Bongel Complete Hausa Novel
Zee Yabour: BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
Bismillaahir rahmanir raheem
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai'
SHAFI NA D'AYA
GGC KABOMO
Yara ne mata manya da k'anana duka sanye da uniform na makaranta, kowa da abunda yake yi, wasu na wasanni, wasu na cin abinci wanda ke nuni da lokaci ne na break, Yanayin yaran zai tabbatar maka iyayen su ba masu hali bane, makaranta ce ta gwamnati wacce ana jeka ka dawo kuma akwai b'angaren yan' kwana.
Budurwa ce yar' kimanin shekaru 17 da haihuwa zaune a aji ita kad'ai, littafi a gabanta tana bitar karatu, "Bongel sarkin boko, wai bakya gajiya da karatu" Cewar Asiya da shigowar ta kenan, itama ba zata gaza shekaru 17 da haihuwa ba, Ta d'ago kai ta kalle ta tace "Hmm Asiya kenan, wannan shine matakin k'arshe na sakandire wanda ya kamata nayi k'ok'arin ganin na fita da sakamako mai kyau, haka karatun nan shine gatana, shi zanyi na taimaki iyayena, basu da buri da ya wuce ganin na samu ilimi mai zurfi, saboda shi na baro ahalina" Asiya ta jinjina kai da cewa "Allah ya bada nasara", "Amin" Ta amsa, ta juya ta cigaba da karatun, Asiya ta zauna kusa da ita, itama tana d'auko nata littafin.
"Sannu Baffa, Allah ya tashi kafad'un ka" Dattijuwar mata wacce ba zata gaza shekaru arba'in ba ta fad'a da k'arasawa da hawaye, Wanda aka kira da Bappa kansa ya girgiza yace "Ko bayan raina kada a cire Bongel makaranta ita kad'ai Allah ya bani ikon sawa makaranta, Dan Allah ku cika mun burin nan nawa na ganin tayi ilimi mai zurfi", "Baffa In Shaa Allahu kana tare damu, zaka tashi ka cigaba da rayuwarka", Kansa ya girgiza ba tare da ya sake cewa komai ba,
Bongel komai yau sukuku take yin sa, duty d'inta na ranar kawai tayi sa ne, ta fito hostel, Tun shigarta aji bata cewa kowa komai ba, dama ita ba gwanar surutu ba ce, sai dai shirun yau yasha bambam dana kallo, Ta rasa dalilin da yasa bata jin dad'in ranta, ga gabanta dake yawan fad'uwa.
"Hafsat Aliyu" Taji muryar Vice principal d'insu na kiranta, Ta amsa da mik'ewa, "Zo" Ya fad'a yana yin gaba, ta biyo bayansa har zuwa admin, Hamma Bala ta tarar a zaune ofishin vice principal, "Hamma ina wuni?" Ta gaishe sa cikin sanyin murya, "Lafiya lau" Ya amsa murya a raunane wanda daga yanayin sa ya tabbatar mata zuwan nasa ba na lafiya bane, Rubutu VC d'in yayi a takardar ya mik'awa Hamma Bala, Ya juya kan Bongel "Idan akwai abunda zaki buk'ata a gida, kije ki d'auko zaku je gida", "Gida" Ta nanata a ranta, yayin da k'irjinta ya doka, ko shakka babu ba lafiya ba, tsawon shekarun da tayi a makaranta tun js1 ba'a tab'a zuwa d'aukarta ba, biki ko suna Bappa baya bari saboda yadda ya d'auki karatun ta da muhimmanci, "Bana buk'atar komai" Ta fad'a dan a halin yanzu burinta ta ganta a gida dan sanin meke faruwa,
Babur na Hamma Bala ta hau, yaja su zuwa malumfashi kasancewar babu nisa, Taron mutanen data gani a k'ofar gidansu, yasa jikinta tsinkewa, ko shakka babu mutuwa ce, wani daga cikin yan' gidansu ya rasu, Tana dosar k'ofar shiga ta fara jiyo koke koke, jikinta ya soma rawa da k'yar ta rab'a mutane ta shiga ciki, idonta ne ya sauka kan mahaifiyarta wacce ke faman zubar da hawaye, da gudu ta k'arasa kusa da ita ta fad'a jikinta,
"Mun rasa Bappa Bongel Allah ya k..." Bata k'arasa ba sakamakon sumar Bongel, mutane sukayo kanta ana yayyafa mata ruwa, A hankali ta bud'e idonta tace "Nene Dan Allah kice mun mafarki nake bamu rasa Bappa ba", Hawayen data gani shimfid'e kan fuskar Nene ya k'ara tabbatar mata gaskiya ne,
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Take nanatawa idonta a runtse, hawaye na ambaliya saman fuskarta, mutanen da ke wurin ta basu tausayi matuk'a sanin irin shak'uwar dake tsakanin ta da Bappa.
Ta jima zaune a wurin tana zubar hawaye, kiran sallar la'asar yasa kowa mik'ewa zuwa gaida ubangiji, Bongel ta d'ago rinannun idonta da suka koma jajir saboda kuka suka sauka kan Dije da Fatsuma wanda suke cin tuwo hankali kwance babu d'igon hawaye a kan fuskar su, Kanta ta kawar gefe cike da takaicin su, bata d'auka rashin imanin su ya kai haka ba, Alwala tayi a famfon dake tsakar gida ta shiga d'akin Nene, ta dad'e tana addu'o'i,
"Adda! Adda!" Ta d'ago tana kallon k'anwarta Ramla yarinya yar' kimanin shekara 14, hannun ta rik'e da k'aramin k'anensu dan' shekara hud'u, "Adda Bappa ya tafi ya barmu" Ramla ta fad'a tana fashewa da kuka, ta fad'a jikin Bongel, K'aramin k'aninsu Abu shima ya fad'a jikin Bongel, ta k'ank'anme su jikinta, suna kuka mai tsuma zuciya.
Goggo Hajjo wacce k'anwar Nene ce ta dad'e tsaye a d'akin tana kallonsu cike da tsantsar tausayi, Kafin ta nisa tace "Haba Bongel kece babba cikin su, ke da ya kamata ki lallashe su kin sasu gaba kuna kuka, Bappa addu'ar ku yake buk'ata ba kuka ba, nasan da ciwo amma haka zaku jure, mutuwa na kan kowa",
Muryarta da k'yar take fita ta dishe tsabar kuka tace "Ashe haka mutuwa take da d'aci da rad'ad'i, mun rasa Bappa Goggo dole muyi kuka", Kusa dasu ta duk'a ta kamo hannun Bongel da Ramla ta soma lallashin su tare da musu nasiha, a hankali sukaji natsuwa na saukar musu sun tsagaita da kukan.
Da zazzab'i Bongel ta kwanta, ana cewa bacci b'arawo sam bai sace ta ba a daren ranar, Ramla da Abu sun samu yin bacci, Nene itama haka ta kwana lazimi tana rok'arwa Bappa rahamar ubangiji.
Kwana uku ana zaman makoki, kowacce rana da irin halayyar dasu Dije ke nunawa, har mutane sun fuskanci basu damu da mutuwar ba, haka kowa ke tafiya dasu a baki.
"Na sha jin labarin facaloli amma ban tab'a ganin kishin matan sauri irin naku ba" Cewar Hajjo, Nene ta numfasa tace "Nasu dai, ni kaina abun yana matuk'ar bani mamaki da d'aure kai, ban k'ara tsinkewa da lamarin su ba sai rasuwar nan", "Ni kaina na k'ara shaida Dije da Fatsuma basa sonki kuma bana jin zasu tab'a sonki", Nene tayi murmushin takaici tana girgiza kai, Bongel shiru tayi tana k'ara nazarin rayuwa irin ta ahalin su, yadda ake gudanar da masifaffan kishi tsakanin matan gidan, su ba kishiyoyi amma har sun fi kishiyoyi kishi.
Bongel da Ramla suna zaune kan tabarma dake shimfid'e a d'akin, Nene na zaune kan katifa ta jingina da bango, Abu yayi matashi da cinyoyin ta, kowannensu yayi shiru yana sak'ar zuciya, yayin da d'imbin kewar Bappa ta zagaye zukatan su, a irin wannan lokacin sukan zauna suna hira, cike da nishad'i.
Nene ta dubi Bongel tace "Gobe ya kamata ki koma makaranta", "Gobe Nene ko sadakar bakwai fah ba'a yi ba", "Jiran me zaki tsaya Bongel, kina matakin k'arshe na kammalawa, kada kiyi wasa da karatun ki, Bappa bai bar wasiyyar komai ba sai na karatun ki, yana da burin kiyi ilimi mai zurfi, Dan Allah ki cika masa burin sa", A raunane ta d'aga kai tare da cewa "In Shaa Allah zanyi k'ok'arin cikawa Bappa burin sa, haka zaku yi alfahari dani", "Allah ya yarda" Cewar Nene, Dukkansu suka amsa da "Amin"
Washegari Hamma Bala ya mayar da ita makaranta, ta koma da k'udurin k'ara zage dantse wurin ganin ta cika burin Bappa, da son ganin ta taimaki mahaifiyarta da k'annen ta, Asiya tayi murna sosai ganin Bongel ta dawo, itace aminiyarta rashin ta kwana biyu yasa tayi kewarta sosai, Ta mata gaisuwar Bappa, kuma tace ana yin hutu ita da yan' gidansu zasu je yi ma Nene gaisuwa.
"Mahaifin yarinya ya rasu ko bakwai ba'a yi an tura ta bokon iskanci" Fatsuma ke yada habaici a tsakar gida, Dije ta kama mata da fad'in "Taya ni gani, dama wanda ya mutu ai shi ya mutu, tun kan ayi sati iyalinsa ma sun soma manta shi", Nene bata tanka su ba, idan da sabo ta saba da halayyar su, sam bata biye musu, ba'a tab'a jin ta da kowa ba, sai dai suyi tsakanin su, a zahiri zaka ce soyayya da zaman amana ne a tsakanin Dije da Fatsuma, amma a bad'ini kishi, kyashi da hassadar juna suke.
Ku biyoni cikin littafin BONGEL, wanda zai k'ayatar daku, ya nishad'antar daku IN SHAA ALLAH
LABARI MAI D'AUKE DA
K'IYAYYA
SOYAYYA
RUD'ANI
TAUSAYI
NADAMA
*OUM MUHRIZ*
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO..*
SHAFI NA BIYU
ASALINSU
Aliyu Ard'o shine mahaifinsu Bongel, asalinsa d'an garin katsina ne k'aramar hukumar malumfashi, bafullatani ne gaba da bayansa, Mahaifiyarsa Hafsa shi kad'ai ta haifa, Allah ya mata rasuwa, bayan ta rasu ya sake aure, ya auri Hanne ta haifa masa yara biyu maza Bala da Siddiku, Hanne bata k'aunar Aliyu duba da yadda mahaifinsu ke son shi, yake tausayin sa saboda rashin uwa, haka suma su siddiku suka tashi da k'iyayyar sa, duk da Bala na dan’ b'oye tasa k’iyayyar, Mahaifinsu ba mai k'arfi bane, manomi ne, da suka isa aure, ya musu k'aramin gini na k'asa, kowannen su yace ya fitar da mata, Aliyu ya fara samun mata,Nene zuwa tallar nono daga rigarsu, suka k'ulla soyayya, bayan shekara d'aya Bala da Sidddiku sukayi aure suma, Bala ya auri fatsuma, Siddiku ya auri Dije, matansu haka suma suka d'arsawa ransu tsananin kishin Nene, duk da irin mugun hali da suke nuna mata, bata bi ta kansu, Bongel ce yar'su ta farko wacce taci sunan kakarta Hafsa, Bappa ya saka mata Bongel saboda kyawunta, kaf yaran gidan babu wanda ya kaita kyau, fari da gashi, Bala nada yara hud’u Hamza, Lawal, Sa’ade, Habiba, Hamma Siddiku nada uku Hassan da Husaini, Saudat, Duka yaran gidan babu wanda ya samu ilimin boko sai Bongel, Bappa nada burin ganin yaran sa sun samu ilimi, sai dai rashi da talauci yasa Bongel kad’ai ya samu sakawa, Siddiku da Bala basu damu a saka yaransu ba a cewar su a boko yaro ke lalacewa, ba irin k’ananun maganganun da basuyi ba kan saka ta makaranta, Bappa ya toshe kunnen sa.
***************
Bongel sun soma zana jarabawar WAEC wacce sam bata wasa da karatu, duk jarabawar data shiga bata jimawa take fitowa saboda sauk'in da take mata, yau ma maths sukayi kusan kowa ka kalla cizon biro yake saboda wahalar da jarabawar tayi, wasu na raba ido ko zasu samu satar amsa, sab'anin Bongel da kanta ke duk'e kan takardarta tana faman calculation, lokaci kad'an ya d'auketa ta kammala ta fito,
Zama tayi bakin hall d'in tana jiran fitowar Asiya, istigafari ta soma kar tayi zaman banza, kusan awa d'aya da zamanta kafin Asiya ta fito, "Bongel nikam wacce irin baiwa ce Allah ya baki, yadda jarabawar nan tayi wahala amma kika kammala da wuri", Murmushi tayi tace "Allah dai ya bamu sa'a", Asiya ta amsa "Amin", Bongel ta mik'e suka tafi hostel.
A kullum safiya da tunanin Bappa, Bongel take tashi haka dashi take bacci, bakinta baya gajiya da rok'ar masa rahamar ubangiji.
Sati shida suka d'auka suka kammala jarabawa, a cikin sati shidan suka zana jamb, wanda Bongel tafi kowa samun sakamako mai kyau a cikin d'aliban makarantar, d'ari uku da sha biyar ta samu, Tayi murna sosai haka duk wani masoyinta ya taya ta murna,
Ranar da suka kammala jarabawa aka sallami kowa gidan iyayen sa, sai sakamako ya fito su dawo su karb'a, kowa ka gani fuska d'auke da farin ciki, ana ta faman rubuce rubuce a rigunan juna, da karb'ar numbobi, sab'anin Bongel data koma gefe tana zaune kan akwatin ta, wannan shine karon farko da bata zumud'in zuwa gida, lokutan baya tun ana saura sati d'aya hutu take soma had'a kayanta tsabar zumud'i, ba wanda tafi muradin gani kamar Bappa dan tarba ta musamman take samu daga gare sa, a ranar raba dare suke suna hira gaba d'ayan su, tana basu labarin makaranta da abubuwan da suka faru,
Ta jima zaune tana jiran zuwan Hamma Bala shiru, har kowa ya fara watsewa, tun fara makarantar bata tab'a kai lokaci kamar haka ba'a zo d'aukarta ba, addu'a ta soma Allah yasa lafiya,
Har kowa ya watse ya barta ita kad'ai, Jikinta ya k'ara yin sanyi tana ji a ranta ba lafiya ba, ta yanke shawarar samun machine ya kaita gida, ba tare da b'ata lokaci ba ta samu machine, ya fad'i kud'in da zata basa, Tace "Idan mun isa gida zan shiga ciki na karb'o maka", Harara ya watsa mata yace "Kinga idan baki da kud'in na tafi abuna", "Wallahi muna zuwa zan shiga na d'auko na baka", "Na sha d'aukar irinku kuna guduwa, dan haka ki nemi wani" Yaja babur d'insa ba tare da ya jira cewar ta ba, Tabi bayansa da kallo cike da takaici,
Kusan machine uku tana tara suna k'in yarda, da k'yar ta samu wani tsoho ya d'auketa, Yana ajiyeta bakin gidansu, bai tsaya karb'ar kud'in ba, yace ta tafi kyauta ya kawota, ta masa godiya sosai, Daidai k'ofar shiga taci karo da Ramlat na fitowa, "Adda kin dawo, yanzu Nene tace naje gidan Goggo Hajjo nace Dan Allah taje ta d'auko ki", "Ina Hamma Bala ne?" Bongel ta tambaya da mamaki, Ramla tace "Yace ba zai je ba", Bongel ta jinjina kai cike da mamaki, ba tace komai ba, suka k'arasa cikin gidan,
Kallo d'aya tayiwa mahaifiyarta tasan ba lafiya ba, Jiki a sanyaye ta zauna kusa da Nene ta gaisheta, Bata amsa gaisuwar ba tace "Bongel ya akayi kika dawo gida, ko wani ya dawo dake?", "Ni na dawo da kaina", "Dama zaki gane hanya", "Haba Nene shekaru shida ina bin hanyar", Nene ta jinjina kai tace "Ga abincinki can a kwano sai dai kiyi hak'uri da tarbar da kika samu wannan karon", Bongel tayi murmushi tace "Kowacce irin tarba ce indai daga wurinki ne Nene haka nake ji tamkar daga Bappa ne", Nene tayi murmushin farin cikin ganin Bongel ta karb'i komai da sauk'i.
Wanka ta fara yi, ta canza kaya zuwa atamfa doguwar riga, ta d'auki kwanon abinci ta soma ci, Tace. "Nene nikam meya hana Hamma Bala zuwa d'aukata makaranta yau", Nene ta sauke nauyayyen ajiyar zuciya tace "Dan' adam mai wuyar gane hali, haka gane masoyin gaske sai Allah, Bala ya bani mamakin da ban tab'a zata ba", "Me yayi Nene?" Bongel ta tambaya cike da k'aguwa, "Yau tun safe
yazo ya sameni kan cewa ba zai iya zuwa d'aukar ki ba, ya gaji ni naje, Nace masa ina takaba, kuma idan yayi hak'uri wannan shine k'arshe tunda kin kammala, bud'ar bakinsa yace ba wata takaba da nake, ai ban damu da mutuwar tasa ba, tunda na tura ki makaranta tun kan ayi bakwai, idan zanje da kaina naje, idan ba zanje ba nasan tayi, dan shi babu inda za shi, a zatona ko kowa bai fahimceni, Bala zai fahimce ni" Nene ta k'arasa da hawaye, Bongel mamaki ne ya cikata bata tsammaci haka daga Hamma Bala ba, duba da
shine mai sauk’i a gidan, yana d’an nuna kulawar sa kan su,
"Nene ki daina zubar da hawayenki akan mutanen da basu san girma da muhimmancin zumunci ba, In Shaa Allah ni zan share muku hawayen ku", Nene ta share hawayenta da fad'in "Allah ya yarda", "Amin" Bongel da Ramla suka amsa,
Bongel ta juya ta kalli Abu tace "Shi ya kamata ya samu ilimin boko kasancewar sa namiji amma bai samu haka ba, In Shaa Allahu zanyi iya k'ok'arina wurin ganin ka samu ilimi mai zurfi Abu", Ta juya kan Ramla "Na kan ji bak'in ciki na rashin ilimi boko da baki samu ba, amma idan na tuna kin samu na arabiyya sai naji sanyi, Allah ya jik'an Bappa", Suka amsa da "Amin",
Bongel tayi shiru tana tunanin yadda zata taimaki mahaifiyarta da k'annen ta, ta gama sawa ranta ta hanyar yin ilimi mai zurfi, ta samu aiki kad'ai zata taimaka musu.
Asiya da iyayenta sunzo musu gaisuwa, iyayen Asiya nada rufin asiri babu laifi, mahaifinta driver'n VC ne na jami'ar umaru musa, Dubu biyar yaba Nene da zasu tafi, kyautar ba k'aramin dad'i ta musu ba, sun tashi yau yan' sauran kayan abinci dda Bappa ya bar musu ya k'are, Nene naira hamsin kad'ai ce da ita, tana tunanin inda zata samu musu abunda zasu saka a baki.
Bongel taba kud'in ta siyo musu kayan abinci na maneji, yadda rayuwa tayi tsada, dubu biyar ba komai ba ce, Bongel ta soma zuwa gidajen masu kud'in garin tana musu wanki, su biyata, da kud'in suke cin abinci, Suna gani Hamma Bala da Hamma Siddiku ke shigowa da cefane na matansu, amma ko da wasa basu tab'a kawo musu ba, abun ba k'aramin ciwo yake wa Bongel ba, Duk da kasancewar su yan' uba, amma lalacewar zumuncin bai kai haka ba, Ramla ta soma awarar siyarwa akan layin unguwarsu take d'aura kasko, da haka suke rufawa juna asiri, Bongel na zaman jiran sakamakon jarabawar su ya fito.
Bayan wata d'aya da kammala makarantar su sakamakon su na WAEC ya fito, Bongel ranar tayi juyi na murna, tayi ta godiya ga ubangiji, A da B ne kawai,
"Yanzu tunda sakamako yayi kyau sai shirin zuwa jami'a", Nene ta fad'a cike da farin ciki, Bongel tace "Eh Nene, zan fara karatu, na cikawa Bappa burin shi, kuma dashi zan taimake ku", "Allah yasa miki albarka a ciki", "Amin", Ta amsa,
Mak'wabtansu ta shiga, ta ari waya ta kira Asiya, bugu d'aya ta d'auka, bayan sun gaisa ta sanar da ita sakamakon jarabawar ta, itama take gaya mata taci, Sukayi wa juna murna, Asiya tace "Ba cin jarabawar ba, samun admission shi ke da wuya, yanzu sai kana da hanya, idan ba Allah ya taimake ka ba", Bongel jikinta yayi sanyi sam ta manta da hakan, ta nisa tace "Hakane Asiya, Allah ya shige mana gaba, yasa mu samu cikin sauk'i", "Amin, naji ance Neco itama wani sati za'a saketa, nan da wata biyu za'a fara rabon admission", "Allah yasa muna da rabon shiga jami'a" Bongel ta fad'a a sanyaye", "Amin Amin", Sukayi sallama ta kashe wayar, ta ba matar gidan wayarta, ta mata godiya ta fito.
Ramla ce ta fad'o cikin d'akin kamar an jefota, tana yi tana waiga baya, "Lafiya? Me ya faru?" Nene da Bongel suka tambaya a tare, Jikin Nene ta fad'a ta fashe da kuka, "Dan Allah ki fad'a mana meke faruwa kukan ki na d'aga mana hankali", Bongel ta fad'a tamkar itama zatayi kukan,
Cikin shesshek'ar kuka tace "Wani ne ya biyoni sai ya kasheni", "Subhanallah kisa me kika masa?", Nene ta tambaya a razane, "Zuwa tab'ani yayi wai na yarda dashi, na huta da siyar da awara kan layi, yasan talauci ne yasa haka, zai bani kud'i masu yawa, naja baya ina cewa ya k'yaleni ya k'ara matso ni, shi...nee na mare sa, ya biyoni yana cewa sai ya kasheni", Bongel idonta ta runtse tana ji rad'ad'i a zuciyarta, banda rashi babu abunda zai sa Ramla soyar awara har wani da' namiji yaso jan ra'ayinta da kud'i, ya zama dole ta nemi ilimi, dan kub'utar da k'annenta.
Nene tace "Kinyi kuskure na mare sa, baki san waye shi ba, baki san me zai iya aikatawa", Bongel cikin zafin rai tace "Bai isa ya mata komai ba sai abunda Allah ya k'addara, meyasa ake d'aukar talaka ba bakin komai ba, meyasa rayuwar talaka kullum take cikin gagari", "Duniyar ce haka, shugwabanni ne mune basu da adalchi, ina rok'on ku da Allah kada ku tab'a siyar da mutuncin ku saboda wani abun duniya, k'ima da darajar mace ta kai budurcin ta gidan mijinta, dukiyar da aka tarata ta hanyar zina k'azamtacciya ce kuma bata da Allah, nasan irin tarbiyar da muka baku amma ina rok'on ku da Allah ku k'ara tsare kanku, ku rik'e maraicin ku, kada ku barwa mahaifinku abun fad'e, matuk'ar kuka yi haka baku masa adalchi ba, a kullum tunanin sa da burinsa ya inganta rayuwarku, kuyi k'ok'arin zama abun koyi da alfahari", Nene ta k'arasa tana duban su, "In Shaa Allah" Suka amsa a tare, "Tashi kije kiyi wanka, kiyi alwala kiyi sallah da karatun qur'ani, zaki samu natsuwa", Nene ta fad'a, Ramla tace "Toh" ta tashi.
OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
SHAFI NA UKU
Tun daga ranar Ramla ta daina yin awara, ta koma aiki a wani gida, tana jeka ka dawo, a wata ana bata dubu uku, Bongel sakamakon su na neco ya fito, tayi k'ok'ari sosai, admission ya fara fitowa har list na farko ya fito, list na biyu suke jira, Bongel kullum cikin fargaba da zullumi take, a rana sai ta kira Asiya sau uku dan jin ko akwai wani bayani,
Suna tsakar gida suna wanki ita da Ramla, yaron mak'wabtansu ya shigo, Yace "Wai Bongel tazo inji maman mu", Gabanta taji ya fad'i tasan kiran na Asiya ne, hannunta ta tsame daga ruwan kumfan, ta wanke, taja mayafinta dake kan igiyar dake shanye tsakar gidan tabi bayansa, Fatsuma ta yatsina baki tace "Ayi dai mu gani idan tusa na hura wuta"
Bongel bata bi ta kan maganarta ba ta fice gidan,
"K'awarki ce tayo waya tana son magana dake", Cewar Maman Jabeer tana mik'a mata waya, Tana karb'a kiran Asiya na sake shigowa, Ta d'auka,
"Lafiya dai ko?", Cewar Bongel, Asiya tace "Lafiya ba lafiya ba toh zance, Baba ke sanar dani wannan karon admission yana matuk'ar wahala sai kana da hanya, amma yace mu had'o takardun mu ya rok'i VC ya taimaka", "Amma nagode sosai Asiya, kiyi wa Baba godiya, In Shaa Allahu gobe zan zo da kaina na kawo", "A'ah ba sai kinzo ba, ki aiko ta mota kawai", "Toh shikenan nagode",
Da murna ta koma gida tana sanar da Nene da Ramla, "Kai yarinyar nan da iyayenta mutanen kirki ne, Allah ya saka musu da aljanna" Nene ta fad'a, "Amin Amin".
Sati biyu da tura takardun ta, suna zaune tsakar gida suna hira, suka jiyo sallamar Asiya, Bongel ta mik'e da fad'in "Asiya zuwa ba sanarwa", Asiya tayi murmushi tace "Tare muke da Baba", "Kice zuwan ba naki bane ke kad'ai", Nene tace "Ki masa iso ya shigo" Ta shiga d'aki ta d'auko hijabin ta,
Bayan an gama gaisawa sun sha ruwa, Baba ya numfasa yace "Da farko dai ina fara baku hak'uri, kuyi hak'uri Dan Allah komai kuka gani muk'addari ne daga ubangiji, kamar yadda Asiya ta sanar da Bongel ta tura takardunta, ni na buk'aci haka da niyyar taimaka musu su samu admission tare, amma sai dai hakan bai yiyu ba, d'aya ta samu d'aya bata samu ba" Bongel k'irjinta ne ya duka, jikinta yayi sanyi ta gama sarewa, Baba ya cigaba da cewa "Wallahi ba da son raina haka ta kasance ba, Asiya suka ba admission, itama VC cewa yayi dan tana yar' cikina shine zai taimaka, kuma ko da yara biyu ne nawa d'aya zai d'auka, nayi k'ok'arin aba Bongel admission d'in, Asiya ta hak'ura dan tana gaya mun burin Bongel na son karatu, wallahi sam yak'i yarda da cewa admission ya riga ya fito da sunan Asiya, kiyi hak'uri Bongel wallahi bani da wata hanya, k'asar tamu ce sai dai muce Allah ya sawwak'a"
Tuni hawaye suka wanke fuskar Bongel, ta kasa cewa komai, Nene duk da yadda zuciyarta ke soya tayi k'arfin halin cewa "Haka Allah ya k'addara, mun gode sosai da k'ok'ari baban Asiya Allah ya bar zumunci", "Amin" Ya amsa, Ramla ma jikinta yayi sanyi matuk'a, gaba d'aya hope d'insu akan Bongel yake, yanzu komai ya yanke, Baban Asiya ya jima yana basu baki kafin suka tafi, Asiya ma rai babu dad'i ta tafi.
"Wannan k'asa tamu Allah ya kawo mana sauk'i, na kasa cika burin Bappa na son ganin Bongel tayi ilimi mai zurfi, kayi hak'uri Bappa bani da wata hanya, talaka bashi da galihu a k'asar nan" Ta k'arasa da hawaye, "Ki daina d'aurawa kanki laifi Nene, haka Allah ya k'addaru bazan yi ilimi mai zurfi ba, watak'ila haka zamu k'are rayuwar mu duk da bawa baya yanke rai ga rahamar ubangiji", Abu duk da kasancewarsa yaro ya nuna rashin jin dad'in sa, "Yanzu shikenan nima bazan shiga makaranta ba"
Ya fad'a a sanyaye, Bongel ta jawosa jikinta "Idan da rabo zaka yi ilimin boko Abu", "Allah yasa", Tace "Amin" cike da tausayin sa.
Bongel ta koma sukuku, walwalarta ta rage, rashin samun admission ba k'aramin tab'a ta yayi ba, gashi kullum rayuwa k'ara wuya take musu, babu mai taimaka musu, dangin Nene ba masu k'arfi bane, suma suna fama da kansu, iyayenta ma suna rugar ard'o can wurin funtua.
Asiya wurin printing takardar admission d'inta taji wasu yan' mata na hira, "Wallahi kin taimakeni da kika kaini wurin Hisham, gashi na samu admission cikin sauk'i" Cewar d'aya daga cikin yan' matan, "Ai Hisham sai idan baka je wurin sa ba, admission kamar ka samu amma fah..." Bata k'arasa ba sukayi dariya da shewa, Jin haka Asiya ta k'arasa wurinsu, ta musu sallama suka amsa, "Dan Allah kuyi hak'uri na saurari hirar ku, wata yar'uwata zaku taimakawa itama ta samu admission", Suka kalli juna, D'ayar tace "Ba damuwa bane", "A ina zamu samesa Dan Allah", K'aramin kati ta fito dashi daga jaka ta mik'a mata, Ta karb'a tana mata godiya,
Ta kasa bari ta koma gida, nan take ta soma kiran wayar Maman Jabeer, anci sa'a Bongel ta shigo itama ta kira Asiya kwana biyu basu yi waya ba, "Kinga yar' halak na kira" Cewar Maman Jabeer, Bongel tace "Aikuwa" tana karb'ar waya,
"Albishirin zan miki, na samu wata hanya da zaki samu admission" Cewar Asiya da k'arfi kamar zata fasa mata dodon kunne,"Da gaske?", "Wallahi da gaske nake, idan zaki iya ki shigowa katsina gobe", "Ko a yau kike so zan shigo", "Toh sai kinzo", Ta kashe wayar cike da farin ciki,
Nene farin cikin daya bayyana kan fuskarta ba k'arami bane, haka Ramla da Abu, tun a daren Bongel ta had'a kayanta kala uku da abunda zata buk'ata cikin jaka, Tunda safe ko kari batayi ba, ta shirya tafiya, Nene tabi ta addu'o'i na nasara da kariya, wurin maman jabeer ta ari dubu biyu da zatayi kud'in mota, Fatsuma da Dije nata yada habaici bata ce musu komai ba suna fad'in haka za'a je a dawo.
