Recent Updates

Auren Yarjejeniya 9-10


🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾


  ❤‍🔥👩‍❤️‍👨AUREN YARJEJENIYA👩‍❤️‍👨❤‍🔥


🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾


    it's rometic love story❤‍🔥💔



      Story & written by mommyn fareesa



   last free page 9&10🙌


........wajen k'arfe 7 na dare ummu tayi sallama ta shigo tsakar gidan su"gabanta na tsananta fad'uwa sbd ganin baba datayi"yana zaune tsakar gidan yana cin Abinci"gashi Akwai nefa"goggo luba na zaune gefensa tana cin tsire daya siyo mata"babu wanda ya Amsa mata sallamarta Acikinsu sai kallon tsana da mahaifin nata ke jifarta dashi"ta nufi d'akinsu dake bud'e zata yaye labulen ta shiga"da Alama Aminu da umar da mahmood suna ciki...K! dan ubanki zo nan"cewar baba"gabanta na fad'uwa ta nufi Inda yake ta duk'a"daga gidan ubanwa kike yanzun bayan sallar mangarib??"yo dg inafa inba yawon gantaliba da uwarta ta d'aure mata gindi tanayi ko?"idan Anyi mgn Ace wajen Aiki take zuwa"to Ai yau Asabar ce"cewar luba"bazakiyi mgn ba dan uwarki?"dg gidansu lawisa nake baba, munje sunan  k'awarmu data haihu"ba shakka"shi wannan ciwon dake jikinki da wannan jinin na uban meye??"bigewa nayi goshina yafashe"sauk'in ki guda hajara bata nan"Amma zata dawo gobe"daga ke har ita zaku sani"nagaji da irin zagin dakike jamun Agari"kina yawon banza da sunan Aiki kink'i yin Aure ko?"to bari kiji bazan lamunci iskanciba"na baki nanda sati d'aya zuwa kwana 10 ki fitomun da mijin Aure"ko kuwa nayi sadaka dake kona huta"wannan wane irin bala'ine?...."kayi hak'uri dan Allah babah "Akwai mubashshir dake zuwa guna Amma sai nan da shekara 1 zai turo lokacin yagama ginin gidansa....bbu Abinda yadameni idan da gaske yakeyi yaturo saiya kama muku haya idan Anyi Auren"na riga na gama mgn"bazan canzaba"idan kin fito da miji ceton kanki kikayi"idan kink'i zan baki mamaki keda uwarki"tashi ki bani waje mutuniyar banza....kuka mecin rai ummu ta saki, tana tashi ta shige d'akinsu"ta sami k'annanta zaune jigum jigum kamar masu zaman makoki "sbd duk cin mutuncin da mahaifin nasu yamata suna ji"kiyi shiru dan Allah Anty ummu"insha Allah za'a samu mafita"kidage da Addu'a"Amma muddin ina numfashi wlh bazan bari babah yakashe miki rayuwa ta hanyar yi miki Auren dole kuma sadaka ga wani"ya zanyi Aminu??"bayan mubashshir bana zaton Akwai wanda zan iya fitarwa"duk wanda yazo wajena kamar za'a yi saiya dena zuwa"gashi najama mama b'acin rai idan tadawo ta samu nata kason"kuyi hak'uri muyita Addu'a"Amma duk Abinda babah keyi matarsa da mahaifiyarsa ne ke zugashi"cewar umar"ummu dai tayi shiru tana sauke Ajiyar zuciya"sun jima suna bata baki harta yi shiru"ta tashi tayi sallah da wanka"tsabar damuwa ko dinner bata yiba ta kwanta bacci....washe gari ma cikin damuwa ta tashi "bayan sun gama Abinda yadace"mazan suka fita wajen neman nakansu"mahmood yatafi islamiya"sannan ta gyara d'akin ta wanke kayan jiya tayi wanka"wajen k'arfe 12 pm ta Aza girki Anan parlourn"sbd ta kira mama ta sanar mata zuwa k'arfe 3 na yamma insha Allah ta iso gida"gaba d'aya damuwace samqn fuskar ummu tana tunanin miye mafita?"bataso tayiwa mubashshir zancen yaturo iyayensa sbd karyaga kamar Angaji da ita Agidansu"to idan yaji zaki Auri wanifa??"wata zuciyar ta tamabayeta"Afili tace"dole nasanar masa gaskiya"sbd kar yaji wani Abu yace"naci masa Amana"zan sanar masa Anjima"Amma bara dai mama tazo naji ta bakinta"na kuma sanarwa lausy naji itama ta bakinta"da wannan tunanin ta gama girkin ta goge wajen tayi sallar Azahar....

