazarin ayshan yake gami da dorata a mizanin da zuciyarshi ta shawarceshi a kai,saidai baiga wata qofa dake nuna tana ra'ayinsa ba bare sukai ga bigiren da zuciyarsa ke hasashen masa,ta yaya zai koya mata sonshi?,ta yaya zabi da ita ta karbeshi ta fuskar da yakeso?,ya tabbatar da cewa irin aysha tun a wancan lokacin dai daikune cikin jinsin 'yammata,faruwar lamarin ya sake tabbatar masa da wannan.
Hannunshi yasa ya dauki cokalin dake cikin madarar yana juya cornflaske din bayan ya dauke idonsa daga kanta wanda take ta faman gutsira kankanar kaman ba zata gama ba
"Wannan shi zakici a matsayin breakfast?" Kai ta gyada ba tare data dubeshi ba,baice mata komai ba saiya dibi cokali daya yakai bakinsa yana taunawa,shi a rayuwarshi har mantawa yake da abin nan,ya manta rabonshi daya cishi,kadan kadan ya dinga diba yana ci sai gashi yana shirin tashi dashi,batasan sanda ta saki baki tana kallonshi ba gaba daya wanda dama shi haka yakeso,aje cokalin yayi sannan ya soka yatsunsa cikin na juna,cikin cool voice dinshi wanda ba hayaniya sam a ciki ya furta
"Am sorry"
"Bayan ka cinyemin abuna?,da kanaso saika fadamin na hada maka wani" murmushi ya saki sai kuma taji kunya da nauyi,kaman gidanmu?,kaman bashi ke aje komai ba?,qasa ta danyi da kanta,kamar ya fuskanci haka saiya jawo locker da suke aje kayayyakin ya dauki wani cup din ya zuba ruwan dumi ya hada mata wani
"Gashinan na biyaki,ke naki ma da ruwan sanyi kika hafa babu dadi,ni kuwa dana dumi nayi miki"
"Na gode" ta fada tana boye murmushin jin kunyar da take
"Kiyi haquri naje na zauna ba tare dana nemeki ba,ni kuma nayi hakanne don na baki damar yin masters dinki cikin nutsuwa,duba da yadda kike qaunar karatunki"
"Babu komai",dukkansu shuru sukayi saboda jiyo tashin wata murya kamar ta rahama na doso kitchen din.
Katsam babu tsammani taji gaba daya taji ya rungumota ta baya hannuwanshi saman cikinta,faduwar gaba da kaduwa suka sameta lokaci daya
"Karki motsa" ya rada mata akunneta wanda sautin da dumin fitar furucin ya ratsa har bargonta
"Khalipha me kakeyi a kitchen?,kaman wanda baida mata" muryar rahama dake cike da iyayi da kwainane ta cika kitchen din,juyowa yayi gaba daya har yanzu aysha na cikin jikinsa
"Tare da matar muke,kinsan se ana mata dure bata son cin abinci,ban sani ba ko baby na ke wahalar da ita" wani abu taji ya daki tsakiyar kanta,maganarsa da yadda ta ganshi manne a jikinta,duk da qoqarin basarwar da take amma hakan.sai daya bayyana saman fuskarta ya sauya duk wata walwalwa data shigo da ita
"Ohkey....ohkey" ta fada cikin murmushin yaqe tana bude frdge ta dauki ruwa ta fice ba tare data sake cewa komai ba.
Tayi zaton zai saketa ne bayan fitar ta amma saitaga baida niyyar hakan,tana jin saukar boyayyar ajiyar zuciyar daya saki ta qirjinsa da kanta ke saitin wajen,dumin jikinta ya masa dadi,qamshinta kamar bai taba jin turare mai dadin nata ba,saiya miqa hancinsa zuwa wuyanta da zummar shinshinawa,da sauri ta saki gyaran murya cikin rawar murya
"Su baba atika na iya shigowa koda yaushe fa" banza yayi kaman baijita ba cikin salo na waskewa,wayarshi ya ciro bugu uku aka daga,anni ya kira
"Anni,waisai yaushe ne rahama zata bar yawo tsakanin nigeria da nijer?,yanzu me ya kawota fisabilillahi?" Bata ji me anni tace masa ba,sai taji ya sake cewa
"Bana son damuwa ne anni....ohk to" ya katse wayar yana maidata inda ya dauko sannan ya saketa
"Ina fata baki manta maganar dana taba gaya miki ba abaya,wannan karon any mistake kikayi bazan daga miki qafa ba" ya kai qarshe yana daga girarshi cikin nuna da gaske yake mata
"Duk wani abu da kikai ba dai dai ba idan ba haka nakeso ya kasance ba zanyi yadda ya kamata ne koda kuwa a gaban anni ne,ina fata kin gane?" Kai ta daga mishi
"Oya....take ur cornflakes mu wuce tare,banaso ki zauna yau a sashen nan" bowl din ta dauka gaba daya,sai ya dubeta ta dan kauda kai,ya fuskanci me take nufi,amshewa yayi daga hannunta ya aje saman canter din
"Muje kya hada wani a can" babu musu ta bishi a baya suka fice.
Ranar gaba daya a sashensu ta wuni,shima kuma yana study room di shi yana wasu aikace aikace na office daga gida,da yammaci ya fito ya dubeta yana cire glass din idanunshi
"Ki koma ciki zamuyi wani dan aiki" tattara kayan karatunta tayi ta shige kaman yadda ya umarceta,ashe kitchen aka shirya mata da spare din dan madaidaicin dakin dake cikin ainihin dakinsa na motsa jiki.
Qarfe hudu na yammacin washegarin ranar bayan ta kammala abinda take tashiga wanka wanda bata samu yi ba saboda gyaran kayan sawarsu datayi,harda na khalipha wannan karon nata qyake ba dui da batasan ya zai dauki abinda tayin ba,bata gane kurenta ba sai data fara gyaran don batasan haka kayan keda uawa ba,hakana komai nashi a tsare yake a muhallinsa,kamar side sin tie socks boxers da sauransu kowanne daban daban,dole ta maida tsarin yadda ta gashi.
Tana shirin shafa mai wayarta tayi tsuwwa,murmushi ta saki ganin maman hunaifa ke kira
"Mutuniyar nan anya ba wani ne ya riqe mana ke ba?,kin riga mu tahiwa gashi har yau baki dawo ba koni gashi na haqura na dawo duk da baban hunaifa bai koma ba?"
"Kinga barta dawowar tata duk a suna ne,sun maidani abin tausayi ita da mijinta,a gabana take fecewa mijinta kwalliya duk sanda basu da lactures su fice yawo abinsu,yanzun ma kin ganta gaban kayan kwalliya tanayi" cewar hanan wadda ta amshe wayar ba tare data bar mmn hunaifa ta qarasa fadin abinda takeson fada ba,dariya aysha ta saki,duk sai taji tayi missing nasu,batasan me yasa khalipha ya tsaidata daga komawar datayi niyya ba dazun da safe
"Allah aysha saimun rama,Allah yakai damo ga harawa bari muna muyi auren nan saita ri ga rufe idonta"
"Idan ban wa mijina ba nikam duk banga amfanin ma kamfanin sutura da kayan kwalliya ba,kuma idan yazo kanku ban yadda ku saurara ba" mmn hunaifa dake gefe ta fadi,dariya suka sa gaba daya sannan suka soma gaisawa tare da tambayatta lafiya,sa kawai tace musu basu da lacuters ne dalili kenan amma tana kan hanya,hira suka yi sosai sai data ji kiranabban hunaifa na shigiwa alamar ya iso sannan sukayi sallama,aysha na dariya ta aje wayar,a hankali ta dora idonta kan fuskarta data bayyan a gaban mudubi,murmushi taci gaba dayi tana tuna yadda ma'auratan ke bawa junansu kulawa,abun na mtuqar bata sha'awa da burgeta kaman yadda yake burge hanan,sai kawao ta sami kanta da yin kwalliya sosai duk da cewa a yanzun mawuyacine ka ganta ba kwalliya koda lite ce.
Sosai tayi kyau uta kanta ta gani,siririyar sarqa ta saka da dan kunenta tana hade da zobe mai kyau ta feshe jikinta da turare sannan ta yafa yalolon mayafi daya dace da adon nata,gurin anni takeson shiga sai ta dauki litattafanta ta fita dasu tana son ta duba.
Ba kowa a falon sai rahama dake faman waya,wani kallo tabi aysha dashi tun daga sama har qasa,sauyawar yarinyar na bata tsoro,dudud wata nawa amma kaman an maya wankan engine,amal ce ta shigo daga wata qofa wadda zata kaika bayan gidan,itama kallo tabi ayshan dashi,duk ta lura dasu saita rasa na meye kallon?,a baya sam bata taba tsayawa dubawa ba bare ta tantance,saidai zuwa yanzu rashin jituwa tsakanin amal da rahama ke bata mamaki da tambyar kanta meye sila,uwa uba yadda amal din ta sake ja baya da ita ta rasa daliki,koma meye dukansu ba damuwarta bane,tana qoqarin sauke nauyin da musulunci kawai ya dora mata,haka nan taji zaman falon bai gamsheta ba,saboda haka ta jiya kawai ta fuce zuwa can bayan gidan inda ya wadatu da yawan shuke shuke,ta bude takardunta ta soma dubawa daya bayan daya.
Bata nima da zama ba taji shigowar motocinsu haidar,da alama daga office suka dawo,saitaqi tashi zuwa cikin gidan,don karatin ya soma mata dadi,duk da cewa akwai ma'aikatan dake gayafn flowers din wajen dake wucewa jifa jifa,amma da yake ba hayaniya suke ba basu dameta ba.
Sosai ta duquf tana duba wata paper dake hannunta,sai hancinta ya dinga jiyo mata wani qamshin turare nadaban wanda kamar ta sanshi,hat ta basar taji qamshin na sake daduwa cikin hancinta,saita daga kanta,khalipha ke dosowa inda take,bayanshi yaro shi nasir na biye dashi dauke da wasu fikes,juyawa taga yiyi yayi mahana kadan da shi saitaga yadan rusuna cikin girmamawa ya juya yabar wajen,shi kuma yaci gaba da qarasowa inda take,faduwar gaba tasamu wadda ta zame mata jiki aduk sanda ya kalleta ko suka kadaice daga ita saishi
"Sannu da zuwa" ta fada a yangance wanda ita batasan tayi din ba,idnunshi a kanta ya amsa shima cikin nashi salon.
Ticket din dake hannunshi ya miqa mata guda daya tana duban kwalliyar da tayi ta yau wadda tayi masifar burgeshi,buba ce da zani saidai kuma an danne gefe da gefanta dai dai jikin mai ita,sosai qirar jikinta ta fita,dan siririn mayafin data yane kanta bai rufa asirin gashinta ba da yasha gara yake qyalli,hakanan qamshin jikinta bai bar buso mishi ba tare da iska mai sanyi irin ta la'asar din da akayi dace aka samu raguwar yanayin zafin da ake ciki,fararen qwayar idanunta ta saka tana karanta ticket din,legos?,me zasuje yi a legos din?,kamar ya karanci abinda yake kai kawo a zuciyarta yace
"Gobe zamu wuce,kada ki damu da abinda zamuje yi" ya qarashe maganar yana bin yatsunta da kallo da har yanzu jan lallen dake jikimsu yake ci gaba da burgeshi hakanan
"Toh" ta furta a sanyaye tana ninke ticket din,haka kawao jikinta yayi sanyi take jin fargaba,hannunshi cikin aljihun wandonshi ya juya ya fara takawa,sai kuma ya tsaya cak yana duban gilmawar masu ya kan fulawar dake gyara a wajen,haka kawai yaji wani abu ya taba ranshi,saiya dawo da baya a sanda take ci gaba da rubutun assigment dinta
"Ko zaki koma ciki?,nan din maga bake kadai bace" kai ta girgiza tana shakkar hada ido dashi,batasan me yasa sau tari idan yana gab da ita take yawan jin hakan ba
"Duka bamu takura ba babu komai" bai sake tanka mata ba ya duqa ya soma tattare takardun,saita soma binsa da kallo,baiko dubeta ba har ya gama,hannunshi ya sanya ya zare biron dake tsakiyar yatsunta sannan ya juya ya soma tafiya,ta fahimci me yake nufi dole ta sauko daga saman lilon ta zira takalmanta ta biyo bayanshi.
A fakaice take qarewa tafiyarshi kallo,idan baka sanshi ba sai kayi tsammanin yana sane yake irin tafiyar,kamar saraki ko mai jinin sarauta a jikinsa haka yake takawa cike da nutsuwa
"Kinsan idan namiji ya amsa,sunanshi yanayin tafiyarsa ma kawai abun kallo ce" ta tuna kalaman hanan data sakata a agaba tana koya mata yadda zata gane ta fada soyayya da wani,da kuma siffofin qasaitaccen namiji wanda ba lallai sai mai kyau ne yake da su ba,duka shirme take daukan abun,sai gashi a yanzu batasan dalilin da yasa daya bayan daya komai yake dawo mata ba aduk sanda khalipha yayi wani motsi.
40
Tunda suka doshi sashen anni suke jiyo muryar rahama,hira suke da mus'ab amma kamar musu musu haka,anni na gefe bata sa musu baki ba tana sabgar gabanta,suna shiga ta bisu da idanu,idonta kan litattafan dake rungume hannun khalipha,duk wata walwalarta ta bace tsaf kunnuwanta da idanunta dukka suna kansu,idanu suka hada da aysha ta daga mata gira bayan ta sakar mata murmushi,ta mata sign na toya kika gani? Da idanunta,saita dauke idonta ta basar tamkar bata gani ba,saidai har yanzu kunnuwanta na wajen
"Gobe zamubi jirgin qarfe biyu anni in sha Allahu"
"To Allah ya bada sa'a,Allah ya nuna mana goben"
"Amin" ya fada cikin hikima yana karantar yadda hankalin rahama ya raja'a a kansu,littafi daya ya zaro cikin wadanda suke hannunshi ya dan buga ma ayshan kadan
"Wuce muje ki qarasa aikinki" kunya ce ta kamata,amma ya riga yayi warning dinta tun jiya,idan ma bata bishin ba zaiyi abinda yafi haka ne gaban annin kamar yadda yace mata,dole ta miqe,ya tasata a gaba suka fice.
Zube litattafan yayi saman kujera sannan ya harde hannunsa a qirji,ya zuba mata ido kaman yadda ya saba,baisan me yasa idanuwanshi suke qawatuwa da kallonta ba,amma har yanzun yaqi yarda da hakan dari bisa dari
"Ki sauya wasu kayan kafin mu sake fita" ya fadi yana sauke hannayenshi,kayan jikinta ta kalla,duka duka nata wuce awa daya da sanyasu ba,saboda ta riga data dauki corse wajen maman hunaifa,ba zaka taba rasata cikin tsafta da qamshi ba ko daga bacci ta tashi bare da ranar Allah,ya fahimci me take nufi tsaf,sai ya soma takowa zuwa gabanta wanda bata ankara da shi ba sai daya zo gab da ita,cikin hanzari tayi niyyar ja baya saiyayi caraf ya riqo hannunta,idanunshi cikin nata yace
"Kwalliyarki tayi kyau,qamshinki yana tashi zuwa ko ina,kawai inason ta darsa a ranta cewa akwai dalili na sauyin kayan da kikayi daga shigowarmu na awanni biyu kacal" wayyo,ji tayi kamar qasa ta tsage ta shige,gashi yaci gaba da kallonta ne bayan ya gama maganarshi ba tare daya sakar mata hannu ba,fatanta daya ya sakar mata hannun saidai yaqi
"Ko baki ji ba?" Ya fada yana murza yatsunta wanda hakan ya haifar mata da wani yanayi cikin jikinta da nashi gaba daya,gaba daya jikinsa ya amsa shi yasa ta samu damar zare hannunta saboda kasalar data saukar masa
"Naji....toh" ta fada da sauri tana zamewa ta nemi wajen zama,sai ya juya kawai shima ya wuce cikin bedroom.
Yatsun nata take lanqwasa idanuwanta na a rufe,tana son tantance wane baqon yanayi ne haka take ji cikin jikinta sa zuciyarta,idanu da fuskar khalipha na mata yawo cikin tunaninta,yaba kwalliyarta zuwa qamshinta da yayi sai take jin kanta na kumbura,baqin kalamaine a duniyarta,sai take jin kamar hira ce irin ta tsakanin masoyi da masoyi,murmushi ya qwace mata tana hasaso gata ita da khaliphan kamar yadda take ganin hanan da saddiq,kamar wadda aka tashi a barci ta gargadi kanta,saidai ire iren wannan tunanin ya kasa barin kwanyarta,a haka ya cinye duk awoyinta har ta soma jiyo kiran sallar magariba sannan ta miqe ta zauna sosai tana tattara nutsuwarta waje daya.
Sanda ya fita sallah ita kuma ta shiga ta shirya hadi da dauro alwala,taga shigar da hayi na qananun kayan marron and black,tana sane ta gidda wata gown maras nauyi saidai tana da duhun kala wadda take guda biyu ta ciki marron mai dogon hannu tana hade sarqar wuya saita sama baqa armless,tayi rolling da maroon vail,kwalliya kadan tayi ta gogawa tausasan lips dinta lipstick marron,hakan sai ya sake fidda kyanta ya kuma fitar da shape din qaramin bakinta,dan siririn abun hannu mai guda daya da zobe ta sanya a hannunta sannan ta yiwa kanta ruwan turaruka masu sanyin qamshi,ba qaramin kyau shigar tayi mata,kafin ta gama sallar magariba taji shigowarsa,bata fita ba saboda tasan sai sunyi isha'i zasu shiga,ana idar da sallar isha'i kuwa ta fito daga dakin.
Yana tsaye gaban t.v batasan me yake dubawa ba,yadan bawa qofar fitowa daga dakin baya,takun takalminta duk da plate ne ya sanyashi juyowa,baisan ya akayi ya tsinci kanshi da kallonta ba,wannan karon muraran ko alamun kunya bare ya waske babu
"Hi....na shirya",aje remote din hannunshi yayi ya nuna mata hanya da hannunshi alamun tayi gaba,ko sau daya bai dauke idonshi daga kanta ba sanda take takawa,kamar wadda ake busawa sarewa haka take takawa,gab da zasu shiga sashen taji an riqo hannunta ta baya ya janyota baya,saura kadan ta fada qirjinsa,ta daga kai tana dubanshi,qwayar idanunsu suka hadu da juna,saiya saukar da idanunshi zuwa kan dan qaramin bakinta daya qawatu da jambaki ya qara masa taushi,yatsanshi ya saka ya lakaci jambakin yana ci gaba da duban fuskarta
"Kinsan yadda jambaki ke miki kyau kuwa?,Allah yasa bakya sakawa a makaranta"abinda yakeosn fadi mata kenam don iya gaskiyarsa kenan,saidai kuma baiso ta fassara maganar da wata siga ta daban,a daidai lokacin rahama dake zaune ta cikin falon tana hangosu,ranta yayi qololuwar baci,tana ji a yau saita nunawa aysha iyakarta,sai ta miqe tsam kawai ta isa saman teburin,wanda tun dazu mus'ab ke mata magana tazo bata taso ba,don yau anni ba zata samu saukowa ba saboda ciwon da qafarta ke dan mata.
Dauke kanta aysha tayi tana jin wani nauyi na ratsata,shima saiya basar yaci gaba da riqon hannunta har zuwa cikin falon.
"Ina anni?" Khalipha ya soma tambaya sanda suke tsaye shida ayshan bayan sun gama gaidashi
"Tana sama qafartace tadan matsa mata"
"Ohk bari mu ganta" ya fada yana danyin gaba aysha zata bishi mus'ab din ya sake cewa
"Ammm....yaya,tace idan kunzo ku fara cin abinci tukunna" yasan ta fadi haka ne saboda tasan halin kowanne cikinsu
"Anty ko wata fita ta musamman zakuyi da yaya?" Haidar ya fada yana murmushi yana duban aysha,itama sai tayi murmushin tana cewa
"Me ka gani?"
"Wannan kyau haka?"khalipha dake zuba ruwa a cup yana daga tsaye ba tare daya zauna ba ya daga kai ya dubi haidar din,haka kawai yaji wani iri,itakam ayshan bata lura da haka ba tayi murmushi
"Bana son zolaya haidar"
"Allah ko,ga guri ki zauna dama inason muyi wata magana dake" ya fada yana nuna mata kujerar dake daura dashi,duk da cewa akwao empty chair guda daya a tsakaninsu
"Zauna nan" khalipha ya fada a kausashe yana ja mata kujerar da yake tsaye a bayanta,yanajin wani irin ba dadi cikin ranshi wanda baisan dalili ba,bai ankara ba sai da yaga suna kallonshi shida rahama,don mus'ab ya duqufa danna waya wanda bai wuce charting yake ba,yayin da amal ta maida hankali wajen zuba lemo tana sha wanda idan ka qare mata kallo hankalinta ba wajen yake ba itama,sai data zauna shima yaja ta kusa da ita ya zauna
"Amal,zuba min abincin" ya fada a dake,dubanta takai ga amal din,sai taga fuskarta ta washe ba kamar dazu ba,ta aje cup din hannunta ta miqe tsaye tana dauko platw wamda yake daga gaban ayshan,haka kawai taji haushi ya kamata,me kenan me yake nufi,raini yakeso yaja mata ko kuwa,dafe hannun amal tayi suka hada idanu,saita sakar mata murmushi
"Yi zamanki,shi ala dole yau bazanyi komai ba,bayan ya sani idan ina kusa dashi lokacina duka nashi ne" ba amal kawai amsar ta taba ba,hatta da rahama dake gefe taba karantar kowa d'ai d'ai dashi kanshi uban gayyar daya tsokani abun,wanda shi kansa baisan me yasa yayi hakan ba,yasan dai baiji dadin yabawar da haidar ya yima adonta ba
"Love is...."sauri mus'ab yayi,yayi yayi gum da bakinsa daga sunutar bakin dayaso yi,saiya soma zungurar haidar yana masa gulma,
"uhmmm...kya fadi gaskiya idan ma kishi kika ji,tunda dai shi ita yace ta zuba mishin ko?" Rahama ta fadi tana qarashewa da dariya duk da cewa dariyar bawai har cikin ranta ita kenan ba da biyu ta fadi hakan
"Babu damuwa idan ma kishin ne,ai na isa ne" itama ta maida.mata rai kwance kai kace wasa take mata,sai taja plate dinta rahaman ta soma juya abincin tana cewa
"Namiji dai mijin mace hudu ne"
"Is enought....kici abincinki kawai" yace da rahama,sai ya dubi aysha
"bani abinci naci" ya fada yana zubawa aysha ido,shi kadai ya gano bacin rai kwance a fuskarta a bayan murmushin dake kan fuskarta,fushin na meye?,abinda bai taba gani tattare da ita ba?,miqewa rahama tayi tabar abincin nata ta sauka daga wajen ta fuce daga falon ma baki daya,tsit wajen yayi,cikin nutsuwa ta zuba mishi komai ta tura gabanshi sannan ta samu waje ta zauna bayan ta zuba kunun gyada cikin cup wanda anni aka yiwa shi tasha ta rage mata saboda kusan ita da annin sunfison cima daya,haidar da mus'ab ne suka miqe a tare suka bar gun cin abincin suma
"Wannan sanya idon na rahama ya soma yawa,ya kamata yah khalipha ya dauki.mataki fa" haidar ya fada cikin jin haushi
"Idont know why suka addabi mutane ma,kowacce ya zauna gidansu ta kasa" mus'ab ya amsa yana jan tsaki.
daga idonta tayi ta dubi amal,sai taga tana satar kallonsu,yau duka sai tayi maganin masu shegen sa ido,sai ta dire cup din hannunta ta janyo plate din dake gaban khaliphan ta amshe cokalin hannunshi ta debo lomar abincin
"Uhummm" ta fada tana gyada kanta,cikin mamaki yake kallonta saita bude mata dukkan idanunta wanda hakan yasa suka sake girma suka fito sosai
"Karbi mana,kacemin dazun kana jin yunwa" ta fada a shagwabe wanda hakan ya taba zuciyarshi sosai,murmushi ya sakar mata idanunshi cikin nata,tana jin nauyinsu sosai a kanta amma ta dake
"Dont bother pls,zanci da kaina,banaso ki wahala" ya furta cikin wani irin salo da ya kusa tarwatsa zuciyar amal wanda ya tilastata barin wajen da hanzari,yayi tasiri mai girma cikin zuciyar aysha daya sanya jikinta yin laushi,sakar masa tayi ganin amal tabar wajen,cikin sauri ya kamo hannunta ya riqe gam cikin nashi
"Baki isa ba saikin qarasa abinda kikayi niyya,kinsan akwai 'yan sa ido dake shige da fice ko?" Haka dole ya hanata tashi daga wajen duk da taqi yarda ta bashin,saiya ci gaba daci da kanshi jifa jifa idanunshi a kanta,yana mamakin me yakeson sauyashi daga ainihin halayyarsa haka.
Ita ta soma gaba taje ta gaida anni,bata tsaya jiranshi ba ta wuce,hakanan yau takejin haushin amal da rahama gaba daya wanda batabtaba jin hakan ba kamar yau.
Tunda wuri tayi shirin kwanciya saboda tafiyar da yace mata zasuyi gobe wanda batasan ta mece ba,ko cikin gida bata qara shiga ba,kuma dama bata da sha'awar shiga din,don ta tsani kallon qwaqwqwafi da rahaman ke mata,ta dinga binsu da kallo ita da khaliphan kaman wanda ke zaman dadiro,tsako taja saboda tuna hakan da tayi,ya kamata ta yiwa tufkar hanci,koma meye fa khalipha ya biya sadakinta no need a samu wasu mutane da zasu dinga sanya musu idanu,tayi kyau cikin red night gown ta lullube kanta da farin mayafi,saika rantse ba shigar bacci tayi ba sabida yadda kayan sukayi mata kyau,qaramar jakarta ta bude ta zuba kayanta kala biyu da duk wani abu da zata buqata,duk da batasan adadin kwanaki ko kwana nawa zasuyi ba,ta hada komai tsaf,saita ciri tashi jakar mai kyau ta buda kayanshi shima ta zabi kala biyu ta shirya masa komai da komai a ciki,sai data kammala duk wata sabga tata sannan ta dauki system dinta da haidar ya siya musu su biyu shi da ita kala daya ta fito parlour,tana son kallon wani film da ta taba ganin tallanshi ta baiwa haidar ya mata downlod dinsa.
Saman doguwar kujera ta miqe abinta ta dora system din saman cinyarta ta kunnata,saida komai ya daidaita ta lalubo film din ta soma kalla,sosai hankalinta ta tafi kan film din dalili daya sanya bataji takun shigowarsa ba,ya hangi bayanta,saiya wuce bedroom din.
Tsayawa yayi yana kallon kayan data shirya din,komai a tsare daga gani kasan tasan me takeyi,a qa'idarshi bai tafiya da kaya idan tafiya ta sameshi amma wannan karon sai yaji bazai iya ignoring ba,maida jakar yayi ya zuge yana murmushi sannan ya sake dawowa falon.
A hankali ya taka ya tsaya a bayanta hannayenshi harde kamar yadda al'adar tsaiwarshi take,ya zubawa screen din system din ido yana kallon abinda take kallo daya dauke mata hankali haka,murmushi take saki lokaci lokaci saboda yadda film din ya tafi da ita,soyayya ce ake bugata sosai,ta tuna sanda hanan ke bata labarin film din,a sannan kallon shirme takewa hanan din da batawa kai lokaci,wani irin feeling naso da qauna taji yana shiha zuciyarta,yadda jaruman ciki ke tafi da soyayyarsu mai ratsa zuciyar masoya ce.
Miqa tayi tana ware hannayenta gami da fidda murmushi daga fuskarta sanda aka gama wani sin wanda hakan yasa ta dunguri khalipha dake tsaye a bayanta shima yana tayata kallon ba tare data sani ba,da hanzari ta waiwayo suka hada idanu,yadda ta ganshi a tsaye tasan ya jima a wajen,gabanta ya fadi kunya ta kamata,yanzu haka duk yaga yadda take appreciating film din,Allah ya rufa mata asiri ba wani film din banza take kalla ba,waskewa tayi tana tsaida film din tana son rufr system din,hannayensa ya saki yana zagayowa inda take,shi kansa film din yaji yana taba wani sashe na zuciyarsa,zai iya cewa tun wancan lokacin daya shude zuciyarsa ke a rufe,bai taba bada qofa ga wata ba bare yaji me ake ji koya dan dana irin abinda masu soyayya ke dan danawa,hannayensa yasa zai gyara qafafunta dake miqe don ya samu wajen zama,santala santalan qaurinta yabi da kallo wanda,cikin sauri ta tanqwashe qafarta tana dan hade rai,baice komai ba ya sanya hannunshi ya ya dauki system din ya janyo qaramin tebur gabansu ya aje samanta ya dannan play film din yaci gaba dayi,ji take ba zata iya zama su kalli film din tare ba,duk da bana badala bane amma soyayya ciki mai zafi ce akwai kunya,tana jin nauyinsa sosai saboda haka ta miqe da sauri,caraf ya kama tsintsiyar hannunta ya janyota baya wanda hakan yasa ta koma da baya ta zquna ba tare data shirya ba,har zaman datayi yafi na dazu kawo kusanci a tsakaninsu
"Zauna ki kalla abinki,ni tayaki kawai zanyi" ba yadda ta iya saboda yadda ya dabibayeta da idanunsa ta zauna din,tun tana a takure harta dan saki kadan fim din yaci gaba da garawa,ji tayi ba zata iya daurewa ba abun ya mata nauyi da yawa aka,ga zamanshi a gefanta dake qara raurawa zuciyarta,haka kawai zuciyarta taji kamar zata narke,saita rarumi system din ta soma yunqurin kasheta gaba days,a hankali ya dora hannunshi saman nata,dagowa tayi tana kallon qwayar idanunshi karo na farko,wani irin kallo yake binta dashi kamar wanda ke jin bacci,manyan idanunshi nan sun rusuna sun rage girma,wani abu taji yabtsirga mata saita soma yunqurin zame hannunta ta gudu tabar masa system din ma gaba daya amma yaqi bata space din yin hakan
"Kinsan me?" Ya fada cikin sanyi da taushi
"Indai kaga mutum na yawan kallon fina finan soyayya to aure yakeso" idanunta ta zare tana dubanshi,aure kaman yaya?,me yake nufi xai fassarata?
"Yaushe kika soma kalla humairaaa?" Ya kira sunanta da wani irin tune wanda ya qarawa zuciyarta bugu,saita kasa daurewa taci gaba da yunqurin zame hannunta amma duka a banza,tafin hannunshinya saka cikin nata yana murzawa a hankali yana ji cikin jikinsa kamar zai fita da control dinsa amma ya kasa tsaida kanshi,shi kansa baisan me yakeji haka cikin jiki da zuciyarsa ba
"Uhmm...tell me mana"
"Pls ya khalipha...ka sakarmin hannu" ta fada a narke kaman mai shirin sakin kuka,saidai kasalar daya saukar mata ya sanyata fidda sautin cikin wannan yanayin.
Sautin kidan da wayarshi ya dauka shiya dawo dashi,ya zame hannunshi daga nata a hankali ya soma laluben wayar,hakan ya bata damar miqewa ta fice daga falon zuwa dako cikin gudu gudu sauri sauri,binta yayi da kallo ta koma kamar qaramin yaron da aka biyo yakeson ya cimma mamanshi ya buya bayanta,mahmoud ne ke kiransa,sallama yayi bayan ya daga wayar
"Kana ina miscal kusan uku?"
"Da yaushe kenan?"
"Yanzu mana wannan ne kira na hudu dana yi maka fa" cikin mamaki ya daga wayar daga kunnenshi ya kalli screen din,tabbas ga alamun miscal nan ya nuna amma saiya dake
"To nidai banji ba"
"Kacemin kawai kana angonci,tunda ka dawo ba wanda yaji motsinka daga company" kalmar angoncin ita ta sashi sakin sihirtaccen murmushi,yana son yayi nazqri akanta amma surutun mahmoud ya hana,hakanan ya biye mishi suka tattauna maganganun dq zqsu tattauna,daga qarshe ya buqaci ko zai shigo company
"A'ah fa,gobe zanje legos"
"Kayi me a can?"
"Nida humairaaa ne"
"Honeymoon?" Ya tambaya cikin shaqiyanci
"Laifi ne?"
"Ko kadan na wajena,amma legos inaga ta muku kadan fa,ka manta tsohon tuzuru ne kai daya ga 'yammata kala kala?" Ya fadi cikin tsokana,dariya taso kubce masa ya danne abarsa,shi sam baima kai can inda mahmoud din yakai ba ko kadan a ransa
"Kaga sai da safe"
"A miqamin gaisuwa" bai saurareshi ba ya yanke kiran abinsa yana murmushi,yana juya maganar da sukayi da mahmoud,haka ya dinga juya maganar cikin ransa kamar dai tana so tayi masa tasiri,a nutse ya janyo system din tata zai kashe mata,babban hoton haidar ne aka screen din,cikin shigar qananun kaya,yayi kyau sosai suna diban kaman dashi qwarai fiye da mus'ab,haka kota fannin halayya,saiya tsaya yana duban hoton,tsaki ua danja,sai ya juya bayan system yaga irin ta haidar dince sak,tsaki yadanja wanda baisan dalilinsa ba,kasheta yayi ya hada da charger din ya nufi study room dinshi da ita ya ajeta a can.
Tunda ta shiga dakin take kwance rub da ciki saman gado a side din da yake kaman nata ne nan take kwanciya shi kuma daya side din tun sanda ya tasota daga falo ta dawo ciki,a hankali komai ke dawo mata cikin qwalqwalwarta,wani yanayi da batasan na neye ba yana bin jiki jini da zuciyarta,ta jima a haka kafin ta gyara kwanciyarta ta juyar da fuskarta daya sashen,hoton fuskar khalipha ta soma yi mata yawo,manyan idanunshi masu kyau da haske,kwantancen sajen fuskarshi daya zagaye haba zuwa qasan hancinsa,dogon hancinsa mai dan tudu kadan,pink din labbansa suma masu tudu kadan,cikakken gashin gira daya sake qawata fuskarshi da zara zaran eyelashes,fararen haqora,saita cure waje daya tana jin kunya na kamata,cusa kanta tayi cikin filo tana tuhunar kanta me ya kaita fasalta siffar da namiji idan ba rashin ta ido ba,murmushi ya qwace mata tana sake cusa kanta tsakanin filalluka,ita daya kamar wadda za'a kama.
41
Qarfe goma na safe suna tsaye harabar farfajiyar gidan,motoci hudu ne kowacce da drivernta suna jiran fitowar boss khalipha,daga ciki aysha ce tsaye zaune gaban anni riqe da kofin kunu mai dumi da qosai wanda tunda safe su atika suka shiga kitchen sukayishi da umarnin annin,ta tsare ayshan tana sha
"Maza ki shanye wannan na haunnunki,ayi tafiya ciki babu komai,zaki biyema wancan mai tsarin da abincin safe sai hantsi ya dubi ludayi" ta fadi tana duban ayshan cikin so qauna da tausayi,tana mata fatan wannan karon sauran matsalarta ta kawo qarshe,tana mata fata yau ta kasance cikin farinciki,ta tabbata batasan inda zasu ba da tuni zuwa yanzu hankalinta na a tashe ne,murmushi ayshan tayi ta dire cup din hannunta wanda ta tilastawa kanta ta shanye din kodom farincikin anni
"Yauwa koke fa" anni ta fada tana jin dadin yadda ta cika cikinta
"Na gode anni" ta fada kanta a qasa,tana qoqarin danne raunin xuciyarta,haka kawai umminta ta fado mata,kulawar data samu wajen anni a iya dan zaman da sukayi da ita bata taba ganin kwatankwacinta ba daga wajen umminta,ta lura sa sauyawar fuskar ayshan,batason ta fuskanci komai ko yanayinta ya sauya tun yanzu
hakan ya sanya tayi nufin bagarar da zancan
"Ayshatu sarkin godiya" murmushi suka saki a tare,sai shuru yadan ratsa falon,cikin haka takun takalman khalipha suka soma ratso falon,a hankali ta daga kai da niyyar satar kallonshi caraf ya kamata,tayi qoqarin dauke idonta daga kanshi amma kamar ya riqeta ne da wani mayen qarfe,yayi wani mugun kyau cikin suits kamar yadda suka zama sune kusan rabi da rabin rabin shigarsa,komai nashi daban yake cikin gayu tsafta da nutsuwa,da qyar ta qwaci ganinta ta dauke kanta.
Gaisawa sukayi da anni ya dora da tambayar lafiyarta,suna tsaka da haka rahama ta shigo parlour din dauke da kofunan tangaran biyu a hannunta qananu
"Ya khalipha ga coffe" ta fada cikin salo tana miqa mishi bayan ta zauna dab da aysha tana sin tantance rigar dake jikin ayshan,ayshan ce ta amsa takai hancinta ta shanshana,saita yamutsa fuska kadan tana dubanshi
"Zaka sha ne?" Tayi tambayar tana dan takure fuska da hancinta,saiya kashe mata idonshi daya sannan ya mata nuni da a'a,hakan ba qaramin dadi ya yiwa aysha ba,saita waiwaya tana duban rahama
"Sorry anty rahama,ya qoshi" ts fada qasa qasa ta yadda anni bata ankare ma da abinda ke faruwan ba,ba qaramin shaqa rahaman tayi ba,uwa uba kiranta anti da ayshan tayi,eh ta girmeta don sa'ar khaliphan ce,amma babu abinda ta tsana a duniya irin a qara mata shekaru ko a bayyana shekarun nata a duniya,mamaki take cikin ranta na yadda ayshan keyi a ayanzu,kishinta fiye dana baya ya cika ranta,bata taba tsammamin yarinyat xata iya canzawa haka lokaci guda ba kuma cikin qanqanin lokaci ba tare data cimma burinta ba.
Anni da khalipha na gaba aysha na baya ita da rahama data shirya wai zasu sauketa a asibiti tana son taga likita,tsaf ta karanci rahaman amma ta qyaleta don tasan meta taka,tunda tasan rahaman bata taba yarda ta fita ba mota ba,kuma koda motar ma ita tafi ganewa tayi driving da kanta,daga valcony anni ta tsaya tana musu Allah ta kiyaye ta koma ciki abinta su kuma sukayo gaba.
Da sauri daya daga cikin yaran ya budewa khalipha bayan daya daga cikin motocin ya shige,aysha ce ta rufa masa baya tana shiga ta rufe qofar bayan ta dage glashin sashen datake wanda shi kadaine a sauke,sun glass din dake hannunta ta manna a fuskarta wanda ya qarawa shigar tata armashi da kwarjini,ya kuma fitar da kyanta qwarai,ta fuske kaman batasan me ake ba,shi kuwa driver ganin khaliphan da aysha sun shigo sai ya tada mota ya soma reverse don fita daga harabar gidan,mamaki fal zuciyar khalipha yake dubanta,tana ji a jikinta yana kallonta amma saita fuske taqi duban sashen da yake
Yadda ta tsume taci magani saiya fito da dan qaramin bakinta wanda ya qara mata kyau sosai,sai yaji hakan datayi ta burgeshi,murmushi yayi a boye yana kada kai,daga jiya zuwa yau duk acting dinta jinsa yake tamkar da gaske take har cikin jikinsa
Baisan me yasa yake yawan jin baqin lamura a kanta ba wanda baida tabbacin meye su,qarar wayarta ita ta sanyata janyo jakarta dake gefe ta bude ta ciro wayar tata,aliya ke kiranta,murmushi ta saki har kumatunta na lotsawa ta latsa cikin farinciki ta kara a kunneta,cikin yanayi na sabo da shaquwa suka soma gaisawa,duk abinda take idanunshi a kanta yana karantar yanayinta,kaf tsayin rayuwarsa bai damu da wata mace ba bare ya tsaya karantarta ba baya ga anninsa,sai yanzu gashi ya dora hankalinsa kacokam kan ayshan,idanunsa ya janye ya lumshesu ganin wayar tasu bata qare bace yana jin sautin muryarta cikin kunnensa gaba ratsa kowacce gaba ta jikinsa
"Ya salam" ya ambata qasa qasa yana jan earpiece dinsa ya cusa a kunnensa dan ya daina jin muryarta ko ya samu sassauci kan yadda tsigar jikinsa ke tashi.
Har suka isa airphort basu gama wayar ba,saida motar ta tsaya sannan sukai sallama da aliys kan zata kirata.
A tsorace take taka matattakalar jirgin,karo na farko a rayuwarta data tana shigowa airphort ma baki daya balle ta doshi jirgi,yana daga gefanta ya lura da tsoron dake tattare da ita,a hankali ya matsa gefanta ya zura hannunshi daga gefan kafadarta ya jinginata da tashi kafadar,juyowa tayi suka hada idanu,saiya mata nuni da qwayar idanunshi da wasu ma'aurata dake gabansu hannunsu cikin na juna,sai ta sako ajiyar zuciya tana shaqar qamshin turarensa da har yau ta rasa wanne iri ne,haka koda wasa bata taba jin mai irin qamshin ba.
Sosai ya matse hannunsa cikin nata sanda jirgin ke shirin tashi,ruf ta rufe idanunta tana karanto addu'ar hawa abin hawa,wanda hakan ya qara mata nutsuwa,saida komai ya daidaita sannan ta sauke numfashi ta bude idanunta a hankali sai cikin na khalipha,girarshi ya daga mata alamar tambaya,saita girgiza kai tana sake maida idanunta ta lumshe.
Qarfe sha daya na safe suka sauka a legos abinka da tafiyar jirgi,wasu motoci ne guda hudu iri daya sak masu dauke da wani tambari da bata lura dana meye ba suke tsaye suna jiran isowarsu,daya daga cikin motocin aka budewa khalipha ya shiga aysha tabi bayansa,daga bisani motar ta gyara tsaiwa ta fice daga airphort din sauran na biye da su,dukka hankalinta nakan titunan da suke wucewa,karon farko data taba barin jihar kano zuwa wata jaha ta daban wadda bata taba zuwa ba,saidai taji sunanta kawai a baki,sosai garin ya burgeta,yanayin weather dinsu irin wadda takesoce,don a sannan suna samun saukar ruwan sama,duk da bai kankama ba amma hakan ya sake qawata yanayin garin da iska mai dadi da sanyi.
Joygate hotel and suites suka sauka wanda ke lateef salami street don yafi kusa da airphort,a harabar hotel din duka sauran suka dakata shi da ita ne kawai suka shiga ciki,executive suite yayi booking dama tun daga gida,shi ya bude qofar yana kan gaba tana binsa a baya har cikin dakin,cikin yan mintina qalilan aka shigo da abinci da sauran abinda mutum zai buqata
"Ki huta nan da two to three hours zan dawo ki shirya kafin nan zamu fita"
"Ohk" ta fada tana gyada kai
"Akwai damuwa?" Ya tambayeta manyan idanunshi a kanta,kai ta kada alamun a'ah sai ya juya ya fice yana ja mata qofar idanunshi a kanta.
Dakin tabi da kallo yayi mata kyau sosai kaman ba cikin hotel ba,gefan gadon ta samu ta zauna tana tunanin me sukazoyi lagos?,har yau bata san dalilin tafiyar tasu ba
Wayarta ta ciro ta kira anni ta sanar mata sun iso,sannan ta duba taga da saura kafin lokacin sallar azahar ya shiga,sai kawai ta kunna tv din dake dakin ta sauya tasha zuwa arewa.
Qarfe daya da rabi na rana tayi sallah,sannan ta bude abincin da aka kawo mata taci,sai daya dan fada mata sannan ta shiga bandakin dakin ta sake wanka ta fito ta shirya cikin wani material mai azabar kyau da tsada mint green cotton ne amma mai dan qarfi,ta nannade gashinta tayi daurin nan da ake a gaban goshi wanda gashinta data yiwa parking ta kama jelarsa ta kitsa ya zama jela daya ya fito ta qasan daurin,sarqa da dan kunne da kuma abin hannun da tayi amfani dasu duka set ne sirara masu ruwan gold,ba qaramin kyau tayi ba fuskarta tayi fresh sosai,gogewar da fatarta ta sakeyi ita kanta yana mata kyau,dai data tsaya gaban mudubi ta tabbatar komai yayi sannan ta koma saman kujerar.
Tana shirin xama akayi knocking qofar,saita fasa zaman ta isa bakin qofar ta murda muqullin ta bude gami da ja baya,khalipha ne ya shigo hannunshi riqe da top din suit dinshi daya hannun kuwa wayoyinsa ne,kana kallonshi ko ba'a gaya maka ba kasan a gajiye yake,da kallo ya bita cikin nutsuwa yake qarewa adonta kallonta,ba qaramin burgeshi adon nata yayi ba,sai yaga kaman canza ta akayi daga fitarsa zuwa dawowarsa,yana son qaryata hakan amma zuciyarsa taqi karba
"Sannu da zuwa" ta fada cikin sanyinta tana mamakin yadda yau ya ware ido yake kallonta kai tsaye
"Yauwa" ya fada yana zama saman kujea gami da cire takalmi da safar qafarshi,tana daga gefe tana wasa da yatsunta saboda yadda kallonshi ya mata nauyi yayin da shi kuma yake ci gaba da satar kallonta,shuru ya ratsa dakin,sai daya rage kayan jikinsa sannan ya tambayeta me suka kawo mata,tashi tayi ta dauko masa ta bude mishi
"Zubamin" yw fada yana kallon lallenta da kamar kullum turashi ake,nan tayi serving dinsa yaci sannan shima ya shiga wanka.
Tana tsaka da kallon maimacin wani indian hausa a tauraruwa t.v ya bude qofar bandakin ya fito lullube da towel a jikinsa,ya daura wani duk da mai yalwa ne amma duka singalalin qafarsa a waje yake,dauke kanta tayi da sauri tana jin wani feeling cikin ranta,ya jima kafin daga bisani qamshin turarensa ya game dakin,wanda ya haifar mata da kasala,ta lumshe idanuwanta tana jin motsinsa cikin dakin,bata bude ba har sai data tabbatar daya gama shiryawa
"Mu wuce ko?" Ya fada yana sanya takalma a qafarsa sabanin wadanda ya cire daxun,sai a sannan ta bude idanunta,yayi kyau cikin dinkin kufta,batasan me yasa idan ya saka manyan kaya ba saiya koma mata kamar wani saraki,cikin mutuwar jiki da kasala ta miqe ta soma nannadawa jikinta laffaya,ta cikin mirrow yake kallonta,duk wani motsi idan tayi shape dinta ne ke fita,irin shape da daidaikun mata Allah ya yiwa baiwa dashi,ajiyar zuciya ya kuma saki can qasa,baisan me yake damunshi ba sam,baisan me yasa baya iya controlling idanunshi ba a kanta
Tare suka jero har zuwa bakin motocin dake fake a wajen,ga mamakinta da kanshi ya bude mata gidan gaba,saita daga kai ta kalleshi suka hada ido,kafeta da ido yayi yana mata nuni da hannunshi kan ta shiga,a hankali ta zura jikinta kafin ya sanya qafafunta ya maida murfin motar ya rufe sannan ya zagaya,sai taga ya shiga sashen driver ga mamakinta ya sanya muqulli ya tada motar da alama da kanshi zaiyu driving,dubanshi take da mamaki saiya waiwayo caraf suka hada ido,girarshi ya dage mata
"Me naci ban baki ba?,karki cinyeni mana wannan kallo haka tun daxun?" Kunya taji saita kauda kai tans yunqurin danne murmushin daya subuce mata,cikin salon kare kai tace
"Da wanne idon kasan ina kallonka,ni me zan kalla" yanq tada motar ya bata amsa
"Abubuwa da yawa mana"
"Kamar?" Ta tambayeshi tana murmushi fuskarta na kallon window din motar ta yadda bazai iya ganin fsukarta ba
"Idan kin isa juyo ki kalleni saina baki amsa" tilas murmushin dake kan fuskarta ya subuce saidai bata yarda sautinsa ya fita ba
"Kidai rage kallona karki je ki soma sona,bayan ni kuma na riga dana siyar" dan dakewa tayi jin abinda yace,saboda ita batayi qorafin yawan kallonta da yakeyi ba shine shi xaiyi mata qorafi,shuru ne yaci gaba da ratsawa a motar,baka jin komai sai tashin qarar ac,da kuma anguwanni da suketa wucewa.
Sun danyi nisa kadan taji yayi gyaran murya
"Ayishah" ya kirata sunanta wanda salon yadda sautin lafuzan ya fita tilas kowace ke ki juyo ki kalleshi,sunan yayi dadi da matuqar tsaruwa a bakinsa,saidai tayi mamakin yadda ya iya kiran sunan kai tsaye duk da sunan anninsa ne
"Duka wani dan adam da kika gani a arayuwarshi daya cimma nasara yana da nashi tarin qalubalen daya taba fuskanta,hakanan babu wani mutum daya a rayuwa da yau zaice bashi da wata damuwa ko matsala koda kuwa ya wadata da komai bai rasa lalura hakane?" Kai ta gyada tana yarda da kowanne lafazi dake fita daga bakinsa
"Hakane" ta furta cikin sanyi gabanta na faduwa,don batasan meye abu na gaba da zai fito daga bakinsa
"Dukkan nasara tana tare da qalubale,hakanan idan kanason cimma nasara saika jajirce kayi tafitar ruwa da duk wani qalubale da zaka fuskanta,ka dauki wannan qalubalen tamkar wani mataki ko tsani ne da zai maka jagora izuwa cimma nasararka"kai ta sake gyadawa tana jiran jin ko xaice wani abu,saidai babu abinda ya sake cewa har suka isa wata anguwa,saiya rage gudun motar tashi ya soma ga garawa cikin layin wanda baida kwalta,unguwar nada kyau dai dai misali,hakanan gine ginenta a tsare suke ba wani cunkuso ko hayaniya mai yawa wanda bata zaci haka ba,ta dauka yadda takeji ana cewa cunkus dakin tsumma ta zaci ko inama haka yake,saidata gama qarewa unguwar kallo har qofar gidan da suka tsaya sannan ta waiwayo ta dubeshi,ashe ita yake kallo shima,bayansa na jingine da sit din da yake zaune,sake kiran sunanta yayi karo na biyu wanda sai dayasa tsigar jikinta zubawa
"duk duniya mahaifiya qwaya tak Allah yake halittarma dan adam saboda muhimmancinta,ina da yaqinin duk wani da zaki samu a rayuwa ba zaki taba samun cikakken kwanciyar hankali nutsuwa da walwala ba matuqar kina tuna alaqar dake tsakaninki da mahaifiyarki,gidan mahaifyarki na kawoki,inaso ki samo soyayyar mahaifiyarki da kanki ba tare da kowa ya shiga tsakani ba....inason inga iya jarumtarki da kuma adadin yawan yanda kike sonta" tuni qwalla ta soma wanke mata fuska,tsoro da fargaba gami da rauni keson shigarta,saidai kalaman da khalipha yaci gaba dayi su suke son tsaida zuciyarta qyam waje guda su bata qwarin gwiwa
"Banason na sake ganin qwalla a fuskarki,aiki zakiyi tuquru saboda ki samawa kanki da zucuyarki salama" ya fada yana miqa mata handkherchief dinsa,amsa tayi sai kawai ta dorashi saman fuskarta ya manne a fuskar yana tsotse sabbin hawayen dake fitowa,yayin da qamshin dake tashi jikin handkherchief din ya dinga sanyaya mata zuciyarta,daga bisani ta zare handkherchief din,daidai lokacin da wasu yara dake sanye da kayan makaranta ke yunqurin shiga gidan da yace ya kawota din
"Basmah" ayshan ta furta tana dubansu,ganinsa yakai inda yaga tana kalla,saiya sauke glass din motar da sauri,cikin muryarshi mai taushi cike da nutsuwa yakirata
"Basmah" waiwayowa tayi tana dubanshi alamun baqunta da rashin sanin fuskarshi,takowa ta dinga yi bakin motar,sanda ta iso gab da window din motar idanunta ya fada kan na aysha,ihu ta saki tana zagayowa bangarenta,itama aysha balle murfin motar tayi da sauri ta fito suka rungume juna
"Anty indo!,wayyo anty indo kece?!,ummi ce tace kizo?" Kai ta kada tana shirin zubda wata qwallar
"Ba ita bace basma tsoron shiga nakeji" riqe hannunta tayi qyam
"Zo muje anty indo ni zan tayaki bawa ummi haquri,tunda kikazo har garinmu zata haqura,dama kinsan gidanmu anty indo?" Waiwayawa tayi ta dubi khalioha suka hada ido dashi,da ido ya bata qwarin gwiwa yana jijjiga mata kai tare dayi mata sign na tayi addu'a,gyada kai tayi ta soma takawa tana bin basmah dake faman jan hannunta tare da zuba mata surutu da tambayoyi kala kala,sai da suka isa bakin qofar gidan ta lura da sauran yaran,duka sun girma,suka zuba mata ido alamin sun ganeta amma ba wanda ya iya cewa komai saida basmah tace
"Anty indonmu ce fa,ku gaisheta" kaman a tsorace suke haka suka gaidata sannan suka bude dan madaidaicin gate din gidan suka saka kai ciko,yayin da khalipha ya fito daga cikin motar ya rufe,ya haye daman booth din motar ya tasa gidan a gaba bayan ya harde hannayensa a qirjinsa yana zaman jiran tsammani.
[26/02, 8:54 PM] +234 810 044 6653: 42
Ko ina na 'yar harabar gidan har zuwa cikin gidan fes yake,tasan za'a rina saboda tana da labarin yadda ummin nata keda matuqar tsafta,don har gorin tsaftar tata take mata abun dariya,donsu a wajensu gani suke tamkar wani iyayi ne kawai na naja'atu,ko tana son nuna cewa tafi kowa,ba zata zauna tayi rayuwa yadda tazo ta tars da sauran matan gidan nayi ba.
Ci gaba tayi da binsu har zuwa cikin falon gidan,falo ne mai dan yalwa wanda yake shima tsaf,sai qamshin girki dake fitowa daga kitchen din dake cikin falon
"Ummi!" Basma ta qwala mata kira sanda yaran kowannensun ya nemi wajen zama yana cire takalmansa da kayan makarantar dake jikinsu
"Ban hanaki wannan iskancin ba basma?,shekara goma sha biyar idan baki hankali ba bansan sai yaushe ba" muryar ummin dake kitchen ta ratso falon,sai aysha taso tanemi nutsuwarta ta rasa,tsoro da fargaba suka cikata
"Ummi kinyi baquwa ne fa?"
"Tohm,su zauna ina zuwa"ta fada daga kitchen din
"Ki xauna anty indo" basma ta fada tana nuna mata kujera,murmushin qarfin hali aysha tayi kawai,fiye da rabin hankalinta nakan kitchen din,haka ta dosana ta zauna gefan kujerar tana rarraba ido a falon,kitcheb basma ta shiga ta dauko mata ruwa da lemo,tana tajanta da hira saidai itasam aysha hankalinta ba'a jikinta yake ba.
Shudewar kusan minti goma sannan ta jiyo takun fitowa daga kitchen din,ummince ta bayyana cikin dinkin riga da zani na atamfa,kanta daure da dankwalin kayan wanda sokashi kawai tayi,miqewa tsaye zumbur aysha tayi idanunta akan ummin,zuciyarta kamar zata fito saboda tsabar bugawar da take
"Basma ina....." Maganar ummin ta maqale sakamakon hada idanu da sukayi da aysha,kallon kallo sukayi na tsahon mintina biyu,tuni hawaye ya cika idanun aysha,bata isa ta tsaidasu ba a irin wannan yanayin saboda haka ta barsu suka soma zuba,juyawa ummin tayi zata koma kitchen,cikin muryar kuka rauni da kuma karyewar zuciya ayshan ta soma magana kuka na rirriqe wasu kalmomin nata
"Karki koma don girman Allah ummi,karki sake juyamin baya ummi,ki tausayamin ki dubi 'yarki,ina sonki ummi bani da kamarki duk duniya,ina da buqatarki,inason in rayu dake,ina buqatar kulawar uwa,inason inji duminta a jikina kamar yadda kowanne yaro kejin haka" bata waiwayo ba sai taci gaba da takawa zata wuce kitchen din,da gudu aysha ta zube jakar hannunta ta bi bayantq,kafin takai ga shigewa kitchen din aysha ta cafki hannunta ta baya ta riqe gam,saita sulale ta duqa kan gwiwarta
"idan kika barni wa kika barwa ni ummi?"
"Ummi me anty indo tayi miki ke wai haka da bakya sonta,kome tayi miki ummi ta dade fa tana baki haquri yaci ki haqura,ki kalla fa kiga irin kukan da take..."
"Rufemin baki basma,uban ya baki damar sanya bakinki kan wannan maganar,har yaushe aka haifeki da kika isa saka bakinki!" Ummin ta fada cikin wata murya dake cike da fushi cakude da rauni daga boye a can qasanta
"Idan kina son salama a rayuwarki ki tashi ki tattara kibar gidan nan,bama gidan ba garin gaba daya nakeso ki bari" ta fadi still har yanzu ayshan na bayanta bata bari taga fuskarta ba,ta sabule hannunta ta shige kitchen din gami da rufe kanta a ciki.
Kuka sosai aysha ta saki har yana fidda sauti sosai ta duqe a wajen
"Don Allah ummi don Allah" shine abinda take iya fadi kenan,cikin bacin rai basma ta tako inda ayshan take tana qoqarin dagota
"Yi haquri anty indo ki tashi,kiyi tafiyarki anty indo tunda har bata sonki karki sake nemanta,tashi ki tafi Allah yaga zuciyarki" da sauri ummi data hada kanta da qofar wanda ita bata fito ba ita bata koma ciki ba ta daga kanta,cikin hanzari ta bude qofar kitchen din ta isa gabansu,hannun basma ta fincika sannan ta zabga mata mari,janta tayi har zuwa dakinsu ta turata ciki ta rufesu ita da basman baki daya,kasa tashi aysha tayi kuka take bilhaqqi,ta kusa a qalla minti goma sannan ta iya miqewa da qyar tana jin jiri na daukarta ta lalubi hanyar fita.
Tunda ya kafawa gidan ido bai dauke idanunshi ba,cikin jikinsa yake jin akwai matsala,da hanzari ya duro daga saman motar sanda ta fito daga gidan ya nufeta,kama hannayenta yayi jin yadda jikinta ke rawa sai ya hadata da qirjinsa ya lullubeta da dukka hannayensa yanajin yadda take nishin kuka bugun zuciyarta na sake yawa,a qalla minti biyar sukayi a haka sannan yaci gaba da takawa da ita a hankali zuwa bakin motar,gidan baya ya bude ya sakata shima ya shiga,har a sannan kuka take sosai,gorar ruwa mai sanyi ya dauko da handkherchief sannan ya sake komawa bayan gab da ita ya zauna yana fuskantarta yana kallon yadda takr kuka kaman babu gobe,ranshi ya soma baci,tausayinta ya sake ninka nada cikin ranshi,ko ba'a gaya masa ba yasan amsar data biyo baya,tsahon shekaru har yau bata haqura ba?,tsahon wannan zamanin har yau jiya iyau?
"La'ilaha ilallah,Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla,wa'anta taj'alil hazna iza shi'ita sahla" ya dinga fada cikin taushin murya da sanyi,a hankali itama ta kama suka dinga maimaitawa tare,sannu sannu kukan nata ya ragu,hawayen ya soma daukewa,sai ya bude gorar ruwan ya miqa mata,bata musa ba ta karba tasha,saidai ba wani abu dataji ya ragu na quncin da take ji,ta kusa minti goma tana zuqar ruwan da kadan da kadan,don da qyar yake wuce mata,daga bisani ta miqa masa robar,yasa hannu zai amsa yaji alamun jikinta ya dauki dumi,goshinta ya dafa dai yaji jijiyoyin kanta suna harbawa,hakan kan ya dauki zafi
"Zazzabi kike ji?" Ya tambayeta cikin tausayawa
"Kaina...ke ciwo"
"Ya salam" ya fada yana qarasa hade gap din dake tsakaninsu,wanda hakan ya bata damar jingina sosai da kafadarshi.
Wayarshi ya ciro cikin aljihun wandonsa ya kira wata lamba,ba'a wuce minti goma ba wani matashi ya iso,cikin wani yare da aysha ke kyautata zaton yarbanci ne sukayi magana da khalipha cikin girmamawa,ya shiga ya tads motar suka bar unguwar.
Lokaci lokaci yakan dora hannunshi saman goshinta yaji ya dumi jikinta yake,jin zazzabin na sake hawa yayi masa magana ya juya dasu xuwa asibiti,kafin ko suje asibitin har ta soma rawar dari.
Aminity aka basu bayan 'yan gwaje gwaje da likitan ya sanya aka yi mata aka sanya mata qarin ruwa sannan ya buqaci ganin khalipha,cikin murmushi likitan ya yiwa khalipha barka da zuwa sannan sukayi musabaha da juna
"Madam na cikin damuwa qwarai,gaskiya tana buqatar kulawa,tana buqatar abinda zai kwantar mata da hankali ya debe mata kewa....yanzu zamu dan riqeta haka zuwa ko nan da gobe ne idan muka ga yanayin jikin nata zaku iya tafiyama a yau"jinjina kai khalipha yayi sannan ya yiwa likitan godiya ya fita daga office din.