Tafiyar awa d'aya da rabi ya d'auke su, suka isa garin katsina, suna isa tasha, ta ari waya ta kira Asiya, ta mata kwatancen unguwar su, mai napep ta samu ta fad'a masa unguwar, ya kaita har k'ofar gidansu Asiya, ta sallame sa ya tafi, gida ne k'arami sosai, kana gani kasan suma basu da hali, d'akuna biyu ne sai band'aki a tsakar gida, da k'aramin kicin, Cike da far'a mutanen gidan suka tarbeta, Asiya ta sauketa d'akinsu ita da k'annenta mata uku, haka suke gwamatsawa,
Asiya ta sanar da ita komai, ta fiddo katin ta nuna mata, hakanan Bongel ta tsinci kanta da fad'uwar gaba, "Amma Asiya kina ganin babu matsala", "Wacce matsala Bongel, zuwa zamuyi mu rok'esa mu fad'a masa buk'atar mu In Shaa Allah zai taimaka ki samu admission", "Toh shikenan yaushe zamu je?", "Yanzu ba zamu tsaya b'ata lokaci ba", Bongel tace "Toh" tana mik'ewa, ta d'auki k'aramar jakarta da takardun ta ke ciki, fuskarta kad'ai ta wanke da ruwa, saboda zufar da tayi, kasancewar lokaci ne na zafi,
"Daga zuwa ba hutawa sai fita" Cewar Mama dake tsakar gida tana yankan alayyahu, Asiya tace "Mama da zafi zafi ake dukan ice", Mama tayi dariya tace "Allah ya bada sa'a", Suka amsa "Amin",
H&H GLOBAL RESOURCES
Shine sunan da suka gani manne a tafkeken ginin dake gabansu, wanda jikinsa duka glass ne yana walk'iya, Bongel ta kalli Asiya tace "Anya bamu kawo kanmu inda yafi k'arfin mu ba", Asiya duk da tasha jinin jikinta ganin girman ginin, ta dake tace "Ki cire tsoro Bongel bakya son shiga jami'a ki cika burin Bappa", Bongel tayi saurin gyad'a kai, Tare suka jera zuwa building d'in, Bongel na ambaton Allah a ranta,
Securities dake tsaye bakin wurin sukayi checking d'insu, suka k'arasa, suna zuwa wurin shiga k'ofa ta bud'e, Karon farko a rayuwarsu da suka ga k'ofa na bud'ewa da kanta, a tare suka zaro ido, Suna shiga sanyin Ac mai rab'a ya soma dukan fatar jikin su, kalle kalle suka tsaya yi, basu san ina zasu yi ba, suna tunanin wacce duniya ce suka kawo kansu, tsabar had'uwar wurin sai suke jin tamkar ba'a k'asar suke ba,
Wata mata ta nufo su da fad'in "May i help you", Cikin daburcewa Asiya tace "Wurin Hisham muka zo", "This way floor 2" Ta nuna musu hanya,
Elevator ne a wurin sukayi tsaye suna faman k'wankwasawa a zaton su nan ne office d'in sa, K'ofar suka ga ta bud'e, budurwa mai ji da kyau da gayu kanta yasha attach ta baza su shi har baya, da fixed nails, zaka rantse ba musulma bace, ta fito banzan kallo ta watsa musu ta wuce, Asiya taja tsaki , Bongel tace "Mu muka kawo kanmu",
Wani babban mutum ne yazo shiga, suka gaishe sa har k'asa ya amsa, a ransa ya yaba da natsuwar su, Yace "Wa kuke nema?", Asiya tace "Hisham", "Muje" Ya fad'a, Suka bi bayansa,
Mamaki ya kama su ganin inda suka shiga, suka ga ya danna abu wurin wasu numbers, sama suka ji ana yi dasu suka had'iye yawun tsoro tare da k'ank'ame juna, dariya suka so su bashi yadda yaga sun tsorata,
Suna ganin k'ofar ta bud'e, suka fito a guje, "Can zaku je nan ne office d'in" Mutumin ya fad'a yana nuna musu wata k'ofa, Mun gode Baba", Asiya ta fad'a,
"Meye muka shiga yanzu mai kamar jirgi" Cewar Bongel, Asiya tace "Nima ban sani ba, ban tab'a ganinsa ko jin labari ba", "Allah yasa mu koma gida lafiya idan ba mun kawo kanmu inda za'a yanka mu ba", Asiya tayi dariya tace "Har kin bani dariya, duniyar ce da fad'i, Allah ne bai tab'a kawo mu ba, wuri ne na masu naira", Bongel bata ce komai ba, har suka kai bak'in k'ofar, Knocking sukayi, Suka ji wata murya tace "Yes", A hankali Asiya ta murd'a k'ofar suka shiga, wata mace suka tarar zaune tana rubuce rubuce a takarda, Ta kallesu tace "Ku k'arasa ciki",
Asiya na gaba Bongel na bin ta a baya, kusan mutuwar tsaye sukayi ganin had'uwar office d'in, hankalinsu bai k'ara tashi ba, sai da suka ga wanda ke zaune kan kujerar dake nuna shine mallakin office d'in, had'uwar sa da kyansa yasa suka k'ara shan jinin jikinsu,
"Ku k'araso mana" Suka tsinci muryar sa, wanda basu tsammaci jin haka ba, A sanyaye suka k'arasa, ya nuna musu kujera su zauna, k'amshin turaren sa mai dad'i ke ziyartar k'ofofin hancin su, idonsa k'yam akan Bongel, duk ta tsargu da irin kallon da yake mata,
Asiya tayi k'arfin halin cewa "Dan Allah taimaka mana muka zo kayi", "Wane irin taimako kenan?", Ta nuna Bongel, "Ita ke neman admission, wallahi munyi iya k'ok'arin mu ta kasa samu shine aka ce muzo wurin ka", Murmushin gefen baki yayi yace "Admission kamar ta samu ta gama but akwai sharad'i", Bongel tayi saurin cewa "Ko wane sharad'i ne zan bi", "Ki dawo gobe ke kad'ai, ga numberta i will let u know inda zamu had'u" Ya k'arasa yana ajiye mata k'aramin katin sa, tasa hannu ta d'auka tana masa godiya, Suka mik'e zasu fita har sun kai k'ofa ya kira Bongel, ta dawo, bandir na 500 ya mik'a mata, Tayi saurin cewa "A'ah mun gode", a tsawon rayuwarta bata tab'a ganin kud'i masu yawan su ba,
"Bana kyauta a mayar mun" Ya fad'a cikin dakewa, Kwarjini taji ya mata ta kasa k'ara musa masa, Hannu biyu tasa ta karb'a da fad'in "Allah ya saka da alkhairi", "Amin" Ya amsa, Ta juya zuwa k'ofar fita, yabi bayanta da kallo, yayi juyi kan kujerar sa yana murmushi.
Har suka isa gida suna jinjina kyautar kud'in da ya musu, suna zuwa suka nunawa Baba, ya musu fad'an karb'a da sukayi, yace kada su k'ara daga yau, suka ce toh, Bongel baccin farin ciki tayi na jin zata samu admission, tana alla-alla safiya tayi sai wani b'angare na zuciyarta na saka mata tunanin meyasa zai ce tazo ita kad'ai.
OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
SHAFI NA BIYAR
Safiyar yau Bongel sukuku ta tashi, duk da tana k'ok'arin b'oye damuwar ta, Asiya taso ta fahimta sai dai bata tambayeta ba, sanin mutum ce mai zurfin ciki, idan ba ita tayi niyyar fad'a maka abunda ke damunta ba, tambayar duniya amsar d'aya ce babu komai,
Ita ta taya Asiya suka gyara gidan suka dama kunu wanda dashi kusan kullum su Asiya ke karin safe, Bongel kad'an ta sha tace ta k'oshi, bata jin sawa cikinta komai,
"Ina tunanin yau zan koma", "Kai haba ba zaki bari ki mana kwana biyu ba", "Ina so na koma na sake shirin dawowa makaranta, naga saura sati d'aya a fara registration, kuma banda abun ki ni da zan dawo garin ku", "Hakane, bama garin mu kad'ai ba gidan mu, dan anan zaki zauna, jiya Baba yace na fad'a miki", Murmushi tayi tana jin dad'in yadda Asiya da iyayenta ke nuna k'auna gareta.
12 na rana ta shirya wucewa, a tsakar gida ta samu Baba da Mama, Bongel har kin shirya wucewa" Baba ya fad'a, Tace "Eh Baba", "Toh ga kud'in da mutumin nan ya baku, kunfi mu buk'atar su, ki kaiwa mahaifiyar ki kwa rage wani abu", Saurin girgiza kai tayi tace "A'ah Baba", "Ki karb'a Bongel, reg na makaranta kina buk'atar kud'i, naira ba zamu tab'a cikin kud'in nan ba wallahi" Ya k'arasa yana mik'awa Asiya "Karb'a ki sa mata a jaka", Asiya ta karb'a ta bud'e jakarta ta jefa, Godiya ta musu sosai, ta tafi da tunanin karamci irin nasu, Asiya da K'anwarta Aina'u suka rakata har tasha, sai da suka tabbatar ta shiga mota, suka taho gida.
***************
Tsaye yake bakin balcony na office d'in sa, hannun sa rik'e da k'aramin mug yana sipping hot tea, ta glass na wurin yake hango motocin dake wucewa ta titi, Kallo d'aya zaka masa kasan akwai abunda ke damun sa, Komawa yayi cikin office d'in, ya zauna kan kujerar sa, ya jawo drawer dake manne da teburin dake gabansa, wani file ya d'auko yana dube dube a ciki,
Hisham cikin sanyin jiki ya tura k'ofar office d'in ya shigo da sallama, Haidar yaji sallamar yayi tamkar bai ji ba, har ya k'araso ya zauna kan kujera tare da fad'in "Yaya Haidar sannu da aiki", takardun ya cigaba da dubawa ba tare da yabi ta kansa ba, Jikin Hisham ya k'ara yin sanyi, bai tab'a masa irin haka ba,
"Yaya Dan Allah kayi hak'uri", Still bai tanka sa ba, "Yaya kada kayi fushi dani", A fusace ya d'ago yace "Tashi ka fita Hisham, is your life ka cigaba da duk abunda kaga dama", "Yay...", Yayi saurin katse sa "I said out", Hisham ya mik'e yana jin duniyar ta masa zafi, So shak'uwa da k'auna ce mai k'arfi tsakanin su, tun tashin sa bashi da abokin shawara kamar Haidar, duk wata matsalar sa shi yake kawowa, basa k'aunar b'acin ran junan su, fushin Haidar a gare sa yasa komai ya jagule masa.
"Ya zama dole na nuna masa fushina wannan karon, ko hakan zai sa ya shiryu, ya gyara halayyar sa" Haidar ya fad'a yana cigaba da duba takardun,
Ya d'auki lokaci yana dube dube kusan kowacce drawer a office d'in sai da ya duba, kansa ya dafe ya furta "Ya Allah" ganin bai samu abunda yake so ba, "Ya zama dole naga Abba", Mik'ewa yayi ya fita office d'in nasa, elevator ya shiga zuwa floor 3,
Wata aljannar duniya kenan ba k'aramin tsaruwa da had'uwa floor d'in yayi ba, Kai tsaye office d'in Abba ya shiga ba tare da ya jira an masa iso ba, Yaci sa'ar samun Abba shi kad'ai yana karatun newspaper,
Ya gaishe sa cikin ladabi, Ya amsa da sakin fuska, Bayan ya zauna, Abba ya ajiye newspaper dake hannun sa yace "Tunda na ganka a irin wannan lokacin nasan akwai dalilin zuwan", Kansa ya gyad'a sama yace "Eh ina da magana Abba", "Ina jin ka" Abba ya fad'a yana tattaro hankalinsa kan Haidar,
"Abba ina tunanin lokaci yayi da ya kamata mu cirewa Maigoro share d'insu ya zama business d'inmu babu share na kowa a ciki", Haidar ya fad'a, a ransa yana addu'ar samun goyon baya daga mahaifinsa, Abba ya gyara zaman sa yace "A ko da yaushe tunanin mu yakan zo d'aya da kai, na dad'e ina wannan tunanin sai dai bansan ta yadda zan b'ullowar al'amarin ba", Yaji dad'in jin haka sai dai zancen Abba na k'arshe ya sa shi fargaba,
Abba ya cigaba da cewa "Before muyi hakan dole sai munyi tunanin wata hanya na bunk'asa kasuwancin mu ta yadda raba business d'inmu dasu ba zai tab'a mana kasuwanci ba, duk da cewa munfi so k'arfi a ciki, mu muka fara kafa business d'in, ya zama dole mu k'ara ilimin yadda zamuyi running business d'in mu individual", Haidar ya numfasa yace "Wane irin ilimi Abba, ina da PHD akan business admin, degree da masters on economics,
Abba yace "You still have to learn more", "How?" Ya tambaya, "You have to be a lecturer in economics department", "Lecturer" Haidar ya fad'a a razane, "Yes" Abba ya fad'a yana d'aga masa kai, "Amma Abba taya zan zama lecturer, ba zan iya lecturing ba", "Haka zaka daure, ta hanyar lecturing zaka k'ara samun ilimi kan kasuwanci, lecturer dole zai rik'a research kullum da zurfafa tunani, ta lecturing zaka k'ara samun experience", Shiru yayi yana nazarin yadda zai zama lecturer, gaba d'aya yana jin hakan ba ajin sa bane, gashi sam baya son hayaniya, "Kayi hak'uri ka bi abunda nace, ta haka zamu cimma burin mu In Shaa Allah, idan kayi hak'uri na dan' lokaci ne zaka yi", Abba ya fad'a yana assuring nasa, "Allah ya shige mana gaba" Ya furta yana jin sarewa a tare dashi, Abba ya amsa da "Amin".
************************
Har k'ofar gidansu driver ya kawota, tare da wata tsohuwa ya kawo su unguwar, tun daga can aka biya ya kawo tsohuwar har gida, ita ya fara ajiyewa kana ya kawo Bongel,
Tana fitowa cikin motar sukayi ido hud'u da Hamma Siddiku mugun kallo ya jefa mata ya wuce cikin gida, jikinta yayi sanyi, tayi wa mutumin godiya yaja motar sa ya tafi, Ta d'auki k'aramar jakarta zuwa cikin gida, tun daga k'ofar gida take jiyo muryar Hamma Siddiku yana zuba ruwan bala'i,
Tsaye yake kan Nene yana sauke mata bala'i, "Iskancin yarinyar taki har ya kai k'ato ya ajiye ta da mota bakin gidan nan, dama nasan ba wata makaranta data tafi nema katsina, yawon karuwanci kawai kika tura ta, toh ba zai yiyu ba, ba'a k'ofar gidan nan ba, taje can tayi yawon karuwancin ta", Nene har cikin ranta take jin zafin kalmar karuwanci da yake jifan yar'ta dashi, hak'uri irin nata yasa ta kasa ce masa uffan, sai d'aki da ta shige abunta, Ramla suka rufa mata baya, "Au shigewa kika yi baki da lokacina ko, toh wallahi bara na shaida miki duk ranar da tayo abun kunya sai kun bar gidan nan ku dukan ku",
Bongel bata san sanda zuciya ta d'ibeta tace "In Shaa Allah ba zanyi abun kun..." Bata k'arasa ba ya kife ta da mari, kafin ta d'ago ya k'ara mata, Da gudu Abu da Ramla suka fito daga d'akin suna kama Yayar su, Hamma Sidddiku ya cigaba da zage zage, Bongel duk da zafin marin da yadda zuciyarta ke k'unar b'acin rai, ta dake bata bar d'igon hawaye ya zuba kan fuskarta ba, bata son ganin damuwa kan fuskar mahaifiyarta da k'annen ta,
Tana shiga d'akin tayi saurin fiddo jamb admission letter d'inta ta mik'awa Nene da fad'in "Na samu admission" Tayi hakane dan kawar musu da b'acin ran da Hamma Siddiku ya saka su, Nene a take murmushi ya sub'uce mata tace "Alhamdulillah Alhamdulillah Allah abun godiya bazan iya misalta farin cikin da nake ciki ba" Abu ya tashi yana ta tsalle, Ramla ma bakinta ya kasa rufowa,
Ta fiddo kud'i cikin jaka ta ajiye kan cinyar Nene, "Ina kika samu wannan kud'i masu yawa?" Nene ta tambaya tana zaro ido, "Wanda ya bani admission ne ya bani yace nayi hidimar shiga makaranta", Karon farko a rayuwarta tayi wa Nene k'arya dan sam bata son abunda zai tada mata hankali, "Toh ai sai ki karb'a ki ajiye wurin ki", "A'ah Nene dubu ashirin kad'ai zan karb'a na lallab'a dasu, sauran ayi cefane da sauran hidimar gida, ki cire ko dubu goma ce ki fara k'aramar sana'a", "Allah ya miki albarka, yasa ki fara karatun a saa", "Amin Amin",
Bongel a ranar data cika kwana biyar gida, ta shirya komawa katsina makaranta, a cikin kwanakin babu irin bak'ar maganar da basu sha ba wurin su Fatsuma, a cewar su Bongel yawon karuwanci taje katsina, ta samu kud'i, gashi har sunyo cefane, idan ba yawon banza ba, ina zata samu kud'i, Daga Nene har Bongel ba wanda yabi ta kansu.
Bongel ta had'a kayanta tsaf na tafiya, Goggo Hajjo ta kawo mata yaji, k'uli k'uli da garin kwaki tace ta k'ara, Ta mata godiya sosai da nuna jin dad'in ta, Haka Nene ma ta yabawa Goggo dan tafi k'annen mahaifinta da ko abunda ba'a so basu bayar ba, kuma dukkansu ta musu sallama, amma ba wanda ta samu amsar kirki daga gare sa,
"Maganar zaman ki gidansu Asiya sai nake ganin rashin dacewar haka, suna fama da kansu kije ki k'ara musu lalura, babu wurin kwana ne a makarantar taku" Cewar Nene, Bongel tace "Akwai Nene", "Toh me zai hana ki zauna a can", "Sai nake ganin kamar idan nayi haka ba zasu ji dad'i ba, dama ina tunanin neman aikatau na d'aukewa kaina wasu lalurori", "Kinyi tunani mai kyau, rayuwa tayi tsada yanzu, kowa yana ji da kansa, baka k'arawa mutum d'awainiya ba", Ta jinjina kai alamar gamsuwa da zancen Nene, "Allah ya tsare ki ya kare ki, Allah ya baki ilimi mai amfani da albarka", "Amin"
Har k'ofar gida suka mata rakiya, ta tafi da burin watarana zata kawo sauyi a rayuwar ahalin ta.
**********************
Bongel ta koma katsina da kwana biyu suka soma registration na makaranta, ranar farko ba k'aramar wahala suka sha ba, kasancewar su sabon shiga, ko'ina sai sun jira layi bana wasa ba, sunyi applying scholarship gwamnati zata rik'a biya musu kud'in makaranta,
"Wai Allah! wallahi na gaji, haka zamu rik'a fama kullum", Asiya ta fad'a tana tsayawa, Bongel tace "Nima na gaji, amma ya muka iya tunda ilimi muke nema", Asiya tace "Hakane amma Dan Allah tsaya mu huta", Bakin wata bishiya suka zauna, sun d'auki kusan minti ashirin kafin suka tashi,
Sai yamma suka dawo gida a gajiye, wanka suka fara yi, suka ci abinci, kowacce ta kwanta tana huce gajiya,
********************
"Ya kamata zuwa yanzu an kai k'arshen komai, amma kullum babu wani bayani, idan ra'ayi ne bakwa yi ku fito ku fad'a" Ammi da wayar ke kunne ta tana sauraran mai maganar tace "Ba haka bane Hajiya Mariya, ina so ku bamu nan da sati d'aya", "Kullum maganar d'aya ce dai, a baku lokaci kaza, idan lokacin yazo kuma babu wani bayani", "In Shaa Allah wannan karon hakan ba zata faru ba", "Allah yasa, Ina Irfan banji motsin sa ba", "Gashi nan", Ta mik'a masa wayar yana mata gwaranci, kafin ta kashe,
Ammi shiru tayi damuwa d'auke a fuskarta, har Haidar ya shigo bata ji shigowar sa ba, "Ammi barka da dare", Sai muryarsa kawai taji, "Barka kadai" Ta fad'a a sanyaye, Yana zama Irfan ya d'are cinyar sa,
"Ammi ina fatan lafiya?" Ya tambaya cike da kulawa, Ta sauke ajiyar zuciya tace "Hajiya Mariya ce ta kira k..." Saurin katse Ammi yayi ta hanyar yin tsaki yace "Suna nema su zamarwa mutane liability, ana dole ne", Ammi tace "Wallahi bani da damuwa sai su", "Ki daina damuwa Ammi, kada ki sawa kanki wani ciwo, In Shaa Allah ba da jimawa ba zamu kawo k'arshen komai", "Allah ya yarda", "Amin In Shaa Allah",
Hisham ne ya shigo da airpods a kunnen sa yana jin wak'a, sai dai yazo saitin Ammi ya cire ya gaisheta, ya juya kan Haidar yace "Yaya barka da dare", "Yawwa" Ya amsa ganin Ammi, sanin rashin amsarwa zata so jin ba'a si, Hisham sanyi yaji a zuciyarsa na amsarwa Yaya Haidar, tun ranar ya daina masa magana, ko yayi baya amsa masa, yasan ganin Ammi ne, dan haka da gangan ya rik'a jan Haidar d'in da hira, dan dole ya rik'a amsa masa, har ya saki jiki suna hira har Ammi.
OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
SHAFI NA HUD'U
Ta shirya tsaf cikin atamfar ta d'inkin riga da skirt, sai hijabinta iya gwiwa, "Bazan gaji da cewa kinci sunanki Bongel ba, wallahi ke kyakkyawa ce Hafsah", Cewar Asiya, Bongel tayi murmushi tace "Kema ai kyakkyawa ce", "Ban kama k'afarki ba, kefah kafin a samu mai kyau irinki sai an tona", "Uhmm ni dai muje ki rakani bana son zuwa ni kad'ai" Ta fad'a a marairaice, "A'ah kar mu fara da karya masa sharad'i, dama ce muka samu kada mu bari ta sub'uce", Bongel tace "Hakane kuma, kira sa naji ina zan same shi",
Hisham fitowarsa daga wanka kenan, yana goge gashin kansa da k'aramin towel wanda ya taru kamar na mace sai dai gashin ya k'ara masa kyau, Wayar sa ta soma ruri, ya kai dubansa ganin bak'uwar lamba yasa a ransa yarinyar jiya ce, dan baya expecting kira da sabuwar number yau a wannan lokacin, yayi receiving tare da saka handsfree,
"Assalamu alaikum" Ta fad'a cikin natsuwa, "Wa alaikis salam", "Ina wuni?", "Lafiya lau", "Nice ta j.." Ya katse da fad'in "Na gane, mu had'u a bakin company", Ta amsa da "Toh", Ta mik'awa Asiya wayar, "A'ah kije da ita, ko da buk'atar amfani da ita zata taso", Tace "Toh",
Kusan minti ashirin da tsayuwarta a wurin, dallelliyar mota tayi parking a gabanta, tented ce shi ya hana mata ganin na cikin motar, glass ya sauke ya mata alama da hannu tazo, Ganin Hisham ne ta k'arasa bakin mota, "Shigo" Ya fad'a, Kai ta girgiza tace "A'ah", "Baki shirya karb'ar admission ba kenan", "Na shirya" Ta fad'a da sauri, ganin yana shirin tada mota tayi saurin bud'ewa ta shiga, ba abunda ke tashi cikin motar sai kid'a, sam bata son kid'a, sai yatsina fuska take,
Daidai wani k'aton gida taga yayi horn, security ya taso ya bud'e, tayi mamakin ganin gida suka zo, "Fito" Yace mata, Jiki a sanyaye ta fito, tana bin harabar gidan da kallo, dan ba k'aramin kyau ya mata ba,
"Mu shiga ciki ku gaisa da Matata", Ya fad'a yana murmushi, tabi bayan sa, a ranta tana ayyana matar sa ta dace da miji mai tsantsar kyau, gayu had'i da dukiya,
Falon sam bai nuna akwai d'an adam dake rayuwa cikin sa ba, "Bara na kirata" Ya fad'a yana shiga ciki, Few minutes ya fito, Yace "Ki sameta ciki, tace kanta na ciwo, kinsan masu laulayi", Bongel tayi murmushi a ranta tana mamakin kirki irin nasa, dama akwai masu kud'i masu sauk'in kai,
Tana shiga d'akin ya rufa mata baya, tare da saurin saka key ya kulle ya zare mukullin,
Jin an rufe k'ofa ta juyo a razane, "Dan Allah kar ka cutar dani ka barni na tafi", Murmushin gefe baki yayi yace "Kina tunanin a banza ake samun admission" Yayi dariya ya cigaba "Ki kwantar da hankalin ki, ki bani kanki yau kad'ai, ki samu admission cikin sauk'i da kud'ad'en kashewa", "Dan Allah kaji tausayina ka k'yaleni kada kamun komai, Dan Allah ka rufa mun asiri", Tana fad'a tana ja baya, yana biyota har ta fad'a kan gado kwance, ya hau kanta ya cire hijabinta da k'arfi ya wular, ya soma romancing d'in ta, hawaye ke ambaliyi saman fuskarta, tana nadamar kawo kanta, ko shakka babu tayi babban kuskure na biyo sa,
*********************
Namiji ne da ya amsa sunansa namiji, yana cikin jerin maza ajin farko, mai jini a jika, kyau, had'uwa had'i da gayu duk ba'a bar sa a baya ba, Fari ne sosai wanda ya had'u da na halitta da hutu, fatar sa kad'ai zaka kalla kasan naira da hutu sun ginu a wurin, Tsaye yake bakin dressing mirror na tantsamemen gadonsa royal, yana combing kwantaccen gashin sa na fulani, comb d'in ya ajiye a ma'ajiyar sa, ya fesa turare sun kai kala biyar, ya gyara zaman necktie d'in sa, Ya fito d'akin cikin takunsa na k'asaita,
Da sauri escort d'in sa ya taso da zumar bud'e k'ofar mota, "Zan shiga gidan Ammi", Ya fad'a a takaice, yana bin wata k'aramar k'ofar da zata sada shi da gidan, ba tare da yabi ta gate ba, ganin babu motocin Abba, ya tabbatar masa ya fita aiki kenan,
Dattijuwar mata yar' kimanin shekaru hamsin na zaune falo wanda aka narkawa dukiya, ta sha ado na matan manya, hutu da naira ya b'oye tsufanta zaka rantse ba zata haura shekaru arba'in zuwa da biyu ba, yaro dan' kimanin shekara biyu yana zaune kan cinyarta tana bashi chips, "Ammi ina kwana?" Ya gaisheta yana russunawa, "Lafiya lau",Ta amsa da sakin fuska, Yaron ya sauka jikinta yana nufar sa, yana fad'in "Daddy" cikin gwarancin sa, "Wato kaga babanka ko", Ammi ta fad'a tana dariya,
D'aukar sa yayi ya soma masa wasa yana cilla sa sama, yaron kuwa sai dariya yake, ya jima yana masa wasa, kafin ya mik'awa Ammi shi, Yace "Ammi wai ba zaki samu mai tayaki hidimar yaron nan ba, kema kina buk'atar hutu", Ammi ta nisa tace "Yaran ne na kasa dacewa, kowacce da nata matsala, lokaci yayi ma da ya kamata ace ka k'ara aure, shekarar Hafsah biyu da rasuwa, ya kamata ace ka dangana, ka samar wa yaron ka wacce zata maye masa gurbin uwa da ya rasa", "In Shaa Allah" Shine kad'ai abunda yace yayi saurin fita, sam baya son ana masa maganar aure.
