Recent Updates

AUREN YARJEJENIYA 5-6

 


🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾


  ❤‍🔥👩‍❤️‍👨AUREN YARJEJENIYA👩‍❤️‍👨❤‍🔥


🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾


    it's rometic love story❤‍🔥💔



      Story & written by mommyn fareesa



   Free page 5&6


...... Ab'angaren ummul khairy kuwa"gabanta nata fad'uwa ta iso layin gidansu "Aranta tana Addu'ar Allah yasa babanta yatafi masallaci wajen sallar magrib"sbd tasan idan yaganta saiya gaya mata mgn me zafi"cikin sa'a ta samu soro bbu kowa"Ahankali ta shigo tsakar gidan da sallama"mama na zaune tana Alwalah"goggo luba na tuk'in tuwon dare"Amsa sallamarta mama tayi tana fad'in kun dawo ne?"Eh lawisan ma ta wuce gida......A hayye nanaye! Ayi dai mugani idan tusa na hura wuta"Anje yawon banza An fake da wani batu daban"cewar goggo luba tana tab'e baki"Aranta tana ganin yaka mata ta koma gun bokonta, ta koma sabon shiri sbd kar ummu ta Auru"dan ta lashi ta kobin ummu baza tayi Aureba tafi y'ay'an ta hutawa"bayan kyawun halitta data fisu dashi....ummu da mama kuwa gefen da goggo luba take basuma kallah ba"sbd sun saba da mugun halinta"kullum Addu'ar mama Allah yabama ummul khairy miji na k'warai tayi Aure ko hankalinta dana ummu zai kwanta"d'aki mama ta shiga maganganun goggo luba na sukar zuciyarta ta kabbara sallah"ummu kuwa Alwalah tayi ta shigo parlourn ta samu mama na raka'ar k'arshe"itama sallar ta kabbara"bayan ta idar taci gaba da Azkhar"Abinda yafaru tsakaninta da Abdallah yana mak'ale Aranta"tarasa meyasa data tuna shi sai taji fad'uwar gaba?"Addu'a ta shafa ta fito tsakar gidan da kud'i Ahannunta sbd ta samu yaron da zata Aika Asiyo mata credit"lokacin kuma goggo luba na kwashin tuwo"mariya ummu ta kallah tana fad'in mariya Amshi siyomun kati MTN dan Allah na 500....babu Inda zataje da daren nan"keda kika dawo daga wajen yawon gantali me yahana Acan baki siyo katin ba??"yawon gantali kuma goggo?"Eh mana"kullum kina fita Ana fakewa da wajen Aiki kike zuwa ko Anguwa to munsan kom..wa'iyazubillah! ki kyautata zato sbd zato zunubine koda yakasance gaskiya"kuma na barki da Allah....eyye?ni kike gayawa mgn ummulkhairy?kafin ummu tayi mgn babanta ya shigo tsakar gidan"kukan munafurci goggo luba ta saka"gaban ummu ya fad'i"baba yakalleta yace"lafiya lubabatuna kike kuka?"zagina ummulkhairy tayi mlm! sbd nace dare yayi bazata Aiki mariya siyen kati ba....dan ubanki ita kika zaga?"wato uwarki ta turoki ko?"ke y'ar iska zaki zageta"kin gand'amemun Agida" har Asiya k'anwarki ta hud'u tayi Aure ke kina nan tulke Agida?"shine Abin naki yazo kan matata ko?yafad'a cikin d'aga murya"ummu ta fashe da kuka Aguje ta shige cikin d'akin su"babah ya dinga bama goggo luba hak'uri"tana kukan munafurci ta nuna bbu komai"zuciyarta kuwa fari k'ar"gefen tabarma baba ya zaunah yanata zage zage"harta gama rabon Abincin ta Ajiye masa nasa"ta kira mahmood yazo ya d'auki nasu data ligara musu"wanda su basuma dogara da Abincin gidan ba"mama ta dubi ummu tana murmushi me ciwo sbd taji komai daya faru tace"kiyi hak'uri ummulkhairy"Aure da mutuwa da haihuwa duk lokacine da yazo za'a yi"kici gaba da Addu'a mahakurci mawadacine wata ran Inda rabo"inaji Ajikinah zaki zama Abin kwatance wata ran"kuma insha Allah hawayen da muka zubar Agidan nan bazasu tashi Abanzabq"duk bak'in ciki da b'acin rai na d'a namiji da kishiya nagani na had'iya"cikin ganima nakeyi"Amma yanzun Abubuwa sunyi sauk'i Akan da sbd dogaro da Allah da mukayi"sbd haka ki manta da komai kiyi Abinda ke gabanki....sosai taji sanyin kalaman mama Azuciyarta"tayi shiru batace komaiba"Ahaka umar ya shigo cikin matsakaicin  parlourn dake d'auke da kujeru name rufin Asiri"umar ka dawo ne?"Eh mama"Anty ummu lafiya naga kamar kinyi kuka?"babu komai ungo Amsomun kati"no barshi na siyo miki inada kud'i"batace komaiba yafita dg cikin d'akin"kular jalop d'in wake da shinkafa mama ta d'akko ta zubama umar idan yadawo yaci"sannan itama ta zuba nata"tabar sauran sbd ummu da mahmood da Aminu idan zasuci"dan ita mama batama cin girkin goggo luba"girkinta takeyi daban kullum....