A hankali ya tura qofar dakin idanunsa akanta da take kwance saman gadon barin hannun damanta wanda hakan shi yasa fuskarta ke fuskantar bakin qofa,bacci take sosai wanda hakan baya rasa nasaba da ruwa da alluran dake cikin ruwan dake shiga jikinta,kanta babu mayafi sai dankwalin dake daure a kanta wanda shima ya zame ya bayyanar da rabin gashin kanta,har ya qaraso wajen batasan me ake ba,kujera yaja gaban gadon saitin kanta ya zauna.
Tayi wani fayau tayi kyau,haskenta ya sake fitowa sakamakon kukan data sha daya sanya fuskarta ta sake yin jaa,dan qaramin bakinta na tsuke hakanan girarta a tattare take alamun ba dadin baccin take ji ba,tausayinta ne ya dinga ratsashi,ya shiga tunani kan maganganun da likita ya gaya mishi,ta jima a rayuwarta cikin damuwa dole hakan yayi affecting lafiyarta,ya dade zaune gabanta yana tunanin abubuwan daya dace yayi,har sai da lokacin sallar la'asar yayi sannan ya daura alwala ya fita can masallacin daya gani gefan asibitin don bada farali.
Har ya dawo baccin take,sai ya sake komawa gurbin daya tashi ya zauna,yanayin kwanciyarta yaga ya sauya cikin dabara ya gyara mata gami da lullubeta zuwa qugunta,kallonta yaci gaba dayi tausayinta na ratsashi,a hankali ya laluba hannunta dayan wanda ba qarin ruwa ya sanya tafin hannunshi cikin nata,tasowarta tun daga quruciya,irin gwagwarmayar data fuskanta cikin rayuwata har zuwa yau,wani rauni zuciyarshi keson yi,dauko tashi rayuwar a baya yayi ya soma hadata data aysha,sai yaga ta wani fanni rayuwarsu na kamanceceniya,yanayin gwagwarmayar da fadi tashi,qalubale mai tarin yawa,a hankali zucuyarsa yaji tana gaya masa cikin nutsuwa da yanayi mai ratsa jiki,wataqila rayuwarsu tayi kamanceceniya ne saboda sun dace da juna,wataqila Allah ya shigo da kowa cikin rayuwar d'ayanshi saboda dacewar hakan,ba shakka babu wani abu yanzu dazai goge mata dukka wani tabo na rayuwarta idan ba soyayya ba,saidai ta yaya zai sanyata ta soshi?tana buqatar soyayya lallai ba shakka Allah ya aikosu ne cikin rayuwar junansu saboda kowanne nada buqatar dan uwanshi,cikin zaren tunaninsa har baisan sanda ya matse hannunta cikin nashi ba
"Ayshaaahh" ya furta cikin wani irin sanyi.
Tamkar cikin mafarki taji muryar na kiranta,muryar da bazaiyuwu ta mance da itaba tsahon rayuwarta,sai taji kamar umarni yake mata ta bude idonta,a hankali cikin bacci take bude idanun nata,fuskarshi ta soma gani zaune dirshan a gabanta,saita soma zaton cikin mafarki ne,saboda haka ta bude bakinta daya mata nauyi
"Ya khalipha taqi saurarona,taqi ta kalleni,bata sona,ummi bata sona waye zai soni?" Matsowa da fuskarshi yayi gab da tata har suna musayar numfashi,cikin muryar da babu maijin amonta koda mutum na cikin dakin yace da ita
"Ni muhammad khalipha,ni zan soki aysha idan kin yarda" shuru tayi tana tunanin idanu biyu ne ko a farke,yanayin yadda numfashinsa mai cakude da qamshin turarensa ke bugun fuskarta yasa ta tabbatar a farke take,nauyin maganarsa yasa ta lumshe ido kaman wadda ta koma.bacci,saidai ba haka bane,abu biyu ke mata kara kaina,lafuxansa da haduwarta da ummi yau wanda lamarin kecin jiki da zuciyarta,ci gaba yayi da duban fuskarta dayau tayi masa kyau muraran fiye da kowanne lokaci,ya gane ba bacci ta koma ba amma ba aqalla yana jin bari ya bata space sai yaja da baya ya jingina jikinsa da kujerar da yake kai.
Batasan awa nawa ta kwashe a haka ba,itadai taji shigowar likita,bata ankara ba ta ji hannunshi saman kanta yana kiran sunanta,idanunta ta runtse gam,saiya duqa saitin kunnenta
"Taimaka ki tashi likita ya shigo" hannunta ya kama ba yadda ta iya ta miqe ta zauna sosai da taimakonsa,saiyaqi matsawa saidaya gyara mata dankwalinta ya lullubata shi kaman mayafi.
'Yan tambayoyi likitan yayi mata ya sake gwada ta sannan ya dubi khalipha,cikin harshen yarbanci sukai magana wanda bata ji komai suke cewa ba,daga bisani likitan ya juya ya fita,kujerar tasa ya sake komawa ya matso da ita dab da aysha har qafarshi na gogar tata,yayi qoqarin su hada idanu amma taqi yarda da hakan,baisan me yasa take da matsananciyar kunya irin haka ba
"Yanzu me zakici?" Kai ta kada
"Babu komai"
"Bazaiyiwu ba" ya fada yana danna wayarshi,kira yayi na mintina sannan ya kashe
"Humaira" ya kira sunanta a tausashe,
"Humaira" ya sake kiran sunan nata duka tana jinsa,kasa dagowa tayi ta dubeshi sai amsawa da tayi kawai
"Dubana nakeso kiyi" shi baisan me kusancinsu haka ke haifar mata ba,baisan me take ji idan ya kira sunanta ba,yana shirin sake cewa wani abu akayi knocking qofar ya tashi ya bude ya amshi saqon ya dawo ya zauna inda ya tashi.
Saman cinyarta ya aje ledar da aka kawo,ya fidda duk abinda ke ciki ya shirya sannan yace mata bayan ya debo abincin cikin cokali
"Uhmm,bismilah"
"Na....."
"Shhhhshh...." Ya fada yana dora yatsanshi akan lebansa
"Banason kice komai just open ur mouth" hakanan ta bude bakinta ya dunga bata abincin a hankali har suka kammala,shi ya taimaka mata tayi alwala tayi sallah sannan yace mata
"Zamu iya komawa gida?" Kai ta gyada don itadinma bason zaman asibitin take ba,cikin mintuna qalilan drivern ya iso,tana rungume jikinshi har suka isa hotel din da suka sauka.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Shuru falon saika dauka babu kowa a ciki,dukka yaran baki dayansu jikinsu a sanyaye suke,abincin da suka saba zama suci tare koda yaushe yau ba wanda yaci na kirki,hasalima basma da mai bi mata yusrah har yanzu suna zaune wajen amma babu wanda yaci abincin a cikinsu,tunda take dasu irin hakan bata taba faruwa tsakaninsu ba,tasan kuma bai rasa nasaba da ganin basma ba cikinbwalwala ba ya shafi duka sauran,saboda suna da hadin kai tsakaninsu yaran gaba daya,sharesu tayi itama tanata qoqarin ganin tayi al'amuranta kamar yadda ta saba,saidai kuma hakan taci tura,don itama juya abincin kawai take ba tare data ci komai ba,shurun ne ya isheta sai ta daga kai cikin hade fuska
"Kai abba,hadim ku dauki abincinku kuci"kai suka girgixa a tare
"mun qoshi ummi"
"Ku dauki abincinku kuci nace!" Ta sake maimaita musu cikin tsawa da qaraji,wanda ya sanya babu shiri suka ja kwanon abincin gabansu suka soma kaiwa baki kamar basaso
"Yusra basma,zoki zuba abinci kuci" ta fada tana tsareta da ido,Dole yusra taja itama plate din ta soma ci kamar dole,yayin da basma ta tashi daga falon da gudu ta shige daki tana sakin kuka,ta jima tana tausayin anty indo,tun batasan ciwon kanta ba har zuwa yanzu,da kallo ummi ta bita,cikin zuciyarta takewa inna yelwa Allah ya isa,har zuwa yanzu bata daina ganin illar matar da sharrinta ba har ya zuwa yanzu?,saita danne abinda ke taso mata ta zubawa yarn ido dake cin abinci kamar dole,a haka babansu yayi sallama,dukkaninsu suka miqe suka taryeshi,saidai ba yadda suka saba ba,tunda yaga hakan yasan lallai akwai abinda ya faru,ko kuma ta tuna da ayshan ne kamar yadda aka saba,zama yayi saman kujera bayan yaran sun koma sun zauna ya tambaya yana dubam fuskarsu daya bayan daya
"Me ya faru?" Sai suka soma kallon kallo aka rasa mai bada amsa,yusrah ce tayi qarfin halin cewa
"Anty indo ce tazo gidan nan dazu ita da mijinta" zumbur ummi ta miqe tabar falon,saiya bita da kallo har ta shige dakinsu,sake duban yarab yayi yana sake tambayarsu,yusrah ta kwashe komai ta gaya masa,ya jima yana nazari kafin daga bisani yace
"Shikenan kuci abincinku,kar wanda yasa damuwa a ranshi,zanje naga umminku" ya fadi yana miqewa suka amsa da to abba gaba dayansu.
*************************
Zaune take saman kujerar dake cikin dakin hotel din wadda ke daura da gadon baccinsu,tana sanye cikin kayan bacci masu kyau da kauri kanta yana da mayafi,tana nade saman kujerar idanunka kan t.v da suke hasko wani wasa,saidai kusan fiye da rabin hankalinta ya karkata ne kan tunanin abinda ya faru da ita dazun da safe tsakanina da umminta,shawarar da basma ta bata tana mata yawo cikin qwaqwalwarta,khalipha ne yayi clapping hannunshi gaban fuskarta wanda ya dawo da ita daga tunanin data tafi,yana tsaye a kanta yana dubanta
"Kin saba alqawarinmu,kin manta?" Dan siririn murmushi ya subuce daga lebanta,sam ta mance da maganar daya gaya mata kafin ya shiga wanka,saita maxe kawai,yanayin yadda ta basar din saiya burgeshi,ta tsuke dan bakinta waje guda ba tare data sani bama,agogo ya kalla yaci ace sun kwanta bacci saboda haka ya qarasa ya kashe kayan kallon yana fadin
"Time for sleep" maimakon ta tashi ta hau gado saita gyara zamanta a saman kujerar alamar anan take shirin kwana,dubarta yayi sai baice komai ba yaci gaba da shirin kwanciya barci,sai daya kammala komai zuwa sannan tana zaune idanunta nakan system dinshi daya kunne ya aje a wajen zaiyi aiki,tanata nuno hotunan dake cikinta daya bayan daya,takawa yayi ya kashe qwan dakin ya kunna mara haske,a nutse ya qarasa gaban kujerar ya zauna gab da ita har kafadunsu na gogar juna,ta jishi sarai amma sai taqi nuna hakan,tadanja wani littafi dake gefan system din din bataso ya fuskanci kamar tunani taci gaba dayi,system din yaja gabanshu yana dauke idanunshi daga kanta ya soma aikinsa,wanda galibi na office ne wanda ya kamata ace a matsayinsa na shugaba ya dubasu da kanshi.
Idanunta nakan littafin tana bin pages bayan pages tana dubawa,duk rubutun dake cikin littafin yana dauke da kwanan wata da time kowanne rubutu,duk layi daya data karanta mamaki ne yake kamata,bata fahimtar komai saidai rubutun kamar yana bada labari ne kan wani abu daya faru lokaci zuwa wani lokacin,buron hannunshi ya aje ya jingina da kujerar da yake kai gami da hade hannayenshi waje guda,ya lura da yadda ya shiga rudu kadan da mamaki,zuwa yanxu yana ganin ba wani boye boye tsakaninsu,ya kamata tasan su su wayesu duk da bata taba tambayarshi ba,tamkar ma bata damu ta sani ba
"Wanene khalipha?" Ya furta cikin sanyi yana ci gaba da kafeta da idanunsa,da hanzari ta daga kai suka hada idanu,sai taji tambayar tazo mata a banbarakwai,abinda ta jima tana tambayar kanta da kanta kenan,abinda ta jima tana son sani,saidai koda wasa bata taba gigin tambayarsa ko wani nasa ba,saboda tana ganin a matsayin wadda kamar alfarma akayi mata karanta baikai tsaikon ta tambaya din ba,sake dubanshi tayi wannan karon idanunshi nakan biron hannunshi dake jan wasu layuka saman farar takardar dake gabanshi
"Kowanne dan adam yana tare da nashi qalubalen a rayuwa,karki zaci ko tsammaci ke daya kike fadawa matsala ko kika fada,dukkan tsanani yana tare da sauqi haka ubangiji ya fada cikin qur'aninsa" sai yayi shuru yaba ajiyar numfashi,tunaninsa ya luluqa ya koma can baya wasu shekaru da suka shude.
*_muhammad khalipha_*
"Cikakken sunan mahaifinsa shine muhammad sa'id mai goro,haifaffen garin kano dan kasuwa wanda ya shahara da sana'ar saida goro a fadin qasar nan,kusan ya gaji sana'ar ne daga wajen mahaifinsa,wanda yake da mata biyu,uwargidansa ita ta haifa masa yara maza guda biyar ta shidan autarsu mace anty ruqayya,idris shine babba,hamza,habibu,munzali,sai saminu,matarshi ta biyu har ta koma ga Allah yaronta daya wato mahaifina muhammad sa'id,a sannan dukkansu suna ganin babu wani abu da mutum xai iya xama cikin sana'ar saida goro sai duka suka qita,mahaifinsa shiya karbeta hannun biyu ba tare da rainata ba,hakan ya yiwa kakana dadi saboda dama duk cikin yaran sa'id halinshi daban,sai Allah ya sanya yafi qaunarshi,dalili kenan daya saka ya dinga fuskantar qiyayyar 'yan ubanci mai zafi,sai ya tashi a kyare a tsangwame,gashi kome za'ayi masa mahaifiyarsa khadijah da ake kiranta kubra bata daga kai kotace wani abu saboda mutum ce mai tsabar haquri,haka rayuwarshi ta kasance a tsakanin 'yan uwansa,babu wata qauna sai tsabar yan ubanci da nuna banbanci,ruqayya wadda ita ta kasance qanwa gareshi kuma me binsa ita kadai take sonshi,a irin haka Allah ya yiwa mahaifin nasu rasuwa,mahaifin khalipha da innarshi suna gani akayi rabon gadon rashin gaskiya,saidai innarshi bata ce komai ba kamar yadda shima baice ba,suka rungumi abinda aka raba aka basu,sa'id bai zauna ba ya koma kasuwa,wajen abokan arziqi da sukayi zaman lafiya da mahaifinshi masu irin sana'arshi,sanin halayensa na gaskiya da amana,hankali da nutsuwa yasa suka karbeshi yaci gaba da sana'a a qarqashinsu,wato babu maraya sai rago,hakanan babu nakasashshe sai kasashshe,kyau da samartakar sa'id ko daya basu sanya masa girman kai ba ya kama sana'arsa ka'in da na'in,hakan kuwa yayi matuqar taimakawa don nasu raba abincin ci ko suturar sanyawa ba,yayin da a bangaren su hamza kuwa komai ya tsaya cak,rigima ta dinga tashi tsakaninsu,kowa yana ganin shi ya cancanci a baiwa gadonshi dana 'yan uwanshi ya juya,kowa yaja ya kafe kan ra'ayinsa,tilas aka sake gutsuraws kowa aka miqa masa nasa kason,inda mahaifiyarsu daga qarshe ta karbi nata itama dana ruqayya 'yarta,saiyw zamana komai nasu ya soma lalacewa saboda hadin kai,kowa ya tasamma cinye dukiyarsa ba tare da yasan ina tayi ba,hakanan suka dinga fada tsakaninsu kamar zasu yaqi junansu,a haka rayuwa taci gaba da garawa kowanne bangare.
Cikin shekarun da suka biyo baya Allah ya sanyawa dukiyar sa'id da innarshi albarka,yayi kudi mai ban mamaki,yasha fada cewa gaskiya da riqon amana sune ginshiqi kuma matakin nasararsa,sai abu na farko tsoron Allah da kuma bin iyaye,kuma haka yake,duk wani dan adam dake neman cimma wata nasara a rayuwarshi to yayi riqo da wadan nan matakan da taimakon ubangiji zaikai inda yasa gaba.
Zuwa sannan dukka yayyenshi sunyi aurensu,saiya zama babu da talauci ta saukar musu,ci da iyalin na neman ya gagaresu,ruqayya da suke ruqo dalilin mutuwar mahaifiyarsu saita soma passing passing daga hannun wannan zuwa na wancan,a nan ne suka soma rabowa wajenshi,kowa ya soma kwantar dakai dayi masa biyayya kamar zasu kwanta mishi,innar sa'id ita ta umarceshi da kada ya fasa taimakawa kowa a cikinsu ko bayan ranta,to shima mai sauqin raine da haquri,saboda haka sai ya zama shine lalurar duka gidajen nan gida biyar,yayin da sukaci gaba da nuna mishi soyayya da qauna ba don Allah ba,ko sau daya bai taba kawo komai a ran shi mara kyau game dasu ba,haka yaci ga ada taimaka musu har Allah ya kawo rasuwar innarshi,abinda bai sani ba shine a bayan idanunshi murna suka dinga yi da faruwar hakan,suna ganin abu mafi sauqi shine su aikashi lahira su cinye gadonshi,tunda a yanzu baida wani wanda zaici gadonshi tunda ba aure gareshi ba.
Zakaran da Allah ya nufa da cara,suna can suna nasu shirin a sanda Allah ya hada soyayyar sa'id da aishatu buzuwa daga niger,Allah shi yakai sa'id garin ta silar kasuwancinsa suka hadu da ita,soyayya suke da juna tuquru da gaske a lokacin da ayshan tuni yayanta kuma mariqinta ya bada ita ga wani dan uwansu,sam tama mance da wannan batun don bashi takeso ba,ba tsoro ta aika sa'id gaban yayan nata ya gabatar da kansa a wajensa,yayi mamakin yadda aysha ta manta da batun da sukayi da ita,amma ya kauda wannan yayi masa bayanin cewa an bayar da ita,aysha ta sakawa ranta sai sa'id yayan nata ya dage sai wanda ya zaba mata,duk da bata taba fito na fitodashi kan lamarin ba amma duk wanda ya santa yana kallonta yasan tana cikin damuwa,abinci na mata wuyar ci,da yaga dai da gaske take saiya amshi neman aurenta da sa'id yake,amma bisa sharadin idan ta tafi dadi ko wuya karya dawo musu da ita,tace ta amince da hakan,saboda dukka wata nagarta da mace ke nema wajwn mijin aure sa'id nada ita,wanda ko kwatan haka bata gani ba daga wajen wanda yayan nata ya zaba mata ba,duk da yake dan uwanta amma tasan yana da raunin nagarta,akan wannan sharadin akayi aurensu,ya daukota daga nijer zuwa nigeria,yayi mata dukkan wani gata,ya riqe anni da kyau cikin qauna da soyayya da kuma kulawa da juna,itama ta riqeshi da irin biyayyar nan da akasan matan aure nada dashi.
[26/02, 8:54 PM] +234 810 044 6653: 43
Soyayya suke gudanarwa mai kyau da tsafta,ya karbo ruqayya daga hannun 'yan uwanta ya dawo ma da anni ita,hakan ya yiwa anni da bata da kowa dadi,saitake kallon ruqayya a matsayin 'yar uwa,suna zamansu lafiya,yayin da daga gefe guda 'yan uwan sa'id nacin dunduniyarshi duk da cewa shine komai nasu,cinsu,shansu,suturarsu,karatun yaransu,kuka da lafiyarsu da sauransu duk yana wuyanshi,haihuwar farko anni ta haifi muhammad khalipha,nan fa hankulansu suka sake tashi saboda suna ganin sun rasa damarsu,tunda har ya haifi da namiji tasu ta qare,suna ji suna gani suka haqura,suka ci gaba da tatsarshi da tatsar dukiyarshi ta hanyoyi daban daban,yaki halal yaki haram,haihuwa ta biyu anni ta samu mace,ruqayya nata murna ta samu 'yar uwa amma ana yayeta ta rasu,a haihuwa ta uku ma sai aka sake samun namiji haka ta hudu,sai ata biyar Allah ya kawo hajar.......,har a sannan daga dangin anni ba wanda ya nemeta,ita kuwa kullum zancansu na cikin bakinta,saidai tasan bata isa ta matsa kusa da inda suke ba saboda sun mata sharadi tun farko.
Dukkan wani qauna tattali da soyayya tamu tana kan hajar mu duka baki dayanmu,kasancewarta auta kuma mace a cikinmu,hatta da anni na qaunar hajar,yarinyar hallayyarta daban take,tana da haquri,sanyin hali shuru shuru da rashin surutu tun tana qaramarta,tana da biyayya bata da rashin kunya sam.
Hajar nada shekara goma aka aurar da anty ruqayya,mijinta ma'aikacin gwamnatin tarayya ne,tu a alokaci. Gwamnati na tura ma'aikatanta qarin karatu qasashen waje aka turashi ya dauki ruqayya suka tafi,wata hudu da tafiyarsu babban tashin hankali ya samu iyalin muhammad sa'id mai goro,Allah ya daukeshi sakamakon jinya da yayi wadda batagi ta wata guda ba,tashin hankalin da matarsa da iyalansa suka shiga a sannan bazaiyiwu baki ya musaltashi ba,da qyar aka samu kan iyalin nasa saboda kowa a cikinsu a dimauce yake,ruqayya batasan da wannan ba sam saboda a lokacin wayar tafi da gidanka bata yawaita ba ba'asan number ko layin da za'a sami mijinta a sanar masa ba.
Ba yadda bawa ya iya da hukuncin Allah,haka daga bisani suka haqura suka dauki dangana.
Kwana uku kacal 'yan uwan alhj sa'id suka soma zirya kan dukiyarsa da abinda ya bari,yau suce a bada muqullin kaza,gobe suce meye password na safe dinshi,jibi suce a bada muqullin mota,gata suce ina takaddun kaza,a lokacin anni da kallo kawai take binsu,kasancewar har yau batayi normal ba,saboda mutuwar tayi mata duka bana wasa ba,alhj sa'id shine gatanta uwa kuma uba a gareta,ko mutuwar iyayenta bata shiga wannan yanayin ba saboda a sannan bata da wani shekaru duka duka bata wuce shekara uku a duniya ba,haka suka dinga karbar abubuwa d'ai d'ai da d'ai d'ai ba tare data ce musu komai ba,uwa uba bata da kowa bare yace zai tsaya mata,khalipha da yake shine babba a sannan bazai wuce shekara goma sha shida ba,duk da haka yaso tasowa da nuna rashin amincewarsa kan abinda ke faruwa,to amma qarancin shekaru da kuma duk sanda ya doshi anni da maganar maimakon ta bashi hadin kai sai kawai ta saka kuka,tana ganin kamar ta dukiya kawai suke bayan wanda suka rasa yafi dukiyar da duk abinda ke cikinta,hakan yasa ya janye ba mataimaki babu mai qwarara masa gwiwa.
Kafin kace meye wannan sun kwashe duk wata kadara daya mallaka,suka debo kauyoyin bogi da sunan duk dukiyar alhj sa'id banki sun karbe saboda bashin daya cicci kafin barinsa duniya,abinda ya rage musu kawai shine gidan da suke ciki sai motar hawanshi guda biyu,wanda shima easa muqullin akayi,muqullan kuma khalipha ne ya kwashe ya boye sanda suka haukace da nemansu,basu da tsayyaye gakan ya sanya dole suka haqura da qaryar da suka yanka musu,ko a sannan khalipha sai daya qaryatasu ya kuma yi maganganu son ransa saboda yasan duk abinda suka fada qarya be,basu ji kunya ko nauyin idon mahaifiyarsa ba,basuji tausayin maraicinsa ba suka mishi duka suna zqginsa kan bashibda mutunci baisan darajar na gaba dashi ba,yarin dasu kansu sun shaida sanda mahaifinsa nada rai ko kallon banza basa iya masa,bawai don wani abu ba A'ah,duk sharrinka da hassadarka idan kaga iyalan sa'id kasan sun samu tarbiyya fiye da duk wani yaro dake cikin danginsu,basu fara ji a jikinsu ba saida kowa ya watse ya kama gabanshi,aka barsu saisu yasu,suka soma cin abinda tayi saura daga kudin hannunsu da kuma store din gidan,don ko daya alhj sa'id ya gatanta anni bai barinta ta saida komai(kira a garemu mata,kada gata da dadin da miji yake baki yasa ki rungume hannunki kiqi sana'a komai qanqantarta,saboda ba wanda yasan ya rayuwa zata kaya mishi,ko babu talauci akwai mutuwa akwai tsufa).
Zara bata barin dami,sannu a hankali komai nasu ya tasamma qarewa,a nan anni ta shiga tsantsar tashin hankali,yaranta basu saba da wahalar rayuwa ba cikin qaramin lokaci saiga talauci na bayya a jikinsu,makaranta aka korosu ganin anci tearm biyu ba kudin makaranta ba dalilinsa suka koma zaman gida,duk wanda tasan suna huldar arziqi da maigidanta ta nemi taimakonsa amma kowa ya janye hannunshi yaqi tabuka komai,masu ragowar imanin ciki ne zasu taimaka daya biyu suma saisu watsar(irin rayuwar da muke ciki kenan a yanzu,kaci arziqin mutum amma bayan qasa ta rufe idonshi kana kallo iyalinsa su shiga halin ni 'yasu ba damuwarka bane,bamusan cewa kukan maraya cikin al'umma musifa da bala'i bane a cikinmu,kina ko kana katanga daya da maraya zai iya kwana baici abinci ba amma ke washegari kina da sauran da zaki zubar a bola,bamusan tashin hankalin dake jiran duk mutumin da zai kwana a qoshe maqocinsa ya kwana da yunwa ba koda kuwa ba marayu bane,ta yaya zamu rabu da ganin musifu da bala'i a rayuwarmu d'aya nabin d'aya?,ga cin dukiyar maraya data zama ruwan dare,Allah S W T yana fada cikin qur'aninsa mai girma , *_wadan nan da suke cin dukiyar maraya da zalunci haqiqa suna cin wuta ne a cikinsu,da sanju zasu shiga wutar sa'ira_* ,bama dukiyar maraya ba kawai,hatta da haqqin wani idan kaci ranar gobe qiyama duk abinda kaci din haka zaka zo dashi a kafadarka gaban zatin Allah komai girmansa komai qanqantarsa saika dauko shi,gaban mutane da aljannu qwari da dabbobi,tun daga zamanin annabi adamu har zuwa zamanin annabi muhammadu a gaban idanunsu za'a maka hisabi,Allah da kanshi yace *_haqiqa ubangiji baya zalunci dai dai da qwayar zarra_*
Allah ya shiryemu yasa mu gyara dabi'unmu,ya rabamu da cin haram da cin haqqin daba namu ba Allahumma amin.)
Duk wani fadi tashi ba kalar wanda bata runguma saboda farincikin 'ya'yanta da walwalarsu,Duk wannan abun yasan tana yine saboda farincikinsu,tun quruciya yaro ne mai son iyaye da son faranta musu,shi yace ta daina saida komai nata,zai fita yaga yadda zaiyi ya dinga sama musu abinda zasuci din,sam ta hana shi tace bata amince ba,abata haquraba anni sai data qarar da duk wani abu nata mai daraja.
Abu na gaba daya kunno musu kai shine yawan hauro musu gida da aka shiga yi,ga zaton masu haurowar tarin dukiyar da alhj sa'id ya tafi ya bari tana narke a gidan,wannan abun shi ya tsoratasu,musamman anni da take tsoron mutuncinta dana diyarta hajar,hakan ya sanya suka tattara kayansu sukayi balaguro zuwa gidan babban wansu alhj sa'id din wato saminu,wanda dukansu tare suka rabe dukiyar a tsakaninsu.
Sanda suka je matar gidan damai gidan dukansu basa nan,sanin su waye a wajen masu gidan ya sanya mai aikin ta saukesu sauka mai kyau,saidai tana mamakin suturar dake jikinsu,anan suka zauna sukaci suka sha cimar da suka jima rabonsu da ita.
Kafin wani lokaci hajar ta lafe jikin anni bacci ya dauketa saboda sanyin acn dake busowa,wanda rabonta dashi ta jima,a haka matar gidan damai gidan suka dawo tare da alama taren suka fito,tun shigowar saratu ta soma binsu da kallon banza kamar taga kashi,matar da ada kamar zata yiwa ummi sujjada,shima mai gidan abinda ya soma ce musu shine
"Kai yaya?,ya akayi ne mu kukazo yi" da qyar ya amsa gaisuwarmu,ummi tayi masa bayanin abinda ke tafe damu
"A gaskiya gidana babu wajen zamanku,saidai kuyi haquri aisha kuje koda gidan hamza wataqila shi yana da daki spare,ni yarana ma so nake kowa nayi masa nashi dakin daban,saidai ga wannan kwa sayi abinci don wataqila harda yunwa ma ta saku shirya wannan qaryar" ya fada yana ciro dari biyar ya miqa musu,mus'ab zai karba zuciya ta ciyo khalipha ya tankwabe hannunshi kudin ya fadi qafar alhjin,saiya daga kai ya kalleshi,dama neman qofa yake,nan yahau zage zage da tsine tsine,yana kwashewa khalipha albarka,ya kuma yi musu wuta wuta kan su fice masa daga gida bazai iya zama da mara tarbiyya ba,haka suka debi kayansu 'ya'yanshi na wajen suna sake turasu da sauran kayansu haka suka bar gidan.
Daga nan gidan qaramin cikinsu suka nufa,hakanan yana dan qananun maganganu ya karbesu
"Yanzu kaji ana tuno da tsohon zance,kawai don an siya maka gida kuma sai ayita bibiyarka" daki daya can falle a bayan gidan ya basu,dole khalipha ke kwana a waje sauran su kwana a ciki.
Kwata kwata zamane da babu dadi ko 'yanci ko ba'a gayawa masu karatu ba,raini da wulaqanci daga wajen masu gidan da 'ya'yansu kawai ya isa ya sawa zuciya baqinciki da bacin rai,sam basa qaunarsu,rashin tarbiyya qarara da izgili,har anni basu bari ba,abinda ya dinga qona zuciyar khalipha kenan,sau tari yakan yunqura zai dauki hukuncinsu anni ta dakatar dashi,abinci sai anga dama ake basu shi,ba ruwan mai gidan da sutura man shafawa da sabulun wankinsu,hakan ya qarawa khalipha himma,kullum ta Allah saiya fita,duk aikin halak da yasan zai sama mishi kudin da zasu dan kashe buqatar data taso musu komai qaqancin aikin koda kwasar kashi ce zaiyi ta,suna zaune ne kawai akan lalura,wannan shine gidansu amal,mahaifiyar amal macace mai shegen kissa da kutungwila,tun kan wannan lokacin haka take tun zamanin da duniya keyi dasu tafi kowa shishshige,amma a yanzun yadda take saika rantse da Allah Batasan ummi ba,mus'ab da hajar kuwa basu isa su sake ba dayake sune qanana a sannan,karma hajar taji labari,haka suke zaune sam babu wani dadi takowanne bangare sai haquri kawai,suna rayuwa babu makaranta bare suturar kirki,saidai duk tsiya ba zaka samesu cikin qazanta ba,zaka samesu fes dasu,hakanan annin ta tsaya tsayin daka wajen yi musu karatun addini dana boko iya wanda Allah ya hore mata,a haka suka rufa shekara a gidan da qyar.
Qarshen zamansu a gidan kuwa ya faru ne sanadiyyar dukan hajar da amal tayi,anni ta jata tana mata nasiha tare da nuna mata hajar qanwarta ce,abinka da sun samu daurin gindi sai kawai ta zunduma ihu,yarinya qarama a lokacin da ba zata wuce wasu shekaru ba ta zabgawa anni Allah ya isa,khalipha na wajen zuciya ta ciyoshi,dama dannewa kawai yake ya jima yana jin ciwon abinda sujewa annin,mari ya zabgeta dashi mai shiga jiki,gigitaccen ihu ta saki wanda ya sanya har mahaifiyarta dake sashensu sai data jiyo,a gigice ta fito tana neman amal din,sai kuwa suka ci karo a hanya,ta daga hannunta dake dafe da fuskarta saiga shatin yatsun khalipha kwance a kai rudu rudu,ashariya ta dannan ta finciki hannun amal din suka koma sashen su annin bayan ta gama tambayar amal ba'asin abinda ya faru,dai dai lokacin da annin ta balbaleshi da fada kan marin amal din da yayi kamar zata ari baki
"Wato kuna zaune a gidan ubanta kuna cin arizqinsa shine zaku taru ku kashemin diya ko?,to wallahi bazaiyuwu ba,saidai ku fita ku bar gidan nan matuqar haka zaku dinga yiwa yaraba,kowa ya kasa zama daku mu mun haqura mun zauna daku shine zaku takurawa rayuwarmu"da sauri anni ta bude baki zata bata haquri khalipha ya tsaida annin cikin bacin rai
"banga dalilin da zaki bada haquri ba anni kiyi shuru kawai da bakinki,duk abinda yaran nan sukeyi a gidan nan a idonki mama ake amma kin taba tsawarmusu?"
"Iyyee,ni xaka zaga khalipha,to zageni,zageni.....dama ana fadar halinka ashe da gaskene,to zamanku ya qare a gidan nan wlh" ana cikin haka mai gidan ya dawo,mama na ganinsa ta saki kuka qarya da gaskiya ta soma shirya masa,nan ya hau ya zauna daram,dama mai neman kuka an jefeshi da kashin awaki,nan ya dinga lailayo ashar kai kace khaliphan ba danshi bane,kai kace bai sanshi ba basu taba hada alaqa dashi ba,bai taba cin wani abu na arziqin mahaifinsa ba,hasalima ba zaka ce gadonsu na wajensu sun lamushe shi ba,a sanda yake wannan tada jijiyar wuyar tuni khalipha ya gana hada musu kayansu tsaf,haka ya dauki wasu aliyu da mus'ab suka dauki wasu suka fice daga gidan,har bakin qofa ya musu rakiya yana jifansu da muggan kalamai kala kala,wadanda suka sanya anni zubda qwalla,yayin da khalipha idanunsa suka kada sukayi jawuri saboda bacin rai,zuciyarshi ce kawai ke tafasa,ji yake kaman ya koma ya rufeshi da duka,saidai yasan koda yaso hakan anni ba zata taba barinsa ba.
A bakin layi anni ta sake yanke shawarar suje gidan habibu,sam bayaso yayi musu da ita,hakan ya sanya baice mata komai ba suka kama hanya a qafa,duk da nisan dake tsakanin gidajen haka suka taka har gidan,tun daga yanayin yadda matar gidan ta tarbesu farkon zuwan gidan nasu sukasan cewa akwai babbar matsala,tunda khalipha yaga yadda yaran gidan ke sangarta yasan tafiyarsu ba zata taba dai dai ba,tunda suka je aka zubesu a falo ba wanda yabinta kansu,har aka gama girkin rana a gabansu yaran suka baje suka ci abinsu ba wanda ya basu koda loma daya,a sannan hajar ta soma yatsina fuska tana radawa anni cewa yunwa takeji,haquri annanin ta bata saboda tasan cewa da zarar khalipha yaji ba zaman lafiya saiya samo ya bata,wata iriyar qauna da shaquwa ce tsakaninsa da ita fiye da sauran 'yan uwanta,tun tana yi a boye har khalipha ya fuskanci abinda ke faruwa,tunawa yayi duk cikinsu babu wanda aka yiwa iyaka da abincin gidansu a sanda suke dashi idan sunzo,daga babba har yaro idan yaje kanshi tsaye yake wucewa ya zabi kalar abinda yakeso a dafa masa,sai kawai ya nufi kitchen din gidan da kanshi,yarinyar gidan ya taras (zeenart a sannan)da mai aiki tana dafa mata indomie,ya tambayi mai aikin abinci,budar bakin yarinyar sai cewa tayi
"Ba za'a bayar ba makwadaita kwadayayyu" ta fada tana murguda baki,zuciya ta tasowa khalipha yayi yunqurin danneta sabida fadan anni daya fado masa,sai ya zari plate kawai ya bude tukunya ya zubo abincin ya fito,aikuwa ta biyoshi tana ihun barawo,umma ga barawon abinci bawai kuna don batasan khaliphan ba,kawai tsabar rashin tarbiyya ce.
Mai gidan da tunda sukazo akace musu yana barci bayan sunsan tabbas yaji zuwansu shi ya sauko daga samanshi yana tambayar zeenart din ya akayi
"Alhaji zuwa yayi har kitchen ya diba mana abinci" hannu yasa ya wafci abincin yana rufe khaliphan da fada
"Wannan wanne irin sakarcin banza ne da wofi,saboda tsabar rashin tarbiyya har takai ka dauki abinda ba naka ba ba'a baka ba?,to ni wannan iskancin ba'a gidana ba" haquri anni ta soma bashi khalipha na kallo zuciyarsa na tafasa,sai daya mula don kanshi yana hura hanci yasa aka basu daki,abinci ko yace saidai su jira na dare,saboda bacin rai khalipha wuni yayi a waje bai zauna agidan ba,ba laifi wunin da yayi a waje yayi masa rana,don neman kudi yayi sosai,bai dawo ba sai bayan sallar isha'i,ya shigo gidan a matuqar gajiye,cikin tausayawa anni ke dubanshi,qwalla ce ta cika mata idanu amma saota maida saboda tasan yanzun hankalinsa zai tashi,tuna tsantsar gata da suka samu daga mahaifinsu take,amma yau rana daya rayuwa ta juya musu baya cikin qiftawa da bismillah,dubansu yayi daua bayan daya,ya tambayi kowa lafiya ko suka amsa masa da eh,awara ya ciro mai zafi ya miqawa kowa tashi,saidai ta 'yar lelen tashi hajar daban take,ya qara mata da goba irin manyan nan da yaga tana yawanso,ba qaramin dadi suka jiba kuwa,anni ta dauko wani ragowar abinci cikin kwano ta tura gabanshi
"Ga naka abincin nan kaci mu munci namu,hala ma fushi kake damu tunda ka fita baka dawo ba sai yanzu" murmushin yaqe yayi yana amsawa da annin da a'ah,tunda ya kalli abincin yasan cewa ba qoshi sukayi ba,saboda haka ya juye tashi awarar akai yace kowa ya matso yasa hannu suci abincin yafi albarka.
Da murmushi anni ke dubansu sanda suke cin abincin,ta dago wayon khalipha,zuciyarta cike da tausayinsu da kyakkyawar addu'a da kuma fata da data dinga binshi dashi,ta tabbatar cewa Allah ya bata jarumin d'a,daya tamkar da dubu.
*mrs muhammad ce*
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
44
Duk da cewa bai tashi a wahala ba bai kuma saba da ita ba amma data riskesu yasa hannu bibbiyu ya karbeta,ya kuma shiga bilhaqqi da gaskiya yana qoqarin ganin farinciki da walwalarsu
"Anni kema kici" khalipha ya fada yana dubanta,kai ta girgiza
"Kuci khalipha,ni cinku shine kwanciyar hankalina" sai shima ya tsame nashi hannun yaqici,sai data lallabashi da qyar sannan ya maida hannun nasa,a hakanma kusan sai suyi loma uku baiyi daya ba.
Zamanta a gidansu zeenart shima dai zama ne maras dadi,zaman qunci da takura,wulaqanci kyara da tsangwama,rashin kunya fitsara da sangarta babu wanda anni bata gani ba daga wajen yaran gidan,tsana da kyara qarara,yayin da khalipha ya dage ta wani fannin,duk hanyar da yasan zai samu kudi indai ta halas ce zaiyi komai kashinta,baida girman kai lalaci ko son jikinsa,amma da yake qasar tamu ga yadda ta zama samun sai addu'a kawai,ana samun amma da qyar,hakanan abinda ake samun bai taka kara ya karya ba,da haka ake jalautawa rayuwar yau fai gobe tsumma.
Barinsu gidan shima sanadiyyar sharrin sata da matar gidan ta dorawa anni,dukka yaran kuma suka dorar da cewa eh sun ga sanda annin ta dauka suna daki ta zaci bacci suke,haka aka musu korar kare a sannan khalipha baya nan ya tafi neman kudinsa,a qofar gidan suka wuni da kaya a gabansu,ga yunwa baci ba sha,sai yamma lis ya dawo ya samesu zube a wajen,cikin gigita ya qaraso wajensu yana tambayarsu
"Anni....lafiya?,me kike anni a waje?,kalli kayanki yadda sukai qura?,wadan nan kayanfa anni ke zakuyi dasu?" Murmushin qarfin hali ta soma saki duk don ta kwantar masa da hankali,haidar da shima ranshi ke bace tun a sannan shi ya shaida masa komao,cikin wani matsanancin fushi ya durfafi gidan gaba daya jijiyoyin kanshi sun tashi saboda bacin rai,cikinnzafin nama anni ta damqoshi,da qyar da iya tsaidashi
"Indai na isa dakai karka taka musu gida,ka wuce mu tafi" tilas ya dakata,saidai zubewa yayi a wajen ya saki kuka,yau ya kasa daurewa,bacin ran dake cin zuciyarsa yayi yawan da bazai iya daureshi ba a yau,hajar ita ta taso tana kuka ganin khaliphan na kuka,ta iso gabanshi ta soma share masa hawayen fuskarshi,kallonta yake rausayinta na kamashi,idan duk su maza ne zasu iya daurewa rayuwa,zasu iya rayuwa koda babu kayan more rayuwa babu qyale qyale ita kuma fa?,ta soma zama budurwa amma babu duk wani kayan alatu kona qyale qyale irin wadda diya mace keda buqata tattare da ita,bayason kukanta ko kadan,sai ya sakar mata murmushi yana riqe hannayenta,miqewa yayi tsaye ba tare daya ce da kowa komai ba ya isa gaban kayansu,ya goya daya ya riqe biyu a hannayensa yayi gaba,shi kadai yasan me yake ji cikin qirji da zuciyarsa,takawa ya soma yi zuwa bakin titi wanda hakan ya sanya suka bishi da sauran kayan.
Mota ya tsare musu,yana fadin sunan unguwar da zasu anni ta dubeshi,yana nufin zasu koma gidansu su zauna ne
"Khalipha,kanaso mu koma gidanmu kenan?"
"Allah yana sane damu anni yana kuma tare damu,mutanen nan dukkaninsu babu wanda zai iya riqemu,babu wanda ya tuna da halaccin abba a garesu sanda yana raye dai dai da rana daya,komawarmu gidanmu shine gata na farko da zamu yiwa kanmu" bata sake tankawa ba,duk da qarancin shekarunsa amma yana da zurfin tunani da kaifin hankali.
Tamkar kango haka gidan ya koma,babu komai a cikinsa,basusan wanda ya shigo ya kwashe sauran furnitures din dake cikin gidan ba,amma koma wane duk yadda akayi yana da spare key din gidan,duba da yanayin ginin gidan gini ne irin na masu kudi mai cike da security,ba yadda suka.iya haka suka gyara sauran abinda ya rage a gidan,suka hadu suka share gidan tas,abinda basu taba ba bazasuma iyaba saboda girmansa masu aiki ke musu,amma yau babu ko mutum daya daya zauna dasu cikin ma'aikatansu kowa ya kama gabanshi.
Khalipha shi yaci gaba da daukar dawainiyarsu,ya hana annin yin komai,duk wani aikin qarfi kona wahala yana ciki,saidai kuma qoqarin nashi yana gazawa,sakamakon dan abinda yake samun bai taka kara ya karya ba bazai wadacesu ba,nan da nan wahala ta sake bayyana muraran ajikinsu,kana kallonsu kasan yunwa ta samu gindin zama a jikinsu,ba'a maganar sutura dama ko karatu duk wannan tuni ya jima da fin qarfinsu,dole anni ta soma sana'a itama,wanda wankau ne zuwa daka,sai ya zamana ba'a samu sosai saboda yanayin yadda unguwar tasu take,uwa uba ma duk wanda ya kalli gidan nasu daga waje zaiyi dariya ne kawai yace rainin hankali akeso a yiwa mutane,jama'ar dake da gida irin wannan me zai kaisu yin wankau ko daka?,hajar ita ke fita maqotan unguwanninsu tana amso musu wankin ko daka ba tare da sanin khalipha ba,ranar daya sani din kiwa kwanan bacin rai yayi,yayi kuka yayi kuka har yaji babu dadi,kanshi kawai yake tuhuma yana ganin kaman qoqarinsa ya gaza,bayan kuma duk wani qoqari yana yinsa,duk wani aiki daya fado hannunsa matuqar bana haram bane to zaiy ya sama musu abinda zasuci koda kuwa kwasar kwata ne,ita kuma anni tausayinsa take,tana ganin wahalar da yakeyi tayi yawa,dalili kenan daya sanya ta kama sana'ar.
Tafi tafi sai aikin qarfin ma ya zama sai kana da hanya ko.kana da wani daya sanka,zaman gida saiya auri khalipha,yanaji yana gani gidan block din aljh idris yayan mahaifinsa yaje neman aiki suka hanashi,anni ita ta bashi shawarar yaje ya sameshi a gida suyi magana wala'alla yasakasu su daukeshi,da fari yaqi saboda shikam ya sare da halayyarsu gaba dayansu ya aje ta tasu a gafe,musamman alhj idris da dukkansu ya fisu mugun hali,daga bisani ne ya amince don baisan me annin ta hango ba.
Randa yaje din yayi kusan awa biyu yana jiran idris din bai bada umarnin ya shigo ba,sai daga bisani ne yaronshi ibrahim wanda baifi shekara daya ya baiwa khalipha ba yazo ya kirashi suka shiga falon alhj idris din tare
"Cire takalmanka mana malam" ibrahim din ya fada yana katsawa khalipha tsawa,dubanshi khalipha yayi donshi nashi takalman na daure a qafarshi bai cire ba,sai a sannan ya lura,takalmi ne da abbanshi shi ya siyo musu,kudinsa yakai dubu talatin ya dauka ana khaliphan ya baiwa ibrahim daya,nashi kam ya dade dacin kasuwarshi a lokacin da hajar bata da lafiya,basu da kudin magani babu dalilinsa ya saida ya siya mata magani,dama ba wani tayi arziqi suka masa ba kwata kwata dubu goma aka sayeshi.
Saida khalipha ya gama bayaninsa kaf sannan alhj idris yace
"To nidai bana jin akwai abinda zan iyayi gaskiya,don tuni na miqawa yakubu haqqin kula da wajen,baiga dacewar ya daukeka ba shi yasa bai daukeka ba,saboda haka sai kayi haquri" shuru khalipha yayi ba tare da yace komai ba
"Ka tashi kaje" ya fada yana nuna masa hanya,tsam ya miqe ya fice daga falon,yana gab da ficewa a gidan yarinyar gidan daya taras dasu a falo ita da mahaifiyarta ta qwalo masa kira,tsayawa yayi cak
"Abba yace kazo" kaman baxai koma din ba,amma yadda yarinyar ta tsaya tana kallonshi yasa yajuya yabi bayanta.
"Binta tace a barka,basu damai share share ya tafi jinyar babanshi,idan kanaso zaka iya karbar aikin nasa kafi ya dawo sai a san yadda za'ayi,za'a dinga baka albashi a wata dubu biyar,sai abincin rana dana dare amma fa ba kullum ba zaka yi?" Kai ya jinjina saboda kudin koda baikai hakan ba zai iyayi,matuqar zai samu abinda zai kaiwa 'yan uwa da mahaifiyarsa.
Sanda ya koma gida yake baiwa anni labarin yadda sukayi taji dadi koba komai zai samu abinda zai riqesu,saidai kuma wani bangare na zuciyarta suya yake mata sosai,ace yau idriss shi zai dauki dan sa'id boyi boyin gida?,sa'id a sanda yana raye numfashi ne kawai baiyi musu ba,shine cinsu shansu suturarsu da duk wani kasuwanci da sukeyi,uwa uba sune suka kwashe duk wata dukiya ta sa'id din da sunan bashin banki yaci,ba ita ba hatta da khalipha sun sani sa'id din tunkan yayi bunqasar da yayi mutum ne mai tsoron bashi koda na naira biyar ne kuwa,balle har yakai kanshi banki ya karbi dukiyarsu.
Aikin da akace khaliphan zaiyu sai yatadda yaci uban hakan,gida ne mai matuqar girma wanda mahaifinsa ne ya ginawa idriss din dab da zai rasu mai dauke da dakuna da sassa sassa ginin zamani,shi zai share gidan komai girmansa,idan ta kama ma har dakin ibrahim dansa namiji tilo da yake gwadawa gata khaliphan ne zai shiga ya share,wani lokaci hatta da falon gidan hajiya binta saita hada masa da shi,baya ga haka idan i rahim ya bushi iska saiya hado masa kayansa yace ya wanke masa,haka aike lokuta mafiya yawa shike musu,dukka wadan nan hidimomin cikin kudinsa ne,bawai wani albashi na daban aka qara masa ba.
A qalla khalipha sai daya shekara uku yana wannan bautar gidan yayan mahaifinsa,cikin gidan da mahaifin nasa shiya gina masa shi,a qafa yake zuwa a qafa yake dawowa,aninci kuwa sai a debi kusan kwana hudu ba'a bashi na rana ba bare dare,duk ranar da aka bashin kuwa bawai ci yake ba,yana hadewa ne idan ya tashi tafiya ya kaiwa qannensa,wani lokaci idan yaga aikinnyi akan hanya yakan tsaya ya karba yayi kafin ya qarasa gida dinsu samu abun batarwa kafin wata ya cika a bashi albashinsa,don shi kanshi albashin idan alhj idris yaso sai wani watan ya shiga yayinkwanaki goma sha bai bashi ba,ya dinga kuma qananun maganganu shi daya yana fadin dadin ya yiwa khalipha yawa,ga cinyarwa gashi ana biyanshi kudi?,shi ai ya cancanci ma ayi masa jinjina sabida yayi abinda dukka sauran 'yan uwanshi suka kasa,khalipha bai taba daga kai ya dubeshi koya tanka mishi ba,yakanyi qoqarin danne fushinsa sarai duk sanda wani abu mara dadi ya faru,suna cin albarkacin anni data roqeshi kada ya yarda ko sau daya ya biyesu ayi wani abu mara dadi,dalilin barin gidan ya fara samo asali ne daga sanda jama'ar gidan haj binta da ibrahim suka soma qorafin ana musu dauke dauke,kusan kullum Allah ne dakullum sai anyi cigiyar an nemi abu an rasa.
Rabon za'ayi ranar da khalipha ya shiga dakin dakin ibrahim yi masa shara,khalipha tun asali mutum me maison ado da qamshi,kwalliya na burgeshi qwarai,dalili daya sanya koya ya samu kudi bai rasa siyiwa hajar abun kwalliya na mata koda jambaki ne kuwa dan naira hamsin,koda shi bai saka ba ita ta saka,to ibrahim ba laifi akwai qwalisa da ado,duk sanda yayi kwalliya khalioha kan kalleshi,yana tuna sanda mahaifinsu keda rai,duk juma'ar duniya sababbin kaya suke sakawa,wani lokacima anko suke da babanshi,akwai wani turare da ibrahim din ke amfani dashi,kalipha na matuqar son qamshin turaren,ranar yaje yi masa shara saiya dauka ya fesa sau daya a jikinsa,yana shirin ajewa ibrahim ya shigo dakin,nan ya soma cuccusawa ma khalipha ashar yana fadin ashe shine barawon gidansu,ya gaya mishi don ubanshi mai ya dauka
"Babu abinda na dauka maka sai turare dana fesa,wanda shima nasan nayi kuskure kuma kayi haquri don Allah" khaliphan ya fada tunda yasan laifinsa ne,kafewa ibrahim yayi yace bai yarda ba sai khalipha ya tube ya dubashi
"Bazqiyiwu ba tunda na rantse maka ban dauka ba ban dauka ba,dana dauka din kai tsaye zan gaya maka na dauka,don nafi tsorin mahaliccina fiye dakai"
"Ni kake gayawa ba tsorona kake ba,kayimin sata ka dinga gayamin baka tsoro na?" Saifa ibrahim ya rufe khalipha da duka,a sannan ya girmeshi hakanan khaliphan ya rame ibrahim ya fushi gabaran jiki,hakan shi ya baiwa ubrahim damar yiwa khalipha duka bana wasa ba,ya gwara kanshi da bango sosai wanda yayi sanadiyyar sunewarshi,bai farfado ba sai a asibiti,tunda ya samu sauqi aka sallemshi ya koma gida,duk sanda ya tuno da abin yana qona mishi rai,sharrin sata abu ne ba qarami ba,amma anni tace ya barsu da Allah,ta kuma yi masa fadan fesa masa turaren da yayi,ta gaya masa shine silar komai,dabai fesa ba da duk hakan bata faru ba,wannan shine silar abinda ya gadarwa khalipha cuwon kai mai tsanani da yake shan wuya duk sanda ya tasarmasa har kwanan gobe.
sanda abun ya faru saura kwana biyu a biyashi albashinsa,kwana biyu na cika saiga kawu idris da albashin khaliphan,sunyi mamakin ganinshi don sunsan bata yadda za'ayi ya biyoshi da albashinsa,ilai kuwa bayan ya miqa albashin sai ya sassauta murya cikin murmushi,a lokacin khalipha na dakin annin yana kwance don bai gama murmurewa ba
"Wata magana nazo miki da ita mai muhimmanci aisha,wadda idan har kika amince da ita ni dake gaba daya kowa zai amfana"
"Inajinka,Allah yasa alkhairi" ta fada tana dubanshi a darare don ita har yanzu bata amince da zuwanshi ba
"Nace ba....me zai hana muyi aure ni dake,idan yaso saiki kwaso 'ya'yanki naci gaba da kuka dasu,'ya'yan sa'idu ai 'ya'yana ne" a zabure khalipha dake kwance ya miqe,cikin azama ya tashi tsaye ya fito falon
"Tashi ka fitar mana daga gida" kallonshi idris yayi
"Meyw haka khalipha?"
"Nace tashi ka fitar mana daga gida maciyin amana kawai,Allah ya tsare anni da aurenka har abada wallahi tafi qarfinka"
"Me kake haka khalipha?" Anni ta fada tana qoqarin tsawatar masa gajin yadda yataso haiqan kaman zai daki kawu idris,sam bai saurari zancan anni ba bai saurarawa kawu idris ba sai daya danganashi da gate din gidan sannan ya dawo,idanunshi kamar garwashin wuta haka suk a kada sukayi jajur,haka kawai ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda bacin rai ya dinga kai kawo
"Anni,duk randa mutumin nan ya sake dawowa gidan nan saina nakasta shi" haka ya dinga fada saida annin ta tsawatar masa
"ka shiga hankalinka mana khalipha,ni din bansan me nake ba koko yaya?,idris ne fa na sanshi na kuma san halinshi da manufofinsa kaf tun kafin a haifeka" da qyar anni ta iya control dinsa,haka yake bai iya fushi ba,ya kuma qaro zafin zuciya sanadiyyar tsangwama da rashin kirki da azabar da suka dinga gwada masa da 'yan uwanshi.
Tun daga ranar bai sake waiwayarsu ba kamar sauran,su kadai suke rayuwarsu,su kadai suke fadi tashinsu,su kade suke cin wahalarsu,wataran subsamu wataran suyi kwana biyu uku basu samu ba.
Wata biyu da zuwan kawu idris da wannan maganar hajar ta soma wani irin ciwon ciki mai tsanani,idan ta fara wani lokaci har suma take,anyi gwaje gwaje ya tabbatar da appendixs ne kuma saidai ayi aiki,kasancewar babu babu kuma mai basu haka suka haqura suka zubawa sarautar Allah ido,haka hajar ta dinga fama,yau lafiya gobe babu,idan ciwon ya tasar mata kamar ba zata kai ba,ba wanda yasan halin da suke ciki ballantana ya nuna kulawarshi.
Idan ajali yayi kira ko babu ciwo aje,safiyar wata laraba ciwon ya tasarwa hajar sosai,a lokacin khalipha ya fita wajen nema musu abinda zasuci,don wayewar garin basu tashi da qwayar hatsi da zasu iya sanyawa a bakinsu ba,haidar ne ya dinga yawon nemanshi duk wajen da yasan za'a sameshi,da qyar ya samoshi wajen wani fili da ake kwashe bolar ciki za'a soma gini,khalipha na cikin masu kwashe sharar,a gigice ya tafi wajen ogan nasu ya masa bayanin halin da ake ciki,ya lissafa iya kai nawa khaliphan yayi aka biyashi,ya tausaya masa har qari yayi masa akai suka taho gida tare da haidar,kafin su qarasa tuni hajar ta galabaita ta fita hayyacinta,abun ya tsoratar da khalipha sosai don bata taba irin haka ba duk ciwon da take,nan suka kwasheta sai asibiti,a canma dan abunuwan da suka saya gwaje gwaje da sauransu duk sun cinye dan kudin daya riqo,duk da cewa asibitin gwamnati ne amma sunan a baki ne,kusan komai talaka shike ma kansa,duk abubuwan daya kamata gwamantin tayi ta saki.
Daga bisani likitan ya shaida musu cewa tilas a gaggauta yi mata aiki nan da awa ashirin da hudu,idan ba haka ba komai zai iya faruwa da ita.
Fadin irin tashin hankalin ma da suka shiga bata baki ne,hankalin khalipha ya kuma tashi sanda ya koma dakin ya iske hajar riqe da cikinta tana faman kuka annin na riqeta,idanunta kan khalipha,tsananin tashin hankali yasa ya kasa qarasowa,yana jin sautin kukanta a kunnensa ya fice daga asibitin,duk inda ya samu kawai jefa qafarsa yake,tunani yake ina zai samu kudin nan da awa goma sha?,abinda bai taba ba a ranar shi yayi wato roqo,saidai ba wani abun azo a samu ba ya samu har dare ya soma tsalawa,kawai sai ya siyi abinda su anni dasu haidar zasu iyaci ya koma asibitin,ai kuwa suna zaune waje daya yunwa ta addabi kowa,hajar kuwa barci ya kwasheta,haka ya bude musu suka rufu suka cinye tas,yacewa anni zai wuce gida gobe zai dawo da kudin da yardar Allah,dubanshi kawai take tana kallonshi,har yau khalipha da sauranshi game da halayyar mutanen duniya,wadanda basusan taimako ba,wadanda basu san kowa ba sai kansu,basu damu da damuwar kowa ba sai tasu,son kawunanmu yayi mana yawa,idan dai kai daya zaka rayu to ba matsalarka bace kowa ma ya mutu,idan dai kai daya zaka tsira ba matsalarka bace kowa ya cutu,har kullum kowa burinsa yaga komai nashi yana tafiya masa daidai ba ruwanka da halin da dan uwanka zai shiga sanadiyyar wani abu daka aikata masa,bata sace masa gwiwa ba,ta bishi da fatan alkhairi,ya fice zuciyarsa cike fal da tausayin mahaifiyarsa kamar yadda itama tata zuciyar cike da tausayinta da qannenshi,a qafa ya daba har gida ya shige ciki ya kwanta,saidai cikin wannan daren duk iya satar bacci bai samu nasarar daukeshi ba,duk juyin da zaiyi anni da hajar dasu haidar be cikin ranshi,cikin daren ya yankewa kanshi dole ya dangana da wajen kawun nan nashi,yana kyautata zaton a wannan karon zasu dubi halin da hajar din ke ciki su tausaya musu.
Asubar fari bayan ya idar da sallah daga masallaci ya zarce gidan kawu hamza,duk da halin da suke ciki bai taba yarda sallah asuba ta kubce masa cikin jam'i ba,sanda ya ganshi fada ya soma balbaleshi da shi kafin ya saurara yaji abinda ke tafe dashi,sai daya gama tsaf sannan yace dashi
"To nidai yanzu bani da abinda zan baku ko qwandala kuwa,saboda nima kudin makarantar yara da zan biya nake nema,tunda yanzu babu maiyi mana dole na tashi ka nema da kaina" hakanan ya fito jiki ba qwari ya tunkari gidan kawu munzali,kawu habibu,kawu saminu
"Tabdi,amma bansan baka da hankali ba yaro sai yau,yanzu wake neman kudi wajen jama'a kowa tashi ta isheshi?"
"Ni ta kayqn sallar yara na nake,dama mahaifinka kedan tabukawa yanzu ko babu shi kaga dole mu tsaya mu share musu hawaye a madadinsa"
"Motar maryam ta lalace wata takeso na sauya mata,saidai ka jira nan da qarshen wani watan ina bin wani maqofcina akasuwa bashi ya yimin alqawarin zai bani,sai kazo ko rabi ne na bayar"
"Tashi ka bani waje,kun gama diga mana rashin mutunci wato sai yanxu kuka san damu" wannan shine ire iren kalaman daya gamu dasu a dukka gidajen,gida na qarshe daya je shine gidan kawu idris,bai taba tunanin zuwan ba amma zuciyarshi ta bashi qwarin gwiwar zuwan.