Ganin fitowar sa, Escort d'insa yayi saurin tasowa ya bud'e masa gidan baya, ya shiga, ya mayar ya rufe, Driver yaja motar,
Wayarsa ya jawo ya soma kira, amsa d'aya ake basa a kashe, idan ya kira wayarsa yaji a kashe yasan babu inda zai same sa sai guest house, "Muje guest house" Ya umarci driver, "Ok Yallab'ai" Ya fad'a cike da ladabi, Banda yana buk'atar takardun dan kusan akansu ne zasu zauna meeting da wasu yan china, zasu mishi signing da ba abunda zai kai sa can,
"Ba sai ka shiga ciki ba" Ya fad'a, a bakin gate yayi parking, Escort yayi saurin fitowa ya bud'e masa, ya fita, Kai tsaye ya shiga cikin gida, alamun kamar kuka ya soma jiyowa daga d'akin, Yana sa kansa ciki daidai lokacin Bongel ta d'ago kanta, idonsu ya sark'e cikin na juna, da sauri ya runtse idonsa yana cizon pink lips d'insa na k'asa, ya fice d'akin, bai tab'a mummunan gani irin na yau ba, lokaci d'aya yaji tsanar yarinyar da yaga k'aninsa a kanta, ya tsani zina, yana k'yamatar ta, yasha yi ma Hisham wa'azi kan neman mata baya ji, bai tab'a gani da idon sa ba sai yau, "Meyasa mata basu da hankali, basu san daraja da martabar da Allah ya musu ba, suka zab'i zubar da mutuncinsu akan titi, mata da yawa kyaunsu ke cutar dasu, k'aramar yarinya ta lalata rayuwarta" Ya girgiza kai yana jin haushi da tsanar yarinya na k'aruwa a zuciyar sa, yana jin tamkar ya koma ciki ya mata tsinannan duka sai ya raunana ta,
Hisham yaji shigowar mutum wanda yasan babu wanda zai shigo sai Yayansa Haidar, a daburce ya sauka kanta, ya fito d'akin,
"Yaya kaine, ina fatan lafiya?" Ya fad'a murya na rawa, duk da yasan Yaya Haidar d'in yasan yana neman mata amma bai tab'a kama sa red-handed irin na yau ba, Ko kallo bai ishi Haidar ba yace "Documents na jiya zaka bani", "Ai suna gida d'akina", Tsaki Haidar yayi ya mik'e ya fita, "Me ya hanani duba d'akinsa, da banga wannan k'azantar ba", Yana zancen zuci tare da yin tsaki,
Drivern sa da Escort daga ganin yanayin sa suka san ransa ya b'aci, "Mu koma gida" Shine kad'ai abunda ya fad'a,
Hisham zama yayi falo ya kasa komawa d'aki, kunya ta ishe sa, Yaya Haidar ya kamasa da mace, bai tab'a ganin b'acin rai akan fuskar yayan nasa ba irin yau,
Bongel ta fad'i Alhamdulillah yafi cikin kwando, zuwan wannan bawan Allah ya ceci rayuwarta, Hisham na gab da rabata da budurcinta Allah ya jefo sa, Hawayen idonta sun kasa tsayawa, tsantsar nadamar biyo sa ne shimfid'e a zuciyarta, meya rufe idonta ta kasa tunanin hakan zai iya biyo baya ta amincewa shiga motar sa, ta biyo sa gidan sa, ko shakka babu sunyi ganganci na saurin yarda dashi, "Meyasa maza tunanin su d'aya ne akan yaran talaka, suna ganin da kud'i zasu rud'e su lalata su, ba'a taimako Dan Allah, sai yaushe rayuwar talaka zata inganta a k'asar nan?", Ta k'arasa da girgiza kanta tana saukowa daga kan gadon, ta d'auki hijabin ta da ya jefar k'asa, ta saka tabi hanyar fita d'akin, jikinta ko'ina ciwo yake saboda fisge fisge data rik'a yi na k'wace kanta, Ganin Hisham a falo, tayi saurin juyawa baya, Ya ganta ya mik'e ya biyota,
"Dan girman Allah kayi hak'uri, ka dubi maraicina, kada ka tona asirin mahaifiyata", Jin haka ya tsaya cak, yana bin ta da kallo, yadda take kuka sai yaji tausayinta ya shige shi lokaci d'aya, Karon farko da ya tab'a jin tausayin wata ya' mace ya shige sa, haka bai tab'a attempting raping wata ba sai akanta, itace macen farko da yaji masifaffan sha'awar ta, duk macen da ya kwanta da ita da amincewar ta, idan yayi sau d'aya da mace sai ta dawo, wasu yana cigaba da mu'amla dasu, wasu kuwa da ya cire kwad'ayin sha'awar sa na ranar baya sake waiwayar su,
"Tashi tashi daina kuka", Ya fad'a tare da sa hannu a aljihu ya mik'a mata hanky, ta karb'a tana share hawayen ta, jikinta na kyarma, "Ki natsu bazan miki komai ba, and admission d'inki is ready, tun a jiya nasa a karb'a, da niyyar idan na samu abunda nake so daga gareki na baki, idan ban samu ba shikenan, kece mace ta farko da zan ba admission kyauta ba tare da na samu abu daga gareta ba", Ya mik'a mata takardar admission d'in, kamar tak'i amsa, tuna muhimmnacin karatun nata, da burin Bappa tasa hannu biyu ta karb'a da fad'in "Nagode" Godiyar bata kai zuci ba, dan babu yadda zatayi ne,
"Am sorry for everything ki yafe mun", Ya fad'a tare da had'a hannyen sa biyu, Mamakin canzawar sa lokaci d'aya ya kamata, duba da yadda ya zamar mata d'azu tamkar mara imani, tabbas ko shakka babu lokacin shaid'an ne ke kad'a masa ganga, ko ba komai yaji tausayin ta, kuma ya bata admission free, Ta tsinci kanta da cewa "Allah ya yafe mana baki d'aya", "Amin ko da wasa kada ki sanar da kowa abunda ya faru", Tayi nodding kai,
"Muje na kai ki gida", Tayi saurin cewa "A'ah zanje da kaina", Kallon da ya jefata mata yasa tayi shiru, tana jin tsoron kar ya mata wani abu, tabi bayansa ta shiga motar sa ba tare da son ranta ba, gabanta nata fad'uwa tana ganin kamar wani wurin zai kaita ya lalata mata budurcin ta,
Sunan unguwar da ya tambayeta yasa taji sanyi a ranta, har k'ofar gidan ya kai ta, ya bata kyautar kud'i wannan karon tak'i karb'a, Tana shiga gidan, Asiya ta taso da sauri wurinta, "Kin tada mana hankali Bongel, na kira waya yafi a k'irga baki d'auka ba","Wayar tana cikin jaka, kaina ya rik'a ciwo da jiri", "Subhanallah sannu kije d'aki ki kwanta, bara a aika a siyo miki magani", Cewar Mama, "A'ah nasha magani" Tayi saurin cewa, "Sannu kinji", Ta amsa da "Yawwa",
Kwanciya tayi shiru tana tunanin abunda ya faru da ita yau, yayin da take godewa Allah da ya kawo mata mafita cikin sauk'i, hakan kuma ya zama izna gareta ba zata sake yarda wani yace su had'u ba taje, tsabar son admission yasa ta tashi rasa abu mai tsada da daraja a rayuwarta,
Asiya tayi farin ciki sosai ganin Bongel ta samu admission economics, course d'aya da ita.
Idonta ta runtse kamar mai bacci, mutumin data had'a ido dashi ya soma yi mata gizo, da sauri ta bud'e ido tana addu'ar kada Allah ya k'ara had'a ta dashi ko a mafarki.
Haidar wunin ranar tunanin Hisham da yarinyar da ya gansa a kanta, ya kasa barin zuciya da k'wak'walwarsa, yayin da idonsa ke masa gizo da fuskar yarinyar, duk sanda zai tuna ta, sai yayi Allah wadarai da ita, tare da jin tsanarta da k'yamatar ta na d'arsuwa a zuciyar sa.
OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
SHAFI NA SHIDA
Bongel kwanaki hud’u suka d’auka suna registration kafin suka kammala, Ranar farko da zasu fara shiga aji lecture, bakinta ya kasa rufowa saboda murna da zumud’i,
Asiya na tsaye gaban k’aramin madubi dake manne bango d’akin su, tana shafa janbaki, “Wannan kwalliya taki k’arewa kamar wanda zata gidan biki, sai kin ja mana latti”, Bongel ta fad’a cikin k’aguwa, “Yau ce rana ta ta farko a jami’a, dole na gyara kaina”, Bongel tayi murmushi tana girgiza kai, ita kam bata ga amfanin wata kwalliya ba, tunda karatu kaje, Hijabinta ta saka dogo har k’asa, Asiya kuwa mayafi ta yafa,
A tsakar gida suka sami Mama, ta musu addu’ar nasara, da jan kunne kan su tsare kansu, Suka amsa da “In Shaa Allah”
Napep suka tara zuwa jami’yar umaru musa, Yana ajiye su, Bongel tayi saurin fito da kud’in zata bayar, Asiya ta rik’e mata hannu tace “Baba ya bayar da kud’in zuwan mu da dawowa”, Bongel tace “Angode Allah ya saka da alkhairi” A zuciyarta tana jin ba zata zauna yana biya mata kud’in mota ko da yaushe ba, sanin su ba masu k’arfi ba ne.
Suna cikin mutane na farko da suka fara zuwa, seat na farko suka zauna, Bongel hakan ya mata dad’i sam bata son seat d’in, a ganinta marasa k’ok’ari ke zama baya, tafi son zama gaba tana jin duk abunda malami ke cewa.
*****************************
Kaya kusan kala uku yana sawa ya cire, tsaki yayi yana jawo wata shadda light blue, yasan students da raina malami, baya son yayi shigar da za’a raina sa, mutum ne shi mai son girma, ya tsani raini, duk abunda zai sa a raina shi baya yi, haka baya tolerating wulak’anci daga wurin kowa, yanayin k’asaitar sa zaka rantse jinin sarauta ne idan ba an fad’a maka ba, haka zalika mutum ne shi kaifi d’aya,
Shaddar tayi masifar kyau a farar fatar sa, ya d’aura hular sa kan gashin kansa da ya d’an taru, apple watch d’insa ya d’aura, ya fesa turaruka wanda tuni d’akin ya gauraye da k’amshin sa, wayar sa ya d’auka k’irar iphone 13pro max,
Hamma yayi alamun bacci, tsaki yayi dan daren jiya bai samu isasshen bacci ba, saboda research da ya dad’e yana yi na lecture da zai yi yau, Tabbas ya yarda da zancen Abba da yace ta hanyar lecturing zai yi research sosai, da abunda zai sa ya hana idonsa bacci daren jiya.
Agogon wayarsa ya duba, 7:20am, lecture 8:00am ce zai d’auka, “Definitely Ammi na bacci” Ya fad’a, Kai tsaye wurin motar sa ya nufa, ba tare da ya biya gidansu Abba ba,
Kamar kullum Escort d’in sa ya taso da zumar bud’e masa k’ofa, Da hannu ya dakatar dashi alamar ya tsaya, Ya tsaya cak cike da fargabar ba wani laifin yayi ba, “Am going alone” Ya fad’a yana mik’awa drivern sa hannu alamun ya basa key, ya mik’a masa cike da ladabi, ya karb’a ya shiga motar yaja,
Driver ya kalli escort yace “Yau oga da jan mota da kansa”, “Nima shi nake mamaki”, “Ina jin ya kusa kawo wata sabuwar amaryar ne”, Cewar Driver, Sukayi dariya.
Office d’in da aka tanadar masa da zai zauna na d’an lokacin ya fara nufa, ya ajiye wasu takardu, duka malaman department d’in cike da girmamawa suke gaishe sa, har da wanda suka girme shi, shima yana amsawa da sakin fuska.
***************************
“8:00 tayi nasan yanzu malamin zai shigo, bara na fiddo handout” Cewar Bongel, tana jawo jakarta,
K’amshi mai masifar dad’i da sanya zuciya natsuwa ya daki hancin ta, “Kai turaren nan ya had’u”, tayi zancen zuci,
Tuni ajin aka soma k’us k’us, wanda duk maganar had’uwar malamin da ya shigo suke, yan’ mata da yawa sai faman gyara jikinsu suke dan tuni ya tafi da imaninsu, hatta mazan ajin yaba had’uwa da tsaruwar sa suke, suna ganij yafi k’arfin zama lecturer, dan kallo d’aya zaka masa kasan yana tare da hutu had’i da daula, da yawansu suna ayyana a zuciyar su, meyasa yake lecturing,
Gyaran murya da yayi yasa kowa natsuwa, a lokacin Bongel ta d’ago kanta, idonta sai cikin nasa, muguwar fad’uwar gaba taji, tayi saurin sunkuyar da kanta k’asa tana fad’in “Innalillahi wa inna ilaihi raji’u” a zuciyarta,
Haidar lokaci d’aya yaji fad’uwar gaba, yayin da ranar da ya gansu da Hisham na dawo masa tar a idon sa, “Tasha hijabi kamar mutuniyar arzik’i” Ya ya fad’a a zuciyar sa, yana sake jin tsanar ta,
B’angaren maza ya koma kallo, Ya soma da cewa “Am Haidar Abbas Maishanu”, Mamaki ya cika fin rabin yan ajin jin cewa yaron Abbas Maishanu ne,
Ya cigaba da cewa “I have my rules, wanda ke son zama lecture na dole ya kiyaye, idan na shigo aji ba wanda zai k’ara shigowa, mobile phones off, surutu i won’t tolerate, if you miss two attendance baza ka zauna jarabawata ba”, Bai k’ara da komai ya soma lecture cikin natsuwa, da yawa yan’ matan basa fahimtar mai yake cewa suke ba, sunyi nisa wurin kallon sa.
Bongel kuwa tunda ta sunkuyar da kanta k’asa bata k’ara d’agowa ba, sai dai duk abunda yake fad’a a cikin kunnen ta, ganinsa ba k’aramin d’aga hankalin ta yayi ba, sam bata so ya zama malamin ta ba, ta tabbata ba zai tab’a ganinta da k’ima a idon sa ba,
Lecture awa biyu ya d’auke su, ya fita bayan ya basu assignment mai wuya,
“Nikam malamin nan yayi mun kama da Hisham baki ga kamar su ba” Cewar Asiya, “A’ah ban lura ba” Bongel ta fad’a a tak’aice, “Wallahi suna kama sosai”, “Muje library muyi assignment d’in kafin mu tafi gida”, Bongel ta fad’a tana k’ok’arin kawar da zancen Asiya, “Lecture d’aya ce damu yau?” Asiya ta tambaya, “Eh”,
Sun jima a library suna duba littafai kala kala, basu samu amsoshin assignment d’in ba, sai bayan sunyi sallar azahar sun dawo, suka samu amsar uku cikin biyar, Bongel ta nuna damuwarta k’arara, “Haba Bongel kiji dad’i ma mun samu ukun”, Bongel tace “Haba Asiya ai kamata yayi ace mu samu duka”, “Munyi iya k’ok’arin mu mun kasa ba sai mun hak’ura ba”, Bongel ta d’aga kai sama, rai babu dad’i suka fito makarantar zuwa gida, tana ganin kamar hakan fad’uwa ne gareta ta kasa amsa sauran biyun.
******************************
“Hy my boy” Rauda ta fad’a tana shigowa, Irfan yaje da gudu ya rungume ta, Ta d’auke shi, tana k’arasowa cikin falon, “Afternoon Ammi” Ta fad’a tana zama kujerar kusa da Ammi, Ta d’ago tana kallon ta cike da takaicin rayuwa irin nata kanta yasha attach gashin ta zuba shi har gadon baya, ta yafa k’aramin mayafi kan gashin, wanda dashi da babu d’aya, doguwar riga ce english wear a jikinta, k’atuwar ledar da ta shigo da ita, ta mik’awa Irfan tace “Your favorites” Ya karb’a yana bud’e ledar chocolates ne da sweets kala kala, ya fiddo d’aya ya mik’awa Ammi yace “Bud’e mun”, “Baka gajiya da shan zak’i Irfan”, “Ammi ai gara yasha abun sa”, Ammi murmushi kawai tayi, tana bud’e masa ya karb’a ya fara sha,
Rauda gyara zamanta tayi ta soma ba Ammi labari, wanda bashi da kan gado, Ammi sauraren ta kawai tana bata amsa ba dan ranta yaso ba.
******************************
Haidar daga school, company ya wuce direct, acan ya tarar da ayyuka da yawa, duk da haka bai hana masa tunanin yarinyar da ya gani makaranta ba, “Angel at face devil at heart, ina jin kamar na bar lecturing d’in nan, na tsane ta, i don’t want to see her face ever again, why yau na ganta, kuma zan cigaba da ganinta har zuwa lokacin da zan gama”, Hannun sa ya buga kan teburin dake gabansa cike da takaici.
**************************
Bongel tunanin ganin mutumin ranar ya kasa barin zuciyarta, “Shin yasan Hisham k’ok’arin raping d’in ta yayi, ko kuwa ya d’auka ita ta kawo kanta dan hakan ta faru?” Ta jerowa kanta tambayoyin da babu mai bata amsa, Shigowar Asiya d’akin, ta tashi zaune tace “Dan Allah na tambaye ki?”, Asiya tace “Allah yasa na sani” Tana tattaro dukkan hankalinta kan Bongel, “Kece kika ga saurayi kan wata budurwa a gidansa, shin wane hukunci zaki yankewa budurwar”, “Wani hukunci da ya wuce na yar’ iska, me zai kaita gidan nasa har ya hau kanta idan ba yar’ iska bace”, Bongel ta jinjina kai yayin da take jin tsoro na dabaibayeta wanda ta rasa na menene, tana jin tamkar ta mayar da hannun agogo baya, ta goge bin Hisham da tayi, “Amma meyasa kika tambayeni?” Asiya ta katse mata tunani, “Babu komai kawai jiya naji wasu na muhawarar a makaranta”, Asiya tace “Ohh gashi inji Baba yace na baki mu rik’a siyan abinci a makaranta duk ranar da zamu dad’e”
Bongel ta girgiza kai tace “A’ah Asiya, abun sai yayi yawa, Dan Allah ki mayar wa Baba da kud’insa yayi wani abu dasu”, Asiya ta watsa mata harara tace “Baba ya baki kud’i kice a mayar, lallai Bongel sai yau na shaida baki d’auki baba matsay….”, Tayi saurin sa mata hannu a baki tace “Dan Allah kar kice haka Asiya, wallahi ina jin Baba tamkar mahaifina, kawai ina duba yanayin rayuwar ne, idan bamu taimakawa Baba ba, bai kamata mu k’ara masa hidima ba, ga kud’in mota ga kud’in cin abinci sai nake ganin yayi yawa”, Asiya tace “Bai yi yawa ba Bongel, kuma shi yaji zai iya ai”, Bongel ta nisa tace nasan da haka, amma yau da gobe sai Allah shiyasa nake so na fara aikatau”, “Aikatau” Asiya ta fad’a da mamaki, “Eh aikatau”, “Aiki zakiyi ko karatu, kina tunanin aiki zai bar ki kiyi karatun”, “Haka zan lallab’a duk lokacin da bani da lecture, zanje wurin aiki”, “Dan Allah ki bar maganar aikin nan, ki tsayar da hankalin ki kan karatu, idan dan hidimar ki ce Baba ya d’auka”, “Ina son abunda zai rik’a taimakawa su Nene, Bappa ne mai nema rai kuma yayi halin sa, yanzu basu da mai basu sai Allah” Ta k’arasa da hawaye, Asiya ta soma share mata hawaye da fad’in “Kada kiyi kuka Dan Allah, Bappa addu’arki yake buk’ata banda kuka, Nene kuma Allah yana tare dasu”, Bongel ta jima tana kuka na kewar Bappa da ya taso mata, kafin tayi alwala tayi sallah raka’a biyu na nema masa rahamar ubangiji.
Mama da Baba sun so hana Bongel aikatau, ganin yadda ta nuna tana so suka k’yaleta, Mama tace zata samu mata gidan mutanen kirki, idan ba zata wahala ba ko su wulak’anta ta, taji dad’in kulawar Mama gareta.
**********************************
Har satin ya k’are Haidar bai sake d’aukar su lecture ba, hakan ba k’aramin dad’i yama Bongel ba, a ranta tana addu’ar Allah yasa ya bar makarantar gaba d’aya,
Kamar kullum yau ma suna cikin mutane na farko da suka fara zuwa, sai dai kafin 8 ajin ya cika, cikar da bata tab’a gani anyi ba irin wannan lokaci da wuri, wasu duk sai ana lecture suke zuwa, Bongel sam ta manta da dokar Haidar ta saka haka, Sam bata san shigowar sa ba, sai dai taji ajin yayi shiru, hankalinta na can wurin k’ok’arin jawo biro d’in ta da ya shige k’ark’ashin kujera, ta kai hannunta zata jawo ya datse da k’arfen kujera, “Auchh hannuna”
Ta fad’a da k’arfi wanda duka hankalin yan ajin ya dawo kanta, Haidar na kai dubansa yaga itace ba tare da wani ja ba, Yace “Out” Yana nuna mata hanyar fita, Jikinta ya soma kyarma na tsoro, ta mik’e ta fita, Ya juya ya cigaba da lecturen sa, a ransa yana jin dad’in korar ta, ganin haka yasa yan ajin kowa ya k’ara shan jinin jikin sa,
Bongel gefe d’aya ta rab’e, tana hawaye na bak’in ciki biyu, bak’in cikin korarta da yayi waje abunda ba’a tab’a mata ba tun fara makarantar ta, kuma ai ba laifi tayi ba, hannun ta ya datse ya kamata a mata uzuri, bak’in cikin rasa lecture ranar.
Ko da suka fito lecture idonta ya kumbura tsabar kuka, “Haba Bongel meye na kuka”, Cewar Asiya tana nuna rashin jin dad’in ta, “Muje kimun bayanin lecture da akayi” Tana kawar da zancen kukan, “Yanzu muna da wata lecture, muje idan mun fito sai na miki”, Bongel ta jinjina kai.
************************************
4:30 daidai suka fito makaranta zuwa gida, Daidai k’ofar gidan suka ga dallelliyar mota fake, Asiya tace “Wane bak’o ne mukayi” tana mamaki, Bongel bata ce komai ba, amma a zuciyarta tana mamakin waye, suka nufi shiga gida, Horn da suka ji na cikin motar na musu yasa suka tsaya, suna bin motar da kallo, baka ganin na ciki saboda tent, K’ofar motar aka bud’e Hisham ya fito, ganin sa yasa gaban Bongel fad’uwa “Me ya kawo sa?, me yazo yi?”
OUM MUHRIZ
[2/14, 15:55] Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
SHAFI NA TAKWAS
Murya a sanyaye tayi sallama, Yana zaune yana duba wasu textbooks, sallamarta ta sauka cikin kunnen sa, jin muryar mace bai d’ago kansa ba, Sai gyaran murya yayi alamar meke tafe da ita, Bongel cikin rawar murya tace “Dan Allah kayi hak’uri ka karb’i assignment d’ina”, Yana jin haka yasan yarinyar nan ce, “So she have the gut na biyoni office d’ina, tana tunanin nima irin mazan nan ne”, Ya fad’a a ransa, A zahiri yace “Kinzo kiyi seducing d’ina ne kome, rashin kamun kan naki har ya kai ki biyoni office d’ina, ni ba irin lecturer bane masu neman yan tasha irin ki, So out”, Ya k’arasa cikin tsawa,
Bongel jiki a sanyaye ta juya ta fita, zuciyarta na k’unar maganganun sa, idan tasan haka zai d’auka da bata zo ba, gara ta rasa assignment data k’ara rasa mutuncin ta a wurin sa,
“Ina fatan ya karb’a”, Asiya ta tambaya cike da kulawa, Bongel ta girgiza kai tace “A’ah”, “Ya salam gaskiya yana da tsaurin ra’ayi”, “Allah yasa hakan shine mafi alkhairi”,
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
ASHIRIN DA D'AYA
Dube dube suka soma na hanyar da zata sada su zuwa cikin gida, kasancewar gidan ya kasu kashi kashi,
Haidar ne ya fito yaje wurin Ammi bata nan, kan maganar auren da ake shirin yi masa, ko akwai wata hanya da za'a bi dan ganin ba'a yi ba,
Idon su k'yam a kansa tun ba Feedo ba data kasa b'oye zalamar ta, kamanin sa da Hisham ya tabbar musu Yayan sa ne, har ya k'araso kusa dasu Feedo idonta na kansa, "Ina wuni" Suka gaishe sa suna d'an duk'awa, "Lafiya lau" Ya amsa ba tare da ya kalle su ba, da zumar wucewa, Ihsan tace "Dan Allah wurin Ammi muke tambaya", "Bata nan" Ya basu amsa kai tsaye,
Feedo ta tab'o ta da yi mata alama da kai, Ihsan tace "Tunda bamu sameta ba, bara mu sanar da kai, dan ina da tabbacin kai Yayan Hisham ne", Haidar gabansa ya fad'i yana fatan ba wani abun kunya Hisham d'in ya jawo musu ba, dan yana kyautata zaton yan' matan sa ne, Haidar ya gyara tsayuwar sa yana cusa hannun sa cikin aljihun riga yace "Ina ji",
"Ina ce kowane dan'uwa burin sa yaga dan'uwan sa ya auri mace ta gari, toh Hafsah yarinyar da ake shirin auren su da Hisham, ba kowa bace face karuwa, wacce bata tsayar da kanta kan namiji d'aya ba, taxi no garaje ce, idan banyi b'atan lissafi ba ta zubar da ciki ya kai sau biyar, har asibitin da take zuwa ana zubar mata na sani, so taya mace irinta zata zama uwa ta gari ga yaran da zasu haifa gaba", Haidar sai da ya gama sauraren zantukan Ihsan tas, Yayi gyaran murya yace "Ina da tabbacin kema budurwar sa ce, wanda zafin zai auri wata yasa kika zo kina fad'in zantukan nan, so you are not welcome here" Ya nuna mata hanyar wucewa, Ihsan tayi shu'umin murmushi tace "Idan ma hakan ne ba laifi bane, soyayyar sa tasa nake k'ok'arin kub'utar dashi", Haidar yayi murmushin takaici dan ya tuna fuskar yarinyar itace suke rigima da Bongel ranar a makaranta, wato dukan su taron yan bariki ne, abunda bai gane ba shine yaushe aka soma zancen auren Hisham da yarinyar bashi da masaniya, idan kuwa gaskiya ne in dai yana numfashi a doron k'asa ba zai tab'a bari jininsa ya had'a jini da ita ba,
Ihsan ta wuce, Feedo na take mata baya.
************************************
Dada ta shirya komai na zuwa neman auren Bongel, yayyen Abba su biyu, k'annen sa su biyu, sai yayyen Ammi su uku, Komai da ake buk'ata na zuwa neman aure an tanada, kama daga goro, sweets da sauran tarkace, goro kanshi k'warya ashirin, su sweets kuwa carton carton da kud'i naira dubu d'ari biyu, wanda da gayya Dada tasa kayan suyi yawa haka,
Bongel ta samu a d'aki tana karatun wani littafin addini,
"Yanzu za'a tafi neman auren ki Bongel", Dada ta fad'a da murmushi d'auke a fuskar ta, K'irjinta ya doka sai take jin fargaba, Dada ta k'ara da cewa "Suna da kwatancen gidan ku zaki fad'a mun", Ta sanar da Dada, Ta jinjina kai tana ficewa,
Nauyayyen ajiyar zuciya ta sauke tana addu'ar Allah yasa komai ya tafi lafiya lau.
***********************************
Jabeer ya gaji da yawon hankalin da Hamma Siddiku ke masa, yasa an kama shi zuwa police station, Hamma Siddiku sai had'a gumi yake ganin sa a station, Ansa yayi report kan cewa nan da kwana biyu zai kawo kud'in ko a rufe sa, Da tsananin b'acin rai da haushin su Nene ya dawo gida wanda yake ganin sune silar komai, da mutuncin sa a kai sa ofishin yan' sanda, tun a hanyar sa ta dawo gida yake masifa, Yana shigowa gida kai tsaye wurinsu Nene ya nufa,
Tukunyar dake tsakar gida, yasa k'afa yayi wurgi da ita, labulen dake sak'ale bakin k'ofar d'akin su ya d'age da cewa "Ku fito yau wallahi sai kun bar gidan nan, zama daku bashi da wani amfani, Bongel ta tafi yawon karuwanci ba zaku ja mana zagi a gari ba, dan ina da tabbacin Ramla ma ta kusa bin sahun ta, waya sani ma ba gidan aiki take zuwa ba, yawon shashanci take zuwa, dan inda naggen gaba tasha ruwa nan saura ke bi", Nene ta fito rik'e da hannun Abu, ta zube gaban Hamma Siddiku tana rok'on sa,
"Dan Allah Dan girman Allah ka rufa mana asiri, kaji tausayin marayun nan ka barmu mu zauna, wallahi bamu da wurin zuwa", Hamma Bala yace "Dole ku bar gidan nan wallahi, babu amfanin zama daku", Hamma Siddiku da Hamma Bala suka shiga d'akin suka soma yi musu wurgi da kaya, Nene tana kuka, Ramla da Abu suma suna yi, Fatsuma da Dije na gefe na murna cike da tsantsar farin ciki,
Sa'ade da Habiba ne suka shigo gidan sun dawo daga gidan kitso, Sukace "Ga manyan motoci nan masu kyau sosai sun tsaya bakin gidan nan", Jin haka Hamma Siddiku ya tsaya da abunda yake, Yace "Kun tabbata nan gidan", Suka ce "Eh dan sai da suka tambaye mu nan ne gidansu Bongel muka ce Eh", "Ahaf ai sai ita, na tabbata cikin kwartayen ta ne, wani ya biyota", Yayi hauri da kayan dake gabansa, yana nufar hanya fita, Hamma Bala yabi bayan sa,
Turus suka yi ganin motoci har uku, masu azabar kyau da had'uwa wanda a tsawon rayuwar su basu tab'a ganin irin su ba, Suka kalli juna, A tare suka bud'e motocin suka fito, Ganin manyan mutane cikin shiga da kamala, sanye da shadda wanda kallo d'aya zaka yi kasan mai tsada ce, jikinsu yayi sanyi, kowannen su ya basu hannu suka yi musabaha, Alhaji Yusuf yace "Ko zamu samu masauki", Hamma Siddiku yace "Eh eh bismilla", Hamma Bala yayi saurin shiga ciki ya d'auko tabarmi ya shimfid'a musu, Suka zazzauna, da yawa a zuciyar su, suna mamakin irin gidan da Haidar ya nemi mata, duba da arzik'in sa da na gidansu, da kuma irin gidan da matar sa ta fito,
Alhaji Yusuf yayi bayanin daga inda suke kafin daga bisani yace "Mun zo ne nemarwa dan' mu auren yar' ku Hafsah", Hamma Siddiku sai da cikin sa ya juya saboda tsananin mamaki da tashin hankali mai k'unshe da hassada, Hamma Bala shima kusan hakan, dan sai da tarin dole ya taso masa, suka soma yi masa sannu, Cikin k'arfin hali da son b'oye bak'in cikin sa yace "Ai an mata miji", Kallo kallon suke wa junansu da mamaki, Alhaji Nasiru wanda Yayan Ammi ne yace "Toh ya haka, da amincewar yarinya muka zo nan, anya kuwa tana son zab'in da kuka mata", Alhaji Yusuf yace "Maganar tana son sa bata taso ba, dan da tana son sa, ba zata bari muzo ba", Hamma Siddiku ya had'iye yawun b'acin rai, Alhaji Nasiru ya cigaba da cewa "Ni dai ina baku shawara ku bar yarinya ta auri wanda take so, auren dole bashi da wata fa'ida, Hamma Siddiku kwarjinin da suka masa ya kasa musawa, Yayi shiru, ganin haka Alhaji Yusuf ya umarci a fito da kayan da suka zo dashi, kasancewar shi babba mai shekaru da yawa, wanda yayi mu'amala da mutane kala kala, ya fahimci akwai hassada a lamarin,
Hamma Siddiku da Hamma Bala ganin kayan da ake shigo dasu, Mamaki ya cika su, basu k'ara tsinkewa ba sai da Alhaji Nasiru ya ajiye kud'i a gaban su, Hamma Siddiku ai tuni ya soma washe baki da kuwa ya had'e rai, "Ashe arzik'i ke kirana ina neman shure sa da k'afata" Yayi zancen zuci, A fili yace "Ai dama yaron ne ya matsa kan yana sonta, ita bata son shi, mutuncin baban yaron yasa da za'a aura mata shi, amma tunda ga wanda take so ai shikenan, dama rashin tsayayye yasa", Kowa mamakin shi ya kama sa, ganin yadda ya canza lokaci d'aya dan abun duniya, Hamma Bala yace "Toh yaushe kuke ganin ya dace a saka ranar bikin", Alhaji Yusuf yace "Mu a shirya muke ko yaushe", "Muma haka" Cewar Hamma Siddiku, Suka musu sallama suka tafi.
****************************
"Ku kwashe kayan ku, ku mayar ciki" Hamma Siddiku ya fad'a, Da mamaki Nene ta d'ago ta kalle sa, Da sakin fuska kamar ba shine ya gama juye musu kwandon rashin mutunci ba yace "Neman auren Bongel aka zo, ashe mune bamu fahimceta ba yawon karuwanci ta tafi ba" Duk yana yi ne dan ya kwashe kayan da aka kawo da kud'in, Nene mamaki ya cikata neman auren Bongel, yaushe ta samu miji a can kuma waye zata aura, sune suka fara zuwar mata a rai, ba kayan da taga an shigo dasu bane gabanta, Hamma Siddiku dubu goma kad'ai ya bata, bai fad'a mata ainihin yawan kud'in ba, su alawa ma carton d'aya d'aya ya bata, da goro k'warya d'aya, Nene bata damu ba, duka ta tarkata ta ajiyesu wuri d'aya ba zata tab'a har kud'in ba, sai taji daga Bongel,
Fatsuma da Dije hassada fal zuciyar su kamar su had'iye zuciya su mutu.
Hamma Siddiku har majalisar su Jabeer yaje ya watsa masa kud'in sa dubu ashirin, yace ga tsiyar sa nan, abun ya so zamar musu rigima, mutanen wurin suka raba su.