   Mlm rufa'i haifaffan d'an garin kaduna ne kowa nasa na Anan"ya had'u da hajara datazo suna Anan kd suka kama soyayya"wacce ita y'ar Asalin maiduguri ce"basu jimaba sukayi Aure"Aka kawo hajarah kaduna"danginta basuson Auren dandai tanace shi takeso"suna zaman lafiya da soyayya"kasancewar ga gidan mlm rufa'i ga gidan iyayensa"hjy yaya itace mahaifiyarsa su biyune kawai ta haifa duk maza shida jafaru"kafin kuma rufa'i yayi Aure mahaifinsu yarasu"kowa yasan y'an mai duguri da iya kirsan zaman Aure da Ado da lalle da turaruka"tuni hajara tayi katutu Azuciyar rufa'i"baya ganin kowa gabansa sai ita"sannu Ahankali tun hjy yaya bata damuba har y'an gulma suka fara tsogumin an mallake mata d'a"Aikuwa ta fara nunawa hajara k'i"wanda lokacin harma An haifi ummulkhairy"dg ita sai Aminu sai Umar"wanda Ana goyonsa ne hjy yaya ta tada fitinah sai rufa'i ya Auri lubabatu y'ar k'anwarta dake masifar sonsa"hajara"wato mama ta tashi hankalinta"shima rufa'i duk yadamu sbd beson Luba"haka dai Akayi wannan Aure sbd bin umarnin mahaifiyarsa"kasancewar gidansa nada girma"itama Aka gina mata ciki da parlour Aka kawota"da farko lafiya qlau suke zaune da mama"sai bayan tashiga jikinta sannan tafara nuna mata mugun hali da k'i"daga farko babah yana Adalci"Amma Luba na haihuwar y'arta ta farko Asiya ta dawo dg wankan gida"gaba d'aya baba ya burkice kanta"banbanci k'arara yake nunawa"ga hjy yaya na nuna so ga Luba da goyon bayanta kan komai"lokacin kuma mama takoma haihuwa Amma bbu rai"saima tayi Allura"sbd gaba d'aya hidimar yaranta 3 tadawo kanta"yayinda Luba keyin ciki da goyo"kuma Abin Allah ya'y'a mata take haihuwa"saida tayi Asiya,humaira, Amina,mariya , zqinab"lokacin kuma data haifi mariya mama na goyon mahmood Autanta"Luba kuwa hankalinta yatashi dataga batada d'a namiji sai y'ay'a mata har biyar"mama kuwa maza 3 gareta mace guda wato ummulkhairy"gashi kuma ummu tafi duka yaran gidan kyau"hakan yasa Luba ke nuna hassadarta k'arara"tayi Asirin da babah yadena hidima dasu"mama ta dawo itace komai nasu"Abinci kawai yake basu"in bacin bataso tabar y'ay'an ta datuni tarabu dashi"gashi mahaifinta yarasu sai mahaifiyarta innah"da yayanta kawu salisu sai k'aninta kawu kabiru"suna kuma matuk'ar taimaka mata sbd suna dashi"mama tayi Aikatau da wankau da markad'e sbd tasamu Ilimin yaranta ya inganta"musammun ma ummu data taso da kwazo da hazak'a"cikin ikon Allah ummu ta gama primary taje secondary school"bayan ta gama taci gaba da jam'ia"har tayi digree shekara guda data wuce tasami Aiki na koyarwa tana d'aukar Albashin ta duk wata 80k"yayinda Aminu yana label 2 yanzun"umar kuma ya kammalah SSCE nasa last year zaije jam'ia"mahmood kuwa yana js1"tunda ummu ta fara tasawa ta fahimci irin wahalar da mahaifiyar su kesha Agidan su "ya zama ubansu yatsanesu basu rabarsa"mama itace komai nasu"tayi b'ata da kowa mamace komai nata"tun ummu nada 15yrs maza suka fara yimata caa"saidai mama bata barinta kula kowa sbd tanada burun tayi karatu me zurfi"lokacin datayi SSCE kuwa tak'ara zama cikakkiyar budurwa"maza masu hannu da shuni nata