A falon gidan ya taddashi zaune shida ibrahim suna lissafin kudi,yana ganinsa ya miqe tsaye cikin hayagaga da hargowa
"Ubanka kazo yimin cikin gida?"kai ya girgixa masa
"ohhhh,uwar kace kenan ta sake turoka kazo ka qarashe cin mutuncin da baka gama yimin ba kenan ko?"
"Ba haka bane kawu kayi haquri,hajar ce a asibiti bata da lafiya sosai za'a yi mata aiki,to kudin aikin da suka fada din bamu dasu....."
"Shine kazo gamai indararo mai aikin banza ko,Allah yana bani ina watsarwa" ya fada yana ware hannayensa kamar mai shirin yin daquwa
"A'ah kawu,ka taimaka wallahi tana matuqar buqatar taimako tana jin jiki sosai kawu,ko bashi ne ka bani nizan biyaka daga biya in sha Allahu"
"Kaga kudaden nan?" Ya fada yana nuna daurin kudin dake gabanshi,har zuciyar khalipha ta soma sanyi ya gyada kai,sai ta jefeshi da mummunan furucin da har yau idan ya tuna sai yaji tsanarsa
"To ko ubanka dake kabari ne zai fito bai isa in bashi kudin nan ba,koshi yayi kadan ballantana kai,hajar kuwa tama mutu mana asara ta ce?,kai gwara ta mutu ma mun rage iri mun huta aurarwa" daga jajayen idanun sa khalipha yayi ya zubawa kawu su,wanda shi kansa sai daya tsorata da sauyawar da yayi lokaci daya,ji yayi idan ya qara minti daya a gidan zai iya mutuwa,ji yayi kamar kawun ya yuwa hajar baki mutuwar zatayi,tamkar iskar guguwa ya miqe ya fice wanda badan ibrahim yayi saurin matsawa ba tafiyar yaaji zaiyi dashi.
Yana fita yaci karo da motar kawun sanuwa wadda cikin gadonsu da suka wawashe suka kasafta ya siya,idamunshi suka sauka kan wani qaton dutse dake girke a gefe,baiyi wata wata ba ya cirashi yabi dukka gilasan motar ya fashesu tas ya kuma lallotseta ya qara gaba.
Asibitin kawai ya nufa don yaga halin da suke ciki,tun daga harabar asibitin yaji haka kawai gabanshi ya yanke ya fadi,qafafunsa sunyi sanyi,haka ya dinga takawa har dakin da aka kwantar da hajar.
Anni na tsugune gaban wani abu dake shimfide a gabansu,gefa haidar da mus'ab kowanne cikinsu kuka yake banda anni data zubawa abin ido,take qwaqwalwarsa ta gaya masa hajar ce ta tafi,haka ya dinga takowa kamar gunki yayi tsaye a kansu anni,sai a sannan ta lura da zuwanshi
"Yauwa khalipha,kamata mu tafi,hajar ta tafi ta huta,kaga hadonma har an dora wani a kai" anni ta fada tana miqewa tsaye,kallo daya yayi mata ya fuskanci ba cikin hayyacinta itama take ba,duk da bala'in da yayi masa yawa haka ya dinga kiran sunan Allah ya sami nutsuwar daya juya ya samo abun hawa suka sanya gawar hajar badon yana da kudin da zai biya mai taxin ba,cikinsu ba wanda yake cewa da danuwansa wani abu sai haidar da mus'ab dake faman kuka,annin ce ke yawan ce musu
"Ku daina kuka,hajar hutawa tayi", bayan mai motar ya saukesu ya buqaci kudinsa,sai a sannan ya tuna baida ko sisi
"kayi haquri bamu da abun biyanka,kayi haquri nayi kuskure daban gaya maka ba tun wuri"
"Babu komai....Allah ya jiqan rai yasa ya huta"daga kai khalipha yayi ya dubeshi,don baizaci jin haka daga bakinsa ba,ya shirya yaji jafa'i da alkaba'i daga bakinsa kaman yadda sauran mutane suke,cikin mamaki ya amsa ya dinga jera masa godiya,dama har yanzu akwai sauran mutane masu imani a duniya?,akwai mutane masu tausayi?
('Yan uwa ku duba halin da khalipha suke ciki,wallahi azim acikin al'ummarmu akwai mutane kwatankwacinsu sunfi dubu,wallahi wallahi muji tsoron Allah,mu tallafi marayu,muji tsoron haduwarmu da ubangiji,muji tsoro randa zamu tashi Allah ya tambayemu ya kayi da haqqin wane maqocinka ko makusancinka mu rasa amsar da zamu bawa ubangijinmu).
*DAURIN BOYE*
45
Haka khalipha yaje masallacin unguwar ya fada,aka hadu aka yiwa hajar sallah aka kaita gidanta na gaskiya,sai a sannan anni tayi kuka,irin kukan da tunda suka shiga wannan halin bata taba yarda tayi gaban yaranta ba saboda karta karya musu gwiwa,daya daga cikin aninda ya hadarwa khalipha kenan ciwon kanshi ya tashi,yayi jinya sosai,Allah ya taqaita musu wahala ya warke ba tare da an dauki dogon lokaci ba.
A wannan karon anni bata yarda ta sake zama haka ba,domin tana tsoron faruwar abinda ya faru a baya,sana'a ta kama wanda duka dai bai wuce wankau ba,abinka da bata saba duk,sanda tayin sai hannunta sun kumbura suyita ciwo,amma gobe haka zata sake yin wani,tun suna kumbura har suka daina,daga bisani ta samu aikatau na shara da wanke wanke a wani gida dake bayansu,aikine mai shegen yawa,duk randa taje ta dawo zaiyi wuya bata kwana sa zazzabi ba sabida yawan aikin da take tilliqa,gashi dama tunda hajar ta rasu bata qara lafiya ba,khalipha shi ya hanata zuwa saboda yanayin lafiyarta,haka ta haqura taci gaba da wankau da sauran sana'o'in hannu.
To tunda hajar ta mutu anni batayi cikakkiyar lafiya ba,sannu sannu sai ciwo itama ya kwantar da ita,hankalin khalipha yayi mugun tashi tamkar zai zauce,yana ganin kamar zasu rasa annin ne kamar yadda suka rasa hajar dinsu,suka shiga sintirin asibiti duk da basu dako sisi,hawan jini ne yayi mata mummunan kamu ya haifar mata da matsalar qoda,wanda tana buqatar ayi mata aiki,wanda indai akayi mata akan lokaci shikenan zata warke sumul kamar bata taba yiba,amma matuqar aka jinkirta tofa la shakka ciwon zai girmama ne ya zame mata wani abu na daban.
Shawara ta qarshe da khalipha ya yankewa kanshi shine su saida gidan da suke ciki abiya maqudan kudaden aikin,tunda yana da yaqinin idan ba hakan sukayi ba saidai annin ta mutu ta barsu kamar yadda hajar tayi.
Akan hanyarsa ta zuwa neman dillalan da zasu sayi gidansu ne ya tsinci jakar kudin daddy har ya zama sila na biyan kudin aikin anni,zuwan ibrahim kuwa da 'yan sanda kawu idris yaji labarin saida gidan ne,so yayi ya qullawa khalipha sharrin da za'a kaishi birsin,shi kuma ya samu damar saida gidan ya kora anni daga ciki.
Bayan samun lafiyar anni khalipha bai fasa saida gidan ba bisa shawarar anni,saboda babban abinda hankalinta ya karkatu akai shine ya samu ya koma karatu,saboda shine gatan duk wani dan adam,Allah ya taimakeshi sukayi masa tayi mai kyau suka karbi kudin,qaramin gida suka sami wanda daki daya ne ciki da falo da bandaki,sai dan mitsitsin tsakar gida suka siya,sai wani dakin a soro,sauran kudin kuwa suka cire wanda zasu fara sana'a dashi sannan ya musu duk wani kai kawon makaranta a ciki,gaba dayansu makarantun gwamnati suka koma,cikin qanqanin lokaci al'amuran suka soma dan daidaita,tunda a qalla suna da abincin da zasuci susha,sun dan sauya suturu ga makaranta sun koma islamiyya da boko,sannan anni na sana'o'inta sosao wanda Allah ya dubi maraicinsu ya soma sawa abun albarka.
Zuwan khalipha makarantar cikin qanqanin lokaci yayi suna yayi fice,sakamakon tarin baiwa da basirar da Allah ya bashi,bugu da qari kuma ya samu background mai kyau don makarantar da yayi a baya duka ba qananun makarantu bane,qoqarinsa har ya wuce tunani,sai aka kaishi ss3 kawai,don sunce da akwai ajin gaba dahaka ma can zasu kaishi.
Bayan ya kammala secondry dinsa yana zaune gida suna qulla yadda zaici gaba da karatunsa katsam saiga kira daga makarantar daya gama,khaliphan yazo ya samu schoolarship,abinda bai taba zata ba ko tsammani koda cikin mafarkinsa,cikin makarantun gwamnati tasa aka bata dalibai bibbiyu masu hazaqa,ba bata lokaci akayi dukkan abinda ya dace khaliphan ya daga yabar qasar.
Koda yaje din sai ya zama dalibi na daban,karatu babu kama hannun yaro,bai zauna acan ba saboda neman kudi daya shiga jikinsa,ya dinga karbar duk aikin daya shigo hannunsa matuqat bai kauce hanya ba yanayi yana turowa annin da kudin,duk da cewa basu da wata matsala a yanzu ta rashin ci sha ko sutura,har wanke wanke khalipha da dafa coffe yayi a gidajen abinci nacan.
Cikin haka wani mai kudi ya saka gasar zane a can qasar,zai gina companynsa yana buqatar a zana masa yadda zai kasance,khalipha nada tarin baiwa ta wannan fannin,kamar wasa ya dawo daga aikin da yake a wani restaurant yaga takardar tallar,bai taba zaton zaici ba ganin yawan mutanen da suka shiga gasar,sai gashi yazo na daya,ya rabauta kuwa da tarin kudade masu dimbin yawa da bai taba mafarkin samunsu ba.
Yana can anni ta hadashi da ruqayya a wayar daya siyawa annin ya aiko mata da ita wadda sai a lokacin Allah yayi dawowarta gida ita da mai gidan nata da yaranta data haifa guda biyu,tayi kuka tayi kuka,tayi baqinciki tayi takaici,tayi Allah wadarao da 'yan uwanta,tayi kewar sa'id da alhinin mutuwarshi kamar ta hadiyi zuciya itama
"Allah sarki yayana makwafin mahaifina,ina can ina jin dadin rayuwa ashe kai ka jima kwance cikin qasa,ubangiji ya gafarta mala,halinka na gari ya bika,Allah yaci gaba da kulama da iyalinka kar ya barsu su tozarta har abada" taso haduwa da khalipha amma Allah baiyi ba harta koma qasar,saidai lambar waya da sukayi musaya ita dashi suke gaisawa,ta tafi tana kewarsu bayan tayi musu alkhairi mai.yawa,cikin 'yan uwanta ba wanda ta waiwaya,haka suka di.ga mata zarya suna zaton samun abun duniya daga gareta,saidai yadda tazo da abinta haka ta koma dashi,abinda sukayiwa zuri'ar sa'id bata jin zata iya baiwa kowa komai nata.
Da wannan kudin ne khalipha ya gina rayuwarshi,ya gina mahaifiyarsa,ya gina 'yan uwanshi,Allah ya albarkacesu ya bude company nashi na kanshi,duk da kamfaninsa bai fasa hulda da wasu kamfanunuwan da yasan sunfi nashi suna ba,bai raina duk wanda ya nemeshi,kafin wani lokaci Allah ya sanyawa dukiyarshi albarka,rayuwarsu tayi kyau,suka manta da duk wata wahala ta rayuwa,fili ya siya mai azabar girma,ya ginawa anni gida na gani a fada,saboda yayi alqawarin dukkan wata wahala data sha a rayuwarta saiya mantar da ita,bazaiyiwu dan adam ya manta sharri ko alkhairi ba,amma tabbas anni ta manta da wata wahala ta rayuwa data sha a baya,haidar da mus'ab kuwa dukkansu saida suka zabi makarantar da sukeso a duk qasar da sukeson yin karatu,ya wadatasu da duk wani abun buqata na rayuwa.
Abu daya ne anni ke fama da khalipha akai danginta na niger,kamar yadda ya gaya mata ne har yau yaqi sakin jiki dasu,duk yadda suke nuna musu qauna da kulawa,yana jin cewa suma suna da tasu gudunmawar da suka bada wajen tabarbarewar rayuwarsu da halin da suka fada,saboda watsar da anni da sukayi da duk lamuranta tunda suka aurar da ita tamkar ba jininsu bace ita,dole daga bisani don babu yadda ya iya ya sauko suke gaisawa da su.
Rahama jikar wannan yayan annin ce,wanda kusan lokaci daya akayi aurensu da anni da babarta,kusan sa'anni suke da khalipha,tunda taga hoton khalipha take mayatar sonshi,saidai shi ko kadan bai taba sonta ba,asali ma cikin dangin nasa baya jin zai iya aurar wata.
Cikin shekara biyu suka zama tamkar basu ba,saika rantse cewa basu taba dadanar zafin talauci ba,Allah ya sanya albarka mai yawa cikin rayuwarsu,ya duba zuciyarsu basu nufin sharri ga kowa,hakanan basu zalunci kowa ba,har lokacin basu manta da hajar ba,shuru shurunta,haqurinta,kawaicinta da yanayin kyawawan dabi'un da take dasu,hakanne ya sanya khalipha ya gina masallatai da.islamiyyu rijiyoyi da borehole borehole duka da sunanta kan Allah yakai mata ladan,hakanan bai manta da mahaifinsa ba,shima yayi gine ginen masallatan juma'a dana kamsusu salawati sadaqatul jariya a gareshi (a nan dan jan hankalin da zanyi ga wadanda Allah yayiwa iyayensu rasuwa kafin suyi arziqi,idan arxiqi yazo musu daga baya suyi qoqarin yin wani abu da Allah zai dinga kaiwa iyayen nasu ladan,koda baka da arziqin gini ko qur'anai ka siya kakai masallaci duk wanda ya karanta Allah zai kai ladan cikin mixanin mamacin,koda qur'ani daya ne,koda rijiya daya ce,koda borehole daya ne,Allah ya jiqan iyayenmu wadanda suka rigamu gidan gaskiya,wadanda ke raye kuma ya qara musu lafiya da nisan kwana mai amfani)
Lokaci guda sunan khalipha ya soma fantsama cikin al'umma,ya soma shuhura tauraruwarsa ta fara haskawa,duk wani mai kudi so yake ya qulla alaqa dashi,duk wani dan kasuwa so yake yayi hurdar kasuwanci dashi,a sannan ne su kawu hamza hankalinsu yadawo kansu,wanda tun bayan rasuwar hajar basu sake ganin gilmawar wani daga cikin iyalin sa'id ba,hakan babu wanda ya nemesu ko ya tambayi ba'asi,ko yabi dalilin shurunsu,sabgar gabansu sukaci gaba dayi,dare daya suka tashi sukaji an fara ambatar sunan khaliphan cikin jaridu gidajen t.v dana redio,nan fa kowa ya kade babbar rigarsa,kowa ya kade tsohon zumunci da suka bunne suna alfahari da dansu ne,suka bazama zuwa gidan khaliphan donsu sabunta kusancin dake tsakaninsu.
Duk wanda yaje gidan a cikinsu saiya jima a qofar gidan yana qarewa gidan kallo cike da mamaki da tambayar kanshi ya akayi khaliphan yayi kudi?,ba shakka ya taka sahun mahaifinsa,babu ko kokwanto arziqi ajininsu yake kenan?,duk cikinsu ba wanda baiyi wannan tunanin ba.
Da fari sanda suka soma zuwa anni qin saurar kowa daga cikinsu tayi,saboda dukkansu ba wanda abinda sukayi musu bai tsaya mata a rai ba,kwantar da kai ban haquri da magiya gami da zirya haka suka dinga yi,daga bisani ita da kanta taga meye riba idan ma ta riqesun?,kafin ita dubu nawa aka yiwa irin haka yau ina suke?,haka ta haqura ta yafe musun.
Duk abin nan da ake khalipha bai qasar yayi tafiya,sanda ya dawo ya taras da abinda ke faruwa ba qaramin tashin hankali yaso yi ba anni ta dakatar dashi,a qarshe ranat bai iya kwana a gidan ba,saboda ganinsu da yayi ba abinda yake tuna masa sai halin da suka jefasu a baya,ba abinda yake tuna masa sai hajar dinsu,ba qaramin daga anni tasha da khalipha ba kafin ya sassauto,duk da haka bai qaunar haduwa dasu kada ma kawu idris yaji labari,domin shi ya sani yanda basu so mahaifinsu ba,basu sosu sanda suna cikin halin ha'ula'i ba,basuso su sanoda duba maraicinsu ba to babu yadda za'ayi a yanzu su sosu fisabilillahi saidon wata manufa.
Ai kuwa ganin sun samu afuwa sai kowa ya soma yunqurin yadda zai samu fada mai girma a wajen,abu na farko da suka soma fafutuka akai shine cusawa khalipha 'ya'yansu ko Allah zaisa ya kamu da soyayyar wata daga ciki ya aura,duk abinda suke kallon takunsu kawai yake,yasan manufar kowa a cikinsu,abun ya sake baiwa khalipha tsoro da mamaki yadda kowa ya koma yana haba haba dashi mahaifiyarsa da 'yan uwansa,kowa so yake ace na hannun daman khalipha ne,kowa 'yarshi yakeso ya bashi,hakanan suma yaran kowacce burinta yace yana sonta,kama daga 'yammatan danginsu dama wadanda bana danginsu ba,kowacce zalamarta ta fito muraran,abinda ya sake tsoratar dashi kenan,yana tsoron ya dauko wadda zata soshi ba don Allah ba,wadda zata zama silar rabuwar kawunanshi shida 'yan uwanshi,wadda zata hana 'yan uwanshi su mori wahalar da suka sha,ta cire duk wata qauna da shaquwa a tsakaninsu,ta cutar masa da mahaifiyarsa shima qarshe ta cutar dashi,dalili kenan daya sanyashi bin hanyar daya bi domin gwajin samun soyayya ta domin Allah.
Qatutuwar ajiyar zuciya khalipha ya sauke yana ci gaba da jan layukan da zuwa yanzu sun qaru kan takardar babu adadi,aysha dake jingine jikin kujera idanunta alumshe hawaye na ratsowa saita rasa abinda zata ce,tsakanin ita dasu khalipha batasan wanda yafi wani fuskantar qalubale matsatsi da wahalar rayuwa ba,batasan wanda yafi wani fuskantar qalubale ba,wacce iriyar rayuwa muke ciki a yanzu?,me yasa zuciyoyinmu babu kyau?,me yasa muka watsar da zumunci muka wulaqanta shi?,muke jin jininmu ahalinmu?,muka fifita mai dukiya akan mara shi?,ashe haka shima ya fuskanci rayuwa?,ashe haka suka sha fama da gwagwarmaya?,zuciyarta karyewa tayi baya ga hawaye sai sautin kukan ya fara fitowa kadan kadan
"Humairahh" ya kira sunanta a tausashe duk da yadda zuciyarsa ke zafi sakamakon tabo wani ciwo da yayi da yake zuciyarsa,saita bude jiqaqqun idanunta akansa ba tare data motsa ba sautin kukanta nason qwacewa,bude mata hannayensa kawai yayi batayi wata wata ba ta isa inda yake ta fada ya maida hannayen nasa ya rufe,kuka sosai ta saki,saiya dinga hadiyar wani abu mai tauri wanda idan ka kalli adam's apple dinsa dake motsawa sama da qasa zaka fuskanci hakan.
46
Misalin sha daya na safe yana tsaye gaban dressing mirrow din dake dakin yana daura agogon hannunshi,yayin da taje zaune daga gefe tayi kyau cikin material doguwar riga da mayafinsa,yatsun hannunta take murxawa,tayi nisa sosai cikin tunani,batasan da wacce fuska zata kalli khalipha ba saboda munana zatonta da tasoyi a gareshi,sai gashi rayuwarsu ita dashi din taso tayi kamanceceniya,anya kuwa zata samu wani kaman khalipha a rayuwarta?,anya kuwa ba dace bane wanzuwarsa cikin rayuwarta,ya fuskanci fiye da abinda takeso ya fuskanta,batajin akwai sauran abinda ya rage kuma,jarumi ne tun quruciya kawo girmansa,zaki ne da yake iya fuskantar duk wani qalubale dake gabanshi,mai qaqqarfar xuciya,kaifin hankali jumuri da juriya.
D'as d'as taji ya murza yatsunsa saitin fuskarta wanda hakan ya sanyata dagowa da hanzari hakan ya tabbatar masa lallai tayi nisa cikin duniyar tunani
"Madam tunanin me kike kuma haka?" Kai ta kada tana fidda qaramin murmushi daya fitar da dimple din fuskarta gami da dauke idanunta daga kanshi,saboda wani kyau da yayi cikin suit din daya tsuke a ciki
"So ya jikin naki?"
"Da sauqi" ta furta da muryar mai sanyi
"Ma sha Allah"
"Sauko muci abinci" sai tadan noqe kadan tana kallonshi,baibi ta kanta ba ya bude komai ya zauna dirshan a qasa yana lanqwashe qafafunsa,sai a sannan ya dubeta da lumsassun idanunsa wanda kullum suke cike da wani irin kwarjini,kasa musa masa tayi,sai ta janyo jiki ta sauko qasan itama tayi irin zaman da yayi,cup biyu ya hada tea ya zuba komai kuma cikin plate daya
"Bismillah" ya furta yana watsa mata kallonshi bayan ya saka chips a bakinsa yana taunawa a hankali,a sanyaye ta sanya hannu ta dauki ruwan tean din ta soma kurba a hankali,nashi cup din ya aje bayan ya zagaye hannayenshi a jikin cup din ya zuba mata idanunshi,yana son yasan dalili ko ya zaluqo abinda ya sanya kulli yaukin yake jin sabbin feelings game da ita,ya sani dai cewa da fari tausayinta ya soma ji,daga bisani sanyinta da yanayinta ya soma yi masa kama dana hajar,a yanzun kuma bazai iya tantance komai ba,baisan dalili ba baisan me yasa ba,bashi da amsar duka tambayoyin dayakewa kanshi.
"Zuwa yanzu ina fata kin gamsu da cewa ba yaudararki koda siffa biyu khalipha yazo miki ba,sannan kin fahimci khalipha shi dinma ba kowan kowa bane,irin rayuwar da kikayi shima ya dan dana ya kuma fuskanci makamanciyarta,ina fata na wanke dukan wani shakku da tarin tambayoyin da kike dashi a kanmu?" Ya qarashe maganar yana qoqarin kallon qwayar idanunta,dan qaramin murmushi mai gajeran zango tayi,saita kasa cewa komai taci gaba da kurbar shayinta
"Kinga na gaya miki gaskiya....koki tashi tsaye ki karbi mijinki ko su qwace miki shi" ya fada cikin idont care manner,ba don kuma hakan bane har zuciyarsa,saidai yayi hakanne saboda ya gwadata,hakanan ta samu faduwar gaba da kalamanshi,tana son ta kalleshi,tana son ta tambayeshi ya dauketa ne amatsayin mata,tana son jin ya canza mata matsayine daga wanka ya bata a baya amma ba zata iya tambayar tashi ba kada ya zaci wani abu.
Cokalin hannunshi ya karkada cikin cup din tangaran din dake hannunshi,wanda shi ya bada sautin daya dawo da hankalinta kanshi
"Daga yau ina buqatar amsar duk wata tambaya ko magana dana miki,shurun kin nan bana buqatarsa alright?"
"Toh" ta furta,sai yaci gaba da kallonta,tayi laushi sosai akan sanda suka taho daga gida da kuzarinta harda tsokanar fada wa rahama,yana ganin tana da buqatar shan iska,saboda haka a take cikin ranshi ya soke tafiyarsu anjima da yayi niyya,saiya buda wayarshi ya tura saqonni sannan.ya rufe ya miqe tsaye yana duba agogon hannunshi.
"Hudu dai dai ki shirya zanzo ki rakani waje waje" tana daga zaune ta daga idanunta har ta kalleshi tana jin faduwar gaban kada dai yace gidan ummi zasu koma,yanayin yadda ta kalleshin sai daya dan sanya bugun zuciyarshi qaruwa,saboda yadda idanun nata suka sake haske da girma
"A dawo lafiya" tace dashi sanda yake fita,ya amsa mata cikin kulawa sannan yaci gaba da takawa har ya fice
Tana kammala sallar la'sar ta isa gaban mudibi ta tsara kwalliya mai kyau da burgewa,tayi kyau cikin atamfa riga da skert wanda kalarta take mai duhu,dalili kenan daya sanya ta sake mata kyau ta haska fatarta mai haske da qyalli,tsaiwa tayi gaban mudubin tana kallon kanta,duk da cewa ranta akwai damuwa amma bai hana kwalliyarta yin kyau da tasiri ba,ita kanta tasan zuwa yanzu ado da kwalliya yabi jikinta,ya zame mata jiki,koda inda zata ko babu ba zaka rasata cikin kwalliya ba.
Tunda ya shigo yake kallonta,komai nata yayi masa kamar tasan ra'ayinsa da tsarinsa game da kwalliya,har ya kammala shiryawa ta tsone masa ido,wannan karon shima cikin shadda ya shirya,cikakkiyar shigar kanawa zam,badai iya sanya sutura ba dama,yana gaba tana binshi a baya zasu fice daga dakin ya juyo cikin wani irin zafin nama,hannunta ya cafka yadan rage tazarar dake tsakaninsu har tana jin saukar numfashinsa,kamar mai rada yace
"Bazan iya daurewa ba,kinyi kyau humairaaah" ya fada saitin kunnenta wanda hakan ya sanya tsigar jikinta tashi,kunya taji ta kamata bugun xuciyarta na daduww,saitayi hanzarin sake ja baya gami da zare hannunta daga nashi,kai ya girgiza mata ya nufarta kamar kuma wanda aka umarta saiya tsaya cak sakamakon tuna wani abu da yayi ya juya ya fice,sai dataga fitarsa sannan ta bishi a baya.
Wata tafiya ce ta alfarma cikin rakiyar motocinsa wanda bata sani ba biyoshi sukayi daga kano ko dama yana da wasu a nan lagos,tafiya suka yi mai dan dama kafin su iso bakin wani beach,wajene mai kyau da tsari,tun daga saukarsu ya burgeta,tana zaune a mota sai da yayi mata magana sannan ta fito,su biyu suka dinga takawa suna zagayawa bakin wajen,wanda daga qarshe suka qare a boat,su biyu ya biyawa saboda haka iyasu ya dauka,ya biya dukka awannin da zasu kashe cikin ruwan.
Iskar dake tasowa daga cikin ruwan mai dadi ce da kuma wani irin sanyi mai armashi,idanunta ta lumshe tana sheqar iskar har cikin zuciyarta take sauka da sanyinta tana wanke duk wata damuwa da qunci da yayi saura a ciki,wani lokaci idan wani jirgin yazo giftasu fallatsin ruwan kan tashi har kan fuskarta saboda tana daga gaba gaba,har lokacin idanunta na lumshe sanyin ruwa yayi mata yadda takeso,murmushi ta saki sanda ta tuno wani scene data gani cikin film din da khalipha ya dage sai ya tayata gani,yadda masoyan ciki suka gabatar da wata zazzafar soyayya cikin jirgin ruwa,saita fara imagination wanda ya sanya murmushinta fadada.
Jin kaman ana shirin rungumota ta baya ya sanyata saurin waiwayawa,khalipha ne tsaye hannayensa goye a bayansa yana kallonta,ya bude baki zaiyi magana wayarta ta dauki tsuwwa,saita juya tana dubawa,aliyace ke kira,latsawa tayi ta kara a kunnenta,dai dai sanda a sake jin ya matso gab da ita fiye da da,don a yanzun ko qwaqwqwaran motsi tayi zata iya fadawa jikinsa,hakan yasa ta hadu tsam ta hada hankalinta waje guda,saidai hakan bata samu ba,don duk yayin da ruwan yayi wasa da jirgin saita gogi jikinsa,hakanne ya sanya ta danna handsfree ba tare data sani ba
"Bakya jina?" Tajiyo muryar nan ta aliya
"Ina jinki sashen,ya gida yasu mama"
"Lafiya lau sashen,na shiga ta wajenku na tadda baku nan,tace min kunyi lagos?,hala amarci aka tafi shahh hh...." Ta qarashe maganar da sigar zolaya tana bayyananniyar dariya,kunya ce ta kama aysha,saurin katse aliyan tayi,duk da tasan idan aliya ce tayi ta banza saita gama amayar da abinda ke cikinta
"Banason iskanci aliya meye haka ne?" Dariya ta sake yi
"Au na manta fa yayanki ne ko?,to ai ba laifi yayanma ai girma ne,amma dai abi a hankali kada komawa wudil ya gagara"
"Dama abinda kika kirani ki gayan kenan aliya koko me?" Ta fada tana dan hade rai kaman tana gabanta,don ji take kamar ya jefa wayar cikin ruwan dake gabanta tsabar kunyar da aliya ke bata,gashi tana iya jiyo yadda khaliphan ke turo kai da alama kunnensa yakeso yaji abinda aliyan ke fada sosai,dariya ke taso masa yana danneta ganin yadda mode din ayshan ya sauya,bai manta abinda mahmoud ya gaya masa ba kusan hakan yace mishi ana ya gobe zasu tafi,da alama bakinsu daya
"To aini kaman qarar ruwa nakeji,ciki kuka kwana ne?"
"Sai anjima,ki gaida mama da kyau" aysha ta fada tana shiriin katse kiran
"Ayyah sashen kiyi haquri,nikam kira nayi na baki saqo wajen boss....abokinshin nan wallahi ya fiya matsa lamba da yawa"
"Zan gaya masa,ki gaida mama bana ji sosai" ta fada tana katsewa saboda kada aliyan ta baarota,don tasan kadan daga aikinta ta fadi maganarta,kuma ita babu ruwanta ita zata bari da jin kunya.
"Mu haka muke,bama kama abu da wasa,idan muka soma sai mun cimma gaci,jarumtarmu a nan take" ya fada yana nuna saitin zuciyarshi da yatsa,saita zame jikinta dake tsakanin qarfen jirgin da khalipha daya katangeta ta baya,kamar hadin bakintana tsaka da takwa don barin wajen kiran hanan ya shigo,shima tana zaune kan wani dan tebur da aka ajiye musu coffe da kayan motsa baki zata soma amsawa taji an zare wayar daga hannunta,handsfree ya maidata sannan ya aje saman teburin ya zagaya kujerar dake fuskantarta ya zauna bayan ya harde hannu ya zuba mata idanunshi,hakanan ta dake ta soma amsawa
"Anya lafiya ko ayshat,kodai wani ya riqe mana ke ne?" Idanunta dan fiddo
"Haba mana hanan,kada muyi haka dake mana ya zaki fadi haka" dariya ta sanya cikin nishadi
"Ah to ni na sani,kinsan soyayya ba abinda bata haifarwa,sauyawar hali da tsarin rayuwa na lokaci guda....wai da hakan zata faru kuwa da nafi kowa murna"
"Me yake faruwa a makaranta?"
"Labiba ta shigo dazu nemanki,tace jibi kuna da C.A" idanu ta zaro don shaf ta mance labiban ta gaya mata dr mahadi ya fadi cewa zaiyi CA din cikin sati duk da bai tsaida rana ba
"Ya salam,ina hanya in sha Allahu"
"To Allah ya kawoki lafiya,kinga matar nan ma tabi mijinta taje tayi bulunbuqui da ita" tasan sarai da maman hunaifa take
"Ba ruwana,maman hunaifa ta waje na ce"
"Hademin kai zakuyi kenan?,zaki dawo ki sameni" ta fada tana dariya dariya da haka sukai sallama.
Cikin narkewar da batasan tayi ba ta langwabar da kai tana duban khalipha,kallon data masa sai ya zama kamar da manufa tayi,gaba daya ya kashewa khalipha jiki,yasan me takeson cewa makarantarta,da qyar ya bude bakinsa yace
"Baki da damuwa".
Sun jima kafin subar nan,daga nan dinma wani wajen suka qara nufa,sai da sukaje waje uku kafin su koma hotel.
Washegari da daddare ma ya sake daukarta suka fita,wani katafaren shago dake saida tufafi irin na igbo da yoruba ta rakashi,sai ya nade hannu yace ta zabi duk abinda taga ya dace,ga zatonta yana nufin shi zata zabarwa,haka tayi ta maza ta zaba mishi kaya masu kyau da quality,harshi kansa mai shagon ma mamakin tasan kan kayanne?,murmushi kawai tayi,inda daga qarshe ta daukawa anni wasu kaya da suka burgeta sosai,dubanta kawai yayi baiga abinda ta dauka ba,saiya karbi accnt num din wajen ya musu transfer fiye da kudin siyayyarsu,tana gaba yana biye da ita a baya,ya bude mata murfinm motar cikin jin nauyin yadda yake matan ta shiga ta zauna,don ko yaranshi bai bari su bude matan shi da kanshi yake hakan,sai daya rufe murfin motar sannan ya koma cikin shagon.
Tsahon mintina goma cikakku aka sake kawo wata ledar sannan ya shiga aka tada motar suka bar wajen.
Nesa dashi kadan ta kwanta,saboda tana tuna yadda suka kwana jiya,batasan yadda akayi ta kwana a jikinsa ba,saida suka tashi sallar asuba sannan ta ganta cikin jikinsa kanta kwance saman qirjinsa,hakanan shima ya shirya yana dan dubanta,gefe daya shima ya kwanta idanunsa lumshe,yana tuna baccin da sukayi mai nauyi jiya wanda ya jima rabonshi da bacci mai nauyi irinsa,da haka bacci ya kwashesu.
Qarfe sha daya na safe suna tsaye cikin airphort,aysha na gefan khalipha,tayi kyau cikin baqar abaya,kusan shigar baqi tayi komai nata har gilashin fuskarta,wanda hakan ya sake bayyana kyau da hasken fatarta,kota ina khalipha gani yake kamar kowa ma kallonta yake saboda kyan data yi masa,dalili kenan daya sanya yaranshi suka karesu a dabarance ta yadda ayshan ba zata fuskanci me yake nufi ba,daidai lokacin da asma'u itama ke tsaye cikin tashin hankali suna sa'insa da daya daga cikin ma'aikatan wajen,kano takeson komawa a yau amma ana gaya mata cewa ticket ya qare,tana jin kuma ya zama dole ta koma a yau din,sakamakon kayanta da abba ya auno mata daga china donta fara business da suka zo,tazo clearance amma tag number dinta ya fadi,kuma ta tabbatar koda kayanta zasu fitan sai taci wuya,shi yasa take gaggawar komawa ta sanar da abba,don ta saka rai da kayan,hakanan ta gama bazawa qawaye da sauran jama'a,kada mu su rainata su dauka qarya take.
Ganin da gaske suke saidai ta bi jirgin gobe ya sanyata cikin bacin rai da qunaquni ta soma takawa zata bar wajen,duk abinda ke faruwa khalipha na ankare,gab da zata gotasu ya dan taka kadan ya matsa inda zata iya ganinshi
"Mrs dan gote" ya fadi hannayensa harde a qirjinsa kamar yadda yake al'adarsa ce,waiwayowa tayi taga wace matar dan goten,sai suka hada ido da khalipha,ta fuskanci da ita yake don ita yake kallo yana murmushi,gabanta ya fadi,kwarjininsa suka cikata,wani kyau taga ya qara mata fiye da yadda ta sanshi a baya
"Ki nemi taimako wajen madam,kamar akwai kujera daya data rage sai tasa a baki kawai" ya fada cikin idont care tune,hararashi taso yi saboda wani takaici daya taso mata,kamar ita zata nemi taimako wajen aysha Allah ya sawwaqe,aisai ta rainata ma,har abada bata jin zata iya yin hakan,sai kawai ta soma takawa zata bar wajen,dai dai sanda idanunta ya hango mata aysha dake zaune idanunta kan wayarta,gabanta ne ya fadi ta tsura mata ido tana kallonta kafin daga bisani ta dauke kai ta wuce,tana fita ta kira abba,saidai ya gaya mata zaiyi iyakar iyawarsa,baida mutane a wajen amma zai gwada,kashe wayar kawai tayi cikin bacin rai,asara ce tasan zasu tafka ta koda kayan sun fito,bata da wani babba data sani da zai shige mata gaba saidai abban,kuma shima yadda yake mata bayani kamar abun zaija lokaci.
Zuciyarta ta bata shawarar ta koma wajen khalipha,to amma itakam gaskiya bata son tayi abinda mutuncinta zai zube,don haka sai ta koma can wani waje da zata iya hangosu,idanunta na gano mata aysha,ta dubi securityn dake tare dasu,haushi da baqinciki gami da takaici ya dinga sakko mata,ba shakka aysha ba itace ta cancanci wannan matsayin ba,ita asma'u ita ta dace dashi,ayshan da batasan dadin komai ba,batasan wani gata ba,bata san so ko qiyayya ba,bata damu da komai ita ta samu wannan bigiren daya kamata ace ita ke ciki?,aysha da masu irin hamid suka dace,ya akayi ma wai ta hadasu ne da khalipha?,ya akayi bata qyaleta ta zabi wani daban da kanta ba,anya ma ba ta san cewa waye ainihin khalipha ba?,anya ba bincike tayi a kansa ba shi yasa tayi laqwas ta qyale har akayi auren?.
Tana zaune tana karanta wannan wasiqar jakin har lokaci ya fara nisa,ta duba agogon wayarta,ba shakka.nan da wasu mintuna jirgin da zai nufi kano zai tashi
"Kije kawai asma'u,ai itama tasan kinfi qarfin roqar duk wani abu daga gareta,koda kin roqa dinma aiku kuka fara mata alfarma kafin tayi muku,banda ku da tunu yanzu qila tana can cikin wani mawuyacin halin da ba'asan ma wanne iri bane,kai gaba daya ma auren nata ai kece silarshi,da wannan shawarar da zuciyarta ta bata ta miqe ta doshi inda aysha ke zaune khalipha na dan tsaye daga bayanta yana amsa waya,bayan ya gama ya tsaya siyen ticket qwaya daya daya rage ta internet.
Tana gab da isowa wajen aysha ta daga kanta saboda gajiya da tayi da danna wayar,tayi haka ne saboda nauyin kallon da khalipha ke binta dashi,sam baya jin kunyar ma yaranshi dake tsaye a wajen,murmushi ta jefi asma'un dashi cikin fara'a tace
"Ah,anty asma'u?,kema kin shigo legos kenan?,hala keda ya hamid ne?ku bata wuri sisterna ce" tayi magana dasu wanda ada basu da niyyar matsawa,fuska a dinke ta qaraso wajen,sai taji kaman ayshan tana sane da tace tare da hamid suke magana ta gaya mata a fakaice
"Zuwa nayi na tafi da kayana da nayi order daga china,so an samu dan minor problem kuma hamid bai qasar bare yayi magana a sakar min,so ban sani ba ko mijinki nada wanda zaima magana akan hakan saboda yau nakeson komawa gida"murmushi ta saki ganin yadda take magana kai tsaye cikin isa isa,amma kona komai tasan ta isa dinne shi yasa harta tako ta nemi alfarma a wajenta,tasan halin asma'un tsaf ciki da bai,ba kowane zata nemi alfarma a wajensa ba saboda tsabar jin kanta da takeyi
"shikenan minti daya" ta fada tana miqewa,a hankali take takawa inda khaliphan ke tsaye yana danne danne da waya ahannunsa,yayin da asma'un ta bita da kallo tana qarewa shigarta kallo,ko hasidin iza hasada yaga aysha yasan ta canza,yanzu classic aysha ce,ba irin ayshan daka sani a baya ba,gefanshi ta qaraso wanda kaman yana ankare dama da tahowarta din yana jin tsaiwarta ya waiwayo yana dubanta bayan ya zuba mata dukkan idanunshi da sukayi mata nauyi,batasan me yasa yake tasiri haka a kanta ba,saita dan sadda kai
"Asma'un kika zo nemawa alfarma?" Ya tambayeta ta wata irin siga da bata gane meye cikin ranshi ba,bata ankara ba taji ya saqalo hannunta cikin nashi cikin wani salo ya soma takawa tilas tabishi.
Gaban asma'un suka tsaya sannan ya soma magana cikin muryarshi mai cike da izza da kwarjini
"Kin nemi alfarma but bata hanyar data kamata ba,yanayin yadda kika yi mata magana baiyimin ba,baya ga haka ma banajin yaron oga zai iya komai akan hakan,dadai ogan nashi yana nan wataqila saiya roqa miki shi,ko kawai ta jirayi dawowar mai gidan nata,may be ma he can do morethan i can" daga kai aysha tayi da sauri tana kwabe fuska tana dubanshi tana girgiza kai,sai yaga tayi mishi kyau sosai,girarshi ya dage mata alamin baiga wani kuskure da yayi ba,yatsansa ya saka yadan taba girarta data tattareta waje daya can qasa yace
"You r beautiful" sai ta saki fuskar tata daga tattaretan da tayi ta koma yi masa kallon mamaki,tuni asma'u dake zaune wani abu ya yunquro mata,sun wani tsaya gabanta suna mata soyayya sai kace kansu aka saukar da wahayinta,dadin abun tun kafin ayi d'aran akai kwand'i,yaushe ma suka fara son junansun,taso ta miqe tabar wajen bayan ta gaggaya musu magana saidai kuma ta tabbatar idan tayi hakan ta barar da damarta,tasan da biyu khalipha ke gaya mata magana saboda babu kalar wulaqancin da itama bata yi masa ba.
Murya can qasa kamar mai rada aysha tayi masa magana don batason asma'u taji
"Kayi mata wannan alfarmar domin girman Allah" wata kasala sosai sautin furucinta ya haifar masa dashi,wanda hakan ya sanyashi lumshe idanunsa ya bude duka lokaci guda
"Taci darajar aisha" kunya taji tadan kamata saita basar,wayarshi ya ciro
"Morning boss" daga daya bangaren kakkaurar muryar ta cika wayar khaliphan
"Morning ahmad mun tashi lpy"
"Lpy lau boss....boss kayi wuyar gani,koda yake manya dama haka kuke irinmu saida haquri kafin mu samu ganinku" murmushi khaliphan ya dan fidda mai sauti
"Kullum qorafinka kenan,bayan daka tashi nemana kasan yadda za'ayi ka hadu dani ai.....ba wannan ba,akwai wata yarinya.....ya sunanta ma yake?" Ya qarashe da low tune yana duban aysha da alama tambayarta yake ta gaya mishi,kunya ta sauko ta rufe ayshan,yana nufin yace ya manata sunan asma'un?,saita gaya masa kawai tana dakewa,bata yarda ta dubi asma'un ba ta share kawai,bayani ya masa bai qarasa bama ahmad din ya tsaidashi kan cewa ba matsala,yanzu za'a duba kayan nata ai tafi qarfin komai,dai dai sanda ya qare wayar lokacin tashinsu yaui,saboda haka ya maida wayar aljihunsa yana cewa
"Saiki gaya mata ta wuce ta tafi gida....mtsweeww,kome mijinta keyi oho" taji duk abinda ya fada,duk yadda ranta yakai ga baci haka ta hadiye,don a yadda ta karanci khaliphan tsaf zai fasa abinda yayi niyya,wanda hakan yana dai dai da tayi asara ne kota jira har daddy yayi mata cuku cuku,hakanan ta miqe tabi bayansu
47
_ga full 47 nan nayi editing na qara yawanshi,banson numbers din littafin yayi yawa,idan na samu damar qara wani anjima zaku jini in sha Allahu_
Cikin jirgin ma daga kujerarsa saita aysha,hakan ya bashi damar samun kusanci sosai da ita,yayin da asma'u ke zaune can baya,duk wani motsinsu idanunta na kai,yana sane yake sake narkewa ayshan,yayin da kunya ta cikata,gaba daya khaliphan ya canza tun daga zuwansu legos zuwa yau.
Baqinciki ne cike a qirjin asma'u yayin da take kallonsu,kota ina khalipha ya yagawa hamid,koda can dinma tana sane da hakan,kawai rashin kudi da bata taba zaton khalipha nada shiba shinya janyo mata komai,ga dukkan alamu sun nuna babu wata matsala tattare da ayshan,ko waye kai ka kalleta kasan bata da damuwa,sai taja numfashi ta kuma fito dashi zuciyarta na ayyana mata abubuwa da yawa,zuwa yanzu ta soma gajiya da zama da hamid din,babu wata alama dake nuna zai sauya,kai babu ma batun sauyi saima sake tabarbarewa da al'amura sukayi,baya ga shegen maqonsa,rashin sanin darajar aure da iyali,sai kuma ta gano wata mummunar dabi'a data fi komai daga mata hankali,wato hamid yana neman mata,matan ma ya rasa wadda zai nema sai 'yar aikinta kafira ba musulma bama,sannan a yanzu haka yarinyar na cikin gidan duk data kamasu amma ya murje idonsa yace karta soma kuskuren korarta,tana ji tana gani ta barsu,Allah ya sani tana son hamid,saidai maganar gaskiya ba zata iya rayuwar takura da mammaqo ba,abu na farko daya sanya ta guji duk wani saurayi a baya data fuskanci babu dandalen arziqi tattare da shi,tunin daya soma konno mata kai ta dinga wassafa da kimanta yiwuwar faruwarsa,zai yiwu kuwa?.
Da wannan tunanin har jirginsu ya iso kano bata sani ba,koda suka fito daga airphort din sai tadan qara sauri ta cimmusu
"Na gode khalipha sosai,Allah ya qara arziqi" ta fada cikin murmushi,cikin mamaki suka dubeta,khalipha shi ya soma kauda kai,ya kama hannun aysha sukayi gaba sannan yace
"Ba donke nayi ba ai,albarkacin princess humaira kika ci" sosai maganar ta daketa,amma saita share ta sake takawa ta cimmasu
"Ko zaka sakamin number dinka don Allah,bai kamata ace bama zumunci ba,abinda ya faru ya riga daya faru insha Allah kuma bazai sake faruwa ba" murmushi yaso.ya subuce masa saboda kalaman rainin hankalin asma'u,sai ya saka hannu ya amshi wayarta da take miqo masa,har ta soma murna taji yace
"Riqe maza don Allah,da wannan wayar kike amfani?" Saita kada kai tana sakin murmushi
"Kiyi qoqarin canza wata don Allah,saura kadan ta jimin ciwo....muje princess" ya fada yana sake riqe ayshan da kyau,binsu kawai tayi da kallo baki bude,wato bai manta duk wani abu data taba yi masa kenan ba?,anya wannan tafiyar zata zama da sauqi kuwa?.
Aysha kam rasa bakin magana tayi,sauyawar asma'u lokaci guda?.....sauyawar asma'un ba abu bane mai sauqi ta santa sarai,wala'alla tana kwadayin abota dasu ne kamar yadda halayyarta take nason abota da suk wani mai kudi,dason ace tana da kusanci dashi ko kuma ta sanshi.
Sanda suka isa gida ta tsammaci zasu shiga sashen anni ne dafarko,sai taga yayi fuska ya kara wayarshi a kunne
"Anni mun iso,amma zamu dan huta kafin mu shigo....ohk" ya fada yana sauke wayar,hada ido sukayi saiya dan basar yana cewa
"Bana son in shiga na soma karo da fuskar wadan can yaran,don haidar ya gayamin maryam ma tazo,so daga yau babu zaman cin abinci a cikinsu" ya fada sanda suka shiga falon.
Qarfe takwas na dare tana zaune gaban annin cikin ado da qamshi ta nannade jikinta da farar laffaya kamar amaryar da aka kawo yau,shigowarta kenan sashen shima gajiya tayi da laqai laqai din khalipha ta gudo yana wanka donta qagu tazo taga annin,nasiha take mata mai kwantar da hankali kan yanayin haduwarta da mahaifiyarta,ta kuma bata shawarar ci gaba da addu'a,sosai duk wani qunci na zuciyarta ya zabge tun a lagos,kukawar data samu wajen khalipha ba qarama bace,taa zauna taayi nazari sosai tun a can,har ta dinga jin kamar tayi aiki da shawarar basma,saidai mahaifiya tafi gaban wasa.
Daganan wata hirar daban suka shiga yi da annin,aysha ta dubi dakin annin sai taga duka baiyi mata yadda takeso ba
"Anni...dakinki kwana biyu yayi kewata gaskiya" murmushi ta sako cikin jin dadi
"Ba dakin kadai ba har masu gidan,haidar cewa yake yayi zaton kwana daya ko biyu xakuyi sai kuka wuce haka" dariya ayshan tayi,kafin tace wani abu akayi knociking qofar dakin anni ta bada izinin shigowa,matashiya ce wadda a qalla ta kusa sa'ar rahama,ta qaraso dakin idonta akan aysha,da qyar take magaba kana kallonta kasan irin yaran nan ne da sakalci da tabara yayi musu yawa,bawai rashin wayo ko dolanci ba alamun rashin kwab'a tun daga quruciya.
Tana magana da anni amma idanunta qir kan aysha lanqwasa yatsunta,hada ido sukayi da ayshan saboda tsabar kallon da take mata yasa taji a jikinta
"Sannu" ayshan tace mata ganin sum hada ido,duk da a qa'ida itace zata soma mata.magana a matsayinta na wadda tazo ta samesu kamar yadda annabi ya koyar
"Yauwa sannunki" ta maida mata tana dauke kai ganin ayshan ta gane kallon qurillar da take mata
"Ya khalipha ya dawo ko?,naga kamar motocinsa"
"Eh ga matarsa nan aishatu sunanmu daya" duban ayshan ta sakeyi sannan ta dauke kai sai kuma tayi shuru.
"Yaushe zaki koma makaranta ne?,kamar kuna tsakiyar karatu ne ko?" Anni ta yanke shurun tana tambayar aysha,dan murmushi tayi
"Gobe...gobe in sha Allah,saboda muna da c.a goben da azahar"
"Batayi candy bane?" Maryam ta tambaya tana duban anni cikin salon dake nuna raini qarara
"A'ah,masters take hadawa" sai ta dan sake kallon ayshan again sannan ta dauke kai tana cewa
"K'nnnnn" a yadda taga shekarun ayshan tayi tsammanin ko degree na farko batayi ba bare aje ga masters,saboda ita gatanan har yanzu degree din taqi haduwa saboda wasa da sakarci data saka a gaba.
Lokacin cin abincin yayi don haka tare suka sauko gaba dayansu,basu kai ga wajen dining ba khalipha ya shigo falon,yayi kyau cikin fararen qananun kaya long sleev shirt da trouser shima fari,idanunshi kan aysha,saidai a dakenshi ya shigo saboda yasan wadanda zai taras a wajen,dan satar kallonshi tayi kadan,ita kanta saiya mata kwarjini ya cika mata ido,hakanan yayi mata kyau sosai,gaidashi sukayi ya karba a dake yana basarwa,fasa hawa dining din anni tayi ta dawo ta zauna a falon tana maraba da khaliphan,saboda haka mutum uku ne a wajen,rahama,maryam da amal,kowacce kanta na fisga tana cin abincinta ba tare data dubi 'yar uwarta ba,saidai dukkansu kunnensu na wajensu anni.
Nan tasa a kawo mata abincinta,hakan yayi masa sosai,tana ci suna hira,shi da ayshan dukkansu ba wani yunwa suke ji ba,don basu jima da shiga ba tayi musu girki suka ci,wanda ya jima baiji dadin cin abinci irin na yau ba.
Haidar ne da mus'ab suka shigo falon suna tafe suna musu da alama wani abu suka gani,harararsu khalipha yayi
"Hala bakusan muhimmancin sallama bako da zaku shigo da surutu a bakunanku" dukkansu basu san ya dawo din ba da basuyi wannan katobarar ba,shafa kai mus'ab ya soma,yayin da haidar yace
"Afwa yaya,mantuwa"
"Next time.." Bai qarasa ba yayi shuru suma kuma sun fuskanci me take nufi gargadine saboda haka suka ce
"In sha Allah" haidar ne ya qarasa gefan aysha yana murmushi
"Shuru anty kunyi tafiyarku?"
"Ai gashi mun dawo ya haidar"
"Gwara kam don wallahi ba qaramin missing dinki mukayi ba,duk gidan dadinsa sai a hankali" ya fada yana murmushi,dubanshi khalipha yayi,wani abu yadan taba ranshi
"Duk mutanen dake cikin gidan ba mutane bane sai ita kadai?"
"Ba haka bane yaya,antyn ...."
"Ohk idan ta wuce makaranta gobe saika bar gidan"
"Da sauri haka daga dawowarku?"murmushi kawai aysha tayi,sai ya juya yana tambayar anni me aka dafa
" jeka ka gani" ganin wadanda ke kan dining din yasashi dukan kafadar mus'ab
"Dalla jeka debo mana abinci,wadancan 'yan zaman dumama kujerar sun wani cike wajen,haka zaka je kana cin abinci suna qarema bakinka kallo kamar wasu mayu", can qasan ranta aysha tayi murmushi,a yanzu ta riga data san me yasa haidar din ke yawan mita akai,a baya mamaki take kan me yasa sam ba hadauwar jini tsakaninsu,ba shakka ma badon uwa ta gari da Allah ya basu ba zuwa yanzu ko kusantarsu dangin ubansu basu isa suyi ba,saidai uwa ta gari da Allah ya basu ya santa zakayi zaton komai bai faru ba,mus'ab na girmama haidar kamar yadda haidar ke bawa khalipha girma,yana game a wayarshi ya isa wajen yaja plate ya zubo musu ya sauko dashi,da yake sau tari sukanci abinci kwano daya idan lokacin cin nasu yazo dai dai,annin ta riga ta saba musu da haka tun lokacin quruciya.
Da d'ai d'ai amal da rahama suka dawo wajen bayan sun gama cin abincinsu,banda maryam data wuce daki tana amsa waya
"Tashi mu wuce" khalipha ya fada bayan ya miqe tsaye
"Tun yanzu?dare baiyi ba da yawa" Rahama ta tambaya idanunta na kansu
"Mun dawo daga tafiya akwai gajiya da take buqatar a wareta" khaliphan ya fada yana hade fuska kamar ya manta anni na wajen,aysha kaman ta zura da gudu haka taji saitaja mayafinta ta sake rufe kanta
"Anni sai da safe"
"Allah ya bamu alkhairi,mu tashi lafiya ayshatu"
"To anni" haka kawai taji kallon da suke binta dashi bai mata ba,tana sane tace
"Anty rahama,sister amal saida safe.....kinsan ya khalipha da son jiki tausa yace yana so" aysha ta fada can qasa saitin rahama wanda tafi kusa da ita,ta yanda idan ba rahaman da amal dake kusa da itaba babu maijin abinda tace,saidai ta makaro,tuni khalipha dake tsaye ya jiyo abinda ta fada din,wato itama ta iya tsokana kenan da cusa haushi ko?,dukkansu zuciyoyinsu kamar zasu fito,basu sake magana ba har suka ida fita daga
Shi ya fara shiga sashen,ya fada saman kujera ya ware hannayensa kan makarin kujerar yana dubanta sanda take shigowa,gab da zata wuceshi ya sanya mata qafa take ta harde tayo kanshi gaba daya,hannunshi yasa ya tallafeta cikin jikinsa
"Me zaki wuce ciki kiyi?,kefa kika ce tausa zaki yimin ko?" Cikin mutsu mutsu ta girgixa kanta tana son qwatar kanta saboda riqon tsauri da yayi mata
"Ohk,yanxu kuma don kinga babu idanunsu zaki canza magana kenan?"
"Kai ka sani na dinga musu haka"boyayyen murmushi ya saki
"Over act kikayi,tunda kuma kika sakamin rai saikin yi,dama am too tired" dage mata yayi kan sai tayi masa idan ba haka ba shi zaiyi mata,da qyar ta kubuta bayan data fake masa da bata karanta komai ba,bedroom ta gudu,ta jima zaune a can sai data dai daita mode dinta sannan ta fito,kanta na a qasa tace
"System dina pls ta rannan..."
"Wadda na kamaki kina kallon fina finan soyayya?" Ya tambayeta ba tare daya dubeta ba,saita kasa amsa mishi
"Nayi seezing,bana so ki sake amfani da ita" mamaki ne ya kamata,me tayi da zai mata seeizing na system?,itakam bata sani ba,saidai koma meye yafi gaban haka saboda haka batace komai ba kawai ta juya ta samu wani guri can daban ta xauna tana duba abinda ya kamata ta karanta.
Sha biyu saura na dare ta tura qofar bedroom din,ga mamakinta saita sameshi zaune dirshan saman gadon da system a gabanshi,tayi tsammani yayi bacci ne,taqi shigowa da wuri don kada abinda ya faru jiya wanda batasan ya akayi ya faru ba ya sake maimaituwa,ta farka ne kawai ta ganta cikin jikinshi,wanda kuma da alama itace ta baro side dinta ta dawo nashi.
A hankali take takowa har zuwa bakin gadon,ba abinda zata yi sai kwanciya kawai,don haka ta aje litafanta kan bedside din dake daura da ita,ta zauna a side dinta ta hada tafukan hannunta ta soma addu'ar kwanciya bacci,bayan ta gama ta hura ta shafe jikinta sannan ta maida duka qafafunta saman gadon,gyaran murya taji yayi wanda ya danja hankalinta,saidai bata juyo ta dubeshi ba
"Bacci zakiyi?" Ya tambayeta yana ci gaba da aikinshi,kanta ta gyada sannan tace
"Eh"
"Gobe zaki koma,hira ya kamata muyi" ya furta a dake kaman bashi yayi maganar ba,dan boyayyen murmushi ta saki
"Cikin wannan satin nima zan koma so ba lallai mu sake haduwa kafin sannan din" ya kuma yin maganar yana kashe system din,rasa amsar sa zata bashi ya sanyata yin shuru,bai sake cewa komai ba shima sai daya kammala komai ya dauke daga wajen sannan ya jingina bayanshi sosai da fuskar gadon bayan ya kara pillow
"Dame dame kike da buqatar tafiya dashi?"
"Babu komai,ina da komai" ta fada cikin sanyin muryarta data bada wani amo da salo ma daban saboda shurun dare da yanayin duhu duhun dakin,wanda hasken wayarshi daya haske fuskarshi mai saye da gilashin qarawa ido gani ya haska fuskarshi sosai,dan yatsanshi ya saka ya gyara glass din sosai sannan yace
"Come closer" daga kanta tayi ta dubeshi,yanzun ma kamar bashi ne yayi maganar ba hankalinsa nakan wayarshi,tsahon sakan goma kafin ta matsa kadan ta rage tazarar dake tsakaninsu ba mai yawa ba can,pillow din dake gefanshi ya dauko ya maida side din da take sannan ya nuna mata inda yake nufi da yatsa ba tare da yace komai ba,a hankali ta zauna inda yace din,tana gab dashi don tana iya jiyo fitar numfashinsa,wanzuwar pillow din a wajen kawai shiya hana cinyoyinsu gogar juba,wayar hannunshi yayi mata nuni da ita saita maida kallonta kai,tana kallonshi ya tafa (www.rahamalls.com) ya shiga,ba dadewa link din ya bude,jerin kayan da store din na rahamalls suke saidawa ya bude,kaya ne babu wanda babu a kai,yaci gaba da dubawa har yazo bangaren computers
"Dubamin...wacce ce tafi kyau?" Ya fada yana scrolling down,da ido ta dinga bin hotunan system din tana kallo,dukka bata banxa ba wadda batayi kyau ba,dai dai kan wata ash tace
"Irinta maman hunaifa...."sai kuma tadan kame bakinta batasan cewa a fili ta fada ba
"ohkey"ya fada yana shiga page din gaba wanda dinkakkun kayan maza suka bayyana,yayi order din wanda zaiyi ya kashe data dinsa,har a lokacin tana zaune a wajen
"bayan na tafi?,me zaki dinga tunawa dani?" So take ta daga kanta ta kalleshi tada da wanne yanayi yayi maganar,amma nauyi da kwarjinin idanunsa dake bisa kanta sun hanata dagowa,a sanyaye tace
"Babu"
"Ni kuma akwai" ya fada kana yayi shuru yana ci gaba da dubanta,batasan sanda ta furta lafazin
"Mene shi?"
"Yanzu nake so ki barmin abu daya da idan na tuna zaici gaba da debemin kewa duk tsahon lokaci" hannunshi ya miqa mata sannan ya kafeta da idanunshi sai ta dan tsaya tana kallon hannun nashi,ya qagu yaji dumin jikinta mai dadi,tunda ya taba dandanashi sau daya har yau feelings din yaqi barin jiki da qwaqwalwarsa.