**********************************
Daga Ammi har Abba har yau basu san yarinyar da Bongel zata aura masa ba, Wanda suka je neman aure bayan sun dawo, da yawansu sun nuna rashin dacewar Haidar da neman aure irin gidan, Dada ta musu tas kan cewa babu ruwansu da gidan, Dan dole suka ja bakin su suka yi shiru.
Bongel tayi farin cikin jin su Hamma Siddiku sun amince, yanzu tasan babu zancen auren Jabeer, kuma Nene zata samu kwanciyar hankali, sai taji hankalinta ya karkarta gida, tasan Nene na son jin k'arin bayani daga gareta.
*****************************
"An je neman auren ka kuma an basu", Ammi ke sanar da Haidar, Haidar wanda ke zaune Irfan na kan cinyar sa ya manne masa kan ya kai sa wurin Aunty, anyi hutu kwana biyu bai je gidan Dada ba, Kansa kawai yayi nodding ba tare da yace komai ba, k'asan zuciyarsa yana jin zafi, Ya rik'e hannun Irfan suka fito, Yace driver ya kai sa, baya jin zuwa gidan Dada, haushin had'in auren da ta masa yake ji.
********************************
Dada ta yanke shawarar auren nan da sati biyu, bata so a d'auki lokaci, gudun abunda zai je ya dawo, Kud'i masu yawa taba Bongel kan ta fara gyara, Bongel ita kunya ma taji, Asiya ta samu mai gyaran jiki tana zuwa gida kullum tana mata, wanda gyaran ba k'aramin kyau yake k'ara mata ba, tana glowing,
Hisham kullum yazo sai yace ta k'ara kyau, yana k'ara jin masifar sonta na shigar sa, Abunda ke bata mamaki shine ko sau d'aya bai tab'a mata zancen auren ba, wanda ta rasa gane dalilin sa na hakan, itama kuma bata tab'a d'auko masa maganar ba.
******************************
Ammi yau ta yanke shawarar tambayar Dada wacece yarinyar, ganin bikin na matsowa ba tare da sun san ta ba, kuma ta soma had'e lefe, tana son ganin yarinyar ko a hoto ne dan sanin taste da ya dace da ita, Ta shirya taje gidan Dada,
**************************
"Dada an soma had'a lefe, gashi bamu san amaryar ba, balle mu san kayan da suka dace da ita", Cewar Ammi, Dada tayi dariya tace "Bongel ce ba kowa ba", Ammi lokaci d'aya taji sanyi a ranta dan ita kanta ta yaba da hankalin yarinyar, da kuma duba da yadda suka shak'u da Irfan, Tace "Au itace", Dada tace "Eh", "Mashaa Allah Allah ya sanya alkhairi", Dada ta amsa da "Amin"
*******************************
Bongel tana gidansu Asiya, tunda akace su Hamma sun amincewa auren ta, ta fara zuwa gidan ba tare da fargabar komai ba, Bayan sallar la'asar ta dawo har lokacin Ammi na gidan, Har k'asa ta duk'a ta gaisheta ta amsa da sakin fuska, tana k'ara yaba hankalinta da jin son kasancewarta surukar ta.
*********************************
Hisham yaji zancen nemawa Haidar auren, wanda Dada ta nemar masa mata, sai dai bai damu da sanin wacece ba, dan a ganinsa ba hurumin sa ba ne, Yau ma yazo wurin Bongel sun jima suna hira kafin ya tafi.
******************************
Bongel ganin kwanaki na k'ara matsowa na bikin, Dada bata yi maganar zuwanta gida ba, wanda a ganinta mutuncin ta shine a d'aura aure a gidansu, a d'auko ta daga gidansu cikin mutunci, Ta yanke shawarar samun Dada kan maganar,
Cikin sanyin murya da ladabi tace "Dada Dan Allah ina so na tafi gida a d'aura aure na a can", Dada ta jinjina kai tace "Kinyi tunani Bongel, hakan shi ya dace, zan shirya tafiyar ki, amma ina so ayi walima anan kafin ki tafi can", Ta amsa da "Toh", tana jin kamar kar ayi walima, tafi so a d'aura aure kawai.
***************************
Dada ta shirya walima babba a gidanta, wanda hadda ango zai zo da abokan sa guda biyu, a decoration da aka yi an ajiye wurin zaman Amarya da Ango.
*******************************
"Wow wallahi kinyi masifar kyau Bongel, gaskiya yau Ango Hisham dole ya rud'e" Cewar Asiya tana faman yi mata hotona, Bongel tayi murmushi, Tayi kyau sosai cikin bud'addiyar gown fara, wacce yadin ta mai tsada, Ammi tasa aka d'in ka mata, Ta fito sak Amarya.
**********************************
Yayi tsaki yafi a k'irga sam baya son zuwa walimar, amma Ammi ta nuna dole yaje, Farar shadda ce a jikinsa mai d'inkin babban riga da yasha aiki, hular sa ta zauna daram a kansa, Yayi kyau matuk'a ya fito sak ango, banda k'amshi ba abunda ke fita a jikinsa, Hisham ne ya shigo yana cewa "Ango Ango" Cikin zolaya, Kallon da ya jefa masa yasa ya tsaya da wasan Yace "Su Fahad na waje kai kad'ai ake jira", Bai ce komai ba, yana gyara takalman sa covered wanda designer ne,
Yana fitowa abokan sa suka soma fad'in "Ango Ango" Ya d'aure fuska kamar bai tab'a dariya ba, ya shiga mota, Abokansa suma suka shiga tasu, aka jera tafiya cikin convoy.
OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
ASHIRIN DA BIYU
Bongel da sauran k'awayenta sunyi kusan minti talatin da zuwa gidan Dada, dan ta koma gidansu Asiya saboda bak'i wanda dan halatar walimar suka zo, Ango bai zo ba, Bongel na cikin mota bata fito ba, Kanta sunkuye k'asa cikin lullub'in da ta sha na mayafi mai net shara shara, "Ango ya iso" Ta soma jin muryar yan' matan dake wurin na fad'a,
Da saurin escort d'insa ya fito ya bud'e masa k'ofa, Haidar ya fara zura k'afar sa d'aya waje, yana jin kamar yayi zaman sa cikin motar kar ya fita dan sam baya maraba da auren, a ganin sa wanda yayi auren soyayya ya cancanta ya halarta event bashi da ake neman k'ak'aba masa ba, "Shin yarinyar tana son sa ko itama auren dole za'a mata", Ya tambayi kansa, "Ko tana sona ko bata sona it won't change anything, ba zata samun gurbi a zuciyata ba" Yayi assuring kansa, "Ka fito mana Haidar, kai kad'ai ake jira, Amarya ta dad'e da zuwa", Iska ya fusgar daga bakin sa, ya fito,
A tare suka jero da Hisham zuwa k'ofar shiga gidan, Asiya ta hango su tare cikin da mamaki tace "Dama Hisham da Haidar sun san juna, kai anya basu da alak'a ta jini dan kamaninnasu yayi yawa", Sam bata kawo ba Hisham bane ango, saboda shima shigar tasa tamkar ango, shadda ce fara a jikinsa d'inkin babban riga,
Asiya ta bud'e murfin motar da Bongel ke ciki, Tace "Amarya fito, Ango is here, angon ki yayi kyau sosai, na riga ki ganin sa", Bongel tayi murmushi, Asiya ta kamo hannun ta, suka fito cikin motar, Kanta na sunkuye k'asa, ta jata zuwa wurin dasu Hisham suke,
"Ina wuni angon mu" Cewar Asiya, Hisham da kallon mamaki yake bin ta dama tasan Amarya, sai kuma wata zuciyar tace mishi duniya da fad'i, watak'ila k'awarta ce duba da yadda ta rik'o amaryar, Murmushi yayi yace "Lafiya lau k'awar Amarya", Ta mayar masa da murmushi,
"Amarya da Ango sai su jera su shigo tare" Cewar Dattijuwar mace wacce take matsayin Yayar Abba, Jin haka Fahad ya jawo hannun Haidar tamkar yaro, yana saita shi gefen Bongel, Asiya mamaki had'i da al'ajabi ya kamata lokaci d'aya, me hakan ki nufi, ko kamanin su yasa ya kasa tantance ango, Ta kalli Hisham taga bai nuna wata alama nacewa shine ango ba kuskuren aka samu, sai far'a da taga yana yi, yabi sahun abokan ango, Kanta ya k'ara k'ullewa ta kasa tunanin komai, balle ta aiwatar da wani abu,
Bongel k'amshin turaren da taji yana ziyartar k'ofofin hancin ta ya bambamta da na Hisham, wanda kuma taso sanin me irin k'amshi sai dai ta kasa tuna ko waye, A jere suka shigo farfajiyar wurin ana saka wak'ar larabci ta tarbar Amarya da Ango, Kujerar da aka tanada dan zaman su, suka zauna, aka kashe wak'ar, Babban malamin da aka gayyata ya soma wa'azi kan ma'aurata mai ratsa zukata, ya fad'i hakk'ok'in miji kan matar sa, da hakk'ok'in mata kan miji, Bongel a zuciyarta tace "Ba k'aramin nauyi ba ne ke shirin hawa kaina, wanda sai nayi taka tsantsan dan samun aljanna ta",
Awa biyu malamin ya d'auka yana wa'azi, kafin aka soma rabon abinci, har lokacin Bongel kanta na sunkuye k'asa, Asiya wacce mamaki had'i da tashin hankali ya dabaibaye ganin Haidar ne angon yasa ta kasa sakewa, wuri d'aya ta samu ta zauna shiru, taso magana da Hisham ko zata ji wani bayani daga bakin sa bata samu damar haka ba, kasancewar yana kusa da ango,
Mutane suka fara tasowa ana hotona, D'aya daga cikin coursemate d'in ta tace "Tashi a mana a tsaye" Ta kamo hannun Bongel, tazo mik'ewa ta take gown d'inta ta baya, tayi suu ta fad'a baya mayafin ta na yaye wa, idon su ya sark'e cikin na juna ita da Haidar, Hisham ma daidai lokacin ya kai duban sa, jin muryar mutane suna fad'in Subhanallah ganin ta fad'i,
Bongel numfashinta ya d'auke na wucin gadi, yayin da zuciyarta ke dokawa da tsananin k'arfi kamar zata fasa k'irjinta ta fito, Haidar sandarewa yayi wurin dan ya kasa gaskata abunda idanun sa ke gane masa, yayin da wata zufa ta tashin hankali ta shiga tsattsafo masa,
Hisham kuwa idon sa ya sake murzawa dan tabbatar da ba gizo suke masa ba, Ganin Bongel ce matsayin amaryar Haidar, kansa ya mugun sarawa tamkar an sara masa takobi, yana jin wani abu ya daki k'irjin sa,
Bongel ganin idon mutane yasa tayi saurin mik'ewa tana gyara mayafinta tare da k'ok'arin tattaro natsuwa, sai dai ganin natsuwar ba zata samu ba, ta rik'e k'afarta alamar kamar taji ciwo tace "Auchh", Sannu aka fara mata, Waleeda ta jata zuwa mota, Jinginar da kanta tayi jikin kujerar mota, kanta na tsananin sara mata, bugun zuciyarta na tsananta, Asiya take buk'atar gani a yanzu,
Asiya na ganin an fito da Bongel, ta biyo bayan su, motar ta bud'e ta shiga, Hamza driver ta umarta ya kaisu gida, ba wanda ya d'aukowa wani maganar ganin bai dace suyi gaban Hamza ba, amma kowa yasan dan' uwan sa na cikin rud'ani.
********************************
Haidar bai k'ara minti biyar a wurin ba ya fita zuwa gida ba tare ya jira sauran abokan sa ba, Yana shiga d'aki ya cire hular sa da babbar riga yayi wulli dasu, Da fad'in "How is that possible, taya ta zama yarinyar da Dada ke son aura mun, wallahi ba zai tab'a yiyu ba, i must ruin everything bazan tab'a bari hakan ta faru ba" Ya fad'a idonsa na kad'awa su koma jajir.
**************************************
"Asiya kaina ya k'ulle, bana gane komai taya Haidar ya zama mijin da zan aura ba Hisham ba, meye alak'ar Dada da Haidar, taya Haidar ya zama mahaifin Irfan", "Nima sune abunda suka d'aure mun kai Bongel, amma ina jin Hisham ya kamata mu nema ko zamu samu wani bayani", "Bana tunanin Hisham nada masaniya a kai", Ta k'ara da cewa "Shiyasa kenan bai tab'a mun zancen auren ba", Ta k'arasa da dafen kanta da take jin tamkar zai rabe biyu, Asiya ta bud'e baki zata yi magana kiran Hisham ya shigo, wanda tun ganin Bongel matsayin matar da Haidar zai aura ya rasa natsuwar sa,
Ta d'auka, Cikin sanyi murya yace "Ina waje", Tace "Toh" tana kashewa ta kai dubanta ga Bongel tace "Hisham ne" Da sauri ta tashi, tana riga Asiya fita waje, Cak ta tsaya dan kallo d'aya ta masa ta hango tsantsar tashin hankali a fuskar sa da tarin tambayoyi, Kafin tayi wata magana yace "Taya haka ta faru Bongel, ki gaya mun taya, dama yaudarata kike kin shirya auren Yayana", Jin kalmar Yayansa ta kalle sa a razane da cewa "Haidar Yayan ka ne", "Kada ki raina mun hankali Bongel, tsawon zaman ki gidan Dada ba zaki ce baki san Haidar yaya na bane", Kuka ta fashe da shi tana cewa "Wallahi ban sani ba Hisham, hasalima kai nake wa kallon mahaifin Irfan, shiyasa ko da Dada tazo da zancen auren mahaifin Irfan na amince, bansan Haidar ba ne" Ta k'arasa tana kuka kamar ranta zai fita, Hisham natsuwa ya d'an ji na jin cewa Bongel bata san da maganar auren ba, Ya numfasa yace "Ki daina kuka Bongel, In Shaa Allah i will try wurin ganin auren ya dawo kaina", "Please try Hisham, ba zan iya auren yayan ka ba", Jin haka ya k'ara sa zuciyarsa tayi sanyi, Sai da ya tabbatar ya lallashe ta, ta daina kuka, sannan suka shiga cikin gida da Asiya, wacce tun fitowar ta bata ce komai ba.
****************************************
Hotonan walima da ake ta sawa a status Rauda ke kallo cikin tsananin b'acin rai da tafasar zuciya, hoton k'arshe da ta kai tayi jifa da wayar k'irar iphone 13, ta fashe, Kuka ta fashe dashi da cewa "Wallahi sai na aure ka Haidar, tun kafin Yaya Hafsah ta rasu nake wa kaina sha'awar miji irin ka, yanzu ga damar samun ka bazan tab'a bari wata ta mallake ka ba", Ta k'arasa da fad'awa kan gado tana kuka tana wulla k'afa kamar k'aramar yarinya.
***********************************
Alhaji Sani ne zaune jigum, ya zurfafa tunani, abincin da Hajiya Mariya ta zuba masa har ya soma sandarewa,
Hajiya Mariya ta shigo tana cewa "Ahh Alhaji baka ci abincin ba", Tana kallon plate dake gabansa, Ya sauke ajiyar zuciya da cewa "Wallahi ba zan iya ci ba Mariya, komai yana neman rushe mun lokaci d'aya, tarin burikana na neman wargajewa", Hajiya Mariya ta dafa kafad'ar sa da cewa "Ka daina fad'ar haka Alhaji, In Shaa Allah sai mun cimma burin mu", "Taya kina ganin an soma bikin Haidar", "Somawa akayi ba'a d'aura ba, ka bari kawai ka gani sai na tabbata auren bai yiyuwa ba", "Taya hakan zai kasance", Shu'umin murmushi tayi tace "Ka bar komai a hannu na",
******************************
Bongel sam bata runtsa ba, raba daren tayi Sallah, tana rok'on Allah zab'in alkhairi a rayuwar ta, Da safe kasa karin kumallo tayi, ruwa kad'ai ta sha, ba yadda Asiya batayi da ita ba, taci abinci tak'i, Yau ya kamata ta tafi malumfashi amma jiran ta bakin Hisham taji ko ya samu nasarar wargaza aurenta da Haidar ya dawo kansa, yasa ta fasa tafiyar.
*********************************
Dada tsaf ta gama sauraren buk'atar da Hisham yazo da ita, nacewa suna son junansu da Bongel, Dan Allah ta maida auren kansu, Ta kalle sa tsaf ta kira sunan sa "Hisham" Ya amsa da "Na'am", "Kayi kuskure tun farko na b'oye soyayyar ka da Bongel, bakin alk'alami ya riga ya bushe, Bongel na riga na zab'ar mata Haidar a matsayin mijin aure dan sunfi dacewa", Zubewa yayi k'asa yana had'a hannayen sa biyu yace "Dan girman Allah Dada ki taimake ni ki aura mun Bongel", Duk da tausayin sa ya kamata, bata jin zata tab'a canza akalar auren zuwa kansa, Tace "Kayi hak'uri Hisham, Allah ya baka wacce tafi Bongel", Kasa tashi yayi da gurfanen sai hawaye da suka soma sauka kan kumatun sa, yana jin kansa na juyawa, a yadda soyayyar Bongel ta kamasa baya jin zai iya jure rasa ta, Dada mik'ewa tayi ta bar falon cike da tausayin sa, dan ba zata iya jure ganin sa a wannan hali ba.
*********************************
Haidar dare d'aya amma duk ya canza kasancewar rashin bacci da bai samu jiya ba, had'i da damuwa da tunani da suka taru suka masa yawa, Kansa ke tsananin ciwo yasha pain relief amma tamkar k'ara masa ciwon kan ake, a daren jiya sai da ya samu hanyar sub'ucewa auren kafin ya d'an samu natsuwa,
Wayarsa ya d'auka ya kira Hisham, Hisham wanda tun fitowar sa gidan Dada, ya samu wani wuri da babu mutane, yayi parking motar sa ya d'aura kansa kan sitiyari cikin tsananin damuwa, Kamar ya share kiran sai kuma ya d'auka, "Kazo guest house kai daa budurwar ka Hafsah", Yana fad'ar haka ya kashe wayar, Hisham ajiyar zuciya ya sauke yana fatan kiran ya zama alkhairi, Motar sa yaja zuwa gidansu Asiya,
Bongel da take jiran zuwan sa, tana jin yana waje, ta saka hijab ta fito, "Ki shigo mota zamu je wani wuri" Shine kad'ai abunda yace mata, Kanta ta girgiza alamar "A'ah", "Zuwa yanzu ya kamata kisan bani da wata manufa a kanki face ta alkhairi, so pls kizo muje", Ta d'an yin jim, kafin ta bud'e murfin motar ta shiga, Yaja su zuwa guest house, Ganin gidan da suka zo gabanta ya fad'i ta kai dubanta gare sa cikin fargaba, "Wallahi tallahi bani da niyyar cutar dake Bongel", Jin haka ta d'an samu natsuwa, Ta fito tana bin bayansa,
Turus tayi k'irjinta na dokawa ganin Haidar hakimce kan kujera, tayi saurin ja baya, Hisham ne ya mata alama da ta tsaya, Cak ta tsaya,
Haidar hannun sa ya soma tab'awa yana tafi, ya mik'e Yace "Wow despite ana shirin auren ki da wani amma kike iya bin saurayi zuwa wurin sharholiyar da kuka saba", Hisham da mamaki ya bud'e baki zai yi magana ya dakatar dashi da hannu "Nasan me kake shirin fad'a, idan bata saba biyo ka nan ba, babu macen data san k'ima da darajarta da zata biyo saurayi gida ko da babu kud'in auren wani a kanta","No Yaya Haidar ba haka ba ne", "Idan baka sani ba Hisham, ina so yau ka sani da idona na ganku", Hisham k'irjin sa ya doka, "Hakan na nufin Yaya Haidar yaga Bongel ranar kenan" Yacewa kansa, Haidar ya juya kan Bongel
"Haidar ba sa'an auren irinki ba ne mai cike da d'auda da dattin zina, Taya kike tunanin zan auri macen data had'a shimfid'a da k'anina, macen data zama tamkar motar haya kowa hawan ta yake, Ni HAIDAR ABBAS MAISHANU bazan tab'a auren karuwa wacce ta had'a shimfid'a da k'anina ba", Cikin zafin rai da hasala da maganganun sa tace "Banyi ba, ban tab'a had'a shimfid'a da kowa ba, ka daina danganta ni da kalaman da ban dace dasu ba" Ta juya kan Hisham tace "Ka fad'a masa gaskiya, ka gaya masa abunda ya faru ranar", Hisham yayi shiru ya kasa magana, Cikin d'aga murya tace "Kayi magana Hisham, ka fitar dani daga mummunan zaton Yayan ka, na gaji na gaji" Ta k'arasa cikin karaji.
FOLLOW, VOTE AND COMMENT
*OUM MUHRIZ*
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
ASHIRIN DA UKU
Hisham ya bud'e baki zai yi magana wani tunani yazo mishi yace "Yes mun had'a shimfid'a dake Bongel, bana tunanin akwai amfanin b'oyewar haka", Ya fad'i hakane sanin Yayan sa ba zai tab'a amincewa auren ba matuk'ar yaji sun had'a shimfid'a, shi kuma ya samu mallakar Bongel,
Ba Bongel kad'ai ba hatta Haidar zancen ya dake sa, duk da yaga Hisham a kanta, amma ji daga bakin sa, ya k'ara hasasa wutar tsanarta a zuciyar sa, ita komai ta had'a k'arya, iya makirci banda makirci yadda take yi zaka rantse babu abunda ya shiga tsakanin ta da Hisham d'in, taso ayi manipulating d'in sa kenan Hisham ya bayar da shaidar k'arya, Ya fusgar da iska mai zafi daga bakin sa a fili yace "Mak'arciya makira"
Bongel kalmar "mun had'a shimfid'a dake Bongel" ke wa yawo a k'wak'walwa, dishi dishi ta soma gani, jiri na d'ibar ta, tuni ta zube k'asa.
A rud'e Hisham yayi kanta, Haidar har yayo kanta shima sai kuma ya tsaya cak kamar wanda aka rik'e, ya juya ya fice falon.
Hisham a rud'e ya d'auko ruwa a fridge yana watsa mata, ta bud'e idon ta suka sauka kan Hisham, tayi saurin runtse su tana jin tsananin haushin sa, "Am sorry please Bongel, ki.....", Da hannu ta dakatar dashi da cewa "Enough Hisham", Ta mik'e ta nufi hanyar fita, da sauri ya sha gabanta yace "Dan Allah ki saurareni Bongel, wallahi tsananin k'aunar ki yasa nayi haka", Wani banzan kallo ta watsa masa mai cike da takaici, tana jin kamar ta zabga masa mari, k'auna zata sa ya zubar mata da daraja,
"Kiyi hak'uri Dan Allah, i have to do this dan ganin mun mallaki juna" Hisham ya fad'a a marairace, A fusace tace "Bana buk'atar mu mallaki juna in har sai mutuncina ya zube a idon wasu, kasan yadda jifar mutum da kalmar zina take da zafi da rad'ad'i, kasan shaidar zina illar da take wa mutum, meyasa ka zab'i wannan hanya ta zama ta silar auren mu", "Ita kad'ai ce hanya Bongel", "Bani hanya na wuce" Ta fad'a cikin b'acin ran ganin bashi da niyyar gyara mistake d'in sa, Ba dan rai yaso ba ya matsa, Ta fita tana bin hanyar zuwa titi, Bak'in ciki da damuwan suka had'u suka cunkushe zuciyar ta wanda ba zai bayyanu ba, shikenan zargin Haidar a kanta zai k'ara tabbata, watak'ila ma yaje ya sanar dasu Dada dan kub'ucewa auren ta, shikenan mutuncin ta ya zube wurin Dada, Hawaye suka soma ambaliya saman fuskarta, wasu na bin wasu, har ta isa gidansu Asiya, taci sa'a bata tarar da kowa a tsakar gida ba, har ta shige d'aki, Asiya kad'ai ta tarar,
"Lafiya kike kuka, me ya faru?"Asiya ta tambaya cikin damuwa, Kanta ta girgiza tace "Ba komai, kawai auren Haidar ke d'aga mun hankali", "Ki kwantar da hankalin ki, kiyi ta addu'ar zab'in alkhairi" Kanta tayi nodding, Ta jawo kayanta ta soma had'awa, ta yanke shawarar tafiya yau, gaba d'aya hankalinta ya karkata gida, tana son jin d'umin jikin mahaifiyarta, ko zata rage wani rad'ad'i, Haka bata son sake had'a ido da Dada, bata san da wane ido zata kalleta ba, zata koma gida ta amincewa auren Jabeer su Dada a mayar musu kayan su, tafi son auren Jabeer akan Haidar, haka ba zata tab'a iya auren Hisham ba, danginsa na mata kallon mazinaciya wanda tasan abu mai wuya ne su amince ya aure ta, ba wanda zai so dan' sa ya auri mazinaciya.
***************************************
Haidar daga guest house kai tsaye gidan Dada ya nufa, da k'udurin lalata auren sa da Bongel, Sama
Sama ya amsa gaisuwar masu aikin, Dada na kishingid'e kan kujera bacci na son d'aukar ta, Ganin Haidar tace "Ka gama fushin, tunda kaji na nemar maka mata ka d'auke k'afar ka daga gidan nan", "Ina wuni?" Ya fad'a yana kawar da zancen, "Lafiya lau Ango kasha mai", Fuska ba yabo ba fallasa ya zuana saman carpet yace "Dada Dan Allah ina neman alfarma a wurin ki", "Ina jin ka", "Dan Allah ki janye zancen aurena da yarinyar nan, budurwar Hisham ce", Murmushi tayi irin na manya tace "Haidar kenan, idan kasan alkhairin da na hango maka tattare da Bongel da baka ce haka ba, shin ko dan yaron ka ba zaka amincewa auren ba", Da mamaki yake kallon Dada, dama itace Auntyn Irfan, itace Irfan ke yawan magana, taya d'an sa ya shak'u da karuwa, Dada ta katse masa tunani da cewa "Kyau, nasaba, tarbiya, natsuwa da halayya nagari ake nema wurin mace ta gari, Bongel duka ta had'a, ina maka sha'awar auren ta dan tarbiyar yaron ka, da kai kanka ka samu natsuwa da kula a tare da ita", Ya bud'e baki zai sake magana Dada ta dakatar dashi da cewa "Auren ka da Bongel kamar anyi an gama, idan kaga ba'a yi ba to bana numfashi a doron k'asa, kai ko bana raye zan bar wasiyyar tabbatuwar auren ku",
Kansa ya dafe, wacce irin masifa ce ya tsinci kansa a ciki, Taya yaron sa zai samu tarbiya wurin wanda ta kai k'arshe wurin tsantsar rashin tarbiya, taya zai samu natsuwa a tare da Karuwa, ko shakka babu ta zama fuska biyu, macijin sare ka nok'e, Dada kallon kitso take wa rogo, ta b'oye ainihin kalar ta, ta nunawa su Dada ita ta kirki ce, matuk'ar ya aure ta sai ta gwammace gidan yari akan nasa, da k'afafun ta zata bar gidan, Ban da baya son jefa Dada da iyayen nasa a damuwa, da cire k'imar k'anin nasa a idon iyayen su, da ko shakka babu yau zai fasa k'wan dan gujewa auren ta, sai dai girman soyayyar dake tsakanin sa da k'annin sa, da gudun b'acin ran iyayen su, dole ya bar abun a ransa, Ya mik'e ya fita ba tare da ya ma Dada sallama ba, tabi bayan sa da cewa "Watarana da kanka zaka yi mun godiyar gatan da na maka",
******************************
"Kina ganin ya dace ki tafi ba tare da kin sanar da Dada ba" Asiya ta fad'a, Bongel ta numfasa tace "Bana son abunda zai mun shamaki da tafiyata yau", "Ni sai nake ganin ba zata tsayar dake ba", Bongel ta girgiza kai tace "Bar ni kawai na tafi, idan na isa zan kirata", "Shikenan Allah ya tsare ya kai ki lafiya", "Amin", Aina'u ce ta shigo tace "Ga napep din an samu", "Yawwa Aina'u zo ki tayani da wannan" Ta mik'a mata k'aramar jakar ta,
Asiya ta mata rakiya har waje, tana cewa sai mun zo.
****************************
Dada ke had'a kayan fitar bikin Bongel, kala biyar masu kyau da tsada, komai ta saka hadda jewelries, su takalmi da mayafi, alkyabba mai kyau wacce za'a saka mata idan za'a kawota, Anty Mami itama yar' Dada ce tace "Gaskiya Dada kina ji da wannan auren, ban tab'a ganin auren da kika dage a kansa ba irin wannan", Dada tayi murmushi tace "Alkhairin ciki nake hangowa", Anty Mami tace "Allah ya tabbatar da alkhairin sa", "Amin, ki kira Basira kuzo ku tafi, ku biyu kun isa ba sai anyi gayya ba", Anty Mami tace "Toh" tana mik'ewa ta nufi sashen Inna.
*************************
Su Aunty Mami suka dawo suke sanar da Dada, Bongel ta wuce, Dada bata nuna musu bata san wucewar Bongel ba, gudun su ga laifin ta, Tace "Au na manta yau ne tafiyar ta, ku ajiye kayan goben sai a kai mata can garin su, tare da katin gayyata da sauran abubuwan da ya kamata a kai", Aunty Mami tayi dariya tace "Dada tsufa ya soma kama ki", "Kinci gidan ku" Cewar Dada, Suka yi dariya ita da Basira,
Dada mamakin tafiyar Bongel d'in take ba tare da ta sanar da ita ba, bayan sunyi kan idan ta shirya ta kirata, zata aika Hamza direba ya kai ta, duk yadda akayi wani uzurin babban yasa tasan Bongel ba zata tafi haka kawai ba, Ta tabbatarwa kanta da k'ok'arin hana zuciyarta ganin laifin Bongel.
***********************
Bongel sun iso garin malumfashi lafiya, Direba da ya d'auke su ta buk'aci ya kaita gida, ta k'ara masa kud'i, Har ya sauketa ta shiga gidan bata ci karo da kowa d'an gidan su ba, Abu ne yazo da gudu ganin ta ya rungumeta, Ramla ma yau bata je gidan aiki ba ta tashi da ciwon kai, Ta taso ta rungume ta,
Nene dake dakan yaji, ta tsayar da dakan tana duban yar'ta cike da farin cikin ganin ta, "Nene jam bandu", "Jam Bongel", Ramla da Abu suka karb'i kayan hannun ta suna shigar mata dashi ciki, Itama tabi bayan su, Nene ta ajiye dakan ta shiga ciki, ba abunda take buk'ata kamar ji daga bakin Bongel, Nene tace "Su Ramla su fita waje zasu yi magana",
Ta kai dubanta ga Bongel da cewa "Bayan tafiyar ki wasu sun zo kan neman auren ki, da kaya hadda kud'i, ina son jin k'arin bayani", Bongel ta bud'e baki da niyyar cewa Nene bata son auren, ba da amincewarta ba, sai kuma tayi shiru da tunanin gara ta fara samun Hamma Siddiku da maganar, "Kinyi shiru", Bongel ta sunkuyar da kanta k'asa tana wasa da yatsun hannun ta alamar kunya take ji, Nene tayi murmushi tace "Na manta jinin fulani kike, shikenan Allah ya tabbatar da alkhairi", Bongel a ranta tace "Kiyi hak'uri Nene da na soma b'oye miki abubuwa masu muhimmanci akan rayuwata, bana son k'ara miki damuwa kan wanda kike ciki",
****************************
Ammi itama bakin rai take wurin ganin auren Haidar da Bongel ya tabbata, haka kawai Allah yasa mata k'aunar Bongel, duk abunda tasan mace na buk'ata a kayan lefe ta had'a akwati goma sha biyar, Haka komai na buk'atar gida ta siya kama daga gadaje, kujeru, kayan kitchen da sauran kayan amfanin gida, yau take son yi ma Hajiya mariya kan su turo a kwashe kayan Hafsa, tun rasuwarta basu kwashe ba, a cewarsu tunda Rauda zata maye gurbin ta, a barsu.