nuna suna sonta"lokacin hankalin Luba yatashi"ta shiga bin malamai sbd ummu ta rasa masoya"dukda haka kuma jifa jifa Ana zuwa wajenta"ummu da lawisa tun suna primary skul suke tare"sun shak'u da juna sosai"gashi kuma Anguwarsu guda"dandai gidansu lawisa na farkon layin su kuma suna dg k'arshe"to har suka girma Amincin su na nan saima Abinda yayi gaba"saidai mahaifin lawisa yanada Hali"yana kuma k'ok'arin yiwa ummu Alkhairi da hidima"danko kaya yana yawan yi musu iri d'aya"hakan na k'ona ran goggo luba sai tayita zuga babah da cewa Ai ummu rok'onsu takeyi"lokacin da ummu takai 23 yrs Alokacin baba da danginsa dasu hjy yaya kakar ummu suka tasota gaba da zancen tak'i Aure ta gand'ame Agida"lokacin tana shekarar k'arshe a skul"sai Allah yakawo mata wani nasir"d'an gayu me wadata suka fara soyayya dashi"lokacin itama lawisa bata jima da had'uwa da nura ba"har kud'in gaisuwa nasir yakawo da nufin bayan ummu ta kammalah  bautar k'asar ta za'a saka musu ranah"Abin tashin hankali saidai mama da ummu sukaji labarin Ansaka ranar Auren nasir da Asiya babbar y'ar goggo Luba me 18yrs"hankalin mama yatashi"Amma sukabar komai ga Allah"ummu batama kula samari Amma sbd tanaso tayi Aure kodan sbd surutun da ake mata saita kulasu"saidai da mutum yazo kamar Abin Arzik'i saiya dena zuwa"Ahaka har tayi service ta gama"kawu kabiru yasamar mata Aiki sanadin wani uban gidansa"lokacin kuma Aka sha bikin Asiya da Nasir"wanda mama da ummu sunyi matuk'ar hak'uri sbd haibaici da Aka dinga sakar musu wai ummu har takai 25yrs batayi Aure ba"Aikinta na koyarwa taci gaba dayi"yayinda Aminu ke karatu yana Aikin kanikanci"umar kuma yana tsaron shagon wani uban gidansa na provision"cikin y'an watanni mama ta canza"Aminu da ummu suka siya mata kujeru da TV k'arama da receiver"sannan suka saka mata tayis a parlourn ta"suka mata fenti"bayan an k'ara kwana 2 kuma ummu ta siya mata fridge k'arami sbd sudinga shan ruwan sanyi"mama kuma tana k'ananun sana'ointa na gida"suci me kyau susha me kyau itada yaranta"tasama baba ido shida muguwar matarsa"dan duk ranar girkin Luba yake kawo Abinci"ranar girkin mama kuma zaice bedashi"sannan saiya jima wani Abu na Auratayya be shiga tsakaninsu da mama ba"wacce tayi kyau Abinta sbd hutun datake samu"dan yanzun da gas ma nan cikin parlourn ta take girki"rabon data kunnah icce tama manta"yayinda Luba duk jiki ya lalace sbd bbu ishashshen hutu da cin abinci me gina jiki"ga hidimar yara"komai tasamu yana wajen bin malamai da bokaye"yara bbu tarbiyya sai zage zage"yanzun haka humaira me 14 yrs d'auke d'auke takeyi dataga An Ajiye kud'i..... mubashshir matashin saurayi ne zaiyi 32 yrs"be jima da had'uwa da ummu ba"tun bata sakashi Aranta ba hardai ta sakashi"suna soyayya yana kulawa da ita sosai"yanzun yana ginin gidansa"yasanar mata saiya ida gini da kammala digree nasa na biyu sannan suyi Aure"ummu batama yadda ta sanarwa kowa ba tayi dai shiru"tana fatan idan tasami wani daya shirya yanzun ta Auresa indai yanada halin kirki"yayinda lawisa An sakq musu rana da nura"itama ta sami Aiki na Anguwar zoma.....