A hankali ta dora tafin hannun nata itama saman nashi kamar yadda ya buqata,sosai ya rintse hannun kafin ya jawota ta fada jikinsa yasa hannayensa ya rufeta ruf yans jin dumi gami da shaqar daddad'an qamshin turarenta dake tashi a jikinta,dukkaninsu kowanne yana iya jiyo bugun zuciyar kowa,ba wanda yake wani qwaqwwaran motsi a cikinsu kowa yayi luf jikin dan uwanshi.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
A kunyace take hada dan abinda tasan tana buqata wanda dashi zata tafi wudil,ta rasa me ya fisgeta jiya har ta amsa tayin khalipha,duk inda yabi saita kaicewa ganinsa,har ya kammala uzurinsa cikin dakin ya rigata fita,batasan meye manufarshi ba akanta shima me yake nufi?,abu guda ta sani har sukayi aure suna kallon juna ne a matsayin wa qanwa.
Riga da skert ne a tamfa a jikinta,qafarta plat takalmi ne mai igiya wanda mahadi ne da jakar hannunta mai azabar kyau da tsari,hijani ta sanya mai hannu iya gwiwa,wanda yake hade da niqab,saita saka glass din da kanyi amfani dashi lokaci zuwa lokaci domin ado,harabar gidan take takowa bayan sunyi sallama da anni,yau duka cikin mutanen nata babu wacca ta gani,kodon da wuri ta fito oho.
Motocin khalipha ta gani jere a harabar gidan,tayi zaton wani guri zashi shima,saita dan tsaya tana duba ta inda zata hangi malam shehu,don wani lokaci shi ko haidar dama wani ke kaita.
Dai dai lokacin khaliphan ya fito da dan sassarfa daga sashen ma'aikatan gidan,da alama wata 'yar ganawa yayi dasu,yana tafe yana duba agogonshi,caraf ya kamata tana satar kallonshi,ta kalleshi ita kanta batasan yakai sau nawa ba,shigarsa ta yau ba qaramin kyau tayi masa ba,haka uwa uba take jin wani ba dadi gami da wassafa adadin kwanakin da zata dauka kafin ta sake ganinshi.
Dauke kanta tayi ita ala dole saita tayi pretending kan cewa bashi take kallo ba,wani sashen na gidan daban ta maida kanta tana kalla,saidai haka kawai zuciyarta taqi biyota,ji tayi an riqe jakar hannunta,abinda ya sanyata waiwayo kenan ba tare data shirya ba,yana tsaye gabanta ita yake kalla,saidai fuskarsa a dinke take,ya mata kwarjini sosai,hakan ya sanya gabanta faduwa,da hannu ya mata nuni data wuce,jakar daya riqe ta kalla alamun ya sakar mata,sai ya dage kafadu yana gaya mata ina ruwanta,sakin jakar kawai tayi tayi gaba,da sauri nasir yaronshi dake riqe masa muhimman abubuwanshi duk sanda zasu fita ya matso da sauri zai karba saiya dakatar dashi.
Gab da zasu isa wajen motocin haidar ya faka tashi motar ya fito,tuni ya riskesu,cikin girmamawa ya gaida khalipha
"Barka da safiya yaya"
"Barkanka....ina fata ka kammala yadda ya dace?"
"In sha Allahu" ya amsa yana murmushi yana duban aysha sai ya kallo khalipha
"Na fito da motane na kaita?"
"Na hutashsheka yau" ya fada yana bude mata murfin motar da kanshi
"Yaya ni nake kaita dama ai,yauma bansan da wuri zata koma bane shi yasa na fita" tsayawa yayi da abinda yake ya zubawa haidar ido,shakka ta dan shigeshi,don khalipha ba daga nan ba wajen kwarjini,ko dan uwanshi namiji ya zubawa ido sai yaji ya a jikinsa
"Sorry yaya...." Ya fada yana hade hannyensa waje guda
"Anty Allah ya kiyaye hanya,asha L....." Sai ya juya da sauri yana dariya zuwa cikin gida,cikin zuciyarshi yana tuna hirat da sukayi jiya shida anni bayan barinsu khalipha wajen
"Haidar....kayi a hankali"
"Me ya faru anni?" Ya tambayeta yana tsayawa da bare bayan wayarshi da yake
"Yayanka ya fara kishinka ne" idanu ya zaro
"Kishi anni akanme?" Murmushi ta saki
"Akan matarsa" idanunsa a waje yaci gaba da duban annin yanason yaji qarin bayani
"Ya kamata ka janye jikinka zuwa yanzu,saboda ya fara soyayya,kasan kuwa illar da soyayya kewa wanda ya fada cikinta ba tare daya sani ba ba kdan bane,zaiyita abubuwa gq zaton na wanda yake kallonsa ko yana cikin hayyacinsa,saidai ina lamarin ba haka bane,shi sha'anin soyayya ya wuce duk tunani" ta qarashe maganar tana tubawa kanta da nata masoyin alhj sa'id,da irin gwagwarmayar da suka fuskanta kafin su cimma gaci
"Lalle ya khalipha ya hau network,ni anni kawai ina respecting din anty saboda na jima banga mai shekaru irin nata dake da hankali da nutsuwa kamar haka ba,sannan tausayinta nake ji tun daga randa na fuskanci tayi shigen tamu rayuwar,uwa uba ina taya yaya kishi ne saboda nasan halin sa'o'inmun nan,suna qyalla ido suka ganta ita kadai ba wani gefanta tsaf zasu iya yiwa ya khalioha shigar burtu....hajjaju anni da alama an tuna da,ya kamata na sanarwa mus'ab harma da ya khalipha muzo mu kwashi darasin soyayya...." Ya qarashe yana dariyar zolaya,daquwa ta watsa masa
"kaci gidanku,tashi ka bani waje ja'iri" yana dariya ya bar wajen yayin data bishi da kallo,na shakka soyayya bata tsufa,don har kwanan gobe bata fasa son sa'id dinta ba,da wannan tunanin haidar ya qarasa cikin gida,lallai zancan annin ya tabbata,tunda suka taso da yayan nasu basu taba ganinshi yana soyayya ba,ah lallai abun zaiyi matuqar armashi,zaiso yaga ya za'a buga wannan game din mai qayatarwa.
48
Ajiyar zuciya ya sauke mai sanyi sannan ya dauke idonsa daga binta da yayi da kallo sanda ta gama shigewa cikin hostel din nasu,a hankalibya sauke hannauensa ya shige motar da tuni aka bude masa murfinta,sauran suma suka shiga tasu suka tashi motocin suka bar wajen.
A tsaye ta sameta a varender din dakunan nasu ita da wata maqociyar dakinsu surayya,da alama hira suke,saidai idanunta na can farfajiyar harabar da motocin khalipha sukayi parking kafin su tashi
"Idonki kenan?" Hanan ta fada tana murmushi gami da jifan ayshan da hararar wasa kafin daga bisani ta nufota
"Kedai bari kawai hanan....sabgogi ne suka sako kai sai godiyar Allah" karbar daya daga cikin qaramar jakar dake hannunta tayi
"Dakin ba dadi gaba daya,kullum hunaifa na bakin gadonki"
"Allah sarko daughter na,yau dai zan ganta" ayshan ta fada tana zama gefan gadonta
"Inafa zaki ganta uwarta ta maidata wajen kakanninta saboda tsabar cin zali,idanu aysha ta zaro
" kai hab,badai yaye ba ai bata rufa shekara biyu bafa"
"Hmmm,kefa mmn huanifa dadi miji" dariya suka saki baki daya kafin daga bisani hanan ta tsagaita
"Ke tsaya....idanuna sun gano gulma fa,wanne handsome dinne ya ajeki haka da jerin motoci?,ko zancena ya tabbata ne?" Murmushi aysha ta sani tana tuna khalipha,yadda da fari yayi kaman baisan sunzo ba,bai bude mata qofa ba bare shima ya fito sun jima zaune a haka
"Yaya na ne" idanu hanan ta zaro
"Da gaske?,....kai amma ma sha Allah,hala dai duka gidanku kyawawa ne" ta tambayi ayshan tana dariya,tsaki ayshan taja itama tana dariya
"Ban sani bani,naxo baki bani komai ba kin cikani da tambaya?,me zan samu" dariya hanan ta saki
"Kinzo a sa'a kuwa,dazu saddiq ya tafi,ungo ci iya cinki" ta fada tana miqa mata wata leda daje saman drower dinta.
Hira suke sosai a haka mmn hunaifa ta dawo daga lacture ta taddasu
"Saura qiris na biyo sahu ko zancan hanan ne ya tabbata wani ya qwamushe mana ke" dariya sosai aysha tayi
"Harda ke mmn hunaifa?"
"Eh to ai gaskiya ne,budurwa mai kyau da aji kamar ke ai dole a samu 'yan takara da yawa" ta fada itama cikin raha,sun jima zaune a nan suna hirar yaushe gamo,aysha nata yiwa mmn hunaifan qorafi kan baro hunaifa gida da tayi
"Yana iya,abbanta yace na barta itama kakartata tafison haka"
"Ai shikenan" aysha ta fada tana dan bata rai.
A hankali ya tura qofar falon sannan ya kunna qayayen wutar haske ya gauraye wajen,takawa ya dinga yi a nutse har ya isa cikin falon ya zube saman kujerar cike da gajiya.
Hakanan yake jin sashen duka ya masa wani iri,sai yaji ya masa girma,a hankali idanunsa suka kai kan takardunta da tayi amfani dasu jiya dake aje a wajen,sai yaji kamar shi daya yake rayuwa,idanunsa ya lumshe yana futar da iska akai akai daga bakinsa,dalili kenan daya sanya ya dade sosai hira wajen anni,a haka ya shafe wasu lokuta kafin ya miqe ya tarkata ya shige bedroom dinsa.
Sai daya gama komai ya haye gadonshi sannan ya rasa abinda yake damunsa,saiya juya daya side din idanunsa kan side din da take kwanciya ko yaushe,filonta da abun rufarta yana nan a wajen,hannu ya miqa ya janyo filon ya cusa kanshi a ciki,qamshin turarenta ya shaqa har cikin kanshi,qamshine mai sanyi da tsayawa a rai,sai ya mirgina ya koma side din nata,baisan me yake damunsa ba rashinta a dakin ya tsaya masa a rai,miqewa yayi ya zauna dirshan kan gadon,ya lalubo wayarshi ya kunna ya tafi nemo lambarta.
Dai dai lokacin da itama take kwance rub da ciki kan gadonta,dakin ya dauki shuru,mmn hunaifa tayi bacci,sai muryar hanan dake waya da take iya jiyowa kadan ladan,duk da bata jin me take fada,littafinta ne a gabanta tana haskawa da torch din wayarta son sun kashe wutar dakin tana duba amsoshin tambayoyin data amsa dazu.
Gida biyu hankalinta ke rabuwa,ko daya bata jin dadin kwanciyar bare karatun da takeyi,bata wuce sakan goma bai fado mata a rai ba,saita aje wayar da takardar hannunta ta qanqame filon da take kai tana sauke ajiyar zuciya.
Qarar wayar tata ce ta sanyata daga kai taga mai kiran,kamar tasan number,haka kawai gabanta ya fadi,ta kira sunan Allah sannan ta jawo wayar ta daga gami da karawa a kunne,sallama tayi cikin sanyin murya,boyayyar ajiyar zuciya ya saki sannan ya amsa mata ya dora da
"Idonki biyu?" Gyara kwanciyarta tayi zuwa rigingine tana sauke numfashi,muryarshi na ratsata
"Eh,baccin baixo ba"
"Saboda me?" Ya tambayeta kai tsaye
"Karatu nake"
"Uhmmm,ban yarda ba,wanne karatu ne har dare haka,kuma ma ai karatu bai hana barci ko?" Murmushi ta saki kadan,batasan wacce amsa zata bashi ba
"Ina anni?"
"Tana nan qalau,na barta zata kwanta"
"Nayi kewarta" ya sani cewa har cikin zuciyarta ta fada,yana alfahari da irin soyayyar dake tsakaninta da annin,ya sani cewa Allah ne ya masa baiwa da samunta,saidai yana ganin kamar a binda shi yake ji ko yake fata daga gareta babu shi
"Dazu ta gama zancanki...." Shuru ne ya ratsa tsakani kowa yayi shuru yana jin fitar numfashin dan uwanshi,shi ya kasa aje wayar kamar yadda itama ta kasa
"Anni kadai kikayi kewa?" Ya tambayeta da wani salo,'yar kunya taji,idan da kara kam baici tace anni kadai tayi kewa ba
"Harda su haidar..."
"Haidar?" Ya tambayeta yanayin muryarshi na sauyawa,take yaji kishin haidar sosai ya kamashi,itama sai data fada din sai taga kaman hakan baiyi tsari ba
"Harda kaima" tayi saurin fada,amma data duba kiran sai taga ya katse,duk sai taji babu dadi a ranta,ko babu komai akwai sadakinsa a kanta,shi ya soma tsamo ta ya kawota cikinsu,shi ya kamata ta fara nunawa damuwa da kulawa bayan anni.
"Ana soyewa ne,ban taba ganinki kina wayar dare ba sai yau,Allah yasa ta samu" inji hanan wadda ta sauko daga gadonta da niyyar shiga toilet saboda fitsarin daya matsota,murmushi ta mata duk da a duhu ne
"Ke kam Allah ya shiryeki hanan,jeki fitsarinki kawai"
"Aiko nayi zan dawo nabi qwawqwafi,ban yarda da wannan canzawar da naga kinyi ba,tun dazu naga kin saka waya a gaba kin kasa karatun arziqi,gwara naji labari tunda wuri na shirya qawata da kyau,don naga batasan komai game da soyayya ba" bilhaqqi hanan ke maganar,yayin data baiwa aysha dariya sosai,bata sake cewa komai ba ta wuce tana murmushi.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Qarfe takwas da rabi na safe tana shiryawa don tafiya lacture tana duba wayarta,hakanan hankalinta ya karkata data kirashi,rabuwar jiya bata ji tayi mata ba sam,har ta gama shiryawa ta hada tea a cup zallarshi ta kurba donta dumama cikinta hankalinta bai bar kan wayar ba.
Sanda zata fita hanan tuni ta fice mmn hunaifa ce tayi saura tayi mata sallama ta fice,tana kan varender dinsu wadda zata kaita inda zata sauka daga saman ta ciro wayarta,saita samu kanta da rubuta masa saqon barka da safiya ta maida wayar tata jaka taci gaba da takawa,jefi jefi tana dan haduwa da wadanda ta sani tana tsayawa suna gaisawa,don zuwa yanzun itama ba laifi tana da mutane da abokan arizqi,da haka har ta qarasa theater din da zasuyi karatun ranar bata ji dawowar amsar saqon ba,basu bar aji ba sai uku na rana.
To hakama washegari kusan wuni sukayi,har a sannan tana zuba ido shuru ba amsa,sai ta soma tuhumar kanta kaman ta zaqe da yawa da saqon data tura mishi,a ranar ma sai wajen uku da rani ta koma daki,bandaki kawai ta wuce ta sake wanka saboda ranar da aka d'ana a ranar,doguwar rigar material mai hade da mayafinta ta zura,tana gyara kanta tana qorafi saboda yadda ya isheta da zafi,neman mai kitso kawai takeyi,'yar madaidaiciyar kwalliya tayi ta feshe jikinta sosai da turare,sosai material din yayi mata kyau saboda dacewa da yayi da kalar fatarta ya haskata qwarai,sallah la'asar ta tayar ganin lokaci ya cimmata,saboda tsabar gajiya ko yunwar ma tayi nata gu,gashi dama bata karya ba ta fita,hakanan ta dawo ta tadda dakin ba kowa da alama dukansu suma ba wadda ta dawo bare tasaka ran samun abinci,dole saita idar kafin tayi tunanin me zata dafa musu.
Hudu da rabi na yammacin motocinsa suka shigo cikin makarantar,kamar yadda suka saba duk inda motocin suka ratsa sai ido ya bisu hakance ta kasance ya riga daya saba da irin wannan har takai ma ga baikulawa zuwa yanzu,wani sakayau yake ji cikin zuciyarsa da wani nishadi kadan kadan yana ratsashi har suka samu gurin daya dace da tsaiwarsu duka suka faka,motar da yake ciki ce kadai ya bata umarnin ci gaba da tafiya har zuwa wajen da yake ganin zai iya tsaiwa,qasan wata bishiya data wadata da inuwa da iska mai sanyi.
Tana saman abun sallar bayan ta idar taji anyi knocking,izinin shigowa ta bada,daya daga cikin security nasu mata ne,suna mutunci da aysha hakanan tana ganin girman ayshan sosai wanda ita batasan dalili ba,bayan sun gaisa da ayshan take gaya mata tayi baqi,cikin mamaki take maimaita baqi kuma?,anya itace kodai hanan,murmushi tayi tace mata itace
"Gani nan" ta amsa tana miqewa gami da qissima su waye zasu zo nemanta?,mayafin doguwar rigar ta sake nadawa sosai a kanta,fuskarta da babu komai sai powder da man lebe ta fito tayi kyau,ta zira takalmi plate,zata dauki wayatta taga alewar da hanannta bata jiya da daddare saita dauketa ta jefa a bakinta waiko zata rage mata rashin dadin da bakinta ke mata saboda yunwa da takeji sannan ta fito,kafin ta sauka ta hadu da laila da zahra duka maqotansu ne suka gaisa sannan ta wuce.
Tun daga nesa rake duban motar cike fal da mamaki,tasan dai tabbas ire iren motocin khalipha kenan,saidai kuma me zaya dawo dashi bayan kwanaki biyu da dawo da ita da yayi,uwa uba ma tana zaton yau ko gobe shina zao wuce cyprus,a hankali yaci gaba da takawa tana duban motar,yayin da shi kuma dake zaune a cikin motar yake qare mata kallo ta cikin baqaqen gilasan da motar ke dashi ba tare data sani ba,tun daga sama har qasa yake kallonta yana jin wani yanayi yana ratsashi.
Qanqame hannunsa yayi waje guda,ya Allah,anya kuwa ba fara son yarinyar nan yayi ba,abinda yakeji a zuciyarsa game da ita bai taba jinsa akan wata diya mace ba,idan baso bane meye wannan?,tun shekaran jiya daya karanta saqonta da safe yaji ya kasa samun nutsuwa cikin zuciyarsa,kasa dauke idanunsa daga kanta yayi har ta qaraso dab da motar ta tsaya tana duban wani sashe daban,da alama neman baqin take.
A hankali ya sauke gilashin motar,qamshin turarensa da sanyin ac dake motar ya soma busowa zuwa waje,wanda hakam shi ya dauki hankalinta,qamshin turaren da take tunanin kamar ta sanshi,a hankali ta waiwayo zuwa sashen da take jin qamshin,idanunta suja sauka cikin nashi,faduwar gabar nan da'a koda yaushe takanji idan ta ganshi ita ta soma ziyartarta,sai kuma mamakin abinda ya kawoshi makarantar,duk ta watsar da wannan cikin sakanni ta sakar masa murmushi bisa shawarar zuciyarta,saita soma takowa a hankali zuwa bakin motar
"Sannu da zuwa" ta furta cikin nuna girmamawa,shima martanin murmushin ya maida mata yana mata nuni data zagayo cikin motar,ba musu ta zagaya daya bangaren ta shiga,saidai tabar murfin motar a bude,tuni drivern dama ya koma can wajen sa saura sukayi parking ya zauna a cikinsu.
Wani yanayi ne ya dinga ratsasu dukkansu tsahon mintuna ashirin kafin ya bude wani waje dage sit din gabanshi ya ciro laptop ya aje a tsakiyarsu
"Yau da daddare zamu tashi in sha Allah.....ga wannan kiyi amfani da ita a madadin waccar" sosai system din ta burgeta,da alama rahamalls sun iya kawo kaya masu kyau da inganci,don wannan tafi waccar tata kyau da tsada nesa ba kusa ba ko a ido ma
"Akwai abubuwa na akan waccan ina sonta na saba....."
"Shshshsh..." Ya fada yana dora yatsanshi kan lebanshi idonsa cikin nata
"Waccan haidar ne ya siya miki bana buqatar kuma ki amfani da ita,ni khalipha nine a haqqu da komai naki,so da wannan nakeso ki amfani,duk wani naki mai.muhimmanci na cire daga kai an dawo miki dashi nan,karma ki sake maganarta don already na riga na bayar da ita" hannu ta sanya ta dauka,bai cancanci musu ba sam sannan tace
"Na gode,Allah ya saka da alkhairi ya qara budi"
"Ameen" ya amsa yana lumshe idanunsa
"Ban amince kuma naga hoton kowa ba akai" saita daga kai tana dubanshi,sam ta mace hoton haidar ne akan screen din waccar,to me kenan?
"Uhmm,zan wuce me zan samu?" Ya fada idanunsa cikin nata,
"Ba komai" ta fada tana murmushi
"Shikenan" ya fada yana daga kafada duk da bai daina kallonta ba,saita motsa kadan ta fidda qafafunta waje sannan tace
"Allah ya tsare hanya ya bada sa'a" sam kasa amsa mata yayi ba,bayason ta wuce,bayason ta tafi,hannunta ya riqo cikin xafin nama da hanzari ganin da gaske ficewar zatayi,sannan ya miqa hannunshi ya rufe murfin motar,fuskarta ya sanya a cikin tafin hannunshi ya hada tsinin hancinsa da nata,cikin sakanni kadan ya kashe mata jiki gaba daya,a hankali cikin muryar dako cikin motar kake baka isa kaji me yake cewa ba yace da ita
"Ba haka nake buqata ba,sallama nakeso irinta masoya,so nake naji ya suke ji duk lokacin da rabuwa tazo....." Idanunta ta runtse gam,wani nauyi na sauka cikin zuciyarta da gangar jikinta ma gaba daya,gaba daya ya gama saukar mata da kasala,bugun qirjinta ya dadu wanda yasanya numfashinta shima sake gudu wajen fita,qamshin lemon dake fitowa daga bakinsa yana ratsa hancinta wanda ya gauraya da turarensa,tattausan lebanta dake gogar nashi ya sanyashi kama leban nata da haqoransa yadan ciza kadan ta yadd ba zata ji zafi ba.
Knocking din qofar da akayi shi ya sanyashi sakin fuskar tata da yayiwa ruqon tsauri,kowannensu ya janye a hankali,ta bangaren aysha ake knocing din saboda haka ta juya ta dannan madannin sauke glass,gilasan suka sauka qasa,hanan ce a tsaye rungume da litattafanta
"Ina can ina bulayin nemanki,keys din daki zaki bani ban fita da nawa ba mmn hunaifa na bari a dakin"
"Ohkey" ta fada cikin sanyi tana yunqurin lalubo maqullin da tuni ya subuce qasan kujerun motar,dagowa tayi ta miqa mata idanun hanan din na kanta,kana kallon fuskarta kasan dariya take hadiyewa,kallon na kamaki ba yadda zakuyi takewa ayshan itama ta fuskanci me take nufi,saboda haka saita waiwaya sashen da khalipha ke zaune cikin sanyi tace
"Meet hanan,my roommate" cikin fara'a hanan din ta gaida khaliphan,shima a sake ya amsa mata yana tambayarta karatu tace komai lafiya
"Ranka ya dade aikinka na kyau fa,saidai a dan sassauta mata karta gagara hada masters din tata" da sauri ayshan ta kalli hanan dake dariya,maganar tata saita baiwa khalipha dariya,can cikin ranshi kuma yana mamaki kan lafazin hanan din,idanu ya kafe aysha dashi
"Wai haka humairaaah?"kunya ta mata dabaibayi sosai,tana kada kai kamar zatayi kuka tace
"Tsokana ce kawai takeyi,batasan waye kai a wajena bane" dariya sukayi hanan din da khalipha,sannan tayi sallama dasu ta wuce
"Waye ni a wajenki?" Ya jefo mata tambayar data rasa amsar daya dace ta bashi
"Matsayin daka dade da baiwa kanka"
"A yanzun idan na sauya matsayin zuwa mataki na gaba yayi dai dai?" Shuru tayi tana nazarin maganarsa,kalma ce mai harshen damo dake da buqatar nazari,hannunta taji ya kama ya sumbata na tsahon sakan goma sannan ya sake mata hannu
"Zan wuce,ki kula da kanki" sai a sannan itama taji wani iri babu dadi,addu'a tayi masa sosai sannan ta zira qafarta ta fito daga motar,harta rufe idanunsu nakan nakan na juna duk da kunyar abinda ya mata dazu dake addabarta
"Baki bani komai ba da zan dinga tunawa dashi" sadda kanta tayi tana murmushi qasan ranta,tome yakeso ta bashi?" Bata gama wannan tunanin ba ta jiyo muryarshi mai taushi
"Allah ya bamu alkhairi,saina dawo"
"Ameen" ta furta,saita kasa tafiya taci gaba da tsaiwa a wajen har ya ryfe gilasan motar ta daga tabar wajen,shi dinma ta cikin mirrow yaci gaba da kallonta har suka bacewa ganin juna.
*_Mutane masu son zuciya ma sunada rana a gareka, koba komai zasu tara maka ladansu ka karɓa a ranar da kowa ke fafutukar neman ƙari a littafin ayyukansa. Dan haka karkai baƙin ciki da zaluncin azzalumi, koda ɓatanci yay maka bisa son zuciya ribace a gareka, shi ko bai gane faɗuwace a garesa sai randa babu wata ƙofa ko damar da zai roƙi gafarar ka._*
49
Tana tsaye tamkar jiran shigowar ayshan take,koda yake hakanne ma,dafeta tayi tana dan ihu,wanda hakan ya sanya zubewarsu saman gadon maman hunaifa,qoqarin qwace kanta aysha take
"Hanan....hanan what r u doing ne?,pls" sai data gama ihunta sannan ta saki qaramar dariya
"Wallahi banga laifinki ba,wannan halitta haka aysha dole ki susuce ki sauya lokaci daya,wallahi kunyi masiiiiifar dacewa,hadin ya hadu wallahi" dubanta aysha take tana hadiye dariyarta,yayin da a zahiri tadan hade gira
"Wai....akanme kike magana ne?dawa muka dace?"
"Ban sani ba 'yar gaba da rainin hankali,kinsan Allah gulmarku kawai ke tashi a varender dana hau,ina can nemanki wajajen department dinku ina zuwa nan nace ke nake nema aka nunan inda kike,kaiiii aysha ashe ba banza ba kike figawa maza dawa ashe ke kin gama gwangwajewa abinki,kai ma sha Allah wallahi d'an d'ashi,dole mmn hunaifa tasha wannan labarin" ta lura idan bada gaske tayi ba hanan zata mata kwaroroto,kusan halinsu daya da aliya,banbancin dan kadan ne
"Wai da kiketa wannan surutun ce miki nayi saurayina ne?,toki rage zumudi wanda dai kika gani yaya na ne,kuma ga abinda yazo kawomin nan" ta fada tana nuna laptop din data aje kan dan teburin da take dora littafanta tayi karatu,dariya sosai hanan ta saki bayan fa kalli system din harda tafa hannu sannan ta samu gefan ayshan ta zauna,hannunta ta dora kan kafadarta
"A qalla na doshi shekara takwas ko bakwai ina soyayya,kin manta wace ce hanan?,to bari kiji wannan tatsuniyar taki bata samu wajen shiga ba,ko wanda ya fara soyayya yau kallo daya zai muku yasan cewa ba qaramin narkewa kukayi cikin son junanku ba,idan ma ba saurayinki bane bari na gaya miki ku binciki kanku,don ba shakka dukkaninku kuna yiwa junanku soyayya mai zafi,idanunku kawai sun isa su gayawa koma waye haka,saidai wataqila kun afka son junanku ba tare dakun sani ba,ko kuna daga cikin masu qaryata cewa sun fara son waninsu" idanu aysha kawai tasa tana kallon hanan gami da yunqurin faffasa maganar cikin kwanyarta,wanne ne a ciki?,wanne ne ba wanne ba?.
"Wa akewa irin wannan sharhin haka?" Mmn hunaifa dake shigowa ta fada bayan ta zauna saman gadon aysha
"Kinzo a dai dai,wallahi yarinyar nan ba banza ba taqi ayi mata maganar kowa,mmn hunaifa kinga guy dinta kuwa?,hasbunallahu wa ni'imal wakil,wannan shi ake kira da komai yaji,kinga wata iriyar soyayya da ake bugawa mai sanyi" ai aysha batasan ta durmawa hanan dundu ba tana fadin
"Zubaida....mmn hunaifa karki yarda da sharrinta
" a'ah nima fa dana shigo daga waje na danji ana qushin qushin,ko maganar ce?"
"Itace daiiii mamn hunaifa,hostel din nan duka ya dauka" ganin yadda hanan ke faman zubawa mmn hunaifa lbr kawai saita barta ta miqe ta cire rolling din kanta ta daurashi a matsayin dan kwali ta hau dora musu girki,don shaf ta mance ma tana jin yunwa sai yanzu,tana aikin amma tunanin maganganun hanan ke mata yawo a ka,da gaske idanunsu na bayyana soyayya kamar yadda hanan din tace?,to wai shin yama soyayyar take bare har ta ganeta,kalma daya da bata santa ba a rayuwarta wato soyayya.
A bun mamaki a daren saita kasa barci,tayita juyi tana tuna zuwan khalipha a yammacin dazu,duk wani motsai daya faru tsakaninsu sai data tunashi kar a kanta,miqewa tayi daga kwancen ta janyo syatem din daya kawo mata ta kunnata.
Hotonta ne ya mamaye screen din,wanda batasan inda ya samu hoton ba,hakanan ba zata iya tuna sanda aka dauki hoton ba,a nutse ta dinga shiga ma'ajiyar adana hotuna,hotunanshi zallah a ciki wadanda yayi masifar kyau kamar a kirashi ya amsa,ya rabata da duk wani hoto na haidar sai nashi zalla me kenan?,
"Kishi" zuciyarta ta bata amsa,kanta ta kada tana qaryata hasashen zuciyar taya,kishi ana yinsa ne ga abinda akeso ai,yaushe khalipha yace yana sonta ma da har zata zaci ganin kishi a qwayar idanunsa?,amma sone kawai yake haufar da kishi aiko?,zuciyarta ta jeho mata tambayar,saita ture gaba daya tunanin gefe guda.
Wajen videos ta shiga,films ne na soyayya sunfi talatin,kuma duka na jaruman nan da ranar ya tayata kallon fim din ta gudu ta barshi,murmushi ta saki ita daya tana rufe fuskarta kamar yana ganinta,wato yana sane kenan,shi da yace aure takeso?,yace kuma me take gani haka,wani murmushin ya sake subuce mata ba tare data shirya ba,tuna maganarshi ta dazun tayi,hakan ya sanyata zama dirshan ta jawo wayarta,a qalla ta kusa kashe minti talatin tana rubuta saqon tana gogewa,inda daga bisani tayi bismillah kawai ta tura,saikuma tayi tsam tana tuna abinda ta tura din,kamar ta wuce makadi da rawa,tunda ya riga daya shiga haka ta haqura ta koma ta kwanta tana kunna daya daga cikin fina finan ta soma kalla.
Gurine da sau tari yakan je ya zauna kawai idan zaiyi karatu ko zai duba wasu mihimman abubuwa da suka shafi kamfaninsu wanda ya zama dole ya duba din,a yau dai babu ko daya daga ciki,yana zaune ne kawai yana shan ni'imar da Allah ya yiwa wajen,bai jima da gama waya da anni ba a nan ya jiyo kamar hayaniya,ta gaya mishi su amal ne ke rigima da zeenart,dama dazun nan ta gama yi musu shari'a,sosai ranshi ya baci ya dinga fada yana fadin basu isa su hanawa uwarshi zama lafiya ba,don haka kowacce ta kama gabanta,dama shi sun isheshi baisan ubanme suke zaune gidan sukeyi ba,annin ce ta dakatar dashi,tace suma duk abinda zayayi zai zama ne saboda Allah ya fifitasu a kansu,bayan basu suka tsamo kansu daga halin da suke ciki ba ganin dama ce ta ubangiji da baiwarsa,hakan ya haqura,amma yayi waya da haidar ya gaya mishi lallai kome ake ciki zaman kowa ya saitu a gidan,amma karya bari anni ta sani saboda zata hana ruwa gudu ne,ya sani haidar din kome zaiyi tamkar yana nan ne,da wannan tunanin da baci da ranshi yayi yaji shigowar saqon,da fari banza yayi dashi sai wani bari na zuciyarshi ya dinga azalzalarsa da ya duba din,fuska a tamke ta soma danna wayar sai gashi ya buge da sakin sassanyar murmushi,gyara zamanshi yayi sosai ya soma maida mata reply.
Tsaida kallon tayi da taji shigowar saqo cikin mamakin ganin number khalipha ce,tana duba saqon tana murmushi,wani abu ya dinga tsumata,saita biye mishi ta sake maida masa amsa,wasa wasa sai da suka dauki mintuna goma suna musayar saqonni,wanda sai daga baya aysha ta dinga duba saqonnin tana zaro ido,ya akayi ta rubuta wannan kalaman?,sai taji kamar yana gabanta saboda kunyar data kamata.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Suna kan hanyar dawowa daga daga aji ita da hanan da suka kammala daukan karatu kisan lokaci daya wayarta ta dauki kida,tana dubawa taga mero ce,cikin zumudi ta daga wayar ta kara a kunneta,gaisawa sukayi daga bisani take shaida mata ta haihu jibi suna,cikin bata rai aysha tace
"Yanzu qawa ki haihu kamarni sai yau kwana biyar nake ji?,ai shikenan babu komai na gode
"Don Allah indo kiyi haquri,wallahi wayarce ta samu matsala saida habu ya sauyamin wata yanzu yanzu aka kawota kena fara kira wallahi" sai a sannan aysha ta saki ranta,hira suka dan taba daga bisani tayi mata alqawarin halartar sunan.
Sai data zo kwanciya ta tura masa masa saqo kamar yadda ta saba koda yaushe ya kuma zame mata jiki,ta gaya mishi zuwa takai din,tana kwance idanunta a lumshe tana tsammanin jin reply kamar yadda ta saba sai taji shuru,duka sai taji yau babu dadi wani banbarakwai,tun tana sauraro har bacci ya dauketa.
Qarfe uku na yammacin washegari suna tsaka da kammala shirinsu na tafiya takai,hanan ita zata mata rakiya wannan karon,ana ya gobe suna ta shirya zasu daman ta dawo ranar sunan saboda washegari tara na safe zasuyi presentation,saidai gaba daya hankalinta kacokam yana kan wayarta,tun jiya data tura mishi saqo har yau bata ji daga gareshi ba,sai taji gaba daya bata dokin tafiyar.
Tana riqe da powder tana shafawa wayar tata ta dauki ruri,da sauri ta aje powder din ta rarumi wayar tana duba mai kiran,khalipha ne kamar yadda tasa capital K a sunanshi,cikin hanzari ta daga ta kara a kunnenta tana aje boyayyar ajiyar zuciya,saidai tuni ya jita,sallama yayi mata sai a sannan ta tuna cewa batayi masa sallama ba,a kunyace ta amsa tana gaidashi,ya amsa mata,shuru tayi tana saurarenshi sanda yake amsa mata gaisiwarta,sai taji muryarshi ta canza ba yadda ta santa ba,kamar ma baida lafiya
"Tun jiya banji daga gareka ba,Allah yasa lafiya"
"Naga saqonki amma ban iya maida reply ba,bana jin dadi ne" hankalinta ne taji ya tashi,take zuciyarta ta karye
"Subhanallahi,me ya sameka ya khalipha?" Karo na farko bakinta yayu subutar ambatar sunanshi,raunin dake muryarta ya fiti qarara,yadda ta ambaci sunan nasa yayi masifar yi masa dadi,har yaji me yasa tunda baice mata bashi da lafiya ba don ya samu irin wannan kukawar daya samu a yanzu?
"Dont bother....ciwon kaina ne ya tashi,kuma baiyi wani worst ba" hawaye ne taji yana son sauko mata saboda tuna silar samuwar ciwon kan nashi,karo na farko da taji bakinta da zuciyarta na Allah wadai da masu hali irin na ahalinsu ita da khalipha,mutanen da basu san qima da martabar zumunci ba,mutanen da basu haifarwa da rayuwarsu komai ba face wani tabo da miki da suka bar zuciyoyi da rayuwarsu,take tafiyarta takai ta fice mata a rai baki daya fit,banda daraj da qimar da mero keda ita a wajenta da ta fasa ba zata dara koda nan da can ba
"Dont cry mana pls...so kike ki daga min hankali?" Ya tambayeta da sassanyar muryarshi da ciwon ya sake sanyayar da ita,cikin mamakin yadda ya fahimci kukanta ba tare daya ganta ba ta goge qwallar data soma sauko mata
"Am sorry" ta fada a hankali
"Allah ya baka lafiya....amma karkace zaka zauna a gida hakanan da ciwo,pls i beg you"idonsa ya lumshe yana jin gardin kulawa daga wajen wata mace baya ga uwa
"In sha Allah,but pls stop crying....will you?" Kai ta kada sannan tace
"Is ohk"
"Ma sha Allah,kin shirya tafiyan?"
"Eh,yanzu muke shiryawa"
"Yayi.....bana son tafiyarki ke daya"
"Eh tare da hanan ne,yanzun zamu wuce tasha mu samu qaramar mota"
"What!,motar me?,no...ki jira nan da minti arba'in akwai wanda na turo zaizo ya kaiku,ban yarda ki sake hawa motar haya ba"
"Thank you" ta fada cikin wani tune mai sanyi wanda ya ratsa zuciyarshi har ya sashi lumshe idanu,ya dora hannunshi saman kanshi ya shafeshi kadan,sai yaji kamar an rage masa ciwon dake damunsa.
Minti arba'in da biyar dai dai ta sake ganin kiran khalipha
"Ki sameshi a wajen hostel ya iso"
"Ohk,shukran" ta fadi tana sauya yanayin muryarta
"Eheeenn" ya iya fadi kawai ta katse wayar ta dubi hanan
"Mu wuce ya iso", ga mamakinta motoci uku ne tsaye suna jiranta,idanu suka hada da hanan dariya ta saki
"Wannan yaya naki yana ji dake,wannan 'yar uwa ce da alama ta musamman wadda babu kamarta" ta fadi tana sheqewa da dariya,shuru ayshan tayi mata kawai tana murmushi don nata da abun fada,kamar yadda suka saba treating nata cikin girmamawa idan khalipha na nan yanzu ma haka ne,su suka bude mata gidan baya suka shiga ita da hanan kana suka rufe suka tashi motocin a hankali har suka fice daga cikin makarantar kana suka harba kan titi.
A hankali ya sauke wayar yana tariyar muryarta da maganganunta a kwanyarsa yana sakin murmushi,sai yaji wani sauqi na musamman ya samu a gareshi,zamewa yayi ya kwanta ta gefan damanshi idanunshi a rufe yana ci gaba da tuna ta.
A hankali yaji kamar ana shafashi,da fari yayi tsammanin irin mafarkin da yakanyi lokaci zuwa lokaci ne,sai kuma yaji sam ba haka bane wannan ya wuce mafarki,da hanzari ya bude idanunshi,sai yaci karo da lili,tube take haihuwar uwarta tana masa wani mayen kallo,cikin azama da zafin nama ya zabura ya miqe wanda hakan yayi sanadiyyar harbata da yayi ta fado daga saman gadon,cikin tsananin bacin rai yake huci,fuskarnan tuni ta hada ja,dubanta yake zuciyarsa na masa zafi ya soma mata magana cikin harshen turanci
"Ban hanaki zuwa min gida ba?,ke wace iriyar shaidaniya ce?" Duk data bugu hakan bai hanata tashi ba tana daurewa zafin data ji,don a duniya bata da burin daya wuce ta mallaki khaliphan,jikinta ta soma girgizawa cikin son jan hankali
"Bazan iya daina zuwa gidanka ba khalipha,ka saki ranka da jikinka mu more rayuwarmu,wai meye kake tsoro a ciki ne kodon kai farin shiga ne?,babu komai fa,ko masu irin addininku nawa ne muke tare dasu,saikai ne zaka dinga wani nuna addininka ya hanaka bayan munsan komai,kawai ka saki jiki saika fara zaka gane me nake nufi" ('yan uwa musulmi mu kula da kyau,duk lokacin da kaje ka aikata wani abu ba dai dai ba tamkar kana wakilatar sauran musulmai 'yan uwanka ne,duk sanda kayi wani mummunan abu kana sunan musulmi kamar kayi tarnishing image na musulmai ne,don duk wanda bai taba cin karo da mumini na qwarai ba sai ya fara cin karo da gurbatacce zai ma dukkan musulmi kudin goro ne yace halinsu daya,Allah ya tsare mu ya tsare mana imaninmu gaba daya amin).
Gigitacciyar tsawa ya daka mata yana gaya mata karta qaraso inda yake,saidai bata ji kashedinsa ba taci gaba da takowa cikin wani shu'umin murmushi har ta iso gabanshi,hannunshi yasa gaba daya ya hankadata baya ta kifa,wanda hakan yasa ta bude sosai ta kuma ji zafi,cikin kakkausar murya yace ta fita daga gidan gaba daya ya bata minti biyar,idan kuma ta wuce haka zata gamu da fushinsa da bacin ranshi,yana gama fada mata haka ya wuce toilet ya kulle kanshi.
A toilet sit ya zauna yana dafe da kanshi da ya sake tsananta masa,tabbas badon mace bace babu abinda zai hanashi yi mata dan banzan duka,shu'umancin lili yana neman wuce tunaninsa,lallai dole ya yiwa kansa rigakafi,saboda shi dan adam ne kamar kowa,zuciya kuma bata da qashi,hakanan tana tare da shaidan.
Sai bayan minti goma sha biyar ya fito daga toilet din bayan ya daura alwala,ba kowa cikin dakin don haka ya fita ya dudduba gidan ko ina ya tabbatar ta fita sannan ya kulle gidan ya koma bedroom dinsa ya samu waje ya kwanta yana maida numfashi.
Tsakanin takai da wudil ba wani nisa bane ko tazara mai yawa,saboda haka nan da nan suka iso
Kai tsaye gidan gwaggo asabe ta yiwa dirvern kwatancen ya kaita,tunda suka shigi cikin garin ido ya dawo kansu,kafin kace meye wannan labarin indo tazo ya fara yawo.
Gwaggo asabe na cikin yin rude na tuwon dare sukayi sallama farfajiyar makeken tsakar gidan nata,wanda aka yiwa gidan wani gyara na musamman aka shafeshi da sumunti yayi mul gwanin sha'awa,fuskarta qunshe da wadatacciyar fara'a ta aje muciyar hannun nata ta miqe
"Wai wai wai,amaryar muhammadu yau a garin namu,lallai yau farar asabar ce" dariya aysha take sosai
"Kai gwaggo,kamar bani zuwa?"
"A'ah to wannan zuwa na yammaci haka?,yaushe rabonki da takan ma" ta fada tana yin gaba suka bita a baya zuwa rumfar dake gaban dakinta wanda ke shimfide da tabarma da alama bata jima da tashi ba akai,lale take musu wanda tana shirin tashi ta debo musu ruwa ayshan ta dakatar da ita,da kanta ta isa bakin randar gwaggon taba debo ruwan cikin kofin silba
"Wannan randa taki gwaggo da tsahon rai take,har yanzu kuma sanyi yake bata fasa ba"
"Ai 'yar amana ce wannan randa ni kaina na shaida...." Bata kai aya ba yara suka fara sallama dauke da kwalaye a kansu
"Wai gahi,kayan indo ne inji wasu mutane a waje a mota" kallonsu aysha take sanda take takowa riqe da kofin sulbar ta aje gaba hanan tana kallon kwalayen,dukkansu na kamfaninsu khalipha ne donga tambarin kamfanin nan rubuce baro baro a jiki,tana tsaye tana kallon ikon Allah sai da aka sauke kwalaye guda goma cif,jakarta ta bude ta dauko dubu daya ta baiwa yaran su raba,suka amshe suna godiya suka cilla suka fice a guje yayin data qarasa saman tabarmar ta zauna tana kallon kwalayen.
Sam batasan da kayan ba har suka zo garin,daga gaya mishi tafiyar kenan zuwa turosun da yayi har yasa aka sayi kaya irin wannan
"Wannan bawan Allah wannan bawan Allah akwai hannun alkhairi,bamu da abinda zamuce saidai ubangiji ya albarkaci aurenku,ya baku zuriyya ta gari,ya yalwata dukiya da arziqi" gwaggo asabe ke fadin haka sanda ta duba kwalayen taga kayan da aka nade da sunanta,dubanta hanan tayi da sauri jin gwaggo ta ambaci aurensu
"Aur...." Da hanzari aysha ta mata alama da ido kan tayi shuru don Allah,hakanan hanan ta hadiye maganar tana duban ayshan cikin mamaki,dama ayshan matar aure ce amma basu taba sani ba?,to meye dalilinta na boyewa?,haka taci gaba da duban ayshan cikin mamaki,wanda ta lura da hakan itama,dariyarta take ta dannewa kawai,don tasan yau za'a sha cakwakiya kam,nan gidan gwaggo sukayi sallar la'asar.
Tana saman abin sallarta taja waya ta soma neman number din khalipha,don tun dazun hankalinta na wajensa,tana son taji yanayin da yake ciki,saboda hanan na wajen da gujewa yawan tsiyar data shirya yi mata saita miqe ta fita daga dakin sanda wayar ta fara ringing.
Har zuwa sannan yana kwance rigingine saman gadon nashi dafe da kanshi,a lokacin ya jiyo qarar wayar saidai sam bashi da kuzarin da zai iya tashi bare ya daukota,haka ga qaraci ringing dinta ta gama,har wajen sau uku tana kira ba amsa,hakan ya sanya a sanyaye ta sauke wayar daga kunnenta ta rubuta masa gajeran saqo
_ya jikin naka?,ina fata dai lafiya,Allah ya qara afuwa yasa kaffara ne a gareka_
Sai data tabbatar yaje sannan ta juya don komawa ciki,sai taci karo da hanan dake tsaye harde da hannayenta tana kallonta
"Sannu mrs khalipha" dariya aysha ta sheqe da ita,don tasam cewa maganar nata cin hanan,don ba yadda zata yine yasa tayi shurh,qarasawa tayi ta kama hannun hanan din
"Me kike ci na baka na zuba?,abinda zamu kwana tare zaki ji komai"murmushi hanan tayi donta qagu taji labarin daga bakin ayshan,tana hango bala'in dacewar ayshan da khaliphan ne,ta hangi cewa wata iriyar soyayya ce ke riqe dasu duka su biyun mai tsayawa a rai
"Promise?" Ta tambayeta tana dariya dariya
"Nayi...muje mu qarasa gidan inna yelwa,itace ta haifi abbana"
"Uhmmm" hanan ta fada suna shigewa ciki.
Sanda suka fito da niyyar wucewa saitaga ashe dukka motocin na tsaye suna jiranta,cikin hanzari suka taso,mamaki ya rufeta,yanzu ashe dama wai suna tsaye,saita kasa shuru ganin kamar hakan bai dace ba,sam sai taji wani iri,suma fa mutane ne kamarta,ita din wace da za'a dinga bata wani tsaro da kulawa haka
"Ai da kunyi tafiyarku,idan yaso in zamu koma kwa zo ku maida mu,ai duka inda zanje ba mai nisa bane duk kusa suke da juna"
50
"duk yadda kika ce haka za'ayi madam,amma mu qarasa dake can gida"
"Shikenan" ta fada tana matsawa hanan ta soma shigewa sannan ta mara mata baya.
Tunda suka shigo layin mamaki ya cikata,saita kasa tantance gidan,don ba gidansu take gani ba,wani gida take gani mai dauke da ingarman katanga wadda duk girmanta mulmule take da sumunti da fenti mai kyau da daukar ido,sanda motar ta tsaya sanya kai kawai tayi cikin gidan cikin rashin qwarin gwiwa,don bata da tabbacin gidanne,hakanan bata da tabbacin jama'ar gidan har yau sune mazauna gidan.
Kamar ko yaushe mafi yawancin matan gidan suna qarqashin bishiyar da zamanta ga zame musu kamar al'ada,saidai a wannan karon bishiyar tafi kyau da qawata gidan fiye da lokutan baya,sakamakon siminti da aka yiwa ilahirin fadin gidan,sallamarta ita taja hankalin duk wanda ke zaune a wajen,gaba daya ido yayo kanta yayin da suka mimmiqe tsaye wasu sukayo gaba inda take
"A'ah,lale maraba sannu da zuwa"
"Maraba da matar allaji halifa"
"Sannunku da zuwa indo,indo mutanen birni"irin wadan nan kalaman dake nuna maraba da mutum su suka dinga furta mata,kowacce fuskarta wasai da fara'a,karo na biyu a rayuwarta da taga soyayya makamanciyar wannan.
Gaba daya suka dunguma dakin inna yelwa,wanda a yanzun ya zama babban falo da dakuna guda biyu a cikinsa,an sauya shi bayan gyaran da aka yi masa lokacin bikinsu,gaba daya mamaki ya cikata na waye ya iya irin wannan aikin a dukka gidan duk da kyau da yake dashi.
Tamkar inna yelwa zata goya ayshan haka ta rasa inda zata ajeta,kyakkyawar daddurma mai girma da taushi aka shimfide mata,kana ta umarci biyu daga cikin matan 'ya'yanta suje su dorawa ayshan wani abun
"karki wahalar dasu inna yelwa,mukam a qoshe muke"
"Ke ba irin cimar da kike zato bace" inna yelwar ta fada tana dariya,murmushi aysha tayi
"Allah mun qoshi inna,amma ban sani ba ko zuwa anjima"
"Toh ina zuwa" ta fada tana ficewa don ta bada sautu a samo mata fura da nono mai kyau,saboda ta sani indon mai son fura da nono ce a baya,saidai sum ranar kasuwa idan 'ya'yanta suka kawo haka za'a dama a rabawa kowa fana kallo bata da rabo duk yadda takai ga son furar,saidai ta sude a kofin wasu,sai tayi saurin kauda wannan tunanin daga zuciyarta,sau tari idan ta tuna saita dinga jin babu dadi ita kanta cikin ranta.
"Gaskiya aysha ke 'yar gata ce,kowa sonki yake?"
"Hmmm,hanan kenan" aysha ta fada tana dan qaramin murmushi,haka rayuwa take,a duk sanda kaga wani bawa cikin wata ni'ima saika yiwa kanka sha'awarta kota birgeka,harma wani lokaci ka yiwa kanka sha'awarta ba tare da kasan irin qalubalen daya fuskanta ba kafin yakai ga wannan bigiren.
Suna zaune aka kawo furar a dame an jefa qanqara a ciki ta dauki sanyi,bude faifan dake kai tayi,kallon furar tayi tana tuna wani lokaci can baya,sai taji gaba daya ta fice mata a kai bata bata sha'awa ba,saboda haka ta turawa hanan gabanta
"Bismillah sis kisha" ja hanan tayi gabanta ta soma shan abinta,ta mata dadi sosai saboda sanyi da suger data sha
"Ke bakya sha indo?" Inna yelwa ta tambayeta,murmushi kawai aysha tayi,a dacan baya wani lokaci daya shude,lokacin da take da buqatarta,lokacin da take sha'awa da qulafucinta aka hanata,hakan ya sanya a yanzu ma sam bata sha'awarta,bata baiwa inna yelwa amsa ba murmushi kawai tayi mata,sai jikin inna yelwan yayi sanyi,kwalin da tasa aka shigo mata dashi ta bude ta fidda tsarabar kowa ta lissafawa inna yelwan,fuskarta washe da fara'a take jerowa ayshan addu'a da fatan alkhairi,sai tayi zugudi kawai tana kallon innan,lafuzan da tunda ta budi ido tasan me duniya ke ciki bata taba jin makamancinsa a kanta daga bakinta ba,saidai ta jiyo akasin hakan
"Allah ya baki miji indo dan albarka,mijin da ina jin kaf zuriyata babu yarinyar da zata samu kamarshi,hannun kyayta Allah yayi masa,ki duba yadda duk wanda ke cikin gidan nan sai daya dandani arziqinki indo,ba shakka kedin mai qashin arziqi ce,ki qara masa godiya bisa aikin da yayi mana,ki duba kaf fadin karkarar nan babu gida ya namu dana kakanki salihu" mamakin khaliphan ya kamata,yaushe duka yayi wannan aikin?,cikin shi ko anni ba wanda ya taba nuna mata anyi ko a fuska,ya Allah,wadan nan wanne irin mutane ne masu kyakkyawar zucuya har irin haka da Allah ya hadata dasu?,dame ita kuwa ayshatu zata sakawa rayuwarsu?,khalipha...khalipha sunan data ringa maimaitawa kenan a ranta har zuwa wani lokaci,bayan hanan ta kammala sha suka nufi gidan mero.
Ta samu mai jego lafiya ita da yaronta,nan ta zauna suka kacame da hira,hirar da suka jima basuyi irinta ba,itama kwali guda ne na tsarabarta,itadai dukka mamaki take,waita yaya khalipha yasan kowa yasan kuma siyayyar data dace da kowa?,waye ya gaya mishi?.
Godiya mero ta dinga yi sosai,kaya ne turamen atamfofi da rigunan jariri masu kyau da tsada,hira suka dinga wadda suka jima basuyi irinta ba,sun tuna baya sosai,sun tuna abubuwa kala kala,na dadi da akasin haka,hanan kam tana waje suna hira da saddiq dinta,basu bar gidan meron ba sai qarfe kusan goma na dare,gidan inna yelwa suka koma,a sannan tuni har an saka musu shimfida,qatuwar katifa ce mai kyau da taushi da bargunan rufa.
Aysha na kwance rub da ciki tana danna wayarta yayin da hanan ke sakawa kanta hula suna shirin kwanciya
"Matar khalipha....baki gayamin ya akayi aka haihu a ragaya ba" murmushi tayi kafin ta kashe wayar ta aje,sannan ta dubi hanan sosai
"Muhammad khalipha mijina ne,munyi aure babu jimawa ya tafi qaro karatu nima nayo kust qaro nawa,yanzu haka aurenmu bai cika shekara ba,saidai mun kusa"
"Kai aysha,ashe duk solamu kawai kike,kuma ban taba ji kinyi maganarshi ba tunda muke dake" numfashi ta sauke tana kwanciya rigingine gami da lumshe idanunta kana ta bude
"Munyi aure ne ba tare da dukkanmu muna son junanmu,tausayi shine abu na farko daya jawo qulluwar aurenmu.....saidai bazan boye miki ba...." Aysha ta fada tana sake mirginawa ta koma rub da ciki saidai ta takore jikinta da gwiwar hannunta tana duban hanan
"Ina jin wani abu na daban akan khalipha wanda bansan meye shi ba,ina jin wata shaquwa aduk sanda muke tare,hakanan inajin wata kewa a duk lokacin da yayi nesa dani,ina jin tausayinsa a duk lokacin dana tuna gwagwarmayar rayuwarshi,akwai abubuwa da yawa da nakeji baqi a kanshi wanda bani da amsar meye su..." Murmushi sosai hanan ta saki wanda yafi kama da dariya
"Akwai ayar tambaya akanki aysha...saidai bazan gaya miki ba nima,kamar yadda kika jamin rai akan sanin kina da aure nima sainaja miki,saida safe" ta fada tana juyawa zata kwanta,dariya aysha tayi tana girgiza kai,bata ce da hanan din komai ba ta juya itama ta kwanta
Bata zata ba don har ta fidda rai taji muryar hanan din
"Aysha....koda baki soma son khalipha ba dab kike daki afka,dukkan abinda kike ji dangane da khaliphan ina kyautata zaton soyayya ce da qauna mai zafi" waiwayowa tayi gaba daya tana duban.hanan gabanta na dukan uku uku kamar taga khaliphan,gira hanan ta dage maya fuskarta qunshe da murmushi tana bata tabbacin abinda ta gaya mata
"Qwarai kuwa,shi so yakan iya farawa da tausayi,wani lokaci kuma daga faduwar gaba,tsoro,daduwar bugun zuciya a duk sanda taga abinda takeso din,yawan kallo,yawan shuru da nutsuwa a sanda kuka hada muhalli dashi,saboda haka nake miki albishir.....barka da zuwa duniyar soyayya" ta qarashe tana dariya,kai ayshan ta girgiza tana duban hanan fuskarta qunshe da murmushi
"Ban yarda da wannan sharhin naki ba malamar love" saita maida kanta ta kwantar
"Ki gama qi fadinki tsaf da kauce kaucenki,baki da wata makawa kan zancena,zaki ce kuma na gaya miki nan da wani qanqanin lokaci" itama hanan din ta fada tana gyara rufarta tare da gyara kwanciyarta,shuru aysha tayi tana sauraronta tana fidda boyayyen murmushi,
saidai can qasan ranta tana taraddadin rashin jin khalipha da bata yi ba har a sannan.
Washegari suna idar da sallar asuba ta zari slippers dinta tayi gidan suna koda akwai wani aikin da zasuyi a lokacin tabar hanan tana bacci,tasan yanayin yadda mutan qauye kesa asubanci,haka kuwa tayita cin karo da mata jefi jefi,tana tsayawa suna gaisawa,wanda hakan yana musu dadi sosai.
Sanda ta isa kuwa ana shirin yanka abun suna,ta gaisa da 'yan uwan mero dake rumfarta ta tsallake uwar daka inda meron take tana shiryawa,mero na dariya tace
"Indo baki manta da al'ada ba,na zaci birni tabi jikinki ai ba zaki iya wannan asubancin ba" dariya tayi ta amshi yaron da tuni anyi masa wanka an shiryashi tsaf cikin daya daga cikin rigunan da khalipha ya sako masa,kyau yaron yayi sosai dama kuma kyakkyawa ne,ya debo babarshi xam,sai taji ya bata sha'awa
"Tushiya masomin dawa mero,ta yaya zan manta usulina"
"Wannan gaskiya ne,aike indo kam Allah ya baki,duk yadda akaso ayi da rayuwarki Allah bai nufa ba,gashi da yake ke din 'yar qwarai ce irin halak daular da kika samu bata sanya kin manta da tushenki ba,bakya qyamatar kowa cikin 'yan garinku,kowa sanbarka yake dake" cewar iyalle kishiyar babar mero wadda ke shigowa dakin ta tsinci zancan da sukeyi,murmushi mero tayi kaman yadda yasha itama shi tayi,tana zaunw suna hira da mero harta kammala shiryawa,tayi kyau cikin atamfa abinta,tanajin an shigo da abun sunan za'a soma gyarawa ta ajiye yaron tana cire hijabin jikinta ta rataye
"A'ah ina zaki kuma?" Maro ta tambayi aysha tana dubanta
"Aiki mana"
"Wanne aiki duk ga mutane nan,kiyi zamanki muyi hirarmu karki bata jikinki,inake ina bakin murhu ma" dariya aysha tayi,duk basusan irin uban aikin data tashi ta saba dashi bane,hakanan bata taba samun sararawa ko salamar aiki ba sai bayan data auri khalipha
"Mero kenan,aikin kuma ai da yana kisa da ban kawo iwar haka ba,bata jiki kuma mero idan a kanki ne ba kayana ba har fatata zan iya batawa,idan kin manta halaccinki a gareni ni bazan manta ba,ke kadaice wadda ta tsaya dani a sanda duniya ta juyamin baya,kin manta randa muka fara qawance,ranar da 'yan uwana suka taddani bakin rafi zasumin duka kika qwaceni daga hannunsu?" Dariya mero kawai take tana girgixa kai,ba shakka alheri danqo ne baya faduwa qasa banza,ita ta mance yadda abun ya kasance amma har yau gashi ita indon bata manta ba
"Tunda sai kinyi jeki kiyi ki dawo muyi hirar" aysha na dariya ta fice,ko su sunso hanata amma ta karbe hanjin ta gyarashi fes ta kuma dorashi kan wuta,sai data gama suyar a sannan rana ta dan fito tacewa meron bari taje ta dawo ta duba baquwarta.
Sanda ta koma ta tadda hanan a bararraje ita da inna yelwa suna kwasar hira kamar sun jima da sabawa,har tayi wanka abinta ta kuma karya da lafiyayyen kunun gyada daya sha madara da kuma qosai,idanun inna yelwar a kanta tunda ta shigo take kaffa kaffa da ita,kiran daya daga cikin surukanta ta kira ta hadawa ayshan ruwan wanka
"Jeki abinci inna karima,zan iya hadawa da kaina" ta fada tana zare hijabin jikinta
"Banda abinki indo da kin bari ta hada mikin,inake ina jan ruwa yanzu" dariya ma maganar ta inna yelwa ta bata,bata mantawa akwao sanda take wani azababben zazzabi haka ta tasota gaba kan sai taja ruwan,data gaya mata tana jin jiri ne tace ko zata fada cikin rijiyar sai taja,haka kuwa akayi wanda da qyar tayi guga uku,tana cikin na hudun jiri ya debeta gugan ya koma rijiyar,ita kuma Allah ya kawo mero a dai dai lokacin ita ta riqeta,bata tankawa inna yelwar ba ta daura zani da hijabi ta fice abinta ta debi ruwanta cikin babban dakin girkin da aka yi musu taja ruwa ta sirka ta shiga bandakin da aka yi cikin daya daga cikin dakunan dake falon inna yelwar,wanda ta shaida mata shine nasu da zasu dinga sauka a ciki.