*********************************
"Yanzu rashin ta idon har ta ka ga ki kirani kina cewa azo a kwashe kayan Hafsah" Hajiya Mariya ta fad'a cikin masifa, Ammi cikin sanyin murya tace "Kiyi hak'uri ba haka bane, dangin amaryar ne suke son yin jere, kwanaki na matsowa", "Dangin Amarya ko dangin tsiya, mai aikin Dada ce fa za'a aura masa, me suke dashi da zasu jera mata, ina jin k'warya da ludayi su za'a cika d'akunan dasu dan naji ance fillo ce", Ammi tace "Ni dai ba wannan ba, kuma ban kira ayi tashin hankali ba", "Tashin hankali ai kun neme shi, tunda kuka k'i jinin mu, kaya dai ba zamu kwashe ba, dan bamu da buk'atar su, aba Amarya dangin tsiya, sannan abu na k'arshe ku fara had'a kayan Irfan, zan zo d'aukar sa, ba zamu tab'a amincewa kulawarsa ta koma hannun bagidajiya dangin tsiya ba", Ta kashe wayar, Ammi ta bi wayar da kallo tana maimaita "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un", Su Hajiya Mariya na neman su zamar musu masifa,
*******************************
Washegari bayan sun gama karin kumallo wanda Bongel tayi sa ne kawai ba dan tana jin dad'in ci ba, Taje b'angaren Hamma Siddiku,
Tayi mamakin ganin sauyi a tare dashi, wanda wannan karon ya sakar mata fuska sab'anin lokutan baya, wanda sakin fuskar ba har zuci ba ne, dan yaci amfanin ta ne, Ta numfasa tace "Kayi hak'uri Hamma da tafiyar da nayi ban dawo ba", "Ah ba komai ai, na fahimce ki Bongel gashi ana shirin auren ki", "Idan ba damuwa ina son a mayar da auren kan Jabeer, bana ra'ayin wancan", Wani mugun kallo Hamma Siddiku ya watsa mata yace "Yau ga yar jakar uba, ke k'undun uban ki, ni zaki mayar mutumin banza, har na bayar da auren ki kizo da wani zance, ban da kina sakarya ga inda arzik'i yake zaki nemi tsiya, toh idan kinga ba'ayi auren ki da dan' birni ma, mutuwa kika yi, tashi ki bani wuri kafin na shure ki", Jiki na rawa Bongel ta fice.
*******************************
An shirya komai na kayan aure da za'a kawo gidan su Bongel, hadda lefe, katin gayyata, goro da sauran tarkace, Mutum biyar mata kad'ai suka shirya tafiya, Cikin motoci biyu jeep prada, kowannen su yasha sutura mai kyau da tsada, Dada wanda tasan basu da gutsiri tsoma ta zab'a, dan kar aje aga gidansu Bongel a dawo ana gulma.
Bongel dake tsakar gida tare da Nene dasu Ramla, Akwati suka ga an soma shigowa dasu, Bongel gabanta ya fad'i hakan na tabbatar mata daga danginsu Hisham, sai dai abunda ta kasa ganewa auren ta da Hisham ne ko Haidar zai tabbata, Da tunanin haka tayi saurin tashi ta shiga d'aki, Nene ma tabi bayan ta, dan tana gani tasan kayan auren Bongel ne,
Dije da fatsuma suka kasa suka tsare, suna yak'e wanda yafi kuka ciwo, ganin uban kaya ya k'ara shaida musu ba k'aramin attajiri Bongel zata aura, ko shakka babu gidan daula da hutu zata, wanda ko a mafarkin su basu zatar mata haka ba.
Su Aunty Mami basu jima ba, suka tafi, bayan wucewar su Nene ta fito, lokacin har Ramla taje da sanar da Goggo Hajjo sunzo, da sauran yan' uwan Nene na garin, mak'wabta ma sun soma cika gidan, kowa na fad'in albarkacin bakin sa, na had'uwa da yawan kayan, Nene tsoro ne ya shiga zuciyarta, su ba kowa ba, basu da komai, taya yarinyar su zata yi auri cikin irin wannan ahalin, hasalima basu da komai da zasu mata kayan d'aki, Data samu Goggo Hajjo da maganar, ta kwantar mata hankali da cewa, Allah ne yayi wannan had'in, ba iyawar su ko dabara ba, kuma su san irin gidan da suka nemi auri, ba zasu buk'aci wani abu daga garesu, kawai suyi k'ok'arin yi daidai k'arfin su, Da haka Dada taji k'arfin gwiwa,
Bongel kuwa kwana tayi juyi kan gado, da tunanin waye ango ta tsakanin Haidar da Hisham, a halin yanzu duka bata sha'awar auren d'aya daga cikin su, Haidar yana munana zato a kanta, da nuna mata k'iyayya k'arara, Hisham haushin sa take ji sosai na d'aura mata zina dan kawai cikar burin sa, hakan na nufin bai san darajarta ba, idan ya sani gara yayi hak'urin rasa ta, akan rusa mata darajar ta, Ta k'arasa da cusa kanta cikin pillow tana hawayen bak'in ciki.
OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
ASHIRIN DA HUD'U
Haidar tashin sa daga bacci kenan wanda da k'yar ya samu runtsawa a daren jiya saboda damuwa da tunanin auren Bongel da suka hana zuciyar sa sukuni, gaf da sallar asuba bacci ya d'auke sa K'aramin agogon dake kan bedside drawer ya kalla, 9:30 daidai salati yayi ya sanar da ubangiji, yana mamakin nauyin baccin da ya d'auke sa, Toilet ya shiga yayi brush ya d'auro alwala ya fito, ya kabbara sallah, yana idarwa kiran Abba na shigowa wayar sa, sai da ya kammala azkar, kana yabi kiran Abba, ya d'auka yace yazo yana son ganin sa.
Ba tare da ya tsaya wanka ba, ya nufi sashen Abba dan sam baya wasa da abunda ya danganci iyayen sa, Kamar ko da yaushe a falon sa ya same sa, Yace "Abba barka da hutawa", "Yawwa Barka", Ya zauna kujerar kusa da Abban, K'aramar jaka ya mik'a masa yace "Katin auren ka ne a ciki, gasu nan sai ka rabawa yan'uwa da abokan arzik'i, ina fatan kasan an kai lefe jiya", Haidar zancen Abba ya k'ara masa damuwa a kan wanda yake ciki, hakan na nufin auren sa da ita babu fashi tunda har an buga kati an kai lefe, taya zai fahimtar dasu wacece ita, da yasan haka da tuni ya amincewa auren Rauda, dan gara ita akan auren Karuwa, Abba ya katse masa tunani da cewa "Kayi shiru", "Toh In shaa Allah" ya furta, yana d'aukar jakar ya fita.
Kan gado ya jefar da jakar, ya shiga band'aki ya sakar ma kansa ruwan shower ko hakan zai rage masa damuwa.
*********************************
Bongel cikin bacci ta soma jin muryar Goggo Hajjo na fad'in "Ina Amaryar take?", Idonta ta mutsitssika tana tashi zaune, baccin bai isheta ba, kasancewar bata samu runtsawa ba sai bayan sallar asuba,
"Au Bacci kike yi, to tashi ga ruwa can na had'a na wankan ki", Cewar Gwaggo Hajjo, Ta yamutsa fuska alamar bata so, wanda Hajjo ta d'auki hakan matsayin kunya, Ba dan rai yaso ba, ta mik'e ta shiga wanka da ruwan turare da had'in wasu itatuwa masu gyara jiki, tayi tsarki da wasu ruwa a buta da ta bata, Ta fito tana k'yalli tana k'amshi, ta shafe jikinta da mai, ta saka atamfa d'inkin riga da skirt cikin kayan fitar biki, tayi matuk'ar kyau, yan Allah sanya alkhairi nata faman kai kawo gidan, Su Dije kuwa bak'in ciki da hassadar fal zuciyar su.
Bongel kuwa tunanin ta ya tafi kan son sanin wa zata aura, tana jin kunyar tambayar d'aya daga cikin yan' gidansu, zuwan k'awayen ta wanda sukayi primary tare, yasa ta d'an ware suna hira dasu a kai kai, Hajaru d'aya daga cikinsu tace "Bongel kin more samun miji Allah ya bamu danshin ki", Saura suka ce "Amin", A zuciyarta tace "Da kunsan irin auren da zanyi babu mai marmarin irin sa, in dai har ya kasance Haidar zan aura", Tana rufe baki, Mairo tace "Hafsah amaryar Haidar", A razane ta d'ago ta kalleta da cewa "Ina kika san sunan angon", Dariya tayi tace "Gashi nan rubuce a katin gayyata", Wasu miyau ta had'i na bak'in ciki had'i da fargabar wacce irin rayuwar aure zatayi da mutumin da ya nuna mata k'iyayya fiye da kowa a duniya, A zahiri tayi k'ok'arin b'oye damuwarta but a bad'ini damuwa ce shimfid'e a zuciyar ta.
*****************************
Alhaji Sani maigoro ya kalli Iv d'in ya k'ara kalla, Cikin tsananin b'acin rai yace "Yanzu dan cin fuska ni Alhaji Abbas zai aikowa katin gayyata hadda goro", Hajiya Mariya tace "Ka daina mamakin halayyar su, ni duk abunda zasuyi yanzu ya daina bani mamaki", Ya jinjina kai yace "Wallahi ko ta halin k'ak'a sai na cimma burina, na daina tsoro ko fargabar komai", "Haka nake so naji kace Alhaji, nima yanzu zanje na d'aura musu nawa", Ta karb'i IV a hannun sa, tana fita.
************************
Ammi na zaune tare da k'annen ta, suna shirye-shiryen yinin biki da d'auko amarya jibi idan an d'aura aure, Hajiya Mariya ta shigo kamar an jefo ta babu sallama, Kowa ya kai duban sa gare ta, Ammi tace "Sannu da z.......", Ta katse da d'aga hannu tace "Dakata ba wannan ya kawo ni ba, ina irfan shi nazo tafiya dashi", Ammi tace "Haba Mariya abun duk bai kai haka ba", Hajiya Mariya ta k'ara gyara tsayuwa tace "Ni fah babu sauran mutunci tsakanina daku, jikana nazo a bani", Anty Binta d'aya daga cikin k'annen Ammi tace "Haba Maman Hafsah, bai kamata ana jin kan ku ba, ina ce an zama d'aya", "Wallahi ba'a zama ba, idan an zama ba zasu k'i jinin mu ba, dan haka kawai a bani Irfan",
Abba ne ya shigo rik'e da hannun irfan, yace "Gashi mun yarda kulawar shi ta koma hannun ku", Kowa yabi Abba da kallo mamaki, Ammi ta bud'e baki da zumar yin magana ya mata alama tayi shiru, Ita kanta Hajiya Mariya was shocked ba haka tayi tsammani ba, jiki a sanyaye taja hannun Irfan d'in tana ficewa ba tare da ta nuna musu ba haka taso ba,
Bayan fitar ta Abba ya wuce d'akin Ammi, tabi bayan sa, sanin hakan na nufin yana son magana da ita,
Bakin gado ta same sa a zaune, ta kalle sa rai babu dad'i tace "Meyasa ka zab'i bata Irfan, kasan irin shak'uwar dake tsakanin sa da mahaifinsa, da ahalin gidan nan", Abba ya numfasa yace "Ina mai tabbata miki Irfan ba zai wuce kwana biyu a gidan su ba, zasu dawo dashi", "Meyasa kace haka?" Ta tambaya da mamaki, Yayi murmushi yace "Ki kwantar da hankali, kuma bana so ki sanar da Haidar komai, idan ya tambayi Irfan, kice yaje kwana biyu", Tace "Toh" tana gamsuwa da mijin nata, tasan ba zai tab'a kawo abunda zai rusa farin cikin su ba.
***********************************
Hajiya Mariya cike da bak'in cikin plan d'in ta bai yi ba ta dawo gida, sam ba haka taso ba, Falo ta bar Irfan wurin yan' aiki, ta shige d'akin ta cike da takaici, taso tada rigimar a bata Irfan, ta yadda hakan zai sa Su Ammi suji tsoron rabuwa da Irfan, a fasa auren da Bongel, ace ya auri Ramla dan Irfan ya zama wurin su, sai gashi tashi d'aya Abba ya damk'a mata shi, zirga zirga take a d'aki, ta kasa zama tana tunanin hanyar b'ullowa al'amarin.
***************************
Hisham walwalar sa ta rage sosai, office ma ya daina zuwa, kullum yana gida, he is depressed, abu biyu suka taro suka jagula masa lissafi Bongel na fushi dashi, ta kasa tsayawa ta fahimce shi, ganin yana gaf da rasata, duk iya tunanin sa na yadda zai hana auren yiyuwa ya kasa, Bai tab'a zaton Haidar zai amincewa auren ba jin sun had'a shimfid'a, yasan ko shakka babu saboda shi ya kasa fallasawa su Dada, anya ba zai samu Dada da kansa ya gaya mata sun had'a shimfid'a da Bongel ba, yana jin ta haka kawai zai samu mallakar ta, yayin da wani b'angare na zuciyar sa ke hana sa.
***************
Rauda ta sawa ranta ko ta wacce hanya sai tabi dan ganin ta mallaki Haidar, zuciyarta ba zata tab'a iya hak'ura dashi ba, ko a lokacin da ta soma ganin su taso ita yake so ba yayar ta ba, yanzu kuwa ba zata bari wata mace ta samu gurbi a zuciyar sa idan ba ita ba, ado tasha sai dai wannan karon ta b'oye gashin kanta da yasha attach, ta saka mayafi madaidaici dan ta fuskanci hadda yanayin shigarta ke sa yake shunning d'in ta, tayi simple makeup tayi kyau dan itama kyakkyawa ce, Mukullin motar ta, ta d'auka ta fice gidan ba tare da sanin Hajiya Mariya ba.
****************************
Haidar yau tun zuwan sa office ba abunda ya aikata, bashi da natsuwar yin komai, gashi tun shigowar sa ma'aikatan wurin ke masa Allah ya sanya alkhari wanda bai ga abun fatan alkhairi ga auren Karuwa ba, takardun dake gabansa kallon su kawai yake ba tare da ya aiwatar da komai ba, shigowar Rauda yasa ya d'aga kai ya kalli k'ofa, ta sakar masa murmushi tana shigowa cikin yanga da yauk'i kamar zata fad'i, Haidar ya d'an kawar da kansa gefe, zama tayi saman kujera tace "Yaya ina wuni", "Lafiya lau" ya amsa da sakin fuska, "Ya aiki?", "Alhamdulillah", Ta soma jan sa da hira, ya d'an sake mata, a zuciyar sa yana jin yayi amfani da ita wurin kaucewa auren sa da Bongel, ko auren ya tabbata ya rabu da ita cikin sauk'i.
*************************
Rauda cike da tsantsar farin ciki ta dawo gida, ta tarar da Irfan yana zaune falo yana kallon carton, ta jawo sa da cewa "Yaushe kazo?", "D'azu granny tazo dani", Ta shafa kansa da cewa "Bara ina zuwa", D'akin Hajiya Mariya ta nufa, cikin tsantsar farin ciki take sanar da ita, irin tarbar data samu daga Haidar yau, Sam zancen bata d'auke sa da muhimmanci ba, a ranta tace "Ya samu wacce zai aura ai dole zaki ga far'ar sa, tunda ya gujewa auren ki", A zahiri kuwa ta nunawa Raudah ta cigaba da basa kulawa, ta haka zata samu gurbi a zuciyar ta, bata son Rauda ta cire rai ga samun sa, dan ba zata yi k'asa a gwiwa ba wurin ganin ta zama surukar gidan Maishanu a karo na biyo, Ta gamsu da zancen mahaifiyarta ta fito tana murna taja Irfan zuwa d'akin ta.
***************************
Ana saura kwana biyu d'aurin aure Asiya tazo malumfashi, Bongel tayi farin cikin zuwan ta, zata samu wacce zata rik'a fad'awa damuwar ta, tana rage nauyin k'irjin ta, ana gobe d'aurin aure Asiya da sauran k'awayen Bongel na garin suka shirya fulani day, Bongel taso hana su, suka ce sai sun yi, a farfajiyar gidan suka shirya, k'awayen amarya sukayi ankon kayan fulani, kowacce rik'e da k'warya da nono, Amarya tayi ado cikin kayan fulani tayi kyau sosai, ta fito sak fulani, kid'an k'warya kawai ke tashi a farfajiyar gidan, k'awayen amarya na chashewa sai dare kowa ya watse, Bongel tun kafin su watse ta koma cikin d'aki, fargabar d'aurin auren ta gobe yasa sam bata walwala, Asiya ta fuskanci haka, ta sameta dan k'ok'arin kwantar mata da hankali.
"Bongel" Asiya ta kira sunanta, "Na'am" ta amsa tana tashi daga kishingid'en da tayi, "Nasan damuwar ki akan auren Haidar ne, ina so ki cire damuwar komai a ran ki, In Shaa Allah Haidar zai zama abokin rayuwar ki nagari, da sannu zaku so juna, baki shan jin labarin wanda sukayi auren da babu soyayya daga baya ya koma soyayya ba, baki san labarin auren Fetta da Suraj ba, sunyi aure babu soyayyar junan su, daga k'arshe suka mutu a soyayyar juna", "Kada ki had'a aurena da na wasu, nawa yasha bambam da saura, Taya kike tunanin mutumin da ya nuna mun k'iyayya fiye da kowa a duniya ya zama abokin rayuwata, ya kike tunanin k'iyayyar sa gare ni ta koma soyayya, hakan ba zai tab'a yiyuwa ba, ki rik'a auna zantukan ki a ma'auni kafin ki furta su", Asiya tayi murmushin takaici, tasan Bongel ba zata fahimce ta yanzu ba, amma tana da kyakkyawan zaton gaba zasu so juna ita da Haidar.
********************************
K'ofar gidansu Bongel ya cika da al'ummar Annabi yan' d'aurin aure, wakilan amarya da ango duka sun hallara, wanda Hamma Siddiku ne wakilin ango sai washe baki yake ganin sa cikin manyan mutane an karrama shi matsayin shi na wakilin ango, Haidar na zaune gefe d'aya, kallo d'aya zaka masa kasan ango ne daga shigar sa, kusan ince yafi kowa shiga mai kyau da tsada a wurin, blue shadda ce d'inkin babbar riga, tayi masa matuk'ar kyau, hular sa zanna ta zauna daram a kansa, sai dai sam babu walwala a fuskar sa, kowanne ango yau ranar farin cikin sa ce, sab'anin shi da aka k'ak'aba masa karuwa da sunan zata kula da tarbiyar yaron sa, ya samu natsuwa a tare da ita, ganin gidansu yasa a ransa yace "No wonder take neman maza, ta kasa rik'e talaucin ta, sai ta samu kud'i ta k'azamtacciyar hanya", Yaja siririn tsaki dashi kad'ai yaji abun sa.
*******************************
Hisham yau kwata kwata bai fito daga d'akin sa ba, balle yasa ran zuwa d'aurin aure, ba zai iya halarta ba, kwance yake k'udundune cikin bargo, zazzab'i mai zafi ya rufe sa, k'asan zuciyar sa yana jin ba zai tab'a hak'ura da Bongel ba, ko anyi auren yana da tabbacin sai ta fito ta aure sa, sanin Haidar ba zai tab'a son ta ba, ya d'arsa abu a zuciyarsa mai wuyar gogewa, yasan mu'amalar aure ba zata tab'a shiga tsakanin su ba, ga sanin halin da yayi wa yayan sa.
*******************************
Bongel tunda taji muryar Hassan na fad'in an d'aura aure, ta nemi natsuwarta ta rasa, zazzab'i ya soma rufe ta, sai dai tayi k'arfin halin rashin barin ya kwantar da ita, Farin cikin data hango zalla a fuskar mahiafiyarta da k'annenta guda biyu ba zata bari ya gushe ba, Haka tayi ta k'arfin halin danne damuwarta, k'asan zuciyarta kuwa zallar damuwa ce had'i da fargaba, yayin da gangar jikin ta ke amsar gashin zazzab'i.
****************************
Haidar daga wurin d'aurin aure, gida ya umarci drivern sa ya kai sa,
Kayan ya cire, ya rage daga shi sai boxer da singlet, wayoyinsa ya jawo da zumar kashewa, baya son damuwa, yana buk'atar keb'ewa shi kad'ai, Kiran Raudah ya shigo, ya d'auka yan sawa a kunne,
Kuka ta fashe mishi dashi tana cewa "Haba dear kasan irin son da nake maka amma ka auri wata, kana so zuciyata ta buga in mutu ko", Kuka da kalamanta haushi suka soma basa, amma ya dake yace "Am sorry kinji, ki daina kuka, ki samu kiyi bacci ki huta, will call u later", Tana shesshek'a kuka tace "Ok, Ina sonka Yaya Haidar please ka tausaya ka auren ni", "Is Ok" ya fad'a yana kashe wayar, tare da dan' dafe kansa, "Anya zaka iya kuwa", Zuciyarsa ta ayyana masa,
Rauda taji sanyi a ranta na ganin alamar soma shawo kan Haidar, duk da k'asan zuciyarta tana jin tsananin kishi da haushin auren nasa.
*NOT EDITED*
*OUM MUHRIZ*
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
ASHIRIN DA BIYAR
Yan' uwa da abokan arzik'i nata kai kawo gidan su Bongel, Abinci ya wadata, kowa yaci ya k'oshi, Ammi ta aiko da kayan abinci da komai na buk'atar hidimar bikin sanin su Bongel ba masu k'arfi ba ne, Nene farin cikin ta ya kasa b'oyuwa, duk wanda ya kalleta zai san tana cikin farin ciki, Ramla da Asiya sai kai kawo suke, suma kallo d'aya zaka musu ka hango zallar farin ciki,
Ana gama sallar la'asar aka soma shirye shiryen kai Amarya, Dan tuni motocin d'aukar Amarya suka zo, da dangin ango kusan mutum sha biyar, kowa ya k'ara shaida Bongel ba k'aramin dangi zata shiga ba, masu taya ta murna nayi, yan hassada suma suna yi.
***************************
Bongel ta rasa meke mata dad'i ko tunanin me zata yi, zuciya da tunanin ta ya cunkushe wuri d'aya, idan taga yadda mutane ke taya ta murna sai taji itama murnar ya kamata tayi Allah yayi mata rahamar yin aure, yayin da ta tuna waye mijin sai taji komai ya tsaya mata cak, ta nemi natsuwa da farin cikinta ta rasa, Zaune take shiru a d'akin Su Asiya nata faman tsokanar ta, bata tanka su, sai ma niisa da zurfin tunani da tayi,
"Ku fito, a tafi kai Amarya" Taji muryar Goggo Hajjo na fad'a, K'irjinta ya doka, tana jin tamkar ace akwai wata hanya mai sauk'i da zata zillewa auren, ba tare da tayi hurting kowa, sam bata sha'awar had'a inuwa d'aya da Haidar, Shigowar Nene ya katse mata tunani, Cikin sanyin murya da kulawa Nene tace "Bongel yanzu kin tashi daga budurwa kin shiga sahun matan aure, wani nauyi ya hau kan ki, ina so ki rik'e gaskiya da amana, ki zama mai ladabi da biyayya ga mijin ki, ki sa hak'uri a rayuwar ki kiyi ta hak'uri da addu'a, Allah yayi miki albarka ya baku zaman lafiya mai d'aurewa", Rungume Nene tayi ta fashe da kuka, tausayin yar' ta taji ya shige ta sosai, amma ya zasuyi dole dama rana irin ta yau na zuwa da aure zai raba su, ko babu aure akwai mutuwa,
Bongel na kuka haka Goggo Hajjo ta raba ta da jikin Nene, aka ja ta zuwa mota, Motocin kai Amarya suka d'aga zuwa garin katsina, Cikin yan' kai Amarya hadda Fatsuma da Dije wanda gulma zata kai su.
**************************
Gidan Dada suka soma zuwa wanda shima cike yake da yan'uwa da abokan arzik'i, Hannun Goggo Hajjo rik'e da na Bongel suka shiga gidan, ana ta faman gud'a, Bongel mamakin al'amarin ubangiji take yadda ya juye komai lokaci d'aya, daga matsayin ta na yar' aiki a gidan, yau gata ta shigo matsayin surukar su, Har gaban Dada aka kai ta, wanda Dada ta buk'aci kowa ya basu wuri, Har su Goggo Hajjo suka mik'e suka fita, Dije da Fatsuma rai bai so ba sun so jin me Dada zata ce.
Dada ta numfasa da cewa "Yau na d'aya daga cikin ranaku mafi farin ciki gareni, ganin auren ki da Haidar, ina da tabbacin had'in nan zai zama alkhairi" Bongel tayi shiru k'asan zuciyarta tana k'ara gaskata soyayyar da Dada ke mata daga Allah ne,
"Bongel kada ki dubi auren nan a matsayin wanda babu soyayya a ciki, kisa a ranki tamkar auren soyayya kuka yi da Haidar, a zamanin mu mace bata ganin mijin da zata aura sai ranar da aka kaita, kuma haka zasu yi hak'uri da juna su zauna, har su fara son junan su, Mace ita ke taka muhimmiyar rawa wurin ganin soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin ta da miji, Namiji da kike ganin sa tamkar sakarai ne akan mace, Bongel kina da komai da zaki iya jan hankalin namiji dashi, kada kiji tsoro ko shakkun rashin samun soyayyar sa, Namiji na son kula, kyautatawa, ladabi da biyayya, uwa uba ki rik'e ado, kwalliya, tsafta da girki, Su kad'ai sun isa su sa ki gina k'auna a tsakanin ku", Bongel shiru tayi tana sauraren Dada, tana kyautata zaton dan bata san irin k'iyayyar da yake mata ba ne take fad'ar haka, watak'ila da babu k'iyayya zata iya shawo kansa ta hanyar abubuwan da Dada ta lissafa, sai dai mutum irin Haidar ba irin wanda mace ke samun kansa ba ne cikin sauk'i, ita sam ma bata sha'awar zaman su inuwa d'aya, kowa yayi rayuwar su, har zuwaa lokacin da Allah zai kawo hanyar rabuwar su cikin sauk'i, Dan tana da tabbacin Haidar ba zai tab'a amsarta matsayin matar sa ba, Hisham ya goga mata bak'in tabo a wurin sa, wanda babu mai fitar da tabon sai Hisham.
Dada ta cigaba da cewa "Zan sanar dake tak'aitaccen tarihin mu, dan kisan family da zakiyi rayuwar aure, kuma kisan waye mijin ki", Bongel ta jinjina kai, Dama ta dad'e tana son sanin hakan, Hisham tana tare dashi ne, ba tare da tasan ainihin tarihin sa ba,
Alhaji Dikko Maishanu(a shafin da ya gabata nayi kuskuren suna na saka Ard'o matsayin mijin Dada) shine mijina wanda matsayin kakan Haidar yake, bafullatani ne gaba da baya, mutum ne mai halin dattako, yana da tarin dukiya wacce ya mallaka da gumin sa, dan' kasuwa ne sosai wanda kowacce sana'a tab'awa yake in dai zata kawo masa kud'i, Mu biyu ne matan sa ni da Salamatu(Inna), yaranta bakwai, ina da biyar Abbas shine babba(baban su Haidar), sai Mu'azu, Rabi'a Mami, Sadiya, Aisha, Duka yaran gidan kansu a had'e yake,
Abbas auren zumunci aka musu da Ammi wacce da mahaifinta da Dikko uwar su d'aya uban su d'aya, tun tana k'arama bata da wurin zuwa hutu sai gidan nan, haka yasa suka shak'u da Abbas har zuwa girman su, soyayya ta shigo ciki aka musu aure, Abbas duk cikin yaran Dikko yafi kowa zafin nema, wanda hakan yasan cikin k'ank'anin lokaci yayi kud'i, kowacce sana'a shima yana yi kama daga man fetur, kwangila, sarrafa masarufai da sauran su, arzik'insa ya shahara ta yadda manyan yan' siyasa suke huld'a dashi, mutane da dama kan biyo ta hanyar sa ya samar musu alfarma, yayi wa mutane silar samun aikin sun fi a k'irga ciki hadda Vice councilor na makarantar ku", Bongel a zuciyarta tace "Shiyasa Hisham yake da damar admission kenan, dan Babanshi ya samar wa VC matsayin shi",
Dada ta cigaba da cewa "Auren su da shekara d'aya Ammi ta haifi Haidar, bayan shekara biyu ta k'ara haihuwar Hisham, daga su bata sake haihuwa ba, sunyi ta neman haihuwar har sun gaji sun daina, Haidar ya taso miskila wanda bai cika son hayaniya da shiga mutane ba, Hisham ya bambamta dashi yana da son mutane, surutu da barkwanci, Duk da bambamcin halayyar su akwai shak'uwa mai k'arfi tsakanin su, kasancewar su kad'ai ne wurin iyayen su, suna k'aunar junan su, d'aya baya son b'acin ran d'aya, Makaranta d'aya aka saka su, Haidar yafi Hisham da aji, Haidar yana da k'ok'ari sosai tun shigar sa makaranta yake ta d'aya, Da suka kammala secondarya ya kai su london wanda a can sukayi degree, bayan dawowar su, Abbas ya yanke shawarar bud'e babban company, Haidar ya bada k'arfin gwiwa sosai wurin ganin ya tabbata, cikin ikon Allah ya gina katafaren company wanda ya zuba mak'udan kud'i, ya jawo Haidar da Hisham ciki, hasalima ma sunan su ya saka ma Company H&H global resources, Ya bud'e da shekara biyu Alhaji Sani Maigoro shima shahararren dan' kasuwa ne wanda abokin sa ne tun yarin ta, yazo masa da buk'atar yana so su had'a kasuwanci, ya bada kud'in sa a saka masa ciki, Girma da nauyin sa da Abbas ke ji yasa ya kasa cewa a'ah amma sam baya son had'a kasuwancin sa da kowa, daga lokacin ya zama Alhaji Sani shima yana da share a ciki, Haidar da Hisham kowane ya bada himma wurin ganin cigaban company, wanda kowannen su Abba ya cire masa share d'in sa, a shekara ana lissafi a gaya wa kowa ribar sa,
Ana haka Alhaji Sani yazo wa Abbas da tayin had'a auren Haidar da yar' sa Hafsah, Abbas bai musa ba, sai ma dad'i da yaji na ganin yana son had'a zuri'a dashi, Daga haka suka tsara Hafsah ta rik'a zuwa gida wurin Ammi, ko Haidar zai ganta su daidaita, Haka kuwa aka yi kusan kullum Hafsah na gidan, har sun saba da Ammi sosai, itama Ammi taji sha'awar Hafsah ta zama surukar ta, kasancewarta mai hankali, natsuwa da ladabi da biyayya, ba zaki ji yar' Hajiya Mariya dan ko kusa bata d'auko halayyar ta ba, Haidar a hankali ya soma sabawa da Hafsah, shak'uwa ta shiga tsakanin su daga baya ta juye zuwa soyayya, ba'a d'auki lokaci ba aka yi auren su, zaman lafiya da kwanciyar hankali ne tsakanin su, Wata tara da auren su Hafsah ta haifi Irfan, wanda yana zuwa duniya, Allah ya d'auki ranta ba tare da tasan me ta haifa ba, Irfan bai san dad'in uwa ba, bai tab'a jin d'umin mahaifiyar sa, ina so ki cike masa wannan gib'in, Haidar ya shiga tashin hankali na rashin Hafsah, ya jima bai dawo daidai ba, rashin Hafsah yasa har yanzu ya kasa bud'e k'ofa ga kowacce mace, Bongel ina so ki maye gurbin Hafsah a rayuwar Haidar, ina so ki fitar dashi daga k'uncin rashin ta, you should make him love again, ina neman wannan alfarma a wurin ki",
Bongel gaba d'aya ji tayi Dada ta d'aure ta, Tausayin Irfan ya k'ara ninkuwa a zuciyarta, haka Haidar shima taji tausayin sa dan rasa mata ta gari ba k'aramin abu ba ne, sai dai abunda Dada ke nema a wurin ta bata jin zai tab'a yiwuwa, ta sani har abada ba zata samu gurbi a zuciyar Haidar ba, ta zama tamkar mujiya a idon sa, baya ganin hasken ta, mummunan zaton da yake a kanta, ba zai bari ya tab'a ganin hasken ta ba, har ta samu soyayyar sa, "Ya Hayyu Ya Qayyum" Ta furta a ranta, ba k'aramin aiki ne a gabanta ba,
Dada ta tashi ta d'auko wani turare ta zuba mata a jikin alkyabbar ta, Tace "Allah ya haskaka rayuwar auren ki Bongel, Allah yaa baku zaman lafiya da zuri'a ta gari, Allah yasa kuyi alfahari dani sanadiyyar had'aku da nayi", Bongel a ranta ta amsa da "Amin" Ba dan tana sa ran yiwuwar haka ba.