    Ummu yarinya ce me sanyi hali"bata son raini da wulak'anci"kuma Allah yayita mai tsabta dason Ado da kwalliya kasancewarta jinin y'an maiduguri"farace ita jajir ba doguwaba ba kuma gajeraba"tanada dogon gashi bak'i me taushi"ummu batada rowa tanada kyauta"kuma Akwaita da son Addini"wanda tarbiyyar mama ce hakan"duk Inda zata shiga zata nuna kamun kai da Ajinta"tun tana label 2 tayi sauka"yanzun haka duk week end da safe tana zuwa islamiya"ummu nada masifa idan Aka tab'ota saidai tanada hak'uri"tun tuni suke zuwa wannan garden d'in itada lawisa bata tab'a ganin su Abdallah ba"sai kwanaki data hangosa cikin mutane"sai wannan had'uwa da sukayi"wannan kenan nan gaba zakuji wani Abun...


   ****************

Kimanin kwana 5 kenan da had'uwar Abdallah da ummul khairy"yaje garden d'in kashi biyu be gantaba"yarasa kuma tayaya zaiyi bincike yasan Inda take kodan ya hukuntata?"sbd tayi sanadin b'acin ransa da b'ata masa lokaci wajen zama yayi tunani"ummu kuwa tsoro ne ya hanata koma zuwa garden d'in"babu yadda lawisa batayi da itaba suje tak'i zuwa....Ayau yakama week end ne"tun wajen k'arfe 6na safe mama ta tafi maiduguri wajen sunan k'anwar ta data haihu Anty mairo"ummu kuwa sai wajen 8 ta tafi islamiya"zuwa 12 ta dawo gida"Autah ne kawai tasamu Agidan"su Aminu da umar suna wajen Aikinsu"ta bud'e d'akin su ta shiga"kayan ta cire ta kwanta samqn kujerah tana tunani"kawai saita tsintsi kanta dason zuwa garden d'in koda zataga Abdallah"Amma bazata bari ya gantaba zata saka eye glass bak'i da face mask"wata zuciyar tace"miye Amfanin kije ki gansa,ko kin manta irin wulak'ancin daya miki??"girgiza kanta tayi ta d'auki wayar ta k'irar spark 10 tafara k'ok'arin kiran lawisa"sai gab da zata tsinke ta d'auka"hellow k'awata"na'am"zamujefa yau gurden d'in nan"dariya lawisa tayi tace kin gama jin tsoron had'uwa da Abdallah kenan?"tsaki taja tana fad'in dan Allah kidena zancensa haushi yake bani"dg haka ta yanke wayar"wajen k'arfe 4:35 pm ummu ta fito cikin zazzafan wanka"milk d'in lace ne Ajikinta d'inkin doguwar riga"yanada zanen yallow da golden"saita saka mayafi yellow"tayi d'aurin d'an kwalin ture kaga tsiya"har tulin gashin kanta ya bayyanah Abaya"babu make up samqn fuskarta"saidai kwalli da powder data shafa"yatsun hannunta da tafin hannunta sunsha lalle ja"tanata k'amshin turare na kaya dana jiki"face mask ta saka tabar glass d'in cikin hand bag nata"fitowa tayi tsakar gidan ta rufe k'ofar d'akinsu"goggo luba dake zaune tana sidar plate d'in dataci d'an wake sbd laulayi takeyi tanata kwad'ayi"tabi ummu da kallo Aranta tace"kamar y'ar wani shege"bbu wanda zaice y'ar gidan nan ce ita"Afili saita tab'e baki tana fad'in za'a fita yawon banza kamar yadda aka saba ko?"gefen datake ummu bata kallaba tayi waje Abinta"Ahanya suka had'u da lawisa tana cikin mota"yayan lawisa bilal ne ke driving d'in"yatsaya ummu ta shigo"bayan ta gaishesa motar ta d'auki shiru"har cikin zuciyarsa yana sonta Amma yarasa meyasa bazai iya furtawa ko nunawa ba??....bayan sun iso garden d'in ya saukesu da basu kyautar 10k kud'in shiga ciki"Ajere suke tafiya"ummu ta zaro eye glass bak'i tasaka"gabanta nata fad'uwa"kinga yadda kikayi masifar kyau kuwa