Tana zaune tana karyawa jifa jifa tana duban inna yelwa,wadda ta taqarqare tana faman jansu da hira,ita a yanzu bata yadda ba qaunarta take?,haka aysha kewa kanta wannan tambayar cikin mamaki,data gama tare suka fice da hanan,wannan karon maimakon gidan mero gidan inna kulu suka nufa,shima dai gidan tun daga waje tasan tabbas aikin khalipha ya sauka ta kanshi,sanda ta gansu ita dinma da yake ba baya bace wajen son abun duniya kamar zata goya ayshan,itadai kallon kowa take
"Mamarki kuwa ina zaton yau zata shigo garin" cewar inna kulu,da mamaki take duban innan,tunda suke bata taba sako mata zancan innarta a tsakaninsu ba sai yanzu,bata ce komai ba wanda hakan yadan sanyayar da jikinta saita sauya hirar,awa biyu kawai sukayi mata suka wuce gidan sunan,a can hanan ta sake abinta,ta dinga yiwa mejego da 'yan suna hoto,ita abun qayatar da ita yake,da yake su iyaye da kakanni 'yan haifaffun cikin gari ne,kusan bata da wani qauye da zata nuna tace na kakanninta ne.
Duk hidimar nan da ake hankali da tunanin aysha na kan khalipha,tana shirin tada sallar la'asar taji shigowar saqo,cikin hanzari ta sanya hannu ta dauko wayar tana dubawa
_ina cikin aminci da kulawar ubangiji,na gode qwarai da kulawa_
Haka kawai taji amsar bata gamsheta ba,amma don kada ta takura shi saita haqura ta tada sallarta.
A ranar suka koma makaranta da yammaci lis,wanda motocin daukarta ma su sukayi jiranta,tana jin zuwan umminta garin a sanda suke shirin ficewa daga takai din,saidai ko kusa ko alama bata kwantanta dosarta ba bare taje wajenta.
Koda wani satin ya kewayo taje gida weekend kuma gida taje wajen daddy,tayi sa'ar samunshi a gida kuwa,sun jima suna hira dashi sosai,wanda hakan ya baqanta ran mummy,irin ci gaba da sauyin da take gani tattare da ayshan ya soma tabata,saita tuna asma'unta,wanda kusan rabin wahalarta ta dawo wuyansu,bata tabaji aysha tace ehmmm dazai nuna tana cikin wani hali ba bare takai ga furtawa har duniya ta sani.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Qarfe biyar ne na yammacin ranar,suna zaune ita da mummyn ta a falon samanta,kayanta ne da suka zo daga lagos a bude suna lissafi ita da mummyn na kudaden kayan da sunan wadanda za'a rarrabawa.
Saman ya hawo yana amsa waya da alama shigowarsa gidan kenan,baiyi ko sallama ba ya ratso falon,suka hada idanu da mummyn,baiko nuna alamun ya santa ba ya samu daya daga cikin kujerun falon yayi zamanshi yana ci gaba da wayarshi,dif asma'u sukayi ita da mummyn ganin ya sanyasu gaba yana waya,sai daya kammala sannan yace
"Barka da yamma" yayi maganar yana latsa wayarshi ba tare daya nuna da mummyn yake ba,hakanan ta amsa saboda tasan da ita din yake,irin gaisuwar da ada idan yazo wajen asma'un yake maya kenan,banbancinta da waccar kawai yana kallonta yake gaidata,a sannan data danyi qorafi sai asma'un tace yanayinshi ne haka,haka mummyn ta qyale maganar ta biyewa son ran asma'un.
Mai aikinsu ya soma qwalawa kira,cikin mintina qalilan sai gata ta shigo,cikin girmamawa ta risina masa ya gaya mata abinda zata kawo mishi,dole mummy ta yiwa asma'u sallama,ganin abun na hamid ba girma ba arziqi.
Sanda mummyn ta fita mai aikin ta shigo ta shirya masa komai sannan ta fice,wata sabuwa kuma ya samo don tuni ya sallami wacar farkar tasa ya gaji da ita,idanunsa nakan kayan da salma ke lissafawa ba tare data ko dubeshi ba,lissafi yake cikin ranshi,so yake kawai ta kulashi suyi wani abu ta yadda zai samu damar cewa ta masa asarar wani abun ya debi lesunan gabanta ga kaiwa budurwarshi.
Tana sane taqi kulashi,don a yanzu ta gaji da hamid ta gaji da aurenshi,kamar ita asma'u tana ganin bai cancanci ta rayu da hamid cikin irin wannan uqubar ba,tana da kyau,tana da gata tana da usuli,ba shakka hamid bai cancanci ci gaba da zama da ita ba.
"Ke...wato saboda wuyanki yayi kauri kina ganin mutane baki iya musu sannu da zuwa ba ko?,kuma saboda rashin tarbiyya a gaban babarki amma bata tsawatar miki kota nuna miki rashin dacewar abinda kika aikata ba" abinda bai sani ba shine,ita kanta asma'un dama hanya take nema,saboda hama ta miqe a fusace cikin daga murya tace dashi
"Dakata hamid,karka sake kiran uwata saboda ita din ba sa'arka bace,sannan rashin tarbiyya aikao za'a tambaya wannan,tunda baka iya zama da matarka ba kaga kuwa daga wajen tsoho aka...." Bata kai aya ba ya wanketa da wani lafiyayyen mari
"Karki sake ki qarasa,wanda kike shirin zagi shi ya bada kudin da kika gani kika maqale min"
"Ni ka mara hamid?,...."
"An marekin ko kina da abinda zakiyi?"kai take kadawa kuka kamar zai qwace mata
"wallahi zakasan ka mareni,ka mari aurenka,yau saika sakeni,saika bani takardata" wata wawiyar dariya ya saki yana jan tsaki,komawa yayi ya zauna saman kujerar daya tashi a kai yana kwance agogon hannunsa mai tsada ya sanya hannunshi cikin abincinsa
"Aikin auru kenan har abada,idan ma kina mafarkin zan sakeki ne to kinyi kuskure,don ni ba shashasha bane,nasan ciwon kudina" daga haka yakai abincinsa baki ba tare daya sake bi ta kanta ba.
Dakinta ta shige cikin kuka ta dauko jakarta da mayafinta ta fito,ko kallonta baiyi ba,itama hakan yayi mata dadi,saidai bata gane manufar sharetan da yayi ba sai data je bude qofa taqi buduwa,sai daga bisani ta gane muqulli ya saka mata,dawowa tayi gabanshi cikin hargagi ta tsaya
"Ka tashi malam ka budemin qofa,don wallahi daga yau na gama aurenka na gaji"
"Ni kuma yanzu na fara aurenki wlh,don ba more komai cikin abinda na kashe miki ba" wani qululun baqinciki ne ya taso ya tokareta,me yake nufi kenan?,yana son yayi mata qwalelen rayuwar da ta shiryawa kanta samu a gaba?,yana nufin fa bazai saketa ba,wanda hakan dai dai yake da cewa haramiyarta rayuwar da takewa kanta hasashe.
51
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
A hankali yake ratsawa ta cikin layin nasu har zuwa qofar gidan da yake mallakinshi ne,kuma a halin yanzu yake zaune a ciki,yayi kyau sosai cikin qananun kaya wanda ya dira jibgegiyar rigar sanyi a kai,yana saka key yana shirin bude qofar gidan wayarshi tayi qarar shigowar saqo,basu jima da gama waya da anni ba wadda ta tashi zuwa saudiyya don tayi umara,wayar ya zaro daga aljihunsa yana dubawa,murmushi ya saki a hankali yana karanta abinda saqon ya qunsa,a qalla ya dauki wasu kwanaki bai.maida.mata da amsa,yayi kuma hakanne saboda ya auna yadda ta damu dashi,shin abinda zuciyarsa take raya masa haka ne?,wani irin yanayi da bai taba hasashen shiga irinsa ba akanta ya samu kansa,bashi da shakku kuma ko kokwanton cewa wannan ba komai bane soyayya ce,yadda yake ji din ya tabbatar da cewa ba qaramin kamu tayi masa ba,yaushe hakan ta kasance duka bazaice ba,yana tsoron kar yayi zurfi da yawa abun ya zame masa matsala,ya kasa samun goyon baya yadda ya kamata daga gareta.
Sosai saqon yayi masa dadi,don har ya shiga parlour din gidan maimaita karanta saqon yake yana murmushi kafin daga bisani ya samu wajen zama.
Daga bangarenta kuwa tana zaune gefan gadon anni bayan sun dawo daga rakiyarta airphort,wadda ta bar mata muqullin dakin nata a hannunta saboda ta tashi ne ran asabar sanda ayshan ke zuwa gida hutu,kasa aje wayar tayi daga hannunta sai juyata take tana jin wani iri babu dadi a ranta,batasan me yasa a duk sanda ta tura mishi saqo take kasa samun amsar sa ba,batasan dalili ba tana jin babu dadi sosai cikin ranta,ko wani laifi tayi masa?,damuwarta tana ganin ko bata rasa nasaba da qoqarin kyautata matan da yake yasa batason itama tayi masa wani abu da yake ba dai dai ba?,duk dai bata sani ba.
Gauruwar ajiyar zuciya ta sauke,jiki a sanyaye ta miqe ta soma kintsawa annin dakinta gami da gyara duk wani da tasan zai iya samun matsala kafin dawowarta,a qalla ta kusa kashe minti ashirin qwarara sannan ta sanya key ta kulle dakin ta sauko zuwa falon gidan.
Rahama,amal maryam harma da zeenrat dukkansu na zaune darshe darshe a falon,kowacce na sabgar gabanta kamar wadda ta samu gidan gyatuminta,hannun ayasha harde a qirji tabi kowaccensi da kallo ba tare da sun ankara ba,dukkansu mamaki suke bata,baya ga wani abu mai kama da haushi haushinsu da yake tasiei gami da mintsinarta can qasan ranta,saidai babu wadda ta taba nunawa haka cikinsu,saboda tana ganin nata da wannan hurumin.
Bata cewa kowa komai ba ta ratsasu zata shige,saboda kacokam amanar gidan anni ta danqa a hannunta ne,wanda hakan tasan ya bata ransu duk da basuyi magana ba,saidai fuskokinsu sun nuna,wani tsaki taji rahama ta ja,bata waiwayo ba bare ta nuna tasan da ita take,tunda suke sallama da annin take wani cika tana batsewa.
Cikin lambun gidan ta samu waje ta zauna,tana son yanayi da iskar wajen,ita kadai wajen shuru,jifa jifa tana tunanin rayuwa da abubuwa da dama da suka shude daga cikin rayuwarta,tun wancan sati taso ta sake zuwa gida taga daddy har ta gayama khalipha saidai bata samu zuwa ba,sabida wancan karon tun ranar lahadi ta koma makaranta saboda monday takwas na safe tana da lacture,ajiyar zuciya ta sauke ta soma danna wayarta,number din anty safiyya ta nema ta kirata,don sukanyi waya duk bayan wasu kwanaki,ko bata kira ta ba ita zata kira,bugu uku aka daga,murmushi ta saki saboda kukan al'amin daya fara yi mata sallama
"Me aka.yiwa dan gida na anty?" Cewar aysha tana murmushi
"Hmmm,rigima kawai yakeji aysha wannan dan gidan naki sai a hankali"
"A lallabamin shi al'amin baya kukan banza" dariya antyn tayi sannan suka soma gaisawa
"Kin shiga wajen daddy ne?jiya ban ganki ba inata tambayarki mummy bata cemin komai ba"
"A satin nan nakeson shiga"
"A'ah,karki cemin bakisan baida lpy ba,jiya fa a asiniti muka wuni daxu da safen ya koma gida" idanu ta fiddo cikin mamaki,don ita ba wanda ya gaya mata
"Me ya sameshi anty?,wallahi ban sani ba ba wanda ya gayamin"
"Wani irin zazzabi ne mai naci wlh sai da aka qara masa ruwa"
"Subhanallah,ai kuwa yau ba sai gobe ba zanje na ganshi,wallahi anty banda na kiraki mummy bata gayamin ba" ajiyar zuciya anty safiyya ta saki,wato har yau mai hali baya fasa halinsa kenan
"Allah ya kyauta,shikenan idan na samu dama nina zan shigo,idan ban shigo yau din ba sai gobe"
"To aunty,Allah ya bashi lafiya" suna kammala wayar ta miqe,hankalinta duk sai taji yaqi kwanciya,tana qaunar daddy kamar nata mahaifin,shine mutumin daya soma saka maqullin alkhairi ya budewa rayuwata dukkan wata qofa da a yanzu ta samu kanta a tsaye,kai tsaye cikin gida ta nufa ta isa sashensu,cikin qanqanin lokaci ta shirya tsaf,kana dubanta kasan ta samu dukkan wata dama ta rayuwa,duk aninda ke sanye a jikinta mai aji da tsada ne,har yau tana jin gajiyar kayanta dake jibge ne cikin gidanta wanda ita ka ta batasan iya adadinsu ba,saidai ba makeup ko daya a fuskarta.
Daya daga cikin muqullan motarta da anni ta damqa mata ne sanda zata tafi take mata fadan ajiyesu da tayi bata taba hawan ko daya ba,saita gangaro zuwa sashen annin,zuwa yanzu daga maryam sai amal da zeenart a falon,amal na kwance tana charting,maryam.na zaune tana kallo,yayin da zeenart ke riqe da kwanon farfesun kayan ciki wanda yake a mazaunin abinda za'a hada cikin anincin dare aci amma tsabar zalama da son zuciya da aka saba ta kasa jira,sam ta kasa zaman gidansu duk da jan kunnen da babanta yayi mata na kada ya sake ganin qafarta gidan annin tunda har khalipha ya wulaqantasu amma ta kasa jurewa,don tace ko dadin da take ci gidan annin ai babu a gidansu,ko iya shi ta samu ai ta more,qasa qasa amal ke kallon ayshan,tayi mata kyau komai nata mai aji da burgewa,duk abinda tayi saiya nuna maka ita din ta dabance mai ilimi da kuma aiki dashi,kitchen ta wuce ta tadda bara'atu daya mai aikin tasu,don inna atika da ita aka tafi umarar wannan karon,da fari anni cewa tayi yayi visa din mutum biyu bayan ita,ko amal da zeenart,ko amal da maryam din,ya amsa mata da to kawai,amma harga zuciyarshi baya jin zai iya cire kudinshi ya biyawa wata daga cikinsu zuwa saudiyya,kosu ko iyayen nasu,saboda haka kawai sai passport din ya aiko mata dashi da komai da komai na baba atika,dama ya jima yana son kai matar,saboda yadda anni kejin dadin zama da ita,uwa uba riqon amana da gsky,hakanan annin bata taba kuka da ita ba,itama annin data gani bata ce masa komai ba bare tayi qorafi,tasan wannan abubuwan da suka faru shekarun baya har yau ke tsikarinsa,ba abu bane na mamaki,dafi ne ko ace gubace da duk sanda ya tuna take taso masa,tama godewa Allah da yakanyi musu alkhairi lokaci bayan lokaci na abinci da sutura,don da fari yadda ya birkice bata zaci tsinkensa zai bari su mora ba,shi kuwa yayi hakane saboda darajar annin da umarnin data bashi wanda bazai iya tsallakewa umarninta ba,da shawara ce da da sauqi.
"Kardai fita zakiyi?" Bara'atu ta tambayeta
"Eh wallahi zanje dubiya ne....don Allah saqo zan baki,idan haidar ko mus'ab wani daga cikinsu ya shigo kice masa ina gidan daddy,amma bazan jima ba can zan dawo,akwai tamfofi da anni ta bayar za'a dinka guda uku tace telanta zasu kaiwa su sun sanshi"
"To a dawo lafiya,Allah ya tsare"
"Yauwa amin" nan ta juya ta fice,koda tazo fita itama bata bi takan kowa ba,sai kallo da kowacce take binta dashi a sace cike da baqinciki kishi qyashi da kuma hassada,maryam ce taja tsaki tana gyara kwanciyarta
"Shi abba yasan khalipha zaiyi kudi ya kasa taimakonsa,ai gashinan yanzu suna ganin arziqi saidai asan mana" take fada cikin zuciyarta
"Ya isheki haka malama,ya muna zaune muna hutawa zaki damu mutane da tsaki ne?,wai shin dawa ma kike ne?"
"Da uban wanda ya tsargu" ta fada tana gallawa zeenart harara,ai kuwa saita aje kwanon hannunta ta miqe tayo kan maryam din
"Ni kike zagi ko uba na?"itama tsaye ta miqe
"duk wanda kika zaba,aikin banza kawai,da kike wannan haqiqancewar wani kika fi har da zaki yiwa wani iyaka dayin yadda yaso,kin isa ki hanani tsaki ko cika gidan nan zanyi da tsaki?,ina cewa babu wanda gidan yake mallakinsa a cikinmu bare wani ya damu wani" nan fada yaso kacema tsakaninsu,sai suka hau 'yar gore gore,rahama ce ta leqo ta gansu sunayi,kallon banza ta watsa musu sannan taja tsaki ta juya ta koma dakinta ta maida qofar ta rufe,ita yanzu duka ba wannan ne yake damunta ba.
Aysha kam bata masan me suke ba,sanda ta fita gidan ba driver ko daya,duk sun tafi rakiyar anni kuma babu wanda ya dawo,malam shehu kuma ya tafi kasuwa cefane,hakanan ta taka zuwa bakin daya daga cikin motocin nata,ta tsaya gaban qaramar ciki tana dan dubanta,bismillah tayi ta saka muqullin ta bude ta shiga mazaunin driver,sai take jin fargaba,tana jin kamar ba zata iya ba,karon farko da zata soma driving,duk da ta jima da iyawa amma bata taba tuqi ba,saita rufe idonta ta karanto addu'ar hawa abun hawa,hakan yasa mata nutsuwa,ta maida qofar ta rufe,ta tashi motar ta daidaitata ta dan danna horn,mai gadi ya bude nata gate din ta fice a hankali cikin nutsuwa.
Sanda take fita su haidar na shigowa,mus'ab ne ya nunawa haidar ita,mamaki ya kamasu,suka dinga yi mata dariya mus'ab na fadin
"Wai yau anty da driving?ko ina zata oho,bari ta dawo yau zata sha tsokana"
"Ni kaina naso muna nan zata fita" haidar ya fada yana dariya,don basa manta yadda take da tsoron driving da kanta,taga shigowar motocin,sai taji kaman ta tsaya ta yiwa daya daga cikin direbobin magana su kaita,sai kuma kawai ta wuce abinta.
Tun daga harabar gidan haidar ya soma jin kaman hayaniya,saboda haka yabar mus'ab anan ya shige zuwa ciki,sanda ya shiga sa'insa tayi nisa,cikin fusata ya katsa musu tsawa nan take kowacce tayi shuru
"Wannan wanne irin iskanci ne da zaku maidawa mutane gida gidan karnuka?,toko wacce ta shiga taitayinta bana cike da rashin mutunci,ku bace ku bawa mutane guri da'alla ko kowacce ta wuce gidansu" hakanan maryam da zeenart suka wuce zuwa dakin suna qananun maganganu da gunguni,amal ya duba wadda ke zaune duk taqaddamar da ake
"Ke ba zaki tashi ba kenan sai nayi quli quli dake!" Ya fada.mata a zabure,ba shiri ta miqe itana ta wuce daki,don tasan halinsa sarai idan ya juye kaman khalipha haka yake komawa ba sauqi,dogon tsaki yaja sanda mus'ab ya shigo yake tambayarsa abinda ke faruwa,yana shafa tsakiyar kanshi yace
"Wadan nan mahaukatan yaran mana,ni na tsaya ma tambayarsu neke faruwa na kora kowacce,zasu zo suna mana hauka kaman gidan su" yana fadin maganar yana wucewa kitchen.
Cikin zuciyarta take hamdala sanda take shigowa layin nasu,sai kuma ta sakarwa kanta murmushi tana dariyar tsoro irin nata,yadda ta dauki abun ma duka ashe baikai haka ba,horna tayi cikin minti daya mai gadin gidan daddyn ya bude mata qifa ta sanya motar tata ciki,tana cikin rufe motar bayan ta fito adaidaita ta shigo gidan,saita daga kai cikin mamaki tana duban adaidaitan,asma'u ce ta fito daga ciki tana miqawa mai adaidaitan kudinsa,canji ya miqo mata saita watsa masa wani kallo
"Kai bana son iskanci yanzu zan saka ayi ma duka kana dai ganin cikin gidanmu ka shigo,yaya za'ayi ka dauki dubu daya daga inda ka daukoni zuwa nan,ko an gaya maka satar kudin ake?"
"Amma dai hajiya aiba haka mukayi dake ba ko?,drop kika ce bakyason na dauki kowa,a qa'idama kudinki sunfi haka,kuma wallahi kibar ganin gidanku na shigo baki isa ki dakeni akan haqqina ba" ashar ta maka mishi tana fadin
"Yau zakasan ubana waye zakaga qaryar iskanci" shi kuwa ganin haka saiya fito daga adaidatan nashi yana fadin idan ta isa tasa a dakeshi din saiya farke mutun wallahi ko waye,kallo daya aysha tayi masa ta karanceshi,irin matasan nan ne masu zuqe zuqe,askin kanshi kawai ya isa ya gaya maka wayeshi,a hankali ta tako ta saitin matashin tayi sallama,saiya tsaya da hayagagar da yake yana dubanta cikin dan layi,kwarjini tayi masa,haka shigarta ta banbanta data asma'un,amsawa yayi ta bude jakarta ta ciro dubu biyu sabbabi kar,wanda tun wancan satin ta ciro su a atm ta yiwa anni siyayyar tafiya a matsayin tata gudunmwar,duk da babu abinda ta rasa amma ance gaida mai gaidaka,miqa masa tayi sannan tace
"Kayi haquri don Allah malam,dauki motarka ka tafi" saiya amshe yana cewa
"Allah dai ya biya,kinga inda akasan arziqi,da alama wannan ba matsiyaciya bace irinki,ke ina jin ma ke 'yar riqo ce ko mai aiki a gidan don irinku sunfi kowa yin haka,matsiyaciya mai qaryar arziqi" ya shuga babur dinsa zai tayar,saita yunqura zata biye masa da sauri aysha ta damqe hannunta,qamshin turarenta da laushin tafin hannunta ya sanya asma'un waiwayawa tana dubanta
"Ba girma da mutuncinki bane anty,bakiga a yanayin da yake ciki ba?" So tayi ta wanke ayshan tas,saboda maganganun daya yaba mata sun qona mata rai sosai,to amma da wani abu ya fado mata a rai wani quduri da ayau takeson ta cimma saita hadiye komai
"Da kin barni na nunawa dan iska iyakarsa ai,basu da mutunci 'yan adaidaitan nan,koda yake ke dakike hawa saikinfi kowa sani ai"murmushi kawai ta saki
"Ki qyaleshi kawai,mun yini lafiya?" Ayshan tace da ita sanda suka soma takawa zuwa ciki,da qyar asma'un ta hadiye abinda ke damunta ta dan saki fuska ta amsa,wanda hakan yayi mata dadi
"Indo motarnan bata rufu ba fa" cewar usama wanda ta barshi yana duba motar daddy data yi parking kusa da ita
"Oh,ohkey,ina sauri ne zanwa mai adaidatan can magana naga kamar a buge yake,don Allah dan rufemin usama idan ba damuwa ka miqo min key din cikin gida"
"Toh ba matsala" ya karba yana yin gaba,su kuma suka cu gaba dayin cikin gida,saidai asma'u ta kasa cewa komai,mota kuma wacce iri?,ina ayshan ta samu mota?,kasa haqura tayi sai data waiwaya taga motar sanda usman ke rufeta,daskarewa tayi wani malolo ya taso mata wanda ta kasa hadiyeshi
"Mota kikayi aysha?"murmushi tayi
"a'ah,tunta lokacin bikina khalipha ya bani,bana hawa ne dai kurum" kan uba,wanne irin kudi wai gayen nan ke da shi ne?,asma'u ta furta cikin ranta,kaman baisan ciwonsu ba?,ko baisan nawa motar take ba,lallai ba shakka ya zame mata dole tayi wani abu,ita ya kamata ace tana cikin wannan yanayin ba aysha ba,taya zata zamewa aysha tsanin da zata taka ta cimma wani abu a rayuwarta?,da wannan saqe saqen zucin suka isa falon,wanda asma'u bata samu damar sake cewa komai ba.
52
Anty halima,anty kubra da anty lubabatu na zaune a falon,da fari sun soma hayaniyar ganin asma'u ganin shigowar aysha ya sanyasu rage hayaniyar tasu,dukkanin idanunsu na kan ayshan,kowa da irin kallo da yake mata,musamman anty halima da komai na ayshan ya tsone mata ido
"Ashe ana ganinku?" Cewar anty luba tana duban ayshan,tana neman abun fada,murmushi ayshan tayi
"Ana ganinmu mana anty luba,makaranta ce kawai ke sakawa wani zubin bana zama available koda yaushe,sai weekens nake dawowa gida" tabe baki anty halima tayi
"Kuma a haka ake zaman auren?" Dubanta aysha tayi,ta karanceta tsaf,ta kuma gogu da zama dasu hanan
"Eh...ba wata damuwa bace ko matsala ai idan akwai fahimtar juna tsakaninka da abokin zamanka"toh baki yasan abun fada baisan me za'a maida masa ba,sai maganar ta dan yiwa anty halima zafi,tunda suke da aysha wannan ne karon farko data soma maida mata amsa dai dai da maganarta,ta fuskanci amsar ta shigeta dai dai yadda ya kamata,don haka saita miqe tana cewa
"bari na qarasa na duba jikin daddyn" ba wadda ta amsa mata.
Da sallama ta shiga falon daddyn,yana zaune qasan carfet ya jingina da kujera,mummy na gefanshi tana hada mishi abinci,a ladabce ta qarasa gabanshi ya zube tana gaidashi da dubashi da jiki,fuskarshi fal da fara'a yake amsa mata,sannan ta waiwaya rana gaida mummy,da qyar take amsa mata,itakam a rayuwa ta rasa me ta yiwa mummyn,idan ma har zamansu ne tare bataso a baya ai zuwa yanzu yaci ace ta aje komai tunda tabar musu gidan,zata tashi daddyn ya tsaidata,hira suke sosai wadda suka jima basuyi irinta ba da daddyn,taji dadin hirar tasu ita kanta ba kadan ba,daga bisani tayi sallama da daddyn bayan ta aje masa kudi masu yawa,da fari qin amsa yayi yace shime bata ne ai
"Nasani daddy kafi qarfinsu,amma abinda kayimin a rayuwa kafi qarfin komai a wajena,badon baka dashi ba na baka,saidon bansan me zan baka din ba,amma wannan ka amsa daddy kasa min albarka ka nuna jin dadinka wannan shine kadai zai faranta min ,ya kuma tabbatarmin da kaji dadin kyauta ta"
"Shikenan indon baffale,Allah yayi miki albarka ya albarkacu rayuwarki,jiyan ma munyi waya da maigidan naki ya dubani da jiki,Allah yayi muku albarka"
"Amin daddy" ta amsa kanta a qasa tana jin wani abu cikin ranta,yaushe khalipha ya kira daddyn amma ita ya shareta,toko laifi tayi masa?,da wannan tunanin ta baro sashen daddyn ta dawo sashen mummy,asma'u ta tadda kawai a falon,sai anty halima dake dakin mummy tana bacci,saura duka sun tafi,da murmushi kan fuskarta ta dubi ayshan
"Ina mai gidan ya kika barshi?"
"Yana lafiya" ta bata amsa fuskarta a sake,saidai zuciyarta cike fal da mamaki,dama akwai sanda asma'u zata tambayi lafiyar khaliphan,tsaki asma'un taja wanda ya katse tunanin ayshan ta sauke wayar data kanga akunne
"Pls aysha bani aron wayarki don Allah zanyi wata waya,bashi nake bin wata mata idan na kira taga numberta ce sai taqi dagawa" wayar tata ta ciro daga jakarta ta miqa mata sannan ta miqe,alwala dama takeso ta daura zatayi sallar la'asar ,don haka ta shige toilet din dake parlour din donta daura alwala.
Cikin hanzari ta dauki abinda zata dauka a wayar sannan ta fita ta aje mata wayar tana murmushi cikin ranta,sanda ta fito daukar wayar tayi ta sanya cikin jakarta sannan ta tada sallah,bayan ta idar ta yiwa mummy sallama ta baro gidan.
Tana cikin revers zata fice daga gidan taga anty halima da asma'u sun fito,da alama wani waje zasu je,hakan ya sanya ta dakata har suka qaraso gab da ita,cikin murmushi tace
"Anty naga kamar wani waje zaku"
"Eh ya akayi?"
"Ku shigo saina rage muku hanya" ta fada tana bude musu qofar motar
"A'ah,jeki kawai" anty halima ta fada tana yin gaba asma'u ta bita a baya,sai dataga sun wuce sannan ta tashi motar itama ta fice a gidan tana girgiza kai kawai cike da mamakinsu,har yau ace jiya iyau alqarasu?,Allah ya kyauta ta furta a sarari sanda take hawa saman titi.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Duk yadda yaso daurewa cikin kwanakin gaba daya juriyarshi ta qare,ya tabbatar wa kansa da cewa soyayya ce ta kamashi,soyayya aysha ce ta masa kamu bana wasa ba,irin soyayyar da bai zaci zai bawa wata diya mace irinta ba,cikin daren ya kasa bacci gaba daya sai juyi da yakeyi,ji yake idan har baiji muryarta ba wani abu xai iya faruwa dashi,dole ya janyo wayarshi yayi kiran layinta.
A lokacin itama tana cikin falon sashensu tana karatu,don tun sanda annin ta tafi bata fiya zama a wancan falon ba,don gaba daya ta kame kanta itama saboda su rahama,sai taso ma sannan suke ganinta,tayi qoqarin dai killace duk wani abu daya kamata,tun randa aka rasa atamfar anni daya cikin ukun data bayar akai mata dinki,idanunta ta daga kawai ta dubi wanda ke kiran,sunanshi ta gani saman screen dinta yana yawo,wani abu mai kama da jan aji ya motsa mata,saita share kiran har ya katse,sake kiranta yayi karo na biyu,nan ma tana sane ta basar da kiran,don ta tabbata cewa lafiya lau ya daina kiranta da replying saqonninta.
Zama yayi daram kan gadonshi sanda yake sake kiranta karo na uku,jikinsa har dan rawa yake yana addu'ar ta amsa ba tare ma da yasan yana yi ba,baisan cewa haka ya damu da ita ba,baisan cewa haka yayi kewarta ba,baisan cewa haka soyayyarta ta kamashi da zafi ba sai yanzu,bata daga din ba sai gab da zata yanke ta kara a kunneta hadi da yin sallama,wata ajiyar zuciya ya sauke da qarfi a sarari wadda ta ratsa dodon kunnen aysha,saita lumshe idanu tana jin muryarshi yana amsa sallamarta
"Uwaishah...." Sai taji sunan yayi mata dadi qwarai har data lumshe ido
"Ya Allah,what a nice name" ta fada cikin zuciyarta,tana jin zuciyarta na mata nauyi dauke da wani abu mai wuyar fassara,gaidashi ta soma yi ya amsa murya can qasa sannan yace
"Uwaish bakya kewata ko?,duk yadda naso na daure na kasa,wannan abun ba lafiya ba" idanu ta zaro don bata fahimci kalmarsa ta qarshe ba
"Me ya sameka kuma ya khaliphah?" Yadda ta ambaci sunanshi karon farko saida murmushi ya subucr daga lebansa
"Asiri kika yimin ko ayeesha?" Gabanta ne ya fadi sosai,tsoro ya kamata,sai zuciyarta ta karye,tuni hawaye suka tsattsafo cikin idanunta
"Ya khalpha?,asiri fa?,na rasa wa zan yiwa asiri saikai?,don Allah ka yimin bayani waya gaya maka haka?" Ta qarashe muryarta na rawa,dariya sosai take cinsa saiya kanne
"Ki jirani zan gaya miki" ya fadi yana katse wayar saboda ya kasa boye dariyarsa,baiso kuma taji,wayar na hannunshi yana jujjuyaya yana kallonta,iya muryarta kawai daya ji ta kwantar masa da.hankali sosai,hakanan cikin jikinsa yaji ayshan kuka take,saboda haka saiya rubuta mata texs
_idan kikayi kuka toki tabbatarwa kanki da kanki baki da gaskiya,hakanan idan kika damu to shima baki da gaskiya,just in kin yarda da.kanki fell free kawai,ki tanadi abinda zaki kare kanki idan nazo tuhumarki_
Saqon nashi ta dinga maimaita karantawa,saita samu kanta da share hawayen fuskarta,ta dinga maimaita karanta saqon nashi,ta wani bangaren yana mata kama da gaske,ta wani bangaren kuma yafi mata kama da wasa da tsokana,to amma yaushe suka fara haka da khaliphan?,sai taji matuqar kewarshi,tana son ganin fuskarshi mai kyau da kwarjini,hakan ya sanya ta ture litattafanta ta jawo system dinta ta shiga inda ya adana mata hotunanshi ta hau kalla daya bayan daya.
Nishadi yake ji sosai cikin zuciyarshi,saiya sauka daga saman gadonshi ya soma duba abubuwa masu amfani a wajensa ya fara hadasu waje guda,bayan ya hau net ya duba idan zai samu jirgin da zai tashi gobe zuwa nijeria ya sayi ticket.
Yana tsaka da wannan kira ya sake shigo masa,sai yabar abinda yake ya duba kiran,salim ne saboda haka ya tabbatar kiran mai muhimmanci ne
"Ya salim ya ake ciki"
"Am sorry boss,zarginka ya tabbata kan mutumin nan....yana amsar kudaden ne yana safarar miyagun qwayoyi,idan ya samu ribar yake dauka ya dawo maka da kudadenka,yanzu haka a rahoton da na samu sunyi niyyar fitar da wasu qwayoyi an kama yaransu,suna kuma gab da fadin sunayen su waye" idanunshi ya runtse sosai,dama ya jima yana tantamar bawa mutumin bashi,banda anni ta sanya baki tun a wancan lokacin da bazai bada ba,lallai ya zama dole ya samu mutumin
"Good job salim,ku jira zuwa ne gobe,but bana son kowa ya sani"
"Thank you boss,Allah ya kawoka lafiya"
"Amin" ya amsa yana katse wayar,ya cillata gefa yana furzar da iska mai dumi daga bakinsa,lalllai bazaiwa mutumin nan ta sauqi ba duk tsufarshi saiya gane baida wayo,ya bata mishi rai qwarao,amma daya tuna chaptershi da ayeeshanshi sai ya saki murmushi yaci gaba da shirinsa yana imagining haduwarsu gobe.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Kwance take saman gadonta,wanda a sannan kusan sha daya da rabi na dare,har a sannan hamid bai dawo ba,ta riga data saba da rashin dawowar tashi wani lokacima sai tsakiyar dare,a da tana damuwa saidai a yanzu sam babu abinda ya shafeta dashi,neman hanyar rabuwarsu kadai ya rage mata donta cimma muradinta.
Cikin shakku da tantama ta soma kiran number khalipha ta farko,nan na'ura ta sanar mata number a kashe take,hakan ya sanya ta tafi kiran daya layin nashi.
Sha daya da rabi da minti biyar wanda yayi dai dai da sha biyu da rabi da minti biyar a cyprus,kwanciyarshi kenan saman gadonshi,kaman bazai daula ba,amma ganin kiran daga nijeria ne ya sanyashi dagawa bayan tayi kamar zata tsinke,jin muryar mace sai ya bashi mamaki,muryar da bai santa ba
"Amincin Allah ya tabbata a gareka"
"Wa'alaikumussalam warahmatullah" ya maida mata da yaren larabci
"Ina fatan kana lafiya kamar yadda nake,duk da ni din sai a hankali tawa lafiyar"
"Amm,idan babu damuwa da Allah zan iya sanin dawa nake magana"
"Kasha kuruminka,ba wata bace illa asma'u,tsohuwar masoyiyarka"
"Asma'u?,asma'u?" Haka ya dinga nanata sunan a ranshi yana son tuna wacce asma'u,asma'un ce ta fado mishi,saidai ita din a yadda ya sani matar aure ce,akanme kuma zatayi kiranshi a irin wannan lokaci?,hasalima bata da numbersa
"Idan baka gane ba bari nayi maka dalla dalla,asma'u dai wadda ka fara cewa kana so tayi kuskure da gangancin hadaka da aysha bayan ita tafi kowa dacewa dakai" gaba daya sai yaji kaman yana magana ne da zararriya,kodai ba cikin hayyacinta take ba?
"Am lafiya kike kuwa?," yana nufin cikin hankalinta take,amma fuskanci maganarsa ba
"Lafiya nake,amma ba lau ba" zuciyarshi ce ta bashi shawarar sauraro kafin yanke hukunci,saboda haka yace da ita
"Uhmm....me yake faruwa?,ina kika samu numberta?"
"Khalipha kenan...."
"Point of correction..." Yayi saurin katseta
"Yaron oga dai" a shagwabe tace dashi
"Haba don Allah,na baka haquri fa tuni,amma bai wuce a wajenka ba?kuna yanzu ma kira nayi na sake baka wani haqurin don Allah ka yafemin komai ya wuce" Tsaki yaja a bayyane wanda ya isa kunnenta
"Me kika yimin da zaki bani haquri?,idan ma kina tunanin akwai wani laifi da kika yimin ma to babu,nikam khalipha saidai nayi miki godiya ma,domin duk abinda kike zaton kinyi alkhairi ya zamewa rayuwata da ita wadda kikayi nufin cutarta,karki sake kirana daga yau,don ni bana magana da matan mutane" yana kaiwa nan yayi hanzarin kashe wayar zuciyarsa na masa wasi wasin kiran asma'u,yanayin yadda take karya mishi murya dayi masa magana kadai ya isa ya karantar dashi akwai wata a qasa,yasan halin mata da yawa hakanan dai dai gwargwado ya karancesu,shikam saidai ya bawa wani labari,kiranta ne ya dinga shigowa babu adadi har sai daya gaji ya danna mata block,sai kuma ta koma sms wanda sukayita shigowa a jajjere,tsaki ya saki sannan ya kashe wayar gaba daya,bayan ya sake blocking yadda bata da damar sake tura masa wani saqo.
Kuka asma'un ta sako sanda ta fuskanci dukan abinda yay mata,saita zauna sosai saman gado tana sharban kukanta,tana jin cewa ba zata iya haqura ba dole tayi hanzarin fita daga gidan hamid,tana tsaka da haka ne hamid ya turo qofar dakin ya shigo,kallo daya yayi mata ya dauke kanshi bai tanka mata ba,sai daya gama sabgar gabanshi sannan ya dubeta da qyar
"Ke kuma waye ya mutu kika zauna kina yiwa mutane irin wannan kukan da daren nan?" Harara ta watsa masa,cikin izgili da rashin mutunci tace
"Ban sani ba,aikin banza aikin wofi,wallahi hamid ko kafi quda naci saika sakeni,don na gama zaman aure dakai"
"Ki iya bakinki tun bai jawo miki duka ba"
"Ai wallahi nabar zama ka taba lafiyata tunda bakai ka halicceni ba,banza wawa sakaran namiji dabai da aiki sai dukan matarsa" nan fa ya harzuqa,baiyi wata wata ba ya kasheta da mari sannan ya miqe yana huci
"Laifi nane dana sassauta miki kwana biyu kinga kina ci kina qoshi,to bari na sake jaddada miki tunda dama can ke jaka ce wadda ta fita makaranta da C.O,aure yanzu na fara,babu saki tsakaninmu har abada" ya juya yabar dakin,ashar takeson danna masa amma tana son lafiyarta,haka ta hadiye sai daya fice sannna ta dinga zage zagenta tare da cin alwashin gobe sai gida.
Zaune yake cikin office din nashi wanda yana sauka a qasar can ya soma zuwa,duk da yadda ya qagu matuqa yayi tozali da ita amma dole ya soma biyawa can,yantsunshi harde cikin juna,yayin daya dorasu saman table din gabanshi,ya kuma zubawa aljh kutama idanu yayin da alhj kutaman ya hada gumi sharkaf,ilahirin jikinsa rawa yake,tsananin tashin hankalin da yake ciki bazai misaltu ba
"Alhj kutama" khaliphan ya kira sunanshi kai tsaye abinda kusan bai taba yiba,kasancewar sunyi mu'amala da mahaifinshi kamar yaron mahaifinsa ne,amma hakan baisa ya daina bashi girma ba
"Alhj kutama" ya sake kiran sunan nashi
"Na'am yallabai,ranka ya dade Allah ya taimakeka...." Ya fada cikin dimuwa da rudu
"Duk abinda kake da kudina dana samu ta hanyar halas,nake baka saboda taimako darajar iyali da kake dashi kaje ka juya ta hanyar halas,duk sanda ka samu riba ta halas ka dawomin da kudina,nasan me kake dasu,haka mukayi dakai?"
"Wallahi yallabai akasi aka samu,ba halina bane"
"Alhj kutama"
"Na'am yallabai"
"Na bala nan da jibi ka tattara dukkan kudina dana ranta maka ka dawo min dasu,ban kuma yardaba ban lamunce ka kawomin wadanda ka samu ta qazantacciyar harqallarka ba" juya kai ya soma yi zai soma roqo da bashi haquri,cikin hanzari khaliphan ya dakatar dashi
"Banason naji komai daga bakinka,magana ce munyita dakai tsahon minti ashirin,duk cikin maganarka babu gaskiya a ciki,hakanan kuma ban sameka ba sai dana sanya aka yimin bincike a kanka,so ka riqe duk abinda kake da shirin fada kayi abinda nace maka" yasan halin yaron sarai,kaifi daya ne,ya riga daya karya duk wani abu da zai sanya ya tausaya masa ko ya janye hukuncinsa a kanshi,hakan ya sanya dole ya miqe yana jan qafa cikin tashin hankalin inda zai samo masa kudinsa ya fice,don dukka kudin ya tattara aka sayi cocain dasu da zummar idan suka wuce zasu samu riba mai yawa,sai gashi an kama yaran kuma suna shirin fadar sunanshi,tabbas daga shi har hamid suna cikin masifa,don har hamid din shima ya karbi bashin kudade masu yawa daga wajenshi,yace kuma dukansu su dawo masa da kudin,kuma baya jin a yanzu akwai kudin wajen hamid din shima,yace ya zuba kudin a wani kamfani da zasu dinga bashi ribar kudade mai yawa duk qarshen sati.
Waya ya dauka ya kira hamid din,yace kome yake yabarshi ya sameshi a gida,sannan ya wuce gidan shima afujajan cikin motocin da yake yawo dasu kamar wani gwamna,yaga alama talauci ne yakeson yayi masa saukar gaggawa alhalin bai shirya taryarshi ba daga nan har randa zai bar duniya,haka motocin suka dinga tafiya da sauri sauri,wannan burgar tashi da nunawa duniya shi lallai wani ne yasa sunanshi yayi suna yayi tambari,bayan kuma baikai inda yakeson ace yakai din ba,hakanan a wajenshi dukka yaranshi suka gado qarya da fafa.
Numfashi khalipha ya sauke yana sakin ajiyar zuciya gami da lumshe idanunshi,ya kara bayanshi da kujerar da hake kai yana istigfari,sosai ranshi ya baci matuqa,ya jima yana baiwa mutumin rance ga zatonshi yana amsa ne donya tallafi kanshi,duk da ya dade yana mamakin salon rayuwarshi,ya daukaki komai nashi bayan kusan qashin bayan arziqin nasa bashi ne,saidai ganin komai na tafiya dai dai tsakaninsu ya sanya ya kauda kai daga gareshi,daga bayane yadda kudim suke saurin dawo masa gami da gwaggwabar ribar da yake gaya masa yana samu a lokaci kadan kan kasuwancin da yakeyi ne yasa masa ayar tambaya,don duk abinda khaliphan zaiyi yakanyi takatsantsan da kaucewa haramun,saboda annabi S A W yana cewa haram a bayyane take hakama halal,saidai tsakaninsu akwai al'amura masu rikitarwa da shubha,wanda ya kiyaye wannan shubhar haqiqa ya kubutar da addininsa da mutuncinsa.
Bazai lamunci ko ya yarda ya ciyar da duk wanda ya danganceshi da haramun ba,walau kana aiki qarqashinsa ne ko kuma kankat mai gaba daya mahaifiyarsa da 'yan uwansa,saboda annabi S A W yayi bayani cewa,duk jikin daya ginu da haram,to wuta ita tafi cancanta da ita(wato wuta ita tafi cancanta ta cinye wannan tsokar,jan hankali a nan a garemu mata shine,muyi qoqari mu dinga tunasar da mazanmu koda yaushe su nemo halal su kawo mana halal,musamman yanzu da babu tayi yawa,albarka ta ragu cikin dukiyoyi da kayayyakinmu,don billhil azim maganar ma'aiki ba zata tashi a banza ba,duk wanda bai kiyaye haramun ba,ya yadda ake ci dashi a tufatar dashi asha dashi da haramun,to babu shakka ranar qiyama ya lissafa kansa cikin wanda wuta zata ci,saboda haka mu yiwa kanmu 'ya'yanmu da mazajenmu gata mu dorasu kan neman halali domin samun dace da tsira ranar da wata rai ba zata tsinanawa wata rai komai ba,matan sahabbai sun kasance kullum ta Allah idan mazanau zasu fita nema,sukan tsaidasu auce,yakai wane kaji tsoron Allah,ka nemo mana halak,don zamu iya haquri da yunwa amma ba zamu iya haquri da azabar Allah ba,Allah yasa mu dace)mutane da yawa sun shaida sirrin yauqaqar arziqinsa da albarkarsa shine kiyaye haqqin Allah da yakeyi a ciki,sannan kuma biyayya ga mahaifa.
Saida ya shiga toilet ya daura alwala sannan yaji zuciyarshi na sanyaya(ki riqe wannan 'yar uwa,a duk sanda kike jin bacin rai,ko wani abu ya bata miki rai,walau tsakaninki da mijinki ko wani daban,kije ki dauro alwala sannan kiyita karanta a'uzubillahi minash shaidanir rajim,da yardar Allah zakiji zuciyarki tana, sanyi)shauqin isa zuwa gida ya dawo mishi fil,sai ya zauna kan kujerar sofa din dake office din ya tura gajeran saqo,cikin 'yan mintina mutum biyu suka shigo,daya ya soma rufe mishi jakarshi,yayin da dayan ke tsaye saman kanshi,duqawa yayi.ya maida safarshi sannan ya saka takalminshi ya miqe yayi gaba suka rufa mishi baya suka fice da kamfanin gaba daya.
53
Tunda gari ya waye ranar bata shiga sashen anni ba,tana sashensu bayan ta gama duka gyare gyaren da zatayi ta sake kwanciya,ta ware fanka da acn dake falon duka saboda zafin da ake zubawa,wanda alamun zuwan damina duka sun gama bayyana,donko a jiya hadari sosai garin ya hada har aka tsammaci samun ruwan sama,saidai ruwan bai samu ba sai yayyafi da akayi wanda shi ya sake tada zafi a garin duka yau,da kuma wani sabon hadarin dake hadowa kadan kadan yana curewa waje daya gami da bada kala mai duhu,hakan ya sanya rana ta kasa samun dama fidda haskenta,qarfe hudu saura ta tashi daga bacci,ta daura alwala ta bada faralin sallah sannan ta shiga bandaki ta saki ruwa mai sanyi ba tare data sirka ba tayi wanka,hakan ya haifarwa da zuciyarta wani irin nishadi,zuciyar da gangar jikin dukka sukayi fes dasu,iskar dake busowa cikin windows din dakin tayi mata dari,sai taji tana bata wani sanyi na musamman dake ratsawa har cikin qwaqwalwa da zuciyarta.
Tana shafawa qafafunta mai murmushi ya subuce a fuskarta sabida tuna hirarsu da khalipha ta jiya,sassanyar muryarshi,yanayin maganarshi dake fita a nutse da sauransu,saita kada kai kawai tana dariya,itama sai taga wautarta,ba lallai yana nufin abinda ya fada din ba,don yanayin maganar bai nuna cikin zafi ko fushi yayita ba,bayan ta kammala ta shafa powder da man lebe kadan don kada ya dameta,jikinta ta feshe da turare sannan ta ciro kayanta da tuni dama sun rine da qamshin turaren wuta na kaya,doguwar rigar material ce cotton mai taushi yadda bazai dameta ba,saidai hannun rigar iya dantsenta ya tsaya,sai kuma mayafinshi wanda tayi rolling daya sauka mata har gwiwar hannu ya rufe hannun nata kenan bayan ta matse kanta da ribbom wanda yasha relaxer jiya,fuskarta ta kalla a mudubi,kayan sun mata kyau sosai,bata taba sanyasu ba saiyau,bata zaci ka zasuyi mata kyau haka ba,plat din takalmi ta sanya wanda ya dace da kayan sannan ta zira carbinta a yatsanta ta fito daga sashen.
Maryam ce kawai zaune a falon,saboda haka sallama tayi mata don fita haqqin addini,ganin ta amsa mata saita wuce kitchen ba tare data ce mata komai ba,don ta lura tunda annin ta tafi kowa kanshi rawa yake,dama ita maryam ba magana take mata ba,hakan ya sanya itama ta yi mata aji irin wanda ya dace da ita ta sanyata.
Bara'atu ke kiciniyar aiki ita kadsi,duk kitchen din a lalace yake kaman wanda akayi dafe dafe na mutum talatin
"Sannu da fitowar uwar masu gida" murmushi ta saki saita tuna da baba atika,tayi kewarsu sosai ita da anni
"Yauwa bara'atu sannu da aiki,ya haka gaba daya kitchen din ya kacame?" Ajiyar numfashi tayi sannan tace
"Ai kinsan aikin su waye,wallahi bansan me yasa suke abu ba bayan sunsan bai kamata ba sarai" sai aysha taji ranta ya baci,karo na farko tun sanda suka soma iskance iskancensu na kowacce ta dafa abinda ranta yayi mata,koda anyi girkin gida in general,koda su haidar dake yaran gidan duk abinda bara'atun ta dafa ci suke,bare ita da abinci bai dameta ba
"Kiyi haquri,komai mai wucewa ne,da zarar anni ta dawo naga wanda zaici gaba da yin hakan" aysha ta fada tana tausar zuciyarta,don bata son tayi musu magana sam,hannu ta sanya tana taya bara'atun gyaran kitchen din,sai da taga komai ya hau saiti sannan ta bar mata sauran,ta samu waje ta zauna suna jira jifa jifa,bayan ta zuba dan abincin da zata ci cikin plate.
Kadan kadan take tsakurar abincin suna hirarsu,bata wani ci da yawa ba zeenart ta shigo kitchen,tana ganin ayshan ta hade girar sama data qasa,tana yiwa ayshan kallon wata babbar naqasu a garesu,wadda ta kawo cikas da kuma hana ci gaban gudanuwar dukkan al'amuransu
"Bara'atu,maza maza dafamin couse jallop,ki saka nama da yawa a ciki yunwa nakeji" a ladabce bara'atun tace da ita
"Gafa abincin da kika asaka a aka dafa dazun baki cinye ba,sannan maryam da anty rahama dukansu an dafa musu abinci gasunan duk ba wanda ya cinye,ki duba ko wani abun a ciki zaiyi miki" ta fada tana buda mata fulasan dake shaqe da abinci
"Dalla malama ban tambayeki wannan ba,couse couse nake sha'awa shi nace ko dafamin"
"Ba za'a sake dafa komai ba a gidan nan sai Allah ya kaimu gobe" aysha ta fada hankali kwance kuma kari na farko tunda suka fara rashin mutunce mutuncensu,,saidai can qasan ranta a hasale take,ta karanci takunsu gaba dayansu babu abinda ke damunsu face tsantsar mugunta da almubazzaranci,saidai muguntar da qetar ma tafi yawa,waiwayawa zeenart tayi tana dubanta
"Au,harda su kaza a cin danqo?,ke kuma waya saka da ke?to bari na gaya miki tun ba'ayi nisa ba baki isa ba"cokalin hannunta ta aje sannan ta amsata
" na isa?,ban isa ba duka wannan bata taso ba ba'akai ga can ba,magana daya ce babu abinda za'a sake dafawa a gidan nan saidai idan har mun iya cinye duk abincin dake gidan nan muna da buqatar qari to wannan fa,barema nasan wannan abincin saidai a fitarwa da mabuqata a waje"
"Ke aisha!'muryar rahama dake takowa cikin kitchen din ta katsewa zeenart niyyar bata amsa da takeyi,hannunta harde a qirji fuskarta a dinke tsaf ta qaraso gaban ayshan,hannu kawai ta miqa mata sannan tace
"Bani muqullin dakin anni"sosai ta dubi rahaman cikin ido sannan tace
"Bamuyi wannan da anni ba"
"Ki bani malama ko,abina zan dauko a ciki"
"Idan kina da buqatarsa saidai ki jirayi dawowarta,saboda amana ce a gareni bazan iya wofantar da ita ba,ni dinma ban sake taka dakin ba tun randa na rufeshi"ta bata amsa tana janyo faranti ta rufe abincin dake gefanta,tsaiwa rahaman ta gyara tana dubanta cikin bacin rai
" ke ki saurara fa,naga alamun kina wuce gona da iri,saboda kinga an zuba miko ido kina yadda kikaga dama,toba tsoronki kowa keji ba"
"Duk saboda taga anni ta daure mata gindi ai take komai,ta fifitata a kanmu" zeenart dake cike ta fada
"Koma meya karki manta auroki akayi,a yau idan aka sakeki.magana ta qare,hakanan ana iya sauya mata amma dan uwa komai lalacewarshi lalala lalala"
"Don Allah anty rahama duka mai ya kawo wannan maganganun marasa dadi haka?" Bara'atu ta fada cikin tsoro da nuna rashin jin dadi,da hannu aysha ta dakatar da ita,murmushi ta saki tana dan kada qafarta kadan kadan sannan ta dubesu daya bayan daya
"Shi dan uwa suna ya tara ai,baku da labari?,da wani dan uwan gwara bare sau dubu?" Dukkansu sai kowacce tasha jinin jikinta,ba zasu so ace tasan komai game dasu ba,ganin karta ramfo wani abu ya sanya rahama sake yunqurowa cikin kurari tace
"Malama ki bani maqullin dakin uwarki anni tunda indai bana uwarrr........"
"Rahama!!" Dakakkiyar muryarshi mai cike da mazantaka ta karade ilahirin kitchen din gami da bada sautin amsa kuwwa,ba rahama ba hatta bara'atu da zeenart hantar cikinsu sai data kada,da hanzari dukkansu suka waiwaya bakin qofa,yana takowa ne cike da nutsuwa saidai kana duban fuskarshi zaka san cewa ran 'yan maza ya baci,tun kafin ya iso zeenart ta samu wajen jingina,yayin da rahama ta gyara tsaiwarta kamar mai shirin tarbar isowarshi saidai sam jikinta ne ke rawa takeson bawa kanta qwarin gwiwa,sai daya iso tsakiyarsu ya dubesu tsaf,sannan cikin wani irin sauti yace
"Matata?,kukewa haka a cikin gidanta?" Ya jefesu da tambayar yana binsu da kallo,zeenart kam babu bakin magana,sai rahama ce don kada ta bada kanta da shekarunta tayi qarfin halin cewa
"Haba khalipha?,kai bakagani ba kuma bakasan duk abinda take mana ba tunda anni ta tafi don kawai ta......"
"Will you shutup kosai nayi qasa qasa dake a nan" zaro ido tayi cikin mamaki,kalmar da bai taba gaya mata ita ba koda wasa,ko vanza yana dan bata girmanta ta wani bangaren saboda shekarunsu da suka kusa zuwa daya,waiwayawa yayi ya yiwa zeenart wani kallo wanda ya sanya take gumi ya rufeta
"Har da ke ko?....stupid,idiot....banda darajar anni da kuke ci ke kin isa kiga matata ma nare ki samu damar yin sa'insa da ita?banda kima da isar da anni ke dashi kin isa cin abincin gida na?,banda anni abincin gidana ko wanda na zubar ne bazan lamunci kuci ba" sai ya waiwaya wajen rahama
"Baki da damar da zaki nuna cewa anni wata ce a wajenki ko ke wata ce a wajenta,sanda muke wahala daga wannan mataki zuwa wancan na rayuwa kuna ina?,sanda muke tsakanin mutuwa da rayuwa kun taba tunawa damu?,kun taba kwana da tunanin ya rayuwar ayshatu zata kasance bayan kun sallamata a dangi?,to na meye a yanzu da muka samu nutsuwar zuciya da gangar jiki duka zaku kutso cikin rayuwarmu ku hanamu sukuni?,mu ba wawaye bane hakanan kyautatawa ba rashin sanin ciwo da darajar kai bane,saka sharri da alkhairi bai nufin ka manta komai daya faru,saka sharri da alkhairi bai nufin kai shashasha ne koka sarayar da dukka haqqi da mutuncinka" waiwayawa yayi ya dubi zeenart cikin kakkausar murya
"Kije ki kiramin dukkan yarinyar da tayi saura cikin gidan nan na baku minti biyu kacal" da hanzarinta ta fice,ba jimawa sai gasu sun dawo gaba daya,yatsunshi ya hada ya murza suka bata sauti sannan cikin kaushi yace
"Na baku nan da awa guda kowacce qarfe shida tayi mata cikin gidan mahaifanta,karku yadda na fito sallar magariba na samu daya daga cikinku...ko wacece kuwa...kome nisan da take dashi" ya qarashe maganar idanunshi yana kan rahama,tasan da ita yake ita da take nijer,wani abu mai tauri ta hadiye idanunta sun sauya launi saboda bacin rai,bai kuma bi ta kansu ba ya damqi hannun aysha da duka take jin babu dadi cikin ranta,tamkar ita ta zama sila kenan ta faruwar komai,batasan ya anni zata dauki hukuncin ba,kada hakan ya zama Silar tabarbarewar kyakkyawar alaqar dake tsakaninsu,haka suka ratsasu suka fice tana biye da shi.
A hankali ya tura qofar sashen nasu ya sanya kai tana biye dashi,sanyi da qamshin dake falon ya cika hancinsa ya haifar masa da wata nutsuwa ta musamman,suna isa falon ya aje jakar hannunshi ba tare daya saketa ba,idanunta ta daga ta dubi qwayar idanunshi,ta sauya kala hakanan kana dubansu kasan an tono wani abu dake zuciyarshi,sai ta zame hannyenta cikin sauri ya rungumoshi ta baya,kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya shi da ita,bacin ran daya tabashi sai taji duka babu dadi,bai kamata daga dawowarsa yaci karo da wata matsala ba,ya kamata zuwa yanzu ya samu hutu da kulawa da kuma dukkan wani kwanciyar hankali daya kamata,bata taba ganin bacin rai a fuskarshi kamar haka ba,bata taba ganin fadanshi kamar yau ba,da alama wannan gyambon dake zuciyarshi ne aka taba,sai taji zuciyarta ta karye,hawaye suka biyo kuncinta,wanda sukayi nasarar taba jikinsa,idanunshi na lumshe ya sanya hannunshi ya dawo da ita gabanshi,ya bude hannayensa ya sakata cikin faffadan qirjinsa ya maida hannayenshi ya kulleta gam,muryarshi can qasa yace
"Meye abun kuka?"
"Bai kamata ace wannan ne abu na farko da zaka tarar ba bayan ka dauki wani lokaci baka gida" ta furta cikin sanyinta da muryarta data bayyana kukanta qarara,tattausan tafin hannunshi ya sanya ya soma goge mata fuska,har a lokacin tana jikinsa
"Abu mafi ciwo shine abinda sukayi miki,me yasa kika tsaya saurarensu da banxayen maganganunsu?,me yasa bakiyu umarnin an fitar miki dasu daga gidanki ba?,ke din ba sa'arsu bace,darajarki da tasu ba daya bace.."
"Kayi haqur....." Ta fada cikin raunin murya da zuciya gaba daya,saidai bai barta ta qarashe furucin nata ba ya hade bakinshi da nata cikin wani irin zafin nama da ba zatan da bata taba tsammata ba.
A hankali ya zare bakinsa kana ya dan dafe kanshi
"Ya salam" ya furta cikin matuqar sanyi,da hanzari ta dubeshi duk da sanyin da jikinta yayi matuqa
"Me ya faru,ya khalip...." Ta kasa qarasawa tana dubanshi,dubanta yayi suka hada idani,duk da yadda kanshi ke sarawa amma hakan bai hanashi tuno yanayin daya shiga ba,idanu daya ya kashe mata kafin yace
"Kaina"
"Sannu am sorry,ka zauna pls" ta fada tana nuna mishi kujera hannunta daya riqe da nashi hannun,sai ya kalle hannayen nasu dake cikin na juna,ya daga yakai bakinsa yayi kissing kafin ya saki a hankali ya koma saman daya daga cikin kujerun ya zauna,tausayinshi take ji,ciwon kan da su suka zama silarshi,gashi kuma basu qyaleshi ba suna haddasa tashinsa lokaci zuwa lokaci,sunkuyawa tayi a nutse ta dauki jakarshi daya aje a wajen ta nufi bedroom dinsu.