      Bayan sallar la'asar mama na kwance kan kujera 3seeter tana hutawa"yayinda ummu kecan bed room kwance tana tunani"mama bayan taci Abinci tayi sallah ne ta kwanta"tunani takeyi meya faru jiya Agidan dabata nan?sbd ta lura ummu na cikin damuwa"dukda ta tamabayeta tace"bbu komai"ciwon dataji kuma tasanar mata bigewa tayi....ina hajara take??"taji muryar hjy yaya"kafin tayi mgn harta shigo cikin parlourn itada bahba dake biye da ita"gaban mama yafad'i tadai dake ta tashi zaune tana gaida hjy yaya"bata Amsa ba tayi tsaye tana fad'in magana mukazo miki da ita nida rufa'i"wannan karon baki isa kisa y'arshi ta bujure masa ba"wai meya faru hjy?"cewar mama"babah ya zauna yace"na yanke hukunci dg nan zuwa sati d'aya har kwana goma"wannan yarinyar ta fiddo mijin Aure kona batada sadaka ga duk wanda naga dama"na gaji da zamanta Agidan nan tana yawon banza tana jawomun zagi Agari... Allah yaraba y'ata da yawon banza"me zarginta ko Aibantata insha Allah sai ubangiji yamana sakayya da hakan...ba shakka hajara"sannu marar ta ido "Aidama nasan komai takeyi kece ke sata"yanzun rufa'in kike gayama mgn koni??"wlh nagaji da irin wulak'ancin da Akemun Anan gidan"wlh wlh !muddin kayiwa y'ata Auren dole zan baka mamakin daban tab'a baka shiba"bangaji da itaba"dakake zancen kagaji da ita"nauyinta kake d'auka?"cinta,shanta,Iliminta ,tufatarwarta kasansune dakake fad'in ka gaji??"cewar mama cikin fushi da d'aga murya...lallai kin isa hajara"dani kike mgn zan nuna miki ikona Akan y'ata"bara kwana 10 d'in yacika bata fitar ba ki gani"Ahh to dadai yafi"karka sake kaji shakkar burgan banzan datakeyi"cewar hjy yaya ta fita itada babah"goggo luba dake lab'e taji kamar ta taka rawa sbd farin ciki......