Dada ganin lokaci yaja sosai tace azo a tafi kai ta gidan ta.
*********************************
Rauda ta fito d'akin ta tana mik'a da hamma alamar bacci bai ishe ta ba, Ta kalli Hajiya Mariya dake faman gyangyad'i kan kujera tace "Mum kema baccin kike", Hajiya Mariya ta bud'e ido da cewa "Ba dole ba, tun zuwan yaron nan bama samun bacci", "Toh ai kece kika d'auko sa Mummy, gashi kaina ciwo yake mun" Ta fad'a tana tunzura baki, Hajiya Mariya tace "Bansan haka abun zai juye ba, nayi ne dan a fasa auren ya dawo kan ki, ban da kunyar kada suce na kasa da tun ranar zan mayar da shi, amma yau zai koma", Rauda tace "Idan kika mayar dashi still zasu ce kin kasa ne just 2days yayi fah", "Yanzu ne lokacin da ya kamata na mayar dashi", "Saboda me?" Rauda ta tambaya da son jin k'arin bayani, "Ina mayar dashi gidan Haidar za'a kai sa, kinga zai hanasu sakewa yadda ya kamata balle bagidajiyar can ta samu shiga wurin Haidar", Raudah tayi dariya tace "Kaii Mummy ina son ki", Sukayi dariya.
***********************************
"Shigo da k'afar dama kiyi bismilla", Goggo Hajjo ta fad'a, Bongel k'irjinta ke wani irin dokawa, tsoro da fargaba suka dabaibaye ta, zata shiga gidan mutumin da ya tsane ta, baya ganin ta da k'ima ko kad'an a matsayin matar sa, ya rayuwarta zata kasance a auren da babu soyayya, Jifa k'afarta take ba tare da tasan ina suke nufa ba, sai jin zaman ta tayi kan lumsassan katifa, d'akin ya gauraya da k'amshin turaren wuta mai masifar dad'i,
"Gida har gida kam, Allah yasa dai a samu zaman lafiya", Ta tsinkayi muryar Fatsuma na fad'a, Dije tace "Amin dai", Sai kuma taji sun koma magana k'asa k'asa wanda ko shakka babu gulma ce.
Kusan awa d'aya tana jin hayaniya, kafin ta fara jin shiru alamun mutane sun soma tafiya, Goggo Hajjo ta zauna kusa da ita tace "Toh Bongel mun kawo gidan ki, Hak'uri da addu'a sune gaba, kibi mijinki sau da k'afa, Allah ya baku zaman lafiya, mu zamu tafi", Ta mik'e, Bongel na jin fitar ta, ta fad'a kan gado ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.
***********************************
Haidar wanda tun dawowar sa d'aurin aure yake d'akin sa, yana sak'a da warwara shi kad'ai, tunanin sa gaba d'aya kan yadda zai fitar da Bongel rayuwar sa, hayaniyar yan' kawo amaryar a kunnen sa, yayi ta faman tsaki, Bayan wucewar su ya fito kitchen ya d'auki yoghurt a fridge ya zauna a falo yana sha a natse, Sip na k'arshe yayi, ya ajiye kofin kan centre table dake gaban sa, Ya mik'e da cewa "Tun yau ya kamata ta fara sanin matsayin ta, ta fara dana sanin auren HAIDAR", Ya d'an ciza lips d'in sa na k'asa, ya nufi d'akin da yake kyautata zaton nan aka kai ta.
*******************************
Sai mu had'u gobe ko😂 nasan kun baza idanu karatun me zai fara mata dashi🤣toh sai gobe🤪
OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
ASHIRIN DA SHIDA
*BANYI EDITING BA*
Bongel wacce tun tafiyar su Goggo Hajjo take kwance tana kuka, ta kasa tsayar da kukan balle ta aiwatar da wani abu, Haidar kai tsaye ya murd'a handle na k'ofar ya shiga, Bongel jin an bud'e k'ofa ta d'ago kanta da addu'ar Allah yasa wani daga cikin yan' uwan ta ne ya dawo, idonta ya sauka kan fuskar sa, k'irjinta ya doka tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa,
"Da kin adana hawayen ki zuwa gaba zasu miki amfani", Haidar ya fad'a ba tare da ya sake kai duban sa gareta ba, Bongel wacce kanta ke sunkuye k'asa sam bata fahimci mai yake nufi da hakan ba,
Gyaran murya yayi jin shiru babu alamar taji zancen nasa, Ya nisa yace
"Duniya da kowa ya shaida an d'aura auren mu, a idon mutane kike matata, amma ki sa a ranki bakiyi aure ba, igiyar aure ko d'aya bata hau kan ki ba, dan bazan tab'a karb'ar ragowar wasu matsayin Matata ba", Ya k'arasa da cewa "And one last thing turaren da kika yi amfani dashi dan seducing d'ina, ba maza irin Haidar ake wa haka ba, ki canza salo", Yana fad'ar haka ya fice, tun shigowar sa yake shak'ar k'amshin turaren, wanda dad'in sa da k'amshin sa yasa yake jin tamkar ya manna jikinsa da nata, wanda hakan yasa yake kyautata zaton tayi amfani dashi ne dan jawo sa gareta,
Bongel hawaye ta cigaba da yi wasu na bin wasu, dama tasan tunda ta aure sa, ta bud'e kofa da wulak'anci kala kala, bata gidan sa ya mata, balle yanzu da take k'ark'ashin sa, Ganin kukan ba zai mata maganin komai ba, ta shiga band'aki ta d'auro alwala, ta soma nafilfili tana rok'on Allah zab'in alkhairi a rayuwar ta, Raka'a goma sha biyu tayi, Kafin tayi shirin bacci ta kwanta, cikin minti biyar bacci ya d'auke ta.
***********************************
Hajiya Mariya driver tasa ya kai Irfan gidan su Ammi, bata san da wane ido zata kalle su tace ta maido Irfan ba bayan tijarar da ta rik'a yi a bata shi,
Irfan da gudu ya shigo falon Ammi, tana zaune tana kallo sai ji tayi ya fad'o jikinta, Ta rungumesa da cewa "Irfan ka dawo", Ya d'aga mata kai yace "I missed you Ammi, can ba dad'i ba zan k'ara zuwa ba", Ammi tayi murmushi da shafa kansa tace "Muje wurin Abba", Taja hannun sa zuwa falon Abba
[2/14, 16:10] Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
ARBA'IN DA D'AYA
Rauda daren ranar sam bata nemi Haidar ba dan ya k'ara gaskata laulayin cikin take sosai, ganin haka ya k'ara tausaya mata yasan wahalar laulayin da Hafsah ta sha, Rauda jikinsa ta shige ta narke tana jan numfashin k'arya, Yana ta faman jera mata sannu har bacci ya d'auke su.
**********************
Bongel asubar fari ta tashi, ta gaida ubangiji, ta shiga kitchen ta had'a breakfast, Ta koma d'akinta kasancewar yau bata da lecture, wayarta ta d'auka ta soma game dan har yanzu bata fara chatting ba.
******************
Haidar shi ya kamawa Rauda tayi wanka, a cewarta idan ta mik'e jiri take gani, ya rik'ota zuwa bakin madubi, ta shirya tasa kaya, k'asan zuciyarta fal farin ciki lallai mummy nada gaskiya, meyasa ma tuni batayi ciki dama a satin farko ya bayyana dan ta rik'a samun kulawar Haidar haka, Ya rik'o hannun ta zuwa dining table, suka zauna tare, Kular abincin ya bud'e irish da sauce d'in k'oda, Rauda tayi saurin toshe hanci tana kakarin amai, yayi saurin mayar da murfin kular ya rufe, Yace "Sannu", Ta mak'e murya tace "Yawwa, bana son k'amshin shi", "It's ok", Koma can ki zauna, Ta mik'e tana tafiya kamar wacce k'wai ya fashewa a ciki, Kan kujerar falon ta kwanta tana numfashi dai' dai',
Haidar zama yayi ya ba ciki hakk'in sa, sai da yaji ya k'oshi, tukuna ya taso wurin Rauda, Langab'ewa tayi tace "Sakwara nake so", wanda da gayya ta fad'a dan kawai a musgunawa Bongel, "Ok", Ya fad'a, Ya soma kiran sunan Bongel, Bongel kamar a mafarki taji kiran kasancewar yau ce rana ta farko yana kiran sunanta daga nesa, Kusan sau uku yana kiran ta kafin ta gaskata shine, k'aramin mayafi ta yafa kan abayar dake jikinta, ta fito,
Rauda kallo d'aya ta mata taga tayi bala'in kyau, karon farko taji kishin Bongel ya soki zuciyarta, ko shakka babu tana da komai na burge da' namiji, "Anya zuwa gaba Haidar ba zai iya fad'awa soyayyarta ba", Tayi zancen zuci, Yayin da ta ba kanta amsa "In dai ina numfashi a doron k'asa bazan bar hakan ta faru ba, Haidar nawa ne ni kad'ai",
Cikin sanyin murya tace "Ina kwana?", "Lafiya" Ya amsa ba tare da ya kai dubansa gareta ba, Ya nisa da cewa "Kiyi wa Rauda sakwara", Ido ta d'ago ta zuba kansa, ba ita yake kallo ba hakan yasa bai ga kallon da take masa ba, Jin shirun ta ya juyo suka had'a ido, Dan' kawar da kanta tayi gefe tace "Kayi hak'uri amma me zai hana tayi da kanta", "Ke na umarta", "Am sorry but ba zan iya....", Bata k'arasa ba yasa yatsun sa biyu ya d'alli bakinta, Hannu tayi saurin sawa ta rik'e baki cikin azaba, Rauda dariya ta tuntsire da ita tace "Maganin mara kunya", Dariyar ta ba k'aramin b'ata ran Bongel tayi ba,
"Ya zama na farko na k'arshe da zance kiyi abu, kiyi mun gardama", Ya fad'a yana juyawa kan Rauda, Ya shafa k'asan mararta da cewa "Ki kular mun da babyna", Bongel saurin runtse idonta tayi tana jin ranta babu dad'i wanda ta danganta hakan da rashin kunyar da yayi gabanta ne, "Rauda ciki ne da ita kenan, shiyasa yace ta mata sakwara", Wani b'angare na zuciyarta yace "Ko ciki ne da ita, ba haka ya kamata yayi addressing d'inki ba", Tunaninta ya katse jin saurin kiss d'in Rauda tana ce masa sai ya dawo, Ya fice,
Bongel rai jagule ta shiga kitchen zuciyarta na ayyana mata ta koya musu hankali, da tunanin haka ta d'aura tafasar ruwan zafi, ta d'auko garin sakwara tayi shi ruwa ruwa, da k'yar ta k'ulla a leda, ta gyara tattasai guda d'aya attarugu goma, Cikin k'ank'anin lokaci ta kammala, ta sake a kula, Ta fito falo,
***********
"Kawo nan ba sai kin d'aura dining ba" Cewar Rauda cikin gadara, Banza Bongel tayi kamar bata ji ta ba, ta ajiye kan dining table, "Aikin banza kawai, ai kin gama mai wuyar tunda kika girka ina kwance", Bongel bata bi ta kanta ba, sanin mai ta shirya mata ta wuce d'aki.
Rauda ta taso hankali kwance, ta zuba abincin, Tana zuba sakwarar ta saki a plate, ta zuba miya, lomar farko taji bala'in yaji, ba shiri ta zubar, Idonta na kawo ruwan azabar yaji, "Allah ya isa muguwa" Ta fad'a tana mik'ewa cikin b'acin rai, ga yunwa sosai tana ji, breakfast d'in d'azu Haidar yaba masu gadi saura, da taci, Ruwan tea ta had'a tasha ba dan ta k'oshi ba, Ta shiga d'aki tana ayyana dole tayi maganin Bongel.
********************
"Assalamu alaikum ina mutanen gidan ba kowa ne" Cewar Dada tana shigowa falon, Bongel ce ta fito cikin ladabi ta gaishe da Dada, Ta amsa da far'a tace "Hala bacci kuke, ina ta sallama shiru", Bongel ta girgiza kai tace "A'ah ina sallah ne", "Ohh shiyasa" Cewar Dada tana zama kan kujera, Rauda ta fito tana tafiya da k'yar tana yamutsa fuska alamar mara lafiya,
"Dada ina wuni?", Ta fad'a a tsaye, "Lafiya lau" Ta amsa, Zama tayi kan kujera da cewa "Wash", "Lafiya dai", Cewar Dada, Sunkunyar da kai tayi kamar mai kunya tace "Laulayi ne mai wahala", Ba Dada ba hatta Bongel sai da tayi mamakin rashin kunya irin na Rauda, Dada tsabar mamaki kasa cewa tayi komai, Rauda jin bata ce komai ba, a zuciyarta tace "Dama nasan ba sona kike ba, tunda ke kika aura masa Bongel, toh sai na haihu cikin gidan nan sai dai ki mutu da bak'in ciki", A zahiri kuwa murmushi tayi tace "Dada ga abinci nan kan dining", Da gangan tayi, Bongel gabanta ya fad'i tana tsoron Dada taci, Dada tace "Wacce cimar kuka yi, kinsan ba kowane girki nake ci ba", "Sakwara ce nasan kina sonta, lokacin ina ganin Ya Hafsah na aika miki", Dada ta jinjina kai tace "Tabbas hakane", Rauda tayi murmushi tana jifan Bongel da shegen kallo, Tace "Ki kawo Dada nan ko, zai fi mata dad'in ci", Bongel babu damar cewa a'ah, ta kwaso kulolin ta ajiye gaban Dada, Ta bud'e ta zuba ta mik'a mata, Dada tun daga yanayin sakwarar zuciyarta ya bata Rauda ce tayi,
Tana kai bakinta taji bala'in yaji, ta zubar tana cewa a bata ruwa, a rud'e Bongel ta d'auko ruwa ta kawo mata, Sai da tasha ta natsa, Ta kai dubanta ga Rauda tace "Rauda wane irin girki ne haka", Ta marairaice fuska tace "Bani nayi ba Dada, Bongel ce wallahi haka kullum take mana girki, ba dad'i ko yaji yayi yawa", Dada kallonta ta kai ga Bongel da mamaki, Bongel kanta ta sunkuyar k'asa tana wasa da yatsun hannun ta, bata san me zata cewa Dada ba kunya da nauyinta taji sun dabaibayeta, Dada tana kallonta ta fuskanci akwai wani abu a k'asa ko shakka babu ba zatayi girkin nan a banza ba, zaman da tayi da ita tasan wacece ita, Amma a zahiri tace "Bongel garin yaya haka ta faru?", Cikin sanyin murya tace "Kuskure aka samu", "Toh ayi k'ok'arin gyarawa", Ta amsa da "In Shaa Allah"
Rauda dad'i taji a ranta, tana ganin ta tozarta Bongel, ta rage mata k'ima a idon Dada, wanda bata san ko kad'an k'imar Bongel d'in bata ragu ba, sai ma ta Rauda da Dada ke ganin tsantsar makirci a tare da ita, Dada bata jima ba ta koma b'angaren Ammi.
************************
"Dan Allah me na muku kuka zab'i kawo ni nan" Cewar Ihsan tana kuka, Garadan maza biyar zagaye da ita, kowannen su d'auke da makami, Babban cikinsu ya fashe da dariya yace "Saurin me kike zaki sani k'aramar yar' iska", Ya nufota yana nuna mata wuk'a, tuni jikinta ya d'auki b'ari, "Ina wayarki?" Ya daka mata tsawa, Hannu na rawa ta mik'a masa, "Bud'e password", Ta bud'e, Ya karb'a ya shiga photos ya goge gaba d'aya hotonan banza da video na Hisham da tace tana dasu, Ya mik'a mata wayar da cewa "Su kenan ko kina dasu a wani wuri", "Wallahi su kenan", "Na rantse da Allah idan naji labarin akwai wasu sai na farka cikin ki, kuma fad'awa wani abunda ya faru daidai yake da tonon asirin ki, had'uwarku ta k'arshe office d'in Hisham ya d'auki video bad'alar da kuke yi ba tare da kin sani ba, su zamu yad'awa duniya", Ihsan kuka ta fashe dashi na bak'in ciki, "Ku d'auketa ku mayar da ita" Ya umarci yaransa, D'aya daga cikinsu ya jawo ta da k'arfi, Suka kaita mota, bayan sun rufe mata ido,
A saman titi suka jefar da ita, ta fad'i ta gurje da kwalta, hannunta ta kalla dake jini, Tace "Na rantse da Allah Hisham sai na d'auki fansa a kanka, bazan tab'a giving up ba, sai na cimma nasara a kanka"
**********************
Hisham dariyar farin ciki yayi da labarin ya kawo masa, ya umarci yaron nasa ya turo masa account number ya k'ara masa kud'i, "Ihsan Ihsan Ihsan baki san waye Hisham ba, mutumin da can go to any extent dan cikar burin sa" Ya fad'a da yin shu'umin murmushi, Ya sauke ajiyar zuciya da cewa "Saura Bongel, kin kusa zama mallakina", Ya k'arasa yana jin son tozali da ita, kwana biyu bai sakata a ido ba, Tashi yayi ya shiga band'aki ya watsa ruwa, ya saka english wears, yayi combing gashin kansa, ya fesa turaruka, Hisham shima ba dai kyau ba, sai dai yayi kyan dan' maciji,
A falon ya tsaya yana tunanin ina zai ga Bongel, Rauda tace ta fito, Suka kalli juna tace "Hisham", Yace "Rauda manyan gari", "Ai kune manya Hisham", Yayi dariya yace "Ina Bongel", Kafad'a ta d'age tace "Oho", Murmushi yayi yace "Kuna gida d'aya", "Toh ina ruwana da ita", "Idan na fuskanta bakya son ta", "Taya zan so ta kuwa, ka tab'a ganin kishiya taso kishiya ne", Yayi dariya yace "Hakane", Zuciyarta ta soma ayyana masa wata dama ce ya samu na yin amfani da Rauda dan cikar burin sa, but kafin nan bara ya fara tozali da muradin ransa.
*Gaskiya yan wattpad vote da comment d'inku na k'asa zan muku yajin aiki*
OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
ARBA'IN DA BIYU
Hisham yayi gyaran murya yace "Ko zaki kira mun ita", Da kallon mamaki tabi sa tace "Na kira maka ita fah kace", Kansa yayi nodding yace "Yes", "Ta maka me?", Shu'umun murmushi yayi yace "Me kike ci na baka na zuba", Rauda ta tab'e baki tace "Uhmm ni ba zanje kiranta ta raina ni", "Ohh Rauda kina nan da halin ki", "Hali zanen dutse" Ta fad'a tana gyara zamanta kan kujera, "Please Sexy lady", Dariya tayi sunan ya tuna mata lokutan baya, Ta mik'e da cewa "Kaci daraja d'aya", Ya d'aga mata gira da cewa "Yawwa Matar Yaya", Tayi murmushi sunan ya mata dad'i,
*******************
"Kizo kinyi bak'o" Rauda ta fad'a kai tsaye, ta juya ta wuce ba tare da ta jira amsar Bongel ba, "Bak'o" ta maimaita da mamaki, sanin bata da kowa namiji da zai kawo mata ziyara, Hijab ta saka iya gwiwa ta fito, Hisham ido ya zuba mata yana ganin ta k'ara masa kyau, Rauda kanta ya k'ulle ganin irin kallon da Hisham ke yiwa Bongel, kallo ne da kowa ya gani zai fuskanci na so,
Bongel da son katse masa kallon tace "Hisham kaine bak'on" Ya sauke ajiyar zuciya da cewa "Eh", "Ina fatan lafiya", "Kema kinsan lafiya kad'ai zata kawoni gare ki", Taja numfashi tana kawar da kanta gefe, gaba d'aya jin ta take a takure, sam bata maraba da zuwan nasa, Kallonsa ya kai kan Rauda yace "Matar Yaya ko zaki dan' bamu waje", Kafad'a ta d'age with i don't care ta shige ciki, a zuciyarta tana sak'a ko shakka babu akwai wata a k'asa tsakaninsu.
"Ina da tabbacin bakya jin dad'in zaman ki da Rauda", Hisham ya fad'a yana kafeta da ido, "Kaga Hisham dad'in zamana da ita da rashi bashi bane yanzu, ka fad'a mun meke tafe dake", "Farin cikin ki shine damuwata Bongel, i want the best for you, baki cancanci rayuwa irin wannan ba, you need to move on, kina buk'atar wanda zai baki so, kulawa, yasan daraja da k'imar ki wanda ba zaki tab'a samun hakan a zaman ki da Haidar ba", "Hisham Dan Allah daga yau ka fitar da kanka cikin rayuwar aurena, nagode da kulawar ka, amma ina so ka sani kusancinmu da kai tamkar k'ara wutar k'iyayya ta ce a zuciyar Haidar", "Ke kuma kina gudun k'iyayyar sa right" Bakinsa ya sub'uce ya fad'a cikin b'acin rai, D'agowa tayi ta kallesa da mamakin ganin b'acin rai shimfid'e kan fuskar sa tace "Ban gane ba", Yayi saurin cewa "Ina nufin bakya so k'iyayyar ta cigaba kamar yadda nima bana so", Kai ta masa nodding tace "Yes", Wani zafi na kishi yaji a zuciyar sa, A zahiri yace "A duniya ina jin nafi kowa son ku daidaita da Haidar, amma sai dai sanin halin sa ba zai tab'a canza ra'ayi a kan ki ba, so ki....", Da hannu ta dakatar dashi da cewa "Please Hisham lets stay away from each other, i think keb'ancewar mu babu wata fa'ida" Tana fad'ar haka ta wuce, ta barsa tsaye yana cizon lips ransa a b'ace ganin bai samu nasarar sake jefa Bongel cikin wasi wasi da son rabuwa da Haidar,
Bongel kuwa zantukan Hisham ba abunda suke sai b'ata ranta, hakan yasan ta zab'i nisanta kanta dashi da kuma gujewa zargin Haidar, duk da tasan ba shi zai sa ta wanke kanta daga zargin sa ba, "Ya Hayyu Ya Qayyum", Ta fad'a tana zama bakin gado.
*************************
Bayan sati d'aya
A cikin sati d'ayan kullum da kalar tsirfan da Rauda ke zuwa dashi, ita a dole mai ciki, Gaba d'aya aikin gidan ya koma kan Bongel, tayi girki ta gyara gida, tayi hidimar Irfan, Rauda ta nad'e k'afa a dole laulayin ciki take, a cewarta ta daina aikin wahala dama tana neman mararraba da aikin, Haidar yaso kaita asibiti tace "A'ah Mummy ta kawo mata maganin hausa", Haka yasa ya k'yale ta.
*****************
Dawowar sa daga office kenan, Ya kalli d'akin nasa kaca kaca, ya kai dubansa kan gado kayan baccin Rauda zube a kai, D'akin tsawon kwana uku bai samu gyara ba, dama shine mai gyarawar tunda ta fara laulayin cikin, kwana ukun bai samu natsuwar kansa ba, Siririn tsaki yayi a ransa ya ayyana bayan laulayi hadda lalaci a al'muran Rauda, Fitowa yayi dan ba zai iya zaman d'akin haka ba, D'akin Bongel ya nufa kiranta tazo ta gyara,
Tsaye take bakin gado, tana tattara gashin ta da ta gama tsefewa, jikinta sanye take da top mai gajeren hannu, ta saman kana hango dukiyar fulanin ta, skirt dake jikinta shima ya zauna d'as ya fiddo madaidaita mazaunan ta, Haidar ido ya zuba mata yana k'arewa surarta kallo, wani abu yaji yana masa yawo tun daga kansa zuwa tafin k'afar sa, yayin da tsigar jikinsa ke tashi, Bongel juyowar da zatayi suka had'a ido, Idanunta cikin nasa ya sake jefa sa a wani yanayi, Tsintar kansa yayi da k'arasawa cikin d'akin, yazo gaf da ita, saurin ja baya tayi, Taji ya fisgota ta fad'u kan k'irjinsa, hannun sa ya kai kan gashin ta, ya shafa har zuwa wutsiyar gashin, santsi da laushi yaji wanda ya cigaba da shafa gashin nata, yayin da k'amshin turarenta mai dad'i da sanyi ke ziyartar k'ofofin hancin sa, Bongel jikinta ya mutu, ta kasa aiwatar da komai, sai mamaki daya cunkushe zuciyarta anya kuwa Haidar da ta sani ne, a yadda ta lura kamar baya cikin hayyacin sa,
Haidar komai yana yin sa ne ba dan son ransa ba, sai dai he can't help it yana bin zuciyarsa da gangar jikin sa ne, kwata kwata bai san meye a kansa ba, muradinsa kawai tarayya da Bongel d'in, Hannunsa ya kai kan dukiyar fulaninta, tayi saurin runtse idonta gam tana jin yar a jikinta, Haka ya dinga sarrafata daga tsaye har suka kai kan gado, Yau kam taji wasu zantukan daga bakinsa wanda tayi imani da Allah ba cikin hankalin kansa yake fad'ar su ba, Haidar ya jima yana more Bongel, sai da ya samu gamsuwa da natsuwa tukuna ya barta, ya koma gefe yana sauke ajiyar zuciya,
Bongel bargo taja ta rufe fuskarta, kunya sosai take ji kamar k'asa ta bud'e ta shige, Haidar ya kai dubansa gareta, Tsaki yaja da cewa a ransa "Meke damun ka Haidar?, kasan dawa ka gama mu'amala yanzu, Bongel yarinyar da k'anin ka ya had'a shimfid'a da ita", Hannu biyu yasa ya dafe kansa cikin tsantsar b'acin rai da takaici, baisan meke damun sa ba, bai san me yake shiga kansa ba, bai san meyasa surar jikin yarinyar ke rud'ar sa ba, ko shakka babu dasu take jan hankalin maza, Ya mik'e ya bar d'akin zuciyarsa na k'unar bak'in ciki idan ya tona Hisham ya had'a shimfid'a da ita.
Bongel jin fitar sa ta tashi ta tsaftace jikin ta, wannan karon bata jigata sosai ba, kamar farko, Doguwar riga ta saka, ta gabatar da sallar magrib, a sujada ta rok'i Allah zab'in alkhairi a rayuwarta, Bayan ta kammala tunanin abunda ya faru tsakaninsu da Haidar yazo mata, tasa hannu biyu ta rufe fuskarta tana jin kunya kamar yana gaban ta,
Haidar d'akinsa ya koma yayi wankan tsarki, yayi sallar magrib ya fito falo, Har lokacin Rauda na d'akinta tana bacci, Irfan yace yaje ya kira Bongel tazo ta gyara d'akin sa, Yaron yace "Toh" ya nufi d'akin Bongel, Irfan na sanar da ita ba musu ta biyo bayan sa, Ganin Haidar zaune falo ta sunkuyar da kai cike da kunya ta wuce, Haidar ma ya d'auke kai tamkar bai gan ta ba,
Rauda ce ta fito tana hamma, alamar tashin ta baccin kenan, "My dear ka dawo", Banza yayi tamkar bai ji ta ba, Kusa dashi ta zauna tace "Am sorry kasan masu ciki da bacci", "Hadda lalaci a al'muran ki Rauda, komai ace ba zaki iya ba", Ya fad'a cikin takaici dan gani yake ita taja masa yaje ya sadu da Bongel, data gyara d'akin ba zai je kiran ta ba, B'ata rai tayi tace "Haba My dear wane irin lalaci kuma, wallahi ina shan wahala fah, dan ma ina da juriya", Bai tanka ta ba saboda takaici ya maida kallonsa kan tv, Kanta ta d'aura kan kafad'a tana masa salo, sam hakan bai burgesa ba, kawai ya k'yaleta ne.
***********************
"Allah yayi wadaran naka ya lalace yar' ka na auren hamshak'in mai kud'i amma baka daina cin tuwon dawa ba", Cewar Hamma Siddiku yana bud'e kwanon abincin da Dije ta ajiye gaban sa, Ta tab'e baki tace "Uhmm dama ai naka sai naka, yaushe rabon da kaga Nene taci tuwon dawa gidan nan", "Hakane ko shakka babu, nasan maganinsu ina ce ni nayi sanadin auren wallahi basu isa su samu su manta dani ba", Ya mik'e yana kakkab'a malun malun sa, Dije tabi bayansa da kallo cike da farin cikin samun nasara, tsabar makircin su yasa tayi masa tuwon dawa, amma duk aka aiko kayan abinci daga wurin su Dada sai Nene ta d'ibar musu, Ita da Fatsuma bak'in cikin ganin Bongel ta samu gidan hutu da arzik'i yasa suka shirya makircin, kayan abincin suka sayar, kowacce tasa kud'in adashe.