Minti uku kafin ta fito ta sameshi idanunsa a rufe
"Ga ruwa can ko watsa ko zaka ji dadin jikinka" a hankali ya bude idanun nashi ya warasu a kanta,sun qara girma hakanan sun sauya launi,sai taji sun mata nauyi da kwarjini da yawa,kanta ta dan dauke tana basarwa,kunya na lullubeta sakamakon tunawa da tayi da abinda ya faru daxu
"Yau garin akwai zafi,hadarine tun jiya kuma ruwa bai sauka b...." Bata qarasa ba ta jita cikin jikinshi,saitayi sak kunya na addabarta,bakinsa yakai saitin kunnenta
"Ki shirya kayanki kafin na fito" a hankali ya saketa yana takawa zuwa cikn dakin gadon yana jin yadda kanshi ke sarawa,yasan mawuyacine idan baiyi jiyya yau zuwa gobe ba,yayin daya barta nan tsaye tana saqe saqen me yake nufi?,watsar da wannan tunanin tayi ta shiga kitchen dinsu cikin hanzari ta soma sama masa abinda zai saka a cikinsa mai sauqi da dad'i.
Har ta kammala komai ta shirya bata ji motsi ko fitowarsa ba,duk sai ta kasa zama,saboda haka ta shirya komai ta tura qofar dakin duk da yadda zuciyarta ke gargadarta.
Zaune yake daure da towel,hannunshi daya dafe da kanshi,yayin da daya hannun yake amsa waya,yanayin yadda yake amsar wayar ya tabbatar mata ranshi a bace yake,magana ta qarshe yayi ya katse kiran,sai ya sake kiran wata number,haidar ya kira yace su dawo gida shida mus'ab,sannan ya sake kiran wani layin shima yayi magana ta 'yan sakanni ya sauke wayar a kunnensa,kashe wayar yayi gaba daya ya ajeta gefanshi,idanunsa suka sauka akanta,ya saki qaramar ajiyar zuciya yana jin bacin ranshi yana zaganyewa,idanunsa ya lumshe cikin ranshi yana addu'ar Allah ya sanya ta zama sanyin idaniya a gareshi,ta fahimceshi ta soshi cikin qanqanin lokaci kamar ko fiye da yadda yake sonta
"Uwaishah!" Ya kirata cikin taushin nan dake kasheta,kasa amsa mishi tayi da.baki saida idanu,wanda hakan ya masa tasiri matuqa
"Taimaka min..." Sai.yayi mata nuni da ma'ajiyar kayanshi,ta fahimci me yake nufi,saboda haka ta miqe a nutse zuwa wajen shi kuma ya bita da kallo,kayan data sanya din sun amsheta sun burgeshi qwarai,sun fidda duk wata qira tata,wani azababben kishi daya sake sanya kanshi sarawa yaji ya saukar masa,saiya dafe kan nashi,har ta dauko kayan tazo gefanshi ta aje masa,ta juya da niyyar fita yace da.ita sanda ya.miqe ya ware kayan zai sanya
"Karki motsa ko ina,samu waje ki zauna" hakanan ta zauna inda ta tashi,ta dan kauda idonta gefe don kada ta kalleshi,ya fahimceta sarai,sai yaci gaba da sanya kayanshi har ya kammala,
Wata jaka ya janyo gabanshi ya soma hada wasu kaya cikin wata jaka,kayan abinci ta aje tana murza tafin hannunta
"Ga abinci nan" ta furta cikin sanyi da nutsuwa,kallonta yayi da idanun nan nasa dake mata kwarjini matuqa
"Ki shirya abinda zaki shirya nan da minti biyar" kamar zata tamnayeshi sai kuma ta fasa,koma meye ta sani bazai cutar sa ita ba,saita qarasa a hankali ta amshi jakar da yake saka kayayyakin a ciki taci gaba da sanya mishi,gefe daya ya koma ya zauna kawai yana binta da kallo ta qasan ido,duk wani motsinta yana biye da ita,duk da ciwon kan dake matsa mishi kadan kadan amma sai yake jin dadin kallonta fiye da tunani.
Bayan ta kammala.itama ta debi 'yan qananun abubuwan da take da buqata ta zuba a tata jakar,sai data gama tsaf ya juyo da niyyar sanar masa taga ita yake kalla
"Na gama" ta fadi tana neman wajen zama,saiya ciro wayarshi tana ji ya kira sunan mus'ab da haidar da alama da daya daga cikinsu yake sake magana,bayan ya gama saiya kashe wayar ya aje,yaci gaba da kallonta cikin zuciyarshi yana wassafa yadda zai dasa mata sonshi da qaunarshi mai tafiya da hankali da kuma ruhi,ba'a dauki dogon lokaci ba suka jiyo knocking,saiya miqe a hankali cikin mutuwar jiki ya nufi qofar fita yana cewa
"Ki sanya mayafinki ki taho" hijabi ta sanya saman kayan jikinta,ta dauki jakar hannunta sannan ta fito falon,suna tsaye su uku,haidar mus'ab da shi khaliphan yana miqa musu key
"Kada yarinyar da kuka sake bari ta zauna cikin gidan nan har anni ta dawo,ku kulle ko ina zanyi magana da securities din gidan"
"Toh yaya" haidar ya fada yana karbar muqullin
"Mus'ab shiga ciki ka daukon jaka ka sameni a mota" ya fada yana yin gaba tana biye da shi.
Motoci biyu ne tsaye suna jiransu,da kanshi ya bude mata mazaunin baya kamar yadda ya dinga mata wancan karon,ta shiga shima yabi bayanta,mus'ab ya sanya kayan a motar ya rufe sannna ya zagayo ya musu sallama bayan ya miqo musu kwandon abincin da ayshan ta hada wanda baici ba,bata sani ba koshi yace ya dauko din,driver yaja motar suka fita daga gidan.
Shuru motar ta dauka,idanunshi na rufe da alama ciwon kan ke takura mishi,duk sai taji bata ji dadi ba,ta dokanta ta ganshi sai gashi yazo cikin bahagon yanayi
"Sannu" ta furta cikin nuna damuwa da kulawa,idanunsa da suka qara girma ya ware a kanta,murmushi ya sakar mata wanda ya sake sanyata cikin rudu,hannunshi yakai ya dora saman nata hannun sai ya maida idanun nashi yadda suke,yana jin yadda laushin fatarta da dumin jikinta ke ratsa shi
Tafiya ce da bata wuce ta minti ashirin ba suka shigo cikin wata unguwa,a ido kawai ya isa yasa ka gane kyau da tsari da kuma yanayin wadata da jama'ar unguwar keda,sai takejin kamar tasan unguwar kota taba ganinta,a hankali motocin suka ci gaba da tafiya har xuwa qofar wani katafaren gida daya tilastata daga kai ta kalleshi,horn daya akayi qofar gidan ta wangale,sai a sannan taga yayi mata kama da gidanta da aka fara kawota.
A harabar aje motoci sukayi parking
"Zauna ina zuwa" ya fada yana ficewa,ta cikin motar tana iya hango abinda ke faruwa,kayan da sukazo dasu aka shiga dasu ciki har kayan abincinsu,tsahon minti biyar sannan ya dawo ya mata izinin fita,wannan karon hannunshi cikin nata suka dinga takawa zuwa cikin gidan,suna tafiya tana sake gane gidan dukda ba wani shahararren kallo tayi masa ba tun a wancan lokacin.
Kwandon abincin dake aje a falon ya sunkuya zai dauka tayi saurin dauka da azama,suka hada ido tadan basar sukaci gaba da tafiya zuwa wani sashe na daban wanda batasan dashi ba cikin gidan,idanu ta ware tana kallon ko ina,bai saki hannunta ba sai da suka dangana da wani bedroom wanda yafi kyau a kirashi da aljannar duniya,idanunta basu taba tozalin ganin dakin bacci mai kyau da aka qawatashi ba irin haka
"Barkanki da dawowa gidanki" ya fada yana shigewa toilet dake cikin dakin,tilas bayan ta gama kalle kallenta ta aje kwandon daura da ita ta samu waje ta zauna kan wata kujera dake can nahiya guda ta dakin saboda yalwar da dakin yake dashi.
Bai jima ba ya fito daure da alwala,tana lura da komai yake yana yine cikin juriya,wani saqo dake cikin dakim shimfide da abun sallah ya shiga ya tada sallah da alama shafa'i da wuturi xaiyi,don tuni sunyi magariba da isha'i a gida.
Ya jima saman abun sallar yana addu'a sannan ya shafa,ya taso cikin nutsuwa zuwa inda take zaune,gefan gadon ya samu ya zauna yana fuskantarta idanunshi akanta.
54
Duk wata juriyarta taji tana neman ta qare,saboda haka saita sauko ta soma zuba mishi abinci
"Sannu,ko zaka daure kaci wannan?" Kai ya girgiza mata yana bata hannunshi alamun ta taho
"Bashi nake buqata ba ke nake buqata...." Idanunta ta janye daga cikin nashi tana jin yadda zuciyarta ke zillo,tana addu'a cikin ranta,Allah ya sanya abinda take ji game da khalipha shima yana ji a kanta,Allah yasa yadda take fama da qaunarshi cikin zuciyarta shi dinma haka ne,tana tsaka da wannan tunanin ta tsinceshi zaune gefanta,yana gab da ita qwarai ta yadda har cinyoyinsu na gogar juna,hannunta ya laluba ya saka cikin nashi bayan ya fuskanceta sosai
"Uwaishah....bazan iya boyemiki abinda nake ji a kanki ba,wata iriyar qauna da banda anni ba wata diya mace da nake jin ina yiwa irinta,abun tamkar jarrabi,duk yadda naso na kauda shi abun ya ci tura,dukkanin qarfina ya qare akan kauda afkuwar abun don baki cikakkiyar dama,ina ganin tamkar idan naci gaba dajin haka a kanki kamar na cutar da damar da nace zan baki ne...kamar na karya alqawarin da nayi na cewa zan dauke ki ne tamkar qanwata...eh duk da cewa har yau ina ganin wasu dabi'un naki ina kuma kallonki kamar hajar din saboda kamanceceniyar dabi'unku,kunyi kama sosai ta wannan fannin....uwaishah....inaji a jikina kamar Allah ya aikomu cikin rayuwar juna ne saboda mu taimaki juna,saboda mu qaunaci junanmu,saboda kuma ya duba koken kowanne dayanmu,yaga cewa mu zamu fi kowa fuskantar yana yinmu da irin rayuwar da muke da buqata....uwaisha zuciyata ya soma qaunarki a wani lokaci da bansan yaushe bane,ban tantance hakan ba sai daga bisani,kota yaya nema humaira kin cancanci soyayya,kin tsallake dukkan wasu tarakuna dana d'ana,wanda mata da yawa suka gaza tsallakeshi,kinci jarabawar da mata bila'adadin suka kasa jumurin cinta,hakan kadai ya isa ya tabbatarmin da cewa kedin ta daban ce....humaira ina miqo qoqon barana da ki soni ki qaunace ni,bana son ki soni saboda wani abu na daban,bana son ki duba komai ko kice zaki soni saboda kaza,nafison ki soni saboda ni nidin khalipha,ina son ki soni saboda zuciyar taki tana sona bawai don wani dalili ba na daban,don Allah.....uwaish....ki soni,kiso khalipha"tuni hawaye ya jiqe mata fuskarta,ta kasa barin idanunta abude,yau wai ita aysha ake furtawa cewa ana sonta?,yau ita ake bayyanawa wasu kalamai da bata tsammanin samuwarsu ba cikin duniyarta?,ita akewa wannan matsanancin son?,wai yau itace mutum mai daraja kamar khalipha ke roqon ta soshi?,wace irin qauna haka khalipha ke mata a rayuwa?,koda bai roqi ta soshi ba tana ji jini da tsoka khalipha halittar da za'a sota ce,tana ji har cikin zuciya tuhi da gangar jikinta khalipha wani abu ne na musamman da Allah S W T ya ajewa rayuwarta ne,to waishinma idan bata so khalipha ba wa zata so a rayuwarta?,baisan cewa ta jima tana qaunarshi ba amma saita tsammaci saboda kyautata matan da yakene take jin haka akanshi?,son khalipha ya zame mata wajibi cikin rayuwarta haka take ji
"Pls uwaisha.....idan ban miki ba kika ce bakisona zan haqura don na cika alqawarinki.....saidai bani da tabbacin yadda rayywata zata kasance anan gaba....bansan ta yadda akai soyayya ta yimin shigar ba zata ba....." Ya fada raunin da bata taba ji cikin muryarsa ba yau ta jishi muraran
"A duniya baya ga anni bana jin akwai wata halitta dake sonka sama dani...!"ta furta kalaman na fita daga cikin ruhi da zuciyarta.
"Ka cancanci dukkan wata soyayya ta diya mace,bawai don abinda ka shiga rayuwata ka yimin ba,a'ah dukkan nagartarka na tattare da kai kuma ita zata iya siya maka kowacce irin soyayya,ina qaunarka ya khalipha....." Dukkanin idanunshi ya waro waje yana jin yadda zuciyarshi take qara bugawa da sauri da sauri wanda hakan ya qara tsananta ciwon kanshi,daga gefe daya kuma wani irin yanayin farinciki da baxai iya fasalta irinshi ba ya dinga sauka cikin zuciyarshi a hankali,sai ya sake matsawa jikinta sosai muryarshi na dan rawa
"Da gaske uwaishhhh....da gaske kina sona?" Kai ta gyada masa don tabbatar masa,saboda bakinta ya kasa cewa komai,itama bugun da zuciyarta yake ya sanya jikinta yi sanyi,baiyi wata wata ba ya rungumeta cikin jikinsa tsam,a cikin kunnenta yake rada mata saboda baya jin zai iya magana mai qarfi,ji yake kaman numfashinsa zai dauke,yana jin kamar kanshi zai rabe biyu
"Na....gode uwaishhh....na gode" abinda bakinsa ya dinga furtawa kenan tsahon wani lokaci ba tare daya barta ta bar jikinsa ba.
A hankali ta lura da yadda jijiyar kansa ke harbawa d'il d'il da yadda jikinsa ya dauki zafi,zare jikinta tayi cikin damuwa tana dubanshi,cikin wata murya mai laushi
"Ya khalipha......jikinka ya dauki zafi sosai,ciwon kan nan ya kamata ya barka haka,ya kamata kaje kaga likita,bakaci abinci ba tunda ka dawo?,na zuba maka abinci kaci don Allah kasha magani saika kwanta,wala'alla ka sake samun relief"
"Kece abincin kuma kece maganin gaba daya uwaishhhh,zamanki a jikina ya fiye min komai" ya fada yana bata hannunshi,batayi musu ba ta miqa masa yayi mata jagora zuwa jikinsa na sake rungumeta fiye da d'azu
"Rungume ni sosai uwaishaahh....sanyi nake ji" ya furta cikin rada,hannayenta ta sanya itama gaba daya ta zagayeshi da shi,duk da bai ratsashi ba amma hakan ya qara masa dumi a jikinsa yadda yakeso,shuru ne mai dadi ya ratsa dakin,wanda ya bawa dukka zukatan yin tunani mai kyau yadda ya kamata,ta tsakiyar shurun bacci ya shigo yayi awon gaba dasu gaba daya,wani bacci wanda ya zama na musamman a garesu ita dashi baki daya.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Tara saura na safe tana tsaye cikin kyakkyawan kitchen din tana shirya musu breakfast,kusan mintuna ashirin kenan data sato jiki ta fito ta barshi a cikin daki,aikinta take hankali kwance tana yi tana sake kallon kitchen din,ko ina cikin gidan mai kyau ne,iya bedroom din kawai zuwa kitchen data gani ya tafi da ita sosai,komai ya tsaru yadda ya kamata,kana kallo kasan aikin masu ilimi ne.
A qalla ya dauki mintuna goma tsaye yana morewa kallonta,karon farko da yaga ayshan sosai,cikakkiyar mace wadda Allah yayiwa baiwar kyau sura da diri,yadda yake ganin dabi'unta kyawawa masu kyau haka Allah ya kyautata halittarta,yana son ya isa gareta ya rungumeta cikin jikinsa suyi aikin tare,saidai kuma ya tabbatar idan yayi hakan dukkan wani lissafinsa da yake qoqarin tattarawa zai ruguje ne,hakanan zai kasa cika muradi da alqawarin da ya dauka ma ranshi,wani alqawari da yake fatan Allah ya cika mishi shi nan kusa,duk da haka sai ya gaza daurewa,ya saki hannayenshi ya soma takawa cikin sanda har ya isa bayanta dab da ita,caraf yayi ya ruqo qugunta sannan ya dan karata a jikinsa yana cewa
"Assalamu alaiki" ba qaramin firgita tayi ba wanda har yasa ta kusa yin bari,saidai Allah ya tsare farantan gabanta ne guda biyu kawai na roba suka biyota,sallamarsa ita ta sanya mata nutsuwa,ta sauke gauruwar ajiyar zuciya,dariya ya dinga mata mai kama da murmushi bayan ya juyo da ita yana duban qwayar idanunta,sai ya tuna sanda ta shiga bandaki ta kulle kanta,yana qoqarin biye dariyarshi yace
"Ba shakka uwaisha tah gwanar tsoro ce,na manta sanda aka gudu bandaki ana nada haquri fa" ya fada yana kashe mata ido daya,murmushin daya qawata fuskarta ta saki tana dan cije lebanta,tana son ta rama tana dan jin nauyinshi,sai kawai tadan saka tafin hannunta ta bugu qirjinsa kadan
"Wash!" Ya fada yana saka hannun nasa yana dafe inda ta doka din,cikin zaro ido tace
"Lafiya meya faru?"
"Zuciyata" ya fada yana narkewa gami da zuba mata narkakkun idanunshi da suka zame mata kamar dabaibayi,cikin qarfin hali tace
"Me ya sameta?"
"Kin mata rauni bad'ini shine zaki sake mata wani a zahiri" murmushi ne ya subuce mata,saita dan taka kadan ta hade tazarar dake tsakinsu,
"Ni bakasan tawa zuciyar ta zama raurananniya ba kake son sake razana ta?"bakinta saitin wuyanshi take maganar,yadda hucin numfashinta dana bakinta yake sauka saman wuyan nashi,lumshe ido yayi tsigar jikinsa na tashi,ajiyar zuciya ya sauke ya bude idon nashi,sai sannan ya lura data janye daga yadda ta tsaya dazu,kamota ya sakeyi gab dashi sosai suka soma musayar numfashi,idanunshi cikin nata suna kallon juna na wani lokaci,da sauri ya saketa yana maida numfashi gami da qoqarin yiwa kanshi linzami da saiti,aikinta taci gaba da qoqarin ci gaba dayi saidai ta lura ta soma hada shirme.
Dariya ya dan saki yana tsaye bayanta yana kallonta bayan ya gama samo nutsuwarshi,ya gama karantarta tsaf,saidai dole dukansu su jira lokaci,hannunta ya riqe da sauri
" yi haquri madam,wallahi kika zuba wannan abincin bazai ciwu ba yau kam"sai a sannan ta dubi abinda take,gishiri ne ta ciko cokali dashi zata zuba cikin qwan da baifi hudu ba,saita sakar masa cokalin gishirin kunya tana kamata
"Nikam.bansan ma waya cs miki ki taso kibar aikinki ba ki barni ina jin sanyi kizo dora abinci,mu tafi kawai an yafe miki" ya fada yana shirin kama hannunta,saita langwabar da kai a narke tana cewa
"Pls ya khalipha....na kusa gamawa,ka bari na qarasa idan ba haka ba zai zama asara,abincin jiya da darema saidai abadashi Allah yasa ma ba mai yawa bane"
"Kai...gsky to matsa na tayaki ki qarasa,wannan muryar bazan iya tafiya nabar mai ita ba" dariya yaso bata,haka ya iya soyayya?,dama haka masoya suke ji cikin zukatansu?,haka ya tsaya daga bayanta yana tayata qananun abinda zai iya,duk da kusan wayo yayi mata morewa kallonta kawai yake,idan ya kasa daurewa yadan matsa kadan ya rage zafi da haka suka kammala komai tare.
Wani irin wuni ranar sukayi tare da juna yana sake bayyana mata kanshi,hakanan itama,kowanne na sake jin dan uwanshi cikin niki da zuciyarshi,so yake ya cire mata dukkan wata kunya tashi da nauyinsa,ya gaya mata soyayya yake da buqatar ta nuna mishi zalla babu algus,qunahe qunahe ko 'yar kunya,yana son ta zama shi ya zama ita,yana son su zama sirrin juna kamar yadda Allah S W T ya fada cewa
_"Su(mata)tafafi ne a gareku,haka kuma(maza)taufafi ne a garesu"_ hatta da wayoyinshi duka a kulle suke,bai bude ba sai bayan sallar la'asar,mahmoud ne mutum na farko daya soma kiranshi
"Haba haba boss,ya za'ayita nemanka amma a rasa ka?,ka bace sama da qasa" murmushi ya saki idanunsa na kan aysha dake hada masa system dinshi
"Kai mahmoud,na gaji wallahi,daga dawowata?,ina buqatar na huta shi yasa,zan hau yanzu zan duba dukkanin saqonnin"
"Alright....mutumin nan fa ya matsa min daga jiya zuwa yau?"
"Wa fa?" Khaliphan ya tambaya
"Alj kutama mana" dogon tsaki yaja
"Rabu dashi don Allah,mutumin banza,ya bani mamaki wallahi,irinsu ne ke amfani da damar da Allah ya basu suke ruguza rayuwar matasanmu ta hanyar shigo da miyagun qwayoyi,bazan qyaleshi ba mahmoud saiya d'an d'ana kudarshi,sai ya dawomin da dukka kudade na cikin kwana uku"
"Banga laifinka ba,koni iya mutuncin da zan iyayi masa kenan,sam mutane basa yiwa kansu da rayuwarsu adalci,ta yayaAllah xai albarkaci bayan irin wadannan?"
"Ka gani" cewar khalipha yana jan tsaki,nan suka kammala tattaunawarsu kafin suyi sallama daga bisani.
Kwanansu uku cikin gidan yana koya mata wani darasi mai wuyar mantawa,wata wutar qaunarshi yake rura mata azuciyarta,soyayya mai tsayawa a rai,tamkar zata zauce wani lokaci haka take ji,yasan dukkan wani salo da matakan gina soyayya cikin zuciyar abokin rayuwa,badon yajin aiki daya ratso musu suke zaune a gida ba ta tabbata mawuyacine taci gaba da fahimtar karatu idan ta koma makaranta,duk wannan abun khalipha na baya baya ne saboda komai ya tafi dai dai da plan dinsa.
Cikon kwana na hudun da wani yammaci tana kitchen tana hadawa khalipha salad,ta baroshi a falo yana kwance yana hutawa,wanda da qyar ya yarda ya zauna don cewa yayi sai yazo ya tayata,tayi kyau qwarai cikin wani lace mai kyau daya zaba mata yau yace shi zata sanya mishi,ba zafi yau garin sai hadarin daya hado,ruwa bai samu sauka ba saiya juye yake bada wata iska mai sanyi da dadi,haka yake kullum a rana sai tayi masa kwalliya uku hudu,bata masa qasa da hala,ta fuskanci mutum ne shi maison mace mai ado,sai Allah yasa ra'ayin nasu ya kusan zuwa daya,ko a baya rashin sukunin rayuwa ne yake hanata kwallia,a yanzu kam duk wanda yasanta ya santa da ado,abin ya mata dai dai,sao kawai ta baje kolin kwalliyarta so ranta.
Tunda ta fito a kitchen din ya zuba mata ido yana kallonta,kullum sabuwa take a wajensa,kullum tayi masa ado sai yaga na yanzu yafi na dazu kyau,sai yaga kamar bai taba ganin kwalliya iri tata ba,tana isowa kusa dashi ta aje tray din hannunta saman teburin gabanshi,batakai ga gama ajewar ba ya miqe ya zauna sosai yana murza ido,murmushi ta saki,tasan da walakin tana fiddo idanunta waje tace
"Uhmmm..."
"Ji nake kamar na hadiyeki na huta wallahi,kinga indai hakan ta faru ba wanda ya isa ya sake ganinki saini kadai" murmushi ta saki mai taushi,harga Allah kalaman khalipha ko da yaushe na sake dilmiyata ne cikin kogin qaunarshi,koda yashe kalamansa na sake nuna mata itama cikakkiyar macace wadda ta cancanci taso kuma a sota
"Ina godewa Allah koda yaushe daya qaddara zaka wanzu cikin rayuwata" shima murmushi yake mata,yana jin kaman ya janyota jikinss,saidai yana tsoron kada qiluta jawo bau,duk da yana fata komai yazo qarshe,saiya daga pillow din kujerar da yayi matashin kai dashi,ya ciro passport ya buda sannan ya miqa mata,hannu ta saka ta amsa,gabanta na faduwa zuciyarta na dukan uku uku,addu'a take Allah dai yasa ba cewa zaiyi zai koma ba,idanunta takai kai,visa ce ta shiga qasar saudiyya,wadda bata kowa bace face tata,idanu ta fiddo zuciyarta kamar zata fito,babban burinta a duniya?,mafarkinta ne zai zama gaskiya koko dai?,kai ta daga tana dubanshi da alamun tambaya,shima ya tattara dukkan hankalinsa da nutsuwarshi akanta,farinciki na ratsashi sakamakon farincikin daya sanyata a ciki
"Ya khalipha....da gaske?" Kai ya jinjina mata
"Da gaske ne uwaishata,rana ita yau in sha Allahu zamu tafi,kije ki gayawa Allah dukkan matsalolinki da damuwarki tsakaninki dashi,sannan mu roqawa kanmu samun dukkan wata rayuwa ta farinciki da ma'aurata kewa kansu fata,ya bamu zuriyya ta gari,yasa zamu fara rayuwarmu a sa'a" rungume passport din kawai tayi a qirjinta ruwan hawaye na bin kuncinta,abinda bata taba tsammatarsa ba cikin rayuwarta,dubanshi kawai take ta rasa bakin magana,idan ta bude baki ma me zata mishi?,dukkan wata kalma da zata fada ya riga daya saba jinta,walau a bakinta ko a bakunan al'umma,ya fahimci haka,saboda haka saiya ware mata dukkan hannayenshi alamar ta taho,ba taba lokaci kuwa ta kwasa zuwa gareshi ta zube a jikinsa tana sheshsheqar kuka,hannunshi ya sanya ya zame dankwalinta wanda tun dazu dama yaso zamewar ta hanashi,ya dinga shafar gashin kanta kawai yana shaqar qamshin jikinta,ganin ta kasa shuru sai ya soma rada mata
"So kike ki fasamin zuciyata kenan" idanunta dage jiqe da hawaye ta dago ta dubeshi dasu,saiya kanne mata ido daya yana murmushi
"Eh mana,kinsan abu mafi muni da kunnuwana zasu ji shine sautin kukanki?" Jin yace haka saitayi qoqarin hadiye kukan,ta kwantar da kanta saman qirjinsa tana goge hawayenta
"Na rasa me zance maka ne,na rasa me zanyi,dukkan wata kalma da zan fada gani nake bata gamsar ba,ka zamemin fitila a rayuwata,ka zamarmin haske mai kore duhu,kai daya ka bani farinciki da daruruwan mutane suka kasa bani,dame zan saka maka nikuwa aysha bayan bani da komai ban mallaki komai ba"
"Ke kike da komai,kuma kece kika mallaki komai" saitayi shuru tana sauraronsa gami da tunanin abinda yace
"Zuciyarki rayuwarki da gangar jikinki nakeso ki mallakamin,ki bani dukkan wata yardarki,ki soni ki qaunaceni,kici gaba kuma da sona domin Allah kamar yadda kikayi a baya" cikin sanyi da kwantar da murya tace
"Indai wannan ne ka gama samunshi har gaban abada"
"Kinyi alqawari?" Saita zauna sosai tana dubanshi cikin ido,wanda hakan ya sanyashi shima gyara zamanshi yana dubanta
"Duk duniya babu wanda ya cancanci samun wannan matsayin sama dakai,idan ma akwaishi bana fatan Allah ya nuna minshi har abada,zan rayu dakai cikin kowanne irin yanayi,bana fata na saba maka dai dai da rana guda kona sauya maka matsayi daga wanda na doraka akai a yanzu,idan wannan yana cikin qaddarata shima ina roqon Allah ya dauki raina kafin lokacin" wani murmushi ya saki,yana jin wani farinciki na ratsashi,tabbas baiyi wuyar banza ba,addu'a bata faduwa qasa banza,hakanan dama Allah yake lamarinshi,haka ya fada cikin qur'aninsa _sau da yawa zaku qi abu amma alkhairi ne a tare daku_ gashinan tabbas hakan ya tabbata a kanshi,saitin zuciyarshi ya dafe da d'aya hannun nasa
"Karki kasheni ni mana tun yanzu,idan kika mutu uwaisha in zauna dawa?" Yadda yayin ya bata dariya,saita saki murmushi mai sauti tana dubanshi sanda yake cusa hannunshi cikin aljihun wandonshi ya ciro wani dan qaramin akwati mai kyau,tana kallonshi ya bude,ya ciro wata nannadaddiyar dubu daya da aka yiwa ninki mai kyau,saiya dagata yana dubanta sannan ya dubi ayshan
"Kin tuna wannan?" Kudin hannun nashi sosai ta kalla kana ta dubeshi tana dan tabe baki gami da girgiza kai,wani kishi take ji yana dan sukarta,tana tunanin ko wata budurwarshi ce ta bashi?,murmushi ya saki yana maidata ciki sannan ya dubi ayshan
"Tun daga ranar da kika bada ita a matsayin biyan bashi a gareni na tabbatar da cewa akwai banbanci mai tarin gaske tsakaninki da asma'u,sannan akwai wata boyayyar halayya da baiwa da kike da ita data sha banban data sauran mata,yau bari na baki labarin da baki sani ba" daiya gyara zamanshi yana daukar cup din coffen data zuba mishi ya kurba,sannan ya soma bata labarin dukkan 'yammatan daya tabayi da yadda suka qarke dasu,mamaki.ne ya kama ayaha,tsoron duniya da mutanen cikinta ya sake kamata,kowa ya lalace?,kowa mai kudi yakeso?,idan a familynka ne sai.kana dashi kake sa wata babbar daraja?,idan saurayine kai ko qur'ani kake hadiya saboda sanin Allah da tsoronshi ba mai baka aure idan baka tara koka aje ba koda kana da sana'ar rufawa kai asiri?,wannan wacce iriyar rayuwace mukeyi?,tunaninta ya katse mata sanda ya tura mata system dinshi gabanta yace
"Duba" ba musu taja ta soma dubawa,order ne da yayi mata daga store na rahamalls wanda tuni suka iso,har an bude katafaren wajen siyayya gashinan da hotunansu an tsara komai dauke da sunan UWAISHAH MALL
"Duk abinda kika gani a nan naki ne humairah ke na tanadarwa,na yiwa kaina wannan alqawarin tunda dadewa bawai yanzu ba,nayi alqawarin ninka miki dubu dayanki tun ba yanzu ba,wannan shine tukuicin da nayi niyyar yi miki a matsayin taimakon da kika yimin sanda ake bina bashin dari biyar kika sadaukar min da dubu daya duk da bakisan waye ba ni" kasa magana tayi wannan karonma,sai ta rufe bakinta kawai da tafukan hannayenta,kai ya girgiza yana jifanta da tattausan murmushinsa
"Karki ce komai,don bana buqata,na riga dana gaya miki abinda nake da buqata" ya fada yana ware hannayenshi,sai kawai ta rungumeshi tana sakin kuka.
Tafe suke a motarshi saidai kana duban fuskarta kasan tsantsar baqinciki da bacin rai ke cinta,a yanzu ba abinda ta tsana irin auren hamid,neman kawai hanyar da zata yakiceshi take,saidai ta lura da idan natayi takatsantsan ba haqarta ba zata taba cimma ruwa ba.
Daga barkar haihuwa suke wanda ita sam batasan ma wadda suka jewa barkar ba,saidai ta cika da mamakin uban kayan da hamid ya siya din yakai,dama shidin ba dai neman suna da son burgewa da gwaninta ba,tunda sukayi aure bai taba yi mata siyayya irin hakan ba,sai gashi yayi ya kaiwa wasu,dai dai nan wayarshi ta dauki kuwwa,ganin kiran babanshi ne ya sanyashi dagawa,bayanin da daddyn nashi yayi masa ya daga masa hankali qwarai,ya tabbatar cewa gagarumar matsala ce take fuskantosu
"Yanzu daddy meye mafita?,ya zamuyi?"
"Ya kamata mu soma dakatar dashi,yanzu haka ancemin yana gidansa,idan kana kusa ka sameni nan titin lodge road saimu qarasa mu bashi haquri,ko qafa ne muce ya daga mana sai muyi tunanin abinda zamuyi a dan taqin"
"Shikenan daddy ganinan zuwa yanzu,ina kundila amma bari na qaraso"
55
ko duban asma'u baiyi ba ya dauke kan motarshi ya canza hanya
"Wai malam ina zaka dani ne?" Banza yayi da ita donshi kadai yasan tashin hankalin da yake ciki
"Kaga malam ka saukeni ina zaka dani nina gaji fa"tsawa ya daka mata sannan yace
"kiwa mutane shuru,ke bakisan abinda yake damunsu ba zaki cikasu da surutu,koma meye kema kin taimaka wajen faruwar abinda ya farun,dole muje dake kema ki saka baki" ganin yana yi kamar zai daketa ya sanyata yin shuru kawai tana huci,haka suka ci gaba da tafiya har suka cimma daddy,cikin tasu motar ya shiga suka tafi yabar motocinsa nan wajen wani cin abinci dake lodge road din.
Qararrwar falon daketa kadawa ya sanyashi miqewa don zuwa duba wanda ke neman izinin shigowa
"Kinga yanzu kikai alqawari ba zaki sake kuka ba,karki karya" kai ta gyada mishi tana binshi da kallo,har cikin ruhinta tana jin wani alfahari na kasancewarsa miji a gareta,daya tamkar da dubu.
Daya daga cikin masu tsaron qofar gidan ne yake shaida masa yayi baqi,baisan su waye ba hakanan suma sun gaya mishi cewa baisan da zuwansu ba
"Qyalesu su shigo" ya bawa mai tsaron qofar umarni,falon ya koma yana dubanta
"Kinga duk kinsa coffen yayi sanyi,dan sake hadamin wani zanje naga wasu baqi,nasan ba jimawa zasuyi ba tunda banyi dasu zan gansu ba,nan da minti biyar zan sallamesu saiki kawomin coffe din a can zan sha"amsa mishi tayi yayin daya dan sunkuya ya sumbaci goshinta sannan ya zura takalminsa ya fice.
Tunda suka shigo gidan gaba daya ya tafi da imaninta,tasan cewa za'a rina hakan,don tun a mota ta fuskanci wajen uban gidan mijin nata zasu je,sai take ganin gidan kamar ta sanshi,sai taga yana mata zubi da gidan aysha da aka kawota,girgiza kai tayi wani bari na zuciyarta na gaya mata
"Haba wane mutum,ta ina khalipha yake da kudi kamar na mutumin nan,ta inama zai ginawa ayshan gida har haka?" Ko kusa bata ankare da khaliphan ba har suka gama parking suka fito,saboda idanunta nakan jerin motocin alfarma dake pake a inda aka tanada saboda ajiyar motoci na gidan.
Hamid da daddy suna gaba tana binsu a baya,zuciyarta cike taf da qyama da dana sanin auren hamid,bata taba tunanin kudin da suke tinqaho dashi ba nasu bane na rance ne ba sai yau,da zasu kula da ita da kyau ta baya kallon wulaqanci take jifansu dashi,gab da zasu isa wani guri datake hango wani mutum can zaune hamid ya dakata ya jata gefe
"Ki tabbatar da cewar kin bude baki kin bada haquri,idan ba haka ba wallahi Allah kinji na rantse miki duk wani abu da nasan na siya miki ke har motar da kike hawa saina saidata,saboda duk da kudin da muka karba da bikinki na cire wani abu a ciki na siya miki" dubanshi kawai take,a fuska gashinan mutum iya mutum,saurayi dan gaye maiji da kanshi,saidai a ciki duka hoto ne kuma kango ne,sam hamid baya burgeta yanzu dai dai da qwayar zarra,hakanan mamaki ma suke bata shida ubanshi duka a yanzu,koda zata bar gidan hamid batason ta rasa abinda ta shigo da shi,ta koma gida a tsiyace,wannan ne dalilin kawai da zai sanyata ta bada bakin,saidai bata ce masa uffan ba har suka qarasa wajen.
Ya amsa musu sallamarsu saidai ya maida kanshi kan wayarshi yana turawa aysha tex kamar ba yanzu ya barota cikin gida ba,baiyi tsammanin su bane da bazai bada damar su shigo ma cikin gidan ba,qamewa asma'u tayi yayin da take qare masa kallo,wani tashin hankali taji yana gewaye ilahirin qwaqwalwarta,wai dama khalipha ne wanda sukazo roqa?,dama alhj kutama surukinta da hamid mijinta dukkansu a wajen khalipha suke amsar bashi?,dama da dukiyar khalipha aka aurota?,take dukkan wani qaimi da kwadayin rabuwa da hakid ya sake ninkuwa cikin zuciyarta,taci gaba da qarewa khalipha kallo tun daga zara zaran yatsun qafarshi zuwa kanshi,tana kuma tantance banbanci tsakaninsa da hamid wanda ya yiwa kanshi mazauni daura da khaliphan,karon farko data soma jin haushin kanta da kanta a rayuwa,tun daga siffa khalipha ya gama cinye hamid murus,me ya kaita yin wannan ragon azancin?,wai me yasa ma batasanya daddy ya nashi jari gida da mota ba asanda take tunanin talakane ta aureshi ba?,inuwar daya gani kusa dashi ya sanyashi dagakai,sai yaga asma'un,yayi mamaki don baisan meye alaqarta da alhj kutama da kuma hamid ba,Allah yasanya ba son kudinta ya kaita qulla alaqa dasu ba,ya furta cikin zucuyarsa
"Ki zauna mana,ya zaki tsaya qerere kan mutane?" Hamid ya fada cikin fada fada,saita ja kujera a kunyace ta zauna,a mutunce ba wulaqanci ya gaida daddg sannan suka gaisa da hamid,duk da bai bashi hannu ba,don a yanzu qyamatarsu yake,yana mamakin yadda kana musulmi zaka iya saida abinda zai zama cutuwa ga al'umma,infact ma ruguza al'umma gaba daya kayan shaye shaye yake,saboda matasa sune qashin gadon bayan al'umma to an ruguzasu me yayi saura?.
Daddy shi ya soma bada haquri sannan hamid,murmushi kawai khalipha yayi sannan kai tsaye ya kira sunan daddyn
"Aikin Allah kayi da kudin da kake tunanin samun sassauci daga gareni?,idan na sassauta maka ma na bada goyon bayan kaci gaba da aikata dukan abinda kake aikatawa kenan?" Gyaran murya asma'u tayi wanda ta gyara zama gami da lanqwasa muryarta ta sona zayyanowa khalipha maganganu,wanda kusan rabi hannunka mai sanda take masa a karan kanta,yadda ya hade yatsunsa waje guda yana kallonta yasa ranta yayi fari qal taci gaba da magana tana juya idanu,sai data gama yaja wani.matsiyacin tsaki sannan ya juya ya dubi alhj kutama bayan ya kira sunanshi
"Kada ka sake nemana idan ba kudina ka kawomin ba nan da kwanaki uku,idan ka tashi kawomin kuma ka daure ka dauko mutane masu hankali su rakoka" ganin yana niyyar miqewa yasa hamid zungurar asma'u kan tayi magana,don iyaka saninsa da khaliphan yana da tausayin mata qwarai,ta fuskanci abinda yake nufi itama kuma ko banza batason rasa dukiyarta,saboda haka ta soma roqonshi,daidai sanda aysha dake dauke da wata butar shayi mai kyau da qananun kofuna,saita soma takawa a hankali ganin kamar baqin nashi basu bati ba,bata ma gane su waye ba,shi ya soma ganinta,saiya miqa hannunshi yana cewa
"Kawo my uwaishahh" cikin nutsuwa take takowa ta dora yalwataccen mayafi mai kyau saman kayan jikinta,qamshin turaren data sake fesawa jikinta na kadawa zuwa ko ina,maganar khalipha ita taja hankalinsu kanta,take kowanne tunaninshi ya banbanta,alhj kutama na farinciki tare da jin dadin ganin fitowar uwar gidan,ko banza yasan idan ya roqeta ta sanya baki wala'alla khalipha ya dage musu qafa ko ya qyalesu,ya danganta da yadda yake jin maganarta,hamid mamaki ne ya daskarar dashi a wajen,dama aysha muhammad khalipha mai goro ta aura?,ya akayi haka?bayan asma'un tasha bashi labarin irin mijin da ayshan zata aura ta qyalqyala dariya tana fadin shi ya dace da ita ai,ya tabbatar asma'u bata da masaniya da tabbas ba zata qyalewa aysha shi ba,idan ko aysha ce matarshi lallai abubuwan zasu zo da sauqi,tun ba yauba ya santa da tausayi da sanyin hali,ba shakka mai yiwuwa tasha musu kan khalipha.
Ta gefan asma'u kuwa wani dan banzan kishin aysha shi ya taso mata,komai na ayshan ya sauya,dukkan wani jin dadi da hutu ya gama bayyanar mata,babu shakka ayshan nason tsere mata tayi mata fintikau a rayuwa,lallai ba shakka ya zame mata tilas tasan dukkan mai yiwuwa ta samu cikar burinta a rayuwa,cikin salo da kwainane asma'u ta sake lanqwasa murya tana roqar khalipha,wani abu kadan hamid yaji ya taba ranshi na kishi,sai kuma yake ganin tunda mijin 'yar uwarta ne me yiwuwa ya haqura din.
Aysha na shirin juyawa ta koma don bai bata damar gaida kowa ba cikinsu khaliphan ya damqe hannunta,cikin yaqe hamid yace
"Aysha ki...."
"Kar na sake jin sunan matata a bakinka,kasan ba kowane ke kishin matarshi ba amma ni nasan me nakeyi" ya gaya mishi magana a fakaice,cikin kwantar da kai yace
"Kayi haquri boss,ranki ya dade ki sanya mana baki mana don Allah boss yayi haquri ya daga mana qafa,kuskure ne munyi da yardar Allah ba zamu sake ba" duban khalipha tayi ranta duk a jagule,sai take jin babu dadi,daddy take tunawa,bai kamata ace diyarshi da mijinta na neman wani abu wajensu ba su gagara yi musu komai,idanu suka hada yana kurbar coffe dinshi,ya fuskanci tana son tankwa ne
"Kayi haquri don Allah ya khalipha ka daga musu qafa duk da bansan akan meye ba am......"
"Wuce ciki ina zuwa ya fada yana sakin hannunta,yanayin maganar tashi ya sanya ta juya zuwa ciki,amma duk bata ji dadi ba a ranta,sai dayaga bacewarta sannannya juya ya dubi alhj kutama
"Kar ka sake.gangancin zuwa min gida,saboda gida na iyalinane ba office bane,donsu kawai na gina,sannan nan da kwanaki uku idan baku dawomin da kudade na ba to ku saurari kiran hukuma" maganarshi ta qarshe duka ta kada hanjin hamid da alhj kutama,hukuma su da suke guje mata ta yaya zasu yarda ya jona su da ita?,haka suka miqe suka wuce gwiwa a sage,ran asma'u a dagule,bacin ran roqon da suka bata lokaci sunayi har a gaban aysha,ga rashin cikar buri,ga kuma burinta akan khalipha da bata ga wani sauyi ko ci gaba ba.
A falo ya sameta sanda ya shiga,ta daga kai tana amsa sallamarshi hadi da aje takardat hannunta,waje ya samu ya zauna kana ya kalleta sosai
"Humairaa"
"Na'am" ta amsa masa a sanyaye
"Banaso ki sake saka baki cikin lamarin da bakisan ya yake ba"
"In sha Allahu" ta fada kanta a qasa ba tare da musu ba
"Na dauki kudina na halak na basu saboda su juya su samu abinda zasu riqe kansu da iyalinsu,sai gashi daga baya suna siyo abinda zai cutatawa al'umma,ya ruguza rayuwa da future din al'ummarmu,kayan maye,kayan shaye shaye,dole na karbi kudina saboda shine kawai hanyar da zan karya su koda hukuma bata cafkesu ba,daga ranar basu da wata dama ta siye da siyarwar kayan mayen" ranta taji ya sosu,tabbas sun cancanci wannan hukuncin na khalipha
"Kayi haquri duka bansan wannan ba da bazan saka baki ba,lallai sun cancanci irin wannan hukuncin".
Cikin tashin hankali su hamid suka isa gida,inda suka zauna daga baya shida mahaifin nasa,sun tabbatar da cewa matuqar ya hadasu da hukuma babu abinda zai hana ba'a gane sune aka kama yaransu ba wajen safarar miyagun qwayoyi
"a shawarce mu siyar da gidajenmu da kadararmu matuqar muna son tsira da rayuwarmu bama son qareta a gidan kaso mu sallameshi,idan yaso sai mu sami inda zamuci bashi mu fidda yaranmu mu tsallakar da kayanmu,indai hakan ta kasance kasan zamu maida ninkin abinda muka rasa harma da riba akai"kai hamid yake gyadawa,tabbas wannan itace shawara,don su siyi kaya na maqudan kudade kuma kadan suka bayar a fita dasu,idan har suka samu saidasu to zasu iya ninka kudinsu na yanzu,don dama abinda ya sanyasu siyan kayan kenan kwadayin kudi da zasuyi.
Yana isa gida ya shaidawa asma'u ta hada iya kayan sawarta kawai zasu sauya gida ne basai ta dauki komai ba,baiyi gigin gaya mata gaskiya ba saboda tabbas yasan idan ya gaya mata inda zasu koma to ta gama zama dashi,shi kuma har yanzu yana son abarsa bai kuma shirya rabuwa da itaba ko kadan,musamman idan ya tuna abinda ya kashe kafin ya samu nasarar aurenta,duk da tana shirin rabuwa da shine amma hakan yayi mata dadi,ko banza darajarta zata qaru tadan wani lokaci,kuma khalipha koda zai aureta yasan cewa ba daga qaramin gida ta fito ba,bataso ma ya gane wahala tasha hannun hamid,tafison su tafi akan cewa kawai sonshi take yanzu shi yasa taqi hamid.
Haka kuwa ya shirya iya kayan sawarta kawai sai dan abinda ba'a rasa ba suka bar gidan,don hatta da motarta a gidan ta barta,bata tashi gane cewa ajine zai fado qasa warwas ba sai da taga gidan daya sauke ta,plate house safecontain,wanda a haka ma zasu zauna ne da uwar mijinta da qannen hamid hudu,babban falo mai dauke da dakunan bacci masu toilet,sai kitchen a falon da wani spare ban daki,toh nata dakin akwai falo kafin bedroom din,wani kallo ta watsawa hamid
"Waime kake nufi banfa fahimceka ba,ina ne nan?"
"Nan shine sabon gidanmu,nayi gwanjon wancan gidan da duka kayan cikinsa zanyi biyan bashi dasu" tuni fuskarta ta sauya saiya juya da jakarta zata fice,tareta yayi cikin hargagi
"Ina kuma zaki?"
"Gidan ubana mana,don bamuyi haka dakai ba ai,idan ka gama uzurinka ka biyoni da takardar sakina,don wallahi bazan zauna dakai ba na gama zama dakai"
"Amma dai ke ba'yar halak bace ba macen zama bace,muci dadi tare kice ba zamuci wuya tare ba,ni zaki yiwa butulci?,kudin da zan biya kusan kece silar cinyewarsu"
"Kai ka sani kuma kai ka jiyo" ta fada tana rabeshi kamar zata bankeshi ta fice,dariya ya saki bayan ta fita
"Idan kinsan wata bakisan wata ba,bari na gama cinikin gidan" kusan duk wata kadara tasu saida suka saida,yayin da suka cika mutane da cewa ai zasu bar nigeria ne shi yasa.
Sanda asma'u ta isa gida qarya da gaskiya ta zauna ta shiryawa daddy,bata damu da rashin cikakkiyar lafiya dabai da ita ba ta zauna ta tsara masa maganganu na qarya,tun baya mutum ne shi mai dattako da sanin ya kamata,saboda haka yace ta koma gidanta zuwa gobe zaizo ya samesu ita da hamid din yaji ta bakin kowa,saidai tana shiga ciki ta sanar da mommy gaskiya,ta kuwa dire tace ba inda diyarta zata koma,dakinta nada tasa aka bude aka share mata ta shige ciki,farinciki.kamar ta taka rawa,tana ganin nesa gab take da zuwa kusa,hankalinta kwance taci abinda ranta yakeso tayi kwanciyarta,sai a sannan take ganin me ya kaitama auren nan don Allaj,ashe rayuwar gidansu tafi dadi.
Qarfe takwas na daren ranar a cikin gidansu asma'u ta yiwa hamid gaban daddy,idanunshi cike fal da qwalla yake cewa daddy
"Jarrabawa ce ta fado mana,munci bashin banki mun siyi kaya suka nutse a ruwa,jirgin wancan satin da aka fada a labarai kusan rabi duka kayanmu ne,banki suka tasomu a gaba mu biya bashin da muka ci,daddy kasan sarai halinsu ba mutunci ko daga qafa,hakan ya sanya muka saida duk abinda muka mallaka nida daddy donmu rufawa kanm asiri muka biya,yau muka koma gidan da muka siya daddy bansan asma'u da gaske take ba zata zauna dani ba wai na zama talaka sai dana dawo na tadda bata gidan,ko hajiya bata yiwa sallama ba tayi ficewarta" ran daddy yayi matuqar baci,wato saboda raini daya ce ta koma gidan ma bata koma ba,waya ya dauka ya kira mummy yace ta turota,tana jin hakan tasan da walakin,saboda haka suka shirya dukkan abinda zata fada sannan ta iso falon
"Daddy....wallahi macuci ne,tun kafin sannan ya dauki dukkan kadarata ya saida min,yanzu haka bani da komai"
"Mijin naki kike kallan tsabar qwayar idanuna kike cewa macuci asma'u?" Daddy ya fada cikin bacin rai,saitayi laqwas data tuna barnar data tafka
"Ashe ke baki cikin matan dake rufawa mazajensu asiri idan babu ta samesu?,koma.meye ya saida nakin ina cewa shi ya malllaka miki shi ko?,idan kuma akwai wansa na mallaka miki shi bani na siya ba?,to na bar mishi har zuwa sanda Allah zai hore mishi ya musanya miki da wani,maza tun muna mu biyu ki tashi kibi mijinki,kiyi haquri sa samunshi da babu,wannan shine cikar mace ta gari" kuka take wiwi kamar ance ga ranar mutuwarta,hamid ya zame mata qarfen qafa kenan,bayan fitarta daddy ya dubeshi shima,yana sane da yadda yakema asma'un qanqamo saboda haka cikin hikima yamasa dan jan hankali
"Duk mutumin dake yalwatawa iyalinshi ba shakka zaka sameshi ko yaushe cikin budi shima da samu,Allah baya taba hanashi,saboda ma'aiki ya bamu labari cewa,ako da yaushe kullum ta Allah wasu mala'ikun Allah biyu na sauka,dayan yana cewa,ya Allah wanda yake ciyarwa ka ninka dukiyarshi,yayin da dayan yake cewa,ya Allah wanda yake riqe dukiyarshi baya ciyarwa ka hadashi da asara,zai iya yiwuwa sanadin quntatawa.iyali da qin yalwata musu Allah ya saukar maka da asara cikin dukiya,ya hana arziqinka ci gaba" sai yaji jikinsa yayi dam sanyi,don na wanda ke masa magana ta wannan sigar,sosai ya yiwa daddyn godiya,qimarshi ta dadu a idanunshi,wanda sanadiyyar haka yayi damarar gyarawa ko yaya ne,sa zasu tafin ya sallami asma'un da wasu kudin haka shima hamid,duk daba'a gaban asma'un ya bashi ba amma sai daya ji girman kan karba,sai kace wanda talauci ya kama?,yake gayawa.kansa,ni kuwa nace uhmm me kake ci na baka na zuba?,tukunna dai,haka ya dauketa tana bala'i da zumbure zumbure suka wuce.
*_wanan littafin na kudi ne,idan kika gani don girman Allah karki tura,ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number_*
56
Cikin satin kafin tafiyarsu umara wani irin sabo da shaquwa mai qarfi ya shiga tsakaninsu,qaunar khalipha babu inda bata jinta cikin jiki da jininta,bata taba sanin tayi nisa a qaunarshi ba sai yanzu,haka ta nashi fannin ya gama sallamawa gaba daya,hakanan ya gama tafiya,dukkan wasu hakaye na aysha wadanda baisan dasu ba a yanzu ya karancesu,komai nata yayi masa,komai nata yadda yakeso ne,irin matar da yake mafarki da fata gami da burin aure a yanzu ya samu,wani lokaci yakanji kanshi kamar bashi ba,ayshan ta sauya dukkan wanin tunani nasa,burinta ya zama nashi nashi ya zama nata,qiris yake jira su zama abu guda,sai yanzu yake jinsa cikin wata sabuwar duniya,jinsa yake kamar an sauyashi,kamar ba shine khalipha ba na ainihi,ta wanke masa duk wani burbushin bacin rai da yayi saura a rayuwarshi,shi yasa yake da fata da kuma burin ya zama silar wankewar duk wata damuwa tata da tayi saura a zuciyarta.
Ana ya gobe zasu tafi da daddare ya sanyata ta shirya don ya kaita suyi sallama da daddy,tsaf ta shirya tayi adonta kamar yadda ta saba ya kuma zame mata jiki dai dai misali mai sanyi ba hayaniya,shi kansa khaliphan yayi kyau cikin shaddar daya buga,ya kawo hularshi gaban goshi shigar cikakken bakano abun sai wanda ya gani 🤪.
Tare suka jero shida ita,duk wanda ya gansu a lokacin saiya juya ya sake dubansu,cikakkun masoyan da sukayi nutso duniyar soyayya suka dandana zaqinta,masoyan da tun a siffa da kama suka dace da juna zuwa ga halaye,bude mishi motar akayi saiya matsa mata ita ta shiga,shi kuma ya bude da kanshi sannan suka rufe suka tada motocin suka fice.
Itace a gaba kai tsaye zuwa sashen daddyn,saboda tun a harabar gidan mai gadin ya shaida mata mummyn na can sashen,dawowa tayi ta shaidawa khalipha saiya gyada kai
"Ki fara shiga ki sanar mishi shigowata ko?,kaman hakan yafi tsari"
"To" ta amsa mishi tana juyawa saiya bita da kallo
"Uwaishahh..." Ya kirata,ta waiwayo tana murmushi can qasan ranta,don idan da sabo ta saba,don khalipha saiya kirata sau nawa kafin taje waje musamman idan tayi kwalliya,kawai sai yace tafiyarta yakeson kalla,ko kuma kai kawonta yakeson gani,hakan kawai ya isheshi abun farinciki,saitinshi ta ranqwafo,saiya miqa hannunashi saitin bakinta
"Ciromin sweet dita,yanzu yaci ace kinsha rabi aiko?" Murmushi ta saki,cikin motarshi ta dauka,suna nan sunfi talatin,amma kawai bazai sha ba sai wadda tasha ta rage
"Kayi haquri ka barmin wannan ka dauki wata mana ya khalipha"ta fada tana langabe kai
"aifa bazaiyiwu ba,amma.idan kina so zan.barmikin,saidai da sharadi" sai yayi qasa da muryarshi yadda ita dashi ne kawai zasuji abinda yace mata,kunya ta tilastata rufe fuskarta da hannayenta tana son tashi a wajen amma ya danne mayafinta
"If kin yarda nima nafison hakan,saboda wannan bakin yafi sweet din dadi nesa ba kusa ba" da sauri ta ciro alewar daga bakinta tana miqa mishi,saiya turbune fuska kadan yana kallonta bayan ya narke kamar qaramin yaro
"Rowa ko?,tona fasa shan sweet dinma"
"Am sorry ba haka bane,yi haquri ka amsa kasha" hannu ya sanya ya karba alewar ya saka a bakinsa,sai ya lumshe ido yana cewa
"Nifa ban taba sanin haka alewar nan keda dadi ba saida kema kika soma sha,duk sanda ta taba miyan bakinki kamar yana qara mata dadi ne" dariya ta saki sosai tana ficewa a wajen,indai khalipha ne yanzu zai shagaltar da ita,tana murmushi gami da miqa godiyarta ga sarki Allah daya mata baiwa da miji irin khalipha har ta isa sashen daddy.
Asma'u dake tsaye can gefen wasu shukoki tana ganin abinda ke faruwa ta saki ajiyar zuciya,wani sashe na zuciyarta na bata qwarin gwiwar tunkarar khaliphan,komai nashi yayi mata,dukkan wani abu da take bida ta ganshi tattare da shi,matuqar zai amince mata kashe aurenta ba wani abu bane mai wahala a wajenta,bare a yanzu da take jin auren tamkar ana dorata saman qaya ne,ko qawaye yanzu ta yanke alaqa da kowa,don kada ma wani ya rabeta ya fahimci halin da take ciki,kayan da daddy ya mata order tuni sun taru sunci uwar kayan da kudin ita da qawaye tun suna wancan gidan nasu,bata iya adani ba,bata iya tattali ba,batasan ta juya biyar ta koma goma ba,ta riga ta saba tun agida saidai ta bid'a a bata,takowa ta dinga yi har zuwa inda khalipha ke zaune cikin motar tayi knocking,ya tsammaci aysha ce saiya sauke gilashin yana murmushi,idanu biyu sukayi da asma'u,take yayi gaggawar gimtse fuskarshi yana dubanta
"Ranka ya dade yau kaine a gidan namu da kanka?"
"Eh...yaron oga ne da 'yar aikin gidan sukazo gaida mai gidan" saita danyi dum saboda tasan magana dai yake gaya mata,cikin barikanci tace
"Banda dai tuna baya,abinda ya wuce ya riga daya wuce,na baka haquri amma na fuskanci har yau baka haqura ba" tsaki yaja yana shirin daga gilasanshi saboda sauraton tama sam baida amfani saita dafe cikin karyewar zuciya
"Don Allah khalipha kayi haquri,ka taimaka ka karbeni kamar yadda ka amshi aysha,ba sonta kake ba tun asali nice wadda kakeso,qaddara ita takawo faruwar komai,kai kadai kai zaka cikamin burina"
"Burinki na kudi ko?,baki da matsala waisaita kudi ne?,a duniya babu wani abu mai daraja bayan kudi?,inasom in miki gargadi na qarshe kar bakinki ya sake kuskuren cewa bana son aysha na aureta,har abada aysha itace zabina,tun kafin nasanta nake qaunarta,tin kafin nasan zatazo cikin qaddarata nakesonta,kin fahimta?"
"Kamar yaya?" Ta yiwa kanta tambayar,saidai bai tsaya bata amsa ba yadaga gilasanshi yana jan tsaki ranshi yana baci,wato a rayuwa ma ka aikatawa mutum ba dai dai ba kazo daga bisani kana jin kunyarshi ka rahama ne?,wannan kenan na nuna zuciyarka akwai ragowar danshi,idanunka basu qarasa qeqashewa ba.
Kallo daya tayi masa tasan yauma baida lpy,hankalinta ya tashi sosai,tunda yayi wancan rashin lafiyar kullum saita kirashi amma ko sau daya bai taba nuna mata yana kwance ba,amma saboda qarfin hali irin na daddy nuna mata yake ba komai,ta sanar mishi tarr da khalipha suke,yace
"maza shigo dashi mana indo,yaron kirki dan albarka".
Tana juyawa daga wajen motar sukaci karo da aysha,kallon data jefa mata shi ya sanya jikin ayshan ya bata akwai wata a qasa,me take jikin motar khalipha?,tasan halin asma'u sarai shekarun da suka diba gida daya ba wasa bane,saita gifta ayshan ba tare data ce mata komai ba,itama ganin haka yasa ta kama kanta tunda tasan ba wani abu data yi mata.