matar manya??"hmm! ke nifa yanzun kome nafef na samu indai yanada halin kirki zan Auresa kodan sbd gorin da Ake mun nak'iyin Aure"kima dena kaini can sama Inda ban kaiba"Allah yatsareki da Auren me nafef "Aure kuma lokacine zahilcine kayiwa mutum gorin beyi ba"cewar lawisa suna shiga ciki"dg can ciki suka wuce suka zauna"fira sukeyi sama sama suna shan drinks"k'irjin ummu sai tsawaita bugawa yakeyi"ta duba time 5:12 pm"kamar Ance ta juya ta kalli bayanta.....gabanta yayi wani irin mugun fad'uwa! sbd ganin body guards d'in big man suna nufo Inda suke zaune"na shiga ukku lawisa"ta fad'a cikin rawar murya"lawisa ta dubeta tana fad'in lafiya dai?"kalli bayanki body guards d'insa nefa"juyawa lawisa tayi ta gansu ta d'auke kanta itama gabanta na fad'uwa"karki damu ki nutsuwa babu Abinda zai faru"saidai nayi mamakin yadda suka ganeki....bata rufe bakiba suka dira gaban table nasu suna tsare ummu da ido"dg ita har lawisa babu wanda yatanka musu"kimanin shud'ewar mintina 2 kafin cikinsu wani yace"wajenki both ya Aiko mu yace"ki tashi muje gunsa mintina 5 yabaki karki b'ata masa lokaci....eye glass d'in ta cire tana binsu da kallon banza tana yatsina fuska tace"bazan jeba! idan ya isa shiyazo da kansa mana"koya isa yayi iko danine?"ta fad'a cikin masifa bbu wani Alamar tsoro Atare da ita"hmm! yaro yarone bakisan waye both ba"Ashawarance ki tashi muje tun kina dariya"in kuwa kinfi son mu biyo miki ta bayan gida to bbu damuwa"dan munayin komai ne Abakin Aikin mune"k'awata tashi kuje dan Allah"cewar lawisa"ummu batayi mgn ba ta mik'e tsaye tana mamakin meyasa Abdallah keson shiga rayuwarta?"gabanta nata fad'uwa tace"tashi muje lausy"ah ah zan jiraki Anan"haushi taji sai batayi mgn ba tabi bayan su suna tafiya" ta kuma sha Alwashin zata nuna masa k'arshen Aji dan baza tayi masa mgn ba"k'asan zuciyarta kuma tana mamakin ta yaya suka ganeta bayan tab'oye fuskarta da face mask da glass??".....zuciyartace ta dinga harbawa sakamakon k'amshin turaren big man daya kaima k'ofofin hancinta ziyara"saima sannan ta fahimci sun iso Inda yake"yana tsaye ya Aza k'afarsa guda samqn kujera"fuskarsa bbu Alamar yasan miye wani abu dariya"ya wanku cikin k'ananun kayan da suka masa mugun kyau"da Alama yau Ammasa Aski"dan sumarsa zuwa bak'in sajen dake zagaye Asaman fuskarsa duk sun kwanta lub gwanin sha'awa suna d'aukar ido"kallon body guards nasa yayi "Atake suka bar wajen suka koma gefen dasu junuid da tj suke zaune"Amma bbu kamal Acikinsu sbd har yanzun fushi yakeyi da big man....ummu kuwa batama kallesaba sai danna waya takeyi tayi tsaye"bbu Alamar tsoro Atare da ita tamayi bala'in had'e rai"Azatonsa yadda ta b'oye fuskarta sbd tsoron karya ganeta data zo yanzun zata duk'a ta bashi hak'uri Amma sai yaga bbu Alamar hakan Atare da ita"saima wata rashin kunya da fitsara daya lura tanaji dashi"kusan mintina 5 tana tsaye dg gefen table d'insa bbu me mgn Acikinsu"sosai  ransa yab'aci"saidai yasha Alwashin zai nuna mata ita batada Aji"idan baza tayi masa mgn ba to su kwana Anan mana"ya Ayyanah hakan Aransa"ummu kuwa na ganin ta cika 6minit A tsaye beyi mgn ba sai kawai ta juya da nufin tabar  masa wajen"Aharzuk'e big man ya finciko hannunta