Nene na bakin murhu tana hura wuta, Ramla na dakan kayan yaji, Hamma Siddiku ya shigo kamar an jefo sa, Cikin ladabi Ramla ta gaishe sa, ya jefa mata tsiyacin kallo kana ya juya kan Nene, "Munafuka mai bak'in hali, wato ni ban muku bak'in cikin silar samun arzik'i ba ni zaku yi ma, komai kun kama kun kanannad'e hatta kayan abinci gidana sai dai muci tuwon dawa, amma gashi ke tuwon shinkafa kike girkawa", Ya nuna tukunyar dake gabanta, Mamaki yasa Nene kasa cewa komai, ko sati ba'ayi ba, ta raba kayan abincin da Dada ta aiko musu rabi, ta basu rabi, toh me yake nufi da zantukan sa banda son ganin laifi da k'iyayya, Ya katse tunanin ta da cewa "Wallahi ku bini a hankali ko kowa ya rasa", Yana fad'ar haka ya bula rigar sa ya wuce, Tunanin kalmar sa ta k'arshe ta d'aurewa Nene kai, me yake nufi da hakan, Sunan Allah ta ambata da neman tsarin da dukkan sharrin su.
****************************
"Wannan ce semester ta k'arshe da zaka kammala lecturing ya kamata ace mun soma tunanin hanyar b'ullowa Alhaji Sani na zance basa share d'insa", Cewar Abba, Haidar ya jinjina kai yace "Hakane nima na soma tunanin, dan wata d'aya ya rage nayi handing over", Abba yace "Gud, sai muyi tunanin hanyar da ta dace", Haidar yayi nodding kai tace "I will try my best wurin ganin hakan bai kawo matsala ko rabuwar kai ba", "Allah ya taimaka" , Yace "Amin", Suka d'auka zancen wani business na gina borehole.
***********************
"Cikin Rauda bai isa asan me zata haifa ba?" Alhaji Sani ke tambayar Hajiya Mariya, Tayi dariya tace "Banda abun ka Alhaji cikin da ko wata biyu bai rufa ba", "Ahtoh na k'osa naji ne kinsan itace bangon jinginar mu yanzu", Hajiya Mariya ta jinjina kai tace "Hakane amma In Shaa Allah namiji ne, kamar yadda Hafsah ta ajiye da' namiji, haka Rauda itama", Alhaji Sani yace "Allahu yasa", "Amin", "Kawo mun abinci", Tace "Toh" ta tashi.
OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
ARBA'IN DA UKU
SHIN KIKA YI REGISTER DA TOP TEN KUWA, IDAN BAKIYI BA TO KI GARZAYA, LITTAFAN HAR GUDA 7 DAGA HAZAK’AN MARUBUTA NA KUNGIYAR HASKE, DA YADDA ZAKI KOYI GIRKI KALA KALA, DA SANIN ABUBUWAN K’ARUWA DA DAMA, DUKA AKAN NAIRA D’ARI BIYAR KACAL
HANZARTA KI BIYA
TA WANNAN BANKIN ZENITH BANK
2083371244 AISHA M SALIS
TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR +447891142004 KO KATIN WAYA TA WANNAN LAMBAR 07043079298
Hamma Siddiku ne ya shigo gida rai a jagule, fuskar sa sam babu far’a, Dije ta tarbe sa da cewa “Lafiya dai Baban sa’ade”, Ya sauke ajiyar zuciya yace “Ina fah lafiya, daga gidansu mijin sa’ade ne suka turo, wai gobe zasu kawo kayan saka lalle”, Dije tace “Toh meye abun damuwa, ina ce abun farin ciki ne”, “Ke wataran sam baki hange nesa, sanin kanki ne bamu tanadi komai na bikin nan ba, ko cokali bamu ajiye mata ba”, Dije taja numfashi tace “Hakane yanzu meye abun yi?”, “Zanje na samu Bongel na d’aura mata nauyin kayan d’aki”, Dije baki ta tab’e tace “Baban Sa’ade da abu kake, wanda kayan abinci ya gagara samu, kayan daki zai samu”, Hannu ya d’aga mata yace “Barni dasu kawai, wannan ya zamar mata wajibi, ba zan musu silar arzik’i suci su kad’an ba wallahi, ba zai yiyuwa ba”, Ya fad’a yana girgiza kai, “Toh shikenan”, Dije ta fad’a dan a ganinta abu ne da bai yiyu ba, kayan d’aki ai ba wasa bane, duk da cewar Bongel na aure gidan daula,
Ya katse tunanin ta da cewa “Bani hula ta, yanzu ma zaan tafi”, Dije ba musu ta d’auko ta basa, Ya saka ya fice gidan.
*********************
Bongel yau da wuri ta dawo kasancewar lecture d’aya tayi, Tana dawowa ta shiga kitchen yin girki dama na safe kad’ai tayi, Rauda na kwance kan doguwar kujerar falo ta d’aura k’ada d’aya kan d’aya, wayarta a hannu tana sana’ar wato chatting, Tana labartawa k’awayenta irin kulawar da take samu daga Haidar, da hutun rashin aiki tunda ta samu ciki, suna k’ara zugata da fasa mata kai, tana jin ba wanda ya kai ta.
****************
Hamma Siddiku masu gadin sun barsa ya shigo jin cewar shine mahaifin Bongel, Kai tsaye falon gidan ya shiga ba tare ya jira an masa iso ba, Kallo d’aya Rauda ta masa tasan daga dangin Bongel ne, ta yatsina fuska kamar taga kashi, Ganinta da yanayin kayan dake jikinta yasa ya koma baya, Rauda ta mik’e da cewa “Ya’ tayi auren kud’i, ana sintirin zuwa gidanta dan’d’anar arzik’i”, Kalmar ta sauka kan kunnen Bongel da fitowar kitchen kenan, K’ofa ta kalla sanin ko shakka babu maganar tana da alak’a da ita, Hamma Siddiku ta gani tsaye ya juya baya, Mamakin zuwan sa tayi amma a zahiri kallonta ta maida kan Rauda tace “Ki iya bakin ki, zan iya tolerating a kaina but banda iyayena”, Ganin zallar b’acin rai shimfid’e kan fuskar Bongel, Tsaki kawai Rauda tayi ta shige ciki, dan taga alamar tayi wata magana Bongel d’in zata iya kai mata duka,
“Hamma sannu da zuwa”, Cewar Bongel da fulatanci, Ya amsa yana shigowa, Kan kujera ya zauna da cewa “Wash wannan lumsassun kujera haka, ai mutum ya samu irinta bashi ba ciwon baya”, Bongel tace “Bara na kawo maka ruwa”, “Idan ruwa ne ina ce su na baro gida, lemo da abun motsa baki zaki kawo mun”, Ta amsa da “Toh” jiki sanyaye, ko bai fad’a ba su tayi niyyar kawo masa, tace ruwa ne hausar bahaushe,
Minti biyar ta dawo d’auke da tray mai shak’e da kayan motsa baki, Hamma Siddiku ya tank’washe hannun riga ya soma fisgar cinyar kaza, “Wannan yarinya anyi muguwa, kina cin dad’i haka kin manta da iyayen ki”, Ya d’auki kwalin lemo ya bud’e yana sha, Bongel na gefe zaune tana addu’ar kar Allah ya jefo Rauda ko Haidar su k’ara rainata, sam bata son abunda zai k’ara jawo mata zubewar mutunci wurin Haidar d’in, Hamma Siddiku sai da yaci ya k’oshi, yayi gyatsa, Yace “Waii ina ma mutum zai rik’a samun haka kullum”, Bongel bata ce komai ba, dan duk ji take a takure, a zuciyarta tana addu’ar Allah yasa yace zai tafi,
Gyaran murya yayi yace “Nazo ne na sanar dake batun auren Sa’ade saura wata d’aya kacal”, Bongel farin ciki ya bayyana kan fuskarta, a tunaninta Hamma Siddiku ya fara sonta da har yazo sanar mata da zancen bikin, Tunaninta ya katse da cewa “Kinfi kowa sanin bamu da k’arfi, bamu da kowa mai shi yanzu sai ke, dan haka ya zama dole kiyi kayan d’aki”, A razane ta d’ago ta kalli Hamma Siddiku, Yace “Kallon uwar me kike mun, mai bak’in hali wallahi dole ne kiyi, meye amfanin yi miki silar auren ba dan muma mu samu ba, toh bari kiji ko kiyi kayan d’aki ko billahil lazi ki had’u da mummunan b’acin rai”, Yana fad’ar haka ya mik’e ya fita yana kufar baki,
Bongel kasa tashi tayi a wurin, sai kanta data d’aura kan kujera, tana ambaton sunayen Allah, wane irin tashin hankali ne k tunkaro rayuwarta, “Ya Allahu ka kawo mun sauk’i cikin al’amurana”, Ta fad’a tana jin zuciyarta ta mata nauyi, Banda son zuciya irin na Hamma Siddiku ya zai ce tayi kayan d’aki ko itace mai kud’in ba wanda take aure ba sai kai, basu tab’a damuwa da wane hali take ciki ba, ya zamanta da Haidar d’in yake, ya lafiyarta, amma yazo mata da buk’ata mai girma wacce tafi k’arfinta, ko akwai soyayya da zaman lafiya tsakaninta da Haidar buk’atar tayi girma balle babu, “Ya Hayyu Ya Qayyum” Take maimaitawa,
Rauda dake lab’e tana ji, Kai ta jinjina tace “Hmm lallai mutan k’auye ba hankali”, Tayi tsaki, ta shige d’akin ta,
********************
Hamma Siddiku a k’ofar fita suka ci karo da Haidar zai shigo, Haidar ya gaishe sa cikin ladabi, Ya amsa tamkar zai gurfana gaban sa, Haidar kunyar haka yaji, Ya bud’e briefcase d’insa dake shak’e da kud’i wanda yaso tsayawa banki ya saka baiyi ba, Ya zaro bandir na 500 ya basa, Hamma Siddiku ya shiga godiya, Ya tafi yana washe baki yazo a sa’a, Yana fad’in “Yaro mai alkhairi amma shegiyar yarinyar nan na hana sa yi mana, sai nayi maganin yar’ banza”, Yayi k’wafa,
Haidar har ya shigo falon Bongel bata ji ba, kallonta yayi yana mamakin yanayin ta wanda yake kyautata zaton yana da alak’a da zuwan Hamma Siddiku, Tamkar zaiyi magana, zuciyarsa ta hana sa da cewa “Meye damuwar ka”, D’akinsa ya wuce, ya ajiye jakar, Ya fad’a toilet ya watsa ruwa, A lokacin Rauda ta shigo tana jiran fitowar sa,
Haidar bai jima da shiga ciki ba, Bongel ta tashi ta koma d’akin ta, Tunanin ta wa zata sanarwa ta rage nauyin dake k’irjinta, ba zata iya sanar da Nene ta tada mata hankali ba, Asiya tazo mata a rai, ta d’auki waya ta soma kiran ta, Bugu biyu Asiya ta d’auka, suka gaisa, Ta zayyane mata komai tana k’arashewa da hawaye, Cikin tsantsar damuwa Asiya tace “Nima kaina ya k’ulle Bongel, wannan al’amari nada girma, amma addu’a zamu dage da ita, bata bar komai ba”, Bongel tace “In Shaa Allah” Sukayi sallama ta kashe wayar, Shigowar Irfan ta koya masa assignment ya rage mata damuwa sosai, dan daga assignment d’in ya soma yi mata hirar school, Duk da tana fargabar shigowar Haidar ya gansu tare, bata ce Irfan d’in ya tafi ba.
****************************
Haidar kamar kullum ya gama shirin sa na office, Rauda na zaune bakin gado tana bin sa da kallo, tana yaba tsantsar kyawon sa wanda take jin sabon kishin sa, ya zama dole ta hana kowacce mace rab’ar sa, ta gaggauta fitar da Bongel a rayuwar sa tun kafin soyayyarta ta d’arsu zuciyar sa take ayyanawa a ranta,
Briefcase d’in sa ya d’auka, ga mamakin sa yaji ta rage nauyi, bud’ewa yayi, Idonsa ya zaro ganin babu fin rabin kud’in, Dubansa ya kai kan Rauda yace “Ina kud’in dake jakar nan”, “Haba my dear ina zan sani nikam, ai ni banma san kud’i ka shigo dasu ba”, “Ke bana son wasa” Ya fad’a cikin dakewa”, “Allah ban d’auka ba”, Ta fad’a itama babu alamar wasa, “Toh wa zai shigo d’akin nan ya d’auki kud’i”, Rauda tace “Ai bayan ni akwai mai shigowa”, “Bongel” Ya furta,
Rauda ta girgiza kai tace “Yawwa ka bincike ta”, A hasale ya nufi hanyar fita, Rauda tabi bayansa, Bongel na gyarawa Irfan takalmin sa, Taji tsayuwar Haidar a kanta “Ke ina kud’ina”, Da zallar mamaki ta d’ago ta kallesa, Shima ita yake kallo ya had’e girar sama da k’asa, Murya a natse tace “Kud’i kuma”, “Malama kar ki kawo mun rainin hankali, ina kud’in da kika d’auka”, Dariya abun yaso ya bata, Tayi gajeren murmushi da cewa “K’iyayyar har ta kai ka tuhumeni kan d’aukar kud’in ka”, Kallon tsaf yake bin ta dashi, sai dai bai ga alamar rashin gaskiya a tare da ita ba, Har ya juya zai koma d’aki Rauda tayi saurin cewa “Ai zaki iya d’auka, tunda kina buk’atar kud’i, ina ce jiya babanki yazo kan buk’atar kiyi wa k’anwar ki da za’ayi wa aure kayan d’aki”, Cak Haidar ya tsaya yana juyowa ya zuba idonsa kan Bongel, Mamaki da kunyar zancen Rauda yasa jikin Bongel sanyi, sam bata so su san wannan al’amari ba, Kanta ta sunkuyar k’asa tana jin tamkar k’asa ta rufe ta shige ciki,
Tunanin ganin Hamma Siddiku da yayi, da kuma
yaga kud’in wanda ko shakka babu shi ya sanar da Bongel, Kunya da muzanta da ya gani a tare da Bongel yasa ya k’ara gaskatawa, Ya soma tab’a hannu da cewa “Wow so shine kika yi deciding sace mun kud’i”, Kanta ta d’ago a razane tace “Wallahi ban d’auka ba, ban tab’a kud’in ka ba”, Hannun ta ya jawo da k’arfi zuwa d’akinta,
“Nasan baki isa fita dasu ba tsakanin daren jiya zuwa safiyar yau, so suna nan, fito mun dasu”, Ya fad’a cikin karaji, Bongel cikin b’acin rai tace “Nace ban d’auka ba, idan baka yarda ba, ka duba d’akin mana”, Gaf da ita ya matso, tana jan baya har ta kai bango, Kansa ya buga kan nata, Ya saka idonsa da suka koma kalar ja cikin nata, hancin sa na gogar nata, Numfashin junansu na cud’anya, Yace “For the last time ina kud’in da kika d’auka”, Cikin zafin nama ta ture sa da cewa “Ban d’auka ba”, Baya yayi cikin k’unar zuciya yake dubanta, Kana ya juya zuwa drawer kayanta ya soma fito dasu d’aya bayan d’aya, sai da ya fitar da duka kayan drawer, ya koma akwati, ya fiddo kayan sai ga kud’in a k’ark’ashi, Wani mugun kallo ya juyo ya watsa mata, Bakinta ta bud’e cikin tsabar tsoro, had’i da kid’ima,
Rafa d’aya ya d’auko ya jefa mata a fuska, Yace “Meye wannan nace meye wannan?”, Kanta take girgizawa hawaye na ambaliya saman fuskarta,
“Wacce irin zuciya ce dake da babu imani ko tsoron Allah a ciki, meyasa baki da wadatar zuci sai kin kai hannun ki ga tab’a abun wani, a yau darajar ki ta k’ara zubewa a wurina, tsanarki ta ninku a zuciyata, kin had’a abu biyu da nafi tsana a rayuwata aikata zina da sata, ya zama dole mu raba inuwa dake, had’uwar mu wuri d’aya sam bai dace ba, baki cancanci zama matata ba”, Ya k’arasa yana fisgota da k’arfin bala’i, Hannunta ta fisge cikin zafin nama tace “Ya isa Haidar, baka yi k’arya ba, bamu dace da juna ba, haka bamu cancanci zama inuwa d’aya ba, na gaji da dukkan zargin ka a kaina, idanuwan ka sun riga sun gushe akan gane gaskiya, kana tunanin kud’i suna da muhimmanci da daraja a rayuwata da har zan kai hannuna ga wanda ba mallakina ba, toh kayi kuskure Haidar, ban ce dole ka yarda dani ba, dan nasan ba zaka yarda ba, amma ina so ka daina danganta ni da abubuwa mafi muni zina da sata, idan ba haka ba ka shirya tsayuwa gaban ubangiji dan bada shaidar hakan”,
Haidar da kallo yake bin ta kamar mai son gano wani abu, sai kuma ya juya, Kud’in dake cikin jakar gaba d’aya ya kwashe ya fita, Rauda dake lab’e bakin k’ofa tana jin komai tayi saurin zabura da cewa “Uhmm ka fito”, Kallonta yayi tsaf kana ya wuce, Tabi bayansa tana cewa “Dama nasan ita ta saci kud’in nan, ita kuwa wane irin mutuwar zuciya ne, sata tabb”, Haidar bai tanka ta ba har ya shiga d’aki,
Kud’in ya jera cikin jakar ya fita, Driver ya umarta ya kai Irfan makaranta, dan zai biya banki kar yaja masa makara,
A banki sun tabbatar babu dubu 3 cikin kud’in, abun yaba Haidar mamakin sanin kud’in a cike ya shigo dasu gida, haka bai bar ko naira wurin Bongel ba, Haka ya bayar da dubu ukun, aka cika kud’in aka sa masa account, Ya fito bankin da tunani kala kala a ransa.
FOLLOW, VOTE AND COMMENT
OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
ARBA'IN DA HUD'U
SHIN KINYI REGISTER DA TOP TEN KUWA, IDAN BAKIYI BA TO KI GARZAYA, LITTAFAN HAR GUDA 7 DAGA HAZAK'AN MARUBUTA NA KUNGIYAR HASKE, DA YADDA ZAKI KOYI GIRKI KALA KALA, DA SANIN ABUBUWAN K'ARUWA DA DAMA, DUKA AKAN NAIRA D'ARI BIYAR KACAL
HANZARTA KI BIYA
TA WANNAN BANKIN ZENITH BANK
2083371244 AISHA M SALIS
TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR +447891142004 KO KATIN WAYA TA WANNAN LAMBAR 07043079298
Bongel kuka take tamkar ranta zai fita, kuka na bak'in ciki da takaici, bata tab'a jin takaicin rayuwar data tsinci kanta irin yau ba, takaicin yau yasha bambam da na duka sauran ranakun, ko a mafarki bata zaci akwai ranar da zata zo, a jefata da k'azafin sata ba, "Shin taya ma kud'in suka zo k'asan akwatin ta?" Shine tambayar da take yiwa kanta yafi a k'irga, sai dai babu mai bata amsar sai ma kanta dake k'ara k'ullewa, Ya zama dole ta fitar da kanta daga rayuwar Haidar, a yau ta k'ara shaida girman k'iyayyar sa gareta, ta hango zallar k'yamatar ta cikin k'wayar idon sa, Da k'yar ta taushi kanta ta sassauta sautin kukan ta, ta koma hawaye wanda ta kasa tsayar dasu, Mik'ewa tayi ta shiga toilet ta d'aura alwala, ta soma nafilfili ta kai goshinta k'asa tana ssnar da ubangiji damuwarta, da rok'on sa ya wanketa daga mummunan zargi, yabi mata hakk'in ta kan wanda ya jefeta da sharrin sata.
*********************
Haidar zaune yake jigum office d'in sa, tunanin abunda ya faru yau ya kasa barin sa, zancen Bongel na k'arshe "Ka shaida tsayuwa gaban ubangiji dan nada shaidar haka", Na masa yawo a kai, yayin da tunanin ina dubu uku suke ke k'ara jefasa tunani, Duk iya hasashen sa ya kasa hasaso komai, sai zuciyarsa dake k'ok'arin canza masa tunanin ba Bongel tayi satar ba, yayin da wani b'angare ke gaskata masa da cewa "Idan ba ita bace ya akayi kud'in suka je akwatin ta", Tsaki yaja tare da buga desk gabanshi yace "Tun shigowarta rayuwata ban huta ba, kullum case, ya zama dole na fitar da ita rayuwata" Yayi assuring kansa, yana cizon labb'an sa na k'asa.
**********************
"Wai yau ba zamu samu girki bane", Cewar Rauda ta fito d'akinta tana hamma alamar daga bacci ta tashi, Bongel na jiyo ta daga d'aki, tana zaune kan sallaya tana karatun Qur'ani wanda shine magani da warakar damuwarta, dashi take samun natsuwa a zuciya da ruhin ta, Rauda jin shiru babu alamar Bongel ta nufi d'akin kai tsaye,
"Sai a fito a d'aura mana girki ko, yanzu pass 5, kinsan yanzu bana jure yunwa", Bongel karatun ta ta cigaba ko kallo Rauda bata isheta ba, "Ko kunyar abunda kika aikata ce ta hana ki fitowa", Bongel sai a lokacin ta juyo ta jefa mata wani kallo tace "Allah yana ji yana gani, baya zalunci shi yasan gaskiya kuma shi zai bayyanata" Ta juya ta cigaba da karatun ta, Rauda baki ta tab'e tace "Hmm salon yaudara", Ta fice d'akin tana nufar kitchen ta had'o cornflakes ta dawo falo ta zauna tana sha.
*************************
Haidar yana dawowa ko hutawa bai yi ba, Rauda ta soma masa complain Bongel bata yi girki ba, Kallonta yayi yace "Me ya hana ke bakiyi ba", Ta marairaice fuska tace "Kasan ni fah ba lafiya ce dani ba", Harara ya watsa mata yace "Ki cire lalaci da ragwanci ki rik'e gidanki", Rauda ta b'ata rai a zuciyarta tana kunkunin ba zata yi ba, Haidar bai sake bi ta kanta ba, ya cigaba da sabgogin gabansa.
Bongel damuwar dake cikinta ta korar mata yunwa, sam bata buk'aci komai ba sai ruwa, wunin ranar su tayi ta d'irkawa cikin ta, daren ranar haka ta raba sa wurin k'iyamul laili da rok'on Allah.
*******************
Rauda ganin Haidar bai sake mata ba yasa ta tafi d'akinta ta kwana,
Washegari Haidar har ya shirya ya fito Rauda na can na bacci, D'akin ya shiga ya kunna fitila haske ya gauraya d'akin, Rauda ba ma'abociyar son haske bace kullum wutar d'akinta a kashe, Haidar dubansa ya kai kanta, yaja siririn tsaki ganin irin kwanciyar da tayi, k'afafunta biyu sun ware da juna, Ya tako zuwa cikin d'aki, Abu yaji ya taka da k'afar sa, kamar takarda ko leda, Ya d'auke k'afar yana kai duban sa, dubu d'aya ce a k'asan carpet d'in, Ya duk'a zai kai hannun sa ya d'auka ba tare da tunanin komai, yaga wasu guda biyu a k'asan, K'irjinsa ya doka da k'arfi yasa hannu ya d'auki kud'in yana bin su da kallo, "Sune kud'in da suka yi missing a nawa kenan" Ya fad'a zuciyarsa na harbawa da k'arfi, Wani wawan duka ya kaiwa cinyar Rauda, ta tashi a zabure,
"Me kud'in nan ke yi a d'akin ki", Jin haka tayi saurin bud'e ido ba shiri, ta kai dubanta ga kud'in dake hannun sa, "Ina tambayar ki kinyi shiru" Ya fad'a a tsawace, Murya na rawa tace "Uhm.. uhmm nima ban sani ba", Kallonta yayi tsaf yana hango zallar rashin gaskiya a tare da ita, Babu alamar wasa yace "Ki fad'a kud'in nan ta yadda suka zo d'akin ki kafin raina ya b'aci", "Nima ban sani ba", K'afar sa ya d'aura kan gadon, yasa hannu d'aya ya jawota gaf da shi, Yace "Ko ki gaya mun gaskiya ko nasa k'afata na tattaka ki", "Kar ka manta ina d'auke da cikin ka fah", "To hell" Ya fad'a cikin b'acin rai, Jin haka jikinta ya sake yin sanyi tana jin tashin hankali na dabaibayeta,
"Kema satar kika mun kenan", Dan sam bai kawowa ransa ita ta kai d'akin Bongel d'in ba, Rauda tayi saurin girgiza kai da cewa "Allah ban sata ba", "Me kika yi toh" Ya fad'a cikin karaji, Murya na rawa tace "Uhmm... ina jin aljanu ne suka kawo d'akina suka kai d'akinta dan su had'a fitina", Kallo mai cike da mamaki yake bin Rauda dashi yace "A yanzu ne kika san aljanu kenan da yazo kan ki", "Kayi hak'uri My dear, amma ina kyautata zaton sune, bayan wucewar ka na samu Bongel na mata magana ta rantse mun bata d'auka ba, na yarda batayi satar ba wallahi, aljanu ne suka kai mata", Shiru yayi yana nazarin Bongel d'in, zai iya yarda ba ita tayi ba, duba da tun zuwanta gidan naira biyar d'in sa bata tab'a b'acewa ba, da halinta ne sata zatayi ko sau d'aya, Haka Rauda baya tunanin zata yi, kuma me zai kawo dubu uku d'akin nata sai dai aikin aljanun,
Karon farko yayi feeling guilty akan abunda ya mata, yana jin bai kyauta ba, wani b'angaren na zuciyarsa na nuna masa ba haka ba, "Ganin kud'in cikin akwatin ta ko waye haka zai yi" Ya fad'a yana son nunawa kansa baiyi wani abu ba, Ya fito d'akin zuwa falon, Daidai lokacin Bongel ta fito da shirin zuwa school, Kallo d'aya ya mata yaga idonta a kumbure alamar tasha kuka, Sai yaji zuciyarsa ta raunana, Ya bud'e baki zai yi magana sai kuma yayi shiru, Ta wuce abunta ba tare da nuna tasan dashi ba,
*********************
A makaranta Asiya tayi ta tambayar me ya faru, tak'i sanar da ita, tace mata kawai yaji ya shigar mata ido, Asiya bata yarda ba, dan kowa ya ganta yasan kuka tayi, Ta rasa zurfin ciki irin na Bongel, suna matsayin aminai wanda sun zama kamar yan' uwa amma abubuwa da yawa dangane da ita, bata sanar da ita, Bongel sukuku tayi a ajin, duk yadda take son b'oye damuwarta abun yaci tura, Lecture Haidar ce dasu ranar, a ajin sam tak'i bari su had'a ido, wanda shima duk yake jin sa unusual karon farko, yana jin sa tamkar mara gaskiya.
*******************
"Bongel da Haidar basu da niyyar rabuwa da juna, ni zan rabasu ta kowacce hanya, na gaji da zaman jira, i want Bongel back in my life, na gaji da amsa sunanta matar Haidar, ina son nan bada jimawa ba ta soma amsa sunan matar Hisham", Hisham ya fad'a yana zagaye d'akin sa, zuciyarsa babu komai ciki sai zallar son kai da son cikar burin sa ta kowacce hanya, Wayarsa ya d'auka ya soma kiran number Rauda da yayi ma saving da Sexy lady, Bugu d'aya ta d'auka da cewa "Hisham manyan gari", Yace "Sexy lady", "Gaskiya suna nan ya fita a bakin ka, yanzu matar yaya", Yayi dariya yace "Toh matar yaya", "Yawwa ko kai fah", Ya numfasa yace "I want us to meet and discuss something very important", Gabanta ne ya fad'i tace "Please Hisham kar ka mayar da hannun agogo baya", Dariya yayi yace "Haba Matar Yaya kina tunanin zan maido abunda ya wuce ne, ko d'aya wani abu ne daban da ya shafi rayuwarmu da cigaban mu", Ta jinjina kai tamkar tana gabansa tace "Toh yanzu ina zamu had'u?", "Idan Haidar da Bongel basa nan, ki sanar dani nazo", Tace "Ok ba damuwa", Sukayi sallama ta kashe wayar da tunanin Me Hisham yake so su tattauna, tana fatan ba wani abu bane da zai kawo mata matsala a rayuwar auren ta.
****************************
Haidar tunanin ba Bongel tayi sata ba, ya hana masa sukuni, yana jin babu dad'i na tuhumar da yayi mata, hakan yasa ya yanke shawarar tura mata text message, wayarsa ya d'auka ya duba numberta wacce yayi saving da Bongel, tun lokacin da ya siyan mata waya, yayi saving ne ba dan yasa wa ransa akwai ranar da zata zo ya kirata ko ya mata text, Yayi ne kawai saboda gudun abunda zai taso,
Bongel tunda ta dawo school ta shige d'akinta ta kwanta, k'arar shigowar text wayarta, yasa ta tashi ta jawo wayar ta duba, "Na fahimci bake kika yi satar ba" Ta karanta ta duba number wacce babu suna, amma tana da tabbacin mai ita Haidar ne, Kaso sittin na damuwarta taji ya rage, jin cewar ya gane ba ita bace, sai dai taso jin waye ya mata sharrin, amma tunda an fahimci ba ita bace, a haka ma ta godewa Allah, Alhamdulillah, Karon farko ta kub'uta daga zargin Haidar, duk da cewa akwai wasu tarin zargin da yake mata, but ta godewa Allah ta kub'uta na sata,
Haidar wayar ya kalla yaga time, yana kyautata zaton zuwa yanzu ta karanta, ya sauke ajiyar zuciya yana jin ya sauke nauyin, Rauda ce ta kwanta kan k'irjin sa, Cikin sanyin murya tace "Please my dear a samu yar' aiki da zata rik'a tayani, wallahi yau ma da k'yar na dafa mana indomie", Janye jikinsa yayi da cewa "Yar' aiki ta gama zama gidan nan, ki tashi kije ki dafa mun jollof na macaroni", "Nace na dafa indomie fah", Hararar da ya watsa mata yasa tayi saurin mik'ewa, tana kunkuni ta fita.