Tare suka jero har cikin parlour din,a sannan mummy na zaune tana hada magunganan daddy daya gama sha,idanunta kan khalipha sanda yake gaisheta,banbanci muraran ta ganshi,qyashi ya cika ranta,saita kasa zama tabar musu falon ta koma sashenta,wanda hakan ya basu damar hira sosai duka su ukun harda khalipha,irin hirar da zata ce ma bata tabayinta da daddy ba,har tayi mamakin dadewarsu sanda suka tashi zasu tafi suna mishi sallama kan gobe zasu wuce umara,dai dai sanda asma'u ta shigo falon,sai ta samu waje ta zauna tana jinsu,cikin farinciki daddy yayiwa ayshan murna,saboda yasa yunqurin kaita sai mummy ta sako wasu qorafe qorafe da zai sanya a dage zuwan da ita koda daddyn bai shiryawa hakan ba
"Uhmmm,ba sabanba,su umara manya,kai bawa da baka taba zuwa ba daka shiga uku" asma'u ta fada qasa qasa yadda ayshan zata jiyota,murmushi tayi sannan itama ta mayar matan ta yadda zata jita da kyau
"Mun godewa Allah da bai banbanta saudiyyan masu kudi da talakawa ba,duka dai gurin daya ne inda kaje nima can zani,Allah ya kirani babu damar dakatarwa" saita miqe ta isa gaban daddy tana masa sallama bayan fitar khalipha wanda yadan basu waje ne suyi sallama
"Allah ya qara maka lafiya daddy,bansan wanne irin abu zan saka maka dashi ba a rayuwarta,don Allah daddy ka tambayi koda abu daya ne a wajena wanda kake buqata daga gareni" murmushi ya saki
"Aysha indo har kullum kedin ta dabance,haka Allah yake tsarinsa cikin halittunsa saiya fifita wani kan wani,dukkan abinda nayi miki nayi miki ne Saboda Allah,na miki saboda a lokacin kina cancanci kuma kina da buqatar ayi mikin,abu guda daya da zan nema a gareki shine,ko bayan raina karki manta dani kici gaba da yimin addu'a"zuciyarta ce taji ta karye da kalamanshi,wani rauni ya kamata,take hawaye ya balle mata,asma'u dake zaune gefe ta tabe baki
"Kalen dangin masifa,kamar ta fimu sonshi,sai kace ita ya haifa bamu ba" ta fada a zuciyarta
"Indai xan manta dakai daddy to lallai zan manta da kaina,baka cikin jerin mutanen da zan iya mancewa dasu har numfashina yabar gangar jikina,ubangiji yayi maka jagora a dukka lamuranka duniya da lahira"
"Amin ya Allah ayshatu,idan na taba yi miki wani abu naba daidai ba tsahon zamanki a gidan nan ina neman afuwarki" kuka ta saki sosai harda sheshsheqa
"Daddy niya cancanci na nema afuwarka da zanyi tafiya,ba zaka taba laifi ba awajena daddy koda naman jikina kake yanka kullum"
"Daina kuka ayshatu,ubangiji yayi miki albarka duniya da lahira,idan kinje kimin dawafi na musamman kiyimin addu'a sosai"
"Zan maka addu'a daddy in sha Allahu fiye da yadda zan yiwa kaina"da haka sukayi sallama,haka kawai taji zuciyarta ta karye qwarai,hakanan taji kamar karta tafi,kukan da take yaqi tsayawa har a cikin mota,tun khalipa na daurewa har ya gaza
"uwaishah,ki taimakeni kiyi shuru,har cikin qirjina nakejin ciwon kukan da kikeyi" bata son bata masa rai ko qanqani,hakan ya sanya dole tayi shuru gami da yin luf a qirjinsa,kusan ranar wuni tayi a sanyaye,tunanin daddy fal zuciyarta.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Washegarin ranar jirginsu ya daga sai saudiyya,a garin makka suma soma sauka,suna sauka a masaukinsu dukkansu sukayi wanka suka dauki harama,saboda tsabar murna da zumudi ma ta rigashi kammalawa,ji take kaman tayi tsuntsuwa ta ganta bakin ka'aba,tana da abubuwa da yawa da zata roqa,tana da mutanen da takeso ta yiwa addu'a sosai,idanunta a kanshi sanda ya kammala daura hiraminshi,idanu suka hada sai suka sakarwa juna murmushi a kusan tare,kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarshi.
Sati guda sukayi a garin makka,iya ibada kam sunyita saidai fatansu Allah ya amsa,bata taba sanin khaliphan ta fannin ibada jarumi bane sai a wannan karon,duk nacinta da son ibada sai taga ashe ya kere mata,sau tari idan ta gaji tayi kaman zata huta sai taga shi a sannan ya saka qaimi,sai ya sake zaburar da ita,tabbas ta yarda ta kuma amince cewa kowacce mace halayenta idan zama yayi zama na kamanceceniya dana mijinta,kota debi wasu dabi'u nashi koshi ya debi nata,idan akayi katari na gari ne sai nagartarta ta ninku,idan kuma akasin haka ne walau ya rinjayeta ta ko ta koyi kaso mafi yawa daga cikin halayensa,shi yasa akeson ko aboki zakayi ka aboci na qwarai,don annabi ya kwantata aboki na qwarai da misalin mai saida turare ne ko.baka siya ba idan ka zauna dashi dole wataran zai san maka,kaima zakayi qamshi,hakanan nara gurbin aboki tamkar abota da maqeri ne,kana zaune feshin wutar zai dinga sauka atufafinka yana bata maka sutura,hakan shike nuna auren miji na gari shine babbar sa'a hakanan abu mafi muhimmanci da gata da mace zata yiwa kanta da zuriyar da zata samu a nan gaba.
Randa suka cika sati guda a garin makka suka wuce madina don suyi ziyara,musamman ya samu motar da zata zagaya dasu duk wani wajen da tarihi yazo dashi a addinin musulunci,farincikin data dinga ji ya zarce wanda taji a garin makka,jinta take fes,zuciyarta qal,kamar babu wani abu daya taba samunta a rayuwa na bacin rai,kullum tana maqale da masallacin ma'aiki tana yiwa kanta khalipha daddy da anni addu'a,dama duk wanda ya ratsa rayuwarta,idan na neman shiriya ne ta nema masa,idan na fatan alkhairi ne tayi masa.
Randa suka cika kwanaki hudu a garin madinan,da wata safiya sun fito zuwa masallaci ita da khalipha,irin wannan yanayin yana mata dadi qwarai,takan jita wata ta daban ta musamman,zuciyarta da ruhinta kan cika da farinciki,tabbas garin madina dabanne,hatta da yanayinsa ma daban yake,tayo bangaren mata shi yayi bangaren maza taji sabuwar wayarta daya siya mata tana ruri,tana dubawa taga sunanshi ne,cikin mamaki ta kara a kunnenta
"Ta wacce qofa zaki shiga?" Ya tambayeta,gaya mishi tayi sai yace ta sauya ta shiga ta daya qofar,bata kawo komai ranta ba ta amsa mishi ta kashe wayar sannan taci gaba da takawa donta wuce zuwa cikin masallacin.
A hankali take takawa cikin zuciyarta tana ta istigfari kamar yadda ta saba tunda suka zo,bata minti daya cikakke bakinta babu ambaton Allah,tana son ta ribaci lokacinta da dimbin falalar da garin yake dashi,dukkan aikin da kayi cikin garin walau na alkhairi kona sharri kana da ninkin lada ko zunubi.
Kamar a mafarki kamar wasa sukayi kacibus da umminta tana shirin fita daga masallacin itama,kallon kallo suka fara yuwa junansu tamkar wasu baqin juna,dukkan wani tashin hankali da fargaba da aysha takeji a sanda suka hadu a yanzu fes take jinta,zuciyarta a taaye take kyam,idanunta cikin na umminta
"Assalamu alaikum"aysha ta furtawa ummin tana dubanta
"wa'alaikumussalam"ta amsa mata itama tana dubanta,idan batayi kuskure ba qwalla take gani cikin idanuwan ummin fal,saitadan gotata kamar zata shige,da sauri aysha ta riqe tsintsiyar hannunta,tsahon minti daya suna a haka kowa ya kasa motsawa,sai ta jiyo sheshsheqar kukan ummin nata,abinda yayi masifar tayar mata da hankali,da hanzari ta sakar mata hannu tasha gabanta,batayi auneba taji ummin ta rungumeta tsam tana sakin kuka sosai
"bazan iya ba,bazan iya ci gana ba"
"Kiyi shuru ummi don Allah" saiga ayshan dake bata bakin tayi shuru itama ta saki kukan,duk yadda taso daurewa ta kasa,kuka suke sosai,ganin masu wucewa zuwa cikin masallacin na kallonsu ya sanya ayshan janye ummi gefe.
"Naja'atu" dukkaninsu suka waiwaya jin an ambaci sunan ummin,wani mutumine wanda aqalla zaikai shekara hamsin da biyar,gefanshi kuma khalipha ne tsaye suna dubansu,kuka ummin ta sake saki tana kauda kanta daga garesu baki daya,takawa mutumin yayi har zuwa inda take tsaye ya riqe hannayenta
"Idan kowa bai isa alfarnar garin nan,da wanda kabarinsa ke cikin wannan waje mai albarka sun isa su sanya ki amshi diyarki"
"Abban basma.....bana so...." Sai maganar tata ta harqe
"Bana son maganar da suka fada ta tabbata akan aisha,banason ta silata wani abu ya sameta" ta fada tana sake barkewa da kuka
"Dukkaninmu ba zamu fahimci abinda kike magana akai ba idan ba bayani kika yi mana ba"
"Ammm....abba,me zai hana mu samu wani waje su zauna a can" cewar khalipha,kai abban ya gyada masa sannan ya riqe hannun ummi naja'atu dake ta kuka.
Shuru kowannensu yayi kafin abba ya daga kai ya dubi aysha
"Khalipha ya cancanci zama yaji kowanne irin abu da naja'atu xata fada,fita kice ya shigo" a sanyaye aysha ta miqe don zuwa kiranshi,saidai duka hankalinta nakan ummin,gani take kaman kafin taje ta dawo xata rasa ummin,kamar kafin taje ta dawo ummin xata sauya ra'ayi,zata fasa fada mata komai,zata fasa karbarta,itama ummin nata idanun nakan ayshan,ita kadai tasan me take hadiyewa a haka harta dawo tare da khalipha,kujerar dake daura da aysha abba ya nuna masa yace ya zauna,da fari baiso zaman ba,saboda yana ganinnkamar wani sirri ne da bai shafi yaji ba,amma abba yace ko daya,miji shine babban sirri na farko wajen matarsa,haka ya zauna kanshi da idanuwanshi a qasa yana harhada cukurkudaddiyar rayuwarsu shida ayshan waje daya
"A ranar dana bar gidan baffale a daren ba'a kwana ba akace ana sallama da baffana,yana fita baifi minti biyar ba muka jiyo hayaniya cikin zauren gidanmu,sai gashi ya dawo yace na fito ana son magana dani,ban musa ba na miqe na fito,saidai wadanda na gani a wajen inda ya gaya min su sukazo tabbas bazan fito ba,gefe daya na samu na tsaya ina dubansu,dukkan yayye da qannem baffale ne mazan sai inna yelwa
"halaa ma dai bakasan abinda ya faru ba?"cewar saya daga cikin yayyen baffale yana gayawa baffana,kai ya jinjina yace kai nake sauraro
" to mudai muna da tantamar indo diyar baffale ce gaba dayanmu,tunda cikinta bai tashi bullowa ba sai da yabar garin nan gaba daya"nan fa ran baffanmu ya baci sosai,duk haqurinshi kuwa,saidai ya hadiye yana dubansu kawai
"Me kukeson ku gayamin,nafi ku sanin wace naja"
"Ai ka tsaya malam duka na wannan ba,abu daya shine zai tabbatar mana da aisha jinin baffale ce kuma jininku" shuru kowa yayi nida baffa gaba daya muna sauraronsu,inna yelwa ce ciki izgili nuna isa da taqama tace
"Daga nan har shekaru goma dai dai da rana daya idan naja ta koda kalli indo kota sake ta nemeta toba jininmu bace,ba baffale ne mahaifinta ba,matuqar jininmu ce to babu ita babu ita,ba ruwanta da ita jininta zasu kula da ita..." Ban tsaya na qarasa saurarenta ba kawai na juya cikin gida na barsu nan da baffa na,maganar ta inna yelwa ta yimin ciwo qwarai,sharrin zina ba abinda ya kaishi muni,na shiga bacin rai sosai a sannan,na sake tsanar inna yelwa da ahalin gidanta gaba daya.
Ana tsaka da wannan saiga inna sailuba,qawar inna yelwa ce sosai,saidai ikon Allah Allah ya hada jinina da ita tana qaunata qwarai,batasan aurena ya mutu ba saboda ba'a garin take auren ba,saidaga bisani tazo ta biyo ta yimin jaje tare da nuna rashin jin dadinta akan aninda inna yelwa tayi,ranar sai gata hankalinta a tashe,ban taba ganinta cikin tashin hankali ba irin ranar,ita take gayan maganar data sake sakawa na janye jikina da.aysha,na nuna mata qyama,na farko ta gayamin inna yelwa ashe ta rabani da baffale tasa aka sanya qiyayyar juna atsakaninmu,har ya mutu yana ambatona yana neman gafarata,sannan yanzu kuma sunyi wani shiri saboda basa son hada jini dani,duk ranar dana yiwa aysha wani kallo na tausayi ko jin qai a ranar ba zata sake kwana a duniya ba,saboda suna da yaqinin babu uwar da zata daurewar azabar da suka shirya suna gana mata iri iri,banso na rasa aisha diyar dana fara samu a duniya,tilas na koyawa kaina kyararta da tsangwarta,duk da a sannan na shaidawa baffa na kafin rasuwarshi yayi addu'a sosai da rubutu,idan baki manta ba mero na baki wani rubutu kisha waina tsari,shike aikawa meron ya bata yace ta baki,koya manta wani lokaci da kaina nake dauka na aika a zuwan baffa ne ya bayar,duk halin da kike ciki aysha ina sane labari yana zuwarmin,na hana 'yan uwana su daukoki kosu karboki ne gudun kada wannan abun da suja qulla har a lokacin yana nan ya zama silar barinki duniya,silar barina qauyenmu bazan iya zama ina nuna miki qiyayya sauran jama'a na nuna miki ba,sai naga gwara nayi aure a nesa,gwara nayi nesa dake,wataqila idan bakya ganina zaki haqura dani,wataqila abinda kike ji cikin zuciyarki zai ragu,kullum ta Allah sai nayi kuka akanki aysha,sai nayi kuka saboda tausayinki,kullum addu'a nake Allah yasanya duk randa zamu hadu wannan mugun abun ya warware,haduwarmu a nan zuciyata ta bani yaqinin duk wani mugun abu bai isa yayi tasiri a waje mai tsarki irin wanna ba,ki yafemin aysha....dukkan abinda ya faru ya farune bawai don ina sane ba ko inajin dadin faruwar hakan....."sai kuka ya qwace mata(a nan ina nemawa wadda ke cikin halin tsana da kyarar mahaifiyarta kamar aysha addu'a,ku sanyata a addu'a Allah yaye mata ya karkato mata da hankalin mahaifiyarta).
Rungumeta aysha tayi itama ummin ta rungumeta tsam suna kuka,sai khalipha ya kasa dauka ya miqe a hankali ya fice daga wajen,ganin haka ya sanya abba miqewa shima ya basu waje.
08030811300
57
Dukkan abinda ya faru a rayuwar aysha daga wanda ta bashi lbr kama da wanda ya faru yanzu ya dinga tariya cikin kwanyarsa,jinjina kai kawai yake,sai yaji yana son magana da anni wadda satin da zasu zo ta gama tata umarar ta wuce dubai inda ruqayya da take aure saboda haihuwa da tayi,shima yana saka ran daga nan can zasu wuce da aysha suga juna,don bata taba ganinta ba,ta kuna takura tana son ganin nata.
Suna soma magana da annin ayshan ta fito,saita koma gefa daya tana kallonshi hannayenta sarqafe da juna,wani iri so nashi da qimarshi na hauhawa cikin zuciyarta,sai yanzu ta fahimci shiya shirya komai,shiya shirya haduwarta da mahaifiyarta kamar yadda ya biya musu umara suma ya biya musu donsu hadu a nan,wanne irin mutum ne shi wanda bai gajiya da alkhairi?,wanne irin so yake mata da har kullum yake bibiye da lamuranta da dukkan mutumin daya rabeta yana aikin faranta musu?,bata dawo daga duniyar tunani ba saidaya miqa mata waya yana cewa zasuyi magana da anni,ta amshi wayar zata kai kunneta can qasa yace
"Ki rage wannan kallon da kikemin idan baso kike ki qarasa zautani ba" murmushi ta saki mai sanyi wanda yasa kumatunta lobawa,saiya shagala da kallonta sanda suke magana da anni,harta gama ta miqo masa bai sani ba
"Nima zaka zautani dinne?" 'Yar qaramar dariya ya saki yana karbar wayar
"Na gode,kin rama munyi one one ko?" Ya fadi yana dage mata gira,wani murmushin ta sake saki
"To yaya?,komai yayi normal?" Ya fada yana wara hannayenshi,kai ta gyada,sai hawaye ya soma bin fuskarta
"Ashe haka uwa take sa dadi ya khalipha?"kai ya shiga girgiza mata
"nooo...kuka kuma dai?,ashe zaki sanya na fasa barinki ki kwana wajenta da nayi niyya" idanu ta fiddo tana share hawayen
"Da gaske zaka barni?" Girarsa ya daga
"Yes,kwana daya zakiyi,amma kiyi alqawarin tanadarmin dukkan wani farinciki a sanda kika dawo ko?" Bata gane me yake cewa ba,saidai tunda yace zai barta ta kwana wajen umminta ya gama mata komai,haka kuwa akayi,ya dauki abba suka wuce nasu masaukin,suka bar uwar da diyarta suka kwana babu bacci suna hira
"Bansan irin qaunar da basma take miki ba,tun daga ranar da kikazo naqi kulaki ta daina walwala har yau" murmushi aysha tayi
"Ki barta,zanyi magana da ita da kaina gobe zan kirata" ranar haka suka kwana dungurgur a zaune aysha na bata labarin yadda ta rayu,kuka wiwiwi ummin ta dinga yi,ta rasa inda zata dora ranta,tayi alqawarin yafewa inna yelwa ne aduk sanda ta gane kurenta ta nemi afuwa banda haka data yi mata Allah ya isa,ta kuma nemi Allah ya fitar mata da haqqinta,ranar ko masallaci basu sake komawa ba,haka suka kwana tare,duk wani motsin ummin aysha na biye da ita,ko hijabinta bata bari ta dauka da kanta,yayin da ummin kebin ayshan da kallo duk inda ta motsa,tausayinya na ratsata,ta goge qwalla a boye tafi sau nawa,itakanta a karan kanta idan ta tuna yadda tabar ayshan tun batasan kanta ba sai taji dama ta tariyo baya ta goge komai,me yasa tabar musu 'yarta bayan tasan basa qaunarta?,me yasa bata tafi da 'yarta ba kome zasu ce suce,da duk wani shiri nasu bayi tasiri ba,data rayu da 'yarta tasan gatan uwa,saidai qaddara ta riga fata,hakanan bawa baya iya gujewa qaddararta,mai yiwuwa data tafi da ita din da a yau ayshan bata samu khalipha ba,da wataqila bata samu matsayin da take dashi na rayuwa ba a yanzu.
Washegari khalipha ya dawo bayan sallar azahar,don abba yazo tunda safe ya gansu ya wuce masallaci,a sannan aysha na ramuwar bacci ummi ta tasheta tace maza taje,haka ta dauraye fuskarta ta fita harabar wajen da yake zaune,idanu ta zuba mata wani abu na tsirga masa harta qaraso inda yake,ji yake kaman ya sureta,yana kallonta yasan bacci take aka tasota,saiya narke mata tun kafin tayi magana
"Wato an samu ummi an manta dani ko?,ba saqon saoda safe,ba saqon barka da safiya,babu na barka da rana,shikenan na gode...kice kawai ba zaki iya kula dani ba tunda kin samu ummi na auro wata kawai" har cikin ranshi da wasa yake,amma abun mamaki saiga qwalla aisha ta fara,abunma kamar yayi dariya amma ganin da gaske kuka zata mishi saiya daure,bai taba zaton yadda ake cewa masu suna aysha nada kishi sosai gaske ne ba kamar yanzu,da qyar yasha kanta,saiya koma seriouse dinshi sosai
"Ki shirya anjima zanzo ki rakani inyi wata siyayya" kai ta langabar
"Ya khalipha....ban gaji ba da ganinta"
"Rakiya nace zakimin ai ko?" Kai ta gyada
"Shikenan" kadan suka taba hira ya wuce shima masallaci,saboda addu'a yakeso yayi yau sosai kan rayuwarsu shida ayshan,harkokin kasuwancinsa,iyaye da 'yan uwanshi.
Gab da magariba ya dawo,yayi kyau sosai cikin shigar larabawa jallabiyya baqa harda hirami,ita kuma ta sanya abaya maroon da baqin niqaf bayan ta nade kanta da mayafin abayar kai kace hijabi ta saka,kallonta yake saboda wani kyau data yi masa,idanuwanta da suka fito ta tsakiyar niqaf din kamar an qara musu girma da kyau,tun a lokacin jikinsa gaba daya ya amsa har cikin zuciya tuhi da gangar jiki,duk wani kuzarin daya taho dashi ya bace,a haka suka lallaba masallaci sukayi magarina da isha'i sannan yace ta fito su tafi.
Katafaren shagon saida kayan ado ne na mata,binsa tayi kawai da kallo sanda ya nufi bangaren kayan bacci bayan ya gama siyan turaruka masu dan karen kyau da tsada,tana kallonshi don yace ba ruwanta ya dinga zaben kayan bacci kala kala,sai daya dauki wajen kala goma dukkansu babu mai qaramin kudi sannan ya biya suka wuce.
Wani shagon suka sake tsayawa nan gaba da wajen kadan,gwalagwalai suke siyarwa,kana ganin yadda suke gaisawa da bashi qima kasan babban custumer ne,hakanan akwai alamun sabo sosai tsakaninsu,kujera yaja mata yace ta zauna,sample aka kawo mata kala kala na sarqa da dan kunne,zobe da banguls khaliphan yace ta tayashi zabe,ta tambayeshi guda nawa yace kowanne bibbiyu,tana zaton anni ko wani zai saiwa saboda haka ta zage ta zabi masu kyau,ita kanta sun bala'in burgeta,basu dade sosai ba ya biyasu sukayi sallama suka fita.
Daganan wajen saida kayan maqulashe ya tsaya shima,yayi siyayya sannan suka shiga motar suka wuce,ta dan gaji hakanan ga kewar ummi,Allah Allah take su isa ya ajeta ta ganta sannan ta huta,sai taga dirven ya dauki wata hanya daban,ba ha yar hotel din da suka sauka ba,hakanan ba hanyar hotel din su ummi ba,dubanshi tayi
"Ina zuwa kuma ya khalipha"
"Masauki zamu koma nayi kewarki uwaisha....kiyi haquri gobe saina maidaki wajen ummi,ni kadaine bana jin dadi" batason bata masa dai dai da rana daya,duk yadda taso ganin ummi saita kada masa kai kawai,sai a sannan ta tuna ma yace mata dama kwana daya zatayi,amma batasan ba zata dawo ba data sake magana da ummin.
Area ce mai wani irin kyau mai kwantar da zukata,hakanan hotel din shima kansa tun daga gininshi da tsarinsa kasan na musamman ne,bata sake tabbatarwa ba sai da suka shiga dakin,duk kayansu yana ciki a shirye,shi ya maida qofar ya sanya muqulli ya rufe,haka kawai a ji jikina yayi sanyi,ta daga kai ta dubi khalipha dake kallonta yana murmushi
"Dakin yayi miki?,ko mu sauya waje?" Murmushu tayi mai sanyi sannan tace
"Sosai ya khalipa"
"Wayyo Allah" ya fada yana aje kayan siyayyar hannunshi,don bai barta ta dauki komai ba kamar yadda bai bar wani ya dauka musu ba
"Wanka da alwala....wazai fara ni koke?" Idanu tadan fiddo
"Ya khalipha...nikam haka zan kwanta bana jin yin wanka"
"No...dole kiyi,so kike ki zama qazama?" Ya fada yana kada kanshi,haka kawai take jin fargaba,saboda kallon da khaliphan yake mata saitake ganin kamar ba wanda ya saba yi mata ba,saita noqe kafada
"Toka fara yi sannan ni" hannunshi ya ware
"Well,hakan yayi" jallabiyar jikinsa ya soma zamewa,saita dan rintse ido kamar yadda ta saba,yana kallonta saidai wannan karon dariya ta bashi,ya qunshe abarsa yana kada kai ya shige toilet din.
Kaman yadda ya saba aqalla yana daukan minti talatin sannan ya fito,tayi wuf ta shige bandakin ganinsa daure da dan guntun towel yau sabanin da da yakan sanya rigar towel,sanda take qoqarin rufe qofar ya sanya hannu ya tokare qofar ya rufa mata baya
"Ya khalipha....don Allah" saita gaza qarasawa ganin ya cimmata ya kaita bango,ya mata rumfa gaba daya,tsoronshi da kwarjinsa wanda bata taba jiba yau ya kamata,so yake lallai ta kalleshi amma taqiya,nunfashinsu ya dinga cakuduwa da juna,murya can qasa yace daita
"Wannan saurin da kike kika fada toilet duk na meye,to sai kin nunamin abinda kike tsoro" kamar zata sanya masa kuka take masa magiya
"Babu komai don Allah kayi haquri,nidai babu komai" wani murmushi ya saki wanda shi kadai yasan ma'anarshi ya janye baya yana cije lips dinshi,saiya nufi famfo ya sake daura alwala sannan ya juy ya dubeta,har yanzu tana tsaye inda ya ritsata
"Kiy sauri ki fito na baki minti goma,idan ba haka ba,zan shigo na daukoki ko baki gama ba"murmushi tayi a kunyace,juyawa yayi ya fice sannan yaja mata qofar toilet din.
Sanda ta fito tuni yana saman abun sallah,sanye da jallabiyya fara qar har daukan ido take,kansa saye da hula tashi ka fiya naci baqa,dakin ya bule da wani irin sassanyan qamshi,wani kyau taga yayi mata sosai,don karta shagala da kallonsa saita kauda kanta,riga ta gani aje ta bacci da kuma after mai kauri gefanta,girgiza kai tayi sanda taga yadda rigar take,amma data tuna zata dora after din saita dauka ta koma bandaki ta shirya acan,ta mulke jikinta da wani turare daya aje mata wanda qamshinsa da dadinsa ya dinga sanyata kasala.
Binta yayi da kallo sanda ta fito daga bandakin,sai yayi mata nuni da gefansa,matsawa tayi ta saita sahu yadda ya dace ya kabbara sallah cikin mamakin sallar meye itama ta tayar,raka'a biyu sukayi sukayi sallama,yaja doguwar addu'a sosai wanda ke tattare da roqon dukkan alkhairi sannan ya shafa,jiyowa yayi ya zauna yana fuskantarta gami da tanqwashe qafa,janye idanunta tayi daga nashi tana jin zuciyarta na bugawa,wata fargaba na shigarta,sunanta ya kira wanda ya sanya ta daga kai ta dubeshi,a nutse yake mata tambayoyi game da abinda ya shafi addininta,sallah tsarki da wanka,kada kai kawai yake yana gamsuwa da bayaninta,kai karantse wata malama ce,sai data kammala sannan ya dora hannunshi ya karanta addu'ar nan da annabi ya umarcemu ga duk wanda Allah ya horewa yayi wani sabon abu,ko mata ko abun hawa,har ya gama tana saurarenshi,hannunsa ya sanya ya janyo ledar dake gafansa wadda suka siyo kayan ciye ciye a ciki,ya fidda komai ya aje a gabansu,itadai nata ido jiki a salube,donta shinshino wani abu,da kanshi ya dinga ciyar da ita,duk da taso ta turje da farko yayi kicin kicin ya nuna yayi fushi,cikin hikima ya dinga janta da hira wanda ya sanyata ta sake,sai gata tana qyalqyala dariya,bayan sun gama ita ta gyara wajen kafin ta kammala ya haye gado abinshi
"Malama a cire hijabin nan da after din mana haka?,banfa ga kwalliyar ba" sai ta dan diririce kadan saboda tuna yanayin rigar dake qasa,girarshi ya dage mata
"Yes....ko so kike nayi asarar kudina?" Ya fada yana zuba mata idanu,hakanan ta dinga fidda kayan kunya na saukar mata,sai daya ragw saura rigar baccin kawai,zuwa sannan numfashinsa ya soma masa nauyi,tunda Allah ya halicceshi bai taba ganin sura irin haka baka,ashe ayshan ta zarta dukkan yadda yake tunani,hannunshi ya miqa mata yana daga zaune saman gadon,bayanshi jingine da fuskar gadon qafafunshi miqe
"Kai zo nan muga wani abu....ya maqale miki a gashi meye haka kamar qadangare?"gaba daya basirarta ta tafi,dama atsorace take haka kawai,sai ta kwasa tayi wajenshi babu shiri,batasan cewa wayo yayi mata ba sai data ji ta shigo hannu,saqonni yake aika mata masu wuyar bijirewa,masu nauyi a qwaqwalwa,masu rikita lissafi,sai daya warware mata dukkan wani lissafinta sannan ya rada mata
"Zanso darenmu na farko ya zama cikin wannan garin mai albarka kamar yadda na jima ina burin haka a rayuwata a duk sanda Allah ya bani matar aure,saboda kwadayin albarkar dake cikin garin,kin bani damar cika wannan buri nawa uwaisha?" Kai ta gyada mishi tana rufe idanunta,tana son ta yaqi tsoto da fargabar dake taso mata
"Na gode,na gode" ya dinga maimaita mata yana cusa kanshi tsakanin wuyanta da sumar kanta ta sauko tayi musu rumfa duka su biyun.
Cikin wannan sassanyan daren,khalipha da ayshan suka zama abu guda,khaliphan ya samu ayshan fiye da yadda yake tsammani duk da cewa shi din farin shiga ne,ya bita a sannu yanda ya kamata saidai hakan bai hanata jin jiki ba,tunda ita dinma baquwa ce a fannin,saidai yanayin yadda ya riritata ya taqaita mata wahala qwarai da batasan yadda zata kaya mata ba.
Hakan gaba dayansu bai hanasu tashi sallar asuba ba,tare sukayi jam'i,ya waiwayo yana kallonta sanda suka idar cikin tausayawa da wata tarin qauna,saidai taqi yarda su hada idanu,wata kunyarsa mara misali take ji,murmushi ya saka a sirrance don yasan kunyar me take
"Khalipha zan mutu,ashe dama baka sona?" Ya fada a hankali,sarai ta jishi kuma tasan ita yake tsokana,saitayi banza dashi saidai bakinta data dan zumburo
"Ina sonki mana my uwaisha,Allah sai yanzu ma nake sake jin wani sabon shauqi game dake,uwaishaahhh zan iya mutuwa saboda ke..." Salon yadda yayi maganar cike da tsokana da shagwaba ya sanyata sakim dariyar dole,shima tayata yayi kafin daga bisani yayi nasarar sanyata cikin jikinta yana shafar gashin kanta,addu'a ya dinga jero mata godiya da fatan alkhairi tana amsawa can qasa kanta na saman qirjinta,a haka har bacci yayi awon gaba da ita,shimfideta yayi a wajen yana gyara mata kwanciya idanunshi a kanta,ya jima ahaka yana kallonta kafin ya miqe yana shawagi kadan kadan a dakin kamar mai gadinta,zuciyarsa fes qal,wani farinciki na musamman na ratsashi,ashe da can ba rayuwa yake ba gashinan ne dai kawai?,ya godewa Allah da tasahon shekarun ya tsareshi ya kuma kare ayshanshi,duk irin gwagwarmayar rayuwar da suka fuskanta hakan bai sanya sun fada gonar daba tasu ba.
Bai taisheta ba sai dayaga lokacin sallar azahar yayi,tana zaune inda tayi sallar yana aukin kallonta yace
"Ko zaki shirya na kaiki wajen ummi?" Kai ta girgiza alamun a'ah,don tana ganin kamar idan taje ummin zata gane wani abu daya faru.
Da la'asar ta sanke wanka da ruwa mai zafo don taji dadin jikinta,taji din kuwa,har ta dan samu tayi mishi kwalliya,tana daura dankwalin kanta taji hannunshi a wuyanta,sarqar gold din da suka siyo ce wadsa duk ciki tafi kowacce kyau da tsafa,bata ce komai ba itadai tana tsaye tana kallonshi,yasanya mata dan kunnenta sannan ya kama hannunta ya zira mata awarwarayen,baya ya danja yana kallonta
"Kamar yadda na zata kin haskasu sosai" ido ta zare tana daga gira alamun neman qarin bayani
"Eh,kin haskasu,don kinfi qarfin su haskaki aysha basu da wannan kyan saidai ke haskasu" tilas ya sanyata dariya,idan yana yabonta wani lokaci yakan sanyata dole taji kanta ya kumbura,taji duk duniya babu macen da tayi sa'ar miji kamar ita
"Wannan shine dan qaramin tukuicin da zan baki kan farincikin da kika sanyani daren jiya" ya rada mata wanda kunya ta sanyata saka tafin hannunta ta rufe fuskarta,kamar yadda ya saba ya hanata godiya yace amma wannan karon ta adana godiyarta sai haduwa ta biyu,murmushi ta saki kawai,khalipha na sata jin kunya shi kuma babu ruwanshi.
Haka sukayi zamansu yana jinyar abarsa yana lelenta,saida sukayi kwana biyu cur sannan suka fita,zuwa sannan ta samu sauqi bata jin komai a jikinta,don ya bata tazara bai sake neman komai daga gareta ba,ranar tare da ummi suka wuni a masallaci,don suna saka ran a satin zasu bar saudiyya.
Cikin satin kuwa khalipha ya dinga daukarta suna zuwa siyayya,har gajiya tayi da siyayya,ya dinga sanyata tana diban kaya kamar banza,batasan cewa ba nijeria zasu wuce ba sai ana ya gobe zasu tafi,ya shaida mata suma zasu suga ruqayya ne,langabe masa tayi tana kallonsa
"Nayi missing din anni pls ya khalipha...."
"Na sani nima haka,amma inaso muje mata ne da babbar tsaraba" sam bata gane ne yake nufi ba sai tace
"Akwai tsarabar dana siya mata,kuma abinda tafiso shi na siya mata,nasan zataji dadinta" bakinsa ya tabe yana kada kai
"Duk tsarabar da zaki kai mata bata kai wanna ba,so nake ki samar mata jika....." Ai bai qarasa ba ta saki ihu tana rufe fuskarta,yayin daya bita ya danneta yana qoqarin saita bude fuskar ya qarasa gaya mata ita kuma ta qiya,daga qarshe shi yayi nasara dole sai rintse idanunta tayi tana saurarenshi a haka.
Karon farko da suka soma haduwa da ruqayya tayi aysha ta kwanta mata sosai,kamar yadda itama anty ruqayya ta kwanta mata,ta rasa inda zata saka ayshan,ta lura akwai sabo da qaunar juna sosai tsakaninta da khalipha,yaranta kamar aysha ta qwacesu,yara masu kyau da tarbiyya.
Tun anty ruqayya na mata hira kan dabarun zama da miji tana jin kunya har daga qarshe ta haqura,a nan ta samu sirrika masu tarin yawa a wajenta,dauka mata wannan tasha,dauko mata wancan ta lasa duk wasu hadin na larabawa ne,sai data tsima ayshan da kyau cikin dabara,donta lura da take taken khalipha wanda ta fuskanci ayshan sam batasan me yake nufi ba,ana sallar magariba ta sanya ayshan tayi wanka da kyau cikin ruwan turaruka,ta bata wata rigat bacci mai kyau saidai tana da dan kauri wadda tasha turaruka kala kala,bayan ta gama shiryawa suna gefan gadon anty ruqayyan ayshan na sauyawa qaramin yaron anty ruqayyan pampers khalipha ya shigo dakin wanda dakin spare ne na baqi mata dake cikin gidan,dubanshi anty ruqayya tayi samda yake tsaye ya tokare bango da qafarsa guda daya daya yana tsaye a kanta,hannunsa harde a qirji ya dan shagala da kallon aysha wadda antyn ta gyara mata kanta yayi kyai qwarai
"Ya ne alhj halifa?" Saiya saki ajiyar zuciya a boye ya maida kanshi gunta
"Zuwa nayi ki bani matata,tunda na fuskanci so ake a qureni ana zaton bazan iya magana ba" dariya ta saki
"Allah ya baka haquri,aysha tashi ki bishi tun bao daukeki da kanshi ba" sauke qafarshi yayi yana tattare hannun rigarshi
"Kamar kuwa kinsan abinda nake nufi kenan ba?"kafin suce meye su duka ya daga ayshan cak yana fadin
"Allah ya bamu alkhairi saida safe anty" kunya kamar aysha tayi me?,sauqin abun daya duka yaran antyn na dakinsu suna assigment,tun daga hanya qamshinta ya soma rikitashi,suna zuwa daki ya qarasa birkice mata,ranar ya more angoncinsa qwarai,taso tayi dauriya amma daga qarshe saidata nuna raki,duk da akwai sauqi akan karon farko,shikam ji yayi kamar ma ranar yake ango.
Washegari qememe ya hanata fita sai daya sake morewa,kunya tasa ma ta kasa fita gaba daya,'yar halak anty ruqayyan saiga aiken breakfast ta turo babban danta ya kawo musu,koda yamma da suka fito zai zaga da ita gari antyn fuskewa tayi kamar ba'ayi komai ba,wanda hakan ya sanya aysha itama ta sake.
Kwanansu bakwai a dubai suna amarci sosai,randa suka dawo daga wani mall tana fitowa daga wanka saiga kiran wayar hanan,ta tsaya da tsane ruwan kanta da take ta amsa wayar,ta gaya mata an dawo daga yajin aiki,suka dan taba hira sannan sukayi sallama ta aje wayar tana duban khalipha dake ninke kayan da suka cire shi da ita,haka yake baida qyuyar aiki,wani lokaci har mamaki yake bata,baida girman kai ko kadan,baya jin yiwa iyalinshi aiki ko wata hidima,wani abunma kafin tayi musu shi yayi
"Komawa gida yazo kenan,kaga hanan ce ta kirani tacemin an koma strike" kanshi kawai ya daga ya kalleta,saiya maida yaci gaba da abinda yake ba tare daya ce mata uffan ba kamar ma baiji abinda tace ba,dubanshi kawai take,ta tabbatar yaji din,amma batasan me yasa yayi banza da zancan ba,saitaja bakinta itama tayi shuru taci gaba da sabgarta,saidai jikinta gaba daya a sanyaye yake.
Har sukazo kwanciya jikinta a mace yake,yayin da shi kuma har a sannan baice da ita komai ba,sai daya gama addu'at kwanciya ya shafa itama ya shafa mata sannan ya janyota jikinsa,a hankali can qasa yace da ita
"Karki wani zafafa da yawa,kar ki saka buri da yawa,Allah ya sani ni kadai nasan me nakeji a zuciyata a kanki,kici gaba kawai da addu'a kan ci gaba da karatunki a wudil,idan babu alkhairi Allah ya zaba miki abinda yafishi alkhairi"sosai gabanta ya fadi tana tsoro da fargabar fa yace ba zata koma ba,amma duk da haka saita danne kawai,tunda shine sila na komai hatta da karatun nata ma.
Cikin dare ta tashi a firgice sakamakon mafarkin da tayi,gidan daddy ya cika anata kuka,shi kuma yana zaune yana ta bin mutane yana basu haquri,ita kuma waisai ta shigo ta fadi tana kuka,saiya dagata yana cewa ta fada kan maciji,sai macijin ya sareshi shima ya fadi anan sai kuma akayo kanshi anata jijjigashi amma ya daina motsi,tana cikin bawa khalipha labarin kawai saita saki kuka,harga Allah zuciyarta tayi gida a sannan,da qyar ya lallabata ya nuna mata sharrin mafarki ne,shi ya sanyata tayi alwala shima yayi suka dasa sallar nafila har asuba,bayan tayi sallar ne bacci ya dauketa.
Tana farkawa kuwa layin daddyn ta soma kira,babu jimawa ya daga,wata wawiyar ajiyar zuciya ta saki sannan ta soma gaidashi,a sake yake amsawa ta tambayeshi jiki yace jiki da sauqi sosai,don bai taba jin dadin jikin nasa irin yau ba,hira sukayi mai tsaho sannan sukayi sallama tace ya gaida mutanen gidan,yace zasuji don safiyya ma mutuniyarta nakan hanya tace saitazo ta kawo masa wani dahuwar nama,tana dariya tace idan tazo daddy kace ta ragemin,yayi dariya yana fadin
"shikenan kuwa zata ji,sai wani lokacin kuma"
"Zan sake kira daddy anjima in sha Allahu"
"Allah ya bamu aron rai"
"Amin" da haka suka rabu,khalipha na tsaye saman kanta yana kallonta yana dariya
"Yar daddy,kin kirashi dai kinji dadi ko,kuma kinji lpy lau yake sharrin mafarki ne,haka kawai jiya kika wani birkice,ina shirin da asuba adan sanmin na d'ana duka aka hanai" juya qwayar idonta tayi cikin kunya tana murmushi
"Hankalina ya tashi ya khalipha,ina son daddy" gefanta ya samu ya zauna
"Mutum ne na qwarai sosai" daga haka hirar daddyn ta balle a tsakaminsu,kowannensu na tuna alkhairinsa gareshi.
A ranar da yamma tana tare da anty ruqayya suna hira khalipha ya shigo yana shaida.mata ta shirya nan da wa daya zasu wuce nigeria,cikin mamaki anty ruqayya kanta take kallonshi bama ita ayshan ba
"Lafiya daiko?" Ta tambayeshi
"Lafiya,aikime kawai ya taso min a kamfani kiran gaggawane ya samu"
"Auto,har naji dadi" ta fada tana sakin ajiyar zuciya,itakam.aysha ba wani zumudi dataji wanda ta tsammaci zataji duk randa zasu koma gida,saita miqe zuwa dakinsu da zummar hada musu kayansu.
[16/03, 11:11 PM] +234 806 544 7089: 58
Wani jiri taji yana niyyar kayar da ita sanda taga tarin al'umma da rumfuna tun daga qofar gidan daddy zuwa cikin harabar gidan dake a wangale,kusan tunda tazo gidan ta gama rayuwarta ciki bata taba ganin an wangale qofar gidan irin haka ba
"Ya khalipha?,me yake faruwa?,me ake haka a gidan?" Ta tambayeshi cike da tsoron amsar da zata fito daga bakinsa
"Kinga saukarmu kenan nace bari na kawoki kiga jikinsa don hankalinki yafi kwanciya,wataqila maqota ke wani sha'anin koma daurin aure ake ne,amma kinsan me za'ayi?,shiga ciki ina nan ina jiranki idan kun gaisa saiki fito mu tafi"
"To" tace tana fitowa bayan ya bude mata murfin motar da kanshi,haka kawai ta dinga jin kamar zata fadi qafafunta sunyi laushi kamar ba'a jikinta ba haka ta dinga takawa har cikin gidan.
Anni ta soma cin karo da ita,mamaki dukka saiya kamata,meya kawo anni gidan to me akeyi?,ko dama ta sansu?
"Allah ya jiqan alhj,ba shakka anyi babban rashin da aka jima ba'ayi irinsa ba" kunnenta ya dauko mata muryar wani daga can wata rumfa dake bayanta da yazo gaisuwa,bata gama wannan ba ta dinga jiyo ihun asma'u tana kiran sunan daddy,da hanzari ta taka don shiga tabi ba'asin meke faruwa sai taji gangar jikinta ta kasa daukarta,ji tayi tana sulalewa zuwa qasa,daga haka bata sake sanin abinda ke faruwa ba.
Sanda ta farka dakin ta dinga bi da kallo sai daga bisani ta gane a asibiti take,a hankali abinda ya faru ya dawo mata kanta,saita fashe da kuka tana fadin
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" a hankali wanda hakan shi ya fargar da khalipha dake saman abun sallah cewar ta farka,gaba daya hankalinshi a tashe yake cikin hanzari ya isa gabanta anni dake zaune can kan kujera ta taso itama,ta dakatar da khalipha dake shirin dagata ta zauna,saiya fasa ya tsaya saitin kanta yana shafa sumar kanta a hankali yana tayata fadin innalillahin,har tsahon wani lokaci bai hanata kuka ba hakanan basu fasa maimaita innalillahin ba tare dashi,daga bisani ne ta saki ajiyar zuciya tana cewa
"Da gaske ya khalipha daddy ya mutu?,dama sallama jiya mukayi dashi kenan a waya?" Ganin shima ba wani a nutse yake can ba saboda yanayin da ayshan ke ciki ya sanya anni matsowa
"Allahn daya haliccemu shi ya fimu sonshi,ya kuma fimu sanin dalilin daya sanya ya dauke abinshi,kada mu yiwa Allah daya bamu shi butulci"
Kai kawai take gyadawa tana ci gaba da ambaton sunan Allah,wanda shi ya dafa mata ta samu nutsuwa,sai da anni ta tabbatar ta nutsu sannan ta taimaka mata ta tashi ta zauna,khalipha ya sanya daya daga cikin yaranshi suka yiwa likitar magana,macace likitan dalili kenan ma daya sanya khaliphan ya kawota wannan asibitin,ta tabbatar mishi komai ya koma normal,saidai ta kiyaye damuwa da bacin rai ta rubuta sallama.
Gidan anni suka wuce kai tsaye tayi wanka,saidai har a sannan hankalinta bai jikinta,ta matsa sai an kaita can gidan makokin,haka khalipha ya dauketa ya kaita.
Karon farko data sake sallamawa Allah lamuranta ta tabbatar lallai mutum koshi waye ba'a bakin komai yake ba,kwana daya tak mummy da asma'u sunfi kowa fita hayyacinsu,tausayin kanta da tausayinsu ya kamata,kuka ta dinga sosai ta manta da duk wani sharadi na likita,anty safiyyace kawai mai qarfin halin lallashinsu,ranar mummy ce ke cewa aysha ta yafe mata,saboda gabanta ita da asma'u daddy ya rasu,sun tsorata matuqa da yadda mutuwa take,fitar rai ba wasa bane,kowanne dan adam lallai saiya taba yaji a jikinsa,saidai fata Allah yasa mu dace.
A nan khalipha yake barinta,kullum sai dare yake zuwa ya dauketa su koma gida,har a sannan aysha bata daina kukan rasuwar daddy ba,saidai tanayi a boye yadda khalipha bazai gani ba hankalinsa ya tashi,don dukkan wani qoqari nasa yana yi don ganin ta sake,saidai ita kanta batasan ma meke damunta ba,hatta da taste din bakinta ya sauya tun daga randa akayi mutuwar.
Ranar sadakar uku su inna yelwa suka zo,tunda sukazo aysha ta lura da ta sauya gaba daya,sai da ana hira takejin bata da cikakkiyar lafiya kwana biyu,yau da lafiya gobe babu,ba'ayi azahar ba umminta ta iso itama ita dasu basma,don ita kanta mutuwar ta daketa,taso qwarai ace Allah ya hada ganawarsu da mutumin daya ceci rayuwar 'yarta,taso sosai tayi masa godiya koda sau daya ne a rayuwarta amma Allah bai nufa ba.
Shuru dakin da suke zaune ya dauka gaba daya,baka jiyo komai sai muryar wata baiwar Allah dake harabar gidan tana wa'azi kan mutuwa,tun daga sanda mala'ikan mutuwa dubi bawa,zarar rai,wankan gawa kwanciyar kabari da yadda mala'iku kebi suna jin yadda jama'a ke fadar halayyar mamaci,da yadda hakan yake tasiri a kansa da sauransu,sosai jikin inna yelwa ya sake laqwas,tunda tazo gidan bata ji mutum daya daya fadi mummunan hali akan daddy ba,yau ga inna yelwa ga ummi,abinda ya dauki tsahon shekaru rabon daya faru,sai inna yelwa ta kasa sakewa gaba daya,sai satar kallon ummi take,ba dadewa fa fashe da kuka,ita kadai tasan me take ji a lokacin,ba abinda take tunawa sai abinda ta aiwatar a rayuwarta a baya,yanzu idan mala'ikan daukar rai ya cimmata fa?,tabbas tasan kadanne masu fadin alkhairi a kanta,idon kowa sai yayi kanta,Allah yasa dukka 'yan takai ne da wadanda suka jibanci aysha,anzo mata sosai saboda yanzun kowa neman fada yake da ita
"Don girman Allah ki yafemin naja'atu,wallahi na cuci kaina na cuci rayuwarki keda diyarki" abinda inna yelwa ta dinga fada kenan tana zabga kuka da majina,tsit dakin yayi,yayin da ummi tayi shuru tana hadiyar wani abu mai tauri,zuciyarta quna kawai take tana yunqurin danneta da cika alqawarin data dauka a gaban dakin Allah.
Inna yelwa ta jima gaban ummi tana kuka gami da gaya mata ita ta rabata da baffale,ita ta shiga tsakaninsu,lumshe idanu ummi kawai tayi,zuciyarta nason tuna mata irin abubuwan da inna yelwan tayi mataba rayuwa,yayin da daya sashen na zuciyarta ke tunasar da ita ni'ima baiwa da kuma musanyan alkhairi da Allah yayi mata ayanzu
"Na yafe miki" kalmar data baiwa inna yelwan mamaki,don bata taba tsammatar haka daga wajen ummin da sauqi ba,hakan ya sake karya mata zuciya,nadama ta shigeta sosai,tana son kallon aysha dake zaune waje daya tana jan carbi tace ta yafe mata amma tana jin kunyarta da nauyinta,tana jin idan tace ta yafe matan tamkar ta zama mai son kai ne,amma ita kadai tasan yadda akwanakin take yawan mafarkin baffale,yana kuka yana ta cuci su aysha,ta gaggauta hada tsakaninsu,ta gaggauta neman afiya da yafiyarsu,ta raba uwa da 'ya,saidai kuma cikin kyakkyawan yanayi take ganinshi,saidai kukan kawai da yake mata,babu randa zata kwanta bacci ta tashi batayi mafarkinsa ba,abun ya takurata qwarai,kusan shi ya haifar mata da lalurar da take fama da ita a yanzu.
"Nasan ban cancanci ki yafemin ba indo,amma na gamaki da Allah duk sanda kike jin kin huce na cancanci yafiya toki yafemin" ta fada tana fashewa da kuka,kai aysha ta kada kawai,itakam me zata cewa Allah banda godiya,komai aduniya da zai samu bawa koya sameshi yana damfare da yanayin rayuwarshi na baya,ba don qalubalen data fuskanta ba da babu lallai daddy ya daukota ya kawota nan,da bai kawota din ba da babu lallai asma'u ta hadata da khalipha,duk da yakedai duk inda bawa yake rabonsa baya kubuce masa
"Na yafemiki,Allah ya yafe mana gaba daya" kusan wannan shi ya kawo daidaito tsakanin gabar inna yelwa da ummi naja'atu.
Qarfe hudu da minti ashirin na yammaci yasa aka kira mishi ayshan,can wani waje da babu kowa cikin gidan suka zauna saman darduma,ya tsareta da idanunshi bayan ya aje abinci a tsakiyarsu,saita zuba mishi ido itama sonshi da qaunarshi na sake karyar mata da zuciya,hawaye ya cika idanunta,haka kawai take jin wani abu ya cunkushe mata wuya wanda shike hanata cin abinci
"Oya,bude bakin" ya fada bayan ya debo abincin a cokali yakai bakinta,sai kawai ta sake masa kuka mara sauti sai sheshsheqa
"Ya salam" ya fada yana aje cokalin cikin damuwa,ya rasa me yasa har yau zuciyarta taqi saki,a yanzun kuka baiyi mata wani wuya,yanzu yanzu ne zata saki abinta,bai manta ba jiya suna kici kicin tahowa zai kawota,zata sanya wata riga taqi shigarta tayi mata kadan,sai zuwa yayi ya sameta a zaune dirshan tana sharbar kuka abinta,daga lallashi nan ma cibi ya zama qari,hannunshi ya miqa mata batayi wata wata ba ta taho,cikin jikinsa ya sanyata tana shafar bayanta a hankali
"Uwaisha ba zaki sanya haquri cikin zuciyarki ba ehmm?,bakisan yadda zuciyata ke quna ba a duk sa'in dana ganki cikin damuwa?,so kike wani abu nima ya sameni?" Saita fashe da kuka tana girgiza kai tana fadin a'ah
"Ya Allahu.....kin zama makokiya gaba daya?" Ya fada yana share mata hawayen dake sauko mata
"Na daina...." Ta fada cikin muryar kuka,murmushi kawai ya saki yana ci gaba da riqeta cikin jikinsa,bai barta ba sai daya tabbatar taci abinci ta kuma sake sannan ya qyaleta.
Kwana goma da rasuwar da wani dare tana zaune gaban anni suna hira,tun dazu khalipha ke kaiwa da kawowa tsakanin sashen annin zuwa nasu,ya gaji yakai maqura yau haqurinshi ya qare,so yake ya dauki matarshi kawai su wuce gidansu amma ayshan tayi qememe kamar ma bata gane me yake nufi,sake miqewa yayi ya nufi sashen cikin qwarin agwiwa.
A nutse ya tura qofar yayi sallama,cikin sa'a ayshan ce kadai zaune tana shan fruit salad na musamman da aka zuba mishi zuma da madara,wanda a fakaice anni ta hada mata shi saboda qarin ni'imar jikinta,ita kuwa tunda ta d'an d'ana taji yayi mata shikenan ta samu abinyi,idonta ta daga ta kalleshi sanda shima yake dubanta bayan ya kalli bowl din gabanta mai dauke da fruit salad din,murmushi ta saki tana nuna mishi kwanon
"Ya khalipha bismillah" harara ya dan watsa mata qasa qasa yadda anni ba zata ji ba yace
"Bana sha...ki tashi ki shirya mu wuce gida" saita langwabe kai,tana jin dadin zamanta da anni sosai
"Ya khalipha ka bar....." Sai ya dora yatsanshi akan lips
"Shshshshsh.....bana son jin komai ki tashi kawai"
"Yaya dai khalipha?" Anni dake fitowa daga toilet ta ambata tana dubanshi,sai ya dan sosa kanshi kadan yana cewa
"Babu komai anni" juyawa yayi ya sake jaddadawa aysha maganar da ido sannan ya juya zai fice
"Zo nan" anni tace dashi tana qoqarin zama,dawowa yayi
"Ka kora min yara shine zaka wuce kubarmin gida ni daya kenan ko?" Ta fada tana dubanshi,sai yayu shuru yana shafa kanshi
"Zauna" ta nuna mishi waje,zaman yayi yana kaucema kallon annin
"Duk inda musulmi yake ana son ya zama mai manta sharri,mara manta alkhairi,anason idan mutum ya maka sharri kai ka saka masa da alkhairi,a sanda duk Allah ya maka sauyin yanayi na alkhairi ganin damarshi ne,sanda Allah yayi maka arziqi ka wadata mabuqata,sabida wannan arziqin ba kai kadai ya bawa ba ya baka ne harda su,sai ya sanyashi a hannunka,babu abinda zai rageka dashi donka kyautatawa wanda ya zalunceka,sai qarin daukaka da zaka samu wajen ubangiji,na yaba maka sosai da yadda kayi haquri kuma kabi maganata,ka dauki ragamar kyautata musu kamar yadda mahaifinka yayi kafin yabar duniya duk da nasan tanqwara zuciyarka kawai kake,a yanzu bazan sake takuraka kan zamansu amal cikin gidan nan ba,don na tabbatar gudun faruwar matsala yasa kayi haka,nima kuma daga bisani na hangi hakan,zuwa yanzu dama yaci ace kowacce ta maida hankalinta jikinta ta fitar da mijin aure tunda gaba dayansu sun kai munzali"
"Hakane anni,kiyi haquri idan kinji babu dadi...yanzu haka mun gama magana da mijin anty ruqayya zai baki nadiya 'yarsa in sha Allahu taci gaba da zama dake,saboda ina tunanin...." Sai kuma ya kasa qarasawa ya soma shafa qeya,tasan yana jin nauyin abinda zai fada mata ne,saita saki murmushi
"Uhmmm"
"Cyprus zamu wuce nida humaira" har qasan zuciyar anni farinciki ne ya lullubeta,abinda take zato ya tabbata,tun ranar farko data gansu taga burbushin haka,dukkan alamu sun suna akwai wata dangantaka mai qarfi atsakaninsu,akwai wani lamari mai girma daya yiwa junansu dabaibayi,amma donson ta sake tabbatarwa sai tace
"Wani irin cyprus?,nata karatun fa?,ba inda zaka daukemin diya ka kaita"
"Wallahi anni bazan iya tafiya na barta ba don Allah karkice na tafi na barta,in kika ce haka kona tafi bazan iya qarasa nawa karatun ba kuma nawa yafi nata muhimmamci...."yayi subutar bakin fadan wadannan kalmomin ba tare daya shirya fadarsu ba
"Dakata..." Tayi hanzarin tsaidashi karya ballo maganar data fi haka nauyi
"Saikun dawo Allah ya kiyaye hanya,ke ayshatu tashi maza ku wuce gidanku nima nan kwanciya zanyi,idan kun fita ku turomin mus'ab ko atika" sai a sannan ya tuna abinda yace mata,kunya duka ta kamashi,amma da yake namiji ne saiya murje ya shigar da godiyarsa,don kada ma ayshan ta bata masa lokaci sai ya tsaya yana jiran ta gama laqai laqai dinta ta tashi,haka ta gama din kuwa ta yiwa anni sallama suka fice.
Tun a gidan annin dama takejin son tayi kuka,wani abu ya takoreta a wuya,tun a can take toshe kukan,suna shiga falon gidansu ta kasa haquri kawai saita saki kukan,juyawa kawai khalipha yayi yana kallonta baki sake,kamar wadda akayiwa wahayin kuka?,bai wani bata bakinsa ba wajen lallashi kawai ya sunkuci abarsa,bai direta ko ina ba sai dakin bacci,sai daya gama budurinsa ya biya dukkan bashin dake kansa sannan ya soma aikin lallashi,nan ta narke masa itama ta zuba shagwabarta son ranta shi kuma ya biye mata,sai daya sha rarrashi sannan ya samu kanta suka shiga wanka tare,wanda kusan al'adarshi ce haka,saboda koyi da fiyayyen halitta annabi muhammad S A W.
Bayan kwana biyu akayi bikin bude katafaren shagon nata,wanda walima tayi dai dai gwargwado,donta rage wani abunma saboda mutuwar daddy amma tayi walima sosai anci an sha anyi sadaka.
Kwanaki bakwai suka qara a nigeria suka shirya don komawa cyprus ita dashi,ana washegari zasu koma taje gidan daddy donta qara ganin mummy.
Ba qaramin tausayi mummyn ta bata ba yadda ta rame tayi baqi ta zabge lokaci guda kamar ba ita ba,ba qaramin duka mutuwar daddy tayi mata ba,fuskarta a sake ta amshi ayshan har hakan ya bata mamaki,don bata tsammaci haka daga gareta ba
"Allah ya kiyaye hanya yasa aje a sa'a" mummyn ta fada cikin sanyin jiki,abinda bai taba hadata da mummyn ba,jakarta ta bude ta ciro kudi dubu dari da khalipha ya bata ta basu ta miqawa mummyn,kai ta girgiza
"Bazan iya karbar komai naki ba ayshah,na gode"
"Idan kika ce haka nima baki daukeni kaman asma'u ba kenan?" Kai ta kada hawaye na cika idanunta ta amsa
"Allah yayi miki albarka,ki yafemin aysha dukkan wata cutarwa dana taba yi miki a rayuwa,shaidan ya rufe idanuna,a sanda kike kyautata min idanuna sun rufe,bana ganin dukkan wani alkhairi naki,duk yadda kika kai ga kyautata mana bamu qareki da komai ba face sharri da makirci da muke bibiyarki dashi,mutuwar daddy babbar izina ce a wajena,tabbas dan adam ba'a bakin komai yake ba"
"Ban taba riqonki ba mummy dai dai da rana daya,na yafemiki mummy,Allah ya yafe mana gaba daya" da haka ta fito daga gidan jikinta a sanyaye,daga nan gidan anty safiyya ya kaita,sosai tayi murna da zuwan ayshan,ta dan jima zaune suna hira da ita,sannan ta gaya mata zancan tafiyarsu gobe,sosai ta mata fatan alkhairi
"Nikam kaman qiba naga kin soma aysha,karfa ki zama bindiga?" Murmushi ta saki
"Haba anty,nida na rasa uba wacce qiba zanyi?"murmushi anty safiyya tayi,har cikin zuciyarta tana jin dadin dace da aysha tayi
" ba daga nan take ba aysha,shi ciwon mutuwa Allah yake daukewa bawa shi,banda haka da mutane da dama sun hallaka saboda ciwon rasuwar makusantansu,kekam kinyi haquri a rayuwarki wanda ya zamemiki alkhairi"sai tayi shuru tana aje numfashi,ta gefe guda tana jin tausayin asma'u,tana jin ciwon rayuwar da take ciki,saidai bata karanci komai na nadamarta ko rashin nadamarta ba
"Ki daure ki yafewa asma'u koda bata nemi yafiyarki ba,ki kuma sanyata a addu'a"
"Ni babu komai tsakanina da ita anty,kusan zan iya cewa itace silar matakin dana ke kai yanzu"
"Batayi don alkhairi ya sameki ba,amma dai ki daure ki yafe mata"
"Nikam na yafe mata duniya da lahira" saida khalipha ya kirata sannan ta fito suka tafi.