         misalin k'arfe 12:35 pm na yau lahadi big man ne ke tafiya cikin nutsuwa baya tare da kowa"yasha gayunsa cikin k'ananun kaya"yanata zabga k'amshi me dad'i"fuskarsa bbu walwala"hakan be hanashi yin kyau ba"yana rik'e da nokia Ahannunsa"Abakin get d'in gidansu leemart yatsaya"masu gadi nata gaishesa yad'aga musu hannu ya wuce ciki"doguwar tsuka yaja sbd hango kamal da leemart tsaye suna mgn "sam ba suma lura dashiba"ita kanta na'a k'asa"kamal kuma ita yake kallo yana maganar"cikin tafiyarsa ta izzah yanufi Inda suke yana koma tamke fuska...wlh da gaske nake miki my leemart"babu wacce nake waya da ita Ajiya sai oganmu dg offi.....doguwar tsukar da big man yaja yasaka kamal yin shiru"leemart ta d'ago kanta ta ganshi tsaye ya had'e rai yana kallonsu"Aguje tabar wajen...malam me ruwanka dani da zakazo kayi sanadin data tafi?"cewar kamal fuska Ad'aure yana kallon big man"shi kuwa sai wannan shan k'amshi yakeyi yana cin magani ya jingina bayansa  jikin bango yana danna waya"ya d'auki kusan second 5"kafin ya d'ago ya kalli kamal yatab'e baki yana fad'in yanzun bakaji kunya ba dan Allah? katasa k'aramar yarinya y'ar cikinka A gaba kana mata rantsuwa sbd ta yadda da kai?wannan Ai jama kai rainine  da zubda girma"hmm! baza kayi dana saniba sai ranar daka Aureta taga k'arshen girmanka tukum zakaga yadda zata rainaka.....wani irin murmushi kamal yasaki yace"Allah yanunamun ranar dazan mallaketa har taga k'arshen girmana"idan ta gani sai me?"nace sai me ?"bansaniba"cewar Abdallah"hmm! 2 days na barka dasu tj da junuid sbd kuci gaba da Abotarku"okay haka kace?"haka nace mana Abdallah"miye ribar zaman da ba'a bama juna shawara ko fad'ama juna gaskiya??"suna tunzuraka kana wulak'anta mutane hakan shine daidai?"har kamata ina maka mgn sbd na isa dakai ka nuna ba haka ba?"wlh big man ka Ajiye wannan Ak'idar taka Akan SO domin baya shawara idan yatashi shiga....look kamal!  idan kasan wannan maganar zakamun kaje ka kirata ku cigaba da firanku"dama Abba zanje na gaida na ganku"babu damuwa bazan koma maka zance Akan soba"saidai inaso kasani muddin baka fita rayuwar ummul khairy ba wlh saina had'aka da Ammi"saidai komai zakayi kayi"ko kuma kasaka Arufeni....yanzun zancen danake maka Abinda yafaru jiya Anata yad'ashi harda bugawa Ajarida"wasu nason yima tambayoyi Akai"matsayinka na babban d'an kasuwa kuma yong bolonia meye hadinka da yarinyar da harka jimata ciwo??"Ayanzun mutum Ake kiwo ba dabba ba"kamar yadda baka damu da rayuwar kowaba kai Andamu da taka"kuma mak'iyanka sun sakq ido sosai Akanka"Ayau da safe naga jaridar gidan buga jaridar gaskiya dokin k'arfe....iya nan kamal yayi shiru"yayinda uban gayyar ke danna waya kamar besan meyake fad'a ba"har kamal yacire ran yaji yayi mgn yanama k'ok'arin tafiya sai yaji yace"wai wannan surutun da kakeyi kodai son kucakar yarinyar nan kakeyi ne??uhmm!  Abdallah kenan"idan ina sonta bana jin kunya ko tsoron sanar maka"ina fad'a maka gaskiya ne sbd idan k'anwata Aka yima haka sai Inda karfina yak'are"kuma tanada hurumin kaika k'ara"saidai sbd kanada kud'i baza'abi mata hakk'inta ba"shin idan sa'ada Aka yima haka ba fata nakeyiba wane mataki zaka d'auka??" nasan bazaka lamuntaba"zakayi koma miye kan wanda yamata haka"idan har baza kaso Ayi ma k'anwarkaba kai meyasa zaka yiwa wata??" dan Allah Abdallah karka koma cutar musu da yarinya"bansanka da cutar da kowaba meyasa sai Akanta zaka fara?"wlh duk Inda baka zato zancen nan yaje"ni kaina bansaniba Amma na sami labari"to dana tuna Abinda yafaru last time a garden yasa na yadda"nasan kuma preety ta sani saika tanaji hujjar kare kanka wajenta...sbd inajin tsoronta kota isa na lallab'ata ko??"Ada zan sanar maka da wani zance Amma na fasa"sai kaje da Abinka idan tayi wari maji"ita kuma yarinya ka koma cutar da ita wlh saina sanarwa Ammi kaji na rantse"tsaki Abdallah yaja yabarma kamal wajen"kamal ya girgiza kansa yana murmushi"shi kansa yasan be iya rabuwa da Abdallah sbd yana k'aunarsa dan Allah"kuma wasu dg cikin halayensa sun masa sosai"Abdallah na burgesa da baya neman mata"ya tabbatar Inda wanine yadda yaga yanada dukiya zaita neman mata"yanzun kuma gashi mutane y'an kuji ku gani har sun fara zancen wai maganar banza yayima ummu shine tak'i yarda saiya wulak'antata"shiyasa dayaci karo da jaridar yak'i bari gidan tv nasu suyi labarai Akanta....