MU HADU GOBE🙂
FOLLOW, VOTE AND COMMENT
OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
ARBA'IN DA BIYAR
SHIN KINYI REGISTER DA TOP TEN KUWA, IDAN BAKIYI BA TO KI GARZAYA, LITTAFAN HAR GUDA 7 DAGA HAZAK'AN MARUBUTA NA KUNGIYAR HASKE, DA YADDA ZAKI KOYI GIRKI KALA KALA, DA SANIN ABUBUWAN K'ARUWA DA DAMA, DUKA AKAN NAIRA D'ARI BIYAR KACAL
HANZARTA KI BIYA
TA WANNAN BANKIN ZENITH BANK
2083371244 AISHA M SALIS
TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR +447891142004 KO KATIN WAYA TA WANNAN LAMBAR 07043079298
"Wallahi dole ma na kori Bongel a gidan nan, ko dan na samu kan Haidar, na tabbata zamanta yasa baya so a d'auko yar' aiki, ta kub'uta na sata amma wallahi ba zata k'ubuta sauran dake tunkaro ta ba" Cewar Rauda tana shiga kitchen cikin b'acin rai.
*********************
Bongel sosai ta samu bacci daren yau, zuciyarta ta rage nauyin da ta mata, haka kaso talatin na damuwarta ya tafi, tunanin ta d'aya yanzu yadda zata k'are da Hamma Siddiku zancen kayan d'aki.
Washegari tunda safe ta fice school, makarantar kusan kowa ka gani da littafi ko handout a hannun sa kasancewar exam ta gabato, Bongel da Asiya ma k'ebantaccen wuri suka samu suna karatu, Bongel ta maida dukkan hankalinta kan karatun, duk tunanin da yazo mata tana saurin datse shi, fatan ta wannan semester kada ta samu carry over ko d'aya, tana addu'ar Allah ya d'aura ta kan Haidar kada ya kayar da ita course d'in sa.
***************************
Haidar na fita office, Rauda ta d'auki waya ta kira Hisham, Yana kwance a d'akinsa bai fita office ba, yana jiran kiran Rauda, Yana ganin kiranta babu b'ata lokaci ya d'auka, "Kazo yanzu duka sun fita", Cewar Rauda, Ya amsa da "Okay" Ya kashe wayar, Ya mik'e da yin shu'umin murmushi, Yayi shirin sa dan daga can zai wuce office.
Da sallama ya shigo falon, Rauda dake zaune kan kujera, bakinta chewing gum ne tana tauna, ta amsa da sakin fuska, Yace "Matar Yaya" yana zama kan kujera, Ta amsa "Na'am Hisham manyan gari", Yayi dariya kana ya numfasa yace "Nasan ki Rauda, nasan kina cikin jerin mata masu tsananin kishi, dan haka nake da k'arin tabbacin bakya son zaman Bongel a gidan nan", Rauda ta sauke ajiyar zuciya da cewa "K'warai, bana k'aunar na bud'e ido na ganta, burina na zama ni kad'ai a wurin mijina", Hisham yayi murmushin gefen baki yace "Yau zan sanar dake wani abu da baki sani ba, Ina matuk'ar son Bongel, so mai tsanani, babban burina shine na mallaketa matsayin matata", Rauda shiru tayi a zuciyarta tace "Ruwa baya tsami k'asa banza, ko shakka babu taga alamar haka daga kallon da yake ma Bongel d'in", Ya katse zancen zucin ta da cewa "So ina so mu had'a k'arfi wurin ganin mun raba su, Haidar ya zama mallakin ki ke kad'ai, Bongel ta zama tawa", Rauda kanta ta jinjina cike da gamsuwa tace "Toh ta ina zamu fara", Yace "Gud, zan sanar dake plan d'in farko zuwa gobe, yau nazo ne dan jin ta bakin ki, ko zan samu goyon baya", Rauda tace "Kai ma kasan dole na baka goyon baya yadda na tsani kishiya, ai duk abunda zai fitar da ita gidan nan, ina maraba dashi", Suka fashe da dariya,
Dariyar ta tsaya cak ganin Haidar tsaye yana kallon su, Mamaki, tsoro had'i da firgici ya dabaibaye su lokaci d'aya, Kafin d'ayansu yayi magana Haidar ya shige ciki ba tare yace musu uffan ba, D'akin ya shiga ya kwanta, ciwon kai sosai ya dawo dashi gida, wanda tunani da stress ya haddasa masa,
Hisham ya sauke ajiyar zuciya da cewa "Wai! Na d'auka yaji zancen mu", Rauda tace "Wallahi nima har hantar cikina ta kad'a", Hisham yayi dariya da cewa "Sarkin tsoro, bara na tafi sai na kira ki", Tace "Ok sai anjima", Ta tashi ta nufi d'akin,
Ganin Haidar kwance tasan ba lafiya ba, bakin gadon ta zauna tace "My dear ina fatan lafiya", "Headache" ya bata amsa a dak'ile, "Ayyah sorry kasha magani", Ya mata nodding kai, Ta kwanta gefen sa tare da saka hannayen ta ta rungume sa, ba dad'in hakan yaji ba but bai hana ta ba, sai idonsa da ya runtse yana jiran zuwan bacci.
******************************
Bongel sun soma exams, kullum bata da lokaci tana makaranta sai yamma lik'is take dawowa, ko jarabawar safe suka yi sai ta tsaya cikin school tayi karatu, Idan ta dawo haka zata yi aikin gidan, dan Rauda da kanta tayi wa Haidar magana ya raba musu girki, ta gaji da yi ita kad'ai, Haidar ba musu yace kowaccen su ta rik'a yi kwana biyu biyu dan shi kansa yana buk'atar girkin Bongel na Rauda cin dole yake masa, Bongel babu musu ta karb'a, duk da k'asan zuciyarta taji babu dad'i wane irin raba girki ne wanann, babu miji ba dan tana son kusancin su da Haidar ba, sai dai a saninta ranar girki kai ke da miji, amma ita hatta ranar girkin nata Haidar yana wurin Rauda, wane irin rayuwar aure ne ta tsinci kanta, ta kan yiwa kanta tambayar lokuta da dama,
Yau ma ta dawo gida a gajiye, ta shiga kitchen tayi girki, kana ta koma d'aki, Bak'uwar number taga na kiranta, Ta d'auka, "Assalamu alaikum Adda" Taji muryar Ramla, "Wslm Ramla ya gida?", "Lafiya lau Adda", "Ina kika samu waya", Tana dariya tace "Yaya Hisham ne ya siyan mun wai mu rik'a kiran ki kullum", "Hisham" Bongel ta maimaita a ranta tana mamaki, Ramla ta katse tunanin ta da cewa "Ga nene", Nene ta karb'i wayar da yin sallama, Bongel ta amsa tace "Nene ina wuni?", "Lafiya lau, ya mutan gida da karatu?", "Alhamdulillah", "K'anin mijinki yana k'ok'ari sosai, ki mishi godiya kullum baya gajiya da mana hidima", Bongel tace "In Shaa Allah" K'asan zuciyarta mamakin Hisham d'in take, hakan na nufin soyayyarta har yau na cikin zuciyar sa shiyasa yake kyautatawa ahalin ta, ko kuwa yana yi ne kawai dan kyautatawa shine ta kasa ganewa, Ta katsewa kanta tunanin da cewa "Nene ya shirin Bikin saude", "Alhamdulillah yanzu ma ai saura sati biyu, zaki zo dai ko", Tace "In Shaa Allah" tana jin natsuwa a ranta dama ta tambayi Nene ne dan son jin ko Hamma Siddiku ya sameta kan zancen kayan d'aki, sanin k'aramin halin sa ne ya tadawa Nene hankali, abunda bata k'auna, Sukayi sallama ta kashe wayar.
***************************
"Ya kamata muje asibiti dan sanin lafiyar cikin ki", Cewar Hajiya Mariya, Rauda dake kange da waya a kunne tace "Toh Mummy", "So ki shirya gobe zan zo na d'auke ki mu tafi", Tace "Toh", "Yawwa sai anjima", "Bye Mummy", Ta kashe wayar tare da shafa cikinta tace "Babyna nasan ma kana lafiya" Tayi murmushi dan ba k'aramin son cikin take yanzu ba.
*****************
"Wai ke ba zaki hak'ura da Hisham ba, mutumin nan fah ba son ki yake yanzu ba, kullum cikin wulak'anta ki yake" Cewar Fido, Ihsan tace "Hmm Fido kenan kina tunanin zan bar sa yaci bulus, wallahi idan kin ga na hak'ura da Hisham to mutuwa nayi", Ta jinjina kai tace "Shikenan Allah ya taimaka", Ihsan ta amsa da "Amin", Tana taunar chewing gum kamar tsohuwar karuwa.
***********************
Yau ranar girkin Rauda ce, hakan yasa dan dole ta tashi da wuri ta shirya Irfan, ta shiga kicin had'a breakfast, ruwan shayi tayi da irish, dan sune mafi sauk'i, Haidar kad'ai yaci a cewarta zuciyarta ke tashi, Bayan ya kammala ci ya mik'e zai fita, Tace "My dear anjima Mummy zata zo muje asibiti duba lafiyar babyn ka", Kansa yayi nodding yace "Ok" ya saka hannu a aljihu ya zaro kud'i masu yawa ya bata sanin asibiti dole a buk'aci kud'i, Tasa hannu ta karb'a tace "Thanks",
***********************
Likita bayan ya gama gwaje gwajen sa ya buk'aci ganin sa office d'in sa, Suka shiga, Ya gyara zaman madubin dake idonsa ya kai dubansa gare su da cewa "A bisa bincike da mukayi gaskiya bata da ciki", "What" Suka fad'a a zabure, Dr ya jinjina kai yace "K'warai bata d'auke da juna ba, face infection wato cutar sanyi wacce ta mata mugun kamu, shine dalilin da yasa period d'inta ya d'auke na tsawon lokaci", Rauda tuni hawaye suka soma zirya kan kumatun ta tace "Na shiga uku wayyo ni Allah na", "Subhanallah ba wani babban matsala bane ai, za'a d'aura ki kan medication wanda In Shaa Allah zaki samu sauk'i, sai dai ki kiyaye inserting abubuwa a gabanki, ba komai za'a baku mata ku cusa a gaba ba, mafi yawa shi ke jawo muku matsala", Hajiya Mariya kad'ai tayi k'arfin halin amsa sa, Rauda kuwa kuka tamkar wacce akayi wa mutuwa,
Dr ya rubuta musu magunguna da allurai da zata rik'a karb'a, Suka fito, Rauda na kuka, a mota Hajiya Mariya ke lallashin ta tace "Ki daina kukan, ai ba cewa akayi ba zaki haihu ba, yanzu ki fara treating infection nasan kina gamawa ciki zai shiga", "Mummy me zan cewa Yaya Haidar yanzu bayan na gama fad'a masa ina da ciki, ga shegiyar can sai tamun dariya", Hajiya Mariya taja ajiyar zuciya da cewa "Kiyi shiru kar ki fad'awa kowa yanzu har sai mun gama maganin infection d'in, ki barsa a cewar kina da ciki", Ta jinjina kai da cewa "Toh", K'asan zuciyarta zallar bak'in ciki ne, har suka isa gida tana kuka, Ta sauka aka wuce da Hajiya Mariya gida.
Tana ganin kiran Hisham tak'i d'auka, b'acin rai da damuwar da take ciki bata jin magana da kowa, yanzu ita bama ta fitar Bongel gidan take ba, jin cewar bata da ciki ga infection yafi komai d'aga mata hankali.
Hisham yayi tsaki yana cillar da wayar gefe, "Ko gidan uwar wa ta ajiye wayar oho" Ya fad'a cikin takaici, yaso samunta yanzu dan aiwatar da plan d'in sa, a yadda yake ji tamkar yaje ya fitar da Bongel daga gidan Haidar ta dawo gidan sa.
FOLLOW, VOTE AND COMMENT
OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
ARBA'IN DA SHIDA
SHIN KINYI REGISTER DA TOP TEN KUWA, IDAN BAKIYI BA TO KI GARZAYA, LITTAFAN HAR GUDA 7 DAGA HAZAK'AN MARUBUTA NA KUNGIYAR HASKE, DA YADDA ZAKI KOYI GIRKI KALA KALA, DA SANIN ABUBUWAN K'ARUWA DA DAMA, DUKA AKAN NAIRA D'ARI BIYAR KACAL
HANZARTA KI BIYA
TA WANNAN BANKIN ZENITH BANK
2083371244 AISHA M SALIS
TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR +447891142004 KO KATIN WAYA TA WANNAN LAMBAR 07043079298
Alhaji Sani maigoro ya yarce zufar data keto masa a goshi jin zancen Hajiya Mariya, Fuska d'auke da zallar damuwa da bak'in ciki yace "Ban tab'a jin labari mara dad'i irin wannan ba, wai ma taya za'a ce babu ciki, shin dama ba asibiti ya tabbatar ba hasashen ku kawai ba tare da wani gwaji ba", Hajiya mariya ta marairaice fuska tace "Wallahi ranar da naji, naga alamar ciki tare da ita", Tsaki yayi yace "Burina da nake ganin ya gabato, yanzu ya k'ara nisa", Ta d'aura hannu kan kafad'ar sa tace "Kayi hak'uri Alhaji, Sannu bata hani ga zuwa sai dai a dad'e ba'a je ba, kuma ai wani jinkirin alkhairi ne", Ya jinjina kai yace "Ko nawa ne ni zan bada dan ganin an kawar da cutar sanyin dake jikin ta, ta samu d'aukar ciki", "In Shaa Allah zan yi k'ok'arin ganin haka", "Allah yasa" Ya fad'a yana fusgar da iskan baki mai zafi.
*************************
Rauda ta d'auki shawarar mahaifiyarta sam bata nunawa Haidar alamar babu ciki ba, Yau ma tashi tayi da kakarin amai, ta shiga toilet tana yi kamar zata amayo yan' cikin ta, Haidar yabi ta ya rik'e ta yana mata sannu, Bayan ta dakata, ya jawota suka dawo d'aki, Ta kwanta jikinsa tana jan numfashi da k'yar kamar da gaske,
"Da kuka je asibiti me Dr yace, banji kimun wani bayani ba" Cewar Haidar, "Yace Babyn lafiya lau, ba wata matsala", "Ina result?", "Ai bai bayar da komai ba, sai magani da ya rubuta mun muka siya", Ya bud'e baki zai yi magana, yayi shiru, Ajiyar zuciya ta sauke da yin hamdala a zuciyarta bai d'ago ta ba.
**************************
Bongel bata da exam sai bayan sati d'aya wacce itace jarabawar k'arshe ta semester, Yau tana gida bata fita school ba, sha'awar waina ta tashi dashi, Hakan yasa tun da asuba data tashi sallah ta jik'a shinkafa, Ana kiran azahar ta kammala ta zuba a kuloli, har da Ammi ta d'ibarwa, ta jere a k'aramin basket, ta yafa mayafinta zuwa kai mata, sam Haidar bai mata iyaka da zuwa b'angaren Ammi ba, duk lokacin da taga dama take zuwa ba tare da ta tambayi izinin shi ba, Fitowar ta d'akin akan idonsa, yana zaune falon tare da Rauda, Kyau yaga ta k'ara masa sosai, ya tsinci kansa da kasa d'auke idon sa kanta, yana jin wani yar, K'arasowar cikin falon yasa yayi saurin kawar da kansa, Cikin sanyin murya tace "Ina wuni?", "Lafiya" Ya amsa ba tare da ya kai dubansa ba,
Har ta kai k'ofa, Ta jiyo muryarsa "Ina zaki?", "Wurin Ammi" Ta bashi amsa, Bai sake cewa komai ba, Jin shiru ta bud'e k'ofar ta fita, Rauda kuwa ta cika tayi fam ganin irin kallon da yake wa Bongel, Bai bi ta kan Rauda ba sai ma mik'ewa da yayi, ya nufi dining, Ya hau ci wainar wanda ta masa masifar dad'i.
*******************
Ammi sosai taji dad'in wainar da Bongel ta kawo mata, Tayi ta saka mata albarka, Tana k'ara yaba hankalinta, Ko shakka babu Dada babban gata tayi wa Haidar data had'a sa da ita, Rauda tun zuwanta gidan bata tab'a kawowa Ammi ko ruwa ba, Bongel ta jima a sashen kafin ta koma, Ammi ta bata kyautar humrah mai masifar k'amshi, ta mata godiya sosai.
*********************
Rauda kwata kwata tak'i ba Hisham damar su had'u, a ganinta sai ta gama da matsalar cikin da akace babu, kafin ta dawo kan fitar Bongel gidan, Hisham ba k'aramin haushin hakan yaji ba, amma ya d'auki alwashin shawo kanta, dan yana ganin da taimakon ta zai cika burin sa, Yanzu ma kiranta yake tak'i d'auka bai fasa kiran ba,
Haidar dake zaune gefen Rauda yace "Ba kiran ki ake ba", "Eh wayar bata da amfani", Ta fad'a tana k'ok'arin kashe wayar wanda kiran ya sake shigowa, Haidar ya kai dubansa sunan Hisham rubuce kan screen d'in, Ya kawar da kansa tamkar bai gani ba, yana cigaba da danna wayar sa.
****************************
"Alhamdulillah yau mun kammala jarabawar level one" Cewar Asiya, Bongel ta nisa tace "Lokaci na gudu kamar jiya muka shigo makarantar gashi har mun kammala level one", Asiya tace "Wallahi kuwa, haka watarana makarantar zamu gama baki d'aya", "Allah ya nuna mana lokacin yasa mu gama a sa'a da nasara" Cewar Bongel k'asan zuciyarta tana fatan ganin wannan ranar, ranar da zata cika burin sa, Asiya ta amsa da "Amin Amin, mu tafi gida ko?", Bongel ta dan' yi jim tace "Jibi za'a fara bikin Saude, jiya Nene ta kirani kan batun zuwana sai dai abu biyu ne zasu katange ni ga zuwan", "Me zai hana ki zuwa bayan kullum kina damuna kan cewar kinyi kewar su", Bongel taja numfashi tace "Na farko ban san ta yadda zan tambayi Haidar zuwan ba, na biyun had'uwata da Hamma Siddiku, nasan ba zatayi kyau ba, nayi mamakin tsawon lokacin da aka d'iba ma bai waiwayo ni ba, nayi imani da Allah matuk'ar naje ba tare da kayan d'akin da ya buk'ata ba sai nayi dana sanin zuwa na", Cike da tausayin ta Asiya tace "Tambayar Haidar zuwan ki ba matsala ba ne, matsalar itace Hamma Siddiku, amma ina so ki sani addu'a bata bar komai ba, ita zamu dage da yi", Bongel ta jinjina kai duk da tana jin karaya, amma tayi imani da Allah, yana sane da ita, shi zai kawo mata mafita a rayuwarta da tayi mata d'aurin goro.
****************************
Bongel tana dawowa gida, tayi wanka ta saka doguwar riga mara nauyi bayan ta shafe jikinta da humra da Ammi ta bata, K'amshi mai sanyi da dad'i na fita jikinta, gashinta tayi bakin, jelar sa ta sauka kan gadon bayanta, bata saka d'ankwali ba, Ta zauna k'asan carpet tana had'a handout d'inta na level one wuri d'aya tana sakawa a ghana must go,
Haidar yayi kusan minti biyar tsaye yana k'are mata kallo, a zuciyarsa ya shaida tana da kyau, had'i da komai ake buk'ata a jikin ya' mace, Sai dai kyan nata a wurinsa yake ganinsa kyan dan' maciji, "Fure a cikin juji" Ya furta wanda caraf a kunnen Bongel, Ta d'ago ta dube sa, ta mayar da kanta k'asa ba tare da ta fahimci me yake nufi da kalmar ba, Hannun ta tasa ta jawo dan' kwalinta dake kan gado, ta rufe kanta, Haidar k'arasowa yayi cikin d'akin, K'amshin humra ke dukan hancin sa yana sake jefa sa wani yanayi, Gaf da ita yazo yasa hannu ya d'agota, K'irjinsu tamkar zai manne da juna, ta runtse ido tana saukar da kanta k'asa, Hannu d'aya yasa ya tallabo hab'arta, bakinsa kawai taji cikin nata, yana tsotsar labb'anta na k'asa, Kasa aiwatar da komai tayi sai k'afafunta dake rawa, Haidar kissing d'inta yake kamar zai cire mata lips, Soma fita hayyacin sa yayi, Yayi k'ok'arin controlling kansa, ta hanyar tureta, tayi baya kamar zata fad'i, Idonsa ya runtse ya girgiza kai, Kana ya bud'e su gaba d'aya sun canza launi, Muryarsa na fita da k'yar yace "Ki shirya gobe kije gida", Ya juya ya fita d'akin,
K'irjin Bongel yayi mummunan dokawa, kar dai ya shirya rabuwa da ita, Kanta taji ya mugun sara mata, Ta soma ambaton Allah, a iya saninta babu soyayyar Haidar a zuciyarta, but ta rasa dalilin jin fad'uwar gaban rabuwa dashi, ta danganta hakan da damuwar Nene da k'annen ta bata son ganin fuskokin su d'auke da damuwa, amma tana fatan rabuwar tasu ta zama alkhairi, tana fatan samun sauyi ne a rayuwarta, "Shin Dada da Ammi sun san ya yanke hukuncin kuwa, da amincewar su ko sab'anin haka?", take wa kanta tambayoyin da babu mai bata amsa, Da sak'e sak'e kala kala ta had'a kayanta a akwati guda d'aya, komai na buk'ata ta saka ciki, Daren ranar bata runtsa ba, k'iyamul laili tai tayi, tana sanar da ubangiji damuwarta.
***********************
Tun tashinta komai sukuku take yin sa, tayi wanka ta shirya, ta saka hijab d'inta jalbab, Ya mata kyau sosai, komai ta kasa sakawa cikinta hatta ruwa, Zaune take bakin gado tayi jigum, Irfan ya shigo yace "Aunty ina kwana?", "Lafiya lau my boy" Ta amsa tana murmushin dole, "Kizo inji Daddy", Mik'ewa tayi taja akwatin ta sanin kiran nada alak'a da tafiyarta,
Haidar na tsaye, Rauda na gefensa, Bongel ta fito, Ta gaishe sa cikin ladabi ya amsa, "My dear bara na gyara maka necktie d'in ka" Cewar Rauda cikin salo tana gyara masa tana wani shafo wuyansa wanda da gangan take yi, Bongel kallo d'aya ta musu ta kawar da kanta, Bai hana Rauda ba, sai hannu da ya saka a hannu ya fiddo envelope ya mik'awa Bongel,
Kanta yayi mummunan sarawa sanin ko shakka babu takardar sakin ta ce, tasa hannu ta karb'a, ya jefa cikin k'aramar jakarta, "Direba na jiranki waje zai kai ki", Ya fad'a, Kasa ce masa komai tayi sai akwatin ta da taja tayi gaba, Irfan yabi bayanta da cewa zan bi ki, Haidar ya jawosa yace "Dawo, school zamu je na kai ka", Bongel na fita, Haidar shima ya fito tare da Irfan,
Rauda tsalle tayi ta fad'a kan kujera da cewa "Wayyo Allah na dad'i, shikenan ya rabu da yar' iska, wai mafarki nake ko gaske", Ta mari kanta, "Wallahi da gaske ne, Allah ya hutar dani, ya rabu da ita ba tare da na wahalar da kaina ba, dole na kira Hisham na sanar dashi wannan labari mai dad'i", Ta taka rawa kana ta soma kiran wayar sa, Bugu d'aya ya d'auka da cewa "Haba Rauda, ya zaki mun haka, tun yaushe nake kiran ki", "Maida wuk'ar, yau dai Allah ya hutar damu Haidar ya saki Bongel", "What, bana son wasa" Ya fad'a da k'arfi, "Wallahi tallahi a gaban idona ya bata takardar ta", Hisham ihun murna yayi ya jefar da wayar gefe, ya fad'a kan gado ta baya, farin ciki yake ji na ratsa shi wanda bai tab'a jin irin shi ba.
**********
A mota Bongel shiru tayi ta jingina kanta kan window k'ofa, ta lumshe idonta zuciyarta cunkushe da damuwa had'i da tunanin kala kala, Jin parking d'in mota da hayaniyar yaran unguwarsu da suka dabaibaye motar ganin mota mai tsada da kyau ya tabbatar masa sun iso, Ta bud'e idonta tana jin fad'uwar gaba na da wane baki zata furtawa Nene aurenta ya mutu Haidar ya saketa, tasan zasu sha gori kala kala da habaici wurin yan' gidansu, amma ya bawa ya iya da k'addarar ubangiji, Allah ya riga ya rubuta faruwar hakan, Da tunanin haka ta k'arfafawa kanta gwiwa ta aro jarumta ta sakawa kanta, Ta saki ranta da k'ok'arin b'oye damuwarta, ta fito motar zuwa cikin gida, Tuni yara sun shiga da akwatin ta.
*Hmmm bakina da goro*🤐😷
OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
ARBA'IN DA BAKWAI
SHIN KINYI REGISTER DA TOP TEN KUWA, IDAN BAKIYI BA TO KI GARZAYA, LITTAFAN HAR GUDA 7 DAGA HAZAK'AN MARUBUTA NA KUNGIYAR HASKE, DA YADDA ZAKI KOYI GIRKI KALA KALA, DA SANIN ABUBUWAN K'ARUWA DA DAMA, DUKA AKAN NAIRA D'ARI BIYAR KACAL
HANZARTA KI BIYA
TA WANNAN BANKIN ZENITH BANK
2083371244 AISHA M SALIS
TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR +447891142004 KO KATIN WAYA TA WANNAN LAMBAR 07043079298
*MAMAN INYASS SHAFIN YAU NAKI NE❤️*
Ramla da Abu da gudu suka zo suka rungumeta, haka sauran yaran gidan, mamaki ya cika Bongel ganin wannan shine karon farko da ta samu tarba daga yaran gidan su, ko da tana makaranta idan ta dawo hutu ko kallon arzik’i bata ishe su ba, Hassan da Hussein kad’ai take samun sauk’i daga gare su,
Nene na zaune d’akinta tana jera kayan ta da aka kawo daga wurin d’inki cikin akwati, Bongel ta shigo, Cikin ladabi ta gaishe da Nene, ta amsa da farin cikin ganin yar’ ta, “Ga tuwo can da miyar kub’ewa busasshiya na miki”, Da kallon mamaki tabi Nene dama tasan da zuwanta, Nene ta katse tunaninta da cewa “Ko baki ji ba”, Tayi saurin cewa “Dama nayi kewar miyar ki”, Nene tayi dariya, Ramla ce ta shigo rik’e da kwanukan abincin ta ajiye gaban ta, “Sannu”, Cewar Bongel, Ramla tace “Kai Adda wai sannu kamar nayi wani aiki”, Bongel tayi murmushi, Bongel taci abincin ne ba dan tana son ci ko jin dad’in sa ba, sai dan kar su Nene su gano akwai wani abu, duk da cewar ya zama dole ta sanar dasu, sai dai ba yanzu ba sai an gama hidimar biki,
“Ai baki wani ci tuwon ba”, Cewar Nene, “Gajiya ce tamun yawa, kwanciya kawai nake buk’ata”, Nene tace “Kamar wacce tayi tafiya mai nisa”, Tayi murmushi tana kwanciya kan katifar dake shimfid’e a farfajiyar d’akin, baya ta juya musu ta yadda ba zasu gane ba baccin take ba, duniyar tunani ta tafi, yayin da idonta ke hasko mata fuskar Haidar a lokacin da ya mik’o mata takardar, tana jin b’acin rai da damuwa na sake shigarta, tana jin kiran Asiya na shigowa wayarta, tak’i d’auka, dan bata san me zata ce mata ba, bata son d’aga mata hankali a halin yanzu.
******************************
Haidar yau yaje makaranta yayi handing over ya tashi daga matsayin lecturer, ko shakka babu ya samu experience sosai, Abba yayi gaskiya da yace ta hanyar lecturing zai k’aru da abubuwa da dama, Daga makarantar company ya wuce, Tun shigar sa office d’insa ya kasa aikata komai sai tunanin Bongel da yazo masa, Meyasa idan yaga yarinyar ko suka keb’e tare da ita sai yaji ya kasa controlling kansa, jiya daga zuwa sanar da ita zuwanta gida ya bige da kissing d’in ta, “Ko shakka babu tana amfani da wani lak’ani dake jawo maza zuwa gareta, dashi take mun amfani” Ya tabbatarwa kansa, Idanunsa ya lumshe ya jingina da kujera yace “I have to get rid of her”, Jin bud’ewar k’ofa yasa ya bud’e idon sa yana kallon k’ofa, Hisham ne ya shigo fuska d’auke da far’a,
“Barka da hutawa Yaya”, Cewar Hisham, “Yawwa barka”, “Ya aiki?”, Haidar ya amsa “Alhamdulillah”, “Papers na kawo maka kayi signing”, Ya fad’a yana mik’a mata, Haidar ya karb’a yana duba takardun, kana ya saka hannu, ya mayarwa Hisham, Hisham ya sauke ajiyar zuciya da cewa “Ashe abunda ya faru kenan, Allah ya kiyaye gaba, banji dad’i ba kwata kwata ba amma haka Allah ya k’addara”, Haidar da tsantsar mamaki yake kallon Hisham sam bai fuskanci inda zancen sa ya dosa ba, Ganin irin kallon da Haidar ke masa, yasa bai sake cewa komai ba, dan a zaton sa maganar ce Haidar baya so, Ya mik’e ya fita ba tare da Haidar yace masa komai ba, sai mamaki da ya cika sa.
**************************
“Ina Bongel d’in naji ance tazo” Cewar Dije, “Eh gata nan bacci take”, Nene ta fad’a, “Idan ta tashi na dawo”, “A’ah zata zo ma da kanta”, Dije tace “Toh” tana murmushin da bai kai zuci ba, Bongel kuwa jij shigowar Dije ya k’ara d’aga hankalinta tana kyautata zaton ko Hamma Siddiku ya aiko a kiranta, amma a yadda tasan halin shi da kanshi ma zai iya zuwa d’akin, but ba abun mamaki ba ne, dan ya aiko Dije.
Bongel bata tashi ba sai ana kiran sallar azahar, ta fito tsakar gida tayi alwala, ta koma ciki tayi sallah raka’a biyu, tana idarwa ta jiyo muryar Hamma Siddiku daga waje, hantar cikinta ce ta kad’a, Ta ambaci sunan Allah,
“Kizo inji Hamma Siddiku” Ramla ta fad’a, Bongel da k’yar ta iya amsawa da “Toh”, Jiki a sanyaye ta fito tsakar gidan, Kanta sunkuye k’asa ta gaisheta, “Lafiya lau Bongel ya hanya?” Ya fad’a da far’a, Jin muryarsa yasa mamaki ya kamata, ya akayi yake amsa mata haka ko ya zata tazo da kayan d’akin ne,
“Kin kyauta, kin zama ya’, auren ki yayi man rana, ashe zaki ji maganata”, Cewar Hamma Siddiku, Bongel tayi shiru kanta na sake k’ullewa sam bata fahimci ina zantukan sa suka nufa ba, Ya cigaba da cewa “Allah yasa ki d’ore haka, idan kina mana irin haka ai babu wanda zai ji mu dake”, Bongel murmushi kawai tayi ba dan ta fuskanci komai ba, Yaja babbanr rigar sa ya wuce, Ta juyo suka had’a ido da Nene ta mata murmushi, D’aki ta koma da tunani birjik, Ramla ce ta shigo, Bongel ta kai dubanta gareta tace “Ramla meke faruwa a gida
No comments