Suna shirin kwanciya bacci saiga kiran anni ya shigo wayar ayshan,a ladabce cikin kulawa suka gaisa
"Bani khaliphan aysha na kira lambarsa a kashe"
"Toh anni" ta fada tana miqa masa dai dai sanda yake fitowa daga wanka,amsar wayar yayi da daya hannun nashi dayan kuma ya janyota cikin jikinshi ya rungumeta,runtse idanu tayi sanda fatar jikinta ta hadu da tashi,lemar ruwan dake gashin qirjinsa ta ratsa towel din jikinta zuwa fatarta,suna tsaye a haka suka gama gaisawa da annin
"Idris ne fa ba lafiya"idanunsa ya dan lumshe,ko sunanshi baison ji
"wanne idris"
"Gidanku,idris kawunka mana,bashi da lafiya sosai yana jin jiki,lafiya akwa kwanta dashi sai ihunshi aka ji,yanzu haka yana asibi an kwantar dashi,kayi qoqari gobe kafin ku wuce kuje ku dubashi"
"Zanje in sha Allahu"
"Yauwa saida safe"
"Allah ya bamu alkhairi" ya kashe wayar yana sake jan ayshan cikin jikinsa yana sauke ajiyar zuciya,dukkaninsu shuru sukayi,tasan yanzun zaya shiga damuwa daga ambato masa sunan idris,daga bisani ayshan ta juyo da wani irin hanzari ta rungumeshi sosai tana cusa kanta cikin qirjinsa,da qafa daya ta janyo tum tum din dake gefansu ta haye sannan ta samu tsahonsu yazo daya,saita riqe kanshi sosai ta hada hancinsa da nata,bakinta tasa tadan ciji lebansa kadan saiya saki qara
"Wayyo bakina anni zata cinye miki bakin yaro" dariya ta qyalqyale da ita tana daneshi
"Kasan kaci bashina jiya,kuma saika biya?...." Bai barta ta qarasa maganarba ya dauketa cak ya cilla saman gado ya bita yana cewa
"Aga matsoraci tsakanina dake,ke kike tsoron biyan bashi bani ba" tattare jikinta ta soma yi tana dariya gami da bashi haquri,bai yarda ba saida suka fafata ya gajiyar da ita tubus sannan yace ya haqura,tayi shuru na maida numfashin kokawar daya sanyata,tana jin dadi cikin zuciyarta na nasarar shafe masa bacin ran daya so yin tasiri cikin zuciyarsa data yi
"Yarinyar nan qiba naga kin fara yi fa" khalipha ya fada yana dora kanshi saman cinyarta,gami da zagaye qungunta da hannayensa,baki ta zumburo
"Ni ba wani qiba,bayan kaine duk ka hanani qibar,kai baka ga yadda ka soma tumbi ba" qayataccen murmushi ya saki yana maida kwanciyarshi rigingine yana shafa cikinsa da tafin hannunsa daya,ta yadda hakan ya bashi damar kallon fuskarta sosai
"Ni aike nakeso na gani da tumbi,irin tumbin da zaki bani baby fa" kukan shagwaba ta sake masa tana bubbuga hannayenta
"Da wuyafa ya khalipha da wuya..." Dariya ya saki
"Kinsan kuwa jiya nayi mafarki kin haifamin twince masu kama dani?kuma duk mata"
"Sonkai?" Ta fada tana zaro ido tana dariya
"Kona tashi maza zan haifa masu kama da anni koni" idonshi shima ya waro
"Da gaske baby girl nakeso ki haifamin uwaisha..."
"Ni kuma baby boy nakeso,so nake na haifa daddy"
"Shikenan,idan kika haifa mace ni zan saka mata suna,idan namiji ne ke zaki saka"
"Na yarda"
"Mu qulla alqawari" ya fada yana miqa mata qarmin yatsanshi,sai ta miqa masa ita wanda ya shammaceta ya jawota ya maye gurbinta.
[16/03, 11:12 PM] +234 806 544 7089: 59
Qarfe goma da wani abu na safiya suke takawa cikin asibitin hannayensu sarqafe da juna,duk wanda ya kallesu saiya sake juyawa ya dubesu,kana kallonsu kasan cewa masoya kuma ma'auratan da suka dace da juna,ba qaramin kyau sukayi ba,shi yana sanye da suit yayin da take sanye da atamfa dinkin doguwar riga,fuskarta tayi wani irin kyau,tayi fresh abinta saika dauka wani makeup tayi,saidai babu komai a fuskar tata sai powder kwalli da man lebe,gab da zasu shiga cikin asibitin ya daga waya ya kira annin ya tambayeta dakin da aka kwantar da kawu idris ta gaya mishi,ya kashe wayar ya maida aljihunsa yana sakin ajiyar zuciya,hannunshi ta riqe sosai tsam saboda tasan yanzun ranshi zaya baci,tasanya daya hannun nata ta zare glass din fuskarta ta lanqwasheshi cikin hannunta,juyowa yayi suka hada idanu saita narke masa tana tsayawa daga takawar da suke zuwa cikin asibitin,gira ya daga mata alamar tambaya,a shagwabe tace dashi
"Ya khalipha pls mana,idan kasan ranka zaya baci ba zaka saki ranka ba ka tsaya ni na shiga,sai na gawa anni kai baka shiga ba" kai.ya kada yana sake mata murmushi,ya kashe mata idonsa daya
"Noo princess uwaisha....muje" da haka suka ci gaba da takawa.
Tun daga varender da dakin yake suka dinga jiyo ihu,haka suka dinga takawa har zuwa bakin dakin,wasu daga cikin yaranshi da 'yan uwa ne tsaitsaye bakin qofar dakin jugum jugum,duk wanda ka kalla alamun tashin hankali ya bayyana qarara a fuskarshi,hango khalipha ya sanya sukayo wajenshi suna mishi sannu da zuwa,amsawa yayi yana zare glass din fuskarsa gami da kallon qofar dakin da ihun ke fitowa,zame hannun aysha yayi daha cikin nashi yadan sunkuya saitin kunneta
"Ki tsaya anan yanzu zan fito" kai ta gyada jikinta a sanyaye itama,bisa dukkan alamu mai mara lafiyan ne ke wannan ihun da qarajin.
Tura qofar dakin yayi bakinsa dauke da sallama,duk da ihun da kawu idris yake kwararawa bazai bari aji sallamar ba,ibrahim ne yake riqe dashi,matarsa tana gefe tana zubda qwalla,tsayawa yayi khalipha yayi yana dubanshi
"Ibrahim nace maka ka kwaramin ruwa,cikina...wuta ce,wutace take ci ajikina,baka ganta ba,nace baka ganta ba,jikina zafi yake min ibrahim jikina"
"Sakeshi" khalipha ya fada yana duban kawu idriss din,sakinsa ibrahim yayi yana share gumi da qwalla,addu'a ya soma yi yana tofa masa a jikinsa, hankali zafin da yakeji ya ragu sosai,ihun da yake ya tsaya sai qananun surutai
"Na gode khalipha,na gode" ya dinga maimaitawa,kana ji kasan sambatu yake
"Na gode khalipha ka yafemin naci dukiyarku,na cinye dukiyarku,nina kasheshi,nina kashesheki" gabansa ne yayi mummunan faduwar,sai ya zuba mishi idanu,a hankali ya bude bakinsa
"Kai ka kashe wa?"
"Babanku sa'idu,nine dasu hamza suka qi saina kasheshi ni kadai,saboda inason ayshatu inason na aureta" wani irin tuquqi yaji qirjinsa yanayi,take idanunshi suka sauya kala,sannu sannu ya dinga ja baya yana kallonshi,ya yunquro zai cafko khaliphan yana cewa
"ka tsaya karka tafi,tofamin addu'a tofamin,zafin da nakeji ya dawo....ka tsaya mana" juyawa yayi ya fice idanunsa jajur,tashin hankalin daya ji ba kadan bane a sannan,mutuwar babanshi da hajar ta dawo masa sabuwa fil,cikin wani irin zafin nama ya ja hannun aysha ba tare daya waiwaya ya dubi kowa ba suka fice yana jiyo ihun idriss.
Tunda suka sauka a gidansu na cyprus ta kasa gane kanshi,duk wani abu tayi amma ba canji,data gaji kawai saita zauna ta sanya mishi kuka,a rude a janyota jikinsa yana tambayarta
"Meya faru uwaisha?,nine ko?,am sorry kiyi haquri,uwaisha.....shi ya kashemin abba na,me yayi masa haka arayuwa bayan tarin alkhairai daya musu?"sosai maganar ta daketa,saita daga kai tana dubanshi,yau taga ahalin da suka fi nata zalunci,taga ahalin da suka dara nata ahalin mugunta da watsi da zumuncin Allah,maganar ta kidimata,saidai ya zama dole ta rage razanar data yi saboda ta maidashi cikin mode dinshi
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,gaskiya ne ya aikata babban xalunci akan ran da bata jiba bata gani ba,abba ajalinsa ya riya yazo,koda kawu idris ko babu shi tilas saiya tafi,tsakaninka da abba yanzu haka addu'a ce,haqiqa Allah baya barin wanda ya kashe wata rai ba tare data cancanci hakan ba,ka zuba ido kaga shima zai tabbata ne a duniya?,komai daren dadewa sai ya tafi inda abban yaje" da kalamai masu dadi tayi amfani ta samu kanshi,ya dinga sauke ajiyar zuciya ajejjere,tsananin fushi bacin rai da rudanin daya shiga suna sauka.
Gab da zasu kwanta wayarshi ta dauki kida,ya duba sai yaga haidar ne
"Ya akayi haidar,ina fata kowa lafiya"
"Eh mukam lpy lau,kawu idris ne ya wuce,baku jima da barin asibitin ba yarasu"idanunsa khalipha ya lumshe,maganganun aysha na dawo masa fes aka,kamar a sannan take gaya mishi,sautin haidar shi ya katse masa tunaninsa
" yaya mutanen nan Allah ne kadai yasan zunubin da suka aikata bayan dukiyarmu da suka cinye,kasan gaba daya fuskar kawu idris tayi baqi?,har ya mutu bai daina kiran cikinsa wuta naci a ciki ba?"
"Allah ya riga daya fada ya kuma gargademu cewa,duk wanda yake cin dukiyar maraya da zalunci haqiqa wuta yake ci a cikinsa,da sannu kuma xai shiga wutar sa'ira,zai iya yiwuwa Allah ya nuna ishararsa ne saboda sauran abokan barnarsa su kawu hamza dake raye"
"Sun girgiza ya khalipha.....kafin a dauki gawar kawu idriss saida suka warwarewa anni komai suna kuka wiwi da neman gafararta saboda yadda sukaga gawar kawu idris ta koma,ya tabbata su suka jefamu a halin talauci a baya,su suka tattare komai namu suka cinye"
"Ai ubangiji baya bacci,kuma gashinan sun gani zahiri,Allah yasa mu dace,yasa muyi kyakkyawan qarshe"
"Amin ya Allah yaya" daga haka sukayi sallama ya kashe wayar yana ajiyar zuciya,gaskiya ne Allah baya zalunci daidai da qwayar xarra,ko yaya ka zalunci musulmi ko kaci masa haqqinsa koda qwayar gero ce bakai ba aljanna saika biyashi,koda iya ladar data rage maka kenan ka shiga aljanna ba ruwan ubangiji saika biya haqqin wani daka ci.
A haka aysha ta shigo dauke da coffe sai tururi yake
"Ya khalipha....."
"Shshshshs...." Ya fada yana katseta
"Daga yau banason wannan sunan,yanzu fa haidar ya gama cemin yaya kema ki fada,meye banbancin kenan?" Ya fada yana dage girarshi yana kallonta,wani sassanyar murmushi daya ratsa zuciyarshi ta saki tana aje coffen a gefanshi,cikin zuciyarta tana jin dadin yadda ya sake,gadon ta hau sosai ta kama hannayensa gaba daya cikin lallausan tafin hannunta tana murmushi
"Ka zabi dukkan sunan da kakeso ni kuma zan kiraka dashi ko a gaban waye" murmushin shima ya saki,yana jin dadin yadda take fifitashi fiye da kowa,take fifitashi fiye da duk abinda takeso a duniya,take zabar farincikinsa saman nata,kamo fuskarta yayi ya sumbaci goshinta cikin alfahari da ita
"Na baki zabi matata,na amince miki ki zaba min dukkan sunan daya dace da ra'ayinki" murmushi ta sakar masa tana matsa 'yan yatsunshi
"Bazan iyakance wani suna qwaya daya da zan kiraka dashi ba,ka cancanci dukkan wani suna dake nuna qauna da soyayya your royal highness" idanu ya zaro yana jin dadj,ba shakka ta cika mace ta gari macen qwarai,wanda ma'aiki S A W yace idan ka kalleta zata faranta maka,idan ka umarceta zata yi maka biyayya,idan kayi rantsuwa zata kubutar dakai,idan kayi tafiya ko baka nan zata kare maka kanta da dukiyarta,shikam me zaya ce da ubangijinsa banda godiya?.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Da sallama ya shigo dakin nata bayan ya bar mahaifiyarshi da qannenshi a babban falon gidan,a hankali ta sauke ajiyar zuciya bayan dogon tunanin data gama yi kana ta dago tana dubanshi,gaba daya daddy kafin rasuwarshi ya gama yi mata dabaibayi da kalamanshi kamar yana sane da abinda take shiryawa na barin gidan hamid,ya gaya mata cewa muddin babu ce zata sanyata barin aurenta indai shi ya haifeta bai yafe mata ba,matuqar mijinta na bata kulawa iyakar qarfinsa to yana umartarta ta zauna gidanta,saidai idan yazo da wata cutarwa da shafeta ko addininta,to a yanzun hamid din ya sauya,ba rashin ci babu rashin sha,duk da cewa duk wani jin dadi dada yake dashi yanzu babu,dalili kenan daya sanya yawan yawan halayensa sauyawa,saidai ita sam ya fita a kanta,kallonshi kawai take.
Da tausayinta kan fuskarshi ya zauna hannun kujerar da take kai,yanzun ya gama tsawatarwa qannenshi kan rashin kunyar da suke mata
"Kiyi haquri asma'u,na tsawatar musu kuma in sha Allahu daga yanzu hakan ba zata sake faruwa ba,kimin addu'a Allah ya sake buda min ba don halina ba,in daukeki na sauya miki gida" kallonshi kawai tayi ta miqe ta shige bedroom dinta,yayin da shima ya bita da kallo,gaba daya ta sauya tun daga mutuwar daddyn tayi wani mugun sanyi,sai ya miqe ya bita,tana zaune gefan gado,kallonshi take da mamaki don ta manta yaushe rabon da tayi masa irin hakan ya biyota
"Ki daure ki yafemin asma'u,nasan cewa harda haqqinki na takureki da nakeyi da rashin wadataki bayan ina da damar haka shi yasa Allah ya jarabceni,duk da cewa ni maison kudi ne amma takaicin yadda kika dinga tatsata,quru quru ya bayyana ba don Allah kikesona ba,hakanan ba zaki aureni ba idan ban miki barin kudi ba yasa nima ma takuraki sanda mukayi auren,ashe Allah ba ruwanshi,na sauke haqqinki kawai dake kaina shine mafitata,ki yafemin asma'u don Allah" kwanciya tayi kawai ta juya mishi baya,a zuciyarta tanason tayi yaqi da khalipha ta karbi hamid,saidai hakan na nufin su zauna a qaramar rayuwa?,to idan ma bata amshi hamid ba ya za'ayi ya samu khalipha?,mutumin data tabbatar daya tsallake baya qasar,ko baya ga haka ita kanta idan ta zauna tana tuna abubuwan da tayi mishi a rayuwa saita dinga jin nauyin abubuwan da mamakin yadda akayi ma tayi wani abun,a lokacin duniyar nayi da ita,duka a ture wannan ya zatayi da nasihar daddy,da wannan tunanin zuciyarta ta yanke mata tilas zama da hamid ya kamata,saidai tasan yadda zata lallashi kanta ta amshi tayinsa ta sabunta sonshi cikin zuciyarta,don idan ma tace batason hamid din ita kanta tasan ta yiwa kanta qarya.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Ya jima sosai tsaye cikin kitchen din yana kallonta bata sani ba,dafa wancan dan dana kiji baiyi miki ba ki aje,ta dora abu kusan hudu dukka lokaci guda saman gas din,wanda daga qarshe ta cakuda kifn gwangwani da irish patatoes dafaffe ta zuba bama a kai shita dinga diba tana ci tana kada kai,alamun duniya tayi mata dadi,dariya ya saki tana rufe bakinshi,donshi mamaki take bashi da dariya,kwanakin nan sam bata da wani tsayayyen abincin ci sai kame kame,kusan tunda sujazo cprus haka abun yake gashi sun cinye watanni biyu
"Ba dole ki dinga qiba ba haijarsu,duba fa duka tukwanen nan hudu abincinki ne,to wanne zaki ci a ciki ne?" Ya tambayeta yana riqe haba,saitayi narai narai da ido kuma tabar cin dankalin tana dubanshi
"Bafa ni kadai zan cinye ba baby...." Idanunya zaro
"Ke dawa zakuci?,badai dani ba wannan jagwalgwalon" aifa saita saki kuka
"Innalillahi" yace uana danne dariyarshi,ta zama kaman wata baure,'yar qaramar magana zaiyi yanzu saita sakar masa kuka,mantawa ma yayi shaf da bai toneta fada ba
"Zo nan,zo kiji,haba mana tawan,ta wajen ya khaliphanta" sai yaja kujera cikin kitchen din ya zauna ya dorata saman cinyarsa
"Nifa wasa nake miki,bayan duk duniya Allah har yau banji abincin da yakai naki dadi ba da tsari baya ga na anni"
"Nifa komai naci bana jin dadinsa,bakina kamar anmin satar taste" dariya ce sosai ta taso masa dama ana satar taste?,amma yasan da yayi yanzu cibi zai zama qari,don haka sukayi dazun da safe,daga tazo saka kaya sun mata kadan yayi dariya ta zauna ta dasa mishi kuka,qarshe dai sai data jawo ya makara a makaranta bai fita akan lokaci ba
"To yanzu ya za'ayi kenan baby nima fa na damu" ya fada yana kwabe fuska can qasa dariya na cinsa,daita tsura mishu ido tana kallonsa tana son gano dariya yake mata?,ci gaba yayi da qunshe dariyarsa don yaga alama rigimar take ji sosai,har wani kalen laifi taje masa
"Dariya kake kin ko?"
"Wa?,ni na isa?,yanzu anni ta hukuntani ai,kinga zo muje kiji wani abu mai dadi,na siyo miki ma wannan abun da kika fiso"ya fada yana tashi da ita a jikinsa ya kashe dukkan gask djn suka fita a kitchen din,toulet ya jata ya hada ruwan wanka cikin bathtube,bata tsammata ba saiji tayi sun zunduma ciki ita dashi,ba yadda ta iya haka ta haqura,saida suka gama baje kolin soyayarsu sannan sukayi wanka suka fito,zuwa sannan ta ware sunata hirarrakinsu.
Ita ta tayashi ya shirya cikin boxer da longsleeve t.shirt,amma ta shurya cikin wasu ruga da skert na wadansu irin yadi mai rawa,shi ya gyara mata kanta ya matse mata cikin ribbom sannan ya sanyata ta dauko system dinta yana cewa
"Tun jiya aka turo miki email da hotuna daga shagonki anma baki duba ba,wannan wacce irin lazy M.D ce?" Tana turo baki ta dauko system din don ita ta gaji bacci bacci ma takeji,amma tayi shuru ta cije don tana fada ta samu abun tsokana wajenshi,don yace raguwa ce sosai,ba dama a gaisa saita hau bacci.
Saman gado sukayi dare dare tana lafe a jikinsa,don a duniya babu inda yakai nan yi mata dadi,ya bude naman daya siyo mata ya aje mata gabanta yace
"Gashinan" sosai taji dadi,tana masifar sonsji,cikin zumudi ta bude,yayin da shi kuma ya kunna system din tata ya soma duba saqonnin,wanda kusan duka kan kayan da suka shigo da wadanda suka fita ne,irin uwar ribar datake samu,Allah ya sanyawa wajen albarka sosai,yana cikin yi mata bayanin wasu abubuwa yaji dif bata amsawa,saiya waiwaya,ga mamakinsa bacci ne ya dauketa,ta bingire a kafadarshi,naman ma bata wani yi masa cin kirki ba,dariya ta kamashi,saidai can qasan ranshi yana mamakin meya sameta ne haka?,tunda suka zo yanayinta kenan,a hankali ya gyara mata kwanciya ya dora kanta saman cinyarshi bayan ya kwashe naman ya adana mata a kan bedside drower,ya sumbaci goshinta da tattausan lebansa yana furta
"I love you uwaisha" ya dan jima yana kallonta kafin ya dauke idanu yaci gaba da aikin shi daya,yana jin wani sonta ja wujijjigashi,har mamakin kanshi yake,bai taba son wani abu a rayuwarshi kamar haka ba,da wannan tunanin ya dinga duba komai daki dako yana baiwa mai riqe da shagon amsa,inda daga qarshe yaga dole ya cire kudinta na ribar da take daga accnt dinsa ya maida mata nata saboda yawansu,bayan an fitarwa da sauran ma'aikatan haqqinsu.
Har ya kammala tana bacci abinta,saiya zare jikinsa ya shiga kitchen da kansa ya sama musu dan abinda zasuci tunda ya fuskanci tunda ta shiga kitchen din bata iya dafa komai ba sai qwalama data yi,hakan khaliphan yake,matsayinsa bai sanyashi girman kai ba,dukkan wata hidima ta gida indai ya iya kanyiwa kanshi ko yayi mata,wani lokaci har hanashi takesonyi amma ya dakatar da ita da cewa
"Sunnah ce ta annabi salallahu alaihi wa sallam,ko bakyaso na samu kadan koyi da sunnah"
'"Inaso mana babay"
"Good,kinsan mu mazan hausawa idan kikaji muna kumfar baki muna jawo aya da fadin zamu dabbaqa sunnah to qarin aure zamuyi" dariya ta kubuce mata yanayin yafda yayi maganar,murmushi yayi yana ci gaba da cewa
"Allah kuwa,bama tashi tuna Allah yace sai munzo qara aure,mun mance da dukkan wadan nan sunnonin masu tarin lada,wanda wani ma zaka samu a qa'ida dukkan sharudan qarin auren bai cikasu ba amma yana fadin sunna ne zai qara"
"Haka maganarka take" ta fada tana jinjina kai,tana tuna rayuwar matan karkara,ba inda aka maida qarin aure da sakin aure ba'a bakin komai ba irin a can,cikin ranta take sake yima Allah godiya,wanda koda yaushe bakinta baya shuru da gode masa walau cikin zuciyarta ko a fili,ya mata baiwa iri iri kala kala.
🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶
Tashinta kenan daga bacci suka kammala waya da aliya kan zancan turowa gidansu da mahmoud yakesonyi umminta ta kirata,sun jima suna hira don khalipha bai barin wayarta ba credti duk don kiran 'yan gida,daga nan ta baiwa basma wadda suke shirin yin candy itama suka taba hira,sai shukra da sauran 'yan mazan kafin daga bisani suyi sallama
"Baby zonan" khalipha ya fada yana aje biron hannunshi da yake wani assigment bayan ya gama nazarin ayshan tsaf,ba musu ta isa gareshi ya miqe tsaye ya kama hannunta yana dubanta
"Shirya muje asibiti ban yarda da wannan qibar taki ba,kada sakacinmu ya jawo mana asara" narkewa tayi zata sa mishi kukan nata
"Banda lafiya hubbi,nima ina jin haka a jikina"
"Don't cray baby,shirya muje".
Suna zuwa ba wani jira ko bin layi sukayi ba sabanin yadda qasarmu take direct suka samu ganin likita,bayan ya gama mata dukkan tambayoyi cikin qanqanin lokaci ya gama bincikensa,cikin murmushi yake shaidawa khaliphan ayshan na dauke da juna biyu na tsahon sati goma sha daya,ji yayi kamar baiji me yace ba saida ya sake maimaita masa
"Alhamdulillahil lazi bini'imatihi tatimmus salihat" ya dinga ambata,itakam aysha qamewa tayi a zaune,yau itace ke dauke da ciki?,ciki fa?,saita sanya hannunta tana shafa cikin nata kamar cikin shi zaiyi magana ya tabbatar mata da kanshi.
Kaman zaiyi kuka haka ya sanyata a gaba yana kallonta,ya rasa irin godiyar da zaiwa ubangiji,ita kanta ayshan jinta take kamar ba ita ba,wai itama zata zama uwa,zataji yanda iyaye keji,wanda daga qarshe sallahr nafila khaliphan ya tashi ya dinga jerowa,itama sai taji joining dinshi suka yi tare.
Bayan anni da ummi babu wanda suka baiwa labarin cikin,haka suka ja bakinsu suka tsuke suka ci gaba da rainon kayansu,dukkan wata kulawa bakin tana samunta daga wajen khalipha,bai barta ta nemi komai ta rasa ba,jinta yake ko ina ajikinsa,ya tabbatarwa kanshi mahadin numfashinsa ce ita.
*_bayan wata tara_*
Tsakanin anni da ummi data dawo kano da zama kowa so yake a bashi aysha ta haihu wajensa,yayin da shi kuna gogan yayi mirsisi da idanunshi yaqi dawo da ita har cikinta ya shiga watan haihuwarta,saida annin tayi masa jan ido sannan ya yarda zai kawotan,hakanan yana dacin rain ya daukota suka taho nijeria,sam shi ba haka yaso ba,so yayi annin ta barshu tunda sun kusa kammala karatun nasu idan ya gama su taho tare gaba daya koda bayan ta haihunne tace sam bai isa ba.
Ranar da zai koma din yanata kumbure kumbure ita kuwa aysha nata masa dariya da tulelen cikinta da haihuwa ko yau ko gobe,hararta yayi a wasance sannan cikin dakakkiyar muryarshi yace
"Idan baki wasa ba zan daukeki ne bada saninsu ba na koma dake"
"Allah ya baka haquri bani nakar zomon ba"kai ya gyada yana ciza lebe
"wato ke sam baki ma damu da rabuwarmu ba ko?" Kai ta kada dariyarta nason fitowa
"A'ah,ni ba haka nace ba,ba haka nake nufi ba,Allah ya baka haquri" qaramar jakarshi daya zuba muhimman abubuwanshi ya zuge
"Shikenan.....kiyita zama anan,saina samo wata na qara mu mu zauna a can" tofa,take ya tunzura mata zuciya,ta cika tayi fam,kuka takeson saki amma yaqi fitowa,saidaya gama shirinsa tsaf ya sumbaci lebanta da goshinta sannan hawaye ya subuce mata,ya gani amma ya juya ya fice abinsa,abinda ya qara tunzurata kenan ta rushe da kuka.
Tunda ya tafi take kuka tana duqunqune a daki,wani kishi da bacin rai yake cinta,tun anni bata fahimta ba har ta gane kuka take
"Tofa ni aishatu,aysha kodai ticket za'a yanko miki ki bishi ne?" Ta fada tana riqe haba,kaita girgiza da sauri hawayen da take riqewa suna saukowa
"Ko an siyo bazan bishi ba anni,yaje ya qara auren" dariya taso subuce mata saita danne,sai yanzu ta dago abinda ke faruwa,kai ta kada cikin fada tace
"Shi yace miki aure zai qara?" Kasa bata amsa tayi sai wani sabon kukan
"Zaici qaniyarshi ne nida shi ne,wannan wanne irin shashancin banza ne?,yarinya na cikin wannan halin kana gaya mata wannan maganar,to don gidansu ya qara auren mu gani,shahsasha kawai,rabu dashi ayshatu zaya zo ya sameni" anni ta fada tana dan bubbuga bayabta,don ta fuskanci harda tension da pressure ta masu tsahon ciki,haka ta dinga lallashinta sadata tabbatar tabar kukan sannan ta bar dakin.
Tsaye yake cikin falon yaja tsaki yafi cikin carbi,komai baya masa dadi gaba daya,abu na farko hawayen aysha da yake gani wanda shine abu na farko daya hanashi sukuni,abu na biyu kuma tashin hankalin rashin jin muryarta,tunda yadawo ya kasa zaune ya kasa tsaye sai daya kirata amma wayar harta qari burarunta ba'a dagawa,abinda bai sani ba anni ce ta amsa zata tayata horashi,abu na uku rashin ayshan a gidan,sai yaji gaba daya qasar ta fice masa aka,ji yake tamkar yana kan qaya ne,sam ko dawowa gidan baya sonyi saboda idan ya dawo din sai ya rasa abinda zaiyi.
Da wannan tunanin ya samu da qyar ya kurbi tea wayarsa na hannunsa yana ci gaba da gwada lambar ayshan saidai koda ta shiga ma ba'a amsawa.
Daga bangaren aysha kuwa basu jima da gama waya da ummi ba ta wayar anni taji mararta da bayanta sun soma riqewa da ciwo kadan kadan,saita zaci fitsari ne ya cika mata mara,hakan ya sanya ta shiga bandaki don tayi,saidai fitsarin duka ba wani mai yawa bane tayi ta dawo ta sake kwanciya,a hankali ciwon ya soma qara yawa,tun tana daukarshi kadan har ya soma matsa mata ta miqe ta fara safa da marwa,daidai lokacin da baba atika ta shigo dakin,donko anni bata shigo da kanta ba zata turo baba atikan,bata taba bari tayi minti talatin ba'a dubota ba
"A'ah uwar masu gida kardai abunne ya taso?"
"Wallahi ban sani ba baba atika,marata ce ke ciwo kamar zata tsage" ta fada tana yarfe hannunta
"A'ah,bari na sanar da hajiya" baba atika ta fita da hanzari don shaidawa anni,saidai kafin a gyara mota a fito da kayan haihuwa ciwo ya kankama tafiya ba zata yiwu a wajen aysha ba,tilas aka haqura anni tabar baba atika a dakin,don sam kunyar annin ta hana ayshan ta sake sosai dole ta fita ta barsu a dakin,saidai bata matsa ko nan da can ba tana tsaye qofar dakin baba atikan na yu qurin ganin ta qarfafi ayshan ta tashi su qarasa asibiti,nishin data soma shi ya tabbatarwa baba atika haihuwa tazo,ta gyara wa ayshan zamanta tana qarfafarta tayi nishin don babyn ya samu ya fito,cikin ikon Allah nishi uku kacal kukan jaririyar ya karade gidan
"Alhamdulillahi" anni ta furta murmushi mai hade da qwalla da na bayyana a fuskarta.
Dai dai sanda khaliphan ya saki nannuyan ajiyar zuciya yana sake gyara zamanshi,tsahon daren duka bacci yaqi zuwa idanunshi hakanan,so yake kota halin qaqa yau yaji muryan uwaishanshi,yasha attempting din kiran anni amma baiso ta gane laifi ya yiwa aysha taqi daga wayarshi,ayau kam yana jin an kai matakin da dole ya kira annin,idan ma fada zata yi mishi tayi masa indai zata hadashi da aysha yaji muryarta da lafiyarta,sai kawai ya danna lambar annin yasa handsfree ya ajeta a gefe yana jiran yaji an amsa.
Kukan babyn daya cika kunnenshi a sanda aka daga wayar shi ya sanyashi tashi tsaye cak kamar wanda aka yiwa allurar sojoji
"Allaaaaaahu akhbar" ya ambata,ko ba'ace masa komai ba,ko ba'a gaya masa ba yasan cewa tabbas wannan jininsa ce,diyarshi ko diyanshi ne yau ya shaqi iskar duniya
"Khalipha,yau Allah ya albarkace da samun diya mace"
"Alhamdulillah,Alhamdulillah anni hajar ta dawo"
"Ma sha Allah" ta fada tana jin dadi har cikin ranta,tana jin kewar diyarta da tuna mutuwarta
"Anni ya humaira take?"
"Tana lpy atika tana shiryata"
"Alhmdulillahi ya dinga maimaitawa sai anni ce ta kashe wayar,kasa zaune yayi ya kasa tsaye,cikin lokaci kadan ya soma turawa 'yan uwa da abokan arixiqi cewa ya samu qaruwa,nan da nan saqonni suka dinga shigo masa ta ko ina,duk yadda yaso jin muryar ayshan anni taqi hadasu tace saita huta,kamar zaiyi hauka,har kusan kuka ya yiwa annin amma ta shareshi.
Sanda anni ta shiga dakin an gama shirya baby da mamanta tsaf,tuni babyn ta shiga bacci,bismillah anni tayi ta dauketa idanunta kan kyakkyawar fuskar yarinyar,khalipha sak haka ta gani,kamar sanda ta haifeshi,komai nata irin nashi ne hatta da yatsun qafafunta,
"ma sha Allah,Alhamdulillahi"Qaunar yarinyar ta ratsata lokaci guda,fuskarta qunshe da murmushi ta dubi aysha dake zaune tana shan tea mai zafi
"Sannu indo aysha"a kunyace ta amsa ma annin
"Allah ya albarkaceta,ya qareku da lafiya,ubangiji yasa cikon musulunci ce"
"Amin" ta furta can qasa yadda annin ba zata ji ba,saboda kara da kunya,
"Ki huta zuwa anjima sai muje asibiti a dubaki da kyau a tabbatar komai lafiya ko?,sai......" Bata kai aya ba kiran khalipha ya shigo wayarta,wannan shine kusan kira na bakwai da ya yiwa annin
"Ungo,karbi mijin nan naki,na tabbatar idan ba bakin nayi ba bazai taba qyaleni na huta ba" ta fada ta ajje mata wayar gefanta,sannan ta dora babyn kusa da ita ta fice a dakin tana kiran baba atika.
Tana kallo sai daya kira kusan sau uku sannan ta daga,kiran sunanta ya fara yi sai tayi fakare dashi kaman bata jiba
"Nasan kina jina uwaisha,na godr,amman don Allah kowanne hukunci zakimin kimin amma banda hanani jin muryarki naji lafiyarki" har ga Allah har a sannan ranta adan bace yake dashi,baisan yadda take kishinsa bane shi yasa ya gaya mata haka
"Me kakeson nace?,kai da zaka auro amarya tunda ni na haihu na tsufa?"
"Wayyo uwaisha don Allah karki sa na kasa bacci yau.....am sorry uwaisha bana son abinda zai sa mu raba muhalli dake uwaisha....yanzun haka wallahi bazan iya zama ba dole na sake biyo jirgi nazo na ganku keda baby na" idanunta ta lumshe,har abada tana alfahari da soyayyar da yake mata
"Ya jikin naki ina baby na dawa tayi kama?" Ya furta cikin sanyin murya dake nuna zumudi zallah
"Dani tayi kama" dariya ya qyalqyale da ita cike da nishadi
"An gaya miki ni rago ne?,to na sani nita debo komai da komai,kina kishi ne ko?" Saita tura baki kamar yana ganinta
"Nida wahala kai da kwashe kamannin" dariya ya kuma yi sosai wanda hakan ya sanya nishadi a zuciyarshi
"Tukunna ma,duka sauran wadanda zasu biyo baya ki zuba ido zaki gani",tun tana sharewa har ta saki jiki sosai,kafin suyi sallama sai daya wanke kanshi fes da soso da sabulu.
Zuwan aliya shiya katse musu hirar dole ba don sun gaji ba,aliya murna kamar tayi me
"ke bamusan kin dawo ba sai labarin haihuwa muka ji"
"Hmmm,kedai bari aliya,kwana ma biyu fa da dawowa,Allah nema yayi bazan haihu ba a can" tare suka zauna da ayshan,ranar haka baqi suka dinga tittudowa,toh abinka da idan kana dashi anayi dakai kowa burinsa yazo yaga jaririya,wasu soyayya ta domin Allah wasu ta abun hannun iyayenta,a ranar ummi ma bata iya kara ba sai datazo da dukka yaranta,basma ta qanqame babyn tana cewa itakam anan zata zauna sai anyi suna,ranar anni da ummi sunsha hira sosai,yawan baqin ya sanya basu samu damar zuwa asibitin bama sai dare,alhmdlh komai lafiya ita da babyn,sai magunguna kawai da suka rubuta mata don qarin lafiyarta,suka siya suka dawo gida.
Washe gari saiga hanan da mmn hunaifa,ranar kam an sha hira sosai,sunyi missing aysha,karatu yanata gangarawa
"Ai dama na fada wallahi,irinku su aysha sumumu kasau din nan baku iya soyayya ba,sai gashi ke data tashi damqarki ma karatun kika aje gaba daya" hanan ta fada tana hararar aysha cikin wasa,dariya aka sanya gaba daya,mmn hunaifa tace
"Ni banga laifinta ba,nima don bbn hunaifa keso,da zaice nima na aje jewar zanyi".
Da azahar saiga mummy abun mamaki harda asma'u,duban tausayi aysha take musu su duka,don duk wanda ya kallesu yasan rayuwa bata gara musu kamar da,duk sai ayshan taji ta tsargu,kaman ta zubda su duk da cewa basa sati basuyi waya da mummyn ba,ran aysha saiya koma duka a bace,har suka gama yi mata barka suka tafi,asma'u tace sai ranar suna mummy kuma tace sai gobe zata dawo.
Kafin washegarin ta sanya daya dags cikin yaran khalipha ya mata bincike kan halin da ake ciki,rashin tattali ya sanya sun sanya su mummy sun sanya gadonsu a gaba sun cinye sai d'an abinda ba'a rasa ba,sai kuma abinda su anty safiyya ke taimakawa mummyn dashi,asma'u kam nata juyawa take,dashi suke kashe buqatun kansu ita da hamid din,don a yanxu ya koma ya zauna,bashi da wata qaqqwarar sana'a,da kanta ta cira kudi cikin accnt dinta wanda ita kanta tasan ba qaramin kudade bane a ciki tayi musu siyayya,don khalipha ko riba ya samu mai yawa a wani harkan saiya fitar mata da wani abun,dukkan wani abu da tasan sun rasa saida aysha ta tabbatar sun sameshi,hakanan ta qarawa asma'un jari yadda zata riqe kanta sosai,kunya ta kama asma'un har taso taqi amsa amma ayshan ta turje
"Ni kamar 'yar uwa na daukeki anty asma'u,qin karbarki bashi ne zaimin dadi ba" hawaye ta dinga sharewa tana kada kai
"Ban cancanci naci arziqinki ba ko wanne iri aysha,bansan ma ta yaya zance ki yafemin ba"murmushi aysha tayi saboda dama tasan abinda ke cinta kenan
"Karki taba sawa a ranki kinmin komai,koma me kike tunani yanzu ina yake anty asma'u,koma meye ya zamemin silar alkhairi,ya zamemin silar haduwa da mijin da samun kamarshi sai an tona,na yafemiki kome kika yimin duniya da lahira" hakanan ta amsa tana mata godiya gami da jin kunyar kanta kan dukkan wani abu data aikata,bata taba zatan cewa a rayuwa wataran wanda kake samanshi zai iya zamowa shine a samanka kai a qasanshi,koda yaushe ka zama mai kyautata mu'amalarka saboda babu wani abu dawwamamme.
Ba zato saiga khalipha ya sauka ranar suna da yammaci,yazo ganin little hajar,wanda ake kira da farha,aysha na cikin jama'a amma sai daya sanya aka kira mishi ita,hadasu yayi duka ya rungume ita da baby farha yana ajiyar zuciya,sai daya dauki a qalla mintuna biyu a haka sannan ya saki ajiyar zuciya yana dagata daga jikinsa yana fadin
"Alhmdlh,Alhmdlh" yana kissing dinta a goshi,murmushi ta sakar masa tana masa sannu da zuwa,a qalla saida ta kusan kashe awa biyu a wajensu yana kallonta kawai baby farha na wajensa,ga jama'a daketa tururuwar zuwa suna anata nemanta,da qyar da sudin goshi ya barta ta fito bayan anni tasa baki,tare da alqawarin gobr xasu wuce gidansu.
Taro ya tashi lafiya baby hajar farha tazo da goshi da alkhairi mai tarin yawa,washegari da magariba ta shirya tsaf ita da farha suna zuba qamshi suka wuce gidansu,suka bar anni da yasmin 'yar anty ruqayya da aka kawo mata.
Baby farha nada wata biyu yace zasu koma ya kammala jarrabawarsa,da fari anni taso yabarsu a gida yaje yayi ya dawo,amma daga bisani ya gaya mata akwai yiwuwar zamanshi a can hakanan suka tarkata suka tafi kowa na kewat baby farha,sun zagaya sallama har takai,zuwa wannan lokacin inna yelwa ta sake sanyi qwarai,ta tabbatar jahilci ya taka muhimmiyar rawa wajen faruwar dukkan abinda ya faru,khalipha bai tafi ba sai daya assasa islamiyya can garin ta matan aure da yara,wanda ya dauko ingantattun malamai masana sunnar Allah da ma'aiki suka hau koyar da al'ummar garin ka'in da na'in,suka yi nasarar yaqar duk wani baqin tunani,da baqar alaqa da dangantaka dake tsakanin fulani da manoma,basu bar qasar ba sai da aka sanya ranar aliya da mahmoud,wanda ya matsa qwarai yana ganin kamar zai rasa aliyar ne ko kuma taqi bashi dama.
Ta bangaren haidar ma tunda yaga basma ya soma kai kawo,wanda daga qarshe ya bayyana muradinsa,ayshan dai batasan ya ake ciki ba har suka bar nigeria zuwa cyprus.
Randa zasu tashin suna tsaka da shiri aka ce ana sallama dashi,hakanan ya fito bai kammala shiryawa ba don yayi mamakin wanda ke nemansa a irin wannan lokacin ya fito zuwa falon da yake ganawa da baqinsa.
Kawu hamza,kawu munzali,kawu habibu da kawu saminu,dukkansu suna zaune qasan tile din dake malale a dakin,suna zaune tsumu tsumu kamar wadanda aka tsoma kaza cikin ruwa,kallo daya zaka yi musu kasan cewa dukkaninsu suna jin jiki na rayuwa dana abinda suka aikata.
Dubansu yake yayin da kowa ya gyara zama yana miqo gaisuwa,amsa musu yayi kadaran kadaham kafin shuru ya biyo baya an rasa wanda zai soma magana a cikinsu,kawu saminu ne yayu qarfin halin soma neman musu yafiyar khalipha,don dukkansu mutuwar idris ta zame musu izinina,daga qarshe ya rufe
"Haqiqa shaidan ya taka muhimmiyar rawa wajen yi mana huduba,da banzayen zukatanmu marasa son Allah,muka bijire muka kwashe dokiyoyinku muka cinye,sannan uwa uba muka kasa kula daku muka yiwa mahaifinku butulci,mutuwar idris kawai ta isa ta nuna mana makomarku matuqar baka yafe mana ba kuma bamu nemi yafiyar Allah ba,iya halin da muke ciki ma yanzu kawai munga ishara babba,bamu da nutsuwa cikin gidajenmu da rayuwarmu,yaranmu duka kowanne da tashi matsalar Allah ya jarrabemu,ka daure badonmu ba badon halinmu ba ka yafe mana"
Iska mai zafi ya furzar da ita daga bakinsa yana qoqarin controlling kanshi,tsahon mintuna biyar shuru ya ratsa falon
"Allah ya yafe mana gaba daya" dukkansu qwalla suke sharewa suna godiya,yana tsaye yana kallonsu har suka gama ficewa daga falon sannan ya juya ya koma ciki,zuciyarshi cike fal da tunani kala kala,rayuwa ita haka take,dukkan yadda ka dauketa haka take zuwa maka,mafitarka daya kabi Allah kabi dukkan dokokinsa.
60
*_BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYU_*
Misalin sha d'aya na safe jirgin dake dauke da iyalan muhammad khalipha sa'id mai goro ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na malam aminu kano dake kano.
Yarinya ce 'yar kimanin shekara goma sha uku ce a gaba riqe da hannun wani yaro d'an kimanin shekara biyar,bayanta wata matashiyar macace fara tas mai matsakaicin tsayi da dogon hanci,wadda kana mata kallo d'aya zaka tabbatar da cewa hutu jin dadi da gayu sun ratsata take biye da ita,fuskarta qunshe da murmushi wanda hakan ya bayyana dimple dinta dake kumatunta na hagu da dama,tana dauke da wani kyakkyawan yaron wanda baifi shekara uku ba,sak kamanninsa na muhammad khalipha ne mai goro,shine ya fito a qarshe yana ruqe da qananun akwatina masu kyau guda biyu,shima fuskarshi na dauke da murmushi da alama magana suke da uwargida sarautar mata ayshatu dake gabanshi
"Farha....oya bani jawad ki amshi trolly dinku" da gudu jawad ya zame hannunshi daga na farhan yana tawowa wajen aysha,harara khalipha ya jefawa aysha mai nuni da zallar qauna
"Hajar din zan baiwa daukan akwati?" Murmushi ta saki don dama ta sani hakan zata kasance,wata qauna yakewa yarinyar tamkar hajar dinsa,haka suka dinga takowa har zuwa inda motocin MAI GORO suke jiransu.
Dukka qofofin motocin a bude suke suna jiran isowar boss din nasu,suna hangosu a hanzarce suka amshi akwatunan hannunshi suka shige mota guda shi da iyalin nashi gaba daya.
Kwabe fuska jawad yayi yana duban aysha
"Anna...ba gidan anni zamu fara zuwa ba?"
"Ban sani ba tambayi abbinku" ta fada tana gyarawa fu'ad kwanciya a jikinta,duban khalipha yake yana son magana yana tsoro,saboda last time da sukazo yace ba zasu sake zuwa su kwana wajen annin ba,saboda yadda suke qiriniya da rashin ji idan sunje,yace ba zasu hana uwarshi hutawa ba,itama farha kallon abbun nasu take,ita kanta tafison gidan annin,saboda tun suna can sunyi waya dasu amra da afaf (jikokin annin yaran basma da haidar,da 'yar mus'ab),Dukkansu suna can gidan anni suna hutu daga kai khalipha yyi ya kallesu sae ya maida kai baice musu komae ba jawad ne yakasa shiru murya a sanyaye yace pls abbu akaimu gidan ammi munyi alqawarin bazamu sake pitina ba baice mishi komai ba ganin hakan shima yaron yaja bakinshi yyi shiru.
Cikin yan mintina suka isa kataparen gidansu dake nasarawa meela road tanpatsetsen gidane da khalipha ygina da yadauki shekaru yana ginashi mention house ne nagani napada a parking space duka motocin suka tsaetsaya su jibiril sukaxo suka bude musu qopa taxuro qaparta xata pito daga motar wayarta ta soma ringing saeta dakata da pitar takira farha ta daukar mata fu'ad duba mekiran tayi inna yalwa ce sae tayi mamaki data ga number nigeria da alama ta dawo gida kenan daga jinyar qaparta da khalipha yapitar da'ita saudiyya sagas a tayi tasa akunnenta gami dayin sallama dagacen bangaren inna yalwa ta amsa
"nayi sa'a kardae kice min kindawo?" Murmushi Aisha tayi gami dacewa "nima yanzu a raina nakecewa ashe kindawo"
"Eh wolh kwanana biyar kenan da dawowa ta"
"Toh yaya jikin"
"Jiki alhmdulilahi nasamu sauqi, kitayani yiwa allaji khalipha godiya Allah yasaka da alkhairi,ya qara budi"
"Amin ai babu komai,cikin satin nan ma zamu shigo takai din in sha Allahu,su mero zasu tare sabon gidansu"
"Ma sha Allahu...an gana kenan?,ke dai indo babu abinda xamu ce dake saidai godiya da fatan alkhairi keda halipha,kaf karkarar nan babu wanda baici arxiqinki ba,babu wanda arziqinki dana mai gidanki baibi ta gidansa ba,Ashe haka rayuwa take,bakasan wanda zaka ci arxiqinsa ba....ki yafemin indo bazan daina neman yafiyarki ba har abada..." Ta qarashe maganar cikin rauni da nuna nadama
"Kai inna,ya wuce fa,sai munzo din"
"Allah ya jiqan mahaifinki indo,ki gaidamin da masu gida na da kishiyata"murmushi ta saki
"zasu ji" ta fada tana kashe wayar ta maidata jaka sannan ta qara fitowa daga cikin motar,zuwa sannan tuni khalipha da sauran yaran sun shiga ciki don haka tabi bayansu a nutse,cikin taku na cikakkiyar mace mai ilimi wadda tasan abinda take,wadda ta gogu da ilimi da zaman duniya.
Bata shiga ciki ba sai data kira mummy bayan ta kira ummi ta sanar mata dawowarsu,ta tabbatar da komai na tafiya lafiya cikin sabon gidan da khaliphan yayi musu,ya dauke shima dukkan wata lalura ta mummyn,don daddy wani mutum ne mai muhimmanci shima a rayuwarshi,bazai taba manta alkhairinsa ba a gareshi,tun daga ranar da yasan abinda ke faruwa ya amshe duk wata dawainiya da da ayshan ta akarba yaci gaba da jan ragamarta,zuciyar khaliphan mai kyau ce,ya manta dukkan wata cuta da wani mai cuta yayi masa,ya rama kowacce cuta da alkhairi,hakan yasa itama ayshan ta qara qaimi,taci gaba da kyautatawa duk wani wanda ya jibanceta na kusa dana nesa.
A nutse cikin nishadi da qaunar iyalin nata ta shiga cikin gidan,ba kowa a falon sanda ta shiga katafaren falon da xai sadaka da sassa daban daban na gidan,dakunan matar gidan,dakunan yaran gidan,ban dakuna,kitchen da kuma sashen baqi mata,sai sashen mai gidan,tunda bata gansu ba tasan ba zasu wuce dakin yaran ba,murmushi ta saki ta zare mayafin rolling dake kanta ta nufi kitchen din gidan don duba masu aikin gidan wadanda dattijan mata be guda biyu rak suke mata aiki,sai guda daya da batakai shekarunsu ba,a yanzu haka tasan suna can don sunsan da dawowarsu.
A mutunce suka gaisa,kai baka ce 'yan aikinta bane,ta dudduba abinda sukeyi sannan ta gaya musu abinda zasu dafawa yara da abinda zasu hada mata wanda zata shigo da kanta ta yiwa khalipha girkinsa.
Daga nan dakin yaran ta nufa,dakin farha na bude saidai labulen a sake yake,budewa tayi ta tura ta shiga don ta dubata,qarar ruwa taji a toilet hakan ya sanya ta saki murmushi tasan wanka take kuma da alamun da qyar idan ba gidan annin zai kaisu ba,ficewa tayi daga dakin ta shiga nasu fu'ad,yana zaune saman gadansu dukka yaran daure da towel,da alama wanka yayi musu,don ga kayansu nan saman gadon yana feshesu da turare,saita samu gefan gado ta zauna kawai tana kallonsu,tamkar yaya da qannenshi,tamkar abokanshi haka wani lokaci yake mu'amala dasu,shi yasa zata iya cewa sunfi sonshi fiye da ita,kusan dukkan wata hidimarsu bai gajiya idan har yana qasar ko yana tare dasu shi yakeyi musu,hakan ya sanya yanzun ma tayi tagumi kawai tana kallonsu tana jin hirarsu da dararrakunsu,a haka ya kammala shiryasu tsaf dai dai sanda farha ta shigo,tayi kyau cikin shadda bubar har qasa yellow mai red din stone work,shigen kayan dake jikinsu jawad yellow and red
"Good qanwata(wani lokaci yakan kira farha da haka),kinfi kowa yin kyau" murmushi ta saki cikin jin dadi,yana son yarinyar sosai saboda kama da take dashi sosai ita da jawad,jawad din ne ya tabe fuska
"Abbi.....abbi" yana langabe kai,yasan me yake nufi saboda haka ya shafa kansa
"Bakaga yadda kayi kyau ba my twinny(shima hakan yake kiransa wani lokacin saboda kamarsa da shi)" sunan yana yiwa jawad dadi sosai,saboda haka ya saki murmushi shima yana sakewa farha gwalo a boye,duka takai masa ya boye bayan khalipha
"Abbi....gwalo yakemin"kamo hannun jawad yayi ya dawo dashi kusa da ita ya kama hancinsa ya dan riqe
"Bana son tsokana,bata haquri" baki a tabe ya bata haquri,shi kuma ya juya ya kallo farha
"Ke kuma big sis ce.....saikinyi haquri" kaman xatayi kuka tace
"Hademin kai suke fa shida fu'ad abbi....."
"Qyalesu qanwata.....ki cewa anna ta samo miki 'yar uwa kinga kema kin huta"juyawa tayi bangaren da aysha take tana kallonsu,hannayenta ta hade waje guda,alamun roqo,dan hararar farha tayi kadan saita juya kaman zatayi kuka ta kalli khalipha ta daga kafadunta dukka biyu tana tabe bakinta tana nuna mishi alamun ayshan taqi,shima narkewa yayi ya mata alama yayi mata na abun tausayi ya girgiza kai yana duban ayshan
"maman yara....pls a taimaka mana a sake bamu baby girl" dubanshi tayi ta masa signa da ido na yadda yaran sukayi shuru suna jiran amsar ayshan,ta rasa yadda yaran keda shegen son yara,hatta da fu'ad da bai wuce shekara bakwai ba idan yaga yaro ko yarinya,sai kawai ta miqe ta fice a dakin tana murmushi qasa qasa.
Kayan jikinta ta fidda ta soma daura towel,tana tsaka da daurawar taji ya rungumota ta baya,amsar daura towel din yayi tana rungume a jikinsa yana daura mata kanshi saman kafadarta yake cewa
"Kinqi kawo mana agaji nida yarana ko?" Murmushi ta fitar kawai bata ce komai ba,yana gama daura mata ya birkitota gaba daya suna fuskantar juna,yana shaqar qamshin turaren jikinta,idanunshi cikin nata yana mata wani kallo mai tafiyar da xuciya
"Da gaske muke annah....muna son yara ba zaki agazo mana ba" hannunta ta dunqule ta dora a qirjinta tana murmushi
"Allah ya kawo abbi" dan jim yayi sannan yace
"Ameen....muje in wanke matata" cak ya dagata yana takawa a hankali tana dariya tace
"Abbi baka gajiya?,ka wanke yara ka wanke mamansu?" Murmushi ya saki
"Dama ce....ai ina da cikakken time ne,idan kuma ban muku hidima ba wa zan yiwa?" Shuru tayi tana gyada kai cike da jin dadi da hamadala ga Allah.
Sai daya sakata cikin bathtube ya juya ya fice yana cewa
"Ina zuwa" minti daya sai gashi ya dawo,tare sukayi wankansu sannan suka fito,tsaf suka shirya,shi ya bata wasu kaya wanda kalarsu daya da nashi da kuma na yaran,shadda ce irinta farha,tana ta tambayarsa me ake ina zasu baice mata komai ba yace su zuba ido zata gani.
Cikin sabuwar motarshi fara qal suka shiga suka bar gidan,ita dai tanata zuba ido,basu sauka ko ina ba sai gidan anni,sam bata gane meke faruwa ba sai da suka shiga cikin gidan,tafkeken falon annin cike yake da decoration da kayan ciye ciye da qyale qyale,matar mus'ab,basma qanwarta kuma matar haidar da yaransu gaba daya a falon,suna shiga dukka qwayayen dake falon masu dauke da kaloli suka kama,wasu rubutu suka bayyana,ta daga kai tana karantawa,sai a sannan ta gane me yake nufi,murnar cikar aurensu shekara goma sha hudu cif cif dayi ya hada musu.
Sun jima a gidan annin ana sada zumunta gami da ciye ciye da shaye shaye,dukkan familyn kana ganinsu kasan cewa cikin farinciki da walwala suke,basu tashi barin gidan ba sai bayan sallar magariba,tun kafin a soma maganar tafiyar dama su jawad suka soma nacin a barsu gidan annin,dama ya shirya hakan saboda haka yace su zauna din,har sun miqe suna mata sallama ta dakatar da khalipha
"Auren amal ya taso fa,inatason gaya maka ita da zeenatu za'a hada" dan sosa kunnenshi yayi kadan sannan yace
"Yanzu ya za'ayi anni?"
"Dukkan abinda ya dace yanda ka yiwa maryam"
"To shikenan ba damuwa.....za'ayi duk abinda ya dace in sha Allahu"
"To Allah ya taimaka ya yiwa dukiya da rayuwa albarka"
"Amin ya Allah anni,amin" da haka suka juya zasu wuce,babban yaron haidar affan dake zaune waje daya yana cin abinci khalipha ya kalla
"Affan ya jikin dai?"
"Da sauqi abbi"
"Ma sha Allah Allah ya qara lpy"
"Amin" ya amsa mishi
"Anty na asha amarci lafiya" fatima matar mus'ab ta fada qasa qasa tana dariya,hararta aysha tayi,sosai jininsu ya hadi da fatiman,tana girmamata kamar yadda basma take girmamata,hakanan itama ta dauketa a qanwa kamar yadda ta dauki basma
"Wane amarci shekaru sha hudu ba wasa ba,ko kin manta daku muka gama murna yanzu"
"Kullum jin kanku da daukar kanku kuke kamar sabbin ma'aurata,abun naku da ban birgewa yake daban sha'awa,kullum hirarku muke da abban ummu salma,wai ba za'a bamu sirrin ba muma mu hau network?" Dariya sosai ta baiwa aysha,tasha jin wadan nan maganganun daga bakin mutane da yawa,kada ma hanan taji labari,har wani lokaci ta rasa amsar basu,itadai tasan qaunarsu daga Allah ce,jigon tafiyarsu shine haquri da juriya,uwa uba kawaici da yiwa juna uzuri,soyayya ta domin Allah bata gushewa haka bata qarewa,indai dukkanku zaku yarda kuna bautar Allah ne sannan kowannenku yayi qoqarin sauke haqqin Allah na dan uwanshi daya da Allah ya dora mishi cikin girmamawa da kyautatawa,wannan sune kalaman data gayawa fatima wadandan ta jima tana yi musu dalla dalla,haqiqa sun qunshi abubuwa masu muhimmanci da dama wanda sai sun samu zama da ayshan sosai zata nemi sani da cikakken qarin bayani akai.
Ita ta soma gama shirin kwanciyarta tsaf ta haye gadon tana jiranshi,duk wani shiri ta gamashi don ta gama karantar mijinta,cikin satin da suke shirin tahowa nijeria yanata zirga zirga bai samu zama ba,tana kallonshi ya gama komai ya isketa,yana murmushi sanyata cikin jikinsa sosai yana shaqar daddadan qamshinta mai shiga rai da tsayawa a zuciya
"Uwaishahh......meye labari,naga bakinki akwai magana da alama" qanqameshi itama tayi sosai,ta zagaya hannunta a bayanshi tana murmushi
"Ina godewa Allah da baiwar da yayimin da kuma ni'imar nagartaccen miji wanda babu tamkarsa kamar kai,kaine baiwa ta farko kuma ni'ima ta farko cikin rayuwata,ina roqa maka alkhairin Allah rahamar Allah da kuma jin qan ubangiji a gareka nan duniya da gobe qiyama......my life...ina maka albishir ina dauke da juna biyu" idanu ya zaro cikin xumudi yake duban idanunta
"Are you seriouse uwaisha?" Kai ta kada
"Da gaske nake maka my babu irin wannan zolayar a tsakaninmu,bazan taba ja maka rai ba kan abinda nasan kana so"
"Allah na gode maka da dukkanin baiwa da ni'imar daka yiwa rayuwata,Allah na gode maka daka bani matar aljanna tun a duniyata,uwaishaaa,duk abinda zan gaya miki a kanki ina kin tamkar na rage darajar so da qimarki da nake gani a rayuwata"
"Ni ya cancani nayi wannan godoyar wa uba giji,farincikin daka baiwa rayuwata baya misaltuwa,ka zama silar warwarewa dukkan wani DAURIN BOYE da ya yiwa, rayuwata dabaibayi,ina sonka abbi,ina sonka sosai abban farha jawad da fu'ad"
"Da unborn ba....." Dariya ta saki tana sake shigewa jikinsa
"Zumudi dai your royal highness"
"Kinga lafina?,yara nakeson dozen biyu.....bari ma kiga ni na sake bada himma ko zasu zama biyu idan kin tashi haihuwa" dariya sosai ya bata,a ranta take cewa ko ina ake haka?,cikin aminci salama da kuma sallamawa suka shiga wata duniya mai cike da nutsuwa da aminci wa juna.
*Alhamdulillahil lazi bini'imatihi tatimmus salihat*🙏🏽
_muna miqa dumbin godiyarmu ga dubun nan masoyanmu da suka kasance damu,suka bamu goyon baya,suka kasance cikin group na zafafa biyar,haqiqa soyayya ba qarya bace,Allah ya qara zumunci ya sadamu da dukkan alkhairinsa,rabbi ya yafemana dukkan kurakurenmi cikin rubutunmu,ya hadamu a ladan amin summa amin_
*subhanakallahumma wabi hamdika,ashahadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa'a tubu ilaika*🤲🏽🤲🏽
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
*ko kuma*
07067124863
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
*ko kuma*
07067124863
*mrs muhammad ce*👑
4
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
*ko kuma*
07067124863_HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
*ko kuma*
07067124863
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
*ko kuma*
07067124863
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
*KO KUMA*
07067124863
*DAURIN BOYE*
_HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
*ko kuma*
07067124863
_Ya Allah ka rabamu da sharrin mutum da aljan_🙏🏽i
*mrs muhammad ce*👑
_Ya Allah,ka rabamu da sharrin mutum da aljan_🙏🏽🙏🏽
*mrs muhammad ce*👑
_Ya Allah ka rabamu da sharrin mutum da aljan_🙏🏽
*mrsuhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
*mrs muhammad ce*👑
No comments