     *One week Ago*

kimanin sati 1 kenan da faruwar wannan sharad'i na babah"yau saura kwana 3 sharad'i yacika"kuma ummu bata fidda kowa ba"ko data kira mubashshir ta sanar masa komai"ya damu sosai yakuma sanar mata da wuya mahaifinsa ya Amince siyi Aure yanzun"Amma ta bashi sati 1"tunda sukayi wayar har yau sati guda be kiraba"gaba d'aya itada mama dasu Aminu suna cikin damuwa"saidai ummu na b'oyewa"ta kuma sanarma mama mubashshir take jira taji ta bakinsa"ita kanta lawisa dataji zancen dukta damu"saidai tabama ummu shawaran ta dage da Addu'ar zab'in Alkhairi"duk wannan damuwar da ummu ke ciki hakan be hanata yawan tuna Abdallah ba"ciwon dayaji mata harta warke sai Abinda ba'a rasaba"kuma tunda sukayi wannan zuwan garden d'in bata koma yadda sunjeba sbd ta tsani wajen.... kasancewar yau satday sai ummu taji kad'aici yamata yawa sosai"gashi mama Anguwa zataje da marece"hakan yasa itama tafara shirin fita"saidai koda ta kira lawisa ta sanar mata zasu fita Amma ba wannan garden d'in zasujeba"saita dinga tsokanarta"ta share takashe wayar"sai bayan sallar la'asar mama ta fita taje gidan y'ar uwarta dake Anan kaduna ,wacce sanadinta suka had'u da babah"gidan wani malami masanin Alk'ur'ani da hadissai umma murja ta kaita"sbd Abata shawara ko wani taimako wanda sharia ta yadda dashi.....duk wani bayani saida mama ta masa dg k'arshe tace"wlh mlm Abin nadamuna"dukda nasan komai na Allah ne Amma ina zargin kamar Akwai saka hannun mak'iya"duk wanda yazo kamar za'a yi dg baya sai yace" yafasa"gashi kuma batun da ubanta yayi yanzun"banaso Ayima yarinya kamar ummulkhairy Auren dole kuma na sadaka....shiru mlm yayi yana nazari"kafin dg bisani yace"Alhamdllh ku cigaba da Addu'a"tabbas na fahimci y'arki An saka mata hannu"saidai hakan nada Alak'a da jinkirin zuwan mijin dazata Aura"sbd wani baya Auren matar wani"y'arki insha Allah zatayi Aure kwana nan"kuma miji na nunawa sa'a zata Aura"sai Abin ya girgiza kowa"saidai Akwai qalubale Acikin Auren"kuje kuyita Addu'a"tun kafin zuwanki nan nayi mafarki jiya naga komai sai gashi Allah yakawoki"kasancewarki na uwa Agareta kiyita mata Addu'a itama tanayi"Ajiyar zuciya mama tasaki suna masa godiya"suka kawo sadaka suka bashi"suka tafi.....