guda"tayi kamar zata fad'i ta dafe table d'in da sauri"yana yatsina fuska yadubeta yace"you have to be careful! bana d'aukar raini"kin isa na kiraki kitafi ne?"sbd ga sa'anki ko?"ya lumfasa yana girgiza kai yace"bakida Aji ko k'imar dazanje wajenki "nadai nuna ikona ta hanyar  Azomun dake nan"meyasa baki bujereba tunda kina ganin ke baki tsoron kowa??banza kucakah muna mata"ke A haukanki kin zata zaki mari mutum kamata ki zauna lafiya?"shine zaki b'oye k'azamar fuskarki kizo ki wuce sbd kina jin tsoro ko?"saidai inaso ki sani bana mantuwa kuma bana yafiya!....iya nan yayi shiru yana jan tsaki"ummu ta kallesa ta zabga masa harara tana fad'in ka gama??sosai tabashi mamaki"shifa bbu macen datake gaya masa magana da nuna raini garesa irin wannan yarinyar"kodai rufeta zai sakq Ayine??cikin fushi ya d'auki glass cup d'in dake Ajiye samqn table cike da lemo exotic ya watsa mata Ajiki da fuska"ya jefeta da cup d'in Asaitin fuskarta"duk yadda taso ta kare Abin yaci tura"saida cup d'in yadaki goshinta ya tsage biyu ya soketa"tamkar Abin shiri saiga jini..... innalillahi wa inna ilaihir raju'un"cewar lawisa data biyo taga lafiya? sbd jin shirun yayi yawa"dafe goshinta ummu tayi hawaye masu zafi na zuba saman fuskarta gwanin ban tausayi"jikinta da mayafinta duk sun b'aci da lemo da jini"big man na tsaye yana huci ko Ajikinsa"lawisa ta k'araso tana fad'in bawan Allah meta maka da zafi Arayuwa da har zaka mata irin wannan zalincin??"ta k'are maganar tana rungume ummu jikinta"kallon up And down Abdallah ya musu  gaba d'aya ya matso" cikin kakkausar muryanshi yace"saketa !jikin lawisa na rawa ta cikata"hannun ummu ya fisga yafara k'ok'arin tafiya da ita"tana gunjin kuka tafara turjewa"su tj dake kallon komai suka taso suna kallon lawisa dake tambayar ina zaije da ita??"ke dallah idan big man na Abu ba'a tsaidashi"idan zaki iya kallo ki kallah"tsaki taja tabisu da kallon banza"ummu kuwa uffan bata furtaba"tana dai dafe da goshinta tana kuma biye dashi"sbd ganin idan bata dena turjewaba zai iya jimata ciwo Abanza"saidai hankalinta yayi mugun tashi tana tambayar kanta ina zayaje da ita?"kodai tayi ihu Azo Ataimaketa??yayinda mutane keta kallonsu kamar TV"hankalin lawisa Atashe take binsu"suna fitowa Inda motocinsu suke fake Aka b'udema big man back sit"da k'arfi yajata suka shiga ciki"da sauri itama lawisa tayi kunar bak'in wake tashiga cikin motar"sbd koma miye zai yiwa ummu yamusu Atare.....✍️


zazzafan sharhi


sauran pages 2 free page yak'are zak'in labarin na'a gaba daure ki biya naki dan adama dake👇


wannan book d'in nakudine 

Normal grp 300

Vip grp 1000

Special people 2k wato 3pages in a day 


zaku biya kud'in ku ta wannan acc number👉2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Kituro shaidar biyanki what's app number d'ina  08100084251 

300 kawai ake turo Kati idan bakida acc amma sauran payment d'in ta acc ne


  banason transfer d'in Kati ko vtu photo d'in katin MTN zaki d'auka saiki turo  dan Allah banda kira❌ 


Y'an nijar kutuntub'i wannan n👉 +227 88 01 90 50

 Normal grp 500f

Vip grp 1000f

Special people 2000f


dan girman Allah da darajan iyayenki karkimun mgn idan baki shirya biyaba

No comments