        Ab'angaren big man kuwa yarasa mafitah shima"ko Ammi be sanarmawa ba sbd yasan tsab zata iya cewa" cikin yaran danginta yazab'a"yayima preety zancen batama bashi had'in kai ba sai tambayarsa tayi" wacece yarinyar daya watsama lemo kuma miye hadinshi da ita??"tsaki yaja yakashe wayar sa Alokacin"ta dinga kiransa yamata banza"Atsarinsa beson zama da mace sama da d'aya"sannan yafison ya Auri wacce ke mutuwar sonsa sbd shi SO ba matsalarsa bane"yadda preety ke nunawa kansa da yimasa biyayya sai yaji zai iya Aurenta"yanzun kuma yasan dayace beda wacce yafitar k'ilan daddy ya Aura masa hafsat"yarinyar dayayi mugun tsana"wacce daya Aureta gara ya mutu bbu Aure Arayuwarsa"yasan wacce zai Aura bazata gagaraba Amma matan ne wasu bbu tarbiyya"Aganinsa gara preety"dukda itama ba komai nata yama saba"Amma Aganinsa gara ita"gashi yana fushi da kamal balle suyi shawara"shi kuma bejin zaima iya sanarwa dasu junuid wannan zancen"Acikin y'an kwanakin damuwa tasaka yanata shaye shaye son ransa"sunje garden d'in nan kusan kashi biyu bega ummu ba"wanda har sakawa yayi Abincika masa ko Anganta sbd ya Ida mata hukunci na k'arshe dalilin tsakin data masa ranar da sukaje Asibiti Amma basu gantaba....

        Misalin k'arfe 5 na yamma"Abdallah ne zaune back sit d'in had'add'iyar motarsa"driver najansa"babuma su junuid Atare dashi yau"sai motar bayansa da body guards nasa ke ciki"yasha zazzafan wanka cikin suit coffee brown"sai y'ar ciki fara"yana sanye da takalmi have cover"suman kansa har walk'iya takeyi da d'aukar ido sbd gyaran data sha"duk wacce ta kallesa sau d'aya baza taso ta dena ba"saida sa'ada tagama wasashi d'azun sadda zai fito sannan ya baro gida"yayi shiru yana tunanin ina zaije yad'an d'ebe kewa?"wayarsa tafara ruri"tsaki yaja sbd ganin preety ce"Amma saiya d'auka yak'i mgn"hellow my baby irin wannan shanyawa haka ?"saida yagama shan k'amshinsa kafin cikin taushin muryanshi yace" laifinkine"kinsan dai bansan yawan tambaya ko?"shikenan Amun Afuwa"2days nayi kewarka ina son nazo na ganka tunda kai bakayi kewata ba"nifa banama gida"kuma yau kinsan babu office"kana ina yanzun sai nazo?"d'an yamutsa fuska yayi yace"mu had'u A gold stone sai muyi maganar dana miki kwanaki"to shikenan swee...bema Ida sauraren taba yakashe wayar"Ahankali yace"muje gold stone"okay both"cewar driver"haka nan big man yaji gabansa yafad'i"wayoyinsa nata ringing"wasu Abokan kasuwancinsa ne wasu matan dake cewa suna sonsa ne"Ahaka suka iso gold stone wajen shak'atawa da shan ice cream"bayan An bud'e masa k'ofa yafito yatsaida body guards nasa su jirashi Awaje"sbd yau yaji duk sun ishesa bema son yawo dasu"cike da Aji da nutsuwa yanufi ciki yanata wani shan k'amshi"samari da y'an mata kowa na harkan gabansa"wajen wani table da bbu kowa yanufa ya zauna yana danna waya"guda dg cikin ma'aikatan ya iso yana fad'in y'allabai me kake buk'ata??"d'an yatsina fuska big man yayi yad'ago kansa da nufin yayi mgn"idanuwansa suka hasko masa ummu da lawisa dake zaune suna shan ice cream"ummu tasha gayunta cikin coffee brown d'in dubai Abaya"sak kalar kayan dake jikinsa"kallon mutumin yayi yace"bbu Atak'aice"dg haka yayi shiru kusan mintina 3"sai kuma yasaki wani shu'umin murmushi yamik'e tsaye cikin izzah da gadara yanufi Inda su ummu ke zaune"harga Allah ummu batama lura dashi ba"saidai kawai tasan tunda suka shigo wajen taketajin fad'uwar gaba..... Abdallah yaja kujera zai zauna"sai sannan taji mayataccen  k'amshin turarensa daya cika wajen"k'irjinta na bugawa ta kallesa suka had'a ido"tayi k'ok'arin danne rikicewar datayi ta had'e rai"lawisa itama tayi mamakin ganin yazo ya zauna nan"saidai batayi mgn ba ta tashi tabar wajen"ummu ma mik'ewa tsaye tayi da nufin tabar masa wajen"Abdallah yayi wuf ya d'auki wayarta da hand bag nata yarik'e"tana binsa da mugun kallo tace"mlm bani jakata da wayata"ina ruwana dakai?"koba An mana tsakani dakai ba??"Akan me zakayita bibiyar rayuwata?"......bazan bayarba saikin zauna munyi mgn"zancen An mana tsakani bansan lokacin da Akayi hakan ba"Abinda nasani ba fad'a ko tashin hankali yakawoniba"to meye yakawoka?"ta fad'a cikin masifa tana ballah masa harara ido cikin ido"saidai bata jure kallon cikin k'wayar idonsaba ta kauda kanta"wai wannan tada jijiyar wuyan da kikeyi duk dan sbd nazo na zauna nan ne?"An fad'a miki kinada Ajin dazan ma kulaki?"tunda har nazo nan na zauna yazama dole ki zauna kiji meye yasa nazo"ko kuwa wlh shiga rayuwarki yanzun nafara"ke kin isa ina fad'a kina mun musu??"yafad'a cikin zafin rai"ta kalli gefensu taga bbu me lura dasu Amma lawisa na zaune nesa dasu tana hangensu"wai dan Allah idan baka tada fitinah da tashin hankali ba Arayuwarka ba bakajin dad'i ne??"bansaniba"ke kuma Allah yayiki da kafiya ko?"to bari kiji! tunda har nazo nan baki isa kitafi ba sai kinji Abinda zan fad'a miki"ko kuwa wlh ranki yayi mummunan b'aci"wai dan Allah ina ruwana dakai ne?"zancen kikeso"yafad'a yana jan tsaki"batayi mgn ba ta zauna kan kujera kusan second 30 kafin tace"to ina jinka ko?"yatsina fuska yayi yak'i mgn"saima danna waya yaci gaba dayi"wai wannan wane irin wulakanci ne?"ka tursasani na zauna kuma shine zaka shareni?"saida yagama shan k'amshin sa kafin yad'ago ya kalleta yace"na shareki d'in ke kin kai mace ma?"bata kulashiba burunta yafad'i komeye yabata hand bag nata da wayarta daya kama ya rik'e"saima Asannan ta lura da kalar kayansu iri d'aya.....dan Allah kabani hand bag nawa naje na bar maka wajen"ke dallah karki dameni mana"dama labarine zan baki saiki bani shawara"ni kuma?"sai Akace duk mutanan dakake dasu nice zaka bama labarin?"ina su y'an koron naka da bazaka fad'a musuba?? "musammun wannan me k'aton kan da wargajejen bakin.... tab'e baki yayi sbd yasan junuid da tj take nufi"K! na gadamar bamawa kuma dole ki tsaya ki saurara"tab'e baki tayi tana fad'in saika fad'a idan labarin me mahinmanci ne"ke wlh zan tattakaki Anan"rashin kunya zakimun kome?"innalillahi! wai dan Allah kai wane irin mutum ne?"kace ba tashin hankali yakawokaba ko?"to kafad'amun menene?"tsaki yaja yana kallonta yace"dama ba wani Abu bane daddy nah yabani 2weeks na fiddo wacce zan Aura"koya Auramun duk wacce yakeso?"yanzun Anci sati 1 saura sati 1 wa'adin daya bani yacika"kuma matsalar yarinyar dake sona sai nan da shekara kofi zatayi Aure....dg haka yayi shiru"sosai tayi mamakin meyasa zai fad'a mata sirrinsa?"saidai dayace yarinyar dake sonsa yabata haushi"wato shi yanuna babu wacce ta isama yasota kenan?"bakiji ne wai?"kin wani tsare mutane da ido"ki fad'amun mafitah mana"shiru tayi sbd ta fahimci disga mutane da yarfasu da masifa jininsa suke"kallonsa tayi tana tab'e baki tace" kwantai kayi kenan?"sai dai kusan matsalarmu d'aya dakai"Amma bazan sanar maka ba sbd bana buk'atar shawaranka"zancen wacce take sonka kuma nayi bala'in tausaya mata data soka"Amamakinta sai taga yasaki wani irin murmushin da bata tab'a ganin yayi irinsaba"ba k'aramin kyau taga ya mataba"harara ta zabga masa tana kauda kanta dan mugun kwarjini yake mata "K!  kifad'amun tun kina dariya"idan kuwa kinaso mu kwashi y'an kallo kece zakisha wahala"iya nan yayi shiru sbd yagaji da surutun"zan fad'a maka mgn kana danna waya?"Amma Ai kunne keji ko?"dan Allah idan nasanar maka zaka bani jakata natafi?"yatsina fuska yayi cike da k'osawa yace"banyi Alk'awari ba"ki fad'amun ta Arzik'i koki fad'amun ta tsiya"zab'i yarage naki"hmm! waikai An gaya maka ka isa ka tursasani ne?? nan gaba kad'an zaki bama kanki Amsar hakan"oya fad'amun nace?"yafad'a cikin zafin rai"wai dan Allah me.....bazaki fad'a ba?"yak'are maganar yana zare mata manyan idanuwansa"shikenan"dama nima babanah yace na fiddo miji ko shima ya had'ani da ko waye"ni saura kwana 3 wa'adin yacika"kuma wanda muke son juna be Ida Abinda ke gabansa ba"yafiso kamar nanda shekara d'aya Ayi Auren mu"shinefa dama labarin.....shiru yayi yana danna waya kamarma bashine take ma mgn ba"yanzun ka bani jakata na wuce Ana jirana....saida ya mula yasha Iska kafin yace"ki jira muyi mgn sbd samun mafitar kanmu"banganeba?"ta fad'a tana kallonsa"yatab'e baki yana d'age kafad'a yace"saiki tsaya ki saurara"to shikenan idan naji mafitar yamun shikenan"Ai bakima isa kice bata miki ba"sbd tunda na b'ata lokacina nazo nan nabaki labari na zauna naji naki labarin kinga kuwa baki isa nace ga yadda za'a yiba kimun musu"yak'are maganar cikin izzah"ummu dai tayi shiru Aranta tace ko masifa yakeyi sai muryarsa tayi dad'i"saidai yanada murd'add'en hali"shirun da yayi yasaka ta kallesa taga ya k'ara waya kunnansa yana fad'in ina ciki ki shigo"dg haka ya yanke wayar yana fad'in lafiya kike kallonah?"itace ta kawo haka"okay yayi kyau"sai kuma yad'an girgiza kansa yana sosa girarsa ta gefen dama cikin nutsuwa ya kalleta yaga bashine take kallo ba"yace"inaga hukuncin dana yanke mana shine" nida ke zamuyi AUREN YARJEJENIYA! daga ni saike da wanda zaki Aura kawai zamu san manufar Auren"bayan Auren da wani d'an lokaci na sakeki na Auri wacce ke sona time d'in ta gama Abinda ke gabanta" kema saiki ki Auri wanda kikeso.....shiru yayi sbd dirar preety Awajen.....✍️


Turkashi🤫🤔😳 wani abun sai a paid grps guys ba'a fara komai ba"yanzun zamu shiga cikin Ainahin zak'in labarin wanda bbu nadama ko dana sani awannan tafiyar dan labarine me tsayawa Arai da sakq nishad'i karki bari ya wuceki hanzarta biyan naki ta wannan hanyar👇



wannan book d'in nakudine 

Normal grp 300

Vip grp 1000

Special people 2k wato 3pages in a day 


zaku biya kud'in ku ta wannan acc number👉2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Kituro shaidar biyanki what's app number d'ina  08100084251 

300 kawai ake turo Kati idan bakida acc amma sauran payment d'in ta acc ne


  banason transfer d'in Kati ko vtu photo d'in katin MTN zaki d'auka saiki turo  dan Allah banda kira❌ 


Y'an nijar kutuntub'i wannan n👉 +227 88 01 90 50

 Normal grp 500f

Vip grp 1000f

Special people 2000f


dan girman Allah da darajan iyayenki karkimun mgn idan baki shirya biyaba

No comments